WACE CE UWA? Hadarin daya taso shiya sanya yarinyar kara sauri. Tana hanzarin ta karasa gidansu kafin ruwa ya sauko. Yara ne 'yan makaranta, kuma daga dukkan alamu daga makarantar aka taso su. 'yan matan sanye suke da kayan makaranta na shudiyar Riga iya gwiwa da kuma wando har kasa, sai farin hijabin daya tsaya iya gwiwarsu. Mazan kuwa Riga ce da wando kala daya Dana 'yan matan sai kuma farar hula a kawunansu. Gungu gungu suke kowa da 'yan group dinsa. Daga gani 'yan makaranta ne tasowar su kenan daga islamiyyar dake kan babban titin unguwar. Wasu sun tsaya suna tattaunawa, wasu suna 'yan kokaye kokayen su na yara. Ita kuwa sai qara sauri take yi. Sauran yaran da suke tare da ita suka dan kwana mata kira ganin tayi musu nisa " sadiya saurin me kike yine"? Inji daya daga cikin su. Ta amsa " sauri nake kar ruwa ya jika min itacen dazan dora abincin dare". Dukkan su suka kwashe mata da dariya "Au ashe fa umma mai tuwo ce sai kikara sauri sai munzo cin dumame inji wata daga cikinsu". Murmushi kawai tayi musu domin ta dade da sabawa da wannan tsokanar tasu. Sai kuma akayi dace ta kasance yarinya mara fushi. Kusan duk abinda akayi mata da kyar ne fuskarta ta nuna bare har takai ga maida martani. Ita ko irin 'yan group dinnan bata dasu. Bata da wata shaqiqiyar kawa kamar yadda yara suke, saboda rashin samun damar hakan. Ta tsallako babban titin unguwar su wadda ke jere da manyan gidaje masu kyau da tsari, kamar ba a kasar nan ba. Gidajene na masu hannu da shuni. Kowanne sakaye yake cikin katuwar katanga sai kuma hanyar shigarsa masu dauke da tangama tangaman kofofi. Da yawansu harabarsu kewaye take da furanni da suka dada kawata gidajen wadanda Idan an bude gate din za'a hango su, yayinda wasu suka kere suka fito ta saman katangar gidajen. Sannan daga waje sukan sanya 'yar gajerar katanga Ko kuma waya su kewaye wata haraba da bata shiga cikin katangar gidan ba. Anan kallon yake domin nan aka fi kawata wa da furanni, da kuma bishiyoyi da suke karawa wajen sanyi da ni' ima. Idan mutum yana wucewa sai yaji wajen yana da sanyi na mussaman ga kuma kamshin shuke-shuke dake fitowa. Sau da yawa in har tazo wucewa takan ringa tafiya a hankali tana nazarinsu. Ita dai yadda suke a jere ga kaloli daban- daban wasu koraye wasu ruwan dorawa wasu jajaye wasu kuma farare yana buge ta. Amma yau bata tsaya kallon furannin yadda ta saba ba. Racing gaba da tafiya kanta a sunkuye tana sauri ta isa gida ko dan ta gujewa fadan innarta tasallah wacce ta kasance Yaya a wurin mahaifinta. Inna tasallah kamar yadda 'ya'yanta suke kiranta dashi itace uwar goyon sadiya. Ita ta budi ido ta gani a matsayin mahaifiyarta saboda kasance war mahaifiyarta ta asali Allah yayi mata rasuwa a lokacin haihuwarta. Ta tashi marainiyarda babu uwa babu uba saboda tsiran iyayenta shekaru biyar ne kacal shima babanta ya rasu a sanadiyyarhatsarin daya rutsa dashi Akan hanyarsata dawowa daga kamfanin da yake aiki a unguwar sharada. Bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta mai suna isiyaku ya sake aure inda ya auri kanwar abokinsa mai suna ramatu. A dan zaman da sukayi da sadiya tayi mata riko na gaskiya, amma ita allah bai bata haihuwa ba harta allah ta kasance a kansa. Bayan rasuwar sa ta koma kauyensu inda ta sake aure kuma anan ne Allah ya azurtata da 'ya'ya maza da mata. Inna tasallah. Wadda sunanta na asali karimatu kuwa sun kasance su uku a wajen iyayensu. Itace Babba sai labaran sannan mahaifin sadiya isiyaku. Ya kasance autansu. Tana da fada bana wasa ba, saboda haka kowa a 'yan uwan shayinta yake yi.2............... Kawu labaran wanda yara suka fi kira da kawun maririmutum ne mai karamin karfi, amma fa mutum ne mai mutuqar San zumunci sai dai shima abubuwan sun sha masa kai. yana so ya taimaka. Amma nauyin gidan sama da qyar yake kaiwa. Yaransa duk qanana ne kuma wani na bin wani kamar bene. Dawainiyar su kadai Tasha kansa. Lokacin da mahaifin sadiya yana da rai shi yana taimaka masa. Hatta gonar da yake nomawa anan mariri isiyaku ne ya saya masa hadi da gidan da yake ciki. Kafin rasuwar isiyaku Allah ya rufa masa asiri inda ya mallaki katuwar gona a wajen hanyar titin farm center. Hatta gidan daya mutu a ciki mallakarsa ne da kuma wasu qananan kadarori. Ita kuwa inna tasallah yaranta guda biyar ne. Maza uku mata biyu. Yaya kulu duk itace babba mace ce mai tsananin yakana da wadatar zuci. Tana aure a unguwar kurna. Da yaranta dukkan su maza guda shida. Mijinta malam sunusi mai karamin karfine. Wannan yasa take sana'ointa na cikin gida don taimaka masa. Yaranta suna da da'a sosai kuma duk da rashin abin hannunsu bai hana su sanya yaransu a makaranta ba. Suna zuwa boko da safe da yamma islamiyya. Kamar yadda sadiya take yi, babban danta mai suna Ibrahim shine sa'an sadiya tsiran su kwana Talatin da biyu ne. Kusan lokaci daya sukai aure da kawunta isiyaku, kuma tasu tazo daya da matar sa wato mahaifiyar sadiya mai suna Maryam. Tana tausayawa sadiya da janta a jikinta kamar yadda uwa zata yiwa danta. Taso tadau riqon sadiya tasallah ta hana ta. Auwalu wanda akewa laqabi da baba saboda sunan kakansa ne na wajen uwa, shine yake bin yaya kulu. Wannan sunan shiya bashi dammar yin sangarta San ransa, dan ma babansa mai dan tsanani ne, da lamarin nasa ya zarce hankali. Da farko ya fara shiri rita ta zaman karta da makamantan su, mahaifinsa ya nuna bazai dauki wannan iya shegen ba. Ya taka masa birki ganin idonsa yasa ya rage wasu abubuwan. Mafi muni a lamarinsa baisan neman na kansa ba. Sai dai duk abinda mahaifiyar sa ta samu ya lallabata ya karbe. Ita kuma wannan bai taba damunta ba. Sai ya kasa.ce indai kana son kaga ta yaba da al'amarinka to kayiwa babanta alheri. Yafi ita kayi mata. Sani ke bin yaya baba. 'yan gida daya masu hali bambam. Yayin da auwalu yake mai tsaurin ido. Rashin kunya. Malalaci. Son kai. Da tsageranci. Sai Sani ya kasance mai kunya ladabi. Biyayya. Mai kawaici haziqi kuma jarumi. Tun yana dan yaro yasan yayi qwadago kodan ya dau wasu daga cikin larurorinsa. Hali sak na mahaifinsa ne sai dai shi yana da sanyin hali ba kamar mahaifinsa ba. Da indai kayi ba dai dai ba zai nuna maka kuskuren ka. Yana da hazaqa da basira, wadda ya bashi damar dai daita ajin karatunsa dana yayansa. Amma a karatun addini saida Sani yayi sauka yana da shekara goma sha hudu, auwalu mai shekara sha shida da qyar ya hada izifi biyar. Shigarsa jami'ar Ahmadu bello ta zariya yasa sadiya ta maida masa suna yayan zaria. Dija ita ke bin Sani. Itace mai kama har hali babu abinda ta bari na babarta tasallah. Halayenta tsaf ta dauke su. Banbancinsu daya ita inna tasallah Mijinta tsayayyene. Ita kuwa na Dija sai dai a slow inji yara. Bata da nisa dasu tana aure a gwammaja. Mijinta malam usman yana koyarwa ne a makarantar 'yan mata ta dala. Karatunta a makarantar shine sanadin haduwarsu,,har takai ga auratayya. Ba laifi suna zaune lafiya indai yayi mata abinda take so. Indai ya dan kuskure ne tofah sai a hankali. Sa'arta daya wajen 'yan uwanshi bata shiga harkar su. Amma karka ta bata domin Komai girmanka bazata saurara maka ba. Salisu shine autan inna ya girmi sadiya da shekara daya da 'yan watanni. Akwai tazara ta shekara shida tsakanisa da Dija. Saboda barin da inna tayi har sau biyu kafin a haifeshi. Bashida wata illa sai shagwaba da tayi masa katutu. Har yakai shekara bakwai bai daina kuka da shure shure ba irin na qananan yara ba. Dalilin da yasa yara basu cika son wasa dashi ba. Yayi rashin kunya ko tsokana ana taba shi ya cillo muku inna. Daidai gwargwado yana da dan qoqarinsa a makaranta. Gaba daya 'ya'yan inna tasallah kamarta sukayi fararen fulani masu kyawun fuska da jiki gami da tsayi da santsin gashi. Dogaye ne daga matan har mazan. Yaya kulu ce ma take dan dibi da fuskar mahaifinta. Amma ita jikinta irin na innan ne. Suka mahaifinsu malam kabiru ya rasu bada dadewa ba domin sadiya nada shekaru bakwai ya rasu. Tsayayyen mutum ne mai zuciyar neman nasa da son wadata iyalinsa. Kafin rasuwar sa babu abinda suka nema suka rasa. Kuma har bayan rasuwarsa 'yan uwan sa basu watsar da iyalinsa ba. Fadan tasallah nema yasa suka rage shiga harkar yaranta. Amma duk da haka basu daina kula dasu ta fannin abinci da sutura da kuma 'yan hidindimunsu ba. Dadin rufin asirin Allah gidan da suke ciki a unguwar Sani mainagge mai dauke da dakunan barci hudu biyu tare da runfa a ciki da kuma biyu a ware gefe guda. Sai kuma babban tsakar gida a tsakanin dakunan wanda shi ya raba gida kashi biyu. Ya kasance mallakarsu ne.3..........Dukkanin yaran gidan babu wanda bai girmi sadiya ba a shekaru amma ba a wahala ba. Tun tana shekaru tara take kwancala girki a gidan. Balle su shara da wanke wanke gami da wanki wannan duk nafila ne. Kasancewarta yarinya mai hanzari shiya dada assasa mata wahalhalun gidansu. Ga misali haihuwar Dija ita take zuwa kullum da safe gidan Mijinta tayi mata shara da wanke wanke hadi da wanki kayan jaririn sannan ta dawo gidansu ta dora da nata aikin gidan data saba. Saboda haka har maijego tayi arba'in sadiya ko makaranta bata samu taje ba. Dan ma Allah yai mata basira bata wasa ba. Ko yaya ta samu aka dora ta a karatu wala na islamiyya kona boko yanzun nan zai zauna mata daram. Da sallama ta iso soron gidansu tana sauri taje kar tayi laifi a wajen innarta. Ita dai ta kasa gane dalili amma sai taga kamar fadan innarta yafi yawa a kanta, ta kuma rasa Dalilin da yasa kullum ita ake yiwa fada duk da qoqarinta na son taga ta kiyaye faruwar haka. Ta karasa falon innarta ta shiga tare da sallama ta same ta ita da baquwa. Maqociyarsu ce nan bata da nisa dasu.mai suna tamasar. Mace ce mai harkoki iri iri, gata da shige shegen gidajen mutane. Domin ko alawar biki kake son a raba a unguwar baiwa tamasar yanzu zata zaga maka da ita. Haka nan inma mutuwa akayi kaji 'yan unguwa suna a wajen tamasar naji. Har gidajen babban layi ance tana zuwa. Takai musu talladega Kusan kowa a unguwar ya santa itama kuma tasan kowa.4..............Ta durqusa har qasa tare da gaisheta sannan ta juya wajen innarta tace "inna na dawo" kafin ta qara magana ta fadada Murmushi ta. Saboda hango yayanta wanda suka fi shiri dashi wato Sani. Da murnarta take fading "yayan zaria yaushe ka dawo? Shima da far'a ya amsa mata "ban dade da shigowa ba. Yaya makaranta? " "Lafiya qalau" ta amsa masa "inata murna ka dawo in fada maka mun ma shiga ajin 'yan sauka" zata cigaba da bayani innarta ta ta katse da cewa "ba kuma sai kiyi hanzari ki dora girki ba. Ai ba tsinkewa zakiyi da labari ba. In har baqo ya isa baqo ai abinci ake qoqarin tanadar masa." Ta miqe da hanzari tana fadin "yaya bari in gama in kawo maka books dina na makaranta ka gani" ya bita da Murmushi baice mata komai ba. Yarinyar tana burgeshi matuqa. Bai taba ganin yarinya mai qarancin shekaru amma da nutsuwa da kuma hakuri kamar sadiya ba. Duka duka yanzu ne ta shiga shekara ta goma sha daya amma kusan duk zuwan da zaiyi daga zaria inda yake karatu cikin hidima yake samunta. Shekararsa daya kenan a jami'ar Ahmadu bello dake zaria inda yake karantar shari'a wato law amma duk da haka kafin ya qara sadiya. A karatu dai dai na shekarunta yakan jima duk da 'yar fashin da takewa makaranta mussaman ta boko wadda saboda ayyukan dake tsareta a gida bata samun zuwa da wuri ko kuma zuwan ma ya gagareta gaba daya. Yayanta Sani ya kasance daya daga cikin malaman su na islamiyya kafin tafiyarsa A.B.U zaria domin hada digirinsa na farko. Tun yana dauke ido a makarantar islamiyya game da dukan makara da ake yi mata har ya kasa daurewa yayiwa malamai 'yan uwansa magana. Yayi qoqarin nuna musu bata da laifi amma bazai iya fada musu dalilin cewa mahaifiyarsa itace sanadi ba. Qorafinsa bai samu karbuwa ba, saboda da yawa daga cikinsu sai suke ganin kamar son kai kawai yake so yayi domin ita yar gidansu ce. Saboda haka hukunci ba sani ba sabo ya cigaba da haka kanta. Mafi yawan lokuta qwaqwalwarta ce take fansarta saboda bata cika bada itaba Yayin da duk aka tanbayeta hadda ko kuma bitar karatun na baya. Abokin yayanta sa'idu shine ya rangwanta mata yawan horon da take fuskanta ta hanyar fito da horon dalibi ya fanshi kansa da karatu maimakon duka da ake yawan yi musu. Wanda baya haifar da komai sai kangara yara da yake yi. A hankali sai wannan horo ya zama shine horon da makaranta take amfani dashi wajen horar da 'yan makara da kuma na fashi. Ai kuwa yara da suka gane hakan duk randa kayi fashi mafi sauqi a gareka ka nemi wanda kuke dasawa dashi ya biya maka karatun da aka wuce ka. Yayanta ne ya koyar da ita tilawar karatunta idan tana ayyukanta. Yakan ce da ita "hannu yayi aiki baki yayi karatu" A wajen Salisu autan inna take samu tana dora karatun data rasa a makaranta. Salisu ya girmeta da shekara daya amma tare yayan zaria ya sanya su a makaranta.5........ Da hanzari kamar yanda ta saba ta cire kayan makarantar dake jikinta tasa doguwar riga 'yar kanti ta fito daga uwar dakin inna zuwa rumfa inda ta sameta tare da baquwarta da kuma yayan nata. ta dan rusuna daga gefe cikin ladabi tace " inna me zan dora"? Innar ta juya ta kalli sani tace "tunda kaine baqo me kakeson ci. Nasan dai baka son cin tuwo da daddare. Duk dakin akasa dariya. Abinda inna bata fahimta ba sani ya lura da cewar duk ranar da sadiya tayi tuwo to da qyar take tsallake dukan inna, saboda zaiji ana fadin ta tuqashi yayi guda kokuma anaci yana wargajewa inna shinkafa ne. Bakin cikin haka ne yake sawa in aka bashi tuwon sai yace baya ci. A tunanin inna tuwon ne baya so. Bata saniba horon da ake yiwa kanwar sa ne yake fitar da tuwon daga ransa. "Ya amsa mata inna koma meye a dora mana". Sadiya Cike da doki tace "inna in dora taliya da busasshen kifi? Nason yaya da son taliya" kuma..... shigowar Awwalu tare da fito ne ya katse mata duk abinda tayi niyyar fada. Ita dai sadiya bata San meya saba jininta sam bai hadu dana yaya baba ba. Gashi dai ba abinda zai sakata batayi masa ba amma bata kaucewa zaginsa da hantararsa. Lokuta da yawa shine yake zama sanadin da inna take yi mata fada wani lokacin harda duka. Qarancin shekarunta ne suka hana ta gane inna bata iya son dan kowa sama da nata. Bata iya kyautatawa wani sama da 'ya'yanta. Sune wadanda ko laifi suka yi bata cika daurewa ta tsawatar musu ba. Ta kasa gane dalilin da Salisu zaiyi abin da yaga dama ya kwana lafiya. Ita kuwa koda kuskure ta gwada rabin-rabinsa jikinta zai gaya mata. Sadiya taso gwada abubuwan da Salisu yake yi kamar qin zuwa aike amma ita koda wasa tasan bazata wanye lafiya ba. A hankali ta gane ba so iri daya inna take mata da 'ya'yanta na cikinta ba. Tana qara wayo tana fahimtar yadda zata kaucewa dukan inna harta gane cewa yi nayi bari na bari ce mai fissheta. Da hanzarinta ta samu ta kammala daga dafadukan taliya 'yar hausa mai wadataccen busasshen kifi ga qamshin attaruhu da albasa yana tashi. Ta zuzzuba a kwanuka kamar yadda inna ta saba koya mata. Saboda indai ba baqi akayi ba ta koyi yadda zata raba abinci dai dai 'yan gidansu. Kafin kiran sallar magriba ta kammala. Ta kuma kaiwa kowa nasa. Bayan ta idar da sallah taci nata abincin sannan ta tattare dakin girkin ta kuma tattara kayan wanke-wanke wanda take yi cikin dare domin ta ragewa kanta aiki karta makara zuwa makarantar boko da safe. Zuwanta hutu gidan yaya kulu ta nuna mata dabaru na yin ayyukan gida a tsare da qoqarin rage aiki a duk sadda ta samu sarari. Fara yin hakan ta gane anfaninsa domin ya rage mata zuwan makara makaranta mussaman ta boko. Inna da 'yan mazanta guda biyu suna zaune suma abincin suke ci. Kowa yayi shiru sai loma suke zubawa. Shiru mugun santi inji 'yan magana. Can baquwar inna wato Tamasar ita ta fara magana tace "yanzu tasallah wannan 'yar taki iya tayi wannan girkin"? "Qwarai kuwa ita tayi shi"Inna ta amsa mata. Ta kuma cigaba da cewa "ai ba abinda bata iya ba kin sanni bana son sangarta yara. Nafi son yaro mai kazar kazar." Wannan kalami na inna son ransa kawai ta fada domin kuwa yaya baba ko mai jego bata kaishi zaman daki ba. Har a bada a daki zaka same shi. Baya zuwa ko'ina tun da ya samu ya qare makarantar sakandire bai ci gaba ba. Tare suka gama da yayan zaria amma shi takardun basuyi kyau ba. Inna tace malaman ne basa son sa sun tsane shi. Wannan abinci da tamasar taci shine ya janyo sanadin da tabawa inna shawara akan sadiya tunda ta yaba da yanda take gudanar da ayyukanta Like · Reply · Edit · 2 hours ago Fatima Binta .......****6****........ Tunda ta yaba da yadda take gudanar da ayyukanta. Take ta sanar da ita cewa wata mata da suka tare a babban layi ta bata cigiyar ta nemo mata yarinya qarama da zata taimaka mata da ayyukan gida da kuma renon yara. Inna taso taqi amma tamasar ta kwadaita mata kudin da za'a samu sai itama ta yarda. Da danlelenta suka yanke shawara. Yana murna harda fadin " inna don Allah ki barta taje in an tara albashin inna kya saya min mashin" ta amsa masa da fadin " mai zai hana ubana, ai duk abinda kake so zan maka. Kuma ma dama me take yi min a gidan, dan kaye kaye ne kuma nayi abina. Ga kuma qaruwa da za'a samu. Inaga ma idan ta fara aikin adashe zan shiga. Domin a tara kudin babur din naka. Kaga har kayan daki na samu na tara mata". Amma dai inna sai an fara siya min mashin din tukunna ko". To tunda kaine babba ai dama ta kanka zan fara." Wai waya ganni da babur ai in na dinga zazu dashi a unguwar nan, dama ina jin haushin shitu dan gidan Alhaji Lawan wai kawai rannan daga na ari mashin dinsa tsautsayi yasa na fasa masa danja, ya ringa yimin bala'i. Ai kawai kyale shi nayi amma da sai nai masa rashin mutunci. Amma kinga inna idan na samu nawa habawa" Kai gandoki jira a fara aikin a samu kudin mashin din ko kafin ka rama abinda akayi maka. Nima ai bana son na rika ganin kana yawo a qafa. Nafi son kaima ka kece raini kamar sauran matasa ' yan uwanka" Allah ya barmin ke inna tawa" ya fada yana dariya Sani bashida masaniyar wannan shawara tasu, kasancewar baici abincin dare a cikin gida ba. Dakin dake tsakar gida Ta hada nasa ta kai masa shida baqonsa sa'idu da shima yazo hutun qarshen mako. Daga jami'ar maiduguri. Kafin yayan zaria ya koma makaranta sai da ya dubi littatafan ta ya kuma yaba da irin qoqarin da take. .......****7****........... Komawarsa zaria ne ya bawa inna damar tura sadiya aikatau. Taja mata kunne matuqa kafin tamasar ta kaita gidan aikin nata. Sadiya tayi mutuqar baqin ciki da afkuwar hakan. Saboda sanin karatun ta yazo qarshe, amma bata da yadda zata yi. Tunda dai bata isa tace bazata je ba. Gidan da za a kaita tayi aiki yana cikin jerin manyan gidajen da suke bakin titin unguwarsu, sabanin nasu da suke a lungu. Misali tara na safiya tamasar tazo tafiya da ita. Tana jin sallamarta bata San sanda hawaye ya fara zubo mata ba. Ai kuwa yaya baba yana lura da ita ya fara zaginta yana fadin " ' yar baqin ciki watau ke baza'a qaru da keba." innarta ta amsa da cewa " qyaleta komai abin tsiyarta sai taje in kuma kika je kika qulla musu abin tsiya nida kene a gidan nan kinsan sauran. Har in suka koroki kin quntuka musu abin tsiya to talla zan dora miki. Ta dago idanuwanta da suka cika da hawaye tace mata " kalleni da kyau, kinsan zan iya. Tana bambamin fadanta suka fita daga gidan ita da tamasar. Ta lungunan unguwar tasu suka bille suka nufi bakin titi. Tamasar tana dada tausarta tare da kwadaita mata alherin dake tattare da gidan da zata kaita. Tace da ita " gidan dazan kaiki ba wani aiki ne mai wahala ba. Zaki ma samu ki huta. Matar gidan so take a nemo mata yarinya qarama da zata dinga taimaka mata da qananan ayyuka. Kuma dadin dadawa daga qasar waje suka dawo gidan 'yan gayu ne inda zakije. Tadan numfasa tajira taji ko sadiya zata furta wata magana taji bata ce komai ba. Taci gaba da fadin "keda zakije kici mai kyau nasan har kayan sawa sai ta baki. Kisaki ranki ai bazan kaiki inda za'a cuce kiba." sadiya ta amsa a zuciyarta "ni dai ai kin cuceni tunda kika raba ni da karatu na" sai kuma ta tuna da wa'azin da aka yi musu a islamiyya inda malamin yake fada musu cewar duk abinda suka ga ya same su Allah ne ya qaddara kuma su kasance masu neman taimako a wurin Allah kadai da kuma dogaro dashi. Insha Allahu zai isarwa duk wanda yayi tawakkali dashi. Wannan tunani da ya darsu a zuciyarta shiya sanya ta tayi ajiyar zuciya. Jin haka da tamasar tayi shiya bata qwarin gwiwar cigaba da nasihar da take yi mata a zaton ta sadiya taji hudubar da take yi mata ne. Taci gaba da fadin " idan kinje ba ruwanki da kowa aiki da aka sakaki shi zakiyi kar ki taba musu yara kuma duk abinda ba'a baki ba Karki dauka. A zuciyarta tace mai cin zalina ma a gida na qyale su balle wadanda naje aiki gidansu. Professor Abubakar Ibrahim da matar sa Hajiya mariya nan ne gidan da tamasar ta samowa sadiya aiki. Gidansu na daya daga cikin manyan gidaje masu furannin da suke burge sadiya anan babban titin unguwarsu. Asalinsu mutanen bichi ne. Amma aiki ya kaishi har qasar barno inda ya koyar a jami'ar maiduguri na tsawon shekaru takwas. Daga nan ya tafi America inda yayi tsawon shekaru hudu domin qaro ilimi. Yanzu haka yana daya daga malaman jami'ar bayaro ta kano. Mutane ne masu mutunci da sanin darajar dan Adam 'yan uwan juna ne dashi da matarsa har Allah ya hada su aure........****8****......... Sun tarar da matar gidan mace mai far'a da cikar kamala ta karbe su da murnarta. Gidan tsaf dashi ko ina sai qamshi ne yake tashi. Bayan sun gaisa da tamasar sadiya ta rusuna ta gaisheta Cike da ladabin data saba gaida mutane dashi. Matar tace " hajiyan masar ina kika samo yarinya kyakkyawa da ita.? Tamasar ta amsa mata da cewar "yarinyar da kika ce a samo miki da aiki ce. Nan da nan ta fadada far'arta tare da nuna farin cikinta ta kuma dora da fadin " kai maddala nagode amma kina ganin zata iya yin ayyukan dazan sakata. Kin ga Inason ta dinga taimaka min a kicin da kuma harkar yara domin na lura dadinsu baya son qabilun nan suke shiga harkar yaransa balle rannan da yaji amira ta fadi wata kalmatil daya tambaya aka sanar dashi fassararta daga yaren gwari. Suka tuntsire da dariya. Tamasar ta amsa da cewar wannan yarinyar nayi miki alqawarin ba abinda zai gagara. Sai kinyi mamakinta. Ai kin san bazan kawo miki mashiririciya ba. Tayi mata godiya ta shiga daki ta hado mata sabulai harda turmin atamfa ta kuma dauko kudi ta miqa mata. Tayi godiya ta sake tsayawa tayiwa sadiya fada sosai akan ta kiyaye ta tsaya tayi aikinta yadda ya kamata. Sannan tayi musu sallama ta tafi ta bar sadiya mai shekaru goma sha daya a baqon muhalli da bata San kowa ba sai dogaro ga Allah. Wanda ta haqiqance shine kawai gatanta. Sadiya ta fara aikinta a gidan mom mariya da kuma dadinsu mai suna Abubakar. Momi tayi mutuqar mamakin yadda sadiya ta iya aiki da kuma girki. Gata da far'a da son yara. Yaran gidan guda uku ne Amir dan shekaru tara shine babba sai qanwarsa Amira mai shekaru bakwai. Sai kuma babyn da Momi take goyo watau Khalifa. Gida ne na tsantsar 'yan boko masu dauke da kyakkyawar akida. Basa nuna mata wariya. Ita kuma bata yi musu shishigi a bisa lamuransu. Aikin sadiya a gidan ya hada da wankin uniform safa da kuma qananan kayan yaran gaba daya. Sai rainon Khalifa da kuma taimakawa Mominsu girki a kitchen. Kaf kaf dinta da kuma taftarta ya sanya Momi ta dada sakar mata wasu al'amura na gidan. Wata rana da la'asar momi tasa sadiya ta fere mata dankali a bayan harabar kicin ita kuma tana daga kicin sai taji amir ya tanbayi sadiya da harshen turanci wani lissafi da aka basu a makaranta. Ya gagara yi. Abin ya bata dariya a zuciyarta take fadin Amir da shirme. Sadiya tama san me kake fadi. Bata kai qarshen tunanin ta ba taji muryar sadiya a nutse tana bawa Amir amsar tambayarsa. Duk da turancin bai kama qafar nasu ba amma tayi masa bayanin daidai yadda zai gane. Bata gama wannan al'ajabin ba taji Amira ita kuma tayi mata tanbaya akan wani hadisi da ustaz da yake biya musu karatu ya saka tayi bitarsa itama sadiya ta amsa mata ta ta tambayar. Al'amarin sadiya bai qara daure mata kai ba saida taji ta dage tana gwama turanci suna hira da dariya dasu Amir. Ga wani qarin abin birgewa da Amir duk sanda tayi kuskure kamar yadda al'adar bature take baya yi maka dariya sai dai ya gyara maka. To haka Amir ya dage da gyarawa sadiya inda ta kuskure har kuma ya sata ta maimaita don ya tabbatar data gane gyaran da akayi mata. Momi abin har tsoro ya bata. Ta kira Amir ta tanbayeshi yaya akayi har sadiya ta iya turanci. Ya amsa da bai sani ba. Ta bar maganar a ranta. Sai bayan yaran duk sunyi bacci sai sadiya dake qoqarin karasa gyaran kicin. Momi tana tare da dadi a falonsa take mayar masa da abin data gani tsakanin yaransu da kuma sadiya. Dadi ya dan nisa sannan yace "any kuwa ba cutar yarinyar nan mukeyi ba. Amma kirawota muji amsar wasu tambayoyi daga bakinta. Momi ta leqa ta kwallawa sadiya kira ta leqo daga kicin da dan tsumman da take goge goge dashi 'gani momi inji ta. Kin Gama ne? "A'a ta amsa mata amma sauran kadan.". "Barshi kawai kinzo inji dadi.=======***9***======= A kan qofar kicin ta ajiye duster tabi bayan momi zuwa falon nasu. Ta shiga da sallama kamar yadda ta saba. Ta durqusa a gefen kujera, ta dada qasqantar da muryarta. Dadi barka da yamma" barka kadai ya amsa mata. Zauna mana da kyau" ta gyara zamanta maimakon durquson da da tayi. Dadi ya ajiye kofin shayin da yake kurba ya kalle ta tace, ina babanki yake Inason inyi magana dashi" nan da nan muryarta ta fara rawa ta amsa masa da cewa "babana ya rasu tun ina shekara biyar." Mamanki fa? Itama ta rasu tun ina baby. Banma santa ba sai dai labarinta da ake gaya min" Ya danyi jim sannan ya sake cewa " to yanzu a hannun wa kike da zama" "A hannun innata yayar babana ce". Ta amsa masa cikin rawar murya. Wadda ta tabbatar masa da cewar ya tado mata da wani tsohon miki na maraicin da tayi. Ya nisa yace " Allah yaji qansu. Dama kin fara makaranta ne?. "Ina makarantar boko da islamiyya. Momi ce wannan karon ta sako tata tambayar "ajinki nawa? A boko zamu zana common nazo nan a islamiyya kuma ina ajin 'yan sauka don munyi izifi arba'in da biyu kafin zuwa na gidan nan." tana magana muryarta na rawa alamar kuka na qoqarin qwace mata. Dadi ne ya fara magana. Yace "tashi kije ki kwanta". Ta miqe da sauri don kar suga qwallar da take qoqarin sharewa. Bayan fitar ta momi ce ta fara magana. " dadin amir yaya kake ganin za'ayi? Ya amsa mata da cewa"daurewa zakiyi kije gidansu gobe mu nemi yardar mariqiyarta mu maidata makaranta". "Nima dama tunanin danayi kenan. Karmu ajiye yarinyar mutane tana mana bauta bamu lura da cigabanta ba. Sai convenience dinmu kawai muka duba" " kin kyauta da wannan tunani naki. Ki tattala da kona waye baka san alherin da zai zamar maka ba. Sai yayi maka alherin da dan cikinka ba zai iya maka shi ba" Washe gari sadiya na qoqarin karasa hada abincin dasu Amir zasu tafi dashi makaranta. Momi ta leqo tace " yi sauri ki hada musu kije kiyi wanka fita zamuyi. Kai bari ma zan qarasa jeki ki shirya" Da qafa suka zagaya suka shiga lungun gidan su sadiya tun da ba wani nisa ne dashi ba. Ga kuma uwar dakin nata ba malalaciya bace. Sun sami inna a rumfarta tare da sarkin fadarta wato yaya baba. Da hanzari inna ta miqe tana maraba amma fa gabanta sai bugawa yake, dariyar yaqe kawai take yi. Amma zuciyarta fadi take Allah yasa yarinyar nan ba abin tsiya ta shuka a gidan da aka kaita aiki tayi ba suka dawo da ita ba. Gashi taji dadin kudinta na wata uku da tazo kwanaki da kanta ta kawo mata. Wanda dasu ta fara adashi don sayen babur din dan lelenta. Bayan musayar gaisuwa a tsakanin su, Sadiya ta miqe ta fice ta barsu domin bata san me zasu tattauna ba. Shi kuwa sarkin hankali yana zaune bashida niyyar tashi. Wai zazzabi ne yake damunsa. Inna dai tayi saqare tana jira taji ta inda labarin zai bullo mata. Harta fara tunanin irin azabar da zata ganawa sadiya in dai har tayi sanadin da aka koreta aiki. Momi tace "sai kika ganmu kwatsam" inna ta muskuta ta hadiye yawu da qyer tace "ai na rasa ma ta inda zan fara. Yaran yau ka haifesu baka haifi halinsu ba. Amma in banda haka wane irin Jan kunne ne ba'a yiwa yarinyar nan ba amma............ Momi tayi sauri ta katse ta tace "kinsan Allah sadiya tun da aka kaita ban taba samun matsala da ita ba. Da kyar ta maimaita kuskure. Kusan duk abinda akayi mata gyara a kansa to da kyar ta sake maimaita makamancinsa". Sai a sannan inna taji hankalinta ya kwanta. Momi ta dora da cewa "alfarma muka zo nema. So muke idan har kun yadda zan maida sadiya makaranta taci gaba da karatunta. Tunda na fuskanci ta fara karatu da can" Wata munafukar gyaran murya yaya baba yayi. Nan da nan inna ta gane me yake nufi. Ya tashi ya shiga uwar daka. Ita kuma ta miqe tana fadin Hajiya bari na samo miki ruwa kisha. Momi na qoqarin nuna mata ta barshi ba komai amma duk da haka ta miqe ta shige dakinta da nufin dauko kwano. Tana shiga ya yafitota da hannu sannan ya rada mata "Karki yarda baki suka hada da ita sadiya. Da anfara za'ace miki kudin aikinta dashi za'a biya mata kudin makaranta". Itama ta rada masa "na gane wayonsu ai. Barin dani suke zancen" ta dauko kwano ta fito ta nufi randa, anan ne ta tarar da sadiya tana qoqarin karasa share mata tsakar gida. Ta harareta kawai ta wuce. Bayan ta shiga da ruwa. Tace to Hajiya anfa gode amma wani hanzari ba gudu ba zan so. Ita sadiya taje ta gayawa wan babanta idan ya amince shikenan. Nama san zai yadda wannan abin alheri haka".=====***10***====== Da wannan momi tayi musu sallama. Bayan tayi wa inna ihsani wanda taji dadinsa sosai. Ta dawo ta bari sadiya akan ta kwana taje ta nebo zini a wajen baffan nata. Tana fita kuwa yaya baba ya dire a kanta. Ta inda ya shiga bata nan yake fita ba. Har yana fadin munafuka ita taje tana fadin asirin gidansu. Inna kuwa fada takeyi tana fadin "kaga min annamimiyar yarinya. Zuwa kikayikina gayawa mutane magana ana ganin kamar ba'a kula dake, dama duk akanki an saka min ido kamar akanki na fara riqon maraya. Nima 'ya'yana duk marayu ne. Kuma haka na riqe su ba tare da kowa yaga gazawata ba. Ehe dan kiji in gaya miki. Ke baki isa kisa mutane su zage ni ba". Ta kuka take fadin " wallahi inna ban gaya mata komai ba. Kawai ji tayi muna karatu da yara shine ta tambayeni a ina na koyi karatu, shine na gaya mata na fara makaranta. Allah inna ban san komai ba bayan haka" "Idan bake kika fada ba wane shegen ne yaje ya gaya mata. Idan kikayi wasa sai in dawo dake daga gidan ki koma talla inga abinda zakiyi." A'a inna ki barta ta koma gida aikin. Amma in taje tace baffa bai yarda ta shiga makaranta ba. In an matsa kije da kanki kice yaqi. Amma ni yanzu inda aka samun rai zan mallaki mashin kuma azo ace an fasa. Ai gaskiya ni aka yiwa. Ta koma kawai taci gaba da aikinta" Da wannan sadiya ta koma gidan aikin nata ta kuma fada musu kamar yadda inna ta shirya mata. Momi bata yarda ba. Ta kuma ya qoqari ta bugi cikinta dan taji komai dalla- dalla. Amma hakan ma bai samu ba. Inda ta gano bakin zaren sai da ta tanbayeta " shi wannan da muka samu a dakin Innar taku waye shi.? Ta amsa mata da cewar yayanta ne. Ta sake tambayarta shi aiki yake ko makaranta. " baya komai shekara biyu kenan daya gama sakandire" "Allah mai iko. To shi bazai fita aiki ba sai ke da kike mace za'a tura neman kudi". Ita dai bata amsa ba. Ta nisa tace ku nawa ne a gidan ta lissafa mata tun daga yaya kulu har zuwa kan Salisu. Ta sake tambayarta. Kowa abinda yake yi. Sadiya ta gaya mata. Momi ta sake cewa. Amma ai naga yayarki Dija tayi makaranta. Ita dai shiru tayi bata ce komai ba. "Ba komai duk abinda ya samu bawa shiryayye ne daga Allah" inji momi. Da dai ya dawo momi ta gaya masa duk abinda ya faru a zuwanta gidan su sadiya da kuma abinda ta gani hadi da kuma bayanan da ita sadiyan tai mata. Ya nuna mamakinsa yace "Karki damu inaga abinda zai faru ta rubuta jarrabawa a makarantar su Amir zanyi magana da principal din sai taci gaba da home study a wajen lesson teacher su Amiran. Haka Inason duk sanda ustaz yazo ki tabbatar taje itama ta dauki karatu" Haka kuwa akayi. Da wannan taimako dasu dadi suka yi mata ta zana jarrabawar common entrance ta kuma cigaba da daukar karatu a wajen lesson da kuma ustaz. Duk gidansu babu wanda yasan da wannan shirin ko yayanta. Yayan zaria. Farko daya kawo ziyara gida aka gaya masa sadiya tana aiki a wani gida yayi baqin ciki matuqa. Saboda ya tabbatar wannan zai zama sanadin tsayawar karatunta gaba daya. Da kansa ya nemi tamasar tayi masa kwatancen gidan da sadiya take aiki. Da la'asar ya shirya ya nufi gidan. Yana isa bakin gate din gidan ya rusuna ya gaida magadin wanda ya kasance dattijo ne. Bayan sun gaisa yace "baba don Allah so nake yi naga sadiya, ni yayanta ne. Baba maigadi ya amsa da cewa "anya zaka ganta yanzu kuwa domin maigida ya hana in dai yara suna karatu a katse musu. Amma bari in yiwa Hajiya bayani" Ya shige cikin gidan yabar sani da dumbin mamaki a fuskarsa. Ko dai ba gidan yazo bane. Mistake yayi bai gane ba. Nida nazo neman mai aiki ana min zancen yaran gida. Kai bari in bar wajen nan inajin ban gane kwatancen da tamasar tai min ba. Yana shirin juyawa ya bar wajen ya hango baba maigadi da saurinsa yana dawowa. Kamar ya gudu sai kuma yaji tsoro kar ya jawa kansa mummunan zato ya dai daure ya tsaya. Mamaki ya sake kamashi da yaji baba maigadi yana fadin ance ka shiga daga ciki.======***11***====== Da jan qafa ya bishi suka shiga harabar gidan. Amma fa a tsorace yake. Wani hadadden falo babba ya shiga dashi. Da sallama ya shiga ya tarar da dadi zaune yana karatu. Shiya fara miqa masa hannu sukayi musabaha. Duk da sani yaso ya noqe. Bayan sun gaisa dadin da kansa ya shiga ya kirawo momi. Fitar sa ce ta bawa sani dammar qarewa falon kallo. Hotunan su daya gani shiya tabbatar masa da cewa shine maigidan. Yana zaune daga qasa duk da tayin kujera da dadin yayi masa. Yaji sallamar momi. Mace mai cikar kamala ta shigo. Bayan sun gaisa. Suka shiga yi masa tambayoyi har suka gano shine yayanta na zaria. Suna nan zaune suna 'yar hira sama-sama mafi yawa akan karatun sani ne. Har suka jiyo hayaniyar yaran alamar sun tashi karatu. Sadiya hanyar kicin ta nufa don ta fara shirin abincin dare. Amma sai ga Amira da gudu tana cewa momi is calling you" sadiya ta amsa I am coming " haka su momi suka hore su da su riqa yi a tsakanin su. Su yawaita yin magana da turanci don ya zauna musu a baki. Hatta ita sadiyan da batai wata hudu dasu ba. Bakinta ya fara murjewa. Haka zalika ita kuma da yake suna muhaddasa a islamiyyar su sai take qoqarin su riqa wasu maganganun da larabci. Inda suka kakare sai ustaz ya gyara musu. Tare suka shigo falon inda take zaton ko wani aiki momi zata sakata. Bata kula da baqon dake zaune kusa da qofa ba. Wanda mamaki da kuma farin ciki suka cika fuskarsa saboda ganin kyakkyawan yanayin da take ciki. Da ganinta kasan bata tare da takura. Ta durqusa gaban momi tace dadi Sannu da hutawa". Ya amsa mata sannan ta juya tace " momi gani" Momi tace "baqo kikayi" mamaki ya kamata tunda tasan tunda tazo gidan aiki ba wanda ya taba zuwa dubata kamar bata da kowa. Ta kuma san inna ce zata hana kowa zuwa. Ta dubi inda momi ta nuna mata. Ai kuwa tana area dashi. Bata San sanda hawaye ya fara zuba a fuskarta ga kuma dariyar farin ciki duk a lokaci daya. Amir yace "yeh tana kuka tana dariya" duk suka tuntsire da dariya. Bayan sun fice daga falon sani ya zuba mata ido. Yana mai jin dadin yanayin daya sameta a ciki. Ga dukkan alamu bata tare da wahala a gidan. Ta murje ta qara kyau. Kyawun ta ya dada fitowa. "Share hawayen mu gaisa sarkin kuka. Ai na dauka kin daina saurin kuka ashe har yanzu kina yi. Ta share hawayen da habar zaninta. Sannan ta gaida shi. A 'yar hirar da suka yine sani ya fahimci alherin daya sami sadiya na samun damar cigaba da karatu. Yayi murna mutuqa. Suna zaune Amir yai sallama dauke da tire mai dauke da lemo da kuma 'yan kayan tande tande ya ajiye yana fadin " momi says not to worry about dinner, she will take care of it". Gyada kanta ne ya bashi damar gane amsarta. Ya juya ya kalleta " har turanci kike ji haka?" tayi Murmushi kawai. Kafin ya tafi har littatafanta na boko da islamiyya saida ya duba. Kiran sallar magriba yasa yai sallama. Ya dauko'yan kudi daga aljihunsa ta bata. Taso taqi karba ganin gidan ba abinda suke saya komai sai dai su ganshi basu San fa akayi aka siyo ba. Amma sani ya dage sai da ta karba. Dadi ne ya fito ya jashi suka tafi massalaci tare dashi da Amir. Ya kuma matsa masa saida yaci abincin dare dasu. Da zai tafi kuma ya bashi kyautar shadda yadi goma da kuma kudi masu yawan gaske.***12***======= Karamcin dasu dadi suka yiwa sani da kuma kyakkyawan yanayin da yaga sadiya a ciki su suka kwantar masa da hankali, ya tabbatar da yardar ubangiji ta samu iyayen daki nagari masu kula da 'ya'ysn wasu tamkar nasu. Samun hutun 'yan makaranta da kuma rufe jami'a domin yin hutun sallah, ya sanya su momi shiryawa don ziyartar garinsu wato bichi. Kafin tafiyar su sai da Momi ta tabbatar kayan sallar sadiya guda hudu sunzo wajen mai shi. Lokacin data miqa mata kayan ba qaramar murna tayi ba. Ta daddagasu tana dubawa. Leshi marar nauyi guda daya. Atamfa sai kuma shadda. Da riga da siket 'yan kanti. Qarin dadi harda mayafai guda biyu kalar leshin da kuma shaddar. Sannan atamfar tata zannuwa biyu manya da riga dinki mai kyau. Dai dai da jikinta. Sai takalmi scholl da kuma wani mai qyalli da kuma dunduniya kamar ta gilas, suma dai dai ita. Tayi murna mutuqa, momi na gode Allah ya saka da alheri". Amin dai inji momi. Tace kinji abinda na gaya miki sati biyu zamuyi. Da mun dawo zan turo su Amir su gaya miki" ta kawo albashinta ta bata. Sannan ta sake debo wasu kudin daban ta miqa mata "ungo ki riqe wannan a hannunki ko zaki buqaci wani abu. Ga kuma kayan abincin can da sauran provision na hada miki". Tayi ta godiya. Momi tace "Karki damu ganinki nake kamar su Amir. Ki kuma kula da holiday assignment din da uncle ya baku. Kije kiyi sallama da Dadi direba ya ajiyeki. Yazo mu kama hanya kar muyi dare". Da tarin alherin da iyayen dakinta suka bata ta isa soron gidansu. Anan suka hade da yayan zaria shima yazo hutu. " ga 'yar gidan momi ya fada da murnar sa" itama da murnar ganinsa ta gaishe shi. Ya tayata suka shiga da kayanta dakin inna. Maganar suce ta fito da yaya baba daga dakinsa na wajen tsakar gidan. Yana fadin uban me kikazo yi nan gidan da sassafe. Ai daman nasan sai kinyi abinda za'a sallamoki daga gidan arziqin nan. 'yar baqin ciki wadda bata San 'yan uwanta da alheri. Babu shiri hawaye ya fara zuba daga idanuwanta. Inna ma tana ganinta fada ta fara yi. "Me ya kawoki gida da sassafe haka. Duk abinda na gaya miki ba kiji ba gani kike kamar bazan iya aiwatar da abinda nace zan aiwatar a kanki ba idan kika baro gidan nan ko?" ta dauko mafici ta wurgeta dashi. "Dena kallona da idanu kamar na mayya" cikin muryar kuka ta amsa Inna ba koroni suka yi ba. "Me kikazo yi gida da sassafe Inba tsiya kika tsula musu ba?" ta share hawayen da suke zubo mata "inna tafiya sukayi ganin gida shine nima sukace inzo gida in huta'. "Ai towoo. Kuma ba sai kiyi magana ba tun dazu" takai dubanta tarin kayan da suke zube a rumfar. "Wadan nan kuma fa mu gani" ta fara bubbudewa. Yaya baba yana tayata. Kayan abinci ne dangin su macaroni da taliya da kuma shinkafa takai rabin buhu. Sai kuma babban kwali mai dauke da kayan shayi da kuma su sabulun wanka dana wanki. Akwatin ma da aka bude kayan sawarta wanda momi ta dinka mata a zamanta a gidan. Da kuma kayan sallar ta. Shida sani yana tsaye yana kallon ikon Allah bai sa musu baki ba balle hannu a abinda suke yi. Da kanta ta kunto hannun zaninta ta miqa mata kudi. Inna da yaya baba har rige rigen karba suke yi. Inna dai tayi nasarar karbar kudin. Ta qirga taga sun haura albashin sadiya. Da sadiya taga ba magana zatayi ba. Balle ta tambayeta bayani akan kudin da taga sun haura sai tayi hanzari tace mata "inna kuma ta qara min wadannana da kika gani a daban. Tace in dinga kashe wa kafin su dawo. Kafin ta amsa mata yaya baba ya cafe da cewar "shi kenan inna sai ki bani in karbi dinkina ki kuma bani kudin hular danace miki ina son saya." "Kaifa dadina dakai kenan. Ka bari mana idan na zuba dashin muga abinda yai saura. Kuma kaga Dija ma kasan mijin nata an dakatar dashi aiki. Saboda haka sai na tsakurar mata. "Amma dai inna ni ina ruwana da wata Dija. Mijinta aikin me yakeyi daba zai kula da gidan sa ba" inna ta amsa baka ganin halin da suke cikine kai me yasa kake abu kamar ba kaine babba ba"? "Hular nan dai kinsan duk samari ita zasuyi yayi. Kuma ni sai ace bani da ita. Kuma baga kayan sallar wannan yarinyar ba. A bata mana ta qara girman su. Kuma ga shinkafa da kayan abinci ba sai ki bata ba. Kawai dai inna ni in bazaki baniba ki fada min. Kuma wallahi idan ba'a bani ba kowa sai ya sani a gidan nan. Yayi qwafa. "Kai dadina dakai rashin hakuri " ta qirgo kudin ta miqa masa. "Gashi inceko shikenan " yasa hannu cikin kwalin yadau sabulai da kuma wani turaren sadiya da Momi take siya mata. Ita ta saba mata amfani dashi. Har ya kasance ko yaushe sukaje sayen kayan amfanin gida sai an sai mata. Harda su man gashi da sauran kayan kwalliya.=======***13***======== Sani ya sunkuyar da kansa kamar yai kuka don takaicin wannan son kai da ake a gidansu. Wani da shan duka wani da karbe kaya. Inna na cikin ware kaya saiga Dija tayi sallama. Suka shigo ita da danta Al amin wanda baifi shekara daya ba. Firgai-firgai dasu daga gani ko wanka basuyi ba suka fito. "Ke kuma daga ina haka da sassafe" Tashi mukayi gidan ba abinda zamu karya shine yace in taho gida. Shima ya tafi gidansu" Idonta akan kwalin da sadiya tazo dashi. Tana bude wa taci karo da qaton gwangwanin Nido irin gugan nan. " kai-kai-kai Inna wannan gara fa daga ina? Sadiya na qoqarin ta gaisheta ta kasa amsawa saboda zalama. Inna tayi mata bayani duk kayan da sadiya tazo dasu. Nan dai ta samu rabon leshin da shaddar sadiyan na sallah. Duk sunyi mata kadan haka ta turmutsa su a jikinta tana fadin akwai alawus. Na bayar a buda min. Itama inna Dija tasa ta dauki atamfar tana fadin ai zani biyu ne sai kikai a gyara miki rigar da dayan zanin. Haka dai suka rabe kayan suna fadin ai nata da aka dinka mata a gidan momi ba abinda suka yi. Saboda haka ta iya sakasu a sallah. Shigarsu daki ya bawa sadiya damar dauke turare guda biyu a qarqashin a kwatin da basu kula da suba da kuma wani man gashi. Da kuma wani silifas mai kyau data siyo shi a dalilin wani Abokin Dadi yazo ya basu kudi aka raba harda ita. Qawar momi ta kawo tallan takalma ta nunawa momi tana sha'awar ta saiwa yayanta. Tayi wuf tashige daya dakin ba tare da sun ganta ba. Ta sake dawowa babu kowa a dakin ta sake daukar sinqin sabulun joy tashige dashi dakin ta hada ta boye. Bayan an idar da sallar tarawi ta iske yayan zaria a dakinsa ta bashi takalmin da kuma turare guda daya. Yayi murna mutuqa ya kuma sa mata albarka. Ranar sallah sadiya bata samu kanta ba sai bayan la'asar lis. Saboda duk aikin abincin sallah ita tayi shi. Hatta da Dija a gidan aka data mata abincin da zatayi rabo dashi. Aka dorawa almajirai suka kai mata shi a kwalla. Mijinta ko banza yana jin dadin wannan bajinta. Ballantana a yanzu da bashida shi. Sai yake ganin sauqi ne ya samu. Baya hangen rainin dake dada shiga tsakaninsa da matarsa. Ta hada musu lemon citta wanda ta koya a wajen momi. Washe garin sallah tai kwalliyarta da riga da siket din yan kanti. Ita da yayanta suka nufi gidan yaya kulu. Takai mata tsarabar turare man kitso da kuma sabulu. Taji dadin ganinsu mussaman yanayin data ga sadiya a ciki. Anan ne sani yake mata qorafin abinda su inna sukayi da kayan sadiya. Ita kuwa tai saurin dakatar dasu tare da cewa "Allah yaya ba komai dama ai su na kawowa" "Amma kayan sallar ki fa, da ko sudin sun bar miki." "Shima din ba komai ba gashi nayi kwalliyata da wadan nan ba". Hakurin sadiya shiya ke sa yaya kulu take dada kaunarta. Sai kuma amincin da sukayi da innarta kafin rasuwarta. Sun fara tattauna wasu batutuwa sadiya ta fice daga dakin ta barsu. Kamar ko yaushe yaya sani yana qorafin halin auwalu na lalaci. Yaqi karatu kuma shi baya aikin komai. Kullum yana gida. Anan suka wuni saida la'asar lis sannan suka kama hanyar komawa gida. Sadiya ta samu ta zaga dangi harda gidan baba labaran da yake zaune a mariri saida taje ta kwana biyu. Shi kam baima San sadiya tana aiki ba saida tazo wannan hutun. Halin yayarsa yasa sai ya shekara bai leqa inda take ba. Shima ganin da yayiwa sadiyan ta samu jin dadi a gidan da take sai hankalinsa ya kwanta da aikin nata. =======***14***====== Kamar yadda su momi suka yi mata alqawari. Sati biyu na cika saiga Amir harda baby Khalifa. Ta dauka ma bazai ganeta ba. Amma yana ganinta ya fara miqo hannu ta dauke shi. Su amira ana tayi mata rakadi a haka suka koma gida. Suna bata labarin da maman Dadi suka zo zata ga likita. A wajen Hajiyar bichi sadiya ta gano inda su momi suka koyi martaba dan adam. Koda ba matsayinsa daya dasu ba. Duk wani kyautatawa da su momi suke yi mata sai taga nafila ne akan na Hajiyar bichi. Ta kuma samu sadiya irin yaran da take so watau yaro ba kyuiya ga kuma biyan buqata. Duk irin aikin da zata sa sadiya da hanzari take mata shi. Sauqin kanta da kuma hakurinta ya dada sa Hajiyar bichi ta jata a jiki. Har ta gama da likitan qashi da take gani a asibitin dala. Sadiya bata taba kosawa da hidimarta ba. Hazaqarta a karatun qur'ani shike dada sa mata farin jini a wajen Hajiyar bichi. Zaune suke a falo suna hirarrakin su. Sallamar anty salma ce qawar momi ta katse su. Daya bayan daya suka gaishe ta. Sadiya tayi dabara ta zame jikinta da zummar kawo abin sha. Ta gudu daga falon.=======***15***======= A gaskiya bata cika son zuwan anti salma gidan ba. Saboda kyararta da tsangwama da take yi mata. Ita a dole momi saita banbanta ta da 'ya'yanta. Watau ta nuna mata ita 'yar aiki ce. Amira ce ta fito da tiren da sadiya ta shirya. Tana jiyo anti salma tana mitar watau itama ta samu wuri har aiken 'ya'yan gida take yi. Bayan dauko ta akayi dan yara su huta. Momi dariya kawai tayi domin ta saba da wannan korafi na salma. Sun shiga dakin da Hajiyar bichi take ciki don su gaida ta. Tana taya momi zuzzuba turaren wutar da ta gama hadawa. Wanda take sanyawa a gidanta. Turaren wuta irin na 'yan maiduguri. "Lah Hajiya dama ke kike hadawa mariya turaren nan in munzo roqo ta ringa yi mana yanga"? Salma ta tambayeta. Hajiyar bichi tace" "ita take hada kayanta da kanta. Qarasa zuba mata a kwalba kawai nake. Kuma yadda naga tanayi kamar ma bashida wuya sosai. Sam bashida wuyar hadawa idan akwai kayan yi a garin nan. Ai gata nan ta iya hadawa zamanta a maiduguri saida ta koya a wurin wata qawarta. Sai dai in kiwa ce irin tata. Amma ba wanda bata iya hadawa ba. Harda turaren humra". Duk suka sa dariya. Salma tace "ai kuwa da zaki hada zan samo miki har masu saye. Kuma inaga kamar ana sayar da kayan turaren a kasuwar kurmi. Kinsan yanzu akwai kanuri mazauna kano da yawa". Bayan komawar Hajiyar bichi momi ta cigaba da sayen kayan turaren wuta tana hadawa masu qamshin gaske. Masu tsada da kuma masu sauqin kudi. Kuma duk salma ce tayi mata hanyar masu sayen. Sadiya kuwa kamar domin ita aka fara hada turaren wutan nan. Tun tana kama ma momi suna yi tare har saida takai sai dai momi tace mata hada turare kaza mai giredi kaza. Tas kuwa zata hada shi. Zamanta da Momi ta koyi abubuwa da yawa bama ya kwalliya da gyaran jiki. Su anti salma da suke kyararta an kuma dawo in zasuyi baqi ko miji yayi tafiya zai dawo a roqi momi ta basu aron sadiya ta taimaka musu da girki da gyaran gida. Wata umara da Momi da salma suka tafi tare nan gidan aka kawo yaran salma suka zauna daga su sai maigadi da kuma matar maigadin da take taimaka musu da wasu ayyuka. Har Allah ya dawo dasu lafiya suka tarar da yara fes dasu. Ba'a taba lattin makaranta ba ko qin zuwa islamiyya. Haka nan home work na makaranta duk sadiya na tsaye akai. Akwai wasu mutane da Allah kan hallita tun suna qanana sun iya kula da na kasa dasu da kuma tattali. To haka sadiya take. Tana da himma wajen tattala yara da kuma qoqarin gyara waje. Ko kiranta momi tayi indai ta durqusa a kasa sai ka ganta tana tsince-tsince akan carpet. Ko dan tsinke ta gani to saita dauke shi. Kullum momi in taga tana wannan abun sai ringa tsokanar ta tana fadin "sadiya karfa muje gidanki ki bamu tsintsiya kice mu share qafarmu kar mu shigar miki da datti". Dadi ne mai tare mata yace "gwara ace kayi tsafta da ace ka fiye datti." hausawa kance halin mutum jarinsa. Da wannan dabi'a tata sadiya ta shiga zuciyar jama'ar momi da dama. *********************** Sadiya nada shekara goma sha biyar wanda yayi dai dai da zamanta dasu shekaru hudu. Ta rubuta jarrabawar qaramar sakandire a makarantar su Amir. Wadda a wannan lokacin ana yinta ne domin tantance ajin da ya kamata yaro ya shiga. Ko dai ya shiga ajin koyon kimiyya watau science a ajinsa na hudu a sakandire. Ko kuma ya shiga na koyon kasuwanci watau commercial class. Ko kuma ya shiga art class. Wanda zai bawa yaro damar karanta kwasa-kwasai irinsu law da makamantan su a jami'a Lesson da ake yi mata a gida ya wadatar da ita har takai wannan mataki. A kuma wannan lokaci ne suke qoqarin karasa yin saukar Alqur'ani ita da Amir =======***15***======= A gaskiya bata cika son zuwan anti salma gidan ba. Saboda kyararta da tsangwama da take yi mata. Ita a dole momi saita banbanta ta da 'ya'yanta. Watau ta nuna mata ita 'yar aiki ce. Amira ce ta fito da tiren da sadiya ta shirya. Tana jiyo anti salma tana mitar watau itama ta samu wuri har aiken 'ya'yan gida take yi. Bayan dauko ta akayi dan yara su huta. Momi dariya kawai tayi domin ta saba da wannan korafi na salma. Sun shiga dakin da Hajiyar bichi take ciki don su gaida ta. Tana taya momi zuzzuba turaren wutar da ta gama hadawa. Wanda take sanyawa a gidanta. Turaren wuta irin na 'yan maiduguri. "Lah Hajiya dama ke kike hadawa mariya turaren nan in munzo roqo ta ringa yi mana yanga"? Salma ta tambayeta. Hajiyar bichi tace" "ita take hada kayanta da kanta. Qarasa zuba mata a kwalba kawai nake. Kuma yadda naga tanayi kamar ma bashida wuya sosai. Sam bashida wuyar hadawa idan akwai kayan yi a garin nan. Ai gata nan ta iya hadawa zamanta a maiduguri saida ta koya a wurin wata qawarta. Sai dai in kiwa ce irin tata. Amma ba wanda bata iya hadawa ba. Harda turaren humra". Duk suka sa dariya. Salma tace "ai kuwa da zaki hada zan samo miki har masu saye. Kuma inaga kamar ana sayar da kayan turaren a kasuwar kurmi. Kinsan yanzu akwai kanuri mazauna kano da yawa". Bayan komawar Hajiyar bichi momi ta cigaba da sayen kayan turaren wuta tana hadawa masu qamshin gaske. Masu tsada da kuma masu sauqin kudi. Kuma duk salma ce tayi mata hanyar masu sayen. Sadiya kuwa kamar domin ita aka fara hada turaren wutan nan. Tun tana kama ma momi suna yi tare har saida takai sai dai momi tace mata hada turare kaza mai giredi kaza. Tas kuwa zata hada shi. Zamanta da Momi ta koyi abubuwa da yawa bama ya kwalliya da gyaran jiki. Su anti salma da suke kyararta an kuma dawo in zasuyi baqi ko miji yayi tafiya zai dawo a roqi momi ta basu aron sadiya ta taimaka musu da girki da gyaran gida. Wata umara da Momi da salma suka tafi tare nan gidan aka kawo yaran salma suka zauna daga su sai maigadi da kuma matar maigadin da take taimaka musu da wasu ayyuka. Har Allah ya dawo dasu lafiya suka tarar da yara fes dasu. Ba'a taba lattin makaranta ba ko qin zuwa islamiyya. Haka nan home work na makaranta duk sadiya na tsaye akai. Akwai wasu mutane da Allah kan hallita tun suna qanana sun iya kula da na kasa dasu da kuma tattali. To haka sadiya take. Tana da himma wajen tattala yara da kuma qoqarin gyara waje. Ko kiranta momi tayi indai ta durqusa a kasa sai ka ganta tana tsince-tsince akan carpet. Ko dan tsinke ta gani to saita dauke shi. Kullum momi in taga tana wannan abun sai ringa tsokanar ta tana fadin "sadiya karfa muje gidanki ki bamu tsintsiya kice mu share qafarmu kar mu shigar miki da datti". Dadi ne mai tare mata yace "gwara ace kayi tsafta da ace ka fiye datti." hausawa kance halin mutum jarinsa. Da wannan dabi'a tata sadiya ta shiga zuciyar jama'ar momi da dama. *********************** Sadiya nada shekara goma sha biyar wanda yayi dai dai da zamanta dasu shekaru hudu. Ta rubuta jarrabawar qaramar sakandire a makarantar su Amir. Wadda a wannan lokacin ana yinta ne domin tantance ajin da ya kamata yaro ya shiga. Ko dai ya shiga ajin koyon kimiyya watau science a ajinsa na hudu a sakandire. Ko kuma ya shiga na koyon kasuwanci watau commercial class. Ko kuma ya shiga art class. Wanda zai bawa yaro damar karanta kwasa-kwasai irinsu law da makamantan su a jami'a Lesson da ake yi mata a gida ya wadatar da ita har takai wannan mataki. A kuma wannan lokaci ne suke qoqarin karasa yin saukar Alqur'ani ita da Amir=***16***====== A wannan shekarar ne kuma sadiya ta kasance makerin yan mata ya fara kerata. Duk da bata gama zama cikakkiyar budurwa ba. Amma kallo daya bazai ishi mutum a kanta ba. Tana da sura mai daukan hankali. Gata fara mai kyawun fata. Hausawa sukace kowa yayi tsaho yayi rabin kyau. A miqe take sambal ga yatsun hannu dana kafa dogaye masu tsari. Gashin kanta kuwa anan aka zuba kyau. Baki ne sidik ga tsaho da santsi. Fuskarta na dauke da dogon hanci wanda ya dada kawatar da 'yar doguwar fuskarta. Digon dake lotsawa a dukkan nin kumatunta Yayin da duk tayi Murmushi. Shike dada kawata fuskarta. Bakinta dan daidai misali mai dauke da wushirya da kuma jerarrun hakware masu tsari fari khal dasu kamar zata tallan makilin. Idanuwanta kuwa farare ne khal sai digon bakin ya dada kawata su. Ko a lokutan da take yawan zubar da hawaye. Watau sanda tana gidan inna to kuwa tana gama kukan zasu koma da haskensu kamar batayi ba. Tana mutukar kama da innarta sai dai tafi inna da duk 'ya'yanta kyau. Yayan zaria nema suka so suyi kunnen doki. Amma tunda ita mace ce saita tsere masa. Tafiyarta a nutse tare da kuma taftarta ita take dada daukar hankalin mutane a kanta. Da Momi ta lura samari suna neman su fara kawo mata har sai ta fara kalleta Inba da dalili ba bata barinta ta fita. Momi ta horeta da kwalliya da tsafta. Dokar gidan ce koba makaranta. To kana tashi da safe wanka zaka fara yi. In kuma kana da aikin yi to da ka gama sai wanka. Momi tana kokarin gyara amira da kuma sadiya. Koba inda zasuje cikin kwalliya zaka same su. Shiyasa da ance tashi muje mu. Sai dai daukan mayafi da takalmi. Babu wanda zaiga sadiya yace mai aiki ce a gidan momi. Yadda su amira zasu wataya haka itama. Irin fadan da za'ai musu in sunyi laifi. Shi za ai mata in tayi irin laifin.=====***17***===== Momi kuma irin matan nan ne masu wayon zama da yara da jansu a jiki. Duk abinda suke ciki ta sani saboda yawan hira da takeyi dasu. Da kyar kaji tana hargowa da sunan yiwa yaro fada. Sai dai nasiha da lallashi. Laifin da yafi jawo maka hukunci a gidan shine karya. Amma duk laifin da zakayi in dai ka fadi gaskiya to za'a sassauta maka hukunci. Haka baka isa kayi gulma ba ko ta waye to za'a titsiyeka a gaban sa. Ka maimaita abinda ka fada. Har abada dan adam yana tare da jarrabawa mussaman mumuni. A wannan lokacin sadiya ta hadu da tata jarrabawar ta farko. A dalilin karin girma da Dadi ya samu. Inda ya samu nasarar komawa jami'ar Wisconsin ta kasar america inda zai jagoranci bangaren kere-kere watau faculty of engineering. Wannan daukaka da Dadi ya samu shiya fara jefa sadiya cikin mawuya cin halin da ta shiga. Tunda aka fara maganar su momi zasu koma America. Kusan kullum sai sadiya ta kulle kanta a bandaki tayi kuka. Ga kukan rabuwa da wadanda ta saba ga kuma tararrabin rayuwar da zata koma a gidansu. Tasan dai karatu kam yasha ruwa. Momi ce ta kwalla mata kira amira ta amsa da tana bandaki. Momi ta sake kiranta akace bata fito ba. Amira tana dariya tace "momi yanzu kullum sadiya sai ta kulle kanta a bandaki bansan me take yiba kuma sai ta dade sosai bata fito ba." momi tasha jinin jikinta. Kasancewar ta mace mai lura tuni ta gano inda zancen Amira ya dosa. Domin itama ta lura da yanda sadiyan tai laushi kamar mara lafiya. Ga kuma dariyar yake data maye gurbin far'arta. Bayan bayanin da Momi tayiwa Dadi tare suka zaunar da ita sukai mata nasiha mai ratsa jiki. Dadi ya nuna mata cewar babu wani dan adam da zai isar wa wani inba Allah ba. Haka zalika ta kasance mai roko da kuma dogaro da Allah amma ba bawansa ba. Ya nuna mata addu'a ce kawai zata tsaya mata amma ba wani mahaluki ba. Momi tace nidai Dadi da iyayenta zasu yarda da sun bar mana ita. Idan ta isa aure sai mu dawo da ita. "A'a momin Amir karki dada karya mata zuciya akan abinda bazai yuwu ba. Wata kasa fa zamu tafi. Kinsan kuwa da wuya su yarda mu tafi musu da 'ya. Ba naga da kyar ma suka yarda take zama da muba. " Duk da wannan nasiha da suka yi mata ranar da zasu tafi kuka ba itaba ba momin baba kuma su Amir ba. Khalifa kuwa da ya budi ido ya ganta a gidansu. Ya dauka 'yar gidan ce. Duka duka baifi shekara ba tazo gidansu. Don haka shi a sanin da yayi mata itama 'yar gidan ce. Ko banza kuma dama tafi shiri dashi akan duk yaran. Tafi kowa tattalinsa da kuma daurewa al'alarsa. Da yaga kowa ya shiga mota. Sai kiranta yakeyi tazo su tafi kar a tafi a barta. Da kyar aka lallabeshi. Tafiyar su ita ta maida sadiya zaman gidan inna tare da tarin alherin da ta samu daga momi. Wanda ya hada da kudi da kuma tarin sutura. Wanda tasan ba ita zata mora ba. Sai kuma ilimi da kuma kyawawan dabi'u wanda su kam ta hakikance lahu suke a gareta. Babu me ara babu mai karbewa sai dai in mutum yaso ya koya. Ga kuma tarin nasihohin da Dadi da Momi suka yi mata. ======***18***====== Kudin aikinta dai babu wanda ya more su kamar yaya baba. Domin dasu aka sai masa mashin. Aka gyara masa dakunan da suke waje aka kara masa daki daya. Ga kuma lefen sa na aure. Duk daga wahalar ta ta shekaru hudu. Gidan kam yayi kyan tsari. Domin hatta dakunan inna da kuma rumfarta an shafe su tare da canja musu kyamare da kuma tagogi. Tsakar gidan ma an raba shi biyu. Aka ware wa yaya baba nasa. Aka fitar masa da bandaki da kicin. Dawowar sadiya ta tarar harda shirye-ahiryen auren yayan zaria akeyi. Tayi masa murna kwarai. Amma shi baisan dalili ba sai yaji yana jin kunyar sadiya yana ga kamar yayi mata laifi. Ganin inna ta auren yaya baba kawai take yi. Gashi kuma ta dage sai sani ya fito an hada da nasa. Yaso ta barshi ya karasa karatun sa tunda baifi saura wata tara ya kammala ba. Koda zai tafi bautar kasa ne sai ayi bikin amma ta dage ayi a haka. Fahimtar da sadiya tayi yayanta na cikin tashin hankali gashi ba zai iya ketare maganar inna ba. Ya sanya ta same shi a dakinsa na zaure. Inda suka koma shida Salisu kasancewar yaya baba zai zauna a wajensu nada. A hankali ta sudade ta same shi a dakinsa. Kunyarta yakeji sosai ya kasa ko hada ido da ita. Ita kam bata kula da wannan sabon canjin data gani ba. Kokarinta ta bashi abinda ta kawo masa. Makudan kudi ta kullo ta ciro daga cikin zaninta ta mika masa. Da sauri ya dago fuskarsa ya kalleta alamar neman bayani. "Kudin da Dadi ya bani ne akan inci gaba da biyan kudin makaranta ko kuma in nemi sana'ar da zan yi. To ni banga yiwuwar ko daya daga cikinsu ba. Kuma naga kamar zaka jawo min delay zuwan yayata. Kuma dama gaskiya kai nayi niyyar bawa koda ba aure zakayi ba. " Shidai ya kasa magana saboda mamaki. Ya rasa mai zaice mata. Kafin yayi magana. Ta sake cewa. "Amm Idan yayata tazo sai in koma inyi mata zaman daki. Kaga saika maida ni makaranta in samu in karasa. Nasan Insha Allahu inna bazata kiba. Tunda naga kamar yanzu muna shiri da ita ba kamar daba da take yimin fada. Abinda bata gane ba shirin inna da ita na ganin tana kawo mata abin duniya ne. Tunda zamanta a gidan momi yasa momi da kanta. Tana yawan yi mata alheri mussaman kayan sawa da abinci. Momi da Dadi Allah ne ya hada su dukkaninsu hannayensu a sake suke. Mutane ne masu son yin alheri mussaman ga mai karamin karfi. Kuma dadin dadawa Allah ya hore musu abinda zasuyi alherin dashi. Tana dariya ta mike da niyyar ficewa har ta fita ta dawo "don Allah karka gayawa kowa". Kafin ma yayi magana ta fice daga dakin. Ta kuma taki sa'a har taje ta dawo ba wanda yaga shigarta da fitarta. Washe gari gidan yaya kulu ya nufa da makudan kudin sa. Suka shiga kasuwa ta hada masa lefe Masha Allah. Su kansu su inna sunyi mutukar mamaki da kayan daya hado. Don har yafi na yaya baba da aka kai. Anan ne shi yaya baba ya ringa gunguni yana fadin "dama munafunci ne don karya taimaka min da komai. Anyi magana yace shi dan makaranta ne yanzu a gidan uban wa ya samo wadan nan iyayen kaya. Shi dai bai tanka masa ba. Yaya kulu cema ta cashe masa wannan karon ta nuna masa inzai mike ya mike don ba wanda zai rike masa mata in tazo. Shi kadai zaiji da kayansa. Ga mashin an saya masa saidai yayi wanka ya fice yawo cikin gari. Ba yadda bata yi da shiba akan ya dinga acaba. Yace yafi karfin haka. Inna kuma ta goya masa baya. A dalilin wai kwanaki ta samu labarin wani daya dauki fasinja zai kaishi wani waje. Saida sukaje inda ba mutane yayi masa duka ya kwace mashin din. A wajen gida ne sani yace zai nemi dakin haya anan unguwar. Amma sai inna tace ga gidan marigayi kawunku isiyaku ba sai ka gyara ka zauna ba kafin Allah ya baka naka. Da kansa ya tafi wajen kawunsu labaran don ya hana inna wannan kudiri nata wanda a ganinsa zalinci ne. Kawu labaran ke rike da gonakin sadiya na gado guda biyu da kuma hayar gidan data gada daga gun babanta. Hatta kudin hayar shiya ke karba da son ya sakata a makaranta. Amma ganin yadda inna ta ture maganar karatun shima sai yayi mata wani shirin da kudin hayar.======***19***====== Inna da Kawu labaran da kuma sani a tsakar gida suna tattauna batun gidan da sani yake so ya zauna. Inna ta matsa da sai sani ya zauna a gidan tunda basu da nisa. Nan ne baya da su kadan duka - duka tafiyar minti biyar ce zuwa bakwai daga gidan inna zuwa gidan. Dagewar da inna tayi yasa Kawu labaran yace a kira sadiya a tambayeta ra'ayinta in ta yarda dan uwanta ya zauna shike nan. Sani bai so haka ba don yasan sadiya bazata taba hana shi kayanta ba. Da aka kirata kuwa da murnarta tace "to ya zauna mana da wani ba gwara shi din ba" Kawu yace to "dole ya biya ki kudin haya" tana dariya tace to ya ringa biyan nera goma. Allah kuma daga hak baza'a kara ko kwabo ba. Kowa yasa dariya a wajen. A ranar sadiya taji kalmar da bata taba jin inna ta kira mata ba watau kalmar Allah yai mata albarka. Har ta mike zata tafi Kawu ya dakatar da ita ya zaro wasu takardu daga aljihunsa. Yace kinsan gonarki ta hanyar gaba da kasuwar tarauni (farm center a yanzu) to gwamnati ta yanka filaye a wajen wanda duk yake da gona an bukaci daya biya wasu kudade ayi masa takardun shaidar mallakar fuloti a madadin gonar. To nima nayi miki amfani da kudaden hayarki na biya. Wannan takardun ne. Inna dai murnar danta ya samu muhalli yasa sai murna take yi tana addu'ar Allah dai yabar zumunci. Cikin farin ciki wannan taro ya watse. An sanya bikin Auwalu da sani sati hudu masu zuwa. Wannan yaba sani damar kammala gyaran gidan da zai zauna mai dauke da dakunan barci biyu da falo a tsakiyar su. Sai dan karamin tsakar gida mai dauke da dan madai daicin bandaki da kuma kicin. Akwai soro da kuma karamin daki wanda za'a iya amfani dashi a matsayin daki ta cikin gida ko kuma shago ta waje. Ana saura sati daya daurin aure Allah yai ikon sa akan mahaifin Zainab watau yarinyar da sani zai aura. Ana tunanin daga biki su Kawu labaran suka ce a'a. A daura aure akai amare sai dai a rage bidi'a. Ana cikin wannan alhini sai ga sako daga mahaifiyar ita Zainab din akan ta fasa ita 'yarta bazata auri dan makaranta ba sai dai ya hakura da auren kafin nan itama tata 'yar ta fara makaranta sai ayi auren. Inna ma tai tsallen albarka tace itama danta bai isa daukar nauyin karatun wata ba tunda yanzu yake taso wa. Tashin hankali ba'a sa maka rana. Duk da auren hadi ne amma hankalin sani ba karamin tashi yayi ba. Su kawu labaran sunje domin a samu maslaha amma ta kekasa kasa taki ta kuma ce duk duniya ba wanda ya isa ya aurar mata da 'ya. Sai dai in sun yadda da wannan sharadi nata. Inna ta dage mahaifiyar zainab ta dage. Har ranar daurin aure babu wata sahihiyar magana. Ana zaune anyi jugum jugum harda su sadiya a zaune a falon inna sai ga wata kawar inna mai suna marka. Ta juya ta kalli inna wacce ke faman share kwalla tana takaicin wannan wulakancin da aka yiwa danta. Tace nifa tasallah da gangan kike wannan kuka. Ga magani a gonar yaro amma ciwo zai kashe shi. " Me kike nufi inji inna. "Zi muje daga ciki ai shawara ce gwara mu kebe. Sun dade suna tattaunawa. Inna ta fito tasa aka kira mata kawu labaran. A dakin zaure suka tsaya suka tattauna. Sannan ya fita waje. A kaje aka daura auren yaya baba da amaryarsa huwaila. Sannan aka dawo nan kofar gidansu aka daura na sani. Sadiya na zaune kawu labaran ya shigo gidan ya kirata cikin dakin inna. Itama Innar tabi bayansu. Cike da ladabinta na hallita ta durkusa. "Gani kawu " ya sanya hannu a cikin aljihunsa ya dauko kudi daga ciki "ungo ya mika mata. Hannunta na rawa tasa hannu ta karba. "Kirga mu gani " ta kama kigawa Amma ba a nutse ba. Kawu yace nera dari biyar ne kuma kudin sadakin kine. An daura miki aure da yayanki sani. Ya dakata yaji ko zatayi magana yaji tayi shiru. Ya cigaba da yi mata nasiha. "Munsan ko a inane ke mai rufawa dan uwanki asirice. Kuma kowa ya lura da hankalinki munsan bazaki watsa mana kasa a ido ba. An daura miki aure da sani! An daura miki aure da sani! An daura miki aure da sani! Shi kadaine abinda kwakwalwarta take iya wassafa mata duk sauran zancen kawu sama sama take jinsu ta kasa ko kwakwaran numfashi. Shi kuwa ko ya kula da halin da take ciki ko bai kula ba. Sai nasiha yake ta tsaro mata. Yana dada nuna mata falalar yin hakuri da kama yadda da kaddara mai kyau ko mara kyau. Inna tace balle wannan ai kowa yasan kaddara ce mai kyau. Auren miji irin sani ai sai wanda bai samu ba. Magori kenan wasa kanka da kanka inna dai tana son son 'ya'yanta. Kuma a ganinta sunfi na kowa.======***20***====== Shigowar yaya kulu ne wanda yai dai-dai da fitar kawu da inna daga dakin wanda kuma ya bata damar hadiye wani abu daya tokare mata wuya. Sai a lokacin taji hawaye ya ya zubo mata. Ta fada jikin yaya kulu tana fadin INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN. Yaya kulu ta rungumeta tana fadin yi hakuri bari kuka. Duk abinda ya sami bawa da sanin Allah. Amma ni inaga hadin aurenki da sani Insha Allahu alheri ne. Cikin muryar kuka tace yaya baya sona nima bana son shi kuma yaya karatu nafa? Yaya kulu tace karatun ba inace kin dade da barinsa ba. Ba tare da sanin Dija na tsaye ba duk ta fayyace wa yaya kulu yadda duk akayi tun zuwan momi tambayar ta da tayi akan ta barta ta sata a makaranta har jarrabawar data zata. Take zaman jiran sakamako. Harda shirin da tayi na komawa gidan sanin da zama domin ta samu damar komawa makaranta duk ta fada mata. Zancen kudin da tabawa sanin ne kawai bata fada ba. Yaya kulu tayi Murmushi tace "to in banda abinki keda zaki gida matar gida tadan sammiki guri ki zauna in bataga dama ba ta kore ki. Allah ya musanya kece da gidan gaba daya me kuma yafi haka? Ni nasan Sani yana sonki koda kuwa kauna ce ta jini amma nasan duk wani buri naki zai taimaka miki dashi. To kuma ke matar malamin makaranta har a gaya miki karatu. Karatu ai sai kinfi Mongo park " maganar yaya kulu ta sanya ta murmushi ganin hakan ya sanyaya ran yayan. Ta dora da cewa "kuma ki kalli kanki a mudubi shi sanin inba don darajar zumunci ba ya isa a bashi ke?" Muryarta a dan raunane wadda ke nuna alamun kukan da tayi ya dan sa zuciyarta tayi sanyi fiye da sanda taji maganar tatsuniyar aurenta. Cikin sanyin murya tace " kai yaya to dame na fishi? "Kaji min shakkiyya ina kushe shi kina kare shi. Kuma kina kukan an aura miki shi. Itama yayan ta amsa mata. Amma duk da haka zaka gane farin cikin da ke tattare da kalamin nata. Saboda ganin canjin da tayi a tare da sadiya wanda yake nuna alamun ba zata sha wahala wajen rarrashinta ba. "Kai yaya ba haka nake nufi bafa. Ta fada tana mai jin kunya. Dija ta juya da baya ba tare da sun ganta ba. Ta samu inna a waje daya ta zayyane mata labarin karatun da sadiya tayi a gidan aikin da aka kaita. Inna ta tabe baki tace "duk ya zama na banza tunda dai sai yadda naso za'ayi" Yinin biki ya kacame a gidan amarya huwaila da angwaye auwalu da sani duk wannan badakala da akeyi sani baida masaniya. Shi dai daga daurin auren auwalu wucewa yayi shagon abokinsa sa'idu tare suke koyarwa a makarantar islamiyya. Dake unguwarsu. Shima yazo hutu daga inda yake nasa karatun a jami'ar maiduguri. Samun dakin da yayi a bude ya shige ya cire babbar rigarsa ta angwanci yayi kwanciyarsa. Da yaga tunanin abinda mahaifiyar zainab tayi masa yana neman ya haddasa masa ciwo. Sai ya mike ya dauro alwala yayi nafila. Bayan ya sallame ya dora da karatun kur'ani mai girma. Ya gama baqara ya fara ali'imrana yaji himma ta dame shi ya ajiye Alqur'anin son ya dan kishingida barci mai nauyi yayi awon gaba dashi. Rabon da ya samu barci tunda aka fara rigimar aurensa da zainab. Duk da dai daki bai koma gwauro ba amma yaji ba dadi da wulakancin da akayi masa. Yana kwance yayi mafarkin abokansa sunzo suna ta neman sa wai don su gaya masa an daura masa aure amma basu ganshi ba. Hayaniya ce ta tashe shi yaji ana gashi nan. Mafarkinsa mai dadi suka katse masa. Sa'idu sale ne ya daka masa duka yace "tashi duk mun hada gari Muna yawon nemanka ashe kai kana nan. Jin dadi ma kake harda barci " "Yo mai zai hana shi barci yasan abinda ya taka banda takalmin kafarsa. Inba haka ba ace an hana mutum aure amma har ya samu sararin yin barci" inji wani daga cikin mutanen da suka shigo dakin "ka tashi muje muyi gaisuwar surukai mu kuma fara shirin saida fura. Shi dai inda kasan rakumi da akala. Haka ya dinga biye musu. Hatta babbar rigarsa sai daya daga cikin abokan ne ya saka masa. Tunanin sa daya in ya tuno irin cin mutuncin da mahaifiyar zainab tayi masa kwana uku daya wuce yasan ba dattijuwa bace wannan ya sanya masa tsoron zama da 'yarta yasan bazai samu zaman lafiya da ita ba. Yana cikin wannan tunani har suka iso gida. Gaba dayan su suka dunguma cikin gidan inna. Suna shiga cikin gidan mata suka lullube shi da guda "ga Ango ga ango" wata mata ta daddage ta rangada masa guda a kansa. Shi dai dariyar yake kawai yake yi "ga angon sadiya" inji wata abokiyar wasansa data fito daga cikin rumfar inna. "Sadiya kuma wasu daga cikin abokansa suka fada wani daga cikinsu yace na dauka sunanta zainab. Shi kam ogan angwaye tsananin mamaki ya hana shi magana. Kansa gaba daya ya dauki caji. Ya kasa tuna wacece sadiyan da inna ta aura masa fitowar yaya kulu ita ta warware masa duk abinda ya faru. Farin ciki da kuma mamaki su suka taru suka cika masa zuciya wanda kuma zuciyarsa ta gaza boyewa har saida ya nuna a fuskarsa. Ya kasa yiwa yaya kulu magana. Fahimtar halin da yake ciki ya sata basu umarnin shida abokansa suje su cigaba da zaman angwancinsu. Masu taya shi murna da masu taya shi mamaki a cikin abokansa suka rankaya suka fita zuwa shagon sa'idu don cigaba da zamansu na angwanci.=====***21***====== Kawu labaran yaso ya daga tarewar sadiya koda zuwa sati na sama don a shiryawa sadiya kayan daki. Amma inna ta dage a tare kawai a Washe gari. A zaton kawun tunda kudin aikinta na hannun ta dasu zata hada mata kayan dakin. Tunda shi kam sadakin daya biyawa angwaye da kyar ya hada shi. Inna kuwa tayi haka ne dan kar kawu ya fahimci kudin sadiya dai babu su duk da tana da bakin da zata kwaci kanta. Amma duk da haka bata son a daga maganar. Sabuwar katifar da yaya kulu ta daure ta siya zata gyara dakinta ita aka dauko aka sa mata a dakinta ko arzikin zanin gado bata samu ba. Kudin sadakin ta dashi yayan ta kukuta tasai mata ledar tsakar daki da kuma 'yan kayan girki dana anfanin tsakar gida. Bayan ta gama da wannan ita ta daddage tana ta faman tattausar sadiya don ma tayi sa'a ita yarinya ce mai jin rarrashi da kuma saurin karbar nasiha. Aure kamar na 'yar tsana haka aka tattara sadiya aka mikata gidan da sani ya tanada domin rayuwarsa da zainab sai dai cikin hukuncin ubangiji ya zama nasa da kanwar sa sadiya. Amarya huwaila ta tare a sashen ta na cikin gidan inna da jerenta kamar zai zuba a kasa don yawansu. Ga kuma tarin gara kamar ta 'yar sarki. Saboda mahaifiyar ta irin matan nan ne masu nema don su huce takaicin su. Ga kuma mahaifinta shima yana da abin hannunsa. Wannan dukiya da aka nannago mata ita ta kara mata farin jini a wajen inna da Dija. Sadiya zaune a tsakar dakinta wanda yafi kama da zaure saboda rashin komai a cikinsa. Kan ledar tsakar dakin take zaune inda su yaya kulu suka tafi suka barta da tarin nasihohi da kuma ban baki da sukaita zubawa kamar sa ari baki. Ita da wasu makotansu da da dangin mahaifinsu. Har yanzu bata daina mamakin wai itace matar sani ba. Murna zatayi ko bakin ciki bata tantance wanne zatayi ba. Bata fita daga wannan alhininba taji muryar maza sunai mata sallama. Dada kudundune kanta tayi ta kuma amsa musu a ciki. Su hudu ne ta cikin mayafinta ta shaida su. Dukkaninsu sadiya ta sansu. Abokanan sani ne tun wanda sukai primary tare. Daya daga cikinsu tare suke koyarwa a islamiyyar nan unguwarsu. Gaba dayan su suka zauna a tsakar dakin suna masu fuskantar inda ta zauna. "Amarya bude fuskar mana mu ganki kema kiga angon naki " inji daya daga cikin aboka nansa. Ita dai tayi shiru bata matsa ba. Wani daga cikinsu ya bada umarnin a bude taro da addu'a ta cikin mayafinta ta daga hannu sukayi addu'o'i masu nagarta suka kuma nemawa ango da amarya zaman lafiya. Tare da ita suka shafa. Aka fara barkwanci irin na angwaye da amare duk da dai ita kam babu kowa a tare da ita sai wata 'yar yar mijin yaya kulu. Da suka zo bikin tare kusan sa'ace ga sadiya shine dalilin da aka barta ta tayata zama kafin a gama sayen baki. Amarya taki magana balle ta bude fuska. Abokan ango sun taya da kudi amma batayi magana ba. Ko nawa suka fada saita girgiza musu kai har suka gaji suka mika biro da takarda wai ta rubuta musu ko nawa ne bakin nata. A wasance wani daga cikinsu ya aikata hakan. Amma ga mamakin su sai suka ga ta mika hannu ta karba. Tayi rubutu a ciki ta mika musu. Sani yayi bismilla ya bude ya karanta sakon amarya kamar haka "na saida bakina in har yaya sani yayi min alkawarin ci gaba da karatu na" tofah kai sani wannan amsa a wajenka take Duk suka tuntsire da dariya. Sani ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa duk sunai masa dariya. Fadi yake aiki babba ya same ni ku dariya ma kuke yi. ***22***======= In za'ayi magana da gimbiya mutum nutsuwa yake yi. Ya dai-daita zaman hular kansa ya ajiye babbar rigar tasa a kan cinyarta "ungo wannan rike mu gani rigar girma ce. Kinsan sai girma ya hau kanka kake mallakarta " ya juya inda abokansa suke suna ta tintsira dariyar wannan drama da ango ya gwagwafe yana yiwa amarya. "Kalle su duka wa kika gani da shiga irin tawa. Ai sai ni da Allah ya martaba yau dinnan. " ita dai da kyar ta kunshe dariyar da take cikinta. Mamakin yayanta take dama yana sake wa da mutane har ya ringa abin dariya irin haka. Suma abokan mamakinsa sukeyi domin basu taba ganin kalar wannan sanin da suka gani yau ba. Wani irin tsugunno yayi a gaban sadiya wanda yai kama da mai yinsa yana gaban principal ko kuma gaban mahukuntan sa a lokacin da yayi laifi. Saboda nutsuwar da yayi. Ya kamo hannuwanta guda biyu ya rike cikin nasa. Ya dai-daita muryarsa ta hanyar gyara ta sannan yace " ni sani mijin Kanwata sadiya nayi alkawarin zan bar mata ta Kanwata kuma masoyiyata tayi karatu har iya son ranta. Mutukar yin hakan bai kaucewa shari'ar musulunci ba. So help me ALLAH. Dukkan ku ina son ku shaida wannan alkawari da nayi mata." "Amin kuma mun shaida " duk suka amsa cikin dariya. Bayan an shafa sadiya ta dan janye mayafin data lulluba har ya sauka daga kanta gaba daya saida sukayi tasbihi saboda kyawun hallitar sadiya da suka gani. Dakin ya dauki shiru na dan wani lokaci. Mamakinsa suke yi da ya tsaya wai har saida innarsa ta gano masa sadiya shi bai ganta da kansa ba. Shi kansa sani sai yaga kamar bai taba ganinta ba sai yau. Wani irin kyau ya lura tayi da bai taba tsammanin akwai mai irinsa ba. Bai San sanda ya jawo mayafinta ya dada rufe mata fuska ba. Gaba daya suka tuntsire da dariya domin sun fahimce shi kar a kalle masa mata ne ya sanya shi yin hakan. Sa'idu sale ya fara mikewa yana fadin "inaga kamar an sallamemu kar ango ya fara kora da kara tunda dai yayi da hali mun gani" duk suka mike suna yi mata sallama. Dayaje raka sune kuma suka bashi kudin da suka tanada wanda abokanai ke tabawa domin sallamar 'yan mata wajen saida fura da kuma alibidi. Banda na sayen bakin. Shi wannan hadashi sukai suka ajiyewa sadiya. Sannan suka yi mata sallama suka fita. Ya fita raka su bai dawo ba sai bayan kimanin awa daya. Saboda sai da Abokanan sa suka sake hada kudi suka sai masa kayan shayi da biredi da kuma kazar amarya. =====***23***===== Ya shiga ya sameta zaune inda suka fita suka barta. Sani ya jima tsaye a kanta yana kallonta kafin daga bisani ya daure yayi magana da muryar da shi kansa baisan yana da itaba. "Tashi kiji magana zamu yi Kanwata. " ta gyara zamanta sosai ta fuskance shi ba tare da tace komai ba. Ya sake yin gyaran murya yace mata "Muna da tarin maganganu dani dake. Ga kuma gajiya da kike tattare da ita. Na kuma san harda yinwa. Saboda haka zaba mana wanda zamu fara yi " Muryarta adan dashe ta nuna alamun ta dade batayi magana ba tace " mu fara maganar da kake son muyi". Ta rasa dalili da yau kadai taji kunyarsa ta mutukar kamata "anya ayi haka inaga mu fara da sauke nauyin dake kanmu. Kinyi sallar isha'i? Daka ta amsa masa. "Very good yanzu je kiyi alwala kizo" A famfon tsakar gidan ta daura alwala yaja su sukayi sallar nafila. Tare da addu'o'in da suka kamata ango mai ilimi ya gabatar. Da wayo da dabara irin na wanda ya girme maka sani yaja hankalin sadiya taci abincin da ya shigo dashi. Ganin ta fara hamma yasa shi ya kwantar da katifar da take jingine a bangon dakin yayi mata matashi da babbar rigarsa ya sata ta kwanta. Kusan kwana sani yayi yana nafila yana godewa Allah na wannan canji da yayi masa. A gaskiya yaji hankalinsa yafi kwanciya da auren sadiya sama dana zainab. Washe gari su yaya kulu ne suka kawo mata akwatin kayanta na gida. Ita kam ganin akwatinta na gidan momi lafiya kalau tunda ta kulle shi da lambasted. Yafi faranta mata rai saboda kayan cikin sunfi kayan lefen da aka hadawa zainab yawa da kuma daraja. Ga kuma sarkarta full set mai dauke da abin hannu zobe sarka da dankunne. Gami da dankunnenta idon bazawara da sarkarta coka. Wannan duk alherin momi ne da kuma kudin da Dadi ya bayar a saya musu gwal ita da Amira a wani zuwa umra da suka yi. Yaya kulu tana dada tausarta take cewa kiyi hakuri yanzu zan koma gida akwai tumakin Abdurrahman da yake kawo a sayar aga koda gadon ne a saya miki da kudin" Ta numfasa Allah ya kyauta halin son zuciya. Yanzu haka na baro su suna ta rubibin raba garar huwaila bama wanda yake ko zancen naki kayan dakin. Wai ace abin duniya ya rufe wa dan adam ido har ya manta da darajar zumunci " sadiya dai batayi magana ba ta sake nisawa. "Kiyi hakuri kinji kawu ma yace bari yake gida ko anfanin gonarsa ne ya sayar ya dan hado miki gara kodan a taimakawa shi sanin" anan ma batayi magana ba. "Inna ce ta takura masa yayi auren nan amma ko ficika bata taimaka masa da ita ba sai ta auwalu take yi. In anyi magana tace ai yana koyarwa. To albashin islamiyya har wani abu ne da zai taimaka ma harkar aure. Kuma ma ince tana sane da cewa tunda ya koma makaranta scholarship ce take a gaza masa. Islamiyyar ba sai yazo hutu ne yake dan s............... shigowar sani dakin ce ta katse mata magana. Ya durkusa har kasa suka gaisa tana bashi baki akan yadda auren ya kasance. Da Murmushi a fuskarsa ya dan saci kallon sadiya yace "anya yaya ba gara da haka ta kasance ba. Nifa hankalina yafi kwanciya da hakan ta faru" "Kai ka ganmu da shakiyan yara ko dai dama da wata a tsakaninku ita jiya bayan daurin aure har kare ka takeyi a gaba na. Yanzu kai kuma kawo kana murna da auren dole da aka yi maka" dariya ya saka Yayin da sadiya ta rufe fuskarta don kunya. Yaya tayi murna tace Alhamdulillahi wannan matsalar ta kau sai muji da ta gaba. Tunda dai ma'aurata suna son juna ai shikenan " "Kai yaya Allah ni ba ruwana shine fa" "Eh na yarda ni din ne" sani ya bata amsa. "Nidai bari kuka inje inga yadda za'ayi a samo muku 'yan kayan amfanin gida" "Mh yaya ina zuwa bari na baki sako". Ta jawo akwatinta na gidan momi wanda ke gefenta sarkarta full set ta dauko ta mikawa yaya kulu "Gashi yaya ki sayar sai kiyi duk abinda zakiyi dasu" " anya kuwa ayi haka ke kuma ba zakiyi kwalliya da kayan ki ba. Kuma ba inace sarkar da Hajiya mariya ta saya miki ce ba."? "A'a ta bata amsa wannan wadda Dadi ya saya mana ce nida Amira. Ita momi kinga wadda ta saya min kuma yaya wannan din ta ishe ni sawa. Kuma ma kar inzo ban mora ba gwal da bashida wuyar faduwa". Sadiya bata bata damar kara magana ba ta dora mata gidan sarkar akan cinyarta ta mike ta fice daga dakin. A sanyaye sani ya bita da kallo har saida ta fice daga dakin. Ga kyau ga nutsuwa wanda aka dada kawatawa da kyawun hali mai nagarta. Mai kuma namiji yake bukata a zaman aure. Gyaran muryar yayan ne ya dawo dashi daga duniyar yabon matar da Allah ya mallaka masa badon halinsa ba sai don shi mai kyauta n izuwa bayinsa koda kuwa basu cancanci wannan kyautar daga gare shi ba. Yadda yayan ta kama shi yana kallon sadiya sai kuma kunya ta kama shi. Ya sunkuyar da kansa yana murmushin jin kunya. Ita kuwa tai kamar ma bata lura da halin shaukin daya shiga ba. Amma fa da za'a tona zuciyarta murna ce fal a ciki. Bayan fitarta ne sani yake gaya wa yaya yanda aka yi ya samu kudin da yayi hidimar aurensa wato wanda sadiya ta bashi. "To ka daiga irin hallacin da yarinyar nan tai maka. Ka rike ta amana." "Kinsan Allah yaya gwanda fa da haka ta kasance. Ni inaga kamar hakan ma yafi." tare duk suka sa dariya. =====***24***===== Daga gidansu yaya kasuwa ta wuce ta sayar da sarka. Donma karta dawo gida inna ta canja mata ra'ayi. Daga sabon gari ta dawo goron dutse ta sai musu saitin gado harda sif da divider na zamani. Ga saitin kujeru mai guda dai-dai guda hudu da kuma doguwa guda daya. Hade da teburin tsakiyar falo. Sarka tai albarka. Ba sai ga yaya ta hado harda labule da zannuwan gado masu kyau ba. Dan canjin da yayi saura dashi ta sai musu kayan masarufi. Ta isa gidan da kaya cikin akori kura. Tayi sa'a inna bata yi mata fada ba. Saboda ko banza zata so a gyara wa danta muhalli. Kuma sadiya ta fitar dasu zargin mutane da zasu ce ba'ayi mata kayan daki ba 'yar gudun mawar da ta tara ta kara bawa yayan tace "gashi koma bakin asibiti ki samo mata kayan jere " sai kuwa gata ta dawo da mai Ross guda shida da saitin samiru masu biyar guda goma. Gidan amarya yayi shar dashi. Inna sai washe baki tana gaya wa 'yan jere donma ba'a shiri akayi ba da sai yafi haka. Sani da sadiya ansha amarci. Ya samu sadiya fiye da duk yanda yake zaton zai sameta. Duk wani dadin dake cikin aure saida sadiya ta samar masa da mafiyinsa. Ladabi. Biyayya. Tsafta. Ga girki. Abin sai wanda ya gani. Dan kayan abincin da Kawu labaran ya hada musu a matsayin kayan gara sun taimaka musu kwarai da gaske. Ga kuma gwana wajen iya girki da aka samu. Wata ziyara da Abokanan sani suka kai musu har suka tsaya suka ci abincin dare a gidan. Wani daga cikin su fadi yake "kai da da wannan a gidan ku sakarci ya kaika neman aure a waje"? "Kyale shi mana inji wani cikin abokan nasa. Da yayi sanya sa ba Karamar asara zaiyi ba" Sani ya cigaba da zuwa makarantar sa zaria. Amma shaukin San zama da sadiya ya sanya shi safa da marwa tsakanin zaria da kano. Wani lokacin da yamma zai shigo ya koma da sassafe. Ko inna baya bari tasan da irin wannan zuwan nashi tunda tana korafin zuwa sati bibbiyun da yakeyi. Allah mai taimakon bawa a duk sanda yaso. Nauyin iyali daya hau kan sani sai kuma ya zamar masa sanadin samun wani rufin asiri. Wani mai sukani ne yake kokarin kammala digirinsa na biyu a kulliyar su sani. Ya bawa da yayi da kokarin sani mussaman fannin Arabic sai ya dauke shi aiki yana masa fassarar binciken da yayi na karatun da zai rubuta project din sa akai. Sani yayi anfani da wannan damar shima ya rinka rubuta nasa project din a lokaci guda da yakan taya wannan dalibin. Dan abinda yake bashi da kuma tallafin da gwamnati take bawa dalibai dasu yake biyan bukatun iyalinsa. Har ya samu ya kammala karatunsa. Auren sa nada wata biyar a wani hutu da yazo wa sadiya wanda daga shi inya koma to ya gama hada digirinsa. Yaga ya dace ya fara maganar karatunta so yake ya bata surprise tunda ya lura tana son tayi maganar karatun amma tana kawaici. Da kansa ya samo mata komawa makarantar su Amir inda ta rubuta jarrabawa. Aka bashi list din littatafai da kudaden da zai kashe na kudin makaranta da kuma kayan sawa na makaranta. Duk yayi kundunbala ya biya mata da dan abinda ke aljihunsa. Yasan dai ikon Allah ne zai kaisu karshen wata =====***25***===== Kafin ya karbi dan albashinsa sai kuma tallafin local government da akayi musu alkawarin basu a cikin wannan satin. Da kayan makarantar sadiya duka ya nufi gidan su domin ya sanar da inna. Bayan sun gaisa take masa mitar wahalar zuwa da yake akai akai ya fada mata ai hutu suke yi. Tayi dai mitar ta gama. Da kansa ya fara yi mata bayanin makarantar da zai maida matarsa. Ai kuwa ina wuta inna ta saka shi. Ta zage shi Tas tace bazata dauki yahudanci ba in aure sadiya zatayi tayi. In kuma karatu karatu. Har tana fadin ga dan uwanka nan uwa daya uba daya shi baka kaishi makarantar kudi ba sai matarka ko. Watau aure yafi dan uwa. To kuwa makwafinta zai hau shi zai shiga wannan makaranta" Gaba daya zufa ta karyo masa baya tuna komai sai alkawarin sa da sadiya ranar sayen bakinta. Haka nan jikinsa ba kwari ya tashi ya karasa gidansa. A falo ya ajiye kaya ya shiga bandaki ko ya rage zafin da inna ta hado masa. Sallamar sa ce ta fito da sadiya daga dakin. Bata ga mutum ba sai kaya a falon. Jin karar ruwa ya tabbatar mata da yana cikin bandaki. Ta fara bubbude kaya ai kuwa tana arba da kayan makaranta. Bata san sanda murna ta kwace mata ta saki shewa ba. Ya fito daga bandaki yana kokarin goge jikinsa. Ta saki kayan ta rike hannuwansa tana fadin nagode nagode Allah ya kara budi. Shi dai ya kasa yi mata magana. Ta daga wannan ta ajiye ta bude jakar littatafai ta futo dasu tana dubawa. Habawa da dadi ya kamata duk da kunya irin tata sai gata ta zubar da komai ta kaiwa sani wata irin runguma. Badan yana da karfi ba to da kuwa saita kada su gaba daya. Kuruciya ce ko kuma tsananin murna ce ta kasa gane halin da yayanta yake ciki. Ita dai sai nanata godiya take yi. Tana godiyar hawaye da kuma dariya duk gaba daya. Washe gari da sassafe ta kammala komai na gidan hatta abincin karyawa ta kammala tsaf. Kafin bakwai na safe kayan makaranta sun hau jikin sabuwar daliba. Ya kalleta tayi mutukar kyau sai ta dada koma masa wata 'yar yarinya ya tuna ko a jiya daddare saida ya kara kokarin rokon inna akan ta barshi ya maidata makaranta. Amma taki da ya isheta da mariya sai tasa masa kuka tana fadin iya zaman ta dashi bai taba yi mata musu ba amma yau akan sadiya yana neman ya bijirewa umarninta. A haka ya bata hakuri ya fito daga gidan. To yanzu kuma ga sadiya yarinyar da yake jinta a ransa kamar yayi mata numfashi. Irin son da yake mata badan tana da hankali ba. Babu abinda bazatai masa ba. Ya daure ya dauke fuskarsa daga kallonta "yaya na shirya muje ka karya kar kasa na makara" hannunsa ya miko yana daga kwance ta kama ta dauka taya shi zatayi ya mike daga kwanciyar. Sai ji tayi ya jawota jikinsa ta fada gadon. "Dan Allah yaya ka bari karka sa mu makara daure ka tashi ka shirya " zaton ta irin wasan daya saba yi mata ne. Don wani lokacin hakan yake mata. Ya juyo da fuskarsa idonsa a cikin nata yai mata kallon ido cikin ido ya daure yace "ni waye gare ki?" ta amsa "yayana" "Bayan haka fa? Mijina ta amsa masa. "Wace dama Allah ya bani a kanki? Shiru bata amsa ba. Nasan kinsan ina da damar baki izini ko in hana mutukar bai kaucewa addini ba. Dan Allah ka daina irin wadan nan maganganun ta fada muryarta na rawa. Dake nuna alamun karaya da maganganun sa. Tausayinta ya kama shi amma yasan dole ne ya zartar da hukuncin da bashida ra'ayi domin cika umarnin mahaifiyarsa. Ya daure ya dai daita muryarsa ya kuma kara daure fuska. Wanda Gaskiyar magana karfin hali kawai yake yi. Amma a zuciyarsa kamar shima ya fashe da kuka. Yace "indai na isa na fada ki ji to maganar karatu na soke ta. " Ai wallahi baka isa ba tab! Ina bama zan taba yarda ba" sadiya ta fada cikin wata murya mai nuna zafin rai da bai taba jin tayi magana da ita ba. "Nidai iyakar maganata kenan. Guda daya ce bata kai biyu ba. Ko kibi ko ki kauce wannan ya rage naki. Idan naki bi sai me" itama ta fada a gadarance. "Gwada wa zakiyi sai kiga abinda zai faru. Shima ya fada da dan zafin rai. A zuciyar sa kuwa fadi yake Allah taimaka min in samu in kubuta daga fushin mahaifiyata. H Inna ======***26***====== Bata tsaya taji abin da zai kara fada ba ta figi hijabin ta a saman kofa ta zura ta fice daga gidan. LAHAULAWALA WALA KUWWATA ILLA BILLAH. Ita kadai sani yake furtawa. Tashi yayi ya dauro alwala ya fara jera nafila yana mai neman dauki a wajen ubangiji. Sadiya data fita daga gida bata san inda zata nufa ba tafiya kawai take bata ganin hanya. Jefa kafarta kawai take bata san inda take wurgata ba. Idanuwanta sai zafi suke ta kasa zubda hawaye. Ga wani kullutu da yazo ya tokare mata kirjinta. Bata ko ganin gabanta. Karo data ci da dutse shiya sata dakatawa. Tana daga ido taga inda take kawai sai taji kuka ya balle mata. Ta zauna kan abinda taci karo dashi. Ta kuma kudundune kanta cikin hijabin ta tana wani irin gunjin kuka. Tun bayan fitarta sani ya dan jira ko zata dawo. Yaji shiru. Yaje makarantar da yai niyyar kai sadiya bata je ba. A wayence ya shiga gidan su ko can ta nufa babu ita. Ya fito ya shiga hayis ya nufi gidan yaya kulu amma itama bayan sun gaisa yaji tana tambayarsa sadiya ya tabbatar ba nan ta tafi ba. Daga nan ya nufi mariri gidan gidan kawu shima ya wayence da zummar yazo gaishe shi. Babu sadiya a gidan. Tabbatar hakan ma sai kayan kadi irin su kuka gwaggo lami matar kawun ta bashi wai ya kaiwa sadiya. Tofa tashin hankali ba'a sa maka rana. Yanzu kam hankalinsa ya jirkita domin bai san inda zai je nemanta ba. Haka gwiwa a salube ya juyo ya nufo gidansa. Tunda safe ya fita gashi har ana kokarin kiran sallar azahar. Kafin a karasa kwanar lungunsu inda zai sauka. Wanda kuma nan ne gidan dasu momi mariya suka zauna ya hango kamar kalar hijabinta. Da hanzari ya tsaida bus din ya sauka. Da gudu ya karasa wajen don ya tabbatar da waye ke zaune akan kwalbatin. Yana isa kusa da wurin ya tabbatar da sadiya ce je zaune akan kwalbatin gidan da su momi suka tashi. Gefenta ya zauna ya kira sunanta a hankali "daure ki tashi muje gida" jin muryarsa ya dada sata ta saki wani gunjin kukan. YA SALAM -YA SALAM" yake ta nanata wa. Har yaji kukan sadiya ya fara komawa shessheka. "Kiyi hakuri mu koma gida koma meye sai mu tattauna a can" " ba inda zani macuci mayaudari azzalumi mai saba alkawari" "Duk naji na yadda duk nine wannan din da kika lissafo. Amma nasan inada sauran sunaye a wajenki. Daure muje gida sai ki karasa lissafo min su. Shiru taki kula shi. Ya dade da sanin ita ba mutum ce mai yawan magana ba. Balle har ta fada maka bakar magana. To yau ma data fada yasan ta kure malejin zaginta kenan da kuma bakar magana. Da kyar da ban baki ya jata kamar rakumi da akala har suka isa gidansu. Da kansa ya cire mata kayan jikinta ita kam bata da kuzari ko kadan. Jin zafin da jikinta yayi ya tabbatar masa da cewar ta dade a zaune a kan kwalbatin nan. Tausayinta ya dada rufe shi. Inama da yadda zaiyi yayi mata abinda take so. Da yayi. Amma dukkansu basu da abin yi sai hakuri saboda bukatarta tafi karfinsu dukka su biyun.======***27***====== Da kansa yayi mata wanka sannan ya umarceta data daura alwala. Ita dai binsa kawai take yi amma har yanzu hawaye basu daina zuba daga idanunta ba. Tsayuwarta akan sallayarta ne ya taimaka wajen dawo da nutsuwar ta. Sani bai samu shiga massalaci ba saboda sanda yayi alwala an idar da sallah a massalacin da yake zuwa. Shiya ja musu sallar azahar da kuma nafila. Ba tare da yayi magana ba ya mikawa sadiya Qur'ani shima ya dauki daya fara karatunsa bada jimawa ba itama ta bishi suka yi tayi saida sukayi la'asar sannan yayi musu addu'a suka shafa. Izuwa wannan lokaci sadiya zuciyarta ta rage zafi. Shaidan dai kam sunyi kokarin sallamarsa daga gidansu yinin ranar ko ruwa baiga bakinsu ba. Saida magriba ne ya tilasta ta tasha tea da biredi yanka biyu. Ganin ta karbi shayin ya sanya da bayan isha'i ya balla maganin barci ya saka mata a shayi ya sake tilasta mata tasha. Ta samu barci wanda ya ragewa sani damuwa amma fa washe gari sai ta koma kurman karfi da yaji inma magana ta dace ta bashi amsa eh ce ko a'a. Sani ya daure amma fa shima kusan abinda takeji. A ranta to shi kam ya fita jinsa. Ganin bata ci komai bane ya sashi tambayarta. Ta amsa masa da ta tashi da azumin kaffarar rantsuwar da tayi. Ya sunkuyar da kansa kawai ya danyi jim sannan yace "zo ki zauna ki karya Allah baya kamaka da rantsuwa ko alkawarin da ka kasa cika wa. Sai dai wanda kaki cikawa da gan gan. Inma kaffarar ce to ni ki bari ta koma kaina. Ina kallonki fa tun jiya banda ruwan shayi babu komai a cikin ki. Kuma ki azumin zaki dauka ai kya tambayi izinina. Tunda dai na nafila ne " A cikin kun kuni tayi magana "ai dama mulki aka iya akan mace amma baza'a fita hakkinta ba" "Me kike cewa ne nafi son duk maganar da take ranki ki fade ta sak. Amma kinsani tun muna gida bana son yaro yai min magana a ciki. Ya dada daure fuskarsa danma kar magana ta dada tsayi ya sake ballowa kansa ruwan tiga dam. Ya kuma san bashida abinda zai tare shi dashi. Saboda haka ya kyale maganar kar ta kara tsayi. Bai gama da wannan matsalar ba saiga Salisu inna ta turo shi wai ya karbi kayan makaranta da kuma littatafai inji inna. Ba tare da yayi magana ba ya nuna masa inda jakar da kuma books din da ya sayo wa sadiya suke. "Yaya uniform din fa da kuma resit din biyan kudin makarantar. "Shima ba tare da yayi magana ba yasa hannu a aljihu ya dauko ya mika masa. "Yaya uniform din fa ". Adan kufule yayi magana muje makarantar gani nan zuwa. Sadiya taso ta fahimci abinda ke faruwa amma shekarunta suka hanata ganeta cewa mijinta umarni kawai yake bi. Shima zuciyarta data raya mata bambanci kawai yake nunawa tsakaninta da Salisu. Tunda da ai komai tare yake yi musu amma yanzu ya nuna mata wariyar launin fata. Suna cikin wannan zama na doya da manja sai kuma wata sabuwa ta bullo. Zazzabi ne mai zafi ya rufe ta. Kwana daya biyu har zuwa uku jiki yaki dadi haka ya tilasta ta suka tafi asibiti. Suna zuwa ciki ya tabbata a jikin sadiya na wata uku. Sani yayi mutukar farin ciki da rarrashi da wayo irin na wanda ya girme ka ya samu sadiya ta hakura da rigimar su. Suka dukufa rainon cikin da Allah ya basu.***28***===== Bayan dawowar sa daga karatu. Makarantar su Amir suka dauke shi aiki. Kafin jarrabawar su ta fito ya tafi bautar kasa. Dan wannan albashin da yake samu ya fara tattalin haihuwar matar sa. Cikin na cika wata tara ta haifo yaranta maza guda biyu. Kamar su daya da babansu aka sanya musu sunan baban sa da baban ta. Wato kabiru da isiyaku. Aka yi musu lakabi da walid da imam. Kusan lokaci daya suka haihu da huwaila matar yaya baba inda ita kuma ta samu zakiyya. Ita dai an hada mata kayan barka an kai mata. Ita kuwa sadiya ta samu sabulun salo da turmin atamfa da 'yan rigunan jarirai guda biyu. Dan inna duk karfinta a matar auwalu ya tafi. Da sunan wai ita bare ce dole a fita kunya. Ita kuwa sadiya ta gida ce ba sai anyi wahala ba tunda duk abin daya ne. Sani shi kadai yayi hidimar matar sa da yaransa. Saiko yaya data taimaka masa. Ita ta taimaka mata kwarai da zaman jego tunda ita ba inda zata wankan gida. Bayan suna kuwa da yaya ta koma shi ya cigaba da kula da ita har tayi arba'in. Su walid nada wata uku sunyi kyau gwanin ban sha'awa dasu. Ga kuma uwar goyon mai tsafta da kuma kula yadda ya kamata. Kullum cikin tsafta zaka gansu. Kiran yayanta ne yasa ta ajiye tsintsiyar da take shara da ita ta nufi daki wajen sa. Har ta shiga baisan ta shiga ba. Saida tayi tafi a kansa. Sannan ya dago a firgice ya kalleta. Fuskarsa ta nuna alamun damuwa Kwana uku kenan tana lura dashi kamar yana boye mata wani abu. Ta kuma so taji abinda yake damunsa a dan kwanakin nan amma ya nuna mata ba komai. Ita dai addu'a ta dinga yi a kwanakin koma menene Allah ya kawo musu shi da sauki. "Yaya gani" ta tsuguna gabansa. Ya daga kansa ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Yace "jeki kawai" jikinta a sanyaye ta mike ta fice daga dakin. Ta lura haka yake yawan yi mata a 'yan kwanakin da ya shiga damuwa. Ita dai ta kasa gano dalilin damuwar sa. Jarrabawar su ta fito kuma sakamako yayi kyau. Posting dinsu tafiya bautar kasa yake jira. Makarantar da yake koyarwa suna biyansa albashi dai-dai misali tunda a ciki har hidimar inna yake dauka. Duk da dai ita kam yi mata yiwa yaya baba ne. Tunda shi yake daukewa. In kuma maganar karatun tane shima bata sake masa magana ba tun rigimarsu kafin ta haihu. Tayi ajiyar zuciya "Allah kayi mana maganin abinda yafi karfin mu" sallamar Salisu ce ta katse mata tunani. Suna gaisawa yayi but ya fito daga dakin a firgice yake magana "kai lafiya wani abu ne? A sakarce ya amsa "inna ce tace nazo na kiraka. " To to muje" ya fada kamar a rikice. Ita dai jikinta yayi sanyi Duk a tsorace take. Bayan kamar rabin awa saiga salisu ya shigo yace itama tazo inji inna. Tare suka juya suka koma. A falon ta tarar dasu harda Dija da ta zama day student a gidan saboda nan take yini sai dare ta koma gidanta. Nan zata ci na safe taci na rana ta kuma ci na dare ta dauka ta kaiwa mijinta. Kuma duk a aljihun sani. Ganin fuskokinsu ba alamar tashin hankali shiya dan rusunar da ita. Amma fa fuskar yayanta kamar zaiyi kuka. Ta tsuguna ta gaida su. Inna ce ta fara magana "duba ki gani" ta turo mata babban akwati da kuma mai binsa. Ita dai jikinta ba kwari ta daddaga kayan sama-sama. "Inna na gani kayan aure ne ko?" inna tace wannan lefen mijinki ne nan da sati biyu za'a daura masa aure da zainab. Naga shi yaki ya gaya miki shi yasa ni kuma nayi masa karanbani" sadiya ta dai daita nutsuwar ta bayan ta samu damar yin addu'a a cikin ranta. "Lallai yaya Allah ya sanya alheri " ta fada da alamar rikicewar murya wanda shi kadai ne da yake jiran yaji ta inda za'a fara ya lura da rudanin da take ciki. Jin kalamanta ya kwantar masa da hankali. Saboda ya tsammaci dubun haka daga wajenta. Tunanin tashin hankalin da yake tunanin zai fuskanta daga gareta ya sanya ya kasa gaya mata maganar aurensa da zainab. Shi dai yasan dalilin dawowar babar zainab da zancen auren su ya faru ne a dalilin wanda taso zainab din ta aura mai hali ne yana aiki a matatar mai ta kasa reshen su na portharcourt. Shi kuma baban ya dage da sani zai baiwa a dalilin tsohon alkawarin da suka yi da mahaifin sani. Wanna yasa yana rasuwa ta tana ballistic tun da dama ba tare suke ba sun dan jima da rabuwa. An hana shi aure. Mai kudi kuma daga portharcourt bai zo ba. Har an shekara daya. To shine mussababin zuwa ta bawa inna hakuri harda turo mata mutane. A gaskiya inna tana son a nuna mata ita wata abaje. Balle irin mutanen da aka dinga turowa daga gidansu zainab manyan mutane. Bayan Taja musu rai ta yadda da auren sani da zainab. Akwatin lefe da suka dawo dashi data hana sadiya shita dauko aka sa sani ya dan kara 'yan kayan da Dija ta tsince bayan da aka dawo da lefen da farko. "Yawwa haka nake son inji karuwar aure karuwar arziki ce. In kinking mijinki ya kara aure to alamar ce ta bakya son shi da arziki. Kuma bakin da yace so bazai taba cewa kiba"=====***29***===== Inji inna. Taci gaba da cewa "dama uwarta ce taso taki auren to itama tayi nadamar abinda tayi. Da kansu suka aiko suna bada hakuri. So nake ku zauna lafiya bana son fitina" "Haba inna nida aka dauke ni aka bashi yayi hakuri ya zauna dani sai kuma nice zance bazan zauna da wata ba. Allah ya kara buda masa ya rike mu dukka" Wata harara ya wurga mata yana mamakin kalamanta. Shin haukan kuruciya ne ke damunta ko kuma tsabar hakuri ne yayi mata yawa. Ko kuma bakar magana tayi niyyar yaba masa. Ya kasa tantance wanne ne daga ciki yake damunta. Inna ta miko mata wata leda tace buda ki gani kayan fadar kishiyarki ne." kai kuji dan Allah wadda bata samu lefe ba ita aka bi da kayan fadar kishiya. Shima ta duba atamfa ce kala biyu sai shadda guda daya da kuma leshi duk masu saukin kudi. Sai takalmi kafa daya da kuma mayafi. Ta fadada far'arta. Inna harda ni madalla nagode. Yaya ka gani " ta mika masa karba kawai yayi ba tare da yayi magana ba. Sai yanzu ya gane dalilin inna na hana shi bawa sadiya lefen da gidan su zainab suka dawo dashi. Watau dama bata hakura ba. Sai ta aura masa ita. Yayi kokarin nuna mata a hakura da auren nan tunda dai yana zaune da matarsa lafiya. Kuma shi ba wani kallafa rai yayi akan ita Zainab din ba. Har korafin rashin yadda zai rikesu su biyun yayi mata. Amma bata dauka ba. Tace masa kowacce mace da arzikinta take zuwa. Abinda sani bai fahimta ba. Kulawar da yake nunawa sadiya da soyayyar da yake nuna mata ita ta haddasa wannan karin auren nasa. A ganin inna sadiya zata maida shi sai yadda taga dama zatayi dashi. Abinda bata taba la'akari dashi ba. Shine irin kyautatawar da sadiyan take masa. A tsakar gida sadiya ta zube bisa gwiwarta su walid ta baro su gidan inna. Hannu ta dora aka ta fasa wani irin kuka mai ban tausayi. Tayi kukan ta ma ishi. Babu mai taimakon ta sai Allah. Ta hakikance inna bazata taba barinta ta sake ba. A rayuwarta. Ita a nata ganin inna ta yarda da aurenta da yaya sani domin kawai taci gaba da takura wa. Rayuwarta. "Kisa a ranki duk abinda ya same ki daga Allah ne kuma shi ya shirya miki hakan. Kuma karki nemi taimakon kowa sai Allah zai isar miki" karaf nasihar da Dadi yayi mata lokacin da zasuyi ban kwana ceta fado mata a rai. Ba shiri ta daura alwala ta dauki kur'aninta tana karantawa tana mai tawassali Allah ya maganta mata abinda duk yafi karfinta. Sani kuwa saboda kunya kasa shigowa yayi saida abokinsa sa'idu ya takura masa da suzo su bata baki tukunna. Ita da Dija ne lokacin da suka zo wajen la'asar tazo tana zolayarta. Fadi take "Kinsan kefa huce haushin muce tunda kuwa yanzu zamu kawo matar da muke so tafa ke hakuri ya kama ki" ta fadi haka da zummar wasan kanen miji da matar wa take mata. Sadiya ta amsa mata hakan ma da aka barni nagode. Zancen su karaf a kunnen su sani. Bayan sun shigo sun zauna sa'idu da kansa ya kira Dija. A siyasance ya nuna mata kuskuren kalaminta har yana ce mata "keda zaki kwantar mata da hankali ki kankare duk wani zargi dake zuciyar 'yar uwarki. Kuma sai ki zamo mai tunzurata". Ta basu hakuri ta nuna musu ita wasa takewa sadiya. Tana komawa gida baifi da minti biyar ba sai kuwa ga inna ta dora gidan da kanta ta kuwa wanke sadiya tas har tana ce mata munafuka zata hada mata 'ya'ya fada " fadi take indai kishi ne yake damunki kiyi da wanda yayi miki kishiyar bada ita ba. Kuma ke din nan baki isa ki raba min kan yarana ba " ta numfasa sannan taci gaba da cewa "kuma karya akayi miki ba hucen haushin akayi dake ba. Kaji min zancen banza. To baki isa ki hada min 'ya'ya fada ba" Sadiya na durkushe tana dama furar da zata mikawa su sa'idu. Bata daina abinda take yi ba hakan nan bata tankawa inna ba. Sai dai hawaye ma bai daina ambaliya a fuskarta ba. Sani kuwa yana daga cikin falon kansa kamar ya tsage domin tsabar takaicin innarsa. A yau kam duk abinda yake boyewa abokanansa dangane da takurar da take yiwa sadiya yau saida ta tona. Sa'idu ne yayi karfin hali ya fito daga falon. "Inna barka da yamma" ya katse mata fadan da take yi. Sai kuma kunya ta kamata "Au ashe Kuna ciki sannu yaya mutan gidan ina Fatan kowa lfya. Sai kuma ta wayence "Haba kaji ni ina ta fada ko. Wai ace kai da dan uwanka ba zaku zauna kalau ba. Yanzu inace Dija da sadiya duk abu daya yayi su" "Kwarai duk daya ne. Yaran ne sai hakuri kiyi hakuri dan Allah zancen ya wuce haka nan. Sa'idu ya fada mata "ai shikenan yaya wajen gwaggon ka kwanaki naje na duba ta da kafar nan ta matsa mata ". "Ai ta samu sauki ya amsa mata. Suka gama gaisawa ta juya tayi ficewarta. Idanuwanta kamar gauta tabi bayansa zuwa ciki. Furar data dama ta shiga cikin falon ta kai musu. Sani ya ko kasa daga fuska ga Kunyarta gata amininsa da yake ji. Sa'idu ne yace sannu madam munzo dan yin gyara kuma inaga kamar barna mukayi mun jawo miki fada ba gaira ba dalili " "Lah Haba ai babu ruwanku. Kuma ina laifin ma yaya Dija don ta tuna min matsayina wata kila gani tayi ina kokarin wuce inda aka ajiye ni" "A'a karki kara tunanin wai baki da matsayi a wajen sani. Duk yanda kike tunanin kanki a wajensa kin wuce haka" Dariya tayi "anya kuwa ina shakkun maganarka. Karfa ka ari baki kac albasa mai bakin yazo yace bai yarda ba. Amma tunda kace haka to shikenan mubar zancen komai ya wuce banda zuwan amaryar sani ". Ta fada tana mai kokarin kakalo murmushin dole. Amma muryarta har a wannan lokacin rawa take yi alamar tana kokari ne kawai kar kuka ya sake kubuce mata.=====***30***===== Shima dariya yasa "to kaji uwargida dai batai fushi ba yanda kake tsammani. Duk kabi ka daga hankalinka. Har kana tattago ni da inzo in taya maka bada hakuri" Ya dago kansa ya kura mata ido na dan karamin lokaci. Itama ta tsaida idonta bata dauke ba. Ba kamar lokutan baya ba da indai yayi mata irin wannan kallon ita bata iya maida masa martani sunkuyar da nata idon take yi. Ya girgiza kansa tare da murmushi mai nuna bacin rai amma ba murna ba "sani sak. Sa'idu tunda nake da sadiya bata taba fadar sunana ba sai yau. Kalamanta da tace an tunatar da ita matsayinta su suka tabbatar min da matsanancin fushin da takeyi dani. Kabar ganinta karamar yarinya. Dani dakai ba lallai mu kaita dabara ba. Zata yi magana. Yace karki katseni ina magana. Ya cigaba da maganar sa cikin bacin rai "ba kowa ne yake gane fushin sadiya ba sai wanda ya santa da gaske. Kai zan iya rantse maka duk gidanmu ba wanda zaice ya san fushin sadiya sai ko ni da yaya kulu ba karamar shock absover wannan yarinyar take da itaba. " kace haka mana tunda kaso inyi kuka inda za'ayi min dariya ban yi ba. Tunda ka rufe ni zancen auren ka. In zaka auri masoyiyyar ka ni na isa na hana ka ne amma sai ka nemi da insani ta hanyar da bazai min dadi ba. A cikin maganganu biyu dole in zaton daya. Ko dai kana shayi na kamar yanda ake fada ko kuma baka yarda dani ba a zatonka zan iya sanadin hana zuwan amaryarka." Sa'idu zaiyi magana da hannu Sani ya tsaida shi. Ta cigaba da magan cikin dan zafi kadan domin kuwa harda take magana cikin yanayi na bacin rai bata daga musu murya ba. Sautin maganarta a hankali yake fita. Shi mijinta da ya santa da kyau shine ya gane a cikin bacin rai take magana. Domin ita in ba ranta ne ya baci ba to bazata taba maida maka martani ba. "Nifa bana son inji kina maganar wai baki da matsayi da kuma rashin yarda da wani wai menene-menene. Kin san Allah Sani gudun bacin ranki ne yasa shi kasa furta miki zancen auren nan. "Amma kana ganin yaya yayi min adalci daya ki sanar dani. Kuma ace wai abin that concern me most sai kuma in zama the last to know. Kawai dai a bar maganar. Anan ta sake share hawayen daya zubo mata wanda take kokarin dannewa. "Kasan Allah ba auren shine ya bata min rai ba amma rashin gaya min na dauka yaya ko mutum ya kashe zai sanar dani domin mu taru mu rufawa juna asiri. Nima bashi ni akayi ya hakura ya zauna dani sai ni in ki amincewa wadda ta zamo dama ita yake muradi ta zo inda nake. Daga anyi min alfarma kuma ai bana zake ba. Kuma dama a rashin uwa akanyi uwar daki randa kuma uwar tazo sai a manta da uwar dakin. Shi dai sa'idu yayi kokarin dada bata hakuri duk da yunkurin da tayi na nuna musu ita komai ya wuce a wurinta. Sani ne ya tare shi da fadin "na fison ka barta ya gaya min maganganu masu zafi ta sauke abin dake cikin zuciyarta ko taji saukin bacin ran da take ganin na haddasa mata. "Wai ni sadiya kike ikirarin bani ke akayi zanyi auren wadda nake so. Naji ke ba zabina bace amma na tabbatar Allah zuciyata ya duba da kuma yawaita addu'a da nake yi na samun mata tagari ya mallaka min ke." ya kura mata ido ya tabbatar da maganganun sa sun ratsa zuciyarta kuma ga dukkan alamu ta yarda da zancen daya fada mata. Ya sake lankwashe murya duk da niyyar rarrashi yace "maganar bani ke da akayi da kike ta nanata wa tafi komai bata min rai amma idan fadar ta zai sanyaya ranki kiyi ta fadar ta. Bazanji haushi ba saboda nasan fada kikeyi kawai dan ranki yayi sanyi "**31***===== Ajiyar zuciya mai karfi tayi wanda shi ya tabbatar musu da saukowa daga fushin da tayi. Suma duka ajiyar zuciyar suka yi. Ta mike da niyyar komawa kicin dinta " yace mata ina zaki kuma bamu gama magana ba Ta sassauta muryarta ba kamar dazu ba tace "Allah yaya maganar ta wuce Allah ya sanya alheri a auren da zakayi. Bari in shiga kicin in samo muku abinci kar dare yayi" tana fita sa'idu yace "sani Allah yasa mu a danshinka. Kaga yarinya karama da kyakkyawan lafazi kamar wata babba. Wannan koda zance aka barta ta kwantarwa da mutum hankali." "Ba shi yasa kaga hankali na ya dada tashi da wannan auren ba. Ba zaka gane baiwar da Allah ya yiwa yarinyar nan ba saika zauna da ita. Ko kasan wancen lefen dana hada zan yi auren zainab din sallamar da uwar dakinta ta bata akan ta koma makaranta shita dunkule ta bani. Koda kunyar wannan aka barni ai ta ishe ni. Sa'idu sale kam ya nuna masa yabawarsa akan halin matar tasa duk da karancin shekarunta amma tana da tarin hankali juriya da kuma tunani. Amarya ta tare a gidan sani. Zamansu lafiya lau ita da sadiya. Itama saiwar sala ce ba sawa ba hanawa. Tafiyar Sani bautar kasa zuwa jihar legas ya sanya inna ta sashi daukar zainab su tafi tare. Yaso ya dan bijire a wannan karon. Amma sadiya da kanta ta nuna masa yafi dacewa ya tafi da ita Zainab din tunda inda yake bautar kasar sun bashi muhallin zama. Rayuwa irinta wancen lokacin ba yanzu ba da abubuwa suka tsananta. Da alawus na bautar kasa sani yake daukan nauyin iyalinsa. Harma dana mahaifiyar sa. Ya gama bautar kasa ya dawo gida a lokacin zainab tana dauke da cikinta ta kusa haihuwa. Ita kuma sadiya nata wata bakwai. Domin yaranta nada wata hudu ta sake samun wani cikin. Tayi bakin cikin faruwar hakan. Amma Sani shiya karfafa mata gwiwa da nuna mata ba'a fushi da kyautar Allah. Basu dade da dawowa kano ba wani yammaci zainab ta tashi da nakuda aka kaita asibiti amma haihuwa shiru daga baya likitoci suka bada shawarar ayi mata aiki. Allah gwani itama 'yan mata biyu aka fiddo mata kyawawa masu kama da ubansu. A wannan zaman ne kuma da akayi a asibiti na zaman jinyar zainab. Da inna da mahaifiyar zainab din suka samu sabani. Kowa a cikinsu dansa kamar ido yake. Abinda ya faru mahaifiyar zainab ce ta bada shawarar Sani ya sayo madara a fara bawa jarirai kafin jikin uwar yayi karfi. Inna kuwa tayi tsallen arziki tace ita fa danta ya gaji da wahala. Yarinya ta haihu da kanta ance aiki. Aka zo aka kashe makudan kudi. Karku dauka wasu kudi ne masu yawan gaske. A'a'a lokacin ba'a biyan kudin asibiti saidai mutum ya siyo kayan aiki. To wannan inna take yiwa mitar. Itama mahaifiyar zainab ta kule tace amma dai ai kinga wahalar da tasha kafin ace ayi aikin" "Yo wahala ai dole ce. An taba haihuwa ba nakuda ne kuma an taba nakuda ba wahala. Ai dole kafin a samu da a wahala. "Yawwa tunda kinsan da wahala kin gani nima ba rawa nayi na samo tawa ba. Nima wahala nayi na same ta. Kuma da baifi da ba. "Inna ta mike har tana cire mayafi. "Au haka kika ce. To ni kuma ba wanda ya isa ya juya min dana. Tunda dai nawa ne sai yadda naso dashi." "Kiyi duk yadda kike so ai na dade da lura dake ke mace ce mai kishin matan 'ya'yanta. Kuma duk tsiyar ki sai dai wata ta zauna dashi" anan ne inna ta saka kuka wai mahaifiyar zainab ta zage ta. Dai-dai nan sani ya shigo inda suke. "Indai nina haifeka ka rubuta musu takardar sakin 'yarta. Sai dai inka yarda ka zauna da mai zagin mahaifiyarka". Ta fadawa Sani tana share hawaye da hannun zaninta. Sani ya fara kokarin bata hakuri da kuma kokarin jin bahasin me ya faru har inna take maganar saki a auren da ita ta hada shi. Tana share hawaye take fadin "Nidai nina haifeka to yau kuwa na umarceka daka saki zainab. Saidai in zaka nuna min ta fini matsayi a wajenka. Ta fyace majina da gyautonta alamar kuka yaci karfinta. "Inna kiyi hakuri mu zauna mu tattauna wannan magana a nutse har mu samu maslaha " "Kasan Allah to wallahi tallahi a yanzu sai ka zaba ko ni ko zainab. Kuma bazan matsa ko nan da nan ba sai ka zabi daya daga cikin mu. "Eh in dai ka cika da na halal bani takardar 'yata nima na gaji da wannan auren na sa ido " inji maman zainab wannan kace nace nasu har sai da ya dauki hankalin wasu ma'aikatan asibitin da kuma majinyata aka taru ana basu hakuri. Amma inna ta dage itama maman zainab ta dage. Zainab dai daga asibitin gida aka wuce da ita. Sanadin rabuwar su da sani kenan. Da farko inna ta dau 'yan biyun zainab akan zata rike amma tun da sadiya ta haifi walida mai sunan mamanta Maryam. Sai inna ta dawo mata dasu akan ta hada da walida ta shayar dasu. Haka nan ta hada jarirai guda uku karima da akayi wa lakabi da shukra ga hauwa'u da suke kira da jidda sai kuma maSai kuma Maryam da ake kira da walida. Ga kuma yayayyun yaranta walid da imam. Duk wanda ya ganta yarinya 'yar shekara sha bakwai da yara biyar a gabanta sai ya tausaya mata. A wannan lokaci kam Sadiya taji jiki na renon yaran nan. Don Allah ya taimake ta mai kazar kazar ce ga jiki na kuruciya bashi da saurin gajiya sannan tayi sa'ar miji mai tausaya mata. Da fari yaso ya dauko mata mai aiki inna tace karfinsa bai kai ba amma fa za'a dora masa wahalar auwalu da iyalinsa. Haka nan yakan zage ya taimaka mata da ayyukan gidan. Kafin ya fita aiki. Haka indai yana gida yakan taimaka mata da hidimar yaran irinsu wanka da kuma canja napkin dinsu kai har ma da wankin kayansu. Suna wannan zaman ne Allah ya taimaka masa ya sami aiki da makarantar horar da malamai ta jihar kano wato kumbotso. Shekarassa daya dasu suka nemi tura shi karatu kasar Sudan domin karo ilimi. Anan inna ceta samo masa auren wata 'yar makotansa Rahina a dalilin Sani bazai zauna shi kadai a Sudan ba. Sadiya kuma ga yara a tare da ita. Rahina yarinya ce mai nutsuwa makarantar islamiyyar su daya da sadiya kafin komawarta gidan momi da aiki. Dija ita ta fara sanar da sadiya zancen auren sani da rahina. A wannan karon sadiya bata nuna bacin ranta ba ta dai sanar masa daya daure ya dinga sanar da ita lamuransa. Bata cika jin dadi ba idan wani ya sanar da ita kafin shi. Hakuri ya bata kamar yadda ya saba ya kuma yi kokarin kwantar mata da hankali tare da nusar da ita wasu dalilai da suka sanya shi yayi wannan aure. Duk da kokarin da yayi domin karta fahimci inna ceta sashi yayi auren. Amma saida ta fahimta. Ta dai yi masa shiru ganin har yanzu kallon karamar yarinya yake mata. Bai kuwa san yana mata kallon biri ne tana masa na ayaba. Duk da kokarin da yake yi na nunawa sadiya rashin hannun inna a aurensa saida ta dago su. Ko don yadda taga inna na nan-nan da auren. Har tana fadin ai shi namiji mijin mace hudu ne. Idan mutum ya dora wa kansa kishi shine zai sha wahala. Ita kam ta cire ran jin dadin zama a karkashin mulkin inna. Sai taga mafi sauki a gareta ta rungumi yaran da Allah ya bata da wanda ta haifa da wanda ta samu ko ta samu tudun dafawa. Duka-duka zaman sati biyu suka yi da rahina suka wuce Sudan ita da angonta. Bata tashi zuwa ba saida Sani yazo hutun karshen shekara yazo da ita da tsohon cikin ta. Ita kam ma zamansu baiyi nisa ba Allah yayi mata rasuwa a haihuwar danta mai suna kamal. Ya dawo da ita gida domin ta haihu anan Allah yai ikon sa a kanta. Gidan kakanin kamal bashi da nisa dasu. Sun so a bar musu shi amma shima inna ta karbe shi tace tafi son a hada shi da 'yan uwansa. Su kam suna zuwa duba shi akai akai. Zainab ce dai wani abin mamaki bata taba zuwa taga yaranta data rabu dasu tun suna jarirai ba. Babu abinda ke faranta ran sadiya irin ta zauna da yaranta tana hidimar su. Allah daya tai make ta kamal ne kadai mai dan taba rigima a cikinsu. Shima idan ta bashi nono yasha ya koshi ta sanya shi a baya sai tayi ta aikinta dashi. Wani zuwa da yaya kulu tazo duba su saida tayi mata magana inda tace " anya zaiyiwu kuwa sadiya kullum da na goye a bayan ki. Dariya tayi "Allah yaya tausaya masa nake yi. Kinga shi maraya ne" "Akwai dan da zai same ki a matsayin uwa yayi kukan maraici sai dai kukan bai san uwar data haife shiba. Kulawar da kike bashi ko uwar da ta haifeshi bazai samu sama da haka ba. Kuma dukkaninsu nake magana bashi kadai ba. Ta gyara goyon kamal a bayan ta " yaya ku dinga taya ni da addu'a in kula da yaran nan yadda ya kamata"***32***===== "Addu'a kam kullum ne sadiya. Ke dai Allah ya baki lada ya kuma kara miki juriya da kuma kokari. Kula da yaro da kuma hakurin zama dashi sai an daure. Inda Allah ya taimake ki bakya iya jurewa kazanta kuma kina da jurewa al'alar su. Inba haka ba kalli huwaila mai 'ya'ya biyu sai yaron cikin data ke dauke dashi amma dakinta in banda karin fitsari ba abinda yake yi. Amma ke wazai shigo gidan kima yace da kananan yara inba ganin su yayi ba " dariya kawai tayi amma a zahiri taji dadin wannan yabo na yaya kulu. Ya kuma bata karfin halin zage dantse wajen kula da yaranta. Duk karancin shekarun sadiya ta kanyi kokarin tashi da daddare ta sanya yaranta suyi fitsari a food. Hatta kamalu da bai cika shekara ba ya fara sabawa da wannan al'ada. Idan har zaiyi fitsari ko bayan gida motsinsa ne yake fargar da sadiya. Kusan koda yaushe hankalinta na kan yaranta tana hankalce dasu. Taga ko suna da bukatar Kulawar ta. Makotanta sukan so su shigo hira wajenta. Amma korafinsu bai wuce na ita idan anzo ba'a samun yin hira da ita ba saboda bata rabo da hidimar 'ya'yanta. "Dariya kawai take musu tace "to ai ni inaga lokacin uwa mai yawansa ya kasance na 'ya'yanta mussaman in suna kanana. Saboda bukatar lokacin ta da sukeyi. Kusan ko yaushe in tana hidimar yaranta momi ce take fado mata a rai. Saboda kasan cewar ta irin iyayen nan masu kula da hidimar yaransu in suna kanana. Duk da tana da halin daukan mai reno amma abin da duk ya shafe su kamar wanka da cin abincin su ita take yi da kanta bata mikawa 'yan aiki. Tuna wannan hali na momi shike dada sanya sadiya rungumar hidimar yaranta. Taga mai kudin biya a taimaka mata tayi da kanta inaga ita kuma da sai dai tayi da kanta din. Ko gaishe da inna sadiya zata je sai ta tabbatar da ta kammala komai na gidanta da kuma larurar yaranta. Wata rana tana zaune a gidanta bayan ta kammala ayyukanta. Makociyarta malama umma wacce take koyarwa a islamiyyar matan aure na unguwar ta kawo mata ziyara. Allah ya hada jininsu saboda yabawa da hakurin sadiya da kuma juriyarta da take yawan yi. Data tashi tafiya ta bata wani Littafin addu'o'i da mutum zai dinga yiwa yaransa. Taji dadin littafin nan kwarai da gaske. Kullum kuwa ta idar da sallar asuba bayan ta gama lazimi ta na safiya da maraice wanda yayanta ya koyar da ita saita dora da addu'ar nan kamar haka: ALLAHUMMA BARIK LIY FIY AULADI WA WAFFIKU LIDA'ATIKA WAR ZUQNI BIRRUHU. ALLAHUMMA YA MU'ALLIMU MUSA ALLAMHU. WA YA MUFAHHIMU SULAIMANU FAHAMHU. WA YA MU'ITIY LUQMANUL HIKMA. ATIMHUL HIKMA WA FADHLAL KHIDAB. ALLAHUMMA ALLAMHU MAA JAHILUU WA ZAKKARHU MAA NASUU. WAFTAH ALAIHIM MIN BARAKATIS SAMA'I WAL ARDHA. INNA KA SAMI'UN MUJIB. Addu'a r nada yawa feji biyu ce bari mu barta haka. Allah ya sakawa wanda ya rubuta addu'ar nan da alheri. Domin kusan duk abinda za'a rokarwa yara 'yan gata na alherin duniya da lahira addu'ar nan ta kunshe shi. Tun tana yi da littafi har saida ta kasance ta iya ta saboda yawaita yinta da take. Ga addu'a ingantaciya da uwa ta gari take yawan yi ga kuma kula da yakana ai sai dai muguwar kaddara tasa yaro ya tashi a fandare. Mai makon yawan wake- wake da wasu iyayen suke yawan yi. Ita kam tana yawaita tasbihi da hailala ne. Wannan yasa su walid sa suke kwaba gwaranci suma suke kokarin kwaikwayonta. ***** A Sudan inda sani yake karatu akwai wata yarinya data ke karatun shari'a a jami'ar su mai suna asma'u ta hadu da Sani a dakin karatu inda take zaune a kujerar kusa dasu. Bayan nan da yake yiwa abokanan bitar karatunsa ne ya dauki hankalinta. Tattaunawar su ta shafi wani aiki da aka bawa ita asma'un. Kuma shine abinda ya kawo ta dakin karatu. Kamar ta kyale su sai taga zata cutu. Tunda dama bata gama gane bayanin da akayi musu a aji ba. Sanye cikin shigarta mai mutunci doguwar riga da hijabin ta tayi musu sallama. Bata yi sanya ba tayi tambaya game da abinda ya shige mata duh. Kasancewar fannin da Sani ya karanta ne ta samu yayi mata bayani dai-dai yadda zata gane. Harma da abinda bata tambaya ba ya sanar da ita saboda kasancewar sa mai yawan bincike a fannin shari'a da fiqhu. Tunda ga wannan rana ita kam ta samu free lesson teacher. Koda yaushe tana like dashi don ta anfana daga ilimin da Allah ya bashi.***33***===== Mahaifinta ya kasance jakadan Nigeria a nan Sudan kafin aiki ya mai dashi saudiya. Sun tafi sun bar Asma'u ta karasa karatunta kafin ta bisu. Yadda Sani yake Shekararsa ta karshe na kokarin hada digiri na biyu haka itama take shekararta ta karshe a kokarinta na hada digirinta na farko. A gaskiya kwakwalwar Sani ita ta fara jan hankalinta kafin kyawun sa. Allah ya sanya mata kaunar Sani a zuciyarta. Amma bata nuna masa ba ta danne ko don kunya da kawaici irin na mata da suka san darajar kansu. Wata rana bayan sun gama bitar karatunsu ta tanbayeshi. Kadan daga cikin tarihinsa. Ya bayyana mata. Amma daya fara gaya mata yana da mata sai kawai tayi dariya tace na dade da jin wannan a wajen wata yarinya. Amma tace don tace tana sonka ne yasa ka fadi haka. Amma ai duk mun san matar taka ta rasu wajen haihuwa. Allah ya jikanta. Kai dai ka gaya mana ko auren alkawari kukayi irin na wasu kabilu da idan daya daga cikin ma'aurata ya rasu dayan ba zai kara aure ba. Kaga kuwa in haka ne sai mu taru ayi maka ruqiyya don mun san ba kalau kake ba. Dariya kawai Sani yayi a zaton sa zolayar sa kawai take yi. Daya tara sani da Allah daya bayyana mata batun sadiya. To shi wani irin mutum ne bai cika son magana da yawa ba mussaman da 'yan mata. Sadiya ce kadai macen da yake sake wa yayi hira harda shirme kamar karamin yaro. Saiko yaya kulu. Domin kusan duk shawararsu saita shigo ciki. Suka bar zancen a haka. Bayan kammala karatun ta iyayenta suka zo bikin kammala karatun 'yar tasu. Ita ta nuna musu Sani ta kuma yi musu bayanin irin taimakon da yayi mata har ta kammala karatunta. Suka yi masa godiya mutuka. Jirgi daya suka shigo domin koma wa gida Nigeria direban sune ya dauke su a airport. Sani suka fara ajiye wa a gidan inna tunda yafi kusa da titi akan gidan nasa gidan. Kuma sanin hali yafi sanin kama. Ya tabbatar yana fara isa gidan sa sai yayi rigima da Innar sa. Iyayen Asma'u da ita kanta sun shiga sun gaisa inna. Da suka tashi tafiya alheri daloli ambassador yayi mata. Inna kam rude wa tayi har ta kasa magana. Ita bama tasan wane irin kudi ne yazo hannunta ba yau. Bayan tafiyar su yaya baba ya gaya mata irin kudin da kuma darajarsu wanda shima a zahiri kintata kawai yayi. Sani dai an ga gaisa ya karasa gidansa ya samu matarsa da 'ya'yansa a cikin kyakkyawan yanayi ga yaran shi guda shida gwanin sha'awa dasu. Walid da imam suna da shekara uku da rabi. Shukra da jidda suna da shekara biyu da waya bakwai. Maryam kuma shekara biyu da wata biyar. Sai kamal mai wata goma sha daya. Dukkansu basu San wata uwa ba sai ummansu sadiya. Ga kuma kyakkyawar matarsa wadda kullum kamar kara mata kyau ake yi. Dan digon da ke kowanne kumatu nata da kuma wushiryarta da idan tayi dariya take kara mata kyau. Farin ciki ya rufe Sani sai ya daga wannan ya ajiye ya dau wannan ya rungume. Daga baya gaba daya ya hada ya rungume fadi yake "wayyo Allah dadi gida" ita kuwa sai dariya take masa. Inna ce tasa yaya baba ya bude akwatunan da Sani yazo dasu ta raba tsaraba taba wa kowa. Amma fa ta yaya baba tafi ta kowa. Yana daga gefe duk abinda aka daga yace "inna ina son wannan" hatta kayan sawar Sani saida suka shiga rabo. Sadiya dai tayi godiya da doguwar riga da mayafi guda daya da aka kai mata. Yaranta kowa riga guda daya ya samu tayi ta godiya. Sani dai yayi shiru shida yayiwa iyalinsa akwati guda amma ga abinda suka bige dashi. Wannan baya gabansa samun iyalinsa cikin farin ciki da wadata yafi komai a gare shi. Wannan kuwa ya faru ne da taimakon amininsa Sa'idu da kuma sa idon yaya kulu.=====***34***===== 'yan kwanaki da dawowar sa. Asma'u ta kawo masa ziyara a gidan inna tunda nan ta sani. Bata same shiba baya nan. Sun gaisa da inna da kuma huwaila matar dan lelenta. Mai hali irin na mijinta. Nan take wuni ko yaushe. Ba kuma wani abu zata taimaka mata dashi ba. Zaman ma tana yinsa a dalilin inna tana da talabijin. Kuma kwanan nan ta tara kudi ta sayi video. Saboda haka nan take wuni tana kallo Tana iya shigowa wajen inna ko shara bata yi a gidanta ba. Amma inna kullum yabonta take yi. Ai tana zuwa tana debe mata kewa. Akwaita kam da iya hira mussaman abin dariya. Inda kasan 'yar drama haka take. Ko labarin mutum zata baka saita kwaikwayi yadda yayi abin da zata bada labarin akai. Sai dai babu cas babu as haka take. Amma duk da haka sadiya mai dafo abinci ta aikowa inna itace mutuniyar banza saboda bata shigowa akai-akai. Har inna kaji tana fadin bata fita sai kace mai konanniyar fuska. Inna bata la'akari da aure da sadiya take darajawa ta hanyar zama a dakinta. Ga kuma yara da take fama dasu. Sannan ita ba kusa take da inna kamar huwaila ba. Zamanta gidan momi ya dada sabar mata da son zaman gida. Momi bata yawo duk da tana da mota da direba. Hidimar gidanta ita tasa a gaba. Kusan koda yaushe jama'unta sunfi kawo mata ziyara fiye da ita yanda take kai musu. Kuma saboda kusan ansan duk sanda aka zo gidanta ana samunta. Baka raba gidan da baki. Da wannan dalilin ne sadiya ta koyi dabarun sarrafa abinda za'a sauki baki dashi cikin gaggawa kuma gwargwadon ikon mutum. Inna tafi son sadiya ma ta ringa zuwa tana zama ana mata bambadanci kamar yadda huwaila take mata. Asma'u ta kawo mata alheri mai yawan gaske wanda ya hada da turmin atamfa 'yar ingila mai ABC Guda biyu. Sabulai da kuma kayan shayi. Tunda inna take babu wanda ya taba mata alheri a dunkule. A lokaci guda kuma mai yawan wannan. Godiya take tana karawa. Ta dan zauna suka danyi hira da inna tana tambayarta mutanen gida ita kuma tana amsawa cikin jin kunya da nauyi. Bayan dan lokaci tayi mata sallama zata tafi yaya baba ya tashi domin yayi mata raki ya ko shima ya samu rabon sa. Sun fita wajen da direbanta yake jiranta yayinda shima yake dada yi mata godiya mai hade da maula. Har suka iso bakin motarta .=====***35***===== "Halan kema abokiyar karatun sani ce" "I to ta amsa masa. Amma ai shi senior na ne. Ya kuma taimaka min wajen karatuna sosai. Yanzu ma dana same shi Abba nane yace a tambaye shi ko yana da ra'ayin zuwa damam ta kasar saudiya ci gaba da digirinsa na uku in har yana so zasu dauke shi aiki a matsayin malamin jami'ar sai kuma yaci gaba da karatu dasu." Ikon Allah ai kuwa sani ba zaiki wannan alherin ba. To ke kuma fa ya dan fada a wasan ce? Ko tare zaku koma karatun? "Haba mu koma karatu kamar wasu mata da miji. "In Allah yayi ba sai a zama mata da mijin ba mai kaunarka ai daban yake." "Ai kuwa auren sani zai min wuya" ta fada tana sunkuyar da kanta" "Saboda me ko dan kinaga matsayinki yafi nasa. Ai shi karatu yakan kaika inda kudi ko mulki ba zasu kaika ba" "Kasan Allah maganar bata matsayi bace. Ni inada wani ra'ayi nawa bazan iya auren mai mata ba. Shi kuwa sani yace min yana da aure. "Inji wa karya yake miki ina ga dai zolayar ki yake yi. Ke kinga yayi kama da mai aure. Ko auren da aka yi masa na farko ai matar ta rasu inaga zancen yake yi miki. Ke kuma baki gane ba. Kuma bai sake wani auren ba. Duka-duka shekararsa nawa. Yanzu nefa zaiyi shekara ashirin da takwas. Inaga dai zolayar ki yake. Inba haka ba tunda yazo garin nan in banda labarin kirkinki ba'a binda yake yi. Don inna kam baki ga inda kika shiga ranta ba. Kullum addu'arta Allah yasa kar iyayenki su duba bambamcin matsayi su bari sani ya aure ki. Kuma duk don saboda yawan maganar ki da yakeyi. Ni naji kamar jiya yace gidanku zaije" Kunsan ance har abada karya dadin jine da ita. Gashi kuma akayi dacen samun magaji mafiyi. Indai shirya magana ne to auwalu ya dame inna ya zarce nan. Yawan zaman sa a cikin mata ya bashi damar koyar kinibibi da kissa yadda ko wata macen sai dai ta koya a wajensa. Ita kuwa wannan zance shine mafi dadin ji a wajenta. Ta dade da burin Sani ya bara da kansa. Ya nuna yana sonta. A kansa ne taji zata iya canja ra'ayinta na kin son auren mai mata ta aure shi. To kuma gashi taji daga bakin da take zaton ba zai mata karya ba. Dan uwa shakkiki kuwa ai a zaton ta ba zai taba yiwa dan uwansa karya ba. Ai nan Asma'u ta hau kan wannan zance ta zauna. Taji dadin wadan nan maganganu na yaya baba. Kudi ta dunkulo daga jakarta bata san ko nawa bane ta rusuna alamar girmamawa ta mika masa "don Allah yaya yi hakuri ka karbi wannan a sayawa madam turare ban san da ita ba sai yau da muka gaisa da ita a dakin inna. Dana taho mata da tsarabar ta dabam. Kasan kuma halin kaninka zurfin ciki gareshi bashi da yawan magana.====***36***==== Hannunsa har rawa yake yi saboda murnar kudin daya samu daga gun asma'u inji wa yana da magana. Mu anan idan ya tsinke da labarin ki ba har sai mun gaji daji ba. Ko rannan daya zauna yana kuranta ki inna har tausayinsa ta ringa ji tace nidai Allah yasa yadda kake kaunar yarinyar nan ita tayi maka koda ravinta ne. Ya fada yana dariya. "Kai yaya inaga dai zolayata kake yi. Amma duk da haka naji dadin zancen ka. Kuma idan sani ya dawo ka fada mishi nazo nemansa baya nan. Sai kuma ka sanar dashi sakon Abbana na batun damam din idan yana da ra'ayi sai ya kawo credentials din nasa da sauri. Ta fada tana kokarin shiga matar data kawota. "Ina wane mutum. Inji auwalu ai kema kin san ba zai kiba. Yana dawowa zan gaya masa. Dana san inda yaje ma da can zan bishi in kirawoshi " karka damu ai ba abin sauri bane. Idan ya shigo din ka gaya masa. Direba yaja mota suka tafi. Har suka kule bai daina daga musu hannu ba. Tun daga soro yake kwallawa inna kira. Ta fito tana gyara daurin zaninta. Inna fito kiga abin data bani. Kudi ne masu yawan gaske. Mai iya cewa tunda yake bai taba rike irinsu ba. Suka zauna suna al'ajabi dama akwai masu kudi irin wannan. Shiya katse tunanin inna. Amma inna in kina son wannan daular ta dore to sai kinyi da gaske yarinyar nan auren sani take son yi amma shi yana gocewa saboda yaji tace bata son mai mata shine yayi saurin sanar da ita. Cewar yana da aure. "Yo in banda abinsa auren mace mai arziki irin wannan ai yana da dadi. Dubi fa alherinta yau dinnan kawai. Wannan in tazo cikinmu aimun warke. Kuma ma ince har addini an halarta auren mace don dukiyarta. "Inna cemun tayi fa babanta zai samar masa aiki a can saudiya in har zai yadda ya aureta. Allah inna ki dage kar wannan arzikin ya wuce mu. In har ya matsa ba zai yi ba kawai ki sashi ya saki waccan yarinyar tun da ai dama ke kika ga dama kika aura masa ita. "Saki a'a bazai yiwu ba ai kaga ga yara da take fama dasu. Inna yara ba sai in kula dasu ba. "Kai da Allah tafi can naka ma inace kwana biyu ne Amma kun kasa dasu saboda tsabar lalar matarka. Nifa bana son ana shiga harkar gidan. Kawai dai kinsan yadda zakiyi da wannan batun. Ya mike yana kunkuni. Baza ka ban komai a kudin da ka samu ba. A'a inna kowa ya rike nasa amma dai ki aika min da kayan shayin tunda naga suna da yawa. "To naji jeka zan aika maka. Ai wannan kaya masu yawa haka har Dija sai na aikawa. Labarin sani da Asma'u taji a wajen yayansa shita labartawa umminta. Ita kuma ta fadawa abbanta da kansa ya koma gidan su sani ya sami inna suka tattauna ya kuma nuna mata shi ba abinda zai hana shi aurawa sani 'yarsa in har suna son juna. Haka kuma ya dada jaddada mata batun sani ya kawo takardunsa domin a fara nemar masa aikin da ya alkawarta masa. Wannan sako shi kadai inna ta sanar wa da sani. Kansa tsaye ba tare da tunanin komai a ransa ba ya kai takardunsa gidan ambassador. Asma'u tazo sun gaisa. Har ma da mamanta shi dai yaga karrama wa ta ban mamaki. Abba sai fadi yake ai mun gama tattauna komai da innarka. Allah dai ya tabbatar da alheri. Da murnarsa ya isa gidansa sadiya na shanyar kayan wankin yaranta a tsakar gida taji kawai anyi sallama kafin ta amsa taji anyi sama da ita. Sani da tsananin murna ta koro shi ya dagata yana juyi da ita a tsakar gidan. "Yi hakuri yaya karka kada ni. Ya ajiyeta yace kyale shanyar nan kizo kiji abinda ya samemu Nan ya zayyane mata duk irin alkawarin da ambassador yayi masa. Ta daga hannun ta sama ta godewa Allah. "Allah ya tabbatar da alheri ashe ka kusan zama Alhajin saudiya. "Ni kadai banda ke ai wadan nan kyawawan yaran naki dake kanki in muka je saudiya sajewa zakuyi a dauka larabawa ne. Tayi masa hararar wasa. "Kaima ai kamar balaraben kake dame muka fita. Dazu ma sa'idu yazo yayi maka sallama shima batun tafiyarsa zaije legas gobe saboda shirye shiryen tafiyar. Ashe shima American zai tafi? "Eh can zai tafi. Bari inje in same shi kinsan Muna shirye shiryen auren sa dan kinsan abbansa yace bazai tafi ba sai da matarsa takardun tafiyar ma nata ake processing ba nasa ne ba. Nasa ai sun dade da haduwa. Itama amaryar makaranta ya samo mata. "Allah ya samu a danshinta. Wani irin kallo yayi mata "danshi wane iri na aure da kika zarta ta ko kuma na haihuwa da da kyar ta kamoki" "Na karatu ta bashi amsa a gajerce. Ajiyar zuciya kawai yayi domin yana tararrabin ranar da duk zata dago zancen makaranta. "Ai karatu Muna zuwa saudiya makaranta zan maida ke " "Allah yasa. "Baki yarda ba kenan. Ni na isa ai dai kana ji addu'a nayi. Bari in tashi in sami sa'idun na San ba zai wuce yana shagon auliya'u ba. Bari inje muyi sallama nima in sanar dashi alherin daya samemu. .=====***37***===== Inna tana yawan takura masa daya kai ziyara gidan su asma'u. Yana zuwa bai san neman aure inna ke tura shi ba. Baifi wata biyu da kai takardunsa wajen ambassador ba. Da kansa yazo har gidan ya kawo masa takardun shaidar samun makaranta da kuma aiki a jami'ar damam. Kuma nan da sati biyu suke nemansa. Ya juya wajen inna yace inaga sai a gaggauta daura musu aure kawai su tafi da matarsa. Domin itama ta samu cigaba da karatunta a can. Kafin sani yayi magana inna tai sauri ta cafe da cewa "Alhaji auren baiyi wuri ba. Karki damu bana bukatar komai sai sadakin kawai. Ai sani yanzu dana ne. Sani wani gami ne yake tsiyaya ta ko ina a jikinsa. Sai yanzu ya gane fassarar karramawar da akeyi masa a gidansu Asma'u kafin ya gama hadiye maganar auren da ake kokarin kaka ba masa sai jin sallamar ambassador yayi inna kuwa tana ta faman zuba godiyar dattijantakar da aka yi musu. Har soro ta raka shi. Ta dawo ta tarar sani zaune kamar babu jini a jikinsa tafin da tayi a kansa ne ya dawo dashi duniyar da inna ta saka shi a ciki mai rudarwa. Muryarsa na rawa "inna don Allah kiyi min rai na hakura da aikin indai sai na auri 'yarsu. Kuma inna yaya zanyi da sadiya don Allah inna ki bar wannan zancen zan nemi aiki anan ko ina arzikin mutum yana tare dashi" "Ka gama ubana" shiru bai bata amsa ba "nace ka gama jira nake ka tashi ka rufeni da duka. Tunda kaine ka haifeni ba nice na haifeka ba. Sadiya kuma da kake tambaya ta yaya zakayi da ita. Saika hadiye ta ka maida ita ciki shi zai tabbatar min da irin son da kake yi mata. Ina kokarin yi maka gata kana neman kayi mana sawarwara. To wallahi ka saurare ni da kyau wannan aure kamar anyi an gama. Kuma baba ya gaya mata karya kake da kace kana da aure baka da kowa baka da komai suma kuma wannan magana suka sani. Ya dago da hanzari ya kalleta. "Kalleni da kyau kuma ka furta mata cewa zancen iyalinka akwai su to ranka sai yayi mummunan baci. Idan an samu daukakar akwai wanda zai fita mora. Ba ita da 'ya'yanta ne zasu fi kowa cin gajiyar duk abinda ka samu ba. "Amma inna an taba boye wuta da hayakinta?" Wannan kuwa zata boyu lokacin da hayakin zai bulla kuma an samu ruwan kashe ta. Nan kuma ta sassauta muryarta kuma sani in banda abinka ni so nake in ta riga ta shigo gidan akayi auren kai kuma kafin nan ka kama aikinka ga kuma karin ilimi da zaka samu. Sai tasan da sadiyar da nata 'ya'yan. A lokacin kaga itama da nata 'ya'yan nasan babu yadda zata yi. Kuma irin son dana ga tana yi maka tsaf zata hakura ku zauna lafiya. To ai inna saboda hakan ne bana son na yaudare ta. Yo yaudarar 'yan mata a kanka aka fara ai inda sabo an saba. Kuma ban taba ganin inda auren ya lalace don an gane yaudara yaron yayi ba. Amma nasha ganin an fasa aure saboda yaro ya fadi gaskiyar lamarinsa. Mutane da kake ganinsu yanzu ba son gaskiya suke ba. Kuma in ba tsananin rabo ba duka-duka nawa kake. Ai babu ma mai yarda kana da yawan iyali haka. Na tabbata ka fada musu ba yarda zasuyi ba zasuga kawai baka son auren 'yarsu ne yasa ka fadi haka. Sai kuma ta fara sharar majina alamar kuka "in ka tona zancen nan sani ni ka ciwa mutunci " "Amma inna randa duk zancen ya fito mutuncin mu ba zai zube ba" " kai dai kyale ni dasu na San yadda zan bullo musu. Ai tana shigowa gidan nan na San lokacin da zan bullo da zancen. Zanyi kokarin nuna mata. Tsananin son da kake mata yasa kayi mata karya. Kuma kaga iyayenta dattijai ne ba zasu goya mata baya a wannan maganar ba. Tunda dama ita da baba sukayi maganar su. Ai sai ta fito a zancen yara kuma in banda kai da abinka ita da zata ji ka ajiye mace da yara ka dauketa ai ta san karshen so kenan. Ai mace ba abinda take so irin a fifita ta sama da wata shikenan ka gama da ita.**38***===== Shi dai kansa yana sunkuye bai samu damar bata amsa ba. Ya san indai fadi in fada ne ba zai taba kure innarsa ba. Saboda ita mutum ce mai son ganin abinda take son gani. Wanda kuwa bata son gani duk kokarin mutum bai isa ya sanya ta ganshi ba. Sai dai su dawwama musu amma ba zata taba daukar ra'ayin da ba nata ba. Ya san duk ta inda zai bullo mata ba zaiyi nasara akanta ba. Wani jiri yake ji yana dibansa. Idanuwansa na masa dishi dishi addu'a kawai yake ja a cikin ransa ba tare da yasan wacce yake karantawa ba. Saboda yawan karanta addu'o'in ne yasa kawai suke zuwa zuciyarsa ba tare da kwakwalwarsa ta san me yake karantawa ba. Ta sake cewa "ahaf zancen kake so kai yanzu kana fara aiki a saudiya akwai kuma wanda zai turkeka ai kaima daga nan ka zama babban mutum. Babu wanda zai sake titsiyeka. Sama -sama yake jin sauran maganar tata. Tunda ya riga ya gane cewa bazai iya canja mata ra'ayi ba ya daina fahimtar me take fada. Jikinsa a sanyaye ya mike ya fice daga gidan. Wannan karan kam har yaya kulu sai da sani ya roka akan ta rokar masa inna ta janye batun auren sa da Asma'u. Amma ta nuna masa yayi hakuri bazata kara shiga harkarsa da inna ba. Anan take bashi labarin irin artabun da suka yi lokacin data nuna son ya auri uwar kamalu. Data nuna rashin goyon bayanta ta zage ta tas ta kuma ce mata duk randa ta kara shiga maganar ta da danta to sai ta tsine mata. Har tana gaya mata ba wani ne ya haifar mata shi ba. Da za'a hana ta iko da abinta. Sani bai hakura ba ya sake nufar 'yan uwan babansa amma nan ma bai sami goyon baya ba. Baffan shi laminu ne ya zaunar dashi yayi masa nasiha akan biyayya ga uwa in har abinda ta saka kayi bai kaucewa shari'a ba. Tunda aure take so yayi ya hakura yayin don samun ladan biyayya a gareta. Sani yasan tsakanin innarsa da tsakuwa tsakaninta da dangin babansa. Sai ya kasa sanar dasu karyar data sashi yayiwa asma'u na rashin iyali a tare dashi kwata - kwata. Ya so su dai daita ita dashi kar kowa yasan zancen don gudun zubewar mutuncinta amma hakan ya faskara. Gidan sa ya nufa ba tare da ya san kalaman da zai gaya wa sadiya ba. Tun daga soro yake jin hayaniya alamar ba ita kadai bace a gidan. Ya shiga tare da sallama. Abokinsa ne sa'idu tare da amaryarsa zuwaira suka kawo masa ziyara. Shaf ya manta sun yi dashi zasu shigo yau domin ya kawo amarya gurin sadiya sannan kuma yayi musu sallama saboda tafiyar su America. A Washe garin ranar. Sadiya kallo daya tayiwa mijinta ta gane cewar nutsuwar sa da sauki. Ga wata zuvewa da yayi ta farat daya kamar ya kwanta rashin lafiya. Sa'idu ma yana mika masa hannu domin su gaisa gaisuwar ta tsaya a bakinsa. " malam baka da lafiya ne? "Lafiya ta kalau me ka gani? "Kai Haba ko dai zazzabi kake yi a tsatsaye. Amma baka ga yadda fuskarka ta fada ba. Kuma naga jiya har kusan magriba Muna tare baka gaya min baka da lafiya ba ". "Ka bari kawai inaga shirye shiryen tafiyar nan ne duk ya hargitsa ni. Ya juya inda zuwaira take zaune amarya sannu da zuwa. Kuyi hakuri kun shigo baku same niba. Na dan fita ne. Suka gaisa ya tashi ya shiga bandaki ya dan watsa ruwa a jikinsa tare da dauro alwala duk domin ya samu nutsuwa. Yana dawowa ya tarar da garar da sadiya ta shirya musu duk da rashin sanar da ita zuwan su da yayi. Gurasa ce ta mu ta hausa ta tirara ta amma maimakon taushe da aka saba ci da ita sai tayi miyar nikakken nama wanda ta nika shi a injin nika nama. Yana danyen sa sannan tayi jar miya dashi ta kuma kawo dankalin bature wanda ta fere ta yanka shi manya manya ta zuba a cikin miyar suka karasa dahuwa tare sai lemon citta data hada musu ga kuma yankakken lemo da aka jera musu akan filet.**39****====== Da irin wannan hidima da hikimar sarrafa dan abin da Allah ya hore mata take burge sani tare da fitar dashi kunyar bakinsa. Babu yadda za'ayi ka shiga gidanta bata baka wani abu da zaka sanya a bakinka ya burge kava. Koda kuwa lemon tsami ne da takan fere ta zuba a blander ta nika tasa sugar ta tace. Gashi dai duk da ya manta bai sanar da ita zuwan bakin ba amma tayi kokarin yin sabon abinci. Dukkansu sunci abincin sun kuma yaba mata. Duk da ita kam yaranta basu batta ta nutsu taci yadda ya kamata ba. Wannan kam inda sabo ta saba kusan kullum sai dare idan ta samu sunyi barci take samu taci abinci sosai da kuma nafilfilun ta sa'arta daya hatta kamal bai cika tashi cikin dare ba. Baifi ya tashi sau daya ba shima kuma ruwa kawai zata bashi ta dora shi a foo ta kuma saka sauran yaran suma suyi fitsari shi kenan shida tashi saida asuba. Amma fa da asubar da kyar take idar da sallah bai tashi ba amma shima da yasa nono zai koma to kuma ba zai kara tashi ba sai tara na safe. Hakan ke bata damar ta kammala hidimar yayyensa da kuma ayyukanta na gida. Bayan nan kuwa idan ya tashi to sai da daddare zai sake bacci saboda kazarniyarsa. Bayan baki sun mata sallama sun tafi ta kammala da yaranta da kuma sauran ayyukan gidan ta. Sannan ta dumfari maigidan nata da son jin abinda yake damunsa. Ba tare da murna a tare da shi ba ya sanar mata da fitowar takardun aikinsa da kuma na karatu. Harma da batun tafiyar nan da sati biyu Shiru baiyi magana ba. Ta daure tace "karasa min sauran maganar data saka bacin rai da tashin hankali" a dan firgice ya dago da kansa daga inda yake kwance tare da sarkewar murya yake magana "me aka zo aka gaya miki kuma me aka ce miki. " ba wanda yazo ya gaya mini komai fuskarka ce ta nuna min akwai matsala a tattare da tafiyar taka. Kuma na San dole ba zata rasa nasaba dani ba. Ta saura ra taji ko zaiyi magana taji shiru. Nan da nan kwakwalwarta ta hada mata 2da 2 suka bata 4 take ta gano inda matsalar take. "Inna tace ba zaka dani ba ko kuma inaga kamar zaka samu gata kamar wanda ka samu lokacin tafiyarka Sudan? " Kamar daga nesa yake jiyo muryarta tana gaya masa abinda ya kasa gaya mata. Shiru bai bata amsa ba ta danyi ajiyar zuciya. "Wacece ka samu kuma bana" shiru ya kasa bata amsa Ganin ta dan jima da masa tambayar amma ya gaza bata amsa ta mike da niyyar ficewa daga dakin domin itama ranta ya fara baci "Sunanta asma'u " taji muryarsa na fadi lokacin data tura kofar dakin tana kokarin ficewa daga dakin "Allah ya sanya alheri " ya tashi ya karasa bakin kofar ya kama hannuwanta ya dawo da ita cikin dakin sannan ya zaunar da ita a bakin gadon shi kuma ya tsuguna a bakin gadon har lokacin yana rike da hannuwanta bai sake suba. Ya kwantar da murya yace " Kiyi hakuri karatu mukayi da ita a can Sudan babanta ya taimaka ya samo min aikin da muje zanyi kokarin sama miki wajen zama da kuma nema miki makaranta sai inzo mu tafi tare "Bana son kana daukarwa kanka alkawarin da na tabbatar ba zaka iya cika wa ba. Kuje kawai tunda dai ita tana da baban da zai sai mata miji ai tayi sa'a " itama ta bashi amsa kaima kasan batun wani tafiya da kake dani wannan duk zance ne. Mts" ta dan ja tsaki "Ina ma anfanin auren namiji mai kyau kowa idonsa na kansa. Ta fizge hannunta ta fice daga dakin. Komawa yayi ya kwanta akan gadon ya kurawa silin ido a fili yake furta "sadiya ki gafarceni na san na cutar dake" Dakin da ta ware ita da 'ya'yanta nan ta shiga ta cusa tsumma a bakinta don ya kare sautin kukan da take son kurmawa. Hakan da take a gidan inna ya sa ba wanda yake gane tana kuka ta dauka ta rabu da irin wannan kukan sai gashi yau ya dawo mata. Tayi abinta ya isheta ta rasa mai zatayi sai kawai ta tattara yaranta gaba daya ta rungume su ta tabbatar da cewa yanzu su kadai ne zata raba taji sanyi. Sani tunda ya gaya mata maganar aurensa shi kam ta fitar dashi a ranta. Ta hakurcewa ranta sa ran zata samu zaman lafiya dashi. Abinda yafi mata sauki shine ta cire shi daga mafarkinta na samun wata ingantaciya rayuwa. Saboda ganin duk sanda tasa ran samun farin ciki tare da shi sai wata kaddarar tazo ta gifta tsakaninsu. Ta tuna yaranta wadanda bata na sa a ranta akwai wani nata da ba nata ba ko a cikin ranta bata taba jin tafi son walid akan su shukra ba. Balle kamal da take jinsa a ranta sama da dukkan yaran da take reno. Bata san dalilin wannan kauna tasu ba. Ita dai tana ganin maraicinsa take tunawa dashi take dada tausaya masa. Tayi ajiyar zuciya sai da sannu ta samu addu'a tazo bakinta tana farawa taji ranta ya fara sanyi ta sake rungume yaranta tare da kudurtawa a ranta zata rungumi yaranta tunda ta hakikance su kam baza su taba butulce mata ba.======****40****====== Tunani ta cigaba da yi zuciyarta ta fara raya mata kema kinsan inna ce zata sashi yayi. Me tayiwa inna ne haka da bata sonta da kwanciyar hankali. Can tayi tsaki. Ta sake raya wa a ranta zato zunubi koda ya zama gaskiya. Ba inna bace bama ruwanta. Inna da kwana biyu da suka wuce har aiken sabulai tayi mata wai a wanke kayan mazanta dana kawayenta. Inna kam ai babarta ce matsalar daga wurinsa take ci gabansa yake tunani. To ai dole yaso ci gaba zuciyarta ta sake tuna mata. Allah ya kyauta ina ma amfanin auren namiji kyakkyawa duk hankalin mata na kansa. Ta fada a fili da dai taga tunani bazai kai mata ba. Sai ta mike ta fito tsakar gida domin ta daura alwala tayi abinda tasan shine zai fissheta. Muryar sani ta jiyo yana karatun Alqur'ani mai girma itama abinda ta kwana yi kenan. Washe gari da suka tashi kowa ya gansu yasan basu yi baccin kirki ba. A sanyaye ta gaida shi. Ba dan ma hankalinsa na kanta ba ba zaiji abinda ta ke fada ba. Ta ajiye masa karin kummalonsa yace kefa naga kin ajiye kin tashi. "Azumi nake yi. Ta amsa masa a takaice. Bai ja maganar da nisa ba saboda ya lura kusan duk sanda ranta ya baci to washe gari da azumi zata tashi. Shima shayin daya hada kadan yasha ya ture sauran ta fito daga daki goye da kamal a bayanta. Zanje wajen yaya kulu in gaisheta. "Kije gaisheta ko kuma karata zaki kai mata " ta juyo ta kalle shi da alamar harara a fuskarta. Shi kam hararar tafi dauke masa kan da take yi. Ko ba komai ya samu sanadin kallon idanuwanta ko don yayi kokarin gano halin da zuciyarta take ciki. Anan kuwa ya fahimci fuskarta ta dan saki ba kamar jiya ba. "Allah ya sawwake kawai don zaka yi aure sai kuma in ringa yawo ina fada. Ni ina ruwana ma da aurenka wanda kayi a baya ma basu dada ni da kasa ba balle wannan. In ma kana tunanin wani abu to ni kam zuciya ta ma har ta saba. "Dame ta saba? Ya tambayeta yafi bukatar su cigaba da magana ko don ta samu ta rage wa zuciyarta nauyin abinda yake damunta. Sanin kansa ne tun farko bata da wanda zata gaya wa damuwarta. Dama shine take dan iya fadawa idan wani abu ya dame ta. To yanzu kuma ya dawo ya zama shine mai haddasa damuwar. " da komai ma ta amsa masa a takaice. Inma kana tunanin wai zan gayawa yaya kulu ta hana ka aure ne sa ranka a inuwa ni tawa ce zata kaini. Kuma da da nake zuwa kara nake kaiwa. Ko dan kawai yanzu ka tsaneni sai ka dinga yi min sharri." "Allah ya baki hakuri ba nufi naba kenan. A zuciyarsa kuwa fadi yake ni da da inda zaki kaini kara ma a hanani wannan auren ai da ba karamin gata kika yimin ba. A fili ya furta mata "jeki kice ina gaisheta. Nima zan shigo wajenta da yamma. Amma ki bar min su walid don karsu dame ki. "Ka taba jin randa nace suna damu na. Dama can basu dameni da komai ba bare yanzu da nake jin su kadai ne............." "Su kadai ne me? Ya katse ta. Shiru taki bashi amsa "shike nan muje na sakaki a tasi. Amma komai dare karki dawo ki bari zan zo mu taho tare. Shiya tayata da rikon 'yan mazan da kuma shukura ita kuma ta rike walida da kuma jidda. Suka nufi bakin titi. Har kofar gidan yaya kulun mai tasi ya ajiyeta kamar yadda sani ya umarceshi. Ta shiga da sallama. Yaya na tsakar gida suka shigo ta amsa musu da murnarta fadi take ga babana ga baffa na ga uwata ga kuma aminiyata ga kuma tawan gaba daya. Ni 'yar gata duk yau ni kadai nake da wadan nan manyan bakin. Tana kunce kamal daga bayanta take cewa yaya kamal zaiyi fushi dake tunda shi ba naki bane ba "ni na isa ince haka. Dan gaban goshin sadiya ince bana maraba dashi. Ku shigo daga ciki. Cikin rumfarta suka shiga aka gaggaisa yaran gidan suka shigo suka gaisheta. Duk da kayan makaranta a jikinsu zasu je tahfiz da suke zuwa asabar da lahadi da safe. "Yaya ina Abdurrahman " yana dakinsa inaga bai tashi bacci ba. Kin san tun da ya dawo daga share fagen shiga jami'ar nan a zaria kamar da bashin bacci ya dawo. "Halan karatun nasu da wuya " To waya sani haka dai yace. Yace sai suyi kwana biyu basu runtsa ba. Suna karatu "Allah ya bada sa'a har yanzu likitanci yake so ya karanta"? Shi din yake son yi in har Allah ya sa yaci yanda ya kamata" "Ai yaya shi kam nasan insha Allahu zaici kinsan yana da kwazo bana wasa ba " "Duba cikin tukunyar nan akwai dumamen tuwo ki sako muku kuci keda yaran. "Yayan tace da ita. "Sai dai su in zuba musu ni azumi nake yi. Kinsan mutumin naki kamal inya samu tuwo baya masa da wasa. Ta fada tana mai buda tukunyar da yayan ta nuna mata. "Ke kuma mai ya kaiki yin azumi da wannan barden goyon naki ga wahalar yara" Dariya ta saka kinsan Allah yaya yaran nan basu da rigima sam. Shi kuma kamal yanzu idan yaci tuwo yakan dade bai nemi nono ba" "Ki yaye shi mana ki huta tunda yana tafiya. Ba inace ya cika shekara daya ba harda wata biyu" ta dan langwabe kanta "Wai da yaya yayi ko da shekara da rabi ne sai in yaye shi" "Ke kam ai akan kamal baki da dauriya. Duk suka sa dariya. Nan ta kama wa yaya ayyukanta har suka karasa. Bayan tagama bawa yaran abinci su walid Abdurrahman yazo ya fita dasu. Su walida suna wasan su. Shi kuwa kamal saboda tashin sa da akayi yau da sassafe barci ya koma.=======****41****======== Tana hankalce da sadiya kamar tana tafe da magana a ranta amma itama tana tararrabin yadda zata tari sadiya da zancen da tazo mata dashi. Itama zancen auren nan yana damunta amma ta rasa yadda zata fara yi mata magana. Sadiya ta gyara kishingidar data yi ta nutsu ta kalli yaya kulu tace "mh yaya nace ba. Don Allah ki bani tarihin mama na tunda kin santa sosai. Yaya taji zancen ba inda ta tsammace shiba. A tunaninta zancen auren sani sadiya zata yi mata. Amma sai taji sabanin haka. "Me yasa kike son jin tarihin mamanki? "Yaya haka kawai naji Inason in sani tunda nake ban taba ganin wani nata yazo wajena ba" Tayi ajiyar zuciya "ba haka kawai suka ki zuwa inda kike ba. Akwai dalili. Asalin maman ki mutuniyar jihar katsina ce sunan kauyensu tsakuwa a cikin karamar hukumar dutsimma. Wata rana sunje biki ita da kakarta kauyen kwari dake nan kusa dasu. Kwanansu hudu da tafiya annobar cutar amai da gudawa ta sauka a garin. Mutane da yawa sun mutu a ciki kuwa harda iyaye da dangin mahaifiyarki. Kinsan zaman kauye ba kamar nan ba zaki ga duk dangi ana zaune gida guda ne kowa da matar sa da 'ya'yansa. To su kuma gidansu Maryam duk maza ne ita kadai ce mace a cikinsu. Da annobar nan ta shiga yau a fita da gawa goma daga nan gidan gobe a fitar da biyar sai da jama'ar kauyen nan suka kusa karewa. Wanda suka rayu ma kaura suka yi suka bar garin. Ita ma kakar Maryam ganin basu da kowa ta kulle dan abinda yai musu saura suka yi kudin mota suka nufo kano. Da farko da tazo mai unguwa ne ya basu gida dan karami mai daki biyu yace su zauna a ciki. Furar kakar Maryam take yi tana sayar wa shi yasa duk muke kiranta baba mai fura. Makarantar allo daya mukayi da ita wanda shine ya zamo silar kawancenmu da ita. Kinga hazakar karatun ki to Maryam tace baki iya komai ba. Zuwa wurina da take yi shi kuma kawu isiyaku yazo wajen inna ya ganta ya kuma nuna son aurenta. Inna taso taki a dalilin wai su baba mai fura kararren dangi ne dasu. Basu da kowa. Amma babanmu yaki yarda da wannan ra'ayi nata. Mai unguwa shiya daura mata aure. Mace ce mai tsananin hakuri da kuma mutunta mutane. A dan zaman da mukayi shakuwa ce ba ta wasa ba a tsakanina da ita ba'a dade da aurenta ba itama baba mai fura ta rasu. Mamanki Maryam ce ta roki babanki da yasa miki sunan baba mai fura na asali wato halimatus-sadiya. Idan har mace ta haifa. Kusan ince tunda baba mai fura ta rasu Maryam bata kara cikakkiyar lafiya ba. Saboda tashin hankalin data shiga. Tana ganin ita kadai tayi mata saura. To itama mutuwa ta raba su. Itama Maryam lokacin haihuwarki Allah ya saukar mata da nata ajalin a dalilin hawan jini da ya same ta. Nan asibitin murtala aka kaita kwananta biyu a dakin duhu Allah yayi mata rasuwa. Bata san mai ta haifa ba. Allah ya jikansu da rahama. Sadiya ta share hawayen da ke sauka kan kuncinta tace "Amin. Amma don Allah in kina da hoton ta ki bani in gani"=====****42****===== Ta tashi ta shiga cikin dakinta ta dauko wata leda mai dauke da hotuna da yawa a ciki ta cigaba da duba su daya bayan daya har tazo kan wani mai dauke da mutum biyu dattijuwa da kuma 'yar matashiyar budurwa hoton mai baki da fari ne. Ta mika mata "gashi ranar aurenta akayi mata wannan hoton. Kinga wannan "ta nuna mata dattijuwar wacce suke mutukar kama da dayar itace takwararki watau baba mai fura ga kuma mahaifiyar ki Maryam. Shi kadai ne hoton ta da nake dashi" Ta kurawa hoton ido na tsawon wani lokaci. Kamar tana nazarin wani abu. Can ta nisa tace "Allah ya jikansu. Amma dan Allah ki bani shi zansa a dada daukar min shi sai na dawo miki da wannan din." "Babu komai ki tafi dashi. Ina shi sanin" ta dada tambayarta bayan ta farko da tayi mata dazu da suka gaisa. "Yana gida " ta amsa mata a takaice "yanzu kenan ni bani da kowa "? Yaya taji maganar kamar saukar duka a kanta. Ban gane maganar baki da kowa ba "? "Wai ina nufin bani da inda zan nufa idan wani waje yayi min zafi" karaf wannan kalami nata a kunnen Sani wanda hankalinsa ya kasa kwanciya da ziyararta gidan yayarsa. Ta sanya shi ya biyo sawunta. Sallamar sa ce ta hana yaya bata amsar tambayarta. Tana jin muryarsa wuf tayi ta shige daki. Ya girgiza kansa kawai ba tare da yayi mata magana ba. Tunda ya lura hakan ne bata so. Sun gaisa da yaya kafin ta kira ta ta kawo masa abinci. Ganinsa a falon sai kawai ta shige kicin din yayan da sunan gyara. Ta gama ta kama aikin abincin rana duk don kar ta zauna wuri daya dashi yaje massalaci sallar azahar ya dawo ya ritsa ta a dakin babu hanyar sake guduwa. Amma wani abin takaici duk yanda yaso su tattauna maganar ko don ya samu ya bata hakuri taki. Da yaya ta takura mata ne tace itafa a wajenta komai ya wuce Allah ya basu zaman lafiya da matar shi. Allah kuma ya bada sa'ar karatu. Yayan ce ma tace "Amma itama da ka dai daita zaman ka a can sai kazo ku tafi." dama shine nufina" ya amsa mata. Ita dai uffan bata ce masa ba.=====****42****===== Ta tashi ta shiga cikin dakinta ta dauko wata leda mai dauke da hotuna da yawa a ciki ta cigaba da duba su daya bayan daya har tazo kan wani mai dauke da mutum biyu dattijuwa da kuma 'yar matashiyar budurwa hoton mai baki da fari ne. Ta mika mata "gashi ranar aurenta akayi mata wannan hoton. Kinga wannan "ta nuna mata dattijuwar wacce suke mutukar kama da dayar itace takwararki watau baba mai fura ga kuma mahaifiyar ki Maryam. Shi kadai ne hoton ta da nake dashi" Ta kurawa hoton ido na tsawon wani lokaci. Kamar tana nazarin wani abu. Can ta nisa tace "Allah ya jikansu. Amma dan Allah ki bani shi zansa a dada daukar min shi sai na dawo miki da wannan din." "Babu komai ki tafi dashi. Ina shi sanin" ta dada tambayarta bayan ta farko da tayi mata dazu da suka gaisa. "Yana gida " ta amsa mata a takaice "yanzu kenan ni bani da kowa "? Yaya taji maganar kamar saukar duka a kanta. Ban gane maganar baki da kowa ba "? "Wai ina nufin bani da inda zan nufa idan wani waje yayi min zafi" karaf wannan kalami nata a kunnen Sani wanda hankalinsa ya kasa kwanciya da ziyararta gidan yayarsa. Ta sanya shi ya biyo sawunta. Sallamar sa ce ta hana yaya bata amsar tambayarta. Tana jin muryarsa wuf tayi ta shige daki. Ya girgiza kansa kawai ba tare da yayi mata magana ba. Tunda ya lura hakan ne bata so. Sun gaisa da yaya kafin ta kira ta ta kawo masa abinci. Ganinsa a falon sai kawai ta shige kicin din yayan da sunan gyara. Ta gama ta kama aikin abincin rana duk don kar ta zauna wuri daya dashi yaje massalaci sallar azahar ya dawo ya ritsa ta a dakin babu hanyar sake guduwa. Amma wani abin takaici duk yanda yaso su tattauna maganar ko don ya samu ya bata hakuri taki. Da yaya ta takura mata ne tace itafa a wajenta komai ya wuce Allah ya basu zaman lafiya da matar shi. Allah kuma ya bada sa'ar karatu. Yayan ce ma tace "Amma itama da ka dai daita zaman ka a can sai kazo ku tafi." dama shine nufina" ya amsa mata. Ita dai uffan bata ce masa ba.======****43****====== Haka suka gama yinin su a gidan yaya suka koma amma fa zama ba sauki. Ita dai bata ce masa ci kanka. Amma duk abinda ya sata zatai masa. Magana ce dai take azumin ta. A rana ta uku da ya gaji da zaman kuramen da suke. Yace mata "ai dai Annabi. Cewa yayi in anyi maka laifi ka nuna bacin ranka amma kar ya wuce kwana uku. Kuma in an baka hakuri ka hakura gudun kar ka zama abokin shaidan" Me nayi kuma. Me nace anyi min da har ake dangana ni da shaidan? Abinda Sani yake so kenan ta buda baki tayi magana ko da baka ce ta gaya masa. Kai shi ko zaginsa ne tayi yafi wannan shariyar da take masa. "Rashin maganar kine nake magana akai ya kamata ki hakura ki zauna mu tattauna matsalar mu ". "Ni kam bani da wata matsala da zan tattauna. Rashin magana kuma ina anfani da hadisin da Annabi (s.a.w) ya fadi cewar ka fadi alheri ko kai shiru" Girgiza kansa yayi "Allah ya kyauta" bata bashi amsa ba shima bai sa ran samun amsar taba. "Yanzu so nake yi ki rubuta min abubuwan da kike so keda yara duka in baki kudin ko kuma muje mu sayo ni da ke" "Ai ni zuciyata ta dade da hakura da samun abinda take so tafi raja'a akan abinda ta samu. Haka zalika ta koyi yin hakuri da abinda ta samu din" ya gane magana take son gaya mishi. Naji amma kin san da haka shine kike tambayar yaya inda dangin mama Maryam suke don ki gudu wajen su. Ko shi ba son zuciyar ki kika so biba" "Au dama labe kake mana. Kuma shima inda kake ikirarin zanje din ai zargi ne kake min. Kuma shima dana ga ba samu zanba ai na hakura. Ta mike zata fita "yanzu kenan ba abinda kike bukata. A takaice tace babu "yara fa? Tambayesu ai gasu ban " ta mike da niyyar ficewa. Duk da rashin nuna sha'awarta na tayin kudi da sani yayi mata. Saida ya ajiye mata kudi masu yawan gaske. Abinda sani bai sani ba. Ba auren sa ne ya tunzura sadiya ba sai dai labarin da Dija ta gaya mata na cewa shi sanin da kansa yace su boye wa amaryarsa batun sadiya da kuma yaranta. Wannan shi yake koma mata rai fiye da komai. Bata so gaskata zancen Dija ba saida 'yan uwan amarya suka zo kawo kayan amarya suka gaisa da ita a matsayin kanwar sani. Saboda inna ta fada musu gidan sa kanwarsa da mijinta na zaune a ciki ko don su kula masa dashi tunda shi ba mazauni bane. Wannan dalili yasa sadiya taji fit sani ya fice mata daga ranta. Da farko ta hakura da auren sani amma ganin yadda ake lamarin auren ba ita a ciki yasa ta dada tabbatar da zancen Dija. Ta tattara shi ta watsar kamar Allah baiyi ruwan tsirarsa ba. Da farko hatta yara ji tayi ta tsane su saboda ganin kamar don su ne ake mata wannan wulakancin da kuma ganin bata da inda zata je. Amma da tayi tunani sai taga su meye laifin su. Yadda aka watsar da ita haka suma aka watsar dasu. Gwara ita aure ne ya hada su za'a iya kare shi. Wanda shine kadai abinda take jira daga gurin mijinta. Amma sufa da basu da wani uban sai shi.=====****44****===== Ta juya ta kalle su. Tafi tausaya wa kamal da bashi da uwa. Uban kuma ya yar dashi. Ta share hawayen da yake zuba daga idanunta. "In sha Allahu daga yau bazan kara zubar da hawaye na akan Sani da inna ba. Zanyi kokari in rike 'ya'yana in basu kulawar da bazasu taba maraicin rashin uwa ko uba ba. Allah ne ya hallicce mu ya kuma kaddara mana rayuwa ta kasance haka a wajensa kawai zamu nemi taimako. Ta numfasa taci gaba da tunaninta. "IYYAKA NA'ABUDU WA IYYAKA NASTA'IN. Ta fada har sau uku "insha Allahu yarana bazasu shiga walagigin rayuwa irin yadda na shiga ba. Zan zauna dasu muddin rai. In Allah ya yarda bazasu dandani madacin maraici ba. Kamar yadda ni na sanshi nake dandana har yanzu. Nasan banida gata sai na Allah. Kuma insha Allah dashi zan dogara. Wannan shine alkawarin da sadiya ta daukarwa kanta da kuma zuciyarta. Ta sawa ranta hakura da sani komai son da take masa. Da kuma duk yadda take kulafucin shinfida rayuwar aure da kuma ginawa 'ya'yansu ingantaciyar rayuwa sabanin irin wadda ta sami kanta a ciki. Ta dauka aurenta da Sani shine zai kawo mata karshen bacin rai da kuma kuncin rayuwa da take ciki. Amma sabanin haka Allah ya shirya mata. Duk da yaran da ta sami kanta a me tara su cikin dan kankanin lokaci. Wannan bai dame taba tunaninta 'ya'yanta. Mijinta kuma wadda Ada take wa kallon masoyi zai tallafe su. A yau ta tabbatar wannan damar ta kubuce mata. Bata kanta take ba ta yaranta take. Su kam ta kudurtawa ranta zata sadaukar da rayuwarta domin tasu ta inganta. Zata yi hakuri da duk wani jin dadi na rayuwa domin yaranta suji dadin da ita bata samu ba. Sani dai kam ta hakura dashi tasan bata da kowa sai yaranta sune madadin 'yan uwanta su kuma kadai take dasu da zata sadaukar da komai nata don su su sami kyakkyawar rayuwa.=====****45****===== Shirye shiryen aure sun kacame inna tasa Sani fito da duk wata ajiya tasa domin yin aure na fitar kunya in jita. Duk da hanawa da baban Asma'u yayi saida inna tasa Sani hada lefe na kece raini. Hatta kayan kunshi da lalle da ake sawa a kwalla shi nasa a kumbo tasa aka zuba. Akwai wani fegi da ta saya saida aka siyar ya shiga cikin hidimar auren. Wata rana sani ya kasa daurewa zuciyarsa ga dauke masa wuta da rabin ransa tayi ga kuma wasuwasin karyar da inna tasa shi ya shuka. Kawai sai yayi kundunbala ya nufi gidansu Asma'u da niyyar samun abbanta ya warware masa duk abinda yake ciki ko su bashi aure ko su hana shi duk daya ne a wajensa. Inna kuma ya shirya duk tashin hankalin da zata yi ya san ya fita gaskiya. Mai gadin gidan ne ya tare shi tunda ya sanshi farin sani. Bayan sun gaisa yace masa amma ka daki gurbi. Ai amaryar bata nan taje karaye sallama da kakanninta shi kuma Alhaji sunje umra shida hajiya sai nan da kwana goma zasu dawo. Sani ya lissafa yaga sai ana saura kwana hudu daurin aure zasu dawo. Asma'u kuwa baiga anfanin tattauna wannan maganar da ita ba. Haka nan ya hakura ya juya gwiwa a sanyaye ya koma gida. Abokinsa daya da yake ganin zai tattauna wannan matsalar dashi shine sa'idu sale shi kuma ya masa nisa. Tun zuwan da suka yi yi masa sallama shida amaryarsa yaso fada masa amma zatonsa zai iya shago kan matsalarsa. Addu'a kawai ya dage da yi akan Allah ya fito masa da mafita a wannan al'amari. Sanin na cikin wannan tashin hankalin har ranar daurin auren sa da Asma'u tazo anyi biki an gwangwaje. Su Dija kuwa sune 'yan kan gaba wajen halartar cocktail party. Fadi take yaya yayi aure a babban gida. Daki falle daya da yake gidan sani shi aka gyara wa amarya tunda ba zama zasu yi ba. Kayan ma sai jingine su kawai aka yi ba tare da an jera ba tunda a washe garin daurin auren zasu tashi. Da daddare ango yaci kwalliya da babbar rigarsa ta shadda wacce yaya baba ya dinka masa a matsayin gudun mawa tunda yasan auren jari ne a gare su. Kusan yafi angon dokin auren. Bayan ya shirya duk ya budewa uwargida hanci da kanshin turaren sa sai kuma kunya ta hana shi fitowa daga dakinsa. Yana jin ta shiga tolet yayi wuf ya fice daga gidan. Anyi party hadadde mai tsari. Ga amarya kyakkyawa ga ango kamar tauraro don haskaka wa da yake yi. Anyi hotuna nasu kyawun gaske da kuma video. Irin wanda ake yayi a wannan lokaci. A gidan inna akayi budar kai saboda jirgin dare zasu bi don tafiya saudiya. Inna da mukarrabanta basu gayyaci sadiya ba. Itama bata nuna sha'awar zuwa ba. Bayan an gama budar kai da kansa ya bukaci amaryar da ta fito zasu unguwa. Gidan yaya kulu suka je saboda bata samu halartar bikin ba. Ta aikowa inna da cewar danta bashi da lafiya amma shi Sani hankalinsa bai kwanta ba. Yasan yaya bata cikin harkar auren ko don wulakancin da inna tayi mata. Yaya ta karbe su da murnar ta bata bari amarya ta fahimci wani abu mummuna daga gareta ba. Harda tsara bar su kuka da daddawa da kuma yaji ta bata. A hanyar su ta dawowa gida Asma'u tace akwai wasu kaya da zata tafi dasu kuma suna gidansa da aka kai mata kayanta. Zuciyarsa na lugude suka nufi gidan sadiya. Tana durkushe tulin kayan wanki ne na yaranta a gabanta tana faman yi. Sallamar da Sani yayi ce taso taki amsa masa. Amma sai taji sallamar mace. Ta dago suka yi arba da ita. Kyakkyawa ce wankan tarwada shigar da ta gani ta alfarma a tare da ita shiya tabbatar mata da cewar wannan amaryar Sani ce. Nan da nan ta kauda bacin ran da ke kan fuskarta ta fa dada far'arta oyoyo oyoyo ga amaryar yaya" ta mike daga wankin da take yi. Da sauri ta dauraye hannunta tana musu sannu da zuwa. Ku shigo daga ciki. Ta fada tana mai shiga dasu cikin falon ta. A tsafta ce yake sai kanshin turaren wuta yake yi irin wanda ta koyi hadawa a gidan momi. "Bismillah ta fada tana mai nuna musu gurin zama. Kamal ya tako da son zuwa wajen babansa amma sai tayi hanzari ta dauke shi shi dai yana zaune kamar kurma. Don duk a tunaninsa da kuma ganin irin zaman da suke da sadiya sai yake zaton wani tanadin rashin mutunci take masa shine take masa shigo shigo ba zurfi. Sun gaisa a mutunce ta gabatar musu da lemon asir wanda take hadawa da lemon tsami da sugar Asma'u taji dadinsa sosai. Su walida suka shigo ta kalle su "kai wadan nan cute yaran fa amma triplets ne" kafin sani ya sake magana ta amsa da eh 'yan uku ne. Kamar da taga sadiya da Sani sunyi shiya dada tabbatar wa da Asma'u cewa ita din kanwarsa ce. Su biyu suke ta 'yan hirarrakisu kuma duk akan yaran da ta gani ne. Su walid da imam bata gansu ba sunje gidan malama umma. Ta mike tace bari na duba wasu kaya na kar muyi missing flight dinmu. Tana shiga sadiya ma ta mike ta shiga kicin kamar wani aiki zata yi saboda bama tason Sani ya sami kafar yi mata magana. Indai bazai iya magana da ita a gaban matarsa ba. To kuwa itama bata da lokacin sa a bayan idonta. Asma'u ta samu nasarar gano kayan da take nema ta fito daga dakin sukayi sallama da sadiya ita kuwa ta shiga daki gaba daya kudin da Sani ya ajiye mata kwanakin da suke rigima su ta dauko ta bawa Asma'u tana fadin "gashi na sayi bakin amarya. Ta. Rakota har soron gidan tana fadin "Allah ya kaiku lafiya. Ya fissheku hanya. Allah ya bada sa'ar abinda abaje nema. Tana amsawa sukayi sallama.**46****===== Ta dawo ta cigaba da wankin ta Sani ya tsaya kawai a tsakar gida yana kallonta. Bata dago ido ba. Duk da tasan yana tsaye. To ita in ta dago ma me zata ce masa. Magana tsakaninsu ai ta kare mema zasu ce da juna. Idan ma shi yana da abin cewa to ita kam bata da shi. Yana nan tsaye kimanin minti biyar tausayi nadama da kuma soyayyar tace take nukurkusar sa. Ya duba yaga yanzu haka wankin yaransa ne take ta fama dashi. Wanda kuma kullum haka take fama da irin wadan nan hidimomin yaran da ba duka ne nata ba. Amma shi kam bai taba ganin koda wasa ta nuna wani bambanci a tsakaninsu ba. Ko don yana namiji bai san cewar ba abinda yake kawo shakuwa tsakanin da da uwa ko ba ita ta haifeshi ba irin shayarwa. Ga misali irin karramawar da Annabi (S.A.W) yake yiwa sayyida halimatus-sadiya shakuwar shayarwa ce ta wanzar da haka. Yana cikin wannan tunani saiga salisu da saurin sa yana fadin "inna tace kuzo ku tafi wai ga motar da zata kaiku airport tazo jiki ba kwari haka yabi bayansa. Har ya fara tafiya ya sake juyowa ya kalli sadiya da tunanin ko zata dago ido ya kalleta amma wanki take kamar bata san da mutum a tsaye a wajenta ba. Haka nan ya hakura ya juya ya tafi ya barta da igiyar auren da bata San makomarta a kai ba. A airport suna zaune asma'u ta bude jakarta ta fito da ambulan din kudin da sadiya ta bata. Ita kanta duk da ta saba da rike kudi masu yawa amma wannan kyauta daga kanwar Sani ta bata mamaki. Ta mika masa "ga gift din sister ka ta bani. Ta mika masa ya karba. Tabbas kudin daya bawa sadiya ne ta maido masa da abinsa ta hanyar Asma'u bai mata magana ba ya karba yasa a aljihu can kuma ya mike "bari in canzo miki su zuwa riyal ko kya bani lada " dariya kawai tayi bayan ya dawo ta sake cewa "Amma Kuna kama da ita bata wasa ba. Inaga duk yaran gidanku kunfi kama da ita. Shi dai bai amsa mata ba ta sake cewa yanzu duk yaran tane wadan nan amma she is too young. Shekararta nawa ne yanzu. Twenty cif. Ya amsa mata a takaice. Ita kam ta yaba da sadiya sai yabon taftarta take yi da kuma kyawun da ta gani a tare da ita. Ta kara da cewa "Amma tana da baby face wama zai ce tafi sha shida. Gata kuma da kyan jiki ba wanda zai kalle ta ya dauka ta taba aure ma balle har ace ta haihu by the way ni ina mijinta be"? Kirjin sane ya bada ragaga yaso warware mata zancen sa da sadiya amma sai ya kasa bakinsa yake jin yayi masa nauyi. Harshen sa kamar an dora masa dutse akai bai san ya akayi ba sai jin bakinsa yayi yana cewa "yayi tafiya "Uhm lucky guy. Zan so in ganshi in gaya mishi yayi sa'ar mata. Ta kishingida a jikinsa cikin shagwaba take fadin "wash Allah gaskiya biki akwai gajiyar wa. Baka ji duk yadda jiki na yake ciwo ba. Tana kokarin jan Sani da hira shi kam hankalinsa baya tare da ita. Hankalinta a kwance ta samu abinda take so. Sabanin nasa da yake tashe. Saboda samun abinda take so wanda yai masa sanadin rasa abinda shi yake so. Kudin da sadiya ta bawa Asma'u shiya dada tabbatar masa da cewa sadiya sako ta bayar a kai masa wanda ya nuna masa cewar ita kam bata da muradin sa a rayuwarta. Ba abinda zuciyarsa ke hasko masa irin sallamar da suka yi. Har yanzu bai daina ganinta a durkushe tana wanke kayan yaranta ba. In dai wahala ce yasan shi take yiwa. Yaran nan da take dawainiya dasu duk shi ya tara mata su. In ya tuna kusan yini take tana fama da hidimar su duk domin ta inganta musu rayuwa ya juya ya kalli Asma'u da take baccinta lakadan ba abinda ya dameta. Ya sake wani tunanin a ransa Inama sadiyan shi ce zata samu wannan gatan. Tayi rayuwa koda ta kwana biyu ce ba tare da damuwar komai a ranta ba. Ya sake tuno kwazo da juriya irinta sadiya. Anya akwai mace ko kuma yarinya mai hazakar ta. Shi kansa inya tuna hidimar da take dashi ya kamata ace tafi karfin abinda yayi mata. Da rana ta yini hidimar gidansa da yaransa. Da daddare ta kashe kusan rabinsa shi kuma tana hidima dashi. Shi kansa yasan yana takura mata da bukatun sa. Amma kasa daurewa yake ya hakura indai tana tare dashi. Wai shin yaushe ma take samu ta huta ne ita kam a rayuwarta.=====****47****===== Ya sake juyawa ya kai kallonsa ga Asma'u a ransa yake fadin ke kam kinji dadinki. Allah ya hore miki abinda zaki sami biyan bukatar ranki a wannan zamani. Wato kudi da mulki. Inama yadda ya tsaro musu rayuwa shida sadiya haka ya same ta. Ubangiji Allah ka bawa sadiya juriya akan wannan jarrabawa data same ta. Ya sake nisawa ya tu.a tun da yarinyar nan ta tashi bata da kowa. Allah ne kawai gatanta. To shi din ma kusan abu daya ne dashi. Ya dade da fahimtar ba kauna iri daya inna take masa shida sauran 'yan uwansa ba domin da yaya baba ne ko Dija. Ko sama da kasa zasu hadu inna bata isa ta sasu abinda basuyi niyya ba. Ita ma kuma bazata taba tursasasu suyi mata abinda basa so ba. Koda kuwa hakan su zai anfana. Kamar dai misali yadda yaya baba yayi biris da karatu inna tace tunda bashi da ra'ayi a kyale shi ai ba kowa yake da nasibi a boko ba. Aka fara zancen sana'a kawu labaran ya nemo masa aiki a gidan biredi yace wuta zata dafar dashi. Inna kuma tace sabara take sawa. Aka ce yayi acaba yace yan daf su take shi ya mutu. Kawu labaran ya samo masa aiki a shagon wani abokinsa a kantin kwari yace bazai iya aiki a karkashin wani ba saboda shi ba zai dauki wulakanci ba. Yaya kulu ta bashi shawarar ya koyi dinki yace zama basir yake kawowa. A nan ne ma taji haushin sa tace ko wacce sana'a akace sai ka kawo kushenta. Idan zaman shagon tela bai saka basir ba ai zaman dakin inna ya saka basir din da kake gudu. Duk da rashin kunyarsa yana shayinta saboda kwarjininta. Gunguni kawai yayi a cikin ransa. Inna tace a kyale shi. Yana nan inda yake arzikin sa zaizo ya same shi. Ya dauka biyayya ce take sa a daukaka wani akan wani. Bai taba jin inda akai auren jari da namiji ba sai a kansa. Shida yake binta sauda kafa shita tursasa ta Zubar da nasa 'ya'yan yara kanana har guda shida tare da 'yar yarinyar matar sa wadda itama kulawarsa take bukata a girme asma'u ta girme mata da shekara daya tunda ita shekara ishirin da daya take ciki. Ya aure ta tana shekara sha biyar ta haifi walid da imam tana 16 sannan walida da rikon shukra da jidda daya sameta tana 'yar 17 shekara biyu tsakani aka sake kawo mata rikon kamal yana jariri. Danye sharaf ya sake jinjinawa ba domin tana da kyawun jiki ba da yaran nan sun tsofar da ita. Ko don shayar dasu da take yi. Murmushi ya subuce a fuskarsa daya tuno kyawun surarta hatta cikinta a shafe yake kamar bai dauki jego hawa biyu ba. Haka nan kirjinta kusan shine abinda yafi so a tare da ita. Ba yadda za'ai kace bana budurwa bane ko yaro zata shayar saidai ta tashi ta zauna saboda dasuwar su bazata iya shayar da yaro tana daga kwance ba. A dan zaman da sukayi na shekara biyar duk da dai a tsitsinke suka yishi. Amma sadiya ta dasu a ransa fiye da duk wani mutum daya taba mu'amala dashi. Ita ma kuma ya tabbatar da ta so shi duk da rigingimun. Aure auren sa daya ringa sakata a ciki. Ya san kwarai tayi hakuri dashi da irin rayuwar da ta samu a gidan sa. Ya san ta kauna ce shi yana yayan ta. Ta kuma so shi soyayya inganttaciya kuma tsaftataciya a lokutan da ya zamo miji a gareta. A yanzu ne dai bai san matsayin da ta ajiye shi ba. Bai kuma ga laifin ta ba. Kaddara ce ta datse wannan kyakkyawar danganta kar da suka faro ta shida ita tun tana karama. "Ya Allah " yayi addu'a a cikin zuciyarsa "Allah ka bani ikon farantawa inna da kuma kyautatawa sadiya da yarana sannan ka bani ikon sauke nauyin Asma'u daya hau kaina" inna uwa ce ya san biyayyarsa tafi bukata zai kuma yita iya kacin karfinsa. Ita kuwa sadiya matarsa soyayyarta ta gama ginuwa a zuciyarsa. Kyautatawar sa take bukata sai asma'u da zai fara rayuwa da ita yanzu. Soyayya dai yasan babu sai dai a hankali bai sani ba ko zata ginu kamar zaman sa da zainab da kuma rahina. "Halimatu na yarinya mai kyawun asali kyawun kuma na zahiri dana badini Allah ya bani ikon kyautata miki da kuma fita daga hakkinki ina kuma fatan Allah ya sanyaya miki zuciya ki yafe min duk abinda nayi mik=====****48****===== Motsin Asma'u ne ya dawo dashi daga tunane tunanen da yake yi. Wanda ya fara tunda suka baro nigeria anan ya fahimci captain din jirgin yana mai sanarwa kowa daya daura belt din kujerarsa domin jirgi ya iso jedda inda zasu sauka. Bayan sun kammala da diban kayansu a airport din jedda suka sake hawa wani jirgin domin zuwa babban birnin saudiya wato riyadh inda ofishin jakadancin nigeria yake. Anan ma kwana daya kawai suka yi suka sake hawa wani jirgin domin isa dammam inda makarantar da zasu shiga don yin karatu shida sabuwar amaryarsa take. Basu samu damar fara amarci ba sai da Sani ya kammala da registration din karatunshi ya kuma yi reporting a wajen aiki. Itama ta kammala da nata. Gidansu dan madaidaici wanda hukumar makaranta ta basu. Daku nan bacci uku da falo biyu da kuma banda kuna guda uku sai katon kicin babu ce kawai babu a cikinsa. Haka nan dakunan kowanne da kayan gado set. Hatta da zannuwan gado an ajiye musu. Suma falukan guda biyu kowanne a tsare yake da kujeru carpet labilaye da kuma kayan kallo. Gidan nasu yana rukunin gidajen kananan malaman jami'ar dogon bene mai hawa ashirin. Su kuma suna hawa na goma sha biyu. Amarci dai kam an sha shi tsakanin asma'u da Sani. Ita kam duk yadda take tsammanin samun shi ya zarta mata haka. Ta kuma yaba masa kwarai. Ta tabbatar wa kanta batayi zaben tumun dare ba. Tsaftarsa da kuma yawan ibadarsa su suka fi birgeta dashi. Duk da bashi da yawan magana amma 'yar hirar da su kan yi da ita tana burgeta. Saboda ko banza tana karuwa dashi da kyar kaji magana marar amfani ta fito daga bakinsa. Asma'u bata gama sanin waye sani ba shiyasa ta gamsuwa da yadda ta same shi. Data taba katarin ganin irin sakankancewar da yake da sadiya da bata yi masa wannan yabo ba. In yana tare da sadiya yana bata dariya wani lokacin har rokonsa take yi daya daina kar cikinta ya kulle. Har rawa wani lokacin yake yi mata idan yaso. Labaran ban dariya kuwa har ta rasa ina yake samo mata su wasu ma sai taga kamar hada su yake da kansa. Sadiya ce kadai filin da yasan zai baje kolinsa ko wane iri ne. Na dadi ko kuma na rashin dadin. Ita kuma har abada tana da store da zata adana masa kayan da ya baje matan. Sati biyu yayi agida yana hutawa kafin ya fara karatu da karantarwa ka'in da na'in haka itama Asma'u lokaci daya suka shiga makaranta tare inda zata yi shekara biyu domin ta samo digirinta na biyu. Yayin da shi kuma zai shekara uku ne wajen hada nasa digirin. Allah ya bada sa'a.=====****49****====== A nan gida Nigeria sadiya ce kwance a doguwar kujerar dake falon ta. Walid da imam suna wasan su. Yayin da shukra da kuma walida suma sun tara 'yan tarkacen tukwanen su na kasa suna wasa. Ita kuwa jidda ta takarkare da biro da takarda wai nan ala dole rubutu take yi. Kamal kuwa dan gata sai ya hau kan ummansa ya sauka kamar ya sami doki. Tunani ne fal a zuciyarta. Dole ta san yadda zata tsara rayuwarta da kuma ta 'ya'yanta. Walid da imam sun isa shiga makarantar nursery amma babansu yayi mata romon baka yace ta bari sai sunje saudiya sai a saka su. Tuno sunan kasar kawai bata mata rai yake yi. Ballantana ta tuno da bakin da tuni sun sauka a kasar. Wannan su suka sani ta sake fadi a cikin ranta yanzu vita 'ya'yana nake yi. Wannan magana na fado mata a rai tayi zumbur ta mike daga kwanciyar da tayi. Kamal yasa kuka na rashin yarda da tashi da dokinsa yayi. "Yi shiru dan gidan ummansa. Bari mu tsara yadda zamu gudanar da rayuwarmu. Ai ni kuma kwanciya bata same niba. Duk da bai san abinda take fadi ba amma muryar rarrashin da tayi anfani da ita wajen tausarsa tasa shi yayi shirun. Biron hannun jidda ta karba tana fadin "yayata ara min biron ki. Umma kinga na rubuta A" ta fada yayinda ta isa wajenta tana nuna mata jagwalgwalon da tayi. Eye jiddan ba inaga dai ke malamar makaranta ce kullum cikin rubutu. To bani aron biron ki kuma dauko min littafi akan drawer gefen gado" ta mika mata ta kuma shiga dakin don dauko abinda aka aiketa. Sai da ta nutsu sannan ta nisa tayi tunani sannan ta dauki takarda ta fara rubutu kamar haka. ABUBUWAN DA 'YA'YANA SUKE BUKATA DAGA WAJENA Ta rubuta da manyan baki bayan jidda ta kawo mata littafin ta rubuta ta karanta abinda ta rubuta ta soke wannan ta rubuta waccan har ta kammala ta kuma gamsu da abinda ta rubuta din list din da tayi ya kasance kamar haka: Abinci Sutura Kiwon lafiya Ilimi Tarbiyya Ta dauki kowanne daya kamar mai yin note din makaranta. Misali da ta dau abinci. A kasan sa ta rubuta yaya zan samar wa yarana abinci. Haka nan tayi ta tsare tsaren ta a rubuce har ta gamsu ta yiwa kanta tanadi mai kyau. Anan kuma wani babban tunani yazo mata. Dame zan samar mana yadda zamu aiwatar da tsare tsaren rayuwarmu? Da biron ta rubuta ban sani ba amma Allah zai shige mana gaba. Wannan rubutu da tayi sai taji kamar da wani ta tattauna wannan damuwar tata har kuma taji kamar shawara wani ya bata. Hakan yayi mutukar taimakawa wajen rage damuwarta. Ta sake duba littafin. Diary da aka bawa yayanta ce ta makarantar da yayi koyarwa. Wato kumbotso. Sai yanzu ta gano hikimar Amir da kusan kullum sai ya rubuta abubuwan da yayi a diary dinsa. Wato ashe abokiyar hira ya samu su suna masa dariya da ganin wautarsa ita da Amira. Allah sarki su Amira ko suna ina? Da tasan inda zata gansu data neme su. A gaskiya bata taba jin tayi maraicin wani nata kamar yadda tayi maraicin su ba. Wannan tunani da tayi shi ta rubuta a kawar sirrinta kamar yadda tasa mata suna. Yanzu ta fahimci me suke bukata ita da yaranta. Sai kuma tayi tunanin yadda zata samar musu dashi. Abu na farko da suke bukata shine kudin da zasu tallafi rayuwarsu. Me akeyi a samu kudi? Zuciyarta ta tambayeta." Aiki ko sana'a "Ta bawa kanta amsa wanne ne ba wanne ne ba. Inji falsfa. Aiki dai bata da karatun da zata yishi. Sana'a kuma bata da jarin da zata fara. In kuma aikatau zata koma gidan mutane tasha jin kawayen momi in suna neman mai aiki sukan ce basa son mai yara. To ita kuwa yara harda yarori sun mata katutu. Ta kalli jerenta ta san da ta cire shi ta sayar yan unguwa zasu fahimci abinda take ciki. Wannan kuwa bashine burinta ba. Ta juya ta sake kallon yaranta "Allah ka kawo min mafita." Sallamar Dija ce ta katse mata tunanin da take yi. Bayan sun gaisa ta dan zolayeta "munje biki mun gwangwaje munsha party amma kinki zuwa. Inma kishi ke damunki gwanda ki sauke shi kin dai ga yayana me tsada ne masu so da yawa" I zuwa yanzu ta saba da bakaken maganar Dija har basa bata mata rai. To ita bayan abinda Sani yayi mata akwai wani abu da zai bata mata rai. Ai sai dai rabuwa da yaranta. Dariya kawai tayi. "Yaya Dija ba fa ki gayyace niba. Kuma kinsan ance haramun ne halartar biki ko walimar da ba'a gayyace kava. In kaje kaci wani abu to kaci haramun. Gudun haka yasa naki zuwa. Yayan ki kuma kinga ai na hakura na barwa mai so kinga babu sauran damuwa " "Gaskiyarki to kizo kiga gara inji inna." Dija ta gaya mata "Wai Allah na kinga ki bawa inna hakuri zan shigo anjima kinga yanzu ga ayyukan gida nan ban karasa ba. Kuma ga su walid yanzu zasu bukaci abinci kuyi hakuri dana gama zan shigo. Sadiya ta fada mata. "Hm inji Dija. "Ai ke dama har abada 'ya'ya ba zasu barki ki sake ba. Uwar 'ya'ya da anyi magana kice yara.***50*****====== Tana dariya ta bata amsa "kai yaya Dija ba haka bane zan shigo yanzun nan. "Ai dai an fita hakkinki tunda an gaya miki " ta fada mata yayin da take fita daga gidan. Murmushi kawai ta bita dashi. Sai bayan la'asar ta shiga gidan inna don tayi mata ban gajiya. A tsaitsaye suka gaisa da inna hankalinta na kan rabon kayan garar da aka cika musu tsakar gida dashi. Kayan abinci komai buhu goma tun daga shinkafa ta dafawa data tuwo. Sai kuma katan katan na su macaroni da taliya da kuma kus-kus suma goma- goma haka nan maimakon gero ko daya sai aka sa musu buhunhunan semovita masavita da kuma gyararren tsakin masara da akeyi a kamfanin fulawa na maiduguri. Kayan zaki ma su nakiya da alkaki dubulan bakilawa da kuma gireba suma gasu nan Bila adadin. Daga gefe kuma ga wasu akwatinan guda biyu daya shadda da boyel kowanne goma-goma da kuma huluna suma goma. Sai daya akwatin mai dauke da turamen atamfa suma guda goma. Duk 'yan holland sai kuma tarin samiru da dankwalaye na dangi. Ita dai da taga duk hankalinsu na kan kayan harda su huwaila sai tayi musu sallama ta wuce gidanta. Bata dade da shigowa ba saiga yara an doro musu buhun shinkafa da kuma macaroni da taliya gami da buhun semovita. Su kawo mata. Tayi musu godiya matuka ta kuma basu tukuici. Bata gaji ba da daddare ta sake koma wa gidan inna a tsaitsaye tayi mata godiya. Saboda gaba daya yaran suna gida. Sunyi bacci ta kulle su tazo. Anan din ma bata samu tarbar kirki ba saboda su yaya baba da suka gwagwafe ana ta daga shaddojin da aka kawo na kan gara. Ko wacce ya daga sai ya ajiye gefen sa yana fadin wannan ma ina sonta Dija ta gaji da hadamarsa tace to kai duka shaddojin zaka kwashe kowama yana so ai. Sai kace kaine angon" "Ke wallahi na babbalaki yanzun nan. Uban me zakiyi da shadda. Ko don ki kaiwa wannan mijin naki mara zuciya. Ya ki aiki ya zauna sai dai komai ai masa. "Marasa zuciya dai" ta amsa masa tare da murguda baki cikin fitsara ta cigaba da cewa "gwanda shi korarsa akayi daga aiki. Yafi wanda bai taba gwada aikin ba. Da kyar inna ta shiga tsakaninsu. Ita dai sallama tayi musu ta fita daga gidan. Washe gari ta tashi ta gama ayyukan ta kamar yadda ta saba. Jidda ce ta dauko takarda da biro tana fadin"rubuta min A" ai kuwa fadar haka taji wani kwan fitila akanta mai haske ya kunnu wani tunani mai dadi ya darsu a zuciyarta. Zuciyar tace take fadin mai zai hana ki yiwa yaranki home study kamar yadda Dadi da Momi suka yi miki kafin ki samu kudin sakasu a makaranta. Kamar wadda aka mintsina ta mike ta shiga daki purse dinta ta ciro kudi ta kuma karbi biron hannun jidda da kuma takarda ta rubuta list ta bawa walid tace " ungo yi sauri jeka shagon mustafa kace ya baka abubuwan dana rubuta. Walid da imam sun saba zuwa shagon bashi da nisa dasu. In abinda take so yana da yawa saita rubuta musu gudun shirme shi kuma mustafa idan ya karanta sai ya zubo musu a leda idan da sanji ya kulle musu a wata ledar don kar su zubar. Da saurin sa ya dawo ya kawowa ummansa sakon ta. Pencils ne guda biyar da cleaner itama biyar da kuma shapner sai kuma littatafan rubutu dana lissafi suma guda biyar-biyar. Anan tsakiyar falonsu akan teburin tsakiyar falon su ummansu ta bude ajinta na farko. Da 'ya'yanta a matsayin dalibanta. Ilimi ko wanne iri ne anfani ne dashi. Kullum kafin karfe tara na safe ta gama duk gyaran gidanta. Tana yi yaranta suna taya ta kaye kaye idan sun gama ta kulle kofar gidanta ta zauna tana koya musu karatu da rubutu da kuma lissafi dai-dai kwakwalwar su. Yara sun sha nonon hazikar uwa. Haba wa kan kace meye wannan sun dauke A-Z da 1-10. Duk suna gane su. Baza su tashi ba sai kusan sha daya na safe. Da la'asar kuwa kakan kamal ne malam mai salati zai turo daya daga cikin almajiran sa ya tafi dasu. Da kansa yake biya musu karatun Alqur'ani mai girma. Idan an tashi kuwa har da dan hasafinsu zaka ga yasa an dawo dasu.======*****51*****====== Wata rana da sadiya taje gaisheshi tace "kuma malam su kullum basa kawo kudin laraba sai dai su biyo su kwace maka naka" dariya ya saka sosai. "Yace kyale su ai dashi nake zubawa, ina nan ina rubutawa duk sai na karba har da riba" godiya tayi masa sosai shi kuma yana fadin halima mune da godiya. Dawainiyar da kike da kamal ba abinda zamu ce miki sai dai godiya. "Babu komai malam ni dai ku taya ni addu'a akan yaran nan gaba dayan su. Rayuwa yanzu tsoro take bani mussaman akan tarbiyyar yara." "Addu'a kullum a cikin yinta muke. Ke dai Allah yayi albarka. "Amin malam. Bari na shiga na gaida gwaggon rahina naji jiya su imam sunce bata da lafiya." "Ai dan zazzabi ne ya kama ta jiya tama ji sauki. Ya amsa mata. Ta mika masa kullin goro farare manya. "Malam gashi inji su walida. "Ke kam ba kya gajiya da dawainiya. Nagode Allah ya saka da alheri. Ta amsa sannan ta shige cikin gidan. Suma bayan sun gaisa sai da ta bata sabulun wanki guda uku. Wannan hali na sadiya duk da bata dashi amma hakan baya hanata alheri. Gwargwadon iyawarta. Takan tuna da fadin momi da takan ce musu kar kuce sai kun gama biyan bukatar kanku sannan za kuyi alheri. Dan adam bukatarsa bata taba karewa. Ku dinga kokarin bayar da abinda kuke so. Malam mai salati shine mahaifin Rahina ita kadai da kaninta suka haifa. Suma din saida girma ya fara kamasu suka same su. Bayan rasuwar rahina yayi musu saura murtala kawai kanin ita rahinan. Sadiya kuwa tana kokarin kyautata musu. Mussaman da Sani yana aiki a kumbotso. Tun da samun nasa ba laifi. Su kuma sun dau 'ya'yanta daya da jikansu kamal. Kasancewar sa mai almajirai ba makarantar islamiyya ba yasa yake koyar da yaranta karatun hadda. Duk ranar alhamis da jumma'a in suka tafi tun bayan azahar to sai la'asar lis zaisa murtala ko wani almajirin sa ya dawo dasu gida. Kasancewar shi gidansa yana bayan nasu layin Zuwan da su walid suke yi gidan malam mai salati shiya bata damar itama idan sun tafi ta shiga wajen malama umma daukar karatu. Takan biya mata littatafan fiqhu da hadisi da kuma karbar haddar qur'ani data cigaba dayi a wajenta. Kayan abincin da inna ta aika mata na garar mijinta zai dauke su lokaci mai dan dama amma babu kudin cefane balle na omo da sabulu. Suma kuma dole ne. Sadiya taga da karfinta da lafiyarta sai ta sanar wa su malama umma Makotanta duk wanda yake da wanki ya kawo har gida zata yi masa. Fita aiki kam ta san ba zai yiwu a wajenta ba.*52*****===== Ta fara karbar wanki tana yi kwandala- kwandala ko zanin gado ne kwandala ce. Haka kuma ko dankwali ne kwandala ce. Ita dai bata taba zuwa ta roki kowa ba. Balle su inna da suke zargin mijinta ya lafta mata dukiya kafin ya tafi. Kayan garar ma da kyar suka bata. Saboda handama da babakere na yaya baba. Duk sanda yaya kulu tazo taga gidanta cike da shanya sai tayi mata karyar makota ne suka yi shanya. Saboda tasan gaya mata daga mata hankali za tayi akan abinda bata da magani. Kuma tayi sa'a bata cika zuwa ba sai dai aike. Dama Abdurrahman ne mai zuwa akai-akai to shima ya sami shiga jami'ar Ahmadu bello dake zaria domin karatun medicine. Akwai wata ma'aikaciyar asibiti mai suna sister Aisha farkon haduwarsu ya faru ne wata rana da kamal ya kamu da wani irin zazzabi da kuma mura hankalinta ya tashi. Da saurin ta ta nufi gidan malama umma. Ita ta raka ta wajen sister Aisha. Ta duba shi ta sanar da ita kyanda ce amma bata kama shi sosai ba. Ta bata shawarar ta daure taje asibiti washe gari. Tayi shiru tana nazari kasancewar yanzu asibitocin sai a hankali indai zaka to kudi ne tsababa a kanka. "Sister indai zai yiwu ki taimaka ki rubuta min maganin ba sai naje asibiti ba. Ina maigidan ki? Ta tambayeta kafin malama umma tayi magana tayi saurin fadin "baya gari yayi tafiya. Ta kalle ta 'yar yarinya karama da ita da gani haihuwar fari ce amma ta fara haduwa da jula-jular namiji. In ba haka ba ya zaka tafi kabar mace da yaro ba ko abinda zasu sayi magani dashi. Yara kuma da ba wuya sun hadu da rashin lafiya ko kuma tsautsayi. "To ke ba kya komai da za ki taimaki kanki. "Sister ina yi. Wanki nake yi a gida kwandala - kwandala. "Wanki" ta fada tana mamakin wannan abu. Kyakkyawar yarinya irin wannan da ko beauty contest aka je tsaf zata lashe. Amma sai ta wahala zata rike kanta ita a nata tunanin kyakkyawar mace kam ai sai dai ta zauna taji dadi ba ruwanta da wahala. Tunda mafiya yawansu ma masu kudi ke aurensu. Ashe abun ba haka bane. Dace ne kawai. In ba haka ba wannan kam ai tafi karfin wulakanci akan namiji. Can kuma ta sake wani tunanin a ranta. Yanzu haka irin yaran nan ne da soyayya kan rufe musu ido. Su auri soyayya kawai su zo suna fama da wahalar rayuwa. Allahu akbar gaskiya malamai da suka ce 'IYYAKUM WAZZANNA' Wato na hane ku da zato domin zato shine mafi karyar zance. Sister Aisha dai ta gama tunaninta ta shiga falon ta. Ta bude firji ta dauko kwalbar septrin da ta ampiclox da kuma priton sai paracetamol duk na ruwa. Ta bata. Bayan ta nuna mata yadda zata bashi kowanne. Sannan ta umarceta da idan jikin baiyi sauki ba to lallai ta dawo suje ta kaita taga likita. Washegari kuwa sai gata da kanta 'yar malama umma hafsa ta rakota gidan. Ganin yara da yawa a gidan suna lesson da uwarsu ya bata mamaki. Take ta cire duk wani zato da take yi mata. Ta zauna suka gaisa ta tambayeta yaya mai jiki. Nan ta nuna mata shi yana ta wasan sa. Sadiya ta bude firji dinta ta dauko lemon data hada na matsatsatten lemon tsami da kuma danyar citta wato ginger drink ta kawo mata cikin jug ta doro akan tire da kuma kofinsa. Gaskiya sister irin mutanen nan ne masu tsantsani da kuma rashin ganin abin burgewa a tare da wani in basu ba. Amma tsaftar gidan sadiya yau kam ta kure ta. Ga yara fes fes dasu. Gida ko ina sai kamshin turaren wuta dan tsinke yake yi ga kuma lemo mai dan Karen dadi da bata taba shan irin saba. Kusan duk ginger da take gani zata ganta tayi duhu alamar bata kankaru ba. Amma wannan shar da ita. Ta yaba mata kwarai har ta bata shawarar data dinga yin na sayarwa. Ai kuwa tayi murna da wannan shawarar data bata. Dama ga fridge dinta da Sani ya sai musu lokacin daya dauki wani kudin sa a kumbotso. Tare ya hada musu da talabijin da kuma decoder ta ABG Da video. Wannan zuwa na sister gidan sadiya shiya sanya ta shiga cikin jerin masu kawo mata wanki. Ba domin Komai ba sai taftarta data yaba da ita. Kudin wankin da sister ta biya ta dashi ta saro kayan yin ginger. Da farko shagon mustafa ta fara kaiwa ai kafin kace meye wannan ya kare sai dai kudinta. Ga na gida da take bari shima in aka dinga sallama mussaman wata dabar samari da suke kusa da gidan. Da suka gane ba karamin ciniki suke mata ba.=====*****53*****===== Wani abin haushi kawai sai ga huwaila tazo wai ta koya mata yadda ake yi itama zata fara. A lokacin suna tare da hafsa. A gabanta ta hada komai ta nuna mata yadda zata yi. Hafsa dai nata kumbure kumburen jin haushi. Sai da ta fita tace. "Allah umman kamal mai yasa kika nuna mata. Kowa yaje ya koyi nasa. Mamaki ne ya kama sadiya na wannan magana da hafsa tayi. Ta rike baki tace "anya hafsa inace ni dake jiya da muka dauki karatu a wajen malama tayi mana bayanin hadisin da aka ce komai ya same ka bai kasance zai kuskure ka ba haka nan komai ya kuskure maka bai kasance zai same ka ba. Kowa da rabonsa a kasuwar nan. Ta tura bakinta tace. "Ai da ita ce baza ta koya miki ko da yake ma tayi wa zai sayi kayan wannan kazamar matar. "Uhm uhm hifzu lisaniy. Ki kiyaye harshen ki. "Wai astagfirullah ashe fa gulma ce nayi. Ta fada cikin dariya.=====*****53*****===== Wani abin haushi kawai sai ga huwaila tazo wai ta koya mata yadda ake yi itama zata fara. A lokacin suna tare da hafsa. A gabanta ta hada komai ta nuna mata yadda zata yi. Hafsa dai nata kumbure kumburen jin haushi. Sai da ta fita tace. "Allah umman kamal mai yasa kika nuna mata. Kowa yaje ya koyi nasa. Mamaki ne ya kama sadiya na wannan magana da hafsa tayi. Ta rike baki tace "anya hafsa inace ni dake jiya da muka dauki karatu a wajen malama tayi mana bayanin hadisin da aka ce komai ya same ka bai kasance zai kuskure ka ba haka nan komai ya kuskure maka bai kasance zai same ka ba. Kowa da rabonsa a kasuwar nan. Ta tura bakinta tace. "Ai da ita ce baza ta koya miki ko da yake ma tayi wa zai sayi kayan wannan kazamar matar. "Uhm uhm hifzu lisaniy. Ki kiyaye harshen ki. "Wai astagfirullah ashe fa gulma ce nayi. Ta fada cikin dariya.****54*****===== Da wannan wanki da kuma ginger drink dinta data kiyi. Ta rike yaranta a haka kuma kaga har alheri take yi. Kusan duk inda akayi haihuwa a makotansu ko kuma ana biki dai-dai abinda Allah ya hore mata zata baka. Ba kuma da niyyar biki don a rama mata kamar yadda mafi yawan mata kanyi ba. Ginger kam ai ta karbu. Tun da tun daga babban layi sai a zo a saya. Wasu ma in zasuyi biki ko suna. Sukan bata tayi mai yawa. Dan asusu ta samu take tara kudinta da niyyar ta saka su walid da imam makaranta. Wata rana taje ta gaida yaya kulu kamar yadda ta saba tanayi lokaci-lokaci ta sauka daga hayis. Taga signboard na wata makarantar koyon dinki da aka bude anan unguwarsu. Ba tare da bata lokaci ba. Ta shiga ta tambaya aka gaya mata nawa ake biya. Ta karbo form ta dawo gida. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kudi dai da zata shiga makarantar nan tana dasu. Ga kuma su walid 'yan shekara biyar da taso su shiga makaranta wannan shekarar. Tunda karatun da ta koya musu a gida ba makarantar kudin da baza su iya shiga ba kuna radam su zauna. In ta gwamnati ce kuwa ko dan aji uku ba zai nuna musu komai ba. A dan lesson din da tayi dasu. Rashin sanin iya abinda ya kamata yara su koya a kowanne zangon karatu yasa ta tsallake ba tare da ta sani ba. Ga haddar da suke yi A wajen malam mai salati wadda kamal ne kawai bai fara zuwa ba. Ga kuma islamiyya da suke zuwa. Ai yara kam karatu radam ba Arabi ba ba boko ba. Kamar yadda ta saba bata cika shawara da kowa ba don gudun tonan asiri. Diary ta dauko ta rubuta matsalarta. Takan ji damuwa ta ragu a zuciyarta duk sanda ta rubuta ta a dan littafin nan. Da daddare kuwa istikhara tayi ta nemi zabi a wajen RABBIL IZZATI. Washegari da ta tashi kuwa sai taji hankalinta yafi kwanciya da ta shiga makarantar koyon dinkin nan. Tun da dai karin samun kudin shiga ne. Ta san Idan yara suka fara makaranta wanki da kuma lemon ginger bazai rike suba. Kuma ko banza ta huta da wankin nan mai azaba. Da wasu zasu kawo maka shi ba sabulun kirki sai kaya masu uwar dauda kayi ta dirza kafin su fita. Inka gama kuma ace za'a aiko ma da kudin. Wani haka zai mula bazai biya ba. Kowacce karuwa bata zuwa sai da matsala. Ita wadda ta hararo yaya zata yi da yara in ta fara zuwa makarantar. Har ta hakura saboda bata ga yadda zata yi da yaranta ba. A wannan jumma'ar taje gaida gwaggon Rahina kamar yadda ta saba. Lokaci-lokaci tana jin dadin hira da tsohuwar nan. Bayan sun gaisa labari ya kawo labari har take bata labarin makarantar data so shiga amma saboda yara ta hakura. "Wane irin hakura ba dadin ji. Gwaggo ta fada. Cikin murya mai nuna alamun rashin jin dadi. "Tattara su ki dinga kawo min su har shi wannan da kika mannewa kin ki rabuwa da wahalar sa sai anyi magana kice wai maraya ne. In ba iya shege ba ace yaro ya haura shekara biyu amma bai wuce goyo ba. Duk kawo su. Suma samu haddar ta dada nisa har shima wannan din. "Amma gwaggo baza su wahalar dake ba. Babu wata wahalar wa. Kuma wata uku kamar yaune. Yo ni duk wanda yayi min a cikinsu ramawa zanyi bazan yadda a ce ni babba bace. Dariya suka saka tare. Ta dan dada kaskantar da murya "Amma gwaggo banda kamal shi sai in dinga tafiya dashi. "Har shi zaki ajiye. Duk wannan makon nasa da kema naki ajiye shi zakiyi. Dama ina cike dashi rannan da kuka zo kika shiga bandaki ya tsaya a kofar bandakin duk sai da ya hada gidan nan. Malam tun daga soro ya taho yana tambayar meya same shi. Ni dan haushi ma kasa magana nayi sai murtala ne yake gaya masa abinda ya faru. "Kai gwaggo sa ido ne kawai irin na murtala kuma shi da yake kawu ai baya biye muku ba tunda ke bakya auren. Haka kuwa akayi da wannan shawara ta gwaggo taci gaba da zuwa koyon dinki. Da sauran kudin da kuma ciniki ginger na wannan zafin ta hada ta sai keken dinki ta ajiye a gida. Allah na taimakon duk wanda ya taimaki kansa. Sadiya wata iri ce. Duk abinda tasa kanta koyo to kuwa sai ta zarce makadi da rawa. Ai kan kace kwabo ta koyo yanka da taku. Kai ganin haka ma a maimakon wata uku da tai niyyar yi sai. Sai kawai ta biya ajin kos din wata shida. Kwalliya kuwa ta biya kudin sabulu. Sadiya ta fito a matsayin kwararriyar tela mai daraja ta farko wato fist class inji masu digiri. Kamar da wasa ta fara dinki. Da yake abin na Allah ne kafin karshen shekarar nan sai da aka santa da dinki a unguwarsu. Wata karin fasaha data samu daga gareta shine dinka kayan 'yan kanti abdulsalam dan wajen yaya kulu na uku ya kawo mata ziyara. Sai taga wani yadi mai kyau a jikinsa. Ta tambaye shi ina ya sayo ya gaya mata a nan kofar wambai ake kawo su a kayan gwanjo amma sababbi ne. Shiya rakata taje ta siyo domin ta dinka wa su walida 'yan riguna. Wani littafin mother care ta samu a wajen sister mai dauke da hotunan kayan yara masu mutukar kyau da kuma tsari tana dubawa ta samo kalolin riga da siket da kuma dogayen riguna iya gwiwa na yara masu kyau. Da yadin nan da ta sayo ta gwada dinka wa. Haba wai aida ta sa musu a jikinsu kai kace 'ya'yan turawa ne dan kyau da suka yi. Ai wannan shi ya zamo mata mai talla shi ke da riba. Malama umma ita ta fara tambayarta inda ta samo musu riguna masu kyau. Har tana fadin idan ba tsada in sayo wa 'yar kanwata. Ta gaya mata cewa dinka wa tayi. Tayi mamaki mutuka. Tace "dama har da kayan 'yan kanti aka koya muku a makarantar.? Ta amsa mata cewar karanbani kawai tayi ta dinka wa yaranta. Ta yaba da fasahar sadiya matuka. Itace kwastoma ta farko a wannan cinikin. 'yan unguwa suka yaba da kayan suma aka dinga zuwa saye. Da wannan ta fara. Shima kuma tana samun ciniki matuka da alheri akai. Wanda take sayen yadi a wajen sa kuwa da ya samu sababbin yadudduka zai turo yaronsa har gida ta zabi wadanda take so ya karbo masa kudinsa.****54*****===== Da wannan wanki da kuma ginger drink dinta data kiyi. Ta rike yaranta a haka kuma kaga har alheri take yi. Kusan duk inda akayi haihuwa a makotansu ko kuma ana biki dai-dai abinda Allah ya hore mata zata baka. Ba kuma da niyyar biki don a rama mata kamar yadda mafi yawan mata kanyi ba. Ginger kam ai ta karbu. Tun da tun daga babban layi sai a zo a saya. Wasu ma in zasuyi biki ko suna. Sukan bata tayi mai yawa. Dan asusu ta samu take tara kudinta da niyyar ta saka su walid da imam makaranta. Wata rana taje ta gaida yaya kulu kamar yadda ta saba tanayi lokaci-lokaci ta sauka daga hayis. Taga signboard na wata makarantar koyon dinki da aka bude anan unguwarsu. Ba tare da bata lokaci ba. Ta shiga ta tambaya aka gaya mata nawa ake biya. Ta karbo form ta dawo gida. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kudi dai da zata shiga makarantar nan tana dasu. Ga kuma su walid 'yan shekara biyar da taso su shiga makaranta wannan shekarar. Tunda karatun da ta koya musu a gida ba makarantar kudin da baza su iya shiga ba kuna radam su zauna. In ta gwamnati ce kuwa ko dan aji uku ba zai nuna musu komai ba. A dan lesson din da tayi dasu. Rashin sanin iya abinda ya kamata yara su koya a kowanne zangon karatu yasa ta tsallake ba tare da ta sani ba. Ga haddar da suke yi A wajen malam mai salati wadda kamal ne kawai bai fara zuwa ba. Ga kuma islamiyya da suke zuwa. Ai yara kam karatu radam ba Arabi ba ba boko ba. Kamar yadda ta saba bata cika shawara da kowa ba don gudun tonan asiri. Diary ta dauko ta rubuta matsalarta. Takan ji damuwa ta ragu a zuciyarta duk sanda ta rubuta ta a dan littafin nan. Da daddare kuwa istikhara tayi ta nemi zabi a wajen RABBIL IZZATI. Washegari da ta tashi kuwa sai taji hankalinta yafi kwanciya da ta shiga makarantar koyon dinkin nan. Tun da dai karin samun kudin shiga ne. Ta san Idan yara suka fara makaranta wanki da kuma lemon ginger bazai rike suba. Kuma ko banza ta huta da wankin nan mai azaba. Da wasu zasu kawo maka shi ba sabulun kirki sai kaya masu uwar dauda kayi ta dirza kafin su fita. Inka gama kuma ace za'a aiko ma da kudin. Wani haka zai mula bazai biya ba. Kowacce karuwa bata zuwa sai da matsala. Ita wadda ta hararo yaya zata yi da yara in ta fara zuwa makarantar. Har ta hakura saboda bata ga yadda zata yi da yaranta ba. A wannan jumma'ar taje gaida gwaggon Rahina kamar yadda ta saba. Lokaci-lokaci tana jin dadin hira da tsohuwar nan. Bayan sun gaisa labari ya kawo labari har take bata labarin makarantar data so shiga amma saboda yara ta hakura. "Wane irin hakura ba dadin ji. Gwaggo ta fada. Cikin murya mai nuna alamun rashin jin dadi. "Tattara su ki dinga kawo min su har shi wannan da kika mannewa kin ki rabuwa da wahalar sa sai anyi magana kice wai maraya ne. In ba iya shege ba ace yaro ya haura shekara biyu amma bai wuce goyo ba. Duk kawo su. Suma samu haddar ta dada nisa har shima wannan din. "Amma gwaggo baza su wahalar dake ba. Babu wata wahalar wa. Kuma wata uku kamar yaune. Yo ni duk wanda yayi min a cikinsu ramawa zanyi bazan yadda a ce ni babba bace. Dariya suka saka tare. Ta dan dada kaskantar da murya "Amma gwaggo banda kamal shi sai in dinga tafiya dashi. "Har shi zaki ajiye. Duk wannan makon nasa da kema naki ajiye shi zakiyi. Dama ina cike dashi rannan da kuka zo kika shiga bandaki ya tsaya a kofar bandakin duk sai da ya hada gidan nan. Malam tun daga soro ya taho yana tambayar meya same shi. Ni dan haushi ma kasa magana nayi sai murtala ne yake gaya masa abinda ya faru. "Kai gwaggo sa ido ne kawai irin na murtala kuma shi da yake kawu ai baya biye muku ba tunda ke bakya auren. Haka kuwa akayi da wannan shawara ta gwaggo taci gaba da zuwa koyon dinki. Da sauran kudin da kuma ciniki ginger na wannan zafin ta hada ta sai keken dinki ta ajiye a gida. Allah na taimakon duk wanda ya taimaki kansa. Sadiya wata iri ce. Duk abinda tasa kanta koyo to kuwa sai ta zarce makadi da rawa. Ai kan kace kwabo ta koyo yanka da taku. Kai ganin haka ma a maimakon wata uku da tai niyyar yi sai. Sai kawai ta biya ajin kos din wata shida. Kwalliya kuwa ta biya kudin sabulu. Sadiya ta fito a matsayin kwararriyar tela mai daraja ta farko wato fist class inji masu digiri. Kamar da wasa ta fara dinki. Da yake abin na Allah ne kafin karshen shekarar nan sai da aka santa da dinki a unguwarsu. Wata karin fasaha data samu daga gareta shine dinka kayan 'yan kanti abdulsalam dan wajen yaya kulu na uku ya kawo mata ziyara. Sai taga wani yadi mai kyau a jikinsa. Ta tambaye shi ina ya sayo ya gaya mata a nan kofar wambai ake kawo su a kayan gwanjo amma sababbi ne. Shiya rakata taje ta siyo domin ta dinka wa su walida 'yan riguna. Wani littafin mother care ta samu a wajen sister mai dauke da hotunan kayan yara masu mutukar kyau da kuma tsari tana dubawa ta samo kalolin riga da siket da kuma dogayen riguna iya gwiwa na yara masu kyau. Da yadin nan da ta sayo ta gwada dinka wa. Haba wai aida ta sa musu a jikinsu kai kace 'ya'yan turawa ne dan kyau da suka yi. Ai wannan shi ya zamo mata mai talla shi ke da riba. Malama umma ita ta fara tambayarta inda ta samo musu riguna masu kyau. Har tana fadin idan ba tsada in sayo wa 'yar kanwata. Ta gaya mata cewa dinka wa tayi. Tayi mamaki mutuka. Tace "dama har da kayan 'yan kanti aka koya muku a makarantar.? Ta amsa mata cewar karanbani kawai tayi ta dinka wa yaranta. Ta yaba da fasahar sadiya matuka. Itace kwastoma ta farko a wannan cinikin. 'yan unguwa suka yaba da kayan suma aka dinga zuwa saye. Da wannan ta fara. Shima kuma tana samun ciniki matuka da alheri akai. Wanda take sayen yadi a wajen sa kuwa da ya samu sababbin yadudduka zai turo yaronsa har gida ta zabi wadanda take so ya karbo masa kudinsa.****54*****===== Da wannan wanki da kuma ginger drink dinta data kiyi. Ta rike yaranta a haka kuma kaga har alheri take yi. Kusan duk inda akayi haihuwa a makotansu ko kuma ana biki dai-dai abinda Allah ya hore mata zata baka. Ba kuma da niyyar biki don a rama mata kamar yadda mafi yawan mata kanyi ba. Ginger kam ai ta karbu. Tun da tun daga babban layi sai a zo a saya. Wasu ma in zasuyi biki ko suna. Sukan bata tayi mai yawa. Dan asusu ta samu take tara kudinta da niyyar ta saka su walid da imam makaranta. Wata rana taje ta gaida yaya kulu kamar yadda ta saba tanayi lokaci-lokaci ta sauka daga hayis. Taga signboard na wata makarantar koyon dinki da aka bude anan unguwarsu. Ba tare da bata lokaci ba. Ta shiga ta tambaya aka gaya mata nawa ake biya. Ta karbo form ta dawo gida. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kudi dai da zata shiga makarantar nan tana dasu. Ga kuma su walid 'yan shekara biyar da taso su shiga makaranta wannan shekarar. Tunda karatun da ta koya musu a gida ba makarantar kudin da baza su iya shiga ba kuna radam su zauna. In ta gwamnati ce kuwa ko dan aji uku ba zai nuna musu komai ba. A dan lesson din da tayi dasu. Rashin sanin iya abinda ya kamata yara su koya a kowanne zangon karatu yasa ta tsallake ba tare da ta sani ba. Ga haddar da suke yi A wajen malam mai salati wadda kamal ne kawai bai fara zuwa ba. Ga kuma islamiyya da suke zuwa. Ai yara kam karatu radam ba Arabi ba ba boko ba. Kamar yadda ta saba bata cika shawara da kowa ba don gudun tonan asiri. Diary ta dauko ta rubuta matsalarta. Takan ji damuwa ta ragu a zuciyarta duk sanda ta rubuta ta a dan littafin nan. Da daddare kuwa istikhara tayi ta nemi zabi a wajen RABBIL IZZATI. Washegari da ta tashi kuwa sai taji hankalinta yafi kwanciya da ta shiga makarantar koyon dinkin nan. Tun da dai karin samun kudin shiga ne. Ta san Idan yara suka fara makaranta wanki da kuma lemon ginger bazai rike suba. Kuma ko banza ta huta da wankin nan mai azaba. Da wasu zasu kawo maka shi ba sabulun kirki sai kaya masu uwar dauda kayi ta dirza kafin su fita. Inka gama kuma ace za'a aiko ma da kudin. Wani haka zai mula bazai biya ba. Kowacce karuwa bata zuwa sai da matsala. Ita wadda ta hararo yaya zata yi da yara in ta fara zuwa makarantar. Har ta hakura saboda bata ga yadda zata yi da yaranta ba. A wannan jumma'ar taje gaida gwaggon Rahina kamar yadda ta saba. Lokaci-lokaci tana jin dadin hira da tsohuwar nan. Bayan sun gaisa labari ya kawo labari har take bata labarin makarantar data so shiga amma saboda yara ta hakura. "Wane irin hakura ba dadin ji. Gwaggo ta fada. Cikin murya mai nuna alamun rashin jin dadi. "Tattara su ki dinga kawo min su har shi wannan da kika mannewa kin ki rabuwa da wahalar sa sai anyi magana kice wai maraya ne. In ba iya shege ba ace yaro ya haura shekara biyu amma bai wuce goyo ba. Duk kawo su. Suma samu haddar ta dada nisa har shima wannan din. "Amma gwaggo baza su wahalar dake ba. Babu wata wahalar wa. Kuma wata uku kamar yaune. Yo ni duk wanda yayi min a cikinsu ramawa zanyi bazan yadda a ce ni babba bace. Dariya suka saka tare. Ta dan dada kaskantar da murya "Amma gwaggo banda kamal shi sai in dinga tafiya dashi. "Har shi zaki ajiye. Duk wannan makon nasa da kema naki ajiye shi zakiyi. Dama ina cike dashi rannan da kuka zo kika shiga bandaki ya tsaya a kofar bandakin duk sai da ya hada gidan nan. Malam tun daga soro ya taho yana tambayar meya same shi. Ni dan haushi ma kasa magana nayi sai murtala ne yake gaya masa abinda ya faru. "Kai gwaggo sa ido ne kawai irin na murtala kuma shi da yake kawu ai baya biye muku ba tunda ke bakya auren. Haka kuwa akayi da wannan shawara ta gwaggo taci gaba da zuwa koyon dinki. Da sauran kudin da kuma ciniki ginger na wannan zafin ta hada ta sai keken dinki ta ajiye a gida. Allah na taimakon duk wanda ya taimaki kansa. Sadiya wata iri ce. Duk abinda tasa kanta koyo to kuwa sai ta zarce makadi da rawa. Ai kan kace kwabo ta koyo yanka da taku. Kai ganin haka ma a maimakon wata uku da tai niyyar yi sai. Sai kawai ta biya ajin kos din wata shida. Kwalliya kuwa ta biya kudin sabulu. Sadiya ta fito a matsayin kwararriyar tela mai daraja ta farko wato fist class inji masu digiri. Kamar da wasa ta fara dinki. Da yake abin na Allah ne kafin karshen shekarar nan sai da aka santa da dinki a unguwarsu. Wata karin fasaha data samu daga gareta shine dinka kayan 'yan kanti abdulsalam dan wajen yaya kulu na uku ya kawo mata ziyara. Sai taga wani yadi mai kyau a jikinsa. Ta tambaye shi ina ya sayo ya gaya mata a nan kofar wambai ake kawo su a kayan gwanjo amma sababbi ne. Shiya rakata taje ta siyo domin ta dinka wa su walida 'yan riguna. Wani littafin mother care ta samu a wajen sister mai dauke da hotunan kayan yara masu mutukar kyau da kuma tsari tana dubawa ta samo kalolin riga da siket da kuma dogayen riguna iya gwiwa na yara masu kyau. Da yadin nan da ta sayo ta gwada dinka wa. Haba wai aida ta sa musu a jikinsu kai kace 'ya'yan turawa ne dan kyau da suka yi. Ai wannan shi ya zamo mata mai talla shi ke da riba. Malama umma ita ta fara tambayarta inda ta samo musu riguna masu kyau. Har tana fadin idan ba tsada in sayo wa 'yar kanwata. Ta gaya mata cewa dinka wa tayi. Tayi mamaki mutuka. Tace "dama har da kayan 'yan kanti aka koya muku a makarantar.? Ta amsa mata cewar karanbani kawai tayi ta dinka wa yaranta. Ta yaba da fasahar sadiya matuka. Itace kwastoma ta farko a wannan cinikin. 'yan unguwa suka yaba da kayan suma aka dinga zuwa saye. Da wannan ta fara. Shima kuma tana samun ciniki matuka da alheri akai. Wanda take sayen yadi a wajen sa kuwa da ya samu sababbin yadudduka zai turo yaronsa har gida ta zabi wadanda take so ya karbo masa kudinsa.=====*****55*****===== Bata tsaya akan kayan mata ba kawai. Ta gwada yanka kayan kanti na maza. Anan ne ma ta dan sha wahala kafin ta gano yan kansu. Suma sai gasu sun shiga jerin kayan sayar warta. Ganin ta samu 'yan kudi masu dama sai tasa yaranta zuwa makarantar dasu Amir suka yi. Wacce kuma itama nan ta rubuta jarrabawar ta. Makarantar ta dada kyau an kawatata. Mai makarantar balarabiya ce amma sun dade a Nigeria ita da mijinta. Makarantar nada kwazo matuka da kuma sababbin hikimomi da dabarun koyarwa hadi da kayan karatu masu inganci. Ta shiga cikin makarantar tana nan kamar yadda ta santa sai dai an dada kawata ta an kuma kara wasu ajujuwan da kuma ofis na malamai. Wajen shugabar makarantar suka shiga ita da kyawawan yaranta guda biyar masu kyakkyawar sutura. Sun gaisa kuma har madam ayush ta gane ta. Tayi mamaki kwarai data ganta da yara ta kuma gaya mata duk nata ne. Ta janyo hannun walida da shukra tana fadin "beauty I like your dress " murmushi kawai suka yi. A zatonta ma basu ji me tace ba. Cikin turanci ta Tambayesu sunayen su da shekarun su suka gaya mata. Taji dadin ganin yaran suna jin turanci tasan matsalarsu zata zamo karama wajen fahimtar karatu. "Who bought this dress for you? Ta sake tambayarsu ga mamakinta sai taji shukra ta amsa mata "our mummy made it her self. "You did? Ta juya akalar tambayarta zuwa wajen sadiya. Dariya tayi ta bata amsa. Madam Ayush ta yaba da yanda rigar ta tsaru. Simple da ita amma dinkin ya dinku matuka. Bashi da wata tawaya kai kace dizaina ne. A lokacin su walid da imam shekararsu bakwai. Shukra da jidda da kuma walida shekararsu shida sai kamal me shekara uku da rabi. An yi musu jarrabawa ai kuwa taga amfanin koyarwar da tayi musu a gida. Aka gwada su aikin 'yan aji daya suka cinye. Kamar wasa aka ce bari a gwada su na 'yan aji biyu shima tas suka cinye. Aka sake basu na 'yan aji uku shima tsaf suka lashe. Aka bada ta 'yan aji hudu shima suka ci fiye da rabi. Tofa madam Ayush ta yaba da kokarin yaran matuka da kuma wannan sakamako nasu. Ita dai sadiya ta nuna tafi son a saka mazan aji uku matan kuma aji biyu. Haka kuwa aka yi. Aka bata lissafin kudin makaranta na littatafai da kuma kayan makaranta. Tofah ba hawan ba saukar inji madugun fulani. Ba samun makaranta mai kyau bace matsalar. Kudin da za'a biya mata shine babbar magana. Kudi kam sun shallake tunanin sadiya. Dan abin data tanada ba zai samata yara biyar a wannan makarantar ba. Ta dan yi jim sannan tace da madam ayush "inaga in saka manyan in yaso ko badi sai in saka matan. Da wannan shawarar taje ta biya kudin a wajen biya. Amma da taje karbar litattafai sai aka gaya mata idan ta gama madam tace ta same ta a ofis. Ta koma ofis din ta same ta. Madam tace "da gaske ke kika dinka rigar jikin yaranki.? Ta amsa da cewar ita ta dinka Harma data jikin yaran maza. "In that case I know how you can pay your children 's school fees. Tana fada tare da murmushi a fuskarta. Kije ki kawo min sanfur ns kayan makaranta a dinke in gani. Sai in baki kwangilar dinka mana uniform. Dama muna son mu canja uniform din makaranta. Da murnar ta tayi godiya sosai. Duk maganganun da suka yi da turanci suka yi su. Daga nan kuwa kasuwar sabon gari ta wuce. Ta shiga inda ake sayar da yadukan dinka wando na maza da kuma yadin shirt. Tayi ta dubawa har daga baya ta tsaida ra'ayin ta akan wani yadi mai dan kauri kadan ruwan toka da kuma yadin shirt fari mai layi layin ruwan toka a jiki. Ta sayo ta hada ta dawo gida. A daren kuwa ta dauko littafin nan na mother care da take daukar samfur -samfur na dinki a ciki. Ta duba har dai ta tsaya akan wata riga da siket da ta gani. Rigar shirt ce amma sikert din ya zarce gwiwa mai manyan tattara. Wadda aka dinka ta iya gwiwa daga nan kuma aka barta. Hakan yasa siket din ya baje daga kasa. Bayan riga da sikert din sai ta hada da wata yar falmaran kalar siket din wadda za'a dora akan shirt din. A jikin falmaran din ta baya aka yi belt wanda za'a ja ya bada shep mai kyau ba tare da ya kama jiki ba. Ta hada da wani samfurin neek tie wanda ba daura shi ake yi ba. Za'a dinka kamar wanda ake daurawa. Amma shi sai ta dasa roba a ramin wuyan yadda yaro zura shi kawai zaiyi. Mazan kuma wando da riga ta dinka musu. Shirt mai dogon hannu da kuma wandonta suma hadi da neek tie din. Da kuma falmaran irinta 'yan matan. Washegari da hanzarinta ta isa makarantar madam ayush tayi mamakin ganinta da wurwur haka. Sannan kuma ta yaba da samfurin kayan data kawo mata kai har ma kalar ta yaba kwarai. Nan akayi lissafin yawan kayan da za'a dinka da kuma farashin kowanne. A gaskiya sadiya bata taba alfahari da kanta irin wannan rana ba. Ranar ta dada yarda da indai ka tashi nema to kuwa allah zai taimake ka. Kudin da aka biya ta a wannan lokaci ba kadan bane. A yadin ma sai da ta sami riba. Sannan kuma ga kudin dinki da aka biya ta. Kudin makaranta tsaf suka fito daga hannun mai makaranta abin da ta biya kuwa sai dawo mata dasu akai. Nan ta biya kasuwar sabon gari ta saro yadin da zata yi amfani dashi da kuma sauran kayan dinki. Ganin ta sami dan canji tayi niyyar yi musu 'yan saye- sayen bukatun gida da suke da bukata. Washegari mota ta hau ta wuce kasuwar rims. Dai dai inda aka sauke shagon wani mutum ne da yake saida kayan turaren wuta dan maiduguri. Nan take wata idea ta fado mata ta yanda zata dada samun kudin da zata yi hidimar gidanta. Ta san dinkin uniform ba zata kuma samun mai yawan na yau ba. Tunda wannan karon uniform din aka canza gaba daya. Saboda haka gaba daya makarantar kowa zai saya. Nan gaba kuwa sai dai masu bukatar canza nasu ko kuma sababbin dauka. Fiye da rabin kudin nan ta zaftare ta sari kayan hada turaren wuta irin su hwi marshush sandal gab-gab. Aya da kuma kayan turaren humra. Dan canjin dashi tayi musu dan cefane da ba zai haura musu sati ba.=====*****56*****===== Makarantar da su walid zasu shiga cikin hutu suke. Amma saura sati biyar su bude. Haka nan ta kama dinki ka'in da na'in. Dan gajiya kam taji jiki. Amma tunanin irin nauyin 'ya'yan dake kanta da kuma nauyin alkawarin data dauka. Shiya ke dada karfafa mata zuciya abisa aikin nata. Ta dau hutu a wajen malama umma wacce ke mata karin litattafan fiqhu hadisi da kuma tilawar alkur'ani. Hatta da nafilolinta bata samu damar yinsu ba a wannan lokaci. Malama umma tace wannan sana'ar ma da take ibada ce domin ba dan ta tara a bin duniya take ba. Ko domin ta sayi kaya na alfarma. A'a tana yi ne don kulawarta akan yara. Farilla ce dai ta nuna mata komai ayyukan da suka sata a gaba ta tabbatar ta gabatar akan lokaci. Ana gobe za'a bude makaranta bata runtsa ba. Amma Allah cikin ikonsa da kaya seti dari biyar ta nufi makarantar. Kowanne dalibi set biyu haka ta kwana hada su guri guda. Madam Ayush kam ta yaba kwarai da ganin kayan da bata tsammace su yanzu ba. Ga wani abin burgewa a gefen siket din 'yan matan sai tasa roba a gefe da gefe wacce ta boye ta a cikin kalmasar siket din. Wadda idan yayi kadan ba sai an bude ba robar zata bude da kanta. Haka shima wandon mazan tasa roba daga bayan wandon. Yadda koda yayi yawa ba sai an nemi belt ba. Rigar kuwa sai tayi kalmasa hawa biyu. Idan tayi kadan farkewa kawai za'ayi ta karu. Ta matan kuma wato manya yan sakandire sai ta dan take ta daga wajen kirji zuwa ciki inda ta bada shep mai kyau ba kuma tare da ta dame ba. Kaya dai kam sun yi kyau da tsari. Mai dinki kuma ta cafki kudinta. Yara sun fara zuwa makaranta saboda haka hayaniya ta ragu sosai a gidanta. Bata koma ta zauna ba. Bayan sun tafi da safe zata gyara gidanta tsaf sai kuma ta hada lemon ginger ta mika wa mustafa mai shago. Malam mai salati a cikin almajiran sa ya samo mata wani almajiri mai hankali da yake shigowa yana taya ta da wasu ayyukan kamar wankin yara da kuma wanke- wanke da aka kwana ta yaba da tsaftar sa sai ya zama na har wanke cittar lemo shi yake mata ya kuma dura a robobi. Samun karin lokaci sai ta fara sana'ar turaren wuta Haba wa unguwa ta dauki kamshi makotanta har cewa suke su ko basu saya ba. Kamshin data bada musu ya ishe su. Amma shima fa tana farawa kamar an buga tambari ko da yake shi hafsa ce 'yar wajen malama umma ta dauka ta shiga gida-gida tana talla tana kuma gaya musu gidan da ake sayarwa. Har kuwa gidajen babban layi sai da takai. Cinikin ma yafi yawa a can. Su walid da 'yan uwansa karatu kawai suke yi. Ga kwakwalwa ga kudin biyan makaranta mai kyau ai shikenan sai himma kawai. Kullum basa tasowa daga makarantar bokon nan sai biyar da rabi na yamma Zasu shiga aji karfe takwas na safe su fito break tara da kwata. Sai goma su koma su fito karamin break sha daya da kwata su koma sha daya da rabi. Sai kuma su tashi karfe daya da rabi suyi sallar azahar a jam'i daga wannan lokacin har karfe uku kowa za'a kawo masa abinci daga gida suci su kuma yi wasa. Uku dai dai za'a koma aji masu home work suyi wanda basu dashi suyi karatu. Hudu saura kwata zasu fito suyi sallar la'asar bayan nan kuwa sai a shiga karatun islamiyya a tashi biyar da rabi. Wani kuma abin birgewa kullum da safe period ta farko karatun qur'ani ake a kowanne aji. Saboda haka da yamma muraja'ar na safen za'ayi sai a dora da karatun sauran litattafai.=====*****57*****===== Babu abinda ke burge sadiya da makarantar irin yadda taji su walid sun kuke suna larabci da kuma turanci saboda su kadai ne yarukan da aka yarda suyi magana dasu a harabar makaranta koda kuwa ba acikin aji kake ba. Ganin haka itama sai ta dauki sarar in sun dawo gidan ma da larabcin ko kuma turancin za'a yi magan hakan ya bata damar muraja'ar nata su kuma suna dada rainon nasu. Daga litinin har alhamis haka rayuwar makarantar su take. Ranar jumma'a ne kawai suke tashi sha biyu na rana. Duk da haka ummansu bata daina tura su wajen malam mai salati daukar hadda ba. Duk ranar asabar da lahadi tun tara na safe idan suka tafi sai azahar suke dawowa. Gida dai ya dawo daga umma sai dan lelenta wanda 'yan unguwa suke mata lakabi da sunansa wato suke kiranta umman kamal. Shi ma yadda ta taso da 'yan uwansa haka ta fara biya masa karatu. Tana dinkinta ko hada lemo ko kuma hada turaren wuta. Zaka jita tana biya masa karatu idan kuwa ka shigo kajita tana hira dashi sai ka dauka da wani babban mutum take magana. A haka rayuwarsu take tafiya. Wata rana ne bayan sun dawo daga ziyarar da suke kaiwa inna duk jumma'a. Wadda sadiya ta maida ta ka'ida ko ita baza ta je ba. Zata yiwa yaran kwalliya ta basu dan abin da ya sawwaqa kona abinci ko kuma abin masarufi kai ko da goro ne sai ta kulle tace su kai mata. Ba dai zasu shiga hannu ba komai ba. Suna cin abinci da daddare sai jidda wadda duk tafi 'yan uwanta magana tace umma meye kwalamammu.? Tayi tsai da cin abincin da take yi wanda suka saba tare take zuba musu a tire suci. Suna ci tana koyar dasu ladduban cin abinci. Kamar su tauna da yadda zaka debe shi. Ta maida hankalinta kanta tace "a ina kika ji wannan kalmar.? Shukra ta amsa mata da cewa "Wai fa dazu ne muka shiga gidan inna suna cin kaza ita da anti huwaila. Shine ita antin tace ga kwalamammu nan sun zo. Shine ta fada miki. Maganar ta bata mata rai matuka. Taga indai kwalama ce to ita kam huwaila sai dai a bata certificate domin haka kawai zata nado zaninta ta shigo nan gidan tace tazo neman abin kwadayi. Kuma ko bata da shi sai tasan dabarar da tayi ta bata wani abu. Banda wannan ma fiye da rabin kayan jeren da aka yi mata mai kwalama tasa ta siyarwa suka ci nama da kudin ita da mijinta. Ta kalle su tace "Amma na hana ku idan kunya mutum yana cin abu ku kura masa ido kuna kallon sa ko kuma ku roke shi. Umma in kayi haka shine ka zama kwalamammu? Inji imam. "Eh ta amsa masa "kuma na gaya muku kwadayi bashi da kyau yana jawo wa mutum halaka. Ta cigaba da fada Imam ya sake cewa "Allah umma muba kwalamammu bane don bamu ga abinda take ciba sai da ta cewa inna ga kwalamammu nan sun zo sannan muka kalleta muka gane kaza take ci. Kuma ta bamu ma muka ce mun koshi. Tunda kince mu daina kwadayi " "To shi kenan mu bar zancen haka. Amma dai ku dinga dauke kanku idan kunga mutum yana cin abinci ko wani abu mai dadi. Idan kuka yi haka in kunzo gida in muna dashi ba sai muci ba. "Amma umma mu kince idan muna cin abu komai dadin sa kuma ko dan yaya yake in munga wani mu sammasa ko. Inji walida. Eh ku sammi shi. Ai rowa bata da kyau. "Kenan umma ita anti huwaila rowa tayi. "Ke kuma kina gulmarta kin san kuma gulma haramun ce. Ba kyau zancen mutum idan baya nan. Da wannan ta samu ta kashe zancen. Amma ta dauki matakin daina tura su gidan su kadai. Sai dai ta daure suje tare. Ko da minti kadan ne su shiga su fito. Bayan haka ma ta lura tarbiyyar yaran huwaila guda hudu da sauki. Zagin juna da kuma fada a tsakaninsu ba wani abu bane ba. Hatta ita inna zasu iya kallonta suce inna uwaki. Kuma duk sai ayi dariya wai duk nan yarinta ce. Alhamdulillahi ita kam bata da abin cewa sai godiya ga sarki Allah. Yadda duk ake gaya mata renon yara da wahala ita komai da sauki yake zuwa ma. Dadi da karawa kusan duk abubuwan data lissafa zata samar wa yaranta suna zuwa sannu kan hankali. Ita kam rayuwarta sai hamdala. ****************************** Alhamdulillahi muhadu a littafi na biyu na dauke da cigaban labarin. H Inna 👨‍👨‍👦