20/03/23, 7:36 pm - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more. 24/03/23, 1:57 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA* 🧕 ( _Romantic luv storie_ ) _(Under the pens of✍️ Merhreeyeart lerwerl & doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyert lawal* _*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*_ Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, wanda ya bani ikon kammala wancen littafi nawa na Ahali d'aya har yanzu nazo muku da wani sabo mai suna *JARUMAR UWA🧕* littafin jarumar uwa wani salon labari ne me d'auke da So, k'auna, cin amana had'e da sadaukarwa, sannan labari ne daya had'a al'adar k'asashe biyu, hausa Fulani da kuma larabawa, Ina fatan zaku kasance tare dani don jin yadda wannan labari zai kasance, kada ku manta dai tare da Alk'alamin👇 _Merhreeyeart lerwerl_ 🌹 Page one 1️⃣ Nigeria, Abuja state, garki area one. Kyakkyawar farar balarabiya ce doguwa take tafiya janye da trolley k'atuwa k'afarta ko takalmi babu, yayinda ruwan hawaye yak'i tsayawa daga kwayar idonta, sanye take da tsadaddiyar doguwar riga bak'a wadda ta wadata musamman wajen b'oye kyakkyawar surar jikinta, gashin kanta ma'abocin kyau da shek'i ya futo kad'an ta saman goshinta sakamakon zamewa da d'an gyalen da tayi rolling kanta yayi kad'an, tafiya take cikin sassarfa tana huce tsilli tsillin motoci da suke shige da fuce a cikin layin, ko kad'an bata tsaya ba har saida takai k'arshen layin, ta juyo da gefen fuskarta kamar zata waiwaya bayanta amma bata k'arasa waiwayawarba, tayi magana cikin harshen larabci, kamar haka👉🏻"kamar yadda nayi alk'awari Suraj! kamar yadda ka buk'ata! zan tafi na bar rayuwarka kuma bazan sake dawowa ba har abada....... kayi abubuwa da yawa na dai dai da akasin shi, haka ka kasance babban b'arawo tunda har ka iya sace rufaffiyar zuciyar surayyah ma'abociyar tsoro da d'ar d'ar ka jefa mata dafi ciki da waje, ka illata ta, ka ragargaza rayuwarta da sunan soyayyah, ka keta iyakar daba taka ba, ka ruguzani sooraj ta yadda rayuwata gaba ta kasance k'ark'ashin sarrafawarka! to ka sani itama surayyah bata kyaleka haka ba, kada ka d'auka Kai kad'ai kayi nasara, a yau surayyah zata tafi maka da abu mafi tsada da daraja wanda zaka dawwama kana bege da mararin had'uwa dashi har k'arshen rayuwarka, something precious and rare more lyk a diamond, sai dai yafi k'arfin ka, sannan ku jira yadda hak'k'in surayyah zai muku". daga nan tayi wani irin miskilin murmushi wanda bai hana b'acin randa take ciki futowa ba. Taci gaba da tafiyarta tana sake sake a zuciyarta har daga k'arshe ta yanke hukuncin taje gidan Auntie Sarah, kamar yadda zuciyarta ta umarceta haka ta d'auki hanyarta sai dai kash! Tana zuwa k'ofar gidan wani abu yayi Mata dabaibayi ya tsaida ita, duk yadda take yak'i da Suraj da K'arfafa jikinta ma'abocin rauni da zuciyarta abin yaci tura, har ta d'ora hannu da nufin danna door bell sai kuma ta janye hannunta, kalaman sauban suka soma amsakuwwa a cikin zuciyarta kamar lokacin yake fad'a mata su, salin aalin ta soma barin k'ofar gidan looseless, she hope to be dat daughter, she also want dat courage but she don't know how and where to find the confidence, daga k'arshe zuciyarta ta bata shawarar ta inda aka hau tanan ake sauka, a garin da bata da kowa, a k'asar da batasan kowa ba sai shi wato ta koma ga mafarin Suraj ko ba komai zata rayu cikin salama ita da abinda zata haifa, dede da second bata so ta k'ara a garin Abuja balle harta kwana, ta yiwa ranta alk'awarin dole ta bar garin a daren yau. Abinda bata tab'a yiba tsawon rayuwarta, inda bata sani ba bata tab'a sanin inda haryarshi take ba ta nufa wato neman motar haya, tayi sa'a tana tsayarda wata mota ta tsaya, abinka da bata sani ba, Sam bata iya banbance motar data tare tafi kama da private car ba ta hayar da take nema ba, don haka ba b'ata lokaci tace, "malam inda zan hau motar Kano zaka kaini". Mutumin ya d'anyi shiru yana nazarin tazarar da take tsakanin tasha da inda zashi a lokacin, kuma dai yaga batayi kama da masu hawa lift ba amma ta tareshi, ko kuma dai tana da lalurar kwakwalwa ne? Ganin yadda take share hawaye sai tausayinta ya kama shi bai ce mata komai ba ya bud'e mata gaban mitar ta shiga rungume da jakar kayanta Sunyi tafiya mai d'an tsayi Kanta a k'asa har Suka k'arasa, sai daya ce mata, "munzo fa". Sannan ta d'ago ta d'auko abinda ya rage mata na kud'i a hand bag da take sakale a jikin trolley ta, "kayi hak'uri wannan ne kad'ai abinda yake hannuna". Kallonta mutumin yayi da mugun mamaki kuma ya kalli kud'in hannunta, US dollers. Wacece ita d'in? Ganin ya tafi tunani ita kuma tana sauri ne gashi har rana ta d'aga sai ta sake mik'a mishi, "bani da canjin naira ne kayi hak'uri". Girgiza Mata kanshi yayi yace, "ki barshi kawai". Sake kallon shi tayi tace, "shukran jazeelan laka". "Ba komai" ya fad'a yaja motarshi ya yi gaba zuciyarshi fal da al'ajabin wannan baiwar Allah. Ta soma tafiya cikin tashar jiki a sanyaye a salub'e, kafun wasu mutane suzo suna tambayar ta inda ta nufa, ba b'ata lokaci ta fad'a musu inda zata, nan suka yi mata jagora har mazaunin da sukayi mata a cikin motar. Ranar surayyah ta d'and'ana kud'arta ba kad'an ba, yadda ta tsani shirgin mutane da shiga ciki sai gata dumu dumu tana gwara numfashi dasu a motar haya, haka ana soma tafiya warin fetur ya soma damalmala mata lissafi, tashin zuciya kamar ta mutu, dole daga k'arshe sai toshe hancinta tayi, ta hak'ura da numfashi yadda ya kamata. Lokacin da akazo maganar kud'in motarta sai ta basu wannan dollers d'in da driver farko yak'i karb'a, suma k'in karb'a sukayi saboda tsoron ko fake ne, dole a k'arshe sai d'aya daga zoben hannunta na gold ta basu donta fanshi kanta a gurin marassa mutumcin drivers d'in, d'aya cikin sune yace, "haba baiwar Allah tun hawanki motar nan muke d'aga maki k'afa, nan da kika gammu bama yadda mu d'auki passenger bai bada kud'i cash an bashi resit ba sai ke, kuma don rainin hankali anyi miki alfarma kin wani d'auko jabun doller kin bamu, sannan mun ki karb'a kin sake d'auko wani zobe wai gold don tsabar kin maida mutane shashashu, to gaskiya hajiya ina ganin gwara mu saukeki a hanya kawai ki Sami wanda zai karb'i wannan zoben ya kaiki". Wannan mutumi da yake zaune gefen driver ya k'arasa fad'a fuska ba fara'a, kuka ta somayi wiwi tana bashi hak'uri da rantsuwar duk abinda ta basu babu jabu, batayi haka da gayya ba wallahi ko 1naira babu a hannunta sai abinda ta basu d'in. Wata mata da tunda suka soma tak'addama take kallonsu, sai lokacin tasa musu baki bayan ta karb'i zoben a hannun surayyah ta k'are mishi kallo, zobe ne mai tsada mai daraja k'irar wani babban company na k'asar Dubai, akalla kud'in shi zasu iya kai 70k a kud'in Nigeria. Jakarta ta duba ta lalubi kud'i ta tambayi masu motar nawa ne kud'in su suka fad'a ta basu, sannan ta kirgo wasu masu yawa ta mik'awa surayyah, "Ni na karb'i zoben ga cikon kud'in da yayi mun saura Ina fatan kin hak'ura da abinda nayi miki, nayi miki haka ne saboda kada in kinyi gaba kici gaba da rigima da wasu mutanen". Karb'a surayyah tayi kawai don alokacin she have no choice. @@@@@@@@@ K'arfe 6:36 dai dai Suka k'araso garin kano anguwa uku motor park, duk passenger Suka futo itama ta futo tana tunanin inda zata nufa, ga yunwa ga har lokacin k'afarta ba takalmi, ga kishirwa, ga gajiya, sannan ga wani irin yanayi da yake hajijiya da ita abinda bata tab'a jiba tunda ta samu cikin jikinta, a sanyaye jikinta ta dinga bin inda taga mutane sunayi neman napep, dai dai inda matar data siya zobenta a mota ta tsaya, sai dai ko kafun surayyah ta kaiga tambayar matar abinda ta zo da nufin tambaya wani mugun amai ya taso mata, haka ta durk'usa a gurin ta shiga kyelaya shi kamar zata amayar da y'ay'an hanjinta. Matar ce ta taimaka mata da pure water bayan ta gama ta d'an wanke bakinta da fuskarta. Matar da son neman maganarta tace, "dama baki da lafiya? Ina kikayi ne da sai in taimaka in nemo miki napep". Zuciyarta sosai ta karye a lokacin tuno da rayuwar data zab'a ma kanta yanzun kamar wata marar galihu ko y'ar kanta, bayan tana da kyakkyawan asali da dukkan gata. "Ni anguwa........ Zani ko kema can zaki". Matar ta sake fad'a tana kallon surayyah da take ta yak'in b'oye hawayenda suka cika idonta. Gyad'a Mata Kai kawai tayi, in few seconds matar ta samo musu napep Suka shiga bayan ta fad'a mishi inda zai kaisu ya fad'i kud'inshi. Tafiyar minti 20 zuwa da y'an mintuna suka isa anguwar ta masu k'aramin k'arfi. Ko kafun surayyah tayi wani abu matar ta biya kud'in har nata, sai tayi Mata godiya kawai ta saita hanya kamar wadda tasan gari don kauce ma bin diddigi irin na matar. Tana jinta tana fad'in ki huta gajiya "Allah ya raba lafiya". Lumshe fararen kwayar idanunta da a yanzun suka sauya colour tayi taja doguwar ajiyar zuciya, yanzu a d'an zaman da sukayi matar nan harta karanci tana da ciki? Surayyah taci gaba da Jan k'afafunta da jakar kayanta tana kewaya anguwar har daga k'arshe Allah yasa ta samu dakalin wani masallaci ta jingina tana sauke lodi lodin ajiyar zuciya, zunbur tayi ta mik'e a lokacin da limamin masallacin ya tada sallar isha'i maza Suka soma yink'urin zuwa su shiga don bin jam'i, sai a lokacin ta tuna rabonta da sallah tun ta asubahi. Sake rintse idanunta tayi ta kifa kanta da gwiwowinta tana jin yadda duniyarta take jujjuya mata. Bayan an idar da sallah duk wanda yazo hucewa sai ya kalleta har kowa ya watse mallam liman ya gama zaman lazumi shima ya futo. Yana Shirin kulle masjid d'in surayyah ta d'ago kanta da idanunta da take gani dishi dishi da kyar tace, "don Allah ka taimakeni........". Iya abinda ta iya fad'a kenan ta zube a gurin babu numfashi, malam hankali a tashe yayi kanta yana salati da sallallami ga dare ya Soma nisa bare ya kira wani ko wasu. Kusan mintuna biyar sun huce babu inda yake motsi ko guda a jikinta, ganin haka sai ya nufi gidanshi wanda yake daura da masallacin, tun daga zaure ya soma kwalawa iya salaha kira, "salaha! Salaha!! Salaha futo mana kina Ina ne?". Da sauri iya data Soma gyangyad'in bacci ta nufo zauren tana amsa Kiran mijin nata, "malam lafiya wannan kira haka kamar sabon makaho". Da sauri ya dakatar da ita "d'auko gyalenki ki biyo ni kiga wani abu". Ba musu ta koma ta yafo gyale tazo ta sameshi. Har inda surayyah take ya kaita ya fad'a mata abinda ya sani game da zuwanta gurin da abinda ta fad'a kafun ta yanke jiki ta fad'i, d'an Jim iya tayi kafun ta nisa sosai tace, "toh yanzu dai duniya ta zama abin tsoro, yanzun nan taimako sai ya jawo maka hau, sannan wannan yarinya ce budurwa, duk inda ta futo ba daga wahala take ba dole akwai wani abu da yake faruwa da ita". Malam yace, "Shiyasa na kira ki ai yanzu ya kike ganin za'ayi salaha?". Ehhh to Ni Ina ganin mu taimaketa da zuciya d'aya tunda macece ta samu mafaka zuwa gobe da safe in ta dawo hayyacinta muji abinda ya rabo ta da gida, inda hali muyi mata naseeha albarkacin mu sai kaga ta shiryu ta koma". "Shikenan hakan ma yayi". Malam ya fad'a iya kuma ta soma kici kicin d'ago ta da kiran ta, da kyar suka samu da yayyafe yayyafen ruwa ta farfad'o malam ya jawo trolley ita kuma iya ta d'an rik'o ta sukayi gidanta. Tana zama ruwa shine abu na farko data soma tambaya, iya ta deb'o mata me sanyi a randa ta had'o mata har da dambun tsakin masarar da tayi a daren ranar. Ruwan kawai ta iya sha ta d'auko ledar magungunan ta a jaka tasha, su dai kallonta kawai sukeyi suna son suji ta bakinta amma bata da niyyar ce dasu komai banda godiya da tayi musu gashi ma kamar bata hayyacinta. Ta jima a jingine kafun magungunan da tasha su soma tasiri a jikinta wani nannauyan bacci ya soma fizgarta, iya ta kawo mata pillow nan ta b'ingire. "Tirk'ashi malam yarinyar nan kamar tana d'auke da juna biyu sannan wannan kwayoyi data afa Allah yasa ba y'ar kwaya bace?". Shiru ne ya biyo baya saboda shi malam harga Allah baya yi mata kallon gurb'ataccen tarbiyyah yafi son ta tashi suji komai daga bakinta. @@@@@@@@ Washe garin ranar kiran sallar farko ta tashi sai dai da wata matsananciyar yunwa, iya tana alwala itama ta futo bayan ta d'auki buta ta tambayi iya bayi ta nuna mata, bayan ta futo kuma ta durk'usa kusa da iya ta soma d'aura alwalar ta itama. Ko kafun ta shiga iya ta shimfuda mata darduma ko zatayi nafila kafun a tada sallah, Zama tayi ta had'a kanta da gwiwa kafun can ta tambayi iya da take ta faman jan carbi bayan ta idar da sallah, "don Allah zan samu abinci?". "Laaa zaki samu y'ar nan bari na kawo miki, iya da k'ok'ari har wutar icce ta hura ta dumama mata sannan. Ko lokacinda surayyah ta kai lomar dambu bakinta Saida ta rintse ido saboda bak'on test da taji ya ziyarci kan harshenta, wato karo na farko data tab'a cin dambu irin wannan a cimar hausawa. Ba laifi taci abincin da yawa kuwa, sai dai fa tashin zuciyar amai yana barazanar tunkud'o mata shi waje ya zama asara, da sauri ta d'auki maganin amanta tasha, sannan bayan wasu mintunan ta tashi ta shiga jero duk sallolinda suka huceta. Akan sallayar wani baccin ya sake awon gaba da ita wanda ya kaita har k'arfe goma da rabi na safe. Lokacin data tashi jiki a sanyaye ta futo tsakar gidan ta samu iya tana aikin d'aura gyad'a mai gishiri a leda, malam kuma yana kishingid'e kan buzunshi yana jan carbi, har k'asa ta durk'usa ta gaishe su cikin mutuntawa, iya tace ga ruwa can idan zakiyi wanka na aiki y'ay'an mak'ota yanzu su sayo miki sabulu da soso, tace ba komai da kin barshi ma Ina da sabulu a jakar kayana da soson. Daga haka ta d'auko soso da sabulun ta shiga wanka, bayan ta futo ta shafa mai ta sauya kayan jikinta zuwa wata doguwar rigar ta atamfa super Holland futowa ta sakeyi tsakar gidan ta zauna a inda iya ta nuna mata. "Kuyi hak'uri tun jiya Ina cikin wani yanayi ban iya tsayawa munyi magana yadda ya kamata daku ba, toh nidai bayin Allah sunana surayyah Adam Kuma ni haifaffiyar k'asar Sudan ce garin Khartoum dake arewacin Sudan. Mahaifina Adam da mahaifiyata mai sunana, mu biyu suka haifa a duniya daga yayana sauban sai ni, dukkannin su Allah yayi musu rasuwa ta silar accident da sukayi a jirgin ruwa, lokacin Ina da shekaru goma a duniya, kusan zan iya cewa a Nigeria nayi rabin rayuwata a gidan yayana dake garin Abuja wanda yake aiki da wani company...... Yayi aure da y'ar can asalin k'asar mu yanzu haka suna da yara uku, abubuwa da yawa sun faru dani a shekarar dana shiga jami'a Ina level 2h babba a ciki shine had'uwa ta da k'addarar rayuwata Suraj, labarina daga nan sirri ne da bazan iya tattauna shi da kowa ba, sai dai ince kuyi hak'uri watarana idan lokacin kuji yayi zakuji komai". Ta Kai k'arshen zancenta tana girgiza kai kawai da share hawayenta da gefen d'an kwalinta. Iya ce tace, "Allah ya magance mana abinda yafi k'arfin mu surayyah sai dai mu d'in da kike gani masu k'aramin k'arfi ne, muna da cin yau muna neman na gobe a gurin Allah, ba lallai ne ma ki iya cin cimar muba? Bare irin rayuwarmu ta wahala da talauci". "Baki da matsala dani akan komai, ni y'ar kasuwa ce, kuma Ina tafe da takardun makaranta na in Allah yasa na haihu lafiya zan nemi aikine a garin nan kuma naci gaba da business d'ina, alfarma d'aya kawai nake son kuyi mun". "Wace alfarma ce fad'i muji yarinya". Ta sake gyara zamanta cikin k'arfi da dakiyar zuciyarta take yin komai a yanzun tace, "so nake ku d'auke ni kamar y'ar ku a gidan nan, y'ay'an da zan haifa su zama jikokinku, labarin da zasu kallah kullum game da kansu ya zama, mahaifin su ya rasu malam shine mahaifina ke kuma mahaifiyata, bana son su samu damar da zasuyi d'igon tunanin akwai wani abu da ake b'oye musu.....". Sai lokacin malam ya mik'e zaune sosai yace kiyi bayani yadda zamu gane yarinya, kina nufin kinbar gidanku kenan har abada? y'ay'a har guda nawa kuma kike nufi? Sannan ki dubi girman Allah ki fad'a mana shin suna da cikakken asali mai kyau ko kuwa ta wata hanyar daban kika samar dasu? Ko iya wannan kad'ai ne ki sanar damu don Allah mu futa daga rud'ani da kwokwanton da kika jefa mu ciki" Mik'ewa tayi tsam ta shiga ta futo musu da takardu har guda uku, tace, "ko akwai wanda ya iya karatu a cikinku?". Iya tace, "malam ya iya karatu don a k'auyenmu kafun mu baro garin har headmaster yayi a wata makarantar firamare". Tashi ta sakeyi ta kaiwa malam takardun ya dudduba, bayan ya gama cikin farin ciki yace, "d'an Damm malam yayi kafun ya dubeta cike da tausayawa, shi kanshi idanun shi Saida Suka tara ruwan hawaye, Allah kenan mai yin yadda yaso a lokacin da yaso, sama da shekara ashirin suna neman haihuwa basu samu ba amma yau ga wata ta samu ta wata hanya daban. Sai yayi murmushi mai kama da dariyar yak'e yace, "Masha Allah yarinya! Allah ya futo mana da twins cikin qoshin lafiya ya hore mana abinda zamu ciyar dasu". Iya kam cikin rashin fahimtar komai tace, "au ni da yake ban iya karatu ba shine ba za'ayi mun bayani ba malam". Murmushi har lokacin akan fuskar malam yace, "zanyi miki bayani anjima insha Allah kuma muna maraba da samun d'iya irinki surayyah, munyi miki alk'awarin sirrinki zai tsira irin yadda kike so a gurin mu har abada". Surayyah tana kuka tace, "nagode malam". Tun daga wannan rana surayyah taci gaba da Zama tare dasu babu raini bare raina matsayin su, komai sukayi zata ci in aka d'auke fura da nono da gyad'a, yayinda take fama da matsanancin laulaulayi daya hanata sak'at, tana son taje hospital amma tana tunanin ta inda zata fara, so take ta siyar da duka gwala gwalanta sai ta samu wataccen kud'in da zatayi komai, ga magungunan tama duk sun k'are shiyasa yanzu komai taci saiya dawo, ita kanta iya ta fahimci magungunan sune suke taimaka mata ashe take d'an zama da kwari. Bayan wata guda, kud'in da suke hannun surayyah da matar nan ta bata a mota duk sun k'are sakamakon taimakawa su malam da takeyi. Gidan ciki da parlor parlor ne guda biyu sai fallen d'aki da sitting room da ba'a gama ba suke kiwon kaji a ciki, fallen d'akin suka bata duk da babu komai a ciki sai labulen net saboda sauro da k'atuwar tabarmar da take kwana a kai in ta shimfud'a bargo, mutanen anguwa y'an tsirko sunyi ta zaryar zuwa ganinta har sun gaji sun daina, wasu sun ganta wasu kuma harsu tafi tana d'akinta don ba wani son shiga mutane take ba sosai. Most of the times she enjoy been alone, tun ba yanzu ba dama haka rayuwarta take. Yau tun data karya da kunun tsamiya da iya tayi da k'osai bata koma bacci ba ta fad'a wanka ta shirya cikin d'aya daga abayoyinta da tazo dasu a akwati. K'aramar jaka ta d'auka ta had'a duka golds d'inta a ciki da kud'ad'en k'ashashen k'etare, tayi kyau saboda har yanzu bata sauya ba kamar ba'a k'aramin muhalli take rayuwa ba, cikinta ya futo d'as ta cikin rigar, idan tana lissafe wannan wata na shida ne ya kama, shiyasa take son ta samu enough kud'i a hannunta kota samu ganin consultant doctor da yasan aikinshi don ya duba ta yadda ya kamata. Lokacin data futo iya tana ta aikin d'auraye kayan ta dana su data wanke, "surayyah badai kin futo ba?". "Eh iya na d'auka ma kin shirya? Wankin Dana ce ki hak'ura iya idan na dawo a kira yarinyar nan data wanke mun kwanaki ta yi mana shine kikayi?". "Uhum! Babu komai surayyah ni wanki baya d'aga mun hankali nama gama bari na d'auko gyale na in muka dawo saina k'arasa shanyawa" "Ai da kin shanya kawai iya saina jiraki". "A'a idan rana tayi ba zamu samu yadda kike so ba, hayaniyar mutane a kasuwa kan iya sa miki ciwon kai ma ki dawo gida ba lafiya". Kusan tare suka futo suka iske malam a zaure yana ta lazumi, sukayi mishi sallama suka huce. Tunda suka futo ake binsu da kallo har surayyah ta gaji ta b'oye rabin fuskarta da gyale, bata San meye abin kallo a shigarta da ita kanta ma in banda abu na mutane. Gurin Gold d'in suka soma zuwa, sark'a guda uku (mai hawa uku) sai zobe da abin hannu, sark'ar k'afa da d'an kunnaye, suka siya da daraja kuwa yadda ya kamata a take suka bata kud'in ta. Daga nan sukayi banki inda aka sauya mata kud'in zuwa naira, basu dawo gidan ba har saida Suka siyi duk abin buk'ata na yau da kullum wanda zasu d'an jima musu iya cikinsu dai ita da iya da malam bai k'are ba. Kwana biyu a tsakani iya ta rakata wani Private hospital taga likita, wanda bata dawo ba har saida akayi mata scanning aka tabbatar da k'oshin lafiyar abinda ke cikinta. @@@@@@@@@ Daga nan surayyah taci gaba da rayuwarta cikin kiyayewa da bin dokokin likita, zuwa lokacin kuma komai yana tafiyar musu dai dai ita da sababbin tsintattun iyayenta da basu tab'a haihuwa ba Suka sameta a sama batare da ko sisin suba take d'awainiya kullum dasu. Tana son yi musu abubuwa da yawa a gidan amma cikin jikinta yasa ta dakata, lokacinda ta shiga watan haihuwarta likitan da take gani yasa ranar da za'ayi mata CS saboda girman da yaran sukayi idan akace zata haifesu da kanta zata sha wahala sosai. Malam da kanshi ya rakasu ita da iya har asibitin, tana kuka ta rik'e hannun iya tace, "su yafe mata duk abinda tayi musu na d'an zaman da sukayi tare, za'a shiga dani theatre ko na mutu ko na rayu iya Allah shi kad'ai yasan wanda zai faru a ciki amma don Allah idan har banyi tsawon rai ba akwai golds da Master card d'ina kiyi amfani dashi ku inganta rayuwar y'ay'a na bana son su tashi cikin wahalalliyar rayuwa, ba wai kuma don na raina matsayinku Kona abinda kuke dashi ba, a'a naci buri naci alwashi indai da raina ina numfashi yarana zasu samu kyakkyawar kulawa da tarbiyyah, toh ko bana raye ina son na cika wannan alk'awarin". Iya tana kuka sosai ta sake rik'e hannun surayyah a nata tace, "ki daina irin wannan maganar surayyah, insha Allah zaki rayu tare da y'ay'an ki, ki basu irin tarbiyyar da kike so, ki kula dasu da kanki". Tana kuka iya na kuka sukayi sallama, aka huce da ita tana d'agowa iya hannu. Somun tab'i kenan, more comment more typing. _Comment and share_ 24/03/23, 1:58 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page two 2️⃣ An yiwa surayyah aiki cikin nasara inda aka ciro mata yara biyu maza kyawawa. Bayan nurses sun gyara su suka futo da yaran aka mik'awa iya da malam d'ai d'ai ita kuma me jego akayi d'akin hutu da ita, iya ma ita sam bata yaran take ba tafi damuwa da uwarsu, basu san ya zasu yi da yaran nan ba muddin ya zamana surayyah ta mutu, basu san daga takamaiman inda take ba bare dangin uwarta kona ubanta, hannun iya har rawa suke a yake a lokacin da ta karb'i yaran, "yarinya Ina fatan mahaifiyar su tana raye cikin k'oshin lafiya ko?". Iya ta tambayi wata nurse "Eh yanzu haka tana bacci ne zaku iya zuwa ku ganta ma". Ajiyar zuciya suka sauke kusan a tare suna hamdala ga Allah subhanahu wata'ala kafun subi bayan nurse d'in har zuwa d'akin da ta kama wato aminity, tana kwance tana bacci magashiyan tamkar mataciyyah hannunta d'auke da ledar ruwa drip yana shiga da kad'an da kad'an. Sai a lokacin suka kalli yaran da kyau, kyawawa dasu Masha Allah, sai dai basu d'auki kamar uwarsu ba ko kad'an har hasken fatar, to ko kamar waye wannan suka biyo? Allahu a'alamu. Surayyah ta d'auki wasu hours masu yawa tana bacci kafun ta dawo hayyacinta, da iya ta soma tozali tana aikin bama jariri guda madarar da nurse ta had'a ta koya mata yadda ake yi, yayinda d'aya yake ta aikin callara kuka, zaune ta mik'e da kyar idonta akan yaran babu ko k'iftawa tana kallonsu, "sannu surayyah" iya ta fad'a tana k'ok'arin matsowa kusa da ita don ta nuna mata abinda ta haifa. Alhassan ta soma karb'a bayan ta rintse idonta tace, "wannan shine abdallah Suraj abdallah (Khaleefa)". Na biyun ma ta d'auke shi tace, "Adam Suraj abdallah kai kuma (Ayman)". Tambayar ta iya tayi bayan ta karb'e su, "sunan wa kenan kika sa musu surayyah". Fuskarta da Murmushi mai ciwo, yayinda kwayar idonta ta tara ruwan hawaye tace, "iya Adam sunan marigayi mahaifina kenan, Abdallah kuma wani kwayar mutum ne guda d'aya tilo daya yi mun abubuwa da yawa, tarin alkhairan da bazan tab'a mantawa dashi da suba har abada a lokacin da yake raye". "Allah sarki Allah ya gafarta musu". Iya ta fad'a tana sake kallon fuskar yaran, tana son tambayar ta dawa suke kama amma tana tsoron kada ta sake d'aga mata hankali duba da a yanzu hakan ma kuka takeyi daga fad'ar sunan yaran, toh amma ya kamata ko yaya ne taji wani abu ko guda a tare dasu, sai ta bari bayan ta nutsu kad'an sannan ta jefa mata tambayar "toh dawa suke kama kenan yaran? Naga dai basu d'auki komai naki ba surayyah". Dam! Dam! Gaban surayyah ya fad'i, zuciyarta ta tsinke idonta ya sake tara ruwa, "wad'annan yara ba kammanin kowa suka d'auko ba iya saina azzalumin mutum! macuci! Mayaudari maha'inci kuma k'addarar rayuwata Suraj abdallah tofa, hak'ik'a iya ban tab'a shiga tashin hankali ba a rayuwa irin wanda suraj ya jefa ni, ya ruguza ni, ya ruguza mun rayuwata, ya raba ni da duk wanda zan rab'a naji sanyi a rayuwa, sai dai kuma nayi nadama nayi alk'awari zan kasance, *JARUMAR UWA🧕* Uwar da y'ay'an ta ba zasu tab'a kukan yin rashin wani abu ba a rayuwa, zanyi aiki tuk'uru na tabbatar da gaskiyar maganar nan da bature yace, "any thing man do, woman can do better" (amma fa idan ya had'u da me k'arfin zuciyar da wutar d'aukar fansa ke turuwa kullum a cikinta), zanyi istigfari iya, in nemi kusanci da mahaliccina, in mik'a mishi dukkan ragamar rayuwata sai yadda yaso yayi dani......" Ita kanta iya ta tausaya mata, kuma taji dad'in furucinta na yanzu da yake nuni da nadamarta a fili k'arara, lallai yaran mu na wannan zamani sun tafi da yawa, in banda lalacewar zamani yaushe mace zata amince da namiji har wani abu na auratayya ya shiga tsakanin su, namijin daba mijin taba! Kae Allah ka tsare mana zuri'a kawai, gashi yanzu abinda ya haifar. Abinda iya ke fad'i a ranta kenan tana kallon kyakkyawar fuskar yaron dake hannunta. Toh tun daga wannan rana surayyah ta sawa ranta jarumta da k'arfin gwiwa na dole akan sabuwar rayuwar da take tunkararta, she promise to be the best mother ever to her children, k'arfin da yake zuciyarta ya kori duk wani rauni na jiki fata fata, satin ta guda a hospital d'in suka sallamota gida da dokar likitoci lifdi lifdi irin wanda duk wata mace da akayiwa CS bata Isa ta tsallake ba. A daren ranar kuma mallam yayi musu hud'uba da sunayen data zab'a musu. Ko sau d'aya surayyah bata tab'a sawa ranta wani abu makamancin lanjere da kwanciya ba, komai da take yi kafun ta haihu bata fasa ba, washe garin ranar bakwai ta ba mallam kud'i ya siyo raguna uku manya aka yanka a matsayin hakika, tasa iya ta nemo mata wata mata anan saman anguwar su da zata tayata kula da yaran da kuma ayyukan gidan da suka yiwa iya yawa, ba don iya taso ba haka dai ta hak'ura ta kyale ta cox ta nuna tausayawa gare ta, duk da ita bata ga yawan aikin ba ta saba yin ninkin ba ninkin d'insu ma. Halima wata macece da miji ya mutu ya barta da y'ay'a har biyar maza da mata take k'ak'anik'ayi da neman yadda zata rufa musu asiri, ta kanyi sirfau, wankau har ma da nanny a makarantun yara koda iya ta tuntub'e ta da batun yiwa surayyah aiki ba musu ta amince saboda duk rintsi aikinta a gida zaifi mutumci akan na makarantun yaran musamman da taji za'ayi mata kyakkyawan biya da d'an abinda surayyan take dashi. Ta fara zuwa aiki tun a washe garin ranar da akayi maganar aikin da ita. *********** Toh watan surayyah biyu da haihuwa ta karkab'e takardunta da 🏧 card d'inta ta futar da kud'i masu yawa aka soma gyaran gidan. Aiki akayi tuk'uru na rushe rushe da gyaran each and every part na gidan aka like shi da tiles da kayan gini na zamani, parlour ne dogo akayi mai d'auke da 3 bedrooms sai kitchen a gefe da fallen d'akin da take rayuwa akayi mishi bathroom sai toilet biyu da sitting room inda malam zai iya harkar malumtar shi. Kud'in data narkar har saida su iya suka ji tsoro don basu san ta inda ta samo su ba, kuma kasancewar har yanzu basu ga wani abun zargi a gareta ba sai suka tafi a yadda tayi musu bayani kurum. (Abinda basu sani ba shine irin wannan kud'ad'en tana da shidan su a account d'inta banda kadarorinta) Surayyah bata tsaya iya nan ba saida ta k'ara da siyo kayan abinci masu yawa da duk wani abun buk'ata da zasu jima suna amfani dasu basu k'are ba. Godiyar da malam ya dinga yi mata har saida ya had'a da kuka, ita kanta kukan ta dinga yi duk suka had'u suka narkar da zuciyar iya itama ta soma kukan. Y'ay'an ta Masha Allah sun sake mul mul dasu kyansu ya sake futowa saboda tsabar kulawar da suke samu, a yanzun watansu uku amma inka gansu saika d'auka sun kai kusan wata biyar saboda girman da sukayi da wayo. A ranar wata litinin da safe surayyah ta shirya ita da yaranta cikin shiga ta mutumci da kamala, takardun makarantarta ta d'auko tun daga primary har jami'a ta zura a cikin envelope ta d'auki jaka ta zuba duk abinda take tunanin yaran zasu buk'ata. Ta d'auki khaleefa (alhassan kenan me sunan abdallah) halima ta d'aukar mata Ayman (alhussain kenan me sunan Adam). Tare suka futo suka tarar da iya na faman aikin suyar gyad'a me gishiri da yake bata rabo da k'ulle k'ulle. Da fara'ar ta ta dube su tace, "y'ar daraja har kun futo". "Eh iya ai munso muyi late ma". "Toh Allah ya tabbatar da alkhairy ya bada abinda akaje nema". Da ameen ta amsa ta nufi d'akin malam, shima addu'ar ya mata tayi musu sallama suka futa ita da halima. Asibitin doctor fatahi ta nufa direct saboda shine kad'ai ta sani har take tunanin zata iya yi mishi bayanin abinda take buk'ata yayi mata. Taci sa'a ranar a nan zaiyi aiki sai dai ance zai kai ten to eleven kafun yazo, guri suka samu suka zauna zaman jiranshi. Koda yazo ita ta fara shiga ganin shi bayan ya daidaita zaman shi a office, bayani tayi mishi na aikin da take nema ga kuma shaidar kammala karatu tare da ita. Sab'anin tunanin ta ashe ba mutumin kirki bane a gurin ba b'ata lokaci ya nemi had'in kanta, aikuwa tayi mishi tatas! Ta zage shi cikin fusata ta tattaro kan yaranta sukayi gida. Daga iya har halima babu wanda ya tambayeta ba'asin sauyawarta ko yadda tayi dashi, ita ma kuma bata fad'a ba. Bayan wata d'aya bata hak'ura ba ta sake futa duk da aikin ma ya fara futa a ranta duka, to amma saboda wasu abubuwa da yawa da suke faruwa da kuma tana buk'atar aikin don kud'ad'en asusunta su tsira shine ta sauya hanya. Amma wannan karon govement hospital taje kamar za taga likita, luckly likitan ya karb'i takardunta da alk'awarin zai nema mata gurbi taje ta saurare shi kawai, ya karb'i phone no ta ta dawo gida amma wannan karon da fara'a sosai kan fuskarta. Tayi jiran a k'alla kwanaki ashirin kafun ta samu kiran shi yana buk'atar ganinta urgent. Ita kad'ai ma ta tafi ta bar yaran a gida. Interview akayi mata aka tabbatar da kwarewarta sannan aka sa mata ranar da zata zo a bata office. Kamar wasa surayyah ta fara futa aiki 7-4 as a medical consultant doctor. Da albashinta mai kwari a wata, bata futa da twins gurin gwaggwo take barsu kafun halima tazo ta d'ora a lura dasu da abincin su, ita kuma tana dawowa aiki ta rungumi abunta suji d'umin jikinta, ta shayar dasu da abincinsu na hak'ik'a. Ta d'auki a k'alla wata uku tana futa aiki a napep kafun ta siya y'ar k'aramar mota irin ta mata don samun sauk'in kud'in transport da delay. Sannu a hankali al'amuran surayyah suka soma yin nisa, yayinda a kullum safiyar Allah take sake ci gaba da samun rufin asiri, taci gaba da business tare da manyan mata y'an kasuwa a gurin aikinta, inda take saro kaya na mata, kama daga sitturu, mayukan shafa, cosmetics and deodorant, ga jeweleries. Tun tana iya business d'inta tsakaninta da ma'aikatan hospital d'in da take aiki har mutanen anguwar su da yawa suka fahimta suka soma k'ulla business da ita. A halin yanzu ta daina tab'a kud'in da yake account d'inta sai albashinta kawai, ribar kasuwancin ta kuma ta soma adanawa future d'in y'ay'an ta. Sannu a hankali gutsiri tsoma da k'ananun munafunce munafuncen y'an anguwarsu ya soma dawo musu ita da iya, Ashe suna ta yayatata wai bata da asali yaran ma basu da uba yanzu ta fake da aikin likita tana futa karuwanci, su kuma su iya sun mak'ale jiki suna taci daga haramun, a ranar surayyah taji wannan magana sam hankalinta bai tashi ba hasalima ba b'ata lokaci tasa k'afa tayi fatali da maganar. @@@@@@@ Surayyah taci gaba da rayuwarta salamun daga ita da yaranta sai su iya da halima kafun Allah ya had'a ta da k'awa ta gari sameera. Sameera sun had'u da surayyah wata rana a asibitin da take aiki, lokacin twins d'inta nada shekara biyu a duniya don ta yaye su tuni, ta shigo antinatal ward zata had'u da wani likita abokin aikinta, har ta huce ta gurin sai kuma ta dawo da baya sakamakon jin maseefar da nurses biyu keyi kamar zasu ba hammata iska. Da farko ta d'auka fad'a suke, sai dai ko data nutsu saita fahimta duk wannan hayaniyar suna yine ga wata kwayar mutum guda da take zaune gefe tana faman share hawaye, ga yara biyu a gefenta duk ba gyara, ita kanta matar wujiga wujiga da ita zani daban mayafi daban kallabi daban, gata yarinyar mace kyakkyawa kuma. Cikin bin ba'asi surayyah tace da nurses d'in, "haba mana zulaiha ya zaku saka mace a gaba kuna zagi don kawai tazo neman taimakon ku akan yadda zata haife abinda yake cikinta". Sassauta murya zulaiha tayi tace, "Allah doctor surayyah matar ce da abun haushi, duk lokacin da tazo awo sai mun rubuta mata maganin da zai k'ara mata lafiya ita da babyn ta bayan wanda gwamnati tasa a basu kyauta, amma kinganta dai ko ba zata tab'a siya ba, y'an kayan vitamins and protein bata ci, shi kanshi zuwa awon sai ta had'a sati uku bata zo ba, sai yanzu da zazzab'i ya kamata ta d'ebo jiki rab'e rab'e ta taho mana nan". Cike da tausayawa surayyah tace, "ayyah aiba haka zaku yi mata ba, da farko ma duk wannan maganar ba'a zo kanta ba tukun, kamata yayi ku jata gefe ku tambaye ta kuda ita bawai ku tozartata gaban mata y'an uwanta ba, kuji meye matsalar ta kuda ita inta taimako ce kutaimaketa y'ar uwar kuce fa mace, haba zulaiha". Duk shiru sukayi kafun surayyah ta sake tambaya, "yanzu taga likitan ko kuma bata gani ba?". "We are sorry doctor insha Allah zamu kiyaye, eh taga ni magani za'a bata ta tafi sai take fad'a mana wai ashe ko kud'in motar komawa bata dashi ga zazzab'i ya sake taso mata ba zata iya tafiya a k'afa ba.......". Da sauri ta d'aga ma zulaiha hannu, "ya Isa nurse na fahimta". Dubanta ta mayar ga matar da take durk'ushe tana sake fashewa da sabon kuka. "yi hak'uri baiwar Allah inba damuwa na ganki minti uku mana a office d'ina". Cikin jin dad'in ganin y'ar gayun likitar da bata fi tsarar age d'inta ba ta nuna tausayawa a gareta tace, "toh". "Am nurse zulaiha raka ta office d'ina". Da toh itama ta amsa mata. Ko bayan ta gama uzurinta ta koma office ta iske matar zaune k'asan tiles duk ta had'a zufa tamkar ba sanyin AC a office d'in yaran suna ta mata kukan yunwa" "A'a d'an samari da y'ar budurwa ya akayi kuma?". Surayyah ta fad'a tana tsugunnawa daf dasu, d'aya daya d'an fi wayo da alama shine babbah yace, "abinci". "Au kukan na abinci ne kenan toh bari Ina zuwa?". Kayan karin ta da iya kesa a biyo ta dashi kullum ta d'auko ta zuba musu abincin mai yawa a plate, tayi amfani da dispenser ta had'a musu tea shap shap, ta zuba musu madara ta kai musu saman carpet. "ga abinci malama amma ku koma kan carpet, kada kiji komai ki saki jikinki dani baiwar Allah". Ba musu taja yaran suka soma cin abincin bayan tayi mata godiya, ita kuwa d'auke hankalinta tayi daga kansu don basu damar da zasu ci abincin su ba d'ar d'ar. Saida Suka kammala matar ta gyara mata gurin sannan surayyah ta koma gareta ta fara jefa mata tambayoyi akan abinda yasa bata kiyaye dokar likita don lafiyar jikinta data babyn ta, kuka ta sanya har Saida tayi ta bata baki sannan tayi shiru, labarinta ta soma bata don haka kurum surayyah taji matashiyar y'ar gayun likitar ta kwanta mata a rai. "Ni dai sunana sameera, haifaffiyar garin Kano, nayi makaranta tun daga primary har zuwa secondary, haka ta b'angaren alkur-ani na sauke hizfi sittin, nayi aure da shekara hud'u yanzun, bayan shekara guda na haifi haydar ga shi shine babbah, bayan wata shekara da wata ukun na sake haifa mishi k'anwa gata itace asiya, itama watan ta bakwai na samu wani cikin wanda shine yake jikina yanzun ina wata na takwas da satittika. Toh da farkon auren mu mijina yana yi mun komai dai dai k'arfin shi, sai dai Ina haihuwar farko ya sauya, ba wadataccen abinci, ba kud'in cefane, bare a kaiga sutturar kirki ta sawa, wulak'anci yake mun iri iri, wani lokacin kona yi fushin zuciya zan tafi gidan mu saina hak'ura saboda yace duk ranar dana bar gidan shi tona tabbata na ajiye mishi duka yaran shi tunda ba dasu nazo ba, yanzu haka Ina zaune ne saboda su, saboda idan na tafi bansan wacce kalar matar zai auro ta rik'e su ba gashi har gobe bai sauya hali ba......". Ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka, hankie surayyah ta bata don ta tausaya mata matuk'a har saida hawaye suka cika idonta, wani lokacin k'addarar mata duk iri d'aya ce, matsala ce akan *AURE* sai dai ita kash tata tasha banban. Sai ta lumshe idonta a hankali ta tashi daga gabanta ta koma kan kujera ta zauna, ta bata damar ta gama kukan ta ko taji sauk'in rad'ad'in dake cikin zuciyarta, sai bayan tayi shiru don kanta sannan surayyah ta sake dawowa gabanta ta zauna tace, "ke kuma bakya sana'ar komai don ki rufawa kanki asiri?". Sameera tace, "Toh ai duk wata sana'a bata yiwuwa saida jari, ni kuma da nake ta abinda zanci.....". Jinjina Kai surayyah tayi tace, "haka ne kam, tabbas malama sameera labarin ki mai tab'a zuciya ne, sannan yadda kika yadda dani har kika bani labarin ki duk da a yau kika fara ganina, toh nima naci alwashin zan taimaka miki da abinda zaki fi k'arfin komai keda yaran ki harma shi mijin naki tunda zuciyar shi ta mutu, sai dai dole zamu ajiye komai har zuwa lokacin da zaki rabu da wannan cikin na jikin ki". Ita dai sameera jinta kawae take, don a lokacin tana ganin kamar ta gama k'are mata bata da wani sauran hope a rayuwa. A ranar bata sallami sameera ba har saida kud'i masu gwab'i ta bata catin ta da phone no tace don Allah data haifu tayi k'ok'arin sanar da ita. Koda ta dawo gida bata b'oye ma iya da halima komai ba, su kansu sun tausayawa matar kuma sunji dad'i da irin taimakon ta da tayi, koba komai Allah mad'aukakin sarki yace "waman sutra muslimun, sutrahullahu yaumal k'iyamati" "Duk wanda ya suturta musulmi zai suturtashi ranar alk'iyama". Kwana ashirin da biyu cif sameera ta haihu a nan asibitin sai dai yaron bai zo da rai ba, a wayar mahaifiyarta ta kira surayyah take fad'a mata a lokacin da ta cika kwana hud'u da haihuwa. Surayyah saboda yanayin aiki bata samu damar zuwa ba sai weekend. Ta tafi kuwa da abubuwa masu yawa, kama daga wasu cikin kayan sawarta har zuwa kan kayan abinci dana shayi, su biyu sukaje sai twins. Aikuwa sameera da yayarta sukayi ala ragab da yaran, don sun bala'in burgesu. Bayan tayi musu ta'aziyya da ya me jiki bata jima sosai ba suka tafi ita da halima bayan sameera ta sa yayyanta sunyi mata godiyar tarin alkhairan ta gare su ita da yaranta. Toh tun daga lokacin huld'a mai k'arfi ta shiga tsakanin su, surayyah bilhak'k'i take taimakon rayuwar sameera, har sun soma business tuni bayan anyi yarjejeniya da mijinta da mahaifiyar ta sun amince. Allah mai had'a mutum da mutum, kafun shekara ta kewayo sameera ta samu rufin asiri ta kama k'asa har tana rabawa mutane kaya sari. Yanzu komai zata yima kanta ta yima yara, tuni ta shirya planning haihuwa sai nan da shekara biyar ta samu abinda zata kula da masu zuwa sosai, yanzun yaronta babbah da k'anin shi har sun soma zuwa private school daga nursery kuma suka fara. _Comment and share_ 24/03/23, 1:58 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page three3️⃣ Rayuwa taci gaba da cud'a musu, yayinda surayyah har kullum take ci gaba yakice maganar mutane. A lokacin da su khaleefa suka cika shekara shida a duniya, lokacin tuni sun shiga primary da islamiyya, yaran Masha Allah sai San barka, ga wayo ga farin jini kowa son su yake kama daga malaman makaranta da mutanen gari, ranar wata asabar surayyah tana zaune kan carpet d'in dake malale a parlon iya tana taya iya d'aurin gyad'a, yayinda take ta zolayar halima da take basu labarin takaicin wai wani bazawari na sonta, ita ta dage baza tayi aure ba bayan da k'uruciyarta, yayinda ita kuma uwar d'akinta ta dage lallai zata iya yin aurenta ai ba haramun bane (haleema kenan). A lokacin ta tura su khaleefa lesson na French language, tunda weekend basa zuwa kowacce makaranta, sai dai bayan minti k'alilan da futar su saiga yaran sun dawo sarkin zuciya ne gaba k'anin shi na biye dashi a baya fuskar nan murtuk kamar zaiyi kuka "Ya aka dawo kuma mazajen iya". Iya keyin wannan maganar tana duban su. Zama khaleefa yayi opposite d'in surayyah yana ta faman kumbura fuska, dama ita surayyah sam bata nemi jin ta bakin shiba, cox tasan he will never say anything at that moment da zuciyar shi take up and down. "Ayman ya akayi?". Ta tambayi Ayman on a serious way da harshen Arab. Satar kallon khaleefan yayi sannan yace, "Auntie ba wani yaro ne na gidan su abulkhair ba kullum in ya ganmu zamu makaranta sai ya dinga ce mana wai 'shegu'". Wani irin Damm k'irjin doctor surayyah ya buga, wannan shine karo na biyu ko uku da yaron yana jifan yaranta da wannan mummunar kalma, bata san kuma ya zata guje ma k'addararorinta ba, dole akwai gurinda yaron ya tsinci wannan magana, bata san dalilin da yasa yaran hausawa suke wasa da kalmomi irin wad'an nan marassa dad'in furtawa ba. Murmushin ta k'ak'alo mai ciwo duk da nufin b'oye damuwarta, shoulder khaleefa ta dafa don shine mai damuwa, "haba khaleefa na, me yasa zaka damu don ya k'irk'iro sharrin shi ya lik'a maka don ya b'ata maka rai kawai, ka daina damuwa kaji babana?" Har yanzu fuskarshi a d'aure take ya d'ago ya dubi mahaifiyar tashi yace, "Auntie Sam wannan baiyi kama da sharri ba, saboda idan sharri ne ai bazai ci gaba da fad'a kullum kullum ba, har fa cewa yayi idan da gaske muna da uban mu nuna musu shi su gani, wai ance tunda kika zo anguwar nan ke kad'ai aka ganki ba'a san asalinki ba, don Allah Auntie ki kaimu gurin mahaifin mu muma mu ganshi har mu nuna musu su daina ce mana shegu plsss Auntie". Shiru tayi tana jinjina maganar yaron, kamar ana karanta mishi zance haka yake zaro shi, sai data sauke ajiyar zuciya mai tsayi sannan ta sake fuskantar shi, "har sau nawa zanci gaba da fad'a muku mahaifin ku ya rasu khaleefa?". Kwantar da kanshi yayi jikin Auntien yace, "I'm sorry mum amma ba yadda zaki sa ya dawo duniya ya fad'a musu shine baban mu sai ya tafi, in suka ganshi nasan ai zasu daina ce mana shegu". Duka a gurin babu wanda baiji tausayin su ya tsirga mishi ba, lallai su d'in abin tausayi ne, rayuwa babu cikakken asali abun tutiya jigo kuma alfaharin kowanne d'a lallai akwai wahala musamman cikin al'ummar mu da basa iya ganin zarau sai sun tsinka. Lallaba su surayyah tayi da kyar suka tafi ita kuma ta fuskanci iya, "iya Ina ganin ya kamata na taka ma yaron nan burki ta wajen iyayen shi, kinga yana son ya Samar mun da sabuwar matsala tsakanina da yarana". Nan take iya tayi na'am don lallai yana da kyau a yiwa rufkar hanci. Ita da halima suka tafi bisa jagorancin halima don ita tasan y'an anguwar sosai. Da sallama ta shiga suka gaisa da uwar yaron da kishiyarta, kafun ta fad'a musu ummul'a'ba'isin zuwanta, take matar ta k'aryata a cewarta sam yaronta bazai aikata hakan ba, tun surayyah na fahimtar da ita har ranta yayi zafi tace tunda ta k'aryata in bai fasa ba toh tabbas zata hukuntashi da kanta. Nan fa mata tace aka tab'a mata d'a ba zata kyale ba, tunda ai ba k'arya yaron yayi ba shegun ne kuma duk anguwa ansan basu da uba. Nan fa akayita d'auki ba dad'i tun suna yin abun su biyu har kishiyarta ta shiga, halima dai tana ta basu hak'uri. Sam surayyah bata iya fad'i in fad'a ba, haka bata San yadda ake tashin hankali ba sai ranar. Anyi rigima ta gaske wadda saida ta dangane da police, y'an sandan da surayyah ta kira suka kulle matar su kuma mutanen anguwa Suka yiwa surayyah caaa, sosai al'amura suka baddale duk anguwa ta rud'e. Malam shine ya tausasa surayyah data kwana batayi bacci ba tana kuka da takaici gami da yin kaico ga rayuwarta. Dole at de end ta hak'ura aka saki matar saboda shigar malam da mai anguwa zancen, sai dai fa an kafa mugun sharad'i akan duk wanda ya kuma sheganta mata yara d'auri ne da tara mai yawa, sannan ba batun yafiya. Malam yayi signing mai anguwa yayi sign, surayyah tayi matar ma tayi. Toh kusan sai ince tun daga wannan lokacin surayyah bata sake samun nutsuwa ba duk da a anguwar wani bai k'ara aibata yaran ba. Sai daifa sun taso da abun a ransu more especially khaleefa da yake da rik'e abu, wasu halayen nashi suna kamanceceniya dana Suraj duk da bai tab'a ganin shiba bai taso a daman shiba balle har ace ko zama tare dashi ne, a waccan ranar iya ta bata shawarar ta nemo mahaifin su muddin hakan zai yiwu, sai dai ta fad'a ma iya ko ta tunkari Suraj yanzu sake b'ata mata rai zaiyi don bazai tab'a karb'ar yaran ba, don haka take ganin a barsu kawai a yadda suka d'auka cewa mahaifin su ya mutu har gaban abadan. Ko khaleefa daya dameta da labari akan mahaifinsu taka mishi burki tayi, ta kuma sa ya alk'awarta mata shida tambayarta waccen maganar har abada. Kalaz aka rufe babin su gaba d'aya. @@@@@@@@@ Rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa gami da wadata, tuni surayyah ta siya wani fili makimanci a irin sababbin anguwannin da ake yankawa inda ake futar mata da tsarin gida mai kyau da tsari na zamani sama da k'asa. A lokacin da aka kammala ginin yaran suna 18 years, sun kammala secondary school zasuyi bikin saukar alkur-ani mai girma nan da two months. Tuntuni take son tashi sai dai ta fi son suyi bikin saukar su a nan gidan iya inda kowa yafi sanin su kafun ta sauya muhalli. Tana office ranar da yamma tana shirin tashi saiga khaleefa ya shigo kamar an wullo shi, "abbana Kaine tafe da yammacin nan?" "Eh auntie na d'auka ma kin tafi har Ina addu'a". Komawa tayi ta zauna tace, "ban tafi ba amma Ina shiri Ina Ayman da iya". Zama yayi kan kujerar da take opposite tata yace, "yana gida a kwance yana bacci". "Daga gidan kake kenan?". Ta sake tambayarshi cikin tsare shi da ido. Kauda kanshi yayi kafun ya sake cewa, "a'a daga gidansu Ahmad nake mahaifin shi ya buk'aci ganina, yanzun kuma da naje kema yace yana son ganinki". Take yanayin fuskarta ya sake d'inkewa ta dawo kicin kicin, ta kalle shi cikin b'acin rae sosai tace, "Wai khaleefa wane irin yaro ne kai, Ina ce tuntuni nayi cancelling tafiyar ka gantalin banza wata k'asa da sunan karatu nace a'a ba zaka je ba, toh tun wuri kaje ka shaida ma mahaifin Ahmad d'in da kanka kamar yadda ka amsa tayin su tun asali ba tare da shawara da kowa ba cewa mahaifiyar ka tace a'a ba zaka tafi ba suda suka ji zasu iya sai su tura d'an su can su k'arata matsalar su ce". Cikin marairaita khaleefa yace, "please Auntie.....". Surayyah yanzun cikin daka tsawa tace, "wallahi summa tallahi yanzun nan ranka zaiyi mummunan b'aci". D'akar da kanshi yayi k'asa shiru yana sauraron bambaminta har ta dire, Jakarta ta d'auka da car key ko tea plask d'inta bata tsaya d'auka ba ta nufi hanyar futa ranta bak'ik'irin, har ga Allah ita gaji da jin magana d'aya da sukeyi kullum kullum da khaleefa ba don Ahmad ya kasance yaron kirki ba da tace tayi nadamar had'uwar shi da khaleefa, tasan dashi ne suka shawarta duk wannan hark'allar, a sanyaye khaleefa ya tashi shima yabi bayanta, ta rufe offishinta suka d'auki hanya. Saida tayi sallama da lebura da suke aiki a yammacin sannan ta shiga mazaunin driver a motarta, shima gefenta ya shiga ya zauna shiru babu wanda yace da d'an uwanshi kanzil har ta fara driving, a hakasuka iso anguwar su. A k'ofar gida Suka samu Ayman zaune kan dakali yana koyama wata yarinyar mak'otan su iya msi suna raihana karatu. Duk suka nufi inda surayyahn take har raihanatu ta durk'usa tana gaishe su, khaleefa bai amsa ba don ko kallonta baiyi ba sai auntie ce ta amsa mata har tana tambayar ta maman ta, Ayman bin bayan shi yayi ya cimmasa a soro ya dafa kafad'ar shi, da sauri ya janye hannun Ayman ya sa kai ya huce cikin gidan, sallamar raihanatu yayi ta hanyar mik'a mata littafinta ya bi bayan auntie da sauri. "Wai meya faru ne Auntie Keda yaya khaleefa? why the sudden change? Nasan dai bazai huce a kan tafiyar shi Germany bane, toh don Allah Auntie ki barshi ya tafi mana indai hakan zai dawo masa da walwalarshi.....". "Rabu dashi Ayman sai dai ya dawwama cikin bak'in ciki amma ni da izinina ba zai tab'a barin Nigeria zuwa wata k'asa da sunan karatu ba, Soo learn how to be with him a hakan". K'arshen abinda ta fad'a kenan ta tashi tabar mysu gurin shida iya. Bin bayanta iya tayi ta tarar tana cire takalmin k'afarta da agogo, zama tayi gefenta ta fara tambayar ta, "surayyah meya had'a ki da magaji ya shigo fuska a d'inke? Nima ta bakin Ayman indai akan tafiyar nan ne kiyi hak'uri ki barshi ya tafi mana". Cikin d'inke fuska har lokacin tace, "iya mubar maganar nan don Allah, yanzun Ina fatan akwai ragowar abincin rana don yunwa nake ji" "Eh akwai d'an wake na fulawa da rogo, nasan kina so shiyasa na ajiye miki dama, sannan akwai ragowar alkubus d'in dana yiwa malam da magaji kinsan har gobe ya kasa sabawa da d'an wake shi". Surayyah tace, "Bar alkubus d'in nan iya ki kawo mun d'an waken zaifi mun dad'in ci". "Toh y'ar albarka" iya ta fad'a tana nufar inda ta adana mata abincin, Ayman ne ya sake biyo ta bayan iya ta futa ya zauna a kusa da ita yace, "mum sai yaushe zaki sa a kawo mana wayoyin mu gashi waec d'in da mukayi daga baya har ta futo tuni, kuma as we promise mun futo da good result bisa amincewar ubangiji". Dafa kanshi tayi tace, "Sunday insha Allah son". Da farin ciki ya mik'e zaune yana fad'in, "really mum". Gyad'a mishi kai tayi, rungume ta yayi tsam yace cikin farin ciki yace "I luv you mum bari naje na fad'a ma khaleefa nasan shima zaiyi farin ciki". Ayman da gudu ya nufi d'akin da y'an biyun nashi yake, ita kuma ta bishi da kallo cike da farin cikin da ya wanke b'acin ran da khaleefa ya haifar mata. Khaleefa yana kwance a d'aya daga d'akunan parlon iya (Wanda malam yasa aka basu da suka kai shekaru takwas a duniya, wanda kafun haka suna kwana ne tare da surayyahn har ma sai sun sata a tsakiyar su suke iya bacci, amma su da kansu suna girma suna sake ja baya da ita har aka basu d'aki sukayi zaman su) Idon shi kan ceiling d'in d'akin Ayman ya shigo ya bama kanshi mazauni kusa da d'an uwan nashi, "we are sorry bro nida Auntie ne ko? Bama son muyi missing d'inka shiyasa bama son kayi nesa damu, but we are Soo sorry plzz". Kallon d'an uwan nashi yayi cike da so da kulawa ya tashi zaune sosai yace, "kasan abinda yasa nake son tafiya Germany twin bro? Saboda a can ne zan fi samun kwarewa a kan physiotherapy da duk wani abu daya shafe shi, Ina son nayi karatu mai zurfi a kan ciwon ta yadda zan zama kwararren physiotherapist doctor" sai ya had'a hannuwan shi biyu, "don Allah Ayman ka fahimce ni a dai dai ka fahimtar da Auntie ma". Ayman yace, "Kada ka damu zata fahimceka insha Allah, nima na amince ka tafi sai dai Ina son ka tafi bisa albarkar Auntie shine kad'ai zaka samu abinda zaka je nema, Ina yi maka fatan dukkan nasara". Rungume juna sukayi kowanne idonshi na kawo ruwan hawaye. Nan suka baje kolin hajar hirar su irinta y'an uwantaka, har Ayman na yiwa khaleefa albishir d'in wayar su da Auntie tace zata zo soon, khaleefa yayi farin ciki shima sosai. ####### Toh a tak'aice an matuk'ar kai ruwa rana kafun Auntie ta amince suje gidan su Ahmad abokin khaleefa, daga yadda mahaifin Ahmad ya dabaibaye ta da maganganu na fahimta da k'arfafa gwiwa ya fad'a mata ko a ina d'anka yake addu'a zakayi mishi kawai amma ba wayonka ba davarar kace take tsarewa sai taji jikinta yayi sanyi har ta amince da tafiyar tashi a take, abinda bata tab'a tsammanin zatayi ba. Mahaifin Ahmad shiya shige musu gaba kuma kud'in registration na makarantar kawai ya amsa sai na apartment da za'a kama musu, amma kud'in jirgi da sauran hidin dimu na makaranta tuni yayi musu komai shida d'an shi. Ya kuma tabbatar ma Doctor surayyah da kanshi zai rakasu har makarantar, idan tana son taje taga komai da idonta zata iya biyo su suje tare. Ko kad'an ba zata iya wannan rashin karar ba, ta amince da mutumin kasancewar shi babban mutum mai nagarta, haka d'an shi ta yadda da tarbiyyar shi tunda kusan tare da y'an biyun nata yake wuni mafi yawan lokuta a nan gidan iya. Ranar da khaleefa yaji wannan albishir kasa bacci yayi yana mik'a godiyar shi ga Allah, yayi farin ciki yayi murna har da kukan murna. Kamar yadda tayi musu alk'awari ta sa an kawo musu waya mai kyau irin wadda ake yayi. Cikin kwana bakwai cif shirye shiryen tafiyar su ya kammala, duk da surayyah taso ya tsaya ya karb'i allon saukar su data rage kwana kad'an yanzun, amma hakan bai yiwu ba, saboda suna sake yin delay zasuyi missing komai nasu. Ana i gobe zasu tafi iya malam da surayyah Suka sashi a tsakiya suka yita mishi nasiha da fad'a kan rayuwa. Alhamdulillah naseehar ta shiga jikin shi sosai, hakan yasa har washe garin ranar daya gama had'a Kaya jikinshi a sanyaye. Ya yima su iya da malam sallama lafiya. Auntie da Ayman sukayi mishi rakiya zuwa airport. AMINU KANO International airport Surayyah data kasance matashiyar mace da kallo d'aya zaka musanta cewar itace ta haifi wad'an nan yara ma'abota kyau da cikar kamala kamanni sak da juna in aka d'auke wasu banbance banbance k'alilan da sai wanda ya zauna dasu zai iya gani, tana tsaye gefenta Ayman da khaleefa, komai na jikinsu iri d'aya hatta da agogo da takalmi da wayoyin hannunsu ba abinda ya banbanta, sai trolley dake rik'e a hannun khaleefa babu a hannun Ayman. Fuskokin su kad'ai zaka kalla kasan suna cikin tarin damuwa. Surayyah ta kamo hannun khaleefa da hannun shi ke rik'e da jakar kayan shi, ta kira shi cikin kwantaccen sauti dake nuni da zallar damuwar da take ciki, "khaleefa". D'ago kanshi yayi cikin ladabi ya amsa kiranta da, "na'am Auntie". Hannuwan shi duka ta had'a ta rintse cikin juna tace, "toh khaleefa yau gaka ga cikar burinka ka samu, duk da nasan kafi kowa sanin kanka don Allah ka lura ka rik'e maraicinka da amanar kanka da zan baka yanzu, sannan ka maida hankali akan abinda ya kaika, a k'arshe Ina maiyi maka fatan samun dukkan nasara, Ina rok'on Allah ubangiji ya baka ilimi mai amfanni wanda zai amfaneka duniya da lahira". Sai ta saki hannun shi tana share hawayenta da gefen gyalenta. Shi kanshi saida hawaye ya taru a idonshi, amma kasancewar shi mai k'arfin hali da k'arfin zuciya, sai bai yadda hawayen sun samu damar futowa ba ya shanye. Cikin sake russunawa a gabanta yace, "insha Allah Auntie, zanyi yadda kike so". Cikin jin dad'i ta shafa sumar kanshi tace, "Allah yayi muku albarka ya cika muku burikan ku my twins". Ya amsa da, "ameen yumma na da banda kamarta". Surayyah ta shafa kanshi tana murmushi mai tafe da siraran hawaye, "Allah ya cika muku burikan ku kai na zama medical physiotherapy Doctor, shi kuma na engineer". Duk murmushi sukayi khaleefa ya leqa fuskar Ayman daya juya mishi baya, kuka yake yi sosae, dafa kafad'ar shi khaleefa yayi cikin kulawa yace, "Ayman kuka haka kamar mace?". Sake zagayowa gaban shi yayi ya rik'e duka shoulder shi yace, "as a man you have to be strong Ayman, idar har k'aramin abu zai iya assasa zubar hawayenka haka to taya zaka iya yak'i da k'addarorinka? Ya kamata tun daga yanzu ka fara sawa ranka hak'uri da juriya, shekaru shida zuwa bakwai zanyi na dad'e da yawa takwas ba shekaru dubu ba" "kayi hak'uri khaleefa bansan ya zanyi da rayuwata ba idan ka tafi ka barni ni d'aya, dole nayi kukan nan don shine kad'ai zai rage mun d'acin bak'in cikin rashinka da zanyi, khaleefa kada ka manta mun saba yin komai tare, cin abinci, yawo cikin gari, tafiya school, da buga football duk k'arshen mako,idan ka tafi ka barni bana tunanin zan iya futa waje cikin mutane har nayi walwala, kayan mu da suke duk iri d'aya bansani ba ko zan iya sawa ni d'aya bayan ba ka nan, tabbas zanyi kewar fushinka, fara'arka, da miskilancin ka idan baka da lafiya, zanyi kewarka gaba d'ayan ka bro.......". Ya k'arasa fad'a cikin kuka had'e da takawa da sassarfa ya rungume shi, ba tare daya juyo ba cikin sake danne zuciyar shi yace, "sorry man ai duk kaine ka raba tsakanin mu da kak'i amincewa mu tafi tare". Girgiza mishi kai ya dinga yi, "bazan iya tafiya na bar Auntie ba shiyasa na zab'i da nayi karatuna a nan gida Nigeria, sai dai zanyi k'ok'ari na dinga biyo Auntie idan zata zo duba ka, a k'arshe ina yi maka fatan samun abinda zaka je nema twin bro, wish you oll de best of luck". Khaleefa juyowa yayi ya rungume shi ya lumshe ido a hankali hawayen da suka taru cikin idonshi da yake ta yak'i da zubar su suka soma biyo kuncin shi, daga nan gurin Auntie yayi ya russuna a gabanta gwiwar shi biyu duka a k'asa "ki gafarceni mum nasan har yanzu ba da son ranki zan tafi karatun nan ba, toh amma Allah ya riga ya tsara hakan a cikin k'addarorin mu ba yadda zamuyi, sai dai ban sare ba haka banyi k'asa a gwiwa ba gani nazo gareki da kokon barar addu'ar ki domin na samu abinda zanje nema duk da kinyi Ina son ki k'ara mun wata a kan wata domin addu'ar ki itace zata zamo silar samun dukkan nasarar abinda zanje nema". Itama cike da tausayin shi matuk'a ta d'ora hannun ta saman kanshi tace, "Allah yayi maka jagora son ya albarkace ka ya albarkaci karatun". "sai abinda zan sake jadadda maka a matsayin naseeha ta a gareka ta k'arshe, "don Allah ka kama kanka ka rik'e addinin ka ba tare da la'akari da rashin ingancin addinin mutanen da zaka shiga cikin su ba, kayi abinda yake halal, ka guji aikata Haram don gujewa fushin ubangiji". He can no more hold his tears at that very moment, kuka yake irin wanda ya kan jima baiyi irin shiba, da kanta surayyah ta d'ago shi ta share mishi hawayen, su duka ta had'a ta rungume a k'irjin ta tana jin sabuwar k'aunar yaran a cikin zuciyar ta. A haka y'an gidan su Ahmad da sukayo mishi rakiya suka same su, sun gaisa cikin mutumci kafun su sallamu yaran su soma tafiya inda za'ayi musu screening, tunda khaleefa ya had'a hannun Ayman da Auntie ya dank'e cikin na juna ya fara tafiya bai waiwayo ba. Kuka yake har lokacin, suna tsaye a gurin har saida ya b'acewa idaniyar su. Comment and share 24/03/23, 1:59 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyaert lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page four 4️⃣ Basu iya barin airport d'in ba har saida suka ga tashin jirgin su khaleefa,ko a cikin mota babu wanda yace da d'an uwanshi kanzil har suka k'arasa gidan k'awarta sameera. Ayman bai shiga gidan ba ya kwantar da seat yayi kwanciyar shi a mota, Ko data shiga gidan ta tarar sameeran tana shirin futa anguwa duk yaran sun tafi school sai baby heedaya da take bacci sab'e a kafad'ar ta hannunta rik'e da car key, komawa tayi suka zauna a parlon, sun gaisa cikin mutumci da mutunta juna inda take bata labarin tafiyar khaleefa Germany yau. Ta taya ta dayi mishi addu'o'i sosai kafun su fad'a hirar business da lissafin shirye shiryen bud'e shagon boutique wanda Ayman da babban d'an sameera haydar zasu kula dashi a ranakun da basu da lectures, ko idan sun taso school haka tunda ita har lokacin tana futa aiki. Sun tab'a hira mai yawa a kan business da k'ullalliyar alaqar da suke son su k'ulla na auratayya tsakanin yaran su don k'ara dankon zumunci. Ko data futo ita ta jasu har gida don Ayman zuwa lokacin yayi laga laga da zazzab'i da ciwon kai. Suna shiga gida ko bi takan iya da take mishi magana bai yi ba ya dusa kanshi d'aki ya kwanta. Da kyar auntie da iya suka shawo kanshi yaci wani abu yasha magani, wasa wasa saiga Ayman ya dangane da likita saboda zazzab'i ne yaci k'arfin shi karurus. Ta b'angaren Khaleefa kuwa kwanan shi biyu a Berlin dake k'asar Germany ya siya sim card ya nemi no's d'insu sukayi magana, ba k'aramin tashi hankalin shi yayi da yaji ciwon Ayman ba, har saida Auntie ta dinga kwantar mishi da hankali sannan, shida Ahmad a wani plat house aka kama musu apartment sai dai kowa cikin su d'akin shi da ban ne, gida ne babbah sama da k'asa d'akuna iri d'aya a jejjere kusan guda ashirin, kowane d'aki da kitchen da toilet a ciki, haka akwai d'an gado k'arami da drower, khaleefa basu sha wahala wajen siyan duk abubuwan buk'ata irin wanda suke so ba, saboda gidan kusan mutum 6 cikin 20 y'an Nigeria ne da suka kwana biyu a garin, su sukayi musu jagora. khaleefa sun fara karatu ba tare da sun Samu matsala da kowa ba a babbar makarantar...... Dake birnin Berlin na k'asar Germany, a wasu lokutan idan basu da lectures yakan je gurin Ahmad su yini tare su jagwalgwola girkin abinda zasu ci wanda khaleefa ya zama jagora don yakan taya Auntie aikin magana wani lokacin a gida idan ta tuna da abincin k'asar su ta Egypt. wani lokacin kuma suje k'aramin eatery suci abinci dai dai da kud'in su. ******** ******** _Nigeria kuwa_ Anyi bikin saukar su Ayman cikin k'ayatarwa inda Auntie ta shirya musu lafiyayyen bikin walima, Ayman shiya wakilci khaleefa har ya karb'ar mishi allo, ranar yini Ayman yayi yana video call da khaleefa yana nuna mishi komai, ko da yamma a wajen walima shi bashi da wasu abokai sai kad'an daga y'an ajinsu da Suka zo mishi, daya sallamesu yaga akwai ragowar take aways sai ya kira raihanatu ya bata ragowar duka yace ta kaiwa y'an gidansu kawai don shi baisan ya zaiyi dasu ba. Da kyar ta karb'a saboda ganin yawan su kamar itace ta shirya walimar, raihanatu duk da kasancewar ta yarinya k'arama a lokacin amma tana da taka tsantsan da mutane, a anguwar ba kowa take kulawa ba sai Ayman d'in da tasu tazo d'aya har yake kiranta da k'awar shi, a mafi yawan lokuta shi yake yi mata assignment ya nuna mata abinda ya shige mata duhu na daga aikin makaranta, duk wannan alak'ar da suke amma ko magana d'aya bata tab'a had'a ta da khaleefa ba, kuma itama bata damu ba. Toh kwanan su Ayman uku da bikin sauka Auntie ta tare a katafaren gidanta da ta gina, kowa ya yaba sai son barka, ranar da zasu koma gidan ma sunsha koke koke ita dasu iya da sukayi musu rakiya, da kyar iya ta iya zuk'ewa ta tafi gidanta ta barsu cike da kewar su da zatayi, halima kam dama ranar a gidan ta kwana saboda aikace aikace da sukayi musu yawa, wannan gida na surayyah ya assasa matsaltsalu da dama a cikin anguwa, inda mutane suka yita maganar su ta bak'in ciki da hassada akan tana mace zataje tayi zaman kanta, bayan tana da masoya masu sonta amma son duniya yasa ba zatayi aure ba, tana yawon bariki tana samun kud'i tana kashewa y'ay'anta a banza, abinda basu sani ba shine surayyah iya kud'in da tazo dasu a account d'in tama lokacin ya isa ta gina biyun irin wannan gidan, kuma alhamdulillah wannan ba asu tayi ba a ribar kasuwancin ta tayi, don kud'in aikinta shi suke ci, kud'in ta suna ajiye har yanzu ba tare da ko kwandala ta girgiza ba, karatun khaleefa kad'ai yasa ta tab'awa. Rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, Ayman yana karatun shi na engineering in ya taso makaranta ya zauna mata a boutique, idan wata yazo k'arshe ta sallame su kai d'aya da haidar. Ta b'angaren khaleefa ma yana rayuwa bisa tsari da taka tsantsan kamar yadda auntien ta yi mishi naseeha, a shekara uku da tafiyar shi auntie ta je ganin su sau d'aya, ta kuma yaba da tsarin yadda suke rayuwar su a Berlin komai dae dae, Ayman yaso ace tare suka je a lokacin amma sai akayi rashin sa'a a lokacin suna da exams hakan bai yiwu ba. Surayyah bata tafi ba saida ta sake bar musu kud'i masu yawa na abinci da sauran hidimar karatu. @@@@@@@ *AFTER SEVEN YEARS*. Abubuwa da yawa sun faru dasu cikin wad'annan shekaru masu dad'i da marassa dad'i, Ayman ya gama karatun shi tuni har ya soma aiki, kuma har lokacin shagon surayyah yana nan saima ci gaba da ake ta k'ara samu, don tuni sun daina zama shida haidar sai wasu amintattun yaran ta samu ta zuba a ciki suke ci gaba da kular mata da kasuwancin. Ayman ya Zama cikakken matashi magidanci, ya k'ara kyau ya dad'a haske, gentle dashi ga nutsuwa ga haiba ga kamala da kyakkyawar zuciya mai iya zama da kowa lafiya. Zuwa lokacin soyayyah mai k'arfi ta k'ullu tsakanin Ayman da nuriyyah y'ar sameera k'awar surayyah, bisa jagorancin iyayen su da Suka k'ulla zumuncin tun basu Kai haka ba, sosai Ayman yake son Nur haka itama, soyayyah sukeyi tsabtattacciya wanda suke fatan ta kaisu bisa turbar aure, nuriyyah fara ce sol kyakkyawa ba laifi, tana da matsakaicin jiki da tsayi dai dai nata, tana da nutsuwa da hankali ga kunya da yakana, duk wasu qualities da ake son mace ta gari ta had'a Nur ta had'a sai son barka. (Bayan haidar da k'anwar shi Khadija da tuni tayi aure shekaru uku da suka gabata, shekaru biyar tazarar tsarin iyali kafun sameera ta k'ara haifar shaheeda wadda daga itane sai Nur bayan wasu shekarun kuma ta haifi auta heedaya) Ta b'angaren rayuwar Ayman kuma har gobe bashi da kamar auntie don ita kad'aice yake iya fad'awa abinda yake cikin ranshi ba b'oye b'oye, bashi da abokai hargitsae sai abokan karatu da aka sake had'uwa cikin aiki, sai raihanatu data kasance wata kwallin mutum guda tal da yake iya hira da ita as his best and closed friend. Itama ta zama budurwa saboda mak'erin y'an matanci tuni ya gama k'erata da a k'alla shekaru goma sha tara zuwa ashirin a lokacin, ita ba fara bace kuma ba za'a kira ta bak'a ba, kalar skin d'inta irin chocolate me haske, ba zaka kirata kyakkyawa k'arshe a fuska ba, haka ba zaka tab'a had'a ko kiranta da mummuna ba, tana da dirin jiki irin na cikakkun mata,doguwace ma'abociyar nutsuwa da kamala, ba mai surutu ba haka bata kasance shiru shiru ba, Soo cool, classy and gentle tana da wadataccen ilimin arabiyyah ana fafutukar neman na boko, ta gama secondary school tuni har mahaifinta ya Samar mata nursing school da ta ke garin bichi a lokacin saura watanni k'alilan ma ta kammala, abinda ya haddasa ja bayar alak'ar ta da Ayman kad'an, madadin da da take gida a kullum yammaci saiya zo gidan iya ya kirata a waya ta shiga sunyi hira, sai ya zamana yanzu sai dai suyi iya waya a kullum safiyar Allah ba fashi kafun ya futa aiki, sannan weekend yana ajiye duk uzurin shi yaje ya ganta, kuma ba zai tafi haka nan ba saida lifidi lifidin hidimomi har kunyar shi raihana take ji, da yawa daga friends d'inta na karatu da suka Santa da Ayman suna tunanin soyayyah suke yi tana b'oyewa ne kurum. A tsayin rayuwar da Ayman yayi tare da raihanatu ya fahimci akwai wani b'oyayyen al'amari mai girma da yake bibiyar rayuwarta, amma saboda zurfin ciki bata tab'a yarda duk yadda suke ta fad'a mishi wani abu ba, duk da yana yawan ganin ta cikin damuwa wasu lokutan ma har tayi kuka a gaban shi, amma ba zata tab'a fad'a mishi kanzil ba sai rok'on ya sakata a addu'o'in shi, kuma baya tab'a mantawa da ita kamar yadda baya mantawa da shak'ik'an shi irin su Auntie, iya, malam, nuriyyah da khaleefa. Alak'ar Ayman da nuriyyah kuwa ta zarce dukkan tunanin mai karatu, sonta yake irin sonda baya iya b'oyewa a gaban kowa, a yini idan baiji muryar taba yakan iya riskar kanshi cikin damuwa mai yawa har yaji shi kamar bashi da lafiya. Haka idan bata da lafiya ya dinga jin kamar ciwon a jikin shi yake kenan har sai ta warke. _Wannan kenan_ @@@@@@ Ta b'angaren khaleefa kuwa rayuwarshi yake single, ya had'a degree d'inshi na farko dana biyu wato masters degree yanzu haka yana wani course ne da zai d'auke shi shekaru biyu kafun ya kammala. khaleefa wani irin bahagon mutum ne, murd'ad'd'e da hali mai wuyar fahimta, sai kayi iya rayuwa tare dashi bakasan inda yasa gaba ba. A kamanni sak kamannin shi da Ayman babu wani banbanci har sumar kai da saje, abu biyu khaleefa yafi Ayman, murd'ad'd'en k'irar jiki irinta ma'abota k'arfi, sai dogon hanci da hasken fatar daya samu ta sanadiyyar zaman wata k'asa ma'abociya lumana da kwanciyar hankali. Y'an mata course mate d'inshi da yawa suna tsoron shi da shakkar shiga shirgin shi saboda sunayi mishi kallon juyayyen mutum mai girman kai, mara mutumci, yayinda a gefe guda wasu da yawa suka mato a kan sonshi da begen shi, abu na uku daya sake banbanta khaleefa da Ayman shine halayyar su, Ayman yana da faram faram da sakin fuska ga kowa, khaleefa kuma bashi dashi, saurin fahimta da sauk'ak'k'en ra'ayin gami da hak'uri a kan komai na rayuwa ga Ayman sab'anin haka ga khaleefa. Wannan tarin abubuwa sune kad'ai zasu banbanta maka wad'annan zaratan matasa idan aka had'e maka su guri guda, shima fa bisa lura da nazari na musamman. Shi khaleefa ko a apartment tunda yaje bai tab'a yarda yayi sabo da kowa ba in aka d'auke Ahmad wanda yake jin hirar shi har yaga murmushin shi, Babu yadda matasa basu so janshi cikin wani gang da sukayi creating na shan shayi da yin dinner tare ba amma furr yak'i, Ahmad ma daya fara zuwa da hikima ya janye shi ta hanyar nuna mishi kuskuren cakud'uwar maza da mata har a addininan ce ma da sunan wani abota, shiyasa shi bashi da wata k'awa mace a cewar shi babu inda mace da namiji akace su dinga cud'anya, a addini ba wani abota Allah ya raba tunda basu zo a jinsi d'aya ba. Kamar yadda kowanne d'an Adam yake da buri da zab'in irin matar da yake so haka khaleefa ma ba'a barshi a baya ba kasancewar shi d'an Adam mai lafiya da numfashi, ya tsara yadda Angel d'inshi zata kasance tun kafun ya kai haka, da farko dai khaleefa yana son mace fara, y'ar siririya ba me k'iba ba, sannan ta zama ma'abociyar kwalliya da k'amshi, ta zama wayayyiya no d'aya kuma me aji. Wannan lissafi yana ajiye a zuciyar khaleefa tun kafun shekarun shi sukai haka, kuma har yanzu daya mallaki hankalin kanshi bai sauya ba. Ranar wata litinin bayan ya dawo school yana zaune a harabar k'ofar d'akin shi, sanye da shirt da dogon crazy trouser, ya kife kanshi da hular sak'a kunnen shi kare da waya, sosai yayi kyau komai nashi gentle and cool, dariya yake yi yana sauraron yadda Ayman yake ta zuba mishi shagwob'ar ya daure inya samu hutu yazo musu gida, tunda shi Allah bai nufi zai je Germany ba. "Ai man sai hak'uri kawai don ni yanzu bazan sake samun hutu ba daga nan har mu kammala, kasan yadda kan mu ya d'au zafi cikin kwanakin nan ma kuwa?". Ta d'aya b'angaren sake had'e rai Ayman yayi (a lokacin yana kwance saman doguwar kujera hannun shi dafe da kanshi, baya jin dad'i wani irin ciwon kaine yake damun shi kwana biyun nan, amma bai yarda d'an uwan yaji ba saboda zai shiga damuwa sosai). "Toh shikenan khaleefa inayi maka fatan sa'a". Khaleefa yana murmushi yace, "no one like you bloody". Daga haka sukayi sallama suka ajiye wayar dukan su. Ci gaba da tsayuwa yayi a gurin yana gaisawa da student maza da suke mak'otaka dashi a gidan suna giftawa jefi jefi. A gajiye ta shigo gidan, daga yadda take yarfa hannu da d'aga k'afafu na gane hakan, sanye take da riga da skirt na material pink ta yane kanta da k'aramin gyale match da takalmin k'afarta, tana goye da jibgegiyar jakar makaranta, hannunta kuma rik'e da wayar ta da LC. Fara ce tass kyakkyawa irin kyawun da kallo d'aya zaka iya ganin shi a tare da mamallakin farar fata. Idonta ne ya fad'a karaf cikin na khaleefa ba tare da zato bare tsammani ba, wannan shine kusan karo na uku da take ganin shi a gurin sai dai shi bai tab'a lura da ita ba har sun had'a idanu ba sai yau, hasalima a wancen lokacin har ta huce baisan da wucewar ta ba, ci gaba da takawa tayi har ta Isa apartment d'inta da yake kusa kusa da na khaleefa. Khaleefa binta yayi da kallo har ta bud'e ta shiga sannan ya sauke ajiyar zuciya, karo na farko a tarihin rayuwarshi da wani abu ya tab'a faruwa dashi makamancin wannan, hasalima shi duk kyawun mace kallo d'aya ne yake raba su. Komawa d'akin shi yayi shima ya rufo yana sake ganin hoton fuskar yarinyar data gifta shi a lokacin. Wasa wasa sai ga wani abu mai girma yana shirin riskar shi, abinda bai tab'a jiba a kan wata d'iya mace, k'arashen yinin ranar kasa tab'uka komai yayi har abinci bai iya ci da dare ba, domin samun nutsuwa dole ya kulle d'akin shi ya tafi gurin Ahmad, sun raba dare suna hira amma duk da haka baya cikin hayyacinshi, har Ahmad d'in yaso ranfo akwai damuwa a tattare dashi, amma ya fuske. Kwana biyu a tsakani khaleefa sam baya cikin walwalarshi, burin shi kawai ya sake ganin koda giftawar yarinyar nan ne amma sama da k'asa bat tayi b'atan dabo ba ita ba alamunta, bai kasance mutum mai sa ido ba amma a y'an kwanakin nan har abinda yafi k'urilla ya koya, haka zai tsaya yana kallon hucewar kowanne d'alibi a harabar d'akin shi duk da sunan nemanta. Sannu a hankali sai ga khaleefa yana neman had'a sati guda ba ita bare labarinta, har ya soma tunanin ko aljana ce tazo donta sashi a wahala ta bud'e mishi idanu. Yau ma tun safe da Suka shiga lectures basu futo ba sai da rana ta take, ko break baiyi ba ga gajiya da take nukurkusar shi, yana ganin idan har sukace sai sun koma gida sunyi girki shida Ahmad zasu ci wani abu to lallai kafun lokacin shi ya jigata, bisa shawarar shi suka nufi wani k'aramin gidan cin abinci dake daura da makarantar su. "ki rabu dashi kawai Amna ni sam bazan iya d'aukar tension d'in shiba, daga wancen sai wannan ni na gaji soyayyah aiba hauka bane mtsss!". "Kada ki zama butulu saleeema ra'ees yayi miki k'ok'ari dai dai gwargwado, kada kuskuren shi d'aya yasa ki zab'i wofantar dashi ki manta duk wad'an can tarin alkhairan nashi, ki daiyi tunani Allah". "Hum kinga ni tashi mu tafi na gaji da jin magana guda". Wannan hirar wasu y'an mata ne da suke zaune gaban table d'insu khaleefa, duk hirar nan akan kunnen sune sai dai basu ji abun ko kad'an a ransu ba, kamar ance da khaleefa d'ago sai kuwa idanun shi suka fad'a cikin nata karaf, take wani reaction yayi aiki na a k'alla dak'ik'a biyar kafun kowa ya basar ta hanyar d'auke kanshi, har suka futa bai sake d'agowa ba sai dai yaji ranshi fess kamar an yaye mishi duk wata damuwar shi. A k'alla dai yaga tana k'asar kuma ba aljana bace. @@@@@@@ _Nigeria_ Sassanyan yammacin damuna ne, iskar hadari na kad'awa kad'an kad'an tana busar da ganyayyakin bishiyar da suke zaune k'asan ta. Raihanatu ce sanye cikin riga da wando na Pakistan ta yane kanta da gyalen kayan, ba'a ganin fuskarta saboda kanta yana durk'ushe kan gwiwarta, Ayman na zaune gefenta ya zuba mata ido yana nazarin maganar data fad'a mishi har cikin ranshi, so yake ya rarrasheta ta daina wannan kukan amma baisan ko ta ya ba, ya yarda k'addarar ta mai girma ce duk da bata bud'e baki har yanzu tace dashi komai ba. Numfashi yaja mai tsayi sannan ya soma magana cikin kulawa, "kiyi hak'uri raihanatu a kullum rayuwar kowanne d'an Adam tafe take da kalubane iri iri, da k'addarori masu rik'e da akalar kowacce nassara, Ina ji a jikina duk wannan abun da yake faruwa dake wata rana sai labari kuma kina gab da futa daga cikin wannan tsattsauran yanayin, hak'ik'a Allah yana tare dake". Share hawayenta tayi da tafukan hannayenta, ta k'ak'alo murmushi ta d'ora saman fuskarta, mik'ewa tayi cikin sanyin muryar da taci kuka tace, "muje na taka maka yaa Ayman kaga hadari a garin ga kuma yanayin da muke ciki ba zanso kayi tafiyar dare ba". Mik'ewa yayi ya tsaya kurum hannun shi zube cikin aljihun shi yace, "har yanzu kink'i amincewa dani a matsayin d'an uwa kuma amini raihanatu, shiyasa kika kasa amincewa dani har naji damuwarki, koda yake ba komai lokaci, muje ki taka mun". Sannu sannu suka dinga tafiya har suka k'arasa inda motar shi ke fake, kamar kullum yauma tsaraba yayo mata me yawa ta abun buk'ata na daga abinci da sauran kayan amfani na yau da kullum. "Don Allah ya Ayman ka daina hidimar nan haka,na last week ma daka kawo har yau bai k'are ba....". Da sauri ya d'aga mata hannu nan da nan yanayin fuskarshi ya sauya yace, "ba ruwanki tunda ai bake kika sakani ba, and I don't want to hear any complain, har yanzu baki San muhimmancin abokin kwarae mai irin halayen kiba, sa'a tace dana same ki as mie closed friend raihanatu". Dole ba don taso ba taja bakinta ta kulle har godiya yak'i saurara, tana ji tana gani ya shiga mota yayi reverse ya bar gurin yana hangen ta ta side mirror ya d'aga mata hannu, itama d'aga mishi tayi. "Allah sarki Ya Ayman Allah ya saka maka da mafificin alkhairy". Raihana ta fad'a tana share hawayenta da gefen gyalenta. Wacece raihanatu salees abdallah ne?? _barkan mu da daren Jumu'at babbar rana, fatan Allah ya had'a mu da dukkan alkhairan dake cikinta ameen_ _Comment and share_ 24/03/23, 1:59 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lawal and doctor Ferhyeez m usman/ as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page five5️⃣ Raihanatu y'a ce ga ruqayyatu lameer da salees abdallah, dukkannin su haifaffun anguwar yakasai ne anguwa d'aya tsiran su layi biyu, salees ya had'u da ruqayyah ne a hanyar shi ta dawowa daga kasuwa da wani yammaci, ita kuma ta dawo daga makaranta, kamar da wasa soyayyah mai k'arfi ta k'ullu tsakanin su wadda itace har ta kaisu ga aure. Ruqayyah taso fara aiki bayan karb'ar kwalinta na diploma bayan aurenta da wata biyu, sai dai sam salees ya nuna bai amince ba, idan har zata dinga futa kullum toh waye zai kula musu da tarbiyyar yaran da zasu haifa nan gaba, dole ta hak'ura tunda dama bata nemi komai ta rasa ba, salees matashi ne hazik'i mai k'ok'arin neman na kanshi a koda yaushe, kuma mutum ne mai d'aukar ragama, tun kafun yayi aure ya saba da hidin dimun gida, shiyasa ko bayan auren sa, d'aukar dukkan nauyin matar shi da gidan su bai gagare shiba duk da kasancewar shi mai k'aramin k'arfi. salees tun kafun ya fara zuwa kasuwa ya had'a degree d'inshi na farko amma kasancewar aiki ya zama abinda ya Zama a k'asar mu sai bai tsaya jiran aiki ba ya fara harkar kasuwancin shi a kasuwar kantin kwari, inda yake saida atamfofi da materials yana samun rufin asirin, shi ya gina gidan shi k'arami a sharad'a inda aka Kai ruqayyah da farko. A farkon aurensu ruqayyah Sam bata samu matsala da dangin miji ba, amma tafiya tana dad'a nisa matsaloli na b'arkowa ta hanyar k'ulle k'ullen makircin salaha matar yayanshi abubakar, su uku kacal mahaifiyar su ta haifa a duniya, amma kishiyarta nada y'ay'a ba laifi. A d'akin su daga Abubakar sai salees, sannan ta ukun su mace mai suna ziyada. Da bala'i da maseefa Inna mahaifiyar salees ta rabo su da anguwar sharad'a Suka dawo kusa da gidan yayan shi suke zaune opposite, a cewarta wai ruqayyah ta jashi wata duniya mai nisa donta raba zumunci, wayyoh Allah ai tunda suka dawo ruqayyah bata huta ba daga wannan maseefa sai wannan sharri, zaman lafiya dai yayi qaura sai zaman hak'uri da shiga d'aka Kai kuka, amma duk da haka ruqayyah tana iya k'ok'arin ta wajen ganin ta kyautata musu ba tare da la'akari da abubuwan da suke mata ba, ta fara haihuwar yaranta, raihanatu ce babbah sai Salma tana binta irin tazarar kwanikar nan, sannan khausar wadda itama tazarar ta da Salma irin ta raihana da Salma ne, daga nan ta jima bata haihu ba kafun ta haifo d'anta namiji mai suna al'ameen, da muhibba nabi masa sai auta jidderh. Su shida kenan ta haifa cip a duniya. Toh Raihanatu itace ta kwashe tsanar da ake yima uwarta tsab saboda itace ta fari kuma a yaran kusan ita tafi d'aukar yanayin ruqayyah hatta da jiki da kuma yanayin magana da tafiyar su iri d'aya ce, abu na biyu daya k'ara zafafa gabar su shine yadda mutane suke son yarinyar wato ta taso da farin jinin mutane, Sam ita ba'a son nata haka, kuma ba komai yasa haka ba sai rashin tarbiyyar yaran nata. Toh haka sukaita wannan rayuwa cikin takura da maseefar umma salaha, abun har yakai yaran suma sun shiga ciki tsakanin su da yaran gidan sai hantara da kyara tamkar basu had'a komai ba, ta b'angaren ci gaban rayuwa kuwa salees mahaifin raihana kullum k'ara ci gaba yake yi, yanzun haka ya k'ara gyara gidan da suke ciki ya zama ginin tsakiya na zamani. Babban parlour (main parlour kenan) me d'auke da bedrooms uku kowanne da bathroom a ciki. Ya sauyawa ruqayyah kujeru na zamani da kayan gado masu kyau, komai dai ya wadata kamar gidan amaryar da za'a kai yau ko gobe. Da farko har Gen ya sauya babbah, kafun daga baya yayi wearing solar, ya siya motar hawa mai kyau duk a shekarar, ya kuma tafi umrah tare da matarshi da mahaifiyar shi da kuma yayan shi, da suke matuk'ar girmama juna da zama lafiya. Nan fa abu ya sake cin tura a gurin salaha, hassadarta da bak'in ciki muraran take nuna su. Duk da irin taimakon da salees yake musu kama daga abinci da suttura hadda solar suma yasa musu. Tuntuni umma salaha taci mugun alwashi akan raihanatu da tafi tsole musu ido duk cikin yaran ruqayyah, sai dai bata samu isar da mummunar k'udurinta ba har saida wata rigima ta had'a suda ruqayyah (ummiey) a wani lokaci da hak'urin ta ya gaza, ta kasa jurewa cin kashin data zo yi mata har gida, a nan fa ita kuma ta samu damar futar da abinda yake cikin ranta, umma salaha taci alwashin indai tana numfashi sai taga uban da ya isa ya auri, ta rantse raihanatu bata da miji a duniya indai tana numfashi, (kuji sab'o fa🤔) wannan maganar ta dad'e a ran salaha kuma bata samu damar furtawa ba sai a lokacin, wannan case da tension da yake bin rayuwar raihanatu da mahaifiyar ta shiya haddasa har yau take rayuwa cikin k'unci, ba dama ayi sabga a familyn dangin ubanta in bata jeba magana, in taje kuma habaici da fad'ar magana, a tsaka mai wuyar da take rayuwa kenan, ga gori da cin mutumcin innah in ta tashi yi take tamkar ba jinin tace ita d'in ba, a yanzu haka anyiwa da yawa daga y'an matan family aure (da yake su ana gama secondary suke aurar da yaransu, babu wadda ta tab'a darawa higher institution sai raihanatu da har yanzu aure yak'i yiwuwa) Sau biyar ana sa ranar aurenta ana fasawa, shiyasa malam salees mahaifinta yaga gara ta tafi makarantar a kan zaman jiran tsammanin warabukka. An yiwa Salma k'anwarta aure yanzu harta haihu ma, khausar ma anyi engaged nan da 2 months za'a yi biki, da farko akwai wani guy da yake son raihanatu ilyas har yayi magana manya sun shiga, da za'a had'a bikin nata ne dana khausar d'in, to shima tana nan makaranta ya fasa suka karb'i dukiyar aurensu, ummien su ta kirata take kwantar mata da hankali kafun ta shaida mata suma sun fasa, bata bata labarin tijarar da Inna tazo tayi ba Cox bata son sake d'aga mata hankali, amma daga yanayin yadda muryar ummien take a sanyaye ta fahimci Inna taji labari tazo tayi tijarar data saba kenan. Tashin hankali da kukan daya taso mata shiya haddasa ta futo daga hostel d'insu tayi bayan gari ta samu kan dutsen da takan zauna a duk lokacin da Ayman ya kawo mata ziyarar k'arshen mako, don b'oyewa su raheela k'awayen hostel d'inta komai, Sai dai luckly tayi gudun gara ta fad'a gidan.... Tana Zama ba jimawa Ayman ya kawo mata ziyarar duk k'arshen mako, ya risketa a haka. Sai ya zamana sun raba damuwar tare, haka ya zauna ya shiga kwantar mata da hankali, duk da bata yarda tace mishi komai ba. Raihanatu ba wai ta d'auki son duniya ta d'ora a kan duk samarin da take yi bane, a'a tashin hankalinta na kasa fahimtar k'addarar da take bibiyar rayuwarta ne, bata San ya zatayi da dangin mahaifinta ba idan ta koma gida hutu, bata manta yadda sukayi da hajiya innah last akan wannan saurayin ba, "takanas dama nazo gurinki y'ar iya gadon bak'in hali da mugun abu, naji ance wani ya kawo kud'in auren ki za'a had'a ayi bikin ki dana khausar, toh saura shima ki kore shi da bak'in jinin ki da mugun abu, don a wannan karon idan har ya fasa auren ki k'auye zanje can garin su baban ku na nemo wani k'aton da yak'i aure in had'a ku kije can dama k'auyen shi yafi dacewa dake, mai bak'in mugun abu, ai wallahi yarinya kin had'u da wulak'anci tunda kika gado mugun halin uwarki tass ga tanan tana jina kamar wata ta Allah". K'asa tayi da kanta tare da kife kan jikin gadon da take kwance had'e da dafe kanta da hannuwanta biyu, "wayyoh Allah ummie na wai me yasa hakan yake ta faruwa da ne? Shin me na rasa da duk wanda yazo zai aureni yake guduna? why! why!! whyyyy!!!". Sai ta k'ara fashewa da kuka mai ban tausayi, "Ashe ya fasa aurena shiyasa tun safe nayita kiranshi baya d'agawa" ta k'ara fad'a cikin damuwa da muryar kuka...... Ringing d'in wayar tane ya dawo da ita hayyacinta, ta mik'e zaune tana duba k'awayenta na d'akin d'aya bayan d'aya, Allah ya taimake ta duk bacci sukeyi data tonawa kanta asiri. Agogo ta fara dubawa, 1:30 am. Wayar ta d'aga ganin Ayman ne yake kiranta cikin wannan uban dare, abinda bai fiya faruwa ba sai da kwakkwaran dalili. "Hello raihanatu" shiru tayi mishi, "kina jina ko raihana nasan ba bacci kike yi ba" Gyaran murya tayi cikin son b'oye damuwarta tace, "yaya Ayman ya kaje gida?". "Lafiya ba lafiya ba raihana gani a gida amma har yanzu na kasa samun nutsuwa, hankalina yak'i kwanciya, sai tunani nake akan halin dana barki, don Allah raihana ki k'ara hak'uri bayan na dawo banje gida ba saida na tsaya gurin iya, ita take bani labarin abinda ya faru wanda in zaki mutu ba zaki tab'a bud'e baki ki fad'a ba, anan na fahimci duk abinda ya haddasa miki shiga wannan yanayin, tabbas ko waye dole ya shiga irin halin da kika shiga ace ana kawo kud'in auren ka ana karb'a har sau biyar! Ya Allah!" Numfashi ya ja mai tsayi taci gaba da fad'in, "sai dai kanshi ya yiwa raihanatu, asarar shine daya bari nagartacciyar mace kamar ki ta subuce mishi, kiyi hak'uri insha Allah mijin ki yana tafe nan bada jimawa ba, dama wad'an can duk cikin su babu mijinki shiyasa.... I'm sorry please raihana". Share hawayenta tayi da tafin hannunta cikin cool voice tace, "na gode da kulawa yaya Ayman insha Allah zan ajiye komai a gefe na fuskanci karatuna, ni dama komai ya fuce a raina tuni". Cikin jin dad'i yace, "Yauwa ko ke fa raihanatu, ki kalli kanki a mirror gobe from up to toe, zaki fahimci irin baiwar da Allah yayi miki wadda ba duk mata ba, kuma saboda su ba mijin ki bane shiyasa suka kasa fahimta har suke iya barin ki, baki rasa komai ba raihana hasalima irin ki a cikin mata k'alilan ne" Murmushi tayi tare da rufe fuskarta kamar yana gabanta tace, "Kae Yaya Ayman Kai dai kake ganin haka tunda muna tare". "Koda wasa dear ni kinsan a har kullum Ina fad'ar abinda yake gaskiya ne, yanzu dai ya kamata ki huta nima tunda naji muryarki komai dai dai zanyi sallah raka'a biyu sai na kwanta" "Au zakayi sallar amma ni kace mun na kwanta? Toh nima sai nayi sallar kuwa zan kwanta". Y'ar dariya yayi yace, "toh ai komai saida nutsuwa ake yinshi, ke a halin yanzu kina buk'atar kiyi bacci kwakwalwarki ta samu nutsuwa sannan ko". "A'a fa kaga ma ni sai anjima dama wannan kira cikin dare kamar wani korarre". Raihana ta k'arasa fad'a k'asa k'asa. "Iyyeh wato kin dawo dai dai har zaki fara ko? Toh shikenan ai zamu had'u ne Zan rama tuwo kika ci......" Hararar wayar tayi tace, "Ina zaka ganni ma? Hun un ai kafun mu had'u ma nasan ka manta". Dariya yayi yace, "toh shikenan zamu gani, dear sai anjima lokaci yana tafiya". "Okay byee have a nice day". "Aha". Daga haka sukayi sallama, alwala ta d'auro tayi nafula raka'a biyu tayi addu'o'inta ta kwanta. Shima Ayman dama akan sallayar yake raka'a hud'u ya k'ara kawowa yayi addu'o'in shi yasa pillow a kan sallayar ma nan k'asa ya kwanta. _Toh sai muce Sweet dreams besties_. *Germany* Tun daga ranar da khaleefa ya ganta a restaurant bai k'ara sake rasa ta ba, yanzu wani lokacin ma tare suke shigowa gidan ko ya riga ta da mintuna, har yanzu basa yin magana amma sukan yiwa juna murmushi. Yau khaleefa tun daya tashi baya jin dad'in jikinshi, hakan ya hana mishi futa ko ina yana kwance a gida, saida yamma ne da yayi sallah ya lallab'a ya futo ya zauna kan barendar gaban d'akin shi yana duba magazine. "Assalam" akayi mishi sallama da siririyar murya. D'ago kanshi yayi ya kalleta, itace dai tsaye gabanshi sanye da farar doguwar riga tayi rolling kanta da k'aramin gyale. Sai ya ajiye jaridar hannun shi yace, "Assalamu alaikum ko hajiya ba wai assalam ba, as a Muslim ya kamata ki gyara". Murmushi tayi mishi cikin sakin fuska tace, "ayi hak'uri toh assalamu alaikum". Shima fuskar shi da Murmushin yace, "waalaikissalam better ai ko". "Uhm gaskiya ne nagode, am dama wani taimako nake nema a gurin ka, mukullin d'akina ne yak'i bud'ewa ko kuma nice na kasa ka taimaka mun dai don Allah". Mik'ewa yayi yabi bayanta har suka isa wajen k'ofar, sai dai yana sawa ya bud'e, "ohh kaga abun mamaki tun d'azu nake wahala yak'i yi amma kai kana gwadawa". Murmushi kawai yayi yanzun ma, ta karb'i keyn ta a hannunshi tace, "nagode sosae". Har ya juya zai tafi tace baka fad'a mun sunan kaba, a nutse ya juyo ya kalleta, "abdallah Suraj Abdallah amma zaki iya kirana da (khaleefa)". "Woww nice name, Ni kuma sameera sulaiman, nice to meet you Mr Abdallah". "Nice to meet you too" ya fad'a yana mamakin sauk'in kanta, tuntuni yake son mata magana amma baisan ko ta yaya ba, a fuska she look Soo classy shiyasa yake tsoron mata magana. Ita ma ta b'angaren ta tunanin da take yi kenan, he's wise ga kirki kuma ba girman kai, tana mamakin kanta da shiga hurumin shi ko Ina jin kanta da aji? Itace fa mace guda da kusan kowanne namiji keda burin k'ulla alaka da ita amma duk basuyi mata ba, da gayya take gwara kan maza, Sam bata d'auka za'a samu namijin da zai sauke mata duk wannan ajin a kusa ba. Da sannu da sannu tafiyar khaleefa da Saleema ta fara zurfi har ta kaiga ya samu damar amayar mata da abinda yake ranta da wani yammaci, babu musu ta amince da soyayyar shi don dama yayi mata dai dai da ra'ayin ta. ************ Tsaye take gaban k'awarta Amna da take ta mata fad'a kan amincewa da soyayyar khaleefa bayan ga ra'ees nan yana ta bin kanta tak'i sauraron shi....." Da sauri Saleema ta katse mata hanzari ta hanyar d'aga mata hannu, "kinga Amna ni dana san abinda zaki fad'a kenan duk da bazan fara ma baki labari ba, kinsan waye Abdallah khaleefa kuwa? Ya zarce tunanin ki Amna he's unique gashi very talent and intelligent ke ya zarce duk yadda kike zato, toh inba ganganci da wauta ba taya zan samu handsome guy kamar shi in wani tsaya kula ra'ees, toh bari in fad'a miki abinda baki sani ba ni ra'ees bai gama fucewa daga raina bama saida na had'u da Abdallah, na raina kaina, na raina ajina dana k'are da kula wani wai ra'ees". Cike da d'unbin mamaki Amna take kallonta kafun tace, "kina cikin hankalin ki kuwa Anya". Wani mugun harara ta balla mata, "zaki iya futa Amna banyi miki dole ki zauna dani ba, in ma hauka nake ina da wanda zai iya d'auka a yanzu, Soo babu laifi don kin kirani mahaukaciya". Cikin hasala yanzu Amna ta mik'e tace, "Ni kike kora yau Saleema akan wani d'a namiji". Saleema ta mata wani irin kallon raini tace, "Ko baki ji bane saina maimaita miki amna nace ki futa!!!". Amna bata sake ce mata komai ba ta d'auki Jakarta ta fuce. Tana futa Saleema ta kulle d'akinta tana jan tsaki, wayarta ta d'auko ta dannawa no khaleefa kira, bai d'aga ba ya katse ya kirata. "hello hubbie yau gaba d'aya ka manta dani". Saleema ce meyin wannan maganar cikin shagwob'a. I'm sorry please kaina ne ya d'au zafi yanzun nan na shigo gidan ma". "Ayyah ama sorrie hubbie yanzun kaci abinci ka huta anjima sai muyi magana" "Nopp ba magana zamuyi ba Ina son mu had'u, kwana biyu nayi kewar kallon wannan kyakkyawar fuskar taki" "Ayyah kasan nima nayi kewarka toh amma naga ai muna yin video call fa!!!". "Video calk kad'ai bai wadatar ba Ina son na ganki zahiri bata waya ba". Murmushi tayi mai k'ayatarwa hadda lumshe ido cikin salo tace, "okay yanzu dai kaci abinci plzz hubbie! see you later". "Thanks lovely see you too". Yana ajiye wayar ya soma cire takalmin k'afarshi, Ahmad da yake gefenshi yana danna waya yace, "yea! Saleema ce hala". Murmushi kawai ya mishi. "Alhamdulillah abokina fa hala an tsinci dami a kala, abun mamaki wai kaine da soyayyah dumu dumu khaleefa, har yanzu Ina mamaki Allah". "Hum meye abun mamaki Ahmad, daman can ban samu wadda tayi dai dai da ra'ayina bane". Dariya Ahmad yayi sosai yace, "kasan Allah kada ka zurfafa don soyayyah daka gani kamar gwari ne ko riba ko fad'uwa......" "Kaga! Kaga da Allah malam kuffa alaika haza..... kasan me bakin ka zai fad'a, kar ka soma had'a mun soyayyah ta da gwari, sannan ka daina yayatani, ga can su Mahmood sai damuna suke ba dama na bud'e wattsapp d'ina sai kaga jama'a sunyi mun caaaa haba Ina dalili soyayyah kamar kaina farau". Dafa kafad'ar shi Ahmad yayi yace, "kayi hak'uri abokina yadda kake so haka za'ayi, Allah ya huci zuciyarka soyayyar taka ce tazo da salo na daban". Bai kula shiba ya mik'e don Samar musu abinda zasu ci. ######## Kwanan Ayman biyar da zuwa gurin raihana k'anwarta Salma ta haifo d'anta namiji sankacece, dole ta tattara yanata yanata washe gari tayi sallama da y'an hostel d'insu tayo gida. Da iya ta soma cin karo a farkon layi ta futo k'ofar gida tana raba yara fad'a. Da fara'a sosai saman fuskarta ta k'arasa suka gaisa da iya, har iya na zolayarta, "kin tafi kin manta damu bulunbuk'ui amma daga jin kun samu baby shine kika wani tattaro kika taho da wata jakar kayan ki hargitsae hargitsae". Dariya raihana tayi tace, "koma dai me zakice iya yau bazan kula kiba, ki lallab'ani in shige miki gaba gurin sabon angon da kikayi ko kuma in ture fadar taki in aza ummaaa". "Kyaci gidan ku ja'ira zan had'u dake ne". Iya ta fad'a tana wullo mata dak'uwa da hannu, ita kuma ta huce gaba tana dariya. Ummie tana zaune kan k'aramar kujera tana d'auraye ragowar kwanukan dasu jidderh suka ci abinci, gidan shiru duk sun tafi islamiyyah. "A'a kece da yammacin nan kuma". Ta fad'a da mamaki tana kallon raihana. "Eh ummie sannu da gida bari na k'arasa miki aikin" kawai saita ajiye kayanta a gefe ta nad'e hannun riga da gyale ko kafun ummie tace wani abu har ta tsunbula hannunta cikin ruwan d'auraya. "Ki barshi kawai aina kusan gamawa ma, amma raihana wannan wane irin zuwa ne ba sanarwa? Kina ganin abbanku ya dawo ya ganki bazai yi fad'a ba?". Raihana tace, "A'a ummie ki barshi kawai na k'arasa ni bazan iya zama Ina kallon ki kina aiki ba, Abba kuma na fad'a mishi a waya kafun na taho". Dole ba don ummie taso ba ta kyaleta suka k'arasa aikin tare, raihanatu ta sharce gurin sannan Suka k'arasa cikin parlour. Kamar yadda na fad'a a baya Mahaifin raihana ba mai kud'i bane amma yana da rufin asiri, sannan ya tsare musu komai kama daga abincin da zasu ci, har zuwa kan karatun su da suttura data zame musu kana. (Ban gama fasalta gidan suba d'azu, bayan parlor da d'akuna akwai wani babban d'aki a gefe na abban su sai sitting room, da harabar da yake ajiye motar shi da machin) Ruwa ta d'auko a fridge tana sha ummie tace mata, "Sai kika ji Salma ta haihu" Ajiye gorar ruwan tayi tace, "eh wallahi kuma fa jiya da rana ma Saida mukayi waya da ita, ashe ita a lokacin ma bata da lafiya tak'i fad'a mun". Ummie tace, "Ai kinsan halinta, balle ga abinda ya faru cikin satin ni kaina fa bata fad'a mun ba ita da mijin ta suka tafi asibiti saida ta haihu ya kirani yake fad'a mun, nace aiba ni ya kamata ya kira ba sai su nemi uwarsu hajara". (Hajara yayar ummie ce, itace ta biyu a gidan su daga babbar yarsu Aisha sai ita sannan ummie da k'anin ta Isma'eel da yuseep sannan saratu da autar su hapsat, duk ummansu ta aurar dasu sai jikoki da suke lek'o ta, marayu ne mahaifin su ya rasu tun da dad'ewa suma.) "Ummie kina nufin baki je kinga baby ba har yanzu?" "Toh yaushe ma ta haihun da zaki ce wani har yanzu banje ba, kuma yanzu ke tunda kinzo ai sai kije a madadina". Dariya raihana tayi ganin ummie tana yi mata kallon wata mara hankali tace, "Allah ummie nasan ma ba zuwa bakiyi ba". "Kinga mu ajiye wannan maganar a gefe, sai kika ji gidansu ilyas sun karb'i kud'in auren d'an su suma ko?". Take yanayin ta ya sauya duk data shanye kaso talatin a ciki, "eh Abba ma ya kirani washe garin ranar da mukayi waya dake". "Raihana Ina fatan baki sa wani abu a ranki ba, dama tunda akayi haka nake ta damuwa nasan halinki, zaki iya zama kiyita wannan kukan na maseefa ki k'i ci ki k'i sha, duk ki damu kanki". Sunkuyar da kanta k'asa tayi tace, "banyi kukan ba ummie, ni komai ya huce ma a gurina har abada don na dad'e da deleting duka no's d'inshi a wayata ma". Ummie tana lura da yanayinta tace, "Naji dad'i da kika fahimci komai daughter dama kowanne d'an Adam da irin jarrabawar da Allah yake mishi, idan kayi hak'uri sai ya saka maka da abinda yafi alkhairy a rayuwa, Ina fatan wannan ya zamo na k'arshe a gareki, kullum Ina yi miki addu'a insha Allah ba zaki wulak'anta ba a rayuwa". Had'iye abunda ya tokare k'ahon zuciyarta tayi, tace, "insha Allah ummie ko bana kusa dake idan na tuna irin wad'annan kalaman da suke futowa daga bakin ki sai Inji kwarin gwiwa da sanyi a raina" Ummie tace, "Masha Allah fatan Allah yayi mana jagora, ki shiga kitchen ki zuba abinci kici in babanku ya dawo nasan zaki tafi gidan masu jego ko". Raihana tace, "Toh ummie amma ni ba yau zanje bama sai gobe" "Toh Allah ya kaimu". Raihana mik'ewa tayi taje ta zuba abincin ta dawo parlor, tana cin abinci suna hira da ummie har ta kammala, a haka su jidderh suka taso school, aikuwa da gudun su suka rungume ta suna mata oyoyo. Tsarabar chocolate da Ayman baya rabo da kai mata tayo musu, aikuwa sukaita tsallen murna suna godiya. Da yamma abbansu ya taso kasuwa, shima yaji dad'in ganinta sosai, sai da suka zauna cin abinci abban yake tambayarta yanzun data taho babu matsala?, ta fad'a mishi babu matsala attendance ne kuma akwai wata k'awarta zatayi mata. A daren ranar take shaidawa Ayman tana gari fa saboda Salma ta haihu, yace eh yaji a gurin iya, zai zo su gaisa kafun ya tafi office gobe. *********** _Da asuba_ Raihana tun data yi sallah bata koma bacci ba saida suka tsabtace gidan tsab ita da khausar suna aikin suna hira har suka kammala. Wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa d'inkin kuwa ya zauna das a jikinta, wayarta da take kashe ta kunna bayan ta duba lokaci, 7:00 am yaran gidan har lokacin bacci sukeyi, khausar tasa ta tashe su su shirya tafiya school. Ita kuma ta zauna tana yin abinda ta jima batayi ba wato kallo. Jinta take free cike da farin ciki da annashuwa, lallai tayi kewar gida don rayuwa a gida babu abinda ya kaita dad'i, tana nan zaune tana lazimi at the same time idonta a kan tivi wayarta tayi ring, as she expect Ayman ne, da sallama ta d'aga bayan ta kai volume d'in tivin k'arshe, "Ina fatan kin tashi lafiya ya kwanan babyn mu" "Lafiya qalou nake fatan kaima". Ehh to ni kaina zuwa yanzu ban sani ba amma gani k'ofar gidan ku Ina sauri zan huce aikine na kusa late". "Okay to minti biyu". Ajiye wayar tayi ta kasa kunne ko zataji motsin ummie, fahimtar da tayi bata tashi ba sai kawai ta fad'awa khausar zata futa su gaisa da Ayman koda ummie zata futo yanzu. Yana tsaye a k'ofar gidan jingine da motarshi ya hard'e duka hannunshi a k'irji. Tana futowa Abba abubakar shima yana futowa. Dam gaban raihana ya fad'i. _Comment and follow_ 24/03/23, 1:59 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyeart lerwerl* Page six 6️⃣ Raihanatu bata san dalili ba amma duk lokacin da zataga d'aya daga iyalan gidan ko masu gidan takan tsinci kanta cikin tashin hankali mara misali. Cikin ladab ta durk'usa k'asa tana gaishe shi, da sakakkiyar fuska ya amsa mata har yana tambayarta an samu hutu kenan, dama shi mutum ne simple kamar abbansu, matar shi da y'ay'an shi sune matsala, sai Inna da sauran yaran kishiyarta masu shiga shara ba shanu da kuma zuciyar hassada, ziyada ma bata shiga sam tana tsaka tsakiya haka yaranta, batace tana tare dasu ba kuma bata ce tana tare da hajiya Inna ba. Shima Ayman har k'asa ya durk'usa yana gaishe shi kamar yadda Raihana tayi. Kasancewar Ayman ba b'oyayyen shi bane sun gaisa har yana tambayar shi mahaifiyar shi mutuniyar kirki da akayi zaman mutumci da Amana. Bayan tafiyar shi, matsawa raihana tayi kusa dashi tana sakin mishi tattausan murmushi, "Ina kwana ya Ayman". Sai ya had'e rai "Da ban kwana zaki ganni, aini fushi nake da kema in baki sani ba....." "Fushi kuma Yaya Ayman? Toh me nayi kuma?". Sake had'e fuska yayi yace, "Ba sau d'aya ba na fad'a miki times without no cewa ki dena kamo hanyar garin nan cikin motar haya, amma kinsa k'afa kin shure saboda Sam baki d'auke ni yadda na d'auke kiba, meyasa raihana?" "K'asa tayi da kanta tana mamakin wannan k'arfin hali na Ayman, for what reason zata dame shi watak'ila ma yana wajen aiki lokacin da zata taho amma wai ta kira shi don neman magana da rigima, toh aikin zai baro yazo d'aukarta "ka gafarceni yaa Ayman insha Allah Zan kiyaye". Raihana ta fad'a carmly. Ayman yace, "Gud Allah yasa! Yanzu Yaushe zaki je ki gano mana babyn?". "Anjima kad'an" ta bashi amsa. "Kwana nawa zakiyi ki koma scul". "Umm nida sai bayan suna zan tafi ma". Zaro ido Ayman yayi yace, "karatun naki fa?, haba ina laifin idan kinga baby yau gobe da sassafe na mayar dake, in yaso ranar suna da safe again nayi alk'awari zanje na taho dake na mayar dake washe garin suna hakan ba yafi ba". B'ata face tayi tana juya yatsun hannunta, "kina son wasa da karatun ki raihanatu gashi kina mafi hadarin watanni, yanzu every slice mistake zasu iya jangwalar abinda zasu lalata miki duk wancen shekarun da kikayi", ganin tana sake had'e rai sai yace, "Amma fa kiyi hak'uri idan da damuwa a magana ta kiyi yadda kike so". Juyawa yayi ya d'auko wata leda a back seat na motarshi ya mik'a mata, "Auntie tace na kawo miki tun waccen ranar mantawa nayi". K'in karb'a tayi tana kallon shi tace "I'm sorry....". "Shhh! Is okay" Ya katse mata hanzari. Ganin ba zata karb'i ledar ba sai kawai ya ajiye mata kan k'afarta ya shige mota abinshi ya tafi. Jiki a sanyaye raihana ta d'au ledar ta shige gida, duk yaran gidan sun tashi har sun shirya cikin school uniform sai hayaniya suke yi kamar za'ayi dambe. Zama tayi k'asan carpet ta dubi khausar da take ta aikin ganin ta raba rigimar da ake yi tsakanin muhibba da al'ameen, "Ashe har yanzu yarannan suna wannan rigimar ta k'a'ida?". Y'ar dariya khausar tayi tace, "ai Auntie raihana Ina ganin sai abinda yayi gaba ma, yanzu ma kinga wai muhibba ce bata wanke socks d'inta ba ta d'auki na al'ameen tasa wai itace tata, shine ake ta rigima, ita muhibba tasan ba nata bane amma don neman rigima taki bayarwa, shi kuma ya kafe saita bashi saboda bashi da wanda zaisa ya tafi school kuma an yaje ba socks d'in duka za'ayi mishi". "Wannan shine abinda ya had'a fad'an?". Ta tambaye su su duka ukun. Matsowa muhibba tayi zata fara mata zayyana ta dakatar da ita. D'akin su ta shiga ta d'auko jakarta akwai farar safa sabuwa dal ta mik'awa al'ameen, "bar mata wancen kasa wannan kaji k'anina". Hadda dariyar shi ya karb'a yasa a k'afar yace, "wannan ma tafi wadda ta d'auke kyau Auntie Raihana". Raihana tace, "wannan shi ake kira da hak'uri mai cimma rabo". Khausar tace, "aikuwa". Kicin kicin muhibba tayi ko shayin ma tak'i sha sai faman hararar al'ameen take a sace har suka fuce. Gidan yayi tsit daga ita sai khausar da ta d'an jima da kammala waec d'inta tun satittikan da suka huce, hira sukeyi jifa jifa har Allah yasa ummie ta futo. Suka durk'usa suna gaisheta, ta amsa musu cikin so da kulawa. Kusan a tare suka nufi d'akin abbansu shima suka gaishe shi. Sun sake tab'a hira yanzun ma da ummie akan karatun ta da yadda komai yake tafiyar mata. Bayan abbansu ya futa, sai da hantsi ya d'aga sannan ta d'auki ATM card da hand bag wayar ta a ciki ta yima ummie da khausar sallama ta tafi gurin y'ar uwarta. A POS ta tsaya ta ciri y'an kud'ad'en ta da take saving a duk lokacin da abbanta ya turo mata da kud'in amfani taga bata buk'atar komai, da wanda Ayman ya d'orawa kanshi duk watan duniya wai ko wani abu zai taso mata ba sai ta fad'awa Abba ba. wani k'aramin store na kayan babie tayi burki, ta siyama baby tsala tsalan riguna kala biyu da saitin mayukan jarirai ta had'a da overall farare tass, har zata fuce wani k'aramin Teddy pink ya d'auki hankalinta, sai ta koma da baya tana duba kud'in jikinshi. Shigowar shi shagon kenan yayi tozali da ita tana duba jikin teddy, lokaci d'aya ta d'auki hankalin shi har yaji bazai iya hak'uri ya rasa wannan tsaleliyar budurwa ba. "Amincin Allah ya tabbata gareki y'an mata". Ya fad'a bayan ya k'arasa inda take tsaye Saida gaban ta ya fad'i taja tsaki can k'asan ranta, shiyasa ta tsani futa waje sam saboda maza da sun ganta basa iya kauda kai sai sun kula ta ko lura da d'aurewar fuskarta basa yi, "kiyi hak'uri idan na shiga rayuwarki amma don Allah ki bani no ki sai muyi magana". Sake d'auke kanta tayi tabar siyan teddyn ma tayi hanyar futa, bin bayanta yayi da sassarfa yana fad'in, "kinga! Am babie pleeze just one mint". Napep take k'ok'arin tarewa amma ya hana sai korar masu napep d'in yake, dole at last ta fusata har tayi mishi magana, "don Allah malam ka kama kanka". "Kamun kan ne ai bazai yiwu ba y'an Mata, na baro kan tun a cikin store inda na fara ganin ki". Duk yadda take cikin fushi saida maganar shi ta bata dariya, amma dai ta gintse gudun kada ta bada kanta yaga lagonta. "Yanzu dai no ki kad'ai nake son ki bani y'an mata, ko har yanzu baki aminta dani ba saina tsugunna nayi magiya a gabanki?". "Bani wayar in saka maka". Raihanatu ta fad'a ganin yana Shirin yin abinda bakin shi ya furta. Da hanzari ya bata phone in, ko a hannu data rik'e wayar tasan waya ce mai tsadar gaske, ita dai ta samu ta zuba mishi no ta mik'a mishi, k'in karb'a yayi yace, "kira muji". Da b'acin rai tace, "kana ganin zan saka maka wrong ne?". Nifa bance ba amma dai ki kira kalas na, danna kiran tayi ba tare da bin la'akari da wanne sim ba, sai kuwa ga wayar ta tana ring a jaka. Ya sauke ajiyar zuciya gami da yin hamdala ga Allah. "Meye sunan gimbiyar?". Ya tambayeta bayan ya karb'i wayar, "duk abinda kasa". "Woow an bani zab'i kenan, godiya mai yawa yanzu sauranki abu d'aya, kizo muje na sauke ki a gida don Allah" Wai anya mutumin nan yana da hankali kuwa? Ta tambayi kanta a zuciyarta. "Princess can we?". A zafafe tace, "what?". Kama kunnen shi yayi yace, "I'm sorry I mean let's go". Fuuu ta hucesa don tana ganin laifinta nema data tsaya magana dashi har wannan lokacin, shi kuma tunda yaga guri ba dole yayi yadda yaso ba. K'aramin gidane sama da k'asa mai d'auke da ginin safe content matattakalar ta sauko ta cikin parlour. Koda tayi knocking mijin ne yazo da kanshi ya bud'e, yana ganinta ya bata hanya ta huce yana mata sannu da zuwa, ta amsa mishi da yauwa. A parlon k'asa ta zauna ta ajiye ledar hannunta tana kallon komai na gidan tsaf tsaf, shima shigowa yayi bayan ya kulle k'ofar, nan suka gaisa har tayi mishi barka. Shiya turo mata Salma da take parlon shi suna breakfast a lokacin, da hanzarinta kuwa ta sauko tana kwala kiran "Auntiena, shiyasa nake ji dake saboda nasan duk kinfi sona" "Ki dai tafi a hankali wallahi inba so kike ki b'arowa kanki wani sabon ciwon ba, kiyi double double". Rungume ta tayi ko damuwa da maganar y'ar uwar batayi ba, "nayi kewarki auntie raihana". "Nima nayi kewarki sosai salmaty". Sake ta tayi tana tambayar, "Ina babyn nawa ma kika wani zo kika mak'ale ni god'ai god'ai dake kamar bake kika haihu shekaran jiya girma ya kama ba". "Tana gurin ummaa". Ta bata amsa, "toh Ina ummaan". Tana ciki watak'ila ma bacci tayi da kin ganta ta futo, huce Salma tayi ta shiga neman inda umman take, a d'aki na biyu kuwa ta sameta kwance kan katifa tana bacci yarinyar a gefenta, raihana d'auko babyn tayi kawai ta futo. Nan suka baje a parlour Salma na faman bata labarin irin wahalar da tasha wai saura k'iris ta mutu, yayinda ita take sauraronta cike da tausayawa ta kasa ajiye yarinyar sai juyata kawai take cike da so da k'auna. Lokaci d'aya taji son yarinyar ya shiga zuciyarta har tana jin kamar karta bawa uwarta ita. Kayan data siyowa babie ta mik'awa mamanta, tsabar mamakinta Salma sake baki tayi tana kallonta, "kin tuna mun jiya fa Yaya Ayman yazo yayi ma yuseep barka da dare baki ga uwar hidimar da yayi ba". Raihana cike da mamaki tace, "wane Ayman kuma?". "Ayman dai naki wanda kika sani y'an biyun Auntie ta iya". "Tab lallaima ya Ayman d'in nan toh wallahi ni bansan ma yazo ba kuma yau da safe mun had'u amma koda wasa bai fad'a mun ba". "Allah sarki bari kiga kayan ma". Sai tayi cikin d'akinta na k'asa ta futo da k'atuwar leda me d'auke da tambarin well care. Tsabar shock sai raihana ta kasa cewa komai sai kallon kayan cike da d'unbin mamaki. A haka yuseep ya sauko zai futa kasuwa cikin shiri, Salma ta nuna mishi kayan da raihana ta kawowa babie, yayi ta godiya yana yaba mata ita da take ta kanta shine hadda wata hidima haka kamar dole, raihana tana dariya tace, "dole ne mana, kyautar y'a guda fa Allah ya bani, kuma ni ban takura kaina ba naga Ina dashi ne inda bani dashi ai ba zanyi ba". "Gaskiya ne Auntie toh muna godiya Allah ya k'ara rufa asiri". Ita dai batace dashi komai ba har ya fuce. Hayaniyar hirar suce ta tashi ummaa daga nannauyan baccin data fara ta futo tana wara idonta da fad'in, "a'a wannan kuma daga Ina?". Daga k'auyen bagwai, raihana ta fad'a tana kallon ummaan, "a'a sai dai k'auyen bichi irin wannan hargitsae hargitsae ba'a dawowa haka in anje bagwai". Dariya raiha da Salma sukayi tana taya su, bayan ta zauna sun gaisa ta dubi raihanatu da kyau sannan ta fara maganar ta, "Anya kuwa raihanatu? Har yanzu ba zaki cire komai a ranki ki saki jikin ki da rayuwa ba, dubi fa yadda kika rame kamar ba ke ba". Shiru tayi ita dai batare da tace komai ba, a naseehance kakarta ummaa ta sake kwantar mata da hankali ta hanyar misali da mutane daban daban. Ranar yini tayi suna hirarsu ita dasu Salma cike da farin ciki da annashuwa ga y'an uwa da suke ta zuwa barka, hadda wad'an da raihana ta jima bata had'u dasu ba. Da yamma ta shirya zata tafi gida saboda maganar da sukayi da Ayman ta shigeta matuk'a, kuma dama saida ummie ta bata shawarar k'in d'auka tayi tana ganin kamar ba matsala har ta koma ba zata samu wata matsala ba. Rikici Salma tasa akan lallai sai dai ta zauna mata gobe ta huce makaranta daga gidanta, da kyar tayi mata bayani ta lallab'a ta kamo hanyar tafiya gida. Kusa da magrib ta isa anguwarsu, har zata huce ta gidan iya sai kuma ta dawo. Da sallama ta shiga cikin gidan, malam na zaune kan carpet kusa da k'ofar parlour iya na gefen shi tana dama mishi fura. "a'a raihanatu ce a garin yau?". "Eh wallahi malam jiya nazo gobe kuma Zan tafi". Raihana ta fad'a tana zama gefen iya, a nutse ta gaishe da tsofaffin biyu ma'abota nutsuwa da kamala. Sun tab'a hirar makarantar su a gurguje da zata tafi iya ta cika ta da gyad'a. Ita kam a kunyace ma ta karb'a saboda yau bata kawo musu komai ba, zuwan ne na bazata. A k'ofar gidan Abba abubakar taga babban yaron shi Mansoor da ya dawo daga kasuwa as usual yana danne_danne a waya, wuf tayi bata yarda ya ganta ba ta shige gidan su. Ummie ce kad'ai a gidan tana k'arasa had'a miyar abincin dare. Kusa da ummien taja kujera ta zauna. "Sannu da gida ummie". "Ke za'a yiwa sannu raihana ya masu jegon". "Masu jego suna can suna zuba tab'arar su son rae kamar basu girma ba". Dariya ummie tayi tace, "hum ba dai Salma bace ai kad'an kika gani, kwanaki gab da zata haihun nan tattaro kayanta tayi wai tazo gida haihuwa da wanka, nace ahir maza ta kama hanya ta koma baza ta zauna ta haihun mun a nan ba, mijinta ya dinga mana sallama safiya dare, raana". Kyalkyalewa da dariya raihana tayi tace, "toh aikuwa ummie kuna can a blacklist tace a gidan nan kaf babu wanda yaje mata barka". "Zata gaji ta goge mune don nikam ba inda zanje yanzun su khausar kuma sun tafi ba jimawa na d'auka ma kun had'u dasu". Raihana tace, "a'a munyi sab'ani, ummie kinji yaa Ayman da k'ok'ari har yaje wa Salma barka jiya da dare, bakiga uban kayan daya kaiwa babie ba". Cike da mamaki ummie tace, "ooh shikam bawan Allah baya gajiya da hidima, toh Allah ya saka da alkhairy ya k'ara rufa asiri". Da, "ameen" raihana ta amsa, sunci gaba da hira rabi duk ta Salma da rigimar tane, abinda takeyi ko khausar ba zatayi ba balle raihana. Saida aka kira sallar magrib sannan raihana take fad'awa ummie gobe da sassafe zata koma school, "Allah ya kaimu". Shine abinda ummien ta fad'a ta k'arasa d'auraye k'afarta ta shige parlour. Sai dare abbansu yaje yaga babie ya taho dasu muhibba, jidderh da al'ameen gida gaba d'aya khausar kuma dole ya barta saboda magiyar da Salma ta dinga yi mishi. Yau raihana da wuri ta kwanta, shiyasa bata zauna doguwar hira da kowa cikin su ba, dama kayanta a had'e suke yadda tazo. Har tayi addu'ar bacci ta kwanta sai ta tuna da Ayman lallai da gaske yayi fushi tunda gashi har war haka bai kira taba. No shi ta dannawa kira sai dai taji shi busy, sai kawai ta rubuta mishi gajeren sak'o kamar haka, "kayi hak'uri Yaya Ayman na fahimci abinda kake nufi tun a lokacin, nasan duk shawarar da zaka kawo gareni mai amfani ce ba wadda zan cutu ba, sannan naga abin alkhairin daka yiwa new born babyn mu Allah ya saka da alkhairy ya ninka dubun su ngd". Tana sending ta koma tayi kwanciyarta, babu jimawa kuwa bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita. @@@@@@@ Ayman kuwa suna rabuwa da raihana office ya nufa, ya tarar da aikin daya sha kanshi shi yasa Sam bai samu damar yin komai ba yinin ranar sai aiki. Da yamma ya taso a gajiye lis zai huce gida, yana son zuwa ya ga nuriyyah amma ya gaji abinda yafi buk'ata a yanzu shine yaje gida yaci abinci ya huta, jinin jikinshi ya koma Normal. Driving yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali har ya k'arasa gida. Babu motsin kowa a gidan nasu yau, jakar system d'inshi kawai ya ajiye ya nufi kitchen ko zai samu abinda zaici. Babu komai haka yayi ta bud'a warmers yana Jan tsaki, yau ranshi in yayi dubu goma ya b'aci, shida ake bin kanshi da abinci a fai fai yana sharewa shine yau yake neman koda cikin cokali ne amma babu. Bashi da zab'i banda ya had'a abu na k'arshe da sai ta kure yake ci a gidan. Sai dai yana mik'ewa wayar shi na soma ringing, koda ya duba Auntie ce, ba b'ata lokaci ya d'aga sai dai yana kara wayar a kunnen shi muryarta ta katse mishi hanzari, "ka kuwa san an kwantar da Nur a hospital?". Cikin tashin hankalin daya dito mishi lokaci d'aya yace, "subhanallah yaushe kuma? Ayyah shiyasa d'azu da safe na kira wayarta ban samu ba a kashe". Asibitin da take aikine shiyasa ko kayan jikinshi bai tsaya sauyawa ba ya zari mukullin motar shi yayi gaba. _Comment and share_ 24/03/23, 2:00 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merheeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page seven 7️⃣ Tafiyar minti k'alilan ce ta d'auke shi ya k'arasa general hospital d'in, no Auntie ya kira ta kwatanta mishi d'akin da suke. Da sallama ya shiga, a d'arare ya samu guri ya tsaya daga gefen su, A d'akin mamie ce sai Khadija da haidar wanda shima zuwan shi kenan. Auntie kuma na zaune gefen bed d'in da Nur ke bacci tana cin abinci a take away, fara cin abincin nata kenan saboda rashin samun nutsuwa tun d'azu, har k'asa Ayman ya durk'usa ya gaishe da mammie ya tambayeta me jiki, ta amsa mishi da, "jiki alhamdulillah ta samu sauk'i". Hannu ya mik'awa haidar sukayi musabiha, Khadija ma ta gaishe shi. "k'arasa kaga jikin nata mana". Haidar ya fad'a ganin yana shirin sake rakub'ewa gefe. Shi kuma nan kunyar Mamie ce duk ta dabaibaye shi, amma da yadda yake ji tuni ya k'arasa har gaban gadon ya ganta. "Kaga al'amarin ubangiji ko Ayman? Lafiya Lou aka kwanta da ita daren jiya amma da safe ta kasa tashi zazzab'i mai zafi da ciwon k'irji sai d'auko ta akayi aka kawo mun ita nan". Auntie ce take fad'a ma Ayman haka, "to ai ni kaina munyi waya da ita daren jiya". Inji cewar Ayman Mamie data ke jinsu ce tace, "dama haka al'amarin ubangiji yake, da mutuwa ce ma tazo hakan ne zai kasance, don ubangiji cikin second yake shafe mutum ya zama tarihi a ban k'asa". Da sauri Ayman ya rintse ido saboda fad'uwar gaban data ziyar ceshi lokaci guda, duk da maganar data fad'a gaskiya ne idan kwana ya k'are babu tsimi babu dabara sai an tafi amma shi baya fatan Nur ta mutu ta barshi a wannan lokacin, saboda sonta yake fiye da yanda yake son kanshi, ji yake zai iya sadaukar da komai daya mallaka a wannan duniyar muddin Nur zata ci gaba da kasancewa tashi har abada. Basu bar hospital d'in ba sai dare, kuma har Suka tafi nuriyyah bata farka ba. A gajiye ya kwanta saman bed hannun shi d'aya dafe da kanshi da yake mugun sara mishi. Ya jima a kwance kafun ya lallab'a yayi wanka, bayan ya shirya cikin kayan bacci farare Sol masu taushi, part d'in Auntie yayi, saida yayi knocking ta bashi izinin shiga sannan ya tura k'ofar ya shiga da sallama. Tana zaune tana k'arasa had'a mishi kisir abincin k'asar su na Sudan da ake iya yinshi sharp sharp aci don maganin yunwa. Kusa da ita ya k'arasa a sanyaye ya zauna. Kallon shi tayi kamar zata yi magana sai kuma ta share. Sai data gama had'a abincin ta mik'e ta Isa ga deep fridge da yake kusurwar parlon ta d'auko mishi fruity mai tsaka tsakiyar sanyi ta cika mishi wani glass cup taf ta mik'a mishi, "oya take". Ba musu ya amsa ya kai baki, saida ya shanye tas sannan ya ajiye kofin, yayi Bismillah ya fara cin kisir d'in a plate guda da ita. Bai wani ci na kirki ba saboda yanayin da yake ciki na tashin hankalin ciwon Nur ya zare hannu, itama dama ba wani yunwa take ji ba sosai sai kawai ta rufe abincin gefe. Kwantar da kanshi yayi jikin sopa da Auntie ke zaune hannun shi kan k'afafun ta ya lumshe idanun shi. Tab'a jikin shi tayi taji ko akwai zazzab'i a tare dashi, jin babu komai sai ta kirawo sunan shi da kulawa, "Abbana". Bai amsa ba sai d'aga kai da yayi yana dubanta, "are you alright?". Girgiza mata kai yayi, "ko kana da ciwon kaine Cox naji jikin ka babu zazzab'i". Sake girgiza mata kan yayi, "toh me yake damunka?". Rausayar da kai yayi ya kasa cewa komai sai idanun shi da suka tara ruwan hawaye. "Yaa Salam! Ayman tell me what's happening?". Auntie ta fad'a cikin shiga rud'ani har tana saukowa k'asa. Zata sake yin magana wayar shi ta d'auki ringing, ya kasa duba wayar ma sai ita ta d'auka don ganin mai kiran, ganin khaleefa ne sai tayi picking, "yaa man lafiya kake kuwa? Yau kwana biyu ko waya bamuyi ba fa". Khaleefa ne me yin wannan maganar, ajiyar zuciya mai tsayi Auntie taja kafun tace, "ba shi bane khaleefa nice". "Ah! Afwan Auntie tun safe Ina Kiran wayarki bakya d'agawa, yanzun ma tunani na idan muka gama waya da Ayman ya kai miki a muyi maganar s tashi". "Ayyah yau na shiga uzuri khaleefa ko wayar ma ban duba ba har yanzu, kasan Nur ce ta tashi da zazzab'i da ciwon k'irji zancen da nake yi maka yanzun haka ma tana asibiti an bata gado". "Subhanallah yau kenan?". "Kwantar da hankalin ka ban dad'e da baro taba jikin yayi sauk'i sosai, wallahi yau da safe ta tashi da jikin". Ajiyar zuciya khaleefa ya sauke yace, "toh Allah ya bata lafiya, yanzun Ina Ayman d'in yake?". Sake duban inda yake tayi, ya had'a kai da gwiwa yayi shiru, "khaleefa Ina ganin kamar akwai abinda yake damun twin bro d'inka, kuma ni baya son naji, gashi kuyi magana tunda kaine watak'ila ya fad'a maka". Tana gama fad'a ta ajiye mishi wayar saitin kunnan shi. Ajiyar zuciya yake ta sassaukewa a jejjere, shi kuma khaleefa a can sai tambayar shi matsalar yake hankali a tashe. Da kyar ya iya shanye damuwar da yake ciki yace, "yaa! Bro how far". "Me yake damun ka ne Ayman ko auntie bata fad'a munba nasan akwai damuwa mai yawa tare da kai". K'ak'alo murmushi yayi yace, "ba komai yaya khaleefa kawai na tsorata da yanayin yadda naga jikin nuriyyah ne a yau, bazan b'oye maka ba khaleefa wallahi Ina tsoron rasata, idan har ta tafi ta barni bazan tab'a samun wadda nake so kwatankwacin yadda nake sonta ba, please khaleefa watanni nawa suka rage ka gama ka dawo ayi maganar auren mu?". Auntie murmushi tayi ta sake ja baya daga kusa dashi tana jin wani k'arin farin cikin. Da alama komai yana tafiya fiye da yanda suke fata. Daga can b'angaren khaleefa kuwa murmushi yayi wanda ya bayyana kyawawan jerarrun hak'oran shi kafun ya tambaye shi, "wannan shine kad'ai matsalar ka Ayman?". "Eh ya fad'a yana satar kallon Auntie". Kau da kanta tayi gefe tana sake murmushin da yafi komai nuna asalin kyau da kyawun zuciyarta. "Toh aikuwa indai wannan ne kad'ai matsalar ka kusan samun abinda kake so Ayman, daga yanzu ka soma lissafi zuwa nan da watanni shida masu zuwa". Cikin farin ciki Ayman yace, "really?". "Sure" khaleefa ya fad'a mishi cikin tabbatarwa. "Toh amma khaleefa kai ta b'angaren ka kana da wata ne?". "Kamar ya kenan Ayman" "Ina nufin kamar wata wadda kake so haka". Murmushi ya sake yi yana tuno Saleema cikin zuciyar shi, "ba yanzu ba akwai sauran lokaci", abinda ya ayyana cikin ranshi kenan shiyasa ya sauya akalar abinda yayi niyyar fad'i ta hanyar cewa, "saurin me kake Ayman? Insha Allah bazan dawo ba saida kyakkyawan labarin da kake son ji". "Toh shi kenan bro Allah ya tabbatar mana da alkhairin shi". Duk suka amsa da Amin. Sunci gaba da tattaunawa su uku har Auntie kafun Ayman ya mik'e cike da kwarin gwiwa yayi mata sallama ya tafi makwanci rai fes. Har yayi Shirin kwanciya bacci sai ya duba wayarshi ko raihana ta kira, aikuwa sai ga missed call na kiran da tayi suna waya da khaleefa a lokacin da kuma text message d'inta. Murmushi yayi bayan gama karanta sak'on. @@@@@@@@ Yauma kamar kullum raihana ta gama duk ayyukan gidan su da wuri har breakfast, da yake Salma ta rik'e khausar sai ya zamana ita kad'ai tayi duk ayyukanta. K'arfe 6:30 dai dai ta gama shiri cikin doguwar riga ta atamfa, d'inkin ya zauna mata da kyau kuma ya fudda ainahin shape na jikinta gaba d'aya. Medium d'in gyale ta yafa kalar takalmin da zata saka, ta d'auko jakar kayanta da handbag d'inta, tana futowa Abban su yana futowa shima ummien su a bayan shi, har k'asa ta tsugunna ta gaishe su, suka amsa ummie na tambayarta "sai tafiyar kenan?". "Eh ummie ba wahala Zan samu mota akan in anjima". Kud'i masu yawa abbanta ya k'ara mata, yayi mata addu'a had'e da sa albarka ta d'auki hanya ta futo. Ummie har hanyar futa ta rakota tanayi mata addu'a, koda wasa bata yarda ta juyo ba, hawayene fal idonta har yanzu ta kasa sabawa a duk lokacin da tazo gida hutu ko yini guda ne idan zata tafi sai tayi kukan nan. Abinda ya mutukar bata mamaki bai huce ganin motar Ayman a k'ofar gidan suba, tana tunanin a rayuwarta Ayman yafi ta damuwa da komai daya shafe ta, shiyasa baya mantawa da duk abinda take ciki, yake kuma taimakawa da jikin shi da zuciyarshi da aljihun shi. Silently taje ta bud'e front seat ta shiga ta zauna. Suna had'a ido ya sakar mata lallausan murmushi, ba b'ata lokaci ta mayar mishi da martanin murmushin shi a sanyaye tayi k'asa da kanta ta soma gaishe shi. "Ina kwana". "Kin so ki makara fa". "Toh ayi hak'uri yaya Ayman "Ina kwana". Ta sake maimaita gaisuwarta. "lafiya Lou Ina fatan kin tashi lafiya". "Nima Ina lafiya Lou" ta fad'a a sanyaye. Daga haka basu sake ce da juna komai ba har Ayman ya tada motar suka fara tafiya, sun d'auki hanya bisa kwalta d'odar sannan Ayman yace mata, "nuriyyah fa bata da lafiya". Da sauri raihana ta dube shi tace, "toh? me yake damunta kuma? Ai daka fad'a mun tun zuwana da naje naga jikin nata" "Toh aranni muje biki sarkin zuwa dubiya, ai sai ki tsaya kiji tun yaushe ta fara ciwon ma tukun". Lumshe idonta tayi ta bud'e tace, "tun yaushe kenan?". "Jiya ne da safe ta tashi da zazzab'i da ciwon k'irji yanzun haka an bata gado a general hospital da auntie ke aiki, kuma alhamdulillah ina ganin zuwa gobe za'a iya sallamota yanzu don yanzu haka daga gurinta nayo nan, naga alhamdulillah jikin yayi sauk'i har munyi magana ma da ita". Cikin jimantawa raihana tace, "ayyah Allah ya k'ara sauk'i". Ya amsa da, "ameen". Sun sake yin shiru kowa da tunanin da yake a zuciyar shi kafun Ayman ya nisa yace, "wata nawa ya rage miki ki kammala karatun ki duka raihana". Da mamakin shi tace, "yau kuma kake tambayata Yaya Ayman". "Eh Ina sane so nake na tabbatar daga bakin ki kawai". "Wata uku ne ya rage". Ajiyar zuciya yayi yace, "zaki riga khaleefa gamawa kenan?". Shiru raihana tayi tana maimaita sunan khaleefa a ranta, saura k'iris ta tambayi Ayman waye ma khaleefa a gurin shi sai kuma dai tayi shiru tana k'ok'arin tunowa da kanta, don ta fahimci tambayar zata iya sawa yaji haushi ko ba dad'i a ranshi tunda zaiga wato duk yadda yake k'ok'arin kyautata mata a y'an uwanta ba wanda bai sani ba a banza, ita ba ruwanta da nashi y'an uwan, shiyasa ma bata san waye khaleefa a tare dashi ba. Kowa da abinda yake sak'awa tsakanin su har suka k'arasa harabar makarantar su. Agogo ta duba a sanyaye kuma ta kalle shi, "Allah yasa kada kayi late gurin aiki". "Noop kada ki damu na bada uzuri daga nan zuwa 3 hour masu zuwa idan naje ba matsala". A tare suka bud'e murfin motar suka futo ya kewaya gidan baya ya d'auko mata jakar kayanta, sai daya had'a da wasu y'an canjin masu nauyi sannan ya mik'a mata, girgiza mishi kai tayi ta zame kud'in ta karb'i iya Jakarta ta kaya. Tamke fuskarshi yayi, "yaushe muka fara haka dake raihana". K'asa tayi da kanta tace, "kayi hak'uri Yaya Ayman bazan iya karb'a ba saboda hidimar da kakeyi dani tayi yawa, ummiena, khausar, Salma da sauran k'anne na kana hidimta musu ba tare dani kaina ka sanar dani ba, kana jinsu kamar naka familyn, ko iya wannan aka tsaya kayi mun abinda ban Isa na biya kaba a rayuwa". Tana gama maganarta ta d'auki hanyar hostel d'insu cikin sauri, bin bayanta yayi yana kiran sunanta sai dai ko saurarar shi batayi ba, haka ta dinga tafiya da matuk'ar sauri yana binta gudu gudu har Allah ya bashi ikon Shan gabanta, tana gab da shiga k'ofar hostel d'in. "Raihana wai me yake damunki haka?, duk abinda nakeyi ke kike sakani? Ko da kud'in ki nakeyi da zaki ce yayi yawa?, sannan idan bani dashi zanyi ne?". "Amma Yaya Ayman......". Da sauri ya katse ta "bana son jin komai" ya karb'e jakar hannunta yasa kud'in a ciki, "gashi nan idan kinso ki kona su a bola ko ki zubar". Yana gama maganar shi ko kallonta baiyi ba ya juya yabar mata gurin, bin bayanshi tayi da kallo yayi nisa sannan ta iya takawa sannu a hankali ta shiga arean hostel d'insu. Su fateema da takwarar ta suna zaune kowa da abinda takeyi sai ganinta sukayi unexpected, aikuwa fateema ta daka tsalle ta rungume ta, "oyoyo sis u are highly welcome, wannan dawowar bazata". Dariya tayi ta zame jikinta ta zauna gefen bed tana duban su duk sun wani tsare ta da ido, "toh kallon na meye haka kuma?". Raheena tukur mai shigen sunanta tace, "ba dole mu kalle kiba keda kikace sai after one week zaki dawo kuma mun ganki yau da sassafe, hala Abba ne ya koro ki?" Girgiza musu kai tayi, "ba d'aya abokin kwarai ne ya bani shawara ta kwarai". "Aikuwa ya kyauta mana don a jiya kad'ai baki ji yadda mukayi kewar kiba, ko d'azu da muka makara sallar asubah ma saida raheenatu tace da kina nan wallahi ba zamu makara ba". Dariya kawai tayi ita dai. "To ya masu jego dasu ummie fatan kin baro su lafiya". "Suna lafiya Lou alhamdulillah, yaeh me yake tafiya a makaranta" Nan fa hira ta b'arke kowa na bata labarin abinda akayi cikin kwana d'aya da bata nan. @@@@@@ Kwana biyu da dawowar ta da wani yammaci tana zaune a hostel tana goge kayanta data wanke, sanye take da body hug riga iya gwiwa kanta babu d'ankwali ta tsefe rabi, rabi kuma doguwar jelar shi na reto a saman kafad'ar ta. Wayarta da take gefenta ta d'auki ringing. Ajiye ion d'in tayi gefe ta d'auki wayar tana dubawa da tunanin ko Ayman ne, sai dai sab'anin hasashen ta bak'uwar no ce. Shiru tayi tana sak'e sak'e a zuciyarta kafun ta d'aga wayar. "Amincin Allah su tabbata ga kyakkyawar zinariyar mata". Sai ta jingina da jikin gadon tana tunanin waye wannan kuma? "Yi hak'uri ban gabatar miki da kaina ba ko? Sunana abubakar Muhammad Imran, nine muka had'u dake kwanaki biyu da suka gabata har na takura miki kika bani no". Tabe baki tayi kamar yana gabanta tace, "ohh kaine". "Ashe baki manta niba?". "Humm!" Kawai tace, shi kuma yaci gaba da maganar shi, "Ina ta tunanin kiranki cikin kwanaki biyun nan sai dai ina tsoro". Nan ma bata ce komai ba, "kinyi shiru ko bakya son kiji tsoron meye?". Yanzun kam hararar wayar raihana tayi tace, "taya zan tambaye ka kaida rayuwarka" "Eh to hakane amma ai ya kamata kisan ko tsoron meye?". "bari ayi yadda kake so to tsoron me?" Murmushi yayi yace, "Tsoron kada nayi laifi a gurinki y'an mata, Ni kuma gani mutum da bana son takurawa rayuwar kowa". "Da kyau ka taimaki rayuwarka kuwa?". Murmushi ya sake yi donshi komai nata burge ta yake, "akwai abubuwa da yawa da nake son mu tattauna sai dai ban sani ba ko zan iya samun address d'inki, I mean addreshin gidan ku". Sake yamutsa fuska raihana tayi tace, "gashi address d'in bazai samu ba Sam". "Me yasa bazai samu ba gimbiyar mata". Ya tambayeta, "humm saboda bani da lokacin saurarar abinda za kazo dashi". Murmushi ya k'ara yi, shi kad'ai yasan yadda yarinyar take d'aukar hankalin shi, "toh me kike tunanin zanzo dashi?". "Tatsuniyar gizo dai ai bata huce ta kok'i, me zaka zo dashi wanda ya huce soyayyar yaudara irin wadda ku matasan zamani baku d'auke ta komai ba". Wata y'ar k'aramar dariya yayi daga b'angaren shi yace, "Amma kin burge ni y'an mata, irin wannan fassara ta farat d'aya ba tare da dogon tunani ko nazari ba, sai dai ni har yanzu bakiyi laifi a gurina ba ko kad'an, saboda mutum baya tab'a fad'in sab'anin abinda yake zuciyarshi koda kuwa bai furta da baki ba za'a iya fahimtar hakan akan fuskarshi, sannan ruwan daya dake ka masu iya magana sukace shine ruwa......". Shiru tayi ba tare da tace komai ba, "baiwar Allah kinyi shiru, ni ko sunan kima baki fad'a mun ba". Da sanyin jiki dana gwiwa tace, "raihanatu". "Raihanatu suna me dad'i". Ya fad'a yana fudda sautin murmushi kafun ya sake cewa, "raihanatu ina ganin kamar akwai wani abu a k'asan ranki dangane da soyayyah da maza! Am I right?". Cikin katse hanzari tace, "babu komai a raina". Wani murmushin ya sake yi, "akwai fushi a kwayar idon ki, sannan akwai zafi a kalaman ki, kina yin magana cikin fushin da yake tasowa daga k'asan zuciyarki, tun a ranar dana fara had'uwa dake, raihanatu dole akwai tabon wani a cikin zuciyar ki wanda yake assasa faruwar hakan". Cikin b'acin rai yanzun raihana tace, "bani da tabo ko mikin soyayyah saboda ni ban bata muhimmanci ba bare ta wahalar dani Kota dameni the fact is Ina da wanda nake sone kawae". "Ba haka bane raihana, idan da ace kina soyayyah da wani kuma kina tunanin auren shi to da tun a waccen ranar zanga soyayyar cikin kwayar idonki, kuma ba zaki dinga magana cikin fushi ba, kada ki manta ko yanzu kince baki ba soyayyah muhimmanci ba which is kin k'aryata kanki akan kalaman ki na k'arshe, dole komai a duniya bazai dinga saurin baki haushi ba, kina cikin soyayyah kowa zaki ganshi abun ban dariyarki da nishad'i coz you are deep love with someone else, sab'anin haka shine kike yin magana cikin fushi da fusata, wallahi ko kin k'i ko kinso hasashena a kanki gaskiya ne, ni yanzu mubar maganar jayayyah! Kina da Wanda kike so koma babu! Tunda ba matar aure bace ke, baki da engaged da wani zan fad'a miki abinda yake zuciyata daya sa na karb'i no ki waccen ranar, Ina son ki! Hak'ik'a ina k'aunar ki raihana, da gaske kuma auren ki zanyi shiyasa nake son ki bani dama, address d'in gidanku kad'ai ma ya wadatar". Wani zazzafan numfashi ta fesar tace, "kayi hak'uri hakan bazai yiwu ba". Tana gama fad'in haka ta ajiye wayar jikinta a sanyaye, tana ganin ya kamata ta saurarawa rayuwarta da jefa kanta cikin matsala, a duk cikin samari biyar da akayi musu engage babu wanda ta tab'a jin tashin hankali wai don su rabu akan soyayyar shi, ita duk tashin hankalinta d'aya ne ya zatayi da kakarta da dangin mahaifinta da basa k'aunar ta ita da ummienta, ya ummienta zata ji idan mummunan labarin fasa auren ya risketa? Abu na uku kuma Hasalima ita Saboda ta k'aryata matar Abba abubakar akan furucinta take amincewa da auren su, yanzu kuma lokaci yayi daya kamata ta farka daga rayuwar tatsuniyar da take ciki zuwa ta zahiriyyah, ta duba wanda ya dace ya cancanci ya aure ta, wanda yasan abinda yake yi, take son shi yake sonta, take son k'are rayuwarta dashi ba wanda ta futar don wani fushi da b'acin rai na k'addara ba. _toh waye haka Raihana?_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page eight8️⃣ Ranar yini tayi sukuku kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, kasancewar basu da lectures sai ta yi kwanciyarta a gado ko abincin rana bata iya ciba, tariyar rayuwarta tayi tun daga lokacin da aka haifeta har zuwa yau. Da yammaci Ayman ya kira ta ya had'a ta da nuriyyah tayi mata sannu da jiki. Ranaku shida sun tashi kamar awanni shida cikin k'iftawa da Bismillah, kamar yadda Ayman ya mata alk'awari haka yauma ya bugo sammako yazo d'aukar ta, dama tun dare ta had'a kayanta, shiyasa yana fad'a mata yazo ba b'ata lokaci ta k'arasa had'a yanata yanata tayi sallama dasu raheena ta fuce. As usual yana tsaye jikin motarshi ya hard'e duka hannuwan shi a k'irji, sanye yake da fararen suit, k'afar shi sakaye cikin bak'in cover shoe, gashin kanshi ma'abocin santsi sai d'aukar ido yake yasha gyara. A nutse ta k'arasa har inda yake tsaye ta d'an russuna tace, "Yaya Ayman barka da safiya". Idonshi a kanta yana nazarin ko akwai wani abu sabo a tare da ita ya amsa gaisuwarta har yana tambayarta ya karatu, ta amsa mishi da alhamdulillah. Shiya bud'e mata front seat, ta shiga ya rufe, ya mayar mata da jakar kayanta baya sannan shima ya shiga mazaunin driver. Suna tafe a hanya suna hira jefi jefi, rabin hirar duk hirar rikicin su da Auntie ne sai labarin iya da shaftarta. Sunyi nisa a hanya ya k'ara satar kallonta kafun ya tambayeta, "kinsan kuwa kin rame sosai raihana?". Jikinta a sanyaye tace, "na sani Yaya Ayman kuma ni ba komai nasa a raina ba yanzu". "Anya kuwa raihanatu, na sanki da ajiye abu a rai ko ki zauna kita kukan kinnan mai d'aga hankali". "Trust me Yaya Ayman duk babu d'aya cikin abinda kake zargi, Allah na saki raina akwai labari ma". Kayataccen murmushi ya saki ya rage gudun motar kad'an yace, "Tom Ina ji Allah yasa na alkhairy ne". Cikin jin nauyin shi tace, "na had'u da wani guy rannan fa". Da sauri ya Kalleta itama shi take kallo tana so taji yadda zai karb'i zancen. Sai ya maida hankalin shi kan titi yace, "wanene shi? Shin ya dace daki mallaka mishi soyayyar ki? Sannan kin tabbar yana da banbanci da wad'an can da kuka rabu ko shima irin sune?". Murmushi ne ya kubuce mata tasa tafin hannunta ta rufe fuska. Dogayen yatsun hannunta yabi da kallo sunsha adon jan lalle, "ba don kar nayi k'arya ba da sai ince tunda kika kai shekaru goma a duniya ban tab'a ganin yatsun hannunki ko bayan hannunki ba lalle ba". Bud'e fuskarta tayi tana kallon shi da mamaki tace, "ya kayi parking kuma muna tafiya, kada fa ka samu matsala gurin aiki ta sanadiyyata". Idonshi cikin nata yace, "raihana bazan iya had'a abu biyu a lokaci guda ba, now am all ears". "Toh ni ta ina Zan fara ma?". "kada ki damu zaki iya farawa kota ina". Rausayar da kai tayi ta soma labarta mishi komai tun daga had'uwar su da guyn har zuwa yanzu da wayar da suka sake yi jiya inda yake rok'on ta data bashi address d'inta. Doguwar ajiyar zuciya Ayman ya sauke, "yanzu ya kike ganin za'ayi". "Ai shiyasa na fad'a maka don ka bani shawara, in share shi ko in bashi dama naji da wadda yazo?". "Indai har yayi miki ki bashi dama mana". Murmushi ta sake yi tace, "toh ni dai bazance ba tunda har yanzu ta waya nayi magana dashi". Ayman yace, "shikenan ki nazarce shi ki tabbatar da nagartar shi in yaso sai ki bashi dukkan damar da zai kasance mijinki, idan kuma shiriritane ya kawo shi... Toh dama nasan ke d'in ba layin shi bace ba b'ata lokaci ya kama gaban shi tunda wuri ma". Kanta a k'asa tace, "toh Yaya Ayman nagode da kulawa da shawara mai kyau". Ayman yace, "babu komai raihanatu Allah yayi mana jagora" tace, "ameen". Daga nan suka ci gaba da tafiya suna hirar su jefi jefi har suka isa cikin gari. Bai kyale taba saida ya kaita har bakin k'ofar gidan su, tayi mishi godiya ta shige gida. Ba k'aramin mamaki ummie tayi da ganinta ba, wankin gida takeyi har ta kusa gamawa ta ajiye tsintsiyar hannunta gefe tace, "raihana kece da sassafen nan?". Tsugunna tayi gaban ummien tace, "eh nice ummie Ina kwana". "Lafiya Lou amma ya kika samu mota da safen nan?". Shiru tayi tana k'ila wa k'alan fad'a mata gaskiya. "Ba amsa kenan?". Ummie ta fad'a tana d'aukar tsintsiyar ta. Tana wasa da gefen gyalenta tace, "Yaya Ayman ne yaje ya d'auko ni?". A wani irin fusace ummie ta juyo tana kallonta, "har yanzu kin kuwa San abinda kike a rayuwa raihana? Meyasa ba zaki zama mai taka tsantsan da mutane da rayuwa bane, kin fi kowa sanin halin da kike ciki a anguwar nan, su kansu Ayman d'in a idon mutane suke sannan daga ni harke mun kasa sanin abinda yake korar duk manema auren ki....." "Kiyi hak'uri ummie insha Allah zan kiyaye gaba". Raihana ta fad'a cikin sanyi. Ummie bata kulata ba taci gaba da aikinta. Sai taja k'afafu jikinta a sanyaye ta shige parlour ta kwanta kasan carpet tayi shiru tana nazarin abinda ummie take son nusar da ita game da huld'arta da Yaya Ayman wanda ita ta kasa fahimta, ita kuma fa komai ne yasa take sakin jikinta dashi ba sai ganin yadda yake d'aukarta kamar k'anwar shi ta jini, zata iya rantsewa tunda ta mallaki hankalin kanta Ayman ko hannunta bai tab'a rik'ewa ba, sannan duk abinda take so shima yana son abun da zuciyar shi duka, haka abinda ta tsana, yana jin bak'in ciki idan abu mara dad'i ya sameta, abu na k'arshe kuma na farko yana kyautata mata ita da familyn ta da jikinshi da aljihun shi, ita dai tana da yak'inin Ayman bazai tab'a cutar da ita ko yaci amanarta ba, sai dai maganar mutane da ba'a tab'a iya musu. Tana wad'annan y'an sak'e sak'en ummie ta gama aikinta ta shigo da tea plask da cups ta dire mata, "ki tashi ki karya kumallo ko kinzo zaki fara zaman yunwar taki ne saboda nayi miki magana akan babban abokin ki k'anin mahaifiyar ki?". Mik'ewa tayi zaune ta k'ak'alo murmushin dole tace, "kiyi hak'uri ummie ni banga laifi a maganar kiba Sam, nasan gaskiya kika fad'a, a matsayin ki na mahaifiyar da tafi kowa sona nasan ba zaki so wani abu na cutarwa ya same ni ba, tabbas nayi kuskure na sake da yawa, gashi yanzu bansan ta yaya zan iya rage kusancin muba, bansan ma kota yaya ba, tunda ba komai ne ya kawo alaqar mu har zuwa yanzu ba sai kyautatawa da tarin halaccin shi gareni". Nazarinta ummie ta k'ara yi kafun ta nisa tace, "Ni fa ba wai ina nufin ku rabu ko bana son alakar ki dasu bane, a'a Ina son ki dinga kiyayewa, babu laifi idan kunyi hira dashi a waya ko a k'ofar gidan ku ko gidan iya, muddin ba abinda ya keta shari'a zaku aiwatar ba, amma a dinga ganin shi yana yawo dake a motarshi za'a samu k'atuwar matsala, mutane da kike ganin su abune mai sauk'i su siyi sharri a kasuwa su lik'a wa mutum bare......." "Insha Allahu zan kiyaye yadda kike so ummie duk da wasu lokutan karantar abinda nake ciki kawai yake ki ganshi, amma zan dinga kauce mishi". Ummie tace, "Allah ya kyauta". Had'a shayin tayi zata sha tace, "ummie ina khausar take tunda nazo ban ganta ba". "Khausar ai tun zuwanki tana gidan Salma bata dawo ba". "Tab su hajiya daru sai da aka samu wanda aka rik'e". Ummie tace, "aikuwa dai". Tana k'arasa fad'a ta mik'e ta nufi d'akinta. Daga nan itama raihana breakfast tayi da daddad'an abincin ummienta data jima bata ci ba, bayan ta gama ummie tace ta shirya ta tafi can gidan masu jego watak'ila suna buk'atar ta wajen shawara da had'a abinda za'ayi. Ko kayan jikinta bata sauya ba ta zunbula hijab da facemask ta huce. ***************** 5:30pm agogon k'asar jamus. A farfajiyar baya ta babban apartment d'insu, zaune suke kan wasu kujeru na roba masu k'ayatarwa, duk da suna opposite juna amma dogon table ya raba tsakanin su, dukkan su sanye suke da kauraran kayan da zasu tare musu sanyin da ake bulbulawa a garin yau. Kallon juna sukeyi tamkar kallon bankwana irin in sun had'u ba zasu sake had'uwa d'in nan ba. Khaleefa ne ya fara sauke ajiyar zuciya suka lumshe idon su a lokaci guda. "Saleema". Ya kira sunanta a tausashe, "my future husband" ta amsa da wata kamilalliyar murya tana sake jifan shi da wani irin kallo na tsantsar so da k'auna. Matsawa ya sake yi daf da ita ya hura mata iskar bakin shi mai d'umi a saman idanunta, "kin kuwa San yadda nake tsananin sonki Saleema?". Girgiza mishi kai tayi tace, "sai ka fad'a". Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi yace, "Ina sonki da yawa Saleema fiye da yadda kalmomin bakina zasu fad'a, ji nake kamar rayuwata ta fara ne daga lokacin dana fara ganin ki, ban tab'a soyayyah ba hakan yasa nasha wahala wajen iya bayyana soyayyata" murmushi yayi mai k'ayatarwa still yaci gaba da maganar shi, "kin kuwa san son wani baya buk'atar wani hujjah, idan har zaka iya kawo hujjar da tasa kake son wani to wannan shi ake kira da soyayyah, idan kuma ba zaka iya ba shine k'auna, Ina k'aunar ki Saleema". A hankali ta mik'e cikin takunta na yauki da kissa ta kewayo gaban khaleefa ta zauna kan table d'in daya raba kujerun su, k'afarta na gugar tashi, numfashinta na sauka saman fuskarshi kamar zata shige jikin shi, ga wani azababben k'amshin turarenta da dama tuntuni yake barazanar kasssara jijiyoyin hancin shi na sake kai mishi farmaki na kusa. Cikin wata siririyar murya tace, "idan har zuciyarka lambu ce, bana son na kasance flower a cikinta, saboda flower k'aramin guri zai iya isarta, amma Ina son na zama kamar ciyawa, Ina buk'atar wadataccen guri, don Allah khaleefa kada ka rage wani gurbi da wata d'iya mace zata samu har ta shiga ta zama kwayar cutar da zata cinye dashen ciyawata....". Tana gama fad'in haka ta dire k'asa kan k'afafunta. Shima mik'ewa yayi suna kallon juna har kamar zai shigar da ita cikin faffad'an k'irjin shi ya b'oye ta. "Every heart has love and pain! Only way of expression is different, ladies hide it in their gorgeous eyes, Saleema koda ba zaki ce komai ba Ina iya kallon komai ta cikin kwayar idon ki, soyayyar ki ta gaskiya ce ba algus a ciki, toh meyasa ni zan kasa baki cikakken guri kamar yadda kika yimun? Wallahi Saleema zan fad'a kamar yadda na saba fad'a, ban fara sonki don na daina ba, kin cike ko'ina na cikin zuciyata baki bar ko d'igon rata da wata zata miki kutse ba". Ya k'arasa fad'a yana zuba mata ido, eyeball to eyeball suke kallon juna. Before they know sai ga goshin su ya had'e guri guda tsinin hancin su na had'uwa. Saukar hannun Saleema da yaji gadon bayan shi shiya dawo dashi cikin hayyacinshi, ya janye jikinshi baya daga gareta, ya duba agogon dake d'aure a bayan hannun shi, "time for magrib prayer Saleema ya kamata muyi sallama". Cikin jin nauyin shi kad'an tace, "okay byee....". Kafun ta k'arasa khaleefa ya dakatar da ita ta hanyar fad'in, "shhhh! kada kice mun sai watarana saboda k'aramar kalma ce da take haddasa rad'ad'i da yawa, ga mutumin da yake sonka sosai kake sonshi kaima". Cikin langwab'ar da kai tace, "toh me zance kenan futurehus". Wani shegen murmushi ya mata yace, "koda yaushe kice sai mun sake had'uwa". Itama murmushin tayi tace, "i will take note from now ma, meet u again". Ta k'arasa fad'a had'e da blinking kiss to him, ya karb'a kamar zai manna a kumatu sai kuma ya wulla mata kayanta. Ta cafe tana dariya. Shima ya juya yana murmushi, tunda ya fara tafiya ko sau d'aya bai waiwayo ba, saida ya kai k'arshen katangar dai dai inda zai shige d'akin shi ya waigo ya kalleta ya d'aga mata hannu da wannan murmushin. Da daddare bayan ya baro apartment d'in Ahmad sai daya tsaya dai dai apartment d'inta yana kallon k'ofar kamar zai ganta a jiki, kafun yaja k'afafun shi jiki a sanyaye ya wuce nashi guri. Ko daya kwanta kasa bacci yayi, moments d'insu na d'azu ya tsaya mashi a zuciya sai tuna kalamanta da sautin daddad'ar muryarta yake, baisan me yasa ba amma komai na Saleema yayi mishi, itace irin zab'in matar da yake so, mutane suna fad'in baka tab'a samun abinda kake so fully amma a had'uwar shi da Saleema ya k'aryata hakan, Allah yana iya mallaka maka komai dai dai yadda kake son shi. Haka khaleefa ya kwana ba wadataccen bacci sama sama, a hakan kuma daya d'an runtsa zai fara mafarkin masoyiyar shi masu kama da zahiriyyah. Tun a waccen ranar khaleefa da Saleema basu sake had'uwa ba, dama kuma shi mutum ne me tsari da yake yin koman shi a tsare, a yini sau biyu suke yin waya, daga safiya sai ko idan ya samu chance da rana, in babu kuma sai dare, a times ma text yake mata da daren kawai yayi kwanciyar shi, farkon soyayyar su Saleema tasha wahala kafun ta fahimce shi da inda yasa gaba, haka zatayi ta damuwa ta yini tana kiran wayarshi baya picking idan ta matsa mishi ma sai yayi switch up na wayar duka, amma daga baya data gane haka tsarin shi yake saita bishi a yadda yake suka zauna lafiya. Zasu had'u duk k'arshen sati, suyi waya duk safiyar duniya shikenan. A wannan karon kam karatu ne yasha kanshi, tana ranshi sai dai bashi da lokacin kanshi bare ya ware nata, haka satin yazo ya huce basu had'u ba. Kullum yana cikin research da practice kai na burning, ko abincin kirki ya daina ci. A wani dare bayan ya gama shirin kwanciya bacci wayarshi ya d'auko zai kirata sai yaga rututun missed call, raba dai dai akayi tsakanin Saleema da Ayman. Bayan kira hadda guzirin text massage. D'aya ne daga Saleema, Amma hud'u daga Ayman ne, sai ya fara duba nata daya gani a farko, "masana sukace ka kusanci wani mutum wanda zai saka farin ciki, amma ka zama mafi kusanci ga mutumin da bazai iya farin ciki ba sai tare da kai, sai kaga banbancin, toh ni tun a yanzu na fara gane banbancin, sati biyu ba tare da ganinka ba, kwana uku babu wayarka na wujijjigu matuk'a har garkuwar jikina ta kasa jurewa na kwanta ciwon rashin ka a kusa future husband I miss you, I miss you more". Murmushi yayi a lokacin daya karanta sak'on Saleema, sai ya duba na d'an uwan shi wanda duk complain ne "kwana biyu sai kiranka nake kak'i picking duk bakaji yadda zazzab'i ya lullub'e ni ba, gaskiya yau ka kirani naji muryarka in ba haka ba bazan iya bacci ba". Murmushin dai ya sake yi yana tunanin wanda zai soma kira tsakanin su, yasan dukka kwantaccen rikici zai riska gurin kowannen su, amma babu wanda yafi tsoro kamar na Ayman, Saleema zai iya shawo kanta cikin sauk'i tunda suna tare a k'asa d'aya gini d'aya, amma Ayman ko abu ya huce ya dinga mita kenan. Lokacin daya kira Ayman waya suke da Nur, amma yana ganin Kiran ya bata uzuri yayi picking, ko sallama bai tsaya yiba bare batun jin lafiyar juna, complain kawai yake, "yau kwana na nawa Ina kiranka fisabilillah? Wato sai yanzu kaga damar kirana, toh nima bani da lokacin ka yanzun lokacin masoyiyata ne......". Kit ya kashe wayar. Shidai khaleefa dariya kawai yayi, ya sake kiran shi sau biyu amma busy. Sai kawai ya share shi ya kira tashi masoyiyar shima, sai dai me? yau bai tari lucky ba itama bata d'aga ba, ba dabi'ar shi bace kiran waya da yawa, shiyasa yana mata kira biyu ya ajiye wayar. Yana son yaji muryar auntie amma dare yayi ta iya yiwuwa ma tayi bacci yanzu haka. Washe gari tunda yayi sallar asubah bai koma bacci ba, gyare gyaren daya kwana biyu baiyi a gidan ba yake, sai daya tabbatar ya gyara komai ya zubar da duk wasu shirgi na gidan sannan ya zauna yayi breakfast, wayar Saleema ya sake trying sai dai har ta katse bata d'aga ba, sai hankalin shi ya soma tashi kuma, lafiyar Allah bazai kira Saleema tak'i d'aga mishi waya ba, there must be something behind, Bayan yayi sallar azahar tsaye yayi a gaban d'akin shi yana kallon d'akinta. Ya dad'e yana k'ila wa k'alan yaje d'akin yaji lafiyarta ko a'a, daga k'arshe sai kawai ya kasa jurewa ya nufi d'akin. Knocking yayi duk da yaji shiru kamar ba kowa a ciki. A hankali Saleema da take kwance ta taso tazo ta bud'e k'ofar, sanye take da riga iya gwiwa Ash colour sai dogon wando bak'i daya saukar mata har k'asa kanta babu d'ankwali sai manyan kitson attached daya sauka har gadon bayanta. Kana ganin yanayinta zaka fahimci tana cikin halin ciwo har y'ar rama tayi. Fad'ad'a fara'ar fuskarta tayi tace, "au kaine? Ni na mayi fushi". Shi kam khaleefa kasa cewa komai yayi sai kallonta yake kawai yana nazarin abubuwa da yawa a tare da ita, yadda ta rik'e k'ofa gam like her life defends on it kad'ai ya isa ya bayyana gab take da fad'uwa in taci gaba da tsayuwa. Sai ya cire takalmin shi ya shiga cikin d'akin, aikuwa juyawar da zatayi wani irin juwa ya d'ebe ta, khaleefa ya tafi zai tarye ta da hanzari sai kuma Allah ya bata sa'a kafun ya kai hannun shi jikinta ta rik'e jikin window. "sannu Saleema, tun yaushe baki da lafiyar ne? Kinje asibiti ma?". Rintse idonta tayi a lokacin da khaleefa ke jera mata wad'annan tambayoyi, hannunta guda dafe da kanta, a sannu tayi k'asa ta zauna sosai tana sauke ajiyar zuciya. Khaleefa ne yayi k'arfin halin rufe mata k'ofar yazo gabanta ya zauna yana Kiran sunanta, "Saleema! Saleema kina jina? Ko asibiti zamu tafi ne?". Girgiza mishi kai tayi da kyar ta bud'e idonta tace, "naje tun kwana uku da suka gabata, don Allah khaleefa me nayi maka ka daina d'aga wayata ka daina kirana?". "Saleema ni bakiyi mun komai ba, ban samu lokaci bane har a karan kaina ban samu lokacin kaina ba sai jiya, amma duk da haka kina cikin raina, ina jin Allah Allah na gama abinda nake nazo na ganki Saleema". Cikin dauriya ta sakar mishi tattausan murmushi, "wane taimako zanyi miki Saleema, kinci abinci? Kinsha magani?". Girgiza mishi kai ta sake yi cikin sanyi tace, "bazan iya cin komai ba my love, tunda na ganka nasan zan dawo normal ko babu abinci babu magani, dama rabin ciwon na rashin kane". Murmushi khaleefa yayi mai k'ayatarwa shiyasa yake sake jin Saleema a ranshi da zuciyarshi sosai, kamo hannunta yayi duka cikin nashi yana kallonta eyeball to eyeball yace, "I love you, I love you Soo much Saleema, Tashi muje na taimaka miki kici wani abu kinji mie love". Ja baya yayi ita kuma ta mik'e da kyar ta nufi hanyar bathroom, sai a lokacin na samu damar k'arewa d'akin nata kallo, komai dai dai dana khaleefa in aka d'auke banbancin kyale kyale da mata basa rabo dashi a d'aki sab'anin maza. Toilet tayi shi kuma ya fara gyara mata d'akin. Ko kafun ta futo ya share d'akin tass duk da ba datti sosai saboda Saleema ba dai tsabta ba, macece data tsani datti komai k'ank'antar shi, yanzu ma saboda rashin lafiyar data kwanta gashi sunyi fad'a da Amna da take taimakon ta. A kitchen yaga duk abun buk'ata na had'a sauk'ak'k'en abinci da za'a iya ci cikin sauri, nan ya fara had'a mata abinda zata ci kafun tasha magani. Yana gab da gamawa ta biyo shi kitchen d'in, "sannu daga zuwa ziyara na had'a ka da aiki". Murmushi ya mata yana k'are mata kallo cikin sabuwar shigar da tayi cikin wata doguwar riga fara sol mai had'e da vail ta nad'e kanta da vail d'in jikin rigar, alama tana son fararen Kaya. "Gaskiya kinyi kyau Masha Allah kamar ba yanzu kika tashi daga ciwo ba". K'arasa shigowa ciki tayi sosai ta jingina da carbinet tana kallon shi da sabon murmushi, "meka dafa mun?". Ta tambaye shi. "Abu mai sauk'i da zaki iya ci, Ina fatan zaki lallab'a kici koba yawa". "Ai ya zame mun dole ma cin wannan abincin naka koda in naci cikina zai fashe kuwa". Lakace mata hanci yayi yace "in kika k'ara cewa komai ko? Sai kace wani ita kad'ai take sona". Farrr tayi da idanunta tace, "Ai koba ni kad'ai nake sonka ba sonda nake maka yafi naka......". Wani k'aton jug ya d'auka yayo inda take daf har tana jin hucin numfashin shi yace, "in kika sake cewa komai....." Saleema tana guntse dariyarta ta kama bakinta da hannunta. Ajiye jug d'in yayi yana dariya, itama dariyar tayi cikin shagwob'a tace, "sai wani zaren ido kakeyi nida bani da lafiya, kamata yayi ma fa ka lallab'ani". Shafa sumar kanshi yayi ya koma ya k'arasa juye mata abincin a plate ya d'auko cokali d'aya da ruwa, yana gaba tana bayan shi suka futo, ya tambayeta magungunanta ta d'auko. Kusa dashi ta zauna, ya zaro wayar shi a aljihu yace, "oya kicinye mun abincin nan tass". Shagwob'e fuska tayi tace, "Allah fa har yanzu ban gama warkewa ba ka k'arasa ladanka ka bani da hannayenka masu albarka sai nafi ci da yawa ma......". Wani irin kallo da khaleefa ya jefa mata yasa ta kasa k'arasa abinda tayi niyyar fad'a sai k'asa k'asa. _fatan Allah ya gafarta mana zunuban mu, marassa lafiya na gida dana asibiti Allah ya basu lafiya, mu kuma da muke da lafiya Allah ya qara mana lafiya, Wanda suka rigamu zuwa gidan gaskiya Allah ya jikan su yayi rahama a gare su, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani, barkan mu da ranar juma'ah_ _naji wasu sun rikice a lissafi, suna tambayar novel ranar laraba da weekend, ni kuma ranakun posting d'ina na fad'a muku, kwana hud'u a sati ne, Monday, Tuesday sai Thursday and Friday_ _Maryam sulaiman ummu elmustapha Ina godiya da jinjina ga ruwan comment d'inki, Ina yinki sosai kuma Ina jin dad'in comment dinki😍👍👍 na dangwala miki wannan page ma na baki shi kyauta_ _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page nine9️⃣ Ganin ta tsorata dashi sai ya sassauta yanayin fuskarshi yace, "kici da kanki ba saina baki ba zaki fi k'oshi". Marairaice mishi tayi kamar zata yi kuka tace, "kayi hak'uri amma don Allah muci tare". Tsare ta yayi da ido kurum yana karantar yadda tayi maganar da iya gaskiyarta, sai kuma ya mik'e tsam ya wanko hannun shi yazo ya zauna yace, "Bismillah". Tare suka ci abincin suna ci suna hirar su irinta ma'abota soyayyah. Saleema ji take tamkar su dawwama haka, tana son khaleefa k'arshe shiyasa take tunanin komai nashi yana da banbanci da sauran maza, a yanzun da suke cin abinci tare sai take k'ara gasgata gaskiyar hasashenta, komai nashi gwanin burgewa, ranar tare suka wuni suna hirar su ta soyayyah, ko sallah tare sukayi ita dashi bai bar apartment d'inta ba sai dare bayan ya tabbatar tasha maganinta ta kwanta bacci. Sai bayan ya dawo gida ya kira Auntie suka gaisa, itama tayi complain akan rashin samun shi kwana biyu, ya bata hak'uri ya gabatar mata da uzurin shi. Sun dad'e suna hira da ita har tayi mishi albishir na zuwanta nan da 3 months watak'ila tare da Ayman idan ya samu hutun k'arshen shekara a gurin aikin su, sosai khaleefa yayi murna yayi ta addu'ar Allah yasa taren ma zasu taho. Sai da suka gama waya da ita sannan ya kira Ayman, anci sa'a yau ba'a samu wata matsala ba sukayi hirar su lami lafiya, shi abinda yafi damun shi kawai yake mishi k'orafi, yayi k'ok'ari ya samu mata daya dawo suyi auren su shi ya gaji, so yake ya mallaki muhallin shi shima, har suka k'arashe maganar su sukayi sallama da juna khaleefa dariya yake yi mishi. Ko bayan sun ajiye wayar murmushi khaleefa yayi yace, "Ayman kenan, Wai yana buk'atar ya mallaki iyalai, wato ni d'in ma kunya ta yake ji". @@@@@@@@ Toh b'angaren raihana kuwa anyi suna lafiya tare da ita, ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Mubarak da Allah yayi wa rasuwa, sai sukayi mata alkunya da samha, Raihana ce ta zab'i sunan ma. Tun da safe da me make-up tazo ta yima Salma aka gyarawa raihana fuska da powder da wetlips, ta shirya cikin riga da zani na wani tsadadden lace, irin wanda akayi musu na kayan sallah da bata saka bane, kowa sai yaba kyaun da tayi yake, sunsha hotuna da me jego da dangin auntien ta sai aunty ziyada da tazo tare da yaranta y'an mata, isowar uwar zuga wato kakarta Inna ce ta korata zuwa saman yuseep da sauri har tana tuntub'e, tayi kwanciyarta a can tana kallo, da yake hayaniya bata dame taba, tana iya yini ita kad'ai ma sai bata wani damu da zaman shirun ba. Hajiya Inna kuwa dama zuwan neman magana ne, tana zama raihana ta fara tambaya, cikin mutanen da suke gurin babu wanda yace mata kanzil har ziyada kuwa, haka ta k'ari bambaminta na banza da wofi da fad'an ita bata ga amfanin wannan karatun da take na boko ba ace, yarinya ko mutuwa akayi a dangi sai dai in tazo hutu tazo dama bikin aure tuni ta soke zuwa bare wani suna. Ganin mutane sun fara taruwa gudun kada aje ayi ta yayata mahaifiyar tasu a duniya sai ziyada ta tausheta, tace ta bari idan aka gama suna taje har gida tayi fad'an ta a can. Da farko hayayyak'owa ziyadan tayi, saida su Salma suka fara bata hak'uri da sauran y'an uwan ummie sannan ta sauko ta hak'ura tayi shiru. Har yamma tana gidan wai kada taje ta tafi a cuci danginta da zasu zo shiyasa ta kasa ta tsare, haka ta dinga zubawa mutane abinci a leda suna tafiya dashi bayan wanda suka ci, lemo kuwa duk kusan mutanen tane suka shanye da wanda yuseep ya ajiye da wanda abban su raihana ya kawo duk ta tattare ta rabar, sai data gama neman rigimarta tsab da sun kewaya matar Abba abubakar na zugata ba'a kulata ba da daddare ta tafi. Salma da raihana suna zaune a parlon sama inda raihana ta wuni, suna tattauna matsalar hajiya Inna, sai suke ganin abun nata kamar ma k'ara gaba yake, ita dai jin dad'in Salma d'aya da Allah yasa kaf fad'in taron ba y'an gidansu yuseep sunyi taron su a can gidan kakannin shi sai yamma suka zo mata kuma basu jima ba suka tafi. A ranar raihana da khausar sai y'ar yayar ummie basu kwanta ba sai bayan sun tsabtace gidan tass! Sun gyare ko'ina. Da sassafe kuwa Ayman ya kirata, bayan sun gaisa yake tambayar ta, "yea zaki tafi yau d'in ko sai gobe". Shiru raihana tayi tana tunanin yadda zata kauce mishi, "Ina ganin sai gobe da safe saboda yau akwai aiki da yawa". "toh Allah ya kaimu a gaishe da Salma a shafa mun kan baby samha" "Zataji" raihana ta fad'a jiki a sanyaye tana ajiye wayar, tunanin yadda zasu kwashe dashi kawai take a duk lokacin da ya samu labarin tayi tafiyarta bata jira shiba..... "Abincin da kika d'ora zai kone Auntie raihana". Cewar Amina y'ar yayar ummie. Da gudu tayi kitchen d'in tana faman zabga salati, tana zuwa ta murde gas ta sauke tukunyar k'asa tana sauke ajiyar zuciya. Ranar bata tafi ba sai yamma bayan an d'iba mata naman suna da yajin daddawa da yawa da zata kaiwa k'awayenta. A gurguje ta gama had'a yanata yanata saboda ta samu damar yin sallama da ummie ta tafi akan kari, tana futowa daga gidan Salma wayarta na fara ringing, silencing d'inta tayi taci gaba da tafiyarta, saida taje gida ta huta sannan wani kiran ya sake shigowa ta d'aga "na rok'e ki kona mintuna biyu ne ki yadda na lek'o mu gaisa naga muhallin ki please raihana". Wannan mutumi nacin shi yayi yawa, raihana ta fad'a a ranta, sai kuma tayi wani tunani, tana ganin ta bakin Ayman ta bashi damar ta gani. Sai tayi b'oyayyiyar ajiyar zuciya. "Zan turo maka address ko na d'ara minti biyu bazan huce sha biyar ba saboda Ina da abubuwa da yawa da zanyi yau". "Ba matsala turon da address d'in". Raihana address ta mishi sending ta text message. Ai kamar yana k'ofar gidan su saiji jin kira tayi bayan few minute, ko data yi picking sanar da ita yake gashi a k'ofar gidan su "Wane gida kenan?". Raihana ta tambaye shi tana tunanin ko bai gane address d'in bane, "anguwa...... Gida mai no..... Shine inda nake tsaye yanzu haka". "Toh fa" raihana ta fad'a tana mik'ewa tsaye "d'an bani minti 5 Ina zuwa". Tana ajiye waya gurin ummie taje da take aikin had'a abincin dare, ta zauna a gefenta tana tunanin ta yadda zata fara sanar da ita, "am ummie.... Ummie dama... Dama dai wani ne muka had'u ranar da naje gidan Salma, toh..... Toh ya dameni tun a lokacin wai sai yazo ya gabatar da kanshi... Toh shine yanzu wai yazo..... Kuma" D'aga mata hannu ummie tayi babu yabo babu fallasa tace, "ki daina wannan kame kamen raihana, kije amma dai kina sane da yau zaki koma makaranta ko?". "Eh ummie" ta fad'a a sanyi, "toh ki kula". Hijab dogo ta zunbulo kan kayan jikinta ta zura takalmi ta nufi hanyar futa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Yana tsaye jikin gidan su k'afar shi d'aya tokare da ginin, sanye yake da shadda milk, fari ne ba dai sol d'in nan ba, ba laifi kyakkyawa dashi, kallo d'aya zaka fahimci ilimi da kud'i sun jika shi. Yana ganinta ya k'araso gabanta ya tsaya, a nutse yake k'are mata kallo ta cikin sun glasses da yake idon shi, "barka dai y'an mata". D'auke kanta gefe tayi tace, "barkan ka dae". "Yakike ya mutanen gidan?" "Kowa lafiya qalou". "Masha Allah". Shiru sukayi 4 a while kafun ya sake cewa, "lastly yau na sake ido hud'u dake bayan dogon jan aji da yanga da akayi mun". "Hum jan aji ne ma?". Cire glass d'in idon shi yayi yana k'ara wara idanun shi a kanta sosai, "Jan aji mana irin na mata masu aji". Shiru ita dai raihana tayi, "toh gashi kince mun baki da wadataccen lokaci, ni kaina daga kasuwa na gudo kada na jima alhajin mu ya fara nemana, Soo am bani dama na gabatar da kaina?". "Me zai hana" ta fad'a fuskarta na kallon wani guri, "toh kamar yadda na fad'a miki nidai sunana Abubakar Muhammad Imran, haifaffen garin Kano anguwar...... Na girma a Kano nayi karatu gwargwadon iko yanzu haka ina kasuwanci tare da mahaifiyana a kasuwar hajj camp, nine na hud'u a gidan mu ina da k'anne uku da suke bina, raihanatu maganar gaskiya na jima Ina neman mace irin ki, kece dai dai da ra'ayina, shiyasa tun a waccen ranar ban yi wasa da damata wajen karb'ar no kiba, duk da daga baya na sare naji tsoron bazaki bani damar da zamu had'u ba haka alak'ar zata kare a waya yadda ta fara. Toh Amma yanzu nagode Allah gani a k'ofar gidan ku raihana, Ina fatan Zan samu amsuwa hannu bibbiyu". Numfashi ta ja mai tsayi kafun tace, "Ni kuma sunana raihana salees abdallah, an haife ni a Kano na girma a Kano tare da mahaifina da mahaifiyata, muna zaune tare lpy nida y'an uwana, yanzu haka Ina karatu a nursing school dake garin bichi". Imran idon shi a kanta yace, "wacce shekara kenan kika fara zuwa makarantar? Don in bakiyi nisa ba sai mu hak'ura da karatun a nemar miki admission a nan cikin gari ko?". Wani kallo raihana ta mishi a ranta tace, "wato guy nan ganin na saki jiki Ina magana dashi yana d'aukar kamar na amince zan aure shine". "Eh mana kinyi shiru kina kallona". K'asa tayi da kanta ta sarke yatsun ta guri guda tace, "wata biyu ya rage mu kammala, yanzu haka muna under teaching practice ne". "Masha Allah har naji dad'i a raina raihana, kinga shikenan kina yin graduation da wata uku sai ayi hidimar auren mu". "Auren mu?". Ta tambaye shi tana zare ido, "eh mana na fad'a miki Ina sonki kuma auren ki zanyi, yanzu kina ganin da wane lokaci zan samu shi abban namu?". Shiru raihana tayi, "kinyi shiru dear". "Ina ganin lokacin dana baka ya huce tun d'azu ma k'arasa saurar maganar a waya". "Okay shikenan nagode babie sai munyi waya". "Okay ka sauka lafiya". Ya d'aga mata hannu ya huce, ita kuma ta koma gida. Sallah kawai tayi ta d'auko kayan tafiyarta, "Nina tafi ummie sai Allah ya k'ara had'a fuskokin mu kuma, nasan dan yanzu ba zamu samu hutu ba sai ko mun kammala exams din mu gaba d'aya". Nasiha ummie ta k'ara yi mata sannan sukayi sallama ta futa. @@@@@@ Raihana ta samu su raheela lafiya, ta basu kayan suna cikin wanda ta taho dasu, ta had'a suda Salma sukayi mata godiya Toh washe garin ranar data dawo sukayi waya da Imran yake tambayar ta ko zai yiwu yau yazo ya gana da mahaifinta. Ita kam raihana har yanzu ta kasa daina mamaki, duk cikin samarin da tayi bata tab'a samun wanda ana fasa aurenta ya shigo da k'arfin shiba irin wannan, sai dai ita har yanzu bata wani jin shi a zuciyarta hasalima binshi take yi kawai saboda ita yanzu bata da wani zab'i ko buri akan mijin aure, shiyasa ta barwa Allah dukkan zab'i, ta fad'a mishi ita ta koma makaranta amma zai iya samun abban ta a gida bayan sallar isha'i, kowanne lokaci idan ya shirya. Yayi mata godiya suka ajiye wayar. A cewar Imran da zafi zafi ake dukan k'arfe, a ranar da daddare ya shirya cikin manyan kaya yaje ya gabatar da kanshi gurin alhaji salees mahaifin raihana, akan yana so a bashi dama ya turo magabatan shi idan har raihana ta amince dashi ayi maganar auren su. Abun ya d'aurewa alhaji salees kai, dama suna tare ne tasan da zaman shi ko kuwa fara mik'o kanshi yayi. Abba ya sallame shi akan idan sukayi magana da raihana zai neme shi da kanshi tunda mahaifin shi ba b'oyayyen mutum bane. Ko bayan ya shiga gida Saida ya tuntub'i ruqayya mahaifiyar raihana da zancen, ta fad'a mishi iya abinda ta sani, tabbas tasan wani yazo sun gaisa jiya da rana amma bata San ko shi bane ko wani ne daban. Sai suka ajiye magana akan zai tambaye ta da kanshi abinda tace su dama basu da wani zab'i sai nata iya kaci dai su taya ta da addu'a. Kamar da wasa saiga tafiya tana Shirin mik'awa. Mahaifinta ya kirata yayi mata tambayoyi akan zuwan Imran ta kuma tabbatar mishi da tasan da zuwanshi. Abu na gaba daya tambayeta shine, "ko tana son shi ta amince da auren shi, saboda shi yayi dukkan bincike baiji an fad'i wani abu na aibu a gurin wanda suka tabbatar da sun sanshi sunsan mahaifin shi wasu har mahaifiyar shima, itace kuma take da d'an matsala itama bame zafi ba, matsalar kawai saboda ta bashi wata y'ar k'awarta ya aura yak'i ne, shine ta cire hannunta akan lamarin auren gaba d'aya. Shida mahaifin shi suke kid'an su suna rawar su. Raihana ta amince da auren Imran saboda ta duba ta hanga bata ga wata makusar shiba, haka kuma yana iya bakin k'ok'arin shi wajen nuna mata so da kulawa, a duniya tasan burin mamanta d'aya taga ta aurar da ita, shiyasa itama ta tattara dukkan attention d'inta yanzun akan aure. An kawo kud'in auren raihana dubu d'ari biyu da hamsin a karo na shida, kud'i mafi yawa a cikin duk kud'ad'en da ake kawowa na aurenta, an tsaida rana nan da wata shida masu zuwa, mutane sunso su bashi shawara me zai hana a d'aga na khausar sai a taru ayi lokaci d'aya, Abba yace Sam ba zai yiwu ba ba'a haka ai kowa da lokacin ta, zasuyi bikin khausar da wata uku ayi na raihana. Lokacin da matar Abba abubakar taji labarin yaron da ya kawo kud'i a wannan karon hankalinta sake tashi yayi, ta shiga damuwa da tunanin yadda kullum yarinyar take k'ara samun masoya da yin gaba, banda haka ace duk wanda ya tafi wanda zai zo sai ya fishi kud'i da komai, yanzu ga irinta nan d'an abubakar Muhammad Imran da kanshi yake son yarinyar, kowa a anguwar yasan familynsu masu kud'i ne gaba da baya. Ranar kasa bacci tayi sai sake sake da tunanin yadda zata tunkari wannan tashin hankali sabo na saurayin da raihanan ta kawo. Ko da Wasa raihana bata fad'awa Ayman abinda ke faruwa ba saboda shi yayi fushi da ita tun waccen ranar data tura mishi text da dare tace ta koma makaranta yayi dogon fushi irin wanda yakan jima baiyi irin shiba. Ta kira shi ba adadi baya d'agawa, sai kawai ta tattara shi ta ajiye a gefe taci gaba da harkokinta amma Allah kad'ai yasan yadda ta damu da al'amarin a cikin zuciyarta, saboda fushin da Ayman yayi yasa lahadi biyu tana hucewa ko zuwa mata baiyi ba. Hakan ya sake d'ingimata har Imran yaso fahimta in suna waya, saboda sai yayita magana bata amsa mishi tana can tana tunani. Shi kuma Imran yanzu damuwarshi d'aya ne yana son ta bashi dama yazo su gaisa sai kewarta yake, tunda fa Suka had'u sau d'aya basu k'ara had'uwa ba, in suna chat ko video call k'in d'agawa take pic d'inta kuwa basu huce uku yake dasu ba har yanzu. Ita kuma tana sone saita fad'awa ummienta abinda tace shikenan. @@@@@@@@ _After one month_ Safiya ce misalin k'arfe 10 da rabi na safe, raihanatu sanye take cikin riga da skirt na les pink colour, kanta babu d'ankwali sai tulin gashi da tayi parking a k'eyarta, fuskarta ko powder babu sai siririn gashi da suka kwanto har gaban goshinta da gefen fuskarta, kallon kanta tayi a mirror sannan ta dubi raheelat tace, "yae nayi kyau ne?". "Sosai ma kuwa banda tsabar iskanci mijin da zai aure ki yazo ganin ki tun daga cikin gari amma ki futa fuska ko powder babu sannan wai don k'arfin hali har tambayata kike wai kinyi kyau". Dariya raihana tayi ta dafa kafad'ar raheelat tace, "raheelatu tawa toh kwalliya itace me?". Fatima ta galla mata harara tace, "oho miki dae amma Allah ki sauya hali, bani powder na shafa mata raheela" raheela ce ta d'auko powder suka zaunar da ita gefen bed suka gyara mata fuska hadda wetlips, ita dai raihana ta zama y'ar kallo sai yadda suka ga dama suka yi da fuskartata a yau. Ta tsaya saroro tana kallon kanta a mirror Fatima ta jawo hannunta, "zo mu tafi ni inba so kike ya gaji yayi fushin zuciya ya koma inda ya futo ba". Duk su ukun suna dariya suka futo raheela ta rufe k'ofar d'akin. Suna tafe suna hira har suka isa inda ya kwatanta mata yana jiranta, ya sha wankan shadda light blue kanshi babu hula amma sumar tasha gyara sai d'aukar take. As usual yanzun ma k'afar shi d'aya a cake take jikin dalleliyar motar daya zo cikinta. Fatima ce ta dank'e hannun raihana dake cikin nata da kyau ta ce, "woww what a nice guy dear". Murmushi kawai raihana tayi ta d'an kai mata naushi a kaikaice, ta dafe gefen cikinta tana fad'in, "ouch a gaban saurayin naki ma sai kin yiwa mutane mugunta in ban koma ba wallahi". Da sauri raihana ta k'ara damke hannunta tace, "I'm sorry toh". Sun k'arasa har inda Imran yake suka gaisa dashi cikin mutumci, shidai rabin hankalin shi duk na kan raihana, saboda a yau yake sake ganin wasu sirrikan kyau da take tattare dasu, wanda a baya duk baisan dasu ba. Bayan sun gama gaisawa zasu tafi kud'i masu yawa ya basu amma suka k'i karb'a, sai da yayi da gaske sannan raheela ta amsa ya basu wata babbar leda ta shopping yace su tafi mata dashi, raheela ce ta sake karb'a suka yi mishi sallama bayan sun gama zuba godiya. "Yae! Baby zamu k'arasa ne?". Kallon shi raihana tayi galala sannan ta kalli inda yake nuna mata, "kana nufin mu shiga cikin motarka muyi hirar a ciki?". "Eh to meye" ya fad'a yana wara idon shi a kanta. Sai tayi k'asa da kanta tace, "babu komai amma me zai hana mu zauna k'asan bishiyar can". Ba musu ya amince tayi gaba yana bin bayanta yayinda yake sake k'arewa duk wani takunta kallo, kai yarinyar nan ta mishi to the extent, komai nata da sanyi abun kallo da burgewa, dole maman shi ta kyale shi akan maganar auren nan saboda shifa harga Allah yayi mata dai dai da ra'ayin shi irin wadda ya dad'e yana mafarkin samu". Ita ta fara zama kan iccen sannan shima ya zauna gab da ita, sunso suyi kusanci da yawa, ta kuma yi niyyar yi mishi magana sai dai yayi mata kwarjini, sai ta kauda kanta gefe ta russuna tace, "Ina wuni ranka shi dad'e". "Ranka shi dad'e kamar wani sarki, Wai raihana har yanzu bakiji ya kamata na samu wani matsayi koda gutsire ne a cikin zuciyar ki ba?". Murmushi tayi tana wasa da tsinken hannunta tace, "akwai wani matsayi dama bayan na amincewa da aurenka?". "Raihana" ya kira sunanta babu wasa, ta amsa a sanyaye ba tare data kalle shiba, "raihana d'ago idonki ki kalleni" ba musu ta d'ago ta zuba kwayar idanunta cikin nashi, sai dai bata iya yarda ta kalli kwayar idonshi da yawa ba ta maida idonta k'asa tana wasa da yatsun hannunta, Dai dai lokacin motar Ayman ta Parker daga nesa da inda suke, zuba musu ido yayi gaban shi yana fad'uwa raihana ce tare da wani guy suke hira, "waye shi" ya fad'a a zahiri, sai kuma wani tunani ya fad'o mishi, "toh ko shine wanda jiya suna hira da iya take bashi labarin ya kawo kud'in auren raihana?". "shin baki ga wani abu bayan matsayin matar da Zan aura cikin kwayar idanuna ba?". Shiru tayi mishi still tak'i cewa komai, "raihana say something mana please shin ba kiga soyayyar ki fal kwayar idanu na ba?". A hankali taji tunaninta yana tafiya wani waje, hancinta suka fara shako wani extra ordinary perfumes, ta lumshe idanunta a hankali ta bud'e kan k'afafun shi da suke zube cikin bak'in takalmin fata, tun daga k'afar ta soma kallonshi har zuwa kan kyakkyawar fuskarshi da bata rabo da murmushi mai k'ayatarwa amma fa a yau babu, kallonta yake da wani irin yanayi kamar ba shine Ayman ma'abocin faram faram da wasa ba. _Comment and share_ 24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page ten 🔟 "Laah Yaya Ayman! Kaine?". Raihana ta fad'a da mamaki, shi kuwa Ayman murmushi ya wanzar take a saman fuskarshi ya mik'awa Imran hannu tare dayi mishi sallama. Shima mik'a mishi hannun yayi sukayi musabiha irinta addinin islama. Ayman bai ko sake tsayuwa a gaban suba kota dede de second ya koma cikin motarshi ya zauna. Imran ne yake tambayar raihana, "waye kuma wannan?". Cikin basarwa don harga Allah ta tsorata da yanayin data gani da farko a tare da Ayman d'in tace, yayanta ne. Imran da bin diddigi sai ya sake tambayar ta, "the same father or the same mother?". "Noop ba d'aya". Ganin tayi kici kicin alamun bata son maganar taci gaba saiya kyaleta. Sunci gaba da hirar su fiye da hour d'aya, ita dai raihana duk ta k'agu ya tafi taje taga Ayman, bata san dalili ba amma duk sai take jinta ba nutsuwa, kamar tayi wani abu ba dai dai ba, shi kuma Imran yak'i tafiya yana nazartar inda hankalinta yafi karkata, yana zargin akwai wata a k'asa tsakanin su ta wani raina mishi hankali da yayanta ne. Ko daya tashi tafiya yaga tana shirin yin sallama dashi a nan gurin b'ata fuska yayi yace, "dear ba zaki rakani gurin mota ba?". Duk'ar da kanta k'asa tayi tace, "okay to muje". Tare suka jera Imran na zolayarta kasancewar shi gwanin barkwanci, sai data kaishi har gaban motar shi, ta jingina kanta jikin motar sannan tace, "sai ince ka gaida gida Allah ya tsare ka ya kare ka ya maida kai gida lpy, a gaishe da hajiya...." "Ban gane me kike nufi ba y'an mata, kina nufin a nan zaki barni?". Cikin rashin gane maganar shi raihana ta tsaya tana kallonshi galala, kashe mata ido d'aya yayi ya d'an matsa gabanta kad'an, "ta Ina ma na shigo nan gurin ne? In baki futar dani ba Zan b'ace fa, In kuma na b'ace keda hajiyata don sai taci tararki, zatace tun kafun ta bani ke d'ungurun gum har kin fara mata wasa dani" Yanayin yadda yayi maganar dole yasa raihana ta murmusa. Shi kuwa a hankali ya bud'e mata front seat yace, "Bismillah". Yanzun ma dai da idon rashin fahimta ta kalle shi sai yayi saurin rik'e kunnuwanshi, "alfarma ce dai na nema iya bakin titi zaki futar dani sai ki dawo". Kamar ta kyale shi saboda taga samun gurin nashi yayi yawa sai kuma zuciyarta ta tuna mata wani abu data manta, "shifa bak'on kine, kuma bak'on ka annabinka ne, kiyi mishi alfarmar nan koda iya ta yanzu ne ko don albarkacin son da yake nuna miki". Ko kafun ta shiga motar saida ta saci kallon motar da Ayman ke ciki dake rufe ruf. Murmushin cin nasara Imran yayi ya kewaya mazaunin driver. Abun mamaki shida yace iya bakin titi sai gashi ya d'auki hanyar shiga cikin gari, ya sake bata wani hak'urin wai yana son ganin garin bichi da kyau. Duk yadda Raihana taso tayi ja inja dashi game da hakan kasawa tayi, daga k'arshe sai kawai ta zubawa sarautar Allah ido, haka yayita shawagi da ita layi layi yana bata labarin daban daban game dashi da y'an uwanshi, wanda raihana sam bata ganewa. Sun d'auki lokaci me tsayi kafun ya d'auki hanyar maida ita inda ya d'auko ta, raihana kawai mazewa take Amma tuni ta cika tayi fam, a ranta abu d'aya kawai take jaddadawa, "kaida sake d'auka na a motar ka har abada". A bakin titi ya sauke ta shi kuma ya huce. Sam bata d'auka zata tarar da Ayman ba saboda lokacin data d'auka yaci ace ya gaji da jira yayi gaba abun shi, jiki a sanyaye ta k'arasa inda motar shi take, ta d'ora hannu da nufin bud'ewa ta shiga kawai ya mata key yayi reverse ya bar gurin. Duk inda hankalin raihana yake in yayi dubu yau ya b'aci, how on earth mutum zai taho tun daga guri mai nisa dominta su samu matsala irin wannan, dama ta fahimci kwana biyu kamar yayi fushi da ita ne shiyasa ba Kiran waya ba zuwa. Ko data koma hostel guri d'aya ta samu ta nutsu tana ta tunane tunanen ta duk maganar dasu raheela suke da kod'a Imran sam hankalinta baya kai, bama ta fahimta k'ark'ari dai in akayi abu tayi murmushi. Daga k'arshe ma sai kawai ta juya musu baya tayi kwanciyarta. ********* Shikam Ayman ta b'angaren shi Sam bai fahimci a halinda yake ciki ba tun daga lokacin daya samu raihana tana hira da wani bashi ba a inda suka saba zama duk lokacin daya zo mata weekend, da farko yayi niyyar juyawa sai dai ya kasa tafiyar kuma, burin shi bai huce ya ga tafiyar guy ba saiya tafi, yana nan still sai yaga sun taho raihana ta shiga motarshi, koda wasa bai tab'a d'auka bayan shi raihana zata iya sakewa da wani namiji har ta shiga motarshi su futa ba, ko fad'a mishi akayi bazai yarda ba, amma sai gashi yau a gaban idon shi tabi wani saurayi bayan gashi yana jiranta ta sani kuma tana kallo. Still kuma suka jima basu dawo ba, yana tunanin ma ta manta dashi, bai ji ranshi ya sake b'aci ba saida ta nufo inda yake tabbacin tana sane da wanzuwar shi a gurin yana jiranta, a wannan lokacin ne ya kasa hak'uri, toh in tazo me zata ce mishi ma, yasan raihana bata kasance ma'abociyar k'arya ba, ba zaiso kuma a kanshi garin kare kanta ta fara ba. Shiyasa tana zuwa yaja motar shi yayi gaba. Wannan abu daya faru tsakanin raihana da Ayman shine ya zamo abu na farko daya fara tsoratata har tunanin ta yaje inda bai tab'a zuwa ba a kanshi. Shima kuma shine karo na farko da wani abu ya tab'a zuciyar shi, yana ganin tunda take yin samari bata tab'a irin wannan daya gansu tare ba, duk dashi mutum biyu ya tab'a gani a cikin biyar d'in da suka fasa aurenta, amma duk da haka yana ganin babu mai rawar Kai daya tsorata Ayman kamar Imran, ko don duk wad'an can masu aure ne sun huce shekarun yin abu na samar taka irin nashi sai wannan. Da rana a kwance Auntie ta same shi kan carpet kamar wani mara galihu, ba bacci yake ba amma yana jin shigowarta ya maza ya rufe ido kamar me yin baccin, tasan Sarai ba baccin yake ba amma tunda ya nuna hakan yana nufin baya son takura ko magana da kowa a lokacin. Don haka saita juya a nutse ta fuce daga d'akin. Daga baccin gujewa tambayoyin auntie sai gashi na gaske ya riske shi nan k'asa. Da yamma bayan ya farka, wanka ya sake yi ya shirya cikin wasu kayan riga da wando na yadi d'inkin irin na matasa da suke yayi a lokacin, kayan sun amshe shi sosai yayi kyau kwarai, saida ya fara gabatar da sallar la'asar data kwace mishi sannan ya kira wayar Nur ya fad'a mata yana hanya ta had'a mishi abinci mai sauk'i da tasan in yazo zaici, lokacin daya kira Nur bacci take yi cikin magagi sukayi magana, amma tana jin abinda ya buk'ata take ta watstsake kuma ta tabbatar mishi da zatayi kamar yadda yaso, murmushi yayi bayan ya ajiye wayar. Hannun shi rik'e da car key ya nufi parlon auntie. Bayan yayi knocking ta bashi izinin shiga tura k'ofar yayi ya shiga bakin shi d'auke da sallama, tana zaune tana aiki da system ya k'arasa gareta gently ya zauna kusa da ita yace, "Auntie barka da yammaci". Kallo d'aya tayi mishi ta maida kanta ga abinda takeyi tace, "barkan ka dai, d'azu naje na tarar kana bacci, Ina fatan kaci abincin ka?". D'an b'ata face yayi yace, "eh na d'an kwanta na huta ne, yanzu gidan su Nur zani nasan Zan samu abinda zanci a can". "Anya kuwa har yanzu kana sakewa kaci wani abu a gidan mami?". Murmushi yayi tare da mik'ewa tsaye yace, "noop but insha Allah yau zanci". "Toh Allah yasa". Daga haka sukayi sallama ya d'auki hanyar futa daga parlon. Gidane babbah mai k'aton compound da parking lot a gefe, zaune suke kan brown kujerun katako gaban su well round table cike da flate flate da glass cups masu kyau da tsada. Kyakkyawar yarinya ce fara, mai matsakaicin tsawo da k'iba, tayi kwalliyar ta sosai cikin riga da zani na lace maroon, ta yafa gyalenta match da kayanta a gefen kafad'ar ta, kallo d'aya zata fassara maka ita d'in asalin jinin sameera ce saboda kamannin da suke yi, gefenta Ayman ne zaune ya d'ora k'afar shi d'aya saman d'aya yana dariyar hira mai dad'i da Nur take yi mishi a lokacin. "Allah sweetheart ya kamata kaci abincin nan kafun a jima kace mun kai tafiya zakayi sai wani lokacin". Nur ce meyin wannan magana cikin siririyar muryarta. Ayman yana dariya still yace, "ai kece babie kika d'auko hanyar cika mun ciki da dad'ad'an labarun ki, shiyasa koda yaushe bani da burin daya huce nazo na ganki, ke ni kaina har mantawa nake da kaina a duk lokacin da muka kasance tare da ke balle wata yunwar cikina, Ina sonki da yawa matuk'a Nuriyyata". Murmushi nuriyya tayi ta fara zuba mishi abincin data girka da hannunta domin shi a plate tana fad'in, "yau dai duk wayonka sai kaci abincin nan in ba so kake kuma mu b'ata ba....". "Nina isa ai yau ba zan tab'a k'in cin abincin dana tashe ki a bacci nasa kika yiba". Sai ta tsaya da abinda take ta kalleshi, idanun shi ya lumshe mata yace, "duk da baki fad'a ba amma na sani, ai naji yanayin muryarki". Murmushi kawai tayi ta girgiza kai Tura mishi plate d'in tayi gaban shi bayan ta gama had'a mishi komai tace, "Humm nifa ba bacci nake ba, in ma baccin nake aikin ka ai yafi shi muhimmanci". Ayman yana kallonta yace, "Allah ko sweetheart?". "Sosaima" ta fad'a da murya k'asa k'asa. Sunci gaba da hira cikin happie ta b'angare guda Ayman yana cin daddad'an abincin data dafa mishi. Sai da yaci da yawa sannan yasha Ginger and lemon masu sugar baya baya, shima yayi dad'i cox Nur ta samu horo indai ta b'angaren aikin girki ne, sam sameera bata saba musu da sangartacciyar rayuwa ba, aiki suke kamar kowanne yara dan ita gidanta ma ba me aiki, suna tasawa ta sallame ta. Ayman bai bar gidan su Nur ba ranar sai daf da magrib shima don ya yakice ne da sai yayi sallah a anguwar Nur zata barshi ya tafi. Tuni ya manta da tension d'in wani raihana ko ya tunata baya jin irin wancen b'acin ran da tashin hankalin, tafiya yake slowly kamar ba shine ya futo daga gida a hargitse ba, shiyasa yake son ganin Nur kowanne lokaci saboda tana d'ebe mishi kewa, ba don kunya da take tsakanin shi da mamin suba da kullum sai yazo gidan. _Wannan kenan_ Toh raihana kuwa duk cikin satittikan da suka biyo baya sukuku tayi su, ga Imran da takurar Kiran wayar shi, ga Ayman da ya juya mata baya, ko wayarta baya d'agawa, gashi ita kuma alk'awari ne saita kira shi da tunanin ko ya huce fushin nashi amma har tsyi ring ta gama baya d'agawa. Ranar da sati ya cika cif da zuwan Imran, raihana tana shanya gama wankin innerwears d'inta kenan, taji wayarta tayi k'ara, kamar karta duba don tasan Imran ne shine baya gajiya da da kira da text, sai kuma tayi tunanin ko daga abban tane, don lokacin tana tsammanin shigar kud'in abincinta daya d'auko hanyar k'arewa. Tana dubawa kuwa taga kud'in ne aka saka amma ba daga abban taba daga Ayman. Zama tayi gefen bed ko tsayawa saurarar surutun su raheela batayi ba ta dannawa no shi kira, dama a satin kwana biyu ne kad'ai bata tab'a shiba itama tayi zuciya, katsewa yayi ya mata text kamar haka, "Ina inda muka saba had'uwa". Raihana ai da sauri ta mik'e tana duba shigar jikinta, a lokacin wata bubu ce a jikinta ta roba robar yadi ta kamata kad'an, ganin Ayman ne sai kawai ta zunbula hijab dogo ta fuce, "yana zaune kan iccen bishiya ya duk'ar da kanshi k'asa. Raihana ta Isa da sallama, sai ya ajiye abinda yake ya sake gyara zaman shi donta samu gurin zama. Raihana ta zauna tana gaishe shi, "Yaya Ayman Ina wuni". "Lafiya Lou ya karatu". Raihana tace, "alhamdulillah, sai naga sak'o yanzun, nagode Allah ya k'ara rufa asiri" "Ba komai gani dai banyi zuciya ba na sake dawowa. Kallon shi tayi narai narai da idanunta kamar zatayi kuka tace, "kayi hak'uri Yaya Ayman don Allah... Ranar ne gaba d'aya kawai dai kayi hak'urin ma zance, tabbas na b'ata maka kuma nasan ban kyauta.....ba". Murmushi kawai yayi ya sake maida cikakken duban shi gareta, "u are changing raihana, sauyawa kike a kullum safiyar Allah, sai dai bansan dalili ba, kinga da farko haka rannan munyi magana dake zan dawo dake makaranta sassafe, kikayi tahowar ki baki jira niba, na biyu ashe an kawo kud'in auren ki, shima nida ke baki fad'a mun ba, na uku ban tab'a zaton zaki iya amincewa da wani namiji har ki sake mishi irin yadda naga kin yiwa saurayin ki a waccen ranar ba, raihana ya kamata kiyi taka tsantsan da rayuwa da samarin yanzu ma kansu gaba d'aya". Sai ya kife kanshi a tafin hannun shi yaja dogon numfashi ya fesar da iskar ta bakin shi, "a gaskiya har na fara tunani anya kuwa kin d'auke ni irin yadda na d'auke ki a cikin zuciyata? Raihanatu anya kina kallo na da fuskar d'an uwanki abokin ki abokin shawarar ki....". Shiru tayi jigum tana sauraron maganganun shi da take ganin bai fahimtar ta bane kawai, kuma yanzu tunda ya fahimceta ba dai dai ba, bazai tab'a gane abinda zata fad'a cikin sauk'i ba, sai kawai ta had'a hannuwanta tace, "I'm sorry Yaya Ayman, I'm really sorry, insha Allah zan tabbatar maka da gaskiyar yadda komai yake, da sannu zaka gane matsayin ka ya huce na yadda duk kake zato ko tsammanin baka kaiba". "Toh Allah yasa raihanatu". Sunyi shiru kafun raihana tace, "ya Auntie da Nur?". "Auntie tana lafiyarta qalou, Nur ko jiya da yamma ms muna tare, kinsan auntie weekend ne lokacin bibiyar business d'inta, sauran ranakun tana wajen aikinta, to Ina kwance kawai naji zaman gidan ya isheni shine na tafi gurinta muka sha hira ta d'eben kewa, yauma Auntie bata san na taho nan ba saboda tun safe ta futa solving wani case". "Allah sarki nuriyyah ma kwana biyu bamu gaisa ba, ya karatun ta kuwa? Sun kusa gamawa ko?". "Ina fa.... da saura sosai, almost a year ma". "Ayyah na d'auka course d'inta ai 2 years ne" "A'a 3 years ne ba 2 ba". Raihana tace, "toh Allah ya basu sa'a suma? Yasa a gama lafiya musha biki". Zaro ido Ayman yayi yace, "au kina nufin har sai nan da shekara za kusha bikin? Bayan kema auren ki zakiyi ba da jimawa ba ki tafi ki barni". Raihanatu tace, "eh idan zaka iya jira har shekarar dama nake nufi, idan kuma ba zaka iya ba zaku iya yin auren ku ko yanzu in yaso saita k'arasa a hankali a gidanta". Ayman yace, "Ina kinsan Allah raihana ban k'i ba ko yanzu a d'aura mana aure da Nur, amma ba komai insha Allah nan da watanni shida za'a yi maganar auren mu, dalili d'aya ne zai kaini ma jiran wata shida ko bakwai nan gaban". Raihanatu cikin taya shi murna sosai tace, "Kai Masha Allah ai haka nafi so nima Allah yasa bikin mu ya zama lokaci d'aya......". Sai kuma ta k'arasa fad'a slowly da sagaggen gwiwa a ranta tana fad'in, to nida ba lallai wannan d'in ma ayi dashi ba. Shima jikin shi a sanyaye ya amsa mata da "ameen". Jin tayi shiru sai Ayman ya tambayeta, "raihanatu kina lafiyarki kuwa?". Raihana cikin basarwa ta k'ak'alo murmushi ta wanzar a saman innocent face d'inta. Ayman tsayawa yayi yana kallonta a lokacin da ta ware fararen hak'oran ta tana murmushi mai kama da dariyar yak'e da sunan farin ciki. Yana tunanin ba abinda yafi k'ara mata kyau da futo dashi kamar dariya ko murmushi, shiyasa yake son yaga dariyar raihana ko murmushinta a lokacin da suka kasance tare. "Wata nawa aka sa auren ki?". D'an sassauta yanayin tayi ta juyo opposite d'in shi tace, "wata uku ne". Dum! dam! K'irjin Ayman ya bada, sai ya kasa fahimtar kanshi a lokacin shin farin ciki yake ko akasin haka, cikin bak'on yanayin daya farmakeshi lokaci guda yace, "yanzu fa shikenan da kinyi aure mun rabu ko?". Sai lokacin itama gabanta ya fad'i, tayi shiru tana kallon shi eyeball to eyeball, abubuwa da yawa suke tunani a ransu a lokacin kafun yayyafin ruwan sama ya fara sauka a kansu. Sai a lokacin duk suka ankara suka baro cikin duniyar mafarkin da suka fara shiga, suka mik'e tsaye suna kallon yadda gari ya had'a hadari bak'ik'irin, toh duk me sukeyi haka basu ankara ba? Ayman ne yace, "raihana mu k'arasa cikin motata kada ruwan nan ya tab'a ki ki soma wannan murar da zazzab'i da basa jin magani". Tsayawa raihana tayi tana kallon shi maganar da sukayi da auntie na kai komo a cikin ranta. "Taho mu tafi mana raihanatu". Jikinta duk a sanyaye tabi bayan shi lokacin tuni ruwan ya soma k'arfi saida gudu gudu suka k'arasa motar ya bud'e musu gidan baya suka zauna. Raihana kwantar da kanta tayi jikin kujerar motar tana sauraron daddad'an k'amshin turaren shi daya kama motar. Hijab d'inta duk ya jik'e da ruwa da yake roba ne sai duk ya fara lik'ewa a jikinta. Kallo d'aya Ayman yayi mata a yanayin ya d'auke kanshi yana duba cikin motar, akwai k'aton bargon auntie sai ya bata ta sauya hijab na jikinta dashi. Hannunta biyu rungume duka a k'irjinta ta kwantar da kanta tana jin yadda ruwa me k'arfi yake zuba kamar da bakin kwarya a lokacin, shi kuma Ayman ya d'auko wayar shi yana dannawa, a wannan yanayin raihana tayi bacci wanda yasa har aka gama ruwan bata sani ba. Tsayawa Ayman yayi yana kallon fuskarta saboda dad'in bacci har bargon ya zame daga kanta sai manya manyan kitson kalba da suka sauko saman kafad'arta suna shek'i, a hankali yaja bargon ya k'ara rufe mata kanta ruff sannan ya sauke ajiyar zuciya. Agogon hannun shi yake dubawa lokacin sallah yayi har ya huce ana ruwan nan. A datsin lokacin raihana ta farka ta dubi Ayman da idanunta da suka sauya kala, sai kuma ta watstsake fuskarta sosai, "yaaa Salam yau na rik'e ka ko?" "Bake kika rik'e niba raihana ruwan da akayi ne". Tare suka futo daga motar ita dashi hannunta d'auke da jik'ak'k'en hijab d'inta shi kuma leda, gabanta ya kewayo ya mik'a mata ledar ta karb'a tana yin godiya. A gurguje sukayi sallama saboda duk gari ya d'au sanyi. Raihana tana shiga hostel raheela ta tarye ta tana fad'in, "Amma dai ba'a inda kuke zama da Ayman yauma kuka zauna ba, saboda ana ruwan nan da hankalina yak'i kwanciya har lek'a ku nayi naga bakya nan". Hijab da ledar hannunta ta ajiye, fatima tace, "ai da kin daina tunanin saurayin tane raheela, bashi bane Yaya Ayman ne tunda naga wannan ledar me tambarin M". Matsowa raheela tayi kusa da ita tace, "har naji hankalina ya d'an kwanta indai Yaya Ayman ne ai munsan shi shekara da shekaru da sauk'i, wancan d'in ne dai har yanzu bak'o a gurin mu bamu gama sanin shiba tukun" Raihana da fatima duk dariya sukayi mata. Ledar daya bata ta zazzage turaruka ne masu tsada guda biyu, da kayan kwalliya na mata dangin su powder da janbaki, sai chocolates masu tsada guda hud'u. Turaren d'aya ta d'auka, ta basu d'aya, powder da sauran tarkacen ta zuba su cikin kayan shafar su tace mun k'ara samun na shafawa, ta d'auki chocolate biyu ta basu dai d'aya. "Ummm! Gaskiya raihana Yaya Ayman yana ji dake, kinji dad'in chocolate d'innan kuwa?". Raheela ce me yin wannan maganar. Kallonta raihana tayi hadda wani lumshe ido take tana cin chocolate d'in da iya gaskiyarta, zungurar fatima raihana tayi tace, "kisawa mutuniyar ki waigi". Fayima tana dariya tace, "lallai kam Yaya Ayman ya iya kyauta, Allah kisha kiji da gaske take chocolate d'in da dad'i ba wai Santi bane". Raihana tana zaro ido tace, "au kema?". "Allah gata irin wadda kike so less sugar kuma creamer". Guda d'aya ta d'auko cikin wanda tayi nufin ajiyewa muhibba mayyar kayan zak'i, ko data gutsira itama ala dole ta lumshe idanunta, raheela ta dafa kafad'ar ta tace, "raihana kinji ko? Wallahi Yaya Ayman ya iya kyauta, gaskiya ya kamata ki kirasa ki k'ara yi masa godiya". Girgiza kai raihana tayi bayan ta gama cinye ta bakinta tace, "wannan ba kyautar Yaya Ayman bace, ta Auntie ce". _Monday Tuesday, Thursday and Friday_ _comment and share_ 24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page Eleven1️⃣1️⃣ "Wacece Auntie kuma?". Raihana tace, "Kae! Auntie fa mahaifiyar Yaya Ayman ce". "Au wai dama maman su kike nufi in kuna waya inji kina tambayar ina auntie". Fatima ce me yin wannan tambayar tana jefa chocolate baki. Ita kam raihana murmushi kawai tayi ta gyad'a mata kai. Haka dai suka yita cin chocolate suna magana kamar wasu tab'ab'b'u, a daren ranar raihana bata kwanta bacci ba saida sukayi waya da Ayman suka k'ara tabbatar da komai ya huce tsakanin su. @@@@@@ Tun daga wannan rana raihana da Ayman suka ci gaba da zama lafiya kamar yadda suke a da, karatun su raihana ya d'au zafi saboda k'aratowar final year exams d'insu. Zuwan Imran biyu bayan wancen zuwan, shima duk bada amincewar taba sai dai ta ganshi unexpected, amma ana katari duk cikin zuwan bai tab'a zuwa ranar lahadi ba shiyasa basa had'uwa da Ayman da duk Sunday sai yazo har yanzu ba fashi. Sosai Imran yake kashewa raihana kud'i har account no ta ya d'auka da wayo a wayarta yayi saving a wayarshi, lokaci bayan lokaci yana mata transfer na kud'i masu nauyi, ita dai raihana bata tab'a d'aukar irin kud'ad'en shiba har tsoro take ji ta nuna a gida, don tasan fad'a za'ayi mata ace tana sane ta bashi account d'inta, ba zasu tab'a fahimtar komai cikin sauk'i ta waya ba, amma tayi alk'awarin data koma gida zata fayyacewa ummie komai yadda zata fahimta. @@@@@@ Rana na sauri wajen bada kwana, yayin da kwana yake saurin taruwa ya had'aa satittika, haka satittika suka bada watanni har gashi yau watanni biyu sun cika cif. Raihana sun zana jarrabawar k'arshe lafiya har ana maganar a gobe in Allah ya kaimu za'a d'anka musu kwalin kasancewar su cikakkun malaman jinya wato (nurse), sunyi shirye shiryen su na d'alibai komai ya kammala, haka gidansu raihana ma shiri suke babu kama hannun yaro, saboda gida biyu da hidimar tasu ta kasu hadda na bikin khausar a week after raihana's graduation. A daren ranar raihana kwana sukayi basuyi bacci ba suna koke koken rabuwa da juna da zasuyi, kowa ka gani cikin su idonta a kumbure saboda yawan kuka, ba dama d'aya ta kalli d'aya su had'a idanu sai kawai su b'arke da kuka, har cewa suke dama iyaye d'aya ne suka haife su su duka ukun. _nace sai hak'uri dama haka sabo da shak'uwa suke_ Misalin k'arfe takwas na safe suka shirya cikin white and black uniform dukkannin su d'alibai 200 da za'a yaye a wannan rana. An gayyaci manyan mutane masu muk'ami daban daban sunyi jawabai, haka wasu daga cikin d'alibai ma sunyi jawabin su. Abun gwanin burgewa da k'ayatarwa gurin kallo. Basu tashi taron ba sai kusan 12 bayan ai baiwa kowa result d'inta a cikin su. Nan fa kowa yayi gurin familyn shi don su gana, raihana da Ayman ta fara cin karo a lokacin da take futowa, kusa dashi Nur ce tayi kwalliya cikin wata tsadaddiyar doguwar riga maroon, tayi kyau sosai. Tun daga nesa data hango raihana take washe baki tana d'aga mata hannu, raihana ma tana murmushi ta k'araso suka rungume juna, "kece yau har garin mu Nur? Ni yaushe rabon ma dana ganki". Nur tana murmushi ta karb'i kwalin hannun raihana tana fad'in, "ai dole nazo raihana tunda ta kama ni dole". Duk sukayi dariya, sai lokacin raihana ta gaisa da Ayman daya kafeta da idanu yana kallon duk wani motsinta, tayi mishi kyau k'arshe sanye da kayan kamar ba uniform ba. Sun tayata murna a nan kafun su futo tare su k'arasa inda y'an gidan su suke. Ga mamakin raihana sai taga auntien su Ayman tare da ummienta da iya suna hira k'asar rumfar da aka tanada domin bak'i, sai y'an matan familyn su dangin ta y'ay'an yayyen ummie guda biyu, har k'asa raihana ta durk'usa tana gaishe su, Suka amsa suna tayata murna, iya nata zolayarta, ita dai nauyin surayyah duk ya hanata kula iya yau, a gurin ma kasa tashi tayi saida auntien ta kamo k'afad'un ta duka ta mik'ar da ita zaune. Kusa da ummienta ta k'arasa ta zauna gefenta ta kwantar da kanta a kafad'ar ummien, ummie ta dafa kanta tana tayata murnar kammala karatunta lafiya, jidderh da muhibba ma saida sukayi mata congrats, raihana ta mannawa auta jidderh peck a kumatu tace, "thank you auta". Sunyi hotuna da wayoyin su na hannu da photographer da Abban raihana ya turo don shi bai samu damar zuwa ba, daga ummie sai muhibba da auta jidderh ne a y'an gidan su sai su hapser da sukazo su biyu. Ragowar family suna gida suna dakon isowarta. Basu bar makarantar ba saida raihana ta nemo su raheela suka gaisa da y'an gidan su, suma ta gaisa da nasu familyn. Sun rabu akan sai sunzo bikin khausar. Wajen tafiya ummie da motar Abba suka koma, don a ita suka zo, surayyah kuma ta d'auki iya, raihana tabi motar su Ayman da Nur bisa takurawar Nur d'in. Suna tafe suna hira da nuriyyah da take front seat gefen habeebynta, duk rabin hirar akan banbance banbancen karatun su nema da wahalar da suke sha akan common diploma, Nur tana tayi mata complain na nadamar da tayi data sani ma degree ta nema tun farko kamar yadda auntien ta shaheeda tayi. Yayinda raihana take ganin diplomar ma ba laifi don dai an had'a suda wahalallen course me cin lokaci ne. Suna k'arasawa anguwar su kowa yayi nashi guri don surayyah ko gidan bata shiga ba sukayi gidan iya ita dasu Ayman, (Surayyah da ruqayyah suna huld'a amma irin baya bayan nan, idan abu ya faru na farin ciki ko jaje da taya murna, sukan jewa juna in sun samu labari, haka idan sun had'u suna gaisuwar mutumci, tsakanin su kowa na ganin girman d'an uwan shi). Raihana kam godiya da sallama tayi musu ta shige gidan su. Can ta tarar dasu Salma da baby samha, y'an uwan ummie da y'ay'an su duk sunzo anyi girke girke na alfarma, nan fa raihana aka had'u da family ana ta hirar yaushe gamo. Ummie komai da sukayi na taro saida ta aikawa su auntie dashi gidan iya. Babu dangin abbansu ko mutum guda, sai abun ma yafi musu dad'i akan suzo suna d'auki ba dad'i. Haka sukayi taron su suka gama cikin lafiyar Allah. Dama a daren ranar raihana kashe wayarta tayi saboda takurar kiran wayar Imran. ********** Washe garin ranar duk yadda Raihana take da sammako kasa tashi tayi saboda gajiya, duk jikinta banda nuk'urk'usa babu abinda yake yi. Koda ta tashi a late ta gabatar da sallolinta komawa tayi ta kwanta, har eleven tana bacci saida ummie tasa a taso ta kada yunwa tayi mata lahani sannan. Bayan tayi breakfast ummie tasa aka d'auko kayan lefen khausar ta gani, babu laifi guy yayi k'ok'ari kusan set shida na akwatuna masu kyau da daraja, haka kayan ciki ya zuba kaya best quality masu tsada da kyau. Raihana addu'o'i tayi sosai ta taya y'ar uwar tata murna da fatan samun zaman lafiya mai d'orewa a gidan aurenta. A satin gadan gadan aka kama hidimar biki ba kama hannun yaro, shiri suke bana Wasa ba suna b'atar da kud'i kamar ba'a tab'a bikin wata yarinya a gidan ba Family na kusa dana nesa duk sun hallara ana I gobe traditional sitting, Salma kuwa dama tun kwana uku da suka gabata ta tattaro tazo, gida ya cika Masha Allah sai son barka. Ana I gobe kamu da safe ummie ta rabawa su raihana ankon su da aka kawo daga gurin d'inki, atamfa ta yini sai less da shadda, a hakan ma ummie complain take da ba'a yiwa raihana les d'in ba saboda sababbin kayanta ma da bata tab'a sakawa ba sun kusa goma. D'an kunne kuwa da sark'a ba'a k'aro mata ko guda ba, taji da wanda auntien Ayman ma take aiko mata lokaci bayan lokaci. Salma da take karyawa a lokacin tayi ta mata dariya, tana fad'in in bata so a tattaro mata ita tunda ta k'i sawa. Ummie da take zaune a parlon har lokacin tace, "Eh ke kuma ki kai naki tsumman ina? Ba gara raihana ba za'a ce rashin samun lokaci ne duk abinda za'ayi tana makaranta ko an mata anko sai dai a ajiye dole, ke kuwa kayan ne gasu nan lifdi lifidi ba kyauta ba sadaka wasu ma kin manta dasu suna can suna tsine miki a wardrobe". Hucewa d'aki raihana tayi da kayanta tana dariya k'asa k'asa. Dama ummie ce maganin Salma ai wani lokacin. Duka riga da skirt ne d'inkin sai shaddar akayi mata doguwar riga, kayan sunyi mata kyau sosai. Tana ninkewa su hapser suka dawo daga gantalin nemo k'osai a anguwa. Su duka hud'u suna dariya suka shigo suna fad'a ma raihana ai basu samu k'osai ba sai wata jagwalgwalalliyar awara a idoma idan ka ganta kamar ayi amai. Dariya raihana ta dinga yi musu, "ai na fad'a muku ba zaku samu k'osai a anguwar nan ba kuka k'i, nima wanda naci kuna bacci iya ce tayi ta aiko mun, tunda Yaya Ayman ya fad'a mata Ina son k'osai toh kuwa indai tayi Ina gida saita aiko mun dashi". Xee ce ta balla mata harara tace, "gaskiya raihana bakiyi ba, amma ko guda baku rage mana ba kika bammu da jin k'amshi". Salma da take parlour tana jiyo su tace, "toh sarakan son banza ni kaina da nake jego bata ajiye mun ba bare wasu ku". Duk waje sukayo gurinta dama a k'iris suke sukayi mata caaa suna fad'in, "ai ke wannan ke kika so, muka ga da mijin ki da komai kika wani tattaro kika barshi wai kinzo kwanan biki". Hapser tace, "fad'a mata dai xee aini ko baki raihana tazo zatayi saina hana haka kurum". Ido bud'e Salma ta kalle su, "au hakane ma abun?". Ameena da bata ce komai ba ta samu kan kujerar dake kusa da Salma ta zauna tana fad'in, "yanzu saboda Allah Salma ke kin yarda mijin ki duk safiya yazo nan ganin ki da dare kuma ki ajiye mana samha ku tafi yawon barbad'ar cin abinci restaurant". Raihana ma futowa tayi rik'e da wayarta tana replying text d'in Imran, Zama tayi bayan gama abinda take cikin k'asa da murya tace, "ba sai in ma gidan cin abincin suke zuwa ba.....". Duk a gurin kowa zaro ido yayi, xee da k'arin abun haushi hadda tafa hannuwa, "kice wani gurin da ban sukeyi?". Salma tayi narai narai da ido tace, "kiji tsoron Allah dai Auntie raihana". Raihana tace, "toh da tsoron ki zanji keda yuseep d'in ai duk manyan y'an iska ne, abun daya fi wanda na fad'a ma zaku iya yi, in kuma ba tsoro ba ki k'aryata ni yanzu in bud'e miki aiki, kinsan dai....?" Kamo hannunta Salma tayi tana dariya tace, "haba auntie na kar mu fara yin haka dake mana, kinga gasu zee da ameena nan sun zubo mana ido" Dariya raihana tayi, ameena tace, "don Allah Salma ki k'aryata raihana muji abinda yake b'oye". Mak'e musu kafad'a tayi tace, "umm umm ai ba kyau ma k'aryata wanda ya girme ka koda second uku ya baka a duniya kuwa balle Auntiena data bani kusan shekara". Wata irin dariyar shak'iyanci duk sukayi a d'akin zee tace, "Allah raihana kece maganin Salma". Ameena kuma tace, "ai ba Salma kad'ai ba raihana maganin kowa ce don dai tana shiru ne". Haka sukayi ta hirar su irinta y'an matan da suke ganiyar k'uruciyar su, a tsokani wannan a tsokani waccen, Salma dai da taga zasu tire ta k'arshe sai tabar musu d'akin. Har amarya ta dawo daga gidan gyaran jiki. Washe gari suka tashi da kamu, a wani k'aton kango da Abba ya siya aka gudanar da walimar kamun, anci ansha anyi wa'azi mai shiga jiki da sanyaya gab'ob'i, amarya tayi kyau cikin lafaya milk and brown data haska ta sosai, su raihana kuma cikin d'inkin doguwar rigar kamfala mai kyau da tsada, tsabar bak'in ciki dangin abbanta duk wanda suka had'a ido saiya zabga mata harara, kamar kowanne lokaci in ana biki ko suna sukan yi k'ananun maganganu da yada habaici wannan karon ma ba'a barsu a baya ba, ita dai ummie tuni ta saba da halayyarsu y'an uwanta kawai ta jaddadawa duk abinda zasuyi don Allah suyi hak'uri karsu kulasu, da an gama bikine zasu kama gabansu kowa tayi nata guri. Alhamdulillah an tashi kamu lafiya kowa yasan inda ya nufa. A daren ranar kusan kwana su raihana sukayi suna hira saboda k'aruwa da sukayi da kusan mutum 6 sa'o'insu masu aure da y'an mata. (Tunda su familyn su na wajen uwa ba masu matsala da takura bane, y'ay'an su basa aure har sai sunyi NCE ma, wasu ma suna tsaka da karatu a university Allah yake kawo musu miji suyi aure ba k'aramar magana bare gajiyawa da y'ay'a) Ranar Saturday ango ya shirya k'asaitaccen dinner party a d'aya daga mafiya kyau da sauk'in kud'in event center. Amarya tasha kyau cikin blue black net da yaji d'inkin gown mai kyau irinta amare. Fuskarta tasha make-up mai kyau da tsari. Raihana yau ankon lace d'insu tasa wanda akayi mata d'inkin riga da skirt dai dai jiki, d'inkin ya zauna mata dass gwanin burgewa, ita yau tayi make-up amma light ko eye lashes bata yarda an saka mata ba. Anyi biki dangin amarya da dangin ango y'an mata sunsha rawa samari na musu lik'i, ita dai raihana tana gefe, Sam bata da rawar kai irin na y'an mata, ko d'an zirga zirgar kula da bak'i batayi kamar y'ar gayyata. Bayan an tashi biki gidan su ya cika fal da mutane saboda d'aurin auren gobe, sai ya zamana sun rasa inda zasu kwana ma, d'akunan su tuni dangi sun gaje, gashi su ba wani huld'a suke da mutanen anguwa sosai ba in aka d'auke gidan iya babu gidan da take shiga a layin bare su shiga suyi dabdala. Wani tunani ne yazo ranta a lokacin da suke zaune a parlour jigum suna tunanin abinyi ita dasu xee. Sai ta nufi d'akin ummie direct, suna zaune ita da mammie (yayarta kenan) sun saka khausar a tsakiyar su suna maganar da raihana bata san kota meye ba, da sauri raihana tayi baya tace, "kuyi hak'uri na shigo muku ba excuse". "Ba komai ki shigo dama ruqayya yanzun ta gama cigiyar ki". Mammie ce keyin wannan magana. K'arasa shiga raihana tayi ta jingina da closet. "Kun samu inda zaku kwanta kuwa?". Ummie ta tambayeta. Da sauri raihana tace, "a'a ummie amma dani cewa nayi ko zamu tafi gidan iya kawai mu kwana a can kona iya yau ne". D'an jim ummie tayi don ita har ga Allah bata fiye son wannan had'in hark'allar ba, "Ina ne gidan iyan?". Mamie ta tambaya. Kafun raihana tace wani abu Auntie tace, "gidan limamin masallacin anguwar nan ne, shine wanda kuka amshi cooler d'azu a gidan". Mammie tace, "Okay to suje can mana idan babu damuwa?" "Kuna da yawa ai kuje" ummie ta fad'a sannan ta dubi raihana da muryar gargad'i tace, "ki kula". Raihana tace, "insha Allah ummie". Raihana tana zuwa kayansu ta had'a kawai tace kuzo muje. Kusan su takwas suka nufi gidan iya. Har malam ya sakaya kyaure da tuni ma ya rufe tafiyar Ayman kawai suke jira ya tafi, shi kuma Ayman tunda ya samu hirar zamantakewar mutan da sai ya kasa tashi a gurin yana ta sauraron labarin abun gwanin burgewa a gurin shi. A haka su raihana suka shigo da sallama. Iya da Ayman muryar raihana suka gane duk a ciki saboda itace suka fi sani, amma tunanin abinda zai futo da raihana cikin wannan lokacin yasa tace, "kamar muryar raihana ko?". Raihana Zama tayi gefenta kan tabarmar da suke zaune tace, "eh nice iya munzo ne mu kwana a nan idan babu damuwa saboda gidan mu ya cika taf da y'an biki" Iya cikin jin dad'i tace, "laaaah babu laifi sannun ku da zuwa, ki shigar da k'awayen naki ciki mana, koda yake kuzo muje na kaiku don wannan indai donta itane". Murmushi raihana tayi, iya tayi gaba su kuma suka bi bayanta. Littafin da yake gaban Ayman ta d'auka sai kuma ta d'ago ta kalle shi, ya zuba mata ido yana kallonta, marairaice fuska tayi tace, "Yaya Ayman kallon fa?". "Uhm Ai dole na kalle ki raihanatu tunda kika shiga hidimar biki gaba d'aya kin manta dani, wayarki switch up oll the time". "Ayyah Yaya Ayman bafa mantawa nayi dakai ba, kawai dai nayi busy, toh wai zaman me kake yi anan goma fa ta huce". Shiru Ayman yayi kafun ya sake d'agowa yana mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa farat d'aya. Itama shiru tayi tana kallonshi kawai, doguwar ajiyar zuciya yayi yace, "yanzu fa shikenan raihanatu kina yin aure mun rabu?". B'ata face tayi tace, "Toh meya kawo wannan maganar kuma don Allah, nidai a'a ko nayi aure ba abinda zai raba mu har gidana ma zaka dinga zuwa lokaci bayan lokaci muna gaisawa". Wani irin murmushi Ayman yayi ya shafi gashin kanshi yace, "Anya raihanatu?, da hakan zai yiwu da nafi kowa jin dad'i da farin ciki ai". Murmushi itama raihana tayi tana tuna gaskiyar maganar shi, abinda ya fad'a haka yake, duk inda suka kai da shak'uwa da kusanci yanzun tana yin aure sun rabu, k'arshen tama ita da sake wata doguwar hira dashi har abada. Wani abu taji ya caki k'ahon zuciyarta, sai kawai tayi k'asa da kanta tana tuna yadda farkon soyayyar shi da Nur taso raba tsakanin su, ta tashi hankalinta kullum cikin rigima dashi, shi kuma yak'i rabuwa da ita, a cewar shi ai ba ita ta had'a suba, hasalima tun kafun ya nuna yana sonta suke tare da raihanatu, idan tayi hak'uri in lokacin su rabu yazo zasu rabu da kansu ma, gashi kuwa lokacin daya fad'a Yana gab da zuwa. Lallai Ayman ya cika aboki na kwarai kuma cikakken mutum mai magana guda, yanzu gashi da kanta Nur data fahimci gaskiya take neman had'a alaqa da ita. Iya ce ta katse musu tunanin da suke ta hanyar fad'in, "ya kamata kazo ka tafi ganan mamanka tana tambayar ko anan zaka kwana ne? Tace tana ta kiranka baka d'agawa". Shafa idon shi yayi da hannun shi ya zura hannu cikin aljihun wandon shi ya zaro wayar, tun d'azu yake jin vibration amma ya kasa ciro wayar ya duba har kiran ya katse. Mik'ewa raihana tayi tace, "Yaya Ayman ka gaida gida ka gaishe da auntie". Bai ce da ita komai ba ya mik'e hannun shi rik'e da mukullin mota, ya yiwa iya sallama ya tafi. Sai bayan futar shi raihana tace, "iya wane d'aki kika zab'a mun ne? Ina fatan an kunna mun air-conditioner yadda zanfi jin dad'in bacci kinsan kishiyar farko saida kulawa, in ba haka ba kuma yanzu tayi out data ciki". Iya tace, "ke tafi can y'ar son jin dad'i wato ke har wata AC kike nema a gurin matar da zaki yiwa kwacen miji, toh Ina laifi ma dana baki d'aki jikin nawa koda yake dana sani ma na kusa da kwata na ajiye ki" Raihana tana dariya tace, "ai baku da d'aki kusa da kwata iya indai ba toilet d'inki zaki kaini ba, kuma kinsan mai ran k'arfe yana zuwa zaici tarar ki". Dariya iya tayi a lokacin da raihana ta gama maganarta ta shige cikin parlon. Yau bata yarda tayi magana da kowa ba tayi kwanciyarta bacci Cox ta gaji over. Washe garin d'aurin aure raihana tunda tayi sallah da asuba ta sake komawa ta kwanta har 10 bata tashi ba, duk su hapser sukayi budurin su suka gama, har me make-up tazo tayi musu, iya tayi musu break suka karya aka ajiye mata nata. Iya ce ta sake lek'owa d'akin nasu tace, "Wai har yanzu bata tashi baccin ba?". Zainab tace, "eh iya yanzu nake son na tashe ta dai saboda me make-up d'in zata tafi". "Ya kamata kam gashi ba abinda taci ma". Saita k'arasa shiga d'akin tana d'an bubbuga k'afarta da hannunta, a hankali raihana ta bud'e ido tana karanta addu'ar tashi daga bacci, "tashi raihana kada a d'aura auren ke kina nan". Mik'ewa tayi zaune tana bin y'an matan d'akin da kallo d'aya bayan d'aya. Duk sunci kwalliya cikin shaddar d'aurin aure. "Tashi maza na had'a miki ruwa me zafi kiyi wanka". Mik'ewa tayi ta zari zanin da maama ta cire already da k'aramin hijab jikinta ta bi bayan iya, har toilet iya ta rakata sannan. Da soap tayi wankan da ruwa ta d'auraye bakinta da toothpaste ta d'auro alwala ta futo. Sad'af sad'af ta wuce d'akin iya da gudu saboda Jin muryar Ayman da tayi suna magana da malam a sitting room. Shap shap ta shirya su ameena sunata azalzalarta wai make-up artist d'in zatayi tafiyarta in bata zoba, ko breakfast batayi ba ta zauna bayan ta gama shard'anta mata dokokin kar a cika mata fuska kamar tasu. Shaddar pitch colour ce an mata adon aiki da zare milk and dark blue. Sosai tayi kyau kamar itace amaryar. Duk sai yaba mata sukeyi, nan suka shiga hotuna suka cika parlon iya da hira, da kuwa tsit dasu kamar basu ba. Iyace da ta shigo ta tsaya tana kallon raihana kafun tace, "a'a a'a kece nan aka ranbad'a miki jan baki da kwalli haka?". Duk sukayi dariya Salma da take feeding baby samha a lokacin tace, "ai bata yarda anyi mata yadda ya kamata bama iya" iya na zaro ido tace, "a hakan? toh Ina fatan dai ta karya ko in aka maka wad'annan kayan ja ido da ja hancin ba'a cin komai?". Raihana ta bud'e baki zatayi magana karaf idonta ya fad'a bakin k'ofa, saita kasa cewa komai sai zaro ido da tayi tana kallon k'ofar. _A gaskiya Ina jin dad'in comment d'inku, ta hakane nake gane asalin yadda muke tafiya tare, sorry 4 de late update naje bikin k'awata ne, Aysha aleeyu Ina yi mata fatan zaman lafiya mai dorewa a gidan mijinta da zuri'a d'ayyiba_ *Ku muje zuwa my fans* _Comment and share_ 24/03/23, 2:01 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twelve 1️⃣2️⃣ Da sauri ta daka tsalle taje ta rungeme su. Su kansu cikin farin ciki suka rungume raihanar suna murnar had'uwa da juna kamar wanda sukayi shekara basu had'u ba. Cikin parlon iya ta k'arasar dasu. Sun gaisa da mutanen cikin d'akin har iya don basu manta ta ba tun a waccen ranar. Ai tuni raihana ta ware anan sunata hira tuni ta manta ma da wani karin kumallo. Salma ce ta kawo musu ruwa da lemuka, hadda tuwon safe da akayi. Iya ganin raihana zata ci gaba da zama da yunwa don bata cin miyar taushe, sai ta kamo hannunta bayan ta kai mata abincin sitting room inda su malam suka tashi. A tsakar gidan suka tsaya. Raihana kam murmushi tayi tace, "iya bamu gaisa ba fa dake kema ko?!". Saita d'an russuna a gaban ta, "iya Ina kwana". Iya tace, "lafiya tashi muje ni ki karya". Kamo hannun ta iya tayi, bata sake hannunta ba kuma har saida ta dangane ta da sitting room d'in, tayi tunanin zata tarar da Ayman sai kuma taga ashe babu kowa ma a ciki, Zama tayi kan tum tum iya ta ajiye mata abincin a gabanta. Tana futa Ayman na shigowa kare da waya a kunne yana murmushi kai da gani babu tambaya kasan da Nur yake magana. Zama yayi kan kujerar da take fuskantar ta yana ci gaba da maganar shi, raihana kallo d'aya tayi mishi ta maida hankalinta kan abincin ta, Ayman kuwa kamar television haka ya zuba mata ido yana kallonta, da yanayin yadda take cin abincinta gwanin burgewa, ya dad'e da fahimtar komai nata tana yin shi ne with passion. Tak'aita hirar da suke da Nur yayi sukayi sallama ya ajiye wayar, sai a lokacin tace, "Yaya Ayman Ina kwana?". "Ina kwana ko Ina wuni? Kina can kina bacci har aka d'aura auren aka gama, sai yanzu kin tashi kusan 11,30 kina breakfast a makare zaki wani cemun Ina kwana". Ayman ne me yin wannan maganar yana kallonta ko cikakken k'iftawar ido babu. Murmushi kawai tayi ba tare da ta sake ce dashi komai ba, sake gyara Zama yayi yace, "kin je kin wani ciko fuska da powder to ni dai Zan baki shawara kar ki sake ki futa waje a haka, don zaki sha dariya gurin mutane y'an biki". Sai a lokacin ta kalle shi, "bafa tsoron ki zanji ba, so kibar ma zare mun ido". D'auke idonta tayi k'asa k'asa da murya tace, "toh aini dama ba don su nayi ba, shiyasa ko futa waje su ganni bazan yi ba ma". Yadda tayi maganar da iya gaskiyarta sai abun ya bashi dariya, amma dai baiyi ba ya gimtse. "Toh kenan don wa kikayi? Wannan saurayin naki me idon...... Umm bari dai nayi shiru zaifi". Ya k'arasa fad'a yana rik'e bakin shi. Sai a lokacin raihana ta fahimci so yake yau ya kaita geji kawai, don haka ture abincin tayi daga gabanta tace, "shima ba don shi nayi ba, ni yanzu ina ma zan ganshi". Tab'e baki Ayman yayi yace, "tom nidai koma don me kikayi bari na yaba miki ko kyaji sanyi a ranki, kin d'an yi kyau ba laifi". Kan kujera raihana ta zauna sosai tana dariya tace, "ka hutar da bakin ka, ba sai naji wani abu daga gare kaba". Dariya yayi ganin ta ramfo shi. Ya bud'e baki zaice wani abu hapser ta shigo da sallama, saida ta tsaya suka gaisa da Ayman sannan tace, "raihana ummie tana neman ki fa". Mik'ewa tayi tace, "okay kice mata Ina zuwa". Tare suka futa bayan ta tsaya tayi sallama da Ayman don ba lallai lokacin da zata dawo yana nan ba, taji yana fad'awa Nur a waya d'azu yana hanya. Su raheela ta kira suka huce gidan su direct, anguwar ta cika taf da mutane Masha Allah, haka cikin gidan nasu ma. A parlour ta ajiye su suka tafi nemo ummie. Ameena ce ta nemo mata ummie ta had'a su sannan ta tafi, ummien kanta tayi kyau cikin shadda irin ta jikin raihana har d'inkin, ba make-up a fuskarta ko wetlips da kwalli bata saba amma duk da haka tayi kyau sosai. "Wane irin bacci kika yi yau har aka d'aura aure baki tashi ba? Ina fatan dai ba wai baki da lafiya bane kika b'oye don nasan halinki sarai". Girgiza mata kai tayi tace, "a'a ummie lafiyata Lou kawai gajiya ce". Ummie tace, "Toh Allah yasa, dama su yuseep ne suke ta tambayata ina kike?". Cikin mamaki tace, "laaah ummie Yaya yuseep yazo? Suna Ina?". "Suna sitting room". Ai ummie na gama fad'a mata tayi waje da hanzari, da Salma taci karo a hanyarta, "yauwa ai nemanki nake, har gidan iya inda muka kwana naje tace mun yanzun kika futa da friends d'inki, saurayinki sunzo d'aurin aure shida mahaifin shi da wasu samari dai haka ko k'annen shine". "Imran ko? Toh ni me zanyi musu, da yayi tafiyar shima". Salma tace, "ai bai nemi had'uwa dake ba shi kanshi, kawai cewa yayi in ya kira no ki baya samu, na fad'a mishi kin kashe wayar ne, shine yace a fad'a miki don Allah ki kunna zakuyi magana". Samha ta karb'a a hannun Salma dake ta b'angale mata baki ta tace, "aikuwa bazan kunna wayata yanzu ba, dame zanji? Hayaniyar mutane ko d'aga wayar shi". Ko k'ara sauraron Salma batayi ba ta huce zuwa sitting room abinta, ita ko Salma da mugun mamaki tabi bayan y'ar uwar tata da kallo, Ashe har yanzu tana nan da halinta bata sauya ba? Ta d'auka tsawon 2 years da sukayi ba tare ba ta bar halayen ta na ko in kula, ko ada tana tunanin anya ba biris d'in da takeyi da masoyan ta ne ke korar su har su fasa aurenta ba? Iya sanin ta mutum d'aya raihana take saurara har taba lokacin ta fiye dako wane namiji, shine wani kwayar mutum guda da basu da wata kwakkwaran alak'a ta soyayyah, hasalima shi sama da shekaru uku yana da wadda yake so zai iya aure a ko wanne lokaci daga yanzu. A ranar data kasa hak'uri zama tayi kurum ta rabka uban tagumi tana nazarin matsalar raihana, kallo d'aya data yiwa Imran yau taji ya kwanta mata a ranta, sai taga duk cikin samarin da raihana tayi babu mutum kamarshi, ko don duk babu saurayi a wad'an can?. Raihana kuwa da hanzarinta ta k'arasa sitting room d'in bakinta d'auke da sallama, duk suka amsa mata cikin sakin fuska, a k'asan carpet ta zauna suka fara gaisawa dasu d'aya bayan d'aya, yuseep ne da matarshi sai sauran y'an uwan ummie. Ta jima rabonta dasu musamman yuseep don ba a garin yake ba, sai in abu ya faru irin haka yazo. Ta jima suna d'an hira jefi jefi kafun ta futo daga d'akin. Gurin su raheela taje ta kaisu Suka gaisa da ummie da amarya sukai musu Allah ya sanya alkhairy, saboda cikowar mutane a gidan sai kawai ta mayar dasu gidan iya, nan Suka baje kolin hirar yaushe gamo, itama Fatima ansa ranar aurenta da wani cousin d'inta, nan da eight month biki. Sosai raihana ta taya ta murna da fatan alkhairy, sai yamma suka tafi da alk'awarin sai bikin raihana suda dawowa. Wannan karon dangin abban su a gidan Abba abubakar suka yi nasu yinin shiyasa akayi lafiya aka gama lafiya, ba d'auki ba dad'i irin Wanda Suka fara jiya, aka tafi da amarya gidanta lafiya bayan tasha ruwan naseeha daga dangi da abokan arzik'i, iya ce da umma suka kamo hannunta kamar yadda suka yiwa Salma haka itama suka yi mata a wannan karon har gidan mijinta. Sai gidan nasu ya zama shiru saboda yawancin mutane sun tafi gidan amarya da yake ba nisa tsakanin su dashi. Ita dai raihana bata jeba, tana sallar isha'i ma kwanciyarta tayi can k'uryar d'aki. Sai k'arfe d'aya da y'an mintuna na dare ta farka, su kuma lokacin y'an kai amarya sun dawo har sun kwanta bacci. Wayarta ta d'auko cikin Jakarta ta kunna, nan massage suka fara ribdigun shigowa, biyu ne daga Ayman, amma kusan hud'u daga Imran ne. Sak'on farko, "Na kira ki wayar ki a kashe Ina fatan kina cikin k'oshin lafiya". Na biyu "me yasa kika kashe wayar ki?, raihana ganin ki a yau yasa da nazo gida na kasa bacci bansan me yake shirin faruwa dani ba, amma daga na rufe idona fuskarki nake gani tana mun gizo cikin kwalliyar ki kamar kece amaryar da ake biki, ba komai nake tunani ba raihana sai nan da watanni biyu masu zuwa alak'a ta dake zata zo k'arshe, wani zai raba mu bayan duk tsawon shekarun da muka kasance tare, tun baki mallaki hankalin kanki ba, raihana na taya ki murna Ina kuma miki fatan Allah yasa wannan guy dashi za'ayi a wannan karon, amma Ina tausayin kaina da zanyi rashin da har abada bazan tab'a maye gurbin shiba, don Allah raihana da kinga text massage d'ina ki kirani ko zanji sanyi a raina". Shiru raihana tayi bayan gama karanta sak'onnin biyu da suka zo daga d'an uwa kuma aboki na gari wato Ayman. Tayi yink'urin kiran shi yafi sau uku tana fasawa saboda tunanin yana tsakiyar bacci a lokacin, daga k'arshe sai kawai ta share ta fara duba sak'onnin Imran, duk na fatan alkhairy ne sai d'aya na complain me yasa zata rufe wayarta, ya shiga damuwa sosai gashi yazo d'aurin aure har ya tafi basu had'u ba. Raihana ranta da zuciyarta cinkushewa sukayi da abubuwa da yawa, daga k'arshe sai kawai ta kife kanta jikin gwiwarta tana zubda hawaye, soyayyar Imran tana so tayi tasiri a zuciyarta, lallai taga alamun karyewar lagonta a wannan karon duk da yak'i da take da zuciyarta, tsoronta d'aya har yanzu bata sa a ranta za'ayi auren ta dashi ba, Cox ita ta dad'e da sarewa, tana ganin a k'addararta har yanzu mijinta bai zoba tukun, tana ji a jikinta shima tafiya zaiyi ya barta kamar wad'an can samarin da tayi. Ta wani gefen kuma ga Ayman, ita kanta ba k'aramin tashi hankalinta yake ba idan ta tuna da k'aratowar rabuwarsu a kullum dare da safiyar Allah, tasan ba abune mai sauk'i rabuwarta dashi bayan kwashe tsayin shekaru goma da d'oriya tare. Tana wannan y'an tunane tunanen wayarta ta fara ruri,,,,,, Ayman ne, saita saisaita yanayinta ta share hawayenta sannan ta d'aga a nutse, "assalamu alaika". Ya amsa da "Ameen wa'alaikumussalam" ya fad'a shima a d'aya b'angaren. Raihana cikin sanyin jiki tace, "Yaya Ayman kaine kira da daren nan". Cikin muryar bacci yace, "ya zanyi raihana na kasa samun nutsuwa, bacci na fara amma baccin ma ba dad'i, ban d'auka zan samu wayarki bud'e ba ma yanzun". "Ayyah nima yanzu na bud'e dana farka, toh amma Yaya Ayman me yake damunka da zai hana maka bacci? Duk yadda kake da son bacci?". Jinginar da kanshi yayi jikin fuskar gadon da yake kwance yace, "Ni kaina bansan me yake damuna ba raihanatu, the only thing I know is jina nake cikin tashin hankali, wanda yake k'ara hauhauwa a kowacce safiyar Allah". Ajiyar zuciya raihana ta sauke tace, "kuma kana yawaita addu'o'inka? Duk da nasan baka da wasa da addu'ah amma ka dage sosai, yanzu bari muyi sallah raka'a biyu mu kaiwa Allah kukan mu, dama shi yafi sanin damuwarmu kuma shi zaiyi mana maganinta". Cikin jin dad'in kalamanta da nutsuwar ta Ayman yace, "toh shikenan raihanatu, insha Allah zan dage da ninka addu'ah akan wadda nake yi". Daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye waya. Alwala ta d'auro bayan ajiye wayar ta kabbara sallarta inda tayi ta kai kukanta ga Allah subhanahu wata'ala daya yi mata zab'in abinda yafi alkhairy a rayuwarta. Shima Ayman hakan ya aikata. Duk mutanen d'akin suna bacci har ta gama ta koma tayi kwanciyarta sak'on gud night ta gani daga Ayman, tayi mishi reply ta ajiye wayar gefenta. Da safe ragowar bak'i suka had'a ya nasu ya nasu suka huce, zuwa yamma gidan su ya dawo daga ummie sai su sai kuma Salma wadda zata huce a daren ranar itama, sai a lokacin ummie ke nuna mata kyautar da Imran da mahaifin shi suka kawo, drinks ne kusan katon goma sha biyar, abun har mamaki yaba raihana. Saita tafi d'akin su da sauri ta nemo wayarta inda ta ajiye ta dawo d'akin, Ashe ma ya kirata, sai dai kiran bana yau bane tun daren jiya dai dai lokacin da suna wayar nan da Ayman. "Ya Salam to yaushe kuma Imran ya kirani ban gani ba?" ta fad'a tana zama saman kujera, no shi tayi dialing kamar kullum har ta gama bai picking ba, a tunaninta zai biyo baya sai ta ajiye wayar taci gaba da harkokinta, sai dai me? Har yuseep yazo ya tafi da Salma da dare bai kira ta ba. Hakan ya d'an d'agawa raihana hankali kad'an har ta shiga damuwa, lallai akwai wani abu saboda lafiyar Allah baya iya yini ba tare daya kirata ba, sai dai ko in ita tak'i d'agawa saboda dakushe k'arfin alak'ar su. Har dare su muhibba suna gugar uniform d'insu na makaranta don Abba yace dole su koma gobe ai an gama biki, ita kuma tana zaune jigum rik'e da waya, ta kirashi yafi sau hud'u a iya zamanta anan ma amma baya d'agawa, al'ameen ne ganin suna ta magana bata jiba yazo ya dafa k'afarta, sai ta d'ago ta kalle shi, "ga kayan kinan iya ta bayar a kawo miki". Karb'ar kayan tayi ta shige d'akin su da a yanzun ya zama nata ita d'aya. Ranta cinkushe da d'ar d'ar da kewar y'ar uwarta ta nemi guri ta kwanta tana karanta addu'o'in bacci, tana ji ummie na tambayar su muhibba a parlour ina take, jidderh tace ta kwanta bacci. Da mamaki ummie tace, "tunda wuri yau kuma? Kodai waya take?". "Wallahi ummie ta kwanta na shiga fa na ganta" jidderh ce meyin wannan maganar". Rufe ido tayi da tunanin ko ummie zata shigo duba ta sai kuma taji ta huce. @@@@@@ Kamar da wasa saiga raihana ta d'auki cikakkun kwana biyu babu Imran bare wayar shi, tun tana mishi text na tambayar ba'asin shirun shi har ta fudda rai ma gaba d'aya. A kullum safiya sai sunyi waya da Ayman yaji lafiyarta wannan alk'awari ne, haka ta wattsapp indai taci nasarar samun shi online zasu yi chat, shine ma dasu raheela ke d'ebe mata kewa wani lokacin. Yau da yammaci tana zaune k'ofar kitchen ta gama had'awa ummie miyar tuwon dare kenan tana hutawa d'an aiken iya yazo kiranta, ummie da take zaune gefenta ta kalla sai taga tace da yaron tana zuwa, ajiyar zuciya ta sauke a hankali saboda yadda taga ummie bata son alak'ar ta da Ayman bata d'auka zata yarda taje kiran da bata raba d'ayan biyu shine ummul'a'ba'isin shi. Doguwar rigar material ce a jikinta wrapper, d'inkin ya mata cas cas, d'an madaidaicin gyalen kayan ta d'auko a d'aki ta yafa don b'oye gashin kanta da batasa d'an kwali ba. "Ummie saina dawo". Ummie tana kallon rawar k'afarta tace, "ki tafi ma malam da tuwon sannan ki tabbatar kin dawo kafun abbanku ya dawo". Cikin jin dad'i tace, "insha Allah ummie". Daga nan kitchen tayi ta d'auko plask ta zuba miya ta d'auki tuwon malmala biyu tasan maybe Ayman yaci tasa a leda ta futa. Da sallama ta shiga gidan iya, babu kowa a tsakar gidan, daga parlor iya ta amsa mata, saita k'arasa ta shiga parlon, tana ta aikace aikacen ta, Ayman kuma na zaune kan kujera yana operating system idon shi sakaye cikin farin glass. Sanye yake da t shirt sai dogon wando Ash. Ajiye tuwon tayi kan table k'arami dake gaban shi, "yanzu haka akeyi raihana sai ki b'ace b'at bake ba labarin ki kamar ke muka kai d'akin mijin". Iya ce ta fad'i haka, Had'a ido sukayi da Ayman, lokaci guda gaban su ya bada rass! Iya kam ko lura da yanayin da suka shiga batayi ba ta ci gaba da maganarta, "koda yake kamar yau ne kema zamu mik'a ki naki d'akin da shekara ta kewayo muje mu d'auki y'an uku". Ayman kwantar da kanshi baya yayi had'e da lumshe idanun shi da sauri yana imagining ga raihana tayi aure har da ciki. Yayinda ita kuma tayi k'asa da kanta ba tare da tace komai ba, "me aka kawo mun yau kuma? Kayan ki suna cikin d'akina na wanke na ajiye miki ban samu wanda zai kawo miki ba, yanzu wannan yaron ma da Adam ya tura kiran ki da kyar ya je Saida na had'a da bashi k'arin gyad'a". Jiki a mace ta kai tuwon gabanta tace, "ai suna da kyuya ummie ce tace a kawowa malam tuwo". "Ita dai ruqayyah bata gajiya duk lokacin da tayi tuwon nan, a tak'aice ma dai yau ba malam aka kawowa ba Ayman kika kawowa don tunda yana nan sai yaci gashi dama har malmala biyu". Shi dai Ayman Murmushi kawai yayi ya gyara zaman shi, idon shi na kallon raihana da kullum take k'ara sauyawa mishi. Ita kuwa gaisawa tayi da iya sannan shima ta gaishe shi, ta tafi d'akin iya da suka kwana wancen ranar ta d'auko kayanta a gefen gado. Kusa da Ayman ta zauna tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren shi, "Yaya Ayman wai baka da lafiya ne yau?". "A'a raihana amma me kika gani". Ya fad'a yana tsare ta da ido. Sai ta juya kanta gefe tace, "babu komai". "ai koda komai ma ba zaki fad'a ba indai kece". Ita dai murmushi kawai take, iya da kanta taje kitchen ta d'auko plate ta zuba mishi tuwon, ta zuba mishi miyar daban a wani d'an bowl. . Har gaban shi ta ajiye tayi hucewarta harkokinta na k'ulle k'ulle a tsakar gida, bai wani ci na kirki ba duk da irin yunwar da yake ji kuwa ya rufe duka tuwon da miya. Raihana shiru tayi tana nazarin shi kafun ta nisa tace, "Allah Yaya Ayman baka da lafiya kawai baka son naji ne". K'ak'alo murmushi yayi ya d'auke mata hankali ta hanyar kawo wata hirar ta daban, sun jima suna hirarsu kafun ta dai daici lokacin dawowar abbanta tayi mishi sallama ta tafi gida, Allah ya taimake ta bai dawo ba sai dai tana shiga ba jimawa ya dawo, hira da Ayman ta d'auke mata hankali da yawa, taji dad'in futar don ta d'ebe mata kewa ba kad'an ba. Takan jima kafun suyi hira taga dariyar shi irin ta yau, lallai yau ya tuna mata da abinda ta jima da mantawa dashi, hirarraki dai iri iri. Shima Ayman ta b'angaren shi abinda ya faru kenan, a lokaci guda ya tsinci kanshi cikin farin cikin daya shafe mishi dukkan wani k'unci daya shiga lokaci guda a yammacin. Bai bar gidan iya ba saida yayi sallar isha'i tare da malam a masallaci. Lokacin daya shiga gida ummie tana tare da bak'i abokan kasuwancin ta a sitting room, sai bai nemi ganinta ba ya huce kawai bayan sun gaisa da halima mai aikin su, bathroom ya fad'a yayi wanka ya shirya cikin kayan bacci milk masu taushi, zama yayi gefen bed sannan yayi dialling no nuriyyah, tana zaune ta duk'ufa kan laptop d'inta ko me takeyi dai da alamu ta bashi muhimmanci, ko ring d'in bataji ba sai da k'anwarta heedaya ta d'auko wayar har zata kai mata sai taga sunan mine da emoji na love a jiki, ta fahimci no yaya Ayman kad'ai tayi saving da haka, sai tayi sauri ta d'aga sannan ta kara a kunnenta, Ayman tacan b'angaren cewa yayi cikin kwantar da murya, "baby yau ko nema na bakya yi". Dariya heedaya ta sakar mishi a kunne cikin k'iriniyarta da rashin ji tace, "ba babyn bace Yaya Ayman nice da ka yiwa fake promise, yanzu fad'a mun Ina chocolate d'ina". Dafe kai Ayman yayi a ranshi yace, "dis girl was very stubborn". A zahiri kam ce mata yayi, "Wai ke heedayar mammie baki da maganar komai sai a baki chocolate?". B'ata face tayi tace, "toh ai kaine kace zaka zo har gida ka kawo mun chocolate na!". Ayman sani idan ba lallab'ata yayi ba zata yi mishi haramiyar jin muryar Nur yau sai ya kwantar da kai yace. "Ayyah afwan heedaya Zan kawo miki k'aton vanilla ice cream and 🍫 idan zanzo gidan ku amma yanzu ki kaiwa baby waya zamuyi magana". Aikuwa heedaya na jin haka ta daka tsalle ta hau ihun murna, sai a lokacin Nur ta d'ago saboda ihun heedaya da ya d'auki hankalinta har ta juyo tana kallonta, "heedaya ki kama kanki tun kafun na......". Saita fasa k'arasa waccen maganar saboda ganin wayarta a hannunta tana juyi da ita. "Au wayar tawa ce a hannun ki?". Matsawa baya tayi tare da mata gwalo, aikuwa Nur ta bita suka zuba tsere har gaban mammie a parlour, bayanta heedaya tayi ta b'oye tana fad'in, "mammie kinga auntie Nur zata dake ni ko?". Nur data tsaya daga bayan mammie tace, "mammie wayata fa ta d'auke mun tana tsalle tsallen ta dashi salon ya fad'i ya fashe". Juyowa mammie tayi ta kalleta, "me yasa kika d'auke mata waya babie?". Shagwob'e fuska tayi kamar zatayi kuka tace, "mammie gaisawa fa mukayi da Yaya Ayman". Saita harari Nur da take faman kumbura baki tana fad'in, "Allah mammie she's lying". "yanzu donta gaisa da Ayman d'in kike binta ki doketa! Shikenan bamu wayar mu bata tsoro takeyi wai kada ki kwace mata shi". Mammie ta k'arasa fad'a tana karb'ar wayar a hannun heedaya, duba screen d'in da zata yi sai taji nauyi ganin har lokacin yana kan layi, "karb'i mu ki b'ace mana a nan" ta mik'awa Nur, Nur tazo ta karb'a tana hararar heedaya don ba damar duka ta fuce, wayar ta kara a kunnenta tace, "hello lovely...". Ayman kam k'ayataccen murmushi yayi akan fuskarshi yace, "Ina jinki nuriyyah ta, me ya d'auke mun hankalin ki kika manta dani gaba d'aya". Zama tayi kan kujera kamar tana gaban shi ta zaro ido, "nifa ban manta dakae ba, akwai dai wani abu da nake shirya maka na musamman Kuma bazan yarda ka gani ba sai lokaci yayi shine ya maidani busy?". "Lokacin me! Nurienerh nidai ki fad'a mun yanzu kawae please". "Shiyasa na fara fad'a maka ba zai yiwu ba, kayi hak'uri kawae saboda idan kaji yanzu lovely ai ya dawo ba surprise ba kenan, a'a nidai riga na yiwa raina alk'awari". Murmushi ya sake yi komai na Nur mai sauk'i da k'ayatarwa, shiyasa rayuwarta take burge shi. "Tom yanzu dae albishir d'inki". Da sauri cikin son jin abinda zai fad'a Nur tace, "goro fari k'al ma". _Dear fans Muna fatan kuna bibiye da littattafan in-identical twins cikin littafan mu na👉🏻 JARUMAR UWA da kuma DARAJAR HAK'URI, Wanda muka shirya tsab don futar muku da wani salon labari na musamman da zai jijjigaku ya girgiza ku a k'arshe kuma ya k'ayatar daku ya Kuma saku nishad'i_ *Dubun godiya da jinjina gare ku masoyan asali da nake ganin comment d'inku babu kaukautawa, wanda yake sake k'ara mun kwarin gwiwar muku typing koda kuwa Ni Zan takure kaina ne. Nagode👍👍👍😍* _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page thirteen1️⃣3️⃣ "Har da saurin ki?, toh nima na fasa fad'a miki sai kin fad'a mun abinda kike shiryawa idan ba haka ba kuma.... Kowa ya bar komai a ranshi". Cikin had'e rai Nur tace, "Allah dama ba kayi niyyar fad'a ba". Murmushi ya sakeyi kafun yace, "yaushe ya kamata na shigo na ganki? Kwana biyu aiki bai barni na nutsu ba, kuma ni kunyar mammie nake, ke kuma yanzu ko d'an kwana biyun ma da kike zuwa yiwa auntie kin daina". Y'ar k'aramar dariya tayi, "Zan zo mata kwanan nan jira nake auntie shaheeda ta dawo daga gidan Aunty suhaila saina zo, ai munyi magana da auntien ma rannan da tazo". Ayman d'an k'aramin tunani ya tafi akan shaheeda, duk a gidan su ba wadda jinin su bai had'u bama kamarta, shiyasa har mantawa yake da ita, tana da alfahari da mugun d'aukar kai wata tsiya shiyasa kwata kwata basa shiri da ita, "kaji me nace kuwa lovely?". Da sauri ya dawo daga d'an k'aramin duniyar tunanin daya fara tafiya "da naji dad'i kuwa! Allah yasa ta dawo da wuri ma". Nur tace, "ameen amma ni dariya kake bani duk lokacin da zaka ce wai kunyar mammie ke hanaka zuwa sosai". "Humm ba zaki gane ba Nur". Sunci gaba da tattaunawa kafun bacci ya cika mishi idanu fal suyi sallama ya kwanta, ranar ko auntie bai je yiwa gud night ba. Sai itace da taga motar shi take tunanin yaushe ya shigo, tazo d'akin shi taita knocking shiru, tana bud'ewa ta ganshi kwance saman bed yana baccin shi hankali kwance, k'arasawa tayi har gaban gadon ta dafa goshin shi ta karanta mishi addu'o'i sannan ta futo taja mishi k'ofar d'akin tayi nata guri. @@@@@@@ Raihana kuwa ranar da aka cika sati da yin bikin gidan su tana zaune k'ofar kitchen tana yanka salad da cabbage saiga yaro ya shigo wai ana kiranta waje inji wani yace sunan shi Imran, "Imran?". Raihana ta maimaita sunan a bakinta da mamaki, "eh haka dai yace". Ummie da take jin komai tsakanin su tace da yaron, "kace tana zuwa". Yaron ya futa ita kuma ta shiga d'aki ta sauya riga armless da 3 quarter skirt da yake jikinta a lokacin ta futo cikin wasu kayan da zunbulelen hijab, makullin sitting room ummie ta bata tace, "ki kula". Da toh ta amsawa ummie sannan ta nufi k'ofar futa. Yana tsaye jikin motar shi yana danne danne a waya, da fuska kadaran kadahan, bata k'arasa inda yake ba tayi tsayuwarta a k'ofar gidan su hard'e da hannu tana nazarin anguwar tasu, a haka Imran ya lura da zuwanta ya zura wayar aljihu ya k'arasa inda take. Kallon kallo suka fara yi kamar zasu ce da juna wani abu sai kuma suka basar, Imran ne ya fara ajiye kanshi gefe yace, "amincin Allah ya tabbata a gareki raihana". Raihana cikin d'auke kai tace, "tare da kai, mu k'arasa ciki ko". Ba musu tayi gaba yabi bayanta ita bata yi tsammanin ma zai shiga ba. Madaidaicin parlour ne zagaye da kujeru da center carpet a tsakiya sai fridge a gefe da table. A two seater ya zauna ita ma ta nemi kujerar dake gefen shi ta zauna, cikin nutsuwarta ta soma gaishe shi, ya amsa yana kallonta, shiru yayi na a k'alla wasu mintunan, fahimtar da yayi zasu iya k'are zaman su anan har su tafi bata ce dashi k'ala akan rashin zuwam shiba saboda miskilancin ta, sai shi ya sauke nashi na aro yace, "sai kika jini shiru kwana da yawa, bana kiran wayarki, banzo inda kike ba kuma in kin kirani bana d'agawa alhali ina gani, baki ji duk kina son sanin me yasa ba?". Girgiza mishi kai raihana tayi tace, "ko kad'an, ai mutum baya yin abu babu hujja musamman wanda yasan abinda yake yi kamar ka". Imran ya jinjina d'aurin talalar da tayi mishi cikin hikima, sai ya sake gyara zaman shi ya ce, "hakane sai dai raihana ni fushi nayi". Saita kalle shi a bazata, "fushi da me kuma?". Imran yace, "very good! Raihana na fahimci har yanzu ni kad'ai nake kid'ina da rawata a kanki, da farko kenan, na biyu nayi mamaki yadda kika rufe mun wayarki tsawon kwana biyu bakiji daga gareni ba kuma kina yin rayuwarki ko a jikin ki? Haka nayi ta kiran wayarki kamar tab'ab'b'e har abokan aikina nayi mun dariya, na uku nazo d'aurin aure tare da mahaifina muka had'u da k'anwar ki tace bari ta nemo mun ke, nace a'a ta barshi kawai amma ta fad'a miki ki kunna wayarki zamuyi magana, shima kikayi burus! Toh a barshi kina cikin uzurin biki na hak'ura da hakan, sai dai abu na k'arshe daya tabbatar mun da zargina kuma yasa jikina sanyi zuciyata ta karaya, na kasa cikakken bacci saboda tunanin ki raihana, hakan yasa na gwada kiran ki a lokacin da ban tab'a gwada kira ba, infact ban tab'a tunanin in na kira ma za ki d'aga saboda lokaci ne da kowanne d'an Adam yake kwantar da hak'ark'arin shi don ya huta, sai dai kash na same ki busy kina waya a dai dai wannan lokaci, ban yarda ba ban hak'ura ba haka nayita jera kira har saida na had'a miki 3 missed call". Ajiyar zuciya Imran yaja sannan yaci gaba da maganar shi idon shi na kallon glass table dake gaban shi d'auke da drinks data kawo mishi "raihana a wannan daren na d'auka ko uzurin k'arya ai kya kirani don ki bani a matsayina na wadda kika amince zaki aura ku shimfid'a rayuwar aure me kyau da tsabta har mutuwa, sai baki yi hakan ba, Ina tunanin a lokacin ma Sam baki San na Kira ba sai washe gari da misalin k'arfe hud'u da minti talatin da uku, me kike tunanin zan d'aga na saurara daga gareki? Me zaki fad'a mun kuma?". Raihana shiru tayi jikinta a matuk'ar sanyaye tana sauraron shi, tunda ya d'auko maganar da farko ta fahimci inda zancen ya dosa, tasan dai dama ba zai huce ya tuntub'i ba'asin wayarta da Ayman ba. Sai ta rasa abinda zatayi a lokacin, gashi ya zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma, da jiran jin amsar da zata bayar donta kare kanta. "Kayi hak'uri". Ta fad'a da jiki a sanyaye, murmushin takaici Imran yayi kafun yace, "kad'ai! Kina nufin nayi hak'uri shine amsar duk wad'annan jerun gwanon maganganun nawa?". A sanyaye raihana tace, "toh aini bani da abinda zance maka bayan hakan". "Ke kuwa kike da abun fad'a, ko baza kice komai ba tunda wani abun sirrin kine bance dole sai naji ba amma a k'alla ki fad'a mun da waye kike waya a waccan ranar", dam! Dam! Taji luguden bugu a k'irjinta, tana tsoron ambaton sunan Ayman a gurin Imran saboda ya d'auki dangantakar ta da Ayman da zafi fiye da zato. "Kinyi shiru ko matsayina bai kai naji waye shi ba?". Ganin abun zai sake tsamari gashi bata iya k'arya ba sai tace, "Yaya Ayman ne shima akwai maganar da yake son zamuyi dashi bai same niba sai a wannan lokacin dana kasa bacci na kunna wayata, kuma ni bana waya da kowa cikin dare, shima ranar kawai a katari ne......" Imran jikin shi har rawa yake wajen d'aga mata hannu ya mik'e tsaye a mugun zafafe yana fadin, "idan har naci gaba da jin maganar Ayman daga bakin ki ko shakka babu zuciyata zata iya tarwatsewa, na kasa fahimta! Na kasa fahimtarki har yanzu raihana, ta Yaya ma za'ayi mace ta k'ulla alaqa da wani d'a namiji da sunan friendship? Ni wallahi har gwara kice mun shi saurayin kine akan jin wannan mummunar kalma ta aboki a tsakanin ku". Har tsorata raihana tayi saita sake takurewa gefe tana kallon yadda k'irjin shi yake up and down, matsalar shi kenan zuciya, a d'an zamanta dashi ta fahimci mutum ne mai azababben kishi. Shi kuwa Imran tsam ya mik'e ya koma gefen kujerar da take zaune ya had'a hannuwa biyu a gabanta, "don Allah ki taimake ni raihana, ba don niba ba don na Isa ba sai don darajar soyayyar da take tsakanin mu indai har da gaske kina jina a ranki koda rabin cokali ne ki rabu da wannan Ayman d'in", wani irin kallon kana hankalinka kuwa raihana ta wurga mishi, shi kuwa cikin rufewar ido yaci gaba da maganar shi, "yess ki rabu dashi raihana, ki bani sim d'inki na taune ki daina bin duk hanyar da zata had'a ku tunda ai ba a anguwar nan yake ba na sani, kinga shikenan daya kwana biyu baiji daga gare kiba zai hak'ura, hankali kwance alaqa tazo qarshe". Mik'ewa tsaye raihana tayi cikin b'ata fuska tace, "bazai yiwu ba Imran, sai dai kayi hak'uri amma Sam bazan iya aikata abinda kake so ba, Yaya Ayman ya huce duk yadda kake tunani, kamar Yaya d'an uwa na jini yake a gurina, tarin alkhairan shi da d'awainiyar da yake yi a kaina ma baza su iya bari rana tsaka na watsa k'asa a ido na rabu dashi ba, sai dai kayi hak'uri.......". Ai Imran da yake jin kalamanta kamar tana watsa mishi garwashi kasa jure har takai k'arshen zancenta yayi, hakan yasa cikin zafin nama ya had'e ta da jikin shi ya rungume ta tsam tsam unexpected, "hasbunallahu wani'imal wakeel". Raihana ta fad'a a zuciyarta tana jin yadda zuciyarshi take kaiwa da kawowa a dai dai wannan lokacin, gashi yayi mata wani mugun rik'on tsauri da bata isa ta kwaci kanta cikin sauk'i ba saida dabara, sai dai a yadda take a fusace d'in nan sam ba zata iya tsayawa wani b'ata lokaci ba. Cikin zafi da k'una ta fara k'ok'arin barin jikin su ta hanyar soma ture shi, Imran kuwa jujjuya mata kanshi yake a goshin su daya had'e tare da fad'in, "Ina so kiji yadda nake ji a zuciyata raihana, raihana Ina sonki ta yadda bazan iya jure ganin ki tare da wani namiji ba komai k'ank'antar shi, Ina sonki Ina son ki da yawa har ni kaina bansan adadin ba, raihana nayi soyayyah da y'an mata daban daban amma ban tab'a samun wadda nake sonta koda quartern yadda nake son kiba, raihana ban k'iba na kewaya garin Kano Ina ambaton sunan ki da bayyana adadin son da nake miki ga kowa babba da yaro k'arami ko babbba, Ina sonki raihana wallahi Ina tsananin sonki sosai". Raihana cikin fushi da fusata tace, "naji ka sake ni". Ba musu ya sake ta ya koma mazaunin shi ya zauna tare da dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu. Raihana kam ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jejjere a jejjere kamar wadda tayi tsere. Kafun Imran ya ankara har tabi hanyar futa daga sitting room d'in sai k'arar rufe k'ofar ta kawai yaji. Allah ya taimake ta bata had'u da kowa cikin familyn gidan ba har ta kewaya d'akinta ta shiga ta fad'a kan katifa ta fashe da wani irin kukan takaici, me yasa Imran zai mata haka? Me yasa zai nuna cewa jikinta yake so a aikace bayan a bakin shi kullum yana furta ita yake so? Ashe shima mayaudari ne kamar ragowar matasa masu kawo caffa ga rayuwarta don su ruguzata, shine ya sauya hanya ya turo da kud'in aure don ta saki jikinta dashi tunda aurenta zaiyi? "Imran me yasa". Haka tayi ta kuka tana katse kiran daya ke jera mata, kafun daga k'arshe ya mata, text kamar haka, "shikenan raihana tunda kin kasa fahimtata kiyi yadda kike so, sai dai Ina so ki sani ko gaisawa kukayi dashi bayan igiyar aure na ta hau kanki toh bazan tab'a yafe miki ba! Nina tafi ki turo su jidderh su d'auki sak'o a inda na tashi". Raihana ta karanta massage d'inshi yafi sau uku, mamaki take yadda yayi maganar shi hankali kwance tamkar baisan ma akwai wani kuskure daya aikata mata ba yanzun. Da sauri ta mik'e ta shige bathroom jin alamun tahowa da maganar ummie. Sai data saisaita yanayinta ta wanke fuskarta sannan ta futo, lokacin ummien ma ta futa. A parlour ta same ta zaune tana duba text book d'in jidderh dake zaune gefenta. "Na shiga kina ban d'aki". Raihana tace, "alwala na d'auro". "Imran d'in ya tafi Ina makullin?" Sai ta mik'e kawai ta futa daga parlon, a jikin k'ofar taga makullin, sai ta k'arasa rufewa ta zare key d'in kawai. Ta mik'awa ummie bayan ta shiga parlon. ★★★★★ Toh tun daga wannan rana sai Imran ya kasa gane kan raihana, ta sauya gaba d'aya ko wayarshi bata d'agawa, haka in yazo data futo sun gaisa take komawa gida tayi zamanta, sai dai ya k'ara ci tsayuwarshi har ya gaji ya tafi. Tun yana share ta da tunanin zata sauko sai gashi ya zamana abu kullum hauhawa yake, dole daga k'arshe ya dinga rubuta mata text na magiyar ta fad'a mishi abinda ya faru don Allah. Kamar ta kyale shi sai kuma taga makaho fa baisan ana ganin shiba sai an zungureshi, sai ta rubuta mishi abinda yayi wanda Sam bata so. Shi dariya ma abin ya bashi, yasan ba zata d'aga wayarshi ba, sai ya sake mayar mata da amsa ta hanyar text massage d'in, "emoji na dariya, kin bani dariya wallahi babie, aini ban d'auka d'an hug d'in dana miki wancen ranar ne ya haddasa wannan fushi da gabar ba, na d'auka kina yin hakane saboda nace ki rabu da saurayin ku, yanzu don Allah ki fad'a mun meye laifi dan ka tab'a jikin matar da zaka aura? Ai ba wani abu bane, balle ma ni nayi ne cikin zafin zuciya bansan ma nayi ba". Wannan text d'in sai yafi na farkon kona mata rai, wato baisan ma yayi ba, a gurin shi ashe k'aramin abune hug?. Aikuwa lallai zata ja baya a huld'arta dashi da sannu zai gane kuren shi. Daga nan sai raihana ta sauya salon mu'amular ta dashi a hankali, sun shirya amma bata sake mishi irin yadda take mishi da farko, haka takan dad'e kafun ta yarda yazo gidan su, ranar da zaizo kuma bayan tsawon lokaci toh zata tabbatar ba makaranta ta shirya muhibba ko jidderh taje dasu sitting room d'in. In yaso sai su zauna daga nesa dasu. Duk wannan abun Imran ya gane don shi takeyi, a tunaninta ai bazai tab'a ta a gaban yaran ba, shi kuma abinda bata fahimta dashi ba shine, yana yin komai nashi Kai tsaye, zai iya yin abinda yafi runguma a public tunda ai matar shi ce nan da watanni kad'an, toh shi baiga wani abun aibu a ciki ba. Sannu sannu kwanaki suna ta dad'a mik'awa, har gashi yanzu khausar tayi wata biyu a gidan mijinta, wanda yake nufin bikin raihana saura wata biyu ciff itama. Ranar wata juma'ah Salma tayi musu sammakon zuwa k'arfe takwas na safe ko karyawa ba suyi ba. A d'aki ta samu raihana ta futo daga wanka tana shirin saka kaya, da matuk'ar mamaki ta nufe ta tana fad'in, "Masha Allah kune da asubanci haka?". Ta k'arasa fad'a tana karb'ar samha a hannunta, Salma jakar hannunta ta ajiye ta zaune gefen katifa tana fad'in, "wash daga mota zuwa nan dana d'auko ta duk na gaji". Raihana harararta tayi ta zauna itama tana kallon yadda yarinyar tayi girma Masha Allah. Sun gaisa kamar koda yaushe in sun had'u Salma sai complain take raihana tak'i je mata sai dai a waya kullum tace zata zata. Raihana tace, "shine ke kika buga uban sammako haka kika zo, to ai kin kyauta". B'ata fuska Salma tayi tace, "nima ba zuwan ku bane takanas, gidan waccen matar da baki tab'a zuwa ba nazo na d'auke ki mu tafi tun kafun lokacin bikin yazo ki shiga uzuri". Dariya raihana tayi bayan gama jin abinda Salma ta fad'a tace, "lallai ma Salma da wannen safen zamu je musu gida kamar wasu korarru". Baki Salma ta saki tana kallonta kafun tace, "a'a kamar dai wasu y'an iska, nifa ba wai yanzu yanzu nake nufi ba, sai anjima rana ta d'aga sosai". Sai a lokacin raihana tayi dariya. Suna hirar su da salma ta k'arasa shiryawa suka d'auko baby samha suka dawo parlor. Duk yaran sun tafi makaranta tun 7:30 tare suka karya kumallo suna yi suna hira har suka kammala. Ummie da take bacci a d'aki hayaniyar suce ta futo da ita, ita kanta tayi mamakin ganin Salma da wannan safiyar, koda yake wannan ma ba shine karo na farko da take zuwan sassafe ba. Sun gaisa da ummie har tana d'aukar samha tana k'ara kallon yadda tayi wayo sosai. Ranar yini suka yi suna hirar su ta y'an uwantaka, sai k'arfe uku ma suka shirya tafiya gidan khausar d'in. Kamar koda yaushe raihana bata yi wata uwar kwalliya mai yawa a fuskarta ba, ta shirya cikin riga da skirt na material masu shegen kyau da tsari. Ta yane kanta da gyalenta wadatacce ta rufe rabin fuskarta da face mask. Gidan khausar ma Masha Allah, madaidaicin gida mai d'auke da wadatattun d'akuna da aka cika fal da kaya, kujeru ma set biyu akayi mata kamar yadda akayiwa Salma, haka kayan gado, babbah da k'arami, farin cikin da khausar tayi na ganin su yana da yawa, ta rasa inda zata ajiye su don murna, data fara d'ebo musu lemuka a fridge kuwa saida raihana tace, "muda waye zamu Sha duk wannan". Sannan ta dakata tana dariya. "Auntie ai ku d'inne kuka rikitani da zuwan bazatar ku, sai dai waye ya bada shawarar ayi zuwan yamma?". Raihana kallon Salma tayi, aikuwa khausar ta marairaice mata, "Kai don Allah auntie Salma ya zaki ce a bari sai yamma". Salma mik'ewa tsaye tayi ta rik'e k'ugu tace, "kin ji had'in borm ko? Toh wallahi wannan ta zaune a gaban ki badon niba da ita da gidan ki sai bayan aurenta, bazata tab'a zuwa ba tab yauma kinsan daya na d'ebo ta muka zo, abban samha fa na biyo k'arfe takwas ma a gidan su tayi mun a can na karya". Khausar dake kallonta had'e fuska tayi, "hakane auntie raihana? Zuwa tayi tun asuba ta d'ebo ki?". Murmushi raihana tayi tace, "eh mana tunda ni d'in ruwa ce ko kaya ba". Duk dariya sukayi. Kafun su fara hirar yaushe gamo, nan khausar ke basu labarin hajiya Inna (kakarsu) tazo mata tun bayan sati biyu da auren, tayi ta basu labarin yadda sukayi hadda had'o mata su yajin daddawa su tukud'i, da sauran abubuwan buk'ata na gargajiya". Raihana tace, "Ina ruwan hajiya innah baiwar Allah,kwana biyu ta d'aga mun k'afa har na manta rabon da mu had'u ma". Salma tace, "eh ta d'aga miki k'afa kam amma ai basu fasa k'aramar maganar suba, don ko rannan da na kai samha asibiti na biya ta gidan don mu gaisa, kinsan kana kwana biyu baka jeba zata hau complain ta ce ummie ce ta hana ka, toh shine fa da naje suke ta fad'in wai bakya son zuwa aike kin fi k'arfin kizo takanas gaishe da kowa a cikin su, ko sabga akeyi bakya zuwa, maganganu dai iri iri hadda wanda umma salaha take kaiwa". Tabe baki raihana tayi tace, "oho musu dai su suka sani suda kullum cikin yi musu laifi nake". Khausar tace, "kuma dai ya kamata auntie raihana ki daure kije ki gaisheta, ai ba zaki daka ta halinta ba don Allah zaki yi don Abban mu kuma data haifa". "Zanyi k'ok'ari" shine kawai abinda raihana ta fad'a. Salma tace, "ai dakin bar wahalar da bakin kima indai auntie raihana ce, wanda suke son ganin tama mutanen kirki bata je musu ba sai gidan hajiya Inna da take jiran k'iris da ita, ni kaina bana goyon bayan taje ma wallahi saboda a karon banza za su b'ata mata rai ta dawo tayi ta kukan nan nata mara jin ban hak'uri". Raihana da take jinsu tana nazarin maganganun su d'aya bayan d'aya mik'ewa tayi don amsa kiran da Ayman yake yi mata a lokacin. Bayan sun gaisa dashi shima complain ya fara mata na kwana biyu ko neman shi bata yi, har zazzab'i ya kwanta kwana uku baya futa office bata sani ba saboda yanzu ta watsar dashi ba ruwanta da neman shi ta mijinta kawai take da aurenta, hak'uri kawai ta bashi saboda ita har ga Allah rikita rikitar data shiga ta Imran ce ta maida kwakwalwarta busy har ta manta da wasu abubuwan ma, amma fa duk da haka shi yana ranta. Sun d'an tab'a hira har tayi mishi alk'awarin zata zo gidan iya tayi mishi waina cikin weekend saboda ya mata k'orafin ya rasa appetite, baya iya cin komai sai tea tsura, aikuwa cikin jin dad'i ya fara mata godiya da fad'in data kyauta mishi kam, raihana dai dariya tayi ta mishi kafun suyi sallama ta ajiye waya. Dawowa tayi gurin su Salma da khausar da suke ta hirarrakin su, tunda suke maganar su bata ce musu kanzil ba, in ka ganta cikin su saika d'auka itace k'anwa sune yayyen saboda sauk'in kanta, dama ita Sam ba mutum ce mai fad'a da shiga shirgin mutane ba, koda yaushe tana yin rayuwarta ne ita kad'ai khausar ma kusan yanayin su d'aya, amma Salma kamar ba umkiem su ta haifeta ba, Sam bata d'aukar raini yanzun nan za'ayi wacce wacce kowa ya kama gaban shi. Basu suka bar gidan ba sai bayan sunyi sallar magrib, suna shirin tafiya gida khausar nata k'orafin wannan ziyara bata Isa ba sai sun k'ara zo mata zuwa na musamman, suka samu suka lallab'ata akan lallai zasu tsaida rana su dawo kafun bikin raihana, da haka dai sukayi sallama ta rako su har bakin get bayan ta had'a musu kayan snacks da biscuit a kaiwa su jidderh, da kyar suka karb'i kud'in data basu su hau mota, raihana ma gaba tayi sai Salma ta rik'e ta mak'alawa, a napep raihana take fad'a ma Salma ita fa so tayi sai kud'in ta sun had'u ta siyawa khausar gift na abu mai kyau da zata ji dad'in shi sannan tazo, Salma tace, "don takurawa kai ba? Koda yake kada na hana ki yi mata bayan nima kinyi mun na zama mai hana alkhairy, amma gani nayi bafa wani abu kike siyarwa ba, sannan har yanzu baki fara aiki ba abinda yake hannun ki ga biki yana ta k'aratowa, a k'a'ida kin shiga lokacin da ko kika fi kowa buk'atar kud'i a hannu saboda hidindimu". Murmushi raihana tayi tace, "noop akwai abinda yake hannuna da zanyi mata hidima dashi, kuma kinga ni bani da wata hidima a gabana, komai ummie ta gama siya tun a wancen lokacin ma, in baki manta ba lokacin da aka fasa aurena na k'arshen nan komai abbah ya sauya mun sababbi iri d'aya dana khausar, ni kuwa me zanyi da kud'i". Salma cikin jinjinawa tace, "haka ne kuma tabbas, toh amma dai kada ki yiwa hannun ki kakaf, kuma muna nan muna addu'a insha Allah an gama fasa auren ki, in Allah ya yarda wannan sai anyi dashi.....". Murmushin takaici raihana tayi tana tuna abinda yake tsakaninta da Imran d'in ma a yanzu tace, "Ni na dad'e da fudda tsammani Salma, na barwa Allah dukkan lamuran rayuwata, shi kad'ai yasan abinda yake bad'ini, kuma shi yasan abinda yake mafi dacewa ga rayuwar bayin sa". Salma tace, "wannan haka yake, toh Allah ya tabbatar miki da alkhairin shi". Ta amsa da "ameen". Sai wajen isha'i suka Isa gidan su, aikuwa ummie taita musu fad'an kaiwa daren da suka yi, dama raihana tayi tsammanin za'ayi haka, kuma duk sun haddace wannan dokar gidan suce tun ta k'uruciya, basa futa bada izinin Abban suba, sannan basa kai magrib a waje ko gidan wa suka je, idan kuwa har suka kai dare to tare da abban su zasu dawo. Salma tana zama don tayi sallah ta huta mijin ta yazo d'aukarta, aikuwa ummie ta fatattakata tace sallar ma tayi a d'akinta in taje sai tafi lada. Raihana dai tana tsaye sai dariya take mata ciki ciki. *********** Washe gari ya kama asabar, tun da wuri raihana ta gama aikinta na gidan ta had'a musu abincin karin kumallo, ko data je gaishe da abban su da safe sai ta tambaye shi tana son zata je ayi mata lalle nan kan titi gurin Zahra, Abba da yake tankwashe da k'afa kan sallaya yana yin lazimi ajiye carbin yayi a gefe ya fuskanceta da kyau kafun yace, "toh ba damuwa nawa ne ake yin lallen?" raihana tace, "bak'i ne kad'ai ma za'ayi mun dubu d'aya da d'ari biyar ne". Dubu biyu ya bata yace sauran tayi wani abun dashi, bata karb'a ba tace, "Abba ai akwai kud'i ma a gurina da ka barshi kawai". Had'e fuska yayi yace, "rok'on Imrana kud'i kikeyi?". Ta girgiza kanta da yake k'asa tace, "a'a Abba". "toh kenan Ina kika samu kud'i bayan bakya juya komai a hannun ki". Sai tayi tsuru tsuru cikin rashin sanin abinda zatace, "ke nake tambaya kinyi shiru?". Cikin tsoro tace, "Abba akwai ragowar kud'in da ummie ta bamu na gyaran gashi da lalle dasu kwalliya a lokacin banyi amfani dasu duka ba". Sai lokacin ya d'an sassauta yace, "toh da sauk'i amma ki karb'a ko wani abun ba sai kiyi dasu ba tunda hidindimun ku kullum basa k'arewa". Cike da jin dad'in yadda ya fahimce ta ta amshi kud'in tare da yin godiya. Shiyasa har yanzu bata nuna kud'in da Imran ya dinga zuba mata a account ba saboda tasan fad'a za'ayi mata bana wasa ba. Har ta tashi zata tafi sai abban ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, "raihanatu dama Ina son yin wata magana dake". Raihana Saida gabanta ya yanke ya fad'i ta dawo jiki a sanyaye ta sake durk'usawa gaban shi, dai dai lokacin ummie ta shigo rik'e da tray na abincin karin shi. Dubun godiya da goyon baya my fans, Ina yinku fiye da yadda kuke yina👍👍😍 _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page fourteen1️⃣4️⃣ "Ina fatan komai yana tafiya dai dai babu wata matsala tsakanin ku dashi Imrana d'in ko?" Saida gabanta ya fad'i sannan jiki a salub'e tace, "babu wata matsala Abba". "Toh Masha Allah ki ci gaba da yawaita addu'a insha Allah, Allah zai zab'a miki abinda zaifi zama alkhairy ga rayuwarki". Gyad'a mishi kai tayi "insha Allah Abba zan dage sosai" ta mik'e ta fuce daga d'akin. Misalin k'arfe sha d'aya da rabi tayi sallama da ummie ta d'auki kud'i da wayarta ta fuce daga gidan. Wani shago dake kusa dasu na kwalliya, gyaran jiki da lalle ta nufa direct, bayan sun gaisa da ma'aikatan gurin, zama tayi jiran me lallen ta gamawa wadda akewa a lokacin itama tayi mata. Allah ya taimake aka gama da wuri suna d'an hirarrakin su da mutanen gurin lokaci bayan lokaci. Tun ba'a dad'e da gama mata ba sukayi waya da Ayman yake shaida mata yana gidan iya, ta fad'a mishi ita kuma tana zahra's saloon in ta gama zata zo, yaso biyota tun a lokacin ta hana shi saboda zai dad'e yana jiranta a k'ofar shagon kafun lallen ya kama jikinta ta wanke. Tana shirin sallama dasu aunty Zahra bayan an gama kiran shi ya sake shigowa, bata d'aga ba ta futo da sauri tasan ya gaji da jira ne, sai ta tsaya da mamaki tana kallon shi tsaye hard'e da hannu a k'ofar shagon, sanye yake da JC black and white dai dai jikinshi, sai kanshi rufe da hula ta sak'a fara sol. A hankali ta k'araso gaban shi bata dai ce komai ba. Ayman ne cikin shagwob'ewa sosai yace, "raihanatu lallen nan ya dad'e almost 2 hours fa ina jiran ki". Cikin had'e rai itama tace, "toh ba dama na fad'a maka lalle ana dad'ewa ba, ka had'a komai da komai ne?". Murmushi Ayman yayi yana kallon k'afarta da hannunta yace, "gaskiya ne lallen ya miki kyau sosai, gashi ba don ni akayi ba amma kuma nina fara gani". Ya k'arasa fad'a da neman magana. Raihana fuskarta a had'e har lokacin tace, "toh wa yace daka gani ka yaba?". "Saboda idanuna ba zasu iya ganin abu komai k'ank'antar shi a tare dake bakina bai magantu ba". D'an hararar gefen shi tayi tace, "toh anan zamuyi wainar ne naga muna ta tsayuwa lokaci na tafiya". "Toh ai kece kika tsayar damu a nan d'in, ni kuwa yana iya yadda kike so haka za'ayi gimbiyar mata". Murmushi kawai tayi ta fara yin gaba yabi bayanta da sauri suka jera, suna tafe suna hira kai inka gansu saika d'auka wasu shahararrun masoya ne na k'arshe d'in nan. Saida ta saci kallon k'ofar gidansu da zata huce, gidan a rufe yake ruff! Iya nata aikace aikacen ta suka shigo da sallama kusan a tare. Cikin farin ciki tace, "haba ai tunda naga Ayman yana duba agogo tun d'azu nasan ke yake jira, Ina shiga d'aki in futo na nemi mutum na rasa, nace toh ya tafi ya taho dake". Ita dai raihana bata ce komai ba sai gefen iya data samu ta zauna tana gaishe ta da tambayar malam. "Malam yau ya tafi kasuwa zai had'o wasu turaruka". "Ayyah Allah ya dawo dashi lafiya" Suka amsa da "ameen". Saida suka fara yin sallah sannan ta duba duk abubuwan da zasu buk'ata na waina a kitchen d'in iya, kusan tare suka had'a ko tace Ayman ya barshi baya bari sai yayi a cewarshi wai yunwa yake ji yau sosai. Iya dai inta kallesu murmushi kawai take taci gaba da ayyukan ta. Haka aka soma soya wainar fulawa ta mutum biyu, in ya zuba ta gasu raihana ta juya ta kwashe a plate, saida suka tara da yawa suka ba iya, ta karb'a bayan tayi godiya ta zauna ta fara ci, wata suka k'ara tarawa, raihana ta d'auki plate d'in takai kusa da iya tace da Ayman, "Ka zauna kaci don Allah ni na gode da tayin aikin wanda kayi ma Allah ya bada lada". Mak'e mata kafad'a yayi kamar k'aramin yaro, "bakya son kici tare dani ko raihana?". "A'a Yaya Ayman saboda kace kana jin yunwa ne idan ba yanzu ba sai yaushe zakaci kenan?". "toh ni bazan iya ci ba tare dake ba yau ko yunwar zata kashe ni kuwa sai an kafa tarihi". Saita dafe kanta oohh Yaya Ayman rigima, "Ni dai Allah kaci abincin ka nima zanci ai in na gama". "A'a fa" ya fad'a yana yin kicin kicin da face, Dole raihana ta hak'ura a k'arshe Suka gama wainar tare suka zuba wadda zasu iya ci sauran ta rufewa iya a cooler. Gefen iya suka zauna kan tabarma suna cin wainar. Ayman kam sai zuba loma yake saboda wainar tayi mishi dad'i ba kad'an ba, a duniya baya jin za'a samu wadda ta iya wainar fulawa irin raihana, yana ganin har degree tayi indai ta fannin iya sarrafa kowanne kalar abinci ne. Ita kuwa raihana dake d'osane tana d'an yafuta da kad'an kad'an wani tunanin take yi daban, tun tana iya cin wainar har ta daina ta zabga tagumi ta lula duniyar tunani, maganar Ayman ce ta farkar da ita ta juyo tana kallon shi, "bakya cin wainar nan fa Ina lura dake raihanatu, ni kuma nafi son kici sosai saboda daga yau ba lallai na sake samun damar ganinki irin haka ba, abincin ma nasan zai zama sau d'aya a tarihi". Sai kuma ya sake yin kalar tausayi ya tsame hannun shi daga abincin yaci gaba da maganar shi, "yanzu fa shikenan kin kusa zama matar wani raihanatu, zakiyi auren ki ki tafi ki barni bayan lokaci k'alilan ki manta dani ......". Raihana tana kallon kwayar idanun shi itama cike da tausayin yadda zatayi kewarshi tace, "har abada bazan tab'a iya mantawa dakai ba Yaya Ayman, ka zamo mun d'an uwa garkuwa jigo da zan iya bugar k'irji nayi alfahari dashi a ko'ina, wallahi yaya Ayman da zan haifa d'an da nake da ikon bashi suna saina saka sunan ka, tabbacin zan dinga tunawa dakai all the times". Shiru Ayman yayi wani abu abu mai wuyar fassaruwa shimfid'e saman fuskarshi, duk sunyi shiru kamar wanda aka aikowa da sak'on zagi, iya da take gefen su har lokacin sun ma manta da ita, gyaran murya tayi tace, "toh waye zai cinye muku abincin?". Kallonta kawai Ayman yayi ya maida hannun shi cikin abincin, raihana ma ci gaba da cin abincin tayi jiki a sanyaye, ba wanda yake iya cewa komai sai kallon kallo da Murmushin yak'e. Iya dai girgiza kai take inta kalle su tana k'ara karatun kowanne motsin su. A dai dai wannan lokacin surayyah tayi sallama, duk suka d'aga ido suna kallonta. Sanye take da doguwar rigar super Holland ta yafa gyalen ta wadatacce, fuskarta washe da fara'a ta k'arasa shigowa, yara nabin bayan ta da kayan lemukan gidan da taga sun k'are da kayan shayi. A hankali raihana ta cire hannunta a abincin ta koma gefe. Surayyah kam zama tayi kan tabarmar, yaran suka ajiye kayan a gabanta ta sallamesu da y'an kud'ad'e da kayan snacks cikin wanda ta kawowa iya. Shima Ayman dena cin abincin yayi ya zaro wayarshi ya bada attention d'inshi a can. "Ina yini Auntie?". Raihana ta fad'a kanta a k'asa, da fara'ar ta sosai tace, "a'a raihanatu yakike ya maman naki". "Tana lafiya qalou". Auntie tace, "Toh Masha Allah ki gaisheta". Ta amsa da "zataji insha Allah". Suna gama gaisawa ta mik'e ta yi musu sallama zata tafi, iya tace, "au har zaki tafi raihana?". Tace, "eh iya a gaishe da malam". Iya tace, "tom ki gaida gida da ummien taki na gode kinji Allah yayi miki albarka". Mik'ewa Ayman da yake zaune yayi yabi bayanta, har takai k'ofar gida ya cimmata, "kin yiwa kowa sallama amma banda ni, meyasa?". Juyowa tayi ta kalle shi, "Tom kaima sai anjima Yaya Ayman". Murmushi ya k'ak'alo yace, "bari na taka miki". Sunci gaba da tafiya shiru kowa da abinda yake tunani har suka Isa k'ofar gidan su, har sunyi sallama zasu rabu raihana tace, "ooh Yaya Ayman dama Ina son in mun had'u mu k'arasa maganar nan, sai naga kud'i wancen watan? Ni kuma sai naga yanzu tunda na gama karatun.......". Da sauri tayi shiru tana kallon yadda ya d'aga mata hannu rai a had'e, "Ina ce mun riga mun gama wannan maganar dake tun a waccen ranar? Toh Ina ruwan ki don nayi miki abinda ba dole kika yi mun ba? Koda yake har yanzu baki gama fahimtar irin matsayin da kike dashi a gurina ba ko?". Ita dai raihana shiru tayi ba tace komai ba, "Ina magana kinyi shiru raihanatu". Girgiza mishi kai tayi slowly tace, "kayi hak'uri Yaya Ayman". "Good ki gaida ummie dasu jidderh". Da gyad'a kai ta amsa ya d'aga mata hannu ya juya, itama shigewa gida tayi. ######### Auntie ce zaune ta tattara nutsuwarta tas tana sauraron iya da take magana a lokacin, "abinda nake so na tambaye ki shine, "shin yaran nan haka zaki zuba musu ido ba maganar aure?". Murmushi auntie tayi tace, "iya akwai maganar auren su mana, Ayman akwai y'ar k'awata sameera nuriyya da suke soyayyah, khaleefa zai dawo nan da watanni biyu masu zuwa, idan yana da zab'in matar da yake so ba dole, amma idan babu toh akwai yayar Nur shaheeda har tafi Nur kyau da aji tana karatu yanzun haka a maitama sule, nasan bazai k'ita ba don ta futa son kowa k'in wanda ya rasa, saina had'a duka na aurar dasu hakan yayi ko iya". Iya girgiza kai tayi tace, "idan har kin yaba da tarbiyyar yaran babu laifi, kuma idan sun amince suda kansu hakan yayi, Allah ya tabbatar mana da alkhairin shi". Iya ta fad'a tare da had'iye abinda tayi niyyar fad'a game da raihana da Ayman a lokacin. @@@@@ Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, bikin raihana sai dad'a k'aratowa yake, gidan su Imran sun kawo kayan lefe akwati mai daraja saiti takwas, sunyi komai dai dai k'arfin su har an tsaida lokacin biki nan da sati uku masu zuwa, duk wani shirye shiryen biki ya kammala saboda suna jin k'amshin da gaske wannan karon za'ayi da Imrana. Saboda a duk samarin da take yi babu wanda maganar shi ta tab'a kaiwa tsawon wannan lokacin har a karb'i lefe. Ranar da aka kawo wannan Kaya umma salaha kwana tayi bata yi bacci ba saboda tashin hankali, yaron ya cika taurin kai duk wasu sharud'd'a sai daya shallake su, bata manta karo na k'arshe da tasa akayi mishi magana a kan yarinyar y'ar iska ce yawon bariki take, cewa yayi ko a gidan karuwai take haka yake sonta, zai aure ta domin Allah. Na farko dama da aka fad'a sam baiyi tasiri ba, hakan yasa ta fara shirya bita da k'ulli da zagon k'asa, ranar da taje saloon da k'unshi suka tafi tare da Ayman har hoto tasa aka d'auke su a k'ofar gidan, aka tura mishi hadda doguwar wasik'a kamar wani abun arzik'i har shagon kasuwar da yake, kuma a dai dai inda zai gani ya karanta, ba komai aka fad'a ba sai Ayman shine wanda suke soyayyah da raihana sama da shekara takwas suke tare, ya gama lalata rayuwar yarinyar gaba d'aya, shiyasa sau biyar ana sa ranar aurenta duk wanda yayi bincike ya gano saiya barta, kaima kana tare da itane saboda bakasan ainahin wacece ita ba. Maganar ta shige shi sosai ya Kuma ji haushi kwarai musamman duba da yanda suke ta fafatawa akan Ayman d'in tak'i rabuwa dashi, koda yake bari yaba kanshi maslaha Allah ne ya d'ora mishi masifar son raihana, kuma yau ko kanjamau ce a tare da ita ba abinda ya Isa yasa shi fasa aurenta, sannan matsalar Ayman ya riga ya dad'e da gamawa da ita, jira kawai yake a d'aura auren su, ko gaisuwa bazai k'ara yarda ta had'a ta dashi ba, dole wannan dangartakar ta k'are tunda dai shi d'in aiba Muharramin ta bane bare ace. Da wannan tunanin yaji sanyi a ranshi da k'arfin gwiwa. Da hoton da takardar yayi musu kyakkyawan adani. Na biyu munir aka sa yayi mishi magana face to face, still dai abu d'aya aka k'ara fad'a, nan ma yayi watsi, sun d'auka abun ya shige shi sai gashi da kwana biyar an kawo lefe, tashin hankali yasa ta kasa katab'us tunda abubakar ya fad'a mata, musamman da taji akwati har takwas, ko su Salma basu samu irin wannan lefen ba bare y'arta data aurar a wahale, k'arshe mijin bashi da komai duk k'arya ce ya dinga tsula musu, yanzun kusan su suke taimaka mata, don kar auren ya mutu nema asirin su ya tonu aji halin da suke ciki amma ita tuni ta gaji da wannan jeka na yikar aure. shine yanzu hankali tashe take neman yadda zata b'ullowa wannan aure na raihana. ( _Ku kuji fa, madadin ta kula da abinda yake gabanta ta kashe wutar gabanta, ta k'are da neman lalata auren wata don ta cusa bak'in ciki ga rayuwar iyayenta, toh hassada dai ga mai rabo_........) Gidan su raihana kuwa y'an uwan ummie na kusa dana nesa duk sunzo sunga kaya sun yaba kwarai, ta b'angaren Abban suma mom ziyada tazo tare da babbar y'arta, kakar sukam tace sai biki ita ba zata iya gantalin zuwa ganin abinda ba tabbas ba, ai ba girin girin ba dai tayi mai, ta kuma hana kaf y'ay'anta zuwa da y'an majalisar ta, matar Abba abubakar kam a wannan karon bata hanu ba saboda tana son gani da idonta donta tabbatar da abinda y'an anguwa suke ta rad'e rad'in fad'a. Saboda tsabar bak'in ciki da hassada kasa b'oye bak'in cikin ta tayi, gashi zane k'iri k'iri fuskarta ta nuna, haka ta dinga kyab'e baki da fuska tana yatsine yatsine. Har dai ta tafi ko ala sanya alkhairy ba tace ba. Soyayyar raihana da Imrana kuwa sai abinda ya dad'a k'aruwa ma, yadda ta fahimci yana sonta sosai sai itama ta bada hankalinta a kanshi, tun waccen ranar bata k'ara had'uwa da Ayman ba sai dai waya, itama ba sosai ba yaja baya da ita sosai a hankali saboda ya ragewa kanshi rad'ad'in ranar da zasu rabu, ta bayan fage yana ta tunanin abinda zai siya mata as a wedding gift da zai burgeta sosai. Iya ma nata had'a mata magunguna irin na gargajiya da ake yiwa kowacce yarinya idan zatayi aure tun zamanin da. Da kanta takai mata da taje ganin kayan lefe, ta zaunar da ita ta karanta mata yadda zata yi amfani da kowanne a ciki. Ita dai ta karb'a tana dariya ta shige d'aki cike da kunya. ★★★★★★ Raihana tana zaune a d'aya daga kujerun parlon gidan su, sanye da doguwar rigar kinomo ta ciki kuma riga ce body hug da straight skirt da yabi lafiyar shape d'in jikinta ya zauna, tayi rolling kanta da k'aramin gyalen rigar blue, kayan ciki kuma black. Fuskarta akwai light make up data k'ara mata kyau matuk'a, gaisawa tayi da k'awayen ummie da Suka zo ganin kaya, suka amsa suna zolayarta wai ta saka su ummie a ranta duk ta rame, ita dai dariya kawai tayi don har ga Allah bata ga ramar da suke fad'a ba, d'aya cikin su da ummie take kira suwaeba tace da ita, "ya maganar ci gaba da karatu ko aiki? Da fatan ya amince zaku d'ora bayan auren ko". Girgiza mata kai tayi idonta na kallon k'asa, ummie ce ta yi musu bayanin yace shi bai yarda ba, baban ta kuma bai matsa ba, tunda gasu Salma da khausar nan ko y'ar higher institution d'in da tayi ma babu wadda tayi a ciki. Suwaeba tace, "kuma dai don d'an kasuwa ne da ma'aikaci ne Ina tunanin zai iya barinta", ummie tace, "anya kuwa? Abun fa ra'ayi ne wani ko shine ya haifi boko bazai yarda matar shi taci gaba da karatu ko ta futa aiki ba". D'aya cikin su tace, "haka ne kam kema haka akayi miki gashi raihana ta gaje ki". Dariya duk sukayi, mik'ewa raihana tayi ta nufi d'akin ummie, bin bayanta ummien tayi tana shirin kwanciya gefen bed tace, "ba tun d'azu al'ameen yace miki ya kaishi sitting room ba?". Saita mik'e zaune kurum, ummie tace "bana son shashanci kin fi son sai ya gaji ya fara kiran ki a waya wato". Tace, "a'a ummie yanzu zan tafi ai". "Ya daifi" tana fad'a tayi hucewarta waje. Ita kam raihana tunanin abunda zai je yazo kawai take, tafi son ace su muhibba suna nan ta tafi tare dasu, don tun wancen ranar bata k'ara yadda sun had'u ba y'an rakiya ba sai kwana kwanan nan, ummie tayi fad'a harta gaji ta kyale ta kawai don ba fad'ar dalilinta zatayi ba in abun zai kashe ta kuwa. A sanyaye ta futo ta zura plat shoe a k'afarta ta nufi sitting room d'in. Yana tsaye a tsakiyar parlon hannun shi duka biyu goye a bayan shi ya zuba ma saman d'akin ido fuskarshi na fudda wani annurin farin ciki. Jingina tayi itama jikin k'ofar tana kallon shi kamar wadda aka turo, sauke idon shi yayi a kanta a nutse yana binta da tsantsar kallon so da k'auna. "Mrs Imrana Muhammad Abubakar" sai data lumshe idonta ta d'ora hannunta a k'irjinta tana murmushi mai kama da dariya. Slowly ya tako gabanta sai bud'e ido tayi ta ganshi daf da ita har numfashin shi na sauka saman fuskarta, "alhamdulillah burina ya kusa cika raihana, Zan mallake ki a matsayin matata". Juyar da fuskarta tayi yanayin ta na sauyawa kad'an daga na tsantsar farin ciki zuwa na d'aure fuska ta soma tunanin yadda zata kauce mishi, Imran kam hannun shi yasa ya tokare gefe da gefenta ya k'ara kusantar da fuskarshi gare ta, cikin b'ata fuska sosai ta kalle shi idonta ba wasa a ciki tace, "me kake yine haka don Allah ka matsa.....". Ai bai bari ta k'arasa ba ya d'ora yatsar shi guda akan lips d'inta yace, "shhhhh! Yau dai d'aya raihana, yau d'aya ki barni naji d'umin jikin ki, na sumbaci wannan lausasan lips d'in. Only light romance baby". Ya kai k'arshen maganar yana shirin had'e bakinta da nashi. _raihana kina ruwa tsilli tsilli🙆‍♀️_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page 1️⃣5️⃣ Da wani irin sauri raihana ta ingije shi ta matsa gefe can nesa tana sauke ajiyar zuciya kwayar idonta na tara ruwan hawaye, Imran dafe kanshi yayi ya juyo yana kallonta, yadda take jifan shi da wani irin kallon takaici kad'ai ya isa ya nuna mishi ta Kai mak'ura wajen fushi da jin haushin shi, k'ara matsawa yayi amma bai k'arasa har gabanta ba ya tsaya daga baya baya ya soma fad'in, "kiyi hak'uri my love ni ban d'auki kiss and hug as something different ba, ina tunanin in babu so da k'auna ba abinda zai shigo dasu cikin alak'ar mu, naga kina kallona wani iri, amma kiyi hak'uri na fahimci baki so shiyasa tun waccen ranar ban sake kwatanta aikata hakan ba, duk da yadda ni nake da ra'ayin hakan ga matar dana tabbatar zan aura, a yauma na kasa control yadda nake ji a kanki ne shiyasa, ji nake kamar har mun riga mun zama d'aya, bawai nayi da nufin b'ata miki rai ba". Sai ya durk'usa a gabanta bisa gwiwowin shi, "amma don Allah kiyi hak'uri ki gafarceni". Duk yadda raihana taji zafin shi saida zuciyarta ta d'an sassauto taji sanyi da nutsuwa kad'an. "ka tashi kada wani ya shigo ya ganka a d'auka wani abun ne". Girgiza mata kai yayi "sai zuciyar ki tayi sanyi kince kin hak'ura sannan". Fuskarta babu yabo babu fallasa tace, "toh nace ya huce shikenan?". Sake girgiza mata kai yayi yace, "umm umm ki fad'a har ranki da gaske bada sigar na takura miki ba". "Toh na hak'ura don Allah ka tashi". Mik'ewa tsaye yayi ya samu guri ya zauna, itama zaman tayi. Shiru babu wanda yace da d'an uwanshi kanzil har na tsawon wasu mintuna kafun raihana ta fara maganarta cikin sanyi da fad'in, "kayi hak'uri duk da na yadda dakai, na yarda abunda ya faru yanzu ya huce har abada bazai sake faruwa ba, Cox we have no much time da irin hakan zata sake faruwa ma, toh sai dai duk da haka ni bazan fasa yi maka magana ba akai, farko daka tab'a hugging d'ina kwanakin baya na d'auki fushi dakai sosai nasan baka manta hakan ba ae?". Gyad'a mata kai yayi, tace, "good toh bazan b'oye maka ba babu irin tunanin da banyi ba a lokacin, ciki harda na yanke alak'a ta dakai saboda na kalle ka a matsayin gama garin mayaudaran maza dake amfani da kud'in auren su dake gidan su yarinya su lalata mata rayuwa daga k'arshe su tsallake su gudu su barta. Sai dai a hankali d'abi'un ka suka dinga fad'a mun gaskiya a kanka da yadda ka d'auki alak'ar mu har na gane baka daga cikin jerin irin wad'an can da nake maka kallo a lokacin, sai dai kana da ra'ayin soyayyar zamani da y'an mata da samari kan gudanar a matsayin ba komai ba duk cikin so da k'auna ne which is totally wrong, da farko dai haramun ne ka sani har a addinan ce ka tab'a jikin matar daba muharramar kaba, na biyu shin duk munsan abinda zai faru damu gobe? Toh taya kenan zamu tabbatar da cewa mu mullakin juna ne? Ba fata nake ba amma cikin second ubangiji zai iya juya dukkan al'amuran shi ta fuskar da bamu tab'a zato bare tsammani ba, shin wane suna zamu kira kanmu dashi kenan? Mun yaudari kanmu ko kuma mun yiwa kan mu adalci? Mata ko mijin da Allah ya juyawa al'amarin kansu shin mun kyauta musu kenan, kada ka manta kowanne namiji yana fatan auren mace innocent, haka ma mu mata, idan son samun ku ne zaku ce wadda namiji bai tab'a rik'ewa hannu ba, itama macen wanda bai tab'a rik'e ko tab'a jikin wata d'iya mace ba, shin mun cuce su ko bamu cuce suba? Allah zai yafe mana ranar gobe k'iyama kuwa? Ni dai da haka nake rok'on ka don girman Allah ka cire wancen abun daga cikin zuciyarka, kayi yak'i da zuciyarka aikin sab'o da duk abinda yake haram su daina burge ka, ka dinga niyyar abu mai kyau a zuciyar ka wanda Allah zai baka ladan niyyah in baka samu damar cikawa ba, ba wai Haram da zaka k'are da zunubi ba, Ina fatan zaka yiwa maganganu na kyakkyawar fassara ta hak'ik'a bata son zuciya ba duk da dai tuni ne" Tunda raihana ta fara magangana Imran ya kafe ta ido yana kallon other side of her, lallai dole yaci gaba da son yarinyar nan, domin abar so ce ga kowa da yasan abinda yake yi a rayuwa. Bai bar kallonta ba har saida takai k'arshen maganar ta, doguwar ajiyar zuciya yaja ya furzar da iska mai huci daga bakin shi kafun ya fara magana da, "alhamdulillah! alhamdulillah!! alhamdulillah!!! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala daya bani ke kyauta a matsayin matar aure raihana, tabbas samun irin ki cikin dubu sai an tona, domin kinfi kowanne kalar mata tsada musamman a wannan zamanin da muke ciki, hak'ik'a nayi nadama dana kasance cikin samari masu bin ra'ayin yahudu ta b'angaren soyayyah, har a minti biyar da Suka gabata kafun yanzun ina d'aukar waccen soyayyar a matsayin soyayyar da tafi kowacce siye zuciyar mace cikin sauri raihana, sannan na d'auke ta hanyar expressing feeling d'ina at sad or happiest moment, shiyasa na yi attempting gwadawa a kanki duk lokacin da nake cikin b'acin rai ko farin ciki, amma insha Allah raihana hakan bazai sake faruwa ba har sai ranar da naji an shafa fatiha". Raihana rufe fuskarta tayi tana k'unshe dariyarta, cikin matuk'a jin dad'i da farin cikin yadda ya fahimceta cikin sauk'i har yayi nufin gyara kuskuren shi. Sun ci gaba da hirar su rabi duk kan yadda zasu tsara shagalin bikin su, bai tafi ba sai yamma lis don sallar la'asar ma a nan yayi cikin sitting room d'in. Daga nan Komai yaci gaba da tafiya lafiya, yayinda raihana da Imran Suka ci gaba da tsananta addu'a akan maganar auren su, y'an uwa da abokan arzik'i na taya su. Ayman kuwa..... Ba zan iya tantance muku halin da yake ciki a yanzu ba, sai dai ya maida kanshi over busy a gida ko office, yak'i yake da zuciyarshi sosai akan raihana da al'amuran aurenta, a kullum dare yakan hana idon shi bacci yayi ta addu'ar da bansan wacce iri bace kuma a kan wa. Yanzun ya sake nisanta kanshi da raihana gaba d'aya, ya k'ara kusanta kanshi da nuriyyah, ko abinci wani lokacin baya iya ci sai ya taso office ya biya ta gidansu Nur yaci wanda ta dafa da hannunta, yana kallon kyakkyawar fuskarta yana jin dad'ad'an kalamanta, ko Auntie bai fiya yiwa doguwar hira ba, iya kuwa tuni ya yiwa gidan ta yaji baya son ko hanyar gidan ya tuna bare yaje. Iya tayi cigiyar shi har ta gaji, haka malam ma. @@@@@@@@ _masu iya magana sukace waiwaye.........._ *GERMANY* zamu iya cewa komai yana tafiya dai dai a rayuwar khaleefa kama daga rayuwar sa a makarantar Humboldt zuwa kan yadda yake iya k'ok'arin shi wajen ganin ya samu nasara akan abinda ya zaunar dashi, haka alak'ar shi da Ahmad suna zaune lafiya duk da sun d'an ja baya kad'an saboda yanzun yafi bada muhimmanci a soyayyar shi da Saleema, ya zamana a yanzun ta d'auke kaso biyu a rayuwar shi wato budurwa kuma k'awa. Soyayyah suke yi tsantsa irinta Nigerians and hausa by tribe da suka rayu cikin masu jan gashi (turawa), duk da kasancewarta y'ar wata k'asa daban, a kowacce rana kusancin su fin na kullum yake yi suna k'ara samun shak'uwa da fahimtar juna, breakfast, lunch and dinner duk zasu yi tare a plate guda, su yini tare suna baiwa juna labarin ban dariya da d'ebe kewa a wasu lokutan hadda na k'uruciyar su daya gabata. Sai dai duk wannan abun da yake faruwa khaleefa bai tab'a yarda sunyi cud'anyar jiki da juna ba, so yake suyi soyayyar su mai tsabta da bazata lalata musu zamantakewar aure ba nan gaba. A yanzun khaleefa yasan wacece Saleema ciki da bai, har yana gaisawa da wasu cikin familyn ta a waya ma. Saleema Omar asalin ta y'ar k'asar Niger ce garin zinder, mahaifinta shahararren d'an siyasa ne daya keda kud'i da k'arfin iko, su biyu kawai iyayen su suka mallaka a duniya, daga ita sai k'anwarta da take matakin secondary a k'asar su. Iyayen ta suna matuk'ar ji da ita, hakan yasa suka amince da tahowarta Germany karatu ba don ransu na soba. Suna bata goyon baya a karatun ta kuma suna sakar mata kud'i bana wasa ba don taji dad'in yin karatu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Ta b'angaren alak'ar ta da khaleefa bil hak'k'i take son shi da zuciyarta d'aya, hakan yasa ta bada attention d'inta duka kanshi fiye da sauran samarin da tayi a baya. Duk da kasancewarta sangartacciyar y'ar masu kud'i amma ta samu kulawa da tarbiyyah mai kyau daga iyayenta duka biyu. Hakan ya taka rawar gani wajen sa ta yin takatsantsan da samarin banza da gujewa sharholiyar k'awaye, macece mai matuk'ar aji da k'afulle inba khaleefa ba ba wani namiji data tab'a sakewa har ya shigar mata d'aki kota je mishi da sunan soyayyah ballantana har taji tana son ya bata abinci da hannun shi a baki. Wannan kenan. ★★★★★ Misalin k'arfe sha d'aya na daren ranar alkhamis, khaleefa ya futo shirye cikin English wears, rigar bak'a ta sanyi mai kauri ya zame hular ta sauka k'eyar shi, sai zaren mad'aurin rigar guda biyu da suka futo ta y'ar k'aramar hudar gaban rigar. Dogon crazy trouser daya d'ame k'afar shi ta k'asa shima bak'i sai socks ta hannu da k'afa. Daga yanayin yadda yake tafiya yana d'age k'afad'u zaka gane sanyin da ake a garin yana matuk'ar ratsa jikin shi. Direct motar haya ya tare, yayi locating inda zashi. Bayan tafiyar adadin wasu mintuna aka sauke shi gaban wani k'aton mall an rubuta sunan shi daro daro a jikin sunan haske na blinking a cikin duhu *BAYSHORE MALL* a nutse cikin tafiyar shi ta nutsuwa da nuna cikar kamala ya shiga ciki, bai jima sosai ba ya sake futowa rik'e da kwalin siyayya guda biyu, ya k'ara hawa motar da zata mai dashi gida. Dai dai k'ofar shiga apartment d'insu ya sauka ya shiga ciki da sauri. K'ofar d'akin shi ya bud'e da hanzari ya shiga, ya cire takalmin shi da socks na hannu, agogo ya duba, he still have 15 mint left, murmushin gefen baki yayi ya d'auko wayarshi da wasu sink'in flowers White and red masu shegen kyau da k'amshi, wani tsadadden zobe ya ciro mai kyau da d'aukar hankali ya had'a kusa da flowern, da wani round kwali na wata Choco. Bathroom ya shiga a gurguje ya sake shiri cikin wasu kayan daban da suka fi wad'an can kyau da d'aukar hankali. Ko'ina na d'akin azababben k'amshin shi ke tashi mai bala'in dad'in shak'a. Wayar shi ya duba 5 mint left to 12. Text ya yima Saleema kamar haka, "hope ba kiyi bacci ba, I'm on mie way, coming to express my love to you on dis very day of your birthday Saleema". Seconds kad'an da tura sak'on reply ya dawo kamar haka, "bazan tab'a iya bacci ba tare dana bari ka cika alk'awarin ka na tayani murnar k'arin shekara ba, Ina jiranka hope kana duba lokaci dai". Murmushi ne yayi escaping kan lips d'in shi a lokacin da ya gama karanta sak'on Saleema. "I promise I will be at your door at exactly 12:00 am". Ta k'ara mishi reply da, "I will definitely open my door room at exactly dat time u mention". Girgiza kai yayi ya duba lokaci again, 3 mint left. Rufe k'ofar shi yayi hannun shi rik'e da tulin abubuwan daya shirya kai mata as birthday gift, sai dai ya b'oye hannun a baya, sai wanda yake rik'e da wayar shi ne kad'ai a gaba yana typer wani abu. Opposite to d'akin Saleema ya jingina yana duba lokaci, at 12 am as he promise ya tura mata da sak'on "barka da zagayowar ranar haihuwar ki Mrs Abdallah (khaleefa)". Bud'e k'ofar akayi a lokacin da sak'on ya tafi, Saleema ce tsaye daga ta ciki sanye da wata had'ad'd'iyar gown fara sol, yadin ta mai sulb'i yabi jikinta ya lafe. Rigar tun daga wuyanta har zuwa hannayenta shara sharan farin net ne daya bayyana farar fatarta mai d'aukar ido, yayin data bayyana saman k'irjinta kad'an a waje. Gashin kanta kuwa anyi mishi wani irin gyara da farin bit masu kyalli, fuskarta kuma powder ne kad'ai sai lip balm da idonta da tayi lining da bak'i. Ta matuk'ar yi kyau kamar wata amarya. Ja baya tayi kad'an, hakan ya bama khaleefa damar shigowa ciki tare da tura k'ofar da k'afar shi ya rufe. Kusan a tare suka k'arasa cikin d'akin har zuwa tsakiya inda suka shirya candle light da cake an rubuta sunanta a tsakiya in passion. Da wayar shi yayi amfani ya soma haska ta a hotuna a duk wani k'aramin motsinta, yayi mata pic kala da yawa shi kanshi baisan adadi ba kafun itama ta fara yi mishi da wayarta, a k'arshe kuma suka had'u don su d'auki kansu selphie, Saleema jikin khaleefa kad'an ta shiga tana d'aukar su, saida khaleefa yaji shock yaja jikin shi baya kad'an. Had'e face tayi tace, "common". Ta k'ara zagayowa ta gefen shi ta sak'ala hannunta ata wuyan shi d'aya kuma ta d'auki hoton dashi, da saleema zata lura a lokacin khaleefa is totally in some where saboda yadda ta shiga jikin shi make him feel some how. Sai da ta gama yin hotunanta in different style sannan taja hannun shi suka koma gurin cake in. Ta hure wutar cake d'in yana mata video, a hankali cikin nutsuwa ta yanko madaidaicin cake ta nufi bakin shi dashi gently, kauda kai khaleefa yayi ya tura wayarshi aljihu ya matso kusa da ita gab, ya sak'ala hannun shi a gadon bayanta yana kallon cikin kwayar idonta, itama shi take kallo cike da so har lokacin hannunta rik'e da gutsiren cake d'in data yanko, bud'e mata bakin shi yayi kad'an ta zura mishi cake d'in a ciki ya gutsira ya saka mata ragowar a bakinta. Bakin shi ya kai saitin kunnenta ya soma yi Mata magana cikin whisper, "May this birthday just be the beginning of a year filled with happie memories, wonderful moments and shining dreams, also wish you long life and prosperity, happie birthday once again Saleema Omar, Mrs Abdallah khaleefa in future". Saleema tsabar farin cikin data shiga data rasa yadda zatayi sai kawai ta soma yi mishi dariya. Yayinda ya tsaya kamar wani gaula yana kallon jerarrun hak'oran bakinta da suke haske shi kamar camera flash. Kafun ya kamo hannunta ya mayar da ita inda ya ajiye kayan hannun shi. Kamo yatsar hannunta yayi ya murza sannan ya zira mata zoben gold mai d'an karan kyau a yatsarta ta tsakiya, ya kai hannun bakin shi ya bata peck da ya sata lumshe ido ba tare data shiryawa hakan ba. Flower ya d'auko itama yasa mata cikin hannunta. Ta kai flower saitin hancinta ta shak'i wani daddad'an k'amshi da suke yi, cikin matuk'ar jin dad'i da yabawa da kyautar masoyinta tare da tunanin abinda zata bashi tukuici ta tafi da gudu ta rungume shi kam kam cikin sanyin muryarta tace, "I love you Abdallah, I love you... Moreeee". Shima rik'e ta yayi sosai tare da d'ora kanshi cikin gashin kanta ya saki mata wani kiss d'in. Sun jima a haka kamar kar su rabu da juna kafun a hankali su janye jikin su. Murmushi da ajiyar zuciya khaleefa ya sauke a tare, yadda jikin shi yayi weak ya assasa mishi zama kan sofa bayan ya d'auki kyauta ta uku. Duka abubuwa ukun nan abu ne da yasan Saleema tana matuk'ar so. Adana flowers d'in tayi bayan tayi pic rungume dasu, tayi switch up d'in wayarta duka sannan ta dawo inda yake zaune yana duba lokaci a wayar shi. Kwalin hannun shi ya mik'a mata, "oya take your Choco". Da sauri ta amshi kwalin ta soma kiciniyar bud'e shi har Allah ya bata sa'a ta ciro wani guda d'aya takai bakinta, saida ta lumshe ido zak'i da dad'in sweet d'in na kaiwa har cikin brain d'inta. Ajiye kwalin tayi gefe ta zari wata ta nufi bakin khaleefa da yake zaune yana kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa farat d'aya. Kan jikin shi ta hau ta tura shi baya har saida kanshi ya jingina da jikin bango sannan ta zura mishi a baki, har hannunta ya had'a yana tsotsa, yayinda suke kallon juna ido cikin ido. Saleema ce ta fara bin yatsunta biyu da suke cikin bakin shi da kallo har lokacin kafun ta zame a hankali tana sake kallon su kamar me nazarin wani abu, saukar electric shock da taji a wuyanta yasa ta maida duban ta gare shi cikin son sanin abinda ya aikata tana kallon kwayar idon shi, wani kiss d'in ya sake mata wanda yasa ta jin viberate oll over her body. Kafun ta farga ta fahimci takamaiman abinda yake yi sai jin lips d'inshi tayi cikin nata yana bata wani irin passionate kiss mai tafiya da gangar jiki da ruhi, at the first time da suka tab'a tsintar kansu cikin yanayin su duka daga ita har shi. Saleema Cikin tafiya duniyar emotions ta soma shafa gadon bayan shi zuwa k'eyar shi tana k'ara shigewa jikin shi sosai. Shikam Cikin zaucewa ya fara yin k'asa da hannun shi yana shafa ilahirin jikinta da salo na musamman. Wani irin light romance ya dinga binta dashi cikin lura da kiyaye inda hannun shi ke zuwa🙈 At that moment they have gone somewhere, Saida suka d'auki a k'alla tsayin wasu mintuna kafun su tsagaita da abinda suke yi ba don bin umarnin zuciyoyin suba sai don su kiyaye kada su zurma jiki da yawa. A hankali Saleema ta sauka daga jikin shi ta zauna k'asan k'afar shi tare da kwantar da kanta jikin k'afar. K'asa yayi da kanshi ya kira sunanta cikin sanyin murya, "Saleema". "uhm?". Ta fad'a can k'asan mak'oshi, "Ina sonki Saleema, Ina sonki da yawa fa". Tana murmushi itama tace, "nima Ina sonka khaleefa so mai tsanani da yake bani tsoro a duk ranar da akace watanni biyun da suka rage maka sun cika zaka koma k'asar ku ka barni anan cikin kad'ai ci da tunanin ka". Saukowa k'asa yayi ya zauna a gaban ta ya tankwashe k'afafun shi, "kada ki k'ara irin wannan tunanin Saleema, ko na koma Nigeria gangar jikina ce kawai zata kasance a can amma ruhina da zuciyata zasu kasance a nan tare dake, sannan na fad'a miki bada jimawa ba zan gabatar da soyayyar mu aje har zinder a nema mun auren ki, zan dawo aiki tare da Doctor raazee d'an asalin k'asar ku, k'ark'ashin andal. Kinga sai muci gaba da zaman mu kina ci gaba da karatun ki bayan auren mu". Shafo fuskar shi tayi da hannunta na dama tana kallon shi still tace, "toh amma futurehus kana sane da har yanzu baka gabatar mun da kanka ba kuwa? Bayan ni na gabatar maka da kaina tuntuni". Fuskarta ya rik'e cikin tafin hannun shi yace, "Ina sane Saleema insha Allah soon zaki san waye ni wata d'aya kafun na bar Berlin". Ya k'arasa fad'a yana murza hannunta mai taushi da laushi. Light kiss ya Kuma sake mata kafun ya mik'e, "Cherie please ka kwana kawai a nan" Saleema ta fad'a cikin shagwob'a. Shiru yayi yana nazari kafun yace mata, "zai je yayi Shirin kwanciya saiya dawo". Har k'ofa ta raka shi ya tafi kamar kar ya rabu da ita, itama haka take ji sai dai babu laifi tunda yanzu zai dawo su kwana tare. Wani irin tsalle ta daka tana tuna romantic scene d'insu na yau, bayan duk wasu abubuwan data gama gani tare dashi at the end ya iya soyayyah k'arshe haka ashe. Shikam khaleefa bayan mintuna k'alilan shiryawa yayi cikin fararen kayan bacci masu taushi. Sai da yayi nafila raka'a biyu ya rok'i Allah akan soyayyar shi da Saleema sannan ya d'auki wayar shi da key ya futo. Lokacin daya koma itama ta shirya cikin nightgown iya gwiwa mai kauri hawa biyu, hakan yasa ba'a iya gani jikinta sosai, ta d'ora k'aramin bak'in hijab ata sama wanda ya sauka mata ya b'oye k'irjinta gaba d'aya. Zama sukayi gefen bed Saleema ta kwantar da kanta jikin khaleefa tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren shi. Hira suke yi k'asa k'asa wadda su kad'ai suke jin abinda suke fad'a kafun khaleefa ya d'auke ta cak ya dire akan gadon. Kwanciya yayi bayan ya kashe globe d'in d'akin duka rungume da ita a k'irjin shi. Ya karanto musu addu'ar bacci ya tofe duk kusurwowin d'akin ya sumbaci forehead d'inta. A haka wani sumamemmen bacci yazo ya tafi da su mai cike da dad'ad'an mafarkai. Asubah ta gari American cooples.. _Noo comment noo update tomorrow🤗_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page sixteen1️⃣6️⃣ Saboda dad'in bacci har kusan kwace musu sallar asubah tayi, Allah dai yasa khaleefa ya fara tashi ya tashe ta itama. Alwala suka d'auro ya jasu jam'i, saboda yasan tana da lectures 7 am wannan ranar, shikam yana hutun final semester wadda da sun dawo zasu zana final exam su jira sakamako. Saida ya gama morning azhkar sannan ya mik'e daga kan sallaya, ya kalleta nad'e abinta akan gado tana lazimi da hannunta rabi kuma tana gyangyad'i. "Gud morning Cherie". Ta fad'a cikin magagi, "morning" khaleefa ya fad'a yazo a nutse ya shafa gashin kanta zuwa kuncinta, d'ora hannunta tayi akan nashi tana kallon shi da idanunta da suke cike da bacci, "kiyi bacci na minti 30 kawai". Gyad'a mishi kai tayi cikin bacci ta maida idonta ta lumshe. Khaleefa gyara mata kwanciya yayi yaja mata bargo ya tafi kitchen. Abincin k'asar Nigeria ya had'a mata mai sauk'i na break. Ya gyara mata d'akin tsaf ya kammale komai a muhallin shi kamar mace, ya saita mata alarm, yana gamawa keyn d'akin ya d'auka ya futa, d'akin shi yaje yayi wanka da brush ya shirya cikin wasu kayan farare Sol. A rayuwar khaleefa yana son farin abu, yana daga abinda yasa saleema take k'ara burge shi, kusan sunyi tarayyah wajen son abu iri d'aya mabanbanta. Lokacin daya shiga ta tashi harta yi wanka tayi shirinta ta had'a komai na tafiyarta school. Tattausan murmushi ya sake mata a lokacin da yake k'arasowa cikin d'akin, "I thought Zan tarar har yanzu baki tashi ba ai". Ya fad'a Yana zama gefenta. Itama murmushin ta mishi tace, "ba alarm ka saita ya tashe niba, yanzu na fahimci yadda akayi kake yin komai kan lokaci, ashe lissafa komai kake yi, to wai a gurin wa kake samun irin wad'annan dabarun ne?" Shiru yayi yana kallonta da murmushi a idon shi still kafun yace, "a gurin Auntiena, she's very reasonable person me tafi da rayuwarta cikin taka tsantsan, komai tana yin shi with seriousness, lokacin da nake gida kafun na taho nan karatu, idan muka kwanta bacci da rana ita kuma zata futa, bata tab'a had'a iya (kakarmu) da aikin tashin mu bayan cikar adadin mintunan data d'aukar mana, saboda kota fad'a iya was busy doing her work mantawa take, fak'at sai ta saita mana alarm. Alarm na k'adawa zan tashi a baccin da nake komai nauyin shi. Tunda nake a gida ban tab'a yin baccin cikakken hour biyu ko uku da rana ba sai in bani da lafiya, a haka har na saba, kasancewar twin bro na muna kama sak dashi, ga wad'an da basu gama tantance muba idan Suka zo gidan mu suka kwana biyu, da yawan baccin rana suke gane Ayman dani, Cox Ayman yaga dama auntie tasa mishi alarm ya tashi ya kashe yaci gaba da baccin shi har sai in anyi sallah ni ko iya mun tashe shi tukun........". Tunda khaleefa ya fara magana da yaren jamus Saleema ta zuba mishi ido tana kallon shi ko k'iftawa babu tamkar mai d'aukar darasi, for the first time daya tab'a yi mata magana akan familyn shi, ko Ayman tasan d'an uwan shine amma bata tab'a sanin twins d'inshi bane sai yau, Auntie ma sunan take ji yana yawan ambata in suna waya a wasu lokutan, haka iya. Ganin kallon k'urillar da take mishi sai ya d'an tafa hannuwan shi, "ya dai madame kallon meye duk hakan?". "Uhm! Cherie Ina kallon mamakin yadda kake iya shanye komai a cikin ka da ranka ne? Don Allah ka koya mun ajiye muhimman abubuwa irin yadda kake yi? Da naji kad'an daga labarin auntien ma yanzu, sai naji Ina son nasan abubuwa da yawa game da ita, don Allah ka bani labarinta nasan itama dole zata zama y'ar gayu kamar dai kai?". Murmushi khaleefa yayi yace, "kiyi hak'uri time is coming da zaki san tarihina da komai game da Auntiena, abu d'aya da zan iya yi miki a halin yanzu shine in nuna miki hoton ta, shima sai mun fara yin break kada abincin nan su huce". Ba musu Saleema ta gyara zamanta cikin happie suka fara cin abincin tare dashi bayan sunyi basmala. Toasted bread ne with eggs da chips, sai tea na zallar ganye. Saleema taji dad'in cimar hakan yasa taci da yawa fiye da yanda take cin abincin safen ta. Saida suka gama ya nuna mata wani pic d'in Auntien da Ayman ya tura mishi, asalin hoton sameera ce ta d'auke ta a wani occasion, tana zaune kan kujera nad'e da lipaya mai shegen kyau orange colour an yi mata adon lace a k'asanta maroon da milk. Hannunta rik'e da Jakarta tana dariya, hoton bai huce 4 to 5 weeks ba. Saleema kasa d'auke idonta tayi akan pic d'in tana al'ajabin yadda wannan zata kasance mahaifiyar zabgegen saurayin dake gabanta, idan khaleefa yace mata yayar shice wannan ko da wasa ba zata musa ba? Kuma ko yanzun don tasan bai kasance ma'abocin k'arya ba da sai tace ya raina mata hankali ne kawai. Sake juya wayar tayi a hannunta tana kallonta, duk yadda mamanta take ji da kwalliya da ado wannan ta damata ta shanye, da kallo d'aya ta fassara ta da rik'ak'k'iyar y'ar gayu da bokon da aka tsabtace da wadataccen ilimin addini, sannan mace mai tsayayyen ra'ayi akan komai, basa kama da khaleefa sai ta jini amma a kwayar idonta tana iya kallon wasu abubuwa dake tare da khaleefa. Lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya a lokacin da taji an zare wayar a hannunta, "duk me kike kallo haka?". Bud'e idonta tayi akan khaleefa da yake kallonta shima tace, "Ina kallon tushe, asalin Abdallah khaleefa, da gaske wannan itace ta haife ka?". Murmushi yayi yana duba lokaci yace, "kingan ki ko? Zaki jawa kanki late fa, oya tashi muje ki huce". Mik'ewa tayi ta d'auki duk wani abun buk'ata na makarantar ta. Tare suka futo ita da shi, ya rakata har inda ta shiga mota sannan ya dawo. D'akin shi ya gyara yayi d'an sauran abinda zaiyi ya kwanta baccin mintuna 40. Yana tashi ya soma k'ok'arin had'a lunch saboda saleema na gab da dawowa makaranta yasan kuma hungrily zata dawo. Yana cikin had'a easy recipe tayi mishi knocking, ko daya bud'e mata k'ofar rungume shi tayi, "I miss you future husband". Rik'e ta yayi shima yace, "I miss you too". Yana fad'in haka ya janye ta a jikin shi ya karb'i jibgegiyar jakar bayanta ya maida k'ofar d'akin ya rufe. Zaunar da ita yayi saman sofa ya shiga bathroom sharp sharp ya had'a mata ruwan d'umi mai d'an yawa. Gurin ta ya dawo ya zauna tare da rik'e hannunta ya sumbata, "nasan yau kin gaji sosai, kiyi wanka ga can ruwan masu zafi na had'a miki". Saleema zuba mishi ido tayi tana kallon shi cikin narkewa a so da k'aunar shi tace, "kana ji dani futuruhus! Nagode sosai...". Girgiza mata kai yayi, "bani keyn d'akin ki wane kaya zaki sauya?". Mik'a mishi mukullin tayi tace, "duk wanda kaga yayi maka". Murmushi ya sake yi ya mik'e ya fuce. Ita kuma ta shige bathroom d'inshi, galala Saleema ta saki baki tana kallon yadda ya shirya d'akin wankan kamar wani gurin da za'a dawwama ba abu na lokaci d'aya a futa ba. Tsabtar khaleefa tana burge Saleema, shiyasa a wasu lokutan take ganin komai nasu a opposite, in aka d'auke hali na miskilanci da jin kanshi. Sai tace kusan ta jima batayi wanka mai dad'in wannan ba, ga wasu irin body wash masu k'amshin dad'i mai tsayawa a rai da zuciya. Ta jima kafun ta sake futowa d'aure da d'aya daga cikin bathrobe nashi da suke ajiye cikin kayan towels da innerwears d'inshi. Yana zaune yana operating system ta futo gashin kanta na d'igar da ruwa, kallo d'aya yayi mata ya maida kanshi ga abinda yake yi saboda wani irin yarrr da yaji a duk ilahirin jikin shi, itama ganin haka sai ta d'auki kayan daya ciro mata a gaggauce ta koma bathroom d'in ta shirya kanta, wasu riga da wando ne ya d'auko mata, wandon tight yayinda rigar kuma ta kasance mai fad'i da girma ta sauka mata har gwiwarta. Sosai tayi kyau musamman data yane kanta da siririn gyalen daya had'o cikin kayan donta sirranta gashin kanta da bai bushe ba har lokacin. Shi kuma a bashi da kayan gyaran gashi irin nasu na mata. Wani irin k'ayataccen murmushi khaleefa yayi mai nuni da aji da zallar izza, "kinyi kyau princess". Itama murmushin ta mishi k'asa k'asa tace, "thank you futurehus". Gefen shi ta zauna, shi kuma ya tashi ya nufi kitchen, zuba ma computern ido tayi tana kallon wani video da yayi playing yana kallo kafun ya tashi, shiru tayi tana kallon yadda k'ashin d'an Adam ke had'ewa bayan yayi broken, sosai ta duk'ufa tana kallo har jikinta na rawa don razana. A haka ya futo da trayn abinci, daga yadda take kallon shi tana zare ido ya gane abinda take yiwa hakan, rufe system in yayi ya kamo hannunta suka zauna k'asa gab da juna, zatayi magana ya d'ora yatsar shi saman labbanta, dole taja bakinta ta tsuke suka fara cin abincin daya had'a. Suna cikin cin abincin ne k'ofar shi tayi k'ara. Tsam ya tsame hannun shi yaje ya bud'e, Ahmad ne tsaye kare da waya a kunne, cikin farin cikin ganin juna suka mik'awa juna hannu tare dayin side hug. Bashi guri khaleefa yayi ya shigo ciki shi kuma ya rufe d'akin. Yana Shirin zama gefen bed ya ankara da Saleema da take zaune da trayn abinci a gabanta, sai sannan ya ankara da abinci suke ci tare ashe. Katse wayar da yake a lokacin yayi suka gaisa da ita sama sama, saboda itama bata wani sakewa mutane sosai, mik'ewa yayi yace, "yeah ni zan huce sai munyi waya ko?". B'ata fuska khaleefa yayi yace, "Ahmad ka tsaya muyi lunch mana tare yaushe rabon dana ganka ma da idona, yanzu kuma kazo ko minti biyu bakayi ba kace wani zaka huce, haba mana". Ahmad Kallon agogon hannun shi yayi yace, "I'm in hurry but later zamuyi dinner tare ma, saboda Ina son ganin ka dama". "Alright Allah ya tsare sai mun had'u d'in". Daga haka suka yi sallama ya tafi shi kuma ya dawo gurin Saleema. Ko da suka gama cin abincin sun jima suna hira kafun ya rakata har nata apartment d'in, da kyar suka rabu tana ta zuba mishi shagwob'a yana rarrashinta. ********** _8:25pm Northtown coffee, Arcata, CA, United state_ Zaune suke a babban gurin cin abincin sun tattara hankalin su da nutsuwar su kacokan ma juna. Khaleefa ne ya gyara zaman shi bayan gama sauraron doguwar maganar da Ahmad yazo da ita, "Ina ganin shawarar ka tayi Ahmad, babu laifi idan har zasu biya mu da kyau fiye da na k'asar mu Nigeria, sai muyi aikin tare dasu, Auntie zata zo cikin watan nan insha Allah sai mu tattauna da ita". Ahmad yace, "Kai khaleefa kana da damuwa, yanzu ya kamata kayi mata maganar ba wai sai lokaci yazo gab ba, toh idan tace bata amince bafa?". Da sauri khaleefa yace, "ya da mugun fata da wuri Ahmad? Insha Allahu zata amince". "Toh amma idan ka duba zaka ga saida aka matuk'ar kai ruwa rana kafun ta yarda muzo Germany karatu, shine yanzu kake zaton zata barka ka dawo aiki na dindindin sai dai kaje musu da ziyara ka gan su". Shiru khaleefa yayi yana nazari kafun can ya nisa yace, "mu barshi sai tazo d'in Ahmad kafun nan zanyi addu'a ka tayani kaima Allah yasa muyi rinjaye akan ta". Ahmad yace, "ameen insha Allah zan taya ka mu duk'ufa addu'a khaleefa". Duk shiru suka sake yi kafun Ahmad yace, "sai magana ta biyu akan Saleema, yanzu kana ganin babu matsala a soyayyarka da yarinyar nan da kuma yanayin yadda kuke tafi da mu'amular ku?". Shiru khaleefa yayi, Ahmad ya sake dafa kafad'ar shi, "kayi hak'uri idan nayi maka katsalandan da rayuwarka, ba komai yasa na shiga cikin abinda baka saka niba sai guje maka heart broke da rashin tabbas na mata yanzu, saboda Amna k'awar Saleema ta tabbatar mun akwai wani da suke soyayyah ra'ees babu irin soyayyah da kulawar da bai nuna mata ba, amma tana samunka lokaci d'aya ta watsa mishi k'asa a ido ta rabu da shi......" Tunda Ahmad ya fara magana khaleefa ya kafe shi da ido yana kallon shi kamar ya wanke shi da mari, lallai Ahmad ba don yasan shi d'in mai k'aunar shi bane daba abinda zai hana yaja mishi layi take yanke, toh amma yasan lallai Ahmad yana yin maganar nan da kyakkyawar niyyar kubutar dashi, bayan sharri ne da gadar zare, sai ya saisaita yanayin shi yace, "calm down and cool your mind, Sam Saleema ba irin y'an matan da kake tunani bace, nasan kaima don bakasan komai bane shiyasa, toh amma alhamdulillah da kanta ta bani labarin yadda suka rabu da ra'ees da abinda ya raba su, har ita k'awar tata da takai maka wannan maganar yanzu haka basa tare, too ba wani abu bane duka zamu iya cewa rashin fahimta aka samu". Ahmad yace, "toh Ina fatan haka, sai maganar hot love na....." Sai kuma yayi dariya. Shima khaleefan dariya yayi ya gane abinda Ahmad yake son fad'a sai yace, "shima kada ya dame ka khaleefa yana kiyayewa ako da yaushe, duk wani abu da kake tsoro bazai kasance ba Ahmad insha Allah". Ahmad yana dariya yace, "Allah yasa kam, abokina naga alamun ka zamo expert a soyayyah fa zamu zo a bamu formula". Mik'ewa tsaye khaleefa yayi, "Hum let's go zan kira auntie da Ayman a waya kada suyi bacci kuma". Mik'ewa sukayi kusan a tare suka futo daga eateryn suna magana suna had'a hannuwa da dariya abun gwanin burgewa. @@@@@@@@ Kusan tun daga wannan lokaci soyayyar khaleefa da Saleema ta sake zama hot and romantic, sosai suka k'ara d'inkewa sau goman yadda suke a da, zasu ci abinci tare, hira tare, karatu tare, futa guraren shak'atawa tare, yawo bridge bridge ma tare, har takai yanzu komai khaleefa zai siya biyu yake siya na maza dana mata, haka itama takan zage wajen kyautata mishi da bakin alhihunta. A iya zaman shi a Germany har rasa yadda zaiyi da kud'in account d'inshi yake, amma yanzu sai gashi yana neman yiwa kanshi karkat akan Saleema. Soyayyar su tayi shura ta karad'e lungu da sak'o na makarantar sai gashi suna shirin k'afa tarihin zama masoyan da suka kusa danne kowanne masoya shak'uwa da iya soyayyah a Humboldt university, ko sau d'aya basu tab'a samun rashin jituwa ba bare ta kaisu ga yin fad'a, tuni sun k'aryata, sunyi fancakali da maganar da masu iya magana suka ce wai duk soyayyar data cika soyayyah sai an samu fad'ace fad'ace da rashin jituwa a cikinta. Sun d'auki kiss as the only way to express sad or happiest moment, and the only way to thank each other a duk lokacin da wani ya kyautatawa wani cikin su. Rik'e hannu kuwa sun mai dashi tamkar farilla, ko tafiya suke basu sark'afe hannuwan juna ba basa jin dad'i, sukan d'anyi light romance amma ba koda yaushe ba, saboda khaleefa baya son su k'arar da soyayyar tun kafun auren su. Sau biyu suka tab'a kwana a gado d'aya, daga ranar da tayi murnar cikar shekararta sai wata rana da tayi wani rashin lafiya. Soyayyar su takai gejin da ko ciwo d'ayan su yake sai d'an uwan shi ya kwanta irin ciwon, haka zasu taru suyi jinyar tare. Rayuwar su a hankali ta dinga tafiya, d'an lokacin daya ragewa khaleefa na zaman karatu a k'asar yana k'arewa a kullum wayewar garin Allah. Tuni ya gama tsara yadda zai gabatarwa da auntie abubuwa biyu a lokaci guda, wato soyayyar shi da Saleema sai kuma maganar aikin shi a general hospital german. So yake idan ta amince aje a nemo mishi auren Saleema a can zinder sai taci gaba da karatun ta tana gidan shi har Allah yasa ta kammala shi kuma yana aikin shi. Shiyasa yanzun ya dage da sallolin dare yana kai kukan shi ga Allah subhanahu wata'ala akan Allah ya d'ora shi kan auntien su ta amince idan tazo. Yana nan yanata lissafin zuwanta ita kuma tana wasu lissafe lissafen nata daban, a lokacin da ta samu hutun shekarar akwai tafiyarta ta kasuwanci Egypt da Dubai sannan ga khaleefa a Germany tana son je mishi shima, tayi tunanin cikin wata d'aya zata iya yin duk wannan abubuwa sai gashi Kuma abun ya faskara, at the end sai kawai ta bashi hak'uri akan sai dai daf da dahowar shi zata yi k'ok'ari maybe lokacin Ayman ya samu hutun k'arshen shekara ma sai suzo tare. Khaleefa bai ji dad'in hakan ba sam, toh amma babu laifi idan har zata zo k'asar kafun su suje can Nigeria. Toh akace tafiya sannu sannu kwana nesa, da sannu dai gashi yanzu saura 1month su kammala karatun su gaba d'aya. Kansu ya d'auki chargy shiyasa kwana kusan uku rabon shi da Saleema, kuma dama da zarar yayi busy ko suna tare sad'ad'ewa yake ya barta yaje yaji da al'amuran shi. Yau ma tun safe daya fuce bai samu kanshi ba sai kusan gab da magrib, saboda har meeting sukayi da doctor raazi, Su bakwai aka yiwa tayin aikin Soo su 7 d'inne ake jin aji ta bakin kowanne d'aya daga cikin su. Alhamdulillah duk sun suna amincewar su, sai dai kowanne ya buk'aci da'a barshi ya nemi dama daga manyan shi idan sun koma gida bayan kammala wannan course d'in. Tafe suke shida Ahmad suna tattaunawa a tsakanin su har suka k'araso gida, bai nufi apartment d'in shi ba yabi Ahmad. Saida sukayi sallah yaci abinci sannan ya tattara komatsan shi yayi mishi sallama ya tafi. Yana tafe yana jin yadda temperature jikin shi take high, da yadda kanshi yake bala'in sara mishi, kamar zazzab'i yana shirin kama shi haka. Yana zuwa a k'ofar shi yaci karo da Saleema rungume da wasu uban tulin littattafai, rataye da y'ar k'aramar jaka sai wayarta a hannu. Tana ganin shi ta shagwob'e tana fad'in, "Wai Ina ka shiga ne tun ranar Friday ko nema na bakayi ma". Murmushi yayi mai kyau da k'ayatarwa ya k'araso gabanta ya kama kunnen shi, "apologize madame kinsan one month ya rage mana mu yanzu". Saleema tace, "ayyah Allah yayi jagora". Bud'e musu d'akin yayi suka shiga tare, a k'asa ta zube tulin littafan da jakar ta fad'a bathroom da hanzari ta d'auro alwala ta futo. Shikam khaleefa Zama yayi kan sofa yana kallonta da matuk'ar mamaki, yayi tunanin idan suka had'u zai tarar tayi mugun fushi dashi sai ya had'a da rarrashi amma........ Saiya saki murmushi, shi tunda yake ma tare da Saleema sun tab'a yin fad'a ko cacar baki irin na masoya kuwa? Tana sallar yana y'an tunane tunanen shi har ta idar, tayi tasbihi ga Allah sannan ta juyo ta fuskance shi, "kasan ina sallar nan kuwa na tuna da wani abu? Labarin familyn ka da kace zaka bani wata d'aya kafun barin ka Berlin". Tsare ta yayi da ido kafun yaja gwauron numfashi ya mik'e, "am let's get you something to eat nasan kina jin yunwa kam". _happie juma'at Mubarak, may all our dreams come true🤲🤲🤲_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page 1️⃣7️⃣ Had'e fuskarta tayi kamar zatayi kuka tace, "noop ni ai bance maka Ina jin yunwa ba". Yanayin yadda tayi maganar saida ta bashi dariya amma dai ya gimtse. Kusa da ita ya dawo ya tankwashe k'afa ya zauna yana kallonta, "ta Ina zamu fara ne?". Saleema tace, "Ni duk ta inda ka fara ma". Sai yayi gyaran murya ya fara magana da fad'in, "Toh nidai sunana Abdallah Suraj Abdallah kamar yadda kika sani, sai k'anina twins d'ina Adam Suraj Abdallah, tare aka haife mu rana d'aya a lokaci guda, kawai ki kwatanta yadda so da shak'uwar mu zata kasance, mahaifiyata, surayyah Adam akwai kyakkyawar zamantakewa tsakanin mu da cikakkiyar kulawa, mun taso duka tare a gidan iyayenta malam da iya. Auntie ta fad'a mana mahaifin mu ya jima da rasuwa kuma ya tafi bai bar ko hoton shi guda d'aya ba, hakan yasa bamu tab'a sanin yadda kamannin shi suke ba, nan yaci gaba da bata labarin cikakken tarihin shi da yadda suke rayuwar su tare da auntie da gorin da y'an anguwa suke yi musu wani lokacin suna Kiran su da shegu, khaleefa yaci gaba da ba Saleema tarihin shi yayin da take kallon shi da fuskar tausayawa har yazo kan inda ya taho karatu Germany bayan an matuk'ar kai ruwa raana. Ya d'ora da fad'in, "babban abinda yafi d'aure mun kai guda biyu shine, mahaifina ya rasu mun rayu bamu San shiba kuma Auntie bata so ayi mata hirar shi koda wasa, bare ta bamu koda labarin shine muji sanyi a ranmu, na biyu dangin mahaifina tunda muke rayuwa basu tab'a zuwa don su gan mu ba Auntie ce kad'ai take wahala damu da abinda take samu a kasuwancin ta da aikinta" sai ya soma girgiza kanshi, "wannan abubuwa biyu da su nake rayuwa a kowanne dare Saleema, abun yana cin raina da zuciyata, gashi har Alk'awari mun d'aukar ma auntie lokacin muna yara cike da k'uruciya cewa ba zamu k'ara tambayarta wani abu game da mahaifin mu ko dangin shiba......". Saleema data zuba mishi ido tana kallon shi da wani bak'on yanayi kan fuskarta mai wuyar fassaruwa farat d'aya, hawayen idonta daya taru ta soma sharewa kafun ta mik'e tsam ta tattare duk wani shirgi data shigo masa d'aki dashi ta d'auki hanyar futa, da mamaki khaleefa ya tashi ya bi bayanta yana kiran sunanta, "Saleema". Tsayawa tayi tana kallon shi da idanunta da hawaye suka fara sintiri. Hannu yasa yana share mata hawayen, shi kanshi ji yake kamar yayi kuka a lokacin, ba don yana da kyau tasan waye shiba daba abinda zaisa ya fara bata cakwalkwalallen labarin rayuwar shi mai cike da hargitsi da zargi a gurin mutane, gashi ba mutum ma'abocin k'arya ba bare ya k'irk'iri wani k'agaggen labarin ya mak'ala. Cikin sanyin jiki dana murya yace, "I'm sorry Saleema, kiyi hak'uri ki daina kuka akan abinda kika ji game dani yanzun.... Duk da nasan dole zaki yi kuka wa rayuwa ta da......" Da sauri ta d'aga mishi hannu ba tare data bari ya kai aya ba, "labarinka yafi k'arfin a koka mishi ta wannan hanyar, wannan ba kukan komai nake ba khaleefa saina rayuwata, rayuwata nake koka ma a yanzun ba kai ba....." . Tana gama fad'in haka ta fuce da gudu tana kuka mai sauti. Zama yayi a k'asa jiki ba kwari yana harhad'a maganganun saleeman da tunanin yadda zai fassara kowanne a ciki. Ganin yana wahalar da kanshi a banza bayan ba gane komai yake a halin yanzun ba sai ya fad'a kan gadon shi kamar wani kayan wanki ya haska madubi a zuciyar shi yana kallon rayuwar shi tun daga lokacin daya zama matashi yafara mallakar hankalin kanshi har kawo yau. Da kyar ya iya yin sallar isha'i ranar, ko daya sake kwanciya kasa bacci yayi sai tunane tunane cinkushe cikin ranshi. Sai da b'arawon gwanin iya sata yazo yayi wuff dashi tsakiyar dare. Yau na fari khaleefa ya kwana da kayan daba na bacci ba a jikin shi, na biyu ya makara sallar asubah har lokacin futar su yayi har ya huce bai tashi ba, saida Ahmad ya gaji da kiran wayar shi yazo ya dinga buga mishi k'ofa da k'arfi sannan ya farka. K'ofar ya fara bud'ewa sannan ya dawo ciki yana kallon yadda gari yayi haske. Ahmad zama yayi kan k'aramin table yace, "I cannot believe kaine yau kake bacci har rana baka yi sallah ba". Bai ce dashi komai ba shi dai ya shige bathroom. Shap shap yayi wanka ya d'auro alwala, sai daya zura kaya sannan yayi sallar, suka gaisa da Ahmad yaso had'a musu abinda zasuyi break sai dai lokaci ba zai basu damar hakan ba, sai ya d'auki briefcase da wayar shi da jakar system suka futo tare. Yana rufe k'ofa Saleema na rufe tata itama, "minti biyu please" yace da Ahmad sannan ya nufi inda take takowa itama da fuskarta kumburarriya, ya bud'e baki zaiyi mata magana tayi saurin d'aga mishi hannu, kamar walk'iya kuma tayi sif ta hucewarta ta barshi nan tsaye. Ahmad da komai ya faru gaban idon shi d'auke kanshi yayi a lokacin da khaleefa ya fara dawowa don su huce. Ko a clinic yana lura da yadda yake gaba d'aya a dame, ko abinci bai ciba ranar through out. Haka suna tashi bai k'ara jira ba ko dede da second ba yayi gida abun shi. Wulli yayi da komai ya kwanta a k'asa yana sauke numfashi. Ahmad ne ganin yanayin yadda ya futa kamar bashi da lafiya cikakke ya biyo bayan shi, yau ko d'akin bai rufe ba yana zuwa ya shiga, ganin shi a k'asa sai ya k'arasa kusa dashi da hanzari yana kiran sunan shi, bud'e idon shi yayi ya kalli Ahmad da yake durk'ushe gefen shi, "Wai yau me yake faruwa da kai ne khaleefa? Ko baka da lafiya?". Da kyar ya yink'ura ya tashi zaune ya d'ora kanshi jikin gwiwar k'afar shi. "ko mu je nearest clinic a duba ka?". Cikin dakiya da kuma basarwa khaleefa yace, "ba abinda yake damuna Ahmad just help me with something to eat". Bai yi musu ba ya tashi da hanzari ya zari waya da master card d'inshi ya futa, in less than 20 minute yaje ya dawo mishi da abincin da zai iya ci mai sauk'i, yana yadda yake har yanzun. A gurguje ya d'auko plate bayan ya had'a mishi tea mai mugun zafi ya juye a mug. "Ka fara shan tea khaleefa in yaso sai kaci abincin". Girgiza kanshi kawai yake yaja jiki da kyar ya nufi jikin bed ya jingina. Ahmad sai faman jera mishi sannu yake, shi ya taimaka mishi yasha tean sannan abincin ma, ba laifi yaci da d'an yawa, sai gashi har ya samu kuzarin shi ya d'an dawo, dama yunwa ce ta sake galabaitar dashi. Ahmad ya had'a mishi ruwa ya shiga yayi wanka ya d'auro alwala, ya zura wasu riga da wandon parkistan na maza, yayi sallolin da suka huce shi bai samu yayi ba. Yana idarwa ya samu kan sofa ya kwanta, Ahmad na gefen shi cike da damuwa yana mishi sannu, da ka kawai yake amsawa, wayar shi yasa Ahmad d'in ya bashi, da yake a silent take anyi mishi kira rututu bai sani ba, ko dubawa bai tsaya yiba ya shiga kiran Saleema, sai dai har ta katse bata d'aga ba, hakan yasa ya k'ara mata wani kiran, shima bata d'aga ba. Sai kawai ya ajiye wayar gefe yaci gaba da tsurawa guri d'aya ido yana tunanin abinda zaisa Saleema ta d'auke mishi wuta daga jin labarin shi, meyasa zata jefa kanta cikin damuwa shima ta jefa shi bayan tasani sarai babu abinda ya tsana kamar ganin damuwarta ko tashin hankalinta, shin idan ma tana taya shi bak'in ciki ne me yasa ba zata saurare shi tazo suyi alhinin tare ba, balle ma yana ganin wannan k'addarar shice abinda ya shafe shi shi kad'ai bai shafi wani ba. Yana Wannan y'an tunane tunanen Ahmad ya dinga yi mishi magana bai jiba har saida ya tab'a shi sannan ya dawo hayyacin shi, "auntie tana kiran ka a waya" Ahmad ya fad'a yana mik'a mishi wayar, kauda kanshi yayi gefe yace, "ka barshi kawai ahmad". Ba musu Ahmad ya ajiye wayar a gefe, ranar bai bar gurin shiba har dare bayan ya tabbatar yaci abinci ya kwanta bacci. Ko daya futa sai da yayi tunanin ya tsaya ya yima Saleema magana don ya tabbatar tana da masaniya akan halin da khaleefa ya riski kanshi a ciki, toh amma da yayi wani tunani sai ya ga bari ya kyale su ya zuba musu ido kawai watak'ila sun samu d'an rashin fahimta ne ba wani abu mai zafi ba, kuma dama a kowacce soyayyah ba za'a rasa cin karo da matsaloli iri iri ba, toh amma shi abinda yafi bashi mamaki shine yadda khaleefa ya d'auki abun da zafi har yake son kwantar dashi, yasan halin khaleefa ciki da bai sai dai yaba wani labarin shi, mutum ne murd'ad'd'e mai matuk'ar k'arfin hali dana zuciya, ko ciwo yake sai yaci k'arfin shi wani yake iya sani, haka zurfin cikin shi baya ma bari aji damuwar shi har sai yayi maganinta da kanshi, in tafi k'arfin shine makusantan shi zasu iya ji, sannan abu na k'arshe baya d'aukar komai da wasa musamman abinda yake so kamar ita saleeman. Da wannan tunane tunanen Ahmad ya isa apartment d'in shi ya bud'e ya shiga. ★★★★★★★ Saleema kuwa tana can cikin tashin hankali da muguwar damuwa, labarin khaleefa ya tab'a ta ba kad'an ba, kuma ya shiga cikin alak'ar soyayyar su matuk'a, hakan yasa ta kwana tana kuka ranar bata runtsa ba, sai tsakiyar dare, da kyar kuma ta iya tashi asubar fari jikinta duk yayi weak kamar mara lafiya, ta dai daure ta lallab'a ta shirya, bata da lectures da sassafe amma tana son tabar gidan kota samu sauk'i in ta had'u da course mate d'inta, gashi ita ba wata k'awa ba da zata tattauna damuwarta da ita, Amna ce kuma sun rabu tun farkon haduwarta da khaleefa. Ta futo shima ya futo shine yaje don yayi mata maganar nan, ita kuma a halin da take ciki lokacin bata buk'atar sake sauraron duk wani abu da zai futo daga bakin shi, ya barta taji da kanta ma. Shiyasa yana fara magana ta dakatar dashi tayi hucewarta. Haka ta wuni kamar marar lafiya, lokaci bayan lokaci takan tuno da wani abu, sai zuciyarta ta karye ta fara share hawaye. Bata yarda ta koma apartment ba sai yamma lis ta shiga ta kulle dama already ta taho da abinda zata ci ba girki zata yi ba. Tana cin abincin ta kora maganin headache ta kwanta a nan k'asa sai bacci, ba ita ta farka ba saida garin Allah ya waye don ma Allah ya taimake ta ba sallah zatayi ba, kuma bata da lectures. A gurguje ta shirya kanta a d'akin wankan ta futo ta zura wata y'ar k'aramar doguwar riga data sake fudda ainahin sirantar ta. Bata buk'atar cin komai ga cikinta da yake uban ciwo har yana neman kayar da ita ga miki a zuciya. Wayarta dama tun jiya da taga khaleefa ne yake kira ta wurga cikin jaka bata sake yarda sun k'ara ido hud'u ba har yau. Haka ta gama murk'ususunta ba wanda yasan tana yima bare ya kawo mata d'auki. Sai zuwa can cikin ya lafa ta d'an sha hot milk da magani ta sake kwanciya, ba jimawa wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita. Cikin baccin ne kuma taji ana faman Danna mata door bell at the same time ana mata knocking, cikin magagin bacci ta tashi zaune ta dubi kayan jikinta, hijab d'in sallarta ta zura don bata san wa zata tarar a wajen ba. Ko data bud'e khaleefa ta gani tsaye hard'e da hannu yana kallonta kamar wanda ya shekara yana jinya. Saleema take zuciyarta ta karye, tayi narai narai da ido kamar zatayi kuka, cikin d'an saurin kuzarin daya rage mata ta tura k'ofar zata rufe, duk da shima ba kuzari a jikin shi amma ya fita k'arfi ba zama a had'a ba nesa ba kusa ba, cikin k'arfin hali ya ture k'ofar ya shiga kanshi tsaye ya mayar da k'ofar ya rufe hadda murza key. Cikin b'acin rai Saleema ta fara masifa tana fad'in, "malam waye kai da zaka shigo mun d'aki just like that?". Khaleefa yana nuna kanshi yace, "Saleema ni kike tambaya waye ni?". Cikin sake had'e gira tace, "yeah I say who the hell are you? toh nasan kane?". Wani irin karyewa zuciyar shi yayi ya zuba mata ido yana kallonta cikin mabayyanin tashin hankali, da yafi k'arfin miskilancin shi ya b'oye. Itama kallon shi take idonta cike da hawaye, burinta d'aya ya futa ta samu tayi kukan nan ko taji sanyi a ranta. Shi kuwa tun yana iya tsayuwa da k'afafun shi sai gashi k'afafun sun gagara d'aukar shi, sai ya zube nan k'asa ya had'a hannu da kai da gwiwa. "innalillahi wainna ilaihi rajiun! Saleema me yasa kike son ganin baya na lokaci guda? Me yasa kike yin duk wannan abun? Akan wani dalilin ki marar tushe kike son azabtar da zuciyarmu akan me? Ni da abun ya shafa ma ban tab'a yin irin abunda kika yi ba balle ke da labari kad'ai na baki.......". Da wani irin zafin rai mai cakud'e da muryar kuka tace, "sau nawa kake son na fad'a maka ni ba kai nake kokawa ba? Naji tausayin ka tabbas, amma nafi tausayin kaina da fad'awa soyayyar da nayi da kai har nake mafarkin auren ka mu rayu tare, dolee nayi kuka Abdallah! Dolee! Saboda ka gama jefa zuciyata cikin ha'ula'in da bansan ta yadda zan futa ba! Bansan ta yadda zan cire sonka a raina ba, wayyoh Allah ni Saleema, hak'ik'a nayi nadama matuk'a na jefa rayuwata cikin tashin hankalin da Ina tunanin shi zai zamo ajalina......". Shi kam khaleefa kasa fassara zancen ta yayi farat d'aya, tun jiya yake auna maganar wai bashi take kokawa ba kanta take kokawa, toh kanta take kokawa kamar yaya? Kuma akan me? Yaga abunda ya shafe shine shi kad'ai ita meye nata a ciki? Shin tana nufin labarin rayuwar shi zai kawo k'arshen alaqar sune..........". Sai yayi saurin girgiza kanshi da k'arfi da kuma k'araji yace, "noooop! Sam ba haka bane? Saleema ba zata rabuwa dani ba har abada, zamu rayu tare dake doleee! Baki da masoyin daya kaini Kuma ba zaki samu ba duk fad'in duniyar nan in aka d'auke iyayen da sukayi silar zuwan ki duniya........". Saleema kam cikin tsoro da razanin ganin yadda ya rikid'e mata lokaci guda yana maseefa kamar ba khaleefa data sani ba, tana tunanin gwara ta had'a ya nata ya nata tabar mishi d'akin tun kafun ya karairayata a banza, don ta fara zargin watak'ila yana da matsalar kwakwalwa bata sani bane, shiyasa ko a soyayyar su lokaci zuwa lokaci yake mata wasu kalar d'abi'u kamar ware kanshi daga cikin mutane na tsawon wasu mintuna. Shi kuwa mik'ewa tsaye yayi ya soma nuna kanshi yana tunkararta, ita kuma ta fara jan jiki tana ja baya tana kuka mara sauti. *Note👇* _love romance wata haramtacciyar soyayyah ce da masoyan turawa suke gudanarwa, sun d'auke ta kamar ruwan sha tunda ba addinin islama a tare dasu, sai dai Kash! Wani abun tashin hankalin mutanen mu y'ay'an hausawa, hausa Fulani da aka haifa cikin addinin musulunci aka tarbiyyantar dasu da hanyoyin sanin Allah da yadda zasu bauta mishi, babu jahilci ko guda a tare dasu, amma wani abun al'ajab sun d'auki wannan d'abi'a sun rataya a wuyan su, a gurin wanda suke d'abbak'a wannan soyayyah akwai mutanen gaskiya da auren zasuyi a lokacin akwai kuma na banza da k'arya ce ta kaisu, in sun kai ki sun baro ko kyallin keyarsu ba zaki k'ara gani ba, wannan soyayyah takan jawo matsaloli da yawa ciki harda gurb'atar tarbiyyar yara matasa masu tasowa da wanda ma basu gama tasowar ba, yaudara ta shiga cikin soyayyah tayi kane kane duk ta sanadiyyar love romance, aure yana lalacewa duk akan love romance, shin masu gudanar da wannan soyayyah suna da tabbacin zasu auri juna ma da farko? A'a ko kuwa su sunsan rayuwarsu tun daga farko har k'arshe? Shin suna tunanin ya rayuwar auren su zai kasance bayan shallake wancan soyayyar ta banza? Dole zargi zai shiga cikin rayuwar auren su, daga ranar da namiji yasan mace a titi bata k'ara daraja ko k'ima a gurin shi, ko bayan auren ma haka zaita ganinta a banza, data d'aga hankalinta zata yi wata fuffuka zai iya yanke mata kowanne irin hukunci ciki hadda rabuwa da ita_. _Abubuwa da dama dai duk gasu nan suna faruwa kuma wallahi ta silar wannan gurbatacciyar soyayya, Sannan abu na biyu daya kamata mu fahimta, shi bature mutum ne mai alk'awari, zai iya auren mace yayi ta rayuwa da ita tsawon lokaci da iya romance, basu d'auki sex dole ba kuma basu d'ora shi a k'ok'on ransu kamar mutanen Africa ba, shiyasa suke iya raba romance da sex. Wanda mu a k'asar mu ba'a iyawa. Zasu fara kamar gaske da option 1 kafun su farga sai kigan su tsumu tsumu cikin option 2 . Soo mind you Mutanen Africa ba zasu tab'a zama turawa ba. Da haka nake Jan kunnen mu don girman Allah Mata, mu kama kanmu da bawa ire iren wad'annan matasa fuska, da yak'i tuk'uru akan su. Don akwai abinda yake faruwa yanzu sam ba za'a kira shi da sakacin iyaye ba, iyayen mu suna iya yinsu wajen bamu tarbiyyah tun daga ranar da suka haife mu, toh mu kuma ya kamata mu d'ora daga lokacin da muka fara mallakar hankalin kanmu, har ma mu taimaka musu wajen kwabar k'annen mu. Mu sani fa cewa duk abinda San gaba ya taka......._ _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page eighteen 1️⃣8️⃣ "Wayyoh Alla kuzo ku taimake ni yau khaleefa zai kashe ni a gidan nan?". Ta k'arasa fad'a tana yin kuka mara sauti jikinta babu inda baya rawa, shikam bai masan abinda yake yiba saboda zaucewar tunani. Sai da yaga ta kai k'arshen bangon d'akin ya dakata da binta da yake, fuskar shi a had'e idanun shi a rine yayi magana cikin daka tsawa, "ki fad'a mun abinda kike nufi da cewa rayuwarki kike yiwa kuka Saleema?". Saleema kam cike da tsoro wani tunani ya d'arsu a ranta take a gurin, ko ba komai ya kamata na kawo k'arshen alak'ar nan ko na samu na rabu da khaleefa da matsalolin shi gaba d'aya, ta tabbatar idan har baiji hukuncin data yanke ba to bazai kyale ta taji da kanta ba, idan kuma yaji zai yi zuciya ne ya barta har abada, abinda ita kuma tafi so kenan a halin da take ciki. Sai ta saisaita yanayinta ta aro jarumta da dakiyar zuciya tasa a ranta, sannan ta dube shi ido cikin ido ba ruwan hawaye a cikin nata idanun tace, "mu koma can mu zauna zan warware maka komai". Bai yi musu ba wajen komawa dandagaryar k'asa ya zauna itama ta mara mishi baya. Suna opposite d'in juna duk hankalin khaleefa d'ungurungum na kanta kamar ya shiga cikin zuciyarta yaji abinda zata fad'a. Ganin tayi shiru tana ta ruwan hawayen da yau ko tasu khaleefa ba yayi kawai yaji matsayin soyayyar shi a gurinta yace, "ke nake sauraro Saleema". Share hawayenta tayi da bayan hannunta, kafun ta fara mishi magana da disasshen murya, "a gaskiya bazan b'oye maka ba kamar yadda al'adun mu suka banbanta haka tsarin tafiyar da rayuwar muma ya banbanta, mahaifina ya kasance mutum mai tsanani da magana d'aya, shiyasa duk abinda ya fad'a bana ja dashi don wahala zanyi a banza kuma ba zai fasa abinda yayi niyyah ba, a dunk'ule Ina nufin ko zan had'iyi zuciya na mutu a gidan mu ba za'a tab'a bari na auri wanda bashi da cikakken asali ba......." Wani irin dum dum khaleefa yaji a k'irjin shi, sai ya rasa a yadda zai fassara koya fahimci zancenta, tana nufin shi shine bashi da cikakken asali? Saleema kam saida ta had'iye wani abu mai d'aci a mak'ogwaro kafun ta ci gaba da maganar ta, "shiyasa na yanke alak'a ta dakai tun wuri ba sai lokaci ya k'ure kace na yaudare kaba, sannan na d'aura d'amarar koyar yadda zan cire sonka a zuciyata kwata kwata ko naji dad'in fuskantar karatuna inyi abinda ya kawo ni ........". Khaleefa bai bari takai k'arshen zancen ba ya tare ta da hanzari ta hanyar fad'in, "idan na fahimce ki kina son kice ni bani da cikakken asali kenan? Bayan ni dake na fad'a miki mahaifina rasuwa yayi tun kafun a haife mu? Taya kuma na zama marar tunshe Saleema?". Duk da halin da take ciki saida tayi murmushin takaici mai ciwo, "kana nufin kace duk iya tsawon shekarun daka d'auka a duniya baka fahimci mahaifiyarka kawai y'an dabaru take muku akan mahaifin ku ba? Toh ni yau zan fad'a maka abinda wani bai tab'a yi maka warwara a kai ba, mahaifinka yana raye shiyasa tak'i yarda ku ga hoton shi, tunda duniya da fad'i kada wata rana ku had'u dashi ko mai kama dashi kubi diddigin shi, abinda take b'oyewa ya futa, shiyasa tace ya mutu a nufinta sai kuci gaba da rayuwa cikin rigar yara masu mutumci ku zam d'aya da y'ay'a na halak". "Na biyu lallai akwai wani abu data rik'e game dashi shiyasa bata tab'a yarda tace muku komai a kanshi, na uku daga yadda mutanen anguwa suke yi muku gorin baku da uba mahaifiyar ku tazo da cikin ku ta sauka gidan iya ta haife ku? Shin me yasa tun da can bata tab'a neman iya a matsayin mahaifiyar taba saida ta samu cikin ku rana tsaka, su kuma mutanen anguwa da tazo akan idonsu suka fara goranta abinda suka sani game daku tunda Nigeria ai ba kamar k'asar Germany ba........akwai abubuwa da yawa daya kamata ka fahimta wanda cikin sauk'i zai tabbatar muku da asalin ku d'in suwaye ba sai anyi muku hasashe bama, da wannan nake rok'on ka don girman Allah kaje kayi rayuwarka nima ka barni inji da tawa, magana d'aya tak ta k'arshe kuwa itace, kun kasance baku da uba, bi ma'ana mahaifiyar ku bata halastacciyar hanya ta samar daku ba......…..". Wani irin guduma khaleefa yaji tayi mishi rotse tun da ga kanshi har zuwa gab'ob'in yatsun k'afar shi, tun da mutane suke cewa ana iya dukan mutum da magana bai tab'a yarda ba saida ta faru a kanshi yau, lallai ya yarda za'a iya kashe mutum ma da magana. Wacce irin banzar magana ce yau Saleema take mishi haka? Shin tasan wacece auntien su kuwa? Shin tasan yadda take da gudun duniya da tsoron maza ma kuwa? Toh taya mace kamar ta mai nutsuwa da cikakken Kamala zata fad'awa aikata haramci har ta Samar dasu ta hanyar haramun kuma ta dinga alfahari dasu, ai data kashe su tun suna yara ba sai sun girma ba? "Ya ilahi ka kawo mun haske na fahimci komai yadda yake a wannan duniyar?". Khaleefa ya fad'a yana mai rik'e kanshi da hannuwan shi biyu, ita kam Saleema Jan jiki tayi ta koma jikin bangon d'akin ta jingina ta rufe bakinta da hannunta duka biyu ta fashe da wani irin kuka mai tuk'uk'i da cin rai. Sun d'auki lokaci mai tsayi ita tana kuka shi kuma ya kasa yin kukan ma sai ajiyar zuciya da yake saukewa akai akai, tsabar tashin hankali ya kasa yin kukan ma. Da kyar ma ya iya tattara y'ar sauran jarumtar data rage mishi ya ja k'afafun shi daga d'akin ya futa. Ko daya komao nashi b'angaren sai ya kasa shiga ya zube nan k'asa rik'e da key a hannun shi, ya dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu. Gaba d'aya duniyar ta soma juya mishi ya fara ganin hazo hazo. Wani mak'ocin shi d'an k'asar India mai suna khaleed daya dawo daga waje ko shopping ya danje rik'e dai da kwalin kanti, har ya huce shi saboda ba wani shiga harkar mutane khaleefan yake ba in aka d'auke gaisuwa in ya had'u dasu a hanya, amma ko irin yaga kwana biyu baya ganin mutum shi bai iya zuwa yaga ko lafiya ba, sai suyi ciwon su su gama bai sani ba gasu gashi, don haka yanzun ma daya ganshi baiyi niyyar kulawa yaji me yake faruwa dashi ba tunda shima ai haka yake musu, sai dai abunka da zuciyar musulunci me cike da Imani taf, ko da khaleed ya duba Allah sai ya dawo yana tambayar shi, "are you okay?". Bai iya ce mishi komai ba sai key daya d'anka mishi, ya karb'a ya bud'e mishi d'akin ya ajiye kwalin ya taimaka mishi suka shiga ciki, wayar shi ya jawo gefen bed d'in daya kwanta da kyar ya bud'e lock d'in jiki yace ma khaleed, "please call me Ahmad". Khaleed ya karb'a yana nema mishi no, "Ahmad with emoji heart is he the one?". Khaleed ya tambaye shi, gyad'a mishi kai yayi, khaleed yayi dialing no, bata jima tana ringing ba yayi picking yana tambayar, "yeah man watts up? Nazo d'azu ma fa baka nan Ina ka tafi kuma kaida baka da lafiya?". Khaleed yace, "he's not the one, Ahmad it's khaleed his neighbor, he ask me to call you, I see like he's not feeling okay Soo please come to him now". "Okay" kawai Ahmad yace sukayi sallama. Da yake yana cikin gidan ba jimawa sai gashi yazo, khaleed na ganin Ahmad yazo yayi musu sallama dama ya tafi. Ahmad ne ya dinga jera mishi sannu da tambayar abinda yake damun shi, banda juya kai ba abinda yake yi, ya kasa zama ya kasa kwanciya ya kasa tsayuwa, gaba d'aya duniyar yaji tayi mishi zafi tana jujjuya mishi, shi kanshi Ahmad ganin yanayin da yake ciki hankalin shi tashi yayi, k'arshe kawai sai ya koma gefe ya zuba mishi ido yana kallon yadda yake kaiwa bangon d'akin duka cike da tausayawa. Har hannun shi ya fashe yana jini bai daina dukan bangon ba, hakan yasa Ahmad ya taho ya rik'e hannun yana mishi magana cikin d'aga murya, "so kake ka illata kanka khaleefa? Na tambayeka me yake damun ka kak'i fad'a mun saboda kana ganin ban isa nasan damuwarka ba, nace muje asibiti kak'i yanzun kuma ka fara neman hanyar da zaka illata kanka, well zan tafi in barka in yaso ma ka halaka kanka don banga amfanin zamana a tare dakai ba....... ". Kafun ya k'arasa fad'a khaleefa ya kwantar da kanshi jikin gwiwar shi ya fashe da wani irin kuka mai cin rai, kuka yake irin wanda ya kasa yi tun d'azu yake cin zuciyar shi, duk wannan abun yana yine don ya samu hawaye ya zuba ko yayane yaji sanyi a ranshi. Dafa kanshi Ahmad yayi cikin tausayin shi yace, "kayi hak'uri khaleefa komai yayi tsanani maganin shi Allah". Sai a lokacin ya d'ago kanshi ya d'ora hannun shi saitin zuciyar shi, "ba zaka gane ba Ahmad, jina nake kamar ba niba da ace zan mutu ma a wannan lokacin sai nafi kowa farin ciki da dai in dinga ganin bak'in ciki da tashin hankali irin wanda nake gani a yanzun.......". "Subhanallah da hankalin ka kake fad'in haka da bakin ka khaleefa? Don Allah ka nutsu kasha ruwa mai sanyi zaka ji sanyi a ranka". Ya fad'a tare da tashi ya d'auko mishi ruwa mai maseefar sanyi da kofi, ya tsiyaya ruwan a cup ya kai mishi bakin shi, aikuwa daya fara Sha sai daya ga ya shanye tass sannan ya d'auke kai yana sauke ajiyar zuciya, a hankali kuma ya ji sanyi na kwaranya ruhin shi har ya samu ya dawo hayyacin shi, "kaci wani abu kuwa?". Ahmad ya tambaye shi, girgiza kai yayi kurum, tashi Ahmad yayi ya had'a mishi ruwan tea ya soya mishi chips sama sama ya juye a plate ya kawo mishi, da kyar ya iya shanye tea d'in yaci chips d'in shima kamar zaiyi amai, da first aid box d'inshi Ahmad yayi amfani ya mishi treating d'in raunin shi na hannu, ya bashi maganin ciwon kai don yasan bazai rasa ciwon kan ba, ya taimaka mishi ya kwanta saman bed, bai nemi jin komai daga gare shiba don yasan har a yanzu bazai tab'a fad'a ba, amma akwai sauran lokaci indai matsalar soyayyah ce tasa mai k'arfi ma ya sunkuya, da sannu zai magantu da bakin shi. Ba jimawa bacci yayi gaba dashi, Ahmad bai tafi ba saida ya gyare mishi d'akin fess ya sake dafa mishi d'an abinda zaici in ya tashi, ya futo mishi da kayan da zai sauya sannan yaje ya dawo. Ko daya futa saida ya saci kallon apartment d'in Saleema, ita kanta ya fahimci kwana biyu bata da cikakkiyar lafiya haka bata da nutsuwa Sam, ya tabbatar akwai abinda ya had'a su yake wujijjiga zuciyoyin su. Sai kawai yayi murmushin gefen baki ya ci gaba da tafiya yana tunanin yadda soyayyah tasa khaleefa zubar da hawayen shi masu tsada daba kowa ke iya ganin suba, zai iya rantsewa da Allah tunda suke a k'asar Germany bai tab'a ganin hawayen khaleefa haka ba sai yau, sannan duk sammakon ka ba zaka tab'a samun khaleefa bai yi abu biyun nan ba, sallah da wanka, shiyasa ya saka ayar tambaya a kanshi tun daga ranar da yaga ya makara sallar asubah da shirin futa makaranta, ga gyaran gida tsabta ko mace albarka, kayanshi haka zaka gansu a killace a adane bayan wankewa a washing machine har ioning d'insu anyi sai zabga k'amshin turaren shi suke. Lallai soyayyah daban take, abinda Ahmad yake tunani a ranshi kenan har ya isa inda ya nufa a lokacin. Toh khaleefa mai bacci da k'a'ida kuwa sai gashi yau yana bacci sama da hour biyu ba ko juyi babu balle alarm da zai tashe shi a lokacin. Azahar da la'asar duk saida suka je daf da magriba da Ahmad yazo ya tashe shi ya d'aura alwala ya gabatar a gurguje, yana idar da sallah Ahmad ya had'a mishi ruwan wanka irin wanda yake so, saboda yanayin sanyi da aka shiga cikin k'asar yasa kafun ya futo ya kunna room heater. Kaya ya zura masu sauk'in nauyi ya shafa mai da kyar a jikin shi ya koma ya kwanta kanshi na kallon rufin d'akin, hannun shi d'aya saman goshin shi ya dafe kanshi dashi. "sannu ya kake jin jikin naka?". Ahmad ya tambaye shi, "ba ciwo" ya fad'a ba tare daya motsa daga yadda yake ba. Shima Ahmad bai sake ce dashi komai ba yaci gaba da research cikin system d'inshi, babbar damuwar shi a ciwon nan na khaleefa shine suna gab da sanin makamar su? Nan da kwanaki k'alilan zasu yi interview dasu bakwai d'in da aka zab'a suyi aiki tare da general hospital orthopedic Berlin. Yanzu kuma gashi shi ya kwanta ciwo don ma Allah yasa sun gama exam d'insu tun last week da baisan ya khaleefa zai yi ba. Gashi nan Sam ba irin Nigeria ba da za'a iya ma mutum magud'i ko attendance in bai halarci lectures ba. Toh har kasun kwanaki biyu jikin khaleefa ba wani sauk'i, Dole Ahmad ya d'auko katifar shi da wasu cikin kayan sawar shi ya dawo nan yana kula dashi, jinya yake sosai kuma yana yin jiki, gashi ya rufe wayar shi Ahmad ma baisan inda ya wulla taba, yak'i yadda suje asibiti haka yak'i yadda y'an gidan su su sani, har cewa Ahmad yayi in ya fad'a musu bai yafe mishi ba, gashi cikin kwanakin sai damun shi Ayman da auntie suke a waya, tun yana d'agawa ya fad'a musu k'arya har k'aryar shi ta k'are ya daina d'agawa ma, gashi kullum ba sauk'i a ciwon nashi sai abinda ma yayi gaba, ko abinci baya iya ci sai ruwa da tea. Sosai Abubuwa suka taru suka yiwa Ahmad yawa, ya daina zuwa makaranta da clinic sai yini tare da majinyacin shi. Khaleed ya shigo sai biyu yana duba shi, shi kanshi ya tausaya da yaga halin da khaleefan yake ciki a lokacin, ya basu shawarar su tafi suga likita tunda su abun yafi k'arfin su. Ahmad yayi na'am da shawara hakan yasa ya kashe wayar shi gaba d'aya ya tattara nutsuwar shi wajen ganin ya zai shawo kan khaleefa har ya amince? Saleema kuwa kwananta biyu tana jinya a tsaitsaye gashi bata da kowa da zai taimaka mata, ita da sauk'i bata kwanta kamar khaleefa ba amma fa ciwon kai kamar tayi hauka wanda yawan kuka ya haddasa mata, da kyar take iya jan jiki tayi wanka ta samu abinda zata ci ta sake komawa ta kwanta, tuni ta ajiye komai a gefe tana ji da kanta. Yadda take son khaleefa ya huce duk tunanin ta, ita kad'ai tasan daurewar da take wajen ganin ta k'arasa datse alak'ar su. Babu wanda take iya kulawa cikin y'an gidan su, haka wayar zata k'araci ring ta katse ba tayi picking ba. Tunda khaleefa yazo ranar da sukayi maganar nan bata sake ganin shi ko ji daga gare shiba, tasan dama mutum ne mai zuciya da komai, ba so ba tana ganin ko rayuwar shine zai iya sadaukarwa da dai ya wulak'anta. Tana cikin y'an tunane tunanen ta wayarta ta kad'a alamun shigowar sak'o, kamar ta share sai kuma ta d'auko tana dubawa, "nayi alfahari da samun ki matsayin matar aure na a farkon alak'ar mu, ashe mafarki nake. Na soki hadda hasashen irin yaran da zamu haifa ashe shifcin gizo ne, Sam ban d'auka ba zamuyi rayuwa tare dake k'ark'ashin inuwa guda ta aure ba, shin Saleema dama mutum na iya yin mafarki ido bud'e? Ashe masoyi zai iya rabuwa da masoyin shi akan dalilin da bai taka kara ya karya ba? Shin ni kike so dama ko asalina? Na kasa fahimtar ki har yanzu Saleema, don Allah ki wayar mun da kai na da yake cikin duhun rashin sani.......". Murmushin takaici kawai tayi ta fara mishi refly kamar haka, "tabbas ka fad'i gaskiya, sai dai ba kai kad'ai ka shiga cikin duniyar mafarki ba hadda ni, na fara mafarki hadda yaudarar kaina akan abinda sam ban fahimce shi a dai dai ba, Abdallah duniya taci gaba, kan mutane ya waye, idan baka sani ba Ina son ka san cewa yanzu da uba ake ado, ko yau ka nemo asalinka Saleema a shirye take ta aure ka, babu shi kuma yana nufin babu kai ba Saleema da soyayyar ta har abada". Tana sending massage d'in ta d'ora wayar saitin zuciyarta ta rintse idonta ta fashe da wani irin wahalallen kuka, she's suffering for all dis she's doing...... @@@@@@@@@ Kusan haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin tashin hankali da bak'in ciki, sun kasa fahimtar juna yayinda suke wahalar da kansu don ganin sun yak'i zuciyoyin su wajen ganin sun cire son juna daga ransu gaba d'aya, musamman ma Saleema da tafi shi shiga tashin hankali a al'amarin. A wata ranar asabar da yamma ta kasa jurewa ta lallab'a bayan tayi wanka ta futa da dafa bango taje apartment d'in Amna, tana zaune tana waya da y'an gidan su a lokacin, kamar a mafarki haka taga Saleema tsaye cikin halin ciwo, da sauri Saleema ta k'arasa jikinta ta rungume ta tana fad'in, "ki yafe ni Amna". Amna ma rungume ta tayi a jikinta tace, "me ya faru kuma Saleema?". Da kyar taja k'afarta ta zauna k'asa wanwar ta tattakura ta rushe da kuka mai ban tausayi da al'ajabi a gurin Amna. Sai duk ta gigice tana tambayar ta shin me yake faruwa dake? Me akayi miki. Kuka kawai takeyi ba amsa har Saida tayi mai isarta, tasa Amna ta bata ruwa tasha ta d'an samu nutsuwa. @@@@@@@@ _Gida Nigeria_ Auntie ce zaune parlon sameera tayi shiru cike da damuwa tana nazarin maganganun k'awar tata, "yanzu kina ganin zuba ido zanci gaba dayi kusan sati banji daga khaleefa ba, shi kanshi abokin nashi ya daina d'aga wayata yanzu ko na kira ma bata tafiya, fisabilillah haka zan zuba ido yara su b'ace a wata k'asa?". Auntie ce meyin wannan maganar cikin damuwa. Sameera da take sauraronta cikin tausayawa da kulawa tace, "ba haka nake nufi ba k'awata, Ina nufin ki nemi iyayen Ahmad kiji ko akwai wani abu da yake faruwa suka b'oye miki in yaso in kika ji wani abu da bai gamshe kiba sai ki ajiye komai kije har k'asar ki bincika". Gyad'a mata kai tayi cikin gamsuwa, sai yanzu ta gane abinda k'awar tata take nuna mata tun d'azun. Sameera taci gaba da kwantar mata da hankali har zuwa lokacin da taji d'an sanyi a ranta. Shaheeda ce ta shigo parlon da sallama, suka amsa suna kallonta, (doguwar budurwa ce kyakkyawa ba laifi suna d'aukar kamanni da Nur amma tafi Nur cikar jiki da dogon hanci sai hasken fata data k'ara da mai, sai dai budurwa ce ma'abociyar nutsuwa da aji, kallo d'aya mutum zai iya gane hakan, bata da yawan fara'a haka bata da d'aurarriyar fuska tsaka tsakiya, a rayuwarta ma ba wanda yafi ganin fara'ar ta kamar mamin su sai ko Auntie da tasu tazo d'aya da yayarta khadeeja, Cox shaheeda tana son mutum d'an gayu mai kyau, kamar dai auntien). Sanye take da riga har gwiwa da skirt mai tsaga a baya, tayi d'aurin ta simple mai kyau ta yafa siririn gyale da takalmi da jaka. Yadda take tafiya cike da yanga da yauk'i kad'ai ya isa yasa ta d'auki hankalin maza da yawa. A k'asan k'afar Auntie ta zauna tana gaishe ta, auntie ta k'ara fad'ad'a fara'ar fuskarta ta amsa tana tambayar ta kwana biyu, tace, "kwana biyu naje gurin auntie suhaila ne zan mata hutu". Auntie tace, "Eh mammie ta fad'a mun". "Okay to Ina can ma tayi miscarriage shine ta k'arawa hutun nawa tsayi". "Ayyah Allah ya maida alkhairy duk mammie ta fad'a mun har munyi waya da itama na mata sannu". "Okay" ta k'ara fad'a. Har zata tashi sameera ta yiwa surayyah inkiya da ido tayi mata magana, sai tayi saurin kallonta tace, "Toh ni yanzu ko sai zuwa yaushe za'a zo ayi mun kwana biyu?". murmushi tayi tace, "insha Allah in mun samu hutu sai nazo miki auntie". "Kamar nan da yaushe kenan zaku samun hutun?". Shiru tayi tana nazari kafun tace, "nan da 3 months dai". Zaro ido auntie tayi tace, "3 months sunyi yawa shaheeda ina laifin ma kizo mun end of this month, da kaina ma zanzo mu tafi". Wani murmushin ta sake yi tace, "Allah ya nuna mana auntie, Mamie Nur ta dawo kuwa?" Sameera tace, "eh tana ciki kinsan ta da bacci". Auntie tace, "kamar dai Ayman kenan? Ko wane irin zama za'ayi ma ni surayyah". Sameera tace, "wallahi kuwa suje can su k'arata dai, in ma yini zasuyi bacci duk babu matsala". Sukayi dariya su duka. Hucewa shaheeda tayi ciki da salon tafiyarta. Ajiyar zuciya sameera ta sauke tace, "kinga ta amince da yake tana sonki, shiyasa nake ji a jikina ke zaki iya shawo kanta ta amince cikin sauk'i tunda taku tazo d'aya, kinga da yadda taje gurin suhaila kuwa? Wallahi saida ta had'a da mijinta da yaran ma duka sannan". Auntie tace, "ai ki kwantar da hankalin ki insha Allah duk zasu amince, shima khaleefan irinta yake yadda kika ga shaheeda haka yake, sai ya kwana biyu a d'aki lokacin da suna secondary, daga sallah sai cin abinci ke futo dashi, kuma shi ba kamar Ayman ba, baya bacci sai uban research akan duk wani abu da ya shafi physiotherapy, cikin irin binciken ne ya nemo wannan makarantar da suke yi ta Humboldt a Berlin, bai samu nutsuwa ba kuma saida ya tafi". Sameera tace, "Allah sarki khaleefa ai ankusa gamawa a tattara a dawo gida Nigeria a fara aiki kuma". Auntie tace, "aikuwa kam, har nayi magana da doctor salihu ya tabbatar mun ana yunwar masu irin kwalin su a k'asar nan, muddin wannan course d'in da suke yi yanzun sakamakon shi yayi kyau toh tabbas sun samu aiki sun gama, sai sun zab'i state d'in da zasuyi aikin ma". Cikin jin dad'i sameera tace, "Masha Allah! Allah ya amince ya basu dukkan nasara". Sun sake hira a tsaitsaye duk akan had'in auren da zasuyi tsakanin khaleefa da shaheeda, tuni sun gama tsara komai khaleefa kawai suke timming ya dawo k'asar asan wadda ake ciki. Shine dabarar auntie na janta gidanta end up month dai dai da lokacin da zai dawo, tasan bazai tab'a cewa shaheeda bata yi mishi ba, don ta futa irin wadda suke so a wannan zamanin. _wannan kenan_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page 1️⃣9️⃣ *Germany* Saleema kuwa saida ta nutsu bayan Amna ta kwantar mata da hankali da kalamai masu taushi sannan ta kwashe komai daya faru tsakanin ta da khaleefa ta fad'a mata, shiru Amna tayi lokaci d'aya kanta ya kulle ta rasa ta yadda zata kamo bakin zaren, "Ni na tab'a jin labari irin naku ma kuwa Saleema? Ya tashi ba dangin uwa, bai tab'a ganin mahaifin shiba, ke kuma kin rabu dashi saboda kina ganin shi shege ne? And you still love him, toh yanzu ke meye sunan ki a gurin shi, meye matsayin soyayyar ki, kinga a tak'aice kin nuna mishi origin d'inshi yafi soyayyar da kike mishi muhimmanci kenan". Dafe kai Saleema tayi tace, "Amna I don't know what come over me I just......". Sai ta dafe kanta da hannunta kurum. Zama Amna tayi kusa da ita tace, "babu wani abu da yazo kanki daman halin kine Saleema, haka kika yiwa ra'ees, bakya dogon tunani kafun aiwatar da abu". Girgiza mata kai Saleema tayi tace, "ba zaki gane ba Amna, wannan matsalar ba irin ta ra'ees bace, sannan ba daga ni bane daga mahaifina ne, wallahi ko zan had'iyi zuciya na mutu ba zai yarda na auri wanda bashi da cikakken asali ba......". "Tabdijan! Ni bansan ma ta yadda zan fasalta wannan al'amari naki ba, amma bari mu gani zuwa kwana biyu nayi tunani". Da haka suka rufe wannan babi, Amna ta dinga d'auke mata hankali har Allah yasa ta saki ranta kad'an, ta komawa abinda ya kawo ta k'asar. Ta b'angaren Khaleefa kuwa Ahmad ya samu nasarar kai shi asibiti gurin d'aya daga likitocin da suka koyi aiki a hannun su, Sun kwanta na a k'alla kwana hud'u kafun jikin shi ya dawo normal yaji sauk'i sosai. Ko da suka dawo ma Ahmad ci gaba da kula dashi yayi ya rage damuwa ba laifi amma Ahmad ya kula yana yawan duba wani sak'o a wayar shi wanda yake sake jefa shi a damuwa. Sosai ya sake zama silent ba baki sai amsa da ido, har yanzu bai ce da Ahmad komai akan Saleema ba, shima ya zuba mishi ido kawai yana kallon shi, ya tabbatar yanzu in zasu shekara a haka bazai tab'a bud'e baki yace mishi ga damuwar shiba, sai kawai shi ya shirya tambayar shi da kanshi don yasan ta hanyar da yake ganin zai sama mishi maslaha. Yana zaune sanye da 3 quarter da singlet, ya hard'e k'afafun shi biyu hannun shi rik'e da d'an k'aramin bowl yana cin farfesun kifin sannu sannu yana had'awa da romon me yaji sosai, waya ce kare a kunnen shi yana waya da auntie da take magana da harshen Arab cikin fad'a, "kasan yadda hankalina ya tashi kuwa? Cikin kwanakin nan bana iya baccin kirki komai nawa saida ya tsaya cak na kasa tsinana komai a office, k'iris ya rage na biyo flight nazo makarantar na ganka". Madadin da da in sukayi waya da ita ko cikin damuwa yake yana jin sanyi yanzun sai ranshi ma ya sake bak'ik'irin, ji yake kamar ya rushe da kuka saboda jin muryarta da yayi. "kayi shiru baka ce komai ba khaleefa". Murmushi ya k'ak'alo idon shi ya kawo ruwan hawaye yace, "na d'an shiga busy ne auntie amma kuna raina keda Ayman shiyasa ina samun dama ku na fara kira, shi beyi picking bama maybe yana fushi dani ne". Auntie tace, "Anya kuwa? Sai dai ko yana da over work nima na kira shi bai d'aga ba". Khaleefa yace, "toh Allah yasa". Ta sake cewa "ameen" sun sake yin shiru kafun auntie tace dashi, "Wai yau saura kwana nawa ya rage ka dawo Nigeria?". Ajiye bowl d'in hannun shi yayi ya tafi nazari kafun can ya nisa yace, "nan da cikakken sati biyu nake tunanin zamu kammala gaba d'aya". Cikin jin dad'i tace, "Masha Allah ina ganin zaiyi dai dai da hutun Ayman sai muzo tare wannan karon". Khaleefa shiru yayi bai sake cewa komai ba, ganin haka sai auntie tayi sallama dashi. Yana ajiye wayar Ahmad ya dawo kusa dashi ya zauna. "Yeah man jikin naka da sauk'i sosai ko?". "Umm" kawai yace can k'asan mak'oshi, sake gyara zama Ahmad yayi yace, "khaleefa sai nake ganin kamar rashin lafiyarka yana da alaqa da sab'anin da kuka samu da Saleema cikin kwanakin nan". Kallon shi khaleefa yayi jim kafun yace, "me yasa ka fad'i haka? Ita tace maka mun samu matsala da ita ne?". "a'a ba ita bace, hasalima ni nafi sati biyu ban ganta ba, kawai lissafa ka nayi kamar yadda kake lissafa rayuwar mutane, toh ni dai banyi maka dole ba, idan kaso kaci gaba da b'oye damuwarka, nima bance dole sai naji ba, sai dai ina son ka riqe cewa alfarmar dana nema mana ta zaman jinyar ta k'are daga gobe, soo ko ka saki ranka ka manta da komai, ko kuma ka rushewa kanka shekarar k'arshen nan sai ka sake wata, Ni in na futa daga yau ba sake ganina zakayi ba har mubar k'asar, don banga amfanina a tare dakai ba tunda har zaka iya b'oye mun wani abu na daga rayuwarka baka son na sani". Ahmad yana gama maganarshi ya soma had'a kayanshi da duk wani abu da yasan nashi ne a d'akin, khaleefa yana zaune ko motsi baiyi ba bare ya bud'e baki da nufin dakatar dashi, abinda ya sake tunzura zuciyar Ahmad kenan ko gama had'a kayan baiyi ba ya nufi hanyar futa, sai lokacin khaleefa ya mik'e ya d'auki wayar shi dake bedside yace, "zaka tafi ka manta abu mafi muhimmanci naka Ahmad". Juyowa yayi ya kalli khaleefa da yake tsaye ta bayanshi yana mik'o mishi wayar shi, sai ya dawo da baya da nufin karb'a, sai da yazo gab khaleefa ya maida hannun shi baya yayi taku biyu zuwa tsakiyar d'akin sannan ya fara magana, "a wasu lokutan in kayi abu sai ka bani mamaki, Ahmad na d'auka kai zaka fara bada labarin khaleefa saboda sanin da kayi mishi babu wani mahaluki daya sanshi haka, sai gashi a aikace kana nuna kamar wannan maganar tawa hasashe ce, Ahmad na zab'i yin shiru ne saboda a wasu lokutan ba abinda yakai shiru dad'i da sanya zaman lafiya tsakanin al'umma". Sai ya dakata yaja dogon numfashi kafun yaci gaba, "abinda ya faru ko yake faruwa dani ban raina kaba amma abu ne da ba zaka iya yimun maganin shiba, Ahmad nayi Imani naji a jikina duk duniyar nan ba mai iya yimun maganin damuwata sai Allah, shiyasa shi kad'ai nake kaiwa kukana a yanzun........". Yana kai k'arshen maganar ya koma kan sofa inda ya tashi ya had'a kanshi da gwiwa yayi shiru yana nazari. Ahmad jikin shi a sanyaye ya matso kusa dashi shima ya zauna ya dafa kafad'ar shi, "ko baka cemun komai ba naji sanyi a raina khaleefa, tabbas ka gama magana saboda Allah shine madogarar bawa, shi kad'ai zai yi mana maganin abinda yafi k'arfin mu, Ina taya ka da addu'ar Allah ya yaye maka damuwarka yayi maka maganinta, a k'arshe na fahimci ka dad'e da yakice komai daga ranka garkuwar jikin kace kawai bata dawo dai dai ba". Khaleefa rik'e hannun Ahmad yayi gam ya rintse ido ya karanta addu'o'in kore damuwa sannan ya soma labarta mishi duk abinda ya faru tsakanin shi da Saleema daga ranar da taji tarihin rayuwarshi, abin ya girgiza Ahmad matuk'a, duk yadda yake tunanin abun sai gashi ya zarta tunanin shi, ehhh lallai ya yarda wannan matsala ta abokin shi maganinta sai dai Allah. Ya d'auki a k'alla wasu dak'ik'u shiru kafun yace, "wannan duk ba abinda zamu iya shiga bane, da farko dai ita Saleema ka ajiye ta a gefe, ni har yanzu bansan ta inda zan fara fassarata ita da soyayyar ta gare kaba, kai tsaye bazan ce ta yaudare kaba, saboda ni ban tab'a ganin yaudara a idanunta ko a tare da ita ba, sannan a aikace bata nuna maka hali na adalci ba, ta yadda ta yanke alak'ar ka da ita farat d'aya ba tare da dogon nazari ba. Abu na biyu sai dai kayi hak'uri amma akwai k'amshin gaskiya a zancenta, ni bance ku ba halastattu bane amma lallai mahaifin ku yana raye kamar yadda Saleema ta fad'a, shiyasa Auntie tak'i yarda ku ga hoton shi, take ta b'oye muku komai game dashi, maybe kuma ya rasu kamar yadda ta fad'a amma akwai rikici mai girma tsakanin ta da familyn mahaifin ku shiyasa tak'i yarda ta nemo su kota had'a su daku, khaleefa a cikin biyun nan dole za'a samu d'aya, sannan idan ka duba da kyau zaka ga babu kama kota farce tsakanin Auntie, iya, da malam, iya da malam suba farare bane kamar auntie, sannan iya tana d'an jin fulatanci kuma bata iya larabci ba, auntie kuma tana jin larabci bata iya fulatanci ba, toh ta Ina kenan kake ganin sun had'u? Daga kamannin mahaifiyar ku, ko makaho ya shafa tsantsar kyawunta da hasken fatar ta zai gane ta futo ne daga jinsin Arab, sam bata kama da Nigerians........ Lallai ya kamata ku fahimci hakan tun kafun Saleema ta fad'i waccen maganar ta b'atan ci gare ku, da cikin sauk'i baka fad'a mata tarihin kaba......". Shiru khaleefa yayi yana k'ara d'aukar haske kan yadda mu'amular su ta dinga tafiya da auntie a gidan iya, shi dama ya dad'e da fahimtar akwai wani abu da take b'oye musu shiyasa take takatsantsan dasu duk tsawon wad'an can shekarun, shine dalilin da yasa tasa suka yi mata alk'awarin basu ba sake tambayarta wani abu game da mahaifin su ko dangin shi. Sai ya dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu, "innalillahi wainna ilaihi rajiun, Ahmad maganar ka fa gaskiya ce, yau na sake ji a jikina lallai mahaifin mu yana raye.... Ahmad na tabbatar da haka....." Zuba mishi ido Ahmad yayi cike da tausayin shi kafun yace, "yanzu Ina matsayar soyayyar ka da Saleema?". Girgiza kai yayi cikin takaici ya nemo SMS d'inta ya mik'awa Ahmad sannan yace, "har abada ba zan tab'a daina son Saleema ba saboda sonta a jinin jikina yake, kuma itace mace ta farko dana fara Soo a rayuwata, sai dai bazan k'ara k'ulla wata alak'a tsakanina da ita a yanzu kota gaisuwa ba, zan duk'ufa wajen neman ahalin mahaifina na gabatar musu da kaina, su da kansu nake so suje nemo mun aurenta k'asar su gurin mahaifin ta, Ahmad koda ya kasance Auntie bata samar damu ta hanyar halas ba bazan tab'a b'oyewa familyn Saleema ba, idan sun so su bani ita a haka, idan kuwa suka hanani aurenta to tabbas ya tabbata bani da rabo a soyayya da aure". Maganarshi ta k'arshe ta tab'a zuciyar Ahmad sosai, khaleefa yana nufin idan har bai same taba bashi ba sake yin soyayyah bare aure? _tirk'ashi_ Ahmad bayan ya jinjina al'amarin kallon shi ya sake maidawa kan khaleefa yace, "kada kayi saurin yanke hukunci insha Allah zaka samu Saleema ni kaina Ina jin haka a jikina, duk wata soyayyar data cika soyayyar gaske ta asali tafe take da k'alubale, kuma dole ku shiga cikin sa ba zaku kub'uta ba, sai dai Ina ganin anya babu kuskure kace zaka yanke alak'a da Saleema kamar yadda take so? Idan bayan wani lokaci ta amshi soyayyar wani fa? Tunda mu bamu san kai tsaye inda zamu samu y'an uwan mahaifin naka ba? Bare mu k'ayyade lokaci, bamu san ainahin tsayin lokacin da zamu d'auka wajen neman suba?". Murmushin takaici khaleefa yayi yace, "kamar baka duba sak'on ta sosai ba? Insha Allah zamu samu nasara a k'asa da shekara guda ma". Cikin K'arfafa gwiwa Ahmad yace "insha Allah" Sunci gaba da tattaunawa duk akan yadda zasu shawo kan lamarin. @@@@@@@@@ Saleema kam tana can taci gaba da rayuwarta cikin tarin damuwa da sauraron tunanin da k'awarta Amna take akan matsalar ta, ganin har kwanaki goma sun shude Amna bata ce da ita komai ba sai ta fara tunanin tambayarta kota manta da lamarin ta ne ma, gashi ko a hanya bata had'uwa da khaleefa bare a cikin school ta ganshi taji sanyi a ranta, sai yanzu take ganin kuskurenta na yanke hukuncin datse alak'ar da take tsakanin su rana tsaka, ta d'auka abu ne me sauk'i da zata iya, sai gashi ya zamo abu mafi wahala ga zuciyarta da ruhin jikinta, ga wutar son shi sai k'ara ruruwa take a cikin zuciyarta, sai yanzu da suka rabu take iya fahimtar tsananin son da take mishi, gashi abu na farko da take tunani game da jin shirun shi shine, tasan mutum ne shi me tsananin zuciya, duk abinda ya bari baya tab'a waigen shi har abada! Tsoronta d'aya kada dai khaleefa yana nufin ya rabu da ita ne har abada kamar yadda taso da farko. A zaune take saman stool sai gata ta silmiyo k'asa wanwar ba tare data sani ba, glass cup da yake hannunta ya sunlube ruwan zafin ciki ya kwaranye saman cinyarta, ko zafin ruwan ba taji ba saboda rad'ad'in da yake zuciyarta yafi k'arfin wannan rad'ad'in nakan fata da zai iya warkewa cikin sati d'aya zuwa kwana goma. A wannan yanayin Amna ta futo daga kitchen ta ganta, sai ta taho gurinta da sauri, "subhanallah Saleema meya same ki kuma? Yanzu fa na barki lafiyar Allah a nan?". Kallon Amna tayi da idonta da suka sauya launi tace, "Amna da gaske zaki nemo mun mafuta ko kuma zaki barni nayi asarar miji mai nagarta kamar Abdallah?". Murmushi Amna tayi cikin son ganin ta kwantar mata da hankali tace, "haba mana dear wannan shine kad'ai damuwarki? Ina nan ina nemo miki mafuta as I promise, sai dai ina son na fara jin ta bakin shi tukun in na had'u dashi, Soo cool down your mind insha Allah khaleefa mallakin kine k'awata, kuma y'an gidan ku zasu fahimci irin son da kuke yiwa juna su barki ki aure shi naji hakan a jikina tabbas". Cikin muryar kuka tace, "don Allah Amna kada ya zamana kina fad'ar haka don kawai ki kwantar mun da hankali......". Sake k'ak'alo murmushi Amna tayi tace, "wannan naji ne a jikina ba hasashe nake ba Saleema". Kwantar da kanta tayi a gefen kafad'ar Amna tace, "Ina alfahari dake k'awata ina k'ara neman gafarar ki akan abinda na aikata gare ki kwanakin baya". Amna da kulawa tace, "ki daina damuwa da haka mubar abinda ya huce har abada please". Saleema cikin farin ciki ta rungume Amna tana kuka sosai a gabanta, itama Amna kuka take yi cikin tausayin k'awartata da wannan badakalar soyayyah tasu. *********** *Nigeria* Surayyah ce zaune a madaidaicin office d'inta tana rubuce rubuce jikin wani file na wata marar lafiya da aka kawo, irin mutanen k'auyen nan da idan suka ji ciwo basu san suje hospital ba sai jike jiken magungunan gargajiya har sai abun yaci k'arfin su su taho asibitin cikin birni a haukace. Tana duba file d'in tana jinjina wannan al'amari na bayin Allahn nan, sanye take da riga da zani na atamfa sai labcourt a saman kayan da k'aramin gyale, tuntuni wayarta take ring tak'i dubawa saboda tayi aikin da yake gabanta cikin nutsuwa, bayan ta mik'a musu takarda mik'ewa tayi don gabatar da sallar zuhr da tayi a lokacin, ko data futo ba'a fasa kira ba har tayi sallah taje donta ziyarci gidan cin abinci tayi lunch. Still wayar taci gaba da ringing, sai ta d'auka donta duba me kira a lokacin, Ayman ne, da sauri tayi picking tasa a kunnenta, "yaa Ayman hope ba jikin bane?". Ayman da yake office a lokacin yace, "eh auntie nasha magani kafun na futo Ina office amma duk hankalina yak'i kwanciya shine na kira naji lafiyarki". Duk da gabanta ya fad'i amma sai da ta sauke ajiyar zuciya tace, "Ina lafiya Lou Ayman, yanzu haka zan futa yin lunch ne, fatan kaci abinci ba aiki kamar agogo ba". Yana daga inda yake zaune yace, "in na futa sallah zan tabbatar nayi yadda kike so kafun na koma office". Tace, "good!" Daga nan suka yi sallama ta futa don yin abinda zata yi. ★★★★★★ Da yamma koda ta tashi office bata je gida ba saida ta tsaya gurin doctor Salihu suka sake magana akan aikin khaleefa da yake gab da dawowa k'asar, ya sake bata tabbaci akan ba za'a samu wata matsala ba insha Allah, indai kwalin yaron yazo da kyau irin wanda suke so. Cike da farin ciki da jin dad'i ta futo, ta gaji sosai amma sai taji tana son biyawa gidan sameera k'awarta don ta tayata murnar wannan kyakkyawan albishir. Don haka saita juya akalar motar ta zuwa anguwar...... A dai dai wannan lokacin sameera tana zaune tare da wata k'awarta hajiya tafeeda, hajiya tafeeda irin matan nan ne masu son kansu, babu ruwan su da kowa kansu kawai suka sani suke Soo, a dai dai wannan lokacin labarin abinda ya dame ta take ba sameera, yayinda ita kuma sameeran take sauraronta kurum tana jinjina zallar son zuciya dake ƙunshe cikin furucinta, ko dana kasa kunne magana take cikin fushi da b'acin rai, "ai wallahi ya had'u da rashin zaman lafiya daga gare ni shida mahaifin nashi da yake goya mishi baya, sakaran yaro kawai, yanzu da yabi yadda nake so da ba shaheeda zai zo ya aura ba, yarinya Masha Allah irin wadda mazan garin Kano ke rububi, shine ya b'ige da yarinyar da mutane da yawa sun tabbatar da bata da tarbiyyah, ance idonta fa a bud'e yake......". Sai a lokacin sameera ta tari numfashinta, "toh ke waya fad'a miki duk wannan? Kada ya zamana fa kema kin shiga sahun mutanen da suke yadda da jita jitar mutanen gari y'an hana ruwa gudu da basa son suga an k'ulla abun arzik'i?". Wani irin kallon takaici ta yiwa sameera taci gaba da maganar ta, "humm ba zaki gane ba maman haeydar, kinsan Allah da gaske yarinyar ance bata da tarbiyyah, kina ji wani k'aton saurayi ta k'ulla alak'a dashi tun bata kai haka ba da sunan wai aboki, uwar kuma wata banza gagaso ta sakar mishi basa nan basa can gaba d'aya fa ance ya gama lalata mata rayuwa har makarantar da tayi a wani gari yake binta yayi kwanaki suna gantalin su sannan ya dawo, haka in zata dawo gida ma shi yake d'auko ta ya dawo da ita su d'ora daga inda suka tsaya, kar kiso kiga zuciyata da naji labarin irin dukiyar da suka narka ga wannan gantalalliyar yarinya suka kai da sunan lefe.....". Ita dai sameera cike da al'ajabi take sauraron tafeedan saboda tana ganin zallar wauta a kalamanta, magana take akan Ayman da raihana wanda ba wai don surayyah tata bace zata iya rantsewa da girman Allah surayyah bata daga cikin iyayen da suke zubawa yara ido suna yin abinda ransu yake so a gari ba. Koda yake itama ba tayi magana akan surayyah ba duk buhun k'iyayyar ta akan raihana da mamanta take saukewa, wannan kuma matsalar suce can da ita da zata zamo surukar su. Ta bud'e baki zata yi magana taji ihun heedaya tana kiran Auntie! Auntie!! Sai ta maida idonta k'ofa tana jiran taga ta inda aminiyar tata zata b'ullo. Aikuwa sai gata rungume da heedaya ta d'auko ta, saman kujera ta ajiye ta tana nishi, sameera tace, "sannun ki da k'ok'ari kema yanzu wannan garsamemiyar budurwar kika wani d'auko?". Tana murmushi ta shafa kan heedaya tace, "ke kike kallonta garsamemiyar budurwa ni a gurina har yanzu y'ar jaririya ce". Duk dariya sukayi abun har yaba heedaya kunya ta shige cikin gidan da gudu tana b'oye fuska. Gaisawa suka yi da sameera sannan tafeeda ma dai suka gaisa sama sama, don tasu bata zo d'aya ba sam, sameera sawa tayi aka kawowa auntie ruwa da abinci, ta dai sha ruwan amma abincin babu gurbin shi. Sameera ce tace, "kinsan yanzu nake niyyar kiran ki a waya kayan nan sun iso ummie zata yi clearing komai ta tafi ma tuni". Surayyah tace, "Masha Allah amma sunyi ba zata". Sameera tace, "sosaima". Daga nan suka yi shiru, surayyah ta zaro wayarta tana dubawaa don bata son amayar da abinda yake cikinta gaban wannan magananniyar matar don ita sam bata son mutum mai irin halinta. _dubun godiya da jinjina ga d'aukacin mabiya litattafan *in-identical twins* hak'ik'a muna jin dad'in comment d'inku na so da nuna goyon baya 100% fatan alkhairy gare ku baki d'aya_. _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty 2️⃣0️⃣ Ita kam tafeeda ganin sunyi shiru ci gaba da bata labari tayi, duk wani k'anzon kurege da k'aryar da ake kawo mata ta hau ta zauna daram. Shiyasa ta tsani raihana kamar ta soka Mata wuk'a ta kashe ta a huta. Auntie da take zaune wayarta take dannawa tana harkokin gabanta hankalinta sam baya kansu, kuma dama itama sameera abinda take so kenan, don wannan kwab'a da jik'a aiki da tafeeda take da ta jita kam ba zata ji dad'i ba, surayyah ganin tafeeda nata magana bata da shirin tafiya gashi har lokacin komawarta gida zai k'ure tana waje, saita mik'e ta yi musu sallama ta tafi. Ko bayan futar ta tafeeda kallon sameera tayi tace, "nifa sai dai kiyi hak'uri amma wannan k'awar taki sam bata yi mun ba, ruwan munafukai ne da ita, ga shegen jin kai da d'aukar kai wata tsiya bayan duk mutanen gari sunsan bata da cikakken asali, haka tazo garin Kano da cikin da babu wanda yasan ubansu suka had'a kai da malam yusha'u da iya suna fad'awa mutanen gari wai y'ar shi ce, koda yake ke duk abinda zan fad'a ma ba yarda zakiyi ba tunda ga yaran nan sun girma kina shirin d'aukar y'a ki bayar sabo........." Ai da sauri Saleema ta d'aga mata hannu bata bari ta k'arasa ba, "kinsan abinda yake yawan had'a mu dake kenan ko tafeeda, toh wallahi ki iya bakin ki ba ruwanki da tsakanina da ita, tsakanin mu dake daban tsakanina da surayyah ma daban, ku kullum mutanen garin nan in baku jefi mutum da mummunar kalma ba ba kuji dad'i ba, toh bari kiji tafeeda su wanda suke kawo miki gutsiri tsomar suka hana ki zama k'alau da mutane in kin sake had'uwa dasu ki fad'a musu ba nuriyyah kad'ai zan bawa Ayman ba har khaleefa da yake karatu a Germany zan bawa auren shaheeda, sai su samu sabon abun yad'awa, Soo gwara ma tun wuri kibar Imran ya auri raihana in Kuma ba haka ba zaiyi babun bad'ilahu, ba wan ba k'anin". Tunda sameera ta fara magana cikin fushi da fusata bata dakata ba har saida takai Aya, cikin sanyin jiki tafeeda tace, "oooh k'awata wannan sababi haka daga magana? Toh Allah dai ya baki hak'uri ni tashi ma zanyi in tafi". "Ai kece bakya iya kiyaye harshen ki tafeeda, kowanne kare da doki in yazo miki da gulma da funafunci sai ki share guri ki zauna ki saurara duk gashin nan ai sun gurbata miki tunani kema kin fara zama irin su". Tafeeda tace, "ke wani abun fa ba maganar munafunci bane gaskiya ce tsagwaronta bakya son a tab'a masoyiyar k'awar kine kurum, yanzu ke sameera in tambaye ki? Tunda kuke da ita ta tab'a baki labarin rayuwarta? Ko asalin tushen yaranta? A'a ko kuwa ta tab'a nuna miki dangin uban su da ta cika gari da k'aryar cewa ya mutu, ko kuwa ta fad'a miki yadda ta sami yaran? Toh kinga ashe har yanzun nan da kuke Shirin k'ulla zumuncin auratayya bata gama yarda dake ba, tunda gashi har zata iya b'oye miki sirrikan ta bayan ke kin yarda da ita babu sirrin ki da bata sani ba......". Tafeeda ko data gama maganar ta bata tsaya jin dogon sharhi ba ta d'auki jakarta, don tasan yadda ta mulmulo wannan uwar magana lallai zasu iya fad'a da sameera kafun ta tafi, ita kuma ba abinda ya kawo ta ba kenan. Har ta yiwa sameera sallama ta tafi bata motsa daga yanda take ba, abubuwa da yawa ne suka fara mata yawo aka, amma cikin k'arfin hali bata yadda shaidan ya rinjayi tunanin taba a lokacin ta yakice komai ta zubar taci gaba da harkokinta. Surayyah kam koda ta futa direct gida tayi, a parlon k'asa ta samu haleema da bak'i, suka gaisa ta haura stairs. Ayman da bai jima da dawowa office ba yana zaune da remote a hannu yana ta sauya channel kamar wanda aka sa dole, fuskarta washe da fara'a ta zauna opposite d'inshi tace, "engineer! Ya jikin naka fatan akwai sauk'i ko?". Girgiza mata kanshi yayi yace, "babu wani sauk'i Auntie yanzu haka kaina ciwo yake". D'an zaro ido tayi kad'an tace, "ba kyau cewa ba sauk'i a ciwo fa! Yanzun ka tashi kasha magani zaka ji relief insha Allah". "Bar maganin nan auntie kawai, wai kina samun khaleefa a waya kuwa?". "Ya za'a bar maganar magani zai yiwu kuwa? Toh ni bazan saurare kaba har sai ka sha koda paracetamol ne, dama zuwa gobe ka shirya muje kaga likita". Shagwob'e fuska yayi ya mik'e, "zansha maganin amma don Allah ki fad'a mun kina samun khaleefa a waya?". Itama mik'ewar tayi tace, "eh Ina samun shi amma ba koda yaushe yake d'agawa ba". Ayman shiru yayi ya k'urawa guri d'aya idanu kafun can ya nisa yace, "Auntie can't you see khaleefa is changing gradually?". Auntie tace, "Anya kuwa? He's busy dai gaskiya these days saboda k'aratowar bikin kammala 2 years course d'in su, baya ga haka ni banga wani sauyi daga gare shiba". Jiki a sanyaye Ayman yace, "toh Allah yasa". Tare suka k'arasa har ma'ajiyar first aid box ta bashi magani yasha, ya kishingid'a na mintuna k'alilan kafun kiran sallar magrib ya tashe shi. Sai daya sauya kayan jikin shi sannan ya futa masallaci, a k'ofar gidan su yau yayi zaman shi yana kallon mutane masu hucewa har akayi isha'i ya koma masjid ya sauke farali sannan ya koma cikin gida. Haka kurum yake jin kanshi cikin damuwa ba tare dashi kanshi yasan kota meye ba, yadda khaleefa ya watsar dashi baya neman shi haka shima yayi mishi, raihana kuwa ko kira tayi baya d'aga wayarta tuni ya haramtawa kanshi, Nur ma da yake jinta maganin unknown damuwar shi kwana biyu ya saurara da kiranta a waya akai akai, ko wayar sukayi ma baya doguwar hira suke yin sallama. ★★★★★ B'angaren su raihana suna ta shirye shiryen su na biki, kowa ya fara sakin jikin shi ana al'amuran biki saboda har invitation card ma sunsa a buga tunda bikin yanzu ten days ya rage. Amarya raihana kam an fara shan gyara gurin wata kwararriyar mai gyaran jikin matan gida dana amare, shagon ta yana opposite orthopedic hospital dake gwammaja, (domin son turaren wuta na amare da kuma naku matan gida, gyaran jiki lungu da sak'o maza ku hanzarta baitul aroos ku futo kuna zunbud'a k'amshi na d'aukar hankalin me gida, ga duk wanda yake so sai tayi contacting d'ina ta no wayata kamar haka 08134288477) Babu inda take zuwa daga gida sai shagon gyaran jiki, dama kuma ita d'in ba ma'abociyar gantali bace, Imran ma ta dakatar dashi da zuwa saboda bata son ya dinga ganinta don bazai ga kyawun gyaran jikin ba kamar in aka kammala gaba d'aya. Alak'ar ta da Ayman kuwa tuni ta ajiyeta a gefe tunda ta tabbatar k'ararriya ce da zarar an d'aura auren ta da Imran, shiyasa take ta yak'i da zuciyarta, in aka kwana biyu dai takan kira shi a waya saboda kar yaga don zata yi aure ta watsar dashi, kuma tunda ta kira biyu uku taji be picking ba bai biyo kiran daga baya ba, bata sake kiran shiba ta kyale shi. Ranar wata asabar tana kwance da safe tana bacci saboda ta tashi bata jin dad'in jikinta gaba d'aya, shiyasa tana gama aikinta na safe ta koma ta sake kwanciya, tana tsaka da baccin wayarta ta tashe ta da ringing, tana dubawa taga Imran ne, da hanzarinta ta mik'e ta d'auki wayar ta kara a kunnenta, cikin murya k'asa k'asa yake mata magana, "babyy bani da lafiya fa Ina kwance hospital an bamu gado". Saida gabanta ya fad'i ta mik'e zaune dirshan tace, "da gaske baka da lafiyaa ko dai zolayana kake dear". D'an tari yayi cikin sark'ewar murya yace da gaske Ina kwance wallahi, matsanancin ciwon ciki da zazzab'i". Sai taji hankalinta ya tashi, ta gigice tana tambayar shi ya jikin naka fatan dai akwai sauk'i ko? "Kwantar da hankalin ki raihanata shiyasa tun jiya nace kar a fad'a miki saboda kada ki tashi hankalin ki da yawa, amma yanzu jikin da sauk'i doctor yace zan d'an zauna tsawon kwana biyar ne kawai, kinga still dai za'a d'aura auren mu kwana hud'u bayan futowa ta hospital". Cikin tausayin shi raihana ta mishi addu'ar samun sauk'i suka yi sallama, daga nan bata sake kwanciya wani bacci ba ta mik'e ta futo parlon su, ummie ce kad'ai a gidan tana waya da ummaaa mahaifiyar ta su muhibba duk sun tafi makaranta, Zama tayi gefenta tayi shiru tana tunanin ta inda zata soma tambayarta abinda Imran ya fad'a mata, ummie kuwa bayan ta ajiye wayar tab'a gefen wuyanta tayi tace, "jikin ki har yanzu da zafi kad'an raihana, ki karya yanzu sai kisha magani" tace "toh ummie" sun sake yin shiru kafun ummie tace, "kinsan Imran yana asibiti kuwa?". "eh yanzu yake fad'a mun amma yace jikin nashi ma da sauk'i". Ummie tace, "toh Allah ya k'ara sauk'i wai poisoning d'inshi akayi jiya, yanzu haka bincike suke yi, an tabbatar a abinci aka sa mishi gubar, amma an kasa fahimtar wanda ya aikata hakan, jiya ai mahaifin shi yazo gurin abban ku ya nemi alfarmar a d'an k'ara bikin zuwa nan da wasu sati biyun masu zuwa, kafun nan sunyi settling komai ta daga b'angaren su". Ita dai raihana bata ce komai ba, abun ya matuk'ar bata tsoro wai anyi poisoning d'inshi a abinci, Allah sarki watak'ila kada hankalinta ya tashi shiyasa yace mata ciwon ciki da zazzab'i. Washe garin ranar ummie tasa suka shirya ita da hapser da zainab (y'ay'an yayarta) aka tanadi kayan dubiya suka je suka ga jikin nashi, yana kwance baya iya ko tashi zaune amma bakin shi rad'au duk da ba wai doguwar magana yake iyawa ba har yanzu. Mahaifiyar shi hajiya tafeeda ko kallon su bata yiba bare amsa gaisuwar su, sai y'an uwan tane suka amsa da kuma Imran d'in da yake ta kallonta kamar yaga bak'uwar halitta. A d'arare dai ita kam raihana take, har suka gama d'an zaman su sukayi musu sallama suka koma gida. ************ Auntie ta d'auki hutun sati biyu saboda tafiyarta Germany, Ayman ma hutun k'arshen shekarar shi yazo dai dai da tafiyar da auntien zatayi, hutun wata guda ya samu. Tuni auntie tayi musu booking ticket ta shirya musu yadda tafiyar zata kasance, kwana biyu kawai zasuyi su taho har khaleefan. Mishkila guda da aka samu washe garin taron zasu sauka k'asar. *Germany* Saleema ce zaune a k'asan d'akinta ta zubawa Amna da take aikin pressing kayanta ido, Amna ganin Saleema sai kallonta take kamar taga wata bak'uwar halitta sai ta dawo gabanta ta zauna dirshan tace, "nasan dai akwai magana a bakin nan naki". Doguwar ajiyar zuciya Saleema taja, "Ina nan Ina tunanin yadda kullum kike yaudara ta ba tare da kin nemo mun mafutar da kika ce zaki nemo mun ba har gashi khaleefa yana gab da barin Berlin.........". Murmushi Amna ta k'ak'alo tace, "ki kwantar da hankalin ki Saleema nifa nayi miki alk'awari, toh kuma me kike ci na baka na zuba? Akwai abinda na shirya wuyarta na had'u da khaleefa ne kici gaba da addu'a kurum, insha Allah khaleefa mallakin kine k'awata". Saleema sai taji d'an sanyi sanyi a ranta tace, "toh Allah ya yarda". Khaleefa kuwa sun gama hattama komai, a ranar litinin k'arfe 3:00pm dai dai aka basu kwalin su da cikakkiyar shaidar kammala course na musamman akan physiotherapy, Alhamdulillah shine abinda su khaleefa suke ta maimaitawa don nuna godiyar su ga Allah bisa nasarar da suka samu a wannan karon ma. Dukkan su suna sanye da black trouser da white shirt sai LC a sama, basu wani yi dogon taro na kuzo mu gani ba suka gama duk abinda zasuyi isu isu suka kama gaban su, Khaleefa suna tare da zab'ab'b'u bakwai da zasuyi aiki tare da Doctor raazi bisa jagorancin matashiyar balarabiyar k'asar Sudan doctor Fatima. Basu futo meeting ba ranar har sai kusan yamma. Aikuwa suka futo a gajiye lis, LC d'in ma sai a hannu yake rik'e da ita. Suna tafe suna tattaunawa su uku har suka k'arasa wani gurin shan coffee na kusa da inda suka futo, hot coffee kawai suka sha suka futo a nan Muhammad course mate d'insu yayi musu sallama ya huce. Su kuma suka nufi masaukin da uncle d'in Ahmad yake, sun same shi lafiya sun gaisa shima ya taya su murna matuk'a, ya yaba musu kuma musamman wajen jajircewar da suka nuna da bada himma akan karatun har suka futa da wannan sakamakon. A gurin shi sukayi sallar magrib da isha'i, sannan khaleefa ya musu sallama ya tafi don ya basu guri ko suna da sirrin da zasu tattauna tsakanin su. Tafiya yake gently bayan ya futo daga mota har ya k'arasa ginin da apartment d'insu yake ciki. Kamar a mafarki haka ya tsinci Saleema jingine da k'ofa kwayar idonta na kallon sararin samaniya, ga dukkan alamu ta jima tana jiran shi a gurin. Tsayawa yayi daga gefenta ya fuskanci gaban d'akin ya hard'e hannuwan shi a k'irji yana jiran yaji da wadda tazo, ganinta kawai da yayi yanzu saida gaban shi ya fad'i. Ita kanta Saleema gabanta faduwar yayi musamman da taga fuskarshi a d'aure kamar khaleefan data sani watanni da yawa baya, tana tsoron kada ya zam da gaske khaleefa ya yanke hukuncin barinta har abada kamar yadda ta buk'ata da farko, da batasan ya zatayi da rayuwarta ba. Khaleefa kuwa da d'aurarriyar fuskarshi yace, "ya akayi Saleema? Ko akwai wani abu da kika manta baki goranta mun ba kika zo first to first ki k'arasa gorantawa ki tafi?". Shiru tayi jikinta ya d'au b'ari, murmushi yayi yaci gaba da maganar shi, "Saleema a yadda na d'auke ki da irin matsayin dana baki a rayuwata sam ban d'auka zaki iya juya mun baya irin yadda kika yiba, na d'auka soyayyah tana nufin yarda da karb'ar masoyi a duk yadda yazo mai kyau ko akasin haka, tunda ba koman shi kike so ba shi d'in kad'ai kike kallo abokin rayuwa a tare dake, ke dai fatan ki ya kasance kin gyara komai kun rayu cikin so da k'auna....... Koda yake kin fahimtar dani abubuwa da yawa da tunani na ya kauce daga kansu, zanje nayi bincike akan asalina Saleema, sannan zan dawo don na baki mamaki". Zoben azurfar dake hannunshi irin nata ya zare ya dank'a mata a hannunta yana kallonta da idonunshi da suke cike da sonta da k'aunar ta yace, "Zan dawo miki da soyayyar ki kamar yadda na karb'a, amma fa ki sani bada jimawa ba zan dawo irin dawowar da zata banbance tsakanin Aya da tsakuwa, bada sunan khaleefa ba, da sunan Abdallah Suraj Abdallah Tofa, a lokacin nake son ki amsa sunan Mrs Abdallah, good bye". Khaleefa yana gama maganar shi ya kewayeta ya shige d'akin shi bai bata dama ko kad'an da zata iya furta wani abu ba. Haka Saleema taja k'afafun ta da suke rawa ta bar gurin tana kuka, ta kasa fassara kalaman khaleefa a yau, Inta fassara kalmomin shi na k'arshe yana nufin zai aure ta kenan? Toh amma idan har haka yake nufi me yasa zai ce ya dawo mata da soyayyar ta kamar yadda ya karb'a? Wannan kalmomin dunk'ulallu guda biyu sun d'aure mata kai kwarai har ta kasa zama data koma apartment d'inta, ganin zata cazawa kanta lissafi ba tare data fahimci komai ba, sai ta d'auko gyalenta tayi gurin Amna. Amnan ma bata nan amma ba nisa tayi ba tana kiran wayarta ta hallara a gurin, ko data bud'e k'ofa suka shiga kasa zama tayi sai safa da marwa kurum da take tana share ruwan hawaye, da kyar Amna ta shawo kanta ta bata labarin komai da khaleefa ya fad'a, ita kanta Amna kanta ya kulle, a iya y'ar hausar data iya bata ga gurbin da zata ajiye wad'an nan maganganu ba. Daga k'arshe sai suka ajiye khaleefa da maganganun shi masu d'aurin goro gefe suka fuskanci abinda yake gabansu Amna na dad'a kwantar mata da hankali. Khaleefa kanshi ganinta ba k'aramin Miki ya sake tado mishi ba, sai ya zauna kawai yana tunanin maganar da doctor raazi ya fad'a mishi a lokacin daya tashi ciwon nan, kasancewar doctor raazi mutum mai saurin fahimtar halin da mutum yake ciki, bugu d'aya ya fassara damuwar shi da matsalar soyayyah, hakan yasa ya bashi shawarwari a lokacin "a kowacce soyayyah akwai gwagwarmaya a cikinta, duk soyayyar da babu k'alubale bata cika soyayyah ba, ka karb'i rayuwa a yadda tazo maka Abdallah sai kaga ka zauna lafiya da zuciyarka, ka cire ta daga zuciyarka ba don ka rabu da ita ba ko ka daina sonta, a'a sai don kaji dad'in gano bakin zaren da zaka d'ago, ka fuskanci duk abinda ya tunkaro ka da iya k'arfin ka, sai kaga kaci galaba akan komai cikin sauk'i kuma ka samu masoyiyarka a k'arshe". Wani irin murmushi ne ya wanzu saman fuskarshi ya tsaya kurum yana hasaso fuskar Saleema a lokacin daya bata zobenta, ya tabbatar har gobe tana sonshi itama, wannan zaisa ba zata tab'a karb'ar soyayyar wani ba har zuwa lokacin da komai zai tafi mishi yadda yake so ya nemi aurenta su rayu tare. @@@@@@ Auntie ce zaune kan carpet kusa da iya, malam na zaune daga can gefe yana sauraron surayyah har ta gama bayanin ta kafun yace, "kwana biyu zaku yi kenan sai ku taho tare dashi?". Surayyah tace, "eh insha Allah". Malam yace, "toh madallah! Allah ya tsare ya kare ya kiyaye hanya, ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya". Cikin jin dad'i auntie ta amsa musu da "ameen". Sun sake tattauna muhimman batutuwa dasu ciki harda tsayar da ranar auren Ayman da Nur da zarar khaleefa ya dawo da kwanaki, so take auren kada ya d'au lokaci da tsayi, don a tafiyar da tayi kwanaki tuni ta fara had'a kayan lefe a b'oye, gida kuma bata da matsala zasu zauna tare da ita zuwa wani lokaci, (da yake a gidanta akwai babban part da yake rufe ba'a tab'a bud'e shi bama, sama da k'asan duk iri d'aya ne anyi mishi gini irin na zamani me kyau, a ra'ayinta, kowa zai zauna a part guda ne cikin su, don bata son suyi nesa da ita) malam baice mata komai ba sai iya ce take tambayar ta, "surayyah kuma kina ganin ba matsala sameera zata baki duka yaranta biyu ki aurawa yaranki?". Ko kad'an surayyah bata kawo komai a kanta a duk lokacin da akayi maganar sameera k'awar ta, tana ganin don basu san sameera bane shiyasa take kawo irin wannan tunanin a kanta. "da amincewarta muka shirya komai iya, insha Allah ba za'a samu wata matsala ba, in ma an samu toh daga khaleefa ne, don shine yake da baud'ad'd'en ra'ayi, amma Ina fata shi d'in ma ya amince don shaheeda bata da makusa tako Ina". Iya ta rausayar da kai tace, "toh Allah yasa!". Bata jima ba tayi musu sallama ta kira no Ayman da tunda suka zo bata ga inda ya wulla ba. Shi kuwa Ayman yana tsaye k'ofar gidan iya yana kallon gidansu raihana tamkar zai ganta ta futo, ji yake kamar ya kirata ta futo ya ganta ko yaji sauk'in bak'on abinda yake ji game da ita, zuciyar shi azalzalar shi kawai take da son ganinta, da ganin a wane hali take. Tunani ya fara tun daga lokacin da suka fara shiri da ita har zuwa yadda ta dinga girma suna tafiyar da alak'ar su cikin mutumci da mutunta juna, har kawo yau da ta zama babbar budurwa ake maganar aurenta, d'aya bayan d'aya haka memories d'innan suka dinga wulgawa ta cikin kwakwalwar kanshi. Sai yaji wani abu mai kama da mashi ya cake shi a k'ahon zuciya, dafe saitin gurin yayi had'i da lumshe idon shi ya bud'e lokaci guda yana karanta duk addu'ar da tazo bakin shi, a haka wayarshi tayi ring, ganin auntie ce sai baiyi picking ba ya nufi cikin gidan direct ya shiga da sallama. Duk suka amsa mishi suna kallon yadda yake tafiya da jiki a sanyaye, kusa da malam ya zauna. Dafa kanshi malam yayi yace, "ya zaka ware kanka a waje Ayman bayan ka jima rabon mu dakai? Ai ya kamata kazo muyi hirar yaushe gamo ko?". Murmushi kawai yayi baice komai ba sai Auntie ce tace, "ai ganin shi nake kwana biyu ma kamar baya jin dad'i". Iya zatayi magana ya tari numfashinta da sauri da fad'in......... _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty one2️⃣1️⃣ "Kawai rashin hutu ne iya, amma tunda na samu hutun wata d'ayan nan nasan zan dawo normal insha Allah". Iya tana k'ara nazarin shi tace, "Allah yasa". Daga nan basu kuma doguwar hira ba sukayi sallama dasu malam suka tafi, a motar shi suka zo yanzun a ita suka koma shiya jasu ma. Suna tafe auntie na mishi hirar da sam ba fahimta yake ba har suka k'arasa gida, shi ya futa ya bud'e get ya shigar da motar ciki ya daidaita parking a parking lot. Shiya fara futa direct ya haura stairs ya shige d'akin shi ya kwanta rigingine idonshi na kallon sama, ganin yanayin shi duka sai auntie ta bishi da text massage, "zamu bi jirgin k'arfe takwas gobe". Ko daya duba baice komai ba ya ajiye wayar, yana ajiyewa kuma kiran khaleefa na shigowa, a yanayin da yake baya son magana kowa, sai kawai yayi switch up d'in wayar duka. ★★★★★ K'arfe takwas da mintuna suna tsaye a filing tashi da saukar jirage na AMINU Kano international airport, babu b'ata lokaci suka hau kan screening akayi duk abinda ya kamata suka shiga cikin jirgi suka lula gajimare. *Brandenburg airport, Berlin* Khaleefa na hango da Ahmad a wannan filin tashi da saukar jirage tsaye da yammacin wannan raana, sunyi kyau cikin shigar shadda sky blue da mahaifin Ahmad ya d'inka musu cikin jerin kyaututtukan shi gare su, d'inkin manyan kayan baya rasa nasaba da ganin most of their pics da k'ananun kaya suke yi, kawai sai yayi hasashen maybe basu da manyan kaya ko guda d'aya, shine ya d'inka musu su kusan kala biyar biyar, irin d'inkin da matasa suke yayi a lokacin, ya kuma zauna musu dass a jikin su kamar anyi measuring da tip. A nutse Auntie da Ayman suke k'arasowa har suka zo inda suke, wani irin bak'in ciki ne ya lullub'e khaleefa from no where lokacin da yayi tozali da fuskar mahaifiyar shi, sai ya kasa k'arasawa ya tarye su har saida Ayman yazo ya rungume su shida Ahmad yana musu congrats. Da kyar ya iya k'irk'iro murmushi ya wanzar saman fuskarshi yana kallon Ayman cike da tausayi, "ta samar damu ta hanyar da bata dace ba, ta had'a mu yak'i da k'addarorin mu! Mutane har sun fara kyamatar mu a k'asar daba ruwan wani da wani ma Ina ga mun koma Nigeria kuma?". Khaleefa shi kad'ai yake wannan maganar a cikin zuciyarshi yana kallon fuskar Auntien. Ahmad ne ya fara k'arasawa gabanta ya russuna yana yi mata sannu da zuwa, shi kam khaleefa yana daga inda yake tsaye yana kallonta da wannan murmushin dai har lokacin. Cikin farin ciki surayyah tasa musu albarka idonta cike taff da hawaye tana kallon su, basu yi wata doguwar magana ba suka hau taxi suka kaisu Hotel d'in da suka yi musu booking d'aki. Har suka sauke su khaleefa baiyi wata doguwar magana da kowa ba, yanayin shi ba k'aramin fargaba da zullumi ya wurgawa Ayman ba, ya dad'e da fahimtar khaleefa ya sauya wata d'aya kafun kammala karatun shi, ya yiwa Auntie maganar tace yayi busy ne, yanzu kuma gasu sunzo gurin shi babu wani d'okin ganin su ko murna, sai Ahmad ne yake haba haba dasu. Ni kam tsayawa kawai nayi ina kallon tsananin kamar da take tsakanin wad'annan twins da har yanzu bata sauya ba, sai banbancin haske da khaleefa yafi Ayman kad'an da d'aurarriyar fuska, da wasu sauye sauyen na tsarin aiwatar da abu ga wanda ya samu kusanci na kusa dasu kad'ai zai iya gani. Room and parlour ne, suna shiga auntie ta shige bedroom d'in da k'aramar jakarta, shi kuma Ayman ya zauna a parlon, khaleefa basu zauna ba shida Ahmad suka tafi nemo musu abinci. Kafun su dawo sun yi uzurirrikan su sun sauke faralin dake kansu tuni. Auntie bata ci wani abincin kirki ba Ayman d'in ma haka, ita kanta ta fara ankara da yadda khaleefa ya koma gefe kamar wani bak'on mutum sai Ahmad ne yake musu kamar shine jinin su. Sun yi mata bayanin abubuwa da yawa, Ahmad hadda labarin no yabo da aka bawa khaleefa a jiya yake bata. Ta sake jin dad'i ta musu addu'o'i sosai. Basu bar gurinta ba har dare, Ahmad yaso su tafi da Ayman ya kwana apartment d'in wani a cikin su sai dai yak'i sam, dole suka hak'ura suka barshi zai kwana tare da Auntie. Toh Tafiyarsu gida Nigeria ta banbanta data Ahmad, saboda shi ba gida ya nufa ba kai tsaye k'asar turkey yayi inda zaiga wata y'ar wan mahaifin shi da yake zaune din din din a can. Sun gama shirya komai dama tun kafun ya gama karatun shi, har sun daidaita da yarinyar a waya ganin juna kawai zai je suyi ayi maganar aure. A daren ranar kusan raba dare sukayi yana taya khaleefa had'a abubuwan shi muhimmai suna kuma hirar su akan k'udururrukan su, shi Ahmad yaso su fara gabatarwa da Auntie maganar aikin tun kafun subar k'asar, sai dai khaleefa yace a bari abi komai sannu a hankali, In sun nutsu sai su had'u su tunkareta da maganar su biyu, maganar binciken su akan familyn mahaifin khaleefa kuwa tuni sun gama shirya yadda komai zai kasance da zarar khaleefa ya koma gida. Koda zasu rabu ba k'aramin sanyi jikin su yayi ba, ji suke kamar in sun koma Nigeria ba zasu ci gaba da kasancewa tare kamar yadda suke a nan ba. Dama masu iya magana suka ce sabo........ @@@@@@@ A yau da misalin k'arfe shida da rabi jirgin su khaleefa ya sauka a Nigeria, bayan shafe adadin shekaru tara cip yana karatu a Germany bai tab'a zuwa hutu k'asar shiba ko sau d'aya tunda ya tafi. Koda khaleefa ya shak'i iskar k'asar shi saida yaja gwauron numfashi yayi hamdala ga Allah subhanahu wata'ala daya dawo dashi lafiya kamar yadda ya tafi, A yau ga khaleefa ya dawo da tarin ilmummuka da nasara akan abinda yaci burin karanta don ya taimakawa al'ummar k'asar shi dama na wasu k'asar baki d'aya. Auntie suna sauka a jirgi ta ware gefe ta kira sameera a waya saboda da ita ne suka shirya agender zata turo shaheeda ta d'auke su a motar ta, khaleefa da Ayman na tsaye gefe guda ba wanda yake iya cewa da d'an uwanshi kanzil k'ark'ari dai in sun had'a idanu su yiwa juna murmushi. Sun d'anyi jira na a k'alla adadin wasu mintuna kafun shaheeda ta k'araso, ko kafun tazo khaleefa har ya k'osa sai faman duba agogon hannun shi yake. Auntie ce da take rataye da jakarta ta kira su suka taho Ayman rik'e da babbar jakar kayan khaleefa shi kuma khaleefa rik'e da wata y'ar k'arama suka zo gaban motar suka tsaya. A idanun khaleefa wata kyakkyawar budurwa ce fara sol ta bayyana, kallo d'aya yayi mata ya fad'a kogin tunanin inda ya santa? Ganin bai tuna ba saiya watsar da tunanin a gefe, ita kuwa rungume Auntien tayi tana mata sannu da zuwa, auntie cikin farin ciki tace, "sannun ki da k'ok'ari kema". Ayman ma k'arasawa yayi yace, "big Auntie sannun ki fa". Fuskarta da fara'a har lokacin tace, "Kai za'a yiwa sannu Yaya...." Sai kuma tayi shiru ta saci kallon khaleefa daya d'auke kai tamkar ma baisan da wanzuwarta a gurin ba, a ranta tace wannan sarkin jin kan shine khaleefan kenan, sai kuma ta tab'e baki ta bud'ewa auntie front seat zata karb'i Jakarta ta zura mata, "a'a barshi shaheeda zan zauna a baya nida Ayman". Tana fad'in haka ta shiga gidan baya Ayman ma haka, ko kanzil khaleefa baice musu ba ya shige mazaunin driver, kallon shi shaheeda ta kuma yi a karo na biyu, ganin Sam ba fuska a tare dashi har yanzu sai ta kalli Auntie, "feel free dear ya hutar dake ma". Murmushi kawai tayi ta shiga gefen shi ta zauna kurum. Slowly yake tafiya da motar suna nuna mishi hanya har suka Isa anguwar malam kuma tsohuwar anguwarsu ta da. Nan ma khaleefa bin komai yake da kallo tamkar bak'o a garin. Yana tsaye a k'ofar gidan ya zuba mishi ido kamar wanda yake karantar wani abu, ganin haka sai Ayman ya k'arasa gaban shi ya dafa mishi kafad'a, "welcome back home bro". Murmushi ya tattaro da kyar ya yiwa d'an uwan shi sannan ya tsallaka yabi bayan su auntie da har sun shige gidan. Iya tana zaune tsakar gida ta shimfud'a k'atuwar tabarma ta shirya cikin atamfarta mai kyau kamar wadda zata futa wani kwarya kwaryan biki. Tana ganin su ta k'ara fad'ad'a fara'ar ta ta fara yi musu lale marhabin. Kusan a tare khaleefa da Ayman suka k'arasa suka durk'usa a gabanta, dafa kansu tayi d'aya bayan d'aya tana tuno da lokacin suna yara. Shaheeda kam gefe guda ta zauna ta ciro wayarta a jaka tana daddannawa. Malam ma da yake sitting room jin motsin su ya futo dashi, yazo suka rungume juna cikin farin ciki da tsantsar murnar ganin su cikin k'oshin lafiya, musamman khaleefa da suka d'au shekaruuu basu ganshi ba, sai dai gashi nan sun ganshi kamar Ayman. Cikin girmamawa su duka suka gaisa da malam, ya amsa su da fuskar dake nuni da farin cikin ganin su. Abinci iya ta soma d'ebowa tana ajiye musu a gaban su kala kala da lemukan da tayi musu duk na gargajiya. Abun har dariya yaba khaleefa a ranshi yake tuna iya nanan da kirkinta in mutum yazo saita k'arar da abincin gidanta kaf a kanshi. Ayman ne ya magantu, "iya wa kike tarya da wannan tarin abinciccikan, mu ko khaleefa?". Harararshi iya tayi tace, "a'ah! Kaji ka kai kuma da wani batu, kuda kullum muna tare duka tafiyar taku ta jiya ce fa, toh magaji na shiryawa duk wannan sai in yaso ya san muku". Dariya auntie da malam sukayi suna kallon khaleefa daya ke bin kwanukan abincin da kallo kamar me nazarin wani abu, cikin sigar zolaya Ayman ya sake cewa, "toh ai sai kiyi mishi bayanin duk abinciccikan don ya manta su fa da alama". "Da gaske magaji ka manta cimar ka ta gado sai irin abincin masu jajayen kunnuwa?". Fuska a had'e khaleefa yake kallonta, duk gurin babu wanda baiyi dariya ba har shaheeda da take zaune tana kallon su a gefe saida ta murmusa. "Kinsan fa duk duniya khaleefa ya tsani a kira shi da sunan nan". Ayman ya fad'a yana sake dariya k'asa k'asa. Iya ce tace, "au toh meye khaleefa meye magajin? Duk abu d'aya ake nufi dai in baka sani bama yau in fad'a maka ga uwar ka nan tana ji ai ta fad'a maka da bakinta kaji". K'ara tamke fuska yayi ya kalli malam da yake kallonsu kurum yace, "me ran k'arfe Allah zan bar gidan nan". Malam yace, "a'a kunga ku kyale shi don Allah, yaci abincin shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali". Duk guntse dariyar su sukayi, khaleefa kam hankalin shi kacokan ya mik'awa iya da take mishi bayanin sunan kowanne abinci na gurin dalla dalla, a ciki biyu kawai zai iya ci itama iya donta manta waye khaleefa, Sam bai iya cin d'an wake ba tun yana yaro, sai yasa ta zuba mishi dambun shinkafa daya ji zogale da gyad'a. Ai koda ya koma gefe sai kawai ya fara mik'a loma baji bare gani, suma sun zuba wanda suke ganin zasu iya ci a gurin, auntie ta tambayi shaheeda, "wanne zaki ci cikin girkin iya, gasu nan dai sai ki zab'a". Murmushi tayi tace, "Ni ko dambun ma kika bani". Aikuwa auntie ta zubo mata dambun fal plate ta had'a mata da zob'o drinks don wannan kam tasan favorite d'inta ne ko bata tambaya ba. Shikam oga khaleefa ginger and lemon yasha, babu laifi yaci abincin da yawa kuma yaji dad'in shi, rabon daya ci wani abinci mai yawan haka har ya manta ma shi. Auntie da iya nata hirar su tana basu labarin irin nasarar da khaleefa da abokin shi Ahmad suka samu, malam sun yaba shida iya sunata addu'o'i. Khaleefa ne ya soma mik'ewa ya wanke hannun shi ya d'aura alwala ganin ana gab da kiran sallar magrib, malam ma tashi yayi yaje yayi tashi alawalar sannan ya futa masallaci, khaleefa da yake tsaye daga gefe bin bayan shi yayi, sai dai bai k'arasa masjid d'in ba ya tsaya jiran a kira sallah a nan k'ofar gidan, ko kad'an baiyi mamakin ganin yadda mutane suke tayi mishi magana ba, don yasan zuwa yanzu sun manta dashi sai dai ko in suna yi mishi kallon Ayman ne. A haka Ayman d'in ma ya futo ya same shi bayan an kira sallah har an tayar. Suka bi jam'i suka yi sallah, ko da aka sallame su kam basu futa ba suka ci gaba da zama tare da malam da masu zuwa yana yi musu k'ari har lokacin da mukhtarin isha'i ya shiga. Sai da sukayi sallar isha'i cikin jam'i sannan suka jero su uku suka nufo gidan. Malam ya shige sitting room su kuma suka shiga parlon iya inda duk suke, suma da alamu idar da sallar su kenan. Basu yi wata doguwar hira ba yanzun kam sukayi sallama da iya, malam ma suka je sukayi sallama dashi sannan suka tafi khaleefa da alk'awarin sai ya dawo zuwa na musamman gurin malam. Yanzun kam auntie ce take driving, Ayman a gefenta, shi kuma da shaheeda a baya, ya rasa dalilin da yasa ake ta cusa mishi zama guri d'aya da yarinyar nan shi kam. Babu jimawa suka k'araso gidan su, Ayman ne yayi amfani da key na gurin shi ya bud'e get, auntie ta cusa hancin motar ta ciki, bayan ta daidaita parking duk futowa sukayi, khaleefa da yake bak'o ya tsaya yana kallon gidan, kamar ba shine gidan da suke zuwa ganin aiki shida Auntie kafun ya tafi Germany ba, sannan kamar ba shine gidan da sukayi video call da Ayman ba ranar da suka tare a ciki. Auntie direct taja hannun shaheeda suka yi part d'in su, Ayman kuma ya tsaya a parlon k'asa yana nunawa khaleefa gidan ciki da waje, main parlour mai d'auke da d'akuna hud'u da sitting room a k'asa, sai k'ofar stairs guda biyu d'aya a bud'e inda zaka bi zuwa saman dasu Auntie suka bi, sai d'ayar da take rufe ruff da key. A jikin spare key Ayman ya duba ya bud'e k'ofar, nan stairs na hawa sama ya bayyana, ta wata k'ofar daban kuma parlour, khaleefa ya haska torch ta wayar shi saboda duhu ko'ina, shima parlour ne wadatacce hadda dinning area, sai bedrooms guda uku sai sitting room a ciki, da kitchen wadatacce mai k'ofa biyu, d'aya tabi ta cikin parlon, d'aya kuma ta futa ta bayan vantilation d'in gidan, gurin akwai k'aramin corridor. Khaleefa tunda suka shiga yake kallon part d'in, har dai ya kasa shiru ya tambayi Ayman da yake ta aikin mishi k'arin bayani "yanzu wannan part d'in sama da k'asa zaman me Auntie take dashi ba kowa? Ai gidan nan ya muku girma indai ku kad'ai zaku rayu cikin shi". Murmushi Ayman yayi ya dafa kafad'ar shi yace, "wannan b'angaren da zamu zauna ne ni dakai bayan munyi aure, amma fa batayi mana Dole ba duk wanda yake da kud'in yin ginin shi daban zai iya gina nashi ya zauna koya kama haya ita vata da damuwa". Wata irin fad'uwa gaban khaleefa yayi dum! dum! Sai yaji duk k'afafun shi sun sage mishi kamar ba zasu iya d'aukar gangar jikin shi ba, ba shiri ya samu gefen wani d'an tudu ya zauna tare da dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu, a yau gaba d'aya sai yanzu ya samu sa'idar tuno ta, tuni ranshi ya koma bak'ik'irin ya manta da tunanin komai sai kalmar da take mishi yawo aka, """koba kasan kowanne mutum da uba yake ado ba..... A zuciyar shi yaci gaba da tambayar kanshi, toh mu kuma da muke shegu dawa zamuyi ado kenan?""". Ayman ganin ya shiga damuwa sai ya zauna gefen shi ko la'akari da k'urar gurin baiyi ba yace, "kayi hak'uri khaleefa dama ita Auntie bata tsawwala ba tace mutum zai iya kama haya a duk inda yaga yayi mishi". D'ago da kanshi yayi ya girgiza mishi kai yace, "noop ko kad'an ni bani da dogon buri a rayuwa tun da can kai ka sani bare yanzun". Ayman cikin aminta da zancen shi hundred percent yace, "na sani kam, toh amma tunda ka dawo na fahimci wasu tarin sauye sauye a tare dakai, don Allah d'an uwana ka fad'a mun me yake damun ka? Kasan fa a duniya bamu da kamar juna......". Yanzun ma sake girgiza mishi kai yayi ya mik'e tsaye, "Babu wani sauyi a tare dani Ina nan yadda ka sanni rashin samun cikakken nutsuwa ne maybe yasa kaga hakan yanzu ma". Sai ya kalli b'angaren saman yace, "saman ma kamar k'asa yake kenan?". Ayman babu yabo babu fallasa don yasan ya b'oye mishi ne, kuma dama a yadda yasan khaleefa indai har ba sauya hali yayi ba, sai abu ya kusan kashe shi yake bud'e baki ya fad'a ko damuwa ce kuwa, sai yace, "eh iri d'aya ne muje ka gani mana". "A'a ka barshi kawai, ya kamata ace by now munyi wanka mun huta gajiyar tafiya kuma". Cikin gamsuwa duk suka futo daga b'angaren, saida Ayman ya rufe sannan Suka bi hanyar da Auntie tayi. Parlour ne suka tarar zagaye da komai blue, sai dinning me d'auke da kujeru k'alilan. Tsayawa khaleefa yayi turus yana jira yaji inda zasuyi, shima Ayman baiyi magana ba ya nufi nasu part d'in, shima matsakaicin parlour ne amma komai orange kalar da khaleefa yafi so, auntie tasa akayi gyara na musamman gab da dawowar nan tashi, bedroom biyu ne a ciki kowanne da bathroom. Zama yayi kan center table da yake tsakiya ya tambayi Ayman, wanne ne room d'ina a ciki? Da mamaki Ayman ya dube shi, ganin kamar bai fahimci abinda yake nufi ba saiya sake maimaita tambayar shi, dai dai lokacin ne kuma auntie ta shigo rik'e da tray na shayi ita da shaheeda, a dawowarta yanzu harta had'a shayin da zasu sha. Mik'ewa khaleefa yayi ta ajiye trayn akan table d'in daya tashi, shi kuma Ayman cikin mamaki da jin abinda bai tab'a zato daga d'an uwan shi ba yazo gaban shi ya dafa kafad'ar shi, "na d'auka komai muna yin shi tare ne dama nida kai tun kafun tafiyarka karatu...., ka tuna yadda muke cin komai a plate guda mu kwana a muhalli d'aya? Mu saka Kaya iri d'aya....". Wani murmushin gefen baki khaleefa yayi ya girgiza mishi kae, ya cire hannun shi daga gefen kafad'ar shi yace, "ai wannan abu ne wanda ya dad'e da zama tarihi, tun daga ranar dana taka k'afata Germany na kwana biyu ba tare dana ganka ba, ba tare da munci abinci tare ko kwana tare ba na dad'a tabbatar da zan iya rayuwa ni kad'ai ko banji daga kowa ba....... Soo ka nuna mun wanne ne d'akin ka a ciki". Yadda Ayman yayi surrender haka auntie da shaheeda dake tsaye bayanta. Babu musu ya nuna mishi nashi d'akin, sai ya nufi na kusa da wanda Ayman ya nuna a matsayin nashi zai murd'a handle ya shige, maganar Ayman ta dakatar dashi, "khaleefa idan na fahimce ka a dai dai, maganar ka tana nufin zaka iya rayuwarka kai kad'ai koda bana raye a duniyar nan ba tare da kaji kewata ko wani abu na daban ba.....". Bai k'arasa zancen ba Auntie ta d'auka, "ba Kai kad'ai ba Ayman hadda ni, yana nufin zai iya rayuwar shi shi kad'ai ko babu mua tare dashi.......". _Comment and share_ 24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty two2️⃣2️⃣ Bai juyo ba ya bud'e k'ofar kawai ya shige, duk suka bishi da kallo har shaheeda da take tsaye bayan Auntie, yau ta tabbatar da abinda auntien take yawan fad'a akan khaleefan a duk lokacin da mammie tayi maganar halayenta, auntie takan ce khaleefa baud'ad'd'en mutum ne mai baud'ad'd'en ra'ayi da hali sab'anin na mutane. Bayan d'aukar lokaci mai tsayi shiru, auntie ce ta ce da Ayman daya shiga damuwa, "ka d'auki duk wani abu da kasan nashi ne ka kai mishi ciki, kada ka sake ce dashi komai". Cikin ladab Ayman yace, "insha Allahu Auntie". Tace, "gud ga tea nan akwai snacks da nayi tun kafun mu tafi shaheeda zata kawo muku anjima kad'an,and please in shi bazai ciba kai nasan kana so kaci abinka". Girgiza mata kai yayi cikin sanyi "a'a Auntie ki barshi kawai naci abubuwa da yawan gidan iya am okay". Sai da tayi nazarin shi kad'an kafun su futa daga parlon ita da shaheeda, tana ganin Ayman ranshi ne ya b'aci kurum, kuma da zarar an d'au wani lokaci zai huce shi da kanshi don baya iya dogon fushi da kowa haka zuciyarshi take. Shi kuwa khaleefa matsalar shi.......... Sai kawai taja ajiyar zuciya. Khaleefa kuwa yana shiga d'akin bin komai yayi da kallo, babu komai a ciki sai uban girman d'aki fetal, zama yayi a k'asan gurin ya had'a kanshi da gwiwa yana ambaton sunan Allah, ya kasa had'iye damuwarshi shi, ji yake kamar yayi ta ihu a duk lokacin daya kalli fuskar auntie ya tuna ta samar dasu bata hanya me kyau ba, hanyar da duk wani musulmi me Imani yake kyamata wato *Zina*, wannan abu yasa yake misbehaving duk lokacin da zasu kasance tare, wannan kalma ta *shege* tana dukan ranshi tana cin zuciyarshi kwarai, musamman in ya tuna akan haka zai rasa Saleema, macen daya fiso bayan auntien shi a duk duniya, wayyoh Allah sai yaji kamar zaiyi hauka a garin nan don tashin hankali, rashin uba ba k'aramin gararanba rayuwar mutum take fad'awa ba, bana rashin abinci da abin sha ko sauran buk'atun rayuwa ba, a'a rashin baya jigo majingina kuma garkuwa a tare dasu, tabbas uba gata ne ga kowanne yaro musamman a wannan zamanin da muke ciki. D'ago kanshi yayi jin an bud'e k'ofar d'akin shi, Ayman ne ya tattaro duk wani abun da yasan zai buk'ata ya kawo mishi, suka dubi juna lokaci d'aya kowa ya d'auke kanshi gefe, haka Ayman yayi ta shiga yana kawo mishi abun amfanin shi na yau da kullum, ya kai na bathroom ya ajiye mishi, ya dawo ya shimfid'a mishi carpet ya ajiye mishi praying mat a kai. "Thanks" khaleefa ya fad'a mishi a lokacin da zai fuce daga d'akin. Uhm! Kawai shima Ayman ya fad'a yayi hucewar shi. Ko bayan ya futo wanka shiryawa yayi cikin kayan bacci farare k'al ya nemu guri gefe d'aya ya zauna ya kunna wayarshi, so yake yaji daga Ahmad ta hanyar watsapp sai dai koda ya duba shiru, sai no Saleema da aka ajiye mishi sak'o, yana bud'ewa yaga voice note uku sai rubutu a k'asa inda tace, "I'm really Sorry it's not my fault, try to understand me khaleefa.....". Tsaki yaja me tsayi a fili har zeyi playing voice d'in nata sai kuma ya fasa gudun kada ya sake jin wani abun b'acin ran ko sare gwiwa da zai sake jefa shi cikin tashin hankali da damuwa. Tuni ya sanya su a delete ya sauke layin ya kakkarya shi. A fili yayi magana kamar wani yana sauraron shi, "daga yanzu har zuwa lokacin da zaki zamo tawa baza ki sake ji daga gareni ba, nayi alk'awari saina shayar dake ruwan mamaki Saleema. _(nikam nace ayyah khaleefa rashin sani yafi dare duhu)_ Asalin abinda ya faru a Germany. 👇 Saleema ta kasa jurar rashin khaleefa, ta shiga tashin hankali data tabbatar da yabar Germany ba tare da yaji wani abu daga gare ta ko ya neme taba, k'awarta Amna ta tabbatar mata da cewa khaleefa yana nufin ya barta ne har abada, ai dama ta shaide shi akan zuciya in yabar abu ya barshi kenan fintinkau baya sake waiwayen shi Hakan yasa a washe garin ranar ta kasa nutsuwa har saida tayi mishi voice na kwantar da hankali da K'arfafa gwiwa, ta fad'a mishi mahaifinta zai iya saukowa saboda albarkacin soyayyar da yake mata, na biyu yayi k'ok'ari ya samu ko mutum d'aya ne daga dangin mahaifin shi suzo ayi maganar aurenta, daga k'arshe ta nemi yafiyarshi ta fad'a mishi kuskurenta akan karyewa da zuciyarta tayi da farko, yanzu kuma data fahimci ba zata iya rayuwa ba tare dashi ba saita bawa kanta kwarin gwiwa shima take k'ok'arin bashi. Shi kuwa khaleefa a rashin sani ya goge duka muhimman sak'onnin. (Nikam nace rashin fahimta, tuntub'e dad'in gushi......) ★★★★ Kamar yadda yake bisa al'adar khaleefa sallar subh bata tab'a huce shi haka yauma ya tashi da wuri, ya fad'a bathroom ya d'auro alwala ya sauya kayan jikinshi zuwa jallabiyyah brown colour. Kusan tare suka futo da Ayman lokacin da aka tada sallah. Take Ayman ya shanye komai ya k'irk'iro murmushi akan fuskarshi ya mik'a mishi hannu, shima hannun ya bashi sukayi musabiha sannan suka d'auki hanyar masjid a tare. Ko bayan da aka idar da sallah ma tare suka dawo khaleefa yana sake k'arewa gidan kallo, suna tafe kan stairs ya kasa hak'uri yace, "yanzu wannan gidan auntie ita da waye zasu zauna a ciki haka?". Cikin jin dad'i Ayman ya kalle shi don bai d'auka wannan sabon khaleefan zai sake yi mishi wata magana ba, sai yace, "tun jiya kake maganar nan, toh ai babu laifi muna aure zakaga mun cika mata gidan taffff!". Murmushi khaleefa yayi a zuciyar shi yana tausayin k'anin nashi, da baisan abinda shi ya sani game dasu ba, ko waye zai bashi aure babu uba da dangin shi? A nan parlour suka zauna su duka, Ayman ya danna switch haske ya gauraye ko'ina, khaleefa ya fara lazimin shi shi kuma ya kwanta ba jimawa ya koma baccin shi. Sai da gari yayi haske sosai sannan khaleefa ya shiga d'akin daya zab'ar wa kanshi, ya sake gyara ko'ina ya had'a ruwa a heater ya shiga wanka. Bayan ya futo ya shirya cikin d'aya daga shaddojin da mahaifin Ahmad ya basu, ya tsaya jikin windown d'akin yana kallon yadda wasu yara matasa maza guda biyu ke faman share harabar gidan da k'alk'ale shi. Wasu tunanika ya fad'a, lokaci guda ya fara tuno komai daki daki tun daga tasowar su a gidan iya. Yana nan tsaye goye da hannun shi a baya yaji ana knocking k'ofar shi, daga yadda yake ya bada izinin shigowa, wata yarinya ta danno kanta ciki zata shigo hannunta rik'e da mopper da long broom. "wait!" Ya fad'a da fuska ba annuri, saita dakata tana kallon shi, "me zakiyi a nan?". Cikin firgici da ganin yadda ya tamke fuska shaidar baya son wargi tace, "amm ehh dama nice nake gyara wannan b'angaren". Khaleefa cikin sake d'aure fuska yace, "toh ki futa ni bana buk'ata". Saita juya kurum ta futa tana tunanin ko me ya samu Ayman yau? Taga kullum ita take gyaran b'angaren bai tab'a cewa don me ba sai yau, sai tayi fucewarta dama ta gama gyara parlon ne zata gyara d'akin daba kowa sannan taje ta gyara mishi nashi, tunda yace baya so kuma falillahil hamdu ya sauk'ak'a mata aikinta ma. Ayman kuwa bayan ya gama baccin shi da gari yayi haske sosai tashi yayi ya shige ciki, yayi wanka ya shirya cikin yadi golden colour, so yake ya gama da wuri Cox akwai d'aurin auren wani abokin aikin su da yake son halarta wanda za'ayi k'arfe goma na safe. Lokacin daya futo har zai shiga d'akin khaleefa sai kuma yayi tunanin maybe ya koma bacci a lokacin, ga abun mamaki yarinyar nan ta gyara parlon su tayi gaba ba tare data jira in ya futo ta shiga ta gyara mishi nashi d'akin ba. Auntie kuwa yau da kanta ta shiga kitchen don ta had'a irin breakfast d'in da tasan khaleefa yafi so don yaji dad'i a ranshi in ya futo. _(Allah sarki uwa)_ koda haleema tazo ta tarar da ita kane kane tana aiki a kitchen dariya tayi tace, "kice yau kin tuna da girkin mutanen k'asar Sudan". Tana dariyar itama tace, "sannun ki da zuwa mama haleema kin cika alk'awari yau gaki kinzo da wuri". "Ai dole uwar d'akina, a jiya fa muka dawo cikin dare". Surayyah tace, "Kai baki ji tsoro ba". Haleema tace, "toh ya zamu yi abune daya kama mu dolee, da zamu taho kuwa baki ga uban kukan data dinga yi ba ni dai na baro mata k'aramar k'anwarta nayi tahowa ta". Surayyah cike da tausayawa tace, "ayyah Allah sarki mufeeda bata ji ance aure yak'in mata ba". Haleema tace, "aikuwa kam, bamu gaisa bama Ina kwana fatan kun dawo lafiya". Surayyah tayi murmushi tace, "lafiya Lou alhamdulillah!". Haleema tace, "Masha Allah ya y'an biyu fatan an kammala karatu cikin nasara". Surayyah tace, "shima yana lafiyar shi Lou, kinsan tare muka taho yana ciki yana bacci". "Allah sarki bari na k'arasa aikin kije ki huta haka". Haleema ta fad'a tana Shirin matsawa kusa, dakatar da ita surayyah tayi tace, "ki barshi mama haleema yau da kaina nake son yin girkin nan saboda dawowar khaleefa kinsan shi ba'a iya mishi". Haleema tace, "haka dai kuke yawan fad'a". Surayyah tace, "humm! Baki ji akace Kaya da Yani sai uwar d'iya ba..... Kema don kin manta shine.". Dariya haleema ta sake yi tace, "toh ni da nake cewa ma zan taimaka miki nasan yadda ake had'a girkin ne?". Auntie tace, "zaki iya mana ai ba wahala". "Anya kuwa wannan girki na y'an gayu ai sai ku". Surayyah tayi d'an dariya again. Sunci gaba da hirar su tana girkinta har zuwa lokacin da Ayman ya futo, bayan ya dudduba ko'ina bai ganta ba, k'amshin abinci da yaji shine yasa ya taho kitchen don ya tambayi haleema ko ta futa ne. Sai kuma ya sameta a kitchen d'in. Su kuwa duk kallonshi sukayi, ya russuna suka gaisa da mama haleema, tana ta zolayar shi ai dole yau yayi late tunda yayan shi ya dawo kuma, shi dai yanata mata murmushi baice komai ba. Itama Auntien gaishe ta yayi, sannan ya d'ora da complain d'inshi, "auntie ke kika hana yarinyar nan ta share mun d'akina yau?". Saita tsaya tana nazarin shi, "bata gayara muku part d'in bane?". Ayman yace, "iya parlor ba". Ta corridor kitchen ta lek'a ta kwalawa yarinyar kira sannan ta dawo, ba jimawa kuwa sai gata tazo ta russuna kan gwiwowinta a gaban auntien, "me yasa yau baki gyara wa Ayman d'akin shiba" kallon shi tayi sai kuma ta maida kallonta ga auntien, "kiyi hak'uri hajiya shi yace mun na barshi baya buk'ata" da sauri ya kalleta yace, "Ni kuma? Yaushe kenan" ita kanta yarinyar saida ta kalle shi sai kuma ta shiga rud'ani, d'azu aiba wannan kayan ne a jikin shiba, auntie kuwa a take ta d'ago bakin zaren tace, "a Ina ya ganki kukayi haka dashi?". Nan ta fad'awa auntie duk yadda sukayi da khaleefa, daga ita har Ayman shiru sukayi auntie ta girgiza kai kafun ta fad'a mata, "twin d'inshi ne baya son hayaniya sam, inda kika same shi nan ne d'akin shi, Soo take note saiki kiyaye baya son hayaniya ko a shiga shirgin shi, yanzun in kin shiga ainahin bedroom d'in Ayman zaki gyara ba ruwan ki dashi" Da "toh" ta amsawa auntie ta mik'e ta fuce. Shima Ayman futa yayi ya koma parlon auntien ya zauna, alk'a'idar tunanin shi dai ya koma, yanzu dai yasan bai huce kwanaki k'alilan a d'aura auren raihanatu ba, da zai iya ya kamata ya biya ta gidan su in ya dawo d'aurin auren nan yau su gaisa, sai dai sam baya jin hakan, ba zai iya jurar ganinta tana shirin zama matar wani ba, k'ara mishi damuwa kawai zatayi a banza, gashi itama dama kwana biyu ta futa harkar shi, sai text massage d'inta daya gani cikin satin nan tana tambayar fatan yana lafiya, ko refly mashi baiyi ba, wata zuciyar ce tace dashi, to kai da kake abokinta meye ma naka na shiga damuwa da tashin hankali akan aurenta,yadda raihana tasha wahalar nan da matsalolin data dinga fuskanta a maganar aurenta ai kamata yayi ma kafi kowa murna da taya ta farin ciki matsayin babban abokinta na kusa, sai gashi kana nema ka wulla kanka cikin jerin y'an bak'in ciki da hassada da Sam basa son ci gabanta. sai daya kai k'arshen tunanin shi sannan ya sauke doguwar ajiyar zuciya, Shi tunda yake bai tab'a jin yana bak'in ciki da kishin alaqarta da wani kamar wannan lokacin ba, ya kasa fahimtar abinda hakan ke nufi. Yana nan zaune haleema ta fara jera kwanukan abincin da suka dafa saman dinning, motsinta ne ya farkar dashi daga mafarkin ido zaune daya fara tafiya, yana mik'ewa wayar shi tana fara ring, sai ya koma ya zauna, ganin Nur ce sai yayi rejecting kiran shi ya kirata, gaisawa suka k'ara yi ta tambayi lafiyar shi da Allah ya k'ara huce gajiya. Sunci gaba da wayarsu irinta masoya har auntie tazo ta shige shi, d'akin da shaheeda take ta shiga ba jimawa kuma ta futo shaheeda na bin bayanta. Sallama Ayman yayi da Nur a waya ya mik'e tsaye da murmushi saman fuskarshi suka gaisa da shaheeda. Sanye take da doguwar rigar material ta yane kanta da k'aramin gyale kalar kayan, d'aya daga sababbin d'inke d'inken auntie ne ta bata tunda bada shirin kwana tazo musu gidan ba. "Wai d'an uwan ka bai tashi ba Ayman" ta tambaye shi da harshen Arab. Ayman yayi y'ar mik'a yace, "shi zan je na duba yanzun". Yana gama maganar shi ya nufi hanyar part d'insu, futowar shi kenan Ayman ya shigo, "na d'auka har yanzu bacci kake". Yamutsa fuska yayi kad'an yace, "ai tunda nayi sallah ni ban koma bacci ba". Ayman yace, "ai ni bansan sai zuwa yaushe zaka fahimci martabar bacci ba kai kam koda yake Auntie ce tace na duba ka ta gama shirya table". "okay dama zanje bamu gaisa da ita ba". Tare suka jera har babban parlon sama, ita da shaheeda ne zaune kan dinning ko hira suke shaheeda dai tana ta faman dariya tana rufe baki. A gaban auntie ya d'an russuna yace, "barka da safiya auntie". Tana kallon shi tace, "barkanka dai khaleefa fatan ka tashi lafiya" Ciki ciki yace, "Ina lafiya alhamdulillah" jan kujerar kusa da Ayman yayi ya zauna, shaheeda ce ta gaishe shi, sama sama ya amsa ba tare daya kalli inda take ba. Auntie ce tayi saving d'insu da abinda tasan kowannen su yafi ci wajen karin Kumallo, as she expect khaleefa yaci abincin da yawa kafun ya tashi ya koma inda ya futo. Ayman kuwa koda ya gama zama yayi kan d'aya daga kujerun parlon yana ya dubo no haedar saboda guy d'in d'an anguwar sune. Sun tattauna inda zasu had'u su tafi tare kafun ya mik'e, Sallama ya yiwa Auntie ya koma ya d'auki mukullin motar shi, khaleefa na zaune a d'akin shi ya tankwashe k'afa yana duba abinda yake bincikawa ta cikin system d'inshi lokacin da Ayman ya shigo. Daga bakin k'ofa yayi mishi sallama bayan ya fad'a mishi zai tafi d'aurin aure ne ba jimawa ya dawo, da tak'aitacciyar addu'a khaleefa ya raka shi yaci gaba da abinda yake yi. Shi kuma fucewa yayi Yana k'ara mamakin d'an uwan nashi, a kowanne motsi na khaleefa sauyi yake gani, sai ya dinga ganin kamar ba asalin khaleefa nashi da ya tafi Germany shekaru tara zuwa goma baya ba. @@@@@@@@ Raihana tana zaune a parlon gidan su, ta zubawa television ido kamar tana fahimtar abinda akeyi, nan kuwa tayi nisa ne cikin duniyar tunani, a cikin kwanakin har rama tayi saboda shiga damuwa da yawan tunani, ga Imrana a asibiti har yanzu yana karb'ar allurai, ga Ayman ya futa daga harkar ta gaba d'aya, ko y'ar wayar ma da suke gaisawa bayan kwana biyu yanzu ta gagara, gaba d'aya ta rasa abinda yake yi mata dad'i cikin kwanakin nan, kenan Ayman yana nufin daga haka zasu rabu? Kamar wasu maƙiya ko alagar nesa, ita Kam bata so haka ba, ta sone suyi rabuwa ta mutumci dashi ba irin wannan ba. Sai taja doguwar ajiyar zuciya ta sauke idonta kan ummie da take shigowa parlon rataye da jakarta, hannunta rik'e da jidderh. Saita mik'e tsaye tana fad'in, "sannu da zuwa ummie ya kuka baro su?". Ummie ta fad'a kan sofa tare da cire gyalen jikinta tace, "lafiya lou suna gaishe ki". Raihana tace, "aikuwa Ina amsawa". Kitchen ta tafi ta kawo wa ummie ruwan lemon data had'a da rana. Ummie ta karb'a tana sha sanyin shi na ratsa y'ay'an hanjin ta, ta sha da yawa kafun ta ragewa jidderh da take zaune gefenta saura. Kallon raihana tayi ta sake cewa, "na shiga gidan iya mun gaisa har tana tambayar ki". Raihana tayi y'ar dariya tace, "Allah sarki iya zan shiga ai mu gaisa cikin satin nan" ummie tace, "da kin kyauta dai kam". Daga nan suka ci gaba da tab'a hirar su har zuwa lokacin da ummie ta shige d'akinta, ita Kuma ta tafi wajen wayarta. Tayi zaton zata samu missed call d'in Imran sai taga babu sai text massage daya mata, "yakike raihanata fatan kina lafiya, hak'ik'a addu'ar ki tana tasiri sosai a kaina, yanzun haka likita yace zai iya sallamata nan da kwana biyu ko uku masu zuwa, naji sauk'i alhamdulillah kuma ina futowa ke zan fara zuwa na gani, saboda nayi kewarki fiye da yadda ke da kowa kuke zato.... I love you Soo much raihana". Koda Imran ba kiranta yayi ba amma taji dad'i da taga massage d'inshi, ta fahimci idan yana tare da maman shi baya tab'a kiranta, itama kota kira ba zai d'aga ba, tun wani lokaci sau d'aya daya kirata suna cikin waya taji muryar maman tana ta maseefa har yau bai k'ara yadda ya kirata in tana kusa ba, bai fad'a mata baki da baki ba amma kasancewarta mutum mai saurin fahimta tuni ta d'ago shi. Sai da ta mishi refly sannan ta sake dawowa parlon hannunta rik'e da wayarta. Tana zama kamar jira sai ga alart daga Ayman, saida ta jinjina kafun tayi dialing no shi, kamar kullum yau ma bai d'aga ba, sai ta mishi text na godiya kawai ta ajiye wayarta. ******** ******** Auntie kuwa a yinin ranar ta had'awa khaleefa d'akin shi kamar yadda ta had'awa Ayman, k'aramin gado da k'aramin carpet a k'asa sai wani madaidaicin table a gaban gadon, sif mai biyu sai drower. Yana zaune a parlour har suka gama had'awa suka yi mishi sallama suka tafi, auntie kuma da kanta ta kawo mishi duvets fari da mayafin rufa da duk sauran abinda tasan zai buk'ata. _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: https://chat.whatsapp.com/CKR7E0qHjy0L9W04t8Acc2 *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty three2️⃣3️⃣ Da yammacin ranar yana zaune still a parlor yana operating system akan aikin da yasa gaba a yanzun, ya fara jiyo hayaniyar mutane da yawa suna nufo d'akin. Yana daga kanshi suna fara shigowa cikin d'akin, auntie da sameera ne sai baby heedaya da Nur a baya. Suna shigowa heedaya ta daka tsalle tayi inda khaleefa yake zaune ta d'ane bayan shi, "na kama ka, yau sai ka biya mun duk chocolate d'ina da kullum kullum kake yimun alk'awari ta waya kak'i kazo ka kawo mun". Murmushin gefen baki yayi ya janye ta daga bayan shi ya zaunar da ita gefen shi, su kuwa duk guri suka nema suka zauna a kujerun parlon. Nur dai ta kasa daina kallon shi, a dole ita so take ta fahimci Ayman d'inta ne wannan ko kuma khaleefa, bata fahimci komai ba har taji muryar shi yana gaishe da mammin su. Ta amsa mishi tana k'ara kallon shi itama, kallon surayyah tayi bayan sun gama gaisawa da khaleefa tace, "wato surayyah tunda nake ganin twins ban tab'a ganin masu tsananin kama da juna kamar su Ayman ba, kinga ni yanzu ban fahimci waye a cikin suba fa". Dariya auntie tayi tace, "ba kums zan fad'a miki ba sai dai ki canka da kanki". Nur dai tana gefe tayi shiru tana kallon yadda ya d'auke kanshi yana ci gaba da abinda yake yi a cikin system, a ranta tace Anya wannan Ayman ne kuwa? Tasan Ayman be kai hasken wannan ba kuma bashi da shariya irin haka. Heedaya kuma ganin ya share ta bai biye mata kamar Yaya Ayman ba sai tasa hannunta a screen d'in system d'in ita ala dole ta rufe tace, "Ni dai ka fara bani chocolate d'ina sai kaci gaba da aikin ka irin na Yaya haeydar". Khaleefa ganin zata dame shi sai kawai ya nemo wayarshi da take gefen shi ya dannawa no Ayman kira, ringing uku hud'u ya d'aga, "yae man ka futo Ina ganin kana da bak'i fa". Yana gama fad'ar sak'on shi ya ajiye wayar gefe yaja kumatun heedaya data zuba mishi ido, "ya sunan ki?" Ya tambayeta yana kallonta, cikin iyayi da iya reto tace, "heedaya". Murmushi ya kuma yi yace, "Nice name baby heedaya me bakin kwad'ayi, yanzu zai kawo miki chocolate d'in naki". Y'ar dariyar jin dad'i tayi, a maganar shi bata fahimci komai ba sai za'a kawo mata chocolate. Sameera tana shirin fad'awa auntie ta gane su sai kuma ga Ayman ya futo. Aikuwa heedaya na ganin shi ta tashi da gudu ta b'uya a bayan auntie tana fad'in, "aljani, auntie aljani mai kama da Yaya Ayman b'oye ni kada ya kamani". Sai a lokacin Nur da mammie suka gane lallai wanda ya futo yanzu shine Ayman. Shi kuwa heedaya da take lek'o shi daga bayan auntie ya zarowa ido yana fad'in, "Bari kiga nazo na d'auke ta zuwa duniyar aljanu gaba d'aya.....". Aikuwa ta rintse ido tana sake mak'ale auntie da faman kiran ta b'oye ta. Cikin jin nauyin mammie ya durk'usa suka gaisa daga inda yake, itama a haka ta amsa mishi. Kusa da khaleefa ya koma ya zauna. Sai a lokacin sameera tace, "Masha Allah khaleefa an zama physiotherapy Doctor saura aiki da aure kuma......". Shiru yayi jim kafun ya d'ago kanshi yace, "Aure ai da sauran lokaci, aikine dai munyi magana da wani likitan k'asar Germany zamuyi aiki tare dashi a wani asibitin k'ashi dake Berlin inda mukayi karatu". Saida gaban auntie ya fad'i, ta d'ago kanta daga danne dannen wayar da take ta zuba mishi ido tana kallon shi, shi kuwa tuni ya maida kanshi ga abinda yake a system d'inshi. Kallonta sameera tayi suka had'a ido sai ta gyad'a mata kai, meaning taci gaba da maganarta. Sai tayi gyaran murya again ta sake cewa, "Allah sarki Allah yayi jagora yanzu can Germanyn zaka koma da zama kenan?". Sai ya rufe system d'in gaba d'aya ba don ya samu matsaya kamar yadda yaso ba yace, "eh to kusan hakan dai". Mamie tace, "okay fatan nasara toh amma zakayi auren ne kafun ka bar k'asar nan ko? Ina ganin dai kamar zaifi ai?". Sai a lokacin ya kalli Auntie ta d'aure fuska tamau ba alamun annuri. D'auke kanshi yayi cikin basarwa. Ayman da yake rakub'e gefe saboda wanzuwar mammie a gurin kallon shi kawai yake, wato duk burin da yaci akan yana dawowa k'asar suyi aure shine zai watsa mishi k'asa a ido? Lallai khaleefa akwai abinda ya taka duk wannan d'abi'un da yake timming ne, don yasan khaleefa farin sani ciki da bai, mutum ne me rik'e abu a rai yayi ta riritashi b tare daya fad'awa kowa ba har sai an matuk'ar kai ruwa raana sannan. Yana sauraron duk hirar da suka dinga yi shida mammie akan karatun su da banbance banbancen kowanne a cikin karatun likita a k'asa Nigeria, abun ya burge auntie kwarai a lokacin da take sauraron yadda yake bayani da zallar kwarewa kan abinda ya karanta, yanzun ta sake tabbatar da ba'ayi asarar kud'in da aka kashe akan karatun nashi ba. Saida aka kira magrib sannan suka mik'e su duka har Nur da baby heedaya da tayi bacci jikin auntie tun tsoratar da tayi na ganin Ayman. Shima d'akin shi ya shige don ya d'auro alwalar sallar magrib data k'arato. Ayman ma alwalar ya tafi ya d'auro yabi d'an uwanshi suka tafi masjid tare. Auntie tana zaune a parlon ta tayi shiru tana kallon sameera da take zaune kusa da ita, "matsalolin khaleefa kullum gaba suke k'ara yi sameera, kinsan tunda ya dawo nake ganin bak'in halaye tare dashi kuwa? Gaba d'aya nema yake ya ware kanshi daga cikin mu shiyasa ya k'irk'iro tafiya aiki Germany,,,, da yake ban isa ba a gurin shi ko amincewa ta bai nema ba shi da kanshi ya yankewa kanshi hukunci, tunda shi d'an kanshi ne....". Sameera da take zaune kusa da ita tace, "kiyi hak'uri surayyah, ni gani nake kamar miskilancin shine yafi futowa yanzu, kuma kinsan namiji dama yana girma yana sauya halaye, dole kiyi hak'uri da bak'in halayen da zaki gani daga gare shi har zuwa lokacin da zaki lallab'a shi yayi abinda kike so, sannan abu na biyu kada mu shiga hak'k'in shi akan maganar auren nan, mu ajiye maganar shaheeda a gefe ki tabbatar ya futar miki da matar da yake so kafun komawarshi Germany, shine kad'ai hanyar da zaki samu nutsuwa bayan tafiyarshi k'asar da uwa ba kwab'a uba ba harara..... Sannan kada ki hana shi aikin nan...". Doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon sameera still da damuwa a fuskarta ta sake cewa, "kina nufin na soke zab'in da nayi mishi na matar da zai aura? Toh aikuwa sameera indai khaleefa ne sai dai zuciyata ta buga da bak'in ciki na mutu shi bashi da asara da dai yayi abunda nake so, don bazai tab'a aure cikin datsin nan ba Ina mishi magana zaice bashi da zab'in irin matar da yake son aure". Murmushi sameera tayi tace, "kada ki fara fassara shi zuwa ga abinda baki sani ba k'awata, ki bari dai kiji daga gare shi tukun, sai dai bada hayaniya ba, ki bishi a nutse da y'an dabaru, in kika so ma kice mishi zaki amince ya tafi Germany amma ba zaki yarda ya tafi ba matar aure ba, a wannan lokacin sai ki ji abinda zaice miki, yadda na fahimci yana son aikin nan tsab zai amince da zab'in matar da zaki mishi don ya samu cikar burin shi cikin sauk'i,,, sannan ni banga abun damuwa da komawar shi Germany ba". Cikin gamsuwa da shawarar k'awar tata tayi na'am lokaci guda, shiyasa lokuta da yawa idan kanta ya kulle game da matsalolin yaranta sameeran take samu su shawarta, da yake ta fita yawan yaara nan da nan zata d'ago mata bakin zaren. Shaheeda kuwa da take tsaye jikin windown bedroom d'in da Auntie ta bata na jikin d'akinta, tashi hankalinta yayi da jin furucin auntie da kuma irin shawarar da mamanta ta bayar, sai taji kamar ta futo ta yak'i komai ta nemi shiga a gurin khaleefan, daga jiya zuwa yau data ganshi gaba d'aya ta kasa samun nutsuwar ruhi, haka kurum ya shiga cikin zuciyarta ya zauna da baud'ad'd'en ra'ayin shi da halayen shi, ba don komai ba sai don abu guda data fahimta tun farkon ganinta dashi, Dole zai zama daban a cikin maza, kuma mai kwakwalwa, ita Kuma irin mijin da take so kenan tun da jimawa, take mafarkin had'uwa dashi oll dis time, yanzu kuma ta samu mamanta tana shirin yi mata..... Sai ta daki k'arfen window da hannunta d'aya cikin takaici. Ta lashi takobin duk hanyar da tasan zata bi don tasa khaleefa ya sota sai tabi, kuma tana ji a jikinta dole zai sota ma tunda batayi kala da matan da namiji zai k'i ba duk aji da kyanshi ko kud'in shi kuwa, saboda tasan ita d'in mai kyau ce tun tasowarta, haka k'awayenta suke yawan kod'ata bata gasgatawa har zuwa yanzu data mallakin hankalin kanta ta tabbatar da gaskiyar abinda suke fad'a game da ita. Murmushi tayi a zahiri bayan ta tsaya gaban mudubi ta sake k'arewa kanta kallo, a zahiri ta furta, "khaleefa da sannu zaka so ni ba tare dana yarda ka fahimci soyayyarka da take cikin zuciyata ba, zanci gaba da jan girma da ajina har zuwa lokacin da zaka zube k'asa a gabana kana neman soyayyata". Sai ta sake sakin wani murmushi na K'arfafawa kanta da kanta gwiwa. _(Toh fans ga shaheeda da jin kanta zata fad'a mafarkin ido biyu, ga khaleefa wanda ya fita baud'ewa yayi nisa cikin soyayyar Saleema a gefe)_ @@@@@@@@ Khaleefa kuwa yayi nisa cikin binciken family of Abdallah tofa, binciken shi ya tabbatar mishi da cewa Abdallah tofa wani shahararren d'an siyasa ne daya rik'e muk'amai da yawa a k'asar Nigeria, ya tab'a rik'e ambassador Nigeria a k'asar turkey ma, hakan yasa ya daina harkar siyasa gaba d'aya, ya zauna a k'asar turkey kusan shekaru goma sha tara kafun a sauke shi ya dawo Nigeria da zama din din din. Abdallah tofa ya rasu shekaru talatin da uku wannan shekarar ta silar accident a hanyar zuwa Kano daga Abuja. Khaleefa yaci gaba da bincikawa sai dai baisan sunan y'ay'an shi ko guda d'aya balle yabi diddigi yaji tunda shi Wanda ya fara bi a matsayin kakan su ya rasu, duk da dai khaleefa tuni ya sare jin k'aton familyn da binciken shi ya kaishi, yana ji a jikin shi ba daga babban family irin wannan suka futo ba. Sai ya zubawa computer gaban shi ido kawai yana nazarin ta inda zai b'ulla ko Allah zaisa ya dace da abinda yake nema, zuciyar shi ta bashi shawarar ko ya rubuta sunan mahaifin su??? Knocking k'ofar shi da akayi yasa cikin sauri ya rufe system d'in ya tura ta gefe sannan ya tashi da kanshi yaje ya bud'e. Ayman ne tsaye hannun shi duka biyu goye a bayan shi yana fuskantar k'ofa, "sannu da dawowa daga aiki Mr engineer" khaleefa ne yayi wannan maganar, Saida yayi kamar ba zaice mishi komai ba sannan yace, "ban futa aiki ba yau saboda Ina hutun k'arshen shekara na wata d'aya". "okay" kawai ya fad'a ya bashi hanya ya shiga cikin d'akin sannan ya maida k'ofar ya rufe. Duk zama sukayi a gefen gado sukayi shiru kowa da abinda yake tunani a ranshi kafun Ayman yace, "me yasa ka fad'i abinda ka fad'awa mammie jiya". Kai tsaye khaleefa ya bashi amsa, "saboda abinda na fad'a shine abinda yake raina kuma ban iya k'arya ba kaima shaida ne bare na shirya mata k'arya don na burge ta". D'an jim Ayman yayi yana son yaga ko zai iya fassara abinda khaleefa yake nufi, bai fahimci komai ba hakan yasa ya sake cewa, "na fuskanci kamar kana son nisanta kanka damu shiyasa ka nemo aikin k'asar Germany". Numfashi ya sauke me tsayi kafun ya ci gaba da magana, "nasan ka reasonable person baka tab'a yin abinda babu cikakken hujja ko dalili, sai dai nayi iya nazarina don ganin na nemo kuskuren da mukayi maka nida auntie har yanzu ban iya tunowa ba, shine nazo na rok'e ka don girman Allah khaleefa ka taimaka ka fad'a mana sai mu nemi yafiyarka muci gaba da zama lafiya kamar yadda muke da farko......". Zuba mishi ido khaleefa yayi kamar zaice wani abu sai kuma ya basar cike da tausayin d'an uwan shi rabin ranshi, Ina ma Ayman yasan abinda auntie take b'oyewa game dasu, Ina ma yasan da gaske basu da cikakken asali?? Da bazai k'ara mishi kallon zargi akan duk wani bak'on hali da zai nuna ba, sannan ya tabbatar bazai sake ganin farin auntie ba har abada. Sai ya durk'usar da kanshi yana tuna kalaman Saleema da suke mishi amsa kuwwa a cikin kunnenshi kamar yanzu take furta mishi su, wannan kalma ta da uba ake ado ta kasa barin ranshi, k'ona shi take da kowanne motsi ko yink'uri da zaiyi, ba don Saleema ta kasance macen daya fiso a duniya in aka d'auke mahaifiyar shiba, da har abada shida sake kallonta bare ma har ya fara tunanin aurenta a yadda ta jefe shi da mummunar kalmar da babu wanda ya tab'a jifan shi da kwatankwacinta, toh amma soyayyah!! Allah ya d'ora mishi soyayyarta a k'ok'on ranshi har yana jin idan bai same taba bazai sake rayuwa cikin farin ciki ba har abada...... Ayman sake matsawa kusa dashi yayi ya had'a hannuwa biyu yana rok'on shi kamar ya zubar mishi da hawaye, "khaleefa ba don niba, ba don na isa ba, ka taimake ni don Albarkacin soyayyar tagwaitaka da take zukatan mu da mak'otakar zaman wata tara a ciki guri guda ka amince da maganar auren mu ko nima na samu Nur cikar burina, kada ka zamo silar da zan rasa Nur saboda Ina sonta da gaskiya kamar yadda itama take sona, sannan ka soke maganar komawarka Germany don girman Allah......". Hannuwan shi biyu yasa ya saukewa Ayman hannun shi k'asa daga alamun rok'on shi da yayi, "ka daina had'a ni da girman Allah Ayman, ko yanzu zaka iya yin auren ka ba dole sai tare dani ba, maganar aikina kuwa bakin Alk'alami dad'e da bushewa..... amincewar auntie kawai nake nema....idan har bata amince ba na hak'ura zanyi aiki a k'asa ta, amma fa idan ta amince ko second bazan k'ara a Nigeria ba zan b'acewa ganinka". Kallon shi kawai Ayman yake kafun ya mik'e don ya futa daga d'akin, don baiga amfanin ci gaba da magana dashi ba, har yakai k'ofa ya dakata ba tare daya juyo ba yace, "auntie tana son magana dakai, tace ka same ta a parlonta". Bai amsa ba hasalima kamar bai jishi ba ya mik'e jiki a sanyaye yabi bayan Ayman d'in, shi a nan parlour ya kwanta, shi kuma khaleefa ya tafi don amsa kiran auntie. Lokacin daya shiga parlon babu kowa sai shaheeda zaune saman sofa tana rubuce rubucen ta. Sanye take da doguwar riga y'ar kanti sai gyalen rigar data d'aura a kanta, fuskarta ba hayaniyar kwalliya daga powder sai pink jan baki. Zama yayi daga kujerar da take nesa da inda take, tunda ya kalleta da farko ya fahimci ba auntie bace bai sake duban inda take ba koda wasa, ita kuwa shaheeda da kyar ta iya d'auke kanta ga barin kallon shi, ba don kar tayi k'arya ba da sai tace tun ranar da suka karya a dinning da safe bata sake ganin shiba sai yau. Cikin basarwa da d'auke kai ta gaishe shi, ya amsa ko kallon inda take baiyi ba. Ya d'auki adadin wasu mintuna kafun auntie ta futo rik'e da wayarta me shegen tsada da kyau, waya take yi, saita samu guri daga gefen inda yake ta zauna tana kallon wayar hannun shi, yana daga abinda yake burge ta da khaleefa, bai fiya damuwa da abubuwa irin na matasan zamani ba, wayar nan ta hannun shi tare ta siya musu da Ayman, bayanta Ayman ya lalata wayoyi hud'u ko biyar ma, amma shi har yanzu tana nan rik'e a hannun shi, ga k'aramin misali kud'in da take tura mishi duk k'arshen wata, baya almubazzarantar dasu a banza, sai dai in siyayyar abu na dole ta taso mishi yayi amfani dasu, kyale kyale ko kyallin duniya basa d'aukar hankalin shi kuma basu dame shiba, sannan bashi da zarmewa a son abun duniya kwata kwata, shiyasa har gobe ta kasa fahimtar abinda ya d'auki hankalin shi da aiki a k'asar Germany, tabbas tasan ba don abinda zasu biya shi ya amsa tayin wannan aikin ba.... To don meye??? Wasu lokutan idan ta kalli rayuwar khaleefa da kyau tsarin yadda yake tafi da rayuwar shi Soo simple sai taga kamar tana kallon rayuwar Suraj mahaifin sune. Haka yake mutum mai aiki da hujja amma me shegen taurin kai da zurfin ciki. Jin ana faman kira mata hello hello a kunne sai ta dawo daga tunaninta ta tuna ashe fa waya take,,, "I will call you later" ta fad'a tare da datse kiran, "Ayman ya fad'a maka Ina son magana da kai?". Ta tambayi khaleefa, "eh ya fad'a mun" ya bata amsa shima, shaheeda da take ta harkar gabanta ta kalla tace, "shaheeda ko zaki bani guri nayi magana da yayanki". Ba musu tace toh ta had'a tarkacen littafanta ta shige d'aki. Sake fuskantar shi tayi da kyau kafun taci gaba da maganarta, "khaleefa na kira kane saboda naji meye takaimaman matsalarka, kada ka fara yimun k'arya kasan ba dabi'ar ka bace kana yi zan gane gaskiya daga nan bazan k'ara yarda da duk abinda zaka fad'a mun daga baya ba, komai muhimmancin shi kuwa har abada... Sannan zan fasa abinda nayi niyyar yi maka". Shiru khaleefa yayi kanshi a k'asa yana jinjina girman matsalar shi da yadda zata fahimci gaskiyar koya fad'a, sanin bazai samu abinda yake so daga gare taba yasa ya gwammace yin shiru da bata amsar tambayarta. Ganin sun d'auki lokaci bashi da niyyar bud'e baki bare ya furta wani abu sai ta fahimci ba zai bata amsa ba kenan, sai ta d'auki tambaya ta biyu, "tunda baka da amsar wannan, ya batun maganar da kayiwa mamanka sameera jiya, shin gaskiya ne abinda kuka shirya aiwatarwa kenan kaida Ahmad?". Sai a yanzu yaji zai iya magana, "Eh auntie duk abinda na fad'a mata babu k'arya a ciki ko zolaya, toh taya ma zan zolayeta tana matsayin uwa a gurina, a cikin wad'an da mukayi course d'in nan dasu, an zab'e mu mu bakwai zamuyi aiki k'ark'ashin wani team don mu k'ara samun kwarewa, kuma sunyi alk'awarin zasu yi mana kyakkyawan biya, bance zanyi aiki abadan dasu ba, amma akwai abinda nake timing dana samu zan baro k'asar na dawo gida Nigeria a amfana da abinda na karanta, sai maganar aure da mammie tayi jiya, shima bance bazan yiba don mutum baya cika cikakken mutum saida iyali, kuma ni tun watanni shida baya Ina da zab'in matar da nake Soo in aura, shima akwai abinda nake so ya kammala bada jimawa ba zan gabatar miki da ita". Duk maganar da yake auntie shiru tayi tana sauraron shi har ya kai aya, Amma fa tayi shock da taji cewar yana da matar da yake so ya aura, babu zato taji wannan maganar, koda yake dama amma dama itama bata shirya yi mishi dole akan ya karb'i shaheeda ba sai dai zata so ya auri matar da aka santa a k'asan asalinta, ba wai ya d'auko mata daga wata duniyar ba, su basu san halinta da d'abi'un ta ba itama ba tasan nasu ba, ya kawo musu ita cikin su ta zame musu k'arfen k'afa. Astagfirullah ta fad'a kuma da sauri a ranta tana addu'an Allah ya nisanta su daga irin wannan matar. _shin kune biye da littattafan in-identical twins? Albishir gare ku masoyan mu, litattafan mu sunzo muku da wani sabon salon soyayyah da sadaukarwa ba irin wanda kuka sani a wannan duniyar ba, ku dai kuci gaba da kasancewa da 👉🏻 *Doctor Ferhyeez m usmern DARAJAR HAK'URI* & *merhreeyeart lerwerl JARUMAR UWA, together as in-identical twins*_ _i need your prayers plzz Ina kwance bani da lafiya, k'anwar sisi nama tana kwance bata da lafiya a asibiti_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: https://chat.whatsapp.com/FL6vlC2CnStDUNk6BOW3Ob *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty four2️⃣4️⃣ Shawarar sameera ce ta fad'o mata zuciya a take, sai ta gyara zamanta kamar babu komai a cikin ranta tace, "Masha Allah naji dad'in hakan matuk'a kayi mana bazata mu duka nida Ayman, nasan shima in yaji labari zaiyi farin ciki sosai, na amince da komawarka Germany a karo na biyu, sai dai da sharad'in zaka gabatar da ita a nema maka aurenta sai ku tafi tare". Khaleefa duk da yaji Damm da farko amma amincewarta da aikin shi sai yaji kwarin gwiwa, yana fatan ya samu madafa kafun lokacin da aka d'iba musu na hutu ya k'are, sai ya russuna a gabanta yace, "Ina godiya auntie insha Allah zan kammala duk shirin daya kamata na gabatar miki da ita nan bada jimawa ba, saboda watanni biyu suma suka bamu a can duk wanda bai koma bayan wad'an nan watannin ba cikin sauk'i ya bayyana cewa bai amince da aiki tare dasu ba" Wani murmushin cin galaba auntie tayi a ranta tace, ""Kaine no one cikin wanda za'ayi cancelling kuwa don babu inda zan yarda ka koma"". A fili kuma addu'ar samun nasara tayi mishi tare da sanya albarkarta. Da haka sukayi sallama ya tashi zai futa, har ya kai k'ofa ta kira sunan shi a sanyaye, "khaleefa!". Saiya juyo da raunananniyar zuciya ya kalleta ba tare daya iya amsa kiranta ba, itama a yanayin data ke kallon shi kenan cikin sigar tausayi ta fara mishi magana, "don Allah khaleefa ba don niba ba don na isa ba, ka sauke duk wani abu da kake ji k'asa ko don Ayman ya bar damuwa akan ka da sababbin halayen da kake gwada mishi, khaleefa tun kafun ka dawo 9ja rabon da naga walwalar shi, Ayman da a duniya bashi da zancen daya huce naka!! Amma shine mutum na farko da zaka fara kuntatawa da hukuntashi akan laifin da bai san dashi ba,,,, shin ka yiwa kanka adalci kenan?....". Tun data fara magana ya sunkuyar da kanshi k'asa bai yarda ya d'ago ba har ta dire, a nutse itama ta mik'e ta k'ara taku kad'an zuwa gaban shi ta tsaya goye da hannaye a baya kafun taci gaba, "nasan halinka, fiye da yadda nasan halin Ayman da nake kwana dashi kullum nake tashi dashi.... Tabbas wannan laifin nawa ne ko baka furta da bakin ka ba zan iya fahimtar hakan daga kwayar idon ka.....". Khaleefa rintse ido yayi ya d'ago da idon shi da suka sauya colour ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya murd'a handle ya futa da sauri. Ita kuwa ajiyar zuciya ta sauke bayan futar shi ta koma inda ta tashi ta zauna tana al'ajabin wai khaleefa yana da wadda yake son gabatar mata tuntuni matsayin matar auren shi?? toh wacece wannan yarinyar kuwa??? A wace duniyar ma ya had'u da ita tukun shida bai rufe sati da dawowa k'asar ba. Da wannan tunanin auntie ta k'arasa yinin ranar gaba d'aya. Shima ranar yuni yayi yana juya maganganun ta a cikin zuciyar shi, tabbas auntie tayi gaskiya shi kanshi yasan a duniya ba wanda yasan halin shi irin yadda ita ta sani, a shekarun baya ko abinci zasu ci daga kallon da yakewa abinci take gane zaici ko bazai ciba. Sai abu na gaba daya kamata zuciyar shi tayi laushi a kanshi shine, kowanne mutum tafe yake da k'addarorin shi da bai Isa ya tserewa ba, sannan har yanzu bashi da tabbas akan waccen magana da Saleema ta jefa mishi, idan zai yiwa kanshi adalci bai kamata ya dinga huce fushin wani akan wani ba,,,,, sai ya matsa daga inda yake tsaye ya koma kan gadon shi ya jingina yana sake kawo gyara cikin mu'amulolin shi. ★★★★★ Tada sallar asubah da akayi a masallaci yasa khaleefa futowa da hanzarin shi. A jikin k'ofar shi ya tsaya yana tunanin abinda ya hana Ayman futowa, a k'a'ida duk lokacin daya futo zai tafi masallaci yana samun shi tsaye a k'ofar d'akin shi yana jiran shi, sai dai yau bai ganshi ba, sai yayi tunanin watak'ila ko ya tafi ne, don haka sai yayi hucewar shi shima. Ko bayan sun idar da sallah ma bai tafi ba ya tsaya yana duba masu futowa har suka k'are ya tabbatar baizo masallacin ba yau sannan ya kamo hanyar komawa gida yana tunanin abinda yasa har sallar asubah ta kwace mishi yau. Kamar kullum yakan zauna a parlour yayi lazimummukan shi amma a yau sai yaji Sam bashi da nutsuwa, shin Ayman makara sallah yayi ko kuma wani abune daban yake faruwa dashi? Ganin tunanin shi yana rarrabuwa sai ya mik'e tsam yaje yayi knocking k'ofar shi, ya jima shiru kamar zai juya don ga zaton shi ko bacci yake, sai kuma wata zuciyar ta bashi shawarar ko bacci yake ai yana da kyau ya tashe shi yayi sallah ko shima ya rabauta da falalar da take cikin sallar asubah a lokacin ta, ya bud'e k'ofar ya shiga a hankali. Tun daga bakin k'ofa ya fara cin karo da pillows a k'asa duk an wurgo, gadon shi a hargitse shi kuma yana durk'ushe k'asan d'akin hannun shi a saitin cikin shi. Da sauri khaleefa ya k'arasa gare shi yana fad'in, "subhanallah Ayman, Ayman meya faru da kai kuma?". Ayman cikin tsananin azabar ciwo ya rik'e hannun khaleefa da hannun shi daya d'au zafi rau, khaleefa kuwa duk kid'imewa yayi ya rasa ta inda zai fara taimakon shi, kawai daga k'arshe sai ya rintse hannun shi da yake cikin nashi ya zuba mishi ido yana kallon shi cikin so da tausayi, ya fara tofa mishi duk addu'ar da tazo bakin shi, sun jima a haka kafun ciwon ya lafa mishi ya samu nutsuwa kad'an, har lokacin kanshi na cinyar khaleefa hannun su cikin na juna. Sai a sannan khaleefa ya tambaye shi abinda yake damun shi, da murya k'asa k'asa yace, "cikina k'irjina, bayana......". "dama kana fama da ciwon ciki tun kafun yanzu" da kyar ya ce, "Eh akwai magani na a drower zaka ganshi a farin kwali....". A hankali khaleefa ya janye shi daga jikin shi ya bud'e drower, shine a farko ma, gaba d'aya drower magunguna ne kamar za'a bud'e chemist lifdi lifdi, shi dai khaleefa ya d'auki iya wanda ya fad'a mishi ya tsaya yana dubawa, "wane likita ne ya rubuta maka wannan maganin". Ya tambaye shi da damuwa,,, Da kyar ya iya fad'a mishi "doctor Umar ne". Ajiye maganin khaleefa yayi ya d'auki mukullin motar shi ya tambayi Ayman, "akwai wani pharmacy kusa damu nan?". Girgiza mishi kai yayi ya yink'ura da kyar ya d'auko wayar shi dake yashe a k'asa ya lalubo wata no yai dialing, ringing uku ana hud'u ya d'aga, "ka futo pharmacy don Allah yanzu akwai maganin da yayana zai karb'a a gurin ka..... Ka bashi address zai taho da wayata". Daga can mutumin yace, "alright bashi wayar toh". Sunyi magana da khaleefa ba me tsayi ba, kafun ya futa da sauri, shiya bud'e get ya cire mota waje, ya dawo ya rufe sannan ya tafi. Tunda yazo in aka d'auke masjid ba inda ya tab'a futa sai yau, da yake yasan garin kwana biyu da yayi baya nan ne anguwannin suka kwanta mishi baisha wani wahala wajen had'uwa da mutumin ba. Bayan sun gaisa yake tambayar khaleefa shine abdallah da suka tab'a makaranta tare kafun ya futa waje karatu, khaleefa yace, "eh nine kayi hak'uri amma ni ban wani tuna ka ba fa", "ayyah ai shekarun da yawa shiyasa" nan ya mishi kwantace har ya tuno shi, aikuwa suka sake gaisawa, suna tafe a hanya suna hirar yaushe gamo har suka Isa shagon ya bud'e, khaleefa ya rubuta magungun da yake so ya shiga ya duba mishi. Koda ya bashi kud'i k'in karb'a yayi, haka nan sukayi exchange na phone number juna yace ayiwa Ayman sannu suka rabu kowa yayi nashi guri. A gurguje ya dawo ya haura stairs, Ayman a haka har yayi alwala ya gabatar da sallar subh, _(kasancewar shi mutum ma'abocin addini)_ yana kan sallaya a lokacin da khaleefa ya shigo, ya ajiye ledar maganin a kusa dashi yace, "ya kake jin jikin naka?". Yace, "da sauk'i". "toh Allah ya k'ara sauk'i". Sake futa yayi ya lalubo kitchen d'in gidan ya shiga, tea ya tafasa mishi ya juye a d'an madaidaicin cup. Saida ya bashi shayin ya tilasta shi ya shanye tass kafun ya b'alle mishi maganin ya sha". Bai zauna ba ya gyara mishi saman gadon ya hau ya kwanta shi kuma ya gyara d'akin fess. Ba jimawa bacci me nauyi yayi gaba dashi shi kuma ya d'auko system yaci gaba da zama tare dashi yana aikin shi lokaci bayan lokaci yana kallon yadda yake baccin shi sadidan da alamu ciwon ya lafa. Har gari yayi haske suna tare bai tafi ba, yana jin yarinyar nan me aikin su ta gama gyare parlon tazo tana knocking k'ofar Ayman, bai motsa ba bai Kuma ce mata kanzil ba, tana murd'a handle taga khaleefa dama taja jikinta baya da sauri ta b'ace a gurin. Auntie kuwa ganin har raana babu Ayman bare khaleefa da yake zuwa su gaisa duk safiya ya d'auki break d'inshi ya tafi, sai ta kasa samun nutsuwa, Ayman baya tab'a kaiwa war haka ba tare da yazo ya ganta ba, in kuwa hakane lallai akwai abinda ke faruwa shirun nan ba lafiya ba. Bayan ta shiga d'akin shaheeda da take ta zabga bacci lakadan ta tashe ta donta karya kumallo, part d'insu ta nufa direct, saida ta fara tsayawa d'akin khaleefa tayi knocking taji shiru, koda ta bud'e baya ciki, hakan yasa ta murd'a k'ofar d'akin Ayman. Yana zaune kan gadon Ayman d'in ya mik'e k'afafun shi laptop d'inshi akan pillow a cinyarshi, sai Ayman d'in a gefe yana bacci rabin jikin shi rufe da bargo. Sai a lokacin ta sauke b'oyayyen ajiyar zuciya, khaleefa zare glass d'in idon shi yayi ya ajiye laptop d'in gefe ya sauke k'afar shi k'asa. Har hard'ewa k'afar ta take wajen saurin ta k'arasa ga Ayman da yake kwance, hannunta ta d'ora a gefen wuyan shi taji jikinshi sanyi k'alou, "naji jikin shi ba zazzab'i gashi alamu sun nuna bashi da lafiya me yake damun shi kenan?". Khaleefa saida ya fara gaishe ta kafun ya fad'a mata cikin shine yayi ciwo, zama tayi gefen bed d'in tana kallonshi kafun ta fara magana cikin fusata fusata, "Ayman ne baya ji wallahi khaleefa, na hana shi zama da yunwar nan amma yak'i, idan yaci abincin safe baya sake cin wani abu sai yamma ko dare, ba dole ulcer ya rik'e mishi k'irji da ciki ba, akwai wasu magungunan shi cikin drower can yasha?". "A'a na sauya mishi wani shine ma yaji dama dama, saboda wad'an can d'in..... Ni bansan ma wane shashashan likitan bane ya bashi su". Kwalin maganin khaleefa zai d'auka sai kuma ta riga shi d'aukewa, Saida ta duba maganin ta karance kwalin tsaf sannan ta mik'awa khaleefa. Ya karb'a ya zura cikin drower. Haka Auntie tayi ta mita kan rashin son cin abincin shi khaleefa na bata hak'uri. Da kanta tasa shaheeda ta kai musu abincin karin kumallo har d'akin Ayman d'in. Duk da babu datti ko d'igo a jikinta, amma saida ta sake gyara jikinta ta shafa turarenta, taja siririn gyalen dake kanta ta d'auki trayn abincin tayi d'akin. Saida ta nemi izini khaleefa ya bata, lokacin shima Ayman ya tashi yana zaune dai kan bed bai tashi zaune ba. Ta cikin glass khaleefa ya kalleta, bai manta taba itace tazo d'aukar su waccen ranar a airport, sai ya maida kanshi ga abinda yake yi, a kusa dashi ta ajiye abincin ta fara gaishe su d'aya bayan d'aya ta d'ora da yiwa Ayman sannu, ya amsa cikin kulawa. Tana futa khaleefa ya dawo da duban shi kanshi, "sannu da jiki, hope yanzu kana jin jikin naka da sauk'i dai". Murmushin k'arfin hali yayi yace, "da sauk'i sosai ma, nayi mamaki kaida kake likitan k'ashi amma kasan wancen maganin na ciwon ciki". Murmushi shima yayi don tambayar d'an uwanshi ta bashi dariya ne, "ba maganin daya kamata yake baka ba, wannan dana rubuta maka shine wanda zaka dinga sha a duk lokacin da kaji alamun tasowar ciwon, sannan auntie tayi complain akan baka son cin abinci, magani bazai tab'a yi maka amfani da yunwa a jikin ka ba, ka tabbatar ka tsayawa cin abinci akan lokaci insha Allah zaka samu lafiya a jikin ka ko baka sha maganin ba, kayi k'ok'arin fara tsira da wannan saika zauna lafiya". Cikin jin dad'in kulawar khaleefa Ayman yace, "insha Allah zanyi yadda kace nagode da kulawa....." Katse mishi hanzari yayi, "Kada kace komai na had'a maka ruwan wanka masu zafi shiga ka futo mu karya kumallo, kafun nan nima zanje na shirya na dawo, cikin na'am Ayman ya lallab'a ya mik'e. Shima khaleefa mik'ewar yayi. Ko bayan duk sun shirya tare suka had'u suka ci abincin, abinda ya jima bai faru ba tun tsawon lokaci kafun tafiyar shi Germany. Yadda khaleefa ya bawa Ayman cikakken lokacin shi sai ya taimaka wajen warwarewar garkuwar jikin shi ta dawo normal da wuri. Ranar wuni sukayi tare cikin farin ciki suna hirar su ta zumunci da abubuwan da suka faru a bayan idon khaleefa, har futa auntie tayi ta dawo, haleema ta tabbatar mata tana aikinta tsakanin parlour da kitchen duk futar su sun dawo suna tare a ciki. Sai taji wani sanyi ya kwaranya ruhin ta, yau ga yaranta kansu yana shirin sake had'uwa su koma kamar yadda suke da farko. Suna parlon d'akin su, khaleefa yana kwance yana saita sabon sim d'in da Ayman ya kawo mishi tun jiya a wayarshi, shi kuma Ayman yana zaune yana kallon wani program da ake gabatarwa. Tana yin sallama duk suka mik'e zaune suna yi mata sannu da dawowa, Zama tayi a kusa da Ayman ta ajiyewa khaleefa mukullin mota a gaban shi, "kyauta ta na tayaka murnar kammala karatun ka cikin nasara". Wani d'an ihu Ayman yayi yace, "khaleefa irin motar da kake mafarkin samu tun muna yara, auntie thank you, thank you Soo much we really appreciate.... We have no one like you sweet mum". Murmushi tayi hankalinta na kan khaleefa don taga yadda zai karb'i kyautar tata, ta mishi ko batayi ba. Shikam juya mukullin motar kawai yake a hannun shi, cikin nutsuwa da sanyi yayi mata godiya, ba irin nuna farin cikin nan da ihu kamar yadda Ayman yayi don ta mamaye su ba zato. Kallon Ayman tayi ashe shima ya kalleta sai suka had'a ido, shi kuwa khaleefa mik'ewa yayi rik'e da mukulli da wayar ya sake mata godiya ya huce bedroom d'inshi, a jikin k'ofar ya kifa kanshi ya fara kokawa da zuciyarshi, so yake ya daure ya danne abinda yake ji a kanta a duk lokacin daya tuna Saleema da yadda zai rasata saboda ita,,,,, Auntie kuwa ajiyar zuciya ta sauke mai tsayi tacewa Ayman, "ya fad'a maka yana da yarinyar da yake so?". Girgiza kai Ayman yayi, nan auntie ta labarta mishi komai da ya fad'a mata. Yayi murna sosai ya nuna farin ciki da jin dad'in shi a fili, abun da bai tab'a zato ba ko a mafarki shima. Kwana biyu a tsakani binciken khaleefa ya kammala, hakan yasa ya shirya futa wajen iya da malam. A d'akin auntie ya samu Ayman yana breakfast nuriyyah a gefen shi suna hirar su cikin farin ciki. Tana ganin khaleefa ta durk'usa tana gaishe shi, ya amsa kai tsaye ya d'auke kanshi daga kansu gaban shi yana fad'uwa, baya son alak'ar Ayman da yarinyar nan, haka kawai yake jin wani abu a kanta mai kama da zargi, tsoron shi d'aya kada ta karyawa d'an uwanshi zuciya irin yadda Saleema tayi mishi, ya fahimci yanzu a rayuwar nan ba wanda zai basu auren y'ay'an shi ba tare da ya san asalin suba, ganganci ne da kuskure auntie take shirin aikatawa. Koda yake ta hakane zata gane duniya taci gaba, mutanen cikinta sun waye, kowanne d'a da ubanshi yake ado. Ganin yadda yake neman part d'in auntie sai Ayman yace mishi, "tana ciki mammie ce tazo suna tare". Kan d'aya daga kujerun parlon ya zauna yace, "akwai abinda kakeyi yanzu?". "a'a wani abu ne?". Ayman ya tambaye shi, khaleefa shafa sumar kanshi yayi yace, "eh gidan iya nake son zuwa". Mik'ewa Ayman yayi "da gaske! ai ko akwai abinda nake yi zan barshi saboda uzurin ka yana gaba da komai nawa.....". Shima khaleefa murmushin yayi, yana nan zaune har Ayman ya sake futowa cikin shiri, sai ya fara sauka k'asa don ya basu guri suyi sallama da juna. Ba suyi doguwar magana ba Ayman yayi sallama da Nur ya futo ya same shi, saida suka tsaya gurin Auntie da mammie suka gaisa sukayi musu sallama sannan suka futo. A sabuwar motar khaleefa suke tafiya, Ayman yana tuki yayinda hankalin khaleefa ke gefen window yana k'arewa garin kallo, jinshi yake kamar bak'o a garin musamman daya lura da sababbin gine ginen da akayi akan hanya. Babu laifi an samu ci gaba kad'an akan sanda ya tafi. Juyowa yayi ya kalli Ayman da yake tuk'in shi hankali kwance yana bin wakar turanci ta love you baby, rage sautin wakar yayi yace, "Ayman wannan dana ganku yanzu itace Nur". Ayman da yake jinshi yau cikin farin ciki na haka kawai yace, "Eh itace princess d'in yaka ganta bro". Shima murmushin ya mayar mishi, "tayi!! ba laifi tana da kyau, gata fara gata doguwa kyakkyawa dai ta k'arshe, sai dai ina fatan Allah yasa yadda fuskarta take haka zuciyarta take". Rage gudun motar shi yayi ya d'an kalleshi da wani yanayi mai kama dana sanyin jiki da sagewar gwiwa yace, "da kayi wannan maganar saika tuna mun da raihana, itace mai yawan fatan zuciya iri d'aya da fuskar mutum, toh ni dai gaskiya tunda nake da Nur ban tab'a ganin abu makamancin mummunan hali ko rashin tarbiyyah ba, ba wai don auntie tana tare dasu ba a'a sai don gaskiya duk inda tazo a fad'e ta, kaf y'ay'an mammie sun samu tarbiyyah irin wadda addinin islama yazo da ita, shiyasa nake fatan rayuwa cikin farin ciki bayan auren mu da Nur". Nazarin kalaman shi khaleefa yayi kafun ya nisa yace, "Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairin shi". Ayman yace, "ameen". K'aro mishi volume din wakar shi yayi, basu sake cewa juna komai ba har suka k'arasa gidan iya. Khaleefa ya bud'e murfin k'ofa ya futa shi kuma Ayman ya tsaya yana kallon gidan su raihana ba tare daya futo daga ciki ba........ _Na kasa fahimtar Ayman ni kaina, shin sabo ne yake sashi jin kewar raihana ko kuma dai akwai wani abu da yake shirin faruwa dasu_ _Bazan fasa jinjina muku ba masoyan asali, Maryam sulaiman, ummee sa'eed abdallah, khadija maman khaleefa, maman mu'awiyya, mardiyya mai damashi, k'awata, aminiyata, in-identical sis d'ina Dr Ferhyeez m usmern, Fatima Abdullahi...... da dukkannin d'aukacin members na JARUMAR UWA fans group da sauran masu bibiyar novel d'in mu, comment d'inku shike sake k'ara mun k'arfin gwiwa a koda yaushe, na jinjina muku dukkan ku, much love_ _*littafin JARUMAR UWA tun daga farko har k'arshe sadaukarwa ne ga mahaifiyata, farin cikina, best & close friend to me, first love d'ita, lovely ummata......... I'm froud of you mom like no other*_ Happier Jumu'at Kareem to oll Muslim umma A sama zaku ga link na group d'in *DARAJAR HAK'URI* ne domin samun littafin mahadin jarumar uwa akan kari. Ngd _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page twenty five2️⃣5️⃣ "Me kake kallo kuma?" Khaleefa ya tambaye shi, sai ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya yace, "ba komai" tare suka jera har cikin gidan iya. Iya da take parlour tare da bak'i suna magana sama sama kamar fad'a, ganin su yasa ta futo da sauri da fara'ar ta tana musu marhaba, ganin da mutane a d'akin sai basu shiga ba suka tsaya daga tsakar gida khaleefa ya nemi kujerar roba fara ya zauna, Ayman ma kusa dashi ya zauna, sun gaisa da iya tana tambayar su yadda suka baro surayyah, sukace "tana lafiya alhamdulillah". Daga nan bata ja dogon zance ba ta koma d'aki ta sauyawa bak'in ta masauki zuwa sitting room na gidan, kamar ma bata so su khaleefan suka gansu ba, dangin sune dai na can k'auyen su a karo na farko da wani ya biyo bayan su tunda suka zo maraya, khaleefa yabi su da kallo bayan sun gaisa yana sake tabbatar da zargin shi akan iya da mahaifiyar su. Cikin parlon tasa suka shiga, suka zauna kan kujera, gidanta fess kamar a zuba ruwa a k'asa asha, dama tun can sun shaida iya a b'angaren tsabta, macece mai tsabta da yin komai tsab tsab, gidanta ko shirgin nan babu kamar ba gidan tsohuwa ba, ruwa da lemuka ta kawo musu masu sanyi, ta k'ara da zubo musu d'umamen tuwon shinkafa ne miyar kub'ewa da yasha man shanu da yajin daddawa. Ayman saida ya lumshe ido a lokacin daya shak'i k'amshin abincin, "daga jin k'amshin tuwon nan nan dole ma zaiyi dad'i". Duk dariya sukayi mishi, khaleefa yace, "tun kafun kaci ka fara santi". Iya tace "aikuwa dai kam", ruwan wankin hannu ta kawo musu suka wanke sannan suka fara cin abincin da Bismillah. Shi kanshi khaleefa tuwon ya mishi dad'i, in banda abincin iya da auntien su a da ba abincin wanda yake iya ci komai iya girkin mutum kuwa, kuma har gobe ba kowanne abinci yake iya ciba saina wad'an da ya aminta dasu. Yaci tuwon da yawa don bai yi breakfast ba yau duka, kafun ya zare hannun shi ya wanke, iya da ta shimfid'a tabarma saman carpet tana k'ullin gyad'a ya tambaya, "yau malam baya nan ne?". tace, "yana ciki akwai abinda yake yi kana son ganin shine?". "Eh Ina son akwai maganar da zamuyi dashi in ya gama". Iya tace, "ba damuwa yana gamawa zan fad'a maka sai ka shiga ku gaisa". Ayman saida ya sid'e kwano har iya na tambayar shi ko ta k'aro mishi ne, yace, "a'a iya in kika k'aro wani kuma ai cikina saiya fashe". Iya tayi dariya khaleefa kuma da yake gefe yayi murmushi, sunci gaba da hirar su shida iya shi dai khaleefa danna wayarshi kawai yake sai in sunyi abun dariya yayi murmushi, suna hirar iya ta ciko plate da gyad'a ta ajiye musu, aikuwa Ayman yana ganin gyad'a ya soma murmushe ta yana aikawa cikin shi, sai khaleefa ya tsaya kurum yana kallon shi, kafun ya magantu, "Dole ka zama Mr fat ashe in kazo gidan iya komai na gidan saika cinye kake tafiya". Shi dai Ayman gyad'ar shi yake taci sauri sauri yana satar kallon iya kamar mara gaskiya. Itama maganar khaleefa ce ta d'auki hankalinta har ta d'ago tana kallon Ayman d'in, "a'a yau nake ganin mugun abu! Ya zaka cinye gyad'ar dana baku ku biyo? Kai magaji kana kallon shi fa....". Da sauri Ayman ya d'auke wayar shi da plate in gyad'ar yaja baya kusa da d'akin gadon iya sannan yace, "kin manta iya khaleefa baya cin gyad'a tun muna yara". Aikuwa iya ta saki baki tana salati da tafa hannu, shaf ta manta khaleefa baya cin gyad'a tun da can, ta yink'ura zata tashi da nufin karb'e gyad'ar ta, ya shige d'akinta da gudu ya rufo. Saita koma ta zauna tana fad'in, "ai shi kenan! Amma gaskiya bazan yi shiru ba laifin kane magaji, fisabilillah kasan na manta baka cin gyad'a dazan baku ba sai ka tuna mun ba? Shi wancen kamar an mishi k'auri da kurege goman wannan ta gabana ma sai ya cinye ba gajiya yake ba, ka barni kana kallo na dunguje mishi ribar gaba d'aya". Banda dariya ba abinda khaleefa yake ciki ciki Cox iya da Ayman sun bashi dariya matuk'a yau, Ni kam sai na tsaya kurum Ina kallon wani b'oyayyen kyawun shi da banbancin shi da Ayman wanda sai mutum ya nutsu zai iya gani, duk da a yanzun ma sun banbanta sosai. _Kwanaki biyu kafun yau_ Raihana ce zaune kan sallaya da talatainin dare tana kai kukanta ga mai duka, sarkin da babu wani sarki a gaban shi ko bayan shi, sarkin da yake da k'arfin iko da mulkin sarrafa kowa da komai na wannan duniyar, shi kad'ai ne zamu rok'a yayi mana mu sake rok'on shi ya sake yi mana, koda zamu k'are rayuwar mu muna rok'on shi ba zai gajiya wajen yi mana ba, rabbil izzati ubangijin sammai da k'assai. A yau raihana Kukanta take kai mishi akan ya magance mata matsalolin da suke tunkarota, a wannan karon ta fara damuwa da maganganun mutanen gari da dangin su, so take tayi aure kota kawo k'arshen matsalar nan su huta ita da ummienta haka, koda ace Imran zai sake ta a washe garin auren su ta amince zata aure shi muddin zasu shaida cewa ta tab'a aure ko a tarihi, ta fahimci cikin datsin ummie kanta hankalinta a tashe yake da wannan sabon ibtila'in daya tunkaro su, duk da koda wasa Imran bai tab'a sub'utar bakin fad'a mata cewa maman su bata son ya aureta ba, ya b'oye mata komai hakan yasa ta sakankamce har tana tunanin k'arshen matsalolin tane suka zo, sai gashi rana tsaka ana sake shirin tada musu zaune tsaye, mahaifiyar Imran da kanta take aiko musu da mugayen bak'ak'en maganganu akan ta rabu mata da d'anta, in ba haka ba zatayi dana sani don karo da ita ba dad'i, tabi guri guri ta fad'awa mutane da y'an dubiya cewa raihana ce me bak'ar k'afa tunda Imran ya had'u da ita masifu suke ta bibiyar rayuwar shi daga wannan sai wancen, bar gashi yanzu rayuwar shi tana shirin salwanta ata sanadiyyarta, saboda binciken y'an sanda ya nuna musu wani akayi harin poisoning Imran ya fad'a tarkon. Kuka take sosai tana rok'on ubangiji ya kawo mata d'auki a cikin wannan rayuwar, bata fasa neman zab'in Allah ba don har gobe lamuran ta gaba d'aya ta mik'a su gare shi. Ta jima tana addu'a da kuka akan sallaya kafun ta shafa, bata iya komawa kan gadon ba ta kwanta a nan k'asa tana tunane tunanenta har bacci me nauyi yayi awon gaba da ita. @@@@@@ Washe gari ta tashi jikinta duk a mace, haka dai ta lallab'a tayi duk abinda zatayi a gidan, ta yiwa jidderh wanka ta shiryata cikin uniform, ta zaunar dasu suka karya suka huce makaranta, itama wankan tayi, bata son cin komai amma tasan fad'an auntie in ta tabbatar bata ci komai ba, haka dai ta tuttura, abban su kafun ya futa da kanshi ya kirata ya dinga K'arfafa mata gwiwa da ban hak'uri akan abinda yake faruwa, taji sanyi a ranta ba kad'an ba, koba komai ya bata sabon hope. Da yammacin ranar tana kwance a parlon su tana kallon wani series wayarta da take gefen kanta ta d'auki ringing, da sauri ta d'auko zata duba tunaninta ko Ayman ne ya tuna da ita yau, ko kuma Imran ne ya samu faragar kiranta in maman shi ta futa. Ba d'aya a cikin su, k'awar tace raheelatu, sai tayi picking da sauri tasa handsfree ta ajiye wayar a gefenta, sun gaisa cikin farin ciki tare da tambayar lafiyar juna da y'an uwa, sun d'auki lokaci k'alilan suna waya kafun suyi sallama, bata ajiye wayar ba saida ta kira Fatima itama suka gaisa taji lafiyar ta da y'an gidan su sannan, itama kamar raheela ta tambaye ta ya maganar bikinta, ta fad'a musu da saura zata fad'a musu in lokaci yayi. Taci gaba da kwanciya har bacci yayi nasarar d'auke ta, a cikin baccin ne kuma taji kamar ana kiran sunanta. Tana bud'e idonta taga ummie tsaye a kanta, saita tashi zaune tana mutstsitstsike idanunta, "kina son baccin la'asar d'innan raihana kuma bashi da amfani, kije Imran yana jiran ki a sitting room". Da mamaki tace, "Imran kuma? Toh yaushe ya futo daga asibitin?". Ummie da take kallonta tace, "toh ni ina nan taya zan sani?". Sai kuma ta mik'e sum sum ta shige d'akinta, hijab ta zubo zunbulele akan kayan jikinta ta yiwa auntie sallama ta nufi sitting room d'in. Yana zaune ya jingina kanshi da kujerar da yake zaune kai, idon shi a lumshe ya fuskanci sama, k'amshin turaren ta kad'ai yaji ya tashi zaune sosai ya zuba mata ido. Ta samu guri nesa dashi ta zauna ta zuba mishi ido itama, saida ta gama karantar yanayin shi gaba d'aya sannan ta sauke ajiyar zuciya tace, "ya jikin naka yaushe aka sallamoka ba labari". Shima ajiyar zuciyar yayi yace, "jiya da daddare, na kasa hak'uri raihana, na kasa hak'uri gaba d'aya shi yasa na taho na ganki, ko a gida ba'a san na taho ba daga tattaki na yo nan, Alhamdulillah yanzu kam tunda na tabbatar kina cikin k'oshin lafiya na samu nutsuwa". Yak'e raihana tayi Wanda yafi kuka ciwo, Imran ya rame kwarai sai dai ya k'ara haske, bawan Allah yana can yana mafarkin aurenta, maman shi kuma tana shirin raba su, yana asibiti yana jinya baisan har warning ta turo musu ba, ita dai kam data kalli idon wannan bawa me nuna kulawa gareta da tarin Soyayyah tace ta fasa auren shi, gwara ta aure shi duk abinda maman shi zatayi daga baya tayi hak'uri ta karb'a, dama ita tuni ta saddak'ar da rayuwar nutsuwa a gidan miji bayan aure, tasan yadda ummienta ta rayu cikin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali gurin dangin abban su itama haka zata rayu, sai kawai ta lumshe idanunta, tana karanta duk addu'ar da tazo bakinta a lokacin har Allah yasa ta had'iye kukan ta. Ta bud'e idonta akan Imran da yake faman tambayarta lafiya take kuwa, ta k'ara k'irk'iro wani murmushin tace, "lafiya Lou nake naji dad'in ganin ka dear a k'alla nima hankalina ya kwanta na tabbatar kaji sauk'i kamar yadda kasha fad'a mun a waya". Murmushin shima yayi yana ta kallonta, har kallon yaso tsorata raihana ta tafa hannu a saitin fuskar shi tace, "ya dai?". "Ina tunanin kwanakin da suka rage a d'aura auren mu ni dake, raihana yanzu a duniya bani da wani burin daya huce a d'aura auren nan na ganki a gidana matsayin matata, Kai Anya zan iya barci kuwa a wannan rana? Kwana zanyi Ina mik'a godiyata ga Allah subhanahu wata'ala, domin samun ki babbar nasarar rayuwata ne, rasa ki kuma zata zama mafi munin asara a tare dani?". Raihana sake lumshe idonta tayi tana jin shigar kowanne harafi cikin kunnenta, zancene na gaskiya da gaskiya Imran yake yi, abinda ya fad'a har zuciyar shi haka yake, wani irin dad'i taji a ranta koba komai idan Imran yana sonta zata samu wani sassaucin. Kusan duk hirar shi ta yau bayyana mata yadda yake sonta yake da alk'awarin kasancewa da ita muddin ranshi, saida raihana tace za'a iya neman shi a gida sannan ya tafi da kyar, don har waje ta raka shi tana d'aga mishi hannu. Ko data dawo Bata koma d'akin ba ta zauna a k'ofar kitchen inda ummie take aikin had'a abincin dare, shiru tayi kanta a k'asa tana tariyar kalaman Imran na yanzu a kwanyarta, "kin fara wannan tunanin naki ba?". Ummie ta fad'a tana kallonta, "a'a ummie me zan taimaka miki dashi". Kallonta tayi kurum sai kuma ta mik'o mata albasa a kwando da wuk'a, "yanka wannan ki zuba a naman can", ba musu ta fara yanka albasar kamar yadda ta umarce ta. Kusan tare suka gama girkin ta zuba wanda zata iya ci ta zauna, lokacin gidan ya cika da hayaniyar su jidderh da suka taso makaranta babu abin dake tashi sai sautin muryar al'ameen da muhibba, ganin sun hanata jin gari saita gudu d'akin auntie ta zauna kan drower mirrow tana cin abincin tana duba watsapp d'inta, hira suke yi da Imran don yanzu ba yawan waya sai text ko chat. Kuma dama ita bata son yawan wayar saboda bata fiya son takura ba, yawan d'aga waya kuma Yana daga abinda yake takura ta. _ranar da muke ciki, ci gaban labari_ Washe gari tana wankin gida d'an aiken malam yazo ya sanar da ita malam yace yana son ganin ta anjima zai bata wani sak'o. Da toh ta amsa taci gaba da aikinta, bayan tayi wanka, wata doguwar rigarta ta zura ta zauna a parlour tana karya kumallo tana kallon program d'in da akeyi a channel d'in da ta kama, ita da kallo bai dame taba sai gata yanzu bata iya zama shiru sai da tivi, koda yake yanzun ma ba komai take fahimta ba donta ragewa kanta tunani ne kurum. Bayan ta gama har ta kwanta a d'aki sai ta tuna da kiran malam, ta zura hijab ta rufe fuskarta da nik'ab ko wayarta bata d'auka ba ta fad'awa ummie kiran da malam yake mata ta tafi. Tana futa taci karo da matar wan babansu tsaye ita da wasu mata uku suna magana k'asa k'asa, umma salaha na ganinta ta fara nuna musu ita da baki, aikuwa duk matan suka kalleta, ita kam d'auke kanta tayi tana tunanin kamar taga wad'an nan fuskokin lokacin da taje duba Imran a asibiti, toh meya had'a su da matar Abba Abubakar kuma? Koda yake su suka sani ba damuwarta bace su k'arata can. A k'ofar gidan iya taga sabuwar mota, tasan maybe malam ko iya ne suka yi bak'i, har tayi nufin komawa sai kuma taga ita da zata karb'i sak'o bari ta shiga kawai aiba zama zatayi ba, tun a tsakar gida take kwad'a sallama, hango takalma a sitting room sai ta fahimci bak'in suna ciki, don haka kanta tsaye ta nufi d'akin iya tana fad'in, "nazo cin gyad'a". Iya da take aikin k'ulla gyad'ar ta sake baki tayi tana kallonta da fad'in, "wannan kuma waye haka? Ni har na manta dake ma". Tana k'arasa shiga parlon tayi dariya tare da zama a hannun kujera, bata d'aga nik'ab d'inta ba don ba zama zatayi ba, a haka suka gaisa da iya. Saida ta nutsu sosai ta ga Ayman a parlon, yana zaune ashe ta shigo yana jinta ya ganta da idon shi? Abun mamaki amma yayi kamar baisan da shigowarta ba? wato abun har ya ta'azzara haka? Anya kuwa ba wani laifin tayi mishi yak'i fad'a mata ba, k'arshe ya yanke alak'a da ita haka ba! Duk a ranta take wannan tunani, Har tayi nufin kyale shi sai taga kada su zama d'aya in shi ya manta da ita, ita ba zata tab'a iya mantawa dashi da tarin alkhairan shiba, zata bud'e baki iya ta riga ta da fad'in, "kinyi shiru raihanatu ya gidan ya maman ku? Fatan kowa yana lafiya". Sai ta sake murmushin da ita kad'ai tasan tayi abinta ta cikin nik'ab tace, "duk suna lafiyar su qalou, Ina me ran k'arfe d'azu ya aiko yana nema na ai". Iya tace, "yana ciki akwai lazimin da yake ya bada sak'on ki na ajiye miki don nasan shi kika zo karb'a da baza mu ganki ba sai in mun had'u a gurin biki, shine zaki zo hadda wani yimun siyasa wai kinzo cin gyad'a sai kace in an baki ci kike da gaske". Wata y'ar dariyar ta sake yi ta saci kallon khaleefa da zaton Ayman ne, wayar shi rik'e a hannun shi har lokacin kamar baisan da wanzuwar su a gurin ita da iyan ba. Abun yana d'aure kanta, Anya kuwa Ayman....... Maganar iya ce ta k'ara d'aukar hankalinta, "ki duba kitchen d'ina kan drower ta farko zaki ga jarka a bak'ar leda ki d'auko". Mik'ewa tayi har zata huce ta gaban khaleefa saita tsaya ta d'an lek'a cikin wayarshi k'asa k'asa muryarta tace, "Yaya Ayman yau ko magana babu? Hala chat kake da mutuniyar? To a mik'a sak'on gaisuwata gareta". Sai a lokacin khaleefa ya d'ago cikin takaici yaja mata tsaki! Har tayi gaba taji tsakin shi sai ta waigo ta kalle shi kanta a d'aure da al'amarin Ayman na yau "au wato abun har ya kai da yimun tsaki haka Yaya Ayman?" D'auke kanshi yayi ya kwantar bayan kujera ya rufe idon shi kamar me yin bacci, taff ta cika shi da takaicinta, a ranshi yake mitar shi Ayman kowacce ballagama kulawa yake, banda tsabar bata san abinda takeyi ba shi zata kalla ta kira da Ayman, ga wani k'arin takaicin ta wani nane fuskarta da wannan bak'in abun sai kace ita tafi kowa kyau a duniya, sai ya sake Jan wani tsakin idon shi a rufe still, iya data gane kan komai ce tace da raihana da take tsaye satoto da baki tana kallon khaleefa, "kema da neman maganar ki kije ki d'auko sak'on ki ki rabu da wannan". Har ta d'auko sak'on ta futo tana jin sautin tsakin shi a kunnenta, Wai Ayman ne yau hadda yi mata tsaki?. Kawowa iya sak'on tayi, ta fad'a mata rubutu ne malam yayi mata na kwana uku, ko bata samu damar futowa ba ta turo gobe da jibi a karb'ar mata, tsarin jikine dai. Har k'asa ta sake yiwa iya godiya kafun tayi mata sallama ta tafi. Tana futa Ayman yana futowa? har lokacin kare yake da waya yana magana da Nur, kusa da khaleefa ya zauna shi kuma ya tashi zaune sosai ya had'a kai da gwiwa, Ayman kamar wanda aka zabura ya shiga dube dube a d'akin, lokaci d'aya ya dakatar da wayar da yake yace, "iya raihana ta shigo gidan nan". Kallon shi duk sukayi kafun iya tace, "Kai mu ba wata raihana data zo mana, ka gama cin gyad'ar dana baka data Allah ya Isa?!". "ba maganar wasa iya da gaske raihana ta shigo gidan nan har parlon nan naji hakan a jikina". Abun har mamaki ya ba iya, so da yawa haka tasha faruwa tsakanin shi da raihanan, a duk lokacin da tazo ta futa indai bata fi minti ashirin ba yana shigowa zai fad'i cewar tazo, ta rasa ta yadda yake gane hakan. Shiru iya ta mishi madadin ci gaba da kula shi saita je dubawa khaleefa malam, tana futowa tace ma khaleefa, "ya gama zaka iya shiga ciki yanzun". Ba musu ya mik'e ya zura wayar shi a aljihun wandon shi ya nufi d'akin da malam yake". Ayman da yayi shiru kamar me tunanin wani abun arzik'i ta kalla ta tab'e baki, ta kasa fahimtar wannan majagular tasu Sam, taso ace lokacin da ta tab'a yiwa surayyah maganar Ayman suna soyayyah da raihana ya amince, tun kafun ta fara wannan makarantar, lalacewar maganar aurenta na uku, sai ya k'aryata, da yanzu shine zai aure ta ba wani ba, gashi yanzu tana lura da yadda yake shirin shiga wani yanayi na daban don zatayi aure, sukam suna taya ta murna, baza suso Kuma ta k'ara samun irin waccen matsalar ba a wannan lokacin. Khaleefa kuwa bayan sun gaisa da malam shiru yayi a gaban shi tankwashe da k'afafu kanshi yana kallon k'asan d'akin, "Ina jinka likita bokan turai fad'i abinda ya kawo ka don nasan wannan shirun akwai magana a bakin ka". Sake gyara zama yayi yace, "malam wata alfarma ce nazo rok'a gurin ka fatan zaka yi mun". Malam da yake kallon shi yace, "insha Allah khaleefa in dai ba abinda yafi k'arfina bane". Sai yaji kwarin gwiwa yaci gaba da fad'in, "wato malam wani k'ulli ne ya d'aure mun kuma duk duniya babu wanda zai kwance mun shi sai kai, shiyasa na taho kai tsaye gareka da kokon barana, Ina fatan zaka share mun hawayena da hannun ka bibbiyu, sannan Ina son maganar da zamu tattauna da kai ta zamo sirri bana son kowa yaji musamman ma auntie". Shiru malam yayi yana nazarin yaron, a kullum ya kalle shi sai yaga wata b'oyayyar baiwa ta daban a tare dashi wadda ba kowa yake iya gani ba, a zahiri surayyah suna kallon shi baud'ad'd'e amma yafi su tafiya sak. "Ina jinka khaleefa tuntuni nace ka fad'i buk'atar ta indai bata fi k'arfina ba .......". "Insha Allah! Malam zuwa nayi ka fad'a mun gaskiyar abinda yake b'oye a kan mu, ma'ana ka warware mun iya abinda ka sani game damu da mahaifiyar mu da marigayi mahaifin mu, nayi maka alk'awari wannan maganar da zamuyi indai ba kai ka fad'awa auntie ba zata zama sirri a gurina har abada babu mai ji". _toh fah! khaleefa yana son ya had'a jagwal tsakanin Ayman da raihana, shin ko malam zai fad'a mishi gaskiya gashi dai ya d'au alk'awari_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JvifMdt9UyYA2lbehzAMbO *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty six2️⃣6️⃣ Malam kam shiru yayi yana kallon yaron, tun suna yara da ana rigingimun nan ya fad'awa surayyah za'a iya samun matsala fa idan suka girma, tace ba wani abu zatayi duk yadda zata iya ta shafe musu zargin komai a ransu, ba zata bar musu k'ofar da zasu zarge ta akan wani abu ko dede da kwayar zarrah ba, kuma yasan tayi k'ok'ari wajen kula da yaran da tarbiyyar su kamar yadda ta alk'awarta, tayi aiki tuk'uru ba dare ba rana don ganin ta sama musu ingantacciyar rayuwa, ta basu tatacciyar tarbiyya wadda za'ayi alfahari dasu a cikin al'umma, sai dai yana ganin yanzu lokaci yayi da abinda take b'oyewa zai futo sarari, lokacin da zata nuna musu mahaifin su indai har yanzu bai mutu ba yana raye, koda ya mutu dole ta d'anka su ga ahalin shi, abinda ya faru baya ta hak'ura ta yafe mishi ta d'auka hakan a matsayin k'addarar ta kamar yadda ta d'auka tun farko, sai yaja gwauron numfashi, lallai wani abu mai girma yana tunkaro surayyah.... Gyaran murya yayi ya ajiye carbin hannun shi gefe ya fara magana da fad'in, "Toh fa wannan shi ake kira alk'awari kan alk'awari, a zahirin gaskiya khaleefa ba zan b'oye maka ba nayi alk'awarin bazan tab'a yin magana a kanku ba tun kafun kuzo duniya, ko a iya nan na tsaya nasan kasan girman alk'awari akan bawa idan ya d'auka, toh kaga kenan bazai yiwu na fad'i abinda na yiwa kaina alk'awarin bazan tab'a futar dashi ba, duk bama wannan ba ya kamata da farko nasan abinda yasa har kazo mun nan da wannan maganar bayan a shekarun baya bamu tab'a yin maganar da kai ba". Khaleefa kam tunda yaji maganar farko da malam ya fad'a yaji zuciyarshi ta karye, lallai ba k'aramin shiri auntie ta yiwa girman suba, sai kawai ya k'ak'alo murmushin yak'e a fuskarshi yace, "wato malam zahirin gaskiya naji hakane tun lokacin dana fahimci duniya taci gaba, kan mutane ya waye, yanzu ba da komai ake ado ba saida uba, na fara jiye mana tsoron sharrin mutane idan har akace yau munyi aure mun haifi y'ay'a, muma ana fad'in ba'a san asalin muba, ana kiran mu shegu kaga yaran mu sun zama y'ay'an shegu kenan?, zasu tashi ba k'ima ba daraja ana goranta musu a gari, shine kawai dalilin ba wani abu ba". Saida ya gama jinshi tsab sannan yace, "toh maganarka abun dubawa ce khaleefa, sai dai kayi hak'uri ka bani lokaci kad'an zansan ta yadda zan binciko maka abinda kake son ji Insha Allah". Khaleefa ya sake cewa, "na gode sosai malam Allah ya k'ara girma, sai abu na gaba bance lallai sai ka nemo mun wani abu data bunne bata son muji ba, kawai ka had'a ni da dangin mahaifin mu ko a b'oye ne sai naje na binciko komai ta yadda ba zata san kai ka fad'a mun ba don Allah na rok'e ka malam ko iya wannan alfarmar ce kayi mun.....". Ina ruwan sabatta juyatta, toh shi yasan dangin tane ma bare wasu dangin ubansu? uban da iya zaman su sun san dai ita kad'ai ba zata tab'a samar dasu ba faqat amma banda sunan shi har gobe ta k'i yarda tace wani abu a kanshi, shine yau za'a ce su fad'i inda za'a samu dangin shi?. Cikin hikima da son kwantar wa yaron hankali malam yaci gaba da mishi magana da hikima, "toh da yake kasan yadda rayuwa ta koma, anyi watsi dasu tsawon shekaru ko kamannin ku basu sani ba, yanzu kai tsaye ka tafi gare su ai abun saiya tashi kura, irin k'urar da mahaifiyarku ta nisanta kanta da ita tun tsawon lokaci, kayi hak'uri dai khaleefa mubi a hankali ta kanta har ta sauko ta yafe su a zauna qalou, tunda kaga a matsayinta na uwa dole mu bata hak'k'in ta, zuwa yanzu nasan ita kanta hankalinta ya kusa zuwa inda naka yaje, nan bada jimawa ba zata kai ku gare su da kanta dole,,, k'iris ya rage ka k'ara hak'uri dai". Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace, "toh Allah yasa malam,,,, nagode sosai da shawara insha Allah zan bi a sannu kamar yadda ka buk'ata". Malam yace, "yauwa Allah yayi maka albarka kaida d'an uwan ka da mahaifiyar ku gaba d'aya". Khaleefa ya amsa da, "ameen". Wani rubutu ya d'auko irin wanda ya yiwa raihana ya bashi jarka d'aya da wani a k'ok'o "ka shanye yanzu a gabana sai ka tafiwa Ayman dana jarkar" khaleefa ya karb'i bak'in ruwan tawwada a hannun malam yana k'are mishi kallo kamar zai ga wani abu ya lissafa ya futar mishi da branch branch, "shiyasa nace a gabana zaka sha saboda nasan halin bokayen nasara ba komai suka yadda dashi ba.....". Murmushi yayi ya d'auki kokon ya kafa a bakin shi bayan yayi basmala ya shanye rubutun ciki tass sannan ya ajiye kwaryar, lallai ba don kada malam yaga ko bai yarda dashi ba ko wani abu daban, da ba abinda zaisa yasha wannan rubutun, shifa duk wad'annan abubuwan bai yarda dasu ba tun da can, ko ciwo ne ya dame shi gwara yayi tofi, tofin ma yanzu baya sha sai dai ya karanta kawai. Malam ne ya katse mishi tunanin shi da fad'in, "Yaushe za'ayi maganar aure khaleefa kaga d'an uwanka cikin satin nan za'a kai kud'in auren shi". Ya kalli malam shiru kafun yace, "me auntie tace daka tambayeta ni nawa auren sai yaushe?". ""Kamar yana gurin mukayi magana da ita,,, malam ya fad'a a ranshi, a zahiri kam sai yace, "cewa tayi akwai wadda kake so amma da sauran lokaci kafun ka gabatar da ita". "Hakane abinda ta fad'a haka yake, akwai abinda nake son ya kammala kafun auren, ga maganar komawarmu Germany aiki". Malam yace, "au da gaske ne kenan da tace kace mata zaka koma aiki can k'asar masu jajayen kunnuwa inda ka futo?". Khaleefa yace, "da gaske ne malam sai dai naga kamar batayi na'am ba". Malam ya gyara zama, "ba amincewa ne batayi ba, hankalinta ne yake tashi a duk lokacin data tuna kana son barin k'asar nan zuwa wata uwa can duniya ba matar aure, nima kuma abinda bai kwanta mun ba kenan, ba wai muna yi maka kallon wani mutum marar nutsuwa bane, a'a nayi Imani ko kafun ka dawo muna da kyakkyawan yak'ini a kanka zaka rik'e kanka bisa jagorancin nutsuwarka da addinin ka, yak'inin da nake dashi a kanka bani dashi akan Ayman d'an uwan ka, nasan zaka iya rayuwa a k'asar da babu namiji ko d'aya tsakiyar mata ba tare daka fad'awa haramci ba, toh amma duk da haka shi aure daban ne, martabar shi daban ce, mutum baya cika cikakke idan babu mace a gefenshi duk kud'in shi duk ilimin shi da limancin shi kuwa". Wani irin nauyi khaleefa yaji a kanshi kamar malam ya d'ora mishi wani mugun gungumen dutse, kalaman shi sun mishi nauyi aka, sai yake ganin kamar malam yasan irin haramtacciyar soyayyar da sukayi shida Saleema a k'asar Germany, wadda yayi imanin da sunsan akwai idon wani da suke shakka a kusa tare da ba zasu fara kai ga aikata abinda sukayi ba, tun wancen lokacin sai yanzu yaji wani abu mai kama da nadama ta tsirga mishi karo na farko a tarihin soyayyar shi, sai yake ga kamar a gaban malam suke love romance shi da Saleema watanni kad'an da suka gabata, iska ya furzar me huci daga bakin shi ya gyara zaman shi da kyau yace, "malam da gaske auntie tana nufin zata amince idan har na gabatar mata da matar dazan aura?". Malam da yake sake nazarin duk wani motsin shi yace, "Ina kyautata zaton haka, Allah yayi muku jagora a dukkan al'amuran rayuwar ku". Ya amsa da "ameen". Daga nan basu ja wani dogon zance da tsayi ba ya yiwa malam sallama ya futo. Iya kad'ai ya tarar a parlon, a tsaitsaye itama yayi mata sallama ya tafi, ta raka shi har tsakar gida tana mitar baza su tsaya suci abinci ba gashi ta kusa saukewa. Khaleefa yana tafiya kad'an yace, "yanzu Ina sauri ne sai wani lokacin iya kada ki damu". Addu'a ta mishi suka k'arasa sallama ya huce, shi ya manta ma tare da Ayman suka zo saida yaci karo dashi akan dakalin k'ofar gida ya zubawa guri d'aya ido, "yaeh zamu tafi ne ko a nan zan barka?". Khaleefa ya tambayi Ayman, sai ya mik'e zaune yana karkad'e k'urar kan gurin daya zauna yace, "a'a mu tafi kawai". Wannan lokacin khaleefa ne yake driving Ayman a gefen shi, tafe suke kowa da abinda yake tunani a ranshi har suka k'arasa gida. Kamar a haukace haka khaleefa ya dinga had'a stairs bibbiyu yana tsallakewa har ya haura saman, auntie da mama haleema suna zaune a parlour sai wasu mata uku bak'inta, kaya ne da yawa zube a gabanta tana y'an rubuce rubuce da lissafin kaya, da farko d'auke kanshi yayi zai huce saida mama haleema ta kira sunan shi, ya saita yanayin shi kad'an ya dawo da baya ya gaishe da matan, Ayman da yake bayan shi sai lokacin ya k'arasa shigowa parlon, shima ya gaishe su, sai suka saki baki suna tambayarta dama twins ne d'an tannan namiji, murmushin yak'e kawai ta musu ta k'ara nazarin su d'aya bayan d'aya musamman khaleefa da kwayar idon shi ta soma sauya launi, ganin yadda take duban shi saiya tambayi mama haleema, "kina nema na ne" Mama haleema tayi y'ar dariyarta tace, "a'a auntie ce take son ganin ka, yanzu tasa na duba ka ashe kun futa kaida Ayman". Kallon auntien yayi, tace, "ka jira ni a d'akina". Bai bata amsa ba ya huce d'akin nata shi kuma Ayman ya tambayi mama haleema ko Nur tana nan, tace, "a'a sun tafi da mammie". Har ya tafi saiya juyo, "shaheeda fa". "Ina tunanin ita wannan ta tafi makaranta ne". Khaleefa tun kafun ya d'aga labule k'amshin turaren d'akin ya shiga kafofin hancin shi, har yanzu auntie tana nan da wannan k'amshin nata, shiba mai sanyi da yawa ba, bame hawa kai ba, k'amshin turare ne me sanya nutsuwa da kwantar da hankali, saman sofa ya kwanta tare da lumshe idon shi yana shak'ar daddad'an k'amshin daya jima da kama komai nata, a hankali nutsuwa ta soma saukar mishi har yaji yayi k'asa sosai ba b'acin rai da tashin hankalin nan da suka tsiro from no where, shi dai malam ba zagin shi yayi ba, ba fad'a ya mishi ba magana kawai sukayi, maganar ma da kwantaccen murya bada gargagi ba, amma tuno saleema kawai da yayi yasa duk yanayin shi ya zama haka, d'an k'aramin tsaki yayi a fili kamar me magana da wani yana tuna yadda ta iya rufe ido ta fad'a mishi maganar da bai tab'a zato bare tsammani ba, har yanzu ya kasa tantance a ajin da zai ajiye Saleema,,, bare ya fahimci tarin soyayyar da kullum take kururuwar tana yi mishi. Well shikam yana sonta kuma baya jin zai iya barinta no matter what,,,,, Da wannan tunanin bacci b'arawo ya sad'ad'o yayi wuff dashi. Auntie kam saida ta sallami kowa suka d'auki kayan da zasu karb'a suka tafi sannan tasa mama haleema ta had'a musu lunch saboda sameera tana dawowa anjima. Da fuskarshi ta soma tozali, bacci yake amma ranshi a b'ace sai cin d'aci yake, a kusa dashi ta zauna ta d'auki kanshi a hankali ta mayar kan cinyarta ta dafa kanshi tana k'are mishi kallo na tsab da tsanaki kamar zata iya fahimtar damuwar shi, tabbas Suraj yayi gaskiya ya mata illar da ba zata tab'a iya mantawa dashi ba, amma kuma ya bata kyauta, kyautar da zata dinga kallo tana godewa Allah a duk ranar duniya, wad'annan yara guda biyu tana jin ko kanta bata so yadda take son su yanzu, zata iya hak'ura da komai ta sadaukar da komai, ta rayu babu dangin iya bare na baba a duniya mabanbanta indai tare da sune, tana son su tana k'aunar su Allah ma ya sani, sune sanadin baro kowa da komai ta taho zuwa wannan rayuwar. Ta manta da soyayyar Suraj tuni, haka ta manta da wawakeken ramin daya gina a cikin zuciyarta, ta shafe babin shi a cikin rayuwarta ya zamo tarihi, sai dai ta kasa mantawa dashi kamar yadda ya fad'a a rana ta k'arshe da zasu rabu, Allah ya azurtata da yara biyu sai dai basu d'auki komai nata ba, sai guda d'aya daya keda irin d'abi'un ta da sanyin halinta, amma don khaleefa ko motsi yayi Suraj take gani a tare dashi, yanayin sa! Tafiyar sa! Maganar shi ta kai tsaye! Da miskilancin shi na maida kowa ba kowa ba da baud'ad'd'en ra'ayin shi duk na Suraj ne! Saika rayu da Suraj tsawon lokaci bakasan abinda yake cikin zuciyar shiba, da irin haka itama ya zurma ta ta d'auka da gaske yana sonta, ta saki jiki ta afka kogin soyayyar shi, ta saki jiki dashi k'arshe ya kaita ya baro ta...... Wasu irin zafafan hawayen takaici da bak'in ciki ne suka dinga futa daga idanunta suna sauka kan fuskar khaleefa da kanshi yake saman cinyarta, tun tana kukan silently har ta gagara, k'arshe haka ta duk'ar da kanta ta dinga kuka, amma da yake khaleefa yayi nisa a duniyar bacci duk wannan abun bai jiba, Saida tayi kukanta son rai sannan ta fara magana da raunatacciyar murya, "Allah ya Isa tsakanina da kai Suraj! Allah ya Isa tsakanina da hauwa data kasance ummul'a'ba'isin fad'awa ta cikin wannan rayuwar, da yanzu Ina rayuwata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali tare da yayana sauban". Wani kukan ta sake fashewa dashi kafun ta tsagaita ta d'ora da maganarta, "Ashe d'an Adam zai iya aikata kuskure sau d'aya hukuncin yayi ta bibiyar shi har k'arshen rayuwar shi? Wayyohh Allah ni surayyah......". Yadda take kuka da sambatu saida ta bani tausayi. Haka ta gama kukanta ta rarrashi kanta da kanta tayi shiru, wayar khaleefa da take gaban aljihun shi ta d'auka, tunda ya dawo ta kasa gane kanshi, yanzu lafiya anjima ba lafiya ba, tayi iya yinta amma ta gaza, shine yau zata yi abinda bata tab'a aikatawa wani a rayuwarta ba wato *bincike*. Wayar ba tsaro ko d'aya, kan fuskar wayar tana dannawa hoton wata kyakkyawar yarinya ne fata sol, half d'inta ne amma duk da haka tayi kyau kwarai, hoton anyi shine cikin flowers tana watsa musu ruwa tana dariya, kayan jikinta farare Sol. Ta jima tana kallon yarinyar kafun ta fara tafiya kan applications na wayar, ba game ko d'aya ba duk wasu kafafen sada zumunta na social media, de de da watsapp babu shi a ciki, toh me zata bincika ta gano bakin zaren matsalar d'an nata, wata zuciyar ce tace ,,ki shiga ma'adanar hotuna mana,, aikuwa tayi na'am, hotuna iri biyu ne dashi kacal, daga wattsapp image sai na camera, na watssapp d'inshi ta shiga sai dai yak'i bud'ewa watak'ila saboda ya goge watsaapp d'in ne ko kuma wani dalilin oho, saita koma na camera, eqyawanci duk pics d'inshi ne, wasu taree da Ahmad wasu da matasa abokan karatun shi su da yawa haka! Wasu kuma a gurin surgery, duk gasu nan dai kuma kaf ciki babu inda ta ganshi da mace shi kad'ai sai ko suda yawa a cikin lab ko wani gurin practice da duka course mate d'insu, mafi yawa ma su bakwai take ganin sunyi rukuni duk maza, har ta fudda tsammanin samun wani abu sai taga wani folder tsakiyar camera pics d'in. Tana bud'ewa ta fara tozali da wani hoto da sukayi kan bridge, hoton basu suka d'auke shiba yi musu shi akayi, Saleema ce tsaye khaleefa yana tsaye gab da ita kamar zasu shige jikin juna, ya rankwafo da fuskarshi kad'an hannun shi da k'afar shi tokare jikin k'arfen gadar da take jingine, duka suna sanye da kaya farare k'al, hannunta rik'e da red flowers, daga kallon da suke jifan juna auntie da take neman bakin zaren ta samu zaren gaba d'aya. Ta jima tana k'arewa hoton kallon zuciyarta na tsananta gudu, sai ta fara tambayar kanta, wace irin rayuwa khaleefa yayi a Germany? Wacece wannan yarinyar da suke kallon juna haka tsirara, ko a iya nan ta tsaya zata iya fassara wannan soyayyar tasu da haramtacciyar soyayyah, har zata d'ora hannunta ta jawo hoto na gaba sai ta dakata, ""Wala ta jassasu"" zuciyarta ta kwab'e ta, "akul kefa uwace, bai kamata ki dinga tsananta bincike akan abinda ya zai d'aga miki hankali ki kasa zaune ki kasa tsaye, baya ga haka kowa yana da personal secret nashi da baya so wani ya gani, watak'ila khaleefa shima hakane". Sai ta rufe mishi wayar ta mayar da ita inda ta d'auka ta zuba mishi ido tana kallon shi da zarge zarge iri iri a kanshi, tsoronta d'aya kada tarihi ya maimaita kanshi..... Duk wahalar da tasha akan su, tak'i aure ta sadaukar da gaba d'aya lokacin k'uruciyar ta saboda su da lokacin ta data k'arar wajen ganin ta basu tarbiyyah irin wadda kowacce uwa da tasan kanta take bawa yaranta ta tashi a banza ko me? koda yake hadda soyayyar Suraj ta hanata aure, duk namijin data kalla sai taga kamar be kai Suraj ba, a hali da dabi'a da tsarin tafiyar da rayuwa Suraj yayi mata karantsaye tako ta ina, duk da kasancewar shi bahagon mutum haka take son shi har kwanan gobe, da farko tana tunanin saboda abinda ya had'a su ta daina sonshi, amma daga baya ta fahimci soyayyar shi a jinin jikinta take sai dai ta mutu da ita amma bawai ta cire ta daga rayuwarta ba. "Allahumma ajirni fil musibati.... Waklifni khairan minha". Ta fad'a da k'arfi a fili tana zubda sabon hawaye A haka Ayman ya shigo parlon ya same ta, aikuwa tayi saurin share hawayenta da duka hannuwanta, tayi k'asa da kanta kamar wani abu ya fad'a mata ido. Shima yau jikin shi a sanyaye yake ya k'araso har gabanta ya zauna ya d'ora kanshi jikin k'afarta ya fashe da kukan da shi kanshi baisan takamaiman na meye ba, ji yake a duniya in bai futar da abinda yake ji game da raihana ba a wannan karon bazai tab'a samun nutsuwa ba. Ngd da addu'o'in ku mah fans, Ina ganin tarin comment d'inku na K'arfafa gwiwa na jinjina muku kyauta😍👍👍👍 _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty seven2️⃣7️⃣ A hankali auntie ta soma k'ok'arin zame kan khaleefa daga cinyarta, sai dai ya hana mata damar hakan ta hanyar rik'e hannuwanta kamar me rok'o yana magana k'asa k'asa, saida tasa kunne sosai sannan taji abinda yake fad'a, "kada ki tafi, don Allah kada ki tafi kema ki barni..... rayuwata bata tab'a shiga rud'ani ba sai datsin had'uwa ta dake, sannan kin zamo kamar haske me yaye duhun dake cikin zuciyata.... Don Allah ki kasance tare dani har k'arshen numfashin mu..... Duk da kina ganin har yanzu bansan meye so ba, amma indai abinda nake ji a kanki shine Soo! Toh tabbas Ina sonki! Ina sonki so me tsanani!! Auntie tana d'ago kanta yana mik'ewa zaune firgigit kamar wanda aka zabura, doctor surayyah ta bishi da kallo, shima kallonta yake yana yamutsa sumar kanshi da fuskarshi, abinda ya kanyi a duk lokacin da kanshi ya d'au chargy, a lokaci guda kuma ya zaro wayarshi ya duba hoton Saleema da yake kan fuskar wayar, saiya fara sauke ajiyar zuciya ajejjere atleast yasan zai sameta watarana wancen kawai mafarkine. Ayman kam kuka yake baji ba gani kamar wanda aka turowa da sak'on mutuwa, sai Auntie ta dawo da hankalin ta gare shi ta d'ago shi kusa da ita cikin kulawa take tambayar shi abinda yake faruwa dashi, bai iya ce mata komai ba sai share hawaye da yake, sai suka jefa auntie a rud'ani ta rasa dawa zataji a cikin su, Ayman da yake kuka ko kuwa khaleefa da ya d'ora hannu aka yana jujjuya kai kamar wanda aka turowa da wani mummunan sak'o, kawai data rasa yadda zatayi sai ta fashe da kuka, a mugun gigice da d'imauce duk sukayi kanta suna tambayarta lafiya take kuwa? Sai a lokacin khaleefa ya fahimci kuka Ayman yake d'azu kenan? Shi kuwa Ayman dama da muryar kukan yake bata hak'uri, khaleefa ma ji yayi zuciyarshi ta tsinke, amma dai ya daure baiyi kukan ba sai basu baki ita da d'an uwanshi, da haka suka lallab'a ta tayi shiru. Khaleefa ta fara tattarawa duka hankalinta ta tambaye shi meye damuwarshi, me yake bibiyar rayuwarshi, cikin dakiya da shanye komai yace, shi babu wani abu da yake damun rayuwar shi, tasan bazai fad'a ba ko zatayi me, don haka sai ta koma ga Ayman, "kaifa meye sanadin kukan naka?". Shima Ayman kukan da yayi yasa yaji sanyi ba kad'an ba, sai yaji damuwar tashi ta lafa har yaji ya hak'ura da fad'a mata abinda yayi niyyah da farko, to amma don ya kwantar wa da auntie hankali sai yace, "auntie yaushe za'ayi maganar auren mu da nuriyyah?". Saida ya fad'a ya fahimci sub'ul da bakan da yayi, sai ya basar ta hanyar wulla kanshi gefe kamar bashi yayi maganar ba, duk da auntie bata cikin mood d'inta sai da tayi dariya, tasan Ayman ya dad'e yana son aure ita da malam sun dak'ile shine kawai saboda khaleefa, yanzu kuma tunda taga khaleefa yana Shirin yin wala wala ba zasu k'ara tsayawa jiran shiba, auren shi zatayi mishi, hannunta ta d'ora a kanshi da cool voice tace, "nasan kana son aure tuntuni Ayman ko baka fad'a ba, sannan kana son Nur ma, shiyasa nake son anjima kad'an sameera tana zuwa zamu k'arasa tattaunawa da ita akan maganar auren ku insha Allah, murmushin jin dad'i yayi ya yima auntie side hug yana dariya, shima khaleefa kanshi ya d'ora a d'aya b'angaren kafad'ar ta yana murmushi cikin jin dad'i yace, "congrats Man!". Ayman mak'e kafad'a yayi yana dariya. Haka suka tsinci kansu cikin farin ciki kamar basu ne suke zaune a bai bai tun ranar da khaleefa ya dawo har zuwa jiya ba. A nan haleema ta kawo musu abinci suka ci su uku, Ayman yana ta zolayar khaleefa da son yaga ya tunzura shi, shi kuwa gogan ya fuske abinshi yana cin abincin shi ko kallon shi beyi ba. Da yammacin ranar kamar yadda sameera tayi alk'awari sai gata bayan ta dawo daga gidan sunan data halarta, a bedroom d'in Auntie na sama suka k'ule suna tattaunawar sirri, inda surayyah take mata magana cikin tsantsar farin ciki, "k'awata maganar muce ta taso fa?". Sameera itama cikin farin cikin tace, "Toh doctor surayyah wacce magana kenan? naga tunda nazo yau bakin ki yak'i rufuwa". "Ba dole ba! Ai yau bakina bazai rufu ba mammie, maganar auren Nur da Ayman nake miki kinsan d'azu na fad'a miki yadda mukayi da khaleefa too zan ajiye maganar shi a gefe har zuwa lokacin da zai sake d'auko mun maganar zai koma inda ya futo, a lokacin ne ni kuma zan murza kambu na, shi kuma Ayman bazan tauye shiba, a fad'awa mahaifin Nur gobe insha Allah su malam zasu zo da dukiyar auren su, nan da 4weeks ayi biki tunda already an gama shirya komai, har na yiwa malam d'in ma waya" Saida gaban sameera ya fad'i da taji abinda ya futo bakin k'awarta a yau, sai ta tsaya kawai tana kallonta da sakakken baki, wato saboda y'ay'anta y'ay'an mace ne shine take tunanin itama nata yaran hakan take, toh duk lalacewar mahaifin su matsayin mahaifin su yake bata tauye masa hak'k'in shi akan yaran shiba, d'awainiyar suce da yaji bazai iya d'auka ta yau da kullum ba ita ta d'auka har shima zai shiga ciki ya samu mafaka albarkacin yaranta. "yaa k'awata tunanin me kike kuma?,,,,,". Saita sauke ajiyar zuciya a b'oye ta sake kalmashe k'afarta a gaban k'awar tata, "Ina jinki likita yadda kike so haka za'ayi, sai dai wani hanzari ba gudu ba yau mun share a k'alla shekaru talatin ba kad'an tare cikin aminci, kinsan ni! Kinsan asalina! Kinsan mijina! Kinsan iyayena! Babu wani abu b'oyayye ko bak'o da baki sani a tare dani ba, sai dai ta b'angarena ni ke kad'ai na sani sai su iya, har yau ko a sub'utar baki, baki tab'a fad'a mun labari d'aya daya danganci mijin da kika tab'a aure ba, duk da yadda mutanen gari suke munafuncin ki da yaranki hadda su iya ma amma baki tab'a bani labarin wani abu da zai warware gaskiya ba, shin surayyah baki ji kin aminta dani a iya tsawon wad'an nan shekarun bane?". Tunda sameera ta fara magana surayyah ta tsaya tana kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa farat d'aya, sai take ganin kamar ba sameera data sani ce yau keyi mata wannan maganar ba, koda yake fiye da haka ma zata tambaya tunda itama d'an Adam ce me numfashi kamar kowa. Sai ta d'auke idon ta gefe ta mik'e tsaye ta goya hannayenta duka biyu a bayanta, taku biyu zuwa uku tayi ta tsaya a tsakiyar parlon ta soma maganarta cikin murya mai nuna tsantsar b'acin rai, "kin fad'i gaskiya sameera, tabbas bai kamata ki d'auki y'ar ki Nur kiba d'ana aure rana tsaka mu gudu miki da ita inda ba zaki sake ganin ta ba, k'arshen butulci, nasan wannan shine tunanin ki ba? In ba haka ba kuma kada kije ki had'a zuri'a da yaran da basu da asali cikakke bari na ari kalmar taku *shegu*. Nasan dai abu biyun nan ne suka sa kike son kisan wani abu daya danganceni nida yarana,,,,, Toh sai dai Ina so ki san cewa tarihina wani shud'ad'd'en al'amari ne dana dad'e da binne shi cikin k'ark'ashin k'asa ya nitsa can k'asan k'asa, ban tab'a bawa baki amanata ba komai amincin da muke yi da mutum kuwa, saboda duk maganar da ruhi yaji bakin shi baya iya hak'uri watarana sai ya furta ta, Soo try to understand bake kad'ai ba a tsawon wad'an nan shekarun dama sama dasu ban tab'a bawa wani tarihin rayuwata ba ko na yarana,,,, tun yana raye a cikin zuciyata har zuwa yanzu daya mutu ma..... Idan kin yarda dani ki tsarkake ranki ki futar da maganar mutane a cikin zuciyarki mu k'arasa ladan mu...." saita k'ara takowa ta durk'usawa gaban sameera ta dafa kafad'arta, "mu manta da waccen maganar k'awata shin kin amince zaki bawa Ayman auren Nur?". Shiru sameera tayi tana kallonta da tsantsar mamaki da zargi kala kala, lallai akwai k'amshin gaskiya a maganar tafeeda k'awarta, duk tushen da aka cika b'oye shi bashi da kyau, toh amma yadda surayyah take da mutumci da taka tsantsan da maza ko ita bata dashi haka,, sau da yawa in suna tafe tare maza da yawa sunsha kawo mata hari, tun kafun tayi shekarun haka ma a lokacin da take ganiyar k'uruciyar ta, manyan mutane masu fad'a aji kuma, amma bata tab'a kulawa ba bare har ta shaide ta akan bariki, idan kuwa har a yanzu tana kyamatar had'a alak'a da duk wani namiji shaida ce da take nuna lallai da k'uruciyar tama batayi barikin ba, toh y'ay'anta in hakane ba zata kira su kai tsaye da shegu kamar yadda mutanen gari kan kira suba, toh amma kuskure d'aya fa! A lokuta da yawa idan suna hira sai taji tana bada misali da kuskure d'aya da mutum in yayi har ya k'arashe rayuwar shi gaba d'aya yana karb'ar sakamako...... Sake kallonta sameera tayi, idonta ya ciko da hawaye yana sauka d'aya bayan d'aya kan kuncinta, amma kwayar idonta wani irin bak'in ciki da b'acin rai ne ke kai komo a cikinta. Sanin maganarta a yanzu ba k'aramar kwab'a zata jik'a ba, sai ta d'auki Jakarta da mukullin motarta ta mik'e tsaye tana kallon surayyahn, "Ina ganin mu ajiye maganar auren yaran nan a gefe, idan har babu Amana to banga amfanin k'awance ba, ki zauna kiyi dogon tunani akan maganata, banyi haka da nufin yi miki butulci ba, har abada bazan manta tarin alkhairan ki a gare niba doctor surayyah, saboda kin taimake ni a lokacin da kowa yake guduna saboda ana ganin na zama wahala, a lokacin da nake tsakanin rayuwa da mutuwa, a lokacin da takaicin d'a namiji yake neman shafe tarihina a wannan duniyar, kece dai doctor surayyah mace d'aya tilo da ban tab'a ganin me kyawun zuciya da yin abu domin Allah kamar ta ba, amma haka ba yana nufin bakya kuskure ba, tabbas kinyi kuskure, duniya taci gaba haka mutanen cikinta, ki ajiye b'acin ran da yake zuciyar ki, ki nemo dangin mahaifin yaran ki su sauke nauyin da Allah ya d'ora musu na aurar dasu, domin sune a hak'k'u dasu aikata haka......" Sameera tana gama maganarta tayi gaba, sai dai har ta kusa futa daga parlon surayyah ta biyo bayanta ta rik'e rigarta ta baya, da muryar kuka take magana yanzu, "har abada!!! Indai sai na koma ga Suraj da ahalin shi zaki bawa Ayman auren nuriyyah toh Allah ya had'a kowa da rabon shi.....". Tana gama maganarta ta saki mata rigar, itama sameeran bata juyo ba saboda zuciyarta zata iya karyewa in ta ganta tana kukan nan, haka ta huceta a gurin, ta shiga motar ta da take parkee a k'ofar gida ta bata wuta a guje tabar arean anguwar. Haleema da take sak'a a cikin parlon auntien a gabanta surayyah ta biyo bayan sameera ta furta mata wad'annan maganganu dai dai k'ofar bedroom d'inta, ta tabbatar wani abu marar kyau yana faruwa, sai ta ajiye k'ulun hannunta ta mik'e ta nufe ta, sai dai tun kafun ta k'araso ta d'aga mata hannu, ta shige d'akinta da gudu ta murza keeyyy. Kan gadonta ta fad'a ta fashe da wani irin kukan mai ban takaici da cin rai. @@@@@@ A yammacin ranar iya da malam suna zaune kan tabarma tare da bak'in su don su kawo dai daito tsakanin su, neman yafiyar malam suke akan biriskullen da sukayi dashi a shekarun baya, hakan ya samo asaline daga rashin fahimtar shi da sukayi, malam da yake jinsu yace, "ya huce har abada mun yafe muku tuni, dama kuma bamu tab'a rik'e ku da komai ba". Malam yana ajiyewa iya da take jira ta d'auka, "A'a malam kai dai ka yafe musu bani ba..... Don nikam bazan tab'a yafe musu b'ata mana suna da sukayi a k'auyen nan ba, kuma wallahi ba wata nadama da sukayi, saboda sunga ka samu abun duniya suka lallab'o suka dawo zasuce wani a yafe musu, ba wani nadama ni ba abinda zan sake saurara a gurin su, neman hanyar da zasu k'ara cutar damu kawai suke". Tana gama maganar ta kakkab'e jiki ta tashi tabar musu gurin, harira zata bi bayan ta malam yayi saurin d'aga mata hannu, "rabu da ita yanzu ta d'au zafi ba zata fahimce kuba, in ta huce anjima zata fahimta a hankali". Sai Suka koma suka zauna tare da gyad'awa malam kai cikin nadama mai tarin yawa. Da daddare tana zaune a cikin d'akinta malam yazo ya sameta, zama yayi a gefenta aikuwa ta sake d'aure fuska ga zaton ta ko maganar su harira yazo yayi mata, sai taji sab'anin hakan daga maganar daya fara, "wani abu mai girma yana tunkaro surayyah". Sai ta sassauta fuskarta ta kalle shi, "tun kafun khaleefa ya dawo kake fad'ar haka ni na kasa fahimtar me kake nufi". Malam jinjina kai yayi yace, "Ni kaina bansan meye ba abinda na fad'a miki shi kad'ai nake ji a jikina, shiyasa cikin satin nan nake tsananta addu'a ta akanta da yaranta, sannan Ina ganin lokaci yayi da abinda take b'oyewa zai futo sarari, lallai lokaci yazo da zata futar da abinda yake ranta take b'oyewa tsawon shekaru". Shiru iya tayi tana jinjina al'amarin, duk abinda malam ya jinjina shi ya sake jinjina shi lallai ba k'aramin abu bane, toh ita dai tana fatan Allah yasa alkhairy ne zaisa ta fallasa abinda yake b'oyen. Itama sai tabi da addu'a kawai, "yanzu yaushe zaku kai kud'in auren Ayman d'in?". "gobe insha Allah amma zan jira naji daga gareta kafun nan". Allah sarki Ayman Allah ya tabbatar da alkhairy yasa abokiyar arzik'in shice, ni khaleefa naso ya fara yin auren ma wallahi". Malam yace, "toh shima dai yana hanya mu taya shi da addu'a kawai". Daga nan suka rufe wannan matter, suka shiga wata. ************ Sameera kuwa tana Isa gida wayar shaheeda ta fara kira, cikin sa'a ta d'aga, "kina Ina?" Ta jefa mata tambayar kai tsaye, "mammie yanzu na futo daga makaranta" "toh maza ki taho gida yanzun nan". Daga nan d'akin nuriyya tayi, ta sameta zaune tana chat a waya, "mik'o mun wayarki" ba musu ta bata, tana karb'a ta futa daga d'akin, shaheeda ma tana zuwa wayarta ta karb'e ta had'a data Nur tayi switch up d'insu ta adana su a d'akinta. Duk saita jefa yaran cikin tunanin abinda yake faruwa. Suna nan zaune a parlonta tsuru sun kasa yin komai saboda tsorata da sukayi da yanayinta har baban su ya dawo, heedaya ce ta fara taryar shi tana fad'a mishi mammie tana ciki tace bata son kowa ya dameta, tambayar shaheeda yayi, "Wai hakane?". Shaheeda tace, "eeh Abba tun d'azu take rufe tak'i cewa kowa komai". "toh Ina haeydar kuma?". "bai dawo ba". Suka bashi amsa kusan a tare, Lokaci ya duba yace, "har yanzu? Toh meya tsaida shi?". Babu wanda ya bashi amsa cikin su, sai ya nufi d'akin da take ya murd'a handle ya shiga, tana kwance a k'arshen gado ta zubawa kasan d'akin ido, kan drower kusa da ita ya zauna y zuba mata ido yana kallonta, daga yanayinta ya tabbatar yau ranta a mugun b'ace yake. Sai ya kira sunanta bada hargagi ba cikin kwantaccen sauti, da kyar ta iya amsawa, yaso da farko ya rabu da ita amma kasancewarta mai kula dasu da walwalarsu a gidan sai yaji bazai iya share ta yana kallonta cikin damuwa ba, koba komai masu iya magana sunce gaida me gaishe ka, ko bazai amsa ba. "me yake damun ki sameera?". Sai ta tashi zaune ta kalle shi tace, "damuwa ta ba wadda ta shafe ka bace, kuma kona fad'a ba zaka iya yimun maganinta ba, toh abinda zaifi don Allah ka barni inji da abinda yake damuna kawai". Kamar ya tashi still dai kuma sai ya kasa yace, "kina ganin wannan itace amsar daya kamata matar kwarai ta ba mijinta?". Bata ce mishi komai ba sai ya sake kiran sunanta, "sameera!" Ta amsa mishi tana kallon shi, "ki fad'a mun meye damuwarki". Sai data nisa sosai kafun ta labarta mishi duk yadda sukayi da surayyah d'azu, shi kanshi abun ya d'aure kanshi, gaba d'aya da ita da k'awartata basuyi tunani ba, sai ya gyara zama don ya kawo musu gyara da maslaha, "duka kunyi kuskere sameera, amma naki kuskuren yafi nata". "dama nasan haka zakace wallahi, kai komai nayi sai kace banyi dai dai ba, kana nufin Ina ji Ina gani saina d'auki y'ata na ba d'anta auren shi bayan ta b'oye mun asalinta mun shafe tsawon shekaru tana nuna min halin rashin yarda.....". Saida ya bari takai Aya sannan ya fara magana, "Toh ai baki bari kinji abinda zan k'arasa fad'a ba kawai kin hau fad'a, ni ba Ina nufin ki bata auren Nur ba, wannan tunanin tun farko ya kamata kiyi shi, tabbas itama bai kamata ta b'oye miki komai a yadda kika d'auke ta ba, sirrin ki komai kin d'anka a hannunta amma ita bata tab'a yarda kinji komai nata ba, tun a lokacin da kuka shirya auren Nur ya kamata ki mata tambayar da kika yi mata yau, abu na gaba kuma iya zaman ki da surayyah kin tab'a kamata da wani abu na laifi kamar ballagazanci ko wani abu makamancin haka.....?" Shiru tayi batace komai ba, sai yaci gaba da maganar shi, "toh kinga ashe ba zaki d'auki wancen zargin zuwa kanta farat d'aya ba, watak'ila akwai abinda take b'oyewa yaran da bata son yaje kunnen su shiyasa bata tab'a yarda da wani dan Adam me baki ta fad'a mishi sirrin taba, a family ai ba'a rasa rigingimu tsakanin matar da aka auro da dangin mijinta, maybe itama hakan ne, shiyasa tak'i yarda su san dangin uban su tunda uban ya mutu take ta fad'i tashi dasu ita kad'ai..... Toh yanzu da kika hana auren ma ya zakiyi da yaran da Suka zurma cikin son junan su...". Abun duk saiya taru ya yiwa sameera yawa, ta rasa da wanne zataji, tabbas ta yiwa ranta alk'awarin ba zata tab'a bada y'arta ga mace ba, Dole ta nemo dangin uban su suma ta basu hak'k'in su da Allah ya d'ora musu akan yaran. Sai taja dogon ajiyar zuciya, "Allah ba zan bawa Ayman auren Nur a hannun surayyah da malam ba, saboda shi kanshi malam d'in an dad'e ana rad'e rad'in basu had'a komai ba, tabbas surayyah macece mai mutumci nutsuwa da kamala had'e da kamun kai, amma ina ji a jikina wannan yaran sunzo ta silar kuskure guda d'aya tak da bazai gyaru ba har abada... Wannan kuskuren da take yawan fad'a, yanzu kuma lokaci yayi daya kamata ta ajiye komai a gefe, in ma family issue ko wancen abu daya faru ta bawa dangin ubansu hak'k'in su da yake kan yaran a kawo maslaha ta daina tafiya dasu a duk'unk'une........". _shiyasa akace rayuwar duniya a komai kada ka zurfafa........_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty eight2️⃣8️⃣ Abun mamaki yaba shi, sai ya saki baki yana kallonta da d'unbin al'ajabi, shi ko a mafarki bazai yarda sameera zata iya yiwa doctor surayyah irin wannan danyen rashin mutumcin ba, kamar wadda aka shiga tsakanin su,, sai ya mik'e tsaye saboda abinda zai fad'a bame dad'in ji bane, "idan har ke idonki ya rufe bakya iya fahimtar komai bakya gane komai sai kanki, toh ni bazan goyi bayan wannan butulcin da zaki yiwa matar da ta taimake ki a lokacin da kika fi buk'atar taimako ba, ta maida ke mutum mudubin kallo ga kowa, har yaran ki ta maida su kamar y'ay'an cikinta, ba don kwad'ayin wani abu da Suka mallaka ko neman shiga ba ni zan je da kaina naba Ayman auren Nur ko kin amince ko baki amince ba,,,, in yaso ki janye tallafin da kike yi mana ni dasu gaba d'aya........". Yana gama maganar shi ya fuce ko jiran jin abinda zatace beyi ba A parlour ya samu yaran cirko cirko, saiya shiga cikin su ya zauna, "k'unci abinci kuwa?". Girgiza mishi kai sukayi, shaheeda ta tambaya, "me yake damun mammie". Kallon yarinyar yayi da tausayawa yace, "bata jin dad'i amma tasha magani yanzu zata samu bacci kuje maza kuci abinci ku kwanta gobe kowacce a cikin ku tana da makaranta, shi haedar har yanzu bai dawo ba?". Suka bashi amsa da, "ehh" "maza kuje kuci abincin ku Allah yayi muku albarka kunji". Ba musu suka ja hannun heedaya suka tafi suna tunanin da gaske mammie bata da lafiya ko kuwa dai abban su ya b'oye musu ne. ★★★★★★ Gidan surayyah kuwa mama haleema kasa matsawa daga jikin k'ofar d'akinta tayi tana ta dakon futowarta cike da zullumi da fargabar abinda ka iya zuwa yazo, ta tsorata da yanayin auntien a yau, har lokacin tafiyarta gida yayi ya huce tana nan tsaye tana sak'awa da kwancewa, daga k'arshe kawai saita nufi b'angaren y'an biyun, da Ayman ta fara cin karo zai futo, sai ya matsa baya don ya bata damar shiga parlon, itama tunga taja ta tsaya tace, "anguwa zaka ne?". Sai ya futo wajen shima yace, "a'a gurin auntie zani cikina ya fara kiran...." Sai ya k'arashe da murmushi, mama haleema ta gane abinda yake nufi, sai ta fasa fad'in abinda tayi niyyah don idan suka ji ba zasu iya cin abincin bama, madadin haka sai tace, "dama kuwa abincin tace a fad'a muku an gama tuntuni a kawo muku shi nan" "Toh tana ina auntien....". Har ta fara inda inda zata had'a wani abun sai ya k'ara cewa, "koda yake bari na biki na amso mana abincin kawai". Tare suka je har kitchen ta had'a musu abincin a tray kamar yadda taga auntie tana yi musu duk dare, Ayman ya karb'a ya tafi ita kuma ta nemi guri a parlon ta zauna. Khaleefa yana zaune da three quarter wando da riga armless, k'afar shi tankwashe akan gado yana karanta wani littafin addu'o'i dad'ad'd'e da auntie ta basu. A nutse Ayman ya shigo da trayn hannun shi, kallon shi kawai khaleefa yayi har ya k'araso ya ajiye abincin saman table k'arami da yake gefe, "dinner is ready" ya fad'a yana zama don ya saving nasu, khaleefa ajiye littafin yayi a gefe ya sauko yazo ya zauna kusa da Ayman, abincin yake kallo har Ayman ya gama misu saving ya tura mishi, lomar farko da yakai bakin shi ya gane wannan girkin sam bana Auntie bane, duk da tarin yunwar da yake ji sai yaji abincin ya futa a ranshi, haka dai ya tuttura ya kora shi da tea me zafi, yana kallon Ayman yana cin abincin shi a tsanake. Saida ya gama ya kwashe komai ya mayar kitchen sannan mama haleema tace suzo shida khaleefa, yana fad'awa khaleefa ya mara mishi baya suka taho tare suka sameta, nan ta basu labarin iya abinda idonta ya gani da yadda auntie ta shige d'aki ta rufe sama da hour uku tana ciko. Duk hankalin su tashi yayi, sai suka rasa abinda zasuyi ma, khaleefa ya tambayeta, "kin buga bata bud'e miki ba kuma?". "A'a tace bata son kowa ya dameta". Sai ya tafi jikin k'ofar ya soma buga mata da k'arfi. A lokacin ta idar da sallah kenan sai dai idonta har kumbura yayi saboda kuka, kamar ta share sai taji muryoyin su Khaleefa da haleema ne, a sanyaye ta tashi sanye da hijab d'in sallar ta ta bud'e k'ofar, kallonta khaleefa yayi sai ya sauke ajiyar zuciya a b'oye ganin tana lafiyarta lou, guri ta basu duk da batace komai ba amma sun gane tana nufin su shigo, aikuwa suka shiga gaba d'aya suna binta ita da parlon da kallo, "mama haleema baki tafi gida ba? Kada fa kisa Inna ta fara kira tana tambayar zaman me kikayi". Tana kallon yadda fuskar surayyan ta dawo luhu luhu tace, "Ai na fad'a mata yau anan zan kwana". Murmushin yak'e tayi tace, "toh yayi". Ayman da yake kallon yanayinta kasa hak'uri yayi saida yace, "auntie meya same ki haka?". Sai data k'ara danne hawayenta kafun tace, "lafiya lou nake meka gani". Sai yayi k'asa da kanshi kurum. Haka suka zauna jigum sai kallonta suke suna son su tabbatar da lafiyarta, khaleefa ne ya fara musu sallama ya tafi makwancin shi, sannan Ayman, ya rage daga ita sai haleema, gyara zama tayi ta kalli haleeman ta tambayeta, "kin fad'a musu wani abu ne?". Shiru tayi kafun can tace, "tsorata nayi da ganin yanayin ki d'azu da yadda kika kulle kanki shine na fad'a musu saboda ina tsoron ko ba lafiya kike ba". Sai taja ajiyar zuciya ba tare da tace komai ba ta mik'e don taje ta kwanta, itama haleeman makwancinta da take kwana a duk lokacin da tazo gidan ta nufa. @@@@@ Raihanatu kuwa tana komawa gida ta shige d'akinta ko ummie bata nunawa rubutun da malam ya bata ba, ita ta manta ma sai bayan da tazo zata kwanta ta tuna ta d'auka ta shanye ta nemi guri tayi kwanciyarta, sunyi waya da Imran sama sama saboda baccin da take ji k'arshe suna wayar bacci ya sadaddafo yayi gaba da ita, sai ya kashe wayar kawai yana murmushi. Kwana uku a tsakani tana karb'ar rubutun malam tana sha ko ummie bata fad'awa ba har ta cika adadin kwanakin cif. A rana ta hud'u ta tambayi abbanta tunda sassafe kafun ya futa kan tana son taje ta gaishe da ummaa (kakarta ta wajen uwa). Ta gama abinda take yi tunda wuri ta yiwa ummie sallama ta tafi, a can ta tarar da su Amina sunje suma kamar sun san tana tafe, aikuwa suna ganinta suka d'au murna da sowaa ga amarya ga amarya. Ita dai tayi murmushi kawai ta zauna kusa da ummaa, bayan sun gaisa itama zolayarta ta dinga yi har saida tace zata tashi ta tafi sannan ta kyale ta. Ranar suka yini suna hirar su da budurin su har yamma, nan ta yiwa ummaa sallama ta taho gida. Auntie kuwa a washe garin ranar da abin nan ya faru tana zaune da safe wayarta ta soma k'ara, ganin bak'uwar no tana kiran private sim d'inta saita d'aga tare dayin sallama, bata gane me muryar ba duk da a haka tana ji kamar tasan muryar, har suka gama gaisawa ya gabatar da kanshi, mahaifin Nur ne, sai tace, "oohh Allah sarki ya kake ya mutanen gidan". Daga can b'angaren yace, "suna lafiya Lou alhamdulillah, dama kira nayi inji k'arfe nawa masu kawo kud'in zasu zo?". D'an Damm tayi kafun ta nisa tace, "ai mun soke wannan maganar bata fad'a maka ba?". Yace, "Ni ba ruwana da abinda ya had'a ki da ita, ni nine nan mahaifin Nur kuma a shirye nake dana ba Adam idan kun shirya ko anjima zasu iya zuwa a tsaida magana". Shiru surayyah ta sake yi kafun ta kuma cewa, "toh aini bansan yadda zan ce maka ba, maganar gaskiya ni tun jiya na kawo k'arshen maganar auren yaran nan, don Allah mu ajiye komai a gefe, ban rik'e sameera da komai ba, tabbas batayi laifi ba ya kamata ace na nuna yarda gareta ko yaya ne, sai dai abinda bata sani ba shine na jima da yiwa raina alk'awarin har abada bazan tab'a iya bada labarina ga wani ruhi ba saboda baki bazai iya hak'uri ba in kunne yaji saiya furta shi,,, na fad'a mata ba ita kad'ai ba kowa ma ban yarda dashi ba har jinina da muka futo ta tsatso d'aya,,, shine kawai...... Da haka nake maka godiya kaima.... Nagode nagode da kulawa Allah ya bar zumunci" Tana gama maganar ta bata tsaya jin ta bakin shiba ta katse kiran, har ta ajiye wayar sai ta sake d'aukowa tayi dialing no malam, bayan sun gaisa shima tambayar daya fara yi mata shine, "kince da safe za'a kai kud'in auren ne gashi muna ta jiran ki tun d'azu shiru har malam mukhtari ya kirani a waya..". Ajiyar zuciya taja tace, "malam maganar auren nan mu barta zuwa wani lokaci.....". Cike da mamaki shima ya tambayeta, "a'a me yasa? Fasawa kukayi?". Tace "ko kad'an malam akwai abinda nake son ya kammala nan da wani lokacine.." ta k'arasa fad'a tana toshe bakinta da hannunta gudun kada sautin kukan ta ya futa, shima saida ya jinjina sannan yace, "toh Allah ya taimaka". Da kyar ta iya cewa "ameen" ta katse wayar. Switch up d'inta tayi gaba d'aya ma ta ajiyeta gefe. Ta kife kanta jikin gefen gadonta ta fashe da sabon kuka, shikenan yaran ta basu ba aure har k'arshen rayuwar su, indai saida wani cikin dangin ubansu ko shi uban za'a basu auren ta gwammace su rayu ba aure har k'arshen numfashin su.... don ta yiwa ranta alk'awarin har abada ita da neman Suraj ko dangin shi indai akan rayuwar yaranta ne, itace uwarsu, itace ubansu, itace koman su basa buk'atar ubansu da yake matsayin matacce a gurin su...... Knocking k'ofarta da akayi yasa tayi saurin share hawayenta da tafukan hannunta ta mik'e daga sallayar sannan ta bada izinin shiga, haleema ce ta shigo da k'aramin tea plask da cups akan tire ta ajiye gabanta, suka gaisa da surayyah sannan ta futa, da kyar ta iya shan ruwan tea d'in don bakinta har wani d'aci yake mata, haka dai ta daure ta shanye k'aramin cupi d'aya ta shiga bathroom tayi wanka ta shirya cikin yaloluwar doguwar riga marar nauyi ta rufe kanta da k'aramin gyale ta futo parlon. Ba jimawa Ayman ya sameta, khaleefa ma yazo, duka sun damune akan yanayinta na jiya, ba laifi sun ganta ba kamar jiya ba amma fa Sam bata da walwala. Khaleefa bai zauna da yawa ba ya futa ya barta ita da Ayman. Toh sai muce kusan kwana biyu a tsakani doctor surayyah bata da walwala sam, duk k'arfin halinta a wannan karon ta gaza, saboda an tab'a wani abu da yake rauninta a rayuwa wato Suraj. Mama haleema kwananta biyu a gidan ta kasa barinta saboda tsoron kada tana tafiya wani abu mara dad'i ya faru, haka y'an biyunta suna zuwa dubata akai akai barin ma Ayman da yafi nuna damuwarshi a fili. A tarihin doctor surayyah bata tab'a yin kwana biyu ba tare data futa ko k'ofar gida ba, amma a wannan datsin ta tashi cimma kwana hud'u ko parlon k'asa bata sauka ba,, harkokin business d'inta da komai ya tsaya. Ayman kuwa yana can cikin kwanakin sai trying no Nur yake baya tafiya, bai kawo komai a ranshi ba sai tunanin k'ila lalacewa wayar tata tayi, har ya fara tunanin irin wayar dazai siya mata sabuwar yayi da zai burge ta. A ranar da yamma ya siya mata sabuwa dal a kwali ko gidan bai shigo da ita ba ya barshi a mota. Abu biyu ne suka zame mishi tsaiko da tuni ya kai mata, yanayin da suka tsinci kansu a gidan na rashin walwala yasa bai samu kwarin gwiwar zuwa gidan su Nur d'in ba tuni. A yammacin ranar lahadi khaleefa yana zaune kan gadon d'akin shi, bayan tattara duk wani binciken shi guri d'aya adanasu yayi yana tunanin yadda zai had'u da Ahmad ya nuna mishi don Susan yadda zasu b'ullowa komai, bayan ya ajiye komai dake gaban shi gefe kwanciya yayi rigingine kanshi jingine da fuskar gadon, k'afarshi d'aya a tokare jikin gadon d'aya kuma a k'asa. Tunanin Saleema yake yana tuna duk moments d'insu da ita na k'asar Germany, sai yaji kamar ya tariyo baya ya goge labarin rayuwarshi daya bata har sai bayan ya aureta. Yana Wannan tunane tunanen Ayman ya shigo da sallama, daga kwance ya kalleshi ba tare daya motsa ba, "it seems like kana da babban bak'o yau....". Fuskarshi kadaran kadahan yace, "who is he". Matsawa Ayman yayi sai ga Ahmad ya bayyana cikin d'akin, ai khaleefa baisan lokacin daya dire k'afafun shi k'asa ya mik'e tsaye yana kallon shiba, shima Ahmad Kallon shi yake kafun yaci gaba da takowa zuwa inda khaleefa yake suka rungume juna. Ajiye jakar hannunshi yayi a nan d'akin khaleefa suka zauna suna gaisawa, khaleefa da kanshi ya kawo mishi ruwa me sanyi. Sun tab'a hira su uku kafun Ayman ya tashi ya basu guri, da sauri khaleefa ya d'auko system d'inshi ya nuna mishi sakamon binciken shi, koda Ahmad ya gama dubawa shiru ne ya biyo baya yana nazari kafun can ya nisa yace, "kasan duk abinda nakeyi kana raina kuwa khaleefa? Shiyasa ina dawowa jiya na biyo hanya yau nazo na ganka, amma fa kayi k'ok'ari matuk'a, sai dai ka manta wani abu wanda ka samo mai suna Suraj Abdallah tofa babban d'an kasuwa ne daya mallaki manyan kamfununuwa a kasashen duniya dama gida Nigeria, har yafi Abdallah tofa kud'i da shahara a b'angaren kasuwanci tunda shi dama d'an siyasa ne, toh sai dai wani hanzari ba gudu ba ba don kud'in da wannan mutumin ya mallaka ba, Ina ganin kamar ba akanshi ya kamata kayi binciken kaba, tunda ku mahaifin ku ya mutu baya raye ko ka manta ne?". Dafe kai khaleefa yayi don shi har ga Allah mantawa yake da mahaifin su baya raye tun lokacin daya fahimci auntie tana b'oye musu wani abu mai muhimmanci na daga rayuwar su, "kasan me Ahmad ni mantawa nakeyi da wannan shap, sannan a yaran Abdallah tofa wannan kad'ai nayi nasarar samu duk da sunkai su kusan shida, sannan shi zan bibiya tunda shine naji tsarin rayuwarshi, asibitin da zamuyi aiki a Germany yana zuwa check-up duk bayan watanni biyar gurin doctor andal itace amintacciyar likitar shi, Ina ganin zamu same shi ta hannun ta, idan muka tabbatar bamu had'a komai ba shikenan sai na hak'ura Ahmad". Shiru Ahmad yayi kafun caan yace, "toh hakane maganarka, komai ma auntie zata iya b'oyewa ta silar b'acin rai ciki hadda tura rayayye rami a baki, sai maganar aiki ko kayi mata magana?". Nan ya warwarewa Ahmad duk yadda sukayi da ita akan aikin shima da sharad'in data gindaya mishi. "Toh fa wannan shi ake kira ana wata ga wata". Ahmad ya fad'a, khaleefa yace, "Humm ka bari kawai". Ahmad yayi dariya kad'an yace, "kasan me! Nifa har na fara tuno Duk wannan turka turkar watarana sai labari da sannu komai zai huce faaa". "Anya kuwa Ahmad?". Khaleefa ya fad'a cikin sarewa, "haba man babu abinda yake dawwama a duniya sai ikon Allah". Khaleefa yace, "hakane kuma, amma kanajin sharad'in da auntie ta gindaya, bayan ga k'udurin da nake dashi akan neman auren Saleema, ni sai yanzu ma nake jin kwarin gwiwar yin aiki a Germany.....". Haka dai suka ci gaba da tattaunawa a tsakanin su, Ahmad yaba khaleefa labarin yadda suka daidaita kansu da Yasmin har an tsaida lokacin biki nan da wata hud'u masu zuwa, khaleefa ya taya shi murna sosai daga k'arshe yayi mishi addu'ar fatan alkhairy, tsawon lokaci suna hirarrakin su kafun su tashi don suje ya gaishe da Auntie. Suna futowa Ayman ma yana futowa kamar had'in baki, "yaah! Anguwa za'a futa ne". Ahmad ya tambayi Ayman, murmushi yayi yana kad'a mukullin motar da yake hannun shi yace, "ehh zan lek'a gurin gimbiyata ne". "kaji manya da kyau ace manyan yayye suna gaisheta". Ahmad d'in ya fad'a yana d'an dariya, shima Ayman dariyar yayi yace, "sai dai na fad'a mata manyan gwagware daya kamata su huce gaba k'anin su yabi bayansu, amma suka coge a baya suka tura k'anin nasu gaba sunce suna mik'o gaisuwa". Dariya suka sakeyi su biyu khaleefa kam murmushi yayi yace, "sai ka gyara zancen ka Cox Ahmad is engaged". "Ah haba really" Ayman ya tambaya da mamaki, shikam baice komai ba sai murmushi daya sake yi, ahh lallai abu yayi kyau Ahmad Allah ya sanya alkhairy ya nuna mana lokaci, ya kawo namu muma". Ahmad yace, "ameen thumma ameen". Shi kuwa khaleefa kallon Ayman d'in yayi a lokacin daya k'arasa musu sallama ya tafi, abun tausayi baisan watak'ila mu bamu da rabon aure ma a duniya ba. Khaleefa ya fad'a a ranshi. Sun shiga parlon auntie da sallama su duka biyu, a lokacin tana magana da mama haleema ne kan taje gida su ganta ita lafiyarta lou ta daina damuwa da yanayin da take ganinta ciki y'an kwanakin, gobe goben nan ma zata koma aiki,,,,, shigowar su Khaleefa ya katsewa haleema hanzari akan abinda tayi niyyar fad'a, sai ta d'auki ledar da surayyah ta ajiye mata a gabanta kawai ta mata sallama zata huce, Ahmad gaisheta yayi sannan ya durk'usa har k'asa ya fara gaishe da auntien, cikin farin cikin ganin shi auntien ta amsa tana tambayar shi mutanen gidan su. Ya fad'a mata duk suna lafiyar su lou Sunyi shiru kowa da tunanin da yakeyi a tsakanin su kafun khaleefa ya fad'a mata an tsayar da ranar auren Ahmad nan da 4 months, sake fad'ad'a fara'ar fuskarta tayi tace, "Masha Allah son Allah ya sanya alkhairy ya nuna mana lokaci da rai da lafiya,,, ahh Masha Allah....". Shikam sadda kai k'asa yayi yana murmushi, bayan sun sake yin shiru auntien ta yiwa Ahmad magana, "kazo a dai dai Ahmad dama Ina son magana dakai" saita kalli khaleefa da shima yake kallonta tace, "ko zaka bamu guri". Ba musu ya mik'e ya fuce daga d'akin, ita kuma ta dawo da dubanta ga Ahmad tace, "magana nake son yi dakai ta sirri akan abokin ka,,, kayi mun alk'awari ba zaka fad'a mishi ba ko da sub'utar baki, saboda bana so yasan nasan abinda yake ciki" A madadina da d'aukacin members na JARUMAR UWA fans club. Muna mik'a sak'on ta'aziyya ta ga y'ar uwata, mahadin Alk'alamina Dr Ferhyeez m usmern akan rashin da mukayi na y'ar uwa k'anwa gare mu nida ita hasseena. Fatan Allah ya jikanta ya gafarta mata ya haskaka kabarin ta, mu kuma ya kyauta namu zuwan. Happie juma'at Mubarak. A yau nayi k'arin shekara guda a duniya,,,, Ina son duk wani fans d'ina ya tayani da addu'ah da fatan alkhairy😊. _ina godiya da comment na nuna goyon baya,,,,, Ina yinku fiye da yanda kuke yina😍😍😍 much k'auna_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page twenty nine2️⃣9️⃣ Saida ya jinjina girman alk'awari kafun yace, "toh insha Allah". Gyara zamanta tayi kafun ta fara mishi magana cikin nutsuwa, "shin wani abu ya faru da khaleefa gab da tahowarku Nigeria? Ina nufin meye musabbabin wannan sauyin nashi?". Ahmad d'auke wutaa yayi kafun ya nisa can yace, "eh to gaskiya a halin yanzu ba zance miki ga takamaiman damuwarshi ba, saboda kinsan dama shi ba mutum ne me yawan magana ba musamman akan damuwar shi, Auntie bazan b'oye miki ba ko a makaranta sai nayi futu futu na b'ata rai yake fad'a mun matsalar shi ko ciwon shi, shiyasa ni har muka dawo banga wani sauyi a tattare dashi ba gaskiya". Shiru tayi tana kallon Ahmad da sake nazarin shi, tana ganin kawai bazai fad'a mata bane saboda sirrin khaleefan ne da bai kamata kowa yaji cikin suba, koda yake akwai inda dole sai yayi bayani ai. Sai ta sake cewa, "hakane! Sai abu na biyu, rannan yana bacci da rana naga hoton wata kyakkyawar yarinya a wallpaper shi wacece ita?". Wayyoh Allah! Ahmad ya fad'a a ranshi a zahiri kuma yak'e yayi yace, "yarinya kuma? Ya kamanninta suke....". Shi kanshi baisan bakin shi ya furta hakan ba, sai tayi murmushi mai kyau tana sake tsare shi da ido, "kana nufin y'an matan da yawa kenan?". Da saurin shi yace, "a'a Auntie ba wai haka nake nufi ba, sai dai ni ban sanshi da wata mace ba gaskiya indai koba......". Sai yayi shiru ya saci kallonta, ta zuba mishi ido kuwa taji ta inda zai tsaro ta anan kuma. Sai yayi murmushin yak'e ya sake cewa, "eh yarinya d'aya nasan shi da ita gaskiya, kuma ba wata kwakkwarar alak'a a tsakanin su gaskiya in aka d'auke ta friendship da kasancewarta neighbor d'inshi a gidan da muke zaune". Sai ta murmusa. "Ni kuma dawowar khaleefa yace mun akwai wata yarinya da yake so zai aura... Ita kuma wacece?". Ta sake jeho mishi wata tambayar, Ahmad saida yaji Kamar ya dafe k'eyar shi ya saita a guje da yaji wannan tambayar itama, don har ga Allah baisan cewa khaleefan ya yiwa auntie irin wannan maganar ba, sai dai ya daure da iya gaskiyar shi yace, "wallahi Allah ni bansan da wannan maganar ba, bansan akwai wadda zai yiwa maganar aure a kusa ba.....". "humm" kawai ta fad'a ta mik'e tsam ta shiga bedroom d'inta, ba jimawa ta futo da car key damk'e a hannunta ta zauna inda ta tashi, "sai abu na k'arshe cikin ku waye jami'in k'irk'iro maganar komawa Berlin aikin nan.... Shin me yasa ba zaku dawo gida Nigeria ku taimaki al'ummar mu da ilimin da kuka samu ba?". Shiru yayi wannan karon har Saida ta sake mishi magana sannan yayi gyaran murya ya fara yi mata bayani da gundarin gaskiya, "a gaskiya bazan b'oye miki komai ba wannan aikin wani likitan Nigeria da yake aiki a k'asar ne ya bamu shi, saboda munyi practice da yawa a gurin shi ya Kuma yaba da jajircewar mu a lokacin, shine ya zab'e mu mu bakwai zamuyi aiki tare dashi na tsawon shekara biyar don mu sake gogewa a fannin aikin kula da duk abinda ya shafi k'ashin d'an Adam. Sunyi alk'awarin zasu bamu wadataccen kud'in da zamu tsira da abubuwa da yawa a k'asar mu, sannan idan mutum yaso zai zama parmanent doctor a gurin, idan baiso ba kuma sai yayi tafiyarshi k'asar shi bayan cikar wad'an can shekaru, sai dai mafi muhimmanci da Jan hankali gare mu duka shine, mun samu damar aikin nan bisa jajircewar khaleefa da kwazon shi, a yau idan kika nuna rashin amincewa kan komawarshi Germany toh yana nufin muma babu maganar aikin mu gaba d'aya, sannan shi khaleefa aikin nan ba wai sam ya d'ad'ara shi da k'asa neba, saboda indai matsalar kud'i ne bai kasance mutum mai handama da son abun duniya ba, yaji zai amince ne base on two main reasons, na farko yana da b'oyayyen burin shi da yake son cimma a Germany da bansan ko akan meye ba, na biyu cikin wad'an da mukayi karatu akwai wanda suka samu nasarar kaiwa wannan mataki k'ark'ashin scholarship, wannan damar itace kad'ai hanyar da zasu samu rufin asiri har su taimaki y'an uwan su su samu su tallafi wasu kafun lokacin da zasu bar k'asar ko suci gaba da zama, khaleefa yana ganin idan yak'i amincewa asibitin suka rushe upper da suka bamu kamar ya rugujewa su Muhammad kwarin gwiwa da burin da Suka ci na rayuwar su ne gaba d'aya......". Sai ya durk'usa k'asa gabanta kan gwiwowin shi yace, "don girman Allah auntie, kada ki hana khaleefa aikin nan munyi alk'awarin da zarar mun gama five years d'innan ba zamu sake zaman koda minti d'aya ne a k'asar Germany ba zamu tattara mu dawo gida, muma burin mu a amfana da abinda muka karanta bawai mu yita k'arawa mai k'arfi k'arfi ba". Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tace, "tashi zaune Ahmad ka daina durk'uso haka a k'asa". Sai ya mik'e ya koma mazaunin shi kanshi a k'asan d'akin yayi jigum yana jiran yaji hukuncin da zata yanke. Cikin taushi da sanyi yanzun ma take magana, "kamar yadda na fad'a mishi kaima Zan maimaita maka,,, wallahi babu inda khaleefa zai d'ara muddin bai futar da matar aure ba....". Shiru Ahmad yayi yana nazarin ta yanda khaleefa zai futa daga wannan d'aurin goron mai dabaibayi da auntie tayi mishi. Ita kuwa mik'ewa tsaye tayi ta ajiye mishi mukullin motar hannun ta gefen shi tace, "kyautar ka ta murnar gama karatu cikin nasara...". Bata jira jin abinda zaice ba ta shige d'akinta ta rufo, ta zauna gefen bed tana tunanin zurfin ciki irin na Suraj da khaleefa ya gado tass! Yanzu meye lefin bud'a baki yayi mata irin wannan bayanin da Ahmad ya mata, a wasu lokutan kalami masu dad'i kan sa mutum yaji zuciyarshi tayi sanyi har ya sauka daga k'adamin da ya hau na tsauri duk tsananin shi kuwa a lokacin. Ahmad kuwa Mukullin data ajiye ya d'auka yana dubawa, sai ya mik'e tsaye fuskar shi washe da fara'a ya furta, "motar da ake yayi nake burin siya tunda daddy yak'i yarda ya siya mun". Sai ya futa daga parlon da sauri don ya nunawa khaleefa ya taya shi murna da godiyar da auntie tak'i bashi damar yayi mata. _toh mubi hajji Ayman mana👉🏻_ Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya dinga jan motar shi a wannan yammaci yana bin kira'ar shuraim dake tashi cikin suratul Maryam har ya k'arasa gidan su nuriyyah, a k'ofar gida yayi parking yau ya kwankwasa k'ofa, wani da yake musu aikace aikace kamar yaron gida yazo ya bud'e mishi yana mishi sannu da zuwa, ya amsa da yauwa sannan ya k'arasa shiga cikin harabar gidan, inda suka saba zama ya tsaya ya kira wani matashi da yake durk'ushe gefe guda yana musu wanki, ya k'araso gaban shi ya russuna, "gani ranka shi dad'e". "Nur tana nan kuwa?". Ya tambaye shi, "eh tana nan". Ya bashi amsa a ladabce, "okay d'an yimun magana da ita". Ya bashi umarni. Ba musu ya d'auki hanyar cikin gidan. Bayan mintuna k'alilan ya dawo ya shaida mishi mammie tace Nur ba zata futo ba, Sam Ayman bai fahimci abinda aiken yake nufi ba don haka sai ya tambayi yaron, "ka fad'awa mammie injini kuma?". "eh yallabai na fad'a mata". Sai ya zaro 1k a aljihu ya bashi yace su raba shida d'an uwan shi, ya russuna yana godiya ya karb'a ya tafi. Ayman kasa tafiya yayi ya kuma kasa shiga ciki, sai yaci gaba da tsayuwa a gurin yana ta tunane tunane har haeydar ya dawo, bayan ya daidaita parking ya futo hannu ya mik'awa Ayman suka gaisa yana mishi complain akan duk lokacin da yazo sai yayi ta tsayuwa a waje kamar wani bak'o, kanshi ya shafa ba tare daya ce komai ba, haeydar har zai huce sai ya tambaye shi, "to tasan kazo ma kuwa? Kwana biyu ban san meya samu wayoyin suba ko lalacewa sukayi ni ban sani ba dai amma in na kira su bana samun su, nasan kaima baka samun Nur a waya ko?". Gyad'a mishi kai Ayman yayi yace, "gaskiya kam, nima bana samun ta sam, yanzu kuma nazo ance mammie tace ba zata zoba, toh ina tunani ko bata fahimci nine nazo ba,,,,". Da mamaki haeydar ma yace, "a'a mammie da kanta kuma yau? Waya fad'a maka?". Ayman yace, "wancan da yake wanki". Kwala mishi kira haeydar yayi, ya taho da hanzarin shi, cikin b'acin rai haeydar ya fara mishi fad'a, "wato kaima ka fara k'arya irinta sahabi ko? Yaushe mammie tace maka Nur ba zata zoba kasan waye wannan kuwa?". Cikin tsoron haeydar d'in yace, "don Allah kayi hak'uri wallahi na fad'a mata ita da kanta tace a fad'a mishi Nur ba zata zoba...". Zai sake yin magana Ayman ya dakatar dashi, "kaga jeka abun ka nima bari nazo na tafi". Da sauri haeydar ya sake dakatar dashi, "a'a Ina ganin bata fahimta ba fa, kaima laifin ka da idan kazo kake cogewa a wajee, mu shiga ciki...". Ayman kamar yace a'a sai kuma ya fasa don yana son tabbatar da lallai mammie bata gane shi Ayman d'in ake nufi ba. Lokacin da suka shiga da sallama parlon da ita suka fara cin karo hakimce kan kujera tana kallo a tivi. A k'asa ya zauna ya fara gaisheta, ta amsa mishi kadaran kadahan, har lokacin bai kawo komai ba, haeydar ne yace, "tun d'azu fa yazo mammie yana tsaye a varender wai kince Nur d'in ba zata futo ba". Kallon haeydar tayi sannan ta dire k'afarta duka k'asa tace, "hakane da gaske nina hana Nur futowa.....". Cikin katse hanzari haeydar yace, "mammie why??". Saita galla mishi harara, "dakata mun malam" ta maida dubanta kacokan ga Ayman tace, "Kai mahaifiyar ka bata fad'a maka an tashi maganar aurenka da Nur a aiki ba....?". Saida gaban shi ya yanke ya fad'i, haeydar ya zaburo zaiyi magana ta daka mishi tsawa, Dole yaja bakin shi ya tsuke. Ganin kan Ayman d'in ya d'aure saita fara yi mishi Dalla dalla yadda zai gane, "Naga kana kallona a bai bai bari nayi maka gundarin bayani irin wanda surayyah ba zata tab'a zama tayi maka ba, shin tun tasowarka zaka iya kirga mun suwa da waye dangin ka? Sannan tsakanin ka da Allah ka tab'a ganin hoton mahaifin ku da tace ya mutu tun kafun kuzo duniyaaa ko a hoto? Ko kuwa ta tab'a baku labarin wani abu daya shafi mahaifin ku wanda ya shud'e lokaci mai tsawo a rayuwar auren su? Shin kuna ganin kunyi min adalci na d'auki Nur na baku babu cikakken asali ko tushe, ku haifi yara gaba su tashi a tantal batete.... Ya zamo dole a wannan karon idan har tana sonka da Nur ta futo da abinda take b'oyewa a kanku tsawon shekaru ciki kuwa harda rashin had'a dangantaka kota farce tsakanin ku da iya da kuke yiwa kallon kakarku......". Tunda ta fara magana Ayman yaji Kamar an d'auki guduma an buga mishi a tsakiyar kanshi, wani abu mai girma da d'aci yana mishi yawo a kanshi zuwa gangar jikin shi, take kwakwalwar shi ta fara tariyo mishi abinda ya faru shekaru aru aru baya lokacin suna yara, yadda sukaita rigima da wani yaro d'an gidan su abulkhair daya fara kiransu da sunan shegu,,,,, ya tuno yadda auntie take shiga tsananin tashin hankali a duk lokacin da aka danganta su da wannan mummunar kalma, sun girma suna ganin kamar sun girmi waccen kalma komai ya huce sai gashi mutanen da basu tab'a zato ba suna neman dawo musu da ita cikin rayuwarsu rana tsaka,,,,, yoo meye banbancin ba'a san uban ka ba da shege, ai kawai don kar a futo a kira ka da shege ne direct aka sakaya da haka...... Lokacin daya mik'e ko gaban shi baya iya gani sosai ya futo daga cikin gidan yana tafiya har ya fuce, da kallon tausayi haeydar ya bishi, lallai ba don tsoron mamie ba daba abinda zai hana shi bin bayan shi, amma ya fahimci mamie yau tana sama ba sauk'i in ya takura da yi mata shishshigi komai ma zai iya faruwa. A daddafe Ayman ya shiga cikin motarshi ya bata wutaa, tafiya yake ba don yasan inda zai nufa ba, a cikin ranshi babu abinda yake kai komo sai raihanatu, haka yayi ta bulayi a gari kafun caan yayi wani tunaniii, sai kawai ya d'auki hanyar zuwa gidan kaamil, wani abokin aikin shi da yayi aure ba jimawa, kamar a mafarki haka kaamil d'in ya ganshi bayan ya kira shi a waya yace mishi yana k'ofar gida, murmushin yak'e kawai yake mishi a lokacin da yake mishi tayin shiga cikin gidan bayan ya gama yaba k'ok'arin shi na iya gane gidan bayan sau d'aya ya tab'a zuwa tun ana aikin gidan. "Kaga a gurguje nake ka shigo nan muyi magana ni bazan shiga ciki ba...". Ayman ya fad'a mishi kawai, sai ya bud'e front seat ya shiga, a gurguje suka gaisa kaamil na tambayar shi ko lafiyar shi, yamutsa fuska yayi kad'an yace, "kawai headache! Yauwa kwanaki mun fara magana dakai a office akan friendship da love relationship, shine nazo yanzu ka k'arasa warware mun yadda abun yake". Galala kaamil ya saki baki yana kallon shi, Shi tuni har ya manta sun fara wata magana irin haka banda yanzu daya tuna mishi, don a lokacin katse shi yayi bai saurare shiba Sam. Sai ya tambaye shi, "ko zaka sake dawomun da farkon bayanin, nan Ayman ya dawo mishi da bayanin daki daki kamar yadda ya fara mishi bayani a wancen lokacin, saida ya dire Aya sannan kaamil yace, "na gane komai, amma akwai y'an tambayoyi da zanyi maka, wacce kafi kishi tsakanin k'awar ka da budurwarka?". Shiru yayi kafun can yace, "toh aini bansan kishin ba saboda Nur bata tab'a yin wani saurayi bayan niba". Kamil yace, "okay ita waccen k'awar fa?". Da sauri yace, "kai ita aure ma zatayi". Sai kaamil d'in yace, "yawwa ya kake ji a duk lokacin daka ganta da saurayinta....?". Saida ya rintse ido saboda tuno da abinda yake ji d'in, Cox abinda yake jin bamai dad'i bane, nan ya fad'a mishi dallah dallah har kawo yanzu ma daya daina kulata baki d'aya, Saida kaamil ya gama jin bayanan shi gaba d'aya sannan yayi murmushi yace, "abu mai sauk'i Sam ba budurwarka kake soba, wannan k'awar taka kake Soo tunda dad'ewa kai kanka bakasan da haka ba,,, exchange d'in matsayi ka musu ita da budurwarka da babu komai a ranka game da ita sai shak'uwa da zumunci na y'an uwan taka, Amma fa ba makawa daga dukkan alamomin da suka bayyana wannan k'awar taka da kakewa text kullum safiya kake so, gwara kaje ka shaida mata tun da wuri kafun lokaci ya k'ure maka Ayman, a k'arshe ka k'are da auren matar da baka da wani buri ko fata a kanta gaba d'aya". Cikin tausayin kanshi da tunanin yadda zaiyi babun bad'ilahu ya kife kanshi a sitiyeri yace, "lokaci ya jima da gama k'ure mun kaamil, da naasani tun farko na saurare ka a lokacin daka fara yimun wannan bayanin, watak'ila da yanzu ni zata aura nan da kwanaki k'alilan,,,,, koda yake itama ba lallai ta iya aurena ba......". Ya k'arasa fad'a yana jujjuya kanshi jikin sitiyerin motar. Kaamil ga zaton shi Ayman yana cikin damuwar rashin raihana ne shiyasa yake duk wannan sambatun, sai ya dafa kafad'ar shi da son ganin ya K'arfafa mishi gwiwa yace, "kayi hak'uri abokina indai ba'a d'aura auren ba har yanzu kana da sauran dama, za'a iya zuwa wajen d'aurin aure ma a fasa indai rabon kace ita d'in, Soo kada kaji komai abokina kada kayi saurin sarewa". Gyad'a mishi kai yayi kamar gaske duk dashi yaji a jikin shi ma sam hakan ba mai yiwuwa bane. Sai ya k'ak'alo murmushi kamar gaske yace da kaamil d'in zai k'arasa gida, nan sukayi sallama yana k'ara kwantar mishi da hankali suka rabu. Koda Ayman yayi gaba kamar gaske kasa ci gaba da tukin yayi saboda nauyi da duk wata gab'a ta jikin shi tayi, sai ya Parker gefen hanya ya fashe da wani kukan zallar bak'in ciki da tashin hankali, da gaske mammie ce yau take jifan shi da mummunar kalmar rashin asali da bakinta, itace ta hana mishi auren Nur, a k'arshe gashi y'ar tata ma ba ita yake soba raihanatu yake so, raihanatun data jima dayi mishi nisa sai dai ya d'aga kai ya hangi k'urar ta bayan ta huce. Sai ya fara dukan sitiyerin da hannun shi yana kuka had'e da girgiza kai. Saida ya kwashe a k'alla wasu dak'ik'u masu yawa a gurin yana kuka sannan ya samu sassaucin yanayin da yake ciki, yaja motar a hankali yabar gurin. Lokacin daya koma gida auntie bata nan sai bai bi takan kowa ba ya shige d'akin shi ya rufo k'ofa. Shi kuwa Ahmad koda ya futo a parlon d'akin su ya samu Khaleefa zaune yana jiran shi, mukullin mota ya d'ora mishi kan cinya, "kyautar da auntie ta bani". Sai ya d'auka gami da taya shi farin ciki. Nan sukaita hirar su, yawan cima akan abinda ya faru suna makaranta ne na dariya ko ban haushi suke tattaunawa, duk don ya d'aukewa khaleefa hankali akan abinda suka tattauna da auntie, baisan bama shi ko a jikin shi bai damu ba ko kad'an, tunda yasan dole akwai abinda zasu tattauna da bata son yaji shiyasa tace ya basu guri. Ta b'angaren auntie kuwa tana shiga d'akinta sauya kaya tayi daga na zaman gida marassa nauyi zuwa nad'in lafaya, yau ko jaka bata d'auka ba sai mukullin mota da ATM card. Gidan iya ta nufa bayan ta tsaya a store d'in kusa da anguwar ta sai musu duk abubuwan amfanin su na yau da kullum, don tasan ko k'arewa yayi ba zasu tab'a bud'e baki su fad'a mata ba. A k'ofar gida ta tsaya ta samu yara suka dinga shiga da kayan ciki ta sallame su sannan ta shiga ciki itama. Dasu harira ta fara karo a tsakar gidan iya suna gyaran kayan miya, bata tab'a ganin suba amma kallo d'aya ta musu tasan y'an uwan iya ne wad'annan duk inda suka futo, sai taji gabanta ya yanke ya fad'i, kenan y'an uwan su sun neme su! lallai watan tonuwar asirinta ya kama..... _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page thirty3️⃣0️⃣ Iya da take aikin shiga da lufdin kayan abincin cikin store tana ganinta ta fad'ad'a fara'ar fuskarta tace, "sannu da zuwa doctor surayyah d'iyar albarka". Itama tana murmushin yak'e tace, "sannun ki dai iya". A nan tsakar gida kan tabarma ta zauna suka gaisa dasu harira, iya ma Suka gaisa bayan ta zauna. Malam da yake sitting room yana rubutu futowa yayi yazo suka gaisa dashi shima, sukaita mata godiyar kayan abinci dashi albarka, ita dai batace musu komai ba sai murmushi da tayi, don inda sabo ta saba da jin irin wannan godiyar daga gurin iya da malam d'in a duk lokacin data aiwatar da nauyin data dad'e da d'orawa kanta shi, duk sunyi shiru tsakanin su, ta b'angaren su iya so suke su fahimci halin da take ciki duk tazo musu yau jiki a sanyaye haka ba yadda suka saba ganinta ba, ita kuwa ganin harira ne ya k'arasa sage mata gwiwa gaba d'aya, tsoronta d'aya kada su iya suce zasu bita k'auye su barta ita kad'ai a duniyar da bata da kowa sai su. Malam ne ya katse shirun su da cewa, "ina Adam da Abdallah". Surayyah ta gyara zamanta tace, "lafiyar su qalou, nima zuwa nayi don na fad'a muku gobe zan koma aiki saboda hutuna ya k'are tun wancen satin...". Malam yace, "Allah sarki Allah yasa a koma a sa'a, Allah yayi jagora". Ta amsa da ameen. Ba ita tabar gidan ba ranar sai bayan sallar isha'i. Tayi sallama dasu iya dake cikin gida ta tadda malam shi kad'ai a d'akin bak'i shima tayi mishi sallama, shi kuwa wata sabuwar godiyar ya k'ara yi mata hadda share hawaye, itama kamar zatayi kukan tace, "don Allah ka daina kukan nan malam...". Malam yace, "Dole nayi kuka surayyah, kin gama mana komai a rayuwa, cin mu, shan mu, tufafin mu duk kece, kin share mana hawayen rashin haihuwar daba mu tab'a yiba, ba abinda zamu ce miki sai fatan Allah ya saka miki da gidan aljannah firdaus....". A sanyaye ta amsa da "ameen" sannan ta d'ora da fad'in, "nima ba abinda zance muku malam, kun share mun hawayen abubuwa da yawa, Ni dai fatana kayi mun alk'awarin zaku ci gaba da kasancewa kakkani ga yarana, yayinda ni zan ci gaba da amsa sunan y'ar ku duk wuya duk rintsi kada wani cikin yaran nan yasan akwai wata a k'asa". Malam yace, "insha Allah nayi miki wannan alk'awarin doctor surayyah". Sai tayi murmushi ta k'arasa sallama dashi ta futa. @@@@@@@ A washe gari Monday ta shirya da wurwuri ta tafi aiki ko break bata iya tsayawa had'awa ba, don a yanzu ba abinda tafi so kamar taga ta fatattaki sabon raunin da yake son shigarta ya kawo nak'asu da tawaya ga jarumtar ta. Koda khaleefa suka futo yin breakfast shida Ahmad, a parlour suka samu Ayman yana safa da marwa hannayen shi duka goye a baya hannun shi rik'e da wayar shi, sun gaisa dashi sama sama khaleefa na karantar sabon sauyin dake tattare da k'anin nashi, bai zurfafa ba ya tafi da kanshi ya karb'i kayan Karin da mama haleema yau ta had'a. A nan k'asan carpet duk suka zauna don suci abincin, kusan Ahmad ne ya tallafe su don a cikin su kowa tura abincin yake more especially khaleefa da girkin auntie kad'ai yafi so a duk cikin girke girke. Bayan sun gama Ahmad yayi musu tayin futa suga gari, Ayman ya bashi uzurin akwai d'an aikin da zai kammala, khaleefa ma zai bada nashi uzurin Ahmad yace wallahi be Isa ba dole shi ya shirya suje. Haka khaleefa ya shirya ba don yaso ba yabi Ahmad d'in suka futa, shi kuma dabarar Ahmad ta sasu yawo ba don komai bane sai don ya d'ebe musu kewar rashin walwalar da suke ciki su duka biyun. Alhamdulillah kuma yayi nasara don tuni ya korewa khaleefa zaman tunani da jigum. Kwana biyu Ahmad yaso yi amma sai gashi ya tasamma had'a kwana biyar a gidan, sosai yake iya yinshi wajen ganin ya fahimci matsalar su duka mutum biyun nan had'e da solving d'inta kafun lokacin da zai huce, auntie kullum zata futa aiki shi kuma baya tab'a barin su shiru musamman khaleefa don Ayman ya saki kad'an, sai dai har yau ya rasa ta hanyar d zai tunkari auntie da zancen da sukayi da mammie, gashi ita d'in ma bata samun wadataccen lokacin zama dasu kamar da farko yanzun. A ranar da Ahmad ya cika sati ya shirya barin garin Kano, khaleefa da Ayman kamar suyi kuka har auntie ma saida taji ba dad'i saboda an saba dashi a gidan sosai, har mama haleema don itama ba kyale ta yayi ba, inya sameta a kitchen tana aiki ya dinga tambaye tambaye da mata karambani kenan. Toh shi mutum ne dabai saba zama shiru kamar su Khaleefa ba ko a gida. Kyautar turarukan maza masu tsada auntie tayi mishi, ta bashi su khumra ya kaiwa maman shi, ta bashi wani again ya kaiwa mahaifin shi, ya karb'a yana godiya sukayi sallama a daren. Washe gari sassafe khaleefa da Ayman suka rakashi airport saboda mugun gargadi da jan kunnen da mahaifin shi ya mishi kan cewa lallai kar ya sake yace zai biyo mota zuwa Abuja. Soo motar shima anan gidan su Khaleefa ya barta za'a turo kwararren driver ya d'auka daga can. Har ya tafi suna d'aga mishi hannu yana d'aga musu. Ko a mota suna tafe ne kawai cike da kewar shi da zasuyi har suka k'arasa gida, ko karyawa khaleefa beyi ba yabi lafiyar gadon shi ya kwanta sai bacci, bashi ya farka ba sai raana, wayar Ahmad ya fara nema yaji ko ya isa gida lafiya, sai dai bai tafi ba. Haka ya shiga bathroom d'inshi ya sake wani wankan ya futo cikin shirin white shirt and blue trouser, duk inda ya gilma ba abinda ke tashi sai lafiyayyen k'amshin turaren shi. Yayi sallar zuhur anan d'akin shi ya d'auki makullin motar shi ya futo ba tare da yasan inda ya nufa ba, tsit gidan nasu kamar babu kowa sai shi kad'ai, a hanyar sauka k'asa yaci karo da mama haleema zata hawo, sai ya bata hanya ta fara hucewa tukun, sai dai harta gilma shi ta dawo da baya, "kaci abincin ka kuwa khaleefa?". (Da yake yanzun ta sake banbance su musamman da halayya). "ai mama bar abincin nan kawai in na futa zan nemi wani abun naci". Mama haleema tace, "ooh to ba damuwa, d'an barkwanci ashe kuma ya tafi". Sai yayi y'ar dariya yace, "ehh Ahmad ba". Mama haleema tace, "Allah sarki sai yaushe zai dawo kuma?". Khaleefa yace, "Anya zai dawo ma... Toh maybe ko in zamu huce Germany ya taho ta nan". "Ayyah Allah sarki". Ta fad'a tana yin gaba don taga kamar ya k'osa da amsa tambayoyinta, shima waje yayi yana tunanin Ahmad da sauk'in kanshi, ya iya zama da mutane shiyasa duk inda yaje mutane son shi suke. Tafiya yake ba don yasan Inda ya nufa ba, ga cikin shi dake aikin kiran chiroma ba k'auk'autawa. _Flash back_ Raihanatu kuwa sun ci gaba da shirin bikin su hankali kwance ba tare da sunsan wainar da ake toyawa a gidan su Imran ba. Ta can d'in mahaifiyar shi tana zaune da raana sai ga d'aya daga masu aikinta sun zo sun shaida mata tana da bak'uwa. Kamar tace a fad'a musu bata nan sai kuma ta fasa don batasan ko su waye ba, "kice musu Ina zuwa..." Hajiya tafeeda ta fad'a cikin ginshera. Ko bayan futar me aikin ma saida ta gama shan k'amshin ta sannan ta tashi ta futo. Umma salaha da take zaune tana ta k'arewa gidan kallo a ranta tana jinjina girman daular da raihanan zata shiga ta huta bayan su y'ay'an su gasu can a wahala, sai kuwa cewa tayi hu'umm ai wallahi ko zanyi yawo tsirara ba'a Isa ayi auren nan ba, wannan babban family haka....tab. Tana ganin hajiya tafeeda ta saita kanta. Ta zauna suka gaisa har tana tambayarta ya shirye shirye, bata amsa mata ba don a duk lokacin da akayi maganar auren Imrana ji take kamar ta kashe kanta don takaici, "wacece ke kuma" ta tambaya da gatsali. Sai ta k'are washe hak'oran ta waje, "ai dama nasan ba lallai ki shaida niba, kuma har asibiti mukaje kwanaki muka duba jikin yaron ki, toh nidai sunana salaha matar wan surukin d'anki Imrana" sake gimtse fuska hajiya tafeeda tayi cikin daka tsawa tace, "dallah malama tashi ki bani wajee". Da sauri umma salaha tace, "haba hajiya ai kya tsaya kiji abinda yazo dani ko?" Wani kallon banza ta kuma yi mata, ita kuwa cikin ko'in kula ta fara maganarta don hassada ta gama rufe mata ido tuni, "Kin ganni nan ba ruwana da harkar yarinyar da uwarta, don ni raihana ko gaisuwa ban ishe taba tana ganin ba ubanda ya Isa ya fad'a Mata taji, haka uwarta, kinsan Allah ba k'aramin mamaki nayi da akace d'anki ne zai auri gantalalliyar yarinyar nan ba, ta gama yawonta a gari na shek'e aya da wani yaron mak'otan mu, sau ba adadi uwar tana d'aukarta aje a zubar da ciki, ke ba don kar kice k'arya nake ba sai ince har haihuwa tayi a b'oye ba wanda ya sani, kinganni nan ba k'aramin aminci nake da ruqayya ba ada, babu sirrinta da ban sani ba, haka ba irin gaskiyar da bana fad'a mata amma bata d'auka, shine nidai na kasa hak'uri nace bari na nemeki na warware miki zare da abawa har makasudin auren raihana da Imrana ma saina fad'a miki....". Nan ta baje kolin hajar munafunci da sharri gami da aibatawa ga raihana da uwarta, itama kuwa hajiya tafeeda ta baje kunnuwa tana saurare dama a wuya take da maganar auren yarinyar yanzu kuwa gashi ta k'ara jin tabbaci kan rashin ingancin ta, haka ta gama karyayyakinta ta tashi zata tafi, har kyautar dubu biyar hajiya tafeeda ta mata da godiya bisa ga labarin data kawo. Umma salaha kuwa ta futo tana dariya da fad'in, "ahh ga kyauta ga fahimta, maga ta tsiya ai ba sai ayi auren mu gani ba". Ita kuwa hajiya tafeeda a washe garin ranar ta sake samun Imran da titsiyewar shin ya shirya rabuwa da raihana ko sai ita ta rabu dashi! Hankalin shi tashi yayi, da yana murna kwana biyu ta rabu dashi da zancen ashe ita tana nan akan bakanta bai sani ba. Sai ya fashe da kuka ya durk'usa a gabanta yana kuka yana mata magiya kan ta barshi ya auri raihana shi yana sonta duk yadda take. Aikuwa ba k'aramin tashin hankali ya gani ba saida yayi da kace akan furucin shi, haka ta gama maseefa ta bashi wa'adin cikin nan da kwanaki uku ya yanke hukunci, ta barshi a gurin ba tausayi ba Imani kamar ba itace ta durk'usa ta haife shiba, haka Imran ya shiga mawuyacin hali a cikin y'an kwanakin, yana son zancen yaje kunnen mahaifin shi amma yana tsoron hukuncin da alhajin zai d'auka don dama ya dad'e da gargadin ta akan shiga shirgin maganar auren Imran d'in, a cikin datsin ko raihana bai samu sukunin kira yadda ya kamata ba, da zarar yaji lafiyarta data y'an gidan su yaji muryarta shikenan zai kashe wayar shi ya fad'a tunanin mafuta. Kwana uku ya huce harda doriyar kwana biyu bai yarda sun had'u da ita ba suna ta wasan b'uya, a ranar da yamma ya taso kasuwa da k'udurin had'a kayanshi ya gudu gidan auntie rahama (matar babansu) ya rok'e ta kada ta fad'awa kowa yana gidanta har sai bayan an d'aura aure raihana ta zama tashi halak malak, a wannan lokacin yasan ya tserewa duk wani hargaginta kuma. Cikin rashin sa'a yana kulle d'akin shi yaci karo da ita tana tahowa gurin shi, gaban shine ya tsinke ya fad'i har ta kaiga ya saki jakar kayanshi bai sani ba, kamar yaga wata maseefa haka ya dinga ambaton sunan Allah a ranshi. Ita kuwa fuska a d'aure ba annuri tace, "wato Kai shirin guduwa ma kakeyi?? Toh in kaso kabar duniyar ma gaba d'aya amma bayan ka warware wannan shegen auren na rashin albarka daga kanka". Duk jikinshi ba inda baya rawa, ganin kamar k'afarshi ba zata iya d'aukar shiba sai ya zauna dabas a gurin ya had'a kai da gwiwa. Cikin halin ko'in kula tace, "ka shirya aiwatar da abinda na umarceka ko sai na tsine maka albarka kamar yadda na tsinewa auren....". Bakin shi yana rawa ya d'ago ya kalleta da fuskar tausayawa yace, "Ni bani da wani zab'i don bansan me zance da raihana ba amma duk yadda kika ce haka za'ayi". Cikin jin dad'i hajiya tafeeda tace, "good zakayi nadamar zab'in daka bani kuwa indai nice, kafun nan biyoni d'akina kada abban ku yazo ya ganka haka ka sani a uku kuma.....". Haka ta tisa shi a gaba har d'akinta ta murza key sannan ta karb'i wayar shi bayan ya cire mata a lock, tak'aitaccen rubutu tayi kamar haka, "raihanatu a yau ni Imrana ina farin cikin sanar dake cewa na fasa auren ki bisa kyakkyawar shaidar gani da ido ta gurb'acewar tarbiyya a tare dake, daga yau babu ni! babu ke!! Allah ya had'a kowa da rabon shi". Sai data bashi ya karanta zuciyar shi kamar ta futo tasa shi yayi sending, cikin tsananin tashin hankali da muryar kuka ya durk'usa har k'asa yana mata magiya kan a sauya abinda za'a fad'a. Ta wani daka mishi tsawa tana fad'in, "ko mutuwa zakayi Imran saika rabu da yarinyar nan a yau, zakayi sending ko sai na tsine maka kabi duniyaaa". Ba shiri yayi sending ya durk'usa kasan tiles yana kuka sosai, (ko marar Imani yaga Imran a wannan lokaci saiya tausaya mishi, Ni kaina na soma kwokwanto akan haihuwar shi, Anya hajiya tafeeda ta haife shi kuwa??). Saida ta tabbatar sak'on yaje sannan tayi deleting, ta sake tsara mishi abinda take so ya fad'awa mahaifin shi a daren yau,,,,, haka yana ji yana gani ya amince sannan ya tashi jiki a sanyaye ya futa daga d'akinta, banda auntie rahama ta sake yi mishi mugun gargadi akan mahaifiya da shawarar binta sau da k'afa duk munin halin da zata zo dashi da tuni ya jima da yanke alak'a da ita ya tattara ya bar mata gidan, saboda ya jima da fahimtar bata k'aunar farin cikin shi a rayuwarta gaba d'aya. Saboda son kanta farin cikinta shine gaba da komai. . Raihanatu kuwa a dai dai lokacin da ya tura mata wannan sak'o tana aikin ninke kayanta da wani almajiri yazo ya wanke mata. Koda taji shigowar sak'o da sauri ta d'auko wayarta da take kusa tana murmushi zata duba, sai dai me?? Wani mugun tashin hankali ne ya diro mata lokaci d'aya taji duk hankalinta ya tashi, sai ta kira no shi a lokacin ya zauna a d'akin shi kenan cikin yanke k'auna ya d'aga, da raunatacciyar murya gwanin tausayi ta fara tambayar shi, "da gaske ne sak'on dana gani daga gare kane Imran". Da kyar ya iya saita yanayin shi yace, "Eh raihana ki yafe ni, fatan Allah ya had'a fuskokin mu da alkhairy ya baki miji na gari wanda ya fini". Bai jira jin ta bakinta ba ya kashe wayar ma gaba d'aya yayi jifa da ita, don baiga amfaninta ba tunda gashi ta zamo silar rabuwarshi da masoyiyar shi. Ita kuwa tsabar tashin hankali da rudu bata san lokacin da wayar ta zame a hannun taba ta daku da k'afarta. Saita rasa abinda zatayi a lokacin, kuka ko dariya ko duka biyu! Sai kawai ta zura hijab daga k'arshe cikin rashin sanin takamaiman abin yi ta fuce daga gidan su ba tare da tasan inda ta nufa ba rik'e da wayarta a hannunta, ko data kalli gabas! yamma! Kudu! Arewa! Bata ga wata madafa ba sai kawai ta rubutawa Ayman tak'aitaccen sak'o, "Ina cikin matuk'ar tashin hankali,,,, bansan me yake bibiyar rayuwata ba Imrana ya fasa aurena shima a karo na shida, Ina so kazo mu had'u yanzu....". Ko da tayi sending bata ci gaba da tsayuwa a k'ofar gidan ba tayi gaba. Tafiya take zuciyarta tana up and down tun tana gane inda take zura k'afarta har kanta ya kulle ta daina gane komai. Cikin rashin sani ta hau kan titi motoci suna ta horn bata sani ba sai ji tayi kamar an daki k'afarta da k'arfe me k'arfi,,, ta durk'ushe a gurin tare da rintse ido mutane suka yo caa a kanta suna salati da sallallami. _Shin kuna bibiyar littafan in-identical twins? Toh maza garzaya ki karanta DARAJAR HAK'URI na doctor fayeez m usmern. Kada a barki a baya. Da JARUMAR UWA na merhreeyeart lerwerl👉🏻don jin irin sak'on da suke d'auke dashi_ _Masu comment Ina godiya da jinjina 😍😍kune k'arfin gwiwa ta a koda yaushe,,,,,fatan muna tafe tare masoyan asali_ _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Mareeyeart lawal* Page thirty one3️⃣1️⃣ Sam ta kasa bud'e idonta bare tasan ainahin abinda yake wakana a gurin har zuwa lokacin da hancinta ya soma shak'o mata wani k'amshin turare na daban, ba zatace batasan irin k'amshin ba amma wanda ta tab'a shak'ar irin k'amshin a tare dashi ya kwanta mata. Shi kuwa cikin zafin rai da b'acin rai mai tsanani ya fara mata maseefa, ba don hakan ya kasance halin shi ba sai don zafin b'acin ran daya futo dashi tun daga gida ya rasa inda zai sauke Allah ya had'a shi da ita yanzun a dai dai, tunda ya ganta tsakiyar titi yake faman zabga mata horn da yink'urin kauce mata hakan bai yiwu ba har saida ya daki gefen k'afarta. "ke wacce irin mahaukaciya ce, bakya gani ne zaki hau tsakiyar titi kina tafiya....". Sai da ta sake rintse idonta a lokacin da mummunar kalmar hauka ta shiga kunnen ta, abu na k'arshe da take fad'awa wanda duk ya dameta da yawa a rayuwa, saboda a ganinta duk girman zagin da mutum zai mata in ta kira shi mahaukaci ta fanshe. Idonta ko bud'ewa sosai baiyi ba amma a haka ta mik'e ko rad'ad'i da zugin da k'afarta take bata tsaya sauraro ba ta fara mayar mishi da amsa cikin zafi, "Kaine babban mahaukaci da baka iya ganin gaban ka idan kana tafiyaaaa". Ta k'arasa fad'a cikin maseefa tare da komawa ta zauna a gurin lokaci d'aya sakamakon wani mugun zafi da zugi da k'afarta ta k'ara. "wayyoh Allah na!!!" Ta fad'a k'asa k'asa tana jujjuya kanta cikin azaba. Duk da yaso fad'a mata bak'ak'en maganganun da saita raina kanta bisa gangancin dangantashi da kalmar hauka da tayi, amma ganin halin data shiga sai ya danni zuciyarshi ba don ya hak'ura ba,,,,, sai don tsoron abinda zai biyo bayan aika aikar da yayi a k'afar a sanadin tafiya ba kulawa da fad'awa dogon tunani a lokacin da bai kamata ba. Ganin ya kasa d'aukar wani kwakkwaran mataki ga yarinya durk'ushe tana matagugun ciwo sai mutanen gurin da suke kallon komai suka fara yi mishi fad'a, "kada ka zama mara Imani mana dubi halin da yarinyar nan take ciki, dukkannin ku kunyi laifi, Kuna tafiya kuna tunani har bakusan inda kuke sa k'afar kuba.... Wanda hakan yake babban kuskure". Wani tsoho ne meyin wannan magana, wata mace da take cikin adaidaita sahu itama kusan taga komai akan idonta ce ta futo da alama nurse ce ko likita, sanye dai da fararen kaya tazo ta d'ago raihana, "bud'e mana motar ka". Matar ta fad'a ba wasa. Shima ba annuri har lokacin a fuskarshi yace, "me zakuyi a motata". "Ba kai ka bige taba? Asibiti zaka kaimu a duba mata k'afar ka biya duk abinda ya biyo baya". Ko kafun yace wani abu mutanen gurin sunce wannan haka yake, kuje dashi asibiti ya tsaya a tabbatar an duba ta yadda ya kamata. Raihana kam a lokacin don bata da bakin magana ne amma data fad'a musu sam bata buk'atar taimakon wannan marar Imanin mutumin. Shima baice komai ba, ya bud'e musu k'ofar aka shiga da ita cikin motar shima ya shiga ya fara tafiya. "Wanne asibitin zamu". Ya tambayeta, matar tace, "city star". "can you locate please". A ranta tace ashe ma bak'o ne kai a garin, a fili kuma tace, "okay ba damuwa". Suna tafe tana kwatanta mishi har suka isa, yanzun ma ita ta taimaka mata suka shiga har cikin asibitin, a wani empty room ta ajiye ta shi kuma ya samu gefe guda ya zauna ya ciro wayarshi a aljihu yana dubawa. Ita kuma nurse d'in ta futa ta kawo kayan aiki, sai a lokacin raihana ta d'aga dogon hijab d'in jikinta ashe taji ciwo sosai a k'afar har yana jini, satar kallon shi tayi, bata ga fuskar shiba har yanzu saboda ya juya mata baya. Taso taga wannan shugaban marassa Imanin da bayan ya bige ta har yake da bakin kiranta mahaukaciya, mtsss! Taja dogon tsaki a fili tare da kauda kanta gefe. Ya jita sarai amma ya share ko motsi beyi ba. Ganin lokaci yana tafiya ga nurse d'in sai safa da marwa take tsakanin d'akin da reception zuwa office sai khaleefa ya mik'e yana tambayarta, "is there any problem". Dafe kanta tayi da hannunta tace, "Babu doctor da zai iya duba mata raunin cikin k'ashin a asibitin ne". Sai yayi d'an jim kafun ya saci kallonta, duk data kauda kanta gefe amma kallo d'aya zakasan she's in pain, ga k'afar sai d'igar da jini take har ta fara jik'a gurin ma. Baice da nurse d'in komai ba ya k'arasa gaban gadon ya zauna ya tsurawa k'afar tata ido, har yanzu bata yarda ta sake kallon shiba duk da tarin k'amshin shi daya cika mata hanci. Slowly ya saka socks ta hannu ya matso da kayan treatment kusa ya janye rigar jikinta zuwa gwiwar ta, ko kafun raihana tasan me yake ciki tuni ya soma jan k'afar yana mik'ar da ita had'e da d'an jijjigata kad'an, tsananin azabar daya kai mata har kwakwalwar kanta yasa ta rintse ido tare da d'ora hannunta kan hannun shi ta rik'e shi gam. Sai daya saci kallon fuskarta, sai jujjuya kai take. Matar da take gefe kuwa cike da tsoro take faman jera mishi tambayoyi, "bawan Allah! Kada ka nakasa y'ar mutane saboda rashin fahimtar ka na banza da wofii fa!!! Malam! Malam!! Kai likita ne ko kuwaaaa, security malam kada ka illata yarinyar nan faaa!!". Duk wannan sambatun da take yi bai kulata ba har ya daidaita k'ashin gurin daya targad'e ya mayar dashi dai dai ya mata treatment d'in raunin saman fatar. Sake kallon fuskarta yayi har yanzu idonta a rufe yake ta datse lebenta na k'asa da hak'ori. Shikam ba don kada yayi k'arya ba sai yace yasan wannan yarinyar amma ya manta a ina. Nurse d'in kam ajiyar zuciya ta sauke tana faman jera mata sannu, bata iya amsa mata ba, sai hannunta data d'auke daga saman nashi ta kife kanta jikin k'arfen gadon da take zaune, matar ce ta dawo da dubanta gare shi ya koma inda ya taso yana ci gaba da danne dannen shi a waya hankali kwance, cikin lokaci k'alilan yayi aikin da a asibitin su likita d'aya ne zai iya yi kuma bada sauri haka ba, sai taji ba zata iya hak'uri ba sai ta tambaye shi, don haka ta matsa gaban shi ta sake tambayarshi, "how do you help her? Are you a physiotherapist?". Murmushi kawai ya mata, zata sake yin magana wayarta ta d'auki ruri, "excuse me please" ta fad'a tare da fucewa. Ita kuwa raihana tuno da k'alubalen da yake gabanta sai taji hankalinta ya sake tashi, shin waya kamata ta fara kaiwa kukanta? Waye zai taimaketa ya shawo kan Imrana ya janye daga fasa aurenta? A duniya yanzu bata da buk'atar data huce taga ta auri Imrana komai wahalar da zata Sha bayan auren shi kuwa,,,, Tasan tabbas iyayenta suka ji abinda ke faruwa ba k'aramin tashin hankali zasu shiga ba, musamman ummie data fita damuwa akan fashe fashen auren nan nata, har ta fara tsoron ko haka zata k'are rayuwarta ba aure,,,, gefe guda ga umma salaha da taci mugun alwashi akan ta, ya kamata ayi auren nan ko don a k'aryata ta "Ya Salam! Allah ka gaggauta kawo mun d'auki". Ta fad'a a fili ba tare da tasan maganar ta futo ba. Wani tunani ne ya fad'o mata saita duba wayarta da Allah yasa duk abun nan tana hannunta ta nemo no Ayman, gajeren sak'o ta sake tura mishi ba dogon tunani kafun aiwatarwa. "Ka taimake ni ka ajiye duk wani kuskure nawa da yasa kake fushi dani a kanshi wanda bansan ma na aikata maka ba cikin ajizanci irin nawa,,,,kazo ka taimake ni na futa daga matsalar da nake ciki please.....". Tana tura sak'on ta ajiye wayar ta gefe a ranta tana jin dole ta bar gurin nan a yanzu yanzu, ta dire k'afarta d'aya me lafiyar zata ajiye me ciwon tsoro ya hana ta, shi kuwa motsin tane ya sa shi d'ago kai ya dube ta, ta sauko da k'afa d'aya kuma ta kasa komawa ga mazauninta. Kamar yayi banza da ita tunda ba jaririya bace ita d'in sai kuma zuciyar Imani ta hane shi da aikata hakan. Sai ya mik'e ya k'arasa gaban gadon ya mik'a mata hannun shi, sai a lokacin ta d'ago ta kalle shi, "Yaya Ayman" ta kira sunan duk da tana iya ganin wannan ba irin Ayman d'in da ta sani bane, shima kamar ba zaice mata komai ba sai kuma ya wayar mata dakai, "Ni ba Ayman bane". Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta kira sunan shi da murya k'asa k'asa ba tare da tasan ma ta aikata hakan a fili ba, "khaleefa". Da mamaki ya sake kallon fuskarta "a Ina kika sanni". Bata bashi amsa ba sai k'ok'arin zama a gefen gadon da take amma ta kasa, kamar ya taimaka mata yanzun ma,,, sai kuma ya barta, ganin da gaske ba zata iya zama da kanta saman gadon ba saida taimakon shi, k'afar me lafiya ya d'age mata ta zauna da kyar bayan ta rintse idonta tsananin azaba na kai mata har cikin kwanyarta. Sai a lokacin kukan ta ya samu damar futowa fili, kuka take wanda ya zarta na zafin ciwon da yake jikinta...., khaleefa yayi imanin indai za'a gyara mata k'ashi ba tayi kuka ba lallai wannan kukan da take na wani abun ne daban. Sai ya koma gefe ya zauna yana sauraron yadda take kuka sadidan kamar an turo ta, kuka irin mai buk'atar ban baki da rarrashin nan. Tun khaleefa na iya sauraronta har ya gaza, Cox she mutum ne da baya son jin sautin kuka cikin kunnen shi sam, sai ya sake mik'ewa daga inda yake zaune ya dawo kusa da ita ya zauna ya tsura mara ido yana kallonta, "baiwar Allah! Me nayi miki zaki hukunta ni da sautin kukan ki haka.....". Karo na farko da yayi magana da wani cikin tausasawa tun bayan daya dawo gida Nigeria. Sai ta rage sautin kukan nata ta soma share hawayenta da tafin hannunta, farin hankie ya zaro a aljihu ya mik'a mata, ta karb'a bayan ta saci kallon shi da rinannun idanunta, bayan ta share hawayenta ajiyar zuciya ta fara saukewa a jejjere. Koba komai kuka rahama ne Shikam tsura mata ido yayi yana nazarin tarin damuwar data bayyana saman fuskarta, "a wasu lokutan saka abu a cikin rai kan assasa damuwowi da yawa masu tushe da marassa makama, kamar yadda futar da magana daga cikin ciki kan rage rad'ad'i da zugin dake cikin zuciya... Wani abu yana damun ki wanda kike jin ba zaki iya tattauna shi da kowa ba,, wata k'ila saboda gudun kar ya shiga kunnen mutane da yawa,,,, har yakai kunnen ma'assasa damuwar.....". Sai yaja ajiyar zuciya yana ci gaba da kallon targad'addiyar k'afarta da tasha nadi a gurin shi d'azu kafun ya d'ora da fad'in, "idan kin yarda da duk abinda na fad'a da gaske.... Toh ki tattauna damuwarki dani insha Allah sirrin ki zai zama safe a gurina......". Kallon shi raihana tayi na y'an dak'ik'u tana nazarin shi, shima ita yake kallo haka kawai lokaci d'aya yaji ya aminta da yarinyar, nutsuwarta da kamalarta suna sanar dashi asalin wacece ita. Itama kusan abinda taji a ranta kenan game dashi, tana iya ganin rib'anyar kyawawan halayen Ayman fiye da goma a tare da wannan giant d'in (Nikam nace ta ina😨). Sai taji ta aminta zata iya futar mishi da abinda bata tab'a fad'awa wani mahaluki ba, hatta Ayman da yake tare da ita tsawon shekaru kuwa. Yamutsa fuskarta tayi kad'an ta d'ago suka k'ara had'a ido, sai tayi mishi murmushin k'arfin hali. "Sannu ya kike jin k'afar". Ya tambaye ta da kulawa, Da disasshen muryarta ta amsa, "da sauk'i". Ta jima shiru zuciyarta na kai komo kafun ta sake mishi wata maganar, "shin idan na fad'a maka matsala ta zaka nemo mun mafuta?". Direct ya bata amsa, "idar har ina da yadda zanyi na nemo mikin baa". Sai ta tsura mishi ido zuciyarta na ingizata kan ta fad'a mishi damuwarta kawai, watak'ila zai iya taimaka mata wajen ganin ta samu mafuta ba tare data karya zuciyar iyayenta ba sun d'aga hankalin su, ita kad'anta tana neman zama matsala gare su. A hankali cikin nutsuwa ta fara mishi bayanin abinda yafi damunta a duk cikin matsalolin, "yau shekarata uku kan na hud'u ana saka ranar aurena ana fasawa sau kusan biyar, duk an yiwa k'annena da suke bina aure, haka sauran y'an matan familyn mu, duk da kasancewar Ina da burin yin zuzzurfan karatun likita amma na sadaukar da wannan buri nawa tuni ga wata kwallin mutum guda tal data ke iya sadaukar da komai domin mu,,, wato mahaifiyata da a kullum safiyar Allah dare da rana bata da addu'ar data huce Allah ya kawo mun miji na gari nayi aure kamar kowacce yarinya,,, hakan yasa nima na karkata hankalina ga abinda naga tafi so a tare dani wato nayi auren,,,, kamar yadda yake babban burin mahaifina shima yaga cewa sun aurar dani lafiyar Allah ko don sauke nauyin da Allah ya d'ora musu a kaina, sannan ta gefe guda akwai tarin k'alubalulluka akaina daga gurin wasu tsirarun mutane da suka kasa fahimtar ba laifina bane dana iyayena nakai har yanzu banyi aure ba, haka zasu zo su juye buhu buhun cin mutumcin su ga mahaifiyata da suka d'orawa karan tsana ba li bare la a duk lokacin da aka fasa aurena, sai kace itace ta hana ni yin auren, ta wani gefen kuma ga wata mata da taci alwashin indai tana numfashi bani da miji a duniyaaa tayi alk'awari....Wanda duka nida ummiena bamu san dalilinta ba". Ta k'arasa fad'a dakyar cikin muryar kuka, khaleefa girgiza kanshi kurum yayi yana al'ajabin halin mutanen mu na yau, baice mata kanzil ba har ta gama share hawayen ta ajiye mishi hankien shi gefen shi, taci gaba da magana da rawar murya mai cike da rauni. "a wannan karon na k'arshe na had'u da wani saurayi Imrana, ban tab'a tsayawa nayi soyayyah da wani mahaluki ba sai shi duk cikin samarina, tafiyar mu tayi nisa sosai har na fara tunanin me yiwuwa shine zai zamo mijina a wannan karon, su kansu y'an gidan mu tun suna d'ari d'ari har suka saki jiki suna shirye shiryen biki hankali kwance, har an kawo lefe an gama komai kwatsam! D'azu da yammaci Ina ninke kayana ya turo mun sak'o kamar haka.....". Hannunta har rawa yake ta nemo sak'on ta nuna mishi, taci gaba da maganar ta kuma "ko bayan ba duba dana kira shi sai yake bani hak'uri yace mun wai shima ya fasa aurenaaaa,,,,, na rasa wanda zan fad'awa damuwata shine na futo don na nemowa kaina mafuta ba tare da nasan inda nake nufa ba har Allah ya had'a ni da kai ka bugeni........". Ajiye mata wayarta yayi a lokacin da ta kai aya a zancenta, ya mik'e tsaye ya fara safa da marwa cikin matuk'ar tausayinta, sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa d'azu ta hau titi tana tafiya kamar sabuwar mahaukaciya, bata jin horn bata ganin inda take jefa k'afarta ma gaba d'aya. Sake dawowa yayi kusa da ita ya zauna yana kallon yanda take kuka bilhak'k'i da duka gaskiyarta, wato shi tunda yake ma rayuwar wani mutum bata tab'a bashi tausayi kamar tata ba in aka d'auke tasu damalmalalliyar rayuwar. Yarinya k'arama kamarta, daya kamata ace yanzu tana can wajen fafutukar Isa ga muradanta, amma gata a nan tana fad'a da k'addarorin ta! Babban abin bak'in cikin ma akan aure? Sai yaja tsaki a fili yana sake auna zantuttukan ta kafun wani tunani ya fad'o mishi, lallai k'addarar ta tayi shige da tasu ta wani b'angaren. Sai wani tunanin ya sake fad'o mishi from no where, Kuma ba tare da dogon nazari ko lissafi ba yayi na'am da shawarar zuciyarshi ta lokacin a take. Sai ya kalleta yana tambayarta, "Yanzu kwana nawa ya rage auren?". "Kwana shida" ta bashi amsa a sanyaye, sai yayi jimm a ranshi, kafun ya k'ara kallonta yace, "toh nidai a halin yanzu bansan wata mafuta da zan kawo miki da zata sa saurayin ki ya dawo ya aureki dole ba, amma akwai wata shawara, shin zaki aureni?" Da hanzari ta d'ago ta kalleshi ba tare ma da tasan ta aikata hakan ba, wannan wane irin mutum ne yana nufin ta aure shi daga had'uwa a yau d'azun nan, hakanan ba dogon tunani ko nazari, bare a kaiga tushen abinda ke had'a alak'ar aure. Khaleefa ganin tana yi mishi wani irin kallo na rashin fahimta, sai ya fara k'ok'arin gyara zancen shi da fahimtar da ita ainahin abinda yake nufi, "yi hak'uri naga kina kallona a bai bai, kamar yadda kika bani labarin ki, nima zan baki labarin soyayyata bazan b'oye miki komai ba" sai yaja dogon numfashi kafun yaci gaba, "na kasance Ina yin rayuwata single a makaranta, ban tab'a kallon wata mace da fuskar soyayyah ba, duk da a raina ina da zab'in irin matar da nake son aure a rayuwata, amma duk da haka a lokacin ba abinda nasa gaba sai karatu, kwatsam ba tare da zato bare tsammani ba na had'u da wata yarinya, hak'ik'a ta kasance mace ta farko data fara d'aukar hankalina, tazo cif da irin matar da nake hasashen mallaka matsayin matar aure na,muka fara soyayyah da ita cikin aminci da aminta da juna, har mun gama tsara yadda zamu tafi da rayuwarmu bayan auren mu, Babu zato sai wani abu ya gindaya marar dad'i a tsakanin mu wanda ya zamo silar da bama tare a halin yanzu maganar da nake miki, sai dai akwai mafuta da yiwuwar zan sameta cikin sauk'i idan har na cika wani sharad'i a gurin mamana, sharad'in da zai kaini Isa ga b'arakar dake tsakanin mu na d'inke ta mu zauna tare har abada, sai dai bisa wani sharad'in shima,. Sai dai shi bana komai bane sai aure, tace dole sai nayi aure kafun ta amince da wancan sharad'in da zanbi izuwa ga cikar burina, anan sai naga munyi tarayyah kan abu guda, ke kina son kiyi aure koda na yini guda ne, ni kuma Ina son matar boge da zata taimaka mun na Isa ga cikar burina, shine na kawo mana maslahar aure me kama dana deal, nayi alk'awarin zan inganta rayuwarki ta yadda kaf mak'iyan ki sai sun dawo karkashin ki sun jingina da inuwar ki zasu huta, zaki samu cikakkiyar nutsuwa da damar zab'ar duk irin mijin daya dace dake bayan shekaru biyar a lokacin na tabbatar mun kaiga samun cikar burin mu, zaki ci gaba da karatun ki, sannan zan ni da kaina zan taimaka miki wajen ganin kin samu miji dai dai da ra'ayin ki, mai sonki so na gaskiya ba wanda wani guntun dalili zai sashi fasa auren kiba, amma yadda kika gani, zan baki kwana biyu kiyi tunani akai sai ki sanar dani hukuncin da kika yanke"...... Tunda ya fara magana take kallon shi tana sauraron shi da mugun mamaki har ya dire, wannan abu kamar a shirin firm? Ita a firm kawai tasan ana Contract marriage sai gashi yau abun yana shirin fad'owa kanta zahiri, tunani biyu tayi a lokacin taji tayi na'am da buk'atar shi ba tare da dogon tunani ko nazari ba, na farko matar Abba abubakar data lashi takobin bata Isa tayi aure kamar sauran mata ba, na biyu ummienta, ta d'aga hankalinta sosai akan y'ar hatsaniyar da aka fara samu cikin kwanakin nan, tana tunanin idan ummie taji mummunar labarin fasa aurenta da Imrana komai ma zai iya faruwa da ita, sai ta k'ara kallon khaleefa ta fara magana da karyayyiyar murya me cike da rauni, "ba sai kayi mun komai ba, na riga na jima da zama hopeless a rayuwa, a yanzu bani da burin daya huce na samu mafaka koda ta kwana biyu ce a gidan wanda zai amsa sunan mijina, muradina kawai duniya ta ga na tab'a aure koda sau d'aya ne a tarihi......". Sai ta tsaya tana sheshsheka kafun taci gaba, "na amince da auren ka,,,, na amince ba sai nayi tunani baaaa". Cikin jin dad'i da farin cikin da baisan kona meye ba ya k'araso gabanta kad'an yasa hankie yana share mata hawayen fuskarta, bata iya yin kwakkwaran motsi ba har ya goge mata fuskar ba tare da ya yadda hannun shi ya tab'a koda gefen fuskarta ba ya ajiye mata hankien a gefe. "Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shin kina ganin iyayen ki zasu yarda ki auri mutumin da bashi da cikakken asali". Wani irin kallon mamaki ta bishi dashi kafun ta sauke kanta k'asa cikin jin nauyin maganarshi, "Ni ban tab'a d'auka akwai wani abun nema ga iyaye a gurin mijin da zasu aurar wa da y'ar su wanda ya huce na kyakkyawar tarbiyya mai kyau abun koyi ga kowa ba, kuma nasan auntie tayi iya yinta wajen ganin duk kun samu haka kaida d'an uwanka..... Toh meye kake son fad'a bayan wannan". Girgiza kanshi kawai yayi a ranshi yana ganin kawai bata gane abinda yake nufi bane, duk da kalamanta na farko sun so yin tasiri a zuciyar shi ainun, amma sai ya bagarar saboda shi idon shi duka sun rufe, Saleema kawai yake gani sai tsanin da zai taka ya Isa gareta, burin shi d'aya ya kaiga dangin mahaifin shi ya samu abinda shima zaiyi alfahari dashi a cikin al'umma. Khaleefa ya tambayeta sunanta da anguwar su, koda ta fad'i sunan saida yaji kamar ya tab'a jin sunan a gurin wani amma ya manta a ina ne, saida ta fad'i anguwar sannan ya tuna lallai yasan tane a gidan iya. Sunci gaba da zama jiran nurse don ta sallame su, kowa cikin su ya mama gaban shi musamman ma raihana da kiran Abba da ummie keta faman shigowa tana rejecting. Koda nurse ta dawo ta gansu tare suna magana jifa jifa mamaki tayi sosai, kenan sun shirya daga futar ta amsa kiran doctor? Khaleefa tambayar ta yayi ko nawa ne bill d'in su na asibitin. Ta fad'a mishi Inda zaije ya biya, ya futa ita kuma ta dawo kusa da raihanan tana tambayar ta "ko zaki iya tafiya da k'afarta ?" Raihana tace, "watak'ila sai na gwada dai". Koda ya dawo har ta sauko daga gadon, hakanan ta tattaka k'afar tayi sallama da nurse suka nufi hanyar futa tare kowa da abinda yake tunawa cikin ranshi. (Nikam nace sun zo a bai bai, zasu koma a dai dai🤔😄). Har gurin motar shi suka je sai dai ta k'ek'asa k'asa tace ita sam ba zata shiga ba gwara ta hau napep,, shima bai damu ba ya nema mata napep ya biya kud'in bayan sunyi exchange phone number ta tafi. Saida ya jima tsaye a gurin tuni sun k'ule sannan ya iya tafiya wajen motarshi ya shiga, har yanzu baiga wani abu ba dai daiba a cikin abinda yake shirya jefa rayuwar shi a ciki wato yaudara, zai yaudari mahaifiyar shi abinda bai tab'a yiba tunda suka taso sai yau ta sanadin kace *********. ********* Raihana kuwa har k'ofar gida me napep ya ajiye ta, ta futo tana d''ogasawa ta nufi cikin gidan su, lokacin tuni anyi magrib prayer, ummie da Abba suna shirin sake gwada no ta sai gata ta shigo bakinta d'auke da sallama, ummie ko lura da yanayin data shigo ma ba tayi ba ta zabga mata wani uban mari daya assasa mata ganin taurari ba tare data shirya ba. "Daga gidan uban wa kike a daren nan?". A daren ranar Ayman yana kwance da damuwar inda d'an uwan shi yayi tun yammacin yau har yanzu bai dawo ba, wayar shi ta fara ringing, koda ya duba Auntie ce take kiran, "kazo malam yazo har zai tafi". Abinda ta fad'a kenan a lokacin daya kara wayar a kunnen shi, ta katse kiran, sai ya yink'ura ya tashi ya taho parlon k'asa don malam baya tab'a hawa sama in yazo. Yana zaune kan kujera suna hira da auntie akan abinda ya shafe su su kad'ai, sai dai Ayman na shigowa suka bar zancen, shi kuwa bayan sun gaisa da malam abinda ya fara tambayar shi shine, "shin malam da gaske ne abinda naji cewa an fasa auren raihanatu?". Malam da mamakin shi yace, "Anya kuwa? A ina kaji wannan tatsuniyar ta k'anzon kurege kuma". Sai yayi shiru bai sake cewa komai ba, tunda raihana ta mishi massage d'innan ya tabbatar da gaske hakane an fasa d'in, don bata tab'a yi mishi k'arya ba, toh amma tunda malam basu sani ba shi bazai sake cewa komai a kai ba don ba zai yarda aji mutuwar sarki a bakin shiba. Daga Auntie har malam basu sake bi ta kan maganar Ayman d'in ba har suka gama hirar su yayi musu sallama ya tafi. Yana tafiya khaleefa na shigowa, da kyar ya bawa Ayman da yake faman tambayar shi inda yaje tun d'azu hannu suka gaisa, ba tare daya bashi amsa ba yayi hucewar shi d'aki don yayi sallah da wanka ya sauya kayan jikin shi kuma ya kwanta Ayman kam kasa hak'uri yayi da abinda raihana ta fad'a mishi har saida ya sake kiran malam bayan ya tabbatar zuwa lokacin ya koma gida, sake tambayar shi yayi, sai dai a wannan karon malam yana komawa yaji labarin a gurin mahaifin raihana yana neman shi za'a mayar wa su Imran kayan auren su daga bakin iya shima yaji wannan sak'on, saboda an k'ara samun matsala shi ma imrana yace ya fasa aurenta. Ai bai jira ya gama jiba ya katse wayar cikin matuk'ar farin ciki ya daka tsalle tare da kaiwa iska naushi, ashe dai da rabon raihana zata zama tashi mallakin shi. Bai yi wata wata ba ya nufi d'akin auntie don ya fad'a mata abinda ya jima a cikin zuciyar shi. Yau ko sallama sai bayan ya shiga parlon nata yayi, tana aikin had'a ordabur da zasuyi dinner dashi a daren ranar, futar mama haleema kenan shi kuma yana shigowa. Tunda ta d'aga ido ta kalleshi sau d'aya taga tsantsar farin ciki da annurin da yake kan fuskar shi tasan wani abu mai dad'i ne ya same shi. K'asan k'afarta ya zauna cikin happy ya bud'e baki zaiyi magana khaleefa ya shigo, sai ya fasa fad'ar abinda yayi niyyah har sai d'an uwan shi ya zauna ya fad'a don shima ya taya shi murna, duk da yana jin tsoro da fad'uwar gaba, wanda ya ta'allak'a su da tsoron yadda y'an gidan su raihana zasu d'auki abun,, Shima a kusa da Ayman ya tankwashe k'afar shi, ya kalle shi suka had'a ido, take duk suka sakarma juna murmushi. Auntie kallon khaleefa tayi shima, duk da yanayin fuskarshi bai sauya ba amma dukkan alamu sun nuna akwai magana a bakin shi shima, sai ta ajiye trayn hannunta gefe tace, "yau dai da alamu yarana suna tafe da wani labari me dad'i da suke son sanar dani?". Murmushi Ayman yayi kanshi a k'asa, shi kuma khaleefa shafo sumar kanshi yayi yace, "eh Auntie nazo miki da maganar yarinyar nan sai dai a k'urarren lokaci, Soo nake a nema mun aurenta nan da gobe sai a d'aura auren nan da kwanaki biyar masu zuwa". Daga Auntie har Ayman basu san lokacin da suka kalle shiba, "wannan wace irin magana ce haka khaleefa? Aure ai ba'a tab'a yin shi haka da gaggawa, dole ana buk'atar a gabatar da wasu shirye shirye kafun aiwatar da neman auren har aje ga d'aurin auren". Shikam sake cewa yayi, "kada wannan ya dame ki auntie, basai kin wahalar da kanki akan komai ba, akwai y'an kud'ad'e na da nake zaton sun Isa ayi duk abinda ake buk'ata na tsare tsaren biki insha Allah, saboda aikin da mukayi na shekara d'aya cikin biyu na course d'in da mukayi duk biyan mu akayi, kuma kud'in suna nan a account d'ina ban tab'a amfani da ko 1 naira ba, Ni dai burina d'aya ki amince da abinda nazo dashi yanzu...... please auntie". Gaba d'aya khaleefa ya gama kullewa auntie da Ayman kai sai suka tsaya suna kallon shi kurum suna jujjuya zancen shi da mamaki, Ayman ne ganin bil hak'k'i da gaske abinda yake nufi kenan yace, "Toh wai a ina ma ka had'u da ita, sannan wacece ita wannan yarinya.....?". Khaleefa Saida yayi d'an jimm kafun can ya nisa yace, "sunanta raihana salees Abdallah, gidan su yana nan kusa da gidan iya ba tazara sosai.......". Ai bai kai k'arshe ba Ayman daya shiga wani mugun tashin hankali ya mik'e tsaye babu shiri Yana kallon shi had'e da nuna shi da yatsa, cikin rawar baki da d'aga murya yake fad'in, "bazai yiwu ba,,,,, raihana ba zata tab'a auren kaba,,,,, saboda ita d'in ba matar ka baceee,,,, ya Isa haka..... Wasan ya Isa haka don Allah,,,,, har abada raihana ba zata tab'a auren wani namiji ba saboda ni ne nan...........". _Nikam 🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️ d'ora hannu nayi aka Ina kallon su har bansan lokacin da Alk'alamina ya fad'i k'asa ba_ _Da wannan nake sanar daku cewa zanje hutun sati d'aya insha Allah zaku ci gaba da jina next week Friday in na dawo,,,,, ku huta lafiya✍️_ _comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty two3️⃣2️⃣ Ganin duk sun zuba mishi ido kallo yana Shirin komawa kanshi sai ya soma ambaton sunan Allah a cikin ranshi ya koma ya zauna a inda ya tashi ya dafa kafad'ar khaleefa, "don Allah khaleefa kada ka saka kanka a matsala.... Raihana fa duk mun shaida bikinta saura kwanaki k'alilan da Imran taya yanzu kuma zakace kai zaka aureta?". Khaleefa kallon shi kawai yake yana tunanin abinda ya d'aga mishi hankali daga maganar zai auri raihana lokaci d'aya har ya birkice mishi haka, "Ayman akwai wani abu ne?". Ayman daya rasa abinda zaice ma sai kawai yayi shiru yana kallon shi da tarin zarge zarge a cikin ranshi, yayinda zuciyarshi take tsananta bugu, khaleefa ya lalata mishi duk wani burget d'inshi! Ya gama jefa shi cikin garari, yana ganin raihana kamar itace hasken da zata yaye mishi duhun daya cika zuciyarshi,,, sai gashi khaleefa ya mishi shigar sauri ya kawo maganar wa auntie..... Sai kawai ya tallabe hannun shi a k'afar shi da gwiwar hannun shi, ya zabga uban tagumi yana ambaton sunayen Allah a cikin zuciyar shi don ya kawo mishi d'auki da sassauci da gaggawa. Auntie kanta zuba musu ido tayi tana musu kallon tuhuma, barin ma khaleefa, ko a wasa, ko a mafarki bata tab'a zaton zai zo mata da irin wannan maganar ba, a yau da Ayman ne yayi mata wannan maganar ba zatayi mamaki ba, don tasan dole biri zaiyi kama da mutum, shak'uwar dake tsakanin su a kowanne lokaci zata iya rikid'ewa ta dawo soyayyah mai tsanani, musamman a lokaci irin wannan. Khaleefa koda ya d'aga ido ya kalleta yaga ta rik'e hab'a tana kallon shi marairaice mata yayi, "please Auntie yarinyar kirki ce kada kice baki amince ba.....". Sai ta dogare hannunta a k'asa tana ci gaba da kallon shi tace, "Ni kuwa zan fad'a maka haka,,,, yarinyar daka tafi kusan shekara goma ka barmu tare da ita,,, kaga kuwa sai dai ma ni na baka labarinta,, yanzu kaje kawai zamuyi magana da malam zuwa safiya zan neme ka". A hankali ya tashi yayi musu sallama ya futa, amma fa zuciyarshi sai kai komo take akan yadda Ayman ya d'auki maganar,,,, har yanzu ya kasa fahimtar abinda yasa yanayin Ayman d'in sauyawa lokaci d'aya daga cewa zai auri raihana, koda yake bari su gama tattaunawa da Auntie dole a yau sai yayi mishi bayanin komai. Auntie Kam ko bayan futar khaleefa saukowa k'asa tayi ta zauna kusa da Ayman ta dafa kafad'ar shi tace, "Ayman akwai wani abu da yake faruwa ba dai dai ba? Shin meye ma'anar khaleefa ta auren raihana.... Don ni na tabbata ba soyayyah suke ba.... Yaushe ma ya santa tukun mutumin da kullum yana nad'e a cikin gida.....". Ajiyar zuciya me k'arfi ya sauke a b'oye, ya sake daidaita kanshi da nutsuwarshi ya k'ak'alo murmushi mai kama da kuka yace, "toh ni kaina Auntie ban sani ba,,, amma tunda kika ji shida kanshi har yace zai aureta, to Ina ganin yana sonta ne, don in baya sonta bazai tab'a cewa zai aure taba, haka nasan khaleefa....". Nazarin kalaman shi tayi sosai kafun ta sake jefa mishi wata tambayar, "Toh kai dama ba sonta kake ba tuntuni....?". Baisan lokacin da idon shi ya tara ruwan hawaye ba, amma dai ya daure da kyar ya had'iye su tare da wani abu mai d'aci daya tsaya mishi a mak'oshi. "mutumcine kawai da gaisuwar mutumci amma ba wani abu mai kama da soyayyah a tsakanin mu,,,,". Ganin zata k'ara mishi wata tambayar sai ya mik'e tsaye,,,, "Auntie ya kamata naje na kwanta dare ya fara yi....". Itama mik'ewa tsayen tayi tace, "bamu gama magana da kai ba Ayman... So nake nasan dalilin da yasa da khaleefa yayi magana da farko ka so ka k'alubalance shi.... Idan baka sonta me yasa yanayin ka zai sauya farat d'aya? Sannan me yasa khaleefa zaice ze aureta??". Wata irin jarumta yasa a wannan karon ya juyo yana fuskantar ta, "har abada.... Babu wani abu mai kama da wanda kike zato tsakanina da yayana, saboda khaleefa a shirye yake daya sadaukar mun da duk wani abu dana nuna Ina Soo a rayuwa... Nima kuma haka, dukkan mu muna da kyakkyawar alak'a da kusanci da juna.... Sannan ni ban tab'a son raihanatu ba.... Da Ina sonta da ban amince da soyayyar Nur da aurenta baaaa... Sannan abinda kika gani a tare dani ba komai bane illa tsorooo!! Tsoron yadda iyayen raihana zasu karb'i maganar khaleefa..... Shin ko zasu iya bada auren y'ar su ga wanda bashi da asali me kyau, ake zaton ma shefe ne???" Sai yayi shiru har na wasu dak'ik'u kafun ya sake cewa,,,, "Auntie idan har k'awar ki aminiyar ki da kuka d'auki shekaru tare, tafi kowa sanin ki ciki da bai, lokacin muna yara har muna zaton ku y'an uwane zata hana d'anki auren y'arta,,,,, taya kike tunanin wani can a gefe zai baki.....". Jikinta a matuk'ar sanyaye ta samu gefen gurin ta zauna had'e da zabga uban tagumi,,,, duk yadda take b'oyewa Ayman wannan rashin fahimtar da suka samu da sameera saida yaji??? Toh taya kenan?? Lallai ta yarda baki shege nee... Shiyasa bata tab'a aminta da wani kunne yaji sirrinta ba don baki bazai iya hak'uri ba saiya fad'a..... Ayman kam bai sake ce da ita komai ba ya fuce daga d'akin da mugun sauri don ya isa ga bedroom d'inshi koya samu damar yin kukan shi yadda ranshi yake so.... Ita kanta auntien kuka take irin wanda takan jima batayi shiba,,,,, maganar Suraj gaskiya ne,,,, tabbas ya fad'i gaskiya da yace babu yadda zata rayu koda bata tare dashi ta iya mantawa dashi, ya riga ya gama yi mata tabo da illar da ko bata koma gare shi da yaran shiba ba zata iya rayuwa cikin sa'ida da salama ba. Sai ta sake fashewa da wani kukan kamar k'aramar yarinya,,,, Saida tayi me isarta sannan ta d'auki wayarta ta kira no malam. Bayan ya d'aga sun gaisa take sanar dashi abinda ake ciki maganar da khaleefa yazo mata dashi, shi kanshi malam abun ya d'aure mishi kai, a tunanin shi Ayman ne zaice Yana sonta har ma ya aureta,,,, sai gashi khaleefa.... Ganin magana ba zata yiwu a daren ba sai yace ta bari da safe zai zo gidan. ★★★★ Ko bayan sunyi sallama shirin kwanciya bacci tayi, ta tofe duk kusurwowin d'akin da addu'a sannan ta kwanta. Ayman kuwa da khaleefa ya fara cin karo a parlour, ya d'auke kanshi zai huce khaleefa ya rik'e gefen rigar shi ta baya, sai ya tsaya ba tare daya juyo ba yace, "bacci nake ji ka rabu dani na tafi khaleefa...". Tattaki yayi zuwa gaban shi ya tsaya ya kalleshi da kyau yace, "babu baccin da kakeji kada ma ka fara yimun k'arya.... Abu d'aya kawai zan tambayeka...". Sai baice komai ba ya tsaya yana sauraron shi. Khaleefa yace, "shin kasan wannan yarinyar da nace zan aura ne dama??... Koda yake dole ma zaka santa. Amma meye dalilin da yasa ka fara maganar da kayi da farko? Ayman kada ka b'oye mun komai....". Da ido kawai Ayman ya dinga kallon shi har saida yaji kallon ya isa yace, "why are u staring at me just like dat". Sai ya samu gefen table ya zauna ya had'a kai da gwiwa. Shima khaleefa zama yayi kusa dashi ya dogare hannunshi duka biyu. "Ka daina tunani ko kokwanto akan maganata khaleefa,,,, Ni damuwata bata da alak'a da auren ka sai tsoron kada kaima irin abinda ya faru dani akan Nur ya same ka..... Shin ko kasan auntie da Mamie yanzu haka basa tare?". Duk da abun yaba khaleefa mamaki amma bai nuna ba ko a fuskarshi yace, "hakane! Nasan dole watarana zasu rabu,,, saboda mutane ba mahaukata bane... Shin Kai bakaji a jikin ka akwai wani abu dangane damu na rashin gaskiya ba ko k'ank'ani??? Ayman bance auntie batayi k'ok'ari ko wahala damu ba, sannan bamu nemi komai mun rasa ba a rayuwar mu, amma ita kad'ai ba zata wadatar wajen zaman mu cikakkun mutane ba har sai da taimakon uba ko dangin shi.... Sannan maganar raihanatu ina ji a jikina ba zasu hana ni aurenta ba.... saboda dalilai da yawa masu alak'a da wani sirri nasu daban..... Da wannan nake baka shawarar ka ajiye komai a gefe, insha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe...". Khaleefa yana gama yin maganar shi ya mik'e tsam ya barshi a gurin ya shige d'akin shi. Shima Ayman k'afafun shi yaja ya tafi nashi d'akin ya kwanta, sai a lokacin ya samu damar futar da hawayen daya cika idanun shi fal! A wannan dare Ayman yayi kuka yayi kuka har ya godewa Allah, daga k'arshe da bacci ya gagara sai ya k'arasa daren da tasbihi da tahmidi. ******Raihanatu kuwa ko da ummie ta cire yatsunta a fuskarta dafe kuncin tayi tare da duk'ar da kanta k'asa. "Fad'a mun daga gidan ubanwa kike cikin daren nan?". Kasa cewa komai tayi sai idanunta da suka tara ruwan hawaye. "ba zaki fad'a mun ba raihana?" Ummie ta sake tambaya cikin d'aga murya yanzu. Sai a lokacin Abba ya k'araso kusa ya taka mata burki ta hanyar d'aga mata hannu, "kinga don Allah ki bita a hankali kada ki sauke mata fushin da ba ita ta sabbaba miki shi ba a kanta". Sai ya k'ara fuskantar raihana da kulawa yace, "Ina kika tafi duk tsawon wannan lokacin raihana.... Kinsan kuwa yadda kika so ki d'aga mana hankali?". Raihana data fara kuka cikin muryar kukan tace, "kayi hak'uri Abba ban futa da niyyar zama ba,, mota ce ta buge mun k'afa saida muka je asibiti sannan". Sai a lokacin hankalin su ya kai kan k'afarta da take nad'e da bandage. Ummie shigewarta tayi ciki sai Abba ne yace, "ayyah ta yaya?" Ganin ta kasa ce mishi komai sai kuka, sai yace "Shiga ciki ki daina tsayuwa a nan kinji....". A hankali ta ci gaba da tafiya har ta isa k'ofar parlon su ta shige, bata tsaya anan parlon ba duk da yadda su jidderh suka damu da ganinta cikin wani yanayi har suna yi mata sannu. *****A daren ranar mahaifin raihana yana zaune saboda sab'anin da suka samu da ummie d'azu da yamma, wayar shi dake daura da ita tayi ringing, batayi k'asa a gwiwa ba wajen mik'a mishi wayar har yanzu fuskarta a d'aure. Ganin wanda yake kira a wannan dare saida gaban Abba ya fad'i, a fili ya furta "hasbunallahu wani'imal wakeel". Addu'ar data janyo hankalin ummie kanshi tana kallon shi, a handsfree ya saka wayar don suji komai shida ita, bayan sun gaisa da alhaji abubukar cikin girmamawa kamar koda yaushe, shiru duk sukayi, shi Abba yana jiran yaji da wadda alhaji abubukar d'in yazo, shi kuma alhaji abubukar yana jin nauyi da girman abinda zai fad'a har cikin zuciyarshi, baisan meya samu Imran d'in ba, baisan dalilin daya sa yazo mishi afuja'atan a yammacin ranar da magiya gami da rok'on ya gaggauta soke maganar auren su shida raihana ba tunda sauran lokaci basai anzo gab da biki ba. Kakkarfar ajiyar zuciya ya sauke kafun ya fara magana da dukkan nutsuwar shi, "bansan me zance muku da zan iya wanke kaina har ku fahimce ni cikin sauk'i ba alhaji,,,,, saboda yaron nan......." Nan ya labarta mishi duk yadda sukayi da Imran a yammacin ranar. Shiru Abba ya sake yi kafun yace, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ummie da take gefe ta furta k'asa k'asa sai kuma hawaye ya soma bin kuncinta a nutse yana gangarowa k'asa. Abinda bata tab'a yiba duk tsawon lokacin da aka d'auka ana saka da fasa auren raihanar. Dama tunda taji wayar cikin daren nan tasan akwai matsala. "Kada wannan ya dame ka,,,, bashi ya ganta yace yana sonta har suka daidaita kansu? Kuma yanzu yace ya faasa? Toh duk kai meye naka a ciki yallabai..... Don Allah kada ma wannan ya dame ka,,, haba ai mun zama d'aya babu wani banbanci,,, Allah yasa hakan shi yafi alkhairy". Duk yadda yaso nuna b'acin ranshi akan abun Abba ya hana shi koda furta mummunar kalma akan abun har Allah yasa suka gama maganar su sukayi sallama, duk da lefe kad'ai suka buk'ata Amma Abba yace sam dole a had'a musu har kud'in auren su a tattara a mayar musu duka. Cikin k'arfin hali da dauriya ya tashi ya tafi gidan malam. Bayan yasa an mishi sallama da malam ya futo, kwashe duk yadda sukayi da alhaji abubukar yayi ya fad'awa malam d'in, shi kanshi malam ya jinina girman al'amarin a ranshi da zuciyarshi, sosai tausayin yarinyar ya kama shi, gata dai k'aramar yarinya amma tana fuskantar k'addara me girma. Malam ya jajanta mishi kwarai a k'arshe ya bashi shawarar a rufe maganar ga kowa kada a fad'a, sannan kamar yadda yayi niyyah kada ya fasa mayar musu da komai nasu har dukiyar auren su. Ba musu Abba yayi na'am da shawarar malam, don shi kanshi baya buk'atar kwayayato da yamad'id'in mutanen gari a kanshi dama iyalan shi gaba d'aya. A wannan dare ne kuma auntie tayi waya da malam bayan tafiyar Abban raihanah. _ci gaba_ Washe gari kamar yadda malam ya fad'a sassafe ya zo gidan, a parlon k'asa ya zauna suna magana da auntie, bayan ta gama warware mishi yadda sukayi da khaleefa dallah dallah, shiru yayi yana jinjina abun kafun can ya nisa yace, "tabbas an fasa auren yarinyar nan da wannan yaro d'an gidan alhaji abubukar tun a daren jiya mukayi magana dashi mahaifinta, yanzu anjima kad'an zasu zo su karb'i dukiyar auren su da kayan lefe". Shiru auntie tayi kafun zuwa can tace, "kwana nawa ya rage bikin". Malam yace har yau kwana hud'u kenan cif". Sake yin shiru tayi kafun ta sake cewa, "kana ganin zasu ba da auren y'ar su ga khaleefa? Khaleefan da bashi da wani cikakken asali uwarshi tazo da cikin shi gari har gobe ba wanda zaice ga uban shi....". Malam baisan lokacin daya d'ago ya kalleta ba jin irin furucinta. Ga mamakin sa hawaye ya gani bisa kyakkyawar fuskarta had'e da wani rauni daya mamaye ta lokaci guda. "Da bakin ki yau kike aibata y'ay'an ki irin yadda sauran mutanen gari kan aibatasu surayyah". Da gefen hannunta ta share hawayen fuskarta tace, "toh ai gaskiyane malam, akace ranar wanka ba'a b'oyon cibi,,, sai dai duk wuya duk rintsi nayi alk'awarin khaleefa ba zasu tab'a jin komai daya faru tsakanina da Suraj shekaru talatin har da d'oriya daga bakina ba". Sai taja gwauron numfashi, "bansan dalilin khaleefa na auren wannan yarinyar ba, bayan na tabbata baici ace sun fad'a soyayyar juna a d'an tak'aitaccen lokacin had'uwar suba,,,, kai ko da ace daga dawowar shine ma, bare jiya jiya.... toh amma duk da haka ba zamuyi k'asa a gwiwa wajen nema mishi aurenta ba...Ni da kaina zanje na warware musu zare da abawa,, idan har sun amince dashi a haka sai ayi maganar aure....". Sai ta mik'e tsaye tana girgiza kai kafun taci gaba da fad'in, "Amma fa nayi alk'awari malam,,, indai khaleefa da wata manufa zai auri yarinyar nan... Saina shayar dashi ruwan mamakin da bai tab'a zato ba, sai ya raina kanshi a hannun raihana sannan auren su mutu ka raba". Tana gama maganar ta ta haura stairs a gurguje. Ko data sauko cikin shiri take nad'e da lafaya da jaka had'e da mukullin motarta. "Muje malam ai yanzu baiyi sassafe ba ko?". Malam yace,,, "eh amma me kike shirin aikatawa haka". Sai datayi murmushin gefen baki sannan ta bashi amsa da, "abinda babu wata suruka ta hausa data tab'a aikatawa". Daga nan malam bai sake cewa komai ba yabi bayanta suka futa. *****A dai dai k'ofar gidan su raihana tayi parking, ta futo ita da malam suka tsaya suna nazarin abinda ya kamata suyi a lokacin, shin zasu shiga babu iso ne ko kuma zasu fara neman yaro ya musu sallama da me gidan? Ganin zata k'ara b'atawa kanta lokaci sai kawai tace da malam tana zuwa. Ta cusa kanta cikin gidan bakinta d'auke da sallama. A lokacin su hibba ne kawai suke budurin su a cikin gidan. Daga ummie har raihana ba'a samu wanda ya iya futowa don gabatar da ayyukan gidan kamar kullum ba, ba wai don basu tashi daga bacci ba, a'a sai don dukan da maganar jiya tayi musu, musamman ma ummie,,, data kwana da wannan tashin hankali a ranta, har tsoro take gari ya waye su Abba abubakar su mayar da kayan auren nan matar shi ta samu abun yad'awa cikin dangin salees,,, barin ma Inna taji labari ta kwaso jiki ta taho da tulin tijararta gidan. Ita kuwa raihana da tunanin wannan bahagon al'amari daya tinkarota ta kwana,,,, ta auna ta duba ta birkita amma har yanzu bata ga aibun abinda take shirin aikatawa ba, duk ta inda ta b'ulla sai taga auren khaleefa shine babbar maslaharta, koba komai zasu samu nutsuwar ruhi ita da mahaifiyar ta,,, ta d'ora da karatunta kamar yadda take mafarki a shekarun baya kafun ta fahimci tarin k'alubalen daya ke tattare da rayuwarta gaba d'aya. Da wannan tulin tunani da kuma k'afarta data kwana tana zugi ta kwana, ko da asuba da kyar ta iya mik'ewa ta d'aura alwala ko daba sallah zatayi ba,,,, ta koma ta sake kwanciya. Al'ameen ne ya d'an fi hankali duk cikin su muhibba, don haka shiya yiwa auntie iso har cikin parlon ummie da yake tashin k'amshin room freshener kamar ba safiya ba. Ko data zauna idonta akan k'aton hoton raihanan ya fad'a, ta k'urawa hoton ido tana kallon yarinyar duk da ba wai yaune karon farko data fara ganinta ba. "Tace tana zuwa" shine abinda ya shiga kunnenta, kuma ya sabbaba dawowar ta daga d'an k'aramin tunanin data fara tafiya.... Da sakakkiyar fuska ta shafa kan jidderh data kawo mata wannan sak'o tare dashi mata albarka. Mintuna k'alilan da zamanta a parlon ummie ta futo cikin dogon hijab,, ba k'aramin mamakin ganin auntien tayi da wannan uban safiya ba. Haka dai ta saki fuskarta sosai ta k'arasa har kujerar dake kusa da tata ta zauna. Suka fara gaisawa. Bayan duk sun gama jin lafiyar juna, auntie ta fara gabatar mata da abinda ya kawota,,, "Da farko dai nasan zakiyi mamakin ganina a gidan ki da wannan safiyar ko,,, to sai dai ba abun mamaki bane in kika ji abinda nazo dashi, amma kafun nan tare da malam muke, sannan in ba damuwa ko zan iya ganin mahaifin raihana da ita kanta raihanar?". Tunda auntie ta fara magana ummie ke kallonta tana nazarinta sosai har takai Aya. Ajiyar zuciya ta sauƙe a boye kafun ta mik'e tace, "Babu damuwa bari nayi mishi magana, ita kuma tana ciki ko bacci take ma...." Saita kwalawa al'ameen kira, yazo da sauri tace ya kira mata raihana a d'aki. Yaron ya tafi da gudu don isar da sak'on da aka bashi,, ita Kuma ta futa don tayi magana da salees. Shima ya tashi already yana zaune gefen gadon shi yau ko sukunin lazumi bai samu ba sai tunani daya cika kwanyarshi fal. Ko da ummie tayi sallama bai iya motsa bakin shiba sai a zuci ya amsa. Daga jikin k'ofar ta sanar dashi akwai bak'uwa da take son ganin shi a parlour. Kusan tare suka futo shida ita har inda aka ajiye surayyah,,, kamar had'in baki itama raihana a dai dai lokacin ta futo sanye da dogon hijab har k'asa tana d'ingisa k'afarta. Daga jikin k'ofa ta tsugunna ta gaishe da auntien, ta amsa tana k'ara yabawa nutsuwa da kamalar yarinyar. ****Saida ta gaisa da mahaifin raihana sannan ta fad'a mishi malam yana waje tare suke. Sai ya tashi da hanzari ya futa zuwa wajen su kuma ya barsu nan zaune cirko cirko da fad'uwar gaba da take had'e da tunanin abinda ya kawota a wannan safiyar. Ko da Abba ya tarar da malam a waje, har k'asa ya durk'usa suka gaisa saboda matsayin uba daya ke ba malam d'in. Da kanshi yayi mishi jagora har cikin parlon inda duk suke, saboda a gurin su malam ya huce matsayin bak'o da zai tsayar a k'ofar gida. *****Bayan sun tattaru a guri d'aya cikin nutsuwa da tausasan lafuzza surayyah ta fara koro bayaninta kamar haka........ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo dai dai da zama, Maryam sulaiman (maman almustapha), tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, gwanancewa da iyawa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka👉🏻 08028175615* _Comment anda share_. 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty three3️⃣3️⃣ "Kamar yadda kuka sanni, surayyah Adam nake, tsintacciyar y'a ga iya da malam, saboda a zahirin gaskiya bamu had'a komai dasu ba....." Cikin rashin fahimtar abinda take son aiwatarwa malam ya kalleta, sai ta gyad'a mishi kai, "kamar yadda na fad'a maka malam ranar wanka ba'a boyon cibi". Sai ta maida hankalinta gasu ummie da Abba taci gaba da fad'in, "duk da kasancewata ba cikakkiyar bahaushiya ba, amma na rayu cikin k'asar hausa tare da hausawa babu wani banbanci tsakanina dasu ni a gurina..... Ba zan kira kaina da mara cikakken asali ko tushe ba, saboda na futo ta tsatso mai kyau, da asalin gata da tarbiyyah, sai dai wani abu mai girma da k'arfi ya futo dani daga rufaffen muhallin da nake rayuwa cikin tsaro da mutumcin da a duniya ba wanda ya Isa ya Samar dashi sai iyaye ko wakilan su na kwarae, k'addara ta raba ni da d'an uwana da bani da kowa sai shi a duniya, wato sauban,,, k'addarar kuma bata komai bace face ta haihuwar y'an biyuna khaleefa da Ayman, tabbas wad'annan yaran a yanzu su kad'ai suka rage mun kuma sune rayuwata, zan iya sadaukar da komai dana mallaka a duniya indai zasu tsira....suyi rayuwa cikin aminci da mutumci". Ajiyar zuciya mai tsayi ta sauke kafun taci gaba da bayaninta, "duka Ina baku wannan labarin ne ba don komai ba, sai don neman auren y'ar ku da d'ana khaleefa yake son malam ya shige gaba yayi mishi,,,,, amma fa idan har kunji zuciyarku ta nutsu daku bashi auren a yadda yake,,,, ba dangin uban shi, bare uban daya jima da mutuwa a idon shi,,,, nayi alk'awarin indai sai dangin Suraj sun saka hannu a rayuwar yarana zasu zama wani abu,,,, toh wallahi gwara mu dawwama nida su baci gaba a yadda muke, koda ace hakan zai zama silar mutuwa ta kuwa......" Yadda takai k'arshen maganar da wani irin fushi mai futa daga can k'asar muryarta kad'ai ya bayyana tsantsar b'acin ran da take ciki, sai babu wanda yace mata komai, amma zuciyar ummie fal tausayinta, a zuciyarta har tana tunanin irin girman laifin da wad'annan mutanen sukayi mata da take irin wannan ik'irarin. Tana cikin tunanin taji taci gaba da magana, sai ta sake bata hankalinta kacokan. "Idan har kun amince muna son a d'ora daga inda aka tsaya a maganarta da Imrana, wato bi ma'ana nan da kwanaki biyar a d'aura auren da khaleefa instead of Imran daya janye". Daga ummie har Abba shiru sukayi bayan gama sauraron ta, hatta raihana da take gefe saida taji kanta gingirin, duk da dama tasan da maganar tunda sun shirya hakan da khaleefa already. Malam dama tuni ta kashe mishi baki ya zuba mata ido yaga yadda zata kaya da mutanen nan bayan gama fallashe musu duk wani b'oyayyen sirrinta, da suke jin wai a gari. Abba ne ya kalli raihana da kanta yake a k'asa ya kira sunanta da nutsuwa, "raihana". Bata iya amsawa ba saboda bakinta daya mata nauyi sai d'ago kai da tayi ta kalle shi. "Shin kin amince da auren khaleefa kamar yadda mahaifiyar shi ta buk'aci a bata?". Sake mayar da kanta k'asa tayi hawaye na biyo kuncinta marassa tushe bare cikakken makama. Ganin haka sai surayyah ta mik'e ta koma kusa da ita ta d'ago kanta, da kyar ta iya kallon auntien kafun ta kawar da kanta gefe da sauri, "kada kiji komai raihanatu ni d'innan matsayin uwa nake a gurin ki koba maganar aure, Ina fatan kunyi magana da khaleefa kafun zuwana....?". Gyad'a mata kai tayi alamar eh. Ummie ta bita da kallon mamaki, auntie ce ta sake cewa, "Shin khaleefa tursasa miki yayi ki aure shi dole?". Girgiza mata kai tayi,,,, "toh me yasa kike kuka ko baki amince da auren shiba? In bakya so kada ki b'oye mun komai ki fad'a mun don bazan yi miki dole ba, Cox bani zan zauna miki dashi zaman aure ba". Shiru ta sake yi kanta a k'asa, auntie ta sake cewa, "iyayenki suna son suji amincewar ki daga bakin ki". Sai a lokacin ta d'ago ta saci kallon ummienta don ganin reaction d'in kan fuskarta, kadaran kadahan yanayinta,,,, sai ta maida kanta k'asa idonta yana tara ruwan hawaye, so take ta fahimci yadda ummienta ta karb'i zancen, idan har taga amincewar ta da maganar saita yarda da auren, idan Kuma har batayi na'am ba toh shikenan sai tace Allah ya had'a kowa da rabon shi. Ganin bata da niyyar cewa wani abu sai abbanta yace, "Wai ba tambayarki muke ba raihanatu?". Auntie tana murmushi tace, "ayyah ka bita a hankali tana shawara da kanta a zuciyarta ne". Ummie data gama nazarinta tsaf sai a lokacin tayi magana, "wannan shirun nata fa yana nuna amincewar tane a fili ba sai ta furta ba". Shi kanshi malam murmushi yayi don ya lura da haka, sai yace, "tabbas! Raihana kuwa akwai kunya". Cikin jin dad'i auntie ta kamo hannunta tace, "na fad'a miki kada kiji kunya ta, ki d'auke ni kamar ummienki don kema y'ata ce kamar su Ayman". Wannan karon da gefen hijab d'inta ta rufe fuskarta tana k'ok'arin tsaida hawayenta, ambaton Ayman yasa taji wani iri a zuciyarta harda fad'uwar gaba. Abba ne yace, "Toh Masha Allah raihana shiga ciki zamu k'arasa magana". Ta mik'e tsam ta shige d'akinta da sauri. Auntie ta bita da kallo cike da so har ta shige, Allah yasan tun da jimawa take son yarinyar nan, shiyasa ko lokacin da take tare da Ayman bata tab'a jin haushin alak'ar suba, hasalima ta fahimci kamar akwai wani abu tsakanin su ita da Ayman a lokacin. Kuma tasha tambayar shi a farko farko sai yace shi babu wata alak'a a tsakanin su, hakan yasa ta watsar da zancen itama, saboda a lokacin y'ay'an sameera take son had'a zumunci dasu, tana ganin kamar sunfi kowanne yaran wannan zamanin tarbiyyah da hankali, baya ga haka ma tana ganin uwarsu cikakkiyar masoyiyar ta da zatafi kowa fahimtar ta in aka d'auke su malam,,,, ashe su abun a gurin su Sam ba haka bane. Sai ta sauke b'oyayyen ajiyar zuciya. Abba kuma yayi gyaran murya don karkato da tunaninta ya dawo dai dai kafun ya fara magana da fad'in, "duk naji bayanan ki doctor surayyah, sai dai ni banga wani abun aibu a cikin maganarki ba gaba d'aya, ko suna da cikakken asali ko basu dashi ni abu d'aya zan duba, nagartarku keda su malam da kuma tarbiyyar yaran da nagartarsu su kansu ma, duk da bansan shi wanda za'a nemawa auren raihana a cikin su ba, amma nasan duk d'an da ya taso k'ark'ashin kulawarku keda su malam bazai tab'a kasancewa fitinanne ba, kuma naga zahirin hakan a gurin Ayman, saboda tsawon shekaru tsakanin shi da kowa a anguwar nan gaisuwar mutumcine, da wannan yak'inin na baku amanar auren y'ata raihana, da kyakkyawan zaton cewa zaku kula da ita cikin aminci,,,,". Ko daya dire aya malam ne ya karb'i zancen inda yake cewa, "hak'ik'a naji dad'in wannan maganar da kayi Abubakar matuk'a, wannan abun da kukayi ya tabbatar mana da ku d'in mutane ne na gari da suke kallon kowanne yaro d'aya da nasu yaran ba wani banbanci,,,, sai dai wani hanzari ba gudu ba, da kud'in auren da sadakin da lefe zamu kawo su duka ranar juma'ar da za'a d'aura aure, sannan abu na gaba shin ka tab'a yin tunani akan fashe fashen auren yarinyar nan kusan karo shida ko biyar da akeyi?" Girgiza kai Abba yayi yace, "ko da wasa ban tab'a kawo tunanin komai a raina ba, kawai abu d'aya na sani komai na Allah ne". Jinjina kai malam yayi yace, "wannan haka yake, shiyasa a wannan karon nake son kayi hak'uri kada ka fad'awa kowa abinda yake faruwa, kamar yadda aka raba invitation card da sunan Imran a bar mutane a hakan in sunzo wajen d'aurin auren saga sauyin da aka samu,,,, kuma har d'an uwanka Abubakar ina so kada ka sanar mishi zancen fasa auren a wannan karon, Ni nan zan nemo shaidu su kasance a tsakiya a lokacin da zamu mayarwa alhaji abubukar kayan auren su,,,, Ina fatan babu illa a cikin shawarata". Shiru yayi yana d'an tak'aitaccen nazari, sam baiga fa'idar b'oyewa d'an uwan nashi ba, amma tunda har malam d'in ya bashi shawara ba zai k'i biba tunda baisan abinda ya hango ba. Da haka ya amince da shawarar mallam. Suka rabu girma girma cikin mutumci, Abba ya raka su har k'ofar gida. Ko da suka tafi ummie zama tayi tare da zabga uban tagumi tana tunanin rayuwar d'iyar tata, raihana tana ganin k'addara kala kala a rayuwa masu kyau da akasin haka, toh ita dai tana fatan alkhairin Allah ya kasance tare da wannan auren nasu da har yanzu bata daina mishi kallon hargitsatstse ba, tana y'an tunane tunanenta Abba ya shigo d'akin, kusa da ita ya zauna yace, "kina tunanin inda rayuwar raihana zata fad'a ko?". Girgiza mishi kai tayi, sai yaci gaba da maganar shi, "nasan zaki ce nayi hakane saboda na gaji da ita so nake kawai naga na aurar da ita ga koma waye...". Shiru ta mishi yanzun ma, "Abu biyu nake so ki fahimta a tare da kalaman wannan baiwar Allahn, na farko, lallai akwai wani b'oyeyyen al'amari da yake bibiye da ita da bata son kowa ya sani, kai tsaye bazan kira yaranta da shegu ba, saboda ni a har kullum Ina kyautatawa d'an Adam zato, sannan ko a gabana tayi cikin shege ta haife yaranta, ni bazan fasa wanke y'ata na basu aurenta ba muddin suna da nagartar da za'a iya basu auren, balle ma surayyah ba tayi kama da marassa kintsi da nutsuwar da za'a ce ta aikata irin wancen al'amari ba,,, da haka nake rok'on ki kan kisa ranki a inuwa, ki sawa zuciyarki salama, insha Allah babu wani abu da zai biyo bayan auren nan sai alkhairy". Ummie gyara zaman ta tayi tare da girgiza kai kafun ta fara cewa, "a wasu lokutan in kayi magana sai naga kamar baka sanni ba salees, shin kana tunanin akwai wani hukunci da zaka yanke akan raihana har naja da kai? Sannan yadda ka kalli surayyah nima haka na kalleta, Cox a iya sanina da surayyah macece mai matuk'ar kirki da take zaune da kowa lafiya da zuciyarta d'aya,,,, haka d'anta dasu malam ma, kaga ko iya wannan mutum ya tsaya akai hujja ce data isa tasa a k'ulla kyakkyawar mu'amula da ita". Murmushi Abba yayi yace, "zancen ki gaskiya ne, bari mu gani yanzu ko shima za'a ce an fasa?". Girgiza kai ummie kawai tayi, tana tuno yadda maganar Imran ta rushe ya zam babu ita cikin d'an k'aramin lokaci har ta khaleefa ta shigo, ko y'an uwanta ta kasa fad'a musu fasa auren daga jiya zuwa yau, gashi sun raba catin biki guri guri,,, Allah yasa ma ita raihana ba mai son bidi'a bace ba abinda ta shirya sai kamu mai had'e da waleema, duk da sunan mother's event,,, angon ne dai yake maganar zaiyi dinner da reception. Saita sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ta mik'e don ganin kwamacalar dasu muhibba sukayi mata a gidan yau. Raihana kuwa kwanciya kawai tayi ta zubawa rufin d'akin ido tana tariyar kalaman auntie na d'azu cikin kunnenta, da gaske dama haka mutanen gari suke cewa su Yaya Ayman basu da uba? Toh ai ita bata tab'a jiba koda wasa, ko da yake suna tare ai ba lallai ayi maganar a gabanta ba, sannan ita da ba shiga wani shirgin mutanen anguwar takeyi sosai ba, taya zata san abinda yake faruwa? Sai ta mik'e zaune sosai tana kallon k'afarta da take nad'e da bandage, sai a lokacin ta tuno ko magungunanta bata sha bama, yamutsa fuskarta tayi kad'an tuno da irin zugi da rad'ad'in da k'afar take a duk lokacin data taka ta a k'asa. ******A gidan iya. Malam da surayyah ne zaune sai iyan a k'asan carpet dake malale tsakiyar parlon, bayan sun gama bawa iya labarin komai daya faru a gidan salees basu b'oye mata ba, ita kanta ta jinjinawa wad'annan bayin Allah da basu kawo zargin komai a ransu ba, lallai ta dad'a yarda mutum baya gane masoyin shi sai abu irin haka ya taso. Sai a lokacin iya take warwarewa surayyah yadda sukayi da sameera kwanaki can farkon samun matsalar su, "sameera fa tazo har gidan nan bayan mun gaisa take fad'a mun tazo ne saboda kun samu wani d'an sab'ani da ita akan auren nuriyyah da Ayman, ta bani labarin duk yadda kukayi sannan ta d'ora da cewa, ita ba wai ta hana Nur auren Ayman bane amma tafi son komai ayi shi da k'a'ida da tsari, aga dangin ubansu Ayman kamar yadda aka ga na nuriyyah, shine kawai sannan a k'arshe tana k'ara baki hak'uri saboda ita har abada ba zata tab'a butulcewa alkhairan kiba, sannan har gobe tana jin nadamar juyawa juna baya da kukayi, tace a fad'a miki kiyi hak'uri ki yafe mata". Ajiyar zuciya surayyah ta sauke kafun can ta nisa tace, "Allah ya yafe mana gaba d'aya". Malam ne yayi gyaran murya ya fara magana da fad'in, "Masha Allah anzo inda nake son bada shawarata nima, saboda lokaci yayi daya kamata ki watsar da komai ki bayyanawa yaran nan abinda kike b'oyewa akansu tsawon shekaru, ya kamata ko basu ga uban suba suga dangin shi don Allah ki taimaki yaranki surayyah, ai ba don kanki zakiyi ba". Tunda aka fara maganar nan surayyah bata ce komai ba kanta a k'asa tana yak'i da hawayenta da suke barazanar bayyana kansu ga su iya don su nuna rauninta, Wanda ita kuma tayi alk'awarin an daina gani a tare da ita tun shekaru ashirin da doriya da suka gabata. Cikin dakiya da kwarin gwiwa tace, "kayi hak'uri malam, ba wai nak'i bin ta taka bane amma Ina son don Allah wannan maganar mu barta zuwa wani lokaci". Gyad'a kai malam yayi yace, "insha Allah an barta kamar yadda kike so". Sun k'ara shirya yadda komai zai gabata kafun tayi musu sallama bayan ta gaisa da harira, don ragowar sun tafi tuni sai ita kad'ai ta rage zata kwana musu biyu, ita d'in ma ance cikin satin zata tafi don komai ya daidaita tsakanin su, tuni sun fahimci gaskiya sunyi nadama ta gaske,,, itama iya ta sauko ta hak'ura tuni. A ranar da yamma malam da mahaifin raihana da wani limamin babban masallacin juma'ah na anguwar suka mayar da kayan lefe da kud'in auren da aka kawo na Imran har gida. Farin ciki a zuciyar hajiya tafeeda bakinta ma ya kasa rufuwa, shi kuwa Imran koda yaji labari a bakin k'annen shi kasa cewa komai yayi, a k'arshe ma ya shige d'akin shi ya rufe kanshi da key gaba d'aya. Ko a jikinta Ita kam har ta gama tsara yadda zata tafi da al'amuranta ma da an kwana biyu, ya gama farfad'owa daga rashin raihanatu ta tursasa shi ya nemi auren shaheeda, don itace dai dai dashi, yarinya mai kyau me aji suruka ta futa kunya, don tayi alk'awarin sai Imran ya riga raihanatu aure yadda zasu fi jin ciwo. *********** Toh cikin satin gidajen biyu shirye shirye suke ba kama hannun yaro a b'oye ba tare da kowa yasan me ake ciki ba. Umma salaha takai labarin fasa auren raihana da Imran tuni gidan su innah, a cewarta su zuba ido zasu gani koba yanzu ba, don haka suma sai suka zuba ido zuwa lokacin da zata fasu kowa yaji, yayinda zeeyada ta d'ora alamar tambaya ga salahar karo na farko cikin maganar rayuwar gidan yayanta salees, sai dai bata furta komai ba kamar yadda take akan katanga tun dacan. Wasa Wasa tun su Inna na saka ran jin labarin fasa biki har ya rage kwana uku d'aurin aure amma ba zance bare dalilin shi, hakan yasa ta kira salees a waya ta tambayeshi ko ya maganar auren raihana gashi duk an rarraba cati, murmushi kawai yayi yana tunanin ko suma sun d'auka ba za'ayi auren ba yanzun ma, sai ya fad'a mata biki yana nan anjima zai kawo musu get pass na hall d'in da mamanta zatayi mother's day da kamu, abun sai ya taru ya d'aurewa innah kai, tana gama waya dashi ta k'ara kiran umma salaha ta fad'a mata ko dai k'arya ne abinda taji saboda ga yadda sukayi da salees a waya yanzu. Umma salaha tace, "ba k'arya bane iya daga dangin mahaifin yaron naji daga bakin uwar d'an ma, wallahi har kayan lefen da aka mayar ma na gani da idona, ta yuwu akwai dai abinda suke b'oyewa, nima sun bani get pass d'in d'azu". Ajiyar zuciya innah ta sauke tace, "toh ta yiwu hakan ne zamu gani ai tunda ba'a tab'a d'aura aure ba miji ba". Kamar yadda salees ya alk'awarta, bayan ya tashi aiki da kanshi ya kawo mata cards masu yawa yace ta rabawa duk wanda taga ya kamata ya halarci taron, ko anan saida ta sake tambayarshi auren dai Yana nan ko? Wannan karon dariya yayi yace, "Wai innah akwai wanda ya baki wani labari daban ne a gefe". Tace, "a'a kawai dai naga yadda abubuwa suke tafiya ne sai anzo kamar za'ayi sai abu ya rushe". Shiru yayi kafun ya sake cewa, "ehh toh muna fatan komai zai tafi dai dai wannan karon insha Allah". Kamar gaske Innah tace, "toh Allah yasa". Kamar yadda Abba yakai musu get pass haka ma ummie ta rabawa y'an gidan su da makusantan ta, ta ajiyewa raihana na tsirarun k'awayenta, duk da ita har yanzu tana kwance tana jinyar k'afarta don ta kanta take sosai, har zazzab'i ya sakar mata,,,, sai ya zamana ita kad'ai take kid'inta sai su khausar da Salma, da suka saki jiki saboda ganin alamun lallai da gaske wannan karon za'ayi auren kenan da alama? Ita dai bata iya basu amsa cikakkiya a duk lokacin da sukayi mata wannan tambayar take fad'awa harkokin gabanta. Ita kamun ma don auntie ta takura ne ta k'awata shi ta d'abbak'a shi, ta kuma mayar dashi compulsory shiyasa ta amince, amma da kamar yadda raihana bata da wani interest akai itama haka. Ana gobe kamu y'an biki suka fara cika gida na nesa dana kusa, Salma dama ta riga kowa zuwa sai neman amarya take lungu da sak'o, kamar kowanne biki yanzun ma babu dangin abbansu ko d'aya da suka zo musu har kawo yanzu. Raihana tana cikin d'aki ta k'ule tana bacci saboda kwanakin gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, komai na gidan ta daina yi sai dai kullum tana kwance, ba laifi yanzu kumburin k'afar tata ya ragu amma ciwon dai sai a hankali duk da tana taka k'afarta tafiya ba mai nisa ba sosai. Yanzun ma bata jima da futowa daga wanka ba tasha magani ta kwanta ko abinci bata iya ciba duk da yadda ummie take yawan fad'a akan zamanta da yunwa. Ta fara bacci me dad'i hayaniyar Salma da y'arta suka tashe ta. Ta bud'e idonta da yake ciki da bacci fal ta dubi Salma da itama take kallonta tace, "Wai ke har yanzu ba zaki girma ba?". Shagwob'e fuska Salma tayi tace, "haba auntie raihana don Allah, bikin kifa akeyi, ya kamata ace by now kin manta yadda ake yin bacci gaba d'aya saboda shiga busy, amma kika zo nan kika kwanta, ba k'unshi ba kitso kamar ba amarya ba, haba dubeki fa don Allah! yanzu ma ummie take fad'a mun ba abinda kike shirin yi, ko make-up yanzu bakiyi booking ba? salon duk y'an biki su fiki kyau....." Ta k'arasa fad'a slowly tana kallon k'afar raihana dake nad'e da bandage. Sai kuma ta kai hannunta k'afar tace, "ayyah meya same ki haka a k'afa". Raihana yamutsa fuska tayi ba tare da tace komai ba ta janye k'afarta, ta karb'i baby samha tana yi mata wasa cikin k'arfin hali. Yarinyar kuwa ta dinga b'angala mata dariya. Salma ce ta mik'a hannunta ta karb'e samha a hannunta ganin sai magana take bata sauraronta, "ki saurareni anan please,,, ya za kije gurin event d'in gobe da lanjererren k'afar ki haka?". Sai a lokacin tayi magana, "don Allah Salma ki barni naji da abinda yake damuna ni haba daga zuwanki zaki fara damuna....". Tsura mata ido Salma tayi tana nazarinta kafun ta mik'e ta bar mata d'akin, ba tayi wani dogon tunani ko nazari ba, shiyasa bata kawo komai a ranta ba don tasan tun asali haka raihana take bata fiya damuwa da komai ba. Ita ta dinga shige da fuce a ranar don ganin tayi duk abinda ya dace wanda zai futo da amaryarh gobe da kyau sosai. Ko zuwa yamma gida ya cika taf da jama'a da y'ammatan amarya su zee. Ai saida raihana taji kamar ta gudu tabar musu gidan don hayaniyar da suka dingayi ta hau kanta fiye da kima. Da dare kuwa d'akin su muhibba ta shige tun da wuri tayi kwanciyarta cikin su, dama wayarta tun ranar data had'u da wancen accident d'in take a kashe. ★★★ Washe gari su zee suka gyare gidan fess suka had'a break,,, har inda take suka kawo mata nata suna yi mata sannu, tunda suka fahimci da gaske bata da lafiya sai suka kama kansu suka shafa mata lafiya,,,, k'arfe tara d'aya daga ma'aikatan Zahra saloon tazo har gida bisa umarnin Salma aka zana mata bak'in lalle iya hannayenta. Aka yiwa ragowar y'an biki ma, auntie ma aka zaunar da ita akayi mata ja. Sosai amarya ta haska ita kanta sai jujjuya hannunta take. Khausar ma tazo, Amma kwana biyu mijinta ya amince tayi, shima da kyar. Aikuwa Salma ta fara mita hadda bata shawarar ta k'ara lallab'a shi ko kwana biyu ya k'ara mata akai, saboda zasu taya ummie kintsa gida bayan tafiyar y'an biki. Akayi sa'a Salma tayi shuka idon ummie, aikuwa ta mata tatas kan karta sake jin abu makamancin irin wannan, bayan biki zaman uban me zasu zauna suyi mata, toh ita d'in ma da an kai amarya ta tabbata ta kwashe duk wasu shirginta ta bar mata gidanta. Hak'uri duk suka bata ganin da gaske ranta ya b'aci. Misalin k'arfe biyu na rana y'an gidan su amarya sai shirye shiryen tafiya kamu suke don 3pm akasa a catin, amma amarya tana zaune bata da niyyar tashi kamar ba itace jigon duk wannan taron ba. Zee data gama had'a kaya zatayi gurin kwalliya tana ta zolayarta, "wai daga gobe ta zama Mrs Imrana". Ita dai kallonta kawai takeyi, duk lokacin da wani yayi mata maganar Imran sai taji gabanta ya fad'i, don yanzu ba maganar shi akeyi ba ta khaleefa ne,,,, saida gabanta ya fad'i saboda ambaton sunan khaleefa musamman data tuna aurene suka shirya bisa yarjejeniya,,,,, ita duk har yanzu ma ta kasa gasgata bikinta akeyi tare da wani wanda bata tab'a zama dashi ko hira ta wani lokaci ba, mutumin data d'au wasu shekaru bata ganshi da idanunta ba, a k'alla fa ana maganar kusan shekara goma sha d'aya, kuma a karo na farko data had'u dashi ya fara da jifanta da mummunar muguwar kalmar data tsani taga an danganta wani ma da ita ba ita ba, musamman musulmi d'an uwanta da ita wato hauka!,,, Anya ta aure shi kuwa ta yiwa kanta adalci? Sai ta sauke b'oyayyen ajiyar zuciya a lokacin da ummie ta shigo d'akin, sai da duk suka futa sannan ta fara magana da ita cikin taushi, "nasan har yanzu akwai abinda kike b'oyewa a ranki raihana, wanda nake da tabbacin shiya haddasa miki shiga damuwar da kike ciki da kika kasa shanyeta a fuskarki har kika fara janyo hankalin mutane kanki suna tambayar ko akwai abinda yake damun ki bayan ciwon k'afar?". Jinjina kai ummie tayi taci gaba da fad'in, "ban nemi jin komai daga gare kiba raihana, Soo kada ka ki fara yink'urin kawo mun uzuri ko dalili, shawara ce dai guda d'aya nake son na baki, duk abinda zakiyi a rayuwa kiyi shi domin Allah, ba don ki kuntatawa wani ko ki burge wata ba,,,,,". Damn! K'irjin raihana ya bada, kalaman ummie sunyi mata tasiri a jiki sosai har sun sake assasa mata laushin jiki da sagewar gwiwa, da ummie tayi wannan maganar, sai taji kamar tasan abinda take shirin aikatawa ne. Jikinta yayi sanyi lakwas, koba komai yana da kyau ta warware wannan auren kafun komai ya faru tazo tana data sani. Har ummie ta tashi zata futa, tayi saurin rik'o hannunta, sai ta tsaya tana kallonta. Ita kuwa k'asa tayi da kanta tana tunanin ta inda zata fara warware mata komai dai dai da yadda zata fahimta. Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman (maman almustapha) tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 👉🏻 08028175615 _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty four3️⃣4️⃣ Zama tayi kusa da ita cike da tausayinta tace, "ya akayi ne raihana?". Idonta taji ya ciko da hawaye, bakinta ya kasa furta abinda tayi niyya da farko, k'arshe ta k'are da fad'in, "ummie ki yafe mun?". Ta k'arasa fad'a tare da fad'awa jikin ummie ta fashe da kuka mai ban tausayi. Rungume ta ummie tayi tsam a jikinta tana shafa bayanta alamun rarrashi, ta kasa furta komai sai hawaye da idonta ya tara itama. "Kiyi hak'uri raihana kowacce mace da haka ta tafi kuma ta saba, Ina fatan zaki saka hak'uri da juriya a ranki tun yanzu.....". Sai data share hawayenta sannan cikin rawar murya tace, "ummie zanyi kewarku in na tafi". Ummie tace, "muma zamuyi kewarki raihana, amma na y'an kwanaki ne kowanne a cikin mu zai d'au hak'uri ya dangana, ki tashi ki sake yin wanka bari na had'a miki ruwa, nan da 20 mint Auntie zata zo d'aukar ki,,,, dama ki tabbatar kin had'a duk wani abu naki me muhimmanci saboda bak'i, kuma ki kunna wayarki nasan mutane sunata neman ki". A sanyaye muryarta har yanzu tace, "Salma ta had'a kayan jiya, wayar ma tana hannunta d'azu na bata". Ummie tace, "yauwa" Ko data had'a mata ruwan sai data taimaka mata saboda dad'ewar da tayi a zaune. Sharp sharp ta sake yin wankan ta shirya cikin doguwar riga milk, ta zura wadataccen hijab, ko zama batayi ba ummie ta turo a fad'a mata auntie tana jiranta a waje. Sai ta zura flat shoe a k'afarta ta futo ta yiwa su ummie da auntie hajara sallama ta nufi k'ofar gida. Bata ga kowa ba sai mota ash glass d'inta mai duhu ba'a iya ganin na ciki. Auntie tana ganinta ta k'arasa kusa da ita ta sauke glass d'in gaba. Suna had'a ido ta sakar mata murmushi, ita kuma tayi k'asa da kanta. Da d'ingishi ta k'arasa har mazaunin gaba ta bud'e ta shiga, cikin ladabi ta gaishe da auntien, ta amsa mata cike da so da kulawa tana tambayarta k'afarta. Tace, "ai naji sauk'i". "toh Allah ya k'ara sauk'i". Ta amsa da, "ameen" k'asa k'asa. Satar kallon auntie ta k'ara, kamar ba ita ta haifi su Yaya Ayman ba, tayi kyau sosai cikin wani dandatsetsen less pitch and golden, doguwar riga ce sai madaidaicin gyale data yafa a saman kanta, Suna tafe tana mata hira jefi jefi har suka k'arasa wani babban studio. Ta gyara parking suka futo su duka, amma ita hannunta rik'e da wata y'ar madaidaiciyar jaka, tana gaba ita kuma tana binta a baya har cikin k'awataccen gurin kwalliyar. Wata macce y'ar gayu wadda shekarunta ba zasu gaza talatin zuwa da biyu ba na ganin su ta taho da hanzarinta ta taryi auntie tana mata barka da zuwa, ta basu gurin zama suka zauna, tasa yaranta suka cika su da drinks, duk suka gaisa da ita cikin faram faram da barkwanci. Auntie tace, "ga y'ar tawa fa munzo sai dai bama son delay". Kallon raihana tayi har lokacin fuskarta da murmushi tace, "doctor surayyah y'ar ki ko k'anwar ki, naga bakwa kama kuma bama zaki haifi kamarta ba". Y'ar dariya kawai auntie tayi tana kallonta da mamakin maganarta, matar tace, "Allah da gaske likita". Ganin abun nata na gaske ne sai tace, "na fad'a miki tun farko bama son delay fa". "Toh angama ranki shi dad'e" Ta gama fad'a tana murmushi, sai ta yiwa raihana magana ta mik'e tabi bayanta zuwa gaban wani glass da kayan cosmetics cike fal, raihana tsayawa tayi kurum tana kallon komai na gurin. Ita kam auntie wayarta ta d'auko tana tunanin yadda komai yake sauyawa yana tafiya ba yadda ta tsara shiba, da farko taso ace yaranta duka biyu tare zasuyi aure a rana d'aya, ayi gagarumin biki na gani na fad'a mai kyau da k'ayatarwa, irin wanda zai girgiza ya gigita zuciyar maƙiya, sai gashi da farkon farawa khaleefa ya dawo da juyayyun al'amuran shi, a lokacin sai tayi tunanin watak'ila sai Ayman yayi aure har matar ta haihu khaleefa baiyi aure ba yana zaune k'asurgumin tuzuru dashi, nan ma ta shiga damuwa, ashe bata sani bama khaleefan ne zai riga Ayman d'in aure. Sai ta k'ara sauƙe ajiyar zuciya tana tunanin ko sameera zata zo gurin bikin kamar yadda ta bata cati da pass na traditional sitting d'in yau. Wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa tana ganin yadda auren raihana ya sake raunata y'ar rud'ad'd'iyar zamantakewar gidan ya sake wargaje su gaba d'aya, kowa ya kama gaban shi cikin su. Har Ayman gwanin juriya da shanye abu a wannan karon ya kasa saisaita yanayin shi. Gashi tayi iya yinta amma har yanzu bata gane abinda khaleefa yake b'oyewa ba, batasan mak'asudin shi na neman auren raihana ba, bayan ta ganshi a pic yana jifan wata kyakkyawar yarinya da kallon so da tsantsar k'auna, ta kuma tabbatar zai auri raihana babu soyayyar juna ko guda a cikin ran kowannen su. Ga Ayman gaba d'aya ya sauya, sauyin da kullum safiyar Allah saita tambayi musabbabin shi amma yak'i fad'a mata komai. "Kai wannan rayuwa! Allah yayi mana maganin abinda yafi k'arfin mu" ta fad'a k'asa k'asa. Wayarta ta d'auko daga jaka bayan ta gyara zamanta ta fara duba sak'onnin da aka ajiye mata. Ita kuwa me kwalliya ba jimawa ta gama tsantsarawa raihana kwalliya mai kyau da d'aukar hankali had'e da aji, yadda ta futo tayi kyau abun ba'a cewa komai sai son barka. Ita ta dawo gurin auntie ta karb'i kayan da amarya zata saka, wata tsadaddiyar lafaya ce milk and brown duk jikinta walwali yake na d'aukar ido da hankali sai rigarta ta ciki doguwa brown, da takalmi me matsakaicin tudu da jaka duk milk, sai su jeweleries na gold masu kyau sosai suma. Saida ta shiga wani kewayyen guri ta saka kaya sannan ta futo aka k'arasa had'a ta, ko da suka gama sai da akayi mata short videos da pics sannan aka futo da ita inda auntie take zaune tana jiranta. "Masha Allah" shine abinda Auntie ta fad'a a lokacin data ga yadda raihana take walwali da d'aukar ido kamar an sauyo ta. Hotuna akayi musu tare anan gurin, duk da raihana tak'i sake jikinta saboda kunya, kafun auntie ta sallame su su futo daga gurin, duk da k'afarta ta warke amma har yanzu tana d'ingishi kad'an. Wannan karon gidan baya ta bud'e mata tace ta shiga, raihana bata ce mata komai ba amma sai taji kunya da nauyin aikata hakan, madadin tayi kamar yadda tace, sai ta rufe ta koma mazaunin ta na d'azu ta shiga ta zauna. Ita kanta auntie sai data ji dad'i da hankalin yarinyar, wato tana jin nauyin ta shiga baya ita ta zama drivern ta. Hakan yasa ta sake jin yarinyar a ranta fiye da koda yaushe ma,,,,, lallai hajiya tafeeda ba k'aramar asarar suruka ta gari tayi ba, yanzu kowacce za'a je a d'ebo mata kuma oho? Koda yake ita duk ba abinda ya shafeta bane. *****Wani katafaren hall na gani da aka shirya table table kewaye da kujerun zama, a k'alla d'akin taron zai iya cin mutum d'ari biyu zuwa da hamsin haka. Ya cika makil kuwa mutane rukuni rukuni, waje waje, da y'an taya murna da kuma y'an ganin kwakwaf. Can gefe guda na hango umma salaha dasu innah da y'ay'an kishiyar innan, sai mom ziyada da y'ay'anta biyu. Sai sauran jama'ar su duk gasu nan a zazzaune. kowanne a cikin su ya zura ido yaga yadda zata kaya, musamman ma umma salaha da har lefen da aka mayar taje gidan hajiya tafeeda ta gani ta kuma tabbatar. Shine yanzu ta taho don taga kwal uwar daka da idonta, tasan dai maybe kawai pretending zasuyi gudun kada mutanen gari suyi musu dariya. Saita kyalkyale da dariya ita kad'ai a ranta tana ayyana idan sun b'oye yanzu ai zata ga yadda zasuyi gobe ranar d'aurin aure, tunda dai ba'a tab'a d'aura aure ba miji, duk da tayi mamakin yadda suka iya mayar da lefe ba tare da an sanar da Abba abubakar mijinta ba, abun nan ya girgiza ta matuk'a. Tana cikin wad'annan y'an tunane tunanen uwar amarya ta k'araso tare da wasu mata guda biyu, dukkannin su sanye da shiga ta alfarma ta gayu. Har kusa da seat d'in amarya ta ajiye su. Kowa cikin y'an hall d'in kallon ummie take, barin ma su innah da sauran maƙiya da basa sonta. Duk da ba kwalliya tayi ba, Amma tayi kyau cikin tsadadden leshin data sa jikinta. Tayi kyau sosai kamar ba maman amarya ba. Mutane sai kallon kallo suke, su fa har yanzu sun kasa gane abinda suke son gabatarwa a gurin. Gashi dai jama'a sunzo iyaye da k'awaye. Su Fatima da raheela ma sunzo tuni har Salma ta basu front seat. Sai dai duk cikar hall d'in nan da batsewarshi ba sautin kid'a ko guda, sai hayaniyar mutane, gashi lokaci nata tafiya har an fara kawo abinci lafiyayye mai kyau da dad'i. Nan ma kwalalo ido kawai sukayi suna kallon yankan nama manya manya rabin plate, ga ruwa da lemuka a karo na biyu ana sake rabawa. Ummie tana ta gaisawa da mutane dake yi mata Allah sanya alkhairy, daga can ta wani kusurwa na gano sameera a zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya gefenta shaheeda ce zaune. Danne dannenta take a waya amma rabin tunaninta yana wajen abinda ya had'a surayyah da ruqayyah har ta aika mata da catin bikin raihana, sannan raihanan da tafeeda ta shiga ta futa da masifa da bala'i ta hana d'anta aurenta, aka mayar musu da komai na auren su magana ta rushe ita d'in ganau ba jiyau ba, cikin kwana biyar Ina ta samu wani mijin ma da har za'ayi biki?, Toh ko Ayman surayyah ta nemawa auren tunda ta hana shi auren Nur? Sai kuma yanayin fuskarta ya sauya har ta kaiga ta ajiye wayarta kan table tana tunanin gaskitar hasashenta ba tare data sani ba, in kuwa hakan ya tabbata lallai Nur tana cikin matsala,,,,, duk da har yanzu bata yadda sunsan gundarin abinda yake faruwa ba, don har gobe tana jin takaicin yadda surayyah ta d'auki zafi har take shirin futa hanyar ta gaba d'aya, har take maganar a raba duk wani business da sukeyi tare kowa yaci gaba da tafi da nashi. Tasan kuwa lallai idan ya tabbata Ayman zai auri raihana, Nur sai ta kusa yin hauka a garin nan saboda tashin hankali, don ta tabbatar tana son Ayman sosai fiye da zaton kowa,,,, Tana tsaka da wannan tunanin taji ana neman k'awayen amarya suzo su shigo da ita. Sai ta koma da kujerar ta saitin shigowa don taga ko zata ga wani abu da zai tabbatar mata da zarginta. ****Daga waje kuwa raihana tana tsaye gefen auntie da take rik'e da hannunta na hagu har k'awayen amarya suka k'araso, suka gaishe da auntie sannan suka kewaye su suka fara takawa sannu a hankali zuwa cikin hall d'in, har lokacin auntie tana rik'e da ita. Koda suka shigo hall duk d'auke wutaa akayi, hadda masu dawo da abinci daga bakin su saboda tsananin mamaki da fargaba data d'arsu a ran da yawa daga mutanen gurin. Auntie bata sake hannunta ba har saida ta kaita mazauninta sannan ta samu gefe guda ta zauna ta zuba kunnuwa da ido don sauraron lecture da manyan malaman musulunci zasu gabatar akan zamantakewar aure. Aikuwa ba b'ata lokaci aka fara gabatar da lecture mai sanya nutsuwa a zuk'ata da kwantar da hankali gami da karya k'ashin bayan y'an hassada na gurin. Tuni hall ya dawo tsit baka jin komai sai bayanin wad'annan mata masana addinin islama, inda suke bayani akan zamantakewar aure da yadda mace zata sauke hak'k'ok'in mijinta a kanta, da kissoshi iri iri, musamman na tsabtar jiki da tufafi yasa da yawa suka fara d'ago kuskuren da suke tabkawa a gidajen su. Amarya taja gefen lufaya ta rufe rabin fuskarta tana share hawaye da yatsun hannunta, ana gamawa auntie tayi mata kamu irin na matan larabawa na zallar turaren khumrah dana garwashi, nan da nan kuwa guri ya d'inke da k'amshin mayen turare me kama jiki da muhalli. Aka rarraba kayan gargajiya ga duk wanda ya halarci wannan guri, aikin maman amarya kenan. Amma da d'akin taro da abinda aka ci duk surayyah ce, har masu lecture ita ta gayyatosu, ta kuma raka su da sha tara ta arzik'i rigijib har bakin motar su suka tafi. Ta gaisa da jama'a sama sama, ta d'auki amarya kamar yadda ta kawo ta da tsirarun k'awaye ta tafi. Har k'ofar gidan su ta ajiye su, raihana bata futa ba saida duk suka futa sannan ta kalli Auntie da idonta daya tara ruwan hawaye tace, "nagode auntie Allah ya k'ara rufa asiri". Sauke mata hannun k'asa tayi tana murmushi tace, "bar yimun godiya raihana, don a gurina keda Ayman da khaleefa duk d'aya nake kallon ku". Saita share hawayenta da tafin hannunta tayi mata sallama tana d'ingisa k'afa ta shiga gida. A can ta samu su raheela suna ta shirin d'aura alwalar sallar magrib data k'arato. Cire lafayar jikinta tayi ta samu kan kujera ta kwanta tana tambayar su Fatima tun yaushe suka zo? Raheela tace, "au duk yadda muka dinga shige da fuce a gabanki baki ganmu bama saboda tsabar shiga busy". Girgiza musu kai tayi tace, "toh y'ar jiran k'iris nidai kar ki had'a ni da Fatima, ba wai ina nufin a gurin taro ba a nan gida tun yaushe kuka zo...". Kusa da ita raheela ta dawo tace, "au toh na fahimta, kina futa ba jimawa muka zo". Sai ta tashi zaune sosai itama tana kallon su tace, "Amma dai kwana zakuyi ko?". "Eh insha Allah" sai ta fad'ad'a fara'ar fuskarta, Fatima tace, "Amma fa kinyi kyau Masha Allah raihana, duk da dama ke d'in me kyau ce, sai dai naga kamar kina d'ingishi da kika shigo me ya samu k'afar ki?". Raheela tace, "Ina shirin tambayarta kika rigani". Yamutsa fuska tayi kad'an tace, "Na had'u da tsautsayi ne". Ta k'arasa fad'a tana janye musu rigar jikinta don suga k'afar tata. "Ayyah sannu raihana". Duk suka fad'a da damuwa saman fuskar su. Sunyi shiru zuwa wani lokaci kafun ameena ta shigo itama ta zauna kusa da ita, tana yaba kyaun da tayi har da tambayar me kwalliyar. Ita kuwa raheela taso tambayarta game da sauyin data gani a tare da yanayinta, amma ko data tuna ciwon jikinta da suka gani yanzu sai ta danganta rashin walwalar ta da hakan. ****Haka dai ranar suka hanata bacci akan lokaci har sai zuwa can nisan dare ta samu ta watsa ruwa tasha magungunanta ta kwanta. Ko data kwanta kasa yin baccin ma tayi sai juyi kurum, daga k'arshe dai dole ta tashi ta zauna dirshan a tsakiyar gadon ta had'a kai da gwiwa, wannan wacce irin rayuwa ce take shirin cusa kanta a ciki? Ita bata tab'a sanin ana aure babu soyayyah bare a kaiga maganar fahimtar juna ba sai data had'u da khaleefa har hakan yake shirin faruwa da ita gobe, toh Amma fa haka shine kad'ai mafutar ta, ta hakane zata tsira daga maganar mutane da sharrance sharrancen su innah da umma salaha, har ta samu nutsuwa ita da mahaifiyar ta itama ta sarara kamar kowanne mutum, Saita kife kanta jikin gwiwar hannunta tana fad'in "Allahumma ajirni fil musibati,,, waklifni khairan minha". Hakanan ta sake komawa ta kwanta tana sake k'issima abubuwa da yawa a cikin ranta. ★★★★★ Ta b'angaren Ayman kuwa dama tunda abun nan ya faru ya d'auke wutaa gaba d'aya kamar ba Ayman ma'abocin faram faram da barkwanci ba, duk da a haka yana kwararawa kanshi gwiwa ne, tuni ya cire rai da raihana ya hak'ura da ita har abada saboda khaleefa ya fishi cancantar ta, duk da shima har yanzu bai daina mamakin yadda khaleefa ya had'u da raihana har suka fara soyayyar data kaisu ga batun aure ba. Ya zama hopeless a satin gaba d'aya amma a hakan sai daddannewa yake yi, shi kad'ai yasan ciwon dake cikin kowacce dariyar shi d'aya idan yayi. Yana kallo aka shiga hidimar biki gadan gadan a gidan, duk da ba wasu mutane auntie ta tara ba, amma kullum bata samun zama. A ranar da Auntie ta shirya zata futa kamu, yana kwance a parlon su ta shigo ta same shi, sai ya tashi zaune yana kallonta, ba wata kwalliya tayi a fuskarta ba amma tayi kyau sosai. "Ina son zan kai raihana gurin kamu da walima, ko zaka samu damar yi mun rakiya". Yamutsa fuska yayi wani sabon abu yana taso mishi, laa shakka ba don auntie ce tayi mishi wannan maganar ba,,,, da lallai sai ya ci kwalar mutum yaji dalilin da zaisa yayi mishi irin wannan maganar. Cikin dakewa da dannar zuciyar shi yace, "Auntie bana jin dad'in jikina gaba d'aya, Ina ganin anjima kad'an ma ganin likita zan tafi". Cikin kulawa tace, "gaskiya ya kamata,,,, dama a satin nan Ina ankare dakai, kuma nasan ba komai ya haddasa maka haka ba sai wannan damuwar da kake ajiyewa a cikin ranka har yanzu.... Na fad'a maka ka cire komai daga ranka Ayman ka barwa Allah, kana zaune Allah zai kawo maka matarka har gida, ka manta da Nur ka shafe babinta gaba d'aya cikin rayuwarka, sam baka buk'atar mace irinta, wadda zata soka a yadda kake kake nema, ba wadda saika taka wani matsayi a rayuwa ba, ba gashi d'an uwanka da zargin da komai an bashi aure ba....yanzu in banda sharrin mutanen mu ma, mutumin daya mutu aka fad'a musu baya raye...shine zasu dinga bi guri guri suna cewa yaran shi shegu kamar a gaban su akayi cikin shegen aka haife... Mtsss!." Ta k'arasa zancen da jan tsaki. Ayman daya zuba ido yana sauraronta murmushi kawai yayi bayan gama sauraron kalamanta na son zuciya a gurin shi, duk da maganarta ta sosa ranshi amma ba yadda zaiyi da ita tunda uwa ce. Amma duk da haka yana da kyau ya dinga tunasar da ita wasu abubuwa da tunaninta yake kwacewa a kansu. "Auntie nifa har kullum bana ganin laifin mammie, iya gaskiyarta ne ta fad'a mun, tace ita bata hanani auren Nur ba amma inje in fara binciko waye mahaifina,,, kuma suwaye dangin shi da bakya son mu sani.... Toh meye laifinta, ba ita kad'ai ba duk inda naje neman aure za'a iya fad'a mun haka,,,,ba kowane irin iyayen raihana ba, da zasu iya bada auren y'ar su ga mutanen da basu san asalin suba, mutane masu dattako da kyakkyawar zuciya, wanda zasu iya sa mayafi su lullub'e duk wani tabo da tambarin da yake tare da wani mutum da basu tab'a doguwar magana ko zama tare dashi ba..... Irin mutanen nan sunfi komai k'aranci a wannan duniyar da muke ciki...". Duk data fahimci inda maganar Ayman ta dosa amma saita basar ta sake cewa, "mu saka kyakkyawan yak'ini akan kowa Ayman, nayi imanin zaka samu irin wad'annan surukan kaima, ba zasu k'are a iya kan iyayen raihana ba...." Fahimtar in yaci gaba da zama zai iya ci gaba da ja da duk wata magana da zatayi sai ya mik'e don ya bar mata gurin, "auntie bari naje na kwanta". "Ya kamata dae". Taku biyu yayi yaci karo da k'afar khaleefa,,,,, kamar kullum yanzu ma sanye yake dogon wando bak'i, sai white shirt mai ratsin bak'i itama. Ya hard'e hannuwan shi duka a k'irji yana kallon su shida auntie, fuskarshi d'auke da wani yanayi mai wuyar fassaruwa farat d'aya. Kewaye shi Ayman yayi zai huce, don a duk lokacin daya ganshi wani tuk'uk'in bak'in ciki ne ke zuwa ya tokare mishi wuya. A duniya yanzu ba wanda yake ganin bak'in shi kamar Auntie da khaleefa, saboda yana ganin sune ummul'a'ba'isin raba shida masoyiyar shi raihanatu. Har ya huce sai khaleefan ya dafa kafad'ar shi ta baya, aikuwa ya juyo da sauri idon shi cike fal da ruwan hawaye ya janye jikinshi daga rik'on daya mishi. Zai sake hucewa khaleefa yasha gaban shi yana kallon cikin kwayar idon shi. Tuni hawayen da suka taru a idonshi sun soma biyo kuncin shi suna sauka a hankali. Jikin khaleefa a matuk'ar sanyaye ya rungume Ayman d'in yana jin idonshi shima yana tara ruwan hawaye. "Ka gafarceni Ayman....." Ya fad'a da kwantaccen sauti k'asa k'asa. Ita kanta auntie da take tsaye bayan su kallon su take da karyayyiyar zuciya. Tana jin wani luguden bugu a k'irjinta. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty five3️⃣5️⃣ "Wane laifi kayi mun da zaka nemi yafiyata?". Ayman ya tambaye shi bayan ya janye jikinshi daga nashi bai yarda koda wasa d'an uwan yaga hawayen idonshi ba. Shima khaleefa daga haka bai sake ce dashi komai ba ya bishi da ido har ya shige d'akin shi ya murza key. K'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya sauke, yasan sana'ar tashi da ya sake maida ita dabi'a cikin y'an kwanakin yake wato kuka. Auntie ce ta k'araso har inda khaleefa yake ta kira sunan shi a sanyaye, ya amsa bayan ya sunkuyar da kanshi k'asa. "Wai khaleefa kana nufin babu wanda zaka gayyato gurin d'aurin aurenka na gobe? Na duba cards d'in duka daga kai har Ayman ba wanda ya tab'a shi ma". Kanshi a k'asa har lokacin yace, "ai ni bani da wasu friends da zan gayyata a garin nan". Kama hab'a tayi tana kallon shi da matuk'ar mamaki, "kenan haka zakaje gurin d'aurin auren kai tsuranka?". Bai iya ce mata komai ba, don shi har ga Allah baya son kowa yasan da maganar wannan auren nashi, yafi son ayi shagali na ainahi a lokacin auren shi na gaske da Saleema, "Toh Ina son magana dakai anjima da dare, yanzu zan futa kamun raihana ne.....". D'an k'aramin tunani ya tafi akan sunan raihana data ambata yanzu,,,, kafun caan ya tuna kamar yarinyar nan ma sunanta raihana ko? "Kayi shiru ba kace komai ba". Ta sake tambayarshi cikin kafe shi da ido. Sai a lokacin ya d'ago ya kalleta, "Allah ya tsare hanya Auntie". Yana fad'in haka ya nufi hanyar d'akin shi shima. Ita kuma ta futa zuciyarta fal wasi wasi, shi kam koda ya shiga d'akin shi zama yayi yana nazarin gaba d'aya lamuran Ayman da sauyawar da yayi lokaci d'aya, dama tun cikin y'an kwanakin ya fahimci kamar akwai damuwa tare dashi. Sai dai bai tab'a d'auka rashin walwalar shi nada alak'a da yarinyar da yake so ko mamanta ba, lallai suna cikin matsala shida d'an uwanshi, indai har na jikin auntie ma sun fara zarginta da abinda sauran mutanen gari ke zarginta toh waye zai futo ya kare su a wannan garin. Sai ya sake girgiza kanshi, ba shakka wannan rik'on alk'awari na auntie yana azabtar dasu. Wayar shi da take ringing ta zaburar dashi daga nazarce nazarcen da yake yi. Sai ya d'auko ta daga gefen shi yana duba no me kiran, Ahmad ne,,,, dafe kanshi yayi don shap ya manta ya sanar dashi abinda ake ciki ma. Bai iya d'aga wayar ba har ta katse wani kiran ya sake shigowa. Saida ya kusa tsinkewa shima sannan yayi picking. Bayan sun gaisa complain Ahmad ya fara mishi kan kwana biyu ya manta dashi gaba d'aya. Hak'uri ya bashi kafun ya fad'a mishi ainahin abinda yake faruwa. "Man gobe fa zan d'aura aure...". Ahmad a kwance yake amma baisan lokacin daya mik'e zaune ba, "khaleefa are u serious, please let's keep joke aside". Khaleefa yace, "Ni ne fa nake yi maka wannan maganar Ahmad ba kai kake yimun ba....so tun wuri ma ka gane ba zancen Wasa a maganata". "I can't believe it khaleefa! In na fahimce ka fa kana nufin wata zaka aura ba Saleema ba, toh daina son saleemar kayi ko me? Sannan ni yanzu daka fad'a mun a late, taya zanyi booking tickets har na taho Kano gobe kafun a d'aura aure.....". Mik'ewa tsaye yayi bayan ya furzar da iska me huci daga bakinshi, ya Isa gaban k'arfen windown d'akin shi ya rik'e da hannunshi d'aya sannan yace, "ka adana tambayoyin ka zuwa ranar da zamu had'u in warware maka komai Ahmad,,,, and sannan kada ka damu kanka ba lallai sai kazo wajen bikin ba, don ba wanda na gayyata ma, duka IC na y'an gidan ku yana hannuna suma ba sai sunzo ba kawai". Cikin sake jinjina al'amarin Ahmad yace, "Zan iya hak'uri har zuwa sanda zamu had'u kuwa? Toh wai ko auren dole Auntie zata yi maka ne man?, tunda ta rantse ba zaka bar k'asar nan babu aure ba..... Ni dai kam zan fad'awa dad dole sai nazo a gobe ma kuwa....". "Ahmad ka daina k'ok'arin maida k'aramin abu babba don Allah, nan da 13 days ma dole zamu had'u ai". Ahmad kanshi har lokacin a d'aure yace, "Wai ka san abinda kake fad'a kuwa? Khaleefa auren mutum fa bana y'ar tsana ba,,,, toh kaidawa zaka gurin d'aurin auren.....". Zuwa yanzu khaleefa ya fara gajiya da magana akan abu d'aya, don haka cikin k'osawa yace, "ba maganar da zamuyi a waya bace,,,,, kuma nima ba zuwa zanyi gurin auren ba khalas na!". Shi dai Ahmad har yanzu a bai bai yake kallon komai, amma duk da haka sai ya bishi da addu'a "toh sai nace Allah ya sanya alkhairy......" Da sauri khaleefa ya katse mishi hanzari,,,, "ohh kana da matsala Ahmad, wa yace maka kayi addu'a irin wannan kuma?" Zai k'ara yin magana khaleefa ya sake katse shi, "as I said earlier, ka ajiye komai zuwa lokacin da zamu had'u". "Alright shikenan". Ahmad ya fad'a, Daga haka sukayi sallama khaleefa ya ajiye wayar, yana tunanin ta yadda zai fuskanci rigimar auntie da take son lallai saita tursasa shi yin abinda bai shirya yin shiba, aure nawa akayi ba ango a gurin, ko a Germany yasha ganin ana d'aurawa abokan karatun su aure a turo musu da matan, basu jeba bare wasu abokan su daba su zasu zauna musu da matan ba, kuma har ayi a gama ba'a samun wata matsala, auren be fasu ba.... Da wannan tunanin ya k'arasa duk wani abu da yake shirin yi a ranar. Ayman kuwa yana shiga d'akin shi yaji kamar ana wujijjiga shi, cikin dauriya da dakiya ya dafa bangon d'akin yana rintsee idanun shi duka biyu, yayinda zafafan hawayen shi suka fara futowa suna sauka sala sala. Sai ya durk'ushe a gurin yana tuna duk lokutan da suka kwashe tare da ita, tun tana k'aramar yarinya a lokacin da yake koya mata assignment, har akazo kan sanda khaleefa ya tafi Germany ya barshi da ita, rashin abokin hira yasa suka sake samun kusanci matuk'a, yasha hira da ita akan abubuwan da suke damun shi, tun bata mallaki hankalin kanta ba, a wasu lokutan ta bashi shawara me kyau data zarce tunanin shi, a wasu lokutan kuma ta kyalkyale mishi da dariya, wani yaji haushinta suyi fad'a ta bashi hak'uri, wani kuma ya taya ta su dara tare. Tafiyarta nursing school da yadda suka ci gaba da rayuwa cike da kulawa da mutunta juna har zuwa kan yadda kishin zata auri Imran yasa ya janye jikin shi daga gareta a hankali, bai sani ba a wancen lokacin ashe damace aka bashi, irin damar da masu iya magana ke cewa sau d'aya take zowa mutum a rayuwa. Sai ya daki k'asan d'akin da hannuwan shi, bai damu da yadda suke zugi da rad'ad'i ba ya fara magana cikin muryar kuka, "me yasa zaka yimun haka khaleefa! Meyasa!! Meyasa!!!" Ya k'arasa fad'a yana kifa kanshi jikin gadon shi yana jujjuya kanshi. . ★★★★ A daren ranar ran auntie yakai mak'ura wajen b'aci a lokacin data ritsa khaleefa bai shirya ko kayan da zaisa na d'aurin auren gobe ba,,,, kanshi a k'asa har ta gama bambaminta sannan ya bata hak'uri tare da kawo mata uzurin baya jin dad'i, baya ga haka ma baya tunanin zai samu zuwa gurin d'aurin auren gaba d'aya, wannan karon kallon shi kawai ta dinga yi zuciyarta naci gaba da raya mata abubuwa da yawa na manufar auren raihana da khaleefa ya shirya zaiyi. Sun jima shiru kafun ta mik'e ta bashi umarnin ya biyota zuwa sashenta. Set d'in akwatuna ne guda biyu, amma kalar su mabanbanta, bakwai iri d'aya bakwai iri d'aya. A gefe ya zauna yana sauraron maganar da auntie take yi bayan gama nunnuna mishi kayan cikin akwatunan. "Wannan kayan lefen kune dana dinga had'awa a b'oye, naka dana Ayman da ban d'auka wani cikin ku zai iya riga wani fara yin aure ba,,,,. Toh yanzu tunda al'amura sunzo a juye Ina ganin zamu barwa raihana duka wad'annan kayan...." Maganarta ta k'arshe ta d'au hankalin khaleefa har baisan lokacin daya juyo ya dube ta ya sake duban kayan ba. Ta gane kallon da yake sarai amma tayi kamar bata gane manufar shiba taci gaba da bayaninta. "Da farko nayi niyyar yi muku bazata da wad'annan kayan lefen a lokacin da auren ku zai taso, amma yanzu tunda matar ka kad'ai za'a barwa dole ka biya farashin su, kayana masu kyau da tsada ne, kusan duk ba'a k'asar nan na had'a suba, da kud'in su da kud'in aure da sadaki duk kai zaka biyawa kanka babu wanda zan iya d'auke maka a ciki, tunda Allah yasa akwai kud'i a gurinka....". Fuskarshi sam bata sauya daga yanayin yadda take ba, bare auntie ta fahimci yadda ya karb'i zancen, da dakakkiyar murya ya tambayeta, "meye total na duka kud'in". Wani murmushin mugunta tayi ta d'anyi jim tana had'a lissafin jimillar kud'in a ranta, kafun ta fara mishi bayani dalla dalla. "Dubu d'ari biyu na kud'in aure (kasan hausawa suna kai kud'in gaisuwar iyaye), dubu d'ari da hamsin kuma na sadaki, sai kyautar motar million biyu ko biyu da rabi haka da nake son kayi mata.....". A wannan karon khaleefa kasa hak'uri yayi har saida ya tambayeta da mamaki, "Toh ni yanzu ina zan samu motar da zan tabbatar da ingancin ta har ayi cikini a biya kud'inta kafun gobe?, Sannan motar ita kuma ta meye...?". Murmushin gefen baki tayi tace, "Kaine nake son ka aureta da daraja har haka khaleefa, saboda kafi sanin muhimmamcinta, sannan mota kada ka wani damu na sameta already har anyi ciniki kud'i kawai zaka musu transfer a kawota". Kanshi ya rik'e da hannun shi biyu yana juya maganganun auntien, toh meyasa auntie take yin hakane wai, so take ya aureta da tsada saboda kada ya saketa ko meee? Shin batasan auren deal bane da bazai huce wa'adin shiba? "Khaleefa kai nake saurare shin ko akwai abinda baiyi maka bane a cikin abubuwan dana lissafa a soke.... Duk da sokesu yana dai dai da soke auren gaba d'aya..... Ga lissafin kayan lefe, duka mu barshi 1.5million". Wayarshi da take aljihu ya zaro ya tambayi account d'inta, tana fad'a yayi mata transfer 4million, ya tashi zai tafi ta dakatar dashi. "Ka tabbatar ayman ya rakaka inda ake siyar da ready made, ka karb'o farar shadda hula da takalmi, don gobe in bakaje wajen d'aurin auren nan ba....." Sai ta gyad'a kai kurum. Futa yayi amma kuma ya kasa shiga cikin d'akin, sai ya tsaya daga jikin k'arfen benen yana lissafa auren da zaiyi gaba d'aya tare da aza shi bisa mizani, har yanzu baiga wani kuskure ko wani abu da yayi ba dai dai ba akan maganar auren nan, sai dai tsoron shi d'aya Auntie data fara gindaya mishi tsauraran sharud'd'a tun kafun aje ko'ina. Hango tahowar Mama haleema yasa shi saurin kaucewa daga gurin, don yanzu sai ta hau zolayarshi tana addu'ar da bai sata ba. Ko k'asa ko sama ya rasa Ayman a gidan, gashi sai kiran wayarshi yake a kashe. Bai sanar da kowa ba yayi kwanciyarshi don baiga abun tashin hankali da zai wani damu kanshi kan lallai sai ya nemo wasu fararen kaya a yammacin nan ba, shi kuma Ayman maybe ya futa ne yaje ya dawo zuwa jimawa. Auntie kuwa mayar da kayan tayi ma'ajiyar su tana tuna yanayin da khaleefa ya shiga akan maganar kud'ad'en data lissafa, tana sane tayi charging shi kud'i masu yawa saboda aljihun shi ya jijjiga sosai ta yadda ko sunan raihana bazai so yin wasa dashi ba bare aurenta. *****Washe garin ranar suka tashi da bak'i k'awayen Auntie y'an biki da wad'an da zasuyi jagorancin kaiwa su malam kayan lefen har gida, don a can auntie ta shirya gudanar da yininta tare da tsirarun abokan aikinta, duk daba wani yawa ne dasu ba amma hayaniyar su duk saita damu khaleefa saboda maganar ba a hankali suke yinta ba, shi sai ya dinga jin ma kamar har wata y'ar shewa shewa akeyi a gidan nasu yau. Ita dai Auntie tana zaune tsakiyar su duk jikinta a salub'e, rabin hankalinta yana kan khaleefa da tunanin ko yayi abinda ta umarce shi jiya? Ganin ta lula duniyar tunani sai d'aya a cikin su ta kira sunanta, "surayyah". Bata amsa ba sai d'ago kanta da tayi ta kalleta, "kamar akwai damuwa a tare dake, sannan ni tunda nazo nake son tambayarki Ina sameera naga ban ganta ba..". Murmushin yak'e tayi a lokacin da doctor Rabi'a ta kai aya, don kore musu zargi sai tace, "kwana biyu bata da lafiya, amma Ina tunanin anjima in jikinta yayi sauk'i zata zo...". "Toh Allah ya sauwak'e" suka bata amsa a tak'aice. "Minti biyu don Allah ina dawowa". Ta fad'a a lokacin da take mik'ewa tsaye. A nutse take takawa zuwa b'angaren nasu, babu kowa a parlour, hakan yasa tayi knocking k'ofar bedroom d'in khaleefa, wanda a dai dai wannan lokacin yana zaune gefen gadon shi ya had'a kanshi da gwiwa, ya rasa abinda yake mishi dad'i a duniya gaba d'aya, ga yawan fad'uwa da gaban shi yake yi. Jin kamar ana tab'a k'ofar shi, sai ya tashi da sauri, instead of ya futo yaga me k'ok'arin shigowa, sai ya d'au towel ya fad'a bathroom da mugun sauri. Koda auntie taga bashi da niyyar bud'ewa, tura k'ofar tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama da murya k'asa k'asa, babu kowa a ciki, sai wayoyin shi zube a gefen bed, d'akin duk a hargitse ya futo da rabin kayan shi ya jibge saman bed d'in. K'arar ruwa da taji ya tabbatar mata wanka yake yi, saita sauƙe b'oyayyen ajiyar zuciya ta koma da baya ta futa. Kamar zata huce, saita tuna da Ayman yau ko gaisheta baije ba, hakan yasa shima ta buga mishi k'ofa kafun ta shiga, babu kowa a ciki, sai dai d'akin neat dashi, shedar me aikin nan tayi aikinta tuntuni a ciki,,,, batayi tunanin bai kwana a gidan ba, shiyasa hankalinta kwance taci gaba da harkokinta, duk da a k'asan ranta tana tunanin abinda ya hana shi zuwa ya gaisheta yau ★★★K'arfe goma da mintuna biyar, khaleefa yana zaune gefen gadon shi k'afar shi d'aya a k'asa, d'aya kuma a saman gadon, yayi maseefar kyau cikin shadda sky blue, (D'aya daga cikin kayan da Dad ya d'inka musu ne, wannan ita ce kusan babbar riga da tazo da malum malum a duk cikin kayan nasu, basu tab'a sasu ba shida Ahmad saboda sun barsu cikin kayan da zasuyi amfani dashi a bikin Ahmad). Hularshi brown, haka takalmin shima, tsintsiyar hannun shi d'aure da agogon fata da kallo d'aya zai tambara maka kud'in shi, wayarshi rik'e a hannun shi ya zubawa d'aya daga hotunan birthday d'inta ido, a zahiri idanun shi suna kallon tane, amma ta cikin zuciyarshi sam ba ita yake tunani ba a lokacin, tunanin shi gaba d'aya ya karkata ne ga Ayman da tunanin abinda yake faruwa cikin rayuwarshi, sannan ina ya tafi ya barshi shi d'aya a rana irin wannan, koda ba auren gaske bane zaiyi ai ya kamata ya kasance tare dashi a gefenshi. Sai ya ajiye wayar gefe ya sake kwantar da kanshi jikin fuskar gadon da yake zaune, zuciyarshi na k'una da suya a duk lokacin daya tuna wani abu da yake shirin faruwa dashi nan da mintuna k'alilan. Sallama yaji da muryoyi kamar nasu Ahmad, bai motsa ba saboda yana zaton ko gizo ne kunnuwan shi suke yi mishi. Amma jin muryoyin na k'ara kusanto d'akin da yake ciki, sai ya bud'e idanun shi da har sun fara sauya launi ya zubawa k'ofar shigowa. Da d'aya da d'aya suka fara shigowa, su kusan biyar duk sanye da shadda mabanbantan kaloli. Kai da ganin su zakasan matasan y'an boko ne da suka k'oshi da ilimin addini dana zamani, wayayyu da yanayin mu'amular su da mutane ya bayyana wayewar su. "Ango! Ango!!" Ahmad ya fad'a bayan ya hard'e hannuwan shi a k'irji yana kallon khaleefan, bai iya ce musu komai ba, sai hannu daya dinga basu yana gaisawa dasu. Kayan kan gadon shi ya janye gefe don su samu gurin da zasu zauna. Da kanshi ya tafi parlour ya kawo musu drinks masu sanyi. Suka k'ara gaisawa sai zolayarshi suke "Ashe wai duk zai riga su shiga daga ciki?". "Yae da wannan beb d'in za'ayi ne ta makaranta..?" Wani cikin su ya tambayeshi bayan Muhammad ya jefa mishi tashi tambayar,,, bai iya ce musu kanzil ba sai Ahmad da yake jefawa kallon tuhuma, don shi babu wanda ya gayyata cikin su. Tuntuni Ahmad ya gane abinda yake nufi amma sai ya basar don abinda khaleefan yake so sam ba mai yiwuwa bane, ko a tarihin iyaye da kakanni baiji wani tarihi makamancin wannan ba, dad'in dad'awa kuma a jiya auntie tayi mishi bayanin komai yadda ya kamata. Kusan Ahmad ne dasu Muhammad sukaita hirar su amma babu khaleefa da ya raba hankalin shi gida da yawa. Kiran auntie ya alamta mishi lokacin tafiya wajen d'aurin aure yayi, sai ya turawa Ahmad gajeren sak'o kamar haka, "ka tattaro su lokaci yayi da zamu tafi......". Ahmad ya kalle shi bayan gama duba text d'in, yana tsaye still fuskarshi kadaran kadahan, kamar bashi za'a d'aurawa aure nan da lokaci k'alilan ba. Ahmad ne ya fad'a musu lokacin tafiya wajen d'aurin aure yayi, aikuwa wani cikin su ya dinga yiwa Ahmad tsiya, wai shine bakin khaleefa da komai shi yake fad'a ba khaleefan ba, wannan ai wakilcine me wahala ya baka, yanzu ba don Allah yasa ka tuna da cards d'in mu daka karb'a a hannun shi ka tafi ba, daga baya kazo kana kiran mu a waya d'aya bayan d'aya na, da baza musan ya d'aura aure ba ma wannan mutumin. Muhammad yace, "aikuwa fa". Tare suka jero kowa da abinda yake fad'a a cikin su, ko yanzu kafun ya futa saida ya k'ara duba d'akin Ayman ya ganshi wayam. Jikin shi a mugun sanyaye yaci gaba da jan k'afa har zuwa harabar gidan. Da motar shi da wadda Muhammad yazo a ciki sukayi amfani wajen tafiya gurin d'aurin aure. ★★★★A dai dai wannan lokaci raihana tana zaune sanye da doguwar rigar shadda fara, da akayi mata aiki da golden zare da stones, ta yafa wadataccen gyale da takalminta da jaka match da kayanta. Fuskarta ba hayaniya light make up ne shima da kyar ta yarda akayi mata shi, tana zaune a sitting room k'awayenta kewaye da ita suna ta zolayarta, kamar yadda yake dabi'ar da yawa daga y'an matan amarya, yayinda ita take zaune kamar an dasata, gaba d'aya ruhinta da zuciyarta basa tare dasu a dai wannan lokacin. A can cikin gida kuwa ummie na hango da kafatanin yaranta har al'ameen sunyi ankon shadda butter milk, a cikin su Salma ce kawai tayi kwalliya sai k'anwar ummie k'aramar su, sun gama aikin gidan tuni, abinci kuwa dama aikin shi ta bayar, an gama tunda jimawa an kammale shi cikin coolers, gidan cike yake dam da mutane, sai shiga ake ana futa. Abinda y'an uwan Abba suka jima basuyi ba wato shigo mata a lokacin da ake wata sabga, shi sukayi yau, don kuwa zugarsu guda har da innah da sauran jama'ar gidanta suka zo, so suke suga kwal uwar daka, da suka tara jama'a haka,,, dawa zasu d'aurawa yarinyar aure, bayan ance wancen ya fasa. Wata yayar ummie ce taga shigowarsu, ta taho da hanzarinta tana yi musu sannu da zuwa, ko amsawa innah batayi ba tace, "Ina ita ruqayyahn take? Ko kuwa ita ta turo ki ki tarye ni saboda gata isashshiya ban kai matsayin da zata zo ta bani masauki ba.....". "Haba Innah akwai mutane fa y'an biki kada ki tada hatsaniya a gidan nan don Allah...." ziyada ce me yi mata wannan maganar k'asa k'asa. Aikuwa ta daka mata tsawa, "rufe mun baki ni.... Lusara da bata san ciwon uwarta ba...". Dole taja bakinta ta tsuke, aikuwa taci gaba da hargagi da kwala kiran ruqayyah! Ruqayyah!! Da gudu gudu sauri sauri ummie ta katse abinda takeyi ta taho gurinta. "Sannu da zuwa innah", ta fad'a da ladabi, da kanta ta shiga parlour ta tashi na gurin tayi musu iso zuwa ciki. Tana bambami tana komai ta shiga ta zauna, su umma salaha ma aka shiga ita da y'arta ana ta rarraba idanu. Cooler guda da lemuka ummie tasa aka kawo musu duk don ta toshe mata baki kada tayi mata irin tijarar data saba cikin mutane. "Ita magajiyar bak'in halinki ba zata zo ta gaishe niba?". Innah ta tambaya, a lokacin ummie har ta kai k'ofa zata futa. Ummie ta gane wadda take nufi, don haka tace, "Bari naje na turo miki ita". Ta futa jiki na b'ari. Tab'e baki innah tayi, ziyada kuma tabi bayan ruqayyah da kallo cike da tausayinta. Raihana tana zaune ummie ta shigo da sallama, duk y'an matan suka amsa mata har suna yi mata sannu da aiki, saboda tun cikin dare data farka bata sake kwanciya bacci ba, "ku raka ta taje ta gaishe da innah". Abinda ta fad'a kenan ta futa. Akaci sa'a Salma tana gurin, aikuwa ummie na futa salma tace su bari tana zuwa, Nemo inda hajiya innah take tayi, taje suka gaisa ta fad'a mata raihana tana da ciwo a k'afarta da kyar take iya taka k'afar, shiyasa ba zata samu zuwa gaisuwar ba,,,,,, salati Inna ta saki hadda tafa hannuwa, "wato ke kece marar kunyar da ruqayyah ta turo tayi mun diban albarka....." Sai ta mik'e tsaye, "Ina ita raihanatun take?". Salma bako d'arrrrr tace, "Tana sitting room". Aikuwa ta d'auki k'afafu bushur bushur tayi gaba wasu ciki na take mata baya. A dai dai k'ofar shiga sitting room d'in ta tsaya turus ganin ana shigo da akwatuna daga k'ofar waje, "wannan kuma daga Ina?" Ta fad'a tana kallon matasan yaran, "cewa akayi mu shigo dasu nan". Suka bata amsa. "Ku biyo ni" ta fad'a tana juyawa inda ta futo, "dama mune bamu ga lefen ba, saboda tana bak'in cikin kada ta bamu zannuwan mu da aka saka da sunan mu". Aiko aka dinga jibge akwatuna a parlour, ita dai umma salaha sai binsu da kallon mamaki take, don sam wad'annan akwatuna basuyi kama da wanda tazo ta gani ba kwanaki, ga k'arin mamakinta, suna kirge saida aka shigo da akwatu goma sha hud'u ciff. Sai kuma aka shiga kallon kallo tsakanin Inna da y'an majalisarta. A can k'ofar gida kuwa jama'a ne mak'il y'an d'aurin aure, duk da auren a masallacin anguwar za'a d'aura, amma anan k'ofar gidan alhaji salees za'a had'u, Koda suka Isa masallaci Abba abubakar shiya bada auren raihana ga malam da wani abokin shi, su kuma suka damk'a sadakinta a hannun Abba Abubakar da tunda yazo yake ta mamakin sauye sauyen da aka samu, amma bai kai ga tambaya ba saboda komai yana buk'atar nutsuwa. A wannan rana ta juma'ah d'aruruwan mutane suka shaida d'aurin auren Raihanatu salees Abdallah da angonta Abdallah Suraj Abdallah tofa akan sadaki naira dubu d'ari biyu da mukullin mota lakadan ba ajalan ba. Nan fa guri ya sake hargitsewa baka jin komai sai hayaniyar mutane, a hankali khaleefa yaga mutane sun fara rabe mishi gida bibiyu zuwa uku uku, sai ya taka a nutse cikin takunshi na nutsuwa da nuna cikakkiyar kamala ya dafa kafad'ar Ahmad saboda wata hajijiya da yaji anayi dashi, a take kanshi ya fara juya mishi, sai Ahmad ya janye shi gefe yana tambayar shi abinda yake faruwa. Bai iya furta mishi komai ba idanun shi sukayi luuuuh!..... A lokacin malam yana can yana gaisawa da jama'ah, akazo aka sanar dashi ga ango can ya yanke jiki ya fad'i k'asa baya numfashi....... "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...." Malam ya furta yana dafe kanshi da hannuwan shi bibbiyu. A ranshi yace, "Allah yasa ba abinda ya gani a mafarkin shi bane yau yake shirin tabbata a zahiri......" *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty six3️⃣6️⃣ Duk hankalin mutane ya fara kaiwa inda khaleefa yake rungume jikin Ahmad ba numfashi, yayinda Ahmad d'in yake ta faman kiran sunan shi da tunanin abinda ya faru dashi bayan lafiyar Allah suka futo daga gida har zuwa yanzu da aka d'aura auren nan yanayin shi sam bai nuna bashi da lafiya ba. Malam ma yazo gurin yana tambayar su meya faru dashi? Hankali tashe, ba wanda ya iya amsa mishi sai wata murya daga ta bayansu da tace, "meya faru da d'an uwana?..... ". Wannan murya ita ta ankarar dasu malam waye rik'e a hannun Ahmad, sai duk sukayi sak, Ahmad ya fara kallon kayan jikin shi da sam ba irin sune a jikin Khaleefa a lokacin da zasu futo ba, a nutse ya k'araso cikin matuk'ar tashin hankali ya janye d'an uwan nashi yana faman ambaton sunan shi da k'arfi, "Ayman! Ayman!! Ka tashi kada ka tafi ka barni Ayman,,,, bani da kowa bani da komai a wannan duniyar sai kai......". Ya k'arasa fad'a had'e da rintse idanun shi, yana jin yadda abu mai zafi da k'una yake d'iga cikin zuciyarshi. Da kyar su Ahmad suka saka Ayman a mota akayi asibiti dashi. Don khaleefa ya rik'e shi tsam ya hana a tab'a shima. ***** A gidan su amarya raihana kuwa, innah tana shirin bud'e akwatunan lefe wata y'ar dattijuwa ta shigo gidan tana tsanyara gud'a kafun muryarta ta cika gidan gaba d'aya, "alhamdulillah! Yau dai alk'awarin Allah ya cika, Raihanatu ta zama matar aure, matar Abdallah khaleefa kan sadaki naira dubu d'ari biyu da mukullin mota sabuwa dal! Lakadan gasu a hannuna...". Wannan magana ta katse hanzari da kuzarin su innah daga abinda suke shirin yi, umma salaha kuwa cikin wani irin mugun tashin hankali da d'imuwa ta futo tsakar gida tana maganar da batasan ma tanayi ba, tsabagen yadda zancen yayi mata dirar mikiya. "wallahi k'arya ne! K'arya akeyi wallahi!! Mu za'a rainawa hankali ace wai an d'aura mata aure da wani Abdallah, waye shi Abdallahn ma..... Wallahi k'arya ake alk'awarina bazai tab'a tashi a banza ba,,,, kamar yadda na fad'a raihana bata da miji indai ina numfashi a wannan duniyar.....". Gaba d'aya mutanen gidan zuba mata ido sukayi suna kallonta cike da al'ajabi, shin wannan matar haukacewa tayi ne ko kuwa? Ganin irin kallon da ummie da y'an uwanta suke binta dashi sai ta zura takalmanta bako waiwaye ta fuce daga gidan, zuciyarta taf da bak'in ciki da tashin hankalin yadda akayi raihana ta samu irin wannan mijin ta aura, bayan duk abinda ta dinga yi. Y'arta ma jakarta ta d'auka da gyale ta saka takalmi cike da kunyar abinda uwarta ta aikata tabi bayanta. Innah ce ta fara nad'e tabarmar kunya da hauka, gudun kada aga y'ar gaban goshinta tayi kuskure, duk da itama a ranta saida taji wani iri, amma sai bata nuna ba ko a fuska, "toh meye kuma gayyar na ayyeh aka zuba mana ido ana kallon mu,,,,, Ni bana son tsegumi da tsugudidin banza, kinga ziyada bani jakata ma kiga nabar musu gidan su, don in mukaci gaba da zama muma bamu san me za'ayi mana ba". Ba wanda ya kula ta cikin mutanen da suke gurin, saima ci gaba da harkokin su da sukayi suna juya zantukan umma salahar a cikin ransu, yau har y'an tawagar tata masu zugata babu wanda yace mata ci kanki, don yau jikinsu ba k'aramin sanyi yayi ba, don ba don tayi da gaske ba, sai dai ta tafi ta barsu anan babu wanda zai biyota cikin su. Ziyada kam cewa tayi indai ta futa to fa ba dai gidan umma salaha ba sai dai nata gidan, don ita ba zata bi bayanta ba ace duk tare suka dinga k'ulle k'ullen yadda aka hana yarinya aure. Haka dai Inna ta ciccirgud'a ta fuce daga gidan, su kuma suka mara mata baya. Ummie tasa aka bisu da kayan abincin su cooler guda can. Sai dai ba Inna kad'ai ba kowa a gidan bakinshi d'auke yake da alamun tambaya, so suke suji dama tasan da maganar sauyin ango da aka samu, ko kuwa abun ya wanzu a iya yau ne. Duk da ummie kanta ta fahimci yadda kansu yake a kulle amma batayi yink'urin yi musu bayanin komai ba saboda mutane, tafi son sai komai ya lafa, amarya ta tafi tukun ta warware musu zare da abawa. A sitting room raihana tana zaune taji shelar da matar nan tayi, duk jikinta ya sake yin sanyi ba abinda yake tsattsafo mata sai gumi tako wacce kafar gashi dake jikinta, yanzu fa shikenan ta zama matar khaleefa..... Matar yarjejeniya da zata tafi nan da adadin wasu shekaru ta dawo gida da sunan aurenta ya mutu... Anya kuwa ta yiwa kanta adalci data aikata haka ga iyayenta da y'an uwanta da suke murnar ta samu miji zata tafi ta rayu kamar kowacce mace?, toh amma yata iya ya zamo mata dole ne ba yadda zatayi, auren khaleefa shine kad'ai hanyar tsiranta..... Khausar ce ta shigo d'akin kamar an wurgo ta, ta zauna kusa da raihana tana tambayarta, "kinsan kuwa da wanda aka d'aura miki aure auntie raihana?". Ameena da zee har suna had'a baki wajen fad'in, "Ni kaina abinda nake son tambayarta kenan". Sai ta d'ago kanta wasu zafafan hawaye suka soma silmiyowa kan kuncinta suna sauka k'asa, ta kalle su d'aya bayan d'aya da raunatacciyar muryarta tace, "na sani". Basu sake ce mata komai ba, sai tausayinta da sukaji ya tsirga musu, har khausar data tsura mata ido tana kallonta kuwa. A haka Salma ta shigo itama donta sanar da ita abinda ya faru wajen d'aurin aure, amma yanayin data gani kad'ai a tare da raihanan ya tabbatar mata da tasan komai. Sai ta nemi guri d'aya itama ta zauna ta zabga uban tagumi, a ranta tana jin haushin yadda su ummie zasu yiwa yayar tasu auren dole irin wannan, don kawai anga tana samun matsala ta wajen aurenta, ana saka rana ana warwarewa, sai a aura mata kowanne irin miji ma, haba shiyasa tunda tazo taga yanayin raihanan a hargitse, kuma daga ita har ummie suka k'i fad'a mata gaskiya, da anyi magana suce bata jin dad'i ne. (Su duk a zaton su salma auren dole aka yiwa raihana). Babbar Yar su ummie auntie Aysha da kanta ta kawo musu abinci da lemuka, ta kama hannun raihana ta futo da ita daga cikin su saboda sai kuka take. Su kuma duk sun zuba mata ido ba mai iya ko rarrashin ta, madadin haka ma sai wasu cikin su suka soma tayata kukan. A d'akin ummie aka ajiyeta, auntie hajara ta had'a mata tea mai zafi me kauri don an fad'a mata ko karya kumallo batayi ba, da kyar ta shanye shayin, bata kyale taba saida taci abinci rabin k'aramin plate. Jin jikinta da zafi, saita bata paracetamol tasha ta d'an kwanta ta huta. Aikuwa tana kwanciya bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, baccin daya d'auke ta har kusan five hours kafun ta farka, ya hanata sanin abinda ake ciki a gidan dama anguwar gaba d'aya. Lokacin data farka fuskarta ta wanke ta rama sallolin da suka huceta a ranar. Tana idar da sallar auntie hajara na shigowa, "yauwa dama zuwa nayi naga ko kin tashi, ummie sai fad'a take wai a tashe ki kiyi sallah wanne irin bacci ne haka". Murmushi tayi ta nad'e sallayar da take kai ta ajiyeta a gefe. Ruwa ta had'a mata na zafi a bathroom d'in ummie ta shiga wanka, koda ta futo wata atamfa mai kyau da tsada ta bata ta sauya, d'inkin doguwar riga dai dai jikinta daya zauna mata dass! Da mayafi wadatacce da takalmi da jaka duk y'an gida d'aya. Tayi kyau matuk'a gaya duk daba tarin kwalliya tayi a fuskarta ba. Lokacin data futo tsakar gidan cike da y'an biki, ta durk'usa tana gaisawa dasu rukuni rukuni, kowanne a cikin su sai Allah ya sanya alkhairy yake mata da addu'ar fatan alkhairy. Su xee suna zaune inda ta barsu d'azu, duk sunyi kwalliya cikin ankon atamfa sai shafta ake sha, musamman da suka had'u da raheela. "Woww! Masha Allah! Amma fa kinyi kyau raihana, kin futo a amaryarki zam". Fatima ce me yin wannan maganar. D'an harararta raihana tayi tace, "nifa bana son sharri". Aikuwa suka kyakyale mata da dariya kusan su duka, raheela har tana kwaikwayon salon yadda tayi maganar, sake had'e fuska tayi ita ala dole tayi fushi. Suka k'ara samun nayi, har raheela na fad'a mata wai ba sune angon ba irin wannan shagwob'a haka.... Ganin suna neman tuburata sai tayi banza dasu, sai da suka gama zolayarta son ran su sannan suka fara d'aukan pic da ita. Daga nan sukaci gaba da hirar su har zuwa lokacin da Abba ya buk'aci ganinta. Yana zaune kan kujera, ta durk'usa kusa da k'afar shi kanta a k'asa tace, "Abba sannu da hutawa". Da kulawa yace, "yauwa sannu raihanatu, ya hidima ya taro, koda yake ance mun ma d'azu bakya jin dad'i....". "Eh amma yanzu jikin da sauk'i". Yace "Toh Allah ya k'ara sauk'i". Tace, "ameen". Abba yayi shiru kafun yaci gaba da maganar shi, "toh raihana kinga dai yadda rayuwar y'a mace take, gaki yau kema zaki tafi gidan auren ki, nan da k'ank'anin lokaci ki zama matar gida ki haifi y'ay'an ki da zaki tarbiyyantar, babban abinda zan miki misali dashi shine rayuwar mahaifiyarki, halayenta, dama yadda take take mu'amulantar mutane, ko halayenta kad'ai nace kiyi koyi dasu a gidan aurenki zaki zauna lafiya da uwar mijin ki da mijin ki,,, da muke yiwa kyakkyawan zaton basu da wata matsala, abu na gaba hak'uri, don hak'uri shine babban makamin da zaki rik'a ki yak'i kowa masoyi da mik'iyi, misali na biyu hallau dai da mahaifiyar ki zan k'ara yi miki, nasan kina sane da yadda zamantakewarta ta kasance da mahaifiyata da wasu cikin y'an uwana, basa sonta basa k'aunarta har matar yayana abubakar, amma hakan bai tab'a hanata kyautata musu ba iya iyawarta, tasa k'afa ta shure duk wani sharri ko k'ulli da zasuyi mata, a wasu lokutan har sai inji haushin su ita bata jiba, kuma ko nace bazan yi musu abu ba in suka k'ure ni sai tasan yadda tayi ta sani nayi musu ko bana so, ba tare data duba komai da sukeyi mata ba na rashin kyautatawa. Alhamdulillah da Allah yaso saka mata saita rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin da babu wanda ya samu irin shi cikin su sai ziyada, itama saboda tana rayuwarta lafiyar Allah ne". Ajiyar zuciya ya sauke me tsayi kafun yaci gaba da maganar shi, "kamar yadda na fad'a rayuwa da kika ganta gaba d'ayan ta y'ar hak'uri ce, yi nayi, bari na bari, kiyi k'ok'arin rik'o da addinin ki da irin tarbiyyar da muka baki, a k'arshe Ina yi miki fatan zama lafiya a gidan auren ki, Allah yasa ki shiga a sa'a, yasa mutuwace zata raba ku.... Tashi kije Allah yayi miki albarka ya bada zuri'a dayyiba". Tunda ya fara yi mata magana jikinta yayi lakwas, banda kuka ba abinda takeyi har ya dire, duk daya sallameta amma saita kasa tashi saboda sanyi da duk gabban jikinta sukayi. Shi kanshi Abba a yau ji yake kamar yayi mata kuka saboda matuk'ar tausayinta da yake ji a cikin ranshi. Shiyasa bai iya ce mata komai ba har ummie ta turo k'ofar d'akin ta shigo, da sauri ta tafi ta rungume ummien tana kuka, ita kanta ummie idonta hawaye ya tara fal, sannu a hankali hawayen ya soma gangarowa bisa kuncinta, sai tasa tafin hannunta ta share hawayen da sauri ta janye ta jikinta a sanyaye, Abba da yake kallonsu ta kalla tace, "sunzo d'aukar amarya, ance kuma surayyahn har yanzu tana asibiti kan marar lafiyar nan, in dasun hak'ura ai da sun bari a kaita daga baya....". Da sauri Abba yace, "kull! Kar ki k'ara ma irin wannan maganar, abokin angon ya tabbatar mun ta dawo gida, angon da malam suna tare dasu, saboda haka insha Allah raihana yau a gidanta zata kwana....". Ummie bata sake cewa komai ba ta kamo hannun raihana har zuwa ga ummaanta da wadda tazo tafiya da amarya, (wata aminiyar auntie doctor seera sai iya). "Allah ya kare ki daga dukkan sharri raihana.... Ya baki zaman lafiya a gidan auren ki... Fatan alkhairy". Iya abinda ummie ta fad'a mata kenan sukayi gaba da ita, tana kuka tana komai amma ba'a kyaleta ba har zuwa cikin motar da za'a d'auki amarya. _Wasu awanni da suka gabata can baya_👈🏻 Auntie tana zaune gidan iya suna tattauna yadda zasuyi taron su gaba d'aya ita da mutanen data gayyata da wanda iya ma ta gayyata a nan gidan iyan, tayi kwalliyarta yauma cikin shadda milk da aka shiryawa lafiyayyen aiki mai kyau da tsari, hallau doguwar riga akayi mata amma ta tsaya cak a jikinta, sauk'ak'k'en d'auri tayi wanda ya bayyana lallausan gashinta ta k'asan dankwalinta, gaba d'aya hankalinta yana kan iya da take bata labarin zuwan Ayman gidan, da yadda ya kwana ya yini baya iya cin abinci sai ruwan tea ko kunu inta takura, gaba d'aya yanayin shi ya nuna bashi da lafiya kuma yana jin jiki, shiru auntie tayi cike da tunanin abinda yake damun shi haka, tunanin daba tun yau ta fara shiba, ita a tak'aice ma jiya bata ankara da bai kwana a gidan ba, duk da da safe tayi mamaki da taga har rana baizo gaisheta ba kamar yadda ya saba. Koda zasu futo dasu doctor seera a motar seeran tare da akwatunan lefe dasu malam zasu kai ta d'auka yana tare da tawagar angwaye. Ashe shi ya baro musu gidan ma tuni. Tana cikin wad'annan y'an tunane tunanen mama haleema ta shigo, itama sanye da kaya masu kyau, kusa da iya ta durk'usa ta sanar dasu ga wani can ya yanke jiki ya fad'i wajen d'aurin aure ana zaton ma ko khaleefa ne. "Hasbunallahu wani'imal wakeel, Allahumma ajirni fil musibati waklifni khairan minha.....". Ta fad'a bayan ta dafe goshinta da hannunta. Sai kuma ta yink'ura ta mik'e kamar wadda aka zabura, ta yafa gyalenta a gefen kafad'ar ta da jakarta tace wa iya "ya kamata naje....". Yadda iya taga duk ta rud'e har jikinta yana rawa, sai ta fara yi mata naseeha kan ta nutsu insha Allah ba wani abun tashin hankali bane. Gyad'awa iya kai kurum tayi ta tambayi mama haleema, "yaushe kika ji labarin". Mama haleema tace, "Ni yanzu dana futa ne naji wasu maza suna tattaunawa, amma ance tun d'azu nema abun ya faru bayan an d'aura auree, malam da wasu cikin abokan shima duk suna can asibitin da aka kaishi....". Bata ce komai ba sai hucewa da tayi gurin su doctor seera, ta karb'i mukullin motarta ta kira malam don taji wane asibitin ne, sai dai harta katse bai d'aga ba, hakan ya sake tashin hankalinta matuk'a har idanunta suka fara sauya launi, ta k'ara kiran layin nashi nan ma shiru, ganin ba zata samu malam ba saita nemo no Ahmad, shima har yayi ring ya gama bai d'aga ba. Sai tunaninta ya fara bata ko ya mutu nema suke b'oye mata, hakan tasa ta kira layin shi khaleefan. A lokacin yana jingine jikin bango ya had'a kanshi da bangon Emergencyn hankalin shi a matuk'ar tashe saboda tunda suka shiga dashi ciki ba wani cikakken bayani, Saida kiran ya kusa katsewa ya d'aga, "a wane asibitin kuke?" Shine tambayar data yi mishi kai tsaye, ya fad'a mata sunan asibitin da b'arin da suke. Ba tare da b'ata lokaci ba ta shiga motar doctor seera ta nufi asibitin a 360. Ko bayan futar ta fad'a sosai iya ta yiwa mama haleema kan maganar da tazo ta fad'a mata, yanzu gashi bata nutsuwarta amma a haka ta tafi har zatayi driving ma, Saida iya ta gama fad'an ta tsab sannan ta bata hak'uri tare da kawo mata uzurin ita a matsayin jita jita taji labarin bata da tabbaci a kai, sannan ai koba komai ya kamata ta sani ko akwai abinda zata iya tunda itama likita ce da tasan aikinta. Gaba d'aya y'an biki sai suka koma jingun jingun a lokacin data fasu kowa yaji abinda ake ciki. Doctor surayyah kam haka taje ta had'u dasu malam suka dinga safa da marwa, duk likitan daya futo su bi bayan shi suna tambayar shi halin da ake ciki. Sai dai Kash babu wata gamsashshiyar amsa bare makama d'aya da zata nuna abinda ya faru dashi. Ko kafun wani lokaci mutane sun cika emergency kamar ana wani kwarya kwaryan biki. Duk cikin su malam da khaleefa, Auntie da Ahmad babu wanda bai rikice ya rud'e da wannan hali da ake ciki ba, sunci gaba da tsaiwa har zuwa lokacin da aka futo dashi kwance kamar baya numfashi aka nufi wani d'aki dashi na daban. Aikuwa khaleefa da auntie suka bi bayan likitan zasu shiga su ganshi ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannu, "we are sorry please! But we cannot allow any of you to see him right now, maybe after some hour's in munga yanayin jikin nashi ya daidaita.....". Duk sai suka tsaya turus suna kallon shi, "calm down your self jikin shi da sauk'i amma yana buk'atar hutu, saboda stress ne ya had'u da deffresion ya kayar dashi k'asa har ya suma. Sai a lokacin suka sauke y'ar b'oyayyar ajiyar zuciya, "thank God da Allah yasa yana raye har yanzu". Auntie ta fad'a cikin ranta. Gaba d'aya sun manta da wani abu da akeyi na daga harkar biki, abu d'aya dai data tuna mama haleema ta kirata a waya ta fad'a mata inda ta ajiye mukullan b'angaren amarya saboda za'a kai kayanta, kasancewar an k'ara sabunta fentin gurin Mukullin suna kusa batayi nesa dasu ba, Sunci gada da tsayuwa har zuwa lokacin da auntie ta fahimci yamma ta fara yi, malam ya sallamu abokan ango saboda zasu je taho da amarya, Sannan gurin sam ba gurin zama bane, ga mutane y'an dubiya suna ta zuwa, sun sa likitoci sai fad'a sukeyi musu. Auntien ma bayani yayi mata saboda in aka kawo amarya su waye zasu taryeta, dole ita d'in ce dai da iya zasu karb'e ta. Da haka dai aka lallab'ata ta tafi ya rage daga malam sai khaleefa dako me za'ayi bazai tab'a barin asibitin ba. ***** Ahmad ne ya d'auko amarya da iya da doctor seera da take ta faman waya da surayyah lokaci bayan lokaci don taji ko zasu isa gidan a dai dai. Sai yayar ummie Auntie Aysha. Ragowar motocin kuwa duk k'awayen amarya aka d'auko da y'an uwan su. Doctor surayyah na zaune kan d'aya daga kujerun parlonta, gefenta su mama haleema da sauran mutanen biki ne y'an tsirari da basu gama tafiya ba, kallo d'aya zakasan bata cikin cikakkiyar nutsuwarta da hayyacinta, hannunta tallabe da habarta zuciyarta nacan tare da habeebqalbeenta Ayman,,,,, "Allah ya baka lafiya,,,, ya tashi k'afad'un ka Ayman d'ina". Abinda take nanatawa kenan a cikin zuciyarta tunda ta zauna. Duk cikin gurin jigum jigum sukayi kowa zuciyarshi cike da tausayinta. A dai dai lokacin da aka shigo da raihana iya na rangad'a gud'a kamar ta fasa bangon gidan, raihana sake k'ank'ame jikinta tayi guri d'aya tare da sake fashewa da wani irin wahalallen kuka marar sauti. Duk da auntie bata cikin yanayin farin ciki amma saida ta fad'ad'a fuskarta da fara'a, da kanta ta isa gare su ta rik'e hannun raihana ta kawo ta har kan kujerar da take kai ta zaunar da ita kusa da ita, su auntie hajara da sauran y'an kawo amarya manya da suka tako musu baya duk guri suka samu suka zauna ana gaggaisawa, har suna tambayarta me jiki, ko a yanzu saida raihana taji kamar ta tambaye su waye ba lafiya amma bata da wannan yancin da zarrar. Basu b'ata lokaci ba suka mik'a amanar raihana a hannun auntie da iya..... *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics,toh maza garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty seven3️⃣7️⃣ Daga nan sukayi da amarya b'angarenta dake a k'asa, da k'afar dama su auntie hajara suka sata ta fara shiga, da Bismillah d'auke a bakinta, kanta rufe da lullub'i haka aka ratsa parlon gidan inda su zee ke zaune aka shiga da ita har d'akin baccinta, a gefen gado auntie hajara ta zaunar da ita. Suka kewayeta suna mata naseeha mai kashe jiki game da rayuwar aure, har a lokacin raihana kuka kawai takeyi duk jikinta a sanyaye. Suna futa ta kwanta tare da rufe k'afarta da bargo ruff! Saboda kanta da yake wani irin sara mata, so take taji waye ba lafiya a gidan sai dai bata da mai bata amsa ba tare data tambaya ba, ita kuma batasan wa zata tambaya ba. A haka y'an matan suka shigo d'akin duk suka haye kan gadon suna kuzuzuta mata kyan da gidanta yayi. Da farko banza tayi dasu, amma duk da haka basu rabu da ita ba saida suka sa ta mik'e zaune ta zauna sosai tana kallon su, kusan kafatanin y'an matan k'awayenta ne suka yo mata rakiya, har dasu Fatima da raheela, Salma ma tazo amma bata ga khausar ba, hakan yasa ta tambayi zainab, "Ina khausar?". "Bata samu damar zuwa ba mijinta yazo sun tafi tun yamma, amma yace zai kawota da kanshi in an kwana biyu....". Zuciya bata da k'ashi, kuma tsakanin d'an uwa da d'an uwa akace sai Allah, sai Raihana ta ji ba dad'i da bai barta tazo mata rakiya ba. Kamar Salma tasan abinda take tunani kenan a ranta, sai ta k'arasa kusa da ita ta zauna, "khausar fa ummie ce ta azalzala mata ta tafi ba don taso ba, saboda kamar bata jin dad'i don a kwance ta yini ma yau, kinsan jinin ku iri d'aya ne bakwa son shiga hayaniyar mutane". Murmushi raihana tayi ba tare da tace komai ba amma a cikin ranta taji sanyi tunda ai rashin lafiya bai huce kan kowa ba, sannan dad'in dad'awa tasan halin khausar tun ba yanzu ba, sun d'anyi shiru kafun ta tambayi su raheela, "Amma dai ba yau zaku tafi ba ko?". "Eh sai gobe da sassafe insha Allah". Fatima ta riga raheela bata amsa. "Shikenan ma sai ku kwana anan kafun goben ku huce...." Duk kwalalo ido sukayi suna kallonta, ameena ta kalli xee suka had'a ido kafun su kwashe mata da dariya. Had'e rai raihana tayi tace, "kufa ba mutumci kuka cika ba meye abun dariyar kuma....". Fatima tace, "a'a rufa mu ki sayamu raihana, da inba hakabba ina mu Ina kwanan gidan amarya?". Zee tace, "aikuwa dai kam". Sai suka sake fashewa da wata dariyar. Salma data gama goya samha a bayanta tace, "Ni kam Ina nan har sai kun gaji dani kun kore ni da kanku keda angon, zan kira Abban samha shima ya taho". Wata cikin cousin d'insu tace, "zaki aikata, don daga ke har mijin ki irin ku d'aya, sai ki kira shi maza ya had'o muku kayan ku....". Aikuwa suka sake saka dariya. Cikin had'e fuska Salma tace, "haba auntie hapsert haka ma zaki ce salon kisa su auntie zee su samu abin yi...". "Aikuwa dai don gasu nan kashe da kunnuwa....". Wata ta fad'a cikin su. Mik'ewa tsaye zainab tayi tace, "toh ni kuma Salma Allah na tuba astagfirullah meye naki ban sani ba?...aike d'innan rufe k'ofa ce, har yanzu in kikayi abu kamar y'ar bayan ki". Duka cikin d'akin ba wanda baiyi dariya ba har raihana data ja gele ta rufe rabin fuskarta gudun kada ta aikata laifi, musamman da suka ga abinda Salma takeyi da fuska, exactly kamar samha yadda zee d'in ta fad'a dai. Salma tace, "ai shikenan ba wani abu, habeebty mu tafi ko tunda korar mu sukeyi...". Ta fad'awa samha dake bayanta. "Kunji ba da samha take shawara fa wai!". Zee ta k'ara fad'a tana nunata. Suka sake yin wata dariyar, ita kam salma Jakarta ta d'auka ta fuce zuwa parlour gurin su auntie hapsert k'arama. Itama raihana tashi tayi jin an kira sallah a masallaci. Nikam na tafi lek'o muku gidan amarya😜 bedroom uku cikin k'aton parlour da aka rarrabashi kowanne guri daban, daga can gefe guda wata kusurwa k'awataccen gurin dinning ne, kalar milk, labulaye da carpet duka maroon, sai kujerun parlonta da k'aton carpet masu kyau da tsada suma milk. Three bedrooms kuwa da suke cikin d'akin, set na kayan gado ne guda biyu d'aya maroon, d'aya kuma fari sol. Duka an shimfid'a bedsheet mai tsada da kyau, d'aya d'akin kam basu saka komai a ciki ba sai carpet da curtains brown colour, kitchen kam ba'a magana, komai an k'awata shi da kayan amfani sahihai sai d'aukar ido sukeyi kamar kaga hoton kanka a jiki, gashi wadatacce duk da komai na gidan babu k'untata bare k'untatawa, dede da sitting room an shirya shi da kayan furnitures na alfarma. Ko'ina ba abinda yake tashi sai k'amshin sabunta daya had'e dana room freshener da aka fesa. Ranar haka su Fatima suka dad'e suna d'ebe mata kewa da shaftarsu har saida su Ahmad suka dawo d'aukar su zasu mayar dasu. A lokacin zee ta zage tana ta basu dariya wai ita a lallai lecture takewa amarya. Auntie Sarah d'aya daga cikin k'annen ummie na shigowa d'akin duk sukayi shiru suna kallonta kamar marassa gaskiya, itama kallon su tayi kafun ta k'arasa shiga d'akin, kusa da raihana ta zauna ta fara yi mata magana da tattausan kalami, "alhamdulillah raihana yau gaki a gidan auren ki, kai tsaye bazan ce auren dole akayi miki ba don ummienki tace mijin da kika aura zab'in kine ba wanda yayi miki dole cikin su. Toh daga yanayin uwar mijinki da mijin ki a d'an sani da tarbar da muka samu a gurinta mun fahimci mutanene masu son zaman lafiya da lumana, kuma kema nasan ba mutum bace me matsala, sai dai yau da gobe da akace bata bar komai ba, shiyasa nake rok'on ki don Allah kiyi iya yinki ki tabbar baki sauya daga yadda muka sanki ba, ki rungumi rayuwar auren ki, ki kyautata ibadar ki, don shi aure dukan shi ibada ne, a k'arshe Ina miki fatan kasancewa macen data fi kowacce mace nagarta....." Saita dawo da dubanta ga sauran y'an matan, "naseeha ta ba iya raihana na yiwa ba, nayi ne ga dukkannin ku don nan da lokaci k'alilan dukan ku zaku riski kanku a irin matsayin data hau kai yanzu....". Duk ba wanda jikin shi baiyi sanyi ba a cikin su, sai suka tsaya kurum suna sauraronta a ransu suna gasgata maganarta. "Abokan ango sun dawo inda wad'an da zasu tafi yanzu cikin ku.... Muma hucewar zamuyi saboda Ina tunanin ango bazai samu damar zuwa akan kari ba saboda shi aka baro akan hussainin shi da yake kwance a gadon asibitin......". Wani irin rass! Raihana taji a cikin zuciyarta tunda taji kalmar k'arshe data futo bakin auntie Aysha, Yaya Ayman bashi da lafiya toh me yake damun shi? Ta tambayi kanta a zuciyarta, duk jikinta a sanyaye take kallon su a lokacin da suka gama yi mata sallama suka fuce. Haka tana ji tana gani kowa ya tafi aka barta ita d'aya. Misalin k'arfe goma da rabi na daren ranar, raihana tana kwance kan lafiyayyen gadonta ta nad'e k'afafunta da bargo idonta na kallon saman d'akin, ta lula cikin duniyar tunani, abinda ya assasa har bata ji knocking k'ofarta da akeyi ba. Mama haleema kam jin tana ta tsaiwa a cikin parlon ba alamun akwai wani mutum mai numfashi, saita fara duba bedrooms d'in dake cikin parlon. A sa'a d'akin data fara shiga (don shi kad'ai ta gani a bud'e) ta samu raihanan, ta k'arewa d'akin kallo ta cikin hasken daya mamaye d'akin, daga inda take ta kwad'a uwar sallama, raihana bata iya amsawa ba sai mik'ewa zaune da tayi. Mama haleema k'arasa shiga tayi amma ba ciki da nisa ba ta tsaya daga jikin k'ofa tace, "Ina yuni amarya". Raihana kallonta tayi, ganinta babbar mace sai taji nauyin amsawa, a madadin haka sai ita ta gaisheta, "sannu Ina yini...". Mama haleema ta amsa da, "lafiya Lou, dama auntie ce tazo na kawo miki abinci, idan zaki iya kwana ke kad'ai shikenan, idan ba zaki iya ba kuma sai kije side d'inta saboda khaleefa ba zai samu dawowa akan lokaci ba", kamar jira takeyi kuwa zumbur ta mik'e ko kayan jikinta bata tsaya sauya ba ta zura hijab d'in da tayi sallah. Kallonta mama haleema tayi kamar ta kyaleta sai tace, "Amma dakin sauya kayan jikin ki zuwa na bacci ko....". Ita kanta raihana zata so hakan, don kayan sunyi mata nauyi zasu iya hanata bacci tunda ba sabawa tayi ba, wardrobe d'inta ta fara duddubawa saboda d'azu taga Aunty Sarah tana zuba wasu kaya har tana fad'a mata wanda zata sauya ne in tana da buk'atar hakan, cikin sa'a ta samu wasu riga da wando cotton milk colour masu kyau ta ciro, zata shiga bathroom mama haleema tace, "Bari na jira ki a parlour". Ta gyad'a mata kai, ko bayan ta sauya kayan tayi ta zura hijab d'inta dogo ta bi bayan ta. Saida suka kulle k'ofar futa sannan suka fara haura stairs, k'awataccen parlon Auntie tabi da kallo, ba abinda yake tashi sai k'amshin turaren ta irin na Sudanes mai kama komai na gida har bango, "nan zaki shiga". Mama haleema ta fad'a tana nuna mata k'ofar wani d'aki, ba musu ta shiga d'akin, a gyare yake ko'ina fes fes, babu yawan tarkace daga k'aramin gado sai sallaya da labulaye. A gefen gadon ta zauna, mama haleema ta kawo mata abincinta ciki. A daren ranar kasa runtsawa tayi kamar yadda ta kasa saka komai a cikinta, Babu abinda take sai juyi zuciyarta fal da tunane tunane, kowacce amarya akan kawo ta gidanta da yarda da yak'inin ta rabu da duk wasu matsaloli na yaudarar maza, bisa amanna kan cewa tazo din din din babu abinda zai rabata da mijinta sai mutuwa, sab'anin nata auren da tazo da nufin futa nan ba da jimawa ba tabi sahun matan da ake kira zawarawa, ta yaudari iyayenta da wannan mutuniyar kirkin ma'abociyar nutsuwa da kamala, matar data tsaya kan jiki kan k'arfi wajen ganin d'anta ya aureta da darajar data zarta ta sauran mata...... Shin ya auntie da ummienta zasu ji idan akace dasu yau khaleefa ya saketa?..... Bisa wace hujjar za'a rattaba sakin?. Ganin tunani zai haukatata da hankalinta saita sauko daga kan gadon ta d'aura alwala ta fara jero sallolinta na dare. Tayi addu'a sosai akan Allah ya futar da ita lafiya da auren khaleefa, ta yiwa Ayman addu'a duk da batasan abinda yake damun shi ba, haka y'an uwanta da iyayenta har ma auntie data fara zama wani sashe nata a yanzu bata manta da kowa ba cikin addu'o'in ta. *****Khaleefa kam a zaune ya kwana a d'akin da aka maida y'an biyun shi bayan numfashin shi ya dawo dai dai jikin shi ya fara karb'ar treatment d'in da ake mishi, tunda ya saka kujera ya zauna gaban gadon da Ayman yake kwance bai runtsa haka bai motsa ba yana rik'e da hannun shi yana noticing duk wani motsin shi, Ahmad ma da yake tare dashi kusan sai can nisan dare ya samu damar kwanciya. Shi kuwa khaleefa kwana yayi d'aga wayar auntie duk bayan wani lokaci sai ta kira taji yadda ake ciki. Koda aka kira sallahr asuba da kyar ya iya tashi suka yi jam'i shida Ahmad anan ciki, ji yake kamar inya futa ya barshi kafun ya dawo zai tarar ya mutu. Misalin k'arfe bakwai da y'an mintuna Ayman ya farka bakinshi d'auke da salati, da fuskar khaleefa ya fara tozali yana jero mishi sannu da tambayar ya yake jin jikin shi. Ya motsa bakin shi da kyar yace, "da sauk'i....". "Alhamdulillah" khaleefa ya fad'a a k'asan mak'oshi. Shiya taimaka mishi ya mik'e har ya shiga toilet. Koda ya futo sallayar dasu khaleefa sukayi sallah ya shimfid'a ya fuskanci alk'ibla, saida ya rama duk sallolin da suka huce shi sannan ya had'a kanshi da gwiwa yayi shiru yana wassafa wasu al'amura a cikin zuciyarshi, zuwa yanzu ya gama cire rai da raihana, don yasan ta dad'e da zama mallakin khaleefa har ta kwana d'aya a gidan shi, ba don dalilin rashin lafiya da tasa khaleefa kwana tare dashi a nan ba da zuwa yanzu yasan wani zancen ake ba wannan ba. Sai yaja k'ak'k'arfar ajiyar zuciya tare dasa k'arfi yayi facali da wannan tunanin daga cikin zuciyarshi. Khaleefa yana daga inda yake amma kusan tunani ne fal kwanyarshi, abubuwa da yawa yake tunani game da Ayman da nuriyyah y'ar mammie k'awar auntie. Yana son yiwa Ayman maganar amma har yanzu bai samu nutsuwar da zai tunkare shi da zance irin wannan ba, tunda komai da muhallin shi. Amma fa a zuciyarshi yana yabawa jarumtar shi da k'arfin halin shi ainun. Kuma tun can dama Ayman yana da dauriyar ciwo. ★★★★★ Kamar yadda raihana ta kwana ba tayi bacci ba, haka auntie ma baccinta rabi da rabi ya kasance, mintuna k'alilan sai ta kira khaleefa taji yanayin jikin Ayman har zuwa lokacin da tayi sallar asubah. Ko data idar kitchen ta shiga direct ta fara had'a sauk'ak'k'en abinci da patient zai iya ci. Tana cikin aikin mama haleema ta shigo, ganin bata da wani kuzari aikin ma da k'arfin zuciya takeyi, saita taimaka mata suke aikin tare, saida suka kammala ta had'a tea mai zafi tasha, rabonta da abinci harta manta ko ruwa ba zata iya tuna when last tasha ba. Daga nan wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga tayi rolling da gyalenta, wayarta kawai ta d'auka da Mukullin motar ta ta futo a dai dai lokacin Ahmad ya shigo. Saida ya tsaya suka gaisa har ya k'ara kwantar mata da hankali akan ciwon Ayman sannan ya huce ciki don ya watsa ruwa ya sake komawa. kan kujera auntie taci gaba da zama, yayinda Mama haleema take ta aikin gyaran parlon, "ko raihanatu ta tashi bacci kuwa?". Auntie ta tambaya Mama haleema tace, "Bari na duba miki ita....." Ta fad'a tana nufar d'akin da aka sauki raihanan jiya, bata shiga ba saida ta kwad'a sallama har biyu, a lokacin ta kwanta kenan taji sallamar mama haleema, saita mik'e zaune tana amsa mata, Koda ta shiga gaisheta raihana tayi, ta amsa tana tambayar lafiyarta. "Dama auntie ce tace nazo na duba ko kin tashi?". Tana jin abinda ta fad'a saita sauko gaba d'aya daga kan gadon, ta tambayi mama haleema ' "tana Ina?" "Tana parlour" ta amsa mata Kusan tare suka futo mama haleema a gaba ita tana bin bayanta. Auntie tana ganinta ta fad'ad'a fara'ar fuskarta. A k'asan carpet ta zauna ta fara gaishe da auntien cikin girmamawa, ta amsa tana tambayarta bak'unta. Tayi murmushi kanta a k'asa, tana son tambayar auntie meya samu Yaya Ayman akace mata yana asibiti ba lafiya amma ta kasa saboda nauyinta da take ji. Surayyah kam gyara zama tayi ta fara magana da fad'in, "kinzo kin same mu a hargitse raihana, khaleefan ma can ya kwana a asibiti tare da Ayman, amma alhamdulillah khaleefa yace mun jikin shi da sauk'i har ma ya tashi yayi sallah da safen nan". Tunda ta fara magana raihana ta zuba mata ido kurum tana kallonta gabanta yana tsananta fad'uwa, da kyar ta harhad'a kalmomin bakinta tace, "yanzu yana can asibitin shi Yaya Ayman d'in?". "Eh amma jikin da sauk'i sosai khaleefa ya fad'a mun.... Duk da nima yanzu zanje gurin shi, ga breakfast nan ki daure ki karya kumallo sai kije kiyi wanka". D'an Jim tayi ganin har Auntie ta mik'e zata tafi sai tace, "Auntie zan biki naga jikin nashi". Shiru auntie tayi kafun tace, "jikin shi da sauk'i ki kwantar da hankalin ki, anjima kad'an y'an uwanki zasu zo kada mu tafi Kuma suzo su tarar bakya nan...". Mik'ewa tsaye tayi tace, "ba damuwa koda sunzo zasu jirani....". Auntie ganin da gaske take bintan zatayi saita koma ta zauna, "tom jeki shirya amma fa ki tabbatar kinyi break...." Kai ta gyad'a mata ta nufi hanyar futa daga side d'in duka. K'asa da minti talatin tayi wanka tayi brush da sababbin kayan wankan data gani a bathroom d'inta. Ta shirya cikin wata atamfarta sabuwa d'aya daga cikin kayan da Abba ya d'inka mata sababbi da bata tab'a sakawa ba. Riga da zani ne d'inkin, saita zura k'aton hijab daya saukar mata har k'asa tasa takalmi ta futo a gurguje bayan ta rufe k'ofar parlon. Tana zaune inda ta barta tana amsa waya, bata tsaya gurinta ba ta nufi dinning inda mama haleema ta jera kayan abincin. Tea ta had'a mai zafi tasha, ta d'anci chips kad'an ta tashi. "Gaskiya ban yarda da wannan karin ba....". Auntie ta fad'a tana kallonta, murmushi tayi cikin sanyin muryarta tace, "Allah na k'oshi alhamdulillah". "Tohm na yarda muje, ita ta d'auki basket d'in suka yiwa mama haleema sallama suka futa. *******Hajiya tafeeda zaune da safiyar ranar juma'ah a katafaren parlonta tana kallon labaran safe imran ya sauko sanye da jallabiyyah fara, gaba d'aya ya rame yayi duhu kamar bashi ba, tunda abun nan ya faru har yanzu bashi da wata cikakkiyar lafiya ko nutsuwa, gaba d'aya a gidan an daina ganin walwalarshi kamar ba wannan ma'abocin faram faram da barkwancin ba. A gefen d'aya daga kujerun da suka yiwa parlon k'awanya ya zauna, idonshi na kallon wani b'angare na d'akin yace, "gani Mom ance kina son ganina...". Kallon shi tayi na wasu sakanni sannan ta tab'e baki tace, "yanzu fisabilillah Imran haka kurum zaka k'untatawa rayuwarka ka kwarzabi kanka ba gaira ba sabab da tunanin banza da wofi?, raihana ce tuni anyi zancenta an gama ta zama tarihi, ka k'addarawa ranka ma baka tab'a sanin wata mai kama da ita ba a duniya gaba d'aya..... Ga matanan tururu a gari sai wadda ka zab'a fa, wallahi in da zaka bi ta tawa da saika riga ta yin aure ma don taga tabbacin bata gabanka kuma ajinka yana nesa da nata". Tunda ta fara magana Imran bai nuna ma alamun yana sauraronta ba har ta gama, wayarshi dake rik'e a hannun shi ya bincika ya duba hoton invitation card da aka mishi sending ta wattsapp jiya ya nuna mata. Karb'a tayi tana dubawa kafun zuwa can ta tambaye shi, "abokin ka Abdallah zata aura kenan? Oho dai aiko banza Abdallah bai kai mahaifin ka kud'i da suna ba,,,,". Imran cike da takaicin halayen mahaifiyar shi a wannan karon yace, "ba Abdallah da kika sani bane,,,,, wannan yayan Ayman ne d'an doctor surayyah,,,,, finally burin ki bai cika ba don gashi raihana ta rigani aure, da mijin daya zarce tsara, miji na nunawa sa'a,,,, da haka nake rok'on ki don girman Allah ki barni inji da jinyar rashin mace ta gari ma'abociyar addini da kiyaye dokokin ubangijinta irin raihana da nayi.... Mom duk yadda zanyi miki bayanin raihana ba zaki tab'a ganewa ba, don ta huce kafatanin tunanin ki.... Sai abu na k'arshe da na manta ban fad'a miki ba, munyi magana da Abba last week zan koma can Lagos na kula da harkokin kasuwancin shi na can har zuwa wani lokaci da zan gama jinyar zuciyata, and kibar son k'ak'abamun kowacce yarinya don ban shirya aure yanzu ba.". Ya k'arasa maganar shi tare da mik'ewa ya haura stairs inda ya futo. Sakatoto hajiya tafeeda ta tsaya tana kallon shi kamar wata sakarai har ya huce. Wanene khaleefa kuma d'an Doctor surayyah da Imran yake magana akai? Ba dai surayyah data sani k'awar sameera ba? _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty eight3️⃣8️⃣ Kasa zama hajiya tafeeda tayi a lokacin sai safa da marwa kawai tsakanin farkon parlonta zuwa k'arshe, ta kira sameera kusan sau biyar amma ba tayi picking ba, so take taji tabbacin abinda Imran ya fad'a mata yanzun daga gareta don tasan dole zata sani. Tana ta tsaiwa har ta gaji ta samu guri ta zauna. Can jimawa sameera ta biyo kiran, tana d'agawa ta fara magana a hargitse, "Wai kinsan abinda naji kuwa? Tukunna ma ina kika shiga nayita neman no ki bana samu?". Hajiya tafeeda ce meyin wannan maganar a rikice. Ta b'angaren sameera ma hankalinta a tashe ta fara bata amsa, "Humm bana auren khaleefa da raihana ba? Naji yanzun nan daga bakin haeydar wai ashe har d'aurin auren yaje yanzun nan ya dawo ma, ni dama tunda ta bani catin mother's day da akayi jiya nasan akwai wata a k'asa, in ba haka ba me zai had'a surayyah da ruqayyah matar salees? lallai surayyah ta d'au zafi dani da yawa kina gani fa komai nata ta tureni gefe ita kad'ai take harkokinta.....". Tab'e baki hajiya tafeeda tayi, cikin kyashi tace, "ai wallahi naso a fara yin auren Imran da shaheeda, banso raihana ta riga shi yin aure ba, koda yake ma to meye Allah na tuba astagfirullah yaran da basu da asali.....". "Kinga dakata don Allah! Kinsan abinda yake had'a mu dake kenan tun farko tafeeda, kiyi magana akan abinda ya shafe ki kad'ai ba ruwanki da surayyah da yaranta don itama ba damuwa tayi da al'amuran kiba....". Sameera ce meyin wannan maganar cikin d'an fusata. Ita kam sake tab'e baki tayi kamar tana ganinta tace, "oho dai ku kuka sani keda ita, anjima in kina nan Ina so zan shigo don an samu matsaya a maganar da muka fara yi sake Imran yana son b'allo mun ruwa". "Anya kuwa Ina nan? Da Ina son zanje asibiti duba jikin Ayman, ance ana gama d'aura aure ya yanke jiki ya fad'i akayi hospital dashi baya numfashi....". Sameera ta bata amsa. Tafeeda tace, "Toh sai dai gobe kenan na shigo ko?".. Sameera tace, "eh toh Allah ya kaimu". Daga haka sukayi sallama kowa ta ajiye wayarta. *******A zaune take cikin k'aton d'akinta ita d'aya, tunda Mamie ta karb'e wayarta hankalinta ya kasa kwanciya, gani take kamar akwai abinda mammien take b'oye mata, banda haka ya zata sauya mata rana tsaka harda tsauraran matakan tsaro, daga makaranta sai gida komai ma ta hana ta zuwa, Ayman kuwa tace duk ranar data ari wayar wata k'awa ta kira shi Allah ya Isa bata yafe mata ba. Gaba d'aya ta maida kanta sukuku ba wani armashi bare jin dad'i. Yau kam ma tunda ta tashi taji bata jin dad'in jikinta ko makarantar bata jin zuwa saita nad'e kan katifarta abinta, duk yadda heedaya ta dinga zargadilar kiranta tazo ta karya k'in tashi tayi, a k'arshe ma data takura ta saita dinga mata maseefa don dole ta hak'ura ta barta. Har ta fara bacci mammie ta shigo da kanta d'akin, jin kamar muryar mammie saita tashi zaune tana kallonta. A shirye take da alamu futa ma zatayi, a gefen katifar ta zauna tare da zuba mata ido tana kallonta. "Anya kin d'auki hanyar da zata b'ulle miki kuwa Nooriyyah? Yanzu saboda kawai na hana duk wata hanya da zaki had'u ko kiyi magana da Ayman shine kika takura rayuwarki haka kamar shi yayi silarki zuwa duniya?". K'asa tayi da kanta murya a sanyaye tace, "ba haka bane mammie kawai yau na tashi bana jin dad'in jikina ne". Kallon d'akin tayi tace, "toh ai shikenan, yanzu ki tashi ki shirya kizo ki karya zaki rakani wata y'ar anguwa, amma fa idan zaki iya". Ba don kar tayi mata musu ba da tace kawai ta d'auki shaheeda ta rakata, don ita kam bata son futa ko nan da can. "Kinyi shiru ko bazaki bane?". Mammie ta tambayeta. Saita girgiza kai da sauri ta fara k'ok'arin mik'ewa don ta sauka daga saman katifar. Cike da tausayinta ta bita da kallo har ta shige cikin bathroom ta rufo k'ofa, Allah yasan tafi kowa son auren Nur da Ayman, sai dai kash surayyah tana shirin ruguza da lalata duk wani burget nata, taso ace ta nemo dangin tsohon mijinta anyi sulhu komai yazo k'arshe ata silar auren Ayman da nuriyyah,,,, kamar yadda taso ta zama silar gyara duk wata b'araka dake tsakanin su,, sai dai kash tun ba'aje ko'ina ba alamu sun nuna hak'arta bazai tab'a cimma ruwa ba ta hanyar data biyo, tunda gashi har mutanen gari wagairahun da basu tab'a doguwar mu'amula da ita ba sunyi mata abinda ita data had'a rabin rayuwarta tana binta da alkhairy tana wahalta mata ta kasa yi mata, tabbas mijinta ya fad'i gaskiya da yace, ko buta batayi tsiran komai ba ai tayi na ruwan alwala, ya kamata ace tayi dogon tunani kafun yanke hukunci.... Ajiyar zuciya ta sauke ta mik'e tsaye jikinta a sanyaye ta futa daga d'akin, a ranta tana fatan komai ya huce tsakaninta da surayyah a wannan karon idan ta tunkareta. Cikin mintuna k'alilan Nur ta shirya cikin doguwar rigar material milk da Ash, ya haskata sosai tayi kyau tamkar ba itace kwance yanzu hargitsai hargitsai ba. Saida ta tuttura abinci sannan suka d'auki hanya ita da mamie ko heedaya gurin shaheeda aka barta saboda a yau bata son wanzuwarta a gurin don zata damu mutane da maganarta mara amfani ne. ★★★★A parking lot surayyah ta Parker motarta ta futo, raihana ma futowa tayi ta bud'e k'ofar baya ta ciro basket d'in da aka shirya abincin karin a ciki. Murmushi Auntie tayi tana kallonta tace, "sannu da k'ok'ari". Cikin jin nauyi tayi k'asa da kanta don ita bata ga wani k'ok'ari da tayi ba, abincin daba ita ta dafa ba sai dako ya zama aiki. Tare suka shiga ward d'in, Auntie a gaba raihana tana bin bayanta. Ayman yana zaune kan gadon da aka kwantar dashi, khaleefa kuma tsaye a gefe yana sauraron bayanin da Ayman yake rattabowa likitan da yake tsaye gaban shi suka turo k'ofar suka shigo da sallama. Kusan a tare su duka ukun suka juya suna kallon su, Ayman da likita suka amsa sallamar su a fili, yayinda khaleefa ya amsa su a zuciyarshi. Ko a yanzu wani irin yanayi Ayman yaji a lokacin da idanun shi suka sauka akan raihana da take tukunta cikin nutsuwar data zama jini a jikinta. Khaleefa dama kallo d'aya yayi musu ya d'auke kanshi, a baya da inda suke ta tsaya ta fara gaishe su, a ciki likitan ne kawai ya amsawa, ganin haka sai taja bakinta ta tsuke, dama ta manta ne amma Ayman akwai tsohuwar gaba a tsakanin su dashi, gabar da har yau batasan abinda ya assasa taba, shi kuma khaleefa har yanzu bak'o ne a gurinta. Surayyah ta gaisa da likitan tana tambayarshi jikin Ayman, yace, "ah jiki da sauk'i hajiya anjima kad'an ma zaku iya tafiya dashi gida kamar yadda yake so, sai dai matsala d'aya ce koda ya koma gidan muddin bai bi sharud'd'an da zamu gindaya mishi ba toh fa za'a dawo dashi ranga_ranga fiye da yadda aka kawo shi da farko, Saboda kamar yadda nayi muku bayani rashin cin abinci ya tashi mishi ulcer, ta had'u da stress da deffresion sukayi sanadiyya har ya yanke jiki ya fad'i k'asa a sume.... Duk da alhamdulillah yanzu mun shawo kan komai amma fa dole saiya cire damuwar da take ranshi ko kuna ganin shi lafiyar Allah kamar yadda yake a baya". Shiru tayi tana nazarin maganganun likitan kafun ta nisa tace, "alright insha Allah zai kiyaye". Saiya mik'awa khaleefa takardar magungunan daya rubuta yace, "malam kai kuma kayi k'ok'arin samo mana wannan". Ya amsa tare da matsawa baya, a karo na biyu idanun shi suka sake sauka akan raihana da take tsaye still hannunta rik'e da basket. D'auke kanshi yayi ya nemu guri nesa da inda take ya zauna..... Damuwa! Damuwa!! Damuwa!!! Ya rasa wacce irin damuwa ce take bibiyar rayuwar Ayman da har take barazanar raba su dashi a wannan duniyar, gashi yace sam ba matsalar Nur da mammie bace damuwarshi a halin yanzu. Likitan ma sallama yayiwa auntie ya futa bayan ya sake gargad'inta akan a kula dashan magungunan shi a k'a'ida. Juyawa tayi tana kallon raihana tace, "a'a raihanatu kamar wata bak'uwa kike ta tsayuwa salon kisa k'afafun ki su k'age, kinga zauna a can ki zuba musu abincin don nasan khaleefa ma ko da safe jiya bai karya ba haka yake ta zaune da yunwa". Auntie ta k'arasa maganar tana zama tare da kallon khaleefa daya had'a kanshi da gwiwa. Kamar yadda auntie ta mata umarni zama tayi a nesa dasu ta fara had'a musu tea me zafi a cups, Ayman ta fara kaiwa, da sanyin muryarta tace,. "sannu Yaya Ayman ya jikin naka?", d'agowa yayi ya kalleta kamar ba zaice mata komai ba sai kuma yayi k'asa da kanshi yace, "da sauki" tace, "Allah ya k'ara sauk'i". Bai kuma amsa taba saboda ruwan hawaye da suka cika a idanun shi, shayin ma kamar wanda zai tab'a wuta haka ya karb'a a d'arare, ganinta ba k'aramin dagula mishi lissafi yake ba. Ajiyar zuciya ta sauke a b'oye ta koma da baya ta d'auki d'ayan cup d'in, khaleefa kam koda ta mik'a mishi saida ya d'auki some seconds kafun ya amsa ba tare daya kalleta ba, sai dai adanun shi da suka sauka akan yatsun hannunta da suka sha adon jan lalle. Auntie duk tana lura dasu. Abincin Kam bata yiwa kowa tayin karb'a ba ta ajiye mishi a gefen shi ta koma mazauninta. Khaleefa sam bai tab'a komai ba saida yaga Ayman ya fara shan shayin da aka bashi, sannan shima yasha nashi, abincin kam bai iya ciba duk da Yana kallon yadda Ayman yake tuttura nashi, gashi yana matuk'ar jin yunwar sai dai dole sai yayi brush sannan zaici wani abu ya zauna cikin shi lafiyar Allah, tashin zuciya bai biyo baya ba. Sunci gaba da zama shiru kowa da abinda yake tunani a cikin ranshi, kafun sallamar su sameera ta katse musu zaren tunanin su. Banda khaleefa da yake aikin latsa wayarshi amma kowa a d'akin saida ya d'aga ido ya kalleta a lokacin da take shigowa ita da Nur data zuba ma raihana ido tana kallonta da tunanin abinda ya kawota nan, koda yake ashe fa k'awar Ayman ce,,, ta tuna hakan a ranta, take b'acin rai yayi karan tsaye akan fuskarta. Saita sake d'aure fuskarta tam. Surayyah ba yabo ba fallasa ta tarye su hadda basu gurin zama, suka zauna Nur tana gaishe da auntie, sameera ma gaisawa sukayi tana tambayarta, "ya me jikin? Tun jiya fa naso zuwa Allah bai nufa ba kinga sai yau". Surayyah tace, "ayyah ai komai sai Allah ya nufa, jiki da sauk'i kam". "Toh Allah ya k'ara sauk'i yasa kaffara". Tace, "ameen". Kusan a tare Ayman da khaleefa suka gaisheta, ta amsa tana sake tambayar shi jikin shi, yace, "da sauk'i Alhamdulillah!". "Allah yasa kaffara" ta sake fad'a ya amsa mata da ameen. Sai a lokacin raihana ta gaisheta, ta amsa tana zolayarta da amarya tasha k'amshi, ita dai raihana bata ce da ita komai ba sai murmushi data wanzar a saman fuskarta. . Nur kuma ta sake binta da kallon mamaki, amarya kuma? Ba Imran zata aura ba aka fasa toh yanzu kuma me takeyi tare da auntie? Sannan amaryarwa ake nufi? Yaushe ma tayi aure basu da labari? Sannan ga Ayman har da kwanciya a gadon asibiti? Duk bata da labari, ita dai tana fatan ba Ayman ta aura ba ake b'oye mata, Kai dole wani abu yana faruwa ta wani gefen. Saita gyara zamanta ta kalli saitin da Ayman yake zaune tace, "sannu Yaya Ayman ya jikin naka?". bai d'aga ido ya kalleta ba yace, "da sauk'i" ta sake cewa "Allah ya k'ara sauk'i". Bai amsa mata ba sai plate d'in abincin shi daya ajiye gefe don abincin ya k'ara fucewa daga ranshi. Sun d'anyi jim kafun Auntie ta dubi khaleefa da duk ya takura a gurin tace, "ko zaku fara yin gaba kaida raihana kada y'an uwanta su dawo basu sameta ba, sannan Ahmad ma kace ba sai ya dawo ba tunda muma ba jimawa zamu taho gidan gaba d'aya". "An sallame ku kenan?" Sameera ta tambayeta. "Umm!" Kawai surayyah tace. Khaleefa saida yayi kamar kar ya tafi sai kuma dai ya mik'e ya lalubi mukullin motarshi, ganin raihana bata da niyyar tashi sai auntie tace da ita, "maza ki tashi ku tafi tare, nasan abinda ya hana shi cin abinci anan, dama da kunje ku huce side d'inku ki had'a mishi ruwan wanka me zafi, ki sama mishi wani abun da zaisa a cikin shi me sauk'in sarrafawa....". Cike da jin kunya raihana ta gyad'a mata kai ta mik'e a lokacin kanshi yana kusa da Ayman yana yi mishi magana k'asa k'asa da babu wanda yaji kaf cikin d'akin har ni duk bin kwakkwafina. Saida ta yiwa su mammie sallama sannan ta futa ta jira shi a wajen d'akin. Wasu maza biyu har sun gota ta sai suka dawo da baya, d'ayan yace, "wooww! Kaga wata had'ad'd'iyar beb a nan?". D'auke kanta tayi da sauri, a lokacin matasan suka k'araso suna yi mata magana, banza ta musu tana neman tsari daga shaidan abin k'i. Sun tsaya sai zuba mata zance suke yayinda tayi banza dasu kamar bada ita suke ba, ita tsoron ma bud'e bakinta take bare tace musu wani abu taje ta aikata haramci. A haka khaleefa ya futo kare da waya a kunnen shi, kallo d'aya yayi musu ya d'auke kanshi ya fara nufar hanyar futa daga Ward d'in, da sauri sauri tabi bayan shi har kamar zata ci tuntub'e ta fad'i, basu fasa bunta suna maganar suba har suka isa inda khaleefa yayi parking motar shi, "ba dai tafiya zakiyi ki barmu ba y'an mata, haba ai ko phone numberki kya tsaya ki bamu mana please...". Yadda yasha gabanta yana maganar saura k'iris taci tuntub'e ta fad'a kanshi ga k'afarta data hard'e, tayi saurin ja baya tare da satar kallon inda khaleefa yake tsaye, akayi sa'a idonshi a kansu yanzun ma don bai shiga motar ba yana jingine jikinta hannun shi a samanta yana ci gaba da wayarshi duk da fuskarshi ta nuna alamun damuwa, watak'ila ba magana mai dad'i ake fad'a mishi a wayar ba. Kewaye shi tayi da sauri ta isa inda khaleefa yake waiko zai zamo mata garkuwa su rabu da ita in suka gane tare take dashi. Isowarta yayi dai dai da gama wayarshi, hakan yasa ya bud'e front seat ya zauna, kamar ta bud'e gidan baya sai taga kada yaga ta raina mishi hankali, madadin haka saita bud'e front seat gefen shi ta zauna. Mutanen nan suna tsaye don maseefa suna kallonta har yanzu sunk'i matsawa, khaleefa har zai tashi motar sai ya k'ara ankara dasu, kamar sune ai suke bin ta tun daga ciki. Saiya fasa tashin motar yace, "Wad'annan ba zaki saurare su kiji da wadda suka zo ba?". Ya tambayeta ba tare daya kalleta ba. Wani irin rass! Raihana taji har batasan lokacin data d'aga ido ta kalleshi ba, wane irin mutum ne wannan? Da aurenta yake nufin ta dinga kula kowanne kare da doki? Ya ankara da irin kallon da takeyi mishi ta gefe, wanda suka alamta mishi na rashin fahimta ne, sai ya tattaro duka nutsuwarshi ya tsaida idanun shi a kanta a karo na biyu a tarihi daya kalleta face to face irin haka yace, "kada ki manta sharad'in auren mu har ki nemi takura kanki da tunanin igiyar aure na da bata da maraba da rehu a kanki,,,, munyi yarjejeniya duk lokacin da kika samu wani namiji daya kwanta miki a rai har kika ji zuciyarki ta aminta kan cewa zaki iya auren shi, toh zaki bashi duk wata dama don ku fahimci juna... Don haka kada ki cuci kanki, idan har sunyi miki ki basu dama don wulak'anci bashi da kyau, idan kuma basuyi miki ba ki basu hak'uri sai Allah ya had'a kowa da rabon shi.....". Shiru raihana tayi tana jujjuya maganganun khaleefa da sukayi mata nauyi a kwanyar kanta kamar zasu rinjayi gangar jikinta, sannan shi yana yin wannan maganar ne da iya gaskiyar shi, tabbas sunyi yarjejeniya kamar yadda ya fad'a amma ita ba zata iya aikata irin abinda yake nufi da igiyar auren shi a kanta ba, ta yadda dai duk ranar da suka rabu ta samu wanda nutsuwarshi da hankalin su yazo d'aya ta saurara amma fa bada igiyar auren shiba, don ba zata fara gangancin kai kanta wuta da k'afafun taba, gaba d'aya aure ba abun wasa bane bare ita ta fara yin wasa dashi irin haka. Ganin bata bashi amsa ba sai ya tab'e baki ya fara k'ok'arin tada motar a nutse, yana ganin shikam ya futa har ga Allah. Har suka d'auki hanya bata ce dashi komai ba saida suka Isa gida, a lokacin an bud'ewa Ahmad get zai futa da mota su kuma suka k'araso. Yana yin parking ta futa, shi kuma Ahmad ya k'araso yana zolayarta, "amaryah gaskiya dole muci tarar Ayman daya futar dake a washe garin ranar da aka kaiki gidan mijin ki.... Kai kuma fa laifin nashi ma shi ai da yawa, sai dai babban ciki shine rik'e miki ango da yayi ya kwana gurin shi hospital a ranar da aka kai ki gidan shi....". Murmushin yak'e tayi ta russuna ta gaishe dashi, ya amsa yana shirin sake cewa wani abu ta d'auki hanyarta da sauri don sam bata jin zata iya tsayawa magana dashi a yanayin da take ciki, tana hucewa Ahmad ya maida akalar zolayarshi kan khaleefa, "fuskar ka kad'ai dana kalla ta tabbatar mun lallai Ayman ya samu". Khaleefa yace, "alhamdulillah kam anjima kad'an zasu taho Ina ganin ma basai ka koma ba". "Anya kuwa zasu barshi a yau?". "Zasu barshi ai ya warware". Khaleefa ya fad'a mishi. Tare suka jera zuwa saman b'angaren su gaba d'aya, Ahmad yana ta zolayarshi irin yadda ya zolayi raihana, shidai bai kula shiba don ba abinda yake gaban shiba kenan. Raihana kuwa kamar yadda auntie ta mata umarni haka tayi, kai tsaye part d'in su ta shiga, tana bin komai na d'akin da kallo, sai yanzu take gasgata maganar su Fatima da suke ta kod'a gidanta da yaba kyawun shi. D'akin da aka ajiyeta jiya ta shiga ta shiga bathroom, bata jima ba ta futo ta fara duba ragowar d'akunan, d'aki na kusa da nata ta shiga, gidan fes fes ba datti ko d'aya, saboda jiya saida suka gyara ko'ina kafun su tafi, ruwan wanka masu matsakaicin d'umi ta had'a mishi ta fuce daga ciki zuwa wanda ta fara zama ta nemi gefen bed tayi kwanciyarta, ba jimawa wani bacci mai mugun dad'i ya fusge ta yayi awon gaba da ita...... *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page thirty nine3️⃣9️⃣ Shima khaleefa ta b'angaren shi bai kula Ahmad da zancen shiba ya shige bedroom d'inshi ya watsa ruwa a daddafe ya futo, ko kanshi da yake matuk'ar sara mishi bai bi ta kai ba ya samu gefen gadon shi ya kwanta sai bacci, ko abincin bai ciba, baya ji da ganin komai a wannan lokacin sai bacci. A asibiti kuwa raihana da khaleefa suna futa sameera ta fuskanci surayyah da kyau ta fara magana da duka nutsuwarta ta fuskar neman salama da lumana da k'awartata a yau, "duk da laifina mai girma ne a gare ki surayyah, nasani sam banyi miki adalci ba kamar yadda na kasa fahimtar ki, na munana miki zato akan abinda ko a mafarkina na gani zan k'aryata na tashi da gudu na wanke fuskata nace k'arya ne.... sai gashi abun kunya nice da kaina na fara bada k'ofar da wasu ma zasu mara mun baya, duk nadama da kunya sun rufe ni musamman da naga ruqayyah ta aikata abinda ni ya kamata ace na aikata shi tun farko, ruqayyah ta d'auki y'arta mai tarbiyyah da nutsuwa had'e da nagarta kwatankwacin ta yaranki ta bawa khaleefa aure, kuma ba tare da sun kallesu ta wata fuska daban ba, tabbas wannan abu yana daga abinda ya sake hanani sukuni har naji bazan iya k'asa a gwiwa ba sai nazo na nemi yafiyarki, don Allah surayyah kiyi hak'uri komai ya huce muci gaba da mu'amular mu kamar yadda muke da farko....". Tunda ta fara magana surayyah take sauraronta har ta dire, sai a lokacin ta saki wani miskilin murmushi ta kalleta tace, "Toh ni me kika yi mun ma sameera? Kin fad'i iya gaskiyar kine fa, kuma ni ko a lokacin sam banga laifin kiba Kuma banji haushin kiba shiyasa ban tab'a rik'e ki da komai ba...". Shiru ta sakeyi jikinta a sanyaye kafun ta sake cewa, "haka dai kika fad'a surayyah amma a aikace ai kin nuna haka, in badon haka ba nasan ba yadda za'ayi a tsaida maganar auren khaleefa da raihana baki fad'a mun ba, sannan muna business dake shekara da shekaru bamu tab'a maganar zamu raba hanya ba ko a wasa, sai da abun nan ya farun kika ce a raba hanya kowa ya zamana yana juya kud'in kanshi da kanshi,,,, kuma kice duk baki rik'e ni da komai ba". Wani murmushin ta sakeyi tace, "sameera kenan! Ai gani nayi lokaci yayi daya kamata kema ki rik'e jarin kanki, auren khaleefa kuma yazo ne duka a hargitse shiyasa ba wanda na fad'awa engage d'in sai goron biki dana bayar". Nur dai tana sauraron komai tana ba tambayoyin bakinta amsa. Sameera tayi kamar tayi shiru, sai dai ba zata iya ba, shirunta yana nufin komai ciki hadda rashin Ayman da Nur zatayi. "Toh yanzu ya maganar auren su Ayman d'in? Nina hak'ura zan bawa Ayman Nur ko daga iya ni sai kene....". Wannan karon wani irin kallo surayyah tayi mata carmly tace, "lallai sameera har yanzu baki gama sanin wacece surayyah ba, bana zance d'aya, kamar yadda bana yaudara a rayuwata, idan na baki tarihina kikaji abunda ya raba ni da Suraj harma nak'i neman dangin shi da nawa nake rayuwata kamar wata marar galihu sai kinyi mamaki kwarai, mamaki irin wanda watak'ila har ki gama rayuwarki ba zaki daina shiba, don haka ki ajiye maganar Nur da Ayman a gefe, a gurina ta dad'e da zama tarihi bansan ba ko shi a gurin shi tunda gashi nan yana jin mu aiba yaro bane....". Yadda sameera take kallonta da mamaki haka nuriyya ma ta zuba mata ido gabanta yana tsananta bugu. Ta kalli auntie ta kalli Ayman da kanshi yake k'asa kamar abinda ake tattaunawa bai shafe shiba. "Ya rabb me yake shirin faruwa dani ne? Auntie don Allah kada ki yanke hukunci cikin fushi irin wannan, wallahi nida Ayman muna son junan mu.... Ayman ka fad'a musu kar su raba mu don Allah". Nur tayi wannan maganar cikin tashin hankali tana rarraba idanunta tsakanin su mamie da Ayman. Babu wanda ya kulata cikin su har Ayman, hakan yasa ta sake gigicewa da shiga rud'ani, saita mik'e tsam ta isa gadon da Ayman yake zaune ta dafa k'arfen ta kira sunan shi. Da kyar ya iya amsawa ba tare daya d'ago ya kalleta ba. "Ka fad'a musu kana sona kaima don Allah kar ka bari su rabamu". Tayi maganar cikin rawar murya kamar zata fashe da kuka zuciyarta na up and down. Har yanzu kanshi yana k'asa, baya tunanin akwai wani abinda ya rage dazai iya furta mata a halin yanzun, koda yana sonta bazai tab'a iya aurenta ba, saboda yana da matuk'ar zuciya, bece zai rik'e mamie a ranshi ba amma zaiyi wahala ya manta da maganganun data fad'a mishi, ta kasance mutum ta farko data tab'a goranta mishi rashin uba tun bayan wanda akayi mishi lokacin yana yaro, sannan itace ta fahimtar dashi abinda sanin shi sam bai mishi amfani a rayuwa ba, hasalima sai maseefa da yake k'ok'arin zame mishi, in badon ya danni zuciyarshi k'arshe ba da bazai tab'a iya ci gaba da gaisawa da d'an uwanshi khaleefa ba, bare har yayi mishi cikakken kallon arzik'i, yaci gaba da kallonshi matsayin d'an uwa, raihana!!!! Khaleefa ya zamo silar rabuwarshi da raihana a lokacin da yake gab da cimma burin samunta matsayin matar auren shi. Lokacin da yazo dai dai nan a tunanin shi, zaren tunanin katsewa yayi, sai ya sake runtse ido yana ambaton sunan Allah a cikin zuciyar shi. "Kiyi hak'uri Nur, tun asali kinsanni farin cikin mahaifiyata shine gaba da kowanne farin ciki nawa,,,, sannan na amince da soyayyar kine dama saboda mahaifiyata....a yanzu kuma data nuna auren mu ba mai yiwuwa bane Ina ganin sai mu hak'ura da juna kurum". Nur tsabar tashin hankali sam batasan lokacin data d'ora hannunta aka ta rushe da ihu ba, "wayyoh Allah Ayman, don Allah kada ka juya mun baya, wallahi niko daga sama ka fad'o Ina sonka zan zauna dakai....". Ta k'arasa fad'a tana durk'ushewa a gurin. Daga auntie har mamie ba wanda baiji tausayinta ya dirar mishi a cikin zuciya ba, haka shima Ayman d'in don yasan dama dole za'a cutar da ita, bilhak'k'i take son shi da zuciya guda irin soyayyah marar algus! Tsam sameera ta mik'e a dai dai lokacin da ummie da Abba suka yi sallama a d'akin. Bata tsaya kallon suba ta kamo hannun Nur ta d'auki Jakarta, saitin inda surayyah ke zaune ta tsaya tace, "shikenan surayyah duk hukuncin da kika yanke dai dai ne a k'arshe Allah ya had'a kowa da rabon shi na alkhairy.....". Saita kalli Ayman shima tace, "Allah ya k'ara lafiya Ayman nagode.....". Daga nan ko amsoshin bakin su bata tsaya jiba ta d'auki hanyarta ta fuce daga d'akin a zafafe har kamar zata buge su ummie da suke tsaye daga wajen k'ofa. Da kallo auntie ta bita kafun ta mik'e tana yiwa su ummie maraba, ta basu guri suka zauna aka gaggaisa, sukayi mata ya me jiki. Shima Ayman har k'asa ya durk'usa ya gaishe su, sukai mishi sannu da jiki. Sun d'an zauna jimm kafun su tashi tafiya. Fruits da drinks suka ajiye, aikuwa auntie tayi ta godiya. Har wajen k'ofa ta raka su sannan ta dawo. Wannan karon gefen gadon da Ayman yake ta samu guri ta zauna ta kira sunan shi da sanyi a muryarta, "Ayman" bai amsa ba amma dai ya d'ago kai ya kalleta, bata damu ba taci gaba da cewa "kasan dai ni d'in nan mahaifiyar kace ko?" Sai ya gyad'a mata kai, "sannan kasan a duniya baka da kamarni ko". Sake gyad'a kai yayi, "kasan da haka amma kake nuna mun halin ko'in kula, baka fad'a mun matsalar ka bare wani abu daya shafi rayuwarka mai muhimmanci da zan iya taimakon ka, tun kafun kazo nan nake yi maka fad'a kan ka rage damuwar da take ranka kak'i, yanzu ga likita ma abinda yake fad'a kenan, ko kafi son na rasa kane Ayman?". Kanshi a k'asa yake sauraron kalamanta har ta gama, bai iya ce da ita komai ba. Itama tayi shiru na wasu sakanni kafun taja gwauron numfashi tace, "game da maganar daka fad'awa Nur in na fahimceka kana nufin ka hak'ura da ita kenan?". Sai yanzu ya kalleta, "Auntie Nur dama zab'in kice, yanzu kuma da kika nuna bakiyi ammana da ita ba, ni bani da wani zab'i sai bin yadda kika so". Gaba d'aya maganganun shi sun kashe mata baki, ya d'aureta da jijiyar jikinta har batasan me zata ce ba kuma, tabbas ta dad'e tana bin takun Ayman abinda ya fad'a haka yake a gurin shi, bai tab'a d'aukar Nur da wani matsayi sab'anin na zab'in mahaifiyar shiba, baya ga haka yana da mugun zuciya in yabar abu ya barshi kenan har abada, yana da sauk'in kai yayi wasa yayi dariya, gashi da bala'in hak'uri ba komai ne yake b'ata mishi rai har yayi magana ba,,,, amma fa zuciya,,,,, banbancin shi da khaleefa komai son da yake yiwa abu zai iya barshi muddin ya zamana da matsala, shi kuma khaleefa yana da naci akan abinda yake so sam baya zuciya, sannan bashi da yawan magana ko shiga shirgin mutane, saboda bashi da hak'uri, bazai iya jurar abinda Ayman zai jura ba, sai dai abinda bata gama fahimta ba har yanzu shine, shin Ayman ya shiga damuwa ne saboda gorin da sameera ta mishi ko wani abun daban ne yake damun shi? ******* A yini guda da suka k'ara a asibitin Mutane sai zuwa sukeyi y'an dubiya, likitan ya sallame su tuni amma tafiya ta gagara saboda cikowar mutane, wasu ma batasan inda suke samun labari suzo ba, su Muhammad duk sun dawo duba shi hadda abun arzik'in su. Kaya Kam a asibitin rasa inda surayyah zata zuba su tayi, k'arshe dai ta had'a wasu cikin patient d'in asibitin dasu suka tattara suka tafi bayan iya ta k'araso. Ahmad yana zaune a parlon su Khaleefa dasu Muhammad da suka taho nan daga asibiti, hira suke irinta tuna baya, rayuwar makarantarsu suke tunawa, wani abun suyi dariya wani su jimanta. A lokacin khaleefa yana bacci ya dinga jin tashin hirar su ta cikin mafarkin shi, tun yana ji sama sama har ya dawo shiga kunnen shi tangaran k'arshe ya tashi ya zauna. Agogon hannun shi ya fara dubawa, 02:50pm sai ya mik'e da sauri yana kallon kayan jikin shi zuwa kanshi, sai ya dafe kanshi da hannun shi kafun ya mik'e da sauri. Wanka yayi ya d'auro alwala sannan ya shirya cikin riga da wando na shadda ruwan madara, suma suna cikin sababbin kayanshi da bai tab'a sakawa ba, saida ya gabatar da sallar zuhr yayi addu'o'in shi sannan ya k'arasa shafa mai ya taje sumar kanshi data d'an taru, yabi jikin shi da mayen turaren shi sannan ya fara takawa gurin y'an maganar shi k'afar shi ba takalmi. Su uku ya tarar a parlon ragowar sunyi nasu guri tun farkawar shi, sai ya rage saura Ahmad! Nazeer! Da Muhammad. A kujerar da take kusa da inda suke ya zauna yana kallon su. Ahmad yace, "ka tashi kenan?". Hannayen shi ya mik'ar yace, "ehh ya kuke ya k'ok'arin ku? Nagode sosai Allah ya bar zumunci". "Ah haba meye wani abun godiya da fatar baki, ai Man rama mana kawai zakayi in auren mu ya tashi, ga Ahmad nan dama shine angon gobe". Murmushi yayi ba tare daya sake ce dasu komai ba. Sunci gaba da hirar su kamar gaske kafun ya fara jin wata muguwar yunwa tana taso mishi da shirin yiwa rayuwarshi illa, har ya d'auki wayarshi sai ya kalli Ahmad yace, "Man akwai wani abu a gidan kuwa?". Ahmad yace, "au ni zaka tambaya ma?". Khaleefa yana laluben cikin fridge d'in parlon yace, "toh wa zan tambaya?". "Ah matar ka mana, ko ka manta yanzu kai d'in me iyali ne?". Ahmad ya fad'a mishi yana kallon shi. Khaleefa da baya ya dawo ya zauna don shi shaf ya manta ashe wai yana da wata mata ma, kuma ko yanzu daya tuna ba wani amfani tunawar zatayi mishi ba, tunda shi dai yanzu ko karen hauka ne ya cije shi bai isa ya tunkareta da maganar wani abincin shiba tunda baya daga cikin k'a'idojin auren su. Ganin ya tafi wani tunanin sai nazeer yace, "Ahmad ina ganin fa mutumin ya manta yayi aure ga dukkan alamu, kasan sabo da rayuwar gwauran taka". Muhammad yace, "tabbas naga alamun haka kam nima". Shi dai khaleefa bai ce dasu komai ba. Ahmad hadda gyaran murya kafun yace, "taya kuke tunanin khaleefa zai tuna yayi aure bayan ya kwana a hospital cikin sanyi da sauro tsakiyar tashin hankali". Aikuwa suka fara mishi dariyar shak'iyanci suna zolayarshi. A wannan karon shima sai daya murmusa yasa hannu yana shafo sumar kanshi, yana ganin basu san dawar garin bane shiyasa suke kallon shi cikakken ango. Ganin inya biye ta tasu yunwa zata kaishi k'asa bai shirya ba sai ya mik'e ya nufi kitchen. Kitchen d'in tas tas dashi babu ko d'igon datti, mama haleema da sauran ma'aikatan gidan suna ta hada hadar had'a abincin da zasu taryi auntie da mutanen gidan. Suna ganin shi suka fara russunawa suna gaishe shi, ya amsa kamar koda yaushe da fuska kadaran kadahan. Gefe guda ya tsaya ya cewa mama haleema, "sannu da aiki". Mama haleema ta juyo tace, "yauwa sannu khaleefa ya gajiyarka?". Yace, "ta huce, nace ko zan samu ruwan tea me zafi da wani abinci sauk'ak'k'e". D'an Jim tayi kafun tace, "za'a iya samun tea amma abincin ku yana b'angaren amarya cikin sitting room naga kana da bak'i". D'an jim yayi kafun ya sake cewa, "don Allah ko zaki iya sawa a dawo mana da abincin parlon mu na sama?". Mama haleema tace, "ai tana da bak'i y'an uwanta sun kawo kayan gara, yana da kyau ma kaje ku gaisa dasu tunda auntien bata nan". Har ga Allah shi baya son wannan yawan gaishe gaishen da shige shigen mutanen da baka sani ba, toh amma ya ya iya tunda ya kama shi. Juyawa yayi ya futa kitchen d'in. Su Ahmad ya tarar inda ya barsu, Ahmad yana ganin shi ya tari numfashin shi da cewa, "yauwa yanzu mukayi waya da doctor namu yana maka congrats, ga sauran mate d'in muma duk suna taya ka murna, ya kamata ka kunna wayar ka naba wasu new no ka nasan zasu kira ka.....". Khaleefa baisan lokacin daya zauna bai shirya ba, ya dafe kanshi da duka hannuwan shi yana nazarin wannan uban aiki da Ahmad yake jik'a mishi. Mik'ewa yayi ya d'auki wayarshi ya dube su, "am Ina ganin zamu k'arasa can zan gaisa da y'an uwan raihana ance sunzo, sannan abincin muma yana can". Duk mik'ewa sukayi suna mamakin abinda ya sosa ranshi har yanayin shi yana sauyawa. Kusan tare suka futo, sai dai har sun fara tafiya khaleefa ya jawo rigar Ahmad baya yace, "Wai wa yace maka ka fad'awa kowa da kowa???? Kai kana d'aukar auren nan kamar na gaske ne ko?....". Da mamaki Ahmad ya tsaya yana kallon shi yace, "toh da na wasan yara ne". Bai tanka shiba yayi gaba ya barshi a nan, shi kam murmushi yayi yabi bayan shi. ******A dai dai lokacin Raihana tana zaune kusa da auntie hajara tana sauraron bayanin sak'on da ummie ta aiko mata tana rik'e da hannun shukura . Ko a yanzu sanye take da k'aton hijabin sallarta daya saukar mata har k'asa. A waya ta rubuta abinda ba zata iya rik'ewa ba gudun samun matsala, duk da tana ji a ranta ba iya shan wad'annan tarin itacen zatayi ba. Su uku ne suka rage a cikin wad'an da suka kawo gara da mahaifinta yasa ayi, ragowar sun tafi sai Auntie Sarah, Auntie hajara da Auntie hapsert k'arama. Suma sun gama komai har y'an gyare gyaren da zasuyi mata a gidan, sun maida mayafan su suna shirin tafiya raihana ta tsaida su da sake tambayar yadda za'a had'a maganin da ummie tasa a kawo matan, su suka bata shawarar tayi saving a waya tunda ta kasa haddacewa. Ta gama tattare ledar magungunan kenan khaleefa ya shigo parlon da sallama, cak raihana ta tsaya daga shirin mik'ewa tsayen da take, har ya k'araso tsakiyar parlon bata iya d'aga idonta ba bare ta kalle shi. Daga gefe ya durk'usa ya fara gaishe su, suka amsa da fara'a akan fuskar su. Bai mik'e daga tsugunnen ba har suka tashi zasu tafi, yarinyar Auntie hapsert k'arama me suna shukura ta tafi gurin raihana tana yi mata Byeee, da yake koyon magana take bata iya bye bye d'in ba sai bibibi, saita tafi kamar gaske saita sake dawowa ta d'agawa raihana hannu ta sake cewa, "bibibi". So take raihanan ta tayata ita kuma wanzuwar khaleefa a gurin ya hanata kwakkwaran motsi bare ta taya ta kamar yadda ta sabar mata. Tun uwar tana jiranta har ta gaji ta futa zuwa wajen parlon ta tsaya ta a can saboda nauyin khaleefa da take ji. Khaleefa kam yarinyar burge shi tayi, yanayin yadda take tafiyar taje ta dawo tace, "atti bibibi" yake burge shi, hakan yaja hankalin khaleefa har yake binta da kallo yana murmushi, a lokacin ta koma tana jawo raihana kan tazo su tafi tana kiran sunanta. Ganin tana shirin mata kuka saita ajiye ledar hannunta ta d'auke ta, khaleefa ya bisu da kallo ita da yarinyar har ta fuce, sai lokacin ya mik'e yana murmushi kan fuskarshi, yarinyar ta shiga ranshi lokaci d'aya da gwarrarriyar hausarta. Shi dai yana son yara ko don basu rayu tare da yara a gidan suba. "Masha Allah raihana amma mijin ki mai kyau dashi d'an gayu, kamar Ayman wallahi muryar suce kad'ai ta banbanta sai yanayin maganar su. Sai dai kamar ba raihana dana sani me aji ba daga ganin shi duk kika wani diririce zaki bada kanki a gaban shi....". Auntie hapsert ce keyi mata wannan maganar k'asa k'asa tana karb'ar shukura a hannunta, ita dai murmushi kawai tayi, suka k'arasa sallama tace su jirata minti biyu tana zuwa, da hanzari ta tura k'ofar parlon ta shiga. Bata ganshi a parlon ba, hakan yasa ta d'auki ledarta zata nufi bedroom d'inta da sauri ko zata samu abinda zata bawa baby shukura kafun su tafi. "Yauwa nace ko akwai kud'i a hannun ki?" Tambayar data shiga dodon kunnenta kenan har ta assasa mata tsayawa tana kallon direction d'in da maganar ta futo. Yana tsaye daga wani sashe na d'akin, "idan akwai ki aramun 7k zan mayar miki dasu". Cikin kud'in da suka kawo mata ta zari 7k d'in ta tafi zata kai mishi maganar shi ta sake katse ta, "ki basu suyi kud'in transport". Saita juya da sauri ba tare da tace mishi komai ba, a lokacin har sun gaji da tsaiwa sun kusa futa daga harabar gidan ta k'arasa da hanzarinta ta d'anka kud'in a hannun shukura tace ku hau napep, da mamaki suka tsaya suna kallonta, "raihana ba zamu karb'i ko kwandalar kiba....". Auntie hajara ta fad'a. D'aga hannayenta tayi tace, "Auntie bani na baku ba, cewa yayi kuyi kud'in mota". Jin haka sai suka yi godiya suka ce ta musu godiya a gurin shi. Tana d'agawa shukura hannu har suka futa daga gidan. Koda ta dawo bata same shi a parlon ba bare ta mishi godiya, kuma bata bi ba'asin komai ba ta d'auki ledarta tayi cikin d'akin gadonta. A sitting room ya samu su Muhammad da suka shiga ta k'ofar baya, shiya musu saving abincin suka fara ci, suna hira suna zolayarshi har suka gama. Saida aka kira sallar la'asar sannan suka futa don sauke farali, shi kuma yayi amfani da wannan damar ya kira auntie yaji ko lafiya suka dad'e haka basu dawo ba...... *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty4️⃣0️⃣ Suna tare har su Auntie suka dawo su hud'u, Auntie! Doctor seera! Iya sai Ayman. A parlon auntien aka saka mishi pillow ya kwanta saboda bawai jikin shi yayi kwari bane har lokacin. Duk sunzo sun musu sannu da zuwa, tare da yiwa Ayman fatan samun lafiya dawwamammiya. Basu bar gidan ba sai after magrib, ya rage daga khaleefa sai Ahmad da yake son shima ya tafi nan da kwana uku ko biyu in komai ya daidaita. Iya ma saida malam ya kawowa Ayman tofin da yayi mishi, sannan suka tashi zasu tafi, sai a lokacin iya take tambayar khaleefa, "Wai Ina raihanatun ne magaji! Tunda nazo kai kad'ai nake gani ban ganta ba ita, ko kullenta za'ayi mana". Kafun ya bada amsa Auntie ta riga shi da cewa, "taci abinci ma kuwa? Baiwar Allah d'azu da safe ma saida ta bini taga jikin Ayman". Iya tace, "ai raihana ba dai kirki ba, naji dad'i da kika samu suruka ta gari irinta, zaku zauna lafiya da ita kwarai". Auntie tana murmushi tace, "ai daga dukkan alamu, ni ko da can nasan yarinyar ta samu tarbiyyah, fatana d'aya Allah yasa khaleefa ya rik'e ta bisa gaskiya da Amana". Khaleefa da yake sauraron duk maganganun su baice dasu kanzil ba, hasalima yi yayi kamar bai tab'a sanin wadda suke magana a kanta ba, Ayman kam sake rintse idon shi yayi gashi ba damar ya hana kunnuwan shi sauraron maganar su. Malam yayi addu'o'i sosai, kusan abinda su auntie suka fad'a shima shiya d'ora, kyawawan halayen raihana suka dinga kwad'aita mishi had'e da shawarar ya kula da ita yadda ya kamata. "Insha Allah raihana ba zatayi kuka dani akan komai ba". Kacal abinda ya fad'a ya maida kanshi, malam yace, "Toh Allah yasa". Tana daga cikin d'akinta gefenta gado tana amsa wayoyi daban daban daga y'an uwa da abokan arzik'i, wanda basu samu damar zuwa ba suke ta mata Allah sanya alkhairy, wasu kuma ta text massage. Bayan ta gama dasu, saita fara kiran wanda suka zo tana musu ban gajiya da godiya had'e da addu'ar Allah ya bata ikon rama musu tarin alkhairan da sukayi mata. Suma sunata godiyar kayan cosmetics da ta bayar aka kai musu. Ba ita ta samu kanta ba sai bayan sallar magrib, ta d'aura alwala tayi sallarta. A hankali ta tura k'ofar parlon ta shiga bakinta d'auke da sallama, daga Auntie sai mama haleema a parlon da Ayman da yake zaune kusa da ita yana sipping tea. "A'a raihanatu". Cewar Auntie. Da sauri Ayman ya had'iye shayin bakin shi ya ajiye sauran. K'arasa shiga tayi ta zauna daga k'asan parlon ta fara gaishe su, duk suka amsa Auntie har tana tambayar ya gajiyarta. Murmushi tayi bisa al'adarta a ranta tana mamakin yadda Auntie bata gajiya da tambayarta gajiya duk k'ank'antar aikin da tayi. Mama haleema ce ta kawo mata tray me d'auke da k'ananun cup da tea flask akai. Kad'an tasha shayin bayan ta zuba mata ta ajiye saboda rashin sabo. Sai hira Auntie da mama haleema keyi mata, ita dai nata sauraron su, Ayman kuwa maida kanshi yayi ya langwab'ar yana Allah Allah khaleefa ya dawo ya bar musu d'akin. Khaleefa bai zoba sai wajen tara da y'an mintuna. Lokacin tuni mama haleema ta tafi saboda yaranta da mamanta suna buk'atar ganinta suma, Auntie ma ta shiga d'akinta ta futo, daga ita sai Ayman, itama jira take auntie ta dawo ta mata sallama ta tafi saboda idonta daya cika fal da bacci. Futowar Auntie yayi dai dai da shigowar khaleefa, su biyu kawai suka kalle shi, ya sauya kayan jikin shi da wad'an da yafi ganewa wato riga da wandon jeans. "Yauwa khaleefa Ayman yana taso kazo ka taimaka mishi zuwa d'akin shi, ga raihanatu nan ma ta fara gyangyadi kazo ku huce haka". Hucewa yayi ya taimakawa Ayman ya mik'e, rik'e dashi suka fara tafiya a hankali har suka isa parlon su, Ahmad da yake duniyar waya da yasmin a lokacin ya mik'e ya taimaka mishi suka k'arasa har cikin bedroom d'inshi ya zaunar dashi gefen gado. Khaleefa yana tsaye gefe guda hannun shi hard'e a k'irji yayi crossing legs yana kallon shi. Ahmad a mute yasa wayarshi ya dubi khaleefa, "Wai ba munyi sallama dakai ba ya kuma ka dawo?, ko akwai abinda kake jira ne". Da sauri Ayman ya kwanta ya sake rufe idon shi ruf, shi kuma khaleefa yaja k'afar shi ya futa bayan ya musu sallama. Raihana tana zaune a inda ya barta sai wasa take da k'asan hijabinta, auntie kuma tana waya ya sake shigowa d'akin, Daga tsaye ya tsaya har ta kammala wayar ta kalli raihana, "daughter nasan kin gaji ko? Ga nan khaleefa yazo ai zaku tafi, oya kuje Allah ya huta gajiya". A nutse ta tashi tace "auntie saida safe". Auntie tace, "Allah ya bamu alkhairy". Khaleefa shiya fara futa sannan itama tabi bayan shi. Babu wanda yace da d'an uwan shi ci kanka har suka bud'e k'ofar parlon suka shiga da sallama, khaleefa zama yayi kan kujera yana jira yaga d'akin data d'auka, ba b'ata lokaci kuwa tayi d'akinta ta rufo k'ofa, mik'ewa yayi bayan ya kashe hasken gurin ya nufi wanda yake tsakiya, had'ad'd'en d'akin bacci me d'auke da gado na alfarma komai milk, sai ya tsaya yana bin d'akin da kallo, Anya kuwa raihana ba wannan ne d'akinta ba? Tunda shi yasan bai shirya d'akin baccin shi a side d'in ba, ba don Ahmad da auntie sun takura mishi ba da a part d'insu zai ci gaba da zama har zuwa lokacin da zasu tafi. *Bayan wasu kwanaki* Tuni Ayman ya watstsake tangarau sai abinda ba'a rasa ba, amma a hakan ya shirya komawa bakin aiki yau saboda zaman gidan ya ishe shi, Ahmad ma ya tafi tun bayan kwanaki biyu da biki, amma fa bayan ya dunk'uli gudun mawa mai tsoka ya ajiyewa khaleefa. Auntie kam har yanzu tana cikin hutun biki data d'auka, mutane da yawa sunzo mata Allah sanya alkhairy, wasu ma har da abin arzik'in su kwatankwacin yadda take kyautata musu. A kullum safiyar Allah kafun raihana su tashi bacci tasa ma'aikatan gidan y'an mata sun k'alk'ale musu part d'insu, sannan lafiyayyen kayan breakfast data shirya da kanta da hannunta su biyo baya. Haka da rana da dare duk ita take musu girki mai kyau ta aika musu. Zuwa yanzu khaleefa ya had'a kayan shi da duk wani abun amfanin shi zuwa sabon muhallin daya sauya, bai sauya daga baud'ad'd'en khaleefa da suka sani ba har yanzu, sai dai yakan yi k'ok'arin danne zuciyarshi wajen ganin ya zauna da kowa lafiya a gidan. Tsakanin raihana da auntie zama suka d'auka mai kyau mai cike da girmamawa da mutuntawa irin na surukan da suka san ciwon kansu. A kullum raihana zata je ta gaisheta har tana riga khaleefa ma zuwa, kasancewar gidan ba wani aiki ne dasu ba bare tace zata taimaka, rabin nasu ma an sauk'ak'e musu sai ya zamana suna gama gaisawa take komawa tayi wanka ta shirya ta karya kumallo, k'afarta ta warke sosai tuni tana iya takata ba d'ingishi. Wani lokacin bak'i sukan kawo musu ziyara daga y'an uwan ummie ko masu makwabtaka dasu wani lokacin kuma ta yini ita d'aya, a irin wannan lokacin take kwantawa ta huta, tunda tazo gidan ko ruwan tea bata tab'a tafasawa ba, yini ake kawo musu shayi ita da bak'inta, abinci da rana ko sunkai su goma za'a kawo wanda zai ishe su suci su k'oshi, haka da dare ma. Raihana tun washe gari ta tattara fiye da rabin kayan snacks na cikin gara da aka kawo mata dana abinci ta baiwa mama haleema aka kai part d'in auntie, da farko Auntien fad'a tayi tayi kuma ta k'i karb'a amma daga baya da raihana ta mata bayani yadda zata fahimta saita amsa ta d'ibarwa su iya da duk wanda ya kamata ta bashi. Ba zata ce suna zaman lafiya da khaleefa ba, ba kuma zata ce suna fad'a ba, saboda kowa harkar gaban shi yake ba ruwan wani da wani, in suka had'u Ina yini ko Ina kwana ta raba. Yauma tun safe data lek'a suka gaisa da auntie ta dawo ta sake kwanciya bata tashi ba har sai wajen k'arfe sha d'aya da yunwar cikinta ta takura mata, sanye take da doguwar rigar material ta yane kanta da wadataccen gyale, hannunta rik'e da wayarta ta futo ta isa inda ake ajiye musu abincin su, ruwan tea ta soma tsiyaya ta d'umama cikinta dashi sannan ta d'auki gasashshen bread ta fara ci a nutse, daga yawan abincin ta fahimci yau khaleefa bai ciba kwata kwata. Bata damu ba ta gama abinda take yi ta koma d'akinta, sake gyara d'akin tayi da kyau sannan ta zauna tana duba wasu daga cikin kayan lefenta, saboda auntie tace ta d'ebo wasu ta bawa khaleefa a d'inka mata. Yawan kayan ba k'aramin tsoratata yayi ba har ta kasa yin abinda tayi niyyah ta tsaya kawai tana kallon su. Wannan uban kaya duk ita da waye zasu saka su? Anya ba mistake akayi aka had'o mata da wad'an da ba nata ba? Toh amma waye a gidan su zaiyi aure nan kusa da za'a ce lefen tane ko lefen shine aka kawo mata. Duk da haka bataji zuciyarta ta nutsu ba saida ta kira ummie, bayan sun gaisa take tambayarta "ummie duk wannan kayan na waye?" Ummie daga can b'angaren murmushi tayi tace, "na kine raihana wani abu ne". Zaro ido tayi kamar tana gaban ummien tace, "ummie ai sunyi yawa". "Tom saiki fad'awa doctor surayyah da mijin ki su rage miki su tunda su suka kawo su haka". Rufe bakinta tayi tace, "Kae! ai bazan iya fad'a musu haka ba". "Toh tunda ba zaki iya yi musu magana ba nima saiki daina tambayata". Shiru tayi tana sake kallon yawan kayan kafun ta sake cewa, "toh kuma ummie ba za'a iya rabawa mutane ba? Sai kuma ku d'auka wasu a ciki?". "In banda ke raihana ina kika tab'a ganin an rabar da lefe, na dai rabawa k'awayen ki kayan kwalliya sai Inna dana d'aukar wa atamfa itama saboda gudun matsala tunda ana su khausar ma duk saida na bata atamfofi". Raihana tace, "toh ummaa fa? Ita ba'a d'aukar mata ba?". Ummie tace, "a'a ita ummaa bata da matsala, ko an bata ba lallai ta karb'a ba". D'an jimm raihana ta sakeyi kafun tace, "shikenan ummie sai anjima ace dasu hibba bana gaishe su tunda sun kasa zuwa mun har yau". Ummie dariya tayi tace, "ba ruwana ni kam bana bada sak'o irin wannan". Daga haka ta kashe wayarta tana murmushi, in banda ma raihana ina ake d'ibar lefe a rarrarabar aje a samu matsala da dangin miji, ita kam ko ba za'a samu matsalar bama ba zata iya tab'a kayan nan ba tunda ga da sunan wadda aka siya. Kusan kala bakwai ta futar, atamfa leshi da wani shegen material. Kwaso kayan tayi ta nufi b'angaren saman Auntie. *****Sameera kuwa tun a waccen ranar da suka baro asibiti bata yi burki a ko'ina ba sai gidan hajiya tafeeda. A lokacin tana shirin gama abinda takeyi taje gidan sameeran, yanayin su data kalla kad'ai tasan lallai ba lafiya ba, saita zauna tana tambayarsu, "lafiya kuwa k'awata na ganki haka?". Girgiza mata kai sameera tayi ta warware mata duk yadda sukayi da surayyah a yau, tab'e baki hajiya tafeeda tayi bayan gama sauraron duk bayanan bakin sameera, "kinga abinda nake fad'a miki kullum ko? Dama ke kika d'auki surayyah wata mutuniyar arzik'i har kike shirin bata aurin y'ar ki, Amma Allah na tuba astagfirullah surayyah har mutum ce......". Da sauri Mamie ta d'aga mata hannu, "ai kinji matsalar ki tafeeda, bansan me surayyah tayi miki ba da yasa bakya iya fad'ar alkhairy a kanta sai sharri,,,,, Ni yanzu abinda ya kawo ni shine, zuwa nayi ba dama kina son had'a Imran da shaheeda aure ba? Toh don Allah ki fasa da shaheedan ga nuriyyah nan mu had'a auren da ita madadin y'ar uwarta,,,,,, shiru hajiya tafeeda tayi tana tunanin yadda zata karb'i Nur d'in don ita tun farko ba ita taso ba shaheeda take so, itace irin zubin surukar da take fatan samu don ta fudda ita kunya cikin k'awaye". *Bayan wasu kwanaki* ******Tsaye take gaban mirrow ta tsurawa kanta ido tana kallo wai dole saita gano muninta kota inda ta gaza, a lokacin tana sanye da riga iya gwiwa kamar gown sai dogon wando tight daya kwanta a jikinta yabi fatar k'afarta ya lafe. Sai riga marar nauyi white data d'an kamata kad'an daga sama, ta bud'e daga k'asa. Sallamar Nur ta sata sauƙe k'ak'k'arfar ajiyar zuciya tare da lumshe idonta, kan drower mirrown nuriyyah ta zauna ta fashe da kuka mai ban tausayi, a tsanake ta juyo duk da yadda zuciyarta ta tsinke da jin sautin kukan Nur d'in. Zuba mata ido tayi ba tare da tace komai ba tana kallon yadda take risgar kuka. Bata tambayeta ba'asi ba har tayi mai isarta ta fara bata labarin abinda yake faruwa, "kinsan Allah na tsani kaina na tsani wannan rayuwar da nake ciki a halin yanzu, me yasa mamie take son lallai sai taga bayan rayuwar mu sai kace ba ita ta haife muba?, Da farko ta raba ni da Yaya Ayman yanzu kuma tana son lallai saita had'a ni da wanda sam bana ra'ayin shi shima bece yana sona ba......". Sai a lokacin shaheeda ta dafa kafad'arta tasa hannu tana share mata hawaye da tafin hannunta, "kiyi hak'uri Nur kowanne mutum da kike gani da k'addarar shi a rayuwa, sannan wani abun sam ba alkhairy bane a rayuwar mu muke nacewa a kan son shi, watak'ila Ayman ba shine mijin ki ba shiyasa komai yake shirin zuwa k'arshe a tsakanin ku cikin lokaci k'alilan,,,,,," shiru ta sakeyi kafun taci gaba da maganarta, "waye shi wanda ake son a had'a kun?". Nur dakatawa tayi da kukan da take kad'an tace, "Imran ne d'an hajiya tafeeda....". Wani irin murmushi shaheeda tayi a ranta tana k'issima yadda zata juya al'amarin izuwa ga mafarin shi, lallai ya kamata hajiya tafeeda ta girba abinda ta shuka na izgilanci da shiga hususiyyar ubangiji ko yayane. Saita sake gyaraa zama tace da Nur, "to ke meyasa ba zaki amince ba, ko kin fison kiyi bawan ba k'anin, ga rashin Ayman ga rashin mutum kamar Imran". Cikin muryar kuka yanzun ma tace, "kinsan fa waye Yaya Ayman, haka zalika kinsan wanene Imran tunda ai da dake ake son had'a shi auren,,,, ko k'afar Ayman Imran bai kama ba a hali da d'abi'u masu kyau na rayuwa, kuma fa shi bawai yana Sona bane, meyasa ma zan auri tsohon saurayin raihana da maman su ta shiga ta futa ta raba su ba tare da tayi mata laifin komai ba, shine ni kike tunanin in na aure shi zata bari mu zauna lafiya,,, wallahi bazan aure shiba yaya ko zan rasa raina sai dai duk abinda za'ayi mun ayi amma wallahi bazan aure shiba....". Ta k'arashe fad'a tana sake fashewa da wani sabon kukan. Rungume ta shaheeda tayi tsam a k'irji atana rarrashi da fad'a mata dad'ad'an kalaman da zasu kwantar mata da hankali, cikin hikima da dabara kuma ta dinga zugata kan karta amince ta yadda ta rasa masoyinta Ayman, don ba zata samu kamar shiba a wannan duniyar. Shaheeda ta nuna mata cewa zata goya mata baya ta tsaya mata da iya k'arfinta har ta kaiga cimma burinta na auren masoyinta Ayman. *******Yana zaune a office d'inshi ya had'a kanshi da table, sanye yake da suit black colour ya sakaye k'afar shi cikin cover shoe samfurin.... Biro ne a hannun shi na dama da wata bugaggiyar takarda da alama zaiyi signing ne. Da sallama kaamil ya turo k'ofar office d'in ya shigo, baiji sallamar ba har ya k'araso gaban table d'in dake gaban shi yaja kujera ya zauna. Da farko ya d'auka bacci yake yi amma daga baya saiya gane idon shi biyu kawai yayi zurfi a duniyar tunani ne. Buga table d'in yayi kad'an da hannun shi, abinda yasa Ayman yayi firgigit ya d'ago kanshi had'e da dafe kan da hannun shi d'aya tare da lumshe ido a lokaci guda. "Kamar baka da lafiya Ayman? Ko har yanzu jikin ne? Ai dama kayi saurin dawowa bakin aikin bayan hutun kama bai k'are ba har yanzu". Kaamil ne yayi wannan maganar da tarin kulawa. Bud'e idon shi da suka sauya launi yayi ya maida hannun shi kan takardar yayi signing ya turawa kaamil ita gaban shi. D'auka yayi yana dubawa, ya mayar da ita cikin kundinta ya sake tsayar da idanun shi kan Ayman da yayi relax kan kujera still idon shi a rufe. "Engineer Ina ganin ka tafi gida haka ka huta nasan zakaji sauk'in abinda yake damun ka, and please kar ka dawo har sai ka warke". Hankie yasa ya share zufar fuskarshi sannan ya tsaida hankalin shi kan kaamil yace, "kaamil ba zaka gane ba, zamana a nan zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali akan zama inuwa d'aya da ita Ina kallonta da jin duk wani motsinta a cikin jinina yana gudu,,,,,, kaamil bansan ya zanyi na cire ta daga zuciyata ba,,,,, Ina ganin sonta shine zai zamo ajalina don a yanzun ta tsere mun tserewa irinta har abada....". Cikin matuk'ar tausayin shi kaamil yace, "matsalar soyayyah ce kenan? Tana raye ita masoyiyar taka kota mutu? Don naji kana ta tsere maka". Girgiza mishi kai yayi ya sake bud'e bakin shi daya mishi nauyi da kyar yace, "bata mutu ba". Kaamil yace, "toh ai da sauk'i,,, tasan kana sonta?". Sake girgiza mishi kai yayi yana yak'i da ruwan hawayen shi da suke gudu wajen ganin sun fallasa kansu ga kaamil. Dukan table d'in kaamil yayi da k'arfi yace, "no wonder! gaskiya mana kake son kashe kanka a banza, ai kai kaso ka wahalar da kanka Ayman, ka tab'a ganin inda aka dinga dakon son mutum ba tare da an sanar dashi ba,,,, how do you expect she know all that you are feeling....". "Ba zaka gane ba kaamil ta riga ta gama fin k'arfina zuwa yanzu saboda zata kasance k'ark'ashin shak'ik'ik'ina..... Khaleefana, y'an biyuna......". Ayman yayi wannan maganar kamar me yin fad'a da wani irin tune, sai a lokacin hawayen shi suka samu damar futowa. Shikam kaamil shiru yayi na adadin wasu mintuna kafun ya mik'e tsaye yayi tattaki zuwa gaban Ayman ya tsaya, "tabbas tafi k'arfin ka kamar yadda ka fad'a nima na yarda, sai dai ka amayar mata da abinda yake cikin zuciyar ka, ba don ka jawo hankalinta zuwa gareka ba, a'a sai don kaji sauk'i da sassauci a cikin zuciyar ka, ajiye soyayyarta daga kai sai kanka shine yake cin ranka yake hanaka sukuni, amma da zarar taji zaka nemi rabin damuwar ka rasa insha Allah.....". Daga kallon da yake mishi ya gane sam Ayman bai fahimci abinda yake nufi ba, ba kuma zaiyi ba,,,, sai dai fa shi yana ganin hakan shine kad'ai maslaha, da zarar ya futar kuma zai samu nutsuwar zuciya, in Allah ya taimake shi har ya fara mantawa da ita da babin wata soyayyar ta gaba d'aya. A d'arare ta shigo parlon duk da bata ji alamu ko motsin wani a ciki ba, har yanzu sanye take da kayanta na d'azu har gyalen, sai dai rungume da tulin kayan data d'auko za'a kai d'inki kamar yadda auntie ta bata umarni. A d'aya daga kujerun parlon ta zauna ta ajiye kayan gefe tana kallon wani tabkeken hoton su da sukayi su uku, Ayman da khaleefa a gefen auntie, ta rungumo su jikinta gaba d'aya ta sasu a tsakiya tana dariya. Sunyi maseefar kyau a hoton, kuma hoton an yi shine tun kafun tafiyar khaleefa karatu Germany. Hankalinta da tunaninta sun tafi gaba d'aya wajen kallon hoton shiyasa har bataji shigowar shi parlon da sallamar da yayi ba. Duk da dama ba wai bud'e baki yayi sosai yadda zata ji ba. _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty one4️⃣1️⃣ Gyaran murya yayi bayan ya ajiye k'atuwar jakar system d'inshi gefe, sai a lokacin raihana ta lura dashi, aikuwa ta kama kanta da sauri hadda gyara zamanta gabanta yana tsananta fad'uwa. K'arasawa yayi kujerar dake kusa da wadda take zaune ya zauna daga d'an nesa da ita yace, "barkan ki da gida Mrs khaleefa". . cikin diriricewa da inda inda tace, "ya Yaya Ayman an wuni lafiya....". Wani abu mai d'aci ya had'iye yace, "kamar yadda kike,,,, koda yake halinda muke ciki ya banbanta, don ke ga dukkan alamu kina cikin k'oshin lafiya cikin nutsuwar zuciya data ruhi, sab'anin ni da nake a hargitse, nake kwana da ciwon Soo nake tashi dashi har yana neman hanyar da zaiyi ajalina,,,,,". Ba tasan lokacin data juyo ta kalleshi ba har saida ta tsinci kwayar idanunta cikin nashi.. Saita d'auke idon da sauri ta dafe saitin zuciyarta da hannunta. Shima d'auke idon shi yayi yana korar shaid'an daga cikin zuciyarshi, ba tare daya kalleta ba yaci gaba da cewa, "a baya mun d'auki lokaci mai tsawo muna gaisuwar mutumci da sunan friendship wanda yake sam ba haka ba a cikin zuciyata, da farko na fara jin shigar wasu sababbin abubuwa cikin zuciyata sannu a hankali da bansan a yadda zan fassara suba lokacin, na d'auka Nur nake so bake ba shiyasa ban tab'a kallon ki da wata siga ta daban ba, a hankali wannan soyayyah ta dinga ginuwa a cikin zuciyata tana sake k'arfi, na dinga kishin ki ba tare da nasan dalilin aikata hakan ba, har takai na kasa jurar alak'a dake a lokacin da Imran yake dab da aure ki, Ina ganin kamar shi zai shiga tsakanina dake, ban k'ara tabbatar da matsayin kiba saida muka samu sab'ani da Nur, a lokacin na gane lallai ke nake so tsawon lokacin nan ba tare dana sani ba,,,, gashi a lokacin Ina gab da rasa ki gaba d'aya, anan hankalina ya sake tashi na sake shiga damuwa mara misali. Na samu dama ta farko a lokacin da kika turo mun da text na rabuwar ku da Imran, nayi farin ciki nayi murna har na fara mafarki da tunanin watak'ila dama ke d'in mallakina ce, shiyasa maganar auren ki ta dinga lalacewa har karo shida,,,, na tambayi malam da zumud'i tunda a bakin su nake jin labarin duk wani rugujewar auren ki, sai dai a wannan karon su kansu basu sani ba, haka yasa na sake jinkirtawa har zuwa sanda zancen zai fasu sai in fad'a musu a nema mun auren ki. Koda dare yayi na kasa bacci da hak'uri saina yanke shawarar fad'awa auntie kawai, sai dai wani tashin hankalin khaleefa ya riga ni kai maganar neman auren ki gabanta, wannan ya d'aga mun hankali ya sake dilmiya ni a damuwa, sai dai bani da yadda zanyi don khaleefa yafi k'arfin komai a gurina kamar yadda shima ba abinda bazai iya sadaukar mun a duniya ba, nayi kuka a fili nayi a zuci har bansan adadi ba, tun ina ciwo a tsaitsaye har takai na kwanta magashiyan, bikin ku yana k'aratowa ciwona yana dad'a tsananta, na kasa taimakon khaleefa da komai duk yadda na dinga dannar kaina da zuciyata kuwa saboda wutar kishi da take cin raina. A k'arshe na tattara na bar gidan zuwa gidan iya, amma duk da haka ban tsira ba, nayi alk'awari duk yadda zanji dani za'a d'aura auren nan, sai dai jarumtata ta gaza a lokacin da aka shafa fatiha na tabbatar na rasa ki kenan har abada...... Take naji wata hajijiya tana wujijjigani kafun na cewa Ahmad komai ganina da jina had'e da numfashina sun tsaya cak, sai bud'e ido nayi na tsinci kaina a gadon asibiti likitoci sun kewaye ni suna fafutukar ceto rayuwata, a lokacin da ni kuma nafi son na mutu ma nabar wannan rayuwar duniyar......". Doguwar ajiyar zuciya yaja cikin dauriya yaci gaba da cewa, "tabbas Ina sonki raihana,,,, kwatankwacin son da zan iya yiwa rayuwata, Ina sonki fiye da yadda duk kalmomin bakina zasu fad'a,,,,, kuma har gobe bance zan daina sonki ba don bazan samu makwafin ki a rayuwa ba har na koma ga Allah..... Raihanatu ba wai Ina fad'a miki haka don ki soni ko don ina saran zan same kiba, a'a ina fad'a miki ne don na rage rad'ad'i da mikin da yake cikin zuciyata..... Duk dani bansan irin auren da kukayi da khaleefa da soyayyar gani da kallo d'aya data kama zuciyoyin ku ba, amma a zuciyata bana fatan wata rana ki futa daga rayuwar shi, domin a duk inda kike ke haske ce me yaye duhu.... Kuma zaki kasance haka a rayuwar khaleefa dama ta Auntie baki d'aya naji haka a jikina....". Tunda ya fara magana raihana ta d'auke wutaa tana sauraron shi ko kwakkwaran motsi ta kasa yi har ya dire, inda bacci take data jima da farkawa don kunnuwanta sunji abune da bata tab'a zaton zasu jiba ko a cikin mafarkinta. Yaya Ayman yana sonta! Ta Yaya?, Saita dafe kanta da hannunta duka biyu tana kiran sunan Allah ya kawo mata d'auki. Shikam mik'ewa yayi yana jinshi sakayau zuciyarshi babu wannan nauyin, jakar daya shigo da ita ya bud'e ya ciro wani abu a farin kwali yazo ya d'ora mata saman cinyarta, "your marriage gift". Bata d'auki kyautar ba kamar yadda bata motsa daga yadda take ba har ya fara k'ok'arin barin parlon. Kamar daga sama ya tsinkayi maganarta don bai tab'a tunanin zata bashi amsa ba. "Ka keta iyakah! Kayi magana da matar wani! Magana irin wadda addinin mu ya haramta!!! sai dai watak'ila k'arshen matsalolin kane da nata zasu zo ta hanyar aikata wannan zunubin,,,,,". Taku kad'an ta sake yi ta rage nisan dake tsakanin su taci gaba da fad'in, "aurena da khaleefa ya kasance wani b'oyeyyen sirrin mu da bai kamata ka sani ba, sai dai nayi alk'awari duk ranar da wa'adin auren mu ya cika.... nayi alk'awarin duk ranar dana bar rayuwar khaleefa....., bazan manta da soyayyar daka nuna a kaina da tarin sadaukarwa ba, zan kasance a rayuwarka koda ka auri wata bani ba indai har zaka soni a lokacin....". Saita ajiye mishi kyautar shi k'asan k'afar shi tace, "na gode amma bazan iya karb'ar kyautar nan ba, iya d'awainiyar da kayi dani a baya ma Allah ya bada lada.....". Jin kamar motsi a bakin k'ofar shigowa parlon yasa duk suka kalli gurin ba tare da sun shirya aikata hakan ba, iska ce kawai ta kad'a murfin, kudun kada wani ya same su a lokacinya zargi wani abu sai raihana ta d'auki hanya zata futa a d'akin, Ayman yayi saurin shan gabanta hannun shi rik'e da kwalin kyautar shi, cikin marairaicewa yace, "kada kice mun zaki futa daga rayuwar khaleefa don ki dawoo cikin tawa! Kin riga kin zama tashi mallakin shi watak'ila ma nan da lokaci k'alilan zaki haifi d'an shi ko y'arshi,,, beside matar khaleefa ma ta haramta a gareni har abada......". Ya kai k'arshen zancen yana jin wani tuk'uk'in bak'in ciki a zuciyarshi. Girgiza mishi kai tayi tana sake ja baya tace, "ko ban futa daga rayuwar shiba shi zai futa daga tawa, raihanatu zata zama mallakinka da komai nata, bisa kyakkyawan albishir na cewa ko hannunta khaleefa bazai samu nasarar rik'ewa ba nasan shine tunanin ka". Sai yanzu murmushi yayi escaping saman fuskarshi, "lallai akwai wani abu cikin auren ku tunda kika yimun irin wannan alk'awarin,,,, yadda kike haka khaleefa yake, baya wasa da alk'awari kamar yadda baya wasa da abinda yake so, zai bi kowanne mataki komai rintsi indai zai samu cikar burin shi,,,,, alhamdulillah bisa ga wannan kyauta da Allah yayi mun, raihanatu kece farin cikin rayuwata...". Murmushi tayi ta maida kanta k'asa itama tana jin wani tarin farin ciki a cikin zuciyarta. (Ko'ina tunanin raihanaa da Ayman yayi?) Ayman ya d'an kalleta na adadin wasu mintuna a ranshi yana raya kamar ma k'ara mata kyau akayi, kafun ya kori shaid'an da hanzari ta hanyar barin kallonta. Kwalin kyautar daya mata ya soma k'ok'arin d'anka mata a hannunta yayinda ita kuma tak'i karb'a tana girgiza mishi kai, turo k'ofar parlon akayi shigo da sallama. Muryar auntie ce, hakan yasa duk suka juya da sauri,,,, daga bakin k'ofar ta tsaya nad'e da lafaya hannunta rik'e da Jakarta da Mukullin motar ta, kallon su take irin kallon tuhuma da zargi. Khaleefa kam da yake bayanta kallo d'aya yayi musu ya kewaye ta ya k'arasa shigowa cikin parlon ya nemi gefe d'aya ya zauna had'e da kwantar da kanshi saman kujera ya lumshe ido yana jin wata masifaffiyar yunwa na farmakar shi. Ayman k'arasa zura mata kwalin yayi ya d'auki jakar shi ya tunkari k'ofar. "Sannu da zuwa auntie". Ya fad'a bayan ya tsaya gefe guda, murmushi tayi tace, "Kai za'a yiwa sannu ya jikin ya aikin kuma". Murmushi yayi shima yace, "ai na warke insha Allah naji sauk'i". "Toh Allah yasa" auntie ta fad'a tana k'arasa shiga cikin d'akin shi kuma ya futa. "Sannu da zuwa auntie". Raihana ma ta fad'a kanta a k'asa. Har yanzu fuskar auntie fad'ad'e da fara'a tace, "yauwa raihanatu, baki iya yiwa mijin ki sannu da dawowa ba amma kin iya yiwa wata mata can a gefe...". Satar kallon inda yake tayi, cikin jin kunyar auntie kamar ta nutse a gurin tace, "kiyi hak'uri auntie insha Allah zan gyara". Dafa kanta tayi tace, "ba komai raihana, mama haleema tazo kuwa?". Raihana tace, "nima ban dad'e da shigowa ba maybe tazo kafun nazo ta tafi". Zama tayi a kujerar da khaleefa yake zaune tace, "Anya kuwa? Jiya tace mun bata jin dad'i watak'ila jikin ne har yanzu". Raihana tace, "ayyah Allah ya bata lafiya". Auntie tace, "ameen". Futa tayi zuwa kitchen donta sama musu abinda zasu ci taga kamar a gajiye suke, ita Kuma auntie ta dawo da dubanta ga khaleefa "khaleefa kana lafiya kuwa?". Ta tambaye shi da harshen Arab. "Ana bikhair". Ya fad'a ba tare daya motsa daga yadda yake ba. "Allah yasa!". Ta fad'a tana d'aukar wayarta data fara ringing. Raihana bata sha wahala wajen had'a musu tea mai kyau irin na k'asar Sudan ba saboda mama haleema tayi rannan a gabanta taga yadda ta had'a komai. Shap shap ta shirya musu indomie iya wadda zasu ci su biyu ta d'auki trayn tayi parlour. "sannu raihana mun saki wahala ko?". Auntie ta fad'a tana karb'ar trayn ta ajiye kan glass table k'arami dake gabanta. Komawa tayi ta kawo musu ruwa da lemu ta had'a da kofuna. Auntie sai jera mata sannu takeyi kamar wadda tayi wata uwar aiki, har tasa tana jin kunya. Ita ta zuba musu shayin a funjalai biyu ta bawa auntie nata ta kaiwa khaleefa ma nashi, "ga shayi" ta fad'a ganin baisan tazo gurin ba. Sai a lokacin ya tashi zaune sosai, ya karb'i shayin yana bin yatsun hannunta da kallo, ganin jan lalle a yatsunta sai yaja k'aramin tsaki a ranshi yana ayyana, wai ita wannan kullum saita saka wannan abun a yatsunta, taji tsakin shi sarai auntie ma kuma taji, amma sai cikin su babu wanda ya nuna mishi ko yabi takai. Auntie ta fara zuba ma indomien ta mik'a mata bayan tasa fork, ta d'auki wani tray zata zubawa khaleefa auntie ta dakatar da ita ta hanyar fad'in, "khaleefa baya cin indomie, in akwai ragowar dankali ki soya mishi chips". Da "toh" ta amsa ta tashi da hanzarinta ta tafi don cika umarnin auntie. Bayan ta futa auntie gyara zamanta tayi ta kalle shi da kyau a lokacin da yake shan shayin hannun shi tace, "khaleefa me yasa ka yiwa raihana tsaki?". Shiru yayi ya dakata da shan shayin, "kayi shiru Ina tambayarka? Yanzu tsakani da Allah ka kyauta kenan? Kana gani fa muna shigowa yarinyar nan da rawar jikinta ta tashi donta sama mana abinda zamu sa a cikin mu saboda taga yanayin kowa a cikin mu, tuntuni nake kwab'ar ka saboda tsaki mummunar dabi'a ce da take hana zaman lafiya tsakanin mutane, gashi yanzu matar ka da take iya k'ok'arin ta wajen ganin ta kyautata maka ita ka yima tsaki, gaskiya bana so kada ka kuma". Ba tare daya kalleta ba yace "insha Allah za'a kiyaye". Auntie tace, "tom". Raihana bata d'au lokaci mai tsawo da yawa ba ta had'a mishi chips d'in ta kawo mishi, yanzun ma saida ya kalli yatsun hannunta yana d'arsa wani abu a cikin ranshi, kad'an ya rage yaja tsaki ya tuna da kashedin Auntie, madadin haka sai yace, "Ki dawo ki d'auke ni bana ci". Ya fad'a bayan ya gama k'arewa abincin kallo. Har ta juya zata d'auko kamar yadda yayi umarni muryar Auntie ta dakatar da ita, "raihana dawo ki zauna, domin shi kina gama wani aikin ko hutawa bakiyi ba na k'ara tashin ki, kuma sai yaci". A d'arare raihana ta zauna gefenta tana wasa da gyalenta, shikam khaleefa banza yayi da plate d'in abincin ya d'auki wayarshi yana latsawa. "Wad'an can kayan fa waya kawo su?". Auntie ta tambayi raihana tana nuna mata direction d'in data ajiye kayan data kawo d'azu. Raihana da sanyin muryarta tace, "dama wanda kika ce na kawo akai d'inkin nan ne". Auntie "Kai! Iya wad'annan kuma? Ai sunyi kad'an ki k'aro kamar biyun su yanzun nan". Ba don karta yi mata musu ba da tace haka sun isa, duba da uban kayanta da aka kawo ta dasu, a haka ma ummie iya sababbin ciki tace a d'auka mata, ragowar duk ta bayar, wani ma sawarta d'aya ummie duk ta had'a dasu taba mutanen da suka fita buk'ata. A nutse ta mik'e ta futa daga d'akin don cika umarnin auntien. Futar ta yaba Auntie damar yiwa khaleefa magana a karo na biyu, "matar ka zaka nunawa ban isa da kai ba kenan?". Ajiye wayar yayi tare da yamutsa fuska idon shi kan plate d'in yace, "kinsan matsalata fa Auntie". Auntie tace, "matsalarka ta banza ta wofi,,, abinda zaka duba wannan ai umarnina ne, nasan da matsalar kuma nayi umarnin,,,". Baice mata komai ba sai kanshi da yake k'asa, ta tab'e baki a lokacin data mik'e zata shiga bedroom d'inta tace, "khaleefa duk tsaftar kafa ba zaka kai raihana ba,,,, Soo ka daina kallon kanka wani abu daban,,, ka iya cin abincin restaurant da bakasan waya sarrafa shi bama, sai a nan zaka futo da wani fi'ilin banza.....". Ta kai k'arshen maganar tare da shigewa d'akin baccinta. Shikam juya chips d'in ya dinga yi a plate kafun a d'arare ya d'auki d'aya ya saka a bakin shi. Ba don ya kwanta mishi a rai ba ya dinga tutturawa har yaci da yawa, dama yunwa yake ji sosai tsabar iyayi ne ya hana shi ci. Koda raihana ta shigo da sallama bai d'aga ido ya kalleta ba ya amsa, don yana ganin in ya kuskura ya kalleta abincin nan haramiyar shi. A inda ta ajiye wad'an can ta ajiye wad'annan ma ta koma gefe ta zauna tana buga game a wayarta. Da sallama aka turo k'ofar aka shigo, ta amsa ba tare data d'ago kanta ba, Ayman ne ya k'arasa kusa da inda khaleefa yake zaune sukayi shaking hands sannan ya zauna. Lokacin khaleefa ya gama tuttura chips d'in dole kenan ya ajiye plate d'in gefe. Ita kam raihana mik'ewa tayi a ranta tana tunanin ko tayi karambani ta d'ora musu abincin dare? Amma bari dai ta gwada. Sai ta ajiye wayarta a nan ta mik'e tsam ta futa daga parlon, Ayman yayi iya yinshi wajen ganin bai kalleta ba har ta futa. Bata sha wahalar gano inda komai yake a store na gidan ba, ta soma tunanin me zata dafa musu da zasu iya ci, a irin abincin da ake aika mata ta fara laluben d'aya, sai dai kash duk irin abincin k'asar Sudan ne auntie take zama ta shirya da kanta, a k'arshe saita hak'ura ta dafa musu jallof rice da taji wadataccen kifi. A parlour kuwa a haka auntie ta futo ta same su, ta tambayi "ina raihanan kuma?" Ayman yace, "ta futa". Kayan data dad'o ta d'auka ta shige d'akinta itama. Sunci gaba zama har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib kowa ya tashi don sauke farali. Bayan ta kammala girkin ta gyara kitchen d'in, ta adana komai a muhallin shi warmers din da ta zuba abincin ta d'auka ta kai dinning na parlon ta ajiye. Har lokacin khaleefa da Ayman suna zaune ba kuma hira sukeyi ba, hasalima football channel da Ayman ya kama duk suke kallo. Ita kam so take ta tafi amma ba tayi sallama da auntie ba. Saita zab'i zama a parlon itama zuwa lokacin da auntien zata futo. Ball d'in ta taya su kallo 4 de first time a tarihin rayuwarta data tab'a kallon ball. Suna zaune kamar kurame sai ihun y'an ball daya cika d'akin taf, koda auntie ta futo da kallon mamaki ta bisu kafun tace, "toh aini ban d'auka akwai mutane a parlon ba, Ina ta sauri in gama lissafin can in zo in sama muku abinda zaku ci sharp sharp". Raihana ce tayi magana, "ayyah auntie ai da kin gama aikin ki a tsanake, na dafa mana abincin tun d'azu ma...". Auntie tace, "Toh Allah dai yasa kada aci tara na, na tura Amarya kitchen tun yanzu....". Murmushi tayi tana rufe fuska, ita kuma Auntie tayi y'ar dariya... Daga k'amshin abincin auntie tasan zaiyi dad'i kwarai. "Akwai wanda zaici abinci cikin ku yanzu?". Auntie ta tambaye su. Ayman ne ya fara cewa, "aini zaman jiran shima nakeyi...". Khaleefa kam yamutsa fuska yayi, auntie ta tambaye shi, "Kai baza kaci ba?". Yace, "noop am okay". Ayman ta zubawa abincin ta kai mishi har inda yake, itama ta d'auki kad'an don bata jin yunwa Sam. Ta zubawa raihana nata ta mik'a mata da ruwan lemon. Ta karb'a itama ba don tana jin wata shahararriyar yunwa ba. Tana jin auntie suna ta hirar su da Ayman har ta gama cin adadin wanda gurbin cikinta zai d'auka ta ajiye ragowar a gefe. Ta d'auki wayarta da Mukullin k'ofar part d'inta tace, "Auntie Yaya Ayman saida safen ku". Duk suka amsa da Allah ya bamu alkhairy. Saida ta futa da adadin wasu mintuna sannan khaleefa ma ya tashi zai tafi, bayan ya musu sallama auntie tace, "gobe tunda safe dama ka fad'awa raihana ta shirya kuje gurin d'inkin nan ayi measuring d'inta ga kayan nan ta kawo, daga nan har passport ayi mata". Da toh ya amsa ya dusa kai ya huce abin shi. Bayan futar shi Ayman yake tambayar auntie, "tare zasu tafi Germany ne?". Auntie tace, "toh me yasa ya aureta". Gyad'a kai Ayman yayi yana nazarin wasu abubuwa a cikin zuciyar shi, ko iya zaman da sukayi yanzu a parlon auntie ya dad'a fahimtar abubuwa da yawa a rayuwar auren su. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty two4️⃣2️⃣ Kamar kullum yauma raihana bayan ta gama gyaran d'akinta ciki da waje, tayi wanka ta shirya cikin atamfarta mai kyau da tsada, bata d'aura d'ankwali ba saboda gashin kanta data tubke a k'eyarta himili guda, yanzun ma hijab ne a jikinta take shigowa parlon da yake ta d'aukar ido kamar mirror saboda gyara da yake samu, kusan sau uku kenan tana zuwa duba auntien bata samunta, duk sai ta shiga damuwa da tunanin ko lafiya.... Yana tsaye jikin windown parlon hard'e da hannu a k'irji, yadda ya zubawa harabar gidan ido kad'ai zakasan akwai abinda yake tunani. "Ina kwana". Raihana ta gaishe shi bayan ta russuna, Saida yaja iska ya furzar sannan ya bata amsa da "lafiya". Gaba tayi zata shige d'akinta sautin muryar shi ya katse mata hanzari, "ke nake jira zamu futa". Kallon kanta tayi, tako ta ina ba makusa a shigar jikinta, saita juyo kawai tace, "okay". Kallonta yayi kamar ya tambayeta wai ita bata da kayan sawa sai irin wad'an nan zunbula zunbulan hijjaban, sai kuma yaga ba hurumin shi bane ita taji zata iya. Shiya fara yin gaba ita Kuma tabi bayan shi. Da catin hannun shi ya lalubo katafaren gurin d'inkin, daga waje ta cikin glass robot ne na mace kusan guda shida an saka musu kaya daban daban na mata, kallon y'ar tsanar yayi yana yaba tsarin d'inkin dake jikin kowacce d'aya a cikin su, ga surar jikinta well shape, yana tunanin a duniya babu mata masu irin wannan shape d'in sai dangin su robbot d'in. Take Saleema ta fad'o mishi a rai, itace yasan jikinta ciki da bai, ko ita duk kyawunta a iya fuska ya tsaya, amma ta surar jiki bata da wani shape irin wannan, siririyace ajin k'arshe, koda yake shi ba komai nata yake kallo ba ita d'in gundarinta yake so da k'auna. Wayarshi ya zaro ya zuba numbobin jikin katin yayi dialing, bugu hud'u akayi picking, "muna waje". Abinda raihana taji khaleefa ya fad'a kenan, Daga can b'angaren aka ce, "okay kune doctor surayyah ta kawo kayan ku d'azu ba?". "eh" khaleefa ya bata amsa a tak'aice. "Ina futowa yanzu". Ta fad'a suka ajiye wayar gaba d'aya. Kwantar da kanshi yayi baya ita kuma raihana ta k'ame har zuwa sanda taji ana knocking murfin motar. Wata macece y'ar gayu ta ajin k'arshe kamar Auntie take tsaye daga gefen mazauninta, "sannu da zuwa Mrs Abdallah khaleefa" matar ta fad'a a lokacin da raihana ta futo, ita dai k'asa tayi da kanta ta russuna tana gaisheta, shima khaleefa futowa yayi ya d'an durk'usa kad'an yana gaisheta, Saida ta gama yi mishi kirarin rashin zumunci sannan ta amsa tana sake yi mishi Allah sanya alkhairy. "Zaka bamu 30 mint muna dawowa". Kai ya gyad'a mata ya kalli direction d'in da raihana take, sai ya ganta daban a gurin kamar irin typical matan auren nan na ajin k'asa. Sai ya d'auke kanshi yana kwab'ar kanshi da shishshigi wa lamarin rayuwarta. Matar ita ta fara yin gaba raihana tana bin bayanta har suka shiga gurin, babban shagon d'inki ne da suka kware wajen futar da kowanne design na mata daya gaji da had'uwa, a kujera suka zaunar da ita aka gabatar mata da drinks masu sanyi. Matar tasa an futo da kayan zuwa gaban raihana ta tambayeta yadda za'ayi mata da kowanne d'aya, raihana tace, "kuyi shi duk yadda ya kama". "An bamu wuk'a da nama kenan". Matar ta fad'a tana dariya k'asa k'asa. Wata matashiyar ta k'ara kira tazo zatayi measuring d'inta, ganin duk mata ne a gurin sai hankalinta yafi kwanciya ta cire hijab aka aunata sosai. Suna gamawa ta maida hijabinta, tare suka futo yanzun ma bayan tayi sallama da y'an shagon masu kirki da suke ta nan nan da ita. Yana zaune saman mota kunnen shi d'aya sak'ale da Bluetooth yana danna waya hankali kwance. K'arasowar su gurin yasa shi d'ago kai yana duban su, "mun gama doctor surayyah tace kai zaka biya duka kud'in ko?". Duk da ba suyi haka da auntie ba amma yasan dama ba zata futar da ko kwandalar ta ta hidimtawa matar shiba, baisan dalilinta ba. A take ya yiwa matar transfer na duka kud'ad'en data lissafa, sukayi sallama ta tafi su kuma suka shiga cikin mota. Tak! Babu wanda yace da d'an uwanshi har suka k'arasa wani gurin hoto, wannan karon saida ya futa sannan itama raihana ta futo, tabi bayan shi a lokacin har ya fara mata nisa. Nan ma shi yayi magana da mutanen gurin, batasan ko akan me ba ta daiga sun buk'aci ta shiga cikin gurin, hoto akayi mata akace ta d'an jira na wasu mintuna. Ta samu gefe d'aya ta zauna har aka mik'o mata hotunan a envelope. Ta karb'a ta futo. Yanzun ma yana jikin motar shi a tsaye, yana ganin ta k'araso ya mik'a mata hannu, duk da bece komai ba amma tasan dai bazai huce hotunan ba, saita mik'a mishi su, ko a yanzu daya kalli yatsun hannunta saida yaji takaici fal zuciyar shi, abubuwa da yawa a rayuwar raihana da take yi da yana da iko daya haramta mata su saboda shiya tsane shi..... D'auke kanshi kurum yayi ya zagaya driver seat ya zauna, bata da zab'i itama sai bin bayan shi. *****. "Yae engineer wai meye sirrin ne yau tunda kazo naga sai kyalli kake, kumatun ka har sun ciko". Wani kwakkwaran naushi Ayman ya kai mishi a gefen kafad'a, ya goce yana dariya,,,, shima dariyar yayi ya huce office d'in kaamil. Bai zauna ba ya mik'a mishi hannu suka gaisa, "yau ba zaka zauna ba". Kaamil ya tambaye shi yana kallon shi. Ayman yace, "Kai ai ko office ban shiga ba zaman nan bazai yiwu ba, zuwa nayi dai na fara maka godiya,,,, nagode kwarai naji dad'in shawarar daka bani". Kaamil y'ar dariya yayi yace, "yana aiki kenan". Ayman yace, "ahh sosai ma, sai dai nayi mamaki kaida ba likita ba Ina ka samu irin wad'annan dabaru?". Kaamil saida yayi dariyar shi son rai sannan yace, "Wai bakasan soyayyah ba department d'in da ba ta shiga ta koyar ba? Tana jin kowanne yare har da wanda ba me jin irin shi a wannan duniyar da muke ciki". Cikin gamsuwa Ayman yace, "na yarda da kai kam". Sai ya dubi agogon hannun shi, ya gyara zaman tabaran fuskarshi yace, "kaamil ya kamata na tafi muna da meeting nan da 2 hours soo yana da kyau na shirya kafun lokacin". Sake gaisawa sukayi Ayman ya futa shi kuma ya sake duk'ufa kan system d'inshi. ****Yana gama daidaita parking ta bud'e k'ofar zata futa, "dakata" ya fad'a da dakakkiyar muryar shi, saita janye hannunta ta saci kallon shi, waya yake dannawa, "meye account d'inki". Shiru tayi kamar ba taji abinda ya tambayeta ba, har saida ya sake maimaitawa, "ki fad'a mun account number ki zan dawo miki da kud'in da nasa ki aramun waccen ranar". Girgiza mishi kai tayi cikin sanyi da taushin muryarta tace, "Ni ba rance na baka ba,,,, ka bar shi kawai". Khaleefa fuskantarta yayi sosai yana kallonta, "bana son kyautar ki fad'a mun account d'inki nace......". Yadda yayi maganar yasa taji shakkar shi sosai, amma sai ta dake saboda tana ganin don yasa ta bawa y'an uwanta kud'in mota har sai ya biyata.... "Ni kuma nace na yafe". Ganin kamar tana jin dad'in jayayya dashi saiya zare wayarta dake kan cinyarta, tabi wayar da sauri zata rik'e yayi gefe da ita cikin zafin nama, ya wani irin zare mata ido yana mata kallon gargad'i, "ki kama kanki yarinya,,,, baki san waye Abdallah khaleefa ba ko? Tom". Fucewa tayi daga motar a nutse tana tab'e baki, a ranta tana maimaita maganar shi, "Wai batasan waye shiba, waye shi kuwa in ba wani kwallin mutum mai bak'ar zuciya da nunk'ufurcin maseefa ba kullum fuska a d'aure, nikam kada Allah ma ya bani miji irin shi....". Shima a nashi b'angaren abinda yake ayyanawa a ranshi shine, "Lallai yarinyar nan sai yayi da gaske zama da ita, don yaga take takenta tana da raini da rashin kunya....". Wayar ma bai samu abinda yake so a cikinta ba saboda tayi locking d'inta. Ganin lokacin sallah yazo dab sai ya juya ya futa daga gidan. Yini guda yau Auntie bata nan bata san inda ta tafi ba amma taje yafi sau hud'u ma'aikatan gidan suna fad'a mata bata dawo ba, ga mama haleema yau bata zoba itama, suma y'an matan da suke nan lokacin tafiya islamiyyar su yana yi suka shirya suka tafi sai kuma gobe, dama su haka tsarin aikin su yake, mama haleema ce dai take yini wata rana ma har ta kwana. Sai taji gidan yayi mata tsit duk ba dad'i. Yau ma ita tayi girkin rana a kitchen d'in auntie, ta d'auki nata ta ajiye musu nasu a warmers. Parlonta ta koma rik'e da plate d'in abincin ta zauna zata ci, har kallo ta kunna don ya d'ebe mata kewa, tana cin abincin tana kallonta a tivi har ta kammala ta ajiye plate d'in zata tashi ta d'auko ruwa. Turus tayi ganin shi zaune a parlon ya zubawa tivin idanu shima yana kallon firm d'in da ake haskawa. A d'arare ta kewaye shi ta huce, saida ta d'auko ruwan ta dawo zata sake hucewa sannan khaleefa ya mik'a mata wayarta da wasu kud'i. Tasa hannu ta karb'a k'asa k'asa tace, "nagode Allah ya k'ara rufa asiri". Bai d'auka zata karb'a har tayi mishi addu'a irin wannan ba, sai yaji zuciyarshi tayi sanyi, salin alin ta warware k'udurin da yake ranshi har ya dinga tunanin sauk'in kai gareta haka ko kuma shi d'in ne ta gani babu wasa ta kama kanta shi dai kam bai sani ba. @@@@ Ranar auntie bata dawo da wuri ba har sai yamma, kusan da matuk'ar farin ciki raihana ta taryeta tana mata sannu da zuwa. A daren ranar auntien take shaida mata ta koma bakin aiki, sai dai tana son zata nuna mata wasu sirrika irin na matan sudaniyya a kullum daga k'arfe bakwai na dare zuwa tara har na tsawon sati biyu, sannan akwai gyaran jiki na musamman da take so ta had'a mata dashi. Raihana duk da batasan ko akan meye ba amma tayi na'am, don tasan bazai tab'a zama cutarwa a gare taba. Washe gari ma kafun ta futa saida ta turo musu da karin kumallo. Raihana har kunya taji data gani, tana ganin tunda ta koma aiki ya kamata ta dinga hutawa ita ta karb'i girkin. A ranar ma saida suka futa da khaleefa, shirye shiryen tafiya ake mata ba tare data sani ba, bai kuma yi mata bayani ba. @@@@@ kwanaki da yawa sun shud'e, abubuwa suna ta faruwa a rayuwar gidan, raihana sun daidaita da Ayman suna zaune lafiya da gaisuwar mutumci a duk lokacin da suka had'u, koda wasa basu ji a ransu zasuyi wasa da aurenta na boge da khaleefa ba, basa nuna wata alama ta soyayyah a tsakanin su, saboda Ayman ya ajiye komai har zuwa lokacin da game d'in da suke bugawa da khaleefa zai zo k'arshe. Wani lokacin in ya taso aiki da yunwa, yakan yi mata text message yace ta sama mishi abinda zaici kafun ya dawo, majority ma wainar fulawa yake sawa tayi mishi. Kafun ya dawo kuwa ta had'a mishi ita ta kammaleta a dinning na parlon auntie tayi nata guri. Duk da khaleefa yana ganin yadda take b'ata lokaci wajen girki a kitchen, ta ajiye Ayman yazo ya cinye amma hakan bai tab'a damun shiba, baya jin komai akan duk yadda taga dama tayi da rayuwarta bazai sa mata ido koya takura taba. Sai a yanzu yake gane da tun can akwai kyakkyawar alak'a tsakanin ta da Ayman, wadda ba zaice ga abinda ya raba su yanzun ba. A kullum dare auntie tana koya mata wasu sirrikan gyaran jiki da turare kala kala na jiki masu kama zuciyar namiji ya tsaya bisa ra'ayi guda. Haka girki ma kalar na mutanen Sudan ta nunnuna mata, gaba d'aya ta tashi maida ita wata rik'ak'k'iyar y'ar gayun jinsin Arab cikin kwanakin, sirrikan data ajiye kunya ta bata a naira million ba za'a bata shiba. Mata me d'inki ta kawo mata kayanta har gida, lokacin ma auntie bata dawo gidan ba saboda biyawa ta gidan su iya da zatayi, sai raihana ce ta taryeta ta karb'i kayan, koda auntie ta dawo taga tsarin yadda akayi d'inkin ta yaba sosai, wasu riga da zani, wasu da skirt, wasu kuma akayi mata dogayen riguna. Komai ya kammala har dana shirye shiryen tafiyar su Germany. Ya rage saura kwanaki k'alilan auntie tasa khaleefa suje da dare ya gaishe da iyayen raihana, daga nan yayi musu bayanin tafiyar su da kanshi. Da dare raihana tana zaune a parlonta tana waya da ummienta bayan tayi sallama da auntie ta taho nata b'angaren, mita take yiwa auntien akan dalilin rashin zuwan su al'ameen gidanta har yanzu. Tana wayar khaleefa ya shigo parlon da sallama, ta d'aga idonta ta kalleshi, as usual yana sanye da white shirt da ash trosser, sumar kanshi a kwance luf yasha gyara sai d'aukar ido yake yi, tana daga inda take amma k'amshin turaren shi yazo har inda take tun kafun ya k'araso. A d'aya daga kujerun parlon ya zauna ya kalleta a lokacin da ita kuma ta d'auke kanta daga kallon shi, itama kamar kullum bazai iya tantance kayan jikinta ba saboda wani uban zundumemen hijab data kirma ko zafi bata ji. Sai ya d'auke kanshi yana sake gargad'in kanshi da shiga hurumin ta. Ganin kamar khaleefa yana son magana da ita sai ta tak'aita wayar tayi sallama dasu, a lokacin ma da hibba take waya tana ta biyewa shagwob'ar ta. Tun tana waya take ganin kamar kira yana shigowa bata maida hankali ta duba ba har ta gama, khaleefa ya bud'e baki zaiyi magana kenan wani kiran ya sake shigowa. Saita kai dubanta ga screen d'in wayar, zatayi rejecting kiran ya hanata ta hanyar cewa, "ki d'aga amma kar kiyi maganar sama da minti goma da koma waye, saboda nima ina son magana dake......". Raihana kallon shi tayi da mamaki tana al'ajabin wannan k'arfin hali da k'arfa k'arfa, shi ko kunya bwyq ji wayar ma har sai ya fad'a mata adadin lokacin da zata d'auka, ba don kada ta dinga ja dashi su samu matsala ba da ba zata d'aga kiran ba. Da sallama ta kara wayar a kunnenta, sautin muryarta daya ratsa dodon kunnen shi ya assasa mishi lumshe idanun shi tare da jin wata fad'uwar gaba, jin shiru sai raihana ta sake maimaita sallamar ta. Da kyar ya iya bud'e bakin shi da rawar baki da murya yace, "Raaiihaaanaaa". Saida ta saci kallon inda khaleefa yake zaune, hankalin shi kacokan yana kan wayarshi, sannan tace "wayee?". Ta tambaya ba wasa a tattare da muryarta. "Imran ne raihana.... Ina yi miki fatan alkhairy,,,, na kira ki ne kawai don naji muryarki karo na k'arshe a tarihin rayuwata......". Raihana batasan lokacin data zare wayar a kunnenta ta kira sunan shiba, "Imrana?". Shi kuwa tuni ya katse kiran ya had'a da kashe wayar duka, kanshi ya had'a da gwiwa a lokacin shi kad'ai yasan abinda yake ji. Ita kuwa raihana cike da tausayin shi ta sauke wayar tana maida ajiyar zuciya. Duk abinda ya faru a idon khaleefa, saiya tab'e baki don shi a tunanin shi saboda shi ta katse wayar. "Dama ina son ki shirya gobe da dare zamu futa". Khaleefa ya fad'a bayan ya mik'e yana shirin futa daga parlon. Abin ma takaici yaba raihana, wai ta shirya zasu futa bama yau ba gobe, ta d'auka wata k'atuwar maganar yazo da ita shine hadda gindaya mata sharad'i haka. Tab'e baki itama tayi ta tashi ta shige d'akinta ta rufo. *****Kamar kullum washe garin ranar ma raihana kafun ta tashi auntie ta aiko musu da break. Bayan ta gama gyara d'akin gadonta zuwa bathroom, don shine kad'ai aikinta a gidan, shiryawa tayi cikin riga da zani na wata atamfarta mai kyau, ta d'auki hijab d'in sallarta ta saka ta futo parlon donta samu sukunin cin abincinta. Koda ta gama bata koma d'akin ba, ta kunna kayan tivi tana kallon wani series. Sanye da jallabiyyah fara sol ya futo yana mik'a da salati,,,, kallo d'aya raihana ta mishi ta juyar da kanta tana duba lokaci, Sha d'aya saura y'an mintuna. "Ina kwana?". Raihana ta fad'a tana duba wayarta da sak'o ya shigo. Bata ji amsar daya bayar ba don daga labban shi sai hak'urin shi suka san ya amsa. "Aslm,,, raihanatu fatan kin tashi lafiya,,,, yau ban futa office ba saboda na tashi bana jin dad'in jikina, sai dai na futo babu komai naci a gidan auntie ta tattare komai ta aiko part d'inku keda mijin ki kuci ku rayu mu ko oho!!!". Saida murmushi ya sub'uce mata a lokacin data gama karanta sak'on, Yaya Ayman yana gida bai futa ba kenan? Saita tashi a nutse ta shiga kitchen d'inta ta d'auko plate, yana zaune kan dinning yana cin abincin shi ta k'araso a nutse,,,,, abinci ta zuba mai d'an dama ta juya tabar gurin. Babu kowa a part d'in Auntien sai mama haleema da bata dad'e da zuwa ba itama. Suka gaisa da raihana ta ajiye plate d'in a k'aramin center table dake tsakiyar parlon ta futa, saida ta koma ta tura mishi k'aramin sak'o, "kamar yadda ka buk'ata,,,, abincin ka yana part d'in Auntie,,,,". 4 mint da tafiyar sak'on ya turo mata, "thanks". Murmushi tayi ta sake gyara zamanta tana ci gaba da kallon ta. Hajiya tafeeda tana hakimce a parlonta na k'asa dai dai lokacin da Imran yake saukowa daga saman shi, ko yanzu daya ganta saida gaban shi ya fad'i, yasan saboda shi ta kasa ta tsare anan. Instead of ya huce ga abinda ya futo dashi, sai ya k'arasa cikin parlon ya durk'usa gefe yana gaisheta. Yamutsa fuska tayi ta kyab'e baki, "da ka bar gaisuwar ka Imran har zuwa lokacin da zaka gane gaskiya ka daina gaba dani,,,,,". "Kiyi hak'uri Mom" abinda ya fad'a kenan ya mik'e zai futa. "Dakata! Ina son magana da kai ai". Inda ya tashi ya koma ya durk'usa kamar wani maraya ko marar gata ya rakub'e. "Zuwa kayi zaka had'a mun case da baban ku saboda kai shashasha ne ko? Toh na soke tafiyar ka Lagos gaba d'aya, kuma auren ka bazai huce nan da wata d'aya ba insha Allahu,,,,, sai kaje ka sake yi mishi bayani.... Wannan karon ma in kaje kace mom ce ta hana kaga yadda zamu kwasheta da kai a gidan nan". Baice mata komai ba ya yink'ura ya tashi,,,,, ko kad'an baiji b'acin ran komai a ranshi ba, daga soke tafiyar har takurarren auren data shirya. Tunda ya rasa raihana gaba d'aya rayuwar shi ta dawo hopeless. Komai ya rasa yana ganin ba zai kai raihana daraja da tsada ba. Yana futa daga parlon ta lalubi number sameera ta kira, bata jima tana ring ba ta d'aga, bayan sun gaisa anji lafiyar juna take tambayarta ko Nur ta amince kuwa? Girgiza kai sameera tayi tace, "ki bari kawaii! Wallahi yarinyar nan ta k'i amincewa fafur, Ni har na fara tunanin ko mu maida auren kan y'ar uwarta kawaii". Shiru hajiya tafeeda tayi tana hamdala a cikin zuciyarta, don dama ita harga Allah shaheeda taso Imran ya aura ba nuriyyah ba,,,, Amma tunda maman su ta nuna ta bashi Nur don a rage mata rad'ad'i da tunanin masoyinta Ayman saita hak'ura dasu haka, yanzu kuma da Nur d'in tak'i amincewa sai tace falillahil hamdu. Sun ajiye waya da alk'awarin zata zo gidan in aka jima. ******Zaune take gaban mammie da hajiya tafeeda da suke kira mom, tayi ladab tana sauraron duk bayanan bakin su, "kamar yadda muka shawarta da mahaifiyar ki, tunda Nur ta k'ek'asa ta nuna sam bata son auren Imrana, mun yanke shawarar maida auren Imran da Nur kan ki, amma yanzu mun kira ki muyi shawara dake ne,,,, idan har kin amince ba b'ata lokaci mu dawo da magana izuwa ga mafarinta, Ina fatan kina sane da komai ko?". Shaheeda shiru tayi bayan ta gama jin duk abinda mamien ta fad'a, "idan har kin amince ga hajiya nan ki fad'a mata da bakin ki....". Murmushi tayi kanta a k'asa tace, "yadda kuke so mom na amince". Cike da farin ciki tafeeda ta dafa kanta tana fad'in Allah yayi miki albarka shaheeda, yasa kece abokiyar arzik'in Imrana. Mik'ewa tayi tana murmushi ta huce side d'in su, tana zuwa inda zata shiga bedroom d'insu ta sauya yanayinta zuwa na jimami sannan ta shiga, Nur tana kwance rub da ciki tana operating system d'inta shaheeda ta shigo, saita tashi zaune tana kallonta a lokacin data zauna gefen katifah ta had'a kai da gwiwa. Da taushin murya Nur ke tambayarta "meya faru Yaya?". D'ago kanta tayi tana kallon k'anwar tata kafun tace, "na amince da auren Imrana,,,,, indai hakan zaisa su hak'ura su barki da muradin ki". Cike da tausayinta Nur tace, "ayyah kada kiyi haka Yayaa,,,, don Allah kada ki saka kanki cikin matsala saboda ni,,,,,,,". Dafa kafad'arta shaheeda tayi tace, "kada wannan ya dame ki k'anwata insha Allah ba abinda zai biyo baya sai alkhairy,,,,, Zan iya sadaukar miki da komai kamar yadda kike yi mun... Fatan Allah yasa hakan ya zamo silar samun cikar burin ki...". Sai suka rungume juna Nur tana kuka tana yi mata godiyaaa.......... *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _shin kuna bibiye da littattafan in-identical twins,,,, in-identical twins sun shirya tsab wajen ganin sun nishadantar da mabiya littattafan su, merhreeyaert lerwerl da littafinta na👉🏻 JARUMAR UWA, sai doctor Ferhyeez m usmern da littafin👉🏻 DARAJAR HAK'URI masoyan mu kune alfaharin mu😍😍😍_ May all our dreams come true 🤲Happie juma'ah Mubarak,,,,,,,,, _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty three4️⃣3️⃣ Koda ta fahimci mama haleema ta d'ora girkin dare kitchen d'in tayi, duk da auntie ta hana ta shiga tace zatayi girki amma sabo da karakaina irin tata sam ba zata iya zaman ba, ita ma mama haleeman data ganta saida ta kwab'e ta, "kaddai kice girki kika zo taya wa". Tana y'ar dariya tace, "mama niba girki nazo ba kawai nazo na taya ki hira ne". Mama haleema tace, "hirar ma na yafe kije ki taya miskilin mijin ki gashi can kwance parlon Auntie wai yunwa yake ji" Raihana kujera taja ta zauna tana murmushi tace, "mama kinji abinda kika ce fa, miskili, miskilan mutane basa son magana da yawa bare wani tayin hira". Mama haleema tayi dariya, "aikuwa dai musamman irin su Khaleefa, nifa tsawon lokacin dana d'auka Ina aiki a gidan nan, bamu tab'a hirar minti goma cikakke dashi ba" cikin jinjinawa raihana tace, "Hun un". Mama haleema taci gaba da cewa, "Ayman ne dai na mutane,,,, shi kowa nashi ne". Raihana tana wanke mata albasar data yanka tace, "ai Yaya Ayman akwai son mutane, dama kinsan kowa da yanayin shi". Mama haleema tace, "sosai ma kuwa,,,, Kai raihana wannan ai wayon aiki ne, ga can shayin dana had'awa y'an biyu ki kai musu, akwai snacks a tray ki kaiwa Ayman me sugar khaleefa kuma me gishiri". Ba don taso ba ta tashi zata kai musu kamar yadda ta umarta. Suna zaune a parlon, khaleefa yana operating system shi kuma Ayman yana bashi labari, da gaske kamar yadda ya fad'a bashi da lafiyar, don ga zahiri nan har idon shi ya fad'a ciki. A gefen kowa ta ajiye mishi nashi, zata tafi Ayman yace, "thanks matar twin bro". Saita juyo ta mishi murmushi ta k'arasa futa daga parlon. Ko data koma dole mama haleema ta barta sukayi aikin tare har zuwa lokacin da auntie ta dawo taje mata sannu da zuwa, kallon khaleefa tayi a lokacin da raihana ta shigo ta fahimci ba inda suka je tace, "haka mukayi da kai?". Kallon inda raihana take zaune yayi, sannan ya kalli auntien yace, "zamuje zuwa dare, da ranan ne banjin futa". "Meyasa kake yin haka khaleefa?..... Ka kai yarinya tun safe da yamma ka koma ka d'auko ta kake jin kyashi?" Shiru yayi kanshi a k'asa bai iya ce mata komai ba, raihana kam futa tayi daga parlon. Ayman da yake zaune ganin ran Auntie ya b'aci sai yace, "kiyi hak'uri Auntie! Khaleefa yana da gaskiyar shi, maybe ya bari suje da daren ne saboda yana jin kunyar had'a ido dasu ummie da rana....". Wani kallo da Auntie ta mishi yasa shi sunkunyar da kanshi ba shiri, shi kanshi yasan ya fad'a ne kawai don ya kare d'an uwan shi, amma ba don ya fad'i abinda yake gaskiya ba. Mik'ewa tayi a lokacin da zata shige d'akin gadonta tace, "ka tabbatar kana yin sallah dama ku tafi". Kai ya gyad'a had'e da bata hak'uri. Ta shiga d'akin su kuma suka tashi don sauke farali. Raihana tana zaune bayan ta idar da sallah kan darduma a d'akin gadonta khaleefa ya turo k'ofar, bai shiga ba amma wani mayataccen k'amshi ya mishi sallama,,, irin mayen k'amshin turaren auntien shi da yake matuk'ar so, tunda take a gidan bai tab'a lek'a d'akinta ba sai yau,,, itama saita tsaya tana kallon shi da tunanin abinda ya kawo shi, ko wanka ya sakeyi oho ita dai ta ganshi da sabuwar shiga ta manyan kaya hadda hula. "Ke nake jira". Abinda ya fad'a kacal ya juya ya futa. A hankali ta futo a shiryenta, ta kukkule k'ofofin part d'in, auntie take son yiwa sallama sai dai khaleefa ya hana ta a cewar shi zata sake ja mishi delay. Har sun fara tafiya taga sun tsaya a wani babban mall, ita kam zamanta tayi a mota bata da niyyar futowa, ganin haka sai khaleefa ya tambayeta, "ba abinda zaki siya musu?". Tambayar mamaki taba raihana kwarai, wai ba abinda zata siya musu? Toh su suwa? Girgiza mishi kai tayi, yayi hucewarshi ita kuma taci gaba da zamanta. Bai jima sosai ba ya dawo da manyan ledoji biyu ya saka a booth suka ci gaba da tafiyar su. Ko kafun raihana ta banbance anguwarsu khaleefa yayi parking a k'ofar gidan su, saita kalle shi ta kalli k'ofar gidan. Lallai ma khaleefa! Dama gidan su auntie tasa ya kawo ta tun raana? Sannan su yake tambaya ba abinda zata kai musu kamar wasu bak'i a gurinta. A nutse ta yink'ura zata futa daga cikin motar ya dakatar da ita ta hanyar cewa, "wait! Idan muka shiga zakiyi musu bayanin tafiyar mu Germany tare nan da y'an kwanaki,,,,, sannan ki tattaro duk wasu takardun makarantar ki,,,, fatan kina sane da alk'awarina?". Kai kawai ta gyad'a mishi jikinta a matuk'ar sanyaye, toh yaushe tayi da khaleefa zata bishi wata uwa can duniya? Saita dafe kanta da hannunta tana tunanin yadda zata iya binshi wani guri me nisa..... Shin wacce irin rayuwa zasuyi a inda babu idon wanda yake shakka kamar auntie? Wai a haka ma yana rage wasu abubuwan saboda kada a gane ba son juna suke yi ba, shine har zai d'auke ta a motar shi ya futa da ita ya kaita tayi uzurinta ya jira su dawo tare kamar gaske. A nutse ta d'ago jin abu me nauyi saman cinyarta, babbar leda ce guda d'aya ya d'ora mata, "lokutan ki suna tafiya faa". Ya fad'a yana duba agogo. Sai a lokacin raihana ta kalle shi, yana daga waje amma hannunshi hard'e a k'irjin shi. Itama futowa tayi tana kallon shi tace, "yaushe mukayi da kai zan bika wata uwa duniya?". Murmushi khaleefa yayi yace, "dallah dallar bayani ne banyi miki ba amma na fad'a miki tun a ranar da muka fara had'uwa,,,, na fad'a miki zan samu yarinyar da nake sone kad'ai idan na cika wani sharad'i a gurin mamana, sharad'in bana komai bane face aure, gashi kuma na cika itama zata cika mun nawa, Ina fatan kin tuna.....". Ajiyar zuciya ta sauke ita kam ba zata iya fad'awa su ummie wannan maganar tafiyar ba..... Wane irin mutum nema khaleefa wai. Kamar wadda ta shekara bata zo gida ba haka taji a lokacin da take taka k'ofar gidan su. Ta sauke ajiyar zuciya mai sanyi ta k'arasa shiga gidan da sallama. Kusan su al'ameen gaba d'aya suka runtumo da gudu sukayi kanta, ta rungume su tana murnar ganin su. Tun kafun ta shiga parlon ummie suke faman bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta. Ita dai rabi ma duk ba ganewa take yi ba saboda baza ido da son zak'ulo inda ummienta take. Ajiye ledar hannunta da khaleefa ya had'o ta da ita tayi, ta zauna tare da zaunar da hibba ma kusa da ita ta tambayi al'ameen, "Ina ummie?". Kafun ya bata amsa hibba ta riga shi da cewa, "tana d'akinta tana muraji'a bari na fad'a mata kinzo Auntie raihana!". Ko amsar da raihana zata bata tsaya jira ba ta mik'e da gudu ta tafi, da ummien taci karo tana shirin shiga ita kuma tana shirin futowa. "ummie auntie raihana ce tazo.... Gata can tana jiran ki". Hibbah ta fad'a cikin tsananin farin ciki tana nuna mata inda raihana take zaune. Kamar yarinya haka raihana ta tafi da gudu ta rungume ummie cikin farin cikin ganinta da tarin k'auna. A nan parlour suka zauna, da mak'urar farin ciki suka gaisa da ummie taji lafiyar kowa cikin jama'ar gidan har abban su, shaf ta manta da wani khaleefa suka zo saida ummie ta tambayeta ya auntie da me gidan nata. "Ohh! Na manta ashe tare muka zo yana k'ofar gida...". Da mamaki ummie ke kallonta kafun tace, "wannan wane irin shashanci ne? Mijin naki kika bari a tsaye a titin Allah kamar wani bak'o?". Da muryar shagwob'a tace, "ummie toh ai mantawa nayi". "Aikuwa maza kije ki shigo dashi". Ummie ta fad'a da fuska ba wasa. Kamo hannun jidderh tayi ta mata rakiya suka futa inda yake waje. Yana nan tsaye yadda ta barshi. Har k'asa hibba ta durk'usa ta gaishe shi lokacin da suka k'arasa, abun ya burge khaleefa kwarai musamman yadda yara k'anana suka san su martaba babba irin haka. Ya amsa tare da d'ago kanta yana kallonta, yarinya k'arama amma ma'abociyar hankali da nutsuwa. "Ka shigo,,,,," raihana ta fad'a tana juyawa zuwa ciki. Shida jidderh suka jero har cikin gidan. Duk su al'ameen sun nutsu a gefe d'aya suna jira ya shigo su gaisa dashi su futa kamar yadda ummie ta musu umarni. Duka cikin ladab suka gaishe shi, ya amsa yana tambayar sunan kowanne d'aya a cikin su, "al'ameen! Hibba! Sai ke kuma jidderh abi?". Khaleefa ya tambayi jidderh da take zaune gefen shi don ita ta rattaba mishi sunan kowa. Su al'ameen da muhibba sun tashi zasu futa khaleefa ya hana su, dole suka koma suka zauna suna satar kallon raihana da batasan ma suna yiba, kacokan hankalinta yana kan khaleefa tana mamakin yadda yake ta jan su jidderh da surutu,,,,, ashe ya iya magana da yara haka? Amma bai iya da manya ba? Ko kuma sune yake yiwa magana a tsaitsaye ba russunawa oho mishi? Futowar ummie ce ta katse kowa daga abinda yake yi, babban gyale ta rufo har kanta, daga wajen k'ofar d'akinta ta tsugunna, shima sake russunawa yayi yana gaishe ta. Ta amsa a gurguje ta tashi ta koma d'akinta. Kamar jira yake su gama gaisawa ya tattara shima ya mik'e ya bawa su al'ameen kud'i yace ma raihana bari ya jirata a waje. Yana shirin futa Abba yana shirin shigowa, sai ya durk'usa a nan shima suka gaisa ya k'arasa futa shi kuma Abba ya k'arasa shigowa. Har d'akin shi raihana taje ta gaishe shi, ya amsa cikin jin dad'in ganinta da sauyawar da tayi, duk da ba k'iba ko fari tayi ba amma ta samu nutsuwa da ganin yanayinta. Ta jima suna hira har ta karb'i takardunta na makaranta da suke gurin Abban amma koda wasa bata fad'a musu batun tafiyar ta da khaleefa Germany ba. Ko data dawo gurin ummie naseeha mai ratsa jiki ta k'ara yi mata mai had'e da jan kunne, tayi shiru tana sauraron ummien har ta gama. K'ara rashewa tayi tana ta hira da k'annenta kamar a gidan zata kwana bayan taci abinci, ganin bata da niyyar tafiya sai ummie ta tambayeta, "Wai yaushe zai dawo ku tafi? Ko kuma anan zaki kwana?". "A'a yana k'ofar gida nice ban tashi tafiya ba har yanzu ummie......". Saroro ummie tayi tana kallonta da mamaki kafun tace, "raihana mijin naki kika shanya a k'ofar gida kamar wani yaron ki ko drivern ki?, Yanzu fa na gama yi miki naseeha ashe aikin banza nayi tabi ta bayan kunne". Raihana shiru tayi a ranta tana tunanin shiya sani,,,,, da ya kawota tun da wuri kamar yadda auntie taso ai data sake kamar kowa a gidan su yadda ya kamata. "Maza kije ku tattara ku tafi". Ta tsinci muryar ummie a kunnenta tana fad'a cikin bada umarni. Mik'ewa tayi ummie ta bata duk abinda zata bata ta tattara ta har wajen k'ofar parlon tana yi mata sallama da addu'a, "ki gaida gida ki gaishe da doctor surayyah, mun gode da ziyara mijin kima kiyi mana godiya a gurin shi..... Su hibba sunga sak'o Allah ya k'ara rufa asiri". Cikin muryar shagwob'a tace, "ummie kora ta kuke yi....". Ummie tace, "ehh tafi gidan ki tunda dai nan ba gidan ki bane". Y'ar k'aramar dariya tayi tace, "Allah ummie zan iya fasa tafiya ma....". Ummie tace, "toh fasa mana kiga in zaki samu gurin bacci a nan...". Dariya tayi, ummien ma tayi murmushi. "Ummie zanyi kewarku" raihana ta fad'a kamar tayi kuka. Ummie tace, "muma zamuyi kewarki muna kan yi ma,,,, maza ki gaida mutanen gidan". Murmushi raihana tayi daga haka sukayi sallama ta futa. Yana zaune cikin mota ya kwantar da seat yana kallon k'ofar gidan su, lokaci bayan lokaci kuma yakan ja dogon tsaki,,, kafun ta futo kuwa ya cika yayi fam kamar zai fashe. Kallo d'aya raihana ta mishi ta d'auke kanta a lokacin data shiga cikin motar. Yaa jima kafun ya tashi motar yayi reverse ya fara gangarawa gidan iya. Wannan karon tare suka futo, ya d'auko ledar tsarabar su, yana gaba tana bin bayan shi suka shiga cikin gidan. Malam yana kishingid'e kan madaidaicin carpet a tsakar gidan, gefen shi radion shice yana sauraron taskar labarai. Ganin su ya sashi mik'ewa zaune had'e da fad'ad'a fara'ar fuskar shi yana musu lale marhaba. A kusa dashi khaleefa ya zauna, raihana kuma ta zauna d'an nesa da inda yake tana gaishe shi. Malam ya amsa mata cikin sakin fuska har yana zolayarta "wannan tafiya ta dare ince ko anan zaku kwana....?". Murmushi tayi had'e da gyad'a mishi kai, malam yace, "yauwa koda naji". Sai a lokacin suka gaisa da khaleefa shima. Turus! Iya ta tsaya ganin bak'in da bata saka ran zuwan suba a wannan tsohon dare. Saita k'araso a hankali ta ajiye damammiyar furar malam data sa mishi a firinji wai ta d'anyi sanyi. "Wad'an nan kuma daga ina ni jikar Indo cikin uban daren nan". Murmushi raihana tayi, khaleefa kuma ya d'auke kanshi kamar baiji ta ba. Maficin gefen malam ta kwandalo mishi a keya, "kana jina ina magana kayi shiru....". Khaleefa ya dafe k'eyar shi inda maficin ya sauka yana fad'in, "ouch! toh nikam me zance miki iyaaa? Zuwa fa mukayi mu gaishe ki keda malam". "Kuka zo gaishe ni ko kuka zo kwana a gidana?". Kusan su duka murmushi sukayi saboda yadda iya tayi maganar cikin ban dariya. Sun gaisa da ita itama, kafun khaleefa ya ajiye musu ledar daya shigo musu da ita gaban su. Duk sukayi godiya. Sun jima kad'an iya hadda jan raihana d'akinta suka had'u da harira suka yita hira. Khaleefa kuwa shiru yayi a gaban malam, abinda ya alamtawa malam akwai magana a bakin shi, sai ya fuskance shi da kyau yace, "khaleefa kamar akwai abinda kake son fad'a?". Khaleefa ya kalli malam, sannan ya sauke kanshi k'asa yace, "Eh Ina son naji ko ka tuntub'i Auntie da maganar nan da mukayi dakai farkon dawowata?". Murmushi malam yayi irin nasu na manya yace, "kad'an k'ara mana lokaci, maganar tana buk'atar nutsuwa". Khaleefa yayi shiru yana wani nazari a cikin zuciyar shi kafun ya sake cewa, "na kusa komawa Germany fa! sai dai ba damuwa zanci gaba da sauraron ka". Malam yace, "Masha Allah! Surayyah ta fad'a mun waccen ranar da tazo,,, fatan Allah yayi jagora ya bada dukkan nasara...". Khaleefa yace, "ameen". Sunci gaba da tattaunawa akan aikin da abinda ya shafe shi, tare suka sha furar da iya ta kawowa malam, kafun iya ta fargar dasu dare da ya fara nisa. Yana duba lokaci kiran auntie yana shigowa, sai ya d'aga ya kara wayar a kunnen shi "da gaske baku dawo ba?". Ta tambaye shi kai tsaye. Khaleefa yace, "eh! Amma yanzun nan zamu taho". Da sauri auntie tace, "cikin daren nan kake nufin zaka taho da yarinyar mutane,,,, idan kai ka saba wasa da rayuwarka toh ita bata saba ba, ku kwana a nan da safe kawai sai ku taho". Khaleefa zaiyi magana auntie tace, "bani malam d'in". Sai ya mik'awa malam wayar yana tunanin yadda zasu kwana a gidan bayan basu zo da shirin kwana ba. Tayi magana ta mintuna da malam kafun suyi sallama malam ya bashi wayar shi. Iya da take gefe tace, "Magaji idan ba zaka kwana ba, ba dole zaka iya tafiyarka amma kai kad'ai, don raihana tayi bacci a parlour tuni". Malam yace, "ai bazai yiwu ya tafi kuma ya barta a nan ba,,,, zasu kwana tare saboda shima akwai lazimin da zan bashi yayi cikin dare". Iya tace, " zai iya kuwa? Nasan Magaji da bacci fa" malam yace, "banda neman rigima dai,,, khaleefa ne fa ba Ayman d'in da kika saba yiwa tsiyar ba tohh". Sai a lokacin khaleefa yayi murmushi. Iya kuma ta tashi ta tafi tana dariya. D'akinta ta gyarawa raihana ta bata sabuwar rigar bacci dal a ledarta fara, ta had'a mata ruwa me zafi tayi wanka ta futo ta shirya cikin kayan. Ta nad'e a lafiyayyen gadon iya sai bacci. Shima khaleefa alwala ya d'auro, malam ya fad'a mishi yadda zaiyi komai daki daki, d'akin da aka sauki raihana iya ta mishi jagora da sallayah sabuwa. Saida yabi komai na d'akin da kallo, d'akinta a gyare kamar a yada tuwo k'asa aci. Dama indai ana maganar tsabta iya k'arshe ce. Kusan kwana yayi yana sallah da addu'o'in da malam ya bashi. Tun raihana na farkawa cikin dare ta ganshi har baccin ta yayi nisan data daina farkawa ma. Da asubah ita ta fara farkawa, ta ganshi a zaune kan sallaya ya jingina da gefen gadon yana bacci. Karo na farko data tab'a tsayawa ta kalleshi, yana kama da Ayman irin kama ta sak da sak d'in nan, sai dai yafi Ayman haske sosai da murd'ewar jiki, komai nashi me sanyin kyau ne in aka d'aukewa baud'ewa da izzar maseefa fal ranshi. Hucewa tayi bayan ta gama yi mishi kallon k'urilla, a bathroom d'in ta d'auro alwala, tana futowa ta ganshi a zaune kan gadon ya had'a kanshi da gwiwa. Bata bi ta kanshi ba ta shimfid'a sallaya ta gabatar da raka'atainil fajr. Ko data idar bata tashi ba ta d'ora da addu'o'in ta har zuwa lokacin da aka kira sallar asubah, tana jin shi ya d'aura alwala ya futa ita kuma ta tada tata sallar. Kafun khaleefa ya dawo ta gyara d'akin duk da ba wani datti yayi sosai ba, ta maida kayan jikinta na asali da hijabinta, ta zauna can k'arshen gadon tana laziminta, a haka khaleefa ya dawo ya same ta. "barka da safiya" raihana ta fad'a bayan ta d'ame zuciyarta don cika umarnin auntie. "lafiya" ya amsa mata kamar kullum. Wayoyin shi ya d'auka da mukullin motarshi yace, "zamu tafi yanzu ko zaki taho anjima". Mik'ewa tayi itama ta d'auki wayarta. Ita ta fara futowa sannan shi, har k'asa ta durk'usa ta gaishe dasu iya da harira da take aikin had'a abin karin kumallo. Suka amsa iya na d'orawa da tambayarta, "ba dai har zaku tafi ba?". Khaleefa da yake bayanta yace, "eh iya tafiya zamuyi". Iya tace, "haba magaji ai ka bari rana ta futo ko?". Durk'usawa yayi ya gaishe su d'aya bayan d'aya. Suka amsa da sakin fuska. Ya tambayi ko malam ya dawo zaiyi mishi sallama, iya ta fad'a mishi malam bai dawo ba,,, watak'ila shida shigowa ma sai rana tayi haske. Ba don iya taso ba sukayi mata sallama suka tafi. *****Malam yana zaune yana cin abinci iya na gefen shi, labarin tafiyar khaleefa Germany yake yi mata da ranar da zasu tafi d'in. Iya da mamaki take tambayar shi, "Amma khaleefa ba dai zurfin ciki ba, kasan Allah bai fad'a mun ba, koda yake zamu gidan nida harira kwanan nan zan had'u dashi ai". Malam ya jinjina kai yace, "shin wai ko kinsan yaran nan basa son junan su kuwa?". Da mamaki iya tace, "wad'an ne yaran kenan malam?". Malam yana sake jinjina al'amarin yace, "Abdallah da raihana nake magana a kai". Iya shiru tayi kafun can malam ya sake cewa, "Ina tunanin akwai abinda yake shirin faruwa tsakanin uwa da yaranta, lallai wani abu mai girma yana tunkaro surayyah". Rausayar da kai iya tayi, don inda sabo ta saba da irin wannan maganganun na malam, har yanzu ta kasa fahimtar abinda yake tunkakar surayyah da malam yake magana a kai, gashi kota tambaya baya wani tsayawa ya mata cikakken bayanin da zata fahimta. Sai ta mik'e tana fad'in, "toh Allah ya iyakan ce mata". Malam ma yace, "ameen" a lokacin da yake gyara hannun rigar shi zai fara cin abinci. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty four4️⃣4️⃣ Da yamma raihana tana tsaye a kitchen d'inta tana kallon kayan kitchen d'in da bata tab'a amfani da komai a cikin suba, saboda auntie data haramta mata aikata hakan, a cewarta akwai inda ake buk'atar girkinta fiye da nan gidan. Yanzun ma sanye take da doguwar rigar atamfa, sai dai ko kalar atamfar ba'a gani saboda yadda hijabin ya sauka kamar zai rufe tafin k'afarta. Ajiyar zuciya ta sauke ta futo a hankali ta zauna cikin parlon, tana daga nan taji dawowar Auntie, sai da ta bari aka d'auki wasu mintuna ta tabbatar ta nutsu ta huce gajiyar aiki data d'auko sannan ta tashi ta nufi saman. Sai dai kamar tare suke da khaleefa tana zama ko gama gaisawa ba suyi ba shima ya shigo. Saida suka gaisa auntie ta fara tambayar shi yadda sukayi da iyayen raihana jiya. Khaleefa yayi k'asa da kanshi yace, "ita zaki tambaya auntie". Kama hab'a auntie tayi tana kallon shi, cikin had'e rai da harshen Arab tace, "khaleefa dama munyi haka da kai? Toh wallahi ka kama hanya anjima da dare kaje kayi musu bayani da kanka tun kafun naja layi tsakanin ka da Germany kowa ya huta...". Baice mata komai ba, har ta gama maganarta ta tashi ta bar musu gurin, raihana ma mik'ewa tayi ta futa, ta rasa abinda yake had'a khaleefa da auntie rigima,,, Koda bata ji abinda auntie ta fad'a ba tasan fad'a ne takeyi akan wani abu daya yi mata ba dai dai ba, abinda bata tab'a ji ko gani sunyi da Ayman ba, magana d'aya ce take had'a su ta raba su, amma khaleefa saita b'ata rai yake yin abu komai muhimmancin shi. A daren ranar ba don yana so ba ya shirya ya koma gidan su raihana, Abba ya yiwa maganar tafiyar, a take kuwa ya nuna amincewar shi, "tunda matar kace mu meye namu a ciki khaleefa! Ka d'auketa ku kewaye duniya ma". Ya d'ora da mishi addu'o'in fatan alkhairy da samun nasara. Sun rabu yau ma bayan khaleefa ya gaisa dasu hibba ya basu tsarabar biscuits, sukayi godiya suka bashi sak'on ya gaishe musu da Aunty raihana". Yace zai fad'a mata, ya musu sallama ya tafi. Yau ko gidan iya bai tsaya ba, sai number haeydar daya kira ya tambaye shi ko yana gida. A k'ofar gidan su yayi parking ya fad'a mishi ya k'araso, koda haeydar ya futo yaso su shiga daga cikin gidan ya gaisa dasu mammie, sai dai khaleefa ya nuna mishi yana sauri ne sai ko in ya sake dawowa. Suka gaisa a gurguje ya huce gida. Rayuwa taci gaba da tafiyar musu lafiya kamar yadda suka fara, suna zaune cikin mutumci da mutunta juna, tsakanin raihana da khaleefa suna gudanar da rayuwarsu ba takurawa ko tsawwalawa ga juna. Khausar da Salma sunzo mata yini, taji dad'i kuwa suka yini suna hirar su ta zumunci, har Salma na mata albishir da cikin khausar,,, taji dad'i ta taya ta murna sosai, ko kafun ta tafi saida ta raka su gurin auntie da yamma suka gaisa da ita, khausar aka fara d'auka sannan Salma ma mijinta yazo suka tafi daga baya. Har suka gama yinin su suka tafi basu ga khaleefa da idon suba, saboda ranar ya tashi baya jin dad'in jikina shi kusan wuni yayi a kwance cikin d'akin shi. Shirye shiryen tafiyar su Germany ya kammala, auntie ta had'awa raihana turaruka kala kala, ta adana mata su yadda ba zasu fashe ko su zube cikin kaya ba. Ta sake k'ara mata wasu itace na hawa dasu dilke da yadda zata had'a ragowar kayan gyaran jikin kamar yadda ta koya mata, sai dai ta umarceta da kar ta fara amfani da komai inba turaren wuta na d'aki dana jikinta ba har zuwa lokacin da zata cika wani adadin lokaci, in lokacin yayi kuma ita da kanta zata fad'a mata. Sam raihana bata gane kan karatun Auntie ba, kuma bata takura kanta lallai saita gane d'in ba. @@@@@@ Cikin satikan da suka biyo baya aka tsaida maganar auren shaheeda da Imran, basu sa da yawa ba don bazai huce nan da watanni biyu masu zuwa ba. Farin ciki a gurin hajiya tafeeda ba'a magana, sai yanzu taji hankalinta ya kwanta d'anta zai auri irin matar da take so, gashi yanzu Imran ko musu baya yi mata akan komai, ranar data tura shi ganin shaheeda ma uban shopping d'in da ya mata, saida tayi ta saka mishi albarka bata shirya ba, don yayi abun da bata tab'a zato ba. Mahaifin shi kam ya tattara ya zuba musu ido, yaga iya gudun ruwan hajiya tafeeda, dama tun daga fasa auren raihana da Imran yayi afuja'atan yasan akwai wata a k'asa, bai sake tabbatarwa ba saida maganar shaheeda ta shigo,,, saiya zab'i yin shiru yaga iya gudun ruwanta akan yace komai. Sameera kam har office d'in surayyah taje a wani yammaci tana gab da tashi daga aiki. Ta zauna kan kujerar da takan ga patient tace, "sannu da aiki doctor surayyah". Surayyah da take aiki a system d'inta tace, "yauwa sannun ki". Sameera tace, "nasan zakiyi mamakin ganina a office d'inki ko?". Surayyah ba tare da tabar aikin da take yiba tace, "ba abun mamaki bane sameera, tunda nan asibiti ne, maybe kinzo ganin likita, duk da baki bi tsarin da ake bi na ganin likitan ba...". Murmushi sameera tayi ta sake cewa, "zaki iya tunanin haka tunda kin manta wacece ni a gurin ki". Rufe computer gaban ta tayi ta fuskanci sameera tana kallonta da kyau tace, "meya kawo ki?". Duk da sameera taji ba dad'i da tambayar da surayyahn ta mata, amma saboda ita sulhu take nema saita dake tace, "zuwa nayi in fad'a miki an tsaida maganar auren Imran da shaheeda". A hankali ta zame farin medical glass d'in idonta ta mik'e tsaye hannunta biyu hard'e a k'irjinta tace, "Allah ya sanya alkhairy yasa abokin arzik'in tane....". Sameera tace, "ameen, kece mutum ta farko dana fara fad'awa saboda a cikin k'awayena bana da kamark har gobei". Murmushi surayyah tayi tace, "kina da wadda ta fini mana, ko hajiya tafeeda a yanzu aita fini a gurin ki sameera... Shawara d'aya dai dazan baki shine,,,, *kibi komai a sannu, akwai alak'ar da sam bata buk'atar kusanci me yawa ko ja a jiki, Ni kaina bansan haka ba sai cikin shekarar nan data zomun da tarin sauye sauyen alkhairy da sabon karatun mutanen duniya*" Sameera da tayi tsam tana sauraronta cikin son rarrabe abinda take nufi da kowacce kalma d'aya data fad'a amma ta kasa, murmushi tayi tace, "kamar kina son cewa wani abu kan maganar auren Imran da shaheeda zatayi?"" dogon numfashi surayya taja kafun ta sake cewa, "sameera rayuwa da kike ganinta ta huce duk yadda muke tunani da tsammaninta, magana ta ba akan shaheeda ko Imran nayi ba......". Ta k'arasa fad'a tana had'a jakarta don lokacin barinta office yayi. Sameera kam sake tara hankalinta tayi, tasan surayyah ta fita wayewa, ilimi da gogewa a harkar jama'a, bata kasance ma'abociyar shagwub'e da k'ananun maganganu ba, sai dai batasan dalilinta na fad'a mata magana me harshen damo ba a yanzun. Bata da wani zab'i wanda ya huce ta kama hanyarta, don surayya ta rataya Jakarta tuni tana neman key ta futa a office d'in. Tabi bayan surayyah da har ta kusa k'ofar futa tace, "Nima tafiyar zanyi ai, Nagode da shawara k'awata, na barki lafiya". Gyad'a mata kai surayyah tayi tana murmushi, har ta fuce idanunta suna kanta, tana iya ganin wauta tsirararta cikin mu'amular sameeran, sai dai masu iya maganar bahaushe suka ce duniya tafi bagaruwa jima kuma bari ba shegiya bace da ubanta. Saita girgiza kai ta k'arasa futa daga office d'in a tsanake. Ya rage kwana uku raihana su tafi Germany, auntie ta wakilta khaleefa ya kaita tayi sallama da duk wanda ya kamata, sannan ya jirata har ta futo, inda ya dace a ganshi a sanshi kuma ya shiga ya kwashi gaisuwa. Khaleefa ji yayi kamar ya d'ora hannu aka ya rushe da ihu lokacin da yaji tsattsauran takunkumin da auntie ta d'aure shi dashi, Babu yadda ya iya haka ya wuni yana yawo da raihana da uban zundumemen hijabin daya rasa ubanda take b'oyewa a cikin shi, ta gidan su ta fara, bayan ta gama kukan yadda zatayi kewar su inta tafi, ummie ta had'a ta da d'an abinda take tunanin zai bata wahalar samu a can, ta kuma tursasa mata ta shiga gidan wan mahaifinta ta gaishe su tayi musu sallama, dama daga nan tace direct ta k'arasa gidan Innah. Ba don ran raihana yaso ba ta k'ara neman wasu mintuna a gurin khaleefa ta shiga gidan, rabonta da gidan harta manta, muneer yana zaune a tsakar gidan yana cin abinci, ummukulsum kuma tana wanke wanke. Duk turus sukayi suna kallonta, daga gefe d'aya ta rakub'e tana gaishe da muneer, ya amsa mata babu yabo babu fallasa, ganin shiru shiru gidan kamar sai su biyu a ciki saita tambayi ummukulsum, "ummah salaha bata nan ne?". Ummukulsum tace, "eh ta futa asibiti ganin likita". Raihana tace, "ayyah in tazo kice ina yi mata sannu". Ta yink'ura zata tashi Ali ya futo ashe yana ciki, Saida gaban raihana ya fad'i data ganshi don basa kwasheta ta dad'i dashi, ya tsaya a gabanta yana tambayarta, "uwar me kika shigo yi mana a gida...". Bata tanka shiba don tuni cikinta da yake murd'awa kad'an kad'an ya sake hautsinewa, sai ta fara neman hanyar da zata rab'a ta futar musu daga gidan su. Sai dai Ali ya hana ta wai lallai saita fad'a musu uban da ta shigo yi gidan. Ga muneer a zaune yana kallo amma ya d'auke kai kamar baya gurin. Ganin in bata zage ta kwaci kanta a gurin Ali ba zai iya yi mata haukar shi sai tace, "zuwa nayi in gaishe da umma salaha kuma tunda bata nan ka bani hanya in huce....". Wata uwar tsawa ya daka mata, "k'arya kike munafuka ba abinda ya kawo kiba kenan.... Zuwa dai kikayi kinji k'ishin k'ishin Yaya muneer ya dawo toh ta Allah ba taki ba, kwanan nan zai koma ba dawowa yayi dindindin ba ehe, sai aje a fad'a musu wad'annan munafukan guda biyu na gida da suke ganin kowa a banza suna ganin kamar ku kad'ai zaku ci gaba....". Nau'ikan cin mutumcin da Ali yake yasa ta silalewa ta gefen shi kamar zata gogi jikin shi ta fuce ba tare data saurare shiba, madadin ya rabu da ita tunda ta futo saiya biyota har k'ofar gida yana wasu maganganun na rashin mutumci. Khaleefa tun tana ciki yake jin zantukan Ali sama sama, baisan da raihana yake ba saida yaga ya biyota har waje yana maganganun. Bata saurare shiba taci gaba da takawa har inda khaleefa yake jiranta a saman mota, ta bud'e murfin da nufin shiga ciki ko zai rabu da ita, yayi saurin datse k'ofar, "dallah malama ki saurara, ke har kin isa Ina magana ki share ni? Wacece ke? Me akayi aka yiki banza a wofi...". Dafe kanta tayi da hannunta d'aya tana Allahumma ajirni fil musibati waklifni khairan minha, khaleefa da yake gefe yana kallon su baiyi yink'urin sa musu baki ba don baisan alak'ar da take tsakanin suba, watak'ila family issue ne irin nasu da bai shafe shiba. Mutane har sun fara tsayawa, ganin haka sai raihana ta sake k'ok'arin bud'e murfin motar a karo na biyu, wannan karon da k'afa ya buga motar yace, "ki saurara mun keda wannan banzar gwangwanin da aka siya da kud'in Haram, kud'in zinaaa! Mijin naki duk garin nan waye baisan uwarsu karuwa bace data haife su shegu,,,,, ko bakisan munsan shida wancen d'an uwan shed'ancin naki da kuka gama gantali hotel hotel basu da uba ba......". Raihana wannan karon kasa hak'uri tayi don ya gama k'ure hak'urin ta, tace cikin fushi har idonta na sauya kala, "ka fad'i duk abinda zaka fad'a a kaina amma kada ka sake ka tab'a Auntie, don banga had'in ka da ita ba, baiwar Allahr da bata jiba bata gani ba....". Kamar abinda yake jira kenan ya d'aga hannu zai zabga mata mari aka rik'e hannun shi ta baya babu zato. Tare duk suka waiwaya, khaleefa ne tsaye yake kallon shi fuska ba wasa, yau raihana taga abinda bata tab'a gani daga gare shiba wato fushi, yana da wani irin ra'ayi na baud'ewar hali da rashin fahimtar komai a yadda yake, amma zaiyi wahala kaga fushin shi cikin sauk'i, don yana da shanye abu. Da wata irin murya me fudda sautin fushi yace, "ka fad'i duk abinda zaka fad'a a kaina da mahaifiyata amma kada ka sake kace zaka tab'a ta,,,, don ita ba tsarar ka bace". Yadda yayi maganar kad'ai ya firgita Ali ya shiga rawar jiki daga ta ciki, zubi, tsari da zarrar duk ba irin nashi bane, ya tabbatar ya shiga hannun wannan giant d'in bazai sha ba. Sai ya fara k'ok'arin warce hannun shi, sai dai ba rik'on wasa khaleefa ya mishi ba, gashi sai wani irin kallon gargad'i yake jefa mishi. Saida ya tabbatar yayi ladab sannan ya saki mishi hannu ya bud'ewa raihana front seat ta shiga ta zauna, shima ya kewaya mazaunin driver ya shiga. Har suka bar layin Ali bai ce k'ala ba sai ajiyar zuciya da yake ta saukewa a b'oye. A ranshi yana fad'in, Wannan karon kam tasha amma next time suka had'u babu wannan guy d'in sai ya yagata yaga uban daya tsaya mata. _nikam nace inka ganta kenan😜 lolll_ Suna tafe tana satar kallon khaleefa daya cika mak'il. Da kyar ya iya bud'e baki ya tambayeta anguwar da suka nufa, ta kwatanta mishi har suka k'arasa. Ko data shiga gidan innan duk zuba mata ido jama'ar gidan sukayi suna kallonta, mutane k'alilan suka iya amsa sallamarta. Saida ta gaishe su sannan ta tambayi ko Inna tana ciki, Inna tana daga ciki amma kunnenta na waje, sai kuwa cewa tayi, "eh Ina nan waye yake nemana?". Raihana salin alin ta nufi d'akin, sai dai daga bakin k'ofa ta dakatar da ita, "tsaya daga nan.... Yau kuma wanne sharrin da gayyar maseefar aka d'ebo aka taho mun dashi gida? Dama da farko kar ki fara fad'a mun mijin ki ya sake ki kinzo nan yaji, gidana beyi kama da mafakar y'an iska ba, Ni dama nasan a rina wannan uban lefe akwati Sha hud'u kamar me yankan kai ai wallahi nasan da walakin goro cikin miya, ba iya rik'e ki zaiyi ba atohh! Shiyasa dai a rayuwar nan ka dinga ajiye kanka inda Allah ya ajiye ka, bawai ka dinga zurma kai kana shiga inda Allah bai kaika ba". Tunda ta fara magana raihana tayi shiru tana kallonta ko kwakkwaran motsi ta kasa yi, har yanzu ta kasa yarda wannan ita ta haifi Abban ta. Saida taja mata addu'o'i sannan ta russuna ta fara gaisheta,,,, aikuwa nan ma ta d'aga mata hannu da sauri, "ki fad'i abinda ya kawo ki ba sai kinji lafiyata ba, Ni banson tsugudidi da munafurcin banza". "Haba innah aikya bari kiji abinda ya kawota tukun ko? Ina ganin zuwa fa sukayi su gaishe ki tare suke da mijinta yana k'ofar gida". Wata daga cikin y'an uwanta da suke gidan ta fad'a. Sai a lokacin Inna ta sassauta tace, "wato shine kika barshi a waje salon kija ya tafi dani a baka yana barbad'awa mutane bani da mutumci, toh ai sai ki ce masa ya shigo ko?". A nutse raihana ta juya ta futa, khaleefa yana tsaye a k'ofar gidan ya tokare k'afar shi d'aya jikin gini, a gefe ta tsaya cikin taushin murya sosai tace, "ka shigo ku gaisa da Inna". Kallonta yayi kafun ya yamutsa fuska yace, "wacece innah". A tausashe tace, "ita ta haifi Abbana". Wayar shi ya mayar cikin aljihun shi kusan duk abinda ta fad'a akan kunnen shi, don ba a hankali take maganar ba, kuma gidan duk da an zamanantar dashi ba'a k'ara mishi tsayin katanga ba, "muje". Ta sauke b'oyayyar ajiyar zuciya, don da khaleefa yace bazai shiga ba nan ma wata ce daban, abun har ummienta sai ya shafa. Mutanen gidan kallon su suka dinga yi, don da yawan su sun futo ne su ganshi, suga wanene ya auri raihana, tunda lokacin biki basu samu ganin shi ba gaba d'aya. Saida ya gaggaisa dasu sannan suka k'arasa ciki gurin innah suka bar su nan suna k'us k'us. Wani abun mamaki Inna har da shimfid'awa khaleefa darduma ya zauna, itama saita rab'a gefen shi taci albarkacin shi. Tarba ta mutumci hadda ruwan Sha me sanyi a fridge. Shikam tunda suka gaisa bai iya cin komai ba. D'akinta fes fes kamar a yada tuwo aci, ga ko'ina a gyare kamar ba gidan tsohuwa ba, (saboda Abba ba k'aramin gyara yayi mata a gidan ba). Inna ta shangare baki tana ta bawa khaleefa labarin dangin su da mutumcin kowanne mutum ciki, tana ta kushe raihana da mamanta kuma, shi dai yana jinta kawai. Da suka tashi tafiya ya ajiye mata kud'i masu yawa, raihana gudun kada taji labarin tafiyarsu ta bar mamanta cikin matsala saita tsaya ta fad'a mata batun tafiyar su Germany nan da kwanaki k'alilan. Ai da gudu Inna ta futo ta tara jama'ar gidan tana fad'a musu raihana zata tafi k'asar waje,,,,, "gaskiya dai rukayya munafuka ce, ashe tun asali kunsan da maganar tafiyar amma kuka ja baki kuka tsuke saboda bak'in mugun abu,,,, Kai Allah ka raba mu da sharrin rukayyah....". Ita dai raihana shiru tayi kanta a k'asa ta kasa cewa komai. "Toh yanzu da kika fad'a mun, me kike son ni nayi akai". A sanyaye raihana tace, "ba komai dama.... dama sallama zanyi miki" Sake kyab'e baki tayi tace, "oh! Toh Allah ya kiyaye hanya". Jiki a sanyaye raihana tace, "ameen, sai anjima". "Toh sai a gaida gida ko" y'an gidan suka fad'a, a lokacin da take huce su jiki a sanyaye. Khaleefa yana tsaye jikin bangon gidan, sai dai duk abinda ya faru akan kunnen shi wannan karon ma yaji komai. Koda suka fara tafiya raihana kasa rik'e hawayenta tayi, saita kife kanta a gwiwarta ta fashe da kuka mai ban tausayi, ta rasa wannan wane irin bala'i ne, dangin uban su amma kamar basu had'a komai ba, a hankali khaleefa ya rage gudun motar yana kallonta da tausaya, don shi a rayuwarshi ya tsani sautin kukan mace gaba d'aya, saboda shine abu na farko da yake nuna rauninta. A hankali ya gangara gefe yayi parking motar, shiru motar ba sautin komai sai sheshshekar kukan ta. Kuka takeyi irin mai ban tausayin nan. Hannun shi ya d'ora saman kanta ya d'ago fuskarta da take sharkaf da ruwan hawaye. "Kiyi hak'uri don Allah! Amma kukan ki.... Komai yayi farko dai yana da k'arshe raihana, da sannu gaskiya zata fallasa kanta.... Soo kiyi hak'uri kawai....". Khaleefa ya samu bakin shi da fad'a cikin sigar rarrashi bayan ya d'ago kanta ya jingina ta da jikin kujerar da take kai. Da tafin hannun shi ya dinga share mata hawaye yana sake bata hak'uri. Kamar wata sakarai haka raihana ta zuba mishi ido tana kallon shi, sam bata d'auka ya iya magana da tattausan harshe irin haka ba. Janye hannun shi yayi ganin tayi shiru ya fara k'ok'arin tada motar yana tambayarta, "sai wacce anguwa kenan?". "Layi na gaba da wannan". Ta bashi amsa fuskarta na kallon gefe. Baisha wahalar gane gidan ba, saboda tsiran ba yawa sosai, saida ta sake daidaita yanayinta zata futa daga motar ta tsinkayi muryar shi yana cewa, "in kin shiga ki fad'a musu zan shigo mu gaisa". Gyad'a mishi kai tayi a sanyaye ta nufi cikin gidan. Khaleefa ya bita da kallo har ta shige, haka kurum yaji yana son sani da ganin da yawa daga cikin danginta, yana son rairaye da tantance abinda yake wakana cikin rayuwarta, ta wata fuska rayuwarta abun tausayi ce kamar tasu, duk da bata tab'a ce mishi ga matsalar taba amma yau d'aya ya fara wani karatu cikin rayuwarta, ya kuma sake cin k'udurin inganta rayuwarta ta yadda watarana duk sai sun raina kansu idan suka ganta, suka ga mijin da take aure, sai ya sake kwantar da kanshi jiki yana duba kiran da yake shigowa wayarshi akai akai, Muhammad ne sai dai baya jin d'aga kiran kowa a cikin su a halin yanzu. Raihana kuwa koda ta shiga ummah tana d'aura alwalar sallar la'asar a bakin famfo, da murnarta ta taryeta tana yi mata lale marhabin. Har cikin parlonta ta kaita sannu da zuwa tak'i k'arewa. Saida suka gaisa raihana take fad'a mata tare suke da khaleefa a waje. Aikuwa Ummah ta kora ta taje ta shigo dashi. Raihana ta futa tana dariyar fad'an da ummah takeyi bilhak'k'i kan me tabar khaleefa a waje ai shima d'an gida ne. Yana cikin mota tayi knocking glass d'in side dinda yake. Kusan tare suka jero har cikin gidan. Raihana ta shige d'akin gadon ummaa ta barsu tare nan a rumfa suna gaisawa. Kwanciyarta tayi har saida taji ummah tana kwad'a mata kira sannan ta futo, a kusa da ita ta durk'usa tace, "gani ummaah". "Maza ki zuba mishi ruwa a buta zaiyi alwala, ki shimfid'a mishi darduma yayi sallah". Da toh ta amsa, ta kalli inda khaleefa yake zaune, by lucky idanun su suka fad'a cikin na juna. Sai taga ya sakar mata murmushi. A ranta tace toh sabon salo Ta d'auke kanta kamar bata gani ba ta nufi waje. A k'aton tsakar gidan ta d'auki buta dake can k'asan bishiya ta tarar mishi ruwan. Kafun ya gama alwalar ta shimfid'a mishi k'atuwar darduma a gefe d'aya. Yana tada kabbarar sallah tayi cikin d'akin ummah ta sake kwanciyar ta, duk yadda take son daurewa ciwon cikinta ta kasa, hak'urin ta yana neman gazawa. Khaleefa koda ya idar da sallar zaman shi yayi dirshan yana ta hira da ummaah hadda cin abinci, haka kurum yaji matar ta kwanta mishi a rai, da nutsuwarta da tsabtar ta da addininta sai yake ganin kamar iya tasu. Shida kanshi ya yiwa ummah bayanin tafiyar su Germany, ta yita musu addu'o'i da fatan samun nasara. Lokacin daya tashi tafiya ummaah ta dinga kwalawa raihana kira bata jiba saboda bacci daya fara fizgarta. Har saida ta shiga d'akin da kanta ta tasota tana mata fad'an baccin la'asar, hadda fad'awa khaleefa duk lokacin da yaga ta kwanta da la'asar kada ya saurara mata. Khaleefa yayi murmushi yana sake yaba nagartar baiwar Allahn. Itama saida ya ajiye mata kud'i masu yawa sannan ya tafi, raihana ma sukayi sallama ta tafi. Bata iya zuwa gidan kowa ba daga nan saboda yadda ta gaji ga ciwo da cikinta yake sai gida. Suna zuwa yana parking dama ta futa gudu gudu sauri sauri ta shige d'akin gadonta, ta fad'a kan bed ta kwanta tana jin yadda ciwon yake sake nuk'urk'usarta. Khaleefa kamar ya bita yaji abinda ke damunta sai kuma dai ya share, yana rufe murfin motar shi Ahmad yana futowa daga saman part d'in Ayman. "Man wai ina ka shiga ne, nazo tun safe ina neman layinka baka picking". Murmushi yayi a lokacin da Ahmad ya k'araso sukayi side hug yace, "Kaine kake kirana ko Muhammad? Don ni kiran Muhammad nake ta gani". Ahmad yace, "Muhammad d'in ma yana neman ka, nima kuma ta number Muhammad d'in na kira ka". . "Amma lafiya kuwa?". Khaleefa ya tambayi Ahmad yana kallon shi. Ahmad yana y'ar dariya yace, "lafiya lou kawai ka basu shawara ne kyauta.....". Happie juma'at Mubarak mah fans, fatan kuyi hutun k'arshen mako lpy. Kwana biyu sai nake ga kamar JARUMAR UWA ya fara futa a kanku shiyasa bakwa comment yadda ya kamata🤦‍♀️ Ina so dai a kullum ku sani, comment d'inku shine kwarin gwiwar mu marubuta _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty five4️⃣5️⃣ Cikin rashin fahimtar inda zancen Ahmad ya nufa khaleefa yace, "kayi mun bayani yadda zan gane Ahmad''. "Toh aure zai d'aura gobe". "Ah haba! Amma ya mamaye mu, dama anyi engaged ne?". Ahmad yace, "a'a duka baifi one week dayin maganar auren ba, wai ya koya daga gare ka, akwai abinda ka hango idan ka koma Germany ba aure, kasan shi dama kullum me kwaikwayon kane". Murmushi yayi suka jera zuwa cikin parlon, bai expecting ganin taba shiyasa suka shiga ba tare da sun nemi izini ba. Turus! Khaleefa ya tsaya daga bakin k'ofa, karo na farko da yaji bari ya taimaka mata wajen kare mata mutumcinta kamar yadda take takatsantsan a koda yaushe, mukullin hannun shi ya kad'a mata. Ta tashi zaune da sauri tana kallon direction d'in da yake tsaye. Ganin kamar akwai mutum a bayan shi sai taja jikinta tayi cikin bedroom d'inta da sauri. Koda suka shiga khaleefa saida ya d'aukowa Ahmad ruwa me sanyi da copi sannan ya zauna suka gaisa, ya tambayi lafiyar y'an gidan su dashi kanshi Ahmad d'in. Shiru ya biyo baya tsakanin su kafun Ahmad yasha ruwa ya tambayi khaleefa, "Man kasan tun waccen ranar a duhu ka ajiye ni fa". Kallon sakanni uku zuwa hud'u ya mishi yace, "game dame fa". "Auren ka ba shiri da yarinyar dana tabbatar babu b'urb'ushin sonta a zuciyar ka, tunda ni dakai duka munsan Saleema kake so, kake son aure...". Khaleefa Koda ya gama sauraron shi murmushi yayi ya gyara zaman shi da kyau kafun yace, "maganar ka tana hanya Ahmad, duk da a halin yanzu bazan iya ce maka komai ba in banda na jaddada maka abun nan dai daka sani, Ina son Saleema kuma bana mafarkin rayuwa da ko wacce mace bayanta,,,, amma aurena da raihana na baka wuk'a da nama ka fassara shi ta kowacce fuska da tayi maka.....". Da matuk'ar mamaki Ahmad yake kallon shi, sama da shekaru ashirin suna tare tun lokacin k'uruciya amma har yanzu ya kasa fahimtar wane kalar mutum ne shi, Koda yake shi zuwa yanzu ma ya kamata ya daina mamakin al'amuran khaleefa gaba d'aya, ya taya shi da addu'a kurum. Sai ya wanzar da murmushi take a fuskarshi yace, "Tom Allah ya zab'a maka abinda yafi alkhairy a rayuwar ka". Khaleefa ya amsa da "ameen" ba don addu'ar ta gamsar dashi a zuciyarshi ba. *****A daren ranar raihana kasa bacci tayi saboda tsananta da ciwon cikinta yayi, dama saida auntie ta lura da yanayinta tun farkon dare ta tambayi ko akwai abinda yake damunta, tace ita fa lafiyarta lou, a lokacin bata d'auka ciwon zaici gaba bane sai kuma gashi, haka ta gama murk'ususunta ta tashi ta d'aura alwala ta dinga karanto duk addu'ar da tazo bakinta, a haka ciwon ya gama sharafin shi ya lafa. Da safe ta tashi kamar batayi ciwon komai ba, sai dai duk jikinta ba kuzari, ta shirya cikin shigarta mai kyau ta d'ora hijab d'inta ta futo parlour tana kallo. Tana nan khaleefa ya futo cikin riga da wandon shadda, kanshi babu hula sai gashin kan da aka saisaye aka rage mishi yawa. Kallo d'aya raihana ta mishi ta d'auke kanta ta mayar kan tivin dake magana a parlon. Saida yazo dab da inda take zaune sannan ta gaishe shi, bai amsa ba sai zuba mata ido da yayi yana kallonta kamar me karantar wani abu. Cikin murya mara amo kuma yace, "ko zan iya samun abinda zansa a cikina kafun na futa". A nutse ta mik'e ta isa gurin da mama haleema takan ajiye musu abincin karin su duk safiya. Plate biyu tayo saboda itama bata ci komai ba, ta mik'a mishi nashi, itama tayi gefe da nata. Har ya gama ci ya ajiye mata plate d'in ya fuce bata fara cin nata ba, sai tsakura da take kad'an kad'an. ****An d'aura auren Muhammad a anguwar su dake...... Bayan d'aurin aure sun gudanar da reception da ango ya shirya don abokan shi kad'ai. Da zasu tafi Ahmad da khaleefa suka ajiye mishi kud'i masu yawa gudunmawa. Ya karb'a da kyar bayan sun takura mishi yana godiya. Lokacin da suka dawo a saman part d'in Ayman suka sauka, saboda raihana ta samu bak'uncin su al'ameen, Abba da kanshi ya kawo mata su da safe, yace in yamma tayi ko al'ameen zai iya dawo dasu gida in aka sasu a napep. Farin ciki a gurin raihana ba'a magana, ranar wuni tayi suna budurin su ita da yaran, da yamma da auntie ta dawo ta kai mata su suka gaisheta, sai a lokacin khaleefa ya ga ashe sune bak'inta da yaji hayaniyar su tun rana. Ya kuwa dinga jansu da hira har abun yaba auntie da raihana mammaki, suma yadda suka sake dashi kamar sun shekara da sanin shi. Da suka tashi tafiya Auntie ta had'a su da tsaraba me yawa, khaleefa kuma da kanshi ya kaisu har k'ofar gida, bayan ya tsaya dasu a supermarket ya k'ara musu da nashi kason. A daren ba suyi bacci da wuri ba, auntie da kanta ta dinga taya raihana had'a duk abinda tasan zata buk'ata, saida ta tabbatar ta had'a komai yadda ya kamata sannan ta tafi ita kuma ta samu ta d'an rintsa. Safiyar ranar da zasu tafi ta futo wanka da safe d'aure da guntun towel, tana tsaye gaban mirrow tana sharce gashin kanta da cumb, aka mata knocking, saita jawo hijab da sauri ta zura sannan taje ta bud'e k'ofar, khaleefa ne tsaye kamar kullum yau ma cikin shigar k'ananan kaya da suka dace da zubin halittar shi, fuskarshi ba wannan d'aurewar yau kafun tace wani abu ya riga ta da cewa, "barka da safiya". Raihana saida ta d'an diririce sannan ta amsa da, "barka fatan kana lafiya". "Lafiya Lou, amm yauwa takardun nan zaki bani, saboda zamu tafi dasu za'a kaiwa k'anin dad d'in Ahmad". Ba musu ta juya ta d'auko mishi a inda ta ajiye su ta sake dawowa ta mik'a mishi bayan ta russuna. Har ya juya zai tafi ya sake waigowa ya kalleta, tana nan tsaye rik'e da k'ofa, "ki shirya flight d'in k'arfe goma zamu bi". Ta gyad'a mishi kai sannan ta juya don k'arasa abinda takeyi a ciki. Misalin k'arfe takwas na safe ta gama shirinta tsab tana zaune a parlon auntie tana tuttura abincin data tsare su suci gudun tafiya da cikin yunwa, yau bata saka wannan uban hijabin ba, sai kwalliyarta da tayi me kyau cikin doguwar riga abaya golden, rigar daga sama ta d'an kamata kad'an, sannan daga ciki tayi shape me kyau, daga k'asa kuma ta bud'e sosai. Ta tubke gashin kanta ma'abocin tsawo da yawa a k'eyarta, tayi rolling da madaidaicin gyalen rigar, fuskarta powder ce kawai sai wet lips, sai kwalli data zirara a idonta, a tak'aice dai kwalliyar ta mata kyau ta kuma dace da ita, a yau kam khaleefa tunda ya ganta ya kasa d'auke idon shi a kanta, so yake yaga abinda yake fusgar hankalin shi akan kwalliyarta ta yau, yaga abinda yake k'ara mata kyau bayan bata kasance fara ko mai irin zokalelen hancin nan da manyan idanu ba, ko kuma a'a don bata zurma wannan uban hijabin nata bane? Raihana kuwa tana zaune duk jikinta a sanyaye. Daga ita sai shi a parlon Ayman ya shigo bakin shi d'auke da sallama, duk suka amsa mishi suna kallon inda yake tsaye, ya mik'awa khaleefa hannu suka gaisa, raihana ma ta gaishe shi, ya amsa mata sama sama saboda kiyaye hak'k'in auren yayan shi dake kanta. Anan yayi musu sallama had'e da bada uzurin general meeting da zasuyi da duka ma'aikata, duk wanda bai kasance a gurin ba kuma zai shiga matsala. Da kyau khaleefa ya amshi uzurin shi, suka rungume juna suna sake yin sallama da juna. Yana futa raihana ya turowa raihana sak'o kamar haka. "Zuciyata ta aminta dake, shiyasa har ciwona ya warke lokaci guda dana ji irin alk'awarin da kika d'aukar mun, raihana son da nake miki wani lokacin har tsoro yake bani, a yanzu dana ganki kusa da khaleefa sai naji tsorona ya sake ninkuwa, bansan wacce irin rayuwa zakuyi keda twin bro na a wata k'asa ba duk da nasan waye khaleefa, ba wai ina nufin na shiga tsakanin ki keda mijin ki ko mu shiga hak'k'in shi saboda ni ba,,,, don Allah ki kula da rayuwar khaleefa, in kikayi haka shine zaki tabbatar mun da soyayyah ta,,,,, kema ki kula da kanki.....". Raihana ta karanta sak'on Ayman yafi sau hud'u amma ta kasa fahimtar takamaiman abinda yake son fad'a a dunk'ule, tana tunanin kamar ko baya hayyacin shi ya rubuta sak'on shiyasa ya kakkamo zantukan ya had'a. Daga ita har khaleefa sunyi zurfi shiyasa har Ahmad yayi sallama ya shigo cikin shiri basu ji shiba, saida ya tab'a kafad'ar khaleefa sannan, ita kuwa raihana bata ji nata gani ga uban tagumi data rabka da wayarta a hannu. Ahmad har gaisheta yayi bata jiba, haka khaleefa ya kira sunanta sau biyu bata jishi ba. Duk sunyi mamakin abinda ya d'auki hankalinta haka har tayi nisa cikin wata duniyar daban. Futowar Auntie ce ta dawo da ita hayyacinta tayi firgigit tare da sauke b'oyayyar ajiyar zuciya. Khaleefa ta saci kallo sai gashi idon su ya fad'a cikin na juna a sa'a. D'auke kanta tayi, shima ya d'auke nashi yana tunanin abinda ya faru ta zama haka lokaci d'aya. Saida auntie ta k'araso suka gaisa da Ahmad, sannan itama ta gaishe shi, ya amsa yana ta zolayarta wai ya shigo tana can tunanin zata bar k'asa da familyn ta. Ita dai murmushi kawai tayi. Kamar yadda suka tafi wancen ranar haka yauma zasu k'ara tafiya a karo na biyu, sai dai da tarin sauye sauye, a wannan karon sunfi girma akan wancen lokacin, sannan an samu k'arin raihana, babu kuma Ayman. Daga gefe d'aya na hango raihana da auntie tsaye a gefe guda, idonta ya ciko taf da hawaye, ita kanta auntien idonta ruwan hawaye ya tara, ba don kada ta sake karyawa raihana zuciya ba da itama kukan zatayi, masu iya magana suka ce sabo turken wawa, yau auntie da raihana suka sake tabbatar da hakan, don kuwa a d'an zaman da sukayi tare wata irin soyayyah da shak'uwa ce ta shiga tsakanin su marar iyaka, da gaske suke jin kewar juna kamar su cancelling tafiyar su zauna tare. Saida auntie tayi gyaran murya sannan ta fara yiwa raihana magana da sanyin murya, "Toh raihanatu, yau dai gaki zaki kasance a k'asar da baki da kowa baki da komai sai khaleefa, wani bahagon mutum da Allah ya baki a matsayin miji, Ina son kiyi mun alk'awari zaki kasance garkuwa a tare dashi, ki kasa ki tsare ki yak'i duk wani abu marar kyau da zai shigo cikin rayuwarshi kamar yadda kowacce uwa take yi a rayuwar d'anta, ki saki ranki kiji a jikin ki kamar muna tare, kada kiji shayi ko tsoron yi mishi magana akan komai daya sab'awa shari'a da k'a'idar aure da iddinin islama, Ina fatan ranar dazan kawo ziyarar farko Germany na tarar da wani khaleefan daban ba wanda kuka tafi tare ba....". Raihana sunkuyar da kanta k'asa tayi cikin taushi da laushin murya tace, "ki gafarceni auntie, insha Allah zanyi kamar yadda kika ce". Ta k'arasa fad'a tana share hawayen da suka taru a idonta. Auntie rungume ta tayi a jikinta tana share mata hawayen, ji take kamar kada ta bawa khaleefa raihana saboda ta fahimci bai gama sanin ciwon taba, sai dai tafiyarshi ba ita kamar ta bashi wani lasisi ne nayin yadda yaso a k'asar da babu wanda yasan shi, ba wani babba da zai kwab'e shi, baya ga haka ma suna buk'atar kusanci na kusa don suyi karatun juna yadda ya kamata suga abinda mutane suke gani a rayuwar su dasu basa gani har yanzu. Duk yadda auntie taso kasa daurewa tayi har saida ta zubar da hawaye. Tabbas iyayen raihana sun kasance masu yakana da matuk'ar d'auke kai, ita kenan da ba ita ta haife taba take jin kewarta Ina ga uwa da uban da suka kawota duniya. Tasan Allah kad'ai yasan abinda yake ransu a yau a halin yanzu ma. Tattaki kad'an Auntie tayi bayan raba raihana da jikinta, ta kaita inda khaleefa da Ahmad suke tsaye, ga jakunkunan kayan su a kusa da k'afar su, hannun khaleefa ta kama ta had'a dana raihana sannan tace, "khaleefa ga amanar raihana nan, ka tabbatar ka kular mun da ita fiye da yanda zaka kula da kanka..... Ina fatan Allah ya baku nasara akan abinda zai mai daku". Duk kallonta sukeyi har Ahmad a lokacin data fara juyawa da nufin barin gurin, saida tayi tafiya mai nisa sannan ta waiwayo ta kalle su ta sakar musu murmushi, ta sake ci gaba da tafiyar ta. Raihana ta zabura zata bi bayanta, khaleefa ya hana mata damar haka ta hanyar sake rintse hannunta da yake cikin nashi hannun, saita juyo ta kalleshi, ya sakar mata lallausan murmushi, yana jin laushi da d'umin hannun har ta cikin jinin shi. Bai sake hannunta ba suka fara takawa a haka, hannunta d'aya janye da trolleynta, shima rik'e da jakar kayan shi. Suna gaba Ahmad na bin bayan su har suka k'arasa inda za'ayi musu screening. K'arfe hud'u da minti ashirin da shida jirgin su ya sauka a Berlin Brandenburg international airport dake Germany. Tafe suke su biyu a gaba, ita kuma tana bin gefen da mijin ta yake a baya a baya daf dashi a d'arare har zuwa wajen filin jirgin. Dole ranar a hotel suka sauka saboda sun sake apartment d'insu tuni. Raihana tana zaune a harabar Sorat hotel Brandenburg ..... har suka shiga sukayi booking d'aki khaleefa yazo ya mata magana suka tafi tare. Suna tafe Ahmad na zolayarta, Wai duk tayi laushi da wuri daga y'ar wannan tafiyar, ita dai murmushi kawai ta mishi ba tare da tace komai ba. D'aki daban daban suka kama Ahmad da khaleefa, sai dai kusa dana juna. Lokacin da suka shiga raihana bin ko'ina na d'akin tayi da kallo, akwai k'aramin gurin hutawa kafun a shiga d'akin, me d'auke da k'aramin dressing mirrow da resting chair, Sai k'ofa guda d'aya. Koda tabi bayan khaleefa ta shiga d'aki ne babba guda d'aya, me d'auke da k'aton gado da cupboard sai tivi a gefe da madaidaicin table me d'auke da kujeru biyu a gefe. Khaleefa yana ajiye jakar kayan shi ya d'auki abinda zai d'auka ya fad'a bathroom. Ita kam gefe guda ta zauna kan sopa a d'arare tana rarraba ido kamar wadda za'a sace a gurin. Kallon komai take daban a fuskarta, tana tunanin yadda zasu rayu a muhalli d'aya har na tsawon lokaci me tsayi tare haka, sai take ganin kamar akwai takura ai. Tana zaune khaleefa ya futo da kayan daya cire ya ajiye cikin cupboard dake jikin bango, ya futa daga d'akin ba tare daya ce mata k'ala ba. Saida ta d'auki lokaci har ta fara tunanin ko khaleefa ya tafi nema kenan sannan ta tashi ta shiga cikin d'akin wankan, tayi wanka ta shirya cikin riga mara nauyi ta futo ta samu kan sofa tayi kwanciyarta, duk da yunwar da take ji amma gajiya ta rinjayeta kafun wani lokaci tayi bacci. Koda khaleefa ya dawo da abincin daya mata order tsayawa yayi yana tunanin yadda zai tashe ta daga wannan bacci me cike da azabar yunwa. A gurguje please Ina cikin uzururruka🙏 _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty six4️⃣6️⃣ Ya dad'e a tsaye kanta yana kallonta, hallau sanye take da k'aton hijab ta nad'e har k'afarta, bacci take sadidan kamar wadda ta shekara bata runtsa ba, khaleefa kamar ya rabu da ita sai ya kasa, a k'arshe yayi k'undunbala ya fara duba saitin inda zai samu k'afarta, kamar me tsoron wani abu ya fara d'aga hijabin jikinta har chocolate k'afarta ta bayyana, wani irin jan lalle ne aka zana mata shi can k'asan k'afa irin na auntien shi, saboda kamawa har ya sauya colour daga ja zuwa maroon, wani takaici ne ya turnuke khaleefa lokaci d'aya da yaga lallen nan, ranshi yayi bak'ik'irin har yana takaicin kanshi daya tsaya tashin ta ma har yaje ya gani. Fucewar shi yayi ya fasa abinda yayi niyyah. Raihana kam ta jima tana bacci kafun ta tashi, ta shiga bathroom tayi uzurinta ta futo sannan ta ankara da abincin daya ajiye mata, yunwar da take ji tasa ba zata iya hak'ura ba sai taci koma na waye. Lomar farko data kai bakinta saida ta rintse ido, wani kalar test da harshenta bai tab'a tasting ba, saboda yunwa dai haka ta rugungunta taci kad'an ta maida ragowar gefe inda ta ganta ta ajiye. Har dare yayi ta sake komawa wani baccin khaleefa bai shigo ba. Shi kuwa ta b'angaren shi yana tare da Ahmad suna meeting kan aikin da zasuyi da yadda zasuyi, sam basu rabu ba sai nisan dare. Lokacin daya shigo raihana ta dad'e da yin bacci kan sofa, Saida ya duba abincin yaga kad'an taci, ya tab'e baki ya sauya kayan jikin shi zuwa na bacci ya kwanta kan gadon. _asuba ta gari_ Washe garin ranar ma khaleefa tun da wuri ya sake futa ko breakfast bai tsaya yiba, haka ta yini ita kad'ai da jagwalgwalallen abincin Germany daya Sha banban da wanda ta saba ci a k'asar ta. Har dare bata iya cin komai ba, ga yunwa da take neman ganin bayanta. Bai dawo da wuri ba ranar ma har dare, tana son yin bacci amma yunwa ta hanata. A nutse ya turo k'ofar ya shigo bakin shi d'auke da sallama, da ita ya fara cin karo a zaune kan carpet ta hard'e k'afafunta ta zura kanta a tsakanin cinyoyinta. Kallo ya bita dashi farom up to toe, yanzun ma sanye take da doguwar rigar bacci mai kauri, ta d'ora madaidaicin hijab daga kanta zuwa gwiwar k'afarta. Motsin shi yasa ta d'ago kanta tana kallon shi da idanunta da suke nuna kamar tayi kuka. Kamar ya tambayeta ko wani abu yana damunta? Sai kuma dai ya share, yana ganin in akwai abinda yake damunta zata fad'a mishi tunda ba jaririya bace ita d'in. Tana nan zaune har yayi shirin kwanciya bacci, yayi addu'o'in shi ya kwanta, don tuntuni suka ci abincin su shida Ahmad a gidan cin abincin da suka saba ci. Wani abun mamaki sai ya kasa baccin yana tunanin abinda yasa har war haka ba tayi bacci ba, tabbas daga yanayinta daya kalla kad'ai yasan ba lafiyarta ba, toh amma meya hanata fad'a mishi in ma bata da lafiyar? Sai ya tashi zaune ya soma bin komai na d'akin da kallo, kafun ya sauko duka ya duba abincin yau da aka kawo mata, suna nan ta tare su kan table bata tab'a ko guda ciki ba. Abinda ya d'aure kan khaleefa kenan? Sam tunanin shi bai bashi nau'in abincin ne bata saba dashi ba. Gefen bed ya koma ya zaune ya tsura mata ido yana kallonta ta cikin dim light, kanta jingine da bango idanunta a lumshe, kamar ba zaice komai ba sai kuma yace, "Ina fatan dai kina lafiya". Ba tare data kalle shi kota motsa daga yadda take ba tace, "umm!". "Toh me yasa baki ci abincin kiba?". Ya sake tambayar ta. Sai yanzu ta motsa ta hanyar yamutsa fuskarta tace, "bazan iya ciba". "Me yasa?". Ya sake tambayarta still idon shi a kanta. Tashi tayi zaune sosai ta kalle shi sau d'aya ta d'auke kanta, "wannan ba irin abincin dana saba ci bane". Ta fad'a da murya a sanyaye. Sai yanzu ya gano bakin zaren. Agogon wayar shi ya duba yaga lokaci, kafun ya mik'e ya futa. Abincin da yasan zata iya ci ya tafi ya nemo mata, yasha wuya kafun ya samo mata, burger da maultaschen, yana ganin kamar zata iya cinsu, don gidan abincin da suke samun Nigerian dishes tuni sun kulle, ko kafun yazo tayi laga laga ta kusa mutuwa saboda yunwa data galabaitar da ita. A k'asa ya zauna nesa da ita kad'an yace, "ga irin wanda zaki iya ci". Da kyar ta tashi, khaleefa ya mik'o mata tea me zafi daya had'a mata, ta amsa da sauri ta shanye har jikinta yana rawa rawa. Abincin ma hannu baka hannu kwarya ta ci wanda ya sauwak'a ta ajiye ragowar a gefe. Saida ta wanke bakinta ta d'auro alwala ta futo sannan khaleefa ya sauke ajiyar zuciya ya kwanta. Itama ta samu guri ta kwanta. @@@@@@@ Kwanaki biyu suka k'ara a hotel d'in suka samu masaukin su da zasu zauna, k'aramin plat ne me d'auke da parlour! Da 2 bedrooms sai kitchen da harabar gaban gida da aka cika ta da shuke shuke kamar garden. Da taimakon Ahmad suka shirya gidan da duk wani abun buk'ata na amfanin yau da kullum, suka tattaro raihana daga d'akin hotel zuwa gidanta. Raihana sai taji tafi sakewa akan wancen takurarren muhalli. Komai na parlon light ash ne, dinning kad'ai fari sol. D'akunan gadon kuma kala biyu, wanda khaleefa ya d'auka white bedroom ne, ita kuma nata pitch. Tana zaune a parlon tana hutawa Ahmad sai zolayarta yake wai har ta fara gajiya da Germany bayan ko sati bata rufa ba, ita dai murmushi tayi mishi ba tace komai ba, don in akwai abinda yafi gundara ma tayi da k'asar, yanzun ita inda khaleefa zai taimaketa daya had'a ta da auntie da y'an gidan su taji muryar kowa kota samu nutsuwa in taji lafiyar su. Agogon bango dake mak'ale a wata kusurwa can ta parlon ta gani, saita tashi don sama musu abinda zasu ci don taga alamun basu da niyyar futa yanzu, aiki ma suka fara ta system d'in khaleefa. Abinci mai sauk'in sarrafawa tayi don ta gaji burinta kawai da tayi sallah ta kwanta, tana gamawa ta jere musu a dinning ta shige d'akinta. Tunda ta tafi hankalin Ahmad ya koma kan dinning inda ta jere abincin data gama girkawa yanzu, dama ga k'amshi ya cika musu hanci tuntuni. Ganin khaleefa kamar baya jin yunwa sai ya magantu, "yae! Man nifa abincin can ya tafi dani, Ina ganin bari nayi sallah nazo na....". Bai k'arasa ba sai y'ar dariya da yayi. "Ohhh! Sorry lokacin sallahn ma ya kusa hucewa", ya k'arasa fad'a a k'agauce yana rufe system d'in ya mik'e, shima Ahmad mik'ewar yayi. Saida sukayi sallah sannan khaleefa ya mishi jagora zuwa dinning d'in. Ahmad da zumud'i yake ta k'ok'arin saving kanshi, duk wannan k'amshin ba wani abinci na daban bane, jallop rice and beans ce sai had'in ordabur da ta musu. Da basise. Ko a ido yadda abincin ya had'u ya matuk'ar tafiya da hankalin khaleefa, amma abu guda daya tuna yaji abincin ya bashi haushi ranshi ya dawo bak'ik'irin, haka ya tashi daga gurin da sauri ya koma inda suke zaune da farko bayan ya tsiyaya ruwa a cup. Ahmad da mamaki yake tambayarshi, "lafiya kuwa?". Yamutsa fuska yayi yace, "normal am okay". Shiru Ahmad yayi yana tunanin dalilin da yasa khaleefa ba zaici abincin ba duk yadda yayi dad'i ya samu gyara na musamman daga matar da suke da tabbacin tsantarta. Shi dai kam saida yaci ya k'oshi sannan ya baro dinning yana magana da d'an k'arfi yadda raihana zata iya jiyowa. "Madame munci abinci yayi dad'i Allah ya saka da jannatul firdaus....". Tana kwance ma ita tayi nisa a duniyar bacci sam bata san wainar da suke toyawa a gidan ba. Yana zama khaleefa ya tashi yace, "muje ko?". Ahmad baisan ko'ina yake nufi ba amma sai ya tashi ya mara mishi baya suka futa a gidan. Gidan cin abincin Haveli suka nufa inda suka saba cin abinci lokaci zuwa lokaci yayi order, abun ba k'aramin mamaki yaba Ahmad ba har saida ya kasa hak'uri ya magantu, "Man nifa ban gane maka ba, ka bar abinci me kyau a gida kazo kana cin wannan". Sake b'ata fuska yayi kamar ba zaice komai ba sai kuma da kyar dai yace, "baka ga hannu da k'afar raihana ba?". Ahmad dafe kanshi yayi, bai gani ba kam tabbas, amma yasan indai jikinta da lalle bazai tab'a iya cin abincin taba. Cike da tausayin yadda zai dinga missing abincin raihana masu dad'i yace, "Man lokaci fa yayi daya kamata ka danne zuciyarka akan rashin son lallin nan, indai ba har in kaci zai dawo bane....". Shiru yayi ma Ahmad ba tare daya ce mishi kanzil ba, yana ganin Ahmad don baisan irin tsanar da ya yiwa lallin bane, ko auntie don ya gama tabbatar da ingancin tsabtar ta yake iya jurewa yaci duk rintsi, amma wannan raihana kam, bazai iya ba. Har ya gama suka tafi basu sake ce da juna komai ba tsakanin su. Basu koma anguwar ba sai bayan da suka gama duk wani uzurun su a gari, kasancewar gidan Ahmad yana kusa dana khaleefa sai gasu sun dawo kamar yadda suka tafi, sai dai wannan karon kowa nashi guri yayi. A lokacin raihana ta sake gyara gidan ta dafa sabon abinci amma bada yawa ba don taga wancen basu ci na kirki ba. Tana zaune kan kujera ta kanannad'e jikinta kamar me jin sanyi, wayarta ce rik'e a hannunta ko me take dubawa oho shi dai daya shigo yanzu bai sani ba. Raihana sam bata ji sallamar shiba don baya yinta yadda zata ji d'in, rufe k'ofa da yayi yasa ta d'ago da sauri tana kallon k'ofar. Takowa yake sannu zuwa cikin d'akin da tafiyar shi me bayyana zallar aji da nutsuwa. "Sannu da zuwa". Ta fad'a k'asa k'asa tana d'auke kanta ga barin kallon shi. Saida yasha k'amshin shi son rai ya gama k'arewa komai na gidan kallo da tunanin daga inda wannan k'amshi mai shegen dad'i yake futowa sannan yace, "yauwa". Zama yayi cikin kujerar yayi relax yana sake shak'o nau'in k'amshin daya zarta wanda yasani tare da auntien shi dad'i da sanya nutsuwa a ruhi. Raihana dama bacci ne fal idonta, zaman shi a gurin yasa ta takura don haka ba dogon sharhi ta d'auki wayarta tayi cikin d'akin gadonta. Bayan tayi addu'a me tsayi ta tofe duk kusurwowin d'akin tayi kwanciyarta. Shi kam saida ya d'au tsawon lokaci yana tunani kafun ya mik'e ya shige d'akin shi shima ya rufo. @@@@@@@@ Sosai khaleefa ya shiga busy cikin satin, a sati na gaba kuma suka fad'a bakin aiki. Ranar farko da khaleefa ya ganshi zaune a office matsayin kwarrren likitan (physiotherapy) saida ya kai goshin shi k'asa yayi sujudushshukur yayi addu'o'i ya godewa Allah bisa wannan muhimmiyar rana daya nufe shi da gani. Office d'inshi shida wasu mutum biyu cikin rukunin su bakwai yana k'ark'ashin doctor andal, su kuma Ahmad zasuyi aiki tare da wancen likitan. Ranar ko daga yanayin yadda raihana taga ya shigo gidan ta tabbatar yana cikin tsananin farin ciki. Ta jima tana son neman alfarmar ya had'a ta koda auntie ne taji lafiyarta tare data mutanen gidan su, amma ta rasa ta inda zata fara tunkarar shi, kullum sassafiyar Allah ya futa baya dawowa kuma sai ta kwanta bacci, bata san ina yake tafiya ba,,, me yake yi da har yake d'aukan lokaci me tsawo haka a waje, shiyasa ta fara ganin baiken Auntie da take tunanin zata iya kawo gyara wa rayuwar mutumin da mantawa yake yi da ita ma gaba d'aya cikin babin rayuwar shi. Tun tana ajiye mishi abinci a dinning ta d'auka yadda ta barshi har ta gaji ta daina. A yau ma bata tsammaci dawowar shiba, bayan ta gama komai da yammacin ranar gajiya tayi da zaman kad'aici ta lek'a ta wajen window tana kallon anguwar da take tsit ba alamun mutum ko guda, sai motoci da suke hucewa tsilli tsilli. Kamar koda yaushe yauma sanye take da wadatattun kayan da suka suturta jikinta da kyau, duk da garin ba sanyi sosai amma ita har yanzu garkuwar jikinta bata gama sabawa da k'asar ba, shiyasa take jin sanyin da kyau. Akan idonta suka zo a motar Ahmad, ya futo ya lek'a ta windown motar ya yima Ahmad magana ta sakanni ya nufo hanyar gidan, shi kuma Ahmad ya tsaya nan gida na kusa da nasu. Zuba mishi ido raihana tayi tana kallon yadda yake takun shi har ya fara k'ok'arin bud'e k'ofar. Saita kautar da idonta ga barin kallon side d'in da yake tana sauke ajiyar zuciya. Shima yana shigowa idanun shi ita suka fara gani, ya bita da kallo kamar me karantar wani abu a tare da ita kafun ya k'arasa shigowa parlon ya zauna cikin d'aya daga kujerun da suka k'awata d'akin. Kamar bata san dashi ba tace, "sannu da dawowa". Shima ba tare daya d'ago ko ya sauya daga yadda yake ba yace, "fatan kina lafiya". Tace, "lafiya lou". Shiru ya sake biyo baya na wasu mintuna kafun ta kawo mishi ruwa me sanyi da marar sanyi da cup a tray. Saida ya lumshe idonshi a lokacin da tazo gab dashi wani mayen k'amshi ya shiga hancin shi. Ita kam neesa dashi ta zauna cikin d'ari d'ari kamar tana tsoron wani abu tace, "dama.... Dama Ina son don Allah nayi magana da Auntie idan babu damuwa". Shiru yayi bayan ya had'iye makwarwar ruwan daya zuba a bakin shi yace, "Zan saita miki sim d'in Germany gobe sai ki kirata da kanki". Da "toh" ta amsa shi ta tashi ta bar mishi parlon, khaleefa ya dafe kanshi yana tunanin yadda Auntie take son dagula mishi lissafi k'arfi da yaji. Fisabilillah yanzu wannan turaren, ga lallen k'afarta kamar ma bashi da niyyar bin ruwa koya daina zargadilar EVE ANO yana neman abincin k'asar Nigeria safe da rana da dare, kamar babu ita a gefen shi. (Nikam nace kamar matar gaske🤔😜) ************ Yammaci ne misalin gab da sallar magrib. Zaune take a kan d'aya daga fararen kujeru biyu da suke a harabar gurin, hannunta rik'e da wayarta ta lula ciki da alama chat take, kallo d'aya zaka fahimci mabayyanin farin cikin da take ciki. Tana nan a saleemarta babu wani sabon abu ko bak'o tare da ita. Ta jima a gurin kafun k'awarta Amna ta k'araso a gajiye ta ajiye jakarta gefe tana cewa, "sannu da zaman jira! Na barki kina ta jirana ko?". Saleema murmushi ta wanzar a saman fuskarta ta ajiye wayar hannunta kan table d'in daya raba kujerun su tace, "ba komai nasan akwai abinda ya rik'e ki". Amna tace, "wallahi kuwa". "Ke nifa jiya da kyar na iya bacci, so nake kawai kizo don tunda naji kince akwai maganar da zamuyi nasan muhimmin al'amari ne ya taso....". Amna tace, "humm! Sosaima kuwa, amma kafun na fad'a miki maganar nan dai da bakya so zan k'ara jaddada miki, ki dinga yin dogon tunani kafun aiwatar da komai na rayuwarki, kiyi hak'uri ba wai shishshigi zanyi miki ba amma.......". Saleema ta d'aga mata hannu da sauri tana kallonta, kafun cikin had'e girar sama data k'asa tace, "don Allah muyi magana akan abinda ya kamata! A ganina zaifi ko?". Amna tace, "hakane tunda bakya son gaskiya! Toh khaleefa dai ya dawo k'asar Germany zaiyi aiki a matsayin physiotherapy doctor............." 🤦‍♀️sai hak'uri not edited _fans please kuyi hak'uri da jina shiru kwanaki da yawa, na shiga matuk'ar uzuri yanzun ma dakyar na samu lokacin dana muku wannan, gashi nan dai ba yawa_. _Comment and share_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty six4️⃣6️⃣ Murmushi tayi me kama da yak'e, ta mik'e tsaye ta juyawa Amna baya tayi taku biyu zuwa uku sannan tace, "nasan da labarin dawowar shi, tun a ranar da jirgin su ya sauka.....". Saita juyo ta kalli Amna data zuba mata ido itama tana kallonta kafun taci gaba da cewa, "inda nasan wannan labarin zaki bani.... Da bazan fara b'ata awowi cikin muhimman lokutana ina jiran ki a nan ba". Tana gama fad'ar haka ta d'auki wayarta zata bar gurin, da sauri Amna ta dakatar da ita, "ai baki ji k'arshen labarin ba, mufi muhimmanci a ciki kuma, ko kinsan dame khaleefa ya dawo Germany a wannan karon??....". Sake d'aga mata hannu tayi, wannan karon a d'an zafafe tace, "me yasa dole sai kinsa raina ya b'aci ne Amna????, Tuntuni nasan akan me kike duk wannan y'an kewaye kewayen. Toh ya ishe ki haka ki barni nayi rayuwata yadda naga dama tunda ba taki bace,,,, khaleefa bake kika had'a ni dashi ba, kuma baki Isa kice zaki raba muba". Da wani mugun mamaki Amna take kallonta, kafun cikin jin zafi tace, "ki dinga sanin abinda bakin ki zai furta mun Saleema? Wace irin maganar banza ce zaki ce Ina k'ok'arin raba ki da khaleefa!". . Saleema bata bata amsa ba sai tsaki da taja ta d'auki hanyarta. Da kallo Amna ta bita tana magana cikin d'aga murya yadda zata iya jiyo ta, "Saleema Ina ganin lokaci yayi daya kamata mu raba hanya kowa yaje yayi rayuwarshi, don banga amfanin zaman mu tare ba tunda ba zamu iya amfanar juna da komai har shawara akan abinda ya kamata da zai amfani rayuwar mu kuwa.......". Ko waiwaye Saleema bata yiba duk data jita sarai, sai a ranta da tace, "sai yanzu kika san haka kenan.... Aikin banza". *NIGERIA* Tafe take sannu a hankali cikin motarta tana tuk'inta cikin tsanaki, a gajiye take tibus burinta kawai ta Isa gida ta kwanta ta huta don cikin satin gaba d'aya bata jin dad'in jikinta k'arfin hali kawai take yi da office d'in ma baza taje ba. Tana k'arasowa Ayman daya dawo aiki a lokacin shima yana shirin cusa hancin motarshi cikin gidan, saita jira ya shiga itama ta bi bayan shi. Kusan tare suka futo, ya k'araso gurinta yana mata sannu da zuwa. Ta amsa da murmushi tana kallon shi da yadda ya sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa, hakan na mata dad'i a koda yaushe inta ganshi. Koda suka shiga cikin gidan mama haleema tana zaune cikin shirin tafiya, jira take kawai cikin auntie ko Ayman wani ya dawo ta tafi gida. Aikuwa auntie tana zama gaisawa kawai sukayi ta bata sak'on da wata yarinya ta kawo a ajiye mata, ta mata sallama zata tafi. Auntie ta karb'a tana tambayarta, "da wuri kuma yau?". Mama haleema tana dariya tace, "Eh wallahi akwai abinda zanyi a gidan kinsan in kana da y'ay'a kullum cikin raba case". Auntie tace, "aikuwa damma Allah yasa ba fitinannu a ciki". Mama haleema tace, "duk da haka sai godiyar Allah kinsan sha'anin yaran yanzu ". Auntie tace, "Toh Allah dai ya k'ara shiryawa" Mama haleema ta amsa da "ameen" ta sake mata sallama, har ta kai k'ofa auntien ta tsayar da ita, "wannan sak'on baki fad'a mun ko daga Ina ba kuma?". Shiru tayi tana nazari kafun can tace, "toh ni dai wata yarinya ce ta bani shi, haka dai take doguwa me matsakaicin jiki, fuskarta har ta bani ta tafi a rufe da takunkumi". Itama auntien shiru tayi tana nazarin ko zata iya gane wacece, kafun ta fara duba ledar don koma waye in taga sak'on zata iya ganewa. Ko data bud'e invitation card ne guda uku da kwalin chewing gum, sai pass na event har hud'u. Sunan shaheeda data gani yasa ta gane sak'on daga k'awarta sameera ne. "Bikin yazo kenan? Toh Allah ya sanya alkhairy". Ta fad'a a zahiri kafun ta tashi ta shige bedroom. Suu kuwa gidajen biyu ta ko'ina shirye shiryen biki suke babu kama hannun yaro, akwatuna sha biyun da aka kaiwa raihana aka karb'o aka sake kaiwa shaheeda bayan an sauya wasu daga cikin kayan da wanda suka fisu tsada da kyau. Ango dai kam sai yadda akayi dashi, tun da aka fara maganar bikin bashi da wani abu guda d'aya a cikin tsare tsaren daya yishi don ra'ayin kanshi, komai yayi musu shi yadda suke sone, akan abu guda yaja da maman shi da tace shaheeda zata zauna a sabon gidan shi inda ya tsara zai zauna da raihana, yace sam sam ba zai zauna a can ba sai dai su zauna tare da maman a nan gidan mahaifin shi. Ran hajiya tafeeda da sameera kuwa ba k'aramin b'aci yayi ba da sukaji abinda yace, kuma koda hajiya tafeeda taso ta matsa masa kan lamarin, nan da nan abban su ya takawa abun burki da saurin shi, a cewarshi ai akwai rufaffen b'angaren da ba'a amfani dashi sannan ko a saman gidan zasu zauna meye laifi in akayi haka. Dole tana ji tana gani ta amince da tsarin Imran ba don ranta naso ba sai don ba yadda zatayi. Ta b'angaren sameera kuwa daga mijinta har mamanta sun zuba mata ido suga iya gudun ruwanta. Saboda mahaifiyar ta har gida ta kirata da taji labarin abinda ya faru tsakaninta da surayyah, ta bata shawara tun wuri taje ta janye abinda ta furta ta bar yara suyi auren su, amma baiwar Allahn nan tayi funfurus tayi watsi da maganar don tana ganin itace akan gaskiya ba surayyah ba, Kuma har asibiti taje ta bata hak'uri amma ta nuna sam bata buk'atar Nur da Ayman tare, gashi yanzu ma ta raba hanya da ita k'arshe kenan, toh meye kuma zata sake je mata da maganar a karo na biyu. Amarya shaheeda tasha shiri da gyara in and out. Musamman aka ajiye mata me gyaran jiki bayan hajiya tafeeda ta caji kud'i daga Imran. Abin ka da farar mace nan da nan tayi d'au sai walwali take. Sun shirya event kala kala ita da k'awayenta ranar farko zasuyi lunching, sai rana ta biyu henna, rana ta uku kuma bridal sai dinner da za'a gabatar last. (Amma fa duka ita da k'awayenta kad'ai zasuyi ko dinner ango ya bada uzurin ba zai samu damar zuwa ba) Ta b'angaren iyaye suma sunyi shirin su kama daga kamuu,,, shagalin su na ranar iyaye,,,, da yini. Ba k'aramin kud'i suka futar wajen yin shagalin bikin nan ba, y'an uwa da abokan arzik'i kuwa na kusa dana neesa duk sunzo ba'a cewa komai sai son barka. Tunda suka fara taron bikin sameera take sakaran ganin surayyah amma babu ko inuwarta har sai ranar da aka d'aura aure da yamma tazo mata Allah sanya alkhairy. Aikuwa ta rasa inda zata ajiyeta saboda karramawa. Abinci kuwa cikin na bak'i na musamman ta kawo mata haka ma drinks. Ita kam dama a k'oshe take bata iya cin komai a gurin ba sai ruwa. Data tashi tafiya ta bata kyautar mayun turarukan sudanniyyah masu tsada da wani set d'in flask. Har wajen motarta sameera ta rakata tana ta mata godiya. Ita dai ta kama hanyarta, daga nan ma gidan su iya tayi don kwana biyu basa nan sunyi tafiya ita da malam zuwa garin su sai jiya suka dawo. Anyi taro lafiya an tashi lafiya, y'an uwa da k'awaye sun raka amarya gidanta lafiya. Sai dai sun kwafsawa hajiya tafeeda, don tana can ta kwafe a parlonta ita da hamshak'an k'awayenta tana jira a bata girma ta hanyar shigo musu da amarya ta nemi albarkar su sai suka ga sab'anin haka. Aikuwa ba tayi wata wata ba ta dokawa sameera kira tana tambayarta bata fad'awa y'an uwanta yadda tsarin yake ba, da farko bata gane abinda tafeedan take nufi ba sai daga baya da tayi mata dalla dallar bayani. Hak'uri ta bata tace suyi hak'uri zata kira su zasu zo yanzun nan. Hajiya tafeeda ta ajiye waya tana fad'awa k'awayenta yanzu za'a kawo amaryar. Sameera kuwa koda ta kira k'anwarta ta fad'a mata maza maza su kai amarya b'angaren surukarta ba musu suka amsa mata, sai dai Amarya tana jin batu ta buga tsalle ta dire tace ita ba inda zata, suka kad'a suka raya shaheeda tace ba zata iya jure sake sauka da hawa ba. (Da yake ita a sama take) Daga k'arshe suka kira sameera tace a had'a ta da ita a waya, nan ma tak'i karb'an waya. Dole sameera ta kashe wayarta tana takaicin shegen taurin kai da kafiyar shaheeda, shiyasa kwata kwata bata so aka had'a su gida d'aya da tafeeda ba, don tasan k'awarta sarai ba hak'uri gareta ba, ita kuma shaheeda taurin kai da bak'in rik'o, gashi komai k'ank'antar abu akayi mata bata yafiya, dama ba don Nur tak'i ba itace lafiyar Allah. A gidan amarya kuwa Tsabar haushin abinda tayi yasa y'an uwan mammie sukayi fushin zuciya suka dundungure mata kai sukayi tafiyarsu ba'a bar mata ko mutum guda ba sai k'awaye. Suma har k'annen mammie sun futa suka sake shawara suka dawo suka sallamu kowacce cikin su ta kama gabanta aka barta ita d'aya. Itama hajiya tafeeda kafun su tafi suka biya suka bata uzurin k'arya na cewar amarya bata da lafiya sun baro ta dai a kwance tasha magani. Ba don ranta yaso ba ta karb'i uzurin, don yau taso k'awayenta suga surukarta ta nunawa sa'a, ko ta futa kunya itama, toh amma ko yanzun ai babu laifi tunda zasu had'u da an kwana biyu, zasu k'ara ganta. Ranar babu wanda yaga k'eyar Imran sai nisan dare, a lokacin shaheeda ta dad'e da sauya kayan jikinta zuwa na bacci ta kwanta tuni. Saida ya shiga bedroom d'inshi da yake kallon nata ya shirya tsab sannan ya d'auko ledar daya shigo da ita ya nufi d'akin ta. Ya murd'a handle a hankali ya shiga cikin d'akin da baya tashin komai sai wani irin k'amshi me dad'in shak'a. Saida ya kunna glove haske ya mamaye d'akin sannan ya ajiye ledar hannun shi gefe, shi kuma ya jingina da bangon da aka jingina gadon yana k'arewa matar da ake cewa tashi kallo. Baccinta take sadidan, ta rufe daga k'afarta zuwa rabin cikinta, uban kitson gashin dokin da aka mata ya zubo har gadon bayanta saboda sake shi da tayi. Fara ce tas kyakkyawa shi kanshi zai iya shaida hakan, sai dai kwata kwata baya jinta a ranshi ko kad'an, saboda shi a rayuwarshi mace kalarta bata tab'a burge shiba, raihana yake so da komai nata, itace tsarar shi tsarar soyayyar shi, tsarar auren shi, a itane kad'ai yake ganin natural beauty ba wanda kyale kyale ko hasken fata ya k'ara futar dashi ba. Sai ya sauke ajiyar zuciya me tsayi, ya k'arasa gaban gadon sosai yana k'ok'arin tashin ta, don yayi alk'awarin bazai tab'a wasa da duk wani hakkinta da yake wuyan shiba, don baya son abinda zai kaishi wuta ranar gobe kiyama. Cikin magagin bacci ta bud'e idonta tana kallon shi dishi dishi kafun ta mik'e zaune da sauri tana kallon shi. Gefen gadon ya zauna ba tare daya kalleta ba yace, "ki tashi ki d'auro alwala zamu yi salllar nafila raka'a biyu". Banza tayi dashi kamar bata jishi ba har saida ya maimaita abinda ya fad'a sannan tace, "zaka iya yi kai amma ni bazan yiba". Imran baisan lokacin daya waiwayo ya kalleta ba jin amsar data bashi kai tsaye da tsayayyen harshe. Ta juya fuskarta gefe d'aya kuwa kamar ba ita tayi maganar ba. Sai bai sake ce da ita komai ba yaja sallaya ya shimfid'a yayi sallarshi, ya jima yana addu'o'i kafun ya sallame ya d'auko ledar daya shigo da ita. "Zaki iya tasowa muci abinci?". Ya nemi sani don yaga saida tambayar. Girgiza mishi kai tayi tace, "Ni na k'oshi". Bai damu ba ya mayar da komai gefe ya ajiye tunda shima ba wai yunwarce dashi ba, kafun ya baro gidan auntie saida ta cika mishi shi da abinci mai kyau. Ya kashe kwan d'akin yabi gefen gadonta ya kwanta daga can k'arshe, da farko shaheeda sauka tayi daga gadon tana kallon shi da kaifafan idanunta, shi kuwa ya juya baya ma sam baisan tana yiba don abinda take tunani ba shine a ranshi ba, ko kad'an baiji komai a kanta ba, duk daya ganta daga ita sai wannan fingilalliyar rigar bacci. Ta dad'e a tsaye kamar y'ar patrol, bata sake kwanciya ba kuma saida taji yana sauke numfashi tabbacin yayi bacci. *Imrana ango*😜 *Germany* Tun washe garin ranar khaleefa kamar yadda ya fad'a ya kawo mata sim na k'asar ya saita mata. Aikuwa ta kwashe kaf contact d'in y'an uwanta na kusa dana nesa, haka k'awayenta su fatima babu wanda ta bari wai don tayi aure, don a rayuwar makaranta sun yiwa juna amfanin da ba zata iya yada su donta fara taka matattakalan nasara ba, ko me ta zama a rayuwa ba zata sauyawa y'an uwa da k'awayenta ba wannan alk'awarine ta yiwa ranta. A ranar kasa hak'uri tayi har saida taji muryar ummienta, Auntie da abbanta, sannan tabi ragowar y'an uwa duk taji lafiyar kowa. Ta jima da raheela suna waya tana bata labarin abubuwan da suke faruwa game da auren Fatima da gurbin karatu da zata samu ita kanta ta had'a degree a A. B. U zariya bada jimawa ba. Sosai raihana ta taya su murna da fatan alkhairy kafun suyi sallama kowa ya ajiye wayarshi. Rayuwar raihana a Germany ta kasance lami ba wani armashi, sai ta kwana biyu ba tayi magana da khaleefa kota gaisuwa ba, saboda a kullum ya taso aiki gidan Ahmad yake shiga baya dawowa sai dare, haka weekend ma a can yake yini, ita harta fara tunanin ko aikin nasu har weekend ne ba hutu ma. Bata fara zuwa makarantar da khaleefa yake k'ok'arin sama mata gurbi ba sai bayan da suka share watanni hud'u a k'asar ta Germany da zama. Admission d'in yazo dai dai da lokacin bikin Ahmad da aka k'arawa wata guda, kamar wancen karon haka wannan ma ya shirya mata tafiya ba cikakken bayani, ita dai tana kallon ikon Allah, saida ya saura kwana biyu su tafi Nigeria a d'aura auren Ahmad khaleefa ya shirya tunkararta da zancan don tayi shiri kafun ranar. Tana kitchen tana had'a abincin da zata ci a daren ranar, don girkin ma yanzu ba kullum take yiba tunda cikinta ita d'aya. Sanye take da doguwar riga mai fad'i tayi rolling da k'aramin gyalen rigar, hakan yasa gashin kanta data tubke tuli guda ya samu damar zama a k'eyarta har ya bada shape me kyau. Aikinta take tayi kanta a k'asa batasan da shigowar shiba sam, kuma koda wasa bata d'ago ba. Khaleefa kuwa abinda ya sake bashi damar zubawa fuskarta ido da son gano inda makusarta take kenan, ko daya cika kallonta sai ya fara ganin wasu sirrikan kyau da a baya bai tab'a sanin su a tare da ita ba. Gashi kwana ki biyu da bai ganta ba har wani haske ta k'ara a idon shi da sihirtaccen kyau. Fulawa take ta kwab'awa zata yi doughnut da zata dinga breakfast dashi na kwana biyu. Kamar me koyon girki haka ya dinga bin komai da take yi daki daki, a nan ya sake tabbatar da tsabtar ta ganin yadda take komai tsaf tsaf ga nutsuwa. Raihana bata ganshi ba sai daf da zata gama k'arasa had'a komai. Cikin sa'a ta kama shi yana kallonta. Binshi tayi da kallo a kaikaice, kamar koda yaushe yauma sanye yake da k'ananun kaya, riga bak'a wando fari da ratsin bak'i, hannun shi rik'e da wayar shi ya hard'e su a k'irji, da alamu ba daga office yake ba, ya jima da dawowa ko kuma bai futa bama.... Kamar marar gaskiya haka ta hau duru duru kafun tace, "in... Ina.... Ina kwana". K'arasa shiga kitchen d'in yayi ya d'auki cupi a kusa da ita ya tsiyaya ruwa yasha sannan yayi mata magana da murya can k'asa, "hala yanzu kika tashi bacci?". Girgiza mishi kai tayi kamar me tsoron wani abu, yatsun hannunta da suka sake futo da zanen lallenta maroon da kullum cikin tisashi take kamar yadda auntie ta koyar da ita ta kuma bata shawara yabi da kallo. Tab'e baki yayi take yaji haushin kanshi ya kama shi har ya fara tuhumar kanshi uban me ya shigo dashi ma har idon shi yaga abinda baya sooo, gashi ranshi ya kwad'aitu da k'amshin girkinta da yaji ya gani a lokaci guda kuma lallenta zai mishi shamaki da abincin. Har ya juya zai futa sai ya tuna ashe fa magana yazo suyi da ita, daga inda yake tsaye ya juyo ya kalleta yace, "ranar laraba zamu Nigeria saboda Friday za'a d'aura auren Ahmad, sai ki zama ready". Wani irin farin cikine ya kamata har batasan lokacin da ta d'ago ta kalleshi hak'oranta duka a bud'e ba. Haka kurun Khaleefa sai yaji kyashin yadda zata b'ata mishi rai ita tayi farin ciki, yasan tunaninta shine a Kano ne ta yadda zata ga familynta, sai yayi murmushin mugunta yace, "dama kin daina murna... Iya Abuja kad'ai zamu". Take kuwa farin cikinta ya koma ciki, amma duk da haka sai taci gaba da yak'e, koba komai in taje Abuja zata ji k'amshin Kano ba kamar yanzu da take nan ba. Ko daya futa tuhumar kanshi ya dinga yi akan abinda yayi mata yanzu, shin ya kyauta kenan daya kawo mata labarin da zatayi farin ciki ya lalata shi da b'acin rai? Ko kuma ita laifin tane da kullum take labta lalle a hannunta ta dinga cika mishi hanci da k'amshin girki? Shin ya tab'a fad'a mata baya son lallenta shida karan kanshi yaga taci gaba dayi? Sai ya samu kanshi da zama a parlour abinda yakan jima baiyi ba, tar tar hoton fuskarta ya fara dawowa kwanyarshi da yadda tayi dariyar data bayyana duka hak'oranta waje, ba k'aramin kyau tayi a lokacin ba, lallai yayi missing daya lalata mata farin ciki bai gama k'irga hak'oran taba. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* Comment and share 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty eight4️⃣8️⃣ Haushin kanshi yaji akan yadda ya zauna yana ta tunaninta da lissafo jadawalin b'oyayyen kyawunta kamar wani marar abinyi. Tsaki yayi kafun tsam ya tashi ya shige d'akin shi ya rufo. Ko daya zauna a gefen gadon shi kasa nutsuwa yayi, idanun shi nata hasko mishi zara zaran yatsun hannunta da suka ci adon jan lalle, sai k'amshin turaren jikinta da yasha banban da sauran duk wasu turaruka daya sani a duniya, ga kayan snacks da take soyawa sunyi ja a cikin mai suna fudda k'amshin su, a gaba d'aya duniyar khaleefa ba abinda yafi so kamar snacks, ko yanzu a Germany kullum cikin yawon cin burger yake. Dafe kanshi yayi da duka hannuwan shi ya runtse ido amma still hoton fuskarta tana wannan murmushin sai gilma mishi yake a majigin kwakwalwar shi. Mik'ewa yayi tsaye ya kaiwa katifar gadon shi naushi wai ko zai ji ya daina tunanin ta, amma bai daina ba, ya zauna ya tashi, ya k'aro gudun AC dake aiki a d'akin amma duk ba sauk'i saima tsigar jikin shi data fara zuba saboda sanyi daya k'ara bayan wanda akeyi a garin. Daga k'arshe sai ya d'auki wayarshi ya futo daga d'akin ya bar mata gidan gaba d'aya. A harabar gaban gidan ya tsaya, yana k'arewa anguwar da shuke shuken harabar gaban gidan kallo, Saleema ce ta fad'o mishi ranshi, take yaji matsananciyar kewarta kamar yayi tsuntsu ya ganshi a gabanta yanzu, yana son ganin kyakkyawar fuskarta yayi kissing wannan cute lips d'in nata, yayi hugging d'inta da wannan plat tummy nata da yake wa ritsawa d'aya da hannun shi. Lokaci d'aya yanayin rayuwar da sukayi a baya ya fara dawo mishi daki daki. Abinda ya taimaka matuk'a wajen sauya mishi yanayin shi gaba d'aya cikin lokaci k'alilan. Gaba d'aya kanshi ya d'aure ya fara sarawa da d'aukar sabon ciwo har jijiyoyin kan na tashi rud'u rud'u. A haka Ahmad ya futo gidan shi ya hange shi, saiya taho zai k'araso inda yake saboda dama gurin shi zaije, fuskantar haka da khaleefa yayi ya fara juyawa zai koma inda ya futo ba tare daya nuna ya ganshi ba koda wasa, saboda a yanayin da yake baya son magana da kowa. Shi kuwa Ahmad zama dashi yau da gobe yasan kafatanin halayen shi, tabbas yasan ya ganshi ya nuna bai ganshi ba, me yiwuwa hakan baya rasa nasaba da yana buk'atar kad'aici, shima dama akwai abinda yake so ya same shi suyi shawara a kai, kuma yanzu muddin ya takura zasu iya samun matsala dashi, don haka sai shima salin alin ya shige gidan shi. *Bayan kwana ki biyu* Tun kafun ranar da zasu tafi raihana ta had'a kayanta a jaka guda, duk da kayan da zata tafi dashi bai huce kala biyu ba, sai undies da kayan bacci da dogon hijab da gyale d'aya. Yau kuwa data kasance ranar da zasu tafi da wuri ta shirya gudun samun matsala da man, tayi kyau cikin shigarta ta doguwar rigar lace A shape data zauna mata das a jiki ta bada shape me kyau wa surar jikinta. Yau bata saka hijab ba sai wadataccen gyalen data d'ora har saman kanta ya lullub'e ta ruf. Kusan a tare duk suka futo ita dashi kowa rik'e da jakar kayan shi, cikin ladab raihana ta gaishe shi, ya amsa ta kadaran kadahan. Yadda tayi kyau haka shima yayi kyau da shigar manyan kaya hula ce kad'ai babu. Ko raihana a ranta saida ta yaba kyawun da yayi, don ita a kaf dressing na maza ba wanda tafi k'imantawa kamar na manyan kaya. A kan d'aya daga kujerun parlon ta zauna ta barshi nan tsaye yana danna waya. Shi kuwa direct Ahmad ya kira ya tambaye shi ko yana sane da zasuyi late in bai futo ba yanzu? "Gani nan nima ai". Abinda Ahmad ya fad'a kenan k'it ya katse kiran. Raihana yabi da kallo duk da yadda ya dinga kwab'ar kanshi da k'ok'arin d'auke kwayar idonshi amma ya kasa, ba k'aramin kyau ta mishi cikin shigarta ta yau ba, gashi abinda yafi mishi dad'i yadda yau bata zuba wannan uban hijabin tasa in sun fita a dinga kallon su a k'asar daba tasu ba, abu na biyu yadda take da matuk'ar taka tsan tsan, tunda sukayi aure ba zaice ga abu d'aya da tayi mishi na laifi ba, duk abinda ya bata umarni karb'a d'aya take yi mishi, ko yanzu tafiyar nan da zasuyi ko lokacin tashin jirgin bai fad'a mata ba amma ta futo a ready kamar ta sani, kuma ko ranar daya sanar mata tafiyar bai b'ata bakin shi wajen yi mata dogon sharhi ba. Knocking k'ofa da akayi ya ankarar dashi Ahmad ya k'araso, sai ya d'auki jakar kayan shi yayi gaba itama ta biyo bayan shi, saida ya tsaya ta futo ya rufe gidan sannan suka nufi inda Ahmad yake tsaye da motar haya da zata kaisu filin jirgi yana jiran su. Duk suka gaisa da angon kamar kullum yauma har yana tsokanar raihana ya taji yau da zata Nigeria bayan kwashe watanni a Germany? Kamar kullum ba tace komai ba sai murmushi da tayi. Ko a cikin mota raihana da khaleefa kusa da juna suka zauna amma baiji wannan tashin k'amshin turaren ba, ba k'amshin ne babu kwata kwata ba, akwai amma mastad'a'a banda sunyi kusa ma ba zaiji ba. Misalin k'arfe uku da rabi na rana suka sauka a Nnamdi Azikiwe international Airport dake Abuja. Ba b'ata lokaci kuwa Ahmad ya d'auki waya zai kira y'an gidan su a turo driver ya tafi dasu, khaleefa ya hana, "haba man! Ga motocin haya nan da yawa ba sai mu tafi a su ba". Haka kuwa sukayi khaleefa ya samo motar haya ya fad'a mishi anguwar da zai kaisu. Sun samu tarba ta mutumci daga maman Ahmad da y'an uwan shi, barin ma raihana, da yake akwai k'annen Ahmad biyu da sukayi aure sunzo gidan suma biki sai suka yi ala ragab da ita. Khaleefa dama yana b'angaren Ahmad, zaman mintuna k'alilan sukayi, shima saboda sallah da cin abinci, suka sake futa basu dawo ba sai dare. Gaba d'ayan su a gajiye suke burin su d'aya da sunci abinci su kwanta, sun samu gidan da k'arin wasu cousins d'in Ahmad guda biyu suma da suka zo biki daga nesa. khaleefa koda Ahmad ya kawo musu abinci kasa ci yayi ya koma gefe yana danna wayarshi. Ahmad yasan sarai ko yana jin yunwa zai iya kwana a haka, saboda kasancewar shi d'an matuk'ar takura kai da yin abinda zai cuci gangar jikin shi. Ko shawara baiyi dashi ba ya nemi k'anwarshi khadija ya fad'a mata tasa raihana ta shirya mishi tea da wani abu mara nauyi da bazai d'auki lokaci ba. Ta kam da wuri ta gama shirin baccinta tayi kwanciyarta kan gadon d'akin da suke ita dasu ummu aphnan, da mamaki ummu aphu tace, "bacci da wuri kuma raihana? Don Allah ki tashi kada kanki ya shiga duhu nan ba gidan da zakiyi bak'unta bane" Mik'ewa tayi zaune ta kalli ummu aphnan data k'araso kusa da ita ta zauna ta dafa kafad'arta "Raihana mijin ki yana da kawaici da kara kamar yadda kike, a shekarun baya ban tab'a zaton Khaleefa zai auri mace sak da sak irin shiba, saboda masana tarihin soyayyah sunyi ittifakin ba'a zaman lafiya a gidan da aka had'a hali sak da sak, sai dai yanzu na k'aryata kaina ganin yadda kuke da mijin ki kuma kuke zaune lafiya,,,,, sai dai don Allah raihana kada idon mutane yasa ki cutar da khaleefa, tunda kuka zo ba ruwanki da bibiyar lamuran shi bare kiji ko yaci abinci ko yana buk'atar wani abun haka....". Gaba d'aya tunda ta fara maganarta har ta gama raihana bata fahimci abinda take nufi ba, tunda dai tasan khaleefa ba k'aramin yaro bane bare ace komai sai anyi mishi. Kamo hannunta ummu aphnan tayi tace, "yanzu ki taso muje na had'a miki komai Ahmad yace kin iya dafa Sudan tea irin na k'asar ku". Murmushi raihana tayi don tunda tazo suke ta kallonta y'ar k'asar su Auntie, hijabinta wadatacce ta d'ora saman riga da wandon baccin dake jikinta. Ummu aphu da kanta ta rakata har kitchen tana taya ta da hira har ta had'a tea d'in ta juye a plask, ta had'a faten doya da kwai da wadataccen kifi, kafun wani lokaci kitchen ya cika da k'amshi, khadija kam kasa hak'uri tayi saida ta zuba kad'an taci, tana ci tana ta yabawa raihana wai komai ta iya kamar rainon auntien su Khaleefa, raihana tana dariya a ranta tace ai d'alibarta ce. Duk yadda khadija taso hanata raihana k'in hanuwa tayi saida ta tsabtace duk inda tayi aiki ta had'a komai a tray, ta d'auki d'aya ummu aphnan ma ta d'au d'aya suka tafi. Suna zaune su kusan hud'u a lafiyayyen parlon, kusan duk sanye suke da kayan bacci, hira suke me kama da musu duk sun cika parlon da manyan muryoyin su ko sallamar da su raihana sukayi ba suji ba. Daga gefe ummu aphnan ta tsaya tana kallon su kawai, yayinda raihana take daga bayanta tana kallon khaleefa tana ganin yadda yake ta mayar musu da zance cikin nutsuwa da tattausan lafazi, tunda take dashi bata tab'a ganin yana magana da k'arfi kamar haka ba sai yau, kuma lallai akan abu me matuk'ar muhimmanci yake magana. Shima sanye yake da fararen kayan bacci sol a zaune kan k'aramin table dake tsakiyar parlon. Ahmad ne ya fara lura da shigowarsu ita da khadija, sai yayi gyaran murya ya mik'e yace, "guys ya Isa haka! Nima na yarda da gaskiyar khaleefa,,,, mu ajiye wannan maganar a gefe,,,,, Bismillah ku k'araso raihana". Sai a lokacin khaleefa ya d'ago ya fara laluben inda zai ganta a parlon, tafiya take amma kanta a k'asa har suka k'araso tsakiyar d'akin suka ajiye trayn a gurin. "Sorry Madame, mun saki aiki cikin dare.... Kinsan man ne iyayi gare shi kamar me laulayi, ba komai yake ciba". Ita dai ba tace komai ba sai murmushi da tayi. Kallon gargad'i khaleefa yayi ma Ahmad ba wasa yace, "ka dinga sanin me zaka fad'a a kaina". Ahmad yana y'ar dariya yace, "toh", khadija da take dariya itama tace, "aikuwa ta mishi girki me dad'in gaske". D'aya daga cousin sis na Ahmad mai suna jafar kallon raihana yayi yace, "toh Madame ai sai ki saving d'in mu ki k'arasa ladan ki ko". Aikuwa baiwar Allah sai ta fara k'ok'arin bin umarnin shi, sai dai Ahmad da khadija har rige rigen hanata sukeyi, "wane irin lada kuma a bawa k'aton banza abinci, raihana yi tafiyarki Allah ya bamu alkhairy". Saiya kalli khadija data rik'e mata hannu yace, "idan muna buk'atar wani abu zamuyi miki magana". Kai ta gyad'a taja hannun raihana suka tafi. Ita kuwa dama duk a takure take tunda suka zo ta kasa sakewa, da zata gaishe suma kamar marar gaskiya haka ta bud'e baki, yanzu kuwa da aka sallame su har ajiyar zuciya ta sauke. Jafar dama tana futa ya kalli khaleefa, "yae! Wannan yarinyar fa". Khaleefa da yasan za'a rina duba da irin kallon da yaga jafar yana yi mata, murmushi yayi yace, "jafar da magana ne?". Da sauri jafar yace, "me kyau ma kuwa, yarinyar ta burgeni sosai ga nutsuwa ga aji". Wani miskilin murmushi khaleefa ya sake yi lallai raihana tana da farin jini yana sane da duk inda suka je sai tayi saurayi, sai dai duk cikin tarin samarin nan har yanzu bai ga wanda zai iya bawa dama ya sameta ba, saboda har ga Allah nutsuwarta da hankalinta sun zarta na duka mazan, yana son raihana ta samu miji nagartacce na gasken gaske, yana son ta samu mijin da zai sota kwatankwacin yadda yake son Saleema yasan shi kad'ai zai iya rik'e ta amana. Shiyasa yanzu ya fara yiwa wani mutum mai matuk'ar daraja da k'ima tanadin ta, toh amma bari yaba jafar dama yaga ko zaisha....... "Kayi shiru khaleefa so nake ka huce mun gaba tunda y'ar uwar kace yadda bazan sha wahala ba". Wani murmushin khaleefa ya kuma yi yace, "kada ka damu zan mata maganar, duk da yanzu bata da lokacin soyayya". Zaro ido jafar yayi, a lokacin da Ahmad da takaici ya cika sa har takai ya kasa sa musu baki a zancen su ya mik'o mishi shayi. "bar shayin nan Ahmad hankalina bazai kwanta ba har sai mun gama magana da khaleefa". Khaleefa kuwa har ya karb'i shayin ya tuna da yatsun hannunta daya gani waccen ranar, saiya maida kan tray ya ajiye, da mamaki Ahmad ya kalle shi, "Wai kana nufin har yanzu jikinta da lallen". Da sauri mukhtar da shima bai sa musu baki a zancen suba saboda wasu abubuwa da yake tunani tsakanin raihana da khaleefan yace, "kamar ya fa". Saida Ahmad ya zauna sannan yace, "zancen mune nida shi duk ba zaku gane ba okay....". Zai sake cewa wani abu khaleefa ya katse mishi hanzari, "mubar maganar nan Ahmad please". Shiru duk sukayi kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarshi kafun jafar ya katse shirun nasu da cewa, "Ni dai don Allah khaleefa kayi mun magana d'aya". Wannan karon Ahmad ne yayi magana, "wannan fa jafar ba d'aya take da sauran matan daka sani ba....". "Hum! Ai fahimtar hakan nema yasa na kasa hak'uri saida na magantu". Cewar jafar. Wannan karon gyad'a kai Ahmad yayi kafun yace, "yayi mayen mata, toh wannan yarinyar dai matar aure ce". Wani irin kallo jafar ya mishi, kafun kuma ya sake cewa, "relax abokina abinda kake tunani sam ba haka bane, wannan sonta nake da gasken gaske aurenta zanyi, sannan Ina ganin da tana da aure khaleefa zai fad'a mun ai". Wannan karon kafun Ahmad yayi magana khaleefa ya riga shi da cewa "toh ai baka tambayeni wannan ba....". Mik'ewa tsaye yayi yana kallon Ahmad da khaleefa, mukhtar da yake zaune ya kyalkyale mishi da dariya, "dama na fad'a maka ka kiyayi zama tsakiyar mutanen nan biyu, ni nasan ma kawai matar khaleefa ce". Shima jafar da son tabbatarwa ya kalle su. Khaleefa dai mik'ewa yayi don dare yaja, sai Ahmad ne yace, "of course matar khaleefa ce". Jafar tsabar takaicin yadda suka mai dashi mahaukaci da hankalin shi yasa ya kasa cewa komai sai nuna Ahmad da hannu kawai, mukhtar da Ahmad kuwa banda dariya ba abinda sukeyi. "Wato duk a mahaukaci kuke kallo na?". Ya tambaye su Ahmad yace, "Haba jafar a gaban ka fa na kira khadija nace tasa matarshi ta shirya mishi wani abu yak'i cin komai, sannan ta shigo nace Madame kana nufin duk kanka bai kawo haske ba?". Jafar zama yayi yana tuna tabbas duk anyi haka, kawai abu d'aya da ya kwashe duk tunanin shi shine yadda yaga daga ita har khaleefa basu nuna akwai y'ar guntuwar alak'a tsakanin suba koda ta gaisuwa. Sai ya sunkuyar da kanshi yana matuk'ar jin nauyin khaleefa,,,,,, Mukhtar da Ahmad kam sun samu aikin yi a gaba d'aya daren ranar, magana kad'an zasu zolaye shi suyi dariya, tun yana taya su har ranshi ya b'aci ya bar musu gurin. Tun daga wannan lokaci har ranar d'aurin aure jafar bai sake sakewa da kowa ba, har rawar kanshi ya rage, dama Saleem abokin shi yasha fad'a mishi idan bai bar halayyar kule kulen y'an mata ba watarana saiya jawowa kanshi abun kunya, gashi kuma ya gani. Raihana kam tana can tare dasu ummu aphnan ta manta da babin ma wani khaleefa da matsalolin shi. Yayinda gidan biki suke gudanar da bikin su mara hayaniya, babu event ko guda ta b'angaren su sai d'aurin aure da aka gudanar ranar juma'ah bayan an idar da sallah, a ranar ne kuma auntie da Ayman suka k'araso. Raihana da yake tunda tazo ba suyi waya ba shiyasa bata san da zuwan taba. Surayyah kuwa koda suka gaisa da ummie ta mata Allah sanya alkhairy, hira suka tab'a ta yaushe gamo akan yara da aiki, (da yake kusan itama tsohuwar ma'aikaciyar banki ce, data ajiye aikinta ba don lokacin barin aikin yayi ba). Ayman kuwa dama tawagar angwaye yayi. Surayyah tana tason tambayar raihana amma ta nuna halin kara da kawaici, ita kuma ummie tana son taga wani cikin yaran gidan tasa a nemo wa auntien ita. Cikin sa'a kuwa sai ga Rabi'a, ita ta fad'awa tasa khadija ko Fatima su turo mata raihanan. A lokacin tana kwance can k'arshen gadon d'akin, sanye da doguwar rigar shadda data sha d'inki mai azabar kyau, ba headtie sai rolling da tayi da d'an k'aramin gyale tunda ba futa waje zata yi ba, fuskarta ba komai sai powder, man leb'e da kwalli, cikin gidan ma ba wanda yayi wata heavy make-up duk kamar kwalliyar fuskar raihana ce a fuskokin su. A lokacin da sak'on isowar auntie ya risketa da wani irin sauri ta tashi zaune tana tambayar inda take. Fatima ce ta rakata har parlon da auntien take, da tarin farin ciki ta tafi da gudu kamar zata rungumeta sai kuma kunya ta kama ta, daga auntie har ummie dariya sukayi mata, a gefen k'afar auntien ta zauna ta d'ora kanta jikin k'afar idonta cike da hawaye. Dafa kanta auntie tayi tace, "daga gani na sai kuka kuma?". Murmushi ta k'ak'alo a nutse ta fara gaisheta, ta amsa mata da tarin kulawa. Gwanin burgewa ummie ta dinga kallon su kamar uwa da y'arta, tana fatan Ahmad yayi sa'ar samun halayen yesmine kamar na Raihana. A daren ranar auntie tana zaune a d'akin da aka sauketa zata yi kwana d'aya ta koma, ta gama shirinta na kwanciya bacci tsab amma bata kwanta ba sai tagumi data rabka ta tafi duniyar tunani, idan tana lissafe yau sama da shekara talatin kenan rabon da k'afarta ta taka garin Abuja, kuma ko yanzu da tazo Allah Allah take gobe tayi ta bar garin ko hankalinta zai samu kwanciya, Zama gari d'aya da Suraj zai iya haddasa mata komai ciki hadda bugawar farat d'aya. Knocking k'ofarta da akayi yasa ta sauke ajiyar zuciya taje da kanta ta bud'e, raihana ce d'auke da tray na shayi. Saita bata guri ta k'arasa shiga ta maida k'ofar ta rufe. Saida suka sha shayin sudaniyyah sak da sak yadda ta koya mata sannan ta kalleta cikin tsanaki da tattara hankalinta guri d'aya ta kira sunanta, "Raihana". "Na'am auntie". Ta amsa da bata dukka hankalinta. Saida ta sake kallon k'afarta da hannunta ta gansu rad'au da lalle kamar sannan akayi shi sannan ta sake cewa, "wani abu nake son tambayarki game da rayuwar khaleefa! Amma kiyi mun alk'awarin zaki fad'a mun iya gaskiyar abinda kika sani". *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page forty nine4️⃣9️⃣ Raihana saida ta jinjina girman alk'awari, cike da tsoron abinda auntien zata so sani tace, "insha Allah zan fad'a miki gaskiyar abinda na sani". Auntie tace, "Good! Nace kina yin turare dai kullum idan kika futo wanka kamar yadda na koyar dake ko?". ... Gyad'a mata kai tayi. Saita sake tambayar ta, "kina barin lallen jikin ki ya futa kafun sake yin wani?". Ta sake jefa mata wata tambayar. Raihana tace, "a'a kafun ya futa nake k'ara saka wani...." "Good girl, khaleefa yana cin abincin ki idan kika dafa?". Tambayar tazo mata a bazata gashi tayi alk'awarin fad'ar gaskiya, tana tsoron kuma kada amsar da zata bayar ta tashi rigima tsakanin shi da mahaifiyar shi, don haka sai tayi shiru ba tace komai ba, "raihana tambayar ki nake". Ba tare data d'ago ta kalleta ba ta girgiza kai, "ba ya ci". Murmushi auntie tayi tace, "alright! Abu d'aya da zan sake tunasar dake dai shine, kinga lallen nan raihana, kada ki kuskura kiyi wasa dashi ki rik'e shi hannu bibbiyu kamar yadda nasha fad'a miki a baya, saboda wannan yana daga sirrin matan sudan da yasa a duniya suka shiga gaban kowanne mata musamman a gurin mazajen su, amfanin lalle a jikin mace yafi k'arfin kid'aya bare a iyakance shi, shiyasa a al'adar mu budurwa bata yin k'unshi da duk wasu sauran kwalliye kwalliye na mata har sai ranar da aka sata a lalle, daga wannan rana kuma ba za'a sake ganin k'afarta fari ba har tsufan ta, kinga lalle, kinga turare, kinga zaman iccen dukhan, girki, k'unshi, kitso, kwalliya da ladabi da biyayyah duk duniya su nasan muna rik'ewa mu zauna lafiya a gidan miji ba boka bare malam ba, toh ke girki da turare kad'ai ma kika rik'e ina da yak'inin saikin fasa zuciyar khaleefa komai taurinta raihana, ke dai kici gaba da hak'uri lokaci yana tafe da zaki juya khaleefa a hannun ki kamar masa". Duk wannan bayanin da auntie take raihana shiru tayi tana sauraronta kanta a k'asa, nauyinta take ji sosai shiyasa ta kasa d'agowa ta had'a ido da ita sai murmushi da tayi don kalmarta ta k'arshe ta bata dariya, wai ta juya shi kamar wani d'anta, a zuciyarta kuwa tunani take ko wane irin so wannan mata take mata da yasa har take bata manyan lagon d'anta haka kyauta. Ko a yanzu kafun ta tafi saida auntie ta k'ara mata wasu kayan lallen masu yawa tace ta k'ara akan nata gudun kada su yanke mata kafun ta kawo musu ziyara. Raihana bata tafi ba sai can dare shima bacci ne ya cika idonta, bayan sunyi sallama da Auntien ta d'auki hanyar futa daga d'akin tana murd'e mabud'i shi kuma yana turo murfin zai shigo, abinka da namiji ma'abocin k'arfi kamar an hankad'a ta haka ta tafi taga taga zata fad'i, cikin zafin nama yayi saurin rik'o ta, yadda ta shiga rud'anin fad'uwa yasa duk jikinta ya d'auki rawa, hakan yasa khaleefa ya kwantar da kanta a k'irjin shi yana buga bayanta. Sai ajiyar zuciya take saukewa a jajjere donta saddakar sai taje k'asa a lokacin. Ayman da yake bayan su cikin wani irin mawuyacin yanayi ya tsinci kanshi kamar an watsa mishi garwashin wuta a zuciya, da kyar ya iya d'auke idon shi daga kansu ya huce cikin d'akin yana karanto duk addu'ar da tazo bakin shi don yak'ar shaid'an la'anannen Allah. Khaleefa kuwa saida ya tabbatar nutsuwarta ta dawo jikinta sannan ya janyeta daga jikin shi ya k'arasa shiga cikin d'akin, ita kuma ta k'arasa futa da sauri. Duk abinda ya faru auntie ta gani sarai duk da kwayar idanunta bawai tana kallon su bane direct. A ranar khaleefa ya jima yana hira tare dasu don da gaske yayi kewar su gaba d'aya, bai tafi ba sai nisan dare sukayi mata sallama shida Ayman suka tafi makwancin su. Sai dai Ayman ranar kasa bacci yayi sai juye juye, a duk motsin shi sai ya hango kan raihana rungume a k'irjin twin d'inshi. Daga k'arshe da yaga nutsuwa tana neman gagarar shi sai ya d'auro alwala ya fara karatun alqur-ani da k'ira'a k'asa k'asa gudun kada ya hana khaleefa bacci. ******** Washe gari su Auntie zasu bi jirgin takwas na safe su kuma raihana sha biyu na rana, hakan yasa raihana ta shirya da wuri cikin doguwar rigar atamfa wrapper, d'inkin ya mugun zauna a jikinta kamar a jikinta aka d'inka, bata sa turare ba amma duk da haka tashin sassanyan k'amshin daya zauna a jikinta take, da wadataccen gyale tayi rolling ta futo suka gaisa dasu Fatima ta gaishe da ummie da sauran mutanen gidan sannan ta tafi gurin Auntie, ko breakfast bata tsaya yiba, sai data nemi izini daga auntien sannan ta shiga cikin d'akin. Tana zaune ita kad'ai a tsakiyar d'akin sanye da lufaya maroon colour da aka yiwa ado da manyan flowers black sai stones a jiki kamar yadda dai tazo jiya, a kullum raihana ta kalli matar nan sai taga kamar ba ita ta haifi su khaleefa ba saboda baiwar kyawun jiki da Allah ya mata, da kasancewarta ma'abociyar son kwalliya da k'alk'ale jiki kullum ba datti, iya zaman da tayi tare da ita ta fahimci duk sammakon ka ba zaka tab'a ganinta cikin datti ba, kamar ita su Yaya Ayman suka gada. "Raihana k'araso mana ya zaki tsaya kuma". Ta fad'a tana kallon raihanan da yaba nutsuwar ta, komai nata a sanyaye bada zafi ba. A k'asa ta zauna suka gaisa da auntien taji lafiyarta "Raihana wanko hannun ki ki tayani mu cinye abincin nan dama yayi mun yawa". Ba tayi mata musu ba ta tashi ta wanko hannun ta fara cin abincin a tsanake, suna ci auntie tana janta da hira, wani abun tayi dariya wani kuma tayi murmushi a haka khaleefa ya shigo bakin shi d'auke da sallama, kallo d'aya yayi musu ya d'auke kanshi ya durk'usa gefe ya fara gaishe da maman shi, ta amsa da fara'a kan fuskarta kamar babu komai. Itama raihana ta gaishe shi da girmamawa. Bai jima da zama ba Ahmad da Ayman ma suka shigo. Duk suka gaisheta, ta k'ara yiwa Ahmad Allah sanya alkhairy da gajeriyar naseeha kan hak'uri da rayuwar aure. Ko data tashi tafiya gudunmuwa mai yawa taba ango da maman shi, raihana kam tana kuka suka rabu bayan ta mata alk'awarin tana tafe Germany nan da watanni uku insha Allah. Babu wanda ya rakata airport cikin su don cewa tayi ta yafe tunda suma tafiyar zasu zo suyi bada jimawa ba. Tare da aphnan raihana ta k'arasa zaman jiran lokacin tafiyarsu, wannan karon daga ita sai khaleefa sukayi sallama da kowa Ahmad ya sauke su airport suka d'auki hanya sai Germany. Su biyu suka koma wannan karon ba kamar yadda suka zo ba, saboda Ahmad zai huce turkey ya taho da amaryarshi Yasmine ne. Wannan karon ma sai yamma suka sauka a gajiye lik'is. Tare suka jero suna tafiya sannu a hankali har suka isa inda zasu samu motar hayar da zasu hau. Koda suka shiga gida babu wanda ya kalli d'an uwanshi suka raba hanya, da kyar ta iya yin wanka ta sauya kayan jikinta ta rama sallolin da suka huceta ta kwanta sai bacci. Shima khaleefa wankan yayi ya rama sallolin da suka huce shi ya kwanta don ya huta kad'an kafun ya tafi nemo abinda zaisa a cikin shi. Bashi ya farka ba sai nisan dare da wata irin azabtacciyar yunwa kamar ya ci babu. Yana duba agogo yasan kashin shi ya bushe don ba wani gidan abinci da zai tunkara a daren nan har ya samu abinda yake so, ruwan da baya rabo dashi a bedside ya d'auka yasha, aifa kamar wanda yasha guba haka yaji, gaba d'aya duniyar shi ta fara juyawa kamar ana hajijiya dashi, da dafa bango ya laluba ya futo daga d'akin ya zauna kan kujera d'aya dake cikin parlon ya had'a kai da gwiwa. Itama raihana ta b'angarenta yunwar ce ta farkar da ita, sai kuma ta tuna da sallar isha'i da ba tayi ba, hakan yasa ta fad'a bathroom da sauri tayi alwalah ta futo. Ko data idar da sallar hijab ta zura ta futo parlon donta samawa kanta abinda zata ci, a lokacin khaleefa yana zaune kan kujera ya had'a kanshi da gwiwa yana tunanin yadda zaiyi da rayuwarshi, dama tunda suka je bikin gidan su Ahmad bai iya cin wani abincin kirki sosai ba, a yau da zasu tafi ma k'in cin komai yayi yana ganin har zai ziyarci gidan abinci idan jirgin su ya sauka Germany ya samu abinda zaici, sai gashi gajiya ta hana mishi damar hakan, yanzu kuma yadda yake jinshi gani yake tak'i kad'an ne tsakanin shi da mutuwa gaba d'aya baisan abinda ya kwance mishi ba. Raihana kuwa koda ta kalle shi sau d'aya hucewarta tayi kitchen, ta samu kitchen d'in k'ura fal kamar ta shekara bata nan, tasan dama za'a rina duba da iskar da ake bulbulawa a garin. Abinda zata yi amfani dashi kad'ai ta duba, tea ta fara had'awa don warware hanji, kafun ya tafasa kuma ta had'a abinda zata yi sauk'ak'k'en abinda zata ci don magance yunwar cikinta a lokacin. Tana cikin aikin khaleefa ya shigo a wani irin jirkitaccen yanayi, saida gaban raihana ya fad'i data ganshi, stool yaja ya zauna don bazai iya tsayuwa ba, ya kife kanshi jikin middle drower kitchen d'in, cikin damuwa da nuna kulawa raihana ta tambaye shi, "are you okay?". Girgiza mata kai yayi, hakan yasa ta shiga rud'ani har takai tana k'ara tambayarshi abinda ya same shi. Shi kuwa tsabar azabar da yake ji tasa ya kasa magana sai jujjuya kai da hannu kurum, abinda ya sake jefa raihana a tashin hankali har ta kaiga ta yanke hukuncin kiran auntie a waya ta fad'a mata. Sai dai tuna nisan dare ne yanzu musamman a Nigeria da tashin hankalin da zata sasu yasa ta hak'ura, amma gaba d'aya ta kasa nutsuwa sai kallon shi take da tarin damuwa tana jero mishi sannu. Shi kuwa khaleefa ta b'angaren shi azaba yake karb'a ba daga ko'ina ba, Kai tsaye a lokacin ba zaice ga takamaiman abinda yake damun shiba ma, abun da yake ji yana soya mishi k'irji had'e da murd'a cikin shi bai tab'a jin kwatankwacin shi a tsawon rayuwar shiba. Tun yana iya juya kanshi da addu'a har hakan ya gagara, sai kawai ya kwantar da kan ya d'auke wuta, abinda ya sake furgita raihana kenan ta d'ora hannunta aka ta fashe da kuka cikin matsanancin tsoro. Kamar me tsoron wani abu kuma haka ta dinga k'arasawa gaban shi tana k'ara volume d'in kukanta. Hannunta ta d'ora saman kanshi ta kira sunan shi a sanyaye, karo na farkon a tarihin rayuwar khaleefa da yaji sunan shi a bakinta "khaleefa!!". Bai iya amsa mata ba sai hannun shi daya d'ora saman nata don ya tabbatar mata yana jinta, aikuwa ta dinga sauke ajiyar zuciya a jejjere tana hamdala da Allah yasa bai mutu ba yana raye. Janye jikinta tayi nesa dashi bayan ta d'auke hannunta daga kanshi ta kashe gas da yake aiki. Tana nan dai tsaye kamar soja sai sannu take jera mishi lokaci bayan lokaci kuma tana share hawaye. Shi kuwa saida ya samu ciwon ya lafa mishi kad'an ya tashi zaune yana kallonta da idanun shi da suka dawo dishi dishi. "sannu ya kake jin jikin naka?". Bai iya amsa mata ba saboda wani mugun amai daya yink'uro mishi, ya mik'e da sauri don ya futa daga kitchen d'in sai dai taku d'aya ana biyu ya durk'ushe a gurin ya fara kelaya amai. Gaba d'aya raihana ta rud'e ta rasa inda zata tsaida k'afarta sai jera mishi sannu take, ko daya gama ita ta bashi ruwa ya wanke fuskarshi da bakin shi tunda kayan jikin shi basu lalace ba, taja mishi stool ya zauna ita kuma ta fara wanke gurin, saida ta tsabtace gurin tass duk yana kallonta sannan tazo ta had'a mishi tea me kyau ta mik'a mishi, ya karb'a da kyar yana bin yatsun hannunta da kallo, bashi da wani zab'i a yau. Saida ya rintse idonshi ya toshe hancin shi gudun kada yaji warin lallenta sannan ya fara sipping tea d'in kad'an kad'an, kafun ya gama kuma tayi sauri ta had'a mishi betroos, sweet potatoes, egg and mayosauce ta juya mishi sun gauraye guri guda ta ajiye mishi plate d'in a gaban shi. Ya d'auka ba tare daya kalleta ba ya fara ci a nutse, yaci zai kai rabi ya maida plate d'in gefe. Sai a lokacin hankalin raihana ya kwanta har ta tuna da yunwar cikinta itama, ta tsiyaya tea tasha, ta ci ragowar abincin daya rage tunda dama shi kenan ta dafa. Abinda yasa ta matuk'ar baiwa khaleefa tausayi kenan, sau biyu tana nuna mishi sadaukarwa, yana sane a waccen ranar ma ba irin zagin da ba'a yi mata ba ta jure amma ana tab'a mahaifiyar shi ta maida raddi, gashi a yauma ta dafa abincinta don taci ganin shi a mawuyacin hali ta hak'ura daci har saida shi yaci ya rage, toh da bai rage ba kuma shikenan sai dai ta kwana da yunwa?, Anya kuwa akwai irin wannan yarinyar a zamanin nan? Toh ko Saleema dai iyakacin abinda zatayi mishi kenan. Khaleefa bai tashi daga inda yake zaune ba har saida ta wanke kayan da tayi amfani dasu a lokacin, bata jin bacci sam cox abinci da shayin da tasha yasa idonta ya bushe, hakan yasa ta yanke shawarar goge k'urar data cika mata d'akin girkin. Khaleefa yana zaune ya kasa tashi sai bin duk wani motsinta yake da kallo har ta gama, a nan ya sake tabbatar da tsabtarta kamar auntien shi. Ita kuwa saida ta gama ta d'auki hanyar futa a kitchen d'in ta kalleshi tace, "Saida safe Allah ya k'ara lafiya". A sanyaye ya amsa da, "ameen nagode". Ba tace dashi komai ba ta huce, shi kuwa khaleefa shiru yayi yana nazarin wasu abubuwa masu girma tattare da ita, ya jima a gurin zaune kafun ya kashe wutar d'akin girkin ya futo, a parlour yayi kwanciyarshi don sam baijin komawa cikin d'akin shi. *NIGERIA* Amarya Saleema tana zaune a parlonta da safiyar washe garin kaita gidan mijinta, tayi kwalliyarta me kyau cikin riga da zani na wata atamfa blue tayi parking gashinta dokinta a k'eyarta tayi d'auri a saman shi. Wayarta ce a hannunta tana yin chat da k'awayenta. A dai dai lokacin Imran ya futo shirye cikin shaddar shi dakakkiya, tak'aitaccen kallo yayi mata ya d'auki hanyar stairs zai sauka, ba tace mishi ba shima baice mata ba har ya futa. Kai tsaye gidan auntien su ya nufa ya sameta tana aikin had'awa yara abun kari, a parlonta yayi zaman shi yana taya k'aramar k'anwarshi assignment kafun auntien ta futo ta ganshi, saita saki baki tana kallon shi da mamaki, "ango ne da wannan sammakon gidana?". Murmushi yayi ba tare daya bata amsa ba ya fara gaisheta. Ta amsa tana tambayar lafiyar Amarya, ya bata amsa da, "tana lafiyarta". Ci gaba da taya baby assignment yayi ita kuma ta gama aikin had'awa sauran yaran breakfast ta had'a kansu har baby don suyi su karya taje ta ajiye su school gudun kada suyi late, Sam bata d'auka yau zai buk'aci abincinta ba tunda taga dai ai yanzu yana da aure ba irin da ba, shi kuwa Imran kusan abinda ya kawo shi kenan don haka sai baiyi kara ba ya tambayeta abincin. Saida ta gama zolayarshi Wai ta yaye shi sannan ta shiga kitchen ta had'o mishi a plate. Ko daya gama breakfast shiya huce mata da yaran makaranta kamar yadda ya saba a duk lokacin daya je musu gidan da safe, ya raka su har harabar makarantar sannan ya huce kasuwa. Saleema kuwa tana nan zaune hajiya tafeeda tasa aka turo mata da lafiyayyen abinci, taci ta k'oshi tabar kayan a nan dinning ko Imran zai dawo yaci ita kuma ta shige d'aki tayi kwanciyarta. Hajiya tafeeda tun tana saka ran saukowar Saleema ta gaisheta har ta gaji, ragowar bak'i y'an biki da suka tashi tafiya suka ce zasu je suga amarya, bata hana suba sai dai har suka shiga suka gama sallamarsu a parlon bata kula suba tayi banza dasu saboda sunzo a lokacin da take waya da k'awayenta, haka suka gaji da zama suka tafi ba suga ko k'eyar amarya ba. Ko da suka fad'awa hajiya tafeeda ba tace musu komai ba sai shiru da tayi tana tunanin ko bacci takeyi? Ko Kuma har yanzu dai jikin ne. *********** A hankali ranaku suka dinga tafiya har gashi kusan sati da auren Imrana da Saleema amma ko sau d'aya hajiya tafeeda bata samu arzik'in gaisuwa a gurin shaheeda ba, tun tana kawo uzururruka a zuciyarta har ta daina, har yanzu bata fasa aika mata da abinci sau uku a yini ba, amma ko d'and'ane Imran bai tab'a yiba, a kullum safiya zai sauko ya gaishe ta a matsayinta na mahaifiyar shi, daga nan kuma yayi tafiyarshi gidan auntien su ya karya ya huce kasuwa don tunda yayi aure bai d'auki hutu ba, toh hutun mema zai zauna yayi, matar da ba ra'ayin shiba. Idan suka tashi kasuwa yakan zauna tare da abokan shi a majalisa ko ya tafi gurin dad d'inshi ko kuma ya dawo gidan ya shige d'akin shi ya kwanta kafun lokacin bacci yayi ya shirya ya tafi d'akinta don bai tab'a raba makwanci da ita ba kamar yadda bai tab'a neman komai a gurinta ba. Yauma kamar kullum ya dawo gidan wajen k'arfe tara na dare bayan ya biya gidan auntie ya cika cikin shi taf, tana zaune hamshak'iyar ta mik'e k'afarta kan doguwar kujera tana danne danne a waya, ya k'araso cikin parlon yana yi mata sallama, ta amsa tana yi mishi sannu da zuwa, baice mata komai ba ya ajiye mata ledar fruits a gefenta shi kuma ya shige d'akin shi. Da kallo ta bishi har ya shige sannan ta dawo da idonta kan wayarta tana jan siririn tsaki, ba laifi shima guy nan ya had'u amma ba kamar khaleefa ba, banda wannan matar ta shigar musu hanci aida yanzu itace khaleefa ya aura ba raihana ba. Da dare tana kwance bayan ta sauya kayan jikinta zuwa na bacci ta sake feshe jikinta da turarukan ta kwanciya tayi tana karanta addu'ar bacci a zuciyarta. Tana jin shigowar Imran ta d'auke wuta kamar tayi bacci, shi kuwa yau yazo ne ya maida ita cikakkiyar matarshi don bashi da wani zab'i. A gefen gadon ya zauna yana waya da wani abokin shi abokin kasuwancin shi da ya tafi Lagos a madadin shi, duk wayar akan abinda ya shafi harkar kasuwancin sune, ya jima suna tattaunawa kafun suyi sallama ya ajiye wayar, Saida yayi addu'o'in shi ya shafa sannan ya kwanta yana fuskantar bayanta, ya dad'e yana tunanin raihana a zuciyarshi kafun ya matsa jikinta yayi hugging d'inta tightly a k'irjin shi. Wani irin rass! rass!! shaheeda taji a lokacin data jita gaba d'aya a jikin shi karo na farko a tarihin rayuwarta. Shi kuwa a nutse ya dinga aika mata da sak'onnin shi, ba tayi yink'urin hana shiba saida taga ya fara hargitse mata kamar ba shine yake tafiyar da ita gently ba, take maganar da sukayi da k'awarta feena ranar da tazo ta dawo mata a rai, tsoro da firgici suka shige ta aikuwa ta mik'e da sauri taja duvet tana jifan shi da wani irin kallo duk jikinta ba inda baya rawa. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty 5️⃣0️⃣ Dafe kanshi yayi da duka hannuwan shi, ita kuwa ido rufe cikin maseefa take cewa, "futa! Ka futar mun daga d'aki Imran tun kafun nayi maka rashin mutumci a cikin daren nan, dama wannan ne dalilin da yasa kake shigo mun d'aki kullum dare? Toh wallahi tunda wuri ka kama kanka don ba zaka tab'a samun abinda kake so daga gare niba.....". Yadda ta rufe Ido tana fad'in duk maganar da tazo bakinta sai kawai Imran ya saki baki yana kallonta. Duk da maganar da takeyi ta k'ona mishi rai amma ko a zuci baiji zai iya kulata ko ya bata amsa a lokacin ba. Jiki a sanyaye ya sauka daga gadon yaja jikin shi ya futa zuciyarshi na k'una, wai shi wannan yarinyar take zagi da fad'awa duk abinda yazo bakinta kamar wani sa'anta. Shaheeda kuwa saida ta murzawa d'akinta key ta tabbatar ta tsira sannan ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. A daren ranar kasa hak'uri tayi saida ta turawa feena k'awarta text, "Wai me yasa kika sani nasha wannan maganin? Kuma sai yaushe zai daina aiki a jikina". Tana tura sak'on ta ajiye wayar ta kwanta don tasan ba samun refly zatayi a wannan lokaci da dare ya fara nisa ba. Ranar haka shaheeda ta dinga bacci ko sallar asubah bata iya tashi ba har saida gari yayi haske. Cikin baccinta taji kamar ana buga wani abu tsakiyar kanta. Aikuwa ta tashi a razane, saida ta nutsu sannan ta gane k'ofarta ake bugawa haka, ta tashi a hankali ta nufi k'ofar tana tunanin wanda yake mata wannan bugun tashi ka mutun da safiyar Allah. Tana bud'ewa idanunta suka fara tozali dashi, yana tsaye da shirin futa kasuwa, saida gabanta ya fad'i da tsorata da ta ganshi donta d'auka sake dawowa yayi, hakan yasa ta fara k'ok'arin maida murfin zata rufe, Imran cikin sabon b'acin rai ya tura ta daga ita har k'ofar ya shiga cikin d'akin yana mata wani mugun kallon gargad'i. A lokacin ba abinda take sai zare ido da muzurai, Saida Imran ya gama mata kallon k'ask'anci up and down sannan ya huce ta ya shiga ya d'auki wayarshi inda ya barta jiya. Tana nan tsaye rakub'e da murfi tana sauke numfashi yazo zai huce, har ya futa ya tuna da wani abu sai ya dawo, ya auna ta daga sama har k'asa ya tab'e baki, "meye sunan kima?". Cikin yaba rainin hankalin shi shaheeda baki na rawa tace, "shaheeda". K'ara tab'e bakin yayi ya kalli gefe guda yace, "hajiya shaheeda ke yanzu a tunanin ki saboda me na aure ki?". Shiru tayi kanta a k'asa ta kasa amsa mishi, "tambayarki nake kinyi shiru kina jina". Girgiza mishi kai tayi a d'arare tace, "nima ban sani ba". "Gud! Daga yau zan fad'a miki idan kina zaton na aure kine don wani abu ki daina, ni na aure kine saboda mahaifiyata ba wai don soyayyah ko wani abu daban ba, sannan kamar yadda ban musa mata maganar auren ki ba, bazan yi yink'urin cutar dake ko shiga hak'k'in kiba, wannan yana daga dalilin da yasa kike ganin sassauci a tare dani, sannan shine dalilin da yasa na nemi hak'k'ina dake kanki a daren jiya ba wai don kin isa mace, ko kina da wani abu da yaja hankalina ba, in aka d'auke kyaun fuska baki da wani abu da zakiyi tak'ama dashi, kada ki manta akwai millions of mata marassa aure a garin nan, kuma a cikin su zan iya samun wanda suka fiki komai a yau ba sai gobe ba,,,,, Soo ki kama kanki niba irin mazajen da za'a ciwa mutumci akan k'aramin abu bane Ina fatan kin fahimta?". Da kyar ta iya gyad'a kai, yasa kai ya futa daga d'akin ita kuma ta durk'ushe a gurin tana kuka, wato tunda take a rayuwarta wani mutum bai tab'a ci mata mutumci irin yadda Imran ya mata ba a yau, wato itace yake nufin bata da suffa irinta mata saboda kawai bai samu abinda yake so daga gareta ba? Mik'ewa tayi taje gaban mirrow tana sake k'arewa kanta kallo wai ko zata ga gaskiyar abinda yake fad'a. Ta jima a gaban mirrown tana kuka da tunane tunanen zuci kafun ta share hawayenta, ta wanzar da murmushi saman fuskarta. Ta lashi takobin saita nunawa Imran ita d'in ta huce yadda yake zaton ta, sai yazo har inda take ya rok'e ta akan ta soshi. (🤔 Shaheeda kina son lasar takobi da wuri) Yauma kamar kullum tayi wanka tayi kwalliyarta cikin k'ananun kaya da suka zauna a jikinta, tana zaune tana tunanin abinda ya hana a kawo mata abincin kari har gashi lokaci yaja, ga ko masu aikin da ake turo mata ma yau basu zoba tun d'azu sai zuba ido take yi. Ganin tana tunkarar yini guda ba ko d'aya daga abinda aka sabar mata da shi a gidan sai ta tashi da kanta ta nemawa kanta abinda zata ci, ko data gama cika cikinta aikin ma da kanta tayi. Washe gari ma haka ce ta kasance, wata washe garin ma haka, tun shaheeda na kid'aya har kwana ki suka yita tafiya ba y'an aiki bare abincin da ake kawo mata. Gashi abinda tayi ranar da aka kawota yasa mammie ta hana su Nur da duk wani makusancin ta zuwa gidan, sai k'awayenta da suke d'an zo mata time to time suma sai in an tashi lectures da wuri ne. Gaba d'aya shaheeda ta shiga damuwa a rayuwar gidan, tun ranar da suka samu sab'anin nan da Imran bai sake ko kallon inda take ba, d'akin nata ma ya daina zuwa. Ga a satin nan take son komawa makaranta don k'awayenta sun fad'a mata gab suke da fara exams, ta kira mammie a waya ta fad'a mata tace ita ba huruminta bane mijinta zata fad'awa tunda yasan da maganar karatun tun farko. Shiru shaheeda tayi tana tunanin ta yadda zata iya tunkarar Imran da zancen komawa makaranta, ita da ko gaisuwa bata had'a su. Sosai ta shiga damuwa cikin satin, sau uku tana zuwa hanyar d'akin shi tana komawa, ta rasa ta yadda zata iya je mishi da maganar. A k'arshe dai saita hak'ura ta koma d'akinta ta d'auko wayarta ta kira feena k'awarta ta rok'e ta don Allah tazo gidanta akwai shawarar da zasuyi, hak'uri ta bata don ita inba ranar makaranta ba bata samun damar futa ko nan da harabar gidan su. Haka shaheeda dai ta hak'ura har sai nan da kwana biyu inta futo makarantar. Aikuwa kafun kwana biyu shaheeda duk ta k'osa, ranar da feena zata zo ko abincin safe bata iya dafawa ba bare taci. Feena kamar yadda ta mata alk'awari ta futo da wuri a gida kafun lokacin shigarsu lectures. Direct gidan shaheedan tayi ta parking motar ta a k'ofar gidan ta shiga. A lokacin shaheeda tana tsaye a balcony ta k'osa da zaman jiran zuwan feena ta fara kiranta a waya kenan sai kuma gata ta shigo. "Kina da damuwa k'awata". Ta fad'a bayan ta zare farin glashin idonta, ajiyar zuciya shaheeda ta sauke tana kallonta kamar tayi kuka tace, "ai kece feena kin kasa fahimtar a halin da nake". "Toh kin fad'a mun halin da kiken ne? Naga cewa kikayi kawai kina nema na". Feena ta kai k'arshen zancen tana zama kan d'aya daga kujerun parlon. Itama shaheedan kusa da ita ta zauna ta rik'o hannunta da damuwa tace, "kwana na uku a gidan nan bana iya bacci sai b'arawo, feena na rasa ta yadda zan tunkari Imran da maganar komawata makaranta". Dariya feena ta kyalkyale mata dashi ta kalleta da mugun mamaki tace, "see you don Allah! Ke yanzu ko kunyar kanki baki jiba wai kin kasa bacci sai b'arawo saboda wani can da baisan kina yiba,,,, don Allah k'awata kada ki maida kanki bagidajiya ni miji har saina tsaya neman wani yardar shi kafun aiwatar da abinda ya zamo mun dole? Bada karatun ki ya ganki ba?". Da k'arin damuwa shaheeda ta girgiza mata kai, "ba zaki gane ba feena! The fact is mammie ce tace dole saina nemi izinin shi kafun komawa makarantar,,,, kuma ke kinfi kowa sanin abinda ya had'a mu wancen ranar,,,, da muna da guntuwar alak'ar kwanciya muhalli d'aya da kuma gaisuwa, amma a yanzu ko kallon banza ban ishe shiba bare har nace naga fuskar da zanyi mishi wata magana irin wannan....". Mik'ewa tsaye feena tayi ta d'auko ruwa me sanyi a fridge tasha, ta sake kallon shaheeda data zuba mata ido tana jiran a sama mata mafuta, "Wai baki da wani abinci a gidan ki ne shaheeda, saboda azalazalarki fa ko breakfast ban samu nayi ba na futo daga gida". "Allah safeenatu kina da matsala! Ya ina miki magana mai muhimmanci kina kawo mun shiriritarki, waccen ranar akan maganar maganin nan mafa haka kika yimun kika barni ba gamsashshiyar amsa". "Ohh! Shaheeda kina nufin yunwar cikina ce shiriritar?". Feena ta fad'a tana nuna kanta "Eh mana toh nima ko abincin ban iya ci ba tun safe, infact ban dafa komai bama yau". Tab'e baki feena tayi tace, "ke kika ji zaki iya,,,, muyi mu gama maganar mu in tafi inda zan samu abinda zanci don akwai lukutar matsala in naci gaba da zama a haka". Saita sake zama kusa da ita tana tambayarta, "Wai kina nufin tun waccen ranar bai sake waiwayar kiba". "Eh mana! Ba abinda nake ta k'ok'arin fad'a miki ba kenan waccen ranar da kika zo amma kika k'i saurarona,,,, wallahi feena na rasa yadda zanyi". Shaheeda takai k'arshen maganarta kamar tayi kuka. Feena ganin yadda shaheeda ta d'auki maganar serious saita kama kanta itama ta zama serious, "yanzu ya kike son ayi shaheeda? Ni kike son naje naba mijinki hak'uri ko kuma yaya". Cikin damuwa shaheeda tace, "haba feena ki fahimci abinda nake nufi mana, mutumin nan ko kallona baya yi fa". Feena cikin k'osawa da jin magana d'aya a gurinta tace, "toh ke sai kace ba mace ba, kibi duk hanyoyin daya dace mana ku shirya saiki tambayeshin tunda b'uruntun bakin ki yasa kin fad'awa mammie harta kafa miki sharad'i,,,,, sannan naji kina batun wai maganin dana baki kwana ki menene....". Shiru shaheeda tayi tana nazari kafun can tace, "na tambayeki ai yaushe zai daina aiki baki fad'a mun ba". Dariya sosai feena ta mata kafun ta d'an tsagaita tace, "ke nifa ba wani magani dana baki tsokanarki nake wallahi,,,,". Cikin rashin fahimtar ta shaheeda tace, "ban gane ba". Feena tana dariya tace, "ai dama ba zaki gane ba,,, toh in banda kema taya zaki yarda da duk abinda na fad'a miki sai kace baki san wace niba.....". Tsabar takaici shaheeda sai kawai ta fashe da kuka tana kallonta tana fad'in, "Amma feena ban yafe miki ba wallahi,,, yanzu fisabilillah taya kike tunanin zan shawo kan Imran har mu daidaita mu zauna lafiya? Kinsan fa ni ba fiye jure tashin hankali nayi ba". Feena tana dariya har lokacin tace, "toh ni taya zan sani nida ba matar aure ba,,, abu d'aya kawai dana sani ki cire girman kai ki bashi hak'uri,,,,, shima dai don wani irin baud'ad'd'e ne in banda haka taya zai iya d'auke kanshi daga zukekiyar budurwa kamarki k'awata....". Ta kai k'arshen zancen tana share mata hawayen fuskarta had'e da bata hak'uri. Da kyar ta samu ta shawo kan shaheedan ta hak'ura, tare suka shiga kitchen suka dafa abinda suka ci, feena bata tafi ba har saida ta kusa yin late suna ta shawarta me yiwuwa ita da k'awarta, shaheeda har bakin get ta rakata duk k'annen Imran sun ganta amma bata shiga cikin gidan donta gaishe da hajiya tafeeda ba, Koda wasa tunanin hakan baizo kanta bama. Washe garin ranar da wuri ta tashi tayi duk abinda ya dace, tayi kwalliyarta mai kyau cikin doguwar riga y'ar gaske ta zauna dakon futowarshi, bata jima da zama ba kuwa ya futo da shirin futa office kamar kullum. Saita tashi da sauri ta russuna tana gaishe shi, ya d'auke kanshi tamkar bai ji taba, ganin ya d'auki hanya da gaske zai futa sai tayi shahada tace, "Ina son zan koma makaranta". Ba tare daya waiwayota ba yace, "zaki iya fad'awa mom don ita ta auro ki kuma zamanta kike". Yana gama fad'a ya dusa kanshi ya fuce. Shaheeda a gurin ta zauna tana tuna kalmar mom daya fad'a, in banda yanzu daya ambaci sunan mom ta manta da ita gaba d'aya a cikin babin rayuwarta, tunda ya fad'i haka ba wata mom da zataje tambaya tafiyarta kawai zatayi ai aurenta ba'a hannunta yake ba. @@@@@@@@ Washe gari shaheeda ta shirya tunda wuri ta d'auki katin cirar kud'i ta fuce a gidan tayi tafiyarta makaranta, abinda ya d'aure kan mom kenan don an tabbatar mata anga futar shaheeda a safiyar yau,,,,,, zuwa yanzu lamarin shaheeda ya fara shallake tunaninta, amma bata son yiwa mahaifiyarta magana tukun zata ci gaba da d'aga mata k'afa har zuwa lokacin da zata tabbatar da abinda yarinyar ta taka. Bata dawo gidan ba sai dare da tulin handout da past question papers, sallah kawai tayi don taci abincinta a capteria, ta baje takardu tana duba abinda ya huce ta cikin satikan da suka gabata. Kusan kwana hud'u shaheeda tana futa kuma duk bata dawowa gidan sai dare, don ko sun tashi lectures group discussion take zama tare da tsirarun y'an department d'insu don a lokacin kansu ya d'au zafi kowa burinta ta samu five point, don wannan tana daga second to the last year d'insu su kammala had'a degree na farko... Shaheeda kam dama ko bayan ta dawo gidan tsinke bata iya d'aukewa, in banda wanka daya zamo mata dole ko kayan jikinta inda ta cire nan take barsu gidan duk yayi kaca kaca musamman d'akin barcinta. A rana ta hud'u hajiya tafeeda ta gaji da wannan sabon al'amari da sam bata gane kanshi ba a gidan ta kira Imran a waya tace in ya taso kasuwa lallai lallai tana son ganin shi. Rabon daya shiga gidan da dare har ya manta sai yau,,, su hamra ne kad'ai a parlon amma ita tana d'akinta, cikin parlon ya zauna suka dinga gaishe shi d'aya bayan d'aya, ya amsa su cikin kulawa yana kallon su da tausayin yadda mom take son shiga rayuwarsu k'arfi da yaji, don a zaune take duk abinda kayiwa d'an wani sai an yiwa d'anka. Yana nan zaune ta futo daga cikin d'akin ya russuna yana sake gaisheta, ta amsa kadaran kadahan ba tare data zauna ba ta tambaye shi, "tun yaushe ka shigo d'an suwaiba? Don ni yanzu na tattara ka na bar mata tunda ita ka zab'a matsayin sabuwar uwarka data fini,,, yanzun ma na kira kane don naji koda d'aurin k'ark'ashin ka shaheeda bata zaman gidan nan?". Shiru yayi yana nazari kafun can yace, "nima ban sani ba kwanaki dai tace mun tana son komawa makaranta sai nace ta tambaye ki". "Ta tambaye ni? Ni a suwa? Ka mai dani mutum ne bare itama ta maida ni". Imran kanshi a k'asa yace, "kiyi hak'uri mom". Yamutsa fuska tayi tace, "daka daina bani hak'uri ma,,, don ba fasa halinka zaka yiba, abu d'aya dai dazan fad'a maka shine kabi sannu don duk matar daka hurewa kunne kasa tak'i bin mahaifiyarka kaima ba zaka ji dad'inta ba". Ko kad'an Imran bai fahimci inda maganganunta suke son tafiya ba, tana nufin shi zai zuga shaheeda kenan ko me? Bai dawo daga tunanin shiba yaji muryarta tana ci gaba da fad'in, "shaheeda dai y'ar k'awata ce kusan a gabana ta taso nasan halinta ciki da bai, dalilin da yasa ma na takura wajen nema maka aurenta kenan,,,, amma tunda sakayyar da zaka yimun kenan ba matsala gaka ga duniya nan, suwaeba kuma had'a kai da ita maza ka bada himma". Tana gama yin maganarta tabar shi nan durk'ushe yana jujjuya maganganunta a cikin ranshi. *Germany* Cikin satin daya biyo baya Ahmad da y'an uwan shi kuma y'an uwan amaryarshi biyu suka sauka a k'asar ta Germany tare da amarya Yasmine. Su suka sauya gidan da sababbin furnitures da sauran abun buk'ata yayi kyau dai dai da gidan sabuwar amarya. Kwanan su uku a garin suka koma inda suka futo suka bar ango da amaryarshi. Tunda suka tafi khaleefa bai sake ganin k'eyar Ahmad ba saida ya kwana biyar. Shima saboda ya shiga asibiti ne a yammacin ranar tare da matarshi. A lokacin khaleefa yana shirin barin office suka shigo, saiya dakata har saida suka zauna suka gaisa, ba laifi yarinyar fara ce tas kyakkyawa da ita Masha Allah. Sun tab'a hira da Ahmad kan abinda ya shafi harkar aikin su da maganar karatun raihana da komai ya kammala cikin satin ma zata fara zuwa d'aukar darasi. Kusan tare suka futo shi ya huce gidan shi, su kuma zasu kewaya cikin asibitin ya gaisa da mutanen shi. A mugun gajiye khaleefa ya shigo gidan bakin shi d'auke da sallama, babu kowa a parlon sai mayataccen k'amshin raihana daya cika ko'ina, saida ya lumshe idon shi ya bud'e wani sanyi da tarin nutsuwa suka kwaranya a ruhin shi. Bai shiga d'akin shiba saida ya zauna a parlon ya shak'i k'amshin sosai yasha ruwa ya huta gajiyarshi. Ita kuwa a dai dai lokacin tana d'akinta tana aikin dole data k'irk'irowa kanta saboda kad'aici da rashin abunyi, tana jin lokacin da aka bud'e k'ofar parlon aka shigo, tasan babu wanda zai shigo mata sai khaleefa don shi yake da copyn key, kasancewar Germany k'asar da babu ruwan wani da wani kowa rayuwarshi yake bare wani yazo don ya shiga rayuwarka, mamaki take yadda cikin kwanakin khaleefa baya dad'ewa a waje kamar da,,, ko aikin nasu ne yayi sauk'i a office oho. Ita rabon dasu had'u ma tun washe garin ranar da yayi ciwon nan cikin dare. Rayuwarsu suke babu ruwan wani da wani bare takurawa ko shigarwa juna hanci. Shi kuwa khaleefa ta k'ark'ashin k'asa yake ta gudanar da binciken shi akan surajo Abdallah tofa ta hannun basudaniyar likitan k'ashin da suke aiki tare, zuwa yanzu ya fahimci mutumin yazo medical check-up tun lokacin da suka tafi Nigeria, yanzu haka sai after 4 months zai sake dawowa don a shekara sau biyu yake zuwa farko da k'arshe. A wannan karon khaleefa ya lashi takobin sai ya samu wannan mutumin insha Allah, hakan yasa ya fara tsananta addu'a da tashi cikin dare duk bayan wasu kwanaki, yana fatan ta silar mutumin nan ya ruguje tubalin ginin rehun da auntie tayi musu tsawon shekaru, ya fallasa gaskiyar abinda take b'oyewa kowa ma yaji. Ranar data kama weekend khaleefa bai futa ko'ina ba through out yana gida don tunda Ahmad yayi aure ya daina zuwa gidan shi. Kullum tambayar shi Ahmad yake yaushe zai kawo raihana su gaisa da yasmine, don already ya had'a su k'awance shiyasa sai damun shi take da son sanin wai wacece wannan raihanan da ganinta yafi ganin sarki tsada. Duk lokacin da ya yiwa khaleefa magana sai yace zai samu lokaci suzo, tun Ahmad yana saka ran ganin su har ya gaji ya shirya da yammacin yau suka taho da kansu shida Yasmine d'in yau dai taga wannan raihanan. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty one 5️⃣1️⃣ Ga zaton yasmine ta d'auka zasuyi tafiya mai nisa ne kafun suje gidan sai taga sun nufi gidan da yake fuskantar nasu, kasa shiru tayi har saida ta magantu, "ba gidan abokin ka khaleefa zamu ba?". "Eh gashi ma har munzo". Ya fad'a yana kallonta da k'ok'arin knocking k'ofar da hannun shi. Da wani k'arin mamakin tace, "yanzu nan kusa damu ne ya gagare su zuwa kullum ka kira shi a waya yace zai samu lokaci?". Murmushi Ahmad yayi yace, "bakisan waye khaleefa bane". "Na san shi mana ba wanda muka je office d'inshi ranar ba". Wannan karon y'ar dariya Ahmad yayi kafun ya sake cewa, "bafa irin wannan sanin nake nufi ba, ba zaki tab'a ganewa ba mu bar maganar kawai". Shiru tayi shi kuma ya lalubo no khaleefa don yaga duk bugun nan da suke tsawon lokaci daga shi har raihana basu da niyyar bud'e musu. A lokacin dukkannin su bacci suke sadidan, ko da wasa babu wanda yaji bugun k'ofar da Ahmad yake. Cikin tsakiyar baccin shi mai dad'i me cike da dad'ad'an mafarkai yaji ringing na wayarshi da take gefen shi kamar ta fasa mishi kunne. Mik'ewa yayi da addu'a a bakin shi ya lalubo wayar, kiran har ya katse wani ya sake shigowa. Ganin Ahmad ke kiran sai ya d'auka ba tare da yace komai ba ya kara a kunnen shi. "Man wane irin nisa kayi ne haka da ka shanya ni a k'ofar gidan ka kamar get man zaman jiranka, hala baka son bak'uncin mu a wannan yammaci" "Ohh! Sorry Ina zuwa" ya fad'a tare da ajiye wayar ya tashi daga kan gadon da sauri. Saida ya wanke fuskarshi sannan ya futo a gurguje, kallon d'akinta yayi a ranshi yana ayyana bacci tayi kenan itama, don yasan ido biyu ba zata k'i jin zuwan su Ahmad ba. Da k'orafin Ahmad ya fara bayan ya bud'e mishi gidan, "Allah saura k'iris mu tafi". Khaleefa ya mik'a mishi hannu suka gaisa yana sake bashi hak'uri, a lokacin suka bawa yasmine hanya itama ta shigo ya maida k'ofar ya rufe. Anan parlon suka zauna su duka suka gaisa da jin lafiyar juna. Yasmine dai tana tsakiya sai rarraba idanu take taga ta inda wannan diamond raihana zata futo, gashi su sai hirar su suke kamar sun manta da itama a gurin. Sake matsawa tayi jikin Ahmad tayi k'asa da muryarta dai dai saitin kunnen shi tace, "shi kad'ai ne a gidan wai". Ahmad bai bata amsa ba sai tambayar khaleefa daya d'auke kanshi gefe don basu dama suyi maganar su da yay, "Man wai sai mun biya kud'i ne baby zata ga k'awar tata". Shiru yayi yana kallon Ahmad kafun ya tashi ya nufi d'akinta. Da zoben azurfar da yake hannun shi ya kwankwasa mata,,,,, tun bata jiyo shi har yaci nasarar tashin ta baccin gaba d'aya. Doguwar riga ce a jikinta, hakan yasa ta jawo mayafi ta yafa don bata raba d'ayan biyu khaleefa ne, tunda su biyu suke rayuwa a gidan. Lokacin data bud'e k'ofar ya gama knocking har ya juya baya, hango kawunan su Ahmad da suka juya baya da tashin k'ananun dariya yasa ta gane dalilin zuwan nashi. Hijab ta sauyo wadatacce ta rufe k'ofar ta k'araso cikin parlon, a lokacin shi har ya koma mazaunin shi ya zauna. Da fara'a sosai akan fuskarta suka gaisa da Ahmad da yasmine ma da take ta son ganinta. A ranta take raya (Lallai wannan itace jinta yafi ganinta, duk da ake fad'a mata raihana raihana ta d'auka zata ganta wata y'ar gayun wayayya lambar k'arshen nan, sai kuma ta ganta da wani uban zurmemen hijab tabbacin bata kai yadda take zato ba). "Toh yasmine yau dai ga raihana matar khaleefa, raihana ga matata Yasmine da kuka kasa zuwa ganinta". Kusan a tare duk suka sakarma juna murmushi, kafun yasmine tace, "nice to meet you raihanatu". "Same" raihana ta fad'a a tak'aice. Sunci gaba da zama shiru, khaleefa na aikin danna waya, yayinda yasmine kema Ahmad gulmar wai miji da matar sam basu dace ba, a wane k'auyen ma had'ad'd'en guy kamar mijinta yaje ya d'auko wannan matar. B'ata fuska Ahmad yayi ya lakace mata hanci can k'asa muryarshi yace, "to ke Ina ruwan ki, daga mata ganin farko zaki yanke mata hukunci baby hakan babu kyau fa". Kwantar da kanta tayi gefen hannun shi cikin shagwob'a tace, "am sorry". Kiss ya mata a gefen kunci, "love you wife". "Nima haka". Ta k'arasa fad'a tana sake shigar da kanta jikin shi. Raihana da take zaune tana opposite d'insu tuni ta mik'e ta shige kitchen don kawo musu ruwa tea, tunda dai ta fahimci khaleefa bay kawo musu ko ruwa ba. Shima khaleefa mik'ewa yayi don ya basu guri da kyau, kasancewarshi mutum ba mai son yawan takura ga kowa ba. Tray biyu ta had'a, na farko ruwa, na buyu shayi. Ruwan ta fara kawowa bayan ta rabka uwar sallama tun kafun ta k'araso gurin, duk don susan da zuwanta su gyara daga yadda suke manne da juna, madadin haka sai sake shigewa jikin shi da yasmine take kamar wadda za'a sace. Ita dai ta ajiye musu ruwan ta sake kawo musu na tea. "Thanks raihana". Yasmine ta fad'a tana tsiyaya ruwa a cup, don ita dai batasan ana shan tea kowanne lokaci bayan lokacin breakfast ba. Ganin Ahmad ya tsiyaya a k'aramin cup ya kai bakin shi sai itama taji tana son shan tea d'in. Ta tsiyaya kamar yadda taga yayi ta kai bakinta. Sai gashi ta shanye shi tass hadda k'arawa. A lokacin khaleefa ya dawo cikin parlon.... Shima kamar dai raihanan, yadda ya barsu haka ya dawo ya same su, sai yaja k'aramin tsaki a ranshi ya k'arasa ciki ya zauna. A lokacin yasmine ke aikin zuba santin raihana ta iya dafa tea, Ahmad nata mata dariya, raihana kam murmushi tayi ba tace komai ba. Shi kuwa khaleefa d'auke kanshi yayi don baiga wani abun burgewa a iya dafa shayin nata ba. Hira suka ci gaba dayi jifa jifa har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib suka tafi don sauke farali. Suma sallar suka tashi zasuyi. Raihana har d'akin barcinta ta yiwa yasmine jagora, Saida ta lumshe idonta ta bud'e tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren daya manne da d'akin tana bin komai da kallo, yadda d'akin barcin ya tsaru sai abun ya burgeta har ta magantu a zuciyarta, "gata dai a haka kamar bagidajiya amma komai tana yinshi da nutsuwa da aji kuma a waye". Yasmine bata sake raina kanta ba saida suka idar da sallah ta tafi kitchen don had'a musu abinda zasu ci ta bita. Tana aikin suna hirar su ita da yasmine jefi jefi har ta kammala ta shirya musu shi a dinning. Y'ar hirar da sukayi ta fahimtar da ita wacece raihanan cikin sauk'i, anan ta gane ba wayewa ce bata dashi ba, kawai tana da nutsuwa da sauk'in rawar kai irin na y'an matan wannan zamanin, gata da aji sai dai ta cika miskilanci kamar mijin nata. Koda suka zo cin abinci raihana d'aukar nata tayi tunda khaleefa bacin abincinta yake ba ta bar musu dinning d'in. Aikuwa suka dinga ci suna santi daga miji har matar aka rasa gwani. Ita dai komai sukayi sai dai tayi murmushi. Khaleefa da yake zaune cikin parlon kuwa ya cika b'am, haushin su Ahmad da wannan magananniyar matar tashi me rawar kai da k'afar nan mak'il a zuciyarshi, sun zauna ko kunya basa ji tana yaba kwarewar wata sai kace ita ba mace ba, ita kuma sai wani murmushi take. "mattss!". Yaja tsaki a fili a ranshi yana fad'in, ko meye ma abun burgewa don wasu can sun yaba girkinta ba mijinta da suke tare ba, mtssss!". Ya k'arashe da Jan wani tsakin. Duk da ba kusa dashi take ba amma taji tsakin shi sarai, bata damu ba tunda ba wani abu tayi mishi ba. Ranar basu bar gidan ba sai dare, raihana ta rakasu tana musu godiya da alk'awarin zuwa musu bada jimawa ba itama. Tana aikin gyaran parlon inda bak'inta suka ci abinci khaleefa ya futo rik'e da Mukullin gidan zai futa. "Allah ya kiyaye hanya". Ta fad'a bayan ta d'auke kanta ga barin kallon shi. Ko amsa ta baiyi ba tsabar takaicinta daya cika mishi zuciya, ba don kada ya kwana da yunwa ya samu matsala ba da ba abinda zai futar dashi galantoyin neman abinci da wannan daren, ada kafun Ahmad yayi aure tare suke yawon, yanzu kuma da yayi aure shi kad'ai ya bari yana gararamba, zuwa yanzu yasan d'ai d'ai daga masu gidan abinci da basu sanshi ba a garin Berlin, kuma duk ta silar wannan banzan lallen da yak'i futa a k'afarta kamar tisashi ake kullum. (Yoh toh ai tisashin ake kamar karatu😂😂) ____________***** Washe garin ranar ya sameta da safe a kitchen tana aikin had'a breakfast, bai shiga ba ya tsaya daga bakin k'ofar yana kallonta da shigar tata ta yau, karo na farko daya tab'a ganinta ba zumbud'ed'en gyale da hijjab, koda yake wannan d'in ma,,,,, amma dai laba'asa tunda straight skirt ne da riga me dogon hannu, sai gyale siriri data yafa shi ya rabu gida biyu yabi ta kowacce kusurwar hannunta, saboda santsin gyalen daya zame sai ya futar da gaban gashinta ma'abocin kyau da santsi yana haske idon duk mai kallon shi. Kamar kullum fuskarta babu komai zai lip balm da kwalli data zirara. Aikinta take tana voice call dasu al'ameen, rabi duk hirar suce ta shirme da rigingimun su da baya k'arewa a kullum safiya, ita dai tana sauraron su tana dariya wani abun kuma in taji ta tsawatar. A dai dai lokacin da hibba ke kawo k'arar al'ameen ya sake kwace mata socks har yana dariya wai tunda auntie raihana tayi musu nisa bata nan zaiga me bata wani, "ai zaki kawo mun wata ko auntie raihana tunda ban kula shiba kuma ummie tace ba kiyi nesa damu ba tunda muna iya waya dake ko?". Murmushi tayi a wannan karon bayan ta murd'e gas data gama girki tace, "rabu dashi hibbah zansa a kawo miki socks masu kyau da idan ya gani saiya kusa kuka". Cikin farin ciki yarinyar ta daka tsalle, "yeee! Ai dai auntie nace ke ni kad'ai ko?". "Eh mana ke dai kawai duk abinda aka saki ki dinga yi, shima Yaya al'ameen ko me zaiyi kar ki kula sa, Ni kuma insha Allah na dawo tsarabar ki sai tafi ta kowa yawa". Cikin farin ciki hibba ta sake daka tsallen murna har ummie data futo zata shige d'akinta na warning kada a fasa mata waya. Ita dai raihana tayi dariya don tayi kewarsu ba kad'an ba. Shi kanshi khaleefa da yake bayan su abun ya k'ayatar dashi, kuma har lokacin duk abun nan da yake faruwa bata ganshi ba, tsayuwar mutum daf da ita yasa ta saurin d'agowa ta zuba mishi idanunta lokaci d'aya kuma taja jikinta baya, wayar hannunta ya zare ya tsura ma screen d'in ido yana ci gaba da sauraron hibba da take ta bata labarin abubuwan da sukayi da bata nan kashi daban daban. Murmushi yayi ya kira sunanta idanun shi akan raihana "hibbatullah!" Daga can shiru yarinyar tayi don bata gane shiba. "kun manta dani sai auntien ku kad'ai kuke kira". Al'ameen ne ya fara gano shi ya rad'awa hibba, sai suka hau rige rigen gaishe shi. Ya amsa yana tambayar lafiyar kowa. Sunci gaba da magana dashi idon shi akan screen d'in wayar yana kwashe no's d'in a kwakwalwar shi. Yadda yaran suka sake dashi suna magana abun har mamaki yaba raihana, sai kace sun shekara da sanin shi. Saida ya ajiye wayar yake fad'a mata abinda ya shigo dashi, "ki shirya anjima kad'an Ahmad zai zo ku futa". Kacal abinda ya fad'a ya juya salin alin ya fuce hankalin shi kwance, da kallo ta bishi a ranta tana mamakin wane irin mutum ne wannan, Ina kuma zata shirya taje da abokinn shi? Bata dame bata amsa shiyasa itama saita d'auki wayarta da abincinta ta futo a kitchen d'in. Cikin satin Ahmad ya yiwa raihana duk abinda ya dace na shirin shiga makaranta, tunda shine a k'asa bai koma aiki daga hutun biki ba. Alhamdulillah ta samu addmision inda zata karanci BSc nursing kamar yadda khaleefa ya gani a rubuce jikin kwalin diploma da tayi a kano. Kusan tare da yasmine akayi komai don itace y'ar rakiya. Haka raihana ta dinga shiga tsakanin ma'auratan a komai yasmine ta dinga nanewa mijinta kamar wata chewing gum, tun raihana tana kunyarsu har ta daina don ta fahimci ita yasmine ma ko a jikinta bata d'aukar hakan a matsayin komai. Koda Ahmad ya kammala komai khaleefa ya samu da dare ya warware mishi duk yadda akayi. Ranar da zata fara shiga makaranta k'arfe tara zasu shiga lectures amma ko kafun lokacin tuni ta shirya tsab cikin doguwar riga me mayafi irinta matan Sudan. Jakarta da wayarta rik'e a hannunta tana zaune a parlon, saboda zumud'i ba abinda ta iya ci sai tea da tasha funjali biyu. A shiryen shi ya futo tsab cikin kayan da suka dace da jikin shi, waya ce sak'ale a kunnen shi hannun shi rik'e da LC jakarshi rataye a gefen kafad'ar shi. Yana rufe k'ofa idon shi ya fad'a kanta, kallonta yayi na adadin wasu sakanni yana ci gaba da amsa wayar har ya gama. Saida ta russuna ta gaishe shi, ya amsa mata kamar kullum. Sake kallonta yayi yana nazarin wani abu cikin ranshi, lallai yarinyar nan tayi kama da wadda ta karanci halayyar d'an Adam, duk wani abu daya yink'ura zai sata tayi sai yaga tayi. Yanzun ma ya d'an jinkirta futa ne saboda ita, yasan ba lallai ta iya kai kanta makarantar ta dawo da kanta ba, tunda bata san sunan anguwar da take zaune ba bare inda zata samu motar haya ta shiga. Ajiyar zuciya ya sauke yace, "zamu iya tafiya yanzu?". Gyad'a mishi kai tayi ta tattaro duk abun buk'atar ta ta nufi hanyar futa a gidan. Shiya tsaya ya rufe gidan ya k'araso inda take suka fara tafiya a gefen titin anguwar. Shiya tare musu motar haya suka shiga har zuwa makarantar, ya sallame su suka futo yaci gaba da mata jagora har ciki. A wani keb'antaccen guri da babu yawaitar mutane ya barta, ta zauna tana jin dad'in yau matsayin ranarta ta farko a makaranta. Wasu nau'in kud'i ya d'ebo a aljihu ya ajiye mata saman cinyarta da mukullin gidanta, "Nottingham Ln, ocean pines, MD 21811, ki rik'e wannan address d'in in an tashi shi zai maida ki gida,,,,, ranar ki ta farko a makaranta, fatan alkhairy". Yana gama fad'a ko sauraron komai bai tsaya yiba yayi gaba abunshi, da kallo ta bishi har yayi nisan daya b'acewa idanunta. Saita rubuta address d'in a wayarta tare da sauke ajiyar zuciya. Sun shiga lecture da misalin k'arfe tara dot, ko kad'an bata sha wahalar gano yadda komai yake a cikin makarantar ba saboda kwata kwata bata da duhun kai. A ranar komai bai mata wahala ba don anyi musu karatun ne da harshen turanci sab'anin tunanin ta. (Abinda raihana bata sani ba, dama makarantar kusan international student sunfi yawa a ciki) Da address d'in da khaleefa ya bata tayi amfani ta koma gidanta. Koda ta koma a k'alilan na lokaci tayi duk abinda ya dace, ciki hadda wanka da girki ta turare gidanta tsab kafun wani lokaci k'amshi ya gauraye ko'ina. Ranar khaleefa bai dawo da wuri ba, ita Kuma bata bar parlon ba ta zauna dakon shigowar shi tana d'an duba littattafanta. Tana nan har ya dawo ya murza key ya shigo, kallo d'aya da raihana ta mishi ta fahimci a matuk'ar gajiye yake. Shi kuwa saida ya shak'i daddad'an k'amshin turaren ta ya lumshe idon shi wata nutsuwa na saukar mishi, gajiyar daya kwaso na sake sauka a duk gabban jikin shi tana nuk'urk'usar su, k'arasawa yayi cikin parlon ya zauna ba don komai ba sai don saboda wannan tsumammen k'amshi daya cika ko'ina banda d'akin shi. "Sannu da zuwa". Ta fad'a da tattausar murya. Bai iya amsa taba sai kanshi daya kwantar baya yana lumshe ido. Ruwa ta kawo mishi mai sanyi da mara sanyi a tray ta ajiye k'asan k'afar shi. "Mai sanyi?". Ta tambaya da kulawa. Zama yayi sosai k'amshin turaren jikinta na kaiwa k'ofofin hancin shi marfaki, girgiza mata kai yayi. Ta tsiyaya ruwan da sauri don rage kusancin da sukayi ta bashi. Ya karb'a ya kai bakin shi nan da nan ya shanye ya sake mik'o mata kofun, har ta koma mazauninta ta sake dawowa ta tsiyaya mishi wani, ya k'ara shanyewa, ta k'ara mishi ya sake shanyewa, zata dad'a mishi na hud'u ya d'aga mata hannu ya d'auki duka gorar ya bulbule a bakin shi. Kallon shi kawai raihana take a zuciyarta tana tunanin shi kuwa wacce irin k'ishin ruwa ya kwaso haka! Had'a ido da sukayi dashi yasa tayi saurin maida kanta k'asa, shima d'auke kanshi yayi kamar yadda tayi. Ita kuwa had'e komai tayi guri guda ta durk'usa kan k'afafunta ta fara mishi godiya, "Na gode Allah ya saka da mafificin alkhairy, ya baka abinda kake so duniya da laheera". Kamar wanda aka watsawa ruwan sanyi haka yaji tasirin addu'ar ta a cikin jikin shi, addu'ar data mishi Allah ya mallaka mishi abinda yake so nan duniya dai dai yake da tace Allah ya bashi Saleema tunda itace abinda yake so fiye da komai a duniya in aka d'auke mutum biyu, abinda yake so a laheera kuwa abu ne da kowanne musulmi yake fata da burin samu wato jannatul firdaus, sai dai shi da k'arin haka, don yana son Saleema ta kasance matarshi har a can ma. Tattausan murmushi yayi bayan had'a addu'arta da tunanin shi waje guda yace, "na gode da addu'a, amma na cika alk'awari nane kamar yadda kema kika cika naki tun a Nigeria". Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta har zuwa wani lokaci data gama jin zama inuwa guda dashi ta had'a kayanta zata tafi, daga bayan shi ta sake russunawa, "bazan fasa godiya ba don ka zamo silar dana jini gab da cikar muradaina a yau,,,, BSc nursing shine burina na tun k'uruciya,,,, nagode Allah ya faranta maka kaima kamar yadda ka faranta mun". Tana gama addu'ar ta juya zata tafi saboda hawaye daya cika idonta, har ta fara tafiya maganarshi ta sata tsayawa cak ba tare data juyo ba. "A watannin baya, nayi neesa da wani abu mai matuk'ar muhimmanci gare ni har na fara fidda ran samun shi gaba d'aya, sai dai a yanzu ta sanadiyyarki na jini kusa dashi saboda kusanci har muna iya jiyo numfashin juna..... *Saleema* itace farin cikin rayuwata, kiyi mun addu'a Allah ya bani ita". Maganar a bazata ta zowa raihana, shi yasa ta kasa duk wani motsi tana son tabbarwa kanta wai khaleefa ne yake maganar wata mace da gaske gareta. _nayi typing mai yawa zan muku update Monday a rashin sani naje na share shi gaba d'aya saida na sake rubuta wani yanzun🤦‍♀️🤦‍♀️ saboda rashin lokaci nayi muku shi in briefly_ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty two5️⃣2️⃣ Murmushi ta sake yi ta juyo rungume da tulin littattafanta tace, "toh Allah ya baka Saleema". Kamar ya tashi ya d'ora ta a kanshi ya kewaya Germany da ita haka yaji a lokacin, baya jin a duniya akwai abinda za'ayi mishi a lokacin da zaifi wannan addu'ar ta raihana mishi dad'i. Har ta shige d'akinta bai iya d'auke idon shi a kanta ba, nutsuwarta, kamewarta, ladabinta da tarbiyyarta duk basu tab'a sa ta burgeshi kamar wannan addu'ar ta yau ba. A yau ya fara zana sunanta cikin b'angaren manyan masoyan shi daya yiwa aji na musamman a wani yanki dake cikin zuciyar shi. ★★★★ Rayuwarsu tana tafiya a sannu a sannu bada gaggawa ba, raihana sosai ta maida hankalinta akan karatun ta da yafi d'aukar hankalinta a yanzun, shi kuma khaleefa kan aikin shi da binciken shi ta k'ark'ashin k'asa, duk da suna rayuwa a gida d'aya basu fiya had'uwa ba sai irin weekend da baya futa aiki in ya gaji da zama cikin d'akin shi ya futo parlon, bai fiya futa kowanne gidan cin abinci ba a irin wad'annan ranakun, mafi yawan lokuta raihana tana kaucewa yake shiga kitchen ya jagwolgwola abinda zaici da kanshi, da yammaci wani lokacin inya gaji da zaman gidan kuma ya futa k'ofar gida yasa kujera ya zauna yana shan iska, wani lokacin idan Ahmad ya lek'o ya ganshi yakan zo suyi y'ar hirar su, idan kuma y'an futar basa kanshi yayi zaman shi a gida tare da matarshi, don yanzu an samu banbanci tsakanin shi da khaleefa. Yasmine ma takan zowa raihana lokaci bayan lokaci don ma raihanan ba mazauniya bace, yayinda har yau Allah bai ba raihana ikon je mata ba kamar yadda ta fad'a, ba k'aramin mamakin yadda raihana take iya duk ayyukan gidanta dama na kanta ba tare da gazawa ko nuna gajiyawa ba Yasmine take, duk sammakon da zatayi na futa lecture bata barin gidanta da d'igon tsinke bare aga datti, haka data dawo zata wanke k'urar data kwaso ta sauya kayan jikinta zuwa na zaman gida ta sake k'alk'ale gidan, lallen k'afarta kuwa tunda yasmine tasan ta tasan k'afarta dashi bata tab'a ganin k'afar fari ba. A d'an zuwan da take yi gidan ta fahimci kamar kowa harkar shi yake tsakanin miji da matar, (don a tsarin su basa pretend na nuna alak'a mai kyau ta k'arya a idon mutane alhali ba haka suke zaune a zahiri ba, sukan yi komai kansu tsaye musamman ma khaleefa) da farko tayi tunanin ko fad'a sukayi, amma bayan ganin irin bahaguwar zamantakewar kusan sau ba adadi sai kanta ya d'aure, sunsha zuwa gidan da dare suci abinci ita da Ahmad amma khaleefa yayi order. Abun ya d'aure mata kai da yawa har takai ta kasa hak'uri saida ta yiwa Ahmad maganar, sai dai Ahmad ya nuna mata tsabar miskilanci ne na miji da matar, haka suke rayuwarsu tun kafun yanzu, da haka ya toshe mata tunaninta gaba d'aya daga kan abinda taso fahimta wai ko zata iya kawo gyara wa lamarin. (An samu banbanci tsakanin Yasmine da raihana, don kuwa Yasmine tana da wayewa ta ilimin boko fiye data addini, amma tana iya k'ok'arinta wajen ganin ta kiyaye dokokin addininta, tayi karatu tun daga matakin secondry har zuwa University, sannan ita ba tayi rayuwar Nigeria ba sai in tazo hutu lokaci bayan lokaci, a gidansu su hud'u maman su ta haifa, akwai yayyenta biyu maza sai k'anwarta da take bi mata, iyayen su suna da matuk'ar rik'on al'ada, wanda hakan yasa suka raine su da yaren hausa, amma in bacin haka da ba zasu san komai a hausa ba, tana da kirki da sauk'in kai amma bata da hak'uri, ta iya girki irin na mutanen k'asar data rayu tare dasu gwargwadon iko, hakama na k'asar Nigeria, bata son aiki da yawa saboda garkuwar jikinta bai saba da wahala da yawa ba, shi kanshi Ahmad a abubuwa da yawa hak'uri yake da ita. Ta b'angare d'aya kuma akwai kyakkyawar alak'a ta soyayyah tsakaninta da mijinta wadda ta k'aru da 70% bayan auren su) A iya d'an zaman raihana da yasmine ta k'aru da abubuwa da yawa da ba zasu k'irgu ba, ta fannin kula da jiki da girke girken k'asar Africa, ranar data bata turarukan ta na shafawa kuwa washe gari Ahmad suna futa aiki ta taho mata, sai dai ta daki gurbi don raihana a yau ta riga su ma futa zuwa makaranta, kuma bata dawo ba har yamma, lokacin da raihana ta dawo ita kuma ta shiga harkokin girki hakan yasa basu had'u ba. Da daddare tana zaune cikin d'akin barcinta har tayi shirin kwanciya barci don tana da futa gobe da wuri ma aka mata knocking k'ofa. Kwan! Kwan!! saita mik'e zaune ta kunna fitilar gefen gado tana kallon k'ofar, ci gaba da bugun akayi abinda ya assasa mata saukowa ta d'auki hijab d'inta dogo ta saka. Khaleefa ne tsaye ya juyawa k'ofar baya hannun shi duka biyu hard'e a bayan shi, ganin baisan da futowarta ba sai tace, "yauwa". Ba tare daya juyo ba yace, "Bismillah k'araso". Ya gama fad'a yana yin gaba, itama bayan shi tabi tana kallon Ahmad da yake zaune cikin kujerun parlon. Daga gefe ta tsaya ta d'ora hannunta jikin kujerar suka gaisa. "Sorry Madame mun taso ki kina baccin ki ko?". D'an murmushi tayi, "ai ban ma fara baccin ba". "Alright dama mutuniyar ce jiya ta rikita mana gida da wani kalar turare na gargajiya mai sanyin k'amshi, koda na tambayeta sai take cemun ai ke kika bata, kuma tabbas ina jin irin k'amshin shi a gidan nan,,, Soo shine nazo naji ko zamu iya samun shi a k'asar nan?". Satar kallon inda khaleefa yake tsaye tayi, ya fuske kamar baiji abinda abokin shi ya fad'a ba, ita kam shiru tayi kafun can tace, "minti biyu Ina zuwa?". Komawa tayi cikin d'akinta ta d'ebo da yawa fiye ma da wanda ta bata da farko ta dawo parlon ta mik'awa Ahmad. "Ka k'ara kai mata wannan". B'ata fuska Ahmad yayi, "bama son haka! Inda zamu samu kawai muke son sani". "Ai ba zaku samu a k'asar nan bane, nima auntie ce ta had'a mun shi". Kallon khaleefa Ahmad yayi yace, "man kace sirrin daga gare kune ma". Sai a lokacin ya d'ago da kanshi ya dubi Ahmad ba tare da yace komai ba ya mayar da kanshi bisa wayarshi. Godiya mai yawa Ahmad ya mata ya d'auki kwalaben turaren, komawa tayi d'akinta shi kuma yayi sallama da khaleefa ya tafi. Koda Ahmad ya fad'awa Yasmine yadda sukayi da raihana ba k'aramin mamaki tayi ba, "mahaifiyar mijinta ce auntie dama?". Ahmad yace, "kwarai kuwa!". . "Toh aini na d'auka maman tace data haife ta". Ahmad yana kallon Yasmine yace, "ai matar ce k'arshe ce, ke a duniya babu wani mutum mai mutumci da zan baki kwatancenta dashi suyi dai dai, ita d'in ta kasance k'arshe a cikin masu mutumcin mutumci, soon zata zo k'asar nan zaki ganta ai". Ita kam Yasmine abun ya bata mamaki, kenan duk wasu sirrikan matan Sudan ita taba raihana? She can't believe za'a iya samun irin wad'annan iyayen mijin, ganin kirkin maman Ahmad yasa ta d'auka a duniya ba wadda ta kaita sa'ar suruka, sai gashi taga wadda ta ninka ta kirki sau trillion. @@@@@@@@@ *NIGERIA* Yanayin da take jin jikinta cikin watannin ya tabbatar mata lallai bata da cikakkiyar lafiya, k'arfin hali kawai take da kwarara kanta don bata son gazawarta ta futo ko abinda zai nuna rauninta. Hakan yasa bata fasa futa office ba a kullum safiyar Allah. Yauma tunda safe ta shirya cikin wadatacciyar suturar da take suturta jikinta a koda yaushe, ta d'ora rigar likitoci a sama. Tana futowa engineer ma yana futowa. Har k'asa ya durk'usa ya gaisheta cike da ladabi kamar koda yaushe, ta amsa shi da murmushi a fuskarta, ita ta fara shiga motarta shi kuma ya tsaya amsa waya. Harta yiwa motar key tana k'ok'arin fara murza steery ta kasa, hakan yasa ta d'ora kanta jikin steering tana jin yadda zuciyarta ke tsananta bugu, "allahumma la sahala illah ma ja'altahu sahala, wa anta taja'alul hazni iza shi'ita sahala,,,,". Abinda take faman maimaitawa kenan a cikin zuciyarta. Ayman da yake waya daga inda yake yana kallon yadda tayi ta gaban farin gilashin motarta katse wayar yayi ya taho inda take. Knocking glass d'in yayi, ta d'ago a nutse tana k'ok'arin daidaita yanayinta, ta sauke glass d'in tana kallon shi. "Kina lafiya kuwa auntie". Ya tambayeta da larabci. Gyad'a mishi kai tayi tana k'irk'iro murmushin da iyakacin shi kan lab'b'anta. Sanin lallai ba zata iya driving da kanta ba saita futo bayan ta zare keyn motar. "Muje ka sauke ni". Ta fad'a tana nufar inda motar shi take. Shima bayanta yabi yana girgiza kanshi don yasan lallai ba lafiya ba tunda har ta kasa driving, bazai iya tuna karo na k'arshe data tab'a shiga motarshi don ya rage mata hanya ba kasancewarta mace mai dakakkiyar zuciya, tuna wannan ya sake tabbatar wa Ayman lallai bata da lafiya sai dai kuma zurfin cikinta bazai tab'a barinta tace komai ba yanzu ko ya tambayeta. Har suka k'arasa asibitin ba tace dashi ba shima baice mata ba. Yana gama parking ta d'auki jakarta ta futa tare da mishi addu'ar, "Allah ya kiyaye" ya amsa da "ameen". Yana d'aga mata hannu. K'in barin gurin yayi har saida yaga shigarta ward d'in da office d'inta yake, sannan ya sauƙe boyayyiyar ajiyar zuciya yayi reverse ya futa hospital d'in. Da doctor seera kawai suka gaisa ta shiga office d'inta ta fara aikin duba tulin patients da suke zaman jiranta. ____________★ Da yamma sauri sauri Ayman ya futo daga office saboda kada tace zata hau motar haya a yanayin da take, lokacin daya shiga clinic da yawa daga cikin ma'aikatan asibitin sun fara watsewa don yamma tayi sosai. Kai tsaye ofishinta ya nufa a ranshi yana addu'ar Allah yasa bata tafi ba. Doctor surayyah tana kwance kan kujerar hutu doguwa da take a gefen office d'in, ba bacci take ba amma ta lula cikin duniyar tunani, tana a haka aka turo office d'in aka shigo, bata tashi ba sai bud'e idonta da tayi tana kallon k'ofar, doctor seera ce tsaye da shirin tafiya gida. "Na d'auka ma kin tafi, amma lafiyarki kuwa?". Ta tambaya da tarin kulawa bayan ta maida k'ofar ta rufe. Mik'ewa tayi da kyar ta zauna tace, "ban tafi ba kin ganni gaba d'aya na tashi yau bana jin dad'in jikina, kuma bansan me yake damuna ba". "Subhanallah! Amma kika k'i zuwa kiga doctor Saleh". Girgiza kanta tayi, "seera ba matsalar Saleh bace, wannan matsala ce da take buk'atar addu'a ki tayani da addu'a kurum". Da kulawa seera tace, "toh Allah yayi miki maganin abinda yake damun ki,,, Naga kamar yau baki zo da mota ba ko zaki taho muje saina sauke ki". Jakarta da wayarta ta d'auka "ina tunanin Ayman zai dawo d'auka ta saboda d'azu shiya ajiye ni, toh kada na tafi kuma yazo bai same niba ba zaiji dad'i ba". Tana rufe bakinta ana knocking k'ofa, "come in" Suka fad'a kusan a tare ita da doctor seera, da sallama a bakin shi ya turo k'ofar ya shigo. "D'an halak yak'i ambato". Doctor saira ta fad'a tana kallon shi. Murmushi yayi ya k'arasa shiga office d'in ya durk'usa yana gaishe da doctor k'awar auntie. Sallama ta musu don har ta kusa huce lokacin tafiyarta. Itama surayyah bata zauna ba ta d'auki wayarta da keyn office d'in suka futo Ayman rik'e da Jakarta. Koda suka Isa inda ya parker motarshi, shiya bud'e mata front seat ta shiga sannan ya kewaya mazaunin driver. Suna tafe suna hira jefi jefi har suka k'arasa gida, Ayman bai rabu da ita ba saida ya rakata har part d'inta ya tabbatar ta zauna mama haleema ta kawo mata ruwa mai sauk'in sanyi tasha, har ya tafi zuciyarshi bata gama aminta da auntien tana lafiya ba, cox yasan halinta ciwo inba yaci k'arfinta ya kwantar da ita ba bata tab'a yarda ta nuna ma kowa bata da lafiya, duk a gudun kada ta d'aga musu hankali. Kamar yadda yake lura da yanayinta haka mama haleema ma take ankare da duk wani motsinta cikin kwanakin, shiyasa a yau data gama aikinta ta zab'i kwana a gidan tare da ita, don taga yau abun Kamar yafi na kullum. Da daddare tana kwance don yau tunda wuri ta shige bedroom ko abinci bata ci na kirki ba saboda zazzab'i daya fara taso mata. Tana kwance taji ringing d'in wayarta, da kyar ta mik'e zaune ta jingina da fuskar gadon ta d'aga kiran. Raihana ce ta kira ta don su gaisa, kwana biyu basu gaisa ba saboda yawon makaranta da yake cinye mata rabin lokacin aiwatar da komai. Har suka gama wayar bata yarda raihana ta fahimci wani abu a cikin muryarta ba. ________★★★ washe gari duk inda doctor surayyah ta kaiga nuna ita d'in *JARUMA* ce saida abun yaci tura, gaba d'aya bayan tayi sallar asubah kasa tashi tayi ko daga kan sallaya zazzab'i mai zafi ya rufe ta, saboda zafin zazzab'i hak'oranta har kad'uwa suke suna dukan junan su. Ayman da bai gama samun gamsuwa da yanayinta na jiya ba, k'arfe bakwai yana futowa wanka kayan shi kawai ya zura ko mai da turare bai sakawa jikin shi ba ya futo ya nufin sashenta. Tun daga parlour yake sallama shiru har ya nufi jikin d'akin barcinta. Yayi bugun yayi sallama amma shiru kake ji babu alamun akwai mutum mai motsi ma a d'akin. A gigice ya tura k'ofar gaban shi yana tsananta fad'uwa. Tana kwance magashiyan ko hannunta bata iya d'agawa. Aikuwa ya nufe ta yana kiran sunanta da gudu. Kanta ya d'ago yana faman jera kiran sunanta "Auntie! Auntie!! Auntie!!!" Da kyar ta bud'e kwayar idonta data canja launi ta kira sunan shi, "Aaaayyyymannn". "Na'am! Auntie me yake damun ki? Tun jiya nace baki da lafiya kika k'i fad'a mun kika ce lafiyarki lou,,,,,,". Girgiza mishi kai tayi tana k'ok'arin mik'ewa ta zauna amma ta kasa, abinda ya sake gigita Ayman kenan har ya futa da gudu ya d'auko mukullin motarshi. Da yake mama haleema a gidan ta kwana, tana futowa don kama ayyukan gida taga giftawar Ayman da gudu, saita bishi da kallo kafun ta nufi d'akin auntien don tasan lallai daga can ya futo. Da taimakon ta auntie ta tashi suka sauko k'asa inda Ayman ya futo da mota. Direct wani private hospital na abokin shi ya nufa da ita bayan ya kira shi a hanya ya sanar dashi zuwan su. Suna zuwa emergency aka karb'e su hannu bibbiyu aka shigar da ita don ceton rayuwarta. Zuwa lokacin ita kad'ai tasan yadda take ta fafutuka da rayuwarta. An d'auki awowi da yawa kafun a futo da ita a gadon marassa lafiya tana bacci. D'aki aka bata duk hankalin su Ayman a tashe sai tambayar nurses abinda yake damunta suke, har suka futa d'akin basu ce dashi komai ba abinda ya sake dagula mishi lissafi, saida wata nurse ta dawo tace yazo doctor farouk yana son magana dashi. A hargitse ya nufi ofishin likitan ko zama baiyi ba bare a kaiga maganar gaisuwa ko jin lafiyar juna yadda aka dad'e ba'a had'u ba ya fara da tambayar, "likita me yake damunta mamana?". Seat ya nuna mishi, "ka zauna Ayman sai muyi magana". Dafe kanshi yayi ya d'aga kai sama cikin danne hawayen daya cika idon shi yace, "ka fara fad'a mun abinda yake damunta farouk!". Duk yadda likita farouk yaso shawo kanshi suyi magana a nutse k'i yayi. Daga k'arshe ma sai kawai ya fara hawaye, dafa kafad'ar shi doctor farouk yayi cikin son kwantar mishi da hankali yace, "ba wani mummunan abu bane yake damunta, zazzab'ine da stress sai jininta daya hau da d'an yawa". Cikin son tabbatar da abinda yake fad'a Ayman yace, "don Allah kada kayi kun k'arya don ka kwantar mun da hankali na rok'e ka ka fad'a mun gaskiya farouk,,,,,". "Kaima kasan bazan fara aikata abinda kake nufi ba, wallahi zazzab'i da hawan jini shine kad'ai matsalar mahaifiyarka da bincike na ya gani". Ajiyar zuciya ya sauke kad'an yana share hawayen fuskarshi da hankie. Sai a lokacin ya zauna suka gaisa da farouk ya k'arasa mishi bayani. Ranar gaba d'aya a asibitin suka wuni tare da ita ba tare da sun fad'awa kowa ba har dare. Ko abinci babu wanda ya iya ci a cikin su tun safe har daren, basu iya samun kwanciyar hankali ba saida suka ga ta motsa ta bud'e idanunta, har rige rigen yi mata sannu suke shida mama haleema. Bata iya amsa suba ta sake komawa wani baccin, sai a lokacin mama haleema ta d'anji kwarin gwiwa ta futa don samo musu abinda zasu ci har mara lafiyar idan ta tashi. Ayman kasawa yayi ya tsare ko gud'a yak'i yarda ya tab'a jikin wannan baiwar Allah mai tarin sadaukarwa a gare su fiye da wadda Allah ya d'orawa duk wata uwa a duniya. Koda mama haleema ta dawo kasa cin abincin yayi duk yadda taso ya daure ya lallab'a yaci wani abun kasawa yayi. A daren ranar yana kallon kiran khaleefa na shigowa wayarshi akai akai amma ya kasa d'agawa. Haka ya kwana sur bai runtsa ba kamar me gadi. Auntie bata farka ba saida iskar sanyin asuba ta kad'a. Ayman ta fara gani gefenta ya zuba mata ido ko k'iftawa babu yana kallonta, yayin da hawayen idon shi ya fara sauka kad'an kad'an. Hannunta ta mik'a ta kamo hannun shi cikin nata ta rintse tana girgiza mishi kai, "ka.. kwantar da hankalin ka.....". Girgiza mata kai shima yayi ya kai hannun ta bakin shi ya sumbata tare da rik'e hannun gam gam yana zubar da hawaye. Ita kanta kukan take yi na tausayin su shida d'an uwan shi, tana tsoron ta mutu ta barsu a wannan halin, shin ya rayuwarsu zata ci gaba da kasancewa cikin wannan al'ummar ma'abota gutsiri tsoma da shiga hurumin da bai shafe suba bayan ba ranta?. Shin Ayman zai samu matar aure da bak'in tambarin da aka lik'a mishi na rashin uba kamar yadda khaleefa ya samu da kyar? Shin zasu yafe mata bayan ranta idan suka gano mahaifin su yana raye ta b'oye musu tsawon shekaru saboda wani dalili nata da alk'awari data d'aukar wa ranta ita d'aya? Hak'ik'a tana tsoron ta mutu ta bar baya da k'ura ga yaran da basu jiba basu gani ba, hasalima basu suka samar da kansu ba, tako wacce hanya samar dasu akayi....... _ina jinjina da nuna goyon bayan ku masoya littafin JARUMAR UWA, comment d'inku shine kwarin gwiwa ta a koda yaushe, sai dai masu jin haushin Saleema ku koma ku bincika ainahin yadda ake soyayyah ta gaskiya, sannan lamarin raihana sannu sannu bata hana zuwa, komai da takeyi akwai dalilinta, zaku gane hakan bada jimawa ba insha Allah_ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty three 5️⃣3️⃣ "Oohhh Allah ka kawo mun d'auki a cikin wannan rayuwar". Ta fad'a a zuciyarta, a zahiri kam cikin son kwantar wa Ayman hankali tace, "me likita yace akan ciwo na?". Da kyar ya iya had'a lab'b'an shi biyu yace, "zazzab'i.... Jinin ki kuma ya hau da yawa, sai stress da yake damun ki". Shiru yayi kafun yaci gaba da cewa, "am sorry Mom amma lokaci yayi daya kamata ki ajiye komai ki huta saboda shekarun ki sun fara nauyi,,, idan nace komai Ina nufin har aikin ki da harkokin kasuwancin ki.... Alhamdulillah hak'ar ki ta gama cimma ruwa, yanzu duk muna da rufin asirin da zamu ci gaba da d'aukar nauyin rayuwar ki da tamu ma har zuwa k'arshen numfashi...." Murmushin yak'e tayi tace, "ka kwantar da hankalin ka Ayman kabi komai a sannu". "Taya hankalina zai kwanta auntie bayan kinsan bazan iya jure rashin ki ba, kece mahaifiyar mu, mahaifin mu, babbar abokiyar da tafi kowa sanin kowa a cikin mu, abokiyar shawarar mu,,,, shin kina ganin zamu iya jurar rashin mutum guda da yafi mutum goma muhimmanci da amfani a tare damu,,,, ya kike tunanin rayuwarmu zata kasance idan akace yau babu ke.......?". Ya kai k'arshen zancen yana kifa kanshi jikin k'arfen gadon ya fashe da kuka mai cin rai. Ita kanta kukan take yi saboda maganganun shi sun tab'a zuciyarta ainun.... Haka suka taru sunata kuka har mama haleema data farka kusan lokaci guda da auntien take sauraron su tuntuni. Tabbas surayyah ta kasance bango majinginar bayin Allah da dama, wanda suka santa da wanda ma basu santa ba, wanda ta bayyana da wanda ma ta barwa kanta, a girme tasan zata yiwa surayyah fintinkau a shekarun haihuwa, amma tayi mata abinda ko uwar data haifeta iyakar abinda zata mata kenan, ta d'auki nauyin cinsu, shansu, suturar su harma da wasu nauye nauye na rayuwar mutane ta yau da kullum, y'ay'anta mata uku data aurar duk bata sanin lokacin da auntie take zuwa ta d'auki amarya ta zab'i furnitures masu kyau da sauk'in kud'i sai dai kawai taba mama haleema resit taji da siyan sauran kayan kitchen. Sannan taja da baya ta gyara jikin amarya ta had'a ta da turarukan Sudan masu k'amshi da d'aukar hankali. Lallai rashin wannan mata a gareta dai dai yake da fallasuwar asirinta da yake rufe tsawon shekaru, duk da a yanzu y'ay'anta itama sun kawo k'arfi kowa ya samu abinyi cikin su alhamdulillah. Ita ta sulale ta kira wata nurse tazo don duba yanayin jikin auntie, ta kuwa dinga zabgawa Ayman fad'a don ya mugun b'ata mata rai, suna iya bakin k'ok'arin su yazo zai dawo musu da aiki baya ta hanyar wannan kukan da yasata, duk da wani lokacin kuka ma rahama ne, akwai tashin hankalin da in yakai k'ololuwa ba'a iya mishi kuka. An sake yi mata allurai masu k'arfi, ba jimawa kuwa bacci ya sake kwasheta. A washe garin ranar mama haleema ta fad'awa su malam, duk da auntie tayi warning kar a fad'awa kowa, sai dai sanin in suka ji daga baya ba zasu tab'a jin dad'i ba sai ta fad'a musu, su kansu har kuka sukayi da suka zo asibitin suka ganta. Duk yadda take K'arfafa kanta da zuciyarta wajen ganin tayi yak'i da ciwon hakan ta gaza cimma ruwa yayi. Sai gata da shafe sati guda har da d'oriyar wasu y'an kwanaki tana jinya a gadon asibiti, yayinda suka b'oyewa su khaleefa basu sanar dasu komai ba. Tun a lokacin da khaleefa ya damu da rashin samun layinta ya tambayi Ayman yace wayarta ta samu matsala ne sai bai sake tambayar shiba duk da yadda abun yake damun shi ya shanye,,, raihana kam ba waya sukeyi da Ayman ba sai gaisawa ta hanyar text massage, Koda ta kasa samun layin auntien ma bata tambayi kowa ba ta bari a ranta ko wayar ce ta lalace. Mutane da yawa sunzo duba ta ciki hadda sameera da bata san inda ta samu labari ba, su doctor seera kuwa zuwan su ba zai k'irgu ba. Ayman da mama haleema kamar su suke jinyar saboda yadda suka sawa ransu damuwa da tashin hankali akan ciwon. Alhamdulillah zamu ce don jikin auntie yayi sauk'i sosai har an bata sallama ta dawo gida, sai dai likita ya kafa mata wasu tsauraran matakai da zata bi akan hawan jininta in tana son d'orewar lafiyarta. Tunda ta dawo take yak'i da Ayman kan komawa office amma fafur yak'i, tun tana lallab'a shi har ta dawo mishi fad'a, ba don ranshi yaso ba ya shirya a safiyar yau ya tafi office, amma fa wuni yayi kiran wayarta data bud'e a safiyar ranar yana jin yanayin jikinta. Da yamma kuwa daya taso hold up ya rirrik'e shi a hanyar komawa gida ba k'aramin cinkushewa ranshi yayi ba. Tunda ya shawo kwanar layin yake kallon yarinyar kamar ya santa, matashiyar budurwa ce data sha kwalliya cikin suttura ta hausawa, riga da zani na atamfa sai gyale data yafa a kafad'arta ta rik'e hand bag a hannu, ta rufe rabin fuskarta da mask shiyasa ba'a gane ta sosai. Ayman koda ya k'araso bai ko sake kallon inda take ba ya fara danna horn yana addu'ar Allah yasa tukur yana kusa ya bud'e mishi ba sai ya futo ba. Addu'ar shi bata karb'u ba don yayi horn kusan sau uku ba'a bud'e mishi gate d'in ba, hakan yasa ya futo da kanshi zai bud'e. Da sassarfa ta k'araso gare shi duk da a tsorace take kada wani ya ganka ya kaiwa mamanta rahoto. "Assalamu alaikaa?". Fuska a d'aure ya amsa, "wa'alaikissalam". Shiru tayi ta rasa abinda zata ce gashi har ya fara k'ok'arin huce ta, da sauri ta zare face mask d'in ta kira sunan shi da murya me taushi, "Ayman.....". Tsayawa yayi ba tare daya juyo ba, sai tayi taku kad'an zuwa bayan shi ta fara mishi magana da rawar murya, "yanzu kana nufin shi kenan, duk soyayyar da muke yiwa juna wani k'aramin abu ya raba mu?......". A matuk'ar fusace ya juyo tana dire zancenta ya fara bata amsa da, "ba k'aramin abu ne ya raba mu ba Nur, babban abune da yafi k'arfin kan mu nida ke bare wata soyayyar mu ta rehu, kije ki tambayi mahaifiyarki kiji kota shirya bawa shege marar asali y'arta a yanzun...... Sannan wannan ya zama karo na k'arshe da zaki dinga nema na guri guri kamar wanda yaci muku bashi". Yana gama yin maganar ya huce ta da sauri ya barta nan tsaye ko bi takan ta baiyi ba. Yammacin ranar gaba ki d'aya haka ya kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali,,,,, duk yadda ya dawo da zumud'in son ganin auntie ta cire mishi haka a ranshi, k'arshe bai shiga ganinta ba sai dare, tana kishingid'e kan doguwar kujera tana waya da raihana,,,,, sun jima suna hirar kafun suyi sallama ta nemo layin khaleefa da shima take ganin kiran shi yana shigowa a lokacin da take wayar. Shima sunyi hira dashi ba mai tsayi ba kafun suyi sallama ta ajiye wayar, hankalinta ta tattarawa Ayman d'ungurungum tace, "Ina fatan dai lafiya" squeezing face yayi kad'an yace, "lafiya qalou, me zan samu a gidan yau". "Mama haleema zaka tambaya kasan itace a kitchen yanzu". Tashi yayi yaje ya zubo abincin ya dawo nan kusa da ita ya fara ci, gaba d'aya Nur ta gama jagula mishi rai, ganinta da maganar data tuna mishi suka taru suka sake tuna mishi matsayin su da ya fara mantawa. Auntie data ke can wata duniyar ta tunani ma nisawa tayi ta dawo da dubanta gare shi tace, "tafiya ta kamani zuwa Germany cikin satin nan da zamu shiga". Da kyar ya iya had'iye abincin bakin shi ya tambayeta, "wani abu ya faru ne a can". "A'a". "Toh me yasa! Daga futowarki asibiti sai d'aukar doguwar tafiya kuma?, Ni ina ganin ki bari sai an kwana biyu kin sake warwarewa". Murmushi tayi ganin yadda duk ya fututtuke baya son ta d'ara ko nan da can. "Ba zai yiwu bane Ayman! Na yiwa raihana alk'awari kuma wannan tafiyar a gare ni ta dole ce". Ganin yaja taja bata saki ba sai ya sawa zuciyarshi salama ya kyale ta kurum, Amma kwata kwata baya son tafiyar nan tata. Kamar yadda ta fad'a Cikin satin aka kammala mata komai na tafiya sai lokaci kawai da take jira. ********* Kamar kullum yau ma bayan ya tashi office bai koma gidan ba sai bayan sallar magrib, ya karb'i abincin da zaici a eve eno ya d'auki hanyar gidan. Tana zaune tayi baja baja da littattafanta tana nazari ya murza key ya shigo gidan, bata d'ago kanta ba tayi mishi sannu da zuwan da batasan ba ko ya amsa, ko bai amsa ba don ita bataji komai ba sai k'arar rufe k'ofar d'akin shi da k'arfi. Saita fara had'e kayanta gudun kada ta aikata laifi a gare shi kafun wani lokaci ta b'ace wa ganin su. Shi kuwa b'acin raine ya kama shi da ya bud'e k'ofar d'akin shi yaga komai a hargitse yadda ya barshi, gaba d'aya cikin satin baya samun lokacin da zai gyara muhallin shi, ko yanzu daya shigo a mugun gajiye yake ga maganar da sukayi da Ahmad d'azu. Tsaki ya dinga ja har yayi wanka yayi sabon shiri cikin kaya marassa nauyi, yayi sallar isha'i da shafa'i da wuturi. Tun kafun ya gama lazimi kiran Ahmad yake ta shigowa wayarshi yana katsewa har ya gama, wani sabon tsakin yayi a k'asan ranshi yana mitar Ahmad ba dai azalzali ba. Koda ya futo bai sameta a parlon ba yasan maybe ta kauce zuwa d'akinta, sai ya nufi d'akin ya mata bugu uku zuwa hud'u. A lokacin ta idar da sallah tana muraji'ar karatunta na al-qurani bugun k'ofar shi ya katse ta. Riga ce doguwa a jikinta milk wadatacciya, saita yafa k'aramin gyalen rigar a saman kanta taje ta bud'e mishi k'ofar. Kallo d'aya yayi mata yace, "in ba abinda kike zamu futa yanzu". Gyad'a mishi kai tayi ta koma ciki ta d'auko wayarta ta dawo inda yake jiranta. Har suka futo a gidan bata daina tambayar kanta inda zasu da wannan daren kamar wasu munafukai ba. Gidan da take kyautata zaton na Ahmad ne suka nufa, daga gaban gidan suka tsaya khaleefa ya kira shi ya shaida mishi isowar su. Aikuwa a tare Ahmad da yasmine suka bud'e musu gidan, yasmine har ta kasa hak'uri saida tazo ta rungume ta tana mata oyoyo! Karo na farko da raihana ta ziyarci gidan su, ba k'aramin farin ciki Yasmine da Ahmad sukayi ba da ganin su. Ina jin komai na gidan saida ta kawo musu duk a sonta na ganin ta tarye su da kyau irin tarba ta mutumci. Ruwa kad'ai raihana tasha, shi kam khaleefa ko ruwan k'in sha yayi (kunsan dai mutumin naku😜) Suna gama gaisawa Yasmine ta janye raihana zuwa d'akin barcinta suka basu guri, ta bita da abinciccikan data shirya dominta kusan kala uku, kallon abincin raihana tayi tace, "nifa Saida naci abinci na futo". "Niba ruwana da kinci abinci, wannan dana shirya da sunan ki ko baki ciba sai kin tafi dashi gidan ki...". Sanin hali akace yafi sanin kama, tsab zata aikata abinda ta fad'a. Sai ta d'auki abincin salin alin ta fara ci tana sauraron hirar da Yasmine take yi mata. Khaleefa da Ahmad ma hirar su sukeyi akan abinda ya shafe su na k'ashin kansu, cikin hirar ne Ahmad yake mishi k'orafin rashin samun auntie a waya kwana biyu, ya k'are da tambayar, "Ina fatan dai tana lafiya". "Lafiya lou Ayman yace kasan koba lafiya ba zasu fad'a ba, yanzu zaka sameta ta bud'e layinta jiya har munyi waya ma". Ahmad yace, "insha Allah zan kirata zuwa gobe koda safe ne". Kallon agogo khaleefa yayi yace, "yea! Man dare fa ya fara nisa". Ai shiyasa kuka k'i zuwa da wuri saida dare ya fara yi don ku gudu da wurwuri, Ni dai gaskiya ban karb'i wannan zuwan wayon ba". "Hum! Ba zaka gane bane". "Taya zan gane bayan ba'a yimun bayani yadda zan gane d'in ba". Murmushi khaleefa yayi a wannan karon yace, "toh Allah ya huci zuciyarka". ya mik'e tare da yin doguwar mik'a, da gaske bacci yake ji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi. Shima Ahmad mik'ewa yayi yace, "tom mun gode da ziyara Allah ya bar zumunci, bari na kira madame, ko zaka barta a nan su kwana da k'awarta". Khaleefa baice mishi komai ba, hasalima yi yayi kamar baiji shiba Ahmad lalubo no Yasmine yayi cikin wayarshi ya fad'a mata raihana tazo zasu huce. A lokacin har ta fara gyangyad'i sak'on su ya iso gareta ta hanyar Yasmine. Kamar jira take kuwa ta tashi da hanzari har yasmine na fad'in wai gidanta ba dad'i duk ta k'agara ta tafi ko, tayi murmushi kurum suka jero tare. Har waje suka rako su suna ta musu godiyar ziyara. Raihana dai duk a tsorace take da yanayin anguwar data sake zama tsit ba'a jin motsin komai sai haske tarwai daya haske ko'ina. Tsoronta yasa ta kasa nesa da khaleefa take binshi daf da daf. Har sun fara tafiya Ahmad ya mishi magana da yaren jamus, "ba kaji ba". Juyowa yayi ita kuma raihana taci burki ba tare data juya ba. "Wai kuwa kana nan akan bakan ka game da Saleema?". Tambayar saita zowa khaleefa a bazata, kwata kwata bai d'auka abinda Ahmad d'in zaice ba kenan. "Me yasa ka tambaya?". Khaleefa ya fad'a yana kallon shi. Murmushi yayi ya sake cewa, "saboda naga ka daina bibiyar ta da lamuranta gaba d'aya, wanda naga hakan yana da kyau a matsayin ta na matar da kake son aure watan watarana, shareta ba itace mafuta ba yana da kyau tasan matsayinta a gurin ka". Ajiyar zuciya khaleefa ya sauke yaci gaba da bashi amsa da yaren German, "kasan fa a inda muka ajiye zancenta ni da kai tun a wancan lokacin, meyasa zaka dawo da maganar yanzu bayan kana sane da ban samu komai cikin abinda zai kaini ga samun ta ba". Wani kalar bahagon murmushi Ahmad yayi, a zuciyarshi yana ayyana abubuwa da yawa masu girma da k'arfin gaske, Sam khaleefa baya fahimtar abu cikin sauk'i, shiyasa gaskiya take wahalar dashi kafun ya ganta ya santa a yadda take. Takowa Ahmad yayi har kusa dashi ya dafa kafad'ar shi, "khaleefa shiru ba amsar da zata wadatar bace, babu wanda zai fahimci abinda ka ajiye a cikin ranka in bakai ka fad'a da bakin kaba, masu iya magana suka ce waiwaye adon tafiya..... Ya kamata ka waiwayi Saleema ka mata tuni game da alak'ar soyayyar ku......". Duk shiru sukayi kafun khaleefa ya gamsu da shawarar Ahmad d'in suyi sallama ya shige gidan shi, su kuma su k'arasa nasu gidan. Yana bud'e k'ofa ya kunna haske ya gauraye ko'ina, a parlon ya zauna ya had'a kanshi da gwiwa yayi shiru yana nazari. Raihana dai dama suna shiga bata tsaya ba saida ta dangane da gadon barcinta ta kwanta, ko kayan jikinta bata iya tsayawa cirewa ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. ******* Kamar kowanne hutun k'arshen mako, tun safe khaleefa bai futa ko'ina ba yana aikin gyaran d'akin shi, yana aikin maganar da sukayi da Ahmad na dawo mishi daki daki. Da yamma bayan yayi wanka ya shirya cikin shigar da tafi amsar jikin shi wato k'ananun kaya riga da wando farare k'al, gashin kanshi yasha gyara duk inda ya gifta sassanyan k'amshin turaren shi ke tashi. Key da mukullin motarshi kawai ya d'auka ya futa daga gidan ba tare da raihana ta sani ba. *****Rabon shi da apartment d'in tun ranar da suka bar Germany zuwa Nigeria hutun kammala karatun su, rabon shi da ita kuma tun ranar da yaje gareta ya mayar mata da zobenta. _in few hours na muku shi sai hak'uri zaku ganshi ba edit_ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty four 5️⃣4️⃣ Tsayuwa yaci gaba da yi kamar get man ya tsurawa gaban part d'inta ido, ya jima yana k'ullawa da kwancewa saboda har ga Allah baya son ya koma gareta a yanzun ba tare da ya samu cikakken hujja da zaiyi yak'i da abinda ya raba su da farko ba kamar yadda yayi alk'awari. A nutse ya fara juyawa zai bar gurin, har ya fara tafiya sai yaga giftawar wata kamar Amna, sai ya juya da sauri ashe itama bayan ta gifta ta ankara dashi, hakan yasa suka juyo kusan a tare. Amna ta fad'ad'a fara'ar fuskarta ta k'araso inda yake, shima sakin fuskarshi yayi suka gaisa da ita kafun ta tambaye shi, "sai yau ka tuna damu?". Baice mata komai ba, dama tasan ba zaice d'in ba. Sake d'auko wani zancen tayi, "kun had'u da ita ne?". "Ba zuwa nayi don ta ganni ba". Ya bata amsa kai tsaye ya fara k'ok'arin barin gurin. Dakatar dashi Amna tayi ta hanyar sake cewa, "shin ka hak'ura da Saleema ne?". Juyowa yayi ya kalleta da kyau, fahimtar kamar akwai magana a bakinta sai yace, "har abada bazan tab'a iya hak'ura da Saleema ba kema kin sani, itace kacal macen dana fara so zanci gaba kuma da so har k'arshen numfashina.......". Murmushi itama tayi a wannan karon, "shin wannan alk'awarine da kuke rik'e dashi kaida ita ko ita kad'ai take rik'e dashi?". Bai bata amsa ba saida ya gama juya maganganun ta, "Ina ganin kamar akwai magana a bakin ki Amna! Well ni yanzu bani da lokacin jaddada magana akan abinda na neesa damu ma sun sanshi bare ke,,, Soo ina ganin sai anjima ko?". "Ka fad'i gaskiya sai dai kak'i bani damar da zan fad'i gaskiyar dana sani nima,,,, shin kana tsoron kada ka jima a waje matarka ta rufe maka k'ofa ne". Cak ya tsaya daga tafiyar daya fara yi, tsabar yadda maganar ta shige shi saiya kasa juyowa ya kalleta sai itace ta k'araso gaban shi, "waya fad'a miki nayi aure" ya tambayeta fuskarshi babu alamun wasa. "Ah abun duniya yana b'uya ne? Musamman yanzu da mutane suka zama y'an jarida! Ina ganin yadda wayoyin hannun mu suke saurin isar da sak'o ko y'an jaridar albarka". Ta k'are zancen tana murmushi. Khaleefa dafe kanshi yayi da hannun shi, wannan yana daga dalilin da yasa ya dinga hana Ahmad yayatawa mutane auren shi, yanzu ga irinta nan zai jik'a mishi ruwa a guri mai wuyar bushewa. Yasan tunda Amna ta sani lallai Saleema ma ta sani. Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi ya tambayeta, "yanzu Ina saleeman take?". "Ban sani ba don kaga nima shigowata kenan! Ga lokaci ya fara ja har na fara gajiya da tsayuwa,,,,, Ina ganin sai anjima ko?". Ya fahimci Amna duk magana take yab'a mishi a kaikaice.... Har ta fara tafiya khaleefa bai iya barin gurin ba saida ta bud'e k'ofarta ta shiga sannan yaja k'afafun shi ya fara barin gurin shima. Murmushi Amna da take kallon shi ta window tayi, a zahiri kuma saita ce, "yanzune za'a fara wasan! nasan duk inda zanyi a garin nan sai ka nemo ni ko don tunanin ta yadda zaka gyara alak'ar ka da Saleema! Alak'ar data dad'e da yankewaaa". Wani murmushin ta sakeyi tana girgiza kanta kurum, zuciyarta cinkushe da abubuwa da yawa. Gaba d'aya khaleefa ya kasa samun sukuni, yafi hour d'aya a gaban gidan bai shiga ba yana tunanin yadda zasu kwashe da Saleema idan tayi ido hud'u dashi. Baisan me zaice mata akan auren raihana da zai wadatar har ya kare kanshi ita kuma ta fahimce shiba. "Wayyoh Allah". Ya fad'a yana sake jingina kanshi da bangon gidan. Ko bayan ya shiga gidan ma tunanin daya d'ora kenan, lallai Ahmad ya kwanto mishi kura, a tsarin rayuwarshi mace d'aya ce zab'in shi, shiyasa bai auri raihana don ya zauna da ita ba, ya aureta ne don ya rabu da ita da zarar deal ya cika kowa ya gama samun abinda yake so cikin su, tun yana under 20 years ya tsara rayuwarshi mijin mace d'aya cal da y'ay'an su, kuma koda suna soyayyah da Saleema ya fad'a mata shiba mijin mata da yawa bane, ita kad'ai ta ishe shi rayuwa da yaranta uku da zata haifa mishi, (don saleema bata son haihuwa da yawa a tsarinta, khaleefa kuma yaji ya amince a lokacin). Toh taya kenan zaice mata auren yarjejeniya sukayi da raihana don cikar burin shi na samunta? Shin ko zai shekara mata bayani zata gane kuwa? Da wad'an nan tunane tunanen bacci b'arawo ya sad'ad'd'afo yayi wuff dashi. Washe garin ranar raihana ta tashi da zazzafan ciwon kai, komai kasa yi tayi tun safe sai kwanciya daga farkon gado zuwa k'arshe. Bata ji dama dama ba saida rana ta futo sosai Yasmine suka zo gidan ita da Ahmad. Har bedroom ta biyo ta ta sameta nannad'e cikin bargo gashin kanta a hargitse k'arewa ma ko kayan bacci bata sauya ba. Koda ta tambayeta lafiyarta kuwa? Bata fad'a mata abinda yake damunta ba ta tashi ta fad'a bathroom a gurguje tayo wanka ta futo d'aure da towel, gaban dressing mirrow ta zauna tana shafa mai yasmine na mata fad'an ya kamata ta shirya suje saloon a k'ara gyara kan nan, murmushi tayi tace "to ba komai hajiya kisa mana lokaci". "Aini ko yanzu ma". Zaro ido raihana tayi tace, "inke kin shirya ni ban shirya ba". B'ata fuska Yasmine tayi, "aikuwa indai kece ba samun lokaci zakibyi ba haka zaki ta cewa sai kin samu lokaci har na gaji da jiran ki na hak'ura.... Gaskiya bari ma na fad'awa hubby ya kamata muje saloon d'in nan yau". Ko jin ta bakin raihana bata yiba ta fuce zuwa parlon inda suke zaune shida khaleefa zaman kurame, don ba hira suke yiba kowa aikin gaban shi yake cikin su. A kusa dashi ta zauna ta shige jikinshi kamar ta tsaga jikin shi su zama abu d'aya, ta kanainaye hannayen shi ta kwantar da kanta gefen wuyan shi tana magana da zallar shagwob'a, "hubby don Allah ka kaimu saloon nida raihana ayi mana gyaran kai yanzu". Khaleefa da ya kalle su tab'e bakin shi yayi a ranshi yana ayyana, "wannan marar kunyar matar Ahmad d'in tazo za taita nanik'e shi ko kunya bata ji". Tashi yayi kamar koda yaushe ya basu guri. "Yaushe aka tashi zuwa saloon d'in? Waye jami'in shirya tafiyar? Indai kece ma ba zaku ba". Sake shagwob'ewa tayi tace, "hubbyyy pleaseeee". "Na fad'a miki ba inda zaku duk salon kar kibar mutum ya huta, yau weekend d'in ma sai kinje yawo". Fushi tayi ta mik'e zata bar gurin tana jejjefa k'afa kamar yarinyar goye ya rik'o hannunta, "Ni ka rabu dani". "Nifa da Wasa nake miki, taya ma zan hana ki bayan ni za'a yiwa gayu". Murmushi tayi ta dawo ta rungume shi tare da sake mishi kiss😘 a kumatu tana godiya. Da kallo ya bita har ta koma ta shaidawa raihana data gama saka kaya cewar ta futo Ahmad ya amince. Tsayawa da dube duben neman abunda take tayi ta tambaye ta, "har khaleefa kika tambaya?". "Kai! Wane ni! wannan mijin naki me d'aure fuska ko hak'orin shi ba'a ganiiii ta Ina ma zan iya tambayar shi,,," sai kuma tayi k'asa da murya taci gaba da zancenta, "Allah bazan iya tunkarar shi na tambaye shiba, yana gani nama ya bar gurin". K'aramar dariya raihana tayi tace, "aike d'in ce kin kasa fahimtar abinda yasa da kinje gurin mijin ki yake baku guri". "Na sani yadda kuke yine ke dashi bazan iya ba, haka kurum kaida mijin ka saika dinga wani d'auke mishi fuska kamar auren dole,,,, Wai bakya ganin yadda kuke yine a gaban mutane kamar wasu marassa gaskiya,,,, feel free kiyi rayuwarki babu kallon kowa bare idon wani yayi miki shamaki". Murmushi raihana tayi ta girgiza kai tana jinjina maganar Yasmine d'in, toh in banda yasmine ita daba irin auren su sukayi ba ina zata ga fuska a gurin khaleefa, kuma koda auren soyayyar sukayi ma ita ba zata iya irin rashin kunyar nan ta yasmine ba, tana ganin ita kanta yasmine d'in donta rayu a k'asar data sha banban da wadda suka rayu a cikine shiyasa. Mayafinta ta yafa saboda Yasmine da take ta azalazalarta, tama k'i barinta ta d'auko magani tasha saboda ciwon kanta daya lafa kada ya sake dawo mata idan aka tab'a kan. Riga da skirt ne a jikinta daya zauna mata cif, har zata yafa gyale saita fasa ta d'ora hijab bayan ta tubke gashinta, ta d'auki wayarta suka futo yasmine nata mitar tayi dressing me kyau ta maka hijab ta rufe. Lokacin da suka futo parlon khaleefa ya dawo yana ci gaba da operating system d'inshi. Daga gefe d'aya ta zauna ta fara gaishe da Ahmad cikin nutsuwarta, tunda ta futo bai d'aga ido don ya kalleta ba, saida Ahmad yace, "khaleefa na fad'a maka fa zamu yi musu rakiya saloon kayi banza ba kace komai ba". "Sorry! Kuje kawai ni bazan iya zuwaa ba". Ya bashi amsa hankalin shi akan aikin da yake yi. "Har raihana fa zamu". Ahmad ya sake jaddada mishi. "Ahmad kuje mana" ya fad'a cikin k'osawa da zancen. Ahmad ne ya fara yin gaba Yasmine mak'ale dashi, sai raihana da take take musu baya, har ta giftashi sai ya kira sunanta, "Raihana!". Ta amsa da "na'am" tana dawowa baya. Master card d'inshi ya mik'a mata, "kiyi amfani da wannan". Ba tayi mishi musu ba ta russuna ta karb'a ta mishi godiya tabi bayan su. A motar Ahmad sukayi tafiyar, Yasmine kamar y'ar gari ita ta kaisu har gurin. Koda suka shiga Ahmad ne yayi magana dasu ya biya su kud'in ya tafi anjima zai dawo ya d'auke su, rigima sosai yasmine tasa akan abinda yasa bazai jira suba yake son tafiya ya barsu su d'aya. Haka nan ya hak'ura ya zauna cikin mota zai jira a gama musu. Ita aka fara yiwa da yake bata da cikar gashi nan da nan aka gama, sannan aka yiwa raihana ma. Tun a gurin Yasmine take yaba yadda suka gyara musu me kyau har suka k'arasa gida zancenta kenan. Yana nan inda suka barshi sai dai ya kwantar da kanshi kamar me bacci saboda nisa daya fara yi a duniyar tunani ko sallamar su bai jiba. Ahmad ne ya zauna a parlon yana kiran sunan shi su kuma suka shiga cikin d'akin gadonta, ta adana mishi catin shi a guri me kyau suka yi alwalar sallar azahar data kwace musu. Raihana ta riga Yasmine idarwa tana idarwa ta shiga kitchen ta had'a musu abinda zasu ci a sauk'ak'e ta jera musu a dinning ita kuma ta d'au nata ta shige d'akin barcinta. Ranar ma basu bar gidan ba sai dare bayan sunci abincin dare, gaba d'aya har suka gama hirar suka tafi Ahmad bai fahimci kan khaleefa ba, ya fahimci a wani irin ruguje yake baya iya gane komai da kowanne zance sai wanda ya ajiye a ranshi yake cin ranshi. Da dare raihana harta kwanta ta tuna da catin shi, saita diro kan gadon ta d'auki card d'in a inda ta adana shi ta nufi d'akin shi direct, yana kwance ya tsurawa rufin d'akin ido, Koda ta buga bashi da wani sauran k'arfi ko kuzari na mik'ewa, hakan yasa ya bata izinin shiga ba tare daya motsa daga yadda yake ba. Ta tura k'ofar ta shiga da sallama, karon farko data tab'a shiga d'akin shi tundaa take a gidan, wani sassanyan k'amshi da d'umi me dad'i ya dake ta, daga jikin k'ofa ta tsaya tace, "card d'inka dama na kawo maka". Ba tare daya kalleta ba yace, "me yasa bakiyi amfani dashi ba". "Ahmad ne ya biya duka". Baice mata komai ba ya barta tana ci gaba da tsayuwa har ta fara gajiya da kanta ta sake ce mishi "ga catin". Sai a lokacin ya mik'e zaune ya jingina da fuskar bed ya mik'a mata hannun shi still ba tare daya kalleta ba, ta k'araso a nutse cikin taku mai bayyana hakan ta d'ora mishi catin a hannun shi. Yabi lallen hannunta da kallo, k'amshin turaren ta na barazanar ruguza mishi kafofin jinshi saboda shigar da sukayi mishi ta sauri. Ya lumshe ido ya bi bayanta da kallo har ta fuce. ****** Kwana kin da suka biyo baya duk ya jera sune cikin rashin walwala har a office ma, so yake ya nemo Amna ya warware mata zancen auren shi cikin fahimta yadda zata gane, yasan zata iya fahimtar da Saleema cikin sauk'i fiye dashi. Da yamma koda ya tashi office kiran doctor andal ya tafi amsawa, tana tsaye ita da wani kyakkyawan matashi ga dukkan alamu fad'a take yi mishi cikin harshen larabci, Koda khaleefa ya lek'o yaga hakan juyawa yayi nufin yi sai ta dakatar dashi ta hanyar kiran sunan shi. Dawowa yayi cikin office d'in, ta bashi seat ya zauna ita kuma taci gaba da kallon matashin tana nuna shi da yatsa cikin harshen Arab tace, "wannan ya zamo karo na k'arshe da zaka zo mun da shirmen zantuttukan ka har k'asar da nake aiki irin wannan, in su da suke zuga ka basu da hankali kai ai me hankali ne, sannan kamar yadda na fad'a muku da farko suhana tana shekarar k'arshe a karatun ta, ni kuma saboda ku bazan hana ta k'arasawa ba, you better wait for her ko ka hak'ura wannan duk ya rage naka". Tana gama zancen ta bar gaban shi ta koma cikin office d'in taja seat ta zauna ta had'e kanta da table dake gaban kujerarta tana k'ok'arin shanye b'acin ranta, sam batason abinda zai b'ata mata rai akan auren nan har suja ta fasa abinda tayi niyyah. Saboda wani shirmen zancen su can suke nufin ta katse karatun y'ar ta a watannin da zata kammala ta basu aurenta, bayan ba barta zasuyi ta kammala ba in anyi auren. Mtsss! Ta sake jan tsaki tare da tashi zaune da kyau tana duban sashen da khaleefa yake. "Yi hak'uri na barka kana jirana ko?". "A'a ba komai". Ya mayar mata da amsa. Tsabar yadda ta shiga rud'ani ta manta da yaren Arab ta mishi magana saida taji ya mayar mata amsa da yaren. Da mamaki ta kalleshi, "kana jin larabci dama?". Gyad'a mata kai yayi, saita sake cewa, "toh amma kana Nigerian me ya had'a ka da labarci?". "Yaren mamata ne". Tana son sake tambayarshi maman shi sudaniyya ce? Don larabci daya mata zam na Sudan ne, amma tana tsoron kada yaga ta dame shi da tambayoyin bin kwakkwafi, hakan yasa ta hak'ura amma abun yana zuciyarta. Sun tattauna akan abinda ya shafi surgery da suka yiwa wani d'an wasa a k'afar shi, a k'arshe ta dire da tambayar lafiya ta ga yanayin shi ya sauya kwana biyu, "bana jin dad'in jikina ne" amsar daya bata bata wani gamsar da ita ba amma tunda ya fad'i haka saita barshi da yadda ya fad'a d'in. Direct tsohon apartment d'insu ya nufa bayan ya baro office, kai tsaye ya nufi sashen Amna, yana d'ora hannu zai buga tana bud'e k'ofar cikin shiri zata futa, ja da baya tayi tana kallon shi, bai shiga ba duk daya gane nufinta yaci gaba da tsayuwa a inda yake, "ka shigo mana". Juyar da kanshi yayi yace, "ba futa zakiyi ba?". "Noop ai futar ba mai zafi bace, zanje cin abinci ne". "Alright toh mu k'arasa can sai muyi magana". Haka kuwa akayi suka tafi tare har zuwa gidan cin abinci mafi kusa. Baici komai ba baice komai ba har saida ta gama cin abincin da aka kawo mata. Yana ta buga game a waya ta goge bakinta da tissue ta fara mishi magana, "Ina sauraron ka". Ajiye wayar yayi kan table ya fuskanceta da kyau ya fara mata magana cikin nutsuwa, "Amna ki fad'a mun gaskiya a gurin wa kika samu labarin aurena?". "Me yasa kake son sanin abinda bashi da wani muhimmanci, na d'auka zaka fi damuwa da son sanin shin Saleema tasan kayi aure ko kuwa?". "Hakane?". Ya tambayeta kai tsaye cikin tsare ta da ido. Murmushi tayi bayan ta kawar da kanta don ba iya jure kallon kwayar idonshi zatayi ba, "Eh s ganina ba". "Ni kuma sai nake ganin ba yadda za'ayi kisan wani abu a kaina ace Saleema bata sani ba, hakane?". "Ehhh! Toh kusan hakan, Amma kuma a wannan gab'ar batasan komai ba, saboda a ranar daka dawo na ganka tare da wata yarinya, koda nabi diddigi don nasan ba harkar mata kake ba sai na gano cewar matar kace daka auro a Nigeria komawarka hutu, a gaskiya bazan b'oye maka ba banji dad'in auren da kayi ba saboda Saleema har gobe tana sonka duk da zuciyarta ta fara hak'ura da kai, ba kuma da bakinta ta fad'an haka ba a ayyukanta na fara fuskantar hakan,,,, bazan b'oye maka ba a ranar da naje zan fad'a mata ka dawo da wata matar daka auro, sai tak'i saurarata gaba d'aya tak'i fahimtata ma saboda na tafi da zancen da son dakatar da ita ga barin aikata wani abu da takeyi da bana so. So a ranar mukayi fad'an da har yanzu bama tare". Numfashi taja mai tsayi kafun taci gaba da cewa, "a gaskiya khaleefa duk ranar da Saleema ta fahimci gaskiyar magana a kanka ba zata tab'a yafe maka ba, saboda babu yadda za'ayi kana sonta har ka iya auren wata (duk da dama alak'ar ku ta samu tangard'a kafun faruwar komai bisa jagorancin rashin yin cikakken tunani kafun aiwatar da abu daga ku duka biyun)". Shiru yayi yana kasafta kowanne zance daki daki, "kina nufin na yaudari Saleema?". "Ba yaudararta kayi ba, yaudarar juna kukayi, duk da a halin yanzu ba zaka gane komai da zance ba har sai lokacin dana kawo muku maslaha da kyakkyawar fahimtar da zata sa kowa a cikin ku ya daina wahalar dakon soyayyar d'an uwanshi, zuwa yanzu ya kamata zuciyoyin ku su huta ta hanyar fahimtar gaskiya,,,, idan Allah ya kaimu gobe, da misalin k'arfe biyar na yamma, kazo garden na apartment d'inmu, nida Saleema zamu kasance a gurin muna jiran ka". Khaleefa ko kad'an bai gane abinda Amna take son cewa ba, toh amma tunda har zata had'a shi da Saleema ta kawo musu gyara yana ganin ba laifi gwara ya fuskanceta ayi wadda za'ayi kawai, don yayi imanin yana yiwa Saleema bayani don ita yayi komai zata fahimce shi bi'izinillah. Saida ya biya kud'in abincin da taci sannan sukayi sallama ya tafi gida ita Kuma ta koma cikin makaranta. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty five 5️⃣5️⃣ *Nigeria* Shirye shiryen tafiya Germany Auntie take ba tare data fad'awa kowa a cikin raihana ko khaleefa ba, shi kanshi Ahmad sai kamar saura kwana biyu ta taho da sukayi waya take sanar dashi, amma ta nuna bata son khaleefa su sani saboda zata musu bazata ne. A daren ranar da zata tafi suka zauna da Ayman, hak'uri take bashi da lallab'a shi da kalamai masu taushi da kwantar da hankali don tasan har yanzu baya son tafiyar a zuciyarshi, Saida taga ya sake ta fara zolayarshi da cewa, "soon zan maka aure saima sai kaje can ka dingawa matarka kullen". Murmushi yayi tare da kwantar da kanshi jikin k'afarta cikin jin kunya yace, "I will much miss you Auntie,,, don Allah kada ki dad'e tunda kinga ni kad'ai zaki bari a nan". Dafa kanshi tayi tausayinshi na ratsa jikinta da ruhinta, ba don akwai wata manufa a tafiyar tata ba da ba zata fara k'ok'arin barin shi a wannan halin ba, so take bada jimawa ba ta kawo mishi gyara a rayuwarshi kamar yadda take k'ok'arin ganin ta kawowa d'an uwanshi khaleefa,,,,, duk da har yanzu akwai sauran rina a kaba amma zatace alhamdulillah komai ya fara lafawa, tasan zuwa yanzu khaleefa ya fara saduda. Wannan kenan. _ina labarin shaheeda ne?_ Imran tun bayan titsiyen da maman shi ta mishi akan komawar shaheeda makaranta yaje ya mata fad'a bai sake ganin fuskarta ba saida ta kammala exam d'inta suka shiga hutu, itama bata bi takan zancen ba saboda a lokacin ta tara hankalinta ne guri d'aya wajen ganin ta samu abinda take so kamar kowanne jajirtaccen d'alibi. Sosai ta sauya salon rayuwarta a gidan cikin hutun, don wanka take d'auka na jan magana da haddasa fitina, yayinda ta dinga shiryawa Imran tarko kala kala bisa jagorancin shawarar k'awarta feena, tun yana iya kauce mata a dalilin shi na rik'e abinda ta mishi farkon auren su ya kasa mantawa, har ya bada kai bori ya hau🤪. Rayuwa suke zubawa ta zallar soyayyah, Imran har hutun sati ya d'auka a gurin aiki saboda tarairayar da yake samu daga shaheeda, bai tab'a d'aukar zai samu farin ciki a tare da ita ba, haka itama bata d'auka zata samu kanshi cikin sauk'i yadda taga yana daddaure fuskar nan ba. Basu yaudari kansu da cewa suna son juna ba, amma suna matuk'ar begen juna, Cox dukkannin su shekarun su sunkai shiyasa ba zasu iya cewa a'a ga abinda zuk'atansu da gangar jikin su ke soba. Ba laifi mamanta ta huce don Imran da kanshi ya kaita gidan a wani dare, sunji dad'in ganinta sun nuna kuma don rasa abinda zasu bata da zai burgeta k'arshe sukayi. Data tashi tafiya mamie ta sake mata nasiha mai narkar da zuciya musamman akan uwar mijinta, ta sake gargad'inta daja mata kunne sosai akanta (duk da har yanzu bata k'ara kai k'arar shaheedan ba tun bayan na lokacin da aka kawo ta). Ta gaban kunne ta shiga ba tare data rab'i ko fatar kunnen ba bare ta shiga ta zauna a ciki. Da zasu tafi Imran ya bawa k'annenta kudi masu yawa yace su sha ice cream. Suna godiya suka karb'a ta musu sallama suka tafi. Daga futar su har dawowar su akan idon masu tsegumin mom ne, sun kuma kai mata labari dai dai da abinda suka gani, kafun su shiga sashen su Imran ya tambayeta ba zata zo su k'arasa ta gaisa da mom ba tunda d'azu basu shiga ba, babu ko kara bare kawaici tace ita ta gaji bacci take ji gaskiya, bai takura mata ba ya barta ta tafi shi kuma ya nufi parlon mom d'in. wannan karon kasa hak'uri mom tayi don hak'urin ta ya k'are akan abinda yarinyar nan take yi shi kuma yana goya mata baya. Da kyar ta iya amsa gaisuwar shi ta fara da masifa akan rashin mutumcin matarshi, saida ta wanke shi tas a cewarta ai duk da sanin shi take aikata komai, shi yake goya mata baya. Hak'uri ya bata don bashi data cewa, tunda shi har ga Allah bai d'auka shaheeda bata zuwa gaisheta ba, tunda yaga dai yarinyar zab'in tace, y'ar hannun damarta, ita tasan yadda ta shiga ta futa ta rabata da duk samarinta kamar yadda ta raba shi da RAIHANA ta had'a su aure, shiyasa yake tunanin ba yadda yarinyar zata kasa girmamata. Lokacin daya shiga tana kitchen tana k'ok'arin had'a mishi abinda zaici don ita taci tare da y'an uwanta, shi kuma fafur yak'i cin komai saboda kunyar su da yake ji. Tsaye yayi k'ofar kitchen ya zuba mata ido yana kallonta duk data juya baya bata san da zuwan shi ba, kallonta yake da kallon duk wani motsinta cikin fingilgilar riga armless iya cinya ,ba laifi yarinyar kyakkyawa ce ba k'arya, sai dai baisan matsalarta da mom ba, duk da yasan mom da d'aukar maganar mutane fiye da komai. K'arasa shiga kitchen d'in yayi ya d'auki ruwa ya tsiyaya a cup yasha, fuskantar ta yayi da kyau kafun ya tambayeta, "da gaske tunda kike a gidan nan baki tab'a zuwa kun gaisa da mom ba?". Kallon shi tayi kai tsaye ta bashi amsa, "Eh". "Meyasa?" Ya sake jeho mata tambaya. "Saboda ba zamanta nake ba". Ta k'ara bashi amsa direct. "Amma kina sane da cewar ni da kike zaman nawa neman albarkarta nake? Ko bakisan sab'a mata zai iya silar rugujewar rayuwata ba". B'ata rai tayi tace, "Kai da kake d'anta kenan? Ni kuma da nake matar kafa?". "Dole zaki bita matsayin kina wadda take k'ark'ashina". Banza tayi dashi don in taci gaba da ja abun zai iya zama musu fad'a. Shima sai baice mata ba don in yaja abinda sukayi fad'a bazai samu abinda yake so a gurinta anjima kad'an ba. Da haka ya futa a kitchen d'in ita kuma taci gaba da aikinta. _(Note: a rayuwa kada ka tab'a k'in hana b'arna saboda wani abu na samun cikar burinka ba, komai sonda kakewa mutum ka nuna mishi kuskuren shi a lokacin da yayi ba dai dai ba donka takawa abun burki, koda zaka shiga d'aki kayi kuka bayan kayi tsawatarwar kuwa,,,,,, wannan yana daga major problem da yake d'awainiya da al'ummar mu, musamman iyayen mu mata in akazo ta b'angaren yara, da yawan iyaye y'ay'an su suna aikata ba dai dai ba a gaban idon su, amma saboda kada ran yaran ya b'aci suyi kuka sai su zuba ido suna kallon su, wasu ma in akayi magana har suce yarane ai basu da hankali basu isa kwab'a ba, sun manta icce tun yana d'anye ake tankwarashi, wannan k'aramin abun da muke gani ba komai ba shi yake girma ya zama babba nan gaba har yafi k'arfin mu, wannan b'acin ran nasu da bama so shi yake zama namu b'acin ran a gaba... yana da kyau mu dinga tuna cewa y'ay'a Amana ce a gare mu, kuma Allah zai tambaye mu yadda muka tafi da ita ranar gobe alk'iyama... Allah yasa mu gyara)_ Da wannan kuskure Imran ya kyale shaheeda take abinda ranta yake so musamman a gurin hajiya tafeeda, Sam baya tsawatar mata duk dashi yana binta sau da k'afa a matsayinta na mahaifiyar da tayi silar zuwan shi duniya. ********** Zaune take cikin filin tashi da saukar jirage na Aminu Kano international airport, ita kad'ai ce a gurin kare da waya a kunnenta ga dukkan alamu kira take, ana picking kuwa ta isar da gajeran sak'on da take son isarwa ta ajiye wayarta. Sake waiwaya hanyar da Ayman yabi tayi, ko alamun shi babu hakan na nufin yayi nisan da ba zata iya ganin shiba. A hankali ta soma share hawayenta da hankie a ranta tana addu'ar Allah ya bata aron rai da lafiya ya bata ikon kawo gyara a rayuwarshi, ta kyautata mishi kamar yadda kullum yake da burin kyautata mata shima. A duniya tashin hankalin Ayman ya ganta cikin damuwa ko halin rashin lafiya, yana nuna kulawar shi gareta a zahiri koda yaushe. @@@@@@ Tunda ya tashi yau yake jin jikin shi a sanyaye kamar wanda aka zarewa laka, yasan hakan baya rasa nasaba da had'uwar shi da Saleema da kwantacciyar rigimar da zai tarar. Har ya gama shirin shi ya futa a gidan ya isa office bai daina jin fad'uwar gaba lokaci bayan lokaci ba. ******A mugun gajiye ta shigo gidan, Jakarta da wayarta ta ajiye kan table k'arami da yake parlon ta shiga kitchen da hanzari ta tsiyaya tea a cup ta had'a shap shap ta fara sipping tana sauke ajiyar zuciya, a zuciyarta take fad'in, lallai yunwa zata iya haukata mutum yau ta sake tabbatarwa data futa bata karya ba. Tana gama shan tean ta gyara gurin, ta k'ara tattare parlon ta kammale komai a guri d'aya ta saka turare gidan ya d'au k'amshi. Sannan ta samu sukunin yin sabon wanka ta shirya cikin doguwar rigarta maroon irin mai kamawa daga saman nan ta bud'e daga k'asa. Ta nad'e gashinta ta turare jikinta da turare kala kala, ta yane kanta da k'aramin gyale ta futo. Kitchen taje ta d'ora apron ta fara simple girki cin mutum biyu don tana son anjima ta kaiwa yasmine idan khaleefa ya dawo ta nemi izini. Tana aikin tana bin suratul Maryam cikin jin dad'i da farin ciki mara iyaka, don yau jinta take kamar sabon mutum zero tension. @@@@@@ Ahmad da yake aiki yana duba time, da wuri ya tashi office gudun kada ta sauka ta yita faman jiran shi. Khaleefa ma dai da lokacin da Amna ta bashi yayi amfani ya tashi at exactly 4:50pm. Ko jakar system d'in a nan ya barta ya d'auko iya wayar shi da LC ya futo. Saida ya tsaya ya siya colour flower da yasan tafi so, sannan ya d'auki hanyar apartment na d'aliban gaban shi yana tsananta fad'uwa. Bai shiga ba saida ya gama karanto addu'o'in samun nasara a kanta da kyakkyawar fahimta. Da Amna ya fara cin karo tsaye a farkon lambun, fuskarta d'auke da murmushi mai cike da ma'anoni, ba tare da dogon tunani a kanta ba khaleefa ya k'arasa suka gaisa. Wayarta ta bashi, "sorry samun no ka a nan first". Baiyi musu ba wajen karb'an wayan da zuba mata digit d'in ya sake mik'a mata wayarta. Tayi saving ta mayar cikin aljihun kayan jikinta tace, "muje ko?". "Na ganki ke d'aya, Ina saleeeman?". Ya tambayeta yana kallonta. "Me kake ci na baka na zuba, mu k'arasa ciki mana". Bai mata musu ba yabi bayanta yayinda idon shi ke kallon inda yake takawa da takun Amna cikin tsanaki. Turus! Yaga k'afarta ta tsaya daga tafiya, sai shima ya ajiye tashi sannan ya d'ago a hankali ya sauke idon shi a gurin da suke fuskanta,,,, Saleema ce gaban shi don ko shekara dubu yayi bai ganta ba baza ta tab'a b'ace mishi a kwayar idon shi ba. Da wani irin zafin nama ya ture Amna da rabin jikinta ya shige mishi gaba baya iya ganin komai yadda ya kamata, ta tafi kamar zata fad'i Allah yasa ta rik'e jikin bishiya tana rarraba idanu kamar wadda ta yiwa sarki k'arya. Khaleefa baisan lokacin daya saki flower hannun shi da wayarshi suka fad'i k'asa ba, k'arar fad'uwar wayar ce ta d'auki hankalin Saleema har ya kai inda suke tsaye shida Amna. Gaba d'aya jikin khaleefa babu inda baya fudda gumi na zallar razani da shiga tashin hankali, bai tab'a zato ba, bai tab'a tsammani ba ko a mafarki da tunanin shi. Lokaci d'aya ya mugun fusata har jijiyoyin kanshi na futowa, nan da nan idon shi ya sauya launi kallo d'aya ba zaka so mishi gani na biyu ba. Da wani fusataccen yanayi ya juya inda Amna take ya watsa mata wani mugun kallon daya kad'a hanjin cikinta yayi taku uku zuwa gaban ta ya had'a ta da jikin bishiyar data ke jingine har saida ta rirrik'e hannun shi gam ba tare da tasan ma ta aikata hakan ba. "Daman kin kira nine saboda ki nuna mun adadin nisan da k'awar ki tayi mun?????". Yadda yayi maganar da k'arfi ba alamun sassauci a muryarshi ya sake d'ugunzuma hankalin Amna, gashi guri ba maceci bare tasa ran wani zai iya kwatar ta, yadda ta raina kanta farat d'aya haka Saleema data ke gefe ma ta raina kan nata, a hankali ya dinga matsawa bayan ya sake ta tana maida numfashi har ya koma inda wayarshi ta fad'i ya d'auka ya juya a zafafe ya futa daga gurin, don tabbas yaci gaba da tsayuwa zai iya illata Amna ta yadda ba zata iya morar kanta ba. Da k'afa ya dinga takawa da mugun sauri har yayi tafiya mai nisan gaske sannan ya samu mota ya hau, komai yana yinshi ne da k'arfin zuciya don jikin shi babu sauran kuzari, duk gabban shima jinsu yake kamar ba'a jikin shiba. ***Tun kafun passengers su fara futowa Ahmad yake tsaye a cikin airport d'in yana dakon futowar auntien, ya d'an jima yana jira kafun ya hangota tana tahowa rik'e da jakar kayan ta. Kafun ta k'araso ya tafi da hanzari yana mata maraba, dafa kanshi tayi tana jin dad'in ganin shi cikin k'oshin lafiya. Shiya karb'i jakar kayanta har zuwa inda yayi parking motarshi, ya zura kayan a baya ya bud'e mata gefen driver ta shiga, ya maida murfin ya rufe shima ya zagaya d'aya side d'in ya shiga ya fara tuk'a motar a nutse yana k'ok'arin barin gurin. Suna tafe a hanya suna hira har suka d'auki hanyar shiga anguwar su. A zuciyar Ahmad kawai tunanin irin farin cikin da khaleefa da raihana zasuyi idan suka ganta yake, a lokacin da motar su ta shiga farkon layin. ***Raihana tana zaune tana chat ta tuna da lallenta da zata tisa kafun ta kwanta bacci anjima, sai ta ajiye wayar ta d'auko plastic bowl ta zuba kayan kallen a ciki da ruwa ta fara kwab'awa, nan da nan parlon ya cika da k'amshin muhallabiyyah da kayan lalle. Tana cikin kwab'awa taji ana murza mukulli a parlon yak'i shiga, tasan khaleefa ne don shi kad'ai zai zura mata key yace zai bud'e mata gida, kasancewar akwai key a jiki bata cire ba sai k'ofar tak'i bud'ewa, abinda ya sake b'atawa khaleefa rai kenan ya fara yiwa k'ofar wani kalar duka had'e da danna bell har saida raihana ta d'an tsorata don komai beyi kama dana lafiya ba. Tana murza key ko gama bud'ewa k'ofar bata yiba ya turo ya shigo yayi cilli da wayarshi gefe guda, ya dafe kanshi da hannun shi yana shak'ar mummunan warin lalle abu na k'arshe daya tsana a rayuwarshi. Raihana data gama karantar a yanayin daya shigo d'auke wayarta tayi da bowl d'in lallenta da nufin gudu ta bashi guri, sai dai tana zuwa zata gifta ta gaban shi yaji warin kusa dashi, aikuwa a harzuk'e ya fincike bowl d'in garin hanzari har yana had'awa da wayarta da yatsun hannunta yayi wulli dasu duka kan tiles suka tarwatse a tare, sai ya dawo da duban shi gare ta ya fara nuna ta da yatsa yana takawa inda take tana ja baya har suka kai k'arshen bangon d'akin, tuni raihana ta gama tsorata banda zare ido ba abinda take yi, shi kuwa cikin d'aga murya yace, "wannan ya zamo na farko na k'arshe da zaki had'a wannan abun a inda kikasan idona zai gani......". Tsabar tsorata duk jikin raihana ba inda baya rawa har bakinta, kallon shi kawai takeyi da auntie da take bayan su ta tabbatar baisan da shigowarta ba, don sun shigo ne ita da Ahmad a dai dai lokacinta da yayi wancakali da kwanon lallenta. Daga ta bayan shi Auntie ta tafa hannayenta biyu tace, "da kyau! Da idanuna naga yadda kake tafiyar da amanar da kasa na karb'o a gurin masu k'aunarta iyayenta na baka kaima Amana don ka kula da ita,,,,,". Raihana da gudu ta shige d'akinta don ba zata iya yin kuka a gabanta ta k'ara mishi laifi ba. Shima k'afar shi yaja don zuwa yanzu ya fara daina gane mutanen da suke gurin, zai iya aikata komai ga kowa cikin rufewar ido. Daga auntie har Ahmad da kallo suka bisu kowa zuciyarshi fal tunane tunane. Gaba d'aya jikin auntie yayi sanyi da ganin irin wannan mummunar zamantakewar da take wakana tsakanin mutanen da tazo da kyakkyawan yak'inin samun su sun fara rayuwa cikin farin ciki da k'aunar juna , amma sai gashi a ranarta ta farko taci karo da abinda ya shallake tunaninta bare guntun mafarkin ta da take yi a can gida Nigeria ido rufe ko bud'e. _shike nan yau mutanen raihana sun samu abun fad'a🙆‍♀️🙆‍♀️_ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty six 5️⃣6️⃣ Ahmad ne daya ga duk jikin auntie a sanyaye tama kasa zama ya ajiye mata jakar kayanta cikin parlon yace, "ki zauna auntie wannan abune da.....". Da sauri ta katse shi ta hanyar d'aga mishi hannu. Shiru yayi yana kallon yadda gaba d'aya jikinta ya gama zama lakwas. Ta jima a tsaye kafun ta zauna cikin d'aya daga kujerun parlon. Kusan mintuna da yawa kafun ta bud'e bakinta ta tambayi Ahmad, "dama haka khaleefa yake treating Raihana kamar ya siyo baiwa a kasuwa, ka fad'a mun gaskiya". "Wallahi! Wallahi auntie kwatankwacin abu irin wannan bai tab'a faruwa tsakanin suba, yau d'in ma akasi aka samu ya huce fushin daba nata ba a kanta". Saida ta nisa sannan ta sake tambayar, "fushin wa kenan?". Cikin inda inda Ahmad yace, "ehh.. a'a....ina.... ina ganin ko a gurin aikine wani abu ya had'a shi da wani? Ban sani ba nima tunda gaskiya na riga shi futowa office". "Kenan a can ka barshi?" Ta sake tambayar Ahmad. "Eh na barshi yana aiki ma don har ta office d'inshi na biya kafun na tafi d'auko ki". "Kenan yana da wanda suke rigima a office d'in?". Ta sake jeho mishi wata tambayar. Zuwa yanzun Ahmad ya fara tsorata da tambayoyin na auntie, don yana ganin idan yaci gaba da amsata zata kaishi har inda baya son aje. "Toh ai shi ba harkar kowa yake shiga ba, bare har akai ga samun sab'ani tsakanin shi da sauran ma'aikata aboksn aiki". "Toh kaga ashe b'acin ran nashi ba daga office ya futo dashi ba kamar yadda ka fad'a da farko, lallai yaje gurin wani da ya b'ata mishi rai kafun ya k'araso gidan shi, ko kuma rigimar dama ta fara tsakanin su tun kafun ya futa daya dawo ta d'ora". Shiru Ahmad yayi cox anje inda bashi da amsar da zai bayar wajen ganin ya kare khaleefa. Ita kanta ta fahimci haka daga yanayin Ahmad d'in shiyasa taja bakinta ta tsuke amma ba don tambayoyinta sun k'are ba. So take tasan musabbabin abinda ya tashi zafun zuciyar khaleefa, don tabbas k'aramin abu baya tab'a shi har yayi irin abinda yayi akan idonta d'azu. Kuma yadda tasan raihana duk da ba'a shedar mutum tasan zaiyi wahala in daga itane matsalar ta fara. Sun d'auki adadin wasu mintuna a zaune kafun raihana ta futo yafe da gyale madaidaici, duk data wanke fuskarta amma har yanzu idanunta sun nuna alamun tayi kuka. Kusa da auntien ta k'arasa ta durk'usa kan k'afarta ta fara gaisheta. Auntie ta amsa cike da tausayin yarinyar, saida suka gama gaisawa taji lafiyar kowa daga mutanen Nigeria sannan ta gaishe da Ahmad ma. Shima dai cike da tausayawa yake dubanta har suka gama, bayan sun gama gaisawa ta maida kanta k'asa shi kuma Ahmad ya futa daga gidan bayan yayi musu sallama. Itama sai a lokacin ta tuna ko ruwa bata kawowa auntien ba, hakan yasa ta tashi da sauri taje kitchen ta had'o mata tray guda na ruwa da tea, bata zauna ba saida ta had'a da zubo mata abincin da ta ajiye zata kaiwa yasmine. Ko ruwa auntie kasa sha tayi sai bin yarinyar da kallo duk inda tayi, ita kanta har yanzu jikinta a sanyaye yake burinta kawai auntien taci wani abu ko ba da yawa ba. ***Ahmad yana zaune a gidan shi ya tasa abincin da yasmine ta ajiye tsakiyarsu ido yana ta faman juya cokali a ciki. Kallon shi Yasmine tayi da kyau kafun tace, "Anya baka b'oye mun wani abu ba? Tun d'azu daka shigo na fahimci yanayin ka duk ya sauya, na tambayeka kace lafiya ni kuma banga alamun lafiyar ba,,,,, don Allah hubby kada ka fara shigo mun da dabi'ar b'oye b'oye tun yanzu". Ajiyar zuciya yaja ya ajiye cokalin gefe yana kallonta ya bata amsa da, "Yasmin damuwar ba tawa bace ta khaleefa ce, kuma kona fad'a miki baki da maganinta tunda nima da nake tare dashi tsawon lokaci na kasa samun mishi magani,,,, gashi auntie tazo d'azu da yamma". Da sauri Yasmine tace, "what! Auntie maman su khaleefa? What a very big surprise". Ganin ta tafi wata jahar sai yaci gaba da tayata "yea! ita fa yanzu haka ma tana gidan sai gobe insha Allah zamu shiga ki gaisheta". Had'e fuska tayi tace, "kana nufin baza muje yanzu ba". "Haba Yasmine wane irin yanzu kuma kalli lokaci dare fa ya fara yi". "Toh ai ba wani dare ne yayi sosai ba, Ni dai don Allah Ina son na gantaaaaa" ta k'are zancen kamar zatayi kuka. Had'e kai da gwiwa Ahmad yayi yana ci gaba da sauraron yasmine da magiyar da take mishi kan ya kaita taga auntien, shi kuma ba daren ne damuwar shiba kawai baya son taje gidan a yanzu da yake a hargitse, koda safen ma sai ya shiga in yaga komai ya daidaita sannan zai kaita su gaisa d'in,,,, don wannan family issue ne daya shafe su bai kamata kowa cikin shi ko ita suyi musu shishshigi a ciki ba. Sai ya k'ara sauke ajiyar zuciya ya matsa kusa da ita ya jawota jikin shi don kawo k'arshen wannan rigimar tata. ***Khaleefa kam tun bayan shigarshi d'akin shi yake kaiwa da komowa ya kasa samun nutsuwa ko guda, gaba d'aya ya rasa inda zai jefa rayuwarshi yaji sanyi, ko idon shi ya rufe hoton fuskar Saleema yake gani data fara zama bak'ik'irin a zuciyarshi daga yammacin yau zuwa yanzu, ya zauna ya tashi ya dinga kaiwa ginin d'akin duka har saida duk ya jiwa hannun shi ciwo. Lallai kuka ma rahama ne, a yau yaso ace ya kasance kamar Ayman d'an uwan shi da yake da saurin hawaye, da yaji dad'i don koba komai zai rage rad'ad'in dake cikin zuciyar shi. A k'arshe sai bathroom ya shiga ya tara ruwa me yawa cikin bathtub ya shige gaba d'ayan shi da kayan jikin shi, tsananin sanyin ruwan ya dinga tab'a jikin shi yana bin kowacce kafar gashi yana shigewa, tun yana jin sanyin ruwan har ya gama bin jikin shi duka ya daina jin shi. Ya jima zaune a ciki yana hasaso abubuwa da yawa kafun ya iya futowa bayan ya d'auro alwala, ya sauya kayan jikin shi zuwa wasu riga da wando milk ya tada kabbarar sallah, bai bar kan dardumar ba saida ya jira aka kira sallar isha'i ya gabatar da sallar, still bai tashi ba yaci gaba da zama yana lazimi da tunanin da yake neman zama sashe na rayuwarshi ta yau. Baya jin yunwa, baya jin k'ishin ruwa bare har ya tuna wani abu daya cancanci ace yayi shi a lokacin, burin shi d'aya ya daina ganin hoton Saleema a majigin kwakwalwar shi gashi abun ya faskara. Adadin ganinta da yake, adadin tashi da hankalin shi yake k'ara yi. ***Auntie kuwa da kyar ta iya tsakurar abincin da raihana ta dafa mata sabo don kada ta zauna da yunwa, tasha tea me d'an yawa saboda kada raihana ta d'auka ko akwai wani abun a ranta,,,,,, a yau duk jikin su yayi sanyi babu wata hira ko dogon zance tsakanin su har lokacin kwanciya bacci yayi, raihana ta shiga d'akinta ta gyarawa Auntie kayanta a ma'ajiyar data ba kayan, ta sake gyara mata saman bed inda zata kwanta, ta dawo ta risketa a parlon inda take ci gaba da zaune har yanzu. Ta durk'usa cikin ladabi tace, "Auntie ya kamata ki huta haka nasan kinsha tafiya ga zaman jirgi me wahala, shiyasa har na gyara miki gurin da zaki kwanta ma". Shiru tayi tana nazari kafun can ta nisa ta mik'e zuwa cikin d'akin raihana na take mata baya. Saida ta shiga bathroom ta d'auro alwalar kwanciya bacci kafun ta shirya cikin kayan bacci masu kauri, bata hau saman gadon ba ta had'a barguna uku a k'asa masu laushi ta fara k'ok'arin kwanciya, raihana data sake shigowa taga abinda take k'ok'arin aikatawa hana ta tayi ta hanyar cewa, "a'a auntie don Allah kada ki kwanta a k'asan nan bayan ga kan gado na gyara miki". Murmushi tayi irin nasu na manya tana kallon raihana da take magana cike da wauta ta k'uruciya tace, "ba komai nan d'in ma yayi". Ba don taso ba ta kyaleta, amma fa abun sai taji ya mata wani iri ace auntien tana k'asa ita kuma ta hau kan bed tayi d'erere. Zama tayi a gefen gadon tayi shiru tana nazarin abubuwa da yawa, itama auntien shirun da tayi tunanin khaleefa kawai take, tana son taji halin da yake ciki saboda tunda ya shiga d'akin ya rufo kwakkwaran motsi baiyi ba har ta baro parlon, ga raihana tana shirin kwanciya muhalli d'aya da ita saboda kunya. Tashi tayi zaune da kyau tace, "shi wancen haka zai kwana ba tare da yaci komai ba kenan?". Shiru raihana tayi kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, "kiyi hak'uri raihanatu amma ba don halin shiba don hak'k'in aure da kasancewarki matar shi dafa mishi coppee ki kai mishi, sannan koda wasa kada kice don kunyi fad'a da mijin ki zaki raba makwanci dashi wannan kuskurene me girma, so daga nan kiyi zaman ki Allah ya bamu alkhairy". Da kyar ta iya mik'ewa saboda dabaibayin da auntie ta mata, haka a kunyace jiki a sanyaye ta mik'e don cika umarnin auntien. Duk da kayan jikinta ba marassa kauri bane amma saida ta d'ora hijab iya gwiwar k'afarta fari sannan ta k'ara ma auntien sallama ta tafi. Raihana tasan khaleefa ko ruwan hannunta basha yake ba bare wani coppee saboda kyankyami watak'ila, rana d'aya da yaci abincinta shine ranar da yaji zai mutu da yunwa cikin dare. Ta jima tsaye a kitchen bayan ta had'a mishi kofi d'aya na coppee da abinda zaici iya zallar cikinshi shi kad'ai sai tea daya sha kayan k'amshi, ci gaba da tsayuwa tayi tana sak'e sak'enta da k'ulle k'ulle har ta gaji sannan ta d'auki tray d'in tayi k'undunbala zata nufi d'akin. Saida ta tsaya ta kwankwasa mishi, a lokacin yana zaune kan resting chair ya had'a kai da gwiwa, bai d'ago ba ya bata izinin shiga daga inda yake, ta turo k'ofar ta shigo bakinta d'auke da sallamar da amsawarta ta gagara a gurin shi. Har gaban shi ta ajiye tray d'in ta matsa can nesa kan drower gefen gado ta zauna tana sake k'arewa d'akin kallo da yabawa mamallakin d'akin musamman yadda ya tsara komai. Gashi very neat bako d'igon datti kamar ba d'akin namiji ba. Ya jima a durk'ushe kafun ya d'ago ya sake zubawa trayn data shigo dashi ido. A hankali kuma ya karkata akalar ganin shi har inda take zaune tana wasa da cumb data samu a inda ta zauna. Baisan dalilin zamanta a d'akin ba don shap ya manta da auntie ma tazo gidan a yau. Sake kallon trayn yayi, kafun ya tsiyaya tea a k'aramin glass cup ya kai bakin shi da sauri ya shanye, sake zuba wani yayi ya sake shanyewa ya k'ara a haka har saida yasha 5 cups of tea ya hak'ura yana sauke ajiyar zuciya. Ya mik'e ya shiga bathroom bayan tsawon lokaci ya sake futowa ya ganta inda ya barta, sai yaja tsaki a k'asan ranshi yana tunanin abinda zaisa ta shigo mishi d'aki a irin lokacin da yafi buk'atar kad'aici. Cikin sake had'e rai ya fara tambayarta, "akwai abinda kike buk'ata ne". Ta fahimci inda tambayar tashi ta dosa shiyasa ta mayar mishi da amsar, "auntie ce....." Sai kuma ta kasa k'arasawa sai kanta data mayar k'asa. Khaleefa dafe kanshi yayi da yake tsananin sara mishi yana tuna zuwan auntien, gaba d'aya ya manta tazo don komai ba tunawa yake ba. Agogon bangon d'akin ya kalla yaga dare ya fara nisa watak'ila ma tayi bacci yanzu. Sai baice komai ba ya koma inda ya tashi yaci gaba da zama. Ta d'auke trayn ta mayar gefe ta sake komawa taci gaba da zama kan drower. Anta kiran wayarshi baya picking yayinda suke ci gaba da zama jigum daga shi har ita data ke matuk'ar jin bacci, ga d'akin shi bata ga komai da zata kwanta a kai ba sai gado falle d'aya shima ba wani kato irin wanda zasu buk'ata ba. Ko data ga zata rikito kan drower tashi tayi ba tare data kalle shiba tace, "Ina jin bacci, Ina son zan kwanta". . Sake kallonta yayi kamar yace mata to ni na kawo ki, sai kuma dai ya basar, ya k'ara shafe adadin wasu mintuna har ta fudda ran samun amsa daga gare shi sannan yace, "zaki iya kwanciya a gadon". Kamar abinda take jira kenan ta nufi gadon ta kwanta daga can gefe ta karanta addu'o'inta ta shafa, sai dai fa tana kwanciya bacci ya gagara yiwuwa, na farko ta fara tunanin abinda yake damun khaleefa don tasan lallai ba haka yake ba, na biyu ga haske ita bata iya bacci inda haske. One hour! Two hours!! Three hours!!! Tana kwance amma ba bacci take yi ba duk data rufe har kanta ba inda ake gani amma barci ya gagareta, saita yanke hukuncin d'aura alwala tayi sallolin nafilarta zasu fi akan tunane tunanen banza da wofi. Sai dai ga mamakinta koda ta tashi zaune khaleefa yana nan inda ta barshi kamar an dasa shi ko kwakkwaran motsi baya yi. Zuwa yanzu ta fara tsinkewa da lamarin na khaleefa, toh shi kuwa me ya same shi haka zai raba dare a zaune cikin tashin hankali haka?". Fasa aiwatar da abinda tayi niyyar aiwatarwa da farko tayi, taci gaba da zama tana nazarin shi kafun can tayi magana yadda zaiji cikin murya mara amo, "komai yayi zafi maganin shi Allah! Abun duk daba zamu iya magance shi da kanmu ba sai mubar mishi shi yasan yadda zai tafi da komai......". Har tayi zancen ta gama bai nuna alamun ya jita ba, har raihana ta fara tsoron khaleefa kuwa anya da numfashi? (Toh wa ya sani ma koya had'iyi zuciya ya huta da rayuwar😜). Sai zuwa can sannan ya d'ago saboda tsabar damuwar da yasa a zuciyarshi idon shi yayi wani irin jaa. Duk daba kyakkyawar mu'amula a tsakanin su amma yaji dad'in maganar da tayi mishi, koba komai an samu wanda zai kwantar mishi da hankali. (Dama shi a zuciyarshi Kashi uku nau'in fushin shi ya rarrabu, Allah yayi khaleefa wani irin mutum mai zafin zuciya barin ma idan ranshi a b'ace yake, yana iya yankewa mutum kowanne irin hukunci kowaye shi a lokacin da yake cikin fushi, shiyasa yafi buk'atar kad'aici a irin wannan lokacin, yanki na biyu kuma da zarar ya gama tunani da irin hukuncin da zai yankewa mutum toh yana buk'atar kafad'ar da zaiyi kuka tunda shima mutum ne kamar kowa, yana kuma buk'atar rarrashi da shawarar yadda zai fuskanci koma meye ya tunkaro shi, na uku kuma shine baya rik'o amma yabar abu ya barshi har abada kamar Ayman, wannan kuma zuciya ce da bamusan gurin gwanin da suka samo ta ba uwa ko uba). So ko a lokacin da raihana tayi magana ya gama kaiwa limit na tsakiya. Hakan yasa ya tashi yaje ya wanke fuskarshi ya futo ya kashe glove d'in d'akin saina bedside kawai ya bari ya k'arasa kan gadon ya zauna daga k'arshen gadon kamar yadda tayi, ya zura rabin jikin shi cikin duvet ya jingina kanshi da fuskar gadon idon shi bisa rufin d'akin ya tsura mishi ido..... A zuciyarshi yake tunanin ko ya amince da ita yau taji wani yanki na sirrin shi kamar yadda ta yadda dashi ta fad'a mishi nata a ranar data fara ganin shi, don ajiye zance a rai kamar yadda ya fad'a ba abinda yake sai sake assasawa mutum damuwa da jefa shi cikin tashin hankali. Ya jima yana nazari kafun can ya sauke doguwar ajiyar zuciya ya kalli sashen da take zaune. Itama a dai dai lokacin ta juyo da nufin satar kallon shi saboda ajiyar zuciyar shi ta d'au hankalinta sosai, sai kuwa cikin sa'a idanun su suka fad'a cikin na juna. Kowa a cikin su kasa d'auke idonshi yayi saima son karantar sak'on da yake cikin idon kowannen su day suka fara, hakan yasa suka lula duniya mai nisan da saida raihana tayi da gaske ta iya futowa a ciki, saita lumshe idonta a hankali tare da juyar da kanta gefe. Shima ta b'angaren shi hakan ce ta kasance, shiru ya sake biyo baya kafun yayi gyaran murya ya fara magana da disashshiyar murya irinta wanda yaci kuka ya godewa Allah. "kiyi hak'uri d'azu na huce fushi na a kanki alhalin ba kiyi mun laifin komai ba". Har lokacin kanta a k'asa tace, "na fahimci hakan, kuma duk da haka nayi maka laifi sai dai a rashin sani ne tunda baka tab'a fad'a mun baka son warin lalle ba". Juyowa yayi ya fuskanceta, ya akayi ta fahimci haka? koda yake dole zata gane yadda yayi mata fancakali da kwano. "Hakane! Duk da ba wai bana son lallen bane kwata kwata, a'a ina kyamatar shi ne a zuciyata, amma nasan lalle yana daga alamar mace y'ar gayu ta gasken gaske ma'abociyar tsabta da ado kamar dai mamana". Murmushi ne ya sub'ucewa raihana har hak'oran bakinta na bayyana, "ai ita Auntie ta kasance ta musamman ko a cikin mata dubu samun irinta sai an tona". Shima murmushin gefen baki yayi duk da ba wai ya futo sosai ba ya sake cewa, "me yasa kika ce haka!". "Saboda dalilai da dama". Ta fad'a cikin shagala da manta da wanda take tare. "Toh ko zan iya sanin wasu daga ciki". Sake jan bargo tayi ta k'arasa rufe fiye da rabin jikinta sannan taci gaba da maganarta, "sai dai na fad'a maka muhimmai daga ciki duk da nasan ma ka sani". "Ehem go ahead!". "Shin a rayuwarka ka tab'a ganin auntie da datti koda tana aikin gida irin aiki yasha kanta d'in nan?". Abun dariya yaba khaleefa don ya d'auka wani k'atoton dalili zata d'auko mishi, amma dai ya dake baiyi ba, madadin haka ma sai ya bata amsa da, "a'a ban tab'a gani ba". "Yauwa sai na biyu, ka tab'a ganin ta cika fuskarta da kyale kyale ko aji gidanta ba da ita kanta ba k'amshin turare?". "A'a" ya sake bata amsa idon shi a kanta, so yake kawai takai k'arshe yaji dalilin nata. "Abu na uku daya kasance ba akan ado ba shin ka tab'a zuwa mata da kukan ka ta barka bata share maka hawayen ka ba?". Tsam yayi da ranshi ya tafi tariyar rayuwarsu tun daga yarinta har kawo yanzu da suka mallaki hankalin kansu, tabbas itace mai share musu hawayen su kuma bata tab'a gajiyawa da hidimta musu ba, Jin yayi shiru sai taci gaba da cewa, "Toh kaga ashe ta kai nagartacciyar uwa k'arshe fiye da duk wata uwa da muka sani a duniya". "Hakane uwar alfahari ce Auntie, duk da ba wai bata da wani laifi ko kuskure ba a rayuwarta ba". Jim raihana tayi kafun ta sake cewa, "shin ka manta a rayuwa alkhairin mutum yana dannar sharrin shi, ai duk d'an Adam baya rabo da sharri amma abun so da alfaharin shine ace alkhairin mutum ya danni sharrin shi kamar dai ita". Sake jinjina maganarta khaleefa yayi, da yake jin tana wannan maganar akan auntien sai yake ga kamar ita ta haifa ba shiba, "idan na fahimce ki dai dai kina nufin iyaye mata sunfi iyaye maza muhimmanci a rayuwar y'ay'an su?". Ya k'arasa fad'a yana tsura mata ido da son jin amsar da zata bashi. "Kowanne da nashi sashen, idan ana maganar jigon iyali uba kenan, amma fa in akazo maganar uwa toh ita rufe k'ofa ce, don tana taka muhimmiyar rawa a tarbiyyar yara dama rayuwarsu baki d'aya. Komai kaga tayi tana da nata dalilin babu wani abu na kuskure da zata ma yaranta da gangan tana sani". Ta kai k'arshen zancen tana satar kallon shi, shima kallonta yake babu ko cikakken k'ifta ido a zuciyarshi yana rairaye kowanne zance d'aya da take fad'a da iya gaskiyarta. Jinjina kai yayi kafun ya sake ce mata, "koda ace ta aikata tabkeken laifi ga yaran? Taya ma kike tunanin uwa zata iya tafiyar da iyali ita kad'ai babu jigo (wato uba) kamar yadda kika fad'a?". Wannan tambayar khaleefa yayi ta ba don yasan ta futo daga bakin shiba. Itama kanta saida taji tambayar kamar da gangan ya yita, shiru tayi kanta a k'asa kafun can ya nisa ta bashi amsa, "Ina tunanin wannan tambayar ba don neman amsa kayi ba, tunda ga misalin irin iyayen nan a tare daku, Ina ganin mahaifiya ko haihuwar d'a tayi ta barshi haka nan a duniya ba tallafinta bare sa hannunta har ya girma ya zama wani abu toh ta gama yi mishi komai, idan zai tara duk abinda yake cikin duniya ya bata bazai tab'a biyanta ba.... Balle ku da kuka tashi cikin asalin gata, ko masu uba a anguwar nan ba zasu fad'a muku komai ba, auntie ba iya matsayin uwa ta d'auka a rayuwar kuba, ta d'auki matsayin uwa! Uba! Bango! Jigo kai matsayin komai ma a rayuwarku gaba d'aya, ita ta kasance d'aya tamkar da dubu, da ace wanda ya mutu yana dawowa, toh da tabbas mahaifin ku zai dawo don kawai ya jinjina mata bisa ga sadaukarwar da tayi". Raihana tana kaiwa nan tayi shiru tare da jan dogon numfashi kafun ta k'ara kallon shi ta saki k'aramin murmushi tace, "yi hak'uri zaka ga kamar Ina ta magana akan iyaye mata kamar saboda ni mace ce, a'a Ina fad'in abinda yake gundarin gaskiya ne, kuma zan iya tsayawa a gaban kowa nayi irin wannan bayanin musamman ma wad'an da suke k'ok'arin kushe mana iyayen mu mata kan k'ok'arin da sukeyi damu, a nan kam zan iya cewa sai inda k'arfina ya k'are". Sai a lokacin khaleefa daya zuba mata ido kamar robbot ya motsa tare da janye kwayar idon shi daga kanta. Wane irin sani da so wannan yarinyar take yiwa auntien su haka? Koshi data haifa bai tab'a magana a kanta irin haka ba, haka tunda sukayi maganar can da Saleema ya daina yabawa duk wani k'ok'arinta da jajircewa kamar yadda take yi a baya, ba gaira ba sabab ya fara zarginta da jin haushinta duk da bata fasa yin iya k'ok'arinta wajen ganin ta faranta mishi ba, ko akan maganar auren raihana sau d'aya ya nuna yana so, amma bata nutsu ba saida taga an d'aura auren raihana ta zama mallakin shi, meyasa tayi haka? Don kawai ya samu cikar burin shi, shi kuma me yayi mata? Akan soyayyar wata can data tsince shi da hak'oran shi talatin rana tsaka yake k'ok'arin mantawa da matsayinta na wadda tafi komai da kowa muhimmanci a rayuwarshi, ya fara neman k'asar da zai cika mata ido da ita. Abun kunya sai gashi yau wata tana magana a kan ita wannan matar data zama silar zuwan shi duniya kamar ita ta kawo bashi ba shiba. Kallon sashen da take yayi, a kwance take amma ta duk'unkune jikinta sosai, take ranar da matashin nan ya futo yana mata cin mutumci ta dawo mishi, duk zagin daya mata bata kula shiba amma yana tab'a auntien ta nuna fushinta muraran. _Wannan fa shi ake kira tuntub'e dad'in gushi_ *Littafin JARUMAR UWA gaba d'aya sadaukarwa ne ga ummata, amma a ciki wannan fejin mallakine ga duk wata uwa da ta ke duniya dama wanda suka riga mu gidan gaskiya, dama wanda suke shirin kasancewa iyayen nan gaba kad'an. Fatan Allah ya k'arawa iyayen mu lafiya da nisan kwana* Hak'ik'a naga ruwan comment d'inku a update da nayi jiya, naji dad'i sosai kuma na jinjina muku bisa yadda kuke nuna mun asalin yadda muke tafiya tare 👍👍👍😍😍😍 na dangwala muku kyauta. __kada ku jirayu update gobe, naso ace na kokarta mun koma kwana biyar a sati amma hakan bai yiwu ba saboda uzururruka da suka sake sha mun kai, amma insha Allah zaku jini Thursday and Friday. Nagode_ Kada ku manta dai kuna tare da Alk'alamin in-identical twins, merhreeyaert lerwerl da doctor ferhyeezz m Usmern duk abu d'aya ne🤝 _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty seven5️⃣7️⃣ Khaleefa ya jima a kwance yana wassafa wasu abubuwa masu nauyi akan mahaifiyarshi da rayuwarsu tare da ita, sai yanzu yake iya rarrabe komai daki daki yana kaishi muhallin daya dace. Bacci bai samu ba gare shi a wannan dare hakan yasa ya k'arasa raya daren da sallah da addu'o'i, cikin hukuncin Allah zuciyarshi ta k'ara yin sanyi yaji nutsuwarshi tana dawowa. Bai tashi a dardumar ba har mukhtarin sallar asubah ya shigo. Koda ya sake komawa bathroom ya futo da nufin tashin raihana sai ya ganta a zaune gefen gadon tana jiran futowar shi. Suka kalli juna a tare lokaci d'aya kuma suka d'auke kai, da bathroom nashi tayi amfani ta kama ruwa da alwala ta futo tana santin d'akin wankan da yasha tsari irin na asalin matasa ma'abota gayu da tsabta. Shiya jasu jam'i. Suna idarwa raihana a daddafe tayi addu'o'inta suka gaisa ta koma kan gadon ta nad'e cikin tattausan bargon shi da yake fudda k'amshi me dad'i da sanyaya rai. Bata jima da kwanciya ba khaleefa ma yabi bayanta, daga can k'arshen gadon ya kwanta, ba dad'ewa wani daddad'an bacci yayi awon gaba dasu. *****Ta b'angaren auntie kam baccinta tasha don ta gaji over kuma dama ba wai garkuwar jikinta ta gama dawowa dai dai bane, har yanzu tana shan magani. Lokacin data tashi bakwai saura y'an mintuna, sallah ta fara gabatarwa kafun ta gyara inda ta kwanta, ta tsabtace d'akin gaba d'aya ta kunna turare ta turare d'akin sannan ta futo parlon, duk da babu datti saida ta sake gyara shi ta d'auke wayar raihana data fashe ta ajiye kan center table ta kawo turare nan ma, a k'arshe kuma ta dire a kitchen, nan kam babu abinda ta tab'a sai abincin karya kumallo data fara had'awa. Koda ta gama tea kawai tasha ta jere abincin a dinning tana sake duba lokaci. Rana har ta futo amma babu alamun raihana bare khaleefa, da farko tayi tunanin jiran su amma ganin lokaci nata tafiya saita d'auki nata ta rufe musu ragowar. ****Tsaye take a gaban k'ofar shiga d'akin Amna, da kallo d'aya zaka fahimci sam bata cikin nutsuwarta, tun a daren jiya take son had'uwa da amnan abun ya faskara, tsabar takaicin data had'a mata bata iya runtsawa da kyau ba bacci sai b'arawo. A shirye amnan ta futo cikin shirin futa, turus ta tsaya ganin Saleema tsaye a gabanta. Niyyar hucewa tayi sai dai saleeman ta hana mata damar hakan ta hanyar tunkud'eta ta shige ciki ta maida k'ofar ta rufe. "Me ya kawo ki?". Amna ta tambayeta cikin k'arfin hali bayan ta ajiye wayarta gefe. "Har kina da bakin tambayar abinda ya kawo ni bak'ar munafuka! Yau nazo ayita ta k'are koni ko ke don na gaji da irin abubuwan makircin da kike k'ulla mun, dama akace sai ka d'auki tsawon shekaru da mak'iyinka ba tare daka sani ba, yanzu nake fahimtar haka daga sharrance sharrancen da kike k'ulla mun.....". Ta k'are zancen tana zare k'aramin siririn gyalen jikinta ta ajiye gefe d'aya. Murmushi Amna tayi ta k'ara matsowa har gabanta tace, "kina wasa da rayuwarki Saleema, abinda na miki jiya kin manta na tab'a fad'a miki zan aikata? Koda yake ni yanzu sunan maƙiyiya nake amsawa a gurin ki saboda ina son ganin na ceto rayuwarki daga fad'awa halaka.... Well muje a hakan watarana ai gaskiya zatayi halinta, sai abu na gaba khaleefa naki yaji jiya amma shima akwai nashi laifin da baki sani ba, don yayi aure zuwan shi gida Nigeria". A zabure Saleema taji zancen don ya shiga ne da gudu ta kafofin jinta, "what? Aure? how comes?" Tayi tambayar a rarrabe tana juya hannunta. "Aure dai irin wanda kika sani, koda yake ai bai kamata na fad'a miki bama tunda ke dashi kunyi equal babu wanda ya huce ya zalinci wani, sannan labarin nan tunda zafin shi na kawo miki shi kika gwasale ni baki karb'a ba sai yanzu daya huce....". Durk'ushewa Saleema tayi a gurin ta rabka uban tagumi, "shikenan tasan ba ita ba khaleefa kuma har abada, don khaleefa bai shirya rayuwar shi da auren mace sama da d'aya ba bare tace maybe yana nufin aurota daga baya, kuma koba haka ba sunyi alk'awarin ba kishiya, toh taya ma zai lalata musu duk wani shiri da suka yima rayuwarsu. Tsam ta sake yi da ranta tana tuna yadda suka rabu, daman khaleefa ya shirya haka gareta shiyasa daya tashi tafiya ya dawo mata da zobenta a nufin shi ya dawo mata da soyayyarta kenan?, Tab in hakane kuwa yayi kuskure don ba zata iya rayuwa da wanin shiba, lallai saita tabbatar ta raba shi da koma wacece koda ba zata same shi ba. Mik'ewa tayi tana share hawayen daya cika idonta ta dubi Amna da take jin kamar ta shak'e ta ta mutu kota huce takaicin abinda tayi mata. "Ke kuma zan dawo gare ki". Murmushi Amna tayi ranta fes tace, "da zaki yi hankali wannan zai zama manuniya a gare ki dashi kanshi khaleefa na fahimtar lokaci yayi da zaku hutar da zuk'atan ku ku tunkari rayuwar gaskiya, don ke ba zaki tab'a samun mai sonki kamar muslihu ba". Wani mugun kallo kawai Saleema ta jefa mata don ba zata iya cewa komai ba tsabar tashin hankalin data tsinci kanta ciki, da gudu gudu sauri sauri ta futa bata ko rufe mata k'ofar ba. Murmushi mai kyau Amna tayi a fili tace, "da sannu zaki dawowa gaskiyar da kika gujewa Saleema". *****Auntie tana kallon news taji ana tab'a door bell, a nutsenta ta mik'e taje ta bud'e k'ofar, Ahmad ne tsaye, saita bashi hanya ya shigo ciki ta maida k'ofar ta rufe. Har k'asa ya durk'usa suka gaisa kafun ya zauna saman d'aya daga kujerun parlon, hira suke yi jifa jifa, ya fahimci kamar ita kad'aice a gidan hakan yasa ya tambayeta ko khaleefa ya futa ne. "A'a ina tunanin bai tashi bane". Kallon agogo yayi ya maimaita kalmar "bacci? Aikuwa yanzu zan tashe shi". Murmushi ita dai tayi ta sake tattara attention d'inta kan labaran da take kallo. Saida ya fara rubutawa Yasmine gajeren sak'o don yaga komai ya tafi dai dai a gidan, sannan ya fara kiran layin khaleefa. Raihana ce taji ringing d'in, hakan yasa ta tashi zaune da sauri tana karanta addu'ar tashi daga bacci had'e da yin mik'a. Sashen da khaleefa yake ta kalla taga baccin shi yake sadidan kuma yana jin dad'in baccin da dukkan alamu. Da sauri ta d'auke wayar tayi rejecting kiran tayi silencing wayar baki d'aya, don daren jiya bata jin ya runtsa kona second d'aya. Fuskar wayar ta tsurawa ido har yanzu hoton Saleema ne, sai tayi murmushi a ranta tana ayyana watak'ila itace yarinyar da yake so d'in nan. Tana shirin ajiye wayar gajeren sak'o ya shigo daga Ahmad, "Ohh shine ka katse mun kira,,,, Anya ma kuwa baccin da auntie ta fad'a kake?,,, koma dai meye ya kamata a k'are shi haka azo a gaishe da tsohuwa". Da sauri raihana ta ajiye wayar tare dajin tsananin kunyar kalaman Ahmad d'in, bathroom d'inshi ta shiga ta wanko fuskarta. Koda taje wajen k'ofa da nufin futa kasawa tayi, na farko kunyar Auntie ce ta diro mata dashi kanshi Ahmad d'in daya sauya musu fassara, sai kayan jikinta na bacci duk da riga da wando ne wadatattu kuma da wadataccen hijab a sama amma tasan Ahmad ba muharraminta bane da zatace ba komai don ya ganta a haka. Tana nan tsaye Yasmine ma ta shigo gidan, har suka gaisa da auntie tasha tea a kunnenta, tana jin Yasmine na tambayar auntie raihana, Ahmad yayi zaraf ya bata amsa da bacci takeyi, ita kanta saida ta kalli agogo zata k'ara magana ya harareta, ya tura mata sak'o, "ya kamata ki kama kanki kina gaban maman mune". Had'e fuskarta tayi ta mishi refly da, "toh ina ruwan ka ai dai nima mamana ce ba taku bace ku d'aya da zaku goranta mun". Murmushi kawai yayi ya girgiza kai, suka ci gaba da hirar su ita da auntie, rabin hirar Yasmine duk yabone ga raihana, sai jaddada mata take raihana ta iya kaza ta iya kaza a k'arshe tace kai aita iya komai ma. Ahmad ganin khaleefa da gaske ba futowa zaiyi ba sai yayi ma auntie sallama ya futa, sai a lokacin raihana ta samu damar futowa. Ta k'arasa har kusa da Yasmine ta durk'usa ta gaishe da auntien. Suka gaisa da yasmine ma sannan ta shiga d'akinta tayi wanka ta shirya cikin kayan da suka fi amsar jikinta, Allah ya taimaketa basu da lectures yau data gane kurenta, don ta kuskura tayi missing saita jima kafun ta fahimci abinda ya huce ta. Koda ta futo ba k'aramin santin dressing d'in nata dashi kanshi d'inkin yasmine tayi ba, gashi yau Allah ya rufa asiri bata labto wannan uban zurmemen hijabin ba, tana zama auntie ta gabatar mata da abincin karin kumallo, ta karb'a cikin jin kunya tana godiya, tunda ita ya kamata ta tashi ta had'a abincin ba bak'uwa irin suruka ba. Koda ta yiwa yasmine tayi cewa tayi ta k'oshi. Auntie da take kallon su tace, "nima saida na zuba mata bata ciba dama haka kuke wannan rayuwar?". Murmushi raihana tayi tace, "a'a da gaske ta k'oshin ne indai kuma ko ba kunyarkice ta hana ta ciba". "Ah haba! Ke kin tab'a ganin y'a taji kunyar cin abinci gaban mamanta". Yasmine ta fad'a. Duk dariya sukayi marar sauti kafun Auntie ta tashi ta koma cikin d'akin raihanan. Matsowa kusa Yasmine tayi tace, "Ashe bani kad'ai bace bani da kunya?". Tasan me Yasmine take son cewa don haka ta katse mata hanzari da saurinta, "kar ki kaimu inda bamu jeba, ah toh makara mukayi kema kin sani". Y'ar k'aramar dariya tayi, "yada kama kai haka da sauri". "Ai nasan abinda zaki fad'a shiyasa na taryi numfashin ki". Sai suka sake dariya su dukan su. Hirar su suka ci gaba har raihana ta gama cin abincin. Suna cikin hirar ne kuma kiran Ahmad ya shigo, Koda ta d'aga tambayarta ya fara, "daga gaisuwa kuma sai kiyi zaman ki madame? Ko kin koma can da zama ne?". Bata bashi amsa ba ta katse kiran bayan ta mik'e tsaye ta maida gyalenta tace ma raihana, "hajiya am about to go na samu urgent call daga boss". Dariya kawai raihana tayi, a times in Yasmine tayi abu sai taga kamar k'anwarta Salma, halin su iri d'aya kamar uwa d'aya uba d'aya. Auntie ta k'arasa ta yiwa sallama sannan ta fuce a gidan. Ranar khaleefa bai tashi a bacci ba saida aka kira sallar zuhr. Raihana tana zaune gefen auntie kan darduma tana lazumi, auntien ma lazumin takeyi ya kwankwasa k'ofa suka bashi izini ya shigo. Raihana ta kalle shi da dressing d'inshi daya taimaka wajen k'ara futo dashi a gentleman, shi kam ta b'angaren shi wani irin sanyi ne ya kwaranya ruhin shi a lokacin daya shak'i k'amshin turaren daya manne da d'akin nata. Ta tashi a nutse ta futa daga d'akin don bashi guri ya gana da mahaifiyar shi. A k'asa ya durk'usa ya fara gaisawa da auntien, ta amsa da fuskar ba yabo babu fallasa. Shiru sukayi bayan hakan kafun khaleefa ya fara magana da cewa, "kiyi hak'uri auntie jiya kin same ni..... Shiyasa ma banzo mun gaisa a jiyan ba..... Amma yanzu..... am very sorry dai kawai". "Matar ka zaka bawa hak'uri khaleefa bani ba". Ta bashi amsa still ba fara'a kan fuskarta. Shafo sumar kanshi yayi kanshi a k'asa still yace, "ai na bata hak'uri tun jiya komai ya huce". Gyara zama Auntie tayi taci gaba da cewa, "wato khaleefa har yanzu kana nan da halin ka na zafun rai da kasa mallakar kai a lokacin da kake cikin b'acin rai, sanadiyyar haka har gashi kana jibge buhun rashin mutumci akan yarinyar da bata jiba bata gani ba..... Gaka a haka kamar mai k'arfi ashe ta gina bata shiga bane, don annabi S. A. W yace, ""laisashshadidu, walakinnashshadidu, allazey yamluku nafsahu indal gadabi"" (fassarar hadisin da hausa shine👉🏻mai k'arfi bai zamo ba, kad'ai mai k'arfi, wanda yake iya mallakar kanshi yayin fushi) don Allah khaleefa ka dinga tunawa da wannan hadisin da kuma kiyaye b'atawa ruhin da yake kyautata maka". Tunda ta fara maganarta har ta gama kanshi a k'asa yake, saida ta gama zancen ta kaf sannan yace, "insha Allah za'a kiyaye Auntie...". Cikin jin dad'in yadda ya karb'i kuskuren shi da kuma son ta jarraba shi tace, "Toh Allah yasa! Amma Ina ganin idan na tashi tafiya zan d'auke Raihana ta mu koma gida tare". Rass! Khaleefa yaji gaban shi ya fad'i haka kurum ba tare da zato bare tsammani ba, duk da a cikin zuciyarshi babu komai. "Kayi shiru baka ce komai ba?". "Eh ba damuwa zaku iya komawa taren". Ya bata amsa a zuciyarshi yana ganin auntien ta fad'a ne kawai tunda dai tasan raihana ta fara zuwa makaranta ai. Zancen ya shiga Auntie a bazata, koda yake tafi kowa sanin halin khaleefa, zai iya b'oye komai a cikin shi komai girman shi, sai in yaso aji yake futar dashi, galibi ma bai fiya fad'ar magana da baki ba sai dai ya nuna a aikace. "Amma Auntie sai naga kamar kin rame?". Khaleefa shima ya mata tambayar a bazata, b'oyayyen ajiyar zuciya ta sauke tace, "kwanakin da suka gabata nayi fama da rashin lafiya amma ynz alhamdulillah". Shiru ya sake yi kafun ya nisa ya tambayeta, "akwai abinci kuwa?". "Eh yana dinning raihana zatayi saving d'inka". "Ita ta dafa?" Ya sake tambayarta. "In ita ta dafa ba zaka ciba kenan?". Shafo sumar kanshi ya sake yi yace, "a'a kawai nayi missing abincin kine mamana". Ya k'arasa zancen yana marairaice mata kamar k'aramin yaro. Dariya tayi sosai khaleefa yana tayata, sunci gaba da hira har zuwa lokacin da yaji yunwar cikin shi ta fara uzzura mishi ya futa dinning, yaci abincin da yawa ba laifi don da gaske yayi kewar girkintan nan. Da daren ranar ma raihana a d'akin khaleefa ta kwana, har tayi bacci yana aiki a system batasan nisan lokacin daya d'auka ba, ita dai ta tashi da asubah tagan shi kan sallaya yana sallah. Alwala tayi itama tayi tata sallar. Khaleefa yana shirin komawa bacci sak'o ya shigo wayarshi da bak'uwar number, "kayi hak'uri da abinda ka gani waccen ranar, nasan zaka dinga kallona matsayin silar ganin abinda zai zamo maka tashin hankali a rayuwa, ko mai son raba ka da masoyiyar ka Saleema, sai dai hakan shine kad'ai damar da zanyi amfani da ita wajen ganin na ceto rayuwarku kaida ita, na kuma fahimtar daku abinda kuka kasa fahimta a soyayyarku tsawon lokaci..... Nagode Amna". Khaleefa yayi ta juya maganganun amnan har zuwa lokacin da bacci ya sake sad'ad'd'afowa yayi awon gaba dashi. Raihana bata yarda an sake abun kunya irin na jiya ba, hakan yasa tak'i komawa bacci, da kitchen ta fara, ta shiga don shirya lafiyayyen abincin breakfast. Ko zuwa lokacin da auntie ta futo ta sameta ta kusa kammala aikinta gaba d'aya. Bata yarda ta tayata ba don dole ta hak'ura ta koma ta zauna. @@@@@ Ranar Monday tunda sassafe khaleefa ya gama shirin shi na futa office as usual, ya futo rik'e da jakar shi da wayarshi yana magana da Ahmad. Raihana tana aikin jera food warmers a dinning taga futowar shi, yayi maseefar kyau cikin shigar tashi ta yau fiye da kullum ma. K'asa tayi da kanta a lokacin daya k'araso gurin, baice mata komai ba yayi knocking k'ofar bedroom d'inta aka bashi izinin shiga. Ya samu auntie suka gaisa tare da yi mata sallama. "Amma zaka karya kafun ka futa ko?". "Ehh! A'a gaskiya ba lokaci zan iya yin late in na k'ara wasu mintuna". "Toh Allah ya tsare ya bada sa'a". Ya amsa da ameen yana fucewa. Da kallo ta bishi a ranta tana tunanin abinda yasa baya son cin abincin, ko har yanzu baya cin abincin raihanan? Koda yake ai tana nan da sannu zata kama shi. Yana zaune a office aiki yasha kanshi, wasu uban files ne yake ta dubawa yama kasa gane wannene ainahin wanda yake nema a ciki, saboda rarraba hankalin shi da yake yi. Ganin ba fahimtar komai zaiyi ba daga k'arshe sai kawai ya matsar da files d'in gefe ya kifa kanshi jikin table d'in da yake gaban shi, hoton abinda ya faru waccen ranar yana dawowa cikin kwakwalwar shi dalla dalla yana hucewa kamar video, shi yasan cikin kwanakin k'arfin hali kawai yake yi amma abun yana cikin zuciyarshi, yini baya farawa ya k'are bai tuna ba, dole ba yadda zaiyi abun so yake ya zama wani yanki na b'acin ranshi, ko abin bak'in cikin rayuwarshi da baya son tunawa. Ya lula duniyar tunani shiyasa har aka turo k'ofar office d'in aka shigo bai sani ba. Itama bata damu ba ta k'arasa har gaban shi taja kujera ta zauna. Zuba mishi ido tayi tana kallon shi tare da jin wani mugun kishin sa, a duniya babu abinda zai hanata samun khaleefa, kuma ko meye zata iya kau dashi kota wacce hanya wannan alk'awari ne........ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty eight 5️⃣8️⃣ Bak'on k'amshin turaren da yaji cikin office d'in ne ya taimaka wajen dawo dashi hayyacin shi, a nutse yake binta da kallo fuska sam ba annuri. Itama kallon shi take yi shakkun shi na shigarta. "Tashi ki futar mun a office don baiyi kama da gurin shirme da shirita ba". Marairaice fuska tayi ta mik'e daga kujerar ta fara k'arasawa har gaban shi tana magana da sigar ban tausayi, "me yasa zaka yimun haka khaleefa? Kasan kuwa adadin yawan son da nake maka da kishin ka? Amma shine har kaje ka auri wata kake rayuwa da ita bayan alk'awarin da kayi mun......" Ta k'arasa fad'a cikin rawar murya tana nufar shi kai tsaye zata d'ora hannunta jikin shi. Da wani mugun sauri ya hankad'a ta har saida kanta ya daku da jikin bango, cikin tsawa yace, "ki futa Saleema! Ki futar mun a office!! Na tsane ki bana son ganin ki, bana son jin muryarki.... Banza ballagaza, ke yanzu har kina da bakin magana akan aure na bayan duk abinda kikayi....." Yadda ya rufe Ido ya balbaleta da maseefa kad'ai ya tabbatar mata da zai iya aikata komai gareta a lokacin, jikinta gaba d'aya yayi lakwas takaicin Amna da nadama ta cika zuciyarta a karon farko, amma fa koda ha maza ha mata saiya aureta tunda har ya kuskura ya lasa mata zumar soyayyarshi toh sai dai fa ya rayu da ita kad'ai bai Isa ya rab'i watan ta ba. Jiki a sanyaye fuska sharkab da hawaye taci gaba da tsayuwa a offishin tama kasa d'aga k'afa bare ta iya futa kamar yadda yake buk'ata. Yayinda shi kuma hannun shi ke mata nuni da k'ofar futa. A haka doctor andal ta shigo office d'in ta tsaya tana kallon su su duka biyu kafun ta tambayeshi, "tsayuwar me patient take a office d'in likita?". Khaleefa k'asa yayi da kanshi a sanyaye yace, "ita ba patient bace". "Toh me takeyi kenan ko batasan yanzu lokacin aikinka bane". Saita dawo da dubanta ga Saleema da take faman rabzar kuka tace, "hajiya u can wait for him somewhere in ya tashi office ya same ki a can". Bata iya cewa andal komai ba ta fuce a office d'in da mugun sauri bayan ta k'aro k'arfin sautin kukanta. Doctor andal taja kujerar gaban table d'inshi ta zauna, shima zaman yayi amma kanshi a k'asa "Be careful khaleefa". Doctor andal ta fad'a ba wasa akan fuskarta. Gyad'a mata kai kurum yayi yana k'ok'arin saita yanayin shi. Tsabar tashin hankalin da yake ciki doctor andal tana iya ganin yadda physique chest d'inshi yake up and down. "Wash your first and calm down your mind tafe nake da magana me muhimmanci". Ba musu yabi umarninta yaje ya dawo ya koma mazaunin shi ya bata dukka nutsuwarshi. "Akwai wani patient d'ina da yake zuwa check up 2 times a year kwana ki mun tab'a maganar da kai remember?". Khaleefa ya gyad'a mata kai. Tace, "good! Toh shine yayi accident ya samu karaya a hannu, an mishi aiki a k'asar shi cikin nasara har hannun yaci gaba da aiki normal, bayan lokaci mai tsayi Kuma yanzu ya dawo yana mishi ciwo, duk da ciwon ba wai ya mishi zafi bane amma hannun yana damun shi sosai, yanayin aikin shi yasa ba zai samu damar shigowa check up ba wannan karon ga kuma ciwo, Soo Ina ganin zanyi magana da doctor raazee Upper week kuje kaida Muhammad da kuyi mishi aiki har k'asar shi a d'aya daga orthopedic hospital da suke dashi zan baka details d'inshi idan komai ya kammala". Sake Gyad'a mata kai khaleefa yayi bayan gama sauraron duk jawabanta. Itama daga haka bata sake cewa komai ba ta futa a office d'in. Saleema kuwa koda ta futa a harabar asibitin ta zauna taci kukanta ta godewa Allah, ta dad'e tana sakawa da kwancewa kafun a k'arshe ta samu mafuta d'aya, no Amna ta lalubo cikin wayarta don tasan a hannunta kad'ai zata samu abinda take so tunda itace ta kawo mata wancen labarin da bata san dashi ba. (Wato ranar dole sai dole) Bugu uku Amna ta d'aga, shiru duk sukayi kafun Saleema ta nisa tace, "ki turon da address d'in gidan khaleefa". Shiru Amna tayi a nata b'angaren tana tunanin abinda zaije yazo idan taje gidan, ganin ba zata iya aiwatar da komai ita kad'ai ba sai tace mata tana zuwa bari ta duba taga. Tana katse kiran direct layin Ahmad ta kira duk da tasan yana office kuma bai cika d'aga waya ba a lokacin aikin shi. Tana shirin katsewa ya d'aga ya ce, "fad'i maganarki idan bata huce minti biyu ba Cox Ina tsakiyar aiki". "A'a ba doguwar magana bace Saleema ce ta buk'aci address d'in khaleefa kana ganin na bata". Da sauri Ahmad yace, "a'a maman shi tana gari batasan komai ba, kice mata zaki turo mata gobe ni kuma in na futa office zan kira ki sai muyi magana". Yana gama fad'a ya tsinke wayar. Haka kuwa akayi Amna ta fad'awa Saleema duk yadda sukayi da Ahmad. Ba don ta gamsu ba ta hak'ura zuwa goben sai don ba yadda zatayi. ***Da yamma lik'is ta shigo gidan yauma tana tafe a matuk'ar gajiye, ta samu auntie a parlon suna ta hirar su da yasmine da take mugun yinta, don tace matar tayi a rayuwa ga ado ga k'amshi da girki kamar Raihana. Suna ganinta duk suka fara mata maraba, ta zauna kusa da auntie tana mata barka da gida. Auntien sai tarairayar ta take yi kamar ta maida ta ciki, sai kace ita ta haifa ba mijin taba, kafun wani lokaci ta cika ta da tea da abincin data dafa da drinks masu sanyi. Cikin jin dad'i taci abincin suka ci gaba da hirar da sukeyi har ita data zo yanzu na taya su. Labarin k'asar Sudan da al'adun su take basu suna ta mamaki da al'ajabi. Bata bar gidan ba saida su Ahmad suka dawo suka huce tare bayan auntie ta wanko mata plask d'in abincin data kawo mata da safe, ta had'a da bata kyautar turarukan data had'o mata. Aikuwa taita godiya har Ahmad na tayata sai kace shi aka bawa turaren 😂. Khaleefa da yake zaune a parlon kam sharewa yayi kamar baisan badalin da ake ba, a tare dashi ga gajiya ga yunwa ga tashin hankali da rashin nutsuwar zuciya. Sama sama sukayi sallama da Ahmad ya tafi shi kuma ya tashi tsam ya shige d'akin shi. Daga auntie har raihana suka bishi da kallo, kafun auntien ta dubi raihana tace, "Raihana lallen k'afar ki da hannun ki ya futa ga makarantar nan ta sako ki a gaba". Murmushi mai kama da yak'e raihanan tayi har zatayi shiru sai kuma dai tace, "Ni bana tunanin ci gaba da yin lallen nan saboda khaleefa baya so". "Na sani tun yana yaro baya son lalle, kuma ba lalle kad'ai ba abubuwa da yawa ma baya son su amma a hankali ya sauko, shima lallen da sannu zai sauko ya mik'a wuya saboda haka cikin kwanakin nan kiyi k'ok'arin maida shi". Gyad'a mata kai tayi cikin karb'ar umarnin auntien. "Yanzu ki kai masa tea da kisr d'innan, ki had'a mishi ruwan wanka masu kyau". Da toh ta amsa cikin karb'ar umarnin auntien ta mik'e zata nufi kitchen. Har ta d'au hanya auntie ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, "Raihana". Ta amsa da, "Na'am" tare da waiwayowa, "ki rage jin kunyata don nima maman kice". Murmushi tayi tare da gyad'a kanta. Yana zaune a gefen bed ya had'a kanshi da gwiwa a lokacin data nemi izinin shiga d'akin, bai iya bud'e bakin shiba sai tashi da yayi da kanshi ya bud'e mata k'ofar, ganinta da tray saiya bata hanya ta shiga ya maida k'ofar ya rufe. A k'aramin table ta ajiye komai ta nufi hanyar bathroom d'inshi. Ta had'a mishi ruwan mai d'an zafi duk da batasan da irin wanda yake wanka ba. Ta futo ta same shi yana zaune gefen gadon ya sake had'a kanshi da gwiwar. A gefe d'aya ta tsaya tayi shiru tana tunanin abinda ya dame shi cikin kwana kin gaba d'aya har yasa baya iya gane kanshi. Kamar me tsoron wani abu tace, ruwan wankan ka zai iya hucewa fa. Kamar mai ciwon k'afa haka ya mik'e ya nufi cikin bathroom d'in. Ta sauke ajiyar zuciya ta kalli sashen data ajiye tray d'in nan, tasan yana matuk'ar jin yunwa kuma muddin bai samu tabbaci daga wanda tayi girkin ba tsakanin ita da auntie bazai ciba, k'aramar paper ta samu da biro ta mishi gajeren sak'o kamar haka (kisr! girkin da auntie tayi da hannunta don farin cikin ka) ta ajiye takardar inda zai gani ta fuce a d'akin. Khaleefa ya jima yana wanka kafun ya futo, duk da ruwan data had'a yaso mishi zafi da yawa amma saida yaji dad'i data nuna kulawa a gare shi, baisha wahala wajen ganin takardar ba, hakan yasa yana shiryawa ya d'auki abincin yayi saving kanshi ya fara ci. Yaji dad'in abincin sosai shiyasa yaci da yawa, tabbas ya tabbata girkin auntien shi don yasan wasu kayan amfanin da za'a had'a kisr d'in tazo dashi ne daga Nigeria. ***Da dare raihana ta shirya cikin kayan bacci pitch colour doguwar riga mai sakakken jiki da k'aramin hannu, bayan ta shafe jikinta da turaruka masu k'amshi ta d'ora hijab a saman kayan ta yiwa auntie sallama ta tafi sabon d'akin baccinta. Yau a kwance ta same shi rungume da pillow ya lula duniyar tunani, bata ce mishi komai ba ta zauna daga k'arshen gadon kamar yadda ta kanyi kafun ta kwanta bacci, kwana biyun nan da batayi magana da y'an gidan su ba duk sai take jin kewarsu na damunta, gashi wayarta tasan ta tashi a aiki, shi kuma baya cikin nutsuwar da zata rok'i ya bata aron wayarshi. Tun tana jingine da fuskar bed har bacci yaci k'arfin idonta ta kwanta sosai ta lula duniyar bacci. ***Washe gari raihana ta tashi da mugun ciwon kan nan da take yi cikin kwanakin da suka gabata, a haka dai ta daure tayi duk ayyukan gidan ba tare da nuna gazawa ba. Akayi sa'a yau har khaleefa sukayi breakfast kafun ya futa, sau biyu kenan daya tab'a cin girkinta tunda suke tare dashi a gidan. Kusan tare suka futa yau shiya huce asibitin su ita kuma tayi makaranta. *****Amna kamar yadda tayi alk'awari haka ta tura mata address d'in, sai dai na makarantar su raihana ta bata da hoton raihanan kamar yadda suka shawarta da Ahmad. Bata gane kan komai ba hakan yasa ta tambayi ba'asi, nan Amna ta k'arasa yi mata gundarin bayani har dai dai lokacin da raihana zata futo lecture yau. Duk da Saleema ba haka taso ba haka dai ta hak'ura, don taso ace address d'in gidan ne yadda zata iya zuwa kowanne lokaci, toh amma hakan ma ba laifi tunda ai a gidan ma gurinta zata je. Tun saura mintuna 20 su futo lecture Saleema take tsayuwar jira a kusa da k'ofar futa makarantar har suka futo, tafe take ita da wata yarinya y'ar asalin k'asar India suna hira akan darasin su na yau, sanye take da lafaya data zauna a jikinta kamar an zanata, tayi matuk'ar kyau. Har Saleema saida taso razana data mata kallon farko kafun ta matso kusa. Sai dai koda tazo kusa taci gaba da kallonta sai taga ba wata shahararriyar kyakkyawa bace har ta fara tunanin abinda khaleefa zaiyi da wannan yarinyar gata ba fara ba duk da ba zata shiga cikin bakake ba, gata ba za'a ce mata siririya ba bayan shi siririyar mace yake so kamarta, ta tashi ta lafto irin wannan kaya kamar a k'auyen Nigeria 😜. Duk wani abu da khaleefa yake so a tare da mace raihana bata dako d'aya amma wai a haka ya aureta?. Ita kuwa ba tare da tasan da wanzuwarta a gurin ba tayi sallama da yarinyar ajin sun tazo zata gifta ta kusa da ita, aikuwa Saleema ta wani fuzgo ta baya tana mata makaskancin kallo tun daga sama har k'asa. Da mamakin wannan fuska da inda ta santa ya kwanta mata tace, "wacece ke?". "Matar da mijin ki khaleefa zai aura". Saleema ta bata amsa kai tsaye. Hard'e hannu raihana tayi a k'irji tana kallon ikon Allah. Yanayin yadda take kallonta kad'ai ya sakawa Saleema shakkun tunkararta don idanunta babu alamun tsoro ko dar ga wani kwarjini da tayi mata. "Iya abinda kika tsayar dani ki fad'a mun kenan?". Raihana ta mata tambayar tana jifanta da wani kallon banzan. Yamutsa fuska tayi ta sake tattaro kwarin gwiwarta tace, "aini raina ajin ki nayi kuma nazo ne in tabbatar miki dama ki tattara kayan ki tass! ki fuce daga gidan khaleefa kafun zuwana". Sai a lokacin raihana tayi wani miskilin murmushi tace, "kin gama?". Ta fad'a tana k'ok'arin kewayeta ta huce, tsabar mamakinta da takaici don saleema rasa yadda zata yi da ita, duk wani rashin mutumci da buhu buhun wulak'anci data tattaro zata yiwa raihana kwarjinin ta ya tokare ta ta ko'ina, Sam abinda ta fad'a bashi ta shirya fad'a ba kawai diriricewar da tayi ne yasa maganganun suka futa yadda bakin ta ya furta ba yadda ta tsara ba. Ganin raihana ta d'auki hanya zata bar mata gurin sai tabi bayanta da hanzari ta dafa kafad'arta ta baya da k'ok'arin fuzgo ta kamar yadda tayi mata d'azu. Da wani irin sauri raihana ta janye hannun Saleema a jikinta tare da tsinka mata tagwayen maruka hagu da damanta, ta fara murza yatsunta uku a gaban fuskarta tace, "ya zamo second and last da k'azamin hannunki zai k'ara gangancin tab'a jikina, matsalar ki da khaleefa ne bada raihana ba.... Soo ta tsaya tsakanin ku can". Ta k'arasa fad'a cikin jaddada kashedinta kafun ta juya ta bar mata gurin. Saleema durk'ushewa tayi a gurin don tsabar shigar da marin ya mata k'afarta rawa take tama kasa tsayawa, wacece wannan yarinyar? Y'ar uban wace da har zata d'aga hannu ta zabga mata mari a public irin haka? Lallai kuwa saita sakata nadama a irin wannan gurin tayi alk'awari. Raihana tafiya take amma cikin tsananin b'acin rai da takaicin abinda Saleema ta mata, tunda take a rayuwarta in aka d'auke abu na k'uruciya bata tab'a rigima da wasu har ta kaiga anci kwalarta haka ba sai yau ata sanadiyyar mutumin da bata da wata alak'a kyakkyawa ta kusa kota nesa dashi ba. A inda ta saba hawa motar haya a duk lokacin da tazo makaranta zata koma gida ta tsaya, ajiyar zuciya ta dinga saukewa akai akai har tana mamakin kanta da k'arfin halin da tayi..... Sai a lokacin ta tuna inda tasan fuskar yarinyar, lallai hoton ta ta gani a fuskar wayar khaleefa, sannan bata raba d'ayan biyu itace yarinyar da yake matuk'ar Soo Saleema. "Ya Allah" ta fad'a tare da dafe kanta da hannunta. Ranar har ta dawo gida yanayinta a dame yake, duk da k'ok'arin data dinga yi wajen ganin ta saisaita kanta. Koda auntie taga sauyin yanayi kad'an a tare da ita bata tambayeta ba'asin komai ba saboda yau da gobe sai Allah, watarana mutum haka nan zai tashi yaji baya jin dad'in jikin shi. ****Amna ce kare da waya a harabar gaban d'akunan su bayan ta gama bawa Ahmad labarin komai daya faru a makarantar su raihana yau, bayan ta gama bashi labarin ta d'ora da cewa, "naji tsoro fa sosai wallahi don yadda naga yarinyar so silent na d'auka Saleema zata iya ci mata mutumci kan abinda bata jiba bata gani ba, sai gashi ta bakin yarinyar ta nuna mata zarrah". Daga d'aya b'angaren da mamaki sosai Ahmad yace, "Ni kuma marin da kika ce tayi ne yafi bani mamaki, in hakane raihana tayi fiye da abinda nake tsammani, nifa abinda yasa na yarda a bata address d'in raihana saboda nasan ba zata tab'a kula taba har tayi duk haukar ta tafi, kuma koba komai an d'auke mata hankali har zuwa lokacin da auntie zata bar Germany ba zatasan komai ba,,, amma dama Saleema ai tayi kuskure data fara d'ora hannunta jikin matar mutane,,,,, raihana tana da nutsuwa k'arshe fiye da yanda duk zanyi miki bayani sai dai dama da ganinta kinsan ba zata d'auki raini ba, sai dai amma fa marin nan zai b'allo ruwa mai fad'i.....". "Abinda nake son fad'a maka kenan yanzu, Saleema taci alwashin rama ninkin abinda tayi mata har ta fara had'a gang na wasu cikin k'awayenta za'a had'u aje makarantar su raihana cikin weekend idan ta shiga discussion aci mata mutumci". Shiru Ahmad yayi kafun can ya nisa yace, "ki kyale su ke dai kici gaba da bibiyar su har ki samu tabbacin ranar da suka shirya aiwatar da komai ki fad'a mun, Ni kuma nayi alk'awarin zaki ga yadda wasan zai juya kanta har yanzu bata san waye khaleefa ba shiyasa take wasa dashi.......". Amna tace, "toh Allah yasa a wannan karon ta gane gaskiya tabi". Ahmad yace, "ameen kam, zan shiga gida saina jiki". Amna tace, "alright a gaishe da madame". Yace, "zata ji" daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye waya. Ranar khaleefa bai samu shigowa gidan ba sai dare, a lokacin daga raihana har auntie suna parlon, duk da babu wanda yayi maganar jimawar shi cikin su a zahiri amma a zuciya duk abu d'aya suke tunani. A nutse ya murza key ya shigo, a kan raihana idanun shi suka fara sauka, tana zaune amma ta had'a kanta da gwiwar k'afarta idonta na kallon k'asa, sallamar shice ta sata d'ago kanta tare da gyara yafen jikinta. A gefe d'aya ya tsaya ya amsa sannu da zuwan da tayi mishi. Auntie kam tambayarshi ta fara, "lafiya kuwa yau ka jima baka dawo ba?". Lumshe idanun shi yayi ya dafa kanshi yana jin yadda yake tsananin sara mishi kafun ya bud'e idon yace, "da wuri na tashi akwai inda na biya ne?". Ya k'arasa fad'a idon shi akan raihana data k'araso gaban shi ta mik'a hannu zata karb'i jakar system d'inshi, bata jakar yayi ya bita da kallo har ta shige d'akin baccin shi sannan ya sauke b'oyayyen ajiyar zuciya. Auntie data gama kallon shi a sace tray na kayan shayi ta tura mishi gaban shi, ya kalli shayin ya girgiza kanshi ba tare daya zauna ba yace, "ban jin shan tea d'in nan yanzu". "Kuma shine dai dai dakai yadda ka dawo a gajiyen nan". Auntie ta fad'a tana kallon shi. "Okay toh bari na futo" ya fad'a tare da yin gaba, duk da yunwar da yake ji amma baya jin cin komai, yaji ma da tension d'in nan daya dame shi. Yana k'ok'arin shiga tana k'ok'arin futowa, sai kuwa karaf sukayi karo kanta ya daki k'irjin shi, da sauri duk sukayi baya kowa na k'ok'arin ba d'an uwan shi damar kaucewa. Ganin ta koma ciki sai ya k'arasa shiga ya maida k'ofar ya rufe ya tsare ta da ido yana kallonta. Ita kuwa abinda ta aikata ga masoyiyar shi d'azu ne ya shiga dawo mata, a ranta ta fara ayyana watak'ila ya samu labari shiyasa yake jifanta da kallon tuhuma da kashe di🙆‍♀️ A hankali ya fara nufarta tana ja baya har ta kai k'arshen bangon d'akin ta jingina tare da rintse idanunta tana jiran saukar mari irin ko ninkin wanda ta yiwa budurwar shi d'azu. _tab raihana ta kwakwaso da yawa🤭_ _kuyi hak'uri ban samu damar shigo muku weekend ba kamar yadda na fad'a, k'arshen makon ne ya same ni da abubuwa da yawa_ _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page fifty nine 5️⃣9️⃣ Yatsun hannun shi ya murza saitin fuskarta, ta bud'e idon da kyar a d'arare tana kallon shi, shi abun ma dariya ya bashi hakan yasa yayi murmushin gefen baki ya juya kurum ya shige bathroom. Ajiyar zuciya ta sauke tabi bayan shi da kallo har ya shige, da gaske ta tsorata da yanayin shi ta d'auka dukanta zaiyi. Kasa futa tayi a d'akin tana hasaso lokacin da yake bin bayanta, da lokacin da yazo daf k'amshin turaren shi ya dabaibayeta. Ta ko ta ina khaleefa ya cika cikakken namiji da mace zata so, toh amma meya had'a shi da wannan budurwar har ta bibiyeta da neman rigima??? Ko kuma ya b'oye mata gaskiyar maganar auren su yanzu taji labari shine tazo mata warning har makaranta?? Kai Anya kuwa??? Tunane tunanen da tai tayi kenan bata futa ba har saida taji alamun futowarshi. Ta kwasa da gudu gudu ta bar d'akin ba tare da ko waige ba. Lumshe idanun shi yayi bayan gama binta da kallo, murmushi na escaping kan lips d'inshi. Raihana tana futa auntie ta had'a tray na abinci tasa ta kai mishi, ba musu ta d'auka sai dai ta kasa shiga saboda tasan yanzu yana tsaka da sauya shiryawa ne, inda Allah ya taimaketa auntien ta shige bedroom d'inta, sai ta dawo parlon ta ajiye trayn har zuwa lokacin daya futo ya nufi harabar gidan rik'e da wayarshi, a lokacin ta faki ido ta shiga da trayn d'akin shi ta ajiye ta futo. Da dare khaleefa yana zaune ya tasa wayarshi a gaba yana kallon wani abu da batasan ko meye ba, ta jima da kwanciya amma bacci ya kasa zuwa mata sam sai tunane tunanen duniya da kewar ummienta, koda tana hostel bata tab'a d'aukar kwana ki biyu ba tare da taji muryar ummienta ba, amma sai gashi a yanzu da tafi buk'atar ji daga gare su hakan ya gaza samuwa. Tana kwance har khaleefa ya ajiye wayarshi tsakiyar su ya maida dim light. Saida ta kintaci dai dai lokacin da take zaton yayi bacci sannan ta tashi zaune da kyau ta jingina da fuskar gadon, kamar barauniya haka ta soma lalubar wayarshi har ta samu, juya baya tayi ta tsurawa pic d'inta idanu. Da gaske budurwar shice, toh ita meye had'in ta da ita zata bita har makaranta? Shiru tayi tana nazari kafun ta maida k'afarta cikin bargon ta juyo da nufin mayar mishi da wayarshi inda ta ganta. Cak! Ta tsaya ganin shi a zaune yana kallonta sai tama kasa ajiye wayar, haske ya k'ara cikin d'akin ya mik'a mata hannu, ba musu ta zura mishi cikin hannun shi ta sunkuyar da kanta cikin jin tsananin kunyarshi don zaiyi tunanin ko wani abun ne daban. Shiru ya biyo baya kafun khaleefa yayi magana cikin taushin murya, "d'azu munyi waya dasu ummie sunce basa samun layin ki in sun kira". Bata d'auka da ita yake ba saida ta d'ago suka had'a ido dashi, shiru tayi don batasan amsar da zata bashi ba, bayan shiya fasa wayar da kanshi. Shima abinda ya tuno kenan yasa ya share zancen. Sunci gaba da zama shiru kafun Raihana tayi magana, "dama Ina son tambayarka wani abu idan ba zaka damu ba". Sake jingina kanshi yayi jikin fuskar gadon yace, "fad'i tambayarki ina ji". Saida ta saci kallon shi sannan ta fara maganar da in bata yita ba zata iya hana ta runtsawa da kyau, don ta tsaya mata a k'ahon zuci haka kurum take son jin ba'asi, "amm me zai hana ka bani labarin soyayyar ka da saleema?". Zancen nata a bazata yazo mishi, ya kuma bashi mamaki had'e da d'aure mishi kai, saiya gyara zaman shi yace, "me yasa kike son sani?". "Kawai Ina son ji ne" ta bashi amsa tana kallon kai tsaye cikin kwayar idon shi. Shima ita yake kallo, lokaci d'aya yanayin shi ya k'ara sauyawa. Da irin kallon da yake mata ta fahimci lallai ba zai aikata abinda ta fad'a ba, don haka salin alin tayi kwanciyarta had'e da juya mishi baya. Ta b'angaren shi kuwa saida ya sake nisawa sannan ya fara magana, "Saleema itace mace ta farko data fara d'aukar hankalina har na fara sonta, saboda tazo cif cif da tatsuniyar karatun zuciyata irin wanda yakan faru a zuciyar kowanne matashi ko budurwa. Na had'u da Saleema a wani yammaci da bazan tab'a mantawa ba, sai dai na kasa tunkararta a lokacin saboda ban san me zance mata ba. Bayan wannan ban sake ganinta ba har na fara tunanin ko aljanace tazo take son bud'e mun ido, Allah da ikon shi sai gashi mun k'ara had'uwa a wani yammacin har ma ta nemi na taimaka mata k'ofar ta tak'i bud'ewa, tun daga nan gaisuwar mutumci ta fara tsakanin mu har muka fad'a soyayyar juna, munyi soyayyah tsantsa irin wadda ta zarce tunanin hankali, munyi abubuwan kuskure duk da sunan soyayyah ba tare da tunanin akwai wani abu da zai iya zama shamaki wa auren muba......". Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya sake duban raihana data gama tattara mishi duka hankalinta tana sauraron shi. Yaja gwauron numfashi kafun yaci gaba da bata labarin soyayyarshi, bai b'oye mata komai har love romance da sukayi da yadda lokaci d'aya ta juya mishi baya daga Jin tarihin rayuwarshi, dawowar shi gida Nigeria da musabbabin aurenta da yayi har kan dawowar su Germany da binciken y'an uwan mahaifin shi da yake yi a b'oye ba tare da auntie ta sani ba. "Na d'auka yadda na adana kaina nake tattalin rayuwata haka itama take yi a bayan idona, na d'auka bata tab'a sanin irin waccen soyayyar ba saita sanadiyyata,,,,,,, Ashe ita yaudara ce tab cikinta da jininta take bin ko'ina na jikinta, Ahmad shiya tunasar dani akan naje gareta na mata tuni kan soyayyahta, Amna k'awarta kuma tayi mun jagora zuwa gareta, tasa nayi mummunan ganin da har yanzu ya kasa b'acewa kwayar idona,,,, Amna tasa naga Saleema kan cinyar matured namiji saurayi yana kissing d'inta, hak'ik'a nayi nadamar saninta da tarayyar da nayi da ita a baya, na yanke hukuncin barinta har abada tun daga wannan rana.......". Sai ya kwantar da kanshi fuskar gadon ya d'ora duka hannun shi a kanshi, ya dad'e a haka kafun ya d'ago yaci gaba da cewa, "raihana Ina da matuk'ar kishi! Ina da kishi irin wanda ban yarda matar da zanyi rayuwar har abada da ita ba tazo mun da guntun tabon wani namiji ya tab'a rik'e hannunta ko jikinta bare har a kaiga irin abinda na gani sunayi ita da wani namiji.... Bazan tab'a shiring mace da jikin kowanne banza ba, dole matata ta zamo tawa ni kad'ai...... Shiyasa na hak'ura da Saleema har abada ko sunanta ma bana son tunawa wani lokacin Cox na tsane ta! Na tsane ta bana sonta kwata kwata......". Ya kai k'arshen zancen yana wulli da wayar shi ta daku da tiles, tsoro ya kama raihana shi kuma haka b'acin ranshi yake na jawo asara. Tana son mishi magana amma tana tsoron yanayin shi, gaba d'aya jikin shi ba inda baya rawa musamman k'irjin shi sai up and down yake, ga idon shi yayi ja....... Sun jima a haka kafun taga ya dire k'afafun shi ya had'e kanshi da gwiwa. Daga inda take zaune tana fara fad'in, "Allahumma la sahala illa ma ja'altahu sahala wa anta taja'alul hazini iza shi'ita sahala....". Abinda tayi ta maimaitawa kenan har shima ya d'auka yana taya ta suna fad'a tare. Tun kanshi yana k'asa sai gashi ya d'ago ya tsura mata ido yana kallon yadda bakinta yake futar da harrufan a tare da nashi. Saida ta tabbatar ya dawowa nutsuwarshi sannan tayi shiru, shima shirun yayi yana sauke ajiyar zuciya a jejjere.... Shiru ya wanzu a d'akin kafun raihana ta fara magana da cewa, "Ni kuma da naji tarihin soyayyarku sai naga kamar babu soyyayar juna a tare daku, da farko ita ta rabu da kai akan k'aramin abu, sannan tasa kana zargin matar data sadaukar da rayuwarta a kanku, muje ma a yadda ta fad'a d'in ku baku da cikakken asalin, shin ita da take sonka fisabilillah ya kamata aji haka daga gare ta? Na d'auka masoyi shine wanda zai b'oye sharrinka komai girman shi, ya yayata alkhairin ka komai k'ank'antar shi, Na biyu taya zata yankewa mahaifinta hukunci tun kafun ta kaika gare shi? Idan akace soyayyah toh anje k'arshe za'a iya fuskantar komai cikin yak'i da so, ni nan naga budurwar da ta dinga futo na futo da iyayenta ba tare da tasan ma kuskure take aikatawa ba saboda soyayyah ta rufe mata ido, amma ita one time ace ta tuna hakan sunan tana cikin soyyayah kuma? Toh wace irin soyayyah take maka data kasa makantar da ita duk wad'annan abubuwan kenan?". Har numfashi khaleefa yaji kamar ya d'auke yana kallonta cike da mamakinta. Murmushi tayi don tasan bazai fahimci komai da take fad'a ba yanzu, ita kuwa taci gaba da maganarta, "kaima bawai kana asalin sonta bane tunda dai har ka iya cewa ka rabu da ita don tayi maka k'aramin kuskure, Ina matan da suke wulak'anta kansu? Ina matan da suke irin soyayyar da kukayi da samari bila adadin? Ina matan da k'arewa ma suke rayuwa a gidan karuwai, duka ansan da wannan lambar amma cikakkun masoya gare su suke auren su, in hakane suce sun daina son su ba zasu aure suba tunda dai sunyi so so so so and so thing. Amma madadin haka sai suka gyara su suka inganta rayuwarsu ta hanyar aure. Abu na gaba Ina ganin abin duk da kasan baka so toh kar ka fara yiwa wani, ita d'in ba matar kaba amma ka dinga rayuwar da ranka yake so da ita, ba tare da tunanin abinda zaije yazo gaba ba, ashe kaga duk wanda ya aureta a k'a'ida kai da ita sai kun nemi yafiyarshi kun kuma sanar dashi abinda ya wakana tsakanin ku a bayan idon shi. Amma a shawarce abinda zaifi muku ku sasanta tsakanin ku kuyi aure, Ina ganin duk duniya babu masalahar da tafi muku wannan, sannan ni ban cika maka baki ba amma sai ka kusa kewaye duniya yanzu kafun ka samu irin matar daka fad'a, don rabin y'an matan wannan zamanin koma ince fiye da rabin su zaka same su da irin tabon da baka so, macen da ko hannunta wani namiji bai tab'a rik'ewa ba Ina ganin zaka wahalar da kanka ne kurum,,,, rayuwar da kukayi da Saleema ta kewaye ko'ina birni da karkara......". "Kina nufin harke duk nutsuwarki da kamun kanki?". Ya samu bakin shi da fad'a ba shiri. Murmushi tayi tace, "kar muzo maganata yanzu, don tsarin rayuwata da naku ba d'aya bane". Shiru yayi a zuciyarshi yana ci gaba da nazarin maganganun ta. Itama koda ta kwanta ta jima tana juya labarin soyayyar khaleefa da Saleema, dama sun d'auki tsarin da ba zai kaisu ko'ina ba, kuma ko aure sukayi ba zasu zauna lafiya ba sai sun had'a da hak'uri. Da irin wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita. @@@@@@@@@@ Kwanaki biyu a tsakani raihana tana lissafin rayuwar khaleefa, ta rasa ma ta inda zata iya kawo mishi gyara a al'amuran shi kamar yadda take so. Shi kuma ta nashi gurin maganganun Raihana yake ta juyawa cikin ranshi, meyasa a lokacin da yake bulayin neman masoyiya bai tab'a dogon tunani kan abinda zaije yazo ba? Meyasa kyawun fuskar Saleema ya rud'e shi har ya hana shi banbance tsakanin nutsuwa da wadataccen ilimin addini, meyasa bai tab'a k'iyasta adadin had'arin da wani kyawun fuskar yake dashi ba? Me yasa bai nemi mace irin raihana ba, ma'abociyar nutsuwa, kamala, kaifin kwakwalwa da wadataccen ilimin addinin daya danne na zamani har ya b'oye wayewarta, mai kiyaye dokokin ubangijinta da gujewa son zuciya da gudun fad'awa halaka?...... Astagfirullah wa'atubu ilaik ya Allah ka yafe mun kurakuraina! Kaji k'aina ka bani yarinyar da zata zamowa y'ay'ana uwa ta gari. Irin tunanikan da khaleefa yake yawan yi kenan a gida ko a office. ******Raihana kuwa cikin kwanakin ta samu lokaci ta maida lallenta, tare da yasmine sukayi don tana maseefar son lallen jikin Raihanan, ga duk yawonta a garin ta kasa samun inda ake henna mai kyau black or red one bare taje a mata. Duk da raihana a d'arare tayi lallen saboda khaleefa hakan bai hanata shiga kitchen ta had'a dinner ba, gashi yau suka dawo office da wuri tare da alamun yunwar da suke matuk'ar ji, koda ta gama ta shirya table ita ta kai musu har parlour shida Ahmad bayan ta b'oye hannayenta cikin gyale. Bai kawo komai cikin ranshi ba har suka cinye abincin shida Ahmad. Ranar ma har dare Yasmine bata tafi ba suna ta hirar su ita da auntie raihana na sauraron su, in anyi abun dariya tayi in na takaicine tayi har Ahmad ya gaji ya kira wayarta. Tare suka futa da raihana bayan duk sun yiwa auntie sallama. "sau d'aya kika tab'a zuwa gidan mu amma yasmine kullum tana tare dake a gidan ki". Ahmad ya fad'a cikin sigar zolaya. Murmushi tayi tace, "ai insha Allah nima zanzo bada jimawa ba, zan rako auntie ma kafun ta tafi". "Toh Allah yasa!". Mata da mijin suka fad'a kusan a tare, duk sai sukayi dariya banda khaleefa da yake tsaye gefe hard'e da hannuwan shi biyu a k'irji. Har waje raihana ta raka Yasmine sannan ta dawo, ta same shi yayi relax kan kujera, kitchen ta nufa zata had'a mishi sabon tea don sun shanye duka na gidan. "Raihana" ya kira sunanta... Bata amsa ba sai dawowa da tayi ta dafa jikin kujerar da yake zaune. Ya shak'i k'amshin turaren ta ya lumshe idon shi ya bud'e sannan ya jawo jakar dake gefen shi ya mik'a mata, ta karb'a tare da kewayowa ta zauna da kyau. Koda ta bud'e laptop ce mai kyau da waya da agogo da sauran complete. Koda ta d'ago ta kalle shi da neman k'arin bayani murmushi ya mata yace, "naki ne don jin dad'in karatun ki". Har k'asa ta durk'usa bakinta ya gaza rufuwa saboda farin ciki ta fara jero mishi godiya, d'aga mata hannu khaleefa yayi, saita tsaya tana kallon shi har yanzu bakinta a bud'e. "Kiyi mun addu'a Allah ya bani mace kamarki". Shiru tayi bayan ta maida kanta k'asa tana nazari kafun can ta nisa tace, "Allah yasa Saleema ta koma nagartacciyar macen da zakayi alfahari da ita a rayuwarka....". Kujerar da yake zaune a kai ya daka da k'arfi yace, "noo! Saleema ba zata tab'a zama kamarki ba,,, kawai kimun addu'a na samu kamar ki raihana". Kasa cewa komai tayi sai tunanin abinda take dashi da har zaiso matar da zai aura ta kasance kamarta? Sai take ganin maganarshi kamar gaisuwane da rok'on iri, duk da tasan khaleefa ba zai tab'a sonta ba..... "Addu'ar ba zata samu ba ko Raihana?". Ya fad'a da sigar ban tausayi Murmushi tayi ta d'auki jakar kyautar daya mata, "toh Allah ya baka wadda tafi ni,,,,, Ina sake godiya". Ta k'arasa fad'a tare da juyawa ta nufi d'akin gadonta, ta samu auntie har tayi bacci. Bata iya hak'uri ba saida ta duba cikin wayar, ga mamakinta sai taga an saita mata komai nata sim card d'inta kuwa tuni dama ya dad'e da tsufa a ciki. Ranar data kama weekend khaleefa dole zasu shiga office saboda doctor andal da ta buk'aci ganin su su uku, itama raihana tana da abinda zatayi cikin makaranta a ranar hakan yasa data shirya futa ta jira shi suka huce tare bayan sun yiwa auntie sallama. Dressing d'inta na yau ya matuk'ar ba khaleefa mamaki don baiyi kama da irin wanda ta saba futa dashi ba, doguwar riga ce jikinta ba laifi kuma ta futar da well shape structure ta, saita kawo madaidaicin gyale tayi rolling kanta dashi. Da Ahmad suka had'u a gaban gidan zai shigo gurin khaleefan, hakan yasa ta basu guri bayan ta gaishe shi. "Yea! Man ba dai office ba?". Ahmad ya tambayeshi da sigar mamaki. "Eh amma bazan huce 1hour ba". "Tare zaku dawo da madame kenan?". Ahmad ya sake tambayarshi. "Anya kuwa!" Ya fad'a yana duban gurin da take tsaye. "Ni kuma sai nake ganin ka biya ta makarantar su bisa b'oyayyen dalilin da nake son ka gani da idon ka idan ka futo office". Shiru khaleefa yayi yana kallon shi, a zuciyarshi yana tunanin akwai wata a k'asa kenan don tabbas hakanan Ahmad ba zaice mishi yaje makarantar su raihanan ba, koma dai meye Allah yasa ya zamo alkhairy ba irin wancen bak'in ganin da yayi ba. "Alright zanyi k'ok'ari na je". Ya fad'a tare da sake bawa Ahmad hannu suka gaisa. Hakanan khaleefa ya samu kanshi da rakata har makarantar, ya bata kud'in da batasan me zatayi dasu ba ya mata sallama ya huce office. A gurin meeting Doctor andal take sanar dasu soke tafiyar su Nigeria da doctor raazee yayi saboda k'in aminta da hukumar asibiti tayi, sakamakon hakan patient zai shigo Germany k'arshen watan amma su zasu jagoranci aikin Kamar yadda ta fad'a da farko. Duk sunyi na'am don an sauk'ak'a musu aikin su gaba d'aya. Bayan sun tashi meeting khaleefa bayan doctor andal yabi, har ta mishi nisa ya k'ara da sassarfa yana mata sallama. Ta amsa tare da tsayawa, "khaleefa is there any problem?". Ta tambayeshi . Sunkuyar da kanshi k'asa yayi yace, "noop kawai Ina son sanin real name na mutumin da kika gama maganarshi yanzu". "Wayyoh Allah!" Ta fad'a had'e da zare farin tabaran idonta tana sake duban khaleefa da kyau a zuciyarta tana sake maimaita sunayen nasu duka a tare. "Sorry ba kowanne patient nake rik'e sunan shiba, amma zan duba maka bayanan shi kafun zuwan shi surgery". "Yauwa nagode doctor". Ya fad'a tare da yin gaba. Har yayi nisa doctor andal tana tsaye a gurin, tafiyarshi tabi da kallo wani abu daya tab'a faruwa shekaru talatin da d'oriya na dawo mata daki daki cikin kanta. ****Khaleefa kuwa yana futa sak'o na shigowa wayarshi, Koda ya duba Ahmad ne yake mishi tuni kan zuwa makarantar su raihana. Shi har ya manta ma ba don ya tuna mishi ba. Raihana ta futo daga libry rungume da littafanta hannunta rik'e da k'aramar hand bag. Tafe suke ita da matashiyar yarinyar nan da take son karatu kamar ita suna d'an hirarrakin su. Ko kad'an bata lura da Saleema data tattaro k'awayenta kusan biyar har ita ta shida ba, saida tana cikin tafiyarta taga ansha gabanta. Cak ta tsaya tana binsu da kallo d'aya bayan d'aya, kafun tayi wani yink'uri sun kewayeta sun tunkud'e k'awarta meerah da take tambayar me raihanan ta musu. Wani banzan kallo Saleema ta mata a ranta tana tunanin abinda zatayi da zai k'ololuwar b'ata mata rai taji ta tsani kanta da sake nunawa mutane fuskarta. Ga gurin ya fara tara mutane y'an kallo don babu wanda ya tambayesu ba'asi. "Yau gaki a hannuna, zanga ko zaki iya kwatar kanki boss?". Murmushi raihana tayi duk da y'an matan sun kewayeta amma bata ji tsoron suba ko d'ar, k'arshe dai tasan suce zasu daketa. Ganin ba zata kula taba sai ta janye madaidaicin gyalen abayar jikinta, take kuwa tulin gashinta data parking a k'eyarta ya futo waje mutane suna kallo. Raihana saida ta rintse idanunta sannan tace, "kuyi mun duk abinda zaku yimun amma kada ku kuskura kuce zaku tsiraita ni". Dariya sosai Saleema tayi, abinda ta tuna kenan, don taga yadda ta rufe jikinta ruf waccen ranar, da yadda ta dinga gyara yafen lafayarta su suka tabbatar mata jikintane bata so a gani, shiyasa ta yanke shawarar bud'e ta tsirara ga wad'an nan samarin da suke kewaye da gurin, tasan shine kad'ai zata ji sanyi a ranta, taji ta huce takaicin abinda sukayi mata ita da khaleefa. "Guys ku yage mun rigar jikinta ta ganta tsirara a wannan gurin. Aikuwa cikin amsar umarninta suka rirrik'e hannun raihana wata taja zif d'in gaban rigar tayi k'asa dashi........🙆‍♀️😨 Ita kuwa raihana cikin saddakarwa ta rintse idanunta tana girgiza musu kanta hawayen da suka cika idonta suka soma sauka bisa kuncinta. _haba madame khaleefa kin manta in aka ga mace y'ar uwarki tsirara kamar ke aka gani🤔_ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty 6️⃣0️⃣ K'ok'arin fizge jikinta take amma ta kasa don sosai suke gwada mata k'arfi, an dire zip d'inta k'asa amma daga ta ciki akwai doguwar riga armless data fara sakawa kafun ta d'ora abaya a samanta, wannan riga ita ta ceceta ta suturta ta ba'a ganta duka a waje ba. Ganin haka sai bak'in ciki ya sake kama Saleema tace, "ku cire ta saman had'e da ta cikin ma, soo nake yau na ganta tsirara....". Ta k'arasa fad'a tana murmushi da kallon yadda raihana tayi la'asar kanta a k'asa sai ruwan hawaye daya k'i tsayawa a idonta. Raihana yau kam tasan babu mai ceton ta sai Allah, tana ji tana gani suka fara jan rigarta baya zasu fizgeta. Ta sake rintse ido da sauri tana jujjuya kanta alamun suji tausayin ta. Cak! Numfashinta ya nemi tsayawa jin hannu ata gaban rigarta an rik'e gaban rigar gam rik'o bana wasa ba,,,,,, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da hancinta ya shak'o daddad'an k'amshin turaren shi, bata gama tantance komai ba ta tsinci kanta tsakiyar k'irjin shi hannun shi saman gashin kanta. Wani mugun fusataccen kallo ya fara jifan Saleema da tawagarta dashi, take kuwa duk suka fara k'ok'arin barin gurin cikin tsiro, ita kuwa mutuwar tsaye tayi ganin khaleefa rungume da wata mace a gabanta ko kunyarta baya ji saboda tsabar yaudara.... Bata dawo daga tunanin taba ta tsinkayi muryarshi cikin kunnuwanta. "hak'ik'a nayi nadamar sanin ki a rayuwata Saleema, kuma ban tab'a sanin ke mahaukaciya ce ballagaza ba sai yau, idan baki sani ba Ina so ki sani.... adadin yawan haukan da kike yi adadin nisan da Abdallah yake wa rayuwarki...... Shin kun d'auka itama irin kuce data saba nunawa kowanne banza da wofi jikinta? Toh ita jikinta mai daraja ne daba kowa ke gani ba sai halaliyar shi.... Ku bani gyalenta". Ya kai k'arshen maganar yana sake binsu da kallo d'aya bayan d'aya. Wata a cikin suce ta iya k'arfin halin d'auko vail d'in da yake yashe a gefe ta kawo mishi. Ya fizge tare da saurin rufa mata gashin kanta dashi, da kanshi ya durk'usa ya maida zip d'in rigar da suka zuge mata, ya d'aukar mata littafinta da jakarta ya kamo hannunta ya d'auki hanyar barin gurin. Tsabar bak'in ciki yasa Saleema yin suman wucin gadi, babu abinda yafi tsaya mata kamar rungume yarinyar da khaleefa yayi a k'irjin shi da maganar daya fad'a wai sun saba rabawa maza jikin su a titi..... Tabbas wannan abu biyu ya tsaya mata har yasa ta kasa hak'uri saida ta biyo bayan su tayi magana da k'arfi yadda zai iya jiyo ta, "tabbas ba kayi k'arya ba muna rabawa maza jikin mu, amma maza ire iren ka ba wanda suka san ciwon kansu ba...... Sannan koda kake kallonta a haka ba tsira kayi ba don babu macen da zaka samu bata rabawa maza jikinta ba kamar yadda muka rayu da kai haka itama ta rayu da wani.....". Duk da sunji abinda ta fad'a amma cikin su babu wanda ya nuna yaji ta bare har su juyo. Suna futa suka tarar da motar Ahmad tana jiran su. Gidan baya suka shiga su duka shi kuma yaja motar ya fara barin gurin. Har suka k'arasa gida raihana kuka takeyi yayinda khaleefa ya kwantar da kanshi a seat d'inshi yana sauraron kukan nata kalaman Saleema na amsa kuwwa cikin kunnen shi, ko a shifcin gizo bai tab'a tunanin Saleema zatayi duk wad'annan abubuwan ba, ko yanzu ba don ya ganta da idon shiba in fad'a mishi akayi saiya iya k'aryatawa..... "Sai dai kiyi hak'uri raihana, Allah ma ya taimake ki man yazo akan lokaci". Bata iya furta komai a gare shiba, sai sautin kukanta daya k'aru. Ganin haka sai taba khaleefa haushi ya futo a motar a zafafe cikin fad'a yace, "ai saiki futo mu tafi ko tunda hak'urin ne baza ki iya ba". Babu musu ta zuro k'afarta ta futo, khaleefa ya bita da kallo ganin ta d'auki hanyar tafiya gida tana ci gaba da kukan. Ahmad ya dafa kafad'ar shi yana mishi magana amma sam baya fuskantar me yake cewa, burin shi d'aya kada raihana ta shiga gidan a yanayin da take. Ganin da gaske so take ta tona mishi asiri sai ya zame hannun Ahmad yabi bayanta da sauri. Tana gab da k'ofar shiga gidan ya rik'o hannunta tare da jawo ta ta baya har saida gefen jikin su ya had'u, electric shock yabi ta jinin jikinsu ya isarwa da kwakwalwar su sak'o cikin seconds, ture hannun shi take son yi amma ya hana mata damar haka saima hannun shi daya kewaya ya rik'e k'afad'un ta duka biyu ya fara mata magana da taushin murya me kama da rad'a kusa da kunnenta, "kiyi hak'uri mana raihana..... Duk wanda kika ji ance yayi hak'uri an cuce shi, sannan duka laifi nane tunda ni na jawo miki komai amma don Allah ina mai neman afuwarki....". Madadin tayi shiru saima ta sake rushewa da wani kukan, lamarin daya sake tsinkewa khaleefa zuciya hankalin ya sake k'ololuwa wajen tashi, baisan kuma me zaiyi mata tayi shiru ba indai har bata hak'uri da fatar baki bazai wadatar ba. Sunyi shiru tsawon lokaci a gurin kafun khaleefa ya juyo da ita suna fuskantar juna, zuba mata narkakkun kwayar idon shi yayi yana kallon yadda ta rufe ido amma sala salar hawaye na sauka bisa kuncinta, tafin hannun shi yasa yana share mata hawayen but still hawayen nata yak'i tsayawa..... Duk wani abu da yasan in yayi zata sakko ta hak'ura ranar khaleefa yayi amma ta kasa daina kukan, yanzu babu sautin kukan ma sai hawaye kurum da ajiyar zuciya da take saukewa a jejjere. A matuk'ar fusace da al'amarin nata wannan karon ya fizgi hannunta har k'ofar gidan Ahmad, a waya ya kira shi yasa ya kawo mishi mukullin motar shi. Yana futowa bai amsa mishi magana ko guda d'aya ba ya karb'i key d'in ya huce da ita ya bud'e front seat ya jefa ta shima ya shiga mazaunin driver ya fizgi motar a 360. Ahmad da yake tsaye ya kama hab'a tare da bin bayan su da kallo a zuciyarshi yana fad'in, "aifa yau aiki ya samu Man......... Tafiya yake ba tare da yasan inda yake tunkara ba har saida ya yiwa anguwarsu nisa da yawa sannan yayi parking motar gefen titi ya had'e kanshi da steery. Raihana takure jikinta tayi tana sauƙe ajiyar zuciya still idonta Yana futar da ruwan hawaye, kota k'uduri niyyar hak'ura ta daina kukan da zarar ta tuno tozarcin da Saleema tayi mata a bainar nass sai taji ranta ya sake k'ololuwa gurin b'aci, da aga jikinta da take tattali da b'oyewa ta gwammace su taru su mata d'an banzan dukan da zata kasa tashi,,,, sai ta sake yin wata sheshshekar da tasa khaleefa dukan steering da duka hannuwan shi kafun ya had'a hannuwan waje guda yana kallonta bakin shi har rawa yake gurin fad'in, "toh kawai ma ki cinye ni indai hakan zaisa kiji sanyi a ranki har kiji kin hak'ura......". Tsit tayi ba tare data shirya aikata hakan ba, cikin matuk'ar tsorata da yanayin nashi ta zuba mishi idanunta tana kallon shi tana zazzare nata idon. Gaba d'aya yanayin shi ya sauya daga asalin khaleefa zuwa wani fusatacce tamkar mayunwacin zaki..... Idonshi yayi jaa haka fuskar nan tamkar bai tab'a murmushi ba. Ganin yadda ta dawo kuma sai duk ta bashi tausayi,,,, yasan tabbas abinda Saleema ta mata shine k'arshen cin mutumci a gurin dukkan wata d'iya mace da tasan mutumcin kanta, musamman ita da kullum cikin saka zurma zurman mayafai da hijabai tana b'oye jiki,,,,, toh amma tunda har abun nan ya faru bisa tsautsayi ai sai ta d'auki hak'uri ko? Yawan kuka maganin me zaiyi inba ya k'ara mata damuwa da tashin hankali ba....... *After 15 minute* Ruwa ya d'auka a ciki ya Bud'e murfin motar ya futo ya kewaya ya bud'e k'ofar side d'inta, ta gane abinda yake nufi don haka ba musu ta futo. Ruwan hannun shi ya bata ta karb'a tana son jin k'arin bayani. "Kisha ki wanke fuskarki". Nan ma batayi musu wajen aiwatar da duk abinda ya umarceta ba. A hankali ta dinga jin wata nutsuwa na kwaranya ruhinta tana bata sabon kwarin gwiwa. Ranar basu koma gida ba saida ya tabbatar ta dawo dai dai yadda auntie ba zata fahimci komai a muryarta ko yanayin taba, abinci ma tare suka ci a gidan cin abincin shi daya zamewa babban customer. Yayi mata shopping na kayan mata masu kyau da set na kayan shafa masu gyara jiki da mayukan gyaran gashi ganin gashinta d'azu yaji a ranshi tana buk'atar su. Ita kam auntie ta zab'a ma irin abinda tasan zata so na daga kayan mata da amfanin yau da kullum. Khaleefa dai banda kayan amfanin gida bai d'auki komai wa karan kanshi ba. Saida ya tsaya a k'ofar gidan Ahmad yayi parking motar ya kira shi a waya ya bashi key suka fara tattaki don su k'arasa nasu gidan. Raihana tana daga bayan shi yasa key ya bud'e gidan suka shiga da sallama hannun shi rik'e da siyayyarta, ita kuma rik'e data auntie. A lokacin da suka shiga auntie bata parlon amma jin shigowarsu yasa ta futo daga d'akin baccin raihana. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta musu sannu da dawowa. Suka amsata kusan a tare. Sun zauna ita kuma ta shiga kitchen ta kawo musu ruwa da shayi. Ta cikawa kowa k'aramin glass cup da tea ta basu, babu wanda yayi magana cikin su suka amsa kawai suka shanye. "Hankalina har ya tashi da naji shirun yayi yawa ashe kuna tare?". Auntie ta fad'a. Kafun raihana tayi magana khaleefa ya karb'e zancen da fad'in, "eh ta makarantar su naje muka d'an zagaya taga gari..... Kumaaa muka yi siyayyah". Yakai k'arshen zancen kamar mara gaskiya yana kallon inda raihana take zaune, sam yi tayi Kamar bata ji shi bama tana k'ok'arin mik'awa auntie kwalin siyayyar da suka mata. Ta karb'a tana tambayar "hadda ni! Toh ina godiya Allah ya kawo zuri'a d'ayyiba". K'asa k'asa khaleefa yace, "ameen" yana ma raihana kallon kasan ido, itama kallon shi tayi sai kuwa karaf suka had'a ido, da sauri ta d'auke kanta tare da mik'ewa ta shige d'akinta da siyayyar ta. Shima khaleefa mik'ewar yayi sai dai auntie ta hana shi d'arawa ko'ina saboda tace tana son magana dashi. Bayan ya tattara duk hankalin shi a kanta ta kira sunan shi ba wasa tattare da muryarta ko yanayinta, a duk lokacin da auntie tayi magana da seriousness toh lallai ba maganar wasa zatayi da mutum ba, hakan yasa ya sake shiga taotayin shi fiye da a farkon maganarta. "Nan da kwanaki uku zan tafi sai dai ba gida zan koma ba zan huce saudiyyah ne umrah saboda na rok'i Allah sauk'i da sassauci cikin al'amuran rayuwata da suka fara d'aukar mun zafi cikin kwanakin nan..... Game da zamantakewar ku da raihana kuma ina sane da komai, da farko ka aureta don ta zamo maka tsanin da zaka taka ka tsallake zuwa ga samun cikar muradin ka, babu laifi idan kun shirya wani abu kaida ita wanda Allah ne kad'ai ya sani, sai dai Ina son ka sani aure ba'a shirya shi dako wacce manufa inba ta yad'a sunnar ma'aiki ba, watak'ila zuwa yanzu ka d'ago wani abu cikin maganata ko?". Girgiza mata kai yayi cox da gaske bai fahimci komai ba. "kwanakin baya ka nuna mun hoton wata yarinya da sunan itace kake so ka aura shin meye gaskiyar magana a kanta?". Shiru khaleefa yayi yana nazari..... A duniya yana tsoron irin wannan titsiyen na mahaifiyar su, don a irin wannan zaman take kama mutum da laifi ba tare daya farga ba. "Wato har yanzu in ana magana dakai sai an maimaita maka zance sai bibiyu uku uku kake iya bada amsa!". Auntie ta sake fad'a tana kallon shi. Numfashi yaja mai tsayi kafun yace, "wannan maganar ta huce a gurina tun lokacin dana kai miki maganar auren raihana". "Kenan ka yiwa magabatan ita waccen yarinyar bayani? Ko kuma ka kyalesu suyi ta kallon ka suna ganin ka yaudare musu yarinya". "A'a ai ban kaiga ganin magabatan ta bama, sannan zuwa yanzu itama tasan na rabu da ita.....". Khaleefa ya fad'a da saka ran ya kawo k'arshen tambayoyin nata gaba d'aya. Itama tsura mishi ido tayi, tasan inba ita d'in ba ba uban daya isa ya zaunar dashi yana mishi irin wannan titsiyen. Saboda haka sai tayi wani killer smile tace, "toh Masha Allah! Sai dai ina da wani sharad'i da zan gindayawa auren ku kaida raihana kafun tafiyata zan fad'a maka.....Amma yanzu ina fatan kana sane da tafiyata tare da raihana ko?". Gyad'a mata kai yayi bayan ya kauda komai da yaji daga ranshi. "Good zaka iya tafiyarka". Da haka suka kawo k'arshen hirar ya tashi a gurin salin alin ya shige d'akin shi na gado ya rufo k'ofar. Shiru yayi yana nazarin maganganun da sukayi da raihana akan Saleema daren ranar, duk abinda ta fad'a gaskiyane tunda ita ta riga ta mishi nisa kuma bawai dama sun shirya zama na har abada tare da juna ba.... Amma a shawarar raihana gwara ya shawo kan Saleema su daidaita su maida soyayyar su ko don ya kawo gyara wa rayuwarta, shi kuma hakan ne bazai iya ba, da ace bai ganta da kanshi ita da wani a wancen lokacin ba da sai ya iya karb'arta bayan yaji labari, amma yanzu koya aureta bazai iya sake had'a jikin shi da ita ba kyankyamin tama yake ji, wanda yayi a baya ma bisa kuskurene da rufewar ido cikin soyayyah, kuma da ace Saleema ta kama kanta ta dakatar dashi tun a farkon fara tafiyar kafun suyi nisa da basu je inda suka jeba...... Koda khaleefa yaje dai dai nan a tunanin shi saiya dunk'ule hannu ya kaiwa bango naushi zuciyarshi tana matuk'ar yi mishi rad'ad'i da k'una had'e da zallar nadama. Raihana ma ta b'angarenta irin tunanin da takeyi kenan,,,,, Sam bata fatan wani abu mai kama da k'addara yazo ya had'e ta da khaleefa ta zama matarshi ta har abada,,,,,, ba zata iya ba sam ba zata iya had'a jikinta da wanda ya kasa killace kanshi ga mata marassa kamun kai ire iren saleema ba. Tana da matuk'ar hak'uri amma tana da mugun kishi musamman ta b'angaren y'an mata marassa kamun kai,,,,,shiyasa Ayman yake burgeta a rayuwa, ada tana kallon tsarin rayuwarsu iri d'aya ne da khaleefa, sai dai a yanzun ta fahimci yayi ma khaleefa fintinkau a nutsuwa hankali da kame kai daga aikata kowanne irin mummunan aiki..... Ba k'aramin asara zatayi ba inta yadda ta rasa Ayman........asara irin wanda ba zata tab'a maye gurbinta bama kuwa...... _not edited_ _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty one 6️⃣1️⃣ Daga khaleefa har raihana kowa d'auke wuta yayi, haka suka ci gaba da zama sai kallo da ido, yayinda ako wacce rana suke samun kusanci da juna. Ana gobe Auntie zata tafi suka futa su duka gidan khaleefa ya jibgo mata uwar siyayyah tamkar bada kud'i ya biya ba, jaka guda ya had'awa twin bro d'inshi ta abin duk da yasan yana so, duk da Ayman d'in fushi yake dasu a cewarshi sun rik'e mishi auntien shi,,,, baya kiran no kowa a cikin su. Daren ranar da zata tafi ta damk'awa raihana wani madaidaicin diary data rubuta shi a d'an zaman da tayi dasu a k'asar Germany...... Koda raihana ta kalleta da neman k'arin bayani murmushi tayi tace, "wannan kundin tarihin rayuwata da k'addara tane, raihana ban tab'a yarda wani yaji sirrina ba amma ke na amince dake bisa sharad'i......". Raihana shiru tayi tana sauraronta bugun zuciyarta na k'aruwa. "Na k'are gaba d'aya rayuwata kan y'ay'ana y'an biyu na,,,,,, Alhamdulillah cikin su babu wanda bana so ko nafi so sai dai wanda zuciyata tafi karkata gare shi,, wanda nafi tausayin shi wato mijin ki khaleefa, a zahiri mutane da yawa suna ganin kamar Ayman yafi sona akan shi wanda sam ba haka bane,,,, Ayman yafi nuna kulawarshi a fili amma khaleefa yakan ajiye komai a ranshi, a lokacin da suke under 15 going to 16 year's na tab'a kwanciya wani ciwo a gidan iya, kullum Ayman yana zaune a gefena baya iya matsawa ko'ina, yayinda khaleefa ya sake nisantata sai dai shima ya kwanta jinyar kanshi, yayi ciwo mai tsanani kamar ba zai tashi ba abinda ya rabawa Ayman hankali gida biyu ya rasa wanda zaiyi jinya a tsakanin mu. Bayan naji sauk'i khaleefa ma yaji sauk'i, sai iya take tambayarshi wata rana cewa ya akayi shida ba kullum yake wuni a gurina ba amma ya kwanta jinya har ya kusa mutuwa? A lokacin murmushi ya mata kamar ba zai bata amsa ba sai kuma yace, saboda naji ciwonta ata jinin jikina... Naji tsoro kada wani mummunar abu ya sameta, da ace auntie ta mutu a wannan lokacin la shakka da nine na biyu dazan bi bayanta. Tun daga wannan ranar na dinga auna komai da yake nufi, tabbas yana da matuk'ar k'awazuci fiye da zato sai dai yana da dakakkiyar zuciyar da take iya d'aukar komai har ya iya b'oye shi a ciki, ba komai khaleefa yake yiwa kuka ba, daga tashin shi zuwa yanzu saina k'irga miki adadin lokacin da naga hawayen shi". Sai taja dogon numfashi sannan taci gaba, "raihana abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwar khaleefa a k'asar jamus, wanda a baya suka sa ya fara juyawa zuwa wani mutum mara son hayaniya, mutane da fassara kowa a yadda yaga dama,,,,,, sai dai zaman ki dashi yasa naga sauyi mai yawa a tare dashi, so nake kiyi iya k'ok'arin ki wajen ganin kin k'arasa aikin da kika fara,,,,,, so nake kimun wata sadaukarwa ki rayu da khaleefa domin yafi buk'atar ki fiye da Ayman...... Ta hakane kad'ai zai samu nutsuwar zuciya irin wadda ya rasa a silar fad'awa soyayyar wannan yarinyar......". Da mugun sauri raihana ta kalli auntien tana tambayar kanta a zuciyarta shin dama auntie tasan da maganar su da Ayman ne ko kuwa Ayman d'in ne ya fad'a mata da kanshi? Murmushi tayi ta sake damk'a mata diaryn cikin hannunta tace, "kada ki damu kanki da tunanin yadda akayi naji sirrin ku keda Ayman,,, sai dai wannan sak'on dana baki kiyi iya yinki ki tabbatar khaleefa baisan abinda yake ciki ba". Shiru tayi ta sake tafiya nazari tabbas suna tsaka da hira ita da Ayman a waccen ranar sunji motsin mutum ata jikin k'ofa daga baya kuma auntie ta shigo, sannan kallon da tayi musu a ranar ya tabbatar mata taji komai sai dai ba tayi tunanin haka ba sai yanzu. Da haka sukayi sallama raihana tayi shirin barci ta wuce d'akin khaleefa bayan ta yiwa diaryn kwakkyawan b'oyo cikin ma'ajiyar kayanta. Washe gari suka tayata ta shirya kaya sun futo su rakata airport suka had'u dasu Ahmad sun futo suma da nasu sinkin tsarabar, sai suka rankaya su duka zuwa filin tashi da saukar jiragen...... Sai a lokacin taba khaleefa k'aramar takarda tace kada ya duba sai k'arshen watan da ake ciki. Tafe suke su hud'u, shi yana gaba sanye da farar shadda sol riga da wando da malum malum ya rufe fuskarshi da facemask, mutum uku na take mishi baya sanye da suit black. Auntie ta taho tare da raihana itama fuskarta rufe da rabin gyalenta, suna tafe tana jaddadawa raihana kada tayi wasa da duk wani sirri data bata, Shi kuma mutumin yana magana dana bayan shi. Sam hankalin su baya kan hanya shiyasa basu ankara da juna ba saida sukayi karo wayar hannun shi ta fad'i, da sauri auntie ta kauce raihana kuma ta durk'usa da nufin d'auko mishi wayarshi, har ta kai hannu saita kasa d'auka saboda wani hoto data gani kan fuskar wayar,,,,,, inba gizo idanunta suke mata ba kamar tasan ta cikin hoton. Ganin yadda tayi sai escort d'inshi suka ce mata, "excuse me madame". Ja baya tayi suka d'auki wayar suka ba mutumin suna sake bashi hak'uri, "sorry boss". Da hannu ya amsa su ya huce gaba suka mara mishi baya,,,,, auntie da take tsaye a gefe tabi bayan shi da kallo gabanta yana tsananta fad'uwa. A gurin ta dakatar dasu suka k'arasa sallama. Kuka sosai Yasmine da raihana suka sanya a lokacin da take rungume dasu. Bayan ta gama saka musu albarka da fatan alkhairy juyawa tayi ta fara tafiya.... Duk suka bita da kallo suna d'agawa bayanta hannu har ta b'acewa idaniyar su. Juyawa sukayi Ahmad rik'e da yasmine yayinda raihana da khaleefa suke tafe cikin sanyin jiki. Har suka k'arasa gida babu wanda yace ma d'an uwan shi kanzil kowa da abinda yake tunani cikin zuciyarshi, lokaci bayan lokaci kuma raihana tana share hawaye. Tana zaune a parlonta shiru don gidan yayi mata ba dad'i, gani take kamar zata ga auntie ta kawo mata tea, ko ta futo da trayn abincinta mai dad'i tana mata barka da zuwa. Sai kawai ta fara kuka, dai dai lokacin da khaleefa ya rabu da Ahmad ya shigo gidan, jikin kujerar da take zaune ya k'araso yasa hannu biyu ya dafa kujerar cikin taushin murya yace, "kiyi hak'uri". Juyowa tayi gaba d'aya tana kallon shi da murya me laushi tace, "I'm missing her....". K'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya sauke yace, "meee tooo". Yinin ranar haka suka k'arasa shi sukuku kamar kajin da kwai ya fashewa a ciki. Da dare bayan sunci abinci ta gyara gurin d'akinta tayi shigewarta ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta. Dama khaleefa bai saka ran ganinta a d'akin shiba, koba komai yau shima zaiyi bacci cikin nutsuwa yayi birgima a gadon shi yayi juyi irin wanda ya jima baiyi ba. ***Saleema tana can cikin damuwa da tashin hankalin ramuwar gayyar da khaleefa zaiyi mata donta tabbatar ba kyaleta zaiyi ba yadda taga ranshin nan ya b'aci, ga tawagarta tun a waccen ranar suka kwaye mata baya, a cewarsu tasan yarinyar tana da wanda zai tsaya mata ta yaudare su tace bata da gata bata da kowa saida suka je suka ga ashe tana da aure, kuma mijinta yana da dukkan dama da ikon d'aukar mataki a hukumance tunda aiki yake wa k'asar, yanzu su in taja yakai report a makarantar su ya zasuyi kenan..... Duk yadda taso fahimtar dasu wani abu kin sauraronta sukayi, suka dinga aman rashin mutumci basu tafi ba saida suka mata tatas suka goranta mata mai son maso wani. Wannan abu daya faru yasa ta sake zama tamkar mahaukaciya sabon kamu, ta daina zuwa schl ta daina d'aga wayar y'an gidan su, ta rufe kanta a b'angarenta bata da wani aiki sai kuka. Tausayi sosai take ba da yawa cikin wad'an da suke makotaka da ita, sai dai basu da hanyar taimakon ta. Amna ta futo lectures a wani yammaci wayarta ta d'auki ringing koda ta duba mahaifin Saleema ne yake kiranta, bata d'aga ba don batasan k'aryar da zata mishi yau ba kuma, (da yake duk fad'an da zasuyi basa yarda su fad'awa y'an gidan su). Haka taita kallon wayar tana ringing da katsewa har aka gaji aka daina jera kiran. Shiru tayi a gefe d'aya tana tunanin ta yadda zata iya shawo kan Saleema har ta fahimci gaskiya, hanya d'aya ce dai ta rage yanzu wato ta inda aka hau,,, khaleefa kenan wanda batasan ta inda zata fara tunkarar shi da maganar taimakon saleeman ba...... Shin zaima saurare ta? ****Har ya shirya futa office bai ga alamun taba, ya daiga breakfast shirye a dinning, yana sane tun ranar da Saleema ta mata tozarcin nan bata sake zuwa makaranta ba, ko nufinta ta daina zuwa? Yana d'aura agogon shi a hannu ta futo rik'e da cup, kaikaitaccen kallo ya mata tun daga sama har k'asa, tayi maseefar kyau cikin straight skirt da riga mai tsagu gefe da gefe, kanta ba d'ankwali sai gashin da yasha nad'i kamar doughnut, ta d'auka ya futa a gidan shiyasa ta futo kanta tsaye. D'auke wuta khaleefa yayi sai kallon yadda d'inkin ya zauna a jikinta atamfar kuma ta haska ta, bai tab'a zaton haka atamfa take mata kyau ba sai yau da yaganta ba gyale ba hijab. "Masha Allah lak'uwwata illah billah....". Ya fad'a kan harshen shi k'asa k'asa. Kanta a k'asa tace mishi, "Ina kwana". "Laafiyaa" ya amsa still idon shi a kanta. "Me yasa kwana biyu bakya zuwa makaranta?". Shiru tayi bata ce mishi komai ba, hakan yasa ya sake maimaita tambayarshi da d'an k'arfi. Sai a lokacin ta d'ago ta dube shi, k'arara yake ganin tsoro a kwayar idonta, sake taku biyu yayi har gabanta ya tsaya dab da ita k'amshin turaren ta na isar da sak'o ta hanyar amfani da kafofin jinshi. Ya lumshe idon shi ya bud'e a kanta sannan ya fara magana da wani keb'antaccen sauti, "Banda yau! Amma gobe ki tabbatar kin koma makaranta,,,,, ki saka ranki a inuwa indai Saleema ce tana can cikin tsoro ba zata sake yink'urin fara tab'a kiba, idan kuwa har ta sake wannan gangancin!...... Hummm". Yana gama zancen ya huce kai tsaye dinning, ganin taci gaba da tsayuwa a gurin sai yayi mata magana, "yau ba za'ayi saving d'ina ba?". Saida tayi kamar ta juya d'akinta ta d'auko gyale, sai kuma dai ta fasa ganin yadda yake ta kallonta. Da takun nutsuwa ta Isa dinning ta had'a mishi abincin, koda ta kai plate in gaban shi yatsun hannunta yabi da kallo zata d'auke yayi caraf da hannun yana kallon yadda hatta farcenta yayi maroon. "lallen nan dai da nace bana so ba za'a daina shiba?". Yadda yayi maganar da sanyi ya bata kwarin gwiwar mayar mishi martani, "kayi hak'uri Auntie ce ta shard'anta mun yinshi akai akai". Murmushi yayi ya saki mata yatsun ya fara juya abincin gaban shi, "wato auntie dai so take ta ganki kamar ita, ni kuma na dinga yawo gidajen cin abinci?". Bata ce komai ba sai murmushi da tayi kawai ta juya a nutse ta fara barin gurin. Bai iya hak'uri ba saida yabi bayanta da kallo, musamman k'afafunta da take wata irin tafiya dasu tamkar bata so. Ya sauƙe k'ak'k'arfar ajiyar zuciya sannan yaci gaba da cin abincin shi. *Bayan wasu kwana ki* Raihana ta koma makaranta har ma ta maida hankali akan karatun ta, shi kuma yaci gaba da concentrating kan aikin shi, daga ita harshi sukan yi waya da auntie lokaci bayan lokaci haka y'an gidan su raihana, bata sanin lokacin da khaleefa yake kiran ummie ko Abba sai in tayi waya dasu suce mata ai khaleefa ya kira su jiya ko d'azu, su al'ameen kuwa dama sun zama kamar abokan shi, wani k'arin mamakin raihana ma har no ummaa kakarta yasa aka bashi suke waya, Ayman dai da gaske fushi yake dasu don yak'i magana da kowa a cikin su, koda khaleefa ya tambayi su iya sai suke fad'a mishi suma kwana biyu yayi musu yaji baya zo musu, tun khaleefa na ganin abun wasa sai gashi abun ya fara damun shi ganin da gaske d'an uwan nashi yake. Cikin lokacin daga khaleefa har raihana sun kasa bud'e sak'on auntie, ga zaman shirun da suke ya fara damun kowa a cikin su musamman ma khaleefa don yaji dad'in hirarrakin da sukayi da ita a lokacin da suke kwana tare muhalli d'aya. Yauma har ya kwanta kamar wanda aka tsikara da allura saiya tashi, ya k'ara haske a d'akin ya futa a ciki. Harta kashe glove d'in d'akinta sai dim light data bari hannunta rik'e da diaryn da auntie ta bata tana nazarin yadda zata fara karanta shi. Babu zato taji bugun shi, saita k'ara haske a d'akin da sauri ta bashi izinin shiga ba tare data motsa daga yadda take ba Ya tura k'ofar ya shiga idon shi ya fara hasko mishi littafin da take rik'e dashi, kamar wanda aka ja da magnet ko rufe k'ofar baiyi ba ya shiga kai tsaye da nufin karb'ar littafin ganin handwriting ta baya kamar na auntie, da sauri ta damk'e littafin tana tuna gargad'in da auntie ta mata a kanshi. Kai tsaye khaleefa ya mik'a hannu da nufin zare littafin, tayi saurin zura shi cikin duvet tana girgiza mishi kai, sai ya kama hab'a yana mata kallon mamaki kafun yace, "hadda saurin ki hajiya? Handwriting na gani kamar na auntie shiyasa..... Bani na gani". Had'e fuska tayi tam ta turo k'aramin bakinta gaba, "gaskiya ni bana son irin haka, meya kawo ka d'akin mutane da daren nan?....". "Wani abu daban sai kuma naga wani daban... A sauk'ak'e ki bani littafin nan na duba abinda nake son gani in dawo miki dashi simple and fine". Cikin shagwob'a tayi magana wannan karon wai ko zai barta, "don Allah kayi hak'uri ba irin littafin ka bane?". "Toh irin na waye?". Ya kwaikwayi salon yadda tayi magana, kife kanta tayi jikin cinyoyinta tana tsoron kada ya dage lallai fa sai ya gani. Da sauri ta d'ago jin k'amshin turaren shi kusa da ita, ta zaro ido tana kallon shi ganin ya zura hannu ta k'asan bargon da take ciki, kafun ta tantance me yake shirin aikatawa ya d'aga ta cak daga ciki ya sauke ta kan k'afafun ta. Bata yarda ya kalle taba tayi saurin rungume shi donta b'oye jikinta saboda wata shegiyar sexy nightie ce a jikinta, cikin kayan daya siya mata ta ganta, daga gwaji sai bata cire ba tunda tasan ba shigo mata yake ba, koda ya buga ma bata d'auka zai shigo ciki ba. Shi kuwa tunanin shine ya tsaya cak, notikan kanshi suka fara juyawa zasu kwance, yana kallon littafin amma ya kasa mik'a hannu ya d'auka.... Da kyar ya iya k'arfin halin fara janye jikin shi, sai dai yana motsawa take sake shige mishi, zuwa yanzu ya fahimci bada gangan take aikata hakan ba, Koda ya fahimci rigar jikinta kamar take son b'oyewa, hannun shi ya kai kan switch duhu ya mamaye ko'ina, da mugun sauri tabar jikin shi ta shige cikin bargon gaba d'ayan ta. Murmushi yayi kurum ya juya ya futa da manyan taku. Ko bayan ya koma d'akin shi kasa nutsuwa yayi,,,,, gaba d'aya tariyar mintunan da yayi a d'akinta yake yi tsigar jikin shi na tashi, duk ta inda ya juya sai yaji ta da motsinta ata jikin shi...... Itama yana futa bacci b'arawo bai bata damar yin kowanne tunani ba yayi gaba da ita. *****Tun daga wannan ranar khaleefa ya kasa d'auke kanshi akanta, har Allah Allah yake ya tashi office yazo yayita kallon kwalliyarta da gilmawarta cikin gidan, duk wani abu daya kasance ba dabi'ar shiba ya maida shi dole cikin kwanakin, kamar yawan kallo shiga cikin harkokinta da son jin k'amshin jikinta ko muryarta, kawai yana zaune sai ya hau sata aiki kusa dashi mara dalili don kawai tazo kusa ya shak'i daddad'an k'amshin turaren ta. Duk yadda yaci burin ta bar mishi d'akin shi yayi yadda yake so yanzu kuma sai abun ya gundure shi, kullum dare ya kwanta sai yaji kewarta abun har ya zame mishi jiki....... @@@@@ tsaye yake gabanta hannun shi duka hard'e a bayan shi yana fuskantar ta, "tsawon shekaru goma da d'oriya Ina zuwa gurin ki saboda neman y'ar k'aramar hujjar dazan rik'e ta kaini ga isa gare ta, sai dai a kullum amsarki d'aya ce ba'a ganta ba, baki ji labarin taje Sudan ba, duk da haka baki tab'a kirana da karan kanki ba sai wannan karon...... Andal tunda na shigo Germany nake jin matuk'ar kusanci da surayyah ata jinin jikina da zuciyata, tun a airport nake jin k'amshin ta har yanzu da nake tsaye gaban ki ban daina jiba..... Andal ki gaggauta fad'a mun tana Ina don nayi imanin tana tare dake a nan Germany?......". Happie juma'at Mubarak toh all Muslim Ummah🕋 *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty two 6️⃣2️⃣ Mik'ewa tsaye tayi ta nuna mishi kujera da hannunta, "please sit Mr sooraj". "I don't come here just to sit and listen to kowanne dogon labari.... Doctor andal Ina take? Ina surayyah Adam take?". Zufa andal ta share da hankie, tana son mishi cikakken bayani kan abinda ta gani yadda zai fahimta sai dai babu alamun zai iya bada goyon baya, duk da itama bata da tabbaci hasashe ne kawai.... "Andal ki fad'a mun gaskiya nasan wannan kiran naki yana nufin abinda na dad'e ina mafarkin gani tsawon shekaru.....andal a shirye nake dana gyara kuskurena ta hanyar neman yafiyar surayyah da shirya kyakkyawar rayuwa ninkin wadda na shirya a baya Allah bai nufa ta tabbata ba..... Wallahi zan auri surayyah auren da zan iya k'arar da komai dana mallaka.....". Da sauri likita andal ta d'aga mishi hannu. "Ban kira ka don na had'a ka da surayyah ko muyi ta tattaunawa akan labarin tsohuwar soyayyar kuba! Ni na kira kane saboda na damu da lafiyarka..... Kama daina mafarkin k'ara ganin fuskar da kaine silar b'acewarta ga kowa da kowa, ka shiga rayuwarta da sunan soyayyah ka lalata mata duk wani jin dad'i da walwalarta ka raba ta da familyn ta, ta yadda ta gwammaci ta kasance matacciya a idon su kan ta tunkare su..... sooraj indai baso kake ka k'ure k'arshen hak'urina da kawaicin da nake maka tsawon shekaru ba, to mubar wannan maganar, mu fuskanci abinda yake gaban mu. Na saka date na ranar da za'a yi maka surgeryn hannun ka da kace yana damun ka da ciwo, amma kafun nan kasan dole za'ayi hoton hannun don a gano inda matsalar take ko, to na nemo kane saboda naga baka da niyyar zuwa ga lokacin yana gab da k'urewa.... Wannan shine". Yadda ta fara zancen cikin fad'a yasa sooraj yin shiru yana sauraronta, ko kad'an baya jin haushin duk wanda zaiga laifin shi kan b'acewar surayyah, da gasken gaske laifin shine sai dai ya aikata komai ne cikin fushi da k'iyayyar da baisan lokacin data shiga zuciyarshi har tayi gini mai tsayi a lokacin ba, duk daya shafe shekaru yana ganin doctor andal as his personal doctor bai tab'a jin kwarin gwiwa da kuma kusanci ga abinda yake nema a tare da ita ba kamar wannan lokacin,,, Soo zaiyi hak'uri da komai da zata mishi matuk'ar zai kai ga isa ga muradin shi. Sai yaja sit ya zauna ya tallabe fuskarshi cikin tafin hannun shi. Doctor andal tayi banza dashi sai aikinta da take cikin system tamkar ba shine shahararren d'an kasuwa sooraj ba, kamar bata san da wanzuwar shima a gurin ba, dauriya kawai take amma zahirin gaskiya maganar surayyah ta taso mata da duk wani rauninta,,,,, akan soyayyar surayyah da sooraj ta k'aryata duk wata soyayyah a duniya, ta gane kowa zai iya shiga rigar soyayyah ya cimma mugun nufin shi ko k'udurin shi kan kowa,,,, ture computer tayi gefe ganin ta fara daina gane komai. Sam ba zata ba sooraj damar ganin hawayenta ba, hakan yasa ta shiga toilet da yake cikin office d'in. Ta jima a ciki kafun ta futo su k'arasa tattaunawa kan abinda ya kamata. A yau andal ta sake tabbatar da duk wani zarginta sai dai zata tafi da komai a hankali ko Allah zaisa taga y'ar uwarta d'aya tamkar da million data b'ace musu tsawon shekaru. *****Cikin satin gaba d'aya raihana bata samu zama ba, data dawo school zata tafi gidan yasmine, wani lokacin ma daga makarantar take hucewa saboda laulayi mai d'an karen wahala daya same ta, gashi gaba d'aya ta sake jikinta abinda ya k'ara futo da ciwon nata ma kenan. Iya k'ok'ari raihana take wajen taimakawa yasmine d'in, wannan yasa ta k'ara matso da lokacin tashin ta a bacci kusa saboda ta gama aikace aikacenta kan lokaci tayi na yasmine d'in ma. Tun ranar data rungume khaleefa a d'akinta har yanzu bata sake yadda sun had'u ba, da taji alamun futowarshi take guduwa d'akinta ta murza key,,, mafi yawan lokuta ma sai in ta k'ure take kaisu ga hakan amma a k'a'ida kafun ya futo ta shirya mishi karin kumallo ta matsa daga gurin. Ko rashin lafiyar yasmine daga bakin Ahmad ta nemi izinin shi ya lamunce mata ba wai ita da kanta ta tambaye shiba. Yau data kama weekend raihana tana idar da sallar subh ta fara aikin had'a gidan azhkar ma a kitchen tayi, so take tunda bata da karatu ta had'a abinci irin wanda ta jima ba tayi ba a gidan. Tana aikin girkinta tana hira da khausar k'anwarta da itama cikinta yayi girma haihuwa kusa, hira suke akan abinda ya shafi matsalolin matar kawunta da kakarta, kusan yanzu sun samawa maman su lafiya sai dai fa ta had'o su da Mom ziyada. Don yanzu ba b'oye b'oye take nuna bata tare dasu k'iri k'iri, rigima tayi tsamarin da har Abba saida ya shiga amma abu yak'i sasantuwa, hakan yasa daga Abba har Abba abubakar yin fushin zuciya su futa harkar umma salaha da ziyadan, hajiya innah kuwa dama ba tace komai ba saboda ta fara zargin salaha kan had'a makirci da yawa cikin al'amuran rayuwarsu, musamman tsakanin rukayyah da fashe fashen auren y'arta da aka dinga yi. Dama tun ranar da aka kawo lefe tayi wannan sub'utar bakin ta fara dasa mata alamar tambaya, tayi shiru ne kad'ai gudun kada ta kwaye mata baya gaban rukayya da danginta ta bad'a mata k'ura bayan kullum cikin goyon bayanta take akan komai da zata aiwatar. Abu da yawa raihana takan ce Allah ya kyauta, ko Allah ya kiyaye har aka gama bata labarin ta d'ora da musu addu'ar sake samun shiriya da tsayawa gaskiya sai barin hassada, don duk ba komai ya had'a wannan wutar gabar tsakanin ummie da umma salaha ba sai hassada da kyashin yadda Abba yafi mijinta rufin asiri. Sai gab da zata k'arasa kammala aikin sukayi sallama kowa ta katse kiran ta k'arasa tattare komai ta gyara gurin. Tana shiga d'akinta tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga wrapper ta material data zauna a jikinta das, ta d'aura d'ankwalin material d'in ta turare jikinta da mayun turarukan da auntie ta had'a mata, tasa na d'akinta da parlour kamar kullum. System d'inta ta d'auka ta fara operating d'inta a hankali don ba wani iya aiki tayi da ita sosai ba, tunda bata tab'a zama aji na musamman wai don ta koyi sarrafata ba. Tana cikin danne dannen ta tuna da littafin nan, rabon data d'auko shi tun ranar da khaleefa ya shigo d'akinta, ta yink'ura da nufin mik'ewa aka fara buga k'ofarta, la shakka tasan khaleefa ne, hakan yasa ta yafa madaidaicin gyale ta bud'e k'ofar. Yana tsaye bakin k'ofar sanye da dogon wando sky blue da farar t shirt, yayi kyau sosai duk da fuskarshi kadaran kadahan ya barta. Tunda ta bud'e k'ofar ya zuba mata ido yana kallonta tamkar wata sabuwar halittar da tasha banban da jinsin mutane da bai tab'a gani ba, baisan adadin yadda yayi kewar kallon fuskarta, shak'ar k'amshin turaren ta da giftawarta ta gaban shi a lokacin da yake zaune a parlour yana aiki sai yau, hee miss much about her. Ganin bashi da ta cewa sai kallon maseefa yasa ta russuna tana gaishe shi. Saida yaja doguwar ajiyar zuciya sannan ya amsa yana sake ci gaba da kallonta yace, "ya wasan b'uya kuma?" Bata ce dashi komai ba, sai ya sake cewa, "d'akina nake son ki gyara mun idan ba zaki damu ba...". Ya k'arasa fad'a a ranshi yana fatan tasa mishi irin turaren d'akinta ko shima yaji k'amshi mai dad'i da sanyaya zuciya. Lokaci ta kalla sannan tace, "toh ba damuwa! Sai dai ina son mik'awa yasmine abincin dana dafa ko zata iya ci....". "Alright! Yana ina in kai mata?". Da kanta ta d'auko ta bashi ya amsa tare da futa a gidan. Daga k'ofar gidan shi ya kira wayar Ahmad, saida yaga futowar shi ya k'arasa suka gaisa yaji jikin yasmine sannan ya bashi k'aramin plask da raihana tasa a kawo mata. Ahmad ya karb'a Yana godiya da tambayar khaleefa, "yau ba zata samu damar zuwa ba? Tun safe yasmine take son ganinta". Harararshi khaleefa yayi yace, "tunda kana gida yau ai saika kula da matarka ko?". Dariya Ahmad yayi yace, "man maida wuk'ar nasan indai kaine ba hana ta zuwa zakayi ba, tunda kota zauna a gidan ba wani abu zatayi maka ba....". Cikin rashin fahimta khaleefa ya had'e rai yace, "me kake nufi". Ahmad ya sake yin dariya had'e da rage sautin muryarshi, "Ina nufin bata da amfani da zatayi maka irin na kowanne miji ga matarshi.....". "Ahmad!". Ya kira sunan shi a zafafe. Dafa kafad'ar shi yayi fuskarshi har lokacin da fara'a yace, "sorry man! Na fad'i haka ne saboda nasan kai ba d'aya kake da sauran mutane ba....". "Ohh! Na futo da sanyin safiya don na faranta ranku shine ka k'are da cimun mutumci". "I'm sorry bhaiyya.... Mun gode Allah ya saka da alkhairy sai madame d'in tazo ko?". Zuwa yanzu khaleefa ya gama fahimtar Ahmad magana yake fad'a mishi a kaikaice, har yanzu ya kasa fahimtar meyasa mutane suke saurin gane irin zaman da sukeyi shida raihana, koda yake Ahmad dole zai fahimci komai, amma wannan yana daga dalilin da yasa yak'i yadda Muhammad ya kawo matarshi ko su suje gudun kada ma wani zumunci ya k'ullu su dinga mishi zarya kullum...... Juyawa yayi baice dashi komai ba ya koma gidan. Ahmad ya bishi da kallo yana murmushi mai kama da dariya. Raihana kuwa koda ta shiga d'akin nashi saida ta gama bin ko'ina da kallo sannan ta fara gyarawa kamar yadda ya buk'ata. D'akin ma ba wani datti kawai neman magana ne irin nashi. Lokacin daya shigo ta gama aikin harta turare d'akin kamar yadda yayi fata. Tana shirin komawa d'akinta yasa ta kawo mishi breakfast har d'akin, ba musu tayi duk yadda yake buk'ata, tana sane da yadda yake bin duk wani motsinta da kallo. Har ta mishi sallama zata tafi ya k'ara tsayar da ita ta hanyar tambayarta, "akwai abinda zaki yine a gidan Ahmad?". Girgiza mishi kai tayi, "Then saurin me kike". "Ba komai". "Ko zaki jirani minti biyar in gama abinda nake?". Ba tayi mishi musu ba wajen samun gefe d'aya ta zauna. Yana cin abincin yana tunanin maganganun Ahmad..... A zahirin gaskiya zuciyarshi tana sake aminta da raihana, sai dai yana yak'i da wannan kusanci nasu a kullum dare da ranar Allah, yana son cika alk'awarin daya d'auka a zuciyarshi tun ranar daya fahimci gaskiya akan soyayyarta........ Duk da yasan inba ita ba babu wata mace da zata tsallake maganar data mishi da wadda Saleema ta mishi...... Ya riga ya zama marar buri game da aure da matar auren.... Inta kama sai ya rayu shi kad'ai har abadan abada, da dai ya auri ballagazar mace da tayi irin rayuwar Saleema. Abincin ma baici na kirki ba ya ajiye shi gefe, ya kalli sashen da take zaune yaga ta tallafe hab'arta da hannunta, matuk'ar tausayinsu ya kama shi, har yaji ya fasa futar daya shirya da ita don ya d'ebe mata kewar zaman gidan, saboda ya fahimci hakan zai k'ara musu kusanci sosai da juna, kusancin da zai hana shi cika alk'awarin shi. Jingina kanshi yayi da fuskar gadon da yake zaune yace, "zaki iya tafiya". A nutse ta mik'e ta futa daga d'akin, khaleefa ya bita da kallo har ta b'ace sannan ya maida kanshi ya kwantar tare da sauke ajiyar zuciya. ****Tana shiga d'akinta a gefen gado ta zauna tayi shiru tana nazarin abubuwa da yawa game da rayuwar khaleefa da Auntie take magana a kai, shin da gaske zata iya kawo gyara wa rayuwar shi kamar yadda mahaifiyarshi take fata,,,,,, littafin nan ne ya sake fad'o mata a rai, ta rasa meyasa take mantawa dashi ko don kwana biyu bata samu zama ba, saita mik'e da sauri ta d'auko shi ta bud'e shafin farko tana duba abinda yake rubuce kamar haka👇 "Sooraj Abdallah,,,, da surayyah Adam". Zagaye cikin hoton zuciya. Page na gaba ta bud'e mai d'auke da rubutu kamar haka, "Kamar yadda kika sanni... Sunana surayyah Adam haifafiyar k'asar Sudan garin Khartoum, mahaifiyata da mahaifina duka haifaffun k'asar ne, mu biyu suka haifa a duniya.... Yayana sauban daya bani kusan shekara goma sha shida a duniya, sannan aka haifeni naci sunan mamana,,,, mahaifina ba mai kud'i bane amma yana da matuk'ar rufin asirin da yasa muke rayuwa cikin gata kafun rasuwar iyayena ata sanadiyyar had'arin jirgin ruwa, hakan yasa gaba d'aya akalar rayuwata ya koma gurin yayar mamana, a lokacin sauban ya samu gurbin karatu a jami'ar Abuja dake Nigeria, ban nemi komai na rasa a sabon gidan da nake rayuwaba duk da mijinta yana da k'aramin k'arfi sosai ba kamar mahaifina ba. Nayi karatuna tun daga primary har zuwa matakin junior secondary tare da y'ay'an gidan da nake da k'awayena, musamman k'awata guda d'aya da bazan iya mantawa da ita ba, irin k'awa ta k'uruciya. Kafun sauban ya samu aiki a garin Abuja ya dawo nan garin mu Khartoum yayi aure.... Sarah y'ar kawuna ce kuma yayanta abokin sauban ne tun na k'uruciya da sukayi fad'i tashin neman ilimi tare. Da farko daya nuna yana son na koma gurin shi da zama hanawa y'an uwan mamana sukayi saboda suna ganin kamar ya raina kulawar da suke bani ne, amma daga baya daya zauna ya fahimtar dasu dalilan shi sai suka amince zamana ya koma k'ark'ashin ikon shi da matarshi, a lokacin bazan huce shekaru goma sha hud'u ba. Naci gaba da zama tare da sauban da matarshi cikin farin ciki da soyayyah, a lokacin kusan rabin abinda sauban yake samu ni yake kashewa saboda Allah bai basu haihuwa da wuri ba, nan da nan na sake wani irin sihirtaccen kyau mai d'aukar hankali... Aikuwa samari suka yimun caa, wanda sauban ya dinga taka musu burki, sai ya zamana ba mai iya tunkurata da shirmen maganar soyayyah saboda tsoron shi dana matakin da zai d'auka in yaga mutum ko yaji labari, hakan yasa har na kammala secondary na shiga jami'a bani da wani tsayayyen saurayi,,,, kafun k'addarar sooraj ta shigo cikin rayuwata...... An raba gadon mu tuni sauban ya fara business yana juya nawa da nashi yana adana mun ribar da ake samu cikin account d'ina". *Waye sooraj Abdallah tofa?* Asalin mahaifin sooraj Abdallah haifaffen wani k'auye ne a Kano da ake kira tofa, yayi karatun shi na primary a k'aramar primary da take k'auyen su, tun a lokacin da ilimin boko ba kowa ba sai wanda iyayen su suka toshe kunnuwan su daga sauraron zagin mutanen gari, yaci jarrabawar common entrance a ajin k'arshe na firamare, sai ya tafi boarding school dake gwarzo. Ya kammala secondary a k'arshe ya samu gurbin karatu a A.B.U Zaria.... Yana cikin karatun aka bashi auren wata matashiyar yarinya da ba zata huce shekaru sha uku a duniya ba mai suna Maryam..... Da auren ta yaci gaba da karatun shi tun daga matakin degree har izuwa master's, yayin da itama bai barta haka nan ba, ya maida ita makaranta ta k'arasa had'a karatunta na sakandire tsab. A lokacin suna da yara uku duka maza, salis! Mukhtar!! Abubakar!!! Abdallah ya fara lecturing a makarantar da yayi karatu kafun ya fad'a harkokin siyasa, ya rik'e muk'amai da dama tun daga k'anana har zuwa manya, kafun a k'arshe ya k'are da samun babban matsayi na zama ambassador Nigeria a k'asar turkey. A lokacin matarshi da suke kira maryam ta k'ara haihuwar yara uku, sooraj sai Aysha da Fatima! Duk da kasancewar mijinta rik'ak'k'en d'an boko da yake rayuwa a cikin turawan larabawa basu d'auki tsarin yahudu na k'aiyade haihuwa ba, suka haifi yaran su tamkar asalin Nigerians suke kuma kula dasu da kyakkyawar kula da tarbiyyah ingantacciya don matarshi normal house wife ce, ba irin matan da kullum suke gantali akan hanya makaranta ko aiki ba. Tun asalin sooraj ya tashi wani irin bahagon yaro mai murd'ad'd'iyar fahimta, yana da matuk'ar kaifin kwakwalwa da basirar data zarce ta duka y'an uwan shi, sun fara karatun su a turkey mataki mataki kafun su tattara su dawo Nigeria gidan mahaifin su dake garki.... A hankali rayuwa taci gaba da tafiyar musu har kusan matasan biyu suka kammala karatun su suka samu aiki d'aya a B. U. K Kano d'aya kuma yake aiki matsayin babban likita a garin Zaria... Taufeeq da sooraj kuma suna gab da kammala degree na biyu. Shekaru sunyi nauyi wa Abdallah, ya daina harkokin siyasa tuni, yanda shekarun shi sukayi nauyi saiya daina tunanin komai don adadin abinda ya tara yasan zai ishe shi ya k'arasa kula da rayuwar iyalan shi har bayan ranshi. Taufeeq ma ya samu aiki a babban bankin Abuja sai dai sooraj ya nuna sam bashi da sha'awar aikin gwamnati ko zama k'ark'ashin wani company. Yayyen shi sunso ja dashi sai dai basu samu goyon baya daga mahaifin su daya kasance mutum mai ra'ayi da magana d'aya ba. Ya dunk'uli kud'i masu yawa ya bashi yace ya fara business, ya fara harkar kasuwancin shi da kad'an kad'an har Allah yasa mishi albarka cikin k'aramin lokaci ya mallaki company nashi na k'ashin kanshi. Koda aka zo maganar aure, maman su taso shima tayi mishi zab'in d'aya cikin yaran family had'in auren zumunci kamar yadda ta yiwa sauran y'an uwan shi daga mazan har mata da tuni dama su tuni akayi musu aure, kowa ya karb'a banda sooraj da akazo kanshi ya nuna sam bashi da ra'ayi akan aure yanzu. Yayan shi saddik tuni yayi auren shi matar ta tare a gidan tunda babban gida ne da aka gina shi da tsarin had'a extended family.....". Nannauyar ajiyar zuciya raihana ta sauƙe ta mik'e donta gabatar da sallah, tayi girki tunda khaleefa yana gida yau ba futa zaiyi ba..... Cikin zak'uwa da son jin k'arashen labarin ta shiga d'akin wankanta ta futo ta shimfid'a darduma ta kabbara sallarta. Tana idarwa ta b'oye littafin k'asan pillow ta futo daga d'akin. Dai dai lokacin da khaleefa ya shigo gidan shima.... Duk suka kalli juna lokaci d'aya kuma suka d'auke kansu..... *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty three 6️⃣3️⃣ A parlon ya zauna ita kuma ta shige kitchen. Har ta gama aikin ta futo yana inda ta barshi a kwance yana kallo. A k'aramin table na gaban shi ta had'a mishi komai ita kuma ta koma kitchen taci nata, tana cin abincin ta kira yasmine suka gaisa taji lafiyarta, ba laifi yadda taji muryarta kad'ai ma tasan da sauk'i sosai, tayi mata tayin abinci tace bata cinye wanda ta kawo mata na safe bama. Sunci gaba da tab'a hira kan wahalar da take sha na laulayi, kafun suyi sallama kowa ta ajiye wayarta. Har ta ajiye wayar zata wanke hannunta ta futo wayarta ta bada k'arar sautin shigowar sak'o. Da sauri ta wanke hannun tazo ta duba, daga Ayman ne, "Assalam! Mrs Abdallah fatan kina lafiya?", murmushi tayi ta mayar mishi da reply kamar haka, "lafiya k'alou nake fatan kaima? Ya fushi damu?" "Fushi na huce tunda auntien munyi waya kun saketa tana umrah". Dariya tayi kad'an lokacin data gama karanta sak'on shi, ta sake mayar mishi da amsa, "toh Allah ya k'ara hutar zuciyarka". "Ke kad'ai kika iya wannan addu'ar banda mijin ki". "Shima ina baka hak'uri a madadin shi". "Ai hak'urin ki ya wadatar tunda keda khaleefa a gurina duk abu d'aya ne, ki mik'a sak'on godiyata ga twin bro na, kice in ya gama fushin ya kira ni ina son naji muryarshi kada abun ya taru yayi mun yawa....". "(😸😸) Insha Allah zan isar mishi da sak'on ka fatan alkhairy". "Thanks matar bro..... Fatan alkhairy gare ku baki d'aya". Murmushi tayi bayan gama hira dashi ta text message ta mik'e da sauri ta futo a kitchen d'in. Khaleefa yana zaune ko yaci abincin da aka kawo mishi ma? Ita dai ta ganshi ya had'a kai da gwiwa. Har zata huce d'akinta sai ta dawo da baya don isar dashi sak'on Ayman, "amm Yaya Ayman yana son magana da kai da alama yana ta kiran ka wayar bata kusa shiyasa baya samun ka, a k'arshe yana maka fatan alkhairy yace yana sauraron kiran ka...". Tana gama maganar tayi hucewarta, shi kuma yabi bayanta da kallo kafun ya mik'e don wayar ma cikin d'akin shi ya barta". Raihana koda ta shiga d'akinta gyare gyaren ta tayi har zuwa lokacin da akayi sallar la'asar, dama tana idar da sallah ta koma kitchen don girkinta zai iya kaiwa dare inta zauna. Duk abinda take yi zuciyarta tana kan gab'ar labarinta data bari ne, burinta tayi ta gama ta k'arasa jin yadda zata k'are,,,,, A tak'aice bata sake samun damar zama ba sai yamma, ko abinci bata tsaya ciba, ta dai ajiyewa khaleefa nashi a dinning, ta bud'e diaryn zata ci gaba da karatu taji ana tab'a kararrawar k'ofa, ba tayi saurin tashi ba saboda tana zaton khaleefa zai bud'e k'ofar, sai dai jin ana ci gaba da danna kararrawar had'e da dukan k'ofar saita mik'e ta zura dogon hijab ta nufi k'ofar. Koda ta murza key ta bud'e Ahmad ta gani kamar a gigice yana tambayarta, "Ina man d'in? Ya jikin nashi?". Ita da batasan ma bashi da lafiya ba, bashi hanya kawai tayi ya shiga ita kuma ta rufe k'ofar, ganin Ahmad bai shiga d'akin khaleefan ba sai tace mishi, "yana ciki ai". "Noop! Ba saina shiga ba ki bashi wannan magugunan, amma ki tabbatar yaci abincin shi kafun.....". Ta karb'a tare da gyad'a mishi kai, daga nan ya fuce a gidan ita kuma ta rufe k'ofar. Ta jima tana knocking k'ofar d'akin baccin shi amma babu alamun za'a bata izinin shiga, har tayi nufin tafiyarta sai kuma taga rashin dacewar hakan, toh amma taya zata iya kutsa kanta d'akin shi kai tsaye? Tayi ta tunane tunanen ta kafun tayi kasada ta tura k'ofar ta shiga a d'arare. Yana kwance fuskarshi na kallon ceiling ya dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu, hankalinta a kanshi ta k'arasa tana mishi sannu, bai iya amsa taba saida ya jima da kyar ya tashi zaune ya zauna har lokacin dafe da kanshi, raihana ta sake mishi sannu cikin tausayin halin da yake ciki, wannan karon ma bai amsa ba sai hannu daya mik'a mata, ta gane sak'on shi da Ahmad ya kawo mishi yake so. Bata bashi ba saida ta fara gabatar mishi da abinci, da kyar da taimakonta yayi cokali hud'u zuwa biyar ya kora magungunan shi da ruwa ya koma ya kwanta, ba jimawa bacci ya kwashe shi mai nauyi. Bata iya barin shiba kamar me gadi har yayi baccin ya tashi kan nashi da sauk'i. Cikin kulawa itama ta sake matsawa kusa tana mishi sannu da tambayar ya yake jin jikin nashi? Ya zuba kwayar idon shi a kanta ya lumshe ya motsa bakin shi da kyar yace, "da sauk'i". "Allah ya k'ara sauk'i". Ta fad'a, Wannan karon a zuciyarshi ya amsa. Sun jima shiru kafun tayi tunanin had'a mishi ruwan wanka, ya shiga wankan kafun ya futo tayi karambani ta ciro mishi fararen kayan bacci kamar yadda ta lura yana yawan sawa. Yana futowa d'aure da bathrobe ta futa d'akin da sauri, yabi bayanta da kallo har ta futa sannan ya k'arasa gaban mirrow yaja stool ya zauna yana kallon kanshi da sauraron yadda har yanzu yake sara mishi kad'an kad'an cikin shi kuma yana kiran yunwa..... Har ya gama shiryawa bata dawo d'akin ba, hakan yasa ya futo daga d'akin shi. K'amshin girki daya buso daga kitchen yasa shi lumshe idanun shi cikin shi na nuna tsananin buk'atar shi da abinda hancin shi ya shak'o. Ya fara takawa a nutse har zuwa kitchen d'in ya tsaya daga bakin k'ofa yana kallonta tana ta hidimar juye abinci a plate, ita kuma wannan yarinyar bata gajiya da girki? Ya tambayi kanshi, a plate ta juye mishi abincin zata futo idanunta suka sauka a kanshi, saita tambaye shi, "akwai abinda kake buk'ata ne?". Numfashi ya sauke yaci gaba da takawa ya d'ibi ruwa a glass cup yasha. Kusan tare suka futo ya zauna a parlour, sai ta ajiye mishi abincin a gaban shi ya fara ci itama tayi gefe d'aya tana cin abincin gaba d'aya zuciyarta da tunaninta yana kan jin k'arashen labarin auntie. Saboda jikin khaleefa kad'ai ta zauna a gurin amma da tuni ta k'arasa karance labarin. Gashi har yanzu taga kamar jikin nashi sai a hankali, don abincin ma bai iya cin na kirki ba ya barshi ya jingina kanshi ya lumshe ido. Har dare ya fara nisa suna zaune a gurin, sai sannu da take yi mishi a duk motsin shi, tana tsoron barin shi ciwon ya mishi zafi, ganin lokaci na tafiya gashi ta gaji ga parlon da sanyi saita shiga d'akinta ta sauya kayan jikinta zuwa na bacci masu kauri ta k'ara hijab ta d'auko pillow, a d'auko pillown ne taga littafin data ajiye a k'asan shi, saita had'a har littafin ta dawo parlon. Yana kwance yanzun amma hannun shi dafe a goshin shi. Itama kwanciyar tayi ta soma neman shafukan data tsaya ta d'ora. "Na had'u da Suraj a ranar wata juma'ah da bazan tab'a mantawa ba, a lokacin mun samu hutu a makaranta zan tafi Sudan gurin y'an uwan iyayena da k'awata d'aya tilo da muke rayuwa da buri iri d'aya duk da muna zaune a mabanbantan gurare, a rayuwa bana gajiya da zuwa Sudan don haka kurum nake tsintar kaina cikin shauk'i na musamman in naje k'asar, shiyasa bana mantawa da zuwa musu duk bayan shekara d'aya ko biyu, Tun a airport Suraj ya ganni amma ko a fuska bai nuna komai ba har saida muka shiga cikin jirgi da Allah yasa tafiyarmu tazo d'aya. Koda ya tashi sauka P.A d'inshi yasa yabi bayana har gidan k'anin babana (da yake can na fara sauka). Kwana na uku da sauka a k'asar Sudan Suraj ya gama abinda ya kawo shi zai tafi yasa aka rako shi gidan mu kafun ya huce, direct yayi magana da k'anin mahaifina yana son a bashi izini ya nemi aurena, k'anin mahaifina ya nuna mishi sam aurena baya hannun shi yanzun tunda ina zaune garin Abuja tare da yayana, a nan Suraj yake fad'a mishi ai shima garin da yake zaune kenan, sun tattauna sosai kan muhimman abubuwan da ya kamata a sani a kanshi, a k'arshe aka bashi adreshin sauban da shawarar ya fara yin magana dani kafun ya isa ga sauban d'in. A haka suka bar matsaya Suraj ya jirani cikin d'akin bak'in da suka gama tattaunawa a ciki. Muna zaune cikin gida muna hirar mu nida andal da bama rabuwa da juna tunda nazo, hira muke kan rayuwar makaranta da irin yadda ake challenging d'inta akan karatunta, yayinda nake K'arfafa mata gwiwa da kwantar mata da hankali had'e da bata shawarwari masu kyau. Koda uncle ya fad'a mun ina da bak'o nayi mamaki sosai tunda nasan ba saurayi gare niba. Tare da andal muka same shi. Da kallo d'aya Suraj ya tafi da hankalina da duk wani tunanina tun kafun ya kaiga furta komai a gare ni, Cox ya kasance d'an gayun matashin daya fara huce shekarun rawar kai. Mun gaisa dashi gaba d'aya kafun muyi shiru muna sauraron muji da wadda yazo. Shi kuwa da murmushi kan fuskarshi ya fara da tambayata, "surrayah ko?" Banyi magana ba sai andal ce ta amsa shi. Ya sake cewa, "toh surayyah Ni dai sunana Suraj Abdallah tofa, d'an asalin k'asar Nigeria garin Abuja, na ganki tun ranar da muka shiga jirgi d'aya, Ina fatan zaki iya aurena?". Da mamaki duk muka kalle shi, mun d'auka kowanne saurayi da soyayyah yake fara magana har a kaiga batun aure, amma sai gashi karo na farko munga mai neman aure ba tare daya nemi soyayyah ba. Haka Suraj ya dinga zayyano abinda yake ranshi kai tsaye, duk da naga baud'ad'd'en hali a tare dashi amma a haka nayi na'am dashi har na bashi full address na gidan yayana Sauban a karo na biyu. Bai tafi ba saida ya bar mana kud'i masu yawa. Muka shiga gida muna al'ajabin halayen shi nida andal. Sati na uku cif a Sudan na koma Nigeria da dashen soyayyar Suraj da tunda na ganshi sau d'aya ban sake sanyashi a kwayar idanu naba sai tunanin shi da nake kwana da tashi dashi. Ina dawowa na tarar da sabon tashin hankali a gurin yayana, fad'a yake ta inda ya shiga ba tanan yake futa ba, Wai tunda na zab'i aure saina hak'ura da karatu, sannan ko auren nema shi yana da wanda ya zab'a mun matsayin mijin aure na. Nan fa hankalina ya tashi na dinga bashi hak'uri nida aunti Sarah har muka samu ya hak'ura sai daifa cikin satin ya turo mun wani abokin shi d'an asalin k'asar mu daya dad'e yana sona ya nemi soyayyata dana dad'e da bada kyautar ta ga mutumin da baisan ma ina yiba, bansan yadda sukayi da sauban ba tun zuwan farko gurin shi, watak'ila korar shi yayi shi kuma ya hak'ura. Ina cikin wannan tsaka mai wuyar na koma makaranta naci gaba da karatuna cikin sabuwar damuwar data fara ginuwa cikin zuciyata. Ta b'angaren Suraj ma kai tsaye maman shi da duka y'an gidan su suka k'alubalan ce shi akan maganar auren, a cewar su bayan ya dad'e baiyi aure ba shine zai d'auko musu yarinyar wata k'asa da al'adarsu ta banbanta da ita,,,, Sam basu amince ba. Ko kad'an hankalin Suraj bai tashi ba saboda shi bai tab'a jin ba zai same niba koda wasa, sannan yasan indai mahaifin shi yana raye ba zai barsu su zama katanga ga abinda yake matuk'ar so ba. Haka kuwa akayi mahaifin shi yayi futu futu ya hana aci gaba da maganar ba'a sona a gidan, yayinda ya kafa musu hujja da komai yana faruwa da dalili, shi Suraj yaga nashi dalilin har ya fara sonta, su Ina nasu na k'inta? Duk sukayi shiru, yayi fad'a sosai musamman akan momy hapsert data ke babba amma ba tayi tunani ba. Da haka ya toshe bakin kowa babu wanda ya sake magana gidan, daga yayyen Suraj har k'annen shi. Suraj yaci gaba da bibiyata har Allah yasa soyayyah ta k'ara k'arfi a tsakanin mu, ranar da yayana ya gane muna tare nan ma ya dinga masifa hadda rantsuwar ba zai tab'a bari na auri wanda basu san muhimmancin aure bare har su iya rik'e shi da kyau ba. Haka akayita rigima, bazan manta ba mahaifin Suraj da kanshi ya taka yayi ma Sauban nasiha da kwantar mishi da hankali had'e da alk'awarin zasu kula mishi da k'anwarshi ba tare da wata matsala ba. Saboda ganin dattakon mutumin daya kasance babban mutum mai kud'i da iko yazo takanas gurin shi yana bashi hak'uri da son nemawa d'anshi aurena, sai sauban ya sauko har ya amince aka tsaida maganar auren mu amma fa ya gindaya mun tsauraran sharud'd'a, idan wani abu ya same ni ko nan da shekaru ashirin ne, kar na kuskura na taho gidan shi da sunan yaji, idan kuwa har hakan ta kasance toh lallai kada na tuna cewa ina dashi, idan kuwa har na yarda da dawowa gidan shi na zauna, toh bani ba Suraj ko y'ay'an da zamu haifa tare. A lokacin na makance kuma na kurumce Suraj da soyayyar shi kad'ai nake ji da gani cikin kwayar idona, bana kawo wata rana zata zo da har Suraj zai iya yanke hukuncin rabuwa dani. Auren mu bai d'auki lokaci da tsawo ba akayi komai aka gama, na tare a wani sashe na cikin gidan su Suraj. Mun shimfid'a rayuwa mai kyau da tsabta, a lokacin naga tsantsar soyayyah gurin Suraj har na sake gasgata lallai babu wata rana da zata zo har Suraj ya iya rabuwa dani. Matsala ta farko dana fara samu dashi shine, shi ya kasance ma'abocin yawo k'ashashen duniya ni kuma ina shekara ta biyun k'arshe a karatuna, bazan iya barin komai in dinga gantalin binshi guri guri ba, sannan a lokacin sauban ya tattaro duk ribar kud'ad'ena na gado da yake juya mun ya dawo mun dasu hannuna har da uwar kud'in ma. Da taimakon Suraj daya k'ara mun wasu kud'ad'en na bunk'asa harkar kasuwancina. Tsakanina da y'an gidan su Suraj muna huld'a amma baya baya bada yawa ko takura juna ba, na kanje sashen momy a kullum safiya mu gaisa da ita da alhaji, haka lokaci bayan lokaci har abinci nake dafawa mai kyau na kai musu, musamman alhaji dana lura yana son girki na sosai. Muna zaune lafiya kowa da baya sona ya had'iye k'iyayyar shi in aka d'auke matar mukhtar! (Yayan su na biyu) data ke matuk'ar kishi dani kamar mijinta nake aure. Tun dana fahimceta na sake jan jikina bana shiga harkarta, da yake ma wani lokacin tana bin mijinta Zaria gurin aikin shi sai nake mantawa da ita cikin jama'ar gidan. Nayi aure da shekaru uku amma ko b'atan wata ban tab'a yiba, hakan yana damun Suraj don yana bala'in son yara sai dai ya shanye ko a fuska bai tab'a nuna mun ba, a lokacin na sake fad'ad'a harkokin kasuwancina har k'asashen waje nake futa nayi order kaya. Tuni na gama karatunaa na ajiye kwalin a gefe. Andal ma ta gama karatun ta har an saka ranar aurenta. Lokacin bikin ya zo ban samu damar zuwa ba, saboda ya same ni cikin tashin hankalin rasuwar bango, jigo, k'ashin bayan wannan family wato tsohon ambassador Abdallah tofa, a sanadiyyar had'arin mota a hanyar shi ta dawowa daga Kano zuwa Abuja. Mutuwar wannan bawan Allah ta gigitani matuk'a daga ni har Suraj haka muka gigice muka d'imaucewa. Sannan mutuwarshi itace ta zamo matakin farko data fara bani matsala da mutanen gidan, saboda ganin idon shi ya kashe k'iyayya ta ga mutanen gidan wanda a bayan idon shi ta dawo. Tun a gurin rasuwar k'anwar matar muktar ta had'u da Suraj ta mato a sonshi, musamman data fahimci yana da kud'i fiye da kaf y'ay'an gidan. Sun had'a kai ita da yayarta inda suka fara kunno mun wuta ta gurin shi akan rashin haihuwa. A wannan gab'ar bansan ya suke so nayi ba saboda mutum bashi yake yiwa kanshi komai ba, haka Suraj ya b'ata ranshi yak'i bada goyon baya akan maganar auren da suke so mishi ya k'ara. Haka dai naci gaba da rayuwata cikin nutsuwa da godiyar ubangiji. Ban fasa kyautatawa kowa da zuciya d'aya a gidan ba har wata matsalar ta sake tasowa akan gyaran jikin da nakeyi, nan ma Suraj da yayen shi suka dakatar da komai, a wannan gab'ar hatta momy da Fatima basu goyi baya ba. Ban gama tserewa matsaloli a zamantakewata dasu ba har andal ta haihu muka tafi Sudan ganin ta ita da baby, haka mukayita santin baby boy kyakkyawa data samu. Bamu tafi ba saida Suraj ya cika ta da abun arzik'i, daga nan muka huce k'asashen da Suraj yafi harkokin kasuwancin shi muka sauke farali, muna sake tsananta addu'a akan samun rabo, bamu dawo ba sai bayan watanni. A lokacin na dawo da sauye sauye jikina kuma naga sauyi a tare da mutanen gidan kansu, sai dai ban zargi komai a raina ba har Allah ya yiwa yaron da andal ta haifa rasuwa. Suraj ya hana ni zuwa ban hanu ba saboda yadda mutuwar ta dake ni, haka na lallab'a shi na tafi bayan na yiwa mutanen gidan dana fahimci sun daina sake jiki dani ko abu na basu basa amfani dashi, kamar tsorona ma sukeyi sallama. Sai dai abinda yakan bani mamaki bai huce ganin yadda matar mukhtar take nan nan dani ba ita da k'anwarta mai son Suraj haleema, komai zasuyi a sashena duk daba wani damuwa nake da shirgin su ko shiga ciki ba. Yawanci lokutan da haleema take zo mun gab da dawowar Suraj ne, zata ci kwalliya gwargwadon wadda tasan ni da nake matarshi zanyi, sai dai a tsarin Suraj shi mutum ne da yake rayuwarshi kai tsaye, tun farkon zuwan haleema ya nuna mun sam baya son ganinta a tare dani, saboda a lokacin har office ta bishi ta karb'i no shi duk ba sa'a bata samu fuska daga Suraj ba, shine ta sauya salo. Ni kuma wanzuwarta tare dani yakan yimun shamaki da kulawar dana saba bashi a duk lokacin daya taso office. Wannan ya sake tunzura Suraj a ganin shi na zab'i mutanen waje a kanshi. A wannan rintsi da rashin fahimtar tafiya ta kama ni, har na tafi ba'a son Suraj ba, ko airport bai mun rakiya ba sai driver yasa ya kaini, ban damu ba saboda nasan koba komai zanyi abinda ya kamata a lokacin daya kamata ne, fushin shi kuma da zarar na dawo zai k'are komai ya huce. Tunda na sauka a Sudan ban zauna lafiya ba, ba wai ciwo nake ji a jikina ba amma sauye sauyen da nake ji kullum k'ara ta'azzara sukeyi, koda na ba andal labari shawara ta bani kai tsaye akan naje naga likita, ita ta kaini har asibitin da take aiki. Naga likita yayi mun tambayoyi k'arshe ya dangane damun scanning. Abun mamaki saiga sakamako ya futo da shaidar ciki na tsawon wata shidda a jikina kuma twins. Wannan labari yayi mana dad'i sosai nida k'awata, haka mukaita farin ciki da nuna godiyar mu ga Allah, tun kafun na bar Sudan nake neman layin Suraj in sanar dashi kyakkyawan albishir bana samun shi, nayi mamaki don bai tab'a dogon fushi dani akan komai ba, naci gaba da sharewa saboda nasan da zarar yaji labarin samuwar cikin jikina farin cikin da zai riski kanshi ciki zai d'auke mishi hankali har ya manta da fushin. Lokacin komawata gida yayi har da sati d'aya a kai ban koma ba, haka kurum nake jin kamar kar na tafi nayi ta zama tare da familyna da k'awata da aure ya sake nesanta mu da juna. Ranar da zan tafi har a airport muna sake jaddadawa juna rik'o da alk'awarin da muka d'auka........ Haka na tafi muna kewar juna. Lokacin dana dawo gidan Suraj baya nan, kuma koda naji dawowarshi na taho da nufin taryarshi k'in bani damar ganin shi yayi ya rufe kanshi a d'aki. Ina lissafe saida nayi kwana uku ban saka Suraj a idona ba bare na saka ran zai saurareni. Ga mamakina na biyu haleema tunda na dawo bata zo part d'ina ba ko sau d'aya, haka yayarta ma, kowa a gidan sai wani irin bahagon kallo yake mun. A rana ta hud'u Ina zaune cikin d'akin baccina na zabga tagumi na rasa me yake mun dad'i a duniya, hannuna rik'e da takardar sakamakon cikin dake jikina, naji an turo k'ofa an shigo da sauri na d'aga idona. K'anwar Suraj ce fateema fuska sam ba fara'a take kallona. Banyi k'asa a gwiwa ba na tashi ina mata sannu da zuwa duk da ta shigo mun har k'arshen d'aki ba tare da neman izini ba. Da sauri ta d'aga mun hannu tace nazo ana nema na a parlon momy na k'asa. Na tashi jiki a sanyaye gwiwa a salub'e na tafi, kusan gaba d'aya familyn gidan sun taru a parlon banda yaran su, kowa fuskarshi a d'aure babu mai alamun walwala, akan mutum biyu idanuna suka fara sauka, haleema da take kwance kamar matacciya ba inda yake motsi a jikinta duk ta rame, sai Suraj da yake tsaye hannun shi hard'e a k'irjin shi, yatsun hannun rik'e da habarshi ya sakaye idanun shi cikin farin glass. A nutse na k'arasa har gaban momy zan durk'usa a gabanta tayi saurin dakatar dani da fad'in, "dama kin daina wahalar da kanki wajen nuna mana ladabin banza da wofi kina cutar damu da hakan..... Abu d'aya kawai zan tambayeki shin da gaske kina da hannu a cikin ciwon haleema k'anwar Aysha?". Tambayar a bazata tazo mun, na kasa fahimtar takamaiman abinda suke nufi sai binsu da ido da kallo. A haka wani mutumi ya shigo sanye da kayan fatun namun daji, shima yayi ta maganganun da ban fahimta ba har a k'arshe ya nuna ni yana fad'in lallai lallai saina rabu da haleema wai ni nayi mata tsafi ta kwanta ciwo......... Haka Ina ji ina gani aka k'ulla mun sharrin abinda bansan ko meye ba, a k'arshe mutumin nan ya takura mun na karb'i wani ruwa a hannun shi na zubawa haleeema duk jikinta, sai gashi ta fara karkarwa tana yin wani irin abu har daga baya ta tashi zaune tana kuka tana tambayar a ina take. Kowa fuskarshi fal mamaki yake kallona in aka d'auke Suraj kad'ai daya kasa kallon kwayar idanuna. Haka na durk'ushe a gurin na kasa ma kowa magana ina gunshek'an kuka da rantsuwa dede da raina Ina sanar dasu gaskiyar niba matsafiya bace. Momy ce ta fara yin magana da cewa, "kin bani mamaki surayyah, a gidan nan mun yarda dake sai gashi a k'arshe kin ci amana, tunda muke a familyn mu bamu tab'a samun bara gurbi ba saboda duk munsan kanmu ke kad'ai ce bare.... Alhamdulillah da Allah yasa baki samu damar aiwatar da k'udurin kiba asirin ki ya tonu, kumaaa godiya ta biyu da bamu had'a zuri'a dake ba.... Suraj aiki ya rage naka ina fatan baka manta yadda mukayi da kai ba?". Har lokacin Suraj bai d'ago daga yadda yake ba, a tunanina yana tunanin bazan tab'a aikata abinda suke zargina a kai bane, sai na nufe shi Ina ganin shi kad'ai ya rage mun, sai dai koda na durk'usa a gaban shi na dafa k'afar shi da sauri ya warce k'afar har yana had'awa da hankad'a ni nayi baya na fad'i a gurin, kafun na dawo nutsuwata zafafan kalamanshi masu kama da digar ruwan dalma sun fara ratsa dodon kunnena, "na dad'e banyi aure ba saboda tsoron kaidi da sharrin ku mata..... ke kad'ai naga haske irin wanda ban tab'a gani tare da kowacce mace ba, naga yarda nutsuwa da kwanciyar hankali ashe duk na jabu ne, a k'arshe keda nake ganin a duniya bazan samu kamar kiba kin watsa k'asa a idon wannan yardar da nayi miki, kina neman ruguza mana familyn da muka gina shi da aminci da kyakkyawar fahimta..... Hak'ik'a nayi nadamar sanin ki a rayuwataaaa, ki tafi kawai bana son sake ganin fuskarki abadaaannn....". Lokaci d'aya tashin hankali ya diro mun wanda yasa na kasa gasgata shin da gaske ne duk miyagun maganganun nan suna futowa ne daga bakin sooraj? Na kasa yadda. Ban sake tabbatarwa ba saida yaje part d'inshi ya d'auko duk wasu kadarorina da takardun makarantata da suke hannun shi ya d'anka mun cikin hannuna. Jakar kayana dama tunda na dawo Sudan ban cire komai ciki ba itama ya d'auko mun ita a yadda take ya koreni daga gidan su yana sake tabbatar mun babu ni babu shi. Cikin dauriya da k'arfin gwiwa na dubi Suraj a harabar gidan su y'an aikin sun taru suna kallon abinda yake faruwa, don sake tabbatar da abinda nake gani a karo na uku nace, "tabbas zan tafi kamar yadda ka buk'ata sooraj, sai dai ba zan tafi da dakon nauyin auren ka ba......". A firgice raihana ta birkito zaune har littafin yana fad'uwa k'asa ta dafe kanta da hannunta tana fad'in, "aaaa'aaaaa auntieee". Yadda tayi d'in ya nuna kamar komai yana faruwa a kan idonta ne a lokacin. Khaleefa da barci ya fara d'aukan shi sautin maganarta tasa shi mik'ewa zaune yana kallonta....... *Kuyi hak'uri da jina shiru gaba d'aya kwana biyu ban samu zama ba sai yau, Ina godiya da jinjina gare ku masu bibiyar littattafan in-identical twins👍muna matuk'ar alfahari daku😍😍 k'auna mai tarin yawa* *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty four6️⃣4️⃣ "Are you okay?" Ya tambayeta yana kallonta, bata bashi amsa ba ta damk'e littafin a hannunta ta shiga kitchen tasha ruwa ta tsaya tana maida numfashi. Koda ta futo khaleefa yana zaune yana duba wayarshi, itama ta d'auki tata wayar ta duba time sai taga lokaci yaja da yawa, dab ake da kiran sallar subh. Abin mamaki ashe raba dare tayi tana karatu? Tattare yanata yanata tayi ta shige d'akinta, khaleefa ma d'akin nashi ya tafi. ***** zaune take gaban dressing mirrow d'aure da towel, powder ta shafa da wetlips ta zirara kwalli a idonta sannan ta shirya cikin dogon wando tight sai riga half bubu matching colour da wandon, ta sake gyara gashinta ta yafa madaidaicin gyale ta yane kanta zuwa kafad'un ta, tayi kyau na hak'ik'a cikin sauk'ak'k'en dressing d'inta. Cikin takun da yake bayyana asalin wacece ita ta futo daga d'akin, yadda ta tsammata khaleefa bai futo ba, hakan yasa ta nufi d'akin shi ta kwankwasa. Ya bata izini ta tura k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama, yana kwance ya k'udundune jikin shi gaba d'aya fuskarshi kad'ai ake gani. Tunda ta shigo ya kasa d'auke idon shi a kanta tamkar wadda ta shigo da sirrin magnet, ita kuwa kanta a k'asa ta k'arasa kusa dashi, nan ma saida ya lumshe ido yana shak'ar daddad'an k'amshin ta daya cika d'akin. Gaishe shi ta fara da tambayar jikin shi, ya amsa still yana kallonta yama kasa d'auke idon shi, ganinta yake kamar mutum ta daban sabuwa ba raihanan daya saba rayuwa da ita gida d'aya ba. "Na kawo maka breakfast d'inka nan?". Ta tambaye shi da murya mara amo. Nan ma khaleefa saida ya lumshe ido yana jin farmakin da muryar take kai mishi all over his body, yasan muddin yaci gaba da kallonta da jinta very close to him zata iya rufto mishi da ko wanne tunani bahagon tunani kanshi. "Ki taimaka mun da had'in ruwan wanka,,,, kada suyi zafi da yawa". Cikin amsar umarnin shi ta gyad'a mishi kai ta mik'e. Yanzun ma saida tayi ta santin d'akin wankan kafun ta aiwatar da abinda ya kaita ta futo. Yana kwance inda ta barshi ta futo ta fad'a mishi ta gama, ya gyad'a mata kai yana jiran ta k'arasa futa a d'akin saboda ba komai jikin shi sai boxer, wankan yake son shiga tun d'azu amma ya kasa tashi har Allah ya kawo ta. Har ta murda handle zata futa ya kira sunanta, "Raihana". Bata amsa ba amma ta juyo, "ki jirani a dinning few minute zan futo". Ta gyad'a mishi kai ta k'arasa fucewa. Yadda ya fad'a..... tana zaune a dinning rik'e da wayarta tana tab'a chat ya futo cikin shadda milk sai zabga k'amshi yake, Koda ta kalle shi suka had'a ido cute smile ya sake mata, itama ta mayar mishi da raddin nata daya bayyana hak'oranta farare tass a waje. Ya k'araso yaja kujerar da take fuskantarta ya zauna, ita tayi saving d'inshi sannan tayi saving kanta, suna karya kumallon amma ya kasa d'auke kanshi daga kanta, barin ma yatsun hannunta da sukayi maroon suka haska shiny skin hands d'inta,,,,, Gaba d'aya abincin bai huce rabin plate yaci ba yaji ya futa a ranshi, kwalliyar raihana ta yau ta fara sauya mishi yanayi daga na khaleefa zuwa na matured Abdallah...... Duk yadda yake son d'auke kanshi a kanta kasawa yayi, haka ya dinga kallonta kamar zai cinyeta d'anye. A rayuwar khaleefa yana son shiga irin wadda tayi a jikin mace, shiyasa yake ganinta local a duk lokacin da ta kirma wannan uban hijabin ko ta saka atamfa, gani yake kamar rashin wayewa ne yake sa take yi duk haka, amma yanzu daga yau ya fara fahimtar babu rashin wayewa ko d'aya a tare da raihana, komai tana yinshi da saninta ne..... Yak'i yayi da zuciyarshi ya yakice komai ya ajiye gefe ya tashi daga gurin ya koma parlour ya bud'e system d'inshi da take charging ya tsura ma pic d'in Ayman idanu, hoto ne daya turo mishi tun lokacin da yake karatu, abubuwa masu tarin yawa suka shiga dawo mishi cikin kanshi daki daki tun daga kan rabuwar su shiya taho karatu har kawo jiya da suka jima suna waya dashi suna tattauna batu irin wanda sukan jima basu tattauna shiba, matsalolin da suke kewaye da rayuwarsu data mahaifiyar su,,,,,, ga kuma Raihana....... Bayan ya gama zaman tunanin rufe computer daya kasa tab'uka komai cikinta yayi ya kalli sashen da raihana take aikin gyaran inda suka ci abinci. "Ki shirya zamu futa". Ya fad'a da muryar data b'oye asalin yanayin da yake ciki. Raihana hijab kawai ta zubo saman kayan jikinta ta futo rik'e da wayarta, kallo d'aya khaleefa ya mata ya d'auke kanshi yaci gaba da wayar da yake har ta rufe k'ofar tabi bayan shi suka fara tafiya shi kuma yana ci gaba da wayarshi cikin harshen jamus. Sunyi tafiya mai d'an tsayi kafun su tsaya a k'ofar wani gida, ya ciro wayarshi yayi magana ta minti uku zuwa hud'u ya ajiye wayar. Basu jima ba wani matashin saurayi Nigerian yazo ya bud'e musu k'ofa yana ma khaleefa magana da hausa, "Man sai yau Allah ya nufa kenan?". Raihana tana jin haka tasan abokin shine, khaleefa ya mik'a mishi hannu sun gaisa sannan itama ta russuna tana gaishe shi. "Au kema daga nan madame khaleefa?". Raihana tayi murmushi kanta a k'asa. Shi yayi musu iso har cikin gidan, tsarin ginin su ya banbanta da nasu khaleefa don wannan gidan yafi wanda suke ciki wadatar d'akuna da komai. Matarshi ta kawo musu abincin Nigeria daya sarrafu da kyau ga drinks data had'a duk na gargajiya wanda suka nuna dukkan alamun tasan da bak'uncin su. Muhammad sun gaisa da raihana da matar shi nadeeya, ba laifi itama tana da kirki ga nutsuwa, basu jima sosai ba don k'in cin komai sukayi sai ruwa har suka tashi zasu tafi. Nadeeya ta rako ta har bakin k'ofa tana mata godiya ita da Muhammad tare da Alk'awarin zuwa bada jimawa ba. Suka tafi kowa na farin ciki da ziyartar juna. Kamar yadda suka zo haka yanzun ma suka koma, sai dai raihana kasa hucewa gidanta tayi a lokacin da taga k'ofar yasmine, tayi zaton khaleefa zaice su shiga sai taga yayi gaba, ita kam tana son duba ta tunda jiya bata je mata ba gaba d'aya, "Ina son duba yasmine". Ta fad'a da d'an k'arfi tana bin bayan shi da sauri. "Ba zaki jeba, mijinta yana gida zai kula da ita". Ya bata amsa ba tare daya tsaya ba. "Don Allah Ina son na ganta". Ta fad'a bayan ta matsa kusa dashi kad'an, A dai dai lokacin Ahmad ya futo daga gidan shi, basu lura dashi ba kwata kwata. Khaleefa fasa bud'e gidan yayi (dama keyn yana gurinta) ya matso daf da ita yace, "okay zaki je ki fad'a musu ke baki da wanda yake buk'atar kulawarki kenan?". Zancen gaba d'aya a bai bai raihana taji shi, hakan yasa ta sake had'e fuskarta ta turo k'aramin bakinta gaba, "Eh ai ba wani abun zanyi maka ba a gidan.....". Yadda tayi da bakin kamar zata shagwob'e ba k'aramin tafiya tayi da tunanin shiba har ya fara shagala a kallonta , da sauri kuma kamar wanda ake gargad'a ya d'auke idon shi ya sake matsawa kusa har hucin numfashin shi na sauka ta saman fuskarta ya kamo tafin hannunta, laushin hannun ya kai sak'o na kai tsaye har cikin kwakwalwar shi. "Man a hanya kuke fa" Ahmad ya fad'a da d'an k'arfi yadda zasu jiyo shi yana had'awa da musu dariyar shak'iyan ci. Zare keyn gidan da yake hannunta khaleefa yayi yaja jikin shi baya da sauri ya nufi k'ofar gidan ba tare da ko waiwayen inda Ahmad yake ba. Raihana ma gaba d'aya jikinta yayi sanyi shiyasa ta janye k'udurin ta tabi bayan suka shige salin alin. Direct kitchen ta dire ta had'a musu simple recipe don daga ita har shi ba abinda suka ci a gidan nadeeya sai ruwa. Lokacin data gama bata tsammanin ma yana gidan, saboda haka a nutse ta shirya mishi abincin kan k'aramin table da yake tsakiyar parlon ta d'auki nata ta fara ci. . Tana cin abincin zuciyarta na hasaso mata khaleefa a lokacin daya matso gab da ita k'amshin turaren shi ya cika mata hanci tafff! Hucin numfashin shi na ci gaba da sauka a fuskarta kamar lokacin yake tsaye gabanta. Cokalin ta ajiye tare da sauke doguwar ajiyar zuciya. Bud'e k'ofar parlon akayi khaleefa ya shigo da kaya niki niki zai huce kitchen, daga inda take zaune ta yi mishi sannu da zuwa, koya amsa ko bai amsa bama oho.... "Raihana" da taji an kwala kira yasa ta mik'ewa tare da nufar kitchen d'in da sauri, ta shigo ya nuna mata nama da kifin daya zuba cikin fridge "kisan yadda zaki yi da wannan kada su lalace". Gyad'a mishi kai tayi, ya futa ita kuma ta shiga jera komai a inda yake, saida ta sauya kayan jikinta zuwa doguwar riga armless ta d'ora k'aramin hijab a sama sannan ta fara aikin ta. Tana gamawa ta d'ora da girkin dare, haka ta k'are kusan rabin yinin a kitchen tana aiki ranar, gashi tana da research da take son yi ta manta shap saida tayi kaca kaca da aiki a kitchen ta tuna. ****Da dare bayan ta had'awa khaleefa tray na abinci da shayin shi a dinning hucewa d'akinta tayi ta fara aikinta tun kafun bacci yaci k'arfin idonta. Bayan ta gama futar da ma'anar komai a littafi shiru tayi tana nazarin ta inda zata samu k'arin bayani, khaleefa ba b'angare d'aya suka karanta ba bare ta tambaye shi, gashi tun asali sunyi da meerah zasu had'u da k'arfe biyu a makaranta, tasan sunyi ta jiranta har sun gaji tunda cikin su bame no ta. Hijab ta d'ora saman kayan baccin jikinta ta futo parlon, yana zaune yana cin abinci. Saita k'arasa futowa ta samu gefe guda ta zauna, bai kalleta ba har ya gama cin abincin ya rufe sauran, ya tsiyaya shayi a glass cup yasha. Sai a lokacin ya maida hankalin shi kanta yasan duk yadda akayi akwai magana a bakinta, itama ganin ya gama saita futo da littafin hannunta daga hijab, "dama k'arin bayani nake so kamun, ban sani ba ko zaka gane". Mik'a mata hannu yayi, ta bashi littafin, saida ya gama dubawa sannan yace mata, "matso kusa". Matsawar tayi amma ba yadda zata dame shiba, ya fara mata bayani dalla dalla da harshe biyu don tafi ganewa. Yadda yake zuba bayani sai raihana ta saki baki tana kallon shi, sai taga ko lecturer da yake musu lecture albarka. "Raihana ba'a kaina zaki saka idon kiba". Khaleefa ya fad'a yana kallonta. Sunkunyar da kanta k'asa tayi cikin jin nauyin yadda ya kamata tana kallon shi hadda tafiya tunani.... Har ya k'arasa mata bayanin ya mik'a mata littafin bata daina mamakin shi a zuciyarta ba. "Kin fahimta kuwa?". Ya tambayeta. "Eh" ta bashi amsa kanta akan littafinta data karb'a a hannun shi. "Then explain". Ya fad'a bayan ya kwantar da kanshi baya ya lumshe idanun shi duka biyu. A nutse ta fara maimaita abinda ya fad'a dai dai gwargwadon fahimtarta. "Raihana kina da sharp brain, ki godewa Allah". "Har na kai ka? Kaida kayi mun bayanin abinda babu shi a cikin karatun ka, ba'a tab'a zaunar da kai an karanta maka ba.....". Murmushin gefen baki yayi yace, "toh ai in aka ce health ana magana akan gaba d'aya sassan jikin d'an Adam, ka biya karatu a d'auke shi kafun ka gama sauƙe numfashi is something different.... Zamu iya kiran shi baiwa irin wadda ba kowanne mutum Allah yake yiwa ba". "Toh aikuwa indai ni y'ar baiwa ce, kai kuma za'a iya kiran ka da asalin baiwar.....". Murmushi kawai yayi ba tare da ya sake ce mata komai ba. Itama had'a littafanta tayi ta mishi godiya da sallama ta huce d'akinta. ****A saudiyyah auntie ta duk'ufa tuk'uru tana addu'a babu dare babu rana kan Allah ya kawo mata sauk'i da rangwame, cikin harkokinta da al'amuran rayuwarta da yaranta gaba d'aya, more especially raihana da khaleefa, tana son mutanen nan su tsaida hankalin su guri d'aya su karb'i juna a yadda k'addara tazo ta had'a su, Sam bata son auren nan ya katse da sunan raihana zata futo ta auri Ayman. Wannan wani kwad'o ne dako bayan ranta bata fatan a had'a shi. Ranar data cika kwana biyar a k'asar ta futo daga masjid da dare tana tafiya taji an rik'e hannunta an kira sunanta, "surayyah". Kafun ta juya taji kamar tasan muryar. Koda ta juyo ido hud'u tayi da matar mukhtar (yayan su Suraj). Da sauri ta shanye al'ajabin ta na ganin matar tace, "hajiya lafiya?". "Surayyah kina nufin baki gane niba?". "Wata Surayyahn kike nema bayan wadda kuka kashe tun shekaru talatin da suka gabata? Malama sake mun hannu na huce....". Ganin bata da niyyar sakinta sai ta fizge hannun ta juya ta bar mata gurin, sauri sauri ta b'ace mata a zuciyarta tana jaddada lazim ma ta bar k'asar nan tunda har dangin Suraj sun fara ganinta. Ita kuwa fasa shiga masallacin tayi ta koma masauki sauri sauri, ta dinga kiran layin mukhtar baya picking, saida ta tsaida hankalinta ta jiyo ring d'in wayar na tashi cikin d'akin baccin su, ta k'arasa ta d'au wayar tare da dafe kanta da hannunta. Mukhtar yana shigowa ko zama bata barshi yayi ba ta tarye shi da maganar, "surayyah! Mukhtar yau naga surayyah da idona, da idona na ganta wallahi". Kama ta yayi ya zaunar da ita yace, "kinga ki nutsu tukun sai kiyi mun bayani yadda zan fahimta, kina nufin surayyah matar Suraj kika gani a k'asar nan?". "Eh wallahi naga surayyah matar Suraj da idona har munyi magana da ita". "Toh fah, Suraj ya tafi surgery Germany, ke kuma kinga surayyah da idon ki a nan, idan har Suraj yaji labari cewa surayyah tana nan, toh zai ajiye komai ya taho nan koda ba zai same taba, ke koda zai rasa hannun ma gaba d'aya k'arewar ciwo, Soo Ina ganin yadda za'ayi mu duk'ufa nemanta da kanmu ko zamu sameta.... Mtss! Koda yake neman me ma zamuyi mata bayan komai ya k'are tsakaninta da Suraj.....". . Matar shi tace, "ta ina komai ya k'are bayan kullum Suraj yana fad'in ta tafi mishi da wani abu mai daraja da muhimmanci a rayuwarshi,,,,,, mukhtar ko don farin cikin Suraj ya kamata mu nemi surayyah". Mukhtar yace, "haka ne kuma? Toh amma yanzu ta ina kike ganin zamu fara nemanta, k'asa sama da mutum dubu.....". Duk sunyi shiru kafun ta sake cewa, "Ina da wata shawara". ******Gaba d'aya cikin kwanakin da suka biyo baya raihana bata samu damar ci gaba da bibiyar labarin auntie ba, duk da kullum dashi take kwana take tashi a ranta, kullum ta shiga school bata samun lokacin kanta, haka da zarar ta dawo gida ma aikin gida ba zai barta ta nutsu ba. Khaleefa ma ta b'angaren shi kusan hakan ne, tuni andal ta karb'e ragamar aikin Suraj a hannun shi ta mik'awa Ahmad, don dama shine na biyun khaleefa a kwarewa, tunda suke surgery a asibitin ba'a tab'a samun matsala ba. Yauma kamar kullum raihana ta dawo school a gajiye, da yake yau da wuri ta futa kuma lecture d'aya sukayi shine har ta samu kanta, tayi tunanin shiga gidan Ahmad sai kuma ta tuna kamar khaleefa baya son taje kwana biyu, hakan yasa tayi shigewarta gida. Wanka kawai tayi tasha tea ta d'auki littafin auntie zata ci gaba da dubawa, yau ko girkin ba zatayi ba kowa ya hak'ura da yunwar cikin shi kamar yadda ta hak'ura da tata. Auntie taci gaba da cewa👇 "Ashe duk hasashen da nake kan tsanar da Suraj yake mun abun ya zarce tunanina, ban tab'a d'auka zai iya yanke igiyar aurena ko guda ba sai gashi ya yanke har uku akan abinda bansan hawa ba bansan sauka ba......". Da matuk'ar mugun sauri raihana ta ajiye littafin gefe ta tallabe kanta da hannunta bibbiyu, take idonta ya kawo ruwan hawaye..... Banda innalillahi babu abinda take maimaitawa a bakinta. Saida taci kuka ta gode Allah sannan ta d'auki littafin taci gaba da dubawa, "ko kad'an idona bai kawo hawaye ba, saboda zuciyata ta bushe a lokacin, haka duniyar ma ta fuce mun a rai ban k'iba nabi bayan iyayena, tun a lokacin na hak'ura na saddakar babu wani mai Amana da rik'on gaskiya daya rage a duniya, mutanen kirki sun k'are saina banza, fajirai majanunai da basa son abinda addinin islama zai ci gaba. Ki futa surayyah! Suraj ya dawo dani hayyacina ta sanadiyyar fad'in hakan cikin daka tsawa. A lokacin murmushi nayi na Isa har gaban shi nace, "Naga mutane iri iri a duniyaa, amma ban tab'a ganin mayaudari maci amanar k'auna irin kaba, ashe akwai ranar da zaka yi mun irin wannan butulcin? Ashe soyayyah ba tana nufin sadaukarwa da kyakkyawar fahimta ga juna ba?, Insha Allah soyayyata saita azabtar da kai ba zata tab'a bari ka huta a rayuwarka ba, kamar yadda Allah yayi alk'awarin jarrabar duk wanda ya saki matarshi cikin fushi, saki irin wanda kayi mun da zazzafar soyayyarta......". Cikin takaici Suraj yace dani, "soyayyarki ba zata tab'a azabtar dani ba saboda ban yaudare kiba, hasalima sai dai soyayyata ta azabtar dake, Ina sonka! Ina sonka! Ina sonka Suraj, wannan kalmar kin dinga maimaitata kenan har k'arshen numfashin ki.....". "Kamar yadda surayyah zata tafi maka da abu mai tsada da daraja da muhimmanci na rayuwarka.....". Na juya ga sauran mutanen gidan nace, "ban zalince kuba amma duk wanda yazo mun da sharrin tsafi ba zan tab'a yafe mishi ba abadaan.....". Wannan shine maganata da had'uwata ta k'arshe da mutanen gidan su Suraj Abdallah. Bazan ce mutanen gidan su Suraj sun zalince niba, saboda komai d'orawa sukayi daga samun fuska a gurin Suraj, dad'in dad'awa bansan abinda aka k'ulla a lokacin da nayi tafi gurin aminiya y'ar uwa a gareni wato andal,,,, sai dai koma meye nasan ya k'aru ne da fushin dana tafi na barshi yana yi..... Ko yanzu aka tambaye ni wanene Suraj abinda na sani game dashi zan fad'a, ya kasance bahago kuma baud'ad'd'e mai baud'ad'd'iyar fahimta da kasa fahimtar gaskiya cikin sauri....... Raihana kowanne d'an Adam tafe yake da ajizanci, nima ta b'angarena hakan ne, fushin zuciya yasa nayi alk'awari akan abinda ba hak'k'ina ba ni kad'ai, na taho da cikin su khaleefa, na haife su a inda ba'a iya gani ayi shiru ba har mutanen gari suna kallon su da kiran su da kalma mafi muni da had'ari wato *shegu*. A zahirin gaskiya tun kafun aje da nisa soyayyar Suraj ta fatattaka zuciyata ta hana na kalli kowanne namiji da sunan soyayyah, na kasa aure duk da nasan nida Suraj har abada sai gani sai hange daga nesa. Sai dai nayi gagarumin kuskure, na yiwa yaran k'arya da cewa mahaifin su ya mutu alhalin yana raye, sannan kowanne uba yana da hak'k'i akan yaran shi kamar yadda nake dashi amma shi na hana shi wannan hak'k'in,,,,, raihana ko yanzu Allah ya d'auki rayuwata zan tafi da soyayyar Suraj da kuma hak'k'in yaran shi dana tauye. Raihana naga abubuwa da yawa a tare dake irin wanda na jima ban gani a tare da wani mutum ba, shiyasa na yanke hukuncin had'a ki da gagarumin aikin bayyanawa khaleefa gaskiya cikin sauk'i ta yadda zai fahimta har su kai kansu ga mahaifin su don ni kam nayi alk'awarin bazan tab'a kaisu gare shi da kaina ba, sannan bazan gajiya da rok'on ki sadaukar mun da soyayyar da kike yiwa Ayman ta zama ta khaleefa ba, ki mantar dashi d'aci da bak'in ciki had'e da rad'ad'in daya yake cikin soyayyah irin wanda ya kurb'a, ki sashi yayi aman gubar daya sha da sunan soyayyah, ki nuna mishi ke tukuici ce kuma kyauta ga wahalar da yasha a rayuwar shi ta baya. A k'arshe Ina fatan ku kafa sabuwar daular soyayyar da babu irinta a gaba d'aya arewacin Nigeria. Allah yayi miki albarka daughter...... Your mother's ever surayyah Adam. (Dama ba kowanne labarin soyayyah ne yake k'arewa da abinda mutane suke so ba, yawancin soyayyar data cika bata k'arewa da kyau irin yanda zamu ga hak'oran mu a waje, misali kamar Laila da khaiz, Romeo da Juliet....... Kowacce soyayyah akwai k'alubale mai girma a cikinta, amma wadda ta girmi kowacce yanke alak'ar masoya take💓💓💓) *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty five 6️⃣5️⃣ Koda raihana ta gama karantawa shiru tayi tana tunanin komai daki daki cikin kwakwalwarta, bata tashi a gurin ba taji shigowar khaleefa gidan, ta duba lokaci da sauri gab ake da sallar magrib inda Allah ya taimaketa ma tana da sauran lokaci tasan bai fiya cin abinci a farkon dare ba, kamar yadda ba yaci tsakiyar dare, a tsarin rayuwar khaleefa komai nashi a tsare yake. Bathroom ta shige ta d'aura alwala ta futo ta shimfid'a darduma ta tada kabbarar sallah. Tana cikin sallar taji ana knocking k'ofarta, tasan khaleefa ne tunda dashi kad'ai take rayuwa a gidan, bai shigo ba har saida ta idar da sallah ta bud'e k'ofarta, sanye yake da jallabiyyah fara sol saboda tsabar yunwar da yake jima ya kasa tsayawa da k'afafun shi sai jingina yayi, tana bud'e k'ofar bai jira umarninta ba ya shige d'akin, (dama ya tsaya ne gudun kada ya shiga baisan a yanayin da zai same taba...) Raihana ta bashi hanya tana kallon yanayin shi, direct kan gadonta ya zauna ya had'a kanshi da gwiwa, ta k'arasa kusa tana tambayar, "kana lafiya kuwa?". "Abinci... Kawo mun abinci raihana yunwa nake ji kamar naci babu...". Shiru tayi tana kallon shi a ranta tace, "Toh kawai kaci babun mana....". Ta fad'a k'asa k'asa ba tare da tasan maganar zucin da take ta futo fili ba, ya d'ago da mamaki ya kalleta sai tace, "Babu abinci a gidan yau sai dai na dafa maka mafi sauk'i yanzu....". "Yaaa Salam! Meyasa yau? Ko shiryawa zaki shirya muje Eve Eno?". "Har na dafa fa, it will not take much time bari nazo....". Ta k'arasa fad'a tana juyawa da nufin futa... Batasan lokacin daya mik'e ba sai ji tayi kawai ya rik'o hannunta ta baya. Ta juyo tana kallon shi, ya marairaice mata fuska kamar zaiyi kuka, "put down your hijab kawai, cox I can't wait har sai kin dafa wani abu....". Cikin kwaikwayon salon da yayi magana raihana tace, "Ni bana jin zuwa ko'ina zaka iya tafiyarka kai kad'ai". Muryarshi k'asa k'asa yace, "kina d'aukan komai wasa, am serious wllh ji nake kamar zan fad'i". "Nafa ce kayi tafiyarka, me yasa ma sai dani". Ta fad'a cikin shagwob'a shagwob'a. "Saboda jikina babu k'arfi, in muka tafi tare zaki iya taro ni idan na tafi zan fad'i". Ya k'arasa fad'a yana sake hannunta hango hijab d'in nata can k'arshen bed. Da kanshi ya warware shi ya zura mata fuskar sama a k'asa (irin yadda tsofaffi sukeyi🤪) "Muje mana please Allah in na kasa tafiya zaki san yadda zakiyi dani". "Toh a haka zan tafi kuma.... kalli yadda kasa mun hijabin fa?". Ta sake fad'a cikin shagwob'a. Khaleefa jingina yayi da bango yana kallonta da lumsassun idanun shi, yama kasa bud'e bakin shi yace wani abu saboda tsabar yadda yake jinshi. Gaba d'aya ya sakankance zai dawo ya tarar ta gama abinci as usual, shiyasa ko lunch baiyi ba dama breakfast yau a gurguje yayi shi. Ganin da gaske zai iya kaiwa k'asan sai itama ta zama serious ta gyara hijab d'in suka futa. Inda Allah ya taimake su a farkon layin suka samu motar haya suka shiga. Ko a motar ma sai jujjuya kai yake har suka k'arasa inda zasu ya biya kud'in motar da katin shi suka futo. Bai zauna ba saida yayi order abincin da zasu ci. Suna zama aka gabatar musu da komai, aikuwa Bismillah kawai yayi ya fara cin abincin sauri sauri.. Bai lura da raihana bata ci komai ba saida ya kusa cinye rabin plate d'in gaban shi, ya kalleta sannan yace, "sorry ban tambaye ki abinda zaki ciba nayi order, me zaki ci". Girgiza mishi kai tayi, "Ni yunwata bata kai taka ba, zan iya jira har sai na dafa da kaina in mun koma gida". Shiru yayi yana nazarinta kafun ya k'arasa cin adadin wadda zai tsaida mishi yunwar da yake ji a lokacin, duk yadda yake matuk'ar jin dad'in abincin su yau yaci ne kad'ai alallalurati, sam jin abincin nasu yayi a wani bai bai, ba taste kamar ba'a yi shi da maggi ba. Banda yana matuk'ar jin yunwa ba abinda zai sashi cin abincin. Bayan ya gama sun futo suna tafiya ya fahimci raihana tana mishi dariya ciki ciki, kamar ya shareta sai kuma ya kasa had'iyewa ya dakata da tafiya ya tsare ta da idanu yace, "mahaukaci na zama kike mun dariya kuma?". Had'iye dariyarta tayi tana kallon shi kamar za tayi dariyan tace, "Man tunowa nayi fa d'azu kace wai in kazo fad'uwa na tare ka? Koda wane k'arfin.....". Ta k'arasa fad'a tana sakin sabuwar dariya. Shi kanshi dariyar yake yi saboda a lokacin yayi maganar ne bilhak'k'i da iya gaskiyar shi. Haka suka taru suna dariya mara sauti a gurin kafun khaleefa ya fara tsagaitawa yana kallonta da yadda dariyar ta bala'in sake futo da sirrin kyawunta. Ba tare daya ankara da abinda ya keyi ba cikin shagala a kallonta ya fara matsawa kusa har saida yaje daf sai saukar hannun shi kawai sukaji yana shafa siraran lab'b'an ta. Take ta had'iye dariyarta ta maida fuskarta guri d'aya tana kallon shi da jin yadda yake kewaya d'an yatsar shi saman lips d'inta, lokaci guda kuma tsigar jikinta ta fara zubewa. Shima sai lokacin ya lura da abinda yake yi ya koma baya cikin matuk'ar jin nauyinta yaci gaba da takawa, itama tabi bayan shi har inda zasu samu motar da zasu koma gida. Daga nan tafiyarsu taci gaba da kasancewa silently har suka k'arasa gida. ****Bayan ta gama shirinta na kwanciya bacci, addu'o'in ta tayi ta tofe duka kusurwowin d'akin, taja bargo ta rufe har kanta, hannunta ta kai ta shafa lips d'inta kamar yadda khaleefa yayi d'azu, take kuma murmushi ya sub'uce saman lab'b'an nata, ta sake k'udundune kanta a ciki. *****Shi kuwa khaleefa yana zaune yana operating system d'inshi moment d'insu na d'azu ya shiga dawo mishi, ya tuna saura k'iris ya aikata mummunan kuskuren da bazai tab'a iya yafewa kanshi ba.... Mtss! Yaja tsaki a fili yace, "Wai me yake k'ok'arin sauya kane? Man ya kamata ka kama kanka sam ba haka ya kamata ka mu'amulanceta ba". Ya k'arasa fad'a yana sake jan wani tsakin, ya rufe laptop d'in duka ya k'arasa hawa kan gadon ya kwanta ya rufe idon shi...... *Nigeria* Ayman ya futo cikin shirin futa office, kitchen ya shiga ya samu mama haleema tana ta k'ok'arin had'a mishi karin kumallo, tana ganin shi ta fad'ad'a fara'ar fuskarta tace, "ba dai har ka futo ba, yau na makara kaga shayin kawai na dafa abincin bai kammalu ba, gashi kai baka iya cin bread ba bare ka had'a da tea, in kuma kana da sauran lokaci mintuna k'alilan ya rage na gama". Fuskarshi fad'ad'e da fara'a yace, "kada ki damu mama zan sha iya tea d'in ma in naje office saina samu wani abu naci insha Allah". Mama haleema tace, "aini bana son naji kace zaka karya a office d'in nan Ayman, saboda ba karyawan kake yiba saika kawo uzurin aiki yasha kanka, da dai ka bari na k'arasa ko tafiya dashi ma sai kayi, indai baso kake kuma doctor surayyah taci tara taba in ta samu d'an amanarta ciki fal yunwa". Dariya ya sake yi yace, "kada ki damu had'a mun shayin kawai, ko gaisawa ma ba muyi ba". Ya fad'a yana durk'usawa har k'asa ya fara gaisheta, ta amsa tana kiciniyar had'a mishi shayin sauri sauri tana sake jaddada "Allah daka jira kaga Amanar ka auntie ta bani, in ta same ka da yunwa naci Amana kenan....". Dariya ya sake yi ya karb'a shayin yana sake cewa, "ba zata gani ba sai dai ma taga nayi k'iba da kumatu". Duka sukayi dariya, Ayman dai yana daurewa ne kawai amma cike yake da kewar mahaifiyarshi, ba zaice mama haleema bata k'ok'ari ba, itama tana iya nata banda rauni na shekaru daya tab'a ta, amma lallai auntie bata tab'a bari ya futa war haka bai karya ba har ranar aiki kuwa. Haka dai ya gama lallab'awa ya fuce a gidan. Da yamma ya taso office yana driving yana bin wak'ar balaraben mawak'in nan maheer Zayn, Yana son zuwa duba su iya yau ko don ya rage zaman kad'aici da tunani a gida. Sai dai ba zai tafi musu haka ba, hakan yasa ya tsaya a store d'in da yake kan hanyarshi ya musu shopping na kayan ciye ciye dai dai gwargwado. Ya shiga anguwar yana tafe a hankali yana gaisawa da mutane har ya k'arasa k'ofar gidan. Da malam ya fara cin karo a k'ofar gidan tare da bak'i, bayan yayi parking ya futo ya k'arasa suka gaisa da malam da bak'in shi sannan ya shiga gidan. Iya tana zaune a k'ofar d'akinta tana aikin tuk'a tuwo, baki kawai ta saki tana kallon shi har ya k'araso kusa da ita ya zauna, "wannan kallon fa kamar kin fara rasa idanun ki?". Ya fad'a da sigar zolaya. "Kaci gidan ku kaida rasa idanun, yo ba dole na kalle kaba kaida kayi mana yajin aiki kamar mun yi maka kashi a gado". Murmushi yayi yace, "yajin aiki sai kace wasu gwamnati? Hutu naje yanzu kuma na dawo, gashi nazo ma a dai dai". Ya fad'a yana nuna tukunyar tuwon gabanta. "Aifa gashi na gani". Ta fad'a tana dariya, shima dariyar yayi suka gaisa yaji lafiyarsu ita da malam sannan ya bata kayan daya taho musu dashi. Ta karb'a tana mishi godiya da sanya albarka. Sunci gaba da hirar su har aka kira sallar magrib malam ya shigo suka d'aura alwala tare suka huce masallaci. Basu dawo gidan ba saida sukayi sallar isha'i. A parlon iya suka zauna suna tab'a hirar su shida malam inda yake tambayar yaushe zaiyi aure, yayi murmushi yace, "mai ran k'arfe da sauran lokaci". "Kullum haka kake cewa toh Allah yasa muna da rabon gani". "Insha Allah da ranku da lafiyarku malam, to su waye ma mad'aura auren?". "Wanda Allah ya d'orawa duk wani hak'k'i a kanku mana, ko baka fatan ganin su a rayuwarka....?". Ayman ya gyara zama yace, "malam su waye hakan kenan? Dama muna da wasu a hak'k'u bayan ku". Malam yace, "kwarai kuwa, wanda suke da hak'k'i fiye damu ma, in lokaci yayi kuma zaka gansu". Ayman yayi shiru yana nazari kafun ya sake cewa, "toh Allah ya bamu ikon gani". Malam yace, "ameen". A haka iya ta same su ta kawo musu tuwon data tuk'a miyar zogale suka fara ci Ayman na zuba mata santi. Yaci da yawa kuwa don saida yaji kamar wanda yake ci zai dawo mishi ta hanci sannan ya hak'ura. Ranar bai bar gidan ba sai wajen goma na daree, yana zuwa gida shirin kwanciya bacci kawai yayi ya kwanta,sai dai bacci yak'i yiwuwa sai tunane tunanen duniya. Mik'ewa yayi zaune ya kunna hasken d'akin ya d'auko wayarshi ya fara neman layin auntie don ita kad'ai yake rab'a yaji farin ciki a rayuwarshi...... Tana fara ringing ta d'auka, kamar yana gabanta ya fara da cewa, "I miss you mom, yaushe zaki dawo neee". Daga ta cikin wayar tace, "Sai ranar daka girma ka daina shagwob'a". "Haba don Allah ni wace shagwob'a kuma nayi? Mom please idan baki dawo cikin satin nan ba zan ajiye komai na biyo ki...". Murmushi tayi tace, "Ayman so kake na taho ban gama rok'ar maka abinda nake son ka samu a rayuwarka ba". "Auntie tunda kika haife mu kike mana addu'a baki tab'a gajiyawa ba, hakan yasa rayuwarmu ta tashi cikin godiyar Allah, toh meye bamu samu ba da kike mana rok'on shi a saudiyyah har wannan lokacin?". "Cewa zakayi meye baka samu ba don shi d'an uwan ka ya samu! Matar aure ta gari wadda zata soka ta kyautata maka gwargwadon iyawarta...". Shiru yayi ya kasa cewa komai har auntien ta k'ara cewa, "yanzu dai insha Allah Ina tafe cikin kwanaki biyu masu zuwa....". Da sauri yace, "da gaske!". "Da gaske insha Allah". Cikin farin ciki yace, "I love you Mom! Sai yanzu zan iya bacci da naji wannan daddad'an albishir d'in, Allah ya kawo ki lafiya.....". "Daina saurin murna Ina dawowa a fai fai zan kasa ka ko za'a samu wadda zata d'auka tunda kai har yanzu ka kasa tsaida ranka guri d'aya, so be ready...." Ta k'arasa fad'a tana d'an dariya k'asa k'asa. Cikin zallar sangarta yace, "kema haka zaki ce ko? Haka fa malam ma d'azu ya takura mun..... Shikenan tunda kun daina sona....". "Ohhh! Kaina bisa wuyana, nasan kai d'in mai farin jini ne kona kasa ka a fai fai ma ba mai d'auka". "Anya kuwa yabo na kikayi Auntie.....". Dariya suka sanya kusan a tare. Sun jima suna hirar su kafun suyi sallama ya ajiye wayar yana murmushi, a haka bacci b'arawo ya sad'ad'd'afo ya sace shi. Cikin kwana ki biyun kuwa doctor surayyah ta dawo, lokacin Ayman yana office kiran wayarta ya same shi. Da matuk'ar farin ciki ya d'aga yana fad'in, "welcome back lovely Auntiena". "Thank you son! Mintuna goma na baka". "Gani nan zuwa insha Allah". Ya fad'a tare da ajiye wayar. Uzuri ya bayar a rubuce ya futa daga companyn gaba d'aya. Cikin mintuna k'alilan ya Isa airport ya taryo ta. ****Suna tafe a mota yana ta bata labarin yadda yayi kewarta har suka k'arasa gida, mama haleema tayi mamakin ganin auntien a bazata ta kuma ji dad'i kwarai. Nan da nan ta shiga shirya mata abinci da abun sha iri iri a gabanta, saboda tsabar gajiya doctor surayyah kasa cin komai tayi, don ta taho da tarin bacci a idonta. Koda da dare yayi ta samu tasha yoghurt mai sanyi da dambun naman da Ayman ya siyo mata, bata tsaya sallama da kowa ba ta shige d'akinta sai bacci. Washe gari abokan business da aikinta suka dinga zuwa mata sannu da zuwa, haka sauran mutanen gari ma da take mak'otaka dasu duk sun turo mata da sak'on barka da zuwa wasu kuma sunzo da kansu. Da daren ranar su malam ma suka zo, suka jima suna hira har malam ya samu damar mata tuni akan maganar daya tab'a yi mata game da y'an uwan mahaifin su khaleefa, ya had'a da mata nasihar da baya gajiyawa a kullum idan ya samu zama da ita, a wannan karon sosai naseehar ta shige ta har da hawaye, a lokacin ta fad'awa malam ita tuni tayi nadama ta hak'ura, ta fahimci abinda ya dinga nusarshe da ita tsawon shekaru, sai dai ta d'anka aikin fallasa gaskiya a hannun mafi hikima da k'uruciyar da zata iya fuskantar k'uruciya y'ar uwarta ta bayyana mata komai yadda zata fahimta. Malam yaji dad'i ya dinga sanya mata albarka da mata fatan gamawa da duniya lahira, da zasu tafi ta had'a musu tsarabar duk data siyo da sunan su da kuma sak'on khaleefa da raihana gare su. Washe garin ranar data dawo da safe Ayman zai futa office ta bashi dabino dasu bagaruwa da sauran kayan chocolate tace ya biya ta gidan su raihana ya kaiwa su hibba. Baiyi mata musu ba ya karb'a zai cika umarninta, a zuciyarshi yana ayyana in ba don ita data Isa dashi ba, baya jin wani zai sashi yaje k'ofar gidan su raihana a halin da yake ciki yanzun. Tsaye yayi a k'ofar gidan yana tuna abubuwa masu girma da nauyi gami da rad'ad'i a cikin zuciya,,,,, cikin irin tunanin ya tuna had'uwar shi ta k'arshe da raihana, ranar da taje k'unshi Zahra saloon har ma ta soya mishi wainar fulawa yaci a gidan iya. Wata zazzafar iska ya furzar daga bakin shi sannan ya k'arasa k'ofar gidan ya kwankwasa, minti kad'an al'ameen yazo ya bud'e, yaron yana ganin shi ya russuna yana gaishe shi, Ayman ya amsa yana d'orawa da tambayar dalilin da yasa yau baije school ba cikin kulawa, (kamar abinda aka tura shi kenan🤔). "Bani da lafiya". Yaron ya bashi amsa. "Ayyah Allah ya sauwak'e". Ya mik'a mishi jakar hannun shi, "gashi inji auntie ka kaiwa maman ku". Al'ameen ya karb'a bayan ya durk'usa. "Ka gaishe dasu jidderh". Ya k'ara fad'a kafun ya tsallaka ya koma inda ya parking motar shi. *****Al'ameen yana shiga ya mik'awa ummie da take zaune a parlor jakar, "ummie wai gashi inji auntien su yaya khaleefa?". Cikin rashin fahimta ummie tace, "wane khaleefan kuma?". "Mijin auntie raihana fa". "Ohh! Shiya kawo". "Kae! Ummie Yaya khaleefa ya dawo kuma ba muga auntie raihana ba....Yaya Ayman ne ya kawo yace ma a gaishe dasu jidderh". Ummie da mamaki ta fara duba jakar, tsarabar saudiyyah cikin k'atuwar leda daban, sai ragowar kayan da k'aramar takarda anyi rubutu jikinta. Warware takardar tayi ta fara karantawa, "socks da sweeter naki ne hibbatullah, (Kamar yadda kika fad'a a waya, hak'ik'a gangar jikin auntyn ku raihana yayi nesa daku, amma zuciyoyin ku suna kusa da juna) ragowar chocolate naku ne keda su al'ameen gaba d'aya, nasan kunyi kewar auntien ku sosai kamar yadda kuke yawan fad'a a waya, shiyasa na had'a da sako muku kayan snacks data girka da hannunta ba tare da saninta ba, Allah yasa lokacin da auntie zata k'araso basu lalace ba, koda yake in sun lalace ma zaku ji k'amshinta da girkinta da kukayi missing, a k'arshe ku gaishe da ummie sosai... Ku fad'a mata raihana tayi kewarta da yawa....". Murmushi tayi bayan gama karanta takardar ta mik'awa al'ameen da yake ta tambayarta menene a jiki. Ita Kuma taci gaba da duba kayan, koda ta warware kayan snacks d'in meat pie ne da doughnut sai cake, duk da ba suyi komai ba tasan sun sauya d'and'ano, cake d'in ta gutsira ta kai bakinta idonta na cikowa da ruwan hawaye..... Maganar zuci na futowa fili ba tare da saninta ba, "hak'ik'a nayi kewarki raihana, Ina fatan kina cikin k'oshin lafiya kamar yadda kike yawan fad'a a waya". Tasa tafin hannunta tana share hawayen cikin fakar numfashin al'ameen da hankalin shi yake can kan kayan da khaleefa ya aiko musu dashi da takardar. Karb'e jakar tayi a hannun shi ta maida komai ciki tace, "Bari a fara nunawa abban ku tukun sai kuyi duk yadda kuke so dashi ko...". Al'ameen cikin farin ciki yace, "toh, ummie kinga irin wannan chocolate d'in da Abba ya tab'a kawo mana? Hadda shi a ciki fa Yaya khaleefa ya aiko mana". "Na gani Allah ya saka mishi da alkhairy". Ta fad'a tana mik'ewa ta bar gurin. ****Da dare tana zaune kusa da Abban suna hira take bashi labarin sak'on da auntie ta kawo musu, ta k'arasa fad'a tana jawo jakar da take gefe d'aya cikin d'akin. "Allah sarki kunyi mata godiya?". Abba ya k'are da tambaya a lokacin da yake ganin kayan da ummie take d'agawa, "A'a bari nayi ka dawo in na nuna maka kayan sai naje koda dare ne na mata godiya da sannu da zuwa.....". "Ai ya kamata kam wannan uban kayan sweet kamar za'a bud'e shop". Ummie tana dariya tace, "wannan kuma aikin d'anka mijin y'ar". "Wa kenan kinsan yaran ba d'aya na aurar ba". Wata dariyar ta sake yi tace, "toh first Born nake nufi". "A'a raihana, dama doctor Germany taje ba saudiyyah ba?". Ya tambaya. "Ina ganin duka k'asashen biyu taje". Ta k'arasa da d'auko mishi cake d'in da taci da rana cikin tsarabar. "Wannan ku tayiwa tafiyar ma kawai... Hadda cake?". Abba ya sake fad'a yana kallon cake d'in hannunta da take mik'o mishi. Ummie tace, "Kai dai karb'a kaci mana". "Kin manta ni bana cin kayan zak'i". "Wannan ko da zallar sugar aka had'a ba zaka kasa ciba, kuma in kaci ba zai saka tashin zuciya ba cox yazo ne daga hannun wadda ita kad'ai take yi maka shi kaci a duniya.....". Tun kafun ta gama fad'a ya karb'e ledar cake d'in ya fara warwarewa yasa a bakin shi ya tauna..... Ummie tana dariya tace, "ka gane daga hannun wadda yazo ne ka hau ci". "Raihana! Ita kad'ai ce ta dangaci abinda kika lissafa". Tayi murmushi "haka ne kam bata San ma mijinta ya aiko dashi cikin kaya ba". "Allah sarki raihana Allah ya albarkaci rayuwarsu ita da mijinta". Ummie da take gefe tace ameen". Sunyi shiru kafun ummie ta tambayeshi, "yanzu in ka gama sai mu tafi ko?". "Alright ba damuwa zuwa anjima saina kai ki?". Barka da zagayowar sabuwar shekara, fatan Allah ya had'a mu da alkhairan dake cikinta ameen.... Happie new year once again to follower's of in-identical twins.... Wish you guy's all de best😍 *Ga masu tamtama akan saki da ciki👉🏻 a shari'ar musulunci idan aka saki mace da ciki saki d'aya, biyu, uku toh saki yayi, koda zata haihu a take a gurin babu abinda zai k'ara maida wannan auren tunda har ya sake ta sakin daba kome, idan kuma saki d'aya ko biyu ne kad'ai, zai iya maida ita kafun ta haihu, idan kuma akayi sakin koda da minti d'aya ne ta haihu, toh sai an sake d'aura wani auren sakin ya warware wancan kenan. a JARUMAR UWA Suraj ya saki surayyaa sakin daba kome da ciki, auren su ya haramta har abada...... A k'aramin sanina fa amma* Masu comment Ina godiya da jinjina👍👍👍😊 fatan Allah ya bar k'auna💓, Ina yinku fiye da yadda kuke yina. *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty six6️⃣6️⃣ Da dare Abba ya tafi kai ummie yiwa auntie barka da zuwa da godiya har gida, amma fa bayan an jawa su al'ameen kunne banda rigima tunda su aka bari a gidan. Ko futowa a cikin motar baiyi ba sai ummie ce ta shiga gidan, karo na farko data tab'a zuwa gurin surayyahn. Wani matashi da yake musu aikace aikacen gida da aike shi ya yiwa ummie jagora har parlon auntien. A lokacin tana operating computer ta ita kad'ai mama haleema yau ba a nan zata kwana ba, Ayman kuma ya futa gyaran kai da aski zai dawo. Da farin ciki ta taryi ummien, ta shiga suka gaisa ta mata sannu da zuwa, tana son tambayar yata baro su khaleefan sai dai tana kunyar kada aga tayi hakan ne saboda y'arta. Kamar surayyah tasan abinda yake ranta, haka ta dinga bata labarin raihanan da kirkinta, ita dai ummie ta kanyi murmushi, data tashi tafiya ta ajiye mata cooler lafiyayyen dambun shinkafa data shirya da wadatattun kayan lambu. Aikuwa auntien taji dad'i tayi ta mata godiya, har bakin k'ofa ta rakata suka gaisa da Abban sannan sukayi sallama ta tafi. ***Kwana uku da dawowarta Ayman yana bin takunta kamar wadda ta satar mishi wani abu, gaba d'aya ya daina futa office sai a late, ya kasa ya tsare so yake kawai yaji tace zata futa aiki coz yayi alk'awarin ta daina futa office d'in nan, tayi aiki tuk'uru tun suna yara, yanzun kuma lokaci yazo daya kamata ta hak'urar wa ranta aikin ta zauna gida ta huta kamar kowacce mace. Ganin har an shiga weekend bata ce zata futa aiki ba saiya saki ranshi da tunanin ta yadda da maganar da suka yi lokacin data kwanta ciwo asibiti. *Germany* Zaune yake a office d'inshi ya kwantar da kanshi cikin kujerar da yake zaune, k'afafun shi biyu zube kan table dake gaban shi, tun d'azu yake son tashi yaci wani abu kafun shigarshi theatre sai dai yana tunanin me ma zaici yaji d'and'anon shi irin yadda yake so a bakin shi. A haka Muhammad ya turo k'ofar offishin ya shigo bakin shi d'auke da sallama, Ahmad biye dashi ksmar makaho da d'an jagora, khaleefa sam baiji shigowar ko d'aya daga cikin suba bare sallamar da sukayi har saida Muhammad yayi shaking k'afafun shi. Ya bud'e ido yana kallon shi bayan ya janye k'afar ya maida ita k'asa. "Kana son wasa da basudaniyar likitan nan kamar yadda kake son wasa da cikin ka...". Ahmad ya d'auki zancen bayan Muhammad ya aje, "ai shiyasa bata sassauta mishi ko magana zatayi dashi saita fara d'aure fuskarta tam tukun, yanzu dai kasan da ita ta ganka yadda muka shigo muka same ka ba abinda zai hana kasha fad'a ko?....". Squeezing fuskarshi yayi yaja tsaki a fili yace, "Mtss! Am not feeling okay gaba d'aya kunzo ku kuma zaku k'ara mun da maganar ku....". Muhammad yace, "Then why not ka tafi gida tunda komai d'an lafiya ne". "Ashe kuwa zai dawwama a gidan don kullum a haka yake....". Ahmad ya fad'a yana kallon shi. Muhammad ya sake cewa, "kuma fa hakane, lallai Ahmad kasan khaleefa farin sani ni kaina na fara noticing hargitsewar shi cikin watan nan gaba d'aya". "Cikin watan nan kad'ai kaga hakan? Ai man ya hargitse tun wata d'aya saura mu kammala karatun mu.... Koda yake ya d'an samu nutsuwa kad'an farkon dawowar mu..... Duk da yanzun wata sabuwar matsalar ce daban take neman damula mishi lissafin shi.....". "Ayyah Soo sorry man! Komai yayi farko yana da k'arshe haka komai yayi zafi maganin shi Allah, nasan ka sani but ina sake maka tuni da sake mik'a lamuran ka gare shi". Muhammad ya fad'a cikin kulawa. Murmushi Ahmad yayi ya tattara nutsuwarshi rankatakaf ga khaleefan yace, "wannan matsalar tasha banban da irin abinda kake tunani Muhammad, saboda a yanzun khaleefa yana ta yak'i ne da zuciyarshi da gangar jikin shi kan abinda suke sooo, am i right?". Ya k'are maganar da sigar tambaya yana d'auke idon shi daga kallon tsakiyar idanun khaleefa da yake aiko mishi da sak'on gargad'i ta ciki, tea ya tsiyaya a k'aramin plask da yazo dashi cikin funjali ya kai bakin shi ya fara sipping. Muhammad kam cikin jinjina girman k'arfin halin khaleefan yace, "kace kai match ka taro... Akan wane dalilin ma zaka hukunta kanka da mafi zafi da rad'ad'in hukunci?". Khaleefa da yake kallon Ahmad warce plask d'in shayin shi yayi ganin zai shanye mishi tea d'in don sai cika k'aramin cup yake yana shanyewa sauri sauri don salon mugunta.... "A'a rowa kuma zaka fara?". Ahmad ya fad'a yana kallon shi. "Ehh". Ya bashi amsa fuska sam ba annuri. "Toh ai bani zaka yiwa rowar ba tunda Muhammad ne bai shaba". Kallon Muhammad d'in yayi, "Kai malam baka sha tea a gidan kaba yau kafun ka futo?". Da son kunna shi Muhammad yace, "na sha amma wannan d'in ma zansha tunda har naga kana rowar shi nasan zai zama na daban ne....". "Matsa shi ya maka aman wanda yasha don ya shanye hadda rabon ka". Basu iya daurewa ba su duka biyun saida suka mishi dariya, abinda ya sake tunzira shi kenan, ya mik'e yana nuna musu k'ofa, "na fahimci kun cika cikin ku shiyasa kuka zo nan ku k'arar da kuzarin ku gurin dariya kamar shi aka d'auke ku ku aiwatar.... Toh office d'ina baiyi kama da physiatric ba you can silently move out....". Ahmad kam wata dariyar khaleefa ya sake bashi, shi in yaga ya zage yana irin wannan maganar da iya gaskiyarshi abun dariya had'e da mamaki yake bashi, sam d'abi'un shi na yanzu ba suyi kama dana asalin Abdallah Suraj daya sani shekarun baya ba, da gaske yana cikin damuwa ta gasken gaske saboda ya rarraba kwakwalwar shi da tunanin shi rukuni rukuni yasa yake misbehaving haka, kuma a hakan so yake lallai sai ya nuna babu wani abu tare dashi. ata b'angaren Muhammad kuwa shiru yayi yana nazarin khaleefa yana sake tabbatar da gaskiyar abinda Ahmad ya fad'a a kanshi, shiyasa baici gaba da dariyar ba. Kafun suyi wani kwakkwaran motsi akayi knocking k'ofar, "Come in". Khaleefa ya fad'a cikin bada umarni. Ta tura k'ofar offishin ta shigo da sallama, duk suka zuba mata ido lokaci d'aya kuma suka tashi tsaye bayan sun shiga taitayin su. "Dama office yayi kama da gurin had'a majalisar hira....". Dukan su shiru sukayi kafun Ahmad yace, "sorry doctor". "Oya kowa ya koma bakin aikin shi". Babu musu duk suka d'auka hanyar futa, har Muhammad ya murd'a handle ta dakatar dashi ta hanyar kiran sunan Ahmad, "zaku tafi X-Ray tare da mutumin da zaka yiwa theatre jibi, yana jiran ka a offishin ka". Gyad'a mata kai yayi cikin karb'ar umarninta ya fuce, shi kuma Muhammad ya d'auki excuse ya koma gurin khaleefa yana mishi magana k'asa k'asa yadda ba zata jiyo ba, "Babu abinda ya kai yak'i da abinda kake so a zuciya wahala, kai gara ka yak'i maza d'ari a filin daga daka ce zakayi yak'i da zuciyarka akan abinda take soooo... So please man just give up and stop deceiving yourself okay...". Gyad'awa Muhammad kai yayi don ya nuna mishi ya gamsu. Bayan futar Muhammad komawa yayi ya zauna itama taja seat ta zauna tana sake karantar yanayin shi, "Ga yunwa, ga gajiya, ga rashin bacci da damuwa, rashin kwanciyar hankali duk a tare da kai! Taya zaka iya fuskantar aikin gaban ka har kayi abinda ya kamata, farkon fara koyon aikin ka da lokacin daka fara aiki mutum ne kai mai aiki tuk'uru ba wasa, amma yanzu a hankali ka sukurkuce ka koma kana buk'atar kulawar likita kaima,,,,, bare a d'ora maka alhakin kulawa da wani, shin menene ainahin gundarin matsalar ka a rayuwa Abdallah?....." Tunda ta fara magana kanshi yake k'asa bai yarda ya d'ago ba har ta dire, jikin shine ya sake yin sanyi, kwantaccen sautin data yi amfani dashi gurin mishi magana yasa shi jinta kamar mahwifiyar shi. "Ina tambayarkane yanzun ba'a matsayin likita abokiyar aiki ba, sai a matsayin uwa da take da y'ay'a take jinka kamar d'aya daga cikin su". Ta sake fad'a tana sake nazarin shi, Shirun dai ya sake biyo baya daga ta b'angaren shi. Fahimtar da gaske ba zaice komai ba yasa tace, "shikenan! Da yamma in ka tashi tafiya gida ka same ni a office kafun ka huce...". Gyad'a mata kai yayi ta mik'e zata futa, har ta kai k'ofa ta tsaya ta sake tuna mishi, "kada ka manta". Yanzun ma baiyi magana ba sai kai daya gyad'a. *Bayan wasu mintuna* Ahmad ne yake tafiya cikin ward d'in sauri sauri kamar yayi fiffike ya tashi sama, ba don kada ya runtuma a guje mutanen gurin su d'auka bashi da hankali ba da aguje zai isa gurin khaleefa ya sanar dashi abinda ya gani ra'ayal ayn yanzu yanzun nan. Yana tafe tana bin bayan shi itama ba gajiyawa, yawan adadin saurin shi, yawan adadin nata saurin itama, yana kama handle na k'ofar offishin khaleefa zai murd'a ta dakatar dashi ta hanyar riga shi d'ora nata hannun, da mamaki ya tsaya yana kallonta kafun ya tambayeta, "akwai matsala ne doctor?". "Babbah ma kuwa! Wannan amanar ban baka ita don ka bud'e ta ga kowa ba yanzun, biyoni office d'ina". Jikin shine yaji yayi sanyi, bashi da zab'i sai bin bayanta don masu iya magana suka ce ta inda aka hau, ta nan ake sauka,,,,, A office d'inta kuwa Ahmad tattare gaba d'aya hankalin shi yayi gareta yana sauraron jawabinta, "da farko zan fara da tabbatar maka abinda kayi zato har kake sauri ka tabbatarwa abokin ka khaleefa, patient d'in dana d'anka amanar kula dashi a hannun ka, Suraj Abdallah tofa ba kowa bane face mahaifin abokin ka khaleefa". Duk da Ahmad yayi tunanin hakan saida yaji shock da doctor andal ta sake tabbatar mishi, "khaleefa dai doctor?". cikin sake tabbatar mishi tace, "kwarai kuwa khaleefa dai da muka sani ni da kai, da farko ai shina dank'awa ragamar kula da mahaifin shi, toh amma daga baya due to wasu dalilai dani kad'ai na barwa raina sani saina mai dashi hannun ka, Ina so kamar yadda na daure raina kaima ka daure naka, ka gargad'i bakin ka kar kace komai gare shi daga yanzun har zuwa lokacin da zaka gama bawa patient d'inka kulawa ta musamman ya samu lafiya sosai.... Ina fatan ka fahimci abinda nake nufi?". Ahmad cikin ladabi yace, "eh! Insha Allah khaleefa ba zaiji komai daga abinda na sani ba har sai bayan komai da kika tsara ya kammala yadda kike so". Tace, "gud! nagode sai ka jini". Daga haka kuma sukayi sallama ya futa a office d'in ita kuma ta fara had'a yanata yanata. Hannunta rik'e da car key nata da Jakarta ta k'arasa ofishin khaleefan, yana kwance a resting chair ya lula duniyar tunani ko lissafin tafiya gida ma ba yayi lokacin data mishi knocking k'ofar. Bai bud'e ba haka bai bada izinin shiga ba ya tashi yana had'a duk abinda yasan zai tafi dashi gida, rataye da jakar computer shi, hannun shi kuma rik'e da labcourt da tea plask k'arami ya bud'e k'ofar ya futo. B'oyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon shi kafun tace, "har na fara tunanin ko ka tafi ma". "Ai munyi magana bazan tafi ban jira kiba". "Hakane! Toh amma kasan neman me nake maka ne?". "A'a" ya bata amsa. "Gidan ka nake son muje". Da sauri ya d'ago ya kalleta sai suka had'a idanu, wani kwarjinin ta ya cika shi. Baisan ma'anarta ta binshi gidan ba, amma koma meye ba matsala, shiyasa baiyi mata musu ba suka tafi tare har inda ta Parker motarta. ****** Raihana kuwa tana can cikin laluben hanyar da zata shawo kan matsalolin khaleefa da yadda zata fara fuskantar su, gaba d'aya kwanakin da suka biyo baya tunaninta kenan. Tana zaune a parlonta tana nazarin littattafan makarantarta wayarta ta fara ringing, koda ta duba taga no ummie bata d'auka ba don tasan maybe su hibbatullah ne suke son magana da ita ta watsapp. Tana bud'e data taga rututun missed call daga gurin su, tana shirin kiran su suka riga ta, tayi picking ta saka su a handsfree tana fad'in, "Ni na mayi fushi kwana biyu kun manta dani babu wanda ya kira ni cikin ku, Ni in na kira kuma bakwa d'auka.....". Daga chan b'angaren muryar ummie taji cikin wayar tana farawa da mata sallama, saita nutsu suka fara gaisawa da ummien taji lafiyar kowa cikin mutanen gidan dama y'an uwa duk da tana yawan gaisawa da kowa musamman ta watsaapp. "Ina son kiran mijin ki na kasa, don Allah ki mik'a sak'on godiyarmu gare shi...". "Ummie Yaya khaleefan ya muku wani abu ne?". "babba ma", Nan ummie ta bata labarin duk abubuwan daya aikawa su al'ameen, abun ma mamaki ya bata saboda ita dai ba tasan lokacin daya bawa auntie kayan ba. Bata b'oyewa ummie ba ta fad'a mata ita bata sani ba amma zata mik'a sak'on su gare shi inshaa Allah. Basu jima suna tattaunawa ba sukayi sallama bayan raihana ta gama complain na rashin magana dasu hibba kwana biyu, ummie ta mata bayanin sun fara exams ne Abba yace a daina basu wayar har sai sun gama dom sufi maida hankali, raihana ta musu addu'ar samun nasara da fatan alkhairy. Littattafanta ta had'e guri d'aya ta dawo da nufin kwanciya aka tab'a k'ofar. Koda ta bud'e yasmine ta gani, sai ta bata hanya ta shigo ta maida k'ofar ta rufe. A nan parlon suka zauna raihana tana mata sannu. Ko amsawa bata iya ba saida ta kwanta ta huta sannan. "Wai har yanzu jikin ne?" Raihana ta tambayeta. Yasmine cikin shagwob'ewa ta fara kuka tana fad'in, "Ni wallahi na gaji gidan mu zan tafi haka kurum ciwo yana son kashe ni a hana ni yin bankwana da iyayena". Cikin nuna damuwa raihana ta sake dawowa kusa da ita tana sake tambayarta, "wani abun ya sake faruwa ne?". "Meye ma bai faru ba bayan nace a cire cikin nan Ahmad yak'i, kullum fa sai nayi amai, kuma komai ma bana ci naji dad'in shi, ga yawan bacci kamar y'ar syrup.. Allah in na fara baki labarin abubuwan da nake ji a jikina sai mun yini ban gama fad'in komai ba". Raihana dafe kanta tayi a zuciyarta tace, ohh yasmine rigima! A zahiri kuwa gyara zamanta tayi tace, "haba yasmine kada ki bada mata mana tun kafun aje ko'ina! Ke bakya son ganin d'anki ne a duniya kike son kora shi kwata? Sannan taya ma Allah zai haramta abu ke ki hallata shi, kowacce mace ba da haka ta Zama uwa ba? Shin iyayen mu suna kwance ba tashin zuciya suka haife mu? Me yasa su suka hak'ura suka jure komai? in da sun kasa jurewa za'a gan mu a duniya? Amai! Tashin zuciya! Da yawan barci sune kacal matsalar ki? Toh in kika ji matsalar wata ta ninka taki, kuma a haka munna take tana godewa Allah bisa babbar kyautar da yayi mata, wadda babu wanda ya Isa maka ita a duniya sai shi.... Shin mutum dubu nawa ne suke neman haihuwar ruwa a jallo basu samu ba?, ko kinsan akwai wadda ko ana suma ana mutuwa tun daga wata d'aya har tara zata jure? Don haka tun wuri kiyi istigfari kada ma ki kuskura mijin ki yaji don duk sonda yake miki sai ranshi ya b'aci". Cikin sanyin jiki yasmine ta gama sauraron naseehar raihanan, sosai maganar ta shige ta har taji nadamar duk abubuwan data yiwa Ahmad a safiyar yau daya kaisu har da rigima ya futa yana fushi da ita. "Aikuwa na fad'a mishi har munyi fad'a dashi ma d'azu". "Raihana cikin kulawa kanta tace, "ohf! Amma Kinyi kuskure duk da kina da sauran lokacin gyarawa, yanzu dai ki fara K'arfafa jikin ki yadda zai dawo anjima ya ganki kamar sabuwar amarya ni kuma zan Miki dilke da halawa na musamman". Murmushi tayi ita kuma raihanan tayi dariya. Haka ta dinga janta da hira tana mata nasiha cikim hikima har ta sake sakin jikinta da kyau, gyaran jiki mai kyau ta mata hadda turaren jiki dana gashi, nan da nan kuwa ta d'au sirrin k'amshi. Bata bar gidan ba sai yamma lis, shima raihana ce tace tayi maza kada ya dawo gidan yaga bata nan ranshi ya sake b'aci. Koda yasmine ta futa raihana bata zauna ba saida ta gama girkin abincinta na dare gudun kada khaleefa yau ma ya dawo da yunwa irin rannan. Tayi kwalliyarta cikin doguwar riga irin mai kama da laffayar nan in aka nad'a gyalenta, ta nad'e gyalen a jikinta bayan ta shafa powder da lip balm a lab'b'anta, tayi sihirtaccen kyau mai fizgar hankali sai baza k'amshi take duk inda ta motsa. Tana futowa d'akin zata shiga kitchen taji ana murza key na gidan, tsayawa tayi chak ba tayi gaba ba bata yi baya ba har ya shigo doctor andal na biye dashi rataye da Jakarta. "Sannun ki da zuwa". Ta fad'a cikin harshen turanci tana nufar inda khaleefa yake tsaye..... Andal ta zubawa yarinyar idanu tana kallonta da nazarin inda ta tab'a ganinta ko saninta. _kuyi hak'uri wanda basu ga uzurin dana bayar ba, masu comment ina sake godiya da jinjina👍👍_ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty seven6️⃣7️⃣ Har ta karb'i jakar hannun khaleefa suna tsaye a inda suke basu motsa ba, sai ta koma gefe ta sake ce musu "Bismillah". Sai a lokacin duk suka dawo daga d'an k'aramin tunanin da suka fara tafiya andal ta k'arasa cikin parlon ta zauna, khaleefa kuma ya nufi kitchen. Raihana kuma d'akin shi ta nufa da jakar computer shi ta ajiye mishi ita gefen drower. Koda ta futo har khaleefa ya gabatar mata ruwa da tea, daga kujerar da yake zaune ta zauna suka gaisa da bak'uwar tata da bata san daga inda take ba. Ta dai k'ok'arta sun gaisa da Arab. Sai bayan sunyi shiru andal ta gane ashe ba inda ta tab'a saninta kawai yanayin dressing d'inta da k'amshin gidan da taji ne take tunanin ko itama asalin ta Sudanese ce, hakan ya k'ara mata k'arfin gwiwar tambayarta, "ke y'ar wace k'asa ce?". "Nigeria" ta bata amsa bayan gama dogon nazarin fahimtar kalamanta da kyar. "Baki da kowa a Sudan?". Wannan karon khaleefa ne ya bata amsa, "hausa fulani ce bata had'a komai da Arab ba". Shiru tayi tana nazari kafun can ta sake cewa, "Amma zanso sanin yadda ta samu sirrin matan mu har ta rik'e shi da kyau haka?". Khaleefa saida yayi shiru sannan ya bata amsa, "mamana ce!". Wani abu ya sokawa andal a k'ahon zuci, kamar tace surayyah ko? Sai kuma ta sake danne zuciyarta gudun kada ta fallasa kanta da gaggawa ta ba khaleefa damar gano manufarta tun kafun aje ko'ina. Raihana tashi tayi ta zuba ma matar abincin data dafa ta kawo mata. Ganin zata ci abincin sai duk suka tashi don su bata guri. "Ya zaku tafi Kuma! Mrs Abdallah ina son magana dake fa". Ta fad'a da harshen turanci yadda raihanan zata jiyo ta. Komawa tayi ta zauna shi kuma khaleefa ya shige d'akin shi. Taci abincin bada yawa ba tasha tea kafun ta fuskanci raihana da kyau, "sunana andal.... Ni abokiyar aikin khaleefa ce, nazo ne don sanin gundarin abinda yake damun mijin ki har yasa baya maida hankali kan aikin shi idan ba zaki damu ba?". Shiru raihana tayi tana tunanin abinda maganganun matar suka k'unsa, sai kuma sunanta ya sake dawowa cikin kunnenta, "andal" ta fad'a da sauri bayan ta d'ago ido ta sake kallon matar. Itama kallonta take yi, hakan yasa ta maida idanunta k'asa tana ci gaba da maimaita sunan a zuciyarta. "Ke nake saurare meye sunan ki?". Ba tare data d'ago ba tace, "Raihana". Andal tace, "Masha Allah! Sai dai ince kiyi hak'uri raihana watak'ila nayi miki shishshigi cikin al'amuran ki ko? To amma tunda farko na fad'a miki dalilin zuwana, sai dai tunda kin zab'i sakaya sirrin mijin ki ina ganin zan baki wasu y'an shawarwari, a rayuwar auren ki kada ki tab'a yadda ace mijin ki ya samu matsalar da ke baki San da ita ba, ya kamata ace duk abinda ya samu mijin ki ke ya sama ta yadda zaki fishi damuwa da son ganin kin magance mishi duk wata matsalar shi". Still kanta yana k'asa tana wasa da yatsun hannunta. Andal tayi murmushi kawai kunyar yarinyar sai ta shiga ranta har taji ta burge ta, jakarta ta d'auka ta duba lokaci taga ana gab da kiran sallar magrib. "Shawara ta k'arshe kuma mijin ki yana buk'atar kulawa ta musamman daga gare ki ko bai fad'a ba ya kamata ki gane hakan ta hanyar amfani da baiwar da Allah ya baki". Ta k'are fad'a tana mik'ewa tsaye, "Ni zan tafi ina fatan zakiyi nazari akan takaitacciyar shawarata". Itama raihanan mik'ewa tayi tace, "na gode in shaa Allah zanyi kamar yadda kika ce, bari na kira miki shi kuyi sallama ko?". "A'a barshi yana buk'atar hutu don ya wuni aiki na zuci dana zahiri". Raihana tayi murmushi ta raka matar har bakin k'ofa inda zata futa, tana ta son tambayarta wani abu daya shafi Auntie sai dai tana gargad'in kanta, don suna da k'asa sunzo d'aya sai ya zamana itace ake nufi?. Tana wannan tunanin har likitan ta bud'e k'ofa zata tafi. Kamar wadda aka zabura haka maganar ta sub'uce daga bakinta ba tare da tasan ma zancen ya futo ba, "Ni fa gani nake kamar na tab'a jin labarin ki.....". Itama andal kamar jira take aikuwa ta tsaya da hanzari ta juyo tana sake kallon yarinyar. "A gurin wa kika tab'a jin labarina?". "A gurin auntie maman khaleefa". Andal batasan lokacin data k'arasa shigowa cikin parlon ba, cikin gigita take tambayar raihana, "surayyah?". Raihana ta gyad'a mata kai. Ai saita maida k'ofar ta rufe tace, "Zan iya ganin hoton ta?". "Eh" ta fad'a tare da nufar d'akin gadonta, andal ma bayanta tabi ba tare data san ma ta aikata hakan ba, har Saida raihana ta nuno mata pic d'in a wayarta sannan ta fahimci kuskuren da tayi ta juya zata fuce. "Sorry na shigo miki d'aki ba izinin ki, amma tabbas wannan k'awata ce tun ta k'uruciya". Raihana ta yiwa Allah hamdala a zuciyarta sannan tace, "zaki iya zama a nan ba matsala, saboda indai da gaske kece k'awar da auntie tayi rubutu mai yawa a kanta toh ina buk'atar taimakon ki". Komawa tayi ta zauna k'asan carpet ta tankwashe k'afafunta ta tallafi hab'arta da hannuwanta, Anya da gaske ne yau itace take jinta kusa da surayyah? Ko dai cikin irin mafarkan data saba yi ne? "Ohh ya Allah! Alhamdulillah Allah na gode maka....." Sai kuma ta hau girgiza kanta duk da son ganin ta tabbatar ba mafarki take ba. Raihana dai tayi shiru tana kallon yadda matar take abu kamar zautacciya, magana take ita d'aya bata san ma tana yi ba. Kiran sallah da akayi yasa duk sukayi haramar sallah. Sai bayan sun idar da sallah andal ta samu sukunin zama ta fuskanci raihana, "kince kina neman taimakona, sai dai nima Ina son sanin abubuwa da yawa game da k'awata". Raihana tace, "kada ki damu da wannan saboda tayi rayuwa cikin kariyar ubangiji bata samu wata matsala ba, sati biyu da suka huce ma ta kawo mana ziyara nan k'asar.....". Shiru tayi kanta a k'asa tana nazarin abinda zata fad'a kafun taci gaba da cewa, "sai dai ta tafi ta barni cikin tunani da taraddadi....". Nan ta fad'a mata kad'an daga tarihin yadda su khaleefa suka rayu da ita a anguwarsu da yadda akayi ta mata bahagon kallo game da asalin yaran, har a k'arshe ta k'are da bata labarin yadda ta bar mata aikin had'a khaleefa da mahaifin shi data bar address d'inshi a k'arshen rubutun ta..... Andal tayi shiru kafun tace, "Allah mai iko? Komai yana shirin warwarewa cikin sauk'i, shin Abdallah zai iya barin ki futa in kika tambaya ba tare da yabi diddigin inda zaki ba?". "Ehhh toh gaskiya bani da tabbaci saina tambaye shi d'in naji?". "Koma dai yayane Ina son ki same ni a office gobe da misalin sha biyu zuwa biyu na rana akwai muhimmin abinda nake son mu tattauna". Raihana tace, "insha Allah sai dai lokacin da kika fad'a ba lallai na samu zuwa ba saboda zan shiga karatu". "Kina zuwa makaranta kenan?". "Eh" "Toh Allah yayi jagora, Zan ajiye miki no ta da address na asibitin mu,,,,, lallai Ina son ganin ki a asibitin nan jibi koda safe koda yamma...". Cikin gamsuwa ta amsa mata sukayi exchange phone no ta tura mata addreshin. Sun futo raihana zata rakata, khaleefa ma ya futo cikin fararen kaya da alamu sabon wanka ya sake. "kin futo" ya tambaye ta yana satar kallon raihana da take daga bayanta. "Eh zan tafi naji dad'in had'uwa da matarka, munyi magana mai yawa wadda nake fatan ta silarta duk matsalolin ka suzo k'arshe". Khaleefa ya maimaita kalmar -matsalolin ka suzo k'arshe- a zuciyarshi a zahiri kuma yayi murmushi. Kusan a tare suka d'ago suka saci kallon juna kafun su d'auke kansu cikin sakannin da basu huce uku ba. Doctor andal da take tsakiya tayi kamar bata ga komai ba. "Ina muku fatan alkhairy da addu'ar Allah ya bar ku tare abadannn". Duk cikin su aka rasa mai amsawa sai sanyi da jikin su ya sake yi, har ta k'arasa musu sallama khaleefa ya rakata jikin su a sanyaye yake. Suna futa kan layin Ahmad na futowa zasu futa anguwa da yasmine, da sauri ya k'araso gurin suka gaisa ya gabatar mata da Yasmine ma, itama suka gaisa cikin mutumci da girmama juna, har Ahmad ya buk'aci tazo tare dasu ya sauketa sai yaga motar ta kuma...... Lokacin da khaleefa ya shigo gidan raihana tana tsaye hannunta dafe da kujerar da take tsaye bayanta. Ya zauna cikin kujerun parlon ya kwantar da kanshi baya yana yamutsa sumar kanshi da duka hannuwan shi kamar me neman wani abu a ciki. Sai da ta gama k'ullawa da kwance yadda zata tunkare shi da maganar cikin zuciyarta sannan tace,, "na gode fa! Allah ya k'ara rufa asiri ummie ma tace na maka godiya....". Mik'ewa yayi zaune da kyau yana kallonta, kallon daya sauke mata kasala da sanya jikinta sanyi har ta gaza jurar ci gaba da kallon kwayar idon shi ta sauke nata k'asa. "Godiyar me fa?". Ya tambaya don har ga Allah baisan ya mata wani abu da ya cancanci ta mishi godiya ba. "Abun alkhairin daka aika masu al'ameen mana". Ta fad'a tana sake d'agowa ta kalle shi. "Ohh wannan.....". Sai kuma yayi shiru. Kamar ba zai sake cewa komai ba sai kuma yace, "meye abun godiya don Yaya ya siya ma k'annen shi sweet?". "Hakane! Amma sai Naga yana buk'atar a mishi addu'a ko?". Raihana ta fad'a. "Toh na gode! Baki dafa komai ba yau a gidan ne?". Ya k'are wancen zancen. "Sorry bari na kawo maka". Ta k'are fad'a tana nufar kitchen, khaleefa ya d'auke kanshi da sauri daga bin bayanta da kallo yana gargad'in kanshi. Har ta kawo abincin ta had'a mishi baice komai ba, instead of ta tashi kamar yadda ta saba a duk lokacin data ajiye mishi abinci sai ta kunna kallo ta zuba ma rivi idanu, ya sani magana ce a bakinta take tunanin ta inda zata fara. Bayan ya gama ta kwashe duk kayan sai tea plask k'arami da glass cups ta bari ko zai ci gaba da shan tea. "Kamar akwai abinda kike son cewa raihana?". Ta gyara zamanta, "Eh dama tambayarka nake son yi ko akwai abinda yake damun ka cikin kwanakin nan? Kamar na rashin lafiya haka ko....". Murmushi yayi yasan yana daga abinda suka tattauna da likitan nan, "kinga nayi miki kama da marar lafiya?" Ta girgiza kai, "a'a amma yanayin ka ya nuna kana cikin damuwa?". Shiru yayi, hakan yasa ta sake cewa, "nasan har yanzu abun nan ne yake damun ka ko? Dama haka soyayyah take azabtar da zucuyoyi da kowanne k'aramin kuskure, sai dai ina ganin me zai hana kayi amfani da shawarar dana baka a farko, kayi jihadi ka auri Saleema ko ba komai zaka tsamo ta daga rayuwar rashin kamun kai da take zuwa nagartacciyar rayuwa, sanadiyyar haka sai kaga gaba an samu uwar da za'ayi alfahari da ita.....". Tunda ta fara magana ya zuba mata idanu yana kallonta har ta kai k'arshe sannan yace, "kina ganin na dace da mace kamar Saleema? Shin ban cancanci na samu wadda bata da tabon namiji ko d'aya ba? Wadda ta killace kanta daga kowanne namiji take wa mijin aurenta tanadin kanta kad'ai? Haba raihana". "Kayi hak'uri idan maganar da nayi bata maka dad'i ba, sai dai kaima fa a case d'in Saleema ka aikata babban kuskure, a k'a'ida laifin ka yafi nata, taya ma zaka yadda kana namiji da aka sani da hangen nesa kayi rayuwar da zuciyarka ta raya maka da macen ba halaliyar kaba? Idan kuma ya zamana kaine ka fara bud'e mata k'ofar data d'auka waccen soyayyar itace asalin soyayyar dako wanne budurwa da sauri sukeyi fa? Shin hak'k'in ta bazai kama kaba a yanzun da kake shirin juya mata baya?". Khaleefa mik'ewa yayi tsaye yayi tattaki zuwa gabanta ya durk'usa ya rik'e duka hannuwanta biyu yace, "duk yadda zanyi miki bayani ba lallai ki gane gaskiyar abinda nake nufi ba, raihana Saleema fa ita ta bani dukkan dama a kanta ta dinga shige mun tana tura kanta gare ni...". "Me yasa kai baka janye jikin ka daga gare taba?". Ta sake fad'a cikin jin zafin abun a ranta. Khaleefa ya matse hannunta da yake cikin nashi ya sake cewa, "ba zaki gane ba raihana". "Sai dai in baka yimun bayani yadda zan gane d'in ba, toh wane bayani ma ya rage kayi bayan ka....". Sai taji nauyin k'arasa ragowar maganar tayi k'asa da kanta. Khaleefa ya sake rintse hannunta cikin nashi yayi k'asa da muryarshi kamar mai shirin mata rad'a, "kiyi hak'uri raihana amma tazo a lokacin da bazan iya cewa a'a gareta ba, kuma ko a hakan ma na rik'e kaina.....". Sai yayi shiru yanajin zafi da rad'ad'in abun har a cikin zuciyarshi, ta wani gefe kuma yana jin nauyin raihanan. "Nayi nadama! hak'ik'a nayi nadama!! tun farkon dawowa ta gida hutu da mukayi wata magana da malam, na hana idanuna bacci darare da yawa ina neman yafiyar ubangijina....". Yaja dogon numfashi ya furzar da zazzafar iska daga bakin shi yace, "ban cika miki baki ba sam bana daga cikin mazan da suke bin son ransu,,,, nasan kuma insha Allah zan samu irin matar da nake so tunda ba duka aka taru aka zama d'aya ba.....". Raihana ta janye hannunta a hankali ta mik'e tsaye ta d'an ja baya don rage kusancin da suka yi kafun tace, "tabbas Allah gafururrahim ne amma zai yafe iya laifin dake tsakanin ka dashi ne ba laifin daka aikata ga bawa d'an uwan ka ba har sai in bawan da kanshi yace ya yafe.... Kuma kalar matar daka fad'a akwai amma a cikin 100% basu huce 20% ba, taya zaka iya gano tsirarun nagartattun mutane 20 cikin milliyoyin gurb'atattu?". Shima mik'ewa tsayen yayi yace, "tabbas zan gano kuma ko yanzun ina iya ganin d'aya daga cikin su......". Tasan ita yake nufi, hakan yasa ta fara girgiza mishi kai, "ka daina d'auka na d'aya daga cikin su saboda nima ba tsallakewa nayi ba, sai dai ni nayi iya bakin k'ok'arina wajen ganin na kare mu daga fad'awa halaka.........". Ai khaleefa bai bari ta kai k'arshe ba yayi wani irin taku sai gashi gabanta, ya rik'e k'afad'un ta da duka hannuwan shi ya fara girgiza ta, "me kike nufi raihana?". Zuciyarta ta dake duk data tsorata da yanayin shi, "Eh saboda nima wani ya tab'a rungumata a bazata......". . Wani mugun naushi ya kaiwa bangon gefenta cikin tsananin jin zafi har saida hannun shi ya fashe, idon shi ya sauya colour zuwa red bakin shi har wani turiri yake a lokacin da yake tambayarta fuskarshi gab da tata, "twin ne ko? Me yasa twin zai mun haka.....". Sai kuma ya koma baya yana girgiza kanshi. "Bashi bane, tunda nake tare da Ayman bai tab'a attempting rik'e hannuna ba har kawo yanzu da nayi nesa dashi". Safa da marwa kawai yake a parlon kamar zautacce saboda zafun rai k'irjin shi sai sama da k'asa yake. Abinda ya sake razana raihana har ta zab'i sulalewa ta gudu d'akinta don bata manta yadda ya huce fushin shi a kanta waccen ranar ba. Sai dai tana fara tafiya ya dakatar da ita ta hanyar shan gabanta, "wane banzan ne ya samu zarrar tab'a ki ba kuma twin ba?". K'asa tayi da kanta idonta ya ciko da ruwan hawaye. Ya sake daka mata tsawa, "tambayarki nake RAIHANA!". Tuni hawayen daya cika idonta ya samu damar silalowa bisa kuncinta. Sai ya sassauta murya ya sake rik'e hannunta, "don Allah kice wani abu gare ni? Ki fad'a mun ina hannun shi ya tab'a a jikin ki tun kafun zuciyata ta gama tarwatsewa.....". Cikin muryar kuka tace, "ni fa bance maka ya tab'a niba". Ta fad'a tana ja baya har ta samu majingina don masifar khaleefa tasa k'afafunta ma rawa suke kamar ba zasu iya d'aukar nauyin taba. "Kar ki maidani bagidaje mana, an tab'a runguma ba'a tab'a jikin mutum ba?". Ya fad'a yana tokare hannun shi jikin ginin da take jingine, girgiza mishi kai tayi hawayenta suna ci gaba da sauka d'ayan bayan d'aya. Sun jima a haka kafun yasa hannu a hankali ya fara share mata hawayen, abun yazo mata a bazata, ta d'auka yadda ya fusatan nan wanka mata mari zaiyi sai taji sab'anin haka. Shi kuwa jikin shine yaji duk ya zama lakwas, kawai ganin hawayenta yasa yaji jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya sai naseehar auntie ta fara dawo mishi kamar lokacin take mishi hani da iya sarrafa kai yayin fushi. A gurin ta durk'usa donta gaji da tsayuwa, shi kuma ya zauna gab da ita har gwiwar su na had'uwa. Kallonta yake babu ko alamun zai k'ifta ido bare ya d'auke kanshi, kallon daya mata nauyi ta kasa jurewa har saida ta sunkuyar da kanta k'asa tana kallon tafin k'afar shi data ke shan gyara kamar baya taka k'asa. Khaleefa kuwa a lokacin ji yake kamar ya shiga cikin zuciyarta yaga komai da yake ciki, sun jima shiru kafun yace, "na baki labarin soyayyata, amma ke baki tab'a bani labarin taki soyayyar ba.....". Sai yanzun ta d'ago ta dube shi tace, "saboda babu wani abu mai kama da wanda kake sonji a labarina da abinda ya shafi soyayyata". "Har rayuwar soyayyar ki da Ayman......?". Ya sake jefa mata wata tambayar. Shiru tayi tana kallon shi irin yadda yake kallonta kafun tace, "Ni ban tab'a soyayyah da Yaya Ayman ba". "Zai fi kyau muyi magana ta gaskiya don har alk'awarin da kika mishi na aure bayan deal d'in mu dake ya k'are na sani.......". Wani irin sak tayi ta d'auke wuta ta zabga tagumi tana kallon shi a zuciyarta tana tunanin yadda akayi khaleefa da Auntie suka san maganar da ba'a tattauna ta gaban su ba? Toh kodai Ayman d'in ne ya fad'a musu da kanshi?. _please ku k'ara hak'uri dani abubuwan ne da yawa_ _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty eight 6️⃣8️⃣ "Bari na sauk'ak'a miki tunani, har yanzu ni Ayman baice mun komai ba, amma naji komai da kunnena a lokacin da kuke tattaunawa dashi a parlon Auntie. Na taho da niyyar shiga sai na tsaya duba wani massage a wayata a dai dai lokacin da yake jaddada miki kalaman soyayyah, na zab'i dana ci gaba da tsaiwa ba don komai ba sai don kada na shiga hak'k'in ku duk da bani da wani tunani a kanki lokacin...... Tun a sannan na fara nadamar auren ki, don na fahimci da ace nayi jinkirin minti biyu a ranar da zan gabatar dake ga mamana! Toh da Ayman ne zai zamo mijin ki bani ba.... Raihana komai da kika sani a rayuwa yana da mafari...... Kina da nagartar da ko wanne namiji yake nema a tare da matar auren shi, daga soyayyar da Ayman yake miki na fara sanin haka, shiyasa tun a ranar na fara binciken halayyarki da tsarin rayuwarki, saboda Ayman ba irina bane.... Shi mutum ne mai tsinkaye da zuzzurfan tunani kafun aiwatar da komai, nasan ba zai tab'a zab'in abinda ba nagartacce ba. Matakin farko dana fara d'auka shine yin nesa dake saboda Ayman ya same ki bayan auren mu ya k'are, sai dai baka Isa ka yiwa Allah wayo ba, hakazalika k'addara ta riga fata..... Ina tsakiyar sauraren hirarku auntie ta k'araso gurin, nayi yink'urin b'oye komai daga gareta amma ta hanani damar yin kowanne motsi, haka muka gama jin komai tare sannan muka shiga cikin parlon. A lokacin tabi duk hanyar da tasan zata ji wani abu daga bakina game da irin auren mu ban yarda ba, har zuwanta Germany na kwanan nan tana son jin tabbaci akan irin auren da mukayi, shine a k'arshe da zata tafi ta k'are da bani k'aramin rubutu a takarda bayan mun rakata filin jirgi....... Na fara tunanin auntie tana zargin munyi contract marriage ne dake shiyasa tabar mun sharad'in ko bayan ranta na raba auren mu bata yafe mun ba.... Raihana duk tunanina a yanzun shine taya Ayman zai same ki idan har auren mu bai k'are ba? Shin d'an uwa d'aya tilo abokin tagwaitaka ya cancanci samun irin wannan tukuicin daga gare ni? Raihana wannan tunanin dashi nake kwana nake tashi har office in na fara aiki shi yake zuwa min kaina, ta d'aya b'angaren kuma wani b'arin na zuciyata daban yana tunzirani da azalzalata kan wani abu daban shima.....". Shiru yayi kanshi a k'asa yana sake danne zuciyarshi da gudun aiwatar da abinda zai zamo kuskure ko nadama a gare shi, shiyasa baya son gaggawa..... kamar fudda sirrin dake cikin zuciyar shi yanzun..... A hankali raihana ta gyara zamanta, hakan ya samar da tazara tsakanin su, bayan d'aukar wasu mintunan shiru ta fara magana da cewa, "kamar yadda na fad'a maka da farko, Yaya Ayman ba saurayina bane sai dai munyi rayuwa ta sabo dashi........". Daga nan ta fara bashi takaitaccen tarihinta, tarihin daya tab'a zuciyar khaleefa ya sake tado mishi mikin da yake d'ankare a cikin zuciyarshi..... Musamman labarinta da imran, yaji kishin shi sosai fiye dana Ayman cox shine ya samu zarrar tab'a jikinta. Shiru yaci gaba da wanzuwa tsakanin su yayinda raihana ta dinga k'ok'arin tsaida hawayen idonta. A wannan yanayin khaleefa ya sake kallonta, muryarshi a tausashe kamar yadda jikin shi yake a sanyaye, "labarin soyayyarki tafe yake da rikita rikita da makirce makircen mutanen da baki sani ba, sai dai kin burge ni ta yadda kika kare mutumcin kanki baki yarda rud'in soyayyah yasa kin biyewa son ranki da zuciyarki ba kamar yadda mukayi.... Da ace Imrana ya samu dukkan dama a kanki raihana? Toh da bazan tab'a yafe mishi ba..... Har abada......". Shiru yayi yana kallon hannun shi daya dame shi da rad'ad'i saboda naushin daya kaiwa bango d'azu ashe yaji ciwo. A nutse ta share hawayen idonta ta kalli hannun tana kallon yadda yatsun suka kumbura. A firgice ta kai hannun ta gurin ciwon ta shafa tana yi mishi sannu, ya d'auke hannunta da sauri saboda wani zafi da yaji. "Ya kamata mu tafi asibiti fa?". Ta fad'a cikin nuna kulawa. "Zan iya dubawa". Ya fad'a bayan ya mik'e tsaye. Itama mik'ewar tayi, ya d'auki hanyar d'akin shi ita kuma ta tsaya daga nan baya tana kallon shi. Bayan mintuna k'alilan da shigarshi d'akin yazo bakin k'ofa ya kwankwasa, ta gane abinda yake nufi saita nufi d'akin ta shiga bakinta d'auke da sallama. Yana durk'ushe gaban first aid box daya ajiye a d'akin, itama saita k'arasa. Ya nuna mata yadda zata mishi treatment yasa ta b'allo mishi magunguna yasha. Saida ta tabbatar ya samu relief sannan ta futo a d'akin zuwa nata zuciyarta fal tunanin kalaman khaleefa masu kama dana wanda ya mutu a so.... ***** Bayan ta kwanta bacci ta rasa gaba d'aya abinda yake damunta, sun fara magana da khaleefa basu gama ba, gashi ta kwanta bacci yak'i yiwuwa, tsabar fitina sai yanzu yunwa take tsikararta. Tashi tayi zaune ta kunna glove haske ya cika d'akin gaba d'aya, ta dubi rigar jikinta da bata k'arasa sauka mata k'asa ba, ta zura zumbulelen hijab a samanta duk da bata tsammanin samun kowa a parlon. Koda ta tura k'ofar ta futo yana zaune cikin parlon ya had'a kanshi da gwiwa, motsin tafiyarta ya sashi d'agowa sai kuwa cikin sa'a idanun su suka fad'a cikin na juna.... Ta sakar mishi tattausan murmushi ta huce zuwa kitchen, abinci ta zubo cikin plate ta dawo parlon daga nesa dashi ta zauna tace, "ya jikin?". Ba tare daya kalleta ba yace, "alhamdulillah". "Amma ba jikin bane ko?" "Um um". Ya sake fad'a ba tare daya yarda ya d'ago kanshi ba. Har ta gama cin abincin ta maida plate d'in kitchen yana nan zaune a gurin. "Ya kamata ka kwanta haka dare ya fara nisa". "Bazan iya kwanciya ba". Kamar ta tambayeshi dalili sai taga aiba hurumin ta bane, hakan yasa tayi hucewarta d'akinta ta barshi a gurin. Sai dai ko bayan ta kwanta kasa nutsuwa tayi, sai taga kamar bai dace ta barshi a yanayin da yake ba... Sai ta mik'e tsam ta futo parlon, yanzun kanshi ya kwantar jikin kujerar da yake zaune idon shi a rufe kamar mai bacci, tsabar nisan daya yi ko motsin zuwanta kusa baiji ba sai k'amshin turaren ta ne ya ankarar dashi wanzuwarta a gurin. Ya mik'e zaune da kyau yana kallonta. Itama kallon shi take kamar me karantar wani abu cikin kwayar idon shi kafun nauyin shi ya cika ta tayi k'asa da nata idon. "Shin har yanzu baka ji ka aminta dani ba?". Tayi tambayar kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta. K'aramin murmushi yayi yace, "yardar cema tasa na bud'e miki sirrin daba wanda ya sanshi tare dani duk duniyaaaa.....". Shima ya bata amsa ba tare daya kalleta ba. "Idan hakane meyasa kake son b'oye mun wani abu yanzu kuma?". "Saboda fad'ar bata da wani amfani". Ya sake bata amsa. Shiru tayi tana kallon shi kafun can ta nisa tace, "shikenan! Allah yayi maka maganin abinda yake damun ka, am yauwa gobe in na tashi makaranta akwai inda zani idan ba damuwa". "Bakisan gari bafa?". Ya fad'a yana kallonta. "Insha Allah ba zan b'ata ba". Ta bashi amsa kanta s k'asa. "Toh Allah ya kaimu". Ta amsa da "ameen". Sunci gaba da zama har dare ya sake nisa sosai bacci yaci k'arfin idon su suka yi sallama kowa ya tafi makwancin shi. *****Washe garin ranar raihana tayi shirinta cikin doguwar rigar material mai multi color, yau bata samu damar tashi da wuri ba shiyasa ko lokacin data futo bata samu khaleefa ba tuni yabar gidan. Bata futa makaranta ba saida ta gama gyara abinda ta lalata a gidan. Ko a makarantar ma Allah Allah ta dingayi a tashi taje gurin doctor andal taji abinda ta shirya mata. Aikuwa suna futowa lectures ta kira likitan, sukayi maganar da bata huce mintuna biyu ba ta k'arasa titi don tarar abun hawa bayan ta rufe fuskarta da mask gudun had'uwa da khaleefa. A gaban harabar asibitin ta tsaya ta kira likitan ta fad'a mata ta iso, ba jimawa wata nurse tazo ta tafi da ita. Lokacin data isa offishin likitar tana tsaye jikin wawakeken windown daya kewaya ta gefen titi. "Sannun ki da zuwa raihanaaa". Ta fad'a da hausa da kyar kamar me koyon magana, murmushi tayi ta k'arasa cikin kujerun da suka bada round kamar gurin lunching haka da hutawa ta zauna, "sannu doctor ya aiki?". Ta tambayeta da harshen jamus da take koyo yanzun. "Alhamdulillah" ta fad'a tana gabatar mata drinks. Ruwa kawai tasha kad'an ta sake maida hankalinta ga likitan. "Muna magana jiya bamu k'arasa ba gashi yanzu yamma tayi kada ya riga ki komawa gida yasa hankalin shi a kanki ko". "Ehhh toh amma maganar da kika ce zamuyi fa". "Zamu k'arasa ta waya amma kafun ki tafi zamu je dake ki duba wani patient". Ba musu raihana ta amsa mata, Suka mik'e kusan a tare zasu futa, har sunkai k'ofa andal ta tuna mata ta sake rufe fuskarta. A nutse suka dinga hucewa andal tana gaisawa da mutane tsilli tsilli har suka Isa wasu private rooms, Saida ta tsaya ta fara neman izini aka bata kafun ta tura k'ofar ta shiga da sallama raihana na biye da ita. Mutumin yana zaune hannun shi d'aya sak'ale d'ayan kuma rik'e da cup yana shan wani abu, yayinda wasu ma'aikata mata har biyu suke goge goge duk daba wani datti cikin d'akin. Ajiye kofun hannun shi yayi ya zare farin tabaran idon shi yana yiwa andal maraba, su kuma ma'aikatan suka fara fucewa bayan sun gaishe da likitan. Raihana zuciyarta saida tayi darrr kamar ta faso k'irjinta ta futo lokacin da tayi arba da mutumin, kama take gani ta zahiri tsakanin mutumin dasu khaleefa..... Har andal ta samu guri ta zauna saman wasu kujeru tana tsaye bata motsa ba har saida tayi mata magana sannan ta sauke ajiyar zuciya ta k'arasa kusa da ita ta zauna. Saida suka fara gaisawa da andal tayi mishi sannu sannan raihana ma ta gaishe shi ta mishi sannun. Ya amsa yana kallon bak'uwar fuskar bai daice komai ba. Doctor andal ta mishi tambayoyi game da lafiyarshi sannan suka mishi sallama suka futo, daga nan kai tsaye inda zata futa a asibitin sukayi, ta rakata har inda zata hau mota sannan tayi mata magana, "wannan mutumin dana kaiki kika duba shi yanzun, yana da alak'a ta kusa da mahaifin khaleefa amma shi kanshi khaleefan bai sani ba...... Nasan ba saina jaddada miki wannan maganar ta zamo sirri tsakanin muba?". Raihana ta gyad'a mata kai, sai taci gaba da cewa, "yazo an mishi aiki ba tare da kowa cikin ahalin shiba sai escort d'inshi da nurses da suke kula dashi, ba don kuma bashi da family ba sai don ya tsame hannun shi daga duk wani abu daya shafe su, a tak'aice ina son ki d'auki nauyin abincin da zaici daga yanzu har zuwa sati biyun da zai gama jinya ya koma k'asar shi, Ina fatan hakan zai samu ba tare da khaleefa yasani ba......". A wannan karon saida tayi nazarin abubuwa da yawa cikin zuciyarta sannan ta amsa mata da tabbacin duk yadda sukayi dashi zata fad'a mata in ma zai hana. Suka k'arasa sallama ta tafi gida zuciyarta fal tunane tunane, da tambaye tambayen da ba mai bata amsa. Ranar khaleefa bai dawo da wuri ba sai dare, Koda yaci abinci bai tashi a parlon ba har ta futo rik'e da littafinta da waya, ta zauna k'asan carpet nesa dashi tace, "am yau.. ma...ina son k'arin bayani akan wani abu da ban fahimta ba". Ya d'ago idonshi a nutse ya kalleta, zuciyarshi na raya mishi abubuwa da yawa game da ita, "let's see" ya fad'a tare da mik'a mata hannu ta bashi littafin. Ba musu ta mik'a mishi ya ajiye k'asa yana dubawa, Koda ya fara mata bayani tattare gaba d'aya hankalinta da nutsuwarta tayi kanshi har ya gama ta mishi nata bayanin gwargwadon fahimtarta. Ya jinjina mata sosai kamar waccen ranar. Har ta tashi zata tafi ya tambayeta, "kin fara aiki da computer ki kuwa?". Ta juyo tana kallon shi tace, "a'a". "Meyasa?". Ya sake tambayar ta just enjoying how she's starring at him cike da kunya data kalle shi sai ta waske ta hau wasa da yatsun ta. "Ban iya aiki da ita sosai ba". "D'auko tawa muga". "A ina kenan,". "Shiga d'akina zaki ganta". D'akin ta nufa ta d'auko bayan ta ajiye littattafanta a gurin, yana zaune inda ta barshi ko sanyin parlon baya ji. Koda ta bashi system d'in kusa dashi ya nuna mata ta zauna, ya fara operating gently yana nuna mata komai da bayanin amfanin shi yadda ya kamata. Saida ya tabbatar duk bayanin da yayi sun shiga kanta sannan ya d'ora mata computer kan cinyarta bayan ya d'ora pillow a k'asa. "I'm all eyes". Murmushin daya k'ara mata kyau tayi ta fara bin komai daki daki tana satar kallon shi duk. Idon shi a kanta har tazo shiga wani folder da yayi creating yana ajiye sirrikan da baya son wani yasani sai ya durk'uso kanta ya kewaya hannun shi na dama ta d'aya gefen ya d'ora saman nata hannun. Abinda ya assasa mata ja baya da sauri saboda wani yarrr da tsigar jikinta tayi, cikin sa'a kuwa sai gata a jikin shi gaba d'aya. Wani irin yanayi khaleefa ya riski kanshi a ciki musamman da k'amshin jikinta ya shige shi sosai, koda ta motsa da niyyar guduwa ture laptop d'in yayi daga jikinta gaba d'aya ya kewaye hannayen shi ta saman cikinta ya cusa fuskarshi cikin gashinta yana shak'ar wani ni'imtaccen dawwamammen k'amshi da yake tashi a gurin. Tsabar rik'on tsaurin daya mata yasa duk jikinta ya d'auki rawa, idonta ya firfito waje, musamman da taji ya tuje gashin kanta yana yamutsawa. Kwata kwata khaleefa baisan abinda yake aikatawa a lokacin ba har saida wayar shi tayi ringing..... Da sauri ya raba jikin su kamar wanda ya aikata wani mummunan laifi haka ya dafe kanshi yana jin haushin kanshi da kanshi. Ita kuwa a gurguje ta tattara komai nata ta bar mishi gurin. Tana shiga d'akinta Ahmad ya kira wayar khaleefa yace ayi mata godiya. "Godiyar me?". Khaleefa ya tambaye shi. "Kasan maganar da mukayi da kai jiya a office?". Khaleefa yace, "rigimarku da madame?". "Exactly! Toh jiya Ina zuwa na tarar an gyara komai hadda tarya ta musamman daga Yasmine, abinda aka jima ba'a yi mun ba, tun a lokacin nasan ta had'u da nagartacciyar data bata shawara ta kwarai, yau da safe kuwa sai take fad'a mun raihana ce tayi mata nasiha shine jikinta yayi sanyi ta k'uduri aniyar gyarawa, har da bani hak'uri..... Gsky man ba zance maka komai ba sai ka k'ara rik'e matarka da kyau, Cox yarinyar tasan abinda takeyi a rayuwa, idan har ka sake ka rabu da ita zakayi babbar asara don yarinyar nan d'aya ce tamkar da million". "Nagode!". Shine kad'ai abinda khaleefa ya fad'a ya ajiye wayarshi gefe yana nazarin maganganun Ahmad, ya fahimci a kullum Ahmad baya jin dad'i idan bai yabi raihanan ba. ******** Kamar kullum, Amna ta futo cikin shirin futa makaranta, kamar koda yaushe ta tsaya tana knocking k'ofar Saleema duk da tasan ba bud'e mata zatayi ba, ta d'auki adadin wasu lokuta a gurin har daga k'arshe ta hak'ura ta fidda rai ta juya da nufin tafiya. Har ta juya zata tafi sai kuma dai tayi wata shawara, ta koma da baya ta buga apartment d'in da yake kusa da ita, wani matashi d'an asalin k'asar yazo ya bud'e, Suka gaisa Amna ta tambaye shi ko yana jin motsi a part d'in da yake mak'otaka da nashi? Yayi Jim kafun yace, "eh amma ba wai sosai ba". Godiya ta mishi da sallama ta juya taci gaba da tafiya har ta futa daga cikin gidan gaba d'aya. Yau har a makarantar damuwarta ga k'awarta Saleema tafi ta kullum, har Allah Allah ta dingayi su tashi lectures tayi abinda ya kamata don ceto rayuwar k'awa d'aya tilo da bata da kamarta kaf fad'in Germany........ Kuyi hakurinn dai gaashi nan ba editing _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page sixty nine6️⃣9️⃣ Wayarta ta ciro a jakarta ta fara laluben layin Ahmad, har zata kira shi saita tuna indai bai tashi office ba bazai picking call d'inta ba, sai kawai ta rubuta mishi gajeren sak'o kamar haka, "Assalam! Kayi hak'uri na sake dawowa gare ka da k'ok'on barana, ka taimaka kasa abokin ka yayi wani abu akan case d'in k'awata cox kullum abun gaba yake sakeyi..... Nagode". Lokacin da sak'on ya riski Ahmad ya futo sallar la'asar ne, jimm yayi yana nazari kafun ya sauƙe ajiyar zuciya, gaba d'aya komai ya hargitse musu baisan taya zai fara b'ullowa al'amuran gaban shiba, ga case d'in Saleema! Ga wani babban case daya tattara gaba d'aya hankalin shi yanzu akai, ga khaleefan kwana biyu abubuwa sun mishi yawa, ya tabbata ko za'a samu taimakon khaleefa ba yanzu da gaggawa ba. *Nigeria* Kamar koda yaushe yauma ta tashi tun kafun gari yayi haska ta had'a breakfast irin wanda tasan Ayman yafi so, ita kuma ta fara shirin futa office, zuwa lokacin da Ayman ya gama shirin shi ya futo da niyyar karya kumallo tuni ta ratayo Jakarta da duk abinda tasan zata buk'ata ta futo. Mik'ewa yayi tsaye yana kallonta yace, "dama ba kin daina zuwa office ba?". "Yaushe na fad'a maka haka? Ni hutu na d'auka kuma tun last week ya k'are" Nan take ya had'e fuska, "gaskiya ni bana son aikin nan Auntie, tun muna yara fa haba.... Kinyi abinda kikayi Allah ya bada lada yanzu kuma lokacin hutawarkine.....". Fuskarta sam ba alamun wasa itama tace, "Toh ubana mai cikakken iko dani ai saika hana ni zuwa ko?". Ta fad'i haka tana nufar k'ofar futa daga d'akin kai tsaye, da sauri ya riga ta Isa gurin k'ofar ya tura da bayan k'afar shi ya marairaice mata, "please mum aikin nan ya k'are haka in dai baso kike......". "Indai baso nake raina ya b'aci ba? Ayman zan sassab'a maka fa idan baka futa a hanyata ba wallahi kaji na fad'a maka". K'asa yayi da kanshi kamar baiji abinda ta fad'a ba. "Nace ka bani hanya na huce!". Ta fad'a a tsawace cikin fushi. Wayarshi kawai ya ciro ya fara neman layin khaleefa saboda wannan yak'ine da bazai iya shi shi kad'ai ba saida taimakon d'an uwa d'aya tilo. A lokacin khaleefa yana zaune a dinning zaiyi breakfast, sai satar kallon k'ofar raihana yake ko zai ganta, don tunda wannan abun ya faru suka shiga wasan b'uya da ita, kwata kwata bata yarda su had'u. Yayi mamakin ganin kiran Ayman da sanyin safiyar nan, ba zai iya tuna when last sukayi waya da safe ba.... Koda yayi picking yaji dalilin kiran mamakin shi gushewa yayi take kuma yanayin shi ya nuna zallar b'acin rai. Daga ta cikin wayar yanajin maganar da auntie take cikin zafi zafi, "Ayman abinda baka tab'a yi dani ba zamu fara yau? Saboda ubanka khaleefa yana zuga ka dama shi baya ganin girmana kaima yake son kabi layin shi ku juya mun baya gaba d'aya ba?". Khaleefa ya dafe kanshi saboda furucinta yayi mishi girma a zuciya da kwakwalwa. "Bata wayar". ya fad'a cikin bada umarni. Koda Ayman ya mik'a mata wayar k'in amsa tayi sai sababin fad'a kawai take kamar zata ari baki, sai ya mayar da wayar kunnen shi, "tak'i karb'a fa". "Naji maida wayar handsfree". yayi kamar yadda khaleefa ya bashi umarni. "Please ki saurari abinda zan fad'a, don Allah ki zauna muyi magana ta fahimta ba don niba ba don halina ba Auntie please am begging you....". "Khaleefa! Ya kamata ku shiga taitayin ku.... Tun kafun kusan kanku nake aikina kuma, saboda ku ba fasawa zanyi ba tunda bada k'afar kowa cikin ku nake tafiya ba....". Shiru duk sukayi suna ci gaba da sauraron fad'an da takeyi tuk'uru rai b'ace, sukan manta rabon da suga b'acin ranta bare fad'an ta irin haka. "Ayman bud'e mata k'ofar ta tafi zamuyi magana anjima". Abinda kad'ai khaleefa ya fad'a ya katse kiran ya kife wayar saman table da yake gaban shi. Shima Ayman kaucewa yayi daga hanya ya hard'e hannun shi a k'irji jikin shi a sanyaye, ko fuskarta ya rasa zarrar kallo. Har ta bud'e k'ofar zata futa sai kuma ta koma da baya cikin parlon ta zauna ta rabka uban tagumi..... Ayman ya nufi inda take a sanyaye zai durk'usa gabanta tayi saurin dakatar dashi ta hanyar daka mata tsawa, "tafi ka bani guri". "Auntie am.....". "Ka tafi nace!!!!". Ta sake fad'a tana nuna mishi hanya. Wannan karon har saida ya razana saboda yadda tayi maganar. Sukuku ya fuce a parlon don in yaci gaba da takurata zata iya mishi komai yadda ta d'au zafin nan..... Ko breakfast bai yiba ya d'auki jakar shi da mukullin motarshi ya futa a gidan. Khaleefa kam ci gaba da zama yayi wayarshi nata ringing ya kasa d'agawa har aka fara danna k'ararrawar k'ofa ba k'auk'autawa. Abinda ya sashi mik'ewa ba tare daya shirya ba ya d'auki duk abinda yasan zai buk'ata ya futo zai futa daga gidan, yanzun ma saida ya sake satar kallon k'ofar raihana, kafun ya d'auki k'aramar papper yayi rubutu gajere ya ajiye mata k'ofar d'akinta. Yana murd'a k'ofa ya fara da sauraron mitar Ahmad, "kaifa wani lokacin baka yiba wallahi, gaka ga wayar ka kasa picking Allah ka sauya hali". Shafo sumar kanshi yayi bisa al'adarshi yace, "sorry nayi hakane da nufin zaka iya tafiyarka". "Au haka ma zaka ce?". "A'a nifa don kada kayi late nace haka, but am really sorry". Sai a lokacin suka gaisa suka fara takawa har inda motar Ahmad take. Ko a hanya suna tafe Ahmad na mishi mitar motar da yak'i mallaka, shi dai sam bai kula shiba cox inda sabo yaci ace ya saba da jin magana d'aya a gurin Ahmad d'in, shi kuwa sam bai damu ba yana ganin k'asar daba dawwama zaiyi cikin taba, baya ga haka ma motar haya a garin bata da banbanci da motar gida, and shi yanzu matsalolin gaban shi sun take komai da bashi da muhimmanci da bai zama mishi dole ba. Raihana ta futo cikin shirin doguwar riga maroon colour, tayi rolling kanta da wadataccen gyale, tana d'ora k'afarta taci karo da takardar da khaleefa ya ajiye, saita durk'usa ta d'auka ta fara dubawa, "here's my no, call me". Guri d'aya ta samu ta zauna tana tunanin mai yiwuwa har tayi k'undunbala bala ta danna mishi kira, tayi rashin sa'a lokacin wayar bata kusa dashi, saita rubuta mishi gajeren sak'o, "kamar yadda kaso, na kira baka yi picking ba....". Bayan ta gama aikinta kamar kullum yau ma ta shirya tray guda na shayi da lunch ta d'auki wayarta da jakarta ta futo a nutse daga gidan bayan ta sakaye rabin fuskarta a zuciyarta tana addu'ar Allah yasa ta dawo kafun dawowar khaleefa don yau taso yin late. Direct ta d'auki hanyarta, yau ko ta offishin likitar bata biya ba ta nufi d'akin majinyatan, tayi knocking, bayan jimawarta a tsaye aka bata izinin shiga, ta murd'a k'ofar a nutse bakinta d'auke da sallama. Yana kwance yana duba magazine ta shiga ta durk'usa har k'asa daga gefe d'aya ta fara gaishe shi da tambayar jikin shi. Ya amsa ta da kulawa yana kallon kayan abincin hannunta, tunda ta fara zuwa yake son tambayarta daga ina amma kamar an hane shi sai yaji ya kasa, tun baya cin abincin har ya dawo yana ci. Yadda ta iya girki in yaci abincinta sai ta dinga tuna mishi tsohon tarihi. Ta d'an zauna cikin d'akin na wani lokaci kafun tayi mishi sallama zata tafi. Ya ajiye magazine d'in gefe yace, "kullum kina kawo mun abinci amma bansan komai a kanki ba, kamar sunan ki, da dangantarki dani". Kanta a k'asa don bata iya kallon cikin idon mutumin tace, "sunana raihanatu....". Shiru yayi yana maimaita sunan a zuciyarshi harta gama juye abincin ta fuce, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya ya sauko daga inda yake zaune. Wannan karon da kanshi yayi saving kanshi ya fara ci, wani b'arin na zuciyarshi na kwab'ar shi da kiyaye lafiyarshi wani kuma na zak'uwa da son irin d'and'anon girkin, shida ko na jikin shi ya kawo mishi abu sai anyi checking d'inshi in and out ake yarda yaje gare shi saboda tsaro, amma yau gashi k'arewarta ma abincin daya futo daga fuskar da bai tab'a sani ba yake ci.... Yaja k'ak'k'arfar ajiyar zuciya yana tuna ranar data fara kawo mishi abincin ya fad'awa andal ta tafi dashi kuma a fad'a mata baya buk'ata, murmushi tayi a lokacin tace mishi, "Kaine kuwa kake buk'atar wannan abincin sooraj don bai futo daga inda zaka ce a'a ba.....". Sake nisawa yayi cikin duniyar tunanin da yake ciki, tunda yazo ya fahimci akwai magana a bakin likitar, sai shagwub'e take mishi irin abinda ada sam babu a tsakanin su, yakan zo ta ganshi kamar kowanne marar lafiya bata nuna alamun ma ta sanshi, abu d'aya yake tambayarta an samu ganin surayyah kuwa? Zata bashi amsa da a'a daga nan bata sake ce mishi komai har ya tafi,,,,, lallai yana ji a jikin shi wannan karon akwai k'amshin gaskiya duk da gashi yayi rabin zaman shi a k'asar baiji k'amshin gaskiyar ba,,,,, sai dai bazai karaya da wuri ba, zai ci gaba da bin takunta har komai ya futo sarari. Raihana kuwa tana futa sauri sauri ta dingayi don yamma tayi mata yau, in tayi sake khaleefa zai rigata komawa gidan nan. Tana cikin tafiya kamar a majigi idanunta suka hasko mata shi da Muhammad suna tahowa, da sauri ta sake gyara rufar fuskarta taci gaba da tafiya. Shi kanshi khaleefan tunda idon shi ya sauka a kanta ya kasa d'auke kanshi, ko shakka ba yayi wannan raihana ce..... Muhammad yana ta mishi hira amma sam hankalin shi baya kai har suka zo gab da ita zasu gifta juna, sassanyan k'amshin turaren ta ya daki hancin khaleefa har ya sashi lumshe idanun shi da tsayawa cak..... "Yea! Let's go on mana". Inji Muhammad "Wait!". Ya fad'a da nufin tsaida ita yana bin bayanta da kallo bayan ya juyo. Ita kuwa k'ara sauri tayi, ganin haka sai ya kira sunanta yadda zata iya jiyowa, "Raihanaaa!". Cak ta dakata kamar zata juyo saita tuna gargad'in andal da tace kar ta kuskura koda wasa khaleefa yasan maganar marar lafiyar nan..... Taci gaba da tafiya hadda k'ara sauri akan nada. Bin bayanta yayi da sassarfa, Muhammad ya bishi ya rik'o shi, "Muhammad akwai abinda nake son dubawa?". Dariya Muhammad yayi mai yawa kafun yace, "Man wai tsabar soyayyar ce tasa a ko'ina ma ganinta kake yi?". Khaleefa ya janye hannun Muhammad lokacin tuni ta fuce daga inda suke. Koda ya lek'a ta harabar gurin bai ganta ba. Daga nan office d'inshi ya tafi da gudu gudu Muhammad na bin bayan shi, ya had'a duk abinda yazo dashi office d'in ya rufe ko sauraron tambayoyin da Muhammad yake jera mishi baya yi, har zai tafi Muhammad ya rik'e shi yace, "ka manta aikin da yake gaban mu zaka tafi gida? Kada fa ka jawa kanka matsala". Warce rigar shi daya rik'e yayi bai ce mishi komai ba ya tafi da gudu... Ahmad daya shawo kwanar ba zato sukayi karo har wayar hannun khaleefa ta sub'uce k'asa ta fad'i. Gara mishi wayar yayi da k'afa yace, "taho mun da ita". Gani yake in ya tsaya d'aukan wayar kamar zata tsere mishi. Ahmad ya durk'usa ya d'auki wayar Allah yasa ba abinda ya same ta, Muhammad ya k'araso ya dafa kafad'ar shi suka bishi da kallo har ya futa daga asibitin gaba d'aya sannan Ahmad ya tambayi, "me ya same shi?" Muhammad yace, "Muna cikin tafiya......". Nan ya bashi labarin yadda komai ya faru. Ahmad ya girgiza kanshi cikin tausayin shi a wannan karon yace, "he's totally lost". Raihana kuwa tana futa a lucky ta samu motar haya ta tafi gida. Kamar tasan tunanin khaleefa tana shiga gidan ta tura kayan fulasan cikin drower, ta fara cire kayan jikinta ko tsayawa ninkewa bata yiba ta tura su k'asan bed, ta fara neman kayan da zata saka da sauri bata samu ba sai d'aya cikin rigunan data gwada kafun ta futa, rigar iya gwiwar k'afarta ce amma fitet data fudda ilahirin shape d'in jikinta gaba d'aya... Tana jin lokacin da aka tab'a k'ofar shigowa gidan tayi sauri ta zura k'aton hijab saman kayan ta tafi zata futa don kore mishi duk wani zargi. Shi kuwa yana shigowa parlon jakar shi ya ajiye gefe ya fara duba inda zai ganta ko wani abu cikin wanda ya gani a asibiti bai samu ba, tunanin shine ya kai kan d'akin gadonta ya tafi da sauri... Tana shirin futa shi kuma yana shirin shigowa, k'arfin namiji da mace ba d'aya ba tuni ya ture ta baya da jikin shi ta tafi zata fad'i yayi saurin taryota amma ina saida suka kai k'asa gaba d'aya shida ita. Ta rintse idanunta don ma Allah yasa akan hannun shi ta fad'a bata daku sosai ba, shi kuwa wani rad'ad'i da zugi ne suka ratsa hannun shi mai ciwo suka bi jijiya suka kai har kwanyarshi. Cikin dakiya ya tsurawa fuskarta idanu yana mata kallon kusa da kusa.... Sosai ya shagala da kallonta har ya fara manta abinda ya kawo shi d'akin. Sai ya mik'e da sauri ya juya fuskarshi yace, "sorry". Itama mik'ewar tayi. Tana kallon shi ya dinga laluba cikin d'akin hadda bud'e wardrobe da lek'a bathroom kamar wanda ya ajiye wani abu muhimmi, kafun yayi shiru kamar me nazarin wani abu yana kallon hijabin jikinta, kamar wanda ake umarta haka ya tako gently har gabanta yana sake kallon k'asan hijabin daya rufe har k'afarta. Daga yanayin kallon da take mishi ya gane bata da gaskiya. Ba tare da saninta, zaton ta bare tsammanin taba ya d'age hijjabin jikinta gaba d'aya ya wurga shi kan gadon d'akin. Taja jikinta baya da sauri ta jingina da bango tare da rintse idanunta. Baisan yadda zai fasalta abinda yaji ba, gaba d'aya tunanin shi ya tafi a kallonta da tsarin halittar jikinta, sam in bacin daya kalleta yanzu bai tab'a tunanin akwai mata masu irin shape d'inta cikin jinsin hausa fulani ba, yafi yadda da wanda bature ya k'era don tallata kayan siyarwarsu wato roba roba. "Wowww". Ya samu bakin shi da furtawa yana sake kallon yadda rigarta ta zana ta, ita kuwa durk'ushewa k'asa tayi ta had'e jikinta waje d'aya, shima hannun shi ya cusa cikin sumar kanshi yaja gwauron numfashi ya juya ya futa da sauri har yana tuntub'e. Yana futa ta murza key a d'akin tana sauke ajiyar zuciya (kuji yarinyar nan fa🤔). Bata jima jikin k'ofar ba ta nufi gaban mirrow tana kallon yadda rigar ta zauna a jikinta, sai kuma ta tuna abinda khaleefa ya fad'a itama ta maimaita kalmar a bakinta ta juya idanunta had'e da tab'e baki ta bar gurin. Sai a lokacin ta samu nutsuwar b'oye kayan data tura k'asan gado, ta sauya rigar jikinta da wata mai fad'i kamar bubu, ta yane kanta da gyalenta. Koda ta futo parlon ba kowa, direct tayi kitchen don samar musu abinda zasu ci tun kafun ya fara tambayarta. Tana aikin ta dinga jiyo tashin maganarshi cikin taushi, sunan Ayman da yake yawaita kira ya tabbatar mata dashi yake magana a waya, koda taci gaba da sauraron shi sai taji kamar akan auntien su suke magana maybe tak'i d'aga wayar ne. Zuwa can taji yana murza key zai futa a gidan gaba d'aya. Tun wannan futar kuwa da yayi bai dawo gidan ba har dare ya fara nisa, sai ta fara tunanin toh ina ya tafi kuma? Tun tana duba agogo har tunaninta ya tafi akan ta kira wayarshi, sai dai tana d'aukar wayarta da nufin kiran shi tashi wayar ta fara fudda slow music a kusa da ita. Kamar kada ta d'auka sai kuma dai ta duba don taga me kiran, Ayman ne ashe tun d'azu yake jera mishi missed call bata jiba. A kunnenta ta kara wayar bayan tayi karambanin d'agawa. "Da alama mun b'ata ma auntie rai sosai har yanzu tak'i saurarona, gashi kai kuma sai kiran ka nake baka d'auka". "Bashi bane Yaya Ayman raihana ce". "Ohh! Raihana ya kike ya gida? Ina khaleefan?". Ya jera mata duka tambayoyin. "Lafiya lou, ya futa sai dai in ya dawo". "Okay" ya fad'a sai kuma kit ya katse wayar. Tabi wayar da kallo a hannunta, ta yink'ura hannunta rik'e da wayarshi ta bud'e k'ofar parlon. Abun mamaki yana tsaye ya dafa k'arfen gaban gidan yana fuskantar gaban gidan. Tayi turus tana kallon shi da k'ok'arin rufe k'ofar daga ta bayan shi. "Ban futo da key bafa". Ya fad'a ba tare daya motsa daga yadda yake ba, Saita fasa rufewa ta k'araso gab dashi ta mik'a mishi wayar, "Yaya Ayman yana ta kiran ka". Baice mata komai ba sai juyowa da yayi yana kallon ta. Ta maida kanta wani gefen daban don kaucewa kallon kwayar idanun shi. Ya karb'i wayar ta juya zata koma yayi saurin rik'o hannunta, cak ta tsaya da tafiyar data fara har ya tako suka daidaice ya d'auki hanyar komawa cikin gidan rik'e da ita. Cikin kujerun parlon ya zauna ya bata umarnin zama kusa dashi, ta zauna a d'arare tana wasa da yatsun hannunta da suka sha adon han lalle yayi maroon. Yabi yatsun da kallo kamar zaice wani abu sai kuma dai ya fasa. Yana shirin kiran Ayman wayarshi ta fara shigowa, sai ya d'aga ya kara a kunnen shi, sunyi magana ta adadin wasu mintuna kafun yasa Ayman ya shiga d'akin auntien ya maida wayar handsfree, shima tashi handsfreen ya maida ita don bashi da wani abu da zai iya b'oyewa raihana a yanzun. Tana zaune tana operating system d'inta fuskarta sam ba walwala Ayman ya shigo da sallama ya ajiye wayar kusa da ita ya koma gefe ya zauna kamar marar gaskiya yana satar kallonta. Daga ta cikin wayar muryar khaleefa ta fara futowa inda yake magana da fad'in....... _kuyi hak'uri dani.... ba editing_ *Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615* _Comment and share_✍️ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy 7️⃣0️⃣ "Tabbas mun b'ata miki rai, mun kuma kasa fahimtarki duk da mu a gurin mu muna ganin abinda muke k'ok'arin yi shine dai dai.... Auntie kin kasance d'aya tamkar da million a rayuwarmu, kin raine mu da soyayyah da tarin sadaukarwa irin wadda ba kowacce uwa ba, ko iya nan aka tsaya kin mana abinda ba zamu tab'a iya biyan kiba har k'arshen numfashin mu, Amma in aka zo in terms of maganar lafiya, kema kinsan zamuyi iya yin mu wajen ganin mun tsira da lafiyarki saboda in muka rasa ki bamu da wanda zamu rab'a ya zame mana kwatankwacin ki..... Shiyasa a karon farko muka zo gare ki da neman alfarmar ki taimake mu ki ajiye aikin nan, saboda likita ya tabbatar kina buk'atar hutu garkuwar jikin ki yayi rauni duk da kina ta fafutukar yak'i da hakan..... Koda ba'a fad'a mun akan kari ba kinsa an b'oye mun ruhina bai samu salama ba a lokacin da kika kwanta jinya saida sauk'i ya samu gare ki....". Rufe system d'in gabanta tayi ta kira sunan shi, "Khaleefa" Ya amsa da, "na'am". "Yanzu wannan umarnine ko shawara?". Ta tambaye shi. "Babu ko d'aya, neman alfarma ne idan har zai yiwu". Shiru tayi kafun can ta nisa tace, "shekara biyu ya rage nayi retire, yanzu kuna son na hak'ura da aikina duk shekarun dana d'auka su tashi a banza?". Ba wanda ya amsa ta cikin su. "magana nake daku ku bani amsa mana kunyi shiru bayan duk kunsan tsarin aikin Nigeria". Khaleefa ne yanzun yace, "kiyi hak'uri auntie amma da kinyi mana bayani tun farko". "Saboda kune kuke jagorancin rayuwata ko?". Kusan a tare suka fara bata hak'uri, bata ja doguwar magana daga kowannen su ba ta kashe wayar khaleefa shima Ayman ta sallame shi. Khaleefa ya maida duban shi kacokan ga raihana da take zaune gefen shi ko kwakkwaran motsi ba tayi. "Kin tambayeni zaki futa wani uzuri daga makaranta kullum, sai dai ban tambayeki me zaki yi ko inda zaki je ba ke kuma baki fad'a mun ba". Tsilli tsilli tayi da ido ta kasa ce mishi komai har saida ya sake maimaita tambayarshi, "Ina kike zuwa?". Kin ce mishi komai tayi still, hakan ya matuk'ar d'aure mishi kai ya kuma d'an fusata shi kad'an, "abu na k'arshe dana tsana in yiwa mutum magana gani gashi ya share ni.... Wallahi zaki ja na hana ki futa a gidan nan gaba d'aya". Sai a yanzun ta d'ago ta kalle shi jikinta a sanyaye sosai, bata san me zata ce mishi ba shiyasa ta zab'i yin shiru. Mik'ewa yayi tsaye ya d'auke wayarshi ya sake kallonta yace, "daga yau ban amince ki d'ara ko'ina daga makaranta ba in kuma kika karya abinda na fad'a......". Sai yayi hucewarshi nashi guri ya barta nan zaune. Itama bata da zab'in daya huce mik'ewa tayi nata gurin. ***Kwana biyu a tsakani sooraj baya ganin yarinyar, tun yana saran ganinta har ya gaji da ajiye maganar a ranshi ya fad'awa andal a wani yammaci daya futa motsa jiki. Already raihana ta fad'awa likitar yadda sukayi da khaleefa dama, ta kuma goyi bayan tayi biyayyah wa mijinta tunda dai aljannarta tana k'ark'ashin k'afar shi, kuma a k'ark'ashin shi take, shiyasa sooraj yana mata maganar kai tsaye ta bashi amsar mijintane ya hana ta. Sooraj ya tambayeta, "me yasa ko dama baisan tana zuwa ba?". "Eh". "Me yasa zatayi haka ita?". "Saboda in yaji ba zai tab'a barin tazo gare kaba". Da wani mamakin ya sake cewa, "meyasa?". Barin abinda takeyi tayi ta d'ago tana kallon shi kafun ta bashi amsa da cewa, "saboda a duniya bana jin yana da mak'iyin daya huce ka, sooraj kana sane da kuskuren daka aikata a rayuwarka kuwa koka manta? Kasan duk wani makusancin surayyah yaji labarin irin butulcin da kayi mata a rayuwa ya k'ulla gabar har abada da kai mara k'arshe kenan kuma ba zai tab'a bar wani nashi ya rab'e kaba?". "Idan na fahimce ki kina nufin yarinyar nan tana da alak'a da wani cikin dangin matata surayyah?". "Matar daka kasa yiwa adalci dai ka saketa sakin daba kome bayan ka huda zuciyarta da soyayyar ka". "Wayyoh Allah! Har sai zuwa yaushe ne zaki fahimci duk abinda ya faru ba laifina bane? Ko d'aya bani da masaniya akan duk abinda ya faru shekarun da suka gabata, nima an bani komai a juye ne sai daga k'urarren lokaci na gane gaskiya, Amma insha Allahu na had'u da surayyah zan nuna mata nadamata a aikace, zan aureta irin auren da babu saki har abada.....". Mik'ewa tayi tsaye jikinta har tsuma yake cikin tsananin b'acin rai take duban shi tana cewa, "a wanne hadisin akace namiji zai iya sake auren matar daya yiwa saki uku, sannan kai kana tsammanin surayyah zata ci gaba da zama babu aure?....". Wani irin fad'uwa gaban shi yayi, kanshi ya sara tashin hankali ya sake bayyana k'arara kan fuskarshi, abubuwan nan biyu shap mantawa yake dasu in bacin yanzu da andal ta mishi tuni. Sai ya had'a hannun shi biyu alamar rok'o yace, "don Allah ki gafarceni, ba don niba ba don na Isa ba, sai don daraja da albarkacin na tab'a rayuwa da k'awar ki, rayuwa irin wadda ba zata tab'a gogewa a cikin kwakwalwa da zuciyata ba, andal ki fad'a mun meye alak'a ta da wannan yarinyar da kike turowa kawo mun abinci mai suna raihana?". Ya k'are maganar idon shi cike da ruwan hawaye kamar zaiyi kuka. Wani irin sanyi jikinta yayi, tabbas ta karb'i nadamar sooraj a sarari duk da har yanzu zuciyarta bata gama hucewa da sakin k'awarta da yayi ba. Sai ta sauke ajiyar zuciya tace, "yaushe doctor jurgen Zai rubuta maka sallama?". "Kwanaki biyar masu zuwa". "Toh insha Allahu zan fad'a maka iya abinda na sani nan da kwana ki biyar d'in in muna da rai da numfashi". Ganin yayi shiru sai ta sake cewa, "banga surayyah ba amma insha Allah akwai hanyar da zamu bi mu sameta wannan alk'awari nane". Sai a lokacin ya d'an ji nutsuwa kad'an har ya sauke ajiyar zuciya, yasan ba zata tab'a yaudarar shiba. Akan haka suka rabu ya tafi ya fara lissafin kowacce second, minute da hour har a kaiga wuni. ****Raihana kuwa ranar data kama weekend da safe tana kwance cikin bargo tak'i futowa parlon sam bare ta had'u da matsalolin khaleefa da baya rabo da neman magana yanzun, shiyasa tana gama had'a karin kumallo tayi shigewarta d'aki ta kwanta tana ta tsokanar yasmine ta wattsapp, a haka k'aramin sak'o ya shigo daga gurin likitar su khaleefa, sak'on da saida tayi ta juya shi a ranta da tunanin hanyar da zata cika umarnin likitan kafun can tayi k'undunbala ta rubutawa khaleefa gajeren sak'o kamar haka, "Assalam! Fatan ka tashi cikin k'oshin lafiya, Ina ta son maka wata magana amma tayi mun nauyi gashi bansan ta yadda zaka d'auki abun ba..... Shin kasan kuwa mahaifin ka yana rayeee?". Khaleefa yana kwance, gaba d'aya tunda ya tashi sallar asubah bai koma bacci ba yana ta lazumin shin har yunwa ta fara sakad'ar cikin shi ya kasa jurewa. Hakan yasa ya zura takalmin shi ya futo, sanye yake da jallabiyyah maroon colour data haska shi sosai, yana duba dinning yaga ta jere mishi abincin masu rai da lafiya..... Ya fara bud'e pulasan k'amshin abincin na dukan hancin shi yana sake tunzira yunwar shi. Yana saving kanshi zai fara cin abincin sak'on ta ya riske shi, sai ya ajiye cokalin ya bud'e ya fara karantawa..... Lokaci d'aya kanshi ya sara zuciyarshi ta harba, sai ya mik'e tsaye ko neman izininta baiyi ba ya shiga d'akin kamar an wurgo shi ya k'arasa har gaban gadon da take kwance yace, "ke kika turo mun sak'on nan?". Ta gyad'a mishi kai, sai ya durk'usa a gabanta, "ya akayi kika san haka? And kina nufin duk tsawon shekarun nan auntie k'arya take mana". Sauƙe k'afarta k'asa tayi tace, "tayi hakane saboda b'acin rai da alk'awarin data d'aukar wa ranta, kamar yadda yanzu da kanta ta bud'e wannan babban sirrin ta kuma so kuji....". "Innalillahi wa'inna ilaiji raji'un" ya fad'a had'e da dafe kanshi da hannuwan shi yana faman maimaitawa ko zaiji dad'i a ranshi. "me yasa auntie zatayi mana haka? Me yasa! Me yasa!!" Sai kawai ya fara kuka, a karon farko da raihana taga raunin shi har taji matuk'ar tausayin shi ya sake ninkuwa a cikin zuciyarta. Inda ta adana diaryn nan taje ta d'auko ta dawo gaban shi ta durk'usa ta mik'a mishi, ya kalli littafin yana tuna sanda raihana take kan karatun shi harta dinga b'oye mishi, yasa hannu ya karb'a jikin shi a sanyaye ya fara karantawa, Koda ta yink'ura da nufin futa ta bashi guri hanata yayi, haka taci gaba da zama a gaban shi har ya karance abinda yake ciki tas ya fara sauke ajiyar zuciya, wani gefen na zuciyarshi na nuna tsananin tausayin mahaifiyar shi da kishin abinda mahaifin shi ya aikata mata. "Lahaula walak'uwwata illah billahil aleeyul azeem". Sai kuma ya d'aga hannun shi sama yana fad'in "alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah na gode maka daka sa bata haramtacciyar hanya mahaifiyar mu ta samar damu ba...". Sai ya juyo ya kalli raihana kwayar idon shi harta sauya launi, tunanin shi shine meya kamata ya yiwa wannan yarinyar da dubun alkhairan ta gare shi? Ya kalli yadda duk ta kasa sakewa a gaban shi saboda suturar jikinta, riga ce iya cinya da wando tight jeans kanta ba d'ankwali sai tubkar gashinta data sauka har dokin wuyanta, ga gashin yasha gyara sai walwali yake. Sai ya fad'ad'a murmushin fuskarshi yace, "get ready nan da minti biyar kacal". Ko jiran amsarta baiyi ba yayi hucewarshi ya barta nan zaune tana bin bayan shi da kallo. Doguwar riga kawai ta d'ora saman kayan jikinta ta yane kanta da gyale ta zauna tana jiran shi don kada ta b'ata mishi lokaci, zamanta ba jimawa shima ya futo cikin sabuwar shigar data k'ara futo dashi a asalin matashin saurayi mai ji da ilimi da kuma nasaba. A motar haya suka futa sukaje wani babban shopping mall Gropius passagen ya dinga jidar mata kayan duk da hannun shi suka kai kai, tun raihana bata gane ita yake jidarwa wannan uban tulin kaya ba har ta fahimta ta fara k'ok'arin dakatar dashi. A lokacin kallonta yayi ido cikin ido yace, "Raihana! U deserve more than dis". "Na gode sai dai wannan kayan sunyi yawa, inji da wanda na bari a gida ma....". Murmushi kawai ya mata yana ganin duk yadda zai mata bayani ba zata tab'a ganewa ba, daga nan itama fara d'aukar mishi kayan maza tayi masu shegen kyau da tsada har ya gama ya taho gurin da take ko lura da kayan data cika basket d'inta dashi bai yiba. "Ke zaki tayani d'aukar wasu fa". Ya fad'a yana kallonta, "nima baka ga ina da wanda zan d'auka ba?". Sai a lokacin ya ankara da lodi lodin kayan data jibgo na maza, "ke zaki biya hala?". "Eh amma ta hanyar rage wasu daga cikin kayan daka d'auka mun...". Murmushi kurum yayi yana ganin ba zata gane ba. Yana jinta a bayan shi tana cewa ya za'ayi ma kai ba zaka siya komai ba. Bai kula taba yaci gaba da tafiyarshi tana bin bayan shi. Koda suka dawo gida yaga zata shiga kitchen hana ta yayi, sallah kawai sukayi ya sata ta k'ara futa suka tafi wani babban gurin cin abinci. Bata iya cin komai a gurin ba saboda banbancin d'and'ano da yawaitar idon mutane, k'arshe sai biyawa yayi Mc Donald's ya siya mata burger, pizza and chips, ya k'arasa da ita delabuu ice cream ya k'ara mata da kayan chocolate dasu ice cream d'in sannan suka koma gida. Haka ya tara mata kaya na uban kud'i kuma a haka gani yake kamar basu wadatar ba, duk da kayan snacks da sweet basu wani dameta ba sai bata k'i ciba gudun kada ta sare mishi gwiwa. Taci burger da yawa tasha ice cream duk a gaban shi tana had'awa da mishi godiya. Har dare khaleefa yak'i barta ta matsa nesa dashi sai labarin Auntie yake sake jaddada mata, gashi ta hana shi fad'awa Ayman a cewarta a bari sai an samu lokacin daya kamata, ko dinner tare sukayi cikin farin cikin daya wanzu a rayuwar shi daga safe zuwa daren ranar, lallai raihana ta gama musu komai a rayuwa tunda har ta silarta auntie ta bud'e musu babban sirrin da babu kamarshi. *****Washe gari tunda yayi sallar asubah bai koma bacci ba kona 30 mint da yake yi in ya saita alarm yau babu shi sam a idon shi, haka ya shirya da wurwuri ya shiga kitchen neman ruwan da zaisha na safe kamar yadda yake bisa al'adarshi zai sha ruwa kullum da safe kafun yaci komai. Tana tsaye d'aure da afron ash tashin ta kenan daga bacci yau a makare saboda yawon da khaleefa ya jata jiya data kwanta gajiya ta lullub'e ta sai yanzu da kyar ta samu ta farka, tayi sallah a gurguje ko azkhar bata tsaya yiba tayo kitchen gudun kada ya tafi bai sa komai a cikin shiba. Tana fara aikin sai gashi ya shigo, saita russuna tana gaishe shi, ya amsa yana kallonta tun daga k'asa har sama wani abu na tsirga mishi ata jinin jikin shi har ya haddasa mishi lumshe ido ya bud'e kan tulin gashinta da d'ankwalin ya zame k'asa saboda sauri bata tsaya d'auka ba. Sit yaja ya zauna ya tsiyaya ruwa a cup yasha yaci gaba da kallon yadda take aikin da taka tsantsan. Fahimtar da gaske in yaci gaba da kallonta a haka za'a samu lukutar matsala sai ya koma parlon ya bud'e datar wayarshi ya shiga chat na k'arfi da yaji, tun yana d'an fahimtar abinda yake yi har ya gaza gane komai, idon shi ya rufe tsohon tsumin shi ya tashi matarshi kad'ai yake hangowa a idon shi, sai ya dinga jin haushin kanshi daya shiga gurinta har ya tsaya kallonta. "Mtsss!". Yaja tsaki shi kad'ai ya kife wayarshi kan kujerar da yake zaune ya kwantar da kanshi baya yana jin yadda komai yake son cakud'e mishi da yarinyar daya yiwa ranshi alk'awarin bar wa twin d'inshi don shi yafi cancantarta bashi ba. Har ta gama aikin ta jere mishi abincin a dinning tana duban lokaci da yiwa Allah godiya data gama abincin taga yana da sauran lokacin karyawa a tsanake. Bayan tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar material ta sake gyare gashinta daya hargitse gurin bacci, ta shafe jikinta da turare mai k'amshi, ta yane kanta da k'aramin gyale ta futo ta same shi yadda ta barshi, sai ta k'ara duba lokaci, toh yana da sauran mituna goma sha biyar za'a ce, cikin kulawa ta k'arasa gab dashi kamar zata dafa kafad'arshi tace, "kana lafiya kuwa?". Ya bud'e idon shi suka sauka a kanta, k'amshin sassanyan turaren ta na kaiwa cikin hancin shi, baice komai ba ya tashi zaune da murya mafi k'asa yace, "kawo mun abincin nan, kiyi saving d'ina bada yawa ba". Ta juya cikin karb'ar umarnin shi ta kawo mishi abincin har inda yake ita kuma ta koma dinning zata karya a can. Bai wani ci na kirki ba ya mata sallama ya tafi aikin shi yau ko Ahmad bai jira ba yayi tafiyarshi. ****A yammacin ranar doctor jurgen Ya rubutawa Suraj takardar sallama bayan an tabbatar daba wata matsala cikin gyaran da akayi mishi, yayi sallama da kowa har su Ahmad ya tafi gurin andal da zumud'in jin labarin inda zaiga surayyan shi..... Ya sameta suka tattauna, bata fayyace mishi komai ba saboda wasu dalilan, ta nuna mishi wannan raihanar matar d'an surayyah ce amma zuwanta na k'arshe gurin shi mijinta ya d'auke ta sun huce Saudi zasuyi umrah na sati d'aya daga nan su huce Nigeria. Sai ta k'ara da cewa, "Ni nan da kaina nayi maka alk'awarin zanje Nigeria gurin su na tabbatar na Nemo maka inda surayyah take don yarinyar nan ta bani tabbacin tana kan alk'awarin tane shiyasa tak'i neman ka duk tsawon wannan shekarun". A wannan karon hak'urin sooraj ya k'are, ta kaishi limit d'in da bazai iya jurar ci gaba da sauraron labaran tatsuniya daga gare taba, sai kawai ya mik'e tsaye gabanta da raunatacciyar murya tace, "ya kamata ki daina yaudarata haka andal, ba dai don naji dad'i hankalina ya kwanta kike k'irk'irar duk wannan labarin ba? Toh ya isa haka don Allah! Na hak'ura nasan watak'ila nida surayyah har abada, sai dai ko in mun had'u a laheera za'ayi mana hisabi......". Jikinta yayi sanyi fiye da kullum tausayin shi na ratsa ta, sai dai a halin yanzu muddin tace zata had'a shi da khaleefa zata had'a jagwal don hutun data d'aukar musu ita da khaleefa sai sati na sama, and so take har wancen d'an uwan nashi yazo, so take yaran su same shi a family house d'insu kowa ya gansu. "Kayi hak'uri amma wallahi summa tallahi nayi alk'awarin zan zo tare da wanda suka san inda surayyah take har garin ka gidan ka.... Amma kafun nan ina son na d'auki hutu don bazai yiwu na yanke aikina ba tare dana ajiye kwakkwarar hujja ba....". Sooraj shiru yayi bayan gama sauraronta, ya yarda da rantsuwarta amma yana shakkun zuwanta da addu'ar Allah yasa ba yaudara bane, cikin wannan k'ila wa k'alan ya mata sallama ya futa daga cikin asibitin, kwana biyu kacal zai k'ara ya bar k'asar. **** Ya dawo aiki da yamma lis lokacin raihana bata dawo gidan ba, d'akin shi ya shige ya rufo ya kwanta akan gadon shi ko takalmin k'afar shi bai iya cirewa ba. Yana jin wayarshi nata sharara ringing amma ya kasa picking haka kiran ya dinga shigowa yana katsewa ba k'auk'autawa. Raihana koda ta dawo bata fahimci yana gidan ba tayi duk abinda zatayi a gurguje ta shige d'akinta don tara hankalinta ga mutanen da suke ta son magana da ita. _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy one 7️⃣1️⃣ Hirar data jima ba tayi da kowa ba ta samu dama a yau, aikuwa ta gaisa da mutane da yawa da tayi nesa dasu, a k'arshe suka k'are hirar su ita da doctor k'awar doctor inda take fad'a mata ya kamata a tsara tafiyar har Ayman. Suka jima suna tattauna yadda komai zai tafi kafun suyi sallama ta ajiye wayar, tana jin wata matashiyar budurwa na yiwa likitar magana kafun wayar ta katse, kusan duk lokacin da zasuyi waya a gida sai taji maganar matashiyar yarinyar, tana kyautata zaton y'arta ce ko surukarta don tasan a shekarunta zaiyi wuya a rasa d'aya cikin biyun data ayyana. Koda raihana ta duba lokaci sai taga ashe dare ya fara nisa, ta d'auro alwala ta shige cikin bargo tare da wayarta, k'aramin sak'o ta rubutawa khaleefa duk da zaton yayi bacci. "Assalam! Zaka iya sa Ayman ya shirya cikin satin nan ku had'u a Abuja ganin mahaifin ku? Amma fa ba buk'atar ka bud'e mishi komai ya kamata a mishi bazatan dai....". Tana tura sak'on ta wulla wayar gefe ta karanto addu'o'in ta na bacci ta k'ara rufe har kanta. Ba jimawa kuwa wani sumammen bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Lokacin da sak'on ta ya riske shi yana kan darduma ne idar da sallar shafa'i da wuturin shi kenan yana lazumi yaji k'arar shigar sak'o, ya mik'a hannu ya d'auka don tun daya dawo gidan bai duba wayar ba, yasan maybe cikin wanda suka gama jera mishi kiran nan d'azu wani ya kasa hak'uri saida ya mishi txt. Sab'anin tunanin shi daga gurin raihana ne, sai dai ya karanta sak'on yafi sau hud'u bai fahimci abinda take nufi ba, sai kawai ya yanke hukuncin danna kiran no ta don yaji gundarin abinda take nufi, cikin rashin sa'a tayi bacci kuma wayar a silent ta barta. Bazai iya hak'uri ba sai yaji komai duk da tunanin shi ya bashi barci take. Kamar wanda ake azalzala haka ya zura soft sliffas d'inshi ya futo daga d'akin hasken parlon ya haske shi tarwai, ya tsaya ya rage wutar sannan yaci gaba da takawa gently har cikin d'akinta. Ya tura k'ofar ya shiga kamar b'arawo yana bin komai na d'akin da kallo wata nutsuwa na kwaranya ruhin shi, dawwamammen k'amshin d'akin da yake son a dinga sammi shi a nashi d'akin shima na k'ara tsuma shi. Cikin duhun daya mamaye ko'ina ya isa har gaban gadonta ya durk'usa ya fara janye lallausan bargon data rufe jikinta gaba d'aya har fuskarta ta bayyana, sai ya tsurawa fuskarta idanu yana kallonta da yadda take sauƙe numfashi cikin nutsuwa da jin dad'in baccin nata. Ya d'auki lokaci mai yawan da baisan iyakarshi ba a gabanta yana kallon innocent face d'inta sannan yaja mata bargon ya mik'e ya fuce daga d'akin gaba d'aya. Saida yasha tea sannan ya koma d'akin shi, a daren ranar ya jima kafun bacci yayi awon gaba dashi. ****Asubar fari duk suka tashi a gidan ba tare da kowanne cikin su ya sani ba, khaleefa duk da yadda ya kwana da tunanin sak'on ta bai nemi ganinta ba sai bayan daya idar da sallah yayi azkhar d'inshi cikakke, yayi wanka yayi duk abinda yake gabatarwa da safe kafun futarshi aiki. Lokacin daya futo har ta shiga kitchen gidan tsit sai b'uruntun ta kawai da k'amshin girkinta ke tashi, sai ya nufi kitchen d'in bakin shi d'auke da sallama. Tana tsaye tana firar dankali sai dai jikinta a suturce da wadatacciyar sutturar data b'oye surar jikinta gaba d'aya. Tana ganin shi ta russuna ta fara gaishe shi, ya amsa yana kai kofun ruwan daya tsiyaya bakin shi. Daya gama shan ruwan ma saida ya d'auki wasu mintuna sannan yace, "me kike son cewa a sak'on ki na jiya?". Rage gudun futar gas d'in da take aiki dashi tayi tace, "hala baka duba abinda na rubuta ba da kyau?". "Ni abinda ban fahimta ba shine, wa yake shirya komai ta hanyar amfani dake?". Shiru tayi ba tace komai ba, sai yayi murmushi ya sake cewa, "koda yake ba buk'atar na sani yanzu, bari muga har zuwa lokacin da zata fashe ko?,,," ya k'are maganar da sigar zolaya. K'asa tayi da kanta ba tare data yarda ta sake kallon kwayar idon shiba. Har ta gama aikin yana kitchen d'in, danne danne yake a waya rabi kuma yana kallon duk wani motsinta ta k'asan ido, koda ta gama yaga tana shirin had'a tray hana ta yayi, sai tayi saving d'inshi a nan ya fara ci da basmala. Yaci da yawa kuwa kasancewar jikin shi akwai yunwa don tea ne kawai a cikin shi sai ruwan da yasha da safiyar yau. Suna zaune opposite to each other sai dai sam ba abincin take ciba juya cokali kawai take, da gaske ta takura da zaman shi ga kwayar idon shi data mata nauyi aka, ko son d'agowa ba tayi bare su had'a ido. Shima yana lura da ita that's why yana gamawa ya tashi, in less than 20 mint ya gama shirin futa office ya lek'a ya ajiye mata kud'i masu yawa da yakan bata lokaci bayan lokaci ko zatayi wani abu dasu. Tabi kud'in da kallo har ya futa ta kasa furta komai. ****Kamar yadda raihana ta fad'a mishi a rubuce haka ya yaudari Ayman suka shirya zasu had'u a garin Abuja cikin k'arshen satin, ya kuwa amince, ko neman hutu baiyi a gurin aikin shiba, ya tsara dai zai zo Friday Sunday da yamma ya koma. Duk abinda akeyi bai fad'a ma auntie ba don baisan ta inda zai fara tunkararta da zancen ba, gashi twin yace kada ya kuskura tasan dashi zai had'u. Ana saura kwana biyu su tafi ya samu auntien a kitchen, da yake kwana biyu mama haleema bata da lafiya bata samun zuwa, shiyasa tana tashi office kai tsaye gida take zartowa ba wani uzuri da take yadda ya tsaida ita, albasar data yanka taga yasa hannu ya fara wankewa, sai ta tsaya kawai tana kallon shi don tasan lallai akwai magana a bakin shi. Ganin kamar bai fahimci kallon tuhumar da take mishi ba sai ta karb'e bowl d'in da albasar ke ciki, "nagode da tayin aiki, amma daka fad'a mun abinda ya kawo ka basai ka sawa hannun ka warin albasa mai wahalar futa ba....". D'an b'ata fuska yayi ganin ta harbo jikin shi da wuri, da kuma garin neman gira yana neman rasa ido, sai ya had'e fuska yace, "nifa gani nayi aiki ya miki yawaa nazo na taimaka". "Ni dai na yafe taimakon, d'auki morning fresh ka wanke hannun ka same ni a parlour na in na gama sai muyi magana". Kujera yaja ya zauna yace, "ai maganar ba mai tsayi bace, dama tafiya ce ta kamani nassarawa, sai dai bazan huce kwana biyu ba". "Toh Allah ya tsare hanya amma me zaka je yi nassarawa? Ko a can y'ar tawa take?". "Ahm... ah... a'a...bikin wani abokin aikin mune". "Allah ya sanya alkhairy bani invitation card d'in". D'an dam yayi, daman yasan za'ayi haka, Cox duk d'aurin auren da sai anje wani gari tana karb'ar invitation card saboda address, "ai.... Aita....aita online ne aka turo catin, ni ban ma samu nawa ta no ta ba". Ajiye cokalin hannunta tayi tana kallon shi da wannan uwar k'arya daya yanko mata, da yake ba sabawa yayi ba duk ya wani diririce tsabar yadda k'afar shi ta sage sai jingina yayi jikin drower. Ita kuwa Murmushi tayi kafun tace, "Ina fatan kana sane da kai ba k'aramin yaro bane? Am sure da kayi aure akan k'a'ida da yanzun kana da yara biyu ko? Toh Alhamdulillah kasan abu mai kyau da akasin shi, kasan yadda zaka kula da kanka a duk inda ka tsinci kanta ko? Good and fine Allah ya tsare hanya....". Tana gama fad'in haka ta juya taci gaba da aikinta, Ayman kuwa jikin shine ya sake yin sanyi lakwas! Har ya fara tunanin fad'a mata gaskiya sai kuma k'ak'k'arfar gargad'in da khaleefa ya mishi ya dawo cikin kwanyar shi a take, sai kawai ya fuce a kitchen d'in, Auntie ta bishi da kallo tana girgiza kai. ****Da yammacin ranar tafe take sauri sauri don sunyi da doctor andal zasu had'u a gidanta, bata son kuma likitar tazo tayi ta jiranta. Kamar a tare suka taho sai gasu sun sauka kusan a tare. Ta bud'e gidan Suka shiga suka gaisa ta gabatar mata ruwa da tea tasha, sannan ta fad'a mata yadda komai zai kasance, ta d'aukar musu hutu ita da khaleefa na sati biyu yanzu visa kawai ya rage musu. Cikin jin dad'i raihana ta dinga murna, she's just imagining yadda khaleefa zaiyi a duk lokacin da akace gashi ga mahaifin shi, sai taji kamar ta jawo lokacin kusa ace su k'ifta ido su gansu a gaban Suraj Abdallah tofa. Andal ta jima a gidan har sai dab da khaleefa zai dawo ta tafi. ****Da dare tana zaune kan darduma tana muraji'ar karatun al-qurani mai girma, da kwantaccen sauti irin wanda sai kana kusa da ita zaka ji. Daga inda take ta dinga jiyo hirarrakin mutane a cikin gidan, tasan bazai huce Yasmine da mijinta ba shiyasa ta rufe qur-anin ta zura hijab dogo ta futo parlon. Sab'anin tunanin ta Muhammad ne da matarshi yau a gidan nasu. Ta k'arasa da fara'a kan fuskarta suka gaisa dasu, kafun ta kawo musu abinci da ruwa. Basu ci abincin ba da yake ma a gurguje suke saboda dare suka musu sallama suka tafi, khaleefa ya raka su har waje ita kuma taci gaba da zama cikin parlon da takardun da andal ta bata ta ajiye mishi d'azu har ya dawo ya tadda ita. Ya zauna tare da kwantar da kanshi baya. Saita d'ora mishi takardun kan cinyarshi, ya bud'e idon shi da suka fara lumshewa saboda gajiya da bacci yana mata kallon neman k'arin bayani. Maimakon tayi kamar yadda yake so sai tayi k'asa da idon, shima kan papers d'in ya maida nashi idon yana bin komai daki daki har ya gama karantawa, ya sauke doguwar ajiyar zuciya, duk wani abu da yake tsarawa akan yadda zai had'u da mahaifin shi sai tunkaro shi yake gradually, lallai koma waye ya d'aukar mishi hutun nan yana kusa dashi.... Amma zaiga ko waye ranar da zasu tafi. "D'auko mun passport d'inki". Ya baiwa raihana umarni. Ta tashi ta shiga d'akinta mintuna k'alilan ta dawo dashi a hannu ta mik'a mishi. Bai karb'a ba saima bin yatsun hannunta da yayi da kallo, yana matuk'ar k'aunar kallon yatsun saboda yadda lallen jiki ya haska fatar ta, ya kuma dace da jikinta, ci gaba da kallonta yayi har zuwa kan fuskarta data nuna gajiyawa da tsaiwar da take, ya lumshe ido ya sake bud'ewa akan cute lips d'inta da suke ta glowing kamar tasa lip balm, wani irin yanayi ne ya fara taso mishi ata jinin jikin shi yana bin kowacce jijiya yana isar da sak'on da yake ta son gujewa cikin ranakun. Raihana kam gajiya tayi da tsaiwa ta ajiye mishi a gefen shi ta juya zata bar gurin, sai dai cak ta tsaya jin ya sak'alo yatsunta, ko kafun ta gane takamaiman abinda yake shirin yi tuni ya jawo ta baya jikin shi, sai ganinta tayi daram a saman cinyarshi, ya rungume ta tsam a cikin jikin shi yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ita kuwa gabanta ne yayi wani irin luguden bugu, saita fara k'ok'arin sauka sai dai ya hana mata damar hakan ta hanyar nuna mata k'arfinta cikin cokali ne in aka had'a da nashi, ganin da gaske ita ba kowa bace saita fara marairaice mishi tana rok'on shi, "please ka bari manaa...". Taja kalmar k'arshe saboda yadda taji yana murza yatsun hannunta.... "Ka bari don Allah, bana....". Sake yin shiru tayi jin hannun shi na yin gaba zuwa tsintsiyar hannayenta..... Ya kai bakin shi saitin kunnenta in a cool voice yace, "more complain...more.... Kissess". Ya k'are fad'a tare da sumbatar bayan hannunta. Shiru tayi a jikin shi ta kasa kwakkwaran motsi, tana ganin kamar khaleefa baisan abinda yake shirin aikatawa gare taba, shi kuwa hannunta ya kamo ya d'ora saitin zuciyarshi, "kiji bugun zuciyata raihana....". Lumshe kwayar idonta tayi tana jin yadda zuciyarshi take bugu da k'arfi da sauri. Sun jima a haka kowa da abinda yake ayyanawa cikin zuciyarshi har zuwa lokacin da tunanin shi ya fara dawowa dai dai, kwakwalwar shi ta fara tuna mishi matsayinta gare shi, da kuskuren da zai haifar ta silar kusancin da yake son wanzarwa tsakanin su...., sai ya janye hannun shi daga jikinta ya bata dukkan dama. Ta mik'e jiki a sanyaye ta shige d'akinta da sassarfa. ***** Sauran ranakun da suka biyo baya duk na shirye shiryen tafiyarsu Nigeria ne, da kusan komai yazo musu a dai dai itama raihana sun samu hutun kammala exams..... Khaleefa bai samu nutsuwar fad'awa Ahmad halin da ake ciki ba sai saura kwana biyu jirgin su ya d'aga. Shima labari Ahmad d'in yaji a gurin Muhammad khaleefan ya d'auki hutu, shine ya kira shi a waya yake tambayar shi da son jin lafiya dai, bai fayyace mishi komai ba a lokacin yace sai in ya taso office ya same shi saboda maganar bata waya bace dama kuma yana son ganin shi shima. Koda ya tashi office bai shiga gidan shiba ya samu khaleefan a gaban harabar gidan suka fara magana, bai b'oye mishi komai dangane da yadda yasan mahaifin shi yana raye har zuwa kan yadda komai yake tafiyar mishi a duk'unkune ta hannun raihana. Doguwar ajiyar zuciya Ahmad ya sauke, ya taya shi murna sosai, duk da yaso ace khaleefan ya fad'a mishi komai akan lokaci, da dashi za'ayi tafiyar, amma ba komai tunda watarana zai had'u da Abban. Sai dai fa ya matuk'ar taya khaleefa murna, ranar basu rabu ba har sai bayan k'arfe tara na dare. Khaleefa ya rako shi suna sake yin sallama don ba lallai su sake had'uwa ba tunda jirgin su k'arfe uku na washe garin ranar zai tashi, sai a lokacin Ahmad ya samu damar kawo mishi maganar saleema, ta hanyar laluma da nuna mishi kuskuren watsi da lamarinta da yayi a kaikaice ta yadda zai fahimta bada zafi ba don yasan halin mutumin nashi. Shiru khaleefa yayi bayan gama sauraron maganar Ahmad da tayi kama data raihana sak. Har suka k'arasa sallama suka rabu khaleefa na tuna sunan saleema da yadda komai ya rikice tsakanin su har ya iya mantawa da ita da lamarinta gaba d'aya cikin rayuwarshi, a baya in akace zai iya rabuwa da ita ba zai tab'a yarda ba, sai gashi ta silar abu d'aya ya yakice ta da soyayyar ta cikin rayuwarshi, yakicewa irinta har abada. Saiya sauke kanshi k'asa sunan Raihana na fad'owa cikin tunanin shi, har zuci zuci yake ya had'u da Ayman su warware matsalar nauyinta yabar kanshi ko ya samu nutsuwa in tayi nesa dashi........ Ranar kusan kwakwalwar shi sake cinkushewa tayi, ta wani sashen kuma zuciyarshi na nutsawa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, har yanzu jin abun yake kamar tatsuniya, wai suma mahaifin su yana raye? Suna da uba kamar kowanne d'a har zai had'u dashi ma gobe? Kai wannan abu yana yi mishi dad'i sosai in ya tuna...... ****Tun cikin dare kowa a cikin su ya gama had'a kayan shi jaka guda, duk daba dad'ewa zasuyi ba tana fatan khaleefa ya mata alfarma ta k'arasa gida taga iyayenta da take matuk'ar kewar su. So take ta musu bazata shiyasa duk wannan abun bata cewa ummie komai ba sai ranar da suka had'u a nutse ta labarta musu komai. A cikin raihana da khaleefa bansan wanda yafi wani zumud'i da son ganin ya jawo gobe ba, don ranar haka suka kwana zuciya fal da farin cikin tafiyar su bacci ma rabi da rabi duk mafarkai ne...... Ko zuwa lokacin da agogon k'asar jamus ya buga k'arfe tara da mintuna na safe, tuni ta gama had'a karin kumallo ta futar da duk wani abun da tasan zai lalace koya bada matsala bayan tafiyarsu, tayi kwalliyarta cikin riga da skirt na lace milk da adon maroon, ta futo da jaka da takalmi da mayafinta matching colour ta d'ora saman jakar kayanta, so take ta shiga yiwa yasmine sallama don ta fara mata complain ta waya, wai wace irin tafiya ce zasuyi haka ba sallama da mak'ota. Madaidaicin yalolon gyalen ta yafa ta futo rik'e da wayarta tana bin parlon da kallo, tabi food warmers data ajiye saman dinning taga komai yana nan yadda ta barshi tabbacin har yanzu bai futo a d'akin shi ba. Tayi shiru tana nazarin mai yiwuwa har a k'arshe tayi tunanin mishi knocking sai kuma ta fasa, k'aramin sak'o ta tura mishi na neman izinin shi akan futar da zatayi, sai dai mintuna k'alilan da tura sak'on reply ya shigo na k'in amincewa, saita zauna kawai cikin parlon ranta a d'an dame. Tana nan zaune ya futo cikin shigar marrocon jallabiyyah fara sol, gashin kanshi daya d'an taru a kwance bak'i sid'ik sai d'aukar ido yake, jikin shi na fudda k'amshin dawwamammen turaren shi, Koda idon shi ya sauka a kanta kasa d'auke idon yayi saboda wani maseefar kyau data mishi cikin shigar tata ta yau, a take kuma zuciyarshi tayi d'arrr gaban shi yayi mummunar fad'uwa da wani abu ya gifto cikin zuciyarshi. Raihana kam tunda ya futo sassanyan k'amshin turaren shi ya sanar da ita zuwan shi, tana sane ta dake tamkar bata ganshi ba saboda haushin hanata futar da yayi. Ganin yau ko gaishe shi bata yiba shi sai yace mata, "Ina kwana Raihana!". Abun sai yayi mata banbarakwai har yasa ta sauke k'afarta data d'ora d'aya kan d'aya tace, "In...Ina... kwana". "Fatan kin tashi lafiya". Ya fad'a yana sake ci gaba da kallonta, "alhamdulillah" ta fad'a k'asa k'asa har lokacin bata yarda ta kalle shiba. Shima huceta yayi zuwa dinning. Bayan ya gama karya kumallo komawa yayi cikin d'akin shi ya d'auko mukullin gidan da wayarshi ya sake futowa ya ganta inda ya barta. "Bismillah muje ko?". Ya fad'a cikin bata umarni. Ta mik'e kamar zata ce dashi wani abu sai kuma dai ta fasa suka d'auki hanyar futa a gidan gaba d'aya...... ****Saleema kam abubuwa sun sake mata tsanani, gaba d'aya komai ya sake hautsine mata har ya kwantar da ita jinya sosai. Ba k'awa! Ba y'an uwa a kusa! Bare wani mutum da zai iya kawo mata taimakon gaggawa, tun tana iya jurewa da k'arfin hali har ta gaza, a k'arshe dai dole ta dangane da asibiti, ta shafe wasu kwanaki tana jinya har da fudda rai da rayuwar duniya, ciwon daya sabbaba mata bud'e waya don a samu hanyar da za'a sanar da y'an gidan su mutuwarta. Cikin ikon Allah sai gashi ta samu sauk'i ta warke har an sallame ta. Koda Amna taji labari tazo mata sannu bata ce mata komai ba, sai dai har yanzu tak'i sakewa da Amnan don tana son khaleefa har kwanan gobe a k'asan ranta, tana kuma jin zafin Amna da ganinta matsayin wadda tayi silar rabuwar su. Bisa nasiha da shawarwarin da take samu daga likitar da tayi jinyarta ta saki jiki ta komawa asalin rayuwarta, makaranta ce kawai bata koma ba shima cikin satin take shirin komawa in taji kwarin jikinta. Yauma tana zaune bayan gama wayarta da Abban ta, tayi shiru cikin duniyar tunani tana sake nazarin yadda rayuwa ta koma mata, Wai kamar ba itace Saleema y'ar gayu da maza da yawa idon su yake kanta ba! Kamar ba itace khaleefa yake tsara kalaman soyayyah da alk'awari iri iri ba, Sam batasan lokacin da wasu hawaye masu d'umi suka silmiyo saman kuncinta ba saida ta shafa da hannunta taji laima a lokacin da ake kwankwasa k'ofar apartment d'in nata. Ta tashi da sanyin jiki ta wanke fuskarta, ta yafa siririn gyale saman kanta sannan ta bud'e k'ofar. Kamar a cikin irin mafarkan data saba yi haka taga Abdallah khaleefa, sai ta mutstsika idonta don ta sake tabbatar daba gizo idonta suke mata ba, shine dai tsaye a gabanta duka hannuwan shi zube cikin aljihun jallabiyyar da take jikin shi ya jingina da katangar dake kare gaban d'akunan kwanan d'aliban. "Khaleeefaaahhh.....". Ta k'arasa fad'a a sanyaye hango raihana tsaye a gefen shi cikin shigar data sake nuna mata asalin banbancin da yake tsakanin da ita, cikakkiyar mace irin wadda maza da yawa ba zasuyi sakacin mata rik'on wasa ba. Sai taji gabanta yayi mummunar fad'uwa, zuciyarta ta karye, idonta ya ciko fal da ruwan hawaye, jikinta ya sake sanyi lakwas! _Ina godiya da addu'a fatan Allah ya bar zumunci, alhamdulillah naji sauk'i sosai kam sai dai uzururruka sun sha kaina, amma in shaa Allah ina saka ran next week zamu k'ark'are labarin nan gaba d'aya. inda zamu zo muku da wani sabon salon labari na daban nida Dr Fayeeza, masu comment Ina matuk'ar jinjina_ _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy two 7️⃣2️⃣ "Ina son magana da ke". Ya fad'a bayan ya d'auke kanshi ga barin kallonta. Itama cikin k'arfafawa kanta da kanta gwiwa don tana ganin a wannan karon ya kamata ta fuskance shi suyita ta k'are tace, "kazo magana dani amma ka taho da wannan?". Ta k'arasa fad'a tana nuna raihana, saita girgiza kai, "toh ni bazan iya magana da kai a gabanta ba, idan ka manta in tuna maka nice fa Saleema macen data fara bud'e zuciyarka, ta koyar da kai soyayyah har a yanzun wannan yarinyar ta samu gurbin zama a muhallin daba nata ba" ta k'are tana nuna raihana da hannunta, dogon numfashi taja ta sauke ajiyar zuciya taci gaba da danne zuciyarta don kallon raihana ma kad'ai gabanta tsaye khaleefa rik'e da hannunta raise her blood soo high, tayi imanin khaleefa ya barta kenan har abada ko yanzun data kalli kwayar idon shi k'iyayyarta ta gani fal, shiyasa zatayi amfani da wannan damar ta bud'e mishi aiki ta yadda ita kanta yarinyar zata gane shi din kura ce da fatar akuya, tasan babu wani namiji da zaije neman aure ya ya bawa budurwa labarin irin soyayyar da sukayi dashi, lallai kuwa in hakane khaleefa yasan wata ne baisan wata, Shi kuwa ganin tayi shiru saiya hard'e duka hannun shi a k'irji yace, "magana nazo yi dake ba neman fitina ba". Ya rik'e k'afad'un raihana duka biyu, suka kalli juna na wasu sakanni sannan yaci gaba da cewa, "wannan da kike gani saboda shawara da jajircewarta nazo gurin ki muyi magana ta fahimta, sai dai Ina ganin idan hakan ba zai yiwu ba babu lallai babu dole". Sai ya juya da baya ya kamo hannun raihana da nufin tafiya. Jikin raihana a sanyaye matuk'a ta zame hannunta ta tsaya tana kallon shi tace, "kayi hak'uri amma tana akan gaskiyarta ne, komai yana buk'atar sirri a rayuwa... Soo kar ka damu ni zan jira ka a waje". Ta k'arasa fad'a tana jin wani abu na sukar zuciyarta, tun farko da tasan nan zai zo ba zata tab'a yarda ta biyo shiba bare har budurwarshi taji haushinta a banza, saita fara k'ok'arin barin gurin. Sake rik'o hannunta yayi, "Ni dake duk abu d'aya ne raihana! Bazan iya magana da ita muddin ya zamana babu ke ba,,,, kinfi kowa sanin saboda ke da Ahmad nazo gurin ta". Saleema ganin da gaske khaleefa juyawa zaiyi ya tafi saita shanye b'acin ranta, takaicinta, had'e da ruwan hawayen ta tace, "khaleefa yanzu kana nufin wannan tafi ni? Da gaske zaka iya barina har abada saboda kaa same ta? Shin dama haka soyayyah take? Shin wannan shine alk'awarin da kayi mun?.....". Ta gama jera tambayoyin tana fashewa da wani irin kuka. Shi kuwa juyowa yayi yana kallonta, "ga zahiri ma kin gani, in kin manta na tuna miki komai na duniya yana da deadline, Sam a soyayyar da nake miki babu wani abu mai kama da k'arya ko yaudara, ke kika juya komai kika samun k'iyayyar ki cikin zuciya da abinda idanuna suka gani zahiri, sannan ke in banda son zuciyarki taya kike tunanin zanci gaba da sonki bayan na ganki da idona kina..... Wallahi kin bani mamaki, Ashe duk kallon da nake miki ungulu ce ke da kan zabo....". Ya k'are zancen da wani tuk'uk'uk'in bak'in cikin da yake taso mishi a duk lokacin daya tuna irin rayuwar da sukayi a baya. Sai yaci gaba, "duk da haka zan fara da miki godiya, ta silarki gashi na samu mahaifina, a waccen ranar da bamu samu sab'anin nan dake ba, da bazan tab'a tunanin nemo wani daya danganci dangin mahaifina har abun ya kai ga samun babbah jigo da yafi kowa a cikin familyn su muhimmanci ba wato mahaifina! Abu na gaba na janye duk wani alk'awarin aure na a kanki, soo ki saki ranki, kiyi abinda ya kawo ki.... A alak'armu kema kinsan ba cuta ba yaudara, komai ya k'are Ina fatan zaki yafe mun keta iyakar daba tawa ba da nayi.... Wannan shine ainahin abinda ya kawo ni". Saleema da take kallon shi kuka takeyi sosai, ta kasa cewa komai sai kallon shi kawai take shida matar shi, matar data nuna tamkar bata gurin yake duk wad'annan maganganun. Khaleefa kam sake rik'e hannun raihana yayi, ta rintse ido tana jin zuciyarta kamar ta futo, tayi k'asa da muryarta ta yadda saida ya d'an rankwafo kad'an yaji abinda take fad'a, "don Allah ka sake mun hannuuu...na". Wani miskilin murmushi yayi yana kallon kwayar idonta yace, "ko?". Ta gyad'a mishi kai. Tsayawa yayi kawai yana kallonta, yadda gaba d'aya ta kasa sakewa duk jikinta sai rawa yake ya matuk'ar bashi dariya amma baiyi ba ya dake, ga wani kyau na musamman data sakeyi mishi kamar ya saceta ya gudu (toh sace ta mana Ina ruwan wani🤣). Yadda ya shagala da kallon raihana sam sai ya manta da kanshi bare wata Saleema karan kad'a miya da take tare dasu a lokacin. Wadda ita kuma bak'in ciki ne ya sake turnike ta ta sake tunzira tace, "bazan tab'a yafe maka ba kuwa khaleefa don ka matuk'ar cutar dani,,,, tunda har kasan ba zaka aure niba amma ka dinga amfani da soyayyar da nake ma kana rayuwar data keta k'a'ida, khaleefa har ciki kayi mun fa in ka manta in tuna maka... Macuci! Mayaudari!! Mahainci!!!". Kusan a tare raihana da khaleefa suka rintse ido suna jin saukar zancen kamar ruwan dalma me k'arfin narka zuciya, khaleefa kam hannun raihana yaja sukayi gaba don muddin yaci gaba da sauraron kalaman bakinta masalahar da yazo don a samar ba zata samu ba. Sunyi tafiya mai nisa yana rik'e da hannunta, tsabar yanayin da yake ciki yasa baya ganin inda yake d'ora k'afar shi sam. Unexpected yaci karo da wani dutse ya dake shi kuwa, ya saki hannun raihana da take bayan shi da sauri ya durk'usa a gurin yana kallon inda dutsen ya daka har jini ya taru ga k'afar sai zugi take mishi. A nutse raihana ta k'araso gaban shi ta durk'usa itama kamar yadda tayi tana kallon ciwon da yaji da fuskar tausayawa, hannunta ta kai gurin ta d'an matsa, aikuwa khaleefa baisan ya mik'e ba sai ganin shi yayi kawai a tsaye, itama ja baya tayi tace, "sorry". Bai kula taba yaci gaba da tafiya tabi bayan shi. Duk da tazarar dake tsakanin su bai damu ba haka ya dinga tafiya a k'afa bashi da niyyar tare musu motar haya, tun tana kawaici har ta gaza saboda takalmin k'afarta bazai iya d'aukar ta har zuwa inda yake so ba ga tafiyarshi da sauri. Bai fahimci shi kad'ai yake tafiya ba har saida ya daina jin sahunta a bayan shi, Koda ya waiga tana can baya a zaune kan wata kujera ta dafe kanta da hannunta. Sai a sannan ya gano girman kuskuren da yake son aikata mata. Taxi ya nema ya mishi bayanin inda zai kaisu suka k'arasa inda take ta shiga suka huce gaba d'aya. **** Suna komawa ya shige d'aki raihana bata sake ganin shiba saida ta futo janye da trolley waya kare a kunnenta suna magana da likitar. A lokacin shima ya futo cikin sabuwar shiga ta wasu expensive English wears, fuskarshi a d'inke tamkar bai tab'a dariya ba, hakan yasa raihana sake kama kanta ta dakata da wayar sai dai idonta na kan k'afar shi tana kallon yadda yatsu uku suka kumbura, Koda ta d'ago ta kalli fuskarshi ido suka had'a, ta maida kanta gefe da sauri ta nufi hanyar futa. Tsaye tayi a wajen ta k'urawa gidan Ahmad ido, tana fatan yasmine ta lek'o suyi sallama tunda khaleefa ya hanata shiga. Har ya gama rufe gidan ya k'araso gidan take kallo, shima gidan ya kalla sannan ya maida duban shi gareta, "kije kuyi sallama, amma kada ki huce minti uku...". Kamar ta share shi sai kuma taga rashin dacewar hakan, koba komai ba shi zata kalla ba, hak'k'in mak'otaka da mutumcin yasmine d'in zata duba. A nan tabar duka jakunkunan ta ta nufi hanyar shiga gidan. Khaleefa yabi bayanta da kallo yana jin wani irin tashin hankali na musamman na kawo mishi ziyara, "bansan wanda yafi buk'atar kiba nida Ayman! Duk dani tarin laifuffukana zasu iya mun katangar k'arfe da samun soyayyar ki, tabbas zan kasance cikin tarihin mazan da soyayyah tayi wasan kura dasu...... Saleema!". Ya k'are fad'a yana jin sabuwar tsanar ta a ranshi. "Wace irin tafiya kuma a irin wannan lokacin? Ina fatan ba wani mummunan abune ya faru a can Nigeria ba". "Ko d'aya, duk da nima bazan ce komai ba tunda ba nice dalilin tafiyarba khaleefa ne". K'asa tayi da kanta idonta yana cikowa da hawaye, "zamu tafi Yasmine watak'ila ni ba lallai na dawo ba, Ina fatan zaki yafe mun abinda nayi miki na k'untatawa cikin ajizanci da kowanne d'an Adam baya rabo dashi, Allah ya raba ki da abinda ke cikin ki lafiya ya k'addara saduwarmu da alkhairi". Yadda ta k'arasa fad'a tana wiping tears haka yasmine ma ta fara magana cikin kuka, "haba mana ya zaki ce ba zaki dawo ba, so kike nima zaman k'asar ya gagare ni kenan? Raihana don Allah kada ki k'i dawowa, in kuma ba haka ba in bar Ahmad na biyo bayan ki....". Duk yadda raihana take cikin k'unci saida murmushi ya sub'uce kan fuskarta, haka duk suka hau dariya suna share hawaye kafun su rungume juna. Sam Yasmine hana ta futa tayi tana ta karanta mata sak'onnin gaskiya da rok'on ta dawo bada jimawa ba, suna haka khaleefa ya kira wayar raihana, ta k'arasa sallama da Yasmine da sauri ta fuce, har ya tare musu mota ya shigar da kayan ciki. ***** Tafiya suke cikin babban filin tashi da saukar jiragen kowa rik'e da jakar kayan shi, suna tafe raihana nata waigen inda zata hango likitar sai dai basu had'u ba, ta d'ora k'afarta kan matakalar shiga cikin jirgin taji kamar an dake ta har tana neman fad'uwa, koda ta juya wata kyakkyawar matashiyar yarinya budurwa ce, da tafi kama da Arab a fuska ma kamar ta santa, kafun tace wani abu yarinyar ta riga ta da cewa, "am sorry please". Ta gyad'a mata kai taci gaba da tafiyarta har yarinyar na bin bayanta tana ta magana a waya. Kusan a cikin jirgi ma haka ta gama bulayin kalle kallenta amma ba inda taga doctor andal bare mai kama da ita. *After some hours* Jirgin su yayi landing a Abuja lafiyar Allah, passengers duk sun fara sauka, suna tafe ita da khaleefa yanzun ma dav da dab sai bin takun shi raihana take har Allah yasa suka isa inda wata mota ke jiran su, shi ya bud'e mata back seat ta shiga shi kuma ya shiga mazaunin gefen driver. "U are welcome matar big bro" Ayman ya fad'a ba tare daya kalleta ba. Murmushi ta k'ak'alo ta fara gaishe shi, ya amsa a tak'aice ya maida akalar hirar shi ga d'an uwan shi. Haka sukayi ta hirar su har Allah yasa suka k'arasa hotel d'in da ya musu booking d'aki. Suka shiga har Ayman daya taimaka wajen shigar musu da jakunkunan kayan su. Room and parlour ne sai toilet a parlour bathroom a bedroom. Bata zauna a parlon ba tayi bedroom don gabatar da uzururrukanta. Khaleefa ke tambayar Ayman ina ya samu mota? Ya fad'a mishi gidan su abokin shi daya sauka. Daga nan duk sukayi shiru, yana son shiga gurin kayan shi baya son shiga hak'k'inta, k'arshe dai ya hak'ura yayi amfani da toilet na parlon ya d'auro alwala ya futo nan ya sauke faralin sallolin da suka huce shi. Ayman bai yarda sunci abincin hotel d'in ba yaje da kanshi gidan abinci mafi kusa ya musu oder abincin Nigeria irin wanda yasan sun jima basu ciba. Yana tahowa zai shiga ita kuma tana tahowa zata futa, waya ce kare a kunnenta tana magana cikin matuk'ar zafi but a sanyaye, tana yi tana duba bayanta kamar tana tsoron wani yaji abinda take fad'a, tunda ya d'ora idon shi a kanta ya kasa d'aukewa, so yake ya takaita abinda yake ji a kanta amma ya kasa, har tazo dab dashi a lokacin itama idonta ya fad'a kanshi, ta d'auke kanta tana son tuna inda taga fuskar a dai dai lokacin da take k'arasa wayarta cikin harshen Arab, "Eh! To ammie ce taje had'a wasu y'ay'an k'awarta da mahaifin su, Ni kuma ban Isa masauki ba saida na nemi sim card na kira ki don kawai na fad'a miki yadda mukayi dashi, da yadda zamu kawo k'arshen komai ba tare da mun gogawa ammie laifi ba okay". Iya abinda kunnuwan shi suka ji kenan ya gifta ta itama ta giftashi ta huce. Kusa da d'akin daya kamawa su khaleefa wata mata ta futo me dattako da matuk'ar nutsuwa. Har zai huce ta sai kuma yaga tana ta kallon shi, hakan yasa yace mata "sannu". Murmushi tayi da yaren da tasan yafi fahimta tace, "kaga mun had'u a k'asa d'aya ko khaleefa?". Ayman shima murmushin yayi yace, "I'm sorry amma... Ba khaleefan bane Ayman ne". "So he's your twin?". Ta tambaye shi, ya gyad'a mata kai, murmushi ta sakeyi, ya tsaya yana knocking k'ofa, few minute khaleefa yazo ya bud'e mishi ya shiga ciki. Yana zama cikin parlon yana fad'in, "yanzu wata ta ganni ta kira sunan ka, bansan sai zuwa yaushe mutane zasu fara banbance muba". Khaleefa tattare mishi hankalin shi yayi gaba d'aya yace, "a nan Abuja kuma? Cikin hotel d'in nan?". Ayman ya gyad'a mishi kai cikin tabbatarwa kafun ya fara warware mishi yadda sukayi, bayan ya nisa ya sake tambayarshi, "how does she looks like". Ayman ya mishi kwatancenta, a take tunanin shi ya bashi andal ce, toh amma ba zaiyi saurin yanke hukunci aje kuma ba hakan bane. Khaleefa ya mik'awa raihana abincinta, Ayman kuma suka ci tare da d'an uwan shi, bayan sun nutsu yake tambayar shi dalilin wannan zuwan bazatan daya gayyato shi. Murmushi khaleefa yayi don shi kanshi in za'a kashe shi baisan amfanin zaman da zasuyi a hotel d'in ba, abu d'aya daya sani raihana ta tabbatar mishi zai had'u da mahaifin shi that's all he know, shiyasa koda Ayman ya jefa mishi tambayar ya d'auke wuta, bai damu da lallai sai yaji ta bakin shiba shima ya mik'e yana mishi sallama kafun ya tafi. Kamar wanda ake umarta haka ya dinga waigen k'ofar d'akin da yaga budurwar nan ta futo d'azu, hoton fuskarta na gilmawa ta cikin tunanin shi, take wani sabon tunani kuma ya fad'o mishi, saiya tsaya cak gaban shi na fad'uwa da sauri, lallai kam akwai abun dubawa cikin abinda zai kawo ta hotel ita kad'ai ta kama d'aki indai ba tare da mijinta tazo ko wani muharraminta ba? tunda dai nan Nigeria ne, k'asar da y'an k'asa suke kama d'akin hotel ba don sun rasa gidan zama ko sun kasance bak'i ba, a'a sai don kawai suna da harkokin banza da suka maida hotel d'in muhallin aikatawa, to ya kenan idan ya kasance da saurayi tazo? Koda yake ba y'ar k'asa bace, toh ko dai da mijinta tazo?...... Sai ya waiga yana sake kallon hanyar data bullo d'azu, kamar wanda aka umarta kuma yaci gaba da tafiya da sassarfa har ya fuce. ****A daren ranar khaleefa yana da tambayoyi da yawa da yake son yiwa raihana, sai dai bai samu damar hakan daga gare taba, already tayi bacci lokacin daya lek'a ya d'auko jakar kayan shi d'ungurungum zuwa inda ya zab'a ma kanshi matsayin gurin kwana wato parlour. ****A washe garin bayan sun karya kumallo da lafiyayyen breakfast da khaleefa yayi order, raihana tayi shirinta mai kyau cikin kayan da suka dace da jikinta, tana son magana da doctor andal amma batasan ko ta Yaya ba, tana zaune a gefen bed shiru khaleefa yayi knocking yana neman izinin shigowa, ta jawo gyalenta kamar bak'on mutum shi d'in a gareta ta yafa sannan ta tafi donta bud'e mishi k'ofar......... Kuyi hak'uri da jina shiru kwana biyu, wallahi abubuwa da yawa sun sha kaina, amma insha Allah cikin satin nan zanyi k'ok'ari mu rufe littafin gaba d'aya, inda zamu zo muku da sababbin littattafan mu masu d'auke da sabon salo........ Kada ku manta👇 Doctor ferhyeezz m usmern ce, and merhreeyaert lerwerl as in-identical twins _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy three 7️⃣3️⃣ A tsaye yake hannun shi duka biyu zube cikin aljihun wandon shi, yanayin fuskarshi kadaran kadahan ya tsaya yana kallon yadda ta wani rik'e handle, baiyi niyyar shiga ba amma yadda tayi d'in ya sashi nufar ciki direct. Saita kauce ta bashi guri ya shiga ya maida k'ofar ya rufe. "Ina... yin... Ina kwana". Ta harhad'a zancen da kyar, Yace, "lafiya lou fatan kin tashi lafiya". Bata amsa ba, Shiru duk sukayi shi yana ta aikin k'are mata kallo irin wanda ya sata jin matuk'ar nauyin shi, ya kuma kasa d'auke idon shi a kanta duk yadda ya kai ga son aikata hakan. Tuna abinda ya shigo dashi ya sashi mik'a mata farar takardar hannun shi, "doctor andal ta turo wannan a baki". Karb'a tayi ta fara duba takardar mai d'auke da gajeren sak'o kamar haka. "ki zama ready k'arfe uku dot mu had'u a reception" ta d'ago ta kalli khaleefa da yake kallon rufin d'akin, "ita ce ta baka da kanta?". Ya tsaya still yana kallonta da karantar yanayin da take ciki k'arara a kwayar idonta, sai yayi murmushi don ya tabbatar da hasashen shi tun kafun aje da nisa. Baice mata komai ba yasa kanshi ya fuce bayan ya dannawa Ayman kira ya mishi bayani kamar yadda aka yiwa raihana, sai dai ya buk'aci da yazo da wuri kafun lokacin. Haka kuwa akayi Ayman ya tak'aita duk wani abu da zaiyi ya taho da wuri kamar yadda khaleefa ya buk'ata duk da dama bawai yana da abubuwan yi da yawa a garin ba, babban mak'asudin zuwan shi khaleefa ne, kuma yazo da tarin tambayoyi fal a bakin shi, sai dai yana ta hak'uri da dannar zuciyarshi kada ya nuna rashin hak'uri tun kafun aje da nisa. Suna zaune kusa da juna sai dai kowa a cikin su yayi nisa ne cikin zuzzurfan tunani, Ayman ne ya fara nisawa ya d'ago kanshi da yake k'asa idon shi har ya fara sauya launi yace, "kana nufin har yanzu kana nan akan bakan ka?". Khaleefa ya d'ago yana kallon shi da wani irin yanayi yace, "bana da wani zab'i bayan haka....". Wani irin murmushi Ayman yayi wanda yafi kama da yak'e ya kalli d'akin da raihana take ciki kamar zai ganta sannan ya sake maida duban shi ga khaleefa yace, "yanzu ya kake son ayi kenan?". "Kai zan tambaya Ayman!". "Well zaka sake ta kawai na aureta amma sai bayan kun amsa mun wasu tambayoyi kaida ita da amsa ta gaskiya.... Firstly kirawo ta dai ayi komai a gaban idonta....". Dukkan su suka sake d'auke wuta... Kamar wanda ake umarta haka ya tashi ya nufi d'akin, koda yake umarnin nema. Daga inda yayi knocking ta bud'e ya buk'aci ganin ta ya koma cikin parlon ya zauna yana jiranta, ba jimawa itama ta futo a sanyaye ta zauna suka gaisa da Ayman. Sunyi shiru kafun Ayman ya fara cewa, "tambaya ta farko, shin a iya zaman da kukayi da raihana da igiyar auren juna wani abu na auratayya bai tab'a shiga tsakanin kuba.....?". "I don't get you? Wani abu ya faru zance zan saketa ka aureta?". Khaleefa ya fad'a cikin katse mishi hanzari a d'an fusace. "Calm down mana, yada d'aukar zafi tun kafun aje da nisa kuma? Raihana ke ki amsa mun tambayana". Satar kallon inda khaleefa yake zaune tayi sannan ta maida kanta k'asa tace, "a'a". Shiru Ayman yayi yana nazarinta, dama yasan hakan bata kasance ba, shima yana sane yayi tambayar, sai ya sake cewa, "alhamdulillah as i expected! Sai abu na gaba how many kiss and hug? Nasan ba zaku saka mun duk wad'annan a wancan lissafin ba shiyasa zan muku dalla dalla...". "Aymaaaannn! What a silly question". Khaleefa ya fad'a yana mishi wani kallo. Ita kam raihana kunyar Ayman d'in taji, tunda suke dashi magana makamanciyar wannan bata tab'a futowa a bakin shiba, amma yau..... Bata k'arasa tunanin ba maganar Ayman ta katse ta. "Sai kayi hak'uri amma fa dole a amsa mun tambayar nan". Tunani khaleefa ya tafi na lokacin daya dinga attempting kissing d'inta yana kwab'ar kanshi. Itama irin abinda ta fara tunawa kenan. Ganin suna shirin barin duniyar da muke ciki zuwa wata ta daban sai yayi gyaran murya yace, "ba amsa kenan?". "Ayman joke aside please, raihana kije zamu k'arasa magana dashi". Khaleefa ya fad'a da sanyayyayyiyar murya. Kamar an zare mata k'aya haka taji, aikuwa ta bar gurin sauri sauri, khaleefa yabi bayanta da kallo har ta shige sannan ya sauke b'oyayyen ajiyar zuciya. Ayman da yake kallon shi ta k'asan ido yayi murmushi yana lissafa shi, kafun yace, "Ina ganin mubar maganar nan zuwa wani lokaci, yanzu ina zamu tafi k'arfe ukun inta cika?". "Ni kaina ban sani ba, in lokaci yayi zamu gani nida kai........". At exactly 3pm suka futo su dukkannin su, suna gaba raihana na bin bayan su, sanye da wadataccen mayafi saman kayan jikinta, suna Isa reception Ayman da ita ya fara tozali, yanzun ma sanye take da doguwar riga dark blue data haskata, tayi rolling da bak'in gyale, fuskarta ko powder babu amma tayi kyau duk da haka. Doctor andal da take tsaye daura da ita sai dai ta yane har fuskarta da gyalen kayan sai idonta kawai ake gani. Da hannu ta yafuto raihana, ta k'arasa don ganin mai kiran nata, saida taje kusa ta gane likitan ce, tayi murmushi tare da russunawa tana gaishe ta. Bayan sun gaisa ta kalli suhaana da take gefe ta gabatar mata da Raihana. Ta mik'a mata hannu suka gaisa sannan ta fad'awa raihana full address na anguwar kamar yadda auntie ta tab'a bata a rubuce. Raihana komawa tayi gurin su khaleefa ta fad'a mik'a mishi address na anguwar, ya karb'a ba tare daya ce komai ba sukayi gaba ta sake take musu baya. Wata irin tafiya sukayi marar armashi sam a wannan karon ma, kusan tsiran su dasu doctor andal ba yawa suka sauka a katafaren gidan da yafi kama da gari guda. Sun tsaya a gurin har doctor andal ta k'araso, sai a lokacin ta bud'e fuskarta khaleefa ya ganta zahirinta, dama shi tuni ya gane itace zuba ido yayi kawai yaga iya gudun ruwan su, yayinda a zuciyarshi yake ta al'ajabi da tunanin abinda ya shigo da likitar cikin labarin su. Sun gaisa da ita a tak'aice, sukayi shiru likitar na neman layin Suraj a zuciyarta tana fata da addu'ar samun shi a gari a gida tunda ai weekend ne. Khaleefa daya fara gajiya da tsayuwa ya tunkari k'ofar shiga gidan, ya yiwa d'aya daga securities na gidan sallama, suka amsa ya mik'awa d'aya cikin su hannu suka gaisa, shiru yayi yana nazari kafun can yace, "nan ne gidan late Abdallah tofa ko?". Securityn yace, "baka gani ba a rubuce? Just go ahead ka fad'i abinda ya kawo ka?". "Munzo ganin Suraj Abdallah ne". Ya fad'a ba d'ar da zullumin komai". "Yasan da zuwan kune?". Ya girgiza mishi kai, "a'a sai dai munzo daga nesa, kayi mana alfarma mana mu ganshi......". "Ka gafarceni amma yallab'ai baya ganin wanda bashi da appointment dashi ko daga bangon duniya mutum yazo.......". Ya gama fad'a tare da juyawa ciki. . Da sauri khaleefa yabi bayan shi zuwa cikin gidan, wasu cikin securities suka taso suka rik'e shi suna tambayar meye haka zai shigo ba izini. A wannan karon hak'urin khaleefa gazawa yayi, zuciyarshi ta dake ta yadda yake jin sam bazai koma da baya ba tunda yazo sai yaga wannan mutumin daya tara suna sak dana mahaifin shi, he most be his father ma wallahi. "Kome zakuyi mun bazan tafi ba saina ganshi tunda nazo....". Ya fad'a da dakakkiyar murya sam ba tsoro. Wani d'an babba a cikin sune ya k'araso kusa yana mishi kallo na kusa na gaske bayan yasa sun sake shi, ya jima yana nazarin shi hadda kama hab'a kafun ya tambaye shi, "ya sunan ka?". "Abdallah". Khaleefa ya bashi amsa. "Your full name I mean". "Abdallah Suraj Abdallah tofa....". Ai tun kafun ya k'arasa fad'a mutumin ya matso kusa dashi ya rik'e k'afad'un shi da duka hannuwan shi biyu, sai kuma yaja da baya yana sake mishi kallo tun daga sama har k'asa. Duk sauran abokan aikin shi sun tsaya ne suna kallon shi kurum da mamakin abinda yake kallo gurin yaron, shi kuwa da sauri ya juya ya nufi b'angaren da zai sadashi da ubangidan shi. A lokacin yana oarlom shi na k'asa yana tattaunawa mai muhimmanci through system shida wasu abokan business. Tsabar gigitar da securityn yake ciki yasa bai tsaya knocking ba ya cusa kanshi cikin parlon, ya d'ago yana kallon shi, sai ya russuna yace, "sorry boss akwai muhimmin abinda nake son fad'a maka kana da bak'i a waje......". "Haka ya kamata ka shigo mun ko sallama babu, and kafi kowa sanin bana ganin duk wani wanda bani da appointment dashi". Sake russunawa yayi yace, "kayi hak'uri yallab'ai nima nayi yink'urin sallamar su amma d'aya cikin su ya nuna lallai lallai kai yake son gani saboda sunzo ne daga nesa......". Kama hab'a yayi kawai yana kallon shi, tunda har yaga ya ajiye su watak'ila abu mai muhimmanci ya kawo su, sai ya maida kanshi ga abinda yake yi yace, "ka fad'a musu su jirani in zasu iya". Ci gaba da tsaiwa mutumin yayi har saida Suraj d'in ya d'an fusata yace, "yaushe muka fara haka da kai?". Wannan karon durk'usawa yayi kan gwiwowin shi biyu, idon shi still a k'asa yace, "Wanda yazo ganin ka ko makaho ya shafa zai tabbatar da jini iri d'aya ke yawo tsakanin ku, saboda a duniya ni ban tab'a ganin wani mutum da yayi kama da kai sak kamar shiba, sannan yace sunan shi Abdallah Suraj Abdallah tofa wanda yazo d'aya da sunan gidan nan........". Ai tun kafun ya dire zancen shi ya mik'e yana kallon shi, cikin son tabbatar da abinda kunnuwan shi suka jiye mishi ya nufi hanyar futa a d'akin da sauri, mutumin ya mara mishi baya. Khaleefa yana tsaye kyam a harabar cikin gidan ya hard'e duka hannuwan shi a baya. Tun daga nesa daya hango shi gaban shi yake tsananta fad'uwa har yazo dab dashi, a lokacin yaron ya lura da zuwan shi shima ya d'ago yana kallon shi. D'auke wuta Suraj yayi na a k'alla wasu dak'ik'u kafun ya iya motsa lab'b'an shi, "waye kai?". Duk da tambayar ta zowa khaleefa a wani yanayi sai bai fasa bashi amsar data kamata ba, "Abdallah Suraj d'a ga Suraj da surayyah......". A wani irin gigice ya k'araso ya rungume d'an nashi cikin jikin shi yana kiran sunan shi ruwan hawaye na wanke fuskarshi. Abun Kamar a mafarki haka suka jishi su duka biyu, securityn daya fara kasadar sanar da Suraj zuwan khaleefa shiya shigo da ragowar ma ciki. Ayman yayi surrender daga inda yake yana kallon mutumin daya juya bayan shi, da khaleefa da yake rungume jikin shi tsam tsam yana share hawaye. Da hannu khaleefa ya kira shi, saiya k'arasa a sanyaye ta inda zai ga fuskar mutumin, aikuwa sai ga idon su cikin na juna a sa'a, sakin khaleefa yayi yana kallon Ayman dashi kanshi khaleefan, kamar mai tsoron wani abu ya tambaye shi, "shi d'an biyun kane? Sai a lokacin ya tuna takardar da surayyah ta bar mishi mai d'auke da shaidar scanning da result na y'ay'a biyu. Mik'awa Ayman hannu yayi ya k'arasa kusa suka rungume juna, koda baisan komai da yake faruwa ba amma yaji a jikin shi wannan mutumin jinin sune ko daga kamannin da yake dasu zai tabbatar da haka. Sun jima a haka suna kuka raihana da suhaana na jere tare suna kallon su cike da tausayawa, doctor andal kanta hawayen tausayin su take yi. Tana hango tashin hankalin da zasu shiga a gaba, ranar da mahaifin su ya had'u da mahaifiyar su ga soyayyah amma ba aure har abada...... Saida suka jima sannan suka janye jikin su ya tambayi Ayman sunan shi, ya fad'a mishi, sai ya sake jinjinawa surayyah, mahaifinta da mahaifin sa ta samarwa takwarori. Sai a lokacin andal ta k'arasa inda suke tsaye tace, "finally gashi na cika alk'awarina, wad'annan yaran y'ay'an kane, mallakin ka halak malak....". Da sauri Ayman ya nuna shi, "kina nufin wannan shi ya haife mu? Toh waye kenan wanda auntie take nufi ya mutu?". "Magana ce mai tsayi da ba zata yiwu a nan ba". Andal ta fad'a tana kiran su raihana da musu alamun su matso kusa. Suraj ya kalli y'an matan biyu sannan ya kalli andal, "wannan matan sune?". Ta girgiza mishi kai ta nuna raihana ta mishi bayanin itace matar khaleefa, ita kuma wannan suhaana y'a tace, Ayman baiyi aure ba tukun. Ya sake jinjina girman hukuncin ubangiji, ya gama sarewa a rayuwa ba zai tab'a ganin irin wannan ranar ba, ya gama hak'ura da zai ga surayyah a rayuwar shi bare abinda ta tafi dashi a cikinta. Ganin suna ta tattauna abubuwa masu yawa a nan, sai ta buk'aci su k'arasa ciki. A babban parlon gidan ya musu masauki, ba kowa sai wasu matasa guda uku a mabanbantan gurare kowa da abinda yake yi. Suna ganin shi suka mik'e suna kallon shi da russunawa suna mishi barka da futowa. Bai iya amsa musu ba don baya da nutsuwar da zai banbance komai bayan wanda yake gaban shi, "Ina grandma take?". Ya tambaye su, "yanzun nan ta haura stairs". Da kanshi ya nufi matakalar ya haura. Ya sameta tana ta gyara wata y'ar k'aramar baby girl, (wata y'ar dattijuwar mace data manyanta shekarun ta sukayi nisa na gani) bai fayyace mata komai ba ya d'auko yarinyar ya buk'aci data biyo shi don ganin bak'in da yace sunzo ganinta. Turus ta tsaya tun kafun ta gama saukowa tana kallon fuskokin mutanen da suke parlon. Tsabar shock daya shigeta saida taji kamar ta yanke jiki ta fad'i don kanta gaba d'aya juyawa ya fara yi. Saita k'arasa futowa a daddafe tana rarraba ido tsakanin matasan y'an biyun da Suraj tace, "Suraj wad'annan yaran fa? Dama kana da yara bamu sani ba?". Kamo ta yayi ya zaunar da ita ganin duk ta diririce yace, "carm down your mind momma zanyi miki bayani dalla dallah". "Wane bayani kuma bayan gaskiyar dana gani da idona, ai wad'annan yara kam jinin kane abinda kawai ban sani ba shine yaushe aka haife su kuma wacece ta haife su, shin wani auren kaje kayi bamu sani ba?".... Duka ta jera tambayoyin cikin son sanin gaskiyar abinda yake shirin faruwa. Murmushi Suraj yayi har lokacin yana gabanta yace, "duka babu d'aya, wannan yara ne daga matar da a duniya banda kamarta, matar data tafi da dukkan walwala ta, farin cikina, zuciyata d'ungurungum ma....". A hankali yanayin fuskarta ya fara sauyawa, ta sake kallon shi da yaran kamar mai tsoro ko koyon magana tace, "surayyah Adam?". _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy four7️⃣4️⃣ "A ina ka nemo surayyah Suraj kayi shiru ba tare daka had'a mu da ita mun nemi yafiyarta ba?...... Kana nufin wad'annan yaran ita ta haifa maka su? Dama da gaske kana sane da surayyah ta tafi da cikin ka mune bamu sani ba, shiyasa koda yaushe kake cewa kasan kana da y'ay'a inda suke ne baka sani ba?". Saita mik'e har tana tuntub'e ta tafi gurin da suke zaune suna rarraba idanu da kallon ikon Allah har ta k'araso kusa dasu da murya mai rawa tace, "ku matso gare ni y'an biyu nice grandma d'inku.... Ku matso inji jinin surayya da Suraj da yake yawo a jikin ku.....". A sanyaye suka nufe ta suka rungume ta su duka biyun. Kuka take yi karurus, irin mai d'aga hankali da ban tausayin nan tana had'awa da sambatu, ita kanta ba zatace tasan abinda take fad'a ba cox she's out of her sense. A take a gurin ta fara kiran wayar yaran gidan tana fad'a musu suzo maza wani abu muhimmi na faruwa a gida, ko zuwa lokacin da zasu futo daga masallacin gidan bayan sun idar da sallar la'asar gida ya cika fal da yaran gidan hadda jikoki da basuyi aure ba. Babu wanda wannan al'amari bai jijjiga ba musamman matar mukhtar da suka had'u da surayyah a saudiyyah. Fad'in adadin farin cikin da wad'annan Ahali suka shiga a wannan rana ma b'ata baki ne, sunji dad'i sunyi farin ciki sun kuma taya Suraj murna. Kowa sonsu yake da nuna musu kulawa a wannan family, sai ya zamana a gaba d'aya gidan kowa sai haba haba yake dasu cox sunzo gwanin burgewa kamar uwarsu data kasance ta daban. A irin maganganun mutanen gidan andal ta fahimci asalin nadamar da sukayi akan abinda suka yiwa surayyah, da alama tun kafun aje da nisa hak'k'i ya kama sadiya shiyasa a gidan babu ko mai kama da ita. Suraj ya shaida raihana don ba fuska ce da zai iya mantawa ba cikin sauri, don komai k'ank'antar alkhairin mutum a gare shi baya tab'a mantawa, sai a lokacin ya gane dabarar andal da yadda ta shirya komai a sannu sannu bada gaggawa aikin shaid'an ba. Ranar basu suka samu nutsuwa ba sai dare bayan sun nuna buk'atar su ta komawa masauki sai dai da alk'awarin zasu dawo gare su da safe, tun kafun Suraj ya nuna rashin yardarshi momma ta daka tsalle ta dire tace sam ba zasu yarda su koma d'akin hotel ba, saboda tana tsoron kada su b'ace musu murna ta koma ciki, tasan idan har haka ta faru ta mawuyacin abu ne su sake samun Suraj. Duk yadda suka so fahimtar da mutanen gidan k'in fahimta sukayi, a k'arshe dole suka hak'ura aka wakilta wasu matasa biyu da suhaana da zata musu jagora a d'auko musu kayan su da suka zo dasu. Ayman ba don yaso ba yabar suhaana ta tafi da matashi d'aya da budurwa cikin jikikon gidan, sai don yasan ba za'a tab'a barshi ya futa ba amma yana tsoron matashin nan ya mishi shigar sauri don tunda suka zo yake mata wani irin kallo. Suna zaune cikin parlon mahaifin su a daren ranar, a duk yinin gaba d'aya sai yanzun ya samu damar keb'ewa dasu. Yanzun ma saboda dare ya fara nisa ne kowa ya tafi makwanci, suma sunyi shirin kwanciyar cikin tausasan kayan su mabanbanta, suka same shi a zaune bai kwanta ba ya rafka uban tagumi. Sam baisan da wanzuwarsu gurin ba saida suka zauna kusa dashi. Ya sauke ajiyar zuciya yana kallon su sannan a sanyaye yace, "ya doctor surayyah take?". Ayman yace, "tana lafiyarta". "Sai dai tana can cikin b'acin rai da bak'in cikin abinda nayi mata ko? Har yanzu tana ci gaba da gaba dani ko? Shiyasa ta b'oye ku daga gareni tsawon wad'annan shekarun ta maida ni matacce a idon ku tun kafun na mutu.....". Khaleefa kasa magana yayi sai Ayman ne ya bashi amsa da, "tana can cikin kewarka......Amma Bana tunanin ta rik'e ka a zuciyarta don har gobe ba tayi aure ba, watak'ila saboda zaton zaku had'u watarana ku maida auren ku...". "Ni kuma bana tunanin haka.....". Khaleefa ya fad'a ba tare daya shirya ba. Kallon shi mahaifin shi yayi sai yaga shima shi yake kallo. "Meyasa kace haka Abbana?". "Saboda kayi mata abinda bata tab'a zato ba, a kaf cikin tarihin soyayyarku bata d'auka zaka iya rabuwa da ita ba, ta tsane ka tsana mai tsanani shiyasa bayan ta kashe ka a baki ta k'ara da binne duk wani abu daya shafe ka, har gobe Auntie tana kallon ka matsayin....." Sai yayi k'asa da kanshi saboda kalmar tayi mishi tsauri wajen fad'a, "am sorry but kaima bai kamata kayi saurin yanke igiyar auren kuba, at least ya kamata ka d'aga mata k'afa kafun yanke mata hukunci......". Suraj dafa kafad'ar yaron yayi yana kallon shi da idanun shi da suka tara ruwan hawaye..... Kafun yayi magana da raunatacciyar murya, "k'addara! Shine abinda ya faru tsakanina da mahaifiyarku....". Sai ya share hawayen shi, "ku tashi ku kwanta haka saboda dare ya fara nisa, zuwa gobe zaku bani labarin yadda kuka rayu tare da Auntien...". Duk mik'ewa sukayi da sanyin jiki suna mishi murmushin yak'e, shi ya fara haura stairs suma suka bi bayan shi, sai dai har sun fara tafiya khaleefa yace yana zuwa ya koma da baya. Ayman yayi murmushi yaci gaba da tafiya, sai dai shima har ya shiga babban bedroom d'in ya futo ya tsaya ta balcony yana kallon inda twin d'inshi ya nufa, kafun ya biyo bayan shi cikin sand'a har zuwa part d'in hajiya momma, ya tsaya daga inda zai iya gano shi. Shi kuwa khaleefa raihana yake nema ido rufe, don a d'an zaman da sukayi ba tare ba kewarta ta cika shi fal, and yana son had'uwa da ita ya jaddada godiyar shi gare ta don ta gama yi mishi komai a rayuwa. Babu kowa cikin gidan sai wata matashiyar yarinya da yaga ta fara saukowa daga stairs rik'e da system. Tana ganin shi ta fad'ad'a fara'ar fuskarta tace, "Yayaa d'an biyu kana neman wani abu ne". Murmushi yayi jin sunan data bashi yace, "amm ina neman wata cikin y'an matan da muka zo dasu". Shiru tayi tana nazari kafun can tace, "na d'auka ai d'aya matar aure ce dai kamar akace ko, d'aya kuma budurwa....". "Yauwa to matar auren don Allah....". Yarinyar tace, "okay ai tana tare da hajiya momma, na kira maka ita?". "Aikuwa da kin taimaka". Ya fad'a yana murmushi. Itama murmushin tayi ta koma da baya. Raihana tana tare da suhaana suna ta hira a b'angaren momma cikin d'aya daga d'akunan baccinta yarinyar ta shigo ta fad'a mata wani cikin y'an biyu yana nemanta. A lokacin rikicewa tayi a zuciyarta tana tunanin khaleefa ne ko kuwa Ayman? Tasan dai Ayman ba zai turo kiran taba inba wani muhimmin al'amari ne ya taso ba..... A lokacin sanye take da doguwar rigar bacci mai kauri da santsi milk, kanta zagaye da d'an k'aramin hijab daya sauka zuwa kafad'un ta, mik'ewa tayi ta fara neman babban gyale ko hijab, sai a lokacin suhaana ta fahimci abinda ake ciki ta tambayi yarinyar mai suna ihsan da harshen turanci, "wa yake nemanta". Yarinyar ta mayar mata da amsa, "Eh Ina ga ko mijin tane cikin twins ne dai ni da yake ba gane su nake yi ba". Da sauri suhaana ta fizge hijab d'in da sukayi sallah dashi d'azu da raihana ta lalubo zata saka tace, "mijin naki ma sai kin saka mishi hijab da tsohon daren nan? waye ma zai ganki gida kowa yayi bacci?". "Don Allah ki bani.... Bansan fa wanda yake nema na ba, khaleefa nasan tuni yayi bacci maybe sai dai ko in Ayman ne.....". . Suhaana ta sake b'oye hijabin tace, "ba wani Ayman da zai kira ki hajiya wanda ya kasa bacci saboda tunanin ki da kewar kine..... Don haka gwara ki tafi ma tunda wuri kafun ya gaji ya shigo neman ki da kanshi. Masu iya magana suka ce fad'an da yafi k'arfin ka....... Duk yadda raihana taso suhaana ta bata hijabin hanata tayi, dole a k'arshe haka ta hak'ura ta futo da sand'a tana laluben inda zata hango mai kiran nata, don ihsan tuni tayi nata guri. Khaleefa tunda ta futo ya ganta sai dai fahimtar da yayi bata ganshi ba ya sashi ja baya yana ci gaba da kallonta har ta futo sosai. Kusan saida ya d'auke numfashi a lokacin daya ganta gaba d'aya cikin parlon, babu inda bai bincike da idanun shiba a jikinta kafun ya tafi slowly ya rungume ta ta baya. A tsorace ta fara ture shi tana shirin kwalla k'ara, ya rufe mata baki da hannun shi ya fara mata magana cikin kunnenta, "kwantar da hankali, inba niba wa kike tunanin yake da zarrar aikata haka gare ki?.....". Saita dafe hannunta a k'irjin ta tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha tsere don bilhak'k'i ta tsora ta. Koda ya sake ta ma kasa tsayawa tayi da k'afarta yadda ya kamata, sai ya rik'e k'afad'un ta ya jingina ta da bango ya tokare ta da hannun shi duka biyu yana kallonta at the same time yana furzo mata hucin numfashin shi mai d'umi ta saman fuskarta. Kallon daya mata nauyi ga kusancin da suka samu ya fara bada wani yanayi na daban wa gangar jikinta da zuciyarta. "Hak'ik'a kalmomin da zan fad'a da fatar baki sunyi kad'an su bayyana adadin yadda nake jinki cikin zuciyata kona d'auke ki, Raihana u mean a lot to me.... Ina matuk'ar alfahari dake da samun ki matsayin mataaa.....". Ya k'are zancen yana sake kusanta kanshi gare ta, tana son cewa a'a gare shi amma zuciyarta Eh take cewa, abun gaba d'aya ya zarce zato da tsammaninta, kafun ta gama rarrabe asalin abinda take ciki taji saukar hannun shi a bayanta, the next thing kuwa lips d'inshi ya sauka jikin nata cute lips d'in yana gogan shi.... Tana bud'e baki da nufin cewa wani abu ya k'arasa had'e bakin su guri d'aya....... Ayman da yake kallon su yayi saurin juyawa ya d'aga hannun shi sama yana fad'in, "alhamdulillah! Alhamdulillah Allah!!.". Sai ya nufi hanyar futa a parlon, cikin sauri ya huce cikin d'akin shi da mabayyanin farin ciki. Khaleefa kuwa wani irin tattausan kiss yake sake mata mai d'auke da ma'anoni da dama, cikin mantawa da inda suke bare kuskuren abinda yake yi ga matar da yake ik'irarin zai iya barwa d'an uwan tagwaitakar shi yake kissing d'inta passionately, bai barta ba saida ya tabbatar da tayi laushi, sak'on shi ya gama keta zuciyarta yayi male male da kaka gida sannan ya janye.... Ya zuba kwayar idon shi a fuskarta yana son lalubo kwayar idonta amma fafur ta hana mishi damar haka, don gam gam ta rufe idanunta hannunta dafe da bangon da take jingine k'irjinta yana up and down. For the first time da wani abu makanmancin wannan ya tab'a faruwa da ita..... Khaleefa daya tsare ta da ido murmushi yayi ya kira suna ta da gentle and cool voice, "Raihanatu". Bata iya amsawa ba kuma still bata yarda ta kalle shiba. "Say something mana, ko you need more....". yayi tambayar yana yin shafo hannunta zuwa kafad'arta, ai bata bari ya k'arasa inda ya nufa ba ta rik'e hannun shi gam gam tace,, "please stop it....". "Whyyy?". Ya tambayeta da murya can k'asa. Sai a yanzun ta kalle shi ta motsa lab'b'anta, "I don't like it....". "Sure". Ya tambaye ta yana sake kallonta yana ji kamar su dawwama a haka. "Ka bani hanya bacci nake ji, sannan wani zai iya ganin mu a haka kuma.... Kuma... Sai ayi tunanin wani abun daban...". Wani murmushi mai kyau ne yayi escaping saman lips d'inshi yace, "Raihanatu kefa matata ce, waye zai ce wani abu don ya ganmu tare". Narke mishi tayi ganin da gaske yau yana shirin juye mata zuwa wani mutum na daban tace, "Ni dai ka bani hanya,,, Allah bacci nake ji". "Then give me something in return sai kiyi tafiyarki tunda bacci yafi miki hira da mijin ki dad'i". "Ba haka bane, na gaji ne kawai". Ta fad'a a matuk'ar shagwob'e don da gaske ta gaji da tsaiwar haka. "Ni kuma kinga ko kwana zamuyi a haka bazan tab'a gajiya ba..... Raihanatu zan iya b'ata iya tsawon rayuwata tare dake ba tare dana gaji ba a kowanne mataki na rayuwa, kamar ruwan sama mai sauka kamar da bakin kwarya, da tsayuwa cikin tsakiyar rana mai zafi over 40°C, zan jure yunwa da k'ishin ruwa ko halin rashin lafiya, raihanatu kallon fuskarki kad'ai zai bani dukkan farin cikin rayuwata, sauraron daddad'an sautin muryarki kuwa zai sanya mun nutsuwa marar iyaka ciki da bai.... Raihanatu ke haske ce mai yaye duhun dake cikin rayuwar Abdallah, na ganki cikin mafarkina tun ranar farko dana fara d'ora idona a kanki a lokacin da naje gidan iya.....". Tunda ya fara magana raihana take kallon shi, lallai da ace ta fara bacci kiran shi ya risketa zata ce cikin mafarki duk haka take faruwa ba'a zahiri ba, wai itace yau khaleefa yake fad'awa duk wad'annan kalaman? abun al'ajabi. Shiru ya sake biyo ba, shi ya shagala a kallonta ita kuma ta kasa kallon kwayar idonshi, gashi sunyi kusanci sosai don har yanzu hannun shi tokare yake da gefe gefen bangon da take jingine jiki. Ja baya yayi yace, "na barki ki tafi ko?". A hankali ta fara takawa, "ba zaki barmun abinda zan dinga tunawa dake ba duk tsawon dare...?". K'ara sauri tayi sannan ta waigo tace, "Saida safe kawai". Murmushi yayi da yaso hanata ci gaba da tafiya Allah yasa tayi maza ta yak'i zuciyarta taci gaba da tafiyarta da sassarfa. Bai bar gurin ba har saida ya daina ganinta, ya juya ya fara haura stairs yana murmushi. Itama lokacin data shiga suhaana tana kwance, ta d'auka bacci take, saita lallab'a ta kashe glove tayi kwanciyarta tana sakin murmushi mai kyau tana tariyo duk abinda ya faru mintuna biyu zuwa uku kafun yanzun. "Allah sarki Soyayyah, ta karb'e ka ta saka farin ciki, akasin haka kuma ta kusa tura ka lahira". Maganar suhaana ta shiga dodon kunnen raihana, saita juya tana kallonta ta cikin duhun daya mamaye d'akin, murmushi tayi mata, itama ta mayar mata da martani, saita mik'e zaune tana kallonta ta jingina da fuskar gadon, "kamar kina son cewa wani abu?". Murmushi suhaana ta sake yi, "Man yaci rabin lokaci, ya kamata ki kwanta zuwa da safe sai muyi magana kada mu k'arar miki da daren gaba d'aya". Raihana tayi y'ar dariya tace, "Ni bana da matsala da bacci, akan abu mai muhimmanci ina iya k'arar da gaba d'aya dare ba tare dana rintsa ba". Jinjina kai suhaana tayi, "banyi mamaki don matar aure kamar ki ta aikata haka ba, amma kada ki damu da safe zamuyi magana.....". Dariya raihana tayi tace, "Allah ke ko?". Itama suhaanar dariya tayi, haka kurum taji raihanan tayi mata tunda suka had'u, tana jimawa kafun ta sake da mutumin da bata sanshi ba sosai, amma ga raihana sai gashi zuciyarta ta aminta da ita a zaman rabin wuni da kwana d'aya kacal! Ta b'angaren khaleefa baisha wahala wajen gano muhallin da twin d'inshi yake ba, Koda ya tura k'ofar ya shiga a makeken gadon d'akin ya hango mahaifin shi da Ayman suna bacci sadidan, saiya k'arasa ya rufe musu hasken d'akin ya kwanta a d'aya gefen mahaifin nasu suka sashi a tsakiya. Sai dai gaba d'aya bacci yayi k'aura a idanun shi sai tunanin moments d'insu na yanzu yanzun nan, yana tuna komai step by step yana murmushi mai bayyana tsananin farin cikin da yake ciki. Yayi nisa a juye juye da tunanin matarshi kafun wani tunani ya fad'o ranshi..... Saiya mik'e zaune zumbur ya cusa hannun shi cikin sumar kanshi yana yamutsawa da tuhumar kanshi da zak'ewa cikin lamuran raihana, yayi over acting irin wanda bai tab'a yiba don a lokacin daya kusanceta mantawa yayi gaba d'aya da Ayman, Banda su biyu baya hasaso kowa a gefe, ita gundarinta yake gani a zuciyarshi tallin tal! _wannan page sadaukarwa ne ga duk wani masoyin littafin *JARUMAR UWA* Ina fatan kowanne team sun fara gane inda makamar su take...._. May oll our dreams come true🤲happie juma'at Mubarak _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy five 7️⃣5️⃣ Washe garin ranar suka had'a d'an kwarya kwaryar shagali na yiwa y'an biyu barka da dawowa gida, isu isu matasan yaran gidan suka shirya komai, babu wanda ya iya futa office cikin mutanen gidan rankatakaf. Khaleefa duk inda raihana tasa k'afarta zai bita da kallo gaban kowa ba tare da yasan ma yanayi ba, kaffa kaffa yake da ita da samarin gidan kamar ya tsame ta a cikin su, da Allah ya taimake shima ita d'in ba mai rawar kai da son shiga mutane bace, shiyasa ana jimawa ta zame jikinta ta koma gurin ammie (andal) tayi zamanta tare da ita suna ta hirar su har suhaana ta same su tare aka ci gaba da hirar har ita. Kusan ta b'angaren Ayman ma abinda ya dinga faruwa kenan, bai samu salama ba saida suhaana tabar cikin su tabi bayan raihana. Ya fahimci wani matashi cikin yaran gidan gaba d'aya ya fara takura mata, don yana yawan ganin su suna magana lokaci bayan lokaci, daga k'arshe duk inda tayi saiya bita kamar wani jela. So yake ya samu damar da zaiyi magana da ita kafun wani ya riga shi amma baisan tayaya ba, don bai tab'a tsaida budurwa ba tunda yake. Ko Nur ba direct ya tunkareta ba su auntie ne suka gabatar dashi a gurinta, kuma dama suna gaisawa sosai musamman in tazo hutu gidan su. Su kuwa yaran gidan kowa ya gabatar mishi da kanshi a gurin su, babu abinda yafi basu mamaki kamar ganin tulin familyn su amma suke rayuwa daga su sai mahaifiyarsu, ashe sun futo daga babban family da cikakken asali ake tayi musu gorin uba, kusan Ayman kasa jurewa yayi saida yayi kuka, wasu cikin yaran masu irin zuciyarshi na taya shi. Bayan sun k'are budurin su suka samu zama da manyan iyayen su na gidan, aka tattauna dasu akan yadda za'a samu ganin surayyah cikin sauk'i don kowa cikin su a gidan yana son ganinta, Ayman ne ya basu shawarar kada kowa yaje cikin mutanen gidan, tafiyar ya kamata ta kasance ta mahaifin su da ammie, (doctor k'awarta kenan) sai khaleefa ya musu jagora don shine kad'ai yake iya fad'a mata gaskiya komai d'acinta, musamman a case irin wannan daya kamata a tsage gaskiya kowa ya karb'i laifin shi. Da wannan shawara duk sukayi na'am aka ajiye maganar tafiyar zuwa nan da kwana ki biyu da zasu zo. Suraj bayan ya koma part d'inshi number sauban ya lalubo ya tsurawa ido, tsawon lokaci rabon da su gaisa kota waya, sunyi rabuwa irin wadda ba ta yiwa kowa cikin su dad'i ba, amma bai tab'a goge lambar daga wayarshi ba, don cire no dai dai yake da cire duk wani abu na surayyah data tafi ta gadar mishi, su kuma gadon surayyah tamkar soyayyar surayya suke gare shi, soyayyar surayyah kuwa mahad'in rayuwar shine, babu ita tare dashi yana nufin ba ruhi a gangar jikin shi. Sai yaja gwauron numfashi ya gwada dialling no yaji ko tana aiki har yanzu. Aikuwa sai gashi ta tafi, a lokacin sauban yana zaune a office yana aiki kiran ya riske shi, koda ya duba bai tabbatar da abinda idanun shi ke gani ba saida yasa medical glass d'inshi, "Suraj Abdallah kuma?". Ya fad'a a fili tare da picking call d'in, ya kara wayar a kunnen shi ba tare da yace komai ba, daga can Suraj ya mishi sallama, ya amsa shiru ya sake biyo baya kafun Suraj ya kuma tambayar lafiyar shi data iyalin shi. Ya amsa kamar zaice ya fad'a mishi dalilin kiran direct, "dama kira nayi mu gaisa na kuma nemi yafiyarka". "Ayyah Nagode amma komai daya faru ni ya huce a gurina tun lokacin". "Toh Masha Allah! Sai dai ina son zan shigo cikin satittikan nan idan ba damuwa.....". Sai a lokacin raunin sauban ya bayyana, yanayin shi ya sake sauyawa cikin k'arfin hali da dauriya yace, "kayi hak'uri amma ina ganin mubar maganar zuwan nan, ni da kaina zan neme ka inta kama". Suraj yace, "Toh ba damuwa Nagode ma'asaalam". Ya ajiye wayar a sanyaye tare da zare farin tabaran idon shi gefe, ya juyo da hoton ta da yake kan table d'inshi yana kallonta, tunda k'uruciyarta akayi hoton tana dariya da hak'oranta farare tas da suka bayyana a waje..... Hoton ya d'auka ya sumbaci forehead d'inta yace, "I miss you dear sister". Sai ya maida hoton gefe ya fara share ruwan hawayen da suka cika idon shi. Shima Suraj ta b'angaren shi yana gama wayar ya had'a kanshi da babban glass windown da yake tsaye kusa dashi. Khaleefa daya k'araso gurin yaja tunga ya tsaya yana kallon shi cike da tausayawa, magana yazo suyi amma ganin a yanayin da yake saiya fasa ya juya kawai ya bar gurin. ****Ta b'angaren Raihana bayan sun idar da sallah sunci abinci ammie take tambayarta, "sai kika ga mutumin da kike kaiwa abinci matsayin mahaifin ku ko?, Bayan nace miki d'an uwan shine bashi ba". Murmushi raihana tayi tace, "na fahimce ki ammie kin tsara komai ne daki daki bada sanin kowa ba". Ammie tace, "hakane! Saboda a lokacin bana son shida khaleefa wani yaga wani, don ba zaiyi abinda ya kaishi ba, amma yanzu Masha Allah Alhamdulillah tunda komai yana tafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali bada gaggawa ba". "Hakane kam sai hamdala sun karb'i mahaifin su ba tare da wata matsala ba". Sun d'an ci gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da ta futa suka zamana daga ita sai suhaana, sai a lokacin raihana ta karkata akalarta rankatakaf gare ta tana tambayarta labarin soyayyarta, "kada ki damu zaki ji labarin komai sai dai ba yanzu ba please". Raihana da take kallonta tace, "ayyah kada ki damu sannan kiyi hak'uri na dame ki da son jin abinda baki shirya futar dashi ba yanzu ko". "Ba haka bane, abune da bana son tuna shi sam shiyasa amma insha Allah bada jimawa ba zan baki labarin komai". "Kada ki damu Allah yasa mu dace dear". "Ameen ya Allah! Sai dai nima akwai abinda nake son tambayarki idan ba zaki damu ba". "Ko kad'an fad'i tambayar ki direct". "Auren ki da mijin ki..... Ina nufin taya kuka had'u soyayyah ta fara tsakanin ku har ta kai ku ga aure...?". Shiru raihana tayi don ta tuna mata abubuwa da yawan gaske hadda wanda hankalinta suke kaucewa daga kansu. "Ya dai? Na dawo miki da zuciyarki d'anya ko?" Raihana ta girgiza kai, "a'a kawai na tafi tunanin wani shud'ad'd'en al'amari ne, auren mu ba kamar kowanne aure yazo ba, a tak'aice had'uwar mu da kwana biyar aka d'aura mana aure". Suhaana aka ta d'ora hannunta tace, "wayyoh taya soyayyah ta shige ku cikin kwana biyar kacal da had'uwa". A wannan karon murmushi raihana tayi tace, "kuma da yake soyayyah ta shallake duk zato da tunanin mai tunani...... Abinda yafi haka ma yana faruwa, baki jiba akace inda so da yak'i....". Sai duk sukayi dariya, daga nan suka ci gaba da tattaunawa har zuwa inda dare yayi suka kwanta bacci, suhaana nata mata tsiyar ta kwanta bata ji daga mijinta ba anya ta yiwa kanta adalci kuwa?. ****Kamar yadda Ayman ya bada shawara haka akayi, Suraj ya shirya tafiya a private jet d'inshi, shida khaleefa da raihana zasu tafi, sai doctor andal da momma data tubure sai anyi tafiyar da ita zasu biyo bayansu kwana d'aya bayan zuwan su. A ranar da zasu tafi duka mutanen suka zama ready banda raihana da batasan ma ana yiba saida ammie take tambayar ya ta ganta bata shirya ba. "Futa kuma zamuyi ammie?". Ta tambaya, sai a lokacin ammie ta gane ba suyi magana da khaleefa ba gaba d'aya gashi har sun shirya ita kawai suke jira. Sai bata fad'a mata abinda yake faruwa ba a yadda ta ganta shirye tsab tace taje mijinta na jiranta. Ta yafa mayafinta wadatacce ta d'auki wayarta a hannu ta futa, a babban parlon gidan ta same su suna k'arasa sallama da mutanen gidan. Sai ta tsaya kawai tana mamakin inda zasu tafi kuma ga khaleefa da Abban shi rik'e da jakar kaya. Abune da yake matuk'ar yiwa raihana wahala har yanzu sabawa da mutanen gidan, duk lokacin da zata gansu sun had'u a guri irin haka saita diririce, su kuwa ba ruwan su sai haba haba suke da ita. A tak'aice suka gama sallama da kowa suka futa, raihana ce ta karb'i jakar hannun Abban su khaleefa suka futa su biyun tana bin bayan su. Ko a cikin jet d'in ma khaleefa na kusa da ita, ya kwantar da kanshi jikin kujerar da yake zaune, duk da idonshi a lumshe suke amma ita yake kallo ta k'asan ido, komai na yarinyar nan daban ne, yana son nutsuwarta da sassanyan kwalliyarta, komai tana yinshi bada zafi ba. A hankali yasa hannun shi ya rik'o nata tattausan hannun, sai a lokacin ta juyo ta kalle shi, shima ya wara idonshi a kanta ya sakar mata murmushi mai kyau, had'e ranta tayi kad'an tayi k'asa da kanta tana kiciniyar kwace hannunta, sake fad'ad'a murmushin shi yayi ya tashi zaune da kyau yana ci gaba da kallonta, "Ashe zaki iya....". A dai dai lokacin Allah ya bata ikon kwace hannunta duka, sai tayi murmushi k'asa k'asa da muryarta kamar yadda yayi magana tace, "gashi kuwa ka gani". Wani murmushin ya sake yi har hak'oran shi saida suka bayyana. Daga nan basu sake ce da juna komai ba har suka k'arasa, sai dai a d'an zaman da sukayi ya samu cikakkiyar nutsuwar daya rasa cikin kwanakin da suka gabata. Sun sauka lafiya inda suka yada zango a guest house d'inshi da yake a......quarters, gida ne plat part biyu sai k'aton parking lot mai d'auke da motoci na alfarma biyu, duk yadda raihana taso d'auke kanta ga barin kallon tsaruwar gidan amma ta kasa, haka ta wara idanunta tana bin komai da kallo, har khaleefa ya shigo ya same ta, daga bayanta ya tsaya yace, "ya dai madame me kike kallo haka?". "Gidan yayi kyau sosai Masha Allah". Murmushi yayi shima yana yaba yadda aka tsara komai yace, "Masha Allah kam yayi kyau". Sai a lokacin ta juya ta kalle shi, ya sakar mata murmushi had'e da kashe ido d'aya, ta juyar da kanta da sauri tana waige waigen neman Abba gudun kada ace yana parlon. Bata ganshi a gurin ba, saita k'arasa shiga khaleefa na take mata baya har cikin tsakiyar parlon, a lokacin ta fahimci k'urar da muhallin yayi, hakan yasa tabar gurin tana neman inda zata ga mopper ko guntun towel haka.... Khaleefa kam jingina yayi da bango bayan ya shafo k'urar parlon da d'an yatsar shi ya gani. A harabar gidan ta samo dangin su broom, burget, mopper da kyallen da zatayi amfani dasu wajen tsabtace d'akin. Yana nan tsaye ta dawo ta nad'e gyalenta a jikinta ta fara share gurin, ganin tana aikin sai ya k'araso yana kallon yadda take yin komai. Saida ta gama sharewa zatayi mopping ya hana ta, murmushi kawai tayi a lokacin da taga yadda ya zage yana goge k'asan gurin da duka k'arfin shi. Dakatawa yayi yana tambayarta, "meye abun dariyar kuma?". Raihana tana gumtse bakinta tace, "ba komai sannu da aiki". Ya sake had'e girar sama data k'asa yace, "yauwa" Daga nan suka ci gaba da aikin su. Ko zuwa lokacin da Suraj ya futo sun kusan gama gyare arean da saitin kujerun parlon suke, da hanzari ya k'arasa futowa yana fad'in, "a'a kubar aikin nan haka raihanatu, na nemi layin mai kula da gidan ne ban samu ba da tuni ya k'araso da masu aiki sun gyare ko'ina". Raihana kanta a k'asa tace, "Abba bari mu k'arasa kawai tunda mun riga mun fara". Zaiyi magana khaleefa ya rigashi da cewa, "please Abba ka bari mu samu ladan nan". Murmushi yayi cikin matuk'ar sake jin yaran a cikin zuciyarshi yace, "toh shikenan amma ku fara gyara inda zaku gabatar da sallah tukun, ga spare rooms nan zaku iya zab'ar wanda zaku zauna ciki. Duba lokaci khaleefa yayi, sai ya ajiye burget d'in hannun shi don dama ya gama goge gurin. D'aya daga bedrooms d'in parlon ya samu ya shiga sai dai shima komai yayi k'ura, alwala kawai ya d'auro yabi bayan mahaifin shi zuwa masjid, hakan yasa raihana shiga d'akin ta gyara shi tsab, bayan ta gama ta feshe ko'ina da room freshener. Wani abun mamaki sai gashi kafun su dawo ta had'e ko'ina na gidan, sai dai fa kayanta sunyi bud'u bud'u da k'ura, tana son yin wanka amma ba sponge kuma ba kayan da zata sauya, gashi gaba d'aya a jagwale take da ammie ta fad'a mata tafiya zasuyi ba zata yarda ta biyo khaleefa ba shiri ba. Gefen bed ta samu ta zauna tana danne danne a wayarta har Allah ya dawo dasu gidan, tunda suka shigo Abba yake shi mata albarka da yaba mata, a parlour suka zauna ya kunna wutar gidan, khaleefa zai zauna yayi saurin dakatar dashi, duba plate a kitchen ka kai mata abincin mana". Baiyi musu ba wajan juyawa ya d'auko plate d'in da cokula, a lokacin raihana tana kwance rigingine idonta k'ur akan rufin d'akin tana tunanin yadda zatayi da kanta, gashi ta hargitse duk cikin d'akin babu komai don baya daga d'akin da yake gudanar da rayuwar shi inya zo garin bare taga wani abu mai kama da suttura. Abun duk ya taru ya yi mata yawa, tana jin turo k'ofar shi ta tashi da sauri tana kallon shi. A kusa da ita ya k'arasa ya zauna ya fara kiciniyar juye abincin daya musu order har ya gama ya ajiye plate d'in tsakiyarsu yasa cokali ya fara ci bakin shi da basmala. Ganin ta tsaya kallon shi sai ya kalleta, "kici fa tun kafun ma na cinye shi duka?". Kauda kanta tayi gefe don ita a yanzu bata abincin take ba, shima ajiye cokalin hannun shi yayi duk da irin yunwar da yake ji kuwa yace, "what the problem?". K'asa ta sake yi da kanta tana wasa da fingers d'inta yayinda hawaye ya cika idanunta fal, dawowa yayi gabanta ya durk'usa ya kamo duka hannunta ya rik'e yana kallonta, kamar ya zugata aikuwa ta fara mishi kuka sosai, baice mata komai ba sai hankie da yasa ya fara share mata hawayen, "nifa ba kuka nace kiyi ba, ki fad'a mun matsalarki simple and fine". Bata ce dashi komai ba sai dai ta saurara da kukan. "Raihana". Ya kira sunanta da tattausan sauti, ta d'ago ta kalle shi, ya sake narke kwayar idon shi a nata, "baki da lafiya ne?". Ta girgiza mishi kai. "Nine nayi miki wani abu da bakya so ko?". Nan ma ta girgiza mishi kai, "toh menene matsalar?". A shagwob'e tace, "ba kune kaida ammie baku fad'a mun tafiya zamuyi ba, kuka sa na shirya na taho ba kayan da zan sauya, ba soson wanka da sabulu, ba brush da.....". Sai tayi shiru lokaci d'aya kuma ta saci kallon shi, karaf suka had'a idanu taga irin shu'umin kallon da yake jifanta dashi. "Dame kuma? Ai baki gama lissafe lissafen ba". Tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta cikin jin nauyin shi, shi kam murmushi yayi kurum ya mik'e zaune yana kallonta ya koma mazaunin shi, "kinsan me? ki rubuta mun duk abinda kike buk'ata tunda dai kunyata kike ji sai naje nazo miki dasu gaba d'aya, amma fa in mun cinye abincin nan don ba zai yiwu kiyi ta zama da yunwa ba". Cikin jin dad'in yadda ya fahimce ta cikin sauk'i ta gyara zamanta sai dai tana shirin d'aukar 🥄 ya riga ta, ya d'ebo abincin ya nufi bakinta dashi, galala ta tsaya tana kallon shi, "oya take mana". Ya fad'a cikin bada umarni, mak'ale mishi kafad'a tayi "uhm uhm ni dai ka bani zanci da kaina". Sai ya ajiye cokalin ya matsar da abincin yace ta taso taci inta rage zaici shi daga baya, arammiya kam sai gata ta mik'e zata huce shi, unexpected ta jita cikin jikin shi tayi zaman dirshan kan cinyar shi. Bai bata damar da zata iya mik'ewa ba kamar yadda taso don ya mata rik'o bana wasa ba, tun tana kiciniyar kwace kanta har dai a k'arshe ta hak'ura, "kin mik'a wuya kenan". Ya fad'i hakan cikin kunnenta da wani irin sauti na daban, ita kuwa cikin sabuwar shagwob'ar dani mariyatu bansan yaushe ta fara taba tace, "Kai ka sani in na staining kayan ka". Juyo da fuskarta yayi dai dai da tashi ya shafo cute lips d'inta da yatsar shi babba yace, "what! Yarinyar nan na fahimci so kike ki raina ni ko?". Fari tayi da idanunta ta murgud'a mishi baki, yayi murmushi yana sake tsurawa fuskarta idanu, itama tsakiyar idanun shi take kallo tana amsar sak'on da yake aika mata ta cikin kwayar idanun ba tare data shirya ba. Sun shagala a kallon juna kafun yunwar cikin su ta dawo dasu hayyacin su, ta juyar da kanta khaleefa kuma ya d'auko plate d'in abincin ya sake nufar bakinta, wannan karon bata musa mishi ba ta fara karb'an abincin tana ci, yana ci yana bata har suka cinye tas. Sam ba susan adadin da suka ciba saida suka ga plate a gaban su suka farga. Raihana ta yink'ura ta tashi idonta akan inda ta zauna, khaleefa duk yana ankare da ita, zuwa yanzun ya gama fahimtar abinda take yiwa, da so yake sai yayi wanka ya futa amma fahimtar damuwarta yasa ya hak'ura. A waya ta rubuta mishi duk wani abu da take buk'ata ya karb'a ya tafi ya kawo mata few minute bayan futar shi, don akwai k'aramin supermarket kusa dasu, taji dad'i sosai aikuwa ta shiga wanka ta gyara jikinta, inda aka samu matsala bata da kayan da zata sauya gashi ta cire kayanta gaba d'aya ta wanke su ta shanya har mayafin don ya b'ace da k'ura, sai wata tantal bateten riga daya had'o mata ita cikin kaya, rigar dukanta iya gwiwar k'afarta ce, gashi ta kama jikinta, gaba d'aya data kalli kanta a mirror sai taji kunyar futowa ya ganta a haka, haka ta yita tsayuwa cikin bathroom har saida ta tabbatar ta daina jin motsin shi gaba d'aya sannan ta futo. Da gudu gudu sauri sauri ta shige cikin bargo ta rufe har kanta ba don akwai sanyi a garin ba, a'a sai don b'oye shigar jikinta gare shi. Ya jima a parlour tare da mahaifin shi suna hira kafun suyi sallama kowa yayi makwancin shi. Bayan ya gudanar da duk abinda yake yi kafun kwanciya bacci, ya tofe duk kusurwowin d'akin da addu'a ya kwanta ya tsurawa bayanta ido saboda ta juya mishi baya, kafun ya matsa ya rungume ta jikin shi tsam tsam yana kallon fuskarta hannun shi saman kanta yana shafa cikakkiyar sumar kanta data rubke a k'eyarta. A haka wani irin bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi. ******* Washe garin ranar tunda wuri raihana da tayi wanka ta maida doguwar rigar data zo da ita gidan jikinta ta nemi kitchen, so tayi ta had'a musu abinda zasu ci sai dai babu komai na amfanin girki cikin gidan. Ta jima tsaye a kitchen d'in kafun ta juya da nufin futa, sai dai taku biyu yayi burki tana kallon shi da mamaki, mutumin data baro yana bacci. Sai tayi saurin ja baya ta russuna tana gaishe shi, ya amsa yana d'orawa da tambayarta me dame ake buk'ata na girki don yana son girkinta a duniya, ta mishi list ya tafi ya kawo ta fara had'a sauk'ak'k'en girki yana zaune yana kallonta, kunnuwan shi rufe da pod yana sauraren karatun al-qurani. A nan cikin kitchen tayi saving d'inshi don taga yunwa yake ji sosai, aikuwa ya fara da aika sandwich cikin bakin shi, ya lumshe ido ya bud'e yana sake gutsiran na biyu ya kai, a wannan karon kasa hak'uri yayi saida ya magantu, "dear abincin nan yayi dad'i sosai". Tayi murmushi kurum tana k'arasa had'awa Abba tray d'inshi. Tana karyawa a kitchen d'in khaleefa ya kaiwa Abba nashi break d'in har d'akin da yake. ***** Su uku na gani tsaye a gaban gidan, duka su ukun kowa addu'ar da tazo bakin shi yake karantawa, cike da tsoro da d'ari d'ari suka tura k'ofar gidan da suka tarar a bud'e suka shiga, khaleefa ya tambayi wani cikin masu aikin ko Auntie tana gida? Yaron ya fad'a mishi ta d'an futa sai dai kamar ba nesa ta tafi ba don tace ba zata huce minti goma ba. Gyad'a kai khaleefa yayi ya musu jagora har cikin parlonta na sama inda suka samu mama haleema tana k'arasa aikinta. Ta tsaya da matuk'ar mamaki tana kallon su, raihana ce ta fara russunawa tana gaishe ta, ta amsa duka hankalinta naga mutumin da khaleefa ya shigo dashi, bayan duk sun zauna suka gaisa ta fara gabatar musu drink's da kayan snacks da basa rabo dasu a gidan, don yanzun haka aikin sukeyi auntien ta futa ta dawo. Khaleefa da kanshi ya zubawa mahaifin shi ruwa ya mik'a mishi, ya karb'a ya ajiye a gefe yana tambayar mama haleeman, "surayyah bata nan ne?". Mama haleema tace, "eh ta tafi kawo ketchup ne yanzun nan zata dawo?". Shiru duk sukayi mama haleema ta futa raihana tabi bayanta da sauri, don yana mata kunya zama gata ga wannan bawan Allah, baya ga haka ma suna buk'atar sirri don batasan ya za'a kwashe da auntie ba in tazo taga mutumin da khaleefa ya kinkimo mata gida. Suna tare da mama haleema a kitchen tana tambayarta ko mukullin part d'inta yana gurinta, mama haleema tace, "yana gurin doctor surayyah sai dai in ta dawo, amma wannan zuwan na bazata..... Ina fatan komai lpy". "Wa nake gani kamar raihana?". Auntie ta fad'a tana kallon su da mamaki bayan ta ajiye ledar hannunta daga bayan su....... _Kuyi hak'uri jiya wayata bata samu chargy ba shiyasa ban bud'e datan ba gaba daya_ _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy six 7️⃣6️⃣ Shiru tayi sai mama haleema ce tayi k'arfin halin cewa, "ba ita kad'ai tazo ba, ragowar suna jiran ki a parlour". Ras! Taji gabanta ya fad'i, tsoronta d'aya kada ya zam khaleefa sakin y'ar mutane yayi, (kunji wani tunani kuma🤔) hankali a tashe ta nufi parlon, tun kafun ta k'arasa ta cire mayafinta ta rik'e shi a hannu don gumi ne yake keto mata tako ina, sai gyararriyar sumar kanta kawai a waje tana d'aukar ido. Cak! Kwakwalwarta ta tsaya da aiki, numfashin ta ya d'auke na hucin gadi, haka duk jikinta babu inda baya rawa a lokacin da tayi 4eyes dashi. "Su...ra...jjjj". Ta kira sunan shi kamar me koyon magana, shima mik'ewa yayi ya fara takowa zuwa gabanta har saida yazo daf suna kallon juna ido cikin ido sannan tayi k'asa da idonta ta juya a sukwane zata fuce, ya rik'e gefen rigarta da sauri, sai ta dawo tana fuskantar shi, ba wasa ko tsoro a fuskarta tace, "malam waye kai? Taya ma zaka shigo mun har k'arshen gida ba tare da neman izinina ba, silently move out tun kafun na kira maka police...". Ta k'are zancen tana nuna mishi k'ofa. Murmushi yayi duk da jikin shi yayi sanyi, bashi da wani kwarin gwiwa daya rage mishi yace, "kiyi hak'uri! Tabbas ni mai laifi ne a gare ki surayyah, nasan na cutar dake na karya miki zuciya bayan tarin k'aunar da kika nuna mun, I'm serious sorry kiyi hak'uri ki gafarta mun". D'ago kanta tayi ta kalle shi cikin son sake kwararawa kanta gwuiwa tace, "sorry for yourself, ka futar mun a gida malam don bansan shirmen da kake magana a kai ba". Kama hannuwanta yayi duka biyu yana kallonta da rauni sosai ya sake cewa, "surayyah ki kalli cikin idona kice baki sanni ba da gaske". Idanun nashi ta kalla, ta bud'e baki da nufin cewa wani abu khaleefa ya rigata ta hanyar mik'ewa tsaye yace, "enough! Ya isa haka Auntie! Ki daina duk wannan pretending d'in, koda kika kasance nesa da Abba! Soyayyar shi tana nan da ita kike rayuwa tsawon shekarun da kika kwashe, auntie don Allah ba tare da dogon jan aji ko yanga ba ki koma ga Abban mu mijin ki, don auren ku bai k'are ba ni naga shaidar hakan.....". Duk kallon shi suke da mugun mamaki. Ganin irin kallon da suke mishi sai ya gyad'a musu kai cikin tabbatarwa, "nasan me nake fad'a don na samu hujjar ne daga gurin ki, kin tab'a fad'a mun Abban mu was a reasonable person, baya komai saida ajiyayyen hujja, shiyasa na duba cikin muhimman abubuwan da yakan ajiye cikin computar shi, a ciki na samo sak'on sakin ki da adadin nadamar da yayi bayan sakin da komai daya biyo baya, a nan naga abun ban mamaki da al'ajabi don ya k'are rayuwarshi yana neman ki da begen ki, Naga ninkin k'auna sau dubu akan wadda kike yi mishi,,,,,, auntie kamar yadda kika rayu babu aure haka Abban muma ya rayu babu mata, watak'ila ubangiji ya hallici ruhin kune don su kasance tare da juna, shiyasa zuciyoyin ku suke azabtuwa da rashin juna akan wani k'atoton abu daya gifta muke kiran shi k'addara..... Auntie ki duba da kyau ki auna shin a duniya zaki samu masoyi na gaskiya kamar Abban mu?, he's one in earth ba don ya kasance shi ya haife muba sai don babu kwatankwacin shi a halacci da soyayyah, shin kina tunanin kowane zai zauna cikin tsammanin warabbuka akan mutumin da bakasan bama koya mutu, ko yabar nahiyar da kake gaba d'aya....". Sai ya sake matsowa gaban su, "kiyi k'ok'ari ki fahimci waye shi Auntie, zan baku lokaci ku k'arasa warwarewa juna komai, ina zan samu mukullin b'angaren mu?". Jikinta a sanyaye ta sake jan jikinta baya ta jingina da bango tace, "bedside drower ta bedroom d'ina". Sai ya juya a nutse ya d'auko mukullin, ya sake dawowa ya kewaye su ya huce ya futa yabar su a tsaye kamar bak'in juna. Bai nemi raihana ba ya bud'e part d'in ya shiga ya zauna ba tare daya damu da k'urar data cika ko'ina bare tunanin zai b'ata mishi kaya ba, kwantar da kanshi yayi ya lula duniyar tunani.... Ta b'angaren doctor surayyah khaleefa ne ya sanyayar mata jiki kwarai har ta rasa d'an kwarin gwiwar data fara tattarowa zatayi yak'i da suraj, maganganun shi sunyi tasiri a ranta da zuciyarta gaba d'aya sun k'arasa narke ta, musamman da yace akwai ragowar igiyar auren su bai k'are ba? Shin da gaskiya ya fad'a ko kuma yayi haka don kawai ya lausasar da ita? Taya ma hakan zata kasance bayan a gaban idonta momy ta umarce shi da yayi mata saki ukun? Duk da ita a lokacin bata yiwa takardar cikakken karatu ba ta sawa zuciyarta saki uku yayi mata ne a lokacin kawai shiyasa. "Tunda khaleefa ya shammace ni ya binciko abinda nake son bawa mutane mamaki dashi sai ki zauna muyi magana ko?". Suraj ya fad'a a tausashe. A sanyaye ta k'arasa cikin parlon ta zauna a k'asa, shima gefenta ya zauna, bayan d'aukar wani lokaci shiru ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana cikin nutsuwa, "tabbas nayi kuskure, kuskure mai girman da bazan tab'a iya yafewa kaina inba ke kika yafe mun ba, a waccen ranar kina tafiya gaskiya tayi halinta, na duba duk Inda nasan zan same ki amma ban same kiba, nayi jinya mai tsayi har na fudda rai da rayuwa, surayyah komai ya faru cikin rashin sani da yanke hukunci cikin fushi...... Surayyah yaran mu sun bani labarin irin rayuwar da kukayi dasu da sadaukarwa da kikayi a kansu, babu abinda zance sai Allah ya saka miki da jannatul firdaus, yaci gaba da haskaka rayuwarki.....". Shiru tayi kafun can ta motsa bakinta kamar zatayi magana saita kasa. "Surayyah sai dai Ina neman wata alfarma a gare ki, ki taimaka ba don niba, ba don halina ba ki amince a maida auren mu a karo na biyu..... Nayi miki alk'awarin ko zaki kashe ni bazan tab'a sakin kiba....". Ya k'are da kifa kanshi jikin gwiwar k'afar shi. Ita kuwa takardar hannunta take ta dubawa kafun tsam ta mik'e ta futa daga d'akin, a kitchen ta tarar da mama haleema da raihana, duk suka yi shiru musamman raihana da take zaton ganin fushi ko b'acin ranta bisa ga k'aton kuskuren da sukayi mata, sab'anin tunanin ta sai ji tayi ta kalleta da cewa, "Raihana kina nufin har yanzu kina nan a zaune? Ya kamata ki nemi yaran nan masu share share kuje dasu side d'inku su gyara miki abinda ya kamata". Kanta a k'asa tace, "toh auntie". Saita mik'e ta d'auki jakarta kawai ta fuce. Ita kuwa mama haleema ta maidawa hankalinta, "kin gama had'a komai ne?". Mama haleema tace, "a'a saura kad'an dai". "Ina so ki zuba abinda ya sauwak'a ki kaiwa bak'o a parloun k'asa". Mama haleema tace, "toh ba damuwa". Daga haka itama futa tayi har lokacin jikinta a sanyaye, mama haleema kuma ta fara k'ok'arin cika umarninta. Lokacin da raihana ta shiga b'angaren su bata samu kowa a ciki ba, ita ta zage tare da yaran suka gyare sashen gaba d'aya, tayi wanka ta sauya kayan jikinta cikin wanda ta bari a gidan. Sai a lokacin ta nutsu ta fara cin abincin da mama haleema ta kawo musu. Khaleefa kuwa bayan ya futo a gidan kai tsaye anguwar su iya ya nufa, yaci sa'a ya samu malam a k'ofar gida yana karatu da wasu magidanta da sukan zo gurin shi d'aukar darasi duk yammaci, tunda ya futo daga mota yake kallon shi cikin son tantance wanda idanun shi suke gani har yazo gaban shi ya durk'usa yana gaisawa da mutanen gurin. "Ba don kar ace idanun tsufa ba da nace wannan Abdallah ne ba Adam ba.....". Murmushi khaleefa yayi yace, "ka fad'a kanka tsaye malam". Malam da k'arin mamaki yace, "toh Ina fatan dai lafiya? Ko kuma ka biyo jirgi ne kawai don ka gan mu ka koma?". Murmushi ya sake yi yace, "ehh to kusan haka dai, zan shiga gurin iya idan kun gama sai muyi magana". Malam yace, "toh madallah! Masha Allah ba matsala". Iya tana zaune kan tabarma tare da wata y'ar dattijuwar mak'ociyar ta data shigo mata suna ta tattauna hirarrakin su irin nada, rik'e da hab'a iya ta tsaya tana kallon shi har ya k'arasa shigowa, "Kai kuma da baki kamar gonar auduga, da zuwa ba sanarwa ai saika fad'a mun abinda ta haifa tun kafun ka zauna ko?". Dariya yayi ba tare daya shirya ba, ya k'arasa kan tabarmar ya zauna ya fara gaishe da bak'uwar ta. "yau naga shegantaka irinta yaran zamani, yanzu kai ko y'ar kunyar nan da karar yaran fari baka iya ba? Dubi fa yadda yake dariya hajiya rabi matar sa tayi haihuwar fari". Matar data kira da hajiya rabi tace, "to ai shi mai kunya nema cikin yaran zamanin nan tunda dai har a iya fuskarshi ake ganin farin cikin nashi". "Allah ko hajiya?". Iya ta tambaya. "Kwarai kuwa" ta bata amsa da tabbaci. Shi dai khaleefa yana gefe yana ta kallon rikici iyakar shi. "malam baka fad'a mun abinda aka samu ba?". Iya ta fad'a tana kallon shi. "Wai waye yace miki raihana ciki.... Cikine da ita, daga zuwan mutum ko jira ya zauna a gaisa ma baki yiba kin tsare shi da wasu zantuttuka da bansan inda kika samo suba". "Kaci gidan ku! Ai tunda naga hak'orin ka a waje nasan zancen gizo ba zai huce na k'ok'i ba". "Toh ni ba abinda ya kawo niba kenan". Ya fad'a yana mik'ewa zai shige d'akinta. "Kar ka shigar mun d'aki kana bincike mun madafi". Bai kula taba yayi shigewar shi ya kwanta saman doguwar kujerar ta. _Bayan wasu awowi_ **** Malam da iya da suke gaban shi shiru duk sukayi suna sauraron shi har ya dire.... "Masha Allah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Hak'ik'a wannan abu yayi kyau yazo yadda ake saka ranshi, tabbas magaji kayi babban aiki ba abinda zamu ce sai Allah yayi maka albarka, yasa ka gama da duniya lafiya, kayi abinda ya kamata a gab'ar daya dace kam sosai.....". Malam ne mai yin wannan dogon bayani. "Yanzu shi Abban naku yana can gidan ku?". Iya ta tambaya. "Eh! So nake da malam ya gama cin abincin nan ma muje ku ganshi, duk da nasan auntie baza tak'i gabatar dashi a gurin kuba". "Ai abinci bazai k'arasa shiga ba, Ina ganin abinda za'ayi zamu je mu ganshi don kamar yadda ka fad'a da gaske auren su bai k'are ba nima na gani a jikin takardar sakin farkon zuwanta gidan nan". Kusan a tare motoci biyu suka Parker a k'ofar gidan, d'aya su khaleefa ne, d'aya kuma likita andal ce, momma da babban yayan su Suraj, sai suhaana da Ayman. Khaleefa ne ya musu jagora har cikin parlon k'asa inda aka gyara ma Abban su. Duk suka zauna a ciki har su malam da iya da suka zo tare dashi. Sun gaisa kafun Ayman yabi bayan shi su huce sama gurin Auntien, sun sameta tare da mama haleema, ba hira suke ba amma sun zauna ne jigum kowa da tunanin da yake tsakanin su. Shigowar su a tare yasa duk suka d'aga ido suna kallon su, "a'a saukar yaushe kuma Ayman?". Mama haleema ta tambaye shi, Ayman yace, "Eh wallahi yanzun nan na shigo tare da bak'i". Auntie ce ta mishi wani irin kallo tace, "Kai kuma suwa ka d'ebo ka kawo mun gida". Da sauri mama haleema ta katse ta, "duk wannan maganar fa ba taki bace uwar d'akina, tunda an gama magana meye kuma na dawo da hannun agogo baya". Sai tayi k'asa da kanta ta dafe da hannunta d'aya, Ayman dai k'arasawa yayi gabanta ya durk'usa ya d'ora hannun shi kan k'afarta yace, "ki yafe mana Auntie in mun bak'anta miki rai cikin abinda mukayi da sunan gyara, amma bak'in da suka zo yanzun ba irin mahaifin mu suke a gurin kiba, bak'i ne da kuka rabu ba don kunso ba, bak'i ne da kika dinga rayuwa da tunanin su da musu fatan alkhairy tsawon lokaci a duk Inda suke sab'anin Abban mu.....". Da sauri ta d'ago tana kallon shi kwakwalwarta na tuna mata wasu abubuwa da hankalinta ya fara zuwa kai tsakanin d'azu da yamma zuwa yanzun..... Saita mik'e tsaye kamar wadda aka zabura tana rarraba ido tsakanin shi da khaleefa tace, "yayana Sauban....". Khaleefa da yake tsaye daga gefe har lokacin yace, "ba namiji bane macece wannan". Saita kalle shi tsawon wasu mintuna kafun ta sauke ajiyar zuciya ta nufi hanyar futa a parlon sauri don tabbatar da zarginta. Duk suka bita da kallo cike da tausayinta..... Mama haleema ce data tashi zata futa tace, "kunyi abu mai kyau y'an biyu....". Ayman yana murmushi yace, "fiye da kaso 90 cikin d'ari na k'ok'arin khaleefa ne, don shi ya binciko komai nima bai fad'a mun ba sai kaini yayi kawai naga ni da idona". Cikin jinjinawa mama haleema ta kalle shi, shima murmushin yayi yace, "nima bani nayi komai ba, raihana ce ta had'a komai da taimakon wata k'awar auntien y'ar k'asar su". Mama haleema tace, "Allah sarki Allah yayi mata albarka, ai yarinyar nan macen arzik'in kace khaleefa, don Allah kada wani abu na zamani ya rud'e ka watarana kace zaka rabu da ita, don zakayi asara irin wadda ba zaka tab'a maye gurbinta ba, a k'arshe ka k'are da cizon yatsa.....". Kanshi a k'asa yace, "insha Allahu mama haleema zan ci gaba da rik'e ta bisa gaskiya da Amana". Tace, "Toh alhamdulillah Allah yayi muku albarka gaba d'aya kaida d'an uwan ka yaci gaba da haskaka rayuwarku". Suka amsa da ameen ta futa su kuma suka zauna cikin parlon. *****Kamar a mafarki haka doctor surayyah taja tunga ta tsaya tana kallon mutanen da aka kira da suna bak'inta. Ita kanta k'awartata kallon ta take kafun ta tafi da hanzari su rungume juna suka fashe da kuka kusan a tare. Tsit parlon ya sake dawowa baka jin motsin komai saina sautin kukan su, zuciyoyi kuwa sun cika fal da tausayin su musamman ga wad'an da sukasan tarihin k'awancen su da shak'uwar da take tsakanin su. Sai bayan sun gama koke koken surayyah ta durk'usa kanta a k'asa suka fara gaisawa da momma, itama kuka ta b'arke dashi ta durk'usa gabanta tana neman yafiyarta. Surayyah cikin jin nauyin matar tace komai ya huce a gurinta tuntuni ma. Abubuwan da suka biyo bayan wannan had'uwa masu girma ne da ban al'ajabi, don surayyah taga k'auna a gurin mahaifiyar Suraj wadda bata tab'a zaton gani ba ko a mafarkinta. Suhaana dai sai raba ido take tsakanin k'ofofin parlon tana neman inda zata ga raihana tabar cikin wad'annan masu kukan. Surayyah ta gabatarwa malam da iya kowa cikin Suraj da dangin shi harma da k'awarta da y'arta, suma ta gabatar da malam a gurinta, ta k'ara da basu labarin halaccin daya musu a rayuwa ita da yaranta. Duka suka yabawa dattijon taka irin ta mutanen, Suraj kam marking sunan malam yayi a zuciyarshi ya fara laluben tafkeken alkhairin da zaiyi mishi. Bayan an nutsu malam ya kawo shawarar data kawo shi, duk shiru sukayi musamman Auntie dashi kanshi uban gayyar. "Kuma fa abinda ka fad'a haka yake malam yusha'u, ina ganin tunda ga.... Nan sai ya zama wakilin shi Suraj, kai kuma ka zama na surayyah, don yanzu surayyah d'iya take a gurin ka". Fuska ba annuri sam ta mik'e ta d'auki jakar kayan su andal tasa su biyo ta su tafi. Bayan sun futa akaci gaba da tattaunawa tsakanin su malam har daga k'arshe akaci nasarar gyara wannan bantararren aure. *Alhamdulillah! Burin mu ya cika an maida auren surayyah da Suraj*. Khaleefa kuwa bayan futar mama haleema sun d'auki lokaci shiru kafun Ayman yace, "bansan me yasa mutane suke son ganin ka da raihana ba, bansan kuma me suke gani a kanku ba har suke yawan muku addu'ar kasancewa tare har abada bayan munfi dacewa ni da ita.....". Wani mugun kallo khaleefa ya dinga wurga mishi ba tare da yasan ma yana yiba. Cikin basarwa Ayman yace, "meye kake kallona haka don na fad'i gaskiya". Mik'ewa yayi ba tare da yace mishi komai ba zai futa a d'akin don maganar bakin shi ba zatayi dad'in ji ga Ayman ba. Da sauri Ayman ya mik'e shima yasha gaban shi yana dariya k'asa k'asa yace, "Wai meye duk hakane? Bayan munyi magana da kai ita matar ma dukanta tawa ce? Takardar sakinta kawai nake jira ka bani, tayi idda in aureta". Komawa yayi kurum ya zauna ya dafe kanshi da hannun shi ba tare da yace komai ba. Kusa dashi ya zauna yana fuskantarshi da kyau kafun ya fara da cewa, "Khaleefa kana son wahalar da kanka a rayuwa. Da farko waccen yarinyar Saleema, yanzu kuma Raihana, duk da soyayyarta tayi maka kamun kazar kuku amma har yanzu ka kasa amincewa da hakan, kana ta yaudarar kanka wai zaka iya sakinta ni na aureta, ya kamata zuwa yanzun ace ka manta da waccen tatsuniyar ka shiga cikin tunani na zahiri, da farkon farawa kayi duba na tsanaki kan irin al'ummar da muke rayuwa tare dasu, koda ace wani abu bai tab'a shiga tsakanin ka da raihana ba, babu ta yadda za'ayi ma ka saketa na aureta mutane suja bakin su suyi gum suna kallon mu basu tanka ba, sannan ni a karan kaina da nake d'an Adam ba dutse mara zuciya a jiki ba ina jin kishin yadda wani zai rayu da mace koda bai tab'a mu'amulantar taba ni in aureta.... Duk sonda nake wa mace zan iya hak'ura da ita muddin ya zamana ta auri wani na, sannan ni ko lokacin dana furtawa raihana kalmar so bisa shawara ta wani abokin aikina ne, ba kuma nayi donta barka ta dawo gare nine watarana ba, a'a sai don na sauke nauyin soyayyarta a kaina, kuma alhamdulillah a lokacin na samu salama da nutsuwar ruhi, sannan a lokacin na fahimci auren ku gaba d'aya set-up ne duk da bata fad'a mun kai tsaye ba, shiyasa har na amince da abinda raihana ta fad'a mun....". Sai yaja gwauron numfashi kafun yaci gaba da cewa, "khaleefa soyayyar raihana ta shiga zuciyarka ko kak'i ko kaso, saboda raihana mutum ce da muddin ka zauna da ita zaiyi wahala ka yarda ka rabu da ita, bare kuma ace zama ya had'a ku k'ark'ashin igiyar aure, nasan ka fini sanin komai dazan fad'a a kanta yanzun.... Khaleefa tunda naji labarin zaku tafi wata uwa duniya daga kai sai ita ku kwana muhalli d'aya na fudda rai da ita gaba d'aya kaima kuma shirin ka ya rushe, shiyasa na turo mata sak'o mai nuni da hukuncin dana yanke na k'arshe a kanta ranar da zaku tafi,,,,,,,". Sai yaja ajiyar zuciya, "komai na rayuwa yana da iyakarshi, Allah bai tsara zan auri raihana ba tun farko shiyasa duk sonda nake mata ban tab'a bud'e baki na furta mata ba, alhamdulillah finally Allah zai maye mun gurbin ta da wadda zata fi zama alkhairy a rayuwata, bada jimawa ba zanyi yak'i in nemo soyayya kamar kowanne saurayi mai irin shekaruna, sannan a shawarce kaima ka ajiye komai ka nemi soyayyar matarka, don mun fara gajiya da ganin ka tuzuru, nasan auntie zasu so ganin jinin ka zuwa yanzu.....". Dariya khaleefa da yake kallon shi yayi ya mik'a mishi hannu suka dunk'ule hannuwan guri d'aya a tare da d'aya hannun kuma suka sauke ma juna naushi a gefen kafad'a suna dariya. "No one like you". Khaleefa ya fad'a cikin jinjinawa ga Ayman. "Ka fad'i gaskiya kam, auren mu tun farko shiri ne, sai dai tun kafun mubar k'asar nan jikina ya fara sanyi, na fara jin shakkun sakinta don nasan mugun abun fad'a zan bar mata, sai dai dana ji dangantakarku sai naji sanyi a zuciyata, har na fara maka tanadinta don a ganina ka fini cancantarta........". Nan ya k'arasa bashi labarin zaman su in briefly tare da sake jinjinawa Ayman bisa ga kyakkyawar fahimta da sadaukarwa daya mishi. Sunci gaba da hirar su duka Ayman zolayarshi yake, da yaga dai da gaske ba zai kyale shiba ya huta sai ya mik'e yana mishi sallama. "a'ah ya zaka gudu kuma muna hirar mu?". "Na gaji da hira da k'aton tuzuru tunda muka zo gidan nan ban zauna da matata ba". Khaleefa ya fad'a yana kallon shi. Dariya Ayman yayi sosai yace, "har ka samu bakin gori kaida matar ma suna ta tara a gurin ka". "Humm! Haka ma zaka ce bayan saboda kai na takure kaina nayi komai ko". "Toh ni saka nayi malam! A hakan ma kuma dai nasan duk an rage hanya shine za'a lallab'a ace an barmun, wato ruwa tasha ana so ana kaiwa kasuwa". Harararshi kawai khaleefa yayi ya fuce don in ya biye mishi ba zai tafi ba. Yaso shiga parlon k'asa sai dai bazai so ganin fad'uwa ba, yana tsoron yadda auntie take kallon komai har yanzun ta fuskarta. Lokacin daya shiga side d'in raihana ta kauce a parlon tuni don ta gama abinda take yi har abincin shi da mama haleema ta kawo ta adana mishi inda ya kamata. Bai taba komai ciki ba don yaci abinci gidan iya, yadda yake a gajiyen nan kwanciya kawai yake son yi ya huta. Koda ya shiga d'akin shi raihana ta tsabtace shi tas kamar ba d'akin daya futa ya bari da uwar k'ura ba. Yayi shirin shi na kwanciya bacci tsab cikin fararen kayan bacci sol da suka futo da annurin shi, littafin addu'o'in shi da yake bedside ya fara dubawa kafun wani lokaci bacci ya silalo ya kwashe shi. ****Washe garin ranar tunda sassafe ya samu kira daga Abban su, sai ya zura jallabiyyah kurum ya futa don amsa kiran shi, ya same su tare da uncle d'inshi, ya durk'usa a gaban su yana gaishe su duka, suka amsa mishi kusan a tare. Mukullin guest house d'inshi da suka baro jiya ya bashi yace ya d'auko musu kayan su idan ba damuwa, cikin sauri ya karb'i mukullin ya futa daga parlon. Yana futowa kuma ya had'u da Ayman zaije gurin su su gaisa, mik'a mishi hannu khaleefa yayi suka gaisa ya mishi side hug yana tambayarshi gajiyar tafiya, yana y'ar dariya yace, "ai tabi makwanci, ina zuwa kuma da farar safiyar nan na ganka da key". "Abbane ya aike ni d'auko mishi kayan shi a guest house d'inshi da muka sauka jiya". "Bari na shiga mu gaisa dasu saina raka ka muje". Khaleefa yace, "tom zanfi jin dad'i ma kuwa, amma kada ka zauna dogon zance". Ayman yayi gaba yana fad'in, "yadda kake so". Yayi murmushi yana nufar parking lot na gidan. Bai jima ba kuwa ya futo ya same shi, Da motarshi yayi amfani suka je ya d'auko musu kayan su gaba d'aya suka futo Ayman yana yaba kyan tsarin gidan. Suna tafe suna hirar su har suka k'arasa gidan, bayan sun kai mishi kayan ma basu rabu ba don khaleefa jawo shi yayi b'angaren su. Suka zauna a parlour zuciyar khaleefa da tunanin raihana ko bacci take shiyasa ba motsinta kwata kwata. ~~~ ita kuwa bayan futar khaleefa ba jimawa ta futo ta nufi b'angaren auntien don su gaisa, ta shiga bakinta d'auke da sallama, sai tayi turus tana kallon suhaana data ke zaune kusa da momma da wata k'atuwar rigar bacci tayi rolling saman kanta da gyale hannunta rik'e da mug tana shan tea mai zafi. Ajiye mug d'in tayi ta nufe ta da gudu suka rungume juna tana fad'in, "tun jiya nake tambayar auntie ke...". Raihana tace, "ayyah ai bansan kun iso ba....". Saita zame jikinta ta durk'usa cikin parlon ta fara gaishe dasu momma da ammie, suka amsa suna tambayar ina ta shige suke ta nemanta tun jiya, Auntie data futo daga d'akin baccinta tace, "ai raihana ganinta yayi wahala". Momma tace, "ai na fahimci kamar bata son hayaniyar mutane tun a can". Auntie ta k'arasa futowa tana fad'in, "Ina ruwan Raihanatu bata son kwarabniya dama sam". Ita dai da take jinsu murmushi tayi kanta a k'asa tana gaishe da auntien, bayan sun gama gaisawa take tambayar Ina mama haleema, auntie tace, "tana kitchen". Saita mik'e tama suhaana alamun ta biyo ta, aikuwa ba musu tabi bayanta suka futa zuwa kitchen d'in. Stool taja mata ta zauna, ita kuma ta k'arasa kusa da inda mama haleeman take had'a abincin tana fad'in, "Ina kwana mama haleema". "Lafiya lou fatan kin tashi lafiya me b'oye kanta daga cikin mutane". Y'ar dariya tayi tace, "kema haka zaki ce mamaa". Tana dariya itama tace, "eh mana ai gaskiya ne". Sai sukayi dariya, raihana ta tambayi dame zasu iya taimaka mata, mama haleema tasan kota hana su ba zasu bari ba, saita basu ayyukan da zasu rage mata. Raihana ta yarawa suhaana da yaren da take fahimta, ta matso kusa cikin jin dad'i tana taya su aikin. In zata yiwa mama haleema magana saita fad'awa raihana, ita kuma ta juyawa mama haleema hausa, in mama haleema ta bata amsa da hausa kuma sai raihana ta juya mata harshe ta fad'a mata. Haka dai sukayi tayi har suka gama aikin. Mama haleema ta zuzzubawa kowa ta basu suka kai musu. Raihana ce ta kaiwa su Abba nasu abincin daga nan suka gaisa, ita kuma suhaana ta kaiwa matan tunda bata shirya ba. Bayan duk sun kai musu abincin karin kumallon k'arshe ta ba raihana nasu khaleefa tunda ance mata suna tare shida Ayman, ta tambayeta kota had'a musu ita da suhaana. Tace, "eh ba damuwa tare zamu tafi da ita idan ta dawo daga sauyo kayan da taje". Lokacin da suka shiga khaleefa ne kad'ai tare da Ayman, suhaana ta tsaya daga baya raihana kuma ta k'arasa ciki tana sake wata sallamar. Khaleefa ya amsa k'asa k'asa yana binta da kallo, Ayman kuma ya amsa yana d'orawa da fad'in, "Masha Allah sannu da k'ok'ari matar big Yaya". Tayi murmushi bayan ta ajiye trayn tana gaishe da Ayman d'in, ya amsa cikin faram faram. Taso gaishe da khaleefa don basu had'u ba tun jiya ma ita rabon data ganshi, sai dai taji kunyar aikata hakan gaban Ayman. Saita mik'e kawai ta karb'i trayn hannun suhaana data cake a bakin k'ofa sukayi ciki. Khaleefa har ya mik'e da nufin bin bayanta ya fasa don yaga ba ita kad'ai bace, shi kuwa Ayman suhaana yabi da kallo yana murmushi, yaso ace ta shigo ko gaisawa sunyi kamar yadda suka saba a duk sanda suka had'u, sai dai ba damuwa tunda tana tare da matar twin d'inshi komai zai zo mishi da sauk'i. Khaleefa ne yayi saving d'insu suka ci abincin tare suna hirar da tun lokacin da suke rayuwa tare gidan iya. Suna hirar amma rabin hankalin su ya kasu kashi kashi, shi khaleefa kacokan tunanin shi yana kan raihana, yayinda Ayman yake son ganin suhaana, yana ta tsarawa da kwance yadda zai tunkareta da zancen soyayyah don bazai yadda yayi wasa da damar shiba. Su kuwa bayan sun gama karyawa wanka raihana ta shiga, ta futo suhaanan ma ta shiga, lokacin da zata futo tuni raihana ta shirya cikin riga da skirt na atamfarta mai kyau, ta futowa suhaana wata doguwar rigarta da take zaton zatayi mata tunda kusan size d'insu zai zo d'aya. Rigar kuwa ta mata cif cif kamar dama tun asali tata ce bata raihana ba. Suna ta hirar su tana taya raihana k'arasa gyara inda bata gama gyarawa ba jiya, da yawa in tayi abu sai taga kamar yasmine, ohh ita tunda tazo ma ba suyi waya da yasmine d'in ba ko sau d'aya. Sai ta tsaya da aikin da takeyi ta lalubi wayarta tayi dialling no yasmine d'in, sai dai layin yak'i tafiya, hakan yasa ta ajiye wayar gefe suka k'arasa zura ragowar kayan a wardrobe suka rufe, hanyar futa suhaana tayi, raihana ta dakatar da ita ta hanyar tambayarta, "tafiya zakiyi kuma muna hirar mu?". Sai ta juyo tana kallonta, "akwai abinda zanyi yanzun nan zan dawo". Raihana tana kallonta tace, "nasan ba dawowa ma zakiyi ba". Tace, "insha Allah zan dawo". Ta fad'a tana fucewa ita kuma ta zauna gefen gado. Futowarta yayi dai dai da futowar khaleefa zai futa, ganinta yasa shi dakatawa har ta k'araso suka gaisa ta fuce shi kuma ya juya akalar shi zuwa d'akin da raihanan take......... ****Doctor surayyah ce durk'ushe gaban momma tana jujjuya kud'in data bata a hannunta, ta d'ago da niyyar tambayar na meye momman ta riga ta da cewa, "kiyi hak'uri mun sake aikata wani laifin gare ki surayyah, wannan kud'in sadakin kine na auren ki da muka mayar da mijin ki uban yaran ki Suraj..... Ina fatan bamu kasance ma'abota son kan mu da yawa ba?". Shiru surayyah da take durk'ushe tayi ta d'auke wuta.......... *Barka da babbar ranar juma'ah ga d'aukacin y'an uwa musulmi na duniya*. _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy seven7️⃣7️⃣ Kwakkwaran numfashi ma ta kasa yi bare ta iya amsawa momma, ba zata ce taji farin ciki ba haka ba zata ce bata yi farin ciki ba, tana ganin duk abinda malam zaiyi a duniya ba zai tab'a cutar da ita ba, haka itama wannan baiwar Allah data nuna nadamarta gareta a fili. "Kiyi hak'uri surayyah". Momma ta sake bata hak'uri. Tana girgiza kai tace, "ba kuyi kuskure ba, haka duk hukuncin da kuka yanke dai dai ne". "A'a surayyah bafa za'a ce babu kuskure cikin abinda muka aikata ba, sai dai kiyi hak'uri kawai, zaki fi fahimtar komai idan kika samu zama da Suraj ko wani cikin iyalan gidan late Abdallah ya warware miki komai game da auren sa da kuma yadda muka fahimci gaskiyar sharrin dasu haleema da Aysha suka had'a don haleeman ta aure shi". "Insha Allah momma". Ta fad'a jikinta a sanyaye. "Allah yashi miki albarka". Momma ta fad'a ita dai ko amsawa bata iya yiba ta huce abinta. Tana shiga d'akinta ta watsa kud'in saman bed ta kwanta tare da dafe kanta da hannunta, andal da take zaune gefen gadon ta juyo tana kallonta sai dai bata ce da ita komai ba a wannan gab'ar tana buk'atar a barta taji da kanta kafun k'ara mata haske ko bata shawara. Ita kuwa kasa nutsuwa tayi, tunda taji ance auren Suraj taji tana son jin labarin abinda ya faru bayan tafiyarta. Sake futowa tayi ta zauna kusa da k'afar momma tace, "mommy ki bani labarin abinda ya faru bayan tafiyata don Allah". Gyara zama momma tayi dama saboda kada ta hau bata labari bata nemi ji bane. "Wato surayyah bayan tafiyar ki abubuwa da yawa sun faru, Suraj ya shiga matsananciyar damuwa har da kwanciya doguwar jinya, daga nan bai sake samun nutsuwa ba, yayi neman ki duk Inda yasan zai same ki amma bai same kiba, har k'ara yayanki ya shigar dashi court yana tuhumar shi da laifin b'atan ki, anyi shari'a babu wanda yayi winning akan wani saboda rashin kwakkwarar hujja, bayan lokaci mai tsayi saina fara mishi maganar futo da mata yayi aure tunda naga abun nashi bana k'are bane, amma fafur yak'i, kullum akayi magana sai yace kin tafi da soyayyar shi da tarihin auren shi a rayuwa, tun muna ganin abun wasa har ya fara bamu tsoro, a nan muka fahimci lallai abun nashi ba mai k'arewa bane, ta gefe d'aya ga haleema data mato a sonshi da k'aunar shi sai bin kanshi take yana Shashshare ta. Bisa shawara da shige da fucen Aysha muka lik'a mishi haleema aka d'aura musu aure, a wannan lokacin saida yayi zama na musamman dani game da auren, ya sake tabbatar mana bashi da gurbin da wata mace zata samu matsuguni a gidan shi da zuciyarshi, haka dai muka yo mishi rubdugu da fad'a sai bai sake ce damu komai ba, ya koma gurin yarinyar itama ya zaunar da ita ya mata bayanin irin abinda ya mana bayani, amma soyayyah ta rufe idonta har tasa take d'aukan abun kamar mai sauk'i ta furjanye idanuwanta ta shigo gidan suraj. An d'aura aure haleema ta tare a part na kusa da naki tana zaune, tunda taje bata ga k'eyar suraj ba hasalima an kawo ta da kwana uku tafiya ta kama shi wata k'asa cikin k'asashen African nan, haka ya tsallake ta yayi tafiyarshi ya shafe kusan wata hud'u sannan ya dawo bisa tursasawar su mukhtar, sai dai koda ya dawo suna muhalli d'aya bata sauya zani ba, haleema tayi duk kissa da kisisinar da tasan zata iya abun baiyi aiki ba, inta takura ma ranta ne yake b'aci a banza. Duk da haka ba tayi zuciya ba don a gidan Suraj bata rasa ci sha ko suttura mai kyau ba, abu d'aya ta rasa miji da kulawar shi da soyayyarshi. Toh haleema ta jure zaman shekara biyu da rabi a gidan suraj kafun ta gaji ta nemi saki da kanta ba tare da neman shawarar kowa ba, ya d'anka mata takardar sakinta uku bayan ya titsiyeta da tuhumar gaskiyar abinda ya faru game da matarshi, don ya kama su kwana ki suna hirar ita da matar wanshi Aysha, a lokacin ya nuna kamar bai ji suba ashe abun yana ranshi sai da akazo wannan gab'ar, da farko k'in amsa laifinta tayi, har saida ya had'a abun da hukuma, a can ta warware yadda komai ya faru, daga ita har Aysha bai saurara musu ba saida ya hukunta su da hukunci mafi tsanani, sannan mijinta ya k'ara da turo mata sak'on sakinta har gidan iyayenta. Rayuwa fa tayi tsanani wa wad'annan mutane biyu da Suraj don tuni ya sallama komai sai harkakokin kasuwancin shi yasa gaba, yayinda a kullum dare yake mana kukan yana da y'ay'an shi a wata duniya yaji a jikin shi jinin shi suna yawo a doron k'asa inda suke ne bai sani ba. Bamu yarda ba har Allah ya kawo lokacin da yaran suka zo neman shi da kansu. Hak'ik'a surayyah munyi nadama munyi Allah wadai da abinda muka aikata miki na rashin fahimta da makircin shaid'aniya Aysha da suka shirya komai don kawai k'anwarta ta auri Suraj, lallai duk Inda gaskiya take bada jimawa ba take fallasa kanta, wannan shine dalilin da yasa mukayi hanzarin mayar da auren ku, kamar yadda yake fad'a ya tabbata ke kad'ai ce matarshi a duniya tunda bai tab'a karb'ar wata mace bayan ke ba. Surayyah da tayi shiru mik'ewa tayi tsam bayan gama sauraron momma ta shige d'akinta da ba kowa ra rufe kanta..... **** Raihana ta d'ago tana amsa sallamar khaleefa dake tsaye daga k'ofa, shikam k'arasa shiga yayi yaja stool na gaban mirrow ya zauna idon shi akanta. Tunda yake bai tab'a shigowa d'akinta ba sai yau, abinda su duka biyun suke ayyanawa cikin ransu. Nauyin shine ya cikata ta fara gaishe sa daga inda take kishingid'e. "Matar da take mantawa da mijinta inta samu mutane shine take gaishe sa kuma a bayan idon su?". Kamar ta kyalesa sai kuma tace, "waye mijin?". "Okay tambaya na kike ma?". Bata kula saba duk da Yana da kyau ta dinga tuna mishi abinda yake mantawa dashi, "kinyi shiru kina jina kuma?". "Bansan abinda kake son ji daga gare ni game da tambayar da kasan amsarta ba". "Kamar ya kenan?". Ya sake tambaya. Ganin abun nashi nayi ne saita dire k'afafun ta k'asa tace, "wasu lokutan sai ka bani mamaki kamar kana manta matsayin auren mu....". Murmushi ne ya sub'uce saman fuskarshi har fararen hak'oran shi na bayyana, ya d'auki adadin wasu mintuna shiru kafun yace, "yanzu idan nace matar boge ta zama ta gaske nayi laifi?". "Babba ma kuwa?". Ta fad'a kamar ba ita tayi maganar ba. "Hakane?". "Eh saboda zaka ruguza mata plan d'inta, burikanta....muradanta.... A k'arshe ka sata rusa alk'awarin data d'aukar ma wani mutum mai muhimmanci a gurinta, abun da bata tab'a yiba sab'a alk'awari". Ya gano inda zancenta ya tafi kaf don haka saiya mik'e ya nufi hanyar futa daga d'akin, saida ya kai k'ofa sannan ya juyo ya kalleta, "zan shiga gurin su ummie mu gaisa anjima da yamma, idan zaki iya jerawa da mijin boge saina jira ki muje tare". Bata kula shiba har ya k'arasa futa don batasan abinda zata ce dashi ba a wannan gab'ar. Ba don ta zurfafa tunani ba, ba zata d'auka ummie tata mahaifiyarta yake magana ba. Suhaana kuwa saida ta tabbatar khaleefa ya futa sannan ta dawo gurin raihana suka d'an tab'a hira kafun su huce gurin mama haleema su kama mata aikin abincin dare. Da yamma tasa suhaana tayi sabon shiri, itama ta shirya suka zauna jiran khaleefa don tasan halinsa yana ganin basu shirya ba zaiyi gaba abunsa. Cike da d'oki take zaman jiran shi zata ga ummienta. Suna zaune a parlour suka shigo tare da Ayman da shigar manyan kaya iri d'aya. Raihana ta sake jan gyalen kayanta ganin irin kallon gargad'in da khaleefa ke mata, duk da ita ta gyara gyalen ba don shiba sai don ta suturta jikinta gaban wanda ba muharraminta ba. Ayman kam tab'o khaleefa yayi, koda ya juyo saiya nuna mishi suhaana a fakaice yana shafo k'eyarshi. Khaleefa yace, "itace kenan?". Sai ya gyad'a mishi kai yana murmushi. Shima murmushin yayi yana ci gaba da kallon shigar gimbiyarshi ta yau. Ko kad'an ba zaice ya tab'a ganinta da kwalliya irin cab'a cab'a d'in nan ba, amma kullum dressing d'inta abun ayi ta kallo ne. Ita kuwa ganin sunja tunga sun tsaya saita d'auko tray ta d'aukar musu drink's masu sanyi. Ruwa kad'ai suka sha Ayman yace, "muje ko?". Sai duk suka taso, bayan khaleefa ya rufe sashen sallama raihana da suhaana Suka ma mutanen gidan. Haka dai raihana ta tafi da tunanin yanayin da take ganin auntie kadaran kadahan har ta futo a sashen. Kasancewar Ayman ke tuk'a motar sai khaleefa ya shiga baya, har suhaana ta bud'e bayan zata shiga sai taga mijin raihana ne a ciki ta juya, da sauri yace, "Bismillah shigo mana". Ta juya sashen da raihana take sai taga tayi mata murmushi, hakan ya bata kwarin gwiwar shiga ita kuma ta shiga mazaunin kusa da driver. Suna tafe a hanya khaleefa ke tambayar suhaana matakin karatun ta da wasu abubuwa da suka shafe ta da harshen Arab. Ko a ranta bata kawo komai ba haka ta dinga bashi amsa ganin ya saki jiki da ita, Sam bata d'auka ya iya magana haka ba da taga iya gaisuwa ke had'a ta dashi a duk zaman nan da sukayi. Wannan abu da khaleefa yayi ba k'aramin sosawa raihana rai yayi ba, amma ko a fuska ba zaka tab'a ganewa ba, hasalima hira suke da Ayman jefi jefi tana murmushi. Kafun su k'arasa gidan saida suka tsaya a store d'in kusa da anguwar, lokacin da zasu futa k'in futa raihana tayi a cewarta ba tada abin siya, ganin haka sai suhaana data futo ta fara k'ok'arin komawa. Khaleefa ya hanata, duk yadda taso haka ta hak'ura lokacin Ayman har yayi gaba, Koda suka jera suna ci gaba da hirar su saida khaleefa ya juyo ya kalli raihana, ta kuwa zuba musu ido tana kallon su, ganin ya juyo kuma ya sata d'auke kanta da sauri tana jin wani irin abu na soya mata a k'ahon zuci. Haka suka d'auki adadin wasu mintuna sannan suka dawo da kaya masu yawa a hannuwan su suka zuba a boot. Suhaana ta shiga mazaunin ta na d'azu tana ma raihana magana, "uhm!". Kawai tace mata taci gaba da duba wayarta. Suhaana ta d'auka bata ji taba sai take tambayarta, "kinji abinda nace kuwa?". Khaleefa yace, "kinga rabu da ita wannan yanzun in kin samu miji zaki iya hak'ura da karatun kiyi aure?". Ya sauya akalar zancen gaba d'aya kuma cikin harshen turanci yadda raihana zata iya ji. Suhaana kam jikinta a sanyaye take ci gaba da hirar dashi har motar su ta parker a k'ofar gidan alhaji salis Abdallah. Khaleefa ne ya fara futowa ya zagaya boot ya ciro wasu cikin ledojin ya mik'awa suhaana data futo, wasu kuma ya mik'awa raihana da take gyara yafen gyalenta da jakarta. "Ni ai banyi siyayyah ba". Ta fad'a tana kallon ledojin. "Ki karb'a mana ai bakya je musu hannu rabbana ba, kin d'auko hanya mai nisa". Ayman ne me yin wannan maganar. Madadin ta karb'a saita fara tafiya zata bar gurin, khaleefa yabi bayanta da sauri ya sak'alo hannunta cikin nashi yasha gabanta yana kallonta, kauda fuskarta tayi gefe, bai damu ba ya d'anka mata ledojin cikin hannunta muryarshi can k'asa yadda ita kad'ai da take kusa dashi zata ji abinda yake fad'a, "in ke na bawa sai kice bakya so, amma wannan nasu al'ameen ne". Yana fad'in haka yaja jikin shi baya kusa da Ayman yana kallonta. Suhaana da taga duk abinda ya faru ta matso kusa da ita tana mata dariyar shak'iyan ci da tsokana, "soyayyah dad'i! Kinga irin kallo kamar ku biyu kad'ai a gurin". Ita kam sake jin haushin tama tayi, sai bata ce komai ba ta fara takawa suhaanan tabi bayanta. Suka shiga gidan kusan a tare suna kwad'a sallama, da gudu su hibba duk suka futo jin muryarta, aikuwa ta saki ledar hannunta ta rungume yaran tana jin kewar su, abin gwanin burgewa haka suhaana ta tsaya tana kallon su. Ummie da take kitchen ma futowa tayi tana mamaki. "Ashe da gaske ke d'in ce". Ta fad'a daga bayan raihanan. Saita juya gurinta da sauri ta fad'a jikinta tana fad'in, "I miss you ummiena". Sai kuma ta fashe da kuka. Ummie ta d'ago kanta cike daso da k'auna tana share mata hawaye da fad'in, "Nima nayi kewarki raihana amma meye na kuka daga shigowa kuma, gashi naga ma tare kike da bak'uwa". Ta k'arasa fad'a da janye raihana a jikinta tana ma suhaana data tsaya kallon su gwanin burgewa iso. Sai bayan sun zauna a parlon sun gaisa ummie ta gane bak'uwar raihanan bata jin hausa sam, raihana ta gabatarwa suhaana y'an gidan su, suma ta gabatar musu ita suka sake gaisheta. Ta fara sauraren shiriritar su al'ameen ummie ta tambayeta, "Ina fatan dai ku kad'ai kuka zo ba shanya bawan Allah kikayi a waje ba irin waccen ranar". Sai a lokacin ta tuna ta mik'e don tayo mishi iso shima, ummie ta d'auko hijabinta tasa tana mamakin wannan al'amari na raihana, yanzu da bata tambaya ba haka zai ta tsayuwa a waje ta manta dashi. Lokacin data futo suna gaisawa da Abba Abubakar, ta k'arasa itama suka gaisa sannan ta musu iso zuwa cikin gidan. Har parlon ummie suka shiga wannan karon ma aka gaggaisa, su al'ameen suka gaishe su, sun tab'a hira da khaleefa kafun suyi sallama zasu tafi. Raihana tayi banza dasu ba kuma ta da niyyar tashi har saida khaleefa ya magantu, "zamu jira ku a waje saboda zamu k'arasa gidan iya mu gaisheta kafun mu tafi". "Kuje kawai zan biyo ku". Ta fad'a don tana son kafun ta tafi taga abbanta, sai gashi kuwa maganarta karaf a kunnen ummie, ta kuwa yi mata tatas sannan tasa tabi bayan shi lokacin har sun futa ma. Ba don ranta yaso ba haka ta turawa su al'ameen ledojin da suka shigo dashi tace, "gashi akace mu kawo muku". Ummie tace, "toh mun gode Allah amfana shida baya gajiya". Har ta futo fuskarta a d'aure, saida zasu shiga gidan iya ta saki ranta, nan ma saida khaleefa ya had'a su da shopping su kai mata. Iya kam washe da baki take kallon su tana al'ajabin bak'in nata na yau kamar an wurgo su har su hud'u haka. A parlour ta ajiye su ta kawo musu kayan soye soyenta da bata rabo dasu, sai zolayar suhaana take wai ta koyi hausa ko taji dad'in Zama a Nigeria don tafi son ta samu miji a garin nan. Khaleefa da yake sauraron iya yayi zaraf yace, "ai tama samu insha Allah". Ras! Gaban raihana ya fad'i har saida yanayinta ya sauya sosai. Saita mik'e don in taci gaba da zama komai zai iya faruwa, ta dubi iya tace, "Ina d'akina da mai ran k'arfe ya shirya mun". "Ga satar miji ga d'aki? Gatan ai sai yayi miki yawa, sai dai in na baki aron nawa amma ba kyauta ba, shima saboda zuciyar musulunci ne, don kishiya ba abar goyo bace". Murmushi tayi ta nufi d'akin da iya ta nuna mata. Tana shiga ta kwanta a gadon iya ta rufe fuskarta da hannunta. Khaleefa ne ya dubi iya duk da akwai sauran lokacin sallah amma sai cewa yayi bari zan shiga ta bani ruwa nayi alwala. "Kaji dashi ai, waini zai rainawa hankali da wani guntuwar gulmar shi". Iya ta fad'a. Ayman dai yayi dariya, shikam bai kula zantuttukan iya ba yace da d'an uwan shi, "na fara share maka hanya fa". Ayman cikin jin dad'i yace, "ah haba? ai naga alama d'azu fatan dai madame ba fushi tayi ba naga yanayinta ya sauya lokaci d'aya". Khaleefa yana murmushi yace, "zata sauko ne kada ka damu da ita, so nake ta k'aryata kanta da kanta". Ayman yace, "lallai ne amma dai kabi ta sannu mata duk Inda suke saida lallab'awa". Murmushi kawai khaleefa yayi daga nan ya nufi d'akin ba tare daya sake ce dashi komai ba, Ayman kuma ya fuskanci suhaana kamar wani jarumi. Raihana tana kwance taji turo k'ofa, saita rufe idonta da sauri don ta d'auka ko suhaana ce ta biyo bayanta. Daga k'amshin turaren da yake kusantota ta fahimci ko waye, saita sake d'auke numfashi rauninta na sake bayyana, haka tana jin yadda wani abu ke tasowa tun daga k'asan ranta mai kama da fushi ko fusata. Tana jinshi ya k'araso ya d'auke k'afafunta ya mayar kan jikin shi ya tsura ma face d'inta ido. Sosai yake k'are mata kallo yana nazarinta, yasani dama raihana tana son shi, abinda bai sani ba kawai yaushe wannan soyayyar ta fara ginuwa a zuciyarta har tayi k'arfin da idonta yake rufewa kan kishin shi. Koda yake ba abun mamaki bane tunda shima yake jin fiye da haka akanta, inda Allah ma ya taimake shi tasan ciwon kanta, wayewarta a b'oye take da kallo d'aya ba za'a tab'a fahimtar taba sai an zauna da ita. Nutsuwa, Kamala, hankali, tarbiyyah da wadataccen ilimin addini dana zamani babu wanda ta rasa, lallai itace irin macen data dace dashi, irin macen da zai iya sakarwa ragamar tarbiyyar y'ay'an shi ba tsoro ko d'ar. Lallai ba k'aramin kuskure yaso tafkawa ba d'aukar Saleema matsayin mace. Sai yaja doguwar ajiyar zuciya ya lumshe idon shi ya bud'e yana sake godewa Allah a cikin zuciyarshi, yayi gyaran murya kad'an sannan yayi magana, "Ina son magana dake Raihanatu". Bata amsa shi ba, "nasan kina jina sarai". Nan ma bata tanka ba sai ruwan hawaye daya ciko idonta. Shima bai sake cewa komai ba ya durk'usar da kanshi ta yadda har numfashin su na had'uwa, ya d'ago kanta kad'an ya tallafe fuskarta da hannun shi biyu ya had'e fuskarsu har hancin su na gogan juna, abu na gaba da yayi shine fara kissing d'inta gently. Duk yadda raihana taso dakewa a wannan karon kam kasawa tayi, ba tare da neman izinin taba hawayenta ya soma kwaranya, ta bud'e idon tana kallon shi kafun ta tura shi kad'an ta tashi zaune ta cusa kanta tsakanin gwiwowin ta ta fashe da kuka mara sauti. Khaleefa bai yi k'ok'arin hana taba don yasan yadda kuka yake a gurin wanda Allah yake ba damar yi, don rahama ne yinshi a wasu lokutan. Ganin kukan nata ba mai k'arewa bane sai ya haura gadon ya zauna kusa da ita sosai ya d'ora hannun shi a gadon bayanta yace, "I'm sorry". Bata kula shiba yasan za'ayi haka, sai ya d'ago kan nata yasa tafin hannun shi yana share mata hawayen yana sake bata hak'ori. Da kyar ya samu ya lallab'a ta tayi shiru, sai a lokacin ya samu damar tambayarta ba'asin kukan nata. Da murya mai rawa ta fara fad'in, "na gaji, na gaji da halinka khaleefa! Tunda na aure ka baka tab'a bani damar zuwa gidan mu na wuni tare da familyna na sake kamar kowacce mace ba, Ina da k'anne, Ina da y'an uwa, Ina da kakanni amma baka bani damar zuwa musu takanas sai in na shiga na futo kana jirana a waje, Ni duk wannan ma bai dame niba kamar yadda nayi tafiya mai nisa na dawo amma na shiga gidan mu kamar bak'uwa ko gama gaisawa da ummiena banyi ba bare naga Abbana da bai ma dawo kasuwa ba ka azalzala na futo..... I'm tired wallahi na gaji". Ta k'arashe maganar da rawar murya tana sake fashewa da wani kukan. Khaleefa da mamakinta yau ya cika shi jawo ta jikin shi yayi ya rungume yana bubbuga bayanta, "shine kad'ai laifina ko akwai wani?". Ya tambayeta har lokacin yana rungume da ita. Ita kuwa kamar ta mishi maganar suhaana saita basar karya d'auka kishin shi ma take. Madadin haka saita janye jikinta ta jingina da fuskar bed ta lalubo wayarta tana dannawa. Shi kuwa sauka yayi a gadon jin malam ya kwala kiran sallah a masallaci. Agogon hannun shi ya cire ya d'ora mata kan cinya ya ajiye hular kanshi ma ya shiga bathroom don d'auro alwala. Bayan ya futo ya maida agogon shi da hular shi ya fuce a d'akin, tabi bayan shi da munafukin kallo tana jin wani tarin k'aunar shi a zuciyarta. Ita kanta tuhumar kanta take yaushe har ta shak'u dashi take jin wani abu game dashi haka. Kasancewar ba sallar zata yiba saita sake kwanciya tana buga game a wayarta, abu na k'arshe da saita matuk'ar rasa abinyi ta kanyi. Kafun suhaana ta shigo ta hanata game d'in da hira. Ta b'angaren khaleefa kam bashi ya dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, suka futo tare da malam suna tattakawa, sai a lokacin malam yake shaida musu an maida auren iyayen su, ba k'aramin farin ciki sukayi ba kuwa don abun yazo musu da wuri ba yadda suka d'auka ba. Sun shiga gidan suka samu iya raihana da suhaana suna hira a parlonta, rabin hirar ma abun dariya don itace a tsakiya tana musu tafinta. Zuwan su ya dakatar da hirar, iya ta kawo musu abincin su su biyu, shi kuma malam ya shige d'akin shi, sai ya zamana daga iya sai su a gurin. Sunyi hira da iya sosai kafun su mata sallama zasu tafi, lokacin bacci duk yaci k'arfin raihana da kyar ta iya lallab'awa ta futo amma suna shiga mota ta fara bacci. (Da yake wannan karon tafiyar ba kamar wancen lokacin ba, duka mazan suna gaba matan a baya). Bayan sun k'arasa gidan ma saida suhaana ta tashe ta sannan, ko sallama ba ta iya yiwa Ayman ba ta bud'e k'ofar sashenta ta shiga. Suhaana tabi bayanta ta d'auki kayanta zata tafi, hanata futa raihana tayi wai lallai saita kwana a nan, ita kuwa tace ba zai yiwu ba, ita kuma ta tubure, ganin abun nata bana k'are bane sai ta lallab'a tayi guduwarta. Suhaana tana futa ko kayan jikinta bata sauya ba ta maida dim light ta kwanta dama duk abinnan da take bacci ne fal idonta, k'arfin hali kawai take. Khaleefa kam sun d'an jima tare da Abban su suna hira, kafun ya musu sallama ya nufo sashen, yana shiga wanka yayi ya sauya kayan jikin shi zuwa tausasan kayan bacci, har ya kwanta ya jishi in complete ya tashi ya futo daga d'akin bayan ya rufe ya nufi nata. Sai daya k'ara haske ya gano ta a farkon gado juyi d'aya zata iya fad'owa, ya k'arasa da sauri ya gyara mata kwanciyar, saida yaita tunani sannan ya shiga cikin bathroom ya had'a mata ruwa masu d'umi, ya zuba mata turarukan wankanta ya futo. Cak ya d'auke ta bai dire ta a ko'ina ba sai cikin ruwan wankan daya tara mata bayan ya rufe mata gashin kanta da shower cap, kafun ta tantance a yanayin da take har ruwan ya fara ratsa ta, d'umin shi ya sake dilmiyata cikin wani sabon bacci mai dad'i, abun ma dariya yaba khaleefa, sai ya fara shafa mata ruwa a fuska har yayi nasarar tashin ta a baccin. Ta kuwa zabura zata futo ya sake dannata yana girgiza mata kai. Da lalube ya zura hannun shi ta bayanta ya zuge mata zif d'in rigar, ta kuma zabura cike da tsoro, ya d'ora hannun shi akan leben shi yana gargad'in ta, "kada kice komai! Kiyi wanka kurum". Dole ta koma cikin ruwan tana kallon shi zuciyarta na bugawa faster. Bata samu nutsuwa ba saida taga ashe futa ma zaiyi a d'akin wankan, ta sauke ajiyar zuciya ta maza ta murza key sannan ta samu nutsuwar wankan. Bayan ta gama ta d'auki bathrobe daya ajiye mata tasa, sai dai fa ta kasa futowa, ta tabbatar yana cikin d'akin gashi ba komai a jikinta dama kayan jikinta sun jima da jik'ewa. Dole saita futo zata sauya kayan. Kamar munafuka haka ta bud'e k'ofar tana lek'a cikin d'akin, sai taga bata ganshi ba, ta k'arasa futowa da sauri ta nufi jikin wardrobe d'inta, sai dai abun mamaki a rufe take gam kuma babu ko key d'aya da aka bar mata. Saita fara laluba drower kota manta ta mayar ciki, sai dai nan ma babu, har ta yanke hukuncin komawa sai taga kaya saman bed d'inta. Ta tafi da sauri ta d'auka zata saka sai kuma ta fara juya kayan a hannunta, ohh Allah ta fad'a a ranta ganin irin sexy night wears daya kawo mata. Nan fa ta rarraba zuciyarta tasa ko kada tasa, jin kamar ana tab'a k'ofarta saita watsar da kayan ta koma jikin bango ta takure kamar wadda ta yiwa sarki k'arya tana faman zaro ido. Ganin ba'a shigo ba saita fara k'ok'arin saka kayan da sauri sauri, wando ne iya cinya da rigarshi sharara iya gwiwar k'afarta amma bata rufe komai na jikinta ba. Ta shafa turaren da taga ya had'a mata cikin kayan, nan da nan ta d'auki sirrin k'amshi. Bayan ta d'aure gashin kanta da ribbom tsayawa tayi gaban mirrow tana kallon kanta, ita kanta sai data ji kunyar kallon kanta cikin kayan, "taya ma zan iya tsayawa gaban shi a haka". Ta fad'a a fili, aikuwa tana rufe bakinta yana shigowa. Cak ta tsaya ta kasa ko kwakkwaran motsi, shi kuwa Masha Allah Alhamdulillah yake fad'i cikin zuciyarshi. Ya murzawa k'ofar key ya fara takowa ciki zuwa gare ta idonshi a kanta ko kiftawa ba yayi har ya k'arasa wajen da take tsaye, ya tsaya daga bayanta ya dogare hannun shi jikin mirrown, ya sata a tsakiya yana kallonta ta cikin mirrown, kawai runtse idanunta tayi don bata ga banbancin a ganta da wannan kayan da tsirara ba. _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy eight 7️⃣8️⃣ "Kinyi kyau". Ya fad'a da husky voice yana kallonta still ta cikin mudubin. Ita kuwa k'ok'arin kaucewa take daga gurin amma ya hana ta damar hakan fafur, tuno abinda ya faru tsakanin shi da suhaana d'azu sai ya harzuk'ata da k'ara mata k'arfi cassa'in cikin d'ari, (kunsan kishi k'arfin mata💪) ta kuwa d'aga hannun shi ta tafi da gudu zata futa a d'akin gaba d'aya. Shi kuwa sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi, ganin ta dage da gaske tana ta kokawa da k'ofa sai ya kad'a mata mukullin hannun shi. Ta juyo tana kallon shi dai dai lokacin da shima ya juyo yana kallonta. Da sauri ta d'ora hannunta kan switch ta kashe wutar d'akin gaba d'aya. Ta cikin duhun ya fara lalubenta tana b'uya, kamar wasa sai gashi sunata wasan b'uya ya kuma kasa samunta. Raihana tun tana b'uya cike da tsoro sai gashi abun ya zamar musu wasan gaske, har yana sasu cikin nishad'i da tuno lokacin da suke yara ita dasu Salma irin wasan su kenan, in akayi nasarar kama mutum ayi mishi dundu hud'u. Murmushi ne ya sub'uce kan fuskarta ta cikin dahun, sai kuma ta gimtse fuska ganin k'afar shi kusa da inda take durk'ushe, da yake ya juya baya tana mik'ewa yaji k'amshinta kusa dashi ai kuwa taku d'aya ana biyu ta jita cikin jikin shi gaba d'aya. "Wana kama?". Cikin marairaita tace, "kayi hak'uri don Allah". "A'a sakin fad'a mun abinda ya hassala ki kika rufe ni da maseefa d'azu". "Nifa Allah ba komaiii....". Da sauri ya katse ta, "kar ki fara yimun k'arya ko jawabin rehu mai yawa, bazan iya zama da yawa ba cikin duhu". Shiru tayi bata ce komai ba, "ki fad'a mun gaskiya before the count of three" sai ya fara k'irga d'aya, biyu, uku, da sauri tace, "Ni fa ba komai". "Baza dai ki fad'a ba kenan?". "Da gaske ba komai sai hana ni inga Abbana da kayi". "shikenan let's sleep". A hankali ta zame jikinta tana kallon shi ta cikin duhun tace, "okay saida safe". Ya jingina da bango yana kallonta yace, "sleep tight dear". Madadin ya tafi sai taga yaci gaba da tsayuwa, gashi so take ya futa ta kwanta. Saita gyara tsayuwarta tace, "so nake ka futa zan rufe k'ofar". Ya maida hannun shi aljihu yace, "muje". Yayi gaba tana bin bayan shi har yaje kusa da k'ofar kamar zai murd'a handle sai kuma ya juyo unexpected ya jawo ta jikin shi ya rungume ta tsam tsam a k'irjin shi, Ya zura bakin shi cikin kunnenta da husky voice yace, "kin tab'a ganin inda macen arzik'i ta kori mijinta.....? Raihana zan baki dama ki fahimci zuciyata da abinda ke cikinta game dake a wannan daren, open your heart and read it clearly....". Ko kafun ta samu kwarin gwiwar aikata wani abu ya d'aga ta cak....... Ya maida d'akin k'ark'ashin dim light..... Abinda ya biyo bayan wannan dare ya kasance mai girma ga wad'annan bayin Allah guda biyu, the gentle love making under the dim light, abun yazo fiye da zato ko hasashen raihana. A ranar ta san zahirin Abdallah khaleefa, jajirtacce kuma gwarzon namiji da yasan sirrin soyayyah da yadda zai sarrafata, indai har da gaske his action express what's in his mind ta gama tabbatar da soyayyarta mai yawa dankare cikin zuciyarshi. ***Washe garin ranar suka tashi cikin jin matsananciyar kunyar juna, musamman raihana data kasa futa ko gaishe da mutanen gidan kamar yadda ta saba a kowacce safiya. Tana nad'e a gado tun bayan da tayi sallah ta kasa aiwatar da komai sai tuno scenes d'insu na jiya tana fudda sautin murmushi, babu abinda tafi tunawa kamar tsadaddun kalaman da khaleefa ya dinga furta mata. Tana wannan tunane tunanen bacci b'arawo yayi gaba da ita. Lokacin data farka rana ta d'aga sosai, ta mik'e da sauri tana ambaton sunan Allah. Bathroom ta fad'a shap shap tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, tayi d'aurinta mai kyau da simple make-up kamar koda yaushe, ta shafa turaren ta mai sanyin k'amshi da sai in tazo dab ake jinshi. A nutse ta fara takawa tana kallon yadda aka gyare ko'ina tsab, ba tayi mamakin ganin warmers ba tasan break ne auntie ta aiko musu kamar koda yaushe, sai dai kamar ba'a tab'a komai dake dinning d'in ba, tabbacin bai karya ba shima? Sai ta nufi d'akin shi ta d'ora hannu zata mishi knocking sai kuma tayi tunanin maybe bacci yake kada ta tashe shi kuma, saita tura d'akin a nutse tana lek'en cikin d'akin daga inda take. Yana kwance ya rufe jikin shi da duvet sai kace sanyi ake a garin. Ajiyar zuciya ta sauke ta juyo da nufin janye kanta sai taji muryarshi cikin dodon kunnenta, "in kin gama lek'en ki shigo ki had'a mun ruwan da zanyi wanka". Sam bata d'auka yana jinta ba saida yayi maganar, saita shigo a nutse kamar bata son taka k'asa har bedroom d'inshi ta had'a mishi ruwa kamar wanda tasan yana so a wanka. Bathroom d'in ba datti ko digo amma duk da haka bata futo ba saida ta tsaya goge mishi mirrow da sauyawa abubuwan shi da yawa muhalli kamar wadda aka sa🤔, tana cikin aikin ya shigo d'aure da towel daga kugun shi zuwa gwiwar k'afar shi, ta ajiye duster da sauri zata fuce ko kallon shi ta kasa tun sau d'aya daya shigo suka had'a ido a tsautsayi. Da hannun shi d'aya ya tare ta, "Ina zaki kuma baki k'arasa aikin kiba madame". "Zan gyara maka d'akin gadon...". Ta fad'a a marairaice. Khaleefa yayi wani miskilin murmushi yace, "ohh aikin goge tiles da katakwaye har yafi na mijin ki muhimmanci?". Ita dai bata ce dashi komai ba ta silale ta futo tana sauke ajiyar zuciya, tana jinshi yana fad'in, "matsoraciya kawai". Murmushi tayi ta fara had'a mishi d'akin da kayan daya cire sauri sauri. Lokacin daya futo ta jona burner da turare a ciki kenan. Wannan karon ma guduwa taso yi amma bai barta ba, duk rikicinta da tsoronta haka dai ta hak'ura ta taya shi shafa mai a jikin shi, ya gama da taimakonta ya saka kayan data zab'a mishi shadda sky blue da agogo takalmi da hula. Yayi kyau sosai har saida ta fad'a, "kayi kyau fa". "Kinyi k'ok'ari zaki ce ba nayi kyau ba". Tayi murmushi ya kashe mata ido d'aya. Tare suka futo suka zauna a dinning tayi saving d'insu da lafiyayyen break da aunty tasa a kawo musu. Nan ma cike da soyayyah sukayi feeding juna. Bayan sun gama ta tattare gurin tass gyalenta ta d'auko da flat shoe, yana zaune cikin parlon yana danna wayarshi ta k'araso ta dafa saman kujerar daga ta bayan shi tace, "Zan je mu gaisa dasu auntie da Abba". Wayar ya mayar cikin aljihu ya dube ta, "ki d'auko kayan ki set biyu da duk wani abun da kikasan zaki buk'ata a kwana ki biyu kacal". Raihana kamar ta tambaye shi wani gurin zasu, sai kuma dai tayi yadda yace. Shiya karb'i jakar kayanta ita kuma ta futo rik'e da hand bag ta rufe k'ofar parlon. Saida suka fara gaisawa dasu Abba sannan suka haura sama gurin su auntie, bayan sun gaisa da doctor andal da momma da take ta zolayar su wai irin mijin irin matar, murmushi kawai khaleefa yayi ya tambayi Auntie, momma ta fad'a mishi ta d'an futa taje ta dawo. "Okay in ta dawo ki fad'a mata raihana tazo yi mata sallama ne zata d'anyi tafiya ta kwana biyu". Momma tace, "lafiya dai ko?". Khaleefa yace, "lafiya alhamdulillah". Momma tace, "toh Masha Allah! Allah ya tsare hanya raihanatu ya dawo dake lafiya". Khaleefa ya amsa da "ameen" yana mik'ewa. Itama da batasan komai akan maganar tafiyar ba ta mik'e tabi bayan shi. Bayan sun futo suka had'u da mama haleema ma suka gaisa har khaleefa na tambayarta suhaana yaga bai ganta cikin parlon ba. Wani abu ya soki raihana har kwakwalwar ta ta tafi mata tariyar abinda ya faru jiya. "Tana bacci ko a taso ta?". Yace, "a'a barta kawai in na dawo zamu yi magana". Ya k'arasa fad'a yana kallon raihana da har ta huce su tuni, sai ya yiwa mama haleema sallama yabi bayanta. Mama haleema tabi su da kallo tana murmushi. Khaleefa tunda suka futo ya fahimci sauyawar da raihana tayi amma baice mata komai ba saida suka d'auki hanya, "madame what's going on naga kin sauya". Ranta a had'e tace, "nothing". Sai yayi murmushi bai sake ce da ita komai ba, sun tsaya a k'aramin supermarket dake kan kwanar layin su yayi siyayyah sannan ya k'arasa da ita k'ofar gidan su. Yana yin parking ta soma k'ok'arin futa, lock yasa, sai ta tsaya tana kallon shi, shima kallonta yake, "a garin ku haka kika ga ake yi? Kawai daga parking sai ki fuce? At least dai kya tsaya muyi sallama ko?". Gefen windown da take zaune ta juya kanta ba tare da tace mishi komai ba. Shima bai sake ce mata ba ya fara k'ok'arin yin reverse zai bar layin, da sauri ta d'ora hannunta akan nashi tana girgiza mishi kai idonta fal ruwan hawaye tace, "don Allah kada ka fasa abinda kayi niyya, Allah kad'ai yasan ladan da zaka samu". Tsayawa yayi yana kallonta yace, "Amma me yasa dana miki magana kika share ni? Ki kalleni da kyau kinga nayi miki kama da irin mazan da suke d'aukan rainin hankali irin wannan? Tun jiya nake tambayarki in nayi miki wani abu kince ba komai, dubi yadda kike kuka.....". Ya k'are maganar da juya kanshi gefe yana fatan jin abinda yake son ji daga gareta cikin kwanakin. Ita kam share hawayenta tayi ta d'auko powder a jakarta ta gyara fuskar hadda k'ara wetlips. Duk abinda takeyi yana kallonta ta cikin mirrow, saida suka d'auki tsayin wasu lokuta sannan ya bata damar futowa, ya mik'a mata ledar shopping da jakar kayanta. Ta karb'a ta russuna tana mishi godiya da tambayar, "kwana nawa zanyi?". Ya furzar da iska mai huci daga bakin shi yace, "biyu". Ta sake russunawa a gaban shi tace, "nagode". Ya gyad'a mata kai yana kallonta da danne k'in amincewa da wani b'angaren na zuciyarshi yake sonyi yace, "zanyi kewarki raihanatu, nasan ke mantawa ma zakiyi dani da kin samu y'an uwan ki". Ba tace komai ba sai tsayawa da tayi tana kallon shi da wani irin bak'on yanayi, daga kwayar idonta ya fahimci abinda ke cikin zuciyarta. "Zan k'arasa gidan sai Allah yayi mun dawowa?". "Sai kin dawo ko sai nazo d'aukar ki?". Saita tsaya ba tare data juyo ba, shi kuma yayi tattaki zuwa gareta ya tsaya dab da ita yana kallonta, saboda kusancin da sukayi saita d'an janye jikinta baya, shi kuwa cikin tsare gida yace, "ban yarda kije ko'ina ba bayan gidan khausar da Salma, hajiya ummaa da Inna da kaina zan kai ki gidan su kafun tafiyar mu tofa". Ta gyad'a mishi kai cikin matuk'ar jin dad'in abinda ya mata, "ki gaishe da ummie dasu al'ameen". "Zasu ji nagode". Ta fad'a a sanyaye ta d'auki hanyar shiga gidan, saida takai k'ofar gidan ta juyo ta kalle shi, saita samu kanta da mishi murmushi da d'aga mishi hannu. Ya d'aga mata shima bai matsa gurin ba har ta shige. Ya sauke k'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya shige motarshi. Bai koma gidan ba haka yayi ta shawagi cikin gari, tun kafun aje da nisa ya fara gane kuskuren shi, don sosai ya shiga cikin kewarta amma yayi alk'awarin zai danne zuciyarshi ya bata damar sakewa tare da ummien ta da sauran k'annen ta. ***Ita kuwa ummie ba k'aramin mamakin ganinta tayi ba, koda ta fad'a mata yadda sukayi da khaleefa fad'a ta mata sosai da tunanin ko takura shi tayi ya dawo da ita, har saida ta mata bayanin komai dalla dallah sannan ta barta. Sunsha hira kuwa sosai ita da ummien irin wadda suka jima ba suyi ba. Sai a lokacin take warware mata dalilin zuwan su da abinda ya kawo su, ummie tayi al'ajabi kuma ta taya auntie murnar sake komawa gidan mijinta, tace da an kwana biyu zata je mata Allah sanya alkhairy. Da dare Abbanta daya dawo ya ganta yaji dad'in ganinta shima, dama tun jiya ummie take fad'a mishi tazo k'asar. Sun tattauna game da abinda ya shafi karatun ta, a nan ma Abba saida yayita sawa khaleefa albarka da yabawa k'ok'arin shi. Ranar sai nisan dare ta bar cikin su al'ameen ta shige d'akinta. ****A tak'aice kwana ki biyu da raihana tayi a gidan su ya mata dad'i tare da y'an uwanta, taje gidan Salma inda ta sameta tana laulayi sai rigingimu take yi wai daga haihuwa sai haihuwa ba hutu shikenan kuma ita haka zata k'are. A lokacin yasmine ce ta fad'o zuciyar raihana, sai taga sak yadda sukayi da ita farkon laulayinta. Haka dai ta lallab'ata da nasihohi ta gudu ta barta. Khausar kuwa alhamdulillah ta sameta lafiya lou ita da unborn babynta, sunyi hira ta hankali mai yawa da ita kafun ta tafi. A ranar raihana ta kwana da kewar khaleefa da batasan zata yi ba da kuma tunanin hirar su da khausar. Ranar bacci sai b'arawo haka tayi ta juyi har k'arshen dare. Washe gari dama tunda sassafe ta fara shiri don tasan khaleefa da wuri zai zo d'aukarta kamar yadda ya kawo ta. Aikuwa tana zaune dasu ameena da suka samu labarin zuwanta suka zo sai ga aiken shi. Haka tana ji tana gani ta hak'ura da hira dasu saboda azalzalawar da ummie ta mata sukayi mata rakiya zata tafi, bayan sun d'aukar mata alk'awarin zuwa mata wuni guda. Har motar da yazo ciki suka k'arasa suka gaisa suka k'arasa sallama ta shiga ciki su kuma suka juya. "Ina kwana". Ta fad'a bayan ta d'auke kanta gefe. "Lafiya lou yasu ummie". "Suna lafiyarsu". Ta bashi amsa. Daga haka ba wanda ya sake ce da d'an uwan shi kanzil har suka k'arasa gida. Dama bata nufi part d'insu ba direct tayi saman b'angaren auntie. Tana shiga da suhaana ta fara had'uwa, ta kuwa daka tsalle ta rungumeta tana mata oyoyo. Itama sakin fuska tayi ta nuna farin cikin ganinta, bayan ta zauna suka gaisa dasu momma da auntie har suna tambayarta yadda ta baro mutanen gidan. Ta jima a nan har saida kawaici da hak'urin khaleefa ya k'are ya shigo parlon yana tambayarta mukullin d'akin shi. Da mamaki ta tsaya tana kallon shi, ita da ta dawo gidan yau ina zatasan wani inda keyn d'akin shi yake? Toh da bata nan ina yake kwana?. Saita rasa abinda ma zata ce mishi a wannan gab'ar gashi gaban su momma yayi mata maganar, har momma na fad'in ko zata je ta duba mishi, auntie dama yi tayi kamar bata ji suba don tasan shegantaka ce ba wani mukulli, kuma dai ma yayi hak'uri don tafi hour uku gurin suhaana suna ta hira a wani sashe na parlon, tasan yayi kewar matarshi tunda tana ankare dashi kwanakin nan biyu gaba d'aya a dame yake, ita kuma bata son duk abinda za'a ga ta nuna son d'anta k'iri k'iri. Dole ba don raihana ta so ba ta tashi ta musu sallama suka tafi. Tana shiga parlon khaleefa ya murza key, ta kalle shi ya d'aga mata kai, "keda futa kuma sai gobe tunda bakisan zuru ba". B'ata fuska tayi ta zauna cikin d'aya daga kujerun parlon tana fad'in, "dama nasan ba wani mukulli don kawai ka raba nida cikin mutane ne". "Kin fahimta dai dai kuwa". Ya fad'a shima yana zama opposite to her. Sake k'ulewa tayi ta kwantar da kanta baya tayi banza dashi. Shi kam murmushi yayi bayan sun d'auki lokaci shiru a haka kafun yace, "Wai ma kin daina kishin suhaanar ne da kika je gurinta kuna ta hira hadda jin haushi na rabo ki da ita.....". Mik'ewa tayi zata bar gurin tace, "yaushe kuma ni nace maka ina kishi da ita?". "Baki fad'a ba da bakin ki but your acting says". Shima ya fad'a yana mik'ewar. D'akinta ta nufa direct shima ya mara mata baya. Tana ajiye gyalenta taji motsin shi a bayanta, tana juyowa ta ganshi dab da ita, zata ja baya yayi saurin rik'o ta, saita marairaice mishi tace, "what". Hannunta ya d'ora a cikin shi, "cikina babu komai". "Toh ni wanka nake son yi na kwanta kuma....". Sai ya d'aga ta cid'ak, "anzo wajen yarinya nima dama wankan zanyi ai". "Allah fa ba kayi datti ba, Ni nama fasa wankan....". "Kin makara hajiya....". Daga nan bai bata damar furta ko kalma d'aya ba ya shige bathroom da ita, (na tafi zan dusa kai da Alk'alamina 😨 aka banko mun k'ofa a goshi🤣). A wannan rana raihana ta sake tabbatar da gaskiyar abinda yake k'asan zuciyar khaleefa, soyayyah yake nuna mata madararta mara algus, da wannan damar yayi amfani ya warware mata komai dangane da Ayman da suhaana, a k'arshe ya samu nasarar daidaita su yanzu alhamdulillah har sun fahimci juna ma. Raihana taji dad'i ta nuna farin cikinta da taya Ayman murnar yadda ya samu mace mai nagarta kamar suhaana. Murmushi khaleefa yayi da yaga yadda take ta farin ciki a lokacin yace, "kishi da jin haushin khaleefa ya k'are ko?". Sai ta rufe fuskarta tana b'oye fuskarta a hannun shi na dama. Murmushi mai kyau yayi yana kallonta da jin sabuwar k'aunarta a zuciyarshi, sai yaja ajiyar zuciya ya d'ora hannun shi saman gashinta ma'abocin santsi da d'aukar ido ya kira sunanta carmly, bata amsa ba ta dai d'ago ta kalle shi, shima yana kallonta yace, "Ina sonki Raihanatu, Ina k'aunar ki sosai, Allah yasa kema kina Sona haka?". Mik'ewa tayi zaune a lokacin tana kallon shi tace, "toh ni wacece ma da zan yarda nayi asarar classy guy kamar ka khaleefa?". Cike da jin dad'i ya rik'o hannunta yayi kissing, "I much love you, keta musamman ce ko a cikin mata dubu samun irin ki sai an tona, shiyasa nake matuk'ar godiya ga Allah subhanahu wata'ala daya mallaka mun ke matsayin matata da zata zamo uwar y'ay'ana bada jimawa ba, Ina fatan kin karb'e ni matsayin abokin rayuwar ki har abada....". Hannunta ta zame a hankali ta shige jikin shi ta d'ora hannunshi saitin zuciyarta, "zuciyata tana bugawa da gudu saboda soyayyarka, idan akace so ana nufin yarda, aminci, sadaukarwa da komai daya shiga cikin zamantakewar yau da gobe tsakanin ma'aurata, raihana is yours khaleefa sai yadda kaso zakayi da ita.....". Tana rufe bakinta ya sauke nashi ciki yana kissing d'inta tun daga zuciyarshi. Haka suka wuni cikin farin ciki da faranta ran juna, da dare ma shiryawa sukayi suka bar gidan, sosai khaleefa ya nutsa da ita cikin gari suna shawagi kamar wasu tsuntsaye kafun at last yayi burki a wani hadadden gallery, bai bata damar d'aukar komai ba sai shi daya jida mata wasu shed'anun expensive classy English wears. Ita kunya ma taji da suka dawo gida ya titsiyeta tana gwada mishi kowanne d'aya a jikinta, tamkar dama don ita akayi kayan haka suka zauna mata cif a jikinta. Tun kafun aje da nisa ta fahimci kalar mijin da Allah ya bata, yana son soyayyah, tattali da kulawa cikin kaya masu d'aukar hankali, shiyasa ta fara yak'i da yakice duk wani nauyin shi don ta zamo irin yadda yake so sai su zauna lafiya. ****Washe gari suka tashi da shirin tafiya garin tofa su duka gidan, sunsha tafiya sun kuma k'aru da abubuwa masu yawa, sunga tushen familyn Abban su, an karb'e su hannu bibbiyu an kuma taya Suraj murnar samun surayya a karo na biyu (don su sun d'auka b'ata tayi a haka kuma aka barsu) kwanan su biyu suka dawo da tarin alkhairin wad'annan mutane masu karamci. ***** Tsakanin suraj da surayyah kuwa har yanzu basu samu zama yadda zasu fahimci juna ba, bata jin zafin shi ko k'ank'ani cikin ranta, tun lokacin data fahimci irin rayuwar da yayi bayan tafiyarta ta sake saduda da amincewa soyayyar shi gareta mara algus ce. Shi kuwa ta b'angaren suraj ganinta matsayin matar shi kad'ai ya gama mishi komai, ko a yanzu Allah ya d'auki ranshi zai tafi cikin farin ciki salaamun, shiyasa shareshin da take baya wani damun shi, tunda ya fahimci da b'urb'ushin soyayyarshi a zuciyarta ya bata ratar lokaci taja zarenta yadda ranta yake so, yana nan yana wani b'oyayyen shiri cikin zuciyarshi na bayan fage da zarar komai ya kammala sun samu keb'ewa da juna zata tabbatar Soyayyah bata tsufa komai shekarunta. Bayan kwana d'aya da dawowarsu kamar yadda khaleefa ya alk'awari ya kai raihana gidan kakanninta biyu da kanshi. Suka gaishe dasu da zasu tafi ya cika su fal da alkhairy kamar wancen lokacin. Suna tafe a mota raihana tana tunanin sauyawar kakarta inno, gaba d'aya kamar sauyo ta akayi ba wannan hargagin da maseefar, itace hadda sakin mata fuska yau, koda yake watak'ila hakan yana da alak'a da rashin lafiyar da tayi. Khaleefa da yake nazarinta tunda suka taho, kallonta yayi na wasu y'an sakanni sannan ya fara maganarshi da fad'in, "haka rayuwar duniya take, in kayi hak'uri a sannu a sannu gaskiya take fallashe kanta ga kowa, ki daina mamakin sauyawarta, raihana duk wani mak'iyin ki zuwa yanzu kin mishi nisan da sai dai ya d'aga kai ya hango k'urar ki, ba kuma da kud'i ba amma da abinda kud'i baya bayarwa wato kwanciyar hankali da nutsuwa, alhamdulillah na cika alk'awarin dana d'aukar wa raina....". Ya k'are maganar da murmushi yana jifanta da kallon tsantsar so da k'auna. Murmushi tayi tasa hannu tana share hawayenta, "tabbas ban manta ba ka cika duk alk'awarin daka d'auka da wanda ma baka d'auka ba, a lokacin da nima zan d'aukar maka nawa alk'awarin, insha Allah ni raihanatu salees zan kasance mace ta kwarai ga mijina kuma bazan tab'a juya mishi baya ba komai tsananin da zai shiga a rayuwa, zamu gudu tare mu tsira tare mu shiga aljanna tare insha Allahu". Khaleefa lumshe idanun shi yayi, ya gangara gefen titi yayi parking motarshi ya rik'e duka hannuwanta biyu "I love you, I love you soo much raihana, zamu kasance tare har k'arshen numfashin mu it's my word". Janye hannuwanta tayi ta d'ora d'aya saman nashi tana kallon cikin kwayar idon shi. "you know what?". Ya tambayeta, ta girgiza mishi kai. "Some promises are always unbroken, some memories are always unwritten". Sai ya d'ora hannunta saitin zuciyarshi, "feel the magic of the true relation, and you will realize that true feelings are always unspoken, you are the end of discussion raihana, without you my life will become useless......". Lumshe idanunta tayi ta bud'e cikin tsananin farin ciki a lokacin da taji kalamanshi suna sauka har cikin k'arshen zuciyarta, a hankali ta matsa dab dashi ta sumbaci kuncin shi hagu da dama, zata kauce ya rik'o ta tsam ya nuna mata lips d'inshi, marairaice mishi tayi, "muna hanya fa....". "Shhh! End what you start ko na gudu dake inda ba idon wanda kike kunya....". Da sauri tasa hannu ta rufe mishi idanu sannan ta mishi light kiss ta koma mazauninta da sauri ta maze kamar ba ita tayi abinda tayi ba, khaleefa yayi dariya ganin yadda tayi yace, "I like dis your innocent face...". Murmushi tayi ta rufe fuskarta da tafin hannunta, "Ni dai muje please". Yayi murmushi ya tashi motar suka bar gurin....... _kuyi hak'uri ina sane daku ma fans, shiyasa nake ta bakin k'ok'arina wajen ganin na rufe muku labarin nan kafun Ramadan insha Allah, godiya da jinjinar ban girma gare ku masoyan asali😍_ *Ina mik'a sak'on taaziyyata ga maryam sulaiman (ummu elmustapha) bisa ga rashi da sukayi na d'an uwa cikin wannan satin, Ina fatan Allah ya jikan shi ya gafarta mishi, yasa ya huta* _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕 (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Story and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page seventy nine7️⃣9️⃣ _Second to the last🤗_ Satin su d'aya da y'an kwana ki a garin Kano suka tattara suka huce garin Abuja, tare da iya da malam da Suraj ya takura su lallai sai sunzo sunga muhallin shi. Babban shagali aka sakeyi na murnar gani da taryar surayyah, wanda ma basu tab'a saninta ba sai a hoto sun ganta ido da ido, sai kuma yaran gidan suka hau santin ganinta a zahiri, ashe duk yadda suke kallon kyanta da gayunta a hoto, zahiri tafi haka. Ita kam mamaki tayi da ganin yadda zuri'ar Abdallah tofa ta cika ta tumbatsa, Fatima dama kuka ta dinga yi tana neman yafiyarta bisa ga yadda suka yarda da k'ullin Aysha har suka bada goyon baya aka tozarta ta. Surayyah bata rik'e kowa a ranta ba, ta yafe musu duka ta kuma nemi itama dasu yafe mata, a nan suka dinga yabon kyawawan halayenta da fad'in, su me tayi musu, ai su wallahi ba wani abu da zata nemi yafiyarsu a kai. Washe garin ranar suka shirya tafiya gidan sauban, kusan su duka wanda suka zo garin Abuja daga Kano har iya da malam. Kasancewar ranar weekend sai abun yazo a dai dai don tabbas sauban baya futa ko'ina weekend hutawa yake a gida, kowa yasan wannan tsarin shine da baya sauyawa. Lokacin da suka isa gidan doctor surayyah tsura mishi idanu tayi tana kallo da tunanin anya wannan ne gidan data sani shekaru talatin baya? Gaba d'aya wannan baiyi kama da wancen gidan ba amma duk da haka sai batayi k'asa a gwiwa ba tabi bayan su har inda yake ganin bak'i cikin weekends, (da yake akwai wasu shugabannin kungiya ta taimakon marayu da yake meeting dasu kowanne k'arshen sati yaji abinda ake buk'ata, sannan yawanci wanda suka zo wannan satin basu suke zuwa wani satin ba) A lokacin da suka tsinci kansu cikin parlon shiru sukayi barin ma surayyah da zuciyarta take matuk'ar bugawa da sauri. Sun jira na tsawon wasu mintuna kafun ya samu futowa garin su. Aikuwa sallamar farko yayi surrender ya tsaya cak yana bin fuskokin mutanen parlon da kallo, dama da farkon farawa da Suraj ya fara tozali kafun daga baya idanun shi su sauka a kanta. Surayyah kam data kasa nutsuwa tun zamanta a parlon da hanzari ta mik'e ta nufe shi a guje, shima k'arasowa yayi ya rungumeta yana kiran sunanta, "surayyah me yasa zaki tafi ki barni, Ina kika je tsawon shekaru? Me kikeyi a can inda kika je? Surayyah mune mukayi silar tafiyarki ko?......". Duka wad'annan tambayoyin yana jera mata sune a lokacin da take rungume a jikin shi, daga ita har shi kuka sukeyi, cike da tausayin su sauran mutanen parlon ke binsu da kallo. Sun jima suna kukan farin cikin had'uwa da juna kafun sauban yaja hannunta ya zaunar da ita gefe d'aya na parlon, yana son fad'awa Sarah abinda ke faruwa sai dai yana tsoron barinta kafun ya dawo ya zam ta sake b'ace mishi, sai yayi amfani da wayarshi ya kirawo saran yace tazo ta same shi a parlon bak'i, a lokacin tana tare dasu maheer a parlon k'asa, jin wayarshi sai mamaki ya lullub'e ta har ta fara tunanin lafiya kuwa, Abeed ne yace, "Mom wani abu yana faruwa ne?". Maganarshi ta janyo hankalin ragowar y'an uwanshi suma suka dawo da hankalin su kacokan gareta, "dad ne yace inje parlon bak'i yanzu, amma muryarshi tana nuna kamar akwai abinda ke faruwa ba dai dai". Duk mik'ewa sukayi ba tare da sun jira taba sukayi parlon bak'i da yake kusa dasu, itama ta maara musu baya. Dukkan su daga bakin k'ofa suka tsaya suna kallon bak'in fuskokin. "Sarah shigo kiga surayyah, surayyah ce ta dawo da y'ay'anta data haifa". Kamar wadda bata tab'a gani ba haka take shigowa cikin parlon sosai tana kallon ta, sai da tazo tsakiyar d'akin surayyahn ta taho gurinta da gudu ta rungume ta, nan ma suka b'arke da kuka........ *BAYAN WASU AWOWI* Surayyah ce da andal, malam, iya, Sarah, sauban da Suraj a zaune cikin parlon sauban d'in suna maida labarin komai da yadda ya faru, sauban ba k'aramin tausayinta yaji ba, a lokacin yake fad'a mata shi ba da gaske yayi wancen furucin ba, a lokacin idon shi ya rufe baya son ta auri bahaushe kwata kwata shi yasa ya mata wannan barazanar, tunda ta bijire mishi kuma jikin shi yayi sanyi ya hak'ura don baisan abinda Allah ya b'oye a auren su ba. Nan fa kowa cikin su ya fara k'ok'arin neman yafiyar juna, aka sasanta a take komai ya huce. Duk yadda suka so tafiya a ranar hana su sauban yayi, dole Suraj ya tafi ya barsu a nan zasu kwana mishi biyu zuwa uku sai su dawo. Raihana taga karramawa da mutumtawa a gurin matar wan auntie, don tayi musu komai da kanta sai nan nan take dasu. Ita tana tare da matan, su khaleefa kuma suna tare da mazan suna k'ok'arin fahimtar juna da k'ulla k'ak'k'arfan zumunci. Sunyi kwana ki uku a gidan wan mahaifiyar tasu kafun su koma gidan late Abdallah tofa, sun tarar anyi gyara mai kyau na b'angaren suraj inda surayyah ta tare, babu wani biki ko bidi'a ta shige d'akinta. A daren ranar aka tattauna da likita andal game da soyayyar Ayman da suhaana, bata b'oye musu komai game da case d'in da akayi da yaron da aka fara musu engage d'an wan mahaifinta ba, da yadda suka dinga zugo shi kar ya barta ta k'arasa karatun in ba haka ba kuma ya fasa, a k'arshe dai sati biyu kafun tahowar su Nigeria komai ya lalace aka rushe maganar auren. Da wannan ta bada hujjar a neme su ita da Ayman yadda suka ce sai aje Sudan gurin dangin mahaifinta a nemo auren. Anyi kamar yadda taso, aka kira Ayman da suhaana suka tabbatar suna son junan su. Sai duk akayi hamdala da tsaida lokacin tafiya neman auren, lokacin zai zo dai dai dana zuwan surayyah gida. Lokacin da raihana ta samu labari ba k'aramin dad'i taji ba, ta taya su murna sosai haka ma khaleefa. Duk yadda khaleefa yaso d'auke kai ba tare da yaji daga raihana ba, kasawa yayi a wannan gab'ar, saboda yana son ji daga gareta a kullum dare da safiyar Allah sai ya saita mata sim card na k'asar. Su yini suna waya, su raba dare suna video call, y'an matan gidan kan zolayeta wani lokacin barin ma suhaana da take ganin asarar data ne kawai sukeyi tunda gasu kusa da juna. ****Amarya surayyah kuwa suraj bai tunkari inda take da kowacce magana ba saida ta kwana biyu a d'akinta, ta samu nutsuwar kintsa komai dai dai da yadda ya kamata ya kasance. A dare na uku ma saida ta gama shirin kwanciya bacci ya nufi sashen nata. Sunyi magana ta kyakkyawar fahimta da maida komai daya faru a wancen shekarun matsayin k'addarar rayuwarsu, abinka da zuciyar dake cike da soyayyah, nan da nan komai ya huce tsohuwar zuma ta motsa. A wannan rana surayyah ta sake tabbatar da soyayyah bata tsufa sai dai ta mutu in lokacin ta yayi, don Suraj ya sake tabbatar mata da hakan. Kwanakin da suka biyo baya duk masu tsada ne a gurin wad'annan mutane da zuciyoyi ma'abota soyayyah, sun tattauna akan aikinta da yadda zatayi dashi, yadda Suraj ya fahimci tana son aikin sai yace a shawarce ko transfer zai nemo mata ne ita da Ayman, k'in amincewa tayi sam, a cewarta tunda saura watanni kad'an tayi retire tana son aje aikin a asibitin, dole ba yadda Suraj ya iya haka ya hak'ura amma bisa kyautata zaton shima rabin rayuwarshi ta koma can. A kusa dasu ya bawa malam da iya kyautar gida mai d'an karen kyau da tsada, da ticket na tafiya saudiyyah umrahr sati hud'u. Hak'ik'a malam yaji dad'i yayi godiya ya nuna farin cikin shi, amma ya nuna sam bazai iya zama garin Abuja ba, da son samu ne ya k'arasa rayuwarshi a Kano. Shiru Suraj yayi a wannan lokacin ya rasa abinda ya kamata yace ma, saida ya dawo gida sukayi shawara da surayyah sai ta bashi shawarar ya nema mishi wani aikin yi a nan garin inba haka ba bazai tab'a zama ba. Da wannan shawarar yayi amfani ya d'anka mishi kula da masallacin gidan, (wato jan qamsussalawati). Da kyar da sid'in goshi wannan karon aka samu ya zauna. ****Kwana ki sunyi ta hucewa har gashi hutun da andal ta d'aukar musu ita da khaleefa a gurin aiki ya k'are, ba don yaso ba zai tafi sai don gudun samun matsala. Auntie kam taso tafiyar nan a yita tare da andal sai dai hakan bai zai yiwu ba, andal ta tabbatar mata koba don aikinta ba, ba zata k'asar a wannan lokacin ba. Dole a k'arshe tafiyar zata zam a rarrabe. Khaleefa da matarshi, sai suhaana da mamanta suka fara yin gaba. Bayan ansha kukan bak'in ciki da takaicin rabuwa da juna a k'arshe dai kowa ya koma bakin aikin shi. A Abuja kuwa sauban da iyalan shi duka suka shirya tafiya sai Suraj da yayan shi, auntie da Ayman daya jingine aikin shi a gefe bama ya son tunowa bare batun komawa, ya kasa ya tsare so yake kawai suhaana ta zama tashi sai ayi wadda za'ayi. Ranar da zasu tafi kamar maraya haka khaleefa ya dinga jin kanshi, sai yanzu yake ganin nisan dake tsakanin Nigeria da Germany. Tafiyar wuri sukayi shiyasa sukayi sallama da kowa tunda wuri, Ayman da Abban su ne sukayi musu rakiya har airport da dingimemiyar kyautar da basu tab'a tsammani ba su duka hud'un. Khaleefa har sukayi nisa yana waigowa ya kalli wajen da yabar mahaifin shi da d'an uwanshi tsaye har ya b'ace musu. Tun a cikin jirgi ya sak'alo hannun raihana cikin nashi, sai kaffa kaffa yake da ita da duk wani motsinta. Suhaana da take kallon su daga ta baya ba k'aramin burgeta suke ba, tana fatan itama ta samu kwatankwacin irin wannan kulawar daga Ayman bayan sunyi aure. (Nikam nace ba tsohon gwauro ba🤣🤣 zaki samu kuwa). Suna sauka a airport suka raba hanya, kowa yayi nasa guri. Lokacin da suka shiga gidan ba k'aramar k'ura suka tarar ta bud'e ko'ina ba, sallolin da suka hucesu kawai suka gabatar ta ajiye mayafinta gefe ta fara aikin gyaran gidan, khaleefa ma zame kayan jikin shi yayi ya rage daga shi sai three quatre da wata riga armless. Tun raihana na jin nauyin shi harta ware suna aikin tare. Basu gama aikin ba sai nisan dare, lokacin gaba d'aya ta gaji ko hannunta da kyar take iya motsawa, ga yunwa tana sakad'ar cikinta. Ga khaleefa ma tuntuni ya bata shawaran da kitchen ta fara gyarawa ta musu girki suka ci don shi yunwa yake ji ta gaske, tak'i amincewa da tsoron in taci abinci jikinta zai mutu ta kasa aiwatar da komai. Tana kwance tana wannan tunanin taji motsin shi ya gama wankan zai futo, da hanzari tayi kitchen ta taya su aikin ta fara duba abinda zata dafa, gashi bata da ko kwallin kayan miya a gidan, albasar data bari ma duk sun bushe. Ruwa kawai ta d'ora taci gaba da dubo sauran abubuwan amfanin, tana aikin khaleefa ya shigo yaja sit ya zauna yana k'ok'arin saita layukan shi na k'asar, yana gamawa ya kira layin Ahmad ya fad'a mishi dawowar su, sun jima suna waya, saida ya warware mishi komai daya faru kafun suyi sallama. Shi ya karb'i girkin zai kula mata dashi yace ita taje tayi wanka. Lokacin data futo har ya gama girkin ya zuba musu a plate, ya zuba mai da Maggi. A nan kitchen d'in suka ci tare da suka gama ta wanke plate d'in da sauran kayan, khaleefa nata mata fad'an ita wai bata gajiya da aiki ne? Murmushi kawai tayi ta k'arasa kammale komai a muhallin shi suka fuce. D'akinta taso sillewa wai zata had'a littattafanta, khaleefa komai baice mata ba ya d'aga ta cak ya nufi nashi d'akin shi da ita yana mitar ita bata gajiya ne da aiki, koda ya sauke ta akan gado addu'ar bacci ya karanto mata yaja musu duvet ya rungume ta sai bacci........ Komai yaci gaba da tafiyar musu dai dai, tuni ya koma aikin shi ita kuma ta koma makarantar ta, Yasmine da Ahmad sunzo musu tun washe garin dawowar su, inda suka sake nuna farin cikin su da abinda ya faru sosai. Ta b'angaren soyayyarsu kuwa sai abinda yaci gaba, sosai khaleefa ya sabarwa raihana nau'in wata rayuwa..... Ya kulleta cikin duniyar da su biyu kad'ai ke rayuwa suna ganin junan su, khaleefa bai maida raihana cikakkiyar matar shiba sai data gama sakin jiki dashi sosai...... Komai ya tafi musu gentle and romantic cikin tausayawa da nuna kulawa da tattali, ta samu karb'ar dalleliyar kyauta daga khaleefa na samunta matsayin macen data killace kanta daga dukkan shirme da sakarci, ta mallaka mishi abu mafi tsada daga gurin kowacce mace budurwa, abun alfahari da tink'aho a gurin macen da tasan ciwon kanta ba ballagaza data gama bawa samarin banza a titi ba💁‍♀️😒. (Hak'ik'a da ina da wadataccen lokaci dana zayyane muku irin y'ar asalin kulawa da tattalin da raihana ta samu daga khaleefa). *Sudan* Matafiya sun isa lafiya, familyn surayyah ba k'aramin murna da jin dad'in ganinta sukayi ba, itama kuma ta nuna musu asalin yadda tayi kewar su, haka y'an uwa na nesa dana kusa suka dinga tururuwar zuwa suna gaisheta satin farko da tayi a garin. Ayman daya k'agu yaga anyi maganar auren shi da suhaana amma yaga shiru, kasa jurewa yayi har ta kai damuwarshi ta futo sarari auntie na gani daga yanayin shi koda baiyi magana ba. Hakan yasa cikin sati na biyu Abban su ya shirya da yayan shi da dama saboda maganar ya biyo shi zasu je gurin dangin mahaifinta. Da farko sunso su nuna kin amincewar su saboda wancen yaron ba wai ya hak'ura bane, amma daga baya da y'an uwan andal d'in suka ji labari suka shiga abun sai komai ya tafi dai dai aka tsaida magana kan zasu zo a saka rana nan da kwana ki biyu masu zuwa da ikon Allah. Lokacin da auntie ta labartawa Ayman yadda akayi, tsoro ne ya kama shi, hakan yasa ya tubure kan lallai shi sai dai a d'aura auren in yaso ta gama karatun sai ayi biki, cox yana tsoron ya rasa ta yadda ya rasa wadda ya fara so a duniya. Da farko Auntie ba tayi na'am da rikicin Ayman d'in ba, sai dai daga baya k'anwar mamarta ta goyi da bayan hakan don inba haka aka yiba sai dai suji anayi bada suba. Koda ta tuntub'i andal da zancen cewa tayi hakan shine dai dai don ba k'ananun y'an iska bane wad'annan mutane. haka kuwa akayi a ranar da za'a je batun saka rana aka k'are da d'aura aure. Auren daya jawo takaddama da rashin amincewar da yawa cikin familyn mahaifin suhaana da k'asa ta rufewa ido. Sati d'aya suka k'ara daga nan suka tattaro suka dawo Nigeria. Sun sake hutawa kad'an kafun su fara Shirin komawa Kano saboda aikin Ayman da kuma na auntien. Don dai Suraj ba yadda ya iya da ita ne a wannan gab'ar amma da bazai tab'a amincewa taje wani guri da nisa ba, toh amma alfarmar y'an watanni ne zaiyi mata, da zarar tayi retire ba zai sake yarda ta zauna a garin ba, Ayman ma ya gama shirin shi tuni akan su, bata yadda za'ayi ya bar familyn su kowa da duniyar da yake. Ta tafi bisa rakiyar sauban da matarshi, sai Suraj da zai zauna tare da ita na sati biyu ya huce wata k'asa..... Lokacin data dawo mutane da yawa sun shiga mamaki da dunbin al'ajabinta, masu mata kallon y'ar iska, da masu sheganta mata y'ay'a duka sun Raina kansu, hakan yasa da yawan su neman yafiyarta ciki hadda sameera data matuk'ar sake kama kanta, a nan ta sake tabbatar da surayyah tun asali ba ajinta bace, ba kuma tsarar k'awancen ta bace, ita d'in y'ar asali da gata ce gaba da baya, ta yarda abu d'aya ya had'a su shine k'addarar data raba ta da gida. Duka wannan abun da yake surayyah mai kallon kowa da tsarkakakken zuciya ce bata sauya mata daga waccen matar ma'abociyar fara'a da son taimako ba, abu d'aya da ba zata iya ba shine sake aminta da ita ko bata damar shiga jikinta kamar da. Suraj bai barta ta zauna a anguwar nan ba duk yadda take so kuwa, ya d'auke gaba d'aya ya maida ita d'aya cikin gidajen shi dake GRA. *Germany* Rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin tsari irin wanda khaleefa yake so da tsantsar soyayyah mara algus. Hak'ik'a khaleefa yayi nadama, yayi nadama irin wadda bazai tab'a dainawa ba har k'arshen numfashin shi. Da ace yana da damar da zai dawo da hannun agogo baya, daya dad'e da shafi tarihin soyayyar shi da Saleema a doron duniya. _wannan kenan_ Suhaana ta kammala had'a degree d'inta, alhmdllh za'a ce donta futo da result irin wanda ake so. A dai dai wannan lokacin mamarta ta d'auki hutu a gurin aiki suka tattara sukayi gida Sudan don gudanar da shagalin biki irin na al'ada. Sunyi bikin su lafiyar Allah duk da raihana da khaleefa basu samu damar zuwa ba saboda dalilai masu nauyi da suka rik'e su. Khaleefa ya tura mishi kud'i masu yawa matsayin gudunmawar su shida raihana....... Alhamdulillah Yasmine ta haihu lafiya inda ta samu baby girl mai kama da ita da uban gaba ma. Bayan ansha rigima da rikici gurin yasmine akan lallai saita tafi gida tun cikin yana wata bakwai, a nufinta saita haihu gaban mamanta, shi kuma ya hana ta saboda wani family issue nasu can daya shafe su, a k'arshe dai sai k'anwar maman tace tazo da cikin ya shiga wata tara tana kula da ita har akayi haihuwar. Raihana kam ba k'aramin santin babyn tayi ba kamar ta gudu da ita lokacin data ganta, haka ta rik'e y'a gam gam tak'i ba kowa, ganin yadda take son yarinyar sai k'anwar maman yasmine da take tare da ita tace, "na fahimci dai kuna son yaara keda mijin ki, haka shima yayita santin yarinyar nan da yazo jiya, kuma ai bada jimawa ba zaku samu naku tunda naga bake d'aya bace.....". Murmushi tayi ta d'ora hannunta a bakinta tana kallon yasmine, "kinji abinda aunty hafsa tace kuwa?". Murmushi auntie hapsa tayi tana barin gurin. Yasmine tace, "naji nima dai kuma kusan kallon hakan nake miki tun kwana ki, yanayin da nake ciki ne yasa ban tab'a miki maganar ba". "Au kema hakan zaki ce? Nifa Allah bani da komai kece tunanin ki yake baki hakan?". "Humm wai kuwa anya kina kallon kanki a mirrow raihana? Gaba d'aya kin canja ga k'iba da kikayi kin zama big mama wallahi". Harararta tayi sai kuma ta fara tunanin maganar yasmine d'in a zuciyarta, ita kanta tana jin sauyi a jikinta kad'an kad'an, sai dai abinda yasa tunaninta bai tab'a bata ciki bane saboda taga bata amaye amaye da irin laulayin da yasmine tasha. Dariya yasmine tayi ganin ta tafi tunani sai tace, "gwara dai ki fara lissafi kada kiji haihuwa rana tsaka tunda Allah ya sauk'ak'k'a miki ba irin cikin mu bane". Murmushi kawai tayi tace, "humm ba zaki gane ba yasmine nasan fa yadda masu ciki suke shan wahala ke kanki dubi yadda kika koma". "Toh ai abinda nake so ki fahimta kowa da yadda abun yake zo mishi musamman haihuwar farko, amma a shawarce kije kiga likita, koda yake ke kanki zaki iya duba kanki tunda kinsan aikin.....". Raihana ta gyad'a mata kai cikin amincewa da batun yasmine d'in. Sun jima suna hira amma abun a ranta har ta dawo gida...... Har dare tana ta tunanin ta yadda zata tunkari khaleefa da zancen, sai tayi kamar ta fad'a mishi saita share, gashi shi sai tambayarta yake da son sanin damuwarta don wata sabuwar kulawa yake bata ta musamman, ga yawan fara'a a duk lokacin daya kalleta in taga dai dai har ajiyar zuciya yake saukewa wasu lokutan. Da dare suna kwance tana ta mishi santin babyn su Ahmad yana sauraronta, tun yana taya ta har ya gaji da jin magana d'aya ya sake shigar da ita jikin shi ya d'ora hannunta a saitin cikinta, "Ina tunanin kema fa soon zaki samu naki babyn?". Zaro ido tayi ta mik'e zaune tana kallon shi hadda k'ara haske a d'akin, "kar dai kaima abinda kake tunani kenan?". Sai ya mik'e zaune da kyau yana kallonta, "tunanin me?". Sake waro ido tayi, "tunanin wai ciki ne dani". Murmushi yayi har hak'oran bakin shi na bayyana yace, "waye ya fad'a miki haka?". Shiru tayi cike da jin nauyin maganar data mishi, sai kuma ta rufe fuskarta da tafin hannunta. Sake jawota yayi jikin shi ya fara jera mata tambayoyi, "kina jin ba dad'i a jikin ki? Ko tashin zuciya da son wani abu ko rashin son wani abu?". Duka ya jera mata tambayoyin a jere. Girgiza mishi kai tayi, "Ni bana jin komai fa saboda bani da komai". Wani murmushin ya sake yi, "Nima naga alamar hakan, bazan ce miki bakya d'auke da ajiyar babyna ba, iya gaskiyar dana sani ta wadatar cox ni bana son duk abinda zaki wahala nuru qalby Abdallah". Saroro tayi tana k'ok'arin ajiye kowacce magana tashi a muhallinta, da yaga tana neman yima maganganun shi fashin bak'i sai ya maida wasan na manya, ya kuma shafe mata kowanne tunani da kwokwanto a ranta sai nashi. Ranan suna yarinya taci sunan nafeesa mahaifiyar Ahmad. Y'an uwan su da yawa sunzo taya murna, haka y'an uwan Yasmine ma. Raihana dai tana gidanta ranar tun safe ta kasa d'arawa ko nan da can, Cox ita ba wani son shiga hayaniyar mutane take sosai ba, bata futo ba har saida nadeeya matar Muhammad ta shigo mata, sun gaisa ta mata barka daga nan kuma suka shiga gidan yasmine d'in tare. Ta samu yasmine da y'arta sunyi kyau Masha Allah, bayan ta gama sauraron mita da kumbure kumburen yasmine wai tayi fushi, har tayi ta gama ta hak'ura suka shiga hirar su kuma su ukun har nadeeya. Suna tare har mazan suka taso office, yanzun ma kusan tare suka futo da nadeeya, daga inda ta samu Muhammad a waje sukayi sallama, raihana kuma ta bud'e musu gida suka shiga har Ahmad daya k'auracema gidan shi sai dare yake lallab'awa ya shige ya kwanta cikin kwanakin. Ruwa ta kawo musu da abinci duk da basu ce mata suna jin yunwa ba, ta juya zata tafi taji an tab'a door bell, ta tafi don duba ko waye tunda jikinta har lokacin a suturce yake da gyale..... Ja baya tayi tana kallon fuskokin y'an matan biyu gabanta yana tsananta fad'uwa, a cikin su fuskar da ba zata tab'a mantawa a rayuwar taba ta gane, macen data tab'a samun matsala da ita tunda uwarta ta haifo ta duniya...... Saaleema _Comment and share✍️_ 24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA🧕* (Romantic luv storie) _(Under the pens of merhreeyaert lerwerl and doctor ferhyeez m usmern as in-identical twins)_ _Storie and written by_ *Merhreeyaert lerwerl* Page eighty 8️⃣0️⃣ Final💃💃💃 Ja da baya raihana tayi ganin bak'in ba nata bane tace, "sannun ku" da kyar bayan ta danni zuciyarta, amna ce kad'ai ta iya amsata don Saleema kam kasa bud'e baki tayi sai zubawa raihana ido kawai tana kallonta, gabanta yana tsananta fad'uwa. Lokacin da suka gama shigowa cikin parlon raihana juyawa tayi zata shige d'akinta ta basu guri, yayinda a lokaci guda Amna ta kalli Ahmad dashi kanshi khaleefan da suke jifan su da kallon da me kuka zo? "Kuyi.....hak'uri..... munzo magana da kai khaleefa". Amna ta fad'a tana yin k'asa da kanta. Sai a lokacin khaleefa ya ankara da raihana da take k'ok'arin guduwa ya kira sunanta, bata iya amsawa ba, ta dai juyo ta kalle shi. Ya taso tsam daga inda yake yazo har inda take tsaye ya rik'o hannunta, ta narke mishi tana girgiza kai a lokaci guda ta bud'e baki don tayi mishi bayanin da zai fahimta, ya d'ora hannun shi saman lips d'inta yace, "shhh!". Da sauri ta had'iye ragowar maganarta tana kallon shi, har lokacin hannun shi yana kan lips d'inta, madadin ma ya d'auke hannun sai ya fara kewaya leb'en da babbar d'an yatsar shi. Kusan a tare mutum biyu suka lumshe ido, Saleema da raihana, saleema kam a lokacin wasu muguyen harsasai ne suka soki zuciyarta suka raunana ta, a take idonta ya ciko da ruwan hawaye. Shi kuwa murmushi yayi mai kyau, ya hura mata iska saman idonta, da murya mara amo yake fad'in, "kinsan me yasa nake k'ara sonki?". Ta bud'e idonta kad'an tana kallon shi ta girgiza kanta, ya sake matsa hannunta dake cikin nashi da salon soyayyah na musamman ya k'arasa cewa, "saboda ta ko'ina kinsan abinda kike yi a rayuwa, kina da sanin ya kamata irin wanda ba kowanne mutum keda shiba a wannan zamanin, sai dai a wannan gab'ar bazan iya sauraron wad'an can mutanen inba da alfarmar kiba kuma a gaban ki, tafiyarki tana nufin kowa cikin su ya kama gaban shi don bazan gansu ba". D'aya hannun ta d'ora saman nashi ta kalli wajen da suke tsaye suna iya hango su tace, "let's go". Kusan a tare suka tako har lokacin hannun su sark'afe cikin na juna. Daga d'an nesa dasu kad'an ya tsaya yayi magana da dakakkiyar murya, "me ya kawo ku". Saleema da jikinta ya gama yin sanyi ta fara magana da rawar murya, ya juya mata baya da sauri, ta durk'usa ita kuma ta fara neman yafiyar shi, yayi saurin d'aga mata hannu ba tare daya juyo ya kalleta ba yace, "Amna ki fad'awa k'awar ki komai ya faru ya k'are tsakanin mu, ita ya kamata ta yafe mun don ni na dad'e da yafe mata, nine nake neman azurfa sai kuma na samu zinare, kina ganin zanci gaba da yak'i?". Ba Saleema ba hatta Amna saida maganar ta dake ta, a sanyaye ta girgiza mishi kai ta kamo hannun Saleema da tuni ta fara kuka durk'ushe cikin d'akin sukayi waje. Raihana ta sauke ajiyar zuciya tabi bayan su da kallo cike da tausayawa. Saleema kuwa bayan ta futa kuka sosai ta dingayi, Amna bata hana taba har saida ta tabbatar ta samu sassauci a zuciyarta, ta matso kusa da ita ta dafa kafad'arta zata fara magana tayi saurin d'aga mata hannu, "ba sai kin jaddada mun abinda na kusa haddacewa a kwakwalwar kaina saboda yawan ji daga gare kiba, Amna a yau na k'ara tabbatar da irin nisan da khaleefa ya mun, kina kallo Amna saboda k'iyayyah khaleefa ko iya kallon fuskana ba yayi,,,,,, Amna ina zan had'u da ra'ees? Da gaske har yanzu ra'ees yana sona kamar yadda kike fad'a? Indai yana sona ki taimaka ki fad'a mun inda zan same shi domin shine cikakken masoyina, da bai tab'a kyamata a kowanne irin yanayi na rayuwa ba". "Alhamdulillah!! Nagode Allah da kika fahimci gaskiya har zaki fuskanceta, k'awata kamar yadda kika sani ra'ees yana nan da soyayyarki, bari in warware miki asalin gaskiyar da kika k'i tun farkon had'uwar ki da khaleefa, Saleema khaleefa bai zo da niyyar yaudarar kiba, hakazalika bai tab'a mafarkin rabuwa dake ba, kece kika damawa kanki lissafi, shiyasa na zab'i in tona miki asiri a farkon fara soyayyarki da taufeeq, domin yaron yana da matuk'ar had'ari, gashi duk hanyar da nabi don ganin na kawo miki gyara kin k'i yarda, shine dalilin da yasa na kai khaleefa garden waccen ranar, don already tun a lokacin ni nasan yayi aure, nazo miki da labarin farkon dawowarshi k'asar nan kika k'i saurarona, shiyasa a waccen lokacin daya ganki kina kissing taufeeq ya yanke hukuncin rabuwa dake, Saleema da ace kin yi dogon nazari kafun rabuwarki da khaleefa a ranar daya fara baki tarihin shi, da yanzu kece matar da yake aure ba waccen yarinyar ba, but alhamdulillah ta silar ki gashi yanzu ya nemo mahaifin shi, kowa ya fahimci su d'in halastattun yara ne da aka Haifa ta hanya mai kyau, and su sun futo daga babban family a Nigeria". Sosai Saleema take kuka tana fad'in, "nayi nadama Amna, tabbas nasan ke d'in mai k'aunata ce, sannan kin kasance k'awa ta gari mai neman kawo gyara a rayuwata, tabbas hak'k'in ra'ees ne ya toshe mun kwakwalwa, ya kuma hana in samu khaleefa, don nayi butulci gare shi mummuna, ya rasa komai nashi saboda ni, ya dinga wahaltamun a k'asar da bani da uwa bare uba, Amna ki gaggauta kaini gurin shi don Allah ko yafiyar shi na nema.....". Amna ta rik'o k'afad'unta tana k'arasa taya ta share hawayen fuskarta...... Fews months later Abubuwa da yawa sun faru cikin watannin, ciki hardaa haihuwar raihana inda ta samu twins mace da namiji, bayan tasha tsananin wahala gurin haihuwa, da yake cikin familyn su ba wanda yasan cikin ya tsufa, da yawa dai sun d'ago kamar tana da ciki amma basu tabbatar ba sai labarin haihuwar kowa yaji. Aikuwa Auntie tace maza ya nemi ticket subi flight su taho gida a gyara yarinyar mutane inba so yake ranshi ya b'aci ba, ta dinga fad'a kamar zata ari baki don da gaske bai kyauta abinda yayi mata ba, don tace haihuwar fari saida bik'i da kula da gyara. Da yake har lokacin raihana tana asibitin a can ake kula da ita da babyn don ba k'aramin wahala tasha ba, duk can su yasmine da sauran abokan khaleefa suka je ganin yaran suka mata sannu. Tsabar yadda khaleefa ke tausayinta ko futa baya yi yana tare da ita a kowanne motsinta ya dinga jera mata sannu ba iyaka. Cikin satin yayi ciku ciku ya nema musu ticket suka taho Nigeria. Ya tambayeta inda zai kaita, tace ya fara kaita gurin Auntie, ta mishi alkunya ne kawai amma zuciyarta tana gurin ummienta, koda suka sauka a Abuja sukayi waya da ummie take fad'a mata zasu k'araso Kano nan da kwana ki biyu, sai tasa ta had'a ta da surayyahn ta waya sukayi magana, ta nuna mata itama uwace a gurin raihana kamar ita, duk abinda zata yiwa raihana ta riga tayi shi, don haka ta k'arasa zaman wankan jegon kurum a gurinta. Duk yadda auntie taso fahimtar da ita k'in sauraronta tayi don ita harga Allah bata ga abinda za'a kawo raihana ta mata wanda surayyan bata yiba. Anyi taron suna lafiya, taron daya tara manyan mutane da dangi na nesa dana kusa, yayyen ummie da hajiya inna ma duk sunzo. Yara suka ci sunan Abba da Auntie bisa shawara da amincewar miji da matar, saboda alkunya sai ake kiran namijin abie macen kuma anam, da yake raihana ba mai son hayaniya bace ranar sunan ma sashen momma ta gudu ta b'oye kanta sai tsiratun mutane suka san inda take. Kulawa mai kyau auntie take bawa mai jego da yaranta cikin zallar soyayyah da k'auna. Dama khaleefa kwana shida yayi a garin ya koma bakin aiki..... Amma kullum dare sai yayi video call da matarshi yaga yaran shi yadda suke k'ara murjewa da wani sihirtaccen kyau. Gaba d'aya sai ya k'agu ta dawo cox gidan duk sai ya mishi faad'i, tunda sukayi aure basu tab'a rabuwa da juna ba sai yau, koda zasu rayu ba'a tare ba amma still suna a muhalli guda. Gashi ta b'angaren girki ya kasa jurar cin abincin gidajen cin abinci kamar yadda ya saba lokacin yana matashi, ta ko'ina raihana tayi karan tsaye wa rayuwarshi baya ganin iyawar kowa inba tata ba, k'arshe dai sai noodles ya dinga ci da shayi da burger. Watanni uku sun shud'e amma auntie bata da niyyar dawo mishi da matarshi, hakan yasa ya d'auki hutu na sati d'aya a gurin doctor raazi don andal tuni tayi retire yanzu haka tana sudan cikin y'an uwanta. Washe gari kuwa yabi flight sai Nigeria. A lokacin daya sauka raihana tana zaune cikin parlon auntie, sanye da wata doguwar riga ta material mara nauyi, gashinta nad'e a k'eyarta yaci gyara sai d'aukar ido yake da fudda sirrin k'amshi mai dad'i. Kanta a durk'ushe tana ta kiciniyar had'awa anam da take ta tsala ihu madara, gaba d'aya duk ta rikice sai b'arar da madarar da ruwan take har ta samu ta gama ta d'ago yarinyar ta rungumeta tana feeding d'inta. Khaleefa da yake daga bakin k'ofar shiga parlon yayi murmushi ya k'arasa karb'ar jakar kayan shi daga hannun d'aya cikin yaran security daya mishi rakiya har gurin. Sam raihana bata ji takun shiba sai saukar hannun shi kawai kan gwiwar k'afarta, ta d'ago idonta tana kallon shi, har razana tayi zata ja baya sai kuma yayi saurin rik'o ta, "calm down mana kada kisa anam ta kware, dama naga ojoro ake ganin bana kusa, yaushe mukayi dake za'a dinga basu Madara?". Sosai ta shagwob'e fuskarta kamar zata mishi kuka tana kallon shi har lokacin, "Allah ba zaka gane ba amma dole saida madarar". Baice mata komai ba ya mik'e daga gabanta ya zauna gefenta yana duban agogon wayarshi. Sai a lokacin ta russuna tana gaishe shi, yak'i amsata saima laluben wayarshi daya fara, a zuciyarta tace mai hali ai baya fasa halin shi. Saida ta gama da yarinyar ta juya zata ajiye ta ya kamo hannuwanta ya zare yarinyar a ciki ya sumbaci forehead d'inta. Fridge ta nufa ta d'auko mishi drinks cikin taku na zallar aji da k'asaita, khaleefa yabi bayanta da wani jirkitaccen kallo har ta dawo gaban shi ta ajiye plate d'in, ya sauke ajiyar zuciya k'asa k'asa. Sake komawa tayi ta d'auko mishi dambun nama da kayan snacks, tazo ta ajiye zata sake komawa ya ajiye anam ya jawota jikin shi gaba d'aya ya rungume, cikin whisper yake tambayarta, "Wai abincin gidan gaba d'aya zaki kawo mun?". Ta girgiza mishi kai tana son zillewa tace, "a'ah...ai snacks ne wannan..abinci zan kawo maka?". "Nace miki Ina jin yunwa? Ko kina tunanin kayan snacks ya kawo ni". K'asa tayi da idonta tace, "baka fad'a ba kam amma nasan kasha hanya, and kome kaci zuwa yanzu ya zazzage". Ya sake matse ta cikin jikin shi yana k'ara kallon fuskarta yace, "it seems like bakiyi farin ciki da ganina ba ko?". Tayi murmushi mara sauti da shagwob'abben murya tace, "nayi farin ciki mana". "Toh aini ban gani a yanayin ki ko fuskar kiba, sannan ko kewata bakiyi gashi nan kin sake fresh hankalinki kwance sai walwali kike kamar diamond". Ta kai mishi dukan wasa a k'irji tana fad'in, "Allah kaima baka kewana gashi nan kaima kayi fresh". Yabi hannun da kiss yana sake jifanta da kallon zallar so da k'auna, "da banyi kewar kiba bazan datse aikina na taho ganin ki keda babies d'ina bayan ina da tarin abubuwan yi a office ba, kema kin sani". Shiru ta mishi tana k'ok'arin zamewa a jikin shi, "Na d'auka zan tarar kuna shirin komawa fa". Ya fad'a yana d'aukar glass cup. Sai a lokacin tayi nasarar zamewa daga jikin shi tace, "Ina kuma?". Tayi tambayar tana k'ok'arin zuba mishi ruwa a cikin cupin daya rik'e a hannun shi, Cup d'in ya sake mata ya mata alamar ta bashi, saita langwab'ar da kai tace, "Allah wani cikin Auntie ko mama zasu iya shigowa fa". Had'e rai yayi a take yana kallonta ba wasa yace, "kika sake yimun maganar wani Allah zaki tunzurani nayi abinda banyi niyyah ba, ke bakisan dama na fara d'aukar zafi daku ba, duk wankan haihuwar duniya baya huce kwana arba'in amma ni har ana neman huce watanni uku baki da niyyar dawowa, and nazo kuma kina kawo mun shirmen wani wai zai ganmu, you better start your job from here don na daina zama kaman gwauro tunda kina kusa". Shiru tayi kamar wadda ruwa ya cinye har ya gama maseefar yayi shiru, sai bata sake musu ba ta shiga bashi ruwan a cup, tsabar neman dalili kamar me shan tafasashshen tea haka ya dinga sipping. Haka duk ta dinga bashi komai a baki har dambun naman, yana ci in romantic way gently har ya gama, tasa tissue ta goge mishi baki. Mama haleema da tazo bakin k'ofa ba jimawa ta juya zata bar gurin tana murmushi. Tana fara takawa taci karo da auntie, "a'a ya kika fasa shiga kuma ko bata parlon?". Mama haleema tace, "a'a tana ciki naga ba ita kad'ai bane". "Ita da waye kuma?". Ta tambayeta da mamaki. "Bak'o daga nesa". Auntie tana kallonta still tace, "khaleefa ne ya biyo bayan matarshi kenan". "Eh ai yama yi k'ok'ari wata hud'u ake shirin tafiya fa". "Toh bashi ake yiwa gata ba, wannan yaran inta tafi gida daga ita sai shi waye zai taimaka mata dasu, yama gama zaman shi ya tafi don raihana sai tayi wata biyar zata koma shima saboda karatunta ne". Mama haleema tana dariya k'asa k'asa tace, "don mugunta! kyasan yadda zakiyi da rigimar shi ai dama kun saba". Itama auntien dariya tayi tace, "yi musu knocking ina son shiga cikin bedroom na d'auko ma yaron nan magani". Mama haleema ta koma da baya ta kwad'a sallama tun kafun ta k'arasa. Raihana ta sauya direction da sauri tana amsawa, khaleefa ya d'an harareta kad'an, ta d'ora hannunta a baki tana mishi dariya k'asa k'asa. Kusan a tare suka shigo ita da auntien, khaleefa ya russuna yana gaishe su, mama haleema ta amsa shi faram faram har tana zolayarshi, auntie kam sama sama ta amsa don kada ma yaga fuska yazo da wargi😎 Bai wuni a gidan ba yayi fucewarshi gidan twin d'inshi suka sha hirar su ta zumunci da suka jima basu yiba. Da dare ya dawo ya samu auntie tasa an shirya mishi masauki a can nesa da sashen da suke. Bai zauna ba nan ma tafiyarshi gurin Abba sukayi hirar su mai dad'i ta uba da d'a. ****A hankali kwanaki suka dinga shud'ewa, duk wata hanya da zaiga raihana ko su had'u zuwa yanzu ta toshe ta, tun yana zura ido yaga iya gudun ruwan su har ya fahimci ruwan ba mai k'arewa bane gashi yau kwana biyu ya rage komawarshi don baison ya samu matsala gurin aiki. Hakan ya sashi fuskantar auntie a daren yake fad'a mata da kud'urin da yazo, Saida ta gama sauraron shi tass sannan ta nuna k'in amincewarta. A lokacin rasa inda zai saka ranshi yayi, gashi ya gama shirin komawa da ita amma ya fahimci auntie tana son mishi shinge da hakan. Sai ya mik'e yana tambayarta inda raihanan take wai zasuyi magana, daga inda take ta kirawota tazo tace ya fad'i abinda yake son fad'a matan a gabanta. Ya sosa k'eya ba tare da yace komai ba ya futa a parlon. Ba d'an k'aramin rikici ya musu a gidan ba sauran ranakun da suka biyo baya, kowa ya bashi hak'uri sai yace shifa saboda yunwa tana neman kama shi bazai koma ba saida matarshi, (ku kujifa sai kace kaf garin ba abinci sai k'asa🤣). Da anyi magana ya kafa hujja da yunwa kamar itace abincin. Dole Abban su ya shiga rigimar tasu wannan karon, shi ya tausasa Auntie ta hak'ura zata bashi matarshi su tafi amma tace bisa sharad'i. Tun baiji sharad'in ba yace ya amince. Shima dai Suraj saida yayi dariya don ya gane rigima ce zalla irinta surayyah zata rik'e matar mutane ta maida mai aure gwauro. Sharad'inta shine raihana zata je gurin familynta na Kano ta kwana musu biyu, sannan tare zasu tafi da mama haleema ta taya ta rainon. Khaleefa ya sauƙe ajiyar zuciya don ya d'auka sharad'in yafi haka sai yaga abun duk irin wanda za'a iya jurewa ne, mama haleema kam ma dai su za'a yiwa gata. Haka kuwa akayi raihana ta ziyarci Kano na kwana biyu sannan ta dawo aka fara shirin komawarta, wani sabon gyara auntie ta kaita akayi mata in an out. Ranar da zasu tafi kuwa mutane da yawa suka musu rakiya suka tafi Suka barsu cike da kewar twins. Sosai aka bud'e sabon shafin soyayyah da nuna kulawa tsakanin raihana da khaleefa, har saceta yayi suka gudu saboda kunyar idon mama haleema, duk da tana basu rata sosai. Sai a lokacin khaleefa yaga yadda suke kwanan zaune da anam idan ta dira kuka tsakiyar dare, haka raihana za tayi ta jijjigata ko ita ko mama haleema, shima wasu lokutan har karb'ar ta yake ya taya su. A rayuwar khaleefa ya tsani kuka sai gashi Allah ya jarrabesu da yarinya mai kuka...... Har Saida suka k'ara watanni sannan ta fara daina kukan dare. A lokacin tuni khaleefa ya tubure halin raihana tayi da gani haka ta azabtar da ummie da kuka, ita da mama haleema dai sukan yi dariya idan suka ji ya fad'a haka.... A haka raihana take managing tana zuwa makaranta tana kula da yaranta da mijinta, sosai ta zama busy ta ko'ina ba sauk'i saida ta zage dantse ta zama jaruma. *Nigeria* B'angaren Imran da shaheeda kuwa, haka shaheeda ta dinga k'untatawa hajiya tafeeda ba tare da Imran ko sauran mutanen gidan su sun sani ba, zatayi abu amma inka kalli fuskarta saika rantse da Allah bata aikata ba. Tun hajiya tafeeda na juye abun kan d'anta har ta gaji ta fara dawo da laifi kan mai aikata shi, zuwa lokacin mamy har bata son had'uwa da k'awartata cox kullum sai tayi complain akan saleema, harta fara gajiya daji ma, tun tana yiwa yarinyar fad'a harta gaji ta daina tana ganin kawai hajiya tafeeda bata da hak'uri ne. Lokacin da Shaheeda ta fara laulayin ciki mai wahala sai abun ya sake k'ara yin gaba, gashi wata irin soyayyah ta shiga tsakanin Imran da shaheeda, saboda shak'uwa da kusancin da suke k'ara samu a kullum safiyar Allah. Lokacin da cikin shaheeda ya isa haihuwa sai rigima mai k'arfi ta b'arke tsakanin su har ta kai hajiya tafeeda ta kore ta a gidan Imran zuwa gidan su gurin mamanta, ita kuma sameera hakan daya faru yasa ta lashi takobin y'arta tabar auren Imran har abada don tunda akayi auren basu zauna lafiya ba, daga wannan sai wancan sanadiyyar rigimar ko magana yanzu basa yi da tafeedan. Haka Imran ya dawo daga Lagos ya tarar da wannan rikici hadda cewa saiya saki shaheeda. Sosai rigima ta dinga kai kawo har a k'arshe mahaifin Imran ya shiga ita ya yanke nata igiyar auren, yace kuma muddin ta sake magana akan saki to ranta sai yayi mummunar b'aci. Haka ta koma gida jiki a sanyaye a shekarun da ta huce zaman gida. Har shaheeda ta haihu ana d'auki ba dad'i duk da zuwa lokacin hajiya tafeeda tayi kwatakyes, itama shaheeda jin har an saketa sai jikinta yayi sanyi, ta fad'awa Mamie asalin laifinta da musabbabin shi, ranta ya b'aci kuwa ta balbaleta da masifa, ta tusa ta a gaba kuma har gidan su tafeeda ta bata hak'uri, ta bawa dad ma hak'uri ya maida hajiya tafeedan d'akinta. Daga nan sai aka zauna lafiya bayan an raba musu gida da ita don wani kusancin shi yake kawo matsala, sannan halin sune baizo d'aya ba shi yasa indai zasu ci gaba da zama kusa da juna sai an samu matsala....... _Wannan kenan_ *Bayan wasu shekaru* Abubuwa da yawa sun faru cikin shekarun nan na dad'i da akasin su, khaleefa ya gama aiki da asibitin da suka zauna tuni har ya dawo gida Nigeria inda mahaifin shi ya gina mishi babban private hospital nashi na kanshi suna kula dashi shida Ahmad. Yasmine ta k'ara haihuwar yara biyu don haihuwa bata d'aga mata k'afa ba, raihana kuma ta k'ara haihuwar y'arta mace, itama ta gama karatun ta har ta karb'i result, sai dai bata fara aiki ba, batasan ma ko gogan zai barta aikin ba ko a'a. Komai yana tafi musu cikin nasara, watarana zuma watarana mad'aci, dama hakà rayuwar duniya ta gada...... Abba ya basu wani babban gida suna zaune shida Ayman komai iri d'aya. Suhaana ma ta haifi d'anta namiji sai kuma ta tsaya planning don tana tsoron haihuwa tunda tayi sau d'aya taji. Tammat bihamdullah! Da wannan na kawo k'arshen littafin JARUMAR UWA, abinda mukayi na dai dai Allah ya bamu lada, abinda mukayi na kuskure kuma Allah ya gafarta mana albarkacin wata mai alfarma da muke tunkara. Wanda muka b'atawa cikin ajizanci irin na d'an Adam Allah ya huci zuciyarshi. A madadina da twin sieterna doctor ferhyeezerh ina taya d'aukacin y'an uwa musulmi na duniya murnar zuwan wata mai alfarma da albarka watan ramadhan, Ina fatan Allah ya bamu ikon yin ibada lafiya ya karb'i inadun mu, ya samu cikin y'antattun bayi. *RAMADHAN KAREEM* Mie wattsapp no👇 08134288477 Merhreeyaertou✍🏻