[18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs ƙarshen ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 01 Idona tab ƙwalla nake kallon Dr Bilal wanda ya kasance shugabanmu ,ina mai sake maimaita kalmar “Gidan gawa Dr ? Wai ni ce zan kwana da gawa?” Ba tare da ya dube ni ba ya ce “nurse Fatee kin fi kowa sanin ba na magana biyu ki wuce kawai ki tafi, wannan gawar babban mutum ce ya zama dole a bata tsaro na musamman sannan ki tabbatar kin yi bincike a tsanake kin gano mene ne silar mutuwarsa” Ji na yi tamkar ya kwaɗa mini guduma,haka na soma tafiya ina waiwayensa ko Allah yasa ya ji tausayina ya ce na dawo amma ina tuni ya shiga sabgar gabansa.Ina buɗe ƙofar ɗakin gidan gawar na yi tsaye ina kallon gadajen da ke ɗauke da gawarwaki kowanne kuwa da likafaninsa in aka cire gawar mutumin da na zo dominsa. Jiki na ɗan kyarma na soma duduba gawar ina rubuta abubuwan da na samu matsayin result,ƙiiii! Na ji ƙofar da na bari a buɗe ta fitar da sautin.Da mugun sauri na juya sai na ga handle na motsi yayin da kuma ƙarar murza key ta ziyarci dodon kunnena. Cike da firgici na motsa da niyyar guduwa sai dai tamkar da akwai wani abu mai mugun ƙarfi da ya riƙe ni na kasa motsi. “A bani giya na sha na ɗan kurɓe” na ji wata murya ta faɗa amma babu alamun wanda yayi ta saboda ni ɗaya ce mai rai a ciki.Fiƙi-fiƙi haka nake baza na mujiyata waɗanda suke tsiyayar da ruwan hawaye kamar wacce aka zuba wa yaji,dukkan illahirin jikina kuwa rawa yake. Takardar da ke hannuna ce na ji ta soma motsi,dubawar da zan yi sai na ga ta rikiɗa ta zama farin ƙyallen likafani daidai nan kuma na ga abin da ya girmi tunanina.Gawar mutumin ce ta tashi zaune raɗam kan gado,wani irin kallo ne yake jifa ta da shi da wasu IDON SHARRI(MRS SADAUKI) masu matuƙar firgici da kaɗa hantar mutum.Ban san inda ta haihu a ragaya ba sai tsintar kaina na yi kwance a gadon asibitinmu,gefena ƙawata ce Rahinatu ke zaune tana duba yadda ƙarin ruwan da ke maƙale a hannuna ke tafiya. “Ƙawata kin tashi? ” ta furta tana mai tasowa tare da ɗora hannunta kan goshina da nake jin tamkar zai tsage.Ban kai ga bata amsa ba Dr Bilal ya shigo yana mai cewa “baƙonmu ya iso tun da ta tashi ku yi sauri ku fito kafin ya farga babu wani a cikin jerin sunan da za a basa”sai kuma ya fice.Rahinatu ta ja tsuki tana mai cewa“duk duniya na tsani tsatsauran mutum,sam bai da mutumci kawai don ya ga tauraronsa yana haskawa.Kin ga tashi mu tafi don yana iya sawa ma a kore mu” ta ida faɗar haka tana mai cire mini ƙarin ruwan,ina shirin saukowa kuma wata nurse ta sake leƙowa ta ce “Rahinatu Dr Bilal ya ce me kike jira alhalin ke ce za ki gabatar da kalaman farko na buɗe taro?” da wani irin mugun sauri Rahinatu ta fita tana yarfa hannu.Ni kuwa dakyar na iya ƙoƙartawa na tashi,duk jikina ciwo yake kamar wacce aka ɗirkawa na jaki.Baƙon da za a yi yau yana da matuƙar muhimmanci wannan ya aka shirya abubuwa da yawa,ciki kuwa har da jawabin da Rahinatu za ta yi sannan ni kaina an bani topic ɗin da zan gabatar amma tsabar yadda aka jijiga ruhina na manta shaf. Ina fitowa direct ofis ɗin Dr Bilal na wuce so nake na yi ɗan watsa ruwa ko zan ji dama,ina buɗe toilet ɗin na yi tsaye ƙyam tamkar wacce aka shuka.Dukkan illahirin jikina kuma rawa yake,na fito da idona tulu-tulu ina kallonsa sam ban farga na yi suman tsaye ba sai da na ji muryar Dr Bilal yana kiran sunana firgigit na dawo hayyacina sai dai babu mutumen da na gani a yanzu yana fitsari. “Me ki ke jira? Me yasa kike neman hanyoyi da za a kore ki Sweety?” Dr Bilal ya faɗa cikin taushin murya,na turo baki gaba kafin na shige banɗaki na share shi ba tare da na basa amsa ba.Wato Dr Bilal saurayina ne,amma in muna asibiti mancewa yake da wannan alaƙa yana yi mini tsawa kamar sauran da ke ƙarƙashinsa.Sai da na yi wanka na fito,na ɗauki farar rigar likitoci na ɗora daga sama sannan na nufi can saman bene inda ake gudanar da taron. Ina shiga da fuskar mutumen nan na fara cin karo,fari ne dogo mai cikar ƙasumbar saje da kuma gemu.Sumar kansa doguwa ce sosai ba kamar ta sauran maza ba,don har sai da ya ɗan toje ta daidai tsakiya.Fuskarsa sam babu alamun wasa,kana ganinsa ka kai matsalalen nan masu baiwa ahalinsu da kuma na kewaye da su wahala.A takaice dai bayan miskilanci akwai izza,girman kai da ɗagawa a tattare da shi,da sauri na ɗauke idona a kansa ganin ya juyo facing inda nake,na nemi wuri na zauna ina mai sunne kai zuciyata na ɗan dokawa yayin da idona ke hasko mini irin yanayin da na same shi. Zaune dai nake a cikin ɗakin taron amma sam hankalina bai wajensu,tunani ne barkatai ke kai komo a cikin laɓuɓuwar kwanyata da ba ta san komai ba sai soyayya.Ina cikin tunanin wasiƙar jaki na ji muryar Dr Rashid na cewa “Nurse Fateema ta zo kan dandamali domin gabatar mana da jawaben da ta samu dangane da binciken gawar da ta yi” Wani irin rasss na ji,yayin da kuma na ɗago kaina da mugun sauri ina kallon mutanen da ke wurin waɗanda kusan duk kallonsu ya dawo kaina.Dr Bilal na kalla sai na ga yana yi mini wani kallo,sai kuma a yanzu na tuna cewa lokacin da ina toilet ya ce na ɗauki takarda na nan kan teburi. Dakyar na iya miƙewa tsaye na nufi wurin,ƙafafuna na harɗewa cike da tsoro na ƙarasa Dr Rashid ya miƙo mini sifika.Shiru na yi kafin na ɗan lumshe idona nan take kuma na soma jin wasu jawabai na shigo mini kwanya waɗanda tabbas su ne suka faru da ni a lokacin da na shiga ɗakin gawa. “Kamar yadda kuka sani ire-iren mutuwar nan ta zama ruwan dare game duniya,to yau ma irin ta ce ta faru ga yalaɓai Alhaji Lawan.A binciken da na yi na samu raunuka a wasu sassa na jikinsa waɗanda ido ba su iya ganinsu sai dai kyakkyawan ruhi.A takaice dai ƙafarsa ta hagu babu ita,sannan an cire sinadarin idonsa,hatta jinin jikinsa babu globules rouges/red blood cell hakan shi ya baiwa igiyar saita numfashinsa damar tsayawa cak,huhunsa kuma ya bushe ƙamas jijiyoyinsa kuma duk suka tsinke.Waɗannan hare-hare da ruhinsa ya samu su ne kuma suka bai wa shararrun likitocinmu damar saka masa oxygene sai dai abin da ba su sani ba shi wannan bututun iskan ba komai ba ne sai ...sai...sai...” yadda na ji an shaƙe mini wuya ya hana ni ƙarasa abin da nake so,a dole na buɗe idona sai dai babu kowa kusa da ni amma kuma tabbas ina jin hannu a maƙoshina.Cikin abin da bai fi minti biyu ba na fita hayyacina,na zube ƙasa da sauri aka soma bani taimako ina jin muryar baƙon namu yana cewa “ku ɗauke ta ku fitar da ita tana ɓata mana lokaci alhalin da sauran aiki gabanmu” Nurse Rahinatu ce da wata nurse ɗin suka kama ni don fitar da ni,duk da ina cikin mugun hali bai hana ni zuba masa raunatatun idona ba ina kallonsa a matsayin mugu wanda bai da tausayi. “Ku kai ta ofis ɗina ina zuwa” muka ji muryar Dr Bilal a bayanmu,hakan suka yi kuwa.Kan gadon da yake duba marar lafiya suka kwantar da ni,ita ɗayar ta yi tafiyarta yayin da Rahinatu ta zauna tana duba ni. Murya can ƙasan maƙoshi na ce “miƙo mini takardar da ke kan teburi” Zuwa ta yi ta ɗauko tare da miƙo mini,na karɓa na karanta jawaben ƙaryar da Dr Bilal ya rubuta waɗanda su ne yake so na gabatar. Ina riƙe da takardar ya shigo,da sauri Rahinatu ta fita yayin da shi kuma ya matso cikin masifa yana cewa “me kika yi haka? Kin sha ƙwaya ne ko me? Wato ba don na dakatar da ke ba dukkan sirrin za ki sanar?” “Me na yi? Wani sirri kuma kake faɗa Sweety?” na faɗa don ni sam ban ga aibun abin da na faɗa a ɗakin taron ba. “Dalla yi mini shiru kin wani buɗe baki sai zuba kike yi kamar an kunna rediyo mtsww! Tashi ki fita” ya daka mini tsawar da na ji har ƙasan raina. Idona tab da hawaye na ce “amma sweet...” cikin masifa ya katse ni “kin ga Fateema ki fita na ce,ki je gida zan neme ki daga baya” A yadda nake ganin tsantsar ɓacin rai a idonsa yasa ban ƙara minti guda ba na fito ina kuka,idona sun rufe sam ban gani hakan yasa ban ga tawowarsa ba sai ji na yi na kai ma abu karo.Na yi baya zan faɗi ya taro ni,kafin kuma na ida tsayuwa kan ƙafafuna ya yaɓo mini wata baƙar magana cikin amon sautinsa mai matuƙar firgitarwa. “Jarababbiya kawai!” sai ya yarɓa ni gefe,na yi tangal-tangal zan faɗi amma Allah ya tsare ban faɗin ba.Ta ƙasan gashin idona da ya jiƙe sharkaf da hawaye nake kallon lokacin da aka buɗe masa baƙar motarsa ya shiga.Sai da motar ta fita daga harabar asibitin kafin na ɗaga ƙafata na fito,taxi na samu ya kai ni gida sai bayan na sauka ma ne na tuna cewa na baro jakata can asibiti.Sai da na karɓo masa kuɗinsa wurin Mama wacce duk ta rikice na ganina da ta yi cikin halin baƙin ciki. Ina shiga can uwar ɗaka na shige na rufe ƙofa,na ci gaba da rera kukana wiwi tsakanin kalaman Dr Bilal da kuma na baƙonmu sai na rasa na wanne suka fi yi mini ciwo. “Anty Fatee don Allah ki fito ki sanar da mu abin da ke damunki,kin ga muna cikin murna amma kin zo kin ɓata mana tsari” ƙanwata Maryam ta faɗa daga can bakin ƙofa tana ɗan bubugawa. Tashi na yi na buɗe,sai kuma na ƙanƙame Mama na fashe da sabon kuka tare da yi mata bayanin Dr Bilal ya yi fushi da ni.Sanin matsayinsa a zuciyata,yadda nake mugun ƙaunarsa da sonsa yasa Mama ta kira shi a waya don jin abin da ya haɗa mu amma sai da ta jera masa kira kusan biyar a ƙarshe ma sai ya dinga maido mata kiran kafin ya kashe wayarsa gaba ɗaya. Duk ina zaune komai ya faru,abin da ya yi sai ya haifar mini da mugun zazzaɓi.Magani ma ƙin sha na yi,don na gwammaci na mutu kan na rasa Dr Bilal.Towel Mama ke jiƙawa da ruwan sanyi tana ɗora mini a goshi,yayin da kuma ƙanwata Maryam ke yi mini sannu.Ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba,ko da na farka jakata na gani ina shirin tambaya sai ga na tsinkayi Rahinatu kan sallaya. Na ja ajiyar zuciya,ta juyo muna haɗa ido sai ta kawar da kai.Sai na ji jikina ya ƙara yin sanyi,miƙewa na yi ni ma don yin sallah sai dai ina shiga toilet na samu baƙon watana ya zo .Wanka kawai na yi na saka kaya maras nauyi na kimtsa sai na fito,kusa da Rahinatu na zauna ba tare da na ce komai ba. “An bai wa Dr Bilal hutun wani lokaci,yana cikin fushi sosai duk ya farfasa abubuwa da dama.A shawarce ki ɗan basa lokaci har ya sauko” Rahinatu ta faɗa cike da rauni . Idona suka kawo ruwa na ce “ke ma laifina ki ke gani?” Ta ce “eh to kusan haka ne,ke ma me yasa za ki faɗi abubuwan nan alhalin kin san faɗi tashin da ake yi na ƙaryata cewa akwai BAƘIN RUHI (MRS SADAUKI) a kaf asibitocin garin nan mai shayen jini?” Murya a raunace na ce “amma ai abin da na gani ne na faɗa ” “A'a ki ka dai ƙirƙiro,saboda a some aka kawo mana ke kowa ya san yadda kike da tsoron mutuwa da kuma gawa.Abin da ki ka faɗa kuma sam bai taɓa faruwa ba a cikin asibitinmu ba” Na ɗaga kai na dube ta da kyau kafin na ce “ina so ki yarda da ni,wallahi duk abubuwan da na faɗa gaskiya ne” “Kenan ke mayya cewa?”kamar subutar baki hakan Rahinatu ta faɗa ,sosai kuma kalmar mayya ta bugi zuciyata sai na ji kamar na shaƙe ta.Amma na yi shiru na ci gaba da juya na mujiyata ina kallonta da su,cikin tsarguwa da kallon da nake yi mata ta ci gaba da cewa “to in dai ba haka ba ta ya aka yi kika san da duk abubuwan nan da suka faru da Alhaji Lawan? Kuma in ba ki manta ba kwanan baya an yi mana darasin ceton kai inda aka faɗa mana siffofin Mayu da kuma yadda za mu gane mutum mugu ne,ke kuma ba ki da ko ɗaya ko kuwa kin taɓa jin sha'awar cin naman mutum?” “Da a ce ni mayya ce da wallahi babu abin da zai hana na damƙe kurwar Dr Bilal ” na faɗa ina cije leɓe.Rahinatu ta yi murmushi ta ce “yanzu dai zan wuce gida sai mun yi waya” Sai da na yi mata rakiya har bakin ƙofar gida inda motarta take sannan na dawo ciki.Jakata na buɗe na ciro wayata,nan na ci karo da saƙon Dr Bilal wai rabu da ni na je na nemi maye irina. Saƙon na dinga maimataiwa ina karanta shi kamar mai lesson kafin na tambayi kaina “kenan yana nufin ni mayya ce?” sai kuma ga hawaye shaaaa..... [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 02 “Wato Dr Bilal na nufin ni mayya ce? Ni mayya ce ahan ” Ƙarar faɗuwar faranti yayi daidai da dire ayar tambayar da na yi kaina,Mama wacce ta saki farantin hannunta,idonta suka nuna tsananin firgici da tashin hankali ita na nufa ina mai tambayarta “Mama wai ni mayya ce?” ba ta bani amsa ba sai zaman ƴan bori da ta yi tana fitar da gumi,halin da na ganta a ciki sai ya mantar da ni nawa tashin hankalin. “Mama? Mama?” haka na dinga kiran sunanta ina jijigata ganin ta ƙame ƙam kamar ɓeran da lantarki ya damƙe. “Maryam? Maryam zo Mama babu lafiya” na faɗa cikin ɗaga murya,babu jimawa kuwa ta fito nan na ga ikon Allah Maryam na shafar fuskar Mama sai ta dawo normal tamkar ba ita ce shock ya damƙe ba. Numfashi Mama ta ja haɗi da lumshe ido sai wasu guntayen hawaye suka sirnano mata,Maryam ta ja ajiyar zuciya tana mai dubana na wani ɗan lokaci kafin kuma ta ce “don Allah Mama kar ki ce komai ,in kika faɗa hankalin anty Fatee zai tashi sosai” “Mene ne ba ki son a faɗa mini Maryam?” na tambaya. “Ku tashi ku haɗa kayanku” Mama ta faɗa cikin bayar da umarni.Maryam ta soma miƙewa,a dole ni ma na take mata baya juyin duniya ta ƙi bani amsar tambayoyin da nake yi mata sai ma haɗa kayanmu take yi cikin manyan akwatuna. A haka Mama ta shigo ta dube ni sai kuma ta kawar da kai,ta ce “ki ɗauki duk wani abu da kika san yana da muhimmanci ki bi bayan ƴar uwarki ku tafi” “Ina za mu je? Wai Mama mene ne haka?” na tambaya tare da nufo ta.Ta ce “ban son yawan tambayoyi ki wuce ki bi bayanta ku tafi” Idona na zubar da ruwan hawaye na ce “babu inda zan je har sai kin faɗa mini taƙamaimai abin da ke faruwa” “Ba mu da wannan lokacin Fateema ki wuce kawai ku tafi kafin kowa ya san wace ce ke” Mama ta faɗa cikin ƙaraji. Cikin sanyi na ce “wace ce ni kuma Mama? Meke faruwa haka?” ba ta kai ga bani amsa ba muka soma jin jifa ko ta ina haɗi da ashar. Abin da na sani uwa tana bada amanar ƴaƴanta ne ga babba daga cikin yaranta,sai dai a yau karon farko na ga inda uwa ke damƙa amanar ƴarta babba ga ƙaramar ƴarta. “Maryam ki kula da ita duk rintsi kar ki bar ƴar uwarki ta yi kuka,na baki amanarta ku je kawai sai in na same ku a can” Mama ke faɗar haka bayan ta damƙa hannuna cikin na ƙanwata Maryam wacce banda ɗaga kai babu abin da take yi.Ban taɓa sanin gidanmu nada wata ƙofa a baya ba sai yau da Mama ta buɗe mana ita,kaf kayanmu aka jera cikin wata tsohuwar mota ƙirar ta wani shuɗaɗen zamani.Dukkanmu a baya muka zauna,hannuna na dama na cikin na Maryam yayin da kuma na hagu na riƙe Mama gam ina hawaye sam bakina ya kasa furta komai. Wata irin ƙara muka ji wacce ta fi kama da ta ɓalle ƙofa,sai a lokacin kuma Mama ta fizge hannunta da ƙarfi ta koma can ciki yayin da kuma motar wacce babu direba a ciki ta soma gudu da mu. Faɗar tashin hankalin da nake ciki ɓarnar baki ne,kamar wata ƙaramar yarinya na ce “Maryam don Allah ki taimaka ki mayar da ni wurin Mama” Ta ƙara jimƙe hannuna tana mai cewa “anty Fatee zamanki a Kibri ya ida na har abada,ki nutsu ki kwantar hankalinki za mu koma Duwala da zama can babban birni” ina shirin sake yin magana ta yi wata alama da tafin hannunta nan take kuma na ji wani abu ya rufe mini ido ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai da na ji Maryam na tashe ni tana cewa “anty Fatee ki tashi mun iso” Dakyar na ware idona ina kallon yadda ruwan sama ke sauka ta tsohon gilashin motar.Maryam ce ta buɗe murfin muka fito,har zuwa yanzu kuma hannuna na cikin nata ta jimƙe shi.Sanyayyar iskan garin ce ta buge ni,yayin da kuma ta feso mini ruwan tsatsafin da ake a yi a fuska.Na ɗan lumshe ido kafin kuma na buɗe su ina kallon ƙatuwar Palace ɗin gabana wacce iya yadda aka tsara katangarta ma abin kallo ce ga shuke-shuke ko ta ina. Muna ƙarasawa bakin ƙofar Mai gadi ya leƙo ta wata ƴar huda ya ce “su wane ne ku?” Sai da Maryam ta dube ni kafin ta yi gyaran murya ta ce “ka ga motar da ta kawo mu can” Mai gadin na kallon motar sai ya buɗe mana ƙofa muka wuce ba tare na san dalilinsa ba,nan ne na ga ainahin kyawun gidan.Tsoro ne na ji ya kama ni,ko kafin mu ƙarasa a babbar ƙofar da za ta kai mu ainahin falon gidan tuni jikinmu ya jiƙe. Muna yin tsaye ƙofar ta buɗe da kanta,Maryam na gaba riƙe da hannuna muka shiga sai kuma na ja na tsaya cak saboda ƙatoton hotonsa da na gani manne a bangon da ke saiti da ƙofar shigowa. Ƙarar sautin takalmi masu tsini shi ya maida mini kallona ta ɗaya ɓangaren,wata matashiya ce ta fito tana tafiya kamar za ta karya ƙasusuwanta. “Wa kuke nema?” ta tambaye mu cike da wulaƙanci,kafin mu kai ga cewa komai kuma wata dattijuwa ta fito tana cewa “Sarah ki iya bakinki” ta yamutsa fuska kafin ta yi gaba,ni kuwa tambayar kaina nake ko ina za ta je cikin wannan daren a yayin da ake ruwan sama kuma. “Sannunku da zuwa kun sha hanya,ku zo ku zauna” matar ta faɗa tana sakin wani murmushi.Ita ce ta yi mana izinin hawa kan kujeru kafin ta saka masu aiki su kawo mana Coffe ,kasa sha na yi sai raba ido nake ina jin tsoro na sake shigata ga hotunan mutumen da har abada ba zan manta da kalmar da ya faɗa mini ba duk ko ta ina su ne manne da bango. “Ki ɗauka ki sha anty Fatee ” cewar Maryam ƙin kula ta na yi sai ma jikina da na dinga ƙanƙamewa. “In babu damuwa ina son sanin daga wane gari baƙinmu suke” dattijuwar ta faɗa tana mai yin zaune tana kallonmu. Maryam ta soma kame-kame kafin ta ce “wurin mai gidan muka zo” Ta saki ɗan murmushi ta ce “shi ɗin ɗana ne ,ina son sanar da shi ne saboda gudun ya yi faɗa an bar baƙinsa ba tare da ya sani ba” Maryam ta buɗe aljihun rigarta ta ciro wata tsohuwar fatar rago wacce aka yi wa rubutu a jiki ta miƙawa matar,ita kuma ta karɓa tare da soma karantawa tana yi tana ɗagowa tana kallonmu har ta gama. “Ke ce Fateema?” ta tambayi Maryam,ta girgiza kai ta ce “a'a antyna ce” sai ta yi mata nuni da ni.Kallona ta yi na wani lokaci kafin ta miƙawa Maryam fatar wacce take tamkar takardar wasiƙa,sai kuma ta ɗauki waya ta yi danne-danne kafin ta kara a kunne. “Mu'azzam ka zo gida ka yi baƙi daga masu muhimmanci ” shi ne abin da ta faɗa kawai ta kashe kiran,sai kuma ta dube mu ta ce “in ya zo sai ki basa takardar ” sai kuma ta ƙwala kiran sunan mai aiki ita ce ta nuna mana ɗakin da za mu kwanta wanda babu abin da babu hatta gado da frigine. Muna shiga na fizge hannuna cikin masifa nake cewa “sai wani jimƙe mini hannu kike yi kamar ƙaramar yarinya,ina ne kika kawo ni ? Za ki faɗa mini abin da ke faruwa ko kuwa sai na bi dare na tsere?” “Kin ga zo ki cire kayan jikinki ki sauya wasu kafin mura ta kama ki” cewar Maryam.Ji na yi kamar na ƙurmar ihu tsabar takaici ,wai ƙanwata ce ke bani umarni .Na yunƙura zan shaƙe ta sai na soma atishawa,babu jimawa kuma zazzaɓi ya kama ni sai na soma gangame jikina a dole na cire kayan jikina na ƙudundune da zanen gado.Maryam ta saki murmushi ta ce “bari na je na ɗauko kayanmu” tana fita na ƙara ƙanƙame jikina ina jin tsoro. Idona na rumtse gam daidai nan kuma na soma jin wata irin tsawa da cida,babu shiri na diro daga kan gado ina shirin fita wutar ɗakin ta ɗauke daidai nan kuma aka turo ƙofa.Na saki wata irin razananiyar ƙara a sa'ilin da na kai masa karo,na yi baya zan faɗi ya taro ni tare da maido ni kan ƙirjinsa yana wani matse ni.Cikin tsoro ni kuma na gantsara masa cizo haɗi da tura shi sai muka yi baya muka faɗi,na faɗa kan ƙirjinsa. Ido na waro jin sautin muryarsa da ya fitar da “washhh!” ni duk a tunanina ɓarawo ne,ƙoƙarin ƙwace jikina nake yi hakan sai ya bai wa zanen gadon da na yane jikina damar soma walwalewa iska ya kaɗa shi ya rufe idona yayin da nake jin ƙirjina duk a buɗe sam ban san hasken wuta ya dawo ba sai da ya hankaɗe ni na faɗi,ina jin lokacin da yake jan tsuki. “Me kike yi kuma a nan?” sautin muryar Maryam ya daki kunnena.Na tashi zaune ina turo baki tare da gyara zanen. “Anty Fatee ki zo ki kama mini kin tsaya kuma kallona” ta faɗa tana mai jan trollynta,a dole na miƙe na ja ɗayar na kai can ɗaki. Har na buɗe na zaɓi kayan da zan saka tunaninsa bai bar zuciyata ba,babu abin da ya fi damuna irin ƙamshin jikinsa mai kashe ruhi.Cikin kaya masu ɗan nauyi na shirya sannan na haye bed,ina shirin lumshe ido matar gidan ta shigo tana murmushi. Cikin sigar bayar da haƙuri take cewa “halin Mu'azzam ne sai shi,abu kaɗan ke saka shi fushi amma kar ku damu na san da sannu za ku saba.Me ya ce muku?” Maryam sai ta dube ni,tana mai cewa “a'a ni bani nan ya shigo anty Fatee me ya ce?” Rikecewa na yi na soma kame-kame,sai ita matar ta yi murmushi ta ce “kar ki damu yi kwanciyarki” A ɗan rikice na ce “hajiya halan ce miki yayi na...naaa ”sai kuma na yi shiru.Ta ƙaraso ta zauna gefena ta ce “bai ce mini komai ba,sunana Ammy ba Hajiya ba ki kira ni da haka don haka kowa ke kirana da shi” sai kuma ta taɓa goshina da sauri kuma ta ce “zazzaɓi ne ya sauko muku bari na kira Mu'azzam ya zo ya duba ki” tana gama faɗar haka ta fice. ★MU'AZZAM Shararren likitan abin da ya shafi ƙwaƙwalwa ne,bayan haka kuma yana taɓa wasu ɓangarorin aikin jinya da dama.Ƙwarewa a fannin aikinsa da kuma yadda mahaifiyarsa ta tsaya masa shi ya ƙara fito da tauraronsa yake haskawa a ƙasarsa ta haihu Kamaru da kuma sauran ƙasashen ƙetare irinsu Nijar,Tchadi da Nigeria .Bayan aikin likitanci yana kuma taɓa siyasa wacce yake da kujera mai girma ta ministan lafiya, wannan yasa shi yake zaga garuruwan da suka kewaye Kamaru don samo bakin zaren abin da ya adabi nahiyarsu wato ta mace-macen mutanen da kullum farashinsa ke ƙara hauhawa.Sai dai duk wannan ƙwarewa ta Dr Mu'azzam har izuwa yanzu ya kasa nemowa kansa lafiyar cutar da ke uzura rayuwarsa,wato matsalar fitsari.A ƙalla yana yin fitsari kusan duk bayan minti ashirin wasu lokutan in ya kwanta bacci ya kan tsinci kansa tsamo-tsamo cikin fitsari.Duk wani gwaji an yi masa amma babu wata alama da ta tunana mafitsararsa nada rauni,maimakon kuma ya ɗauki ƙaddara sai kuma ya kasa jurar haka kullum cikin tunani yake wanda hakan shi ne silar mutuwar annurin fuskarsa.A irin yawan shiga banɗakin da ya saba yi ne ya haɗu da Nurse Fateema wacce yake jin in akwai wacce ya tsana to bayanta yake,saboda in banda likitocin da suka taɓa duba lafiyarsa babu wanda ya taɓa ganin sirrinsa. Tun bayan da aka gama meeting ɗin da ya je ya shigo jirgi ya koma can babban birnin tarayyar Kamaru Yawunde,kiran mahaifiyarsa ne yasa ya ƙara shigowa jirgi aka kawo shi Duwala cibiyar hadadar kasuwanci. Yana zuwa Ammy ta shaida masa inda ta sauke baƙinsa,yana shiga kuma aka rashin sa'a ya ci karo da Fateema duk abubuwan suka faru da shi.Ganin cikar ƙirjinta har ya fi yi masa ciwo kan buguwar da yayi a kai, wannan yasa ya cilla ta gefe.Yana fitowa daga sashen ya ci karo da Ammy,cikin halin nasa na masifa yake cewa “ban san kuma daga ina bagidajiyar nan ta fito ba mtwsss!” bai kuma ya tsaya ya saurari Ammy ba ya haye can saman bene inda sashensa yake. Duk wasu kayan da ke kan teburi ya shiga zubar wa yana jan tsuki duk don hana ƙwaƙwalwarsa tunano masa abin da idonsa suka gane masa.... [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 03 Duk wata tsikar jikinsa sai da ta tashi duk da kuwa yadda yayi ƙoƙarin hana faruwar hakan.Ido ya soma ƙanƙancewa yana ja da baya yayin da kuma tunaninsa ke basa tamkar ga surar fatalwar budurwarsa nan na tunkaro shi.Kan bed ya zube ita kuma ta yi tsaye tana kallonsa tana yi masa dariya,cikin fitar hayyaci ya jawo inda yake ajiye alluransa dakyar ya iya yi wa kansa allurar.A take zufa ta karye masa sai ya soma maida numfashi,ya jawo blanket ya rufe kansa babu jimawa baccin wahala ya ɗauke shi mai cike da mafarkin nurse Fateema. Lokacin da Ammy ta shigo ɗakin don kiransa tana ganin yana bacci sai kawai ta ƙyale shi ta fita ta sa a haɗa wa Fateema shayi mai kauri sai ta sha magani. ★FATEEMA Ina nan kwance Ammy ta dawo ita da ƴar aiki,har sai da na ja ajiyar zuciya jin wai yayi bacci.Hakan yasa na karɓi shayin na sha shi da maganin,babu jimawa kuma na ji duk zazzaɓin ya sauka.Tunani na ta yi barkatai har ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba. Washegari ko da na farka tuni duk an kawo trollynmu,ban ga Maryam ba sai kawai na shiga toilet na yi wanka na fito na kimtsa sai na yi zaune gefen gado ina tunanin Mama ga shi ban zo da waya ba ballantana na kira ta. Ina nan zaune mai aiki ta shigo ta ce “hajiya ta ce ki fito” da sauri kuwa na miƙe na bi bayanta,a falo na tarar da su idona kuma kansa ya fara sauka yana zaune cikin baƙaƙen suit hannunsa riƙe da wasiƙar jiya yayin da kuma Maryam ke gefensa ta wani sunne kai. “Kin fito? Ƙaraso mana” Ammy ta faɗa tana murmushi,na ɗan sunne kai tare da cewa “ina kwana?” Ta ce “lafiya lau alhamdullah ! Na shiga ɗakinku na tarar kina bacci har Maryam za ta tashe ki amma na hana ta na ce ta bari ki huta.Ɗauki plate ga shi can kan table” Jikina na ɗan rawa na nufi dianing na ɗauko plate ɗin,na dawo ina shirin wucewa ta gabansa ya ɗago ya dube ni da shegun idonsa nan take ƙafafuna suka harɗe na yi kamar zan faɗuwa yasa ƙafarsa ya taro ni,cikin masifa yake cewa “ki kalli gabanki kin wani tawo kina rawar jiki” masifarsa ta saka na saki plate ɗin hannuna ban shirya ba,abin da ke ciki duk ya zube . “Ka bi ta sannu mana Mu'azzam ,kana yi mata tsawa me zai hana ta rikice? Kin ga zo ki zauna nan inda ma can kika zauna kika ci abinki duk da bai takura ki ba” Ammy ta faɗa tare da kamo hannuna ta zaunar da ni,na ɗaga kai a hankali na dube shi sai na ga ashe hararena ne yake yi kamar idonsa za su faɗo.Wani irin tausayin kaina ne na ji,sai na dubi Maryam ina shagwaɓe fuska sai ta kawar da kai. “In ta gama ta same ni a mota” ya faɗa tare da miƙewa ya fice.Wani abincin aka kawo mini sai rarrashina Ammy ke yi a haka dai na samu na ci,sai kuma na ji wani batu wai zan bi Mu'azzam zuwa asibiti. “Wurin me Ammy ?” na samu kaina da tambayarta,sai na ga Ammyn ta dubi Maryam da sauri ta ce “zai duba ki ne” Na ce “ai na warware” “Kin ga don Allah ki tashi ki tafi,ba ki da lafiya shi ne dalilin zuwanmu nan”Maryam ta faɗa tana kamo hannuna a dole na miƙe sai ka ce wacce ta yi wa asiri. Ammy ce ta yi mana rakiya har bakin motarsa,a baya muka zauna direba ya ja mu bayan Ammynsa ta yi masa nasiha da tuni game da girman amana.Ta cikin madubi muke ɗan haɗa ido da shi a haka har muka isa wata asibiti mai kyau.Cike da girmamawa ake gaishe shi har muka isa ofis ɗinsa,wata kujera ya nunawa Maryam ya ce ta zauna ni kuma ya tisa ƙeyata gaba muka shiga ciki. “Ki je ki hau gado” ya faɗa dakyar kamar wanda bai son yin magana.Tsoronsa ya yi mini jagora har na je na hau na kwanta,sai da ya ɗora farar riga sama sannan ya saka safar hannu sai ya zo ya duba idona kafin kuma ya ja kujera ya zauna ya ce mini “wace ce ke?” Da ɗan mamaki na dube shi kafin kuma na ce “Fateema” Ya haɗe rai cikin masifa ya ce “yaushe na tambaye ki sunanki? Cewa na yi wace ce ke?” Tuni idona sun kawo ruwa,na tsani tsawa ko kuma yi mini magana cikin ɗaga murya. “Kin ga ba kuka na ce ki yi mini ba,amsa za ki bani wace ce ke?” Cikin muryar kuka na ce “Nana Fateema Abdullahi ” ido ya ƙanƙance yana kallona kafin ya ƙwala kiran sunan“Maryam???” da sauri kuwa ta shigo tana mai cewa “ga ni ” “Ki tambayar mini antynki wace ce ita” ya faɗa yana wani yin baya yana kaɗa ƙafa. Maryam ta dube ni kafin ta ce “ɓoyewar me za ki ci gaba da yi anty? Kawai ki faɗa masa wace ce ke” Cikin rashin fahimta na ce “Maryam me zan faɗa masa? Na faɗa masa Fatee ce ni,sai me kuma yake son sani?” Wata irin dariya ya tuntsire da ita kafin ya ce “Maryam fita!” ai kuwa ta fice,tana fita sai ya miƙe tsaye yasa hannu ya kama hijabina da sauri na damƙe shi kuwa na ce “me za ka yi?” Ba tare da ya dube ni ba ya ce “a asibiti in patient ya zo likita na duba bugun zuciyarsa ko ba a koya muku hakan ba?” da sauri na cika shi,sai ya yi sama da hijabina da kuma rigata.Safar hannunsa na ga ya cire,ya ɗora dukkan tafukan hannunsa a cikina “kin ga periode ɗinki a jiya ” ya faɗa mini sam ba wai tambayata yake yi ba.A hankali ya soma daddana wurin a nan take kuma na soma jin zafi ina jin kuma lokacin da wani abu ke fitar mini ,ido na rumtse gam a daidai nan kuma na ji ya sake maimaita mini tambayar cikin wani sauti marar amo. “Wace ce ke?” “Mayya ce !” na basa amsa kai tsaye. “Me kike gani a kullum in kina bacci?” ya sake jefo mini tambaya. “Mutane! Mutane zagaye da wuta!” na basa amsa cikin i'ina. “Me suke dafawa?” “Naman mutane” “Su wane su? Faɗa mini fuskokinsu” “A'a Bilal zai fasa aurena ina sonsa sosai ba zan faɗa ba” “Ki faɗa mini fuskokin su wa kike gani” “A'a ba zan faɗa ba hakan cin amanar ƙauna ce” na faɗa ina mai buɗe idona yayin da hawaye suka soma zubo mini ta gefe da gefen ido.A haka nake kallon Mu'azzam har zuwa yanzu hannunsa na kan cikina yana danna shi,a hankali na kai nawa na ɗora na ce “ban so ka bari” Janye hannunsa ya yi ya je ya yi tsaye gaban window,murya a daka yake cewa “ban san mene ne so ba,ban san me ake ji ba in aka kamu da shi da har kuka yarda ku mutu kansa.A shawarce zan so ki amayar da baƙin sirrin nan ko ba komai wutar da ke tafasa TUKUNYAR MAYU na garin Kibri za ta daina ci amma kin zaɓi wanda kike so kan dubban al'umma ” “Ni babu wani sirri da na sani” na faɗa ina tashi zaune.Cikin tsawa ya ce “tashi ki fice mini daga ofis!” Na turo baki ina kallonsa ina shagwaɓe fuska,sam ban san mene ne ya shiga kwanyata ba da ke ta ƙoƙarin canza mini tabi'a. “Ba za ki fita ba kenan?” ya faɗa yana mai nufo ni, da sauri na sauko har ina tuntuɓe kafin na je can inda Maryam take zaune.Tana ganina ta miƙe tana mai cewa “har kin gama basa labarin?” ban kai ga bata amsa ba ya fito yana mai cewa “ku je direba ya maida ku gida” Kallonsa na yi na ga ransa a mugun ɓace duk sai na ji kuma babu daɗi amma sam ban ji zan iya faɗa masa ɗaya daga cikin sirrin Dr Bilal ba.Kamar wata ƴar yarinya haka ta ja hannuna muka fita zuwa can harabar asibitin,direban ne ya ɗauke mu zuwa gida. ★KIBRI A daidai lokacin da motarsu Fateema ta tafi a wannan lokacin ne kuma mutane suka cika falonsu.Mama ta yi saurin komawa can tana fuskantar mutanen gari da kuma ɗaiɗaikun likitoci masu aiki a can asibitin da nurse Fatee take . “Ina take ki fito mana da ita” muryar wata tsohuwa da ke nan cikin layinsu ta daki kunnen Mama,tsohuwa ce sosai ba ta da kowa a garin ita ke ciyar da kanta da kasuwar sayar da soyayyar gyaɗa da take yi. Mama ta yi murmushi ta ce “Iya wa kike nema?” “Mayyar ƴarki wacce ke kashe yaran maƙwabta yau dai asirinta ya tonu ” tsohuwa Iya ta bata amsa. Cikin dakiya Mama ta ce “sanin kanku ne Fateema ba ta taɓa cin naman ɗan kowa ba,hasali ma ku ne kuka tunzura ta har ta kai da mayafin da ya suturta baƙin sirrinta ya yaye.Sannan abu na gaba da zan faɗa muku ta bar Kibri kenan har abad...” ba ta ida rufe bakinta ba ɗaya daga cikin likitocin ya ɗauke ta da mari hakan ya yi sanadiyar fashewar bakinta kan kace wani abu tuni sun rufe Mama da kuka,sai da suka yi mata lis sannan suka bar ta nan kwance rai hannun Allah. Tana nan cikin mawuyacin hali Rahinatu ta zo,dakyar ta iya taimakon Mama ta miƙar da ita tsaye sannan ta ja ta suka fito ta saka ta a mota.Suna gusawa kenan aka cilla wa gidan wuta duk a tunaninsu har yanzu tana ciki.Gudu sosai Rahinatu ke shararawa har suka fita daga cikin gari,hanyar da babu kwalta ta rutsa suka fara shiga ciyayi.Sun yi tafiya mai ɗan nisa kafin ta tsaida motar,sai da ta haƙa wani ɗan ɗaki irin na zamani sannan ta taimakawa Mama ta fito.Wuta ta hura sannan ta gasa wa Mama fuska haɗi da yi mata magani,sai a lokacin ita kuma ta ce mata “na gode sosai Rahinatu ” Shiru ta yi ita kuma tana kallonta,kafin ta ce “ina Fateema?” “Su suka aiko ki?” Mama ta tambaya. Rahinatu ta girgiza kai ta ce “a'a Mama ina son dai sani ne” “Ni kaina ban san inda suke ba,abin da na sani shi ne kawai ruhin mahaifinsu ne ya tuƙa su izuwa maɓuya mai kyau” Rahinatu ta ja numfashi kafin ta ce “ki kwanta ki huta Mama,daga baya za mu yi magana” “A'a zai fi kyautatuwa da ki bar tarin tambayoyinki don kuwa ba zan amsa miki su ba” cewar Mama. “Taimako ne za ki yi Mama,a halin yanzu rayuwar Dr Bilal tana cikin mugun hatsari nurse Fatee ce kawai za ta iya yi masa magani” Mama ta yi murmushi mai ciwo kafin ta ce “sau ɗaya tak ake sarar mummuni,ki sani har zuwa yanzu Fateema yarinya ce ba ta da wayon sanin abin da idanun sauran al'umma ke gani.Duk wani taimako da ta yi wa Dr Bilal sam ba ta san ya danganci baƙin sirrinta da na yi ta ƙoƙarin binnewa tun tana yarinya ba.Shi kuma duk da irin hallacin da ta yi masa sai da ya watsa mata ƙasa a ido” “Mama kin fi kowa sanin Dr Bilal shi ne farin cikin Fateema...” da sauri Mama ta katse ta da “shi yasa na nisanta ta daga garin Kibri,ba zan so ta ga yadda za a tsoma masoyinta a cikin TUNKUNYAR MAYU ba...” ita ma Rahinatu ta katse Mama da cewa “wannan babban kuskure ne wanda a gaba za ki yi da na sani” “Kuskuren da zan yi shi ne barin Fateema a garin nan don ko shakka babu da naman Dr Bilal shi ne abu na farko da za ta fara sakawa bakin maitarta shi”ganin dai Mama ba za ta faɗa mata inda Fateemar take ba sai kawai ta haƙura ta bar ta a nan ta koma can cikin gari. Ofis ɗin Dr Bilal ta shiga,har zuwa lokacin yana kwance tun bayan da aka shaida masa an basa hutun wuccin gadi wanda a cikinsa ba komai ba ne sai zallar azabar ruhi da hana masa abin da yake so.Sam bai yi tunanin yakice nurse Fatee a rayuwarsa shi ne babban kuskurensa sai yanzu. Galabaitatun idonsa ya tsurawa Rahinatu wacce ita ma sai a yau ne ta yarda da cewa tabbas-tabbas da akwai TUKUNYAR MAYU a asibitinsu. “An ƙona gidansu Fateema komai ya ƙone ban samu damar ganin mahaifiyarta ba kuma” ta shaida masa kafin ta fice.Shi kuwa wani irin kuka ne ya fashe da shi yana mai soma lissafin kwanakin mutuwarsa..... [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 04 Dr Bilal na daga kwance yana tunanin abin da ba zai fishe shi ba kawai ya soma ganin inuwoyin baƙaƙen ruhika na ratso ofis ɗinsa.Kafin ƙyaftawar ido duk suka zagaye shi,yawun tsoro ya haɗiye kafin ya soma yin magana cikin rawar murya.“Zan so ku bani damar ƙarshe,na yi muku alƙawarin ba zan sake yin kuskuren da na aikata ba.Zan nemo nurse Fateema zan kuma damƙa muku ita matsayin sacrifice ɗin shagalin murnar cikar shekara ɗaya da kafuwar wannan daular tamu ta Mayu.Ku sani soyayyar nurse Fateema ba ta yi kamar raina ba,zan iya haƙura da ita domin tseratar da tawa rayuwar” yana gama dire kalamansa sai shugaban asibitin gaba ɗaya wanda ya kasance babban likita ne sai ya ce “za ka iya yi wa kowa ƙarya ya yarda amma banda ni,ka yi tunanin ban san cewa ka aika nurse Rahinatu zuwa neman Fateema ba? A tunaninka za ta iya taimakonka a wannan gaɓar? ” Idon Dr Bilal na tsiyayar da hawaye ya ce “shugaba ina son ka yarda da ni Please ka bani wannan damar” Sai da ya yi ɗan jimmm kafin ya ce “nan da watanni uku za mu cika shekara ɗaya a wannan tafiyar,zan so kafin wa'adin lokacin ya cika ka gurfanar mana da nurse Fateema ” Cike da murna ya ce “an gama shugaba” kamar walƙiya haka duk suka ɓace daga ɗakin,a nan take kuma Dr Bilal ya nemi cutar da suka saukar masa ya rasa.Tashi ya yi ya soma binciken inda zai samu nurse Fateema sai dai da dukkan alamu wayarta na cikin gidansu kamar yadda aka nuna masa. ★DUWALA Direba na ajiye mu duk sai muka doshi ƙofar da za ta kai mu cikin falon.Cak na tsaya jin tamkar ana ƙare mini kallo,wurin da nake jin kaifin idon na fitowa na duba sai na ga babu kowa sai motar da ta kawo mu jiya. “Ni kam Maryam wane ne ya tuƙo mu jiya? ” na tambaye ta ina mai dubanta. Ba ta bani amsa ba har muka shiga falon, Ammy ce ta tarbe mu tana tambayar jikina na amsa mata a takaice da “alhamdullah!” “Fatan Mu'azzam bai takura ki ba?” ta tambaye ni tana mai kamo hannuna ta zaunar da ni kan kujera tana sakar mini wani murmushi.Sai da na kalli Maryam kafin na girgizawa Ammy kai,na buɗe baki da niyyar yin magana kuma ya shigo kamar an jefo shi daga sama. Barina Ammy ta yi tare da nufarsa tana cewa “lafiya Mu'azzam?” bai ce mata komai ba sai matakala da ya soma takawa ita kuma ta take masa baya.Na ɗan taɓe baki ina jin haushinsa har cikin raina,Maryam ta zo ta zauna kusa da ni tana cewa “anty Fatee ya kamata fa ki saki jikinki ki...” da mugun sauri na katse ta “na saki jiki kamar yaya? Kin ga ni gida zan koma wurin Mama sam ban yarda da mutanen gidan nan ba,yo gida kamar na ƴan yankan kai dubi komai na gidan daban yake da na mutane” Sai da ta yi ƴar dariya kafin ta ce “wallahi tunaninki ne ke faɗa miki banza-banza amma wallahi mutanen kirki ne,inda a ce mugaye ne da Mama ba za ta ce mu zo nan ba” Shiru na yi ina nazarinta,wai ƙanwata da duka-duka ba za ta wuce shekara goma sha bakwai ba ita ce ke faɗa mini abin da ya fi dacewa da rayuwarmu.Cikin sanyi jiki na miƙe tsaye zan tafi ɗakinmu sai kuma ga su Ammy sun soma saukowa har da uban tsamin rai. Da ido na ƙure shi ina kallon tamkakar fuskarsa wacce tsabar yadda ya haɗe ta yasa ba a iya ganin kyawunta.Idonsa ya sauko cikin nawa yayin da kuma laɓansa suka motsa,duk da ban ji sautin ba amma zan iya gane abin da bakin nasa ya furta.“Jarababiya!” shi ne abin da laɓansa suka ayyana,na waro ido tare da nuna kaina “ni?” Har sai da ya sauko bai bani amsa ba sai kuma ya kawar da kansa gefe,tare da yin tsaye ƙiƙam. Ammy ce ta yi magana,“Maryam je ki haɗa kayanku kamar kala biyar haka za ku wuce Yawunde” “To Ammy ” ta faɗa kafin ta yi gaba,yawun bakina ne na ji sun ƙwafe na kasa furta komai sai sumar kansa da na kafe da ido ina kallo saboda yadda ya bani baya. Babu jimawa kuwa Maryam ta fito jaye da ƙaramin trolly,yanzu ɗin ma hannuna ta kama ta jimƙe.Ita kaɗai ta san sirrin,amma ni dai nawa shi ne yi mata biyayya haka muka fita zuwa harabar gidan.Wannan karon da kansa ya tuƙa mu kuma wata motar ce daban,har muka isa wani tabkeken wuri wanda nake kyautata zaton filin jirgi ne Maryam ba ta sakar mini hannu ba. Wasu sojawa ne suka zo suka tarbe mu,su ne kuma suka kai kayanmu har can cikin jirgin yayin da shi kuma gogan ya koma can gefe yana waya. Wani soja ne ya zo ya ce mana “ku zo na nuna muku inda za ku zauna” haka muka take masa baya,karon farko a rayuwata da na shiga jirgi.Kusa da kusa muka zauna ni da Maryam abin sha aka kawo mana,ita kaɗai ta sha ni kuwa ta window nake leƙensa sai wani zagaye-zagaye yake yana waya. ‘Ko da wa yake waya?’ na tambayi kaina a zuci na kuma bai wa kaina amsa ‘ bai wuce budurwarsa! Baiwar Allah amma na tausaya mata da take son maloho irinsa’ sai kuma na saki murmushi jin sunan da zuciyata ta kirasa da shi.Daidai nan shi ma na ga ya juyo yana murmushi kafin ya nufo jirgin yana mai janye wayar daga kunnensa ya maida ta cikin aljihunsa. Wata irin ajiyar zuciya ta tsoro na sauke jin ƙamshin jikinsa ya cika jirgin,ido na rumtse don ban ƙaunar ganinsa.Ina a haka na ji muryarsa yana cewa “ku saka belt!” Maryam ta ce “ban san ya zan yi ba ” “Ki jawo waccan sai ki manna shi jikin nan”ina jin ya faɗi haka sai na buɗe ido don ganin yadda za ta saka sai dai tuni ta saka ɗin.Fiƙi-fiƙi na yi da ido ina kallonsa,bai ce mini kanzil ba sai hannunsa da ya kawo ya jawo bel ɗin zai saka mini.Cikin sauri na ce “ban so ka bari zan yi da kaina” ina ƙoƙarin ƙwace belt ɗin ya buge mini hannu da ƙaton zobensa da ke babbar yatsarsa ta tsakiya. “Baƙauya kawai!” ya faɗa bayan ya saka mini,sai kuma ya yi gaba.Haka kawai na ji zuciyata tana azalzala amma babu yadda zan yi dole na ja bakina na yi shiru,a haka jirgin ya tashi da mu sama bai sauka ba sai babban birnin tarayya Yawunde. Yadda motoci suka zo tarbenmu sai abin ya bani mamaki,cike da girmamawa kuma aka ja mu izuwa motar da za ta ɗauke mu wacce iya ni da Maryam ne kawai.Wani tsoron ya sake riska ta na soma dube-dube ina waiwayen baya,sauƙinta da na ga sauran motocin na bin bayanmu wasu kuma a gaba amma sam ban wace ce daga ciki Mu'azzam ke ciki ba har muka isa masauki.Wani katafaren gida ne wanda har ya fi na can kyawu da girma,muna shiga da wata mata muka ci karo mai kama da waccan matashiyar ta gidan Ammy.Kamar ta ga wani kashi haka ita ma ta ɓata rai tana wani ɓoyewa alamun tsoro duk ya bayyana a fuskarta. “Mu'azzam su wane ne? Me yasa ka tawo da su gida madadin asibiti?” ta faɗa tana toshe hanci. Cikin zafin rai ya ce “saboda nan ɗin gidana ne! Joy? Joy?” ya shiga ƙwala kiran wani,babu jimawa kuwa wani inyamuri ya zo da gudu yana cewa “na'am yalaɓai” “Ka kai su masauki sannan su faɗa maka kalolin abincin da suke ci daga yau za ka dinga dafa musu,in ka gama ka same ni a ɗakina” yana gama faɗar haka sai ya wuce can sama yayin da shi kuma Joy ya ja trollynmu ya kai mu wani ɗaki.Abin da na lura shi ɗin ma a ɗan tsorace yake yi mana magana,yana fita na cewa Maryam “wai kin lura tsoronmu yake ji?” “Zan shiga wanka” shi ne abin da ta faɗa madadin amsar abin da na ce mata, sai bayan ta fito sannan ni ma na shiga nan ne na yi arba da wani baƙin jini da ya cika mini pad.Ido na lumshe ina tuna yadda yake danna mini ciki,na ɗauki tsawon lokaci a haka kafin na samu na yi wankan.Towel ɗin da na gani rataye na ɗaura sannan na fito,cike da mamakin yadda Maryam ba ta baƙunta na soma mita ina yi mata addu'a.Da na buɗe trolly sai na ga sam ba ta sako mini pad ɗina ko ɗaya ba,kaya na saka sannan na fito ina baza ido kamar marar gaskiya. Babu kowa falon sai masifafiyar matar nan sai tsawa take yi wa ƴan aiki tare kuma da zaginmu ,duk ba wannan ba ne damuwata ba sai jin yadda take alaƙanta mu da mahaukata shi ya fi damuna. Ina nan tsaye duk idona sun raina fata,sai duban hanya nake yi don ganin ta ina Maryam za ta ɓullo sam ban ga saukowarsa ba sai ƙamshinsa ne ya ziyarci hanci ne. “Mene ne? Tsayuwar me kike yi a nan? Wuce ki zauna ki ci abinci ” ya faɗa fuskar nan tamau babu annuri,idona na shiga juyawa kamar an jefa ƙwarya a ruwa so nake na shaida masa ban cikin halin da zan zauna kuma ina son sanin inda Maryam take,sai dai ba ƙaramin kamu tsoro da shakkarsa suka yi mini ba. Tsawa ya yi mini,sai kawai hawaye suka shiga zubo mini sai a lokacin kuma na ga Maryam ta fito daga wani wurin da nake kyautata zaton kitchen ce .Da bala'in sauri har ina yin tuntuɓe na je gare ta tare da ƙanƙame ta ina mai sakin wani marayan kuka.Sam na kasa fahimtar taƙamaimai ni wace ce,tun da ya shigo rayuwata komai nawa ya soma canzawa. “Anty Fatee lafiya kike kuka me ya faru?” Maryam ta faɗa tana ɗan janye ni daga jikinta,ita ɗin ta fi ni tsayi sai ni kuma na fi ta ƙiba.Ɗan waiwayawa na yi na dube shi,sai na ga kuwa mu yake kallo.Cikin muryar kuka na ce “please kar ki ƙara tafiya kina barina tsoro nake ji a duk lokacin da kika yi nesa da ni ” Hannuna ta jimƙe tana mai cewa “to ki yi shiru gani na zo” ta faɗi haka tare da jana muka koma can ɗakinmu,sai a lokacin take kwatanta mini ta shiga kitchen ne saboda Joy ya buƙaci haka. Muna nan zaune sai ga shi ya shigo,fuskarsa ta ɗan sassauto da alamun kamar tausayi a shimfiɗe da ita ya miƙo mini wata leda.Ƙin karɓa na yi sai hannunsa da na kafe da ido wanda gashi ya kwanta luf sai sheƙi yake.Cillo mini kedar ya yi kafin ya fice,sai na buɗe nan na ga ashe pad ce sai pant amma da dukkan alamu za su yi mini kaɗan.Toilet na shiga,sai na ga ashe duk na ɓata jikina har a ƙafata ya ɓace sai da na sake yin wani wankan sannan na kimtsa. Da na fito sai na ga ƴar aiki tana goge ɗakinmu,ashe duk na ɓata wurin ba tare da ni na sani ba.A kunyace nake kallon Maryam wacce na ga zuwa yanzu kamar ita ma tana son mu koma wajen Mama. ★MU'AZZAM Sosai ya ji zafin irin yadda Fateema ta ɓoye masa sirrin Dr Bilal,har ya yi fushi sai kuma ya ga da buƙatar ya kaita can asibitinsu ta Yawunde inda za a saka ta yin magana da ƙarfin tsiya ba tare da ta shirya ba, wannan dalilin ne yasa shi dawowa gida cikin ɗayar motarsa da kusan kullum a asibiti take kwana.Tun daga balaguron da suka yi a cikin jirgi har izuwa yanzu da ya kawo mata pad idonsa na kanta,yana jin tsanar da ya yi mata zaune daram a zuciyarsa yayin da gefe guda kuma ya soma jin tausayinta musamman lokacin da ta ruga ta rungume Maryam wanda a nan ne ya fahimci har pad ɗin tana buƙata wannan yasa ya shiga ɗakin Zeezi ya binciko pad da pant ɗinta waɗanda ba ta yi aiki da su ba. Tsuki ya ja a karo na barkatai yana jin zuciyarsa na azalzala game da abin da ta yi masa na ƙin karɓar ledar hannunsa.Wayarsa ta bado haske alamun shigowar saƙo,ya ɗauka ya duba sai ya ga abokinsa ne Dr Jabeer.Bayanan da ya turo masa ya karanta sai ya ajiye wayar ya shiga toilet,wanka ya yi ya shirya cikin kayan ƴan ƙwallo adidas baƙaƙe masu dogon wando.Sai da ya gyara sumar kansa ya bar ta a baje sannan ya fesa turare ya ɗauki wani ɗan ƙaramin littafi ya fito yana addu'ar Allah yasa kar ya gamu da ƴar matsalar can Fateema ai kuwa har ya fice ba su haɗu ba. Can wurin da aka tanada wurin motsa jiki ya nufa,littafin ya ajiye kan ɗan ƙaramin teburi sannan ya soma zagayen tabkeken wurin.Sai da ya zagaya shi ya fi a ƙirga sannan ya tsaya don hutawa,da mugun sauri Joy ya zo ya miƙa masa gorar ruwa da kuma ɗan ƙaramin towel.Murfin ya buɗe ya soma wanke fuskarsa ,sai kuma ya cire rigarsa da duk ta jiƙe da gumi da kuma ruwa.Har zai zauna sai kuma ya ɗauki littafinsa ya ƙara gaba. ★FATEEMA Muna zaune ni da Maryam masifafiyar matar nan ta aiko a kira mu,cikin masifa take bamu umarnin mu juya ƙattan kujerun da ke falon alhalin ga ƴan aiki nan maza.Banda masifa babu abin da take zubawa,raina ne na ji yana ɓaci yayin da kuma yawu suka soma cika mini baki idona kuma na wata irin rufewa kamar ƙwan lantarkin da yake gargadar mutuwa. Da sauri na nufi ƙofar fita don tofar da yawun,gijifff na ji na kai wa wani abu karo na yi baya zan faɗi amma yatsunsa masu mugun sanyi suka cabko ni tare da maido ni gaba sai ga kaina kwance a ƙirjinsa.A hankali na ɗan ware idona na dube shi,wani irin jana ya yi waje ya duƙar da ni tare da kama mini wuya nan na soma kakari ina zubar da baƙaƙen yawu.Tsawon lokaci ina a haka kafin na soma jin sassauci,da kansa ya wanke mini bakina kafin ya kira masu aiki su tsabtace wurin.Ina ƙoƙarin tashi kawai jiri ya kwashe ni,cikin fitar hayyaci na ji ya sungume ni tare da shigar da ni can ciki na yi tunanin a falo zai ajiye ni amma sai ya haura da ni can sama.Wani ɗaki ya kai ni mai kamar asibiti ya shimfiɗe kan gado,agajin gaggawa ya bani na farko kafin ya ɗauki waya ya yi kira. “Ki buɗe idonki kar ki rufe su” ya faɗa yana mai kama tafin hannuna na hagu ya soma mirza shi da ƙarfi,motsi na soma ji a cikin maƙoshina yayin da maduban idona ke hasko mini matar nan wacce na fi kyautata zaton goggonsa ce. Ƙofa aka turo aka shigo,a ɗan rikice su biyu suka haɗu suka soma yi mini magani wanda ya sha banban da na asibiti.Sun ɗauki sama da minti talatin a kaina kafin na dawo normal,a yayin gudanar da agajin na ji abubuwa da dama a cikin jikina waɗanda ban san na mene ne ba. “Ƙwayoyin sun fara bazuwa a jininta ” abokin nasa ya furta. Shi kuma Mu'azzam ɗin ya ce “yau ne suka samu damar ɓallewa suka kutsi jininta ka ga muna iya yin wani abu.Please Jabeer ina son ka ƙara binciko mini wannan ƙwayar ” Wanda ya kira da Jabeer ɗin ya ɗan dube ni kafin ya ce “me kike ji a yanzu?” Shiru na yi ban ce komai ba sai Mu'azzam da nake kallo,shi kuma tsuki ya ja yana mai cewa “na faɗa maka taurin kan tsiya ne da ita,dole sai an saka mata hullar gaskiya” yana gama faɗar haka sai ya nufi ƙofar fita,abokinsa ya take masa baya suka bar ni a nan ni ɗaya. Saukowa na yi daga gadon na soma ƙarewa ɗakin kallo,wani abu ya ja hankali shi ne fitilar ƙwai amma ba ɗaya take da sauran ba.Hannuna na rawa na kai shi na taɓa ƙwan,nan take ya kawo haske sai kuma na soma jin muryoyi na kawo mini farmaki yayin da kuma wani iska ya soma kaɗawa mai mugun ƙarfi ,ga wasu inuwoyi da suka soma yin rawa a jikin bangon ɗakin.Yadda ake mini raɗa haɗi da yi mini dariya duk sai na ruɗe na ƙwala ƙara haɗi da janye hannuna daga jikin fitila,nan take ɗakin duhu ya ziyarce shi.Wani ihun na sake yi a karo na biyu jin an jawo ni an matse ni ga bango,zan sake buɗe baki na ji yatsansa a ciki haɗi da sautin muryarsa “shuuut!” tsit na yi ina sauraren bugun zuciyoyinmu da suke gudu a tsiyace lokaci guda........ [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 05 Da sauri na lumshe ido haɗi da jan ajiyar zuciya jin yana busa mini iskan bakinsa a fuska.Murya can ƙasan maƙoshi ya ce “faɗa mini me ki ka gani?” Tambayarsa ita ta hararo mini abu na ƙarshe da ya razana ni,da wani mugun sauri na jimƙe gefen cikinsa ina jin wani tsoro na sake riskata.Kuka na soma yi ƙasa-ƙasa ina jin duniyar ta ishe ni,a hankali ya ɗan janye daga gare ni tuni kuma na buɗe idona ina kallonsa.Kamar wata mahaukaciya na ce masa “don Allah wace ce ni ? Ita kuma wannan budurwar da na gani daidai can tana kukan jini?” Bai bani amsar tambayoyin ba,sai ma hannunsa da ya saka ya cire nawa da ke gefen cikinsa.Gadon da na tashi akai ya je ya kwanta tare da kiran sunan Jabeer,shi kuma kamar mai jira ya shigo yana wani kallona kafin ya nufi Mu'azzam da ke faman kama kansa.Magani ya shafa masa mai wani mugun ƙarfi kamar na aljanu sai na ga ya miƙe daram yana wani hararena kafin cikin masifa ya ce “matsala ce ke! Duk in mun haɗe sai kin tono mini masifa,gaba ɗayanki matsala ce fita ki bani wuri” ya ƙarashe cikin tsawa,duk kuma sai na tsorata jikina ya soma rawa. “Haba Mu'azzam ka yi haƙuri mana,tun da ka soma wannan aikin ai dama dole ka dinga samun matsaloli a rayuwarka kuma ma ai ba ita ce farkon patient ɗinka da ka fuskanci makamanci haka ba” Jabeer ya faɗa cikin rarrashi. A zafafe ya ce “don Allah fitar mini da ita malam kai ma ai har da kai ake saka mini ciwon kan” Jabeer ya ɗan yi murmushi kafin ya ce “zo mu tafi” sai ya yi gaba na take masa baya ina mai waiwayen Mu'azzam wanda ke aiko mini harara.Muna fita daga ɗakin na ja ajiyar zuciya,sai na ji numfashina ma ya fi tafiya daidai in ban tare da shi.Har muka sauko ƙasa Jabeer na bani labarin Mu'azzam ɗin yadda yake da saurin fushi da kuma kirkinsa,ni dai iyakata saurare amma ban ce komai ba.Muna saukowa Maryam ta zo da sauri ta rungume ni tana mai shafar fuskata ta ce “fatan ba ki yi kuka ba?” Kujerun na duba sai na ga an mayar da su yadda suke tun farko,dama can masifarta ce ta sa ta tado mu.Murya a raunace na ce “don Allah Maryam mu koma gida” “Za mu koma har lokacin tafiyar ya yi,kin ga zo mu koma ɗaki” ta faɗa tare da jan hannuna.Ko da muka isa sai na ji hancina na fizgo mini irin ƙamshin nan da na ji a ɗakin sirri na Mu'azzam tamkar kuma ana ankare da ni haka nake jin ido na bin duk illahirin jikina.Banda tausayin kaina babu abin da nake yi,sam na kasa yarda Maryam ta gusa ta bar ni ko toilet in zan shiga sai ta je kusan ƙofa ta yi tsaye kuma ba na saka key.A wunin dai cikin ɗaki muka yi shi,hatta abincinmu Joy ne yake kawo mana shi. A washegari sai wani sabon al'amari ya riske ni shi ne kasa riƙe kaina.Kwaɗayi kawai nake ji yawuna suna tsinkewa,amma sam banda tabbacin mene ne nake so.Da abin ya dame ni haka na fita na nufi kitchen,har tuntuɓe nake yi jin ƙamshin nama na tashi ina shiga kuwa na tarar babu kowa sai ƙatuwar tukunyar da ke kan gas.Sam ban damu ba haka na buɗe ta na soma tsamo naman,da zafi da komai haka na dinga ci ina haɗiyewa kafin na farga na cinye nama tasss sai ruwan romo kawai su ma haka na soma lasarsu ina siɗar hannu kafin na gaji na bari na koma ɗaki.Da na shiga na tarar da Maryam na aiki da system,ban tambaye ta ina ta same ta ba kawai na haye bed na soma lumshe ido ina son yin baccin gajiya saboda gudan aikin da na yi na cinye naman ƴan gida. Babu jimawa kuwa na faɗa duniyar mafarki,kamar kullum yau ɗin ma mutane ne na gani masu yawa sun saka ƙatuwar tukunya a gaba suna rawa da juyi haɗi da waƙa.Wutar murhun sai ƙara ci take yayin da naman mutanen da ke cikin tukunyar sai tafasa yake yi.Kamar mai neman wani abu haka na soma dube-dube ina kallon ko ina na wurin har idona suka sauka kan Dr Bilal yana zaune daga gefe duk alamomin damuwa sun bayyana a gare shi.Ina dab da na yi masa magana na ji wata mahaukaciyar tsawa wacce ta yi silar fizgo ruhina daga waccan duniyar zuwa wannan.Dakyar na iya buɗe idona da suka yi mini nauyi na zube su kan turɓunaniyar fuskarsa mai cike da masifa.Har na buɗe baki zan tambaye shi lafiya amma ya wani fizgo ni a tsiyace,babu shiri gangar jikina ta rabu da gado na zo na faɗa kan ƙirjinsa.Wata irin muguwar matsa ya yi mini yana mai cewa “wato bacci ma ki ke yi saboda kin raina ni ? ” Ƙoƙarin ƙwace kaina na soma ina mai yin nishin azaba “washhhh! Ka bari don Allah ” ya nuna mini yatsa kenan zai ƙara yi mini wata masifar muka jiyo muryar wani babban mutum na kira sunansa,haka ya wani ja ni ƙiiii har muka fito babban falon nan na tarar da kowa na gidan tun daga ƴan aiki har wani dattijo da nake kyautata zaton mahaifin Mu'azzam ne saboda yadda suke mugun kama da juna. “Ke muguwa mayya uban wane ne ya baki izinin shiga kitchen ki cinye dukkan naman da ake soyawa Yayana? To yanzun nan zan sa ki amayo shi”Goggonsa ta faɗa tana mai nufo ni amma shi Daddyn ya dakatar da ita “Kabira ki bar maganar nan. Mu'azzam faɗa mini wace ce wannan?” Maimakon ya bai wa mahaifinsa amsar tambayar sai kuma ya soma yin masifa,“ Daddy yanzun nan ka gama masifar kan sai an nemo wanda ya cinye naman kajinka yanzu kuma da aka fito da ita ka koma yin magana cikin ruwan sanyi kana tambayata cikin sanyin murya” Daddy ya dubi kowa ya ce su watse kafin ya ce “zo nan ƴata” Mu'azzam na duba ina son ya sakar mini hannuna,sai da ya murɗe shi kafin ya sake sa shi ɗin ma saboda Daddy ya ce ya yi.Kamar mai tsoron taka ƙasa haka na je na yi tsaye gaban Daddyn na kasa ɗaga kai na dube shi. “Faɗa mini ƴata ke ce ki ka cinye naman kajin?” ya tambaye ni,da yake ban san kunya ba na girgiza kai na ce “ba ni ce ba Daddy kum...” da sauri Mu'azzam ya katse ni yana cewa “ke maƙaryaciya don Allah ki yi wa mutane shiru don kowa ya san ke ki ka cinye shi” Na girgiza kai ina kallon Daddy na ce “da gaske ban ci ba Daddy kar ka yarda da shi ƙage yake yi mini saboda ya tsane ni” ina rufe bakina Mu'azzam ya wani dungure mini ƙeya yana cewa “dubi can” ya nuna mini tv,ina dubawa kuwa na hangi kaina a ciki sai fizgar naman nake yi ina yarfa hannu. Wata irin kunya ce ta luluɓe ni da sauri na sunkuye kai,ina mai cewa “Daddy ka yi haƙuri!” Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce “zo ki zauna nan ki faɗa mini irin muguntar da yarona ke yi miki ” inda ya nuna mini ɗin na zauna shi ma ya zauna yana mai kallona tare da jefo mini tambaya “a ina kuka yi haɗuwarku ta farko ke da my hero?” Da sauri na ɗaga kai na dubi Mu'azzam wanda firgici duk ya bayyana a fuskarsa,da wani mugun sauri ya ce “haba Daddy mene ne na wani tambayarta? Ke tashi ki koma ciki” Dariya ya bani wannan yasa na toshe bakina, wato yana tunanin zan sanar da Daddy na ce a cikin toilet ne.Lura da ba zai so hakan ba yasa cike da tsokana na ce “Daddy mun haɗu ne a cikin ...” yadda ya wani zo shuuu ya kai hannunsa ya toshe bakina shi ya haifar masa da faɗuwa ƙasan capet kusa da ƙafafuna. Na fiddo ido waje ina kallon tsakiyar nasa idon da suke ɗauke da wani irin ƙwarjini da razani.Tsawon lokaci muna kallon junanmu kafin Daddy ya yi gyaran murya,da sauri ya janye hannunsa tare da tashi tsaye ya wani cabki kafaɗata ya miƙar da ni tsaye ya soma jana. Banda kallonsa babu abin da nake yi,yadda sumar kansa ke wani tashi cikin iska jijiyoyin gaban goshinsa na daɗa fitowa da alamu ransa ya ɓace ne.Sai da ya kai ni har bakin ƙofa sannan ya tura ni gefe,bayana ya mannu da bango yatsa ya nuna mini yana gangame fuska,tsabar masifar tasa ta kai ƙololuwa bai iya furta komai ba. Da dukkan hannuwana na dafe ƙirjinsa don tunkuɗe shi amma ko gezau haka yake currr kan ƙafafunsa,sai na janye su da sauri tare da sunne kai .Can ƙasan maƙoshi na furta “ka yi haƙuri ni ma ba zan iya faɗawa Daddy irin halin da na ganka ba a haɗuwarmu ta fark...” ban ƙarashe faɗar kalmar ƙarshe ba ya shaƙe mini wuya,duk idona suka fito sai da ya kusa sheƙa ni lahira sannan ya janye hannunsa tare da tafiya ya bar ni ina faman tari.Dakyar na ƙarasa ɗakinmu,na ɗauki ruwa na soma sha ina bubuga ƙirjina da nake jin tamkar numfashina zai ɗauke. Da na gama shan ruwan na yi tunanin Maryam za ta tada mini zancen kaji da na cinye amma shiru ta yi sai alamun damuwa da na ga dai a fuskarta.Haka na raɓa gefenta na zauna ina kallon system ɗin,sosai abin da na gani ya ɗauki hankalina.Ba komai ba ne sai hotunan wasu cover masu ɗauke da abubuwan ban tsoro da kuma firgitarwa.A duk cikinsu babu wanda ya fi ɗaukar hankalina sai na wani da aka yi zanen harshe da kuma takaitaccen bayani.Ban yi nauyin baki ba na ce “Maryam wannan ɗin duk na mine ne?” “Bincike nake yi” ta bani amsa tare da rufe system ɗin,ina shirin yin wata tambayar Joy ya yi sallama tare da cewa “Daddy na kiranki” a yadda ya kalle ni yasa na fahimci ni ce ake kira,da sauri kuwa na tashi saboda haka kawai na ji Daddy ya kwanta mini a rai ko don ban tashi na ga mahaifina ba oho. A falo na tarar da shi ya saka tv yana kallo,sai da na rusuna sannan na ce “Daddy ga ni” Remote ya ɗauka ya ƙara sauti,ya yi mini alama da hannu na matso.Ƙasan capet na zauna,murya can ƙasa-ƙasa ya ce “faɗa mini daga wane gari kuke?” “Kibri!” na basa amsa ,sai ya washe baki ya ce “ni ma asalina can yake,aiki ne ya kawo ni Yawunde.Faɗa mini a wacce unguwa kuke a Kibri?” Ina shirin yin magana Mu'azzam ya ratso falon kamar wanda aka jefo daga sama, remote ya ɗauka ya kashe tv sannan ya wani zubo mini mugayen idonsa,da sauri na sunne kai ina turo baki gaba. “Daddy me ka ke yi haka? Wannan ɗin patient ɗina ce,kar ka soma jawo ta a jiki kawai don larurarku ɗaya da ita.Kuma ka bar ƙoƙarin cusa mata wasu abubuwan a kanta sam ban son haka” Mu'azzam ke faɗa yana wani kumbura kamar fulawar da ta ji yis. Shiru Daddyn ya yi na wani lokaci kafin ya ce “babu ruwanka don na yi hira da ita ,kai da ita duk matsayi guda ki ke a wurina ita ma kamar ƴata haka na ji Allah ya ɗora mini ƙaunarta” Mu'azzam ya waro ido yana mai cewa “daga ganinta yau shi ne har ka yi mata matsayi irin nawa? Ke taso mu je” ya faɗa a tsawace har sai da na zabura.Ina kumbure-kumbure na bi bayansa har muka isa bakin mota,shi ya buɗe mini murfi na shiga na zauna yayin da shi kuma ya zauna mazaunin direba.Gudu ya soma yi kamar zai tashi sama har muka isa wata asibiti,ko ta ina mahaukata ne ke shawagi duk an ɗaure musu ƙafafu da kaca.Tsoro ne na ji ya saukar mini ganin ya zagayo ya buɗe mini tare da bani umarnin na fito,idona da suka cika da ƙwalla na sauke cikin nasa sai na hango zallar ƙiyayyata a ciki.Finciko ni ya yi yana masifa,“saboda wannan shegen kallon da ki ke yi mini sai na ƙwaƙwule miki shegun idon nan naki masu kama da na mujiya” haka ya dinga jana har muka shiga wani sashe,cike da girmamawa likitan ya zo ya gaishe shi tare da basa kujera tsabar tsiya irin tasa ƙin zaman ya yi sai ni ya zaunar tare da canza harshe zuwa English ya soma yi masa bayanin da ban san na mine ne ba amma lokaci zuwa lokaci likitan yana ɗan dubana. Can ya ɗauki waya ya yi kira ,babu jimawa kuwa sai ga wata mata ta shigo da hannu ya yi mata nuni da ni ita kuma ta kama hannuna.Kai na soma girgizawa ina mai kallon Mu'azzam,yayin da hawaye suka soma yi mini ambaliya.Wata irin wawar runguma na yi masa tare da ƙanƙamesa na fasa kuka mai tsuma rai,duk yadda ya so ya fincike ni kuwa ya kasa don ba ƙaramin riƙo na yi masa ba. “Kar ka bari su tafi da ni wallahi ni ba mahaukaciya ba ce” shi ne kawai abin da nake nanata masa,daga bayana na ji shigar tsinke a damtsena wanda ko tantama babu allura ce aka tsira mini.A nan take na ji duk jikina ya saki,doli dangin naƙi tasa na saki Mu'azzam yayin da nurse ɗin ta tallabo ni ta ɗora kan weelshair.Wani bacci-bacci nake ji ,shi ne ya gyara mini zaman kaina yana mai cewa “ki kula da ita sosai sannan ki tabbatar kin yawata da ita duk wani sashe da lungu na cikin asibitin nan” yana gama faɗar haka ta soma tura ni,haka na dinga binsa da ido har muka fice daga ɗakin.Ta wata doguwar hanya ta bi da ni mai shegen duhu da kuma kukan tsuntsaye haɗi da ƙarar faɗuwar matattun ganye da ƴaƴan bishiya.Jin wannan abu sai ya soma hasko mini wani baƙin al'amari da ya taɓa faruwa a shuɗaɗiyar rayuwata..... [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 06 Tana daɗa tafiya da ni cikin duhun hanyar ina kuma daɗa samun wankin ido game da rayuwata.Tun abin yana zuwar mini da sauƙi har ya kai kaina ya soma matsanancin ciwo tamkar zai tawartse yayin da kuma dukkan illahirin jikina ya soma yin ƙaiƙayi haɗi da motsi.Ba tare da na shirya ba na ƙwala wata gigitaciyar ƙara,daidai nan kuma hancina ya soma ambaliyar jini sai kuma numfashina ya soma barazanar ɗaukewa.Da bala'in sauri ta ida ƙarasawa da ni wani ɗaki wanda ƙwayaƙwayin lantarki suka haska.Taimakon gaggawa ta soma bani don tsayar da jinin da ke zuba,yayin da ni kuma hankalina da tunanina ya soma shawarar ta wacce hanya zan bi na damƙe kurwarta.Haka kawai na samu maƙogorona da soma yin rawa yayin da idanuna suka soma juyawa suna kaɗawa kamar garaya,cikin abin da bai fi minti biyu ba na ci galaba kan nurse ɗin na damƙe kurwarta sai dai fa haɗiye ta ya gagare ni.Baya da baya na ga ta soma yi tare da danne ƙirjinta da ya yi mata nauyi,da gudun bala'i ta fice. Idonta kamar za su rufe haka ta ƙoƙarta ta koma can ofis ɗin babbansu,tana kawowa ta zube ƙasa idonta na juyewa. Hankali tashe ya soma ambaton sunanta,ganin ta kasa cewa komai ya je bakin ƙofar toilet wacce Mu'azzam ya nemi a barsa ya shiga don juye larurarsa ta yawon fitsari. “Dr Mu'azzam Please ka yi sauri ga nurse ɗin da na wakilta don kula da patient ɗinka nan ta dawo cikin mawuyacin hali” Cikin azama kuwa ya fito,kallo guda ya yi wa nurse ɗin ya fahimci abin da ke faruwa.Maimakon hankalinsa ya tashi a'a sai ma wani murmushin gefen baki da ya yi,sannan ya ƙarasa ya taɓa goshinta ya soma karanto wasu addu'o'i nan take ta soma yin gumi sai kuma bacci ya ɗauke ta. Mu'azzam ya ce “a kaita wani keɓaɓen wuri,kar wanda ya tayar da ita zan kula da komai” yana gama faɗar haka ya fita,idonsa ya lumshe ya soma jefa ƙafafunsa ruhinsa na yi masa iso izuwa ɗakin da nurse Fateema take .Yana ƙara matsawa yana kuma ƙara jiyo hargowar baƙin ruhin da ke mallakar gangar jikinta sai cika yake yana batsewa,yana isa kuma ƙofar ta buɗe da kanta. Tun bayan fitar nurse ɗin nake ta ƙoƙarin haɗiye ruhinta amma tamkar an yi wa maƙogorona dabaibayi haka nake ji.Yana shigowa ɗakin na tsaya cak da abin da nake yi,na zuba masa idona da suka rikiɗe suka zama tamkar wuta. Cikin wata murya da ba tawa ba na ce “Agent Mu'azzam ko kuma na ce Dr hahaha!” Sai a lokacin ya buɗe idonsa yana mai yin murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa ya ce “ban san wace ce ke ba! Haka kuma ban buƙatar sani,sai dai da dukkan alamu abin harina tuni ta san da zamana ” Wata dariya na ƙara jin na yi kafin na motsa bakina “zai fi kyautatuwa ka fita daga hanyata don ni ɗin ba ire-iren ruhikan da ka saba cin karo da su ba n...” ban ida rufe bakina ba Mu'azzam ya ɗaga hannunsa na dama yana mai cewa “daga Allah muke,gare shi za mu komawa,sannan a gare shi muka saka dukkan yardarmu ” tamkar feshin wuta haka kalamansa suka samu tasiri a gangar jikina,wata irin banƙarewa na yi ina zalzalo harshe yawu suka soma zuba.Cikin hargowa na buɗe bakina na soma yin magana wacce ainahi ba daga tunanina take ba.“Kar ka sake ambaton sunan Allah a inda nake ban son ji,ban son kuma mutane masu sonsa” Dr Mu'azzam ya ƙara tawo kusa da ni idonsa na wani irin hasken imani,ya ce “tun da har ba ki son haka to ki fita ki koma duniyarku,ki bar gangar jikin nan ta zauna lafiya” Murya a shaƙe ruhin da ke cikin jikina ya ce “gangar jikina ce,saboda ita ɗin tawa ce kuma babu wanda ya isa ya mallake ta in ba ni ba ” Mu'azzam na jin haka ya soma yin wasu addu'o'in masu mugun ƙarfi wanda hakan ya saka ruhin jikina don dole ya koma ya lafa sai tunanina ya dawo.Wata irin gajiya ce na ji a jikina wacce ban san dalili ba,don duk abin da ya faru da ni na manta ban riƙe komai ba. Shi ne ya zo ya miƙar da ni tsaye, toilet ya kai ni bayan ya yi addu'ar shiga.Fuskata ya wanke mini da bakina da kuma hannu da ƙafa,ya motsa baki dakyar ya ce “ki ida wanke sauran jikinki sai ki saka wannan ” sai miƙo mini irin rigar wankan nan da ake sakawa kafin ya fice. Hijabina da rigata da suka ɓace da jini na cire da kuma sauran suturar da ta rage,na jawo pampon na ida watsa ruwa ga dukkan jikina bayan na gama na saka rigar kamar yadda ya ce sai dai fa ba zan iya fita da ita ba saboda ba ta saka ƙasa ba. “In kin gama wankan ki buɗe ƙofa ki karɓi wannan ” na ji muryarsa daga bakin ƙofa,sai na je na ɗan buɗe tare da miƙa masa hannu sai ya miƙo mini leda na karɓa na maida ƙofar.Da na duba sai na ga iya auduga ce babu pant ga kuma wanda nake da duk ya jiƙe,dole tasa na yi dabara na saka ta haka nan sai kuma na ƙara zuwa bakin ƙofa na yi tsaye. “Ki fito” ya faɗa a dake,cikin rawar jiki na fita ina ƙanƙame jikina.Ya ja wani dogon tsuki kafin ya kamo hannuna,ganin zai fita da ni murya na ɗan rawa na ce “na baro pant ɗina a toilet,kuma...kuma haka zan fita?” “Kin ga malama ki yi mini shiru da bakinki,shi pant ɗin a tare aka haife ku? ” ya faɗa yana hararena,idona suka kawo ruwa na ce “rigar ba ta sauka ƙasa ba ƙafafuwana a fili” Cak ya tsaya ya soma yi mini masifa “to me za a kalla a jikinki? Wa ki ga yana da lokacin kallonki a kaf asibitin nan? Ko ba ki ga duk mahaukata ne ba su sun san wani abu kallon jiki?” “Kenan kai ma mahaukaci ne?” na samu bakina da furtawa.Wata irin damƙa ya yi wa hannuna har sai da na saki ƴar ƙara kafin ya soma jana ƙiiiiii har muka fito harabar asibitin,cikin sauri na ce “ka tsaya ƙunzuguna ya faɗi!” tamkar zai shaƙe ni haka ya tsaya yana kallona daidai nan kuma wasu likitocin maza suka nufo mu.Da mugun sauri ya buɗe mota ya tura ni ciki,ya duƙa ya ɗauki audugar da na yi amfani da ita ya cillo min abata. Daga inda nake zaune na ga suna magana da likitocin amma ban ji abin da suka ce ba,can kuma ya buɗa mota ya shigo tare da yi mata key muka bar asibitin. Yana tsaka da tuƙi ya soma jan tsuki wanda ban san dalili ba,da na ga ya mayar da tsukin kamar mai jan casbi na ce “ya dai meke faruwa?” A zafafe ya ce “ina ruwanki da ni ? Ki iya da taki matsalar ki bar mini tawa ” Cikin sanyi na ce “ka yi haƙuri na yi tunanin ko zan iya taimakonka ne” bai ce mini ufan ba har ya zo wajen irin toilet ɗin nan na kan hanya ya tsaya,sai da ya da ya rufe fuskarsa da wani ƙyalle sannan ya ɗauki gorar ruwa ya fita ni dai ina kallonsa har ya shiga banɗakin. Mu'azzam na shiga toilet ya ga hannunsa da kumfan jini har ya bushe,ya ja tsaki ya fi sau goma yayi ta wankin hannunsa a zuci yana cewa ‘ tun da ta shigo rayuwata muka ƙulla alaƙa da matsala,in ba masifa ba mene ne abin yin sakaci har ƙunzugunta ya faɗi ƙasa’ kusan ruwan a wankin hannu suka ƙare,yana gama fitsarin ya fito ya yi cilli da gorar yana hararen nurse Fateema da ke can zaune cikin mota. A yadda ya rufe murfin da mugun ƙarfi na fahimci cewa yana cikin fushi,sai na ƙara kama kaina da tunanin ta ya zan shiga cikin gidansu da wannan rigar wankan? Me ƴan aikin gidan za su ce waɗanda har zuwa yanzu ban san adadinsu ba tsabar yawansu? Tamkar ya shiga tunanina kuwa sai na ga yana satar kallon ƙafafuwana da suke a fili,wani ƙaton mall ya tsaya ya saya mini doguwar riga ya cillo mini yana wani haɗe rai amma ban damu ba na kuwa saka har da ƴar guntuwar godiya na yi masa. Muna isa sai na tarar da Ammynsa ta shigo,wani irin farin ciki ne na ji ya mamaye ni har ban san lokacin da na je a guje na rungume ta ba. “Har kun dawo? Ban jima da shigowa ba ni ma,ina shi Mu'azzam ɗin?” Ammy ta tambaya.Daga can baya ya ce “ta ya za a yi kin ganni tun da kin canza yaronki da baƙuwa” a sautinsa za ka iya tsinkayo tsantsar kishi.Sai kuma ya tako inda muke tsaye yana mai cewa “malama matsa daga nan na ji ɗumin mahaifiyata ” da mugun sauri kuwa na je zan jaye jikina daga na Ammy amma ta dakatar da ni tana mai cewa “rabu da shi ai saboda ke na zo garin,ina can ina tunanin halin da kike ciki da na kasa jura shi ne na zo ” Wasu yawu na haɗiye na tsoro ganin yadda Mu'azzam ke ƙara gangame fuska, murmushin ƙarfin hali na yi ina mai cewa “Ammy zan shiga daga ciki in kun gama gaisawa sai na fito” “To Fateemana ki je zan zo da kaina na same ki” Ammy ta faɗa tana murmushi kafin ta kama hannun Mu'azzam kamar wani yaro su haura sama.Ni ma can ɗakinmu na wuce ,abu na farko toilet na shiga na haɗa ruwan ɗumi na yi wanka sannan na zo na kimtsa.Wata irin yunwa nake ji hakan yasa na fita a tsorace zuwa kitchen,Maryam na tarar da Joy suna hira kuma da dukkan alamu gulmata suke yi. Ya ɗan sunne kai yana mai cewa “ga ma ta nan ta shigo Please ki sanar da ita” Maryam ta yi ɗan murmushi tana mai cewa “kar ka damu Joy zan yi mata magana,ungo wannan ka kai kan dianing” ya karɓa tare da ficewa.Sai a lokacin ta dube ni tana gimtse dariya,na ce “ni dai yunwa nake ji ki fara bani abinci kafin wannan shirmen ” Ta ce “ban ƙarasa ba amma ga snack ki ci” ta zuba mini shi cikin plate jikina har rawa yake na karɓa,ina shirin fitowa muka yi karo da Joy ina shirin faɗuwa ya kamo hannuna yana wani murmushi haɗi da bani haƙuri. Wata mahaukaciyar tsawa muka ji ,da mugun sauri ya saki hannuna jikinsa ya soma yin ɓari yayin da shi kuma shugaban ƴan tsamin rai ya ƙaraso yana zuba masifa har da cewa in iskanci Joy ya sa gaba zai kore shi daga aiki,bawan Allah shi kuma har da hawayensa.Bayan ya gama yi wa Joy bala'i ya juyo kaina,plate ɗin hannuna ya karɓe ya miƙawa Joy kafin ya damƙi hannuna ya soma jana. Tsabar masifa bibiyu haka yake taka step ɗin har muka isa can sama,wanda yake tamkar wata fadar sarki.Yarɓi ya yi da ni yana mai nuna mini hannu,sai dai kafin ya yi magana Ammy ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunan da ke jere tana mai tambayar “meke faruwa a nan? ” “Ki tambaye ta! ” ya faɗa cikin ɓacin rai,haka kawai na ji kuka ya zo mini na je bayan Ammy na ɓuya. “Kaf patient ɗin da na taɓa samu babu wacce ke caza mini kai irinta,banda wahala da matsala babu abin da take kawo mini” ya faɗa kamar zai fashe. “Ka yi haƙuri Mu'azzam ba ka ganin har yanzu ita ɗin yarinya ce?” Ammy ta faɗa . “Babu wata yarinta kawai mahaukaciya ce,ina ce Maryam ƙanwarta ce amma kin taɓa ganin ta yi shirme irin nata? Yanzu fa don sakalci a tsaye na ganta tare da Joy yana yi mata murmushi har da wani riƙe hannunta,amma da yake ita sokuwa ce ko kaɗan ba ta damu ba” Ammy ta yi murmushi tana shirin yin magana Joy ya zo yana cewa “yalaɓai ka yi baƙuwa ta ce na baka wannan ” Karɓa yayi ya karanta sai na ga ya dube ni kafin kuma ya fice.Zuciyar Mu'azzam har wani dokawa take da sauri,a can bakin ƙofar shigowa ya je ya tsaya a daidai lokacin kuma mai gadi ya yi masa da nuni da hannu sai ya nufi ɓangaren. Daidai tsohuwar motar da ta kawo su Fateema ya ja ya tsaya yana kallon matar wacce take duƙunƙune cikin wani tsohon bargo. “Taso mu shiga daga ciki” ya faɗa ,Mama wacce jikinta yake cike da rauni ta yi ƙarfin halin tashi tsaye.Bargon ta jawo ta rufe fuskarta da shi sannan ta take masa baya suka shiga daga ciki,suna tafe yana addu'ar Allah sa Ammy ta ja mahaukaciyar yarinyar can sun bar sashensa ai kuwa ba su nan. Wani ɗaki ya kai Mama,wani haɗin magani ya yi mata mai kyau ta sha sai kuma ya je ya shiga toilet ya yo fitsari ya dawo ya zauna ya tisa ta a gaba. Cikin rauni ta soma yi masa magana “sunana Halimatu,na fito daga garin Kibri a wani ƙauye da ke nan kusan rugar farko ta Fulani .Ƴata guda Maryam,sai kuma Fateema wacce ta kasance ƴar kishiyata ” tana kawowa nan sai ta yi shiru.Mu'azzam ya ce “kenan ba ke ce ainahin mahaifiyar Fateema ba?” Ta jinjina kai kafin ta ci gaba da cewa “Hindu ta kasance kishiyata amma sam ba mu yin irin wannan mugun kishin,hasali ma tamkar ƴar uwa haka ta ɗauke ni.Mijinmu malam Abdu ya kasance manomi sannan makiyayi,a kullum cikin kawo mana kayan lambu da sauran abubuwan masarufi yake da kuma kawo ciyawa wa dabbobinsa hakan yasa gidanmu bai rabo da macizai kusan kullum sai ya fitar mana da su. Wata ranar Alhamis ina madafa ina tuƙa tuwo sai na ji ihun Hindu tana cewa “na shiga uku maciji ! Maciji a shimfiɗar Fatee” a daidai lokacin da nake fitowa a wannan lokaci ne kuma da idona na ga Hindu ta saka wani mashi ta tsire macijin tare da cilla shi can cikin ciyayi sai kuma ta ɗauke ƴarta Fateema wacce a lokacin ba ta fi wata shidda ba da haihuwa. Na ƙarasa tare da yi mata jajaye kafin na koma madafa na ci gaba da yin girki.Bayan na gama ne na kira Hindu don cin abinci,a nan ne fa muka ga wani sabon al'amari hannun Hindu ya kumbura ya yi suntum ya cika da ruwa” Mama na kawowa nan sai ta yi shiru tana goge ƙwalla,yayin da Mu'azzam ya ce “jira na shiga banɗaki na dawo” sai ya je ya shiga toilet cak ya tsaya saboda inuwar mutum da ya gani a tsaye cikin ɗan madaidaicin madubin da ke manne da bango....... Ga masu son fara yin payement,regular group 500, VIP group 1k via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 07 Kafin Mu'azzam ya yi wani motsi madubin ya yi wani irin motsi yana bado haske mai ƙuna,ya kai tafin hannunsa ya kare fuskarsa.Ƙarar tarwatsewar madubin shi yasa ya maido dubansa ga bangon,a gaban idonsa inuwar ke ƙara nitsewa tana shigewa cikin bango har ya bar ganinta.Fitsarin yayi sannan ya fita ya samu Mama wacce har yanzu ba ta bar hawayen ba,ya nemi wuri ya zauna yana mai cewa “ina jinki” Sai ta ci gaba da cewa “wani irin matsanancin kuka ne Hindu ke yi Fateema na taya ta,duk sai na rikice na rasa da wanne zan ji sai kawai na fita ƙofar gida a guje.Cikin sa'a kuwa na ci karo da malam ya shigo layin.“Lafiya meke faruwa Halimatu?” ya tambaye ni,na basa amsa “Hindu ce babu lafiya hannunta sai ƙaba yake yana tara ruwa” hankali tashe ya yi gaba muka koma can gida.Tuni Hindu ta fita hayyacinta,haka na goye Fateema na nemo maƙwabta suka taimaka muka kai ta asibiti. Da isarmu kuwa a fara yi mata aiki,ba a ɗauki lokaci ba kuma aka bamu result wanda ya nuna tana ɗauke da cutar suga ne.Kuma kar ka ji wani abu dukkanmu mun yi amanna da hakan hatta ita Hindun,sam ko da wasa ba mu kawo a ranmu wai macijirin da ta kashe ne silar ciwonta.Kwana uku muka yi asibiti kafin a sallamo mu,sosai hannun nata ke daɗa yin sauƙi haka na dinga girka mata duk wani abu da mai cutar suga zai ci.Cikin abin da bai fi wata biyu ba Hindu ta rame sosai,sai dai hannun nata tuni ya kame har ma ta kama aikin gida mun dawo walwala kafin kuma wata rana da dare muna tsaka da cin abinci ta miƙe tana cewa dukkan jikinta ke ciwo .Shimfiɗa ta yi ta kwanta,ƴarta Fateema sai ta je gun mahaifiyarta tana kuka ita kuma sai ta soma shayar da ita wacce wannan shayarwar ita ce ta zamo ta ƙarshe a rayuwarta don kuwa washegari da ciwon nono Hindu ta tashi.Malam ya nemo mata magani ta shafa sai dai tamkar wacce aka shafawa acid haka abin ya ƙara ƙamari,ka ji dalilin da yasa Fateema ta dawo hannuna na ci gaba da kula da ita.A cikin ciwon Hindu babu sauƙi ko kaɗan,kullum cikin ƙara ƙaruwa yake,tun muna zuwa asibiti mu dawo har ta kai da an riƙe mu can.Ba mu taɓa sanin ciwonta ba na asibiti ba ne sai wata rana da muka fito waje a farfajiyar asibiti don shan iska,wata mata bararoji irin masu bayar da magani ta zo ta yi tsaye tana kallon Hindu. “Ke kam me ya kai ki shiga hurumin da ba naki ba? Kin tayar da mugu yana bacci shi kuma ya baza miki guba a duk illahirin jikinki.Ki koma gida shi ya fi don kuwa maganin asibiti ba zai yi miki komai ba sai ma ƙara cutar da ke” shi ne abin da matar ta faɗa tare da yin gaba,sai Hindu ta dube ni a galabaice ta ce “kar dai a ce macijin da na kashe ne matar nan ke magana?” “Tabbas da ƙamshin gaskiya a maganarta amma bari malam ya zo” na faɗa ,ai kuwa da Abban Fatee ya zo muka shaida masa sai ya nemi a sallame mu muka koma gida muka soma yin maganin gargajiya.Sannu a hankali ciwon ya fara sauƙi sai dai kuma Allah ya hukunta shi ne silar mutuwarta ” tana kawowa nan sai ta yi shiru, Mu'azzam ya yi ƴar gyaran murya kafin ya ce “Allah ya jiƙanta ya yi mata gafara! Haƙiƙa ta yi babban kuskure na kashe maciji a tashin farko saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce *Macizai da ake samu a gidaje ana kashe su ne bayan an kira su sau uku su fita, saboda tsoron kar da su kasance cikin Aljanu, sai dai (nau'i biyu): Al-abtar da dhut-Tafifatan waɗanda ake kashe su koda a gidaje ne saboda Annabi (SAW)kawai ya haramta shi ga sauran macizai. _Al-Bukhari, babin farkon halitta n°3297 da n°3298 da Muslim, babin aminci, n°2233._ *- Al-abtar (الأبتر) shine wanda wutsiyarsa ta yi gajere,* *- dhut-tafifatayn (ذو الطفيتين) shine wanda yake da zane biyu a bayansa.* Wajibi ne a kashe waɗannan macizai guda biyu a kowane hali, saɓanin sauran da ake kashewa sai bayan an kira su su fita har sau uku, ta hanyar cewa misali: "Na kira ku ku fita daga gidana" ko kuma wani hukunci da zai yi gargaɗi ne kuma ya na nuna masa cewa an hana shi zama a gidan. In duk mutum ya yi haka amma macijin bai fita ba,hakan na nufin ba aljani ba ne,in ma shi ɗin ne to bai cancanci darantawa ba a kashe shi. Amma idan maciji ya kai masa hari, sai a bar shi ya ture shi, ko da a karon farko. Idan har hakan ya haifar da kashe maciji ko kuma a iya daƙile harin ta hanyar kashe shi, to a nan muna da hakkin yin hakan, kare kai ne. _Fatâwa Islamiyya juzu'i na 4, shafi na 450 da 451._ _Sheikh Muhammad Ibn Salih Al-Utheymine(r)_ To amma ni ban san wane irin nau'i ne ta kashe ba ko kin gansa da idonki?” Mama ta jinjina kai ta ce “ni kuwa na gansa,a hannun Fateema amma lokacin tuni ya bushe gawarsa ce ta tono bayan wani lokaci ”sai ta soma yi masa bayanin yadda macijin yake. Mu'azzam ya waro ido yana cewa “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” da sauri kuma ya tashi ya buɗe wani akwati ya ciro wani ɗan ƙaramin littafi ya shiga dubawa zufa na karyo masa.Cikin hukuncin Allah ya samo ainahin zanen macijin,jikinsa har rawa yake yi ya nunawa Mama ya ce “shi ne wannan?” ta jinjina masa kai,ya ce “ki kwanta ki huta zan fita ” Mama ta ce “ina son ganin Fateema” Ya ce “abu ne da ba zai yiyu ba,saboda a halin yanzu dodon da ke jikinta tuni ya farfaɗo ya fara mallakar tunaninta har ya yi nasarar kwantar da wata baiwar Allah,har yanzu kuma ban yi mata magani ba” Wasu sabbin hawaye suka zubowa Mama ta ce “don Allah ka yi ƙoƙari sosai ka tabbatar ta samu lafiya,ita ɗin amana ce mai matuƙar girma a gare ni ” Mu'azzam ya ce “kar ki damu wannan shi ne aikina shekara da shekaru ” “Na gode” ta faɗa tare da yin kwanciya,yayin da shi kuma ya fice. ★FATEEMA Sosai na ji daɗin yadda ya yi saurin tafiyarsa da aka ce ya yi baƙuwa.Ammy ta kama hannuna muka sauka ƙasa,can ɗakinmu muka je na nuna mata inda muke bacci sai kuma ta soma yi mana tambayoyi in ba mu fuskantar kowacce irin matsala.Ina shirin bata labarin abin da Goggo Kabira ta yi mana sai kuma Maryam ta katse mini hanzari tana mai cewa “Ammy me yasa kika zaɓi ki zauna can Duwala madadin nan?” Ammy ta yi murmushi ta ce “saboda kasuwancina,sannan Mu'azzam na yawan samun baƙi a can fiye da nan.Amma kar ku damu na kusa dawowa nan ɗin ko don saboda ku” Na ce “Ammy ai mu mun kusa komawa gida,kin ga mun baro Mama a can Kibri ita ɗaya” na ƙarashe faɗa da alamun damuwa a fuskata.Ammy ma duk sai ta nuna rashin jin daɗinta kafin ta ce “ki sa a ranki tamkar Mamarku tana tare da ku,sannan ina ku ɗauke ni tamkar uwa ” “To Ammy ” shi ne kawai abin da na iya cewa,kamar abin asiri haka Maryam ta zo ta shafi fuskata sai na soma gani dishi-dishi a dole na samu wuri na kwanta ina kallon lokacin da ta ja hannun Ammy suka fice. Bacci ne ke ta kawo mini farmaki,har na lumshe idona sai kuma na ji motsin ziyara haɗi da kaifin ido.Ban sani ba ruhina ke magana ko kuwa mine ne amma tambayar da na yi ita ce “wace ce ke?” budurwar da ke tsaye a gabana wacce wannan shi ne karo na biyu da na ganta ta bani amsa da “ki tambayi Mu'azzam shi zai baki wannan amsar,ko da yake na san bai son a yi masa zancena saboda yana tsoron kar na ɓata masa shirinsa ” “Wane irin shiri? ” na tambaye ta.Sai da ta yi wata gigitaciyar dariya kafin ta ce “duk wanda Mu'azzam ya kawo gidan nan saboda ya cutar da shi ne,ya yaudari ƴan mata bila'adadin da farko zai nuna miki yana sonki da zarar kin saki jiki sai ya miƙa ki izuwa TUKUNYAR MAYU ”tana gama faɗar haka ta ɓace a nan take kuma dafin da Maryam ta jefa mini ya saki jikina,da wani mugun sauri na diro daga kan gadon ƙofofin hancina na shaƙo mini warin fatalwa irin dai wanda na taɓa ji a ɗakin Mu'azzam.A tsorace na fita ina gudu sam ban ga tawowarsa ba sai ji na yi na kai masa karo,yayi baya da mu duk muka faɗi ƙasa sai dai ni a kan ƙirjinsa nake.A ɗan tsorace na ɗaga kaina ina kallon tsakiyar idonsa kamar yadda shi ma yake yi,na shagala sosai a kallonsa na ji ya yi cilli da ni gefe.Kaina ya bugu jikin bango,ban dawo daga cikin raɗaɗin da na ji ba ya soma yin masifarsa da ta zame masa sabo. “Jarababiya kawai in ba ki taɓa jikina ba sam ba ki jin daɗi,shi yasa kike tafe ba ki kallon gabanki.Kullum cikin gudu kamar mahaukaciya mtswww!” ya ja tsuki.Na tashi zaune dafe da kai ina kallonsa,duk masifar nan da yake faman zazzaga mini bai hana ni yi masa magana ba. “Fatalwa na gani cikin ɗaki” na faɗa tare da nuna masa ƙofa,shiru ya yi yana kallona kamar mai yin nazari kafin ya nufi ɗakin.Na take masa baya , dube-dube ya soma yi yana buɗar hanci can ya ce “me ta ce miki?” Shiru na yi don kuwa na manta,ya matso kusa da ni cikin ɗaga murya ya sake cewa “me ta ce miki?” Cikin rawar murya na ce “na manta” ya dungure mini kai yana cewa “saboda ƙwaƙwalwar kifi ce da ke shi ne ki ka manta abu mai muhimmanci mtswww sokuwa” sai ya fice tare da bugo mini ƙofa na zabura na je zan buɗe amma tamkar abin tsiya ƙofar ta ƙi buɗewa.Cikin kuka kuwa na soma jijiga ta ina kiran sunan Maryam,na fi minti biyar a haka kafin a buɗe ƙofar.Don mugunta ashe tun ɗazu bai tafi ba yana nan tsaye,wani murmushi ya saki yana mai jawo hannuna ya fiddo ni waje.Cike da jin haushi na soma kai masa duka shi kuma banda dariya babu abin da yake yi mini,wato burinsa dama shi ne na tsorata shi yasa ya rufe ƙofar. Dukkan hannuwana ya kama ya riƙe gam,fuska shaɓe-shaɓe da hawaye nake kallonsa.Cikin taushin murya ya soma magana,“ban san me mahaukaciyar nan ta faɗa miki ba,amma ina so ki yarda da ni kar ki saki ki saurare ta ko kuma ki yarda da soki burutsun da za ta faɗa miki.Ita ɗin muguwa ce,ba mutumniyar kirki ba ce don haka ina so ki aje hankalinki wuri guda ki yarda ki gane ba ki da lafiya” yana gama faɗar haka sai ya sakar mini hannuwa ya tafi,na bi bayansa da kallo har ya fice. Ko da na ƙaraso falo sai na tarar da Ammy da Maryam a zaune suna karatu,amma sam ba na Alkur'ani ba ne wani littafi ne daban .Gefen Maryam na zauna ina mai baza idona kan rubutun abin mamaki sai na ji wai zan iya karanta shi,amma sam ba da baki a'a ta ido kawai.Wani irin sanyi ne na soma jin jikina na yi kamar wacce aka saka a ƙanƙanra,yayin da kunnuwana suke tariyo muni wata murya wacce rabon da na ji ta tun ina ƴar shekara uku.Wannan murya ba ta kowa ba ce sai ta aljana macijiya,matar da take fito mini a zahiri ba wai cikin mafarki ba.Tunanina da lissafina ba su yi wani jinkiri ba suka ɗingiza ni izuwa shekaru ashirin da suka shuɗe a baya. A tsaye nake gaban wutar da ake dafa tumu,Mama da Abba suna yin hira jefi-jefi yayin da kuma gefe guda Abba ke ƙara juyara zangarniyar gero wanda yake farkon fitowa wanda kuma shi ake kira da tumu.Daga cikin wutar nake hango wasu manyan idanuwa masu mugun haske suna kallona,sam ban ji tsoro ba kasancewar shekara ta uku kacal a duniya sai ma abin ya burge ni har ta kai da na sa hannu a cikin wutar na kamo su sai dai ba iya idanu ba ne har da wani dogon bindi wanda ya kasance na maciji.A jikin bindin gasashen tumu ne jere rasss,haka na sa hannu ina ɗebowa ina ci yayin da idanuwan nan masu mugun haske suke daɗa yi mini wani kallo . Ina tsaka da morewa Abba ya ce “Fateema ungo wannan ki ci” Mama ce ta ce masa “ai ba za ta karɓa ba sai ta cinye wanda ke hannunta” ta ƙarashe faɗa tana mai hasko mini fitila,sai na ga ta yi cilli da ita tana salati a nan take kuma abin da ke riƙe da hannuna ya sulɓe mini ya koma cikin wuta.Abba ya ce “lafiyarki?” muryar Mama na rawa ta ce “busashen maciji ne a hannun Fatee” sai dai da Abba ya haska fitila babu komai a hannuna,sai ya ce kawai don har zuwa lokacin Mama ba ta fidda zancen maciji a ranta ba.Haka dai muka ci tumun muka kwanta,sai dai nawa baccin sam bai yi wani nisa ba na farka saboda wata murya da ke kiran sunana.Haka na tashi na soma takawa har na isa inda sautin muryar ke fitowa,cikin ciyawa ne,sai na ja na tsaya.Fararen idanuwanta masu matuƙar haske su ne abu na farko da na fara gani kafin ta ida fiddo ainahin jikinta wanda shi ma yake walwali yana fitar da wani hasken wuta abin sai ya burge ni na duƙa na ɗauke ta.Sosai muka yi wasa da ita wanda a ƙarshe ta kai ni wata duniyar mai cike da macizai irinta tana nuna musu ni tana cewa ƴarta ce ni.···· Sanyin ruwan da na ji a jikina shi ya farfaɗo da ni daga duniyar wankin idon da ake yi mini na tuna rayuwata ta baya.Maryam na gani a tsaye riƙe da bokiti yayin da kuma Ammy ke faman busa wutar hayaƙi,a hankali nake ƙara ware idona ina kallonsu so nake na basu labarin abin da na gani amma tamkar an toshe mini maƙoshi haka na ji ba zan iya bada labari ba.Miƙewa na yi na fita harabar gidan ,wani irin canji na riskata wanda sam ban san farkon tono baƙin sirrina ne ba.Can cikin jardin na ja na tsaya tare da nutsuwa ina sauraren wani amon murya wacce ba ta ƴan adam ba,sai da na nutsu irin sosai ɗin nan sannan na fahimci cewa sautin na fitowa ne ta cikin ciyayi.Haka na zube kan gwiwana na soma buɗe korin shuke-shuken har Allah ya kai ni ga wata daula ta tsutsotsi...... Only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 08 Tamkar yadda mutane ke kafa daula su yi gidan sarauta haka idanuna suka gane mini masarautar tsutsotsi.Kamar wata zararriya haka nake kallonsu suna ta hidindimu,abin da ya fi ɗaga mini hankali shi ne yadda aka yi har nake jin maganar da suke yi. Jikina ne ya soma yin rawa jin topic ɗin da suke tattaunawa a kai ba na komai ba ne sai na yadda za su yi su kashe Mu'azzam.Ban gusa ba sai da na ji ta yadda suka tsara plan ɗin,na miƙe da sauri ina tafiya ƙafafuna na harɗewa na nufi can wajen direba . Kame-kame na fara kafin na ce “Mu'azzam ya ce ka kai ni can wurinsa” na faɗi haka ne sanin shi ne direbansa.Ba tare kuma da yin gardama ba kuwa ya buɗe mini mota,na shiga gidan baya na zauna muna tafe ina tunanin abin da na gani ɗin. A can ɓangaren Mu'azzam kuwa yana fita direct babbar asibitinsa ya wuce.Bai iya duba kowanne patient ba ya dai samu wuri ya zauna suna hira da babban abokinsa Jabeer inda yake faɗa masa matsalolinsa shi kuma yana basa shawara. “Wallahi abokina tun da yarinyar nan ta shigo rayuwata duk komai ya ida cakule mini,kana ga fa a yanzu ko minti ashirin ɗin ban yi haka nake zaryar shiga toilet.Abin da ma na lura kamar in na samu kusanci da ita matsalar ta fi saurin taso mini,ina ga saura ƙiris ni ma na dinga saka pad ɗin” Mu'azzam ya faɗa yana wani kama kai. Jabeer ya ce “duk dai komai ya kusa zuwa ƙarshe tun da an samo bakin zaren ka gano kalar macijin da Ummarta ɗin ta kashe” “Babu wani sauƙi don har zuwa yanzu ban samu na yi magana da ita Fateemar ba,kuma abin takaici abokina ta ƙi yarda ba ta da lafiya to ta ya za a yi mata magani? Kuma fa Nadiya ta soma yi mata fatalwa tana fito mata,kai abin dai sai godiyar Allah ” Mu'azzam ya faɗa yana tashi tsaye ya nufi toilet,jimmm kaɗan ya fito yana haɗe rai. Jabeer ya ja numfashi kafin ya ce “amma me yasa da ka kai ta asibiti ba ka jona mata hullar gaskiya ba wacce za ta saka ta yin bayani don dole?” Mu'azzam ya basa amsa da “ta ya za a saka mata hulla alhalin dodon jikinta har ya riga ya bayyana,ni babban tashin hankalina ma bai wuce kar ta ƙi sakin kurwar nurse ɗin” Jabeer shi ma ya miƙe tsaye sannan ya buɗe wani ɗan ƙaramin littafi ya ce “ina ga kawai hanyar da ba ka son bi ɗin za mu ɗauka muddin muna son ceto kurwar nurse ɗin,ka ga masu amfani da maitar maciji abin da suka ƙi jura shi ne hayaƙi me zai hana ka ɗauko Fateemar a gwada yin haka ɗin ?” Mu'azzam ya ce “wannan solution ce mai haɗari,don ana iya wajen ceto kurwar ita Fateemar numfashinta ya tsinke tun da ainahi ba ita ce ke yin maitar ba,saka ta ne ake yi” sai kuma duk suka yi shiru suna nazari. Sosai direba ke sharara gudu har muka iso,shi ne ya yi mini jagora har zuwa ofishin Mu'azzam wanda a jikin ƙofar ma an rubuta sunansa.Ba tare da neman izini ko yin sallama ba na buɗe ƙofar da ƙarfi,a tare duk suka juyo suna kallona ni kuwa sam ban damu da irin kallon da suka yi mini ba na nufi Mu'azzam ina mai basa labarin abin da idona suka gane mini amma sai na ga suna kallon juna kamar ba su yarda ba. Cikin son sai na sa sun gaskata na ce “wallahi da gaske nake,in kuma ba ku yarda ba ku zo na nuna muku” .Harshe Jabeer ya canza sai kawai na ga Mu'azzam ya kama hannuna yayin da shi kuma ya take mana baya,cikin wata mota ce daban muka shiga inda Jabeer ya tuƙa mu.Duk da ban san gari ba amma na gane hanyar asibitin nan ce ta mahaukata,ina ji ina gani kuwa suka shiga da ni. Tamkar wata ƴar kaso haka Mu'azzam ya ɗaure ni jikin kujera,wanda kafin ya iya yin haka sai da ya sha fama da ni don har cizonsa na yi. “Jabeer kunna hayaƙin” Mu'azzam ya faɗa,shi kuwa tamkar jira yake ya buɗe wani akwati da ke cikin ɗakin sannan ya fiddo komai tare da haɗa komai. Ina ganin hayaƙi ya fara tashi na ƙara ƙaimin kuka ina mai ce masa “ina da cutar toshewar numfashi don Allah ku kash....” sauran maganar ce ta maƙale mini jin harshena ya soma zazzalowa yana ƙara tsayi har yana taɓo cinyata.Hayaƙi ya turniƙe mini hanci da maƙoshi,tamkar an zuba mini wuta haka gangar jikina ta ɗauki zafi.Ba a ɗauki lokaci ba kuma wannan abin da ke cikin jikina na ji ya soma yin magana,“in ma dai niyyarka ka kashe Fateema to ka makaro domin kuwa hatta cutar toshewar numfashin da take magana ni ce nan na haifar mata da shi,kuma ba zan baku abin da ku ke so ba yadda ka ƙulle hanyar da zan haɗiye kurwar nurse ɗin nan haka ni ma zan ƙulle maka ƙofar da za ka janye ta daga gare ni” Mu'azzam ya ce “Jabeer miƙo mini ruwan floris sannan ka ƙara zuba turaren a ciki” wata gora ya miƙo masa ya buɗe ta sannan ya soma watsa mini ruwan ,nan take kuwa na soma yin ihu ina son kubcewa ruhin da ya ɗauki mallakar tunanina kuwa sai kuma ƙara nanata wa yake yi ba zai bayar da kurwar ba. Tsawon lokaci da Lahaula Wala ƙuwata illa billahi sannan na ji wani abu ya gangaro maƙoshina ya fito da gudun bala'i.Tamkar dunƙulen gulusuwa haka yake,sai dai fari ƙal yake yana gama fitowa bakina ya fashe tare da yin sama cikin iska sai kuma a lokacin na dawo hayyacina. Cikin wata irin muguwar tsana nake kallon Mu'azzam don ni sam duk abin da ya faru a yanzu na manta shi shaf.Da kansa ya kwance mini igiyoyin da ya ɗaure ni da su,ya ɗauki wani ƙyalle ya fara goge mini hijabina da duk ya ɓace.Cikin jin haushi na ture shi tare da tashi tsaye,ban kuma yi jinkiri ba na ruga a guje na ɓalle ƙofa na fita. Yadda nake gudun da sauri yasa ban ɗauki lokaci ba na fito harabar asibitin sai kuwa na yi rashin sa'a a daidai wannan lokaci ne wani mahaukaci ya kubce.Cak na tsaya ina waro ido yadda ya nufo ni gadan-gadan,da wani bala'in gudu na yi baya zan koma inda na fito sai na ci karo da Mu'azzam.Banda wani zaɓi wannan yasa na nufe shi don tseratar da kaina sai dai ina tuni mahaukacin ya kwashe ƙafafuna sai da na yi sama kamar zan faɗi,amma wani irin haske ya fita idona ya daki ƙasa sai gani ina yawo cikin iska sam gangar jikina ta ƙi taɓa ƙasa. Da yake mahaukacin nada rabon wahala haka ya ja ƙafata ta baya,wanda ban san a ina na samu ƙarfin buge shi ba sai ga shi ya faɗi warwas. Daidai nan na yi tsaye kan ƙafafuna,yayin da kuma likitoci suka zo suka ɗauke shi.Ni kuwa sunne kai na yi ganin kallon da Mu'azzam ke aiko mini,kamar wata ƴarsa ya damƙi hannuna ya ƙara mayar da ni can ciki.Wani sashe na musamman muka shiga mai ɗauke da wasu zane-zane da ban san ma'anarsu ba. Hannuna ya saki tare da cewa “zauna can” ya nuna mini wata kujera mai hoton zaki,na maƙe kafaɗa na ce “ni gidan zan koma” rikitatun idonsa kawai ya zuba mini babu shiri na je na zauna. Wata hulla ya ɗora mini a kai sannan ya saka mini wani gilashi wanda ya kasar da duk hasken ganina.Tamkar makauniya haka na koma,abin mamaki kuma sai na ji na kasa yin motsi.Ina cikin sabon yanayin ne na ji tambayar Mu'azzam kamar daga sama. “Nana Fateema ina son ki bani labarin kanki,sannan wace ce ke ? Wasu irin laifuka ki ka aikata tun ƙurciya zuwa yanzu da kike zaune a gaban dodon Mayu?” yana gama dire kalamansa haka na ga rayuwata a cikin idona kamar wacce aka kunnuwa tv. “Kamar yadda ka sani sunana Nana Fateema a wannan duniyar,yayin da kuma a ɗayar duniyar ake kirana da Goddess/déesse.Rayuwata ta kasance ruwa biyu ,rabi ta normal mutum rabi kuma ta keɓaɓiyar duniya ta waɗanda ba su baccin dare sai na rana.Kamar yadda na gani a wani wankin idon waiwayen bayan rayuwata,a ranar da Abba yana gasa mana tumu a wannan ranar ce na yi gamdakatar da Jinniya wacce ta ɗauki matsayin uwa mahaifiyata sakamakon ɗanta da Momata Hindu ta kashe.Tun daga wannan lokaci sai ta soma zuwar mini a mafarki da kuma rayuwar zahiriya.Babban zunubin da na fara aikatawa shi ne na kashe matar Abbana wacce ya auro saboda jinkirin haihuwar da Mama ta samu .Tun daga ranar da ta shigo gidan Abba duk ya canza,ni kuma na kasa jura wata rana da dare na damƙe mata kurwar a cikin daren kuma ta mutu.Mutum na biyu kuma shi ne ƙanen mahaifina na kashe shi a lokacin da na cika shekara biyar a duniyar sakamakon zargina da ya soma yi ,duk wannan bai ishe shi ba ya soma bin didigina a garin nemo gaskiyar ni wacce ce na rikiɗa na zama macijiya na kashe shi har lahira” ina kawowa nan na yi shiru. Mu'azzam ya sake cewa “amma ta ya aka yi aka toshe miki hanyar ci gaba da yin mugunta?” “Mama mutum ce mai baiwa,tana ganin abubuwa a cikin mafarki wanda kuma ba kowa ke sanar da ita ba sai aljanunta.A cikin mafarki ta ga komai, amma da yake ta iya takun saƙarta sai ta yi shiru da bakinta ba ta sanar da kowa ba har Abbana.Ban san a ina ta samo maganin raba ni da ruhin dodon jikina ba kawai na samu kaina da rashin sinadarin.Sosai kuma na fahimci canjin da na samu, amma babu wanda zan iya yi wa magana sai dai abin yana damuna saboda kewar uwa Jinniya wacce ta ce ita ce mahaifiyata.Yawan tunaninta yasa na soma yin mummunan mafarkai na dinga zabura haɗi da yin suratai, wannan dalilin ne yasa Mama da Abba yanke shawarar kai ni wajen mai magani da ke can wani ƙauye mai nisa.Yayin wannan dogon balaguron mun haɗu da ƙalube da dama a bisa hanya,ciki kuwa har da lalacewar motarmu wacce Abba ya aro.Muna tsaka da tafiya ta tsaya cak, Abba ya fita yayi ƴan taɓe-taɓe kafin ya ce “ku fito ina ga sai na nemo mai gyara” Mama ta buɗe murfi muka fito tana mai cewa “a ina za a samu mai gyara cikin wannan dokar dajin?” “Zan dubo! Bari na fiddo muku tabarma ku zauna kafin na dawo” ya faɗa tare da buɗe Boot ya ciro mana tabarma.Mama na karɓa sai ya tafi,yayin da ta ja hannuna muka ƙetara can gaban wata inuwar bishiya.Tabarmar ta shimfiɗa tare da yin zaune ni kuwa tsaye na yi ina kallon wata mata mai fararen kaya hannunta na riƙe da ƙwaryar nono. “Fatee zo ki zauna” cewar Mama tana nuna mini gefenta. Na maƙe kafaɗa saboda hasken idon matar ba za su barina har na samu damar isa can ba,ban san dalili ba amma ƙila saboda ruhin dodon da ke kwance a jikina a dabaibaye. “Zo ki zauna” ta sake faɗa tare da miƙo mini hannunta,na girgiza kai na ce “ki cewa wannan macen da ke bayanki ta bar kallona” A tsorace Mama ta juya sai dai da dukkan alamu ita ba ta ganinta,jikinta na ɗan rawa ta miƙe tare da cewa “don Allah ki yi haƙuri kar ki cutar da mu motarmu ce ta lalace shi ne muka zo mu zauna kafin a gyara amma za mu gusa ” wani murmushi na ga matar ta yi kafin ta ce “haƙiƙa ko a bil'adama akwai masu kyakkyawar zuciya, waɗanda suke ɗaukar ƴaƴan kishiyoyinsu tamkar nasu.Allah ne kaɗai ya san dalilin da yasa motarku ta lalace a daidai kuma bakin ƙofar gidana,ƙila don na tura motar kyakkyawan burinki ta kai ga ci” da dukkan alamu hatta Mama ta ji wannan furicin don kuwa sai da ta mayar mata da amsa inda take cewa “na gode sosai da kika fahimce ni,kin ga ni ma daga yau na yarda cewa har a mutanen ɓoye akwai na kirki na bar ki lafiya” sai ta naɗe tabarmar,sai dai fa matar ba ta bari muka gusa ba sai da ta zo ta ratsa gangar jikin Mama ta shige tamkar yadda ruwa ke huda ƙasa su nitse haka na gani.Ina shirin yin magana Abba ya dawo shi da mai gyara,sai kawai muka tafi wurinsa.Ba a ɗauki ko da minti biyu ba motar ta tashi wanda na yi imani cewa ƴar bafulatanar nan ta jikin Mama ce ta warware sharrin da yasa motar ta tsaya.Ko da muka shiga ciki sai Mama ta jawo ni ta rungume a ƙirjinta,tamkar ana gasa ni haka nake ji sai dai na kasa kubcewa haka na daure har muka isa wajen wani mai bada magani. Duk da mun tarar da jira haka ya sa aka zo aka ja mu,da muka shiga ciki sai da ya dubi Mama na wani lokaci kafin ya ce “duk da na ga kun samu wacce za ta taimaka muku sai dai ku sani ruhin dodon Jinniya nada mugun ƙarfi saboda zaluntarta da aka yi,sannan kamar yadda na samu labarin zuwanku tun kafin ku zo to haka na ga mummunar ƙaddarar da za ta faru da ku nan gaba.Amma babu komai,zai zo da sauƙi ku tashi ku nemi wuri ku kwanta kun yi doguwar tafiyar zan sa a kai muku abinci ita kuma wannan ku bar ta nan” haka kuwa aka yi a bai wa su Abba masauki bayan sun ci sun sha ni kuwa kasa ci na yi,a wannan daren ne Mama ta samu cikin ƙanwata Maryam wacce zaɓi ce daga ƙaddarar rayuwata. Bayan tafiyar su Mama wankan magani ya yi mini sannan ya ɗaura mini wata laya a wuyana wacce shigarta kenan na ida jin komai da ya danganci ɓoyayyar duniya ya tsaya mini cak na dawo normal yarinya ƴar shekara biyar. Washegari kafin mu tafi mai bada magani ya shaidawa iyayena kar su bari layar nan ta bar wuyana.Daga nan muka ɗauki motarmu ta komawa can gida,a nan ne wani mummunan hatsari ya same mu.Cikin irin soyayya ta uwa Mama ta ƙanƙame ni gam,tare da buɗe motar muka fito daidai nan kuma mota ta soma ci da wuta alhalin Abba na ciki.Muna kuka muna kallo motar ta toye ƙurmus a dokar daji,faɗar tashin hankalin da muke ciki ya fi gaban misali.Haka Mama ta goya ni muka soma tafiyar ƙasa,wacce duk tako ɗaya da za ta yi ya fi taki ɗari da wannan muka isa gida a wannan dare.A washegari Mama ta sanar da rasuwar Abba aka yi masa zaman makoki mai cike da tsiyar gumi ana cewa ita mayya ce ta kashe kishiyarta yanzu kuma ta damƙe mijinta.Surutun mutane yasa ta sayar da ɗan abin da dangi Abba suka rage mana,ta haɗe kayanmu muka bar gidan muka koma can cikin ainahin birnin Kibri inda muka fara rayuwa mai cike da ƙalubale.Sana'ar ƙosai Mama ta fara haka da haka har cikin jikinta ya tsufa ta haifo Maryam ,wacce zuwanta duniya shi ya yaye ƙuncin rayuwarmu wanda kuma ba kowa ya kawo canjin nan ba sai ƴar bafulatanar nan ta jikin Mama.A ranar suna Mama ta samu kyaututtuka da dama wanda yasa bayan arba'in ta fara sana'a mai gwaɓi har ta saya mana gidan da muke zaune ciki .Haka rayuwa ta shuɗe na tsawon shekaru har na gama karatuna na soma fafutukar neman aiki,wanda a ƙarshe wata asibiti ta yarda na je na dinga yin aiki amma albashin ba wani ba.Mama ce da Maryam suka ƙarfafa mini gwiwa kan na je na soma yi wanda da ace sun san cewa asibitin nan ita ce mafarin tono baƙin sirrina na tabbata ba za su yarda ba. A ranar farkon zuwana wuraren ƙarfe shidda na yamma ne,komai na tafiya daidai ina duba patient har zuwa dare.Inda gizo ya fara saƙa shi ne wani ɗan yaro da ya mutu tsakiyar dare,wanda tun zuwana na ji mugun sonsa.Wannan soyayyar tasa ta haifar mini da ƙawa zuciya har na yi masa rakiya zuwa MUTUWARE,tamkar ni ce uwarsa haka na rungume gawarsa ina kuka daga bayana na ji an dafana da wani irin hannu wanda ba zan iya misalta yadda na ji ba,amma da na juyo sai na ga babu kowa.Wani tsoro na ji har zan fita sai kuma wani akwatin gawa ya buɗe.Kamar wacce ake tatsowa ruhi haka na ji ana fizgata a haka har na isa kusan akwatin .Gawar wani kyakkyawan saurayi ce a kwance,sai dai da dukkan alamu ba mutuwa ya yi ba saka shi aka yi a ciki. “Ki taimaka mini na fito” ya furta,na waro ido jikina na soma rawa.Ya ci gaba da cewa “kar ki ji tsoro kina iya taimakona,ban mutu ba sharrin maƙiya ne suka saka ni a nan.Sunana Dr Bilal shararren likitan nan na garin Kibri...” ina jin abin da ya ce sai na zuba da gudu a guje sai dai ina zuwa bakin ƙofa sai ta dantse...... [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 09 Ko da na juya akwatin gawar na ga yana fitar da wani haske.Jikin ƙofar na jingina tare da rumtse idona ko zan ji sassauci,ashe ma ƙaimi na ƙara don kuwa tamkar fitar iska haka na samu ruhina ya fice daga gangar jikina ya isa can bakin akwatin gawar.Hannu na miƙa masa ina mai cewa “ka zo na cece ka amma da sharaɗin za ka yi mubaya'a kai da sauran doctor's na asibitin nan” na yi wannan furicin ba tare da ni kaina na san me hakan ke nufi ba. “Na amince” Dr Bilal ya furta,yayin da kuma na kai hannu na jawo shi na fitar da shi daga akwatin,kafin ruhina ya zo da wani bala'in gudu ya koma cikin gangar jikina.Wani irin shock na ji ya shige ni tamkar na kama da wutar lantarki daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gadon asibiti. Na tashi dakyar ina dafe kaina da ke yi mini azabar ciwo,sam kuma na kasa tuna abin da ya faru.Haka shugabanmu ya ce na tafi gida sai na huta,godiya na yi masa na dawo gida.Ina shigowa Maryam wacce a lokacin ba za ta wuce shekara sha huɗu ba ta zo ta rungume ni sai kuma ta yi baya tana ƙare mini kallo.Yanayinta na ga ya canza kafin ta ce “anty Fatee me ya faru ki ka dawo gida tun asubar farin? Ba sai ƙarfe goma za ki sauka ba?” “Ni ma ban sani ba Maryam,kin ga banda lafiya ne” na faɗa tare da raɓawa gefenta,sake da baki take kallona tana mai hana ni wucewar har za ta yi magana Mama ta leƙo daga kitchen tana mai cewa “ki barta ta huta mana,in ta tashi sai ku yi magana” “Amma Mama yanayin ƙamshin jikinta ya canza daga wanda na sani kuma ma ...” “Ya isa Maryam!” Mama ta katse ta tare da ce mini “je ki Fateena ki kwanta” kai na jinjina mata tare da wucewa da sauri na shige ɗaki. Ko kaya ban rage ba na haye gado na soma lumshe ido,a can cikin ɓargon zuciyata ina jin cewa da akwai wani abu da ya faru da ni amma na manta .Da na ga kamar ina son jawowa kaina matsanancin ciwo ne sai na ture tunanin na soma sauke ajiyar zuciya ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.Tsawon lokacin ina baccin kafin na farka,wanka na soma yi na canza kaya sannan na fito falo. Zungum na tarar da su kamar ba su cikin walwala,Maryam ta taso da sauri za ta soma yi mini tambayoyi amma Mama ta dakatar da ita sai ma abinci da aka ce ta ɗebo mini.Bayan na ci na ƙoshi sai na je na kwanta kan kujerar da Mama ke zaune,kaina na ɗora kan cinyarta sai da ta ɗan buɗe rigata ta taɓa ƙatuwar layar da ke wuyana sannan ta ce “Fatee ya aikin fatan komai ya tafi daidai?” Na yi murmushi mai sauti na ce “eh alhamdullah,sai gobe kuma zan koma da safe” sai na ga ta kalli Maryam tare da sakin ajiyar zuciya. Wunin ranar dukkan motsina akan idon Mama yake da muka zo kwanciya sai da ta shafa mini wani mai marar daɗi. Washegari haka na shirya na tafi asibiti,sai dai tun daga bakin ƙofa na ga canji saboda yadda kowa ya sha jinin jikinsa.Ina isa na samu abokiyar aikina Farida,cikin sakin fuska na soma yi mata magana amma sai na ga tana haɗe rai ina shirin tambayarta lafiya ai kuwa sai ga wanda ya ɗauke ni aikin ya shigo tare da miƙo mini takarda. Da na duba sai na ga ta sallama ce,na ɗaga kai ina shirin yi masa magana ya nuna mini ƙofar fita cikin tsawa yake cewa “ki fita” babu yadda na iya na fice ɗin. Idona tab ƙwalla haka na soma tafiyar ƙasa ina tunanin me zan cewa su Mama,kawai sai ji na yi na faɗi ƙasa.Na maido hankalina jikina,wani mai mota ne ya kaɗe ni,idona kansa har ya fito ya miƙar da ni tsaye. Cikin sanyin murya yake cewa “fatan kyakkyawa ba ta ji ciwo ba? ” Kai na girgiza masa,murfin motarsa ya buɗe mini tare da cewa “da dukkan alamu akwai abin da yake damunki mu je na rage miki hanya” kamar wacce ya yi wa asiri haka na shiga kuwa.Ya zagayo ya zauna,ya soma driving yana mai cewa “sunana Dr Bilal” Da sauri na dube shi sai na ji tamkar na san sunan da kuma fuskar,sai dai ban iya tunawa ba sai murmushin yaƙe da na yi. Takardar hannuna ya karɓe ya karanta bai ce komai ba haka ya ajiye ta yana ɗan haɗe rai,ni ma sai na sunne kaina.Ban ɗago ba sai da na ji yayi parking,ido na shiga ƙyaftawa ina kallon wata haɗaɗiyar asibiti wacce ta fi waccan girma da kuma kyawu. Fita ya yi,ya buɗe mini ƙofa haka ni ma na fito kamar wata doluwa na take masa baya har muka shiga ciki.Likitoci na tarar birjit,duk suka miƙe tsaye tamkar masu zaman jiranmu.Cike da girmamawa suka gaishe shi kafin shi kuma ya ce “ina mai gabatar muku da nurse Fateema,daga yau za ta fara aiki da mu a wannan asibitin ” duk sai suka shiga taɓa mini suna murmushi,a dole ni ma na murmusa ɗin ina kallon Dr Bilal ina mamakin ta ya aka yi ya san sunana .Nan ya bar ni tare da su,suka soma gabatar mini da junansu a nan ne na haɗu da ƙawata Rahinatu mace mai sauƙin kai da tausayi.Ita ce ta nuna mini ko ina na asibitin,a cikin zagawar da take yi da ni ne take ce mini “kina da matuƙar sa'a tun da har ki ka samu Dr Bilal shi ne da kansa ya kawo ki asibitin nan,a kaf manyan likitocin asibitin nan masu faɗa a ji duk ya fi su tsatsauran ra'ayi kusan saboda kafiyarsa ne akan ra'ayinsa yasa ya shiga komar maƙiya.Tsawon lokaci yana hannunsu sai jiya ne ya dawo” Na ce “ni kuwa ban ga wani zafin kai a tattare da shi ba” . Tana shirin yin magana wata nurse ta zo da sauri tana mai cewa “ Dr Bilal na neman nurse Fateema a ofis ɗinsa” wata irin faɗuwar gaba ce na ji wacce ban san dalili ba,nurse Rahinatu ce ta yi mini rakiya har zuwa bakin ƙofa.Bayan ya bada izinin shigowa sai na tura ƙofar tare da yin sallama,bai amsa ba ya dai zuba mini idonsa masu kashe ruhi da mugun sauri na sunne kai tare da ja na tsaya.Ya taso ya yi tsaye a gabana yana mai kamo dukkan hannuwana,murya kamar mai yin raɗa yake furta mini “ina sonki ƴar cikin Fateema ”yana gama furta haka babu zato babu tsammani na ji bakinsa kan laɓana yana mai tura harshensa....” yadda na ji an fizge gilashin da ke manne a idona haɗi da hullar kaina su suka tsayar da labarin rayuwata da nake gani ana hasko mini. Cikin zafin rai na ga Mu'azzam ya finciko ni da mugun ƙarfi daga kan kujerar,ƙirjina ya bugu da nasa na yi baya kamar zan faɗi amma yadda ya riƙe hannuna gam ya hana faruwar haka. Tsabar yadda yake wani tamke fuska dukkan illahirin jijiyon kansa suka fito,cikin masifarsa da nake mugun tsoro ya soma yi mini ihu. “Wato da yake ke ballagaza ce shi ne daga baki aiki har da yi masa sumbata,ke jarababiya ƙanwar ayyu” Idona suka fara zubar da hawayen azaba,cikin rawar murya na ce “sumbata kuma? Ni ban sumbaci kowa ba” Tamkar wanda ya fita hankalinsa haka ya wani tura ji jikin bango tare da kama wuyana ya ce “in ina magana kina ƙaryatawa sai na shaƙe miki wuya ki mutu kowa ya hutu da fitinarki,ke yanzu ko kunya ba ki ji ni kike faɗa wa Dr Bilal ya sumbace ki? ” muƙut ! Na haɗiye yawun tsoro ina son ƙaryatawar amma ina jin tsoronsa,ni ban ma san taƙaimamai abin da yake magana a kai ba. Hawaye ne suka soma yi mini zarya ina mai kallon tsakiyar idonsa waɗanda masifa ta saka su yin ja sosai.Tsawon lokaci muna kallon juna kafin ya janye daga kusa da ni ya juya mini baya,can kuma ya ce “fita” furucinsa ya tuna mini dagar da na sha da mahaukacin ai kuwa da mugun sauri na koma gabansa ina mai girgiza masa kai.Tsakiyar idona ya duba,kafin ya kawar da kai ya je ya buɗe wata ƙofa ya shiga.Kamar jira take ya gusa haka ta bayyana gare ni tana mai kallona da idonta masu matuƙar firgitarwa.Da wani irin bala'in gudu na bi bayansa,sam ban yi tunanin toilet ce ya shiga ba.Jikina na mugun kyarma na juya masa baya,tsorona na daɗa ƙaruwa ido kawai na rumtse ina jin yadda zazzaɓi ya soma kawo mini farmaki. Ƙiiii haka ya jawo ni waje ,a dole na buɗe idona nan na yi arba da ita fatalwar ya buɗe baki zai yi masifar na ƙanƙame shi tare da yi masa magana cikin fitar hayyaci “fa..tal...ta..talwa ” yadda numfashina ke ta ƙoƙarin tsinkewa yasa a dole na yi shiru. Ina jin lokacin da ya saɓe ni ya fito da ni,wani ɗaki ya kai ni ya kwantar kan gado yana son ɓanɓare ni amma na ƙi sakinsa don har ga Allah tsoron budurwar nake yi wacce ban san wace ce ba. “Ki nutsu ta tafi” ya faɗa cikin taushin murya,jin yanayin da ya yi maganar yasa na sake shi tare da buɗe ido a hankali.Cikin nasa idon na sauke nawa,babu laifi ya saki fuskarsa duk da babu wani annuri.Hannuna na duba sai na ga ashe bottle ɗin rigarsa ne na tsinke,ya juya mini baya kafin ya fiddo waya a aljihu ya yi kiran Jabeer .Babu jimawa ya shigo riƙe da akwatin likitoci. “Ka duba ta sai ka yi mata allura ” Mu'azzam ya faɗa yana mai waigowa ya dube ni,shi kuwa Jabeer ya matso kusa da gadon da nake kwance.Da sauri na tashi zaune ina mai cewa “wallahi lafiyata lau ban so” Jabeer ɗin bai saurare ni ba ya soma ƙoƙarin yi mini allurar,ban kuwa yi wani tunani ba na gantsara masa cizo a dole ya yi baya yana kallona yayin da shi kuma Mu'azzam yake wani murmushi mai fitar da tsantsan kyawunsa. Kamar wata yarinya na dire daga kan gado na je bakin ƙofa ina rarrabar ido, Mu'azzam ya kalli Jabeer ya tuntsire da dariya kafin ya ce “zan wuce gida sai mun yi waya” sai ya zo gabana ya buɗe ƙofar,na take masa baya har mota.Wannan karon ni na buɗewa kaina can gidan baya,na takure wuri guda.Shi ma a slow ya soma tuƙin har muka iso gida yana satar kallona ta cikin madubi.Kusan a tare muka shiga falon sai kawai duk muka yi tsaye saboda yadda aka ƙawata shi ,goggonsa Kabira ta zo da sauri ta kamo hannunsa tana cewa “Zeezi ki sauko ga angonki ya ƙaraso” Daddynsa ne ya soma yin taɓi shi da sauran dangin da aka tara a wurin amma banda Ammy wacce ke kallon fuskar ɗanta. Ƙarar saukowarta yasa na ɗaga kaina sama,budurwar da muka fara cin karo ce a can Duwala gidan Ammy.Ta sha kyawu har ta gaji,kuma babu ƙarya ta haɗu sosai don sai da ta burge ni.Tana isowa falon jikin Mu'azzam ta je ta faɗa ,da dukkan alamu kuma ba wannan ne farkon yin hakan ba duba da ko kaɗan bai yi ƙoƙarin ture ta ba. Taɓi aka shiga yi a karo na biyu,ni ma haka na samu kaina da taɓawar sai dai fa a can ƙasan zuciyata haka nake jin wani abu kamar ban murna da hakan. Goggo Kabira ce har yanzu ta ƙara yin magana “kamar yadda kuka sani an daɗe da ɗaura auren Mu'azzam da Azeeza a yau kuma mun shirya ɗan ƙaramin shagali domin tarewarsu” wata irin langwaɓewa ita Azeezar ke sake yi a jikin Mu'azzam wanda har zuwa yanzu bai nuna farin cikinsa ba,muna haɗa ido da shi sai na ga yana aiko mini wani kallo ya tsayar da dubansa kuma a kaina.Na shagala sosai cikin kallonsa na ji muryarta kusa da ni,“ungo wannan furannin je ki ƙawata ɗakin da za a tarbi amarya”goggo Kabira ta faɗa tana mai miƙo mini wani basket mai furanni sai wani gangame fuska take.Na karɓa tare da juyawa na haura can sama,tsaye na yi ina tunanin to wanne ne daga ciki ɗakin amaryar? Daga bayana na ji motsi ko da na waiga sai na ga ita ce ƴar masifar ta biyo ni. “Zo na nuna miki yadda komai zai tafi” ta faɗa tare da shiga ɗaya daga cikin ɗakunan,tun daga falon wani sihirtacen ƙamshi ne ke tashi ko ina an gyara shi tsaf,ina biye da ita har muka shiga can bedroom nan ne ƙamshin Mu'azzam ya farmaki hancina ban san lokacin da na lumshe ido ba saboda a ɗan zaman da muka yi da shi na fahimci na fara son ƙamshinsa. “Ki canza wannan zanen gadon ki shimfiɗa ɗaya daga cikin waɗannan ” furucinta yasa na buɗe ido na ga zannuwan gadon da pink da kuma fara.Da ɗan murmushina a fuska na ce “ina ga a shimfiɗa pink ɗin za ta fi kyau” “A'a farar za ki shimfiɗa ita wannan gobe sai a shimfiɗata in an cire wannan ” ta miƙo mini farar.Ni kuwa da yake sokuwa ce sai cewa na yi “kamar farar za ta yi saurin ɗaukar dauɗa” Ta langwaɓar da kai ta ce “dama iya daren farko kawai ake buƙatarta” da sauri na sunne kai don zuwa yanzu na fahimta,ina jin lokacin da ta yi murmushi mai sauti kafin ta ce “kin san daren nan ya fi komai muhimmanci a rayuwar ma'aurata,za su san junansu kuma duniya za ta shaida sun zama ɗaya” tana gama faɗa ta fice. Wani irin zafi ne na soma jin yana taso mini daga ƙasan zuciya,ban san na mine ne ba haka na soma gyaran kamar yadda ta buƙata .Bayan na gama sai na koma gefe ina kallon yadda gadon yayi tsaf,wata guntuwar ƙwalla ta zubo mini na yi saurin goge ta kafin na fito. Daga nan saman bene nake kallon yadda dangi ke ta yin hidima,shi kuwa gogan sai faman danna waya yake yi amarya kuwa tana can tsakiyar danginta.A gaban idona Jabeer ya shigo,sai kuma a wannan lokacin ne Mu'azzam ya miƙe ya tarbe shi ina ganin sun tunkaro bene na yi saurin rugawa a guje na shige ɗaya daga cikin ɗakunan . Wani irin duhu ne ke da ɗakin, amma kamar daga sama na soma hango wani haske wanda ya ja ragamar ruhina izuwa gare shi.Ina isa na zube gwiwaina ƙasa tare da kai hannu na buɗe wani ɗan ƙaramin akwati na ƙarfe,da sauri na rumtse ido saboda yadda hasken ya dalle mini ido.Duk da idona a rufe suke hakan bai hana ruhina gane mini wani ɗan mitsitsin littafi ba wanda duk yayi ƙura,page ɗin farko ce ta buɗe kanta harufan da ke rubuce a ciki suka soma karanta mini kansu ba tare da ni na karanta ba,duk wani sirri kuma da ya ambaci kansa haka zuwa cikin kwanyata ya zauna a daidai lokacin da na buɗe idona kuwa wani irin yanayi ne ya riske ni na ƙarfin power...... [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 10 Cikin riga na ɓoye littafin kafin na miƙe na je bakin ƙofa,ganin babu kowa yasa na fice da sauri .Kai tsaye ɗakinmu na wuce ban bi ta wani shagalin biki ba,gudun kar Maryam ta zo ta tarar da ni ina karatun littafin yasa na shige toilet tare da buɗe page ta biyu sai dai tamkar an kunna fanka haka dukkan pages ɗin suka dinga buɗe kansu harufan ciki na tashi sama kamar wasu ledodi.Banda idanu babu abin da na zuba musu ina kallo,pages ɗin na gama idawa littafin ya ɓatan dabo daga cikin hannuna. Wani irin nauyi na ji kaina ya yi mini,kamar makauniya haka idona duk suka disashe.Da lalube haka na samu na fito na kwanta kan bed,gurnani haɗi da nishi nake ji a cikin kwanyata yayin da kuma matattun idona ke nuno mini wani ƙasurgumin daji mai albarkar ruwa masu gudana.A cikin yanayin da ya riske ni sam na kasa sanin taƙamaimai halin da nake ciki. ★MU'AZZAM Tun da suka shigo gidan aka tarbe shi da zancen tarewarsa da Azeeza ya ji zuciyarsa na tafasa.Ji yake kamar ya yi ihu amma ya daure ya ɓoye damuwarsa har abokinsa Jabeer ya ƙaraso. Ƙofar ɗakin ya rufe ko kafin ya ce wani abu Jabeer ya furta “ ya kamata ka nutsu domin kar ciwonka na zuciya ya tashi ” A hasale ya ce “na nawa kuma? Ka duba fa ka gani babu shawara ba komai ake yin walimar nan,Ammy kuma na tsaye ba ta ce komai ba ita kuma mahaukaciyar yarinyar nan har da wani taɓa hannuwa take yi tana murna da kuma zuwa ta gyara gado hum! Ji nake kamar na kama da wuta” Mu'azzam ya ƙarashe faɗa yana mai kawai bango naushi. Jabeer ya ce “kar fa ka manta kai ne da kanka ka ce kana son Zeezi ba haɗa ku aka yi ba” “Amma ai soyayyar ƙurciya ce,ni yanzu ban sonta ” cewar Mu'azzam. “In ba ka sonta wa kake so kenan? Don dole akwai wacce ta canza maka ra'ayi” Jabeer ya faɗa yana mai dafa kafaɗarsa. Shiru ya ɗan yi kafin ya ja tsuki ya ce “ni babu wacce nake so,kawai dai yanzu Zeezi ba ta gabana ” Jabeer ya ɗan yi murmushi mai sauti ya ce “to kawai ka yi haƙuri ƙila ta sake dawowa gaban naka in wacce ta tare mata ƙofa ta gusa” Da wani mugun kallo ya kalli Jabeer kafin ya ce “kar ma banzan tunaninka ya baka wai ni Mu'azzam zan iya son wannan mahaukaciyar ” Yayi ƴar dariya ya ce “ni ai dama ban ce ba kai ne ka furta da kanka hakan na nufin dama tana cikin ranka” Mu'azzam ya haɗe rai ya ce “na kira ka don ka yi mini maganin damuwata amma kana daɗa mini wata” “Abokina kai ne ba ka son gaskiya in kana cikin wata matsala maimakon ka duba gaskiyar lamarin amma sai ka bari ego ɗinka ya rinjaye ka.Da ka ƙi da kaso kana son Fateemah,tun ranar da ka ganta ka kamu da sonta a kallon farko amma saboda girman kai gani kake ka fi ƙarfin ka so mace kamar ta.Ka sani yanzu duniya ta ci gaba ba wani abu ba ne don ka so macen da ba ta waye ba,kai ne za ka wayar da ita ta zama classic.In ka ɗauki Azeeza da Fateema banbancinsu ƙalilan ne,ka ga....” cikin tafasar zuciya Mu'azzam ya dakatar da shi yana mai cewa “kai ka ga ban kira ka nan don ka zo ka yi mini surutu ba,in ba za ka bani shawara ka tafi kawai” Jabeer ya dube shi da kyau kafin ya ce “yanzu ya kake so a yi?” “Inda na san yadda za a yi zan kira ka ne?” “Kana ganin fatalwar Nadiya ba za ta iya kai wa Azeeza farmaki ba?” “Inda za ta yi da tun tuni ta yi,amma ko sau ɗaya ba ta taɓa yi ba.Kaf cikin waɗanda take fito ma irin patient ɗina ne da aka kawo masu jinya” Jabeer ya ce “ka yi wa kanka tambaya don me sai waɗanda kawai suka zo neman magani wurinka?” “Ban san dalili ba Jabeer amma tabbas da akwai shi,amma mene ne?” “Ya kamata mu je wurin teacher shi kawai zai bamu amsa ” “Mu je” ya furta tare da buɗe ƙofar suka fito,har za su sauka idonsa ya kai ga ƙofar rufaffen ɗaki wanda tsawon shekaru ba a taɓa buɗe shi ba. “Mu tafi ba mu da sauran lokaci ” Jabeer ya faɗa .Haka Mu'azzam ya bi bayansa,da suka sauko sosai Goggo Kabira ta so tsayar da su amma ya ƙi saurarenta.A motar Jabeer suka tafi gidan teacher,wani tsohon mutum ne mai farin gashi ya tsufa sosai sannan makaho ne. Amma duk makantarsa ya san ƙamshi dukkan ɗalibansa, wannan yasa su Jabeer na isa ya ambaci sunansu.Gaishe shi suka yi a mutumce kafin su faɗi abin da ya kawo su,teacher ya yi murmushi yana mai cewa “maɗaukakiyar littafin tsira tuni ta bayyana a gidanku,tana ɗaya daga cikin baƙinku.Haƙiƙa mawallafin littafin taswira ya yi gaskiya,kamar yadda ya ce ba za a iya ɗaukar littafin sirri ba sai a ranar da ake gudanar da wani taro a cikin wannan filin gidan.Mu'azzam matarka ta gaskiya ta bayyana,matar da a kullum fatalwar Nadiya ke shakkar zuwanta wannan dalili ne yasa take farmakar patient ɗinka don ta san cewa a cikinsu ne za a samu wannan Goddess ” Kallon juna suka yi kafin Mu'azzam ya ce “kenan tuni an ɗauki littafin sirrin? To amma ta ya za a yi na gane ita wannan Goddess ɗin?” “Ita ɗin ta fita daban da saura! Kammaninta sun banbanta da na mutane,in tana tafiya iska ne abokin tafiyarta zai dinga kaɗa gashin kanta yana haskaka idanunta.Saura ƙiris ta mallaki dukkan wasu sirrika na tafiyar da aikin prophecy,muddin ta mallake su a yau to akwai yi yiwuwar gidan gawa ya ɗauki fasanja ” Ran Mu'azzam ne ya sake ɓaci,da wani irin sauri ya miƙe tsaye yana mai cewa “muddin ina numfashi ba zan taɓa barin hakan ta faru ba.Mu je Jabeer,teacher mun gode sai mun sake dawowa” Teacher ya ce “ Mu'azzam ka kula da kyau,sannan ina so ka sake yin bitar darussan da muka yi a baya sannan ina so ka sani fansar Aljani ba ɗaya take da ta ɗan Adam ba” Ba tare da ya ce komai ba suka fito shi da Jabeer,tsabar yadda yake jin zuciyarsa na tafasa shi ne ma yayi tuƙin ya dinga gudu kamar zai tashi sama.Shi kuwa Jabeer sai ƙoƙarin dannar ƙirjinsa yake a haka har suka isa gida, lokacin tuni an shiga sallar asar dakyar ya yin alwala suka shiga masjid.Bayan sun fito suka wuce can cikin gida,kamar wani zararre haka yake kallon duk baƙin da suka zo amma bai ga alamomin nan ba da teacher ya shaida masa. Ammy ta zo ta ja hannunsa ta soma nuna masa wasu dangin da suka zo bayan fitarsa,sama-sama suke gaisawa sai faman baza ido yake kuwa.Lura da hakan yasa Ammy ta ce “lafiyarka kuwa Mu'azzam? Ko dai patient ɗin da aka kawo ɗin ce aikin ya fi ƙarfinka?” “An kawo wata patient ne?” ya tambaya da sauri. Da mamaki Ammy ta ce “au dama ba a sanar da kai ba? Oh! Ƙila aiki ne yasa na sha'afa suna can ɗakin waje” yana gama ji ya bar Ammy ya nufi ƙofa,Jabeer ya take masa baya. Tun da suka doshi ƙofar suke jin wani irin ɗohi,amma a haka suka shiga.Turus suka yi suna kallon wata matashiyar budurwa wacce jikinta yake da shegen datti ,idonta jawur suke kamar barkono kammaninta kuwa kamar wata halitta daga wata duniya .Sun ƙure ƙarshen fanka sai gudu take wannan ya saka figagen gashin kanta damar kaɗawa. Mahaifiyarta na ganin Mu'azzam ta taso ta gaishe su,ya ce “tun yaushe ku ke nan? ” “Jiya cikin dare” Mu'azzam ya kalli Jabeer kafin ya ce “amma ya aka yi ba ku neme ni ba?” “Wata mata ce ta ce mana mu zauna a nan” ta basa amsa tare da zayyano masa siffar Goggo Kabira. “Tun da kuka zo kenan a nan kuke?” “A'a ɗazu Kando ta fita har zuwa can cikin gidan shi ne na je na nemo ta har muka haɗuwa da wata mata mai kirki ta zubo mana abinci” tana faɗar haka ya gane Ammy ce. Hannun Jabeer ya ja suka ƙara komawa can ciki,sai dai wannan karon can saman bene ne suka haura.Sawun taku ya gani masu cike da dauɗa ,zuciyar Mu'azzam ce ta soma tsinkewa yana addu'ar kar dai abin da zuciyarsa ke raya masa ya zamana gaskiya. Idonsa ne suka kaɗa suka yi ja lokacin da ya shiga rufaffen ɗaki ya tarar da babu wannan littafi na sirri wanda aƙalla ya gwada ɗaukarsa ya fi cikon casbi amma ya kasa. Jabeer kamar ya shiga zuciyar Mu'azzam ya ce “tana iya yi wa kuma ba Kando ba ce ta ɗauki littafin wata ce daban” Jin abin da Jabeer ɗin ya ce sai ya tuna da Mama wacce ya rufe a wani ɗakin kuma.Da sauri ya tafi can sai dai kuma ita kanta ta yi ƙasa ko sama da dukkan alamu ma ba ta cikin gidan,kai ya dafe ya rasa abin da ke yi masa daɗi. Haka suka zauna shi da Jabeer suna ta saƙa da warwara yayin da kuma gefe guda ake ta tsara yadda diner ɗin da za a yi a yau za ta tafi. ★FATEEMA Ban san tsawon lokacin da na ɗauka ba cikin wannan yanayin kafin na samu kaina.Toilet na shiga na tsarkake jikina na zo na yi sallolin azahar da asar kafin na gabatar da magarib.Ina nan zaune kan sallaya aka kira isha'i na miƙe na mayar kafin kuma na yi zaune ina lazumi,a haka Maryam wacce yanzu ta zama ƴar gida ta same ni. “Ga kayanmu waɗanda za mu saka Ammy ta bamu,ki gwada ki gani ko za su yi miki ” shi ne abin da ta faɗa tana mai cillo mini wata doguwar riga pink an yi mata ratsin fari haka kuma an zuba mata duwatsu masu shegen kyawu. “Ina za mu je?” ita ce tambayar da na yi mata.Sake da baki take kallona kafin ta ce “wajen diner na Mu'azzam ko?” Na ɗan taɓe baki don har ga Allah duk na manta abin da ya faru,tashi na yi tsaye na gwada rigar ta kuwa yi mini daidai sai dai ta wurin tsawo ta yi mini tsayi.Sai da Maryam ta gama yaba kyawun da na yi kafin ta shiga toilet ta yo wanka,ni ma sai da na sake yin wani kafin na zo na shafa mai da kwalli sai man leɓe. Da na saka rigar sai na soma dubarar yadda za a yi ta bar jan ƙasa,Maryam da ta lura da haka sai ta ce “ko na karɓo miki takalmi masu ɗan tudu wurin Goggo Kabira?” Kamar na shaƙe mata wuya haka na ji,na ce “matar da ta nuna tsantsar tsanarmu ita ce za ki je ki nemi alfarma ai gwara na fasa tafiya” Ammy ta shigo tana cewa “ya aka yi har yanzu ba ku fito ba?” gaishe ta na yi yayin da Maryam ke shaida mata matsalar da aka samu,“ok ina zuwa.Maryam yi mata kwalliya kafin na dawo” Ammy ta faɗa tare da ficewa. Maryam ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “don Allah anty ki bari na yi miki kwalliyar nan kar Ammy ta ga kamar ba mu yaba da auren ɗanta ba” na buɗa baki zan yi magana kenan sai Maryam ta kamo hannuna,haka na yi shiru kamar kullum na yi zaune ta soma tsantsara mini kwalliya.Tana cikin yi ne wayarta ta yi ringing wacce ban san yaushe ta same ta ba,lambar ƙafata ce Ammy ta tambaya.Har sai da aka kawo mini takalmin Maryam ba ta gama mini kwalliya ba, lokacin da muka ɓata yasa Maryam ba ta tsaya yin tata kwalliyar ba ta saka kayanta ta fice. Jiƙaƙen gashina da ta ɗaura a tsakiya na baje ina turo baki tare da cewa “salon ya yi mini wari ta wani ɗaure mini gashi” mayafin rigar na ɗora a sama sannan na saka takalmi masu tsinin sai na fita ni ma .Tsit falon yake babu kowa amma ina jin ɗan sautin music daga can waje,hakan yasa na yi saurin fita ina tafe ina ɗan riƙe rigar kamar mai koyon tafiya haka nake takawa gudun kar na faɗi sam ban yi tunanin salon tafiyar zai jawo hankulan mutane a kaina ba. Idona banda ɗan ƙyaƙyafta su babu abin da nake yi,wani irin iska ne ke kaɗawa wanda ya yi sanadin faɗuwar mayafina daga saman kai zuwa kafaɗa nan take gashina ya soma tashi sama har yana rufe mini fuska.Baza ido nake yi ina son hango Maryam sai dai ban ganta ba,ina juyawa na hangi Jabeer da sauri na nufi can.Sam ban yi lura da tawowar Mu'azzam ba wanda shi ma hankalinsa yake kan waya sai ji na yi na kai masa karo.Na yi baya zan faɗi amma kuma sai na yi saurin cabko hannunsa hakan yasa na dawo gaba sai dai fa tsayuwa kan ƙafafuna ta gagara.Ga mahaukacin ƙamshin da yake zubawa ya fi na kullum,ga kayan jikinsa waɗanda faɗar tsadarsu ɓarnar baki ne ga kuma rikitatun idonsa da ya tsoma cikin nawa.Duk suka taru suka ruɗa ni,hasken cameraru ne ya dawo da ni daga kogin kallonsa da nake yi ,shi ma da dukkan alamu ya shagala da kallona. Wasu daga cikin waɗanda aka gayyato ne suka soma yi masa congratulations da samun kyakkyawar mata irina.Maimakon ya ce musu ba matarsa ba ce a'a sai ma dai idonsa da yake ci gaba da kallona da su,daga bayana na ji muryar Maryam da sauri na tafi na bar shi har ina shirin faɗuwa. “Shi ne kika wani tawo kika bar ni can ɗaki” na faɗa ina mitsike mata kumatu,ta yi murmushi kafin ta ce “ki yi haƙuri anty Fatee zo mu je ki zauna” haka ta ja ni muka zauna kan kujerun da aka tanada don zama.Maimakon ta zauna ita ma sai ta tafi ta bar ni,duk sai na soma jina a takure ina jin kaɗaici na mamaye ni.Kamar walƙiya haka na soma ganin wani abu mai ƙyalƙyali na wasa da hankalina,a hankali na miƙe tare soma dosar can cikin shuke-shuken .Sam ban farga da na bar cikin gidan ba sai da na soma jin ƙarar ruwa,da na duba da kyau sai na ga ashe ƙasurgumin dajin nan ne na ɗazu.Ina shirin takawa baya don komawa kawai sai ji na yi na rumza ƙafata ta maƙale a cikin wani rame.Daidai nan wurin ya ɗauki matsanancin duhu,sai kuma wata murya da ta cika wurin baki ɗaya. “Ke ce wacce aka zaɓa domin kammala mission mai muhimmanci. Dukkannin ƙarfin iko na power da suke ɓoye a jikinki su ne makulin da za ki ceto duniyarmu wacce aka rushe.Amma kafin nan dole ki zauna ki koyi yarenmu na ƙarnin baya,sannan ki san muhimmancin TUKUNYAR MAYU da kuma abin da take nufi” muryar na gama faɗar haka sai na ji ƙafata ta fito yayin da kuma wata ƴar mitsitsiyar tukunya kamar wacce Bugaje ke yin shayi ta bayyana a hannuna na haggu. Daidai bakin tukunyar shayin wani hayaƙi ya soma fitowa mai yawa,ina taɓa shi wani irin shock ya damƙe ni kamar na lantarki dukkan idanuwana suka firfito yayin da kuma wani girgije ya bayyana a gare ni wanda ya hasko mini dukkan rayuwata ta baya da kuma ta wacce da zan yi a gaba.Lokacin da shock ɗin ya sake ni,sai na ji tamkar na ƙurmar ihu jin wai ba Mama ce mahaifiyata ba,sannan Mu'azzam yana ɗaya daga cikin ƙaddarar rayuwata wanda aka umarce ni da na kare daga sharrin abin harinsa. Ido na lumshe tare da motsa laɓana,iska ne ya fige ni ya kawo ni can gidan Mu'azzam a kuma ɗakinmu.Zaune na yi dirshen a tsakiyar ɗaki ina kallon ƴar butar shayin wacce a zahiri ita ce TUKUNYAR MAYU da duk ƙasar Kamaru da kewayenta ke cece-kuce a kai.A zuci na ce ‘ kenan duk mutanen da ke ikirarin akwai tukunyar mayu a asibitocinsu ƙarya ne?’ wani ɓangare na zuciyata ne ya bani amsar ’eh duk ƙarya ce, wannan ta hannunki ita ce ta gaske kuma mallakinki ce,ke ce Goddess kuma ke kike da alhakin kula da ita’ Wani murmushi na yi na samun wata rayuwa a wata duniya ta daban kafin na yi wani furici kamar ƙyaftawar ido kuwa na tsinci kaina a cikin ƴar ƙaramar tukunyar,ta ƴar hudar nan na fito sai dai ba a siffar mutum a macijiya.Direct wajen taron ƴan diner na fantsama ina gudu haɗi da ziro harshe . Daidai nan free page ya ida,duk mai son shiga paid group za ta biya 509 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822.Don Allah ga detail nan in kina so ki tura kai tsaye ki bani shaidar biya,wacce ta san kuma ba ta shirya ba ki yi wa girman Allah kar ki yi mini Magana *NB:* yanzu nake typing 18.08.25 in kuma na kammala shi 1k ne kuɗinsa.