Compil By Umar Dalha Funtua. Copies By Bil-Fauzee. [12/18/2021, 8:47 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *_TREE BROTHER'S_* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page one* *To Alhamdulallah ala kalli halin ina mai ara yiwa Allah ubangiji godiya, mai kowa mai komai wanda cikin ikon sa ne da buwayarsa ya sake bani damar dawowa gareku, tare da wani sabon littafina mai taken suna TREE BROTHER'S ina mai addu'ar yanda na fara lafiya Allah ya bani damar kammala lafiya Allahumma Amin.* *Sadaukarwa* *Na sadaukar da wannan littafin wa kai ne, hakama wannan k'irkiranran labari ne dan haka ba zan iya yafe wa duk wanda yayi k'oqarin canjamin labari ba. Dan haka a kiyaye sannan kuma dan Allah in kinsan ba zaki yi comment ba to dan Allah karki karanta please na gode.* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 18/12/2021* *Time 01:55pm* *Typing................* *SHINFID'A* Zaune take sai wani hargitse fuska take kallo d'aya tak zaka yi mata ka fahimci cewar ba qalau take ba. Bugun ƙofar da a kai ne yasa ta tashi ta nufi ƙofa dan ganin waye, tafiya take sannu a hankali tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki, ta isa ga ƙofar tare da bud'ewa ta samu mai gidanta tsaye a ƙofa tayi murmushi sosai tare da furta masa kalmar sannu da zuwa, ya amsa yana wani lallausan murmushi ya janyota jikin sa sun shiga ciki sai wani kallonta yake kallo sosai, ya gama fahimtar cewa ba qlau take ba, nan kuwa ya shiga tambayar ta abin da yake faruwa da ita. "Rabin raina qlau kike kuwa fad'a min mai yake damunki dan Allah.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "ba komai Prof zaka iya yarda da ni." Ya girgiza ka tare dajan numfashi yana cewa, "Aisha shin baki shirya sanar dani gaskiyar ba ko a'a kawai kin za'bi da ki cutar da ni ta wannan hanyar fad'a min.?" Magana yake yayin da yake ri e da fuskar ta sai wani kallonta yake kallo sosai, ita ma haka kallonsa take kuma kallo sosai ta nisa tare dajan numfashi cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana. "Ba komai Prof kawai ciki na ne yake yi mun ciwo amma ba wani sosai ba zan iya jure zafin to ba buqatar ka damu sosai ka ji ko." Da sauri ya kai kallonsa ga cikin ta tare da d'ora hanunsa yana shafar cikin, ya qara da sunbata sannan ya mai da kallonsa gareta cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. "Aisha ya kamata mu tafi asibiti a duba ki sabo da ba zanso wannan yanayin naki ya cutar da yaronmu ba, ke kin san irin yanda nake matuqar masifar qaunar yarona to sam ba zan jure ganin wani abu ya cutar da shi ba to mu tafi." "Prof zafin fa kad'an ne zan iya jure wa to sam ba buqatar sai mun tafi asibiti dan Allah." "Aisha ni saidai kawai na baki hak'uri amma dole sai mun tafi asibiti yanzu." Sam bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta amsa masa da to ta tashi sun fita zuwa asibiti. Sun isa asibiti kai tsaye office d'in Dr Mas'ud ya nufa, yayi nasaran samunsa amma kuma yana duba wani sun jira na wani lokaci sannan suka shiga ciki. Bayan sun gaisa Prof Abas ya sanar da shi abin da yake tafe dasu Dr Mas'ud ya mai da kallonsa ga Aisha yana cewa, "tin yaushe hakan yake faruwa dake.?" "Kwana biyu." "watan nin cikin ki nawa.?" "Wata shida ne." Ya jinjina ka yana nazari daga bisani yaci gaba yana cewa, "ok yanzu zan baki Scan ya kamata na san lafiyar Babyn sannan sai nasan wane magani zan iya baki." Ta jinjina masa ka a lamar to nan ya basu takardar Scan sun tashi sun fice, wanda kuma kai tsaye gurin Scan suka nufa ba wani d'aukan lokaci suka gama, sun koma gurin Dr Mas'ud sun kai masa ya duba yayi murmushi sosai yana cewa. "Prof da akwai yuwar madam ta aifa maka twin's insha Allah." Yayi wani gajeran murmushi kad'an sannan ya amsa shi, "Dr Mas'ud kenan to ai Allah ne kawai ya san karatun karma Allah dai ya sauketa lafiya." Ya amsa da Amin yana murmushi cikin harshen turanci suke magana wanda wannan dalilin ne yasa Aisha bata iya fahimtar duk abin da suke fad'a ba, kasancewar ita bata yi makaranta ba sam bata jin turanci. Ya rubuta mata magani ya baiwa Prof takardar ya kar'ba tare dayi masa godiya sannan suka tashi suka fice zuwa gida, ya fara siya mata magani sannan suka isa gida sun shiga ciki ya zaunar da ita shi kuma ya tafi ya d'auko ruwa ya shiga bata magani. Bayan ta sha magani tayi masa godiya ya amsa da ba komai yaci gaba yana cewa. "Aisha ina fatan baki manta duk wani alkawarin da yake atsakaninmu ba? Ina nufin ni na fad'a maki cewar d'a d'aya kawai nake so mu aifa, sannan kuma ke kin yi man alkawarin cewar d'a ďaya kawai zaki bani to ina fatan baki manta wannan ba.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "eh Prof ni ban manta alkawarin da nayi maka ba kuma zan cika alkawari na insha Allah to zaka iya yarda da ni ka ji ko." Yayi murmushi sosai mai tare da ar dariya ya shafi fuskarta tare da sunbatarta yana cewa, "na gode sosai da kika amince da buqata na ina godiya sosai." Ta girgiza masa ka tare da furta masa kalmar, "sam ba buqatar ka gode min sabo ni nayi abin daya dace ne, amma Prof to idan kuma Allah ya bamu tagwaye fa shin ka shirya amsar yaran kuwa.?" Wani irin kallo yake yi mata wanda ya gagara furta mata komai yayi shiru na wani lokaci sosai sannan ya amsa ta, "Aisha ni d'a d'aya kawai nake buqata daga gareki kuma na muji ba mace ba, dan haka karki yarda kiyi kuskuran aifa min yara biyu ko da kuwa sun kasance dukansu maza ne, ni kawai yaro ďaya nake buqata daga gareki kuma shi zaki bani to karki ta'ba mantawa da wannan kinji ko." Magana yake cikin fishi sosai yana kai arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyarsa bedroom, Aisha ta bisa da kallo har ya shige yayin da mamakin sa da tsoron sa suka yi yawan gaske a tare da ita sosai. "Na shiga uku na ni Aisha wane irin muji na aura ne haka? Shi kawai d'a d'aya yake buqatar na aifa sannan kuma na muji yake so ba mace ba, ga shi kuma a can gurin awo an fad'a min cewar da akwai yuwar na iya aifan tagwaye, to ya zanyi kenan mai zai faru dani ko yarana idan na aifi tagwaye ni ba zan iya d'aukar hukuncin sa ba sabo da zai iya raba ni da d'ayan yarona ko yarinyata. A'a ni sam ba zan iya jure wannan ba lallai ya kamata nayi wani abu a game da wannan to mai zanyi kenan? Ya Allah ka taimaken ka aiko man da mafuta Allahumma Amin." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare da ita sosai. Bata ankara ba ta fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai, to zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo sosai. Ta tashi jiki a san yaye ta nufi bedroom d'in Abas ta shiga ciki tare da kyakkyawar sallama ya amsa ba tare daya kalleta ba, wanda hakan ne ya tabbatar mata da cewar yana fishi da ita kuma fishi sosai. Ta nisa sosai tare dajan numfashi sannu a hankali take tafiya har ta isa inda yake ya zauna kusa da shi kusa sosai, sai wani kallonsa take kallo sosai ta kai hanunta ga nasa ta shafi hanun tana murzawa cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita take magana. "Kayi hak'uri ka yafemin dan Allah karka yi fishi da ni sabo da hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai, mujina ni kawai tambayar ka nayi bawai dan na cutar da kai ba, ka sani ni kawai zanyi duk abin da kake so ne kamar dai yanda nayi alkawari to zaka iya yarda da ni dan Allah." Magana take cikin wani irin yanayi tamkar da zata yi masa kuka ya d'ago fuskarsa wanda kuma sai zuwa wannan lokacin ne ya iya kallonta sai wani kallonta yake kallo sosai, lokaci d'aya kuma ya shiga share mata kwalla yana girgiza mata ka a lamar a'a, "ki dena wannan kukan bana so sannan kuma sam bana san ki koma tambaya na irin haka kawai dai kiyi k'oqarin cika alkawarin ki kinji ko." Ta jinjina masa ka a lamar to tana wani gajeran murmushi shi ma abin da yake yi kenan, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta ya qara da furta mata kalmar ina sanki ta amsa shi da ina qaunarka. Ya d'ora kansa a kan cinyarta yana wani shafar cikin ta ya qara da sunbata yana furta kalmar, "I LUV U my Child I Love you so much." Ya fad'a tare da qara sunbatarta a ciki ta nisa sosai tare dajan numfashi tana mai sauke a jiyar zuciya yayin da take magana da zuciyarta. "Ya Ubangiji bani da wani za'bi a kan abin da mujina yake so, ban sani ba ko zan iya ba shi abin da yake so ko a'a duk da cewar ni nayi masa alkawari. Ya Allah ka bani ikon cika masa alkawarin da ni nayi masa na aifa masa d'a d'aya kamar yanda yake fata da kuma buri, ya Ubangiji idan ka bani d'a biyu ina nufin tagwaye ko kuma yarinya mace to ban san ya zanyi ba ya Ubangiji ba zan iya jure ganin mujina yana cutar da d'ayan yarona ba ko kuma yarinya ta, ya Allah karka yi man jarabawar da ba zan iya d'auka ba Allah ka aiko man da mafuta Allahumma Amin." Maganar zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Hawayen fuskarta sun zuba a kan fuskar sa da take kwance a kan cinyarta da sauri ya d'ago fuskarsa yana kallonta, kallo sosai mai cike dajin mamakin ta cikin rawar murya har yana sarkewa yake tambayar ta abin da yake faruwa da ita. "Aisha mai yake faruwa dake ne fad'a min wani abu mai ya saka kike kuka kuma gaskiyar zaki fad'a min dan Allah.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "ba komai Prof ni kawai na tina da Abbana ne shi yasa nake zubar da kwalla, Prof ni ina matuqar qaunar Abba na sosai amma kuma hakan bai hana shi mutuwa ba ni nayi kewarsa sosai." Ya tashi zaune cikin dajin tausayin ta ya shiga share mata kwalla yana rarrashin ta tare da bata magana, bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin suci abinci sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi, bayan sun qarasa ya d'auke ta zuwa gidan Ummarta domin ya kwantar mata da hankali wanda ya d'auke ta har dare sannan ta koma gida. Tin daga lokacin da Aisha ta fahimci yanda mujin ta ya tsani ta aifa masa tagwaye ko mace hankalin ta ya tashi sosai, domin kuwa Allah ne kawai ya san kwanan makaho cikin ne kawai a tare da ita amma bata da sani a kan abin da zata aifa. Tinanin hakan ne yasa duk ta fita haiyacinta yayin da tinani da damuwa suka yi yawan gaske a tare da ita sosai, Prof sai aikin tambayar ta yake mai yake damunta hakama Ummarta amma amsa ďaya take basu ita ce ba komai. Haka dai Prof yaci gaba da tarairayarta yana wani lalla'bata tare da bata cikakkiyar kulawa sosai har zuwa lokacin da cikin ta ya shiga watan aihuwa, duk da cewar qlau take amma kuma Prof ya buqaci da a yi mata C. S. Ya tafi wata kyakkyawar asibiti ta kud'i ya biya anyi shirin komai tare da saka musu ranar kwana biyu, Aisha dai biye kawai take da shi ba tare da ta san a salin gaskiyar abin da yake faruwa ba, har a kayi komai a ka gama sai ma bayan sun dawo gida ne take tambayar sa. "Prof wai mai yake faruwa da ni fad'a min wani abu shin ina da wata matsala ne dan Allah ka sanar da ni ka ji.?" Yayi murmushi sosai mai tare da ar dariya cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Karki wani damu rabin raina kina lafiya sam ba wata damuwa ko matsala a tare dake, Aisha ni kawai ina nai ma maki sauki ne ta yanda ke da kuma yarona ba zaku wahala ko cutuwa ba, shi yasa ni nake duka wannan Aisha zuwa jibi za a yi maki C. S a ciro yaronmu to kiyi farin ciki sabo da yaronmu ya kusa zuwa garemu insha Allah." Wani irin kallo take yi masa mai cike dajin mamakin sa sosai cike da firgici da rud'ani take magana. "Prof wai mai kake fad'a ne haka mai ya saka za a yi man C. S bayan kuma zan iya aihuwa da kai na? Gaskiya ni bana san C. S sabo da ina jin tsoro sosai to dan Allah karka tilassa man na ro e ka. Nayi alkawari zan baka abin da ka buqata daga gareni kuma zan cika alkawari na insha Allah to zaka iya yarda da." Magana take cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai. Ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da una sosai, hakama zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai cikin tautasa murya tare da kwantar da ita yake magana. "Aisha ni bani da niyar cutar da ke to balantana kuma yarona eh na sani na kuma yarda da cewar ke zaki cika alkawarin ki, zaki bani d'a d'aya kamar dai yanda na buqata daga gareki to amma ina san ke da kuma yarona ku kasance cikin k'oshin lafiya sosai, wanda wannan dalilin ne yasa na buqaci da a yi maki C. S to ya kamata ki fahimce ni sannan kuma ki yarda da ni please." Shiru bata amsa ba haka ya shiga rarrashinta yana lalla'bata tare da bata magana, cikin hikima da nuna kulawa yake yi mata magana tare da nuna soyayyar sa a gareta. A zahirin gaskiya tana matuqar qaunar mujin ta sosai wannan yasa take yin duk abin da yake so, sam bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta amince da buqatar sa ta a yi mata C. S yayi matuqar farin ciki sosai da hakan sai godiya yake yi mata ya qara da yin hugging d'in ta yana sunbatarta, yayin da bakinsa yake ta furta mata lafuzza masu tsananin dad'in sauraro hakan ya saka ta farin ciki sosai bayan kwana biyu................. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/19/2021, 8:32 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *TREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page two* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Sunday 19/12/2021* *Time 01:06pm* *Typing..............* Misalin ƙarfe 10:00am a ka shiga da Aisha d'akin tiyata Umma na daga gefe zaune zaman jiran tsammani, yayin da Prof Abbas yake ta aikin kai komo sam ya gagara samun natsuwa, sai fatan cikar burin sa yake na samun yaro ďaya tak kamar yanda Aisha tayi masa alkawari. Bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka da ita sosai a d'akin tiyata sun fito, cikin hanzari tare da nuna kulawa Prof ya isa ga Dr Salim yana tambayarsa mai yake faruwa. "Sam ba buqatar ka damu sosai sabo da mun yi nasaran ciro mata baby boy, yaron kyakkyawa ne sosai kamar iyayen sa Mummyn sa da Dadyn sa to kuyi farin ciki sosai, yanzu zamu canja mata guri zuwa ďakin hutu sannan zaku had'u da babyn a can." Cike da farin ciki da d'auki Prof yayi hugging d'in sa yana furta masa kalmar. "Ina godiya sosai Dr Salim ni sam ba zan iya biyanka wannan ba saidai kawai nace da kai na gode sosai." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake sa daga rungumar da yayi masa, shi kuwa murmushi kawai yake yayin daya gagara furta masa komai, sai ma juya wa da yayi ya koma ciki su kuma sun nufi d'akin da za a kai ta. Zuwan su yayi daidai da zuwan su Dr Salim nurse sun shirya ta a kan gado tare da shinfid'e babyn daga gefen ta, bayan sun qarasa sun juya sun fice Dr Salim kuma ya buqaci ganin sa ya tashi sun fita. Bayan tafiyar su Umma ta isa gurin Aisha ta zauna a kujeran da take kusa da gado, sai wani kallon ta ƴarta take cike da jin tausayin ta sosai ta kai hannun ta ga babyn tare da d'aukan sa, sai wani kallonsa take kallo sosai cike da d'auki da soyayyar sa take magana. "Jikana ina farin cikin had'uwa da kai sosai, na so kuma nayi burin a ce kai ka had'u da Kakan ka tabbas daka samu duka soyayyar sa, amma ni zan kula da wannan zanyi duk wani abin da na san zai saka shi farin ciki sosai wannan alkawari ne yarona, ina sanka sosai Allah ya baiwa Maman ka lafiya Amin." A can gurin su Dr Salim kuma suna fita kai tsaye office d'in sa ya nufa da shi sun shiga ciki ya fara rufe ofar sannan suka zauna. Prof sai wani kallonsa yake kallo sosai domin kuwa ya gama fahimtar cewar ba qlau yake ba cike da firgici da rud'ani yake magana. "Dr Salim fad'a min wani abu shin da akwai wata matsala ne gaskiyar zaka fad'a.?" Yayi shiru kad'an sannan ya jinjina masa ka a lamar eh cike da firgici rud'ani da kuma tashin hankali yake magana. "Dr Salim miye matsalar kawai dai ka sanar da ni koma miye ka ji ko.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa shi, "Prof gaskiyar ita ce Madam yara uku ta aifa amma nayi kamar dai yanda nayi umurni, zuwa yanzu yaran guda biyu sun isa gidan marayun da ka ce a kai su kuma ba wani wanda zai san da wannan nayi alkawari." Prof ya jinjina ka yana cewa, "Dr Salim kawai dai ka tabbatar da hakan domin idan har wannan zancan ya futa to fa ni zan hukunta ka da kai na, lallai karka yarda ka bar wannan sirrin ya fita ko da mai zai faru ka ji ko." Ya jinjina masa ka yana furta masa kalmar, "Prof ba wanda zai san da wannan kai ka biya ni farashin da ba zan iya yi ma yankan baya ba to zaka iya yarda da ni ka ji ko." "Kawai dai ka tabbatar da hakan." Ya jinjina masa ka a lamar to shi kuma ya tashi yayi tafiyar sa wanda kuma kai tsaye d'akin da Aisha take ya nufa. Ya shiga ciki ya samu Umma rungume da babyn cike da d'auki ya isa inda take tare da kar'ban babyn sai wani kallonsa yake kallo sosai, lokaci d'aya yaji soyayyar yaron da qaunar sa suna shigar sa ta ko ina jikinsa yayin da farin ciki yake ta shigarsa, sai wani kyakkyawan murmushi yake mai tare da ar dariya ya sunbace sa a ka da ma fuskarsa gaba d'aya. Umma kuwa sai wani kallonsa take tana murmushi ta gama fahimtar cewa yana farin cikin had'uwa da yaronsa sosai. "Yarona *Adeel* Dadyn ka yana matuqar masifar qaunarka fiye ma da yanda yake sanka, ina sanka *Adeel* soyayyar da ban ta'ba yiwa wani ba a duk fad'in duniyar nan, Allah ya raya ka ya kuma sanya wa rayuwarka albarka Allah ya baiwa Mummyn ka lafiya ta yanda zamu kasance tare da juna." Ya qara sunbatarsa tare da qara saka shi jikin sa farin cikin sa yana faruwa Umma dai sai kallonsa take tana murmushi, sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda Aisha take ya zauna gefen ta sai wani kallonta yake kallo sosai ya shafi fuskarta tare da sunbatarta. "Rabin raina ina godiya sosai a gareki da kika cika min alkawarin ki yau kin bani abin da na jima ina fatan samu, yau gani rungume da yarona *Adeel* hakan yana matuqar saka ni farin ciki sosai, ina fatan ki samu lafiya cikin sauri ta yanda zamu kasance tare da yaronmu ina sanki sosai Allah ya baki lafiya Amin." Farin cikin Umma ya qaru sosai ganin irin yanda Prof yake nuna wa arta kulawa sosai tare da bata duka soyayyar sa. "Abas a zahirin gaskiya ina farin ciki sosai da irin yanda kake nuna wa Aisha kulawa sosai, ni sam bani da wani abin da zan iya biyanka da shi saidai kawai nace na gode sosai Allah yayi albarka ya albarkaci rayuwar yaronku Allahumma Amin." Ya amsa da Amin yana murmushi ita ma abin da take yi kenan. Misalin arfe 06:00pm Aisha ta farka daga dogon barcin da tayi, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e sai wani kallon d'akin take ta sauke kallonta ga fuskar Umma, wadda bama ta san cewar ta farka ba ta ganta rungume da babyn ta wanda bata da sani a kan macace ko namuji. Lokaci d'aya tsoro da firgici suka shigeta rashin ganin Prof ya qara d'aga hankalin ta sosai, lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai bata ankara ba sai kuka, sautin kukan ta ne ya sanar da Umma cewar ta farka da sauri ta kai kallonta gareta cike da firgici ta isa inda take tana fad'ar sunanta. "Aisha mai yake faruwa da ke ne mai kuma yasa kike kuka.?" Ta girgiza mata ka tare da tambayar ta mai ta aifa. "Aisha d'a namuji ne kika aifa Dadyn sa ya sanya masa suna *Adeel* fad'a min wani abu shin yanzu kina farin ciki.?" Ta jinjina mata ka tana mai furta kalmar, "Alhamdulallah Allah na gode ma daka bani ikon cika alkawarin da nayi wa Mujina, na tabbata Prof yana farin ciki sosai sabo da zuwa yanzu burin sa ya cika domin kuwa shi ya samu abin da yake so, hakan yayi kyau Alhamdulallah! Alhamdulallah!! Alhamdulallah!!!" Umma dai kallonta kawai take tana murmushi mai had'e da ar dariya ba tare data furta mata komai ba, ba jimawa sosai Prof ya dawo yayi farin ciki sosai da yanda yaga Umma tana fira da Aisha, wanda hakan ne ya tabbatar masa da cewar tana samun sauki sosai taci gaba da samun kulawar doctor, ta samu mako d'aya sannan a ka bata sallama zuwa gida inda daga bisani suka shirya liyafar bikin suna. An yi komai na ba jinta da ban girma bikin yayi kyau sosai kuma ya qayatar da duk wanda ya halarta, sunci gaba da bawa yaronsu kulawa sosai dukansu suna cikin kyakkyawan yanayi tare da nuna wa yaronsu soyayya musamman Prof bayan wata shida. Zaune take ta buga wani irin uban tagumi ga wasu zafafan hawaye suna fita daga cikin idanuwan ta masu tsananin zafi da una sosai, kallo d'aya tak zaka yi mata ka fahimci cewar tana tare da damuwa mai girman gaske. Tana haka sai ga mai gidan ta ya shigo ya kuma same ta a cikin wannan mummunan yanayin, yayi tsaye jikin ofa sai wani kallonta yake kallo sosai ya nisa tare dajan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya tare da girgiza ka ya nufi inda take. Ya zauna kusa da ita kusa sosai wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake kallo mai cike dajin tausayin ta sosai, ya d'ago fuskarta wadda ta had'a da guiwa tana kuka sai wani kallonta yake kallo sosai ya shiga share mata kwalla, tare da sunbatarta yayi hugging d'in ta yana rarrashin ta tamkar wata qaramar yarinya. "Kiyi hak'uri dan Allah ki yafemin na san cewar ni sam ba muji na gari bane a gareki sabo da na gaza baki abin da kike buqata daga gareni, amma kuma Abida hakan yana matuqar cutar da ni sosai ta yanda ba ma zan iya kallon kai na na kuma kira kai da namuji ba. Shekarun mu uku da aure amma na kasa baki d'a ni na gaza amma duk da haka ni ba zanso kici gaba da cutar da kanki haka ba, Abida wallahi wannan yanayin naki yana matuqar cutar da ni sosai fiye ma da a salin cutar da take tare damu. Abida wani sati ne tafiyar mu jigawa to ya kamata mu fara shirin mu ki sanar da ni duk abin da kike so ni kuma zanyi nayi alkawari." Shiru bata yi magana ba wanda kuma har zuwa wannan lokacin kuka take jin shirun yayi yawa yasa ya anbaci sunanta amma bata amsa ba, ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata ya shiga share mata kwalla yana rarrashin ta. "Abida shin ba zaki dena cutar da ni ta wannan hanyar ba? Dan Allah ki dena a zabtar da ni haka please." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo cike da unci take magana yayin da take kuka. "Yaya Anas ni sam bana ganin gazawar ka a game da wannan sabo da kai kayi duk abin da zaka iya, abin farin cikin shi ne daya kasance cewar dukanmu qlau muke kawai dai lokaci bai yi ba, amma kuma ni duk da haka na damu sosai idan ka yarda to ina san mu d'auki rainon mace ko namuji, ni sam bani da za'bi kawai dai burina na kasance uwa kuma uwa ta gari ga yarona ko yarinyata wannan ne kawai abin da nake so." Yayi shiru yana nazari daga bisani kuma ya jinjina mata ka yana cewa. "Shikenan na aminta da hakan yaushe zamu tafi.?" Cike da d'auki take furta masa kalmar mu tafi yanzu ya girgiza ka yana cewa. "Zamu tafi ne kawai idan ke d'in nan kin yarda kinci abinci." "Eh zanci." "Wai da gaske zaki ci.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh yayi murmushi sosai mai tare da ar dariya, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta sannan ya tashi tare da tashin ta sun nufi tebur domin suci abinci. Sun isa ga tebur yaja mata kujera ta zauna ya fara zuba abincin sannan ya zauna, sunci gaba da cin abinci cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa suka shirya tsab suka nufi gidan marayu domin d'aukar raino. Sun isa gidan sun kuma samu yin magana da shugaban gurin tare da sanar da shi buqatar su, yayi matuqar farin ciki sosai da hakan nan kuwa a ka tafi dasu gurin da yara suke, sai wani kallon yaran suke kallo mai cike dajin tausayin su sosai Abida ta sauke kallonta ga wasu yara su biyun wad'an da ga a lama twin's ne, sai kuka suke kuma kuka sosai cike da tausayin su tare da nuna kulawa ta isa ga yaran tare da d'aukan su ta rungumasu jikinta tana rarrashin su, Anas sai wani kallonta yake kallo sosai mai cike dajin tausayin ta hakama mutanan da suke tare dasu ya isa inda take tare da dafata yana fad'ar sunanta. "Qlau kike.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh yaci gaba yana cewa. "Hakan yayi kyau to yanzu fad'a min mace zamu d'auka ko namuji.?" Tayi murmushi sosai mai tare da ar dariya sannan ta amsa shi cike da d'auki take magana. "Mujina ni na riga dana za'bi wad'an nan yaran da suke kwance a kan kafad'ata sune za'bina." "Rabin raina amma zaki iya hidimar yara biyu a lokaci d'aya kuwa.?" Ta jinjina masa ka tare da furta masa, "eh Abban twin's zan iya kuma zan kasance uwa ta gari ga yarona tare da taimakon ka to zaka iya yarda da ni." "Shikenan ina farin ciki sosai Maman twin's." Ya fad'a tare da sunbatarta a ka dama yaran da suke rungume jikinta ya kuma qara da yin hugging d'in su dukansu yana murmushi ita ma abin da take yi kenan. Shugaba dama jama'ar sa sai wani kallonsu suke suna murmushi bayan sun sake juna shugaba ya sanar dasu duk wasu dokoki a game da raino sunyi duk abin da a ka buqata, sannan kuma daga bisani suka d'auki twin's suka nufi gida dasu yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare dasu sosai musamman ma Abida. Kafin su isa gida sun fara zuwa sunyi wa yaran siyayya ta komai da komai na buqata sannan suka isa gida. Ai kuwa tin daga wannan ranar duhun da yake tare dasu ya gushe suka fara sabuwar rayuwa cikin farin ciki da jin dad'i sosai, yayin da suka d'ora duk wata kulawar su a kan yaran su wad'an da suke jira da Hassan da Hussaini, sun kuma ci gaba da shirin tafiya jigawa kasance cewar a can ne a ka mai da Anas aiki sunyi shirin su bayan kwana biyu suka kama hanyar jigawa. Suna cikin tafiya sai gani su kai an sha gaban su da mota an fashi ne zasu kai su goma koma fiye da haka, lokaci d'aya suka shiga anbatar kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un sun shiga tambayar su kud'i sun basu duk abin da suke da shi. Amma hakan bai sa sun barsu sun tafi ba inda suka rufe su da duka, duka suke yi musu irin na rashin tausayi wanda har sai da suka suma. Hakan bai isa ba sun d'auki yaran sunyi tafiyar su yayin da suke ta tsala ihu kuka suke sosai, wanda zamu iya cewa kukan yunwa ne suke amma ko rarrashi basu iya samu daga garesu ba. Sai ma fad'a da tsawa da suke yi musu Allah sarki yara abin tausayi, bayan wani lokaci Anas ya farka daga suman da yayi ya nufi gurin Abida yana anbatar sunanta tare da d'an buga fuskarta. Ta tashi wani a firgici cike da firgici sun tashi sun fad'a mota wanda kuma a nan ne suka fahimci cewar twin's basa nan, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali sun fito mota yayin da suke anbatar sunayen su, sun duba ko ina na gurin amma basu yi nasaran ganin su ba. A zahirin gaskiya hankalin su yayi matuqar tashi sosai musamman ma Abida sai wani irin kuka take kuma kuka sosai, duk ta kid'ime ta fita haiyacinta yayin da bakinta yake ta anbatar sunan twin's, Anas ya shiga rarrashinta yana bata magana sai wani lalla'bata yake wanda shi ma kuka yake, amma kuma shi kukan zuci yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai. Ya tashi tare da tashin ta sun nufi mota ya bud'e ofa tare da saka ta ciki shi ya shiga sun fice zukatan su cike da uncin rashin twin's.................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/20/2021, 9:23 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHERS* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page three* *Sister Ferdy wannan page d'in naki ne.* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 20/12/2021* *Time 10:00am* *Typing............* "Oga ya zamu yi da waɗannan yaran sai kuka suke da alama yunwa suke ji to ya zamu yi kenan.?" "Ka rufe musu baki ko kuma ku basu abin da muke da shi a nan." "Oga su ďin fa yara ne to ta ya kuma zasu ci irin abincin da muke ci wanda gaba d'aya ba shi da ɗanɗano." Rabi'u ya dakatar da shi cikin tsawa, "T. K ya isa kayi shiru haka, su ďin wasu ahalinka ne da zaka wani damu a kansu? Yaushe zuciyarka ta zama mai tausayi shin ba yanzu nan ka gama dukan iyayen su ba? Amma shi ne kake ƙoƙarin nuna min cewar kai mai tausayi ne, to bara ka ji wallahi tallahi idan har ka qara yi man maganar yaran nan cikin nuna jin tausayi to sai na yanka su, kuma cikin nuna rashin tausayi sabo da sai na fara a zabtar da su sosai kafin na yanka su shashasha kauce min a nan." Magana yake cikin fushi sosai T. K ya shiga basa hakuri sannan ya koma daga gefe, zuciyarsa cike da tausayin yaran sosai a tare da shi waɗanda kuma har zuwa wannan lokacin kuka sosai suke. Rabi'u ya kai kallonsa ga Babawo tare da fad'ar sunansa, "Babawo ka kula da yaran sannan kuma kasa suyi shiru saboda wannan kukan nasu ya fara damuna sosai." Yayi wani murmushi irin na mugunta tare da furta, "an gama Oga yanzun nan zasu yi ko kuma dai suyi barci na har abada." Cike da firgici T. K ya kai kallonsa ga Babawo yana san yayi magana amma ba shi da wannan damar, sabo da ba zai so a cutar da yaran ta hanyar yanka su ba, yasan halin Rabi'u tsab zai iya yanka su kamar dai yanda ya fad'a. Wanda wannan dalilin ne yasa dole yayi shiru Babawo ya kar'bi yaran daga hannun T. K yana ƙoƙarin tafiya Rabi'u ya dakatar da shi. "Babawo ka kula da yaran sosai sabo da jarinmu ne su dole cikin biyu ďaya zai faru, ko iyayensu su biya kud'in fansa ko mu raine su sannan kuma mu bautar da su." "Gaskiyar ka ne Oga dan haka zan kula da su sosai." Rabi'u ya jinjina masa ka alamar to yana murmushi shima abin da yake yi kenan, T. K kuwa sai wani kallonsu yake yayin da tausayin yaran yayi yawan gaske a tare da shi sosai bayan kwana biyu. Zaune take yayin da ta saka photon twin's a gaba da ma kayan su tana kallo yayin da take fad'ar sunan su tana kuka kuma kuka sosai, Anas ya fito daga wanka yayi tsaye sai kallonta yake kallo mai cike dajin tausayin ta sosai, cike da unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake tafiya har ya isa inda take, ya zauna tare da rungumata jikinsa ya qara da sunbatarta cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Kiyi hak'uri dan Allah ki dena cutar da kanki haka kar wani mummunan abu ya faru da ke please." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. "Abban twin's ni kawai na damu ne a kan yaran to ya idan kuma suka cutar dasu fa? Zuwa yanzu ni uwa ce kuma na damu sosai a kan yarana sabo da ina qaunar su sosai, Abban twin's mai ya saka basu harbeni ba a maimakon raba ni da twin's sun raba ni da farin ciki na gaba d'aya. Sunsa ina jin cewa kamar ni ban ta'ba kasancewa a cikin farin ciki ba, duka wannan laifi na ne sabo da sam bai kamata a ce nazo nan ba tare da twin's ba. Ni wace irin uwa ce sam na kasa taimakon yarana ni sam ba uwa ta gari bace ga twin's amma." Ta kuma yi shiru tare da sauke kallonta ga fuskar Anas sai wani kallonsa take kallo sosai, da sauri ta fita daga jikinsa har tana turesa cike da firgici da rud'ani yake fad'ar sunanta zai yi magana tayi saurin dakatar da shi. "Karka fad'i komai sabo da ni sam ban shirya sauraran ka ba, Yaya Anas duka wannan laifin ka ne eh kai ne kake d'auke da alhakin duka wannan, Yaya Anas kai wane irin muji ne kuma wane irin uba ne ga twin's? Ya kamata a ce kai ka kula da komai amma kai ba ma ka iya kare yaranka ba haka ka sanyo ni mota muka zo nan ba tare da kayi tinani a kan yaranmu ba. Kabar yaranmu a hanun wad'an nan mugayen mutanan zuwa yanzu ban san komai a game dasu ba, amma na san cewar su zasu yi kewata sosai sannan kuma zasu buqaci a shayar dasu kuma Maman su ce kawai zata iya yin hakan kuma ni ce wannan. Amma kuma bani zaune a nan na kasa taimakon su da komai tamkar wata mata anfani, kai ma kana zaune haka baka yi komai ba ka fad'a min kai wane irin uba ne sam ka kasa kare yaranmu daga cutarwa? Ni nayi kewar twin's sosai ina san na runguma su a jiki na sannan nayi musu wasa suna yawan saka ni murmushi sosai, musamman idan na sunbace su amma kuma duk da haka ni na kasa karesu amma." Bata qarasa fad'ar abin da yake ranta ba sai kawai gani yayi ta dukurshe ta fad'i kwance a qasa da sauri ya isa inda take yana fad'ar sunanta amma bata amsa ba, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ya d'auke ta ya nufi asibiti da ita yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Sun isa asibiti an shiga da ita ciki shi kuwa sai safa da marwa yake, bayan wani lokaci doctor ya fito tare da ba shi wata ar takarda yana furta masa, "ka tafi ka kawo wannan yanzu." Ya kar'bi takardar cikin hanzari ya fice ba jimawa sosai ya dawo ya shiga ciki ya ba likitan. Ya kar'ba tare da yi masa izinin ya fito ya amsa da to yayin da idanuwan sa suke a kan matar sa jiki a san yaye ya juya ya fita su kuma sunci gaba da abin da suke, bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a ciki tare da ita sun fito cikin hanzari tare da nuna kulawa Anas yake tambayar su jikin matar sa. "Matar ka tana samun sauki amma kuma ita d'in sam bata cikin kyakkyawan yanayi, amma zamu kula da ita sosai ba jimawa zata samu lafiya insha Allah to zaka iya yarda da ni." Ya jinjina masa ka a lamar to tare dayi masa godiya sunyi sallama doctor ya nufi office shi kuma ya nufi gurin Abida. Sannu a hankali yake tura ofar har ta bud'e ya shiga ciki ya same ta kwance, wanda kuma har zuwa wannan lokacin bata farka daga dogon suman da tayi ba ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta cike dajin tausayin ta yake magana. "Ki yafemin eh gaskiyar ki ne duka wannan laifi na ne, ni sam ban kasance uba na gari ga yaranmu sabo da na kasa karesu, amma kuma nima hakan yana matuqar cutar da ni sosai. Abida ban sani ba zaki yarda da ni ko a'a amma gaskiyar ita ce ni ina matuqar qaunar twin's sosai wallahi ina qaunar su sosai, amma ban san ta yanda zansa ki yarda da ni ba ina fatan karki jima a cikin wannan mummunan yanayin Allah ya baki lafiya Allahumma Amin." Misalin k'arfe 08:30pm Abida ta farka daga dogon suman da tayi sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, yayin da bakinta yake anbatar sunan twin's tayi tozali da fuskar Anas cike da nuna kulawa yake anbatar sunanta, kallonsa kawai tayi ba tare data amsa ba ya tashi ya fita ba jimawa ya dawo tare da doctor, Dr Shahid ya duba ta kuma Alhamdulallah yaga tana samun sauki ya sanar da Anas sannan ya juya ya fita. Bayan tafiyar Dr Shahid Anas ya mai da kallonsa ga Abida tare da fad'ar sunanta amma dai bata amsa ba yaci gaba da magana. "Gaskiyar ki ne ni sam ba muji na gari bane a gareki, hakama ban kasance uba na gari ga twin's ba ni ban san ma da wane suna zan iya kiran kai na ba, amma kuma duk da haka ni ba zan fasa nai man afuwar ki da gafarar ki tare da yafiyar ki ba dan Allah ki yafemin. Abida ni sam ba zan iya jure wannan hukuncin naki ba sabo da yayi min tsauri sosai ba zan iya d'auka ba, domin yana da zafi sannan kuma da una sosai ni ba zan iya jure wannan ba sabo da ni ba jarumi bane idan har a kan hukuncin ki ne to ina fatan zaki yafemin dan Allah.?" Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo har zuwa wannan lokacin kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai ba sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ta amsa shi. "Kayi hak'uri da duk abin dana fad'a wanda ba zan iya tinawa ba, Yaya Anas ni kawai na damu ne sosai a kan twin's ina san yaran sosai sannan kuma ni sam na kasa jure rashin su nayi kewarsu sosai." Kukan da take yaci k'arfin ta wanda wannan dalilin ne yasa ta yin shiru taci gaba da kuka, cike da jin tausayin yake rarrashinta yana bata magana cikin hikima tare da nuna kulawa wanda daga bisani ta iya fahimtar sa. Haka taci gaba da samun kulawar doctor ta samu kwana biyar asibiti sannan ta samu sallama zuwa gida. "Babawo ka kula da wannan yaron a nan T. K kai zaka tafi ka d'auko kayan abinci kayi girki, ni dasu Falalu zamu shiga daji yin aiki sabo da muna buqatar kud'i sosai J. B ka d'auko d'ayan yaron mu tafi da shi." Dukansu sun amsa da to sun nufi gurin aiki ba jimawa sosai T. K ya dawo domin ya d'ora girki kamar yanda Rabi'u ya umurcesa, ya samu Babawo yana ta yiwa yaron ihu tare da tsawa shi kuwa sai kuka yake kuka sosai da sauri ya a jiye kayan dake hanun sa ya isa inda yake, da sauri ya fizge yaron daga hanun sa ya shiga jijjigasa yana rarrashin sa cike da 'bacin rai Babawo yake magana. "Kai T. K wai mai ka aikata ne haka shin ka manta da abin da oga ya fad'a ma a game da wad'an nan yaran? Shikenan tin da kana buqatar tabbaci to ka sani ni da kai na zan yanka wannan yaron a yanzu." "Wallahi tallahi idan har kayi yunk'urin cutar da wannan yaron to ni da hanu na zan kashe ka, ba kuma tare da ji nadamar hakan ba to ka kiyaye ka ji ko." "T. K karka yi kamar kana bani umurni sabo da ni sam ba zan saurari komai daga gareka ba, kuma ni zan cika umurnin oga ka tsaya kaga yanda zan yanka wannan yaron a ga ban idanuwan ka kuma ba abin da zaka iya." "Shikenan to kawai ka aikata kila ka qosa gurin ganin ka bar duniya ne, dan haka ni sam ba zan dakatar da kai ba." "Shikenan to mu gwada domin ganin wanda zai yi nasara." T. K ya a jiye yaron daga gefe sun kama kokawa fad'a suke sosai, tamkar da basu san juna ba suna haka T. K ya hangi wani sadaukin maciji yana zuwa kusa da yaron. Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali yayi saurin sake Babawo ya nufi gurin yaron har yana gudu, kad'an ya isa garesa Babawo ya riqo wuyan sa ta baya tare da shage wuyan sosai, "a tinanin ka ni zan barka ka ceci wannan yaron a'a to kayi kuskure sabo da ni ba zan ta'ba barin wannan yaron ya rayu ba. Kawai dai ka tsaya kaga yanda zai mutu a ga ban idanuwan ka ba kuma tare da kayi komai ba." Ganin yanda macijin yake qara kusa sosai da yaron yasa T. K ya tattara duka k'arfin sa tare da jajircewa ya samu, cikin hikima da dabara ya kife Babawo a qasa ya tashi da sauri har yana gudu ya isa inda yaron tare da d'aukan sa. ya kauce daga gurin da sauri Babawo ya nufi gun da yake yana cikin tafiya ba ankara ba sai jin saran maciji yayi a qafarta kuma duka biyun, ya fad'i kwance tare da sakin wani uban ihu yana kururuwa amma a haka ya fito da bindiga daga jikinsa ya daddallawa macijin harbi har ya mutu, ya mai da kallonsa ga T. K wanda yake daga gefe rungume da yaron yayi wani gajeran murmushi yana cewa. "T. K karka yi farin ciki da yawa sabo da ba zai yu na mutu ni kad'ai ba, ni kai da kuma wannan yaron da yake rungume jikin ka to zamu mutu a tare wannan alkawari ne kuma zan cika yanzun nan." Ganin yana k'oqarin harbin sa yasa T. K ya tashi ya kama gudu Babawo yayi wani ihu tare da sakar masa harbi, inda shi kuma yace ga garin ku nan rai yayi halinsa ya mutu, waiyo T. K na cikin tafiya ya ji harbi lokaci d'aya ya kife a qasa wanda bai ma san lokacin da hanun sa ya saki yaron da yake kwance jikin sa ba. Haka yaron yaci gaba da gangara har zuwa wani guri daban wanda zuwa wannan lokacin ya suma................ *Yawan comment yawan typing insha Allah.* *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/22/2021, 9:04 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page Four* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ . *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 20/12/2021* *Time 10:38pm* *Typing.............* Tafiya suke a kan hanya sai jiran wanda zasu tare suke, sun jima a nan ba wani labari kamar saukar aradu suka ji sautin jiniyar motar ƴan sanda, ai kuwa nan suka ce mai zasu yi in ba gudu ba sun fad'a daji da gudu sun nufi ma'buyarsu. Ganin kamar yaron da yake d'auke da shi zai zame masa matsala yasa ya ajiye sa a gefen hanya yayi tafiyar sa, ya bar shi nan yana ta tsala ihu amma duk a cikin su ba wani d'aya wanda ya iya dawowa garesa. Haka suka yi tafiyar su suka bar shi cikin rashin tausayi tafiya kawai suke amma ba mai magana a cikin su tamkar masu gaba, ya koma gefen hanya yayi parking ya fito ita ma fitowa tayi tana mai furta masa kalmar. "Malam miye haka zaka kama kayi parking a nan? Bayan kuma ka san cewar hanyar nan bata da kyau wannan ganganci ne to ya kamata mu tafi." Ko kallon kusa da inda take bai yi ba ballantana kuma ya iya amsa mata, ya buɗe both ya ɗauko ruwa ya juya yayi tafiyar sa, ta bishi da wani wawan kallo mai kama da harara. Ta qara da jan tsaki tana wani juya baki ba jimawa sosai ya dawo ya hangeta ta nufi wani guri sai tafiya take, yayi tsaye sai kallonta yake yayin da takaicin ta ya cika zuciyar sa sosai, ganin sai tafiya take tana shiga daji yasa ya nufi inda take yana fad'ar sunanta. "Wannan yarinyar ta fiye shashancin da yawa ina kuma zata tafi haka? Kawai tana naiman ta 'bata min lokaci a banza lallai ya kamata na hukunta ta." Ya fad'a tare da jan tsaki ya juya ya nufi gunta, tafiya take tana jin kukan yaron yana qara kusa da ita can ta hangesa kwance yana kuka, da sauri cikin hanzari ta nufi gurin sa har tana gudu ta d'auke sa tare da rungumarsa a cikin jikinta tana jijjigasa. Cike da tsoro tare da firgicin ruɗani tare da tashin hankali ta juya domin tafiya, lokaci d'aya tayi ido biyu da fuskar Ahmad wani irin kallo yake yi mata kallo sosai. Sun juya sun nufi mota sun shiga ciki wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake kallo sosai, ita kuma yaron da yake kwance jikinta take kallo wanda numfashin sa yake ƙoƙarin ɗauke wa, da sauri ta kai kallonta ga Ahmad lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar har zuwa wannan lokacin kallonta yake. "Ahmad wai mai kake kallo ne haka shin kai baka ga halin da yaron yake ciki ba? Ya kamata mu kai shi asibiti to ka tuqa motar mu tafi yana buqatar kulawa sosai." Sam bai iya amsa mata ba saidai ya ja mota suka tafi a nan funtuwa suka kai yaron asibiti, an shiga da yaron ciki a na duba shi Ahmad ya maida kallonsa ga Ahlam wacce take ta safa da marwa, tare da fatan yaron ya samu lafiya ya isa inda take ya janyo hannun ta sun koma gefe kafin ya furta komai tayi masa rigagi. "Malam lafiya zaka wani janyo ni nan mai kake buqata daga gare ni.?" "Ke wai mai kika yi ne haka waye wannan yaron kuma mai ya saka kika d'auko sa zuwa nan.?" "Ban sani ba ko an fad'a maka izinin ka nake jira kafin aikata wani abu.?" "Ba buqatar ki nai mi izinin aikata wani abu amma ki sani." Kafin ya furta komai suka ji doctor yana yi musu magana, "am shin ko kune iyayen wannan yaron da a ke duba wa a ciki.?" Ahmad na k'oqarin yin magana tayi saurin yi masa rigagi ta hanyar amsa doctor. "Eh yaronmu ne fad'a mana mai yake faruwa da shi.?" "Am kuyi hak'uri a na kan duba shi ne yanzu amma da akwai buqatar ku sanar damu sunan sa, sabo da zamu cike masa wasu takardu yanzu." Sunyi shiru dukanku sai nazari jin likitan ya maimaita tambayar sa wato sunan yaron ta amsa shi da *Adyan Ahmad Ali.* Ya amsa da ok ya juya ya koma ciki cike da unci Ahmad yake magana, "ke wai kin fita haiyacinki ne ta ya ma zaki yi ba shi sunana fad'a min mai ya saka kika yi hakan.?" "Ahmad wai kai wane irin mutun ne mara tausayi? Shin kai baka ga a irin halin da yaron yake ba? Ni sam bani da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ni ba shi sunan ka, godiya ma ya kamata a ce kayi mun a maimakon wannan mummunan halin da kake nuna wa, ina fatan yaron ya samu lafiya cikin sauri sannan kuma shi ďin zai ci gaba da amsa sunan ka na har abada." Cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana, "Ahlam mai kike nufi da fad'ar hakan.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "Ahmad ban sani ba zaka yarda ko a'a amma dai ni ina da kwad'ayin a kan mu raini wannan yaron." Cikin rawar murya har yana sarkewa yake furta mata kalmar miye, "Eh Ahmad dan Allah." Ya girgiza ka yana cewa. "Ahlam shin wai ke kin fita haiyacinki ne ta ya ma har zaki yi tinanin fad'ar hakan? Ta ya zamu d'auki rainon yaro bayan kuma ba aure muke ba? Ahlam ya kamata ki dena wannan shirmen kawai zamu kai wannan yaron gidan marayu ko office d'in an sanda, da zaran a ka gama duba shi wannan ne hukunci na ba kuma zan canja wannan ba." Wani irin kallo take yi masa mai cike dajin mamakin abin daya fad'a shi ma haka kallonta yake kallo sosai, wani irin kallo suke yiwa juna wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba. "Ahmad wallahi tallahi ni ba zan ta'ba barin ka aikata hakan ba ko da kuwa mai zai faru, sabo da wannan yaron ďana ne shi ďin yaronmu ne kuma wallahi ba wani wanda ya isa ya canja wannan ko da ma kuwa kai ne, to kawai dai ka yarda ka kuma amince da hakan please." Kallonta kawai yake yayin da ya gagara furta mata komai, suna haka sai ga doctor ya fito da sauri cikin hanzari Ahlam ta isa inda yake tana tambayar sa jikin yaron. "doctor ya jikin *Adyan* fatan yana samun sauki sosai.?" Ya girgiza ka tare da jinjina sa sannan ya amsa ta, "Madam a gaskiya yaronku bai ya cikin kyakkyawan yanayi, yayin yaronku yayi tsauri sosai amma zamu ci gaba da ba shi kulawa sosai, zai samu lafiya insha Allah to zaku iya yarda da ni." Cike da firgici take magana, "doctor dan Allah kuyi komai domin ku ceci rayuwar ďana ku fitar da shi daga hatsari." "Eh Madam abin da muke k'oqarin yi kenan kuma zamu nasara yaronku zai samu lafiya insha Allah to zaku iya yarda da ni." "Na gode doctor amma zamu iya ganin yaronmu kuwa.?" "Eh amma ku kula da shi sosai." "Eh zamu yi zamu kula da shi sosai nayi alkawari." "Ke uwa ta gari ce kina san yaronki sosai to Ubangiji zai taimaki yaronku insha Allah." Ta jinjina masa ka tana wani gajeran murmushi shi ma abin da yake yi kenan, da kuma haka suka rabu ya juya ya nufi office ita kuma ta nufi gurin yaron da ta sanya wa suna *Adyan. Ahmad* ya bita da kallo har ta shige ya nisa tare dajan numfashi ya juya ya nufi gunta, ya same ta zaune kusa da yaron sai wani kallonsa take kallo sosai. Lokaci d'aya ta ji wata soyayyar yaron tana dad'a shigarta, yayin da tausayin sa kuma ya cika zuciyarta sosai ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana furta sunan sa. Ahmad dai kallonta kawai yake cike dajin mamakin ta sosai a tare da shi, sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda take ya zauna daga gefe wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake, kallo sosai ya anbaci sunan ta kafin ya furta komai tayi saurin rufe masa baki tana wani girgiza masa ka, ta koma gefen sa ta zauna wanda kuma har zuwa wannan lokacin hanun ta yana kan bakin sa, ta kai bakin ta daidai kunnansa cikin sannu a hankali take rad'a masa kalmar. "Dan Allah ko zaka iya yin shiru sabo da yaronmu yana buqatar hutu sosai please.?" Ta janye bakin ta daga kunnan sa sai kuma zuwa wannan lokacin ne ta janye hanun ta daga kan bakin sa, ta mai da kallonta ga fuskar yaron sai wani kallonsa take kallo sosai, hakama Ahmad abin da yake yi kenan wanda kuma lokaci d'aya ya ji tausayin yaron yana shigarsa, ta ko wane lungu da sak'o na sassan jikin sa haka ya rik'a jin soyayyar yaron tana ratsa ko wane sak'o na jikin sa. Ya kai hanun sa ya shafi fuskarsa ya qara da sunbatarsa tare da furta Allah ya baka lafiya, lokaci d'aya Ahlam ta kai kallonta garesa tayi murmushi sosai tare da rik'o hanun Ahmad sun fice daga d'akin, sun fito waje sun samu guri sun zauna kusa da d'akin ta yanda zasu iya kulawa da yaron. "Ahmad fad'a min wani abu shin yanzu kai ka aminta da mu raini yaron.?" Shiru bai yi magana ba jin shirun yayi yawa yasa taci gaba tana cewa. "Ahmad ni na san cewar mu biyun bama wani shiri da juna, ko yaushe cikin fad'a da musayan baki muke sam ba ma yiwa juna fatan alkhairi amma kuma duk da haka mu d'in ahali ne, Ahmad ko da mai zai faru mu biyun nan ba zamu iya canja gaskiyar ba kai Yayana ne ni qanwarka ce. Ahmad dukanmu mun san cewar hakan yana matuqar yiwa iyayenmu zafi sosai hakan kuma yana cutar da duka ahalin gaba d'aya, Ahmad na ro e ka da mu kawo k'arshen wannan dan Allah ka ji please." Har zuwa wannan lokacin kallonta kawai yake kallo mai cike dajin mamakin ta sosai, wanda kuma wannan dalilin ne ya hana masa iya fad'ar komai. "Ahmad dan Allah ka amsa ni shin kai baka san duka wannan ya wuce.?" Ya nisa tare da jan numfashi wanda kuma sai zuwa wannan lokacin ne yayi magana. "Ahlam nima ina san duka wannan ya wuce ya yanda ahalinmu gaba d'aya zasu yi farin ciki sosai, to amma ai ba daga ni bane ke ce nan wadda take da matsala damuwar a kanki take, sam kin kasa bani damar da zan kasance Yaya na gari a gareki kinsa ko yaushe cikin nuna maki tsana da tsangwama nake. Ahlam wani abin da baki sani ba shi ne wallahi hakan yana cutar da ni sosai, amma kuma ni sam bana da wani za'bi a kan rayuwar da ke kika za'ba mana shi yasa ni nake duka wannan, amma zuwa yanzu duka duhun ya gushe haske ya bai yana a garemu gaskiya ina farin ciki da hakan sosai. Yanzu fad'a min wani abu ya zamu yi da wannan yaron sabo da bana san hakan ya saka mu a matsala.?" "Shin zan iya kiran ka da Yaya Ahmad.?" "Amma ai kinyi alkawari a gaban kowa na cewar ke ba zaki ta'ba kira na da Yayan ki ba, shin kin manta da wannan ne.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "eh ban manta ba tabbas ni na fad'i hakan a gaban duka ahalin, amma kuma na anbaci kalmar insha Allah a k'arshen magana ta Ahmad ni ina san mu daidai ta komai sabo da yaronmu. Ni ba zanso *Adyan* ya fahimci cewar mu biyun ba ma jituwa da juna sabo da hakan zai saka shi unci sosai ni kuma sam ba zanso hakan ba, ba zan bar wani abu ya cutar da yarona ba zan iya jure komai da ko wane irin qalubale domin sa. Ni kawai ina san mu kasance iyaye na gari ga yaronmu wanda shi yasa ni nake yin duka wannan, to dan Allah karka dakatar da faruwar hakan ni zan iya jure duk wani unci kawai dai alfarma d'aya zan nai ma a gurin ka, Yaya Ahmad dan Allah da girman Allah ka yarda ka kasance uba na gari a gurin *Adyan.* Wannan kawai alfarma ce idan ka amince zanyi matuqar farin ciki sosai kuma zanyi alfahari da kai, idan kuma kak'i ka amince da wannan to zan kasance ina fishi da kai na har abada kuma hakan ba zai canja ba. To yanzu fad'a min shin ka shirya amince min gurin rainon *Adyan* ko a'a.?" *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/24/2021, 8:25 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page Five* *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 22/12/2021* *Time 10:25pm* *Typing...............* Wani irin kallo yake yi mata mai cike dajin mamakin ta sosai, wanda kuma wannan dalilin ne yasa yayi mata shiru jin shirun yayi yawa yasa ta fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad dan Allah ka amsa ni shin ka shirya amince min gurin rainon *Adyan* please.?" Magana take cikin wani irin yanayi na ban tausayi yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da una sosai kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Ya nisa sosai tare da jan cikin kwantar da murya yake magana, "Ahlam to ya kuma hakan zata kasance har yanzu mu yara ne, Ahlam yanzu haka muna shirin koma wa school ne sannan kuma ba a nan muke karatu ba, Ahlam ya kamata ki fahimci abin da nake nufi yana da kyau wannan yaron ya koma hanun a salin iyayen sa." Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar a'a, "a'a Yaya Ahmad ni sam ba zan yi hakan ba sabo da zuwa yanzu *Adyan* ďana ne, mu biyun nan mune a salin iyayen sa ba abin da zai canja wannan." Magana take cikin fishi sosai ta tashi domin tafiya yayi saurin dakatar da ita, ta hanyar ri e hanun ta yana girgiza mata ka a lamar a'a ya zaunar da ita tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam yanzu fad'a min ta ya ni zan iya taimaka maki gurin rainon *Adyan* ni kuma zanyi nayi alkawari.?" "Da gaske zaka yi komai na fad'a.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh, "kayi alkawari.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh tayi gajeran murmushi sannan taci gaba da magana. "Yaya Ahmad ina san mu biyun muyi aure ta yanda zamu raini *Adyan* a matsayin ďan mu, Yaya Ahmad ina san mu baiwa yaron kyakkyawar rayuwa wadda zai yi farin ciki sosai. Yaya Ahmad gaskiyar ita ce ni ina matuqar qaunar *Adyan* sosai sannan kuma sam bana san kowa ya san a salin waye shi." "Yaya Ahmad kai kad'ai ne wanda zai iya taimako na a kan wannan, Yaya Ahmad dan Allah karka ce a'a eh na san cewar mu biyun ba ma wani jituwa da juna, bamu ta'ba kasancewa matsayin abokai ba balantana kuma masoya, amma kuma zamu yi aure sabo da yaronmu nayi alkawari ni ba zan ta'ba shiga rayuwar ka. Zama ka iya auran duk wadda kake a duk lokacin da buqatar hakan tazo ma ni ba zan ta'ba dakatar da kai ba, Yaya Ahmad ni kawai alfarma ďaya nake nai ma a gurin ka shi ne ka kasance uba a gurin *Adyan.* Ba kawai uba ba a'a so nake ka kasance uba na gari a garesa to fad'a min shin zaka yarda da hakan kuwa.?" Yayi shiru na jim kad'an yana nazari sannan daga bisani ya amsa ta, "Ahlam amma ta ya hakan zata kasance *Adyan* ba zai 'boyu ba musamman a gurin iyayen mu, sannan kuma ni sam bana jin cewar zasu yarda da hakan cikin sauk'i, Ahlam ni sam bana jin cewar hakan zai yu ya kamata kiyi tinani a kan wannan sosai." "Yaya Ahmad idan har kai ka amince da aure na to zan tabbatar da abin dana fad'a a yanzu." "Shikenan na amince to kawai ki tabbatar." Lokaci d'aya ta saki wani kyakkyawan murmushi tana yi masa godiya, kallonta kawai yake ba tare daya furta mata komai ba ta ciro wayar ta daga jaka ta shiga kiran layin Abbu. Ba jimawa ya d'aga cikin hanzari yake anbatar sunan ta tare da tambayar ta suna ina. "Ahlam kuna ina haka shirun ya fara yawa fatan kuna cikin k'oshin lafiya.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "Abbu gaskiya ba lafiya muna matuqar buqatar taimakon ku sosai kai da Kawu, yanzu zan turo maka adres na inda muka kazo tare da Kawu sannan kuma karka sanar da kowa bayan Kawu dan Allah." "Shikenan ba wanda zai ji nayi alkawari sai mun qaraso." Ta amsa da to da kuma haka suka yi sallama ba jimawa ta tura masa text na inda suke, Ahmad dai kallonta kawai yake yayin da ya gagara furta mata komai ita ma haka kallonsa take tayi murmushi kad'an tare da fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad zuwa yanzu ya kamata mu koma ga yaronmu sabo da zai iya buqatar mu a kusa da shi to mu tafi. Har zuwa wannan lokacin kallonta kawai yake yayin da mamakin ta yayi yawan gaske a tare da shi sosai, wanda kuma wannan dalilin ne yasa ya gagara furta mata komai ta tashi tare da tashin sa sun nufi d'akin da yaron yake. Sun shiga ciki tare da isa inda yake sun zauna daga gefen sa sai wani kallonsa suke kallo sosai. Yayin da suke jin yana birgesu sosai bayan wani lokaci Ahmad ya sauke kallonsa ga fuskar Ahlam tare da fad'ar sunan ta, "Ahlam zuwa yanzu ya kamata kici abinci to fad'a min mai zaki ci.?" Ta girgiza masa ka tare da furta masa kalmar, "a'a ni sam bana jin yunwa sannan kuma ina lafiya to zaka iya yarda da ni." "Ahlam ki fad'a min mai zaki ci.?" "Shikenan shawarma kawai ta isa." Ya jinjina mata ka sannan ya tashi ya fita bai wani jima ba sosai ya dawo, ya bata ledar dake hanun sa ta kar'ba tare dayi masa godiya ya amsa da ba komai. Nan ta fara cin shawarma wanda shi kuma samosa yake ci bayan wani lokaci sai gasu Abbu, sun shiga kiran layin Ahlam ba jimawa Ahmad ya fita sun dawo tare, cike da d'auki Ahlam ta isa inda Abbu sunyi hugging juna bayan sun sake juna, ta ja hanun sa sun qarasa inda babyn yake wato *Adyan* sunan da suka ba shi cike da firgici da rud'ani su Abbu suka tambayar su waye shi har suna had'a baki. "Ahmad waye wannan yaron mai yasa yake tare daku.?" Kafin ya furta komai Ahlam tayi masa rigagi ta hanyar amsa Abbu lokaci d'aya ta sanar dasu komai da ma duk wani plan da suke a game da shi. Abbu sai wani kallonsu yake kallo sosai hakama Abba shi ma kallonsu yake yayin da mamakin su yayi yawan gaske a tare dasu sosai, "Abbu Abba dan Allah karku dakatar damu sabo da muna san yaronmu sosai, sannan kuma mu sam ba zamu jure rashin sa ba to ina fatan zaku aminta da wannan burin dan Allah.?" "Amma Ahlam." "A'a Abbu kawai dai ku amince dan Allah." Abbu ya kai kallonsa ga Abba lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna ya anbaci sunan sa yana cewa. "Yaya to mai ya kamata muyi a kan wannan.?" Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi, "eh Al'ameen muyi hakan ina nufin abin da suka buqata daga garemu shin dama ba wannan bane burinmu ba? To ya kamata muyi hakan tabbas za a yi auran kuma nan kusa insha Allah." Cike da farin ciki Ahlam tayi hugging d'in Abba tana cewa. "Na gode Abba daka amince da wannan ina godiya sosai, amma Abba sam bana san kowa ya san da wannan zancan a game da *Adyan* ko da kuwa Umma da Ummi ne dan Allah, sannan kuma za a shirya wa *Adyan* visa sabo da mu samu damar da zamu tafi tare da yaronmu dan Allah." Abba yayi murmushi sosai yana cewa, "eh Ahlam zamu yi hakan to kawai kiyi farin ciki kinji ko sannan kuma ba wanda zai ji komai a game da jikana ko da kuwa Umma da Ummi wannan alkawari ne." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa, ya sunbaceta a ka tare da furta mata kalmar Allah yayi maki albarka ta amsa da Amin tana murmushi mai tare da ar dariya, Abbu da Ahmad sa wani kallonsu suke suna murmushi Abba ya kai kallonsa ga Ahmad tare da furta masa yazo ya amsa da to ya nufi inda yake, shi ma yayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa ya anbaci sunan sa yaci gaba da magana. "Ahmad fad'a min wani abu shin kana farin ciki da buqatar qanwarka kuwa.?" Ya jinjina masa ka tare da furta, "eh Abba ina farin ciki sosai to zaka iya yarda da ni." "Hakan yayi kyau sosai yarona Allah ya albarkaci rayuwarku data yaronku gaba d'aya." Sun amsa da Amin suna murmushi Abbu sai kallonsu yake yana murmushi ya anbaci sunan Abba yana cewa, "Yaya gaskiya ina farin ciki sosai amma ya kamata mu d'auki *Adyan* zuwa kaduna, zamu kai shi Saudat Care Hospital na tabbata zai samu kulawa sosai a can sannan sai mu fara shirin tafiyar su wanda baifi kwana biyar ba." Abba ya jinjina masa ka a lamar to shi kuma zuwa wannan lokacin ne Abba ya sake su daga rungumar da yayi musu ya anbaci sunan Ahmad yana cewa. "Ahmad ya kamata na had'u da likitan daya duba jikana." Ya amsa da to sun tashi sun nufi office ďin doctor har da Abbu bayan tafiyar su Ahlam ta sauke kallonta ga fuskar *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin barci yake. Ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana furta masa kalmar, "ina qaunarka yarona ina fatan ka samu lafiya cikin sauri ka zama jarumi, sannan kuma ka jure domin Ammie tana matuqar buqatar ka sosai, to ya kamata ka jure zafin sabo da ni da kuma Dadyn ka ka ji ko ina sanka sosai d'ana." Ta fad'a tare da sunbatarsa yayin da take jin soyayyar sa tana zaga ko ina lungu da sak'o na jikin ta, su Abbu sun isa office d'in doctor tare da shiga ciki bayan sun gaisa Abba yaci gaba yana cewa, "doctor a game da jikana ne shin zamu iya tafiya da shi zuwa gida kuwa? Zamu canja masa wata asibiti sabo da mu a kaduna muke to ya kamata a duba shi a can, to ko zamu iya tafiya da shi yanzu ka sanar damu.?" "Shikenan zaku iya tafiya da shi amma yana matuqar buqatar kulawa sosai, sabo da yaron sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi sannan kuma yana da wani miki a zuciyar sa. Sam ba a san wani abu ya gajiyar da shi sabo da hakan zai cutar da shi sosai, to yana da kyau ku kula da shi sosai kunji ko." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali Ahmad yake magana. "Doctor to mai ya kamata a yi a game da yarona sabo da ya kamata ya samu lafiya kayi hakan cikin sauri dan Allah ka ji ko." "Kayi hak'uri sabo da a yanzu dai ni ba zan iya yin komai a game da wannan raunin na sa ba, sabo da wannan ciwon a na d'aukan sa ne daga gurin uwa mace wanda na tabbata dukanku sun san da wannan, sabo da dole Maman sa tana tare da wannan cutar shin gaskiya ni na fad'a kuwa.?" Lokaci d'aya dukansu suka jinjina masa ka tare da furta masa kalmar eh yaci gaba yana cewa. "Amma da akwai wata ar mafuta amma tana da hatsari sosai, abin shi ne a na aikin wannan cutar amma aikin yana da hatsari sosai cikin goma ďaya ne kawai wanda yake rayuwa. shi yasa ba kowa bane yake amincewa da aikin ba sannan kuma a k'asar waje ne kawai a ke aikin ba a yi a nan, to idan kuna da buqata a kan aikin to zaku iya shirya fita da shi sabo da wannan ce kawai damar ku amma kafin nan zan ba shi magana wanda zai sha." Sun jinjina masa ka a lamar to nan ya rubuta musu magani tare da takardar sallama. Sun tashi sun fice sun dawo d'akin da babyn yake ko mu ce *Adyan* sunan da Ahlam ta ba shi, sun shigo ciki zuciyar su cike da tausayin yaron sosai a tare dasu, kallo d'aya tak Ahlam tayi musu ta fahimci cewar da akwai matsala cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali take tambayar su mai yake faruwa. "Abbu Abba Yaya Ahmad ku fad'a min wani abu yana faruwa da *Adyan* ne gaskiyar zaku fad'a please.?" A zahirin gaskiya hankalin Ahlam yayi matuqar tashi sosai da ganin yanayin su, lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai sai kuka yayin da bakin ta yake anbatar sunan *Adyan.* Cikin hanzari tare da nuna kulawa Abbu ya runguma ta jikin sa ya shiga rarrashinta yana bata magana. "Ki dena kuka 'yata mu zamu kula da komai jikana yana tare da wata rashin lafiya amma zamu kula da komai insha Allah kinji ko." "Abbu mai yake faruwa da yarona dan Allah ka sanar da ni please.?" Shiru bai yi magana ba sabo da ba zai iya sanar da ita gaskiyar ba, jin yayi shiru ne yasa Abba yin magana, "am kinga 'yata ki kwantar da hankalin ki jikana zai samu lafiya sannan kuma sam ba abin da zai faru da shi to zaki iya yarda damu yanzu zamu tafi." Ta amsa da to ta hanyar jinjina masa ka nan suka fara shirin tafiya ba jimawa suka tafi. Tafiya suke cikin kyakkyawan yanayi har ya wuce kuma ya dawo tare da yin parking ya fito cikin sauri ita ma haka fitowa tayi, tare da isa inda yake sunyi shiru suna nazari lokaci d'aya kuma suka kai kallonsu ga juna cikin rawar murya har tana sarkewa take magana. "Masoyi shin kai kaji abin da nake ji kuwa.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh taci gaba da magana, "Mujina ni fa kamar kukan yaro nake jiyowa shin kai ma ka ji da kyau kuwa.?" "Eh dalilin da yasa na tsaya kenan yanzu ki koma mota ni zan duba domin na tabbatar." "Shikenan amma dan Allah ka kula ka ji ko." Ya jinjina mata ka a lamar to ya juya ya nufi dajin dake gefen su ita kuma ta koma mota, ya d'an jima sannan ya dawo hannayen sa d'auke da yaro ya shiga mota tare da bata yaron. Ta kar'bi yaron tare da sakin salati tana taslima shi kuma ya ja mota sun tafi, "wace irin uwa ce wannan wadda ta aikata wa yaron ta irin wannan mummunan zunubin? Ta ya uwa zata yi tinanin cutar da yaron ta har haka bayan data riga ta aife sa ni sam na kasa yarda da hakan. Barrister yaron yana da zazza'bi jikin sa yayi zafi sosai ya kamata mu kai shi asibiti." Ya jinjina mata ka a lamar to yayin da ya gagara furta mata komai sai wani kallon yaron yake ita ma haka abin take yi kenan................ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/25/2021, 5:43 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page sex* *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Thursday 23/12/2021* *Time 10:10pm* *Typing.............* Sun isa asibiti cikin hanzari nurse suka kar'bi yaron suka shiga da shi ciki domin a duba shi. Bayan sun shiga da shi Barrister ya d'auki wayar sa kowa zai kira oho Asma'u tayi saurin dakatar da ta hanyar fad'ar sunan sa, "Barrister wa kuma zaka kira.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "Asma'u ya kamata na sanar da an sanda wannan, to abin da nake qoqarin kenan." Da sauri ta furta masa kalmar a'a wani irin kallo yake yi mata cike da jin mamakin ta yake magana. "Asma'u mai kike k'oqarin dakatar da ni.?" Ta nisa sosai tare da jan numfashi cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana. "Barrister ni na dakatar da kai ne sabo da ya kamata muyi magana yanzu." "Magana kuma to a kan me fad'a min ina sauraran ki.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan taci gaba da magana. "Barrister ni da ma ina idan ka amince mu d'auki rainon wannan yaron, masoyi tsayin shekaru biyar mu kayi aure amma har yanzu bamu aihu ba, to shi ne nake san ka amince da rainon wannan yaron dan Allah karka ce a'a please." Wani irin kallo yake yi mata sam ba zai yi mamakin ta ba sabo da yafi kowa sanin irin yanda ta damu sosai a kan taga ta aihu. Yayi shiru yana nazarin sannan daga bisani ya amsa ta, "shikenan masoyiya idan har hakan zai saka ki farin ciki to na amince da rainon sa." Cike da d'auki tayi hugging d'in sa tana furta masa kalmar. "Na gode sosai Mujina ina sanka ina qaunarka sosai." Yayi murmushi tare da sunbatarta ita kuwa ta qara yin kwance jikin sa, bayan wani lokaci doctor ya fito ya isa inda suke kafin ya furta komai sunyi masa rigagi har suna had'a baki. "Doctor to ya jikin yaronmu.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa su da cewar su same sa office, cike da firgici da rud'ani sun juya sun bisa a baya sun shiga office d'in bayan sun zauna doctor yaci gaba yana cewa. "A zahirin gaskiya yaronku sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi ina mai bak'in cikin sanar daku cewar, yaronku yana tare da wani miki a gefen zuciyar sa wanda kuma wannan cutar dole daga gurin Maman sa ya samu, sabo da a nan ne kawai a ke d'aukan wannan cutar shin gaskiya ni na fad'a kuwa.?" Lokaci d'aya suka kai kallonsu ga juna cike da unci bak'in ciki tare da tarin damuwa, Asma'u take amsa masa da eh hakama Barrister doctor yaci gaba da magana. "To yanzu ya kamata ku kula da yaran sosai sannan kuma ku dakatar da shi daga yin duk wani abin da zai gajiyar da shi, sannan kuma ya zama dole daku haka yaronku unci idan kuna so to za a iya yi masa aiki, amma aikin yana da hatsari sosai cikin goma ďaya ne kawai wanda yake rayuwa, shi yasa ba kowa bane yake amincewa da aikin ba sannan kuma ba a nan a ke aikin ba a k'asar waje ne kawai a ke yi, to zan iya cewa wannan ita kawai ce damarku ga yaronku." Lokaci d'aya dukansu suka ji wani iri tashin hankali yana fuskantar su musamman ma Asma'u. Sun tashi jiki a san yaye sun nufi d'akin da yaron yake sun shiga ciki, sannu a hankali suke tafiya har suka isa inda yake sun zauna gefen sa sai wani kallonsa suke kallo sosai, mai cike da jin tausayin sa yayin da tausayin sa ya cika zuciyarsu sosai, ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana cikin kwantar da murya take magana. "Barrister wane suna ka baiwa yaronmu.?" Magana take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo yayin da tausayin yaron yayi yawan gaske a tare da ita sosai. Ya shiga share mata kwalla yana girgiza mata ka a lamar a'a daga bisani kuma ya amsa ta, "Asma'u sunan yaronmu *Adnan* ne fatan sunan yayi maki.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh yayin da take kuka amma kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai. "Mai ya saka kike kuka.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "masoyi ni kawai na damu ne sosai a kan yaron ina nufin *Adnan* yanayin sa yayi tsauri sosai. Ina san na taimake sa wannan yasa nake san na kasance uwa ta gari a garesa, sabo da ta wannan hanyar ce kawai zamu iya taimakon sa ai ka shirya amince wa hakan ko.?" "Eh na amince da yaronmu to kiyi farin ciki nima abin da nake yi kenan, sannan kuma ki dena damuwa sabo da yaronmu zai samu lafiya insha Allah, ni zanyi komai domin ganin yaronmu ya fita daga hatsari to zaki iya yarda da ni kinji ko." Ta jinjina masa ka tana wani gajeran murmushi shi ma haka abin da yake yi kenan. Kwance take tana barci lokaci d'aya ta wani tashi cikin tsoro da firgici sosai nan kuwa ta shiga furta kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un. Tayi zugum sai tinanin abin data gani a cikin mafarkin ta take, ta sauke kallonta ga yaronta wanda yake kwance daga gefen ta yana barci ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yayin da take magana da zuciyarta. "Su waye wad'an nan yaran mai ya saka a ko yaushe nake mafarki dasu? Yaron suna cikin garari sannan kuma suna matuqar buqatar taimako sosai, duk da cewar mafarki ne amma kuma ni ina tare da jin tausayin yaran sosai, ya Ubangiji ina fatan kar wannan ya zama gaskiya Allahumma Amin." Ta qara sunbatar yaronta tare da d'ora sa jikin ta tana mai furta masa kalmar ina qaunarka sosai *Adeel.* Ta rufe idanuwan ta ba jimawa barci ya d'auke ta, sunyi na saran isa garin kaduna lafiya kai tsaye Saudat Care Hospital suka nufa, sun had'u da Dr Bilal wanda shi ne shugaba a nan fannin yara, Abba ya sanar da shi komai a game da yaron amma ba a gaban Ahlam ba. "Karku wani damu insha Allah yaronku zai samu lafiya idan har yana nan a tare damu, sabo da 24hou doctor ne muke kulawa da duka yaran da suke nan to sam ba buqatar ku damu sabo da yaronku zai samu lafiya insha Allah." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi Abba ya amsa shi yana cewa. "Muna godiya doctor Allah ya taimaka ya baiwa duka yaran lafiya." Dukansu sun amsa da Amin nan kuwa a ka fara baiwa *Adyan* taimakon daya dace da shi sunyi sallama da Dr Bilal suka fito, cikin hanzari tare da nuna kulawa Ahlam take tambayar su Abbu mai yake faruwa. "Karki damu 'yata *Adyan* yana samun kulawa sosai a nan, kuma zai samu lafiya insha Allah to zaki iya yarda da." Ta jinjina ka tare da furta masa kalmar, "Na gode Abba ina fatan *Adyan* ya samu lafiya cikin sauri." "Eh Ahlam muma wannan shi ne fatan mu to Allah ya amince da hakan Amin." Dukansu sun amsa da Amin Ahlam da Ahmad sun shiga ciki sun duba yanayin jikin sa bayan wani lokaci suka fito sannan suka nufi gida. sun isa gida ko wannan su part ďin su ya nufa su Abba sun bisu da kallo Abbu ya anbaci sunan Abba yaci gaba da magana. "Yaya ni fa ina jin wani irin a game da wannan sabo da har yanzu Ahmad da Ahlam basa tare da juna. Kawai sun amince da junansu sabo da *Adyan* na rasa dalilin da yasa suke qaunar yaron sosai har haka, Yaya shin kai sam baka jin komai a game da wannan.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "ba buqatar ka damu Al'ameen sabo da su da kansu suka buqaci hakan to na tabbata ba zasu saka mu unci ba, Al'ameen gaskiyar ita ce ni farin ciki nake sosai to kai ma ya kamata kayi farin ciki, sannan kuma ni na yima alkawari insha Allah ba abin da zai faru to zaka iya yarda da ni ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to da kuma haka suka yi sallama kowa ya nufi part ďin sa. Haka dai *Adyan* yayi ta samun cikakkiyar kulawa daga gurin doctor da kuma su Ahlam, yayin dasu Abbu suke ta shirin tafiyar su sunyi shirin su tsab na komai bayan kwana biyar jirginsu ya tashi. Zuwa qasar England tare da yaronsu *Adyan* wanda kuma har suka tafi iyayen su mata basu samu labarin komai ba a game da *Adyan,* kamar dai yanda su Abbu suka yi musu alkawari saidai sunyi farin ciki sosai da auran da a kayi wa yaran wato Ahmad da Ahlam hakan ya saka su farin ciki sosai. A can gurin su Barrister kuwa *Adnan* ya samu tsayin mako biyu asibiti sannan daga bisani ya samu sallama zuwa gida, sunci gaba da ba shi cikakkiyar kulawa sosai tare da nuna masa soyayya da qauna irin ta d'a a zahirin gaskiya suna san yaron sosai shi yasa suke ba shi kulawa sosai. Zaune suke suna fira cikin raha wasa da dariya yayin da Prof yake rungume da yaron sa wato *Adeel,* lokaci d'aya Aisha ta wani toshe kunnan ta duka biyun tare da rufe ido da sauri ta bud'e idanuwan ta tana furta A'a. Da sauri ta tashi ko ina zata tafi oho Prof ya riqo hanun ta tare da zaunar da ita, domin kuwa ya gama fahimtar cewa sam bata cikin kyakkyawan yanayi zai ma iya cewa sam b as ta cikin haiyacinta gaba d'aya. Sai wani kallonta yake kallo sosai mai cike da jin mamakin ta cike da firgici da rud'ani yake magana. "Aisha qlau kike kuwa fad'a min mai yake faruwa da ke ne haka please.?" "Prof shin kai baka jin komai ni ina jin kukan yara sosai a kunne na fad'a min har yanzu baka ji ba? Ni ina jin kukan sosai sannan kuma idan na rufe idanuwana ina ganin wasu yara cikin wani mummunan yanayi musamman idan ina barci, ni ban san mai yasa hakan take faruwa da ni ba fad'a min wani abu shin kai har yanzu baka jiyo sautin kukan yaron.?" Magana take cikin wani irin wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, shi kuwa sai wani irin kallo yake yi mata kallo sosai cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data fad'a yake magana. "Aisha amma tin yaushe ne hakan take faruwa da ke.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "gaskiya ba zan iya tinawa ba sabo da na jima a haka." "Aisha amma mai ya saka baki ta'ba sanar da ni gaskiyar ba.?" "Kayi hak'uri sabo da wani lokacin ko da zanji irin hakan to kai baka gida shi yasa ban iya sanar da kai ba." Ya jinjina ka yana cewa, "shikenan zan kula da wannan yanzu ki huta kinji ko ina sanki." Ya fad'a tare da sunbatarta ya d'ora kanta a kan cinyarsa yana wani shafar gashin kanta yayin da yake magana da zuciyarsa. "Mai hakan yake nufi mai ya saka yaran suke k'oqarin dawowa rayuwar mu? A'a ni sam ba zan bar hakan ta faru ba, ina nufin ba zan ta'ba barin su dawo rayuwar mu ba sabo da ban shirya kar'ban su a matsayin 'ya'yana ba *Adeel* kawai nake buqata, kuma yana tare da ni babu wani dalilin da zai sa ni na buqaci wasu yara kuma, to amma kuma mai ya saka wad'an nan yaran suke bibiyar Aisha mai yasa suke k'oqarin kawo mana qalubale a cikin rayuwarmu? Hakan sam bai dace ba sannan kuma bai kamata a ce su sunyi hakan ba amma zanyi wani abu domin na dakatar da duka wannan. To amma mai ya kamata ni nayi domin dakatar da wad'an nan yaran? Lallai da akwai buqatar su fita daga rayuwar mu gaba d'aya to mai zanyi kenan.?" Haka ya shiga nazari da tinanin abin da ya kamata yayi domin twin's su fita daga rayuwar su, duk da cewar basa tare dasu kuma rayuwar Ummar su suke amma kuma ya damu sosai, to zamu iya kiran wannan da rashin so ko kuma mu kira shi da k'iyayya to Allah ya kyauta Amin. kwance yake yayin da d'ora *Adyan* a kan k'irjin sa ya runguma shi sosai jikin sa, sannu a hankali take turo ofar har ta bud'e ta shiga ciki tayi tsaye jikin ofa sai wani kallonsu take tana murmushi, lokaci d'aya taji suna birgeta ta nufi inda suke sannu a hankali take tafiya tana sand'a tamkar da zata saci wani abu har ta isa inda suke. sannu a hankali take janye hanun Ahmad daga jikin *Adyan* har ta janye tana k'oqarin d'aukan sa Ahmad yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta, ta nisa tare da jan numfashi tana wani girgiza ka sam bata yi tinanin cewar ba barci yake ba ganin yanda idanuwan sa suke a rufe, sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e ya sauke kallonsa ga fuskar ta lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar ita ma kallonsa take sun jima a haka suna kallon juna sannan daga bisani suka sauke kallonsu ga yaronsu wato *Adyan.* Sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya mai da kallonsa gareta ya qara da anbatar sunan ta, magana yake cikin sannu a hankali tare da kwantar da murya duk dan sabo da kar ya tashi *Adyan* daga barci.................. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/28/2021, 10:52 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page seven* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 25/12/2021* *Time 08:14pm* *Typing..............* "Mai kike k'oqarin yi ne.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa mashi, "am ni kawai ina da kwad'ayin na rungumi yarona sabo da na jima bana tare da shi." Magana take yayin da take shafar *Adyan* Ahmad ya sauke kallonsa ga yaron yana murmushi sai kuma zuwa wannan lokacin ya amsa mata. "Ki duba yaron da kyau kiga barci yake cikin kyakkyawan yanayi ga a lama yana farin ciki sosai, to ya kamata ki tafi yanzu sabo da ni ba zan baki damar da zaki d'auke sa ba. A maimakon haka kamata yayi ki tafi ki shirya zuwa school yanzu." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake mata hanu ita kuwa sai wani kallonsa take kallo sosai. "Yaya Ahmad hakan ba daidai bane ni ina iya k'oqari na domin ganin na daidai ta komai amma kuma kai." "A'a Ahlam karki manta da yarjejeniyar da take tsakanin mu biyun, wanda kuma ke ce da kanki wadda ta tsara komai ko dai ke kin manta ko a'a kina buqatar ni na tina maki ne.?" Shiru bata yi magana ba jin shirun yayi yawa yasa yaci gaba da magana, "Ahlam a game da *Adyan* kin yarda cewar zai kwana ďaya a tare da ke nima zai kwana ďaya a tare da ni, na yarda da hakan ba tare dana musanta ba ke kin tsara komai kuma na amince da duka tsarin. To amma mai ya saka yanzu kike k'oqarin ganin laifi na? Hakan rashin adalci ne kuma sam bai kamata kiyi hakan ba to yanzu zaki iya tafiya jeki." "Yaya Ahmad ni bawai ina bijirewa yarjejeniyar bane a'a abin shi ne ni kawai na damu ne sosai a kan *Adyan.* Ina matuqar jin kewarsa sosai ina san na runguma shi jikina, Yaya Ahmad zuwa yanzu ni uwa ce to sam ba zai zama laifi ba idan har ni na nuna kulawa ta a kan yarona, to ya kamata ka fahimci wannan domin ka iya yi man adalci zan tafi kamar dai yanda ka buqata amma ya kamata na shirya yaron yanzu, lokaci ya tafi sam bana san mu makara zuwa school." Magana take cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya fad'ar sa ba. Tana kai k'arshen maganar ta ta juya tayi tafiyarta ba tare data jira taji mai zai fad'a ba, ya bita da kallo har ta fice ya dawo da kallonsa ga *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin barci yake, ya shafi kansa zuwa bayan sa cikin tautasa murya yake magana. "Rabin raina lokaci ya tafi sosai zuwa yanzu ya kamata a ce mun shirya zuwa school, amma kuma ga shi kai har zuwa yanzu barci kake to ta ya kuma ni zan shirya ka a haka. Ya kamata nayi wani abu wanda zai tashe ka ba kuma tare da hakan ya cutar da kai ba to mai ya kamata nayi kenan.?" Ya shiga nazari da tinanin mai zai yi ya tashi zaune tare da rungumasa sai wani kallonsa yake yana murmushi, lokaci d'aya kuma ya shiga sunbatarsa yana yi masa cakulkul, nan kuwa ya bud'e idanuwansa yana dariya Ahmad kuwa murmushi yake mai tare da ar dariya. Ya tashi tare da d'aukan sa sun nufi toilet duk abin da yake a kan idanuwan Ahlam tana kallonsu ta window. Ganin ya shiga toilet yasa ita ma ta nufi bedroom domin ta shirya ba jimawa sosai Ahmad ya fita d'auke da *Adyan* ya fara shirya *Adyan* sannan ya shirya. Hakama a can gurin Ahlam bayan ta fito wanka ta shirya cikin wata kyakkyawar shiga ta doguwar riga shigar ta amsheta sosai, ta fito wanda fitowarta tayi daidai data Ahmad d'auke yake da *Adyan* cike da d'auki ta isa inda suke tana anbatar sunan *Adyan.* Shi kuwa sai wani zillo yake mata yana dariya ta kai hanun ta domin amsar sa, kamar ba zai bata shi ba mai ya gani kuma ya bata shi ta kar'be sa tana yi masa wasa shi kuwa sai dariya yake su kuwa murmushi suke sosai mai tare da ar dariya. Sun nufi tebur domin yin break past bayan sun qarasa Ahlam ta ba *Adyan* madara sannan suka fita zuwa school, haka dai suka ci gaba da baiwa yaron kyakkyawar kulawa sosai bayan wata goma da tafiyar su, Ahmad ya sanar da duka ahalin cewar Ahlam ta aihu ta aifi yaro mai suna *Adyan.* Su Umma sunyi matuqar farin ciki sosai sunyi ta k'oqarin tafiya amma su Ahlam suka dakatar dasu, sam basu da wani za'bi dole suka fasa a can kuma sunci gaba da baiwa *Adyan* kulawa sosai. Haka yake ko a gurin su Asma'u *Adnan* yana cikin kyakkyawar rayuwa yana kuma samun cikakkiyar kulawa a gurin su sosai, kamar dai *Adeel* yana samun kulawa sosai daga gurin iyayen sa musamman ma Prof wanda ya ba shi gaba d'aya soyayyar sa, shi ne abin da yafi so fiye da komai a rayuwar sa barin ma daya kasance yana da rashin lafiya irin ta Maman sa, kamar dai *Adnan da Adyan* bayan shekaru uku har zuwa wannan lokacin Aisha na fama da yanayin firgici na jin kukan yara tare da mafarki dasu, abin har kamar zai ta'ba ta yanayin ta yana matuqar d'aga hankalin Prof sosai da Umma. Wani dare tana cikin barci wani matsanancin ciwan mara ya tashe ta, sai wani juyi take tana murkususu a zahirin gaskiya tana jin ciwo sosai, nan ta shiga tashin Prof ya tashi cike da firgici yake tambayar ta lafiya. "Subhanalillah Aisha mai yake faruwa da ke ne haka.?" Cikin wata irin murya ta rashin lafiya take magana. "Prof mara ta take wani irin ciwo sosai ina jin kamar ba zan iya jure zafin ba." "Kai Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un wannan wace irin masifa ce haka yaushe kika daga daga asibiti jinta yanzu kuma mara, ga kuma wannan mummunan yanayin da yake tare dake gaskiya abin da yawa wai shege da hauka, yanzu dare yayi sosai to kiyi hak'uri da safe sai mu tafi asibiti kinji." Sam bata iya amsa shi ba sai dai ta jinjina masa ka a lamar to yaci gaba dayi mata sannu daga bisani kuma ya koma barci. Lokaci d'aya kuma yanayin ta ya soma canja wa inda ta fara jiyo sautin kukan yara kamar ko yaushe, ta toshe kunnan ta tana fad'in, "a'a." wannan kalmar ce kawai take anbatar Prof ya tashi sai wani kallonta yake cike da rashin tausayi ya tashi ya fita ďakin ya nufi wani bedroom domin ya kwanta. Wanda ita ba ma ta san fitar sa ba kasancewar fuskarta na a sunkuye, Ya shiga bedroom yayi zaune jikin gado yana wani jan tsaki yana furta kalmar. "Wannan wace irin masifa ce haka mai na aikata da a ke hukunta ni ta wannan hanyar? Ina san Aisha sosai amma kuma zuwa wannan lokacin na fara k'osawa da wannan yanayin nata. Wanda har ban san tsayin wane lokaci zai d'auka a tare da ita ba, hakan yana matuqar cutar da ni sosai lallai ya kamata nayi wani abu tin kafin yanayin ta yafi haka muni." Ya jima zaune a nan sannan daga bisani ya kwanta yaci gaba da barci abinsa. Washe gari bayan ya qarasa shirin sa ya fito ya nufi d'akin Aisha ya same ta kwance sai wani juyi take ga a lama bata da lafiya, daga gefe kuma ga *Adeel* nan a zaune yana kuka da sauri Prof ya qarasa ciki tare da isa gurin *Adeel* yana fad'ar sunan sa. *"Adeel* mai yake faruwa da kai fad'a min mai ya saka kake kuka.?" "Dady ni ina jin yunwa Mama bata bani abinci ba." Magana yake yana kuka Prof ya shiga rarrashin sa cike da qaunar sa yake magana. "Kayi hak'uri yarona yau Maman ka sam bata cikin kyakkyawan yanayi shi yasa bata baka abinci ba, amma Dady yana nan kuma tare da kai to zaka samu duk abin da kake so yanzu ni zan shirya maka break past." Magana yake masa cikin soyayya sai wani lalla'basa yake tamkar kwai yayin da yake rungume da shi, ya mai da kallonsa ga Aisha wadda har zuwa wannan lokacin abu d'aya take shi ne juyi sai wani a zabar ciwo mara take ji a tare da ita. Ya shiga yi mata sannu kallonsa kawai tayi ba tare data furta masa komai ba, ya tashi tare da riqa hanun *Adeel* sun fita zuwa kicin domin girka break past. Ya had'a musu shayi da wainar kwai ya shirya komai a tebur ya juya sun koma gurin Aisha, ya same ta kamar yanda ya barta har zuwa wannan lokacin bata cikin kyakkyawan yanayi cike da jin tausayin ya isa inda take yana fad'ar sunan ta. "Aisha har yanzu marar bata saki ba? Subhanalillah kinga yanzu mu tafi muyi break past sai mu tafi asibiti kinji ko." Cikin wata ar murya irin ta rashin lafiya take magana. "A'a Prof kawai ka tafi da *Adeel* kuyi break past sabo da ni ba zan iya cin komai ba a yanzu." Zai yi magana ta dakatar da shi ta hanyar girgiza masa ka a lamar a'a, ya jinjina mata ka sannan ya tashi tare da d'aukan *Adeel* sun fice zuwa gurin break past. Basu d'auki wani lokaci ba suka kammala ya shiga ciki ya rik'o Aisha sun fita zuwa asibiti, sun isa asibiti an shiga da ita ciki domin a duba ta *Adeel* ya anbaci sunan Prof yana cewa. "Dady mai ya saka Mama take kuka.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, "rabin raina tana kuka ne sabo da bata da lafiya amma karka wani damu sabo da zata samu lafiya ka ji ko." Ya amsa shi da to nan Prof ya shiga kiran layin Umma ba jimawa ta d'aga, bayan sun gaisa ya sanar da ita cewar yana asibiti tare da Aisha. "Subhanalillah mai kuma ya faru da ita.?" "Ciwon mara ne yake damunta, sai kuma wannan firgicin da yake a tare da ita." "Ho! Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Allah ya bata tafiya gani nan tafe yanzu." Ya amsa da to ya fara sanar da ita asibitin da suke sannan daga bisani suka yi sallama. Doctor's sun jima sosai a tare da ita sannan suka fito cikin hanzari Prof ya shiga tambayar su jikin ta, "Dr Salim to ya jikin na ta.?" "Prof har yanzu muna kanta karka wani damu zata samu lafiya insha Allah yanzu ka tafi ka kawo wannan." ya miqa masa wata takarda ya kar'bi takardar tare da d'aukan *Adeel* ya fice Dr salim kuma ya nufi office. Bayan wani lokaci Prof ya dawo kai tsaye office d'in Dr Salim ya nufa ya kai masa abin daya buqata a siyo, ya kar'bi kayan sun fito tare Dr Salim ya nufi d'akin da Aisha take Prof ma binsa yayi a baya ya tsaya a gefen ofa. Ba jimawa sai ga Umma nan kuwa ta shiga tambayar Prof jikin Aisha, "tana ciki suna duba ta." "ina fatan ta samu sauki cikin sauri Allah ya bata tafiya." Ya amsa da Amin bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a tare da ita sosai sun fito, su Dr Anisa sun fice zuwa office Dr Salim kuma ya tsaya domin yayi magana da Prof, da sauri Prof ya isa garesa domin jin lafiyar matarsa ya ja hanun sa sun koma gefe cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita yake magana. "Dr Salim kana fa tsorata ni da wannan shirun naka dan Allah ka sanar da ni abin da yake faruwa da matata.?" Ya girgiza tare da sauke a jiyar zuciya sannan ya amsa shi. "Prof gaskiyar ita ce Madam sam bata cikin kyakkyawan yanayi sannan kuma tana cikin damuwa sosai, Prof k'ila Madam tana yawan shiga firgici unci da kuma 'bacin rai a ko yaushe, hakan yana k'oqarin ta'ba ta sosai ta hanyar gusar mata da tinanin ta. Prof ka san cewar ita d'in tana da rauni a zuciya wannan yasa ba a san tana unci ko wani abin da zai gajiyar da ita sosai, Prof Madam tana matuqar buqatar kulawa sosai to ya kamata kayi hakan domin ka taimaka mata ta fita daga hatsari." Wani irin kallo Prof yake yi masa mai cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya ji yana fad'a, cike da unci bak'in ciki firgici rud'ani da kuma tashin hankali yake magana. "Dr Salim wai mai kake fad'a ne haka a kan matata? Sam bai kamata hakan ta faru da ita ba a'a ni sam ba zan bar wani mummunan abu ya faru da ita ba. Dr Salim dan Allah kayi koma miye domin matata ta samu lafiya lallai ya kamata wannan mummunan yanayin ya barta to kayi komai sabo da ta samu lafiya ka ji ko." "Shikenan zanyi iya abin da zan iya ina fatan ta samu lafiya sosai." Ya jinjina masa ka da kuma haka suka rabu Dr Salim ya nufi office ďin sa Prof da Umma kuma sun shiga d'akin da Aisha take, sun same ta kwance duk an sanya mata wasu na'ura a jiki har a kai wanda kuma hakan ne ya tabbatar musu da cewar bata cikin kyakkyawan yanayi. Da gudu *Adeel* ya nufi inda take yana fad'ar sunan ta da sauri Umma ta riqo hanun sa tare da kai kallonta ga Prof tana tambayar sa mai yake faruwa da Aisha. "Karki wani damu Umma zata samu lafiya insha Allah to kawai ki yarda da ni kinji ko." Ta jinjina masa ka a lamar to ya mai da kallonsa ga *Adeel* wanda yake ta fitinar sai ya tafi gurin Aisha, ya d'auke sa yana rarrashin sa sai wani lalla'basa yake har ya samu ya dena kuka daga bisani kuma yayi barci bayan kwana biyu..................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/28/2021, 9:34 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 8* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 27/12/2021* *Time 09:06pm* *Typing..............* Kwance take Dr Anisa ta shigo domin ta duba ta, ta isa inda take ta duba ta Alhamdulallah tana samun sauki, ta juya domin tafiya Aisha ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "Doctor dan Allah ko zamu iya yin magana yanzu.?" Ta jinjina mata ka tare da furta eh tayi wani gajeran murmushi sannan taci gaba da magana. "Likita dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake damuna? Sabo da ina jin wani irin mummunan yanayi a tare da ni ina jin kamar zanyi hauka wani lokaci, musamman idan ina jiyo sautin kukan wad'an nan yaran ko kuma dai in nayi mafarki dasu. Kai na yana d'aukan zafi sosai sannan kuma ina fita haiyacina na tsayin wani lokaci, likita na san cewar kuna kan binkice a kan lafiya ta to dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da ni kinji.?" Doctor Anisa ta zauna daga gefen ta sai wani kallonta take kallo sosai mai cike da jin tausayin ta sosai a tare da ita, sun samu shiru na muntuna kad'an sannan ta amsa ta cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana. *"Maman Adeel* ya kamata ki kwantar da hankalin ki domin tafiya ta samu damar shigarki, sabo da sam ba a san kina yawan shiga firgici, unci, bak'in ciki, da kuma damuwa sabo da hakan barazana ce ga lafiyar ki. To ya kamata ki dena unci sannan kuma ki jure kuna karki yanke qauna ga samun lafiyar ki kinji ko, to ki kula sosai ni zan tafi Allah ya baki lafiya." Ta yunk'ura domin ta tashi Aisha ta dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta. "Likita fad'a min gaskiya shin ni ina tare da juna biyu ne.?" Wani irin kallo take yi mata mai cike da jin mamakin abin data fad'a cike da rud'ani take amsa ta. *"Maman Adeel* kamar kina magana a kan juna biyu haka ne.?" Ta jinjina mata ka a lamar eh cike da jin mamakin abin data fad'a Dr Anisa take magana. *"Maman Adeel* gaskiya naji mamaki sosai da naji kinyi magana a kan juna biyu, ko dai ke kin manta am ina nufin ta ya zaki aihu bayan kuma babu mahaifa a tare da ke.?"Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data fad'a take magana. "Likita wai mai kike fad'a ne ta ya ni na rasa mahaifa a tare da ni? A'a hakan sam ba zai faru ba da ni ba zan ta'ba barin hakan ta faru da ni ba, sam ba zai yu na rasa mahaifa a jiki na ba ni gaskiyar nake fad'a ki yarda da ni sabo da gaskiyar nake fad'a." *"Maman Adeel* dan Allah ki kwantar da hankalin ki sabo da kin fara fita haiyacinki, hakan kuma mummunan a lama ce a tare da ke to ya kamata ki natsu kinji ko dan Allah." Lokaci d'aya kuma ta fara fita haiyacinta sai wani irin abu yake yanayin ta ne yasa dole Dr Anisa tayi mata alluran barci. Ba jimawa sosai tayi barci Dr Anisa kuwa sai wani kallonta take yayin da tausayin ta yayi yawan gaske a tare da ita, tana haka sai ga Umma ta dawo Dr Anisa ta gaishe ta sannan ta tashi ta fice. Umma tayi isa inda take ta zauna sai wani kallonta take kallo mai cike dajin tausayin ta sosai a tare da ita, da yamma lis suna zaune tare da ita sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, sai wani kallonsu take ba kuma tare data furta musu komai ba dukansu sun shiga yi mata sannu amma bata amsa ba. Lokaci d'aya ta tina da zancan da tayi da Dr Anisa kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai. Prof ya tashi daga inda yake ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, zai yi magana tayi saurin dakatar da shi ta hanyar d'aga masa hanu tare da juya masa baya cike da jin mamakin ta yake magana. "Aisha wai mai yake faruwa da ke ne haka dan Allah ki sanar damu kinji please.?" Shiru bata amsa shi ba sai ma kuka da take ya juyo da fuskar ta tare da fad'ar sunan ta, kafin ya furta komai tayi saurin dakatar da shi ta hanyar da bai ta'ba tinani ba, kamar a mafarki Aisha ta sauke masa mari biyu masu kyau a fuska. Cike da firgici da rud'ani Umma take fad'ar sunan ta amma bata amsa ba cike da jin mamakin ta sosai yake magana. "Aisha yau kuma ni kika mara? Eh lallai kin tabbatar da cewar kin fara hauka to ya kamata na nai mi mafuta ko dan sabo da yarona, domin sam ba zanso ki cutar da shi da wannan haukan naki ba." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin da yake fad'a Umma take magana. "Prof wai mai kake fad'a ne haka sam na kasa fahimtar ka shin wani abu yana faruwa da Aisha ne dan Allah ka sanar da ni.?" Kafin ya furta komai tayi masa rigagi, "kai mugu ne na tsane ka kawai ka bar nan ka fita daga rayuwa ta data yarona gaba d'aya." Cike da rud'ani Umma ke magana, "Aisha qlau kike kuwa shin kinji irin lafazin da yake fitowa daga bakin ki kuwa? Ta ya zaki buqaci mujin ki ya rabu da ke cikin sauk'i mai ya saka zaki cutar da kanki har haka Aisha fad'a min mai yake faruwa da ke ne kuma gaskiyar zaki fad'a.?" "Umma shi yasa an cire min mahaifa ba tare da amince wa ta ba, shi ya cutar da ni sosai sam bai kamata ya aikata min haka ba amma." Lokaci d'aya suka ga ta ri e k'irji tana fad'in wash da sauri suka shiga anbatar sunan ta, amma bata amsa ba sai ma wani irin abu da take lokaci d'aya kuma ta suma, cike da firgici Prof ya fita ba jimawa ya dawo tare da doctor ganin yanayin ta ne yasa a ka buqaci dasu fita. Prof ya fara d'aukan *Adeel* da yake kwance a kan kujera yana barci sannan suka fice daga d'akin, nan kuwa su Dr Anisa suka nufa kanta sun jima a tare da ita sannan daga bisani suka fito, cikin hanzari Prof ya shiga tambayar su jikin ta sun samu shiru na jim kad'an sannan Dr Salim ya amsa shi. "Prof a zahirin gaskiya matarka sam bata cikin kyakkyawan yanayi, Prof kamar dai mun fad'a maka cewar matarka bata buqatar unci, bak'in ciki, 'bacin rai tinani, ko damuwa. Sabo da hakan yana matuqar cutar da ita sosai sannan kuma zai iya zama barazana ga lafiyar ta, to ya kamata ku kula da ita sosai ku saka ta farin ciki sosai sabo da hakan ne zai taimakawa lafiyar ta, Prof gaskiyar ita ce idan har irin haka yana faruwa da Madam to fa komai zai lalace zata rasa tinanin ta gaba d'aya, zata koma hauka ko kuma dai ku iya rasa ta gaba d'aya to da akwai buqatar ku kula da ita sosai please." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya ya nufi office hakama su Dr Anisa suma tafiya suka yi, cikin hanzari Prof ya juya ya nufi office ďin Dr Salim Umma kuma ta nufi d'akin da Aisha take. Zaune yake sai dai ba abin da yake Prof ya turo ofa ya shigo ya isa inda yake sai wani kallonsa yake cike da unci da damuwa ya kifa masa wani wawan mari tare da fad'ar sunan sa. "Dr Salim ni d'in nan nayi matuqar yarda da kai sosai to amma mai ya saka kai kaci amana ta? Na baka duk wani abin daka buqata daga gareni har ma qari na yima, amma kuma duk da haka shi ne kai ka za'bi da kaci amana ta mai yasa fad'a min mai ya saka kai ka yaudareni.?" Magana yake cikin fishi sosai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, Dr Salim kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai mai cike da jin mamakin sa kuma a haka yake magana. "Prof wai a kan me kake magana? Ni sam na gagara fahimtar komai daga cikin abin da kake fad'a, ya kamata ka fito min a mutum ta yanda zan iya fahimtar ka fad'a min a kan me kake magana.?" Mst yaja tsaki sannan yaci gaba da magana, "Dr Salim ta ya a kai Aisha ta san cewar babu mahaifa a tare da ita? Karka fad'a min cewar wai ba kai bane ya sanar da ita gaskiyar ba sabo da sam ba zan yarda da hakan ba, fad'a min mai ya saka ka yaudareni ta hanyar sanar da ita gaskiyar.?" Cike da jin mamakin abin daya fad'a Dr Salim yake magana. "Prof wai mai kake fad'a ne haka taya kake tinanin cewar ni ďin nan zan iya yaudaranka har haka? A'a ni sam ban aikata abin da kake tinani ba wallahi tallahi ni ban sanar da ita komai ba to zaka iya yarda da ni." Cike da unci ya wani shak'o wuyan sa cikin fishi sosai yake magana. Mai ya saka za kayi k'arya? Bayan kuma ni gaskiyar nake fad'a, ni dai ne kawai muka yi wannan zancan na biyaka kamar dai yanda ka fad'i farashin ka, har ma nayi ma qari amma da abin da zaka sakamun kenan wannan ne sakamakon da zaka ba ni? Yanzu sabo da kai matata sam bata cikin kyakkyawan yanayi sannan kuma ka d'ora alhakin hakan a kai na, ta hanyar fad'a min cewar ban kula da ita yanda ya kamata ba kai har kama isa, to bara ka ji bawai sabo da ka san sirrina ba sam ban damu da wannan ba sabo da hakan sam ba zai dakatar da ni daga hukunta ka ba idan naso hakan. Kud'i kawai zan ba da nan take za a yi man duk abin da nake so kamar dai yanda kai ma kayi, to yanzu ka fad'a min mai yasa kaci amana ta sannan kuma ka yaudareni gaskiyar zaka fad'a.?" "Prof ni gaskiyar nake fad'a wallahi tallahi ban sanar da Madam komai a game da wannan ba, to ta ya ma ni zanyi tinanin aikata maka haka bayan kuma na san dani a kayi komai a'a ni ba zan ta'ba aikata maka haka ba. Prof ya kamata ka yarda da ni sabo da ni gaskiyar nake fad'a sam ban aikata abin da kake tinani ba, kuma komai lalacewa ta to ba zan ta'ba yiwa rantsuwa a kan k'arya ba to yana da kyau kai ka yarda da ni dan Allah." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana, "Dr Salim to idan ba kai bane wanda ya sanar da Aisha gaskiyar ba to waye? Ka fad'a min waye wanda zai iya aikata hakan wanda ya san da sirrin sabo da dole da akwai wani wanda ya san da wannan zancan, dan haka ni ba zan ta'ba yarda da kai ba har sai idan ka sanar da ni duka gaskiyar waye cikon na ukun mu wanda ya san da wannan zancan kuma gaskiyar zaka fad'a.?" "Prof ni na riga dana sanar da kai duka gaskiyar ban sanar da kowa ba to mai ya saka ba zaka yarda da ni ba." "Wai kai kana magana a kan yarda? To ka sani ka riga daka rasa yarda ta ba kuma zan qara yarda da kai ba, daga k'arshe kuma lallai ya zame maka dole ka gano wannan wanda yake ri e da wannan sirrin, ko kuma dai kai ka san irin abin da zan iya aikata wa a kanka kuma kayi hakan cikin sauri." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa yayin da unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare da shi sosai, Dr Salim ya bisa da kallo har ta fice ya nisa tare da jan numfashi ya qara da sauke a jiyar zuciya ya zauna yana cewa. "To waye kuma wannan wanda yake k'oqarin 'ballomin ruwa ta ya ma a kai wannan zancan ya futa bayan kuma mu biyu ne kawai a gurin, ina matuqar mamaki sosai da hakan ta faru lallai ya zame min dole dana gano ko waye wannan eh zanyi hakan kuma nan kusa insha Allah." Ai kuwa haka Dr Salim ya shiga binkice a kan gado wanda ya sanar da Aisha zancan cire mahaifa, amma sam bai yi nasaran gano komai ba sabo da sam bai ta'ba tinanin cewar Dr Anisa ba ce. Haka dai Aisha tayi ta samun cikakkiyar kulawa daga gurin doctor ta jima sosai asibiti sannan daga bisani ta samu sallama, amma sam bata yarda da koma wa gidan ta ba sabo ta kasa yafe wa Prof abin daya aikata a gareta. Wani yammaci Prof yazo domin tafiya da ita gida ranar gaba d'aya bata cikin kyakkyawan yanayi, zaune take ta had'e kai da guiwa tasa pillow ta toshe kunnan ta yayin da bakinta yake ta anbatar kalmar a'a Umma na daga bayan ta rungume da ita. Da sauri Prof ya nufi gurin ta har yana gudu hakama *Adeel* abin da yake yi kenan yayin da yake fad'ar sunan ta Mummy, yana k'oqarin hawa jikin ta ta ture sa har ya fad'i da sauri Prof ya riqo sa yana rarrashin sa shi kuwa sai kuka yake, ya jima yana rarrashin yaronsa har sai da yayi shiru sannan ya mai da kallonsa ga Umma tare da fad'ar sunan ta. "Umma shin tin yaushe take cikin wannan yanayin sannan kuma yau tasha maganin ta kuwa.?" Cike da unci da tarin damuwa take magana, "ta jima sosai a haka tana magana a kan wasu yara daban gaba d'aya yau bata cikin kyakkyawan yanayi, nima bana tare da natsuwa sabo na damu sosai a kanta na sha'afa shi yasa na manta da bata magani. K'ila shi yasa jikin ta yayi zafi sosai Prof naro e ka dan Allah ka taimaki Aisha ta samu lafiya dan Allah." Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "Umma gaskiyar ita ce Aisha ta riga data samu matsalar ta'bin hankali ko na ce tana tare da ciwon hauka, wannan ne abin da likita ya sanar da ni a kanta nayi shiru ne sabo da ban yarda da abin daya fad'a ba. Amma yanzu da nake ganin a salin gaskiyar to ba zai yu nayi shiru ba, Umma ba zan 'boye maki ba gaskiya ba zan iya ci gaba da zama da 'yarki ba, sabo ba zata yi man wani anfani ba sai dai kawai ta cutar da ni da kuma yarona kinga abin data aikata a yanzu." K'oqarin cutar da shi take to mai kuma kike tinanin zai faru idan ya kasance cewar su biyu ne? To duba da wannan yasa dole zamu rabu tabbas ina san Aisha sosai, hakama nayi ta burin na rayu da ita na har abada amma yanayin ta ya canja komai, a gaskiya ni ba zan iya jure wannan yanayin nata ba sabo da yana da hatsari sosai ita yanzu abar tsoro ce. To bani da wani za'bi wanda ya wuce wannan dole mu biyun zamu rabu sabo da a yanzu ni da ita sam bamu dace da juna ba, Umma kiyi hak'uri da irin abin da nake fad'a sabo da bani da wani za'bi ne shi yasa dole sai hakan ta faru, Umma ni Prof Abas Muh'd na saki matata Aisha Salisu saki d'aya ina fatan wata rana ta samu lafiya sai an jima." Ya tashi tare da riqa hanun *Adeel* domin su tafi da sauri ya cire hanun sa yana fad'ar a'a. Yayi kwance jikin Aisha yana fad'ar sunan ta Mummy shiru bata amsa ba, Prof ya riqo hanun sa tare da fad'ar sunan sa sannan yaci gaba da magana. *"Adeel* ya kamata mu tafi gida karka damu zan siya maka ice cream da chocolate ai zaka sha ko.?" "A'a ni ina san na zauna tare da Mummy to ba zan tafi ba." *"Adeel* hak'uri kawai zan baka domin dole zamu tafi yanzu." Ya riqo hanun sa domin su tafi lokaci d'aya ya saki kuka yana anbatar sunan Mummy kuka yake sosai, haka kukan sa yayi ta mata yawo a ka da sauri ta janye pillow da yake kunnan ta tare da kai kallonta ga yaronta wanda yake ta fad'ar sunan ta. Da sauri ta tashi ta nufi inda yake ta wani ri e hanun sa ta qara da yin hugging d'in sa shi kuwa yayi kwance jikin ta yana fad'ar sunan ta, Umma sai wani kallonsu take hakama Prof shi ma kallonsu yake kallo sosai ya nisa tare da jan numfashi yana cewa. "Aisha a haka kamar kin dawo haiyacinki amma kuma ba hakan bane, gaskiyar ita ce ba zaki iya kulawa da kowa ba dan haka dole zan tafi da *Adeel* ki yafemin a kan hakan dan Allah." Ya kai hanun sa ya janyo *Adeel* domin tafiya shi kuwa sai kuka yake kuka sosai hakama Aisha kuka take, haka cikin rashin tausayi ya d'auki *Adeel* suka fice yayin da yaron yake kuka, Aisha na k'oqarin binsu Umma tayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun tana girgiza mata ka a lamar a'a, ita kuwa sai wani irin abu take ta qara fita haiyacinta Umma ta shiga rarrashinta tana yi mata addu'a............ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/30/2021, 11:50 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 09* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 29/12/2021* *Time 02:07pm* *Typing................* Haka Umma tayi ta k'oqarin ganin ta kwantar mata da hankali, amma sam tak'i ta saurare ta da k'yar Umma ta samu ta iya bata magana, wacce kuma daga bisani barci yayi nasaran d'auke ta. Umma tayi zugum sai wani kallonta take kallo sosai yayin da tausayin ta yayi yawan gaske a tare da ita sosai, ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da ƙuna sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, haka suka kasance na wani lokaci a can gurin Prof kuma lokaci zuwa lokaci ya kan tafi da *Adeel* gidan Umma domin ya duba Mummyn sa. Wacce har zuwa wannan lokacin bata cikin kyakkyawan yanayi, bayan wasu ƴan watan ni Prof ya bar garin Katsina ya koma garin Bauchi da aiki. A kullum a ko yaushe *Adeel* cikin kukan ya kai shi gurin Mummyn sa yake, amma sai dai ya ba shi hak'uri yana rarrashin sa tin yana damuwa har ya fara sabawa da rashin ta, ya cigaba da rayuwar sa daga bisani kuma Prof ya saka shi school. *England* Zaune take tana ta aikin dannar waya ga a lama chart take k'arar da taji ne yasa ta saurin d'ago fuskarta, tayi tozali da fuskar Ahmad ya fito cikin wata kyakkyawar shiga ta k'ananan kaya shigar ta amshesa sosai, yayi matuqar yin kyau sosai sai wani lallausan murmushi yake wanda ya qara bai yana a salin kyan fuskarsa. Hakan yasa ta rufe sa da ido tana kallonsa kallo sosai lokaci d'aya ta sami kanta da jin yana birgeta matuqar birgewa sosai, shi kuwa ta gefen ido yake satan kallonta ganin ya doshi ofa ga a lama fita zai yi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. Ya tsaya tare da juya wa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna sai wani kallon juna suke kallo sosai, wani irin kallo suke yiwa juna wanda suka gagara fahimtar mai suke nufi da shi, sun jima sosai a haka sannan daga bisani ya amsa ta. "Ahlam kamar kin kira ni ko? To fad'a min miye sabo da ina sauri zan d'auko yarona daga makaranta.?" Ha!!! Ta nisa sosai tare da jan numfashi tana mai sauke a jiyar zuciya cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana. "Am Yaya Ahmad shin zamu iya tafiya tare please.?" Magana take cikin wata irin murya mai dad'in sauraro, shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "shikenan zamu iya tafiya amma ki fara shiga ciki ki sauya wannan shigar da take jikin ki sai mu tafi." Ta kai kallonta ga jikin ta tana kallon kanta wata riga ce a jikin ta, wadda tsayin ta iya guiwa ne hakama rigar shara-shara take tayi kwance jikin ta, hakan yasa duk ta fito da surar jikin ta wanda kuma tana yin duka hakan ne sabo da taja hankalin ta a kanta. Dalilin ta na yin hakan kuma shi ne zuwa wannan lokacin ita ta fara san shi, ta mai da kallonta garesa tana wani lallausan murmushi tare da jinjina masa ka tana cewa, "shin wai ba zai yu ni na fita a haka ba.?" Wani irin kallo yake yi mata mai cike da jin mamakin abin data fad'a. "Ahlam shin kin duba kanki da kyau kuwa ta yanda zaki tantance irin shigar da take jikin ki? to ki sani ni sam ba zan ta'ba baki damar da zaki fita a haka ba kawai ki zauna a gida sai na dawo." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa ba tare daya jira yaji mai zata fad'a ba, ita kuwa ta bisa da kallo har ya fice yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi. Yayin da take jin yana birgeta sosai ta juya ta nufi bedroom d'in ta yayin da take magana da zuciyarta, "Yaya Ahmad gaskiya kana buqatar birge ni sosai ina fatan ina da muhalli a cikin zuciyar ka dama rayuwar ka gaba d'aya." Tayi kwance tare da rufe idanuwan ta sai wani farin ciki take ji yana shigar ta sosai. Bayan wani lokaci Ahmad ya dawo tare da *Adyan* sai dai basu sami Ahlam a parlour ba, da sauri *Adyan* ya nufi bedroom d'in ta har yana gudu yayin da yake fad'ar sunan ta Ammie. Ahmad ya bisa da kallo yana murmushi mai tare da ar dariya yayin da yake jin wata qaunar sa tana qara shigarsa. Ya shiga ciki ya same ta kwance da gudu ya hau gadon tare da fad'a wa jikin ta yana fad'ar sunan ta Ammie, da sauri ta bud'e idanuwan ta tayi tozali da kyakkyawar faskar sa tayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa, tana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona shi ma abin da yake fad'ar mata kenan. Duk abin da suke fad'a a kan kunnan Ahmad sabo da yana kallonsu yayin da yake jin suna birgesa sosai, ya juya ya shiga ciki yayi tsaye jikin ofa lokaci d'aya dukansu suka kai kallonsu garesa suna murmushi, *Adyan* ya shiga anbatar sunan sa ya tashi daga jikin Ahlam ya nufi inda yake, Ahmad ya dukursa tare da rungumasa jikin sa yana sunbatarsa tare da furta masa kalmar ina qaunarka sosai d'ana. "Appa mai ya saka kake tsaye a nan kazo ka kusa damu domin mu rungumi juna, hakan zai saka muyi farin ciki sosai to mu tafi gurin Ammie." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi shi kuwa sai wani kallonsa yake hakama Ahlam kallonsa take tana murmushi mai tare da dariya. "Gaskiyar ka ne yarona amma yanzu da akwai buqatar kaci abinci sannan kuma a shirya ka, to ina ga wannan ne abin daya fi komai dace wa a yanzu, to yanzu fad'a min mai zaka ci.?" "Appa yau naci abubuwa da dama a school to shi yasa yanzu ni sam bana jin yunwa." "Shikenan amma duk da haka dole zaka sha madara kuma sam ba zan yarda da kalmar a'a ba ka ji ko." "Eh Appa zan sha yauwa Appa da akwai abin da zan sanar da dukanku." Ahlam ta tashi daga inda take ta nufi inda suke ta zauna tare da shafar kansa ta qara da sunbatarsa tana cewa. "Rabin raina fad'a mana koma miye? Tabbas zamu yi matuqar farin ciki da duk abin da zaka sanar damu, to fad'a mana miye.?" Cike da d'auki yake sanar dasu, "Appa Ammie an d'auke ni cikin yaran da zasu yi wasan tseren keke da kuma kwallon k'afa, ina farin ciki sosai kuma ina fatan nayi nasara a cikin gasar amma kuna farin ciki kuwa.?" Ahlam ce wadda take amsa shi yayin da Ahmad ya rufe shi da ido yana kallonsa, "eh rabin raina muna farin ciki sosai sannan kuma zaka yi nasara sabo da kai d'in na musamman ne, ina yima fatan nasara ďana." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi, a zahirin gaskiya tana farin ciki sosai yayi hugging d'in ta ita kuwa ta sunbacesa a ka dama gefen fuska, tana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona ya amsa ta da nima ina qaunarki sosai. Sun kai kallonsu ga Ahmad wanda yayi shiru tamkar da bai ya gurin sai wani kallon *Adyan* yake yayin da yake magana da zuciyarsa. "Kayi hak'uri ka yafemin yarona sabo da a yanzu sam ba zan iya baka abin da kake so ba, ina nufin ni sam ba zan barka ka shiga wannan gasar ba duk da cewar kana da buri sosai a kan hakan. Zanyi hakan ne sabo da lafiyar ka domin yin wannan gasar zai iya cutar da kai sosai da kuma lafiyar ka to ni sam ba zan ta'ba barin hakan ta faru ba, to ina fatan zaka fahimce sannan kuma ka iya fahimta na ina qaunarka sosai d'ana." Dafashi d'in da tayi ne tare da fad'ar sunan sa da k'arfi yasa shi kai kallonsa gareta ba kuma tare daya amsa ta ba. "Yaya Ahmad qlau kake kuwa fad'a min mai kake tinani? Shin ka ji abin da *Adyan* ya fad'a kuwa amsa min shin qlau kake kuwa gaskiyar zaka fad'a.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "ki shirya shi ni zan had'a masa madara." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi domin tafiya da sauri *Adyan* ya ri e hanun sa yana cewa. "Appa baka yi man fatan nasara ba amma kana farin ciki kuwa.?" Ya dukursa tare da shafar fuskarsa ya qara da sunbatarsa, "eh masoyi ina farin ciki sosai sannan kuma ina yima fatan nasara, yanzu ka tafi Ammie ta shirya ka Appa kuma zai had'a maka madara ka ji ko." Ya jinjina masa ka yana dariya shi kuwa murmushi yake ya qara sunbatarsa sannan ya sake sa daga rungumar da yayi masa ya tashi ya fita, Ahlam tabi shi da kallo har ya 'bace sannan ta dawo da kallonta ga *Adyan* ta fara cire masa kayan jikin sa sannan ta rik'a hanun sa zuwa toilet. Ba jimawa ta fito da shi ta shirya sa sun fito parlour sun samu Ahmad zaune ya tare su da murmushi, da gudu *Adyan* ya nufi inda yake ya zauna a kan cinyarsa Ahmad ya sunbacesa tare da fad'ar sunan sa. *"Adyan* bana fad'a maka cewar ka dena yin gudu ba amma mai ya saka kake yi.?" "I'm so sorry Appa please." "OK yanzu ka sha wannan." Nan ya shiga ba shi madara ya kuma sha sosai bayan ya qarasa ya tashi yana cewa. "Appa Ammie ni zan tafi nayi wasa." "Shikenan yarona kayi ko wane wasa amma banda kwallo, tsalle, da gudu ka ji ko to ka kula sosai." Lokaci d'aya ya 'bata fuska kamar zai saki kuka cikin hanzari Ahlam ta anbaci sunan sa ta kuma ci gaba da magana. "Karka wani damu rabin raina zaka iya yin ko wane irin wasa idan kana so, jeka kayi kwallo, tsalle, da gudu dama duk abin da kake so ka ji ko." Lokaci d'aya ya saki wani kyakkyawan murmushi cike da d'auki ya juya ya fita, Ahmad na kiran sa amma sam bai amsa ba ya fice abinsa Ahmad ya dawo da kallonsa ga Ahlam kafin ya furta komai tayi masa rigagi. "Yaya Ahmad mai yasa kake haka mai yasa kake dakatar da yaron daga farin ciki? Yau yaronmu yana farin ciki sosai sabo da gasar da a ka za'besa amma kuma kai sam baka farin ciki da hakan, yanzu kuma kana k'oqarin dakatar da shi daga yin wasa Yaya Ahmad mai ya saka kake yin duka wannan shin da akwai wani abin da kake 'boye min a game da yaronmu.?" Shiru bai amsa ba sai ma yunk'urin tashi da yayi da sauri ta dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa, tare da zaunar da shi sai wani kallonsa take kallo sosai ta gama fahimtar cewa sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi, hakama da akwai unci da damuwa sosai a tare da shi ta nisa tare da jan numfashi tana anbatar sunan sa. "Yaya Ahmad dan Allah ka amsa ni shin kana 'boye man wani abu a game da *Adyan* gaskiyar zaka sanar da ni.?" Yayi shiru kad'an yana nazari daga bisani ya girgiza mata ka tare da fad'ar sunan ta. "Ba komai ni sam bana 'boye komai kawai dai ni sam bana da buqata da hakan, ina nufin bana buqatar naga yana irin wannan wasan to shi yasa nake dakatar da shi, Ahlam ni ina yin abin daya dace ne a kan yarona to dan Allah karki ce zaki dakatar da ni please." Ya yunk'ura zai tashi da sauri ta dakatar da shi ta hanyar furta masa, "a'a hakan sam ba zai yu ba ni sam ba zan baka damar da zaka dakatar da farin cikin yarona ba, to ya kamata ka dakatar da wannan burin naka sabo da cikar burin yaronmu. Sannan kuma zai yi gasar kamar yanda a ka tsara hakan sam ba zai canja ba to kawai ka amince da hakan ka ji ko." Ya girgiza ka yana cewa, "Ahlam wannan ne abin da ba zai ta'ba yuwa ba ni ba zan ta'ba amince wa hakan ba na har abada, ni abu mai kyau nake sannan kuma rayuwa mai kyau nake baiwa yaronmu to ya kamata ki fahimci hakan sannan kuma dai karki yi yunk'urin dakatar da ni dan Allah." yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyarsa, da sauri ta tashi ta bisa a baya dan ganin inda ya nufa, yana fita kai tsaye gurin *Adyan* ya nufa domin ganin abin da yake. Tin daga nesa ya hange sa yana aikin buga kwallo wanda yake had'awa da gudu, hakama ya gama fahimtar cewa sam ba shi da kuzari sosai da sauri ya nufi inda yake har yana gudu, kamar daga sama ya ga Ahlam ta sha gaban sa tare da fad'ar sunan sa, "Yaya Ahmad ni fa ba zan baka damar da zaka dakatar da shi ba to ya kamata ka fahimci hakan ka ji ko." "Ahlam ki janye min a hanya wai mai yasa ka sam bakya fahimtar abin da nake fad'a ta ya kike tinanin cewar zan cutar da *Adyan?* A'a ni sam ba zan ta'ba aikata hakan ba to kawai ki yarda da ni please sabo da ina yin abin daya dace ne, ya kamata na tafi sabo da akwai buqatar na dakatar da shi yanzu." "A'a ba zaka dakatar da shi ba har sai idan ka sanar da ni a salin gaskiyar. To yanzu fad'a min mai kake 'boye min a game da *Adyan.?"* Shiru bai yi magana ba sai ma k'oqarin tafiya yake domin zuwa gurin *Adyan* amma ta hana shi, sai abu d'aya take maimaita masa ya nisa tare da jan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya. "Shikenan zan sanar da ke kamar yanda kika buqata daga gareni abin shi ne." Kafin ya furta komai ya hangi *Adyan* yana k'oqarin kife wa qasa, da sauri ya janye Ahlam gefe ya nufi gurin sa da sauri har yana gudu, da sauri Ahlam ta kai kallonta garesa cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ta nufi gurin da gudu yayin da take fad'ar sunan sa. Ahmad ya isa inda yake da sauri ya ri e sa ya fad'a jikin sa lokacin yayi daidai da zuwan Ahlam, sun shiga jijjigasa suna fad'ar sunan sa ganin yanayin sa ya soma tsananta sosai, yasa suka d'auke sa zuwa asibiti.................. Please ina buqatar addu'ar ku mura na damuwa sosai. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [12/30/2021, 9:22 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 10* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Thursday 30/12/2021* *Time 12:03pm* *Typing...............* Sun isa asibiti cikin hanzari nurse suka kar'bi yaron suka shiga da shi d'akin gaugawa domin a duba shi. Bayan tafiyar su Ahmad sai wani kai kawo yake ya sauke kallonsa ga Ahlam wacce gaba d'aya ta kusa ta fita hayyacinta, cikin hanzari ya isa inda take cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Ahlam yanzu mai kika aikata kenan? Duk sabo da ke ne hakan ta faru ina ta k'oqarin ganin na dakatar da shi amma kuma ke, sam baki sauraran ba sam kin gagara yarda da ni dama duk abin da nake fad'a, yanzu sabo da taurin kanki yaronmu yana cikin mummunan yanayi Ahlam mai yasa kika kasa saurara na ko da sau ďaya ne shin kin san abin da yafi so zafi? Ahlam ganin abin da kafi so cikin mummunan yanayi yafi komai zafi, Ahlam hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai. Ahlam ke d'in nan kin aikata babban zunubi wanda yake da matuqar girma sosai sannan kuma. Tayi saurin dakatar da shi ta hanyar da bai ta'ba tinani ba, kamar a mafarki ya ji saukar wani wawan mari a fuskar sa, da sauri ya zaro ido yana kallonta kallo sosai mai cike da jin mamakin ta sosai, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa take magana yayin da take kuka kuma kuka sosai. "Mai ya saka kake hukunta ni da zunubin ta? Kai ne a salin mai laifin amma kuma ni ce wacce kake hukunta wa, Yaya Ahmad tin da jimawa nake tambayar ka abu ďaya a game da *Adyan* amma ko sau ďaya baka ta'ba tinanin amsa ni ba. Sai faman 'boye min gaskiyar kake wanda da a ce ni na san a salin gaskiyar to da duka wannan bai faru ba, a kan me kai zaka 'boye min cewar yarona ba shi da lafiya? Ni Maman shi ne to akwai buqatar dana san komai a game da ta yanda ni zan iya karesa, shin baka ta'ba tinanin cewar wannan cutar wa ba ce gareni amma kuma shi ne duk da haka kake d'ora laifin a kai na? Wannan rashin adalci ne sabo da kai ne nan wanda yake da alhakin duka wannan, sabo da kai ne *Adyan* yake cikin wannan mummunan yanayin amma ba ni ba, to ka sani wallahi tallahi ba zan ta'ba gafarta maka ba idan har wani mummunan abu ya faru da yarona ka tina da wannan." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita. Shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai ya gama fahimtar cewa sam bata cikin kyakkyawan yanayi, wanda wannan dalilin ne yasa bai iya amsa ta ba wanda shi ma zamu iya cewa yana cikin yanayi irin nata. Sun samu shiru na tsayin wani lokaci ba mai magana a cikin su, sai jiran fitowar doctor suke domin ya jikin yaronsu, bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a ciki tare da shi sosai sun fito da sauri dukansu suka isa ga Dr Sam suna tambayar sa jikin *Adyan.* Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa su dasu same sa a office, ya juya yayi tafiyarsa suma binsa su kai a baya sun isa office tare sun shiga ciki bayan sun zauna Dr Sam yaci gaba yana cewa. "Shin kun san cewa yaronku yana da rami a zuciya ko mu kira abin da rauni.?" Ahmad ya amsa shi da eh Dr Sam yaci gaba da magana, "to amma mai ya saka baku ba shi cikakkiyar kulawa sosai yanda ya kamata.?" Ko a wannan lokacin Ahmad ne wanda ya amsa shi yayin da Ahlam ta rufe su da ido ta gagara furta komai. "Doctor muna kulawa da yaronmu sosai yanzun ma wani tsautsayi ne ya faru da shi, to zaka iya yarda damu yanzu fad'a mana mai yake faruwa da yaronmu.?" Ya jinjina masa ka sannan ya amsa shi. "Shikenan tinda ka fad'i haka amma dai ku sani yaronku sam bai kamata yayi duk wani abin da zai saukar masa da gajiya ba, sabo da yana buqatar hutu da kulawa sosai hakama yana da kyau yayi farin ciki sosai. Idan kuma irin hakan taci gaba da faruwa da shi to fa zai shiga mummunan yanayi, wanda zaku iya rasa yaronku gaba d'aya dan haka ya zame dole ku ba shi kulawa sosai." "Shikenan doctor zamu kula insha Allah muna godiya sosai." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data ji suna fad'a ta anbaci sunan doctor tana cewa. "Doctor ta ya yarona zai samu lafiya ya rabu da wannan cutar gaba d'aya.?" Magana take yayin da take kuka Dr Sam ya amsa ta, "shin ke kin rabu da wannan cutar ne? Karki fad'a min cewar ke bakya tare da wannan cutar ko dai an yi maki aiki ne.?" Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin abin da yake faruwa, yayin data gagara fahimtar komai daga cikin abin daya fad'a kafin ta furta komai Ahmad yayi mata rigagi. "Eh doctor ita ma har yanzu tana tare da cutar muna dai ta shirin yi mata aiki ne insha Allah." "Shikenan ka kula da dukansu yanzu zaku iya tafiya." Ya amsa da to ya tashi tare da tashin Ahlam sun fita suna fitowa tayi saurin cire hanun sa daga jikin ta tare da fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad wai mai kake fad'a masa ne a kai na wane aiki kake magana a kansa.?" Ha!!! Ya nisa sosai tare da jan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya, "Ahlam ni bani da wani za'bi ne dole sai na sanar da shi haka, idan kuma ba haka to fa shi zai zargemu dalilin da yasa na fad'i hakan kenan." Nan ya shiga sanar da ita gaskiyar komai a game da rashin lafiyar, "Ahlam." Tayi saurin dakatar da shi ta hanyar d'aga masa hanu tare da girgiza masa ka tana furta kalmar a'a. Ta juya tayi tafiyarta ta nufi d'akin da *Adyan* yake domin ganin yanayin jikin sa, hakama Ahmad binta yayi a baya sun isa d'akin ta shiga ciki yana k'oqarin shiga tayi saurin dakatar da shi. "A'a kai sam baka da damar da zaka ga d'ana, a yau ďin nan kai kayi matuqar cutar da ni da kuma yarona dan haka ya zama dole ka kar'bi hukunci daga gareni, hukuncin ka shi ne ba zaka ga d'ana ba to kawai ka tafi sabo da bana buqatar ka a nan to jeka man kawai ka tafi." Magana take cikin fishi sosai yayin da take kuka kuma kuka sosai. "A'a Ahlam ni ba zan tafi ba sabo da ina buqatar na kasance tare da yarona sabo da shi ma yana buqata na sosai a tare da shi. Ahlam ni na riga dana sanar da ke duka gaskiyar a yanzu da kuma dalilin da yasa ni na 'boye maki gaskiyar to mai yasa ba zaki yafemin ba? Ahlam ni kawai bana san na cutar da ke ta hanyar sanar dake rashin lafiyar sa sabo da na san cewar jin hakan zai yi matuqar cutar dake sosai, sannan kuma ni ina kulawa da yaronmu sosai Ahlam ni na yarda da cewa nayi maki laifi, sannan kuma na baki hak'uri idan ba zaki yafemin ba to ki hukunta ni amma bata hanyar nisanta ni da *Adyan* ba. Sabo da ni ba zan iya jure wannan ba Ahlam ni zan iya kama qafafun ki na baki hak'uri idan kina so, to dan Allah ka da ni dakatar da ni daga ganin yarona please." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba sai dai ku misalta. Shiru bata amsa ba sai ma k'oqarin rufe k'ofa da take ganin hakan ne yasa shi dukursawa qasa ya kai hanun sa zai kama qafafun ta, da sauri taja da baya tare da furta a'a tayi saurin rufe k'ofar yayin da take kuka ta nufi gurin, *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin bai farfad'o daga dogon suman da yayi ba. Ahmad kuwa yayi zaune a kan kujeran da take gefen ďakin yayin da k'unci da 'bacin rai yayi yawan gaske a tare da shi sosai, sai tinani yake iri daban-daban yana haka ya jiyo wayar sa na ruri ya ciro wayar daga aljihu ya duba mai kiran sa ganin sunan Umma yasa shi saurin d'aga kiran. "Umma na naji dad'i sosai da kika kira." Cike da firgici da rud'ani take magana, "Ahmad mai yake faruwa da kai ne shin komai qlau kuwa.?" "A'a Umma sabo da Ahlam tana matuqar yin fishi da ni kuma fishi sosai gaba d'aya tak'i saurara na, Umma ita ta hana ni kasancewa tare da yarona duk da cewar ni ina da buqata da hakan sosai. Umma hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da matuqar k'una Umma muna asibiti da *Adyan* ba shi da lafiya sosai, Umma ina san na runguma yarona a jiki na sannan na sunbacesa na kuma fad'a masa cewar ina qaunar sa, amma kuma Ahlam duk ta dakatar da ni daga yin hakan Umma hakan yana yi mun zafi sosai ban kuma san ya zanyi ba. To dan Allah ki fad'a min ya zanyi ta ya zansa Ahlam ta bud'e min k'ofa na shiga na ga yarona.?" Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, sai wasu zafafan hawaye yake zubar wa masu tsananin zafi da k'una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Cike da firgici da rud'ani take magana, "Ahmad mai yake faruwa da jikana? Yaron ba shi da lafiya sosai amma kuma duk da haka ku biyun kuna fad'a? Ahmad dan Allah ku dena wannan shirmen banzan ku kula da yaran sosai, jikana yana buqatar kulawar dukanku to ya kamata ku kula da shi sosai, sannan kuma kayi hak'uri da yanayin Ahlam to amma mai ya saka ita ta dakatar da kai daga ganin *Adyan.?"* "Umma ita tana fishi ne sabo da na 'boye mata gaskiyar cewa yaronmu ba shi da lafiya, bayan ta gano duka gaskiyar shi ne take fishi da ni kuma tana hukunta ni da rashin ďana. Umma hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai dan Allah ki fad'a min ya zanyi please.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "Ahmad dole Ahlam ta hukunta ka sabo da ba wani dalilin da zai sa ka 'boye mata gaskiyar to amma mai ya saka kai kayi hakan.?" "Umma ni kawai na damu da ita ne sosai sam bana san ta fuskanci k'unci sosai, Umma ni na damu sosai a kanta shi yasa na 'boye gaskiyar a gareta amma ita sam ta kasa fahimtar hakan ban kuma san ta yanda zansa ta fahimce ni ba." "Karka damu ďana komai zai yi daidai jikana zai samu lafiya insha Allah to kawai ka jure ka ji ko." Haka taci gaba da rarrashin sa tana ba shi magana, sun jima sosai a kallayi sannan daga bisani suka yi sallama. Bayan ta a jiye wayar Abba ya shiga tambayar mai yake faruwa ta sanar da shi komai ya girgiza ka yana cewa. "Shin su ba zasu iya kulawa da yaronsu ba sabo da sakacin su jikana yana kwance a asibiti su biyun sun cika shashanci zanyi magana da dukansu." Ta jinjina masa ka a lamar to zaune yake a kan kujera sai wani rawar sanyi yake, ya rufe idanuwan sa sai tinani yake iri daban-daban tsaye take a window sai wani kallonsa take kallo sosai, lokaci d'aya taji wani tsayin sa yana shigarta ta ko ina lungu da sak'o na jikin ta. Ta nufi gado ta d'auki zanin gado ta fita ta nufi gurin Ahmad, ta bud'e k'ofar ta fito ta isa inda yake tayi tsaye sai wani kallonsa take kallo sosai yayin da take jin yana birgeta sosai. Nan ta shiga rufe masa jikin sa da bargo sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take, wani irin kallo suke yiwa juna wanda suka gagara sanin mai suke nufi da shi. Sun jima sosai a haka sannan daga bisani ta kau da idanuwan ta daga garesa, ta tashi domin tafiya yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta. "Shin ke kina jin tsoron kar sanyin gurin nan ya cutar da ni? Ahlam amma kuma a nan kin yi matuqar cutar da ni sosai." Ya nuna zuciyar sa ya kuma ci gaba da magana, "Ahlam raunin yana da matuqar zafi sosai sannan kuma yana da matuqar zurfi sosai hakan yasa k'unar take da zafi sosai. Ahlam naro e ki dan Allah ki barni na tafi ga yarona, ina matuqar san na had'u da shi ina buqatar na rungumasa jikina sannan kuma na sunbacesa na kuma fad'a masa cewar ina qaunar. Ahlam dan Allah." Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar rufe masa baki tana girgiza masa ka a lamar a'a. Ta tashi tare da riqa hanun sa sun shiga ciki tare cike da d'auki ya nufi gurin *Adyan,* cike da d'auki yayi hugging d'in sa sai wani lalla'basa yake yayin da yake furta masa kalmar ina qaunarka sosai d'ana. Ita kuwa sai wani kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai, bayan ya sake sa daga rungumar da yayi masa ya gyara masa kwanciya sannan ya mai da kallonsa ga Ahlam. Wacce har zuwa wannan lokacin kallonsa take ya tashi ya nufi inda take cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita yake magana. "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi fad'a min wani abu har yanzu kina fishi dani.?" Har zuwa wannan lokacin kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai ba shi ma haka kallonta yake kuma kallo sosai. Sun jima sosai a haka ba kuma tare da sun furta wa juna komai ba jin shirun yayi yawa yasa yaci gaba da magana. "Shikenan ni ba zan tilassa ki a kan kiyi min magana ba, amma zanyi farin ciki sosai idan kika fad'a min cewar kin yafe min." Har zuwa wannan lokacin kallonsa kawai take ba kuma tare data amsa shi ba, jin tayi shiru na tsayin wani lokaci bata amsa shi ba yasa yayi tinanin cewar tana fishi da shi kuma fishi sosai. Wannan yasa ya juya zai fita har ya kai k'ofa ya juya ya koma gurin *Adyan.* Ya shafi fuskar sa zuwa kansa tare da furta Allah ya baka lafiya Amin, sannan ya juya ya fita Ahlam ta bisa da kallo har ya fice daga d'akin, ya fito yayi zaune a kan kujera ya ciro wayar sa ya kama aikin chart. Ita ma fitowa tayi ta same sa zaune yana aikin chart tayi zaune gefen sa sai wani kallonsa take kallo sosai yayin da take magana da zuciyarta. "Yaya Ahmad kana matuqar birge ni sosai amma kuma kai ga a lama bana gaban ka, sabo da wannan yarinyar da kake kulawa wacce kake kira da Hayatee. Lallai ya zame dole da nayi koma miye domin na tabbatar da cewar ka zama nawa na har abada, wannan shi ne abin daya kamata nayi kuma tabbas zanyi hakan insha Allah." Ganin yanda ya mai da hankalin sa gaba d'aya ya karkata a kan waya yayi uwa bai ganta ba yasa ta kai hanun ta domin amsar wayar, yayi saurin janye wayar tare da kai kallonsa gareta kafin ya furta komai tayi masa rigagi................ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/1, 8:51 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 11* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 31/12/2021* *Typing................* "Meyasa ba zaka barni na gani ba.?" Ya girgiza kai yana wani gajeran murmushi, "a'a wannan sorrina ne shi yasa ba zaki gani ba." "Him fad'a min wani abu dawa kake chart.?" Yayi wani lallausan murmushi sannan ya amsa mata, "ina magana da Auntyn ki ne." Kallonsa kawai take yayin da ta gagara furta masa komai shi ma haka kallonta yake, sun samu shiru na jim kad'an sannan ya anbaci sunanta. "Ahlam dare yayi sosai sannan kuma gurin nan yana da sanyi sosai, to ina ga ya kamata ki shiga ciki domin ki kwanta sai da safe." Har zuwa wannan lokacin kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai ba, sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ta amsa mashi. "Kana buqatar na tafi domin kaci gaba da chart da wannan matar? Ba zan dakatar da kai ba amma dai ka daina kiran ta da Aunty na, sabo da ni ba zan ta'ba zama qanwarta ba amma k'ila na iya zama yayarta. Yanzu ka tashi mu shiga ciki sabo da ba zai yiyu ka kwana a nan ba, sabo da sanyin gurin zai iya cutar da kai da kuma lafiyar ka, to yaron mu yana buqatar mu sosai zamu iya tafiya yanzu sannan kuma zaka dakatar da wannan chart d'in mu tafi." "Amma." Tayi saurin dakatar da shi ta hanyar rufe masa baki tare da girgiza masa ka a lamar a'a, da sauri ya wani zaro ido yana kallonta ita ma haka kallonsa take ya janye hanun ta da yake kan bakinsa tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam karki wani damu ni zan kula da kai na sosai sannan kuma zan kasance lafiya insha Allah to zaki iya yarda da ni." Sam bata amsa shi ba sai ma tashi da tayi tare da riqa hanun sa ya tashi sun shiga ciki, tayi masa nuni da wata kujera sannan taci gaba da magana. "zaka iya kwanciya a kan wannan kujeran ni kuma zan kwanta tare da yarona to sai da safe." Ya jinjina mata ka yana wani gajeran murmushi ita kuwa kallonsa kawai take daga bisani kuma ta nufi gado domin ta kwanta. Ya bita da kallo har ta kwanta shi ma kwantawa yayi tare da d'aukar wayar sa, yana dannawa daga bisani kuma ya d'ora wayar a kan kunnan sa, bayan wani lokaci ya fara magana cikin kyakkyawan yanayi yake magana yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa sosai. "Barka da dare rabin raina fatan ban tashe ki daga barci ba? Kiyi hak'uri muna cikin charting na sauka qanwata ce ta zomin da wani uzuri, to ina fatan ba kiyi fishi ba sannan kuma zaki yafemin dan Allah." Cike da unci bak'in ciki tare da tarin damuwa Ahlam ta tashi ta nufi inda yake, sai wani sauri take har kamar zata fad'i tana k'oqarin amsar wayar yayi saurin janye wayar daga kunnan sa, tare da tashi zaune ya anbaci sunan ta tayi saurin dakatar da shi cike da 'bacin rai take magana wanda shi ma ya fahimci hakan. "Yaya Ahmad kamar dai na fad'a maka cewar ka kashe wayar ka to amma mai yasa baka yi hakan ba? Ka sani ni sam ba zan d'aukar maka hakan ba to ya kamata ka san da wannan yanzu ka kashe wayar sannan ka kwanta." ta juya zata tafi yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da zaunar da ita kusa da shi kusa sosai, sai wani kallonta yake kallo sosai ita ma abin da take yi kenan sun jima a haka sannan ya fara magana. "Ahlam mai ya saka kike yi kamar kina bani umurni bayan kuma ni ina gaba dake? Sannan kuma mai ya saka kika damu da abin da nake shin ke kina da matsala ne da hakan? Kin hana ni chart nayi shiru yanzu kuma kina k'oqarin dakatar da ni kar nayi waya da ita. Mai yasa fad'a min mai ya saka kike yin duka wannan fad'a min kina da matsala da hakan ne.?" Sam bata iya furta masa komai ba sai kallonsa kawai take yayin da take jin soyayyar sa tana dad'a shigarta, a gefe ďaya kuma tana jin kamar ta rasa shi lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Ta yunk'ura domin ta tashi yayi saurin dakatar da ita, "Ahlam shin da akwai matsala ne dan Allah ki sanar da ni? Mai yake faruwa da ke mai ya saka kike kuka ki sanar da ni gaskiyar please.?" "Ta girgiza ka tare da sakin wani saban kuka da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata ka, ya janyo ta jikinsa ya shiga rarrashin ta cikin sannu a hankali yake furta mata kalmar. "Ya isa haka karki tashi *Adyan* barci ya kamata ya huta, to yanzu fad'a min mai yake faruwa dake.?" Shiru bata yi magana ba domin kuwa tin lokacin da yayi hugging d'in ta, ta manta da duk wata damuwar ta sai wani farin ciki yake ta shigarta sosai, sai wata soyayyar sa take ji tana qara shigarta shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai. "Ahlam mai ya saka ba zaki sanar da ni gaskiyar ba hak'iqa kina 'boye min wani abu, ya kamata ki sanar da ni gaskiyar domin na san da abin da zan iya taimaka maki, ina fatan karki jima sosai a cikin wannan yanayin sabo da hakan zai yi matuqar cutar dake sosai." Ya shiga anbatar sunan ta amma bata amsa ba ganin idanuwanta a rufe yasa yayi tinanin cewar barci take. Nan yaci gaba da danna waya daga bisani kuma barci ya d'auke sa bama tare da sanin sa ba, kukan da *Adyan* yake ne ya tashe su daga barci lokaci d'aya suka bud'e idanuwan su, cikin hanzari sun tashi dukansu sun nufi gurin yaronsu Ahmad ne wanda ya d'auke sa ya shiga rarrashin sa. Hakama Ahlam abin da take yi kenan Ahmad yace da Ahlam ta kira doctor ta amsa da to ta juya ta fita, ba jimawa ta dawo tare da likita ya duba shi ya kuma sanar dasu cewar yana samun sauki sannan ya juya ya fita. Bayan tafiyar doctor Ahmad ya kai kallonsa ga Ahlam tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam ki samu kiyi salla sai ki rungumasa nima nayi salla ki tafi yanzu lokaci ya tafi sosai." Ta amsa da to ta tashi ta nufi toilet ba jimawa ta fito ta fara salla, bayan ta idar tayi azkar sannan ta tashi ta nufi gurin su ta fara gaisawa da Ahmad sannan ta kar'bi *Adyan* daga hanun sa. shi kuma ya tashi ya shiga toilet bayan wani lokaci ya fito ya fara salla, bayan ya qarasa ya tashi ya fita bai wani jima sosai ba ya dawo tare da kayan abinci. Ahlam ta had'a musu break past haka dai *Adyan* yaci gaba da samun kulawar doctor dama iyayen sa, ya samu tsayin mako d'aya asibiti sannan ya samu sallama zuwa gida. Da dare suna zaune a parlour Ahlam ta sauke kallonta ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. "Masoyi dare yayi sosai to ya kamata mu tafi ka kwanta ka ji ko." Kafin ya amsa ta Ahmad yayi mata rigagi, "Ahlam karki manta cewar yau *Adyan* tare da ni zai kwana to ki dena wannan zak'ewar kinji ko." "A'a Yaya Ahmad sai dai kawai na baka hak'uri sabo da dani zai kwanta." "Ba zai yu ba Ahlam kawai dai ki amince da gaskiyar kinji ko." Nan kuwa suka shiga gardama *Adyan* sai kallonsu yake sai daga bisani ya fara magana. "Appa Ammie dan Allah ko zaku dena duka wannan? Ni zan kwanta da dukanmu ukun zamu yi barci a tare wannan ne k'arshe dan Allah." Dukansu wani irin kallo suke yi masa kallo sosai, Ahlam ce take amsa shi yayin da Ahmad ya rufe su da ido. "Shikenan masoyi zamu yi hakan dukanmu zamu yi barci a tare, yanzu mu zamu tafi Appa zai zo daga baya to mu tafi." "A'a dukanmu zamu tafi a tare Appa mu tafi ina san zanyi barci." Ya jinjina masa ka tare da furta masa to sun tashi dukansu sun nufi d'akin Ahlam, suna haka Ahlam ta nufi toilet Ahmad kuma ya nufi gado da *Adyan* sun kwanta. Ahmad ya rungumasa jikin sa yana wani jijjigasa ba jimawa yayi barci, bayan wani lokaci Ahlam ta fito daga toilet wanda kuma wanka tayo, k'arar da yaji ne yasa shi kai kallonsa gareta tsaye take daga ita sai wani k'aramin towel, wanda tsayin sa iya cinya rabin k'irjin ta duk a waje sannu a hankali take tafiya tana wani motsa jiki har ta isa gaban madubi. Taja kujera ta zauna ta fara shirin ta, sam ya kasa jure ganin ta a hakan wanda wannan dalilin ne yasa ya tashi zai fita. Sannu a hankali yake janye *Adyan* daga jikinsa ya shinfid'esa sannan ya tashi ya fita daga d'akin, ta bisa da kallo har ya fice ba kuma tare data furta masa komai ba, taci gaba da shirin ta inda ta shirya cikin wata kyakkyawar shiga ta wata ar riga, wadda tsayin ta bata kai guiwa ba iya cinya rigar shara-shara take tayi kwance jikin ta tare da bai yana surar ta. Ta feshe jikin ta da tirare ya had'u da humra sun had'u sun ba da wani daddad'an k'amshi mai dad'in shaqa, ta fito ta nufi bedroom d'in Ahmad kwance yake idanuwansa a rufe ga a lama tinani yake, ya jima a haka sannan daga bisani ya koma kiran layin Hayatee yana haka sai ga Ahlam ta shigo har zuwa wannan lokacin idanuwansa a rufe suke, wanda shi yasa bai iya ganin ta ba tayi tsaye sai kallonsa take cike da unci da bak'in ciki tare da tarin damuwa ta nufi inda yake. Takun tafiyar ta yasa shi bud'e idanuwansa lokaci d'aya yayi tozali da kyakkyawar faskar ta, wani irin kallo yake yi mata kallo sosai har ta isa inda yake ta kai hanun ta, ta fizge wayar sa wanda bama ya san tayi ba tana k'oqarin fasa wayar ta hanyar yin jifa da ita yayi saurin dakatar da ita. "A'a dan Allah karki yi naro e karki fasamin waya please ki dawomin da waya ta dan Allah." Ya shiga rarrashin ta yana lalla'bata har ya samu ya iya ba shi wayar sa ya kar'ba tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam qlau kike kuwa mai ya saka kike cikin fishi sosai haka shin wani abu na faru dake ne.?" Magana yake yayin da ya rufe ta da ido yana kallonta kallo sosai, yayin da yake jin tana birgesa matuqar birgewa sosai. "Kai ne nan damuwa ta kuma kai ne wanda yake saka ni fishi sosai, haka kawai ka fito daga ďakin kazo nan nayi shiru ne sabo da nayi tinanin ko kana san ka watsa ruwa ne, a she sam ba haka bane kawai ka zonan domin kayi waya da wannan 'yar iskar yarinyar, ya kamata ka dawo da hankalin ka jikin ka domin kuwa ni sam ba zan ta'ba baka damar da zaka kasance tare da ita ba na har abada. Ina fatan Allah ya d'auke ranta a daran yau kafin safe ta yanda ku biyun zaku rabu na har abada." Yayi saurin dakatar da ita ta hanyar kifa mata wani wawan mari wanda sai da ta kife a qasa, yasa hanun sa ya riqo ta ta tashi cike da fishin zuciya yake magana. "Idan kika qara fad'ar haka ni da hannayena zan kashe ki ita rayuwa ta ce to dan haka ya kamata ta rayu, ina matuqar masifar qaunar ta sosai wannan yasa nake kiran ta da rayuwata wato Hayatee na. Sabo da ita ne yasa har yanzu nake raye to dan haka yana da kyau ki girmamata sannan kuma kiso ta kinji ko." Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin sa sosai yayin da take kuka kuma a haka take magana. "Kai mugu ne mai yasa kake cutar da ni sosai har haka to kawai ma ka kashe ni, sabo da a yanzu rayuwata bata da wani sauran anfani kuma kai ne nan wanda ya tarwatsa ni da kanka. To garama kai ka kashe ni da kanka ko kuma ni na aikata hakan da kai na kuma ba zan ta'ba barin ka dakatar da ni ba, kawai dai zan sanar da kai wani abu kafin na mutu abin shi ne ka kulamin da yarona sosai, sannan kuma ka fad'a masa cewar Ammie tana matuqar masifar qaunar sa sosai." Kuka yaci k'arfin ta wanda wannan dalilin ne yasa ta yin shiru, ta kama aikin kuka ta juya domin tafiya da sauri ya ri e hanun ta tare da riqa kafad'ar ta ya juyo ta, sai wani kallonta yake kallo sosai ita ma abin da take yi kenan yayin da take kuka kuma kuka sosai. "Ahlam shin da akwai matsala ne fad'a min wani abu shin da akwai wani abin da kike 'boye min a game da ke? Ahlam ni kawai na damu ne a kan Hayatee na sabo da abin da kika fad'ar mata, Ahlam gaskiyar ita ce ni ina matuqar qaunar Hayatee na hakama ina buqatar kasancewa a tare da ita sosai, amma kuma ke kina k'oqarin ganin kin nisan ta ni da ita Ahlam ni sam ba zan iya jure wannan ba, sabo da hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai Ahlam dan Allah." A'a ta fad'a da k'arfi tana d'aga murya cike da unci ta daki bango tare da watse kayan dake kan madubi, yayin da take wani irin kuka abar tausayi sosai kuma a hakan take magana. "Kai mugu ne sam baka damu da kowa ba hakama ba ruwan ka da damuwar kowa sai taka, ka damu sosai a kan karka rasa wannan banzar amma kuma ka amince da ni na rasa ka na har abada." "Yaya Ahmad ni qanwarka ce kuma matarka uwar yaronka amma duk da kasancewa haka kai baka ta'ba sona ba ko da kuwa na rana d'aya ne, nayi duk abin da zan iya domin kai kaso ni amma ka kasa tilassawa zuciyarka taso ni. Yaya Ahmad gaskiyar ita ce ni d'in nan ina matuqar masifar qaunarka sosai fiye ma da yanda nake sanka, amma abin takaicin shi ne kai da kuma zuciyarka wata daban kuke qauna hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai, Yaya Ahmad ni ba zan tilassa maka a kan kaso ni ba amma ka sani idan har kai kayi nasaran yin aure da wata daban to wallahi tallahi ka rasa ni na har abada ni da kuma d'ana. Kuma ni ba zan ta'ba canja hakan ba to kana da lokacin da zaka yi tinani domin yanke hukuncin daya dace." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i wanda kuma har zuwa wannan lokacin kuka take kuma kuka sosai, shi kuwa sai wani irin kallo yake yi mata kallo sosai mai cike da jin mamakin abin da take fad'a, cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana tamkar wani mara lafiya. "Ahlam wai da gaske ke kina so na sosai har haka? Gaskiya ni sam na kasa yarda da hakan amma tabbas tin da jimawa ni na san cewar kina matuqar buqatar wani abu daga gareni. A ko yaushe kina nuna san na kusance ki kamar dai yanda yake a yanzu kinyi wannan shigar ne sabo da kija hankali na, Ahlam ni wannan ne abin dana sani kuma wannan sam ba soyayya ba ce to ya kamata ki amince da gaskiyar, Ahlam gaskiyar ita ce ke d'in nan baki ta'ba sona ba bama ki san ta yanda zaki so ni ba na jima da sanin hakan na kuma amince da gaskiyar, to dan haka ka da ki dakatar da burina ni ina san Hayatee na sosai kuma da ita kawai ne zan rayu ko da mai zai faru wannan alkawari ne kuma ba zan canja hakan ba. Ahlam to kawai ki amince da gaskiyar abin da nima nake yi kenan." "A'a Yaya Ahmad wannan ba gaskiya bane ni ba kamar yanda kake tinani ba ce, eh gaskiyar ka fad'a ni d'in nan ina tare da buqatar ka sosai amma kuma hakan sam bai ya nufin cewar bana sanka. Yaya Ahmad da a ce buqatar ka kawai nake ji to da jimawa na baiwa kai na magani zansa kayi hakan ko da ba a cikin haiyacinka ba, ni sam ban damu ba idan har zan samu abin da nake so, amma kuma dai banyi hakan ba sabo da ni ina san ka kusance ni cikin qauna da soyayya, ta yanda zan gansu da abin da nake buqata daga gareka. Ba zanga laifin ka ba sabo da har yanzu kai baka san gaskiyar ba, amma kuma a yau ďin nan kuma a yanzu ni Ahlam Al'ameen zan sanar da kai duka gaskiyar. Daga nan kuma zan nuna maka irin abin da zan iya aikata wa kai na a lokacin da ni na rasa ka to ka kalla da kyau domin ka gani................. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/3, 11:00 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 12* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 01/01/2022* *Time 09:27pm* *Typing............* Yana kai k'arshen maganar sa ta juya tayi tafiyarta, shi kuwa ya bita da kallo yayin da mamakin ta dama abin da take fad'a yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Cikin hanzari ya bita a baya yana fad'ar sunan ta amma bata amsa shi, yana k'oqarin shiga ciki ita kuma tana har suka yi karo da juna kad'an ta fad'i yayi saurin riqo ta, lokaci d'aya suka saki a jiyar zuciya ya d'ago ta lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna. Wani irin kallo suke yiwa juna wanda ban san ta yanda zan sanar daku shi ba, sun jima sosai a haka sannan daga bisani ta fita daga jikin sa, ta tafi ta zauna ba tare data furta masa komai ba ya bita da kallo har ta zauna. Cikin sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, cikin mutuwar jiki da sanyin murya ya anbaci sunan ta kafin ya furta komai tayi saurin dakatar da shi, ta hanyar d'aga masa hanu tare da girgiza masa ka a lamar a'a taci gaba da danna waya daga bisani ta fara magana. "Abbu kayi hak'uri dana kira layin ka yanzu, kawai dai ni naji ina san nayi magana da kai ne." "Na fahimce ki 'yata shin a kan Yayan ki ne.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "eh Abbu amma karka wani damu sabo da zan iya jure zafin duk da cewar yanayin yana cutar da ni sosai." "Ahlam wai har tsayin wane lokaci zaki d'auka kina 'boye gaskiyar? 'Yata zuwa yanzu ya kamata Ahmad ya san gaskiyar cewa kina qaunarsa sosai, Ahlam wannan fa ya jima na tabbata idan ya san gaskiyar to komai zai yi daidai. Ahlam ke kin fara san Ahmad ne tin a lokacin da baki da wayo, ke kin rayu ne gaba d'aya da soyayyar sa Ahlam to ya kamata ya san gaskiyar kawai ki sanar da shi kinji dan Allah." Tayi shiru na wani lokaci wanda kuma kuka take daga bisani kuma ta amsa shi. "Shikenan Abbu zanyi hakan na gode sosai sai da safe asuba ta gari ka gaida Ummi na." "Sai da safe 'yata Allah yayi maki albarka ki gaishe da Ahmad da jikana." Ta amsa da to da kuma haka suka yi sallama ta tashi domin tafiya, da sauri Ahmad yayi saurin tashi ya sha gaban ta tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam bai kamata ki tafi ba sabo da akwai buqatar mu biyun muyi magana yanzu dan Allah." "Kayi hak'uri dare yayi sosai sannan kuma yarona zai iya buqata na, to a yanzu kana da damar da zaka kasance tare da abar qaunar ka to kayi farin ciki sosai sai da safe." Ta juya gefe taci gaba da tafiya da sauri ya ri e hanun ta tare da janyo ta, ta fad'a jikin sa ya mata wata kyakkyawar runguma sosai sai wani kallon juna suke kallo sosai. "Ni ka sake ni ka barni na tafi." Ya girgiza mata ka tare da furta, "a'a ba zan sake ki ba sannan kuma ba zan barki ki tafi ba, sabo da akwai abin daya kamata ki sani mu tafi d'aki na yanzu." "Shin ka shirya gabatar da ni a gurin budurwa ka ne? To ni ban shirya amince wa hakan ba dan haka ka barni na tafi dan Allah." Magana take cike da unci da tarin damuwa sosai yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai ya shiga girgiza mata ka, "a'a ba abin da zanyi ba kenan ni ba zan ci gaba da cutar dake ta wannan hanyar ba, bayan da na gano a salin gaskiyar Ahlam amma mai ya saka ke baki ta'ba sanar da ni gaskiyar ba.?" Shiru bata yi magana ba ya janyo ta sun tafi sun zauna yaci gaba yana cewa. "Ahlam dan Allah ki amsa ni mai ya saka baki ta'ba sanar da ni gaskiyar ba.?" "Taya ni zan sanar da kai gaskiyar bayan kuma kai kayi zurfi sosai cikin tsana ta, a ko yaushe tsana kake nuna min baka ta'ba nuna min soyayya ba ko da na zama kujera ďaya ce, a duk lokacin da kai ka rungumi *Adyan* ko ka sunbacesa ji nake ina ma a ce nima zan samu hakan daga gareka. Amma kai sam babu tinanin hakan a tare da kai sabo da wannan sakaryar yarinyar da kake kulawa, yau ka d'ora hanun ka a kan fuskar sabo da ita sannan kuma ka tsaya a gaba na ka fad'a min cewar ba zaka ta'ba barin ta ba. Kai ka za'beta fiye da ni da kuma yaronmu dan haka ni ba zan saurari komai daga gareka ba, to kawai ka sake ni ina san zan tafi na kwanta yarona zai buqace ni a tare da shi sosai." Magana take cikin fishi sosai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Wani irin kallo yake yi mata mai tare da so ya qara saka ta jikin sa tare dayi mata kyakkyawar runguma sosai. Lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin ya shiga share mata kwalla ya tashi tare da tashin ta sun nufi d'akin sa, "a'a ni ba zan shiga ciki ba to kawai ka sake ni dan Allah ka barni please." Tayi tsaye tak'i shiga ciki ya girgiza ka tare da jinjina sa lokaci d'aya ya d'auke ta ya shiga da ita ciki, ya fara zaunar da ita a kan gado sannan ya tafi ya rufe k'ofa ya dawo ciki, ya nufi durowa ya bud'e ya d'auko wata 'yar qaramar jaka ya nufi gurin ta ya zauna tare da kai kallonsa gareta, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take sun jima a haka sosai. Sannan daga bisani ya mai da kallonsa ga jakar ita ma haka dan ganin mai zai yi, ya bud'e jakar tare da ciro abin da yake cikin ta gaba d'aya ya mai da kallonsa gareta tare da fad'ar sunan ta. "Zaki iya duba wa dan Allah ki duba please." Ta kai hanun ta tana duba photon da suke gurin ta d'auki wata takarda tana karantawa. "Hayatee na soyayyar ki rayuwata ce ba zan rayu ba sai dake, wanda wannan dalilin ne yasa nake kiran da rayuwata. Ina fatan zuwan lokacin da zaki fara sona duk da cewar hakan yana da matuqar wahala sosai, sabo da kinyi matuqar tsana ta a cikin ranki dama zuciyarki gaba d'aya. Tina hakan kawai yana matuqar cutar da ni sosai sabo da ni dake kawai nake fatan na rayu rayuwa kuma ta har abada." Haka taci gaba da karanta takardun dake gurin tare da kallon photon dake gurin, daga bisani kuma ta mai da kallonta garesa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar shi ma kallonta yake kuma kallo sosai. Cikin mutuwar jiki da sanyin murya take furta masa kalmar, "Shin wannan ita ce Hayateen ka.?" Ya jinjina mata ka tare da furta mata eh, "Yaya Ahmad wai gaskiyar kake fad'a min kuwa.?" "Eh qanwata ke ce nan Hayatee na rayuwata kenan, Ahlam ina matuqar masifar qaunarki fiye ma yanda nake sanki ina qaunarki sosai. A kullum a ko yaushe tinanin samun ki nake yanda zaki zamo tawa ta har abada, amma bani da wani za'bi dole sai na 'boye gaskiyar a gareki, sabo da ni da zuciyata mun yarda da cewa kina tare da tsana ta sosai shi yasa ni na 'boye gaskiyar a gareki. Bama iya ke kawai ba har da ahalina Umma na ce kawai ta san da gaskiyar, Ahlam ni na kasa yarda a ce muna matuqar qaunar junanmu amma kuma a zahiri muna nuna wa juna tsana. Munyi matuqar cutar da juna ta irin wannan mummunan zunubin amma Alhamdulallah yanzu komai yayi daidai insha Allah qanwata ki yafemin a kan komai kinji dan Allah." Magana yake yayin da yake ri e da hanayenta yana wasa da faratanta, ita kuwa sai wani kallonsa take kallo mai tare da so yayin da farin ciki yake ta shigarta ta ko ina jikinta, ta cire hanunta daga nasa ta kai hanun ta a kan fuskar sa ta shafi fuskarsa tare da d'ago fuskarsa wadda ta kasance a sunkuye. Lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna sai wani kallon juna suke kallo sosai, sun jima sosai a haka sannan daga bisani ta fara magana. "Ba buqatar ka fad'i haka kai baka yi komai to sam ba buqatar ka bada hak'uri, Yaya Ahmad abin farin cikin shi ne har yanzu mu biyun muna tare daga k'arshe kuma mun fahimci juna. To wannan kawai ya isa kawai muyi farin ciki ina sanka sosai soyayyar ka ta isa ta biya duk wani kuskuran daka aikata a gareni, to sam ba buqatar ka damu sosai a kan hakan sabo da soyayyar ka ta biya komai hakan ya isa to kawai muyi farin ciki." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa ga wanda ya gani, hakan yasa ya rufe ta da ido yana kallonta yayin da yake jin tana birgeta sosai. "Hayatee na hak'iqa nayi matuqar sa'a dani na same ki, kafin yanzu a kullum kuma a ko yaushe cikin fargaba nake sabo da ina ganin kamar wata rana zan iya rasa ki, hakan ke sawa na shiga k'unci mai girman gaske wanda har nake zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Hayatee wallahi ke kad'ai nake so kuma ke kad'ai zanso har k'arshen rayuwata insha Allah wannan alkawari ne to zaki iya yarda da ni." "Eh na yarda da kai amma kuma da akwai abin da nake san ka sanar da ni." "Miye wannan.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "Yaya Ahmad da wa kake waya a ko yaushe sannan kuma kuke charting.?" Yayi murmushi sosai mai tare da 'yar dariya cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Ba kowa kawai sabo dake nake domin ki fahimci cewar bani kad'ai bane, Ahlam gaskiyar ita ce bana d'ora waya a kan kunne na sai a lokacin da kike tare da ni, haka kuma wani lokaci Game nake a waya amma sai na fad'a maki cewar ina chart da Hayatee na. Dalilin da yasa bana barin ki kar'bi waya na kenan sabo da zaki iya gano a salin gaskiyar, Hayatee na zaki iya yarda da ni sabo da ni gaskiyar nake sanar dake ina qaunarki sosai." Wani irin kyakkyawan murmushi take mai tare da dariya wanda ya hana mata fad'ar komai. shi ma abin da yake yi kenan sun jima a haka sannan daga bisani ya furta mata kalmar, "Ahlam shin zan iya yin hugging d'in ki dan Allah kinji please.?" Ta girgiza ka tare da furta a'a da sauri ya wani zaro ido yana kallonta kafin ya furta komai tayi masa rigagi. "Eh ba buqatar sai ka tambaya kawai ka ai watar nima zanyi farin ciki sosai da hakan." Cike da d'auki yayi hugging d'in ta lokaci d'aya kuma ya shiga sunbatarta ta ko ina fuska zuwa wuya, daga bisani kuma ya dira a kan bakinta cikin wani salo da dabara yake tsotsar le'benta da ma harshen ta. Daga zaune sun kai kwance wai abin nai ma ya samu matar direba ta aifi sitari, nan kuwa suka ci gaba da jin dad'i da juna wanda daga bisani komai yaci gaba da wakana a tsakanin su, wanda a wannan ranar kuma a wannan lokacin Ahmad yayi nasaran kusantarta hakan yayi matuqar yi musu dad'i sosai. Bayan wani lokaci suka tashi suka nufi toilet sunyi wanka sun fito sun shirya daga bisani suka tashi suka nufi gurin yaronsu, sun kwanta tare da rungumasa jikin su dukansu kuma tin daga wannan lokacin rayuwarsu ta canja suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki sosai. Bayan wani lokaci wani Yammaci zaune yake a parlour yana kallon labaru Ahlam ta fito, qarar rufe k'ofar da yaji ne yasa shi kai kallonsa gareta ya tashi ya nufi gurin ta yana fad'ar sunan ta. "Ahlam zonan ya kamata ki huta fatan kina lafiya.?" tayi murmushi sosai mai tare da dariya cikin kyakkyawan yanayi take magana. "Yaya Ahmad ina lafiya to ba buqatar ka damu sosai ka ji ko." "Duk da haka yanzu mu tafi ki zauna kar yarinya ta ta gaji da yawa." Murmushi kawai take ba tare data furta komai ba ya riqa ta sun tafi sun zauna, ya kai hanun sa ya shafi cikin ta tare da sunbata murmushi ya qaru ta anbaci sunan sa ya amsa taci gaba da magana. "Yaya Ahmad cikin wata biyar ne kawai to zan iya kulawa da kai na sosai, yanzu fad'a min mai zaka ci ya kamata na d'ora girki.?" "Qanwata ni zanci gaba da kulawa da dukanku na har abada sannan kuma na kareku iya rayuwata, to ba buqatar ki dakatar da ni sabo da alhaki ne da yake kai na kuma zan iya, yanzu kawai ki fad'i duk abin da kike so nima shi zanci nayi alkawari." "Shikenan zan tambayi *Adyan* naji mai yake so yanzu fad'a min yana ina.?" "Ya fad'a min cewar zai tafi filin wasa to yana can." Da sauri ta wani zaro ido tana kallonsa cikin rawar murya har tana sarkewa take magana. "Yaya Ahmad kuma ka barsa ya tafi amma mai yasa.?" "Ahlam ki kwantar da hankali kafin ya tafi sai da ya min alkawarin cewa shi ba zai yi wasan boll ba sannan kuma ba zai yi gudu ba, Ahlam ni na yarda da yaronmu sosai shi yasa ban dakatar da shi ba yau yana cikin kyakkyawan yanayi to sam bana san na dakatar da farin cikin sa. Ahlam ki yarda da ni zai kasance cikin k'oshin lafiya sosai kuma ba abin da zai faru da shi insha Allah to zaki iya yarda da ni please." Ta jinjina masa ka a lamar to tare da furta masa kalmar, "nima ina fatan haka amma duk da haka ni zan tafi na duba shi." "Shikenan zamu tafi tare." "A'a zan kula da kai na to kawai ka jira a nan yanzu zamu dawo insha Allah." "Shikenan to ki kula sosai dan Allah." "Eh zanyi insha Allah nayi alkawari." Ya jinjina mata ka tare da sunbatarta sannan ta tashi ta fita shi kuwa ya bita da kallo har ta fice, tin daga nesa ta hangi *Adyan* yana lilo ta nufi gurin sa tana wani lallausan murmushi mai had'e da dariya. Kad'an ta qarasa kai wa garesa ta hangi zomo yana zuwa inda yake ga shi kuma yana matuqar tsoransa sosai, wannan yasa ta qara sauri tana fad'ar sunansa amma bai jiyo ta ba, lokaci d'aya *Adyan* ya ga zomon ya tin kari inda yake nan kuwa ya saki ihu yana kururuwa da nai man taimako. Sai gudu yake yana kuka sosai zomon kuma sai binsa yake Ahlam ta shiga anbatar sunan sa wanda ita gudun take, hayaniyar su ce ta fito da Ahmad tana cikin gudu qafarta tayi tinti'be da wani dutse lokaci d'aya ta kife a qasa ta fad'i, yayin da bakinta yake anbatar sunan *Adyan* wanda da gangara ta qarasa kai wa inda yake tare da janyo sa jikin ta. Lokacin yayi daidai da fitowar Ahmad da sauri ya qarasa inda suke har yana gudu yayin da bakin sa yake fad'ar sunayen su, amma cikin rashin sa'a ko da ya qarasa inda suke dukansu sun suma cike da firgici ya d'auke su zuwa asibiti...... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/3, 10:25 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 13* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *Sister 'yar gata kwana biyu na dena jiyo ki, to ina fatan dai lafiya Allah yasa Amin ya hayyu ya kayyum.* *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 03/01/2022* *Time 12:07pm* *Typing.............* Sun isa asibiti cikin hanzari nurse suka shigar da su ciki, haka Ahmad ya dawo tamkar wani qaramin mahaukaci ko wanda ya zauce, to zamu iya cewa ya soma fita haiyacinsa sai aikin kai komo yake yayin da bakinsa yake anbatar kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un. Bayan wani lokaci nurse ya fito tare da ba shi wata takarda, "ka tafi ka kawo wannan." ya amsa da to ya juya ya fice da sauri har yana gudu bai d'auki wani lokaci ba ya dawo. Ya baiwa nurse ďin kayan da ya siyo ya kar'ba ya koma ciki, bayan wani tsayin lokaci sosai doctor suka fito cikin hanzari Ahmad ya isa garesu tare da tambayar su jikin ahalinsa. Dr Sam ne yake magana, "muna yin abin daya dace ne yaron yana samun sauki sosai, hakama Mummyn sa amma munyi rashin sa'a babyn da yake tare da ita bai rayu ba. Kayi hak'uri a kan hakan zata samu lafiya insha Allah to zaka iya yarda da ni please, hakama yanzu zaka iya shiga ciki domin ka duba dukansu.” Wani irin kallo yake yi masa mai tare da firgici yayin da ya gagara furta komai, banda kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un ba abin da yake fad'a. Jiki a san yaye ya juya ya nufi d'akin da suke hakama su Dr Sam suma tafiya suka yi a bakin aikin, sannu a hankali yake tura k'ofar har ta bud'e ya shiga ciki, cikin mutuwar jiki yake tafiya har ya isa inda suke kwance sai wani kallonsu yake kallo sosai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi. Kukan zuci yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, ya sauke kallonsa ga cikin Ahlam ya shafi cikin har zuwa mara cike da k'unci tare da tarin damuwa yake magana. "Yarinya ta bai kamata ki tafi ba sam bai kamata hakan ta faru dake ba, nayi ta burin had'uwa dake hakama Ammie da kuma Yayanki dukanmu muna sanki sosai, 'yata dukanmu muna matuqar qaunar tare da san burin kasancewa a tare dake to amma mai ya saka lokaci d'aya kika tafi? Kin dakatar da duka burinmu da muke da shi a kanki hakan yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai. Ahlam taya zaki iya jure wannan zafin yana da matuqar cutar sosai, *Adyan* kai ma hakan zai yi matuqar cutar da kai sosai sabo da irin yanda ka damu da zancan qanwarka, a kullum cikin tambayar yaushe zata zo gareka kake ga shi kuma ita ta tafi, duka wannan laifi na ne dana kasa kareku gaba d'aya ban kula daku yanda ya kamata ba, shi yasa duka wannan ya faru ina fatan zaku yafemin dan Allah ku gafarce ni please." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Misalin k'arfe 08:30pm *Adyan* ya farka daga suman da yayi ya kuma farka cikin firgici, kamar dai a yanda ya suma da sauri Ahmad ya isa inda yake ya rungumasa jikin sa yana rarrashin sa. *"Adyan* ya isa haka ina tare da kai ba abin da zai faru da ka ji ko." "Appa zomo ne yazo inda nake sai famin bina yake ni ina tsoron sa sosai." Magana yake yana kuka, "Ka dena tsoro sabo da Appa yana tare da kai to kukan ya isa haka yanzu fad'a min mai kake so.?" Ya girgiza tare da furta a'a ya qara shigewa jikin Ahmad yayi kwance, shi kuwa sai wani jijjigasa yake yana rarrashin sa bayan wani lokaci ya anbaci sunan Ahmad yana cewa. "Appa zanyi fitsari." Ya amsa shi da to ya tashi tare da d'aukan sa sun nufi toilet, bayan wani lokaci suka fito kai tsaye gurin Ahlam ya nufi da sauri har yana gudu yayin da yake fad'ar sunan ta. "Ammie ki tashi ina jin yunwa sosai zanci abinci Ammie ki tashi." Magana yake yana kuka Ahmad yana ta k'oqarin ganin ya dakatar da shi amma sai da yayi nasaran tashin ta. Cikin barci ta riqa jiyo sautin kukan sa nan kuwa abin daya faru ya riga dawo mata, lokaci d'aya ta bud'e idanuwan ta yayin da bakinta yake anbatar sunan yaronta wato *Adyan,* ya amsa ta tare da saban ta kukan sa ya fita daga jikin Ahmad ya nufi gunta, da sauri har yana gudu yayin da bakin sa yake fad'ar sunan ta ita ma haka sunansa take fad'a, yana isa inda take ta wani rungumasa jikin ta tana shafar kansa zuwa bayan tare da sunbatarsa fuska zuwa wuya dama jikin sa gaba d'aya. "Ina qaunarka yarona ina fatan ba abin daya faru da kai fad'a min qlau kake mai ya saka kake kuka.?" "Ammie ni ina jin tsoron zomo sosai sannan kuma ina jin yunwa sosai." "Ka dena kuka yarona ni zansa a d'auke zomon daga gidan, zancan abinci kuma yanzu ka fad'i wa Appa duk abin da kake so zai tafi ya kawo ma ka ji ko." "Ammie ni zanci abinci tare da qanwata to ki fad'a mata tazo muci abinci, ina san na ganta sosai sabo da ina qaunar ta sosai." *"Adyan* qanwarka ma tana qaunarka sosai sannan kuma zaku abinci a tare amma ba yanzu ba, sabo da a yanzu bata nan amma tana kusa damu to yanzu fad'a min mai kake san kaci.?" "Ammie ni zansha madara kawai." "Shikenan masoyi yanzu Appa zai tafi ya kawo ka ji ko." Ya d'aga mata ka a lamar to ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana murmushi, ta mai da kallonta ga fuskar Ahmad wanda banda kallonsu ba abin da yake. Lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna tayi masa murmushi sosai shi kuwa kallonta kawai yake, ba kuma tare daya furta mata komai ba sun samu shiru na jim kad'an sannan ya fara magana. "Ahlam to ya jikin naki fatan kina samun sauki sosai.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh taci gaba da magana. "Eh Yaya Ahmad ina samun sauki sosai to sam ba buqatar ka damu sosai ka ji ko, yanzu yaronmu yana jin yunwa to ka tafi ka kawo masa madara ya sha tin kafin yunwar ta cutar da shi sosai." "Eh zanyi hakan to ke kuma fa mai zaki ci.?" "nima zansha madara kamar yarona." "Shikenan ku jira kad'an yanzu zan dawo insha Allah." Ta jinjina masa ka tana murmushi shi ma haka wani gajeran murmushi yake. Ya juya ya fita ya d'an jima sannan ya dawo ya basu abin da suka buqata daga garesa wanda shi ma madarar ya sha, bayan sun qarasa ba da jimawa *Adyan* yayi barci Ahmad ya d'auke sa ya tafi ya shinfid'e sa, ya dawo gurin Ahlam yayi zaune daga gefen ta sai wani kallonta yake kallo sosai. "Yaya Ahmad shin qlau kike kuwa sam baka cikin kyakkyawan yanayi fad'a min mai yake faruwa kuma gaskiyar zaka fad'a dan Allah.?" Kallonta kawai yake daga bisani ya kai hanayensa ga nata ya d'an matse kad'an ta yanda ba zata ji zafi ba, ya qara da sunbatar hanayenta duka biyun cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake furta mata kalmar ki yafemin. "Yaya Ahmad wai a kan me kake magana mai yasa kake nai man yafiya a gareni.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta "Ahlam 'yarmu ta mutu kuma wannan duka laifi na ne, ni sam na kasa baku kulawa yanda ya kamata sannan kuma na kasa kareku, sabo da kuskure na d'aya tak ga shi mun rasa 'yarmu dan Allah ki yafemin." Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin sa sosai cike da damuwa take magana. "Yaya Ahmad a zahirin gaskiya hakan yana da zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una, na damu sosai musamman sabo da *Adyan* shi yana da buri sosai a kan qanwarsa. Ko yaushe cikin zancan ta yake shi yayi matuqar damu sosai a kanta sam bana jin cewar zai iya jure wannan, Yaya Ahmad idan *Adyan* ya san da wannan to hakan zai yi matuqar cutar da shi sosai, ni kuma ba zan iya jure ganin yarona a cikin mummunan yanayi ba ban kuma san ya zanyi ba." "Ahlam shi yasa sam bai kamata a ce shi ya san a salin gaskiyar ba ba zai ta'ba sanin wannan ba. Ni zan kula da komai to fatan zaki yafemin a kan kuskure na dan Allah.?" "Yaya Ahmad wannan ba laifin ka bane to ka dena cutar da kanka haka dan Allah." Magana take yayin da take share masa kwalla lokaci d'aya kuma suka yi hugging juna. Sun jima sosai suna jimamin rashin yarinyar su sannan daga bisani suka yi barci bayan kwana biyu, Dr Sam yake sanar da Ahmad cewa Ahlam ta samu matsala wacce ba zai yu ta iya aihuwa ba. A zahirin gaskiya hankalin Ahmad yayi matuqar tashi sosai da jin wannan mummunan labarin, amma kuma duk yanda ya kai mak'ura to ba zai iya canja kaddarar ta ba, wanda wannan dalilin ne yasa ya sanya wa zuciyar sa salama ya d'auki dangana. Sai dai kuma sam ya gagara iya sanar da Ahlam abin da yake faruwa da ita ya 'boye mata gaskiyar, sabo da sam ba zai iya jure ganin irin k'uncin da zata shiga ba wanda wannan dalilin ne yasa ya 'boye mata gaskiyar. Ahlam ta samu tsayin mako d'aya asibiti sannan ta samu sallama zuwa gida hakama *Adyan* ya samu lafiya sosai, haka suka ci gaba da zama cikin kyakkyawan yanayi ba tare da Ahmad ya sanar da ita komai a game da ita ba, wani yammaci zaune take tana yiwa yaronta karatu wayar ta ta d'auki ruri *Adyan* ne wanda ya tafi ya d'auko mata wayar ya bata, ta kar'ba tana murmushi ta sunbacesa tare da furta masa kalmar Allah yayi albarka ya amsa da Amin yana dariya ita kuwa murmushi take, ganin sunan Ahmad a kan wayar yasa murmushin ta ya qaru ta d'aga kiran tare da fad'ar sunansa. "Yaya Ahmad yau kayi dogon zango ka tafi ka barmu da kewarka sosai fad'a min kana ina.?" "Kina magana da Dr Sam ne ba Ahmad ba, mujin ki ya samu hatsari yana asibiti." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya fad'a take magana. "Dr Sam to ya jikin nasa fatan yana samun sauki sosai.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "ni ba zan iya sanar dake komai a game da shi ba a yanzu kiyi hak'uri please." "Shikenan gani nan tafe yanzu." Da kuma haka suka yi sallama ta tashi ta shiga ciki ba jimawa ta fito tare da tashin *Adyan* sun fita zuwa asibiti, sun isa asibiti kai tsaye office d'in Dr Sam ta nufa sai dai tayi rashin sa'a bai ya ciki ta shiga tambayar sa an fad'a mata cewar yana aiki, bayan wani lokaci ta samu had'uwa da shi cikin hanzari tare da nuna kulawa take tambayar sa jikin mujin ta. "Doctor ya jikin Yaya Ahmad ka fad'a min mai yake damunsa please.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "Madam gaskiyar ita ce mujin ki bai ya cikin kyakkyawan yanayi yanzu haka da akwai buqatar a yi masa aiki cikin gaugawa sosai, to muna buqatar da a cike mana takarda sannan kuma a yi duk wani abin daya dace." "Doctor ni zanyi mu tafi to amma ka sani ya zama dole Mujina ya samu lafiya, lallai ina matuqar buqatar Mujina a tare da ni hakama yaronmu yana buqatar mahaifin sa a tare da shi sosai. To yanzu ina san ka kalli cikin ido na sannan kayi man alkawarin cewar Mujina zai samu lafiya." Magana take yayin da take kuka hakama *Adyan* kuka yake ganin tana kuka, Dr Sam ya jinjina mata ka a lamar eh ta fara kiran layin Abbu ta sanar da shi abin da yake faruwa sannan suka tafi, tayi duk wani abin daya buqata daga gareta bayan wani lokaci a ka shiga da shi d'akin tiyata. Lokaci zuwa lokaci su Abba suke kiran ta suna tambayar ta abin da yake faruwa, haka-haka dai har zuwa lokacin da a ka fito da shi daga d'akin tiyata Dr Sam ya sanar da ita cewar yana samun sauki. Tayi matuqar yin farin ciki da hakan sosai bayan kwana biyu kwance yake yana barci, Dr Sam ya shigo domin ya duba jikin sa bayan ya qarasa ya sauke kallonsa ga Ahlam yana cewa. "Mrs Ahmad ga a lama ke da kuma mujin ki irin kaddaran ku d'aya, hakan yayi kyau sosai sabo da a yanzu ba wani wanda zai cutar da ďaya a cikin ku. Mrs Ahmad gaskiyar ita ce mujin ki ba zai iya aihuwa ba kamar dai ke, abin farin cikin shi ne kuna da wani ďa hakan yayi kyau sosai ina muku fatan alkhairi kyakkyawar rayuwa sai an jima." Ya tashi ya fita ya bar Ahlam cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau yayin da take kuka kuma kuka sosai. Cikin barci ya rika jiyo sautin kukan ta sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e cike da firgici yake yi mata magana. "Ahlam mai yake faruwa dake mai ya saka kike kuka fad'a min wani abu ina *Adyan* karki fad'a min cewar wani abu ya faru da shi.?" Ta sanar da shi cewar *Adyan* yana school ta kuma qara da sanar da shi abin da Dr Sam ya sanar da ita a game dasu. Ya nisa tare da jan numfashi nan ya shiga rarrashin ta yana bata magana cikin qauna da soyayya har ta iya fahimtar sa, sam basu da wani za'bi a game da kaddaran su wannan yasa suka amince da gaskiyar tare da d'ora duka kulawar su a kan *Adyan.* Bayan mako d'aya su Umma suka shigo musamman sabo da su duba jikin Ahmad hakan yayi matuqar yiwa su Ahlam dad'i sosai, Ahmad yaci da samun kulawar doctor har zuwa lokacin da jikin sa ya warware, ya samu tsayin mako biyar asibiti sannan ya samu sallama zuwa gida hakama har zuwa wannan lokacin su Ummi suna nan. Sun samu wata biyu a nan tare dasu sannan suka tafi wanda zuwa wannan lokacin Ahmad ya samu lafiya sosai bayan wasu shekaru............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/6, 11:50 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 14* *Sister 'yar gata ya k'arin hak'uri Allah ya gafarta mata ya mata rahma, Allah ya yafe mata Ubangiji ya bata gidan al'janna Amin Allah ya jikan iyayenmu baki ďaya Amin ya hayyu ya kayyum.* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Tuesday 04/01/2022* *Time 01:25pm* *Typing..............* Zuwa wannan lokacin *Adyan* yana da shekaru takwas, hakama zuwa wannan lokacin su Ahlam sun kammala karatu inda suke matsayin doctor, har sun fara aiki wanda hakan ne ya hana su komawa gida Nigeria. Bayan wani lokaci *Adyan* ya samu hutun makaranta hakama su Ahmad suna hutun k'arshen shekara, ganin hakan ne yasa Ahmad ya had'a musu visa domin kai wasu Abba ziyara. Da fari Ahlam sam bata yarda da hakan ba sai daga bisani sannan ta aminta da hakan, sunyi shirin su tsab na tafiya bayan mako d'aya jirginsu ya tashi zuwa qasar Nigerian. *Nigerian.* Tsaye yake a gefen hanya banda kuka ba abin da yake yana haka sai ga Prof, da sauri ya fito mota ya isa inda yake yana fad'ar sunan sa amma bai amsa ba. ya riqo hanun sa sun shiga mota ya shiga tambayar sa mai yake faruwa da shi cikin muryar kuka yake magana. "Dady gobe da akwai taron Mother day ina kuka ne sabo da ni bani da Mama, ita Mama na ta tafi ta barni sam bai kamata a ce ta mutu a wannan lokacin ba sabo da ina matuqar buqatar ta sosai. Amma ita sam bata wani damu da ni ba hakan yana saka ni k'unci sosai, Dady mai yasa Mama ta mutu mai yasa ta tafi ta barni? Dan Allah kace ta dawo garemu please." Magana yake yayin da yake kuka kuma kuka sosai cike da jin tausayin tare da qaunar sa yake magana. "Ka dena kuka *Adeel* sabo da Dady yana tare da kai, sannan kuma yana nan domin ka *Adeel* ni zan kasance da kai iya rayuwa ta, ba zan ta'ba barin ka ba to kayi farin ciki sannan kuma ka dena k'unci, sabo da hakan barazana ne ga lafiyar ka ni kuma sam ba zan jure hakan ba. Ina sanka yarona ina matuqar qaunar ka sosai zo nan." Ya janyo sa jikin sa yana rarrashin sa yana wani lalla'basa da haka har suka isa gida, Prof ya fito ya zaga ya bud'e masa k'ofa tare da riqo hanun sa ya fito sun shiga ciki, sun fara zama a parlour Prof ya tafi ya kawo masa ruwa da juice ya girgiza masa ka a lamar a'a ya tashi yayi tafiyarsa. Prof ya tashi cikin hanzari ya bisa a baya yana fad'ar sunan sa amma bai amsa ba, ya same sa kwance a kan gado yana ta aikin kuka yayin da yake ta anbatar sunan Mama. Cike da jin tausayin sa ya isa inda yake ya zauna tare da d'ora kansa a kan cinyarsa yana rarrashin sa, yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare da shi sosai ya fad'a a zuciyarsa. "Kayi hak'uri *Adeel* domin kuwa ni sam ba zan ta'ba bai yana maka mahaifiyar ka ba, wannan yasa ni sai dai kawai na baka hak'uri ina fatan zaka yafemin a kan wannan. Ina sanka d'ana kai komai nawa zanma iya kiran ka da rayuwa gaba d'aya." Maganar zuci yake yayin da tausayin yaronsa yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Bayan wani lokaci ya dena kuka Prof ya anbaci sunan sa yana cewa, "rabin raina ya kamata ka shirya muci abinci dan Allah karka ce da ni a'a please." Magana yake yana wani shafar kansa zuwa bayan sa tare da sunbatarsa ya jinjina masa ka a lamar to, Prof yayi wani gajeran murmushi sannan ya tashi ya shiga toilet ya had'a masa ruwan wanka, ya fito tare da sanar da shi ya tashi ya nufi toilet Prof ya bisa da kallo yana girgiza ka, bayan wani lokaci ya fito Prof ya taimaka masa ya shirya sannan suka fita. Kai tsaye tebur suka nufa yaja masa kujera ya zauna ya fara zuba abincin sannan ya zauna, wanda kuma shi ne wanda yake ba *Adeel* a baki yana ci, bai wani ci sosai ba ya tashi Prof ma tashi yayi ya nufi inda yake a zahirin gaskiya yana matuqar masifar qaunar yaronsa sosai. Wannan yasa yake matuqar shiga damuwa idan ya gansa cikin k'unci da 'bacin rai sosai, ya same sa zaune a kan kujera ya zauna sai wani kallonsa yake kallo mai cike da jin tausayin sa sosai. *"Adeel* dan Allah ka dena wannan fishin haka yayi yawa sosai kuma hakan zai iya cutar da kai da kuma lafiyar, *"Adeel* yanzu fad'a min kake so ni kuma zanyi ma nayi alkawari kawai ka fad'a min ka ji ko.?" "Dady ni kawai Mama na nake so to kasa ta dawo gareni please." "Kayi hak'uri *Adeel* sabo da ni ba zan iya baka wannan ba, sabo da ita Maman ka ta riga data mutu kuma ita d'in bata ta'ba sanka ba, sabo da ta tafi ta barka kuma ita ba zata ta'ba dawowa gareka ba na har abada. To ya kamata ka fuskanci gaskiyar kawai kai ma ka manta da ita kamar yanda ita ma tayi gareka ka ji ko." "Eh gaskiyar ka fad'a kawai zan manta da ita kamar yanda ta tafi ta barni, Dady ina sanka sosai kamar dai yanda kai ma kake sona, kai ko yaushe kana tare da ni amma ita Mama kawai sai ta za'bi data barni, hakan yana da zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una. Amma duk da haka ni ina qaunarta sosai dan Allah ka nuna man ko da photon ta ne please." Magana yake yana kuka Prof kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai yayin da tausayin sa yake ta shigarsa, "kayi hak'uri yarona ka yafemin sabo da bani da photon Maman ka ina fatan ba zaka yi fishi a kan hakan ba.?" "Eh ba zanyi ba ina sanka Dady na." "Nima ina qaunarka sosai *Adeel* yanzu yana da kyau mu fita mu zaga gari, sabo da ka manta da wannan k'uncin naka ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to ya tashi tare da tashin sa sun fita domin su zaga gari, misalin k'arfe 02:30pm jirginsu Ahlam ya sauka sun fito sun shiga taxy zuwa gida, wanda sunyi hakan ne kawai domin su yiwa su Abbu bazata. Kasancewar basu sanar dasu labarin zuwan su ba, sun isa gidan su Habu sun shiga yi musu sannu da zuwa tare da riqa musu kaya, sun amsa suna murmushi tare da sake musu fuska, sun shiga ciki wanda kuma kai tsaye part ďin Abba suka nufa. Zaune suke dukansu sai fira suke cikin kyakkyawan yanayi kamar diran mikiya suka jiyo sallamar su Ahmad, da sauri dukansu suka kai kallonsu ga k'ofa domin tabbatar wa idanuwan su abin da kunnan su yaji, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar suma kallonsu suke. Cike da d'auki suke fad'ar sunayen juna musamman ma *Adyan,* sun qarasa ciki cike da d'auki sun shiga yin hugging juna dukansu bayan sun zauna tare da gaisawa da juna Abba yaci gaba da magana. "Ahmad wannan wace irin bazata ne mai matuqar dad'i sosai haka? A zahirin gaskiya dukanmu muna farin ciki sosai da ganin ku kunyi matuqar saka mu farin ciki sosai. Amma duk da haka naso a ce ka sanar damu labarin zuwan ku ta yanda zamu shirya muku kyakkyawar tarba, musamman wannan abokin nawa tabbas dukanmu muna tare da kewarku sosai musamman *Adyan* to sannun ku da zuwa." "Yauwa Abba muna godiya sosai sannan kuma mu kawai muna san muyi muku bazata ne, shi yasa bamu iya sanar daku labarin zuwan mu ba abin farin cikin shi ne dukanku kunyi matuqar farin ciki da hakan sosai, to wannan ma kawai ya isa shin baku ga yanda *Adyan* yake farin ciki da ganin ku ba? Shi d'in yayi matuqar yin kewarku sosai a kullum kuma a ko yaushe cikin zancan ku yake dalilin da yasa muke nan kenan." Abba ya kai kallonsa ga *Adyan* wanda yake zaune a kan qafafun sa ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana cewa. "Rabin raina muma munyi kewarka sosai amma yanzu muna farin ciki sosai sabo da dukanmu muna tare ahalinmu ya cika, kuma duk sabo da kai ne gaskiya kai yaron kirki ne sannan kuma zan iya kiran ka dana musamman." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi su Abbu suka sai wani murmushi suke mai tare da dariya, bayan sun sha ruwa da juice sun tashi domin su tafi su shirya Ahmad ya riqa hanun *Adyan* domin shiga ciki, Ahlam tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad *Adyan* zai tafi tare da ni part ďin Ummi, ni zan shirya sa to kawai ka barsa a nan please." Ahmad ya girgiza ka tare da jan numfashi sannan ya amsa ta, "Ahlam yaron zai zauna a tare da ni sannan kuma ni zan shirya sa ai na gware a hakan to zan iya kinji ko." "A'a Yaya Ahmad *Adyan* kawai a gurin Ammie zai tsaye to kawai ka amince da hakan ka ji ko please." "Ahlam karki yi taurin kai mana na fad'a maki cewar yaron a guri na zai tsaya, kuma ni ne nan wanda zai kula da shi to kawai ki amince da hakan kinji ko." "Yaya Ahmad gaskiya ni ba zan yarda da hakan ba kawai a guri na zai zauna hakan ba zai canja ba." "Shikenan zamu gani yanzu yaron shi da kansa zai za'ba wa kanka inda zai zauna, ni ina da imanin cewa yarona ba zai ta'ba barina ba to kawai muyi hakan." "Na amince wa hakan sabo da na tabbata yarona ba zai bani kunya ba." Magana suke cike da kwarin guiwa dukansu su Ummi sai kallonsu suke suna murmushi mai tare da dariya, lokaci d'aya suka kai kallonsu ga *Adyan* wanda shi ma kallonsu yake Ahmad ne yake magana da shi. "Rabin raina fad'a min wani abu shin zaka zauna da Appa ne ko Ammie.?" Kallonsu kawai yake yayin daya gagara furta masa komai jin shirun yayi yawa yasa Ahlam magana. "Masoyi kawai ka za'ba dawa kake san ka zauna mu zamu amince da duk abin daka za'ba, to kawai ka fad'a dawa zaka zauna.?" Har zuwa wannan lokacin kallonsu yake kuma kallo sosai ya girgiza ka tare da furta musu kalmar. "Appa Ammie ni sam ba zan iya za'ba a tsakanin ku ba, sabo da dukanku kuna da matuqar muhimmanci sosai a gareni da kuma rayuwata ina matuqar qaunar sosai. Appa Ammie shin ba zamu iya zama dukanmu a guri d'aya ba? Ni zanyi matuqar farin ciki da hakan sosai dan Allah." Lokaci d'aya suka kai kallonsu ga juna ba jimawa suka mai da kallonsu garesa suna murmushi Ahmad ya amsa shi. "Shikenan masoyi zamu yi hakan dukanmu ukun zamu kasance tare da juna, to yanzu fad'a min wani abu shin kana farin ciki.?" Ya d'aga masa ka tare furta eh Appa. Lokaci d'aya kuma suka yi hugging d'in sa tare da sunbatarsa suna furta masa kalmar muna qaunarka sosai. Su Abbu sai wani kallonsu suke suna murmushi sun tashi dukansu sun nufi bedroom d'in Ahmad. Su Abba sun bisu da kallo suna murmushi mai tare da dariya, "gaskiya yaranmu suna da matuqar birgewa sosai musamman ma jikana, yana k'oqarin qara had'e kan iyayen sa hakan yana da kyau sosai sai naji na qara qaunar sosai." Umma ta amsa ta da, "Eh Maman Ahlam gaskiyar kika fad'a jikanmu yana da birgewa sosai nima ina jin qaunar sa sosai a tare da ni." "Eh gaskiyar kuke fad'a dukanku to yanzu ku dakata da zancan haka ku tafi kusa a shirya musu tebur. Na tabbata zasu buqaci abinci bayan sun qarasa shirin su musamman *Adyan* to kuyi hakan cikin sauri." "Eh zamu yi Senoter musamman sabo da saban Angon mu daya kawo mana ziyara to zamu tafi yanzu." Wani irin kallo Abba yake yi mata mai kama da harara sannan ya amsa ta, "Maman Ahmad shin ko zaki dena kiran wannan yaron da Angon ku? Ko kuma dai ni nasa ya koma qasar England a yau ďin nan." "Yaya ai ita Aunty gaskiyar ta fad'a mu ďin nan muna matuqar farin ciki sosai da zuwan Angon mu, sannan kuma zamu yi komai sabo da shi idan kuma kasa a ka mai da *Adyan* England, to fa ni da Aunty ba zamu qara yi muku magana ba ba zamu ci abinci ba sannan kuma daga k'arshe zamu yi fishi daku kuma fishi sosai." Wani irin kallo suke yi mata mai cike da jin mamakin ta sosai, sam basu iya amsa ba sai dai suka yi mata murmushi mai tare da dariya ita ma abin da take yi kenan. Ta tashi ita da Umma sun fice su Abbu sun bisu da kallo suna murmushi mai tare da dariya, su Ummi sun samu su Shamsiya a part d'in su sun sanar dasu cewar su tafi zasu shirya wasu Ahmad abinci. Sun amsa da to sun tashi sun nufi kicin dukansu domin yin aikin da yake gaban su, bayan wani tsayin lokacin da suka d'auka a ciki suna shirya wa sun fito dukansu cikin kyakkyawan yanayi, da kuma kyakkyawar shiga sunyi matuqar yin kyau sosai. Su Ummi sun kawo musu ruwa da juice tare da kayan fruit sun shiga yi musu godiya murmushi kawai suka yi musu mai tare da dariya, bayan wani lokaci Shamsiya tazo ta sanar da Umma cewar sun shirya komai a kan tebur ta amsa da to ita kuma ta tashi ta fice. Suma tashi suka yi suka nufi tebur domin cin abinci, sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarsu sosai. Bayan sun qarasa sun dawo parlour sunci gaba da fira cikin kyakkyawan yanayi bayan kwana biyu Ahlam ta kai wa Kawun ta ziyara, wanda tare take da Ahmad da kuma *Adyan* sai fira suke abinsu cikin raha wasa da dariya Anisa ta anbaci sunan Ahlam tana cewa. "Ahlam gobe ne za a yi bikin qarewar su Amir to ina fatan dukanku zaku tafi.?" Ahlam ta kai kallonta ga Ahmad kafin ta furta komai yayi mata rigagi. "Eh Aunty zamu tafi insha Allah." Wunin ranar gaba d'aya a nan gidan suka yi sa *Adyan* sai wasa yake dasu Amir washe gari........ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/8, 8:32 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 15* *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Thursday 06/01/2022* *Time 03:10pm* *Typing.................* Tsaye yake gaban madubi yana wani kallon Kansas, yayi kyakkyawan murmushi mai tare da dariya yana magana da kansa. "Gaskiya nayi kyau sosai na tabbata *Afnan* ma zata fad'a min haka, ya kamata na tafi na had'u da ita yanzu ina fatan ita ma ta qarasa shirin ta." Cike da d'auki ya juya domin tafiya lokaci ďaya yayi tozali da fuskar Mamie, wacce take tsaye jikin bango tana kallonsa sai wani lallausan murmushi take sosai. Shi kuwa dariya yake ya isa inda yake yana fad'ar sunan ta, ta amsa shi tana 'yar dariya shi ma abin da yake yi kenan. "Kayi kyau sosai yarona tabbas *Afnan* zata fad'a maka cewar kayi masifar yin kyau sosai, amma zaka tafi tare damu a can gurin bikin ka ji ko." "Eh Mamie kawai *Afnan* ce zata zo tare damu yanzu zan tafi na sanar da ita, sai mu dawo tare to yanzu fad'a min wani abu ina qanwata.?" Murmushin ta ya qaru sosai ta amsa, "Qanwarka tana parlour tare da Papa kai muke jira domin mu tafi gurin taron, lokaci ya tafi sosai mun kusa mu makara, to yanzu idan ka shirya mu tafi." Ya amsa da "Eh" suka juya suka fita zuwa parlor, sun samu Papa zaune tare da *Alishart* yana ta ya ta wasa, *Adnan* ya isa inda take ya shafi kanta zuwa fuskar ta ya qara da sunbatarta. "Sannu da wasa qanwata kinyi kyau sosai cikin wannan shigr, na tabbata ke ce wacce zata fi kowa ce mace kyau a gurin taron, ina sanki sosai qanwata yanzu ki jira Yayan ki a nan, zan tafi na dawo tare da *Afnan* sai mu tafi kinji ko." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi. Ya qara sunbatarta sannan ya tashi ya sanar dasu Papa cewar zai shiga gidan su *Afnan* ya dawo, "Shikenan masoyi amma karka jima sosai kaga lokaci ya tafi sosai, zamu iya makara hakan kuma bai dace ba ka ji ko." "Eh Papa ba zan wani jima ba kawai zance da ita ta fito mu tafi shi ne kawai." "Shikenan amma ka kula sosai dan Allah ka ji ko?." "Eh zanyi nayi alkawari sai na dawo." Suka amsa da a dawo lafiya ya amsa da Amin sannan ya juya ya fita suka bisa da kallo suna murmushi, bai qarasa fita ba *Alishar* ta bisa a baya tana fad'ar sunan sa yayin da take kuka, da sauri ya isa inda take tare da d'aukan ta ya shiga rarrashin ta ba jimawa tayi shiru tare da furta masa, "Yaya nima zan tafi tare da kai." "Shikenan mu tafi." Ya sauke ta tare da riqa hanun ta sun fice su Mamie sun bisu da kallo suna murmushi. *"Afnan* ki fito mu tafi lokaci ya tafi sosai." Ta fito sai fishi take tana wani turo baki fuskar ta awa zata yi kuka dukansu sai wani kallonta suke Yayan ta ya shiga tambayar ta. *"Afnan* mai yake faruwa dake ne haka.?" "Yaya to ba Ummu bace take ta san mu tafi ba tare da mun jira zuwan *Adnan* ba ni ina san na tafi tare da shi." "Haba qanwata yanzu sabo da wannan ne kike 'bata rai? To ki dena mu zamu jira zuwan *Adnan* kin fasan ke ce sarauniyar gidan, to zamu yi duk abin da kike so kinji ko to kiyi farin ciki sosai kinji ko zonan." Ta d'aga masa ka tare dariya tare da isa inda yake kamar dai yanda ya buqata daga gareta, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta a ka dama gefen fuska cike da d'auki ta fad'a jikinsa, shi kuwa ya runguma ta yana wani shafar kanta a zahirin gaskiya yana matuqar qaunar qanwarsa sosai. Su Ummu sai wani kallonsu suke suna murmushi sai kuma zuwa wannan lokacin ne Abba yayi magana. "Anwar a gaskiya kana sangarta *Afnan* sosai ina jin dad'in yanda kake san qanwarka tare da nuna mata kulawa sosai. Anwar soyayya da qaunar da kake nuna wa *Afnan* ko mu iyayen ta bama nuna mata, Anwar idan kaci gaba da sangarta *Afnan* haka kana shagwa'ba ta to abin zai yi yawa sosai sabo da." "A'a Abba ba abin da zai faru qanwata ta tantanci ta samu duka soyayya ta, ita qanwata ce to zan iya yin komai sabo da ita sannan kuma zata kasance yarinyar kirki sosai kamar dai yanda muke yi mata fata. Abba sangarta yaro bai yasa ya lalace sai idan har ba a yi hakan ta hanyar daya dace ba, to ba buqatar ka damu sabo da ita qanwata daban ce a cikin mata, zata kasance yarinyar kirki sosai kuma zan tabbatar maka da hakan insha Allah." "Ina fatan haka Allah ya amince mana Amin." Suna haka suka ji a na buga masu k'ofa lokaci d'aya *Afnan* ta saki wani kyakkyawan murmushi tare da fad'ar sunan *Adnan.* Ta tashi da sauri har tana gudu ta isa ga k'ofa tare da bud'e wa ta kuwa samu *Adnan* tsaye a k'ofa tare da *Alishart,* sun tari juna da wani lallausan murmushi abin birgewa ga wanda ya gani. "Na gode Allah daya kasance cewar kin qarasa shirya wa yanzu zamu iya tafiya, Papa da Mamie suna jiranmu karmu makara to mu tafi na fara gaisawa dasu Abba sai mu tafi." Ta amsa da to sun dawo ciki tare ya fara gaisawa dasu Ummu, sannan suka tashi dukansu suka fita domin tafiya, sun fito sun samu su Mamie a nan waje bakin mota suna jiran fitowar su *Adnan.* Sun fara gaisawa dasu Abba sannan su *Afnan* suka shiga mota suka tafi, zaune suke suna break past cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa suka fara shirin tafiya gurin taron su Amir. Umma da Ummi zasu tafi ne domin amsa gaiyatar Anisa da Abdulrahim, Abba da Abbu kuma zasu tafi ne domin amsa gaiyatar shugaban makaranta da yayi musu, ya gaiyace sune sabo da kasancewar su manyan mutane sannan kuma gasu 'yan siyasa masu ri e da manyan muqamai. Abba yana matsayin Sanata ne yayin da Abbu yake a matsayin ďan Majalisa, bayan sun qarasa dukannin wani shiri nasu sun tashi sun kama hanyar zuwa gurin taro. Bugun k'ofar da a kai ne yasa shi tashi ya nufi k'ofa tare da bud'e wa, ya kar'bi abincin da yake hanun mutumen da yake tsaye bakin k'ofa tare da furta masa na gode, ya amsa da to ya juya ya tafi shi kuma ya dawo ciki ya a jiye abincin a kan tebur sannan ya nufi gurin yaransa, ya tafi kusa da shi ya zauna sai wani kallonsa yake ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa sannan ya anbaci sunan sa. *"Adeel* mu tafi muyi break past lokaci ya tafi sosai zamu iya makara zuwa gurin taron, kuma hakan sam bai dace ba to ya kamata muyi break past yanzu dan Allah." Magana yake masa cikin qauna da soyayya yayin da yake rungume jikin sa, sai wani sunbatarsa yake ya tashi tare da tashin sa sun nufi tebur domin suyi break past. Sunyi break past cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa sunci gaba da shirin tafiya gurin taro, kasancewar sa sananne matashin mai kud'i yasa shugaban makaranta ya aika masa da sakon gaiyata har garin Bauchi. Sun qarasa shirin su sunyi kyakkyawan shiri sun tashi sun fice zuwa gurin taro, wani babban holl ne wanda a ka k'awata shi da ado gurin yayi kyau sosai. Holl ďin ya tara manyan mutane ne sosai na daga ko ina kama daga 'yan siyasa, 'yan kasuwa, ma aikatan gwamnati, da sauran jama'ar gari na daga ko ina na sassan k'asa. Yara 'yan makaranta sai nishad'antar da gurin suke da wasanni iri daban-daban, hakan yayi matuqar saka yaran dake gurin nishad'i sosai bayan wani lokaci a ka fara cin abinci. "Afra ta tashi ko ina zata oho ta kai kallonta ga *Adyan* tare da tashin sa tana cewa. *"Adyan* mu tafi ka raka ni." Ahlam ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a Afra kawai ki tafi." "Haba Aunty Ahlam dan Allah karki dakatar da ni daga tafiya da shi please." Kafin ta furta komai Umma tayi mata rigagi, "eh Ahlam ki barta su tafi dan Allah." "Shikenan Umma zasu iya tafiya Afra ki kula da shi sosai dan Allah kinji ko." Ta amsa ta da to Ahlam ta mai da kallonta ga *Adyan* tayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa sannan suka tafi. Ta bisu da kallo har suka fice tafiya suke yayin da idanuwan *Adyan* suke a kan yaran da suke wasan boll, sai jin yake yana san ya tafi ya kai kallonsa ga Afra kafin ya furta komai wayar ta ta d'auki ruri, ta d'aga tana wani lallausan murmushi *Adyan* ya zame hanun sa cikin mata ya nufi gurin wasan boll da sauri har yana gudu. Ya shiga cikin wasan ba tare da wani ya dakatar da shi ba hakan yayi matuqar yi masa dad'i sosai, bayan wani lokaci ta qarasa waya ta kai kallonta ga gunda *Adyan* yake, amma tayi rashin sa'a domin kuwa da jimawa *Adyan* ya bar gurin cike da firgici ta shiga anbatar sunan sa. Amma bata yi nasaran ganin sa ba cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ta juya ta nufi gurin su Ummi. Sun jima sosai suna buga wasan boll wanda hakan ne yasa *Adyan* yayi matuqar gajiya sosai, lokaci d'aya jikin sa ya mutu sai wani irin abu yake ji a tare da shi wanda zamu iya kira da kasala. Ya koma daga gefe ya zauna sai wani lumshe ido yake tamkar mai jin barci, kallo d'aya tak zaka yi masa ka fahimci cewar ba qlau yake ba ko ba shi da lafiya, *Adnan* na daga gefe ya hangesa cikin hanzari ya isa garesa yana furta masa kalmar. "Baka da lafiya to amma mai ya saka kai ka shiga wasan? Kai kana da irin cutar da take tare da ni dalilin da yasa nima ban buga wasan ba kenan. Yanzu fad'a min ina maganin sabo da akwai buqatar ka sha magani yanzu to fad'a min ina maganin ka yake.?" Kallonsa kawai yake domin kuwa kalma ďaya bai fahimta ba ga abin da yake fad'a, kasancewar hausa yake shi kuma turanci kawai ya iya cikin wata 'yar murya yake furta masa kalmar. "Bana jin abin da kake fad'a." "Mine hakan yana nufin bai ya jin hausa? Shikenan idan shi bai ya jin hausa ni kuma ina jin turanci to ya kamata na taimake sa." Nan kuwa ya canja harshe ya koma turanci, "am sunana *Adnan Adam* kai baka da lafiya jikin ka yayi zafi sosai fad'a min ina maganin ka yake? Ya kamata ka sha maganin ka yanzu sabo da zai taimaka maka ka damu lafiya sosai." *"Adnan* dan Allah ka taimaken please." Wannan kalmar ce kawai iya fad'ar masa daga nan kuma ya suma, *Adnan* ya shiga jijjigasa yana furta masa kalmar ya tashi amma sai shiru yake ji yana haka ya hangi wani yaro zai wuce, yayi saurin dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar. "Kai zonan zo da sauri." Ya isa inda yake sai wani kallonsa yake ya qara da furta masa kalmar. "Kai mai ya saka kace nazo nan? Sannan kuma ka kira ni da kai fad'a min mai ya saka ka kira ni.?" "Karka yi fishi brother kawai ina san zaka taimaki abokina shi ďin ya suma ne." "Sunana *Adeel Abas* to yanzu fad'a ta yanda a kai shi ya suma.?" "Am ni kuma sunana *Adnan Adam* kayi hak'uri dana dame ka, ba shi da lafiya ne jikin sa yayi zafi sosai to sai kawai ya suma." *Adeel* ya dukursa sai wani kallon *Adyan* yake kallo sosai, daga bisani kuma ya mai da kallonsa ga *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* muyi wani abu kawai yanzu kawai ka sanar da iyayen sa cewar ba shi da lafiya domin a kai shi asibiti." "Eh gaskiyar kane ya kamata nayi hakan yanzu kai ka tsaya nan tare da shi, ka kula da shi sosai ba zan jima ba zan dawo gareku ka ji ko." "Eh zanyi ni zan kula da shi sosai nayi alkawari to zaka iya yarda da ni sai ka dawo." "Na gode sosai brother sai na dawo." Ya fad'a tare da shafar kansa yana wani gajeran murmushi shi ma ya mayar masa da murmushi, da kuma haka suka rabu *Adnan* ya tashi ya tafi *Adeel* ya bisa da kallo har ya fice, bayan tafiyar ya mai da kallonsa ga fuskar *Adyan* sai wani kallonsa yake yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare da shi sosai................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/9, 2:50 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 16* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 08/01/2022* *Time 09:17am* *Typing................* Fira suke cikin raha wasa da dariya sai ga Ahmad ya sauke kallonsa ga fuskar Ahlam tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam ina *Adyan* fatan ya ci abinci, amma me yasa baya nan.?" Cike da firgicin abin daya tambaye ta take magana, "am shi ya fad'a min cewar madara kawai zai sha idan mun koma gida, sannan kuma shi ďin ya fita tare da Afra ya raka ta wani guri amma." Yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu, "ya isa haka amma kin fita hayyacinki ko? To taya ma har zaki yi tunanin aikata hakan? Kin baiwa Afra shi sun fita ba tare da kinyi tunanin sanar da ni ba, kin kuwa san irin girman zunubin da kika aikata a yanzu? To ki sani wallahi tallahi ba zan taɓa gafarta maki ba idan har wani abu ya faru da yarona." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa ta shiga anbatar sunan sa, amma bai amsa ba ya kuma dakatar da ita daga bin bayan sa. Su Umma sun bisa da kallo cike da jin mamakin sosai lokaci d'aya Ahlam ta saki kuka. "Kin gani ko Umma dalilin da yasa tin farko ban yarda Afra ta fita da shi ba, ga shi yanzu Yaya Ahmad yana matuqar yin fishi da ni kuma fishi sosai. Gaskiyar sa ne sam bai kamata na bari ta fita da shi ba na amince ne sabo kinyi magana, Umma ni ban san wane irin hukunci zanyi wa kai na ba idan har wani mummunan abu ya faru da yarona ba. Ni na damu sosai a kansa hakama ina jin wani irin yanayi a game da shi ina fatan zai yana lafiya." Su Ummi sun shiga rarrashin ta suna bata magana ta tashi ko ina zata tafi oho Umma ta shiga tambayar ta. "Ahlam ina kuma zaki tafi.?" Ta girgiza ka tare da furta, "ban sani ba Umma amma dai bai kamata a ce ina nan banyi komai ba, zan tafi domin naga ko zan gansu." Ahmad na k'oqarin fita sai ga Afra ta shigo cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau, yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali Ahmad ya riqo hanun ta tare da tambayar *Adyan.* "Afra ina *Adyan.?"* "Yaya Ahmad nima ban san yana ina ba sabo da." Bata qarasa zancan ta ba ya kifa mata wani wawan mari biyu masu kyau sosai, wanda sai data kife a qasa ta saki kuka ya tashe ta ya kuma shiga fad'a da ita fad'a yake mata sosai. "Ke kin haukace ne da har zaki kalli cikin idanuwana sannan ki fad'a min cewar wai baki san inda *Adyan* yake ba? Taya ma har zaki yi tinanin fad'a min haka ki fad'a min ta yanda a kai yaron ya rabu dake.?" Cikin muryar kuka take magana yayin da tsoron Ahmad yayi yawan gaske a tare da ita sosai. "Yaya Ahmad yana tare da ni na ri e hanun sa sai a ka layi na, shi ne sai na koma gefe ina amsa waya bayan na qarasa ne naga bai ya nan tare da ni." Cike da k'unci da bak'in ciki ya qara kifa mata tafi, "Afra yanzu kina san ki fad'a min cewa sabo da amsa waya kika rasa *Adyan?* Shin ke ba zaki iya kulawa da shi ba kuma kika buqaci fita da shi fad'a min wani abu shin amsa wayar ki tafi yaron muhimmanci ne da baki tsaya kin kula da shi sosai ba? To bara kiji wallahi tallahi idan har wani abu ya faru da yarona to sai kin biya, sabo da ni ba zan ta'ba gafarta maki ba na har abada to karki ta'ba mantawa da wannan kinji ko." Lokaci d'aya kowa ya kai kallonsa ga Ahmad wanda yake ta faman fad'a da Afra, cikin hanzari Abba da Abbu sun isa gurin hakama su Ummi Abba ya shiga tambayar abin da yake faruwa Umma ta sanar da shi komai. A zahirin gaskiya hankalin su Abbu yayi matuqar tashi sosai da jin labarin cewar *Adyan* ya 'bata. Abba ya sanar da security a kan su tafi nai man sa sun amsa da to sun fice, Ahmad ma fita yayi domin nai man yaronsa Abba ya sanar da shugaba abin da yake faruwa. Lokaci d'aya dukansu jama'ar dake gurin sun saki salati suna taslima, sun shiga jajanta musu Ahlam kuwa sai wani irin kuka take kuma kuka sosai tana fad'a da Afra. Cike da firgici Prof ya anbaci sunan *Adeel* tare da mi e wa tsaye ya fita daga holl ďin da sauri har yana gudu, yayin da bakinsa yake ta anbatar sunan *Adeel* hakama Mamie ta shiga anbatar sunan *Adnan* ta kai kallonta ga *Afnan* tana cewa. *"Afnan ina Adnan* mai ya saka bai ya tare dake.?" "Mamie shi yama fa riga ni fitowa bayan mun qarasa wasan, to gaskiya ni sam ban san yana ina ba amma zan iya tafiya yanzu domin na duba shi." Ta girgiza mata ka tare da furta, "A'a 'yata ki barshi ni zanyi wannan tare da Papa to kawai ki huta kinji ko." "Mamie nan fa school ďinmu ne to ni na san ko ina na school ďin shi yasa zan iya gane sa kawai ki yarda da ni sai na dawo." Ta tashi da sauri har tana gudu tayi tafiyarta Mamie ta shiga anbatar sunan ta amma bata amsa ba Ummu ta amsa da cewa. "Karki wani damu su biyun zasu dawo tare insha Allah to zaki iya yarda da ni." "Maman Anwar nima ina fatan hakan." Ba jimawa a ka tashi taron a kaci gaba da nai man *Adyan* a nan cikin school dama wajen school, *Adnan* yayi nisa sosai cikin tafiya ya hangi Ahmad yana tafiya ya nufi gurin sa yana kiran sa da Uncle. "Uncle dan Allah ka taimaki abokina shi ďin ya suma ne." Da sauri Ahmad ya tsaya tare da kai kallonsa garesa cikin wata sarkakiyar murya yake magana. "Miye ya suma waye shi kuma taya a kai ya suma.?" "Ni ban san sunan sa ba shi yasa nake kiran sa da abokina, a game da yanayin sa kuma shi ďin ya buga wasan boll ya gaji sosai shi yasa ya suma. To dan Allah ko zaka iya taimaka masa zuwa asibiti please.?" Ya jinjina masa ka tare da furta, "eh sabo da ni ne Abban sa shi ďin ďana ne tin d'azu nake nai mansa to mu tafi ka kai garesa." Ya amsa da to sun nufi gurin su *Adyan* yake sun same sa kwance yayin da kansa yake a kan cinyar *Adeel.* da sauri Ahmad ya d'auke sa yana k'oqarin tafiya *Adnan* ya dakatar da shi yana furta masa kalmar, "dan tsaya kad'an Kawu dan Allah." Ahmad ya jinjina masa ka a lamar to shi kuwa ya bud'e jakar sa ya d'auko photon sa inda yake tare da *Alishart,* ya juya bayan photon ya rubuta number Mamie da Papa sannan ya ba shi photon yana furta masa kalmar. "Uncle ka ba shi wannan idan ya farka kace da shi daga *Adnan* dan Allah." "Eh zanyi hakan insha Allah *Adnan* kai aboki na gari ne naji dad'in had'uwa da kai sosai." Ya shafi fuskar sa zuwa kansa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar Allah yama albarka, ya amsa da Amin yana dariya Ahmad ya mai da kallonsa ga *Adeel* tare da furta masa kalmar. "Kai ya sunan ka.?" "Ni sunana *Adeel* ne." "Na gode sosai *Adeel* Allah yama albarka." Ya fad'a tare da shafar kansa zuwa fuskarsa tare da sunbatarsa ya amsa da Amin yana dariya, Ahmad kuwa wani gajeran murmushi yake ya juya ya fice zuwa mota domin ya kai yaronsa asibiti bayan tafiyar sa sun kai kallonsu ga juna *Adnan* ya dafasa tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* na gode sosai da kai ka yarda ka taimaki abokina ina godiya sosai, gaskiya kai yaron kirki sosai na tabbata Maman ka tana yawan fad'a maka haka." "Karka wani gode min sabo da ni kawai nayi abin daya dace ne, sannan kuma karka yi magana a kan Mama na sabo da ta tafi, *Adnan* Mama na ta za'bi ta mutu ba tare data yi tinani a kai na ba. *Adnan* ni fa ban ta'ba sanin fuskar Mama na ba kawai ta tafi ta barni sai Dady na, shi kad'ai yake sona kuma shi kad'ai nake da shi yana masifar qauna ta sosai, shi yasa nake matuqar masifar qaunar sa sosai amma ita Mama na bata ta'ba sona ba. Bama ta bari ta rayu da ni ba shi yasa na tsane ta sosai kamar yanda ta min, Dady ya fad'a min cewar ita Mama na bata ta'ba sona ba ko da kuwa na rana d'aya ne dalilin da yasa na tsane ta kenan. Duk da cewar hakan yana saka ni k'unci *Adnan* hakan yana da zafi sosai, sannan kuma da matuqar k'una sosai amma karka damu da ni zan kasance lafiya." Lokaci d'aya *Adnan* yaji tausayin yana shigarsa, duk da kasancewar yaro amma yana da kyakkyawan tinani sosai cike da jin tausayin yake magana. "Kayi hak'uri *Adeel* tabbas kana tare da k'unci sosai, sannan kuma ba laifin Maman ka bane data mutu a islamiya malamin mu ya fad'a mana cewar dole ne sai kowa ya mutu. Yayin da bawa ya mutu kuma to yana buqatar addu'a sosai daga gurin ahalinsa, kamar iyayen sa, Yayyen sa, Qannan sa, abokan sa, 'ya'yan sa dama duniya gaba d'aya. *Adeel* Maman ka tana sanka sosai kaddaran mutuwa ce kawai ta shiga tsakanin ku, to ya kamata kai ma ka sota sosai bawai kaci gaba da tsanan ta ba, *Adeel* a yanzu Maman ka tafi kowa buqatar ka to ya kamata ka biyata ta hanyar yi mata addu'a, malamin mu ya fad'a mana cewar yiwa iyaye biyayya tare da nuna musu soyayya wannan wajibi ne dole. *Adeel* na san kai ma ka san hakan amma mai yasa ka manta? *Adeel* kana da damar da zaka so Maman ka to kawai kayi hakan dan Allah, sannan kuma ka kasance mai yiwa Maman ka addu'ar samun rahma da gafara a gurin Allah, ta haka ne zaka kasance yaro na gari a gareta to ina fatan zaka yi anfani da duka shawara ta.?" *"Adnan* ni duka ban san wannan ba sabo da bana zuwa islamiya, a baya kafin yanzu ina zuwa wata rana a kaman dukan makara shi ne na fad'a wa Dady na, ai kuwa yayi ta fad'a wanda har sai da yasa a ka rufe malamin a gidan kaso. To fa tin daga ranar na dena zuwa islamiya shi yasa ban san duka wannan ba, gaskiya naji dad'in had'uwa da kai sosai a k'alla na san yanda zanso Mama na na gode sosai." Cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adnan* yake magana. *"Adeel* gaskiya rayuwar ka tana da ban tausayi sosai, lallai ya kai kayi koma miye domin ka koma islamiya, domin ka san a salin waye kai addinin ka ne kawai zai fad'a maka haka." "Na gode *Adnan* gaskiya kai d'an uwa na gari ne, nayi alkawari zanyi anfani da duk abin daka fad'a min a yanzu insha Allah." Lokaci d'aya kuma suka yi hugging juna sun d'an jima a haka sannan suka sake juna, *"Adnan* ni zan tafi kar Dady na yayi ta nai mana." "Shikenan zaka iya tafiya ina yima fatan alkhairi a ko yaushe." Da kuma haka suka yi sallama ya tafi shi tafiya yayi domin koma wa gurin ahalinsa, yana cikin tafiya bai ankara ba yaji an runguma sa ta baya, lokaci d'aya ya saki murmushi mai had'e da dariya yana anbatar sunan *Afnan.* Ta sake shi tare da fitowa ta gaban sa tana fad'ar sunan sa. *"Adnan* wai ina ka shiga ne.?" "Ba ko ina kawai ina zaga cikin school ne." "Shikenan mu tafi lokacin tafi gida yayi." Ya amsa ta da to sun fice sun samu su Mamie bakin mota sun shiga mota sun tafi, hakama *Adeel* ya samu Prof sun fice masauki wato hotel washe garin ranar suka kama hanyar Bauchi domin koma wa gida............. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamin ne.* [1/12, 8:22 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 17* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 08/01/2022* *Time 11:20pm* *Typing.................* Ya isa asibiti cikin hanzari nurse suka kar'bi yaron suka shiga da shi ciki domin a duba shi. "Am nima zan iya shiga ciki, ni ya kamata na duba sa, sabo da na san komai a game da rashin lafiyar sa, sannan kuma ni ďin likita ne to dan Allah kar ku dakatar da ni please." Da fari doctor bai yarda ba sai daga bisani sannan ya amince da buqatar sa. Sun shiga ciki nan kuwa Ahmad ya shiga duba sa tare da taimakon Dr Habib bayan sun qarasa duba sa, Dr Habib ya nufi office ďin sa hakama nurse ďin da suke tare da su su ma sun fice. Ahmad yayi zaune gefen sa sai wani kallonsa yake kallo sosai, ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar Allah ya baka lafiya Amin. A can gurin su Ummi kuwa sam basa cikin kwanciyar hankali sabo da rashin ganin *Adyan,* a zahirin gaskiya duk kansu suna tare da tashin hankali mai matuqar girman gaske sosai, ganin Ahmad ya jima bashi tare da su sannan bai nemi kowa ba yasa Abba ya fara shakkar ya anbaci sunan Abbu. "Al'ameen ni fa ina tunanin cewar Ahmad yana tare da *Adyan."* "Amma Yaya mai ya sa kake fad'ar haka.?" "Al'ameen dukanmu a nan mun san yanda Ahmad yake matuqar masifar qaunar yaronsa sosai, kuma na tabbata Ahmad zai yi komai domin ya samu yaronsa ya dawo garesa, Ahmad ya jima sosai da fita amma har zuwa wannan lokacin bai nai mi ko ďaya daga cikin mu ba, wanda ya kamata a ce ya nai mi wani daga cikin mu domin yaji abin da yake faruwa. Dalilin da yasa na fahimci hakan kenan to ya kamata mu tafi gida domin had'uwa dasu." Sun amsa da to sun kama hanyar gida sun isa gida amma sunyi rashin sa'a domin kuwa basa nan, sun shiga tambayar security Ahmad ya dawo sun amsa su da a'a, hakan yayi matuqar d'aga hankalin su sosai musamman da layin sa bai ya tafiya. Sun qarasa ciki zaune kawai suke amma ba mai magana a cikin su, sun shiga nazari da tinanin ina Ahmad da *Adyan* suka shiga kuma mai ya saka layin Ahmad bai ya tafiya. Sun jima sosai a cikin wannan yanayin bugun k'ofar da a kai ne yasa dukansu suka kai kallonsu ga juna, da sauri Abbu ya tashi ya nufi k'ofa tare da bud'e wa ba tare daya tambaya ba, ya samu Jabir tsaye bakin k'ofa ya shiga tambayar sa mai ya amsa shi. "Ranka shidad'e a game da mai gida Ahmad ne ina nufin *Abban Adyan."* Cikin rawar murya har yana sarkewa yake amsa shi, "Jabir shin kun samu wani labari ne a game da Ahmad to jikana fa ina *Adyan.?"* "Sir dukansu suna tare da juna suna asibiti ne." "Asibiti kuma mai kuma ya faru dasu.?" "Sir abin shi ne *Adyan* sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi shi yasa suke asibiti." "Subhanalillah Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un abin da nake yiwa gudu kenan, yanzu fad'a min wani abu suna wace asibiti.?" "Am suna Saudat Care hospital." "Shikenan zaka iya tafiya." Ya amsa da to ya juya yayi tafiyarsa Abbu kuma ya dawo ciki tare da sanar dasu Abba abin da yake faruwa, dukansu sun shiga anbatar kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un cikin hanzari sun tashi dukansu sun nufi asibiti. Zaune yake yayin daya saka *Adyan* a gaba sai kallonsa yake kallo sosai, yana haka yaji a na buga masa k'ofa ya tashi ya nufi k'ofa ya bud'e ba tare daya tambaya ba, ya samu su Abbu tsaye a gefen k'ofa kallonsu kawai yake ba tare da yayi magana ba. Cike da d'aukin had'uwa da yaronta ta nufi ciki da sauri Ahmad ya dakatar da ita ta hanyar rufe k'ofar zata yi magana yayi saurin dakatar da ita yana cewa. "Baki da damar dake zaki had'uwa da d'ana to dan haka zaki iya tafiya." Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin sa sosai, "Yaya Ahmad wai mai kake fad'a ne haka taya ma kai zaka yi k'oqarin dakatar da ni daga ganin yarona? Hakan sam ba abu mai sauki bane a gareki dan haka ni ba zan iya amsa tayin ka ba. To kawai kayi hak'uri sannan kuma ba zan dakata daga ganin yarona ba wannan ce gaskiyar." "Da gaske wai ke kin damu a kan yaronmu? A'a ke sam baki wani damu a kan yaron ba, kamata yayi a ce yaron yana tare dake amma kuma sai kika za'bi da ki baiwa Afra shi sabo da wani dalili naki, da fari naso yaron ya kasance a tare da ni amma kika bani damar tabbacin cewar ke zaki kula da shi sosai. Na yarda dake sosai shi yasa ni na barki domin ki kula da shi sosai, amma kuma ke sam baki yi hakan ba kin barsa ya tafi tare da Afra duk da cewar kin san komai a game da yanayin sa. To sabo da sakacin ki shi ďin ya tafi ya buga wasan boll tare da sauran yara, dalilin da yasa yake cikin wannan yanayin kenan. Ahlam ke d'in nan ke ce wacce take da alhakin duka wannan sabo dake yanzu yaron bai ya cikin kyakkyawan yanayi, shi ďin yana kwance ba shi da lafiya kuma duka sabo da sakacin ki ne. To dan haka ni ba zan ta'ba baki damar da zaki ga yarona ba wannan shi ne hukuncin ki, kuma ni ba zan ta'ba canja wannan ba to yanzu zaki iya tafiya." Dukansu wani irin kallo suke yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, "Yaya Ahmad wai mai kake fad'a ne haka taya ma kake tinanin wai ni zan aminta da abin daka fad'a? A'a ni sam ba zan ta'ba amince wa hakan ba lallai ya zama dole ni ďin nan na had'u da yarona. Yaya Ahmad shin kai a tinanin ka ina farin ciki ne da yanayin da yaronmu yake ciki? A'a k'unci nake sabo da na damu sosai a kansa ni Ammie sa ce kuma shi ďin ďana ne wanda nake matuqar so sosai, ko yaushe buri na shi ne yaronmu yayi farin ciki sosai sannan ya samu duk wani abin daya ke so, hakama ina ta k'oqarin ganin na kasance uwa ta gari a garesa dan haka ka dena hukunta ni haka, ni sam ba zan iya d'aukar wannan hukuncin ba to dan Allah karka dakatar da ni daga ganin yarona please." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da take kuka kuma kuka sosai, amma hakan sam bai saka shi amma sa ba sai ma juya wa da yayi domin tafiya Abba ya dakatar da shi. "Ahmad karka cutar da ita har haka, sabo da ita sam ba zata iya d'aukan wannan ba to ya kamata ka daidai wannan dan Allah." "Abba ko zaku iya fita cikin wannan zancan dan Allah.?" "Amma Ahmad." "Abba dan Allah please." Abba zai qara magana Abbu ya dakatar da shi ta hanyar dafasa tare da girgiza masa ka a lamar a'a, sai kuma zuwa wannan lokacin ne Umma tayi magana. "Ahmad ka dena hukunta ta a kan zunubin da ni na aikata, Ahlam tayi ta k'oqarin dakatar da Afra daga fita da shi sai da nayi magana sannan ta barta suka tafi. Ahmad ita ďin bata aikata wani zunubi ba to dan haka babu dalilin da zai sanya ka hukunta ta, sannan kuma dukanmu a nan mun san cewa Ahlam tana matuqar qaunar *Adyan* sosai. Dukanku kuna qaunar juna sosai hakan abu ne mai kyau Ahmad to dan Allah ka bar komai ya wuce please." "Umma abin shi ne ita ta san komai a game da yaron wanda data sanar dake to da ke ma ba zaki aikata hakan ba. Umma koma dai mai zaku fad'a to ba zai canja gaskiyar ba Ahlam ita ce wadda take da alhakin duka wannan, dan haka ni ba zan bata damar da zata ga *Adyan* ba kuyi hak'uri dan Allah ku gafarce ni please." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya ya koma gurin yaronsa, su Ummi sun bisa da kallo cike da jin mamakin sa sosai yayin da kukan Ahlam yasa banta, su Umma sun shiga rarrashin ta Abba da Abbu sun shiga sun duba jikin sa hakama Ummi, yayin da Umma ta kasance tare da Ahlam ai kuwa kafin su ankara gurin ya fara ci kowa da mutane musamman 'yan siyasa mutanan su Abbu. Su Ummi sun kasance a nan har dare suna ta shirin tafiya gida amma Ahlam tak'i, sunyi iya yin su dan ganin ta tafi tare dasu amma tak'i dan dole suka tafi suka barta a nan, zaune take a kan kujeran dake gefen ďakin da *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin idanuwanta basu dena zubar da kwalla ba. Kukan yaron ne data ji yasa ta saurin tashi ta nufi d'akin amma ta samu k'ofar a rufe, ta shiga buga k'ofar tare da fad'ar sunan Ahmad. "Ahmad dan Allah ka bud'e k'ofar zuwa yanzu ya kamata na had'u da yarona ina buqatar hakan, Ahmad yaron kuka fa kuka yake to na tabbata yana buqata na sosai to dan Allah ka bud'e k'ofar please." Haka ta shiga yi masa magiya tana rarrashin sa har ta samu ya iya bud'e mata k'ofa, cikin hanzari ta shiga ciki ta nufi gurin *Adyan* yayin da take fad'ar sunan sa, tana isa inda yake tayi hugging d'in sa tana sunbatarsa shi ma sunan ta yake fad'a Ammie. Ahmad yana daga gefe sai kallonsu yake ya juya ya fita ba jimawa ya dawo tare da doctor, nan kuwa ya shiga duba sa abin farin cikin shi ne yana samun sauki sosai ya sanar dasu cewar yana samun sauki sosai sannan ya juya ya fita. "Rabin raina fad'a min mai zaka ci yanzu na tafi na kawo ma.?" "Appa ni kawai zansha madara." "Shikenan yanzu zan tafi na kawo ka ji ko." Ya d'aga masa ka tare da furta ok, ya tashi domin tafiya Ahlam ta dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa tare da fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad shin ko zamu iya yin magana yanzu dan Allah.?" Kallonta kawai yake daga bisani kuma ya jinjina mata ka a lamar eh, ya koma ya zauna ta nisa tare da jan numfashi ta qara da sauke a jiyar zuciya sannan ta fara magana. "Yaya Ahmad dan Allah kayi hak'uri a kan komai, eh gaskiyar ka ne duka wannan laifi na ne k'ila ni ban kasance uwa ta gari a gurin *Adyan* amma." Yayi saurin dakatar da ita ta hanyar rufe mata baki yana girgiza mata ka, "A'a Ahlam ba buqatar sai kin bada hakuri duk da cewar kin aika laifi, na san cewa kin damu a kan *Adyan* sosai sannan kuma ke uwa ta gari ce a garesa. Ahlam ni kawai na damu ne a kan yaronmu sabo da ba zan jure rasa shi ba, to dalilin da yasa ni aikata maki hakan kenan to ina fatan zaki fahimce ni sannan kuma ki yafemin dan Allah." "Yaya Ahmad kai kana da matuqar kirki sosai, ka kasance muji na gari a gareni kuma uba na gari a gurin yaronmu, Yaya Ahmad kai kayi abin daya dace to nice kai to abin da zanyi kenan, to sam ba buqatar ka bada hak'uri sabo da ba kayi komai ba to kawai ka manta ka ji ko." Ya jinjina mata ka lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin hugging d'in ta, ya qara da sunbatarta yana furta mata kalmar ina sanki ta amsa shi da ina qaunarka sosai, daga bisani kuma ya tashi ya fita domin kawo ma *Adyan* madara. Zaune kawai yake amma bai ya tare da farin ciki, Mamie ta shafi fuskarsa tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* shin qlau kake kuwa.?" Ya girgiza ka tare da furta mata, "a'a Mamie ni kawai na damu ne a kan abokai na *Adyan da Adeel.* Sabo da dukansu basa cikin kyakkyawan yanayi *Adyan* ba shi da lafiya sosai, *Adeel* kuma yana tare da k'uncin rashin Maman sa data mutu, gaskiya suna matuqar bani tausayi sosai kuma ni nayi matuqar damuwa sosai a kan dukansu." Mamie ta girgiza ka tare da jinjina sa daga bisani kuma ta amsa shi, "masoyi kai yaron kirki ne ka damu sosai a kan kowa shi yasa nake qara qaunar ka, karka wani damu insha Allah dukansu zasu kasance lafiya to ka dena damuwa ka ji ko." Ya d'aga mata ka a lamar to ta janyo sa jikin sa tare da sunbatarsa tana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona, ya amsa ta nima ina jin Mamie Appa yana daga gefe yana kallonsu yayin da yake wani lallausan murmushi abin birgewa sosai. Ya tashi daga inda yake tare da d'aukan *Alishart* ya nufi inda suke ya zauna tare da runguma dukansu. "Gaskiya ina farin ciki sosai da samun ku Allah yayi muku albarka, ina sanku sosai wallahi ina matuqar masifar qaunar ku sosai." Mamie ta amsa shi da Amin tana murmushi mai tare da dariya shi ma abin da yake kenan.............. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/13, 9:12 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 18* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 11/01/2022* *Time 05:45pm* *Typing..............* Ba jimawa sosai Ahmad ya dawo ya baiwa *Adyan* madara, wanda kuma shi da kansa ne yake ba shi a baki har ya k'oshi, bayan ya qarasa ya bud'e ledar daya shigo da ita ya ciro shawarma tare da fad'ar sunan Ahlam. "Ga wannan na san kina santa sosai sannan da akwai ice cream idan kin qarasa ci." "Na gode Mujina *Abban Adyan* to kai kuma mai zaka ci.?" "Madara kawai ta isa." "Shikenan zan had'ama." "ina godiya qanwata." Ya fad'a yana murmushi ita ma abin da take yi kenan. Ta tashi ta had'a masa madara ta sannan ta fara cin shawarma, bayan sun qarasa Ahmad ya sauke kallonsa ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adyan* abokin ka yana da kirki sosai dukansu biyun suna da kirki sosai, sunyi matuqar damuwa sosai a kanka *Adnan* ya bani wani sak'o yace na baka." Yasa hanu aljihu ya ciro photon da *Adnan* ya ba shi ya mai da kallonsa ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adyan Adnan* ne yace na baka wannan." Ya kar'bi photon sai wani kallon photon yake yayi murmushi tare da anbatar sunan Ahmad. "Appa ka kira layin sa ina san zan gode masa sabo da ya ceci rayuwata a yau ďin nan." Ya jinjina masa ka yana murmushi ya d'auki wayar sa ya shiga danna number dake jikin photon, zaune suke a kan tebur suna cin abinci lokaci d'aya wayar Papa ta d'auki ruri, cike da d'auki *Adnan* ya kai kallonsa ga Papa yayin da yake magana da zuciyarsa. "Allah yasa *Adyan* ne sabo da na damu sosai a kansa hakama ina fatan ya samu lafiya sosai." Papa ya d'aga wayar tare da sallama Ahmad ya amsa shi ya kuma ci gaba da magana. "Am kana magana da Ahmad Aliyu *Abban Adyan,* dan Allah ko zaka iya had'a ni da *Adnan Adyan* yana san zasu yi magana.?" "Allah sarki sannu Dr Ahmad ai na gane ka, ashe kai ne *Abban Adyan?* ai tin d'azu *Adnan* yake ta magana a kansa gaskiya ya damu sosai a kansa." "Eh nima naga hakan gaskiya yaronka yana da kirki sosai yau ya ceci rayuwar yarona, ina matuqar godiya garesa yanzu idan yana kusa ka ba shi wayar suyi magana." Ya amsa shi da to yana murmushi ya mai da kallonsa ga *Adnan* tare da ba shi wayar, cikin hanzari ya kai hanun sa ya kar'bi wayar tare da sallama. Appa ya amsa shi sannan yaci gaba da magana, "sannu *Adnan* fatan kana lafiya dama ina san nayi ma godiya ne." "A'a Uncle karka yi dan Allah, kawai ka had'a ni da *Adyan* muyi magana." "Shikenan amma ni sunana Appa ne ba Uncle ba ka ji ko." "Eh Appa." "Yauwa yaron kirki to ga abokin ka." Ya amsa da to yana murmushi Ahmad ya baiwa *Adyan* wayar, ya kar'ba yana murmushi tare dayi masa sallama ya amsa shi ya kuma ci gaba da magana. *"Adyan* to ya jikin ka fatan kana samun sauki sosai? Ni na damu sosai a kanka ina fatan ka samu lafiya cikin sauri sosai." *"Adnan* kai kana da kirki sosai, ni ina samun sauki sosai na gode daka taimake ni ina matuqar yima godiya sosai." "A'a *Adyan* karka yi man godiya sabo da ni nayi abin daya dace ne, sannan kuma bani kad'ai nayi hakan ba har da *Adeel* shi ma ya taimaka sosai. To ba buqatar kayi godiya ka ji ko kawai dai ka kula sosai Allah ya baka lafiya Amin." "Na gode sosai amma zaka zo ka duba ni ko? Sannan kuma waye wannan *Adeel* da kake magana a kansa ni sam ban gansa ba.?" *"Adyan Adeel* yana da kirki sosai amma ya riga daya tafi sabo shi ďin a Bauchi yake da zama." "Allah sarki gaskiya naso a ce na had'u da shi amma ba komai zanci gaba dayi masa fatan alkhairi na har abada." "Karka wani damu aboki na dukanmu zamu qara kasancewa tare da juna insha Allah, sannan kuma zan shigo domin na duba ka zamu zo dukanmu ni Papa Mamie *Afnan* da kuma *Alishart."* "Ina farin ciki da ganin dukanku tare da fatan sake had'uwa da *Adeel* kamar dai yanda ka fad'a." Haka dai suka ci gaba da magana a waya na tsayin wani lokaci sannan daga bisani suka yi sallama, ba jimawa sosai da gama wayar daga bisani *Adyan* ya koma barci bayan wani lokaci su Ahlam suka kwanta barci, washe garin ranar su *Adnan* suka shiga ganin sa *Adyan* yayi matuqar farin ciki da hakan sosai hakama su Ahlam. *Adyan* ya samu kwana biyar asibiti sannan ya samu sallama zuwa gida, wanda kuma babu wata rana wadda *Adnan* bai ya zuwa duba shi, hakan yasa suka yi matuqar shak'uwa da juna sosai hakama iyayen su. Su Ahmad sun samu wata biyu gida sannan suka koma k'asar England, inda kuma zumunci yaci gaba da kasancewa a tsakanin *Adyan da Adnan,* ko yaushe suna tare da juna a waya musamman ma video call sunfi yin sa. Wata rana zaune yake yayi wani zugum sai nazari yake *Afnan* ta dafasa tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* qlau kake fad'a min mai ya saka kazo nan ka zauna shin da akwai matsala ne.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, *"Afnan* ni kawai na damu ne a kan wasan boll ďin da za a yi gobe, *Afnan* ni nayi wasu Papa alkawarin ba zanyi wasan boll ba, ga shi kuma Uncle ya saka ni a ciki *Afnan* ni ban san ya zanyi ba dan Allah ki fad'a min ya zanyi please.?" *"Adnan* ba buqatar ka damu sosai har haka sabo da ina nan kuma zan kula da komai, ni zanyi wasan a madadin ka sannan kuma kai ne wanda za a baiwa kyautar nayi alkawari insha Allah." *"Afnan* hakan yana da matuqar hatsari sosai to ni ba zan barki ki aikata hakan ba. Sabo da idan a ka kama ki to zaki shiga matsala sosai wanda ni kuma sam ba zanso hakan ba, *Afnan* ke ce qawar dana fi so to ba zan ta'ba saka ki a matsala ba nayi alkawari insha Allah." *Adnan* nima abin da nake koqarin fad'a maka kenan, kai ne abokina wanda nafi so to ba zan barka a matsala ba, bayan kuma ina da damar da zan taimake ka, dan haka ni zanyi wasan kuma idan ka dakatar da ni to fa zanyi fishi sosai." "Amma *Afnan* taya hakan zata kasance bayan kuma ke macace? Ni fa ina jin tsoro sosai sabo da ba zan iya yafe wa kai na ba idan har wani abu ya faru dake, *Afnan* dan Allah karki yi kinji ni zan kula da komai please." "Sam karka wani damu a kai na sabo da zan kula da komai ta yanda ba wanda zai gane ni, kuma kai ma zaka ga hakan to zaka iya yarda da ni please." Magana take cikin kyakkyawan shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai yayin ya gagara furta mata komai, sun jima a nan zaune daga bisani kuma suka tashi suka koma class d'aukan darasi. Hakan kuwa ta kasance a ranar wasa *Afnan* ce ta canji *Adnan* ba kuma tare da wani ya gane ba, sabo da tayi shiga irin ta maza to kuma cika wa *Adnan* alkawari, domin kuwa shi ne wanda ya kar'bi kyauta kamar dai yanda ta fad'a. A lokacin da za a ba da kyauta ta fice *Adnan* ya shigo ya kar'bi kyautar, hakan yayi matuqar yi masa dad'i sosai bayan sun bar gurin ya shiga yi mata godiya, kallonsa kawai take tana murmushi ba tare data furta masa komai ba hakan kuma taci gaba da kasancewa, a duk lokacin da za a wasan boll gudu ko wani wasa mai wahala to *Afnan* ce take shiga a matsayin *Adnan.* Hakan yasa *Adnan* ya tara kyautuka masu yawa sosai, yayin da shak'uwa ta qara shigarsu biyun inda suka kasance tamkar twin's, tare suke koman su barci ne kawai yake raba tsakanin su, hakama tsakanin *Adnan da Adyan* qawan can su yana dad'a girma sosai, inda suka kasance abokai na gari ga juna yayin da suke ta fatan sake had'uwa da *Adeel* bayan shekara goma sha biyar. Zuwa wannan lokacin duka yaran sun girma sosai, zuwa yanzu *Adnan* yana matsayin Barrister ne yayin da Papa yake matsayin alqali. Hakama *Adyan* shi ma ya gaji iyayen sa ya zama Doctor a can gurin *Adeel* kuwa yana aiki a company Dadyn sa, dukansu suna cikin kyakkyawar rayuwa abar so suna farin ciki sosai wata safiyar litinin. Tsaye suke suna shirya tebur da kayan abincin break past suka ji a na buga masu k'ofa, *Alishart* ce wadda ta tafi domin ta bud'e k'ofar ta bud'e ba tare data tambaya ba, ta samu *Afnan* tsaye bakin k'ofa lokaci d'aya suka sakarwa juna murmushi. "Sannu da zuwa Aunty shigo ciki." Ta amsa da to tana murmushi sun dawo ciki tare sun samu Mamie zaune a parlour, sun qarasa inda take sun zauna *Afnan* ta shiga gaishe ta bayan sun gaisa taci gaba da magana. "Mamie ya kuma nake ganin ku biyu kawai? Ina Besty na karki fad'a min cewar bai tashi ba.?" Sunyi murmushi sosai dukansu kafin Mamie ta amsa ta sai ga Papa ya sauko, sun shiga yi masa sannu da fitowa ya amsa yana murmushi bayan sun gaisa Papa ya shiga tambayar *Adnan* Mamie ta amsa shi. *"Adnan* yana ciki bai fito ba ina jin ko yau ba shi da shiga office shi yasa." Papa ya girgiza ka yana murmushi kafin ya furta komai *Afnan* tayi masa rigagi. "Ka ji ko Papa muntuna talatin muke da shi amma kuma shi har yanzu barci yake, shikenan zan same sa domin na tunasar da shi abin da yake gaban mu." Tana kai k'arshen maganar ta ta tashi ta nufi bedroom d'in *Adnan* su Mamie sun bita da kallo suna murmushi mai tare da dariya............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/14, 12:31 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 19* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 12/01/2022* *Time 08:38pm* *Typing............* Kwance yake a kan makeken gadon sa ya rufe jikin sa da wani lafiyayyen bargo, duk da cewa barci yake amma kuma fuskar sa wani kyakkyawan murmushi take fitarwa. Sannu a hankali take turo k'ofar har ta bud'e ta shiga ciki tare da rufe k'ofar, tayi tsaye jikin k'ofa sai wani kallonsa take kallo sosai tana wani lallausan murmushi. Sannu a hankali take tafiya tana sand'a tamkar da zata yi zata har ta isa inda yake, ta zauna gefen gado wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonsa take, ta kai hanun ta ga fuskar sa ta shafi fuskarsa zuwa kansa tare da hura masa iska a kunne, ta qara da sunbatarsa a ka da ma gefen fuska ha!!! Ya nisa sosai tare da jan numfashi, yana wata miqa idanuwan sa a rufe yake magana. "Irin wannan tashin barci haka gaskiya yana da matuqar dad'i sosai, to amma mai ya saka ke kika tashe ni daga barci.?" Magana yake cikin wata lallausar murya mai dad'in sauraro, yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa ga wanda ya gani, hakan yasa ta rufe sa da ido tana kallonsa kallo sosai ba tare data furta masa komai ba. Jin shirun yayi yawa ne yasa shi bud'e idanuwansa sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e, lokaci d'aya yayi tozali da kyakkyawar faskar ta wadda take d'auke da wani lallausan murmushi. "Waw Besty na wallahi kinyi matuqar masifar yin kyau sosai, gaskiya ke kyakkyawa ce sosai sannan kuma a kullum kuma a ko yaushe kyanki qara fita yake kin san me.?" "Kafin ya furta komai tayi saurin dakatar da shi ta hanyar rufe masa baki. "Ya isa haka ka tashi ka shirya lokaci ya tafi sosai karmu makara, mintuna ashirin ne kawai suka rage mana zan had'a maka ruwan wanka yanzu." Ya fara sunbatar hanun ta da yake kan bakinsa sannan ya janye hanun yaci gaba da magana. "Fad'a min wani abu shin shi alqalin ya isa koton ne ko dai har yanzu yana gida.?" "Na barsa a parlour amma zai iya yuwa zuwa yanzu ya fita." "A'a ba zai yu ya fita ba sabo da har yanzu muna da sauran lokaci, Besty Papa ya qara mana awa d'aya dalilin da yasa har yanzu nake kwance kenan." "Besty to amma mai ya saka baka sanar da ni hakan ba? Ai dana kwanta a k'alla ko na muntuna talatin ne shikenan ka kyauta." "Ke karki yi fishi har yanzu kina da damar da zaki kwanta zo nan mu kwanta na muntuna talatin kawai." Ya janyo ta zuwa gado tare da kwantar da ita ita kuwa sai wani kallonsa take. "To kawai kiyi barcin ki idan lokaci yayi ni zan tashe ki kinji ko." "Besty wani zai iya shigo ya ganmu a haka to ya kamata na tafi." "Shikenan jeki kawai ki tafi." Ya fad'a tare da juya mata baya ita kuwa sai wani kallonsa take kallo sosai ta anbaci sunan sa amma bai amsa ba, "Besty dan Allah karka yi fishi da ni please." "Mai ya saka har yanzu kike kwance a nan kawai ki tafi." "Ba zan tafi ba." Ta fad'a tare da juyo fuskar sa sun fuskanci juna sai wani kallonsa take kallo sosai, shi ma haka kallonta yake kuma kallo sosai sun jima a haka ba kuma tare da sunji sun gaji ba. "Besty na shin wai kai kana fishi da ni har haka.?" Ya girgiza ka tare da furta a'a, "to mai ya saka ka ce dani na tafi.?" "Sabo da na ga ke sam baki da buqata da ki kwanta a tare da ni." "Besty ni bawai bani da ra'ayi a kan mu kwanta tare bane, a'a ni kawai ina jin tsoro ne sabo da Mamie zata iya shigowa ta riskemu a haka ko kuma *Alishart* amma kayi hak'uri dan Allah ka yafemin please." Da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata ka, "a'a Besty na dan Allah ki dena bani hak'uri sabo da baki yi komai ba, ni kawai na ji wani iri ne sannan kuma naji ba dad'i amma hakan sam bai ya nufin cewar ina fishi dake, Besty ni ba zan ta'ba yin fishi dake ba na har abada nayi alkawari to zaki iya yarda da ni kinji ko." Tayi murmushi sosai mai tare da dariya lokaci d'aya ta samu kanta da shafar fuskarsa tare da sunbatarsa a ka. "Na gode sosai Besty na yanzu bara na had'a maka ruwan wanka sabo da lokaci ya tafi sosai." Ya jinjina mata ka yana murmushi wanda kuma hakan ne ya hana masa iya fad'ar komai, ta tashi ta nufi toilet shi kuwa ya bita da kallo yana murmushi, bayan wani lokaci ta fito tare da sanar da shi cewa ruwan ya had'u ya amsa da to yana murmushi. Ya tashi ya shiga toilet ita kuma ta gyara masa d'aki sannan ta fice daga d'akin. Ta fito ta samu su Papa a parlour suna ta fira abinsu ta zauna Mamie ta shiga tambayar *Adnan,* "Mamie da kyar na samu ya iya tashi yanzu dai ya shiga wanka." *"Afnan* da baki tashe sa ba sabo na na qara masa lokaci wanda nake tinanin zai ishe sa." "Eh haka ya fad'a min bayan na tashe sa." "Shikenan hakan ma daidai ne." Bai wani jima ba ya fito ya shirya cikin wata kyakkyawar shiga ta qananan kaya, shigar tayi matuqar amsar sa sosai sai wani k'amshi yake mai dad'in shaqa ya d'auki rigar aiki da hula tare da takardu ya fita. Ya fito ya same su a parlour sai fira suke cikin raha wasa da dariya ya tafi ya zauna, bayan sun gaisa sun tashi sun nufi tebur domin suyi break past. Sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa su Papa sun fita zuwa office, Papa ya fara a jiye *Alishart* school sannan ya nufi kotu. Zaune take tana danna waya ga a lama charting take Abban ta ya fito ta shiga yi masa sannu da fitowa, ya amsa yana murmushi tare da sanya mata albarka yaci gaba da magana. *"Amna* ina Maman ki.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi. "Abba tana bedroom ďin ta sannan kuma bata cikin kyakkyawan yanayi, ka riga da ka san komai a game da damuwar ta tana cikin k'unci sosai. Nayi ta k'oqarin kwantar mata da hankali amma daga k'arshe sai ta buqaci dana barta ita kad'ai, Abba bani da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa dole nazo nan na zauna." Yayi shiru yana nazari tare da girgiza ka daga bisani ya juya ya nufi bedroom d'in Mama. Zaune take jikin gado yayin data saka photon twin's da ma kayan su a gaba tana kallo, ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. tana cikin wannan yanayin Abba ya turo k'ofa ya shigo sai wani kallonta yake ya isa inda take ya zauna, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake cikin kwantar da murya yake magana. "Maman twin's wai har tsayin wane lokaci zaki d'auka kina tare da wannan k'uncin? Abida wannan yanayin naki yana matuqar cutar damu sosai musamman ma *Amna.* Abida nima nayi matuqar damuwa sosai a kan twin's kawai dai hak'uri nake ina dannewa, Abida Allah shi ne wanda ya aiko mana da kaddaran rasa twin's sannan kuma ya bamu *Amna* a matsayin 'ya. Abida yarinyar mu tana matuqar buqatar ki sosai tana buqatar kulawar ki da kuma soyayyar ki gaba d'aya, Abida dan Allah ki bamu damar da dukanmu zamu rayuwa cikin farin ciki sosai please." Magana yake yana rarrashin ta cikin kasa-kasa da murya tare da tautasa take magana. "Abban twin's taya zanyi farin ciki ba tare dana san halin da yarana suke ba? Yaya Anas yau tsayin shekaru ashirin da uku kenan na d'auka ba tare da yarana na, Yaya Anas ni kawai na damu ne a kansu suna ina a wane irin hali ko yanayi suke ciki? Shin har yanzu suna tare da mutanan da suka sace su ko a'a shin har yanzu suna raye ko sun mutu? Abban twin's wallahi tallahi wannan tinanin yake hana ni sake wa nayi farin ciki, sabo da ni na damu sosai a kansu domin kuwa har yanzu su ďin yarana ne kuma ina sansu sosai. Hakama nayi matuqar farin ciki sosai da samun *Amna* na aife ta a lokacin da banyi tsammani ba, wallahi ina farin ciki sosai da samun ta amma kuma hakan ban saka ni mantawa da twin's ba. Sabo da ina sansu sosai ina matuqar masifar qaunar su sosai, ina fatan na sake had'uwa dasu ko da sau ďaya ne a rayuwa ta." "Nima ina fatan hakan." Ya fad'a tare da rungumata jikin sa yana rarrashin ta daga bisani kuma suka tashi suka fita zuwa parlour, *Amna* ta shiga yi musu sannu da fitowa sun amsa suna murmushi Abida ta anbaci sunan ta taci gaba da magana. *"Amna* kiyi hak'uri da yanayi na ni kawai na damu ne a kan yayyan ki, *Amna* yanzu tsayin shekaru ashirin da uku kenan bama tare ban kuma san komai a game dasu ba, *Amna* hakan yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai. Ina fatan na sake had'uwa da twin's sabo da ahalinmu ya qara ciki ta yanda zamu rayu cikin farin ciki sosai." "Mama nima ina fatan had'uwa dasu ban san suba amma kuma ina tare da soyayyar ina qaunar su sosai." Tayi mata murmushi tare da sunbatarta yana furtamata Allah ya maki albarka, ta amsa da Amin tana murmushi mai tare da dariya bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin suyi break past. Bayan sun qarasa Abba ya nufi office hakama *Amna,* Abida kuma tashi tayi ta koma bedroom tana cikin yiwa yara darasi wayar ta ta d'auki ruri. Duk da cewar ta san mai kiran ta amma bata d'aga ba, taci gaba da yiwa yara darasi bayan ta qarasa ta fita sannan ta shiga kiran layin sa, sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ya d'aga ba kuma tare daya furta mata komai ba, tayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* shin wai kai kana fishi da ni ne.?" Shiru bai amsa ta ba jin shirun yayi yawa yasa taci gaba da magana. *"Adeel* mai yasa ba zaka amsa ni ba? Dan Allah kayi min magana ka ji please." Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa ta. "Ni ban san cewar ke baki da lokaci na ba shi yasa na kira layin ki, amma yanzu na fahimci komai shi yasa ba zan sake kiran ki ba sai an jima." Yana k'oqarin kashe wayar tayi saurin dakatar da shi, "a'a *Adeel* dan Allah karka kashe wayar ka d'an saurare ni mana, tabbas na ga kiran ka amma kuma a lokacin ina yiwa yara darasi shi yasa, to ina fatan yanzu zaka fahimce ni sannan kuma kayi min uzuri dan Allah." Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "shikenan amma da sai kiyi min ko da text ne ta yanda zan iya fahimtar ki amma kuma sam baki yi hakan ba, shikenan ba komai ya wuce yanzu fad'a min ya kike.?" "Gaskiya bana cikin kyakkyawan yanayi sabo da kai kana fishi da ni kuma fishi sosai." *"Amna* ni sam bana fishi dake kawai dai naji wani iri ne da baki d'aga kira na ba, amma yanzu komai ya wuce to kawai kiyi farin ciki kinji ko." "Shikenan masoyi ina godiya da kai ka iya fahimta na to miye labari.?" "Ke ce labari na nayi kewarki sosai rashin ki ba dad'i, gaskiya ina san ganin ki sosai ya kamata na shirya zuwa gareki, amma fad'a min wani abu shin ke kinyi kewata kuwa.?" Tayi murmushi sosai tare da girgiza ka ta qara da jan numfashi, tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi. *"Adeel* wallahi ba zan iya sanar da kai irin yanda nayi kewarka ba, sabo da abin yana da matuqar girma sosai nake kewarka sosai. Yanzu fad'a min yaushe zaka zo gareni.?" "Karki wani damu sabo da abin da nake ta shiri kenan, zanzo inda kike nan kusa kuma kusa sosai insha Allah." "ina farin ciki da zuwan ka rabin raina zan fara shirin zuwan ka tin a yau ďin nan." Kafin ya furta komai sai ga Dadyn sa ya shigo yayi sallama da ita tare da fad'ar sunan Dady. "Sannu da zuwa Dady." "Yauwa rabin raina kana tare da sirika ta a waya.?" Yayi murmushi sosai mai tare da dariya sannan ya amsa shi, "eh Dady nayi kewarta sosai ina san na tafi gurin ta." Dady ya shafi fuskarsa zuwa kansa tare da hura sannan ya anbaci sunan sa. *"Adeel* hakan yayi kyau sosai idan ka shirya tafi sai ka sanar da ni ka ji ko." "Na gode sosai My lovely Dad ina sanka Dady na." "Nima ina qaunarka ďana kai ne d'an daya fi kowa zo nan ďana." Ya fad'a tare da janyo sa ya runguma shi jikin sa yana sunbatarsa, sun jima a haka sannan ya sake sa ya anbaci sunan sa yana cewa. "Rabin raina lokacin tafi gida yayi ta idan ka shirya mu tafi. Ya amsa da to yayi shirin tafiya sun fice bayan kwana biyu da dare *Adeel* ya bud'a durowa komai zai d'auka oho, Allah ya kai hanun sa ga wata 'yar k'aramar jaka ya d'auki jakar ya koma kan gado ya zauna tare da bud'e jakar. Ya ciro photo na masu yawa yawancin photo nan shi da Dadyn sa ne, sai wasu d'aid'ai ku da suke su uku shi Dadyn sa da kuma wata mata, wacce bai santa ba duka photo nan yana yaro ne sosai haka yaci gaba da kallon photo nan har ya gama, yaci gaba da kallon photon wannan matar kallo sosai yayin da yake magana da zuciyarsa. "Wacece wannan matar ko dai ita ce Mama na? To amma idan ita ce Mama na mai ya saka Dady na bai ta'ba nuna min photon ta ba mai yasa kuma mai hakan yake nufi? Lallai ya kamata nayi magana da shi domin ina san na san wacece wannan matar.?" Ya d'auki photon tare da tashi bai qarasa k'ofa ba sai ga Prof ya shigo yayi tozali da photo nan da suke watse a kan gado, ya wani zaro ido yana kallon photo nan sannan ya dawo da kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa........ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/15, 12:56 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 20* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Thursday 13/01/2022* *Time 10:22pm* *Typing................* *"Adeel* mai kake yi ne haka mai ya saka ka d'auko wannan.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa mashi, "Dady wacece wannan matar ko dai ita ce Mama na.?" Da sauri ya kar'bi photon daga hannun sa sai wani kallon photon yake kallo sosai, ya nisa sosai tare da jan numfashi yayin da yake magana da zuciyarsa. "Ka gafarce ni *Adeel* domin kuwa ni sam ba zan iya sanar da kai asalin gaskiyar ba, domin idan har ka san gaskiyar to tabbas zaka buqaci had'uwa da ita, ni kuma ban shirya rabuwa da kai ba, sabo da kai ne abin da nafi so fiye da komai a rayuwa ta. Dan haka ya zame min dole dana 'boye maka gaskiyar na har abada." Sunan sa ne da *Adeel* ya fad'a da k'arfi tare da dafasa yasa shi dawo wa daga duniyar tinanin sa, ya d'ago fuskarsa tare da kai kallonsa garesa ba tare daya amsa ba, *Adeel* kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai daga bisani kuma yaci gaba da magana. "Dady wacece wannan matar shin ita ce Mummy na.?" Da sauri ya shiga girgiza masa ka tare da furta, "a'a ďana wannan ba Mummyn ka ba ce, wannan wata ce daban ita ďin kamar qanwa take a guri na amma yanzu bata nan, to sam ba buqatar ka damu sosai a kanta ka ji ko dare yayi to ya kamata ka huta." "Dady ni nayi tinanin cewar ita d'in Mummy na ce, lokaci d'aya na fara santa yanzu kuma kana fad'a min cewar ita ba Mummy na ba ce, sai naji wani iri sosai k'unci na ya qaru sosai amma zanci gaba da jurewa kamar ko yaushe." Magana yake cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa sosai ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, cike da jin tausayin Prof ya janyo sa jikin sun tafi sun zauna ya wani rungumasa jikin sa yana rarrashin sa. Sai wani lalla'basa yake yana ba shi magana sun jima a nan tare sannan daga bisani ya tashi ya nufi d'akin sa, Dady ya bisa da kallo cike da jin tausayin sa sosai a tare da shi da ma zuciyarsa. Bayan tafiyar sa Prof ya mai da kallonsa ga photon da suke kan gado sai wani kallon photon yake yayin da yake magana da zuciyarsa. "Aisha ina fatan ba zaki koma dawowa rayuwar mu ba, ban sani ba zuwa yanzu ko kin samu lafiya ko a'a, to koma dai miye ba zan ta'ba bai wa yarona damar da zai had'u dake ba na har abada. Wanda wannan dalilin ne yasa ma ni na fad'a masa cewar kin mutu ta yanda bama zai nai meki ba, amma kuma yanzu kina nai ma ki shiga rayuwar sa ni zanyi komai domin na kare ďana wannan alkawari ne." Ya kwashe photo nan ya mayar cikin jaka ya tafi ya a jiye jakar gurin da take, ya juya ya nufi toilet yayi wanka ya fito yayi shirin kwanciya ya tafi ya kwanta. *Adeel* kuwa ya shiga d'akin sa yayi zaune jikin gado sai tinani yake iri daban-daban, ya nisa sosai tare da jan numfashi yana magana da zuciyarsa. "Ni sam na kasa yarda da abin da zuciyata take fad'a min a game da wannan matar, wacece ita mai yasa Dady zai yi photo da ita kuma a tare da ni, sannan kuma yana rungume da ita a jikin sa amma ya fad'a min cewar ita d'in qanwarsa ce, to ina fatan gaskiyar ya fad'a min ta yanda ba zanyi zargin sa ba." Ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin shigar kayan barci ya kwanta, amma sam ya gagara barci ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin *Amna* ba jimawa ta d'aga, sunci gaba da waya na tsayin wani lokaci sosai sannan suka yi sallama suka kwanta. Bayan kwana biyu ya fara shirin tafiya jigawa gurin *Amna* yayi duk wani shirin sa ya kama hanyar, da yamma lis ya isa garin jigawa kai tsaye gidan su *Amna* ya nufa. Zaune suke a parlour suna fira yayin da *Amna* take ta aikin kallon agogo da k'ofa, tana ta takun jiran zuwan masoyin ta lokaci d'aya suka ji a na buga masu k'ofa, cike da d'auki take anbatar sunan sa ta tashi cikin hanzari ta nufi k'ofa tare da bud'e wa ba tare data tambaya ba, ta samu *Adeel* tsaye a gefen k'ofa cike da d'aukin ganin sa take anbatar sunan sa tare da yin hugging d'in sa. "Sannu da zuwa rabin raina." Ta fad'a tare da sunbatarsa a gefen fuska shi kuwa sai wani kallonta yake yana murmushi mai tare da dariya, ita ma haka murmushi take sosai sun jima a haka sannan daga bisani suka shiga ciki. Abba da Mama sun shiga yi masa sannu da zuwa kasancewar dama suna da sani da shi. Ya amsa tare da gaishe su cikin girmamawa bayan sun gaisa Abba da Mama sun tashi sun shiga ciki, bayan tafiyar su *Amna* ta tashi daga inda take ta koma kujeran da yake zaune ta zauna kusa da shi kusa sosai. Shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai yayin da yake jin tana birgesa matuqar birgewa sosai, ya kai hanun sa ya shafi fuskarta tare da sunbatarta a ka cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "masoyiya nayi kewarki sosai ba kiji ba wallahi abin ba dad'i sannan kuma da k'una sosai tin da muka kammala karatu kika dawo gida sai komai nawa ya tsaya, *Amna* ke ce jigona kin taimaki rayuwa ta sosai, *Adnan* wanda ya fara d'ora ni a kan hanya ke kuma kika qarasa, *Amna* ke ba kawai abar qauna ta ba ce a'a ke malama ta ce kuma ni ina alfahari da hakan sosai. Da badan na had'u dake ba k'ila da har yanzu ban samu damar dana sauke Al'qaur'an ba, amma sabo dake na sauke na kuma san wasu daga cikin littafai shi yasa a ko yaushe nake alfahari dake. *Amna* na fad'a ko a'a amma gaskiyar ita ce ke alkhairi ce a gareni da kuma rayuwata gaba d'aya shi yasa nake matuqar masifar qaunar ki sosai, *Amna* ina sanki sosai irin san da ba zan qara mafarkin yiwa wata 'ya mace ba na har abada. To ina fatan zaki amince da aure na duk da kasancewa ta d'alibin ki kuma wanda bai san komai ba, *Amna* yanzu fad'a min wani abu shin ke zaki aure ni.?" *"Adeel* a rayuwa kowa yana da nasa anfani kai ma ka taimaken da dama fiye da abin da ni nayi ma, babban abin daka bani wanda yafi komai a gareni shi ne soyayyar ka kai ka so ni da gaba d'aya zuciyar ka. *Adeel* to wannan ma kawai ya isa to ba buqatar kaci gaba da gode min to kawai ka dena, daga k'arshe kuma ni *Amna Anas* na amince da kai a matsayin mujin da zan aura insha Allah, ina sanka *Adeel* wallahi ina matuqar masifar qaunarka sosai fiye ma da yanda nake sanka to zan aure ka insha Allah." "Na gode *Amna* na gode sosai." "Godiya kuma to a kan me.?" "A kan komai." Murmushi kawai tayi masa ba tare data furta masa komai ba sai daga bisani ta anbaci sunan sa. *"Adeel* ko zaka dena wannan yawan godiyar dan Allah.?" Kallonta kawai yake yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi, ita ma abin da take yi kenan bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin suci abinci. Sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa suka tashi suka fita zuwa wani guri daban, wanda ya d'auke su na tsayin wani lokaci sai dare sannan suka dawo gida. *Adeel* ya samu tsayin kwana hud'u sannan ya koma gida, *England* Zaune yake yana dannar waya yaji a na buga masa k'ofa daga ciki ya amsa da shigo, sannu a hankali take turo k'ofar har ta bud'e ta shigo tare da isa inda yake ya a jiye wayar tare da kai kallonsa gareta. "Ki zauna." Ta amsa da to ta zauna yaci gaba da magana, "mai yake tafe dake? Amma ki fara da fad'ar sunan ki." Magana take cikin wani irin yanayi na rashin lafiya, "am sunana Ahlam." Kafin ta qarasa ya sauke mata tafi cike da 'bacin rai yake magana. "Ke har kinma isa ki shigo har cikin office d'ina sannan ki zagen? Ki bar nan tashi ki fita tashi man ko baki ji bane nace ki bar nan." Magana yake cikin fishi sosai cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. "Doctor wai a kan me kake magana yaushe ni na zageka? Ni kawai nayi abin daka fad'a ne ka tambayi sunana na kuma amsa ma da Ahlam amma." Saukan marin data koma ji ne yasa ta yin shiru, "nace ki tafi to mai ya saka har yanzu kike zaune a nan kawai ki tafi ki bar nan." Ya fad'a tare da buga tebur ďin da yake kusa da shi magana yake cikin fishi sosai, wanda har waje a na jiyo ihun sa nurse ďin dake wajen office ďin sa sun shiga ciki dan ganin abin da yake faruwa. Sun same su suna ta sa in sa Jams ya fita da sauri ya nufi office ďin Appa ya sanar da shi abin da yake faruwa, da sauri ya tashi sun dawo tare sun kuma samu har zuwa wannan lokacin fad'a yake da ita. *"Adyan* mai yake faruwa ne a nan.?" "Appa ni ina ta k'oqarin ganin na taimake ta amma ita kuma zagina take, shi yasa nace ta tafi kuma tak'i sai ganin laifi na take sabo da na mare ta." Cike da firgicin abin daya fad'a Appa yake magana. *"Adyan* wai mai ka aikata ne haka taya ma har zaka yi tinanin marin ta? Sam bai kamata kai kayi hakan ba amma har yanzu kana da dama to kawai kai ka bata hak'uri ka ji ko." Wani irin kallo yake yiwa Appa mai cike da jin mamakin sa sosai ya girgiza ka yana cewa. "Appa taya ma wai kai zaka fad'i haka? Ita fa Ammie na ta zaga amma kuma duk da haka sai kake tinanin cewar ni zan bata hak'uri, a'a ni sam ba zan ta'ba hak'uri ba da a ce ita ďin bata zagi Ammie na ba to da duka wannan bai faru ba." "Shikenan karka bani hak'uri amma ka sani zanyi k'aran ka to kawai ka shirya wa hukuncin ni zan tafi." Ta juya zata tafi yayi saurin dakatar da ita ta hanyar rik'o hanun ta yana cewa. "Wai ke barazana kike yi man? Kin kuwa san da wanda kike yiwa barazana shin kin san da wanda kike tsaye gaban sa a yanzu? To ki sani barazanar ki ba zata yi wani tasiri a tare ni ba, idan har a game da Ammie na ne to a shirye nake da d'aukan ko wane irin hukunci to yanzu zaki iya tafiya." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake mata hanu tana k'oqarin tafiya Appa ya dakatar da ita ta hanyar shan gaban ta yana cewa. "A'a dan Allah karki yi ni zan baki hak'uri a madadin sa shin hakan ya maki.?" Da sauri *Adyan* yace, "a'a Appa hakan ba zai faru ba ni ba zan ta'ba barin kai ka aikata hakan ba to ni zanyi zan bata hak'uri." Nan kuwa ya shiga bata hak'uri ya kuma qara da cewa, "tabbas wata rana sai kinyi matuqar nadama sosai a kan hakan, na tabbata ranar zata zo kuma zaki fad'i a kan qafata sannan kuma ki bani hak'uri, to yanzu zaki iya tafiya sannan kuma ki jira zuwan ranar kinji ko." "Taya ni zan tafi ba kuma tare daka duba ni ba, zan tafi ne kawai idan har kai ka duba ni." Sam bai iya amsa ta ba sai ma juya wa da yayi ya fice daga office ďin, Appa ne wanda ya duba ta tare da qara bata hak'uri sannan ta tafi, bayan tafiyar ta shi ma tashi yayi ya nufi gida domin yana da tabbacin cewa yaronsa yana gida. Tsaye take tana shirya abinci a kan tebur lokaci d'aya taji a na buga mata k'ofa cike da d'auki ta nufi k'ofar tare da bud'e wa, ta samu Appa tsaye a gefen k'ofa sun rungumi juna tare da sunbatar juna sannan ya shiga ciki. Kai tsaye bedroom d'in *Adyan* ya nufa da sauri har yana gudu yayin da bakin sa yake fad'ar sunan sa, cike da firgici da rud'ani tare da jin mamakin Ahlam ta isa inda yake tana fad'ar sunan sa.............. *BY B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/16, 12:26 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 21* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 14/01/2022* *Time 07:10pm* *Typing................* "Yaya Ahmad wai mai yake faruwa ne ina *Adyan.?"* Wani irin kallo yake yi mata mai cike da jin mamakin abin da ta tambaya. "Ahlam karki fad'a min cewar *Adyan* bai ya gidan nan.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh, "miye to yana ina wane gun ya tafi kuma? Hakan yana nufin cewar yayi fishi sosai, *Adyan* mai ya saka ba zaka fahimci abin da nake nufi ba? Ni kawai bana san ka shiga a matsala ne amma kuma kai sam ka gagara fahimta na. Yanzu kana ina ya kamata na had'u da kai to amma kuma ban san inda kai ka tafi ba, *Adyan* kana ina? Dan Allah ka dawo gareni sannan kuma ka dena fishi da ni haka." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Ya ciro wayar sa ya shiga kiran layin sa sai dai kuma yayi rashin sa'a domin kuwa zuwa wannan lokacin wayar sa a kashe take, hakan ya qara d'aga hankalin sa sosai. "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un *Adyan* mai ya saka zaka kashe wayar ka? Sam bai kamata kayi hakan ba ya kamata na nai meka ina fatan nayi nasaran ganin ka." Ya juya zai fita da sauri Ahlam ta dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa cike da damuwa take magana. "Fad'a min ina *Adyan* sannan kuma mai ya faru da shi.?" Ba shi da wani za'bi shi yasa ya sanar da ita gaba d'aya gaskiyar, "wallahi tallahi ba zan ta'ba gafarta mata ba idan har wani abu ya faru da yarona." "Ba abin da zai faru da shi na maki alkawari zan dawo da shi gida cikin k'oshin lafiya insha Allah, to zaki iya yarda da ni kinji ko to ki kula sosai sai na dawo." Ta jinjina masa ka shi kuma ya juya ya fita ita kuwa ta bisa da kallo har ta fice, yayin da tinanin yaronta yayi yawan gaske a tare da ita sosai, lokaci d'aya damuwa ta shigeta sosai bata ankara ba idanuwan ta suka fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo ta d'auki wayar ta nan ta shiga kiran layin Kamela. Ba jimawa ta d'aga tare da gaishe ta ta amsa taci gaba da magana. "Kamela shin kina tare da *Adyan* ne.?" "A'a Ammie ba jimawa na ga ya fita cikin fishi sosai, nayi k'oqarin bin bayan sa amma sai ya dakatar da ni ya tafi shi kad'ai." "Kamela amma baki san wani gurin da zai iya tafiya.?" "A'a gaskiya ban sani ba." "Shikenan na gode sosai." Da kuma haka suka yi sallama, Ammie tayi shiru sai nazari take da tinani ta shiga kiran layin Appa ba jimawa ya d'aga. "Hellow Yaya Ahmad shin ka samu had'uwa da *Adyan* kuwa.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "a'a har yanzu amma zan gano sa insha Allah zaki iya yarda da ni please." "Yaya Ahmad to mai yasa ba zamu sanar da 'yan sanda ba.?" "A'a ba zamu sanar da 'yan sanda ba sabo da bai kamata su san da gaskiyar ba." "Amma Yaya Ahmad nifa ina jin tsoro kar wani abu ya faru da shi, ka riga da ka san komai a game da shi da kuma lafiyar sa to ya kamata mu san inda yake. Ya kamata ya dawo gida ina buqatar yarona ya dawo gida ina buqatar sa sosai." Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa ta, "Ahlam nima abin da nake buqata kenan zanyi komai domin ganin yaronmu ya dawo gida kinji ko." Ta amsa shi da to sunyi sallama tayi zaune tana kuka, haka Appa yayi ta yawo yana nai man yaronsa, ya jima sosai yana nai man sa daga bisani Jey ya kira layin Appa ya sanar da shi cewar ya ga *Adyan* cikin rawar murya yake amsa shi. "Jey yana ina.?" "Yana gurin kallon boll." "Na gode sosai Jey." Da kuma haka suka yi sallama Appa ya juya ya nufi inda zai had'u da yaronsa, ya isa gurin tare da shiga ciki sai wani zaran ido yake yana fad'ar sunan yaronsa ya jima a haka sannan daga bisani ya iya ganin sa. Cikin hanzari ya isa garesa cike da d'aukin ganin sa yayi hugging d'in sa sai wani sunbatarsa yake fuska zuwa wuya, shi kuwa sai wani kallonsa yake bayan ya sake sa ya anbaci sunan sa yana cewa. "Rabin raina shin kai kana fishi da Appa ne.?" Shiru bai amsa shi ba sai kallonsa kawai yake shi ma kallonsa yake kallo sosai, *"Adyan* shin ba zaka yi man magana ba? Dan Allah karka cutar da ni ta wannan hanyar sabo da ba zan iya d'auka ba, masoyi shin zamu iya tafiya gida yanzu domin muyi magana a can dan Allah.?" Sam bai iya amsa shi ba sai dai ya jinjina masa ka a lamar to, "Yauwa rabin raina yaron kirki mu tafi." Ya fad'a tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona. Ya rungumasa jikin sa har bakin mota sai da ya shiga mota sannan ya tafi ya shiga tashi motar suka tafi, sun isa gida tare da shiga ciki sun samu Ammie cikin wani irin yanayi mara dad'i, cike da d'aukin ganin sa ta nufi inda yake tana fad'ar sunan sa tana isa inda yake tayi hugging d'in sa tana sunbatarsa fuska zuwa wuya. *"Adyan* qlau kake kuwa fad'a min shin kai kana lafiya kuwa? Ni na damu sosai a kanka na gode Allah da ba wani abin daya faru da kai, yanzu fad'a min wani abu shin qlau kake kuma gaskiyar zaka fad'a.?" "Ammie ni ina lafiya ina san zan shiga ciki zamu yi magana an jima." "Shikenan ďana ka kula sosai sannan kuma idan kana buqatar wani abu to kawai ka sanar da ni ka ji ko." Ya jinjina mata ka a lamar to ya juya ya nufi bedroom d'in sa Appa ya dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa, *"Adyan* shin wai har tsayin wane lokaci zaka d'auka kana fishi da ni sosai haka? *Adyan* na fad'a maka cewar ni ba zan iya d'aukar wannan ba to dan Allah ka yafemin please." Ya mai da kallonsa ga Appa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna ya nufi inda yake yana fad'ar sunan sa. "Appa ni sam bana fishi da kai sannan kuma ni ba zan ta'ba hukunta ka ta wannan hanyar ba, Appa ni kawai naji wani iri ne sannan kuma naji ba dad'i sosai daka saka na bata hak'uri. Ita ta zagi Ammie na amma kuma duk da haka kai ka saka ni na bata hak'uri hakan yayi matuqar saka ni takaici da k'unci sosai, amma kuma hakan sam bai ya nufin cewar ni ina fishi da kai, a'a ni ba zan ta'ba aikata wannan mummunan zunubin ba, ka yafemin da nasa ka ji wani iri sosai a kan hakan kayi hak'uri." Da sauri Appa ya rufe masa baki yana girgiza masa ka tare da furta. "A'a rabin raina sam ba buqatar ka bani hak'uri sabo da ba kayi komai ba, *Adyan* na san cewar kai ka damu sosai a kan ni da kuma Ammie kana matuqar qaunar mu sosai. Amma kuma hakan ba zai saka mu canja gaskiyar ba, ita wannan matar sunan ta kawai ta fad'a to sam bai kamata kayi fishi ba, ko ba komai hakan zai iya cutar da lafiyar ka sosai wanda kuma hakan zai cutar damu sosai. Masoyi gaskiyar ita ce mu mun damu sosai a kanka da kuma lafiyar ka dalilin da yasa nake duka wannan kenan, *Adyan* kai ďana ne kuma abin da nafi so fiye da komai to zanyi komai sabo da kai, ina sanka sosai yarona kai ba kawai d'ana bane a'a kai rayuwata ne gaba d'aya, kai ne a salin farin ciki na k'uncin ka shi ne babban rashin hankali kuma qalubale ga rayuwa ta. To ina fatan zaka fahimce ni sannan kuma kayi min uzuri a game da abin dana saka ka aikata a yau ďin nan please." Cike da qaunar sa yayi hugging d'in sa yayin da bakin sa yake furta, "ina sanka Appa ina matuqar masifar qaunarka sosai fiye ma da yanda nake sanka ina qaunarka sosai Appa." Abin da yake ta fad'a kenan shi ma haka tare da qara saka shi jikin sa yana sunbatarsa, Ahlam tana daga gefe tana kallonsu yayin da take jin suna birgeta sosai, ta isa inda suke tare da shiga jikin Ahmad tare da sunbatar yaronta tana furta masa kalmar ina qaunarka ďana. Ya amsa ta yana murmushi sun jima a haka sannan suka sake juna suna k'oqarin zama Ahlam ta dakatar dasu ta hanyar fad'ar sunan *Adyan.* "Rabin raina yanzu lokacin cin abinci ne to kawai mu tafi muci abinci Yaya Ahmad mu tafi." lokaci d'aya *Adyan* ya 'bata fuska yana fishi kafin ya furta komai tayi masa rigagi. "Kayi hak'uri na dena ba zan k'ara kiran sa da wannan sunan ba, nayi alkawari insha Allah to zaka iya yarda da ni please." Magana take tana wani shafar kansa zuwa fuskarsa tare da sunbatarsa, Ahmad yana daga gefe yana kallonsu yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa sosai, ya jinjina mata ka a lamar to yana murmushi sun juya dukansu sun nufi tebur domin suci abinci. Sun isa ga tebur Ahlam taja musu kujera sun zauna ta fara zuba abincin sannan ta zauna suka fara cin abinci, bayan sun qarasa *Adyan* ya nufi bedroom d'in sa sun bisa da kallo har ya shige suna murmushi, sun dawo da kallonsu ga juna lokaci d'aya suka sakarwa juna murmushi mai tare da dariya. *"Abban Adyan* ko nace Appa kai kana da kirki sosai kuma zan iya kiran dana musamman, hak'iqa kai alkhairi ne a gareni dama rayuwa ta gaba d'aya ina qaunarka sosai Mujina *Abban Adyan."* Cike da d'auki yayi hugging d'in ta ya k'ara da sunbatarta, "abin da nake koqarin fad'a maki kenan sai kuma ke kika yi min rigagi, amma duk da haka da akwai buqatar na sanar dake wani abu, abin shi ne har kawo yanzu zuciyar Ahmad tana qaunar ki sosai kamar dai a ranar farko, alkawarin da zanyi maki shi ne ni Ahmad Aliyu zanci gaba da sanki tare da baki cikakkiyar kulawa sosai, har zuwa lokacin da zanyi numfashi na na k'arshe." "Na gode sosai Mujina am ko zamu iya shiga ciki sabo ina buqatar wani abu daga gareka yanzu.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh yana murmushi ita ma abin da take yi kenan sun juya sun shiga ciki, yana shiga ciki ya nufi inda laptop ďin sa ya d'auka ya nufi gado ya kwanta. Ya shiga nai man *Adnan* amma bai yi nasaran ganin sa ba mst yaja tsaki yana 'bata fuska, ya kai hanun sa ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin *Alishart* ya samu a na anfani da wayar mst ya koma jan tsaki ha!!! *"Adnan* bai ya online ita kuma *Alishart* tana anfani da waya ko dawa take waya oho? Bara na gwada layin *Adnan* na ga ko zai shiga ina fatan layin sa ya shiga." Nan kuwa ya shiga kiran layin *Adnan* yayi sa'a layin ya shiga ba jimawa ya d'aga. *"Adyan* barka fatan kana lafiya to ya kake.?" Yayi shiru kad'an tare da jan numfashi sannan daga bisani ya amsa shi. *"Adnan* 'yar damuwar kad'an ce to kai fa ya kake.?" "Subhanalillah fad'a min miye damuwar domin naji da abin da zan iya taimaka wa.?" "Dama a office ne wata ta 'batan rai sosai, bayan na dawo gida kuma na duba ka online amma ban same ka, wannan yasa na koma kiran layin *Alishart* ita kuma tana tana waya da wani daban. Hakan ya qara min damuwa sosai amma yanzu ina lafiya sabo da na same ka." *Adnan* yayi murmushi kad'an sannan ya amsa shi. "Eyya afuwan d'an uwa kayi hak'uri a game da wannan matar, a game da ni kuma ina mai baka hak'uri ina a bakin aiki ne shi yasa ban iya hawa online ba. Sannan kuma a game da qanwata ka san bata da wata, da wayar Mamie kuke magana to ina jin Mamie ce take anfani da wayar bawai qanwata ba. Fatan ka fahimci mai nake nufi sannan kuma zaka dena fishi da dukanmu.?" *"Adnan* nifa bana fishi da kai musamman *Alishart* kawai dai ni na damu ne da ban samu nayi magana daku ba. Amma yanzu komai daidai yanzu kawai kayi aikin ka, idan ka koma gida ka had'a ni da *Alishart* muyi magana dan Allah." "Muna godiya sosai karka damu zan had'a ka da qanwata nayi alkawari insha Allah, amma kafin nan kai kuma zaka yi man alkawarin cewa ba zaka yi k'unci ba." Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "eh nayi alkawari ba zanyi k'unci ba insha Allah, na gode sosai da kulawa to kai ma ka kula sosai ka ji ko." Ya amsa shi da to yana dariya shi ma abin da yake yi kenan, da kuma haka suka yi sallama bayan kwana biyu.............. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/17, 4:01 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 22* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 15/01/2022* *Time 07:58pm* *Typing..............* *Nigerian.* Kwance take amma ba barci take ba ta wani lumshe ido, baitin wak'ar dake ratsata ne yasa har take wani rufe ido, lokaci d'aya ta ji Mamie tana kiran ta, ta amsa da k'arfi tare da tashi ta fita zuwa parlour da sauri har tana gudu. Ta fito ta samu Mamie zaune ta isa inda take tare da furta mata gani, *"Alishart* tin da kika qarasa exam kika d'aura aure da sauraran wakokin wannan secret super star ďin, baki da aiki sai sauraran wak'ar sa ni kuma ki banni da aikin gida, kar'bi nan tin d'azu *Adyan* yake kira yana san zaku yi magana." da sauri ta kar'bi wayar tare da furta mata kalmar. "Kiyi hak'uri Mamie ni kawai ina jin dad'in wakokin sa ne, shi yasa ko yaushe nake sauraran sa sabo da yana saka ni nishad'i sosai, sannan kuma ina k'ara fahimtar turanci sosai, karki wani damu sabo da zanci gaba da taya ki aikin gida insha Allah sannan kuma." Ringing ďin wayar da take hanun ta ne ya saka ta yin shiru ta juya ta nufi d'akin ta, Mamie ta bita da kallo tana girgiza ka yayin da take magana. "Yarinya sai d'an banzan surutun tsiya idan ta fara magana sam bata jin ta gaji, Allah ya k'ara shirya mana zuri'a Allahumma Amin." Da gudu ta shiga d'aki ta fad'a gado tare da amsa wayar. "Kin kyauta sosai sai yanzu kike amsa min waya." "Kayi hak'uri *Yaya Adyan* wayar tana hanun Mamie ne shi yasa fatan zaka dena fishi da ni.?" "Waya fad'a maki cewar ina fishi dake a'a bana yi kuma ba zanyi ba." "Na gode Yayana." *"Alishart* wai har yanzu kina sauraran wak'ar wannan secret super star ďin.?" "Eh *Yaya Adyan* sabo da ina sansa sosai sannan kuma yana saka ni nishad'i sosai. Ko k'unci nake da zaran na saurare sa sai na fara nishad'i shi ďin na musamman ne, ya san ta yanda zai ja hankalin mutane sabo da ya iya dad'ad'an lafuzza masu matuqar dad'i sosai da sanyaya zuqata. Gaskiya ina matuqar qaunar sa sosai shi ne jarumi na ina fatan had'uwa da shi." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarta sosai, yayi shiru sai sauraran ta yake har ta qarasa jin shirun yayi yawa ne yasa ta fad'ar sunan sa. *"Yaya Adyan* shin kana jina kuwa.?" Shiru bai amsa ba taci gaba da magana, *"Yaya Adyan* dan Allah ka amsa ni shin qlau kake kuwa mai yasa baka san kayi magana? Shin ni na aikata wani zunubi ne fad'a min shin da akwai wani abin da ba daidai ba dan Allah kayi min magana.?" Still bai yi magana ba sai daga bisani sannan ya amsa ta. *"Alishart* mai ya saka kike san abin da babu shi? Shi wannan mutumen ba mutum bane shin ke baki ga hakan ba? Ya kamata a ce kin fahimci haka tin daga sunan sa babu wani wanda ya san shi balantana wanda ya ta'ba ganin sa, ko a cikin wak'ar sa sam bai ya barin wata a lama wacce zata sa a fahimci a salin waye shi. Amma kuma duk da haka ke kike qaunar sa har haka mai ya saka kike san shi sosai ke kina san shi da yawa mai yasa.?" *"Yaya Adyan* nima ban sani ba abin dana sani shi ne kawai ina qaunar sa sosai to ba zan iya canja gaskiyar ba, sannan kuma sabo da kai ne ni na fara sauraran sa da fara ina k'ara iya turanci, hakan ne yake bani damar da nake yin magana da kai sosai, sannan kuma shi ďin ya fad'i cewa a k'asar England yake ka ga k'asar ku ďaya kenan. Daga k'arshe kuma yana saka ni nishad'i sosai hakan yasa na fara sansa." Ya nisa tare da jan numfashi sannan ya amsa ta. "Eh gaskiyar kika fad'a a nan k'asar England yake amma kuma ba wani wanda ya san shi, amma kuma duk da haka ya tara tarin masoya da mabiya wakokin sa sun zaga duka duniya gaba d'aya. Hakan yasa ko ina na duniya zancan sa a ke waye shi ba wanda ya sani, *Adnan* ya iya turanci sosai to mai yasa ba zaki koya daga garesa? Sam bai kamata ki fara san mutumen da baki san komai a kansa ba." *"Yaya Adyan* da a ce tin farko kai kana jin hausa to da duka wannan bai faru ba, amma idan kana so to ni zan koya ma." "Da gaske ke zaki koya min.?" "Eh zanyi kawai ka sanar da ni idan ka shirya wa hakan." "Na shirya zamu iya fara wa yanzu." "Ba zai yu yanzu ba." "Mai yasa.?" "Sabo da ina san zanyi anfani da laptop d'in Yayana yayin da nake koyar da kai sabo da zaka fi fahimta na." *"Alishart* shin zan iya tambayar ki wani abu.?" "Eh ina jin ka." *"Alishart* shin kina da ra'ayin waya da laptop naki na kanki.?" "Eh amma mai ya saka ka tambaya.?" "Ba komai zamu yi magana an jima, k'ila kuma kafin na ki ganni a gaban ki." Cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. "Miye kana ina karka fad'a min cewar ka shigo Nigerian.?" "A'a ina England amma zan iya zuwa yanzu kawai sabo da na ganki na jima ina mafarkin hakan." "Ai kana gani na ko yaushe idan muna video call." "Wannan kawai a waya ne to ba zai wani wadatar ba, shi yasa nake san na domin had'uwa dake k'ila nazo yanzu." "Sam bai kamata naji mamaki ba, sabo da kai na musamman ne Kakan ka ina nufin Abba shi ne shugaban k'asar nan, sannan kuma d'ayan Kakan ka ina nufin Abbu shi ne gwamnar kaduna, to kana da damar da zaka yi duk abin da kake so kai d'an gata ne sosai." *"Alishart* ko zaki iya yin shiru haka? Sabo da maganar ki ta fara yawa sosai." "Shikenan nayi shiru." Ta fad'a tana 'yar dariya shi ma abin da yake yi kenan, sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama. Suna gama waya *Adyan* ya shiga kiran layin Ameer ba jimawa ya d'aga, bayan sun qarasa gaisa wa *Adyan* yaci gaba da magana. "Am Ameer dan Allah wani taimako nake buqata a gareka." *"Adyan* kawai ka fad'i koma miye ni kuma zanyi nayi alkawari insha Allah." "Na gode sosai am Ameer shin kasan aboki na *Adnan* wanda yake a nan kaduna sannan ka san gidan su.?" Ya amsa shi da eh yaci gaba da magana, "Ameer to zan turo ma da kud'i zaka siyi waya laptop da tap masu kyau sosai, sannan zaka siyi layin waya da kuma katin waya kar yayi k'asa da dubu hamsin. Ragowar kud'in ko nawa ne ka siyi chocolate biscuits da alawa, ka shirya komai yanda zai yi kyau sosai kuma ya k'ayatar sai ka tafi gidan su *Adnan Alishart* zaka baiwa qanwarsa. Duka sakon nata ne fatan ka fahimce ni sosai.?" "Eh na fahimta sosai." "Ok zan turo ma miliyan uku ďaya taka ce ladan ka biyun kuma na siyayyar ne, idan kuma kud'in bai isa ba to kawai ka sanar da ni Ameer amma zaka iya kai mata sakon yau.?" "Eh zan iya yin komai a yau sannan kuma ina godiya sosai Allah ya bar zumunci ya kuma bar qauna Amin." Shi ma ya amsa da Amin da kuma haka suka yi sallama. *"Alishart* wai zaki fito daga ďakin nan ko kuwa.?" Da sauri ta tashi ta fita har tana gudu ta isa parlour tare da isa inda take tana furta mata gani. "Bani waya ta sannan ki tashi mu shiga kicin, rana tayi bana san *Adnan* ya dawo gida ban kammala girki ba to mu tafi." "Mamie hakan yana da sauk'i sosai sabo da shi madara ce abin da yafi so." "Eh haka ne sannan kuma shi ďin yana matuqar san samosa sosai da juice d'in kwakwa, to abin da zamu shirya masa kenan to mu tafi." "Mamie to Papa fa mai zai ci.?" "Zaici duk abin dana ba shi kuma bana buqatar wata tambaya bayan wannan to mu tafi." Ta amsa da to ta tashi sun nufi kicin sun fara aikin samosa, *Alishart* na shafa fulawa Mamie tana nad'ewa ba wani d'aukan lokaci suka qarasa, sun kuma koma ta gurin juice ďin kwakwa bayan sun qarasa sun shirya komai a kan tebur. Sannan daga bisani suka shiga ciki *Alishart* na shiga ciki ta fad'a gado tayi kwance sai wata gajiya take ji a tare da ita, ba jimawa sosai wani barci yazo d'auke ta bayan Mamie ta qarasa shirin ta tsab ta fito, rashin ganin *Alishart* a parlour ya tabbatar mata da cewar tana ďakin ta. Ta juya ta nufi can ta shiga ciki ta same ta kwance tana ta sharan barci tayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan ta. *"Alishart* kenan 'yar laushi yanzu wannan samosar da muka yi ita ta gajiyar dake, har dasu barci kamar wadda tayi duka aikin gidan nan ai kuwa haka zaki ci gaba har ki saba. Ke macace to ya zama dole da ki iya duk wani aiki na mata, kafin lokacin da zaki tafi gidan mujin ki wato siriki na ina sanki 'yata Allah yayi maki albarka Amin." Ta shafi fuskarta tare da sunbatarta sannan ta juya ta fita, *Alishart* ta jima tana barci sannan ta farka kai tsaye toilet ta fad'a tayi wanka tare da d'ora alwala ta fito, ta fara gabatar da salla sannan ta shirya cikin wata kyakkyawar doguwar riga, shigar ta amsheta sosai ta juya ta fita zuwa parlour. Ta samu Mamie ita kad'ai tana k'oqarin zama taji a na buga k'ofa ta juya ta nufi k'ofa tare da bud'e wa, ta samu Papa da *Adnan* tsaye a bakin k'ofa lokaci d'aya ta saki wani kyakkyawan murmushi, cike da d'aukin ganin su take fad'ar sunayen su tare dayi musu sannu da zuwa sun amsa tare da shiga ciki. Cike da d'aukin ganin su Mamie ta shiga yi musu sannu da zuwa Papa yake amsa ta yayin da *Adnan* ya nufi tebur, tafiya yake k'amshin yana k'ara kusa da shi ha!!! Ya nisa sosai tare da lumshe ido yana wani rawa da ka, yaja kujera ya zauna tare da bud'e kayan abincin dake gurin yayi tozali da abin da yafi so wato samosa. Nan kuwa ya fara cin ta Mamie ta shiga tambayar Papa *Adnan* kafin ya furta komai *Alishart* ta saki dariya sannan ta amsa ta. "Mamie ki duba tebur kiga mebi zaki iya samun sa a nan." Lokaci d'aya dukansu suka kai kallonsu ga tebur sun hangi *Adnan* zaune yana aikin cin samosa, lokaci d'aya suka saki wani kyakkyawan murmushi mai tare da 'yar dariya sun nufi inda yake. Sai wani kallonsa suke kallo sosai Mamie ta shafi kansa zuwa fuskarsa tare da sunbatarsa tana fad'ar sunan sa, *"Adnan* shin kana farin ciki da wannan samosar.?" Ya shafi hanun ta da yake kan fuskar sa tare da sunbata cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Eh Mamie farin ciki sosai na gode sosai ina sanki Mamie ina matuqar masifar qaunarki sosai I LUV U SO MUCH Mamie." Ya fad'a tare da yin kwance jikin ta ita kuwa sai sunbatarsa take, "nima ina qaunarka sosai d'ana soyayyar da bata da na biyu kai ne abin dana ina sanka sosai." Magana take cikin kyakkyawan yanayi tare da k'ara saka shi jikin ta tana sunbatarsa. Papa yazo ta bayan ta yayi hugging d'in su tare da *Alishart* yana cewa, "wannan rashin adalci ne zaku rungumi juna kubar mu biyun a ware, ya kamata a ce dukanmu ne muka rungumi juna kamar dai haka." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi, suma abin da suke yi kenan sun jima a haka sannan suka sake juna sun juya zasu tafi, *Adnan* ya dakatar da *Alishart* ta hanyar fad'ar sunan ta. *"Alishart* ki tafi kiyo man kiran Besty ki ce tazo yanzu kinji ko." "Yayana amma duka gidan muna buqatar samosa to amma kuma." *"Alishart* ki tafi ki kira man Besty karki bari na k'ara maimaita maki abin da nake buqata daga gareki kinji ko." Ta amsa da to ta juya ta nufi hanyar fita su Mamie sun bita da kallo suna murmushi, shi ma abin da yake yi kenan su Papa sun shiga ciki shi kuma yaci gaba da cin samosa, *Alishart* ta shiga gidan su *Afnan* tare da sallama ta samu *Afnan* tana k'oqarin hawa sama, ta fara da gaisawa dasu Abba sannan ta mai da kallonta ga *Afnan* tare da fad'ar sunan ta. "Aunty d'an dakata kad'an Yayana yace nazo na kira ki." Tayi murmushi sosai tare da furta mata kalmar mu tafi ta amsa da to sun sanar dasu Ummu sannan suka tafi. Sun isa gida tare da shiga ciki kai tsaye tebur suka nufa gurin *Adnan,* ya tare su da murmushi tare da yiwa *Afnan* ta yin gurin zama, ta amsa tana murmushi ta zauna suna haka sai ga Mamie ta fito wanda kuma kicin ta nufa, *Afnan* ta gaishe ta ta amsa tana murmushi ta nufi kicin ba jimawa ta fito ta nufi bedroom *Alishart* ta anbaci sunan ta. "Mamie ki bani wayan ki da akwai abin da zanyi da ita." *"Alishart* gaskiyar ita ce ina san zanyi anfani da kud'in da yake waya na to kiyi hak'uri." Ta juya zata tafi da sauri *Alishart* ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "Mamie ni ba wanda zan kira kawai fa zanyi Game ne shi ne kawai to zaki iya yarda da ni please." *"Alishart* nace a'a to kawai ki hak'ura kinji ko." Lokaci d'aya ta saki wani kukan shagwa'ba da sauri *Adnan* ya tashi ya nufi inda take, ya shiga rarrashinta yana lalla'bata tamkar wata k'aramar yarinya. "Ya isa haka qanwata kar'bi ga waya na ga kuma laptop d'ina kiyi duk abin da kike so, amma dan Allah ki dena wannan kukan bana so kinji please." Ta amsa da to tana murmushi tayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa sannan ta kar'bi wayar tare da d'aukan laptop ta nufi d'akin ta, sun bita da kallo suna murmushi Mamie ta girgiza ka ta juya ta nufi bedroom *Adnan* kuma tebur ya nufa gurin Besty............. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/19, 4:54 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 23* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Sunday 16/01/2022* *Time 09:28pm* *Typing.................* Ya zauna tare da kai kallonsa ga *Afnan* wacce ita ma kallonsa take kallo sosai. "Kai kana da kirki sosai ka san ta yadda zaka tafiyar da kowa, dubi cikin k'ank'anin lokaci ka saka *Alishart* dariya hakan yayi kyau sosai kai ďin na musamman ne." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi, abin birgewa sosai ga wanda ya gani shi kuwa sai wani kallon ta yake kallo sosai. "Besty karki wani fasa min kai da yawa, ke kin san gaskiyar ni na koyi duka wannan ne a gurin Yaya. Ina ganin yanda yake matuqar bamu cikakkiyar kulawa sosai, tun muna yara kuma har zuwa wannan lokacin ba abin daya sauya hakan, shi yasa nima nake nuna wa Qanwata kulawa sosai ina san na zama kamar Yaya yanzu muci wannan." Ya nuna samosa tayi 'yar dariya tare da fad'ar sunan sa. "Besty ni zanci ne kawai idan har kai ka bani a baki." Murmushin sa ya qaru ya amsa ta, "eh zanyi kuma ina mai farin ciki da hakan." Nan kuwa suka fara cin samosa sun kuma koma ta kan juice d'in kwakwa, bayan sun qarasa sun dawo parlour sun zauna na wani lokaci, sannan *Afnan* ta tashi domin tafiya gida *Adnan* ma tashi yayi domin rakata. Basu qarasa kai wa k'ofa suka ji a na buga masu k'ofa *Adnan* ya qarasa tare da bud'e k'ofar, ya samu Ameer tsaye a bakin k'ofa daga gefe kuma ga sakon *Alishart* daya kawo, lokaci d'aya suka saki murmushi tare da fad'ar sunayen juna. "Ameer shigo ciki." Ya amsa da to yana murmushi *Adnan* ya riqa masa kayan sun shiga ciki, sun k'ara gaisawa bayan sun gaisa Ameer yaci gaba da magana. "Am *Adnan* dan Allah ko zan iya ganin *Alishart* yanzu please.?" Ya amsa da eh ya mai da kallonsa ga *Afnan* tare da furta mata ta kira ta, ta amsa da to ta tashi ta nufi bedroom d'in *Alishart* ba jimawa suka dawo tare, bayan sun zauna *Alishart* ta shiga gaishe sa tare da furta wa Yayan kalmar gani *Adnan* ya mai da kallonsa ga Ameer tare da fad'ar sunan sa. "Ameer ga *Alishart* nan ina dai fatan lafiya.?" Ya jinjina masa ka tare da furta, "eh lafiya qlau kawai dai ina san na bata wannan sakon ne daga *Adyan."* Cike da jin mamakin abin daya fad'a suke anbatar sunan *Adyan* har suna had'a baki. "Ameer shin *Adyan* ya shigo k'asar nan ne.?" Kafin ya amsa shi *Alishart* tayi masa rigagi, "Yayana d'azu shi ya fad'a min cewar zai shigo k'asar nan na wuni d'aya kawai, amma ni nayi tinanin da wasa yake ga shi kuma ya aikata shi ďin na musamman ne, sannan kuma yana da abin mamaki sosai yanayin sa yana da birgewa sosai." *"Alishart* ga sakon ki ya fad'a min cewar zaku yi magana a waya *Adnan* ni zan tafi *Afnan* sai an jima." Sun amsa shi suna murmushi da kuma haka suka yi sallama, bayan tafiyar sa *Alishart* ta shiga bud'e sak'on dan ganin miye a ciki, tayi tozali da laptop waya da kuma tap d'ayar ledar kuma kayan zak'i ne da yawa a ciki. Cike da jin mamakin abin da suka gani *Adnan* ya kai kallonsa ga fuskar *Alishart* tare da fad'ar sunan ta. "Qanwata shin ke kin buqaci wani abu daga garesa gaskiyar zaki fad'a.?" "A'a Yayana ni ba zan ta'ba aikata hakan ba, kawai abin dana sani shi ne d'azu munyi magana a kan zan koya masa hausa, ya buqaci da mu fara a d'azu sai na fad'a masa cewar zanyi anfani da laptop d'in ka to ina ga dalilin da yasa ya siya man kenan. Waya kuma mebi bai ya san yana kiran layin Mamie tap kuma ban san na miye ba." "To amma mai ya saka zai aiko maki da wannan? Ya kashe kud'i sosai kusan miliyan hud'u a ke magana a nan amma zanyi magana da shi." "Amma Yaya." Kafin ta furta komai wayar ta d'auki ruri murmushin ta ya qaru sosai, "la *Yaya Adyan* ne yake kira." Ta fad'a tare da tashi ta nufi d'akin ta da sauri har tana gudu, sun bita da kallo har ta shige sannan suka dawo da kallon su ga juna. "Besty shin kai baka ga yanayin yanda take farin ciki sosai ba? To dan Allah karka dakatar da ita kawai ka barta tayi farin ciki sosai ka ji ko." Ya nisa sosai tare da jan numfashi sannan ya amsa ta, "Besty ni bawai ina hana ta farin ciki bane a'a ni kawai na damu ne sosai a kanta, Besty har yanzu *Alishart* yarinya ce shekarun ta sha biyar ne kawai, yanzu ne ta kammala secondry to sam bai kamata wani mutum daban ya shiga rayuwarta ba. To ya kamata nayi magana da *Adyan* sannan kuma na dakatar da shi da yin duka wannan." "A'a Besty karka yi sabo dasu biyun sunyi matuqar shak'uwa da junan su sosai, idan ka shiga tsakanin su biyun to dukansu biyun zasu shiga k'unci sosai. Hakan zai yi matuqar cutar dasu sosai da kuma mu to ina ga sam bai kamata ka dakatar dasu ba dan Allah." "Besty ni kawai na damu ne a kan qanwata shi yasa." "Karka wani damu zamu saka mata ido sosai ta yanda zamu san abin da yake faruwa da ita, kai dai kawai ka yarda da ni *Alishart* zata kasance lafiya to zaka iya yarda da ni please ka ji ko." "Besty nima ina fatan haka." Suna haka sai gasu Papa sun fito nan kuwa *Adnan* ya shiga sanar dasu abin da yake faruwa, sun cika da jin mamakin sa sosai har suka gagara fad'ar komai bayan wani lokaci *Afnan* ta tashi domin tafiya gida, hakama *Adnan* tashi yayi domin yi mata rakiya ta fara da yiwa su Mamie sallama sannan suka tafi bayan kwana biyu. Zaune suke a parlour wanda kuma a part d'in Anwar suke, kasancewar zuwan lokacin yayi aure har da 'yarsa mai suna Amal, Anisa ta kai kallonta ga *Afnan* tare da anbaci sunan ta taci gaba da magana. *"Afnan* ku tafi kuci abinci." Sun amsa da to sun tashi sun nufi tebur sun fara cin abinci, "Besty kaci abinci mana ka dena wasa." "Besty nifa na k'oshi shi yasa." "Ka fara halin naka ko? To ni sam ban yarda da wannan k'oshin naka ba lallai dole kaci abinci ko kuma na ma ta k'arfi." Kallonta kawai yake yana murmushi ita ma haka ganin ba shi da niyar cin abincin yasa ta tashi, ta nufi gunsa da sauri ya mi e tsaye ya gudu yana murmushi mai tare da dariya ita ma abin da take yi kenan. Ta tashi ta bisa a baya sai wani zagayen parlour suke Anisa na dariyar su, suna haka suka ji a na buga k'ofa Anisa ce wacce ta tafi ta bud'e k'ofar, ta samu Anwar da Auwal tsaye a k'ofa ta shiga yi musu sannu da zuwa sun amsa tare da shiga ciki, da sauri *Adnan* ya nufi gunsa har yana gudu ya 'buya a bayan sa. "Yauwa Yaya na gode Allah daka dawo yanzu kazo a daidai, Besty tana san ta tilassa ni a kan naci abinci kuma ni a k'oshe nake." "Karka yarda da shi Yaya sabo ra'ayin sa kawai yake fad'a amma da akwai buqatar yaci abinci yanzu." Nan kuwa suka shiga gardama shi yana ba zaici abinci ba ita tana sai yaci. "Ya isa kuyi shiru haka zaku barni nai magana ko zaku ci gaba da gardama ne? Mu tafi mu zauna zan san abin da zanyi a game da hakan." Sun amsa da to sun tafi sun zauna bayan sun gaisa Anwar yaci gaba da magana. *"Adnan* shin yau kaci abinci kuwa g zaka fad'a.?" "A'a Yaya amma na sha madara sannan kuma." "Isa haka wannan ba abinci *Afnan* ku tafi ki ba shi abinci, amma kuma kar hakan yasa ki tilassa masa cin abin da yafi k'arfin sa kinji ko." Ta jinjina masa ka tana murmushi mai tare da dariya *Adnan* kuwa sai wani kallo yake yi mata mai kama da harara, lokaci d'aya ta saki dariya kuma dariya take sosai ya mai da kallonsa ga Anwar tare da fad'ar sunan sa. "Yaya ka fad'a mata ta dena dariya ta." "Yaya to fa shi ma ya dena harara na." *"Afnan* ki dena tsokanar sa ko kuma na dakatar dake daga ba shi abinci." "Shikenan Yaya na dena Besty yi hak'uri mu tafi please." Ta tashi tare da tashin sa sun nufi tebur Anisa ma tashi tayi ta shiga ciki, Anwar ya kai kallonsa ga fuskar Auwal wanda banda kallonsu *Adnan* ba abin da yake Anwar ya anbaci sunan sa. "Auwal shin yaran sun birgeka ne? Dama haka su biyun suke suna da matuqar birgewa sosai farin cikin su ne abin da nafi so fiye da komai." Auwal dai sai kallonsa yake ya nisa tare da jan numfashi ya qara da sauke a jiyar zuciya sannan ya amsa shi. "Anwar ni sam basa birgeni sannan kuma ganin su a haka yana saka ni takaici sosai. Ina matuqar shiga k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa sosai idan har na ga su biyun a tare, kuma kai kasan dalilin da yasa nake jin hakan sabo da ina san *Afnan* ina matuqar qaunar ta sosai amma." Da sauri Anwar ya dakatar da shi ta hanyar rufe masa baki yana girgiza masa ka tare da furta a'a, sai wani kallonsa yake ya mai da kallonsa gasu *Afnan* lokaci d'aya ya anbaci sunayen su. *"Adnan Afnan* ku tashi ku shiga ciki mu biyun zamu yi magana." Sun amsa da to sun tashi sun nufi d'akin *Afnan* bayan tafiyar su Anwar ya mai da kallonsa ga Auwal tare da fad'ar sunan sa. "Auwal ina mai gargad'in ka da karka k'ara fad'ar hakan ka ji ko." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake masa baki, Auwal kuwa sai wani kallonsa yake cike da jin mamakin sa yake magana. "Anwar a gaskiya kana da abin mamaki sosai, to ka sani ni ina san *Afnan* sosai kuma ba zan ta'ba 'boye hakan ba, zan kuma sanar da kowa wannan na tabbata duka ahalin zasu yi farin ciki sosai da hakan zanyi auran gida kamar yanda kayi. To ka zama cikin shiri domin nan ba jimawa za a yi aure na da *Afnan* tabbas hakan zata faru insha Allah." "Auwal ya kamata kayi gaggawar tashi daga wannan mummunan mafarkin da kake a yanzu, sabo ko Kaka ba zan bar shi ya aikata irin wannan mummunan zunubin ba balantana kuma kai. Ka sani wallahi tallahi a shirye nake da nayi fito na fito da duk mutumen da yayi k'oqarin raba su biyun, *Afnan da Adnan* ba zasu ta'ba rabuwa ba na har abada kaddaran su a rubuce take, su biyun an yi sune domin su rayu da juna dan haka ni ba zan barka kayi nasaran rabasu ba, sannan kuma zanyi komai domin ganin na dakatar da kai, haka kuma zanyi komai domin ganin su biyun basu rabu ba kuma zanyi nasara insha Allah." "Shikenan Anwar tin da wannan abin daka za'ba ni ba zan ta'ba dakatar da kai ba, amma kuma ka sani ni ba zan ta'ba barin kayi narasa a kai na ba, to zamu gani tsakanin ni da kai waye zai yi nasara." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyarsa Anwar ya bisa da kallo yana girgiza ka yana wani huci, ya k'ara da furta Allah ya kyauta ya tashi ya nufi bedroom d'in sa. Wani dare zaune take jikin gado tana waya da *Adyan Adnan* ya turo k'ofa ya shigo, ya kai kallonsa gareta tare da fad'ar sunan ta da sauri ya wani zaro ido yana kallonta, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana da ita. "Ki kashe wayar nan laptop dama tap ki bani dukansu sannan kuma karki sanar da kowa wannan." Yana kai k'arshen maganar sa ya d'auki wayar ta da laptop da tap ya fara kashe wa sannan ya fice daga d'akin ta bisa da kallo tana kuka............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/20, 10:54 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 24* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 17/01/2022* *Time 09:41pm* *Typing................* "Na shiga uku na ni *Alishart* wane irin zunubin kuma na aikata wa Yayana? Shi yana fushi da ni sosai ba kuma tare daya sanar da ni laifin dana aikata masa ba, ya kuma dakatar da ni daga sanar da kowa a'a ni sam ba zan iya d'aukar wannan ba, ya kamata nayi wani abu domin na samu mafita to mai ya kamata nayi ne.?" Nan ta shiga tunani tana nazari miye mafita. A can gurin *Afnan* kuwa, ganin yanda take ta aikin kiran layin *Adnan* bai iya ɗagawa yasa ta kiran layin *Alishart,* amma tayi rashin sa'a layin a rufe yake ta shiga kiran layin Mamie shi kuma baya tafiya. Hakan yayi matuqar d'aga hankalin ta sosai cike da firgici da rud'ani ta tashi tare da sanya dogon hijabi ta fito, kai tsaye d'akin Papa ta nufa ta shiga buga musu k'ofa ba jimawa Ummu tazo ta bud'e, ta shiga tambayar mai yake faruwa tayi shiru kad'an sannan ta amsa ta. "Ummu wani abu yana faruwa da Besty na shi bai ya d'aga kira na, wayar *Alishart* a kashe take layin Mamie kuma bai ya tafiya, gaskiya na damu sosai a kansa to zan tafi iro zai raka ni gidan, dare yayi sosai to zan kwanta tare da *Alishart* a can ki sanar da Papa." Ummu sai wani kallonta take sam ba zata yi mamaki ba sabo da tafi kowa sanin wane *Adnan* a gareta. "Shikenan 'yata ki kula sosai kinji ko." Ta jinjina mata ka a lamar to ta juya ta nufi hanyar fita Ummu ta bita a baya ta rufe k'ofa, bayan ta dawo ta sanar da Abba murmushi kawai yayi tare da furta Allah ya kyauta. Duk da cewar data fita sai gidan manne suke da juna amma ta buqaci rakiyar iro, sun fito tare da buga k'ofar su Papa Habu ya fito yana tambaya waye, *Afnan* ta anbaci sunan ta cikin hanzari ya bud'e tare da tambayar ta lafiya. Ta amsa shi da ba komai tayi sallama da iro tare dayi masa godiya ta nufi ciki, nan kuwa ta shiga buga k'ofa Papa ne wanda ya fito ya bud'e k'ofar, cike da jin mamakin ganin ta cikin hanzari ya anbaci sunan ta. *"Afnan* lafiya.?" "Papa gaskiyar ita ce Besty bai ya cikin kyakkyawan yanayi wani abu yana faruwa da shi, na kira layin sa amma bai d'aga ba wayar *Alishart* kashe layin Mamie kuma bai ya tafiya, Papa ni nayi matuqar damuwa sosai a kansa dalilin da yasa nazo na duba shi kenan." "Na gode sosai 'yata mu tafi mu duba yanayin sa." Ta amsa da to ta shiga ciki ya fara da rufe k'ofar sannan suka juya suka nufi d'akin *Adnan,* sun samu k'ofar a rufe sun shiga buga masa k'ofa ba jimawa yazo ya bud'e. Sam bai ji mamakin ganin *Afnan* domin ya san zai iya ganin ta, "Papa ina lafiya ka yarda da ni qlau nake ita kawai taji tsoro ne sabo da ban d'aga kiran ta ba, amma ina lafiya to zaka iya yarda da ni sabo da ni gaskiyar nake fad'a." Ya shafi fuskar sa zuwa kansa tare da sunbatarsa yana fad'ar sunan sa. "Ina fatan haka d'ana yanzu zan tafi sai da safe ka kula sosai *Afnan* kema." "Eh Papa zan kula sosai sannan kuma bayan nayi magana da shi zan kwanta a ďakin *Alishart."* "Hakan yayi kyau 'yata Allah yayi muku albarka." Dukansu sun amsa da Amin ya juya ya fita bayan tafiyar sa *Afnan* ta kai hanun ga *Adnan,* wanda shi ma kallonta yake kallo sosai daga bisani kuma ya tafi ya zauna, ta bisa da kallo hakan kuma ya tabbatar mata da cewar yana tare da damuwa sosai. Ta nufi inda yake ta zauna sai wani kallonsa take kallo sosai daga bisani kuma ta fara magana. "Besty zaka iya 'boye wa kowa damuwar ka amma banda ni, sabo da nafi kowa sanin ka a wannan duniyar Besty kawai ka sanar da ni gaskiyar miye damuwar? Domin na san ta yanda zan iya taimakon ka." Kallonta kawai yake ita ma haka kallonsa take sun jima a haka suna kallon juna, ba kuma tare da sunji sun gaji ba bayan wani lokaci da suka d'auka a haka sannan daga bisani ya amsa ta. "Ke kinfi kowa sani na kuma kinfi kowa fahimta na kina gane ko wane irin yanayi na, Besty ni kawai na damu ne a kan qanwata yanzu ba jimawa ni na shiga d'akin ta, na samu tana magana da *Adyan* video call Besty abin damuwar shi ne ita tana sanye da rigar barci ne kawai a jikin ta. Besty ni naji wani iri sosai hakan yasa nayi mata fad'a sosai har tayi kuka ban kuma iya rarrashin ta ba, Besty ni kasa gane dalilin da yasa *Adyan* zai aikata haka? Sam bai kamata ya ganta a cikin irin wannan shigar ba, amma kuma shi yayi hakan Besty mai yasa yayi hakan mai yasa zai ga qanwata a cikin wannan shigar.?" Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ita kuwa sai kallonsa take kallo sosai ta shafi kansa zuwa bayan sa tare da sunbatarsa, a ka da kuma gefen fuska shi kuwa dai kallonta kawai yake ba kuma tare daya furta mata komai ba. "Besty amma kana da tabbaci sosai a kan hakan kuwa? Besty zai iya yuwa kai kawai hasashe ne kake, Besty mu kawai muna yarda ne da abin da idanuwan mu suka gani bawai abin da muka ji ba. To Besty ya kamata ka k'ara tinani a kan abin da kake fad'a kafin yanke hukunci, sabo da kana cikin fishi sosai to zaka iya yanke hukuncin da bai dace ba, Besty *Adyan* aboki na gari ne a gareka to ni sam bana tinanin cewar zai iya cutar da kai sosai har haka. Besty to yana da kyau ka k'ara tinani shin da gaske kai ka yarda da abin ka ji kuwa.?" Yayi shiru sai kallonta kawai yake ita ma haka kallonsa take suna haka suka jiyo wayar *Adnan* na ruri, lokaci d'aya dukansu suka kai kallonsu ga wayar dan ganin wanda yake kira, sun ga sunan *Adyan* ya bai yana a kan wayar sa amma bai d'aga ba ya kira da dama amma kuma bai d'aga ba. "Besty mai ya saka ba zaka amsa shi ba? Ya kamata ka saurare sa dan Allah kaba shi damar da zai wanke kansa a gareka please." Har zuwa wannan lokacin kallonta yake ba kuma tare daya furta mata komai ba, ganin ba zai yi magana bane yasa ta d'aukar wayar sa ta d'auki number *Adyan,* tasa a wayar ta tare da danna kira ba jimawa sosai ya d'aga ta anbaci sunan sa ta kuma ci gaba da magana. *"Adyan* kana magana da *Afnan qawar Adnan."* Da sauri ya amsa ta yana cewa. "Yauwa na gode Allah *Afnan* nayi farin ciki sosai da kika kira, *Afnan* wani abu yana faruwa wanda sam na kasa fahimta, yanzu ne ba jimawa ina magana da *Alishart* sai naji *Adnan* yana mata magana, *Afnan* ni ban san abin daya fad'a mata ba wanda ya saka ta kashe wayar ta. *Afnan* zuwa yanzu layin ta gaba d'aya bai ya tafiya shi kuma bai ya d'aga kira na, *Afnan* ba zan 'boye maki ba ina cikin k'unci sosai sabo da ban san abin da yake faruwa dasu ba, ni na damu sosai a kansu shi yasa ma na fara zuwa garesu gobe ina fatan dukansu suna lafiya." Daga yanayin yanda yake magana ta fahimci cewar yana tare da damuwa sosai, tayi shiru kad'an tare da jan numfashi sannan daga bisani ta amsa shi. *"Adyan* shin video call ka kira *Alishart.?"* "A'a voice call ne amma mai ya saka kika tambaya.?" "Ba komai kawai dai ni ina san na sani ne." *"Afnan* dan Allah ki sanar da ni wani abu a game da dukansu biyun kafin ni nazo." "Shikenan *Adyan* ni zanyi hakan to ka kula sosai sai da safe." "Na gode sosai *Afnan."* Da kuma haka suka yi sallama ta dawo da kallonta ga *Adnan* kafin ta furta komai ya tashi ya fita, ita ma tashi tayi ta bisa a baya yana fita kai tsaye d'akin *Alishart* ya nufa ita ma haka, sun shiga ciki sun samu har zuwa wannan lokacin kuka take kuma kuka sosai, da sauri suka qarasa inda take suna rarrashin ta bayan wani lokaci *Adnan* ya shiga tambayar ta. "Qanwata shin video call nazo na samu kina yi da *Adyan.?"* Ta girgiza ka tare da furta a'a yaci gaba yana cewa, "to mai kike yi da laptop a wannan lokacin.?" "Yayana nifa karatu kawai nake yi masa shi yasa nake anfani da laptop, to amma mai ya saka kai kake fishi da ni sosai shin ni na aikata maka wani zunubi ne.?" Cike da k'unci ya dafe ka hanu biyu tare da furta. "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un mai na aikata ne haka? Ki yafemin qanwata ya kamata nayi magana da *Adyan* yanzu." Ya kar'bi wayar *Afnan* ya shiga kiran layin *Adyan* yana ringing amma bai d'aga ba, ya kira da dama amma bai d'aga ba hakan ya tabbatar wa da *Adnan* cewar ba lafiya. Ya tashi da sauri ya fita dukansu sun bisa a baya wanda kuma d'akin sa ya nufa, sun shiga ciki dukansu da sauri *Adnan* ya d'auki wayar sa, ya shiga kiran layin Appa ba jimawa ya d'aga ba tare da sun gaisa ba *Adnan* ya fara magana. "Appa ya kamata ka had'u da *Adyan* yanzu sabo da bai ya cikin kyakkyawan yanayi." "Ok na gode sosai *Adnan."* Ya amsa shi da ba komai sunyi sallama, "duka wannan laifi na ne ba zan ta'ba gafarta wa kai na ba idan har wani mummunan abu ya faru da *Adyan.* Da akwai buqatar na hukunta kai na ko na samu wani daban ya hukunta ni ina buqatar hukunci sosai, ni na aikata babban zunubi wanda yake da matuqar girma sosai." "Yayana wai mai yake faruwa ne dan Allah ka sanar da ni please.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "ba komai qanwata 'yar damuwar kad'an ce dare yayi sosai ya kamata ki tafi ki kwanta kinji sai da safe." Ta amsa shi da to ta juya ta fita bayan tafiyar ta *Afnan* ta qarasa inda yake ta zauna kusa da shi kusa sosai, sai kallonsa take ta d'ora hanun ta a kan nasa tare da saka faratan ta cikin nasa ta d'an matse kad'an, ta yanda ba zai ji zafi ba kallonta kawai yayi ba tare daya furta komai ba. "Besty dan Allah ka dena hukunta kanka haka sabo da hakan yana cutar da ni sosai, kai ba kayi komai ba kawai kana kare qanwarka ne wannan kuma abin daya dace ne, kiyi magana da *Adyan* na tabbata zai fahimce ka sannan kuma ba zai yi fishi ba." Ya shafi hanun ta da yake cikin nasa tare da sunbata. "Na gode Besty na idan baki to ba zan iya yin komai ba, ke ce gwarin guiwa ta kuma garkuwa ta to ina san kiyi man alkawarin cewa ke ba zaki ta'ba bari na ba na har abada." Ta jinjina masa ka tare da furta masa, "eh nayi alkawari ba zan ta'ba barin ka ba na har abada, zan rayu da kai har k'arshen rayuwata wannan alkawari ne kuma zan cika alkawari na insha Allah. Besty ni gaba d'aya gaskiyar nake fad'a ma to zaka iya yarda da ni." "Na gode sosai Besty." Ya fad'a tare da sunbatarta tayi murmushi sosai tare da janyo sa jikin ta, tare da sunbatarsa yayin da take magana da zuciyarta. "Besty ina matuqar qaunar ka sosai kamar yanda kai ma kake, ina fatan zuwan ranar da zaka sanar da ni gaskiyar cewa kana so na, zanyi farin ciki sosai da zuwan wannan ranar ina qaunarka sosai." Ta kai kallonta garesa ta ga idanuwansa rufe ga a lama yayi barci, murmushin ta ya qaru ta shafi fuskarsa zuwa kansa tare da sunbatarsa, ta wani qara saka shi jikin ta tare da rufe idanuwan ta ba jimawa ita ma barci ya d'auke ta............ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/21, 3:52 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 25* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 19/01/2022* *Time 10:34pm* *Typing............* Kiran salla ne ya tashe shi daga barci ya sauke kallonsa ga fuskar *Afnan* wacce take barci a zaune, wani irin kallo yake yi mata kallo sosai ya tashi zaune, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake kuma kallo sosai. Ya shafi fuskarta zuwa gashin kanta lokaci d'aya kuma ya samu kansa da sunbatarta, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, tayi tozali da fuskar shi, lokaci d'aya ta saki wani kyakkyawan murmushi sosai. Shi kuwa dai har zuwa wannan lokacin kallonta kawai yake kallo sosai, ba kuma tare daya furta mata komai ba ita ma haka kallonsa take cikin kwantar da murya take magana. "Barka da asuba Besty na fatan ka tashi cikin k'oshin lafiya babu sauran wani k'unci.?" "Mai ya saka kika yi haka ta ya zaki kwana a zaune yayin da kike rungume da ni? Besty hakan sam ba adalci bane kuma sam bai kamata ke ki aikata min hakan ba, gaskiya naji wani iri sosai sannan kuma naji ba dad'i, amma kuma duk da haka ina godiya sosai na gode da kulawar ki a kai na na gode sosai." "Besty dan Allah ko zaka dena wannan yawan godiyar haka please? Domin ni a shirye nake da nayi komai sabo da kai musamman wanda zai saka ka farin ciki sosai, lokaci ya tafi sosai an fara ik'ama ya kamata ka tafi masallaci yanzu." Tana cikin magana suka ji Papa yana buga musu k'ofa tare da fad'ar sunan *Adnan,* da sauri ya rufe mata baki tare dayi mata a lamar tayi shiru, ta jinjina masa ka tana murmushi jin Papa yana ta buga k'ofar tare da fad'ar sunan sa yasa shi amsa wa. "Naam Papa na tashi zan shiga toilet nayi alwala ne." "Hakan yayi kyau to ka saman a parlour." Ya amsa shi da to Papa ya juya ya nufi parlour ta sunbaci hanun sa da yake kan bakinta, yayi murmushi sosai mai tare da 'yar dariya sannan ya tashi ya shiga toilet, ba jimawa sosai ya fito ya fita zuwa masallaci ita ma tashi tayi ta shiga toilet tayi alwala ta fito ta fara salla. Bayan ta idar tayi azkar sannan ta tashi ta nufi bedroom d'in *Alishart,* hakan tasa ko da *Adnan* ya dawo bai same ta a d'akin sa ba, ya nufi gado ya kwanta tare da d'aukar wayar sa ya shiga kiran layin Appa, wayar ta jima tana ruri kamar zata tsinke sannan ya d'aga kiran bayan sun gaisa *Adnan* yaci gaba da magana. "Appa *Adyan* fa fatan ba abin daya faru da shi.?" "Eh na isa gurin sa a kan lokaci na samu na ba shi magani sai yayi barci, har zuwa wannan lokacin barci yake na gode sosai da kulawa, ko yaushe kana kare shi daga shiga hatsari kai aboki na gari ne sosai, nayi farin ciki sosai daka shiga rayuwar sa Allah ya ma albarka." "Ba komai Appa ka dena yi mun godiya ni zanci gaba da kare *Adyan* daga shiga hatsari iya rayuwa ta, sabo da shi ba kawai abokina bane a'a ina jinsa tamkar d'an uwa na jini ina qaunarsa sosai wannan ce gaskiyar." *"Adnan* kai kana da kirki sosai Allah yayi albarka na gode sosai." Ya amsa shi da Amin da kuma haka suka yi sallama nan kuwa ya shiga kiran layin *Afnan* ringing biyu ta d'aga. "Mai ya saka kika tafi.?" "Ba komai Besty kawai dai ina san na shirya ne ka san muna da shiga kotu k'arfe goma, to ya kamata ka shirya yanzu sabo da akwai gunda zamu fara tafiya kafin shiga kotu." "Eh Besty ban manta ba kawai dai ina san na k'ara yi maki godiya ne na gode sosai da kulawa Allah ya bar zumunci ya kuma bar qauna da kuma tare Allahumma Amin ya hayyu ya kayyum." "Ko zaka dena wannan yawan godiyar? Lokaci na tafiya ka tashi ka fara shirin ka karmu makara ka ji ko." Ya amsa ta yana murmushi tamkar da yana a gaban ta da kuma haka suka yi sallama. Ya tashi ya nufi toilet domin yayi wanka ba jimawa ya fito ya fara shirin sa, ya shirya tsab ya d'auki wayar sa ya kama aikin chart haka yake ko a gurin *Afnan.* Tayi shirin ta tsab wanda kuma sai lokacin ne ta fito ta nufi gida, tana k'oqarin fita Mamie ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. *"Afnan* ki jira muyi break past mana dan Allah." Ta jinjina mata ka a lamar to ta qarasa inda take tare da gaishe ta, ta kuma ta ya ta sun shirya abinci a tare ba jimawa su Papa suka fito sun fara gaisawa sannan suka nufi tebur, sunyi break past cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa *Afnan* ta tashi ta nufi gida. Tare ta fita da *Adnan* sun shiga gidan sun samu su Ummu suna break past, sun gaisa dasu *Afnan* ta nufi d'akin ta domin ta canja kayan jikin ta, ba jimawa ta fito *Adnan* ya tashi sun fice. *England.* Zaune suke suna fira cikin raha wasa da dariya sai ga *Adyan* ya fito cikin sauri, har kamar zai fad'i da sauri dukansu suka shiga fad'ar sunan sa tare da tambayar sa. *"Adyan* ka tafi a hankali mana, ina ma zaka tafi ne kake wannan uban sauri haka.?" "Appa yau ina da kallon wasa ne to kuma an kusa a fara wasan shi yasa nake sauri sosai, sabo da ba zanso a fara wasan bana gurin ba shikenan ni zan tafi sai na dawo." *"Adyan* kana san wasan tsere sosai amma kuma hakan babban qalubale ne ga lafiyar ka, to ina fatan ba zaka manta da wannan ba? Ta yanda ba zaka yi kuskuran shiga wasan ba." Yayi shiru na jim kad'an sannan ya jinjina masa ka a lamar eh, *"Adyan* to yanzu ina san kayi man alkawari ni da Ammie cewar kai ba zaka yi ko wane wasa wanda yake da hatsari ba." Yayi shiru na wani tsayin lokaci sannan daga bisani ya amsa shi. "Appa kawai dai ku yarda da ni sosai na muku alkawarin zan iya kulawa da kai na sosai, sannan kuma ba zanyi abin da zai saka rayuwa ta a cikin hatsari ba ni zan kasance lafiya." *"Adyan* mu kawai mun damu ne a kanka da kuma lafiyar ka, shi yasa muke dakatar da kai duk wani abin da yake da hatsari to kayi hak'uri a kan hakan." "Appa Ammie kuyi hak'uri ku yafe man a kan komai dan Allah." *"Adyan* mai kuma kake fad'a ne haka? Kai yaron kirki sosai to ba buqatar ka fad'i haka ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to dukansu sun rungumi juna tare da sunbatarsa sannan ya tashi ya fita, tafiya kawai yake amma sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi yayin da tinani iri daban-daban yayi yawan gaske a tare da shi sosai, da kuma haka ya isa gurin wasan a nan cikin mota yayi duk wani shirin sa kamar dai yanda yasa ba. Sannan ya fito ya nufi gurin wasan wanda zuwa wannan lokacin har an fara gudanar da wasan, da sauri ya qarasa gurin har yana gudu ya hau nasa mashin ya bisu a baya, lokaci d'aya gurin ya d'auki ihu tare da anbatar sunan sa *Adlishart* shi ne sunan da a kafi fad'a a gurin, hakan yana matuqar yi masa dad'i sosai tare kuma da qara masa gwarin guiwa sosai. A zahirin gaskiya yana da tarin masoya da mabiya sosai duk da cewar basu san a salin fuskar sa ba, sabo da yana 'boye fuskar sa da fice max ga kuma hular kwano hakan yasa ba wanda ya san fuskar sa. Duk da cewar shi ne wanda yazo na k'arshe a tafiya amma kuma shi ne wanda yayi nasaran lashe wasan, ko yaushe shi ne wanda yake yi nasara a wasan hakan tasa ya tara tarin masoya da mabiya sosai. Sunan *Adlishart* ya zaga ko ina na duniya amma kuma ba wanda ya san fuskar sa, kamar dai tauraron mawak'in nan wanda yayi suna a k'asar England dama k'asashen duniya baki ďaya, wato secret super star wanda wasu mutane suke dan gan tasa da aljan. Ya kar'bi kyautar sa kamar dai ko yaushe yayi photo da masoyan sa sannan ya tafi, wanda kuma kai tsaye office ya nufa a zahirin gaskiya yana tare da gajiya sosai, yana shiga ciki ya nufi firij ya d'auki rubar ruwa ya qarasa inda maganin sa ya sha magani, ya tafi yayi kwance a kan kujera sai wani irin yanayi mara dad'i yake ji a tare da shi ba jimawa sosai yayi barci. *Nigerian.* Gudu take iya k'arfin ta tana furta kalmar ku bani yarona yayin da take wani irin kuka abin tausayi, daga gaban ta kuma wasu yara ne suke tsokanar ta da teady a matsayin yaronta da take nai ma. Tana cikin binsu lokaci ďaya ta ji ta fad'a ruwa cike da firgici ta saki ihu tana kururuwar nai man taimako, yaran kuwa sai dariyar ta suke suna tsokanar ta yayin da ita kuma take kuka. "A'a ku dena nace ku dena a'a! A'a!! A'a!!!." Ihun sa ne ya tashi Prof daga barci ya shiga tashin sa ta hanyar buga pillow da yake kwance tare da fad'ar sunan sa, firgigit ya tashi wani a firgice yayin da bakin sa yake furta kalmar a'a cike da firgici ya fad'a jikin Dadyn sa, shi kuwa yayi masa wata kyakkyawar runguma sosai yana wani buga bayan sa, bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a haka *Adeel* ya fara magana. "Dady wacece ita kuma mai ya saka ko yaushe take zuwa a cikin barci na? Hakan yana saka wa naji wani iri sosai sannan kuma ina shiga k'unci sosai." "Ka dena damuwa yarona sabo da kawai a mafarki ne kuma mafarki ba gaskiya bane, ni ba zan ta'ba barin wani ya cutar da kai ba zanci gaba da kare ka iya rayuwa ta wannan alkawari ne." "Na gode Dady na." Ya fad'a tare da qara shigewa jikin sa shi kuwa ya runguma sa sosai jikin sa, sun jima a haka sannan daga bisani suka koma barci bayan kwana biyu suna cikin cin abinci Prof ya anbaci sunan sa. *"Adeel* ina san na shirya zuwan ka U. K makaranta ina san ka kammala karatun ka na zama Prof, zanyi farin ciki sosai idan har kai ma ka zama Prof to kawai ka fara shirin tafiya." Yayi shiru kad'an yana nazari sannan daga bisani ya amsa shi, "Dady gaskiyar ita ce ni bana san na tafi ko ina, ka riga daka san komai a game da lafiya ta shi yasa ba zan iya yin nesa da kai ba. Dady kai kad'ai nake da shi to ba zan ta'ba barin ka ba na har abada, Dady ni wannan degree dana yi ya ishe ni sam bana buqatar na zama Prof sabo da ina da kai, sannan kuma ina tare da kai to wannan ma kawai ya isa kuma ina farin ciki sosai da hakan ina qaunarka sosai Dady na." "Karka damu *Adeel* sabo da ni zanyi komai sabo da kai ina qaunarka sosai d'ana, kai ne d'an da nafi so kai ne wanda na za'ba fiye da sauran sabo da kai ne wanda nafi so, ina sanka da duka zuciya ta dama rayuwa ta gaba d'aya shi yasa na baka duka soyayya, ina matuqar qaunar ka sosai d'ana." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai. Cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adeel* yake magana, "Dady nifa sam na kasa fahimtar abin da kake fad'a, shin wai kai kana da wasu yaran ne bayan ni.?" Ya girgiza ka yana murmushi sannan ya amsa shi, "A'a ďana ba abin da nake nufi ba kenan ba, ina nufin kai ne kawai ďana sabo da tin bayan Mummyn ka ta mutu, ban k'ara tinanin nayi wani aure ba sabo da kai kad'ai nake so a matsayin ďana wannan ce gaskiyar ďana." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar ina qaunarka sosai d'ana, yayi murmushi sosai yayin da farin ciki yake ta shigarsa sosai, cike da farin ciki da d'auki ya fad'a jikin sa shi kuwa yayi masa wata kyakkyawar runguma sosai. Yana ta shirin fita sai ga Anwar ya shigo Abba ya koma ya zauna bayan sun gaisa Abba yaci gaba da magana. "Anwar dama kuwa da akwai abin da nake san na sanar da kai, jiya Baba ya saka ranar auran *Afnan* da Auwal ta mako hud'u insha Allah." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Abba ni sam na kasa fahimtar abin da kake fad'a Auwal fa kace to ta ya ma hakan zata kasance? Mai ya saka Kaka zai yi haka amma Abba ka sanar da shi cewar *Afnan da Adnan* suna tare.?" "Eh Anwar na sanar da shi amma kuma sam bai saurare ni ba." "Shikenan ni zan kula da wannan zanyi komai domin na dakatar da auran, ni ba zan ta'ba barin wani ya raba su biyun ba wannan alkawari ne, to dan Allah karka dakatar da ni please." "Anwar ina jin tsoro sosai sabo da Baba yana da zafi sosai." "Karka damu Abba kawai ni zanyi abin daya dace ne, to zaka iya yarda da ni please." Ya jinjina masa ka a lamar to bayan wani lokaci suka tashi suka fita ko wannan su ya nufi office ďin sa.................. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/23, 7:33 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 26* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 21/01/2022* *Time 05:25pm* *Typing...............* Yana ƙoƙarin fita da mota sai ga Anwar ya shigo da mota ganin sane yasa shi fitowa, yayi tsaye jikin mota ba jimawa Anwar ya fito ya kuma nufi gurin sa kafin ya furta komai ya masa ƴar rige. "Sannu da zuwa abokina kuma siriki na, yanzu nake ƙoƙarin tafiya zan koma Jos ne gurin aiki, saura kaɗan ka samu bani nan, to mu shiga daga ciki domin kuwa na tabbata gurina ka zo." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai. "Auwal ni sam bana buƙatar shiga ciki domin yin magana da kai, kafin yanzu nayi tunanin cewa kai aboki na gari ne a gare ni, sannan kuma Yaya na gari a gurin *Afnan da Adnan* amma kuma nayi kuskure sabo hakan k'arya ne, Auwal kamar dai ni na fad'a maka cewar karka shiga rayuwar *Afnan da Adnan* sabo da hakan zai cutar da su sosai. Na kuma ja maka kunne a kan cewa kabar zancen iya mu biyu kawai, to amma mai ya saka ka sanar da Kaka wannan? Ta ya ma har zaka yi tunanin aikata hakan shin ka kuwa san irin girman zunubin da kai ka aikata kuwa.?" "To ka sani wannan ba kuskure bane a'a wannan zunubi ne kuma ni zan hukunta ka a kan zunubin ka, Auwal wallahi tallahi koma mai zai faru to zanyi komai domin na dakatar da auran ka da qanwata. Ba zan ta'ba baka damar da zaka cutar da *Afnan da Adnan* ba su biyun kawai an aife sune sabo da junansu, to kuwa zasu ci gaba da kasancewa a tare na har abada wannan alkawari ne kuma zan na cika alkawari na insha Allah." Magana yake cike da fishi da 'bacin rai sosai Auwal kuwa sai kallonsa yake yana murmushi, "Anwar ni na baka damar a kan ka aikata duk wani abin da zaka iya, amma kuma ka sani wallahi tallahi ba zaka ta'ba yin nasara ba sabo da Kaka yana tare da ni. To babu wani abin da zai dakatar da aure na *Afnan* nan da mako hud'u kamar dai yanda Kaka ya saka, Anwar a baya na goyi bayan ka sosai da zaka auri qanwata, amma kuma kai baka san ni nayi aure da qanwarka mai yasa kawai sabo da *Adnan* ne? Shi fa kawai mak'ocin kune kuma bare ni kuma abokin ka kuma ahalinka." Anwar ya dakatar da shi cikin tsawa tare da d'aga murya, "ya isa haka Auwal karka k'ara fad'ar wani abu a kan qanina kuma ka sani *Adnan* ahalinmu, shi ahali bawai yana nufin jini ba a'a kyakkyawar halak'a ita zata canja zuwa ahali. Auwal kasancewar Kaka yana 'bangaren ka hakan baya nufin ka samu qanwata, a'a ni ba zan ta'ba barin hakan ta faru ba wannan alkawari ne kuma zan cika alkawari na insha Allah." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa Auwal ya bisa da kallo har ta fice, shi ma mota ya shiga ya fita wanda kuma kai tsaye gidan Kaka ya nufa inda ya shiga sanar da shi k'arya da gaskiya. Kaka ya shiga rarrashin sa tare da nuna masa cewar yana tare da shi sosai, hakan ya qara masa farin ciki sosai bai wani jima ba kasancewar a hanya yake, yayi sallama da Kaka ya tashi ya kama hanyar jos domin koma wa gurin aiki, bayan tafiyar sa Kaka ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin Abba, ba jimawa ya d'aga kafin ya furta komai Kaka ya masa rigagi ta hanyar furta masa kalmar, "kazo yanzu ina san ganin ka." Yana kai k'arshen maganar sa ya kashe wayar sa ba tare da jira ya amsa shi ba. Hakan yayi matuqar saka Abba cikin sark'ak'iya sosai cikin hanzari ya bar office ya nufi gidan Kaka. Ya samu Kaka cikin fishi sosai cikin hanzari tare da nuna kulawa yake tambayar sa mai yake faruwa, cike da 'bacin rai sosai tare da tarin damuwa Kaka yake magana. "Abubakar ya kamata ka k'ara sauri sosai gurin duka shirin ka domin na dawo da auran Auwal da *Afnan* mako biyu insha Allah." cike da jin mamakin abin daya fad'a Abba yake magana. "Baba shin wani abu ya faru ne mai ya saka zaka dawo da ranar mako biyu? Shin ni na aikata wani zunubin ne da kake hukunta ni ta wannan hanyar dan Allah ka sanar da ni please.?" Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi, "a'a wannan kawai hukunci na kenan kuma ba zan ta'ba canja hakan ba, to ka tafi ka ci gaba da shirin ka yanzu zaka iya tafiya." "Baba shin kai kana fishi da ni ne dan Allah ka yafemin please." "Abubakar ni sam bana fishi da kai to ka dena bani hak'uri Allah yama albarka." Ya amsa da Amin bayan wani lokaci ya tashi ya koma office bakin aiki, yayin da tausayin *Afnan da Adnan* yayi yawan gaske a tare da shi sosai da yamma bayan ya dawo gida yake sanar da Anwar abin da Kaka ya fad'a masa. "Anwar shin ka tafi gurin Baba ne dan Allah ka sanar da ni gaskiyar please.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, "a'a Abba ban tafi ba amma nayi magana da Auwal." Nan ya shiga sanar da shi komai, "Anwar mai yasa kayi hakan na fad'a maka cewar Baba yana da tsauri sosai, yanzu kaga irin hukuncin daya yanke ya dawo da auran mako biyu, ban kuma san abin da zan iya yi ba a cikin mako biyu domin dakatar da auran. Anwar ni ban san ya zanyi ba duk da cewar hakan yana matuqar cutar da ni sosai, ta ya zan iya fuskantar *Afnan* da irin wannan mummunan labarin ba zan iya jure ganin k'uncin da zata shiga ciki ba." "Karka damu Abba ni zanyi komai domin ganin na dakatar da auran kuma zanyi nasara insha Allah, to kawai dai ka yarda da ni sannan kuma karka sanar da qanwata komai a game da wannan please." "Anwar ni ina jin tsoro sabo da Baba zai iya dawo da auran gobe to kawai ka barmin komai, ni zan kula da komai ina fatan nayi nasara a kan abin da muke fata." "Shikenan Abba ina fatan muyi nasaran dakatar da auran." Ya jinjina masa ka a lamar eh suna haka sai ga *Afnan* ta shigo wanda kuma tare take da Amal, da gudu Amal ta nufi gurin Abban ta wato Anwar shi kuwa ya d'auke ta yana murmushi, *Afnan* ta gaishe su sannan ta nufi d'akin ta sun bita da kallo suna girgiza ka cike da jin tausayin ta. Bayan kwana biyu zaune take tana kallo taji a na buga mata k'ofa ta tashi ta nufi k'ofa, ta isa k'ofa tare da bud'e wa ta samu *Afnan* tsaye a gefen k'ofa tayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan ta. "Sannu da zuwa sirika ta kuma Amaryar mu shigo ciki." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai, ita kuwa sai kallonta take tana wani gajeran murmushi sun tafi sun zauna *Afnan* ta anbaci sunan ta. "Aunty wai a kan me kike magana ni sam na kasa fahimtar abin da kike fad'a? Sannan kuma kin kira ni da wani sabon suna mai ya saka kika kira ni da Amarya.?" Murmushin ta ya k'aru sosai sai wani kallon *Afnan* take daga bisani kuma ta amsa ta. *"Afnan* ki dena wani wayancewa sabo da nima na san gaskiyar, a kwana biyun nan zamu fara shirin auran ki amma dai ni ba zan kira ki da Aunty ba, sabo da kin jima kina kira na da Aunty amma k'ila na kira ki da matar Yaya." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin da taji ta fad'a take magana. "Aunty wai a kan me kike magana nifa sam na kasa fahimtar abin da kike fad'a, Aunty dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa mai ya saka kika kira ni da Amarya.?" *"Afnan* karki fad'a min cewar baki san cewar za a yi auran ki da Yaya Auwal ba.?" "Mine ni nayi aure da Yaya Auwal? A'a sam hakan ba zata ta'ba kasancewa ba har abada. Amma Aunty wai gaskiyar kike fad'a kuwa ko dai kina tsokanata ne.?" "A'a *Afnan* ni gaskiyar nake fad'a za a yi auran ki da Yaya Auwal nan da kwana sha biyu insha Allah." Cike da firgici take furta kalmar A'a ta tashi da sauri zata fita lokacin yayi daidai da shigowar Anwar, da sauri ya isa inda take yana tambayar ta abin da yake faruwa da ita. "Yaya ka fad'a min cewa ba gaskiya bane ni ba zan auri Yaya Auwal ba, ni bana san na aure sa to dan Allah ka dakatar da wannan auran please." "Eh qanwata abin da nake ta k'oqarin yi kenan shi yasa ma ba kiji zancan daga garemu ba, *Afnan* har yanzu Yayan ki yana nan kuma zai yi komai sabo da farin cikin ki, to kawai ki yarda da ni kinji dan haka ki dena wannan kukan bana so kinji ko please." Ta jinjina masa ka a lamar to shi kuwa ya shiga share mata kwalla tare da sunbatarta, bayan wani lokaci ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata ta juya ta fita zuwa part d'in Abba, bayan tafiyar ta Anwar ya mai da kallonsa ga Anisa wacce ita ma kallonsa take, wani irin wawan kallo yake yi mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewar yana fishi da ita kuma fishi sosai. Ya juya ya nufi bedroom ita ma tashi tayi ta bisa a baya ta shiga ciki ta same sa sai safa da marwa yake, ta isa inda yake tare da fad'ar sunan sa amma bai amsa ba duk da haka taci gaba da magana. "Yaya Anwar lafiya mai ya saka kai baka san yi man magana.?" "Anisa dan Allah ko zaki iya fita daga nan? Kawai ki tafi ki bar nan duka wannan laifin Auwal ne kuma ni ba zan ta'ba barin yayi aure da *Afnan* ba, idan kin ga dama to zaki iya yarda da kowa wannan amma kuma daga k'arshe ni zanyi nasara." "Yaya Anwar amma mai ya saka kai baka san su biyun suyi aure.?" "Anisa na fad'a maki ki bar nan to ki tafi jeki man ki tafi." Ta amsa da to ta juya ta fita shi kuma yaci gaba da nai man mafia, washe gari bayan ya qarasa shirin ya nufi gurin *Afnan* jin ya kira wayar ta layin ta a kashe, ya shiga gidan tare da shiga ciki bai samu kowa a parlour ba hakan ta ba shi damar shiga d'akin *Afnan.* Ya shiga ciki ya hangeta zaune a tsakiyar gado ta had'e kai da guiwa tana kuka, da sauri ya qarasa inda take yana fad'ar sunan ta ya d'ago fuskarta sai wani kallonta yake kallo sosai, ya shiga share mata kwalla yana rarrashin ta lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin hugging d'in ta, yana sunbatarta ita kuwa tayi kwance jikin sa tamkar wacce za a mai da ciki a aife, sun jima a haka sannan daga bisani ya fara magana. "Besty dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa dake please.?" Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa take sanar da shi abin da yake faruwa, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data fad'a yake magana. "Besty wai kinji abin da kike fad'a kuwa? Ta ya ma hakan zata faru to amma ke kin amince da auran kuwa.?" "Besty shi Baba magana d'aya tak yake to ba zan iya canja hakan ba." "Eh gaskiyar ki ne dama ku biyun ahali d'aya ne k'ila shi yasa Kaka yaga ya dace ku biyun kuyi aure, ina yi muku fatan alkhairi tare da kyakkyawan zama bayan kunyi aure. Babbar qawata kuma aminiya ta zata yi aure ta ya kamata nazo na fara shiri na, sabo da ina san nayi shiri na musamman amma kuma zanyi kewarki sosai, sannan kuma hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai amma zan jure fatan alkhairi Besty na, amma ke zaki yi kewata kuwa fad'a min shin zaki yi kewata kuwa.?" Kallonsa kawai take yayin data gagara furta masa komai sai wata soyayyar sa take ji tana qara shigarta, ta ko ina jikin ta shi ma haka kallonta yake wanda shi ma yana cikin yanayi irin nata. "Hak'iqa zanyi matuqar yin kewarka sosai sabo da ni sam ban saba da rashin ka ba, Besty ni sam bana jin cewar zan iya jure wannan ba sabo da yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai. Besty gaskiyar ita ce ni nayi matuqar sabo da kai shi yasa sam bana san na barka sabo da hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai." "Besty shin ba zai yu ki dakatar da wannan auran ba? Ina nufin kawai ki fad'a wa Yaya Auwal cewar ke bakya sansa ta hakan ne shi da kansa zai dakatar da auran. Wannan ce kawai damar da kike da ita na kasancewa tare da ni na har abada to kawai kiyi hakan." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Ita kuwa sai kallonsa take kallo sosai yayin take jin soyayyar sa na k'ara shigarta sosai, jin shirun shirun yayi yawa yasa ya sake daga rungumar da yayi mata ya tashi yayi tafiyar sa, ita kuwa ta bisa da kallo ba tare data dakatar da shi ba ya isa gida kai tsaye d'akin sa ya nufa. Yayi tsaye jikin bango sai wani kallon photon su yake kallo sosai, ya shafi photon tare da sunbatar fuskar *Afnan* lokaci d'aya ya samu kansa da zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Cike da k'unci ya watsar da kayan da suke kan madubi tare da furta a'a, ihun sa ne yayi sanadin shigo da Mamie cikin d'akin da sauri ta isa inda yake tare da rungumasa jikin ta, ta shiga rarrashin sa tare da anbatar sunan sa ta riqa shi sun tafi sun zauna cike da nuna kulawa take magana da shi. "D'ana mai yake faruwa da kai ne haka dan Allah ka sanar da ni miye damuwar.?" Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake sanar da ita abin da yake faruwa, *"Adnan* shin kai kana san *Afnan* da aure ne.?" "Eh Mamie ina matuqar masifar qaunar ta sosai sannan kuma bana san na rasa ta ga shi kuma zata yi aure da Yaya Auwal. Mamie ni ban san ya zanyi ba rashin Besty zai yi matuqar cutar da ni sosai, amma duk da haka zan jure sannan kuma sam bana san ki sanar da kowa wannan musamman Papa, Mamie ina san kiyi man alkawarin cewa ke ba zaki ta'ba sanar da kowa wannan dan Allah." "Amma ďana hakan zai cutar da ni sosai ni kuma sam ba zanso hakan ba to ya kamata nayi wani abu, sabo da na dakatar da wannan auran sannan kuma na sanar da Abban ka shi ma zai iya taimaka." "A'a Mamie dan Allah karki yi please." Magana yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, ta amsa shi da ba zata sanar da kowa ba ya jinjina mata ka a lamar to ta shiga rarrashin sa tana ba shi magana............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/24, 7:49 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 27* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 22/01/2022* *Time 08:51pm* *Typing.................* Bayan kwana biyu suna ta shirin tafiya gurin break past sai ga *Adnan* ya shigo, ya zauna sun fara gaisawa san nan ya shiga tambayar *Afnan.* "Abba Besty fa.?" "Tana d'akin ta." "Shikenan zan duba ta a can." Ya tashi ya nufi bedroom d'in *Afnan* sukam da kallo suka bi shi har ya shige, sannan suka juya suka nufi tebur domin yin break past. Ya shiga ciki tare da rufe k'ofar san nan ya juya da kallonsa ga gado, amma bai same ta a nan ba ya fad'a a zuciyarsa, "bata cikin nan to tana wane gurin ina kuma ta shiga ne.?" Ya juya zai fita k'arar da ya ji ne yasa shi juyo da fuskar sa nan kuwa yayi tozali da fuskar *Afnan.* Wacce take tsaye jikin k'ofar toilet d'aure take da towel a jikinta wanda tsayin sa bai fi cinya ba, wani irin kallo yake mata wanda ban san ta yanda zan iya fad'ar sa ba, ita ma haka irin wannan kallon take yi masa wanda ya gagara fahimtar mai take nufi da shi, wani irin kallo suke yiwa juna kallo sosai ba kuma tare da sun gaji da kallon juna ba. Bayan wani lokaci ya juya domin tafiya ba kuma tare da ya furta mata komai ba, yana ƙoƙarin bud'e k'ofa tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa ya tsaya cak ba tare da ya juya ba ta ci gaba da magana. "Besty mai ya saka zaka fita ba kuma tare daka furta min komai ba? Faɗa min wani abu shin ni na aikata maka wani zunubi ne gaskiyar zaka fad'a.?" Shiru bai amsa ba yayin da yake jin zuciyarsa tamkar wuta dan zafi, ganin bai jiyo da kallonsa gareta ba ya tabbatar mata da ba zai amsa ba, taci gaba da tafiya har ta isa inda yake ta fito ta gaban sa ya kau da fuskar sa daga gareta. "Besty ka amsa ni shin kai kana fishi da ni ne? To amma wane irin zunubi ne aikata maki dana cancanci irin wannan tsats'tsauran hukuncin daga gareka.?" Shiru har zuwa wannan lokacin bai amsa ta ba. "Besty naro e ka dan Allah ka sanar da ni laifin dana aikata maka please.?" Magana take cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai, ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. Kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, shi ma abin da yake yi kenan kamar ba zai yi magana ba mai ya gani kuma ya amsa ta. "Besty ni bana fishi dake kawai dai zan fita ne domin na baki dama ki shirya, to fatan kin fahimci abin da nake nufi yanzu ki tafi ki shirya idan kin qarasa to ki same ni a gida." "Mai yasa kake hukunta ni haka shin yau ba zaka ta ya ni shirya wa ba? Besty ba yau bane rana ta farko da kai ka ganni a haka sannan kuma ko yaushe kana ta ya ni shirya wa, kamar dai yanda nake yi idan na same ka a haka to amma mai ya saka yau kake kau da kanka a kai na.?" Magana take yayin da hanayen ta suke shafar fuskarsa zuwa wuyan sa, sam ya kasa jure irin abin da take yi masa wannan yasa ya janye sa daga jikin sa, ya bud'e k'ofa yayi tafiyar sa ba tare daya furta mata komai ba ita kuwa ta bisa da kallo cike da jin mamakin sa sosai. "Mai yasa Besty yake fishi da ni mai ya saka sam baya san ya sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da shi? Yana cikin k'unci sosai amma kuma baya san ya sanar da ni, zanyi komai domin na taimake sa sabo da ya fita cikin wannan mummunan yanayin." Ta tafi ta shirya ta fito ta fara gaisawa da Ummu sannan ta nufi gurin *Adnan,* ta shiga ciki ta samu Mamie tana kwashe kayan abincin daga tebur zuwa kicin, ta nufi inda take tare da gaishe ta bayan sun gaisa ta shiga tambayar *Adnan.* "Mamie Besty na fa.?" *"Afnan Adnan* ya fita ni nama yi tunanin cewa ku biyun kuna tare." "Ya fita to ina kuma ya tafi kenan.?" "Ban sani ba amma ki kira layin sa sai kuyi magana." "Ta jinjina mata ka a lamar to ta tashi ta fita Mamie ta bita da kallo tana girgiza ka, *Afnan* kuwa ta shiga kiran layin sa amma kuma wayar a kashe take, "Besty wai kana ina haka mai ya saka zaka kashe wayar ka ina fatan ba abin daya faru da kai? Ya Ubangiji ka hana wani mummunan abu ya faru da Besty na Allah ka kare shi a duk inda yake Amin ya hayyu ya kayyum." Ta koma kiran layin Abdallah ba jimawa ya d'aga ta anbaci sunan sa tare da tambayar sa. "Abdallah kana ina.?" "ina office." "Shin kaga Besty na kuwa.?" "Eh yana office amma baya cikin kyakkyawan yanayi." "Na gode sosai sai na shigo." Ya amsa ta da to da kuma haka suka yi sallama, ta shiga mota ta nufi office ta isa office cikin hanzari ta shiga ciki ta samu *Adnan* kwance cikin kujera, ta nufi firij ta d'auko robar ruwa sannan ta nufi gurin da yake ta zauna tare da bud'e jakar ta, ta d'auko maganin sa tare da kai kallonta garesa cikin kwantar da murya take magana. "Besty tin da ba zaka sanar da ni damuwar ka ba shikenan ba zan matsa maka ba, amma yanzu da akwai buqatar ka sha magani sabo da zai taimaka maka sosai." "Kiyi hak'uri ni kawai nayi mafarki da wannan matar ne shi yasa kika ganni a haka, Besty ni na rasa wacece wannan matar da take zomin ku san ko yaushe a cikin barci na. Yanayin yana da matuqar ban tausayi sosai hakan yana saka wa naji wani iri sosai, Besty ban san komai a game da wannan matar ba amma kuma ni nayi matuqar damuwa sosai a kanta. Besty to ya idan kuma wannan mafarkin nawa gaskiya ne fa mai zai faru da wannan matar kenan.?" Magana yake cike da firgici k'unci da 'bacin rai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. "Ka dena damuwa Besty wannan kawai mafarki ne kuma mafarki ba gaskiya bane, to ka kwantar da hankalin ka ka ji ko yanzu ka sha magani please." Ya jinjina mata ka a lamar to nan kuwa ta fara ba shi magani ya kuma sha ba gardama, bayan ya qarasa sha ta d'ora kansa a kan cinyarta tana shafar kansa zuwa bayan sa, ta qara da sunbatarsa ba jimawa sosai barci ya d'auke sa yayin da ita kuma ta rufe shi dana mujiya tana kallonsa. Ya jima sosai yana barci sannan ya farka ta had'a masa madara ya sha, bayan wani lokaci suka tashi suka nufi gida haka dai kwana ki suka riqa shigewa, zuwa yanzu saura kwana biyar auran *Afnan* da Auwal kwance take amma ba barci take ba, waya take da Yayan ta kuma masoyin ta wato *Adyan. "Alishart* fad'a min wani abu shin *Adnan* qlau yake kuwa? A 'yan kwana biyun nan sam bana gane masa shin wani abu yana faruwa da shi ne.?" *"Yaya Adyan* shi ya damu ne sosai sabo da Aunty zata yi aure da Yaya Auwal." Cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana. *"Alishart* wai kina san ki fad'a min cewar *Afnan* zata yi aure da wani daban ba *Adnan* ba.?" Ta amsa shi da eh yaci gaba yana cewa, *"Alishart* amma mai ya saka *Afnan* zata cutar da *Adnan* ta wannan hanyar? Hakan sam ba adalci bane kuma shi bai cancanci hakan daga gareta ba, zanyi magana da shi yanzu zan koma kiran ki an jima." Ta amsa shi da to da kuma haka suka yi sallama nan ya shiga kiran layin *Adnan* wanda sai a karo na uku ya d'aga. *"Adnan* qlau kake kuwa fad'a min shin ka shirya fad'uwa a soyayyar ka? *Adnan* kana san *Afnan* sosai to ya kamata kayi koma miye domin ka same ta, ni zan taimake ka a kan hakan to ya zama dole ka jajirce a kan soyayyar ka domin kayi narasa. *Adnan* har yanzu kana da damar da zaka kasance muji ga *Afnan* to kawai ka tabbatar kayi hakan ka ji ko." *"Adyan* hakan sam ba shi da sauki kamar yanda kake tunani shi ďin ahalin su ne, Kakan su ďaya kuma shi ne wanda ya bada auran Besty ga Yaya Auwal. To bana jin ni zan iya dakatar da auran amma na sanar da Besty ta dakatar da auran, amma kuma har yanzu banji komai daga gareta ba to ina tunanin ko ita ma ta amince da auran, shi yasa nayi shiru sabo da ba wani abin da zan iya." *"Adnan* har yanzu kana da damar da zaka ceci soyayyar ka, kawai ka fuskanci *Afnan* ka bai yana soyayyar ka a gareta kasa taji ba zata rayu ba sai da kai. *Adnan* kayi komai domin ka same ta zan shigo domin na ta ya ka wannan yak'in." Sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama ai kuwa tin daga wannan ranar, *Adyan* ya fara shirin tafiya gida Nigeria bayan kwana uku jirginsu ya tashi zuwa Nigerian. Tare suke dukansu sun sauka a garin Abuja bayan kwana biyu suka nufi Kaduna, wani yammaci zaune suke a part d'in Anwar sun jima a zaune amma duk da haka ba mai magana a cikin su, *Afnan* ta anbaci sunan sa katin ta furta komai suka ji a na buga masu k'ofa, Amal ce wacce ta tafi ta bud'e k'ofa ta dawo tare da Auwal ya isa gurin Anwar ya zauna. Ya ba shi hanu sun gaisa su Anisa sun gaishe sa *Adnan* ya tashi tare da fad'ar sunan *Afnan.* "Besty zan tafi zamu ci gaba an jima." "Shikenan zaka iya tafiya amma idan ka tafi to karka ta'ba dawo wa gareni, wannan hukunci na kenan kuma ba zan ta'ba canja hakan ba." Tana kai k'arshen maganar ta ta tashi ta nufi d'akin ta ya anbaci sunan ta amma bata amsa, ya juya zai fita Anwar yayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. *"Adnan* ka same ta a ciki na tabbata komai zai yi daidai insha Allah, am yauwa idan ka shiga ciki to ka tabbatar ka rufe k'ofar daga ciki sabo da wani zai iya takura ku biyun." Ya jinjina masa ka ya juya ya nufi d'akin *Afnan* cike da k'unci Auwal ya anbaci sunan Anwar. "Anwar kai wane irin Yaya ne taya zaka had'a qanwarka da wani daban? Anwar mai kake aikata wa ne gobe ne za a yi bikin saka ta lalle jibi za a d'aura mana aure amma duk da haka kana had'a ta da wani mai yasa.?" Magana yake cike da k'unci sosai Anwar kuwa sai wani kallonsa yake yana murmushi, cike da izza da gadara yake magana da shi. "Kanka a ke ji wai mahaukaci ya fad'a rijiya ni bani da lokacin magana da kai sabo ina da abin yi, domin naga a lamar kai baka da abin yi Anisa tashi mu shiga ciki wannan umurni ne." Bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta tashi suka shiga ciki cike da k'unci shi ma ya juya ya fita......... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/27, 10:47 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 28* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Sunday 23/01/2022* *Time 08:21pm* *Typing...............* "Yaya Anwar mai yasa kake yiwa Yayana haka? Shi fa kawai cewa yayi yana san *Afnan* kuma zai aure ta, to amma mai ya saka kake hantarar sa kana cin zarafin sa haka? Yaya Anwar ni nayi tunanin cewa ku biyun abokai na gari ne ga juna, kun kasance a tare tin daga matakin yarinta to mai ya saka zaku bar shaidan yayi nasara a kanku? Yaya Anwar dan Allah ku dena duka wannan please." "Anisa nima nayi tunanin hakan amma kuma Auwal ya canja komai, idan har Auwal bai janye zancan auran sa da *Afnan* ba to nima ba zanyi shiru ba. Anisa *Afnan da Adnan* kawai ta dace ba Auwal ba kuma ni zanyi komai domin ganin su biyun sun kasance a tare, ni ba zan ta'ba bawa Auwal damar da zai shiga tsakanin su biyun ba, to kawai ki fita cikin wannan kawai ki zama 'yar kallo kinji ko." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya ya fita ita kuwa ta bisa da kallo cike da jin mamakin sa sosai. Sannu a hankali yake tura k'ofar har ta bud'e ya shiga ciki ya hangeta zaune a gefen gado, ya rufe k'ofar sannan ya nufi inda take sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda take, ya zauna kusa da ita kusa sosai sai wani kallonta yake kallo sosai, lokaci d'aya ya samu kansa da sunbatarta a gefen fuska cikin tautasa murya tare da kwantar da ita yake magana. "Ni kawai nayi tunanin cewa ku biyun zaku yi magana ne, shi yasa na buqaci tafiya amma kiyi hak'uri ki yafemin sannan kuma karki yi fishi da ni please." Shiru bata amsa ba jin shirun yayi yawa yasa taci gaba da magana. "Besty gobe ne a ke bikin saka ki lalle ke da Yaya Auwal to nayi tunanin zai sanar dake wani abu ne sannan." "Ya isa kayi shiru haka ko kuma dai ka tashi ka fita, sabo da ba zan jure sauraran wad'an nan lafuzzan naka ba to gara kawai ka tafi." "Shikenan zan tafi kamar yanda kika buqata ina fatan karki jima sosai a cikin wannan yanayin." Ya yunk'ura zai tashi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa, sai wani kallonsa take kallo sosai shi ma abin da yake yi kenan, wani irin kallo suke yiwa juna mai tare da so sun jima sosai a haka sannan ta fara magana. "Da gaske tafiya zaka yi zaka tafi ka barni a cikin wannan yanayin ba tare da kayi komai? Shikenan zaka iya tafiya amma ka sani wannan tafiyar da zaka yi, ita ce babban zunubin da zaka aikata min a rayuwa, kuma ba zan iya yafe maka wannan ba na har abada." Magana take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Nan kuwa ya shiga share mata kwalla sai wani kallonta yake kallo sosai, ya shafi fuskar ta tare da sunbatarta fuska zuwa wuya ya sauke kallonsa a kan bakinta, ya kai hanun sa ga le'benta sai wani shafar le'benta yake yana murza wa, ita kuwa ta wani lumshe ido tamkar mai barci ya k'ara matsawa kusa da ita kusa sosai. Ya fito da harshensa ya lashi le'benta tare da d'an cizawa kad'an ta yanda ba zata ji zafi ba, lokaci d'aya kuma ya samu kansa da sunbatarta a baki cikin qauna da soyayya yake tsotsar le'benta dama harshen ta, yayin da hanayensa suke shafar kanta zuwa bayan ta sun jima sosai a haka sannan daga bisani, sannu a hankali yake fitar da bakinsa cikin nata har ya fitar. Yayi tozali da kyakkyawar faskar ta sai wani kallon juna suke kallo sosai, ba kuma tare da sunji sun gaji ba kamar dai yanda basu furta wa juna komai ba, sun jima sosai a haka sannan daga bisani ya janye ta daga jikin sa ya tashi ya fita, ta bisa da kallo har ya fice ba kuma tare data dakatar da shi ba lokaci d'aya taji wani farin ciki yana shigarta sosai. "Besty kana matuqar sona sosai kamar dai yanda nake matuqar masifar qaunar ka sosai, amma na rasa dalilin da yasa ka gagara sanar da ni gaskiyar cewa kana sona, wanda wannan dalilin ne yasa ni amince wa auran Yaya Auwal. Gobe ne a ke bikin saka ni lalle jibi kuma a ke d'aura aure na da Yaya Auwal ina fatan wani abu ya dakatar da auran, ya Ubangiji ka aiko da wani abin da zai dakatar da aure na da Yaya Auwal Allahumma Amin." Ta d'auki wayar ta ta tura masa text d'in na gode, kwance kawai yake yayin da tunani iri daban-daban yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Ya damu sosai a kan auran *Afnan* da Auwal ga shi kuma ba abin da zai iya, yana haka yaji wayar sa tayi k'ara a lamar shigowar sako ya duba ya ga sakon *Afnan.* Ya sunbaci wayar sannan ya amsa ta da ok da dare Papa ya shiga tambayar Mamie, ko ta san wani abin da yake damun yaronsu ta amsa shi da a'a, a zahirin gaskiya ya damu sosai da yanayin sa washe gari yau gidan Abba sai d'aukan mutane yake, kasancewar yau ne ranar da a ke saka *Afnan* lalle tin misalin k'arfe goma ya bar gida ya nufi wani guri daban. Mamie na shirin fita zuwa gidan Abba sai ga *Afnan* ta shigo, bayan sun gaisa ta shiga tambayar ta *Adnan* ta amsa ta daya fita. "Mamie ina kuma ya tafi.?" "Gaskiya ban sani ba sai dai kiyi magana da shi a waya." Ta amsa da to sun juya sun fita dukansu Mamie ta shiga gidan Abba ita kuma ta tsaya sai nazari take, ta jima sosai tana tunani a game da *Adnan* daga bisani ta jinjina ka yayin da take magana da zuciyarta. "Tabbas zuwa yanzu na san a gun da zan same sa insha Allah." Ta juya ta fice ta shiga taxy ta nufi gurin da zata had'u da *Adnan,* zaune kawai yake yayin da k'unci bak'in ciki 'bacin rai tare da tarin damuwa suka yi yawan gaske a tare da shi. A zahirin gaskiya ya damu sosai na rabuwa da *Afnan* da zai yi, sabo da zuwa wannan lokacin abin har ya fara yi masa illa yayin da kuma soyayyar ta take dad'a k'aruwa a tare da shi. Musamman yanzu da ko yaushe suna manne da juna sosai wanda har yana jin kamar ba zai rayu ba idan ya rasa ta, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, yana haka yaji an dafasa ya riga da ya san cewar ita ce domin ita ce kawai ta san da gurin. Sam bai ji mamakin ganin ta a gurin ba sabo da yana da imanin cewar zata zo, ta zauna kusa da shi kusa sosai sai wani kallonsa take kallo sosai ta d'ora hanun ta a kan nasa da yake kan cinyarsa, ta saka faratan ta cikin nasa ta d'an matse kad'an ta yanda ba zai ji zafi ba, ta kai d'ayan hanun ta ga fuskar sa ta juyo da fuskar sa gareta sun fuskanci juna, taci gaba da shafar fuskarsa tana sunbatarsa ta anbaci sunan sa, kafin ta furta komai yayi mata rigagi ya fara janye ta daga jikin sa sannan ya fara magana. "Mai yasa kika zo nan? Kamata yayi a ce a yanzu kina can an shafa maki lalle to mai kuma kike yi a nan.?" "Nazo ne domin na d'auke ka mu tafi ka shafa min da hanun ka, ka murza min shi ta ko wane lungu da sak'o na jiki na hakan zai yi matuqar saka ni farin ciki sosai to mu tafi. Yanzu kana farin ciki dana fad'a maka haka? Shikenan mu tafi ka tashi mu tafi." "Mai ya saka baki zo da bindiga kin harbe ni ba ina ga hakan zai fiye maki sauki a kan abin da kika fad'a yanzu, to ki bar nan kawai ki tafi sabo da ba zan jure sauraran wad'an nan lafuzzan naki ba." "Besty shin kana sona sannan kuma kana tare da burin aure na gaskiyar zaka fad'a.?" "Tin da jimawa ya kamata a ce kinyi man wannan tambayar ba yau da a ke shagalin bikin saka ki lalle ba, ina sanki ko a'a wannan sam ba shi da wani anfani a yanzu sabo da ba zai dakatar da auran ki da Yaya Auwal ba a gobe. Besty tin a ranar da a ka sanar da ni auran ki na ro e ki alfarmar ki dakatar da auran, ta hanyar sanar da Yaya Auwal cewar bakya sansa amma kuma dai ba kiyi hakan ba, wanda hakan ne ya tabbatar man da cewar ke kina qaunarsa sosai sannan kuma kin zab'e sa fiye da ni. Duk da cewar kinyi min alkawarin cewa zaki kasance tare da ni na har abada, kin fad'a min cewar zaki rayu da ni har zuwa numfashin ki na k'arshe, a she duka wannan k'arya ne kuma yaudara ce ke baki ta'ba sona ba ko da kuwa na rana d'aya ne, kin barni ina ta fama da soyayyar ki yayin dake kuma wani daban kike so bani ba. Cikin sauk'i kin manta da duka rayuwar da mu kai shikenan kawai kiyi aure da shi, amma yana da kyau ki manta cewar kin ta'ba rayuwa da ni wannan auran shi ne zai kasance rabuwar mu ta har abada." Magana yake cikin fishi sosai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. Kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, ita kuwa kuka take kuma kuka sosai cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya fad'a take magana. "Mai yasa kai sam baka da adalci ne mai ya saka ka za'bi daka cutar da ni ta wannan hanyar? Besty ni ba zan iya d'aukar wannan ba to ka dena a zabtar da ni haka sabo da ina sanka sosai." "Wai da gaske kina sona? A'a Besty ni naga irin yanda kika k'osa ki rabu da ni sabo dake sam baki da adalci, shi yasa kika za'bi Yaya Auwal a matsayin muji ta yanda zai d'auke ki gaba d'aya daga gareni zuwa jos. Ba tare da kinji tausayi na ba ko kuma halin da zan kasance a ciki, amma kuma a haka kike san ni na yarda da cewar kina sona? A'a k'arya ne kawai yaudara ce." Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin sa sosai, lokaci d'aya kukan ta ya sabanta sosai kuma a haka take magana. "A'a Besty wannan sam ba gaskiya bane ni ban ta'ba yaudarar ka ba, sabo da ina matuqar masifar qaunarka sosai fiye ma da yanda nake sanka. Besty ni na san cewa kana sona amma kuma na rasa dalilin da yasa ka gagara sanar dani gaskiyar." "duk da cewa kin san gaskiyar amma kuma kika za'bi daki cutar da ni ta wannan hanyar? Hakan ne ya tabbatar man da cewar ke d'in nan baki ta'ba sona ba, ni ban ta'ba tsammanin hakan daga gareki ba wannan ciwon yafi cutar da ni fiye da auran da zaki yi da Yaya Auwal. Shikenan na gode sosai ina maki fatan alkhairi ke da mujin ki sai an jima." Ya tashi domin tafiya da sauri ta dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa ita ma ta tashi tsaye, "kai sam ba gaskiyar kake fad'a ba kai kasan cewa ina sanka ina matuqar masifar qaunarka sosai, Besty a tunanin ka haka kawai zan baka damar kasancewa tare da ni? A'a na amince da kai ne kawai sabo da ina sanka sosai, Besty da a ce kai ka sanar da ni gaskiyar cewa kana sona to da duka wannan bai faru ba. Na tabbata da ko Kaka ba zai shirya aure na da Yaya Auwal ba, amma sai ka za'bi ka 'boye gaskiyar dalilin da yasa duka wannan ya faru." "Besty d'an dakata yanzu kina san kice duka wannan laifi na ne? Duk da cewar ke kin san gaskiyar amma kuma kina d'ora laifin a kai na, shikenan to yanzu kiyi abu ďaya zan baki za'bi uku kuma ya zama dole sai ďaya ya faru, Besty dole ki hukunta ta a kan wannan zunubin nawa ta yanda zaki daidai komai, Besty ya zama dole ki dakatar da wannan auran ko kuma ki kashe ni da hanun ki, idan kuma ba haka ba to fa ni zan kashe kai na da hanayena dole ki yanke hukuncin abin da zai faru, kuma zaki yanke hukunci ne kafin a shafa maki lalle zanga irin soyayyar da kike yi man." "Besty wai ka ji irin abin da kake fad'a kuwa ta ya kake tunanin ni zan iya kashe ka ko na bari kai ka kashe kanka? A'a hakan sam ba zai faru ba to kana dena wannan shirmen ka ji ko." "Shikenan to idan har bakya san hakan ta faru to fa ya zama dole da ki dakatar da auran ki da Yaya Auwal, ko kuma dai daga wannan lokacin zamu rabu na har abada sai an jima." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyar sa ba tare daya jira yaji mai zata fad'a ba, Ita kuwa ta bisa da kallo har ya fice yayin da firgici rud'ani da kuma tashin hankali yayi yawan gaske a tare da ita sosai. Cike da k'unci tashin hankali tare da tarin damuwa ta juya ta nufi gida, *Alishart* na shirin fita zuwa gidan Abba gurin bikin saka *Afnan* lalle, sai ga *Adnan* ya shigo cikin wani irin yanayi mara dad'i sai tafi yake kamar zai fad'i. Da sauri *Alishart* ta isa inda yake ta ri e sa yayin da take fad'ar sunan sa, amma bai amsa ba taci gaba da tafiya da shi har suka isa ga kujera ta fara zaunar da shi sannan ta zauna. ta d'auki wayar ta ta shiga kiran layin Mamie ba jimawa ta d'aga nan kuwa ta shiga sanar da ita abin da yake faruwa da *Adnan,* cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ta amsa da gata nan tafe sunyi sallama. ba jimawa sai ga Mamie ta shigo da sauri ta nufi gurin su har tana gudu, ta wani rungumasa jikin sa tana fad'ar sunan sa. *"Adnan* mai yake faruwa da kai ne haka? Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un na shiga uku *Adnan."* Magana take cike da firgici da tashin hankali sosai ya girgiza mata ka tare da furta masa kalmar. "Mamie qlau nake sannan kuma ina lafiya amma." Bai qarasa fad'ar abin da yake fad'a ba yayi shiru Mamie ta shiga fad'ar sunan sa hakama *Alishart,* fad'ar sunan sa take tana kuka amma bai amsa ba sai wani jijjigasa suke suna fad'ar sunan sa, amma bai amsa ba hakama ba wata a lama wacce ta nuna cewa zai tashi, wanda hakan ne ya tabbatar musu da cewar ya suma cike da firgici Mamie tace da *Alishart* ta kira mata Habu. Ta amsa da to ta tashi da sauri ta fita har tana gudu ba jimawa suka dawo tare, Mamie tace da Habu ya d'auki sa zuwa mota ya amsa da to ya d'auke sa sun fita ya sa shi mota sun tafi, wanda kuma *Alishart* ce take tuqa motar Mamie kuma tana baya rungume da shi ta d'auki wayar ta, ta kira layin Papa ta sanar da shi ya amsa da sai yazo sunyi sallama............ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/27, 10:49 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 29* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Tuesday 25/01/2022* *Time 11:53am* *Typing................* Sun isa asibiti cikin hanzari Doctor's suka shiga da shi ciki yayin da suka bar Mamie da *Alishart* suna kai kawo. Baifi da mintuna sha biyar ba zuwa ashirin sai ga Papa ya ƙaraso, yanayin daya samu su *Alishart* a ciki ya tabbatar masa da cewar da akwai matsala, cike da firgici da rud'ani yake tambayar Mamie mai yake faruwa. "Kawai shi ya suma ne.?" Cike da firgici yake magana, "mine ta ya a kai ya suma mai ya faru da shi ne shin ke kin barsa ya aikata wanin abin daya gajiyar da shi ne? Haka kawai ba zai suma ba dole wani abu ya faru da shi, karki fad'a min cewar wai ba abin daya faru da shi kawai ki sanar da ni gaskiyar mai ya faru da shi.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "ban sani ba ni ina gidan su *Afnan Alishart* ta kira take sanar da ni ba shi da lafiya, na koma gida nayi ta k'oqarin tambayarsa mai yake damunsa, amma sai ya amsa ni da cewar qlau yake daga nan kuma sai ya suma." Papa ya mai da kallonsa ga fuskar *Alishart* tare da fad'ar sunan ta. *"Alishart* fad'a min mai ya faru da shi kafin rashin lafiya.?" "Papa ni ina shirin fita zuwa gidan su Aunty ya shigo gida kuma ko a lokacin baya cikin kyakkyawan yanayi." "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un ya Allah ka bawa *Adnan* lafiya Allahumma Amin." dukansu sun amsa da Amin bayan wani lokaci da suka d'auka a ciki tare da shi sun fito, cikin hanzari tare da nuna kulawa Papa ya isa garesu yana tambayar su jikin yaronsa. Dr Habib ne yake magana da shi, *"Abban Adnan* kawai ka saman a office kuzo tare da Madam." Sun amsa da to sun bisa a baya sun shiga office d'in bayan sun zauna Dr Habib yaci gaba da magana. *"Abban Adnan* a gaskiya yanayin yaronku yayi tsauri sosai, a kullum kuma a ko yaushe ina yawan fad'a muku cewar yaronku yana matuqar buqatar farin ciki sosai, hakama yaronku yana matuqar buqatar kulawa sosai domin lafiyar sa. Amma sam bakwa kulawa da shi yanda ya dace mai yasa kuke wasa da rayuwar sa har haka, ku fad'a min wani abu shin kuna buqatar ku rasa yaronku ne na har abada.?" Lokaci d'aya dukansu suka furta masa kalmar a'a Papa yaci gaba da magana. "Doctor dan Allah ka dena fad'ar haka wallahi muna iya k'oqarin mu gurin ganin *Adnan* yayi farin ciki sosai. Sannan kuma muna matuqar ba shi kulawa sosai munyi matuqar damuwa da shi sosai, amma a 'yan kwana biyun nan na dena gane masa kamar dai shi yana 'boye mana wani abu a game da shi, Doctor dan Allah ka sanar da ni a salin gaskiyar abin da yake faruwa da yarona.?" Yayi shiru yana wani jinjina ka sannan daga bisani ya fara magana. *"Abban Adnan* gaskiya naji mamaki sosai daka fad'a min cewar kuna kulawa da *Adnan* sosai, sabo a binkicen da muka yi masa mun fahimci cewar yana tare da k'uncin mai matuqar girman gaske sosai, wannan ciwon da yake da shi a k'arkashin zuciyar sa yana k'ara girma sosai, wanda idan ya jima a haka ko k'uncin sa yafi haka to zuciyar sa zata buga ko ta fashe. Wanda kuma a wannan lokacin ni sai dai kawai na baku hak'uri sabo da kuwa yaronku ba zai rayu ba." "A'a hakan ba zata faru da yarona ba ni ba zan ta'ba barin hakan ta faru da shi ba, to ya kamata nayi wani abu domin na dakatar auran sabo da ba zan jure rasa ďana ba." Ta tashi da sauri har tana gudu ta fita office ďin Papa shi ma tashi yayi ya bita a baya cike da jin mamakin abin data fad'a. Dr Habib ya bisu da kallo yana girgiza ka Mamie na k'oqarin shiga d'akin da *Adnan* yake, Papa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta. A can gurin *Afnan* kuwa ta dawo gida cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau, yayin da take kuka amma zuwa wannan lokacin kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai ta samu parlour cike da jama'a, sai jiran dawowar ta suke domin fara shagalin sanya ta lalle. Kai tsaye d'akin ta ta nufa ba tare data furta wa kowa komai ba, su kuwa sun shiga fad'ar sunan sa yayin da wasun su suke kiran ta da Amarya. Cike da k'unci ta shige d'akin ta tare da rufe k'ofar cike da firgici Ummu ta shiga buga mata k'ofa tare da fad'ar sunan ta, amma hakan sam bai sanya ta bud'e k'ofar ba sai tunani take da nazarin abin da *Adnan* ya fad'a mata. "A'a ni sam ba zan bar wani mummunan abu ya faru da Besty na ba, to lallai ya zama dole da nayi wani abu domin na dakatar da auran nan. Sam ban damu da duk abin da zai faru ba idan har zan kasance tare da abin da nafi qauna, ina san Besty sosai ina matuqar masifar qaunar sa sosai to ya zama dole nayi koma miye domin na same sa." Tana kai k'arshen maganar ta ta juya ta nufi hanyar fita ta bud'e k'ofar ta fito, ta samu su Ummu tsaye a gefen k'ofa ba wanda tayi wa magana sai ma juya da tayi domin fita, da sauri Hajiya ta ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta. *"Afnan* wai mai kike yi ne haka? Tin d'azu muke nan zaune muna jiran dawowar ki, domin fara shagalin shafa maki lalle kin shigo ba tare da kinyi wa kowa magana ba. Muna ta k'oqarin ganin kinyi magana amma baki amsa kowa ba yanzu kuma kin fito zaki fita, *Afnan* shin ko zaki iya sanar damu a salin abin da yake faruwa dake.?" Shiru bata yi magana ba sai ma k'oqarin cire hanun ta cikin na Hajiya take domin tafiya, ganin hakan ne yasa Hajiya tace da Hafsat ta shafa mata lalle. Tana k'oqarin shafa mata lalle *Afnan* ta bige hanun ta tare da furta mata kalmar. "A'a karki yi kuskuran shafa min wannan lallen sabo da ba zan iya cire fatar jiki na ba, to ya kamata dukanku da kuke a nan ku sani na fasa auran Yaya Auwal ni ba zan aure sa ba." wani irin kallo suke yi mata mai cike da jin mamakin ta sosai, *"Afnan* qlau kike kuwa.?" "Eh Aunty Nafisa ina lafiya kawai dai ba zan aure sa ba." Cike da 'bacin rai Hajiya ta kifa mata wani wawan mari ta kuma ci gaba da fad'a da ita. *"Afnan* to bara kiji wallahi tallahi ko zaki mutu sai an yi auran ki da Auwal, wannan umurni ne bawai shawara ba to ya kamata ki yarda da gaskiyar Hafsat ki shafa mata lalle." Da sauri ta fizge hanun ta daga hanun Hajiya ta nufi kicin ba jimawa ta fito, hanun ta ri e da yuk'a dukansu wani irin kallo suke yi mata mai cike da jin mamakin ta, "na rantse duk a kayi kuskure shafa min lalle to fa tabbas sai na kashe kai na, ba kuma zan kashe kai na cikin sauk'i ba tabbas zan a zabtar da kai kafin na mutu kamar haka." Ta rufe idanuwan ta tare da yanka hanayen ta duka biyun jini kuwa sai zuba yake, da sauri Ummu ta nufi inda take tana fad'ar sunan ta tana k'oqarin rik'a ta, tayi saurin dakatar da ita ta hanyar furta mata a'a ta mai da kallonta ga Hajiya taci gaba da magana. "Hajiya zaki iya duka na idan kina so amma kuma ni na za'bi mutuwa fiye da nayi aure da Yaya Auwal, ni ban ta'ba san shi ba sabo da ni da kuma zuciya ta Besty kawai muke qauna, sannan kuma shi ne kawai wanda zai kasance Mujina na har abada wannan alkawari ne." Tana kai k'arshen maganar ta ta juya ta nufi hanyar fita cikin hanzari Ummu ta anbaci sunan ta. *"Afnan* d'an dakata kina zubar da jini ya kamata mu tafi asibiti yanzu." "A'a Ummu qlau nake Besty na zai kula da ni sosai to sam ba buqatar ki damu kinji ko." Taci gaba da tafiya har ta fice daga parlour ta nufi gurin *Adnan* domin had'uwa da shi. Ta isa gidan tin a gate Habu ya sanar da ita cewar suna asibiti, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ta fita ta shiga taxy ta nufi asibiti. *"Ummu Adnan* shin da akwai abin da kike 'boye min gaskiyar zaki fad'a.?" Magana yake cike da k'unci da 'bacin rai cikin firgici rud'ani tare da tsoro da fargaba take magana. "Kayi hak'uri ni bani da wani za'bi ne sabo da ya buqaci da karna sanar da kai, shi ya damu ne sosai a kan auran da *Afnan* zata yi da Auwal, sabo da yana qaunar ta sosai kuma yana buqatar auran ta sosai. A kullum yana cikin kukan rashin ta hakan yana matuqar saka shi k'unci sosai sannan kuma." Papa ya dakatar da ita cikin tsawa tare da d'aga murya, "ya isa haka kiyi shiru mai yasa ke sam ba kiyi tunanin sanar da ni ba? Da a ce ke kin sanar da ni gaskiyar to da nayi komai domin ganin ya samu farin ciki sosai, ni Abban sa to zanyi komai sabo da ya kasance cikin farin ciki to mai yasa ke ba kiyi tinani a kan hakan ba? Sabo da kuskuran ki yanzu yana kwance ba shi da lafiya sosai ke ce wacce take da alhakin duka wannan, ke wace irin uwa ce taya zaki yi k'oqarin cutar da yaronmu har haka? Hak'iqa kin aikata min babban zunubi wanda yake da matuqar girma sosai." "Wanda har ban san ta yanda ni zan hukunta ki ba shikenan yanzu kawai ki tafi, ki bar nan kuma karki koma dawowa sannan kuma idan har wani mummunan abu ya faru da yarona, to fa ki sani ko ni ban san wane irin hukunci zan yanke maki ba, to kiyi fatan ya samu lafiya ta yanda hukuncin ki zai zo maki da sauk'i sosai to yanzu ki tafi ni zan kula da ďana." "A'a sam bai kamata na tafi ba sabo da yarona yana buqata na a nan, to dan Allah kayi hak'uri ka yafemin please." "Asma'u nace ki tafi to kawai ki tafi kinji ko ki tafi." Bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta juya domin tafiya, zuwan *Afnan* ne ya dakatar da ita daga tafiya, tafiya take tana wani rangaji kamar zata fad'i sai wani lumshe ido take yayin da hanayen ta suke ta zubar da jini, da sauri Mamie ta ri e ta tare da rungumata jikin ta sun shiga anbatar sunan ta, yayin da ita kuma sunan *Adnan* take fad'a. "Papa dan Allah ku yafemin sannan kuma karku yi fishi da ni, sabo da ni Besty yana kwance asibiti yanzu ba jimawa sosai shi ya sanar da ni gaskiyar, Papa gaskiyar ita ce nima ina matuqar masifar qaunar Besty sosai ina sansa sosai. To dan Allah kayi komai domin ka dakatar da aure na da Yaya Auwal sabo da." Tana cikin magana ta suma hankalin su Papa ya dad'a tashi sosai, ya kira nurse sun shiga da ita ciki domin a duba ta bayan wani lokaci Dr Habib ya fito tare da sanar dasu cewar tana buqatar jini. "Shikenan mu tafi a duba nawa idan zai yi." "A'a jinin ka ba zai yi mata ba to ya kamata ka kira wani wanda za a duba." Ya jinjina masa ka a lamar to Dr Habib ya juya ya nufi office Papa ya sauke kallonsa ga Mamie tare da fad'ar sunan ta. "Asma'u kamar dai ni na fad'a maki cewar ki tafi to mai ya saka har yanzu kike tsaye a nan? Kawai ki tafi dan Allah ki bar nan sabo dake ne duka wannan ya faru, ke ce wacce take da alhakin duka wannan to kawai ki tafi." Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa ta juya ta fice, yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Bayan tafiyar ta Papa ya ciro wayar sa daga aljihu ya shiga kiran layin Abba, ba jimawa ya d'aga Papa ya shiga sanar da shi duk abin da yake faruwa. Abba ya shiga firgici sosai ya amsa shi da ga shi nan tafe sunyi sallama, Abba ya shiga kiran layin Anwar ya sanar da shi komai da Papa ya sanar da shi ya amsa shi dasu had'u asibiti. Ba wani d'aukan lokaci su Abba suka qaraso asibiti sun had'u da Papa cikin hanzari sun nufi office ďin Dr Habib, ya tashi sun nufi d'akin gwaji inda kuma a kayi narasa jinin Anwar yayi daidai da nata, nan a ka shiga d'ibar jinin sa bayan an qarasa an yi duk wani abin da za a yi, daga bisani a ka sanya wa *Afnan* jini Abba ya kira layin Baba dasu Ummu ya sanar dasu abin dake faruwa. Kafin su ankara asibitin ta d'auki taron jama'a sosai. Misalin k'arfe 12:00pm jirginsu Appa ya sauka Abuja to kaduna, suna fitowa Airport *Adyan* yace da driver su nufi asibiti kasancewar *Alishart* ta sanar da shi komai a waya. Tare suke dasu Kaka wato Abba ko nace Mr President wanda yayo musu rakiya daga Abuja, sun samu su Abbu a nan Airport suna jiran isowar su, sun shiga mota dukansu sun nufi asibiti gurin *Adnan* kamar dai yanda *Adyan* ya buqata.............. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/27, 10:50 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 30* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 26/01/2022* *Time 01:11am* *Typing.................* Sun samu rakiyar jama'ar su zan iya kiran sa da runduna sabo da suna da yawa sosai, ga tarin security sun isa asibiti ba wani d'aukan lokaci suka isa d'akin da *Adnan* yake. Cike da mamakin ganin su tamkar a mafarki dukansu sun shiga yi musu sannu da zuwa, sun amsa suna murmushi tare da sake fuska nan kuwa suka shiga gaisawa da juna. Tare da tambayar jikin *Adnan Adyan* ya shiga tambayar Papa abin da yake faruwa da shi, ya sanar da shi duka gaskiyar cike da firgicin abin daya fad'a yake magana. "Papa ni na san dole sai hakan ta faru da shi dalilin da yasa nazo nan kenan, abokina yana san *Afnan* sosai kuma ita ma tana qaunarsa sosai, wanda dukanmu a nan mun san da hakan to ya kamata a ce su biyun sun rayu da juna na har abada. Papa naro e ka karka bari na rasa abokina sabo da shi ďin aboki na gari ne a gareni, shi yasa nake fatan na rayu da shi Appa Kaka dan Allah kuyi k'oqarin daidai komai, domin idan wani abu ya faru da *Adnan* to fa nima." Da sauri Appa da Ammie suka rufe masa baki tare da furta masa a'a, hakama su Abbu abin da suke fad'a kenan har suna had'a baki. "Karka fad'i komai ďana komai zai yi daidai insha Allah *Adnan* zai samu lafiya, hakama zai kasance muji ga abar qaunarsa wato *Afnan* insha Allah." "Da gaske.?" Appa ya jinjina masa ka a lamar eh shi ma ya jinjina masa ka yana murmushi, ya juya ya nufi gurin *Adnan* wanda yake kwance bama ya san inda yake ba, bayan tafiyar sa Appa ya sauke kallonsa ga fuskar Kaka wato Baba tare da isa inda yake, ya zauna gefen sa daga k'asa ya kama hanayen sa tare da fad'ar sunan sa. "Baba naro e ka daka bar wad'an nan masoyan biyu su rayu a tare, domin kaddaran su ta nuna cewa idan basu rayu a tare ba to fa zasu mutu a tare. Baba gaskiyar ita ce mu zamu yi farin ciki kawai ne idan har yaranmu suna farin ciki, sannan kuma ba zamu iya jure ganin su a cikin k'unci ba. Baba na tabbata ba wasu iyayen da zasu so ganin yaransu a cikin irin wannan mummunan yanayin, abin yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai. Baba ba wani farin cikin da za a samu idan har a kayi auran *Afnan* da Auwal, ka duba kaga yanda take barazanar kashe kanta k'ila a yanzu zamu iya dakatar da ita, to amma idan a kayi auran waye wannan wanda zai yi yunk'urin dakatar da ita.?" "Baba ya kamata muyi nazari sosai a kan wannan kawai muyi abin da zai saka yaranmu yin alfahari damu, ina nufin mu aurar dasu ga juna domin sai idan sun rayu ne kawai zamu yi farin ciki. Baba k'ila kai kana da yara biyu koma fiye da haka, *Abban Adnan da Abban Afnan* dukansu yara biyu ne dasu, amma kuma ni d'a d'aya kawai nake da shi kamar dai Abba na ni kawai ya aifa. Hakama Abbu qanwata kawai ya aifa ina nufin *Ummu Adyan,* Baba ni ba zan iya jure ganin yarona yana cutar da kansa ba, shi ya damu sosai a game da abokinsa dama *Afnan* idan wani abu ya faru dasu biyun, to ba zan iya dakatar da yarona ba hakan zai cutar da ahalinmu sosai sabo da shi ne farin cikin mu gaba d'aya. Baba kai ne kawai wanda yake da ikon daidai ta komai a nan to naro e ka da kabar *Adnan da Afnan* su yi aure please." Nan kuwa dukansu suka shiga ba shi magana inda kuma daga bisani, suka yi nasaran amincewar sa hakan yayi matuqar saka su farin ciki sosai. Cike da d'auki Appa yake sanar da *Adyan* abin da yake faruwa kasancewar da hausa suke magana, a zahirin gaskiya yayi matuqar farin ciki sosai wanda har sai da yayi wa Baba godiya, ya mai da kallonsa ga Appa tare da fad'ar sunan sa. "Appa wannan bai k'are ba da akwai wani abin kuma." "D'ana ka fad'a min miye wannan ni zan daidai ta komai insha Allah to fad'a min miye.?" Ya jinjina masa ka a lamar to ya juya da kallonsa ga *Alishart* wacce har zuwa wannan lokacin idanuwanta basu dena zubar da kwalla ba, murmushinsa ya k'aru sosai ya dawo da kallonsa ga fuskar Appa, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar shi ma kallonsa yake yana murmushi. "Masoyi shin a game da sirika ta ne? Fad'a min wani abu shin kai ka shirya wa auran ta a yanzu.?" "Eh Appa amma ina san naji ko ita ma ta shirya wa hakan." "Shikenan ka tafi kayi magana da ita." Ya jinjina masa ka ya juya ya nufi gurin *Alishart* Appa kuma ya koma gurin su Abbu. "Ahmad mai yake faruwa a can gurin.?" "Abbu shi ya fad'a min cewar zai yi magana da sirika ta." Ya fad'a yana dariya su Abba kuma murmushi suke sosai ya isa gurin *Alishart* ya zauna, sai wani kallonta yake ya d'ora hanun sa a kan nata ya d'an shafa tare da murzawa ya sunbaceta a gefen fuska. "Ke k'uncin ya isa haka sabo da su biyun zasu yi aure to kawai muyi farin ciki, to yanzu ina san zan tambiye ki wani abu *Alishart* shin kina sona kuma zaki aure ni gaskiyar zaki fad'a.?" Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai, abin birgewa ga wanda ya gani ita kuwa sai wani kallonsa take yayin da take jin yana birgeta sosai, sun jima sosai a haka suna kallon juna sannan daga bisani ta amsa shi. "Eh *Yaya Adyan* ni ina sanka sosai sannan kuma zan aure ka nayi alkawari insha Allah." Cike da d'auki yayi hugging d'in ta yana sunbatarta hakan ya tabbatar wa da Appa cewar yayi nasara. Yayi wani kyakkyawan murmushi sosai tare da fad'ar sunan Abban sa. "Abba ni fa ina tunanin cewa d'aurin aure biyu zamu yi a gobe, sabo da yarona ya shirya zama muji na gari a gurin sirika ta. *Abban Adnan* ina fatan kai ma zaka amince da hakan.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, *"Abban Adyan* idan har su biyun sun amince da junansu to ni kawai nawa fatan alkhairi ne da addu'a. *Abban Adyan* amma kuma har yanzu *Alishart* yarinya ce shekarun ta sha biyar ne kawai, sannan kuma secondry ne kawai da ita ina ga yayi wuri da nayi mata aure yanzu. To zamu iya barin wannan zuwa wani lokaci idan ta k'ara girma da hankali fatan ka fahimce ni.?" Kamar daga sama yaji muryar *Adyan* ya amsa shi. "Papa ni ba zan cutar da ita ba hasalima idan a ka d'aura auran to a nan zan barta, taci gaba da karatu ni kawai ina san ta zama tawa dalilin da yasa nake san a yi auran yanzu, Papa dan Allah karka dakatar da faruwar hakan please." Ya jinjina masa ka yana murmushi, "shikenan yarona na amince da auran ka da *Alishart* Allah ya sanya alkhairi Amin." Cike da d'auki yayi hugging d'in Papa har da sunbatarsa yana yi masa godiya dukansu gurin suna farin ciki sosai, nan kuwa suka shiga zan auran inda a ka saka kud'in sadaki dama komai Abba ya ba da umurnin a bada sanarwa ta yanda zata kai ga kunnan kowa. Bayan wani lokaci su Abbu suka yi sallama dasu Papa suka tafi, ai kuwa cikin k'ank'anin lokaci labarin auran *Adyan da Alishart Adnan da Afnan* ya kai inda ma ba a yi tunani ba. Auwal na cikin tafiya Sadiq ya kira layin sa bama tare da sun gaisa ba yake magana, "Auwal shin gaske ne abin da naji a na fad'a.?" "A kan me kake magana fad'a min mai yake faruwa.?" "Auwal karka fad'a min cewar baka san abin da yake faruwa ba.?" "Sadiq shin idan na sani zan tambiye ka ne kawai ka sanar da ni abin da yake faruwa.?" "Auwal to fa ni naji labarin cewa za a yi auran *Adnan da Afnan* a gobe." "Sadiq wannan k'arya ne amma dukansu biyun suna asibiti basu da lafiya wannan ce gaskiyar." "Auwal gaskiya bana jin cewar wannan k'arya ne, sai dai idan kai ne baka san gaskiyar ba sabo da zancan yayi yawa a gari, musamman a kan social media sannan kuma Minister of information ne wanda ya bada sanarwa. Sabo da tare za a yi auran dana jikan Mr President kuma jikan Governor kaduna wato *Adyan da Alishart qanwar Adnan."* "A'a Sadiq hakan sam ba zai yu ba sabo da ni ne kawai wanda zai kasance mujin *Afnan,* to kama dena wannan zancan banzan ka ji ko zamu yi magana an jima." Ya a jiye wayar tare da juya mota ya nufi asibiti domin samun tabbaci a kan abin da Sadiq ya sanar da shi. Ba jimawa da tafiyar su Appa Anwar ya dawo asibiti wanda zuwan sa yayi daidai dana Auwal, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali yake tambayar su Baba gaskiyar abin da yake faruwa. Ai kuwa nan suka sanar da shi komai ya shiga firgici sosai, yayin da farin ciki yake ta shigar Anwar wanda har ya gagara fad'ar komai. "Amma Kaka ta ya hakan zata kasance? Sam bai kamata a yi man haka ba sabo da ina san *Afnan* sosai, to dan Allah karku dakatar da aure na da *Afnan* dan Allah." Kafin wani ya amsa shi Anwar ya anbaci sunan sa. "Auwal tin da jimawa ya kamata a ce an yi hakan amma yanzun ma lokaci bai k'ure ba, sabo dasu biyun zasu yi aure abin dana jima ina fata hakan yayi kyau sosai." "Anwar shin ko zaka dena wannan shirmen naka ka sani ko da mai zai faru to ni ne, kawai wanda zai kasance mujin *Afnan* wannan ce gaskiyar." "Shikenan kayi koma miye amma kuma ba zaka yi nasara ba." Ai kuwa nan suka shiga gardama a tsakanin su wanda sai dasu Abba suka shiga tsakanin su, Baba ya shiga rarrashin Auwal tare da ba shi magana ba shi da wani za'bi dole ya d'auki kaddara, bayan wani lokaci su Kaka suka tashi suka fita zuwa gida domin ci gaba da shirin biki. Ya rage saura su Ummu da yamma lis *Afnan* ta farka daga dogon suman da tayi, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e su Ummu sun shiga yi mata sannu, kallonsu kawai take ba tare data amsa su ba cikin wata 'yar murya take magana. "Ummu ina Besty na fad'a wani abu shin da akwai abin daya faru da shi.?" "A'a ba abin daya faru da shi kawai dai har yanzu bai farka ba, amma an fad'a mana cewar yana samun sauki sosai, sannan kuma Baba ya amince da auran ki da *Adnan* hakama za a yi auran *Adyan da Alishart* duk a gobe." Lokaci d'aya farin ciki ya shigeta sosai wanda har ta gagara fad'ar komai, "gaskiya ina farin ciki sosai yanzu zan tafi na duba jikin Besty na, to dan Allah karki dakatar da ni please." *"Afnan* jikin ki bai gama warware ba ki jira jinin da a kasa maki ya k'are tukun kin ji ko." "Ummu ni qlau nake zan iya tafiya to dan Allah karki dakatar da ni please." Ta jinjina mata ka a lamar to ita da kanta ta cire jinin da a kasa mata Ummu ta rik'a ta sun fita zuwa ďakin da *Adnan* yake............ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [1/28, 8:58 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 31* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Thursday 27/01/2022* *Time 12:44pm* *Typing...............* Sun shiga d'akin sun samu *Alishart* zaune daga gefen sa, ta shiga yi musu sannu da zuwa tare da yiwa *Afnan* sannu ya jiki, ta amsa da Alhamdulallah ta sauke kallon ta ga fuskar *Adnan.* Ta zauna kusa da shi kusa sosai sai wani kallonsa take kallo sosai, ta shafi fuskarsa zuwa kansa tare da sunbatarsa tana furta Allah ya baka lafiya. Su Abbu sun isa gida Ummi sai sannu da zuwa take musu cike da d'aukin ganin su, bayan sun gaisa Appa ya shiga sanar da ita zancan auran *Adyan da Alishart* cike da d'auki take magana. *"Adyan* ka ce ka fara shirin kawo mana kishiya Aunty shin ke kin amince da hakan kuwa.?" "A'a ta ya ma ni zan yarda da hakan a'a kawai dai zamu ba shi wata 'yar k'aramar dama ce, kafin nan kuma zamu san abin da zamu shirya a kai." "Shikenan Aunty ni ina tare dake." Magana suke cikin kyakkyawan yanayi su Abba sun shiga dariyar su, haka suka shiga sanar da 'yan uwa da abokan arziki yayin da labarin ya zaga ko ina, na sassan k'asa ko ina zai zancan a ke a gari yayin da manyan mutane suka fara shirin tafiya d'aurin aure. Zaune kawai take yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai, "ta ya zan iya sanar da *Abban Adnan* irin k'uncin da yake a tare da ni yanzu? Shi sam ya gagara fahimta na gaba d'aya yak'i saurara na, hakan yasa ya yanke min hukuncin da bai dace da ni ba sam bai kamata ya hukunta ni har haka ba. Wannan ciwon yafi komai zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una sosai, ya kamata a ce ina tare da yarona sabo da zan iya taimaka masa da wani abu, ya Ubangiji ka bawa yarona lafiya sannan ka bawa Mujina damar da zai dena fishi da ni Allahumma Amin." Da dare dukansu suna tare a nan ďakin da *Adnan* yake, lokaci d'aya suka ji a na buga masu k'ofa *Alishart* wacce ta tafi ta bud'e k'ofar. Ta samu *Adyan* tsaye a bakin k'ofa lokaci ďaya suka sakarwa juna murmushi, murmushi suke sosai wanda har suka gagara furta wa juna komai, sai daga bisani sannan ta furta masa kalmar shigo ciki ya amsa da to yana murmushi. ya fara gaisawa da kowa da yake gurin sannan ya qarasa gurin *Adnan* sai wani kallonsa yake, ya shafi fuskarsa zuwa kansa sannan ya mai da kallonsa ga Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zan iya ganin file ďin *Adnan* da akwai abin da nake san na duba ne.?" Ya amsa shi da to ya tashi ya fita ba jimawa ya dawo tare da wata nurse, wacce kuma ita ce take ri e da file ta fara yin magana da *Adyan* sannan ta ba shi file ďin ta juya ta fita. Shi kuwa ya shiga duba file ďin cike da firgici da rud'ani yake magana da zuciyarsa. *"Adnan* yana da irin rashin lafiya na shi yasa hakan ta faru da shi, wannan sam bai yi ba amma zan kula da shi sosai shi abokina ne to zanyi komai sabo da shi." Ya mai da kallonsa ga Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zan iya had'uwa da likitan daya duba *Adnan.?"* Ya amsa da eh ya tashi sun nufi office ďin Dr Habib wanda a can ne, *Adyan* yayi magana da Dr Habib a game da rashin lafiyar *Adnan* ya kuwa sanar da shi komai. *Adyan* ya d'auki abin rubutu da takarda yayi rubutu ya bawa Dr Habib yana cewa, "Dr Habib ina buqatar duka wad'an nan abubuwan a yanzu." Yayi wani gajeran murmushi sannan ya amsa shi. *"Adyan* gaskiyar ita ce bamu da irin wad'an nan magungunan da alluran, sai dai ku tafi babban kantin siyar da magani a can ne kawai zaku samu." Cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adyan* yake amsa shi. "Mai yasa ba za a samu a nan ba.?" "sabo da wanda muke da shi a nan ya k'are amma za a kawo zuwa jibi insha Allah." Ya jinjina masa ka tare da furta ok ya tashi sun fita sun dawo d'akin da *Adnan* yake, wanda kuma Anwar ne wanda ya tafi ya siyo maganin da allura bai d'auki wani lokaci ba ya dawo, *Adyan* yayi masa duk wani abin daya dace ya jima sosai a nan tare da *Alishart* suna magana sannan daga bisani ya tafi. Haka dai dukansu suka tafi suka bar Papa wanda zai kwana da shi, bayan dawowar *Alishart* Mamie ta shiga tambayar ta jikin *Adnan* ta amsa da cewar yana samun sauki, tare da sanar da ita duk abin da yake faruwa Mamie taci ka da mamaki sosai kasancewar Papa bai sanar da ita komai ba. Duk da irin yanayin da take ciki amma tayi farin ciki sosai, *Alishart* ta fara had'a lipton tea ta sha sannan ta shiga ciki domin ta kwanta, Mamie ma tashi tayi ta nufi bedroom domin ta kwanta yayin da tunani yayi yawa a tare da ita, washe gari bayan ta qarasa shirin ta tsab ta fito ta gaisa da Mamie sannan ta d'auki abincin *Adnan* ta nufi asibiti. Tin bayan ta idar da azkar ta gaisa da Ummu ta tashi ta nufi d'akin da *Adnan* yake, domin duba jikin sa Papa ne wanda ya bud'e k'ofar ta shiga ciki ta fara gaisawa da shi, sannan ta shiga tambayar jikin *Adnan* ya amsa ta da Alhamdulallah yana samun sauki. Ta k'arasa inda yake ta zauna daga gefen sa sai wani kallonsa take kallo sosai, ta nisa sosai tare da jan numfashi yayin da take magana da zuciyarta. "Besty ina fatan ka samu lafiya cikin sauri ta yanda mu biyun zamu kasance a tare, yau ne a ke auran mu amma kuma har yanzu baka cikin kyakkyawan yanayi, zuwa yanzu ya kamata ka dawo haiyacinka ya Ubangiji ka tashi kafad'ar Mujina ka ba shi lafiya Amin." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai lokaci d'aya ta samu kanta da shafar fuskarsa tare da sunbatarsa, tana mai furta masa kalmar ina sanka sosai Besty Papa sai wani kallonta yake yana murmushi. "Karki damu 'yata mujin ki zai samu lafiya insha Allah to kawai kiyi farin ciki kinji ko." Ta jinjina masa ka tana murmushi mai tare da nuna jin kunya suna haka sai ga Ummu ta shigo, ta gaisa da Papa tare da tambayar sa jikin *Adnan* ya amsa ta da Alhamdulallah yana samun sauki. "Am *Ummu Afnan* idan bakya wani abu ina san ki kula da *Adnan,* ni zan tafi gida nayi shirin tafiya d'aurin aure." "Eh zaka iya tafiya ni zan kula da dukansu." Ya amsa da to tare dayi mata godiya ta amsa da ba komai, suna haka sai ga *Alishart* ta shigo ta fara da a jiye kayan abincin dake hanun ta, sannan ta gaisa dasu Ummu tare da yiwa *Afnan* ya jiki ta amsa da Alhamdulallah, ba jimawa Papa ya tafi bayan tafiyar sa Abba ya shigo ya d'an jima a nan, sannan ya tashi domin tafiya *Alishart* ta dakatar da shi tare da fad'ar sunan Ummu. "Ummu ya kamata ki tafi gida ki samu ki huta gajiya ni zan kula dasu sosai, to dan Allah karki ce a'a kawai ki tafi dan Allah." *Afnan* ta jinjina mata ka hakama Abba ta amsa su da to sun tafi tare da Abba, suna ta shirin tafiya d'aurin aure ganin lokaci ya tafi Appa ya sauke kallonsa ga Ammie tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam *Adyan* fa ya kammala shirin sa kuwa.?" "Gaskiya bana tunanin hakan amma zan tafi na duba shi yanzu." Ya jinjina mata ka a lamar to ta tashi ta nufi bedroom d'in da *Adyan* yake, ta shiga d'akin tana fad'ar sunan sa ta yi rashin sa'a baya nan ta duba shi har toilet, amma dai kuma bata yi nasaran ganin sa ba cike da firgici ta fito tana fad'ar sunan sa. Cikin hanzari Ahmad ya fito sun isa ga juna ya shiga tambayar mai yake faruwa, "Yaya Ahmad *Adyan* baya nan na duba shi sosai amma ban gansa ba, Yaya Ahmad ni ina jin tsoro sosai sabo da ban san inda shi ďin ya tafi ba." "A'a bai kamata ki ji tsoro ba sabo da ba abin da zai faru da shi, yanzu mu tafi gurin Abba da Abbu ina fatan ya kasance tare da ďaya daga cikin su mu tafi." Ta amsa da to sun nufi part ďin Abba sun same su zaune a parlour, cikin hanzari sun shiga tambayar su *Adyan.* "Ahmad mai kake fad'a ne haka ina *Adyan* ďin yake.?" "Abba ban sani ba baya ďakin sa to nayi tunanin ko yana tare daku ne." "A'a bai zo nan ba amma zan kira Al'ameen na ji ko suna tare." Sun amsa shi da to nan kuwa ya shiga kiran layin Abbu ba jimawa ya d'aga, Abba ya shiga tambayar sa *Adyan* ya amsa shi da basa tare, Abba ya sanar da shi baya gida Abbu ya amsa shi da ga shi nan tafe sunyi sallama, da sauri Ahmad ya juya ya fita har yana gudu su Abba ma tashi su kayi suka fita, dan ganin inda zai tafi sun fito sun same sa yana tambayar security yaronsa, Jabir ya sanar da shi cewar ya fita tare da Jibrin. "Kawai ka bani shi a waya." Ya amsa shi da to nan kuwa ya shiga kiran layin Jibrin ba jimawa ya d'aga ya bawa Ahmad wayar ya amsa yana cewa. "Kana magana da Ahmad ne fad'a min ina ďana *Adyan* yake.?" "Ranka shid'ad'e shi ya buqaci dana kai shi asibiti ne, sannan kuma yana cikin k'oshin lafiya na tabbata a kan hakan to zaka iya yarda da ni." "Shikenan na gode." Da kuma haka suka yi sallama ya bawa Jabir wayar sa, tare da sanar dasu Abba abin da yake faruwa sunyi murmushi sannan suka juya suka koma ciki. Sunci gaba da shirin su bayan wani lokaci suka nufi gurin d'aurin aure, bayan wani lokaci daya d'auka a kwance ya farka, sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e, sai wani kallon kansa yake dama inda yake, lokaci d'aya suka shiga anbatar sunan sa tare da yi masa ya jiki, kallonsu kawai yake ba tare daya amsa ba ya sauke kallonsa ga fuskar *Afnan* sannan ya fara magana. "Mai kuma kike nan ya kamata ki tafi yau ne a ke bikin saka ki lalle to mai kuma kike yi a nan? Ya kamata ki tafi sabo da a gida suna jiran ki to kawai ki tafi ki bar nan dan Allah." Kuka kawai take yayin da take kuka kuma kuka sosai, cike da k'unci ta tashi domin tafiya da sauri *Alishart* ta dakatar da ita ta mai da kallonta ga Yayanta tana cewa............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/3, 4:31 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 32* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 28/01/2022* *Time 05:37pm* *Typing...............* "Yaya wai mai kake aikata wa ne haka? Sam bai kamata kayi wa Aunty haka ba godiya ya kamata kayi mata, a maimakon wannan fad'an da kake yi mata cikin tsawa Yana." "Ya isa *Alishart* to kawai kiyi shiru kina san nai mata godiya ne sabo da k'oqarin da take ba bari na? Ko a'a zanyi mata godiya ne sabo da ta za'bi kasancewa tare da Yaya Auwal a maimakon ni? Ko zanyi mata godiya ne sabo da farin cikin da nake ciki a yanzu duk a dalilin ta? *Alishart* ita ta za'bi Yaya Auwal a kai na duk da cewar ta san gaskiyar, wanda kuma hakan ne ya tabbatar mani da cewar ita bata ta'ba sona ba. Shi yasa ta za'bi Yaya Auwal a matsayin muji ta yanda zai d'auke ta gaba d'aya daga gareni, *Alishart* wannan rashin adalci ne sannan kuma hakan yana yi min zafi sosai." Magana yake cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa sosai, ba kuka yake ba amma kuma kwalla ce take bin fuskar sa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. *Alishart* ta tashi daga inda take ta nufi gurin sa ta zauna kusa da shi kusa sosai, tare da kama hanayen sa ta fara da share masa kwalla sannan daga bisani ta fara magana. "Wannan ba gaskiya bane Yayana kawai dai rashin fahimta ne, ita Aunty sam ba haka take ba sannan kuma ita ba zata ta'ba cutar da kai ta wannan hanyar ba. Yayana Aunty tana qaunar ka sosai sannan kuma a shirye take data yi komai sabo da kai, ita har sai da tayi barazanar kashe kanta kawai sabo data same ka, har sai data kusa rasa ranta duka sabo da kai." Nan kuwa ta shiga sanar da shi komai yayi matuqar mamakin abin data fad'a. "Yayana zuwa yanzu ku biyun muji da mata ne to ya kamata ka kula da matar ka sosai, sabo da tana buqatar ka sosai sannan kuma kiyi farin ciki dan Allah." "Qanwata wai gaskiya kike fad'a min kuwa shin ni na ji ko sosai kuwa? *Alishart* wai da gaske ni da Besty zamu kasance muji da mata.?" Ya jinjina masa ka a lamar eh cike da d'auki ya kai kallonsa ga *Afnan,* wacce take tsaye gefen k'ofa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take, sun jima a haka sannan daga bisani ya anbaci sunan ta. "Besty ki yafemin sannan kuma kiyi hak'uri ki dawo gareni please." Cike da d'auki ta nufi gurin sa da sauri har tana gudu, tana isa garesa sunyi hugging juna sun jima a haka sannan daga bisani suka sake juna, sai wani kallon juna suke kallo sosai yaci gaba da magana. "Besty da a ce ke kin yi nasaran kashe kanki to da ba zan ta'ba gafarta maki ba na har abada, sannan kuma zanci gaba da hukunta kai na har zuwa lokacin da nima zan mutu, Besty ina sanki sosai shi yasa sam ba zan juri rashin ki ba, dalilin da yasa nake kwance a nan kenan na gode da kika zab'e ni a matsayin, a matsayin mujin ki wanda zaki k'arasa duka rayuwar ki da shi na gode sosai Besty na." Kallonsa kawai take yayin da take wasa da fuskar sa cikin kyakkyawan yanayi take magana. "Besty kai ne rayuwata ruhina dama zuciyata to ba zan rayu ba idan har narasa ka, shi yasa na za'bi mutuwa fiye da aure na da Yaya Auwal. Abin farin cikin shi ne daga k'arshe munyi nasara kaddaran mu ta amince mana, da mu rayu da juna na har abada zuwa yanzu mu biyun muji da mata ne abin gwanin dad'i sosai." Ya jinjina mata ka yana furta. "Eh da dad'i sosai am Besty kiyi hak'uri sannan kuma ki yafemin a kan abin da ni na aikata maki, Besty ni kawai na kasa jurewa ne ganin wani yana k'oqarin raba mu, Besty gaskiyar ita ce ni ina ban saba da rashin ki ba shi yasa ba zan iya jure rashin ki, to dalilin da yasa ni na aikata maki hakan kenan to ina fatan zaki y dan Allah." Da sauri ta rufe masa baki tana girgiza masa ka yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai, wanda kuma wannan dalilin ne ya hana mata fad'ar komai shi ma abin da yake yi kenan. Cike da shauk'i sun k'ara yin hugging juna *Alishart* dai sai kallonsu take tana murmushi, bugun k'ofar da suka ji ne yasa su sake juna daga hugging d'in da suka yi, *Alishart* ta tafi domin ta bud'e k'ofar ta bud'e ba tare data tambaya waye ba, ta samu *Adyan* tsaye bakin k'ofa sun tari juna da wani kyakkyawan murmushi, sai wani kallon juna suke sosai lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin hugging d'in ta, tare da sunbatarta ya kuma ci gaba da furta mata kalmar yana qaunar ta. Ita kuwa sai kallonsa kawai take tana murmushi ba tare data furta masa komai ba, bayan wani lokaci ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata sannan suka shiga ciki. Cike da d'aukin ganin juna suke anbatar sunayen juna har suna had'a baki, *Adyan* ya isa inda yake cike da qauna da soyayya sun gunrume juna har da wani rufe ido, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna sai wani kallon juna suke, yayin da kwalla take bin fuskar su wacce kuma zamu iya cewa ta farin ciki ce. *"Adnan* bayan shekara goma sha biyar yau mun sake had'uwa da juna, gaskiya ina matuqar farin ciki sosai to ya jikin ka fatan kana samun sauki sosai.?" "Eh aboki ina samun sauki sosai kuma duka sabo da kai ne, *Adyan* na gode sosai daka ceci soyayya ta abin da ni na gagara yi. Na gode sosai sannan kuma ina yi ma fatan alkhairi a kan auran ka da qanwata, amma *Adyan* hakan bai yi kusa ba? Am ina nufin ita d'in har yanzu yarinya ce shekarun ta sha biyar ne, to ba zata iya d'aukan d'awainiyar ba ga shi kuma kun riga da kunyi aure kawai sai dai nai muku fatan alkhairi." "Karka wani damu aboki sabo da ita ďin a nan zata zauna tayi karatu, bayan ko wane hutu zanzo na tafi da ita yanzun ma bayan bikin Ameer zamu tafi tare da ita insha Allah. To ba buqatar ka damu sabo da zan kula da ita sosai kamar rayuwata, ni kawai ina san ta zama tawa shi yasa na buqaci auran ta yanzu." "Kai kana da kirki sosai aboki na gode a kan komai." "Ba buqatar kayi godiya yanzu fad'a min wani abu shin ka samu wani labari a game da *Adeel.?"* "A'a amma ina fatan ya bai yana a garemu nan kusa kuma kusa sosai." "Nima wannan ne fatana." Ya mai da kallonsa ga *Afnan* sun gaisa ya mata fatan alkhairi, ta amsa tare dayi masa godiya shi ma tayi masa fatan alkhairi, ya amsa yana murmushi sannan daga bisani ya shiga duba *Adnan.* Abin farin cikin shi ne yana samun sauki sosai sunci gaba da fira, daga bisani kuma *Adnan* ya shiga tambayar *Alishart* Mamie bata da wani za'bi, wanda wannan dalilin ne yasa ta sanar da shi gaskiyar abin daya faru. Hakan yayi matuqar saka shi k'unci sosai ya kar'bi wayar ta ya shiga kiran layin Mamie ba jimawa ta d'aga. "Hellow *Alishart* shin komai qlau yake a nan.?" Shiru bai amsa ba taci gaba da magana. *"Alishart* ki amsa ni komai qlau ya jikin ďana yake shin yana samun sauki kuwa dan Allah kiyi magana.?" Cikin wata 'yar murya yake furta mata kalmar kiyi hak'uri cikin hanzari ta anbaci sunan sa. *"Adnan* ya jikin ka kayi hak'uri da ban samu na kula da kai ba, amma ina fatan ka samu lafiya cikin sauri domin ka dawo gida, ta yanda zan kula da kai sosai nayi matuqar kewarka yarona to fad'a min ya jikin ka.?" "Zan samu lafiya ne kawai idan ina tare dake, sabo dake ce kawai wacce zata iya kulawa da ni sosai, Mamie ina jin yunwa sosai amma kuma zanci abinci ne kawai idan ke kika bani a baki. To ina fatan zaki yi min wannan alfarmar dan Allah ko kuma ni ba zanci komai." "Eh zanzo ďana kawai ka jira zuwa na yanzu." Hakan ya saka shi farin ciki ba jimawa suka yi sallama *Adyan* ya anbaci sunan *Alishart* yana cewa, *"Alishart* bani wayar ki zan kira Ameer yazo ya d'aukan mu tafi, nima ina jin yunwa to ya kamata na tafi nayi break past ba jimawa zan dawo insha Allah." *"Yaya Adyan* akwai abinci a nan ni zan had'a maka break past." *"Alishart* abin shi ne ina da nawa abincin wanda nake kira da na musamman." "Wannan wane irin abinci ne wanda ya zama na musamman a gareka.?" Murmushin sa ya k'aru sosai ya anbaci sunan samosa da madara, cike da mamakin abin daya fad'a take magana da shi. *"Yaya Adyan* gaskiya ku biyun kuna da abin mamaki sosai, bayan kamannin da kike da juna ra'ayin kuma iri ďaya ne wannan abincin da kake magana, shi ne abincin da Yayana yafi so yana matuqar san abincin sosai." *"Alishart* wai gaskiyar kike fad'a kuwa.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh ya mai da kallonsa ga *Adnan* shi ma ya jinjina masa ka a lamar eh. Murmushin sa ya k'aru sosai ya mai da kallonsa ga *Alishart* tare da fad'ar sunan ta. *"Alishart* hakan ne yake nuna k'arfin abotar mu ina farin ciki da hakan sosai." Suna haka suka ji a na buga masu k'ofa ko a wannan karon *Alishart* wacce ta tafi ta bud'e k'ofar, ta ta samu Abba da Papa a k'ofa ta shiga yi musu sannu da zuwa sun dawo tare. Bayan sun gaisa Papa ya shiga tambayar *Adnan* yayi break past, "a'a Papa ina jiran zuwan Mamie ne domin ta ciyar da ni da hanayen ta." "To amma ka sanar da ita hakan.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh, "shikenan zanyi magana da ita a waya." Ya ciro wayar sa ya shiga kiran ta ba jimawa ta d'aga ba tare da sun gaisa ba yake magana. "Shin kin shirya zuwa asibiti ko a'a.?" "Am dama ina jiran izinin tafiya ne daga gareka." "Yaron yana jin yanzu sosai to kizo da sauri kinji ko." Ta amsa shi da to suna k'arasa waya ta tashi ta nufi asibiti. Ba wani d'aukan lokaci sai ga Mamie cike da d'auki tayi hugging d'in yaronta tana sunbatarsa, daga bisani kuma ta fara ba shi samosa k'amshin ya daki hancin *Adyan,* ya wani lumshe ido tare da jan numfashi ya qara da furta. "Waw k'amshin da dad'i sosai zanso cin wannan sosai." Mamie tayi kiran sa ya tafi nan kuwa ta shiga basu gaba ďaya har da *Afnan.* Hakan yayi matuqar yiwa dukansu dad'i sosai musamman *Adnan,* bayan wani lokaci sai gasu Amar abokan aikin su *Afnan* ganin hakan ne yasa su Papa suka tafi, har da Mamie ita ma tafiya tayi su kuma sunci gaba da fira irin ta abokai, *Adnan* ya gabatar da *Adyan* garesu haka kuma *Adyan* yaci gaba da kulawa da shi, har ya samu sauki ya samu kwana biyar asibiti sannan ya samu sallama. Bayan kwana biyu suka fara hidimar biki tare da *Adyan* a kayi komai da Amaryar sa, an yi komai an gama Amarya *Afnan* ta tare da Angon ta *Adnan.* A nan gidan Papa ta tare yayin da *Adyan* yake ta sintirin zuwa gurin *Alishart,* wani lokaci ya kan d'auke ta zuwa gidan Abbu, bayan wani lokaci a ka fara hidimar auran Ameer wata biyu da auran su *Adnan* wata rana............ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/3, 4:36 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 33* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Sunday 30/01/2022* *Time 04:33pm* *Typing................* Kwance suke rungume da juna wayar sa ta d'auki ruri ya kai hannun sa, ya d'auki wayar ganin mai kiran sa ne yasa shi d'aga wayar tare da fad'ar sunan ta. "Ammie mai yasa kika kira.?' *"Adyan* kana ina? Kowa sai neman ka yake duka ahalin suna san had'uwa da kai, to ya kamata ka zo yanzu kuma ka zo tare da *Alishart* kafin wasu daga cikin su tafi, sannan kuma Ameer yana ta tambaya na fad'a min kina ina.?" "Ammie na fita ne tare da *Alishart* zamu yi siyayyar kayan zuwa dina anjima, amma karki damu zamu zo yanzu kin ji." Ta amsa da to da kuma haka suka yi sallama, ya mai da kallonsa ga *Alishart* wacce take kwance jikin sa, yayi wani kyakkyawan murmushi mai tare da 'yar dariya ya shafi fuskar ta tare da sunbatarta, cikin wata lallausar murya mai dad'in sauraro yake fad'ar sunan ta. Ta d'ago fuskarta ta kallesa tana murmushi wani irin kallo suke yiwa juna mai tare da so. "Masoyiya Ammie tana jiran sabo da zata gabatar damu ga duka ahalin, to ya kamata mu shirya mu tafi yanzu." "Ta jinjina masa ka tare da furta to ya tashi tare da tashin ta sun nufi gurin wanka. Ba jimawa suka fito sun shirya tsab cikin kyakkyawar shiga sannan suka tashi suka nufi gurin Ammie, sun isa gidan nan kuwa Ammie ta shiga gabatar dasu duka ga ahalin, kasancewar shekaru goma kenan da basu shigo Nigerian ba. Duka ahalin sunyi farin ciki sosai da had'uwa dasu biyun, haka suka ci gaba da shagalin biki har zuwa lokacin da Amarya ta tare a gidan Angon ta. Su Appa kuwa watan nin su uku suka koma England wanda kuma tare da, *Alishart* suka tafi kafin zuwan lokacin da zata fara zuwa makaranta, wani yammaci tsaye yake yana had'a coffee a kicin lokaci ďaya wayar sa ta d'auki ruri, ya kai hanun sa ya d'aga tare da karawa a kunne bayan sun gaisa sunci gaba da magana. "Prof barka da wannan lokacin fatan kana lafiya kwana biyu ina *Adeel.?"* "Lafiya qlau Prof Bashir yarona yana lafiya to kai fa ya naka ahalin suke.?" "Suna lafiya Prof Abas lokaci ya tafi sosai amma har yanzu baka shirya yin wani aure ba, ya kamata a ce kayi aure ko ba komai zaka samu wacce zata kula da kai da kuma yaronka. Ko kuma dai kayi k'oqarin dawo da *Maman Adeel* ina ga kamar hakan zai fi, ko ba komai yaron zai yi farin ciki sosai sannan kuma zai kula da ita sosai, kaga a hakan zai samu albarkar ta to ya kamata kayi hakan dan Allah." "A'a Prof Bashir ni ba zanyi hakan ba ina nufin ba zanyi aure ba, sabo da ba zanso wata ta cutar min da yaro ba sannan kuma ba zan ta'ba kuskuran, sanar da shi *Adeel* komai a game da mahaifiyar sa ba, sabo da zan iya rasa shi gaba d'aya domin kuwa yana san Maman sa da yawa, duk da cewar bai yaru da ita ba hasalima ni na boye ta daga garesa, ta hanyar sanar da shi cewar ta mutu ta yanda ma ba zai yi tunanin ya rayu da ita ba." "Prof Bashir ban san ya yarona zai ji ba yayin da shi ya san a salin gaskiyar cewa mahaifiyar sa na raye, duk da cewar hakan zai matuqar wahala shi ba zai ta'ba sanin gaskiyar ba. Sabo da ni ba zan ta'ba barin na rasa yarona ba wannan alkawari ne." "Shikenan fatan nasara ďan uwa." Haka suka ci gaba da magana na tsayin wani lokaci sannan daga bisani suka yi sallama. Abin da bai sani ba shi ne duk abin da yake fad'a a kan kunnan *Adeel* wanda da jimawa ya dawo, amma ko wani gajeran motsi bai yi ba wanda zai sa ya fahimci cewar yana kusa da shi. A zahirin gaskiya ya shiga firgici rud'ani da kuma tashin hankali sosai, da irin abin da yaji Dadyn sa na fad'a lokaci d'aya ya saki wani irin ihu tare da sakin kuka. Ihun sa ne ya fito da Prof daga kicin cikin hanzari ya isa garesa yana fad'ar sunan sa. *"Adeel* mai yake faruwa da kai ne haka mai ya saka kake irin wannan kukan haka.?" Cike da k'unci bak'in ciki 'bacin rai tare da tarin damuwa yake magana. "Dady wannan shi ne karo na k'arshe da ni zan tambiye ka, to kawai dai yanzu ka fad'a min a salin gaskiyar ina Mummy na take.?" Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. *"Adeel* wai mai kake fad'a ne haka? To har sau nawa kake san ni na fad'a maka cewar Mummyn ka ta mutu? *Adeel* Mummyn ka ta mutu to ya kamata ka yarda da gaskiyar, ta yanda zaka dena tambaya na ita ka ji ko." "A'a wannan sam ba gaskiya bane sabo har yanzu Mummy na tana raye, to kawai ka sanar da ni gaskiyar ina Mummy na.?" *"Adeel* ni fa sam na gagara fahimtar abin da kake fad'a amma qlau kake kuwa.?" "Dady shin ko zaka dena wannan wayancewar haka dan Allah? Sabo da na riga da naji komai daga gareka, kai da bakin ka ne kake fad'ar cewar Mummy na tana raye, amma kuma ka 'boye ta gareni sabo da kawai karka rasa ni. Dady mai yasa kayi haka tsawan rayuwata begen Mummy na nake tare da kukan rashin ta a tare da ni, ko yaushe kana fad'a min cewar kana qauna ta sosai to amma ta ya ka iya jure ganin yaronka, a cikin irin wannan mummunan yanayin duk da cewar kana da mafutar damuwar sa? Dady gaskiyar ta bai yana cewa kai kawai cutar da ni kake sabo da wani buri na ka. Shi yasa ni na kasance a haka kamar wani mara gata ban san komai ba na rayuwa, kai ba abin daka ko ya man ko da kuwa addini na, na gode Allah daka had'u da *Adnan* wanda shi ne ya fara ko ya min yanda zanyi rayuwa. Musamman yanda zanso Mummy na wanda kai kuma tsanarta ka sanya min a zuciya ta, Dady ka fad'a min mai yasa kai kayi hakan ta ya cikin sauk'i ka za'bi cutar da ni ta wannan hanyar.?" "Dady naro e ka ka sanar da ni dalilin ďaya wanda yasa ka raba ni da Mummy na? Ba tare da ka ji tausayi na ba sannan kuma daga k'arshe ina san ka fad'a min inda Mummy na take dan Allah." Magana yake cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau yayin da, damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai sai kuma aikin kuka yake kuka sosai, tamkar wani k'aramin yaro cike da jin tausayin sa sosai yake magana. "Kayi hak'uri d'ana ni kawai bana san rabuwa da kai dalilin da yasa na b'oye maka gaskiyar kenan, *Adeel* a lokacin kana yaro sosai shekarun ka uku ne kawai san da muka rabu, na za'bi kasancewa da kai ne sabo da ita ďin ba zata iya kulawa da kai ba. Kayi hak'uri d'ana amma Mummyn ka ita tana cikin halin rashin lafiyar hauka, ina nufin ita ďin mahaukaciya ce har ma tayi k'oqarin cutar da kai. *Adeel* ni bani da wani za'bi ne sabo da ba zan iya ci gaba da zama da ita ba, sabo da ita ďin mahaukaciya ce sannan kuma." *Adeel* ya dakatar da shi cikin k'unci ta hanyar furta mata kalmar A'a yaci gaba da magana. "A'a ka dena kiran Mummy na da wannan mummunan sunan ita ba mahaukaciya ba ce, ita ďin ba kamar yanda kake tinani ba ce to yanzu ka fad'a min ina Mummy na take.?" *"Adeel* ni na raine ka yanda zan iya na baka duka soyayya ta, sannan na so ka da duka zuciya ta dama rayuwa ta gaba d'aya. Amma ta wannan hanyar zaka saka min? *Adeel* koma dai miye ni na aikata maka to nayi shi ne sabo da ina qaunarka sosai, sannan kuma sam bana san na rasa ka domin kai ne kawai ahalin da nake da shi. *Adeel* duk da cewar kai ka san gaskiyar amma kuma ba zan ta'ba sanar da kai inda Mummyn ka take ba, sabo da ba zan ta'ba baka damar da zaka tafi ka barni ba. Kawai zaka ci gaba da zama a tare da ni na har abada, to garama ka dena wannan shirmen naka ka dawo haiyacinka, zanyi ma wata alfarma d'aya kawai kai zaka kasance tare da Mummyn ka a photo, wancan photon daka ta'ba tambaya wacece to Mummyn ka ce, kayi hak'uri da ban sanar da kai ba kawai dai ni bana san ka ji wani iri ne, amma yanzu tin da ka san gaskiyar zaka iya anfani da shi. Baka cikin kyakkyawan yanayi to ya kamata ka huta yanzu ka sha magani ka ji ko." Yana k'oqarin ba shi magani ya ya juya yayi tafiyarsa yayin da yake kuka kuma kuka sosai, Prof ya bisa da kallo har ya shige yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Wanda zuwa wannan lokacin idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai, *Adeel* yana shiga bedroom kai tsaye durowa ya nufa ya d'auko jakar da take d'auke da photo nan Mummyn sa. Ya nufi gado ya zauna tare da ciro photo nan sai wani kallon photon yake yana kuka sosai, yayin da bakin sa yake fad'ar sunan Mummy lokaci d'aya ya fara fita haiyacinsa, Prof ya shigo ya same sa cikin wannan yanayin cike da firgici ya isa inda yake yana fad'ar sunan sa. Amma bai amsa ba Prof ya shiga rarrashin sa a kan ya yarda ya sha magani, "eh zan sha kawai sabo da Mummy na domin ina san na k'arasa rayuwata ta gaba da ita, to ka bani maganin na sha." Nan kuwa ya shiga ba shi magani ya sha ba jimawa sosai yayi barci, Prof ya rufe shi da ido sai kallonsa yake yayin da tausayin sa ya cika zuciyarsa sosai. Bayan kwana biyu har zuwa wannan lokacin *Adeel* bin Prof yake a kan ya sanar da shi inda Mummyn sa take, amma sam yak'i ya sanar da shi komai a game da inda take hakan yasa, *Adeel* yake fishi da shi kuma fishi sosai wanda ko magana ya dena yi masa. Hakama ya dena ci da kuma sha sai azumi yake wanda ba sahur kuma ba bud'a baki, hakan tasa yake ta fama da rashin lafiya ko yaushe Prof ya shiga damuwa sosai da irin yanayin sa. Ba shi da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ya amsa shi da cewa Mummyn sa na katsina a garin Kankiya, ai kuwa nan ya fara shirin tafiya gareta amma mirsisi Prof ya dakatar da shi ya qara da fad'a masa cewa. *"Adeel* sai dai ka za'ba a tsakanin mu biyun idan ka zab'e ni to zaka ci gaba da yin rayuwa kamar sarki, amma idan ka za'bi kasancewa da Mummyn ka to fa zaka rayu ne kamar wani bawa mara gata. *Adeel* zaka bar komai da kake da shi a nan sabo da duk abin daka mallaka nawa ne, to dole a nan zaka barsa wannan shi ne hukunci na to yanzu zaka iya za'ba a tsakanin mu biyun." "Dady ka san me ni na kasa gane kai wane irin uba ne a gareni? Da fari ka raba ni da Mummy na sannan kuma ka raine ni cikin k'arya, yanzu kuma kana goranta min a kan duk wani abin da kayi min. A baya nayi tunanin cewa kai uba na gari ne a gareni, amma kuma a'a kai kawai uba ne mai tilassa wa yaron sa a kan ra'ayin sa, shikenan zan za'ba kamar dai yanda ka buqata daga gareni kayi hak'uri domin kuwa a halin yanzu, Mummy na tana buqata sannan kuma ni ina matuqar buqatar kasancewa a tare da ita sosai. To kawai ka sanar da ni adres na inda zan same ta.?" Cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. *"Adeel* hakan yana nufin cewar kai ka za'bi kasancewa da Mummyn ka fiye da ni Dadyn ka.?" "A'a Dady ni ba zan iya za'ba a tsakanin ku biyun ba, kawai dai ni nayi abin daya dace ne ba kamar kai ba daka za'bi kud'in ka fiye da yaronka. Naso a ce yanda ka bani soyayyar ka kayi k'oqarin kasancewa uba na gari a gareni, amma duk da haka ina yima godiya sosai yanzu ka fad'a min Kankiya a wace unguwar kuma a wane layi Mummy na take.?" Kallonsa kawai yake ba tare daya furta masa komai ba, sai ma juya da yayi ya fice daga d'akin ganin yanda ya k'osa a kan tafiya gurin Mummyn sa, yasa Prof ya dena barin sa fita ko ina ko da kuwa Campany gurin aiki, yayin da shi kuma zai fita sai ya rufe sa ta yanda ba zai iya fita ba. Amma kuma hakan sam bai canja masa ra'ayi daga tafiyar ba wata safiyar litinin bayan Prof ya fita zuwa office, ya tashi yayi duk wani shiri nasa na tafiya ya d'auki duk wani abin buqata. Ya nufi bayan gida ya tashi gobara ya koma k'ofa yana ihu iya k'arfin sa, ganin yanda wuta ke tashi cikin gidan yasa Audu ya nufi k'ofar tare da bud'e wa kasancewar yana da mukulli. Kafin su ankara gidan ya cika da mutane sosai masu kawo d'auki Audu ya kira layin Prof ya sanar da shi, Prof ya fara kiran layin masu kashe gobara sannan ya nufi gida, a nata ruguntsumin kashe gobara a daidai wannan lokacin ne *Adeel,* ya samu damar sulalewa ya fita ya bar gidan ya nufi Kankiya. Ba jimawa sosai sai ga Prof ya k'araso cike da firgici yake anbatar sunan yaronsa, sai k'oqarin shiga ciki yake an ki e sa tare da sanar da shi cewar yaronsa ya tsira. Suna haka sai ga motocin kashe gobara sun fara aikin su yayin da Prof yake ta nai man yaronsa, amma ina sam bai yi nasaran ganin sa ba sabo da ya riga daya tafi. A zahirin gaskiya hankalin sa yayi matuqar tashi sosai domin yana da tabbacin cewa ya tafi Kankiya, *"Adeel* mai yasa baka kashe ni ba a maimakon aikata min haka? Ta ya kake tunanin cewa zan iya fara sabuwar rayuwa babu ka? Bayan kuma kai ne a salin farin ciki na abin da nafi so ina qaunarka sosai d'ana, na so ka da duka zuciya iya yarda zan iya na baka duka soyayya ta gaba d'aya to amma mai yasa ka za'bi ka tafi ka barni.?" Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawa a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma kwalla ce take bin fuskar sa mai tsananin zafi da k'una sosai. Bayan an kashe gobarar ya shiga ciki sai wani kallon gidan yake kallo sosai, bayan wani lokaci ya rufe gidan ya nufi wani gidan daban kasancewar yana da gidaje da dama, yayin da tunanin yanda zai dawo da yaronsa yayi yawan gaske a tare da shi sosai. *Adeel* kuwa yana fita kai tsaye tashar mota ya nufa ba b'ata lokaci ya shiga mota suka kama hanyar Kankiya............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/3, 11:09 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 34* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 31/01/2022* *Time 03:12pm* *Typing.................* Da yamma lis ya sauka garin Kankiya yayi tsaye bakin hanya yayin da yake magana da zuciyarsa. "Na iso garin Kankiya amma kuma ban san ta ina zan fara nai man Mummy na ba, ya Ubangiji ka nunan hanya cikin sauk'i ka had'a ni da Mummy na." Maganar da d'an a cab'a yake ne ya tsinke tunanin sa, "Malan tafiya ne.?" "Eh tafiya ne amma ina san zan tambiye ka wani abu.?" Ya jinjina masa ka a lamar to shi kuma yaci gaba da magana. "Am dan Allah ko ka san wani mutum mai suna Prof Abas Muh'd? Shi ďin yana da kud'i sosai hakama yana tare da manyan 'yan siyasar k'asar nan. Shi a salin d'an garin nan ne amma ya bar nan ba tsayin lokaci ka ga photon sa." Ya nuna masa photon sa ya girgiza ka sannan ya amsa shi, "A'a ban san shi ba amma zaka iya tambayar wani daban, to yanzu fad'a min ina zamu tafi.?" Yayi shiru kad'an sannan ya jinjina ka tare da furta masa, "kawai ka sauke ni a k'aramin hotel." Ya amsa da to sun tafi ya sauka a hotel wanda ya d'auke sa, na tsayin kwana ki yana aikin nai man Mummyn sa inda daga k'arshe yayi nasara. Bayan tsayin kwana kin daya d'auka a hotel yayi nasaran gane gidan da matuqar Mummyn sa take, hakan tasa ya bar hotel ya nufi gidan da Mummyn sa take wani yammaci. Zaune suke a nan cikin harabar gate sai gasu Farha sun isa inda take, kamar dai kullum sun shiga tsokanar ta da teady abin da take gani a matsayin ďan ta. Sun tashi sun gudu suna dariyar ta ita ma tashi tayi ta bisu a baya tana fad'a musu cewar, "ku bani d'ana yana kuka sosai dan Allah ku bani yarona." Magana take yayin da take kuka kuma kuka sosai yayin dasu kuma suke dariyar ta, Maman ta sai binta take tana fad'ar sunan ta tana cikin tafiya lokaci d'aya taji ta fad'a cikin ruwa, ihun ta ya k'aru sosai su Farha kuwa sai dariyar ta suke sosai. Lokacin yayi daidai da shigowar *Adeel* cike da firgici ya cillar da jakar sa, ya nufi gurin ta da gudu ya fad'a ruwa tare da kamata ya d'ago fuskar ta sama, yaci gaba da tafiya har ya isa bakin gab'a ya fito da ita sannan ya fito. Wanda zuwa wannan lokacin ta suma *Adeel* ya shiga danna cikin ta ruwa na fita, yayin da yake fad'ar sunan ta amma bata farka ba ya shiga buga fuskarta, yana murza k'afafun ta amsa bata yi wani yunk'urin farkawa ba. Cike da fishin zuciya ya tashi ya nufi gurin su Farha inda ya rufe su da duka, duka yake musu sosai duk da kasancewar su yara sai da Umma ta kwace su hanun sa. Ya juya da sauri har yana gudu ya koma gurin Aisha wacce take kwance, ya wani rungumata jikin sa yana fad'ar sunan ta yayin da yake kuka kuma kuka sosai. Umma sai wani kallonsa take kallo mai cike da jin mamakin sa cikin tautasa murya take magana. "Yaro waye kai mai yasa kake kiran 'yata da Mummy? Na gode ma daka taimaki 'yata amma banso kayi duka wasu Farha ba, sabo da hakan zai yi matuqar cutar damu sosai ban kuma san ya zanyi ba." Magana take cikin wani irin mummunan yanayi yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai wanda zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, cike da k'unci bak'in ciki b'acin rai tare da tarin damuwa yake magana. "Kaka *Adeel* ne ya dawo gareku sannan kuma sam bana nadamar abin dana aikata wa yaran, sabo da sun cancanci fiye da haka daga gareni nayi tunanin cewa wannan kawai a mafarki ne, amma yau gaskiyar ta bai yana cewa hakan yana yawan faruwa da ita. Kaka sam bai kamata a ce hakan ta faru da ita ba yanzu fad'a min ina zai kai ta, sabo da ya kamata ta bar nan gurin yana da sanyi sosai to zai iya cutar da ita." *"Adeel* kai ne bayan shekaru ashirin yau ka dawo garemu? Gaskiya ina farin ciki sosai zo nan ďana." Cike da d'auki ta wani rungumasa jikin ta sai wani shafar sa take tana sunbatarsa, lokaci d'aya kuma ta saki kuka shi ma abin da yake yi kenan, bayan wani lokaci ya d'auki Mummyn sa suka nufi ciki ya shinfid'eta, a kan wata shamamar katifa mai kama da tabarma ya mai da kallonsa ga Umma tare da fad'ar sunan ta. "Kaka shin zaki iya sanar da ni komai a game da Mummy na dan Allah.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta shiga sanar da shi abin daya buqata, *"Adeel* Mummyn ka tin bayan data aife ka take fama da wannan rashin lafiyar, wanda kuma Dadyn ka ne yake da alhakin duka wannan ya kuma taka muhimmiyar rawa sosai, a game da wannan rashin lafiyar ni ina jin kamar ba zan iya yafe masa ba. *Adeel* a daidai gab'ar daya kamata ya taimake ta ne ya tsinke duk wata halak'a da take tsakanin su, haka ya kalli tsabar cikin idanuwana sannan ya fad'a min cewar ya sake ta, a lokacin da nake rok'onsa a kan ya kai ta asibiti sai fad'a min yayi cewar 'yata mahaukaciya ce bata da wani anfani. Sannan kuma ya d'auke ka daga gareta hakan ya k'ara wa ciwan ta girma sosai, *Adeel* sai da a ka kai fagen ba zan iya biyan kud'in haya ba ga kuma siyan maganin ta." *"Adeel* nayi aiki gidaje da dama sabo da na samu na kula da 'yata musamman abinci da magani, kuma babu wani wanda ya taimaka min sabo Kakan ka ya mutu na aurar da Aisha ga Dadyn ka, duk da cewar tana da k'ananan shekaru a tunani na shi zai kula da ita sosai, kamar dai yanda yayi min alkawari amma ina kawai yaudarar mu yayi, ya kuma yi anfani da takaicin mu a kanmu ba tare daya tausaya ba. *Adeel* da k'yar na iya samun aiki a gidan nan ina musu wanke-wanke da shara, suna bamu abinci bayan ko wane wasa suna bani dubu biyar dasu ne nake samu ina siya mata magani, yanayin ta ya tsananta ne sabo da maganin ya k'are kuma ba a yi min biya ba. To yanzu kuma ban san mai zai faru ba da kai ka daki yaran ina jin tsoro karsu ce mu bar nan, duk da cewar ko yaushe suna tsokanar ta amma sam ba zanso mu bar nan ba, sabo da bamu da wani gurin da zamu tafi *Adeel* shin ko zamu iya tafiya mu bawa yaran hak'uri dan Allah.?" "Hak'iqa Dady mugun mutum ne sosai shi yayi matuqar cutar da Mummy na da kuma ke, nima haka yayi ta cutar da ni ta hanyar saka min tsanar Mummy a raina dama zuciyata, nayi zurfi sosai gurin k'yayyar Mummy na amma Allah cikin ikon sa sai ya had'a ni da aboki na gari, *Adnan* shi ne wanda ya sanar da ni a salin gaskiyar wacece mahaifiya. Da kuma yanda zan san addini na domin samun kyakkyawar rayuwa, daga bisani kuma na had'u da *Amna* ita ta taimaka sosai a game da rayuwata. Yayin da Dady yake ta fama da Campany da kuma kasuwancin sa, ya b'oye min gaba d'aya gaskiya a game da Mummy na domin ya fad'a min cewar ta mutu, ko photon ta bai ta'ba nuna min ba amma kuma daga k'arshe na gano a salin gaskiyar. Kaka kiyi hak'uri da ban taimake ki a kan komai ba amma yanzu ni ne wanda zai ci gaba, Kaka ni zan d'auki d'awainiyar kuma zamu bar duk da cewar bani da ishashshan kud'i sosai, amma kuma hakan ba zai dakatar da ni ba zanyi iya abin da zan iya. Daga k'arshe kuma Mummy na zata samu cikakkiyar lafiya sosai insha Allah yanzu ki bani takardar maganin ta." *"Adeel* hakan zai yi matuqar cutar da lafiyar ka sosai to kawai ka barni naci gaba ka ji ko." "Kaka ni qlau nake to dan Allah karki dakatar da ni please ki bani takardar na tafi." Ta jinjina masa ka tare da yin hugging d'in sa tana sunbatarsa ta k'ara da furta masa Allah ya ma albarka. Ya amsa da Amin yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, ita ma Kaka abin da take yi kenan sun shiga share wa juna kwalla, Umma ta tashi ta d'auko takardar maganin ta ba shi ya tashi ya fita ya d'an jima sannan ya dawo, inda ya samu mai gidan yana ta yiwa Umma ihu a ka sabo da dukan da a kayi wa yaransa. Inda kuma daga k'arshe ya furta mata cewar su bar masa gida cike da k'unci yake magana. "Ba zan maka ihu ba sabo da gidan ka amma ka sani wannan ba qanwarka bace, a k'alla zata kai sa an nin mahaifiyar ka amma kuma kana yi mata ihu, kawai sabo da tana a k'arkashin ka to ko da baka fad'a ba yau zasu bar gidan ka. A game da yaranka kuma suna buqatar kyakkyawar tarbiya ta yanda zasu iya sanin, girman na gaba dasu ko kuma dai duniya ta yi musu horo mai tsananin sosai. Kuma daga k'arshe kai ne wanda zai yi kuka hakama kai ne wanda jama'a zasu ga gazawarka, sannan kuma su zageka to kawai dai kayi abin daya dace." Yana kai k'arshen maganar sa ya runguma Umma sun shiga ciki ya samu Mummyn sa ta farka daga suman data yi, da sauri ya k'arasa inda take har yana gudu yayin da yake fad'ar sunan ta, yayi hugging d'in ta yana sunbatarta cike da d'auki yake magana. "My Mum na ji dad'i kin farka bayan wasu tsayin shekaru, yau mun sake kasancewa a tare ina farin ciki sosai to ya kamata ki sha magani yanzu." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata, sai wani kallonta yake ita ma kallonsa take ya tashi ya d'auko maganin Umma ta ba shi ruwa. Nan ya shiga bata magani bayan ya qarasa ya kwantar da ita tare da d'ora kanta a kan cinyarsa, sai wani shafar kanta yake zuwa bayan ta tare da sunbatarta duk da cewar basa cikin kyakkyawan yanayi, amma ya samu kansa da jin farin cikin kasancewa tare da Mummyn sa sosai. Bayan wani lokaci ya sauke ka ga fuskar Umma tare da fad'ar sunan ta. "Kaka ya kamata mu tafi tare nake da mai mota na riga dana samu gurin da zamu zauna, a hotel ne zamu zauna na kwana biyu kafin na samu gidan da zamu zauna to dan Allah karki ce a'a kin ji please." Ta jinjina masa ka a lamar to nan kuwa ta shiga had'a kaya *Adeel* ya ta ya ta bayan sun qarasa, Umma ta tafi tayi sallama da matar gidan sannan suka tafi. Hakan kuwa ta kasance sun samu tsayin kwana biyar a hotel sannan ya samu gida, ba shi da wani kud'i shi yasa ya siyar da wayar sa da laptop d'in sa ya biya hayar wata uku, sannan ya siya musu kayan abinci ya siyar da duk wani abin sa mai tsada yaci gaba da kulawa da Mummyn sa dama Kaka. Ya mai da ta asibiti amma sam ba wani abin da suka yi mata, sai dai kawai suka ba shi shawaran a kan ya fita da ita k'asar England domin a yi mata aiki. Ganin ba shi da komai yasa ya shiga damuwa sosai haka ya shiga nai man aiki amma bai samu ba, nan ya fara aiki gurin wasu masu gyaran babura da d'an abin da yake samu suke cin abinci, sannan yake siya wa Mummyn magani dama shi kansa wani yammaci yana cikin aikin sa, Kabir yazo yana anbatar sunan sa ya amsa Kabir yaci gaba yana cewa. *"Adeel* wani yana san zai yi magana da kai yana baya cikin mota." "To waye shi mai yasa ya tsaya ta baya.?" *"Adeel* dan Allah ka tafi sabo da ba zai cutar da kai ba." Ya jinjina masa ka ya tashi ya tafi shi kuma yaci gaba da aikin, *Adeel* ya isa gurin da Kabir ya sanar da shi yayi tsaye sai wani kallon motar yake, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa ya juya domin tafiya da sauri ya fito mota yana fad'ar sunan sa. *"Adeel* ďana dan Allah kazo gareni ka dena wannan fishin da ni haka, sabo da rashin ka ya cutar da ni sosai rabin raina ji yanda ka koma kamar ba kai ba, *Adeel* kasa mutane sai zagina suke suna ganin kamar ni na kasa kulawa da kai yanda ya kamata. *Adeel* har yanzu kai yaro ne sam bai kamata a ce ka fuskanci irin wannan mummunan qalubalen ba, ďana ta ya zaka rayu a haka ba abinci mai kyau ko abin sha babu sutura sannan babu kyakkyawan muhalli, *Adeel* ni nayi matuqar damuwa sosai a kanka ko waya baka da shi *Adeel* naro e ka daka dena cutar da ni haka. Yanzu kawai kazo mu tafi mu koma gida dan Allah." "A'a Dady ni qlau nake ina lafiya sannan kuma Mummy na tana matuqar buqata na sosai, to ba zan tafi na barta ba Kaka tayi iya abin da zata to ni zan k'arasa zanyi aiki tuk'uru sabo dasu, abinci mai kyau ko abin sha da sutura zuwa muhalli basu suke nuna mutum zai rayu ko zai mutu ba, sabo da har yanzu Mummy na da kuma Kaka ta suna raye." "Dady shi mutum kawai yana buqatar gwarin guiwa ne sannan juriya da kuma jajircewa, domin cimma nasara na kuma koyi hakan daga gurin Kaka. To yanzu kawai ka tafi sannan kuma karka koma dawowa dan Allah to ka tafi please." "Amma *Adeel."* "A'a kawai ka tafi dan Allah." Yana k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, Prof ma abin da yake yi kenan cike da k'unci ya shiga mota yayi tafiyarsa, bayan tafiyar sa ne *Adeel* shi ma ya nufi gida bayan kwana biyu yau ya jima sosai wajen aiki, misalin k'arfe 08:00pm ya dawo gida cike da nuna kulawa Umma ta shiga yi masa sannu da zuwa. Ya amsa yana murmushi ya nufi gurin Mummyn sa yayi hugging d'in ta tare da sunbatarta, sannan ya zauna ya gaisa da Umma sannan yaci gaba da magana. "Kaka yau nayi aiki sosai hakan yasa na tara kud'i sosai, to ni na siyo wa kowa abin da yafi so Mummy na tana da kayan shayi, musamman madara abin da tafi so sosai ke kuma kina da kaza ni kuma ina da samosa, zan had'a madara sai na sha tare da samosa had'in yana da dad'i sosai." "Kayi hak'uri *Adeel* na san cewar kai sam baka saba da irin wannan rayuwar ba amma kuma yanzu." Da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata ka, "Kaka shin ko zaki dena fad'ar min haka? Sabo da ina jin dad'in yanda nake rayuwa a nan ke da kuma Mummy na kune gwarin guiwa ta, eh a baya ina da kud'i sosai amma kuma bana farin ciki sosai, ko yaushe ina k'unci amma yanzu ina farin ciki sosai sannan kuma na koyi yanda zan tsaya da k'afafu na, sannan kuma na kula da wad'an da suke tare da ni musamman Mummy na. Hakan yana matuqar saka ni farin ciki sosai to ki dena fad'a min haka kin ji dan Allah." Ta jinjina masa ka a lamar to tare da rungumasa jikin sa bayan sun sake juna, Umma ta fara yiwa kaza aiki ta hanyar cin naman *Adeel* kuwa tashi yayi ya had'a madara ya fara cin abincin sa bayan wata uku............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/3, 11:10 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 35* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Tuesday 01/02/2022* *Time 05:39pm* *Typing..............* Zaune yake ya wani rabka wani uban tagumi sai tunani yake, kwana biyu jikin sa ba kuzari sosai shi yasa ya dena fita aiki, ga maganin sa dama na Mummyn sa duka ya k'are kuma dukansu da akwai buqatar su sha magani musamman Mummy. Yana cikin wannan k'uncin ya ji a na buga musu k'ofa tare da fad'ar sunan sa, ha!!! Ya nisa sosai tare da jan numfashi ya tashi ya nufi k'ofa Umma ta bisa da kallo tana girgiza ka. Ya fito ya samu Malan Nura tsaye a k'ofa ya ba shi hanu sun gaisa, bayan sun gaisa Malan Nura yaci gaba da magana. *"Adeel* lokaci sai tafiya yake amma sam baka ce dani komai ba, na baka duk wata dama amma kuma har yanzu banji daga gareka ba. To zuwa yanzu sai dai na baka hak'uri sabo da lokaci yayi da zaku tashi a gidan nan, *Adeel* na baku kwana biyu kawai sabo da ina san zan sanya wasu mutane a gidan, to dan Allah karku b'ata min lokaci kawai ku fita ka ji ko sai an jima." Ya juya yayi tafiyarsa ba tare daya jira ya ji mai za shi fad'a ba, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa ya juya ya koma ciki, yanayin sa yayi matuqar tsorata Umma sosai ta shiga tambayar sa mai yake faruwa da shi. Ya girgiza mata ka a lamar ba komai ya sauke kallonsa ga Mummyn sa wacce take rungume da pillow, a matsayin ďan ta sai wani jijjigasa take tana yi masa wasa cike da k'unci ya juya zai fita, yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, da sauri Umma ta ri e hanun sa ya juyo yana kallonta ta zaunar da shi sannan ta zauna tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* dan Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai.?" Yayi shiru kad'an sannan ya shiga sanar da ita komai magana yake cikin k'unci sosai yayin da yake kuka. "karka yi kuka ďana komai zai yi daidai to kawai ka jure ka kuma jajirce ka ji ko zo nan." Ya jinjina mata ka a lamar to ya k'ara matsawa kusa da ita kamar dai yanda ta buqata, ta rungumasa jikin sa tana d'an buga bayan sa bayan wasu 'yan mintuna ya tashi ya fita, ba tare daya san inda ya nufa ba tafiya kawai yake damuwarsa tana k'ara girma sosai. Hakan yasa yanayin sa ya fara canja wa sai wani rangaji yake tamkar zai fad'i, yasa hanun sa ya ri e k'irji yayin da yake furta kalmar wash abin damuwar shi ne a tsakiyar titi yake, motoci sai hon suke yi masa domin ya kauce wa hanya amma ina zuwa wannan lokacin ya fara fita haiyacinsa. Tin daga nesa ya hange sa wanda kuma ya gama fahimtar cewa sam baya cikin kyakkyawan yanayi, ganin yanda yake tsakanin motoci wad'an da kuma cikin sauri suke yasa shi koma wa gefen hanya yayi parking. Ya fito mota ya nufi gurin sa da sauri har yana gudu cikin hanzari ya janyo sa jikin sa har suka fad'i, *Adnan* ya tashi tare da kai kallonsa garesa ya shiga fad'a da shi fad'a sosai. "Shin ka haukace da kake k'oqarin kashe kanka ko dai kai ka sha wani abin ne.?" "Dan Allah ka taimaki Mummy na." Yana fad'ar haka ya suma cike da firgici *Adnan* ya shiga jijjigasa yana furta masa kalmar, ka tashi amma bansa cike da rud'ani yasa wani ya taimaka masa sun sa shi mota ya nufi asibiti da shi. suna isa a ka shiga da shi ciki domin a duba bayan wani lokaci Doctor ya fito, *Adnan* ya shiga tambayar sa jikin sa yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Am abin shi ne yana tare da tarin damuwa sosai to a yanzu yana matuqar buqatar hutu sosai, to ya kamata ya huta sannan kuma ka kula da shi sosai." Ya jinjina masa ka a lamar to bayan likitan ya tafi shi kuma ya shiga gurin *Adeel,* ya zauna gefe da shi sai wani kallonsa yake kallo sosai yayin da yake magana da zuciyarsa. "Waye shi mai yasa yake cikin damuwa har haka? Mai ya yake faruwa da Mummyn sa sannan kuma mai ya saka yake san ya kashe kansa? Tabbas wani mummunan abu yana faruwa da shi ina fatan ya samu lafiya cikin sauri, domin na samu damar da zan iya taimaka masa da wani abu. Ya Ubangiji ka kare Mummyn sa ka hana wani mummunan abu ya faru da ita Amin." Bayan wani lokaci ya farka cikin firgici sosai yayin da bakin sa yake fad'ar sunan Mummyn sa. Yana k'oqarin tashi *Adnan* yayi saurin dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa tare da furta masa. "A'a ya isa ka dakata dan Allah likita ya fad'a min cewar kana buqatar hutu sosai, to ya kamata ka huta ka ji ko dan Allah." "A'a sam ba zan iya zama a nan ba sabo da Mummy na da Kaka ta dukansu suna buqata na sosai, to ya kamata na tafi na gode sosai daka taimaken." "Wai da gaske kana san ka rayu sannan kuma ka damu sosai a kan ahalinka? To amma mai ya saka kake k'oqarin kashe kanka idan har gaskiyar kake fad'a." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Wai mai kake fad'a ne haka taya ma kai zaka fad'i haka? Ni sam ba zan ta'ba aikata irin wannan mummunan zunubin ba, sabo da Mummy na da Kaka ta suna buqata na sosai to ya kamata na tafi yanzu." "Shikenan ni zan sauke ka gida sannan kuma zanso ka sanar da ni da abin da zan iya taimaka maka.?" "Na gode hakan ma ya isa kai kana da kirki sosai, bayan nan kuma ni sunana *Adeel Abas* kai fa ko zaka iya fad'a min sunan ka.?" Wani irin kallo *Adnan* yake yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, cike da d'auki yayi hugging d'in sa yayin da yake fad'ar sunan sa. *"Adeel* wai kai ne haka mai yake faruwa da kai ne? Shin ka gane ni kuwa abokin ka tin na yarinta *Adnan Adam* shin ka tina ni kuwa.?" Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake sa daga rungumar da yayi masa, sun fuskanci juna wani irin kallo *Adeel* yake yi masa cike da d'auki yake magana. *"Adnan* wai kai ne a nan? Lokaci ya tafi sosai shekaru goma sha biyar kenan sai yau muka k'ara had'uwa. Gaskiya nayi matuqar farin cikin sake had'uwa da kai ina abokin ka? Ina nufin *Adyan* ina fatan zuwa yanzu ya samu cikakkiyar lafiya sosai.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "abokina yana lafiya yanzu yana kulawa da kansa sosai, *Adeel* amma na ji mamaki sosai da na ji kayi magana a kan kulawa da Mummyn ka, wanda kuma a baya kai ka fad'a min cewar Mummyn ka bata raye *Adeel* amma qlau kake kuwa.?" "Eh *Adnan* qlau nake kawai dai a wancan lokacin ban san a salin gaskiyar bane, Dady na ya b'oye gaba d'aya gaskiyar gareni shi ya min k'arya, a game da Mummy na bai fi watan ni hud'u da ni na san gaskiyar ba. *Adnan* Mummy na bata cikin kyakkyawan yanayi ga shi kuma ni na kasa yin komai, duk da cewa abin yana matuqar cutar da ni sosai *Adnan* ya kai ko magani na gagara siya mata, duk da irin yanayin ta *Adnan* hakan yana da zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una." Nan kuwa ya shiga sanar da shi komai magana yake yayin da yake kuka kuma kuka sosai, cike da jin tausayin sa yake magana yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla. *"Adeel* gaskiya ka bani tausayi sosai dama duka ahalin gaba d'aya, *Adeel* ni zan kula da wannan idan ka amince zan d'auke ku zuwa kaduna, a can zan baku gidan da zaku zauna sannan zaka samu aiki kuma Mummy zata samu kulawa sosai. *Adeel* dan Allah karka ce a'a ka barni nayi wannan please." *"Adnan* gaskiya bai kamata kayi duka wannan ba, sabo da wannan d'awainiya ta ne to ba zan d'ora maka nauyin ba na gode da kulawa." *"Adeel* wannan shi ne abin aboki na gari yake yiwa abokin sa, abokai na gari ko yaushe suna taimaka wa junan su ba kuma tare da sunji sun gaji ba. To daga wannan lokacin zasu iya kiran kansu da ahali *Adeel* kaddaran had'uwa da kai ne, yasa ni zuwa nan garin d'aurin auran wani abokin aikin mu, to na ro e ka dan Allah da girman Allah ka da ka dakatar da ni daga taimaka wa please." Ya jinjina masa ka tare da furta kalmar na gode sosai yayin da yake kuka. *Adnan* ya shiga rarrashin sa yana ba shi magana bayan wani lokaci ya k'ara hutawa suka samu sallamar likita, sun tashi sun nufi gida sun fara da siyan magani sannan suka isa gida, *Adeel* ya gabatar da *Adnan* gurin Umma tare da sanar da ita komai daya fad'a masa. Umma ta shiga yi masa godiya ya amsa ta da ba komai bayan sun gaisa *Adeel* yayi masa nuni da Mummyn sa, ya kai kallonsa gareta tare da tashi ya nufi inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, sai wani kallonta yake kallo sosai yayin da tausayin ta ya cika zuciyarsa. Ya sauke kallonsa ga rubobin ruwan da suke rungume jikin ta, ya nisa tare da jan numfashi yana girgiza ka ya mai da kallonsa ga *Adeel* kafin ya furta komai yayi masa rigagi. *"Adnan* abin shi ne tana kiran wad'an nan rubobin da yaranta sam bata rabuwa dasu." *"Adeel* shin tana da wasu yaran ne bayan kai.?" "A'a ni kawai ne d'an ta wannan kawai rashin lafiyar ta ne tazo a haka." *Adnan* ya jinjina masa ka tare da furta Allah ya bata tafiya, da dare suna cikin fira wayar sa ta d'auki ruri yayi murmushi sosai sannan ya amsa kiran. "Aboki barka fatan kana lafiya ina qanwata fatan tana tafiya.?" "Muna lafiya Aboki ta ya *Afnan* da kuma ďana fatan suna lafiya.?" "Dukanmu muna lafiya aboki ina da kyakkyawan labari a gareka." "Ina farin ciki da duk abin da zaka fad'a min." "Aboki ina tare da *Adeel."* "Waw kyakkyawan labari aboki yaushe ku biyun kuka had'u.?" "Yau ne kuma har yanzu mu biyun muna tare." "Aboki shin ko zaka iya had'a ni da shi dan Allah.?" "Ya amsa da eh ya bawa *Adeel* waya tare da fad'a masa wanda yake kallayi ya amsa tare da yin sallama. *"Adeel* barka shekaru goma sha biyar kenan ya d'auke ni ina fatan had'uwa da kai, *Adeel* ni na gode maka sosai a bisa taimakon rayuwata da kayi, na gode sosai kuma nan ba jimawa zanzo domin na had'u da kai na tabbata dukanmu zamu yi farin ciki da hakan." *"Adyan* gaskiyar ita ce *Adnan* ne wanda ya taimake ka, ni kawai na kasance a tare da kai ne har zuwa lokacin daya dawo gareka, shi ďin yana da kirki sosai haka kai ma kana da kirki sosai ni ďin na ji dad'in had'uwa daku." Haka suka ji gaba da magana na tsayin wani lokaci sannan daga bisani kuma suka yi sallama. Washe gari sunka shirya tsab sun fara da kai wa Malan mukullin gida, sun d'auki duk wani abu mai muhimmanci sannan suka koma hanyar kaduna. Misalin k'arfe 03:30pm suka isa garin kaduna Mamie ta shiga yi musu sannu da zuwa, sun amsa Mamie ta kawo musu ruwa da juice mai sanyi *Adnan* ya shiga yi mata sannu. Ta shafi kansa zuwa fuskarsa ta k'ara da sunbatarsa tana furta masa, "rabin raina ba buqatar ka gode min sabo da ina yin abin daya dace ne, nayi kewarka sosai fatan kana cikin k'oshin lafiya.?" "Qlau nake Mamie sannan nima nayi matuqar yin kewarku sosai ina Papa da Besty.?" "Papa bai jima da fita ba Besty kuma tana barci, ka san mai gidan nawa baya san wahala da yawa zaka iya tafiya ka duba su." Ya jinjina ka yana murmushi *Adeel* ya anbaci sunan sa tare da tambayar sa. *"Adnan* shin kayi aure ne sannan kuma kana da yaro? To amma mai ya saka baka sanar da ni ba.?" "Kayi hak'uri *Adeel* bawai na b'oye maka bane kawai na bari ne sai munzo sai na gabatar da duka ahalin gareku, sannan kuma shi yaron naka har yanzu yana ciki bai fito ba, cikin wata biyu ne kawai zaka had'u dasu ba jimawa insha Allah." Ya jinjina masa ka yana murmushi mai tare da dariya hakama Mamie da Umma murmushi suke, bayan wani lokaci suka tashi Mamie ta kai Umma da Mummy masauki, hakama *Adnan ya tafi da Adeel* masauki daga bisani kuma ya nufi d'akin sa, domin had'uwa da kyawawan furannin sa wato Besty da kuma Babyn sa...................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/4, 7:23 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 36* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 02/02/2022* *Time 11:47pm* *Typing................* Sannu a hankali yake tura k'ofar har ta bud'e, ya shiga ciki tare da rufe k'ofar ya sauke kallonsa gareta, sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai. Sai wani kallonta yake ya kai hanun sa ya shafi cikin ta tare da sunbatarta yana furta. "I love you my child i love you so much." Yaci gaba da shafar cikin yana sunbatarta sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, ta sauke kallonta garesa wanda shi kuma cikin ta yake kallo. Ta kai hanun ta tana shafar kansa tare da fad'ar sunan sa ya d'ago fuskarsa, sun fuskanci juna lokaci d'aya suka sakarwa juna murmushi mai tare da 'yar dariya. Ya tashi ya koma kusa da ita ya kwanta tare da rungumata jikin sa, sai wani sunbatarta yake ita kuwa tayi kwance jikin sa tamkar wacce za a mai da ciki a aife. "Besty nayi kewarki sosai da kuma Babyn mu Papa da kuma Mamie, dukanku ina tare da kewarku sosai abin farin cikin shi ne kuna lafiya, to yanzu fad'a min wani abu shin ke kin kula da Babyn mu sosai kuwa.?" "Eh Besty nayi hakan sannan Papa da Mamie suma sun taimaka sosai, gaskiya nima nayi matuqar yin kewarka sosai ina sanka Besty." "Nima ina qaunarki sosai amma kin ji abinci kuwa sabo da ba zanso yunwa ta cutar da Babyn ba.?" "Kayi hak'uri ban samu naci abinci ba sabo da bana san naci duk da cewar ina jin yunwa sosai." "Besty yanayin zai iya cutar da lafiyar Babyn yanzu ki fad'a min duk abin da kike so, ni kuma zan tafi na kawo maki nayi alkawari insha Allah." "Shikenan tin jiya nake da kwad'ayin naci awara to yanzu ka tafi ka kawo min." "Eh zan tafi kuma zan dawo da ita insha Allah bara na tafi yanzu." "Na gode Mujina am yauwa karna manta ina su *Adeel* fatan suna lafiya.?" "Eh qlau suke dukansu an kai su masauki." "Hakan yayi kyau to yanzu zaka iya tafiya." Ta fad'a tana murmushi shi ma haka murmushi yake sosai ya k'ara sunbatarta, sannan ya tashi ya fita ita kuwa ta bisa da kallo tana murmushi har ya fice. Yana fitowa kai tsaye d'akin da *Adeel* yake ya nufa ya buga masa k'ofa daga ciki ya amsa da shigo, ya tura k'ofar ya shiga ya same sa zaune bakin gado ya k'arasa inda yake ya zauna. *"Adeel* kayi hak'uri dana dame ka abin shi ne idan kana buqatar wani abu, to zaka iya sanar da Mamie na sabo da ni zan fita Besty tana buqatar taci awara, ka san yanayin mata masu ciki kamar k'ananan yara suke amma wata rana zaka fahimci hakan. To ni zan tafi ka kula sosai sai na dawo." *"Adnan* zan tafi tare da kai dan Allah." *"Adeel* ya kamata ka huta ka ji ko." "A'a *Adnan* qlau nake to dan Allah karka dakatar da ni please." "Shikenan zamu iya tafiya." Ya amsa da to sun tashi sun fice zuwa nai man awara ya fara sanar da Mamie, dama su Umma sannan suka tafi sun d'an jima a waje sannan suka dawo, abin farin cikin shi ne sunyi nasaran samun awara sun shigo ciki sun samu dukansu a parlour. *Adnan* ya fara zuwa kicin ya d'auko pilet sannan ya isa inda take ya juye mata sannan ya fara bata a baki tana ci, su Mamie sai kallonsu suke suna murmushi Mummy ta tashi daga inda take ta nufi gurin su *Afnan,* ta zauna tare da furta musu kalmar nima zanci Umma zata yi magana ya dakatar da ita yana girgiza mata ka, nan kuwa ita ma ya shiga bata a baki hakan kuma yayi matuqar yi masa dad'i sosai a ransa da ma zuciyarsa. Su Umma sai kallonsu suke Mamie sai murmushi yake yana sanya wa yaronta albarka, *Adeel* ya anbaci sunan sa tare da furta masa kalmar kayi hak'uri, *Adnan* ya girgiza masa ka tare da furta masa ba komai yana murmushi. Da dare Papa ya dawo gida bayan sun gaisa *Adnan* ya gabatar da shi a gurin su Umma, sabo da shi ya riga daya san labarin su a gurin yaronsa *Adeel* ya shiga yi masa godiya, ya amsa shi da ba komai yana murmushi Mamie ta shirya musu abinci a tebur sannan ta shiga ciki gurin Papa. Bayan sunci abinci su Umma sun shiga ciki domin su kwanta, hakama *Adeel* bayan tafiyar su *Adnan da Afnan* tashi suka yi suka fita zuwa gidan Abba, sun kuwa samu dukansu a tare Amal ta shiga d'auki tana yi musu sannu da zuwa. Sun amsa ta suna dariya sun gaisa dasu Anwar sannan suka ci gaba da fira cikin raha wasa da dariya, sun jima sosai a nan suna fira sannan daga bisani suka yi sallama dasu suka nufi gida. Sun samu su Papa suna k'oqarin shiga ciki sunyi sallama da juna sun shige, suna shiga ciki kai tsaye gurin wanka suka shiga ba jimawa suka fito, sunyi shirin kwanciya suka kwanta ba jimawa *Afnan* tayi barci. Ya shafi fuskarta tare da sunbatarta yana murmushi ya kai hanun sa, ya d'auki laptop ďin sa ya shiga kiran layin *Adyan* ba jimawa ya d'aga suka fara magana. "Aboki barka idan kana da lokaci ina san zamu magana yanzu a game da *Adeel* ne." "Eh zamu iya fara wa yanzu ina sauraran ka." Ya amsa shi da to nan kuwa ya shiga sanar da shi komai a game da shi, cike da jin tausayin sa sosai yake magana. "Aboki hakan sam bai yi ba amma komai zai yi daidai insha Allah, yanzu zanyi magana da Kaka na kaduna ina nufin Abbu zan koma kiran layin ka." Ya amsa shi da to sun tsinke kiran bayan wani lokaci *Adyan* ya koma kiran sa ya d'aga tare da fad'ar sunan sa ya amsa shi yana cewa. "Barrister nayi magana da Kaka yace gobe ka same sa a gida ka tafi tare da, *Adeel* sannan kuma ya tafi tare da takardun sa amma kana ganin zai iya ri e matsayin manager kuwa.?" "Doctor kai kana da kirki sosai Allah ya saka maka da alkhairi Amin, eh zai iya sabo da shi ne matsayin daya ri e a company Dadyn sa. Yana da kwarewa sosai a kan aikin company to zaka iya yarda da ni." "Aboki Dadyn sa yana da kud'i sosai har haka, amma yaronsa yake irin wannan rayuwar shi wane irin uba ne wace irin zuciya yake da ita haka? Ya ma kasa kasancewa uba na gari ga yaronsa tir da shi da kuma rayuwarsa gaskiya ba shi da kirki na tsane sa." "Aboki gaskiyar ka ne shi bai kasance uba na gari ga *Adeel* ba sannan kuma ya cutar da shi sosai, amma abin farin cikin shi ne har yanzu yana raye kuma duk da haka yana farin ciki, sabo da Mummy da kuma Kaka sannan kuma muna tare da shi to wannan ma kawai ya isa. To ba buqatar muyi magana a kan Dadyn sa sabo da hakan zai saka mu k'unci ne, kuma hakan sam bai dace damu ba yanzu fad'a min wani abu ina qanwata.?" "Ta fita tare da Ammie to ina Besty da baby na.?" "Qlau suke suna barci ne." Sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama, *Adnan* ya a jiye laptop d'in sa ya kwanta tare da runguma *Afnan* jikin sa. Washe gari bayan sun qarasa shirin su sun fito sun samu Mamie tana shirya abinci a kan tebur, sun tafi sun gaisa *Afnan* ta anbaci sunan ta tana cewa. "Sannu da aiki Mamie kiyi hak'uri dana kasa taimaka maki a kan wannan sabo da." Mamie ta rufe mata baki tana girgiza ka, "A'a 'yata karki fad'i haka sabo da ba laifin ki bane, lokacin da kike lafiya ke ce kike yin duka wannan dan haka ba buqatar ki ba da hak'uri, kawai dai ki kula min da ango na kin ji ko yanzu ki zauna zan tafi na kira Papa ya fito muyi break past." Ta zaunar da ita sannan ta juya domin tafiya *Adnan* yayi saurin dakatar da ita, ta hanyar yin hugging d'in ta tare da sunbatarta yayi wani kwance jikin ta, cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Mamie ke kina da kirki sosai kin fi ko wace uwa kirki, ke d'in ta musamman ce kin kuma kasance uwa ta gari a garemu ina sanki sosai ina matuqar qaunar ki sosai." Ta janyo sa ya fito ta gaban ta ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa, "ina qaunarka ďana fiye ma da yanda nake sanka Allah yama albarka matarka dama jikana." Sun amsa da Amin dukansu suna murmushi sannan ta juya ta nufi bedroom d'in Papa, bayan tafiyar ta *Adnan* ya tashi *Afnan* sun nufi d'akin su Umma sun isa k'ofa tare da buga k'ofar. *Adeel* ne wanda ya bud'e musu k'ofa sun shiga ciki ya sauke kallonsa ga Mummy wacce take ta aikin kuka, cike da firgici rud'ani tare da jin tausayin ta sosai ya mai da kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* mai yake faruwa da ita mai ya saka take kuka.?" Ya nisa sosai tare da jan numfashi yana girgiza ka sannan ya amsa shi. "Tana jin yunwa ne kuma madara take buqata shi yasa take kuka." "Amma kuma kake zaune a nan kana kallonta? Shin kana jin dad'in sautin kukan ta ne shi yasa ka gagara yin komai.?" Yana kai ar maganar sa ya juya ya fita daga d'akin *Adeel* ya shiga anbatar sunan sa amma bai amsa ba. Ba jimawa ya dawo tare da kofin madara a hanun sa cikin hanzari ya isa inda take ya zauna, nan kuwa ya shiga bata madara ita kuwa sai sha take ta kuwa sha sosai. Bayan ta k'arasa sha ya shiga tambayar Umma maganin ta, ta bud'e jakarta ta d'auko ta ba shi *Afnan* taba shi ruwa, nan kuwa ya shiga bata magani kamar ba zata sha ba kuma daga bisani ta yarda ta sha. Zai tashi tayi saurin ri e hanun sa tare da furta masa a'a tayi kwance tare da yin pillow da k'afarsa, ta wani ri e hanun sa tare da lumshe ido bai fi da mintuna goma ba zuwa sha biyar tayi barci. Suna haka sai ga Mamie ta shigo tare da kayan abinci *Adeel* ya kar'bi kwandon dake hanun ta, tare dayi mata sannu da shigowa ta amsa tana murmushi ta zauna tare da gaisawa da Umma, tare da tambayar ta jikin Mummy ta amsa ta da tana samun sauki, Mamie ta bata abincin data shigo da shi Umma tayi mata godiya murmushi kawai tayi mata, ta mai da kallonta ga *Adnan* tare da furta musu su tafi suyi break past. Sun amsa ta da to ta tashi ta fita bayan tafiyar ta *Adnan* ya gyarawa Mum kwanciyar ta, ya mai da kallonsa ga *Afnan* tare da fad'ar sunan ta yana cewa. "Besty mu tafi sannan kuma ki fad'a masa cewar ya fito muyi break past.?" "Besty shin wai kai kana fishi da shi ne wanda har ba zaka iya yi masa magana ba.?" "Besty kawai kiyi abin dana ce dan Allah na tabbata zuwa yanzu yaron yana jin yunwa sosai." Ya jinjina masa ka tare da kai kallonta ga *Adeel* kafin ta furta komai yayi mata rigagi ta hanyar fad'ar sunan *Adnan.* "Kayi hak'uri ni kawai ba yanda na iya ne, duk da cewar na damu sosai da yanayin ta dalilin kenan amma na gode sosai da yanda ka kula da ita." "Ba sabo da kai nayi wannan ba nayi ne a matsayin ďan ta, to kaga sam ba buqatar ka gode min to kawai mu tafi muyi break past, idan mun k'arasa da akwai wani muhimmin gurin da zamu tafi, to ka tabbatar cewa duka takardun ka a shirye suke ni kawai na ji wani iri ne, amma kuma hakan sam baya nufin cewar ina fishi da kai to zaka iya yarda da ni, sannan kuma wani lokacin ina da sauran fishi, amma kuma bana jimawa nake sauka to sai kayi hak'uri da ni ka ji ko to yanzu zamu iya tafiya." *Adeel* yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi. *"Adnan* gaskiyar ita ce ni kamar kai nake wani lokaci ina da saurin fishi amma ina da saurin sauka, zaka iya tambayar Kaka a game da wannan to fa kai ma sai kayi hak'uri da ni." "Waw abin mamaki dukanmu ukun muna da yanayi ďaya kamar dai a fuska muna da kamanni sosai, idan a kazo ta b'angaran abinci kuma dukanmu abu ďaya muke so samosa da madara. sannan kuma yanayin halaiyar mu ďaya hakan yayi kyau sosai, tabbas mu ukun mun dace da kasancewa tare to yanzu ya kamata mu tafi Besty mu tafi." *"Adnan ka ce shi ma *Adyan* hakan yake kamar mu.?" Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, hakama su Umma da kuma haka suka fita zuwa gurin break past................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/6, 4:08 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 37* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 04/02/2022* *Time 12:21am* *Typing.............* Bayan sun ƙarasa break past Papa ya fita zuwa office *Adnan* kuma ya d'auki *Adeel* sun fita, kasancewar *Afnan* tana cikin yanayin hutu sabo da laulayin da take. Suna fita kai tsaye gidan Abbu suka nufa wato Governor, sam basu samu wata matsala ko damuwa ba kasancewar security na gidan, sunyi matuƙar sanin sa sosai wanda a tunanin su ma ahali d'aya ne, sun shiga gaishe su suka yi tare da basu girma sosai. Sun k'arasa ciki Ummi ta shiga yi musu sannu da zuwa. Bayan sun gaisa ta yi musu iso zuwa gurin Abbu sun same sa yana amsa waya, bayan ya qarasa suka gaisa *Adnan* ya gabatar da *Adeel* garesa Abbu ya amsa shi. *"Adnan* nayi magana da masoyi to ga wannan offer d'in sa ce ta fara aiki, wannan kuma mukullin gida gana mota laptop, waya, da kuma tap wannan kuma kud'in shan mai. Jabir yana waje zai kai ku gidan motar na can ku duba gidan da kyau, idan akwai wani abin buqata to kawai ka sanar da ni ka ji ko. Sannan kuma da akwai masu aiki wad'an da zasu kula da Mummyn sa." *Adnan* ya shiga yi masa godiya yayin da *Adeel* ya gagara fad'ar komai sai wasu zafafan hawaye da suke bin fuskar sa, Abbu ya shiga girgiza masa ka tare da furta masa a'a hakama *Adnan,* ya jinjina musu sannan yayi wa Abbu godiya sosai yayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* karka gode min kawai dai ka kira ni da Kaka ka ji ko." "Na gode sosai Kaka." "Karka damu *Adeel* kawai ka kula kuma idan kana buqatar wani abu to kawai ka sanar da ni ka ji ko." Ya jinjina masa ka tare da furta to sun d'an jima a nan tare da shi, sannan daga bisani suka yi masa sallama suka tafi a hanya *Adeel* ya anbaci sunan *Adnan* yana cewa. *"Adnan* gaskiya Kakan yana da kirki sosai kamar Papa, gaskiya kayi dace da kyakkyawan ahali irin yanda kuke san juna, abin yana da birgewa sosai ina yi muku fatan alkhairi sannan kuma ina godiya na gode sosai." *Adnan* yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi. *"Adeel* gaskiyar ita ce Abbu ba a salin Kaka na bane, shi d'in Kakan aboki ne ina nufin *Adyan* Abban Ammie ne, kayi hak'uri da ni ban sanar da kai a salin gaskiyar ba *Adeel* jiya da dare, nayi magana da Doctor kuma na sanar da shi komai a game da kai. To shi ne ya buqaci da Abbu ya baka duka wannan to ina fatan ba zaka yi fishi ba.?" Wani irin kallo yake yi masa mai cike da jin mamakin abin da yake fad'a. *"Adnan* banyi fishi ba amma zanso ka had'a ni da *Adyan* domin nayi masa godiya yanda ya kamata." *"Adeel* sai dai kawai ka gode masa a waya sabo da baya k'asar nan, shi yana k'asar England ne a can yake da zama tare dasu Appa, shi yasa ba zai yu ka iya ganin sa ba amma zaka iya magana da shi video call a waya ko laptop." "Eh zanyi hakan amma shi ma yayi aure kuwa.?" "Eh a rana d'aya a kayi auran mu kuma qanwata ce ya aura, zaka iya tina ranar da a kayi auran jikan Mr President *Adyan Ahmad Aliyu.?"* *"Adnan* kana nufin *Adyan* shi ne wannan yaron jikan Mr President kuma jikan Governor kaduna? Lallai shi ďin na musamman ne suna da k'arfin iko sosai, babban abin farin cikin shi ne suna da kirki sosai." Ya jinjina masa ka yana murmushi mai had'e da dariya da kuma haka suka isa gidan. Sun fito Jabir da ma aikatan gidan sun shiga nuna musu ko ina na gidan, a zahirin gaskiya gidan yayi matuqar yi musu kyau sosai sannan kuma ga shi babban gida. Bayan sun qarasa zaga gidan su Jabir suka tafi bayan tafiyar su ne suka nufi gurin mota, wata kyakkyawar mota ce k'iran Toyota tayi matuqar yin kyau sosai, hakama an sanya komai a gidan har ma da kayan sawa na dukansu, bayan wani lokaci suka nufi gida inda suka shiga sanar dasu Mamie abin da yake faruwa. Umma tayi matuqar farin ciki sosai da hakan Mamie ta shiga yi musu fatan alkhairi, sun amsa suna godiya bayan Papa ya dawo da dare *Adnan* yake sanar da shi, yayi farin ciki sosai tare dayi musu fatan alkhairi sun amsa suna yi masa godiya. *Adeel* ya kira layin *Adyan* yayi masa godiya sosai ya kuma ba Umma ita ma tayi masa godiya, murmushi kawai yayi wanda ya hana masa fad'ar komai sai dai ya furta musu ba komai. Washe gari su Papa suka tafi suka duba gidan sun kuma yaba gidan sosai, hakan ya k'ara saka *Adeel* farin ciki sosai bayan kwana biyu suka tare a saban gidan su. Wata safiyar jumu'a tafiya yake kad'an ya k'arasa office wayar sa ta d'auki ruri, ganin sunan *Adyan* ne yasa shi d'aga kiran kafin ya furta komai ya masa rigagi. "Aboki shin kayi magana da *Adeel* kuwa? Na jima sosai ina kiran layin sa amma baya d'aga wa, na kuma kira campany an fad'a min cewar bai shiga office ba. Aboki gaskiya na damu sosai a kansa sabo da ban san abin da yake faruwa da shi ba, Aboki shin ko zaka iya tafiya gida domin ka duba yanayin sa dan Allah.?" "Eh Aboki to kawai ka kwantar da hankalin ka sabo da yana lafiya jiya har dare muna tare, amma Mum bata cikin kyakkyawan yanayi to ina tsoro in ba jikin ta bane yayi zafi sosai, amma yanzu zan tafi gidan domin ganin abin da yake faruwa zamu yi magana ka ji ko." Ya amsa da to da kuma haka suka yi sallama *Adnan* ya juya ya nufi gidan su Umma, domin ganin abin da yake faruwa ya isa gidan tare da shiga ciki, kai tsaye d'akin Umma ya nufa ya shiga ciki tare da sallama, cike da firgici ya k'arasa inda suke yana fad'ar sunan *Adeel. "Adeel* mai yake faruwa da ita ne haka mai yasa ba zaka kai ta asibiti ba? Ta ji wa kanta rauni tana buqatar kulawar likita sosai to kawai mu tafi asibiti yanzu." Yana k'oqarin tashin ta Umma ta dakatar da shi ta hanyar girgiza masa ka tana cewa. "A'a *Adnan* kawai ka barta a nan tin daran jiya muka tafi asibiti da ita, amma ba abin da a kayi mata yau da safe muka dawo gida." "Umma wane likita ne ya aikata muku haka ya kamata muyi k'aran sa? Shi sam bai san aikin sa ba ya ma kasa duba ta, wannan yana buqatar hukunci sosai Umma mu zamu canja wani asibitin ne, to dan Allah karku dakatar da ni please to zamu iya tafiya da ita yanzu." *"Adnan* duk ma inda zamu tafi to hakan ba zai canja gaskiyar ba, kawai zasu fad'a mana cewar mu siya mata magani ko kuma mu kai ta England, to bamu da wani zab'i shi yasa ka shigo ka same ta a haka, *Adnan* wannan yanayin nata yana matuqar cutar da ni sosai. Amma kuma ba yanda na iya dole nake hak'ura na gode sosai da kulawar ka." *"Adeel* ni abokinka ne to zanyi komai a kan ahalinka, ita Mum tamkar Mamie na take to zanyi komai domin ta kuma bana, buqatar wata godiya daga gareka ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to lokaci d'aya suka yi hugging juna yayin da, *Adnan* yake ta aikin rarrashin *Adeel* wanda shi ma kwalla yake zubarwa. *England.* Kwance take amma kuma ba barci take ba *Adyan* ya shigo, ya isa inda take ya kwanta tare da janyo ta jikin sa yayi mata wata kyakkyawar runguma sosai, ya qara da sunbatarta fuska zuwa wuya ta fita jikin sa tana k'oqarin tashi ya dakatar da ita. *"Adlishart* wai mai kike yi ne haka mai yasa kike hukunta ni haka? *Adlishart* gaskiya ni ba zan iya d'aukar wannan ba, Masoyiya dan Allah ki dena a zabtar da ni haka ciwan yana da zafi sosai da kuma k'una. Rabin raina dan Allah ki dena cutar da ni haka sabo da ina buqatar buqatar ki sosai." Magana yake cikin wata lallausar murya mai dad'in sauraro yanayin sa kuma kamar zai saki kuka, ita kuwa sai wani kallonsa take kallo sosai cike da shagwa'ba take magana. "Masoyi idan kana san duka wannan ya gushe to kawai ka cika alkawarin ka, ina nufin kawai ka had'a ni da Secret super star sannan kuma ka dena kira na da *Adlishart* sabo da sunan namuji ne." "Shikenan zanyi hakan zan shirya had'a ki da secret super star, amma kuma ba zan dena kiran ki da *Adlishart* ba sabo da wannan sunana ne na baki. Sunan mu biyun ne na had'a ya ba da hakan na had'a wannan sunan tin baki wuci shekaru biyu ba, masoyiya ni ina matuqar jin dad'in na kira ki da sunan sosai, nima zanyi matuqar farin ciki idan kika kira ni da sunan, *Adlishart* fad'a min shin zaki ci gaba da kira na da hakan.?" Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, cike da jin mamakin sa sosai take magana. "Masoyi kenan hakan yana nufin cewar kai ne wannan d'an wasan da yake wasan tsere.?" Ya jinjina mata ka tare da furta eh taci gaba da magana. "Masoyi amma su Appa sun san da hakan kuwa.?" Ya girgiza mata ka tare da furta a'a ta nisa tare da jan numfashi sannan taci gaba da magana. "Masoyi hakan bai dace ba sabo da zai iya cutar da kai sosai da kuma lafiyar ka, na tabbata wannan ne dalilin da yasa ka b'oye wasu Ammie gaskiyar. Masoyi k'ila dai yanzu lokaci yayi wanda zaka sanar dasu duka gaskiyar, sannan sai ka dena wasan gaba d'aya idan kaso kuma zaka iya sanar da masoyan ka, waye a salin *Adlishart* na tabbata zasu yi matuqar farin ciki sosai da hakan, musamman idan suka san cewa *Dr Adyan* shi ne jarumin su kuma masoyin su, to farin cikin su zai k'aru sosai to kawai kayi hakan dan Allah." Wani irin kallo yake yi mata mai tare da so cike da qaunar ta yayi hugging d'in ta, sai sunbatarta yake yana furta mata lafuzza masu tsananin dad'i sosai, yayin da yake jin tana dad'a shiga ransa cikin kyakkyawan yanayi yake magana. *"Adlishart* ke kina da kirki sosai na gode da tunasarwa kuma zanyi duk abin da kika fad'a, sannan kuma daga k'arshe zan had'a ki da secret super star nayi alkawari insha Allah." Murmushin ta ya k'aru sosai tare da k'ara shigewa jikin sa, shi kuwa yayi mata wata kyakkyawar runguma sosai yana sunbatarta. Hakan kuwa ta kasance ya sanar dasu Appa gaskiyar cewa shi ne *Adlishart,* sannan kuma ya nai mi afuwar su tare dayi musu alkawarin ya dena. Sun amsa shi da ba komai tare da sanya masa albarka, yayi farin ciki sosai da ganin basu yi fishi da shi ba, bayan mako d'aya wani dare kwance suke rungume da juna ya anbaci sunan ta. *"Adlishart* gobe ne secret super star yake taron bai yana kansa ga d'inbin masoyin sa, to ina ga dukanmu zamu kasance a gurin har dasu Ammie, sabo da dukanmu masoyan sa ne kuma masu yi masa fatan alkhairi. To ya kamata dukanmu muyi shiri na musamman domin had'uwa da shi." "Gaskiya ina farin ciki sosai domin burina na had'uwa da super star ya cika, na jima ina mafarkin had'uwa da shi na gode sosai *Adlishart."* Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarta sosai, shi kuwa sai wani kallo yake yi mata mai kama da harara ta shiga tambayar. "Masoyi mai ya saka kake harara na shin ni na aikata wani zunubi ne.?" *"Adlishart* ni ďin nan sai na ciro harshen ki na cinye, ta yanda zan dakatar dake daga zancan wasu maza, kamar irin secret super star sabo da ina kishi sosai, *Adlishart* gaskiyar ita ce ina sanki sosai ina matuqar masifar qaunarki sosai. Shi yasa nake matuqar kishin ki so zo nan." Ta k'ara matsawa kusa da shi tana dariya shi kuwa murmushi yake ya k'ara saka ta jikin sa, yana sunbatarta ita kuwa sai dariya take sosai cike da nishad'i, sun samu farin ciki na wani lokaci sannan daga bisani suka yi barci.................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/7, 12:45 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 38* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 05/02/2022* *Time 08:02pm* *Typing................* Yau garin London cike yake da mutane masu tarin yawa, wad'anda suke daga ko ina na duniya domin ganin fuskar, wannan b'oyayyen mutumen wanda ya tara tarin masoya masu yawan gaske, wato Secret Super Star mutumin da kowa yake fatan ganin fuskar sa. Bayan ta k'arasa shirin ta tsab ta mai da kallonta ga *Adyan* wanda yake ta sharan barci, ta tashi ta nufi gado ta zauna daga gefe tare da fad'ar sunan sa, amma sam bai yi yunk'urin tashi ba ta shiga buga pillow da yake kwance, idanuwansa na rufe yake magana. *"Adlishart* shin kina buqatar wani abu daga gareni? Shikenan zaki samu duk abin da kike so zo nan." Ya shiga laluba ta jin bai jiyo ta bane yasa shi bud'e idanuwansa, ya hangeta zaune gefen gado ya matsa kusa da ita tare da janyo ta, yayi hugging d'in ta tare da sunbatarta yana k'oqarin janye towel d'in da yake jikin ta, tayi saurin dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa tare da girgiza masa ka. "A'a ka tashi ka shiga wanka lokaci ya tafi sosai zamu iya makara to ya kamata ka shirya yanzu." "Ke d'an dakata mai yasa yau baki jira ni ba kika yi wanka ba tare da ni ba? Gaskiya dole zaki canja wannan wankan sabo da ina da kwad'ayin nayi wanka dake, ko kuma dai mu fasa tafiyar gaba d'aya naga iya wannan rawar k'afar naki." Lokaci d'aya ta wani b'ata fuska tana wani turo baki, shi kuwa sai wani kallonta yake yana murmushi mai tare da dariya, ta k'ara b'ata fuska kamar zata saki kuka ya kamata fuskar ta yana cewa. "Karki yarda ki min kuka sabo da kin san mai zai faru kawai zan janye wannan towel d'in, sannan kuma ka kin fini sanin abin da zai faru damu, to yanzu zaki iya fara kukan ni kuma zan rarrashe ki yanda ya kamata nayi alkawari." Lokaci ďaya ta gyara fuskarta har da wani lallausan murmushi sannan ta amsa shi. "Masoyi nifa ba kuka zanyi ba to yanzu zamu iya tafiya, domin na saban ta wanka na zamu yi wanka a tare kamar dai kullum." "Masoyiya wannan duk sabo da buqatar had'uwa da secret super star ne.?" "A'a sabo da kayi farin ciki ne ka yarda da ni sabo da gaskiyar nake fad'a." "Shikenan zamu iya tafiya yanzu." Ya tashi tare da tashin ta sun nufi band'aki ba jimawa suka fito suka fara shirin tafiya. Sun shirya cikin wata kyakkyawar shiga sunyi matuqar yin kyau sosai, sun fito babban parlour wanda fitowar su tayi daidai data su Appa, sun tari juna da murmushi sun isa ga juna sun fara runguma juna sannan suka zauna. sun gaisa gaba d'aya sannan suka nufi tebur suka yi break past, bayan sun gaisa sun tashi sun nufi babban studio domin had'uwa da secret super star. Sun isa gurin wanda gurin a cike yake da jama'a sosai zaune suke wayar sa ta d'auki ruri, ya tashi ya fita domin amsa waya bayan wani tsayin lokacin da suka d'auka suna jiran isowar sa, ya k'araso tafiya yake sannu a hankali kamar wani sarki, doguwar rigar da take jikin sa ita ta hana kowa ganin fuskar sa kasancewar tana ta hula. Ya isa kyakkyawan gurin da a ka tanadar masa ya zauna, yayin da idanuwan kowa suke kansa nan kuwa 'yan jarida suka fara aikin su, ko wannan su sai jefa masa tambaya yake ya dakatar dasu yana cewa. "Kuyi tambayar ku cikin natsuwa ďaya bayan d'aya ni zan amsa ku kun ji ko." Sun amsa shi da to nan kuwa suka fara, "ranka shidad'e shin ko zaka iya sanar damu dalilin da yasa kake kiran kanka da secret super star.?" "Abin shi ne kawai bana san kowa ya san waye ni." "Amma mai yasa baka san a san waye kai bayan kuma kana da tarin masoya sosai? Ko dai kana jin tsoron wani daban ko akwai wanda kake ganin zai iya cutar da kai.?" "A'a bana tsoro sannan kuma ba wanda zai iya cutar da ni, kawai dai wannan ra'ayina kenan bana san kowa ya san waye ni." "Sir wasu na fad'ar cewa wai kai ba kyakkyawa bane shi yasa kake b'oye fuskar ka ga kowa shin hakan gaskiya ne.?" Lokaci d'aya ya saki dariya kuma dariya yake sosai sai daga bisani ya amsa ta. "Ni ba zan amsa wannan ba nafi da san ku tabbatar wa idanuwan ku gaskiyar." "To ka fad'a mana cewar baka san kowa ya san waye kai, to amma mai ya canja ra'ayin ka yanzu har ka buqaci bai yana kanka ga masoyan ka.?" "Matata ita ce wacce ta canja min ra'ayi, a kullum kuma a ko yaushe zancan ta ďaya na ganin secret super star, tana matuqar sansa sosai ko yaushe cikin sauraran wakokin sa take. Ta damu sosai na rashin sanin waye shi wani lokaci har tana fishi da ni wai na kasa had'a ta da shi, to na damu sosai da yanayin ta wanda wannan dalilin ne yasa na shirya bai yana fuska ta ga masoyana." "Sir kenan hakan yana nufin cewar ko matar ka bata san cewar kai ne secret super star ba.?" "Eh bama iya ita kawai ba A'a har da iyaye na." "Gaskiya Madam tayi matuqar sa'ar samun ka ina ta ya ta murna." "A zahirin gaskiya ni ne wanda yayi matuqar sa'a sosai dana same ta, domin da bata amince da aure na ba to tabbas da ban rayu ba. Sabo da ni na rayu ne da soyayyar ta shi yasa zan iya kiran ta da rayuwata." "Sir kana san Madam sosai haka ne.?" "Eh fiye ma da yanda kike tunani." "To ko zaka iya bai yana mana ita domin muyi magana da ita? Sannan kuma muga wace macace wacce da matuqar sa'a sosai har haka shin zaka bai yana mana ita.?" Yayi 'yar dariya tare da furta a'a, "mai yasa ba zaka bai yana ta a garemu ba.?" "Sabo da ita ďin sirrina ce ba kuma wanda zan bawa damar had'uwa da ita, musamman mazajen da suke a nan sabo da ina da matuqar zafin kishi sosai." "To kace ita ma ta zama secret." Ya fad'a yana dariya shi ma abin da yake yi kenan tare da jinjina masa ka a lamar eh. "Sir to ina ga lokaci yayi wanda zaka bai yana fuskar ka ga duk wani masoyi naka daya zo nan domin had'uwa da kai." Ya amsa da to tare da mi e wa tsaye ya cire rigar da take jikin sa wadda ta hana a ga fuskar sa, amma still fuskar sa tana sanye da fice max irin shigar dake jikin sa, lokaci d'aya gurin ya rika amsa sunan *Adlishart* ya jinjina ka a lamar eh, cikin rawar murya 'yan jarida sunci gaba da jefa masa tambaya bayan daya zauna. "Sir lokuta da dama munyi ma tambaya ko *Adlishart* da secret super star mutun d'aya ne, amma ka sanar damu cewar ko wannan su daban ne, amma kuma yanzu ka fito a matsayin *Adlishart* mai yasa.?" "Eh kamar dai yanda na fad'a a baya kawai bana san a san a salin waye ni." "Sir gaskiya kana da wayo da yawa to yanzu mun shirya wa ganin a salin fuskar ka, shin to ko zaka iya yaye wannan mayafin fuskar domin cika alkawarin ka ga masoyan ka.?" "Eh na riga dana shirya wa hakan." Nan kuwa ya cire mayafin fuskar sa yayin da idanuwan kowa suke kansa, cike da mamakin ganin sa suke anbatar sunan sa. *"Dr Adyan* kai ne.?" "Eh wannan mutumen secret super star da kuma *Adlishart* ba kowa bane face *Dr Adyan Ahmad.* Na san cewa da yawan ku a nan zaku ji mamaki sosai musamman Appa Ammie da kuma *Adlishart,* kasancewar ban tab'a nuna kai na ga kowa ba sai yau na gode sosai masoyana, secret super star da kuma *Adlishart* dukansu biyun suna tare daku nima ina matuqar masifar qaunar ku sosai. Ni naku ne kuma ina alfahari da hakan sosai na gode Allah ya bar qauna Amin." Nan kuwa masoya suka shiga yi masa fatan alkhairi wani d'an jarida ya shiga tambayar sa. "Sir mai yasa kake kiran kanka da sunan *Adlishart.?"* Murmushin sa ya k'aru sosai ya nisa tare da jan numfashi sannan ya amsa shi. "Wannan sunan yana da matuqar muhimmanci sosai a gareni, sabo da sunana ne dana matata na had'a guri d'aya *Adyan da Alishart* sai ya ba da *Adlishart."* "Sir muna maka fatan alkhairi tare da duka masoyan ka." "Na gode sosai." Da haka kuma tattaunawar su tazo k'arshe wasu daga cikin masoyan sa sun shiga ba shi kyauta, sai photo na suke tare dayi masa fatan alkhairi shi kuwa sai godiya yake musu. Su Appa suna daga gefe suna kallonsa yayin da farin ciki yake ta shigarsu sosai, *Alishart* kuwa sai wata soyayyar sa take ji tana qara shigarta sosai, sun jima sosai a nan gurin sannan daga bisani suka nufi gida. Bayan sun dawo ya anbaci sunan *Alishart* yana cewa. *"Adlishart* fad'a min wani abu yanzu kina farin ciki da kika had'u da secret super star.?" "Masoyi ni ba zan iya sanar da kai irin girman farin cikin da nake cikin sa ba, sai dai kawai nace da kai ina farin ciki gaskiya nayi sa'ar samun ka, a matsayin mujina kuma abokin rayuwata ina qaunarka sosai masoyi." Magana take cikin kyakkyawan yanayi lokaci d'aya ya samu kansa da yin hugging d'in ta tare da sunbatarta, su Ammie sai kallonsu suke suna murmushi bayan wani lokaci ta tashi domin shiga ciki, tana cikin tafiya lokaci d'aya ta ji kanta ya sara da k'arfi, da sauri ta dafe kai tare da furta wash lokaci d'aya dukansu suka furta mata kalmar qlau kike. Ta jinjina musu ka tana furta eh ina lafiya taci gaba da tafiya nan kuwa ta fara ganin jiri, bata ankara ba ta kife a k'asa ta suma da sauri dukansu suka isa gareta suna fad'ar sunan ta, amma bata amsa ba Appa yace su tafi asibiti da sauri *Adyan* ya amsa shi da a'a. Cike da jin mamakin abin daya fad'a Ammie take magana. *"Adyan* mai ya saka baka san mu tafi asibiti duk da cewar bata da lafiya.?" Yayi shiru na wani lokaci sannan ya amsa da ba komai, *"Adyan* shin kai kana b'oye mana wani abu ne.?" Shiru bai yi magana ba. *"Adyan* ka amsa ni shin da akwai abin da kake b'oye wa wanda baka san mu sani gaskiyar zaka fad'a.?" Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan fad'e sa ba. "Kuyi hak'uri dan Allah ku yafemin sannan kuma karku yi fishi da ni please ku yafemin." *"Adyan* wai mai yake faruwa da ita ne kawai ka sanar damu? Sannan kuma mai ya saka kake bamu hak'uri kawai ka sanar damu abin da yake faruwa dan Allah.?" "Appa ita d'in tana tare da juna biyu ne." "Mine *Adyan* shin wai ka ji abin daka fad'a kuwa? Ta ya hakan zata kasance sam bai kamata a ce kai ka kusanceta ba, balantana har ta iya samun juna biyu *Adyan* har yanzu ita yarinya ce, shekarun ta sha biyar ne kawai to sam bai kamata hakan ta faru da ita ba. Idan ta samu lafiya to fa dole zamu bar nan zamu koma gida a can ne zata aihu, ta hakan ne kawai zan iya kare ka a matsayi na na uba, sannan kuma ina fatan kar wani mummunan abu ya faru da ita." "Na gode Appa na gode Ammie na gode ma dukanku." *"Adyan* kai d'an mu ne to zamu iya yin komai domin mu kare ka to ba buqatar ka gode mana ka ji ko." Kallonsu kawai yake ba tare daya furta musu komai ba, lokaci d'aya dukansu suka yi hugging d'in sa tare da sunbatarsa ba jimawa suka sake sa, sun mai da kallonsu ga *Alishart* Appa ya d'auke ta sun shiga ciki domin ya duba ta, kasancewar suna da kayan aiki a gida ya duba ta tare dayi mata Scan domin ganin lafiyar Babyn. Abin farin cikin shi ne Babyn yana cikin k'oshin lafiya sosai, bayan wani lokaci ta farka daga suman da tayi haka dai su Ammie suka ci gaba da kulawa da ita sosai, kuma Alhamdulallah tana samun sauki sosai wani dare. *Adnan* ya kira layin sa ya d'aga bayan sun gaisa yaci gaba da magana. "Aboki da akwai abin daya kamata muyi magana a kai." "Aboki kawai ka fad'i koma miye ina sauraran ka." Ya amsa shi da to nan kuwa ya shiga sanar da shi komai a game da Mummyn *Adeel.* "Aboki mai yasa sai yanzu kake sanar da ni? Shikenan zan kula da wannan yanzu zanyi magana da Kaka na Abuja zan koma kiran ka." Ya amsa shi da to sunyi sallama bayan wani lokaci ya koma kiran layin *Adnan,* ba jimawa ya d'aga nan kuwa ya shiga sanar da shi cewar yayi magana da Abba. "Aboki nayi magana da Abba za a shirya wa dukanku visa zaku shigo nan da kwanaki biyar insha Allah. To ya kamata ku fara shirin tafiya amma kana farin ciki kuwa.?" "Aboki kana da kirki sosai Allah ya saka da alkhairi Amin zan sanar da *Adeel* wannan." "Aboki karka gade min kawai kayi farin ciki sabo da zamu samu damar kasancewa tare, wannan shi ne abin da yake da matuqar farin ciki sosai." Sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama. Haka su Appa suka shiga tarban zuwan su *Afnan Adnan* ya sanar dasu Papa, sam basu yi yunk'urin dakatar da shi ba yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare da, *Adeel* ya kira layin *Adyan* yayi masa godiya ya amsa shi da ba komai. Haka suka ci gaba da shirin tafiya bayan kwana biyar jirginsu ya tashi zuwa k'asar England........ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/8, 4:05 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 39* *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Sunday 06/02/2021* *Time 10:35pm* *Typing................* Suna fitowa Airport suka samu *Adyan da Alishart* suna jiran fitowar su, cike da d'auki *Alishart* ta isa gurin Yayan ta tare da fad'a wa jikin shi, shi kuwa ya runguma ta tare da sunbatar ta bayan sun sake juna, ta koma ta gurin *Afnan* sun rungumi juna. Bayan sun sake juna sun k'arasa gurin *Adyan* wanda yake ta aikin furta musu sannu da zuwa, cike da d'auki suka yi hugging juna bayan sun sake juna ya sauke ta ga *Adeel,* yayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan sai ya amsa yana murmushi. *Adyan* ya ba shi hannu suka gaisa, ya mai da kallonshi ga su Umma, yaci gaba da yi musu sannu da zuwa tare da furta musu su tafi, sun nufi mota suna cikin tafiya *Adnan* ya dafa shi tare da fad'ar sunan shi. "Abokina amma qlau kake kuwa gaskiyar zaka fad'a.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh yana murmushi shi ma ya mayar masa da murmushi, sun nufi mota sun fara saka kaya both sannan suka tafi, sun isa gida su Appa sun shiga yi musu sannu da zuwa sun amsa suna murmushi. Bayan sun zauna sun gaisa Ammie tayi musu ta yin abinci sun tashi sun nufi tebur, dukansu suna cin abinci amma banda *Adyan* sai wasa kawai yake da cokali, Ammie ta anbaci sunan ta tare da tambayar sa. "Rabin raina qlau kake kuwa.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh taci gaba da magana. "Rabin raina to mai ya saka baka cin abinci.?" Ya amsa ta da ba komai tare da tashi ya nufi wani gurin daban, Appa na k'oqarin binsa *Adnan* ya dakatar da shi ya tashi ya bisa a baya. Ya same sa tsaye gurin flowers yayi shiru ga a lama tunani yake, *Adnan* ya k'arasa inda yake sai wani kallonsa yake kallo sosai yana wani girgiza ka, ya dafasa tare da fad'ar sunan sa kallonsa kawai yake ba tare daya amsa ba *Adnan* yaci gaba da magana. "Aboki kallo d'aya nayi ma na fahimci cewar ba qlau kake ba, amma kace da ni a'a Aboki naro e ka dan girman Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake damunka please.?" Yayi shiru sai kallonsa yake kallo sosai yana girgiza ka, ya nisa sosai tare da jan numfashi cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Ka yafemin Aboki sannan kuma karka yi fishi da ni dan Allah." "Aboki wai mai kake fad'a ne haka ni baka yi min komai ba to mai yasa kake bani hak'uri.?" "Aboki dama a game da *Adlishart* ne." Da sauri cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. "Aboki shin wani abu ya faru da qanwata ne.?" "Aboki abin shi ne ita." Ya kuma yi shiru yana girgiza ka tare da furta a'a, *Adnan* kuwa sai wani kallonsa yake cike da firgici da rud'ani yake magana. "Aboki naro e ka dan Allah da girman Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da qanwata please.?" "Aboki ni na aikata babban zunubi wanda har ina jin kamar ba zan iya yafe wa kai na ba, sam bai kamata a ce ni na aikata hakan ba amma kuma na kasa jurewa, ko yaushe ji nake ina k'osawa sannan kuma ni na kasa dakatar da kai na, Aboki ni banda wani zab'i ne to ina fatan zaka fahimce ni sannan kuma zaka yafemin dan Allah." "Aboki har yanzu baka sanar da ni abin da yake faruwa ba, to kawai ka sanar da ni koma miye dan Allah ka ji please.?" "Aboki *Adlishart* tana tare da juna biyu na wata biyu." Cike da firgici da rud'anin abin daya fad'a yake magana. "Miye Aboki wai gaskiyar kake fad'a kuwa.?" "Eh Aboki tin a satin da muka yi aure hakan ta faru dan Allah ka yafemin please." "Aboki kai baka aikata wani kuskure ba to ba zan kira wannan da zunubi ba, Aboki ni kawai na damu ne a kan qanwata sabo da har yanzu ita yarinya ce, sannan kuma tana da k'ananun shekaru a wad'an nan shekarun nata, tayi k'ank'anta da a ce ta aihu shekarun ta sha biyar ne kawai, to ya idan kuma wani abu ya faru da ita fa.?" "A'a Aboki sam ba abin da zai faru da ita dukanmu zamu kula da ita sosai, zamu yi komai sabo data kasance lafiya to zaka iya yarda da ni dama iyayena." Ya jinjina masa ka a lamar to *Adyan* yaci gaba da magana. "Aboki amma zaka jima sosai kana fishi da ni.?" Ya girgiza ka yana murmushi sannan daga bisani ya amsa shi. "A'a Aboki ni sam bana fishi da kai kuma ba zan tab'a yin fishi da kai ba na har abada wannan alkawari ne." "Wai da gaske kai baka fishi da ni.?" Ya jinjina masa ka yana murmushi lokaci ďaya shi ma ya saki murmushi, cike da d'auki sunyi hugging juna ba jimawa suka sake juna. "Aboki amma qanwata ta san cewar tana tare da juna biyu kuwa.?" Ya girgiza ka tare da furta a'a, "Aboki ya kamata ka sanar da ita domin akwai buqatar ta sani ka ji ko." Ya jinjina masa ka tare da furta to bayan wani lokaci suka koma babban parlour, sun samu su Appa sun k'arasa cin abinci har sun kai su Mum masauki, *Adeel* ne kawai a parlour sun k'arasa gurin sa sun zauna shi kuwa sai wani kallonsu yake yana murmushi. "Sannun ku da dawowa fatan kuna cikin k'oshin lafiya sosai.?" "Eh muna lafiya kayi hak'uri da muka tafi muka barka a nan to ina su Umma.?" "Ba komai sannan kuma su Mum an kai su masauki Umma na tare da Mum, *Alishart* kuma tana tare da Maman baby to zaka iya duba dukansu." Sun jinjina masa ka sun tashi sun koma ga tebur sunci abinci, bayan sun qarasa *Adnan* ya nufi gurin matar sa ba jimawa *Alishart* ta fito, ganin ta fito ne yasa *Adeel* tashi ya nufi gurin su Umma *Adyan* na dakatar da shi amma ya fice abinsa, bayan tafiyar sa suma tashi suka yi suka nufi d'akin su. *"Adlishart* da akwai abin daya kamata na sanar dake yanzu." "Ina jin ka masoyi zaka iya sanar da ni koma miye." Yayi shiru kad'an sannan yaci gaba da magana, *"Adlishart* dama a game da yaron da zamu aifa ne nake san muyi magana." Lokaci d'aya ta saki dariya kuma a haka take magana. *"Adlishart* to mai yasa zamu yi magana a kan abin da bamu san lokacin zuwan sa ba? Karfa ka manta cewa nan da wata biyu zan koma gida na fara zuwa makaranta. Sannan kuma zan aihu ne kawai bayan na kammala karatu na, kamar dai yanda kai kayi min alkawari to kama dena yi min zancan yaro yanzu ka ji ko dan Allah." Shiru bai yi magana ba sai wani kallonta yake kallo sosai, ya nisa da k'arfi tare da jan numfashi sannan ya fara magana. "Kiyi hak'uri dan Allah ki yafemin sabo da ni na kasa cika maki alkawarin dana yi, Masoyiya abin shi ne ke kina tare da juna biyu na tsayin wata biyu amma." "A'a hakan sam ba gaskiya bane sabo da kai kayi min alkawari to kawai ka fad'a min cewar wasa ne ka ji ko dan Allah." "Ki yafe min Masoyiya sabida ba zan iya canja gaskiyar ba kina tare da juna biyu amma." "A'a hakan ba zai yu ba kai kmin k'arya ba zan k'ara yarda da kai ba." Magana take tana kuka yayin da take ta aikin dukan cikin ta, yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta yana furta mata, "ya isa haka ki dena zaki iya cutar da yaron kuma hakan sam bai dace ba sannan." "Kawai ni ka rabu da ni sabo da bana san nayi magana da kai." "Haba masoyiya dan Allah karki cutar da ni sosai haka sabo da." *"Adlishart* nace a'a to kawai ka rabu da ni dan Allah." Tana kai k'arshen maganar ta ta tashi tayi tafiyarta, ya tashi da sauri ya bita yana fad'ar sunan ta amma bata amsa shi ba, ta nufi k'ofar su *Afnan* ta shiga buga musu k'ofa tare da fad'ar sunan Yayan ta, ba jimawa ya bud'e k'ofar ya shiga anbatar sunan ta dama na *Adyan.* Kafin ya furta komai sai gasu Ammie sun fito nan kuwa suka shiga tambayar su abin da yake faruwa. "Ammie to ita tana fishi da ni ne sosai sabo da na sanar da ita gaskiyar cewa tana tare da juna biyu, sam ta mak'i saurara na har tana k'oqarin cutar da yaronmu, sai dukan cikin ta take sannan kuma ta dakatar da ni daga yi mata magana. Appa ni ban san ya zanyi ba domin nasa ta fahimta sabo da tana fishi da ni sosai." Kafin su Ammie su furta komai *Alishart* tayi musu rigagi ta hanyar amsa shi. "To mai yasa ba zaka fad'a musu duka gaskiyar ba? Ka fad'a musu cewar kai kayi min alkawarin cewa ba zan aihu ba har sai na kammala karatu na gaba d'aya. To amma mai kayi kai kama kasa cika min alkawarin da kayi min, dan haka ba zan k'ara yarda da kai ba sannan kuma ba zan k'ara yi maka magana ba." Tana kai k'arshen maganar ta ta juya ta nufi bedroom d'in su *Adnan Afnan* ta bita a baya tana rarrashin ta, Appa ya nufi inda yaronsa ya janyo hanun sa sun zauna ya shafi kansa tare da fad'ar sunan sa. "Rabin raina na san cewar hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai, amma dole zaka jure wannan har zuwa lokacin da ita zata dena fishi da kai, *Adyan* dole ka jurewa wannan sannan kuma kaci gaba da bata kulawa sosai, ta yanda ita da kuma Babyn zasu kasance cikin k'oshin lafiya sosai ka ji ko." "Appa nima abin da nake koqarin yi kenan amma kuma tak'i ta amince da ni, ta mak'i bani damar da zan iya kulawa da ita da kuma yaronmu, ni kawai ina san na san yanayin lafiyar Babyn sabo da yanda tayi ta dukan cikin ta, amma kuma ta kasa bani damar da zanyi hakan na kuma kasa yin komai bani da anfani." "A'a ďana ka dena fad'ar haka ita kawai tayi fishi amma komai zai yi daidai insha Allah, sannan kuma ni zan duba yanayin lafiyar Babyn ina fatan ya kasance lafiya." Ya jinjina mata ka a lamar to *Adnan* ya k'arasa gurin da suke ya sauke kallonsa ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. "Aboki karka yi k'unci sosai ni zan daidai ta komai insha Allah, yanzu kawai tayi fishi ne sosai amma komai zai yi daidai insha Allah, to zaka iya yarda da ni ka ji ko." "Na gode sosai Aboki kai kana da kirki sosai ina farin ciki sosai da samun ka, a matsayin Abokina sannan kuma ina alfahari da hakan sosai ina godiya sosai a kan komai." "Aboki kai na kana da kirki sosai sannan kuma ina farin ciki da samun ka sosai." Lokaci d'aya suka yi hugging juna suna murmushi hakama su Appa murmushi suke, dama *Adeel* wanda yake daga gefen k'ofa yana kallonsu, su Ammie sun tashi sun shiga ciki hakama *Adeel* juyawa yayi ya shige abinsa. Bayan wani lokaci suka tashi suka shiga gurin su *Alishart* suke, sun samu *Afnan* tana ta tausan ta tare da bata magana, nan kuwa *Adnan* shi ma yasa baki suka ci gaba da rarrashin ta sai wani lalla'bata suke tare da bata magana, wanda har sai da suka samu ta iya fahimtar su ta dena fishi da mai gidan ta. Bayan wani lokaci da komai ya daidai ta suka tashi suka koma d'akin su washe gari Ammie ce da kanta, ta duba lafiyar Babyn ta hanyar yi mata Scan Alhamdulallah Babyn yana cikin k'oshin lafiya sosai. Hakan yayi wa dukansu dad'i sosai bayan kwana biyu *Adyan* ya fara binkice a kan rashin lafiyar Mum, ya duba file ďin ta wanda duka record ďin rashin lafiyar ta yake ciki. Wani yammaci zaune suke a wani kyakkyawan guri, wanda an yi shi ne musamman sabo da hutawa *Adyan* ya kai kallonshi ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* da akwai abin daya kamata muyi magana a kai." "Shikenan zaka iya sanar da ni koma miye." *"Adeel* a game da Mummyn ka ne shin da gaske tana da rauni a k'arkashin zuciyar ta.?" "Eh shi yasa nima nake tare da wannan cutar." *Adyan* ya jinjina ka yaci gaba da magana, "amma da gaske kai kad'ai ne d'an ta.?" "Eh haka ne ni kad'ai ne d'an ta amma mai ya saka ka tambaya.?" "Ba komai kawai dai saboda naga yanda take magana a kan wasu yaran ne amma kawai ka manta, yanzu ka fad'a min wani abu wane irin abinci ko abin sha ita ďin tafi so?". *"Adyan* Kaka ta ita ta fad'a min cewar Mummy na tana matuqar son madara sosai, ko yaushe ita ce kawai abin da take sha tana santa sosai Dady na kuma samosa ce abin da yafi so, shi yana da saurin fishi amma kuma baya jimawa yake sauka. Ina son Dady na sosai duk da irin girman zunubin da ya aikata a gareni, da kuma Mummy na amma hakan sam bai hana ni sonshi ba sai dai kuma ina matuqar yin fishi da shi sosai." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da idanuwan shi suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai, zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. *Adyan* sai wani kallonsa yake kallo sosai yayin da tausayin shi yayi yawan gaske a tare da shi, ya shiga rarrashin shi yana ba shi magana, ya k'ara da yin hugging d'in shi.............. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/9, 4:59 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 40* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 07/02/2022* *Time 41:29pm* *Typing.............* Zaune yake ya ji zaman ba dad'i ya tashi sai safa da marwa yake, yayin da tunani iri daban-daban yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Dafasa ďin da a kai ne yasa shi kai kallonsa garesa lokaci d'aya yayi tozali da fuskar *Adnan.* "Aboki qlau kake kuwa fad'a min abin da yake faruwa da kai? K'ila ba zan rasa abin da zan taimake ba to yanzu fad'a min miye damuwar.?" Yayi shiru sai aikin kallonsa yake yana girgiza ka sun tafi sun zauna, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallon *Adnan* yake, sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi. "Aboki kana matuqar san samosa da madara sosai ko? Sannan kana da saurin fishi amma kuma kana da saurin sauka, haka ne ko a guri na dama *Adeel* sannan kuma dai muna da kamanni da juna sosai, hakama dukanmu ukun muna da rashin lafiya iri d'aya. Ra'ayin mu da kuma halaiyar mu ko manmu iri d'aya ne, Aboki ni sam na kasa fahimtar wannan mai yasa hakan take faruwa damu? A baya sam bana jin komai amma a yanzu ina ta damuwa a kai, na jima ina tambayar kai na a game da hakan amma kuma sam na gagara samun amsar. Aboki dukanmu ukun muna yin mafarki iri ďaya hakan yana da matuqar rikitarwa sosai." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya fad'ar sa ba, amma zan iya cewa yana tare da tarin damuwa sosai *Adnan* ya shiga girgiza masa ka tare da furta. "A'a Aboki dan Allah karka bari tunanin hakan ya cutar da kai, wannan ba komai bane kawai ikon Allah da kuma k'arfin girman abotar mu. *Adyan* kawai ka kai da hankalin ka ga samun lafiyar Mum ka ji ko yanzu mu shiga daga ciki." Kallonsa kawai yake na tsayin wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi da to, sun tashi sun nufi ciki bayan kwana biyu zaune suke Umma tana tare da Mum, yayin da *Adeel* yake ta aikin chatting da abar qaunarsa wato *Amna.* suna haka sai ga *Adnan* ya shigo ya fara gaisawa da Umma sannan ya isa gurin *Adeel,* ya zauna tare da ba shi hanu sun gaisa *Adeel* ya shiga tambayar *Adyan.* *"Adeel* karka fad'a min cewar Aboki bai zo nan ba? Sabo da ya jima da fitowa kuma ya sanar da ni cewar office zai zo, ga shi kuma kai kana fad'a min cewar bai zo nan ba hakan yana nufin bai shigo ya duba jikin Mum ba? Shikenan zan tafi na duba shi a office ďin sa zamu dawo tare insha Allah." *Adeel* ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, hakama Umma wacce take zaune gefen Mum *Adnan* ya tashi ya fita zuwa office ďin *Adyan.* Zaune yake amma ba aiki yake ba lokaci d'aya ya ji a na buga masa k'ofa, daga ciki ya amsa da shigo ciki ba jimawa sai ga Max ya shigo, ya k'arasa inda yake ya fara da gaishe sa sannan ya ba shi takardun dake hanun sa. Ya karb'a shi kuma ya juya ya fita bayan tafiyar sa shi kuwa ya shiga duba takardun domin ganin abin da yake ciki, lokaci d'aya ya ji k'irjin sa yana bugawa da k'arfi tare da zuciyar sa, kansa yana sarawa ya fara fita haiyacinsa sai wani irin gumi yake saukar masa. "A'a wannan k'arya ne hakan sam ba zata tab'a kasancewa ba, a'a wannan ba a salin result ďin bane to sam bai kamata na yarda da wannan ba." Ya tashi ya fita cikin sauri har kamar zai fad'i yana cikin tafiya Dr John ya rik'o hanun sa, tare da fad'ar sunan sa kallonsa kawai yake ba tare daya furta masa komai ba. *"Dr Adyan* mai yake faruwa da kai ne haka.?" "Dr John dan Allah ka barni karka k'aran wani k'uncin bayan wanda nake tare da shi." *"Dr Adyan* k'ila dai zan iya taimaka wa domin ka fita a cikin wannan mummunan yanayin, yanzu ka biyo ni mu tafi zan kai ka inda zaka manta da gaba d'aya wannan k'uncin to mu tafi." Yayi shiru kad'an sannan daga bisani ya amsa shi da to sun juya sun nufi mota. *Adnan* ya isa office d'in *Dr Adyan* tare da shiga ciki sai dai bai yi nasaran samun sa a ciki ba, ya fito cike da jin mamakin rashin ganin sa yana sama ya hangesa tare da Dr John suna k'oqarin shiga mota, kallo ďaya tak yayi masa ya fahimci cewar ba qlau yake ba, da sauri ya juya ya nufi gunsu har yana gudu yana fitowa suna fice wa. Da sauri ya fad'a taxy tare da fad'a wa mai taxy d'in ya bayan motar Dr John, haka suka ci gaba da tafiya har zuwa inda su Dr John suka sauka, cikin hanzari *Adnan* ya fito tare da bawa mai taxy kud'in sa ya juya ya shiga ciki. Wani irin guri ne wanda ya had'a tarin mutane maza da mata, wasun su sai rawa suke wasu kuma caca suke da dai ire-iren su, haka yayi ta dogon wuya yana zaran ido dan ganin inda zai gasu *Adyan.* Ya jima yana abu ďaya sannan daga bisani ya hangesu gurin wani tebur zaune, kamar a mafarki ya ga Dr John yana ba shi kofin da yake hanun sa, wanda kuma yana da tabbacin cewa giya ce a ciki da sauri ya k'arasa gurin yana fad'ar sunan sa. *"Dr Adyan* ya kamata ka sha wannan to duka k'uncin ka zai tafi." Ya jinjina masa ka a lamar to ya karb'i kofin tare da kai wa baki, ya fara sha da sauri ya a jiye kofin yana tari tare da furta, "a'a ba zan iya shan wannan ba ba dad'i sannan kuma yana da d'aci sosai." *"Dr Adyan* wannan ce kawai damar ka idan har kana buqatar ka rabu da wannan k'uncin, zaka iya yarda da ni to kawai ka sha ka ji ko please." Ya amsa da to yaci gaba da sha yana cikin sha sai ga *Adnan* da sauri ya fizge kofin da yake bakin sa, ya a jiye a gefe yana fad'ar sunan sa kallonsa kawai yayi ba tare daya amsa ba, *Adnan* ya mai da kallonsa ga Dr John cike da k'unci bak'in ciki tare da b'acin rai yake magana. "Kai waye da zaka aikata masa haka? Shin ka kuwa san girman zunubin daka aikata kuwa.?" Dr John yayi wani gajeran murmushi sannan ya amsa shi, "sunana Dr John kuma ni Abokin sa ne nazo da shi nan ne sabo da ya samu farin ciki sosai, amma waye kai da kake k'oqarin dakatar da ni shin kai ďin Yayan sa ne? Ko a'a kai ďin twin's brother d'in sa ne sabo da naga kuna da kamanni da juna sosai.?" "Wai da gaske kai Abokin sa ne? To amma kuma ni sam banga hakan ba, kai ba Aboki bane amma zan iya kiran ka da mak'iyi, to gargad'i daga yau karka yarda ka koma yin kuskuran cutar da shi sosai har haka, to ka tabbatar da ka kiyaye wannan sabo da zan iya aikata komai a kan Aboki na." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi *Adyan* sun fita Dr John ya bisu da kallo yana murmushi tare da girgiza ka, suna fitowa *Adnan* ya tare musu taxy sun shiga cikin wata 'yar murya yake magana. "Aboki karka kai ni gida dan Allah kawai ka sauke ni, a Beauty hotel ina da d'aki a can to kawai mu tafi can." Ya amsa shi da to tare da sanar da driver inda zai sauke su, ya amsa shi da to ya ja mota sun tafi sun isa hotel ďin cikin hanzari an kai su d'akin da yake. Sun shiga ciki *Adnan* ya tafi ya kwantar da shi sai wani kallonsa yake. "Haba Aboki mai kake yi ne haka ta ya ma zaka yi tunanin cutar da kanka har haka? Miye damuwar shin wannan Abokin naka yafi Appa Ammie ni ko kuma *Adeel?* Kai ka zab'i sanar da shi damuwar ka fiye damu mai yasa? To shin ko zaka iya sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai k'ila ina da abin da zan taimaka.?" Magana yake cike da damuwa sosai *Adyan* kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai. Lokaci d'aya kuma ya fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, ban ankara ba sai kuka kuma kuka yake sosai sai wani irin abu yake, wanda har yana k'oqarin cutar da kansa da k'yar *Adnan* ya samu ya iya dakatar da shi. *"Adyan* dan Allah ka dena cutar da kanka haka, sannan kuma ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai miye matsalar.?" "Aboki kawai ka barni na ji da wannan k'uncin da yake tare da ni, Aboki da a ce kai ka san a salin gaskiyar to da kai ma ka kasance a cikin irin wannan yanayin nawa. Aboki ciwon yana da matuqar girma sosai sannan kuma ba shi da magani, Aboki ni ina jin ina ma a ce mutuwa nayi ta yanda ba zan fuskanci irin wannan mummunan qalubalen ba, Aboki wannan matar muguwa ce sosai sannan kuma mak'aryaciya ce sosai, to ita d'in sam bata cancanci kulawar mu ba, shi yasa na yanke hukuncin cewa ba zan k'ara duba taba. Sabo na tsane ta matuqar tsana sosai sabo da." Lokaci ďaya kuma wani wawan barci yazo ya d'auke sa, *Adnan* kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai cike da jin mamakin abin daya fad'a. *"Adyan* zanso ka sanar da ni a salin gaskiyar abin da yake faruwa da kai, mai yasa kake fad'ar haka a kan Mum shin wani abu ya faru tsakanin sa da *Adeel* ne? Ya kamata nayi magana da *Adeel* yanzu ina fatan ya sanar da ni duka gaskiyar." Ya ciro wayar sa ya shiga kiran layin *Adeel* ba jimawa ya d'aga. *"Adnan* kuna ina nazo office ďin amma ban same ka ba? Na kira layin ka baya tafiya *Adyan* kuma baya d'aga kira na, ni na damu sosai a kanku biyun sabo da ban san abin da yake faruwa daku ba, yanzu fad'a min kuna ina sannan kuma qlau kuke.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, *"Adeel* muna lafiya amma zanso na tambiye ka wani abu.?" *"Adnan* kawai ka sanar da ni koma miye." *"Adeel* shin kayi magana da Aboki a kan Mum.?" Ya amsa shi da eh tare da sanar da shi komai, *Adnan* amma mai ya saka ka tambaya.?" "Ba komai kawai ina san na sani ne amma kayi hak'uri." "Ba komai *Adnan* na gode sosai da kulawa." Ya amsa shi da ba komai daga bisani suka yi sallama. Ya mai da kallonsa ga *Adyan* yayin da yake magana da zuciyarsa. "Aboki mai yake faruwa da kai ne haka mai ya saka ka tsani Mum haka? Ita bata da lafiya balantana na ce ko ta aikata masa wani abin, sannan kuma shi bai yi sa in sa da *Adeel* to mai yake faruwa ne ya kamata na sani to amma ta ya.?" Nan kuwa ya shiga tunani da nazari ya jima sosai a haka, ganin yanda kansa ya d'auki zafi sosai ga kuma damuwa tana k'oqarin yi masa yawa, yasa shi ciro maganin sa daga aljihu ya tafi ya d'auki ruwa ya sha magani, sannan ya nufi gado ya kwanta kusa da *Adyan* ba jimawa barci ya d'auke sa.... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/12, 1:32 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 41* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 09/02/2022* *Time 07:40pm* *Typing...............* Sun jima sosai suna barci sannan daga bisani suka tashi, *Adyan* ne wanda ya fara tashi motsinsa ne ya tashi *Adnan.* Lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar dukansu kallon juna suke, "Aboki ka tashi to ya yanayin naka fatan kana samun sauki.?" Kallonsa kawai yake ba kuma tare daya furta masa komai ba, lokaci d'aya kuma ya saki kuka cike da firgici *Adnan* ya tashi yana fad'ar sunan sa. "Aboki mai yake faruwa da kai ne haka? Naro e ka a kan ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai please.?" Ya shiga rarrashin sa yana yi masa magiya bayan wani lokaci ya fara magana. "Aboki ni banma san ta yanda zan iya sanar da kai a salin damuwar ba, Aboki ciwon yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai, to ni sam ba zanso kai ma ka fuskanci irin wannan mummunan yanayin da nake ciki ba. To shi yasa bana jin zan iya sanar da kai a salin gaskiyar kawai sai dai na baka hak'uri." "Aboki ni kawai zan yafe maka ne idan har ka sanar da ni gaskiyar, ko kuma dai nayi fishi da kai kuma fishi sosai, sannan kuma zan dena yima magana na tsayin wani lokaci sosai, to kawai ka sanar da ni gaskiyar dan Allah please.?" Yayi shiru kad'an yana nazari sannan ya amsa shi. "Aboki abin shi ne ni kai da kuma *Adeel* ba haka kawai muke san juna ba, ba kuma haka kawai muke da ra'ayi iri ďaya na, sannan kuma ba a banza muke da kamanni da juna sosai ba. Aboki komai yana faruwa ne tare da dalili sannan kuma ba abin da yake faruwa haka kawai, Aboki gaskiyar ita ce dukanmu ukun abu ďaya, dalilin da yasa muke matuqar qaunar junanmu kenan amma kuma." Yayi shiru tare da girgiza ka yayin da yake kuka kuma kuka sosai. "Aboki sam bai kamata hakan ya saka ka kuka ba, dukanmu ukun mun kasance abokai na gari ga junanmu, sannan kuma muna bawa junanmu kulawa sosai, hakan yasa muka kasance tamkar ahali ďaya to kawai kayi farin ciki, sannan kuma dan Allah da girman Allah kayi hak'uri ka sanar da abin da yasa ka tsani Mum? Shin kai kayi fad'a da *Adeel* ne ko a'a ita ďin ta aikata maka wani abin ne cikin rashin sani.?" "Aboki *Adeel* yana da kirki sosai amma kuma yana matuqar bani tausayi sosai, sabo da shi sam bai yi dace da iyaye na gari ba, a baya nayi tunanin cewa Dadyn sa ne kawai yake da butulci, amma yanzu na fahimci komai dukansu irin su ďaya sam basu da kirki, sannan kuma basu da godiyar Allah dukansu munafukai ne shi yasa na tsane su sosai." "Aboki naro e ka dan Allah da girman Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa please.?" "Aboki tin da ka matsa shikenan zan sanar da kai duka gaskiyar, Aboki abin shi ne dukanmu ukun ni kai da kuma *Adeel* ahali ďaya ne, ina nufin dukanmu ukun iyayenmu ďaya." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya ji ya fad'a yake magana. "Aboki wai mai kake fad'a ne haka shin wai kai ka fita haiyacinka ne? Am ina ganin cewar giyar daka kurb'a har yanzu bata gama sakin ka ba, to ya kamata ka kwanta ka huta na wani lokaci idan ka dawo haiyacinka zamu yi magana." "Aboki ni kawai gaskiyar nake fad'a wannan matar da take kwance asibiti, ita ce a salin mahaifiyar mu Aboki bayan da *Adeel* ya sanar da ni komai a game da iyayen sa, sai nayi dogon nazari da tunani a game damu biyun wanda wannan dalilin ne yasa, ni nayi mana gwajin halitta dukanmu ukun da kuma Mum, Aboki yau ne a ka kawon result bayan na duba sakamakon sai na ga duka iri d'aya ne. Wanda hakan ne yake tabbatar mana da cewar dukanmu 'yan uwan juna ne, sannan kuma *Maman Adeel* ita ce a salin mahaifiyar mu." Da sauri *Adnan* ya dakatar da shi cikin tsawa har yana ďaga murya. "Ya isa haka Aboki ka dena fad'ar wannan shirmen ya kamata ka dawo haiyacinka, ka dena fad'a min abin da zuciyata ba zata iya d'auka ba, ta ya ma zaka kalli cikin idanuwana sannan ka sanar da ni cewar *Maman Adeel* wai ita ce a salin mahaifiya ta. A'a hakan sam ba gaskiya bane Mamie da Papa sune a salin iyayena, to kama dena fad'ar wannan shirmen ka ji ko." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, amma zan iya cewa yana tare da tarin damuwa sosai yayin da k'unci yayi yawan gaske a tare da shi sosai. "Aboki ni kawai gaskiyar nake sanar da kai, wallahi naso a ce duka wannan k'arya ne ko kuma a ce mafarki nake, ta yanda zan rok'i Allah a kan ya tashe ni daga wannan mummunan mafarkin da nake. Amma kuma hakan gaskiya ne sannan kuma ba zamu iya canja gaskiyar ba, Aboki dan Allah ko da mai zai faru to sam bana san kowa ya san da wannan zancan, ina san kayi min alkawarin cewa ba zaka tab'a sanar da kowa gaskiyar ba dan Allah." Shiru bai amsa ba sai ma aikin kuka da yake kuma kuka sosai, haka shi ma abin da yake yi kenan lokaci ďaya suka yi hugging juna, cike da jin tausayin juna suke rarrashin junansu cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa *Adnan* yake magana. "Aboki duka iyayenmu suna matuqar masifar qaunar mu sosai, Aboki Papa da Mamie suna matuqar qauna ta sosai fiye ma da yanda suke so na. Ko yaushe suna k'oqarin saka ni farin ciki sosai hakama sam basa jure ganin duk wani k'unci na, ko damuwa ta rashin lafiya ta kuma ita ce babban qalubale a garesu, su ďin sun raine ni da kyau sannan kuma sun bani duka soyayyar su gaba ďaya. Su ďin suna so na da gaba d'aya rayuwar su amma kuma a haka kake san na yarda da abin da kake fad'a, Aboki ni nan nafi kowa sanin irin yanda iyayena suke qauna ta sosai to wannan kawai ya isa, sabo da ba wani abin da zai canja wannan har abada Papa da Mamie sune kawai iyayena, hakan ba zai canja ba to kama dena fad'ar abin da kake fad'a yanzu, sannan kuma kar kowa ya san da gaskiyar ka ji ko." "Aboki nima ina jin duk irin abin da kake ji a yanzu, sannan kuma nima ba zan jure rashin a salin iyayena ba ina nufin Appa da Ammie, sabo da sune kawai iyayena wad'an da nake alfahari dasu. Sannan kuma ba zan tab'a barin susan da wannan ba, to ya kamata mu birne wannan sirrin na har abada dan Allah." "Eh Aboki ba wanda zai san da wannan sirrin na har abada, nayi alkawari to kai ma kayi alkawari ka ji ko dan Allah." "Eh nima nayi alkawari ba wanda zai san da wannan sirrin, amma kuma ya zama dole mu gano a salin gaskiyar abin da ya faru damu, shin zaka taimaken a kan hakan please.?" "Eh zanyi nima zan taimaka nayi alkawari insha Allah." Ya jinjina masa ka a lamar to lokaci d'aya kuma suka k'ara yin hugging juna, wanda kuma har zuwa wannan lokacin idanuwansu basu dena zubar da kwalla ba. Mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, bayan wani lokaci suka sake juna daga hugging d'in da suka yi. Nan kuwa suka shiga tunani da nazarin yanda zasu gudanar da binkicen su, sun jima sosai a nan wanda sai dare sannan suka koma gida, *Adeel* ya shiga tambayar su inda suka tafi da kuma dalilin da yasa basu shiga asibiti ba. *Adnan* ne wanda yake amsa shi yayin da *Adyan* ya gagara furta masa komai. *"Adeel* abin shi ne mun tafi wani muhimmin guri ne sannan kuma mun gaji sosai, to shi yasa muka nai mi wani guri muka huta wannan dalilin ne yasa bamu iya tafiya asibiti ba. To ya jikin Mum fatan tana samun sauki ya Kaka tana lafiya.?" "Kaka tana lafiya amma Mum bata cikin kyakkyawan yanayi ni na damu sosai a kanta, nayi ta k'oqarin kiran *Adyan* yazo ya duba ta amma bai d'aga kira na ba, kai kuma layin ka baya tafiya shi yasa na fara damu sosai a kanku biyun, abin farin cikin kuna cikin k'oshin lafiya na ji dad'in hakan sosai." "Muna godiya sosai *Adeel* kayi hak'uri da ban d'aga kiran ka ba, hakan ya faru ne sabo da na manta waya na a office to ina mai baka hak'uri." "Ba komai d'an uwa amma qlau kuke ka? Na ganku sai a hankali kamar kuna k'unci sosai." Lokaci d'aya suka kai kallonsu ga juna sun kuma mai da kallonsu garesa, "a'a *Adeel* qlau muke muna lafiya kawai ka yarda da ni." Ya jinjina masa ka a lamar to *Adyan* ya anbaci sunan *Adeel* yana cewa. *"Adeel* na gaji sosai ina san zan shiga ciki na kwanta, Aboki kai ma ya kamata ka huta ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to suna k'oqarin tafiya *Adeel* ya dakatar dasu. "Am ni zan koma asibiti kuma a can zan kwana to sai da safe asuba ta gari." *"Adeel* ka kula sosai sannan kuma ka kula da Mum da Kaka, sannan kuma idan akwai buqatar nazo ko Aboki to kawai ka kira ni ka ji ko." "Na gode sosai *Adnan Adyan* ina godiya sosai da kulawa Allah ya saka da alkhairi Amin." Sun amsa shi da Amin ya juya yayi tafiyar sa sun bisa da kallo suna girgiza ka, bayan tafiyar sa sun mai da kallonsu ga juna sun jinjina wa juna ka sannan suka nufi bedroom, tafiya yake wani tamkar mara lafiya cikin hanzari *Afnan* ta tashi zaune tare da fad'ar sunan sa. "Besty qlau kake kuwa fad'a min mai yake faruwa da kai ne haka.?" Ta k'ara shi sun tafi sun zauna sai tambayar sa take mai yake faruwa da shi. "Ba komai Besty ina lafiya kawai dai na gaji ne shi yasa kika ganni a haka." "Besty yau ka jima sosai a waje shi yasa gajiya tayi ma yawa, to yanzu ka samu ka watsa ruwa sai ka sha magani ka kwanta ka ji ko." Ya amsa ta da to ta taya shi ya cire kayan sa sannan suka nufi ban d'aki, ba jimawa suka fito ta taimaka masa ya shirya sannan ta fita, bayan wani lokaci ta dawo hanun ta ri e da kofin madara nan kuwa ta shiga ba shi madara, ya sha kad'an ya furta mata cewar ya k'oshi ta a jiye kofin madara ta shiga ba shi magani, ya sha tare dayi mata godiya ya sauke kallonsa ga cikin ta tare da shafar cikin yana sunbata. "I LUV U MY Child I Love you so much." Ya fad'a tare da qara sunbatar cikin ita kuwa sai wani kallonsa take tana murmushi, ba jimawa yayi barci ita kuwa ta rufe sa da ido tana kallonsa, ita ma kwanta wa tayi tare da rungumasa jikin sa ba jimawa sosai barci ya d'auke ta. Haka yake ko a gurin *Adyan* bayan kwana biyu zaune yake office tare da *Adnan,* Umma ta turo k'ofa ta shigo sun shiga yi mata sannu da zuwa, ta amsa da to sun bata guri ta zauna bayan sun gaisa taci gaba da magana. *"Adyan Adnan* dan Allah ko zamu iya magana.?" Lokaci d'aya dukansu suka jinjina mata ka tare da furta mata eh, tayi shiru kad'an sannan taci gaba da magana. *"Adnan* shin da akwai abin da kuke b'oye mana ne? Sabo da kwana biyun na kun canja sannan kuma *Adyan* ya dena duba Aisha gaba d'aya ko kusa da ita kun dena zuwa, *Adnan* shin ku biyun kun samu wani sab'ani da *Adeel?* Ko Mummyn sa ta aikata muku wani abu cikin rashin sani? *Adyan* mu kamar ahali ne to ba zanso naga rashin jituwa tana shiga tsakanin mu ba. To naro e ku dan Allah da girman Allah ku sanar dani abin da yake faruwa a tsakanin ku da *Adeel.?"* *Adnan* ne wanda ya amsa ta yayin da *Adyan* ya rufe su da ido, kasancewar ba komai ya fahimta ba cikin abin data fad'a cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Kaka abin shi ne mu sam ba wata rashin jituwa da take tsakanin mu da *Adeel,* kawai dai mun damu ne da yanayin Mum sannan kuma muna tinani a kan yaran da take yawan maganar su. Mu muna san mu san ko tana da wasu yaran bayan *Adeel,* Kaka shin ke ce wacce ta karb'i aihuwar Mum.?" Ta girgiza ka tana furta, "a'a sabo da tiyata a kayi mata duk da cewar zata iya aihuwa da kanta, amma Prof ya tilassa a kayi mata tiyata sannan kuma *Addel* ne kawai yaron da a ka ciro mata. Haka kuma yasa a ka cire mata mahaifa ba tare da sanin taba, kawai yayi hakan ne sabo da cikar burin sa na samun d'a d'aya kamar dai yanda yake fata." Nan kuwa ta shiga sanar dasu komai a game da 'yarta dama rayuwar ta gaba d'aya, *"Adnan* yarinya ta tana da kirki sosai kaddaran ta ce ta canja komai, to ina ga ya kamata ku dena shakka a kanta ku yarda da ni, sabo da ni na sanar daku duka gaskiyar gaba d'aya a game da ita." Cike da mamakin abin data fad'a yake magana. "Kiyi hak'uri Kaka muna masu baki hak'uri dan Allah ki yafe mana." Ta amsa shi da ba komai ta tashi tayi tafiyarta sun bita da kallo har ta fice, bayan tafiyar ta *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi kallonsa yake ya shiga tambayar sa abin da suke magana, *Adnan* ya shiga sanar da shi komai ya kuma ci gaba yana cewa............................. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/12, 10:08 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 42* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 11/02/2022* *Time 09:25pm* *Typing..............* "Aboki hakan yana nufin cewar Mum da Kaka bama su san da labarin mu ba, to ina ga sam ba buqatar muci gaba da cutar dasu, ya kamata mu mai da hankalin mu gurin Mum ta samu lafiya." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Aboki ina matuqar mamakin yanda Prof ya aikata irin wannan mummunan zunubin, ta ya ma har zai yi tunanin cutar da Mum har haka? Da fari ya raba ta da yaranta sannan kuma yasa an cire mata mahaifa, daga bisani kuma ya sake ta ya kuma d'auke *Adeel* daga gareta. Ya tafi ya barta cikin mummunan yanayi na ciwon hauka, duk da cewar yana da damar da zai iya taimakon ta, lallai wannan ya k'ware sosai gurin iya zalunci lallai ya kamata mu had'u da shi. Waye shi mai yasa ya aikata duka wannan.?" "Aboki ba shi zamu fara had'uwa da shi ba da Dr Salim zamu fara had'uwa, sabo da shi ne wanda zai sanar damu duka gaskiyar cikin sauk'i, idan muka san duka gaskiyar sannan sai mu sam ta yanda zamu fuskanci Prof. Wannan shi ne abin da zamu yi zamu shirya komai ta yanda wani ba zai san gaskiyar ba, to kawai ka kwantar da hankalin ka mubi komai a hankali, yanzu abu mai muhimmanci shi ne Mum ta samu lafiya ta dawo haiyacinta. Sannan kuma mu kula da ita yanda ya kamata mu kasance yara na gari a gareta, shin zaka yi hakan kuwa.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya jinjina masa ka tare da furta masa eh, shi ma ya jinjina masa ka tare da yin hugging d'in sa. Ai kuwa haka suka d'ora duk wata kulawar su a kan Mum, lokaci d'aya *Adyan* ya fara shirin yi mata aiki an yi shirin komai, bayan kwana biyar a kayi mata aiki ta samu tsayin kwana biyu sannan ta farka. Wani yammaci zaune suke dukansu a nan d'akin da Mum take, lokaci d'aya ta farka daga dogon barcin da take, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e sai wani kallonsu take, suma haka kallonta suke kallo sosai cikin hanzari Umma ta shiga anbatar sunan ta. "Aisha kin farka to ya jikin ki fatan kina samun sauki sosai.?" Ta jinjina mata ka tare da furta mata, "eh Umma ina lafiya na samu sauk'i sosai to fad'a min wani abu ina yarona? Karki fad'a min cewar Prof bai kawo shi gareni ba Umma fad'a min ina *Adeel.?"* Dukansu kallonta suke ba kuma tare da sun furta mata komai ba. "Umma ni na san cewar Prof ba zai tab'a barin *Adeel* gareni ba, zai yi komai domin ya d'auke sa daga gareni shi sam ba shi da adalci, ban san har tsayin wane lokaci zai d'auka yana cutar da ni ba. Naso a ce ya bani damar da zan kasance uwa ta gari ga yarona, ta yanda zansa yarona ya zama likita domin ya samu damar da zai kula da kansa sosai, ko kuma dai ya zama lauya ta yanda zai yi yak'i da zama irin su Prof. Amma ko yanzu ni zan tabbatar cewa yarona ya kasance abin da zanyi alfahari da shi sosai insha Allah, wannan alkawari na kuma zan cika alkawari na insha Allah, Umma ni nayi matuqar kewar yarona sosai ina kewar *Adeel* sosai. Sabo da har yanzu shi yaro ne shekarun sa uku kawai to dole yana buqatar wacce zata kula da shi sosai, kamar dai ni ko kuma ke amma kuma Prof ya d'auke sa daga gareni. Shi mugu ne ya cutar da ni sosai to ina tsoron kar ya cutar da yarona, to ya kamata na tafi nayi magana da shi yanzu." Ta yunk'ura zata tashi da sauri Umma ta dakatar da ita, ta hanyar ri e hanun ta tana girgiza mata ka tare da furta. "A'a 'yata sam bakya buqatar had'uwa da Prof Abas a yanzu, sabo da Ubangiji ya daidai komai a yanzu. Da fari *Adeel* ya dawo garemu yanzu kuma kin samu lafiya, a ta dalilin *Adnan da Adyan* wanda godiya ta ba zata biyasu ba, sunyi komai domin ganin kin samu lafiya kuma Alhamdulallah daga k'arshe sunyi nasara, to ya kamata ki natsu ki kwantar da hankalin ki ta yanda lafiya zata samu damar shigarki kin ji ko." "Umma hankali ba zai tab'a kwanciya ba har sai idan na had'u da yarona, to ya kamata na had'u da Prof domin na karb'i yarona. Har yanzu shi yaro ne to dole yana buqata na sosai a tare da shi to kawai ki barni na tafi dan Allah." "Aisha yaronki yana tare dake sannan kuma shi ďin yana kulawa dake sosai, duk da cewar baya tare dake amma kuma ya rayu da soyayyar ki, shi d'in yaron kirki ne kamar abokan sa wad'an da suka kula dake, Aisha ina farin cikin gabatar maki da yaronki *Adeel* kuma jikana, Aisha wannan shi ne yaronki wanda zan iya kiran sa da na musamman." Aisha ta sauke kallonta ga fuskar *Adeel* wanda shi ma kallonta yake kallo sosai, sun jima a haka sannan ta mai da kallonta ga Umma tare da fad'ar sunan ta. "Umma nifa a haiyacina nake waye wannan da kike kiran sa da ďana? Shi ďana yaro ne d'an shekaru uku to shi nake buqatar had'uwa da shi ba wannan ba, yanzu kawai ki fad'a min ina ďana *Adeel* yake.?" "Aisha lokaci ya tafi sosai shekaru masu yawa sun shige, 'yata yanzu yaronki ya girma sosai wanda har yake kulawa dake. Aisha shekaru ashirin da biyu kenan da kike magana a kai, yanzu yaronki yana da shekaru ashirin da biyar ne ya dawo garemu bayan wani tsayin lokaci, to kawai kiyi farin ciki sosai 'yata sabo da abubuwa sun fara daidai ta kin ji ko." "Umma wai gaskiyar kike fad'a min kuwa yanzu wannan *Adeel* ya girma haka.?" Ta jinjina mata ka tare da furta mata eh tana murmushi, Aisha ta mai da kallonta ga fuskar *Adeel* lokaci ďaya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi ma kallonta yake kallo sosai yayin da tausayin ta yayi yawan gaske a tare da shi. Sun jima sosai a haka lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla shi ma abin da yake yi kenan, cikin wata 'yar murya take furta masa kalmar zo nan ďana, cike da d'auki ya tashi daga inda yake ya nufi gurin ta har yana gudu, yayin da yake fad'ar sunan ta Mummy na yana isa inda take sun wani rungume juna. Ta rungumasa jikin ta sosai tana sunbatarsa shi kuwa yayi kwance jikin ta yana fad'ar sunan ta, Umma sai kallonsu take tana murmushi hakama su *Adyan* kallonsu suke. *Adyan* ya juya zai fita da sauri *Adnan* ya ri e hanun sa tare da kai kallonsa garesa yana girgiza masa ka a lamar a'a, bayan sun sake juna daga hugging d'in da suka yi Aisha ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana furta masa kalmar. "Kayi hak'uri ďana da lokaci bai bani damar da zan kasance uwa ta gari a gareka ba, ka rayu ba tare daka samu kulawa ta ba ni ban tab'a kasancewa uwa a gareka ba, amma kuma duk da haka kai baka gujeni ba sannan kuma ka kula da ni sosai. Na gode ďana ina matuqar yin alfahari da kai sosai zanyi farin ciki sosai idan ka sanar da ni, cewar kana matsayin likita ko lauya dan Allah karka fad'a min cewar baka yi karatu ba. *Adeel* ba zanso ka rayu kamar yanda ni na rayu ba, na rayu ba tare da nayi karatun boko ba wanda wannan ne abin da ya bawa Dadyn ka damar yaudara ta. A gaba na yake magana da Dr Salim amma sam bana fahimtar abin da suke fad'a, sabo da turanci suke wanda da a ce nayi karatu to da duka wannan bai faru ba, to kayi hak'uri dana kasance a haka na kasa kulawa da kai dan Allah ka yafemin ka ji ko ka gafarce ni." Da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata ka, cike da qauna da soyayya yake yi mata magana. "A'a Mum wannan sam ba laifin ki bane to sam ba buqatar ki ba da hak'uri, sannan kuma nayi karatu ina matakin degree ne kiyi hak'uri da ban kasance matsayin Doctor ko Barrister ba. Ina mai baki hak'uri a game da wannan amma zan kasance d'a na gari a gareki nayi alkawari, ke uwa ta gari ce a gareni to ina alfahari da hakan sosai ina matuqar masifar qaunarki sosai Mummy na." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take d'auke da wani lallausan murmushi, ita kuwa sai kallonsa take kallo sosai cike da qaunar sa tayi hugging d'in sa tana sunbatarsa. Farin cikin sa ya qaru sosai su Umma sai kallonsu suke, lokaci ďaya su *Adnan* suka ji wata soyayyar Mummmyn su tana shigarsu sosai, tausayin ta ne yafi yawa a tare dasu sosai sai ji suke kamar su tafi su rungumata. Cike da k'unci da b'acin rai *Adyan* ya cire hanun sa cikin na *Adnan* ya nufi hanyar fita, *Adnan* ma juyawa yayi yabi bayan sa suna k'oqarin fita Umma tayi saurin dakatar dasu, sun tsaya tsak ba tare da sun amsa ba *Adnan* ne wanda ya juyo da kallonsa gareta, yayin da *Adyan* yake ri e da k'ofa kafin Umma ta furta komai *Adeel* ya mata rigagi. "Mum wad'an nan sune wad'an da suka taimaka min sosai gurin ganin kin samu lafiya, Mum *Adyan da Adnan* su ba kawai abokaina bane a'a su ďin na musamman ne a gareni. Sabo dasu ne na samu damar kasancewa a tare dake yanzu su sunfi kowa kirki, suna bina bashin da ban san dame zan biyasu ba, sai dai kawai naci gaba dayi musu addu'ar fatan alkhairi kamar dai ko yaushe." Nan ya shiga sanar da ita komai daya faru duk wani abin da suke fad'a *Adnan* yana sanar da *Adyan* da turanci. Sabo da ba komai ne yake fahinta ba hakan tasa yake fahimtar komai, Mum tayi kiran su sun tafi kusa da ita sun zauna sai wani kallonsu take kallo sosai, suma haka kallonta suke kallo sosai mai tare da shauk'i sosai. "Na gode muku sosai Allah ya saka muku da alkhairi wannan kalmar ce kawai zan iya fad'ar muku, hak'iqa iyayen ku sunyi matuqar samun yaran kirki sosai Allah yayi muku albarka, ya kuma sanya wa rayuwarku albarka ku biyun kuna da kamanni da yarona sosai, kamar dai 'yan uwan juna ko ahali ďaya shin zan iya runguma ku jiki na? Sannan kuma zan iya kiran ku da yarana dan Allah.?" *Adnan* sai wani kallonta yake yayin da shi kuma *Adyan* ya rufe sa da ido yana kallonsa, *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* tare da sanar da shi abin da take fad'a, yayi shiru yana nazari *Adnan* ya shiga jinjina a lamar eh shi ya jinjina masa ka a lamar eh. *Adnan* ya mai da kallonsa ga Mum tare da furta mata eh, murmushin ta ya k'aru sosai lokaci ďaya kuma tayi hugging d'in dukansu biyun. Ta k'ara da sunbatarsu tana furta musu kalmar Allah yayi muku albarka sun amsa da Amin, ba jimawa ta sake su bayan wani lokaci suka tashi suka fita, wanda kuma office ďin *Adyan* suka nufa sun shiga ciki *Adnan* ya sauke kallonsa ga, fuskar *Adyan* wanda yake ta hawa yana sauka ya gama fahimtar cewa cikin fishi yake sosai, shi ma yana tare da k'unci amma zai iya cewa damuwar *Adyan* tafi tasa yawa, ya nisa sosai tare da jan numfashi sannan ya fara magana. "Aboki shin har yanzu kana tare da tsanar Mum sosai.?" "A'a Aboki ni kawai tausayin ta nake sosai tare da jin tsanar Prof a tare da ni sosai, shi ne abin da nafi tsana a rayuwata dan haka ya zama dole ya fuskanci hukunci daga gareni." "Aboki ciwon namu duka iri d'aya ne to tare zamu yi komai ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to da dare su Ammie suka shigo duba ta, wanda kuma tare suke dasu *Afnan Adeel* ya gabatar dasu ga Mum. Ta shiga yi musu fatan alkhairi sun amsa ta tare dayi mata godiya, haka dai Mum tayi ta samun cikakkiyar kulawa sosai har jikin ta ya warware gaba d'aya. bayan mako d'aya ta samu sallama zuwa gida, zuwa wannan lokacin cikin su *Alishart* yana da watanni hud'u, har ya fara bai yana hakan yasa suka fara shirin tafiya k'asa Nigerian, sunyi duk wani shirin su na tafiya Appa yayi musu visa bayan mako biyu jirginsu ya tashi...................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/16, 12:02 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 43* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 12/02/2022* *Time 07:48pm* *Typing...............* *Nigeria.* A garin Abuja suka sauka kasancewar su Abbu daga Abuja sun kawo masu Abba ziyara. Su Ummi sai wani d'aukin zuwan su suke inda suka shiga yi musu sannu da zuwa, bayan sun gaisa sun huta gajiya tare da cin abinci sun shiga yiwa Mum ya jiki, ta amsa da Alhamdulallah tare dayi musu godiya sosai, murmushi kawai suka yi mata tare da furta mata ba komai. Su *Adeel* sun samu kwana biyu a garin Abuja gidan Abba sannan suka fara shirin tafiya, ai kuwa a nan ne gizo ke sak'a domin kuwa *Alishart* ta shiga kukan sai ta tafi tare dasu *Afnan.* A zahirin gaskiya dukansu basu so tafiyar ta ba, amma ganin yanda take k'unci yasa Abba yace su Appa su barta ta tafi, basu da wani zab'i wanda wannan dalilin ne yasa suka amince da tafiyar ta. Suna ta shirin tafiya Abba da Abbu sunyi musu sha tara ta arziki, wanda visa ma a kayi musu Abuja to kaduna *Adyan* yayi musu rakiya, har Airport bayan sunyi sallama suna k'oqarin tafiya *Adyan* ya anbaci sunan *Adnan* yana cewa. "Aboki ka kula da *Adlishart* sosai da kuma duka yaran ka ji ko." "Eh zanyi nayi alkawari amma bayan su baka buqatar na kula da kowa.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Shikenan ka kula da Mum sosai yanzu kana farin ciki.?" "Eh hakan yayi kuma ni zan kula da dukansu nayi alkawari, insha Allah to zaka iya yarda da ni ka ji ko." Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, daga bisani kuma suka yi hugging juna su Umma suna daga gefe suna kallonsu. Ba jimawa suka sake juna *Adnan* ya kai bakinsa daidai kunnansa ya rad'a masa cewa. "Aboki akwai buqatar ka rungumi Mum, Kaka, da kuma *Adeel* sabo da dukanmu ahali ďaya ne, wannan ce gaskiyar kuma hakan ba zai canja ba to kawai kayi hakan dan Allah." Kallonsa kawai yake ba tare daya amsa shi ba sai daga bisani ya jinjina masa ka a lamar to, *Adnan* yayi murmushi sosai tare da sunbatarsa a ka yana furta masa kalmar. "Ina sanka Aboki ina qaunarka sosai zanyi matuqar yin kewarka sosai." "Nima haka Aboki ina matuqar qaunar ka sosai ba zamu jima a nan ba, zamu shigo kaduna a wannan lokacin zamu k'ara kasancewa a tare." Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, sun k'arasa gurin su Mum ya bisu ďaya bayan d'aya yayi hugging d'in su, kamar dai yanda *Adnan* ya buqata daga garesa ya anbaci sunan *Adeel.* *"Adeel* ka tabbatar daka kula da Mum sosai idan akwai buqatar nazo to kawai ka kira ni ka ji ko." "Na gode sosai *Dr Adyan* Allah ya saka da alkhairi Allah kuma ya bar tare Amin." Dukansu sun amsa da Amin *Adyan* ya mai da kallonsa ga *Alishart* tare da fad'ar sunan ta. *"Adlishart* dan Allah ki kula da kanki sosai da kuma yaronmu kin ji ko *Afnan* kema haka kin ji ko." Sun amsa shi da to suna murmushi da kuma haka suka yi sallama, suna fice ba jimawa sosai jirginsu ya tashi zuwa kaduna. Misalin k'arfe 05:00pm jirginsu ya sauka *Adnan* ya tare musu taxy sun nufi gida, kai tsaye gidan Papa suka nufa Mamie na zaune a parlour tare da, Amal yarinyar Anwar ta kawo mata fira bugun k'ofar da a kai ne yasa ta tashi ta nufi k'ofa, ta shiga tambayar waye kamar a mafarki ta ji muryar *Adnan* yana fad'ar sunan sa. Cike da d'auki ta bud'e k'ofar yayin da bakinta yake anbatar sunan *Adnan,* "ďana ka dawo gareni sannu da zuwa rabin raina." Magana take yayin da take rungume da shi a jikin ta sai wani sunbatarsa take. "Nayi kewarka sosai yarona I really miss you so much my sweet son." Ta fad'a tare da qara sunbatar sa, "I miss you too Mamie nima nayi matuqar yin kewarku sosai ina matuqar masifar qaunarki sosai Mamie na." Ya fad'a tare da sunbatarta su Umma sun rufe su da ido sai kallonsu suke suna murmushi. Sai kuma zuwa wannan lokacin ne Mamie ta shiga yi musu sannu da zuwa, bayan data kammala da yaronta ta tafi ta shirya musu tebur da kayan abinci. Sannan ta dawo garesu ta d'auke kallonta ga *Afnan,* wacce take rungume da Amal tare da fad'ar sunan ta. *"Afnan* masoyiya to ya kike ya mai gida na? Ya tafi na tsayin wata biyu ya barni da kewarsa sosai to fatan dukanku kuna cikin k'oshin lafiya sosai.?" Cike da jin kunya da nauyi take amsa ta, "Mamie muna lafiya sannan kuma muna tare da kewarku sosai." Hakan yayi kyau sosai." Ta mai da kallonta ga Mum tare dayi mata ya jiki ta amsa da Alhamdulallah, ta gaisa da Umma da *Adeel* sannan ta sauke kallonta ga fuskar *Alishart* tare da fad'ar sunan ta. "Rabin raina hak'iqa nayi matuqar yin kewarki sosai sabo da mun jima sosai bama tare, sai dai a waya amma kuma yau kinzo garemu nayi matuqar farin ciki da hakan sosai ina sanki 'yata ina qaunarki sosai." Ta fad'a tare da sunbatarta ta k'ara da yin hugging d'in ta, bayan wani lokaci suka tafi suka ci abinci sannan suka tafi domin su shirya. Bayan sun shirya sun fito sun nufi gidan Abba har da *Alishart* suka tafi, sun kuwa samu dukansu a parlour nan kuwa su Yaya Anwar suka shiga yi musu sannu da zuwa. Sun amsa suna murmushi mai had'e da dariya bayan sun gaisa sunci gaba da fira cikin raha wasa da dariya, sun kasance a nan wanda sai dare sannan suka tafi gida sun samu Papa ya dawo, nan kuwa ya shiga yi musu sannu da zuwa sun amsa suna murmushi mai had'e da dariya, sun zauna sunci gaba da fira bayan wani lokaci *Alishart da Afnan* suka tafi domin su kwanta. Bayan tafiyar su ne *Adnan* yake sanar dasu Mamie cewar *Alishart* na tare da juna biyu, sun cika da mamakin hakan sosai daga bisani kuma suka yi mata addu'ar sauka lafiya, ganin dare yayi sosai yasa suka yiwa juna sallama tare da sai da safe, suka nufi d'akin barci su Mum sun samu tsayin kwana biyu a nan gidan Papa sannan suka tafi nasu gida. Bayan mako d'aya *Adnan* ya shirya tsab ya nufi garin Kankiya, wata safiyar litinin zaune yake a office ya ji a na buga masa k'ofa, daga ciki ya amsa da cewa shigo ciki ba jimawa ya shigo, bayan ya zauna sun gaisa Dr Salim ya shiga tambayar sa mai yake tafe da shi, yayi shiru na jim kad'an sannan daga bisani ya amsa shi. "Am ko kai ne Dr Salim.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh *Adnan* yaci gaba da magana. "Am ni sunana *Barrister Adnan Adam Muh'd* nazo nan ne domin nayi magana da kai, a game da wani muhimmin abu to fatan zan samu had'in kanka.?" "Miye wannan sannan kuma a kan me zamu yi magana.?" "A game da Prof Abas ne." Da sauri ya wani zaro ido yana kallonsa kallo sosai, sannan kuma daga bisani ya amsa shi. "Waye shi kuma mai yasa zamu yi magana a game da shi.?" "Ina san na san gaskiyar da kai da shi kuma birne shekaru ashirin da biyar da suka wuce." "Mai yasa kake tunanin cewa ina da sani a kan abin da kake fad'a.?" "Dr Salim na san cewar Prof Abas ya biyaka kud'i mai yawa sosai, ta yanda ba zaka sanar da kowa ba wannan sirrin amma na tabbata basu kai, rayuwar jikar ka ba wacce a yanzu haka bata makaranta. Sannan kuma bata gida Allah sarki 'yar talika ko tana ina? Gata kuma bata da lafiya to ko mai zai faru da ita yanzu? Zunubin Kakan ta ne ya shafe ta amma k'ila Kakan ta zai iya ceton rayuwar ta, ko kuma dai ya cutar da ita ta hanyar rashin fad'ar gaskiyar abin dana tambiye sa. Ni zan tafi ga kati na idan ka shirya magana to sai ka kira ni sai an jima." Ya yunk'ura zai tashi da sauri Dr Salim ya dakatar da shi. "A'a karka saka jikata a cikin wannan ita ďin bata da lafiya sosai, sannan kuma d'ana ba zai jure ganin 'yarsa cikin k'unci ba, ya jima sosai kafin ya aihu yana san 'yarsa sosai. To naro e ka ka da ka cutar da ita dan Allah." "Eh na san da duka wannan amma kuma ni a gurin ka na koyi wannan, yanda a ke raba uwa da yaranta to kawai ka shirya yanda zaka fuskanci yaronka sai an jima." "A'a dan Allah yanzu fad'a min mai kake so.?" "kawai ka sanar da ni gaskiyar abin da yake tsakanin ka da Prof Abas." Ba shi da wani zab'i wanda wannan dalilin ne yasa dole ya sanar da shi komai. "Shikenan yanzu zamu tafi can gidan narayun domin na tabbatar da abin da kake fad'a." Ya amsa shi da to sun tashi sun nufi gidan marayu, sun isa gidan ba jimawa suka had'u da shugaban gidan, bayan sun gaisa Dr Salim yaci gaba da magana. "Alh Mansoor munzo ne a kan wasu yara wad'an da ni na kawo su nan." Nan kuwa ya shiga sanar da shi komai ya jinjina ka sannan daga bisani ya amsa shi. "Eh na tuna da komai amma tin a cikin satin wasu ma'aurata suka d'auki yaran raino, to gaskiya ba zamu iya sanar daku komai a game da yaron ba kuyi hak'uri." Cikin hanzari *Adnan* ya amsa shi da cewa. "Am dan Allah ko ka san address ďin gidan su dan Allah ka sanar damu please.?" Ya amsa shi da eh nan kuwa yasa a ka duba musu address ďin tare da sanar dasu. Sunyi masa godiya sannan suka tafi suka fita kai tsaye gidan su Anas suka nufa, sai dai sunyi rashin sa'a sabo da an sanar dasu cewar, sun bar nan tin shekaru ashirin da biyar da suka wuce, ba kuma wanda ya san inda suka koma suna tsaye jikin mota Dr Salim ya anbaci sunan *Adnan.* *"Barrister Adnan* to zuwa yanzu ya kamata ka sanar da ni inda jikata take.?" *Adnan* yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Dr Salim ni ba kamar kai bane da kake cutar da yara ba ta hanyar raba su da mahaifiyar su, jikar ka tana gida ni kawai nayi anfani da raunin ka ne domin na san gaskiyar, yanzu zaka iya magana da yaronka domin ka tabbatar da gaskiyar sai an jima." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya ya shiga mota, hakama Dr Salim shi ma zagawa yayi ya shiga mota sun fice, *Adnan* ya sauke shi office sannan ya wuce ya koma masauki. Inda kuma ya shiga sanar da *Adyan* komai daya faru ya amsa shi yana cewa. "Am Aboki ya kamata mu had'u da wannan matar sabo da ita kawai ce bata sanar damu, gaskiyar gaba ďaya ina nufin yanda a kayi mu biyun muka rabu da juna, da kuma yanda iyayenmu suka had'u damu dole ita kad'ai ce zata amsa mana wannan." "Eh Aboki nima ina tare da burin haka zanci gaba da nai man ta." Sunci gaba da magana na wani lokaci sannan daga bisani suka yi sallama, washe garin ranar *Adnan* ya koma gida bayan kwana biyu, wani yammaci zaune suke suna fira *Adeel* ya kai kallonsa ga *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* da akwai abin da nake san na nai ma a gurin ka." *"Adeel* kawai ka sanar da ni koma miye." *"Adnan* dan Allah idan kana da dama ina san gobe zaka raka ni jigawa, zamu tafi na had'aka da *Amna* ita ďin budurwa ta ce, to ina fatan zaka amince da wannan tayin nawa dan Allah." *Adnan* yayi murmushi sosai mai tare da dariya sannan ya amsa shi. "Shikenan zamu tafi tare insha Allah." Yayi murmushi sosai tare da furta masa kalmar na gode sosai, murmushi kawai yayi masa ba tare daya furta masa komai ba. Hakan kuwa ta kasance washe gari suka kama hanyar jigawa gurin *Amna,* sunyi nasaran sauka lafiya *Amna* ta shiga yi musu sannu da zuwa, sai wani nan-nan take dasu yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare da ita, bayan sun gaisa *Adeel* ya shiga gabatar da *Adnan* gareta. Sun k'ara gaisawa bayan sun qarasa gaisawa *Adeel* ya shiga tambayar su Mama tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi. *"Adeel* ka riga da ka san komai a game da ita, kamar dai kullum yau ma sam bata cikin kyakkyawan yanayi, tin data samu labarin cewa an kashe wasu 'yan fashi, take cikin wannan mummunan yanayin wanda har sai da ciwan zuciyar ta ya tashi. Wanda har sai data kwana biyu asibiti jiya da yamma muka dawo gida, amma har yanzu bata cikin kyakkyawan yanayi Abba yana kulawa da ita sosai." Cike da jin mamakin abin data fad'a *Adnan* yake magana. *"Amna* amma mai ya saka ta damu sosai a kan wad'an nan 'yan ta'addan da a ka kashe shin da akwai wanda ta sani ne.?" "A'a ita kawai ta damu ne a kan yayuna wad'an da 'yan fashi suka sace daga garemu." Nan kuwa ta shiga sanar da shi komai kamar dai yanda iyayen ta suka sanar da ita. *"Adnan* dukansu sun damu ne sosai sabo da muna tsoron kar twin's su kasance a cikin su, sabo da bamu da sani a game dasu wannan yafi komai cutarwa,, mun rayu ne tare da tunanin cewar wata rana zasu dawo garemu, amma har yanzu ba wani labari a game dasu suna raye ko a'a suna tare da 'yan fashin bamu sani ba.?" "Shin sun samu kub'uta daga garesu idan sun kub'uta to suna ina dawa suke tare? Shin sun samu kyakkyawar rayuwa kuma ingantaciya suna farin ciki kuwa bamu sani ba? Tuna hakan kawai yana saka mu kuka sosai ni ban tab'a sanin yayuna ba sai a photo, amma kuma hakan sam bai hana ni sansu ba ina matuqar qaunar su sosai. Ina fatan zuwan lokacin da zasu dawo garemu ta yanda ahalinmu zai k'ara cika sannan kuma." Kuka yaci k'arfin ta tayi shiru ta kama aikin kuka, cike da qauna da soyayya tare da jin tausayin ta *Adeel* ya shiga rarrashin ta, cikin mutuwar jiki da sanyin murya tare da jin tausayin ta sosai *Adnan* yake magana............ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [2/28, 3:52 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 44* *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Wednesday 16/02/2022* *Time 11:46pm* *Typing............* *Alhamdulallah munyi hidima lafiya mun k'arasa lafiya, Amarya da Ango Allah ya ba da zaman lafiya da zuri'a d'ayiba, Allah ya kau da shaid'an a tsakanin ku Allah yasa mutuwa ce zata raba Allahumma Amin ya hayyu ya kayyum.* *To mu tai zuwa dan jin yanda zata kasance dasu.* "Kiyi hak'uri amma kuna nai man yaran kuwa.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh yaci gaba da magana. "To amma wane ci gaba a ka samu.?" "Ba wani ci gaba sabo da har yanzu ba wani labari a game dasu." *"Amna* Shin ko zan iya ganin photon twin's dan Allah.?" Ta jinjina masa ka tare dayi masa nuni da gefen da photon yake, ya kai kallonsa ga inda tayi masa nuni da shi sai wani kallon photon yake kallo sosai. Ya tashi daga inda yake ya nufi gurin photon yake yayin da yake magana da zuciyarsa. Tabbas ni ne a cikin wannan photon hakan yana nufin cewar wannan Aboki ne, Allah sarki Mama ta rayu gaba d'aya cikin k'uncin rashin ni da Aboki, dukansu ahalin suna da kirki sosai suna qaunarmu fiye ma da yanda suke sanmu. Ya kamata na had'u da dukansu biyun Mama da kuma Abba a yanzu." Ya mai da kallonsa gasu *Adeel* lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar suma kallonsa suke kafin ya furta komai *Amna* ta anbaci sunan sa. *"Adnan* lafiya kamar dai kai baka cikin kyakkyawan yanayi shin qlau kake kuwa.?" "Eh *Amna* qlau nake kawai dai na damu ne a game da twin's sabo da sunyi matuqar bani tausayi sosai, *Amna* dan Allah ko zan iya ganin iyayen ki da akwai abin da nake san na tambiye su please.?" *"Adnan* abin sam ba shi da sauki kamar yanda kake tunani, ita Maman twin's bata cikin kyakkyawan yanayi hakama Abba, to sam bana jin cewar su biyun zasu saurari wani abu daga gareni, amma duk da haka zan gwada insha Allah zan dawo yanzu." Ta tashi ta nufi bedroom d'in Mama su kuwa sun bita da kallo har ta shige, bayan wani lokaci ta fito tayi shiru kad'an sannan ta fara magana. *"Adnan* kayi hak'uri sabo da sam basu aminta da tayin ka ba." Yayi shiru kad'an sannan ta tashi ta nufi bedroom d'in sun bisa da kallo, *Amna* zata dakatar da shi *Adeel* ya shiga girgiza mata ka a lamar a'a, ya isa ga k'ofar tare da bud'e k'ofar ya shiga ciki. Tare da kyakkyawar sallama lokaci ďaya ta suka kai kallonsu garesa, sunyi ido biyu da juna kasancewar shi ma kallonsu yake, sannu ahankali yake tafiya har ya k'arasa inda suke, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallon juna suke, kafin ya furta komai Abba yayi masa rigagi yana cewa. "Waye kai mai kuma kake a nan.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi cikin kwantar da murya yake magana. "Am sunana *Adnan Adam Muh'd* ni abokin *Adeel ne Amna* ta sanar da ni, komai a game da twin's to ina ga zan iya taimaka wa domin gano twin's. Sabo da har yanzu yaran suna raye sannan kuma daf suke dasu dawo gareku, to sam ba buqatar kuci gaba da kasancewa cikin wannan mummunan yanayin. Sabo da hakan yana matuqar cutar da masoyan ku sosai, to ya kamata ku dena wannan k'uncin domin ku samu ku rayu cikin farin ciki na har abada dan Allah." Tin daya fara magana suke kallonsa har ya kai natsaya, cike da jin mamakin sa sosai Mama take magana. "Barrister shin kai ka san wani abu a game da yarana dan Allah ka sanar da ni please.?" "Eh na tab'a jin labarin wasu twin's da suka b'ata to ina fatan su kasance yaranku ne." "A wane gurin? Ya kamata mu tafi can yanzu sabo da ina buqatar na had'u da yarona." "Ba zai yu mu tafi yanzu ba sabo da ina san nayi binkice a kan lamarin, sannan kuma na k'ara sanin wani abu a game dasu, shin zaku sanar da ni wani abu a game da yaranku.?" Sun amsa shi da eh ai kuwa nan suka shiga sanar da shi komai, ta yanda suka rasa yaransu shi kuwa sai wani kallonsu yake, yayin da tausayin su yayi yawan gaske a tare da shi sosai. "Karku wani damu ni nayi muku alkawarin cewa twin's zasu dawo gareku insha Allah." "Mun gode sosai Allah ya ma albarka ya kuma albarkaci rayuwarka Amin." Ya amsa da Amin yana wani gajeran murmushi ba jimawa suka tashi, suka fita babban parlour sun gaisa da *Adeel* sannan suka nufi k'aramin parlour, bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin cin abinci, suna cikin cin abinci *Adeel* ya sauke kallonsa ga fuskar *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* qlau kake kuwa.?" Ya girgiza masa ka tare da furta ba komai, *"Adnan* dan Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai.?" "Ba komai *Adnan* kawai dai na damu ne a game dasu Mama, yanayin su yana da matuqar ban tausayi sosai." *"Adnan* kai kana da kirki sosai sannan kuma ka damu da damuwar kowa, kai kana da halaiya masu kyau sosai na gode sosai da kulawar ka a kan iyayena." Yayi wani gajeran murmushi sannan ya amsa ta. "Ba komai Sister Mama da Abba kamar iyayena suke to zanyi komai sabo dasu insha Allah." Murmushi kawai tayi masa hakama *Adeel* abin da yake yi kenan, bayan sun kammala sun koma parlour sunci gaba da fira cikin kyakkyawan yanayi, sai yamma sannan suka kama hanyar kaduna sunyi nasaran sauka lafiya. Kai tsaye gidan su Papa suka nufa *Adeel* ya sauke *Adnan* sannan ya nufi gida. Da dare bayan *Afnan* tayi barci *Adnan* ya kira layin *Adyan,* ya shiga sanar da shi komai a game dasu Mama wato iyayen *Amna.* "Aboki dukansu ahalin sun damu sosai a kanmu musamman ma Mama gaskiya na tausaya wa dukansu sosai. To yanzu mai ya kamata muyi shin zamu iya sanar dasu gaskiyar a game damu? Sabo dasu dena damuwa a kanmu domin ko ba komai zasu rayu cikin farin ciki sosai." "A'a Aboki ba zai yu mu sanar dasu gaskiyar ba, sabo da hakan zai iya b'ata komai wanda kuma dukanmu ba zamu so hakan ba. To ya kamata kayi tunani a kan iyayenmu, sabo da wannan shi ne abin da yafi komai muhimmanci a garemu dan haka ya zama dole mu b'oye gaskiyar ka ji ko." "Amma Aboki yanayin su Mama yayi tsauri sosai kuma hakan yana matuqar cutar dasu sosai, Aboki su ďin fa masoyan mu ne to bai kamata mu barsu a cikin irin wannan mummunan yanayin ba, bayan kuma muna da damar da zamu iya taimaka wa to ya kamata muyi abin daya dace." "Eh Aboki gaskiyar ka fad'a amma zamu yi magana a game da wannan bayan na dawo, jibi zamu dawo kaduna insha Allah fatan kana kulamin da *Adlishart* sosai.?" "Eh ina yi ina farin ciki da zuwan ku Allah ya kawoku lafiya, Aboki shin ba zaka tambayi Mum ba.?" "Dama yanzu nake shirin na tambiye ta to ya take fatan tana tafiya.?" "Eh tana lafiya." Haka suka ci gaba da fira na tsayin wani lokaci sannan daga bisani suka yi sallama, bayan kwana biyu su Appa suka dawo kaduna tin a ranar *Adyan* ya d'auki *Alishart* zuwa gidan Abbu. Wani yammaci zaune suke suna fira *Adeel* ya kai kallonsa ga Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum gobe zanyi tafiya insha Allah." "Rabin raina ina zaka tafi ne shin zan iya sani.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta. "Mum ina san zan tafi jos ne gurin Dady." Kallonsa kawai take ba tare data furta masa komai ba, shi ma haka kallonta yake ya nisa tare da jan numfashi sannan taci gaba da magana. "Mum dan Allah karki saka damuwa a ranki wani abu yazo ya faru dake, wanda hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai sannan kuma ba zan wani jima ba zan dawo gareki insha Allah." "D'ana ni kawai na damu ne a kanka sabo da ina tsoron kar ya cutar da kai. Sabo da shi ďin tamkar maciji ne zai iya cutar da duk wanda ya rab'esa, to sam bana san ya cutar da kai kamar dai yanda ya min, musamman ma yanzu daya san cewar kana tare da ni d'ana ni na kasa yarda da zuciyata sabo da." "A'a Mum sam ba abin da zai faru da ni sabo da Dady na yana qaunata sosai, na tabbata ba zai tab'a cutar da ni ba to zaki iya yarda da ni dan Allah." Ta jinjina masa ka a lamar to yayi murmushi sosai tare da yin hugging d'in ta, Umma na daga gefe zaune tana kallonsu yayin da fuskar ta take fitar da murmushi. Sunci gaba da fira na tsayin wani lokaci sannan ya tashi ya fita, hakan kuwa ta kasance washe gari bayan sun qarasa break past *Adeel* ya kama hanyar Jos. Yayi nasaran isa garin Jos lafiya ya nufi gida ya isa gidan bayan sun gaisa da Audu yaci gaba da magana. *"Adeel* Dadyn ka baya nan." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Audu ina kuma ya tafi.?" *"Adeel* labari ne mai tsayi bayan tafiyar ka komai ya lalace, babban campaning sa yayi gobara to ba wannan bane abin damuwar ba, *Adeel* wad'an da suke da hanun jari a campaning sun kasa amincewa da kaddaran data faru. Wanda har sunyi k'aransa a kan sai ya biyasu kud'ad'ensu." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Audu yaushe hakan ta faru yanzu fad'a min ina Dady na yake.?" "Yana kaduna a can ne suke shari'a." Ya fara da karb'ar number Dady ga Audu sannan ya juya ya shiga mota, ya kama hanyar komawa kaduna misalin k'arfe 08:00pm ya isa garin kaduna. Cikin hanzari ya shiga kiran layin Dady ba jimawa ya d'aga, ba tare daya furta komai ba cikin wata 'yar murya yake fad'ar sunan sa. "Dady kana ina ya kamata mu had'u yanzu.?" *"Adeel* ďana da gaske kai zaka had'u da ni.?" "Eh Dady kawai ka sanar da ni kana ina.?" "Rabin raina ina Rahma hotel room 224." Ya amsa da ok sunyi sallama yaja mota ya fice, ya isa hotel ďin cikin hanzari ya nufi d'akin da yake, yana zaune ya ji a na buga masa k'ofa ya tashi ya tafi ya bud'e, kamar da wasa ya samu *Adeel* k'ofa cike da d'aukin ganin sa, Dady yayi hugging d'in sa yana sunbatarsa ya janyo sa sun shiga ciki. "Nayi matuqar yin kewarka sosai ďana nayi farin ciki sosai daka yanke shawaran dawowa gareni." "Dady kayi hak'uri dan Allah ka yafemin, na san cewar na cutar da kai sosai da rashina amma." "A'a ďana karka bani hak'uri sabo da baka yi komai, to ba buqatar sai ka bani hak'uri to ya jikin Mummyn ka.?" "Ta samu sauk'i sosai sabo da zuwa yanzu ta dawo haiyacinta, Dady na ji duk abin daya faru a gurin Audu to ina san zan taimaka." "A'a ďana ni sam bana san ka shiga cikin wannan ka ji ko." "Dady ni ba zan zuba ido na barka ba tare da nayi komai ba, sam bai kamata su Uncle Bashir suyi maka haka ba, amma ba komai zamu samu mafuta insha Allah da akwai wani Abokina, shi ďin Barrister ne kuma yana da kirki sosai sannan kuma zai taimaka sosai insha Allah. To yanzu ya kamata na tafi nayi magana da shi sai na dawo." "Na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka." Ya fad'a tare da sunbatarsa shi kuwa ya amsa da Amin yana murmushi. Ya tashi ya fita Dady ya bisa da kallo yana murmushi, tin a mota *Adeel* ya kira layin *Adnan* tare da tambayar sa yana ina, ya amsa shi da cewa yana gidan Abbu tare da *Adyan* ya amsa da ok sunyi sallama. Ya nufi can ya isa gidan ya same su wani kyakkyawan guri, wanda an yi sane musamman sabo da hutawa ya samu guri ya zauna, bayan sun gaisa *Adeel* ya sauke kallonsa ga fuskar *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* ina buqatar taimakon gaugawa sosai daga gareka." *"Adeel* kawai ka sanar da ni koma miye ni kuma zanyi nayi alkawari fad'a min miye.?" Nan kuwa ya shiga sanar da shi buqatar shi garesa. Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, "kayi hak'uri *Adeel* sabo da ni ba zan iya taimaka wa Dadyn ka ba." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. *"Adnan* mai ya saka ba zaka taimaki Dady na ba.?" Ya girgiza ka tare da furta ba komai, "Shikenan na gode sosai sai an jima." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyarsa, su kuwa sun bisa da kallo har ya b'ace............................ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/3, 11:15 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 25* *Sister Fatima Allah ya baki lafiya ya bawa Babyn ki lafiya.* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 28/02/2022* *Time 08:16pm* *Typing.................* Bayan tafiyar su sun dawo da kallonsu ga juna, *Adyan* ya shiga tambayar *Adnan* abin da yake faruwa. Yayi shiru kad'an sannan ya sanar da shi abin da yake faruwa, *Adyan* yayi jim kad'an sannan ya amsa shi. "Hakan yayi kyau ina fatan kar yayi nasara a kan wannan shari'ar, Allah ya hana masa gaske ya k'ara masa duhu fiye da wanda yake tare da shi sosai." "Amin Aboki nima wannan ne fatana to Allah ya amince mana Amin." "Amin bro ka shirya wa gobe domin zamu tafi gurin shari'ar, domin ganin yanda Prof Abas zai fad'i sabo da ba zai tab'a yin nasara ba." "Shikenan Aboki zan shirya wa hakan insha Allah." Magana suke cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar su, take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa ga wanda ya gani. Sun jima sosai a nan tare sannan daga bisani *Adnan* ya masa sallama ya tafi. Cikin rashin sa'a ya dawo masaukin Dady, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi, cikin hanzari Dady ya shiga tambayar sa abin da yake faruwa da shi, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Kayi hak'uri Dady sabo da *Adnan* ya kasa yarda da tayi na, sam yak'i amincewa da buqata na ya fad'a min cewar ba zai iya taimaka maka ba. Ba kuma tare daya sanar da ni wani dalili ba, Dady *Adnan* yana da matuqar kirki sosai amma ban san dalilin da yasa yayi haka ba, amma koma miye na tabbata yana da k'wakk'waran dalili wanda yake da matuqar girma sosai. Naso a ce na san gaskiyar ta yanda zan iya saurin fahimtar sa, Dady ni yanzu ban san ya zanyi ba amma ina ganin a yanzu mafia ďaya muke da shi. Dady kawai ka siyar da wasu daga cikin kadarorin ka, k'aramin Campany, Restaurant, ko ďaya daga cikin makarantu ta yanda zaka samu kud'ad'en da zaka biya su da shi." "A'a *Adeel* ni sam ba zanyi hakan ba ba zan rabu da komai nawa na, sabo da hakan sam ba laifi na bane ni sam ban aikata wani kuskure ba, to bai kamata su hukunta ni ta hakan ba, ďana ko da mai zai faru da ni to ba zan rabu da wani abu daga cikin kadara ta ba, nayi aiki tuk'uru sannan na sha wahala sosai kafin na gina kai na, *Adeel* kai kad'ai kake da hak'i da wannan duniyar tawa, kai kad'ai kake da mallakin duk wani abin dana mallaka, to ba zan tab'a barin na rasa duk wani abin da yake nawa ba wannan ce gaskiyar." "Dady ni kawai zan rayu cikin farin ciki ne idan kana farin ciki, kai nafi buqata fiye da duk wani abin daka mallaka, dan haka kawai kayi abin daya dace dan Allah karka bari su Uncle Bashir suci zarafin ka." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawa a tare da shi, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. Prof ya shiga rarrashin sa yana ba shi magana haka suka kasance, na tsayin wani lokaci sosai sannan daga bisani suka kwanta, washe gari misalin k'arfe goma na safe suka shiga kotu, bayan sauraran ko wane b'angaran na lauyoyi Al'qali ya yanke hukuncin cewa, Prof Abas zai biya su Prof Bashir duka kud'ad'ensu cikin mako biyu. A haka shari'ar ta tashi hankalin Prof Abas ya tashi sosai da hukuncin da Al'qali ya yanke, hakama *Adeel* shi ma yana tare da k'unci sosai tsaye suke jikin mota, suna tinanin mafua sai gasu *Adnan* bayan sun gaisa *Adyan* yaci gaba da magana. "Prof Abas Muh'd ya kamata muyi magana yanzu." "Waye kai kuma mai ya saka kake san kayi magana da ni.?" "Kana magana da *Adyan Ahmad Aliyu* to ya kamata ka saurare ni, sabo da zan iya taimaka wa ga buqatar ka to ya kamata, ka saurare ni sabo da a yanzu ni ne kawai wanda zai iya taimakon ka." "Waye kai da kake magana da ni haka cikin gadara.?" Kafin ya furta komai *Adeel* ya amsa shi ta hanyar sanar da shi waye shi, Dady ya jinjina ka tare da mai da kallonsa ga fuskar *Adyan* yana fad'ar sunan sa. *"Adyan* a kan me kake magana kuma wane taimako zaka yi min.?" "Prof Abas na san cewar a yanzu haka kana matuqar buqatar kud'i sosai, sabo da ka biya su Prof Bashir kud'ad'ensu to ni zan baka idan kana da buqata." *"Dr Adyan* wai da gaske kai zaka bawa Dady na wad'an kud'ad'en.?" "Eh *Adeel* zan ba shi duka kud'ad'en idan har zai siyar min da duka kadarorin sa." Da sauri har yana sarkewa Prof yake magana. "A'a ba zai yuba ni ba zan siyar da komai nawa na." "Shikenan kaci gaba da ri e kadarorin ka amma ka sani kawai zaka k'are ne a gidan yari." Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa *Adeel* yake magana. *"Dr Adyan* mai ya saka kake yiwa Dady na magana haka.?" *"Adeel* ni kawai ina tausayin Dadyn ka ne sannan kuma ina buqatar na taimake sa, amma kuma na gama fahimtar cewa shi sam baya buqatar hakan shikenan ni zan tafi." Ya juya domin tafiya da sauri *Adeel* ya dakatar dasu ta hanyar anbatar sunan *Adyan.* *"Dr Adyan* dan Allah d'an dakata kad'an." Ya jinjina masa ka a lamar to shi kuwa ya mai da kallonsa ga Prof tare da fad'ar sunan sa. "Dady zuwa yanzu bamu da wata mafua to na ro e ka daka siyar da duka abin da kake da shi, ka biya su Uncle Bashir kud'ad'ensu sabo da ba zan jure ganin ka a gidan kurkuku ba. Hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai to dan Allah karka bar hakan ta faru please." Magana yake cikin wani irin yanayi na damuwa sosai, yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Su *Adnan* sai wani kallonsa suke kallo sosai mai cike da jin tausayin sa sosai, sai sun bar abin a zuciyarsu ba tare da sun nuna ba cike da damuwa Prof yake magana. "Shikenan ďana zanyi hakan sabo da kai to ka dena kuka ka ji ko." Magana yake yana wani shafar fuskarsa tare da sunbatarsa, ya mai da kallonsa gasu *Adnan* tare da fad'ar sunan *Adyan.* *"Dr Adyan* zan siyar ma da makaranta da Restaurant amma banda k'aramar ma'aikata." "A'a ni duka ukun nake so musamman ma ma'aikatar ita ce abar da nafi so." "A'a ni ba zan iya rasa wannan campaning ba, sabo da shi ne kawai abin daya ragemin dan haka sai dai kawai na baka hak'uri." "Shikenan kawai mu fasa hark'allar ka ga sai ka shirya wa zama gidan kurkuku." "A'a hakan sam ba zai yu ba Dady naro e ka daka amince da buqatar sa, sabo da wannan ita kawai ce mafutar mu a yanzu." "A'a ďana ya kamata na bar wannan campaning sabo da kai, domin kai ne kawai wanda zai mallaki wannan campaning, sabo da ba zai yu na b'ata rayuwar yarona ba da hanayena. *Adeel* kai ďin ďana ne to zanyi komai sabo da kai ina sanka sosai yarona zo nan." Ya wani janyo sa jikin sa yana sunbatarsa su *Adnan* kuwa sai kallonsu suke. Bayan sun sake juna Prof ya sauke kallonsa ga fuskar *Adyan* yaci gaba da magana. *"Adyan* kawai ka bani kud'in na amince sabo da wannan buqatar yarona ce." Sai zuwa wannan lokacin ne *Adnan* yayi magana. "Prof Abas ga a lama kana qaunar yaronka sosai shin haka kake qaunar sauran yaran naka.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Ni yaro ďaya kawai nake da shi d'an da nake matuqar alfahari da shi, ba kuma kowa bane face *Adeel* shi ne d'an dana mallaka a rayuwata. Shi yasa nake matuqar masifar qaunar sa sosai shi yasa zan iya yin komai sabo da shi." "Hakan yayi kyau sosai, to yanzu sai ka had'a duka takardun guri ďaya ni kuma zansa a shirya kud'ad'en, sannan kuma kazo da mutanan da zasu zame maka shaida nima zanso da nawa shaidun. To muyi hakan zuwa yamma fatan ba zaka canja hakan ba.?" "Shikenan kawai ka sanar da *Adeel* inda zamu had'u da kuma lokacin da zamu had'u." "Hakan yayi kyau sosai ku zame ni gidan Abbu *Adeel* zai kai ka gidan, to ba zaka wahala gurin had'uwa da ni ba kazo k'arfe 05:00pm hakan yayi." Magana yake cikin isa tare da nuna gadara Prof sai wani kallonsa yake ba tare daya furta masa komai ba, sai dai *Adeel* ya amsa shi magana yake cike da k'unci tare da tarin damuwa sosai. *"Dr Adyan* koma dai miye wannan Dady na ne to zanyi farin ciki sosai idan ka mutunta shi, shikenan zamu zo gurin kamar yanda ka fad'a sannan kuma muna godiya sosai." Dukansu kallonsa suke yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare dasu, *Adyan* ya amsa shi ta hanyar jinjina masa ka a lamar to da kuma haka suka yi sallama. Dukansu suka nufi gida sun isa masauki Prof sai kai kawo yake yana huci *Adeel* ya anbaci sunan sa yana cewa. "Dady dan Allah ka dena wannan yawan damuwar sabo da yanayin zai iya cutar da kai sosai." "D'ana dole zan damu a kan hakan sabo da narasa komai a lokaci ďaya, *Adeel* na jima sosai ina shirya wa rayuwarka amma lokaci ďaya narasa komai. Sam ba zanso ka rayu kamar yanda ni na rayu ba, ina yi ma fatan ka rayu cikin kyakkyawar rayuwa ga shi kuma lokaci ďaya, komai ya lalace dan Allah ka yafemin na san cewa na cutar da kai da yawa to ina fatan zaka yafemin." "Dady shin ko zaka dena fad'ar haka? Ni kai na fiso fiye da duk abin daka mallaka, abin farin cikin shi ne kai ka bani duka soyayyar ka to wannan kawai ya isa, sannan kuma ina alfahari da hakan sosai ina sanka sosai." Cike da soyayyar juna sunyi hugging juna Dady sai wani sunbatarsa yake, bayan wani lokaci suka sake juna nan kuwa Dady ya shiga had'a takardu. Sun shirya duka takardun tsab yayin da k'unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare dasu, haka yake ko a gurin su *Adnan* suna isa gida *Adyan* ya fara shirya kud'ad'en, misalin k'arfe 05:00pm daidai su *Adeel* suka iso gidan Abbu. Ba jimawa suka had'u dasu *Adnan* ba wani d'aukan lokaci suka fara abin daya tarasu, bayan sun qarasa Prof Abas Muh'd ya bawa *Adyan* kundun takardu, shi kuwa ya ba shi kud'i an yi takardu sun saka hanu tare da duka shaidu. Bayan sun k'arasa kammala komai su Prof Abas sun tashi sun tafi, bayan tafiyar su sun mai da kallonsu ga juna *Adnan* ya anbaci sunan *Adyan* yana cewa. "Aboki bana tunanin cewa *Adeel* zai iya jure wannan, sabo da yanayin yana da zafi sosai Mum sam ba zata iya jure ganin shi a cikin wannan yanayin ba, to ya idan kuma yanayin sa yayi k'oqarin cutar da ita fa? Aboki ya kamata muyi tunani a game da wannan ina nufin yanayin Mum, Aboki ni kawai na damu ne a game da Mum da kuma yanayin da zata iya shiga." "Na fahimce ka Aboki amma kuma ya kamata muyi hakan, sabo da na tabbata idan Mum ta ji labarin cewa Prof Abas ya rasa koman sa to zata yi farin ciki sosai. To sam bana tunanin wani abu zai faru da ita to sam bai kamata mu samu damuwa ba." "Ina fatan hakan to yanzu miye tsarin mu na gaba.?" "Yanzu dai ni bani da wani shirin komai to kai kuma fa.?" "Aboki nima bani da wani shiri, amma kuma nayi matuqar damuwa sosai a kan *Maman Amna,* sabo da ita ďin tayi matuqar damuwa sosai a kanmu da kuma rayuwar mu, Aboki ni ina ganin kamar ya kamata muyi magana da ita, Aboki ina kamar akwai buqatar ita ta san gaskiyar a game damu, ko ba komai hankalin ta zai kwanta sannan kuma zata samu natsuwa." "Shikenan zamu yi magana a game da wannan wani lokaci." Ya fad'a yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan. Su Prof Abas sun isa masauki yayin da damuwa tayi yawa sosai a tare dasu, musamman ma Prof *Adeel* ya shiga rarrashin sa yana ba shi magana, har ya samu ya iya fahimtar sa haka yaci gaba da kasancewa tare da shi. Washe gari bayan sunyi break past *Adeel* ya sauke kallonsa ga Prof tare da fad'ar sunan sa. "Dady ni ina san zan tafi na duba Mum to ka kula da kanka sosai dan Allah." "Eh zanyi na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka." Ya amsa da Amin yana murmushi lokaci ďaya suka yi hugging juna, bayan wani lokaci suka sake juna *Adeel* ya tashi ya fita, ba jimawa da tafiyar sa Prof shi ma ya tashi ya fita. *Adeel* na cikin fira dasu Umma wayar sa ta d'auki ruri ya d'aga tare da sallama, daga ciki an amsa shi an kuma ci gaba da magana. "Kana magana da Dr Sauban Dadyn ka yana asibiti yayi hatsari." "Mine wane asibiti.?" "Hamdala hospital." Ya amsa da ok sunyi sallama ya fara sanar da Mum sannan ya tashi ya tafi, su Umma sun bisa da kallo suna girgiza ka har ya fice.................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/6, 12:48 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 46* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 04/03/2022* *Time 12:17am* *Typing................* Ya isa asibiti cikin hanzari tamkar wani zararre, nan ya shiga tambayar nurse inda Dadyn sa yake. Bai wani jima sosai ba ya samu isa d'akin da yake, Doctor's sun dakatar da shi daga shiga ciki ya shiga safa da marwa, bayan wani lokaci suka fito Dr Sauban ne yake magana da shi. "Kai ne yaronsa.?" Cikin hanzari har yana sarƙewa yake amsa mashi da eh Dr Sauban ya cigaba da magana. "Dadyn ka baya cikin kyakkyawan yanayi zan kuma iya cewa da kai, yanayin sa ya tsananta sosai yana matuƙar buƙatar taimakon gaugawa sosai." "Doctor dan Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da Dady na.?" "Am gaskiyar ita ce Dadyn ka ya samu karaya a duka k'afafun sa, ya zama dole a yi masa aiki yanzu sannan kuma yana buqatar jini sosai, sabo da ya rasa jini sosai yanzu ka biyo ni zuwa office sai muyi magana a can." Ya amsa da to sun juya sun nufi office ďin Dr Sauban, sun isa office d'in tare da shiga ciki bayan sun zauna Dr Sauban yaci gaba da magana. "Yanzu zamu tafi ka cike takardun tiyata sannan kuma ka bamu jini naka ko na wani daban." "Doctor nawa ne kud'in aikin.?" "Abin da yawa to kud'in zai iya kaiwa d'ari uku da hamsin." Cike da firgici ya wani zaro ido yana kallonsa, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Doctor dan Allah ko zaku iya yi masa aikin kafin na iya had'a muku kud'in please.?" "A'a sam hakan ba zai yuba kawai zamu yi masa aiki ne idan ka biya kud'in aiki." "Shikenan zan kawo kud'in yanzu bara na tafi na kawo kud'in." Dr Sauban ya amsa shi da to shi kuma ya tashi ya fita, zuwa wani gurin daban domin samo kud'in da za a yi masa aiki. Tin a hanya yake kiran layin *Adyan da Adnan* amma layin yak'i tafiya, hakan tasa ya nufi gidan Abbu gurin *Adyan* a nan ma yayi rashin sa'a sabo da baya gida. An sanar da shi cewar ya fita tare da *Adnan* cikin hanzari ya juya mota ya nufi gidan Papa, ganin motar *Adyan da Adnan* ya tabbatar masa da cewar dukansu suna ciki, ya fito mota ya nufi ciki zaune suke suna fira cikin kyakkyawan yanayi tare da matayansu, lokaci d'aya suka ji a na buga masu k'ofa, *Adnan* ne wanda ya tafi ya bud'e k'ofar ya samu *Adeel* tsaye bakin k'ofa. Yanayin sa yayi matuqar tsorata sa sosai cikin hanzari ya shiga anbatar sunan sa, kallonsa kawai yake ba tare daya amsa shi ba *Adnan* ya janyo hanun sa sun shiga ciki. Lokaci ďaya dukansu suka shiga tambayar sa abin da yake faruwa da shi, magana yake cikin wani irin mummunan yanayi mara dad'i yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. *"Adnan Adyan* naro e ku da ku taimaki Dady na, shi yayi hatsari yana cikin mawuyacin hali sosai, ya rasa jini sosai sannan kuma dole sai an yi masa aiki. Suna buqatar dubu d'ari uku da hamsin, mun riga da mun bawa Al'qali duka kud'ad'en to sam bana tunanin zai bani kud'in da nake buqata. To zanso wani daga cikin ku ya bani a ron kud'in ni kuma zan biya kud'in daga baya, *Dr Adyan* dan Allah zanso ka duba Dady na please." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da yake kuka. Lokaci d'aya tausayin sa ya shigesu sosai sun samu shiru na jim kad'an, sannan daga bisani *Adyan* ya amsa shi. *"Adeel* ina mai baka hak'uri a kan abin da ya faru da Prof, sannan kuma ina mai k'ara baka hak'uri sabo da ni ba zan iya duba Prof ba, hakama ba zan iya baka wani kud'i ba idan har zaka taimaki Prof da shi. Amma zan iya yin komai sabo da kai Umma da kuma Mum, to kawai saidai ni na baka hak'uri fatan zaka fahimci mai nake nufi.?" Ya jinjina masa ka a lamar eh ya mai da kallonsa ga fuskar *Adnan,* kafin ya furta komai yayi masa rigagi ta hanyar fad'ar sunan sa. "Kayi hak'uri *Adeel* sabo da ba zan iya canja abin da Aboki ya fad'a ba, amma dai ka da ka tab'a manta cewa dukanmu biyu muna nan domin ka, kuma zamu iya yin komai sabo da kai Umma da kuma Mum, ba zamu tab'a barin wani daga cikin ku ya cutu ba zamu kare ku iya rayuwarmu. Wannan alkawari ne kuma zamu tabbatar da cewar mun cika alkawarin mu insha Allah." Yayi shiru kad'an sannan yana nazari sannan daga bisani ya fara magana. "Na san cewar kun taimake ni da yawa sannan kuma kun kula dani sosai da ma ahalina. Kunyi matuqar damuna sosai a kai na Mummy na da kuma Kaka ta, hakan yana matuqar yi min dad'i sosai shi yasa na fara yi muku kallon ahalina. Amma kuma ni na rasa dalilin da yasa kun kayi matuqar tsanar Dady na sosai, na san cewa Dady na ya aikata laifuka da dama a rayuwarsa, musamman cutar da Mummy na da yayi to amma kuma ku bai wani cutar daku ba, amma kuma duk da haka kunyi matuqar masifar tsanarta sosai, amma kuma duk da haka ni ina alfahari daku sosai ni zan tafi sai munyi magana ina godiya sosai da kulawa." Ya tashi jiki a san yaye ya tafi dukansu sun bisa kallo har ya fice, bayan tafiyar sa *Afnan* ta mai da kallonta garesu, sai wani kallonsu take kallo mai cike da jin mamakin su sosai, cike da jin mamakin abin da suka yi take magana. "Besty wai mai kun ka aikata ne haka? Ta ya ma zaku yi tunanin cutar da *Adeel* har haka? Shi kamar ahalinmu ne yana da kirki sosai sannan kuma yana mutunta ku sosai, dukanku biyun kuna da damar da zaku taimake sa to amma mai ya saka ba zaku taimake sa ba? Hakan sam bai dace ba ya kamata kuyi abin daya dace ina nufin ku taimake sa dan Allah." Kallonta kawai suke yayin da suka gagara furta mata komai, *Adeel* ya fito domin tafiya ya samu Papa tsaye gefen k'ofa, zai fad'i sunan sa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar girgiza masa ka. Ya janyo hanun sa sun nufi wani guri daban Papa ya anbaci sunan sa yana cewa. *"Adeel* na riga da naji komai a game da Dadyn ka, kayi hak'uri da abin dasu *Adnan* suka fad'a a game da Dadyn ka, ni zan kula da komai to yanzu zamu iya tafiya can asibitin ni zanyi duk abin daya kamata." "Na gode sosai Papa Allah ya saka da alkhairi Amin." Ya amsa da Amin yana murmushi sun juya sun nufi mota ko wannan su ya shiga motar sa sun tafi. Sun isa asibitin Papa ya had'u da Dr Sauban sunyi magana a game da aikin, Papa ya biya duka kud'ad'en na komai da komai, *Adeel* ya saka hanu a kan takardar aikin bayan wani lokaci suka shiga da shi d'akin tiyata. Bayan an shiga da shi d'akin tiyata Papa ya sauke kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* dan Allah ko zaka iya sanar da ni wani abu a game da Dadyn ka.?" "Papa ni ban san wani abu a game da shi ba bayan shi karan kansa. Shi kad'ai yake ba shi da kowa sai ni mu biyu kawai muke da junanmu." Cike da jin mamakin abin daya fad'a Papa yake magana. *"Adeel* shin Dadyn ka bai sanar da kai komai a game da shi ba? To kawai ka sanar da ni cikakken sunan sa da garin sa.?" "Eh na san wannan sunan sa Prof Abas Muh'd Kankiya." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Mine Abas Muh'd Kankiya.?" *Adeel* ya jinjina masa ka a lamar eh Papa ya ci gaba da magana. *"Adeel* shin bai tab'a sanar da kai komai a game da ahalinsa ba? Sannan kuma bai sanar da kai komai a game da K'ank'ara ba.?" "A'a sam bai sanar da ni komai ba a game da K'ank'ara ba. To amma mai ya saka kake tambaya wannan.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Am dama da naji ka fad'i cikakken sunan sa sai na ji kamar na san sunan tin da jimawa, amma shi wanda na sani a K'ank'ara yake sannan kuma yana da k'ani, na jima sosai ina nai man sa amma sam ban samu had'uwa da shi ba, to ina fatan Dadyn ka ya kasance mutumen da na jima ina nai ma." "Amin Papa ina yima fatan samun mutumen daka jima sosai kana nai ma, to amma mai ya saka kake nai man wannan mutumen.?" *"Adeel* ina nai mansa ne sabo da na had'a shi da k'anin sa. Wanda a kullum kuma a ko yaushe yake kukan rashin sa tare da fatan sake had'uwa da shi." "Allah sarki gaskiya ya bani tausayi sosai ina fatan ya had'u da Yayansa cikin sauri." Papa ya jinjina masa ka yana wani gajeran murmushi shi ma abin da yake yi kenan. Bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka tare da shi a d'akin tiyata, sun fito cikin hanzari dukansu sun isa ga Dr Sauban, tare da tambayar jikin Prof yayi shiru kad'an sannan ya amsa su. "Mun kai shi d'akin hutu domin ya huta." "Doctor to ya yanayin samun saukin sa shin yana samun sauki sosai.?" "Ba zan iya sanar daku komai ba a game da wannan, sabo da har yanzu baya cikin kyakkyawan yanayi duk da cewar ya fita cikin hatsari, amma zai samu lafiya insha Allah to zaku iya duba shi yanzu." Ya mai da kallonsa ga wani nurse wanda yake tare da shi ya fad'a masa cewar ya kai su d'akin da Prof yake, ya amsa shi da to Dr Sauban kuwa ya juya ya nufi office ďin sa, su kuma sun nufi d'akin da Prof yake sun isa d'akin tare da shiga ciki, da sauri *Adeel* ya k'arasa inda yake sai wani kallonsa yake kallo sosai, lokaci ďaya kuma ya saki kuka kuma kuka yake sosai. Cike da jin tausayin sa Papa ya k'arasa inda yake ya shiga rarrashin sa, sai wani lalla'basa yake yana ba shi magana yayin da tausayin sa yayi yawa a tare da shi sosai. Bayan wani lokaci ya sake sa ya nufi gurin Prof yake kallo sosai, ya sauke kallonsa ga gefen kafad'ar sa sai wani kallon gurin yake kallo sosai. Ya mai da kallonsa ga fuskar sa sai wani kallonsa yake kallo sosai, lokaci ďaya kuma ya samu kansa da zubar da kwalla cike da jin mamakin sa *Adeel* yake magana. "Papa mai ya saka kake zubar da kwalla shin qlau kake kuwa.?" "Ba komai d'ana kawai dai ina farin ciki ne shi yasa har nake zubar da kwalla." "Papa mai ya saka kake farin ciki sosai har haka.?" "ina farin ciki ne sabo da Dadyn ka shi ne mutumen dana jima ina nai ma." "Mine ta ya a kai ka gane shi cikin sauk'i haka.?" *"Adeel* hakan yana da matuqar sauk'i sosai a gareni idan har zan gansa, sabo da nayi matuqar sanin sa sosai duba nan kaga." Ya kai kallonsa ga gefen kafad'ar Prof inda yayi masa nuni da shi, yayi tozali da wani k'aramin tabo ya mai da kallonsa ga Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin kai ka san wani abu a game da wannan tabon.?" "Eh ďana amma zamu magana a game da wannan wani lokaci." Ya jinjina masa ka a lamar to ganin ya jima sosai bai dawo ba yasa *Adnan* kiran layin sa ba jimawa ya d'aga. "Papa kana ina? Lokaci ya tafi sosai amma har yanzu baka dawo gida ba, shin qlau kake kuwa gaskiyar zaka sanar da ni dan Allah.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Rabin raina ina lafiya kawai na d'an biya ta wani guri ne, amma yanzu zan dawo gida insha Allah to ka kula da duka gidan ka ji ko." "Eh Papa zanyi amma dan Allah ka dawo gida yanzu sabo da munyi kewarka sosai, sannan kuma ka kula da kanka sosai dan Allah." "Eh zanyi masoyi Allah ya ma albarka ďana." Ya amsa da Amin da kuma haka suka yi sallama. Bayan sun k'arasa waya Papa ya kai kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* ka kula da Dadyn ka sosai idan da akwai buqatar nazo to kawai ka kira layi na, ni kuma zanzo nayi alkawari insha Allah to zan tafi sai na dawo ka kula sosai ka ji ko." Ya amsa shi da to tare dayi masa godiya Papa murmushi kawai yayi masa ba tare daya furta masa komai ba. Sai ma tashi da yayi ya fita domin zuwa gida ba jimawa da tafiyar su *Alishart* Papa ya dawo gida, bayan sun gaisa sun tashi sun nufi tebur sunci abinci, bayan sun k'arasa sun koma parlour sunci gaba da fira, ba kuma tare da Papa ya sanar dasu komai a game da Prof ba. Sun d'an jima a parlour suna fira sannan daga bisani suka tafi suka kwanta, washe gari bayan sunyi break past dukansu sun tashi sun nufi office. Tin daya fita gida take aikin kiran layin sa amma har safe layin sa baya tafiya, hakan yayi matuqar d'aga hankalin ta sosai wanda ko barci bara iya yi ba, tin da sassafe ta kira layin *Adnan* amma bai tafi ba sai daga bisani, sannan ta iya samun sa yana k'oqarin shiga office wayarsa ta d'auki ruri, ganin wacce take kiran sa yasa shi d'aga kiran bayan sun gaisa taci gaba da magana. *"Adnan* dan Allah ko kayi magana da *Adeel?* Tin yammacin jiya nake kiran layin sa amma baya tafiya, *Adnan* dan Allah ka sanar da ni gaskiyar inda yarona yake.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta. "Mum ina ga kamar ni na san gunda za a iya samun sa, to sam ba buqatar kici gaba da d'aga h ki sosai yanzu zanso na kai ki inda yake." Ta amsa shi da to sunyi sallama ya juya ya nufi office ďin Papa, abin da yafi ba shi mamaki shi ne rashin samun Papa a office, cike da jin mamakin rashin ganin sa ya ciro waya ya shiga kiran layin sa, cikin rashin sa'a layin yak'i tafiya haka ya hak'ura ya juya ya nufi gidan Mum....................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/9, 3:48 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 47* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Sunday 06/03/2022* *Time 03:19pm* *Typing................* Ya isa gidan Mum tare da shiga ciki ya same ta a cikin wani irin yanayi, sai kai kawo take yayin da tunanin inda zata ga yaronta yayi yawan gaske a tare da ita. Umma sai rarrashin ta take tana bata magana cikin hanzari, *Adnan* ya isa inda take yana fad'ar sunan ta ya janyo hanun ta ya zaunar da ita sannan ya fara magana. "Mum mai yake faruwa dake ne haka shin qlau kike kuwa dan Allah ki sanar da ni.?" *"Adnan* ni kawai na damu ne a kan *Adeel* tin yammacin jiya daya fita, har yanzu ban k'ara jin komai ba daga garesa ba, kuma layin sa baya tafiya sannan kuma shi bai kira ba, *Adnan* ni ina tsoron kar wani abu ya faru da shi sabo da ba zan iya jure ba domin." Da sauri *Adnan* ya dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a Mum sam ba abin da zai faru dake shi ma zai kasance cikin k'oshin lafiya sosai, to zaki iya yarda da ni amma kinyi kalaci kuwa.?" Ta girgiza masa ka tare da furta a'a yaci gaba da magana. "Mum lokaci ya tafi sosai zuwa yanzu ya kamata a ce kinci wani abu, yanzu ni zan had'a maki break past bayan kin kammala sai mu tafi gurin *Adeel.* Idan kuma kika ce a'a to da zanyi fishi kuma fishi sosai." "Shikenan zanci na gode sosai da kulawa Allah ya ma albarka." Ya amsa da Amin yana murmushi ya kuma ci gaba yana cewa. "Mum zanyi farin ciki sosai idan kika saka wa Abokina albarka shi ma ina nufin *Adyan."* Tayi murmushi sosai tare da shafar fuskarsa. "Shikenan ďana zanyi hakan Allah yayi muku albarka dukanku." Ya amsa da Amin yana murmushi sannan ya tashi ya nufi kicin, bayan daya gaisa da Umma yana cikin aiki sai ga Mum ta isa inda yake, tare da fad'ar sunan sa ya amsa yana murmushi yaci gaba da magana. "Mum mai yasa kika zo nan.?" "Nazo ne domin na ta ya ka aiki ta yanda zamu kammala cikin sauri." "Shikenan ina farin ciki sosai da zanyi aiki tare dake." Murmushi kawai tayi masa mai tare da dariya shi ma abin da yake yi kenan. Ba jimawa suka kammala sun shirya komai a kan tebur sannan daga bisani suka fara break past, bayan sun k'arasa ya d'auki Mum sun fita zuwa asibiti domin had'uwa da *Adeel.* Zaune suke yayin da suka saka Prof gaba da ido turo k'ofar da a kai ne, yasa su kai kallonsu ga k'ofa dan ganin mai shigowa sunyi ido biyu da fuskar Dr Sauban. Ya k'arasa ciki bayan ya duba jikin Prof sannan ya basu takardar magani, Papa ya karb'i takardar maganin ya fita domin ya kawo maganin. *Adeel* ya shiga yi masa godiya murmushi kawai yayi masa sannan ya juya ya tafi, ba jimawa da tafiyar Papa ya ji a na buga masa k'ofa ya tashi ya nufi k'ofa, ya bud'e k'ofar kamar a mafarki ya samu Mum da *Adnan* tsaye a bakin k'ofa. Cike da d'aukin ganin sa yayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa, bayan sun sake juna ya mai da kallonsa ga fuskar, *Adnan* wanda shi ma kallonsa yake sun samu shiru na jim kad'an sannan *Adeel* ya fara magana. "Mai kuma kake yi a nan mai yasa kazo nan.?" *"Adeel* ni nazo nan ne sabo da Mum, ita d'in ta damu ne sosai a kanka ba kamar kai ba, tin yammacin jiya ka tafi amma kuma baka kira ka sanar da ita wani abu a game da kai ba. Hakan yasa ta damu sosai har ma ta gagara cin abinci, *Adeel* wannan babban kuskure ne ka aikata sannan kuma." "Ya isa haka *Adnan* karka ce zaka koya min yanda zan kula da mahaifiya ta, ita d'in Mummy na ce kuma na san ta yanda zan kula da ita sosai, na san cewar kai ka taimake ni sosai dama duka ahalina musamman Mummy na. Amma kuma na rasa dalilin da yasa kai kayi matuqar tsanar Dady na sosai, na san cewar Dady na ya aikata kuskure sosai a rayuwar sa, musamman ma ta yanda ya cutar da Mummy na, amma kuma ku biyun bai cutar daku ba hasalima bai tab'a sanin ku ba, amma kuma kuna cutar da shi sabo da kune yake cikin kyakkyawan mummunan yanayin. Da a ce kai ka yarda da ka amshi shari'ar sa to da duka wannan bai faru ba, amma sai kak'i dalilin haka yasa yayi hatsari sannan kuma *Dr Adyan* ya gagara duba shi. A baya har na fara tinanin cewar ni daku 'yan uwan juna ne har ina kiran mu da ahali ďaya, amma kuma da hakan ta faru sai na fahimci a salin gaskiyar waye ni a gareku, amma kuma duk da haka ina mai alfahari daku sosai, tare da nuna godiya ta a gareku ina godiya sosai hakama ka isar da sakon godiya ta ga *Dr Adyan."* Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, kafin *Adnan* ya furta komai Mum tayi masa rigagi. *"Adeel Adnan* shin ku ukun kuna fad'a ne.?" "A'a Mum sam ba kamar yanda kike tinani bane, sam bama fad'a da juna *Adeel* ne kawai bai fahimce mu ba, amma wani lokaci zai fahimci komai to ni bara na tafi sai an jima." Ta jinjina masa ka tana murmushi *Adeel* kuwa sai kallonsa yake, ya juya domin tafiya bai k'arasa kai wa k'ofa ba sai ga Papa ya shigo, da sauri ya wani zaro ido yana kallonsa cike da jin mamakin ganin sa yake magana. "Papa mai kuma kake yi a nan? Ta ya ma har kai ka san cewar Prof yana asibiti.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi.?" "Masoyi karka yi fishi sosai haka sabo da zan sanar da kai duka gaskiyar." Nan ya shiga sanar da shi komai sannan yaci gaba yana cewa. "Rabin raina *Adeel* yana matuqar buqatar taimako sosai shi yasa na taimake sa." "Papa ni zan iya yin komai sabo da *Adeel* Mum ko kuma Kaka amma wannan a kan Prof ne, shi sam bai cancanci tausayawar mu ba sam bai kamata ka taimake sa ba. A k'alla ya kamata kayi magana da ni kafin ka yanke hukunci, sabo da bai kamata ka shiga wannan ba sabo da Prof mutum ne mai hatsari sosai. Sannan kuma yana cutar da mutanan da suke da kusanci da shi, shi mugun mutum ne dan haka bai kamata ka taimake sa ba hakan sam bai dace ba." Cike da fishin zuciya *Adeel* ya dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa cikin tsawa, har yana ďaga murya cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Ya isa haka Barrister cin zarafin ya isa haka ba kuma zan lamunta ba, koma dai miye ya aikata shi ďin mahaifina ne kuma kuskuran sa bai hana ni sansa ba. Kai sam baka san waye Dady na ba shi yasa kake muzantasa haka, kuskuran sa ďaya daka sani bai isa ya tabbatar maka da cewa shi mutumen banza bane, ko wane bawa yana aikata kuskure to amma mai ya saka kai ka tsani Dady sosai? To hakan ya isa ya kamata ka dena ko kuma dai kai kaga a salin b'acin raina." Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai, *Adnan* yayi wani gajeran murmushi na bak'in ciki sannan ya fara magana. *"Adeel* ni sam ba zan ga laifin ka ba sabo da kai baka san a salin gaskiyar waye mahaifin ka ba, sabo ya rai neka ne cikin k'arya yana yawan fad'a maka cewar yana sanka, amma kuma gaskiyar ita ce bai tab'a sanka ba, amma zaka fahimci hakan a lokacin da ka san gaskiyar waye mahaifin ka." Ya mai da kallonsa ga fuskar Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zamu iya tafiya yanzu.?" "Rabin raina kamar dai kana cikin fishi sosai? Wannan yanayin sam bai dace da kai ba domin kuwa zai iya cutar da kai sosai, da kuma lafiyar ka hakan kuma barazana ce a garemu, sannan kuma na tabbata Mamie ba zata tab'a yafemin ba to dan Allah ka dena cutar da kanka haka please." "Papa ni kawai na damu ne a kanka, sabo da ba zanso Prof ya cutar da kai ba to kawai ka fita daga rayuwar sa dan Allah." Papa yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi. "Kayi hak'uri ďana sabo da ba zan iya fita rayuwarsa ba, ko da ma kuwa a ce zai cutar da ni sosai kamar yanda kake tunani, sabo da ba zan iya barin sa ba to kayi hak'uri a kan hakan." "Papa wai mai kake fad'a ne haka waye shi ďin a gareka da ba zaka iya barin sa ba.?" Yayi shiru kad'an tare da jan numfashi sannan ya amsa shi. "Rabin raina shi ďin Kawun ka ne sabo da shi ďin Yayana ne, wanda na jima sosai ina nai ma bayan wasu tsayin shekaru jiya na koma had'uwa da shi. Shi yasa ba zan iya rabu da shi ba ina fatan zaka fahimce ni sannan kuma ba zaka yi fishi da ni ba dan Allah." Wani irin kallo dukansu suke masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, cike da k'uncin abin daya fad'a *Adnan* yake magana. "A'a hakan sam ba gaskiya bane sam bai kamata hakan ta kasance ba, ni sam na kasa yarda cewa wai shi ďin Yayanka ne, Papa ta ya a kai ka iya gane sa cikin sauri haka? Papa wannan fa yana buqatar nazari to karka yi saurin amincewa da shi, sabo da zai iya cutar da kai sosai please." "Masoyina gane Yayana yana da matuqar sauk'i sosai a gareni kamar dai kai d'ana, duk da cewar hakan ta faru tin muna yara amma kuma ba zai yi iya goge tabon sa ba, sannan kuma jinin mu ba zai canja ba kamar yanda bai iya sauya a salin sunan sa ba. Tabon dana gani a gefen kafad'ar sa da kuma jini na da a ka sanya masa ya isa ya tabbatar da gaskiyar, shi ďin Yayana ne sunan sa Prof Abas Muh'd ni kuma Adam Muh'd, dukanmu iyayenmu ďaya kai da *Adeel* ahali ďaya ne to kawai kuyi farin ciki." Motsin da suka ji ne yasa su kai kallonsu garesa cikin hanzari *Adeel* da Papa sun isa inda yake, *Adnan* kuwa ya rufe su da ido hakama Mum ita kallonsu take. Wacce kuma har yanzu bata furta komai ba sun shiga yi masa sannu ya amsa tare da tambayar *Adeel* waye Papa, yayi shiru yana nazari jin yayi shiru ne yasa Papa magana. "Am da fari sunana Adam Muh'd K'ank'ara kuma ni ne mahaifin *Adnan* abokin *Adeel.* Yaya ina fatan ka gane k'anin naka.?" "A'a sabo da ni bani da k'ani to zaka iya tafiya kawai ka bar nan ka ji ko." "A'a Yaya dan Allah karka fad'i haka ni na san cewar ka gane ni to mai yasa ba zaka amince da ni ba.?" "Na ce ka tafi to kawai ka tafi ka bar ka ji ko." "A'a Yayana ni ba zan tafi ba sabo da." "Malan ya isa haka na fad'a maka cewar bani da wani k'ani to kawai ka tafi, k'ila kuma gaskiyar ka ne a baya ina da k'ani amma shi wannan k'anin nawa, ya mutu ne a rana d'aya da mahaifiyar sa dalilin da yasa na rayu ni kad'ai kenan. To dan haka kai ba zaka tab'a kasancewa k'ani na ba, to yanzu zaka iya tafiya sannan kuma karka k'ara nuna min wannan fuskar taka, daga k'arshe kuma ka fad'a wa yaronka ya fita daga rayuwar d'ana." Cike da fishin zuciya *Adnan* ya k'arasa gurin su yana cewa. "Kai waye da zaka yi magana da Papa haka? Shi mutum ne wanda yake da daraja da kuma kima a gurin mutane, ba kamar kai ba shi yazo gurin ka cikin qauna da soyayya amma kuma kai, sai kake k'oqarin fusata shi to fa ka sani idan har ka bari ya fusata, to fa ni da kai na zan hukunta ka dan haka ka ki yaye ka ji ko." "Adam irin tarbiyar daka bawa yaronka kenan? Amma banyi mamaki ba sabo da kai ma irin tarbiyar daka samu kenan, shi yasa yaronka shi ma ya tashi haka to ba zan bar irin wannan ya kasance tare da yarona ba. Dan haka ka fad'a masa cewar ya rabu da yarona, sannan kuma kai karka k'ara nuna min wannan fuskar taka na har abada." "Yaya zaka iya hukunta ni ta duk yanda kake so, duk da cewar bai aikata maka wani zunubi ba, amma sam ba zan baka damar da zaka ci zarafin yarona ba. D'ana a gareni tamkar zinari ne azurfa koma na kira shi da lu'ulu'u, babu wani abin da nake so fiye da ďana sabo da shi ne rayuwata gaba d'aya. D'ana shi ne komai nawa a salin farin ciki na zan iya yin komai sabo da shi, ina matuqar qaunar ka sosai Yayana amma bai kai kamar yarona ba. Yanzu kana cikin fishi sosai zamu tafi wani lokacin zamu dawo." Ya mai da kallonsa ga *Adeel* yaci gaba da magana. *"Adeel* ka kula da shi sosai kai ma ka kula da kanka ka ji ko." Ya jinjina masa ka tare da furta to ya mai da kallonsa ga fuskar *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. "Mu tafi rabin raina dan Allah." Ya jinjina ka cike da fishin zuciya yake magana. "Papa wallahi tallahi idan wannan mutumen ya k'ara fad'ar wani abu a kanka, to zan manta cewar shi d'in Yayanka ne na hukunta sa, ta duk yanda naga dama ba kuma tare da nayi dana sanin hakan ba." Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Papa ya shiga rarrashin sa yayi hugging d'in sa yana sunbatarsa, tare da furta masa dad'ad'an lafuzza masu kwantar da hankali, ya ja hanun sa sun nufi hanyar fita domin tafiya, *Adnan* ya sauke kallonsa ga fuskar *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* ka kula da Mum sosai sannan kuma ka tabbatar Dadyn ka bai cutar da ita ba, koma mai zai faru to ka tabbatar ta kasance lafiya ka ji ko." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa, da sauri Papa ya fita ya bisa a baya yana fad'ar sunan sa, su Mum sun bisu da kallo har suka b'ace............... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/10, 10:43 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 48* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 07/03/2022* *Time 11:18pm* *Typing................* Bayan tafiyar su *Adeel* ya maida kallonsa ga fuskar Mum ,lokaci ďaya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take, sun samu shiru na jim kad'an sannan Mum ta fara magana. *"Adeel* karka bari wannan abin da ya faru yasa kayi tunanin, rabuwa da *Adnan* ko kayi cin zarafin sa ko wani abu daban. Abin duba a nan shi ne waye a salin mak'iyin nasa, shi abokin fad'an nasa tamkar maciji ne yana iya cutar da kowa, musamman ma mutanan da suke tare da shi. Kai kariga da kasan komai a game da mugun halinsa, to ya kamata ka bud'e idanuwanka da kyau domin ka karb'i gaskiya, *Adnan* yaron kirki ne sosai sannan kuma yana qaunar mu sosai. Balantana kuma yanzu kuma da gaskiyar ta fita da cewar, ku biyun ahali ďaya ne hakan yayi matuqar yi min dad'i sosai. To kawai kayi abin daya dace ka ji ko, yanzu lokaci ya tafi sosai zuwa yanzu ya kamata kayi kalaci, to mu tafi domin kaci abinci sabo da ba zan iya jure zama a nan ba, kuma sam ba zan jure jin kalmar a'a daga bakinka ba kawai mu tafi dan Allah." Kallonta kawai yake sai daga bisani sannan ya jinjina mata ka, a lamar to ya kuma ci gaba da magana. "Mum shin ba zai yu naci abincin tare da Dady ba.?" "A'a ďana ban shirya hakan ba na kai kawai nayi. Ba kuma zan iya ba shi yaci ba to mu tafi dan Allah." "Amma Mum." *"Adeel* kawai kayi shiru mu tafi." Ya jinjina mata ka a lamar to tare da mai da kallonsa ga Prof tare da fad'ar sunan sa. "Dady zan tafi amma ba zan jima ba zan dawo gareka insha Allah." "Na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka ka kula da kanka sosai, sannan kuma ka kula da Mummyn ka sosai sabo da tana cikin fishi sosai, wani lokacin zan samu nayi magana da ita sai ka dawo." Ya jinjina masa ka a lamar to sun juya sun fita Prof ya bisu da kallo har suka b'ace, sun fito sun samu wani guri daban sun zauna *Adeel* ya anbaci sunan Mum yana cewa. "Mum na san cewar kina matuqar yin fishi da Dady sosai, amma kuma zuwa yanzu ya kamata ki sauki daga wannan dokin fishin, ko dan wannan yanayin da Dady yake Mum ko fa sannu baki yi masa ba, sannan kuma yanzu kin hana shi abinci Mum dan Allah karki zama kamar shi please." *"Adeel* da a ce na kasance kamar shi to da nayi k'oqarin cutar da shi kamar yanda ya min, amma kuma banyi hakan ba rabin raina bayan cutar da mahaifin ka ya min, sai na ji bani da wani babban mak'iyi a cikin wannan fiye da shi. To sam bana jin cewar zan iya taimaka masa da komai kayi hak'uri." "Shikenan Mum ina fatan zuwan rana ko lokacin da zaki yafe wa Dady na." *"Adeel* har yanzu shi Dadyn ka bai buqaci dana yafe masa ba, hakan yana nufin cewar bai shirya nai man afuwata da gafarata ba. Wannan yana nufin cewar bai yi nadamar duk wani abin daya aikata min ba, to dan haka ba buqatar ka damu sosai a kansa ka ji ko yanzu kaci abinci." Ya jinjina mata ka tare da furta mata to, nan kuwa ta fara ba shi abinci bayan sun k'aras ta tashi ta tafi, *Adeel* ya mata rakiya sai da ta tafi sannan ya juya ya koma gurin Dadyn sa. Ya shiga ciki ya same sa kamar dai yanda ya barsa ya isa inda yake ya zauna tare da fad'ar sunan sa. "Dady duk da cewar kai ne wanda ya raine ni amma kuma ka gagara sanar da ni gaskiyar waye kai, kana da k'ani amma baka tab'a sanar da ni ba mai yasa? Dady k'ila a baya Papa ya tab'a aikata maka wani laifi amma kuma hakan bai dakatar da shi daga sanka ba. Yayi komai domin ganin ka samu lafiya har ma jinin sa ya baka, sannan ya biya maka duka kud'ad'en asibiti, kuma yayi hakan cikin nuna qauna da soyayya amma kuma kai mai kayi? Dady sam bai kamata ka dakatar da Papa zuwa gareka ba sabo da shi ďin d'an uwa na gari ne a gareka. Dady naro e ka daka amince da Papa a matsayin ďan uwa na gari a gareka dama *Adnan* dan Allah." Prof yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa shi. *"Adeel* abin sam ba shi da sauki kamar yanda kake tunani, ďana wannan mutumen da yake kiran kansa da k'anina, shi da mahaifiyar sa sunyi matuqar cutar da ni sosai, sam na kasa manta irin abin da suka aikata min shi yasa ba zan iya amincewa da shi ba kayi hak'uri." "Amma Dady." "A'a ďana kawai kayi hak'uri dan Allah." Ya jinjina masa ka a lamar to daga bisani yaci gaba da magana. "Dady lokaci ya tafi sosai ya kamata kaci abinci, yanzu fad'a min mai zaka ci na kawo ma.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka kawai ka kawon samosa abin da nafi so." "Shikenan Dady yanzu zan tafi na kawo." Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan. Ya juya ya fita domin kawo masa abin daya buqata daga garesa wato samosa, ba jimawa sosai ya dawo wanda kuma shi ne da kansa yake ba shi yana ci har ya k'arasa. Tin da jimawa ya gama fahimtar cewa yaron nasa sam baya cikin kyakkyawan yanayi, yana k'oqarin shiga mota Papa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. "Masoyi sam baka cikin kyakkyawan yanayi to ina ga sam bai kamata kayi tuk'i a haka ba, to ni zan tafi tare da kai kuma ba zan amince da jin kalmar a'a ba dan Allah." Ya jinjina masa ka tare da furta masa to, ya rufe motar sa ya juya ya shiga motar Papa sun nufi gida. Ganin yanda yanayin sa yake ta canjawa yasa Papa ya koma gefen hanya yayi parking, yasa hanunsa aljihu ya ciro maganin sa tare da d'aukar bowar ruwa, ya mai da kallonsa ga fuskar yaronsa tare da fad'ar sunan sa. "Masoyi ka sha maganin ka sabo da akwai buqatar ka huta dan Allah." Ba gardama ya karb'i maganin daga hanunsa ya sha cikin tautasa murya yake magana. "Na gode sosai Papa da irin yanda kake kulawa da ni sosai, ko yaushe kana nuna min qauna sosai tare da nuna min soyayya, duk da cewar na girma sosai amma kuma har yanzu kana nuna min cikakkiyar kulawa sosai, kamar sanda nake yaro gaskiya kai uba na gari ne a gareni, ina godiya sosai da samun ka ina qaunarka sosai fiye da yanda nake sanka I love you so much Papa." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, cike da qaunar sa ya janyo sa zuwa jikin sa tare dayi masa kyakkyawar runguma sosai yana sunbatarsa. "Rabin raina kai ďana ne to lalle ya zama dole a gareni dana baka duka soyayya ta, masoyina gaskiyar ita ce kai ne nan abin da nafi so fiye da komai dana mallaka a rayuwata. *Adnan* ni zan iya yin komai sabo da zanma iya baka rayuwata gaba d'aya, ina sanka sosai d'ana Allah ya ma albarka ya kuma sanya wa rayuwarku albarka data yaronku gaba." Ya amsa da Amin tare da k'ara shigewa jikin sa, sun jima sosai a nan sannan daga bisani Papa ya ja mota suka tafi. Sun isa gida zuwa wannan lokacin barci ya fara kama idon sa, Papa ya fito ya zaga ya bud'e masa k'ofa ya rik'o hanunsa ya fito, ya janyo sa jikin sa sun shiga ciki sun samu su Mamie zaune a parlour, ganin Papa ri e da shi ya tabbatar musu da cewar ba lafiya ba, yasa su *Afnan* tashi tsaye cikin hanzari har tana sarkewa Mamie take magana. "Subhanalillah Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un mai yake faruwa da shi ne haka.?" Sun k'arasa ciki Papa ya shinfid'e sa a kan doguwar kujera, kafin Papa ya amsa ta *Adnan* ya amsa ta. "Mamie ina lafiya ki yarda da ni qlau nake to dan Allah karki yi k'unci kin ji ko please." "Rabin raina kawai kana san ka kwantar min da hankali ne, amma gaskiyar ita ce baka da lafiya kuma kana tare da k'unci sosai, wanda kuma hakan barazana ce ga lafiyar ka sosai ya kamata mu tafi asibiti yanzu." "A'a Mamie ni qlau nake ina lafiya sannan kuma." Lokaci ďaya kuma wani wawan barci yazo ya d'auke sa, Mamie ta mai da kallonta ga fuskar tare da fad'ar sunan sa. *"Abban Adnan* ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da yarona? Mai ya saka shi k'unci sosai har haka sannan kuma mai ya saka kazo da shi nan a maimakon asibiti.?" Shiru bai amsa ta ba yayin da k'unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare da shi sosai. Yanayin sa ya k'ara tabbatar musu da cewar ba lafiya ba, cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita *Afnan* take magana. "Papa wai mai yake faruwa ne mai ya saka ku biyun kuke tare da k'unci sosai? Na tabbata wani abu ya faru daku to dan Allah ka sanar damu abin da yake faruwa.?" "Zan sanar daku komai bayan ya samu lafiya." Sun jinjina masa ka a lamar to ganin yanda yake ta kiran layin sa bai d'aga ba, yasa shi kiran layin *Afnan* domin ya ji ko lafiya, zaune suke yayin da suka saka *Adnan* da kallo wayar *Afnan* ta d'auki ruri, ganin mai kiran ta yasa ta d'aga kiran ba kuma tare data furta masa komai ba daga ciki ya anbaci sunan ta. *"Afnan* Aboki fa tin da jimawa nake kiran layin sa amma baya d'aga wa shin qlau yake kuwa.?" Tayi shiru kad'an sannan ta shiga sanar da shi abin da yake faruwa, cike da firgicin abin data fad'a yake magana. *"Afnan* to mai ya saka baki sanar da ni ba? A k'alla zan duba shi sannan kuma na ba shi kulawa sosai gani nan tafe." Ta fara da ba shi hak'uri sannan suka yi sallama, ba jimawa sosai sai ga *Adyan* wanda kuma tare yake da *Alishart.* Ya fara gaisawa dasu Mamie sannan ya shiga duba shi, bayan ya k'arasa ya mai da kallonsa gasu Papa tare da fad'ar sunan *Afnan. "Afnan* shin yayi wani abin daya gajiyar da shi ne? Ko a'a wani ya b'ata ransa sosai wanda har ya saka shi k'unci sosai? *Afnan* ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da Abokina waye wanda yake da alhakin cutar da shi sosai har haka.?" "Ban sani ba Doctor sai dai kayi magana da Papa, sabo da shi ne wanda yake da sani a kan komai." Ya mai da kallonsa ga Papa tare da tambayar sa abin da ya faru da *Adnan,* ganin yanda yake tayi masa magiya yasa ya yanke shawaran sanar da shi. *"Adyan* yayi musayar baki ne da *Abban Adeel* ne." "Mine shi har ma ya isa ya cutar da shi sosai har haka, a'a ni ďin nan zan hukunta shi a bisa zunubin sa, sabo da ba zan tab'a gafarta wa duk mutumen daya cutar da Aboki na ba. Yanzu ka sanar da ni a wane asibiti Prof yake da akwai buqatar nayi magana da shi yanzu.?" Papa ya girgiza masa ka tare da furta, "A'a ďana ba buqatar sai ka tafi can sabo da Abokin ka yana matuqar buqatar ka a yanzu, to ya kamata ka kasance a nan tare da shi ina ga hakan zai fi." Ya jinjina masa ka a lamar to tare da ciro wayar sa, ya shiga dannawa ba jimawa ya kara a kunne ba jimawa ya fara magana. *"Adeel* na san cewar kana tare da Prof to ka saka ni a amsa kuwa zanyi magana da shi." Ya amsa shi da to yayi kamar yanda ya fad'a, shi kuma yaci gaba da magana. "Prof a gaskiya yau ďin nan ka aikata min mummunan zunubi, ta hanyar cutar da Abokina da kayi to kayi fatan kar ya jima sosai cikin wannan yanayin, ta yanda zan sauk'ak'a maka hukunci ko kuma dai na cutar da kai sosai." Yana kai k'arshen maganar sa ya kashe wayar sa, ba ma tare daya jira ya ji abin da za shi fad'a ba...................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/12, 7:55 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 49* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Thursday 10'03/2022* *Time 03:24pm* *Typing..............* Duk kan su sun gama fahimtar cewa yana cikin fushi sosai, sun riga da sun san waye *Adnan* a garesa shi yasa sam basa mamakin sa. Parlour yayi shiru na jim kad'an Papa ne ya kau da shirun parlour ta hanyar fad'ar sunan *Adyan. "Adyan* dan Allah karka yi fushi sosai sabo da hakan zai iya cutar da kai sosai, na san cewar ka damu sosai a kan abokinka, to zai kasance lafiya insha Allah, na tabbata duka wannan zai wuce komai zai zama daidai, ni da kai na zan gyara komai to zaka iya yarda da ni." "Papa wannan a game da abokina ne to zan iya aikata komai ga mutumin, da yayi yunk'urin cutar da shi koma waye Papa na rantse." Da sauri Papa ya rufe masa baki tare da furta masa a'a. "A'a ďana dan Allah karka fad'i komai, kawai ka barni zan daidaita komai nayi ma alkawari insha Allah." *Adyan* dai kallonsa kawai yake yayin da yake magana da zuciyarsa. "Na rantse idan wannan yanayin ya cutar da d'an uwa na, to sai na tabbatar da cewa Prof ya shiga k'unci wanda har sai ya gwammaci mutuwa fiye da rayuwa. Ya aikata abubuwa da dama a rayuwarsa amma wannan shi ne, babban zunubin da zai aikata a gareni wanda kuma zai karb'i hukunci daidai da zunubin sa. Kayi hak'uri Papa sabo da ba zan iya amincewa da tayin ka ba dole na cutar da Prof, wannan alkawari ne kuma zan tabbatar cewa na cika alkawari na insha Allah." Bayan wani tsayin lokaci daya d'auka a kwance ya farka, sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e, sai wani kallon mutanan da suke tare da shi yake suma haka kallonsa suke. Lokaci ďaya kuma suka shiga furta masa kalmar sannu, kamar ba zai amsa ba sai daga bisani ya amsa su, zamu iya cewa har zuwa wannan lokacin baya cikin kyakkyawan yanayi, jiki a san yaye ya tashi ya nufi d'akin sa Papa zai bisa, *Adyan* ya dakatar da shi tare da tashi ya bisa a baya. Ya shiga ciki ya same sa sai safa da marwa yake, *Adyan* kuwa sai kallonsa yake daga bisani kuma ya ja hanun sa suka tafi suka zauna. Sun samu shiru na muntuna biyu zuwa uku sannan *Adyan* ya fara magana. "Aboki mai ka aikata ne haka a wane dalilin ne yasa zaka yi musayar baki da Prof? Aboki hakan bai dace ba sannan kuma ka sab'a wa yarjejeniyar mu, sabo da muna shirya komai ne a tare amma kayi wannan ba tare daka sanar da ni ba mai yasa? A k'alla ya kamata ka sanar da ni ko ba komai zan iya kareka daga cutarwar sa. Kai ba kawai Abokina bane a'a kai ďin d'an uwa na ne kuma abin da nafi so fiye da komai, Aboki bayan Appa da Ammie to kai ne abin da nafi so shi yasa nake matuqar baka kulawa sosai. Aboki nayi matuqar damuwa sosai dana kira layin ka baka d'aga ba, nayi matuqar shiga firgici da rud'ani tare da tashin hankali sosai, a lokacin da *Afnan* ta sanar da ni halin da kake ciki, sam na kasa jure ganin wannan yanayin naka, Aboki da a ce wani abu ya faru da kai fiye da haka to da ba zan tab'a yafewa kai na ba na har abada. Sabo da na kasa kare ďan uwa na wannan abin kunya ne da bak'in ciki a gareni, Aboki wallahi tallahi ba zan tab'a yafe maka ba idan har ka k'ara aikata haka, sannan kuma zanyi matuqar yin fishi da kai sosai to yanzu kayi min, alkawarin cewa ba zaka k'ara yin komai ba tare da sani na ba dan Allah." Yayi shiru kad'an tare da jan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya, cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana tamkar da zai saki kuka. "Kayi hak'uri Aboki bawai dan karan kai na, na had'u da Prof ba a'a wannan buqatar Mum ne, sabo da tana da buqatar had'uwa da *Adeel."* Na ya shiga sanar da shi komai cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adyan* yake magana. "Aboki wai mai kake fad'a ne haka ta ya Papa da Prof suka kasance 'yan uwa.?" "Ban sani ba Aboki amma dai da jimawa na san cewa Papa yana da Yaya, wanda bai san inda yake ba amma ban tab'a tunanin cewar Yayansa zai kasance a matsayin Prof ba. Papa yana da matuqar kirki sosai banso a ce Prof ya kasance Yayansa ba, amma kuma sam bani da wani zab'i sabo da ba zan iya hana faruwar hakan ba, amma kuma duk da haka ina farin ciki ta wani gefen, abin shi ne har yanzu Papa ahalina ne wannan shi ne abin da nafi komai dad'i. Aboki yanzu ka fad'a min mai zanyi musamman ga Papa sabo da Prof yana barazanar cutar da Papa na." "Aboki mafua ďaya muke da shi a yanzu, kawai mu tafi muyi magana da Papa ya sanar damu komai a game da Prof, ina daga nan ne zamu iya sanin abin da zamu yi." Ya jinjina masa ka tare da furta to sun tashi sun fita, sun kuwa samu su Mamie zaune a parlour bayan sun zauna, *Adnan* ya sauke kallonsa ga fuskar Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zaka iya sanar damu wani abu a game da Prof dan Allah.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Masoyi abin shi ne tin muna yara ni ko da na tashi ban samu Baba na a raye ba. Bayan haka kuma mu talakawa ne sosai wanda abinci ma wahala yake mana sosai, wani lokacin abincin kad'an ne hakan ke sawa Mama take bani ta hana Yayana, abin da bata sani ba shi ne hakan yana matuqar saka Yayana k'unci sosai. Ganin yanayin yana dad'a tsananta sosai yasa Mama ta yanke shawaran kai Yayana makaranta almajiranci, ta had'a masa d'an abin da take da shi ta kai shi makaranta, duk da kasancewa ta yaro sosai d'an shekaru biyar amma nayi kuka sosai, sabo da na saba da Yayana sosai hakama bayan tafiyar sa, a kullum a ko yaushe cikin zancan a kai ne garesa nake bayan wasu watanni, Mama ta shirya tare da duk wani abin buqata muka nufi gurin Yayana domin ziyartar sa. Sun isa makarantar cike da d'aukin had'uwa da shi, inda kuma a nan ne malamin su yake sanar da Mama cewa, tin washe garin ranar da a ka kawo shi makaranta ya gudu ba wanda ya san inda yake." "Hankalin Mama yayi matuqar tashi sosai da jin wannan mummunan labarin, wanda har sai da yayi sanadin haifar mata da ciwon zuciya, wanda yayi sanadin mutuwar ta na shiga k'unci sosai a wannan lokacin, wani mak'ocin mu Kawu Bala shi ne wanda yaci gaba da kulawa da ni kamar d'an ta, duk da cewar ba shi da mata sannan kuma bai tab'a aihuwa ba. Haka nayi ta fad'i tashi ina nai man kud'i daga bisani na saka kai na a makaranta wato boko, ina S. S. Two Kawu Bala ya rasu na shiga k'unci sosai sabo da shi ďin uba na gari ne a gareni. Haka dai naci gaba da rayuwa da dad'i da ba dad'i tare da bawa karatuna muhimmanci sosai, nayi nasaran kammala karatuna na secondry har ma na shiga babbar makaranta, inda nake karantar fannin shari'a kuma a can ne na had'u da mahaifiyar ka, mun fara ne da k'awance daga bisani kuma ya zama soyayya, duk da cewar na sanar da ita komai a game da ni da kuma rayuwata amma bata gujeni ba, ta bani duka soyayyar ta sannan kuma ta soni da duka zuciyarta. Ita d'in ta musamman ce a gareni hakama iyayen ta sun amince da ni a matsayin siriki, bayan mun kammala karatu muka yi aure." "Mun aifeka cikin qauna da soyayya bayan wasu shekaru muka aifi qanwarka, amma kuma har zuwa wannan lokacin ban manta Yayana ba. babu wata rana da zata riskeni ba tare dana tuna da Yayana ba, ďana ni na rayu da burin sake kasancewa tare da Yayana amma kuma shi ni matacce ne a gurin sa dama Maman mu, masoyi shi Yayana ko Maman mu bai iya tambaya na ba balantana lafiyar ta. Rabin raina sam na kasa fahimtar abin da yake faruwa da Yayana, ina tunanin da akwai wata cutar da take damunsa ya kamata nayi magana da likitan sa a yi masa a won kwakwalwa, domin gano a salin abin da yake faruwa da shi." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, dukansu sun cika da jin mamakin abin daya fad'a, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana yayin da yake kuka. "Papa sam bai kamata ka damu da mutum irin Prof ba, hakama sam ba buqatar ka saka a yi masa a won kwakwalwa sabo da qlau yake, tsabar rashin mutunci ne kawai a tare da shi, sannan kuma d'abi'ar sa ce cutar da duk mutanan da suke tare da shi. Ya fara ne da Kaka ta da kuma kai Mum da kuma *Adeel* dama wasu da dama, yin hakan halaiyarsa ce to ba wanda ya iya ya canja shi, to ya kamata ka barsa sannan kuma ka dena nuna kulawar ka a kansa. Sabo da sam ba zan jure ganin irin yanda yake cin zarafin ka ba, sabo da ba zanyi k'asa a guiwa ba gurin cutar da shi ba, abin farin cikin shi ne ka kasance d'a na gari a gurin Kaka da Kawu Bala, sannan kuma ka kasance k'ani na gari a gurin Prof duk da k'ok'arin sa na cutar da kai. Sannan kuma muji na gari a gurin Mamie, kuma uba na gari a gareni da qanwata da kuma Besty." "To wannan kawai ya isa dan Allah kawai ka huta, sannan kuma zanso ka bani damar da zanyi magana da shi dan Allah." Yana cikin magana kuka yaci k'arfin sa yayi shiru ya kamata aikin kuka, da sauri dukansu biyun suka isa garesa lokaci d'aya suka yi hugging d'in sa, sun shiga rarrashin sa sai wani lalla'basa suke suna ba shi magana. *Adyan* ma yana cikin yanayi irin nasa wanda shi ma kwalla yake zubarwa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Shi ma sun shiga rarrashin sa bayan wani lokaci *Adyan* ya tafi wanda kuma tare da *Alishar* ya tafi, bayan kwana biyu da yamma lis suka nufi gidan Mum domin su duba ta. Sun isa gidan tare da shiga ciki sun same su suna shirin fita, sun koma sun zauna sun gaisa bayan sun gaisa, *Adnan* ya shiga tambayar su inda zasu tafi Mum ta amsa shi. "Am zamu tafi gurin *Adeel* ne domin mu kai masa abinci, sannan kuma mu duba shi ko yaushe yana asibiti shi yasa muke tare da kewarsa sosai." "Shikenan muma zamu tafi tare daku." "Shikenan ďana zamu iya tafiya yanzu." Ya jinjina mata ka tare da mai da kallonsa ga *Adyan* tare da furta masa kalmar mu tafi, ya amsa shi da to sun tashi sun fice sun isa asibiti kai tsaye d'akin da Prof yake suka nufa. Sun shiga ciki sun samu *Adeel* yana ba shi abinci a baki, cike da d'aukin ganin su yake fad'ar sunayen su, ya tashi ya nufi inda suke cike da qauna yayi hugging d'in Mum. ita kuwa sai wani sunbatarsa take su *Adyan* kuwa sai kallonta suke, bayan sun sake juna ya gaisa da dukansu bayan sun gaisa, Mum taci gaba da magana da shi. *"Adeel* lokaci ya tafi sosai to ya kamata kaci abinci, ni zan baka da kai na to mu tafi." "Mum shin ba zai yu naci abincin a nan ba dan Allah.?" "Rabin raina ni kawai ba zan jure zama a nan ba, amma zanyi hakan sabo da kai zan baka a nan." Yayi murmushi sosai tare dayi mata godiya murmushi kawai tayi masa ba tare data furta masa komai ba. Sun zauna Mum ta fara ba shi abinci su *Adnan* sai kallonsu suke, daga bisani kuma suka mai da kallonsu ga Prof, wanda shi kuma su Mum yake kallo sun juya sun nufi inda yake, hakan yasa ya dawo da kallonsa garesu lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna. Cike da izza da gadara tare da nuna isa yake musu magana. "Mai kuma kazo yi nan? Bayan na fad'a maka cewar ka fita daga rayuwar d'ana, idan ma Adam ne ya sake turoka garemu to ka koma ka fad'a masa cewar ni bana buqatar ku, bawai Adam kawai ba ko dama kuwa a ce Kakar ka ce ta turoka gareni sabo da." Ya isa Prof kayi shiru haka karka ce zaka yi magana a kan ahalina, musamman Papa domin zan manta dangantakar da take tsakanin ku na hukunta ka. Ka gode Allah daka samu k'ani kamar Papa duk da irin zunubin ka, ina ta ya Papa takaicin samun ka a matsayin Yayansa da kuma *Adeel* da yazo matsayin ďanka. Dama wasu yaran da kayi sanadin salwantar rayuwarsu, Prof kai mugu ne kuma azzalumi kaci amanar mutane da dama kuma dukansu ahalinka ne." "Da fari Maman ka k'anin ka yaranka matarka da kuma d'ayan ďanka. A dalilin ka ne Kaka ta ta rasa ranta Papa kuma ya rayu cikin k'unci, bayan wani lokaci kuma kai da hanayenka ka kashe yaranka, bama tare da mahaifiyar su ta gansu ba sannan kuma kayi wa kowa k'arya cewa d'a d'aya ka aifa a madadin uku. Ni na riga da na san duka gaskiyar amma kuma duk da irin wannan mummunan zunubin naka, kana kiran mahaifina mai laifi kai baka tab'a san kowa ba musamman ma *Adeel.* Da Mum kayi musu k'aryan cewa kana qaunar su amma kuma daga k'arshe ka cutar dasu sosai, kaci amanar Mum ta hanyar kashe mata yara kasa an cire mata mahaifa, a dalilin ka kuma ta kamu da cutar hauka ka sake ta a lokacin da take buqatar taimakon ka." "Sannan kuma ka raba ta da d'ayan ďanta, wai kai wane irin mutun ne mai yasa kaddara ta sanya ka a cikin ahalinmu? Prof wallahi naso a ce wannan hatsarin da kayi bai barka ka rayu ba, ta yanda ahalinmu ba zasu yi k'unci ba amma yanzu sabo da kai duka ahalin suna tare da k'unci sosai. Prof wallahi ba zan tab'a yafe maka zunubin daka aikata ba na har abada nayi matuqar tsanar ka sosai." Magana yake cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa sosai, yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Hakama *Adyan* abin da yake yi kenan, cike da jin mamakin abin da suka ji ya fad'a Mum take magana. *"Adnan* wai gaskiya ne abin da kake fad'a kuwa.?" "Eh Mum zama ki iya tambayar sa duka gaskiyar amma kawai kiyi magana da shi." Ta amsa shi da to tana wani jinjina ka shekaru ashirin da biyu kenan, ya d'auke su basu yi magana da juna ba, ta juya kallonta garesa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi ma kallonta yake cikin mutuwar jiki da sanyin murya take magana da shi........................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/15, 12:14 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 50* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Friday 11/03/2022* *Time 05:43pm* *Typing.................* "Bani da wani zab'i sabo da kaddara ta riga da ta k'ara bani damar da zanyi magana da kai, nayi fatan a ce ni d'in nan ban k'ara ganin ka ba, amma mun k'ara had'uwa sabo da *Adeel* yanzu ka fad'a min wani abu, shin gaskiya ne abin da *Adnan* ya fad'a kai ka kashe min yara.?" Magana take cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai. Shi kuwa banda kallonta ba abin da yake wanda kuma hakan ne, ya hana masa iya furta mata komai sai ma mai da kallonsa ga, *Adnan* da yayi tare da fad'ar sunan sa cike b'acin rai yake magana. *"Adnan* a zahirin gaskiya ka aikata min babba kuma mummunan zunubi sosai, waye ya baka damar da zaka yi binkice a kai na ba tare da sani na ba? Ka fara da rashin amsa shari'a ta sannan kuma Abokinka, yayi k'oqarin mallakar duk wani abin dana mallaka. Ya kuma k'ara da rashin duba ni ba jimawa kuma mahaifin ka ya baiya a matsayin k'anina, yanzu fad'a min dalilin da yasa kayi binkice a kai na mai ya saka kake shiga rayuwata.?" "Prof tin bayan da ni na sake had'uwa da *Adeel* na buqaci da na san waye ka, bayan kuma na had'u da Mum yanayin rashin lafiyar ta, yayi matuqar d'aga hankalina sosai sai bayan data samu lafiya ne, sannan na fara binkice a kanka kuma nayi nasaran samun duk abin dana nai ma. Sabo da nayi nasaran had'uwa da Dr Salim sannan kuma ya kai ni can gidan marayun, amma nayi nasaran sa'a sabo da sun tabbatar min da cewar, yaran sun mutu tin suna jarirai sabo da basu da lafiya sosai. Kai d'in gaba d'aya baka da sa'a shi yasa ka kasance a haka." Cike da k'unci bak'in ciki b'acin rai tare da tarin damuwa ta k'arasa inda yake, lokaci d'aya ta shiga kai masa tafi sai kai masa mari take tana kuka. "Mugu azzalumi kai wane irin uba ne wanda zai kashe yaransa da hanayensa? Auran ka da nayi shi ne babban qalubale na a rayuwa, hak'iqa nayi matuqar nadamar auran ka da nayi, na aure ka da zuciya ďaya amma kuma kai dame ka saka min? Kawai sai ka zab'i daka cutar da ni har ma da yaranmu ka daka a ciki, bama tare daka bani damar da naga yaran ba a matsayina na uwa. Wallahi tallahi ba zan tab'a yafe maka wannan ba na har abada." Magana take tana kuka wanda kuma har zuwa wannan lokacin dukansa take, *Adyan* ya k'arasa inda take tare da rungumata jikin sa ya shiga rarrashinta. Lokaci ďaya kuma ta sulale a k'ara ta sume, cikin hanzari dukansu sun nufi gunta suna fad'ar sunan ta, amma sam ba wata a lama wacce ta nuna cewa zata farka. Nan kuwa *Adyan* yasa a ka kai ta d'aki na musamman wanda kuma shi ne da kansa yake duba ta, dukansu ukun suna tare da ita ďakin yayi shiru ba mai magana, *Adnan* ya anbaci sunan *Adyan* tare da furta masa su koma gefe. Ya amsa da to ya tashi sun fice daga d'akin sun samu wani guri daban sun zauna, bayan sun zauna *Adnan* yaci gaba da magana. "Aboki ina ga kamar lokaci yayi wanda Mum zata san duka gaskiyar, ko kuma dai wannan yanayin nata yayi tsanani sosai, Aboki ita d'in mahaifiyar mu ce to ba zata tab'a yin abin da zai cutar damu ba. Zata fahimce mu sannan kuma zata amince da k'udirin mu, to ya kamata muyi abin daya dace dan Allah mu amince da gaskiyar sabo da farin cikin Mum." "Aboki ni kawai na damu ne a kan ahalinmu sabo da bana san wani abu ya cutar dasu, amma shikenan na amince da hakan sabo da Mum." "Na gode sosai daka iya fahimta na." "Aboki shin ko zaka dena wannan godiyar please.?" Murmushi kawai yayi masa mai tare da dariya shi ma abin da yake yi kenan, lokaci ďaya kuma suka samu kansu da yin hugging juna, bayan wani lokaci suka sake juna suka tashi suka koma ciki. Sun samu Umma zaune a kusa da ita yayin da *Adeel* yake ta aikin kai komo, su kuwa sai wani kallonsu suke cikin hanzari *Adeel* ya anbaci sunan *Adyan.* *"Dr Adyan* mai yake faruwa da Mummy na kuma yaushe zata farka.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan daga bisani ya amsa shi. *"Adeel* dukanmu a nan mun san irin abin da yake faruwa da Mum idan har tayi fishi sosai, to kawai tana buqatar hutu sosai sannan kuma ba zan iya sanin lokacin da zata iya farkawa ba. Zata iya jimawa sosai ko kuma a kasin haka to kawai mu jira tashin ta." Ya jinjina masa ka a lamar to tare dayi masa godiya kallonsa kawai yayi ba tare daya furta masa komai ba, ya juya ya fita dukansu sun bisa da kallo har ya b'ace, yana fita kai tsaye d'akin da Prof yake ya nufa. Ya shiga ciki ya same sa cikin wani irin yanayi mara dad'i, kallo ďaya tak zaka yi masa ka fahimci cewar yana tare da k'unci sosai, yanayin daya gansa ciki yayi matuqar d'aga hankalin sa sosai, yana k'oqarin fad'ar sunan sa yayi saurin dakatar da shi yana cewa. "Dady gaskiyar Barrister ne kai ba zaka tab'a san kowa ba, sannan kuma yayi gaskiya daya kira ka da maciji sabo da kana cutar da ahalinka, Maman ka k'anin ka yaranka matarka da kuma ni. A kan me zaka kashe min 'yan uwa? Sannan kuma kayi wa kowa k'aryan cewa ni kad'ai ka aifa, na tabbata kayi hakan ne kawai sabo da wani buri naka, gaskiya ka cutar da Mum da yawa kuma har yanzu abin da kake yi kenan. To bara ka ji wallahi tallahi idan wani mummunan abu ya faru da Mummy na, ni da kai na zan hukunta ka to kayi fatan ta samu sauki cikin sauri, a dalilin ka ne na rasa Kaka ta sannan na ni santa da Kawu wato Papa, ka kuma kashe abokan aihuwa ta sannan kuma ka shiga tsakanina da Mummy na. Dady ni kuwa wane irin zunubi na aikata da a ka hukunta ni da samun uba irin ka, Dady ni ji nake kamar ban tab'a sanin ka ba sabo da k'arya kawai kake fad'a min, amma yanzu da ni na san duka gaskiyar wallahi tallahi." Da sauri Dady ya dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar. "A'a ďana a'a dan Allah karka fad'i komai eh na amince da duka abin daka fad'a, na san cewar nayi ma k'arya a kan komai amma soyayya ta a gareka gaskiya ce, ina sanka ďana wallahi ina matuqar masifar qaunarka sosai. Ko da a ce zanyi k'aryan komai to banda soyayyar ka, hakama ko da a ce zan iya cutar da kowa to banda kai, sabo da kai d'ana ne kuma ina qaunarka sosai dan Allah ka yarda da ni wallahi ina qaunarka sosai." "Dady amma kuma kai ka kashe wasu daga cikin yaranka, to mai yasa nima ba zanyi tunanin cutar lokaci kake jira domin ka cutar da ni ba.?" "A'a rabin raina ni ba zan tab'a cutar da kai ba, sabo da kai ne abin da nafi so fiye da komai sabo da kai kad'ai ne d'an da nake da shi. To dan Allah karka barni naro e ka ka da ka barni please." "Dady Ubangiji ya baka yara uku a lokaci ďaya a maimakon ka gode masa, sai ka zab'i daka butulce masa ina ma a ce bani bane wanda ka zab'a ba, ta yanda ba zan fuskanci wannan mummunan ranar ba. Mai yasa ka zab'e ni a cikin ukun mai yasa sai ni.?" "Rabin raina bani bane wanda ya zab'e ka ba kaddara ce ta zab'a min kai, na kuma yi matuqar farin ciki da hakan sosai sabo da kayi daidai da ra'ayi na. *Adeel* gaskiya ita ce ni banma ga wa 'yan can yaran ba, sabo da farin cikin had'uwa da kai masoyi ni dama d'a ďaya kawai nake da kwad'ayin na aifa kuma kai ne, na gaji wannan a gurin Kakar ka ita ta zab'i k'anina fiye da ni. Tana ba shi abinci ta hana ni daga k'arshe kuma ta kai ni makaranta almajiranci, na kasa jurewa shi yasa na gudu nayi tafiya ta, na had'u da wani mutum wanda ya zama uban gida na. shi ne wanda ya koya min yanda zanyi kasuwanci, daga bisani kuma na shiga makaranta ďana tin daga ranar da, Mama ta kai ni almajiranci na shafe babin ta ita da ďanta. Ban kuma k'ara wai wayar su ba har kawo yanzu da muke magana, to ya kamata kayi min adalci dan Allah karka barni please." "Bani da wani zab'i sabo da Mum tana buqata na a yanzu, to zan tafi gareta ka kula da kanka sosai sai na dawo." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyar sa gurin Mum, ya samu su Umma a tare da ita shi ma ya mai mi guri ya zauna, misalin k'arfe 08:00pm Mum ta farka daga dogon suman da tayi, cikin hanzari sun shiga yi mata sannu kallonsu kawai take ba tare data amsa su ba. Kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, cike da kulawa Umma take magana da ita. "Aisha na san cewar wannan yanayin yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai, amma baki da wani za'bi sabo da ba zamu iya canja gaskiyar ba. To ya kamata kiyi hak'uri ki jure sabo da ba zan iya jure ganin ki, a cikin irin wannan mummunan yanayin ba domin hakan yana matuqar cutar da ni sosai." "Umma ta ya zan iya mantawa da wannan cikin sauki? Ta ya Prof zai aikata min haka ni uwa ce to bai kamata ya aikata min haka ba, ta ya zai rabani da yarana bama tare dana saka su ga idanuwana ba? Umma ta ya ma Prof zai yi tunanin cutar da ni sosai har haka? Ya kasa bani damar da zan kasance tare da yarana, ya kuma hana ni damar kasancewa uwa ta gari a garesu, hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai, wallahi tallahi ba zan tab'a gafarta masa wannan ba na har abada." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da take kuka kuma kuka sosai, Umma ta shiga rarrashin ta tana bata magana hakama *Adeel* abin da yake yi kenan. Su *Adyan* kuwa sai kallonsu suke kallo mai cike da jin tausayin Mum sosai, *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. "Aboki ina ganin cewar yanzu ne lokacin daya dace Mum ta san gaskiyar." Ya jinjina masa ka tare da furta masa kalmar ok shi ma ya jinjina masa ka, tare da mai da kallonsa gasu Umma ya nisa tare da jan numfashi, ya k'ara da sauke a jiyar zuciya sannan ya anbaci sunan *Adeel.* *"Adeel* ina ga ni da Aboki zamu iya daidai komai insha Allah." Kafin ya amsa shi Mum tayi masa rigagi. "A'a *Adnan* kawai ku bari haka na gode da kulawa, amma ba abin da zaku iya yi sabo da ba zaku dawo min da yarana ba. Na riga na rasa su ba tare dana ga ko fuskarsu ba, wannan ne abin da yafi cutar da ni fiye da komai, na tabbata wannan k'uncin zai d'auke ni na har abada." Kuka yaci k'arfin ta tayi shiru ta kama aikin kuka kuma kuka sosai, cike da tausayin ta sun tashi dukansu sun nufi kusa da ita, sun zauna sai wani kallonta suke kallo sosai lokaci ďaya kuma suka shiga share mata kwalla, yayin da suma kwallar suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. *Adnan* ya kama hanayen ta tare da fad'ar sunan ta, magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan sanar daku shi ba. "Mum ni zan iya dawo maki da wannan." Cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. *"Adnan* shin wai kai ka fita haiyacinka ne? Ta ya zaka dawo da yaron da suka riga suka mutu.?" "Eh Mum ni zanyi hakan sabo da akwai buqatar kiyi farin ciki, sannan kuma da ina lokaci yayi wanda zaki rayu tare da duka yaranki. Mum gaskiyar ita ce har yanzu yaranki suna raye, sannan kuma dukansu biyun sun kasance kamar yanda kike fata. Mum gaskiya ke kina da matuqar sa'a sosai a rayuwa, kina samun duk abin da kika yi fata wannan ma farin nasaran ki ne. Ko wane d'a zai so yayi nasaran samun uwa ta gari kamar ki, kin kasance kamar Mamie na da kuma Ammie dukanku iyaye na gari ne a garemu, kuma dukanmu muna alfahari da hakan sosai." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan fad'ar sa ba, dukansu sai kallonsa suke yayin da suka gagara fahimtar abin da yake fad'a, cike da jin mamakin abin daya fad'a Mum take magana. *"Adnan* dan Allah ka fad'a min ina yarana suke? Dan Allah ka fad'a min suna ina sabo da ina buqatar had'uwa dasu sosai to yanzu fad'a min suna ina dan Allah.?" *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi ma kallonsa yake ya kuma jinjina masa ka a lamar ya sanar da ita, ya amsa shi da to ta hanyar jinjina masa ka ya mai da kallonsa ga Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum gaskiyar ita ce kin jima sosai tare da yaranki, kuma ko yaushe kina kulawa dasu sosai kamar dai yanda suma suke baki cikakkiyar kulawa sosai." *"Adnan* wai a kan me kake magana ni sam na gagara fahimtar ka.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta. "Eh Mum ina nufin kin jima sosai tare da yaran kuma zan iya cewa, duka yaran naki suna tare dake Mum ni da kuma Aboki mune yaran da kika rasa." Dukansu wani irin kallo suke yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a. *"Adnan* wai gaskiya kake fad'a kuwa.?" "Eh Kaka ni gaskiyar nake fad'a sabo da nayi binkice a game da wannan tin da jimawa." Nan ya shiga sanar dasu komai daya faru cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. "Tin da jimawa kun san gaskiyar to amma mai ya saka ni baku tab'a tunanin sanar da ni ba.?" *Adyan* ne wanda ya amsa ta wanda kuma sai zuwa wannan lokacin ne yayi magana. "Mum bamu da wani zab'i ne sabo da ba zamu iya cutar da iyayenmu ba, ta hanyar sanin gaskiyar dukanku kun san irin soyayyar da iyayenmu suke yi mana, Mum ba zamu iya yafe wa kanmu ba idan har wani mummunan abu ya faru da ahalinmu ba, musamman iyayenmu shi yasa muka yi shiru bamu sanar da kowa gaskiyar ba. Yanzun ma muna masu rok'onku da karku sanar da kowa wannan gaskiyar, kawai mu bar wannan a tsakaninmu ina nufin ya zama sirri dan Allah please." Magana yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai hakama *Adnan* abin da yake yi kenan, wani irin kallo take yi musu mai tare da so, yayin da take jin qaunar su tana zaga ko ina na jikin ta. Ta shiga share musu kwalla tare da sunbatarsu ta k'ara da yin hugging d'in su, cike da qauna da soyayya take magana dasu.............. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/16, 11:47 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 51* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 14/03/2022* *Time 12:14am* *Typing................* *"Adyan* ni na fahimce ku amma duk da haka ya kamata nima na san gaskiyar, a gaskiya nayi matuqar farin ciki sosai da Ubangiji ya bani ku a matsayin yarana. Ban tab'a tunanin cewar ni ina da sa'a ba har haka gaskiya Ubangiji yana sona da yawa, tin da nake a duniya ban tab'a ganin wasu mutane masu kirki ba fiye da iyayenku. Su suna da matuqar kirki sosai sunyi abin da ba wani wanda zai iya yi, tabbas sun cancanci duka soyayyar ku, hakama sam bai kamata su san a salin gaskiyar ba, sabo da bai kamata mu cutar dasu ta wannan hanyar ba. To ina mai yi muku alkawarin cewa ba wanda zai ji wannan ko da kuwa a ce Prof ne, gaskiya nayi matuqar farin ciki sosai da kuka fad'a masa cewar yaran sun mutu, ta yanda tunanin sa ba zai tab'a kai wa gareku ba. *Adnan Adyan* dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min dani na kasa kasancewa uwa ta gari a gareku, sam na kasa kareku balantana na iya baku kulawar data dace, ni kai na kulawa a ke da ni to kuma ta ya ni zan iya baku cikakkiyar kulawa sosai.?" "K'ila kaddara ta fahimci hakan shi yasa ta had'aku da iyaye kamar, Papa Mamie Appa da kuma Ammie dama duka ahalin naku gaba ďaya. K'ila da kun rayu da ni to da ba zaku samu kyakkyawar rayuwa kamar haka ba, sabo da bamu da kud'i abinci ma wahala yake mana, to kuma ta ya Umma zata taimakeku kuyi karatu, k'ila da burina ba zai tab'a cika ba na aifa likita da lauya. Amma yanzu Alhamdulallah duka burina ya cika, dukanku ukun kuna raye sannan kuma kun kasance kamar yanda nake fata. Ina qaunarku dukanku Allah yayi muku albarka ya kuma albarkaci rayuwarku, data yaranku baki ďaya Allahumma Amin ya hayyu ya kayyum. *Adyan* ta ya a kai yanzu mu biyun muke magana da juna.?" "Mum idan har wannan na'urar tana kunanki to mu biyun zamu iya yin magana da juna." Cike da d'auki ta k'ara yin hugging d'in su tana sunbatarsu, ta mai da kallonta ga fuskar *Adeel* tare da yin kiran sa, cikin hanzari ya nufi inda take ya zauna ta had'asu duka ukun tayi hugging d'in su, tana sunbatarsu su kuwa sunyi kwance jikin ta har da wani rufe ido, Umma sai wani kallonsu take tana murmushi yayin da farin ciki yake ta shigarta sosai. Ita tashi tayi ta k'arasa gurin su cike da farin ciki tayi hugging d'in dukansu, tare da sunbatarsu cikin kyakkyawan yanayi take magana. "Bayan tsayin wani lokaci yau ahalinmu ya k'ara cika, a gaskiya ina matuqar farin ciki sosai wanda har ba zan iya fad'ar sa ba. Sai dai kawai na ce ina farin ciki sosai Allah yayi muku albarka, ya kuma albarkaci rayuwarku data yaran da zaku aifa Allahumma Amin." Sun amsa ta da Amin tare da k'ara shigewa jikin ta, bayan wani lokaci suka sake juna Mum taci gaba da magana. "Umma kamar dai yanda yaran suka fad'a ba wanda zai san a salin gaskiyar, ba zamu sanar da kowa wannan sirrin ba musamman ma Prof. Ba zai tab'a sanin wannan gaskiyar ba na har abada, wannan shi ne sakamakon zunubin daya aikata mana, tabbas ya cancanci fiye ma da hakan daga garemu, idan ma da akwai abin da yafi wannan to ni zan iya aikata wa a garesa. Sabo da ina buqatar ganin sa cikin k'unci fiye da wannan da yake tare da shi, auran sa da nayi shi ne babban kuskurena a rayuwa. Ba zan tab'a yafe masa ba na har abada kayi hak'uri *Adeel,* sabo da na san irin yanda kake qaunar Dadyn ka sosai. To ina fatan zaka fahimce ni ba kuma hakan ba zai saka ka cikin k'unci ba.?" "Mum zuwa yanzu ni na san duka a shi d'in ya cutar daku sosai, abin takaicin shi ne har da yaransa ya saka a ciki, ya cutar da yaran da basu san komai ba. Ya kasa baki damar da zaki kasance uwa a garemu, ya hana ki damar da zaki rungumi yaranki ki kuma shayar dasu, ni kawai sabo da wani buri basa Mum ni narasa wace irin zuciya ce a jikin Dady, ta ya uba zai iya cutar da yaransa tin a ranar da a ka aife su? Bama tare daya ga ko fuskarsu ba sannan kuma ya iya manta hakan, yayi k'oqarin cutar dasu amma Ubangiji ya karesu, dukansu sun samu kyakkyawar rayuwa wadda kowa zai so ya rayu a cikin ta. Godiya sosai a gurin iyayen da suka fi kowa kirki a cikin wannan duniyar, Papa Mamie Appa da kuma Ammie dama duka ahalinsu gaba d'aya. Sai yanzu ne na san dalilin da yasa Doctor da Barrister suke tare da tsanar Dady, shi ďin ya cancanci hakan daga garesu, amma duk da haka ina fatan wata rana rayuwa ta sake bawa Dady na dama, ta hanyar sawa ya zama mutumen kirki wanda zanyi alfahari da shi, k'ila a wannan lokacin ku iya yafe masa ina fatan hakan ta faru nan kusa kuma kusa sosai." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda shi ba k'unci ba shi kuma ba farin ciki sosai ba, a zahirin gaskiya yana matuqar qaunar Dadyn sa sosai, amma kuma hakan ba ya nufin zai goyi da bayan sa. Ya zama dole ya nuna masa kuskuran sa domin yayi k'oqarin gyara wa, *Adyan* ya shafi fuskarsa tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* na fahimci irin yanayin da kake ciki, amma duk da haka ya kamata kayi farin ciki sabo da har yanzu mu ukun muna tare, to ina ga sam bai kamata kayi k'unci ba musamman a kan Prof. *Adeel* abin farin cikin shi ne Mummy na nan sannan kuma yanzu tana farin ciki sosai, duka ahalin muna farin ciki to kai ma ya kamata kayi farin ciki, yanzu abin da yafi muhimmanci shi ne mu fara shirin auran ka da *Amna.* K'ila hakan zai sa ka rage yawan tunani da kuma yawan damuwa a kan Prof, to muyi hakan cikin sauri mako ďaya zuwa kwana goma to ya ka ji wannan shawaran tawa.?" Kafin ya furta komai *Adnan* yayi masa rigagi yana cewa. "Eh *Adeel* domin kuwa *Amna* ma tana matuqar buqatar hakan, to kawai ka amince da abin da Aboki ya fad'a please." Yayi shiru kad'an sannan ya amsa su. *Adnan Adyan* nima zanso hakan sosai amma kuma hakan ba zata faru ba." "Mai zai dakatar da faruwar hakan.?" "Barrister kai kariga da ka san komai a game dasu, har kullum har ko yaushe suna tare da k'uncin rashin twin's, tare da tunanin ina zasu gansu ko labarin su. Barrister abin a baiyane yake basu k'ara farin ciki ba tin bayan b'acewar twin's, duk da cewar sun aifi *Amna* amma har yanzu suna cikin k'unci sosai, gaskiyar ita ce suna matuqar qaunar yaransu sosai shi yasa har yanzu suka gagara manta dasu. To wannan yanayin nasu ne yasa sam bana jin cewar aure na da *Amna* zai kasance kamar yanda kuke fad'a." Dukansu sunyi shiru suna nazari a kan abin daya fad'a, daga bisani kuma *Adnan* yaci gaba da magana. *"Adeel* sabo da wannan dalilin ne yasa zaku yi aure yanzu, sannan kuma za a yi auran naku tare da twin's sabo da ahalinsu zai k'ara cika, nan kusa kuma kusa sosai insha Allah, to kawai ka fara shirin zama Ango ka ji ko." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Barrister shin kai ka san inda twin's suke ne.?" Ya jinjina masa ka tare da sanar da shi cewar shi da *Adyan* ne yaran da suke nai ma, nan kuwa ya shiga sanar dasu komai a game dasu da kuma rayuwarsu. *"Adeel* na tabbata su Mama zasu yi farin ciki sosai da ganin mu, zamu tafi garesu sannan kuma zamu sanar dasu duka gaskiyar, sun kasance iyaye na gari a garemu to zasu amince da duk wani burinmu. Wanda wannan dalilin ne yasa zamu sanar dasu duka gaskiyar, to kawai ka fara shirin auran ka da qanwata, sannan kuma ka fara shirin kiran mu da Yaya sabo da zaka yi aure da qanwarmu." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yana dariya haka suma abin da suke yi kenan. "Na ji mamaki sosai daya kasance cewar ku biyun kune twin's, sabo da irin soyayya da qauna dasu Abba suke nunawa a gareku, to ba wani wanda zai ci basu ne a salin iyayenku ba. Gaskiya ku kuna da matuqar sa'a sosai a rayuwa, sa'ar da kuke da ita ne yasa baku rayu tare da Dady ba, sai Ubangiji ya yanke hukuncin kai ku wani guri daban inda zaku samu ingantatciyar rayuwa. Ni kuma ni ne mara sa'ar cikin ku ina farin ciki sosai da samun ku brother's." "Karka fad'i haka bro dukanmu abu ďaya ne kuma 'yan uwan juna mun kasance *THREE BROTHER'S.* To ba wanda yafi wani a cikin mu wannan ce gaskiyar kuma ba zata canja ba, to kawai muyi farin ciki sannan kuma mu rungumi juna." Sun amsa shi da to suna dariya lokaci ďaya kuma suka yi hugging juna, suna haka wayar *Adyan* ta d'auki ruri sun fara sake juna sannan ya d'aga kiran. "Masoyi ina ka shiga haka? Dare yayi sosai yanzu k'arfe 10:30pm amma har yanzu baka dawo gida ba fad'a min qlau kake.?" "Eh Appa ina lafiya kayi hak'uri da ban sanar da kai cewar na fita tare da Aboki ba, nasa ka damu ba dalili amma yanzu zan dawo gida insha Allah, ina Ammie na *Adlishart* da kuma baby na dama duka gidan fatan kana kulawa dasu yanda ya kamata.?" "Eh rabin raina abin da nake yi a ko yaushe kenan, amma ya kamata ka dawo yanzu sabo da dukanmu muna tare da kewarka sosai ďana, Appa yana san ya rungumaka jikin sa ya kuma sunbaceka, hakama Ammie abin da take buqata kenan dama su Abbu to ka dawo gida yanzu dan Allah." "Eh Appa zanyi ka fara duba agogo mintuna goma zuwa sha biyar zan k'araso insha Allah, ina sanka Appa ka kula dasu Ammie sosai sai na k'araso." "Eh masoyi zanyi to ka kula da kanka sosai ina qaunarka ďana." Ya amsa shi da ok da kuma haka suka yi sallama, ya mai da kallonsa ga *Adnan* tare da furta masa su tafi. Sun mai da kallonsu ga Mum kafin su furta komai tayi musu rigagi. "Na samu lafiya sosai to nima ya kamata na tafi gida." Lokaci ďaya suka saki murmushi dukansu mai tare da dariya sun tashi sun fita domin tafiya. sai da suka raka su Mum har gida sannan suka fice, *Adnan* ne wanda ya sauke *Adyan* gida sannan ya nufi nasu gida. bayan kwana biyu suka shirya tafiya Jigawa gurin su Mama, *Adyan* ya sanar dasu Appa cewar zai raka *Adeel* gurin budurwar sa, hakama *Adnan* abin daya sanar dasu Mamie kenan, sun shirya tsab dukansu sun kama hanyar Jigawa. Sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e yayi tozali da fuskar Papa, cike da nuna kulawa Papa ya shiga yi masa sannu da tashi tare da ya jiki, yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya anbaci sunan sa yana cewa. "Adam mai kuma kake yi a nan.?" "Yaya nazo ne domin na duba jikin ka sannan kuma na kula da kai." "A'a bana buqatar wata kulawa daga gareka ďana zai iya kulawa da ni sosai to zaka iya tafiya yanzu." "Yaya abin shi ne *Adeel* ya tafi Jigawa domin had'uwa da sirikarmu, ya kuma tafi tare da Mummyn sa Umma *Adnan* da kuma *Adyan.* To yanzu k'anin ka ne kawai zai kula da kai kuma ni ne wannan, dan haka kawai ka amince da hakan please." "Adam d'an dakata wai har kai ne wanda zai fad'a mani tafiyar ďana? Irin abin daka aikata min na shiga tsakanina da Mama shi ďanka yake yiwa yarona, wai har kai ne wanda zai fad'a min tafiyar ďana a maimakon shi ya sanar da ni? Adam ka fita daga rayuwa ta sannan kuma ka fad'a wa yaronka ya fita daga rayuwar d'ana dan Allah." "Yaya dan Allah karka hukunta ni da ďana a kan zunubin da kai ka aikata, kai ne wanda ya barmu bamu bane wad'an da suka barka ba. Ita Mama makaranta kawai ta kai ka amma kuma kai sai ka zab'i, daka gudu zuwa wani guri daban ba tare da kayi tunani a kai na da kuma Mama ba. Haka Mama tayi ta fama da k'uncin rashin ka, daga k'arshe ta kamu da ciwon zuciya wanda yayi sanadin mutuwar ta. Nayi k'unci sosai duk da cewar ina tare da Kawu Bala, kuma shi ma yazo ya mutu haka naci gaba da rayuwa cikin matsatsi da k'unci sosai, amma kuma hakan bai hana ni sanka ba tare da fatan sake had'uwa da kai. Amma kuma har yanzu kana fishi damu duk da cewar kai ne wanda ya cutar damu, haba Yaya kai kuwa wace irin zuciya ce da kai haka? Mai kuma yasa kake da san kanka da yawa har haka.?" "Adam garama ka dena wannan wasan banzan na fad'a min cewar Mama ta mutu, Adam sam na kasa manta abin da kai da Mama kun ka aikata min, Adam mai kayi a lokacin da Mama take baka abinci ta hana ni? Sannan kuma wace irin gudunmuwa ka ba da a lokacin data shirya kai ni almajiranci? To ka sani tin daga wannan ranar nasa a zuciyata cewar ni kad'ai nake bani da kowa, na rayu cikin k'unci sosai nayi fad'i tashi sosai domin na gina kai na. Kuma nayi nasaran zama kamar yanda nake fata amma sabo da yaronka yanzu narasa komai, tare da had'in guiwar Abokinsa shi yasa wallahi nayi matuqar tsanar su sosai. Gashi kuma suna barazanar d'auke ďana daga gareni, to zan tabbatar da cewa wannan burin nasu bai cika ba to yanzu zaka iya tafiya, sannan kuma ka fad'a wa Maman cewar har yanzu ina raye, kuma cikin k'oshin lafiya duk da cewar ban samu kulawarta ba, to kawai ka tafi ka bar nan dan Allah...................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/18, 11:13 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 52* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Tuesday 15/03/2022* *Time 05:51pm* *Typing................* "Yaya shi Ɗana ba kamar yanda kake tunani bane, hakama *Dr Adyan* shi ma yaron kirki ne sosai, to duk kan su ukun sun dace da kasancewa abokan juna. K'ila dai kuskuren daka aikata ne yasa ubangiji yake hukunta ka ta haka, Yaya ko acan baya ni ban tab'a yi maka k'arya ba, to ba kuma zan fara a yanzu ba ni gaskiyar nake fad'a ma, Mama ta jima da mutuwa kuma kai ne wanda yake da alhakin mutuwar ta. To ka gode Allah da yasa ita ďin ta kasance uwa ta gari a gare mu, sabo da ta yafe maka duk wani zunubin daka aikata mata kafin ta mutu. Yaya shin wai kai kama yi tunani a kan yanda na kasance bayan mutuwar ta, sabo da a lokacin ina yaro d'an shekaru biyar kawai, nayi k'unci sosai na kuma shiga matsanancin hali sosai. Godiya mai tarin yawa ga Kawu Bala mutumen daya kasance uba na gari a gareni." Nan kuwa ya shiga sanar da shi yanda ya rayu bayan mutuwar Maman su. "Yaya duk da irin yanayin dana tsinci kai na amma hakan bai hana ni sanka ba, sannan kuma ban cire tsammanin cewa wata rana zamu k'ara had'uwa. Ko yaushe ina tare da k'uncin rashin ka ina jin cewar kamar na rasa wani jigo a tare da ni, ina jin cewar ban cika ba sabo da bana tare da kai, sabo da kai ne kawai ahalin da nake da shi kuma ina qaunarka sosai, amma kuma kai baka tab'a tunani a kai na ba hasalima tsanata kawai ce a tare da kai. Ni nayi iya k'oqari na domin na zama k'ani na gari a gareka, amma kuma kai baka tab'a tunanin zama Yaya na gari a gareni ni ba, amma kuma duk da haka ina nuna ma qauna da soyayya, Yaya naro e ka daka da ka ta da duka wannan ka amince da ni a matsayin k'anin ka please." Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Prof kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai jikin sa gaba ďaya ya mutu, da jin irin abin daya fad'a cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Adam wai da gaske kake Mama ta mutu.?" Ya jinjina masa ka tare da furta masa kalmar eh. "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un na shiga uku na lalace, mai na aikata ne haka ta ya a kai na cutar da Mama na irin wannan mummunan zunubin haka? Ni kawai na ji wani iri ne sosai sannan kuma na ji ba dad'i, a lokacin data yanke hukuncin kai ni almajiranci ba tare data yi tunani a kai na ba. A kullum kuma a ko yaushe zuciyata tana fad'a min cewar Mama bata sona, wanda wannan dalilin ne yasa na yanke shawaran na tafiya ta, sannan kuma irin yanda take nuna maka qauna da soyayya yana na fara jin tsanar ka a tare da ni. Adam wallahi banso Mama ta mutu ba naso a ce ni da ita mu k'ara had'uwa, amma mummunar kaddara ta ta hana ni damar k'ara kasancewa tare da ita. K'ila gaskiyar yaronka ne ni ďin nan nafi kowa rashin sa'a a cikin wannan duniyar, na cutar da mutane da dama kuma dukansu ahalina ne, da fari Mama na ce wacce na fara cutarwa, sai kuma kai da wasu mutanan daban ga kuma Aisha, ta so ni da duka zuciyarta dama rayuwarta gaba d'aya. Amma kuma ni sai na zab'i dana cutar da ita kuma mafi munin cutarwa sosai, hakama *Adeel* shi ma na saka shi a cikin lamarin kuma yanayin ya cutar da shi sosai, Adam a zahirin gaskiya ni mutumen banza ne wanda ba wanda zai so ya kasance ahalin shi, Adam kawai ka tafi ka barni naci gaba da kasancewa ni kad'ai, ni na cancanci irin wannan mummunan hukuncin ko ma fiye da haka. Wannan shi ne abin daya dace da ni to kawai ka tafi." "A'a Yaya ni zanci gaba da kasancewa a nan tare da kai, sannan kuma ina farin ciki sosai tare da alfaharin kasancewar ka Yayana. Yaya a rayuwa ko wane mutun yana aikata kuskure, amma mafi alkhairin cikin su shi ne wanda zai gane cewar yayi kuskure sannan ya tuba, Yaya har yanzu k'ofar tuba a bud'e take to zaka iya gyara komai, abin da yafi komai dad'i shi ne ita Mama ta yafe maka sannan kuma ta sanya maka albarka. Haka kuma nima sam bana fishi da kai to na tabbata *Maman Adeel* ita ma zata fahimce ka, sannan kuma zata yafe ma ko dan sabo da yaronku, hakama dai *Adeel* shi ma ba zai jima sosai yana fishi da kai ba. To na tabbata duka wannan k'uncin namu zai kau rayuwa zata k'ara bamu damar da zamu yi farin ciki sosai, sannan kuma daga k'arshe ahalinmu ya cika wannan shi ne abin da yafi komai dad'i, to ka dena k'unci sabo da hakan zai k'ara cutar da lafiyar ka, wanda ni kuma sam ba zanso hakan ba sabo da ina san ka samu lafiya cikin sauri." "Adam kai sam ba zaka tab'a ganewa ba, sabo da ni d'in nan na aikata wa Aisha mummunan zunubi, wanda ba zata iya yafemin ba na har abada kamar dai yanda ta fad'a." "Yaya har yanzu ita ďin uwar ďanka ce kuma tana san duk abin da yaronta yake so, to na tabbata zata yafe ma idan har *Adeel* ya shiga cikin lamarin." "Adam abin sam ba shi da sauk'i kamar yanda kake tunani, amma zansa ka fahimci gaskiyar wani lokaci to ina fatan kai ma zaka yafemin dan Allah." "Ban tab'a d'aukan ka a matsayin mai laifi ba, to ta ya kuma zanyi fishi da kai a'a ba zan tab'a aikata hakan ba, bana fishi da kai Yayana to kai kuma fa shin har yanzu kana tare da tsanata a zuciyarka.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "A'a k'anina bana yi ka yarda da ni ina qaunarka sosai." "Yaya wai da gaske kake.?" "Eh k'anina gaskiyar nake fad'a." Cike da d'auki ya tashi daga inda yake ya tafi kusa da shi ya zauna kusa sosai, sai wani kallonsa yake shi ma haka kallonsa yake sun jima a haka, sannan daga bisani suka yi hugging juna farin cikin su ya k'aru sosai. To zan iya cewa zuwa yanzu komai ya wuce tsakanin Prof da Papa. Sunyi nasaran isa garin Jigawa lafiya *Amna* ta shiga yi musu sannu da zuwa, kasancewar ita kad'ai ce a parlour bayan sun zauna ta tafi ta kawo musu ruwa da juice mai sanyi, ta koma ta zauna tare da gaishesu cikin ladabi da biyayya, bayan sun qarasa g *Adeel* yaci gaba da magana. *"Amna* ina fatan ba ke kad'ai ba ce Mama da Abba suna nan.?" "Eh suna ciki Maman twin's ce bata cikin kyakkyawan yanayi, ka dai riga da ka san komai a irin wannan ranar ce ta rasa twin's, shi yasa yanayin ta na yau yafi ko wane k'unci da muni sosai. Kamar dai kullum muna tare da kewar twin's sosai, bara na shiga ciki na sanar da Abban twin's zuwan ku, amma sai kunyi hak'uri da yanayin sa balantana kuma Mama." "Karki damu *Amna* zamu kula da wannan insha Allah." Ta jinjina masa ka tana wani gajeran murmushi sannan ta tashi ta nufi d'akin Mama, sun bita da kallo cike da jin mamakin abin data fad'a, ba jimawa sosai sai gata ta dawo tare dasu Mama. Abba ya shiga yi musu sannu da zuwa bayan sun gaisa, *Adeel* ya shiga gabatar dasu Mum da kuma *Adyan* a matsayin Aboki, kasancewar sun ta'ba had'uwa da *Adnan* bayan ya k'arasa *Adnan* yaci gaba da magana. "Mama kamar dai yanda na fad'a muku a wancan lokacin, na cewar zan sake had'aku da twin's to nayi nasara, Abba har yanzu twin's suna raye kuma cikin kyakkyawar rayuwa, na tabbata zaku yi matuqar farin ciki da ganin su sosai." Cikin hanzari har suna had'a baki suke furta masa kalmar suna ina. "Mama Abba *Amna* a yanzu haka twin's suna tare daku." Cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. *"Adnan* ni sam na gagara fahimtar abin da kake fad'a, dan Allah ka fad'a min ina twin's suke kuma ta ya zan had'u da yarana.?" "Mama yanzu haka da yaronki kike magana ga kuma d'ayan yaronki a nan." Ya nuna *Adyan* wani irin kallo suke yi musu mai cike da jin mamakin su sosai. *"Adnan* wai gaskiyar kake fad'a kai da *Adyan* kune twin's yarana.?" "Eh Mama ni gaskiyar nake fad'a to zaki iya yarda da ni." *"Adnan* to amma mai ya saka a wancan lokacin baka sanar damu gaskiyar ba.?" "Mama sabo da ban samu Aboki bane amma da ni na gano gaskiyar shi ne muka zo gareku, ku yafemin da ban iya sanar daku gaskiyar ba a wancan lokacin, ni kawai na zab'i dana zo nan tare da d'an uwa ta yanda zaku fi farin ciki sosai." "Karka ba da hak'uri ďana sabo da baka aikata wani zunubi ba, abu mai muhimmanci shi ne har yanzu ku biyun kuna raye kuma cikin kyakkyawar rayuwa. To wannan ma kawai ya isa yanzu kuzo nan ku rungumi iyayenku." Sun tashi sun nufi inda suke cike da d'auki su Abba sunyi hugging d'in su, sai wani sunbatarsu suke sun jima sosai a haka, sannan daga bisani suka sake juna su Umma sai wani kallonsu suke suna murmushi. "Twin's a zahirin gaskiya ba zan iya sanar daku girman farin cikin da muke ciki ba, tin bayan da muka rasa ku bamu k'ara samun wani farin ciki ba. Amma yanzu muna farin ciki sosai godiya ga Allah wanda ya k'ara bamu damar kasancewa tare, Alhamdulallah! Alhamdulallah!! Alhamdulallah!!!." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarsu sosai. Bayan wani gajeran lokaci *Amna* taci gaba da magana. *"Yaya Adnan Yaya Adyan* duk tsawon rayuwata na rayu da burin had'uwa daku, duk da cewar bani da sani daku amma kuma na rayu da soyayyar ku, ko yaushe buri na shi ne ahalinmu ya k'ara cika musamman idan su Mama suna cikin k'unci sosai. *Yaya Adnan* tin a wancan ranar da kazo nan ka kuma kira ni da qanwarka, to tin a wannan ranar ni na fara jin wani irin a tare da kai, naso a ce tin a wancan ranar ka sanar da ni gaskiyar amma ko yanzu ina farin ciki sosai. Sannun ku da dawowa gida muna farin ciki sosai da zuwan ku." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa, suma murmushi suke sosai mai had'e da dariya. "Kiyi hak'uri qanwata da ban iya sanar dake gaskiyar ba, a wancan lokacin kawai ina san nazo nan tare da d'ayan Yayanki. To fatan hakan bai saka ki kai fishi da Yayanki ba.?" "A'a Yayana sam ba wani abu makamancin wannan, sannan kuma abin farin cikin shi ne yanzu dukanmu muna tare da juna. Sannan kuma dukanku kuna cikin kyakkyawan yanayi to wannan yafi komai ina qaunarku sosai Yayana." "Na gode sosai qanwata." Cike da farin ciki tayi hugging d'in dukansu biyun, bayan sun sake juna *Adnan* yaci gaba da magana." "Qanwata dan Allah ki bamu guri zamu yi magana dasu Abba." Ta amsa shi da to ta tashi ta fita zuwa wani guri daban, bayan tafiyar ta *Adnan* ya mai da kallonsa gasu Mama yayi shiru na jim kad'an sannan ya fara magana. "Mama Abba da akwai abin daya kamata na sanar daku." "Rabin raina ka sanar damu koma miye zamu saurare ka.?" Ya jinjina masu ka a lamar to sun samu shiru na wani lokaci, ta daga bisani ya shiga sanar dasu komai a game dasu sam ba abin daya b'oye musu, bayan ya sanar dasu a salin gaskiyar ya kuma ci gaba da magana. "Abba Mama dan Allah bama san wannan sirrin ya fita, munyi matuqar yarda daku sosai wanda wannan dalilin ne yasa muka sanar daku duka gaskiyar. Ku iyaye na gari ne a garemu to shi yasa ba zamu iya b'oye muku gaskiyar ba, to fatan zaku fahimce mu sannan kuma zaku amince da buqatar mu dan Allah.?" Wani irin kallo suke yi masa mai cike da jin mamakin abin da yake fad'a, cike da k'unci bak'in ciki b'acin rai tare da tarin damuwa take magana. "Shikenan ďana zamu yi kamar yanda ka buqata daga garemu, abin farin cikin shi ne har yanzu muna tare sannan kuma kun amince damu a matsayin iyayenku. To wannan kawai ya isa haka kuma zamu yi komai domin farin cikin yaranmu, mu kawai burin mu shi ne ku ci gaba da kasancewa matsayin 'ya'yanmu na har abada." Magana take cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba. Ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, lokaci ďaya kuma *Adyan da Adnan* sun shiga share mata kwalla cike da d'auki tayi hugging d'in su tana sunbatarsu, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna cikin tausasa murya *Adyan* yake magana. "Mama har yanzu mu yaranki ne sannan kuma na har abada, to domin muci gaba da kasancewa a tare na har abada to akwai abin da zamu yi." "D'ana fad'a min ta ya hakan zata yuwu.?" "Mama hakan kawai zai yu ne idan kun amince zaku tafi tare damu." Kafin ta amsa shi *Adnan* yayi mata rigagi. "Eh Mama eh Abba dan Allah ku amince da hakan please naru e ku dan Allah." Mama ta kai kallonta ga fuskar Abba kafin ta furta komai yayi mata rigagi. "Shikenan Maman twin's zamu yi hakan ta yanda zamu samu damar kasancewa tare da yaranmu ahalinmu ya k'ara cika." "Na gode sosai Abban twin's." "Hakan yayi matuqar yin kyau sosai daga bisani dai ahalinmu zai k'ara cika, Mum Mama da kuma Abba zasu kasance a guri ďaya ta yanda ko yaushe zamu kasance a tare da juna." Magana yake cike da d'auki farin ciki da murna sosai, dukansu suna farin ciki sosai bayan sun k'ara wannan zancan, *Adnan da Adyan* sun tashi sun nufi gurin *Amna* sun same ta zaune tana danna waya, ga a lama charting take sun tafi inda take sun zauna cike da d'aukin ganin su take magana. "Yayuna Sannunku da shigowa." "Yauwa qanwata kina zaune a nan? Ai kuwa da akwai abin daya kamata muyi magana a kai yanzu." *Adyan* ne yake magana yayin da *Adnan* ya rufe su da ido yana murmushi. "Yayana ka fad'a min koma miye.?" "Am qanwata abin shi ne zaki b'oye wannan sirrin na cewar mu 'yan uwan juna ne, sabo da fitar da wannan sirrin zai iya cutar da iyayenmu ina nufin iyayen rik'onmu. Sun kasance iyaye na gari a garemu sannan kuma basu tab'a yunk'urin cutar damu ba, ko yaushe suna nuna mana qauna da soyayya tare da cikakkiyar kulawa sosai, sun bamu duka soyayyar su shi yasa ba zamu iya cutar dasu ta wannan hanyar ba, qanwata ke ma zaki fahimci hakan a lokacin da kika had'u da dukansu, to ina fatan kin fahimci abin da nake nufi.?" "Eh Yayana na fahimta sannan kuma ina tare da hukuncin ku, nayi alkawari ba wanda zai ji wannan insha Allah to zaku iya yarda da ni." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai. Suma abin da suke yi kenan bayan wani lokaci suka tashi suka fita zuwa babban parlour, ba jimawa dukansu suka tashi suka nufi tebur domin suci abinci. Bayan sun k'arasa sunci gaba da fira misalin k'arfe 03:00pm su Mum suka kama hanyar tafiya gida, bayan kwana biyu su *Adnan* suka dawo suka tafi dasu Abba, wanda kuma a nan gidan su Mum suka zauna da part ďin su wani yammaci................................ *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/21, 6:37 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 53* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ . *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Saturday 19/03/2022* *Time 12:05am* *Typing...............* zaune suke suna fira Mum ta ambaci sunan *Adnan. "Adnan* shin yau ka had'u da *Adyan* kuwa? Sabo da bai zo nan ba sannan kuma layin sa a kashe yake, gaskiya ni na damu sosai a kansa sabo da ban san abin da yake faruwa da shi ba." "Mum Aboki yana lafiya kawai yana tare da qanwata ne, sabo da yau jikin ta baya mata dadi kin san lafiyar masu juna biyu, sannan kuma ya kashe wayar sa ne sabo da baya buqatar abin da zai saka shi barin ta. Kafin nazo nan sai da na fara zuwa gurin sa yana lafiya to *Adeel* fa.?" "Na gode Allah daya kasance qlau, *Adeel* ya tafi domin ya duba jikin Dadyn sa, Maman *Amna* suma sun fita ni kad'ai ce a gidan sai Umma na. *Adnan* ina ga ya kamata mu tafi mu duba jikin sirika ta yanzu." "Shikenan Mum yanda kika ce." Ya fad'a yana murmushi ita ma abin da yake yi kenan, dama Umma wacce take zaune gefen ta Mum ta mai da kallonta ga Umma tare da fad'ar sunan ta. "Umma zamu iya tafiya yanzu.?" Ta jinjina mata ka tana murmushi sun tashi dukansu sun nufi gidan Abbu domin duba jikin *Alishart.* Sun isa gidan tare da shiga ciki kai tsaye babban parlour suka nufa, sun samu su Appa a nan suna fira su Ummi sun shiga yi musu sannu da zuwa. Sun amsa suna murmushi bayan sun gaisa su Mum, sun shiga tambayar jikin *Alishart* cike da nuna kulawa Ammie take amsa su. *"Adlishart* tana samun sauki sosai sabo ďana yana kulawa da ita sosai. Ba jimawa muka duba su ta samu tayi barci, sannan kuma abin farin cikin shi ne babyn yana lafiya ina nufin jikana. Gaskiya ina matuqar farin ciki sosai da masoyin ďana zai bani jiki, gaskiya zama Kaka yana da matuqar dad'i sosai musamman ma idan kana qaunar yaronka sosai." "Gaskiyar ki ne *Ummu Adyan* duk da cewar yarona *Adeel* bai yi aure ba amma har na fara mafarkin zama Kaka." Magana suke cikin kyakkyawan yanayi bayan wani lokaci, Appa ya tashi ba jimawa ya dawo tare da yaronsa wato *Adyan.* nan ya shiga gaisawa dasu Mum bayan daya zauna ya sauke kallonsa ga fuskar *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. "Aboki mai ya saka baka sanar da ni zuwan su Umma ba.?" "Aboki lokaci ďaya tafiyar tazo mana sun zo ne domin su duba jikin qanwata, dalilin da yasa ban iya sanar da kai ba kenan to karka yi fishi sosai ka ji ko." Yayi murmushi sosai a lamar to sunci gaba da fira cikin raha wasa da dariya, suna cikin fira suka hangi Umma ta tashi daga gurin zaman ta, ta nufi wani guri daban dukansu sun bita da kallo dan ganin inda ta nufa. Mum kuwa ta shiga anbatar sunan ta tare da k'oqarin dakatar da ita, amma kuma sam bata saurareta ba taci gaba da tafiya har ta isa inda take san zuwa, tayi tsaye gurin wani makeken photo wanda yake manne jikin bango, sai wani kallon photon take kallo sosai yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai to zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Lokaci ďaya kuma ta saki kuka kuma kuka take sosai har da a jiyar zuciya, su Ammie sai wani kallonta suke yayin da suka gagara fahimtar komai a game da ita da kuma yanayin ta. Cikin hanzari Mum ta tashi daga inda take ta nufi gurin ta hakama *Adnan da Adyan,* sun isa inda take yayin da suke ta fad'ar sunan ta amma kuma bata amsa su ba, kasancewar har zuwa wannan lokacin kuka take dukansu sun shiga rarrashinta, suna wani lalla'bata tare da bata magana ta sauke kallonta ga fuskar *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adyan* ya kake da wannan mutumen.?" Ta nuna mutumen da yake cikin photo. "Umma shi d'in Abban su Kaka ne sannan kuma Kakan su Appa ne, amma mai ya saka kika tambaya shin ke kin san shi ne.?" "Eh ďana na san shi sosai, *Adyan* Kakan ka na nan ina san zanyi magana da shi yanzu dan Allah.?" "Umma abin shi ne shi Kaka na yana meeting ne yanzu, d'ayan Kaka na kuma Abba yana Abuja amma ya fad'a min cewar jibi zai zo nan domin ya had'u da ni, sabo da dukanmu munyi kewar juna sosai karki damu Umma ni zan had'aki da dukansu." *"Adyan* kayi n samun kyakkyawan ahali wanda kowa zai so ya kasance a cikin sa, *Adyan* naro e ka daka had'a ni da Governor yanzu dan Allah." "Shikenan Umma zanyi." Ya juya ya nufi gurin su Ammie wad'an da suka rufe Umma da ido, ya isa inda suke tare da karb'ar wayar Appa ya shiga kiran layin Abbu, ba jimawa ya d'aga *Adyan* ya sanar da shi cewar ya dawo gida yanzu. "Masoyi shin wani abu ya faru cikin gidan ne.?" "Eh Kaka da akwai buqatar ka dawo gida yanzu." "Shikenan gani nan tafe yanzu." Ya amsa shi da ok da kuma haka suka yi sallama ya mai da kallonsa ga Umma, wacce take ta aikin shafar photo tana kuka ya nufi gurin ta tare da sanar da ita cewar ga shi nan tafe. Ta jinjina masa ka tare da sanya masa albarka cikin mutuwar jiki, Ummi take tafiya har ta isa inda take cikin kwantar da murya take magana da ita. "Maman Aisha ya kamata ki dena wannan kukan haka, sannan kuma ki fad'a mana abin da yasa kika saka photon Baba a gaba kina kuka? Yanzu mu tafi ki zauna na tabbata *Abban Ahlam* ba zai jima ba zai k'araso nan." Ta jinjina mata ka a lamar to Ummi ta mai da kallonta ga fuskar *Adyan,* wanda ya murtuke fuska uwa bai tab'a dariya kuma duka, sabo da Ummi ta anbaci sunan Ahlam ne tayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan sa. "Rabin raina karka yi fishi da matarka sabo da hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai, masoyi ni ba yanda na iya ne sabo da baki na ya riga daya saba fad'ar haka, amma zan dena sabo da kai zan rik'a kiran sa da Abban Ammie. Yanzu fad'a min wani abu shin hakan yayi ma.?" "Eh Kaka hakan yayi sosai ina sanki sosai Kaka ta." Ya fad'a tare da yin hugging d'in ta ita kuma ta k'ara masa da sunbata, bayan sun sake juna sun tafi domin su zauna cike da jin soyayyar sa, su Appa suka isa garesa lokaci d'aya suka yi hugging d'in sa suna sunbatarsa. Mum sai wani kallonsu take yayin da farin ciki yake ta shigarta sosai, bayan wani lokaci sai ga Abbu ya shigo cikin hanzari ya isa inda *Adyan* yayin da yake fad'ar sunan sa. Yana isa garesa yayi hugging d'in sa yana sunbatarsa sannan daga bisani ya fara magana. "Rabin raina fad'a min abin da yake faruwa fatan dai kana lafiya.?" Magana yake cikin soyayya da qauna su *Adnan* sai kallonsu suke cike da shagwa'ba yake amsa shi. "Kaka ina lafiya dama Kakar *Adeel* take buqatar had'uwa da kai cikin gaugawa, ga a lama tana cikin damuwa sosai to ya kamata kayi magana da ita yanzu." Abbu ya sauke kallonsa ga fuskar Umma tare da fad'ar sunan ta. "Sannu ko am mai yasa kike san kiyi magana.?" Kallonsa kawai take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai tayi shiru na wani lokaci sannan ta fara magana. "Sunana Asiya qanwarka shin ka tina ni kuwa.?" Dukansu wani irin kallo suke yi mata mai cike da jin mamakin abin data fad'a, musamman ma Abbu wanda ya rufe ta da ido lokaci ďaya kuma idanuwansa suka fara zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai cikin wani irin yanayi yake magana. "Wai gaskiyar kike fad'a da gaske ke qanwata ce Asiya.?" "Eh gaskiyar nake fad'a to zaka iya yarda da ni." Cike da d'auki da farin ciki ya k'arasa inda take sunyi hugging juna, sai kwalla yake zubarwa ita kuma kuka take zamu iya kiran hakan da farin ciki, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna daga hugging d'in da suka yi. "Asiya ta ya a kai kun ka tsira daga wannan hatsarin da motar tayi ina goggo.?" "Yaya ni na tsira amma Goggo ta mutu wata dattijuwa ce taci gaba da kulawa dani a garin Kankiya, ko yaushe ina addu'a Allah ya sake had'a ni da ahalina musamman, a lokacin da rayuwa ta zame mana qalubale abinci ma yana yi mana wahala. A zahirin gaskiya na rayu cikin k'unci sosai da kulawa amma yanzu komai ya wuce, yanzu fad'a min ina babban Yaya da Baba.?" "Asiya bayan da muka samu labarin cewar kunyi hatsari kuma dukanku kun mutu, a nan take zuciyar Baba ta buga shi ma ya rasu godiyar ban girma sosai, ga Yaya na ga gari kuma abin alfahari wanda ya kasance uba na gari a gareni, ya raine ni cikin qauna da soyayya ba tare da mun san gaskiyar cewar kina raye ba. Kiyi hak'uri damu kasance yayye na gari a gareki ba mun ma kasa, nai man ki zan iya cewa wannan shi ne babban zunubin da muka tab'a aikata wa a wannan duniyar, dan Allah ki yafe mana kin ji qanwata." "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un ya Allah ka ji k'an mahaifina, Allah ka yafe masa kaba shi gidan al'janna Allahumma Amin ya hayyu ya kayyum. Yaya karka hukunta kanka a kan zunubin da baka aikata ba, na tabbata da a ce kun san cewar ina raye to zaku yi komai domin ganin mun k'ara kasancewa tare. Haka Ubangiji ya kaddara mana to ba zamu tab'a canja hakan ba, abin farin cikin shi ne mun k'ara had'uwa da juna to wannan ma kawai ya isa, godiya ga *Adyan* wanda yayi sanadin k'ara kasancewa tare Allah ya masa albarka, tare da sauran 'yan uwan sa dama abin da zasu aifa." Sun amsa da Amin Abbu ya mai da kallonsa gasu Ummi yaci gaba da magana. "Maman Ammie wannan ita ce qanwata wacce na fad'a muku cewar ta mutu, kun dai ji yanda komai ya faru daga bakin ta." *Adyan* ya anbaci sunan Abbu yana cewa. "Kaka to ta ya a kai ku ukun kun ka rabu.?" "Masoyi abin shi ne bayan Maman mu ta rasu a lokacin Asiya tana da shekaru uku ne, sai goggon mu ta karb'i rik'on ta mu muna zaune a Bauchi su kuma suna zaune a Yola, lokaci zuwa lokaci muna kai wa junanmu ziyara, bayan wasu shekaru a lokacin Asiya tana da shekaru bakwai, suka shirya kawo mana ziyara wanda kuma a wannan lokacin ne komai ya lalace, goggo ta mutu Baba ya mutu sannan kuma qanwata ta b'ata, Yayana yaci gaba da kulawa da ni sosai bayan Yayana yayi aure ne muka dawo kaduna da zama, sabo da canjin gurin aiki da a kayi masa bayan an aifi Appa ne nayi aure. Bayan wani lokaci kuma a ka aifi Ammie haka dai rayuwa taci gaba da sarrafa mu daga bisani kuma suka fad'a siyasa, masoyi wannan ita ce rayuwarmu ni da Yayana." "Kaka gaskiya kun fuskanci qalubalen rayuwa sosai, musamman Kaka k'arama ina nufin Kakar *Adeel,* amma yanzu duka wancan lokacin na k'unci ya wuce yanzu kawai muyi farin ciki. Sabo da ahalinmu ya k'ara cika abin da dad'i sosai fatan alkhairi ga ahalinmu." Sun riga da sun san juna wannan yasa basu gabatar da kansu ga juna ba, sun shiga yiwa juna fatan alkhairi Abbu ya k'ara layin Abba ya sanar da shi komai, ya kuma ba shi Umma sunyi magana a zahirin gaskiya Abba yayi matuqar farin ciki sosai, wunin ranar gaba d'aya a tare dasu Abbu suka yi sa, *Adyan* yayi matuqar farin ciki sosai da Mum ta kasance ahali ďaya dasu Appa. Da yamma *Adnan* ya tafi su Mum kuwa sai dare suka tafi, bayan kwana biyu Abba ya dawo gida inda ya had'u da Umma farin cikin sa ya k'aru. Prof ya samu tsayin mako hud'u asibiti sannan a ka ba shi sallama, Papa ya ba shi ďaya daga cikin gidajen sa domin ya zauna. Ganin ya samu sauk'i ne yasa a ka fara zancan auran *Adeel da Amna,* su Appa na ďaya daga cikin wad'an da suka tafi gurin zancan auran, inda a ka saka musu ranar mako biyu ai kuwa duka gidajen uku sun shiga hidima. *Adyan da Adnan* hidima tasu sabo da sune suke tare da Ango, a ranar Jumu'a ne bayan idar da sallar Jumu'a a kayi addu'ar d'aurin auran *Adeel Abas Muh'd da Amna Anas.* Su Mum sun sha shagali sosai a gidan su Abbu a kayi biki, da misalin k'arfe 08:00pm na dare Amarya *Amna* ta tare d'akin ta, da k'arfe 09:00pm suka nufi gurin Dina wanda ya d'auke su har k'arfe 12:00am sannan suka dawo gida. *Adeel* a nan gidan su Mum ya zauna da matarsa hakan ya musu dad'i sosai, to balantana kuma Mum da Mama dukansu suna tare da farin ciki sosai. Zaune yake ya buga wani irin uban tagumi ga a lama tunani yake, *Adeel* ya shiga ya riskesa a cikin wannan ita mara kyau, ya k'arasa inda yake ya zauna tare da dafasa yana fad'ar sunan sa. "Dady mai yake faruwa da kai ne mai ya saka kake cikin k'unci sosai.?" *"Adeel* a game da Mummyn ka ne ita sam tak'i ta saurare ni, to ta ya ni zan iya nai man afuwarta gafaranta da kuma yafiyarta? *Adeel* naro e ka ka saka baki Mummyn ka ta yafe min please." "Dady naso a ce cikin sauk'i zan iya yin hakan, amma ina ita sam ba zata sauraran ba zama ta iya yin fishi da ni kuma fishi sosai. To shi yasa ni ba zan shiga cikin lamarin ba amma duk da haka ni zan taimake ka sosai, domin ganin ta dena fishi da kai ta hanyar yafe maka, gobe zata tafi gidan Papa domin ta duba *Afnan* to kawai ka same ta a can, na tabbata zata saurare ka sannan kuma Papa zai saka baki a cikin lamarin. To zata saurari Papa Dady wannan kawai ce damar da nake da ita ta taimakon ka, to ina fatan abin yayi aiki sabo da zanso ku biyun ku k'ara kasancewa tare na har abada." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i lokaci ďaya Dady yayi hugging d'in sa, ya k'ara da sunbatarsa sun kasance a tare na tsayin wani lokaci wanda sai dare sannan *Adeel* ya tafi gida.................. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/22, 10:18 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 54* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Sunday 20/03/2022* *Time 12:33pm* *Typing.................* Da yamma liƙis ya d'auki Mum zuwa gidan Papa, sun isa gidan tare da shiga ciki Mamie ta shiga yi mata sannu da zuwa, ta amsa tana murmushi mai had'e da dariya bayan sun gaisa, Mum ta shiga tambayar jikin *Afnan* Mamie ta amsa da tana samun sauki sosai. "Kin san idan a ka ce ciki ya shiga watannin aihuwa, to komai sai a hankali lafiya tana k'aranci sosai, amma Alhamdulallah tana samun sauki sosai." "Haka ne hakama *Alishart* ita ma jikin ta yak'i saki, ko yaushe cikin rashin lafiya take Allah dai ya raba su da cikin lafiya." Sun amsa ta da Amin Mamie ta tashi zuwa wani guri daban, ba jimawa ta dawo tare dasu *Afnan Adnan* ya shiga yi musu sannu da zuwa, sun amsa suna murmushi mai had'e da dariya bayan sun gaisa Mum ta shiga tambayar, *Afnan* jikin ta ta amsa da cewar tana samun sauki sosai, ba jimawa sai ga Papa ya fito wanda fitowarsa tayi daidai da shigowar Prof. Nan kuwa Papa ya shiga yi masa sannu da zuwa, ya amsa cikin kyakkyawan yanayi sun tafi sun zauna sun gaisa gaba d'aya, Prof ya sauke kallonsa ga fuskar Mum wacce ita kuma wani guri daban take kallo, lokaci ďaya kuma ta tashi tare da furta musu kalmar sai an jima. Da sauri Prof ya dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a *Ummu Adeel* sam bai kamata ki tafi yanzu ba dan Allah." Ba tare data kalli ko kusa da inda yake ba take magana. "Mai yasa zanci gaba da zama a nan bayan kuma ina da buqatar na tafi.?" "Na san cewar zaki tafi ne sabo da ina nan amma bawai sabo da kina da buk'atar tafiya ba, *Ummu Adeel* dan Allah karki ci gaba da hukunta ni haka, eh na san cewar ni na cutar dake da yawa sosai, amma kuma hakan sam baya nufin cewar ba zaki yafemin ba. Na tabbata kin ji dalilin da yasa na aikata maki duka wannan, Aisha na amince da cewar na yaudareki sosai amma kuma hakan bai hana ni sanki ba, bai zama dole daki yarda da ni ba amma Ubangiji shi yafi mu sanin gaskiyar. Aisha dan Allah ki yafemin ki gafarce ni a kan duk wani zunubin dana aikata maki please." "Wai da gaske kana san na yafe maka to shikenan zanyi hakan amma a bisa wani sharad'i." Cike da d'auki yake tambayarta miye sharad'in, tayi shiru kad'an sannan ta ci gaba da magana. "Prof sharad'in shi ne ka dawo da baya shekaru ashirin da biyar da suka wuce, ta yanda zan samu damar kasancewa uwa ta gari ga sauran yarana daka kashe. Sannan kuma ka kasance uba na gari ga duka yaranmu, kuma muji na gari a gareni siriki na gari a gurin Umma na, ta yanda komai zai wuce a guri na zuciyata da kuma rayuwata gaba ďaya. Idan kuma ba zaka iya yin hakan ba to karka k'ara furta min komai na har abada." "Aisha da a ce ni zan iya yin hakan to da tin da jimawa nayi hakan, amma ba zan iya dawo da baya ba ke ma kin san da haka, to dan Allah karki yi min hukuncin da bai zan iya d'auka ba. A game da yaran kuma nima naso a ce sun rayu, domin na nai mi afuwarsu gafararsu da kuma yafiyarsu, ba lallai ki yarda da ni ba amma nima ina matuqar bak'in cikin abin dana aikata. Musamman cutar da yaran da nayi wannan shi ne babba kuma mummunan zunubin dana aikata a rayuwata, kuma na tabbata wannan k'uncin shi ne abin da zai zamo silar mutuwa ta, amma kafin nan zanso a ce kin yafe min ta yanda zan samu kyakkyawar gobe, Aisha dan Allah da girman Allah kiyi hak'uri ki yafemin please." "Prof k'ila dai wani lokaci amma ba yanzu ba sabo da." "A'a Aisha dan Allah ki dena a zabtar da ni haka domin." Cikin sauri *Adnan* ya dakatar da shi. "Malan ya isa haka ta ce a'a to mai yasa kake san ka matsa mata ne? Karka yi k'oqarin tursasata ga abin da bata da ra'ayi da shi, ta ce wani lokaci to kawai ka jira ko kuma dai ka k'ure hak'urin ta, ta yanda ba zata yi tunanin yafe maka ba to karka bar hakan ta faru da kai domin." "Barrister ko zaka iya yin shiru haka dan Allah? Sabo da sam baka taimakawa to ina ga kawai mu bar wannan a tsaninsu please." *"Adeel* to mai kake san na fad'a ne shin kana san na goyi bayan ta yafe masa ne? A'a sabo da bai cancanci yafiyarta ba cikin sauk'i, zata iya yafe masa amma ba cikin sauk'i haka ba. Sabo da akwai buqatar ta hukunta shi a kan duk wani zunubi nasa, to ka da ka hana ta yin abin daya dace kawai sabo da yana mahaifin ka, domin ita tana yin abin daya dace ne kuma kai ma kanka kasan da haka." "Barrister amma kuma hakan sam ba zai canja gaskiyar ba, shi ya tab'a zama mujin ta sannan kuma har yanzu shi ne uban yaranta, ko da a ce suna raye ko a kasin haka Barrister bawai ina cewa Dady bai aikata kuskure ba, a'a ni kawai ina ganin ya kamata duka wannan ya wuce mu kuma amince da gaskiyar, Dady ya cutar da ita sosai ya kuma amince da hakan sannan kuma ya nai mi afuwarta gafaranta da kuma yafiyarta. Hakama dukanmu a nan mun ga nadamar abin daya aikata a tare da shi sosai, ni d'in nan nafi kowa sanin waye Dady na da kuma yanda yake, sabo da da shi ne nayi gaba ďaya rayuwata Barrister Dady na yana tare da nadama sosai. Kuma ya jima sosai a cikin ta a kullum kuma a ko yaushe, ba abin da yake sai tunanin yanda zai samu yafiyar Mum. Yayin da damuwa tayi matuqar yi masa yawa sosai, wani lokacin ma kwalla yake zubarwa to ya kamata ku kyautata masa zato, Mum ba zan ce ki yafe masa ba sabo da na san kina yin abin daya dace, Dady ka jira kamar yanda ta fad'a insha Allah lokaci zai zo wanda Mum zata yafe maka." "Nima ina fatan haka ďana *Adnan* dan Allah ka fad'a min mai ya saka kake tare da tsanata sosai? Ni dai ban san na aikata maka wani kuskure ba amma kuma kai baka tab'a sona ba, *Adnan* ni Uncle ďin ka ne to ya kamata ka koyi yanda zaka girmama ni. Na san cewar kai ka damu sosai a kan Aisha amma hakan baya baka damar da zaka rik'a fishi da ni sosai, dukanmu ahali ďaya ne to ya kamata muso juna a gurin mahaifin ka na koyi wannan. To dan Allah ka dena cutar da ni sosai haka please." "Mum ni zan shiga ciki mun gode sosai da ziyara, *Adeel* ka kula da ita sosai ina gaida Kaka." Ya yunk'ura zai tashi Papa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. "Rabin raina shin ko zamu iya yin magana yanzu dan Allah.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh Papa yaci gaba da magana. "Masoyi dan Allah ko zaka dena fishi da Yayana kuma Kawunka dan Allah.?" "Shikenan Papa daga yanzu zan kasance d'a na gari a garesa, idan har yayi alkawarin kasancewa Kawu na gari a gareni zanyi hakan kawai sabo da kai, ina sanka Papa ina matuqar masifar qaunarka sosai." Magana yake cikin wani irin yanayi yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai Papa ya tashi daga inda yake ya koma kusa da shi ya zauna kusa sosai. Ya fara da share masa kwalla tare da sunbatarsa sannan ya fara magana. "Nima ina qaunarka sosai d'ana fiye da komai dana mallaka, kai abin da nafi so fiye da komai na gode sosai da samun ka ďana." lokaci d'aya suka yi hugging juna su Mum sai wani kallonsu suke, Mamie ta tashi daga gurin zaman ta ta nufi inda suke, yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai. "Masoyi wannan rungumar ahali ce to sam bai kamata ka bar Mamie a gefe ba, ko da yake wannan lafin Papa ne to banyi fishi ba rungumar ahali." Sun k'ara runguma juna sosai suna murmushi mai had'e da dariya sosai, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna daga hugging d'in da suka yi, wanda kuma har zuwa wannan lokacin su Prof kallonsu suke yayin da suke jin suna birgesu sosai, parlour yayi jim kad'an ba mai magana a cikin su Papa ne wanda ya kau da shirun gurin, inda ya shiga rarrashin Mum tare da bata magana a kan ta yafe wa Prof abin daya aikata mata. A zahirin gaskiya tana matuqar jin nauyin Papa sosai, wanda wannan dalilin ne yasa ta amsa shi da to sam bata da wani zab'i, wanda dole ta furta wa Prof cewa ta yafe masa yayi matuqar farin ciki sosai da hakan, ya shiga yiwa Papa godiya dama ita Mum farin ciki gurin *Adeel* sam ba zai fad'u ba. Sai dai na ce yana farin ciki sosai yayin da *Adnan* ya gagara fad'ar komai, bayan wani lokaci su Mum suka tafi Prof kuwa sai dare sosai ya tafi. Bayan kwana biyu *Adeel* yake yiwa Mum ta yin komawa gidan Prof tayi jim kad'an sannan ta amsa shi. *"Adeel* cewar na yafe wa Dadyn ka baya nufin zan koma kasancewa a tare da shi, a wannan rayuwar idan da akwai wani abin dana tsana to Prof ne, auran sa da nayi shi ne babban kuskurena a rayuwa ko a wancan lokacin mugunyar kaddara ce ta had'a ni aure da shi. To sam ba zanso wannan mummunan kaddarar ta k'ara kasancewa tare da ni ba, kayi hak'uri ďana sabo da ba zan tab'a komawa a gurin mahaifin ka ba, ni da shi mun riga da mun rabu rabuwa kuma ta har abada wannan ce gaskiyar, to ya kamata ka amince da ita ka ji ko." "Amma Mum." "A'a *Adeel* kawai ka amince da gaskiyar sabo da ba abin da zai canja ta ka ji ko dan Allah." Ya jinjina mata ka yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Ta shiga share masa kwalla tana rarrashin sa tare da ba shi magana, ta yanda zai iya fahimtar ta ba shi da wani zab'i wannan yasa dole ya hak'ura da buk'atar sa. Wani yammaci su uku ne kawai a parlour Abba ya sauke kallonsa ga fuskar Umma tare da fad'ar sunan ta. "Asiya ni kuwa zanso na san abin da yasa Aisha bata san ta koma gidan Prof? Shin shi d'in ya ta'ba yunk'urin cutar da ita ne ina san na san gaskiyar gaba ďaya.?" "Eh haka ne shi ďin ya cutar da ita sosai." Nan kuwa ta shiga sanar dasu komai daya faru cike da jin mamakin abin data fad'a Abba yake magana. "Mine shi wane irin uba ne da har zai yi tunanin cutar da yaransa haka? Duk da cewar yaransa ne amma da akwai buqatar na hukunta shi, sabo da kuskuran sa ne yaran suka mutu to ya kamata duniyar ta san wane irin uba ne shi, tabbas ni sai na hukunta shi a bisa mummunan zunubin sa." "A'a Yaya dan Allah karka yi naro e ka ka da ka aikata masa komai dan Allah." "Asiya duk da irin girman zunubin daya aikata kuma kina nuna tausayawar ki a kansa mai yasa.?" "Yaya bawai sabo da shi nake wannan ba a'a sabo da yaran ne, sabo da ba zanso yanayin ya cutar dasu ba." "Asiya a kan wad'an da yara kike magana.?" Shiru bata yi magana ba, "Asiya ki amsa ni a kan wad'an da yara kike magana.?" "Yaya to ai yaran sun rayu kuma suna cikin kyakkyawar rayuwa sosai. Sannan su ne wad'an da suka yi k'aryan cewa sun mutu, sabo da basa san kowa ya san gaskiyar musamman iyayen da suka rayu dasu, wanda wannan dalilin ne yasa suke fad'ar cewar sun mutu wannan ce gaskiyar." Cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana. "To ta ya suka bar gidan marayun.?" "Basu ne suka bar gidan ba mutanan da suka fara d'aukan rik'onsu suka rabosu da gidan, su kuma sun rasa yaran a nan hanyar katsina ta hanyar yi musu fashi tare da sace yaran, to a lokacin ne yaran suka rabu amma abin farin cikin shi ne, dukansu sun samu iyaye na gari kuma abin alfahari sosai." Cike da firgici da rud'ani Abbu ya mai da kallonsa ga fuskar Abba tare da fad'ar sunan sa. "Yaya bayanin ta yana nufin cewar." Da sauri Umma ta dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar. "Eh hasashen ka gaskiya ne to ba buqatar sai ka fad'i sunan sa, sabo da bai kamata wani ya san da wannan ba kuma sam banso kusan gaskiyar ba, amma ba yanda na iya ne sabo da ya zame dole to dan Allah da girman Allah, karku sanar da kowa wannan sirrin musamman su Ahmad sabo da hakan zai yi matuqar cutar dasu sosai, dama shi yaron fatan kun fahimci abin da nake fad'a.?" "Ke kina da kirki sosai sannan kuma kina matuqar qaunar ahalinki sosai, duk da cewar kun san a salin gaskiyar amma baku tab'a nuna wa ba kawai kun bar abin a zuciyarku, gaskiya nayi matuqar farin ciki da hakan sosai, dama ba wanda ya san gaskiyar ko a baya balantana kuma yanzu, da muka san a salin gaskiyar gaba ďaya karki wani damu Asiya sabo da ba wanda zai san wannan." Nan ya shiga sanar da ita komai a game da *Adyan* ya kuma ci gaba da magana. *"Adyan* tamkar rayuwarmu yake to zamu yi komai sabo da shi, yanzu fad'a mana waye d'ayan yaron kuma yana ina.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi da cewa *Adnan,* cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana. "Asiya wai kina magana a kan *Adnan* yaron San Adam Muh'd.?" Ta jinjina masa ka tare da sanar da shi komai Abba yaci gaba da magana. "Ni naga yanda San Adam yake matuqar qaunar yaronsa sosai, zai yi matuqar wahala ka ji ya kira sa a salin sunan sa sai dai masoyi ko rabin rai, gaskiya shi uba na gari ne a gurin yaransa nayi farin ciki sosai daya kasance tare da *Adnan.* Sannan kuma mutum mai matuqar girma da daraja irin San Adam Muh'd bai kamata ya san gaskiyar ba, sam ba zamu cutar da shi ta wannan hanyar ba, abin farin cikin shi ne dukanmu ahali ďaya ne to wannan ma kawai ya isa." Sun jima sosai suna tattaunawa a game da zancan, daga bisani suka tsayu a kan ba wanda zai san gaskiyar, bayan kwana biyu a safiyar litinin ce *Afnan* ta tashi da ciwon nak'uda, cikin hanzari tare da nuna kulawa su Mamie suka d'auke ta zuwa asibiti. Tare suka tafi dasu Anwar bayan sun isa asibiti ne Mamie ta sanar dasu Papa, kasancewar sun fita zuwa office cikin hanzari suka nufi asibiti, ganin ta jima tana abu ďaya yasa *Adnan* kiran layin *Adyan* ya sanar da shi, ya amsa shi da ga shi nan tafe sunyi sallama bai fi da mintuna ashirin ba sai ga *Adyan,* wanda tare yake da *Aliahart* dasu Appa Ammie ta shiga ciki dan ganin abin da yake faruwa. Ta kuwa same ta cikin yanayi na ban tausayi sosai, nan kuwa ta shiga taimaka mata dan ganin ta aihu lafiya, ba jimawa sai gasu Mum kasancewar *Adnan* ya sanar da ita a waya, bai fi da mintuna goma ba sai ga Prof wanda shi kuma Papa ya sanar da shi. Duka ahalin suna nan har dasu Mama jin yanda a ke zancan cewa *Afnan* ta wahala, yayi matuqar tsorata *Alishart* sosai lokaci ďaya duk ta shiga firgici sosai, kafin su ankara wani zazza'bi mai zafi ya rufe ta wanda yazo mata tare da ciwon mara mai tsanani sosai. cikin hanzari *Adyan* da Appa sunyi kanta lokaci ďaya kuma jini ya fara yi mata zuba, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya gani yake magana. "A'a sam bai kamata hakan ta faru da ita ba bai kamata ta shiga cikin wannan yanayin ba, Appa kai ka riga da kasan komai a game da ita to ya kamata a yi mata C. S. Yanzu cikin gaugawa sosai." "Eh ďana nima abin da nake qoqarin fad'a kenan, yanzu mu fara kai ta ciki sannan sai mu shirya komai." Ya amsa shi da to Appa yasa nurse sun d'auke ta zuwa ďakin tiyata, ya fara magana da shugaban asibitin sannan suka fara shirin yi mata C. S. Wanda kuma Prof ne ya bata jini ba jimawa sosai a ka fara yi mata C. S ba jimawa sosai da shiga da ita tiyata, sai ga Ammie ta fito tana yi musu kyakkyawan albishir na cewar ta aifi twin's duka maza, duk da cewar ta aihu lafiya amma basa wata murna sosai ta shiga tambayar su abin da yake faruwa. Sun sanar da ita da sauri ta juya ta nufi d'akin tiyata domin ganin abin da yake tafiya, ta same su sun kusa k'arasa aikin su ita ma ta saka nata gudunmuwa, bayan wani lokaci ta koma fitowa tana mai yi musu albishir na cewar an ciro mata twin's mace da namuji.................. *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/23, 6:22 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 55* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Monday 21/03/2022* *Time 05:44pm* *Typing..............* A zahirin gaskiya ba zan iya sanar da ku girman farin cikin da yake tare da su ba, sai dai kawai na ce suna matuƙar farin ciki sosai, lokaci ďaya a ka fito da yaran nan kuwa suka shiga d'aukan yaran. Appa ya kira layin Abba da Abbu ya sanar dasu, take farin ciki ya shigesu sosai Mum ta kira layin Umma ta sanar da ita, kasancewar tana Abuja tare dasu Ummi haka suka shiga sanar da, 'yan uwa da abokan arziki bayan wani lokaci suka nufi gurin su *Afnan.* Dukansu a d'aki d'aya suke wanda kuma Appa ne yasa a ka had'e su d'aki ďaya, sun samu *Afnan* ido biyu yayin da *Alishart* take ta sharan barci. Su Mamie sun shiga yi mata barka da arziki murmushi kawai tayi ba tare data furta komai ba, sun mai da kallonsu ga *Alishart* tare da yi mata addu'ar Allah ya bata tafiya, *Afnan* tayi matuqar farin ciki sosai da ganin yaranta, dama yaran *Alishart* to balantana kuma su *Adyan* abin ba zai fad'u ba. Misalin k'arfe 03:00pm *Alishart* ta farka kuma ta tashi cikin kyakkyawan yanayi sosai, sun shiga yi mata sannu da ya jiki ta amsa da Alhamdulallah tana samun sauki sosai. Tayi matuqar farin ciki sosai da kyautar da Allah ya bata, dama yaran Yayanta *Afnan* bata wani jima ba ta samu sallama, kasancewar tana lafiya *Alishart* kuma ta samu kwana biyar asibiti sannan ta samu sallama zuwa gida. Yanda a kayi bikin auran su a rana ďaya hakama bikin suna, duka ahalin sai hidima suke kwana biyu da aihuwa su Umma suka dawo, kafin ka ce haka gari ya d'auka inda labarin aihuwar ya zaga ko ina na duniya. Bayan mako biyu suka gabatar da walima a madadi bikin suna, da dare kuma suka yi Dina an rad'a wa yaran *Adnan suna Aarif da Aaryan, yaran Adyan kuma Aarfat da Aarfan* bayan suna da mako biyu su Appa suka nufi Abuja. Amma ba tare da *Alishart* ba sun barta a nan gidan Papa, bayan wasu watanni wani yammaci zaune take a part d'in Mama wato Abida, suka ji a na buga masu k'ofa *Amna* ce wacce ta tafi domin ta bud'e k'ofar, ta bud'e k'ofar ta samu *Adeel* tsaye a k'ofa lokaci d'aya suka saki murmushi, ta shiga yi masa sannu da zuwa ya amsa sun koma ciki su Mama sun shiga yi masa sannu da zuwa, ya amsa tare da gaishe su ya k'ara da fad'ar sunan Mum. "Mum tare nake da Dady wai yana san zai yi magana dake yana bakin mota." *"Adeel* wai mai ya saka kake yi min irin haka a kan me zaka zo da shi nan? To ka tafi ka fad'a masa cewar ya bar nan kuma karya koma dawowa na har abada, sabo da ni sam bana buqatar sa a rayuwa ta ka ji ko." "A'a Mum dan Allah karki fad'i haka shi fa ya canja sosai wanda ke ma kin fahimci haka, Mum ai kin fad'a masa cewa kin yafe masa to mai yasa ba zai zo gurin ba? Mum nima ina san na kusance kamar *Adnan Adyan da kuma Amna,* suna rayuwa kamar sarki da sarauniya sabo da suna tare da duka iyayensu. Amma ni ban tab'a samun hakan ba Mum baki san iya yanda hakan yake cutar da ni ba, ko yaushe kukan zuci nake tin lokacin da ni nake yaro amma Mum baki tab'a amince da hakan ba, eh gaskiyar ni ne Dady ya cutar dake sosai amma kuma ya baki hak'uri har yana zubar da kwalla, sannan kuma kin fad'a masa cewar kin yafe masa duk da cewar har yanzu hukunta shi kuke. Mum ni ba zan iya b'oye maki gaskiyar ba ina san ku biyun ku k'ara kasancewa tare, wannan alfarma ce nake nai ma a gurin ki to ina fatan zaki amince da hakan please." Kallonsa kawai take yayin da ta gagara furta masa komai, shi kuwa ya shiga rarrashinta yana bata magana, *Amna* ma ta ta ya shi amma duk da haka bata furta komai ba, Mama zata yi magana tayi saurin dakatar da ita ta hanyar girgiza mata ka tare da furta. "A'a ni ba zan iya wannan ba sam ba zan tab'a k'ara komawa garesa ba na har abada, kayi hak'uri ďana sabo da ba zan iya baka abin da kake so ba dan Allah ka yafemin." "Shikenan tin da kin zab'a wa yaronki rayuwar k'unci, bayan kuma kina da damar da zaki taimake sa, amma kuma banyi fishi ba to ke ma karki yi fishi da ni dan Allah. Yanzu zan tafi na sanar da shi sak'on ki sai na dawo." Ya tashi domin tafiya Mama ta shiga girgiza wa Mum ka a lamar a'a, ya bud'e k'ofa yana k'oqarin fita Mum tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa, lokaci ďaya Mama da *Amna* suka sauke a jiyar zuciya. *"Adeel* ka fad'a masa cewa zanyi magana da shi, bayan na samu izini daga gurin ahalina amma ba yanzu ba dan haka ya jira wani lokaci." Cike da d'auki yake amsa ta, "eh zai jira har zuwa lokacin da zaki samu izini daga gurin Kaka, sannan kuma duk da haka yana godiya sosai sai na dawo." Ya juya ya fita su kuwa sun bisa da kallo har ya b'ace, ya fito tare da sanar da Prof abin data fad'a yayi wani gajeran murmushi yana cewa. "Shikenan zan jira ina fatan daga k'arshe ta amince da ni, dama su biyu ne nake fatan su amince da ni Mummyn ka sai kuma yaron k'anina. Alhamdulallah yanzu *Adnan* yana kira na da Kawu, hakama *Adyan* tin a ranar data bawa *Alishart* ya fara kira na da Kawu, yanzu sun fara bani girma *Adeel* ni ba sabo dasu na bata jini ba, amma ina farin ciki sosai da hakan ya zama silar da zasu ga girma na. To yanzu kuma Mummyn ka ce duk da irin nadamar da nayi amma sam ta kasa amincewa da ni, amma ba komai Allah ya fimu sanin daidai Allah ya zab'a mana mafi alkhairi Allahumma Amin." *Adeel* ya amsa shi da Amin da kuma haka suka yi sallama, Prof ya shiga mota yayi tafiyarsa bayan tafiyar sa *Adeel* ma juya wa yayi ya nufi ciki. Bayan mako biyu zuwa wannan lokacin Abbu ya dawo daga Abuja, Umma ta sanar da shi buqatar *Adeel* ta Mum ta koma gidan Prof. "Asiya ni ba zance komai ba har sai nayi magana da Yaya, yanzu zan kira layin sa sai muji abin da zai fad'a." Ta amsa shi da to ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin Abba ba jimawa ya d'aga, sun fara gaisawa sannan Abbu ya shiga sanar da shi abin da Umma ta fad'a masa, yayi shiru na jim kad'an yana nazari sannan daga bisani ya fara magana. "Gaskiyar *Adeel* ba wani d'a wanda zai so yaga iyayensa basa tare, amma kuma na san cewar zai yi matuqar wahala sosai, Aisha ta iya amincewa komawa gidan Prof sabo da cutarwar da yayi mata. Duk da cewar yanzu yayi matuqar yin nadama sosai, ni na tabbata Aisha ba zata tab'a yin aure da wani namuji daban ba, sabo da ko yaranta ma ba zasu amince da hakan ba. To ni ina ga kawai ta amince da buqatar yaronta ko ba komai shi zai yi farin ciki sosai, idan kuma ta ce a'a to fa ba wani wanda zai tilassa mata a kan hakan." "Shikenan Yaya zanyi magana da ita zaka ka ji duk yanda muka yi." Ya amsa ta da to da kuma haka suka yi sallama. Ta mai da kallonta ga fuskar Abbu ya jinjina mata ka a lamar eh, ita ma ta jinjina masa ka a lamar to da yamma bayan ta koma gida, take sanar da Mum abin da Abba da Abbu suka fad'a tayi shiru tana nazari, sai tinani take daga bisani ta anbaci sunan Umma. "Umma amma kina ganin su *Adnan* zasu amince da hakan kuwa.?" "Ban sani ba amma mai zai hana kiyi magana dasu domin ki ji ra'ayin su. Ta amsa ta da to ta d'auki wayar ta nan ta shiga kiran layin *Adnan,* ba jimawa sosai ya d'aga tare da sallama ta amsa ta kuma ci gaba da magana. *"Adnan* dan Allah idan kana da lokaci ina san zamu yi magana." "Shikenan sai na shigo." *"Adnan* qlau kake fad'a min wani abu mai ya saka ba zaka fad'i sunana ba.?" "Ina gida tare da Papa da Mamie." "Na fahimta sai ka shigo." Ya amsa da ok sunyi sallama bayan isha ya nufi gidan Mum, domin jin kiran da take masa ya isa gidan tare da shiga ciki bayan sun gaisa yaci gaba da magana. "Mum mai kike san mu yi magana a kai.?" "Ba komai d'ana kawai dai ina buqatar ganin ka ne shi yasa na ce kazo." "Mum kiyi hak'uri wallahi yau mun jima sosai a office shi yasa muka gaji sosai, bayan mun koma gida kuma yau su *Aaryan* fitina suke bama su barni nayi barci ba. Baki ga yanda Besty take ta fama dasu ba dole sai da Mamie ta taimaka mata, kuma kin san qanwata na gida gasu *Aarfan* shi yasa ban iya fita zuwa ko ina ba bayan office." *"Adnan* idan irin haka ya k'ara faruwa to ka sanar da ni, sabo da na tafi na taimaka wa Mamie sannan kuma da akwai buqatar yaran su saba da ni. Ta yanda zan samu damar da zan kasance Kaka ta gari a garesu." Ya amsa ta da to yana murmushi ita ma abin da take yi kenan, suna haka sai ga Umma ta fito bayan ta gaisa da *Adnan* taci gaba da magana. "Aisha kun yi maganar kuwa.?" "Umma ko yanzun ma magana muke." "Aisha a game da wancan zancan shin kin sanar da shi kuwa.?" Kafin ta furta komai yayi mata rigagi. "Umma mai yake faruwa ne ita ba abin data sanar da ni.?" Nan kuwa Umma ta sanar da shi abin da yake faruwa, ya mai da kallonsa ga fuskar Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum to ke wane hukunci kika yanke.?" "Am dama ni ina san na ji ne daga gareku, su Kawu sun amince dana koma ga Prof sabo da farin cikin *Adeel,* amma duk da haka ina buqatar na ji miye ra'ayin ku kai da *Adyan.?"* "Mum to idan kuma muka ce a'a fa.?" "Ban yi mamaki ba sabo da dama na san cewar amsar ku ba zata wuce a'a ba, a baya na yi tunanin cewar Dady shi ne kawai wanda yake da san kansa da yawa, amma gaskiyar ita ce yaransa ma haka suke gaskiya jinin sa yana da k'arfi sosai." *"Adeel* wai mai kake fad'a ne haka.?" "Eh *Adnan* ni kawai gaskiyar nake fad'a, abin da nake cewa shi ne ku biyun ku yaushe kuna samun damar kasancewa tare da iyayenku, a kullum suna runguma ku jikin su sannan kuma su sunbace ku a lokaci ďaya, cikin qauna da soyayya tare da fad'ar muku cewar suna qaunarku sosai to amma ni kuma fa? Sam ban tab'a samun hakan ba ko sau ďaya a rayuwa ta, Mum da Dady basu tab'a shiga rayuwa ta a lokaci ďaya na, tin ina k'aramin yaro nake da burin samun kyakkyawar rayuwa kamar dai yanda yake kai da *Adyan.* Amma kuma mummunan kaddara ta bata bani wannan damar ba, dama ko a cikin ku ni ne mara sa'a shi yasa kaddara ta tazo min a haka, na yi tunanin cewar yanzu ne lokacin da nake jira yazo, amma sabo daku ba zan tab'a samun cikar burina ba. Shikenan tin da abin da kun ka zab'a min kenan ba komai zan ci gaba da jurewa na har abada." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya zai fita da sauri, *Adnan* ya dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa................... *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.* [3/23, 8:45 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *THREE BROTHER'S* 👑👑👑👑👑👑 👑👑👑👑👑 👑👑👑👑 👑👑👑 👑👑 👑 *Page 56* ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍ https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/ *w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* *w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,* *s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.* *Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.* Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa. *INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?* *NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.* Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko. Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa. *Bismillahir Rahmanir Raheem* *Tuesday 22/03/2022* *Time 06:14pm* *Typing...............* 🔚🔚🔚🔚 Insha Allah. *"Adeel* wai mai kake fad'a ne haka? Kai sam ka gagara fahimta ta ballantana ka iya gane abin da nake fad'a, *Adeel* ni na yi matuqar fahimtar ka sosai amma kuma abin da kake so yana da matuqar girma sosai. Kai ka fimu sanin waye Prof da kuma irin abin da zai iya aikata wa, mu kawai mun damu ne sosai a game da Mum, amma shikenan idan kana ganin komawar ta gidan Prof shi ne daidai. Ni ba zanso wannan yanayin naka yaci gaba da cutar da kai ba, sabo da hakan zai bawa shaid'an damar shiga zuciyarka, ya kuma saka maka wasuwasi a kai na da kuma Aboki, to ina ga kawai wannan lamarin ya k'are a yanzu. Ni da kuma Aboki mun baka damar cika burin ka, ina nufin mun amince da duka buk'atar ta to yanzu kana farin ciki.?" Wani irin kallo yake yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a sosai, sam bai iya amsa shi ba sai dai ya nufi gurin sa yana zuwa, cike da d'auki yayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar. "Ina sanka d'an uwa ina qaunarka sosai, kayi hak'uri da irin yanayi na ni kawai na k'osa ne sosai, shi yasa nake yin duka wannan amma kuma daga k'arshe burina zai cika, mafarki na zai zama gaskiya ina farin ciki sosai da hakan." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare da shi sosai, sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake *Adnan* daga rungumar da yayi masa. Ya mai da kallonsa ga fuskar Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum shin ke kin shirya wa hakan kuwa.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh farin cikin sa ya k'aru sosai sai wani lallausan murmushi, yake sosai mai had'e da dariya dukansu sai wani kallonsa suke kallo sosai, bayan wani lokaci ganin lokaci ya tafi sosai yasa, *Adnan* yayi sallama dasu tare da sai da safe ta tafi, ya fara zuwa part d'in su Mama sun gaisa sun d'an tab'a fira kad'an, sannan yayi sallama dasu ya tashi ya tafi. Tin a mota ya kira layin *Adyan* ya sanar da shi abin da yake faruwa, ba shi da wani zab'i a kan abin da *Adnan* ya fad'a, wanda wannan dalilin ne yasa ya amince da hakan. Cike da d'auki *Adeel* ya tashi ya fita duk da cewar dare yayi sosai, kai tsaye gidan Prof ya nufa ya isa gidan tare da buga masa k'ofa, ba jimawa yazo ya bud'e bayan da ya ji cewar waye cike da d'auki yayi hugging d'in Prof yana cewa. "Kayi narasa duka ahalin sun yarda sun kuma amince da cewar Mum ta dawo gareka, a gaskiya na wahala sosai kafin na iya samun amincewar su, sabo da suna yawan tunawa da baya wanda sam sun gagara mantawa, Dady ina ro e ka daka kasance muji na gari a gurin Mum. Ka saka ta farin ciki sosai kasa ta ji cewar tafi ko wace mace sa'ar samun muji a rayuwa, kasa ta manta baya gaba d'aya sabo da a yanzu zuciyar ta cike take da tsoro, firgici rud'ani da kuma fargaba tana ganin kamar zaka k'ara cutar da ita ne. Dady wane irin alkawari zaka yi min a game da Mum.?" Kallon d'an nasa kawai yake yayin da ya gagara furta masa komai, sai wani kyakkyawan murmushi fuskar sa take fitarwa, cike da soyayya da qauna yayi hugging d'in sa yana sunbatarsa. "Na gode sosai d'ana Allah yayi ma albarka ya kuma albarkaci rayuwarka, hak'iqa kai d'a na gari ne a gareni ina matuqar alfahari sosai da hakan. *Adeel* nayi ma alkawarin kasancewa muji na gari a gurin Mummyn ka, zan tabbatar na saka ta farin ciki sosai, zan zame mata tamkar bawa har zuwa lokacin da zata 'yanta ni. Zanyi komai domin ganin na gyara duka zunubin dana aikata mata, wannan alkawari ne to zaka iya yarda da ni d'ana." "Na gode sosai Dady na ina qaunarka sosai Dady." "Nima haka ďana ina matuqar masifar qaunarka sosai, fiye ma da yanda nake sanka ina qaunarka ďana." Lokaci ďaya suka k'ara runguma juna sosai, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna, ganin dare yayi sosai yasa yayi masa sallama ya tafi. Washe gari da yamma lis Prof ya isa gidan su Mum, kai tsaye part ďin su Umma ya nufa zaune suke a parlour dukansu, suka ji a na buga masu k'ofa *Amna* ta yunk'ura zata tashi, da sauri Mum ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a 'yata k'ila mujin nawa yana buqatar hutu sosai to ya kamata ya huta, ni zanyi wannan da kai na to kawai ki huta kin ji ko masoyiya." Cike da jin kunya ta jinjina mata ka a lamar to ita kuwa sai murmushi take, mai tare da 'yar dariya hakama su Mama abin da suke yi kenan. Mum ta tashi ta nufi k'ofa domin ganin waye, ta isa k'ofar tare da bud'e wa ba tare data tambaya waye ba, ta samu Prof tsaye a gefen k'ofa ta ja numfashi tare da furta masa kalmar. "Kai ne to mai kuma kake yi a nan.?" Murmushinsa ya k'aru sosai cikin kwantar da murya yake magana. "Ina ga ba zai zama laifi ba idan nazo gurin uwar yarona, sannan kuma wacce zata k'ara kasancewa matata nan kusa kuma kusa sosai insha Allah." "Prof to komai saurin unguwar zoma zata jira nak'uda, eh gaskiyar ka ne ni ce nan mahaifiyar *Adeel* na ji mamakin da baka manta hakan ba. To ka gode Allah daya kasance da akwai d'a a tsakaninmu, da k'ila mu biyun ba zamu koma kasancewa tare da juna ba na har abada. Amma yanzu sabo da girmama farin cikin yarona na amince zan koma gareka, to yanzu zaka iya tafiya sabo da bana buqatar ka nan." "Shikenan zan tafi amma zan koma dawowa, yanzu ki kasance cikin farin ciki sosai sai na dawo." Ya juya ya tafi kamar dai yanda ta buqata ita kuma ta koma ciki, Umma ta shiga tambayar waye yazo ta sanar da ita, bayan muntuna biyu ta tashi ta shiga ciki sun bita da kallo har ta shige. Bayan kwana biyu Prof ya had'u dasu Abba su Abbu sun yi masa nasiha sosai tare da jan hankali, inda kuma daga bisani suka saka musu ranar mako biyu, a zahirin gaskiya Prof da *Adeel* suna farin ciki sosai, hakama Papa ganin yanda Yayansa yake ci gaba da zama mutumen kirki. Ta b'angaran *Adnan da Adyan* kuma sam basa farin ciki sai ma ji suke, tamkar su dakatar da faruwar hakan amma sam basu da wannan damar, hakan kuwa ta tabbata suna ji suna gani bayan mako biyu a ka d'aura auran Prof da Mum. Umma kuma ta koma gidan Abbu da zama gaba d'aya, kasancewar Mum a nan gidan ta ta tare haka dai Prof yayi ta, k'oqarin kasancewa muji na gari a gareta kuma uba na gari a gurin *Adeel.* Mum ta yi masa gwaji da dama amma yayi nasaran tsallakewa, wanda kuma hakan ne ya tabbatar mata da cewar ya canja, ya dawo mutumen kirki sosai shi yasa ita ma ta yanke shawaran kasancewa mata ta gari a garesa. Sunci gaba da zama cikin kyakkyawan yanayi hakan ya k'ara yiwa *Adeel* dad'i sosai, wani yammaci Prof ya samu *Adeel* zaune wani kyakkyawan guri tare da *Amna,* bayan sun gaisa Prof ya sauke kallonsa ga fuskar *Amna* tare da fad'ar sunan ta. *"Amna* dan Allah ko zaki iya bamu guri ina san zanyi magana da shi." Ta amsa shi da to ta tashi ta fice bayan tafiyar ta ya zauna tare da fad'ar sunan *Adeel.* *"Adeel* ďana ina san zamu yi wata magana mai matuqar muhimmanci sosai, to ina fatan zaka bani had'in kai sosai sannan kuma zaka sanar da ni gaskiyar gaba ďaya." "Eh Dady kawai ka sanar da ni koma miye kuma zan sanar da kai gaskiyar idan har na sani." Yayi shiru kad'an sannan yaci gaba da magana. *"Adeel* dama a game da *Adnan da Adyan* ne zuciyata tana fad'a min wani abu a game dasu." Cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. "Dady mai zuciyarka take fad'a maka a game dasu ne.?" Ya nisa sosai tare da jan numfashi ya k'ara da sauke a jiyar zuciya, sannan daga bisani yaci gaba da magana. *"Adeel* ban san ya zaka d'auki abin ba, amma gaskiyar ita ce ina jin wani irin abu sosai a tare dasu, sannan kuma zuciyata tana fad'a min cewar su ne yarana da a ce sun mutu sabo da." "A'a Dady sam karka amince da abin da zuciyarka take fad'a maka, sabo da ba gaskiya bane kawai yaudarar ka take ya kamata ka fuskanci hakan." *"Adeel* amma kuma komai a bai yane yake dukanku ukun, kuna tare da irin ciwo ďaya wanda kuma mahaifiyar ku ce take da wannan cutar, sannan kuma dukanku kuna matuqar san samosa da madara sosai, kai kafi kowa sanin irin yanda nake matuqar san samosa sosai, Mummyn ka kuma ba abin da take so fiye da madara sosai. Amma kuma ku duka biyun kuke so kuma sosai, ďana wannan ma ya isa ya tabbatar da gaskiyar, sannan kuma dai dukanku ukun kuna da kamanni da juna sosai, hakama kuma dukanku kuna matuqar qaunar junanku sosai. *Adeel* wannan ba zai faru haka kawai ba abin da yawa sosai, ni ina ganin kamar zuciyata gaskiya take fad'a min lallai ya kamata na yi wani abu. Amma kafin nan d'ana shin da gaske baka b'oye min komai dan Allah.?" "A'a Dady ni na riga dana sanar da kai duka gaskiyar to ya kamata ka yarda da ni please." "Shikenan na gode sosai zan tafi." Ya jinjina masa ka a lamar to da kuma haka suka rabu, cikin hanzari *Adeel* ya tashi ya nufi gurin Mum ya sanar da ita abin da yake faruwa. "Mum ina ga kamar lokaci yayi wanda ya kamata Dady ya san a salin gaskiyar, to ni zanyi magana dasu a kan su amince da gaskiyar su bai yana kansu ga Dady, idan har su da kansu suka sanar da shi gaskiyar to zai iya fahimtar su, amma idan kuma shi da kansa ya gano gaskiyar to fa komai zai lalace ne." "Eh gaskiyar ka ne ya kamata ni nayi magana dasu zance su zo nan yanzu." Nan kuwa ta shiga kiran layin *Adnan* ta sanar da shi cewar suzo tana san ganin su yanzu, ya amsa ta da to sunyi sallama abin da basu sani ba shi ne, duk abin da suke fad'a a kan kunnan Prof ya fad'a a zuciyarsa. "Zuciyata tayi gaskiya ba shakka wannan dalilin ne yasa suka tsane ni sosai, tabbas na cancanci hakan daga garesu zan jira zuwan su domin mu fuskanci juna. Ina fatan zasu yafemin sannan kuma su karb'e ni a matsayin mahaifinsu ta yanda ahalinmu zai k'ara cika." Ba jimawa sosai sai gasu *Adyan* sun k'araso zuwan su a kan idanuwan Prof, ba jimawa da shigarsu ciki shi ma ya shiga ciki, ya same su suna magana basu da wani zab'i a wannan lokacin. Wanda wannan dalilin ne yasa su sanar da shi gaskiya, yayi matuqar farin ciki sosai tare da nai man gafaran su, yana mai kaskantar da kansa yayin da yake zubar da kwalla. Mai tsananin zafi da k'una sosai sun kuwa yafe masa hakan yayi wa yi masa dad'i sosai, bayan kwana biyu dukansu zaune suke a tebur domin cin abinci, samosa ce da madara Mum ta had'a cikin hanzari dukansu suka kai hanayensu, ga samosa da sauri Dady ya dakatar dasu yana cewa. "Wannan ta ni kad'ai ce to kawai ku sha madara kun ji ko." "A'a Dady mu ba zamu yarda ba." Sun shiga yi masa magiya ganin kamar ba zai basu ba, yasa suka shiga wasoso tamkar wasu rana Mum sai dariyar su take, cike da soyayya da qauna Prof ya rungumasu jikin sa tare da sunbatarsu, yana furta musu kalmar yana qaunar su sosai bayan ya sake su, ya tashi ya nufi gurin Mum ya zauna k'asa da ita, tare da kama hanayenta sannan ya fara magana. "Na gode sosai da kika shiga rayuwa ta, hak'iqa ke alkhairi ce a gareni dama rayuwa ta gaba d'aya. Da a ce baki dawo gareni ba to dana shiga uku na lalace, k'ila dai da ba zan rayu ba ko kuma nayi mak'ask'anciyar rayuwa, sabo da na jima da mutuwa amma kika k'ara raya ni, ke ce nan wacce ta sake bani sabuwar rayuwa na gode sosai Allah ya saka maki da mafi alkhairi, Allah ya sanya wa rayuwar yaranmu albarka data yaransu ita kuma *Amna* Allah ya sauke ta lafiya Amin." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai, ita ma haka murmushi take sosai wanda ya hana mata iya fad'ar komai, ya sunbaci hanayenta da suke cikin nasa tare da furta mata kalmar i love you. Cike da d'auki su *Adeel* sun k'arasa inda suke lokaci ďaya suka yi hugging juna, bayan sun sake juna suka tashi suka koma tebur suka fara cin abinci, haka dai suka ci gaba da rayuwa cikin kyakkyawan yanayi, dukansu yaran suna farin ciki sosai tare da duka ahalinsu. Ba kuma tare da sun bar wata kafa wadda zata bari wani ya san gaskiyar ba, bayan wasu watanni *Amna* ta aihu ta aifi twin's duka mata, farin ciki gurin su Prof abin ba zai fad'u ba sai dai na ce suna farin ciki sosai. Bayan suna da wata biyu su Appa suka fara shirin tafiya England, su Mum sai ji suke kamar su dakatar da shi amma sam basu da wannan damar, haka suka ci gaba da shirin tafiya bayan mako biyu jirginsu ya tashi, sun samu rakiyar duka iyayensu Mum da Prof Abba da Mama Papa da Mamie da kuma su Kaka wato Abbu. Sun rungumi juna cikin qauna da soyayya sannan daga bisani suka yi sallama, su Umma sun bisa da kallo suna d'aga musu hanu har suka b'ace, suma abin da suke yi kenan har suka fice ba jimawa sosai jirginsu ya tashi, su *Adnan* sun bi jirgin da kallo suna murmushi tare da yi musu bye-bye. Sai bayan jirgin ya tafi ne sannan su *Adeel* suka shiga mota zuwa gida......................... *To Alhamdulallah kuma a daidai wannan gabar ce na kawo k'arshen, wannan littafin nawa mai taken suna THREE BROTHER'S. Ina fatan abin dana fad'a ba alkhairi Allah ya bani ladarsa, inda kuma na samu tintib'en harshe Allah ya gafarta min, sannan kuma Allah yasa muyi anfani da darasin dake ciki Amin. Da kuma haka nake cewa sai mun had'u daku a wani sabon littafina, sai an jima ma'assalam.* *Godiya gareku tarin masoyana mabiyana, masu yi mani fatan alkhairi ina godiya sosai Allah ya bar qauna Amin. Jinjina ga k'ungiya ta wacce ta taimaka min sosai gurin ganin nayi duk wani abin daya kamata, to ina godiya sosai Allah ya k'ara d'aukaka ta ya kuma sanya mata albarka Amin.* *BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*