K'AWAR KARUWAI 💃💃💃 SHORT STORY By FATIMA ABDALLAH KANO (Autar marubuta)📚 _______________________________________fatan za a dau darrisan cikin labarin , abin da ba shi da kyau kuma ai watsi dashi🙏 paga 1&2 Wayar daya daga cikin su ce ta fara ringin, inda mai wayar ta dubi wayar , ganin mai kira ne yasata tsaki ta dau wayar ta kashe, wata mai suna Ruma ce ta kalle ta tana cewa, "auuuu farida Alaji nuhu ne fa" farida taja dogon tsakin takaici tana cewa, "rabu da kwarto, wai ni Alaji nuhu zai cewa nake gyara kaina tsabar rashin mutumci , ai wlh ko mutuwa zai ko me zai ban, bazan sake zuwa gidan shi ba, zai san yayi da ni" ta aje maganar tana hucewa kan cingon din dake bakinta, farida ta wai ga ta kalli ummi baby da hankalinta duu yake kan wayar da take dannawa tana cewa, "ummi baby ba kyajina da mutuniyar taki ne"? ba tare data dago kai ba ummi baby tace, " ina jinku mana , ai ruma tunda yace ki gyara kawai ki gyara, shi yasan dalilin ", farida da ranta ya sake baci da maganar ummi baby cikin fusata take cewa, " me kike nufi ", ummi baby tace " aahhhhh ni ba abun da nake nufi , ai kin mayi kokari domin kin dade kina tare da alajinnan duu ya tsufa", farida tai ajiyar zuciya sannan tace "dani yake zancen aiii". Alokacin ummi baby ta aje wayar dake hannun ta tana kallon farida da ruma , tana cizan lebe, ganin hakan yasa ruma tambaya, " ya ne "? ummi baby ta gyara zama akan katifar da take zaune , wanda still bata dena kallon su ba, " ina san fada muku zan koma legas da zama , nayi missing din mutane na, kano ba kamar legos ba ", ruma da farida suka hada ido alamunsu duu maganar batai musu dadin jiba, " ya naga duu kunyi wani iri ne"? ummi baby ta tambaya ruma cikin yayin rashin jin dadin maganar tace, "legos kuma , gaskiya ummi baby ki zaman ki anan", ummi baby ta mike ba tare da tace dasu komai ba ta bar dakin. ⚡ shin su waye wa 'yannan? sannu a hankali zamusan asalinsu. muje zuwa👇👇 Ba wani babban gida bane, amma tabbas akwai rufin asiri , zaune take a cikin falon gidan, tana danna waya tana murmushi, da alamun tana matukar jin dadin yanayin, alokacin wata dattijuwa mai kimanin shekaru 69 ta shigo falon , wannan tsohuwa idan ka kalleta ba za kace tayi wannan shekaru ba, tana shigowa ta kalle ta, tana cewa, " fadeela kiwa kanki fada wallahi" jin hakan yasa fadeela dagowa tana cewa ," to kaka me ne nayi kuma"? dattijuwar tace ,"tunda naga kina murmushi nasan da wannan KARUWAN ne ba shakka, dan Allah don annabi ki dena kula yarannan, yaran tarbiyya ya za'ai suke zuwa gidan maza suna kwana, amma su ne kawayen ki fadeela, wannan wacce irin rayuwa ce"? fadeela tai murmushi tana cewa, "kaka kenan , suma mutane ne fa, kuma dan Adam ajizine , jawosu a jikin da nake zaisa su gane gaskiya sai kiga sun shiryu", kaka taja tsaki ta koma inda ta fito murmushi fadeela ta sake yiii😊 tana cewa," kaka kenan, suma KARUWAI ai mutane ne " batai zaton ranta zai bace cikin wannan lokacin ba saida taji sallamar wanda batai tunani ba, ganin shigowar shi falon da sallama yasa ta takaici saurayi ne san kowa dogo aje da gemu, yasa jallabiya da hularshi taba kaji hadisi, idan kace dashi ustaz bakai karya ba, kawai fadeela ta mike ba tare data amsa sallamar ba ta shige dakinta😮 saurayin dake rike da jaka a hannunshi yay murmushi yana cewa,"sayyada fadeela kenan, nazo tun daga kaduna dan kee amma wannan ita ce tarba", yay ajiyar zuciya dama yaci ace ya saba da wannan hali na fadeela, kafin ya sake motsawa daga inda yake kaka ta fito , "aahhhhhhh, zakariyya kai ne , ahh sannu da zuwa" , nan take kaka ta tarbeahi cikin yanayi mai kyau. WACE FADEELA? Hajiya mama (kaka) mahaifiyar mlm Ibrahim da Aminu, wanda su Allah ya bata har tsufanta, kafin ace Ibrahim ya rasu mahaifin fadeela, sai ya zama yaronta guda daya ne yanzu wanda yake raye. mlm Ibrahim mutumin kirki ne, ya nunawa fadeela kauna kafin Allah ya dauki ranshi, daman mahaifiyar fadeela tana haifarta ta bar duniya, sai ya zama fadeela ta tashi gurin kakarta Hajiya, wanda yanzu gidan da suke zaune na fadeela ne , fadeela na da hankali a idon mutane da kuma tarbiya, sai dai abin dake son batata wajen mutane kawayenta KARUWAI da take dasu, kanin babanta Aminu yayi iya kokarinshi domin ganin fadeela ta dena kula su, amma abin yaci tura , wanda har gidan shi sai da ya dawo da fadeela, amma ta dena ci ta dena sha, ganin hakan yasa kaka cewa"kar ya kashe mata jika kwalli daya da take da ita, ya dawo da ita gabanta" , aiko fadeela sannan ta samu kwanciyar hankali ko kadan Aminu ba yada nufin cutar fadeela, domin 'yarsa ya dauke ta, duda Allah bai bashi haihuwa ba ya jima yana addu'a yana nema amma Allah bai nufa ba, hakan yasa yake tsayawa fadeela akan harkar karatunta da rayuwar ta hartai aure, duda ta nuna musu sam bata son wanda suke so, ba kuma tare da dalili ba. "ummi baby kin hadu a cikin mata na gaza samun ta biyunki, hakan yasa bazan barki ba domin ko wanne irin yanayi nake ciki da mun hadu nake mancewa da komai" duu yana rike da kugun ummi baby yake wannan maganar, ta dubeshi idanunta cikin nashi tana cewa, "ambassador kenan, to idan baka rabu dani ba aurena zakai ko me"? hannun shi ya cire a kugunta yana taba fuskarta da laushin fuskar ya rikita shi yana cewa," haka zamu ci gaba da rayuwa , amma bana son kowanne na miji ya kusance ki, ni kadai kawai" "aha amma kasan ni ta kowace duu inda zan sami kudi za'a ganni agun" kallon ta yay sama da kasa , sai a lokacin ambassador ya sake kula da suturun dake jikinta, sauri yay ya cire hannun shi a fuskarta yana rintse idanun shi "wow😱 sweet baby " ya fad`a yana kokarin kai hannu jikinta a'irin suturun da babu duu daya. cikin hanzari fadeela take shiryawa sakamakon tayi muguwar makara a zuwa university, kawai Allah-Allah take ta ganta cikin makaranta, lokacin data fita ta bata lokaci ma kafin ta isa zuwa can, zuwanta har an fito daga lecture, wajen friends dinta ta dosa datai hangensu. Allah ka biya bukatun masu share d`in novel dina ka faranta musu🙏🙏 __________________________ K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA __________________________ Page 3&4 Fadeela na k`arasawa wata a cikin k`awayenta tace ,"K`AWAR KARUWAI an iso ke nan", murtike rai Fadeela ta yi tana kallonta da cewa, "Amina Umar bana san rashin mutunci wallahi, ke kullum yadda zaki b`atan rai shi ne abin nemanki , to wallahi ya isheki", ita ma Aminan cikin zafi ta fara mai da mata da martani, abin kamar wasa mutane suka taru a gun saida aka rabasu, daga bisani Amina Umar ta bar gun cikin hassala, sai ya rage daga Zainab yunus a gun sai Fadeela, nan Zainab ta fara rarrashinta tana bata hakuri nan ne Zainab ta d`auko zancen Zakariyya , " wai Fadeela ya Zakariyya ne ya fa kira ni yace yazo ko kulashi baki ba , wa kike da shi sama da Zakariyya, to ni wallahi na fara gajiya da da sulhu kawai zance masa ya hakura", Fadeela ta kalleta tana cewa,"na tsani Zakariyya, kin ga shi dai d`an uwana ne amman wallahi duk san da na ganshi raina yana kuna, kuma da kike maganar wa nake dashi banda Zakariyya kisa ido zaki gani cikin Alaji mansur da Aliyyu sai na auri wani", Zainab tai ajiyar zuciya tana cewa, "to Allah yasa ai mutanen kirki ne, Allah ya mana Zab`i na gari". Anan gidan k`anin baban Fadeela kuwa Aminu zaune yake cikin falonsa yana rarrashin matarshi dake rusa uban kuka," dan Allah ki yi hakuri Jamila duk yadda Allah ya jarrabi bawansa babu yadda ya iya , kuma haihuwar nan wallahi Allah yana sane damu ki dena kuka", yaja dogon numfashi yana cewa, "ni wallahi ma babban abin dake damuna Fadeela ce , nauyi ne a kaina na kula da yarinyar nan kuma ina iya bakin iyawata, tun da ta fara kula wannan K`ARUWAN💃💃💃sam hankali ba ya kwanciya, gashi ita ma Inna wani zubin bata san ina mata fad`a ina tsoron taja mana abin kunya", matarshi Jamila tai ajiyar zuciya tana k`arasa goge guntun hawayenta tana cewa," kasan Fadeela yarinya ce mai hankali da tarbiya, kuma tasan me take ,Allah ne yasan dalilin had`ata dasu wata kila ta zamto silar shiryuwarsu", Aminu yace," zan je wa Inna da maganar aurenta tunda Zakariyya na san ta kawai a bashi domin mun yarda da tarbiyarshi", Jamila tace ,"Allah yasa hakan ne yafi alheri, amma Fadeela yarinya ce mai ilmi idan Zakariyya ya sameta ya more ". Anan gidansu Ummi baby abinci suke ci suna hirar mazajensu😥 Ruma ce tace ," ni fa inajin zan yi tafiya zuwa gombe", rasssss gaban Farida ya fadi ta tsaya tana kallon Ruma, ganin hakan yasa duk suka kwashe da dariya suna kallonta Ruma tace ,"Hmmm ai ni da gombe har duniya ta nad`e",Ummi baby ta kalleta tana cewa, "mutum da mahaifarshi kina fa da 'yan uwa a can", Farida tace " tom ke kina zuwa Niger ne ?garama ni bani da iyaye", fad`owar Fadeela d`akin ne yasa su shewa suna murna ta kallesu cikin girmamawa tana cewa, "wato kun manta dani saboda kuna gudun nasihar da nake muku ko, da zaku bi ta tawa ku tuba kubi Allah domin wallahi kuna da sauran lokaci", shek`ewa da dariya sukai irin ta 'yan bariki 😂😅💃 Ruma ce ta kalli Fadeela tana cewa," ke Fadeela mufa bamajin kira mun san dad`in karuwanci mun san kowanne na miji, kawai idan zaki fad`o ayi da ke shi ne magana", Ummi baby tace ,"kwarai kuwa domin da zaki karuwanci wallahi zaki wataya yadda kike da sama da kasan nan duk kin fi mu fa, kina da kayan aiki Fadeela kawai ki fad`o", Farida tace, "nima dai abin dana gani ke nan kin dad`e kina burgeni", Ruma tace," to kinji kina burge mata bare kuma maza", tafawa sukai✋suna dariya😂 Fadeela tace ,"Hmmm Allah ya ganar daku gaskiya amman wallahi ina ji muku tsoron mutuwa ta riskeku a haka babu abin da zaku ce da mahaliccinku," Ummi baby tai tsaki tana kallon Fadeela,"ni nan ma da kika ganni garin babbar harka zan koma , saboda wannan taron da ake na kyawawan KARUWAI ya kusa, zamu je mu shoshale mu iskance da mutanen mu", "wa iya zu billah", Fadeela ta fad`a Ummi baby ta kwashe da dariya tana cewa nifa yau gidan wani zazzafan Alaji na nufa , dan haka bari na tashi nai wanka", Ruma tace," ai nima yau ba a gida zan kwana ba akwai babbar harka, wai Farida ya kika k`are da Alaji Nuhu ne ,"? Farida tace, " rabu dani da kwarton banza kinji",dariya suka sake yi yayin da Fadeela ta d`aga hannu sama tana cewa👐,"ya Allah ka shirya mu ka shiryar da k`awayena su dawo hanya su koma wajen a halinsu su yi rayuwa mai kyau ", dariya suka k`ara tintsirewa da ita suna tafawa da junansu ✋😂 "sai mu fitattun Karuwai uku💃💃💃 karuwanci dad`i",😂 Shin wace Farida , wace Ummi baby wace Ruma 👇👇 share and comment my fans. Allah ka biya bukatun masu share d`in novel dina ka faranta musu🙏🙏 __________________________ K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA __________________________ Page 3&4 Fadeela na k`arasawa wata a cikin k`awayenta tace ,"K`AWAR KARUWAI an iso ke nan", murtike rai Fadeela ta yi tana kallonta da cewa, "Amina Umar bana san rashin mutunci wallahi, ke kullum yadda zaki b`atan rai shi ne abin nemanki , to wallahi ya isheki", ita ma Aminan cikin zafi ta fara mai da mata da martani, abin kamar wasa mutane suka taru a gun saida aka rabasu, daga bisani Amina Umar ta bar gun cikin hassala, sai ya rage daga Zainab yunus a gun sai Fadeela, nan Zainab ta fara rarrashinta tana bata hakuri nan ne Zainab ta d`auko zancen Zakariyya , " wai Fadeela ya Zakariyya ne ya fa kira ni yace yazo ko kulashi baki ba , wa kike da shi sama da Zakariyya, to ni wallahi na fara gajiya da da sulhu kawai zance masa ya hakura", Fadeela ta kalleta tana cewa,"na tsani Zakariyya, kin ga shi dai d`an uwana ne amman wallahi duk san da na ganshi raina yana kuna, kuma da kike maganar wa nake dashi banda Zakariyya kisa ido zaki gani cikin Alaji mansur da Aliyyu sai na auri wani", Zainab tai ajiyar zuciya tana cewa, "to Allah yasa ai mutanen kirki ne, Allah ya mana Zab`i na gari". Anan gidan k`anin baban Fadeela kuwa Aminu zaune yake cikin falonsa yana rarrashin matarshi dake rusa uban kuka," dan Allah ki yi hakuri Jamila duk yadda Allah ya jarrabi bawansa babu yadda ya iya , kuma haihuwar nan wallahi Allah yana sane damu ki dena kuka", yaja dogon numfashi yana cewa, "ni wallahi ma babban abin dake damuna Fadeela ce , nauyi ne a kaina na kula da yarinyar nan kuma ina iya bakin iyawata, tun da ta fara kula wannan K`ARUWAN💃💃💃sam hankali ba ya kwanciya, gashi ita ma Inna wani zubin bata san ina mata fad`a ina tsoron taja mana abin kunya", matarshi Jamila tai ajiyar zuciya tana k`arasa goge guntun hawayenta tana cewa," kasan Fadeela yarinya ce mai hankali da tarbiya, kuma tasan me take ,Allah ne yasan dalilin had`ata dasu wata kila ta zamto silar shiryuwarsu", Aminu yace," zan je wa Inna da maganar aurenta tunda Zakariyya na san ta kawai a bashi domin mun yarda da tarbiyarshi", Jamila tace ,"Allah yasa hakan ne yafi alheri, amma Fadeela yarinya ce mai ilmi idan Zakariyya ya sameta ya more ". Anan gidansu Ummi baby abinci suke ci suna hirar mazajensu😥 Ruma ce tace ," ni fa inajin zan yi tafiya zuwa gombe", rasssss gaban Farida ya fadi ta tsaya tana kallon Ruma, ganin hakan yasa duk suka kwashe da dariya suna kallonta Ruma tace ,"Hmmm ai ni da gombe har duniya ta nad`e",Ummi baby ta kalleta tana cewa, "mutum da mahaifarshi kina fa da 'yan uwa a can", Farida tace " tom ke kina zuwa Niger ne ?garama ni bani da iyaye", fad`owar Fadeela d`akin ne yasa su shewa suna murna ta kallesu cikin girmamawa tana cewa, "wato kun manta dani saboda kuna gudun nasihar da nake muku ko, da zaku bi ta tawa ku tuba kubi Allah domin wallahi kuna da sauran lokaci", shek`ewa da dariya sukai irin ta 'yan bariki 😂😅💃 Ruma ce ta kalli Fadeela tana cewa," ke Fadeela mufa bamajin kira mun san dad`in karuwanci mun san kowanne na miji, kawai idan zaki fad`o ayi da ke shi ne magana", Ummi baby tace ,"kwarai kuwa domin da zaki karuwanci wallahi zaki wataya yadda kike da sama da kasan nan duk kin fi mu fa, kina da kayan aiki Fadeela kawai ki fad`o", Farida tace, "nima dai abin dana gani ke nan kin dad`e kina burgeni", Ruma tace," to kinji kina burge mata bare kuma maza", tafawa sukai✋suna dariya😂 Fadeela tace ,"Hmmm Allah ya ganar daku gaskiya amman wallahi ina ji muku tsoron mutuwa ta riskeku a haka babu abin da zaku ce da mahaliccinku," Ummi baby tai tsaki tana kallon Fadeela,"ni nan ma da kika ganni garin babbar harka zan koma , saboda wannan taron da ake na kyawawan KARUWAI ya kusa, zamu je mu shoshale mu iskance da mutanen mu", "wa iya zu billah", Fadeela ta fad`a Ummi baby ta kwashe da dariya tana cewa nifa yau gidan wani zazzafan Alaji na nufa , dan haka bari na tashi nai wanka", Ruma tace," ai nima yau ba a gida zan kwana ba akwai babbar harka, wai Farida ya kika k`are da Alaji Nuhu ne ,"? Farida tace, " rabu dani da kwarton banza kinji",dariya suka sake yi yayin da Fadeela ta d`aga hannu sama tana cewa👐,"ya Allah ka shirya mu ka shiryar da k`awayena su dawo hanya su koma wajen a halinsu su yi rayuwa mai kyau ", dariya suka k`ara tintsirewa da ita suna tafawa da junansu ✋😂 "sai mu fitattun Karuwai uku💃💃💃 karuwanci dad`i",😂 Shin wace Farida , wace Ummi baby wace Ruma 👇👇 share and comment my fans. Allah ya biya bukatun masu share d`in novel d`ina👐🙏 _______________________________ K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA ____________________________________ Page 5&6 Farida 'yar asalin Gombe ce da bata da iyaye , tana zaune gurin k`anwar babarta wacce take zaman aure tare da azzalumar kishiyarta,lokacin da tafiya tai tafiya hatta ita kanwar mahaifiyarta Farida sai da ta tsaneta ta gaji da ita saboda makircin kishiyar , Farida ta shiga mummunan yanayi babu wanda ke sata farin ciki ko damuwa da bukatunta, a karshe sanda zata rasu ta gane komai makircin kishiyar ne , ta bawa Farida hakuri ta nemi yafiyarta, bayan ta rasu Farida bata iya jurar wannan kuncin ba da tsana ta mussaman, hakan yasa ta fito yawon duniya inda taci karo da Ummi baby, nan suka zaba Ummi baby ta bata labarinta mahaifinta mai kudi ne a Niger yana san ta , kuma ita ma tana alfahari dasu sosai , bata kaunar bacin ransu ko a kwana a tashi mai faruwa ta faru kan Ummi baby saurayinta ya yi mata ciki , hankalinta ya matukar tashi , bata san inda zata sa ranta ba idan iyayenta suka gano wannan maganar hakan yasa tai kokarin zubar da cikin , amma a lokacin suka sami labari , nan Ummi baby ta rasa inda zata sa kanta , ba za ta juri ganin iyayenta cikin bakin cikinta ba , hakan yasa tun da ta fita bata dawo ba , bata sake wai wayar gidansu ba , nan hankalinsu ya sake tashi aka riinga sanarwa guri-guri da duk inda ya dace amma basu sami dawowar Ummi baby ba suka hakura . Nan suka fara karuwanci su har suka koma makaranta, inda anan ne suka sami Fadeela a matsayin K`AWAR SU suka yaba da kokarinta amma daga karshe suka dena makarantar suka kama harkarsu yayin da kuma suka sami Ruma wanda tun asali Karuwa ce ta taso cikin wata karamar hukuma dake jahar kano ta bayyana musu mahaifinta yana raye , amma yayan mahaifinta shi ke juya komai nashi , ya hanata karatu azzalumi ne shi kuma babansu yana masa biyayya saboda hakurinshi , a karshe yayan babanta ya tilasta mata kan sai ya yi amfani da ita , Ruma tace ga garinku nan ta baro masa garin ta tsinci kanta a wannan hali . Nan suka saba komai nasu tare , ita kuma Fadeela ta kasa rabuwa dasu 💃💃💃 tana ganin nasiharta zata tai make su a rayuwa , ta yi dasu ma su koma gidajen iyayensu amma sun ki , haka dai suka ji suka gani zasi rayuwarsu. DA Aminu da Inna ne cikin gidansu Fadeela bayansun gama gaisawa Aminu ya mik`a wa Inna takardun gidan da suke zaune mallakin Fadeela suna cikin hirarsu Fadeela ta shigo cikin babban shigabi har kasa ta kai ta gaida baba Aminu ya amsa cikin girmamawa "to Fadeela ga takardun gidan " Inna ta fad`a tana mik`a mata Fadeela ta kalli Inna tana cewa, "Inna ki aje a gun ki", Inna ta maida takardun jikinta tana adanawa. Baba Aminu ne yace ," yawwa Inna , ya maganar Zakariyya da Fadeela domin yaron nan jininmu ne kuma yana san Fadeela ", Fadeela ta murtike fuska tana kallon Inna Inna ba tare data kula da yanayin Fadeela ba ta fara magana ," to Aminu yanzu dai Fadeela tana karatu a bari idan ta kammala sai ai maganar domin shi ne burin mahaifinta, Allah ya jik`anshi", "amma ni Inna bana san Zakariyya fa ", Fadeela ta yi maganar tana durkusar da kai ", to wa kike so ba za ki samu sama da Zakariyya ba , bazan zauna na zuba miki ido ba kina girma kina yawo da Karuwai har ki ja mana abin kunya ", Inna ta aje maganar cikin haushi tare da sake fad`in ," zamu zauna a kan wannan maganar Aminu in yaso tayi auren taci gaba da karatun", wani bakin ciki Fadeela taji ya tokare mata zuciya.💔 Yanzu dare ne wajen karfe goma Ruma da Fadeela ne tsaye bakin titi ga dukkan alamu abin hawa suke jira babu jimawa wasu motoci fara da blue sukai parking a gabansu, Farida tsaki tai kawai tana kallon mai tuk`a blue mota tana haraararshi tare kuma da bud`e kofar ta shige suka tafi Ruma ma farar motar ta nufa tana dariya mai motar ne shi ma cikin murmushi yace ,"yau dai wannan murmushin ya tabbatar mini zan huta akwai tanadin da akai mini", ba tare da tace komai ba ta shige motar tana masa wani kallon bariki ,"yau hotel nake san zuwa", murmushi ya sake yi yana cewa, "yanzu kuwa hajjiyata", ya tuk`a motar suka nufi hotel nan daga zuwansu suka ringa tanbad`arsu da iskancinsu niko nace ba a yi a gabanmu ba 🏃🏃🏃😂. " wai dan Allah Fadeela me yasa kike yiwa Zakariyya haka ne",? Zainab ta fad`a ranta a b`ace ita ma Fadeela kallonta ta yi rik`e da wayarta a hannu tana cewa, "wallahi Zainab na tsani Zakariyya, bana san shi fiye da tunaninki", Zainab ta rik`e hab`a tana cewa," ikon Allah! Yanzu mene ne abin gudu wajensa Fadeela ",?Fadeela wani murmushi tayi tana cewa," duk abin da zai rabani da su Ummi baby bana kaunarshi, amma shi Zakariyya yana kiran kanshi ustaz amma ya kasa gane wannan irin jahadin da nake , kullum sai wa'azi Allah ya ce, malam wa ne ya ce , gaskiya ni bazan iya auren Zakariyya ba", da babbar murya mai cike da mamaki Zainab tace ,"tab! Yaushe kika koma haka Fadeela? gaskiya zamanki da karuwai bai amfane ki da komai ba , kin bani mamaki", Fadeela na kokarin maida mata da martani taji wayarta ta fara ruri , ganin wanda ke kiran wayar yasa murmushi da far'a suka bayyana a fuskarta, "wannan kai ne babban burin da nake so mallaka a rayuwa", Fadeela ta fad`a cikin shauk`i dajin zanen Zainab tasan cewa Aliyyu ne ke kiranta . Bayan wasu kwanaki Zainab da Fadeela ne zaune cikin ajinsu fuskar Zainab murtike ita kuwa Fadeela sumul sai shauk`i take domin tana sauraran zuwansu Ummi baby zasu kawo mata ziyara ganin kiran wayar Ruma ne ya tabbatar wa Fadeela sun iso , hakan yasa ta kalli Zainab tana cewa," mu je mana Zainab ", ba tare da Zainab ta kalli inda Fadeela take ba tace da ita ," ba inda zani , a dawo lafiya kije ki tsaya dasu students suna muki wani kallo", kawai Zainab ta yi tsaki ta fice Fadeela ta fice ita ma tare da nufar inda take da tabbacin za ta ga su Ruma , tana isa suka rungume juna suna murna "Aliyyu yace duk yana gashsheku ", Fadeela ta fad`a musu cikin girmamawa " a'a gaskiya ba ma amsawa , kullum sai gaisuwa ya kasa zuwa a gaisa",Farida tayi maganar cikin ya tsine fuska , yayin da Ruma ta ce,"ai kuwa dai", Fadeela tayi murmushi tana kallon hagu da damanta yayin data kula idanun wasu d`aluban a kansu yake, ba tare da yanayinta ya canza ba ta sake kallonsu tana cewa, "to naji insha Allah zaku gaisa da shi , amma ni bama wannan ba , yau idan na koma gida zan yi tafiya", " toooooooo"😯 Ummi baby ta fad`a ba tare da Fadeela ta jira sun tambayi k`arin bayani ba ta sake cewa,"zani biki kwana biyu zan yi na dawo", jin wayarta ta fara ringin yasa ta saurin cirowa wayar a rigarta mai tafe da aljihu , kallon fuskar wayar tayi ta saki dogon tsaki 😑 yayin dasu Ruma suka kalli juna lokaci guda kuma suna shirin jefa mata tambaya. share and comment🙏K`AWAR KARUWAI 💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _____________________________________ page 7&8 "mene ne hakan kuma, wake kira ",? Ruma ta tambaya , Fadeela cikin yatsine fuska tace ," wallahi Zakariyya ne ",ta aje maganar tana ajiyar zuciya sake kallonsu tai tana cewa," bari nai shirin komawa gida domin kar nai dare", Farida tace, "eh haka ne , mu ma bari mu koma", a lokacin Amina Umar tazo wuce wa ita da wasu k`awayenta yayin da take kallonsu Fadeela tana cewa," abokin b`arawo dai b`arawo ne , ato a fito kawai a ce anason karuwanci ", tana aje maganar sauran k`awayenta suka shek`e da dariya , suka wuce abin su ajiyar zuciya Fadeela ta sake yi tana kallonsu cikin rashin jin dad` yayin da wayar Ruma ta fara ringin , hakan yasa kowannensu bai ce komai ba ya maida hankali kan Ruma , Ruma murmushi tayi tana kallon fuskar wayar lokaci guda kuma tana cewa dasu ," Mubarak ne nasan akwai harka yau ", wayar ta kara a kunne tana cewa," bani nasha mutumin ",💃 daga can bangaren aka ce ," Ruma akwai wani Alaji yana hanyar zuwa kano yau , kuma zaki debe masa kewa , amma bari zami magana anjuma ", tace ," ok ", yayin da ya kashe wayar " harka tazo ko",?Ummi baby ta jefa mata tambayar d`aga mata gira Ruma tayi alamun eh, Fadeela kawai ta zuba musu idanu . Bayan Fadeela ta koma gida sukai sallama da Inna , nan Inna ta bawa Fadeela sak`o wanda zata kaiwa k`awar Fadeela da zata bikinta , bayan Fadeela tasa k`afa ta fice duk jikin Inna ya yi sanyi ya mutu .😒 daga cikin adai-daita Ruma ta fito yayin da ta dubi babban gidan da akai parking d`in ta a kofar, taku ta farayi tana dosar gidan tare da duban girmanshi , harta shiga cikin falo , tsayawa ta kuma yi tana duban falon tana murmushi da jin dad`in yadda iska mai sanyi ke ratsata , ba tare da ta ankara ba taji ana kokarin kissing d`in ta, da sauri ta juya tana kallon waye , gajeren wando kawai yasa , ba bak`i ba ne can yana da suma a kanshi mai kimanin shekaru 40 ajiyar zuciya tai tana cewa, "haba Alaji! Ai saika sa na tsorata , ko ciniki ba ai ba kake kokarin cin gyara", murmushi yayi yana kallon ta sama da kasa ," haba baby nifa cikakken d`an bariki ne , kuma nasan farashinki, shi yasa na fara abin da ya kawoni", ya matsa kusa da Ruma ya rik`e hab`arta yana cewa, "karki nunamin kin fini bariki domin zaki sha wahala , ba a maneji dani kad`an daga cikin mata ne ke dawowa gare ni bayan munsan juna", duk Farida jin shi take domin ko tsoro bata ji ba a cikin ranta tace," baka san wace Ruma ba ", Zainab ce zaune a falon gidansu ta kara waya a kunne ga dukkan alamu waya take , daga can bangaren aka ce, " wallahi Zainab, sam Fadeela bata sona , amma ni ina tausayin Fadeela, domin nayi alwashin share mata hawayenta na rashin iyaye amma sam tak`i bani had`in kai ", ajiyar zuciya Zainab tayi cikin muryar tausasawa tana cewa," ka yi hakuri Zakariyya, wallahi kullum ina fad`a mata wannan, amma insha Allah wata rana zata gane ", Zakariyya yace ," to Allah yasa Zainab, yasu umma da yaran", Zainab ta bashi amsa tana cewa, "wallahi lafyar kalau," yace "to Masha Allah aunty Zainab a gashshe mini dasu sosai", Zainab ta d`anyi jimm sannan tace , " uhumm aunty kuma "? Zakariyya yace ," eh mana bama wannan ba bani labari", abin ya sake ba Zainab mamaki tunani tai to kodai ya zata da Fadeela yake magana ne , domin ya tab`a fad`a cewa muryarsu iri d`aya ce . Ni kam nace oho👐 a rungume take jikinshi yana bin laushin fatarta yana shafawa da gani babu tambaya wanka sukai , yadda yake jin laushin fatarta yasa yake yawo da hannunshi ko'ina cikin jikinta ,"I love you Ummi baby ", ambassador ya fad`a yana murmushi " gaskiya babu ta biyunki cikin mata , ban ga wacce ta kama farcen ki ba", Ummi baby tai tsaki ta mike tare da sake tamke towel din dake jikinta , kallonta ya yi yana cewa, "mene hakan", fari tayi da ido tana cewa," dad`in baki ambassador, duk matan da kake nema haka kake fad`a musu , sannan kuma karka mance akwai alkawarin aure da kai mini", murmushi ya yi yana mikewa ya sake kanannad`ota jikinsa yana cewa, "haba baby a kan wannan zaki b`ata ranki, to yi hakuri ki murmushi", baki ta sake tab`emai tana cewa," to idan da gaske ne ka fito mi auren", "haba Ummi kinsan yanzu abubuwa sun cakud`e, amma komai yana daidaita zami aure", cikin shagwaba tana girgiza jikinta tace ", to shi ke nan", ambassador ya fara bin kamshin jikinta yana shaka tare da ajiyar zuciya, kai ambassador ko maye ko kadan baya gajiya da kusantar Ummi baby.😂 Yanzu wajen karfe 11:20 na dare , amma Farida tana tsaye bakin titi tana neman abin hawa , har da 40 tayi amma babu wani abun hawa da ya tsaya da nufin d`aukarta . Daidai da lokacin da tai ajiyar zuciya wata farar mota tai parking a gefenta ko kallan motar bata yi ba sakamakon wani huci da take , sanadi kuwa Alaji Nuhu ne ya b`ata mata rai tunda ta baro gidanshi yake ta kiranta a waya harta gaji ta kashe wayar, wani mahaukacin mutum ne Alaji Nuhu da sam ba ya da hakuri a kan abin da ya keso. " yan mata lafiya kuwa", saurayin dake cikin motar ya zuro kanshi yana fad`a dogon tsaki taja tana sake kau da kanta "yan mata bai dace ba kina mace ,amma kina waje a irin wannan lokacin , ki shigo na rage muki hanya", Farida ta kalli saurayin wanda lokaci guda taji ya kwanta mata tayi murmushin takaici tana cewa," a'a na gode", rufe bakinta ke nan motar Alaji Nuhu tayi parking duk hankalinsu ya karkata wajen , da sauri ya fito yana cewa, "ni zakiwa haka farida? to wallahi baki isa ba, yau ina san kwana dake kuma ina yunwarki dole ki bani hak`k`ina",😁 saurayin dake cikin motar ya saki baki cikin ranshi yake cewa", a she matar aure ce , amma wannan mijin nata ba shi da hankali", Farida ta sake kicin-kicin da fuska cikin isa ta fara cewa. share and comment.... my fans K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY FATIMA ABDALLAH KANO (Autar marubuta) ____________________________________ Page 9&10 "wallahi Alaji Nuhu ka kiyaye ni , dube ka shirgege da kai amma neman mata kamar jaraba , to wallahi ko mutuwa zakai saidai ka mutu amma ni bazan sake mu'amala da kai ba", Alaji Nuhu cikin rad`adin abin yace ," wallahi kin yi karya farida kizo mu wuce kije ki sauke nauyin dake kanki tunkan raina ya b`aci wallahi ", Farida kawai ta bud`e kofar motar wannan saurayin ta shige , shi kuwa saurayin ganin yadda Alaji Nuhu yake zak`ewa yasa shi saurin jan motarshi ya tafi , Alaji Nuhu yabi motar da magana yana cewa," zama ki dawo ki sameni tunda kike mini shocking d`in da ba macen da ta iya wallahi sai kin dawo , ai ba hauka ake ba", ya koma motarshi cikin huci . saurayin tuk`a motar yake yana satar kallon farida a fakaice , zuwa can ne kuma ya fara cewa ,"ki yi hakuri ke irin kaddararki ke nan", Farida tayi shiru jin hakan yasa saurayin sake fad`in, "mijinki ne ko",? Lokaci guda Farida ta kece da dariya 😂 murmushi ya yi yana sake kallonta ," haba mene ne abin dariya", Farida tace ,"Hmmm amma ka bani dariya in rasa wanda zan aura sai wancan bagidajen mutumin, to ka b`ude kunnuwanka da kyau kaji , suna na Farida kuma ni Karuwai ce , abin dana fito yi ke nan ", cak ya tsayar da motar ya tsaya yana kallonta, " karuwa kuma",ya fad`a cikin mamaki Farida had`e rai tayi tana cewa, "oho kana shakka ke nan to wacce macen tarbiya ce zaka ganta a titi yanzu? ai sai mu ", ba tare da ta jira abin da zaice ba ta bud`e kofar zata fita ," tom ni zan wuce na gode da taimako", mutuwar zaune yayi yana binta da kallo harta tsallaka titin ta shiga gidansu, yay ajiyar zuciya. Anan gidan Inna kuwa baba Aminu ne da matarshi suka kawowa Inna ziyara nan suka sha hira sosai . tafiya suke cikin mota yana mata wani kallo Fadeela saidai kawai ta kalleshi tace "uhum", magidanci ne sanye da shadda jaah yake tuk`a motar ," zan yi kewarki Fadeela dan ma Allah yasa nima zan kwana biyu a kanon da bansan ya zan yi ba", Fadeela cikin kunya ta kalleshi tace "haba Alaji sani ai naga ba wani shakuwa mukai ba", " keeeeeeeeh",Alaji Sani ya fad`a "soyayya ke nan , cikin kwana biyu kin mamaye zuciya, gaskiya Fadeela ina sanki", kallon shi tai ta rufe fuska tana cewa," har kasa naji kunya", Alaji Sani ya yi murmushi yayin da ya yi parking kofar gidansu Fadeela "har naji wata kasala da mutuwar jiki ya kamani , bana san na barki Fadeela", ya fad`a yana kallonta ajiyar zuciya tayi lokaci guda tana kallon kofar gidansu tana cewa," to ni dai bari na shiga domin na gaji sosai", yace ,"to shi ke nan sarauniyata ki gashshe mini da Inna kafin nazo", Fadeela ta fice tana masa bye -bye yayin da ya murza kan motarshi yay gaba to ni ko nace zan ga yadda Fadeela zata kai Aliyyu da Zakariyya da Alaji mansur ga kuma Alaji Sani😂 Inna tayi murnan dawowar Fadeela sosai musamman yadda take korafin gida ita 1 "kai duniya ambassador jarababbe ne", Ummi baby ta fad`a tana rike da kugunta tana kallon madubi dariya Farida ta kwashe da ita tana cewa", hhhh dan Allah Ummi baby kije wajen Alaji Nuhu nan ne zakiga masifar jaraba , wallahi Ummi baby ko Alaji Nuhu zai mutu ya dena kusantata", " wai ke farida ba kye yafiya ne tun da ya fad`a miki wannan maganar fa kika tsane shi", Ruma ta kwashe da dariya tana cewa... yanzu wajen karfe ukun asuba Fadeela ta fito daga wanka , b`urun-b`urun din ta ne ya tada Inna zaune tana tsaki "Allah ya yaye miki wannan wankan daren, ace kullum ta Allah saikin tashi irin wannan lokacin kina wanka",😠 Fadeela tai ajiyar zuciya wanda jikinta duk a ma ce ta kalli Inna tana cewa," ki yi hakuri Inna wallahi na saba idan ban yi ba jikina ciwo yake", "to shi ne kuma sai dare abin ya fara damuna kuma na fara jin tsoro , haka mahaifinki fa ya ringa yi kullum wanka a rana sai yay wanka sau nawa , a karshe likita yace mana yana da kansa haka ya mutu muna gani", Fadeela ta fad`i jikin Inna tana kuka😭 " Inna na tuna Abbana , yana fadan kullum cewa yanzu ake yi anjuma sai labari, duk lokacin da ya fad`a dariya nake mai ", Inna ta fara rarrashin Fadeela cikin karyayyar zuciya💔 DA sauri baba Aminu ya farka a bacci yana cewa," Jamila ina jaririn yana ina , bani shi bani shi Jamila", hakan yasa matar shi Jamila saurin tashi tana cewa, "lafiya Aminu ?wanne jariri",? baba Aminu yay ajiyar zuciya yana cewa ," yi hakuri Jamila wallahi mafarki nayi mun haifi jariri", Jamila tace ,"Hmmm " Fadeela ce tsaye kofar gidansu Ummi baby ita da muradinta Aliyyu wayarta ta dauka ta kira Ruma "Hello Ruma muna waje fa", Ruma tace ," to ki shigo da shi mana ai kinsan bama shakkar maza ko", "ke dallah dakata mini , aka ce miki shi kwarto ne ko me? idan zaku fito ku fito ko mu tafi", Ruma tai ajiyar zuciya ta kashe wayar Aliyyu yay murmushi yana cewa," Fadeela ta ke nan , sai kin yi hakuri kuma duk gudun mawar da kike so daga guri da ya shafi shiryuwarsu zan baki", murmushi tayi tana cewa, "na gode", Farida ce ta fara fitowa, sa'ilin da Ummi baby ta biyo bayanta sannan Ruma Aliyyu bin su yake da kallo cikin ranshi yake mamaki wai Karuwai ne💃💃💃😒 " Aliyyun Fadeela ya kake ya shagali", Farida ta fad`a murmushi yay yana cewa, "Alhamdulillah fatan kuna lafiya", Ruma tace", lafiya kalau mu ke", nan suka ringa hira ana wasa da dariya har cikin hikima Aliyyu ke sake Jan hankalinsu a kan kudirin Fadeela, inda su kuwa suke shek`e mai da dariya. su Ruma manyan 'yan duniya ne , niko zanga yadda zasu dawo kan hanya😂 Bayan Fadeela ta dawo gida ta tadda Zainab zaune tana zaman jiranta Inna ce ta fara cewa", kin tafi shiru dake Fadeela, sai kace anyi biyan bashi dake", murmushi Fadeela tayi kafin tace uffan ", taji an kwasheta da wani gigitaccen mari, fad`awa tai kan kujera cikin tashin hankali ", Aminu! Mene ne haka", Inna ta fad`a tana mikewa, yayin da ita ma Zainab ta mike tsaye cikin huci da tsananin b'acin rai baba Aminu ya fara cewa ," koki yarda Fadeela ko karki yadda ni ubanki ne , na gaji da zancen da mutanen gari suke kawowa a kan ki , ni wallahi sam bana yadda da duk wani motsinki, to wallahi na baki wata da`ya ki shirya Zakariyya ne zaki aura", sai a lokacin Fadeela ta fashe da kuka inda Inna ta titsiye baba Aminu da tambaya, "mene aka ce ta aikata haka Aminu",? Inna tai tambayar tana rike da hab`a cikin wannan huci baba Aminu ya fara cewa," Inna matukar na tuna Fadeela na gabana hankali tashi yake , ni yanzu ma wallahi na fara zarginta, kullum sai an kawo mini maganarta taya ne hankali zai kwanta , tunda ta fara mu'amala da wannan yaran duk hankalina atashe yake", yay ajiyar zuciya yana cewa, "na dai fad`a miki ki shirya auren Zakariyya nan da wata d`aya kacal", yana gama fad`a ya fice cikin huci ya tafi gidansa Fadeela ta fad`a jikin Zainab tana wani rurucewa da kuka ", Zainab wannan wacce irin rayuwa ce , mene ne mutane suka gani ina aikatawa, yanzu shima baba Aminu yana mini kallon da wasu mutanen suke mini har ya furta yana zargina", Zainab cikin karyayyar zuciya idanunta sun ciko da kwalla tace ", kiyi hakuri Fadeela, wallahi baba Aminu yana da gaskiya, ki daure ki auri Zakariyya zaki samu farin ciki", Fadeela ta bar jikin Zainab ta doshi inda Inna take ta durkusa kasa tana cewa cikin gagarimin kuka mai gwanin ban tausayi," wallahii Inna ki hana baba Aminu aura mini Zakariyya, ya bani lokaci zan fito da wanda nake so," Inna tace ,"babu abin da zance Fadeela kibi umarninsa , ni barin duniya zan na barku tare duk yadda yay da rayuwarki cigaba yake nema maki", Inna tana gama fad`a ta tashi ta shige dakinta, kuka Fadeela ta sake rurucewa da shi tana kallon Zainab. "lallai ma ambassador ya raina miki hankali, to wallahi idan zaki nemi wani namijin ma ki nema , zama dana miji d`aya asara ne", Ruma tayi maganar tana kallon Ummi baby jin Ummi baby bata ce komai ba yasa Ruma cewa," ni kinga ma anjuma wani sabon chairman nake da shi , zamu je muji irin nashi salon,"ta karasa maganar tana dariya😂. baba Aminu cikin hucin ya koma gida zama ya yi a falo yana ajiyar zuciya Jamila ce ta fito fuskarta cike da farin ciki da annushuwa, ko tambayar halin da yake ciki batai ba ta kama hannayensa ta mik`ar da shi tsaye tana sumbatarshi murmushin yak`e yay mata kawai yana cewa,"mene yake faruwa", rungume shi tai ajikinta cikin wani rurucewa da kuka tana cewa. kuna tare da Autar marubuta share and comment.... my fans🙏. K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _____________________________ page 11&12 ,"ciki ne dani mijina , wallahi ciki ne dani "😭 shima baisan lokacin da yaji idanunshi sun ciko da kwallaba zameta yay a jikinsa yana kallon fuskarta bai iya cewa da ita komai ba , kawai ya sake rungume matarshi yana zubar da hawaye. Anan kofar gidansu Ruma kuwa ,wani saurayi ne tsaye wanda ga dukkan alamu yana jiran wani abun ne, zuwa can Farida ta fito ta tsaya gabansa tana cewa," a she kai ne kake kirana", saurayin yay murmushi yana cewa, "a she zaki gane ni ke nan ", Farida tace ," me zai hana,to amma meke tafe da kai", murmushi ya sa ke yi yana kallon fuskar Farida yana cewa, "kin barni cikin zulumi tun ranar da muka had`u", murmushi tayi tana cewa," Hmmm, nifa malam karuwa ce na fad`a ma gaskiya dan haka ba wani mamaki ba ne", cikin karyayyar zuciya yace ,"kina kama da mahaifiyata Farida, wallahi tun a daren dana ganki kwana nayi ina tunanin mahaifiyata, muna kaunarta sosai amma Allah ya raba mu da ita," Farida sake kallonshi tai tana murmushi sannan tace ,"mene sunanka", cikin girmamawa yace ,"suna na Khalid ". Yanzu misalin karfe 8na dare , Inna na zaune a falo, Fadeela tazo ta wuce ta rufe gida , inda Fadeela ta kalli Inna tana cewa", saida safe Inna", sauri Inna tayi tana kallon Fadeela," yau kuma tun yanzu zaki kwanta", Fadeela tace ,"eh Inna kaina yana ciwo", Inna tace ,"nima kuwa zuwa zan yi na kwanta , domin kwana biyu ina yawan jin Ana hauro mana gida ina jin tsoro," murmushi fadeela tayi tana cewa, "ke dai kawai Inna ki ce matsoraciya ce ke," Fadeela ta shige dakinta tana dariya Inna tace ",kin ji mini yarinya tsoron gidanku ",😂 Inna ta dauro alwala ta shige dakinta Fadeela na shiga daki aiko kiran wayar Alaji Sani na shigowa nan suka sha wayarsu har yake tambayar yaushe zasu had`u, bayan su gama wayar sai ga kiran Zakariyya, amma Fadeela kawai tayi blocking d`in shi , kawai ta kira Alaji mansur, suka sha soyayya bayan duk ta gama abin da zatai wani matsanaicin ciwon mara ya riketa gamm, ta jima tana shan bakar wahala kafin ta samu sa'ida. Ruma ce kwance kan wani had`ad``en gano tana shan 🍦 babban hotel ne na masu abin💴 zuwa can saiga gogannaku ya fito daga bathroom , goge jikin shi yake da towel yana kallon Ruma , harararshi tai tana cewa," to mene kake kallona", tsalle yay ya hau kan gadon yana cewa, "karki sake hararata ko kisha wahalar da tafima ta d`azu, domin ni chairman a kujerata ma ina basu wahala bare a gun mata", tab`e baki Ruma tayi tana cewa," ku fa maza kuna bani mamaki , kawai wannan d`an abin da kamin shi ne shan wahala , to wallahi ko a jikina chairman", haushin maganar yaji ya mike yana kokarin caf kota yana cewa, "to bari ki gani ", da gudu ta tashi ta cillar da bargon dake jikinta tana dariya , shima dariya ya kwashe da ita katan banzan yana cewa," zo kisa kayanki Ruma",ya d`ebi kayan yana mika mata , fari tamai da idanu tana cewa, "mene amfaninka", cewa yay "haka ne ta inda aka hau tanan ake sauka ",ya mike da kayan ya nufi inda take.😎 Zainab na shiga lungun gidansu Fadeela taji Ana kwala mata kira, tabbas idan ta gano muryar Zakariyya ce , aiko tana juyawa ta ga bawan Allah sanye da jakar goyo. Fadeela ce kawai cikin gidan , sakamakon Inna tana gidan baba Aminu, tunda taji Jamila ta samu ciki bini-bini ta shirya ta je yanzu haka ma tana can Fadeela tasa hijab tana shirin fita taji sallama juyawa tai daidai lokacin da take amsa sallamar had`e rai ta yi taja dogon tsaki tana kallonsu Zakariyya da Zainab suka kalli juna cikin mamaki Zainab ce ta karasa gabanta tana cewa", haba Fadeela mene haka ke nan", Fadeela hankad`e Zainab ta yi gefe cikin mummunan bacin rai su ma cikin gagarumin mamaki suke kallonta ", daman ke ce babbar munafukar da ki ke shiga kina fita kan dole baba Aminu ya auran Zakariyya, to wallahi kin bani kunya Zainab", Fadeela ta juya ta kalli Zakariyya tana nunashi da yatsa👉 ", tom ka ji ni da kyau kai kuma maye , na tsaneka Zakariyya bana kaunarka bana sanka , ku fi ce mana a gida", tsananin mamaki ne ya kama Zainab saboda a iya zamanta da Fadeela tasan da cewa Fadeela ba ta da aljanu , to amma mene wannan abun da ta aikata, tsananin fusata Zainab ta yi , amma ba tare da tace komai ba tasa kai ta fita , ganin hakan yasa Zakariyya bin bayanta da 'yar jakarshi da aka zo za'a kwana biyu😂😂 bayan sun fita Zainab tayi nannuyar ajiyar zuciya tana kallon Zakariyya," dan Allah ka yi hakuri Zakariyya ", murmushi yay bawan Allah😂 yana cewa," babu komai Zainab ni yanzu zan koma", sakin baki ta yi cikin tsananin jin tausayinshi sa'ilin da tai ajiyar zuciya tana cewa ",zuwanka fa ke nan Zakariyya dan Allah kayi hakuri, kaje gidanmu ka huta ai kaduna ba wasa ba", shi ma ajiyar zuciya yay yana cewa", da kin barni Zainab hankali duk ya yi gida wallahi", cikin murtuke fuska tace ", to tunda gidan namu ne baka san zuwa , sai mu tsallaka mu je gidan baba Aminu", a ajiyar zuciya Zakariyya ya kuma yi yana kallon Zainab cikin tausayin kanshi , sannan yace ," tom shi ke nan , mu je gidan naku", sannan suka dauki hanya suna tafiya suna hira . Ita kuwa Fadeela cikin b`acin rai ta fita waje , sakamakon Alaji mansur dake jiranta, Farida ce da Kalid a kofar gidansu , suna cikin mota suna hira Kalid ya kalli Farida yana cewa ",gaskiya ke Farida mutuniyar kirki ce, amma ban so kika jefa kanki a irin wannan yanayin ba", kallon shi tai tana cewa," Kalid ke nan ", fuskar shi babu wasa ya kalleta ", zan so ki bani da ma cikin rayuwarki , na zamto miki jigo na ma ye maki gurbin da kika rasa , ya zamto jinina yana yawo cikin jikinki Farida wallahi Farida ina sanki", shiru tayi tana kallonshi🙎 ganin bata ce komai ba yasa Kalid cigaba da cewa ," zan nunawa dangina ke ce nake so , zan baki gudunmawar daidaita rayuwarki, wallahi har zuciyata nake kaunarki Farida ", nannauyar a jiyar zuciya tayi jikinta duk a ma ce , wani kwarjini Kalid yake mata , hakan yasa ta kasa cewa komai ta b`ude murfin motar ta fita da sauri ya fito shima ya sha gabanta yana cewa", Farida", juyawa sukai baki d`ayansu sakamakon k`arar mota da suka ji a bayansu", motar Alaji mansur ce tai parking shi da Fadeela, suka fito yayin da Alaji mansur ya jingina jikin motar tashi yana gyara babbar rigarshi, share and comment.... . K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY FATIMA ABDALLAH KANO (Autar marubuta) _________________________________ page 13&14 Murmushi Fadeela tayiwa Farida tare kuma da d`aga musu hannu ta shige cikin gidan tana shiga ta ga Ummi baby tana gyaran ganyen magarya ",Assalamu alaikum", Ruma ce ta riga amsa sallamar daga fitowarta daga toilet Ummi baby murmushi tayi tana cewa", ai na dauka shuka mu kikai ba zuwa za ku yi ba", durkusa Fadeela tayi gabanta tana cewa", mene zaki da wannan", ta nuna ganyen magarya Ruma ce tai dariya tana cewa", wai maganin sanyi da kuma matsi , ni kam dai bazan amfani da shi ba", Ummi baby harara ta dokawa Ruma tana cewa," rabu da waccen matar, to wallahi wannan ganyen babban magani ne a gurin mata , idan kika bazashi ya bushe ki daka , kina tsarki ko shiga ciki , yana maganin budewar gaban mace", Fadeela tace ",ikon Allah su Ummi baby masu gargajiya", tana dariya ita ma Ummi baby dariyar tayi tana cewa", ke kuwa ba dole ba , ina san nake kashe ambassador da dadi", Ummi baby had`e rai tayi tana cewa", a'a to barni haka", ta mik`e tsaye tana cewa," ni wallahi ma maganin ciwon mara nake so , domin kwana biyu ina shan wahala kuma dah bana yi", Ummi baby ta mik`e tsaye tana cewa ",zan baki wani sirri", ta je kofa tana kokarin fita tsayawa Fadeela tayi tana cewa", ina za ki ne", " waje mana ke ce fa kika ce Alaji mansur yazo", Fadeela tace ",haba sa hijab mana , ke ma Ruma ki fito ku gaisa", ta karasa maganar tana fita . Bayan Tsawon Lokaci yau kimanin sati uku ke nan da mutuwar baba Aminu😭😭😭 ya yi jinya ne Allah ya dauki ransa ba tare da ya ga matarshi ta haihu ba😭😭 tabbas wannan mutuwa ta girgiza mutane, Inna taci kuka sosai mara misali, haka ita ma Fadeela, uwa uba kuma Jamila😭 wannan rayuwa haka take duk sanda lokacin ka ya yi babu jira , Allah yasa mu dace baba Aminu Allah ya yafe maka 😭😭😭 bayan Fadeela ta fito daga wankanta na kaddara(Dare) ta fad`a gado tana murk`ususu mararta kamar zata fita, to banda abin Fadeela taje asubiti mana asan meke faruwa, niko nace waya sani ko wankan darenta ne yaja mata.😒 Wayar Zainab ce take Ring da sauri ta nufo wayar domin tunaninta kiran da take jira ne , tana isowa ta ga Zakariyya ne, tai ajiyar zuciya ta zauna tana kara wayar a kunne, ", Assalamu alaikum ma a bociyar hankali da ilmi", taji Zakariyya ya fad`a wani d`an yammm taji haka , kafin ta amsa sallamar bayan sun gaisa Zakariyya ke cewa", Zainab na gode da dukkan gudun mawar da kika bani dan ganin na auri Fadeela, amma a yanzu ina tabbatar miki na fahimci Fadeela bata kaunata , dan haka na sake sabuwar rayuwa tare da wata , na mance da Fadeela", Zainab tace ", Alhamdulillah, Allah yasa hakan ne yafi alheri, ita ma Fadeela Allah ya bata miji na gari", dariya Zakariyya yay yana cewa", to Amin zainabata, amma bari na fad`a miki wata gaskiya, Zainab yanzu ke nake so , kuma nake son aura, zuciyata ta kamu da sanki Zainab", darau damm dumm Zainab taji a ranta , a take taji kanta ya sara, " kasan dawa kake magana kuwa",Zainab ta fad`a cikin mamaki murmushi Zakariyya yay yana cewa",na sa ni mana Zainab, dan Allah karki mini hali irin na Fadeela ki share mini hawayena da rad`ad`in da nake ciki, ki amshi soyayyata", tsawon minti guda sukai shiru suna sauraran numfashin juna daga bisani Zakariyya tace",dan Allah Zainab ki yarda dani ", Zainab taja dogon numfashi mai zafi tana cewa", Fadeela fa Aminiyata ce kuma dan mu samu matsala da ita hakan ba yana nufin naci amanarta ba", wayarshi ya sake daidaitawa a kunnenshi yana cewa," na nemi Fadeela da aure Zainab tace bata kaunata , to mene abin cin amana dan na soki", a ajiyar zuciya tayi tana cewa",gaskiya bazan iya wannan abin ba kayi hakuri ", ta kashe wayar yayin da Zakariyya ke kiran sunanta. Yanzu misalin karfe 8na dare Ruma da Ummi baby sun gama cin abinci , yayin da Farida ke kwance tana kallonsu ", wai kwana biyu meke faruwa ne Farida? duk kin canza mana fa lafiya kuwa",? Ruma ta fad`a murmushi farida tayi ma ta tana cewa ", kawai yanayi ne", Ummi baby tace " tom ni dai gaskiya zan je taron karuwai na legos , idan zaku sai ku shirya", Farida ce ta kalleta tana cewa ",au haka ne fa , ai nasan ambassador zashi sai ki bishi", ", auuuuu😠 kina nufin ba za ki ba farida",? Ummi baby ta fad`a tashi Farida tayi daga kwanciyar da tai jikinta duk a mace tare da wani yanayi na kasala tace ", a kwai abin da na keson sanar daku", kallonta sukai a tare lokaci guda kuma suna kallon juna , kafin wani yace komai suka ji hoonn d`in mota mai karfi daga kofar gida dogon tsaki Farida taja tana cewa," kunji banza Alaji Nuhu ko, to wallahi ba inda zani tsinan ne", dariya Ummi baby ta keece da ita tana cewa ",bari naje na ce masa ba kyenan", Ummi baby ta ziri mayafi ta fice cikin rawar jiki, tana fita ta karasa wajen motar tunda Alaji Nuhu ya hangota ya fara sid`e baki😋 sauri yay yana fitowa daga motar daga shi sai singlet da gajeren wando, ga shi luk`uti bak`i baki d`aya ita ma Ummi baby taji tsanarshi ta kamata ", Alaji Farida bata nan fa ", ta fad`a ba tare data karasa inda yake ba sauri yay yana takowa inda Ummi baby ke tsaye yana cewa", toooooo,yanzu ya zan yi ke nan kuma wallahi a matse nake , baki d`aya K`AWAR taki ta kaurace mini kuma naga kema ba lefi ko zaki fansheta ne yau kawai", had`e rai Ummi baby tayi tana cewa", me kake nufi Alaji", Alaji Nuhu yay dariya yana cewa", haba yarinya sai kace ba 'yar hannu ba", ya karasa maganar yana aje hannu a kan kirjinta yana cewa", a taimaka mini", mari ta falla masa tasa karfi ta wurgar da shi gefe kawai ta shige gida😂😂😂😂😂😂😂 tana shiga ta fara cewa", gaskiya Farida kina fama da wannan gardin mutumin", dariya suka shek`e da ita yayin da ta basu labarin abin da ya faru , Ruma harda tintsirawa tana dariya cikin b`acin rai da haushi Ummi baby tace ," to dariyar ta isa haka Ruma ", Ruma tana kokarin shanye dariyar tace", sorry na dena", lokaci guda kuma tana sake tintsirewa😂😂 Ummi baby duka ta kai mata yayin da Ruma tai saurin kaucewa, bayan sun yi shiru ne Ruma ke cewa", to Farida mene ne zaki fad`a mana? muna ji Allah yasa cigaba ne", cikin kasalalliyar murya Farida tace ", NA DENA KARUWANCI", sauri sukai suka hada ido cikin tsananin mamaki da rashin gane inda maganar ta dosa, duk ji sukai maganar na musu amsa kuuwa a kunnuwansu, Na dena karuwanci_na dena karuwanci. ...........comment and share my fans K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _________________________ page 15&16 ",nifa ban gane me kike fad`a ba Farida", Ruma tai maganar cikin tashin hankali, kawai Farida ta tashi ta bar musu d`akin yayin da suka bita da kallon mamaki da rashin fahimta. Washe gari🌞 Inna da Jamila ne zaune suna falo, sakamakon tunda Allah yay wa baba Aminu rasuwa Jamila ta dawo gidan , Fadeela kuma tana madafa tana had`a musu abin kari 🍴☕🍲 taji wayarta na ringin , dubawar da zatai kawai ta fara murmushi , Alaji Sani ne ke kira , wayar ta d`aga tana karawa a kunne daga can Alajin yace", barka my sweet", murmushi Fadeela tayi tana cewa", ina kwana fatan ka tashi lafiya", ", kin ganni nan tun asuba nake tunaninki da kewarki, kuma ina son na zo na gaida Inna , ko ya kika ce", a jiyar zuciya Fadeela ta ja tana cewa," ban da abinka kai ne fa zab`ina kuma Inna zata so ganinka ai, kawai kasa rana", murmushi yay yana cewa ",kwanannan zan se miki mota Fadeela, ke dai ki cigaba da mini addu'a", ", da gaske Alaji!,Gaskiya idan haka ne zanji dadi ka ga na koma 'yar bata", Alaji Sani yay dariya yana cewa", to mene ? nawa motar take da bazan siya miki ba , a cikin watannan ma kuwa", a jiyar zuciya mai sanyi ta sauke tana cewa", wallahi ka farantan rai, amma bari zami waya, yanzu ina son kaiwa Inna kayan Kari", Alaji Sani yace"to shi ke nan", tana aje wayar ta doshi inda su Inna suke da nufin tambayar Inna ina sugari yake domin zata zuba a cikin kunu🍺 tana shiga falon Inna ta rufeta da fad`a ", gaskiya Fadeela kin bani mamaki, Zakariyya yazo har kano amma ki saka masa da wannan rashin mutuncin, duk a cikin samarin naki wayakai nagartarshi da ilminsa , daman da Allah bai jarabemu da rashin Aminu ba dah tuni kina d`akinki, to amma yanzu zan tsaya tsayin daka wallahi don ganin kin auri Zakariyya", Inna cikin tsananin fusata ta ci gaba da cewa", uban mene ai bunsa? tom yanzu ni zan tsaya miki uwa uba don ganin kinyi aure ko dan shed`anun💃💃💃 zan je har kadunan zan yi magana da iyayen nashi na basu hakuri, ko kina so ko a'a Zakariyya ne mijinki, ana kokarin sama maki nagartacciyar rayuwa kina hauka", kuka Fadeela ta fashe da shi mai gwanin ban tausayi, tabbas k`in Zakariyya ya ratsa zuciyar Fadeela Jamila ce ta fara bawa Inna hakuri lokaci guda kuma tana rarrashin Fadeela. A cikin bargo suke ,rungume da juna suna shakar kamshin jikinsu, dukkan ilahirin jikinta yake bi yana shafawa yadda yake so ya gadama, Ummi baby murtike fuska tayi tana cewa", ambassador bana san wannan iskancin naka yau", sakin baki yay yana kallonta😒 murmushi tayi tana cewa ",yau baki d`aya ka gajiyar dani ko tausayina baka yi , idan nazo hannunka yadda kaso dani haka kake", hannunshi ya cire a kan jikinta ya d`orasu kan fuskarta yana sumbatarta, yanayin yadda ya kama harshenta ne yasa ta tureshi gefe , baki d`aya ranshi ya b`ace ", me yasa kike son b`atan wannan yanayin ne baby, kin ce kuma ba za ki kwana a nan ba , amma kink`i bari nai abin dana keso", ", auu duk abin da kai dani d`azu bai isheka ba, ai wallahi indai yau na kwana da kai sai naci ubana domin yau na ga wani karfi kake ji", sakin fuska yay yana murmushi tare da had`awa da dariya 😂 rungumota yay yana shafa lafiyayyen gadon bayanta da yake masa dad`in shafawa tare da zarcewa inda yake so ", to ki bani kanki , saboda idan na tafi legos za ki kewata", da sauri ta kalleshi tace", ina son zuwa wannan taron gaskiya, kuma zani , sai kana mini wayo kana zuwa gun wasu matan ni kuma ko oho", kallonta yay shi ma yana cewa", to ai kinga ni namiji ne, duk da taron karuwai ne bana san ki je", ", to wallahi sai naje , indai kaga banje ba to Allah ka fasa zuwa", jimmmmm ambassador ya yi na d`an lokaci sannan yace", to naji ba za ni ba , shi ke nan",? ta girgiza kai alamun ehhh jawota ya yi yana cewa ", to mu kwanta na minti uku ",yana d`aga mata gira😬🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃 Anan kuwa Zainab ta rasa yadda zatai da Zakariyya, domin kuwa kullum kira a kan neman yardarta da ta nunashi matsayin muradinta , amma Zainab ta rasa inda zata sa kanta, tana neman shawara , ya za tayi shin idan ta amshi Zakariyya Fadeela mene zata ji , zatai Mata kallon mai sonkai ko mayaudariya mai jiran a rabu ta samu??? misalin karfe 11na dare yanzu mutuminku Alji Nuhu ya kasa kwance ya kasa zaune yay ta kiran wayar Fadeela amma taki d`agawa harya yanke shawarar zuwa gidannasu, amma sai ya tuna da abin da ya faru a wancan zuwan uban tagumi ya kafta ", gaskiya Farida ba kye kauta mini , na saba dake ba maçen da nake jin dadinta kamar ke , amma kin barni cikin tashin hankali", mikewa yay tsaye yana gyara zaman wandanshi yana cewa", kann uba ai wallahi bazan barki ba Farida wasa farin kirki, amma yau duk inda karuwa take sai na nemo nayi maneji", ya zura kayanshi ya fice . Farida ce kawai cikin gidan sakamakon sauran suna can barbad`arsu kuka take yi mai gwanin ban tausayi mai kuma cike da nadama😭 ", na tuba ya Allah, ka sake bani da ma na canza rayuwa😭 tabbas Kalid bana a kan daidai na gode Allah da zuwanka cikin rayuwata", kuka ta sake fashewa da shi da majina tana fitowa kalaman Kalid take tunawa , idanunshi sun yi jajir ya ke kallonta, ga dukkan alamu kad`an yake jira ya fara hawaye", wannan wacce irin rayuwa ce Farida? ba dai kudi ne ba ina da kudi Farida, babu abin da za ki nema ki rasa na miki alkawari, zan sama maki ahali tare da Farin ciki Farida, ki gyara rayuwarki da tsakaninki da mahaliccinki", ya miko ma ta hannu yayin da hawaye suka zub`o masa yana cewa👋ki mini alkawari Farida, ki mini alkawari Farida kin dena wannan rayuwar", kara zaucewa tai da kuka tana shashsheka da wannan abin da ta tuna ", tabbas Kalid ahali na rasa da kudi, a yanzu nayi nadama ya Allah", gwanin ban tausayi matuka😭 " ina tsoron mutuwa ya Allah, ka bani da mar gyara rayuwata", ta kwanta cikin mummunan yanayi na kuka. "me yasa ba za ki kwana anan ba ne Ruma",? chairman ya fad`a cikin tashin hankali zame towel d`in dake jikinta tai tana share ragowar ruwan da ya rage da tai wanka , bata ce mai komai ba chairman ganin Ruma a wannan yanayin yasa shi saurin tasowa yana janye towel d`in yana yarwa, kafin tace uffan ya jefata kan bed💃🏃🏃 Washe gari tunda Farida tai sallar asuba take zaune a gurin, har bacci ya sake kwasheta su Ruma suna mata 😂😂😂 Fadeela ce a da`akin Inna tana dube-dube duba can duba can ga dukkan alamu akwai abin da take nema , garin hawa saman kwallar Inna ta hard`e da babban hijab d`in dake jikinta sauran kadan tasha kasa , nan mararta ciwonta ya motsa amma ta daure da kyer ta dauki abin da take nema ta fita . comment and share......💖 K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA ______________________________ page 17&18 Jamila na zaune a falo tana waya da 'yan uwanta daga Jos, Fadeela ta wu ce zuwa d`akinta , tana rik`e da mara to wai Fadeela zuwa hospital ne aiki?tabbb😒 wajen kira biyar ya yi mata , amma Zainab na zaune tana kallon wayar ta kasa d`auka , domin ba ta da kalmomin da za ta bayyanawa Zakariyya shigowar kira na shida ne yana kusan tsinkewa Zainab ta kai hannu ta d`aga shiru tai ta kasa kunne tana jiran abin da zai ce murya taji can kasa kamar zai kuka ",haba Zainab dan Allah me yasa za ki ke mini haka? soyayyar dana ne ma ce tasa kike a zabtar dani",? A jiyar zuciya Zainab tai tana cewa ," ka yi hakuri Zakariyya ban san mene ne zan ce ba , amma ka bani lokaci", yay a jiyar zuciya yace ,"to shi ke nan Zainab ", Zainab taji duk tausayinshi ya rufe ta to idan ke ce Zainab mene ya kamata ki yi??? Ruma ce da wani Alaji muhd a kofar gida, ya jingina jikin motar shi yana cewa da ita ", to ya za ki zo da daren ne ko mu tafi yanzu", kallonshi tai tace," sai daren amma gaskiya hotel nake so yau", Alaji muhd yace ,"ba ki da matsala zuwan naki shi ne wahala ", a lokacin Farida ta fito daga gida tasa luk`af da babban hijab girman hijab d`in ne yasa ba zaka iya hangen carbin dake hannunta ba , kai tsaye ta wuce gidansu Fadeela yayin da su kuma suke bin ta da kallo. Fadeela tana d`akinta tana shirya kayanta cikin jakar goyo , sakamakon wani discussion da zasu je a makaranta na kwana biyu Farida tai sallama yayin da ta bud`e fuskar ta suka gaisa da Inna da Jamila dake falo, Inna ba tare da ta gane wace ba tace mata ta shiga ciki domin Fadeelan na ciki duk a tunaninta abokiyar tafiyar ce Farida na shiga d`akin , Fadeela ta kalleta cikin tsananin mamaki ", Farida", Fadeela ta fad`a tana girgiza kai cikin mamaki mai girma murmushi Farida tai tana zama bakin gado haka ita ma Fadeela ta zauna tana kallonta murmushi Farida ta kuma yi yayin da take cewa", na tuba Farida, na dena karuwanci, na koma rayuwata kamar ke , ina kuma rokon Allah ya yafe mini , ina matukar godiya da nasiharki da ke da Kalid ba zan taba mancewa da ku ba", Farida tai maganar idanunta sun ciko da kwalla matukar mamaki ne ya sake rufe Fadeela hakan yasa ta kasa magana Farida ganin haka ya bata da mar cigaba da cewa", na zo ne domin ki magana a sani a islamiyyar ku", ita ma fadeela cikin yanayin fara kuka tace ," kai na ya kulle Farida, a she zan ga wannan ranar , tabbas Allah abin tsoro ne idan da rai akwai rabo", murmushi kawai Farida ta kuma yi yayin da Fadeela tace, "na matukar ji dadi Farida, kamar mafarki duk jikina ya mutu, Allah shi ne abin godiya, amma yau zamu discussion na kwana biyu, matukar muka dawo , zan same ki mu gyara komai", Farida tace ," to Allah ya dawo da ke lafiya ", cikin sabuwar kasala da mutuwar jiki Fadeela tace," wallahi kamar na fasa tafiyar nan , duk jikina ya mutu", cikin kwarin gwiwa Farida ta ta shi tsaye tana murmushi, "to mene ne abin fasawa , kin ga tafiyata Allah ya tsare hanya ", Farida ta fita zamowa Fadeela tai daga kan gadon cikin tsananin mamaki zuciyarta na kiran uku , uku tace ," ya Allah ". Bayan Farida ta koma gida taci karo da Kalid yana zaman jiranta . Washe gari Zainab ce kanta ya kulle hakan yasa ta tafi gidansu Fadeela a yita a gama sai dai tana zuwa Inna take tabbatar mata bata nan sun yi tafiya , nan Zainab take sanar da Inna cewa ba department d`in su d`aya ba hakan yasa ba ta san da tafiyar ba, Zainab ta koma gida tare da alwashin idan Fadeela ta dawo za a yi ta a gama , ko ita ko ita Ummi baby ce ke waya da ambassador cikin bacin rai ," amma wallahi ka bani mamaki ka yaudare ni , shi ne za ka tafi legos bayan mun yi da kai babu wanda zai je", ambassador yace ,"haba baby wallahi ji nai bazan iya ba amma kiyi hakuri ai yau zan dawo", cikin tsananin fusata Ummi baby tace ,"to wallahi za ka zo ka same ni", ta kashe wayar. Kwana biyu Fadeela ta dawo da mugun zazzabi har su Inna sun cire rai da ita , tasha jini tasha ruwa duk ta rame Inna tace babu wani discussion da zata sake zuwa domin sauro ne ya cijeta😂 sai dai a bangaren Fadeela sam ba haka ba ne , ita tasan abin da ke damunta, domin kuwa tayi babban kuskure Alaji Sani ya yaudareta ta biye zancen shi ta d`ebi takardun gidanta ta siyar ta ba shi kudin , da zummar zai sa hannun jari kuma yase mata mota , saidai har yau shiru babu shi babu labarin shi , wanda aka sayarwa da gida akwai wa'adin da ya basu zasu ta shi su ba shi gidansa , sai dai Inna da Jamila ko kadan basu da wannan masaniyar idan Fadeela ta tuna hakan yasa take kwanciya jinya har asa mata jini, wannan babban rashin hankali ne Fadeela ta aikata kuma tana cikin tashin hankali mummuna tana neman mafita . share and comment....... K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA ________________________ page 19&20 Tunanin Fadeela kawai yanzu ta ya za'ai kar Inna su sami labari, ta bawa Alaji sani yarda amma ga abin da yay mata , wajejen biyar na yamma ta samowa kanta mafita, wayarta ta dauka ta kira wata number da ba ai saving d`inta da suna ba . Anan kuwa Farida da Ruma ne a gida suna zaune saiga sakon Alaji Nuhu sakamakon Farida bata d`aga kiranshi , hankalinta ya ta shi hakan yasa ta sanar da Ruma , Ruma ta amshi wayar tana karantawa, "to bari kiji Farida, tunda ba yadda ban yi dake ba kan ki bani kanki kin ki , kinsan ina da hotuna da video naki da kika yi kina tsirara, to wallahi ko ki zo nan da minti talati ki biya mini bukata kona sa a watsa ki a duniya, minti 30 gare ki", Ruma ta saki wata uwar ashar " lallai ma mutumin nan tsinan ne ne , yanzu abin da za ai ta shi za ki muje gidan nasa ni zan tsaya a waje ki yi duk yadda za ki ki dauko wayar tashi ki fito idan kina bukatar taimakona kawai ki kwallan kira", Farida ta kalli Ruma cikin mutuwar jiki tana cewa, "kina ganin hakan za ai", Ruma tace," kinsan mutumin ba shi da hankali wallahi zai aikata miki", Farida ta tashi suka tafi . Ummi baby ce gaban ambassador da wasu fitinannun futsararrun kaya shi kam yana kan gado kugu ta rike a gabanshi tana harararshi ,"na ce ki hakuri na amsa laifina naje legos na sab`a alkawari", ambassador ya fad`a kan gadon ta matsa kusa da shi tana cewa, "aikin banza , kuma ni tafiya ma zan sai ka koma legos din ka samo wata", ambassador ya mike cikin rawar jiki sakamakon tunda tazo gabanshi hankali ya tashi ," na ce ki hakuri ai kuma tunda naje legos din matan duk kin fisu kuma kawai da mace d`aya na kwana", dogon tsaki Ummi baby taja ta juya tana sa kayanta cikin fusata ambassador ya ciro wayarshi a aljihunsa na jus yana kokarin shiga gallery cikin fushi yasha gabanta yana cewa, "to kiyi ta tafiyar kuma zan je gurin wannan domin ta fiki", ya nuna mata photo da sukai shi da yarinyar cikin futsara ya janye wayarshi wani dauu Ummi baby taji a ranta , hakan yasa cikin tashin hankali ta sake karbar wayar tana kallon photon tsananin mamaki ne ya rufeta da tashin hankali, hakan yasa tace ," ina kasan ta", ambassador saboda ya motsa mata kishi yace ,"yarinyar legos can muka had`u so sweet Babyn", kallon photon ta sake yi tana cewa, "Inna lillahi wa Inna........ wannan ia Fadeela ce ," ambassador yay murmushi yana cewa, "kinsanta ashe", mummunan tashin hankali ta sake jin kanta a ciki, Fadeela ce wannan me hakan yake nufi kawai Ummi baby ta tafi gida cikin mummunan yanayi domin sanar dasu Ruma. Anan kam ba a cewa komai domin fadeela ce da wani Alaji a cikin hotel cikin bargo suke tsirara suna yin yadda suka so, " gaskiya Alaji har naji bani da damuwa , ina sanka, " Fadeela ta fad`a cikin sake rungumeshi ,"haba Fadeela ta ai bani da amfani idan ban saki farin ciki b, kuma maganar gida zansa yadda za ai a se wani kinji my baby," Fadeela ta hard`oshi tana dorashi saman kirjinta tana cewa, "to my," typing ba yawa kamar yadda comment ba yawa.😛 K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA ________________________________ Page 21&22 murmushi yay mata yana cewa, "ki tashi ki tafi gida nafi son had`uwar dare domin nafi aiki Fadeela", Fadeela kallonshi tai tana cewa," na fara gajiya kullum fitar dare nafison kazo kofar gida muyi abin mu, kuma kullum na koma sai nai wankan dare Inna ta fara gajiya kuma wani lokacin ma da zan fito kona koma Inna tana jin motsina , sai tace wai Ana hauro mana ", dariya Alajin yay yana sake cakumota jikinsa . Ummi baby har wani layi take a hanya , ya za ai ta ga Fadeela a haka to kodai mafarki ne ko me , abin ya matukar daure mata kai sosai waiiyo duniya . Bayan su Farida sun isa kofar gidan Farida ta shiga Ruma ta zauna tana jiranta ganin motarshi a waje ya tabbar masu yana ciki , Farida na shiga d`akin ta ganshi sanye da gajeren wando kawai ya kece da dariya ," ai nasan za ki zo shi yasa na shirya zo mu shiga ciki ,"yana jawo hijabinta fincikewa tai cikin fusata tana cewa, "ba shi ne abin da ya kawo ni ba , kai azzalumi ne kuma kai da ka sake amfani da ni har duniya ta nade ", Alaji Nuhu yana mata dadin murya ya fara cewa," haba Farida minti uku kawai babu mai sani kuma kema kinsan dadin abun fa, ki zo muje ," Farida kawai duk hankalinta yana kan wayarsa bata da wani da ma da ya bata da zata dauki wayar, ,"haba Farida ta so muje ," ya cacumota yana janta Farida ta mare shi ta gasa masa cizo kawai Alaji Nuhu ya wurgar da ita jikin bango ko shurawa Farida ba tai ba hakan yasa ya nufi inda take yana cewa "Farida, Farida", ko motsi ba tai ba hakan yasa Alaji Nuhu tsorata kawai ya zura kayansa ya fita ya hau mota ya tafi Ruma da sauri ta shiga cikin gidan tana kiran sunan Farida amma shiru ,ta fara dubawa daga bisani ta samota a cikin dakin kiran sunanta take tana tashinta amma shiru . Ummi baby na isa gida ta ga duk basa nan hakan yasa ta fito waje domin shan iska domin abin da ta gani ya bata mamaki shawara ta yanke kawai ta kirasu a waya duk inda suke su zo daidai lokacin Kalid yay parking da motarshi ya sakko cikin shigar kamala suka gaisa kafin ya tambayi Ummi baby shin ko'ina Faridan , wayarta ta fara ringin murmushi tai tana d`aga wayar tare da karawa a kunne ,Hello Ruma kuna ina ne, to wallahi duk inda kuke ku dawo gida , ga Kalid ma yana jiran Farida", daga can bangaren Ruma cikin tashin hankali ta fara cewa ," haba Ummi wacce irin magana ki ke, to kingan mu Alji Nuhu ne bansan mene yay wa Farida ba tana kwance kamar ya kashe ta ", ita ma Ummin cikin sabon tashin hankali tace ," ban gane ba ku na ina , ina Faridan "? bayan Ruma ta fad`a mata komai hankalin Ummi baby ya sake matukar tashi , nan ta sanarwa da Kalid shima hakan yasa suka shiga motar Kalid suka bi adireshin suna isa da gudu Kalid ya banka cikin gidan yana kiran sunanta yana zuwa babu abin da ya canza ko shurawa babu hakan yasa Ruma suka sa ta a mota suka nufi asubiti ,a cikin tashin hankali suke dukkansu asubitin kudi Kalid ya wuce dasu aiko suna zuwa aka basu taimakon gaggawa. Alaji Nuhu yana cikin mota yana ta nazari "shin ko mutuwa tai , haba ba zata mutu ba ai karuwai suna da tsawon rai , to idan kuma ta mutu aka sami gawarta fa a cikin gidana", kawai Alaji Nuhu ya juya motarshi ya koma gidan, yana zuwa ya shiga, kai tsaye dakin nasa dariya ya kece da ita yana cewa," ai ni na sani da man kawai salo ne , ga shi ta tafi , amma yarinyar nan ta cuce ni ai dana sani nayi abina a hakan amma ba komai gobe ma rana ce", ya cire kayansa ya fara bacci . Inna gobe take son zuwa kaduna domin ma harta shirya kayanta tana son taje ai maganar auren Zakariyya da Fadeela ita kuwa Jamila ciki ya tsufa sosai yau kwananta 1a Jos sakamakon 'yan uwanta sun zo sun tafi da ita amma Inna sam bata ji dadi ba , Fadeela tana cikin daki a kwance cikin ranta take cewa ,"haba Inna bana san Zakariyya ne saboda komai yace Allah yace annabi yace , kuma idan ma ya aure ni , ni bazan fasa fita duk inda nake so ba ita kuma Farida da ta dena karuwanci mu yanzu muka sa kafa duk da na dade a ciki", Inna ce ta yanke mata tunani sakamakon kiran sunanta . Alaji Sadi ne zaune cikin farfajiyar babban gidansa , yayin da wayar shi ta fara ruri yay saurin dauka don ganin mai kiran dillalinsa ne Junaidu yana dauka ya fara cewa ,"Junaidu ya akai ne , kasan bana san matsala domin ganin kiranka ba ya wuce an samu matsala ", daga can Junaidu ya fara cewa ," ai Alaji babu wata matsala tunda sun amshi kudin gida kawai ranar tashinsu ce ya rage ," Alaji Sadi yace "yawwa! Lokacin su na cika karsu sake mini ko minti guda domin rushen gidan za'ai samfari za a canzan", Junaidu yace ," babu komai Alaji Allah ya kara daukaka", Yau Zakariyya kamar farin ciki zai kashe shi , ya rasa yadda zai sa ranshi saboda murna dalilin wannan murna kuwa dawowar wakilansa ke nan yanzu daga kano gidansu Zainab, an ba shi aurenta , dalili kuwa ta tabbatarwa iyayenta shi ne zabinta . Anan cikin asubiti kam sai kai kawo suke cikin tashin hankali wajen minti talatin da shigar likitocin amma har yanzu basu fito sun basu wani bayani ba kai kawo suke yi cikin damuwa bari ma ita Ummi baby ga zancen Fadeela na cinta a yanzu dactor John ya fito daga dakin da Farida take shi da wata nurse hakan ya basu damar shan gabansa da sauri don jin wanne hali take ciki Doctor John cikin kwarin gwiwa da hausarshi da bata wadace shi ba ya fara cewa..... Share and comment.🙏 K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _____________,___________________________ Page 23&24 "Ina baku hakurin rashin sister na ku , ta rasu ta mutu sai dai Allah yay mata afuwa , ku yi hakuri ", yana gama fad`a ya wuce zuwan sauran ayyukan da yake da su, Da gudu Ruma ta fad`a dakin cikin tashin hankali , jikin Farida ta fad`a cikin mummunan zautuwa da tashin hankali ita ma Ummi baby cikin mummunan yanayi ita da Kalid suka shigo dakin Ruma ta bude fuskar Farida cikin tashin hankali ta sake rurucewa da kuka tana cewa," mene haka Farida da man mutuwa zaki yau amma kin kasa sanar dani , mene amfanin zaman taren da mukai da har za ki mutu babu mu ," Ummi baby ta zo ta hankade Ruma gefe cikin tashin hankali tana cewa, "ba mutuwa tai ba matukar kika sake cewa ta mutu ke ma sai na kashe ki , Farida samm babu iinda zata ta barmu", Ummi baby ta koma jikin Farida tana cewa," tashi farida, tashi mana dan Allah, na faje na samo wani abin mamaki zan sanar dake yanzu ki tashi mu tafi gida ", tana jijjigata tana dukanta wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Kalid, wani kundululun bakin ciki ne ya tokare masa mak`ogaro tabbas da zai hadiye shi , to shima mutuwarsa ce Ruma cikin sabon tashin hankali ta cigaba da cewa ," Allah ma ya sawwake ki mutu yanzu ," da sauri Ummi baby ta tashi ta fad`a jikin Ruma tana cewa, "Farida taki tashi Ruma wallahi ta mutu wallahi ta mutu , tafa mutu wallahi Ruma ", da wata mutuwar kauna da tausayi suka rungume junansu suna ambaliyar kuka😭😭😭 " me yasa zata mana haka , wannan shi ne shiryuwar da tai , ta koma ga Allah me yasa", inji Ummi baby Ruma ta cireta a jikinta tana sabon kuka ba tare da ta iya cewa komai ba duk idanunsu jajir sukai zai zafi suke musu duk sun fita daga hayyacinsu Allah sarki Kalid kawai fuskar Farida yake kallo yana tuna farkon had`u warsu ya matukar girgiza a halin yanzu. Bayan sun koma gida a kaiwa Farida dukkan wani abu da addini ya tanadarwa mamaci , lokacin da za a kaita makwancinta sabuwar tashin hankali suka sake shiga domin Ruma sammm ta hana a dauke mata Farida , da mar da aka samu lokacin da ta yanke jiki ta fad`i sannan aka tafi da Farida ita Ummi baby ma da zata yanke jikin ta fad`i ma iya cewa tafi jin sauki domin kawai dai gatanan ba gunki ba ,ba mutum ba, bata gane komai da kowa . Da ma duk mai rai lokaci yake jira , kowa na haka ne , amma Farida tayi sa'ar tafiya domin dukkan abin data aikata tsakaninta da mahalicci ne kuma ta ne mi tubarsa sai dai muce Allah yasa idan tamu tazo mu cika da kyau da hasken imani wanda suka rigamu gidan gaskiya kuma Allah ya sa sunje a sa'a. Washe gari Inna da zazzabi ta kwana sakamakon tun jiya da dad dare aka musu waya cewa an sa ranar bikin Zakariyya abin ya d`aga mata hankali yanzu Fadeela ta samu labarin mutuwar Farida aiko cikin tashin hankali ta nufi gidan nasu cikin kuka ta fad`a cikin gidan , duk su Ruma su na kwance mummunan zazzabi ya kamasu haka Fadeela ta zauna tana musu kuka , amma Ummi baby kawai tana kallonta da abin data ji ta gani ba tare da ta sanar da komai ba , Fadeela tayi matukar kukan gaske da rashin Farida. Bayan kwana biyu Kalid da Ruma da Ummi baby ne zaune cikin gidansu, bayan sun gaisa yay musu ya karin hakuri da jiki sai ya fara cewa,"yau kwanan Farida uku da komawa ga Allah, Allah ya kara haske cikin kabarinta ," suka ce ,"amin ," sannan yaci gaba da cewa ,"sai dai akwai nauyin da ya kamata mu saukewa Farida, sabida dole mu fitar da zancen Alaji Nuhu kuma mu kaishi kotu , sannan mu ne mi 'yan uwan Farida mu sanar dasu halin da take ciki, domin bukatar addu'arsu", Ummi baby ta kalli Ruma yayin da tai mata murmushin da ya fi kuka ciwo Ruma ce ta bude baki tana cewa, "wallahi ni ma Kalid ko da baka zo da wannan zancen ba , sai nayi duk inda nayi dan Alaji Nuhu ya fad`i ta yadda ya kashe Farida, kuma koda zan tafi tsirara sai naga an hukunta shi mene tai mai zai kasheta ", ta fashe da kuka Kalid yace ," kiyi hakuri ba zamu yi sanyi ba dole a hukuntashi ko waye ", ita ma Ummi baby taji wasu hawaye sun zubo mata Kalid yace," karku damu kawai ku nemo family dinta ko da yake nasan tsawon rayuwarku da ita kun san hakan ", Kalid ganin suna kuka yasa yabar maganar yace idan ya dawo zasi maganar bayan ya fita Ummi baby tai nannuyar a jiyar zuciya tana share hawaye sannan ta kalli Ruma tana cewa", Ruma sai na wulakanta Fadeela a duniya sai nasa an gujeta an tsaneta ,sai na rabata da duk wani saurayinta dake son aurenta ", cikin mamaki ita ma Ruma da hawaye ta kalleta ," mene ne kuma Fadeela tai miki Ummi , gaskiya karki mata haka ", murmushi Ummi baby tai tana cewa," naso Farida na duniya domin ta ga yadda Fadeela ta ci amanarmu ta yaudare mu ", Ruma ta sake fuskantar Ummi baby cikin rashin fahimta tana cewa," wai ki mini bayani mana ", da mummunan bacin rai Ummi baby tace," na shirya komai na yadda zan tozarta Fadeela kawai wasan za a fara , Ruma wallahi Fadeela karuwa ce ", wani faduwar gaba Ruma taji cikin mamaki ta kalli Ummi baby nan Ummi baby ta sanar da Ruma komai da kuma karin hujjojin da suka tabbatar mata Fadeela karuwa ce wata ashar Ruma ta murgino tana zagin Fadeela " amma yarinyar nan taci abinci a kan mu , wato har legos tana zuwa tabbb to ni ma wallahi ina bayanki don ganin mun yaye mata rigar mutuncin da take yafawa a idon mutane , sai mun kwance mata zani a bainan nasi wallahi ".😂😂 yau ake sanar dasu Inna cewa Jamila ta haifi na miji , Inna tayi murna sosai 👋 "ai wallahi ma Zainab kin yi kokarin zama da Fadeela domin ni wallahi tunda take kula karuwai kallon karuwa nake mata", Amina salisu ta fad`a tana gyara zama a kan gadon Zainab Zainab tace ," a'a Amina ki ringa kyautata mata zato ", Amina salisu ta tabe baki tana cewa", ni fa wallahi ma kawai damuwata mu kai mata ankon ki da Zakariyya domin nasan har yau bata san shi zaki aura ba , naga yadda idon shegiya zai koma ", Zainab dariya tai tana cewa," gaskiya kina da abin dariya ", daga can wajen gidan kuwa mahaifiyar Zainab taji sallama yayin da taga wasu 'yan mata su biyu , suka gashsheta , ganin gun Zainab suka zo yasa ummansu Zainab cewa su shiga Zainab d`in na ciki Sallama suka yi cikin dakin da Zainab da da Amina suke ciki duk mamaki ne ya kashe Zainab da Amina ," innalillahi ", Amina ta fad`a murmushi Ummi baby tai tana kallon Ruma Ruma ce ta kallesu tana cewa ," haba dan Allah sai kace kinga shedanu , muna tafe da muhimmiyar magana ne a kan K`AWAR ki Zainab, wato Fadeela ", Amina Salisu tace ," K`AWAR ku dai ai mu tun tuni mun mance da shafinta domin bata da banbanci da ku , domin abokin b`arawo to shi ma barawon ne ", murmushi Ummi baby tai tana cewa," gaskiya ne sister, amma akwai abin da baki sani ba bayan wannan ", Zainab tai a jiyar zuciya tana cewa ," ku zauna domin maganar zata fi ", murmushi sukai suna cewa ," mun gode ", Anan kuwa Fadeela ce tare da wani saurayi a cikin gidansa, tana zaune a falon gidan amma hankalinta duk a tashe yake domin Alajin da sukai magana zai siya mata gida ba ya d`aga kiranta ya juya mata baya hakan yasa take cikin tashin hankali, ji tai ana shafa mata bayanta , ta kalli kyakykyawan saurayin tana mai murmushi , zama yay jawota ya dorata a cinyarsa yana cewa," baby Fadeela ina sanki sosa", murmushi Fadeela ta kuma yi mai na yake da damuwa tana cewa, "Sadiq ni ma bani da wanda nake so kamar kai , amma sai dai ni Ina yin karuwanci ne saboda jin dadi , amma yanzu dole nai karuwanci mai yawa ba dare ba rana zan yi yawon bariki domin na sami kudin da nake nema ", a jiyar zuciya Sadiq ya yi yana cewa ," wallahi Fadeela da ina da kudi sai na share miki hawaye, amma kinsan yadda nake ", kallonshi tai tana cewa," na sani amma bari na tafi yanzu ",ta mike tsaye saurin jawota yay yana cewa," haba ya za ki to kuma ki tafi , gaskiya ni ban yadda ba ", rigar dake jikinsa ta fara cire mai ta fara gogar bayansa tana sumbatarsa a hankali yake jin shigar sautinta sakonta na kaiwa dukkan ilahirin jikinsa hakan yasa ya rungumeta yay daki da ita ya banko kofar 😂😂 to babu hanyar da zamu leka bare mu kai rahoto😂 share and comment..........🙏 K`AWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _____________________________________ Page 25&26 Ruma ta kalli Zainab tana cewa, "mun zo da maganar da muke son fad`a muku wanda babu wanda ya sani a kan Fadeela, muna fatan zaku am she mu ku fahimta kuma ", Zainab tace," dan Allah mene wai ", Ummi baby ce tace ", Fadeela karuwa ce ", dauu Zainab taji a ranta cikin fad`a ta fara cewa ," wato kuna san b`ata mata suna ke nan saboda kun jawota taki sauraranku ko ", Ruma da Ummi baby suka kalli juna cikin rashin jin dadi Amina ce tace ," haba Zainab ni kam su bamu shaida a baza mu karyata su ba", cikin jin dadin maganar Ruma tace ,"yawwa! Gaskiya ne wannan muna da hujjoji da irin mazan da Fadeela take mu'amala dasu , da hotunanta ke har ido da ido muna da yadda za a kamata ", . Zainab tai a jiyar zuciya cikin kasala da mamaki yayin da Amina tace su gabatar da dukkan abin dake tafe dasu ........... har wajen magariba su Ruma suka kai gidansu Zainab suna ta tattaunawa har suke fad`a musu mutuwar Farida Amina da Zainab duk sun sha jinin jikinsu sun yarda da maganar su Ummi baby sai dai abin ya matukar tada musu da hankali ba kadan ba haka su Ummi baby suka koma gida yayin da sukai musayen numbobinsu suna isa gida sukai salla😂 mutanen ku an fara komawa ga Allah bayan an yi salla wayar Ruma ta fara ringin tana dubawa ta ga Kalid ne nan ya sanar da ita an tafi kama Alaji Nuhu Ummi baby tace," tsinanne kawai ni wallahi ma Ruma wannan harkar duk ta fita a raina tunda Farida ta bar duniya, ambassador tun shekaran jiya yake kirana ", Ruma tace ," Hmmm Ummi baby ke nan , wallahi nima tsoro nake ji , amma anya kuwa zan dena ",tana dariya Ummi baby tace "yanzu kinsan mene shirin da nake", Ruma tace ," fad`a mini dai naji ", Ummi baby tace" yanzu haka ina bibiyar Alaji mansur da Aliyyu wato samarin Fadeela , saboda su ne take ganin zata yaudara ta auri wani a ciki", Ruma ta girgiza kai tana cewa, "tabbas kinyi tunani idan ma ta kama wallahi kawai mu aure su ", Ummi baby taiwa Ruma wani kallo tana cewa", wane zai auremu bayan sun san mu su waye ", Ruma tace ", Hmmm, mu yi kokarin hakan dai domin zuciyar Fadeela zata fi ciwo , ni kam na dau damarar bakanta mata rai , ai wallahi yarinyar nan ta yaudare mu mene ne ta rasa , gara mu koba komai babu yadda zami ", Ummi baby tace ," Hmmm ". Yanzu'yan sanda suka tafi da Alaji Nuhu suka tabbatar masa da ana tuhumarsa da kisan kai, sai dai yace babu wanda ya kashe , sun yi kuskuren adireshi 😂😂 yanzu misalin karfe 12na dare , sako ne ya shigo wayarta sakamakon ko kwanciya ma batai ba hakan yasa ta duban wayar rubutu ne da manyan baki , " Fadeela ki fito ina waje yanzu ", Fadeela ta tashi cikin nutsuwa da iya takunta ta dauki mukulli cikin iyawa ta fita ba tare da Inna ta farka ba tana fita ta tadda Alaji Shehu a waje , cikin bacin rai ta fara cewa haba Alaji ai yanzu dare bai yi ba 12fa mutane zasu iya fitowa ", Alajin da idanunshi jajawur ya kalli fadeela yana cewa," ni fa bazan jira dare sosai ba , yanzu nake so domin ko bacci na kasa , kuma tun tuni na miki transfer na kudi , don haka babu jira ", Alaji ya fara kokarin cire kayansa, yana ajewa a gefe Fadeela ta waiga ko'ina da ina tana cewa," ni wallahi bana san kofar gida da kazo da mota kawai mu tafi gidanka ", kafin ta rufe ba ki kawai taji Alaji a kanta , cikin ranta tace ni da jaraba Alaji Shehu sai da yay mata ......🙊 sun jima a kofar gidan har Fadeela ta matsu ya tafi , ni ko wannan wacce irin jaraba ce ita Fadeela ma abin Nata a cikin dare ne kuma kofar gidansu😭😭 ai shi ke nan Allah yana ganin kowa da komai , misalin 1:20 fadeela ta shiga gida yayin da shi kuma ya koma inda ya fito , wanka ta shiga a lokacin yayin da Inna ta farka tana tsaki da wannan hali da Fadeela. Washe gari Ambassador ne tare da Ummi baby a kofar gidansu juya masa keya tai cikin fushi , ambassador yace, " Haba baby kiyi hakuri mana ". Ummi baby tace , " Nifa wallahi bazan hakura ba sai ka mini abu guda". Ambassador yace, "To zan yi fadi". Ummi baby ta kalleshi tana cewa, " Wannan yarinyar ta wayarka nake son ka mini abu a kanta". Ambassador yace, "Au wai Fadeela, to me kike so za ai". Ummi baby ta fad`a masa komai na yadda take son ai , aiko Ambassador ya yarda ya amince , to Ummi baby ko me take son ai wa Fadeela??? mu dai namu idanu 👀😂 " Wallahi officer ban kashe wannan yarinyar ba, tana nan da ranta ku bincika." Officer da ranshi ya 'baci da maganar Alaji Nuhu ya mike ya fita ya bada umarnin tura shi kotu. Alaji Nuhu cikin zuciyarshi yake tunanin to idan Farida ta mutu wa ne yasan da ita a gidan da har za a shigo a dauketa , kuma bisa hujjojin da 'yan sanda suka gabatar masa ,ya wadatar masa Farida ta mutu , to tabbas kashinsa ya bushe, ba jimawa yayansa yazo aka tabbatar masa da abin dake faruwa , garin bin matansa ya yi kisan kai, Yayan nasa haka ya juya domin ba shi da wani gwarin gwiwar kare Alaji Nuhu. Fadeela na zaune ta ga kiran sabuwar number a wayarta kiran ta d'aga tana cewa, "Hello." Daga can 'bangaren taji ana cewa, "Fadeela ke nan shi ke nan kuma sai a mance damu , bayan an lasa mana zuma." Murmushi Fadeela ta yi tana sake sai ta zaman wayar a kunnenta tana cewa, "Hmmm amma waye yake magana." "Lallai ne Fadeela to wanda ku ka had'u a legos ne." A jiyar zuciya ta yi tana cewa, "To ai mutanen da muka had'u a legos suna da yawa." "To tunda kin kasa ganewa Ambassador Umar ne." Fadeela ta kwashe dariya tana cewa, "Ashe kai ne ." Aiko dai nan suka sha hira har suka sa ranar had'uwa. Ummi baby ce ta kalli Ruma tana cewa, "Ni fa wallahi tunda na gano Fadeela da irin wannan halin duk yanzu na tsani kai na." Ruma kawai ta kalleta tai shiru . Zainab sosai hankalinta yake tashe tunda komai ya tabbatar da Fadeela karuwa ce , to amma tun yaushe Fadeela take aikata wannan abu, ni ko nace wannan amsar sai gun Fadeela . Inna tasa rana zata je ganin jariri ta zauna har suna , Fadeela ta yi kokarin hanata duba da bata jin dadi, amma Inna da gardama tace sai taje, Yanzu labari ya fara jita-jita cewa Fadeela karuwa ce , sai dai mutane da dama suna karyatawa sakamakon an sabai mata wannan 'kazafi, yanzu misalin karfe 8 na dare Fadeela ta dan fita zuwa shago Inna kuwa tana cikin tashin hankali tana tsaye cikin falo tana jiran shigowar Fadeela , Fadeela na shigowa taji Inna ta kwad'a mata mari, abin mamakin ma maimakon Fadeela ce zatai kuka kawai Inna ta fashe da kuka tana zamewa a kasa cikin tashin hankali da rashin sanin abin dake faruwa Fadeela ta kalli Inna tana cewa, "Mene ne Inna, mene yake faruwa." Fadeela idanunta sun ciko da kwalla, Inna ta fara wani irin tari lokaci guda kuma tana kokarin fara magana ........share🙏 'KAWAR KARUWAI 💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _______________________________ Page 27&28 "Fadeela yanzu so kike ki tozarta mana rayuwa? mene abin da kika aikata ke nan , yanzu wani ya zo yake sanar mini gobe zzamu tattara kayanmu , wai kin saida gidan, hankalin ki ya kwanta idan muka koma kwanan titi." Fadeela ta durkusa gaban Inna tana cewa, "Wallahi Inna ban yi dan tozarta...." Inna ta dakatar da ita tana cewa, "Yanzu ina kud'in gidan yake." Fuskar Inna cike da hawaye tai maganar ita ma Fadeela fuskarta cike da kwalla ta fad'a mata yadda Alaji Sani ya yaudareta Inna ta sake fashewa da kuka tana cewa, "Wallahi kin cuceni Fadeela, kin cuceni." Fadeela na kokarin bawa Inna hakuri, amma Inna ta shige d'akinta cikin mummunan yanayi tana kuka . Kamar tun d'azu dai Ruma da Ummi baby suna zaune , ita Ummi baby ta durkusar da kai kasa koma take tunani? Ruma kuma tana danna wayarta , yayin da ta kalli Ummi baby tana cewa, "kinga Kalid yana fad'a mini Alaji Nuhu ya amsa laifinshi kotu kuma ta yanke masa hukunci , gaskiya Kalid yaron manya ne ya taimake mu ." Ummi baby ko d'ago kai batai ba , hakan yasa Ruma shafa mata fuska tana cewa, "Magana fa nake Ummi." Ummi baby ta d'ago idanunta sharkaf da hawaye tana kallon Ruma Ruma ta aje wayar dake hannunta tana cewa, "Me ke faruwa kuma ." Murmushi Ummi baby ta yi tana cewa, "Wallahi kanwata Aisha na tuna yarinyar nan tana so na , haka Dady da momy , ban ta'bajin ina kewarsu ba kamar haka ,sai yau , ko wanne hali suke ciki oho , a gaskiya ahali sun yi a rayuwa." ta share hawayen fuskarta tana murmushi Ruma ita ma murmushi tai tana kallon Ummi baby da cewa , "Idan kuwa haka ne ,to lokaci ya yi da zamu tuba." Da sauri Ummi baby ta kalli Ruma da idanunta da tasha kuka. Fadeela ce kwance a kan gado tana takaicin irin halin da Alaji Sani ya jefata amma taci alwashin dole taci gaba da neman kudinta don kada su rasa matsuguni tashi tai taje ta rufe gida ta kwanta Inna kuwa matukar tashin hankali take ciki da wannan hali da Fadeela ta jefasu hakan yasa ta kasa bacci har zazza'bi ya sake rufeta duk da haka kuka take tana tunanin tsawon lokacin da ta share a duniya da irin 'kalubalen da ta fuskanta na rashin 'ya'yanta Inna kuka tai ta yi tana zubar da hawaye har wajen kimanin karfe 12:30 na dare motsin Fadeela taji babu jan lokaci taji ta 'bude gida ta fita , hankalin Inna tashi ya sake yi cikin tsananin fargabar Inna Fadeela zata a wannan daren, ta fito falo ta zauna cikin tashin hankali Fadeela kuwa na fita gidan Ambassador ta wuce tana zuwa ya yi mata marhabun da zuwa suka shiga cikin d'aki d'aki ne mai matukar hasken gaske tare da had'ad'd'en gado tana shiga tai murmushi tana cewa, "Gaskiya wannan d'akin ya burgeni." Ta karasa maganar tana cirea babban hijab d'in dake jikinta tana wata irin kwanciya a kan gadon , babu komai jikin Fadeela a halin yanzu take kwance a kan wannan gadon Ambassador zama ya yi a kan kujera yana kallon Fadeela yana murmushi yadda taso take juyi a kan gadon tana shashshafa jikinta tana kallon Ambassador Ambassador ba tare da ya taso ba ya fara cewa, "Baby me yasa kika za'bi wannan rayuwar ko dan baki da kowa ne ko kuma kina neman kudi."? Fadeela cikin shagwa'ba tana girgiza jikinta tace ," Ni ka taso , dare fa yayi Inna tana gida yanzu bata jin dad'i." Ambassador yace , "Au kina nufin ba ta san kina fitowa ba." Da sauri Fadeela ta kalleshi tana cewa, "Tabb to kafff duniya babu wanda yasan ni karuwa ce , kuma yanzu na kai shekaru da da ma domin duk taron legos ina zuwa baya wuce ni , zan cigaba da rayuwata a hakan ." Ambassador ya mike tsaye ya matsa gabanta , kafin kace uffan Fadeela ta jawoshi kan gadon ya fad'a kanta . Bayan ta gama duk shed'ancin da ta gadama Ambassador ya rakota ta dawo gida cikin sand'a Fadeela ta fara taku dan gudun farkawar Inna a bacci tana shiga falon ta ga Inna tana zaune tana kallonta , cikin firgici Fadeela ta kalli Inna tana cewa, "Inna jikin ne? me kika fito yi falo."? Inna ta mi'ke cikin mummunan yanayi tana kallon Fadeela da cewa , " Ina kika je Fadeela, naga fitar ki tun d'azu sai yanzu kika dawo ." Fadeela cikin tashin hankali ta matsa kusa da Inna , tana sosa 'keya zata fara magana a wannan lokacin ne Inna ta hangi jikin Fadeela samm babu kaya a jikinta , "Inna da ma akwai wasu kud'i ne...." Inna ta dakatar da ita cikin mugun yanayin yadda ta ga fadeela a wannan hali wasu zafafan hawaye ne suka zu'bowa Inna , ta kalli Fadeela tana cewa, "Yanzu Fadeela fita kikai cikin daren nan ki ka je siyar da mutuncinki , tsirara kika fita Fadeela, innalillahi wa innailaihir raji'un". Inna tana gama fad'a ta fad'i kasa a karkace , da sauri Fadeela tai kanta , Inna ta dakatar da ita da hannunta tana wani irin haki tana cewa, " Bazan yafe miki ba Fadeela. " Inna ta karasa kaiwa kasa cikin hawaye ko shurawa Inna ba ta sake yi ba , tafiyar ke nan , haka Fadeela ta ringa tsandara ihu cikin darennan har ma'kota sai da suka fito suka zo , suka sami gawarta. Washe gari da safe sai ga Amina Salisu da Zainab da Ruma da Ummi baby sun had'u matukar tashin hankali Zainab da Amina suka sake shiga ganin video da su Ummi baby suka nuna mata, Ambassador ne da Fadeela, abin ya zuzuta su matuka hakan ya hassala Amina Salisu wai dole sai taje ta sami Fadeela da 'kyer Zainab ta hana ta sakamakon rasuwar Inna , amma ita ma Ummi baby abin da taso ke nan kawai suje ayita a gama saida Ruma taja hankalinsu kan wani shiri da tai hakan yasa duk suka sami sanyi cikin ransu wayar Ummi baby ce ta fara ruri ta kalli wayar tana cewa, "Mene kuma Ambassador." wayar ta kara a kunnenta tana cewa, "Ya akai." Daga can Ambassador cikin tashin hankali ya fara cewa , "Karfa ki fitar da wannan videon ba a rufe fuskata ba ." Ummi baby ta kwashe da dariya tana cewa, "Ambassador na fadeela, ai karma ka damu , har inda bai dace al'uma su gani ba wanda Fadeela ta bayyana a jikinta zamu rufe , duk da bataji kunyar Allah ba zan mata adalci ." Ambassador yace , "To shi ke nan ." ya kashe wayar Amina Salisu tace , "To ita dabba jaka taya gar yay mata video bata sani ba." Dariya Ruma tasa tana cewa, "Lallai ba zaki gane kan abinba , tana can tana jin dad'inta ai komai zai bazata gane ba." Zainab dai da zancen ya matukar rud'ata tace , "Allah ya kyauta." Amina Salisu tace, "kuma wallahi yau d'innan saina sanar da ita Zakariyya, Zainab zai aura kafin mu jefata cikin wani bala'in." Ita dai Zainab shiru tai tana juyayin mutuwar Inna tare da tunanin da baba Aminu na duniya data jefashi cikin tashin hankali, sai Allah yasa yabar mata duniyar . Bayansu Ruma sun koma gida ,suka sami Kalid yana jiransu a yau suka ziyarci Gombe state suka nemi gidan su Farida, suna zuwa wata mahaukaciya suka gani a cikin gidan tare da wasu yarah kuma suna ta wasa , daga bisani bayansun sami mari'kin Farida suka sanar da shi duk irin rayuwar da Farida ta yi harta koma ga Allah, yaci kuka sosaii yayi nadama duk da ba laifinsa ba ne , ya dad'e yana zuba idon shigowar Farida gida , amma a halin yanzu ya cire rai , haka shima ya basu labarin irin rayuwar wahalar da Farida tai a cikin gidansa , ga rasuwar 'kanwar mahaifiyarta wanda ita ce yake aure ta kuma d'auki Farida sanadin rasuwar iyayenta, su dai su Ruma sun san komai domin ta basu labarin a lokacin mutumin yake nuna wannan mahaukaciya yake sanar musu ita ce azzalumar da tai sanadin komai da ba'kin halinta , domin ma ana zargin da hannunta wajen mutuwar'kanwar mahaifiyar Farida. Da kuka suka rabu da juna Ummi baby kamar yarinya sai da ta d'auki dutse ta kwalawa wannan mahaukaciyar aiko ta fara ruwan ashar , Ummi ba ta sake bige Mata baki . Sun yi matukar dare suka dawo cikin kano. Amina kam kamar yadda ta fad'a tasa Fadeela cikin mamaki a yanzu ta gane Zakariyya Zainab zai haura shi yasa ta ga da yazo gaisuwa ko sauraranta bai yi ba . Washe gari da safe su Ruma suna karyawa sai Ruma take cewa , "Ummi ni a ganina a maimakon yiwa Fadeela hakan , me zai hana kar mu fitar da video, kawai mu mata bazaranar ta fito ta nunawa duniya ga irin halinta , domin kinga ita mace ce abin zai ta siri cikin rayuwarta sosai." Cikin 'bacin rai Ummi baby ta kalli Ruma tana cewa, "ke kinma isa , kamar yadda nai alwashin tozartata to wallahi sai nayi, tana tare damu tana cin dunduniyarmu kuma ke kinsan shekararta nawa a matsayin karuwar sirri , to wallahi ta rugamu farawa , kuma da kike maganar mu sata ta amsa , duk mutane sun san 'kawar mu ce , hakan yasa ake kiranta da 'kawar karuwai to idan mukai haka kowa zai ce mu ne muka jawota ciki gwanda kowa ya ganta 'kiri-'kiri ." Ta aje maganar cikin huci tana kallon Ruma . share and comment.......🙏 'KAWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _______________________________________ page 29&30 Fadeela bayan an sake kawo mata notice yasa cikin dare ta kwashe kayanta , har yanzu babu inda kanta ya kawo mata da zata je domin ko 'yan uwan babanta na Kaduna sun ce ta shirya ta koma can , amma tace dasu idan sun tafi bayan tayi bankwana da mutane zata taho , hakan yasa suka tafi suka barta . Gidan Sadiq ta wuce domin zama , aiko yayi murna sosai da ganinta a wannan lokacin, shi kawai bukatarsa ayi abin da aka saba domin kwana biyu basu ha'du ba duk da Fadeela na fama da zazzabi da ciwon ciki hakan bai hana Sadiq yin yadda yaso da ita ba , aiko ta ci wahala shi kam ko a jikinsa domin ya yi abin da yake so bayan ya fito daga wanka ya sameta shan'bar a kwance jikinnata ya yi tsafi sosai , a lokacin ne mahaifiyarshi ta kirashi a waya cikin murna take sanar da shi gobe yayansa zai dawo don haka ya shirya dawowa gida ya kuma gyara masa gidansa kafin ya sauka, shi dai Sadiq damuwarshi rashin lafiyartaa a halin yanzu , hakan yasa ya nemi kaita asubiti. Washe gari ma'kotan Fadeela suna shirin kai mata abincin rana suka ga gidan a kulle , babu jimawa suka ga anzo ana rushe gidan , bayan sun bincika aka tabbatar musu da ansiyar da gidan , hakan yasa suka fara tunanin ko ina Fadeelan yanzu, wata mai kimanin shekaru iriin na fadeela ce ta fito daga d'aki tana cewa, "Umma ! Ai dole a nemi fadeela a rasa kinga videon ta." Abin ya matukar basu mamaki sosai ji da ganin Fadeela a wannan yanayin. Fadeela na cikin asubiti ita da Sadiq samm basu da labarin video da yake yawo na Fadeela, musamman cikin makarantarsu kowa malamai da d'alubai yasan halin da Fadeela ke ciki Sadiq yana gabanta ri'ke da takardar da dactor ya basu tabbacin wata rashin lafiya dake tattare da Fadeela. Kuka take sosai cikin tashin hankali tana kallon Sadiq tace , "Ka mai dani gidanka Sadiq ni tawa ta 'kare." Sadiq ya kalleta cikin tashin hankali yana cewa , "To Fadeela ke da ba matata ba ni yanzu ina zan kai ki , sanin kanki ne gidan da nake gidan yayanmu ne kuma yanzu ya dawo , nima gidan mahaifiyarmu zan koma , kawai kiyi hakuri ni zan tafi ki nemi wani gun."Ya aje mata takardarta Sauri Fadeela tai ta ri'ko masa riga cikin rurucewa da kuka tana cewa, " Haba Sadiq kar ka mini haka dan Allah ". Sadiq ya fincike rigarshi yana cewa, " Sake ni dallah ni babban tashin hankali na ma wayasan tarin cutukan da kike dasu da likita bai gano ba ." A lokacin Fadeela tai tunanin tun rasuwar Inna ,Alaji Mansur da Aliyyu basu sake waiwayarta ba , hakan yasa ta kalli Sadiq Sadiq tana cewa, "To ara mini wayarka nai kira." Ya cilla mata wayar yana kauda kai , niko nace anci moriyar gan-gan... Ta fara sa number taji an yi sallama hakan yasa ta aje wayar tana kallon masu shigowar cikin kuka Ruma ce ta shigo da Ummi baby sai Alaji Mansur, Aliyyu, Ambassador, Zainab, Amina Salisu. Fadeela ta rasa me zatai murna ko tashin hankali ne yake tunkarota domin tunda ta ga Ambassador a cikin su abin ya d'aure mata kai , kowa shiru ya yi amma Ummi baby zuciyarta tafasa take sosai idan tana kallon Fadeela "Nasan za ki mamakin ganinmu haka to ,sharrin da kika dad'e kina shukawa yau za ki kwashe". Ruma tai maganar cikin jin haushinta. A jiyar zuciya Fadeela ta yi , tasha jinin jikinta cikin kwalla ta kalli Ruma tana cewa, " Wanne sharri kuma Ruma , ni ce fa Ruma." Ummi baby cikin fusata ta kalli Fadeela tana cewa, "Ai wallahi kin bamu kunya kin yi asara." Cikin tashin hankali Fadeela ta sake cewa , "Wai mene yake faruwa ne dan Allah." Amina Salisu da babu tausayin Fadeela a ranta ko kad'an ta fara cewa , "Ku fad'a mata mana shegiya mahaukaciya mun gano ke KARUWA CE". Duk sai da sukaji maganar ta ratsasu duk da ba sabon abu bane . " Wa iya zubillah Amina Salisu, karki mini 'kazafi saboda kin tsane ni." Ta fashe da kuka , "Wato 'kazafi ko macucuya munafuka." Amina Salisu ta sake fad'a Fadeela ta daure ta tashi daga gadon asubiti ta ri'ke hannun Zainab tana cewa, "Yanzu ke Zainab kin yarda da wannan." Zainab ta janye hannunta ta kau da kanta . Fadeela tace , "Na shiga uku ni , Yanzu mutanen da nake son shiryay dasu su ne zasu tozartani .". Aliyyu ya kwashe Fadeela da wani mari da sai da ya yi sanadin komawarta gado ta zauna , " Kin yaudare ni , kin cuci rayuwarki ." Ya ciro wayarsa a aljihu ya nuna mata bidionta da wani gashinan an rufe masa fuska . Sauri tai ta Kalli Ambassador ta rushe da kuka mai 'karfi . Alaji Mansur bai ce komai ba , haka Zainab "Innalillahi wa innailaihir raji'un, kin yi asara Fadeela." Amina Salisu ta fad'a cikin izza da kuka Fadeela ta mi'ke tana cewa, "EH nayi nayi karuwanci, amma ni sam banyi don neman kud'i ba , naji na yaudare ku amma idan na sanar daku mene hakan zai amfane ku." Fadeela ta zauna cikin kuka ta durkusar da kai tana cewa, "Yanzu na tabbatar da nayi asarar duniyata , akwai wata rana wajen shekaru 7 da suka wuce , mun je biki Kaduna tun daga nan komai ya fara . Wani daga cikin abokan angon ya nuna mini yana sona , hakan yasa na yarda , domin ni Allah ya sa mini saurin sabo da yarda da mutane, Ranar da zamu dawo kano ina cikin motarsa , ya fara mini wasu irin maganganu na rashin tarbiya, hakan yasa kawai naji shed'an ya shiga zuciyata kawai na sumba ce shi , tun daga lokacin hankalinsa ya tashi ya tafi hotel dani , ya yi duk yadda ya gadama dani yayin da ni kuma na ba shi had'in kai , a ranar ban dawo ba saida na sake kwana biyu, na sake ne man wasu mazan." Fadeela ta share hawayenta tana cewa, "Bayan na dawo naji bazan iya jure zama ba tare da maza ba , kuma a lokacin sam bana san aure , naci gaba da yi a nan , wanda nake fita duk lokacin da naso , sai baba Aminu ya sa mini ido, hakan yasa ya mai dani gidansa , nayi cuta sosai saboda bazan jure zaman gidansa ba domin bana fita , lokacin da Inna ta ga na rame sosai tace ya dawo dani bayan na dawo na yi matukar farin ciki, hakan yasa na yanke shawarar fita da dad dare, nake zuwa nai abin da naso babu wanda ya sani , bayan shekara biyu sai na had'u dasu Farida, da farko na yi tunanin fad'a musu nima irinsu ce , amma nai tunanin nai shiru kawai zai fi na samu kwanciyar hankali, gudun ace tunda ina tare dasu nima irinsu ce, yasa na farai musu nasiha." Kuka Fadeela ta sake rurucewa da shi tana cigaba da magana, "Yanzu babu Inna babu baba Aminu, na yi zaton zan ci gaba da watayawata ashe ni ma na gama rayuwa, yau tsawon shekaru na 7 cikin wannan rayuwa, amma a yau gani ckin tozarci ." Ta dauko takardar da dactor ya basu tana nuna musu , "Yanzu likita ya tabbatar mini da ciwon cancer ya kama mahaifata , yace ta kai matakin da dole za a cire ko kuma komai ya iya faruwa." Ta sake fashewa da kuka , Aliyyu yaja dogon tsaki yana cewa, "Sam banji tausayinki ba , azzaluma mayaudariya ." yasa kai ya bar asubitin baki d'aya Sadiq ya kalleta yana d'aukar wayarsa a cikinta yana cewa, "Nima na tafi ." Ya tafi tana kuka Ambassador ya kalli Ruma yana cewa, "mu ma mu tafi ko." Ummi baby ta kalli Fadeela tana cewa , "Zamu tafi saidai muce Allah ya sake shiryamu abin da yafi miki ki koma Kaduna wajen family d'inki." Amina Salisu taja hannun Zainab tana cewa, "Taho mu bar nan." Suka fice Fadeela na kallonsu da bakin cikin rayuwa , Ummi baby ta kalleta tana cewa, "Sannan kuma video wanda ki ka yi mun watsa shi a duniya, yanzu babu sauran biyo-boye kowa yasan wace ke ." Kuka ta sake fashewa da shi tana kallon su cikin tashin hankali, yayin da sukai tafyarsu sai Alaji Mansur kawai a Cikin d'akin . Su Ummi baby suna fita , Ambassador ya kalleta yana cewa, "Tom yanzu kuma sai ki cika alkawari , tun yanzu zamu tafi gidana ." Ummi baby wani tashin hankali taji ya ziyartar mata zuciya, ta kalli Ambassador cikin masifa tana cewa, "Sai kace baka ji abin da yake faruwa da Fadeela ba , gaskiya muna cikin tashin hankali Ruma ba za mu bar asubitinnan ba sai munje an yi mana gwaje-gwaje munsan cututtukan dake tare damu." Ruma ita ma cikin tashin hankali ta amshi maganar Ummi baby taja hannunta suka koma cikin asubitin. Ambassador cikin ranshi yace, "To ni mene matsayin."? Share_____ 'KAWAR KARUWAI💃💃💃 BY AUTAR MARUBUTA _________________________________ Page 31&32 Alaji Mansur ya kalli Fadeela dake kuka yana cewa, "Kin yaudari kanki , kin kuma b'ata rayuwarki, yanzu ke nan ba daban wa'yannan Karuwanba shi ke nan idan na aure ki na fad'a cikin masifa Fadeela, kinga rayuwa ke nan ba ki da kowa yanzu duk sun guje ki ,harda al'umar gari ,kinga yadda KARUWAI💃💃💃 sukai wasa dake, daman idan ba ka iya kamun 'barawo ba to shi zai kama ka , yanzu kina cikin mummunan yanayi a cikin garinnan . Sannan kuma har yanzu ina sonki ." Fadeela ta d'ago kai tana kallonshi cikin kuka "Amma bazan iya auren ki ba , yanzu ke abin gudu ce Fadeela." Ta sake rushewa da kuka ya cigaba da cewa ,"Ko kad'an bazan aure ki ba , amma ba zan so rayuwarki ta tagayyara ba , dan haka zan mai dake Kaduna ,zan kuma d'au nauyin yi miki aiki ki samu lafiya , wato a cire miki mahaifa". Kuka ta sake rurucewa da shi tana kallon Alaji Mansur ta kasa cewa dashi komai . Cike da fargaba su Ruma suke jiran sakamakon gwaje -gwajen da akai musu , hankali ya matukar tashi bayan wani lokaci ne aka bayyana musu cewa babu wata babbar cuta a tare dasu , amma suna d'auke da cutar sanyi mai muni a tare dasu, nan likita ya rubuta musu magani da matakan kariya , suka koma gida . Suna zuwa kofar gida suka sami Kalid yana tsaye , aiko suka gaisa cikin girmamawa, yake musu nasiha Nan Ruma da Ummi baby suka rungume suja suna wani kuka mai gwanin ban tausayi, "Wallahi tun rasuwar Farida jikina ya yi sanyi , sannan yanzu naga yadda rayuwar Fadeela take tagayyara, a halin yanzu bani da burin da ya wuce na koma mahaifata Nijer wajen iyayena." Ummi baby tai maganar cikin tashin hankali da kuka , lokaci guda kuma tana sake rungume Ruma a jikinta, ita ma Ruma cikin gawurtaccen kuka ta fara cewa , "Allah ne abin godiya Ummi, ki dubi yadda ya kare mu daga cutuka masu had'ari da muni, ko dan wannan ya ishe mu ishara mu koma ga Allah domin babbar da ma ce ya bamu." Kalid jikinsa ya yi sanyi duk tausayinsu ya kamashi , ya yi godiya ga Allah tare da yiwa Farida addu'a . A lokacin ya kallesu yana cewa, "Tunda yanzu Allah yasa kun gane komai , gobe idan Allah ya kaimu duk ku shirya ni zan mai daku gidan iyayenku insha Allah." Sake rungume juna cikin farin ciki . Kalid yace , "Insha Allah gobe kuna farin cikin ganin 'yan uwanku ." Ruma ta kalleshi tana cewa, "To amma ita fa Ummi baby tana Nijer ne Kalid, koda yake idan ba zaka damu ba , sai duk mu kwana a gidan mu , idan yaso washe gari sai a tafi Nijer d'in domin nima zani ." Kalid yace , "To shi ke nan Allah ya kaimu goben ." A halin yanzu su Alaji Mansur sun isa Kaduna zuwansu ke nan 'kanwar Inna , wato baba Laure tace Allah wadai Fadeela ta zauna mata a gida , sakamakon ta sanadin Zakariyya sun sami labarin komai baba Laure d'amara taci da gyalenta ta kare kofar gidansu, dake babban gida ne da duk 'yan uwa suke a ciki. "Ai wallahi zaki ga ma sakamakonki yadda Allah zai wajugaki , haka kika ki auren Zakariyya ashe akwai abin da kika 'boye tsinanniyar banza , wallahi kin 'bata mana zuriya , kuma ba zamu yafe ba , kuma kika sake kika shigo gidannan yau kwanan lahira za ki ." Baba Laure tana maganar kamar zata rufe Fadeela da duka sai da kyer da sutin goshi tare da taimakon wasu manyan cikin gidan , baba Laure ta amince da Fadeela ta zauna a Kaduna a karshe Alaji Mansur ya yi musu sallama tare da ba wa Fadeela d'imbin kud'ad'en da zasu ishe ta ai mata aiki har ta samu na kashewa , nan yace mata iyakar abin da zai mata ke nan , ya tafi sai wata rana . Ta shiga sabon tashin hankali kuwa , a cikin Daren suka tafi asubitin sakamakon motsawar ciwon nata , Nan Fadeela ta ga ne duniya ba sa ar ta bace ,ta wuce tunaninta , yanzu abin dake yawan fad'o mata mutuwar Inna kalmar ta da tace bazata yafe mata ba , tabbas baba Laure idan taji labarin ta haka Inna ta rasu , Fadeela zata fuskanci sabuwar tsana a cikin family, hakan yasa tai shiru tana rokon Allah yafiya. Washe Gari Duk sun zuba kayansu a mota sun bawa mai gida mukullin gidansa , Ga Zainab ga Amina Salisu da Ambassador, duk bayan sun yi sallama , sai Ruma ta shige mota , Ambassador idanunsa cike da hawaye yake kallon Ummi baby, ita ma da tausayinshi ya kamata tasha gabansa tana cewa, "Ambassador ka yafe mini duk wani abu da nai ma na rashin kautawa, ni 'ya mace ce , kuma tsohuwar rayuwata zan koma yanzu a gaban iyayena , abin da ya kamaceka ka tuba ka koma ga Allah tunkafin duniya tai maka zafi ." Ambassador ya rike mayafin Ummi baby yana cewa, "Dan Allah karki tafi." Ta fisge mayafinta tana cewa, "Ummi baby nake a karuwanci, amma a yanzu Zulaihat ce , ya rage naka shiryuwa ko sa'banin haka , Allah ya had'a kowa da rabonsa." Ta shige ta hau mota , Kalid yaja mota suka tafi , yayin dasu Zainab suke musu bye bye , suma su Ummi baby suna d'aga musu hannu . Kalid 'karamar hukumar bebeji suka nufa cikin wani gari mai suna cutar biki . Zuwansu ke nan wani Farin ciki ya rufe Ruma , wani irin zumud'i take jikinta na rawa, kallo guda taiwa gidansu tasan kwarai arzikin babansu ya karu, sai dai Allah yasa wannan azzalumin yayan baban nasu ya mutu wanda ya yi sanadin shigarta wannan rayuwa, Da gudu ta fad'a cikin gidan tana kuka , taci karo da wani dattijon mutum yana alwahar azahar , tabbas shekara shida ba wasa ba , dattijon da sauri ya mike yana kiran sunan Allah cikin mamaki yana kallon Ruma , da gudu ta rungume sa cikin kuka tana cewa , "Baba ni ce , ni ce baba ." A lokacin su Ummi baby suka shigo suna kallon yadda duk mutanen gidan suke rungume Ruma cikin tsananin kewarta, bayan komai ya lafa Ruma ta gabatar da su Kalid, nan babu 'boye-boye ta sanar musu irin rayuwar da tai , ita dai mahaifiyar Ruma farin ciki take sosai da ganin yarinyar ta , bayan Ruma ta tambayesu ina baba Salisu, suka tabbatar mata da yana gidan yari , sakamakon laifin da ya aikata na yiwa yara fyade a cikin kano , aka kaishi kotu, Wani farin ciki ne ya sake lull'be Ruma , yau kwanan zaune sukai cirrr ana labarin abubuwan da suka faru . Washe gari mahaifin Ruma wato Alaji muhd ya yi musu bizar zuwa Niger a jirgi , da Kalid da Ruma da Ummi baby suka tafi . Matukar zumud'i ke tattare da Ummi baby kan taje ta ga nata a halin , aiko da wajen la'asar suka sauka a Nijer , a halin yanzu Ummi baby matukar shau'ki take sosai ta ga wani cikin a halinta , bayan su isa kofar gidan ta ga babu abin da ya canza kawai sabon fenti ne da bai jima ba , wasu hawaye taji sun zubo mata kawai cikin takun 'yanci ta 'bude kofar gidan wacce ke had'e da gate , suma su Kalid suka bi bayanta ba tare da ta yi sallama ba ta shiga tsakar gidan , kawai wasu hawayene da kasala suke biye da ita, idanunta takai kofar d'akin falon su ,wanda ta ga ta kalma da kuma tashin sautin hayaniya , kawai tasa kai tana kuka ta shiga falon , wata tsohuwa ce mahaifiyar babanta ta mike tsaye , mahaifinta da mahaifiyarta da 'kanwarta Aisha da taji wani arnen kitso da kunshi da gyaran fata , duk suka tashi tsaye . Ummi baby kawai fad'uwa tai ta sume , duk sukai kanta . Bayan ta farka kuwa sai murna ,"me yasa za ki tafi ki barmu aunty Ummi. " Aisha ta fad'a tana kuka , Ummi baby ta basu labarin rayuwarta da kuma sanadin tafiyarta , har yanzu mahaifin Ummi baby yana sonta matuka , ya yi farin ciki sosai , A lokacin ake tabbatar mata bikin Aisha ake domin sauran kwana biyu d'aurin aure . murna dai kamar ta kashesu suma makota da abokan arziki suna samun labari suka ltaho , harda saurayin Ummi baby wanda ya yi mata ciki , yazo da matukar murnarsa. Washe gari Su Kalid suka shirya , mahaifinsu Ummi baby ya tabbatar wa Kalid da yase masa mota tana kano tana jiransa, ya ba wa Ruma kud'i kimanin..........,tare da basu hakuri wai sun zo a ga'bar bikin 'kanwar Ummi baby, aiko sun yi matukar godiya , da kuka su Ummi baby suka rabu yayin dasu Kalid suka dawo kano . Kalid yana isowa ya sami gallelitar motarshi mai tsada da kyau ya yi matukar murna . BAYAN SATI Yau kwanan Zainab biyu a Kaduna gidan Zakariyya, abin ya yi armashi da tsari . A halin yanzu babu abin dake damun zukatan Ruma da Ummi baby suna cikin farin ciki da kwanciyar hankali tare da ahalinsu . Saurayin Ummi baby ya matukar nadama da neman gafara , hakan yasa yake sanar da ita har yanzu yana kaunarta kuma zai aure ya zauna da ita cikin soyayya. A 'bangaren Fadeela kuwa tana samun sau'kin aikin da an kai mata , ta rame sosai tasa tunanin Inna a ranta ga rashin kulawa da bata samu , tana fad'a a ranta cewa tafi kowacce mace a sara a duniya , domin a halin yanzu mace juya ta fita amfani tunda ita akwai mahaifar a jikinta , ita kuwa fa . Amma ta d'an sami sau'ki tunda Zainab tayi aure a kusa da ita , domin tasan tabbas Zainab ba zata gujeta ba . Alhamdulillah Rabbil alamin . Anan na kawo karshen labarina mai suna 'KAWAR KARUWAI, Ina addu'ar kuskuren da nai Allah ya yafe mini , ya kuma ganar dani dan gudun sake aikatawa, abin da nai Daidai Allah ya haskaka mana . Wanda kuma suka hango kuskuren ko matsala su sanar damu mu gyara ba a ringa zaginmu ba ko aibatamu . Ina marhabin da duk shawar-shawarinku masoyana Allah ya bar zumunci da kauna . Sannan kuma ina muku albishir da sabon labarina mai zuwa gare ku . Wanda ya samu ingancin tsari 'kir'kira Shiryawa Mai suna MARUBUCIYA wanda wannan labarin sadaukarwa ne ga dukkan Marubutan kasata . Yana tafe gare ku masoya FATIMA ABDALLAH KANO ( Autar marubuta). Bissalam .