BAYAN WUYA... *By* 💫RUMANAH M. DIGGI💫 (Star writer's✨) *GODIYA*_ Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga buwayi gagara misali, Sarkin sarakuna, shugaban shugabanni, ubangiji makaidaici mai Kowa mai komai. Tsira da Aminci su tabbata ga shugaba ja gaba dan gata annabi Muhammad (s.a.w) da ahalinsa da sahabbansa da dabi'ahn sa baki Daya. *GODIYA TA MUSAMMAN, FARIN WATA WRITER'S ASSOCIATION 🌙✍️🥰 ALLAH YA ƘARA BASIRA MUTANE NA INA ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE💫* *SADAUKARWA* na sa daukar da wannan littafin gabadayan sa ga tashar EL_NAJEEB PRODUCTION YOUTUBE CHANNEL. Allah ka karamusu daukaka da nasara Ameen thumma Ameen 🙏🏼 *Godiya* godiya ta musamman ga abokanan arziki da 'yan uwana na gari bazan taba mantawa dakuba koda ina bakin kura 🦬❤️💫🥰 *Bismillahirrahmanirraheem* BAYAN WUYA... EPISODE 001. *****AJAH ROAD***** *LAGOS NIGERIA* Duniya darasi!!! Hakika duniya darasi ce ga Wanda zai tsaya ya fahimta, rayuwa juyi-juyi ce yayinda tamu rayuwar tayi mana juyin kwado daga ruwan sanyi zuwa ruwan zafi, hakika ƙaddara abace mara tabbas, babu mai iya sauya ƙaddara face ɗayan taccen sarki, kaddara kamar zanen dutse ce da babu wanda ya isa ya goge, a haka tamu kaddarar ta zo, Kuma a haka muka ɗinga binta dalla-dallah kamar zanen kan taswira. Rayuwa mai ƴanci ma gata ne, ganin iyaye a kusa dakai babban gatane koda basuda ko sisi, Iyaye ko ya suke rahma ne, kuma wani sashe ne na jikin ka wanda idan ka rasa kamar ka rasa komai. nayi rayuwata cike da rashin ƴanci da rashin tausayi, ga ƙyama ga kuma cikakkiyar wahalar da ta amsa sunanta. Maraici bashida daɗi ko ya yake, sannan rashi ma bashi da daɗi ko na menene, balle ma ace rashin iyaye gaba ɗaya. na tausayawa marayu kamata, na tausayawa marasa galihu kamar yanda nake. ★★★ Shekaru biyu da suka shuɗe rayuwa mukeyi mai cike da ƴanci da so da ƙaunar juna irin wacce iyalai suke yiwa junan su. Mu biyu ne awajen iyayen mu Ni, sai kuma ƙanwata. mahaifiyarmu itakataice wajen mahaifinmu ma'ana ita kadaice matarsa. Mahaifinmu ba talaka bane Haka kuma baza'a Kira shi da mai ƙudi ba, sabida ko gidan da muke zaune ba gidan mu bane gidan hayane. Mahaifinmu ABBIE HAMRAZ AWAIS yanada karamin shago Wanda yake hade da gidan da muke zaune ma'ana an gina shagon kofar gidan mu. A cikin shagon zuba kayan masarufi sosai da baza'a rasaba, kamar dai Kayan Miya irinsu magi, mai, bushashen danƙwa, da sauransu. Haka Kuma ana siyarda shinkafa, spaghetti, indomie, da Toka, clean, slippers, dadai sauran kayayyakin amfani. Alhamdulillah mahaifinmu yana samun ciniki sosai sabida kayansa sunada arha ba Kamar na sauran 'yan unguwar ba. Haka ma mahaifiyar mu AMMIE FAHEEMA ba'a barta a baya ba tanayin ƴan Sana'oin ta cikin gida a rufawa juna asiri. Kanwata Aleena shekarunta goma ne zuwa sama sabida a wannan shekarar ce zata kammala karatunta na primary, yayinda nikuma nakeda shekaru goma sha biyu kuma ina jss one a wannan lokaci duk muna tare cikin rufin asirin Allah. Iyayen mu na matukar nuna ƙauna garemu ko kaɗan basason abunda zai damemu, domin duk abunda muka nema muna samu a wajen su idan dai baifi karfisuba. ★★★ Yara biyu ne suka shigo gidan, bakunan su dauke da sallama, jikinsu sanya da uniform din islamiyya. Karamar ce ta rugo aguje kan Wata mata Dake zaune tana gyara shinkafa wacce da alamu ana shirin dafawa ne, "Amminmu sannu da gida" yarinyar ta fada tare da ɗalewa bayan matar ta sarƙabo hannun ta kan kafaɗun ta "so kike yi karyani budurwa" matar ta faɗa da fara'ah. "Ahhh amminmu idan na karyaki na hau ƙafarwa toh?" Matar na shirin bata amsa ne sai ɗayan yarinyar ta ƙaraso inda suke zaune "Ammi inawuni ya aiki" "Lafiya kalau LEEYANA ƴan makaranta andawo lafiya, da fatar dai anyi karatu kho" matar ta faɗa tana kallon yarinyar da najie ankira da LEEYANAH. "Ehhh Amminmu nayi karatu sosai kuma na iya harda ta har kyautar littafi aka bani" yarinyar ta fada tana nufar tilon dakin su Dake can gefen gidan. bayan tashiga ta cire hijab dinta ta Kuma ajiye Jakarta Sannan ta fito waje ta dawo inda matar nan ke zaune. ta karbi tiren shinkafar tana faɗin "Ammi bara natayi, wallahi ammi yau nagaji sosai fa nayi tunanin ma an kare abincin nan". "To gara sarkin ci ba'a kareba'" Yarinyar da ke kan ƙafar matar nan ta fada tare da yiwa LEEYA gwalo. Hannu leeya ta ɗago da niyyar ta rankwashi yarinyar sai matar ta rike mata hannu "kullll karki yarda ki dakammin yar budurwata wallahi" Turo baki leeya tayi duk da fuskarta na lulluɓe da mayafi hakan bai hanawa mahaifiyar ta ta gane abun da tayi na, sannan tace, "Ammi kibari nayi mata rankwashi ko ɗayane dan Allah ko zan rage haushin ta danake ji". Leeya faɗa tana yamutse fuska duk da ba ganin fuskar ta nakeyi ba domin a rufe da ke da wani mayafi. " Subhanallah!!" leeya haushin me kikeji nata kuma me tayi miki har da zakiji haushinta? sabida ta kiraki gara sarkin ci ae gaskiya ta faɗa" Ammi ta fada tana shirin miƙewa zata tashi daga inda take zaune. "Ammi wai kinsan yau kasa muka dawo daga IFE AREA kuwa? Komawa tayi zaune daga niyyar tashinda take sannan tace "ƙasa kuma leeya meya hanaku shigowa taxi yau? "Wallahi Ammi Aleena ce ta kashe mana kudin taxi bayan kuma ta kashe wadanda Abbie yabata, kinsan ba class dinmu dayaba Saida aka tashemu sannan take gayamin wai kar ma na tara taxi domin ita ta kashe kudin taxi din, Ammi haka inaji ina gani muka dawo gida a kasa". Aleena da tunda aka fara magana hannunta ke dafe da gabanta tace "Wallahi amminmu wasa nake ban kashe kudin ba nayi hakane kawai sabida mu koyi tafiya a kasa, mukoyi maintaining, Kinga yanzu ni budurwa ce, idan Bana tafiya a kasa Ina miji zai ganni balle nayi aure, ko so kike in wuce lokacin aure kamar yanda yahyah leeya ta wuce?" Ta fadi maganar cike da yarinta tana ware hannayenta alamar tambaya. A yarinta irin na Aleena duk wacce ta kammala primary to itace budurwa kuma idan batayi aure a wannan lokacin ba har wata shekara ta zagawo aka kuma yaye wasu ɗaliban to shikenan ƴan waccan shekarar sun tsufa kenan sun wuce lokacin aure. To ita yanzu take shirin zama budurwar, shiyasa kowa a gidan yake kiranta da sunan. Idan kuma baka kiranta da sunan budurwa to bakaibane wanda kuke shiri da ita ba. Dariya suka kwashe gaba dayansu, sai yanzu na kula da Wani dattijo Dayake shigowa gidan daga can kofar gida. Dattijon ba baki bane, haka Kuma Kai tsaye bazaka kirashi da fariba. yanada dan tsayi, Haka kuma yanada matsakaicin jiki. A ƙiyasi zai iya kai shekaru 45 zuwa sama HAMRAZ AWAIS kenan datijjo mai kamala da haiba. Tun sa'adda Aleena ta fara magana yana jinsu Shima maganartata ce ta bashi dariya. "Assalamu Alaikum" Abbi ya furta sallama yana ƙarasowa cikin gidan. Tare suka amsa masa sallama a lokaci ɗaya. Leeya ce ta fara gaida shi sannan sai Aleena. "ummu-aleena barka da gida" "yawwa barka dai Abu-leeya ya shago?" "shago alhamdulillah mungode Allah". Dubana na Kaiga wacce aka kira da ummu-aleena matar nan ce dake zaune tana gyara shinkafa tun a farko wato Ammi. Naganta macece guntuwa mai faffadan jiki, duk da kasancewarta guntuwa a kallo daya bazaka kirata da guntuwa ba haka zalika ba doguwa bace, gata fara sol zubin fulanin maiduguri wato kanuri Ammi faheema kenan mahaifiyar Leeya da Aleena, mata wajen Abbi Hamraz Awais. "Ke! budurwa kike ko wa?? ki tashi daga kafar matata karki karya min ita" Abbi ya faɗa yana kallon Aleena dake zaune kan kafar Ammi. Maƙe kafaɗa tayi Alamar bazata yi ba, sai ta sauya zancen da faɗin "Abbie yau kasaka kudi a asusuna kuwa?" "batun matata nake, bata asusun kiba" "Abbie nifa bazan tashi ba sai ka gayamin amsar tambayata" "to ban sakaba Amma kizo muje yanzu na baki ki saka da kanki". zabura tayi da gudu ta isa gun Abbie ta miƙa masa hannu alamar yabata, sunkuyo da kansa yayi ya raɗa mata Magana a kunne, sai ta jijjiga Kai alamar ta gamsu da abunda ya faɗa mata sannan tace to "nagane Abbi". Duk abin nan da suke da Ammi da leeya na kallonsu, leeya kam ta ƙasa hakura saida tazo inda Abbi ke tsaye da Aleena tace "Abbie wai asusu akeyiwa Aleena ita kadai ba daniba" ta faɗi maganar kamar zatayi kuka. har Abbie ya buɗe baki Zaiyi Magana Aleena ta karɓe da faɗin "Ehhh asusu yake min ya ranki daɗi ko bakin ciki, nace daɗi ko bakin ciki? To koma dai menene Abbie asusu yakemin kuma kayan aure za'a siyamin tunda ke kinƙi yin aure Ni bazan zauna ina haɗa kafaɗa dake ba, Muna gwada tsawo a gidan nan da ni dake ba ehee" Aleena ta faɗa tana rike kunkuru tana juya idanu kamar itace yayar ba ƙanwa ba. Leeya da taji dalilin da yasa akeyin asusun ta juya tabar wajen, ba tare da tace uffan ba. 𝙇𝙀𝙀𝙔𝘼𝙉𝘼 itace yaya wurin 𝘼𝙇𝙀𝙀𝙉𝘼 ƴaƴan Abbie 𝙃𝘼𝙈𝙍𝘼𝙕 da Ammi 𝙁𝘼𝙃𝙀𝙀𝙈𝘼. basu kadai bane ƴaƴan su ba amma su kaɗai ne araye, idan da za'a lissafa, leeyana ita ƴa ta huɗu wajen su kawai dai yaran basa tsayi ne da zarar an haifesu wasusunsu ko sati basa yi suke mutuwa. A haihuwar su ta biyu ɗane namiji yaron saida yakai wata biyar sannan ya rasu. haihuwar su ta uku ma ɗane namiji saidai ya fara girma domin yana taka ƙafarsa ko ina shima yazo ya rasu ba ciwon wuni babu na kwana. Shiyasa koda aka haifi leeyana basu wani ɗaura mata soyayya ba saboda suna tunanin itama zata mutu ne kamar sauran ƴaƴansu. Saida sukaga kwanaki na tafiya, satuttuka nata tafiya, watanni sunata gudu, shekaru kuma suna shudewa hardai takai anyimata ƙanwa wacce aka sakawa Aleena murna da godiya ga Allah kam bazan iya faɗi ba kawai Ku misalta da kanku. Kodayake basa saka rai ga ƴaƴan nasu har dai sukazo suna sakin jiki dasu a yanzu. Hamraz na matuƙa ƙaunar yaransa yayinda ammi FAHEEMA ke kokari wajen ganin ta tarbiyantar da yaranta. Leeya dabance da Aleena komai na rayuwarsu ya bambanta, kamar tsarin zubin halittarsu da kuma halayensu. IAleena ta kasance rigimammiya ta ƙin ƙarawa, Yayin da leeya ta kasance mai sanyi a halayenta, Aleena batada hakuri ko kadan bata yafiya, yayinda leeya ta kasance mai hakuri sosai da yafiya, bata shiga harakar mutane balle ta tsokano rigimar su saidai ita a tsokaneta. ko a hakan kuma Aleena ce take karɓewa ta tare mata faɗar, Leeya ta kasance tanasamun tsokana a wajen mutane da kuma hantara da ƙyara saboda wani banzan dalili na mutanen. A kaf faɗin unguwar tasu ta ECOCO, LAGOS NIGERIA ba wani mahaluki daya taɓa ganin fuskar leeya hatta ita kanta leeyana bata taɓa ganin fuskar ta ba ko a mafarki. Idan ka cire Aleena, Abbie, da kuma Ammi. Tun tana ƴar ƙaramarta ammi ta saba mata saka mayafi ta ɓoye fuskar ta ga kowa shiyasa koda da fara girma sai bata sha wahala ba wajen ɓoye fuskarta ta domin ta riga ta saba. Sau dayawa in suka fita aka aikesu ko kuma zasuje makaranta, idan har basu sami abin hawa tun a layinsu ba, yanada wahala suje inda zasuje leeya bata haɗu da masu barazanar cire mayafin da take rufe fuskar ta dashiba, tun sa'adda taga mahaifiyarta bataso ana ganin fuskar ta, itama take ƙoƙari wajen ganin ta hana aga fuskar Tata. Wannan kenan..................✍️ Bayan wuya.... *By* 💫RUMANAH M. DIGGI💫 EPISODE 002. ********** Sun jima zaune madaidicin filin gidan nasu kafin Ammi ta kammala Abinci. Bayan mintuna kaɗan aka sauke girkin aka zubawa kowa nashi, saida kuka kammala cin abincin ne Ammi ke tambayar leeya, "leeya kina ganin okene kuwa, nadaina ganin shi kwana biyu" okene wani makwabcinsu ne kuma igbo ne saidai shi ba musulmi bane saɓanin su leeya dasuke cikakkun musulmai. Mahaifinsa shahararren mai kuɗi ne na bugowa ga jarida. Ko kaɗan mahaifan okene basason alaƙarsa da mutanen gidansu leeya, suna gani kamar zasu canza masa ra'ayi, Yace zai fita daga addinin sa ya koma nasu. shiyasa gaba ɗaya suka hana masa fita koda yaushe yana nan gida baya fita ko'ina. Jinin okene ya haɗu dana leeya sosai hasali ma duk zuwan da yakeyi gidan nasu saboda itane, idan zasuje islamiyya tare suke zuwa ko taxi zasu shiga dashi ake shiga. Haka idan suka iso islamiyyar yana nan bazai matsa ko ina ba har sai an tadasu daga makarantar. Okene yakan zamo mai basu kariya ne musamman ma leeya wacce ko yaushe fuskarta ke lullluɓe cikin mayafi, hatta shi okene bai taɓa ganin fuskar ta ba. iya karsa ganin fitinannun idanunta masu razana mai kallonsu, suma idanun nata ba kullum yake ganin su ba sai idan ta saka mayafi wanda zai bayyanar da su. Duk da Yawan mutane suna kiranta da Kowane suna suka samu, saboda Yawan saka mayafin da take, hakan baya damunta sosai dan tasan ba illa bane, domin kuwa da illa ne da amminta bazata riƙa sakamata mayafin ba. bawai okene bayason ganin fuskar ta bane shima, idan za'a tambayi wanda keson ganin fuskar ta wata ƙila shine na farko dazai ɗaga murya domin a fara yayemasa fuskar tata ya gani. "Leeya bakyajin ina tambayar ki, ko kina ganin sa gidan nan ne ya daina zuwa?" Sai yanzu leeya ta ɗago kanta da ke rufe da mayafi sannan tace "Ammi wallahi nadaina ganinsa nima, jiya fa har bakin gidansu naje nasamu wurinda baza'ayi saurin ganina ba na fake domin naga ko zai fito amma ban ganshiba". "To idan kin gama ki duba shi ko lafiya yake kinga ba'a zama haka saboda nasan dakece okene bai gankiba kwana biyu da yanzu ba haka ba" Ammi ta faɗa tana dan murmushi. Da "tohhh" leeya ta amsamata tana miƙewa tare da nufar inda randar Ruwa take. "Ammi wai nace ina Aleena ne?" Cewar leeya bayan tasha ruwa. "Aleena tana bacci tun ɗazu kinsan ai aikin tane bacci kam" Ƴar dariya leeya tayi kafin tace "Ammi ki matsa dai budurwar taki taji kina faɗin batada aiki sai bacci kigani duk shirin nan da kukeyi da ita zai wargaje saboda kinsan bataso ana kiranta sarkin bacci" ammi tace:" "Aikuwa wallahi zamu ɓata da ita nasani, kuma nasan haka kuke so kiji daɗi keda abbinki idan kinga nayi faɗa da budurwa kho, abunda kikeso kenan tho bazamuyi faɗan ba" "Ehh wallahi ammi gayamata ba mu ba faɗa Nida ammi takalmin kaza mutu karaba baza'a ganmu a rana ba ko aure nayi ammi dake zamuje ga ɗakina ga ɗakin ki" can a bakin ƙofar tilon ɗakin nasu suka tsinkayo Muryar Aleena na faɗin haka. Dariya suka kwashe da ita jin abunda budurwa ta faɗa domin basuyi tunanin tana jinsu ba. Cike da son tsokana leeya tace, "Ni idan inaso kuyi faɗa nasan abunda zanyi, injiku tsakar gida Nidai ina ɗaki kinji ko ƴar yarinya" "kam matsifa ammi kinjita ko!? yau ni budurwa Yahyah leeya ke kira yarinya fa ammi, dubeni sama da ƙasa nayi mata kamada yarinya?" Aleena ta faɗa tana karasowa gaban amminsu cike da shagwaɓa Abin ya bawa ammi dariya sosai matuƙa amma sai ta kanne gudun ɓacin ran budurwa tace "inahhh ko kusa. ai ba wanda zai ganki yace miki yarinya, kuma duk wanda yakiraki yarinya shine yaro bai saniba". "Babban yaro ma kuwa" ieeya ta kuma faɗa tare da juyawa ta fita gidan aguje. Tana fita tabi wata babbar hanyar da zata sadata da gidansu okene. tana tafe tana saƙawa da kuncewa domin tasan halin iyayen sa sarai, basa ragamata ganin tanaso ta sauya musu tilon ɗansu wajen binta da addinin ta. Tana tsaka da guntun tunanin da take taji an cafko wuyata ta baya, da sauri ta waiwayo domin ganin wanda ya kawo mata hari. Waiwa yowar da zatayine wani daga cikin yaran su biyu ya fizgi mayafin da ke lullluɓe da fuskarta! Da mugun sauri ta rike masa hannu tare da gantsara masa cizo a ɗan yatsarsa, Yaron ya fasa uban ihu yayinda ɗayan ya juya aguje da nufin yaje gidansu abokin nasa ya sanar. Tana ganin ya saketa ta juya da gudu ta nufi gida tana rushewa da wani irin kuka na bakin ciki da takaici. A ranta take aiyana cewa idan ta koma gida yau saita tambayi Ammi dalilin da yasa take ɓoyewa mutane fuskarta alhali ba ita kaɗai bace a gidan ga Aleena nan tana sakewa kamar kowa saboda ba'a sakamata mayafin a fuska. Tana fita lafiya ƙalau ta kuma dawo ƙalau. saɓanin ita da take fita tana haɗuwa da irin waɗan nan abubuwan ta zama kamar ɓera a tsakanin yunwatattun mage, ba yaune lokaci na farko da aka taɓa yimata hakaba. Idan ma da sabo ta saba kawai dai jurewane bazata iya yiba. Domin kuwa sauda yawa sai ankai Ruwa rana kafin ta iya ƙwatar kanta a hannun mutanen da ke barazanar ganin fuskar ta, a hakan Ba yara kaɗai suke yi mata haka ba, hatta manyan ma da kansu suna yimata haka, wani zubin kawai dai Allah ne yake ƙwatarta hannunsu ba tare da sun idda nufinsu ba. da gudu ta shigo gidan batare da ta kalli kowa ba ta zarce ɗakinsu ɗaya tal tare da banko ƙofar ɗakin ta rufe tana rizgar kuka. A tsakar gidan kuma Ammi ce da budurwa ke zaune suna ɗan taɓa fira kamar yanda suka saba. Murmushi kawae Ammi tayi, ganin yanda leeya ta shigo gidan tana ji a ranta kamar ba ta yimata adalci ba, amma ya zatayi? Duk da itama kanta ba dadin hakan take jiba, batajin daɗin ganin ta a yanda take, domin nema mata kariya ne daga macuta yasa take sakata ta ɓoye fuskar ta ga kowa. Miƙewa tayi ta nufi kofar shiga ɗakin saboda tasan dalilin Wannan kukan. Kuma tasan yanda leeya takeyi idan an taɓota, shiyasa bata wani damuba. shiga ɗakin tayi tare da nufar bakin gadon da leeya ke duƙunƙune tana ta sharɓar kuka, "leeyana!!" ta kira sunanta cikin murya mai nuna alamar ba wasa. "na'am" "tashi ki zauna" miƙewa tayi tare da gyara zaman mayafin da ta rufe fuskarta sannan tace "Ammi na zauna" "Yawwa, Leeya ina so ki fahimci wani abu, nasan kina nan da tambaya a cikin ranki kuma kina tsoron furtamin tambayar. Dan numfashi tajaa taga nan ta ɗora da faɗin "Nikaina banaso kina yawan tambayata akan duk abinda kikaga nasakaki domin duk abunda zanyi inada dalili, leeyana a gani na kinyi ƙanƙanta da sanin komai daya shafi rayuwarmu, amma kisani mu mutanene kamar kowa kuma. Wallahi inada dalilin da yasa nake hanaki yin wasu abubuwa, kinga kamar yanda nasani kema kanki bakisan dalilina na sakaki ɓoye fuskarkiba, kuma bakisan dalilin dayasa na hanaki kallon madubiba. A yanda nasani kema kanki bakisan yanda fuskarki takeba balle wani na waje, to idan har zaki iya ɓoyewa kanki fuskarki mezai hanaki ɓoyewa sauran mutane, har ga Allah banayi haka bane dan na tauyemiki rayuwa ko kuma na hanaki sakewa kamar ƴar uwarki, kisani keda Aleena ba ɗayabane ko kusa baza'a haɗakuba, Allah ne kawai yayi zaku fito ciki ɗaya da ita amma kunada bambanci ba ɗan ƙarami ba. Leeyana kidaina saka ranki zaki cigaba da zama kamar sauran mutane ko yanda suke rayuwar su, kema kanki ban yarjemiki ganin fuskar ki ba harsai ranar auren ki, ko kuma idan kika tabbatar da ba makawa sai anyi aurenki kin tabbatar da ba wata matsala a ranar ne zaki san babban dalilina nayin haka. leeyana ko mijinda zaki aura banyarda da ki bayyana nasa kanki ba har sai lokacin ya cika!! Indai a sonane bana buƙatar yaga fuskar ki harsai an shafe fatihar daurin aurenki dashi, ko kuma a na gaf da yin haka. Hannu ta saka ta tallafo habarta tare da faɗin "dan Allah ƴata kiyimin alkawarin komai tsanani komai wuya, komai zafi da rintsi, komai wahalar da zaki shiga bazaki taɓa bayyanar da fuska ki ga kowaba hatta ke kuwa! ba tare da an ɗauramiki aure ba. "In sha Allah ammi na ɗaukar miki wannan alƙawari kisaka hakan a ranki. Leeya ta dauki alkawarin ne badan ta gane me hakan yake nufi ba. Sae ta kalli ammin Tata da mamaki tace "amma Ammi ku kuna ina ne harda kike tunanin zan shiga wahala, da rintsi, da tsanani" Murmushin Ammi tayi kaana tace"idan Bama kusa dake leeya, ko kuma ke bakya kusa da mu, kinsan ba wanda yasan ranar zuwan ƙaddara, haka kuma ba wanda yasan abunda zai faru gaba. Yau kawai mukasani leeya bamusan me gobe zata haifar ba. Sai da Ammi ta ɗan nisa, sannan ta kai dubanta ga leeya a karo na ba adadi tace, "Toooh ki daina hawayen mana tunda komai ya wuce yanzu duk da bana ganin fuskar ki nasan har yanzu hawaye kikeyi kiyi hakuri wata rana zaki gane dalilina nayin haka kinji" Jijjiga mata kai kawai leeya ta iya yi har zuwa wannan lokacin hawaye basu daina fita a idanun ta ba. Sai yanzu suke jiyo muryar budurwa datake faman balbala bala'i a awaje. da sauri suka fito dakin, inda sukaci karo da abunda ya basu mamaki. momyn Kingsley suka gani a tsaye tana faman ɗura ashar da ƙazamar hausarta da sai ka kula kake gane abunda take faɗa. ita kuma Aleena gata ƴar mitsitsiya a gaban ta amma tana maida mata da martanin zagi kamar yanda take musu, dama hausawa sukace "kowa a gidansu sarki ne" "Na rantse da Allah ƴar ku bata ciji bazan ba, jinin ɗana bazai fita a banza ba kuma ta zauna lafiya, mayya, kawai muguwa, ai dan Wannan muguntarne kika rufe fuskarki tauraruwa mai wutsiya. Me kingsley yayi miji da zaki cije shi harda fitar masa da jini" momyn ya faɗa tana nuna ɗan ta dake tsaye kusa da ita sai faman matso hannun tashi yake saboda jina ya kara yawa. "Wallahi sai munje police station Dan bazan ɗauki dangana ba, haka yanda kika yi ƙoƙarin tsinka masa yarda" maman Kingsley keta ɓaɓatu a tsakar gida ammi kam sai hakuri take bata amma inda take shiga ba ta nan take fita ba. "Ammi kiyi wa Allah kidaina bata hakuri, inace police station kikace zakije kho, hmmm wallahi kin rago tunda a duniya take, bansan ke cikakkiyar mara mara mutunci bace sai kin wuce police station, ki kaimu inda yafi police station kinji, ko kuma idan kin kaimu kice a yanka mu a gasamu da rayuwar mu, kuma da kikace me ɗanki yayi aka cijeshi ai gashi nan a gabanki ki tambayeshi tunda ba wanda ya rufe masa baki munafukai kawai" Aleena ta faɗa cike da matsifa da rashin tsoro. Abbie daga shago yaji hayaniyar tayi yawa ya shigo gidan, tambayar abinda ke faruwa Abbi yayi, amma ta kalleshi cikin sanyi tace, "ɗazune leeya ta fita shine Kingsley da madu suka tareta zasu cire mata mayafin da da rufe fuskar ta" Abbie yadan zaro ido kaɗan sannan ya kalli Kingsley yace "haka akayi?" Ɗaga masa kai yayi kawai domin har yanzu hannun na masa zugi gashi jinin ba tsaya sosai ba, kuma har yanzu kuka yakeyi irindai yarannan da suka ƙware a makirci. Abbie yajawo hannun yaron yacewa mum dinsa tazo suje Chemist a sakamasa magani. dakyar da suɗin gishi ta fita gidan tana balbala ruwan bala'i. budurwa kuwa harda binta da kasa tana watsa mata dan neman rigima. zama sukayi gaba dayansu anata juya maganar, budurwa ce tace ''Wallahi ammi a kyale yayata ta daina saka mayafin nan, Ni abani in saka sai naga ɗan iskanda zaizo yace saiyaga fuskata, da ya tarowa kansa aradu da ka" Ta faɗi maganar cike da matsifa a fuskar ta. murmushi kawai ammi tayi domin itama abun yafara isarta duk da itama ba wannan ne farko ba kuma bashi bane na biyu, kai idan da sabo itama ammi ya kyautu ace ta saba. " Ammi waima na tambayeki dan Allah meyasa tana saka mayafin nan a fuskar ta? wallahi Ammi nima inaso yayata ta dinga buɗe fuskar ta, yanzu fa Ni ko a waje na ganta ba mayafi bazan ganeta ba. saboda nima bansan fuskar taba, koda nasani na manta. "uhmmm zaki sani kinji budurwa amma akwai lokaci har yanzu" cewar Ammi. Dan jimmm budurwa tayi kamar wacce keson tunano wani abu kafin tace: "toh ammi Allah ya kawo muna lokacin lafiya" ta faɗi magana cike da natsuwa bayan ta gama masifa. " Tooooo sabon salo Aleena ce ke magana haka, ammi Allah ya kaiki ga budurwa kuwa wallahi" leeya ta faɗi maganar tana dariya. Taɓe baki Aleena tayi zatayi kuka sai.......✍️ EPISODE 003. ************* Aleena kamar zatayi kuka tace "Ammi kinjita kho dama can ni ba budurwa bace Ammi?" "Ke budurwa mana ki shareta kawai tanajin haushine saboda ita ba budurwa bace" MAFARIN ƘADDARA....... janyota Ammi tayi jikinta sannan tayimata rada a kunne, gwalo tafara yiwa leeya, yayinda leeya ta cika tabbb kamar zata fashe ta ƙulu sosai ta tashi da niyar barin wajen, ammi ta riƙo hannunta tare da maida ita ta zauna, sannan itama ta janyota jikinta tana faɗin "me yayi zafi ƴan matan Ammi, kiyi hakuri da kanwarki kinji ki dinga binta a hankali wata rana sai labari Allah yayi muku albarka" "Ameen" suka faɗa gaba ɗaya yayinda budurwa ke murza wani zobe dake maƙale a ƙaramar yasar ammi. "Ammi kullum idan muka tambaya ina kakan nin mu muna sai live mana sunana, kuma idan na tambayeki ina yayarki kamar nida yayah leeya sai kice mana bakida yayah saidai ƙanwa, idan na ce to ina ƙanwar taki take sai ki nunamin zoben nan, ammi yaudai ki faɗamin labarin zoben nan dan Allah" 𝔸𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕜𝕠𝕞𝕒𝕚 𝕪𝕒 𝕗𝕒𝕣𝕦, 𝕒𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕞𝕒𝕚 𝕒𝕗𝕜𝕦𝕨𝕒 t𝕒 𝕒𝕗𝕜𝕦, 𝕕𝕒𝕘𝕒 𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕞𝕒𝕜𝕦𝕝𝕝𝕒𝕟 𝕜𝕠𝕗𝕠𝕗𝕚𝕟 𝕜𝕒𝕕𝕕𝕒𝕣𝕤𝕦 𝕤𝕦𝕜𝕒 𝕗𝕒𝕣𝕒 𝕓𝕒𝕪𝕪𝕒𝕟𝕒, 𝕒𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕜𝕒𝕕𝕕𝕒𝕣 𝕥𝕒 𝕤𝕠𝕞𝕒, 𝕒𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕜𝕠𝕗𝕠𝕗𝕚𝕟 𝕜𝕒𝕕𝕕𝕒𝕣𝕒𝕣 𝕤𝕦 𝕤𝕦𝕜𝕒 𝕗𝕒𝕣𝕒 𝕓𝕦𝕕𝕖𝕨𝕒, 𝕕𝕒 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒 𝕥𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕜𝕒𝕚 𝕙𝕒𝕟𝕟𝕦n𝕥𝕒 𝕘𝕒 𝕫𝕠𝕓𝕖𝕟 𝕓𝕒, 𝕕𝕒 𝕒𝕔𝕖 𝕝𝕖𝕖𝕪𝕒𝕟𝕒 𝕥𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕥𝕤𝕠𝕜𝕒𝕟𝕚 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒 𝕓𝕒, 𝕕𝕒 A𝕝𝕝𝕒𝕙 𝕪𝕒𝕟𝕒 𝕓𝕒i𝕨𝕒 𝕓𝕒𝕨𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒𝕪𝕚 𝕗𝕦𝕤𝕙𝕚 𝕓𝕒 𝕤𝕒𝕓𝕠𝕕𝕒 𝕒𝕞𝕞𝕚 𝕥𝕒 𝕣𝕒𝕣𝕣𝕒𝕤𝕙𝕚 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒, 𝕕𝕒 𝕒𝕞𝕞𝕚 𝕥𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕣𝕦𝕟𝕘𝕦𝕞𝕖 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒 𝕓𝕒 𝕓𝕒𝕝𝕝𝕖 𝕥𝕒𝕜𝕒𝕚 𝕙𝕒𝕟𝕟𝕦 𝕥𝕒 𝕥𝕒𝕓𝕒 𝕫𝕠𝕓𝕖𝕟. 𝕀𝕟𝕗𝕒𝕔𝕥 𝕕𝕒 𝕒𝕞𝕞𝕚 𝕥𝕒𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒𝕪𝕚 𝕞𝕒𝕘𝕒𝕟𝕒𝕣 𝕠𝕜𝕖𝕟𝕖 𝕓𝕒 𝕓𝕒𝕝𝕝𝕖 𝕙𝕒𝕣 𝕒𝕜𝕒𝕚 𝕘𝕒 𝕨𝕒𝕟𝕟𝕒𝕟. Ammi takai idanun ta kan zoben nan take idan nun ta suka sauya kalla, jaaa ya maye gurbin fari. Sai ga hawaye sun fara rige-rigen fita a idanun ta, janyesu tayi daga jikinta kafin suyi wata magana ta zabura da ƙarfi ta shiga ɗaki tare da rufo ƙofar ɗakin ta fara kuka mai sauti. A duk lokacin da akayimata maganar zoben, ko aka ambata mata wani bayani akan zoben, to takan iya shiga damuwa da sai ankai Ruwa rana kafin ta iya dawo wa kamar yanda take. Yauma kamar yanda ta sabane saboda ta shige daki tanata rizgar kuka "Allah sarki ƴar uwata wallahi bazan taɓa mantawa dakeba dan Allah ku yafemin rayuwata batada Amfani idan har ban sadu dakuba ya Allah ka haɗa fuska ta da ta iyayena koda a mafarki ne" Ammi ke maganar cikin matsanancin kuka mai taɓa zuciyar. Jiki a sanyaya leeya ta miƙe ta nufi hanyar waje domin sanarwa da abbinsu abunda ke faruwa, hannunta Aleena ta rike cikin kuka take faɗin "yayata kada kiyi fushi dani dan Allah wallahi mantawa nayi, kuma wallahi nayi tunanin ta daina yin kuka idan aka taɓa zoben wallahi dabazan taɓa ba, muje ki rakani na bata hakuri dan Allah" sake fashe Aleena tayi da kuka yayinda leeya itama ta fara kukan nata, taso tayi dauriya amma ta kasa, a ƙidime Abbi ya shigo gidan inda ya fara tambayar su, dalilin kukan nasu, leeya ce ta iya buɗe baki ta gayamasa abunda ya faru da sauri jiki na rawa ya isa bakin ƙofar ɗakin, ganin ta ƙofar garƙame yasa ya tattaro dukkan ƙarfinsa ya banke ƙofar take ƙofar ta faɗo ƙasa duk suka ruga cikin ɗakin, turus sukayi a tsaye sakamakon ganin ammi cikin wani hali, kamar dai ciwon tane ya tashi. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un faheema!! faheema!!! faheema!!!" Da ƙarfi yake kiran sunanta, kafin yayiwa leeyana magana da ta fita wajen gidan ta sama musu abin hawa suje da ita asibiti kafin ya fito da. Leeya da jikinta keta kyarma sai ta kasa motsawa daga inda take, banda rawa ba abunda jikinta keyi. Sai faman kuka mara sauti take Da mugun ƙarfi Abbi Daka mata tsawa. Yayi abunda bai taɓa yi ba a rayuwarsa yiwa yaransa tsawa. Ba leeyana kaɗai ba hatta aleena da ba gefensa takeba saida ta firgita da tsawarda Abbie yayi. Ae kuwa ta ƙara rikicewa da kuka yayin da leeya ta ruga aguje tanata kuka itama. cikin Sa'a kuwa tana fita sai ta haɗu da mai taxi alayin nasu ya ajiye passenger, Da gudu ta isa gareshi fuskar ta lulluɓe da mayafi kamar yanda ta saba ta haɗe hannuta wuri ɗaya, ta kasa magana banda kuka ba abunda takeyi sai nuna gidan nasu da hannunta. Driver na ganin haka ya fahimci akwai matsala nan take ya kama hannun ta suka nufi bakin gidan nasu, suna isa kuwa saiga Abbie ya fito tare da ammie kamar wacce ta dade da ciwo ko taka ƙafarta bata iyayi, da sassarfa take tafiyar gwanin ban tausayi, isowa sukayi gaban mai taxi din kafin ya taimaka musu aka sakata a motar, wani asibitin gwamnatin suka nufa dake nan ECOCO. Dayake bawani nisa ne dashi ba, nan take aka iso, suka fitowa da ita aka shiga da ita cikin asibiti, kamar dai yanda kukasan wasu malamam asibiti da halayensu ƙalilan ne suke da tausayi ba'a karɓesu da wuriba, saidaiaka jira wani babban likita yazo kafin aka karɓesu, wani daki aka sakata a ciki wanda ko gado babu. A ƙasa aka kwantarda ita aka dauramata drip kafin likitan yayi kiran abbi a office ɗinsa. "Hamraz awais ko kaine?" Likitan ya faɗa yana cigabada da buɗe wani files dake gabansa. "Ehhh nine doctor" "A gaskiya hamraz matarka tana cikin damuwar wani abu data kasa cirewa a ranta, tun a farko da kuka fara kawota a asibitin nan na gayamuku ku dinga taka tsantsan wajen kiyaye abunda zai sakata tunani, wannan ciwon nata yanason kulawa, kuma nasan kunayi duk da yanzun nan ma bansan abunda ya faruba amma nasan antuna mata da wani abune dayake damunta" ɗan jimmm Abbie yayi kafin ya ɗago kai idanunsa duk sun chanja kala sunyi jajir kamar wanda yaci kuka Sannan yace: "hakane doctor ba shakka antuna mata da wani abu ne dayake damunta, kuma bazai rasa nasaba da wannan zoben na ƴar uwartaba, wanda shine dalilin yin doguwar jinya da muka taɓayi a can baya a asibitin nan. Ni bana nan ina shago naji kukan yara koda nashigo gida suka nunamin tana nan a ɗaki, koda nashiga ma a rufe na tarar da ƙofar, sai da na ɓallata, to ɓalla kofar danayi ne yasa naganta cikin wannan hali. Yanzu dan Allah doctor menene abunyi. ɗan guntun tunani doctor tauƙir yayi kafin yace:" inada wata shawara wadda idan akayi amfani da ita ko matsalar bata kau gaba ɗaya ba tho zatayi dama, bisa ga abarta a haka wata rana wannan ciwon zai iya zama ajalinta, saboda masu irin ciwon nan nata basa shiri da damuwa ko tunanin. Shiyasa kaga ciwon yaki cie, yaki cinyewa saboda taƙi ta fitarda damuwa a ranta. Kuma taƙi ta daina tunani, nasan wannan abun dake damunta ba ɗan karamin abu bane. Amma in sha Allah idan kabi wannan shawara dazan baka za'a samu mafita" Sake gyara zama yayi kafin yace bawata shawara bace nakeso na bada ba, face a arabata da zoben nan! haƙiƙa idan tana tare da wannan zoben damuwa bazata taɓa barin zuciyarta ba, amma idan aka rabata da zoben in Allah yaso abun Zaiyi sauƙi ba kamar yanda takeji ba a yanzu duk da bansan alaƙarta da zoben ba amma rabata dashi shine mafi a'alah tunda shine sillar janyo komai. Cikin alamun tsoro Abbie yake kallon doctor tauƙir fawizz kafin yace:" haba dae doctor, da dai an chanja wannan shawarar gaskiya. Wannan shawara batayi ba, kana gani fa doctor taɓa zoben Nan idan akayi matsala ce dazata iya jefata wani hali na daban, kaga fa ko yanzu taɓa zoben nan ne kawai akayi bawai an cireshi ba, to inaga idan cireshi ne akayi? gaskiya doctor a chanja Wannan shawarar kawai" Abbie ya faɗa idonsa tarrr akan doctor tauƙir fawizz. Cikin wani irin murmushi irin na yarda dakai dr. Tauƙir fawizz ya sake duban Abbi, "haƙiƙa zakaga rashin dacewar wannan shawara dana baka, amma kasani Ni aikinane kuma nasan baka fini sanin aikina ba tunda bazanyi Abunda zai cutar da wani ɗan adam ba. Wannan rantsuwa ce tsakanina da Ubangiji na, bawai ban taɓa cin karo da irin Wannan matsalar bane, ah ah matar ka ba ita kaɗai bace takeda irin wannan ciwon ba, akwai waɗan da damuwarsu dukice, akwai waɗan da tasu ta ƴaƴa ce, akwai waɗan da tasu ta soyayya ce, akwai waɗan da tasu ta iyaye ce ko wata kadara ko aure duk dai akwai waɗanda damuwar nan ke damunsu. Amma kuma ta hanyar rabasu da abubuwan gaba ɗaya a rayuwar su, kesa asamu sauƙi akan damuwo yinsu kuma su manta da komai. Jikin Abbie ne yayi sanyi kafin ya kalli doctor tauƙir sannan yace ''doctor taya za'a rabata da zoben to? kuma ace bazata sani ba, kar kuma ya sake jefata a damuwa, haƙiƙa bazan taɓa yafewa kaina ba idan na bari wani abu yasami fahima, kuma ban cika ɗan halak ba idan har haka ta faru, na amince doctor amma meza'ayi wanda bazai cutar da ita ba". Numfashi doctor tauƙir fawizz yaja a hankali sannan ya jinkina da kujerar shi ya lumshe idanu ya fara gayamasa yanda komai zai tafi "da Farko inaso ayimata allurar da zata sakata bacci na ƴan sa'anni kafin daga nan acire zoben, sannan sai akuma yimata wata allura da zata gusammata da hankali. Kuma idan allurar tasaketa bazata tuna da zoben nan ba, saboda bazatayi tunanin ko an cireshi a hannunta ba balle takawo baya nan a hannunta. Wannan shine shawara ta, ko daga baya idan ta tuna da zoben bazata kawo a nan aka cireshi ba, a haka zata yita tunanin inda ta ajiye shi hardai ta manta dashi ta daina batunshi tunda batada taƙamammen wurinda ta ajiye shi" "Baki abunda kace doctor, kuma wannan shawarar tayi amma Ni bata karbu gaba daya a raina ba. Sai sai muyi addu'a Allah yayi mana jogora" Achan kuma ɗakin da aka kwantarda da Ammi leeya ce tare da Aleena suna zaune kusa da Ammi, Aleena sai kallon amminsu takeyi tanata kuka kamar wacce aka cemata mutuwa zatayi. leeya kuma nata ƙoƙarin kwantar mata da hankali domin tayi shiru ta daina kuka, ita kanta dauriya kawai take yi amma ita kaɗai tasan abun da takeji. ammi kuma tana kwance idanun ta a lumshe suna zubarda wasu siraran hawaye. Sallamar Abbie sukaji ta ratsa ɗakin kafin ya iso garesu Aleena ta tashi aguje ta nufeshi tana kuka "Abbie dan Allah kace Ammi ta tashi sannan kace ta dakeni idan haka zai sakata ta huce ta dawo yanda take, kuma dan Allah kace tayi hakuri wallahi indai nice Abbi ban komawa, bazan sake taɓa zoben ba dan Allah Abbi ka faɗa mata kaga Ni ko kallona batayi idan ina yimata Magana" Aleena ke maganar tana kuka abun tausayi, rungume ta abbi yayi tsam a jikin sa sannan ya shanye hawayenda ke kokarin zubo masa ya ƙaƙalo murmushi ya shimfiɗa a fuskar sa duk domin ya kwantar wa da yaransa hankali. "Haba budurwa kukan me kikeyi kefa budurwa ce ki daina kuka kar leeyana tayi miki dariya kinji, ammin ki zata tashi kuma in Allah ya yarda bazata dokeki ba, kantane yake ciwo shiyasa kika ganta kwance a nan. kuma yanzu da anyimata allura zamu je gida da ita kinji budurwar amminta" Abbie yayi maganar yana shafa bayan Aleena, shima badomin ransa na yimasa daɗi ba kawai dai dauriya yakeyi domin hankalin yayansa ya kwanta. leeya kuma na zaune kusa da Ammi tana cigaba da hawaye, shigowar doctor tauƙir fawizz ce ta katse komai hankalin su duk yadawo kansa. Isowa yayi a gaban Abbi sannan ya miƙa masa guntuwar takarda mai dauke da sunan allurorin da ake buƙata "Hamraz waɗan nan sune allurorin da muke buƙata kuma gashi babu su a hospital ɗin nan saidai idan ka fita cj Chemist, anan bayan layin kaɗan" Da "tohh" Abbi ya amsa shi kafin ya juya wurin ammi ya kalleta kaɗan sannan ya juya ya fita. Bai ɗauki lokaci ba ya dawo da allurorin, cikin Sa'a kuwa koda ya dawo ya tarar ammi ta buɗe idanunta, amma tanata haki kamar wacce tayi tseren gudu. Da sauri Abbi ya iso wurin ya dafata sannan yace "yajikin naki faheema?" "naji sauki" ta faɗa da kyar tana hade kalmomin kamar mai koyon magana. '"Tau Allah ya ƙara sauqi" "Ameen" tafaɗa tana miƙewa kaɗan zata jikina da ginin ɗakin. cikin hanzari abbi ya isa ya tallafa mata ta jingine bayanta sai sannu yake jeramata. Juya yayi zai fita ɗakin domin ya kaiwa doctor tauƙir fawizz allurorin da ya siyo. sai yaji ammi ta kirashi da sunansa na asuli wanda rabon data kirashi da irin wannan sunan aƙalla yakai shekaru ashirin harda dadi. Juyowa abbi yayi fuskar sa fal da mamaki yayin da su leeya ke chan rakuɓe gefe daya. Sai yanzu hankalin su yaɗan kwanta tunda sukaga ammin su ta buɗe idanun ta, kuma har tayi Magana. Karasowa yayi kusa da ita ya zauna yana fuskantar ta, Domin a yanda yaga takira sunansa yasan ba magana bace ƙarama, kuma yasan tanada muhimmanci sosai tunda yaga haka. "Hamraz dan Allah wata alfarma nake nema a wajenka, nasan abune mai matuƙar wuya. Amma kayi kodan yayan mu hamraz. wallahi har ga Allah banajin zantashi daga jinyar nan, kuma sau da yawa Allah yana nunawa bawa alamomin haka, Nima inajin alamar bazan tashi daga jinyar nan ba" Ammi ta faɗa da kyar tana tari a hankali, sai da tarin ya ɗan saketa sannan taci gaba da faɗi "kayiwa Allah hamraz ka taimaka min kadubi alƙawuranda mukayi a tsakanin mu kaduba girman soyayyar mu hamraz kasada leeyana da Aleena ga mahaifana. Hamraz ka nema min gafara wurin mahaifina!! kuma dan Allah na roƙeƙa kacigaba da kula da leeyana itama, kada kabarta ta bayyana fuskar ta ko ta cire wannan mayafin a har sai lokacin da muka ɗiba ya cika, kasan komai, kasan itama da kanta zata iya cutar da kanta idan ba Wannan mayafin a fuskar ta. kuma dan Allah hamraz alfarma ta ƙarshe danake nema kayi min shine kasada yayan mu da iyayena da kuma yar uwata ina ƙara jaddada maka wannan maganar ne saboda karka manta, hamraz ka nema min gafarar iyayena ta faɗa da mugun karfi har sai da su Leeya suka ƙaraso wurin da sauri. Idanun ta sunyi jaaa sosai kamar gauta ta kalli gefen da yaranta suke ta ɗaga hannu da kyar tana murmushin karfin hali tace "budurwa Allah ya muku albarka ya hada fuskokin mu a aljanar sa maɗaukaki, leeyana ki kula da............." bata ƙarasa faɗar abunda take niyyar faɗaba wani wahalallen tari ya turniƙeta, numfashin ta na fita da wani irin ƙarfi. da sauri abbi yayo kanta yana dafata tare da kiran sunanta, zumbur ya miƙe aguje ya fita waje. fitarsa wajen keda wuya yayi karo da doctor tauƙir fawizz. Riƙoshi doctor yayi da sauri domin yaga kamar ba'a hayyacinsa yakeba ''hamraz ince dai lafiya na ganka haka a ƙiɗime meyafaru?" cikin wani irin yanayi Abbi ke nuna ƙofar ɗakin tare da janyo hannun doctor tauƙir fawizz ya ƙasa furta komai, da azama ya biyemasa suka shiga ɗakin. Hatta doctor tauƙir ya tsorata da yanayin ammi kafin ya isa gare ta ya fara aunata, kiran sauran nurses yayi tare dayiwa Abbi da yaransa iznin da su bashi waje ya dubata. leeya kam tunda taga ammi a wannan yanayi take kuka har yanzu yayinda hawayen aleena suka ƙafe kafff, kuka kawai takeyi ba hawaye abun tausayi. janyesu Abbi yayi daga ɗakin ya fita dasu waje sai addu'a yake a fili da ɓoye yana ƙiyasta irin rayuwar da zai shiga idan ya rasa matarsa. A can bangaren su doctor tauƙir kuwa dubata ya fara yi kafin ya cire zoben da ke hannunta ya miƙawa ya nurse ɗinda ke kusa dashi sosai "kije ki kaiwa mijin wannan matar zoben nan" yayi maganar cikin bada umurni. Fita nurse ɗin tayi da zoben a hannunta, tana fita kuwa duk suka rugo kanta banda Aleena da zazzaɓi ya rufeta sosai saboda kukan da tasha. Nurse ɗin na isa batace musu komai ba duk da ganin su da tayi cikin damuwa. miƙawa abbi zoben tayi ba tare da tace masa komai ba, Abbi kam a yanzu ba zoben bane damuwarsa, damuwarsa itace matarsa bai ko kula matar ba yaci gaba da kai kawo da yakeyi a harabar Wurin. Leeya da ta lura saita miƙa hannu ta karbi zoben ta sanya shi a cikin silin gashinta ta haɗe da wani ta daure shi tamau yanda bazai fita ba................. 004 Karɓar zoben da tayi yayi daidai da fitowar doctor tauƙir fawizz daga dakin yana gyara zaman glasses ɗinsa, Ni leeyana: gabana ne ya fara duka uku-uku. Yayin da naga doctor tauƙir ya nufi abbi fuskar sa ba walwala. Ƙara matsowa nayi domin sanin halin da ammin tamu take ciki, isowarta wurin yayi daidai da lokacin da doctor ya dafa kafadar Abbi tare da zaunar dashi kan wata kujera dake wurin, nikuma na ƙaraso dafff da wajen kamar wacce aka cillo. Isowata wurin yayi daidai da maganar doctor tauƙir fawizz dayake cewa: " Hamraz sai dai hakuri kasan ita duniya ba komai bace, tamkar kasuwa ce wacce zamuci mu koma, nasan kaima da kanka kasan hakan saidai ma kagayawa wani, duniya aro akabamu batamu bace, komai yana tafiya da lokaci, kuma ba wanda zai wuce lo..." Doctor tauƙir Bai kai ga ƙarasa maganar ba abbi ya tari numfashinsa a ƙiɗime yace "doctor meyafaru da faheema dan Allah kada kacemin fahima ta mutu meya faru dan Allah?" Abbi ya faɗa hawaye na gudu a fuskarsa, kamar ƙaramin yaro. cikin alamu tausayawa dr. Tauƙir fawizz ya ce da abbi hamraz:" "Hamraz sai hakuri faheema is no more!, haƙiƙa Allah ya ƙarɓi faheema wata ƙila ma tun baku fita a ɗakin ba, a lokacin da muka shigo muma". Jina, motsi na, ganina, nutsuwata, hankalina ɗiffff komai ya ɗauke daga gareni, sharafff najini a ƙasa daga nan ban sake sanin abunda ke faruwa ba. Shuɗaɗɗun sa'anni da faruwar haka,,,,,,,, "Ta farka naga kamar ɗan yatsan ta na motsi" Muryar wata mata danake kyautata zaton makwabciyar mu ce naji Muryar ta a kunnuwana kamar daga sama. A hankali na fara bude idanuna dake lulluɓe cikin mayafi, ji nayi an kamani tare da taimakamin na jingina da ginin da har yanzu ban tantance inda nakeba. Sunana naji ankira, A hankali Na ɗago kaina danake ji kamar zai tsage saboda tsanin ciwo na kalli matar da take miƙo min ruwa. karɓar ruwan nayi na kai saitin bakina na ɗan ɗaga mayafin kaɗan na saka ruwan a baki nasha. Sai kuma a lokacin na samu damar da zan iya juya idanuna ko zan gane inda nake, gidan mu ne aka dawo dani!! sainake ɗaukar komai kamar a mafarki kafin na fara kalle-kallen ƴan tsirarun mutanen da ke tsakar gidan namu kowa na faɗar albarkacin bakinsa, ina baza idanuna ko zanga ammi da abbinmu da ƙanwata. Saidai wani abu danaji ya ƙara girgizani matuƙa ta yanda a wannan lokaci banmasan irin yanayin da nashiga ba, wasu matan unguwar mu ne su huɗu da suka juyamin baya ma'ana suna zauna a ɗan nesa dani sun juyamin, a hankali nakejin maganar tasu na duka a kunnuwana tamkar sauƙar aradu. Daga Nan banƙara sanin inda kaina yake ba sai da dare ya ɗan fara yi, kamar dai ɗazu motsin da naji ne ya tayardani, saidai a yanzu ba a gidan namu nake ba, idan na fahimta daidai gidan wata ƙawar amminmuce, mama hujra ƙara dubawa nayi dakyau domin gasgatawa ko gidan ne da gaske. Da gaske kuwa gidan ne domin Ni a nawa mamaki banyi tunanin ƙara shigowa gidan ba, saboda kwata-kwata mijin mama hujra baya ƙaunata saboda kawai mayafin da nake yafawa a fuskata. A yanda yake faɗa muddin inaso in shigo gidan saina cire mayafina nikuma bazan iya ba shiyasa nadaina shigowa gidan gaba ɗaya. Sai gashi yanzu na ganni a gidan, gabana ne ya yanke ya faɗi sakamakon tunawa danayi da maganar da matan nan sukeyi ɗazu. Nan da nan naji gaba ɗaya tsoro ya rufeni don ina shirin tambayar mama hujra, kuma ina tsoron amsarda zata fito daga bakinta. maganar da tayine ta dawo dani daga duniyar dana lula. Sannu kawai mama hujra ke jeramin kafin tace"sannu leeyana, ki tashi ga ruwa can na sakamiki a kewaye kiyi wanka kizo kici abinci kinji". kai kawai na gyaɗamata sannan na buɗi baki da kyar nace mata "ina Ammi na da Abbi da Aleena?" Miƙar dani tayi tsaye , Ni kuma sai Binta nake da idanu ina saurarar abunda zatace,, "duba can, ga aleena can kwance bata jin daɗin jikin ta" mama hijira ta faɗa tana nun wani ɓangare na gidan da hannunta. Dubana nakai inda take nunamin aleena nagani kwance shimfiɗe tanata rawar ɗari, abunda yaban mamaki shine ba wani ɗari da har zatayi rawar sanyi, dayake rabon da ayi muna ruwa yau kwana biyu kenan sai dai yayyafi can ba'a rasaba. Da gudu na kwashi jiki domin na isa ga ƙanwata naji abunda ke damunta, domin ganin ta a halin nan shafff ya mantarmin da damuwa ta, duk da ban gasgata maganar da nakeji tana min yawo a kwakwalwa ba. "Kiyi a hankali mana leeya jikinki ba kwari fa kinga ma ko yanzu idan ban riƙeki ba faɗuwa zakiyi" kallonta kawai nayi domin da gaske bana jin kwarin jikin nawa, a daddafe nashiga kewayen na watsa ruwa na ɗaura mayafina domin na saba da yin haka ko a gidan mu. fitowa nayi koda na iso kofar ban ɗakin mama hujra na tsaye tana jiran fitowa ta, ina fitowa kuwa ta kamani har muka isa kan tabarmar da ta shimfiɗa mana. Kallona na sake kai ga Aleena wacce ke duƙunƙune har yanzu kamar yanda na barta ɗazu. "mama dan Allah ina so in tambaye ki nasan bazaki rasa sanin abunda zan tambaye ki ba dan Allah ki taimaka ki gayamin gaskiya" Dafa ƙafaɗata mama hujra tayi kafin tace "zan baki ko wace amsar tambayar da zakiyimin idan har na santa in sha Allah karki damu kinji, amma kafin nan sai kinci abinci kin koshi sannan ki kwanta kihuta, idan kin tashi sai muyi magana, yanzu ina jiran Adamu, (wato mijin ta) yadawo inada wasu kuɗi dana bashi ya ajiyemin idan yanada su ya bani sai nakai budurwa Chemist ayi mata allura" Mama hujra tayi magana tare da janyo kwanon abincin gabana sosai. "Lah-lah-lah hujra mezan gani haka wannan yarinyar ce a gidan nan yau? Waike hujratu meyasa kikeda kunnen ƙashi ne, wannan yarinyar kika janyo a cikin gidana, To wallahi bazata saɓuba. wannan aljanar yarinyar bazata zaunamin a gida ba zaɓi uku gareku daga su harke da kika kawosu a gidana, kodai ta cire wannan mugun mayafin nata mai kamada fatalwa sannan tagayamin dalilin sakashi da takeyi, ko kuma ta tashi ta fucemin a gidana, ko kuma ku tashi gaba ɗayanku ku ficemin daga gida" cewar Adamu mijin mama hujra dayake shigowa gidan yanzu. Ɗa gowa mama tayi a raunane kafin ta fara magana cikin kuka tace "haba Adamu kaji tsoron Allah, wallahi a ko ina maraye abun tausayawa ne. ka duba kagani fa duka yau ko kwana ɗaya ba ayi ba da rasuwar iyayenta ba gaba ɗayan su, ka tausayawa waɗannan yara ciwon hawan jini ya kashe mahaifiyarta lokaci ɗaya yayin da mahaifinta kuma zuciyarsa ta buga dalilin mutuwar matarsa, nan ya faɗi ya mutu shima. Akwai waɗanda za'a tausayawa ne daya wuce waɗannan yara du-du-du shekarunsu nawa saboda Allah baibamu haihuwa ba bawai yana nufin bamusan zafin yara bane. Dan Allah Adamu kayi hakuri muzauna da yaran nan mu ingantamusu rayuwa tunda kaga basuda kowa, ka duba ƴar ƙaramar can zazzaɓine ya rufeta tun kafin abun ya faru gashi har yanzu tana fama dashi. Yaran nan marayune Adamu, kada ka manta manzo (s.a.w) yana cewa "kafaɗa daya zamu jera da wanda ya rika maraye riko na hakika zuwa gidan aljanna, Adamu bazakaso kazama cikin Mutanen da Annabi zai yi alfahari dasu a ranar tashin alkiyama ba" Cikin hanzari Adamu ya ƙatseta da faɗin yimin shiru wallahi kafin ranki yayi mummunan ɓaci, ai bansan haka kika iya yin wa'azi ba da na dinga rakaki mumbari, kuma injiraki har ki gama. Ai wadannan yara ba abun tausayawa bane waya sani ma ko muguwar yarinyar nan ce ta kashesu da siddabaru irin nasu na mayu, nidai wallahi na rantse da Allah bazata zaunamin a gida ba kinji na gaya miki, idan kuma kina musu kibari naje na dawo na sameta a gidan nan" Adamu ya faɗa yana shura takalma tare da barin gidan. "Mama da gaske ne abunda naji kina faɗi wai Abbin mu ya rasu!!? Da gaske ne mama, dan Allah ki sanardani, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un Ashe abunda naji matan nan suna faɗi gaskiya ne mama kiyiwa Allah ki tadani daga mafarkin da nake, don Allah mama kice komai ƙaryane, mama ki karyatani dan Allah kice ƙaryane Abbi da Ammi basu mutu ba, kai ina. Mama!! iyayenmu suna sonmu ko ke kin san da hakan , kinsan duk inda zasuje damu suke zuwa, su Abbi bazasu barmu su tafiba" zabura tayi daga inda take zaune ta nufi inda Aleena take kamar wata zautacciya. Dariya ta farayi while hawaye na zubowa a idonta kafin ta yaye zaninda Aleena ke lulluɓe dashi tace "ƙanwata kitashi muje gida su Ammi na can suna neman mu, nasan kema baki yarda sun mutu ba ko Aleena ?Ammin mu bata Mutuba sai taga aurenki kho ƙanwata, ki tashi muje, kinsan kinyiwa Ammi alƙawari idan kikayi aure ga ɗakinki ga nata, budurwa ki tashi muje mu ki cika alkawarin ki da kika dauka, Ammi bazata mutuba saitaga aurenki in sha Allah ki tashi kawai muje gida" Aleena da zafin ciwo ke cinta ido kawai ta zubawa yayar tata yayinda itama hawaye ke zuba a idanunta. hujra ce ta iso wajen tare da rungume su baki ɗaya tana rusa kuka. haƙiƙa duk wani mai zuciyar tausayi yaga wadannan bayin Allah a wannan yanayi dole ne yaji tausayin su matuƙa. Sake komawa Aleena tayi kwancen da take saboda ita kaɗai tasan abunda takeji yayinda leeya ta sake miƙarda ita sannan ta duƙa a gabanta,cikin dauriya da karfin hali, ta fita da kyar ta saɓata a bayanta ta saka zani ta ɗaureta tamau. badan tanada tabbacin zata iya goyata ba kawai itama tayi hakan ne saboda tarasa abunda zatayi a yanzu komai ya kunce mata aka, tana shirin juyawa mama hujra ta riƙeta idanunta sharkaf da hawaye tace "ina zakije leeya kigayamin inda zakije nasani, yanzu ba kamar da bane, yanzu bakuda mai kula da ku leeya kunrasa gatan ku babu faheema babu hamraz ba dangin faheema babu na Hamraz balle ku sami sauƙi dan allah kigaymin inda zakije nasani, ko kuma ki ajiyemin budurwa a gidan nan kafin musan tayi tunda kinga Adamu ke ƙaɗae yace bada itaba" Cikin ƙarfin hali leeya ta fizge daga riƙonda mama tayi mata sannan ta fice gidan, tana fita gidan sai tayi hanyarda zata Kaita gidansu, dama can layin nasu ba'a fiye samun mutane ba a irin wannan lokaci da duhu yaɗan fara yi. banke kofar gidan tayi da wani irin karfi da batasan tanada shiba, turus tayi sakamakon ganin okene zaune a tsakar gidan yanata rizgar kuka kamar shi akayiwa mutuwar, yana ganin leeya da gudu ya taso tare da rungume ta suka yita kuka gwanin ban tausayi, saida suka ɗauki lokaci Kafin leeya ta iya tambayar okene. "Okene da gaske Ammi da Abbi sun mutu, da gaske mun rasasu, shin da gaske zuciyar Abbinmu ta buga bayan Ammin mu ta mutu? dan Allah okene ka ƙaryatani kace duk ƙaryane, ko kuma kace nasamu taɓin hankali ne shiyasa nake faɗin haka" Janye jikinta tayi daga na okene kafin ta nufi hanyar tilon ɗakinsu ta shige tana ta kuka tare da kiran Ammi da Abbi, fitowa ta kuma yi ta ajiye aleena sannan ta koma kofarda zata sadata da shagon Abbinsu. Kai komo ta farayi tsakanin ɗakinsu da kuma shagon na Abbinsu, har saida ta gaji sosai okene yayi kokarin hanata amma ta kasa hannuwa har ya kyaleta ya zubawa sarautar Allah ido. Da dai ta fahimci cewa da gaske ne ba abbi ba ammi sai ta sami wuri daya ta zauna tayita kuka kamar ranta zai fita. Batasan lokacin da okene ya zagayo ta gabanta ba ya durkusawa da gwiwoyinsa ƙasa yana ta kuka gami da harɗe hannayensa biyu alamar roƙo yana magana cikin matsanancin kuka kamar mahaifiyarsa ce mai rasuwa. "Leeya dan Allah kiyi hakuri, idan kinyi imani da Ubangiji ke kashewa ya raya kiyi hakuri leeya, sau dayawa idan na biku islamiyya inaji ana yimiku wa'azi dangane da mutuwa da tawakkali. leeya Meyasa zaki karaya kina cikakkiyar musulma, meyasa leeya!? Idan har kin yarda Allahn da ya baki iyayenki shi ya ƙarɓesu dan Allah ki ajiye hankalinki ki daina kuka kiyi musu addu'a susami rahma da dacewa kinji leeya Please. Nima gobe zanje Church kuma saboda nayimusu addu'a kawai zanje kema ki dage kiyi kinji na rokeki" Okene ya ƙarasa maganar yana ƙara fashewa da kuka. Jikin leeya yayi sanyi likis da jin abunda okene ya faɗa shida yake ba musulmi ba yayi imani da hakan, inaga ita musulma. share hawayen ta tayi kafin tace "shikenan oke nagode Dan Allah kaima kayiwa su amminmu addu'a idan kaje wajen da kuke bauta" Tau kawai yace mata kafin ya ɗauki buta ya ɗebo mata ruwa sannan ya kawo mata a gaban ta tare da faɗin: "tashi kije banɗaki ki wanke fuskar, gida zanje amma zandawo, zanje na sama muku abunda zakuci daga nan kuma nasamawa budurwa maganin da zata sha domin ta samu sauƙi" Godiya tayi masa kafin ta ɗauki butar ta nufi ban daƙi, bayan ta wanke fuskar ta sannan ta tafito ta koma ta zauna tayi tagumi tunani kala-kala na zuwar mata a kwakwalwa. Bata daɗe zaune a wurin ba sai ga oke yadawo ɗauke da abinci amma ya ɓoye shi ta yanda ba za'a gane abunda ya ɗauko ba lokacin duhu yayi sosai dan har an qare sallar Isha. Fitilar da yazo da ita ya haska har hasken fitilar ya kai inda leeya ke zaune. "Leeya! Kuka kikeyi haba dai leeya dan Allah ki daina mana idan nima baso kike nayi kukan ba" Shafa fuskar ta tayi cikin mamaki tajita da danshin hawaye, A mamakance ta kalleshi tace: "okene wallahi bansan ina kukan ba, nima bansan da zuwansa ba" Zabura tayi da sauri ta nufi inda aleena take kwance. Har okene ma saida ya razana da yanda ta miƙe. shafff ta manta da ita tunani yayi mata yawa, tana isa wurin ta tada ita zaune ta jingina ta daidai lokacin da okene ya iso wajen tare da ajiye musu abinci. Tare suka dinga bata abincin tanaci a hankali har tayi musu alama ta ƙoshi ba um bale uhm-uhm. Maganin da ya taho dashi ya balla tare da yiwa leeya umurni taje ta kawo mata ruwa "leeya je ki ɗebo ruwa Aleena ta haɗiye magungunan nan ta samu ta kwanta ko zataji ƙarfin jikinta, zuwa safiya" Tashi tayi da sauri tare da nufar inda ake ajiye ruwa a gidan nasu, yayin da okene ke haska mata hasken tauch light ɗinda ke hannunsa. Bayan ta debo ruwan, aka Bama aleena magani ta haɗiye da ƙyar sannan suka kwantar da ita. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda yake komai, ba kuma wanda ya sake kallon wani a cikin su, har suka fahimci bacci mai ƙarfi ya ɗauki aleena. Nan ne okene yayi wa leeya sallama domin shima ya fara jin baccin ''leeya zan tafi gida domin nima bacci nakeji kuma gashi inajin ciwon kai sosai, banso na barki a gidan nan ku kaɗaiba amma kinsan halin iyayena bazasu barni na kwana wani Wurin ba, duk da ko yanzu ma basusan ina gidan ba, ga wannan touch ɗin kiyi amfani da ita sannan kuma dan Allah karkiyi kuka bayan na tafi kinji, ki ƙaddara yanzu kinshigo wata rayuwa ta daban mai matukar wahala amma kisani komai tsanani sauƙi na nan zuwa BAYAN WUYA SAI DADI ki rike wannan a ranki" Daga haka bai jira abunda zata ceba yafita gidan zuciyarsa nayi masa ɗaci. Bayansa tabi da kallo tana share hawayen da bata san da zuwan suba. "Hakika wannan ƙaddara ce da ba wanda ya isa ya canjamuna ita, haƙiƙa wata mutuwar wa'azi ce, dan a ƙananun shekauna na fahimci haka, haƙiƙa basai kanada ciwo bane za'a kiraka majinyaci, ko rashin mahaifama babbar jinya ce mai wahalar warkewa. Wannan itace ranata ta farko da bazan taɓa mantawa da itaba a rayuwata, yau zan kwana a cikin gidanmu ni kaɗai, dagani sai ƴar ƙaramar ƙanwata babu Ammi babu Abbi. Mutuwa mai raba ƙauna, mutuwa mai tonon asiri, mutuwa mai tarwatsa farin ciki, mutuwa mai razana ƙwaƙwalwa, mutuwa mai yanke zumunta, haƙiƙa mutuwa bakida sabo, ya Allah, Allah ina roƙon ka ya Allah kabani juriyar rashin iyayena" Leeya ke wannan maganar yayinda fuskar ta ta jiƙe sharkaf da hawaye. haka sukayi daren ba wani bacci da ta samu saida sanyin asuba ya sauko Sannan bacci ya kwashe ta, bata farka ba saida rana ta faso sosai. A daren kuma wani mummunan labari ya samu leeya wai jiya da dare ɓarayi sun shiga shagon abbinsu sun kwashe komai ba abunda suka bari, bayan sunyi satarne kuma suka cinnawa shagon wuta ya ƙone kurmus. Hannu ta ɗora aka ta fasa wata gigitacciyar tsawa wacce ke barazanar fasa dodon kunnen wanda yajita. nan ta faɗi sharaff a ƙasa kamar wata gawa, haka mutane suka dinga ketareta suna wucewa ba wanda ya kula da ita, mafi yawan jama'ar wasu tsoron ta ma sukeyi, yayinda wasu suke kiranta mayya ta kashe mahaifiyarta da mahaifinta ga ƙanwarta can a gida zata lashe ta, kuma gashi Yanzu ta kunnawa shagon mahaifinta wuta. haka dai akayita yamuɗiɗi da maganar har ta isa ga kunnen mai gidan, wato wanda ya basu hayarsa, yana isowa wurin kawai ya fara yimusu watsi da kayayyakin su nan tsakar hanya yayita watso duk abunda ya samu a waje kuma har zuwa lokacin leeya na kwance a some bata ma san abunda ke faruwa ba. Da gudu okene ya ƙaraso wajen kamar wani mayunwacin zaki zuciyarsa a bushe kyamas ba alamar fara'a a fuskar sa cikin wani irin ɓacin rai ya nufi wasu mutane da yaji suna faɗin "dama an ƙona ta tana a halin suman nan tun kafin ta farka Dan bata da amfani a cikin mutane" har suna faɗin ayi sauri a ƙonata kafin ta tashi ta lashe musu kurwa. Wasu daga cikin su sunyi na'am da shawarar da aka yanke ta ƙona leeya, wani Christian mai suna taoma ne yayi sauri ya ɗakko fetur tare da ashana a rumfarsa, yana isowa wurin baiyi wata wata ba ya kwalala mata ruwan fetur ɗin tare da kesta ashana. Daidai lokacin ne okene ya iso wurin.....✍️ BAYAN WUYA...... By RUMANA M DIGGI. EP.05 ___________Da wani irin ƙarfin da baisan yanada shiba ya saka ƙafa ya shuri taoma, nan take ashanar tayi wani gefen daban sake komawa kan taoma oke yayi tare da maka masa wani irin naushi a ciki nan take kuwa taoma ya suma, sai mutanen da ke Wurin ne suka rirriƙe okene. Leeya kuwa tun da taoma ya zuba mata ruwan fetur ɗin ta farka daga suman da tayi amma nauyin da takeji na jikinta ya hanata miƙewa, sake jujjuya idanun ta take yi yayinda ta miƙe zaune a hankali tana gyara zaman mayafinta, saidai hankalinta ya ƙara tashi matuƙa yayinda taga abunda mai gidan yayi musu, kifa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi ga wanda yasan menene tausayi. Okene kuwa yana Ganin haka sai ya fizge daga riƙonda akayi masa yazo kanta yanata bata hakuri, amma taƙi kulashi taci gaba da kukanta kamar bazata daina. Taoma da tuni ƴan uwansa sunzo sun ɗaukeshi da sukayi tambaya aka gatamusu abunda yayi niyar yi basu ce komai ba suka ɗaukeshi kawai suka tafi dashi, da haka Mutanen sukayita watsewa kowa ya koma kan lamarinsa sai da wurin ya rage saura su biyar kacal, okene leeya da kuma yaran mai gidan mutum biyu, sai kuma shi kanshi mai gidan da yaketa aikin watso ƴan kayayyakin su. Har yanzu kuma okene bai fasa rarrashin taba kuma yana ci gaba da bata hakuri, fitowa mutumin yayi daga cikin gidan tare da nufar inda take yana isowa ya busa hayaƙin sigarin da ke bakinsa a fuskar ta sannan yace: "ke aljana tun tuni kisan inda dare yayi miki, saboda nidai gaskiya bazan iya barinku a gidan nan ba, tun jiya ma naso nazo nagaya muku amma wata sabgar ta ɗaukemin hankali har gashi kin janyomin hasara to wallahi kinci arzikin matsiyatane ku bakuda ko sisi, da badan haka ba wallahi sai an biyani ko jikar ifirito ce ke ba abunda zaki iya yimin, kuma yanzu-yanzun nan minti ɗaya na baki kishiga ciki ki fito da kanwar nan taki ko itama na watsota waje, kitashi nace" Ya faɗi maganar a tsawace, yayinda okene ya cika dam kamar ya fashe, hannu yasaka ya rarumo wani dutse da niyar ya faskara masa aka. Shi kuwa mutumin ya juya yana tafiya bai ma san abun da ke faruwa ba. Leeya data fahimci abunda yake shirin yi cikin matukar tashin hankali ta riƙe masa hannun daya riƙe dustsin dashi tace "dan Allah oke kayi hakuri ka barshi ae mu mukayi masa laifi, mune muka janyo masa asara fa kaga ko bazamu hanashi yin Magana ba shida abunshi dan Allah ka kyaleshi" A zafafe okene ya kalleta sannan yace "An ƙi a kyaleshi ɗin saboda yaganku ƙananu shine zai wulakanta taku haka, leeya duba kayayyakin ku watse a titi kamar wasu dabbobi, sannan Kuma asara dayake faɗi ae ba shikaɗai yayi ba domin kuma......" tasssss yaji saukar mari ba zato, babu shiri a tare suka ɗago kai domin ganin wanene da wannan aiki, da sauri leeya taja baya saboda ganin momyn sa ce, "Okene bakajin magana bazaka fita harkar wannan mayyar yariyar ba ko" momynsa ta faɗa baki na kumfa taci gaba da faɗin "Har iyayenta ta cinye balle kai da ba kowa bane a wajensa, wata ƙilama ta shanye kurwarka shiyasa kake yi muna jayayya kuma ka kasa fita rayuwar ta, sha-sha-sha kawai" "Ah ah mommy leeya ba mayya bace kuma ba ita ta kashe iyayenta ba Allah ne ya kashesu kuma wallahi kuna dauƙarwa kanku nauyin wannan baiwar Allah..." Tasss tasssss kakeji ta sake ɗaukeshi da wasu maruka biyu nan take bakinsa ya fashe jini ya fara zuba a hankali. Leeya na ganin haka ta dafe kunnuwanta tare da fasa wani kuka mai cike da danasanin abunda ta janyowa okene domin dabadan ita ba tasan ba za'a fitar masa da jiniba. Mommyn shi bata ko kalli inda take ba ta fizgi hannunsa tare da nufar gidan dashi suka bar leeya tsaye a wurin ita kaɗai. shi kuma zuciya tama hanashi ko ya ƙara kallon leeya domin ya tabbatar idan ya ɗaga idanu ya kalleta bazai iya barinta ota kaɗai a wurin ba, sai dai momynsa ta yankashi, shiyasa kawai ya barta a wurin bai kuma kallontaba. Ji tayi an rungume ta tabayan ta, a ɗan razane ta waiwayo dan ganin ko waye jikin ta duk a mace, Suman tsaye tayi saboda ganin abunda batayi zatoba. Nan da nan itama ta rungume ta cikin tsantsar farin ciki kamar ba ita bace take kuka: "budurwa yajinki!? Ni banmasan fitowar ki a gida ba kinji sauƙi kho? Alhmdullillah Allah na gode maka Allah ya ƙara baki lafiya ƙanwata" Ta faɗi maganar hawaye na zubowa a idonanunta ga kuma murmushi kan fuskar ta. ''yayata kukan me kake yi kuma, meyasa zaki yi kuka?? saboda an fito muna da kayayyakin mu a hanya kikasan ko gyara gidan za'a za'ayi? yarhyarh kinsan me wallahi ko an gyara gidan nan abbi da ammi bazasu zauna ba suje can inda suka tafiyar su suka barmu, tunda sunzaɓi su tafiya wani wurin ba tare da sun gayamana ba kuma basuje da muba, kuma sunƙi su dawo har yanzu" Aleena ta fadi maganar idanuwanta na cikowa da kwalla. Share mata hawayen leeyana tayi tun kafin su zubo sannan tace: "na ɗauki alkawarin bazan taɓa barin hawayenki yayi zuba ba indai ina nan da rai da Lafiya, haƙiƙa ammi da abbi sun tafi, tafiya kuma wacce ba dawo, tafiyar da sukayi suma ba sanar musu akayi ba balle mu su sanardamu kiyi hakuri ƙanwata ammi da abbinmu addua kawai suke buƙata kinji ta faɗi" maganar a raunane. Cikin jin haushin abun maganar leeya, aleena tace:" to meyasa da aka sanar dasu zasu tafi suƙaƙi zuwa damu?" "Lokacin mu ne baiyiba, idan lokacin mu yayi muma zamu tafi, yanzu dai abar wannan maganar kinji ta wuce ki dinga yiwa abbi da ammi addu'a kinji budurwa" "Yahyah-leeya to wazai min aure?" "Ni zanyi miki aure Aleena kar ki damu, kuma duk abunda kikeso a sakamiki a ɗakinki Ni zan miki shi in Allahn duka ya yarda. Kizo mu kwashe Kayan nan namu daga kan hanya" Tare suka tattara kayayyakin nasu suka kaisu ɗan nesa kaɗan daga kofar gidan, wajen wasu bishiyu da sukayi wa arean tasu ƙanwanya suka kai kayan suka ajiye, amma har yanzu da saura dan iya abunda suke iya ɗauka suka ɗauka, ''Wai Allah bayana wallahi yarhyarh nagaji dayawa, kuma gashi bamu ida kwashe Kayan nan ba kuma naji kaina yafara min ciwo ga kuma yunwa danakeji." "Subhanallah kanki yana ciwo kuma, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un yazanyi kinga bara naje nayi bara kozan sami kuɗin da zan siyamiki abinci da magani" leeya ta faɗa tana miƙewa cikin tashin hankali. Aleena data fahimci hankalin yayarta ya tashi sai ta rasa abunda zatayi nan da nan ta ƙaƙaro dariya mai karfi cikin dauriya duk dan taga hankalin yayarta ya kwanta " to sarkin tsoro wasa fa nake garau nake ƴar yunwa kawai nakeji ko itama ba sosai ba, saboda haka ki zauna muyi fira kawai" ta karasa maganar tana janyo hannun ta alamar ta zauna ɗin. Sauke ajiyar zuciya tayi Sannan ta zauna ba dan tayi na'am da abunda tace ba "Amma kuma duk da haka bazan zauna ba kibari na tafi na sama mana abunda zamuci ke kuma sai ki jirani anan kafin na dawo kinji" "Yarhyarh a ina zaki sama mana abunda zamuci to??" "Barah zanyi budurwa" leeya ta bata amsa a takaice. "Allah yaya bazakiyi bara ba, a ina ma zakije bara bayan kinsan a ecocon nan yanda mutane ke harinki, kuma kindaisan yanzu ba ko ina ake zuwa ba ansha faɗa mana a makaranta ƴan satar mutane da ƴan bindiga sunyi yawa yanzu, nidai indai dan nice wallahi kiyi zamanki bazaki baraba akainaba, bakisan wani zai iya ruɗarki ba ya cuceki da sunan bara zai baki nidai bazaki bara ba idan kuma kikace sai kinje wallahi nima saina tafiya na barki kamar yanda ammi da abbi sukayi" Rufemata baki leeya tayi tare da faɗin "shikenan ƙanwata wallahi bazanje bara ba shikenan adaina Wannan maganar kinji bazaki tafiba bazakije ko ina kibarni ba" "Tau idan bakyaso nayi tafiya ta wallahi karki ƙara maganar zuwa yin bara" "Bazan ƙaraba kanwata" "Hmmm ka jita wai "bazan ƙaraba kanwata" wacece ƙanwar taki, yanzu tunda ammi batanan shine zaki kirani da ƙanwarki Allah idan ta dawo saina gayamata" Aleena ta faɗi maganar tana taɓe baki zatayi kuka. Da sauri leeya ta durƙusa ƙasa tare da faɗin "natuba budurwa bazan ƙaraba" Dariya suka fashe da ita su duka biyu yayinda sukaji muryar ta uku atare dasu, da sauri suka juya baya Domin ganin waye mai dariyar. "broth O" da sauri aleena ta isa ta rungume shi cikin murna da ɗoki. "budurwar amminta kin warke kenan, haka da kikayi ai sai ki karyani" ya faɗi maganar cikin jin daɗin ganin leeya ta fara sakewa hartana dariya. "Na warke kam amma gaskiya ciwon kai nadamuna sosai da sauri" ta rufe bakinta da hannayenta tare da juyawa ta kalli leeya "wasa nake masa kaina baya ciwo" "kinga zo ga abinci nan kuci, harda magani ma nazowa budurwa dashi. idan kunci sai Kisha maganin kinji, leeya kizo ki zauna mana, ko laifi nayi miki ne da kika koma gefe kina kallona haka, karfa ki cinyeni da wannan kallon kinga ɗan kyakkyawa ko? kinaso ki ragemin kyau tun ɗazu sai kallona kike" Ta ɗan ji kunyar maganar da yayi mata saidai ba tana kallonsa bane da wata manufa, ita kallon da take masa na mamakin dawowarsa ne garesu bayan sanin yanda sukayi da momynsa, mamakin ta ya kasa ɓoyuwa har zuwa wannan lokacin da tazo kusa dasu. ƴar ƙaramar tabarma ta janyo ta shimfiɗa sannan ta kalleshi tace "bismillah zo ka zauna kho" Da murmushi a fuskar sa ya ƙaraso inda shimfiɗar take hannunsa saƙale dana aleena ɗayan hannunsa kuma na riƙe da abincin, suka zauna tare sannan leeya tazo ta zauna har yanzu dai da mamaki a fuskar ta. Ta kasa hakuri saida ta furta tambayarta "okene me kuma ya dawo dakai nan baka tsoron momyn ka ta kuma zuwan nan tayi maka abunda tayi maka ɗazun, kaga har bakinka ma yaɗan kumbura dan Allah ka tashi kaje wallahi bana son kana shiga matsala ta dalilina" Matsowa yayi kusa da ita kafin ya janyo hannun ta itama sannan yace "niba komai yadawo dani wurin kuba Magana ce dani kizauna idan kin gama cin abincin saina gayamiki abunda ke tafe dani" Abincin ya janyo kusa dasu sosai sanna ya ɗauko ruwan pure water dayazo dasu ya miƙawa ko wannen su ɗaɗɗaya, sannan yace "oya kuci sosai sai kun ƙoshi kunji ƙannena" Idanun leeya ne suka kaɗa sukayi jawur yayinda, Aleena ta fara auna abincin hankalinta kwance. Okene ya lura da yanayin leeya daya changer duk yanda yaso ya shareta amma yaji ya kasa, tashi yayi daga inda yake ya nufi wurin da take: ''leeya! Make faruwa? Ba kinyimin alƙawarin ba zaki ƙara zubda hawayenki ga su ammi ba, leeya kin taɓa gayamin fa ba ayiwa wanda ya mutu kuka, hawayen azabtar dasu ya keyi, kinaso ta Dalilin ki Ammi da Abbi su azabtu?" Dasauri da girgiza masa kai "wallahi banaso kuma basu nakeyiwa hawaye ba okene ka taimaka mana ka zamomuna bangon da muke jingina muji sanyi, ka nuna muna so yayinda kowa yake gudun mu, okene bamuda abunda zamu biyaka dashi ina roƙon Allah ya rabautaka da samun tsira da rahmarsa" ta ƙare maganar hawayen da ta riƙe suna zubomata. Murmushi yayi tare da kai hannunsa yana shafa kanta "badai kuka kike ba koh? Wannan bakomai bane kinji ƙanwata nidai abunda nakeso dake yanzu kici abinci kawai ki nutsu magana zamuyi kuma saikin bani hankalinki sosai maganace mai mahimmanci" Hannunta ya riƙo tare da wanke mata shi sannan ya saka hannun ta a abinci yace " kiyi sauri kici yanzu zanje nadawo kinji" da "tho" ta amsa masa kafin itama ta fara cin abincin. miƙewa yayi tare da barin wurin. Suna nan zaune bayan sun gama cin abincin aleena ta bingire sai bacci, yayinda leeya itama taɗan kishin giɗa. Okene yaɗauki lokaci kafin ya dawo ya tarar dasu duk suna bacci kuma da alama sunajin daɗin baccin da suke, saboda haka ya juya da nufin barin wajen domin bayaso ya tadasu kuma a ransa abune biyu ke yawo, yana ganin idan ya tafi yanzu abune mawuyaci ya ƙara saduwa dasu kuma gashi yanada magana dasu mai muhimmanci, kuma a ransa yana ƙudurce bazai iya barin su a wannan halinba sabida baisan hannunda zasu faɗaba, juyawa yayi kawai da nufin ya tafiya saboda yasan sun jima rabonda su sami bacci irin wannan shikuma tausayawar dayake musu bazata bari ya iya tadasu daga baccin ba. Har ya juya zai tafi yaji an riƙo hannun sa, cike da farin ciki ya waiwayo dan ganin waye a cikinsu: "Budurwa dama ba bacci kike yiba?" Murmushi tayi tare da faɗin:"ehh ba bacci nakeba broth O tun sa'adda kazo Nan ina ganin ka" "Aikuwa kin taimakeni da kika tashi" "Taimako kuma?" Aleena ta tambaya cike da zallar mamaki. "Ehh.. Amma dai har yanzu da saura tunda leeya bata tashi ba kuma ni gashi banaso a tada ita, gashi inada magana mai muhimmanci da ita" Okene ya faɗi maganar yana sanya yatsunsa cikin gashin kansa. Ƙafa aleena ta saka a fakaice ta ɗan tsakari leeya nan da nan itakuma leeya ta ɗan juya alamar taji tsakaran da akayimata, Toshe bakin aleena okene yayi gudun karta ƙara wani motsi da zai tada leeya, da gayya ta gantsa ramasa cizo a ɗan yatsa. Babu shiri ya saki ihu tare da janye hannunsa daga bakin aleena, ita kuma ta kyalkyale da dariyarta, yayin da leeya ta zabura daga baccinta a ruɗe ta fara kallonsu su duka biyun fuskar ta da alamar tambaya. Hannunsa biyu ya saka tare da dafe bakinsa " budurwa ke kika tada ita amma mena cemiki ne Allah yarinyar nan bakyajin magana" Cak! Ta tsaya da dariyar da take jin ankirata da wani sunan daban wai yarinya, me yake nufi kenan Ni aleena nice yarinya. Ɗago da kanta tayi ta galla mai harara kafin tace "maimaita abunda kace broth O nice yarinya?" Cike da jan faɗa ya buɗi baki da nufin bata amsa leeya ta kalleshi tare da girgiza masa kai alamar kar ya ƙarasa, nan take ya sauya maganar zuwa wani ɓangare domin ya fahimci nufin ta. "Okene ina kaje haka kajima baka dawo ba muna ta jiranka har mukayi bacci " Naje makoko ne domin tattauna wani batu kuma mungama maganar Yanzu da ku kawai ya rage nayi maganar" "Makoko!?" Leeya ta tambaye shi aɗan tsorace. "Ehhmana makoko na fito yanzun nan, akwai matsala ne, naje ne nayi magana da wani kawuna dake can kuma na sameshi munyi maganar idan kin shirya, attention kawai nakeso magana zanyi dake koma nace daku gaba ɗaya" miƙewa leeya tayi sosai kafin ta janyo ruwan da yabata, ta wanke fuskar ta sosai Sannan ta dawo ta zauna kusa dashi. Aleena ma tazo ta zauna yanda taga leeya tayi. "Leeyana!!" "Na'am" Okene ya kira sunan ta a raunane:"babban dalilin da yasa nakeson magana dake leeya idan baki manta ba a kwanakin dasuka gabata nataɓa gayamiki zamubar garin Lagos ɗin nan kho?" "Ehh" Leeya ta amsa masa muryarta na cracking. "Tho wannan tafiyar ce ta tashi, kuma zamubar garin Lagos mu koma can inda nagayamiki amma.." "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un okene yanzu shikenan rabuwa zamuyi, shikenan tafiya zakayi ka barmu?" kukan da take riƙewa ne ya suɓutomata itama aleena tana ganin haka ta fashe da kukan. Cikin matsanan ciyar damuwa okene ya rungumesu gabaɗaya a jikinsa yayita rarrashin su, cikin rarrashin kuwa har ya sanarmusu ya samamusu inda zasuyi rayuwar kamar sauran yara a can makoko gidan kawunsa kuma "kuyi haƙuri, sannan kuma ku kwantar da hankalinku domin tafiyar da nayi a makoko yanzu saboda nagana da kawuna ne kan batun zamanku a gidan, sun yi na'am da haka kuma sun yarda zasu riƙeku tsakaninsu da Allah, kuma sunce bazasu hanaku kuyi addinin ku ba kunji kho" ya faɗa yana shafa kan Aleena da ta lafe a jikinsa sai ajiyar zuciya take na kukan da tasha. "Okene haƙiƙa bamuda kamar ka, bamusan abunda zamu saka maka ba. Allah ne kaɗai zai yi muna sakayya ta alƙairi tsakanin mu dakai okene Allah ya biyaka, Allah ya kawomaka tsaftatacciyar shiriya dan alfarmar nabiyullah" leeya ta ƙarasa maganar tana zubda hawaye. Gashinta daya sakko a saman mayafin fuskar ta yasaka yatsansa ya gyara mata, wanda sauda yawa shine mutane suke gani su ƙara tsorata da ita saboda idan ta saki gashin nata gabaɗaya zai iya rufe ko'ina a fuskarta har ma ya sakko kamar yafashi tayi. "Saboda Ammi bata nan shine kika daina gyara gashin nan ko?" Okene ya faɗa yana ɗan murmushi domin kwantar mata da hankali. "Nidai bazan iya gyara shi ba kasani ae, Ni ban ma taɓa gyarawa ba saidai ammi ta gyaramin" "Tau meyasa bakya gyarawa?" Okene ya tambaya yana kallon ta "saboda ban iya ba" leeya ta bashi amsa. "Tau idan baki iya ba aini na iya, sai ki kawo na gyara miki kho, sai anyi magana ki wani kin girme mutum" Aleena ta faɗa tana janye mata sauran gashin da ya fito waje. "Lahhhh leeya aina manta ga budurwa nan ta dinga gyara miki mana" Okene ya faɗa yana kallon aleena dake faman mayarda gashin da ya fito inda yake. "Yanzu dai ki tashi ki haɗa kayanda kukeso anan, waɗanda bazakuyi amfani dasuba kuma ki fitardasu gefe a je a siyarwa da ƴan gwangwan, sannan ku tashi muje makoko saboda yanzu haka muma ana can ana shirye shiryen tafiyar tamu" Miƙewa tayi da azama ta fara aikin cire kayan, suma suka tayata aikin su uku, ba jimawa suka ƙare fitarda kayan. Okene da kansa yakira masu saye aka siyarda su Sannan aka basu kuɗin, suka tattara sauran kayayyakin nasu suka shiga napep sai makoko. Basu ɗauki dogon lokaci ba suka iso arear yayinda mai napep yayi parking bakin teku. bayan yayi parking suka fito tare da fitarda kayansu, suka kira mai jirgin kwale-kwale sakamakon unguwar ta makoko tana saman teku ne, gidajen su kuma na saman tekun, kuma sun kasance na katako ne gaba ɗayan unguwar. Bayan mai jirgin ruwan ya iso aka loda kayan nasu sannan suma suka shiga, ba jimawa suka ƙaraso gidan, koda isowarsu kuwa suka tararda kawun na okene tare da matarsa suna jiran ƙarasowar su. Haƙiƙa an karrama su saboda basuyi tunanin samun tarba kamar haka ba, duk da kasancewar suma mutanen ba musulmai bane igbo ne kamar dai okene. Sanin halayen okene da karamcin sa yasa suka daina mamakin ganin haka daga kawun Okene da Matarsa. Abinci irin na igbo mai rai da numfashi aka kawo musu. Bayan sunci abinci sunsha sun ƙoshi sannan aka fara firarraki da labarai. ba sosai mutanen kejin hausa ba, sunayin tane gwanin ban dariya, ganin haka ya nishaɗantar dasu baki ɗaya. Abunda yabawa leeya mamaki shine ganin babu wata ƙyama ko tsorata da sukayi da ita kamar yanda sauran mutane suke yimata, hakan ya bata damar ƙara sakin jikinta da wadannan mutane. "Uchi!" Okene ya kira sunan kawunsa da nutsatstsiyar murya "Ga amana nan na baku nasan zaku iya saboda Nima kaina na zauna daku kuma nasan yanda halayen ku suke, bansanku da ƙyara ko nuna rashin soba, bankuma sanku da wulakanta dan adam ba. Ga leeya da kuma ƙanwarta aleena idan kunzauna dasu lafiya zakuji daɗin zama dasu koba komai, zasu ciremuku kewar rashin yara da bakuda su, Please Nnene ya faɗa yana mayarda dubansa ga matar kawunsa "kece uwa, kece kikasan tarbiyya dakuma sanin zafin yara, bawai dan baki taɓa haihuwa bane zaizamo baki san wannan ba ah ah a ko'ina mace uwace, uchi kaima haka dan Allah kuriƙe amana. Da kuma abunda nakeso na roƙeku dan Allah kar ku damu da wannan mayafin da waccan take sakawa wallahi tun tanada shekaru biyu haka take kuma tun kafin mahaifiyarta ta mutu tayi mata alkawarin bazata cire shi ba har sai lokacin da ta ɗiba ya cika. Uchi, Nnene ina yimuku magana ne matsayina na ɗanku ba kowa ba, ku taimaka ku riƙe amana koda munbar Lagos bayana nufin munbar ku bane ni nayi alƙawarin zan dinga zuwa ina Ganin ku, akai-akai" Da murmushi a fuskar Nnene ta shafa sumar kan okene tare da faɗin "zaka samemu da rike amana Okene" Bata sauke hannunta akansa ba shima uchi ya ɗaura tasa hannun yace " zaka samemu da rike amana eselu. shikuma ya sunkui da kansa ƙasa kamar dai yanda Yake a al'adar tasu ta Igbo. Duk wannan maganar da suke ba abunda su leeya sukaji, sakamakon da yarensu sukayi bada hausa ba. Miƙewa aleena tayi daga inda take tazo ta zauna kusa da okene, tallafe haɓa tayi sannan tace:" broth O hala me kake gayamusu haka?" ta faɗa cikin sigar tambaya. Faɗaɗa fuskar sa yayi da murmushi, tambayar Tata ta bashi dariya baramma yanda tayi da fuska kamar wata babban mutum "gayamusu nake daga yau kun zama ƴaƴansu, kuma zaku dinga tayasu aiki, kuma zaku cigaba da zuwa kuna karatun ku kinji". Daga masa kai tayi sannan tace:" naji gaskiya sun taimaka mana to wanene uchi wanene Nnene?" Dariya suka kwashe gaba ɗayan su jin yanda ta faɗi sunayen n " Wancan shine uchi, cewar okena yana nuna kawunsa, waccan kuma Nnene matar kawuna kenan, Uchi ana nufin kawu ne a yaranmu, Nnene kuma ana nufin gwaggo, Ku ma zaku iya kiransu haka idan zaku iya" Alama uchi yayiwa aleena da tazo wajen sa, da murmushin ta ta nufeshi ya bata wuri ta zauna kusa dashi:"kasan menene sunana? Aleena ta tambayi uchi. "Nasani" ya bata amsa cikin Hausar shi da bai gama iyawa ba. "To menene sunan nawa? "Aleena" Ya bata amsa a takaice sunan nata kuma yayi daidai da bakin shi, da tayi tunanin bazai faɗa yanda akeso ba, sai kuma taga saɓanin haka, shiyasa daya faɗa sai ta haɗe fuska dan bahaka tasoba, taso yana faɗa a kwashe da dariya. "Tho ba aleena bane sunana sunana budurwa" "Budurwa!" yasake tambaya, sai kuma taji ya faɗi daidai har yanzu, nan itama ta sake fuska dan kar a fahimci dariya kawai takeso tayimasa. Haka dai suka kaci gaba da fira kamar waɗan da suka san juna tun fari, anata raha da dariya, saɓanin leeya da taƙi sakin jikinta tayi fira, jefi jefi take sako bakinta ko kuma idan an faɗi wani abu daya bata dariya sai tayi. idan kuma na murmushi ne saitayi murmushi, amma ban da Wannan ba abunda take cewa. Saida rana ta take okene ya tashi da nufin ya koma gida, duk sukayi masa rakiya banda aleena dake zaune wuri ɗaya takasa ko motsin albarka. "Aleena ke bazakimin rakiyar ba?" "Ah ah broth O ka tafi kawai nida ka ganni nan ba inda zan tashi, gidan nan fa tsakiyar babban Teku yake, ina zan tashi daga nan ga nauyin ku, ga kuma nawa ae sai mu nutse gaba dayan mu, ku tafi kawai gobe idan kadawo zanmaka rakiya su sai su zauna kar nauyin yayi yawa tunda kace gobe zaka dawo kho?" Aleena ke wannan maganar tana tankwashe ƙafafuwan ta alamar gyara zama. Murmushi kawai sukayi dan su uchi har sun fara sanin halin ta ita yarinyace mai yawan barkwanci yayinda suka fahimci leeyana daban take da ita.......✍️ BAYAN WUYA. By RUMANA M DIGGI. 007 _____________Bayan fitarta ɗakin sai ta ɗauki buta da nufin ta shiga banɗaki, da yake cikin ɗakin ne kawai da duhu domin kuwa waje akwai hasken farin wata tarrrr. bata wani sha wahalar neman buta ba, saidai bata sami ruwa a cikin butarba, shiga tayi banɗakin domin akwai duro da suke saka ruwa a ciki. Sai da tayi addu'a sannan ta shiga banɗakin, shigarta banɗakin keda wuya taji wani irin sauti daya girgizata matuƙa domin a shekarunta ta isa ta gane sautin kona meye, ("innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un") Ta furta a fili yayinda ta tuna da labarin da uchie yakawo musu jiya da dare. JIYA DA DARE: jiya da dare zaune muke a tsakar gidan mu kamar yanda muka saba dayi duk dare na Allah. Ni, aleena da kuma Nnene. Saiga uchie ya shigo kamar wanda aka harbo daga cikin baka. Zama yayi dirshem agaban mu baicewa kowa komai ba Kowa kuma bai cemasa komai ba. Nnene ce ta ƙatse shirun ta hanyar faɗin "uchie lafiya ka shigo gida a rikice haka" "Inafa lafiya, babu lafiya Nnene kinsan labarinda mukeji na ƴan bindiga a Radio?" "Ehhh" Nnene ta amsa masa da zaƙuwa. "Tho sune sukaje ALARO AREA Jiya, sunyi barna sosai kuma babban abin bakin ciki su Waɗan nan ƴan bindiga basa kashe mata, iya maza suke harbewa sannan su kwashe matan su tafi dasu ba wanda yasan idan suke zuwa dasu" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un na furta a fili domin labarin ya girgiza ni matuƙa, kuma na tsorata dajin labarin domin ina tsoron harbi da bindiga ko ya yake, ko sautin bindigar bana so, nafi tsoron sautin bindiga bisa ga ko wane sauti dana sani. Cikin matukar tsoro na tambayi uchie: "uchie a ALARO AREA sukazo" "Ehhh ALARO AREA dai da kika sani nan sukazo kuma sunyi ɓarna da yawa saidai wanda ya tsira" uchie ya faɗa yana kafe idanunsa waje ɗaya alamar tunani yakeyi. "Yanzu menene jami'an tsaron ALARO AREA sukayi" Nnene ke tambayar uchie. "Ba abunda suka yi domin sun riga sun shirya duk yanda zasuyi kuma tsakar dare sosai ne sukayi aika-aikan nan" Uchie ya kuma faɗi. Mun tsorata sosai dajin wannan labarin domin har Aleena idan aka ganta za'a gane a tsorace take, ba wani abu ya tsoratamu ba kuwa sai don sanin duk abunda yasami ALARO AREA kamar ya sami MAKOKO AREA ne domin kuwa sune makwotanmu, Teku ne kawai tsakanin mu dasu domin idan aka haura za'a iya hango mutanen ALARO AREA ɗin. Wannan shine babban dalilin da yasa muka tsorata baki ɗayan mu, amma uchie yabamu magana sosai yayi ƙoƙarin kwantar mana da hankali har dai muka sake baki ɗaya. shiyasa yau dana shiga damuwa uchie yayi tunanin kamar labarin da yakawo mana jiya ne. ★★★ Tunanin leeya ne ya katse jin ƙarar bindigar data cika makoko, kuma gashi sautin na ƙarasowa kusa sosai, sai ihun mutane kake ji da ƙarar bindiga ta ko'ina. A ƙiɗime leeya ta zunduma cikin duro ɗin da ke gabanta, ta janyo marufinsa ta sama ta kulleshi gammmm, sakamakon jin takun mutanen da kedoso ban ɗakin. Da sauri mutanen suka shigo banɗakin tare da dallara tauch light mai rikitaccen haske, sosai sukayi binciken da zasuyi amma basuga komai ba, sai ɗayan mutumin da ke tsaye kusa da duro ɗin ne yace: "kai nifa banyarda da wannan mazubin ruwa ba zobani tauch light ɗin nan naga menene aciki" Dayan na shirin bashi fitilar ne sai babban cikinsu ya shigo zafafe ya daka musu tsawa "me kukeyi a cikin ban ɗaki kuma, karfa ku lalata mana shiri wallahi kuyi maza ku fito muyi abunda ke gaban mu kar yanzu na kaddamar wa mutum". babban ya faɗi maganar cike da dabanci. Ita kuwa leeya a can cikin duro da take maƙe waje ɗaya, sanyi ya kaimata ko ina sakamakon ruwanda ke tabb da duro ɗin, tunanin ta a yanzu kawai wane hali Aleena, uchie da kuma Nnene suke ciki. Wata zuciyar na bata ta fita taje da dubo, yayinda wani ɓangare na zuciyar ta na bugamata uban kashedi kan karda ta fita, ta zauna a ciki kafin komai ya lafa. Zuciyarta kuma tafi karkata da wannan shawarar da wani ɓangare na zuciyar ta ke bata domin tana gani idan har ita ta sami waje ta ɓuya to tanada yaƙini cewa suma zasu sami waje su laɓe su ɓuya. da wannan zuciyarta ta yarda yayin da taci gaba da zalalo hawaye a hankali domin ita kaɗai tasan abunda takeji, Ta ɗauki lokaci mai tsawo sosai cikin duro ɗin saboda harta jigata kafin taji komai ya ɗauke ɗibbbb. sai ƴan guntayen koke koke da takeji, yanke shawarar jira tayi domin tasan idan har su Nnene basu ganta ba ba abunda zai hanasu suzo su nemeta, idan taji shigowar su kuma sai tayi musu alamar da zasuji tana cikin duro ɗin. Tana nan zaune tana jiransu domin ta galaɓaita sosai, nan take wani tunani ya faɗo mata arai "banji ko motsin su Aleena ba, idan sun ɓoya ae yanzu yakamata su fito su nemeni tunda dai basu ganni ba" nan wata zuciyar tace da ita,,,, "Taya zakice sun ɓuya waɗanda kika bari suna bacci mai nauyi kuma shigar ki nan ba jimawa wannan abun yafaru" tana kawowa dai-dai nan a tunanin nata Ta zabura da ƙarfi tare da izo duro ɗin iya ƙarfinta. Bayan ya faɗi ne ta samu ta fita daga cikinsa, sannan ta fita wajen ban ɗakin a guje. turussss tayi taja ta tsaya Sakamakon arba da tayi da gawar uchie bakin ƙofar ɗakin nasu, shiruuuuu..... Komai ya tsayamata a channn nesa da ita dakejin maganganun mutane na tashi tamkar ma bata cikin duniyar ƴan adam. Zaman ƴan bori tayi gaban gawar ta uchie yayinda ta rasa mezatayi, wani irin sakaran ihu ta kurma, daga chan sai kuma tayi shiru kaɗan domin batamasan abunda ya dace da ita ba, dafa gawarsa tayi muryata na cracking: "uchi dan Allah karka mutu ya kakeso muyi da rayuwar mu idan ka tafi ka barmu, uchie katashi dan Allah ka tashi idan har da gaske ne da kake cewa bazaka taɓa bari aga kukan Aleena........" maganar ta ce ta maƙale sakamakon tunawa da tayi da Nnene da kuma Aleena, Wani irin wawan zabura tayi daga gaban gawar uchie ta nufi ɗakin da suke kwana amma wayamm ba Nnene ba Aleena. da sauri ta fito ɗakin ta fara dube-dube kamar wacce ta samu taɓin hankali haka take bin lungu da saƙo na gidan tana neman su kamar mai neman allura ko wani ƙaramin abu daya ɓata. domin kuwa komai karantar abu sai ta ɗagashi ta leƙa ƙarƙashin sa tare da kiran sunan Nnene da Aleena. Haka leeya taci gaba da kai da komowa tsakanin gawar uchie da kuma lungu da saƙo na gidan, har sanyin asuba ya sakko bata daina wannan gararamba ba. Haka dai taci gaba dayi har rana ta hudo mutane suka fara tururuwa a gidan tare da jami'an tsaro na MAKOKO AREA waɗan da awannan lukacin sukeda alhakin ɗaukar duk wata gawa da aka kashe a kaiwa ƴan uwanta. Bayan sunzo kan gawar uchie ne zasu ɗauka leeya tayi kukan kura ta nufesu a guje, dayake sun saba da samun irin haka yasa basu ɗaukeshi komai ba sunsan duk zafin mutuwar ne ta sanyata haka. Mutum biyu daga cikin mutanen ne akasamu suka riƙeta har aka fita da gawar uchie gidan, sannan suka saketa sukayi tafiyar su, "Haƙiƙa gaskiyar mutane da suke cewa idan tashin hankali yayi maka yawa kuka ma neman sa zakayi ka rasa, Sabida yanda nakeji a yanzu dama zansamu kukan yazo da zaifimin sauƙi, yau ba Abbi, Ammi, da kuma uchie gashi kuma ƴan bindigan nan sun tafiya da Aleena da Nnene, gashi babu okene ya tafiyarsa. Runtse idanuwanta tayi da ƙarfi, domin ji take wani abu yana taso mata tun daga ƙasan zuciyarta tamkar zai fito ta bakinta, da jan ciki ta isa bakin ƙofar ɗakin gidan nasu tare da jingina kan bangon gini, wasu hawaye ne masu zafi suka fara tsartuwa a fuskarta yayinda komai ya shiga dawomata kamar yanzu akayi. Gaba ɗaya leeya ta kasa sanin abunda zatayi taji daɗi, ko ta samu nutsuwar zuciya, domin kuwa ko rufe idanuwanta tayi sai taga kamar ana haskamata hoton fuskokin su uchie da Nnene. Ta ɗauki tsawon kwanaki cikin matsananciyar damuwa, domin kuwa bataci balle tasha ba wanka ba komai, Sallah ce kawai ke tada ita a inda take zama a gidan nasu, komai ruwa da iskan da za'a yi tana nan wurin bazata ɗaga ba. Duk ta rame ta fita hayyacinta domin kuwa idan har bakayiwa leeyana farin sani ba zaka iya rantsuwar cewa ba ita bace wannan leeyanar da kasani. A kwana na tarane da rashin su uchie aka yiwa leeya saƙon mai gidan yana bukatar gidansa domin ya saka wasu masu hayan tun da baza'a bar gidan ba kowa ba. Lokacin da saƙon ya isowa leeya tayi kuka sosai da baƙin cikin barin gidan, bawai barin gidan ke yimata baƙin cikiba, akwai abubuwa da dama acikin gidan da take gani ta dinga tunawa da su uchie da Nnene da kuma ƙanwarta abar begenta dare da rana. Bata kwashi wasu kayayyaki ba, domin kuwa bata san inda zata je daga nan ba, shiyasa bata ɗiba kayan komai ba. Wasu abubuwan da take matukar ƙauna a rayuwar ta ne kawai su ta dauka da suka zamo mata abokan tafiya. Ƴan kudaden da tagani ne wajen binciken nata ta ɗauka tare da barin gidan, tana fita kuwa ta kira mai jirgin ruwa da zai fitarda ita tekun. Daga fitarta cikin tekun ta rasa inda zataje kawai sai ta yanke shawarar zuwa AJAH ROAD tashar motoci, ba kuma dan tayi tafiya zuwa ko ina ba, saboda ko tafiyar zatayi ba inda tasani ko a cikin lagos ballantana wajen Lagos ɗin, ko AJAH ROAD ɗinda taje ta santa ne a hanyar islamiyyar su idan zasuje IFE. Duk nisa da tazarar da ke tsakanin MAKOKO da AJAH ROAD haka tayi tafiyar a ƙafa ko nisan ma bata gani har saida ta ƙaraso a haka. Wuri ta samu a inda ba mutane sosai ta zauna tare da kifa kanta tsakanin cinyoyinta, ta fara tunano komai daya faru a rayuwarta tun daga farko har izuwa yanzu data baro MAKOKO. Daga kanta tayi sama yayin da takai ƙarshe a tunanin da takeyi idonta sharkaf da hawaye, while fuskar ta na lulluɓe. CIGABAN LABARI. Miƙewa tayi daga zaunen da take, ta samu wuri ta ajiye jakarta data fito da ita, sannan ta nufi wani ƙaramin wuri da ake siyarda abinci domin tanada sauran kuɗin da tasamu a gidan su a makoko. Tana isa wurin sauran mutanen da ke zaune suna cin abinci suka ganta, dayawa daga cikinsu sun tsorata da ganin ta, wasu ma har sun fita daga wurin cin abincin. Ganin ta ya tsorata mutane sosai a wajen, domin kuwa kamanninta duk sun chanja, baramma mayafin na fuskar ta, ga gashinta duk ya hargitse gashi da tsawo na wuce misali, gashin ya zubo gaban fuskar ta ya rufe ko ina a fuskarta ta. Sai idan tana tafiya ne take gyara shi domin taga hanyar da zata bi da kyau. Kuma idan ta janye gashin maimakon aga fuskar ta sai mayafi kawai ake gani, da manyan korayen idanunta masu matukar razana mutane, sannan kuma ga wani mayafin da ta rufawa jikinta, wanda ya zamo kamar hijab ne. Sai kuma kayanta da sukayi datti sosai, sabida rabon da tayi wanka tun lokacin da abun ya faru. Ba takalmi a ƙafarta gashi tana tafiya jiri na kwasarta kamar zata faɗi. Haka ta iso wurin da ake siyarda da abinci, aikuwa mutane na ganin ta suka fara guduwa domin kuwa basu zata mutum bace, hatta waɗanda suke aiki a wajen da ake siyarda abincin saida suka bar wajen ƙalilan ne masu ƙarfin halin da suka tsaya suji mai yazo da ita. A lokacin kuma wacce takeda shagon abincin ta harziƙa sosai domin kuwa ta kore mata customer's, gigitacciyar tsawa ta daka mata tana faɗin: "ke wacece ke meya kawoki nan wurin?" Leeya kuwa saboda tsorata da tayi da wannan matar bata iya furta komai ba sai kyarma da jikinta yakeyi saboda tsoro Matar kuwa tana ganin haka ta janyo wani kwano da ruwa cikinsa tare da watsa wa leeya ruwan, ta daka mata tsawa "bar nan kuma idan kika sake dawowa ruwan zafi zan watsa miki" Matar ta faɗa fuskar ta haɗe. Da guda leeya ta bar wajen sai kuka take, inda ta ajiye ta koma, ta rakuɓe waje ɗaya tana ta rawar ɗari. ★★★★★★★★★★★★ NAIJA STATE. SULEJA NIGERIA.. K. WAASIB MANSION. durkushe take gaban wata yarinya da bazata wuce shekaru goma sha daya ba a ƙiyasi. hakuri take bata iya iyawarta amma yarinyar ta kasa ɗaga ko kanta balle ta kalli matar da ke durkushe gabanta. Matar kuma zata iya kai shekaru arba'in zuwa sama. "dan Allah hajiya ƙarama kiyi hakuri wallahi bansan kin parlourn nan bane da ban biyo ta cikinsa ba, tunda nasan dokokin ki, taya zan karya da ganganci, kiyiwa Allah kiyi hakuri" matar ta faɗa tana ƙara sunkui da kanta ƙasa gaban yarinyar. Har wannan lokacin yarinyar bata ɗaga kanta ba balle tayi mata magana, taci gaba da yin game ɗinda take a wata makekiyar tab dake hannunta. Wata murya taji ta daki dodon kunnuwanta, wacce tasan mamallakiyar muryar, mum ɗinta ce: "KHULUD me kikeyi haka, me DAYAMMAH tayi miki ne da zaki sakata durƙusawa a gabanki kamar wata Sa'arki. Khulud ki kiyayeni ranki zaiyi mummunan ɓaci na rantse miki idan baki chanja halayenki ba, menene wannan tho?" Matar ta faɗa a zafafe. Guntun tsaki yarinyar da aka kira da KHULUD tayi sannan ta miƙe a fusace tare dayin cilli da tab ɗinda ke hannuta ta nufi sashenta bata ma kula mum ɗin ta da ke yimata faɗa ba. Zama mum tayi tare da yiwa dayammah izni da ta miƙe daga durƙushen da take: "Dayammah dan Allah meyasa kike biyewa khulud, ita ƙaramar yarinya ce fa sa'ar ƴar da kika haifa da cikin ki, saboda me zata sakaki yin abu kiyi, tunda baya cikin ƙa'idar aikin ki, dan Allah ki daina kinji kiyi hakuri kuma" mum ɗin ta faɗa tare da dafa ƙafaɗar dayammah Alamar ban haƙuri. Murmushi kawai dayammah tayi bata furta komai ba, tashi tayi daga durƙushen da take sannan tace: "ba komai wallahi hajiya, ae hajiya ƙarama batada laifi, duk laifina ne, nina ƙarya dokar da ta kafamin. Amma wallahi bada ganganci nayi ba domin kho bansan da ita a parlourn nan ba shi yasa na biyo ta cikinsa" Ɗan jimmm mum tayi kafin tace: "kuma nagayamiki ki daina kiran KHULUD da wani hajia ƙarama, da badan kar nayi ƙarya ba da zance kinyi jika da wannan yarinyar amma kina kiranta da wani hajia ƙarama ae dolene yarinya ta rainaki" "Uhmmm ah ah babu rainawa hajia, ai ko rainawanne nina rainata tunda kinga itace sama Dani" "A ina khulud zata zama sama dake" Mum ta tambayi dayammah Cikin jin haushin abun da tace. "Hmmmm a ko ina hajiya, domin kuwa na dogara ga Allah, sannan kuma na dogara wajenku, da badan ku ba da bansan yanda rayuwar nan zatayi mana ba" "Toh saboda wannan ne zakice khulud na sama da ke" "Ehh hajiya ko ba don wannan ba, kin manta saida KHULUD ta yarda sannan Alhaji ya ɗaukeni aiki a gidan nan" Dafe goshi mum tayi tare da faɗin:" ohh god dan Allah dayammah ki daina tuna abunda ya faru baya, koda haka ta faru kuma khulud batada wayo koda akayi wannan, babu abunda ta sani a wannan lokaci, kawai ta yarda a ɗaukekine bawai dan tasan amfanin da zakiyi mana ba" "Hajiya kuma a wannan lokacin da khulud bata yarda ba da baza'a ɗaukeni ba, kinga kho dole nane nayi abunda tace na kuma bar abunda tace idan ina son zaman gidan nan" Murmushi kawai mum tayi "Tau Allah ya gyara amma dai gaskiya ki rage wannan da kikeyiwa khulud dan wallahi rainaki zatayi a haka, ko babu komai kin haifi kamar ta koma waɗan da suka fita". "Hmmm hajiya duk abunda nayiwa hajiya karama girmanta ne da Allah ya bata babu kuma abunda zanyi tunda ta shiga gabana, kedai kiyi shirunki kawai komai nada lokaci" Dayammah ta faɗa tana kallon ɓangaren khulud. Taɓe baki mum tayi kafin tace:" ɗazu naji justice na tambayarki ayi list ɗin kayan da babu a gidan nan amma dai bakiyi ba ko?" "Ehh banyiba hajiya, wallahi na ɗan sha'afa ne amma yanzu zanyi in Allah yaso". "Tau babu damuwa kije kiyi dan Allah Saboda tafiya zaiyi gobe zaije visiting Mexico kuma nasan zaiyi one-week shiyasa nakeso kiyi komai yanzu" "Tau in sha Allah yanzu-yanzu kuwa zanje nayi" juyawa tayi ta koma hanyar kitchen taje ta dubo abubuwan da babu a bangaren ta na girki. domin kuwa hakane ɗabi'ar justice KHATTAB WAASIB a duk lokacin da zaiyi tafiya to sai ya samu duk ƴan aikin gidan suyi list ɗin abubuwan da za'a bukata bayan tafiyar sa, ummu-hajara ce House-maid ɗin gidan shiyasa aka umurce ta datayi list ɗin kayan kitchen da babu a kitchen Khulud; banko ƙofar shahararren part ɗin nata tayi kamar zata karya kofar. ɗaki ɗaya ta nufa daga cikin ɗakunan da suke part ɗin, daga isarta ta faɗa kan gado sai wani zafi takeji yana fitowa daga cikin zuciyarta, ta jima tana juye-juye kan gadon kafin ta tashi tsaye. Kai da komowa ta fara a cikin ɗakin tana cije lips ɗinta tare da buga hannun ta ɗaya ƙan ɗaya tana tafawa a hankali tana daga kai tana saukewa kamar wacce ta saka jami'an tsaro a gaba tana yimusu jawabi. "Me mum tayi haka, gaban wata ƙasƙantacciyar talaka, ƴar aiki mum zatayimin faɗa Alhali banida laifin komai, shine zata yimin faɗa a gabanta but it's well dayammah sai kin gane kuskurenki da kika saka ayimin faɗa kuma alhali kece mai laifin ke kika karyamin dokar da na kafawa ma aikitan gidan nan, dama nayi alƙawari duk wacce ta fara karya dokar nan sai nayi mata hukunci gwargwadon laifin da ta aikata, ke kika fara karyawa sannan kuma kika saka aka yimin faɗa, good" KHULUD ke maganar tamkar ba ƴar shekaru goma sha daya ba. Murmushi tayi sakamakon tunawa da tayi da wata shawara da tazo mata a zuciyarta, fita tayi daga part ɗin tare da nufar part ɗin papu wato mahaifin ta, cikin tafiyar ta irin da isa da jin kai tamkar wata ƴar sarki. tafiya take kamar bataso ta taka ƙasa har ta ƙaraso part ɗin papu. Knocking kofa tayi tana faɗin:"excuse me" "Yes" Wata murya ta amsa mata daga cikin wani master bedroom. Da fara'ah a fuskar ta, taƙarasa har ciki tare da nufar papu da ke zaune. "Good morning my kid" "Morning too pa, how's your night going?" "So gud mamanah, ina mum ɗin ki take? Yau kin rigata zuwa tadani kinyimata mata wayo" Papu ya faɗa da murmushi kwance kan fuskarsa. Wani uban tagumi taja tare dayin mirmir da idanu zata yi kuka, Da sauri ya sakko daga kan gadon da yake, ya nufi fabric-bed sofa ɗinda take zaune, hannuta ya riƙe tare da faɗin: "mamana waya taɓamin ke, ki gayamin ko waye nasan dalilin sakaki kuka da yayi" papu ya faɗa yana rungumota jikin sa. Kamar wacce akayiwa ɗan karen duka ta fara magana: "pa, mum ce" "Me mum ɗin tayi miki?" Papu ya tambaya. "Pa a gaban House-maid ɗin nan, talaka da ita ƴar talakawa, a gabanta mum tayi min tsawa" "Tsawa!" Ya faɗa da kakkausar murya kamar wanda akace masa wuƙa aka yanka mata. Ita kuwa tana ganin haka sai ta fashe da kuka mai sauti saboda haƙonta ya cimma ruwa. Tunda tayi kuka a gabansa. Idan za'a tambayi papu abunda ya tsani gani shine ɓacin ran khulud, balle har takai ga tayi kuka. "Haba my kid kuma my mum kiyi hakuri ƴar lelen papu da mum ki tashi muje gaban mum ɗin taki naji dalilin da yasa tayi miki tsawa gaban mutane" "Pa, nifa ba tsawar ce tabani haushi ba inda akayimin tsawarne yasa naji haushi, gaban ƴar aiki fa talaka hmmm" ta faɗi maganar tana ƙara sautin kukanda takeyi. Sosai papu ya rikice ganin ulud na kuka har hawaye wasu na izar wasu, rarrashin ta yayi sosai, amma taƙi ta daina kukan har sai da yace zaije da ita shopping idan zai fita yanzu sannan ya samu ta yarda zatayi shiru kuma koda haka saida aka yi sharaɗi kan cewa zai jawa mum uban warning karta ƙara yiwa khulud tsawa ko tsakaninta da ita ne balle gaban ma'aikatan gidan nasu. Komawa papu yayi kan gadon da ya sakko tare da rufe laptop ɗinda ke ajiye sannan ya dauki phone's ɗinsa tare da barin ɗakin, bayansa tabi tanata dariya a cikin zuciyar ta, idan kaga fuskar ta a fili kuma zakace dukan tsiya akayimata abunka da farar fata har fuskar tata tayi jaaa sakamakon kukan da tasha a ɗakin papu, idanunta kuwa sunyi jajir kamar barkono. * * * JUSTICE KHATTAB WAASIB,,,,,,,, Dan asalin garin kaduna ne, aiki ya kawoshi garin Abuja, amma a suleja yake zaune da iyalinsa, zakuyi mamakin jin cewa a Abuja yake aiki amma kuma yana zaune a suleja da ƴaƴansa da matarsa. wannan kuma tsarine daya fito daga ƴar autarsa wato KHULUD KHATTAB WAASIB, khulud yarince ƙarama, saboda ko a shekaru ma bazata wuce goma sha daya ba. amma tanayin abunda ko babba bayayi domin kuwa batada tausayi ko kaɗan. A duniya babu abunda khulud ta tsana kamar talaka, domin kuwa idan akwai yanda zatayi da saita ɓatarda kowane talaka da yake faɗin duniyar nan. mahaifinta shine babban gishiƙinda yasa khulud keyin yanda taga dama domin kuwa idan ta aza doka ba wanda ya isa yace takkkkk kan abunda tace. Mahaifiyarta HAJIA FANAYA wato (MUM) ita kaɗai take takamata birki a wasu halayen nata, kuma koda haka sai idan mahaifinta baya nan ne, ba ita kaɗai bace ƴa a wajen su justice ba, sai dai itace mafi soyuwa a ransa. Domin kuwa yana matuƙar ƙaunarta har yanda zan kasa yimuku misali, ƙaunar khulud a zuciyar papu dabance data kowa, kuma gashi sunan mahaifiyarsa ce aka sakawa khulud shiyasa papu yaƙi jinin yaga abunda zai taɓa khulud ɗinsa idan ko yana nan sai inda ƙarfinsa yaƙare. Koda ulud tayi kuskure papu bazai taɓa nuna mata kuskure bane komai tayi daidai ne wajensa, kuma komai tsada da wahalar abu idan ulud ta nema wajen papu sai ta sameshi. Babban abunda yake damun mum Bai wuce wannan ba, sau dayawa tana yimasa magana akan haka amma basa kwashe wa da daɗi domin kuwa shima kanshi papu yana matuƙar jin haushin azo a gayamasa laifin khulud, shi a kullum khulud bata laifi a wajensa. "Justice wallahi wannan abun na damuna, dashi nake kwana da shi nake tashi, wallahi wannan ba gata bane justice ace kamar mamana du-du-du nawa khulud take da za'a ce sai abunda tace akeyi a gidan nan kowa bayada ikon kansa sai nata. A gaskiya justice wannan ba ɗabi'a bace. Khulud macece a kwana a tashi yau da gobe girma zatayi a kaita ƙarƙashin wani, wallahi justice ba namijin da zai ɗauki shashancin wannan yarinyar a haka, kho mu da muke iyayenta hakuri kawai muke, kaga koh ba wani namijin da zai ɗaukar mata wannan, gaskiya ka canja kawai kaima domin kuwa wannan ba gata bane. "Kin gama! Nace kingama? Tashi ki fita idan kin gama" papu ya faɗa yana nuna mata kofa fuskar sa a haɗe. Baki sake mum tabi papu da kallo har tsawon wasu mintuna, Da sauri ya buga mata tsaya: "I Said out, koba zaki fita bane ni na fita na baki wuri" Miƙewa yayi yana nufin zura takalmansa, mum ta tashi ta fita da sauri tare da dafe bakinta tana shirin sakin kuka, daurewa tayi kawai tayi tare da barin abun a ranta ta fara ambaton Allah a zuciyarta, kafin ta tsaya ta saita kanta sannan ta fita wajen resting-room ɗin. Sau dayawa idan mum tayi wa papu maganar khulud tayi wani kuskure haka suke rabuwa koma fiye da haka. ~~~khulud kuma Daga fitarsu part ɗin na papu suka nufi master parlour ɗin gidan inda sukeda tabbacin zasu tarar da mum yanzu, tafiya suke ba wanda ya ƙara faɗar komai tsakanin papu da khulud, "Pa, amma dai bazaka gayawa mum nina kawo ƙararta wajenka ba kho?" "Kona gayamata me zatayimiki mamana, ae ba wanda ya isa ya taɓaki, kwantar da hankalinki kinji, kibarni da mum ɗin taki kawai" "Ah ah gaskiya pa karkace nina gayamaka kaga tafiya zakayi wallahi idan ka tafi zata iya yimin abunda yafi wannan" "Hmmmm mamana kenan, kece kike sakawa ranki wannan kawai amma idan mum ɗinki nason ganin farincikina yayin tafiyar nan da zanyi to dolene tayi miki yanda kikeso kuma kidaina sakawa kanki damuwar komai domin kuwa ina nan'' Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta yayinda taji papun ta yayi wannan maganar nan take taji wani ƙwarin gwiwa ya shigeta. Suna ƙarasowa parlour sai khulud ta sami wuri ta tsaya domin ta tabbatar wa kanta bazataje ko ina ba sai taga anyiwa mahaifiyarta warning. "Pa, ka kirata idan batanan saboda banji motsin ta Anan ba kwata-kwata". "Gani anan, lafiya dai kho my kid meke faruwane" faɗin mum dake ƙaraso cikin parlour tana ɗauke da tea flasks zata kai daining. domin haka take bata zama sai anyimata aikace-aikacen gida, tare take aikinta ita da ƴar aikin su wato dayammah domin bata yarda da tsarin sakewa ƴar aiki ragamar gida ba. Juya fuska khulud tayi gefe ta ɗauke kanta daga kallon mum, mum kuma tana ganin haka tayi murmushi domin tasan nufinta tunda ta ganta tare da papunta a wannan lokaci, domin kuwa lokacin yin break fast baiyiba a gidan nasu. Haka yasa ta fahimci khulud ƙara ta kaita wajen papunta. "Morning justice, an tashi lafiya? Kace yau mamana ce taje ta tasoka kho" Da murmushi shimfiɗe a fuskar papu ya amsawa mum gaisuwar da tayi masa: "Lafiya ƙalau hajjaju, kin tashi lafiya? Ya gajiyar aiki kuma ke ga yar aiki ga komai amma bakya zama ki huta" Papu yayi tambayar yana zama kan Pakistan sofa dake gefe. Mum na shirin bashi amsa sukaji muryar khulud ta fashe da kuka tare da komawa part ɗin ta aguje, Zaro idanu papu yayi tare da faɗin "subhanallah!, namanta da ƙararki aka kawomin fa" Bayanta yabi shima cikin sauri, ita kuwa mum murmushi kawai tayi ta tafi zuwa aikinta. Koda papu ya isa harta rufe ƙofar ɗaya daga cikin ɗakin da ta shiga a part ɗinta domin kuwa ɗakuna ne jere har ɗaki shida ita kaɗai. waɗanda suka ƙawatu kuma suka haɗu iya haɗuwa, duk a cikin dakunan ba wanda bata shiga saidai akwai wanda ta tsani ta shigeshi wata wato Library room idan take karatu sai idan mum ta matsa mata sosai ne take shiga ɗakin amma badan tanaso ba. Daga isarsa part ɗin ya nufi ɗakin da yasan tana cikinsa domin kuwa yasan idan aka ɓata mata rai, ko tayi fushi to bazata wuce dakin ba. shiyasa ko yanzu ma ya nufi dakin domin ya rarrasheta ya kuma bata hakuri. Amma sai ya tararda ƙofar ɗakin a rufe, yayi knocking har ya gaji taƙi ta buɗe kofar, rarrashin duniya yayi amma ina ko saurarenshi batayi sai ƙarar abubuwan da take fasawa kawai yakeji. yayi-yayi ta buɗe amma taƙi, shi bama komai ba yanaso ta buɗe kofar ne don kada tajiwa kanta ciwo ne amma taƙi. Mum kuwa taji papu shiru ya jima bai fito ba gashi har lokacin break fast ɗin yayi kuma 10Am Flight ɗinsu zai tashi. gashi har 9:20 kuma sai yaje shopping mall, bayansa tabi itama domin ta kirashi suyi break fast gaba ɗaya saboda haka ƙa'idar gidan yake koda yaushe idan za'a ci abinci tare akeci gaba ɗaya, Shigowa tayi part ɗin ta tarar da papu yana faman rarrashin khulud kan ta buɗe kofa. Sallama mum tayi tare isowa wurin:"justice lafiya meyake faruwa?" "Ba lafiya" "Meya faru? Mum ta kuma tambaya" "Mamana ce ta kulle kanta a ɗaki tana ta fushi gashi kinga lokacin break fast yayi amma taƙi ta fito kuma kinga inaso na tafi kar nayi missing Flight" cewar papu da damuwa shimfiɗe a fuskar sa. Murmushi mum tayi a zuciyar ta amma a zahiri sai ta mayarda fuskarta ta kamar wacce zatayi kuka ta isa gaban Kofar "mamana Please can you open it, badai ni bace na ɓata miki rai I'm really sorry, kiyi hakuri ki buɗe kinji mamanah na daina daga yau" Mum tayi maganar cikin sigar rarrashi. Daga can cikin ɗakin suka ji muryar khulud tana cewa "mum please I'd like to be left alone, ku tafi dan Allah inaso na huta" Khulud tayi maganar daidai yanda zasu jiyota, mum kuwa da papu suna jin haka suka juya domin kuwa sunsan tunda ta faɗi haka to bazata fito ba. Daining suka nufa, suna tafiya ba wanda yace kanzil, har suka ƙarasa. daining chair mum ta janyo wa papu tare da masa alama da ya zauna, da ƴar damuwa a fuskar sa ya zauna kan daining chair ɗin sannan mum tafara serving ɗinshi. Ta kula sosai akwai damuwa a tattare dashi, kuma tasan damuwar bata wuce ta khulud bace domin kuwa yana tunanin halin da take ciki yanzu. "Justice menene abun damuwa kuma yanzu, kamar dai baka san halin mamana ba, kasan tanada saurin fushi ne kawai amma batada wuyar hucewa, yanzu kasamu kaci abinci ka ƙoshi kawai saina gayamaka yanda zakayi ta fito ɗakin cikin sauƙi. Idan ko akayi haka bata fito ba sai a ɗauko extra key ɗin ɗakin nata a buɗe mana" Guntun murmushi papu yayi wanda a iya fuskar sa ne kawai sannan yace, "shikenan amma kada ki zubomin da yawa domin kuwa sauri nake kinsan saina fita shopping yanzu" Yafaɗa yana duba agogon bangon dake rataye daining area ɗin. Basu ɗauki tsawon lokaci ba suka kammala break fast ɗin, inda mum tagaya masa abunda zaicewa khulud ta buɗe kofa. Sake komawa yayi sashen nata cikin sanyi ya fara magana"my kid ki fito mu tafi kar mu makara zuwa shopping ɗin nan kuma kinga by 10 flight ɗinmu zai tashi, idan kuwa bazakije ba sai ki gayamin abunda kikeso na siyomiki" "Zanje pa, gani nan tafe" khulud ta faɗa daga cikin ɗakin. Ajiyar zuciya papu ya sauke a hankali domin kuwa yaji daɗin hakan, yana tunanin idan ya tafi khulud ɗinsa na fushi dashi bazai samu yayi abunda zai kaishi Mexico ba, da wahala ma idan zai iya yin tafiya mai nisa alhali khulud na fushi dashi............✍🏻 BAYAN WUYA... By RUMANA M DIGGI Ep.008 _____________IFE ROAD LAGOS NIGERIA. LEEYA Farkawa tayi daga wahalallen baccin da ya ɗauketa, jikinta duk ba ƙwari sakamakon yunwar da ta addabeta. tashi tayi da ƙyar daga inda take kwance sannan ta janyo jakarta ta fito da kuɗin da suka ragemata domin taje ta sami abunda zata ci, tafiya take da kyar tana jan ƙafa a hankali take takawa, domin kuwa ba inda baya yimata nauyi a jikinta, ciwon da kanta ya fara yimata ne takeji kamar zai tsage, amma haka ta daure taci gaba da tafiya har ta iso kan wani shago. Da sauri ta miƙa kuɗinda ke hannuta tana shirin yin magana sai mutanen wurin suka ruga aguje harda mai shagon suka bar wajen gaba ɗaya, dafe kanta tayi da takeji kamar zai tarwatse, durkushe wa tayi ƙasa tare da fashewa da wani irin kuka, hannu tasa zata yaye mayafin fuskar ta. "Kinyimin alƙawarin bazaki taba bayyana fuskar ki ga kowa ba hatta ke kanki har sai ranar da zan gayamiki, Dan Allah" Maganar ammin tace taji tana dawomata a kunnuwanta tamkar yanzu ne take yimata ita. Nan da nan ta ƙara sautin kukanda takeyi tare da janye hannunta daga kan mayafin, kukanta tayi mai isarta har saida ta gaji don kanta kafin ta tashi tabar wajen. ba wanda ya ƙara kulata har tayi gaba kallonta kawai akeyi idan ta wuce wasu suyi gudu, wasu kuma su kauce su bata hanya domin suna tunanin ko aljana ce ko kuma mahaukaciya. Tah ɗauki tsawon lokaci tana yawon neman abunda zata ci da kyar ta samu wani shago inda mutane suka cika yawa, wa sunsu basu kula da ita ba har ta miƙa kuɗin da ke hannunta, hatta shi mai shagon bai kula ba harya amsa kuɗin tare da furta "me za'a bada" Jin anyi shirune yasa shi ɗago kansa yana ƙoƙarin sake tambayar ta, maganar shi ce ta maƙale sakamakon arba da yayi da yanda leeya take da sauri ya juya zai koma can ƙarshen shago, leeya data fahimci abunda yake shirin yi da sauri da cafko hannusa muryarta na rawa tace "abinci zaka bani, dan Allah ka taimakamin wallahi yunwa nakeji sosai". Kalmar Abinci kawai ya iya fahimta a kalamanta da sauri ya janyo sandar biredi da ruwa biyu ya miƙamata, sannan ya haɗa mata da kuɗinta ya bata, hannunsa data rike ta sake da sauri tare da juyawa tana jan ƙafar tata, tun kafin ta isa inda ta ajiye jakarta da fara yagar biredi tanaci sosai kamar wacce bata taɓa sanin menene abinci ba a rayuwar ta, Koda ta ƙarasa kuwa biredin saura kaɗan, tana gama ci kuma ta ɗauki ruwan ta fara sha saida ta shanye ruwan biyu naki ɗaya sannan tayi gyatsa ta jingina sai bacci ya kuma kwasarta. ★★★★★★★★★★★ KHATTAB MANSION. SULEJA NIGERIA "mamana kefa nake jira ki fito muje banso na makara tafiyar nan". "Pa, kaje kaima ka shirya, kaya nake sakawa idan na saka zan fito" Tana gama faɗin haka papu ya juya yabar wajen, part ɗinsa ya koma tare dayin shiri kamar yanda ulud tace, bayan ya kammala tsafff ya ɗauki car keys ya fita part ɗin nasa. Yana fita kuwa ya tarar da ita ta shirya ita ƙadai zaune a master parlour tana kurɓa juice a glass cup. "Pa, har ka fito? Allah banyi tunanin kaine ka shigo nan ba na ɗauka daga cikin made ɗin gidan nan ne wata ta ƙara karyamin doka. "Mamana Wai wace doka ce kika kafawa made ɗin gidan nan" Taɓe baki tayi kafin tace:"ba wata doka bace papu kawai dai na gayamusu ne banason ganin kowa idan na shigo parlour nan, kuma banaso naga ko wuce anyi har saina ɗaga, balle idan nashigo nayi kallo, ko idan zan sha juice" Khulud ta faɗa tana kaɗa idanuwanta, tare da huro iska daga cikin bakinta, ta juya kanta gefe ɗaya tana ajiye juice cup ɗinda ke hannunta. "Mamana kenan daɗina dake Bakya ɗaukar wasa, kice wannan itace dokar da dayammah ta karya kho" "Ehh pa, shine kuma mum tayi min faɗa a gabanta, dana gayamaka kuma wai kace zaka yimata warning amma ka ƙi" "Uhmm mamana akwai son rigima harda mum ɗin taki sai anyimata rigima kenan, Tau a dinga hakuri dan Allah kinji khuludina" Papu ya faɗa yana shafa kan khulud. "Muje, ko kaima kanaso ka makarane shiyasa" Gaba tayi yana biyo ta baya har suka isa parking space, Suna isowa wajen drivern gidan ya taso da saurinsa ya taryesu: "Alhaji fita za'a yi ne" "Me zai fito damu idan ba fita zamuyi ba, ko ka taɓa ganin mu munzo nan haka kawai idan ba fita zamuyi ba. An ajiyeku ne kawai bakusan aikin ku ba, wallahi next time you try this I Will tell my pa, to fired you. What's all this" Khulud tayi maganar tana sakin tsaki tare da shigewa mota abinta. Da kallo kawai papu da drivern suka bita dashi ba wanda yace kanzil, kana papu yayiwa drivern umurnin ya shiga motar su tafi. ★★★★ IFE ROAD LAGOS NIGERIA. A hankali takejin sauƙar ruwan sama a jikinta, tun tanaji kamar mafarki take har yakai ga tafara jinsu sosai suna saukowa ta ko'ina ajikinta. Miƙewa tayi sosai ta shiga laluben jakarta domin kuwa har duhu yafarayi, cikin Sa'a kuwa takai hannun ta kan jakar, yayinda ruwan suke zuba kamar da bakin ƙwarya. Da gudu ta fita daga cikin ƴar rumfar karanda ta fake, domin kuwa har a cikin rumfar ruwane ke zuba sosai ba bambanci da wajen rumfar. Gudu take sosai iya ƙarfinta domin gujewa ruwan karsu jiƙata, babu inda bai jiƙe ba a jikinta gashi ta gaji sosai da gudun da takeyi da ƙyar take iya yinshi sosai. a hankali ta fara hango wani wuri mai kamar ɗaki, kamar kuma shago, amma bata iya tantance menene, daga nan inda take, hangoshi kawai take sai idan anyi walƙiyane zata ganshi. Duk da haka kuma bazata iya gane ko menene ba, a ranta tana ayyana cewa ko menene idan ta riskeshi shiga zatayi kawai. ƙara hanzari tayi wajen yin gudun domin kuwa ta gaji ainun. Tana isowa bata tsaya ta tantance abunda tagani ba, kawai ta tuma ta faɗa, tare da janyo abunda taga anrufe wurin data shiga itama ta rufe. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da furta"Alhmdullillah" can a ƙasan zuciyar ta. Gefe ɗaya ta samu ta rakuɓe domin kuwa sanyi takeji sosai har tana makyarkyata. Sautin haƙoranta kawai kake iya jiyowa suna kaura da juna, ta duƙunƙune waje ɗaya, a haka wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita batare data sani ba domin kuwa yunwa ce cike fallll a cikinta tunaninta kawai ina zata sami abunda zata ci. Bata wani ɗauki lokaci tana baccin ba sakamakon ji da tayi kamar ana tafiya da ita. Da farko ta ɗauka mafarki take sai da ta buɗe idanun ta ne ta fahimci da gaske ne ba mafarki take ba "hasbunallah wani'imal wakil, me hakan yake nufi, badai mota na shigo ba" Fara dudduba ko ina tayi inda take zaune domin kuwa a yanda takeji ma har an ɗauke ruwan saman, saida ta lura sosai kafin ta fahimci da gaske mota ce ta shigo. kuma mota ma irin wannan datake safaran kayayyaki daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa. Fara bubbuga bayan motar tayi tana faɗin: "dan Allah ku taimakeni ku saukeni anan, wallahi bada ganganci na shiga motarku ba, banmasan mota bace nashiga ne kawai dan na samu mafaka da ruwan sama, dan Allah ku taimaka mini" Faɗi kawai take tana kuka Bama alamar ana jiyota domin kuwa irin dogayen lorry ɗin nan ne, kuma gashi ansaka abun rufewa anrufe motar rufff, haka tayitayi har ta gaji da magana yayinda yunwa ke ƙoƙarin kada ita. ruwa tagani a cikin gora ajiye a chan gefe, da sauri takai hannunta tare da ɗauko ruwan ta ɓalla marufin gorar takai ruwan bakinta. Bata janye ruwan abakinta ba saida ta shanye ruwan kafff, bata kai ga ɗauke gorar bakinta ba cikinta ya ƙulle sosai Mirgina tafarayi tare da riƙe cikinta ta fara fitarda numfarfashi. K. WAASIB MANSION ★SULEJA NIGERIA★ Sun ɗauki tsawon mintuna suna danna horn bakin gate, amma kamar ba kowa a gidan. Kallon driver side khulud tayi tare da furta "kai shuraihu me kake jira da bazaka fita ka buɗe mana gate ba, ko so kake ni nafita na buɗe, ko kuma pa kake so yaje ya buɗe?" Tun kafin takai ƙarshen maganar da takeyi driver ya fita da sauri ya nufi gate ɗin tare da wangaleshi, dawowa yayi cikin motar tare da kunna hancin motar cikin gidan. Tun kafin motar ta isa parking space ulud ta bada umurnin a dakata da tuka motar, drivern ko yanajin haka yayi saurin take birkin motar. Tun kan tayi wani abu saiga wani mutumin daban ya ƙaraso tare da buɗemata ƙofar motar, yana buɗewa kuwa sai gata ta fito daga cikin motar bata ƙara waiwayo ba. Guard room ta nufa, tana tafiya cikin isa da taƙama kamar itace mai gidan ba papu ba. Kwala masa kira ta farayi da karfinta cikin fushi da ɓacin rai. uzairu mai gadi dayake toilet yaji Muryar khulud dake kiransa. Take hantar cikinsa ta kaɗa domin kuwa yasan yau dubunsa ta cika a gidan, da sauri ya fito daga cikin ban ɗaki tare da nufota da aguje. Idan kuwa aunawa za'ayi uzairu mai gadi ya haifi kamar ta ba ɗaya ba balle biyu, sauran ma'aikatan gidan har mamakin irin wannan tsaurin idon irin na ulud. Mutane dayawa suna da haushin ulud a ransu musamman ma wasu ma'aikatan gidan da tasa aka koresu ba tare da wani ƙwaƙkwaran dalili ba, kuma sun ƙudurta a ransu idan suka sami dama zasu a zabtarda ita daidai da abunda ta aikata musu, kawai dai dama ce basu samuba. "Gani hajiya ƙarama, don Allah ayimin aikin afuwa, na rantse da Allah cikina ne baya yimin daɗi tun jiya, kuma banyi tunanin zaku dawo da wuri haka ba da bazan rufe gate ba dan Allah ayimin afuwa" Uzairu mai gadi ya faɗa yana haɗe hannayen sa biyu, alamar roƙo. Kanta ta ɗauke gefe ɗaya: "kaje wurin pa, kace masa nace ya baka ladar aikinda kayi, ka ƙara gaba" Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta juya ta barshi wajen hankalinsa a tashe, kuma yasan cewa shikenan zamansa a gidan ya ƙare tunda a gaban idanunsa tasha yiwa wasu ma'aikatan haka. Kuma shikenan sun koru har abada. Hannunta ta ɗaga tare da yiwa wani mai aiki alama da yazo, cikin azama ya ƙaraso Wajen jiki na rawa domin gudun kar abunda ya faru da wancan shima ya faru a kansa. "So nake kaje ka samo cardboard paper kayi rubutu akai muna neman sabon mai gadi wanda yasan aikinsa ba kamar wancan sha-sha-shan ba, sannan kaje wajen gate ka liƙa domin kowa ya gani. "Tau hajiya ƙarama in sha Allah yanzu zanyi kuwa, wannan ba wani aiki bane. Kuma za'a sami irin wanda kikeso da yardar Allah" Cewar mutumin. Juyawa kawai tayi ba tare da ta ƙara faɗin komai ba ta nufi cikin gida. A parlour ta tarar da mum tare da mai aikin gidan wato dayammah shiga tayi ciki kamar yanda ta saba, ba wanda take yiwa sallama parlourn kawai ta shiga tare da furta "excuse me. Mum I'm back" Khlud ta faɗa tana ƙarasowa gaban mum tare da dafata. "Barka da zuwa my kid, kin dawo lafiya? Ya hanya kuma?' "Hanya Lafiya ƙalau, ina pa?" "Yana part ɗinsa Yana shiryawa yanzun nan zai fito ai" "Okay" kallon ta takai kan dayammah: "what'd you make, me kika haɗa yau?" Khulud tayi tambayar ga dayammah daidai lokacin da mum ta miƙe ta bar wajen tare da nufar part ɗin papu. "Doya da miyar kwai na haɗa" A tsawace khulud ke magana, kuma a fusace"What!!? You make what!!??, how many times do I need to tell you that I'm lactose intolerant, I don't eat eggs, yet should want ahead and the make eggs for me, do you have something wrong with your hearing?" "Ulud!!!!, why talking to dayammah in this manner, meyasa a duk lokacin da zakiyi mata magana sai ki dinga yi kamar Sa'arki?" mum tayi maganar a tsawace itama tana shigowa cikin parlourn. "Mum can You imagine she makes eggs for me, after I told her that I'm lactose intolerant I don't eat eggs" "Saboda ta dafa miki kwai ne kike yimata haka, it's easy idan bakyaso kigaya mata sai ayi miki wani abincin da kike so ko kuma ki faɗa wanda kikeso da kanki sai a girka miki, bawai kizo kisakata gaba kina yimata faɗa ba" "Mum I've told her at several times that I'm a began I'm not eat eggs. Milks, little potion. Idan ta gaji kuma ta bar aikin tunda ba dole aka sakata ba, mu kuma ba kyauta take yimana ba biyanta akeyi. Dama haka talakawan nan suke idan sukaga ana sake musu" "Khulud!!" Mum ta faɗa a fusace. Juyawa kawai khulud tayi batare da tajira abunda mum zatace ba tayi shigewarta. "Dayammah kiyi hakuri Dan Allah. Nidai shine abunda nakeso kicigaba dayi dan Allah, kije kitchen kici gaba da aikin ki" Juyawa mum tayi itama tare da nufar ɗakin khulud, tura ƙofar ɗakin tayi cikin Sa'a ta tarar da ita a buɗe domin a tunaninta ma ta rufe ƙofar. Tura ƙofar tayi tare da yin sallama sannan ta shiga ciki, zaune ta tarar da khulud gefen gado tana cika tana batsewa Zama mum tayi a kusa da ita fara yimata magana cikin sanyi. "Khulud, sau nawa zan gaya miki ki koyi yanda zakiyi magana da manya, dan Allah khulud ki zamo yarinya mai jin maganar iyayen ta, kuma kizamo mai girmama manya kinji" "Mum she's the maid I have the right talk to her the way that I wanted, ita ɗin ƴar aiki ce ba dole ne na girmama taba kamar yanda kikeso, Ni yakamata ta girmama bawai Ni nazo ina girmamata ba, she's the peasant and the we're not the same class" "Rufemin baki sha-sha-shar yarinya, saboda tana ƴar aiki shine zaki yimata magana yanda kikeso wannan ba rayuwa bace" "So mum because of the maid you're talking to me like that, right?" ulud ta faɗa cikin murya kuka. Dogon numfashi mum ta sauke, kafin ta zauna bakin gadon, a tausashe mum ta fara magana a karo na biyu "you're my kid khulud, ko kaɗan bana son ganinki cikin damuwa, a koda yaushe addu'a ta ɗayace Allah ya shiryaki, ya rabaki da waɗannan halayen nan. Ki zamo yarinya ta gari wacce kowa zaiyi alfahari da ita, bazan iya jure ganinki a haka ba, bazan iya ba" "Mum Please, can you leave me alone, I'm so tired, banason ganin kowa kusa dani dan Allah" Khulud tayi maganar tana juya kanta gefe ɗaya. Ɗan jimmm mum tayi tsawon mintuna ba wanda ya sake cewa komai acikin su, sai mum ce ta ƙatse shirun da faɗin "ina home work ɗinda aka baku, bani naga marks ɗinda akayimiki" "Malamin yace sai gobe zai bamu littafan mu" faɗin khulud tana sosar wuyanta kamar mara gaskiya. "Okay Allah ya kaimu goben" mum ta faɗa tana miƙewa tare da barin ɗakin. Mum na fita ulud ta janyo school bag ɗinta, tana ɗan leƙa bayan mum a hankali, note book ta fito dashi da kuma red pen, dudduba littafin ta farayi, guntun tsaki taja, sannan ta ɗauki red pen bayan tagama dubawa ta fara yiwa kanta marks yanda takeso, sannan ta maida littafin cikin school bag ɗinta, fuskar ta ɗauke da murmushi. LEEYA. Ta ɗauki tsawon awa ɗaya harda kusan rabi cikinta bai daina mirɗa mata ba, tana nan dunƙule gefe ɗaya hannunta dafe da ciki sai hawayen azaba ke zalalomata. Sunsha tafiya sosai cikin motar ita dai leeya ta saddaƙar, ta barwa Allah ikonsa domin kuwa bata san a inda take ba a halin yanzu, kuma bata san inda suka nufa ba a nan gaba. "Allah sarki ammi da kinanan da bazan shiga wannan gararin da nakeba, da kinanan baza'a dinga gudana kamar haka ba, da kinanan baza'a dinga min kallon mahaukaciya ko aljana ba, da kina nan, da kina nan" haka dai tayi ta saƙe saƙe cikin ranta. Tashi tayi tare da jingina bayanta jikin motar Yayin da taji cikin ya lafa daga mirdawarda yake mata, yunkurin tashi tayi daga inda take domin kuwa tagaji ainun, ƙafafuwan ta duk sunyi mata tsami, koda ta tashi sai taji kayan da ke motar sun hanata miƙewa yanda takeso, komawa tayi ta zauna dafas tare da sakin siririn kuka "wa ƴannan mutane waɗan ne irin mutane ne da basuda tausayi, ae koda dabbobi aka ajiye ya kamata a kula dasu balle mutum ko mutum ma mace" koda ta kawo nan a zancen zucinda take wata zuciyar tace "haba dai kiyimusa adalci kema ko dan sanin baya bata gani, domin kuwa ta baya kika shigo motar nan bata gaba ba, kuma ba wanda yasan dake a cikin mutanen da ke cikin motar nan. Hakuri kawai zakiyi har kiga hukuncin da Allah zai zatar kan wannan lamari". "Nayi hakurin Allah kasa ba hannun mugayen mutane nashiga ba" ta faɗi a fili cikin muryar kuka, kamar wacce ke magana da wani. Birkin da aka jaaa daga cikin motar ya dawo da ita hankalinta, ƙara komawa tayi ta kwantar da kanta jikin motar domin yanzu ta fitar da ranta da za'a fito taimake ta. Motar tasha tsayawa amma haka zasuyi abunda zasuyi har su gama basu zo sun leƙata bayan motar ba. Shiyasa ko yanzu da suka tsaya bata wani damuba, "Mezai hana kibi ta inda kika shigo ki fita tunda baki san ina motar nan ta nufa ba". Wani gefe na zuciyar ta yayi maganar. A hankali ta janyo jakarta, sannan ta matso daidai da bakin kofar motar inda ta shigo, ta kara kunnenta a hankali domin ta jiyo idan akwai hayaniyar mutane ko kuma cikin daji ne suka tsaya. Cikin ikon Allah kuwa ta dinga jiro maganar mutane a ɗan nesa da inda take daidai lokacin duhun magariba ya fara, a hankali take yaye marufin da aka rufe jikin motar dashi harta kawo daidai da kofar fita. ƙafafuwanta ta fara sakowa Kafin ta fito gaba ɗaya, idanun ta ne suka yimata nauyi sosai sakamakon hasken da ya dokesu domin kuwa ta jima rabon da taga haske a idanun ta duk kuwa da fuskar ta na lulluɓe cikin mayafi, a dudduƙe take tafiya domin kuwa ita ƙaɗai tasan yanda takeji ga yunwar da ke damunta sosai. tafiya kawai take batare da sanin wane gari take ba, bata kuma san inda zataje ba a halin yanzu. Ta san ta fita Lagos yanzu domin yanayin mutanen da take gani a nan suna giftawa basu yi kamada mutanen da ta saba gani a Lagos ba. Tafiya kawai take batare da sanin ina zatajeba, duk hanyar da tayimata binta kawai take batare da dogon tunani ba. A hankali take ganin tana kutsawa cikin gari sosai, domin kuwa inda take nufa yafi inda ta baro mutane. Tana cikin hakan ne ta hango wata rumfa kamar kuma abinci ne ake siyarwa wajen, sai kawai ta juya akalar tafiyarta zuwa wajen, tana isowa taga a she rumfar mai sayarda shayi ce rumfar kuma tabb da mutane sakamakon ruwan sama ta aka ɗauke bada jimawa ba. kamar dai yanda mutane suka sabayi idan suka ga leeya suma mutanen nan haka sukayi. Amma jin tayi sallama yasa ƙalilan daga cikinsu suka tsaya "ke! Mekike nema a nan?" "Abinci" "Ba'a sayarda abinci anan shayi kawai nake saidawa da biredi sai indomie da kwai, wanne kikeso?" "Shayi da biredi zaka bani" "Na nawa kikeso?" Jakarta dake rataye a kafaɗarta ta sauke, hannunta ta saka cikin jakar tana lalubar kuɗinta, sai can ta cirosu sannan ta miƙa masa su gabaɗaya bata ko lissafa ba "ɗari huɗu ne na duka za'a baki?" Mai saida shayin ya tambaye ta. "Ehhh" "Abis ka bata kuɗinta Ni zanbiya mata" Cewar wani dattijo dake zaune a wajen, mai saida shayin kuwa ya bata kuɗin ta tare da haɗa mata shayi da biredi a leda ya miƙa mata, zagayawa tayi har gaban dattijon ta durkusa. "baba Nagode Allah ya saka maka da alƙairi, Allah yayi maka fiye da yanda kayimin" Dashida sauran mutanen da suka rage a wajen zaune suka amsa mata da "Amin" Har dattijon ya fito da ɗari biyu ya daɗa mata, hannu biyu ta saka ta karɓa haɗi da yimasa godiya sosai da Addu'oin alkairi. Tana ɗagawa daga wajen mutanen ta samu wuri a gefen hanya ta zauna, ta buɗe ledar shayi da biredin ta fara sha. K. MANSION SULEJA NIGERIA. ★*★*★ Zaune suke a daining area anata murnar dawowar papu daga Mexico. Mum, khulud da kuma papu duk suna zaune suna cin abinci cikin nishadi da yanayi mai daɗi. "Pa, nayi farin ciki sosai da wannan labarin da kazo min dashi, kuma naji daɗin saukarka lafiya gaskiya mun gode wa AZMAFAT AIR TRANSPORT gashi kaje lafiya ka dawo lafiya" "Bazakice kin godewa Allah ba saidai kice kin godewa AZMAFAT AIR TRANSPORT ai basu sukeda ikon zuwa lafiya sudawo lafiya ba duk Allah ne yakeda ikon, justice kaji mamana kho ɗaukin ganin ka yasa ta faɗi abunda ba daidai ba" "Hakane kuwa khuludina ki gyara kinji" "Naji" "Yawwa mamana, ɗazu ina hanyar zuwa airport zamuje tarbon justice school teacher ɗin ku yakirani, he complain vitally cewa bakya maida hankali a class, yace ko jiya anyi test kinyi filled". "Mum I'm trying my best, kawai dai malamin ya tsaneni ne, shiyasa komai nayi yace bai yiba". "My kid ina kika taɓa ganin malami ya tsani ɗalibinsa, ko wanne malami zai koyar tsakani da Allah yake badan a yabashi ba, saboda haka kidaina faɗin ya tsaneki". "Mum nasan mutane da yawa dana fisu a class ɗin nan amma yana nuna banbanci tsakanin mu" "Uhhhhm What did you score in class today?" Cewar mum. "Ten over ten" "That's my brilliant daughter wow" faɗin papu. "Ten over ten?" mum tayi tambayar cike da rashin yarda da abunda khulud tafaɗa. "Yes mum" "Okay zan iya ganin littafin naki" "Of course, but mum why not the one that told me that I should always observed table minus" "Karki damu inaso na ganshi kawai, wata rana idan zan nemi nagani zan faɗa miki, mum bata jira abunda khulud zatace ba ta fara kiran sunan dayammah!" Kiran dayammah mum tayi sau biyu kafin ta amsa mata da sauri ta fito ɗakin da take ta nufosu. tana isowa wurin da gaida su Sannan ta juya ga mum "gani hajiya babba me kike buƙata" "Littafin khulud nakeso ki ɗaukomin a part ɗinta kiyi sauri kizo" Khulud da ke faman hararar dayammah tun sadda ta fito tace mata "kikula da kyau akwai cc tv camera a ɗakina karki min sata" Ba wanda yace komai tsakanin dayammah, papu da mum. Duk basu ce da khulud komai ba balle ita dayammah ɗin da ba kowa ba, juyawa kawai tayi domin ta aikata abunda aka sakata tayi. Tura kofan ɗakin tayi yayinda hawaye suka zubo a idanun ta, "Allah mai juya al'amari yanda yakeso kuma yanda yaga dama, haƙiƙa daba dan karatun ɗana ba da bazan zauna a gidan nan wannan ƙaramar yarinyar na tozartani ba harda ambata min sata. Allah sarki RAWAAN, Allah ya bayyanar da kai idan kana raye idan kuma baka raye Allah ya jiƙanka nasan da kana na da wannan Abubuwan bazasu faru damuba, da babu inda hajiya ƙarama zata ganmu balle ta ɗinga wulakanta Ni kamar haka" ta ƙare maganar hawaye na gudu a fuskarta. School bag ɗin khulud ta fara nema bata ganta a bedroom ɗin ba, ta fita a cikinsa sannan ta shiga Library room ɗin ta, achan taga jakar sai ta fito da littafin sannan ta fita ta rufe daƙin ta koma daining area ta kaiwa mum littafin. Karɓar littafin mum tayi sannan ta buɗeshi yayinda hankalin papu gaba ɗaya ya koma kan mum yana jiran abunda zatace. "Ten over ten" mum tafaɗa badan ta yarda da marks ɗin ba, kamar ba Malami ne yayi shi ba, amma ta share ba don komai babsai domin tana gudun ran papu yaɓace ne yasa ta faɗi abunda ta gani zane a littafin. "Wow, five-five" papu yafaɗa yana lalewa da ulud "I'm proud of you my kid, zan baki kyauta" "Thank you my pa" "Wannan shine lokaci na farko da naga score ɗinki ten over ten" faɗin mum."but I'm so proud of you my love khulud" "Millions of thanks my lovely mum, can we continue?" "Yes" mum da papu suka faɗi. ULUD Zaune take a Library room ɗin ta, bayan sun tashi daining area ɗin, littafin tane ajiye a gaban ta sai red pen dake hannun ta, marks kawai take zubawa kanta yanda takeso har sai da takai ƙarshe sannan ta ajiye littafin, murmushi kwance a kan fuskar ta, "Zanci gaba da cinye kyautar pa indai zanci gaba da haka, uhmmm I'm really proud of myself" Washe gari, mum ce zaune gaban mirror tana shiryawa, yayinda papu ke zaune kan fabric sofa Yana duba wasu takardu, ƙarar wayar mum ce tacika ɗakin. (Maman twins) sunan da ya fito kan screen ɗin wayar kenan. "Assalamu alaikum" mum ta furta sallama lokacin da ta kai wayar kunnen ta. "Wa'alaikisalam" Aka amsa daga cikin wayar "Maman twins manyan mutane kaduna ta amshe mana ku kho, ba a kiran kowa yanzu kunzama manya" "Hammmm hajiya fanaya kenan ni na isa in manta daku ah ah wlh wuyana baiyi kauri ba tukunna" "Gashi kuwa kin manta maman twins, Ina ga ma saida kikaga nayi magana a group ne jiya nace a dinga sada zumunta koda ta wayane shiyasa kika kirani kho?" "Ah ah Hajiya fanaya duk ba wannan bane ina kawar gidane kawai shiyasa nakiraki mu gaisa" "Ahhh tho Nagode sosai Allah yabar zumunta, ina twins angirma kho?" "Twins suna nan ƙalau amma dai ki ƙara da ɗaya akai don yanzu basu biyu bane su uku ne" Mum na shirin yin magana matar ta kashe waya, ajiye wayar mum tayi kawai tana murmushi domin a zatonta haihuwa matar ta kuma yi. "Justice Dan Allah idan zaka fita aiki ka ajiyemin khulud a school, bazan samu zuwa kaita ba yau, kasan bata son drivers suna kaita school" "Okay wannan ba matsala bane kinji, ina khulud ɗin take?" "Tana daining" "Okay bara na idar sai mu tafi" "Thanks a lot" mum ta faɗa tana murmushi. Zaune akan daining ulud ce sanya cikin school uniform ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. "Wai me kike jirane, kefa nake jira kar nayi letting ki kawomin break fast ɗina" khulud ta faɗa cikin Daga murya tana kallon hanyar kitchen. "Hajiya ƙarama kiyi hakuri yau nima nasan na makara wallahi ɗana ne aka dawo dashi daga boarding school ba lafiya shine Alhaji ya kaini tunda sassafe na dubashi, yanzu dai yaji sauƙi an maidashi a school ɗin amma kiyi hakuri nagama yanzu zan kawomiki" "Who cares, where is my breakfast? Menene damuwata idan ɗanki bashida lafiya mezan yimiki mtswww" "Allah ya huci zuciyar ki, ga breakfast ɗin" Dayammah ta faɗa tana ajiye babban faranti agaban khulud, kayan da ke cikinsa ta ajiye gaban ta ko wanne daban. "What!!?, what is this?" "Breakfast ne na kawomiki" "Ni sa'ar ki ce da zaki bani Wannan wawuyar amsa, me kika dafa anan" "Toasted bread, da meat pie ne da kuma tea Hajiya" Tea cup khulud ta ɗauko tare da zubashi cikin meat pie ɗin sannan ta watsawa dayammah sauran a fuska "next time idan zaki yi girki kizo ki tambayi abunda nakeso bawai kiyimin irin wannan rubbish food ba, idan kuma kinsake haka na rantse sai kin bar gidan nan" Ta faɗi maganar dai-dai da shigowar papu a daining area ɗin shi baima kula da dayammah dake dosƙare a wajen kamar gunki ba" "Hey my kid are you ready for school" "No pa, I'm not" "Why?" "Pa bata bani breakfast ɗina ba tun ɗazu ina nan amma taƙi ta kawo min" "Dayammah by this time why" ya faɗa yana duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa. "Alhaji wallahi ga breakfast ɗin ta nan na kawomata, shine ta haɗe tea da meat pie ɗin nan waje ɗaya ta cakuɗe" "Pa, wallahi ƙarya take nace mata ta idan zata kawomin break fast ta haɗamin da kwai shine takawomin ba kwai a ciki" "Amma Hajiya jiya fa cewa kikayi u're lactose intolerant bakyacin ƙwai shine kuma yanzu zakice kina cin ƙwai" "Karya take pa yaushe na faɗi haka?" "Enough, dayammah na ajiyeki ne domin ki kula min da yarinya, kibata duk abunda takeso, kuma kada ki takuramata, ina fatar kin fahimta" "Na fahimta Alhaji in sha Allah zanyi ƙoƙarin yin haka" "Mamana ki tashi muje restaurant kiyi breakfast kinji I'm sorry". Miƙewa tayi tare da ɗaukar school and food bag ɗinta suka fice gidan. ★★★ LEEYANA. Tana nan zaune wurin da tasha shayin har akayi kiran sallar isha, anan ne hankalinta ya tashi domin rashin sanin inda zata kwana. Miƙewa tayi taci gaba da kutsawa cikin garin da ta tabbatar da koma wanne garine to babban garine domin kuma haske ne ta ko'ina a cikin garin, ta ɗauki tsawon lokaci tana tafiya cikin garin tana bawa idanun ta abinci kafin tafara cimma gidaje. Wata mata ta hango zaune tana soya waina ga mutane zagaye da ita da sauri ta isa laɓin wani gida ta ajiye jakarta, Sannan ta fito da ɗari biyun da dattijon nan ya bata taje wajen mai suyar wainar ta miƙa mata kuɗin "abani abinci na ɗari biyu" "A roba ko a leda" "A leda zaki sakamin" Lissafa wainar matar tayi harta ɗari biyu ta miƙa mata Sannan ta bata ruwan pure water ɗaya, leeya tayi mata Godiya sannan ta juya ta koma inda ta fito, zama tayi ta fara cin wainar hankalinta duk baya kanta, yau haka kawai takejin kawar Aleena na damunta. Harta idar da cin wainar bata daina tunanin Aleena ba, "shikenan duk kun mutu kun barni. babu Abbi, ba Ammie, babu uchie babu Nnene babu ke Aleena Gashi broth okene ma ya tafi ya barni". Wani kukan tafashe dashi mai tsuma zuciyar mai sauraro. Haka tayi kukan harta gaji babu mai rarrashi. Wani zani ta fito dashi, sannan ta sanya ƙafar takalmanta ta share wajen tsafff, sai kuma ta shimfiɗa zanin ta ajiye jakarta ta kwanta ta aza kanta kan jakar ta tayi pillow da ita zanin ta ta kuma lankafewa da rufa jikinta dashi tayi baccinta. K. WAASIB MANSION. "Dayammah! "Dayammah!!" Ulud keta kwala mata kira tana zaune a resting parlour. "Na'am Hajiya ƙarama gani nan zuwa" Fitowa tayi daga kitchen ta tazo wajenta "kina buƙatar wani abu ne hajiya ƙarama?" "Ke rufemin baki kar na saɓa miki a wajen nan, shine ɗazu da safe kikaso ki haɗani da papu kho, kika ƙaryatani gabansa, wallahi summa tallahi dayammah kin kusa barin gidan nan alo tsiya alo danja, tunda nagane keba tsohuwar kirki bace, Aikin me kike yi a kitchen yanzu?" "Jar miya nake haɗawa Alhaji yace ita yakeso yaci yanzu" "Okay kije ɗakina ki ɗauko min tab ɗina ki sameni a parlourn ƙasa" "Amma hajiya ƙarama da kin bari na ƙarasa don Allah, Alhaji yana jirana yanzu ya dawo office" "Iyyeee! Yaushe bakin ki ya buɗe harda zan sakaki aiki ki kawomin wata Magana?, wallahi idan baki tafi inda na aikeki ba saina saɓamiki.....✍🏼 BAYAN WUYA... 009 By RUMANA M DIGGI ★★★ ______________Da sauri tabar wajen, ta nufi part ɗin khulud. Tayi nema duniya a ɗakin bataga tablet phone ba, sai ta yanke shawarar zuwa ta sanar mata amma tana jin tsoron zuwa tagayamata. Tunawa tayi da girkin da take a kitchen kuma tasan Alhaji na jira, fita tayi da sauri ta nufi functional electric pot ɗinda ta jona ta kashe ta bayan shigar ta kitchen ɗin. Tana kashewa kuwa ta buɗeta da fatar red soup ɗinda take bata ƙone ba. Tana buɗe functional pot ɗin taci karo da abunda ya bata mamaki ƙarara domin kuwa ruwa ne cike a cikin miyar anzubamata ruwa harsaida functional pot ɗin ta cika. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" ta furta kalmar daidai lokacin da taji papu na kwala mata kira a daining area. Fita kitchen ɗin tayi jikin ta a sanyaye "Alhaji wani abu yafaru, kuma wallahi bansan waya aikata ba" "Ban fahimceki ba, menene yafaru?" "Alhaji wallahi abincin da na dafa aka zubawa ruwa bansan waya zuba ba" "Kamar ya baki san waya zuba ba kina cikin kitchen, bayan ke akwai mai shiga kitchen ne?" "Ah ah Alhaji ba wanda yake shiga kitchen amma wallahi bani na saka ruwan ba" "Karka yarda da ita pa, karya take ita ta zuba ruwan da kanta" "Da gaske?" Cewar pa Yana kallon khulud da tayi magana yanzu. "Da gaske kuwa pa, jiya da dare na jita tana waya har tana cewa ita ta gaji da aiki a gidan nan saboda ana takura mata bata samun lokacin kanta balle ta samu lokacin ɗanta" "Da gaske ne abunda khulud ta faɗa?" Papu ya tambayi dayammah. "Wallahi ba gaskiya bane Alhaji na rantse maka da Allah gaba ɗaya jiya banyi waya da kowa ba ƙarya take min" "Ni nake miki ƙarya? Talaka dake zanyiwa ƙarya wallahi pa, ba ƙarya nake mata ba" "Kinason aikin ki kho?" "Ehh wallahi alhaji inason aikina" "Okay tau yazama dole idan kinason aikin ki, ki kula dashi idan ko ba haka ba gaskiya zan sallame ki" "Pa a koreta kawai tunda har ta fara gayawa mutane ta gaji da ganinta a ƴar aiki" "Wallahi alhaji bantaɓa faɗar maganar nan ba" "Nidai nagayamiki idan kinason aikin ki riƙe da kyau, My kid lemme get car key to go out and eat something again" "Thank you my pa" Tashi papu yayi daga wajen, ya rage saura khulud da dayammah kaɗai "Hajiya ƙarama dan Allah meyasa kika aikatamin haka bayan kinsan Alhaji bayason ayimai ƙarya kuma gashi ke kinyi mai ƙarya, kinsan bani na aikata abunda kikace nayi ba" "Uuuhhhm Ni na aikata, Ni na zuba ruwa a soup ɗinda kika haɗa Saboda alkawarina ne saina saka pa, ya koreki a gidan nan, tunda idan nace nayi yanda nakewa sauran ma aikata akanki mum bazata bari ba, amma kijira kigani Ni KHULUD KHATTAB WAASIB bana magana biyu, kinzata wasa nake kho? This is just the beginning, zanyita yin abubuwan da zaki gwammaci ki bar gidan nan da kanki basai an koreki ba that's promise" "Kiyi hakuri dan Allah wata rana sai labari, yau gare ka gobe kuma ga wanin ka, hajiya ƙarama ki ƙara hakuri kawai komai yanada lokacin watarana zaki nemeni ki rasa, da badan ƙaddara ba da bansan inda zaki ganni ba balle ki wulakanta Ni" "Mtswww can ta matsemiki ke kika san waɗan nan ni bakya ko gabana, balle na wani da mu da abunda kike faɗa" "Khulud ɗin papu ki tashi ki cire uniform ɗinki tukunna sai mu tafi kho" "Ah ah pa, Ni sai na dawo zan cire uniform, yunwa nakeji sosai bazan iya tsayawa nacire uniform ɗin nan ba" "Dan Allah hajiya ƙarama ki cire na wanke miki kafin ki dawo, kinga gogewa ka kawai za'ayi" "Mtswwww kinga dayammah kifita harakata wallahi idan ba haka ba zaki gane kurenki. Pa, let go Please yunwa nakeji" "Dayammah ki bari idan muka dawo sai ki je kiwanke mata ɗin kinji, yanzu kinga yunwa takeji bazata iya tsayi ta canja kaya ba" "Tau Alhaji babu damuwa Allah ya dawo daku lafiya" "Ameeen" Tana nan zaune a parlour har mum ta fito ta sameta zaune ita kadai kuma ba aiki take ba "dayammah me kike jira a nan?" "Ahhh hajiya babu komai, ina jiran su hajiya ƙarama su dawo ne na wanke mata uniform shikenan na ƙare aikina, saboda inaso na gama da wuri ne fita" "Ina zakije?" "So nake naje na duba ɗana a makarantar su, kinsan jiya aka kawoshi asibiti ba lafiya, kuma ɗazun nakira malaminsu bai ɗaga waya ba, shine nakeso naje na dubashi idan na gama aikina" "Tau ai kin gama aikin kho, ko meya rage, akwai wani abu da baki yibane?" "Ehh hajiya nagama, wankin uniform ɗin hajiya ƙarama kawai ya ragemin" "Wane uniform kuma? Badai waɗan da ke jikinta ba" "Ehh hajiya su" "Dayammah kenan wankin uniform ɗin khulud sune zasu hanaki zuwa duba yaronki, dan Allah tashi kije kawai hala sauran uniform ɗin nata ba wankakku bane?" "Ehh hajiya wankakku ne amma..." "Amma me ki tashi ki tafi kawai kinji bara na ɗauko tsarabar mara lafiya" "Nina tsayarda ita mum, Ni nace tajirani" khulud ta faɗi maganar tana shigowa parlourn da leda a hannunta pa, kuma yana biye da ita. Bata ƙara faɗar komai ba ta wuce bedroom ɗin ta. Dayammah kuma ta bita a baya har suka isa bedroom ɗin ta, khulud bata tsaya ba sai da takai kan gado sannan ta zauna gefen gadon. Dayammah kuma ta shigo bakinta ɗauke da sallama, khulud ko ɗaga kanta batayiba balle ta amsa mata. Ɗan wuri ta samu ta tsaya tare da kafe idanun ta waje ɗaya saboda tasan komai tayi zai zamo laifi wajen khulud. Buɗe ledar da ta shigo da ita tayi tafito da hollandia yoghurt tare da pizza, ta fara ci. Harta gama cin abincin bata kalli dayammah ba balle ta saka ran zata yi mata magana. Baby taddy ta ɗauko ta fara yimata tawai tana wasa da ita kamar bata san da mutum a wajen ba "Hajiya ƙarama ke nake jira dan Allah ki cire ki bada na wanke miki" "Okay kibari idan nagama wasa sai na cire nabaki" "Haba hajiya ƙarama wallahi inada uzurin fita kibari idan kika cire uniform ɗin sai kici gaba da wasan" "Nace miki ban shirya ba idan zaki jira ki jira, idan bazaki iya ba ga hanyar nan" "Kina nufin na tsaya ina jiranki har sai kin ƙare wasa sannan ne zaki ban uniform na wanke miki" "Mtswwww so if you can't wait for me them you go and came back later" "Dan Allah hajiya ƙarama karkiyimin haka kicire kibani kawai wallahi fita zanyi idan kuma nadawo nagaji wallahi saboda tafiya mai nisa zanyi" Tsaki ta kuma ja sannan taci gaba da wasan ta batace komai ba. Cikin jin haushin abunda khulud tayi mata, ta kama neck tie ɗinta da nufin ta cire mata uniform ɗin ita kuma khulud ta riƙe hannuta" Wani sakaran ihu khulud ta ƙwala har takai ga mum da papu sun shigo ɗakin da gudu "menene haka" papu ya tambaya a harziƙe. "Pa marina tayi sannan ta shaƙemin wuya wai saita kasheni tunda na saka kayi mata faɗa" Khulud tayi magana tana dafe da kumatunta haɗi da matsar kwalla. "Dayammah khulud kika mara?" "Wallahi na rantse da Allah Alhaji ban mareta ba ban yimata komai ba" "Ƙarya zata yimiki ne ki duba ki ga yanda take kuka fa" "Pa wallahi ta mareni bana ma gani da idon nan nawa na bangaren dama" Da sauri mum ta zagaya tare da riƙeta tana jijjigata kamar wata ƙaramar yarinya. "Wallahi pa bana gani da idanun nan sau biyu ta mareni" "How dare you slapped my daughter in our house, kina matsayin ƴar aiki zaki zo har gidan mu ki dakarmin ƴa, yazama dole kibar gidan nan yanzu-yanzu" papu yafaɗa cikin ɓacin ra. Da sauri mum ta miƙe zatayi magana"karki sake kice komai hajiya fanaya na riga na yanke hukunci, ko don bake akayiwa haka ba shiyasa kike nema ki kareta, to wallahi na riga na gama magan dayammah bazata zauna a gidan nan ba tunda har tayi tsaurin idon dukan ƴata a cikin gidan na" Kamar yanda papu yace mum bata furta komai ba, dayammah ke kuka kamar ranta zai fita tana rokon papu da khulud suyi hakuri. "ki tafi na riga na gama magana ko so kike na kira a fitar dake gidan nan" Jiki na rawa ta tashi ta fita ɗakin domin kuwa papu yaɗau zafi ba kaɗan ba, ganinsa a haka ya tsora tarda ita sosai, shiyasa tayi gaggawar tashi ta fita ɗakin, tana fita kuwa tanufi part ɗin da aka ware mata agidan ta fito da duk abunda tasan nata ne tabar gidan tanata kuka, ma aikatan gidan da dama sunji ciwon barin dayammah gidan yayinda wasu suke cike da murnar barin gidan da tayi. Zaune a parlour mum ce da papu sai kuma khulud da suka sakata tsakiya, papu sai leka fuskarta yakeyi yana duba idanunta. "Mamana nace kizo muje hospital a duba idanun nan kinƙi" "Ni bazanjeba pa, tunda ta riga ta cuceni da dai ramamin za'a yi a hospital ɗin danaje amma tunda ba ramamin za'a yiba ni bazan je ko ina ba gaskiya" "Justice nifa har yanzu zuciyata taƙi aminta da wannan lamarin, wai dayammah ce zata ɗaga hannu ta mari khulud gaskiya nidai ban yarda ba, da dai ka tsaya kayi bincike kafin ka yanke hukunci" "Hey idan ma batayi, yau ɗin tayi ƴarmu bazata yimana ƙarya ba tunda bata saba yimana ƙaryan ba, kinga kho bazatayi ba saboda mutum ɗaya idan baki yarda da abunda tace ba sai kiyi shiru da bakin ki" papu yayi maganar a hasale. "Ke da gaske kike ta mareki" "Ehh mum Wallahi da gaske nake marina tayi har sau biyu, kuma wasu lokutan idan bakwanan dukana take sannan tace idan na sake na gayamuku ta dukeni saita yanka Ni" "Kinji kho, kinji ma har dukanta takeyi idan bama gidan nan kuma tana barazanar zata yankata, na rantse bazata dawo gidan nan ba, kuma bazata ƙara aiki a gidan nan ba" papu ya faɗa yana wucewa part ɗinsa fuuuuu kamar shi aka mara ba ulud ba. "I'm so sorry mamanah, bayan mari me tayi miki?" "Marina kawai tayi mum" "Ya idanun yanzu?" "Suka kawai nakeji sunayimin yanzu mum" "Kiyi hakuri kinji" "Okay mum" "Na ajiye miki wani abu mai kyau muje ɗakina na baki" "Thank you mum"khulud ta faɗa tana murmushi mai bayyanar da haƙora. "Ur welcome my baby" faɗin mum tana rungumo ulud a ajikinta. * * * * * * LEEYA... Kwance take a inda tayi bacci tunjiya, wato bakin titi kusa ga wani ɗan karamin gida, juye-juye ta farayi yayinda hayaniyar mutane da kuma na abin hawa suka fara dira a kunnuwanta. tashi tayi daga kwancen da take ta buɗe idanun ta tarrr kan inda ta tsinci kanta a yanzu kuma. "Yanzu a nan na kwana" "To wazaki tambaya ai kinsan nan kika kwana tunda kin tashi kinga kanki anan" Wata zuciyar ta bata amsa. Addu'ar tashi daga bacci ta karanta sannan ta miƙe tsaye. Zaninda ta kwanta da shi ta yaye, kana ta kaɗe kurar da ke kan zanen ta ninke shi ta maidashi cikin jakarta. Randar ruwa ta hango gaban gidan da ta kwana, tana hangota ta nufi ranar ta tsoma kofin da tagani ciki sannan ta ɗibo ruwanda ke ciki. wata ƙaramar gora ta janyo ɗan nesa da ita kaɗan ta zuba ruwan a ciki sannan ta koma chan gefe inda mutane basa hangota sosai sai tayi alwala, bayan ta kammala alwalan ne ta dawo inda ta ajiye jakarta sannan ta fito da sallahya ta shimfiɗa ta tada sallah. cikin nutsuwa tayi sallarta har tagama ta zauna ta fara azkar. Gama azkar din keda wuya zazzaɓi mai zafi ya rufeta. anan inda tayi sallah nan ta kuma kwanciya sannan ta ƙara janyo zani daga cikin jakarta ta lulluɓe jikin ta dashi, domin har sanyin zazzaɓi ya kamata. Wata farar mota ƙirar RANGE ROVER ce tayi parking dai-dai inda leeya ke kwance, sauke glass ɗin motar akayi yayinda matuƙin motar tausayin ta ya kamashi yaɗan cije lips dinsa kaɗan, kana ya girgiza kansa a hankali. Kamar mai nazarin wani Abu. Ya ɗauki ƴan sekonni yana nazarin leeya kafin ya tuƙa motarsa yayi gaba. Tana nan kwance a wajen har rana ta hudo ta fara taɓata, anan aka samu masu imani da sukazo suna tambayar abunda yasa take kwance anan kuma cikin rana, sai take gayamusu batada lafiya ne shiyasa. Cikinsu aka sami wani bawan Allah da yaje yasiyo mata magani harda abinda da zata ci. Godiya tayi masa sosai inda mutumin bai tafi ba har sai da yaga taci abincin tasha magani. Sannan yayi mata iznin ta tashi daga nan ta koma ɗan gaba da gidan kaɗan saboda nan ne ba rana sosai. Kayan ta ɗauka gaba ɗaya tare da barin wajen ta koma inda mutumin ya nuna mata taje chan taci gaba da zaman ta. A Kwana a tashi har ta share tsawon sati ɗaya da kwana biyu, alhmdullillah jikinta yayi sauƙi sosai idan ka ganta ma zakayi tunanin ita ce ke zazzaɓi a kwanakin da suka gabata ba. A tsawon waɗan nan kwanaki da ta ɗauka ba wanda ta samu ya taimake ta ko kuma ya bata abinci. Ita take siyawa kanta komai na bukatar ta har kuɗin suka ƙare ta rasa yanda zatayi. Shine ta yanke shawarar ta fara tsintar goruna tana saida wa, da kuɗin nan da take samowa da su take cin abinci. Yauma ta shirya ne da nufin taje tayi tsintar goruna domin ta samu abunda zata ci, tsaye take bakin titi tsayuwar ta kuma yayi daidai da lokacin da akayiwa wasu motoci alamar da su dakatar da tafiya. cikin wurin ta kutsa ta fara tsintar wasu abubuwan da tana da tabbacin zata sami inda zata siyar dasu. Ta gaban wata mota ta wuce da nufin ta ɗauko wani abun data hango. Mace ce mai tuƙin motar. Matar da ke tukin kuma tana ganin leeya ta gifta ta kafeta da idanu sosai kamar mai nazarin wani abu ajikinta. A back sit kuma na motar wata ƙaramar yarinya ce sanye cikin school uniform ɗin ta, glass ɗin back sit ɗin yarinyar ta sauke ta fito da emptyn gora ta jefota waje. Sakamakon lura da tayi da kallonda matar da suke tare keyiwa LEEYA. Aikuwa leeya na ganin an cillo gora ta rugo aguje ta ɗauki gorar tare da sakata cikin buhun da take yawo dashi. "Mum what are you staying at? we are just parked hare and you don't traffic, please can we go home I'm really tired" faɗin yarinyar da ke tare da matar da ta zubawa leeya idanu kawai. "I'm sorry my kid nima haka kawai na tsinci kaina da kallonta wallahi" glass ɗin motar ta ɗaga ta tayar da motar sukaci gaba da tafiya. "Mum" "Na'am mamana" "Me abunda kikayi yake nufi?" "Wane abu kuma" "Saboda me muka tsaya kina faman kallon yarinyar chan bayan kuma an bada damar ko wace mota ta wuce?, she's dirty girl, kuma almajirace fa" "Common, ki daina mana my kid bana jin daɗin irin ɗabi'un nan naki" "Mum, how can you be concerned about total strangers, mum ke ba talaka bace taya zaki damu da lamarin talakawa" "Khuludddd! Please ki gane Allah shi yake ba kowa mana" "Okay mum amma gskiya ki daina irin haka banaso, idan kika ci gaba da kallon wasu talakawan haka ai za'a yi tunanin ko a cikin dangin mu akwai talakawa, especially yarinyar nan mai mayafi danaga kin tsurawa ido yanzu" "Yi hakuri my kid bazan ƙara kallon suba kinji, are you happy now" "Uuuhhhm maybe, let's go home" Tana gama faɗin haka mum taja motar suka bar wajen. ******* Tsaye take jikin wani baho da aka zuba shara bakin wani gida, hannunta ɗaya riƙe da buhun da take saka gorunan ta, ɗayan hannun kuma riƙe take da guntun siririn ice mai dan tsawo da langwasa tana tonon sharar da ke cikin babban mazubin shara da ake ajiye wa, duk abunda tasan za'a siya idan ta ganshi a sharar saita sakashi a buhu. Haka takeyi tsawon wuni, taje nan ta dawo chan har sai da ta sami abunda zata ci. Bayan ta tsinci abunda zata tsinta a wurin sai tayi gaba, saida tayi tafiya mai nisa a unguwar kafin ta cimma wani makeken gida. "Masha Allah, gskiya wannan gidan kam ya haɗu Allah yasa masu shi su more" Leeya ke maganar a zuciyar ta. ƙara saurin tafiyar ta tayi lokacin da ta hangi bahonda ake zuba shara har biyu bakin gidan kuma suna cike maƙiil. Da sauri ta isa tayi tsince-tsincen da zatayi, sosai ta sami abubuwan ta a wurin ba abunda ta bari sai wanda bata amfani dashi domin kuwa buhun da tazo dashi ya cika tabb har ta samu igiya ta ɗaure idan bukatar hakan ta taso. Tayi farin ciki sosai da faruwar wannan al'amari harta ƙudurce a ranta kullum idan ta taso da wajen da take kwana bazata ƙara biyawa ta ko'ina ba, nan zata riƙa zuwa tana kwasar kayayyakinta. Har zata juya ta tafi ta hango ɗayan bahon na shara irin wannan a guje ta isa wurin da ɗayan bahon yake, Isarta wajen yayi daidai da fitowar wani garjejen mutum mai gadin gidan. Mutumin ya kalleta ya daka mata tsawa, "ke!, me kikeyi anan?" "Ba komai ba, kayan bola nake tsinta" "Ƙarya kike yi ɓarauniya ce ke, shiyasa kika rufe fuskar ki dan kar a gane ki, mai yuwa ma kece kika sace ƙaramin generator da aka kunna a masallaci jiya, da ga gani bakyada gaskiya gashi ko Magana kin kasa". Kuka ta fashe dashi jiki na karkarwa, duk ta tsorata da jin an laƙa mata sata daga isowarta wurin, sata ma ba ƙarama ba, Karo na farko taji danasani ta mamaye mata zuciya. "Wallahi thumma tallahi bani bace, bani bace ni ba ɓarauniya bace, wallahi bamma taɓa zuwa nan ba sai yau, Ni Bama ƴar garin nan bace, ban san ma wane gari ba ne wannan na rantse da Allah" "Ohhh ba ke kika ɗauka ba" "Ehh wallahi ban ɗauka ba" ta faɗa tana kaɗa kai alamar ehhh. "Tau tunda bake bace kije kiyi abunda ya kawoki kiyi sauri ki tafi" "Tau na gode, nagode sosai" Ta faɗa tare da nufar bahon sharar da gudun ta. Mai gadin kho yana ganin haka ya janyo bulalar doki ya nufeta gadan gadan, dayake ita bata ganinsa saboda ta juya baya ne, shiyasa bata ganshi ba sai jin saukar bulalar take ajikinta ta ko'ina. Ihu ta fara yi tare da neman taimako, kuka take iya ƙarfinta. Da sauri mai gadin ya juya baya sakamakon ji da yayi an buɗe gate ɗin gidan da karfi. "Kai!, Lafiya me yarinyar da kake duka tayi maka?" "Alhaji irin waɗan nan yaran basai sunyi laifi ake dukansu ba saboda ɓarayine ire irensu" "Meta ɗauka yanzu?" "Me zata ɗauka dai, amma bata ɗauki komai ba tukunna" "Kai wane irin sha-sha-sha ne dazaka kama yarinyar mutane kana duka batare da tayi maka laifin komai ba" faɗin matar gidan da ke ƙarasowa bakin gate ɗin yanzu. "Ayi hakuri Hajiya Babba, nazata itace ta sace generatorn da aka ɗauke jiya" mai gadin ya faɗa yana sosa kansa. "Ka taɓa ganinta anan ne?" "Ah ah bantaɓa ganin taba" "Kana nufin cewa yaune na farko da ka ganta anan" "Ba shakka hajiya babba yaune na farko da na fara ganinta a nan" A tare papu da mum suka furta "kai wane irin wawane, yau ka fara ganin ta a nan shine zaka mata wannan dukan kamar ba wata dabba ko dabbarce ayi mata irin haka. wannan wane irin zalunci ne haka, ga yarinya ƙarama" "Bata ma motsi wallahi" cewar papu yana ƙarasawa inda leeya ke yashe duk ta galaɓaita. "Zo ki kamata mushiga da ita ciki, kai kuma wallahi idan ƴar mutane ta mutu sai kasan abunda zaka gayawa hukuma" mum ta faɗa cikin tashin hankali. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, taya zata mutu Alhaji wallahi ni ban kasheta ba ɗan kaɗan na doketa, wallahi dukan nan bazai kasheta ba, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un yau na bani na lalace Allah ka taƙaitamin wahala" mai gadin ke magana yana kuka kamar me. "Tsurawa leeya idanun mum tayi kafin tace Allah sarki nagane yarinyar nan justice" "Kin gane ta kuma?" "Ehh wallahi na ganeta" "Keko ina kika santa" "Jiya na ganta ɗan doma road tana tsintar kayan bola dana dawo daga daga school ɗin su khulud, wallahi justice dana ganta na tausayamata sosai, kuma yanda ka ganta da mayafin nan yanzu haka na ganta ko jiya ma, na jima ina kallon ta, har sai da khulud taji haushin haka, kuma haka kawai naji yarinyar nan ta shiga raina, naji tausayinta sosai" Jin an ambaci mayafine yasa papu ya ƙara kallon fuskar LEEYA, "Ikon Allah" papu ya furta yana jinjina kai. "Lafiya dai" "Lafiya lau, amma wallahi karkiyi mamaki idan nace miki nima na taɓa ganin yarinyar nan a haka" "Ka taɓa ganin ta kaima justice? ikon Allah, a ina?" "Wallahi a bakin hanya na ganta kwance batada lapiya sati ɗaya daya wuce, na ganta kwance tanata rawar ɗari. Nima saida nayi parking motata na tsaya ina kallon ta domin wallahi Allah Nima taban tausayi" Duk hankalin ya ɗagu sai mamakin yanda wannan al'amari ya faru suke, kawai sukaji tayi ajiyar zuciya, a hankali ta furta"wallahi ni ba ɓarauniya bace" Kallon su suka mayar kanta gaba ɗayansu cikin mamakin yanda akayi ta farka, mai gaɗin ne tsaye a kanta da robar ruwa a hannunsa, kana ganin shi kasan tsorace yake. "Allah ya ceceka ba mutuwa tayi ba wallahi daka yabawa aya zaƙinta domin ni ba ruwana wallahi" "Alhaji kenan dama na gaya maka ai ba mutuwa tayi ba" "Kai dai ka kiyaye idan ko ba haka ba kanason aiki gidan nan zaka barshi" faɗin mum dake janye da hannun leeya tana takawa da ita a hankali domin jikin ta duk yayi tsami. Juyawa papu yayi ya rufawa mum baya suka shige gidan, suka bar mai gadin kaɗai. Master parlour ɗin gidan suka isa da ita, suna isa kuwa papu ya wuce ciki yabar mum kaɗai da leeya. "Sannu, ya jikin?" "Jiki lafiya ƙalau ba abunda yasameni, nidai wallahi bani na ɗauki generator ba. Yau na fara zuwa nan wallahi bani bace dan Allah ki taimakeni sai kema Allah ya taimakeki" "Uhhhhm kwantar da hankalinki kinji, ba komai bane mun san ba ke kika ɗauka ba shima mai gadin yayi kuskure ne kuma ya gane kuskure yayi, kiyi hakuri kinji, yanzu kizo ki zauna na kawo miki abinci kici sannan kisha magani domin wannan dukan zai iya saukar miki da zazzaɓi" "Nagode sosai, Allah ya saka da alƙairi, na gode kwarai da gaske". Ƙarar buɗe ƙofar da akayi ne yasa mum ta mayarda hankalin ta kan ƙofar domin ganin wanda ke shigowa "Awwwwn my kid you're welcome" Cewar mum fuskar ta ɗauke da murmushi, tanayiwa khulud barka da zuwa. khulud kuma tana shigowa master parlour ɗin jikin ta sanye da uniform ta dawo daga school kenan. "My sweet mum, wacece wannan? Khulud ta tambaya tana watsawa leeya wani wulaƙantaccen kallo. "Baƙuwa ce" "Baƙuwa!?, wurin wa tazo a gidan nan ? Kodai ba gidan nan ba mistake tayi kho naga ba talakawa a gidan nan da wannan yarinyar zatazo nema" Mum na shirin magana saiga papu ya fito, "my princess u're welcome, ya school" "School ba daɗi pa" "Haba dae mamana school ɗince ba daɗi" "Ehh wallahi pa, babu daɗi za'a ce ai, karatu kam ae ba daɗi ne dashi ba" "Humm, mamana kenan karki damu zakiji daɗinsa nan gaba kinji" Taɓe baki kawai tayi ba tare da tace komai ba. Kallonsa ya mayar ga leeya wacce ta soke kanta ƙasa, bata san me akeyi ba muryoyinsu kawai takeji, jin kowa yayi shiru ne yasa ta ɗago kanta, ganin papu na kallonta sai kunya ta kamata saboda tasan koba komai yakamata idan taga kamar sa a waje ta gaida shi, balle gata har a gidan shi bata gaidashi ba. "Barka da rana, an wuni lafiya" leeya ta faɗa tana durkusawa ƙasa daga zaunen da take. Ɗan murmushi papu yayi kana ya amsa mata "lafiya lau, ya kike jin jikin naki, dafatar bai jimiki ciwo ba kho?" "Ehh ba inda ya jimin ciwo gskiya" "Tau tashi ki zauna mana durkushen ya isa haka" Miƙewa tayi ta zauna sannan ta mayarda kanta ƙasa yanda tayi a ɗazu. "Gashi ko sunan ki bamu sani ba" mum ta faɗa tana kallon leeya. "Sunana LEEYANA" "Masha Allah, nice name LEEYANA, a garin nan kike?" "Ah ah ba garin nan nake ba, Ni bansan ma wane gari ba ne wannan" Zaro ido mum da papu sukayi, itako khulud ba abunda take sai aunawa leeya harara duk maganar da zatayi. "Kamar ya bangane ba, harsu iyayen naki basusan wane gari ba ne wannan?" Mum ta tambaya. "Ae ni banada kowa" "Bakyada kowa kuma kina nufin ke marainiya ce?" "Ehh ni marainiya ce banada kowa" leeya ta faɗa Muryar ta na cracking. "Allah Sarki, yi hakuri kinji. Dan Allah zan iya jin kaɗan daga labarin ki?. Cewar mum tana gyara zaman ta. "Me zai hana" leeya ta faɗa ataƙayce, gyara zaman ta tayi itama kafin da kwashe labarin ta kafff dagayawa mum. Amma iya labarin Nnene da uchie da kuma Aleena ta gayamasu, kuma bata sanardasu ba su bane iyayenta. "Allah Sarki gaskiya leeya na tausayamiki matuƙa" "Uhum hajiya fanaya wallahi bake kaɗai ba nima na tausayawa wannan labarin nata musamman ma yanda mutane ke gudunta babu dalili" "Ahhh justice ya zakace babu dalili bayan ga dalilin nan a fuskar ta, wannan mayafin da take sakawa" "Ehh hakane kam, amma meyasa kike ɓoye fuskar ki leeyana?" Papu ya tambaya yana kafeta da ido. "Wallahi Alhaji nima bansaniba koda na girma nayi wayo naganni da mayafin nan, kuma a duk lokacin da na tambaya ran mahaifiyarmu yana ɓaci shiyasa nadaina tambaya, wallahi koni kaina bansan yanda fuskata take ba saboda har kallon madubi banayi ta hanani. Tace na ɗaukar mata alƙawarin bazan taɓa buɗe fuska ta ba sai ranar da aka ɗauramin aure, ko kuma idan na tabbatar da aurena da wanda zai aureni ba mahani sai Allah to na buɗe, Ni kuma na ɗaukar mata alƙawarin haka". Cikin mamaki mabayyani mum ta kalli papu da yayi tambayar, shima ya zuba mata ido kawai tsawon mintuna ba wanda yace kanzil cikin su, sai mum ce tayi magana "yanzu shikenan aleena ta mutu" "Ehh" ta faɗa tana sakin wani siririn kuka ta chusa kanta tsakanin cinyoyinta. "Ayyah, yi hakuri kinji ki daina kuka addu'a kawai take buƙata ba kuka ba Dan Allah ki daina kuka kinji". "A ina dangin ku suke"cewar papu. "Wallahi nima bansaniba amma mahaifiyarmu na gayamin mumada dangi muma amma bantaɓa ganinsu ba" "Idan na fahimta kema bakisan dangin naki bakho?. Ɗaga masa kai tayi alamar ehhh, Daga nan papu bai ƙara faɗar komai ba yaje kan sofa ya zauna. "Zaki iya zama damu a nan tunda bakida kowa?" A rikice khulud ta kalli papu kafin ta maida kallon ta ga mum da tayi maganar "WHAT!!!?, mum, you agreed to let her in to this house, papu kaima yarda zakayi ta zauna? Stranger, can't see her dirty mum? Bakya ganin yanda take ne hala? kuma zakice ta zauna damu a nan gidan" Karo na farko da leeya ta ɗago kanta ta kalli khulud, sannan ta sake mayarda kanta ƙasa. "Maman khulud zamu iya hawa sama inaso nayi magana dake" "Me zai hana justice muje saman" Mum da papu suka miƙe suka bar wajen, wurin yarage daga leeya sai khulud kawai. Miƙewa leeya tayi daga wurin da take zaune ta nufi inda khulud take, "sunana LEEYANA HAMRAZ AWAIS and you are...." Leeya ta faɗa tana miƙawa khulud hannu. Miƙewa khulud tayi itama tare da saukar da back bag ɗin da ke rataye a bayan ta, a tsawace ta fara magana "NO one case what your name is, and now listing up, let's me told you, who ever you are and what ever plan is, it will never ever work, and won't allow peasant like you in this house. it's the profound innovation of senselessness for you to think, I khulud Khattab waasib na saka mutane da dama sun bar gidan nan kuma waɗanda suka fiki komai balle ke ƙaramar alhaki" "Haba, it's young for you to do that my sister..." "I'm not your sister mtswww, taja tsaƙi ta tare da ɗaukar lunch bag da kuma back bag ɗinta ta wuce fuuuu tabar leeya ita kaɗai a wajen kamar an dasata...✍🏼 BAYAN WUYA... By RUMANA M DIGGI EP.10 .................Bangaren mum da papu kuma suna isowa upstair papu ya dakatarda mum da faɗin "hajiya fanaya kinyi tunanin abunda kika aikata kuwa, zamu iya yarda da ita a wuni ɗayan nan, kinga Ni ba abunda nakasa yarda dashi tattare da ita yanda take ɓoye fuskar ta. "Wallahi kuwa justice amma ya zamuyi muyi haƙuri kawai mu riƙeta mugani mai hali ba zai ɓoyuba, kuma Allah yaga niyyar mu ta alƙairi koda tayi niyyar cutar damu Allah zai dubi nufin mu ya kuma kare mu daga sharrinta idan ma ta kasance tanada shi, saboda haka mubarwa Allah komai kawai mu riƙeta da zuciya daya". "Toh shikenan Allah ya karemu da koma menene, idan kuma alƙairi ce Allah ya haɗamu dashi, amma kuma wata matsala ɗaya yanzu khulud" "Khulud kuma justice me khulud ɗin tayi?" "Hmmm hajiya fanaya kenan kardai kice min baki kula da duk abun da khulud keyi ba da wani kallon da take yiwa baiwar Allah nan, na santa sarai zata iya cewa bazamu zauna da ita ba" "Haba justice to kana nufin me kenan?, idan khulud tace bazata zauna da ita ba shikenan yana nufin bazamu zauna da ita ba" "To hajiya ta ya zamuyi kin san matsalar fa, yanzu idan na kasa yimata abunda takeso ranta zai iya ɓaci, idan kuma ranta ya ɓaci ciwon ta tashi zai yi. Wallahi kinsan bana son haka ta faru shiyasa nake duk wasu abubuwa dan kiyaye haka, Nima kaina nasan bana kyautawa wani ɓangare amma uzuri kan kauda uzuri" "Duk da haka a wannan karon baza'a biye mata yanda takeso ba, shikenan saboda tanada ciwon zuciya ta riƙa yin komai yanda takeso gaskiya a wannan karon kam bazatayi haka ba domin yarinyar nan bazata bar gidan nan ba" "To Allah ya yayi mana alƙairi" "Amin ya rabbbi" mum ta faɗa. Shigewa papu yayi ɗakinsa ita Kuma mum ta sauƙa ƙasa "leeya lapiya na ganki tsaye alhali kuma zaune na barki" Da sauri leeya ta durkusa ƙasa "lafiya lau hajiya bakomai kawai nagaji da zamane na ɗan tashi tsaye" Ɗan murmushi irin na manya mum tayi ko ba'a gayamata ba tasan akwai abunda khulud tayi mata saboda daga ita sai khulud suka bari a parloun "amma kuma naji muryarki kamar mai shirin yin kuka" Murmushin yaƙe mai sauti leeya tayi sannan tace "wallahi hajiya ba komai" "Okay tau yayi amma daga yau kidaina kirana da hajiya kinji" "To mezan dinga kiran ki?" "Ya kikaji waccan yariyar takirani?" "Mum" "Haka zaki riƙa kirani daga yau Ni mum ɗinki ce kinji, justice kuma papun ki, khulud kuma sistern kice, sai kuma babban yayanku dake can Mexico yana karatu, nan ba da jimawa ba zai dawo" "Okay mum in sha Allah zanyi yanda kikace, Bama yanda kikace ɗin kaɗai ba zan ɗaukeku ƙwatankwacin yanda kuka ɗaukeni domin har fiye da yanda kuka ɗaukeni in sha Allah" leeya ta faɗa cikin Siririyar muryarta mai cike da nutsuwa. "Tau yanzu kina jin yunwa sosai?" Girgiza mata kai tayi alamar bata jin yunwar sosai, "to idan bakyaji kizo muje sama na nuna miki part ɗinku inda zaki zauna, sai kiyi wanka kiyi sallah daidai an ƙare abincin rana sai ki fito daining area idan kikayi lunch sai ki koma ki huta kinji" Har ƙasa leeya takai tana yiwa mum godiya, ɗagota mum tayi daga kasan kana ta jata suka nufi inda zata zauna, a part ɗin khulud ne saidai ko a cikin part ɗin akwai ɓangarori daban-daban kowa kuma da ɓangaren sa. Anan mum ta shiga da ita wani ƙasaitaccen ɗaki wanda komansa iri ɗayane dana khulud, sosai leeya tasha kallo a wannan ɗakin har tana gani kamar mafarki take ba ita bace yau zata kwana a ɗakin nan ba, kuma ita kaɗai "mum nanne ɗakin?" "Ehh ko bai yimiki ba a changer miki wani?" Da sauri tace "ah ah wallahi ba haka nake nufi ba, kawai dai ina mamaki ne wai nida ba kowa ba, ba kuma kowan kowa ba nice zan kwana a ɗakin nan nikaɗai gaskiya mum bansan da wane baki zan iya gode miki ba Nagode, Nagode sosai Allah ya biyaku". "Ameeen, yanzu kizo na nuna miki ban ɗaki kije kiyi wanka ki fito, kici abinci kinji" "Tau muje mum" Mum gaba, leeya kuma tana baya har suka iso kofar ban ɗakin mum ta nuna mata ita kuma ta shige ciki, ta ɗauki lokaci sosai a ban ɗakin tun mum na jira ta fito har ta gaji da jira ta sarkafa mata towel ta fice daga ɗakin. leeya na fitowa ta ɗaura towel ɗin ta iso gaban mirror ta zauna, har yanzu dai mayafin na fuskar ta amma ko da kuskure bata yarda ta kalli mirrorn ba balle taga yanda fuskar ta take ko a cikin mayafin. saida ta kammala shafe jikinta tsaff da mai, sai kamshin takeyi duk da bata saka perfume ba amma kamshin man da ta shafa ya game ko ina cikin ɗakin, mum ce ta shigo ɗakin da sallama, hannuta riƙe da kaya, doguwar rigar ƙanan kaya mai adon stones ƙanana ta ɗan mayafin rigar da ake ɗaurawa idan an sakata. "Har kin fito kenan" "Ehh mum nafito" "Tau ga kaya nan ki saka idan kin gama ki sakko ƙasa kizo daining kici abinci kinji" "Okay mum, Nagode sosai" "Kidaina min godiya kinji, nayine saboda Allah" "To Allah ya baki lada mum" "Ameen sai kin fito" "Okay mum" Mum na fita leeya ta miƙe ta zura rigar, rigar kuwa tayi mata chif-chif, amma a jiki saidai bata ida kai mata ƙasa ba. Mayafin rigar ta ɗakko sannan ta cire wanda ke fuskarta, nan take gashin ta ya zubo gaba ɗaya, kama gashin tayi tare da mirɗeshi waje ɗaya, sannan ta laulaya mayafin rigar a fuskar ta, amma da yake mayafin bayada girma sosai sai bai rufe mata kanta gaba ɗaya ba. Tafiya take a hankali cikin natsuwarta ta sakko ƙasa, tana sakkowa ta nufi daining area ta zauna koda ta isa ba kowa amma ga abinci nan an jera kala-kala. A ƙa'idar gidan gaba ɗaya indai ka kasan ce ɗan gidan ne kai ba ɗan aiki ba to tare ake zama gaba ɗaya a ci abinci. Tana nan zaune a haka tah ɗauki kusan mintuna goma kafin papu ya iso wajen yana isowa kuwa ta tashi da sauri ta isa gaban shi, "papu barka da rana" "Barkanki dai ɗiyata ya jikinki" "Ni ba abun da yasameni papu" "Ah Masha Allah, idan kinci abinci yanzu kije ki huta kinji, anjima da yamma zaku fita da mum ɗinku tayi miki shopping ɗin kayan sakawa kinji" Ƙara durkusa wa tayi har ƙasa sosai ta fashe da kuka, a cikin kukan ne take yimasa addu'a da fatar gamawa da Duniya lafiya. "Tau ki tashi ki zauna godiyan ya isa haka kho" Komawa tayi wajen zamanta ta zauna, sannan ta soke kanta ƙasa tana murza yatsunta, "ki tashi kije part ɗin mum ɗinku ki kirata" "Wallahi papu bansan inane part ɗin ta ba" "Aww hakane fa" "Amma ka kwatantamin zan gane in sha Allah" "Ok tau idan kika hau sama hawa na biyu bangaren hagu nan ne part ɗin ta, dakinyi knocking zatayi fito" "Tau yayi papu, yanzu kuwa" Miƙewa tayi ta nufin saman step ɗin sai kusan gab da zata shiga part ɗin na mum saiga mum ta fito "Ahhh ƴata ina zakije?" mum ta tambaya tana shafa kan leeya. "Mum papu ne yace na kiraki kizo, kuma khulud ma bata fito ba" "Ayyah sorry na barku kunata jira kho, gani nan tafe Bara naje part ɗin ku na kira sistern ki yanzu kinji" "Okay mum a fito lafiya" Leeya na gama faɗin haka ta juya ta koma ƙasa, ita kuma mum ta bi hanyar da zata sadata da part ɗina khulud, tana Isa part ɗin ta fara ƙwala wa khulud kira har ta iso ƙofar ɗakin ta, "Khulud!×2" "Gani nan" khulud ta faɗa a takaice tana fitowa daga bedroom ɗin ta. Juya kanta tayi gefe ko kallon mum bata ƙara yi ba. "Gayamin bakya buƙatar leeya a gidan nan ne nasan duk dan saboda ita ne kika ƙi fitowa cin abinci, kuma nasan saboda ita ne kike wannan fushin kho? Gayamin meye matsalar" "Uhmm first of all mum, she's stranger, and again she's extremely poor girl, she picked the bottles on the street and I will never ever share my father's house with her. Bazan taɓa haɗa wurin zama ɗaya da talaka ba haba dai mum wannan ai raini kika janyomin wallahi" khulud ta faɗa tana huci. "Ajiyar zuciya mum ta sauke a fili kaana tace "saboda leeya ta zauna a gidan nan bashi zai saka a dinga kiranta da sunan gidan nan ba, ba kuma shi zai saka dangin ki su ɗauketa yanda suka ɗaukeki ba, na taimakawa rayuwar leeya ne kawai sabida girmanta bakai yanda za'a kyaleta ta riƙa yawo kan titi tana tsince tsince ba, dan haka dan allah ki sakawa zuciyarki salama ku zauna lafiya keda ƴar uwarki kuma yayarki" "Never mum, bazata taɓa zama yayata ko ƴar uwata ba bazata taɓa zama ba, i was born to be great I'm not being suffer" faɗin khulud tana ƙara juya kanta gefe. "Ohh Bara na gyaramiki maganar ki, ba wanda aka haifa domin yasha wahala, yanayi ne kaɗai zai iya mayarda mutum haka, so munada abunda zamu taimaki mutane me zai hana mu taimake su ɗin my kid" mum ta faɗa cikin sigar rarrashi. "Mum idan taimako zaki bata ki bata taimakon ta tafi mana, amma bazata zauna a gidan nan ba" "Wai meyake damunkine khulud meyasa kike haka? Meyasa!?? this is not my child, kina ɗabi'arda bata dace ba, wannan halin yayi yawa a shekarunki khulud, meyasa? To bara nagayamiki, ba inda leeya zataje tana nan a gidan nan this is the final". "Okay mum" khulud ta faɗa tana rolling eyes ɗinta. "Khulud ni kike yiwa haka, ina yimiki magana kamar bani na haifeki ba..." "Sorry" Faɗin khulud tun kafin mum ta idar da maganar da zatayi. "Hmmm zomuje kici abinci" "I'm satisfied" ta faɗa tare da juyawa ta koma ɗakinta. Zuciyar mum kuwa kamar ta zage ta fito waje saboda bakin cikin halaye da kuma ɗabi'un khulud ƴarta mace tilo. domin kuwa yau ta tabbatar khulud bata tsoronta, a ranta take gani kamar ma ba laifin ita khulud ɗin bane laifin papu ne daya sakkamata komai takeyin yanda taga dama, tana cikin tunanin ne harta sauka ƙasa ta isa daining area, har yanzu kuma leeya da papu na zaman jiranta. "Ina khulud?" Abunda yafito daga bakin papu kenan. "Tana ɗakinta"mum ta bashi amsa "Meya hanata fitowa?" "Tace ta ƙoshi da abincin" Murmushi kawai papu yayi domin yasan abunda ya kawo wannan. "Leeya!" "Na'am papu" "Ki zuba duk kalar abincin da kikeso kici, idan kin gama sai ki zubawa khulud nata ki kaimata ɗakinta". Da sauri leeya ta ɗago kai zatayi magana sai kawai ta fasa maganar batace komai ba ta mayarda kanta ƙasa. "Leeya bakiji justice na Magana dakeba" Ƙara ɗago kai tayi karo nabiyu domin shafff ta manta bata amsa masa ba. "Lahh papu Dan Allah kayi hakuri wallahi a zatonda nake ma na amsa maka, bara ma naje yanzun na kaimata ai". "Ah ah ki bari ki gama kawai batajin yunwa ai, baki ji abunda tacewa mum ɗinku ba" Daga nan ba wanda ya ƙara faɗar komai har suka kammala cin abinci. leeya ce kaɗai zaune a daining area taci abinci sosai ta ƙoshi, sai kuma ta haɗa wa khulud nata Kamar yanda papu ya umurce ta tayi. tana gama haɗawa ta tashi taje ta kaimata. Tura kofar ɗakin tayi bakinta ɗauke da sallama, gabanta na duka uku-uku, domin haka kawai takejin tsoron khulud sakamakon abunda tayi mata yanzu. Ba kowa a ɗakin, ɗan ƙaramin table dake gaban fabric-bed sofa ta ajiye babban faranti da ta sanyo mata abincin, Exercise book ɗinda tagani kan bed ta nufa tare da miƙa hannu ta ɗaukeshi, ta fara buɗewa "Allah sarki khulud, ta faɗi a assignment ɗin nan, da ace ina nan lokacin da tayi shi dana taimakamata dan naga kamar bata fahimci topic ɗin nan ba" Duk da ƙarar buɗe ƙofar da taji hankalinta bai kawo ta daga kanta taga waye ba domin gaba ɗaya hankalin ta nakan littafin khulud na mathematics da take buɗewa. Wani irin wawan fizga khulud tayiwa littafin ta da ke hannun leeya "what are you doing?" "Nothing" Ɗan waro ido khulud tayi domin batayi tunanin leeya najin turanci ba, amma sai ta ɓoye mamakin ta dan kar leeya ta fahimta. Cikin tsiwa da bala'i irin nata ta fara magana, "What do you mean by nothing, what are you staring at my book? By the way, who gained the you access in to this room without knocking?" "Papu ne yace na kawo miki abincin ki" "Then you bounty yourself access?, nagayamiki kifita harakata a gidan nan amma kin ƙi kho, ki tashi ki ɗauki komatsan da kika shigo dasu kifitar min ɗaki" "Allah ya baki hakuri" shi kawai leeya ta iya furtawa sannan ta ɗauki farantin da ta shigo dashi ta fito, sosai taji ba daɗi abunda khulud ta yi mata amma ta kuɗuri niyar yin hakuri da koma meye. Leeya na fitowa daga bedroom ɗin khulud ta dawo daining area ta haɗe kaf kayayyakin da suka ɓata ta shiga kitchen ta wanke su fess, kaana ta dawo ta gyara daining ɗin tsafff kamar ba'a ci abinci kanshi ba. tana gamawa ta koma ɗakin da aka bata shima ta gyarashi, toilet ta shiga ta ɗauro alwalar sallar la'asar tazo ta tada sallah, tana fara sallahn ne sai ga mum ta shigo, bakin gadon ta zauna saida leeya ta kammala sallah sannan tayi addu'a "mum barka da yamma" Da murmushi a fuskar mum ta amsa mata "yawwa barkan ki dai leeya, ya gajiyar aiki kuma? Naga duk aikinda kikayi, gaskiya kinyi ƙoƙari. Allah yayi miki albarka" "Ameeen ya rabbi mum Nagode sosai" "Idan kin gama abunda kike kiyi wanka kizo muje shopping ki zaɓi Kayan da kikeso na sakawa" "Tau in sha Allah idan nayi wankan zaki ganni mum Nagode sosai, Allah ya saka muku da alƙairi" " Ameen amma ki daina yimana Godiya haka mana ki ɗaukemu matsayin iyayen ki, ba komai zamuyi miki kina yimana Godiya ba kinji" "Uhmm tau mum zan gwada na ga ko zan iya dainawa kamar yanda kikeso" "Ki tashi kije kiyi wankan ina nan ina jiranki bara naje na gayawa khulud itama ta shirya" A ɗan razane leeya ta ƙara kallon mum jin da khulud za'a fita, sai takeji kamar tace bazata iya zuwa ba amma idan tayi haka kamar ta watsa musu kasa a ido. "Akwai matsala ne? Naga yanayin ki ya changer ko bakyajin daɗi ne" "Ah ah mum ba komai kawai na tuna da iyayena ne" "Allah sarki, kiyi hakuri kinji ki dinga yi musu addu'a kinji ɗiyata" "In sha Allah mum, Bama su kaɗai ba har da ku" "Madallah dake ɗiyar albarka, Allah ya karɓa" "Ameen mum" Daga haka mum ta tashi tabar bedroom ɗin na leeya. ******** Khulud kuwa tunda leeya tabar bedroom ɗin nata ta fito main parlour ɗin gidan inda ba sahun mutane ko hayani ya, ita kaɗai a katafaren parlourn wanda ya gaji da haɗuwa, sai kai da komowa take tana kumbura, sai dunkule hannu take tana kaiwa iska naushi kamar ta fashe takejin kanta. kan royal chair two sitters taje ta zauna tana tare da jingina kanta tana huci kamar wani bakin kumurci. "Mamana lafiya meya faru" kamar daga sama taji muryar papu da shigowar sa kenan parlourn yanzu. Tanajin papu ne kuwa ta fashe da kuka tana faɗin " pa, Ni ka kyaleni kaji, ba ka sami wata ƴar ba, ka manta Dani, Wai har ni za'a aikowa wannan ƙazamar yarinyar ta kawomin abinci na da zanci, ai basai kun yimin haka ba idan kun gaji dani ku gayamin kawai na koma can kaduna wajen maman twins ai ita tana sona kuma su FANNAH DA MAYA ma suna sona kuma UNCLE-JIF ma yana sona sai ku gayamin in koma wajen masoyana tunda ku kun sami wata ƴar nima naje na sami wasu iyayen" "Haba mamana meye na kuka kuma, dan Allah kiyi shiru ki min bayani abunda ke faruwa waya taɓamin ke, ummm mamana wanene gayamin kinji shalelen papu" "Pa, ba ku bane kuka kawo waccan talakar yarinyar ƙazama da ita, mai tsince-tsince a titi wai ita ce zaku kawo gidan nan matsayin ƴar gidan nan, kuma ta amsa sunan gidan, haba pa wannan ba adalci bane wallahi nidai gaskiya saidai ku zaɓa ko ni ko ita" "What!?, ko, ke ko ita fa kikace mamana wane kare da buzun kure, ai ko kusa baza'a haɗa ba kiyi haƙuri kawai zamane na ɗan lokaci kafin a gano danginta, muna nan muna bincike yanzu haka ana gane dangin nata zamu miƙata garesu, shikenan matsalarki ta ƙare?" "Ehh pa, sai kuma wacce zatazo daga baya" "Ah ah my kiddo ai bama fatar matsalar ta ƙara zuwa" "Okay" "Abunda nakeso dake Yanzu Ki tashi kije ki shirya mum ɗinki na jiranki" "Mum tana jirana a ina? Me zanyimatane pa?" "Ba komai zaki mata ba shopping zakuje" "Okay pa, zan shirya yanzu, ina dai fata bata wannan yarinyar zamuje ba kho?" "Haba dai mamana da ita zakuje mana, Tau ae itace za'a yiwa shopping ɗin kayan sakawa, kinga batada wasu kayan da zatasa" "God forbid, pa wallahi bazamuje da itaba saidai ta tsaya idan munje muyi mata shopping ɗin tunda kun nace kan sai anyimata" "Okay ba damuwa mamana indai don wannan ne, ki shirya kuje kawai Bara naje naga mum ɗin taki na gayamata abunda kikace" "Okay" daga haka ulud bata ƙara cewa komai ba ta juya tabar parlourn, shikuma papu ya hau sama inda mum take. LEEYA Tana nan zaune a bedroom ɗin nata tsawon minti goma sha biyar da shirin ta amma bataga mum ta shigo ba. miƙewa tayi ta fita daga ɗakin, cikin tafiyar ta ta nutsuwa take takawa har ta isa kofar bedroom ɗin mum, tana Isa kofar ta jiyo Muryar papu yana gayawa mum abunda khulud ta faɗa. daga can cikin ɗakin mum ce tsaye hannun ta riƙe da jaka papu kuma yana zaune "yanzu don Allah justice haka za'a zubawa wannan yarinyar idanu tana abunda taga dama, yanzu fitar da zamuyi da wannan yarinyar Leeyana ne siyamata kayan sawa shine khulud zata ce baza'a fita da ita ba? kai kuma ka yarda ka biyemata to gaskiya bazai yiwu ba dole sai an tafi da leeyana ta zaɓi kalar kayan da take so gaskiya" A tsawace papu ya amsa mata maganar da; "Bazaiyu ba fanaya, kije da mamana kawai ai itama ta iya zaɓen kayan, amma bazaiyu khulud ta faɗi magana a ketare ta ba, kin san da bana son matsala, bana son matsala, musamman ma idan ga mamana zata faru......✍🏼 BAYAN WUYA.... By RUMANA M DIGGI EP.11 ________Dafe kai mum tayi tanajin kwalla na taruwa a idanun ta. "shikenan justice kuje da kaida ita ɗin kuyi shopping ni bazan jeba kuma leeya ma bazataje ba ku barmu gidan" Hannun mum papu ya riƙo ganin kamar ranta ya ɓaci har tana hawaye. "hajjaju fushi kikayi?" "Menene abun fushi justice? ba fushi nayiba naga bai kamata abar leeya ita kaɗai a gidan nan ba tunda itama ƴa ce kamar yanda mamana take ƴa, idan har baza'a fita a bar mamana ita kaɗai a gidan nan ba, to itama leeya bai kamata a fita a barta ita kaɗai ba tunda itama ƴace". Jikin papu yayi sanyi sosai da jin abunda mum ta faɗi shima kanshi yasan gaskiya ce mum ta faɗa to amma ya zaiyi tunda ƴar gaban goshi bata yarda ba "yanzu menene abunyi hajiyata" Faɗin papu yana riƙo hannun mum da murmushi mai sanyi domin kuwa yasan ranta aɓace yake kawai bata nuna bane. "Hmmm, wannan kam ai sai aje a tambayi mai gidan kho" "Wacece kuma mai gidan?" "Ulud mana justice!, naga yanzu itace da gidan ai". "Hajiyata kenan, meya kawo wannan maganar kuma, ai Ulud ɗin kanta da bazarki take takawa, kiyi haƙuri kinji, nasan ranki ɓace yake a ya.nzu, amma kiyi hakuri ki gayamin abunda ya kamata yanzu" "Toh tunda abun ya zama haka a fasa fitar kawai" "A fasa fita kuma!?" "Ehh mana" "Haba hajiya idan aka fasa fitar ai leeya aka tauye saboda da abun wani gwara ace naka" "Hakane amma kasan idan akace aje da khulud kawai ita leeya bazata ji daɗi ba, koda bata nuna mana ba nasan zataji abun a ranta" "Tau menene abun yi yanzu shi nake tambayar ki" "Akira leeya kawai tazo ta zaɓa sai ayi online shopping kho?, kaga shikenan ba wata rigima". "Nice, gaskiya wannan shawarar tayi yanzu abunda za'a yi kije ki kira leeya tazo ta zaɓa da kanta kho". Leeya da tunda taji papu ya dakawa mum tsawa ta bar wajen a tsorace ta koma bedroom ɗin ta tanata sharɓar kuka, domin tasan saboda itane papu yayiwa mum tsawa, alhali koda tazo gidan ba haka ta tararda suba. Ƙarar buɗe kofar da taji ne yasa ta ɗago kanta, mayafin ta gaba ɗaya yayi sharkaf da hawaye "subhanallah!!, leeyana, Lafiya? Meyafaru ne kike kuka?" "Mum kaina ke min ciwo sosai bazan iya fita shopping ba, kuje da khulud kawai sai ta zafamin kayan" Tada ita mum tayi tana jeramata sann "ki tashi muje asibiti kinji, bara na ɗauko carkey na kaiki asibitin kinji" "No mum, kiban magani kawai nasha, bazan iya fitar yanzu bane, amma kiban magani idan nasha banji sauƙi ba daga baya sai muje asibitin" "Da hanzari mum ta bar bedroom ɗin, ta koma nata sashen ta ɗauko mata magungunan zazzaɓi, ta kawo mata "karɓi kisha maganin idan kinsha sai ki kwanta ki sami relief kinji" "Okay mum Nagode sosai Allah ya saka miki da alƙairi" "Ameen ɗiyata, wannan ba komai bane Allah ya baki lapiya, idan kinji sauƙi zuwa yamma sai ki zo ki duba kayan da kikeso ayi online shopping ba sai mun fita ba kho" "Tau mum ba damuwa, ai bama saina zaɓa kayan ba kawai ki dubamin waɗanda suka yimiki duk zaɓinda kikaimin shine nawa" "Yawwa ƴar albarka, Allah ya baki lafiya" "Ameen mum". Bayan fitar mum ɗakin, leeya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya domin kuwa ba wani zazzaɓi da takeji, tayi hakan ne saboda kar mum tagane taji maganganun su da papu domin kuwa mum zatayi tunanin kamar laɓe takeyi musu. Mum kuwa tana fita ɗakin ta je ta sanarwa da papu abunda ke faruwa, sosai papu ya tausayawa leeya musamman ma da yaji mum ta faɗamasa halin da ta tarar da ita "Hajia fanaya kina ganin kuwa haka da akayi yayi? Ya kamata abar mai ciwo gida kuwa, ki tashi a kaita asibiti kawai, ko kuma a kira Dr. jif yazo ya dubata a gida" "Bantari numfashinka ba justice, amma ina gani abari kawai zuwa yamman idan mukaga ba sauƙi sai akira Dr. Jif ko a akaita hospital gaba ɗaya" "Okay ba laifi Allah ya sauwaƙe, Ni zan fita office domin akwai wasu files da nakeso na cike, Turab ya sanardani lokacin dawowarsa, domin lokacin da naje visiting ɗinshi ba'a saka musu date ɗinda zasu dawo ba, kuma in sha Allah yau result ɗinsu zai fito ki sakashi a addu'a don Allah" "In Allah yaso kuwa zan cigaba da yimasa addu'a domin kullum yana cikin addu'a ta saidai na ƙara masa" "Tau Allah ya karɓa" "Ameen" Iya shi kaɗai mum ta faɗa bata ƙara cewa komai ba, har papu yafita ɗakin. "Natafi" papu ya faɗa yana fita daga ɗakin. "Allah ya kai lafiya, ya tsare justice" "Ameen ya hayyu ya qayyum" KHULUD Tunda papu ya gaya mata saƙon mum ta koma bedroom ɗin ta tayi wanka, kaana ta shirya tsaff cikin ƙananan kaya riga da skirt, sai kuma band kalar skirt ɗinda ta saka, tayi parking gashinta duk da ba yawa ne dashi ba amma tana bashi kulawa sosai. zaune take a parlourn ƙasa gaba ɗaya, ta ɗan jaaa lokaci a wurin ba wanda yako gifta parlourn, har kusan yamma. Sai da ta gaji da zama ta tashi ta koma ɗakin ta, kuma batayi tunanin zuwa ta kira mum ɗakinta ba ko kuma ta duba idan mum tana lafiya, bata yi tunanin yin haka ba domin tana ganin kamar ba ita ke buqatar fitar ba. tana zaune sai mamaki take abunda ya hana mum fitowa har tayi tunanin mum tayi tafiyarta ne shiyasa bata ganta ba. Zumbur ta miƙe ta nufi part ɗin mum ta duba kar tunanin ta ya zama gaskiya, wato mum ta tafi da leeya ta barta. Ita kuwa leeya baccinta ta kwasa saida ta ƙoshi ta tashi lokacin da aka kira sallar la'asar, banɗaki ta shiga ta ɗauro alwala Sannan ta dawo bedroom ɗin ta shimfiɗa sallahya kaana ta kabbarta sallahr ta. Cikin nutsuwa tayi sallarta har ta gama tayi addu'a, bayan ta kammala ta tashi ta ɗauko tsintsiya da parker ta share bedroom ɗin, sannan ta gyara gado tayi mopping ta saka air freshener da kuma turaren tsintsiya. Part ɗin gaba ɗaya ya game da ƙamshin ɗakin ta. Banɗaki ta shiga tayi wanka, bayan ta gama wankan ne ta ɗauro mayafin ta kamar dai kullum, sannan sai towel mai ɗan girma da yakai har ƙaurinta ta fito. Tana buɗe ƙofar ban ɗakin kuwa taga mum zaune kan fabric sofa sai murmushi take. "Mum ina wuni" "Lafiya ƙalau leeyana, ya ƙarfin jikin?" "Alhmdullillah mum, jiki kam yayi sauƙi fa nikam ae na warke ma zance" Da murmushi a fuskar mum tace; "ai kuwa naga sauƙin, tunda gashi na ga kin gyara ɗakin nan tsaf kamar ɗakin amarya" Murmushi mai sauti leeya tayi itama tace; "mum ai ban so kizo yanzu ba naɗauka ma kina can kina hutawa ne kawai da saina gyara ko'ina na gidan nan sannan in shiga kitchen inyi mana abincin dare ni kaɗai kuma bana so kowa ya tayani" Idanu mum ta zaro waje cikin alamun mamakin abunda leeya tace "duk wannan aikin keka ɗai, ai ba hauka akeyi ba da zakiyi haka inahhh" "To bara kigani mum idan banyi ba yanzu ma tashi zanyi" Mum zatayi magana leeya ta tari numfashinta da faɗin "dan Allah mum karkice bazan yiba Wallahi inason aiki sosai, na riga na saba ne idan banyi ba bana jin daɗin wallahi" Fuskar mum ɗauke da damuwa tace "Bawai na hanaki aikin bane ki bari idan kika ji sauki sosai jikin ki ya warware sannan sai kiyi duk aikinda kike so ba wanda zai hanaki, amma ki duba kiga yanzu fa bakida lafiya" Leeya na shirin magana sukaji ƙarar buɗe kofa da ƙarfi, waiwayawa sukayi gaba ɗayansu kafin mum tace "mamanah menene haka zaki shigowa mutane bako sallama kuma ki banko ƙofa haka kamar mai shirin dambe" "Mum kardai kice faɗa kike min a gaban wannan talakar yarinyar ƴar talakawa, ba komai na shigo yi wannan ƙazamin ɗakin ba, naje part ɗinki ne ban ganki ba nayi tunanin da ita akaje shopping ba dani ba, bayan naje ban ganki bane na dawo part ɗin nan anan naji motsinku shine dalilin shigowar danayi ɗakin nan, dabadan shiba bansan abunda zai kawoni nan ba ehee" Khulud na gama faɗin haka ta sake fizgar kofar ɗakin tayi ficewarta, second ɗaya, biyu, uku ba wanda yace komai tsakanin mum da leeya sai ƙofar suka kafe da idanu kamar masu neman wani abu "leeyana!" "Na'am mum". "Dan Allah leeya kiyi haƙuri da abunda mamana take miki wallahi ƙuruciya ke cinta da kuma sangarta ta da papunku yayi, dan Allah ki ɗinga ƙarfafa zuciyar ki akan komai da khulud zata miki, wata rana ba wannan maganar za'ayi ba, kawai hakuri ne da wuya amma da kinyi zakici ribarsa in sha Allah, kinga kece babba akanta, nasan kin girmemata wannan bata wuce ƙanwarki da aka kashe ba, dan Allah ki dinga hakuri kinji ƴar kirki" "Lahh wallahi mum ba komai aini bana ɗaukar wannan komai, wallahi ban taɓa riƙeta a rai ba, don Allah ki daina ban haƙuri ai sai inji kunya wallahi" Leeya ta faɗi maganar da fara'ah a fuskar ta. Sosai mum taji daɗin jin hakan daga leeya "Allah ya miki albarka leeya, ina ma ace khulud ma haka halayenta suke kinga sai kuyi zamanku lafiya, ba wani tashin hankali. Ni ina ganin ba wani abu da zai dameni a faɗin rayuwar nan, sai idan na tuna da ƴan uwana" "Ƴan uwanki kuma mum!?, meyafaru dasu!?". "Hmmm Kamar yanda ƴan bindiga sukazo suka kashe kowa naki, Nima haka sukazo a Maiduguri amma su mutanen da sukazo ƴan boko haram ne suka kashe mahaifiyata da kuma ƙanina, amma mahaifina da sauran wasu daga cikin dangin mu sun samu sun tsira" Mum ta ƙarashe maganar kwalla na zubo mata. A ƙiɗime leeya ta sakko daga kan bed tazo kan sofa inda mum take, bata masan lokacin da ta fara goge mata hawayenta ba. murmushi mai cike da ma'anoni mum tayi sannan ta buɗi baki tace "hawaye nake kho?" A duk lokacinda na kwatanta bada labarin nan to nasan bazan ƙare badashi ba tare da nayi hawayen ba, saboda abun yana cimin rai, wallahi yana cikin raina" "Mum Dan Allah kiyi hakuri kinji, yanzu kika ƙare ban hakurin naga hawayenki sai ƙaruwa suke mai makon ace sun ragu, amma ƙaruwa naga sunayi dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan, Allah ya saka mana ga azzaluman mutane wallahi ko bamuyi magana ba ma sai Allah ya saka mana, saboda haka ne nake roƙonki ki fitarda komai a ranki" "In sha Allah ɗiyata, yanda kika faɗi haka abun yake ko bamuyi magana ba Allah zai saka mana da abinda sukayi mana a da hakan in Allah yaso" Ƙarar saƙo ne ya shigo wayar mum tana dubawa kuwa bata furta komai ba ta fita bedroom ɗin na leeya. Ita kuwa leeya mum na fita ta cire hijab ɗinda ta saka, sannan ta ɗauko kayan da ta cire da mayardasu jikinta, fita daga bedroom ɗinta tayi Sannan ta nufi kitchen ɗin gidan, tana shiga kitchen ko bata tararda kowa ba. taji daɗin hakan sosai domin tasan ma ba wanda zai shigo kitchen ɗin face mum kuma yanzu suka rabuda ita. Tunanin girkin da zatayi tafara yi, a cikin kalaluwan abincin da daga mum nayi wanda akeci da dare. Dogon tunani tayi kafin ta yanke shawarar yin tuwon doya da miyar ganye. sanin mum nason miyar ganye papu shima ba'a barshi a baya ba, uwar gayyarce kawai bata san yanda zatayi da ita ba domin kuwa a yanda take ganin khulud na kyamatar talaka to ko zinare ta girka mata da hannunta tasan bazata ciba shiyasa ta share maganar kawai ta fara aikinta. Ta ɗauki tsawon mintuna ashirin, tana haɗa miyar gaba ɗaya kafin da kunna gas Cook, sannan ta fito da doya ta fara gyarata wacce zata tuƙa sakwara da ita. tana cikin hakane kuwa sai ga mum ta shigo a gaggauce, ganin kamar ta makara a aikinta na yamma. Baki sake take kallon leeya lokacin da ta buɗe functional electric pot, taga miyar ganye sharrr da ita sai kamshin spices take bugawa "leeya haka kika iya girmi dama!?, bara na fara sonti tun kan naci nasan zatayi daɗi sosai, masha Allah" Mum ta furta tana yamutsa miyar. Murmushi kawai leeya keyi batare da tace uffan ba, duk yanda leeya tayi ta hana mum aikin amma furrrr mum taƙi saida suka ƙarasa aikin gaba ɗaya tare. leeya ta fita da abincin daining, kaana ta koma bedroom ɗin ta tayi wanka domin mum ta ce mata taje tayi wanka tayi sallah ta fito master parlour akwai Maganar da papu zai sanar musu domin itama ta zama ƴar gidan yanzu. Buɗe kofar bedroom ɗin ta tayi sannan ta furta sallama duk da tasan ba kowa a ɗakin. Da mugun mamaki take bin kayan da tagani jibge kan gadon nata, "ikon Allah" Ta furta a hankali tana isa ga kayan, saida ta iso daf dasu sannan ta gane sune kayan da mum ta gayamata zatayi mata online shopping kenan. "Allah sarki mum, Allah ya biyaki da aljanna, Allah ya shirya miki ƴar ki yanda kike buri albarka kacin taimako na da kuke yi". Ta ƙarashe maganar hawaye na zubowa a idanun. Kayane da zasu iya kai kala ashirin, kuma a ganin ido kayan ba ƙanan kuɗi bane dasu, sosai tayi farin cikin ganin kayan, bakayan sakawa kadai ba harda takalma dasauran tarkacen kayayyakin kwalliya, ba ƙaramin mamaki tasha ba ganin niqab kala daban-daban kusan ma ko wane hijab dake wurin akwai niƙab kallarsa. Kayan duk ƙananan kayane masu kyau ba atamfa ko leshi a ciki duk ƙananan kaya ne. Dogayen riguna, riga da skirt, da kuma riga da wando. Miƙewa tayi cikin tsananin farin ciki ta nufi bathroom a gaggauce tayi wanka ta fito, zama tayi kan dressing mirror ta shirya tsaff amma har ta gama shirin bata ɗaga kanta ta kalli mirrorn ba balle ta hango fuskar ta ko wani abu makamancin wannan, domin rashin kallon mirrorn shima yana cikin alkawarin su ita da amminta. Body lotion mai ƙamshin ta ɗakko ta shafawa jikinta kaana ta duba wasu turaruka daga cikin waɗan da mum ta siya mata masu sanyin ƙamshi ta shafa. Tun sanda take duba kayan ta fito da wasu riga da wando, waɗan suka birgeta sosai. rigar kalar pitch ce yayinda wandon tazama kalar pink, sai kuma hular kayan itama kalar Pink da ta kasance ƙaramace mai kyau da akayiwa adon ƙananan stone iri ɗaya da yanda akayi adon rigar. Kayan sunyi mata kyau sosai abun sai wanda yagani. Farin niqab ta ɗauko sannan ta cire kyallen da takeyin mayafi dashi kaana ta ɗaura niqab ɗin a fuskarta, sosai taji daɗin wannan siyayya da mum tayi mata, sai addu'o in alƙairi take yimata a zuci da baki. Sakkowa tayi ƙasa ta koma master parlour ɗin ta zauna, bata tararda kowa a ciki ba saboda hakane ta zauna ta jira su har su iso, wuri ta samu ƙasa ta zauna ga kujeru da yawa a cikin parlourn domin kuwa parlourn babbane sosai yanada girma. set biyu aka saka na kujeru bayan kuma akwai sofa's. Tana cikin zaman ne tajiyo muryan mum da papu suna sakkowa, ƙara daidai ta nutsuwarta tayi kaana ta gyara zamanta tana jiran sakkowansu. Tun suna kan steps ta miƙe da azama ta isa gare su cikin ladabi ta gaida su "mum naga kaya nagode, Allah ya biyaku, ya sakamuku da alƙairi, Allah ya baku abunda kuke nema duniya da lahira" Mum kuwa murmushi kawai take bayan"Amin" da take faɗa. Shima papu murmushi yayi kafin yace "Allah yayi muku albarka ki tashi kije daining ki jira mu gamu nan isowa, idan aka gama cin abincin sai kowa ya dawo idan aka faɗi maganar da za'ayi shikenan kho" Da "tho papu" leeya ta amsa shi itama. Sannan ta tashi ta nufi daining, takun khulud sukaji tana sakkowa daga part ɗinta, domin ita haka ƙa'idarta take duk inda za'a je sai kowa ya rigata zuwa wajen. Wucewa kawai tayi ko sallama batayiba, kuma bata cewa kowa komaiba. Sai papu ne yace"mamanah lafiya kike kuwa?" Da murmushi ta waiwayo papu sannan ta bashi amsa "lafiya ƙalau nake my lovely pa, ai banyi tunanin kana nan ba, na ɗauka kana daining ɗin". "Ah ah ai bazan isa daining ba idan baki fito ba" "Tau muje kho pa, mum ki tashi muje". Fuska a haɗe mum tace"Ashe kin san da zamana wurin nan, amma da kikazo justice kawai kikayiwa magana kho" Dariya khulud tayi mai sauti har saida leeya ta waiwayo, domin batayi tunanin khulud na dariya har haka ba. "Mum kice kinji haushin na fara yiwa pa, magana kenan humm, tho pa, kaji kho mum ta fara kishin mu" Dariya shima papu yayi sannan yace "barta kawai ai tasan tsakanin ƴa da mahaifi sai Allah. five-five yarin yata". Papu na faɗar haka khulud ta miƙo tafin hannunta papu ya haɗa da nashi suka lale cike da nishadi. Hannun papu haɗe da na khulud suka isa daining, nan suka bar mum sake da baki tana binsu da kallo har suka zauna. Kallon sama da ƙasa khulud keyiwa leeya lokacin da suka ƙaraso daining, ita kuwa leeya bata masan tanayi ba, Hankalinta na wurin papu da take yiwa sannu da isowa, sai kuma mum da itama ƙarasowarta kenan. "Mum me kika girka muku hakane? naji sai wani ƙamshi yake". Khulud tayi tambayar. Tun kafin mum tayi magana Papu ya karɓe da faɗin "wallahi kuwa mamana kinyi saurin tambaya kawai Nima na ƙagu naji abunda mumman ki ta dafa mana haka gaba ɗaya arean nan sai ƙamshi yake". Murmushi mai sauti mum tayi Cikin murmushin tace "leeya kinyi shiru bakya cewa komai, har yanzu kin kasa sakewa sosai yanda nakeso" Martanin murmushi leeya ta maidawa mum kana tace"tho mum nayi magana yanzu, haka yayi miki?" "Yayi dama dai amma inaso yafi haka". " mum Please ki kyaleta don Allah, tambayar ki fa mukayi amma kikayimana banza, kina amsawa waccan peasant ƴar talakawa". "Mamana abar maganar nan Please kinji" Cewar papu yana kallon yanayin leeya, idan taji haushin maganar da khulud tayi duk kuwa da yasan zataji haushin. "Okay pa, na daina. Mum me kika dafa wai?? inaso nasani ne idan bazan iya cinshi ba kinga Sai a dafamin wani". Girgiza kai kawai mum tayi kaana ta amsata da faɗin "tuwon doya ne da miyar ganye". "Haba dae mum, shikenan ko yaushe a dinga yin abu daya a gidan nan, gaskiya bazan iya cinsa ba". Da ƙarfi papu ya ɗago ya kalli khulud da faɗin "haba mamana ki daure ki ci wannan kinji, kinga ma jiya aka siyo sababbin spices ba irin waɗan da muka saba amfani dasu ba". Kamar wacce ke magana da sa'anta haka ta kalli papu Sannan tace "ba ruwana pa, Ni bazanci abincin nan ba this is final" Ta karashe maganar cikin tsiwa. Shiruuuu! Kakeji ba wanda ya ƙara faɗar komai a cikinsu, sai bayan wasu mintuna kaɗan mum ta fara zuba abincin ba wanda ya kuma yi takan khulud. Ita kuwa khulud daddaɗan kamshin miyar na isar mata har wani lumshe idanu take a fakaice tana ajiyar zuciya a hankali "okay pa, zanci abincin amma gaskiya bazanci da yawa ba saboda ma na fahimci ranka ya ɓaci da maganata ne shiyasa zanci, amma da badan haka ba ni bazan iya cin wannan kalar abincin ba. Kuma ko yanzu ba dayawa zanci ba" cewar khulud tana janyo abincin gabanta. Papu kuwa kallonta kawai yayi bai furta komai ba. Abincinsa mum ta kawo masa gabansa, itama ta ɗiba wanda zata ci sannan ta kalli leeya tace "gashi ki ɗiba wanda zai isheki kinji" Murmushi kawai leeya tayi batare da tace komai ba. ta janyo kular abincin gaba ɗaya da plate da kuma serving spoon ta ɗiba abunda zata iya ci. Wawan tsaki khulud taja kuma ta na auna abincin kamar ba ita ba ce tace bazata ci ba. Abincin suka ci sosai domin kuwa ba wanda bai ji daɗin abincin ba har gogan taku. "Alhmdullillah leeya gaskiya abincin nan da kika girka yayi daɗi sosai masha Allah, kinyi ƙoƙari sosai da sosai har waɗanda basa ci yau sunci". Faɗin mum tana kallon khulud da kanta yake a ƙasa tana cin abincin ta hankali kwance. Cikin mamaki papu ya ɗago kansa fuskarsa cike da annuri ya furta "Hajiyata kina nufin leeya ta girka abincin nan!?" Ya tambaya da zaƙuwa. Mum kuwa ta bashi amsa da faɗin "ehh wallahi ita ta girka justice bakaji chanji ba?". "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un mum Dan Allah kice ba gaskiya kike faɗi ba, kice ba wannan ƙazamar ƴar talakawa tayi girkin nan danake ci ba" Faɗin khulud hankali a tashe tana kakarin amai. "Ahhh subhanallah menene kuma haka manana Please ki daina kar ki wahalar da kanki dan Allah, Abincin nan ya riga ya shiga ciki shikenan kuma sai a jirayi gaba". Cewar papu yana yowa kanta a gaggauce domin dakatarda ita daga shirin aman da takeyi....✍🏼 BAYAN WUYA... By RUMANA M DIGGI EP...12 ____________Leeya kam ko ajikinta domin kuwa ita har ta fara sabawa da halayenta. a zatonta Yanzu komai khulud zata yimata bazata damuba tunda ta fahimci halayen ta. Mum kuwa dariyar ta taketayi ƙasa-ƙasa dama da gayya tayi maganar saboda taga khulud taci abincin sosai har sai da tayi mamaki shine dalilin da yasa tayi maganar. Cikin kuka da danasani khulud ke magana tana faɗin; "wallahi ba'a yimin adalci, shine dan Rashin adalci Irin na Mutanen gidan nan baza'a iya gayamin ƴar tsince-tsince a titi ce ta dafa mana abinci idan zan iya ci sai naci, idan kuma bazan iya cin sa ba shikenan. Amma za'a zo a kyaleni naci wannan Abincin wallahi sai Allah yamin sakkaya" Khulud ta ƙarashe maganar tana ƙara sakin kuka. Hawayen ta papu ya share sannan yace "kiyi haƙuri my kid hakan bazata sake faruwa ba kinji in sha Allah komai za'a yi a gidan nan za'a sanarda ke ba wanda zai kuma yin abu a gidan nan batare da sanin kiba ƴar gatan papu da mummunta" "Ƴar gatan pa, dai mum kam ai ga ƴar gatan ta can waccan ƴar talakawa da ba'a masan dangin ta ba" Cewar khulud tana jefawa leeya wani wulaƙantaccen kallo. Leeya kam bata masan tanayi ba. Da sauri papu ya furta muje daining mum zata biyomu nayi miki wani kyakkyawan albishir kinji" Papu Yayi hakan ne domin bayaso leeya ta fahimci maganar da suke tsakanin su, kuma yasan idan bai janye khulud ba zata iya yiwa leeya wani Abu mara daɗi, haka kawai yakejin tausayin leeyana sosai shiyasa ita ma yakeso ya kwatanta qaunarta data khulud ya riƙeta tsakani da Allah amma yake Ganin haka bazata yiwu ba tunda khululud bataso. Parlour suka wuce khulud da papu, daining kuma ya rage saura mum kaɗai da leeya. Bayan sun kammala ne mum ta tafi tabar leeya daining area ɗin domin ta tattare kayan wanke wanke. Kitchen ta kai kayan, bata fito kitchen ba saida ta gama wanke kayan kaffff. Kafin tazo ta tsaftace daining area, kana ta wuce master parlour. Da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga parlour yayinda ta sami wuri a ƙasa ta zauna, Papu ne yakai dubansa kan leeya sannan yace " ke! Tashi ki zauna". Jin yanda papu yayi maganar ne ya saka ta miƙe da hanzari ta zauna kan wata one sitter sofa dake gefe. Sosai khulud taji daɗin abunda papu yayi da jin yanda yayi mata magana cikin tsawa, har take ganin jirgin ta ya hango mata dalilin zamansu wurin, domin tana gani kamar koran leeya papu zaiyi yau. itama mum ta ɗan tsorata amma ta dake domin tasan yanada wuya justice ya aikata abunda take tunani. Gyaran murya kaɗan papu yayi domin hankali kowa ya dawo jikin shi. Haka kuwa akayi papu na gyaran murya kowa ya nutsu yana saurarar maganar da papu zaiyi. Sosai papu ya ɗaure fuska kamar bashiba, fuskar sa kamar bai taɓayin dariya ba ya kalli kowa sannan yace" Assalamu alaikum". "Wa'alaikasalam" waɗanda suke iya amsawa suka amsa masa. Ba wani babban dalili yasa nace mu taru anan muyi magana ba sai dan na shaida muku cewa a daren yau muna cikin maɗaukakin farin ciki mara misali. Wanda duk masoyin mu dayake ƙaunarmu ya kamata ace shima yana cikin wannan farin ciki. Babban abin farin cikin da ya samemu shine Turab Khattab waasib ya zama Chief of military health service a safiyar yau aka gaba tardashi gaban kowa da kowa" "Alhmdullillah, alhmdullillah". Mum ta faɗa kwallar farin ciki na sakkowa a idanun ta, yayin khululud keta ihu tana tiƙa rawa Itama leeya hamdalah take kawai duk da batasan akan wa ake magana ba. "Sai magana tagaba" cewar papu. Nan hankalin kowa ya dawo jikinsa a karo na biyu. "Leeyana!" Papu ya kira sunan leeya idanun sa na kanta. Anan wani sabon farin ciki ya sako khulud gaba Saboda tasan ƙarshen zaman leeya yazo a gidan. "Na'am" leeya ta amsa masa kanta a ƙasa gabanta sai dukan uku-uku yakeyi domin itama ta fara tunanin haka. Sosai hankalin mum ya tashi da abunda papu yake shirin yi, domin itama ta fara gane nufinsa. "Leeyana kinyi makaranta?" Chakkk komai ya tsayawa khulud yayinda taji tambayarda papu yayiwa leeya, nan fuskar ta changer yanayi sosai. Domin kuwa indai mutum yanada fahimta dole ya fahimci tsantsar hasada data bayyana a fuskar khulud "Eh papu nayi makaranta" cewar leeya kanta yana ƙasa har yanzu. "Okay a ina kika tsaya a karatun?'' "Ss2"ta bashi amsa a takaice "Okay" papu ya faɗa daga haka leeya bata kara furta komai ba. Cikin tsananin bakin ciki khulud ta kalli papu tare da faɗin; "What!? Mekakeso kace pa, kana nufin school zaka saka wannan yarinyar, meyasa pa, meyasa? So kawai kake in fita ana nuna ni ana faɗin akwai ƴar government school a gidan mu kho?. So kake ka hanani shiga cikin abokaina kho pa, meyasa haka pa? Kaima ka fara yimin irin abunda mum take min kho? Wallahi nidai bada fatar bakina ba pa. sai dai kaje ka sakata ɗin nagani. Munafukar banza ƴar talakawa kawai ƙazamar yarinyar mai tsince-tsince a titi wallahi bari ya-Turab ya dawo nasan sai kinyi danasanin zama a gidan nan ko kwana ɗaya bazaki ƙarayi a gidan nan ba idan ya dawo". Khulud ta ƙarashe maganar cikin kuka, a guje tabar parlourn ya rage saura mum da papu da Kuma leeya. Miƙewa tayi itama tanufi part ɗinsu harga Allah yau kam kalaman khulud sun ƙona mata rai amma haka ta danne domin bataso mum ko papu ɗayan su ya fahimci haka. "Allah ya sauwaqe" shikaɗai mum ta furta bata ma jira cewar papu ba ta juya ta tafi. Washe gari tunda da sassafe bayan sun kammala break fast papu kuma yafita aiki sai mum dake part ɗin ta tana gyarawa. Zaune a parlour leeya ce ta kammala gyara parloun itama tana zaune ita kaɗai tana kallo abinta. Banko ƙofar parlourn da akayi da ƙarfine yasa ta miƙewa da sauri tana jiran ganin wanda zai shigo. Khulud ce ɗauke da kaya wanki niƙi-niƙi. Saida takai daidai fuskar leeya ta watsa mata kayan tare da faɗin; "ga kaya na nan ki wankesu sai sun fita fes, idan kin gama wanke su da hannunki kuma kije ki sakasu a washing machine ki ƙara wanke su dan bazan iya saka abinda ƙazaman hannayen nan naki zasu wanke ba batare da an sake wankewa ba" Murmushi mai sauti leeya tayi cikin murmushi nata take faɗin "yar uwata wannan ba komai bane kinji, Ni a rayuwata Bama abunda nafiso a aiki kamar inga inayin wanki. Saboda haka Ni kin faranta min rai ma da kika bani aikin nan" leeya ta faɗa tana tattare kayan wankin. Cikin jin haushin abunda leeya tace ka kalli fuskar ta a yatsune tace "well, I don't care if you love to Wash cloth, Nidai na gayamiki wallahi karki sake kimin kuskure idan kho ba haka ba zaki yabawa aya zaƙinta, kuma ki tabbata bayan kin gama duk wannan ki goge kayan Gaba ɗaya sannan kizo ɗakina ki jeramin su closet drawer". "Karki damu zanyi komai kinji sister khulud". A tsawace ulud tace "ke! Wallahi karki ƙara kirana da ƴar uwarki, Allah ya kiyaye yamin tsari na zama ƴar uwarki kina talaka, mummuna, kaskantacciya dake ƴar tsince-tsince a titi sannan zaki kirani da ƴar uwarki". Wawan kuka leeya ta saki tare da barin wajen ta nufi part ɗin ta ta mugun gudu ko gabanta bata kallo harta isa part ɗin ta. Ƙofar ɗakin ta janyo ta rufeshi rufff tare da murza masa makulli ta dawo kan gadon ta zube tanata rizgar kuka. Shekaru biyu zuwa uku da suka gabata ta tunano. Wata rana suna zaune ita da amminta da Aleena, lokacin Aleena tana zaune tana wasa da ƴar tsana. Ita kho leeya tana gyara wake a faranti tare da ammi, sai taga kawai ammi ta cire hannunta cikin farantin tayi tagumi idanuwanta na cikowa da kwalla. Cikin matsananciyar damuwa ta ajiye farantin tazo ta durkusa gaban ammi tare da janye hannayen ammi daga tagumin da tayi tace "amminmu lafiya meya faru ne naga yanayinki ya canja yanzu nan, wani abu akayimiki ko kuma kin tuna da wani abu mara dadi ne ammi?. Share hawayen da suka gangaro a kumatunta tayi sannan ta kalli leeya da fuskar Tausayi tace "leeyana inajin tausayinku ne idan na tafi na barku, ina jin tsoron barinku kuyi maraici leeya musamman ma ke da mutane ke farauta. Wallahi a kullum wannan nake tunawa na shiga damuwa domin bansan yanda zaku kasance nan gaba ba. Wata ƙila abbinku ya auro mai imani mai jin tausayin ku. Wata ƙila kuma ya auro mara imani wacce bata jin tausayin ku. Domin kuwa Ni inaji a jikina bazanyi Tsawon raiba" Ammi ta ƙarashe maganar hawaye na gudu a kumatunta. "Haba ammi dan Allah ki daina wannan maganar a gaskiya ammi maganar nan ta tsorata Ni sosai ban masan abinda ya kawo wannan maganar ba. Dan Allah ki daina kuka ammi idan ba so kike mushiga damuwa ba gabaɗaya harda Abbi. Kuma in sha Allah kece zaki riƙamu da hannayen ki ki aurar damu da kanki". Ƙarar bugun kofar da taji ne ya katse mata tunanin da take kamar wacce ta farka daga bacci haka ta zabura, domin gani tayi kamar jiya-jiya abun nan yafaru. Mum daketa faman buga kofa amma shiru ankasa buɗewa, abun yabata mamaki sosai amma dayake mace ce mai yawan uzuri yasa bata kawo komai a ranta ba, ta juya tabar wajen. Parlour ta nufa tanaso ta ji abunda ya faru Yanzun nan domin kuwa tasan idan taga khulud zata gayamata koma menene ya faru, saboda sanin cewa ba wanda ke kuntatawa leeya a gidan sama da khulud. Shigowa tayi parlourn tana ƙwalawa khulud kira har ta iso tsakiyar parlourn bata daina kiran khulud ba kuma bata ganta ba. Khulud shiru-shiru ba magana har mum ta juya zata fita sai ta jiyo Muryar khulud tana cewa "gani anan mum naje kitchen ne na ɗauko juice cup, lafiya?" Khulud tayi maganar a takaice. A hasale mum ta amsa mata da faɗi "lafiyar ce ta kawo haka, me kikayiwa leeya?" "Wacece leeya kuma?" Khulud ta tambaya. Rai a matukar ɓace mum tace"menene haka khulud Ni sa'ar wasanki ce?" "Awww, mum kice min ƴar talakawan nan ƴar tsince-tsince a titi kho, inaga kamar itace leeya, ba komai nayi mata ba. Wanki na bata naga kamar tanaso tayi mini wasa da hankali shine na tuna mata da asalin ta idan ta manta Kamar dai yanda kika sani Nima na sani pa, ma ya sani". Cikin matukar jin haushi da ƙuna mum ta ɗaga hannu zata mari khulud sai taji an riƙe mata hannu ta baya. Da sauri ta waiwayo domin ganin wanda ya riƙe mata hannu "leeya, ki sakammin hannu na koyawa wannan yarinyar hankali kinji". "Ah ah mum kiyi hakuri dan Allah nice silar komai, kuma nice banada gaskiya ki ƙyaleta dan Allah karki daketa mum, wallahi nice ma wacce yakamata a daka saboda nice banada gaskiya" "Ki koma part ɗinki" shikaɗai kawai mum ta faɗa ta juya tare da barin wajen. Khulud sake da baki take bin mum da kallo yayinda ta rasa mezatayi domin ta huce haushin mum da leeya da takeji. "Dan Allah kiyi hakuri khulud, wallahi Ni bada wata manufa na faɗi maganar nan ba. Inason yin wanki da gaske ba nayi bane dan rainin hankali ko wani abu kiyi haƙuri dan Allah" Leeya tayi maganar tana haɗe hannayen ta biyu alamar roƙo. Juice ɗinda ke hannun khulud ta watsawa leeya gaba ɗaya tare da jan tsaki tabar wajen. Gaba ɗaya mayafin leeya da kayan da ke jikin ta suka ƙara jiƙeya bayan ruwan hawaye da suka jiƙe ta. Durkushewa tayi tana ƙara sakin kuka har tayi mai isarta kafin ta tashi ta shiga ciki da niyar yin wanka ta chanja wasu kayan. A ƙofar ɗakin khulud mum ce tsaye tana Kwankwasa ƙofa, Daga cikin ɗakin kuma khulud ce zaune a ƙan gado tana cika tana batsewa. "Waye bakin kofar? Ko waye ya tafi bana buƙatar ganinsa". "Khulud mum ce buɗe kofar". "Bana son ganin ki mum, je ki riƙa Sabuwar ƴarki, naga har kina rungumanta, tafi dan Allah ina buƙatar na kaɗaita banason damuwa" faɗin khulud da har yanzu bata buɗe kofar ba. "Zaki iya daina waɗannan maganganu ku buɗe kofar ko yah?" "No mum, bazan buɗe ba ki tafi kawai. Leave me alone, go away". Juyawa kawai mum tayi da nufin ta tafiya, domin kuwa tasan tunda khulud tace bazata buɗe ba kowa yazo ba buɗewan zatayi ba. Tun daga wannan lokacin khulud bata ƙara ko leƙowa waje ba har safiya ta waye sai misalin ƙarfe biyu na rana sannan ta sakko falo. Zaune a parlourn leeya ce, sai faman wasa take da kayayyakin wasan khulud. "Imagine" khulud ta furta cikin ranta lokacin da take ƙarasowa gaban leeya. "Ke mena ke gani haka meyasa kika ɗaukar min taddy kina wasa da ita har kin isa" khulud ta faɗa a hasale. "Barka da safiya ƴar uwata kin tashi Lafiya, mum ce tabani tace nayi wasa dasu" leeya ta faɗa tana miƙawa khulud hannu alamar su gaisa. "Kada ki ƙara kuskuren taɓa komai nawa a gidan nan wallahi. Get out!" Khulud ta faɗa cikin tsawa, bangazar leeya khulud tayi da kafaɗarta har leeya ta faɗi ƙasa, "get out of this house ki koma inda kika fito" khulud ta kuma faɗa har tana sa ƙafa tana shurinta alhali kuma ta bangajeta ta faɗi ƙasa. "But mum tace ke ƴar uwatace nima ƴar uwarki ce" leeya ta faɗa cikin muryar kuka, tana miƙewa daga kwancen da take. "God forbid that we're sister's, get out" cewar khulud cikin wata irin tsawa tana yarfe hannaye. Rushewa leeya tayi da kuka ta fita parlourn ta nufi hanyar fita baƙi daya daga gidan tanata kuka yanda ta iya. Fitar ta ɗakin yayi daidai ta sakkowar mum daga sama tana cewa "khulud meya faru, me kika yiwa leeya kuma, me kika yimata nace?" "Mum how dare she play with my toys, ita wace da zan ajiye abu ta ɗauka har tayi wasa dashi, kuma tace ke kikace ta ɗauka tayi wasa dasu" cewar khulud tana kallon mum tarrrr. "Menene a ciki, it's Toys saboda ta ɗauka matsala ce" mum ta faɗa tana fita parloun bata ma jira cewar khulud ba tabi bayan leeya a guje. Ita kuwa leeya tana fitowa harabar gidan, fitowar ta yayi daidai da wangale kofar gate ɗin da mai gadi yayi da alama za'a shigo da motane ciki. Kafin mai gadin ya ankara ta wuce ta gabansa a guje ko takalama babu a kafarta, doguwar rigace a jikinta sai niƙab ɗinda ke sanye a fuskar ta ko mayafi batada shi akanta gashin ta a fili. Da gudu mum ta ƙaraso wajen tanayiwa ma'aikatan gidan alama dasu bi leeya baya su dawo da ita, kafin wasunsu su ankara tuni leeya tayi nisa da gudun da takeyi. Mum ta ƙaraso bakin gate ɗin sai numfarfashi take. "Mum-ulud lafiya?" Cewar papu da yake fitowa daga mota tun driver baiyi packing ba. "Justice wallahi leeya ce ta fita aguje ba wanda yasan inda zataje gashi batada ko takalma, gashi tana kuka sosai koda ta fita. sannan kuma ko mayafi babu a jikin ta, dan Allah justice ayi wani abu kasan mutane basuda kyau Yanzu" mum takai ƙarshen tana sauƙe ajiyar zuciya da sauri domin kuwa a gajiye take ɗan gudunda tayi yanzu. Juyawa papu yayi tare da yiwa driver izni daya tuƙa motar su bi bayansu. Leeya kuwa har wannan lokaci gudu take faman yi, kuma ba alamar gajiya a tattare da ita, sai kukan da take yi ƙaɗan kaɗan idan ta juya baya taga dandazon ma'aikatan gidan da suka biyota, sai take gani kaɗan ne babu tsakanin ta dasu. Wani irin wawan birki a jaa gabanta, wanda yasata dakatar da gudun da takeyi amma bata daina kuka mai sauti ba. Buɗe kofar motar papu yayi fuskar sa ɗaure tamau kamar wanda bai taɓayin dariya ba yace" ke shigo mota". Girgiza ƙanta tayi alamar bazata shigo ba ta juya zata ci gaba da gudu sai ga sauran ma'aikatan gidan sun ƙara so, suka cirata sama sannan suka sakata cikin motar suka rufe rufff......✍🏼 BAYAN WUYA.... By RUMANA M DIGGI EP...13 ____________Shigar ta motar keda wuya tayi shiru ta nutsu kamar ba ita ba, har aka ƙaraso gidan ba wanda yace kanzil tsakanin papu da leeya har driver. Koda suka iso gate ɗin gidan mum na tsaye tana jiran isowarsu. Ana buɗen marufin motar leeya ta zabura zata ƙara guduwa mum tayi wufff ta riƙeta ita da wani ma'aikaci da ya lura da guduwa takeso ta yi a karo na biyu. "Leeya me kike shirin yi ki ne wai ki nutsu mana" faɗin mum tana ƙara riƙe leeya. "A nutse nake mum dan Allah ki sakeni na tafi na koma can titi na dinga tsince-tsince dana sabayi, dan Allah ki barni in tafi" Cewar leeya tana ƙara rushewa da kuka. Gigitacciyar tsawa papu ya daka mata yana yimata nuni data koma ciki. Da gudu ta shige ciki tana cigaba da rizgar kukanta. "Hajiyata wai me akayiwa yarinyar nan har haka? Naga baruwanta ai, kuma naga kamar tanada haƙuri. Me aka yimata har haka" "Wallahi justice ita da khulud ne, khulud ce ta zageta sosai kuma ta koreta gidan nan amma ka barni da ita kawai" mum ta faɗa tana shigewa cikin gidan. Shima papu ya rufamata baya suka shige baki ɗaya. Zaune a parlour khulud ce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai wani girgiza ƙafar take tana faman kaɗa kai. tana ganin mum ta shigo ta miƙe da sauri zata bar parlourn. "Khulud!!" Mum ta kira sunan ta da ƙarfi. "Meyasa bakida hankali ne wai, ina kika ɗauko wannan mugun hali, Ni ko mahaifinki ko yayanki wakikaga yana irin wannan halayen na wulaƙanta ɗan adam. Allah da kanshi ya karrama ɗan adam har ke wacece da kika isa ki wulakanta shi" "Ok mum kina supporting ɗin ta kenan" "Could you Shut up, shut up" mum ta faɗa cikin tsawa tun kafin khulud ta rufe bakin ta. "Hajiyata kiyi hakuri abi komai a hankali kinji" faɗin papu yana dafa kafadar mum. Da sauri khulud ta hau sama har tana haɗawa da gudu kamar zata banke mum. "Ka gani, ka gani ko justice duba kaga bankeni fa tayi, takalman da ke kafar mum ta ciro ta wurga wa khulud. Amma baikai ga samunta ba domin har tayi nisa da tafiyar ta. Bayan khulud papu yabi shima suka bar mum a parlour. Da gudu khulud ta banki kofar ɗakinta ta rufe, dai-dai lokacin da papu ya iso. saurin binta yayi a ɗakin tun kafin ta saka key, kan sofa taje ta jingina shikuma papu ya zauna kusa da ita ya riƙo hannun ta yana faɗin. "Khulud my kid, nasan abune mai matukar wahala ki karɓi leeya a matsayin ƴar uwarki nasani, amma inaso ki gwada. Tana da kirki, gashi ba ruwanta batada matsala. Tana bukatar taimakon mu, bazamu watsarda itaba tunda munada abunda zamu taimake ta. Ko kin manta papunki shima da yanda ya fara, da ba'a taimako Ni kaina bazan kai hakaba. Please my kid inaso kiyi hakuri ki karɓesu dan Allah, yanzu na dawo daga makarantar akayimata registration itama ta fara zuwa makaranta kamar sauran 'ya'ya" papu ya faɗi yana shafa kan khulud. "Pa, nifa bance karku taimaketa ba. But i don't want her in this house, she's dirty girl and very, very, poor girl pa. Idan mutane suka sha ruwa suka jefarda robar ruwa, itace take tsinta tana siyarwa, a gaskiya bana buƙatar ta a gidan nan pa" Khulud ta faɗa tana kara jingina kan sofa. "Ki daina maganar nan mamana, itama mutum ce kamar mu, ba ita ta tsarawa kanta yanda takeso ba. Allah ne ya tsara mata kuma haka nan yakeso ya ganta gabanin shigowar mu rayuwar ta. Saboda haka ba yanda ta iya da ƙaddararta. Akwai wani darasi na rayuwa daya kamata ace kinsani, kuma kin fahimta", dogon numfashi papu ya jaaa sannan ya sauke yaci gaba da magana "wanda kika gani talaka a yau, wata rana shi zaki gani ya zama mai kud'in da ya kere kowa idan Allah yaso. Sannan kuma kiga ya taimaki talakawa harma wasu masu kudin. Ina so ki yi tunani akan haka kinji. "Okay pa" "Yawwa my kiddo Allah yayi albarka, sannan wani abu guda daya" "Menene shi papu?" "Kiyimin alkawari bazaki ƙara kwatanta yin abunda kikayi a dazu ba". "Okay pa" "Ba okay ba so nake naji kince kinyi alƙawari" "Nayi alƙawari bazan ƙara kulata ba idan har ba ita ta shigo gonata ba, amma idan ita ta shiga lamarina na rantse bazan rangwanta mata ba" "Nasan leeya bazata shiga lamarin kiba idan har ba ke kika sakata ba in sha Allah" Taɓe baki khulud tayi sannan ta furta "kudai kuka sani" ta mayar da kanta ta kwanta. Miƙewa papu yayi yabar sashen gaba daya ya koma nasa. WASHE GARI, ya kama ranar Monday, ranar da ko wane ɗalibi yake hanzari da gaggawa domin ya shiga school. Sakkowa take daga kan steps cikin tafiyar ta ta nutsuwa, jikinta sanya yake da uniform rigar half gown. Sand colour mai ratsin brown colour. Sai kuma suit data ɗora kan rigar kalar brown, a gefe daya na suit ɗin kuma ɗan karamin badge logo ne da aka liƙa mai tambarin school ɗin wato BUSY BRAIN INTERNATIONAL ACADEMY SULEJA. Sai kuma wuyanta dake sakale da neck tie mai kalar red and white, sai kuma ɗan ƙaramin hijab ɗinda ta saka White colour ne da iya kacinsa kafaɗarta kawai. Niƙab ne sanya a fuskar ta brown colour shima, wanda ya bayyana dara-daran idanun ta, da kallo ɗaya idan mutum yayi musu zai tsorata ko yayi tunanin ba mutum bace. Cover shoe ne a ƙafarta sai kuma socks ɗinda ke sanye a kafar tata kalar brown mai dauke da logo na school ɗin. "Masha Allah" mum ta furta yayinda leeya ta ƙaraso dainin area "ɗiyata kinga yanda kikayi kyau, kamar ke kaɗai akayiwa uniform ɗin nan wallahi" Cikin tsananin farin ciki mara misali da leeya ke ciki ta durƙusa har ƙasa tana gaida mum. Mum ta amsa mata ita ma cikin farin cikin ganin sun zama sanadin shigar marainiyar Allah cikin farin ciki "ki zauna kiyi breakfast kinji, kafin ƴar uwarki ta fito domin ita bata yin breakfast a gida saidai idan taje makaranta" "Nima fa banaci mum wallahi bana jin yunwa" leeya ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauko lunch bag ɗin da aka siyamata" "Kizauna kici abincin ki kada kije yunwa ta dameki" cewar mum tana zuba abincin a plate. "Allah mum bazan ciba idan mutum ya cika cin abinci tunda safe yana toshe ƙwaƙwalwa kuma kona shiga class bazanyi karatuba saidai bacci tunda na ƙoshi. Kinga ko gwanda ma kar inci yanzu" leeya ta faɗa tana kallon khulud da take sakkowa yanzu. Papu kuma yana bayanta. Ƙarasawa leeya tayi da sauri gaban papu ta gaida shi kamar yanda tayiwa mum sannan ta waiwayo ga khulud tace " hi sis, ya kikaga uniform ɗin nan sunyimin kyau kho, kinga yanzu school din mu daya muyi haƙuri mu zauna lafiya, muyi karatu, mu taimakawa juna, mu farantawa mum da papu rai kinji please " Ja da baya khulud ta fara yi a kidime tace "what!??, menake shirin gani pa, mum, kuna nufin school ɗin mu ɗaya kenan a BUSY BRAIN INTERNATIONAL akasakat? no, no, pa wannan bazai taɓa faruwa yazaka min haka pa" ta faɗa cikin tsananin hasada, kamar ta fashe da kuka. "My kid menayi miki kuma". "Pa, makaranta ɗaya kasaka wannan yarinyar tare Dani, no pa you're bringing down my personality. Cewa khulud tana yar fe zufa. "Stop this please, bakiji yanda tace miki bane. Bakyaso kisakamu farin ciki ne, na sakaku school dayane saboda inaso shaƙuwa ta shiga tsakaninku, bakyaso ko a school ɗin a dinga cewa ga sistern ki nan bakyaso?" "No, no pa, wannan bazata taɓa zama sister na ba har abada, ta dauke soyayyar mum daga gareni, yanzu kuma soyayyar ka papu takeso ta ɗauke daga gareni. No!!!" Khulud ta faɗa tare da barin parlourn ta nufi mota da gudu tana kuka. Idanun leeya na cikowa da kwalla ta kalli papu tace" pa, mum dan Allah ku yafemin wallahi ba ason raina haka take faruwa ba, wallahi a yanzun nan idan akwai abunda nafiso bai wuce naga mun zauna lafiya da khulud ba, dan Allah kuyi hakuri" "Ba komai zo muje driver na jiranku" papu ya faɗa yana wucewa gaba leeya kuma tana bayansa. "Mum mun tafi sai mun dawo" "Allah ya baku Sa'a leeya Allah ya tsare kinji" "Ameen ya ilahi mum, bye bye" Nan suka tafi suka bar mum ita kaɗai a gida. SAI MISALIN 2:00pm na rana suka dawo gidan, ko da suka shigo mum ta tsaftace ko ina na gidan har ta kammala girkin ta na rana. Leeya ce ta fara shigowa gidan da gudunta taje har gaban mum cikin farin ciki take magan; "mum ambamu classwork yau kuma score na 10/10" ta faɗa tana fitowa da book ɗin daga cikin school bag ɗinta. Karɓar littafin mum tayi tana dubawa, sai murmushi take. Daidai lokacin da papu ya shigo riƙe da hannun khulud ya ƙaraso wajen. "Barka da dawowa justice, kaga fa ɗiyata taci marks 10/10 a class work ɗinda aka basu yau" cewar mum tana miƙawa papu littafin. "Masha Allah" gskiya kinyi ƙoƙari LEEYANA HAMRAZ AWAIS amma aƙara kinji ɗiyar mum" papu ya faɗa yana miƙawa mum littafin bayan ya duba. "Kinyi ƙoƙari sosai, kuma zan miki kyauta kinji" "Nagode mum" leeya ta faɗa fuskar ta ɗauke da yalwataccen annuri. Zaune suke kan daining mum, papu, khulud sai kuma leeya. Abincin su sukeci hankali kwance ba wanda ya damu da wani. Papu yakai dubansa kan khulud yace "my kid ɗazu naga leeya ta nuna mana score ɗinta amma ke banga kin nuna nakiba" "Pa, malamin mu yace sai gobe za'a bamu litattafan mu" "Kin tabbata?" mum ta tambayi khulud. "Yes mum, sai gobe yace mana" "Ki tabbatar kin kawo littafin gobe nagani" "Okay mum". Basuyi wata gardama ba domin leeya da khulud ba class ɗinsu ɗaya ba leeya tana ss2 ne khulud kuma ss1 take. "Justice gaskiya leeya tayi ƙoƙari she's very brilliant" Spoon ɗinda ke hannun khulud ta sake da ƙarfi tana sauransu. Mum kuma tayi kamar bata jita ba, shima papu haka dama can bai kula tayi haka ba itama leeya ɗin bata kula ba. Mum ce kaɗai ta gane abunda hakan ke nufi. "Ehhh gaskiya tayi ƙoƙari sosai wallahi amma dai ki ƙara kan haka kinji leeyana" "In Sha Allah pa, Nagode sosai". "My kid meyasa bakya cin abinci?" "Nothing pa, I will eat" "Hmmm" kawai mum tace banda haka bata ƙara faɗin komai ba. Har suka kammala cin abincin ba wanda ya ƙara faɗar komai KhUlud ce ta fara tashi daga wurin sannan sai papu. Mum da leeya su suka tattara komai da aka 'bata a wurin. Leeya ta kar'ba ta wuce kitchen ta wanke. Bayan ta kammala wanke-wanken ne ta fito ta koma part d'insu sannan tayi wanka tayi sallah. School bag d'inta ta janyo daga kan bedside drawer ta fito da littafin ta da aka bata assignment ta d'akko sannan ta fita balcony din gidan. Zaune take kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wajan sai lissafi take da yatsun ta tana rubuta wa. Tun zaman ta a gidan bata taɓa zama a nan ba hasali ma bata ganin kowa yana zuwa nan. Ita kanta bata taɓa kula da wurin nan ba sai ɗazu da suka dawo school taga wani ma'aikacin gidan ya fito daga wurin ya tsayar da papu, sukayi magana. Sosai tayi mamaki domin bata taɓa sanin akwai wurin nan a gidan nan ba, ko kuma dai dan bata fita waje ne yasa bata sani ba. Taji daɗin wurin sosai domin ba hayaniya ga sanyi da iska mai daɗi, ga kuma kamshin furanni daban daban, ga tsuntsaye kala daban-daban masu matukar kyau da ban sha'awa. Hankali kwance tayi assignment ɗin ta tagama, bayan haka takai mintuna talatin tana hutawa a wurin domin bataƙi ace tazo nan ta dinga kwanciya ba. Sai da lokacin Sallar la'asar yayi sannan ta tashi ta koma cikin gidan. Da litattafan ta a hannu sai wani nishadi takeji. da sallama ɗauke a baƙinta ta shigo parlourn jin shiru ba'a amsa mata ba yasa ta ɗago kai domin ganin wanda ke zaune. "Lahhh khulud assignment kikeyi, wallahi kuwa bansaniba dana zo munyi tare, gashi kuma mathematics kikeyi kho I'm good in mathematics I can help you, if you don't mind" "I mind!!!, leeya I mind. Stay away from me, bana bukatar taimakon ki. Mtswww taja tsaƙi taci gaba da aikin ta. "Ahhh khulud me yayi zafi dan Allah ki bari na taimaka miki kinji" "Kehh, wai ke bakyada zuciya ne da bazaki iya fita harakata ba, ki tashi daga nan, bar nan nace bana buƙatar taimako ga talakar yarinya irinki ƴar talakawa". KhUlud ta faɗa a tsawace kamar zata daki ta. "Khludddd" leeya ta faɗa Muryar ta na cracking kamar zatayi kuka. "Get out!, get out of my presence. Leave! Bar nan ta faɗa cikin daka murya. Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka leeya ta miƙa ta nufi sashin ta. Huci irin na jin haushi khulud ta ajiye tana faɗin "Ni ban ma fahimci topic ɗin nan ba, kwata kwata banmasan menakeyi ba wallahi. Koda yake bara nayi kawai can ta matsewa malamin ko summit ma bazan yiba, ko dai na kira leeya ta zo ta dubamin mtsss who cares bama zankirataba bana buƙatar hannayen ta masu datti su taɓamin book" Washe gari. Yau ma Kamar jiya sai ƙarfe 2pm na rana suka dawo, mum ce tsaye a parlour tagama turaren wuta. Da sallama dauke a bakin leeya ta shigo ɗakin. Khulud na biye bayan ta, saidai ita batayi sallama ba. "Mum sannu da gida" leeya ta faɗa tana ƙarasawa gaban mum. khulud kuma tayi kamar batasan da mum a wurin ba. "Yar makaranta, an dawo" "Ehh mum na dawo" leeya ta faɗa tana ƙoƙarin sauke school bag ɗinta. Khulud kam bata shige ciki ba tana nan laɓe tana jira taga me leeya zatayi. "Mum, albishirin ki". "Goro fari". "Mum, ba dai goroba. Goro kam ɗaci gareshi". Ɗaga kai mum tayi kamar me tunano wani abu sannan tace"to zuma". Dariya mai sauti leeya tayi. Khulud kuwa ji tayi kamar zuciyar ta zata fashe. "Mum, assignment ɗin da aka bamu jiya danayi shine nafi kowa maƙi a class ɗin mu. Kinga har kyauta aka bani" cewar leeya tana fitowa da kyautar da aka bata......✍🏼 BAYAN WUYA....... By RUMANA M DIGGI Ep.14 ____________dogon tsaki khulud taja tare da barin wajen, mum da leeya duk sunji tsakin da taja amma ba wanda yace mata uffan. "Je kiyi wanka kiyi sallah kizo kici abinci kinji" Mum ta faɗa tana shafa kan Leeya. "Okay mum Nagode" Cikin tafiyarta ta nutsuwa tabar wajen ta nufi sashen su. Tana isa ta fara tuɓe uniform ɗinta sannan ta ɗaura towel ta shige toilet. Bayan wasu ƴan mituna kaɗan ta fito sannan ta saka Kayan ta tayi sallah. tana idarwa ne ta tsahi ta shafa mai da sauran kayayyakin kwalliyarta. Uniform ɗin da ta cire ta ɗauka ta nufi laundry room ɗin gidan kaana ta saka uniform ɗin a washing machine ya wankesu fess Sannan ta fita bayan gidan ta shanya su. Tana cikin shanyawa ne ta hango wurin nan da ta tafi jiya. Dariya mai sauti ta saki tare da faɗin "Hi furanni da tsuntsaye yau ma zanzo na tayaku fira Kunji". Ta faɗi maganar cikin barkwanci ne kawai duk da tasan ba jinta zasuyi ba. Cikin gidan ta koma bayan ta ajiye washing basket ɗinda ta saka uniform ɗin ta. Kaana ta koma bedroom ɗin ta ta gyara ta saka turare sannan ta fito. Daining area ta nufa kamar dai kullum fuskar ta sanye da niqab kalar green mai duhu. Sai kuma riga da skirt ƙanana da kuma hular kayan. "Assalamu alaikum" Leeya ta furta lokacin da take isowa a daining ɗin. "Wa'alaikisalam" Mum da papu duk suka amsamata saɓanin khulud da ko kallon wurin da take batayiba. Durkusawa leeya tayi ta gaidasu baki ɗaya. Bayan ta tashi ta janyo daining sit a kusa da khulud ta zauna. "Sis barka da rana" "Mtswww" khulud ta yi tsaki tana cigaba da cin abincin ta. Abincin ta da aka ajiyemata a wurin da take zama tun kafin tazo, aka ajiye mata. Shi ta janyo ta fara ci. Suna cin abincin hankali kwance har suka kammala. Wayar mum ce tayi ƙara alamar kira ya shigo, "hello, hajiya fanaya" "Yes, Dr.eraa ya aiki" mum ta faɗa tana ajiye spoon ɗinda ke hannun ta. "Hajiya fanaya na kiraki ne kan maganar khulud k. Waasib yarinyar ku" "Okay to Dr. Ina saurarar ki". "A gaskiya hajiya khulud k. Waasib bata maida hankali kwata kwata a class, gwanda ma can baya tana maida hankali ƙadan kaɗan, amma yanzu kam gaba ɗaya bata karatu. Kunga na farko idan tazo bama ta zama aji balle tasan abunda ake, sannan kuma idan aka bada classwork batayi. Idan aka bada homework ko assignment duk batayi gaba ɗaya. Gashi jiya ma anyi test tayi failed gaba ɗaya, gashi kuma promotional exams za'a yi idan bata mayarda hankali ba gaskiya bazata je gaba ba sai next year, kuna ba amafani ace ana biyan school fees over a million thousand of naira amma ba'a mayarda hankali" Wacce aka kira da Dr.eraa ce tayi maganar daga cikin waya. "Okay ba damuwa dan Allah ku ƙara hakuri in sha Allah zanyi magana da ita, Nagode sosai" Cewar mum tana ajiye wayar. Miƙewa khulud tayi zata bar wajen mum ta daka mata tsawa "Khulud, koma ki zauna magana zanyi dake" Ba wani musu khulud ta zauna domin kuwa tasan tanada babban laifi tunda taga haka daga mum. "Wanene ya kiraki Hajiya fanaya?" cewar papu cikin alamun tambaya. "Kiran daga makarantar su khulud ne, sun qara kirane suna complain kan rashin tsayi tayi karatu. Justice me zamu yiwa wannan yarinyar kuma don tayi karatu. Menene bamu yimata ba" mum ta faɗa tana mayarda kallon ta ga khulud. Cikin tsananin ɓacin rai da takaici mum ta fara magana "khulud menene kike buƙata a wannan rayuwar, gayamin? Nida mahaifinki mun samarmiki da komai da kike buƙata. Saboda kawai ki tsaya ki kwantar da hankalinki kiyi karatu, so me kike buƙata kuma. Mun sakaki a maɗaukakiyar makaranta Saboda ki sami ingantaccen ilimi. A kowane wata mahaifinki na biyan kuɗin makarantar ki over a million thousand of naira. Just to learn khulud. What exactly do you want in this life, an ɗaukar miki extra lesson teacher a kowane weekend domin ya koyar dake during the holidays you on vacation. So what are you liking, meyasa bazaki tsaya ki koyi abunda ake koyar da ke ba meyasa khulud?, me yasa koda yaushe kike zuwa poor grades, always zero meyasa" Mum ta ƙare maganar idanun ta duk sunyi jajir saboda tsanani ɓacin rai. Khulud kuwa jikinta duk yayi sanyi likiss a hankali ta furta"mum I'm sorry" tana ƙokarin ta riƙa hannun mum domin bata hakuri. "Khulud idan kika ƙara dawowa da wannan grade a gidan na rantse miki da Allah sai an fitarda ke a Private School an sakaki public school". Cikin tsananin tashin hankalin jin abunda mum ta faɗa khulud ta matsa gabanta "mum don Allah kiyi hakuri wallahi nidai dana zauna public school gwanda na zauna gidan nan. Mum don Allah kiyi hakuri". "Sakar min hannu bana wasa dake, kuma bazan soma ba a yanzu. Kinji dai na rantse miki kho wallahi idan kika ƙara zakiga cikawa da iyawa". "Sorry my kid zo nan Kinji" papu ya faɗa yana miƙa mata hannunsa. Da gudu ta faɗo jikin papu tana ta sharɓar kuka" pa, bana son public school don Allah pa kace mata kar a cireni a BUSY BRAIN INTERNATIONAL please pa" "Kagani kho justice, wallahi kai kake ɓata wannan yarinyar" "It's okay HAJIYATA zamuyi maganar daga baya ki barta hankalin ta ya kwanta yanzu Kinji" "My kid, zanyi magana da mamanki later, amma kiyi min alƙawari ɗaya". "Nayi maka pa, nidai banason public school wallahi" "Kin min alƙawari zaki dinga zama class" "Ehh nayi maka alƙawarin zan dinga zama class, amma banason public school" "Shikenan baza'a saka kiba tunda baƙyaso" "Thanks you pa I really love you so much my wonderful pa". kwanciya tashi, ba wuya a wurin Ubangiji har gashi leeya na ajin ƙarshe a secondary ita kuma khulud tana ss2 kenan zata shiga ss3. Mum da papu sunci gaba da rikon leeya tsakanin su da Allah kuma da zuciya ɗaya ba abunda suka rageta dashi. A bangaren khulud kam game da kiyayyarda take nunawa leeya ba abunda ya ragu sai dai ma abunda ya ƙaru. Yaune ranar da ko wanne mahaifi da yakeda dansa ko diyarsa a BUSY BRAIN INTERNATIONAL ACADEMY SULEJA zaije domin gudanarda gagarumin taron yaye ɗaliban wannan shekarar. Papu da mum kam suna gaba wajen zuwa domin kuwa idan har ba sani kayi ba bazaka taɓa cewa ba subane iyayen leeya na asali ba. Sosai akayi decorations na alfarma a makarantar abun gwanin ban sha'awa. Sahu-sahu dalibai suka fara fitowa, an raba ɗaliban kashi uku kowa da tawagar su. Yayinda ko wace tawaga ta tafi wurin da aka tanadar mata. kowace tawaga a cikin waɗan da suka fito sunada mai jagoranci ta. LEEYANA HAMRAZ AWAIS itace mai jagoranci tawaga ɗaya a cikin sauran sai kuma. Wata students ɗaya a set ɗin nasu mai suna HALAN NURAIN itama tana jagorar wata tawaga aciki yayinda tawagar ta Uku ta kasance namijine mai suna TAWQIR YUNUS. Bayan an gabatar da addu'ar ga musulmai. Sannan aka dawo akayiwa Christian addu'ar su suma. Sai kuma aka fara kiran malumma suzo domin yin jawabi, bayan malamai sai kuma aka kira dalibai. Mutum huɗu aka kira ta biyar ɗin ita ta kasance kasance LEEYANA HAMRAZ AWAIS. Bayan dogon bayani da tayi akan kanta, wanda dayawa daga cikin mutanen wurin sun tausayamata matuƙa. Sai kuma kalaman ta na ƙarshe da suka ƙara sanyaya jikin mutanen wurin. cikin wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tace "Daga ƙarshe ina godiya ga waɗan nan bayin Allah JUSTICE KHATTAB WAASIB da kuma matarsa HAJIA FANAYA. Sune suka zamo jigona, su sukaymin gatar da na rasa ta iyaye, su suka fitardani daga cikin rana suka mayardani a inuwa, su suka soni lokacin da ba wani da zai iya zuwa kusa dani, sune suka zamo gatan maraicina, su suka bani ruwan sanyi yayinda ko wace korama ta rayuwata ta ƙafe, su suka cetoni daga faɗawa wani hali, sune suka fara rufemin ƙofofin kaddarata da suka bayyana a filli. Mum, papu, Allah Ubangiji ya saka muku da alƙairi, Allah ya kyautata muku fiye da yanda kuka kyautatamin Allah ya shayarda ku ruwan alƙausara, Allah ya hanaku jin kunya duniya da lahira, Allah yayi muku kyakkyawan karshe". Leeya ta faɗa yayinda kukan da take ya soma cin ƙarfin ta. Duk da ta saka niqab bai hanawa mutane ƙiyasta yanda take kukan ba domin wasunsu tausayin ta ya hanasu ɗauke idanu akanta. Papu da mum kuwa sai video ake yimusu, sai kuma masu yi musu addu'o'in samun nasara da gamawa da duniya lafiya. Mum kam harda hawaye yayin da papu ya dake saboda shi namijine yanada ƙarfin zuciya. Bayan wurin ya gama kankantuwa aka kira yaran da zasuyi program. Debate competition, aka farayi bayan shikuma sai akayi quiz competition. Daga nan kuma akayi impromptu speech. shine wanda aka rarrabashi a tawaga uku. Bayan ɗaliban sun tafi gaban jama'a kowa yayi choosing topic ɗin da yakeso TAWQIR YUNUS ne ya fara, bayan ya kammala sai LEEYANA HAMRAZ AWAIS ta fara nata itama bayan ta kammala ne sai HALAN NURAIN tayi nata. sosai yaran suka birge domin duk wanda yaje wajen to zuciyar sa fari sol take a wannan lokaci musamman wadanda ƴaƴansu suke ciki. Bayan an gama wannan kuma sai akazo raba kyaututtuka ga ɗalibai. Leeyana kam tasamu kyauta dayawa domin kuwa kowa kaji ita yake faɗi. Kyautar farko da aka bata shine over roll Mark's, kyauta tabiyu kuma most brilliant and intelligent, kyauta ta uku da aka bata kuma tafi kowa nutsuwa da tsafta, sai kuma kyau ta ta gaba shine kyautar ta sami high grades a mathematics quiz ɗinda akayi. Sai kuma kyautar debate competition ɗinda akayi kuma itace tazo second position, sai kuma kyautar impromptu speech da sukayi da tawagar ta. Sannan sai kyauta ta karshe da class master ɗinsu ya bata datazo first class a ajinsa. Tun su mum na ƙarɓar kyautar har suka rasa inda zasu ajiyeta domin kuwa motar su na can parking space sai anyi tafiya mai ɗan nisa. Bayan wannan kuma aka kira iyayen yaran da akayi program dasu domin suyi jawabi, papu ne ya fito ya Tsayawa leeya. Sosai ya ƙara mutunci da daraja a idon mutane don gani suke ba wanda zai iya yin abunda yayi, koda an samu ma da wuya a samu kamarsa. Mutane da yawa sunyi pictures da mum da leeyana da kuma papu, wasu papu kaɗai, wasu mum da leeya wasu kuma papu da leeya, wasu leeya kaɗai. Khulud kuwa kamar da ɗora hannu aka tayi ta ihu domin ta rasa abunda ke yi mata ɗaɗi kamar ba ƴar gidansu bace akayiwa graduation. Sosai ɗalibai da iyayen yara suka yi farinci da wannan taron. Anyi taro lafiya an kare lafiya. Kowa ya ɗauki yaransa aka koma gida. Daga Nan wani makeken mall papu ya nufa dasu sosai ya kashe musu kuɗi baramma leeya data darje ta zaɓi Kayan sakawa, dana kwalliya, turarruka, da sauran kayayyakin amfani. Domin yanzu ta sauya ba kamar lokacin da tazo gidan ba. Daga nan kho restaurant suka nufa, bayan isowarsu ne khulud tace suje ita tana nan bazata fita, papu yayi rarrashi har ya gaji amma furrrr taƙi zuwa ko'ina. Dole papu ya tafi amma saida aka yimata take away. Tuqi papu yake suna fira jefi-jefi a cikin motar papu ya danna wayarsa kaɗan sanna yace "hajiyata wai kinsan ashirin ga wata Turab zai dawo gida NIGERIA? gobe zai dawo daga WASHINGTON zai sauka a MEXICO kwana biyu zaiyi kenan a na uku zai dawo Nigeria in sha Allah" "Justice rayuwa fa gudu take cikin ikon Allah wai yanzu Turab yayi shekaru biyu a WASHINGTON kenan". Da murmushi papu yace "ehh wllh kinga har gashi zai dawo a kwana kin nan, mun kammala bikin graduation ɗin leeya gashi zamuyi bikin samun nasarorin da yayi" "Masha Allah, to Allah dawo dashi lafiya" cewar mum tana ƙoƙarin tada leeya data fara bacci domin ko har sun ƙaraso gidan. A gajiye suka dawo gidan baki ɗaya dama can a ƙoshe suke shiyasa ba wanda ya nemi yaci abinci, sai khulud ce kawai kecin abincinda aka riƙomata daga restaurant. A parlour bacci ya kwashe leeya har aka kira sallahr la'asar papu kuma office ya koma yayinda mum ta shiga aikin gida. Ita kuma khulud sashen su ta koma baccin ta take hankali kwance domin ba damuwa tayi da sallah ba balle tayi, kuma babu abunda tayi balle taji gajiya. Miqewa leeya tayi daga gajiyayyan baccinda ya share ta ko wanka bata yiba. Sashensu ta shiga tayi wanka kaana ta d'auro alwala tafito ta gabatarda sallah. Bayan ta kammala ne ta tsaftace bedroom ɗin ta duk da lafiya ƙalau yake ba abunda ya sameshi. Da ta gama ta sakko parlour da nufin taya mum aikin gidan wanda hakan ɗabiarta ne tun a gidansu..............✍🏼 BAYAN WUYA..... By RUMANA M DIGGI. EP.15 __________kitchen ta tararda Mum. Da sallama ta ƙarasa wajen bayan sun gaisa taje ta fara wani aikin daban. Sai fira suke abunsu har mum ke tambayar leeya. "Leeya wace makaranta kika nemo da kikeso kije, kinsan tun a waccan ranar justice yace ki zaɓa makarantar da zakije gaba" Wuƙar da ke hannunta ta ajiye tare da faɗi "kinganni nan mum wallahi ni banada sha'awar yin karatu mai zurfi, yanda ake tunani" Cikin mamaki mum ta kalleta tare da faɗin "bakida sha'awar karatu mai zurfi kuma, sai me to. Kina nufin aure kikeso kenan, ashe kuwa akwai babban aiki domin papun ku bazai lamunci wannan ba. Yafiso ya aurarda ƴarsa da karatu mai zurfi domin ta sami abun dogaro dakai, kuma ta samarda ingantacciyar tarbiyya a gidan ta, lallai bazaku wanye lafiya ba kenan idan yaji Wannan batu" "No, mum bawai ina nufin bazanyi karatu ne gaba ɗaya ba, inaso ne nayi tunani domin kuwa Ni ko zan shiga school gaskiya sai dai CATERING SCHOOL amma idan ba ita ba bana gani zanyi karatu yanda akeso domin banada sha'awa" Murmushi kawai mum tayi kaana ta furta "to shikenan ba damuwa Allah yayi mana jagora". "Ameeen ya rabbi mum, mum wai nace zaki barni na kwana wancan wurin" Leeya ta faɗa tana janye labulen wurin tare da nuna mata balcony ɗin nan amma ba sosai ake iya hangoshiba sai idan ka kula sosai saboda bata bangaren kitchen area ɗin yake ba. Baki sake mum ke bin wajen ta kallo tace "ke ƴarnan waya nunamiki wancan wajen?" "Mum nina gano da kaina" "Ikon Allah, to ki rufawa kanki asiri a Kwanan nan ki daina zuwa wajen can domin wajen ba bayyanannen waje bane, wanda yasa aka gina masa shi yasa am'boyemasa shi domin ba wanda ya lamuncewa shiga wajen sai shi kad'ai, idan kina bu'katar shiga zaki shiga amma sai dai idan baya 'kasar gaba d'aya, domin idan yana nan duk inda yake a faɗin Nigeria yana iya gani a wayarsa idan wani ya shiga wajen can" Mum ta faɗa tana ƙara nunawa leeya ƙayataccen balcony garden ɗin. Cikin tsananin son tabbatar da abunda mum ta faɗa tace "ta wayarsa kuma mum, kodai yanada aljanu?" "Ko ɗaya" mum ta faɗa tana girgiza mata kai alamar babu. "To taya zai iya ganin wani ya shiga a cikin wayarsa kuma Alhali baya nan suleja". "Eh akwai CC TV cameras a ciki kuma yayi connecting da wayarsa ta hannu ta yanda zai iya ganin komai da cameran ta ɗauka" "Okay mum na fahimta, amma mum meyasa yayi haka yanada wasu sirrukan ne a cikin wajen da bayaso agani?" "Bayada sirrukan da bayaso a gani a cikin wajen, saidai shi mutum ne da bayason takura ko hayaniya, kwata kwata bayason zama a cikin mutane, kuma idan yana nan bayada wurin da ya wuce masa wancan warin, domin yana ƙaunar irin yanayin wajen. Daga cikin abunda yasa yake zama a wajen nan yanada wata jita wacce a koda yaushe yana zama yayita kiɗa jitar har sai bacci ya ɗaukeshi. Idan har kin kula da kika shigo wajen kinga wasu kujeru biyu a can gefe su kaɗai to akwai wani plastic table dake ɗauke da kayan kida, anan ne yake zama koda yaushe domin bangaren yafi ko wane wuri daɗin zama a faɗin balcony ɗin" Mum ta faɗa tana zube blending ɗinda ta kammala a cikin bowl. Sosai leeya taji wajen ya ƙara shiga ranta tana ayyanawa a ranta a kwanakin nan zata dinga ziyartar wajen baramma da taji cewa akwai kayan kiɗa, a rayuwarta ba abunda yake birgeta kamar tayi kiɗan piano ita kaɗai. "Mum to shi Wannan mutumin faɗa yake yiwa mutane ne idan aka shiga wajen" leeya ta tambaya tanason jin ƙarin bayani. "Hmmm, ba faɗa yake ba duka yake wallahi kuma ba dukan wasa ba. Kafin khulud ta daina zuwa wajen ta daku sosai saida justice ya masa rantsuwa karya ƙara dukanta har ya koma a wannan lokacin". "A gidan nan yake mum, ko shine ya-Turab?" "Shine, wallahi sai kunyi a hankali yayan naku ba sauƙi kuma bayason wasa ko kaɗan, duk wannan da kike gani khulud tanayi saboda baya nan ne. idan yana nan sanyi zatayi liƙiss kamar ba ita ba" "Hmmm to mum Allah dai ya mayarda shi lafiya" Leeya ta faɗa zuciyarta na ƙara hasasomata har ta fara kiɗa da piano a garden ɗin ya-Turab" Sosai sukaci gaba da firarsu har suka kammala aikin, daga nan mum ta fita ta bar leeya a kitchen. Ita kuwa mum ta koma daining area. Bayan Leeya ta idarda komai ta fara jidar abincin tana kai daining. saida ta kammala tsaff sannan ta koma part ɗin ta tayi wanka. KADUNA, STATE. ASHMED SPECIALIST HOSPITAL KADUNA. zaune take gaban wani matashin likita idanunta a kansa, yayinda shikuma yake koromata bayani. kana ganin ta kasan ba ƴar ƙananan mutane bace. Kalarta irin chocolate color ɗin nan ne amma mai ƙonuwa, ganin yanda fatarta ke sheƙi da walwali zaka tabbatar ƴar manyan mutane ce. Tanada yalwataccen gashin ido dana gira, wanda suka ƙarawa fuskar ta armashi da kyau da tsari. Yarinyar bazata wuce shekaru sha shida ba a ƙiyasi, saidai zakaji tausayinta idan kasan larurarda ta kawota a asibitin. "Rankiyadaɗe, dole sai kin fitarda damuwa a cikin ranki fa, kinga yanzu stage ɗin da aka ɗoraki a shan magani yakamata ace zuciyarki na samun natsuwa, kuma kibata lokacin da zatayi tunani" "Stop saying please Dr. B. Areef" Yarinyar ta faɗa kamar zatayi kuka. "Zuciya ta batada wani time da zatayi tunani, kawai ka faɗamin menene abun yi yanzu, saboda nasan yanzu dad na waje yana jiran fitowata kuma idan na fito zaizo ya tambayeka idan ansamu wani ci gaba, me zaka faɗa masa Dr. Beeshwah Areef?" Yarinyar ta faɗa tana gyara zaman Glasses ɗinda ke fuskantar ta, cikin tsananin damuwa. Ɗan guntun murmushi likitan da aka kira da Dr. Beeshwah Areef yayi kafin yace mata "gaskiya zan faɗa masa mana, Rukhshanah menene dad ɗinku ya rageku dashi da zaki ɗauki damuwa ki sakawa zuciyarki. Bayan Kuma kinsan damuwarki babban tangarɗace a wannan tafiyar tamu. A yanzu mahaifinki da mahaifiyar ki harma da ƴan uwanki basuda wani buri da ya wuce suga kin sami lafiya. To menene abun da zai sakaki a damuwa Rukhshanah? kinsan fa damuwarki kamar damuwar ahalin gidanku ne gaba ɗayane" Dafe kai yarinyar da aka kira da Rukhshanah tayi, Alamar surutunda yake yafara isarta. Dr. B.Areef ya fahimci abunda take nufi, hakan yasa shi janyo takarda da biro, yayi ɗan guntun rubutu a cikin ta, ya miƙa mata. bayan ta ƙarɓa ta miƙe da nufin ta fita daga office ɗin. Harta miƙa hannu zata buɗe kofar, santsi ya ɗebe ta zata faɗi. Take ta riƙe sopa ɗinda ke wurin amma duk da haka saida glasses ɗin ta ya faɗi ƙasa. Da sauri ta durkusa ƙasa tana laluben glasses ɗin nata. Sai a lokacin Dr.B.Areef ya lura da abuda ya faru. "Subhanallah" ya furta da ƙarfi yana ƙarasowa wajen da gudunsa. Ɗagota yayi, da sauri ya zaunarda ita kan sopa. Sannan ya juya ya ɗauko glasses ɗin ta ya saka mata. Nan komai ya bayyana a ganin ta. Da murmushi ta kalli Dr.B.Areef tace "Nagode". "Ahh ba damuwa Allah ya tsare gaba". "Ameen" ta faɗa tana barin office ɗin. Tana fitowa daga cikin office ɗin wasu 'yan mata biyu sa'anta suka rugo kanta da saurinsu suka rungumeta. "Rukhshanah ya jikinki ina fata dai ansamu ci gaba ko sweet sis?. d'aya daga cikin 'yan matan ta faɗa. "Hmmm, twiney kin rigani magana ne kawai amma abunda nazo na faɗa kenan" Dayar ta faɗa tana shafa kumatun Rukhshanah kamar wata ƙaramar yarinya. Jin tayi shiru bata ce musu komai ba, yasa suka fahimci batason damuwa, "Twiney muje ta huta kafin dad ya ƙaraso kho". "Ok muje ga resting sitter ta zauna. Dayar yarinyar ta faɗa tana riƙo hannun Rukhshanah" A resting sitter suka kaita ta zauna kafin itama ɗayar yarinyar ta zo ta zauna a kusa da Rukhshanah, zaman ta ba wuya sai ƙarar ringing ɗin waya ya fara ruri a cikin hand bag ɗin da ke hannun ta. "Hello, ya-fahad". Yarinyar ta faɗa tana kara wayar a kunnenta. "Yes, FANNAH an fito da ita ne" "Eh, yanzu ta fito muna ƙarasowa tana fitowa" "Okay ya akayi, ya jikin nata fatar dai akwai cigaba a stage ɗin nan data kai kho, kinsan yaune farko da akayi mata gwaji akan magungunan da aka bata a wannan watan" Cikin murya mai alamar damuwa yarinyar da aka kira da FANNAH tace "to wallahi ya-fahad muma abunda muka damu musani kenan amma ba dama, saboda gata a zaune irin dai batason damuwa ko surutu ɗin nan" "Allah sarki abun ya tashi kenan, gaskiya ba haka naso naji ba, but ba damuwa bara nazo na ɗaukeku a hospital ɗin domin Dr. Beeshwah yakira dad yayi masa bayani, yace masa basai yazo ba tunda gaku kuma da driver kuke, shine dad yace na kiraku idan da buƙatar sai yazo. Idan kuma ba bukatar hakan na sanarda shi domin 11pm zasu shiga meeting da Company A.R.P" "Wow Masha Allah, gaskiya nayi farin ciki, kace A.R.P zasu fara aiki a shekarar nan kenan" "In sha Allah" wanda aka kira da ya-fahad ya faɗa a taƙaice. "Okay To kace masa yaje kawai zamu iya dawowa gida ai". "Tau nima dai gani nan zuwa a hanya kujirani, amma ki faɗawa MAYAH DA NU'AIM subi driver su koma ke kuma da Rukhshanah sai kujirani nazo na maidaku gida" "Okay ba damuwa Amma NU'AIM badashi muka zoba mummy tace bazai biyomuba" "Okay to taje ko kuma ke kije" FANNAH kamar zatayi kuka tace "haba ya-fahad taya zakace twiney taje ni natsaya tarefa mukazo, gaskiya bazataje ko'ina ba tare zamu koma gida" Kitttt ya kashe wayar domin yasan idan dai da wayar ne yake mata magana to bazataje ko'ina ba amma idan ya ƙaraso da kanshi dole zataje ko kuma yar uwarta taje. "Menene naji kuna gardama da ya-fahad twiney?" Yarinyar da ke zaune a gefen Rukhshanah ta tambaya. "MAYAH, wai ya-fahad ne yace kije kibi driver ku koma gida, nikuma da Rukhshanah mutsaya mujirashi yazo ya mayar damu" ta faɗa fuskar ta fallll da damuwa. Kamar wacce aka cewa za'a rabasu har abada, MAYAH ta miƙe cikin tashi hankali tace"No FANNAH meyasa ya-fahad zaice haka, motarsa bazata iya daukarmu gaba ɗaya bane kome? Gaskiya nidai bazanje nikadai ba kuma kema bazakije ba". "Iyyeee, nine yayan ko kuma kune yayuna. Na riga na gama magana dayar ku taje driver na wajen gate yana jiranta" Kamar daga sama haka sukaji muryar ya-fahad ya shigo hospital ɗin. Da sauri sukayi kansa suna rokonshi harda yan guntun hawayen su; " ya dan Allah karkayi mana haka, munfiso duk abunda zai sami daya ya samemu mu duka biyu tunda aka haifemu mu biyu bamu ta'ba rabuwa ba. Kuma dan wannan bazaka rabamu ba, munfiso komai zai samemu ya samemu gaba ɗaya" Suka faɗa cikin gamin baki. "Kujimin yara da shashanci ku har yanzu kun girma amma kamar baku girma ba, rabaku nace zanyi? gida fa nace akai ɗaya daga cikin ku dan kada kubar driver nan ya koma shi kaɗai bayan tun ɗazu ya tsaya jiranku amma shine kuke min kuka kamar nace bazaku qara haduwa ba" Abu ɗan ƙarami kamar wasa, suka qi yarda shikuma ya nace kan baza'a bar driver ya koma shi kaɗai ba dole kuma sai ɗaya daga cikin su tabi driver. Sosai mutane suka taru a wajen suna kallon ikon Allah, yayinda Rukhshanah ta rasa inda zata saka kanta saboda batason hayaniya a ƴan kwanakin nan har school ta daina shiga saboda irin wannan. Rigimar bata tsaya ba har saida aka kira dad ya yanke hukunci subi driver su biyu, shikuma ya ɗakko Rukhshanah suzo gida. "Okay dad ba damuwa, amma wallahi dad Yakamata a daina biye musu kan haka nan gaba kaɗan fa aure zasuyi kowa ta kama gabanta" ya fahad ya faɗa yana katse wayar. "Ya-fahad mu miji ɗaya zamu aura idan bazai auremu mu biyu ba saidai yaje ya nema gaba" FANNAH da MAYAH suka faɗa suna barin wajen aguje saboda sanin halin ya-fahad zai iya kaimusu duka. Guntun tsaki yaja yana nufar inda Rukhshanah ke zaune. Da zuwansa ko magana baiyimata ya miƙa mata hannun shi, miƙa masa nata hannun tayi ya tayarda ita tsaye suka fara tafiya. Har suka isa mota ba wanda yace kanzil tsakanin sa da ita, zagayawa yayi ta bangaren hagun driver ya buɗemata ta shiga, sannan shima ya zagayo ya shiga ta bangaren driver ya fara tuƙa motar. "Ya-fahad meyasa kace bazamuje tare da FANNAH da MAYAH ba" Rukhshanah tayi maganar kanta a ƙasa kamar ba ita tayi ba. Cikin mamaki ya kalleta yace" sannu Rukhshanah ya jikin naki, Kina buƙatar wani abune kafin mu isa gida, ko kuma mu tafi kawai". Faɗin fahad yana qoqarin packing ɗin motar. "No ya-fahad bana bukatar komai inaso mu isa gida da sauri naji ko FANNAH da MAYAH suna lafiya domin bazan iya yin Magana ba lokacin da kuke rigimar da nima zan bisu gaskiya" "Humm, Rukhshanah kenan ae saboda ke nayi haka" "Saboda ni kuma ya-fahad?" Sai a lokacin ya fahimci 'kwa'barda yayi domin yayi tunanin a zuciya yayi maganar ashe a fili ya furta ta "to yanzu ya ma zance mata ta karta fahimci nufina" ya faɗa a zuciyarsa amma a wannan karon zancen baifito fili ba. "Kayi shiru ya-fahad bakace komai ba" "Rukhshanah saboda ke nayi haka, nasan da muna tare dasu yanzu zasu isheki be da surutu, kuma hakan zai iya haifar miki da wata illa domin nasan zasu isheki ne da tambayoyi har sai kin gaji da amsa musu" "Uhmm ya-fahad kenan indai dan wannan ne ai ba matsala, kuma Ni nasan bazan ji sun takuramin ba tunda inajinsu har cikin raina, duk a faɗin gidan idan aka cire mummy da dad ba wanda nake son kasance dasu kamar FANNAH da MAYAH" Sosai ya-fahad yaji haushin maganar da ta faɗa "kenan duk irin kulawar da yake gani yana bata, shi baya cikin mutanen da takeson kasancewa dasu a cikin gidan, to meya rageta dashi ne, me twins suke mata wanda shi baya yi mata" "Ya-fahad kayi shiru wani Abu ya faru ne" Murmushi yayi irin wanda kana ganin shi kasan murmushin yaqe ne yace mata "ba komai Rukhshanah kawai inaso ki daina magana haka kibari ki huta Kinji, ki bawa ƙwaƙwalwarki dama tatunano wani abu". "Stop ya-fahad menene haka, Ni zan iya magana da ƙwaƙwalwa tane, ko kuma zan iya bata umurni tabi. Bana son maganar tunanin nan Pleaseeeee" cewar Rukhshanah kamar zata yi kuka. "Sorry our Rukhsha kiyi hakuri bazan ƙara faɗar haka ba Kinji". Fad'ar fahad dai-dai lokacin da ya karaso gate ɗin makeken gidan nasu wanda ya amsa sunansa gida yasha kyau ya gaji da tsaruwa.............✍🏼 BAYAN WUYA....... By RUMANA M DIGGI EP.16 ___________K. WAASIB MANSION, SULEJA NIGERIA. zaune take a ƙayataccen balcony ɗin da ke gefen gidan, sosai takejin daɗin yanayin ƴar siririyar iska na ratsowa tare da kamshin furanni. Piano da ke gabanta take dannawa tanabin kukan tsuntsayen da ke wurin Gwanin ban sha'awa. Wayarta ƙirar iPhone 16 ƴar yayi ta fara ƙara alamar kira ya shigo (my whole world) abunda ya bayyana a screen ɗin wayar kenan. "Mum? Ta furta cikin tsorata da abunda mum zata cemata idan ta ɗauki wayar. Saita kanta tayi tukunna kafin ta ɗauki wayar, "Assalamu alaikum, mum!!" "Leeyana ina kika shiga naje part ɗinki bakyanan kinsa fa gobene taron walimar yayanku, kuma kinsan by 2pm jirgin su zai sauka ba'a gyara masa ɗakinsa ba. Kuma ga baƙi sunata zuwa, ga siyayyarda zakuje kuyi amma ban ganki ba har yanzu" "Lahhhh, mum Dan Allah kiyi hakuri wallahi duk na sha'afa kiban mintuna uku kacal ganinan zuwa" "Azo lafiya" mum ta faɗa tana yanke wayar. Cikin gaggawa leeya tabi ta hanyar da ta shigo wajen ta fita ta laundry room inda ba wanda zai ganta ta koma ɗakinta. Allah sarki Rayuwa, a shekara goma sha Bakwai din nan na leeya gaba ɗaya, ba wanda zai ganta yayi tunanin itace wancan leeya ta baya. Domin kuwa ba abunda bai sauya ba atattare da ita face abu ɗaya zuwa biyu. Niqab ɗin da take rufe fuskar ta dashi, da kuma rashin kallon madubi da take. Amma idan kacire wannan ba abunda bai sauya ba daga gareta, kama daga jikinta, adonta, tafiyar ta, maganar ta, surarta, wayewarta da sauransu. Canja kayan da ke jikinta tayi ta sanya doguwar rigar atamfa, sannan ta ɗakko ɗan kwalin rigar ta yafashi bayan ta saka niqab. Saida ta isa gaban mirror ne da ɗaura ɗankwalin kana ta fita waje. Master parlour ta nufa domin tasan kowa yana wurin, Saboda duk a gidan parlour yafi ko'ina girma. Sallama ta furta yayinda take shigowa cikin parlour. Ancika sosai dangin papu dana mum kamar wani babban taro ake ko family meeting, nan kallo ya koma kan leeya wacce mafi yawa daga dangin basu san da ita ba. Amma dake taro akeyi ba kowa ya damu da sai yasan ko wacece ba sai waɗan suka kware a gulma. Saida tayi duba sosai kafin ta iya hango mum can gefe ita da wasu bakin. "Mum gani me za'a yi yanzu" Takarda ta miƙa mata tare da A.T.M tace "kasuwa zaku fara zuwa ku siyo Kayan nan. Khulud da driver na mota suna jiran ki" "Tau mum bara na dakko mayafina saina samesu a gate kho" "Okay to banda bata lokaci dan Allah kuyi maza ku dawo" "In sha Allah mum" leeya ta faɗa tana juya ta koma bedroom din ta. Bayan ta ɗakko ta fita ta tararda su, khulud na gaba ita kho leeya ta shiga baya. Domin duk zasu fita haka suke idan leeya na gaba baya take shiga. Idan kuma leeya na baya gaba take shi ga. Idan kuma leeya ta matsa ta cimata mutunci tsafff haɗi ta zageta da iyayenta baki ɗaya, shiyasa leeya ta daina faɗin komai akan hakan. KUDUNA. Suna isowa gate ɗin tangamemen gidan Fahad yayi horn, take aka wangale gate ɗin gidan. Ya tura hancin motarsa ciki. A compound ɗin gidan yayi packing ɗin motar sa domin fita zai kuma yi yanzu. Yana fitowa daga mazauninsa ya koma bangaren da Rukhshanah take itama ya buɗemata, fahad ko kaɗan bashida girman kai kamar sauran masu kuɗi. Idan ka ganshi alamace kawai zata nuna kanta shi ɗan manyan mutane ne amma idan ta tashi ce bazakayi tunanin haka. Yana buɗemata ta fito motar, da gudu FANNAH da MAYAH suka yo kanta a karo na biyu kamar dai yanda sukayi a asibitin. "Twins har kun iso kenan" Cikin tsananin farin ciki FANNAH da MAYAH suka dubi juna tare da faɗin "Sweet Rukhsha Kinji sauƙi kenan, Masha Allah" Suka faɗa suna janyeta daga motar suka shige da ita cikin gidan gaba daya. Ya-fahad kuwa tun tuni ya shigewarsa gida ya barsu a wajen. Wani haɗaɗɗen parlour mai ɗauke da kayan ado kala daban-daban, anyiwa parlourn gaba ɗaya ado da pakistan furnitures, da sauran kayayyakin adon da ke parlorn duk na india da Pakistan ne sai kayi tunanin ma ba'a Nigeria kake ba. FANNAH da MAYAH da Rukhshanah suka shigo parlour riƙe da hannun juna, bakunan su ɗauke da sallama. "Wa'alaikumsalam, yan ukun mummy kun dawo" wata farar mata mai zubin manyan matan india ta faɗa. kamaninta daya da FANNAH, MAYAH, FAHAD da kuma NU'AIM saɓanin RUKHSHANAH da fatarta ke da dan duhu ta ban banta da tasu. Faɗawa Rukhshanah tayi jikin matarda ke zaune kamar zatayi kuka tace "mummy wallahi babu wani cigaba". "Subhanallah, duk suka faɗa harda ya-fahad da yake shigowa parlourn. cak ya tsaya da tafiyarsa yace "mum aje da ita US kawai dan Allah wannan wahalar tayi yawa ki duba kiga fa tun ranar Lahadi har yau laraba bata yin wata isashiyar magana data fara magana daya, biyu shikenan. Zata iya kai 3-4h bata ƙara faɗin komai ba" Matar cikin tausayawa tace "wallahi kuwa nima shi nake dubawa haka tasha wahala a idanun nan nata, da taimakon Allah da taimakon Dr. Kanal raghib akasamu ganinta ya dawo a cikin glasses ɗin nan. "Mum to kho Indian za'a kuma kaita" "Hmmm, Fahad kenan duka duka wannan shine wata na biyu fa da mukayi a hospital ɗin nan, har asibitoci nawa za'a kaita kenan Fahad" matar ta faɗa fuskarta fallll da damuwa. "Mummy bawai maganar asibiti nawa za'a kaita bane, duk inda mukaje mukaga nasara nan zamu tsaya. Bawai muzauna tayita shan magani ba wani cigaba ba. Ki duba kiga yanda muka sha yawo da ita kan matsalar idanun nan a nan gida Nigeria, bawata nasara. Amma kiga muna fita da ita ko sati ɗaya bamu cikaba ta fara ganin komai da taimakon wannan glasses ɗin" "To amma ai shi Dr. Kanal raghib ba likitan qwaqwalwa bane, iya idanune nasa taya zamuje masa da zancen nan" Murmushi mai ma'anoni Fahad yayi kafin yace "mum shifa Dr kanal raghib haifaffen India ne BHOPAL yake. Yanzu idan shine yazo yace maki kafff faɗin jaharnan waye kwararren likitan fata wazaki faɗa masa" fahad ya faɗa cikin sigar tambaya "Dr. Ilyass jiƙamahi" mummy ta faɗa a taƙaice. Murmushi mai sauti yayi kana yace" mummy ki duba fa kema ba likita face amma sbd Dr jiƙamahi yayi suna har kika sanshi haka, kuma ke ba haifaffiyar ƴar Nigeria bace. To inaga wanda aka haifa a ciki" Shiru mummy tayi tana jiran ƙarin Bayani. Ɗan gyaran murya fahad yayi sannan yace "mummy likitoci sunsan junansu sosai, ba wai likita kaɗai ba ma mafi yawan ma'aikata sunsan junansu koda ba aikin su ɗaya ba. To balle waɗanda suke aiki ɗaya, kuma agari ɗaya. Kunga zamuje ne mu sami Dr kanal raghib ya faɗamana ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa, a BHOPAL INDIA idan ya faɗa mana sai mu gaya masa matsalar mu ko za'a sami waraka" "Gaskiyane ya-fahad abunda ka faɗa shine daidai Yakamata a koma india da Rukhshanah ko za'a sami nasara domin a gaskiya nan Nigeria babu ƙwararrin likitocin ƙwaƙwalwa domin kuwa da akwai da mun samu, kaga har abuja anje da ita amma ba wani cigaba" cewar MAYAH dake can gefe dasu. "Gaskiya mummy ya kamata ayiwa dad magana kan shawarnan da ya Fahad ya kawo ko ya kika gani ke" FANNAH ma ta faɗa Dason jin abunda mummy zata yanke. "Hakane fahad amma yanzu ku bari idan muka dawo da naija state gobe zamuyi tafiyar, ba'a can Zamu kwana ba idan muka dawo sai a ci gaba da Maganar sake fita da Rukhsha waje" "Me zamuje yi a suleja kuma mummy inace dai ba gidan dad babba zamuje ba kho" MAYAH ta tambaya tana ƙanƙan da idanu. "Menene idan chan zamuje". "A gaskiya mummy mudai bazamu jeba kho twiney" cewar MAYAH tana kallon FANNAH. "Ehhh mummy gaskiya bazamuje gidan dad babba ba mudai". "Kuzo nan" cewar mummy ba wasa a idanun ta. "Mummy kiyi hakuri zamuje" MAYAH ta faɗa kamar zatayi kuka. Wata uwar Tsawa mummy ta daka musu da sauri suka ƙaraso wajen ta. "Sai nace ku zauna kho" cewar mummy. Zama FANNAH tayi tana kama hannun MAYAH suka zauna tare "Mummy kiyi hakuri idan ranki ta ɓaci da abunda muka faɗa, wallahi bawai bama son zuwa gidan dad babba bane, ko domin mum-fanaya zamuje da kuma dad babba. Amma kinsan yanda khulud ke yimana kamar ba jinin taba, tafison ƙawayenta fiye damu ƴan uwanta. Sai tayita mana abu kamar ba dangi ɗaya ba" cewar FANNAH idanun ta na cikowa da hawaye. FANNAH da MAYAH ba kamar kowa bane saboda su abu kadan zai sakasu kuka. Ko yakai ayi masa kuka ko bai kaiba, kuma su a rayuwarsu basa qaunar ganin mahaifiyarsu tayi fushi dasu to wannan shine Babban tashin hankalin su. Kuma ko a Yanzu suna gani kamar tayi fushi dasu ne. "Mummy, wallahi kinji Dalilin da yasa muka faɗi haka" shiru mum batace komai ba. Rukhshanah dake lafe jikin mummy tun ɗazu, ta kalli mummy tace "mummy dan Allah ki duba uzurinsu mana Please, sai magana suketayi amma kinyi shiru". Sai a lokacin mummy ta ɗago da idanunta ta kallesu tare da faɗin "shikenan ku tashi ku tafi, amma ku tabbatar kun fara shirin zuwa suleja gobe zamu ɗauki hanya in sha Allah" "Tau in sha Allah, zamu cika trolly mummy karki damu shekara zamuyiwa dad babba a gidansa" MAYAH ta faɗa tana dariya. Dariya mummy tayi itama kaana tace"to ai shikenan kuje ku cika trolly ɗin kutafi can wajen hajia fanaya koni na huta ai taje ta ƙara kuzama ku huɗu kenan. Harda Rukhshanah a tafi da ita". "Mummy!" Fahad ya kira sunan ta a taƙaice "Na'am fahad ya akayi" "Mummy naji kuna maganar zuwa SULEJA ne gobe kuma banida masaniya" "Sannu dad" MAYAH ta faɗa tana taɓe baki. Dayake itace mai neman rigima dama, FANNAH ba ruwanta da irin haka. Haka itama Rukhshanah batada neman rigima amma MAYAH kam ko za'a yankata indai zata tashi to idan taga abun magana sai tayi. Pillow ya ɗako da gudu ya miƙe da nufin ya jefa mata, ita kuwa tana ganin haka ta tashi da gudunta itama ta fita parlourn tare da janyo ƙofa ta rufe rufff tana ta dariya. "Da kin tsaya da kinga ikon Allah wallahi" Fahad ya faɗa yana komawa inda yake zaune. "Ikon Allah kuma ya-fahad na nawa aini tun kafin a haifeni ake ganin ikon Allah, har aka haifeni ba'a daina gani ba, har na girma na fara gani Nima. Menene saura to" cewar MAYAH tana leƙowa ta window. Sake jefamata pillown yayi daga inda yake ita kuwa ta ƙara fecewa aguje. "Yawwa mum nace yaushe ne za'ayi tafiyar? Fahad ya tambaya. "Gobene ya-fahad amma nima bansan me zamuje yi ba, wata ƙila ziyara kawai zamuje kho mummy" FANNAH ta faɗa tana kallon mummy. "Ehh to, makamancin haka. Amma kuma yayanku Turab ne za'a yiwa walimar kammala karatun sa na likitan sojoji" "Yaushe zai dawo kenan" fahad ya faɗa yana gyara zaman sa. "Inaga tsakanin yau da gobe zai dawo domin gobe za'a yi walimar" "Amma Turab ya rainani mummy yanda nayi missing ɗin guy ɗin nan har zai iya shigowa Nigeria ba tare da nasani ba, wallahi mummy a wannan karon idan kukaji muna masifa karku shiga" cewar fahad. Wayar sa ce ta fara ruri alamar kira ya shigo. "FANNAH miƙomin wayana" Miƙewa FANNAH tayi da sauri ta ɗakko wayar "lahhhh ya-fahad, ya-Turab ne ke kiranka fa" "FANNAH miƙomin wayana banason shashanci ci" "Wallahi da gaske neke duba kagani" FANNAH ta faɗa tana miƙo masa wayar daidai lokacin da kiran ya katse. "Lahhhh wallahi kuwa shine mummy, kenan yana Nigeria ma kinga ma number Nigeria ce" Fahad ya faɗa yana mayar masa da kiran. Sai da wayar ta tsinke ba'a ɗaga ba, "mummy yaƙi daga kiran fa" "Fahad ka rufamin asiri Ni na isa na shiga tsakanin ku da Turab" Har ya buɗi baki zaiyi magana sai ga wani kiran ya shiga "hello" fahad ya faɗa cikin zumuɗi. Cikin husky voice ɗin sa ya amsa " Yes" "Turab yaushe ka shigo Nigeria ne bansaniba. Kuma Baka gayamin ba, alhali ko jiya da dare munyi chat dakai" "Yanzu" Turab ya faɗa daga cikin wayar. Fahad yasan halinsa sarai yasan bayason yin doguwar magana ko kuma zance mai tsawo. "Any problem" fahad ya tambayi Turab. "Dakai za'a zo airport?" "Bana suleja, ina kaduna amma yanzu zanzo in sha Allah" "Ok azo lafiya" Turab ya faɗa yana shirin kashe wayar. "Amma kajirani zanci uban mota yanzu zan ƙaraso" Murmushi kawai Turab yayi batare da yace komai ba ya katse wayar. Fahad kuma da ya fahimci kallonda mummy ke masa tun sa'adda yace gashinan zuwa suleja, ya lura tana masa kallon bakada hankalin ɗin nan. Setting ya shiga a wayarshi sannan ya kunna phone ringing saida yaɗan jima yanayi kafin ya kara wayar a kunnensa. "Hello ranka ya daɗe sir, Barka da aiki. Ya gida ya iyali?" ɗan jimmm yayi kamar wayar yakeyi da gaske kafin ya kuma faɗin "Ahhh mummy da dad duk lafiya ƙalau suke wallahi alhmdllh" Subhanallah, yanzu kana nufin zaman za'a kumayi kenan. Allah sarki gaskiya shari'ar nan tayi tsawo sosai, nikam nace a zauna kawai ayi komai a gaban kowa. Ni lauyan gwamnati ne bazan tsayawa ƙaryaba, saboda haka ku jirani kawai idan nazo komai za'ayi sai naji da kunnuwana" Second ɗaya, biyu, uku baice komaiba sai a second na huɗu ne yace" ahhh ba komai wallahi ranka ya daɗe yanzu kam yamma tayi da zuwa Abuja amma bara nakira dad nayi masa bayani inyaso sai nazo na kwana a suleja gobe tun da sassafe kafin masu binciken suzo mu mufara ganin suspect ɗin". Kamar dai ɗazu yayi shiru kaɗan bai ce komai ba kamar wanda yake wayar da gaske sai da yaɗauki tsawon seconds sittin sannan yace "shikenan ba damuwa yallaɓae yanzu zanyi shiri kafin karfe huɗu zan kuma kiranka in Allah yaso, Yanzu dai bara na fara shirin tafiyar kho, dan inaga nama fasa weekend ɗinda nazo zan dawo gaba ɗaya" "Okay rankashidaɗe na gode mu jima lafiya" cewar fahad yana sauke wayar a kunnen shi. Cikin damuwa ya kalli mummy dake sauraren wayarda yake tun sa'adda ya fara hankalin ta na kanshi yace" mummy, ina labarin shari'ar nan dana baki, wacce akayi kisan kai a makaranta kwana ta maza a abuja". "Eh na tuna" mum ta faɗa tana gyarawa Rukhshanah kwanciyarta da take ta faman bacci tun ɗazu. "Shine aka nemi suspect ɗin aka rasa bayan zama biyu da akayi a kotu, amma anyi nasarar kamoshi jiya da dare. Kuma wasu ne aka aika suka saceshi. Su sun tsere amma shi anyi nasarar cafkoshi, shine aka kirani inaso na gana dashi gobe tunda sassafe kafin a wuje court". Fahad ya faɗa kamar da gaske................✍🏼 BAYAN WUYA.... By RUMANA M DIGGI EP.17 ____________shiru mummy tayi tana kallon sa, domin ta kusa ta harbo jirginsa, ta kusa ta gane duk shirine ba gaskiya bane. Ɗan gyaran murya fahad yayi saboda yaga kamar mummy ta manta dashi zaune a wurin. "Allah sarki, haka akayi kenan? Yanzu kai meye naka da suspect ɗin kaida kake lauyan gwamnati?". "Tau kedai mummy ganemin hanya, Nima bansaniba ba amma ai idan naje da kaine zan san ko menene". Dariya ta kusa suɓucewa mummy ganin yanda yake yi kamar da gaske. "Tau Allah ya tsare ya kaika lafiya". "Ameen thumma Ameen sweetheart, nifa bana ma son tafiyar nan kawai ta kamani dole ne, nida nazo weekend ma. Naso nayi 2weeks wallahi mummy". "Fahad kenan ba komai ka tafi kawai, kaida naji kana faɗin ka fasa weekend ɗinda kazo kayi". "Lahhhh yaushe na faɗi haka mummy" fahad ya faɗa yana ɗan waro idanu. "Ya-fahad ka manta lokacin da kana waya ka faɗawa ogan naku" faɗin FANNAH itama tana dariya. "Awwwn, ashema nace haka, kunga Ni ban masan nace ba ai. Bara dai kugani na tashi kar dare yaymin dama kayana na nan parked ban walwale ba". "Uhmmm" kawai mummy ta faɗa tana barin wajen. Shima tashi yayi ya ƙaraso inda Rukhshanah ke kwance yace"baiwar Allah, Allah ya baki lapiya Rukhshanah. Zan dowa nan bata jimawa ba muje aimiki magani da iznin rabbi kema kiyi walwala kamar kowa" fahad ya faɗa yana shafa goshinta zuciyar sa cike falll da tausayinta. FANNAH itama tausayin nata ne ya kamata nan da nan idanunta suka ciko da kwalla tace" wallahi ya fahad nima ina qaunar naga Rukhshanah ta sake kamar dha Ni inaga ma lokacin da muke innovation specialist magungunan sunfi karɓarta bisa waɗan nan na asibitin Dr Beeshwah Areef. Saida ta fara amfani da sune fa ta zamo haka, bata son surutu, batason yawan yin magana, Batason hayaniya ga yawan bacci" cewar FANNAH cikin tsananin tausayin Rukhsha. "Tau Allah ya bata lafiya ki zauna nan da ita na san MAYAH na nan tana jira na fita ta dawo nan, dan Allah ku kula da ita sosai Please ƙannena, kuma banda damuwa karku sakata surutu Please. Idan kukayi haka gobe zan fita daku shopping idan kunzo naija state" "In sha Allah ya-fahad zamu kula da komai karka damu, Allah ya kaika lafiya ya tsare hanya. Ammafa kaje kayi sallama da mummy karka tafi" "Haba dai ke kuwa, ai dole ne naje nayi sallama da ita. Har dad ma sai nabi ta Company nayi sallama dashi tukunna saboda shima nasan zaizo gobe". Fahad ya faɗa yana shigewa sashensa. Kamar kuwa yasan MAYAH jiransa kawai take, yana fita ta cillo parloun kamar na an harbota "twiney ya-fahad ya tafi kho? mayah ta faɗa kamar mai yin raɗa. "Waya gayamiki ya tafi, kayansa yaje ya ɗakko fa yace bazai bar gidan nan ba sai kun haɗu dash..... " Tun kan FANNAH ta idarda maganar, MAYAH ta zabura aguje zata koma inda ta fito har takai tsakiyar parlourn FANNAH tace "to wasa nake ya tafi, sai jan rigima ga kuma tsoro". Dakatawa MAYAH tayi da gudun da take ta waiwayo itama tace"to waya gaya miki shi nake yiwa gudun Ni, kawai ina exercise ne na rage ƙibar kumatu". Har Mommy dake shigowa parlourn bata san sa'adda dariya ta suɓucemata ba. *ABUJA STATE* Da misalin ƙarfe biyu da kwata jirginsu yayi landing a NNAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA. Sanye yake cikin suit bold colour. Fuskar sa ba alamun fara'ah ko kaɗan, kamar bai taɓayin dariya ba. A ƙasan zuciyarsa kuma tsaki yake yafi dubu. Sai fama kallon tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun sa yake ƙirar Itali. Trollynsa dake janye a hannun sa na dama ya sauya mata hannu zuwa hannunsa na hagu ya ci gaba da janta a gajiye. Hannun sa ya saka cikin aljihun jacket ɗinsa yafito da wayarsa. "Our boss" Number da akayi saving da wannan sunan ya dannawa kira. Kamar jiran kiran nasa akeyi, aka ɗauki wayar da sauri. "Ko na shigo motar kasuwa na dawo gida ne" ya faɗa cikin muryarsa mai kamada wanda ya tashi daga bacci. " sorry son, muna airport ɗin yanzu haka" aka faɗa daga cikin wayar. Katse wayar yayi bayan ya kwatanta masa inda yake, wuri ya samu ya ɗan zauna ya jira isowarsu. Bai jima zaune a wurin ba ya fara hangosu tafe. Hannu yayi masu tun kan su ƙaraso ya taryesu. Papu, Aunty Rahma wato ƙanwar papu, da wasu mutum biyu daga cikin familyn su kazo tarbar Turab. Yana ganinsu kuwa ya ƙaraso wajensu, bai tsaya komai ba ya rungume mahaifinsa, sun jima a haka kafin ya sake shi suka gaisa da mutanen da sukazo tarbashi. Nan suka ɗauki kayayyakin shi aka saka a mota suka ɗau hanyar komawa suleja. K. MANSION SULEJA NIGERIA. "Mum, inaso naje nayi wanka nayi sallahr la'asar sannan na dawo, inaga kafin haka ma duk abincin nan ya ida nina" cewar Leeya tana yamutsa abincin. "Okay ba damuwa kije, kuma karki jima dan Allah. Idan zaki sakko ki karamin khulud justice yace gashi nan sun kusa ƙarasowa, kuma ba'a gyara ɗakin Turab ba banaso yazo ya sami ɗakin da ƙura duk da nasa ba wani gyara za'a yi masa sosai ba" "Okay mum , in sha Allah zan gayamata sai muje mu gyara. Yawwa mum ban faɗa miki ba ɗazu da kika je sashen da ɓaki suke ankira wayanki maman twins tace wai suna hanya" "To Bara na kirasu naji yaushe ne zasuzo yau ko gobe" cewar mum tana danna wayar alamar kira zatayi. Leeya na fita daga kitchen area ta nufi part ɗinsu hankali kwance take tafiyarta domin ba kowa a parlourn duk suna can sashen su na baƙi. Bedroom ɗin ta ta nufa direct ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da yin alwala ta fito, sallah kawai tayi ta saka wasu kaya sannan ta dubi niqab ɗin da yayi daidai ta kayan ta saka ta fito. Bedroom ɗin khulud ta nufa duk da ta ganshi a buɗe hakan bai hanata knocking ba "baki ganshi a buɗe bane bane kike min knocking" khulud ta faɗa a tsawace daga cikin bedroom ɗin. "Sorry sis mum ce ke kiran ki, tace wai kizo muje part ɗin ya-Turab mu gyara sun kusa karasowa" Da sauri khulud ta wuntsilo daga kan gadonda take kwance ta fito ba shiri "me kikace ya-Turab ya kusa ƙarasowa kuma ba'a gyara masa ɗakinsa ba?" "Eh haka nace khulud kizo muje mu gyara masa kinga mu biyune ai yanzu zamu kammala" A karo na farko da Leeya taji khulud tayi mata magana a tausashe"wallahi sis ban iya gyara ɗaki ba, muje dai ke ki gyara" Mamaki ya kusa kashe leeya jin khulud takirata da sis Yau "hmmmm" kawai leeya ta faɗa tana wucewa gaba. Gwalo khulud ta fara yimata tana yimata dariya a can ƙasan ranta "sha-sha-sha, wai harta yarda da zuciya ɗaya na kirata da sis, to wallahi ni bazan taɓa zama sistern kiba har abada, idan ma da akwai wacce na tsana a duniyar nan to tana bayanki. Yanzun ma wallahi idan ba aikin ya-Turab bane banga abunda zai saka Ni jerowa dake ba" khulud ta faɗi maganar a cikin zuciyarta. Har suka ƙaraso ɓangaren nasa ba wanda ya ƙara cewa uffan ulud ce gaba, leeya na bayanta. Dayake khulud tafi Leeyana sanin bangaren. "Akwai key hannunki?" Khulud ta jefawa leeya tambayar tana watsa mata harara a fakaice. "Wallahi babu key, amma Bara na je na karɓo, dakin a buɗe yake ga key can a jikin handle ɗin kofar" Leeya da ta lura da key sarqafe a kofar ta faɗa tana shigewa gaba. Murza key ɗin tayi tare da buɗe kofar ɗakin a hankali kamar mai jin tsoro. Banketa khulud tayi ta shigo ɗakin, sai bayan ta shigone ta juya kanta tace "sorry, bankula dake a wajen ba, ki shigo ki fara aikin" daga haka khulud bata ƙara faɗar komai ba ta wuce bedroom. Tsintsiya ta nema ta rasa a part ɗin gaba ɗaya, saida ta sauƙa ƙasa sannan ta ɗakko duk abunda tasan zata buƙata wajen aikin. Dayake ɗakin baida datti sosai, domin kuwa badan ƙura ba zaka yi tunanin ma akwai mutum a cikin ɗakin. Share parlourn tayi tsafff, sannan ta janyo mopping machine tayi mopping. Bayan haka kuma ta gyara masa show display ɗinsa tsafff, daganan kuma ta ta gyara masa perfume stand show glass. shima ta sake jeren gwanin ban sha'awa, komai na cikin parloun ta gyara masa shi kamar yana nan. Sweet air freshener ta ɗakko ta fesa ko wanne lungu da saƙon na parlorn, take ƙamshin parlourn ya sauya gaba ɗaya. Bedroom ta shiga da nufin shima ta gyarashi ta fito "ikon Allah" Abinda Leeya ta faɗa kenan yayin da taga khulud kwance a kan gadon da take kyautata zaton shine na ya-Turab. Kamar yanda tayi a parlourn nan ma haka tayi saida ta gyara komai da komai. Har zata fita taji faduwar wata drawer cabinet kuma ga alamu kayane ciki. "oh Allah, wallahi drawer nan kinban aiki" cewar Leeya tana ƙarasawa gaban cabinet ɗin. Kayan da suka zuba a ƙasa ta fara gyarawa tana mayarwa a ciki. Ƙarar buɗe ƙofa leeya taji. Bata ɗaga kanta ba kuma bata motsaba, domin ita a tunanin ta khulud ce ta shigo. taci gaba da aikinta. jin anyi shiru ba sallama yasa tayi niyar ɗaga kanta. Amma kuma dataji abunda mutumin yace ta fasa ɗaga kan nata cikin tsoro ta mayar dashi ƙasa gabanta na duka. Cikin ɓacin rai Turab turab ya sake kai dubansa kan khulud yace "tambayar ki nake uban wa ya baki dama ki kwanta kan gadona har ki iya yin bacci akanshi, wato ke isashiyya kho" ya faɗa cikin tsawa. Leeya kuwa zuciyar ta har tsalle take kan tsoro kamar ta fado ƙasa kuma gashi har yanzu ta kasa ɗaga kai ta kalleshi. Shi kuma bai masan da ita a wurin ba saboda bata Ta-ta yakeba. "Zaki zo ki wuce ko saina babbalaki" ya faɗa kamar wanda ya gaji da yin magana. "ya-Turab dan Allah kayi hakuri wallahi nazo na gyara maka ɗakin ne, sai bayan na kammala gyaran ne naji kaina namin ciwo shine na ɗan kwanta nayi tunani gajiyace bacci ɓarawo yazo ya ɗaukeni" Khulud ta faɗa cikin Muryar kuka hawaye na rige-rigen fitowa. "Zo ki wuce nace" turab ya faɗa yana nuna mata Kofar fita. da gudu ta wuce ta gabanshi kamar wacce iska ya koro. Sai a lokacin ya hango leeya ita ma, dauƙe da sauran kayayyakin cikin cabinet ɗin ita bata saka ba kuma bata ajiyeba "kan'ubahh!!, ke kuma binkice kike min, dan ubanki tukunna ma wacece ke. Kina matar aure zaki shigo dakina me kikazo yi" Turab ya faɗa ranshi yayi ƙololuwar ɓaci. Sosai ta tsorata da ganin matashin balarabe a gaban ta saboda tsabar tsoro tama rasa abunda zatace sai idonunta masu ban tsoro da ta tsureshi dasu. Tsawa ya kuma daka mata saidai hantar cikinta ta kaɗa. da gudu tabar ɗakin, baima kulaba kawai ji yayi ta wuce ta gabanshi babu shiri. Gudu take ko kallon gabanta batayi, sai kawai tayi ta faɗi kan stairs. Tayi missing step ta bata kula ba har ta faɗi hannuta ya daki bangon wurin kanta kuma ya bugu a ƙasa, ƙara ta ƙwallah domin ji tayi bazata iya tashi daga wurin ba. Mum dake zaune a parlour tana waya taji ƙarar da leeya ta kwala, da sauri mum ta ƙara so wajen "subhanallah leeyana lafiya" mum ta faɗa tana kokarin miƙarda ita. Cikin tsananin azaba ta miƙe tsaye a daddafe ta sauka daga kan stairs ɗin. "Sannu Leeya, ya akayi kika faɗi har haka" Cije bakinta tayi cikin tsananin wuyarda take sha yayinda tazo lankwasa hannunta da kyar ta furta"mum nayi missing step ne". "Ayya sannu ina ke miki kiwo yanzu" mum ta faɗa tana dudduba jikin leeya. "Ba inda ke min ciwo mum kawai kaina ne ya ɗan bugu kibani maganin ciwon kai" "Anya kuwa ba inda ke miki ciwo banda kanki, idan akwai wani wurin ki faɗa ko asibiti ne aje kokuma a kira Turab ya dubaki" Jin an ambaci Turab yasa ta tattaro duk wata dauriya ta azawa kanta ta miƙe tsaye da kyau tace "No mum dan Allah kar akirashi a bari ya huta yanzun nan ga ya dawo, ki barshi ya huta pls mum Dan Allah. Kibani maganin ciwon kai kawai inaso naje na kwanta" Leeya ta faɗa cikin ƙarfin hali, domin kuwa da ana ganin fuskar ta da za'a a fahimci tanajin ciwo a cikin jikinta. Magani da ruwa mum ta kawo mata ta sha, godiya tayiwa mum daga nan ta koma bedroom ɗin ta. Tana isa ta faɗa kan gadon ta wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita..............✍🏼 BAYAN WUYA...... By RUMANA M DIGGI EP.18 ___________sai kusan karfe huɗu da rabi, na yamma ta farka daga baccin, koda ta farka bata jin karfin jikinta ko kaɗan, ga uban zugi da hannuta ke yimata. A daddafe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito. Tana kaffara sallar mum ta shigo ɗakin tazo ta dubata, sai da ta jirata ta sallame sallar la'asar tayi addu'a. Sai a sannan mum ta kalleta tace" leeyana sannu da jiki ina fatardai Kinji kin ji sauki kho" "Ehh mum wallahi kuwa naji sauƙi sosai alhmdullillah". "To Masha Allah, ai haka nakeso naji, kin ci abinci kuwa?" "Ah, ah mum banciba amma bana jin yunwa, inaga sai zuwa dare zanci". "Ok to Allah ya kaimu" "Ameen summah ameeen mum, nagode sosai". Ficewa mum tayi daga ɗakin. Tana fita leeya tayi kwanciyar ta kan sallahyar da tayi sallah. KADUNA.... "Okay ba da damuwa Dr. Insha Allah za'a yi yanda kace, amma yanzu menene abun yi batun transfer da muke nema" Daga cikin wayar aka amsa masa da cewa" batun transfer wannan ma ba matsala bace idan kun tashi kawai kuzo, duk ranar da kukazo za'a baku" "Ok tau Dr. Muna ƙara godiya sosai Allah ya saka da alƙairi" "Ah ba komai karka damu, Nima Nagode sai anjima" "Yawwa to mujima Lafiya" faɗin dad yana katse wayar. "Hajiya kinji yanda muka yi dashi kho" cewar dad yana kallon mummy. "Ehh naji Alhaji, amma kuma me ka gani game da cewa da yayi taci gaba da shan magungunan, anya kuwa wannan cigaba ne kuwa? Naga kafin ta fara shansu duk bata irin haka. Amma tana fara amfani dasu komai ya taɓarɓare" Shiru yayi na wasu mintuna kamar bazaice komaiba"Nima abunda nagani kenan hajiya, ai shiyasa nayi shawarar mubar ƙasar nan da ita, amma yanzu kinga komai ya kusa zuwa ƙarshe tunda abunda mukeyiwa jira yazo. Gobe ne taron walimar idan an kammala kinga shikenan ba saura, sai muje can BHOPAL ɗin a gwada nasu kho, duk da nasan za'a sami nasara da ci gaba in sha Allah". "Tho Alhaji, idan mun dawo sai a fara shirin tafiyar ba damuwa". Daga haka ba wanda ya ƙara faɗar komai kan maganar nan, fira ta ɓarke a tsakanin su. A chan bedroom kuwa Rukhshanah ce da FANNAH da MAYAH. Rukhsha kuwa sauƙi ya samu sai surutu take zubawa kafin anjima ta riƙice ta daina cewa komai, kuma ta daina sauraren komai dama haka take tun lokacin da ta fara shan magungunan ASHMED HOSPITAL. "MAYAH kice gobe zamuje naija state kenan wow, ba dama waya ganmu" cewar Rukhshanah tana fito da kaya. Dariya MAYAH ta kece da ita tana faɗin"wallahi kuwa gobe akwai chasu, Please RUKHSHA yanda kike chocolate colour ɗin nan mai wahalar samu, ki matsa ki samamana guy ɗan suleja Kinji". Wata uwar harara Rukhshanah ta watso mata kafin tace" ai ke zancewa yanda kike da ƙirar ƴan indian nan ki taimaka ki samamana, gobe fa akwai kallo zanga yanda maza zasu dinga somewa da ganin ƴan india a gabansu". "Hmmm, lallai kho sweet Rukhsha harda su zolaya kenan ba komai mun gode, ke kho twiney bakyacewa komai lafiya kuwa. Faɗin MAYAH tana kallon FANNAH. "Nima abunda nake shirin cewa kenan fa MAYAH amma kika rigani, meyake damunkine sweet FANNAH. "Uhhhhhm nikam ba abunda yake damuna kawai naga kuna maganar samarine, Ni kunsan ƙaramace ban isa ba shiyasa ban shiga batun nakuba". Dariya suka kwashe da ita gaba ɗaya, domin har ga Allah itama FANNAH ta bama kan ta dariya da abunda ta faɗa. "Yanzu dai ba wannan ba, batun yarinyar nan khulud take ko wah?" Rukhshanah ta tambaya tana jiran amsarsu. "Kedai bari Rukhsha wallahi idan muka baki labarin yarinyar nan zaki sha mamaki, da dad ɗin mu da papunsa yaya da ƙani ne mahaifi, da mahaifiyarsu duk ɗaya da dad. Amma wallahi karkiso kiga wulaqanci da take mana idan mukaje gidan, kamar ba familyn gidan bane mu" cewar FANNAH. "Hummm, ai wallahi twiney ke kike hanani kirbamata uban duka, tunda kinga a part ɗaya muke idan mukaje gidan ga bedroom ɗin ta ga namu, amma wallahi yariyar nan idan mukaje bata yarda ta kwana part ɗin nan saidai taje parlour ita kaɗai ta kwana" "Twiney kenan, wallahi kinga duk wannan da kike gani bawai banaso ki daketa bane, ina tsoron abunda zaije ya dawo ne. Mu mukazo gidansu, bamuda ikon mu daketa har cikin gidansu duk abunda tayi mana, kuma Ni banga ma amfanin mu daketa ba domin damu da ita duk abu ɗayane. Bazai yu a taru azama ɗaya ba dole akwai banbanci saboda haka indai duniyace gata nan ita zata karantar da ita". "Gaskiyar kice sweet FANNAH amma kuma wannan ai rainine. kikace akwai shekara ɗaya harda wata uku tsakaninku da ita kho, means kune yayanninta kenan" Rukhshanah ta faɗa cike da tsanar halayen khulud. "Ehh wllh mune yayanninta, amma kinga twiney ce ke janyo mana raini wurinta. Tunda kinga komai tayi cewa take a ƙyaleta" "Hmmm, kedai ki bari kawai. gaskiya gobe saina koyawa yariyar nan hankali idan ta shiga gonata, lafiyarta idan bata kulani ba Nima ba ruwana da ita, bazan kulata ba shikenan. Ni wulaqanci ne banaso kawai" fadin Rukhshanah. "Sweet Rukhsha kenan, ai twiney ce bazata barki ba. Tsoron ta yayi yawa, amma ki bari kigani kawai Allah ya kaimu goben" Haka sukaci gaba da firarsu, da kuma yanda gobe zata kasance garesu idan Allah ya kai mu. *K. MANSION, SULEJA NIGERIA* Misalin ƙarfe 2:13am na dare Leeya ce kwance a bedroom ɗin ta sai faman murƙususu take. Wani irin mirdawa cikin ta ke yimata har yanda baza'a misaltaba. Sai matsar kwalla take cike da azaba. Haka take duk ƙarshen wata sai tasha wahala tukkuna kafin tayi period. Sosai cikinta ke yimata ciwo, Idan kuma mirɗan da yake da ciwo ya dan sassauta sai ta sami lipton mara sugar da kuma paracetamol ta hada tasha, shine abun zai yi sauki. Yanzu ma haka ta duba ba Lipton a ɗakinta gashi kuma Lipton kawai zata samu tayi amfani dashi. To anan ne zataji sauqi. Miƙewa tayi cikin ƙarfin hali ta yanke shawarar fita ɗakin nata taje kitchen ko zata samu. Laluba fuskar ta tayi taji da niqab din ta yana nan bai fita ba, domin a yanda takejin raɗaɗin ciwon hannunta da kuma cikinta dake yimata azabar ciwo sai taji kamar ba mayafin a fuskar ba shine dalilin da yasa ta laluba fuskar ta tah. Wayarta ta fara dudduba wa cikin duhun dakin tana lalubawa, har hannunta ya sauka a bedside drawer ta janyo wayarta. Da haske screen tayi amfani ta dakko wani niqab ta sauya domin ruwan hawaye ya jika wanda ke fuskarta. Wardrobe ɗinta ta buɗe ta janyo dogon hijab har ƙasa tasaka kan rigar baccin da ke jikinta, a hankali take tafiya har ta sakko ƙasan parlourn da jan kafa da dafar bango. Kana ganinta kasan ba lafiya take ba saidai kho karfin hali. Parlourn tsittt ba motsin komai, kuma bakajin ƙarar komai saina agogon da ke like a bango parlourn. Tafiya take kamar mai sanɗa tana waiwaye, kamar wacce tazo yin sata. Tana isa kofar kitchen ta fara buɗe kofar a hankali, ƙarar buɗe kofar yana tafiya a hankali, har ta bude kofar gaba daya. Sannan ta shige kitchen ɗin. ***** A daidai wannan lokacin kuma Turab ne zaune a dakinsa sai faman aiki yake da system. Domin kuwa bayajin bacci ko kadan, hasali ma yafi jin dadin aiki tsakar dare yanda ba hayaniyar komai. Sosai yakejin yunwa domin tun Abincin da sukaci a restaurant bayan dawowarsa airport har yanzu bai saka komai a cikinsa ba, ko fita ma baiyiba yau gaba daya Mikewa yayi ya rufe system dinsa, sannan ya fita ɗakin. down stairs ya sakko da nufin shiga kitchen ya samu ko Noodle ya dafa domin bayajin zai iya bacci idan bai ci abinci ba. Hasali ma yunwar ce ta hana masa jin baccin amma yasan daya koshi shikenan. Saboda baya wasa da Cikinsa ko kadan. Hanyar da zata sadashi da kitchen ya nufa shima, da mugun mamaki ya kara kurawa kofar idanu wacce ya hango ta wangale kuma da alamar akwai mutum a ciki tunda gashi har hasken da ke ciki yana iya hangowa. "To waye a ciki" Turab ya faɗa a zuciyarsa. Kashe fitilar wayansa yayi yaci gaba da tafiya cikin sanda har ya isa daff da ƙofar inda yake hango leeya da duk abunda take. Ita kuwa leeya bayan ta gama hada Lipton din tasha, sai ta jinginar da bayanta da kitchen cabinets domin ita kadai tasan abunda takeji. Sake dauko kofin tayi ta kafa a bakin ta zata kuma kurɓa Lipton ɗin, kamar daga sama taji ance, "wacece ke?" Wata masifaffiyar kaduwa da tsoro suka ziyarceta a lokaci daya har ya haddasa mata sakin Lipton cup ɗinda ke hannun ta jikinsa, ruwan Lipton ɗin masu ɗumi suka zuba a jikinsa kuma sun taba ko'ina a gaban rigar sa. A matuƙar tsorace ta fara kuka, muryar ta na rawa kamar mai iƙina tace "dan Allah kayi hakuri wallahi naji tsoron ganinkane, saboda banji motsinka ba harka shigo nannnn kuma......." Bai jira ta ƙarashe maganar taba cikin tsananin bacin rai da takaici ya fara matsowa kusa da ita, ita kuwa tana ja baya har takai ga bango. Kuma ba yanda zatayi ko dogon motsi ta gagara yi. Sosai ya matso kusa da ita har suna iya jin numfashin juna, hannayensa biyu ya saka gefen damanta dana hagunta ma'ana (ya sakata tsakiya kenan). Cikin matukar ɓacin rai yace" wacece ke, ki buɗe fuskar ki. Kece dazu na kamaki kina Min bincike a ɗakina kho wallahi sai kin gane kuskuren ki, Ki buɗe fuskar ki nace" ya faɗa cikin ɗaga murya. Ƙara mannewa da bango tayi domin tana ganin ko buɗe fuskar zata yi bazata iya ba saboda sunyi kusa dashi sosai, kuka ta fashe dashi domin kuwa tana ji shikaɗai zatayi a wannan lokacin ta sami sauƙi. "Rufemin bakin ki wallahi kona cire shi" ya faɗa yana ƙara tamke fuskar shi. Da sauri ta gimtse bakinta har ta saka hannayen ta biyu ta rufe bakin ta, taji ciwon sosai da hannunta daya ke yimata zogi sakamakon amfani da tayi da shi ciwon ma kamar ƙara daɗuwa yake yi. "Zaki buɗe fuskar ko me kike jira Ni abokin wasan kine da zan tsaya ina maki magana kamar ba dake nake ba" cewar turab a hasale. Ba zato ba tsammani kawae yaji ta banke hannunsa ɗaya tafita wajen da gudu tana dafe da cikinta. Ran sa yayi ƙololuwar ɓaci bisa wannan abun da tayi masa"Ni hmmm, lallai kuwa saidai idan bakya gidan nan amma wallahi sai kin gane dani kike zancen". Turab ya faɗa yana fitowa daga kitchen ɗin domin yunwar da yakeji tama tafi saboda tsananin ɓacin rai. Washe gari kuwa tunda sassafe Turab yayi sallama da mum zaije Abuja gidan Abokin sa dasuke can Mexico a tare, kuma ya faɗamata har fahad ɗin dad ƙarami ma yana can tun jiya, shiyasa yakeso yaje. Jiya duk sun takuramasa da kira. "Me kake cewa ne Turab mun tara mutane za'a barsu ba uban gayya" "No mum, nifa bawai ina nufin naje naƙi dawowa bane sai an kammala taron, ah ah wallahi ko kaɗan inaso naje muyi shirin mu a can idan lokacin farawa yayi sai muzo da shirin mu gaba ɗaya tunda kinsan Ni banida wasu abokai da suka wuce su, kinga kuwa komai suka shirya akai zan zauna tunda nima ina shiryawa su bi abunda nace" Turab ya faɗa yana gyara zaman hular da ke kanshi. "Okay, tou ba damuwa aje lafiya, Allah ya tsare hanya. Kamar ya tambayi mum wacece yarinyar nan mai niqab dayaga tana yimasa binkicen kaya jiya, kuma ya kuma ganin ta a kitchen jiya da dare. Wata zuciyar tana gayamasa kar yayi wannan tambayar domin mum itama zata iya jefa masa wata tambayar akan yarinyar. Haka dai ya bar zancen a ransa yana hasashen ranar da zai ganta ya koya mata hankali, amma kuma yana tunanin kamar matar aure ce kuma tunda ya ganta da niqab. "To matar wa" ya faɗa a zuciyarsa. "Magana kake?" Mum ta tambaya "Ah ah" ya faɗa a takaice. "Kayi sallama da dad ɗin ka" "Tun a masallaci" "Okay, sai ka dawo" cewar mum tana nufar ɗakin khulud. Knocking kofar tayi, kafin ta shiga. Zaune ta tararda ita a bakin gado sai famma danna waya take kuma da alamu brush kaɗai tayi batayi sallah ba domin kuwa ba alamar alwala a jikinta. "Mum, barka da safiya" "Yawwa, kinyi sallah kuwa" "Ah, ah tukunna dai, banyiba" "Meya hana?" Cewar mum tana haɗe fuska. "Wallahi mum harna shiga toilet nayi brush, ina shirin na fara alwala naji shigowar saqo a Whatsapp ɗina, koda na fito na duba na tarar ashe ƴan group ɗin mu ne na school suka fara maganar shirin da za'a yi idan muka kammala makarantar" "Bani wayar, wallahi dama nayi gudun wannan saboda nasan za'ayi haka dama, wanda bai mayarda hankali ga ibadarsa ba, kuma bai mayar ga karatunsa ba shine za'a siyawa waya, ai saidai komai ya ƙara lalacewa. Kiban wayar nace" Kamar zatayi kuka ta ɗago tace" mum don Allah kibar min wayana wallahi Ni yanzu na riga na saba da ita ko minti ɗaya bazan iya yi ba wayar nan ba, balle kice karɓeta gaba ɗaya gaskiya mum bazan bada ba". "Ok ki riƙe ta a hannunki kinji, Ni bazan iya karɓar wayan ba. Amma ai turab zai iya karɓa kho". "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un mum Dan Allah kidaina haɗani da wannan mara imanin ɗan ki, wallahi mum idan bakya sona papuna yana sona, kuma wallahi idan kika saka ya-Turab ya dakeni wallahi saina faɗawa pa, na rantse kuwa da Allah" "Hmmm khulud kenan duka kuwa kam sai dai idan kin bada wayar nan, Amma muddin wayar nan na hannun ki wallahi saina haɗaki dashi Kuma ba abunda zai hanamasa dukanki" Kuka harda hawaye takeyi ta ɗakko wayar ta miƙawa mum tana faɗin" ga wayarnan na baki, ai dan an ƙarɓi waya ba raina aka karɓa ba. Ga ƴar masu gida an karɓemata waya, amma wata banza ƴar bola da titi ƴar tsintuwa Ambarta ta riƙa waya. Wallahi da an kammala taron nan sai mun fita da pa, yasiyomin wata tho a zo a ƙarɓa idan an ganta" khulud ta faɗa tana shikegewa toilet tare da banko ƙofar........✍🏼 ________Bayan sun yi masa rakiya ne suka dawo ciki, gidan ba wani babban gida bane domin ɗaki ɗaya ne jal, sai kuma banɗaki da kuma wurin da suka killace dabbobin da suke kiwo. A can cikin ɗakin kuma sai suka ware wani ɓangare da zasu kwanta kafin dare. uchi kam yasami abokiyar surutu, Da yake shima dai mutum ne mai sakin fuska da son yara kuma gashi da surutu sosai, sai kuma aka haɗe da an dace domin kuwa indai surutu ne ya taɓo Aleena ba'a dai cewa komai. Ita kuma Nnene tana chan tana shirin ɗora girkin dare, leeya kuma sai tayata takeyi dama ita chan bata dama wajen son aiki musamman idan na abincine, Leeya ta maida hankalinta sosai kan aikin da suke ko ba komai tanaso ace ta iya girki kala-kala ko a ecoco haka suke zama ita da ammi tanata koya mata abincin yarbawa yanzu gashi tanaso ta iya na igbo. "Nnene wannan kuma menene"? "Fufu" ta bata amsa fuskar ta ɗauke da murmushi "Fufu kuma Nnene" "Ehh a yaren igbo ana kiranshi fufu, a wani yaren kuma ana kiranshi (cassava dough) Amma bansan ya ake kiransa a yaren kuba" Ƴar dariya leeya tayi cikin jin daɗin samun amsar ta datayi sannan tace a yaren "mu kam ana kiransa (Rogo)" dariya suka ƙara kwashewa da ita suna cigaba da aikinsu. ★ "Uchie dariyar me su Nnene sukeyi ? Aleena ke tambayar uchie. "Shina gani budurwa wata ƙila tsokanace kawai dan muyi magana, kinsan me muyi kamar ma bamusan dasu ba" "Ah ah uchie muma mu rama dariyar mu, kawai haka kawai zasuyi mana dariya muna jinsu mu kyalesu mu rama kawai" "Tau taya zamu rama" Uchie ya tambaye yana gyara zamansa. "Bara kawai muma mu kallesu yanda suka kallemu, sai kawai mu fashe da dariya. Kallonsu kawai uchi da Aleena sukayi sai suka kwashe da dariya harda rike ciki. Abunda ya bawa su leeya mamaki kenan, ganin haka kawai suka kallesu suka kwashe da dariya. sai sukayi tunanin kodai aikin da sukeyine ya sanya su aleena dariya. sharesu kawai sukayi sannan suka ci gaba da aikin su, ba wanda ya ƙara kula wani tsakanin su Nnene da leeya da kuma uchie da aleena. Saida Nnene da leeya suka ƙare girkin nasu tsaff kafin suka bar harabar Wurin da sukayi girkin, hadarine ya haɗo sosai basu kai ga cin abincin ba aka fara ruwa, Ɗaki suka shiga suka nemi mafaka anan sukaci abincin anata fira da ban dariya, Haƙiƙa su Nnene ma sunji daɗin kasancewa dasu leeya domin koba komai sun rage musu raɗaɗinda sukeji na rashin haihuwa, Sai gashi yanzu abun na wanke wa acikin ransu. A ta bangaren su leeya da Aleena suma sunji daɗi sosai dan basuyi tunanin sake kasancewa kamar haka ba. Sunsha fira sosai da labarai daga bakin aleena, har suka raba dare suna fira bako alamar bacci saida uchie yayi musu umarni da kowa ya kwanta har da safe saboda yaga alamar idan ba'a kwanta ba za'a iya kai safe a haka. Dan ƙaramin gadon karan da ke jingine aka sauke musu a ƙasa, sai kuma wata ƙaramar katifa wacce zata ishesu kwanciya su biyu. zanin atamfa Nnene ta ɗauko tare da shimfida musu sannan aka kunna mosquito suka kwanta, wani zanin ta ƙara ɗaukowa mai ɗan girma ta yafa musu sakamakon unguwar tanada sanyi sosai, ko ba lokacin damina bane balle yanzu da ake tsakiyar damina. Baccinsu sukeyi hankali kwance kamar ba abinda ke damunsu, dayake ko a gida leeya ta saba da tashi tun da sassafe miƙewa tayi daga kwancen da take tare da sakkowa daga kan katifar, kallonta takai wurinda taga su uchie sun kwanta amma sai mutum ɗaya kawai tagani kuma batasan ko waye a cikinsu ba. Fita tayi waje da nufin tayi alwala tayi sallah, sai ta tarar da Nnene a cikin barandar ɗakin, inda ruwa bai jiƙa ba tana faman hura wuta. isowa tayi wurin tare da dafata bata cetamata komai ba ta dauki buta, ta shiga ban ɗaki ta ɗauro alwala Sannan ta fito. Inda aka ajiye musu kayansu da sukazo dasu tun a jiya ta nufa tare da ciro hijab da kuma sallaya domin duk ta haɗo dasu kuma tasan zaiyi wuya a samesu gidan nan. Shimfiɗawa tayi inda take tunani Nan ne gabas a gidan ta tayarda sallahr ta hankali kwance, sai da ta kammala kafin ta tashi ta maida komai inda ta ɗaukeshi Sannan ta fito waje "Nnene barka da safiya, antashi lafiya?" "Lafiya ƙalau, ya gajiya" "Ba gajiya" leeya ta faɗa tana nufar inda aka killacewa dabbobi, domin nan ne kawai take tunani bai jiƙe ba da ruwan da aka sheƙa jiya da dare. ta shiga ciki ne domin ta samu abun wuta bushasshe da zasu saka cikin wutar da Nnene ke hurawa cikin Sa'a kuwa ta samu ƙananan karare da sauran hakin da ya ɗan fara bushewa, ta fito sannan taje gaban murhun tare da durƙusawa, gaban murhun. "Nnene bara na tayaki" "Ah ah leeya kije ki huta mana ko jiya fa haka muka sha aiki dake, baki huce gajiyar jiya ba Sannan yau kizo ki daɗa wata akai" Ɗan murmushi leeya tayi wanda tasan Nnene bazata gani ba domin fuskar ta a cikin mayafi take, "ba komai kibani na tayaki kawai, Ae na iya hura wuta kije ki kwanta kawai idan na hura sai nagayamiki idan ta kama" Duk yanda Nnene taso suyi aikin tare leeya taƙi barin ta wurin saida ta tashi ita kuma taci gaba da yaki da wutar har dai ta samu wutar ta kama daidai, Miƙewa tayi ta nufi ɗaki domin ta kirawo ta amma tana juyawa sai gata ta fito "sannun ki da aiki leeya kinyi ƙoƙari sosai" "Nagode"leeya ta faɗa tana murza yatsan hannunta. Tukunya Nnene ta ɗauko ta ɗora suka fara aikin tare ba jimawa suka kammala gabaɗaya. abincin su na Igbo Mai Rai da lafiya suka haɗa ba abunda leeya bata ganeba a Cikin abunda sukayi, domin tana tambayar duk abunda bata sani ba ita kuma Nnene bata gajiya tana gayamata duk abun da ta tambaye ta da kuma amfaninsa. Bayan sun kammala girkin safen ne leeya ta haɗo duk kwanukan da suka ɓata jiya ta wankesu tsaff. Nnene da uchie sunji daɗin samuwar leeya a gidan koba komai zata rage musu wani aiki musamman yanzu da tsufa ya fara kamasu: "leeya sannu da aiki kekam bakya gajiya" Nnene ta faɗa tana murmushi, Leeya ma ta maida mata da martanin murmushin, abincin su sukaci saida suka ƙoshi kafin Nnene ta ɗoro musu ruwan zafin da zasuyi wanka baki ɗaya, bayan ruwan sunyi zafi ta kaiwa uchie nasa a banɗaki yayi wanka, ya shirya ya fita domin yana sana'ar sayarda ƙwai ne a nan makoko, sai itama ta ɗiba nata tayi, sannan bayan ta dawo ta ɗiba tayiwa aleena har ta wanke mata kanta ta kunce mata shi. "Leeya kema kizo na wanke miki kan naki sannan kije kiyi wanka" Da "tho" leeya ta amsa tana miƙewa tare da nufar ta, ƙara gyara mayafin ta tayi yanda ko za'a wanke kan mayafin bazai fitaba kafin ta cire abunda ta ɗaure gashin ta, sai gashinta ya baje gaba ɗaya dama chan anjima ba'a gyara shiba, cikin zallar mamaki Nnene tabi gashin leeya da kallo tana nuna mamakin ta ƙarara, saidai bata ce komai ba saboda ta ba abunda yashafeta bane. Sai da ta wanke mata gashin tsafff kana ta baje mata shi yanda zaiyi saurin shan iska sannan takai mata ruwa banɗaki tayi wanka. Tana fitowa saiga okene ya shigo gidan, sai dai ganinta ya tsorata shi sosai, yanda ta baje gashin nata kai kace fatalwace, domin kuwa da dare ne ya ganta haka ba abunda zai hana masa ihu wata ƙila ma harda gudu zai haɗa. Yatsarta ta saka tare da janye gashin da ya rufe gaban mayafin ta sannan tace: "Okene barka dai har ka shigo" "Barkanki leeya ya gajiya, "Ah ba gajiya" ta faɗa tana ajiye bucket ɗinda ke hannunta tare da nufar inda su Nnene suke zaune, sai yanzu okene ya lura da Nnene datake sakawa budurwa kaya domin harta gama yimata kwalliya ta shiryata tsaff, gaisawa sukayi sosai cikin jin daɗin yanda okene ya tarar da Nnene nayiwa su leeya kamar dai itace ammi, haƙiƙa yaji daɗi sosai bada wasa ba. Gyarawa leeya gashinta Nnene tayi sosai ta shafamata man gashi mai kamshi ta ɗauremata gashin nata sosai ya kwanta yayi sumul gwanin ban sha'awa, tashi taga daga wajen ta shiga ɗaki ta sanya kayanta ta chanja wani mayafi, fitowa tayi tare da zauna wa aka ci gaba da fira da ita har Nnene tana gayawa okene irin ƙoƙarin da leeya takeyi harma take gayamasa yau ita tayi musu abinci. "Wane kalar abincin tayi muku? Cewar okene fuskar sa ɗauke da murmushi, "Fufu dough" leeya ta bashi amsa, tun kafin ya tambayeta. Da mamaki ya kalleta:"yaushe kika iya fufu dough kinsan kho ba abunda nakeso kamar abincin nan. Cewar okene yana kallon leeya cikin mamakin ta. Ita dai Nnene kallonsu kawai takeyi kuma da alama firar tasu tanayimata daɗi. "Tau Ae da sauranshi idan zakaci sai a zubo maka kaci kho" Leeya ta faɗa tana kallon okene "zanci kuwa ki zubomin naci da yawa dan inason kalar abincin nan wallahi" ya faɗi maganar yana shafa cikinsa. Murmushi tayi mai sauti sannan ta tashi ta shiga ɗaki ta zubo masa abincin mai yawa kamar yanda ya buƙata, tazo gabansa tare da ajiyemasa abincin Sai kuma ta juya ta koma ciki, kofi ta ɗauko tare da ɗebo masa ruwa ta dawo ta ajiyemasa, sannan ta koma gefe ɗaya ta ƙura masa ido har ya gama cin abincin tsafff, "Nnene a gaskiya banyarda leeya tayi abincin nan ba akwana ɗaya kacal da zuwanta gidan zatayi wannan, ya kenan idan tayi shekaru" Murmushi Nnene tayi kafin tace:"ehhh mana ita tayi komai, nuna mata kawai nakeyi, sai kuma inda tayi kure na gyaramata" Baki okene ya washe sosai cikin jin daɗin yace:"kenan idan nazo ziyarar ku zanci girki mai daɗi kenan bama acewa komai, tabbb aikuwa idan kika girma restaurant zan buɗamiki irin wannan abinci haka" Sai bayan yayi maganar ne ya tuna tun sadda suka fara maganar Abinci da Nnene bada hausa sukeyinta ba da yaren Igbo ne sukeyinta, "Saura wannan kuma" Okene ya faɗa yana kallon leeya. "Me kenan" Itama ta tambaye shi. "Yare mana" Ya bata amsa . Ƴar Siririyar dariya tayi kafin tace:"shima na iya ta faɗi maganar tana ɓoye fuskar ta da tafin hannayen ta kamar shi okenen ganin fuskar tata yakeyi. "Ae naga alamar kin iya dan gashi nan naga kinyi abincin mu, Nnene kema kice ta koyamiki abincin su na hausawa kar tayi miki wayo ta iya namu bamu iya nasu ba" Ya faɗi maganar cikin yaren Igbo ne shiyasa leeya bata fahimci abunda yake nufi ba. "Ae kuwa hakane kaga ma ɗazun da muke girkin tace gobe zata yi mana tuwon shinkafa" Cewar Nnene. "Iyyeee kice gobe uchie zai chanja abinci kenan ina ma ina nan da nima naci tuwo". Faɗar okene yana ɗaga kansa sama kamar mai tunano wani Abu. "Ae kuwa hakane yau ne tafiyar taku kho" Nnene ke tambayar okene "Ehh shine ma nazo na muku bankwana dan kinsan idan mun tafi shikenan munbar ƙasar Lagos ba abunda zai maidamu saidai ko ziyara" cewar okene yana kallon leeya dayake ita batasan maganar da suke ba shiyasa hankalin ta baya kansu, Firarsu sukayi sosai harda Aleena da ta tashi daga baccin rana da takeyi da kuma uchie daya dawo daga kasuwa yanzu, okene ya jima sosai a makoko kafin yayi musu sallama zai wuce. "Budurwa kinsan yau ne tafiyar tamu kho? Yau zan barmuku garin Lagos" "Lahhhh broth yaune tafiyar taku kho, wane gari ne ma zaku koma? Aleena ke tambayar okene idanun ta na kanshi. Yana shirin bata amsa leeya ta tari numfashinsa:"broth shikenan idan ka tafi bazaka dawo ba, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un muko yazamuyi broth kai kaɗai garemu kaikaɗai muka sani, Gashi zakayi nisa damu. "Haba leeya ga Nnene nan da uchie nasan zasuyi muku fiye da abunda zan yi muku. duk yanda kikeso na zauna Lagos ɗin nan wallahi na fiki son na zauna, haka kawai nakeji kamar na rasa wani ɓangare na jikina kuma nakejin Zuciya ta na karyewa idan na tuna babu ku a inda zanje amma wannan alƙawari na ɗauka miki zan dinga kawo muku ziyara akai-akai abunda kawai nakeso dake shine, dan Allah ki saki jikinki ki ɗauki Nnene da uchie kamar ammi da Abbi nasan basukai Matsayin suba amma za'a iya kwatanta su da irin wannan matsayi saboda suma iyayene daga ƙarshe leeya dan Allah ki dage da karatun islamiyyarki da kuma boko. nayi magana da uchie har ma yagayamin sai sakaku wata makaranta Anan makoko sai kuci gaba da zuwa islamiyyar ku a ife kinji leeya, okene ya faɗa idanunsa na cikowa da kwalla. Tuni ruwan hawaye sun wanke wa leeya fuska ganin da gaske yau okene zai barsu shikenan Okenen ta. ɗagowa tayi ganin ya miƙe take ta isa gareshi da gudu tare da rungume shi tare da fashewa da kuka. rarrashin ta yayi sosai kafin ya samu ta sassauta da kukan da take. "me zaki bani na riƙa tunawa dake wanda idan ina tare dashi zanji kamar kina tare dani?" Dakata wa tayi da kukan da take kafin da ɗanyi tunani, "broth Banada abunda zan baka har na tuna lokacin da ammin mu take faɗin duk ranar da zakuyi tafiyar nan dani za'a je saina ga garin da zaku zauna sannan na dawo" leeya ta faɗa Muryar ta a sanyaye. "Allah sarki tau Allah yayi muku rahma" "Amen" Okene ya faɗa sannan ya kuma cewa:"leeya bakida abunda zaki bani fa kikace" "Broth O wallahi da inada abunda zan baka saboda karka manta dani dana baka. Nima kaina bana so kamanta dani kayimana komai a rayuwar nagode sosai Allah ya sada mu Da alƙairi" leeya ta faɗa Muryar ta na cracking. "Wannan fa?" Okene ya faɗa yana nuna abun hannun da ke daure a hannunta na dama. "Wannan??" ta ƙara tambayarsa itama tana kallon abun hannun da ya nuna mata da ke daure a hannunta. "Shi!" Ya faɗa yana ci gaba da kallo da kuma nuna mata abunda yake so a hannunta. Wannan kakeso na baka?" "Shi nake so ko bazan samu ba na hakura" Da sauri ta cireshi a hannunta ta ɗaura masa da kanta,"ko abunda yafi wannan ka nema indai a wurina ne zaka samu, balle wannan". godiya yayi mata sosai kana yayiwa su uchie sallama suka rakashi har ecoco gaba ɗayan su Sannan suka dawo gida makoko. Bayan sun dawo, suka ci gaba da safgar gabansu, saidai tunanin okene ya kasa fita zuciyarta. **** Shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Nnene, leeya, uchie da kuma Aleena a cikin ƴan kwanaki, ba abunda zasu nema su rasa a gidan. ba wani hantara ko nuna ƙyama, ba kuma wani banbanci da suke nuna musu ata bangaren addinin su, dan har islamiyya suke zuwa ife, kuma suna sallah, har makaranta uchie ya sakasu a makoko, kuma suna riƙonsu da tarbiyya kamar iyayenda suka haifesu. A bangaren leeya kuma tana ƙara kwarewa a iya girkin kala-kala Nnene na koyamata gashi tanada saurin riƙe abu bata da mantuwa sosai. ★★★ BAYAN SHEKARU BIYU, Abubuwa da dama sun faru a rayuwa, ciki kuwa harda rasa wani ɓangare da leeya tayi na rayuwar ta, wanda shine silla ta biyu da ya jefata a wata rayuwar mai tsananin wahala da ƙaƙanikayi, da halin ƙunci da tsananin wuya da azaba. Wata rana da safe a cikin ranakunda leeya bazata taɓa mantawa da suba a rayuwarta. zaune suke a tsakiyar gida ita da Nnene da kuma budurwa anata magana yanda za'a shirya ɗan ƙaramin shagali da uchie yakeso ya haɗawa Aleena da zata kammala examinations ɗinta na JLCE Anan makoko yayinda leeya take ss two a wannan lokaci. "Nnene kinga daidai chan zamuyi decorations zaifi haske domin nan rana take facing" Aleena ta faɗa tana nuna wani ɓangaren a gidan nasu. "Nnene nidai can nace kinga zaima fi kyau da ɗaura balloons, sabida rana bata isowa can, sannan bamusan lokacin da zamu ɗauka anan ba, amma can datakeso idan rana zata faɗi nan take fuskanta, ɗazu ma naga uchie ya shigo da balloons a hannunsa" Cewar leeya. Cikin ƙaguwa da son jin tabbacin abunda leeya ta faɗa aleena ta ƙara tambayar ta:"yarhyarh da gaske uchie ya siyo min balloons ɗinda za'a yi decorations dasu?" "Eh da gaske mana Ae ba balloons kaɗai ya siyo ba harda sababbin kayan da zamu saka gobe ya siyo mana" leeya ta faɗa tana janyo wata leda dake ajiye gabanta. Farin cikin Aleena ya kasa ɓoyuwa har saida ta matso sosai tare da rungume Nnene. "Nnene Yakamata mufara aikin fanken nan kada dare yayi mana a aikin" "Ehh yanzu nake shirin yimiki zancen ai" "Nnene Nima dani za'a yi aikin yau tunda domin ni za'a yi komai ninakeda komai n Kuma laɓaku kawai nayi saboda muna gida ɗaya daku kar a ce nayi rashin kirki" cewar aleena tana miƙewa daga jikin Nnene. Murmushi Nnene tayi batare da tacewa aleena komai ba "leeya ki dauko abun zubewa ki zube fulawar nan sannan ki shiga ɗaki ki ɗaukomin sauran kayan haɗawa sai na nunamiki yanda zakiyi wannan, idan kin gani sai kici gaba ni kuma na fara aikin okra soups wadda na baki labari jiya" "Ohh natuna itace kikace anfi amfani da ita wajen biki ko party koh" "Itace kuwa ashe ma baki manta ba, to kije ki dauko abun da nace miki idan kin ɗauko sai innunamiki yanda zakiyi Wannan idan kin gama sai kizo kitayani muyita, ke kuma budurwa kizo in ki baki aikin da zakiyi tunda kince kema sai kinyi" Miƙewa leeya tayi tare da nufar tilon ɗakin gidan nasu domin ta ɗauko abunda aka aiketa ta ɗauko, bayan ta ɗauko ne ta dawo ta zauna suka fara aikin nasu, sun ɗan ɗauki lokaci kafin su kammala haɗawa daga nan Nnene ta barmata aikin ta karasa ita kuma ta fara aikin okra soups. Haka kawai leeya takejin jikinta a sanyaye yau kuma kome take a kasalance takeyinsa, ji take gabanta yana duka kamar wacce wani babban abu yafaru da ita, haka kawai takejin faduwar gaba. tunawa tayi da addu'ar da ake koyamusu a islamiyya idan kana jin wani abu makamancin wannan ka dinga karantawa, addu'ar ta fara jawowa a hankali tana Binta dalla-dalla hardai ta samu hankalinta yaɗan dawo jikinta. Hatta ita kanta Nnene ta fahimci akwai damuwa a tattare da leeya domin ba haka suka saba aikinsu da ita ba: "leeya me yake damunki?" "Babu komai Nnene ba wata matsala bace, haka kawai nakeji gabana yana faɗuwa inaji kamar wani abu zai faru" Guntun murmushi Nnene tayi sannan tace "kwantar da hankalinki leeya ba abunda zai faru damu, kinga yanayine kawai kuma da gajiya, ki tashi kije ki kwanta ki huta kafin anjima idan kin huta sai muci gaba aikin kinji, yanzu kije zamu idar da wannan nida budurwa" "Ah ah Nnene zan iya muci gaba da aikin nan kawai kinga har yanzu akwai waɗansu ayukkan daban" "Ah ah fa leeya jeki ki kwanta kawai kinji karki damu yanzu zamu kammala komai" Kama hannunta Nnene tayi takaita har cikin ɗaki sannan ta dawo taci gaba da aikin ta. Inda suke kwanciya leeya ta kwanta tare da lunshe idanu abubuwa da dama suna faɗo mata arai, kwanciyar ta wurin keda wuya bacci yayi awon gaba da ita. ba ita farka ba saida yamma sosai, cikin mamakin kanta da baccin da tasha ta fita waje tare da kiran sunan Nnene: "haka nasha bacci amma baki tasheni ba, yanzu ma nasan kun ƙare aikin gabaɗaya kho, gskiya nidai ba haka nasoba Nnene" leeya ta kare Maganar tana buɗe wani babban faranti da aka zube fanken da akayi: "kai amma gaskiya fanken nan yayi kyau Nnene aikuwa duk ranar da broth O zaizo a cikin kalaluwan abincin da zanyi masa harda wannan fanken sai na yi masa" Murmushi Nnene tayi kafin tace:"aiko da kin yimasa ƙoƙari saboda ba wanda za'ayi wa irin wannan sai wanda akeji dashi sosai ko budurwa da kikaga nayiwa inaji da ita ne shiyasa" murmushi itama leeya tayi:" ina Aleenan take naji gidan nan shiru, gidan nan yayi lafiya. Leeya ta faɗa tana ƙara wulla idanun ta inda take tunanin zata ganta. "Batanan tafita ita da uchien ta sun tafi ƙaro sayayya su siyo abunda ba'a siyaba" Idanun leeya ne suka ciko da kwalla bata masan sanda ta rungume Nnene ba saboda ta tabbata koda su Abbi ne da ammi abunda zasuyiwa Aleena bai wuce wannan ba "Nnene mungode, mungode kwarai kunyi mana gata a lokacin da bamuda wanda zai dubemu balle yayi muna, kun suturtamu a lokacin da muke neman wanda zai yimana sutura, kun mutuntamu a lokacin da wasu Mutanen suke nufin wulakanta tamu. haƙiƙa bamuda Kamar ku, ina rokon Allah ya saka muku da alƙairi ya rabautaku da shiga Rahmarsa da shiriyarsa, mungode kwarai Allah ya biyaku ta ƙarasa" maganar tana sakin kuka mai qarfi. Rarrashi sosai Nnene tayi mata tare da gayamata wannan ba komai bane, kawai dai su zama ɗiya nagari masu tarbiyya, kuma su dage da karatu ko don su zama wani abu nan gaba. Bayan haka fira sosai sukayi amma duk a sanyaya leeya take amsa firar domin jikin ta duk ya mutu, ita kanta Nnene saida ta fahimci sauyin leeya a ɗan ƙanƙanin lokaci. Sosai Nnene tayi ta tambayarta domin ta gayamata abunda ke damunta amma ta "wai kekam leeya mayeke damunki ne ko kuma dai kintuna da ammi da abbi ne shiyasa naga kin shiga damuwa" "Nima kaina wallahi bansan abunda yasa ni cikin damuwar nan ba koda tambaya ta za'a yi, Nima inaso naga nadawo Kamar yanda nake amma nakasa, kawai dai nasan yanayi kuma zanfita cikinshi in sha Allah" daga haka leeya bata ƙara cewa komai ba itama Nnene haka. Shiru suka yi baki ɗaya ba wacce ta ƙara cewa komai acikin su, sunɗauki lokaci mai tsawo a haka. Shigowar uchie da budurwa ne suka katse musu shirun da suke: "Nnene lapiya naganku haka kowa shiru" Aleena ta faɗa tana ajiye ledojin ke hannunta "Lafiya ƙalau budurwa andawo ina uchien yake?" "Yana shigowa, tare muke dashi yeryer ko ba lafiya naganki shiru sosai" faɗar Aleena tana zaunawa kusa da Nnene. murmushi mai ma'anoni da dama leeya tayi sannan tace "lafiya ƙalau fa kawai kasala nakeji yau, me aka siyo haka?" Ledar da kayan yake ciki aleena ta janyo tana kawota gaban leeya:"duba kigani yarhyarh, uchie yasiyamana kayakin nan harda kayan kwalliya aka siya miki, gaskiya yarhyarh uchie da Nnene na ƙaunar mu, bamuda abunda zamu saka musu dashi, wallahi nasan ko ammi da abbi ne bazasu wuce mana haka ba" Aleena ta faɗa tana fitowa da kayakin da uchie ya siyamusu. kuma duk wannan abun da akeyi tuni Nnene tabar wajen. shigowar uchie yasa ta tashi daga wajen su taje domin ta bashi abincinsa, kayane na sakawa masu dama Uchie ya siyamusu. kuma kayan masu kyau daidai dasu, harda kayayyakin kwalliya da sauran abunda zasu buƙata. Haƙiƙa sunji daɗi sosai, kuma sunyi farin ciki da ganin kayan, duk da ba wannan ne na karo na farko ba daya taɓa yimusu siyayya amma sunfi jin daɗin wannan musamman ma mai gayya mai aiki Aleena domin ta dalilin ta ne ake wannan hadada da girke-girke da komai:"yarhyarh nidai kinga kayanda zansaka gobe" Aleena ta faɗa tana ɗazo wata gown golden dake hannunta. "Tau Allah ya kaimu goben nima sai in saka irinta kho" "Ah ah wallahi idan kika saka irinta tawan nan Ae baza'a gane Ni nakeda bikina ba, za'a iya cewa mu biyune ai, kedai ki zaɓi wata ki saka kawai kingama ga wasu riga da skirt kho zasuyimiki kyau sosai tun can wajen da aka siyo su, kece na zaɓarwa su" faɗin Aleena tana ɗago da wasu kaga dasuke ninke cikin roll lader. "Naji toh, biki ki saka duk waɗan da kikeso nikuma sai waɗanda kika zaɓarmin zan saka tunda kinsan kece Aunty dama" leeya ta faɗa tana ƙara kallon aleena domin ganin yanda fuskar ta zatayi idan ta kirata da suna Aunty. Ɗan fari da ido tayi sannan tace:"yawwa yarhyarh leeya haka akeyi a dinga bawa babba girmansa bawai yanda kike yi can baya ba, kamar dai banice budurwa" Ta karashe maganar tana ɗan jujjuya bakin ta. Murmushi leeya tayi saboda tanajin daɗin Ganinta tare da ƙanwarta, ƴar uwarta, rabin jikinta sannan kuma cikon farin cikin ta. Labarine kala-kala ya shigo tsakani harda labarin okene aka ɗauko saida rana ta take kafin suka bar wajen leeya ta tashi da nufin taya Nnene aikin da sukeyi na abincin dare. Aleena kuma ta fita zuwa wajen uchie domin can suke wuni tare dashi. Sai da yamma liƙis kafin suka kammala aikin abincin, leeya ta ɗauko kwanukan da ake zubawa ta zubawa kowa nasa. Nnene kuma ta tafi domin tayi wanka dan haka suke a duk lokacin da suka ƙare aikin abinci, sun gama komai tsafff, daga bisani leeya ta fara sharan tsakar gida da takeyi koda yaushe idan yamma tayi. sai da ta share ko ina na gidan fesss kafin taje tayi wanka. Tana cikin sharar ne su uchie da budurwa suka shigo gidan: "sannu da zuwa uchie ya kasuwa?" Cewar leeya. "Lafiya lau leeya ana nan ana ta aiki." "Ehh uchie ae na ƙare sharan wanka kawai ya rage". Zakuyi mamaki sosai idan nace muku ba da hausa leeya tayi magana da uchie ba, ita kanta mamaki take yanda ta iya yaren Igbo a shekaru biyu kacal, hatta tsakanin ta da Aleena batayin hausa a wani lokaci, hakan kuma yasamo Asali ne daga uchie da Nnene domin sau tari idan zasuyiwa ɗayan su magana to basa yimasa Hausa, tun suna ɗaukar abun dariya hardai suka maida hankali sosai, yanzu sai can ba'a rasaba suke magana da hausa kafff gidan nasu. Bayan ta ƙare sharan ne ta ɗibi ruwa sannan ta shiga ban ɗaki tayi wanka ta shirya ta fito tayi musu shimfida. lokacin har anyi sallar magrib, tana gama yimusu shimfida taje tayi sallah sannan ta fito ta dawo ta gaidasu da wuni aka cigaba da yanda aka saba wato fira kafin lokacin cin abinci yayi, idan kuma kana buƙata kaci abinci zaka iya ci ba saika jira sai wani ya tashi cin nasa ba. "Nnene gobe tun da safe ki tadani kinsan sai munje school mun dawo Sannan zamu fara celebrating ɗin namu a gida koh". "Ehhh budurwa ina sane ban mantaba, zan tadake tun da safe kuma ai kinsan anan gida bamuda wata Matsala tunda mun gama shirya komai decorations kawai suka rage ayi, kuma ko decorations ɗin nasan da leeya batajin kasala da angama shi tunda balloons kawai za'a ɗaura" Nnene ke maganar tana shafa fuskar leeya. "Nnene nifa zan iya yin komai dakin gayamin decorations za'a yi tun dazun da na gama ai, amma ae koda haka ba laifi a bari goben kawai" Saida lokacin da sukecin abinci yayi, sannan kowa yaci Abin cinsa daga Nan basu tsaya wata fira ba duk suka shige tilon ɗakin nasu suka kwanta, kowa yayi bacci sai leeya ce kaɗai bata yi bacci ba, sau biyu uchie yana tashi yana tambayar ta abunda ya hanata bacci amma ta rasa dalilin sai ba komai kawai take cemasa. hardai shima nannauyan bacci yayi awon gaba dashi. ita kaɗai zaune ba bacci kuma ta rasa dalilin sabida ko kwanciya ta kasa yie, tashi tayi daga inda take zaune da nufin ta fita waje tayi fitsari, amma tayi lalubar touch light inda take tunanin an ajiyeta amma bata ganta ba. haka ta tashi ita kaɗai ta buɗe ɗakin ta fita kuma ba wanda yaji fitarta da buɗe ɗakin da tayi duk a cikinsu hatta Aleena kuwa da suke gado ɗaya da ita bata ji fitarta ba, domin kuwa baccinsu sukeyi hankali kwance......✍️ BAYAN WUYA.... By RUMANA M DIGGI EP.20 _________bada jimawa ba Leeyana ta fito toilet ɗin itama, koda ta fito ma zohal ta fara shiryawa. Gaban mirror tazo ta ɗauki soft body Cream ɗinda take shafawa. Amma ko ɗaga kanta batayiba balle taga kanta a mirror sanin cewa bata kallon mirror, kuma bata taɓa kallawa ba ma kwata-kwata. Zohal kuwa ganin leeya ta fito batayi mata magana ba, yasakata tunanin ko itama tayi fushi ne "bestie kinga fa hannun kin nan ya ƙara kumbura, ni wallahi banmaso kiyi lallen nan ba. Duk da yayi miki kyau sosai wallahi ɗazun da muka fita waje kai abinci sai nuna lallen nan naki ake" "Wallahi kuwa bestie zohal, Nima naga hannun ya ƙara kumbura, duk da yatsu ne kawai akayiwa" "To Allah ya sauwaqe" "Ameen, bara na kammala shafa lotion na fito miki da kayanki dana saka miki a wardrobe" cewar leeya. "Ah ah, kibari kawai na fito mana dasu, keda kike mara hannu ina nie, ina sakaki aiki". "Lallai ma bestie, nikam hannu biyu ne dani yanda kikeda hannu biyu kema" "Tau shikenan naji, ina ne kayan naki suke na fito miki dasu" "Ki duba inda na saka naki kayan, sannan ki duba a down box ɗin can ki zabamin niqab ɗinda zaiyi match da kayan". "Okay, kawai zohal ta faɗa tana mikewa, "Masha Allah, gaskiya bestie zohal kinyi sosai wallahi, kin ganki" cewar leeya tana kallon zohal da taga kamar ma an chanjatane domin kuwa tayi kyau ɗin da gaske. "Humm, bastie abun har yakai sai anyi zolaya" "Wallahi, bestie badai zolaya ba gskiya nake gayamiki, amma ko ban gayamiki ba ni nasan za'a gayamiki" "Tau shikenan bestie naji, yanzu ki saka kayanki mu fita na ma daina jin motsin mutane sosai wata ƙila ma har an fita" Wani bakin less mai ƙanan filawas red and black ta ɗakko, wanda aka yi mata ɗinkin doguwar riga, wacce tayi mata chif-chif ta saka. Kana ganin less ɗin basai ance komai ba kasan tsadadde ne, kayan sun ƙarɓi jikinta sosai ga kuma kwanci da sukayi a farar fatarta mai sheƙi, gyalenta ta d'akko ta yafa shima red ne wanda aka yimasa aikin bead mai kyau da tsari. Niqab ɗin ta kuwa baƙi ne siɗik wanda ya ƙara fito da hasken idanunta. saidai ba kowa yake iya kallon idanun nata ba, saboda idan mutum yakallah yakan rasa dame zai siffantasu, sosai Leeyana tayi kyau, ga kuma jan lallen da aka yimata sharrr dashi. Plat shoes ta ɗauko kalar gyalen ta ta saka kaana ta ɗauki wayarta suka fita. Cikin tafiyarsu ta nutsuwa, suka fara tafiya har suka iso compound ɗin gidan inda akayi decorations. Sosai mutane ke kallonsu, domin kuwa ba wacce batayi wanka na gani, na faɗa ba acikin su biyun zohal da Leeyanah. Itakam khulud mutuwar tsaye tayi ganin, kayan jikinta iri ɗaya dana leeya "yanzu haka papu zai min" khulud ta faɗa a cikin ranta tana barin wajen da sauri ta koma bedroom ɗin ta domin ta canja wasu kayan. Leeya kuwa da zohal kutsawa suka dinga yi cikin taron mutanen da ke wurin suna neman mum amma basu ganta ba, duk inda sukaje saidai a ce musu yanzun nan ta ɗaga. Hardai suka gaji suka haƙura. Leeya ce a gaba sai kuma zohal da ke bayanta sunada ƴar tazara sosai domin kuwa zohal komai tagani sai tayi video. Tana shirin ƙwalawa leeya kira sai ta hango indiyawan nan wato FANNAH da MAYAH da RUKHSHANAH, saita kanta tayi sosai taje irin ta sansu ɗin nan domin kada su saka taji kunya. "Sannunku" ta faɗa lokacin da take ƙarasowa gaban kujerun da suke zaune". "Yauwa kema sannunki, FANNAH da MAYAH suka amsa kawai saɓanin RUKHSHANAH da ta ɗora NU'AIM kan ƙafarta suna kallon cartoons a wayar ta. "Ki zauna mana sister kinyi tsaye kawai kuma ga wurin zama" FANNAH ta faɗa tana nunawa zohal kujera. "Uhhm, Nagode sosai" "Ahh ba komai" FANNAH ta faɗa da fara'ah a fuskar ta, "ke ƴar garin nan ce" FANNAH ta kuma yin Magana. "Ehh, Ni ƴar garin nan ce kuwa, kefa?" "Nikam a kaduna nake, menene sunan ki?" Cewar FANNAH. "Kaduna kuma!!!?" Zohal ta faɗa cikin tsananin mamaki. "Eh, a kaduna nake mahaifina kuwa cikakken ɗan garin Maiduguri ne, mahaifiyata kuma haifaffiyar BHOPAL ce a India". "Sai a lokacin zohal ta sauke ajiyar zuciya, kamar wacce taga wani abun tsoro". Dariya zohal ta bama fannah harma saida tayi sannan tace" wallahi sister kin ban dariya, sai kace wacce taga wani abun tsoro" "Ai naga abun tsoro, naga mutum ba-indiye harda kayan sakawa na India kuma acemin ɗan kaduna ne ai dole tsoro ya kamani". "Aikuwa dai, Ni ƴar kaduna ce koma nace ƴar Maiduguri". "Ah ah kidaina faɗa dan Allah karki saka ƴan matan Kaduna prouding". "Tau shikenan na daina faɗi, amma baki gayamin sunan kiba har yanzu" fannah ta faɗa da murmushi a fuskar ta. Domin ita haka rayuwar ta take tanada son mutane da fara'a da sakewa kamar dai Fahad. "Sunana ZOHAL KHALIL GIRAH " "Wow nice name ZOHAL KHALIL GIRAH, Ni kuma Sunana FANNAH GAHEES WAASIB, ƴan uwana biyu kuma wannan MAYAH waccan Rukhshanah sai kuma ɗan ƙaramin ƙaninmu NU'AIM, amma fa kinyi kyau sosai Wallahi" FANNAH ta faɗa tana yimata murmushi tare da ɗaga mata kai alamar gaskiyar abunda ta faɗa har ranta. "Nice name sister FANNAH, kuma Nagode sosai kema kinyi kyau wallahi gaba dayan ku ma kunyi kyau, amma dai dakeda wannan MAYAH ƴan biyune kho domin kuwa ni har yanzu na kasa banbantaku". "Haka mutane suke cewa, amma a zahiri gaskiya mu ƴan ukune harda waccan" FANNAH ta faɗa tana nuna Rukhshanah da yatsarta. "Hummm, ke kuma a yanda kikace kenan, amma a zahirin gaskiya bakida kama ko silik da ita kinfi kama da Wannan da kuma yaron nan" cewar zohal tana nuna NU'AIM". "Ah, ah bakisan kama bane kawai" "Nasani mana tunda gashi na gani" "A ina?" cewar FANNAH "Anan" zohal ta bata amsa tana miƙewa. "Ina zakije?" "Tafiya zanyi, bani kaɗai nakeba ina tare da kawata ne bansan lokacin da ta ɓacemin ba kawai naga wankanku ya birgeni shine na biyo ta wurin nan". Murmushi mai sauti fannah tayi domin kuwa harga Allah taji daɗi tace" shikenan sister zohal mun gode, zan iya samin contacts ɗin ki". "While not, kawo na saka miki" zohal ta karbi wayanta ta saka mata contacts ɗin ta. " Bara muyi photo kho" zohal ta faɗa tana ciro wayanta. "Okay, Mayah ki taso ki mana photo" cewar FANNAH tana kallon Mayah. Sai a lokacin Rukhshanah ta ɗago da kanta ta kallesu, sannan taci gaba da kallonda sukeyi a waya. MAYAH kuwa ta taso ta ɗaukar musu photo Kamar yanda FANNAH ta buƙata, ta ɗauka a wayar kowanne su. Tayi musu photon Kala daban-daban sannan ta bawa ko wacce wayanta sukayi sallama ta tafi. Tana barin wajen ta fara duba leeya bata gantaba. Duk inda take tunanin ganinta a wurin ta duba bata gantaba. Wayar ta ta fitar tayi dailing number ta, tayi ringing sau ɗaya ta ɗaga "Assalamu alaikum, bestie kina ina na dubeki ban ganki ba". Daga cikin wayar kuwa leeya ta amsata da faɗin "gani nan inda ake ajiye motoci nan ne kaɗai ba mutane sosai, na neme ki ban ganki ba, haka ma mum duk bangankuba shiyasa na zo nan". "Ke kaɗaice a wurin ko da wani" zohal ta tambaya. "Bangane da wani ba" cewar leeya. "Sorry bestie gani zuwa" zohal ta faɗa tana yanke wayar. Hanyar da zata sadata da packing space ta nufa, harta kusa ƙarasawa leeya tayi mata hannu alamar ta dakata wajen, itama leeyana tana ƙarasowa wajen zohal ɗin ma'ana (ta baro parking space ɗin zatazo filin walimar) Sakamakon ganin wata farar mota ƙirar range Rover ta tunkaro wajen yasa ta ba tashi domin ta bawa motar damar yin packing. Gefe kaɗan da wurin suka samu suka tsaya, leeya ta kalli, Zohal tace "wai ina kika shiga ne haka kawai muna tafiya tare koda na waiwaya ban ganki ba" "Wajen indiyawa na tafi" zohal ta faɗa tana murmushi. A wannan lokacin hankali leeya baya kan zohal kwata kwata domin jin wani ƙamshi daya ziyarci hancinta, wanda bako shakka tagane kamshin turaren waye, a ranta ta furta "baqon balarabe!!" "Kinga zohal dan Allah kizo mubar wajen nan" Zohal ma ta kula da kyawawan samarinda ke fitowa daga cikin motar duk hankalin ta ya koma kansu, domin kuwa ba wanda zai gansu a wannan lokacin basu birgeshi ba. Samarin gaba ɗaga ɗayansu uku kayan jikinsu iri ɗayane saidai kalar kayan ne ta banbanta. Domin biyu daga cikin su American suits kalar pitch and white ne. Yayinda ɗaya daga cikin su yafita daban domin shi nashi kayan kalar pitch ne kawai babu fari ko kaɗan. "Lahhh, bestie kinga ikon Allah, dubi samarin can uku ɗaya ba-indiye, ɗaya bature ɗaya kam Balarabe ne, amma kukam kunada family kala-kala wallahi" cewar zohal tana ƙara bawa idanunta abinci. Gaban leeya ne ya faɗi rassss, jin kalmar balarabe a bakin zohal. Haka kawai takejin wani irin tsoron sa ba shiga ranta. "Zohal na roƙeki da Allah kizo mu tafi, tunda kinga ga wanda akeyi walimar nan ya ƙaraso" "Wallahi bestie kinada matsala bantaɓa ganin balarabe ba sai a TV ko waya, haka ma Bature, haka ba-indiye ma. Shine zan gansu yau gani gasu kice kar in kallah" Zohal ta faɗa tana gyara tsayuwar ta. A bangaren samarin kuma, suna fitowa daga cikin motar ZAFARAN ya dafe saitin zuciyar sa, domin kuwa tunda ya shigo garin suleja yakejin zuciyarsa na bugawa a hankali, sai bayan ya shigo gidan nan kuma ya ƙara jin bugawarda take ya tsananta har saida ya dafeta sosai a gabansa. Fahad daya lura da kallon da zohal ke yimusu yasa ya sakarmata murmushi ya kuma ɗaga mata hannu, yayinda suka fara tafiya. Shiƙaɗai ya lura da ita a wajen ZAFARAN da Turab kam duk basusan ma da itaba. A tsakiyar su suka saka TURAB yayinda ZAFARAN keta hannun hagunsa, sai kuma FAHAD dake damansa kuma saiti da zohal. Sunata tafiya ba wata tazara mai nisa a tsakanin su, har suka kawo daf da ida zasu wuce, sai duk ta daburce domin har yanzu Fahad murmushi yake yimata. "Bestie mu tafi" cewar zohal tana miƙa hannun ta zata haɗa dana leeya. Sai taji wayammm, da sauri ta waiwaya tagni koda kuskuren miƙa hannun tayi, amma data waiwaiya taga ba leeya na alamar ta. kunyace ta kamata duk saita jita wani iri. Daidai lokacin da su fahad suka kawo daff da ita saita ratse ta basu hanya. Dawowa fahad yayi daga baya fuskar sa ɗauke da wani shu'umin murmushi yace, "Yadai ƴammata, kinyi kyau sosai" ya faɗa yana kallon idanunta har yanzu dai da murmushi a fuskar sa. "Nagode" zohal ta faɗa amma kuma ba wani murmushi ko fara'a a fuskar ta. "Amma fa ban fahimci kinada kyau sosai ba, saida kika daina murmushi kamar haka gaskiya kin haɗu" Cewar FAHAD yana kallon kwayar idanunta Murmushi mai sauti tayi kaana tace "kaima u're so cute man, haka indiyawa suke ne da zolayar mutane". "Ba zolaya gaskiya ce ai, kina da kyau sosai baiwar Allah. Kuma Allah yasa zuciyar ma kyakkyawa ce kamar dai ke ɗin nan". "Ameeen ya rabbil ibaddd, Nagode sosai" "Sunana FAHAD GAHEES WAASIB and you?" "ZOHAL KHALIL GIRAH, amma kai yayan FANNAH ne?" Zohal ta fada cikin sigar tambaya. "Nice to meet you zohal, ina kikasan FANNAH, ƙanwatace". "Aiko baka faɗaba nasan ƙanwarkace kaji ba-indiye, kuma FANNAH sabuwar ƙawatace a can muka haɗu da ita ɗazu". "Ban faɗa miki sunana bane ? karki ƙara kirana ba indiye ni Bahaushe ne, bakiji nama fiki iya hausa ba" cewar fahad cikin sigar wasa. "Hmmm, a yanda kace kenan. Amma aini zan iya ɓatarda kai ɓattt a cikin Hausa". "Haaa, yaro baisan wutaba sai ya taka, nikam bazaki iya ɓatardani a hausa ba, tun kan a haifeki nake ɓatar da manyanki balle ke". Ƴar siririyar dariya zohal tayi kaana tace "to ka ɓatar dani nagani". Fahad ya kalleta shima cikin dariyarsa yace "dakin tafi inda bakisani ba kuwa ɓacewa zakiyi kuma idan kinyi gardama kije india kigani". Dariya suka kwashe baki ɗaya kai idan ka gansu zakace sun shekara da sanin junansu. "Byee, zan tafi ana jirana" cewar zohal tana tafiya. "Okay, Nagode sosai mrs, fahad take care please" "Mekace?, zohal ta faɗa tana waiwayo shi. "Cewa nayi sai anjima bahaushiya". Murmushi kawai tayi tana tafiya batace masa komai ba. Leeya kuwa tunda tabar wajen hankalinta ya kasa kwanciya haka kawai takejin tsoron baƙon balarabe na ratsata. Ji tayi an dafa kafaɗarta ta baya, da sauri ta waiwayo ganin zohal ce yasa ta sauke ajiyar zuciya. "Bestie ramawa kikayi kho, shine kema kika tafi kika barni. Yayi miki kyau". "Sorry bestie zohal, wallahi nima bansan meyasa nake matukar tsoronsa ba kuma wallahi hankalina.ya kasa kwanciya har yanzu". "To, sbd me kikejin haka" cewar zohal. "Allah bansaniba nima, kuma ba abunda ya taba haɗani dashi amma wani abu ya taɓa haɗani dashi zo muzauna na faɗa miki. A can gefe sosai suka samu a filin taron suka zauna ba mutane sosai a bangaren domin yanda akayi decorations ɗin ne yazo da haka, saboda yanda aka yi tsarin ajiye kujerun ko daga ina kk indai kana zaune wurin to zaka ga wanda yake gaban ka komai nisanku dashi. Hakama wanda yake gaba zai ganka, kamar yanda Turab da sauran mutanen da ke tare dashi suke ganin kowa, kowa kuma yana ganinsu. Labarin duk abunda ya faru tsakaninsu da turab ta kwashe ta gayawa ZOHAL har sa'adda suka haɗu dashi a kitchen. "Ikon Allah, kice ya-Turab shine dalilin jin ciwon da kikayi a hannunki" Ɗaga mata kai tayi Alamar "ehh" "Tabb amma kuwa naso naga yanda zaigyara targaɗen da hannunsa" cewar zohal tana yimata murmushi. Saida hantar cikin leeya ta kaɗa jin abunda zohal ta faɗa, domin ita ta manta kwata-kwata da mum tace ta sameta idan an kammala taro. "Zohal, ya zanyi wallahi inajin tsoron bawan Allahn nan bazan iyaba gwanda muje asibiti kawai" "Idan ya kasa kenan, amma idan zai iya gyarawa kinsa ba wata asibitin da zakuje, ballema nasan zai iya wanda yake likitan sojoji ai gyaran ɗan targaɗen da kikayi ba komai bane a wajensa" Zohal ta faɗa daidai lokacin da mai gabatar da taro ya fara magana..........✍🏼 BAYAN WUYA..... By RUMANA M DIGGI EP.21 __________Bayan doguwar addu'a da aka saurara a bakin wani shehin malami da papu ya gayyato. Sai kuma karatuttukan Alqur'ani mai girma da aka bayarda dama duk wanda zai iya yafito yayi, Mutum daya ake bukata bangaren maza, haka kuma bangaren mata. Ganin ba wanda ya miƙe cikin mata yasaka Leeyana tashi, daidai lokacin da ZAFARAN yabar wajen sakamakon kiran wayarsa da akayi. Tafiya take cikin nutsuwa har ta isa wurin da ake gabatarda karatun. A gaban wanda zai bada mic ɗin ta tsaya, mutumin kuwa yana ganin ta ya miƙa mata ta fara karatun. Karatu take cikin sanyi da zaƙin muryarta, cikin suratul Maryam. Hankalin kowa ya karkata izuwa karatun da take wurin yayi tsit bakajin sautin komai saina karatun ta, sosai ta birge mutane domin kuwa wasu da za'a bi tasu kamar tayita karatun nan har lokacin kammala taron yayi. TURAB kam tunda ta taso bai ɗaga kansa ba balle ma yasan wacece. duk da shima karatun yayi masa daɗi sosai, domin kuwa har lumshe idanun yake yana bin karatun a hankali cikin zuciyarsa. Yanda ta karanta wata aya a can ƙarshe bai masan lokacin da ya ɗaga kansa ya ƙuramata idanu ba. Lokacin da ta bada mic kuwa duk mutane sukayi kaffara cikin birgewa. Har ta sauka daga wajen anata kallon ta, tare da yaba muryarta da kuma iya karatun Alkur'ani mai girma. Zohal kuwa daɗi kamar ya kasheta jin yanda ake yaba bestien ta. Bayan haka kuma, mai gabatar da taron ya miƙawa papu mic, shima yayi jawabi, daga nan kuma aka Bama mum , itama tayi nata. Sai kuma wasu daga cikin family suma sukazo zukayi guntun jawabi, daga nan kuma aka bawa zafaran da Fahad, daga su kuma aka miƙawa mai gayya mai aiki wato TURAB K. WAASIB. Bayan dogon jawabi da yayi shima, da irin nasarorin da yasamu a gayyatar da aka yimasa a kasashen waje, da kuma award, award ɗin da ake bashi a matsayin kyaututtukan yabo da godiya. Yana cikin jawabin ne idanun sa suka sarƙe dana leeya, wata irin muguwar faɗuwar gabace ta ziyarceta yayin da taga ya dalla mata wata uwar harara. Da sauri da sauke kanta ƙasa tana mamaki sai zancen zuci take, "kenan mutane duk ƙarƴa suke da suke faɗin idanuna tsoro suke basu, amma gashi shi yakalli cikin idanuna har ya harareni, wallahi badan nayiwa ammi babban alƙawari ba da ayau ɗin nan saina kalli madubi" koda leeya takai daidai nan a zancenta ta ɗaga kanta ta kuma kallon turab. Amma a lokacin ba ita yake kallo ba. Sosai mutane sukayiwa turab kyautuka daban daban, haka ma mum da papu ana yita saka masa albarka, har aka kammala taron daidai lokacin da Turab, zafaran, da kuma fahad suka sakko, suka shigo Mutane ana gaisawa da sauran family da suka iso da baya. Koda leeya ta kula da haka sai tayi sauri ta shiga cikin taron mutane domin ta ɓacewa ganinsa, tafiya take tana waige-waige cikin tsoro taji ta bankin wani abu, da ƙarfi ta juyo da nufin taga abunda ta banka. Numfashin ta ne ya tsaya chakkk, tayi suman tsaye sakamakon ganin Turab a gaban ta, tazarar da ke tsakanin su bata wuce taku biyu ba. Idanun ta takai can gefe inda ta jefarda wayar da ke hannunsa, da sauri ta duka ƙasa da nufin ta ɗakko masa wayar. Hannunta na hagu ta saka domin ɗayan hannuta ne bashida Lafiya. Cikin ɓacin rai Turab ya saka ƙafarsa ya takemata yatsu, wani irin ihun azaba ta saki domin kuwa ji tayi kamar yatsunta basa jikinta. Durkushewa tayi zaune domin ta ma rasa abunda zatayi "Dan Allah kayi hakuri wallahi da zafi" cewar leeya muryarta na rawa saboda tsoro, ga kukan da ke neman cin ƙarfin ta. "Kin taɓa ganin inda akayiwa mutum ɓarna, kuma a masa wulaqanci" cewar turab yana murtuƙe fuska. "Wulaƙanci kuma, Ni na isa na maka wulaƙanci? Wallahi da ason rainane bazan yi maka ɓarna ba ƙaddara ce kawai Ni danasan zamu haɗu wallahi bama zan biyo hanyar nan ba". "Saboda ga dodo kho, da kinsan zaki haɗu dani da baki biyo nan ba kho. Dan kin rainani ki bankeni har wayana ta faɗi sannan kuma kisaka hannun hagu zaki ɗauko waya ki bani, ai ko kyauta zaki ban bazaki bani da hagu ba, balle ni nakeda wayana saboda haka bazan karɓa da hannun hagu ba". Turab ya faɗa yana janye ƙafarsa daga hannunta. Janye hannun tayi a hankali ba tare da ta ɗauki wayar ba, kana ganin niqab ɗin ta zaka gane hawaye take, hannunta na dama da yayi sundul ta ta ɗauki wayar dashi da yake bazata iya ɗauka da hannun kaɗai ba sbd kumburin ta yayi yawa, yasa tasaka ɗayan hannunta ta tallafawa wa ɗaya ta miƙa masa wayan. Karɓa yayi tare da yin ƙofa yabar wurin. Ita kuwa leeya yana barin wajen ta ƙara fashewa da kuka domin kuwa tana ganin cewar zamansa a gidan ba ƙaramar wahala zatasha ba, shikenan idan ba'a wurin mum da papu ba, ba inda zata sami sanyi, domin ulud batason ta ko kaɗan haka shima baƙon balaraben nan daga gani baya ƙaunarta. A bangaren zohal kuwa tayi neman leeya har ta gaji bata ganta ba, kuma ta kira wayanta sai taga ashe bataje da wayan ba domin gata nan a cikin jakarta. Tashi tayi daga inda take ta fara ta fara zagayawa cikin mutane. "ZOHAL KHALIL GIRAH" taji ankira sunan ta daga nesa da ita kaɗan. Dakatawa tayi tana jiran ƙarasowar wanda ya kira sunan nata. "Ba-indiye" zohal ta faɗa tana washe fararen haƙoranta lokacin da Fahad ya iso wajen. "Ke nifa na gayamiki ba ba-indiye bane, tun ɗazu inata neman ki ban ganki ba" cewar FAHAD. "To nema kuma, Allah yasa lafiya" zohal ta faɗa tana gyara tsayuwar ta. "Eh, to dama dai za'a ce, amma alfarma ɗaya zaki min" cewar fahad yana ɗaga yatsansa alamar (ɗaya)kenan. "Ohk, Allah yasa zan iya" "Zama ki iya, precious queen" fahad ya faɗa fuskar sa ɗauke da ƙayataccen murmushi. "To nikuwa zohal a ina na zama queen waya bani saurauta". "Anan" fahad ya faɗa yana nuna saitin zuciyar sa. "Thooo, Allah sarki. Yaushe hakan ta faru kuma" zohal ta faɗa da cikin barkwanci. "Hmmm, kedai bari kawai zuciyar fahad tayi nutso, har ta noce q begen wannan sarauniyar daga ɗazu, zuwa yanzun nan". "Allah sarki, aikuwa ka shigo fadar sarauniyar da takeda sarkin da ke mulkin fadar zuciyarta" faɗin zohal tana janye idanun ta daga kallonsa. "Da ace hakane, da zuciyata bazatamin ƙarya ba, Saboda na yarda da zance da zuciya ta taymin akan wannan kyakkyawar sarauniyane yasa nazo mata a bawa, bawai sarki ba". "Hmmm" kawai zohal ta faɗa tana cewa" da ace bawan jarumine ba abunda zai hana saraunyar ta ƴan tashi ya dawo a gefen damarta". "Domin tabbatar da bawan jarumine yasa nake so kizo ki rakani". "Ba damuwa muje" "Yau Hausa girl, ko kefa" A bangare ɗaya kuwa mum-fanaya ce zaune a wani gefe cikin filin da aka kammala walimar, sai kuma mummy-neesah wato mahaifiyar twins sai kuma su kansu FANNAH da MAYAH da RUKHSHANAH harda NU'AIM sai kuma khulud dake zaune gefen mahaifiyarta sai firar yaushe gamo suke. FAHAD ne ya iso wajen bakinsa ɗauke da sallama zohal kuma tana biye dashi, saida suka kusa isowa ta kula da mum harda fannah, cikin tsananin farin ciki take tafiya har ta manta da rakiya take. Jin sallamar da fahad yayiwa su mum ne ya sakata dakatawa da tafiyar da take. "Zohal ina kuka shiga keda ƙawarki tun ɗazu aka yita ɗaukar photo amma bangankuba" cewar mum-fanaya tana duban zohal. Zohal zatayi magana fahad yayi caraffff yace"mom itace sarauniyar da nace muku ta sace zuciyata, gatanan ZOHAL KHALIL GIRAH ƴar nan garin ce, ita nakeso kuma ita zan aura idan har kun yarda itama ta yarda, to ba makawa itace matata In sha Allah, zohal ga iyayena nan da ƙannena shine na tarasu a nan na nunaki a gabansu". Wata mahaukaciyar kunya ce ta kama zohal domin har ga Allah batayi tunanin haka ba, da bazata biyoshi anan ba domin su mum zasuga rashin kunyarta da yawa. Sosai mum tayi farin ciki da haka, koba komai zohal ce yarinya mai kyau ga hankali da nutsuwa, ga yawan barkwanci. Miƙewa mum tayi ta ƙaraso ga zohal ta rungume ta domin ta fahimci kunya takeji. "Lallai mummy ke bazaki taso ki rungumeta bane, shine kika bar mum ita kaɗai" cewar fahad yana tallafe ƙeya. Robber cup, mummy-neesah ta ɗauko dake kan table ɗinda suke zaune ta jefa masa tare da faɗin "bar nan mara kunyan banza". Juyawa yayi aguje yana dariya yabar wajen. Zaunarda zohal mum tayi kusa da ita, zohal kuwa kamar batasan mum ba saboda kunya ko daga kanta ta kasayi balle tayi wani kwakkwaran motsi. Mummy-neesah kuma sai kallon zohal take tana murmushi domin kuwa taganta nutsatstsiyar budurwa ga kyau da ɗie kuma ga kunya. Ta ido mum da mummy sukayi magana sai mum ta mayarda kallonta wurin twins tace fannah ki tashi ki rakata ta wuce. Da murmushi a fuskar fannah ta miƙe ta kama hannunta tace "aunty na muje na rakaki kho" Gwalalo idanu zohal tayi domin da ba domin ganin su mum ba sai tayi magana. Suna fara tafiya FANNAH tace "yadai matar yayana, kinga mun ƙara haɗuwa a karo na biyu kho, haɗuwar mu ta gaba kam in sha Allah kinzama cikin familyn mu kenan, wannan kyawun da kikayi Ni nasan sai kinyi catch, daga shigowar yayana kin kwamushe masa zuciya" Zohal na shirin magana wayar fannah tayi qara, picking call tayi ta kara a kunnenta "OKAY" kawai FANNAH ta faɗa tana katse kiran. "Nan zamu bi" cewar FANNAH sunayi wani ɓangaren. Surutu kawai fannah keyi ita kaɗai zohal kam loma ta ɓace a bakin ta domin ta kasa furta komai. Komai FANNAH tace sai kaga zohal tayi murmushi kaɗai har fannah itama ta fahimci kunyace kawai zohal keji. Kuma itama abun ya birgeta. Ita kuwa zohal Allah-allah take kawai taga leeya domin ita kaɗai takeda muradin gani a daidai wannan lokacin. "Ya-fahad gata nan". Maganar da fannah ta faɗa kenan data tsamo zohal daga tafkin tunanin da ta tsunduma. "Subhanallah" zohal ta faɗa a mamakance domin ita har ga Allah batasan sunzo wurin nan ba. "Maimakon ace bawa ya tsorata sai kuma naga sarauniyar ce da kanta keda alamar jin tsoro". "Cikin sanyin murya zohal tace" idan bawan yakai tantiri ne ake jin tsoron sa, yanzu kam idan ma akwai wani suna da ya wuce tantira to dole a baka sunan domin kuwa duk ka gogemin harda" "Uhmm, shikenan kawai yanzu tunda bawa yayi nasarar kwamushe zuciyar Sarauniya sai ta bada kai bori ya hau kho". Ɗan rankwafarda kai zohal tayi sannan tace"ga kan a kira borin ya hau kho" Dariya suka kwashe baki ɗayansu, daga nan kuma fira ta wanzu tsakanin su. Idan ka gansu zakayi tunanin laila ne da majnoon saboda ƙauna. ******* A bangaren leeya kuma tunda abun ya faru tabar filin taron ta koma cikin gida, sashensu ta shiga tare da cire kayan jikinta tayi wanka sannan ta canja kaya, ta saka rigar yadi mai shara-shara mara nauyi, sai kuma ƙaramin mayafin da ta ɗauka ta yafa bayan niqab ɗinta data saka. Parlour ta sauka ta zauna kan 3sitter sai faman tunani take, har bacci ya ɗauketa. Tana kwance a wurin tsawon awanni biyu, dayake kuma babu hayaniya sosai a parlourn ko mutane ma ɗaɗɗaya ne ke shigowa, ga kuma tarin gajiya dake jikin ta, shiyasa ta dauki tsawon lokaci tana bacci. Kaso chasa'in cikin ɗari da sukazo taron duk sun tafi, domin babu waɗanda ke nesa sosai sai irin familyn su dake Maiduguri. A cikin waɗan da suka wuce kuma harda su mummy-neesah da ƴan ukunta da kuma NU'AIM. Shikuwa fahad yana nan bai tafi ba, dama a abuja yake aikinsa domin shi babban lauyan Shari'a ne. Kamar dai papu, amma ba matsayinsu ɗaya da papu kowa da nasa. Baqinda suka rage kuwa sun koma a masaukin da aka basu Ya rage saura ƴan gidan kawai Sai kuma zohal. Turab kam tun karfe shida na yamma suka ɗau hanya Abuja shi, zafaran, dakuma Fahad. A hanyarsu ta zuwa ne fahad ke yita basu labarin zohal, wanda tun sa'adda aka kammala walimar ba abunda yakeyi face zancen ta tun suna amsa masa har suka fara yimasa banza. Zafaran ne ke tuqin fahad kuma yana kusa dashi, sai turab dake back sit. "Yawwa, zafaran nace ba wani zance kan batun wancan yarinyar? Saboda naga tun yanzu fahad ya fara yimana gorin budurwa". "Kaidai bari kawai man Tk ba wani labari, wallahi Ni inaji a jikina yarinyar nan tana inda na baro yanzu". "Inda ka baro kuma zafaran, suleja kenan?" Gyada masa kai yayi alamar "Eh, haka nake tunani domin inajin alamarta kamar tana suleja Yanzu haka" "Ah ah dai abokina, kadaina saka wannan a ranka idan har labarin da kabani kan wannan yarinyar gaskiya ne to mezai kawota har nan suleja" Turab ya faɗa yana jijjiga kai alamar tunanin zafaran ba daidai bane. Fahad ne ya ɗago kai yana kallon abokin nasu cikin tausayawa ya dafa kafaɗarsa yace" Zafaran kayi hakuri, ka daina saka damuwar nan a ranka, in sha Allah zamu tsaya tsayin daka muyi iya ƙoƙarinmu wajen nemo maka cikar burinka. Ka saka wannan a ranka indai har ka aminta da abotarmu". Wasu zafafan hawayene suka zubowa zafaran har yakai ga ya faka motar gefen titi ya kifa kansa kan steering motar. Cikin tausaya Turab ya buɗe motar ya zagayo mazaunin driver, tare da janyo zafaran, fahad kuma ya koma inda zafaran ya tashi wato driver sit. Shikuwa Turab ya dawo dashi back sit domin ya rarrashi" haba abokina, dan Allah kayi hakuri mana Please, musani akwai zafi kuma duk wanda ya tsinci kansa a halinda ka tsinci kanka dolene a tausaya masa. Kuma mun tausayamaka harga Allah, to meya rage". "Haƙuri" Fahad ya faɗa yana ci gana da driving ɗinsu. "To kayi hakuri dan Allah, in sha Allah munyi maka alƙawarin kasancewa dakai har zuwa lokacin da zaka samota, wallahi danasan wannan labarin Muhsin zai gayamaka a ɗazu da ban bari ka amsa wayar ba, domin na lura tun lokacin da ya gaya maka labarin nan nutsuwa ta kau daga jikinka" Cikin raunananniyar murya Zafaran yace" Tk nifa nasakashi ya bincika min, kuma da yayi binciken yasamo amsa har ya gayamin, to menene laifin Muhsin tunda Ni na sakashi. Amma kuma har yanzu jikina baya bani akan bayanan sa inaso inje dakaina in gani, Fahad ka shirya mana jirgi gobe zamu ɗau hanya in sha Allah" "Zuwa ina zafaran, dan Allah Zafaran banda gaggawa mubi komai a sannu, domin nida kaina nayi binciken sakamakon da Muhsin yazo mana dashi a yanar gizo, faruwa abun shekara biyar zuwa shida ne, domin har ansamu wasu sun maye gurbin waɗancan da aka kashe a arear da abun yaFaru, yanzun nan Bama da tabbacin itama kanta tana raye ko ta mutu, domin a yanda masu rahoto sukace ba wanda aka samu da rai a cikinsu". Runtse idanu zafaran yayi da ƙarfi yanajin yanda kalaman Fahad ke sauka a zuciyarsa kamar ana watsa masa ruwan wuta "yanzun nan bama da tabbacin tana raye, ko ta mutu" "Ah ah Fahad lewa bata mutu ba, bazata mutuba in sha Allah, sai munyi Aure kuma mu haifi ƴaƴa da izinin rabbi" zafaran ya faɗa wasu hawayen na ƙara gangarowa a kumatunsa. Sake dafashi turab yayi yana cewa "ba'a san namiji da ragwanta ba abokina, anason namiji da juriya, wannan halin daka tsinci kanka ka yarda jaraftace kawai. Idan lewar ka ta mutu shikenan ba abunda zamu ko kuma kai zakay...." "Lewa bata mutu ba, inaji a jikina bata mutu ba, domin muhsin daya gayamin ya faɗamin ƴan harin sun tafi da ƴan matane da ƙananan yara, kaga lewa mace ce kuma karamar yarinyace a wannan lokaci" zafaran ya tari numfashin Turab tun kan ya ƙarasa zancensa. "Shikenan, ƙaddara da gaske ne ma sun tafi dasu, a ina suka kaisu?, a ina zasu tafi dasu?, me zasuyi dasu ?, zafaran! Duk kana da amsar wadannan tambayoyi?. Magana fa ake ta shekaru shida baya, shekaru shida fa ba kwana shida bane zafaran dan Allah kayi hakuri kasawa zuciyar ka salama in sha Allah komai zaiyi fine kaji abokina.............✍🏽 BAYAN WUYA...... By RUMANA M DIGGI EP.22 ____________K. MANSION SULEJA NIGERIA. "Nayi farin ciki sosai da Allah ya haɗaki da fahad zohal, haƙiƙa zanfi kowa farin ciki idan haka ta kasance, kuma zanyi iya ƙoƙarina domin ganin hakan ta kasance. Fahad mutum ne mai sauƙin kai ko ban faɗa ba ma kin gani, shi ba kamar Turab bane halayensu nada bambanci sosai, dan Allah kiyimin alkawari ɗaya zohal" mum ta faɗa tana kallon zohal dake zaune gabanta. Leeyana kuma a gefen. "In sha Allah mum, ki faɗi kowane alkawarine indai har zan iya to zanyi miki shi da yardar Allah" "Zaki iya zohal, kan maganar fahad ne. A matsayin da fahad yake kai na aiki yanzu ya kamata ace yanada iyali ko dan kula da wasu abubuwa, amma kuma kinga babu iyalin. Sosai mahaifiyarsa tayi farin ciki da Wannan zancen da ya zomata saboda har tabar garin nan zancen ki muke, domin bata ɗauki maganar da wasa ba. Shima fahad ɗin haka, saboda hakane ma ya kawoki wurin mu, kuma bari kiji mahaifinsa yace a shaidamiki idan kun sasanta kanku sati mai zuwa zaizo da kansa suje suga mahaifinki, kuma su nemi auren ki. Shiyasa ma na zaɓi na gayamiki tun yanzu domin ku fahimci juna dashi. Amma me kika ce game da haka?" "Nidai bazan ce komai ba mum, saidai nace Allah yayi mana jagora, kuma ya shige mana gaba, yasa hakan ne yafi zama alƙairi" "Ameeen zohal, Ubangiji Allah yayi muku albarka, ki tashi kije ku tattauna ta ƙawarki nasan abunda kike matuƙar buƙata kenan, domin alamun ki duk sun nuna. Kije ku tattauna tunda mun jira turab har yanzu bai dawoba" "Mum ina ya tafi" leeya ta tsinci kanta da yiwa mum tambaya. "Yaje Abuja ya raka abokansa, kuma yace min yau zai dawo, naga har yanzu bai dawoba ina ga ko can zai kwana" Miƙewa zohal tayi tana faɗin "mum zan tafi amma zan dawo gobe in sha Allah, leeya kuma zamuyi magana ko a wayane, domin dare yayi yanzu karfe goma na neman shuɗewa, leeya zan kiraki da waya gobe mayie magana in sha Allah" "Leeya ki tashi ki rakata gate zanyiwa driver magana yakaita gida" "Ah ah mum, ki barshi kawai dana fita zan kira gida na faɗamusu ko Aunty zainab ce zatazo ta ɗaukeni ko kuma a turomin driver". "zohal kenan ita zainab ɗin bataso ta hutane da zaki saka a tasota yanzu daga unguwar ku tazo nan ɗaukarki, ai tunda ga drivern gidan ki bari ya saukeki gida kawai" "Tau mum, ba damuwa. Nagode sosai Allah ya huce gajiya" "Ameeen, sai da safenki, kuma karki manta dan Allah idan kinje gida ki gayawa mahaiyarki saƙona ko ki turamin da number ta kawai" "Tau in sha Allah mum zan tura miki tun kan na ƙarasa gida ma" "Okay, sai na jiki". "Muje bestie" zohal ta faɗa tana wucewa gaba, leeya kuma tana biye da ita. Fira suka ɗan taɓa a ƴar tafiyarda sukayi kafin su iso wurin da drivern ke zaune Tare Da mai gadi, nan suka tarar dashi sai fira sukeyi a tsakanin su suma. Suna isowa wurin suka gaidasu cikin girmamawa, suma suka amsa musu cikin girma. daidai lokacin da ake ta faman danna horn a bakin gate. Da sauri mai gadin yaje ya buɗe kofar, wata baƙar mota ƙirar Benz ta shigo gidan, ta gaban su leeya motar ta wuce. leeyana da zohal suke, ratse gefe domin su bawa motar damar wucewa. Parker motar akayi daidai inda suke tsaye. Daga can ɓangaren driver kuma ya buɗe motar ya fito yana nufosu, dayake ba wata tazara tsakanin su domin zagayowa kawai zaiyi motar ce ta shiga tsakani su. akwai hasken electric solar a wajen yasa suka gane ko waye. "Fahad me ya dawo dakai suleja kuma yanzun nan!?" Zohal ta faɗa da mamaki. "Zohal ce ta dawo dani wallahi zuciyata ta kasa samun sukuni, shiyasa na sake dawowa. Wata ƙila idan nayi firar dare dake zan samu sauqin abunda nakeji a kanki, gaba ɗaya soyayyar ki na neman rikitani zohal anya kuwa ba lauje cikin naɗi" Fahad ya faɗa da alamar wasa. "Hmmm, har mashi akwai cikin naɗi Fahad" kaga nifa har na manta da wani fahad" Zohal ta faɗa fuskar nan tata babu yabo ba fallasa. Da sauri fahad ya dafe ƙirjinsa ya jingina da motar da ƙarfi. "lafiya" cewar zohal tana ƙara jaa baya kamar wacce taga wani abun tsoro. "Zohal, kin manta dani fa kikace, wallahi so kikeyi ki illa ta zuciya ta da waɗannan kalaman naki kawai, a yanzu kam na fara ganin alama kan abunda abokaina suke faɗamin, haƙiƙa na zurfafa sosai a soyayyar ki, kuma sun faɗamin idan kika gane haka zaki iya amfani da wannan damar ki cutarda zuciyata zohal. Don Allah na roƙeki idan bakya sona tun yanzu ki faɗamin karki saka ni faɗawa mawuyacin hali na roƙeki Please" Fuskar zohal ce ta sauya sosai zuwa wani yanayi mai wuyar fassara, fushi, ɓacin rai, hasala, zuciya. A wanda yake kallon fuskar ta zai fahimci duk wadannan abubuwan. Tafiya ta farayi cikin isa da taƙama harta matso gab dashi, tsayuwa tayi sosai tana ƙara murtuƙe fuska tamkar ba itaba. Duk abun da yake faruwa akan idon leeya, duk da batasan ta soyayya ba, amma ta fahimci irin tsananin soyayyar zohal dake cikin zuciyar fahad, sosai kalamansa suka bata tausayi, duba da yanda ya marairaice, mamakin zohal ne cike tabbb a cikin ranta domin a tsawon zamanta da ita a ƙalla zasukai shekaru biyu da watanni. Bata taɓa sanin ta da halayyar wulaƙanci ba, kuma tasan zohal sosai tanada son mutane, koda bata sonka bazaka gane ba saboda bata nunawa. Amma sai gashi yau a gabanta zohal na neman wulakanta wani, bayan kuma tasan zaman ɗa yake a wurin mum. "tabbas idan na bari zohal ta wulaƙanta fahad ban kyautawa kaina ba kuma bazan taɓa yafewa kaina ba akan haka. koba komai shi ɗan adam ne wanda ya cancanci karamci a ko'ina, gashi kuma shi musulmi ne cikakken, daɗin daɗawa kuma zaman ɗa yake a wurin mum, haƙiƙa bazan bari kiyi abunda kikeda niyyaba zohal" leeya ta faɗa a zuciyarta tana dakawa zohal tsawa. "Ki dakata daganan zohal" cewar leeya tana yowa kanta. A daidai lokacin turab kuma ya banƙaɗo marufin motar kamar zai ballashi domin kuwa ya hangi wasu abubuwa biyu daya kasa bambancewa a cikin ƙwayar idanun zohal tsakanin soyayya da ƙiyayya. Turab ya fitone da nufin ya janye abokinsa domin yana gani baza'a ci zarafin fahad ba a dalilin soyayyar macen ma dayake gani a idonsa bata kai ba balle ta kawo, domin idan ta shi ne wallahi zohal ko kallo bazata isheshiba. Cakk suka tsaya su biyu yayinda suka ji abunda zohal ke ƙoƙarin faɗa "fahad me kace? In faɗa maka idan banasonka kace?. Zuciyar fahad na bugawa da sauri sauri kamar ganga, Muryar sa kuma na rawa cikin fargaba da kuma tsoron amsar da zata fito daga bakin zohal yace " ehh, idan bakyaso na ki gayamin, wallahi nayi miki alƙawarin zan fita rayuwarki, kuma zan manta dake kamar yanda kema kika manta Dani". "Abu na farko inaso ka buɗe kunnayen sosai kaji abunda zan faɗa maka, FAHAD G. WAASIB, ZOHAL KHALIL GIRAH na sonka, kuma tana ƙaunarka, soyayya zohal a gareka ka gaskiya ce, ba abunda zai sauya haka. Kuma Ni zan zamo matarka in sha Allah, mu rayu tare cikin so da ƙaunar juna saboda Allah" Lumshe idanunu ta yi a hankali kamar bazata buɗe ba taci gaba da faɗin; "A Rayuwar nan tawa ban taɓa jin wani abu ya shiga raina ya sami wurin zama sosai ba sama da soyayya ka, nasan kanasona fahad kuma nima ina son ka, domin inada tabbacin da za'a auna girman soyayyar ka dake zuciya zatafi taka yawa. A lokaci ɗaya soyayya ke shiga cikin zuciya ta ratsa jiki da jinin wanda ke ɗauke da ita, haka soyayyar ka tayimin fahad. A farkon ganina da kai kaima idan zaka fahimta zaga gane yanda na kusa loosing control saboda ɗimauta da nayi, kai baka gane ba?, nasan ka gane Fahad saboda gane War da kayi ne ya janyo hankalin ka kaymin magana. A tashin farko da kaymin magana ba soyayya ko ɗigon soyayyata a zuciyarka, sai bayan mun rabune ka faɗa halin da na faɗa tun a farko, kasan yanda zuciya tayita azalzata akanka kuwa, wallahi fahad da ace ban ƙara haɗuwa dakai ba, da bansan yanda zuciya ta take ba halin yanzu" murya a tausashe ta ƙarashe maganar da faɗin "Abu na ƙarshe fahad na roƙeka kazo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tabbatar da maganar da abokanka suka faɗa ba gaskiya bace. Idan ma zata kasance gaskiyar to kaine zaka yi amfani da girma da kuma adadin soyayyar da nake maka ka illa tamin zuciya, Ina ƙara baku haƙuri gaba ɗayan ku da kukayimin kuskuren fahimta harke bestie, kuyi hakuri duk ku yafemin Ni wallahi ko kaɗan ba abunda yake raina ba kenan" Zohal tayi maganar tare da dunkule hannayenta alamar roƙo. daga nan bata ƙara cewa komai ba tayi tafiyarta ba wanda kuma ya dakatar da ita domin kalaman ta sun sanyaya jikin kowa dake wurin sosai. Sake jingina jikinsa yayi a sanyaye a jikin motar tasu, ya ɗaga kansa sama kamar maison tunano wani abu, domin kalaman zohal sunyi masa daɗi sosai yama rasa me zaiyi yayi farin ciki "ina zataje" fahad yayi tambayar while kansa na sama, kuma yana jingine a motar. Leeya ta fahimci da ita yake shiyasa bata jira kowa ya amsa masa ba domin tasan ita yake tambaya tunda tare ya gansu. "Gida zataje" "Wazai kaita gidan ko a ƙafa zataje saboda abun hawa zaiyi wuya a unguwar nan" "Driver ne zaije ya kaita, nasan yanzu haka tana nan waje shikuma drivern gashi can yana fitar da mota daga parking space" leeya ta faɗa tana kallon wurin. "Tk bani carkey zanje na kaita". Sai yanzu hankalin leeya ya dawo kan wanda aka kira da Tk wato (Turab Khattab). Wani irin tsalle zuciyar ta tayi ta faɗo yayinda tayi arba da fuskarsa, "baƙon balarabe" ta faɗa a cikin ranta. juyawa tayi da sauri har tana harɗewa a yafiyarta saboda tsananin tsoron sa. Turab kam tsaf ya fahimceta domin shima bai ankara da ita a wurin ba saida bayan angama komai. Wani irin haushi ne ya turnuƙeshi, a yanzu kam ya gane tsaff yarinyarnan tsoronsa take, "tukunna ma wacece wannan yarinyar?" "Amsar tambayar ka tana hannun mum" fahad ya faɗa yana shigewa cikin motar. A zaton turab a zuci yayi maganar sai bayan Fahad ya amsa masa ne ya gane a fili. Juyawa yayi ya tafi abunsa, ita kuma leeya har tayi nisa a tafiyarta. Shigowa yayi a parlour bakinsa ɗauke da sallama, da mamakinsa bai tararda kowa cikin parlourn ba. Harya taka stairs da nufin hawa sama sai ga mum zata sakko. "Dama kai nake zaman jira wajannan tun ɗazu, nayi tunanin a can zaka kwana ai". "Jirana kuma mum, Allah dai yasa lafiya" "Lafiya amma ba lau ba" "Subhanallah, waye bashida lafiya mum" "Wallahi ƙanwarkace da ɗan sami buguwar ƙashi". "Allah sarki ina khulud ɗin take" "Hmmm, khulud ce kaɗai ƙanwarka". "Ah ah mum, suna nan dayawa ma kuwa, amma dai gaskiya banji daɗi ba, nasan ma daga cikin baƙine kho, yanzu shikenan za'a ce daga zuwa walima sai dawowa da ciwo" "Tau wannan kam ai ba baƙuwa bace ƴar gida ce" "Ƴar gida kuma ba khulud ba" "Eh, ba khulud bace, khulud kam inaga tashige bacci tun ɗazu" "Wacece mum?" "Leeyanah" "Leeyanah" ya maimaita sunan a bakinsa, ɗan jimmm yayi yanaso ya tunano inda ta taɓajin sunan na" Ya ɗauƙi tsawon seconds sittin a haka kafin ya ɗan jijjiga kansa kaɗan hadi da jin guntun tsaki. "Akwai matsala ne" "No mum, nataɓa jin sunan nan a wani wuri, amma na kasa tuna wurin" "Okay inaga a gidan nan ne" "Maybe" ya faɗa yana komawa cikin parlour. Bayan ya zauna da alama dai jira yake wacce batada lafiyar tazo yace "mum, niko inada tambaya" "Tambaya kuma tame turab" "Mum, wacece wannan yarinyar mai saka niqab" "Leeyana" mum ta bashi amsa a takaice. "Okay, amma mum ita ƴar waye a familyn mu" "Ba ƴar familyn mu bace, amma dai zata zama in Sha Allah" "Ba ƴar familyn mu bace kuma?" Cewar turab da alamar tambaya. "Eh, ba ƴar familyn mu bace, ƴar gidan hajiya saknah ce, ƙawata marigayiya wacce ta rasu a shekarun baya nasan kasanta ai, inaga kamar ma kana nan lokacin da nake nema a bani yarinyar" "Eh, ina nan mum, kuma nasan da rasuwar, amma mum ita wannan ba zuhra bane sunanta" Murmushi mum tayi irin na yarda da kai tace"saidai idan ka manta amma ba zuhra bane sunanta LEEYANA ne" "Okay, to meyasa take ɓoye fuskar ta, tayi aurene" "Ah, ah batayi aureba" kwashe labarin komai dangane da saka mayafinda da leeya keyi a fuskar ta, mum ta bawa turab kamar yanda leeya ta gayamata. Har ita kanta mahaifiyarta bata yarje mata tasan fuskar ta ba sai ranar da za'a ɗaura mata aure koma idan an ɗaura" "Eyeeh, mum kina nufin kice itama kanta bata san fuskar taba kenan" "Tabbas itama batasan fuskar ta ba, saboda hakane take kiyayewa kanta, domin batasan nufin mahaifiyarta nayin haka ba". "Gaskiya mum, abun akwai ban mamaki, to Allah dai ya sauwaqe". "Ameen" mum ta faɗa tana ƙwalawa leeya kira. Kamar kullum ta fito cikin tafiyar ta ta nutsuwa, kanta a ƙasa saidai wannan karon kam ta sako hijab saman rigar da ke jikinta. Zuciyarta sai duka take, gaban mum tazo ta durkusa har ƙasa "Mum, gani" "Kije ga yayanku can yana jiranki, ya duba miki hannun ki Kinji" Miƙewa tayi cikin sanyi ta nufeshi shikuma turab ko inda take bai kalla ba kai kace baisan da zuwanta wurin ba, harta ƙaraso kusa da shi ta zauna a ƙasa har kuma wannan lokacin bai ɗago ya kalleta ba, itama bata ɗaga kai ta kalleshi ba, kuma bata cemasa uffan ba. "Mum, Bara naje na dakko first-aid box ko, akwai wani cream ta zan shafa mata a hannun". "Ok kaje ka dakko, bara na hau sama kafin ka dawo, leeya ki tsaya ki jirashi kinji banda raki" mum ta faɗa tana ɗan murmushin wasa. Daga kanta tayi alamar taji abunda mum ta faɗa, yayinda Turab ya tashi yabar wajen itama mum tabi bayansa. Babu jimawa yadawo hannunsa ɗauke da wata karamar akwati. Daining area yaje ya ɗakko ruwa masu sanyi sosai, da kuma ƙaramar kujera daining sitter. A gabansa ya ajiye kujerar tana fuskantar sa, sannan ya buɗe ruwan ya tsiyaya a cup, ya kuma ɗakko akwatin a gabansa yabuɗeta gaba ɗaya, wani farantin ya fito dashi daga cikin akwatin, kaana ya fito da cream ɗinda zaiyi amfani dashi ya ajiye kan wani ƙaranin Centre table ɗinda ke tsakanin sa da kujerar da ya ajiye. Har a lokacin leeya bata ko ɗaga kanta ba balle tasan abunda yake. Wata uwar Tsawa ya daka mata yana faɗin, "ke so kike nazo na ɗagaki na zaunar dake kan kujerar nan ko me, da kika wani zo kika sakani a gaba sai kace mai neman yafiya" Bata furta masa komai ba ta miƙe kawai ta zauna kan kujerar. Farantin ya janyo har gabanta kan Centre table ɗin, sannan ya janyo cup ɗinda ya saka ruwa shima har kusa da inda hannun ta yake "gashi nan ɗauki ki zuba ruwan nan a inda ya kumbura, ruwan sanyi ne sosai, kuma zakiji ba zogi idan kika zuba ki daure kawai ki zuba kada ki damu da abunda zakiji.........✍🏽 BAYAN WUYA.... By RUMANA M DIGGI EP.23 _____________ɗayan hannunta da baya ciwo ta ɗauki cup din dashi sai ta tara hannunta ɗaya mai ciwon a farantin da ya ajiye mata, ta fara zuba ruwan. lokacin da ruwan suka fara sauka a hannunta saida taji kamar tayi ihu da sauri ta runtse idanun ta tare da cije gefen lips ɗinta na ƙasa. "Sannu" taji ya furta mata muryarsa wasai kamar da ma can sun saba yin magana. Mamakine ya kusan kasheta ganin shi ɗin ne da gaske ya furta mata. "Akwai zafi ko?" ya sake furtawa a karo na biyu. nan ma bata cemasa komai ba domin kuwa har yanzu gani take kamar ba da ita yake ba. Taɓe baki kawai yayi sannan ya fara aikinsa. Farantin ya ɗauke daga wurin ya kuma dauke ruwa da cup ɗinda ya ajiye. First aid box ɗin ya ɗakko ya ɗorata kan Centre table ɗin da ya ajiye. PAIN RELIEVING GEL, ya ɗakko daga cikin akwatin ya miƙa mata "karɓa ki shafa duk inda kumburin yake" Hannu biyu ta saka ta ƙarɓa, tare da buɗeshi ta fara shafawa a hankali, kuma ta shafa ko ina duk inda tasan ya kumbura. hannun sa ya miƙa mata alamar ta bashi Tata. Ita kuwa ta ɗauka Cream ɗin da yabata yake nufi ta bashi, sai ta saka hannun nata mai ciwo ta miƙa masa cream ɗin duk a zaton ta shi yake nufi. Bai ko kalli abunda take miƙa masa ba ya riƙe hannunta dai-dai inda yake ciwon, wani irin zabura tayi da sauri zata miƙe ya saka ƙafarsa ya take mata tata kafar "ina zakije idan na sakeki ki zauna bana son shashanci" turab ya faɗa fuskar sa ba ko ɗigon fara'ah. Komawa tayi ta zauna tana jan wani wahalallen numfashi tana saukewa. Sake dai-dai ta hannunsa yayi a wurin yana sake murzawa haɗi da lankwasa hannun wani gefe. Da sauri ta saki ihu tana miƙewa zata tashi, sake danne mata ƙafa yayi da tasa ƙafar amma a wannan lokacin kam bai sa ta tsaya ba. Miƙewa yayi tsaye shima yana ci gaba da jan hannun, itakuwa bata fasa da janye hannunta ba tare da yin duk addu'ar da tazo mata a baki. Turab kam ko a jikinsa domin shi a rayuwarsa ya tsani irin haka, bayason mutum mai raki ko kaɗan domin a ganin sa raki kawai take, ciwon bai kai da tayi irin wannan kukan ba, abun ya dawo kamar kokawa tsakanin su domin tana janye hannayenta ne shi kuma yana ƙara riƙo hannun ko a jikinsa aikinsa kawai yake baya ma duba yanda take kuka. Jin abun yayi yawa ya saka mum sakkowa tazo parlour "Turab meye haka kuma, gyara tarkaɗene wannan ko kuma gayya, bafa soja bace kasaketa ta huta ai ko tsayuwarnan zata sakata jin zafi balle gashi ka haɗa mata biyu, gata a tsaye kuma baka sassauta mata ba" cewar mum tana janyo leeya jikinta. Leeya ko tanajin kanta a jikin mum ta ƙara fashewa da kuka tana ƙara lafewa a jikinta. Turab da haushi ya kusa kashewa yace"kinga mum ni na tafi idan ta kammala kukan da ba gaira ba dalili ki ƙara shafa mata wannan" yafaɗa yana nuna mata wani magani "domin Ni bazan iya tsayawa kallon wannan abun haushin ba ɗan wannan ne zatazo tanayiwa mutane irin wannan kururuwa sai kace wacce ake zarewa rai " cewar turab yana haɗa kayan da ya baje na first aid box ɗinsa. "Turab wannan ne bakomai ba, duba kaga yanda hannun baiwar Allah ya zama abun ban tausayi. Kuma kai kazo kana gyara mata ba ko sassauci haka, ai dole yarinya ta yi kururuwa" "Yanzu mum wannan ne zai saka mutum ihu har haka, wallahi ni da badan kinzoba sai hannun nan ya dawo daidai kome zatayi ta daɗe batayiba" Cewar turab yana barin parlourn. Washe gari tun da sassafe leeya ta tashi hannunta duk ta sache da kumburin da tayi sai dai sauran ciwo da yake yimata, kaɗan kaɗan, sosai tayi mamakin wannan domin bata zaci hannun zai sache da wuri haka ba, kuma gashi yau tayi aikin da ta jima batayiba saboda ciwon da hannun ke yimata. Bayan ta kammala gyara bedroom ɗinta ta fita ta gyara parlou, sannan ta shiga kitchen ta haɗa breakfast. "Leeya, wai meyasa bakyajin magana" ta tsinkayi Muryar mum dake tahowa. "Mum barka da safiya" "Leeya, waya sakaki yin wannan uban aiki" "Mum, wannan aikin ne wani aiki harda za'a..." "Harda za'a yi me, jiya jiyan nan fa kika gama kururuwa kamar wacce ake yankawa jiki" Tafin hannunta ta saka ta rufe fuskarta alamar taji kunya kai kace mum ganin ta take. "Wallahi mum shine bai sassautamin ba, daya bini a hankali da bazaki ji ko tari na ba balle nayi ihu" "Ai ba'a bin mai irin ciwon nan a hankali, saboda ciwo ke fitarda ciwo da ba'a yi haka ba da kumburin bazai sache ba, yanzu dai kije ki zauna daining ki jirani khulud ta fito, shima turab ya fito. Duk suna chan zaune kema kije kizauna kihuta kinji" "Haba dai mum, kedai ki barni na ƙarasa ladata kawai dan Allah" "Idan ladace wannan ma da kikayi ai zaki samu ladar kije ki huta Kinji" "Mum, nifa ba gajiya nayiba saboda haka kije kawai dan Allah " Mum tayi tayi ta hanata aikin amma furrrr taƙi kuma ta hana mum ta saka hannuta a aiki. "Mum har kin kammala breakfast ɗin" cewar turab dake zaune a wurin. "Ban kammala ba, leeya ce tace naje zata idar da ladar ta" "Wacece leeya mum? Badai wacce hannun ta ke ciwo ba kho" "Ita wallahi" "Ikon Allah, ba'a taɓa hannunba fa har yanzu duk abunda kikaga munyi jiya, ba gyaran targaɗen akayi ba, maganin kumburi ne aka sakamata. Kuma idan ma zaki tambaye ta har yanzu hannun nayi mata ciwo kawai dai babu kumburin idan kika duba yanzu, amma hannun yana nan da ciwon, kuma idan ta cika yin aiki dashi zai iya janyo wata matsalar daban kuma" "Tau ya za'a yi tunda ta dage sai tayi" "Ke! me kike anan da bazaki tashi kije ki tayata ba" turab ya faɗa yana mayarda kallonsa ga khulud. "ya-Turab wallahi ban iya aikin nan da takeyiba, Nima yimin akeyi" "Kamar ya baki iya ba" Turab ya faɗa da mamaki. "Eh yaya wallahi ban iyaba" khulud ta faɗa a tsorace saboda tasan sarai zai iya aikamata da duka daga inda yake. "Mum, ya akayi aka bari yarinyar nan ta lalace haka, taya kamar khulud za'a ce bata iya aikin gida ba, wanda ya kamata ace itace zata koyawa wasu a yanda take yanzun nan" cewar turab a faɗaceh. "Tukunna ma dai Mum ina ƴar aikin gidan nan?" "Ka tambayi khulud gata nan" Wani irin wawan kallo ya jefamata da sauri tace "Yaya ankoreta" "Kamar ya ankoreta dayammah nake nufi" "Eh, yaya ankoreta tunda jimawa ma yanzu" "Laifin me tayi aka koreta" "Marina tayi" "Mari?" "Eh, shine papu ya koreta". "Ya koreta ko kikasaka ya koreta" mum ta faɗa "Mum, ban fahimci ita ta saka aka koreta ba, kina nufin saboda khulud aka kori dayammah gidan nan?" "Wallahi saboda ita aka koreta" Gigitacciyar tsawa ya daka wa khulud "ki tashi ki shiga kitchen, kicewa yarinyar nan nace ta dawo ki kammala aikin, kuma wallahi idan naga ba daidai ba sai kin yabawa aya zaƙinta" Jiki na rawa khulud ta tashi, ba halin kuka da tayi kukan ko zata rage domin da mum ce ko papu suka mata haka, da tun tuni ta rushe da kuka. "Ke kin kammala" khulud ke tambayar leeyanah "Na kammala da kinyi hakuri ai, da Yanzu ma zan fito" "Ke dallah malama rufewa mutane baki ko angaya miki yunwa ce ta kawoni wurin nan" "Allah ya baki hakuri" shi kawai leeya ta furta ta ɗauki hot water a flask tayi tafiyarta. Khulud kuma ta dauko ragowar kayan ta biyota itama. A daining suka iso kusan lokaci ɗaya, leeya ce kawai tayi sallama, khulud kam ko tari batayiba, tun kafin su ajiye kayan turab ya dakawa leeya Tsawa"ke waya sakaki yin aikin da kikayi" "Ba wanda ya sakani" "Ke kika saka kanki kenan" "Eh, na jima bana aiki da hannun nan ne shiyasa yau danaga ta sauka nace bara na taɓa wani aikin" "Ba wanda ya saka ki kenan, to waya gayamiki hannun ya warke, iya maganin kumburi aka saka masa kuma kinga ya sauka amma ba'a saka maganin targaɗen ba. Saboda haka idan aka gama break fast za'a gyara zaman ƙashin" Haka kawai ta tsinci kanta da faɗin"ya-Turab ai hannun ya warke gaba ɗaya" Murmushin gefen baki yayi cikin wani salo irin nasa yace" okay ya warke ko, ba inda yake miki ciwo" Jijjiga masa kai tayi alamar "eh" Wata wawuyar harara ya ɓalla mata nan take tace"eh, ba inda yake min ciwo yanzu ko ina lapiya Ƙalau nake jinsa" "Okay" cewar turab daidai lokacin da papu ke sakkowa shima Yana ƙarasowa wurin duk suka gaidashi, "lafiya ƙalau, leeya kinji sauƙin hannun naki kho, Jiya nake tambayar mum ɗinku ta gayamin ashe kinyi missing step ne kika yi targaɗe" "Eh wallahi, papu amma ai jiya ya-Turab ya gyaramin targaɗen kuma hannun ya warke gaba ɗaya" leeya ta faɗa tana murmushin yaƙe. Kusa da kujerar da mum take papu ya zauna sannan sai khulud ta zauna kusa da tashi, sai kuma turab dake zaune kusa da khulud, sannan sai leeya dake zaune gefen turab itama. Serving ɗinsu mum tayi gaba ɗaya suka fara cin abincin suna fira jefi-jefi. Papu ne ya fara barin wurin yayinda khulud ta zama ta biyu. Aka bar wurin daga mum, turab da kuma leeya. Bayan haka kuma leeya ta tashi ta bar wajen itama kafin su kammala sannan ta dawo ta haɗa kayan da aka ɓata taje ta wanke. Bedroom ɗin ta ta koma sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito. Mirror sit ta janyo ta zauna sannan ta shafa duk abunda take buƙata ta shafawa jikinta. Ƙarar wayarta taji a can gefe alamar shigowar saƙo. Da sauri ta janyo wayar ta buɗe saƙon domin tasan zohal ce, kuma da ita kaɗai take communicate. gaba ɗaya sim ɗin ma number mutum uku ne haɗi da itane ya zama huɗu. Daga mum, papu sai zohal. Cikin matukar mamaki ta tsaya tana ƙara karanta saƙonda taga an turomata da baƙuwar number. "Amincin Allah ya tabbata gareki sarauniya ta, barkanki da wannan lokacin, ina fata kina cikin ƙoshin lafiya. Allah yasa haka (Ameen thumma), jiya kinyi kyau sosai kuma kunshinshi yaya jaa gwanin ban sha'awa, sai dai naga kamar hannunki daya batada lafiya kho? To Allah ya sauwaqe ya baki lafiya my dream girl nayi missing din zazzakar Muryar nan taki kinj, take care byeee". Ta daɗe tana maimaita karatun saƙon nan kamar mai yin hardan shi, "wayakeda number nan ?" Leeya ta tambayi kanta a zuciyarta. Kiran number tayi saidai abunda ya bata mamaki number a kashe take. Ta kira a ƙalla sau biyar amma abu ɗaya ake gayamata not reachable. Goge sakon tayi taci gaba da aikinta. Kayan ta ta saka material Yard kalar brown mai haske ɗinkin ya karɓi jikinta sosai, tayi ɗaurin da ta sabayi wanda ake kira A'isha Buhari. Sannan ta ɗaura niqab ɗinta ta fita. Bata saka mayafi ba ta fita hakan nan yanda take saboda tasan ba wanda zata tarar a parlourn yanzu. Sakkowa tayi daga kan stairs cikin tafiyar ta ta nutsuwa, a hankali take takawa harta ƙara so daining area, tsayawa tayi chakkk da tafiyarda take sakamakon ƙamshin turarensa data jiyo amma ta kasa tantance inda ƙamshin ke fito. Ci gaba tayi ta tafiyarta kawai domin tana tunanin ko ya fita yayi shiyasa kamshinsa baibar parlourn ba har yanzu. Tana isa daining ta tararda kayan yanda tayi tsammanin ganin su. Haɗa su tayi wuri ɗaya ta ɗauki waɗanda zata iya ɗauka ta nufi kitchen area dasu, dayake bawata tazara bace tsakanin kitchen da daining yasa kayan basu takurawa hannun da yake mata ciwo ba. Mirɗa handle ɗin kofar kitchen ɗin tayi, sai ta saka kafarta ta tura kofar a hankali har ta buɗe iya yanda zata iya wucewa, tana shiga bata isa koina ba sai gaban kitchen sink ta zube kayan ta fara wanke wa, cikin nutsuwa take aikin ta, bata kula da komai sai aikinda take. "Ke, baki iya sallama bane da zaki shigo kamar bakiga mutum ba" cewar turab cikin masifa. Da mugun tsoro ta juya domin batayi tunanin jin muryarsaba kamar a sama taji muryar tasa domin kuwa da darene ba abunda zai hanata guduwa. Muryarta na karkarwa tace"wallahi ya-Turab banganka bane shiyasa, kuma na sha'afa gaba ɗaya na ɗauka nayi sallama ai" Ta faɗa kanta a ƙasa tana saiti da turab dake zaune kan fabric sitter ɗaya jal dake kitchen ɗin. "Ki miƙomin juice a fridge, shinazo na ɗauka dama" Bata furta komai ba ta nufi inda fridge yake ta buɗe "wane kalar juice za'a ɗakko maka" ta faɗa jikinta sanyaye. "Apple juice" ya bata amsa Apple juice ta duba ta ɗakko tare da zuwa gabansa ta ajiye masa, sannan ta dawo ta ɗauki cup shima taje ta kai masa. "Kinfi ƙarfin ki zubamin juice ɗin ne" "Kayi hakuri dan Allah, bara na zuba maka" Robar juice ɗin ta buɗe tare da tsiyaya masa"ya isa ko a ƙara" Ko kallon ta baiyiba yaci gaba da danna wayarsa kamar bai san da ita a wurin ba. "ya-Turab Gashi nan na saka" ta faɗa tana niƙa masa kofin. "Ajiye shi anan" cewarsa yana nuna mata wani ƙaramin tables ɗinda ke gaban fabric sitter ɗin da yake zaune. Hannunta ta miƙa da nufin ta ajiye juice cup ɗinda ta tsiyaya masa, ba zato ba tsammani taji ya riƙo hannun ta daidai inda ke yimata ciwo. A ruɗe ta fara jan hannun iya ƙarfin ta domin tsananin azaba da takeji, amma ina yafi ƙarfinta saboda haka ya fara lankwasa hannun tare da jan hannun iya yanda zai iya. "Dan Allah ya Turab kayi hakuri, wallahi na ɗauka wannan table kake nufin na ajiye maka juice ɗin ka" Baiko kulata ba yaci gaba da aikin sa, wani mai ya fito dashi a aljihun sa. Sannan ya sakkamata hannun ta tare da faɗin "wallahi idan kika kuskura kika fita kitchen ɗin nan, ko kuma naji kukanki wallahi saina ɓata miki rai" ya faɗi maganar kamar dai yanda aka saba fuskar sa ba ko ɗigon Annuri. Dayan hannunta ta saka tare da riƙe bakinta domin ta kasa tsaida kukan da take. Tsawa turab ya daka mata da faɗin"rufemin baki sai rakin tsiya, ɗazu dana tambayeki a daining cemin kikayi hannunki ya warke ai, yanzu meyasa kika kuka, means ƙarya kika min kho?" Turab ya faɗa yana tsureta da idanunsa. "Wallahi Ni banyi tunanin taɓa hannun za'a kuma yiba, kuma ma dalilinda yasa ban gaya maka gaskiya ba banaso na kushe abunda kayi ne saboda idan mutum yayi maka magani kuma ya tambaye ka jikinka, bazaiji daɗi ba idan ka faɗa masa saɓanin waraka" "Angayamiki bansan abunda nake bane, ko kin ɗauka ni sha-sha-shan mai magani ne da bansan abunda nake ba, nagayamiki maganin kumburi na sakamiki ba'a taɓa targaɗen ba, domin da hannun bata kumbura ba iya targaɗen za'a gyara, amma dana tambayeki kika gayamin har targaɗen ya warke. Da tun jiya kin kwantar da hankalinki da anyi komai lapiya angama, Yanzu ma hakane ko ki tsaya ayi lafiya ko karki tsaya sai an gyara, yafimiki ma ki kwantar da hankalinki kiyi dauriya na gyara miki kiyi tafiyarki" Wani irin kwarin zuciya ne yazo mata jin abunda ya faɗa, takeji a ranta ko ya taɓa hannun bazata ji komai ba balle tayi ihu kowani abun daban. "Shikenan ya-Turab ga hannun" ta faɗa tana ƙara miƙa masa hannunta. Maganin ya shafa a hannun nata, kafin ya fara gyara mata targaɗen, leeya kuwa ko tari batayiba saboda ta fahimci idan ka nuna bazaka iya bane yake yimaka yanda yakeso, amma idan ka tsaya shima zai bika a hankali. Saida ya kammala komai da komai tukunna ya fito da wasu tablet sachets kati biyu. "Karɓi waɗan nan kije ki sha biyu yanzun nan, idan akayi la'asar kisha biyu, sannan ki sami wuri ki kwanta ki huta. Domin hannun ma yayi tsami sosai saboda kin jima da buguwa kuma kika ƙi yin magana balle a dubamiki" Karɓar maganin tayi tare da furta"nago.....de...sosai" ta ƙarasa maganar kuka na kwace mata domin harga Allah hannun zogi take yimata, ji take kamar an tsinketa daga jikinta. Taɓe baki turab yayi haɗe da jefa mata wani kallo yana ɗaukar juice ɗinsa tare da barin kitchen ɗin.........✍🏽 BAYAN WUYA....... By RUMANA M DIGGI EP.24 ____________juyawa tayi tare da nufar sink domin ta kammala wanke-wanken da ta fara. Amma inah hannun yana yimata ciwo sosai sai taji gaba ɗaya bazata iya kammala aikin ba. Magungunan da aka bata ta ɗauko tana barin kitchen area ɗin, Bedroom ɗin ta koma kaana ta ɗakko maganin da tazo dashi ta balla ko wanne biyu sannan ta hadiya da Ruwan da tazo dasu. Kan Royal sopa ɗinda da ke bedroom ɗin nata ta zauna taɗan kishin giɗa nan da nan kuwa bacci ya tafi da ita. TURAB. Zaune yake kan bed ɗinshi sai faman bincike yake a system ɗinsa, Daga can gefe kuwa waya ce ke faman ruri alamar kira na shigowa, ɗaukar wayar yayi yana karawa a kunnensa. "Hello, zafaran" Banji abunda ake faɗa daga cikin wayarba amma da alama magana ake yimasa saboda yayi shiru alamar yana sauraren sa kenan. "Okay ba damuwa in sha Allah, zankira fahad na gayamasa, sai mu shirya tafiyar. Yanzu haka ma ina shirin tafiya sati mai zuwa" Har yanzu banajin abunda ake faɗa a wayar amma naji turab yana cewa "zanje Kuwait ne, zanyiwa wasu aiki tun wancan satin suka kirani sakamakon sojawansu da aka harba har wuri huɗu mutum ɗaya ne aka ceto rayuwar sa, su kuma sauran ba wani ci gaba shine suka bibiyi page Dina suka min Magana, wai likitocin Kuwait ɗin sun kasa. Ina ga a kwanan nan zan tafi saboda aikin urgent ne gaskiya idan banje da wuri ba za'a iya rasa wasu daga cikin su" "OKAY tau ba damuwa, idan aka saka tafiyar da wuri dani za'a je in sha Allah, gaskiya wannan lewar ta wahalarmin da abokina", OKAY tau sai anjima. Turab ya faɗa yana ajiye wayar. Cigaba yayi da aikinsa, ji yayi kamar ana knocking din kofa "Yes" ya furta cikin husky voice ɗin sa. "Shigowa khulud tayi ɗakin"ya-Turab mum tace nazo na gyara maka ɗaki" "Saboda ke sha-sha-sha ce kuma ba'a koyamiki sallama ba kho" "Yaya, nayi knocking fa" "To knocking da sallama ɗayane khulud, meyasa kike abu kamar wata ƙaramar yarinya, wai meya ɓataki haka ne, Ni wallahi kuna sakani ciwon kai da yawan magana shiyasa gaba ɗaya bana jin daɗin zama gidan nan, kije yanzu ina aiki anjima ki dawo ki gyara ɗakin" Tun sa'adda ya fara magana khulud ke auna masa harara ta ƙasan idanu, har ya kai ƙarshen Maganarsa tanaji kamar tayita dukansa ko zata cire haushinsa da takeji. "Menene kika tsaya akaina, kuma bayan na faɗa miki ki tafi ina aiki yanzu" "Mtswww" tayi tsakin a ranta tana juyawa tare da barin parlourn. Kansa ya mayar ƙasa yana ci gaba da aikinsa. "Khulud" turab ya kira sunan ta da muryarda yasan zata iya jiyoshi. Dawowa tayi ɗakin a karo na biyu, saidai har yanzu batayi sallama ba, domin ba'a riga aka saba da yin ta ba. "Kije kitchen kiyi wanke-wanke" "Wanke-wanke, kuma" ta faɗa tana yamutse fuska kamar wacce taga kashi. "Sai naga kamar bakyada matsalar kunnuwa ai, da kike bukatar maimaici". "Ina Leeyana take da bazata fito tayi ba, sai ni za'a ce nayi wanke-wanken" "Leeyana bazata yiba ke zakije kiyi" "Itafa ta saba yin wanke-wanken yaya, saboda me za'a ce naje nayi nida gidan mu, alfarmar nu take ci da yanzu tana can tana tsince-tsince a titi da bola" Wata irin mahaukaciyar tsawa ya daka mata da faɗin "na rantse da Allah idan kika bari na kammala aikin nan na fito na tarar bakiyi abun da nace ba wallahi saina baki mamaki, amma idan kina musu karkiyi kiga ikon Allah. Ɓace daga nan" Da gudu ta fita bedroom ɗin tana ta rusar kuka, saida ta zauna main parlor tayi kukanta mai isarta kafin ta tashi ta shiga kitchen. ★ Leeyana. Tunda ta kwanta ko juyawa batayiba har aka kira sallahr azahar, miƙewa tayi domin a yanzu kam har zazzaɓi takeji ba iya ciwon hannu ke damunta ba. Cikin sanyin jiki na marar lafiya ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito, kana ganin tafiyar ta kasan batada lafiya. A daddafe tayi sallah, bayan ta kammala Sallar ko addu'a bata samu tayi ba ta maida kanta ta kwanta a wurin. Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana 2:30pm mum ce zaune a daining Area sai kuma khulud sannan da turab. "Khulud ki tashi kije ki kira leeya, tun ɗazu bangantaba kuma na kira wayanta bata ɗaga ba" Turo baki khulud tayi tana magana ciki-ciki, da sauri ta miƙe tunawa da tayi turab na wurin. Shiga tayi part ɗin tun da ta buɗe kofar ɗakin ta hango ta kwance a kan sallahya taɓe baki tayi kawai ta janyo kofar ta rufe. Komawa tayi daining ba tare da tacewa leeya komai ba. "Mum, leeya batajin yunwa" "Kamar ya bata jin yunwa" "Eh, mum bacci na tarar tanayi" "Shine zakice batajin yunwa, alhali ba ita ta faɗa miki da bakinta ba" "Eh mana mum aiko bata gayamin ba ga alama ta nuna domin mai jin yunwa bayga idon da zaiyi bacci ba" "Je ki tasota" "Haba dai mum taya zanje tasota, haram ne fa. Wallahi bakyau" "Menene ba kyau?" "Tada mutum yana bacci mana, ki barta ta huta dan Allah kinsan fa tana aiki sosai, maybe tayi aikin ne sosai tagaji, bacci fa uzurine babba ko bayan haka, domin wanda yake bacci ba'a yarda a ta dashi ba koda sallah akeyi, sai dai idan ya ji ya tashi da kansa" Baki sake mum ke kallon khulud jin tana wata magana mai kamada wa'azi, shikuwa Turab sai hamdalah yake a zuciyarsa yana gani kamar ta fara shiryuwane, a fuskar sa kuwa ko kallon ta baiyiba ba. Ita kuma mantawa ma take yana wurin. "Ki zauna kici abincin ki, ita kuma idan ta tashi daga baccin sai taci nata" "Okay mum, thank you" khulud ta faɗa tana murmushin kamar wacce akayiwa kyauta. A ranta ma farin ciki take domin leeya nacan na baccinta ita kuma sai faman aiki take, yanzu gata tana cie, leeya kuma na can na bacci da yunwa a ciki. "Anyi one-one kenan" ta furta a zuciyarta tana ci gaba da murmushi. Saida suka kammala cin abincin gaba ɗaya, sannan turab ya miƙe mum "ina so na tafi abuja sai na dawo" "Abuja zakaje kuma" "Eh, zanje abuja nagayawa pa ai, so nake idan naje nayi Booking flight a can saboda gobe nake so nayi tafiyar in sha Allah". "Okay, tau yaushe zaka dawo Abuja" "Yau in sha Allah" "Allah ya tsare hanya, a dawo lafiya" "Amin my lovely mom" "ya-Turab ina zakaje danaji kuna zancen Booking flight". "Ƙasar Kuwait zanje khulud". Ɗan zaro idanu tayi cikin mamaki, daga cikin zuciyarta kuwa farin ciki ne fal domin a gaskiya ya-Turab ya takura mata a Ganin ta. "Yaya har zaka koma dan Allah yaushe-yaushe ka dawo daga Mexico" "Ah ah ba komawa zanyi ba, zanje na duba wasu marasa lafiya ne, bazan wuce sati ɗaya ba, zan dawo ai" Murnar da take ne ta koma ciki domin ba haka taso taji ba "kaje dai ai ko sati ɗaya ma zan ɗan huta" faɗin khulud a cikin ranta. Amma a fili tace: "Allah sarki ya-Turab gaskiya ya kamata ka bari ka huta tukunna, Gaba ɗaya yaushe ka dawo har zaka ƙarayin tafiya mai tsawo haka" "Uhmmm lokacin hutawa yana nan tafe khulud" shikaɗai turab ya faɗa domin ba ko yaushe yakeson yin magana ba. ABUJA. parking space ya nufa yayinda mai gadin gidan ya buɗe masa gate ɗin gidan. "Baba, barka da aiki" "Yawwa Alhaji barkanka, tun dazu yallaɓae ke jiran ƙarasowar ka, yazo nan yakai sau huɗu yana tambaya ko kazo" "Allah sarki Wallahi kuwa sai yanzu nake ƙarasowa baba" turab ya faɗa yana ciro kuɗi a aljihun sa tare da miƙawa mai gadin. Godiya sosai da Addu'a mai gadin yayiwa turab kaana ya shiga cikin gidan. Babban gida ne da ya amsa sunansa gida, domin kuwa kana ganin gidan kasan nera ta koka. Gidane mai sashe daban daban kai kace family house ne, saidai bako tsuntsu kwata kwata ma ba alamar akwai mutane a gidan domin duk sassan da aka raba a rufe suke, ba wata alama da zaka gani kace ana buɗarsu. Wani bangare na gidan turab ya nufa inda shikaɗaine buɗe har ya isa parlour baiji motsin kowa ba. Daga cikin parlour kuma wata hanya ya nufa inda yakeda tabbacin samun wanda yake nema. Wani babban ɗakine wanda akayi gininsa da gilashi, gini ne na turawa kana gani kasan aikin turawane, wanda yake waje ne kawai yake ganin na ciki, amma shi na ciki baya ganin na waje sai idan yazo gab da kofar shiga, to anan ne na wajen baya hango komai da ake yi aciki saidai shi na cikin ya hangoshi. A bangare ɗaya kuma tsakanin kofar da kuma wani ƙaramin ɗaki, an sanya wani bango daya katangesu. a jikin bangon wani ƙatoton frame ne daya kusa kai tsawon mutum. Kyakkyawan zanen wata ƙaramar yarinya ce da bazata wuce shekaru 11 zuwa sha biyu ba. An zana hoton yarinyar a kyakkyawan yanayi cikin kwarewa da basira. Ga kuma wasu ƙananan furanni da aka zana a gaban yarinyar. Su kuma furanni wasu manya da ƙananun butterfly's a ka zana kansu kamar suna kewaya furannin. yarinyar da aka zana kuma ta miƙa hannunta da nufin zata kama butterfly's ɗin da ke zagaya wadan nan furanni. Yarinyar nada yalwataccen gashin kai, wanda ya zuba har bayanta, sai dai kuma ba'a yiwa yarinyar fuska ba iya kai akayimata kawai ba tare da an zana komai a jikin fuskar ta ba. A kasan zanen kuma an rubuta IFUNANYA MY LEWA sai kuma zanen heart my fitinannen kyau. Murmushi kawai turab yake domin ya shagala da kallon zanen a ransa yana fatar Allah ya nuna masa ranar da zafaran zai sadaukar masa da wannan photo, kusan kullum idan yazo gidan saiya yiwa zafaran maganar photon nan amma kuma zafaran ya fishi bukatar sa, saboda hakane yake shashace maganar ya sako wata firar daban domin turab ya daina maganar frame ɗin nan. Yauma kamar kullum bayan Turab ya kammala nazarin photon ya wuce ya shiga ɗakin gilashin nan. ba komai a ciki face kayayyakin zane, kala daban daban, kuma ba zanen da yafi yawai ta kamar zanen wannan yarinyar. Akwai zanukan da sukafi wanda aka liƙa a bangon kofar kyau da tsari da komai, domin kuwa zanen da yake yana tafiya ne da ita kamar yanda take a yanzu. (Ma'ana) duk bayan wata ko shekara yakan daɗa wani abu daya canja a jikinta, kamar dai yana ganinta. A yanzu kuma idan ka gani, bazaka taɓa haɗa hoton ta na dha dana yanzu ba domin ta kara girma gashinta ya ƙara tsayi, gashi yana fito da kowane sharp na jikin da daidai da ita, idan ka ka kalli zanenta na shekaru biyu baya da wanda yake yi yanzu sunada banbanci sosai duba da shekarun da akayi. Saida babban abun mamakin shine gaba ɗayan zanukan halittar yarinyar ba wanda akayi da fuska, kawai dai kai mai kallon zanen ka ƙiyasta yanda fuskar yarinyar take. "Bossman, dama na san zan tarar dakai anan shiyasa banyi tunanin neman ka a ko'ina ba sai a ɗakin lewa" Dariya mai sauti zafaran yayi cikin matukar farin cikin ganin abokinsa ya taso ya rungume shi, kai kace sunyi shekaru basu haɗu ba. "Muje mu zauna kho" zafaran ya faɗa yana jan hannun turab kamar wani ƙaramin yaro har suka isa kan Royal sit. "Zafaran sarkin love, kai bakada aiki banda shigowa ɗakin nan kayita zane zane kho, sai na gayawa leedu aikin da kake yi" "Ai Ni dan gatan leedu ne bazai min komai ba dan ka gayamasa. shima da yake tsoho yasan ta soyayya domin kaga tun sa'adda maamma ta rasu bai ƙara aure ba saboda soyayyar ta na ransa" "Wallahi bakada dama ɗan nan har iyayen namu ma" "Ae gaskiya nake faɗa mutumina iyayen mu ma ai sun fimu iyawa Wallahi, mu zama ƴaƴan zamani kawai muka fi su" "Gskiya kana wulaqanci guy, sai soyayya ta motso maka kuma sai kayita mana kuka kamar mace, yanzu haka ma lewar taka na can......" "Karka ƙarasa man turab banson naji ƙarashen maganar ka, saboda nasan......" "Nima karka ƙarasa" turab ya faɗa yana rufe masa baki da hannayen sa. "Shikenan bazan karasa ba yawwa back to our business, yaushe zamuyi tafiyar zuwa ikeja" "Ina fahad yake?" "Baka ganshi a parlour ba" "Ni banga kowa ba, ko motarsa babu a harabar gidan" cewar turab yana ƙurawa wani zane idanu. "Ikon Allah, to ina ya shiga yanzun nan fa muke tare dashi, zohal ta kirashi a waya, shine ya fita yayi waya. Yanzu fisabilillah ace duk faɗin gidan nan bazai yiwa fahad waya ba" cewar zafaran da mamaki. "Kai manta kawai bara na kirashi" "Okay, to kirashi yazo mu ajiye magana tun yanzu" Wayarsa ya fiddo daga aljihunsa yayi da Dialing number Fahad ringing ɗaya ya daga wayar "hello mutumina kana inane tun ɗazu muna jiranka kaƙi ka karaso" "Ehh, wani abun ya tsayardani kana ina haka?" "Ina nan gida, gamu munata zane nida zafaran idan ya kammala zana hoton lewar sa, nikuma yaban in zana hoton my zohal" "Okay kana tare da zafaran ɗin kenan yanzu haka" turab ya faɗa Daga cikin wayar kuwa fahad yace; "Eh mana gamu nan tare dashi, gashi nan ma sai murmushi yake maka" "Da gaske mutumina, bashi waya na gayamasa bazan samu fitowa ba" "Ahhh, haba dai mezai hanaka fitowa" "Ka bashi wayar mana" "Dani da zafaran duk dayane gayamin kawai, kaga yana nan yana min alamar da cewa a gayamin in gayamasa" "Aww, da gaske" cewar turab dariya naso ta kwace masa, ganin yanda fahad ya zage yana sheka karya son ransa. Zafaran kam daya kasa jurewa sai da ya dara, fahad na jin dariyar zafaran ya tabbatar turab na gidan, nan da nan ya tsinke wayar yaci gaba da dariyarsa, domin shima ya bawa kansa dariya irin wannan ƙarya haka. "Zafaran kaji abunda mutuminka yace kho" "Naji man turab, kamar ina wurin ai, naso naga fuskar man fahad yana ƙarya" "Kaiiiiiiiyyyyy, ai Nima naso nagani wallahi, yawwa zafaran nikam na tambayeka mana" "Eh, Allah yasa nasani" "Nikam lewarka batada fuska ne" "Tanada fuska mana, amma ba wacce kowa ke gani ba" "Kana nufin har a zanenta idan kayi kana jin kishi idan an kalleta" "Eh toh, idan ma nace haka ba ƙarya gaskiya" Taɓe baki turab yayi yana faɗin"to Allah ya kyauta" "Amin man turab" Turo ƙofar dakin da suke akayi, a hankali yake tafiya ya kara waya a kunnensa sai faman washe baki yake da alama soyayyar sa yake sha. "Okay babe bye bye, tek care please sai anjima idan mun kammala maganar zan kiraki Kinji my little gurl" Fahad yayi maganar yana sumbatar wayar bayan ya gama maganar da yake. "Barkan ku dai ranku-shidaɗe" "Man fahad ka sami shigowa kenan, wai ina kaje ne" cewar zafaran yana haɗa instruments ɗinsa. "Naje shan iska ne, mutumina ba magana kuma" fahad ya faɗa yana bugo turab a kafaɗa. "Mr. Lauya ansamu shigowa kenan" "Eh nasamu shigowa mutumina, tun da muka dawo da suleja banje gida ba ai a nan nake hutun da na ɗiba. Amma ina saka ran idan zaka tashi zan bika domin geembeeyerh ta na buƙatar ganina" "Ka matsa dai wannan zohal ta haukataka Fahad". "Yoooh, hauka ta nawa kuma man Zafaran. aini na daɗe da yin hauka kan soyayyar zohal, amma kuma kai idan ba'a ce ka haukace a soyayyar lewa ba kai zakacewa wani ya haukace ne" "To kun fara kho, Ni Bara na tashi na baku wuri tunda abun na masu masoya ne" turab ya faɗa yana miƙewa. Saurin riƙoshi zafaran yayi "meye haka man, ina zakaje kuma, ai kabar fahad kawai ai shikadai ne ba Gwauro ba a cikin mu narabina da IFUNANYA shekara bakwai zuwa takwas fa to kaga ni dakai duk ɗaya ne kenan".................✍🏽 BAYAN WUYA...... By RUMANA M DIGGI EP.25 _____________"Tau ai gwanda kai ma kataɓa yin soyayyar ko man Zafaran, ka ganni nan randa nake ban taɓa sanin meye soyayya ba wallahi" "Ai Nima ban taɓa yin soyayya ba wallahi, lewa ce kaɗai a raina kuma da ita zan zauna in sha Allah" "Kaiiiiiiiyyyyy, zafaran cewa kayi baka soyayya?, kuma baka taɓa yiba, ina nooriyyah" cewar fahad yana hararar Zafaran. "noory ba budurwa ta bace course mate ɗinace kawai, kuma muna mutunci sosai da ita, kuma itama tasan da labarin IFUNANYA, kaga kuwa ba yanda za'a yi muyi soyayya. Ko akwai yanda za'a yi ni ba macen da nakeda ra'ayi da buri face lewa kuma ita zan aura da yardar rabbi" "Hummm, nikam suna nan tuli-tuli ko a BHOPAL ma jira kawai ake nazo a haɗani da wata ƙanwata GURZAH amma ba musulma bace" Zaro ido turab da zafaran sukayi cikin mamaki suka kalli fahad kamar gamin baki sukace"ZOHAL fa?" Dariya suka bashi sosai har saida yayi mai isarsa tukunna sannan yace "gurzah ƴar uwa ce kawai zohal kuma matar aurece kowa da sunanshi ai, kuma kowa da matsayin sa" "Ba suna muka tambayeka ba, ya zakayi da ita muke nufi" cewar Zafaran. "Ya zanyi da ita?, to aurenta zanyi mana" Da sauri suka maimaita faɗin"gurzah fa" "Yar uwatace kawai, kuma Ni ba sonta nake ba. Niyyarda nake idan bansamu matar da nakesoba, sai naje na taimaka mata ta shiga musulunci na Aureta, amma tunda Allah ya kawo zohal kunga ai komai yayi fyn". "Hakane kam, yanzu dai mu koma maganar da ta taramu a wurin nan, ya batun tafiyar tamu ne?" Turab ya faɗa yana mayarda hankalin sa gaba ɗaya kansu. Tattaunawa suka farayi yanda tafiyar tasu zata kasance, har aka tsayarda ita a gobe, domin shima turab tafiya zaiyi kasar Kuwait shiyasa ba'a saka tafiyar da nisa ba. Duk da shima a goben yayi niyar tafiya, amma sai ya ɗaga tafiyar tasa saboda uzurin abokinsa. "Shikenan ba damuwa, Allah ya nuna mana goben" "Ameen man turab, yanzu ku tashi muje restaurant mu ci abinci kho, daga nan kuma sai muje azmafat air transport muyi Booking flight tun da wuri" "Mai yasa sai AZMAFAT TRANSPORT" fahad ya tambaya "sune kaɗai jirgin ikeja zai tashi 9:15am, amma duk inda aka bincika tafiyar ta yammace" "Well muje a can kawai, man fahad bara muje azmafat ɗin kawai ko dan ni Please kaga nima tafiyar zanyi, inaso muje da wuri muyi abunda zamuyi mu dawo da wuri, domin nima na ida kimtsa wa" "Ok no wonder, ba wani abubane fa, kawai dai na tambaya ne naga wurin ba kowa ya sanshi sosai ba shiyasa nayi maganar, muje kho". Tare suka jera suna fitowa ɗakin, daidai wurin kyakkyawan zanen yarinyar turab ya tsaya yana shafa zanen tare da yin murmushi, "man Zafaran yaushe zaka ban wannan frame" "Ranar da ya zamo mallakin ka" "Taya zai zama mallakina bayan bakada niyyar mallakamin shi" "Bani bane banada niyyah kawai lokacine bai yiba, lokacin nayi kuma zan baka, karka damu" faɗin zafaran yana bubbuga kafaɗar turab a hankali, domin hakan ya zamar musu ɗabi'ah su duka ukkun idan suna wata magana mai muhimmanci. "Shikenan muje kar mu ɓata lokaci kho" Fahad ne yakai dubansa ga zafaran"bossman yaushe zakaymin zanen little gurl ɗina" "Wacece kuma little gurl, ka sake wata bayan zohal ne" "Wane Ni, har na isa nayi wata kuma ai idan kaji ana faɗin final choice to zohal ce, nikam ita ce karshen zaɓina" "Zane kam bakada matsala karka damu duk sa'adda ka tashi ka gayamin kawai" "Ai dole ne na gayamaka tunda kai zakayi, yadai mutumina shiru kakeji, baka magana ko ka shiga tension ne" "Tension kuma hala nine kai" cewar turab Haka dai suka ci gaba da firarsu cikin nishaɗi yanda dai suka saba, turab ne mara son surutu sosai duk a cikin su, domin wani lokacin ma idan suna tare zai iya shafe wunin baiyi magana sau biyu ba a firarsu. SULEJA NIGERIA. K. WAASIB MANSON. Misalin ƙarfe shida na yamma 6pm. Har a wannan lokacin leeya na kwance ko motsin kirki bata iya yi saboda yanda zazzaɓin yaci karfin ta. A hankali take buɗe idanun ta domin karar shigowar sakkoni da ake turowa duk bayan wasu mintuna. Hannu ta saka ɗan nesa da ita ta janyo wayar ta sakata flight mode ko duba sakonnin batayi ba balle tasan waye. Har kuma a lokacin batayi sallar la'asar ba domin yanda takejin jikin nata ba daɗi, ga kuma azababben ciwon kai dake cinta idan ta miƙe tsaye tanaji kanta kamar ya rabe biyu saboda tsananin azabar ciwo. A bangaren mum, kuma har lokacin bataji motsin leeya ba kuma idan ta aika khulud sai ta ce mata tana bacci har a wannan lokacin. Itama mum da kanta sau biyu tana zuwa dakin amma sai ta tararda ita tana bacci. "Khulud kije ki duba leeya ta tashi kuwa, idan bata tashi ba kizo ki gayamin domin nasan ba lafiyaba indai har yanzu bata tashi ba" "Okay mum bara naje na duba miki ita" Kitchen khulud ta shiga ta ɗakko ruwa masu sanyi sosai, ta nufi ɗakin leeya. Da mugun ƙarfi ta banko kofar tana isa inda leeya ke kwance ta sheƙa mata ruwan da ke hannunta. Wani wahalallen numfashi leeya ta sake, tare da sakin kuka mai ban tausayi. "Tashi baƙar munafuka kinzo kin samu wuri tun ɗazu kin wani kwanta kamar gidan ubanki, ko Ni dayake gidan mu ban kwanta nayi yanda kikayi b......" Tun kafin khulud ta rufe bakinta taji an wanke ta da maruka har biyu, cikin matukar zafin rai turab ke magana. "Khulud yaushe kika zama haka, tambayarki nake yaushe kika zama haka, ashe bakida tausayi, kinsan wannan yarinyar batada lafiya, amma zakizo saboda rashin tausayi da bushashshiyar zuciya irin taki, zakizo ki jiƙata da ruwa. Ko mutum mai lafiya aka zubawa ruwan nan zaiji daɗi balle ita da kina ganinta kinsan batada lafiya" "Wallahi ya-Turab lafiya ƙalau take, munafunci ne kawai irin nata, shine akanta zaka dakeni kho ya Turab, ita da bakowa ba bakuma kowan kowa ba almajira, ƴar bola, ƴar tsintuwa, ƴar talakawa, duk ta kai matsayinda zaka dakeni akanta" cewar khulud cikin kuka. Wasu marukan biyu ya ƙara wanketa da su a wannan karon kam harda bugu. sosai ta kuma na fitar hayyacinta, miƙewa leeya tayi cikin ƙarfin hali tana takowa gabansa. Wata uwar tsawa ya daka mata saida ta ruɗe"wallahi kina ƙaraso sai na haɗa dake, wahalliyar yarinya kawai, Ni da nine ke ko yankata za'a yi bazan kalli wurinda take balle nazo kwatarta" A ƙiɗime mum ta shigo ɗakin tayi kansu tare da shiga tsakanin su, Khulud kuwa tana ganin mum ta shigo ɗakin tayi sauri ta koma bayanta tare da sakin wani irin kuka. "Turab meye haka, me khulud tayi maka data cancanci wannan duka" "Bani tayiwa ba" cewar turab yana nuna leeya data rakuɓe gefe ɗaya sai rawar ɗari take. Da sauri mum ta ƙarasa gareta, cikin tashin hankali tace "innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, leeyana meyasameki haka, turab meyake damunta, duba kaga yanda jikinta ya kumbura baki ɗaya gashi kuma duk kalar fatarta ta canja" "Nina bata magani mum, amma bata shashi a ƙa'ida ba, shine yayi mata haka, inaga overdrogs tayi kuma ba'ayin overdrogs a magungunan da na bata, musamman wanda jininsu bayada ƙarfi. Kuma itama da alama jinin nata ba karfi ne dashiba, amma ki kwantar da hankalinka wannan ba wata babbar matsala bace yanzu dai tana buƙatar drip gaskiya kuma sai an an saka mata su da wasu magungunan daban banda waɗan nan, bara naje na dakko kayan aikin. Wallahi sauri ma nake munzo na dauƙi kayanda zan buƙatane gobe ikeja zamuje tare da zafaran da Fahad kuma morning flight zamubi shiyasa nakeso na kwana abuja" "Yanzu dai ba wannan ba, Dan Allah kayi sauri ka taimakawa wannan yarinyar" "In Allah ya yarda kuwa" ya faɗa tare da barin ɗakin. "Mum yanzu shikenan kun daina ra'ayina a cikin gidan nan, duba kiga yanda ya-Turab ya dakeni a banza kamar wata mara gata, wallahi idan papu ya dawo saina faɗa masa tunda ke bazaki iya yiwa ɗan ki magana ya fita harakata ba a gidan" "Kiyi haƙuri Kinji khulud, bawai ra'ayin ki ne bamayiba. Halin kine bana ra'ayi kuma kin kasa changer wa, yanzu ki duba kiga yanda jikin baiwar Allahn nan ya dawo duk da bansan me kika yimata ba nasan turab bazai dakeki haka kawai ba" "Wallahi mum nifa ba wani abu na mata ba, ke kika aikoni nazo na tada ita, kuma tun kan ki aikoni inada ruwan sanyi a hannuna shine na shigo bankula ba santsi ya kwashe ni ruwan ya zubemata a jiki. Kuma fa na bata hakuri amma Ya Turab na zuwa ya rufeni da duka kawai baimasan meye mafarin ba" "Tau kiyi hakuri Kinji, in sha Allah zanyi masa magana kar ya ƙara shiga lamarin ki a gidan nan" "Is better for you mum" khulud ta faɗa tana barin ɗakin. Turab bai wani dauki lokaci ba ya dawo ɗakin da duk kayayyakin da zai buƙata. Leeya kam har bacci ma ya fara ɗaukarta, domin shikaɗai ne abunda zatayi taji sauƙi a wannan lokacin. "Basai kin tayarda ita ba mum zan saka matane kawai sai in tafi idan drip ɗin ya ƙare sai a cire mata ko kuma idan papu ya dawo ya cire mata" "Tau Allah yasa ayi dace" "Ameen mum, amma na gayamiki wannan ba komai bane in Sha Allah idan aka saka mata drip ɗin nan shikenan angama da matsalar, magungunan ne kawai basu karɓi jikinta ba, amma zaki gani kuma zata wartsake bada jimawa ba" "Allah ya yarda" Daga haka mum bata ƙara faɗin komai ba har turab ya kammala abunda zaiyi ya tafi. Mum ta zauna da leeya ko'ina bata ɗaga ba ko nan da can, kuma ta kira papu ta sanardashi abunda ke faruwa. Shima ya tausayawa leeya sosai kuma yayi mamakin wannan al'amari ace daga shan magani jikin mutum ya kumbura kuma kalar fatarsa ta canja. ★ Turab na fita daga gidan yayi dialing number Zafaran domin duk tare suka taho, saidai shi zafaran ya raka Fahad gidan su zohal kafin turab ya kammala abunda zaiyi a gida. "Hello zafaran kuna ina ne haka" Daga cikin wayar kuma zafaran yace" kafito kawai a first Street na arear ku zamuzo mu dauke ka" "Ok hurry up please karku barni pending" "Ahh, mun isa mubar likita bokan Turai a titi yana jiran mu, wane mu, kaidai ka fito kawai" "Okay ai nakusa na ƙaraso ma" Katse wayar akayi da faɗin "shikenan sai ka ƙaraso ɗin" Ba wani jimawa turab ya iso wurin, saidai abun mamaki koda ya iso ya tararda motar su a packed an ajiye ana jiransa ya ƙaraso. "Har kun iso" turab ya tambaya yana buɗe kofar motar. "Me zamu jira to, mun iso kai kaɗai ka tsayardamu ai amma mun jima a wurin nan ko zafaran" cewar fahad. "Ae nasan kunjima anan professional lie-man" "Ni kake kira professional lie-man, Wallahi kuwa sai zohal taji wannan. Kuma sai ta ɗaukar min mataki" "Idan zohal ta ɗaukar maka mataki, nikuma zan saka lewar mu ta ɗaukarmin mataki kan ka harma zohal ɗin" Sai a lokacin zafaran ya shiga maganar tasu shima jin an ambaci rabin ransa. yana amsa maganar tasu jefi-jefi. Washe gari kuwa tunda sassafe suka yi shirin tafiya, bawani dogon shiri sukayiba domin a ranar zasu dawo. Tafiyar awa huɗu sukayi, kafin su isa inda zasuje. Suna sauka kuwa. Basu zarce ko ina ba sai arean da yasan lewarsa take, unguwar da yake gani kamar itace sillar komai, unguwar da aka kashe iyayen leewa, unguwar da aka salwantar da ita, unguwar da Yana shigowa cikinta da yaga komai ya dawo masa sabo. Wasu zafafan hawayene suka gangaro a kwayar idanun sa yayinda ya ƙurawa wani wuri can nesa dasu idanu. Mai jirgin kwale-kwale ya kira ya shiga dasu cikin Area. Wani gida suka nufa bayan mai kwale-kwalen ya ajiye su, Zafaran ne gaba sannan sai fahad sai kuma turab. daya kasance bayansu gaba ɗaya. Sallama sukayi baki ɗayansu duk da sunsan abune mawuyaci su sami wanda zai amsa sallamar. Domin ba gidan musulmai suka shigo ba. Matan gidan su biyune sai kuma ƴaƴansu da bansan adadin su ba duk dai suna zaune a tsakar gidan nasu. Mamaki kwance a fuskar mutanen gidan ganin baƙin larabawa da indiyawa a gidansu. Zafaran ne ya matsa sosai kusa dasu, yayin da turab da fahad ke tsaya daga farkon gidan. "Barkan ku da wannan lokacin" zafaran ya faɗa da yaren da yasan masu gidan zasuji, kuma shine asalin yaren da zafaran yakeji sosai kafin hausa, saidai shi musulmi ne bakamar mutanen gidan ba. "Wata matashiyar yarinya da bazata wuce shekaru goma sha bakwai ba, ta amsa masa da faɗin" barkanka dai wakake nema" "Mai gidan nan nake nema" "Bayanan amma baiyi nisa ba, jira kaɗan a aika yaro ya kirashi" "Okay Nagode" amma duk wannan da suke Fahad da turab basa fahimtar komai saboda ba hausa suke ba kuma ba turanci ba. Kallonta ta mayar kan Fahad da turab tace a cikin Yaren ta. "Ku shigo ciki ga shimfida ku zauna" Kallon juna turab da fahad suka farayi, domin ba wanda yaji abunda tace. Kallonta ta mayar kan Zafaran ta kuma fadi da yarenta domin batajin hausa ko kadan " basajin abunda nake cewa ne?" "Eh, suba yaren mu bane. Su hausawa ne kawai" "Okay nagane, to ba damuwa ka gayamusu da yarensu, kace masu ga wurin zama". "Guys wai kuzo ku zauna akace" Shigowa sukayi cikin gidan suna nufar inda akayi masu shimfida. "Masha Allah, wallahi kamar sun san a gajiye nake ina neman wurin zama" cewar FAHAD. "Tau ai gashi ka samu yanzu kho" "Eh, nasamu mana, amma ga alama ba gajiya a tattare da man turab domin naga ko magana bayayi" "bakasan idan gajiya tayi yawa tana saka mutum ya kasa magana ba" Fahad na shirin yin magana sai ga mai gidan yazo. Miƙewa sukayi gaba ɗayansu tun kafin ya karaso suka durƙusa tare da gaida shi, duk da sunsan ba Musulmi bane amma hakan bai hanasu yin ɗa'ah ba. Zafaran ne kawai yayi magana domin shi kaɗai yasan abunda zai cewa mutumin da yarensa. "Muje ga shimfida can ku zauna sai inji abun da ke tafe daku" cewar dattijon. Miƙewa sukayi gaba ɗaya suka koma kan shimfida suka zauna. Shi kuma aka miƙo masa kujera ƴar tsuguno ya zauna. "Amma kamar ban wayeku ba kho" "Eh gaskiya baka wayemu ba, muma haka" "Meya kawo nan, naga kamar ku ba ƴan nan bane, kuma naji mamaki sosai danaji kana yin yarenda mukeyi. Ƴan uwanka basa magana ne" "Munzo muyi tambaya ne, kuma ni da ka ganni yare ɗaya nake dakai, saidai Ni Musulmi ne. Kuma ƴan uwana sunayin magana saidai basajin yaren nan, abunda kuma ya hana nayi maka magana da hausa nasan yanada wuya ace kanajin Hausa" "Eh, hakane kam gaskiya, to tambaya akan menene, fatar dai nasani kuma zan iya bayarda amsa" "Muma muna fatar kasani ɗin" "Mecece tambayar taku" dattijon ya tambaya cikin yarensu. "Baba dan Allah ina tambayar wani mutum ne da ake kira ADEBAYO SHOLA" Gyaran murya kaɗan datijjon yayi kafin yace"bansan Adebayo shola ba, amma kuma nasanshi ta labarai da ake bada wa a unguwar nan tamu. Hasali ma nan ne gidan sa daya taɓa rayuwa" "Eh, hakane nan ne gidan sa daya taɓayin rayuwa, wannan shine ma babban dalilin da yasa ina shigowa arean nan na fara shigowa gidan nan domin nasan anan zan sami cikakken labarin abunda ya faru dashi, shekaru bakwai baya" Cikin mamaki dattijon ya kalleshi da faɗin "kai kuwa yaro ina ka shiga tsawon wannan lokaci, sai a yanzu da aka fara mantawa zaka fito kace kana neman labarin sa" "A can baya da daɗewa munyi zama a garin nan sai saidai ba'a wannan bangaren muke ba, ADEBAYO SHOLA ƙanin mahaifiyatane sosai. Canjin wurin aiki da aka yiwa mahaifina yasa muka bar garin nan muka koma Abuja da zama, sosai muna jin labarin su, domin suna kiran mu a waya muma muna kiransu ana sada zumunta. Kwatsam rana ɗaya sai muka wayi gari da labarin cewa anzo an tarwatsa wannan area. Kuma ba'a samu mutum ko ɗaya daya rage mai numfashi ba a wannan area. Labarin ya girgizamu sosai matuƙa musamman ma Ni, domin kuwa harda matata da zan aura, muna cikin jimamin wannan halin ne kuma aka sake yiwa mahaifina canjin matsayi ya koma da yin aikinsa a ƙasashen ƙetare. Duk muka koma can da nufin idan komai ya lafa sai mu dawo mu cigaba da bincike ko Allah zai sa a gano inda wasu daga cikin su suke, domin a zahirin gaskiya waɗan da suka bada rahoto suka ce akwai wasu mutanen da aka gudu dasu saidai ba'a asan inda aka nufa dasu ba. Hukumomi da dama sun shiga binkicen, da muka koma can ƙasar las-vagers kuma sai naci gaba da karatuna a can. Dama mahaifiyata ke ƙarfafamin gwiwa kan wannan lamarin na ɓatar matata da zan aura, to itama bamu jima da komawa las-vagers ba ta rasu bayan ƴar guntuwar jinya da tayi. Daga nan mahaifina ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗoramin kuma baya barina na ɗaga ko nan da can, sai da na kammala karatuna gaba ɗaya, bayan haduwar mu da bawan Allahn nan" zafaran ya faɗa yana nuna turab. shikuma turab bai masan wainarda ake toyawa ba "sai haɗuwar mu dashi ne mahaifina ya aminta na biyoshi muzo Nigeria bayan dogon sharaɗi daya ɗaɗa mana. To kaji ainihin cikkaken labarina kan wannan lamarin da kuma buƙatata agareka................✍🏽 BAYAN WUYA....... By RUMANA M DIGGI EP.26 ______________"naji labarin ka yaro, kuma zan baka kaɗan daga abunda nasani game da wannan batun amma bana tunanin za'a iya samun Adebayo shola a raye, saidai baza'a fitarda ran samun matar da zaka aura ba saboda basu kashe mata da ƙananan yara ba. Amma babban abun lura anan shine ba'a san ina za'a fara neman suba tunda kaga abun ba jiya bane ba kuma yau ba magana ce da aƙalla shekaru bakwai" "Hakane Ameobi, (ma'ana baba) a yaren hausa, Nima wannan abun nake tunawa naji zuciyata ta karaya amma a kullum ina ƙara ƙarfafawa kaina" Nan datijjon ya kwashe labarin da yasani gaba ɗaya ya faɗa masa. kamar dai yanda ya samu labarin a bakin Muhsin idan baku manta ba. "Shikenan Ameobi munji abunda kace kuma muna godiya sosai, in Allah ya yarda zanci gaba da bincike idan rabona ce zan sameta, komai wahala da rintsi da wuya idan lewa mata tace zan sameta" "Hakane ayi ta addu'a kuma kacigaba da hakuri kaji, Bara na kira a kawomuku ruwa kusamu kusha" datijjon yayi maganar yana kallon ƙofar ɗakunan biyu jal dake gidan. "Ah ah mun gode sosai wallahi, ai Bama sai an kawo mana ruwa ba yanzu tashi zamuyi mu koma kuma, saidai wata rana" zafaran ya faɗa yana miƙewa, ganin ya miƙe ne ya saka su turab suka miƙe baki ɗaya. Hannu zafaran ya saka a aljihun sa ya fito da ɗaurin kuɗi ya miƙawa datijjon tare da daɗa yimasa godia. Sosai datijjon yaji daɗi kuma yayita yimasa addu'a irin tasu, da fatar nasara. Haka Zafaran da turab da kuma fahad suka bar gidan zuciyar zafaran ba daɗi. "Man Zafaran, baka bamu labarin abunda kuka tattauna da wancan datijjon ba, duk da kasan Bama jin abunda kuke faɗa". "Kuyi hakuri mutanena, haƙika ba wani abu daya sauya a labarin da muhsin ya bani, amma a yanzu bazan iya cemuku komai ba. Ku bari mukoma gida kawai" Dayake basa son su takuramasa duba da halin da yake ciki yasa suka nuna masa ba komai a bari har a je gidan ya nutsu sai ya basu labarin abunda ake ciki. Komawa sukayi filin jirgin da suka sauka suka jira next flight ɗinda zai koma Abuja da yamma. ★★★★ BAYAN SHEKARA ƊAYA........FARIN CIKI, BAƘIN CIKI, SOYAYYA, SHAƘUWA, SHIRIYA, NADAMA HAƊE DA KUNYA, BAYYANAR ƁOYAYYEN AL'AMARI, SADAUKARWA, CIN AMANA, TARE DA BAYYANAR AHALI. A shekara ɗaya data gabata abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda soyayya mai ƙarfi tsakanin FAHAD GAHEES WAASIB da kuma ZOHAL KHALIL GIRAH. Tsaftatacciyar SOYAYYA suke a tsakanin su, wanda sukeji tamkar su haɗiye junan su. Babban FARIN CIKIN da wannan ahali suke ciki kuwa shine nemarwa fahad auren zohal da akayi har ma an saka rana nan da wata huɗu masu zuwa. Babban abin BAƘIN CIKIN da ahalin gahees waasib suke ciki kuwa, a asibitin da suka kai Rukhshanah can BHOPAL INDIA an tabbatar musu da bazata warke daga cutar da ke damunta a ƙwaƙwalwar ba, saidai zata iya samun sauki ne idan taga abunda ta taɓa sani gabanin cutar ta sameta. Likitocin sun tabbatar musu da cewa idan har suka bi sharaɗin maganin nan, za'a sami waraka ko kuma akasin ta domin maganin bayada tabbatacciyar magana ɗaya, sauƙi ko kuma akasinsa. Domin ba ko wane mai cutar ƙwaƙwalwa ake bawa wannan maganin yayi amfani dashi ba, sai wanda yayi nisa sosai, ita kuwa Rukhsha za'a iya sakata sahun mutane masu irin cutar nan da suka yi nisa sosai, domin duk yanda akayi kanta ko kuma wani bangare na kanta ya bugu sosai har ya haifar mata da matsala a cikin kwakwalwar ta. A bangaren ɗaya kuwa, khulud k. Waasib tayi graduation ta kammala karatun ta na secondary a BUSY BRAIN INTERNATIONAL, kuma ta sami good grades saboda mahaifinta nada abun hannunsa. Kuma aka samamata admission a ROONEY COLLEGE OF SCIENCE AND INNOVATION SULEJA. inda zata fara karatun nursing nan bada jimawa ba. Leeya kuma aka sama mata CATERING SCHOOL inda takeda burin zuwa taci gaba da koyon girke girkenta. Turab kuwa ya shahara ya goge, ya zama zakaran gwajin dafi a ƙasashen ƙetare, domin kuwa yana aikinsa cikin ƙwarewa. Ga sanin makamar aiki, domin har ɗaukan shi anayi aje dashi wurin yaƙi komai wuya da rintsi kuma zai jure, idan aka tafi dashi yakin kuma baza'a barshi a baya ba domin idan ka ganshi ma zakace shine sojan bawai likitan suba. Bangaren aikin sa kuma komai raunin da soja ya samu, ko karaya, ko kuma yawan harbi to yana koƙari kuma da addu'a nan take ake warkewa idan yayi aiki, shiyasa suke bala'in ji dashi, a wata ɗaya sai yayi tafiya aƙalla bakwai ko takwas daga ƙasa zuwa ƙasa yaje yayi musu aiki ya dawo, kuma bazai barsu ba har sai yaga wanda yayi wa aiki ya miƙe da kanshi. Saidai matsalar da turab ke fuskanta a gida, anyi masa tsayin daka kan dole sai ya fito da wacce yakeso a haɗasu su biyu a cikin waasib family wato shi da fahad ayi musu aure lokaci ɗaya. "Turab mun riga mun gama magana nida justice idan har Allah ya Mayar da shi lafiya daga tafiyar da yayi, zaije ya sami auntyn ku Rahma a nema maka auren ikram ƙanwarka" Cikin zallar tsorata da abunda mum ta faɗa muryarsa har tana sarƙewa yace"What!?, me kike faɗa haka mum nine zan auri ikram" Ya faɗa yana nuna kansa da yatsa"wallahi mum kar ma ku soma wannan don wallahi ni bazan aure taba". "Shikenan idan bazaka auri ikram ba, wannan ba wani abu bane dama bamu riga mukayi wa Rahma magana ba balle ka kunya tardamu, kaje gidan dadyn ku gahees kayi magana da mayah domin ita fannah tanada wanda takeso" "Mayah kuma mum, sa'ar khulud ce fa. Mezanyi da mayah gaba ɗaya mayah bata cikin irin tsarin matar da nakeso na aura sam, saboda haka a ajiye maganar mayah" Murmushi irin na wacce tasan abunda take mum tayi kaana ta ɗora da faɗin, anjima ka shirya kaje dalah Street gidan hajiya Balaraba kayi magana da raudha itama ta isa aure ai" Murmushin takaici turab yayi yana tare da cije gefen lips ɗinsa, "mum banason raudha, finally ni ban tashi aure ba, saboda duk ƴan matan da kika lissafamin har ma da waɗanda ke zuciyar ki, da waɗanda kika faɗa da Waɗan baki faɗa ba duk basa cikin tsarina, infact ma mum ni tun dawowa ta Nigeria har yau ban taɓa ganin yarinyarda ta birgeni ba ko inji sha'awar zama da ita matsayin matar aure, saboda haka ki ajiye maganar aure gaba daya beside, ni banada buƙata gaskiya" "Wannan kuma baka isa ba turab, ya zama dole ka fitarda mata kayi aure idan kuma ba haka ba mu zuba dani dakai shege ka fasa, kana gani a gidan nan za'a shigo da mata a matsayin wacce muka aura maka, tun wuri ma kasan abunyi kuma dole sai ka zaɓi ɗaya daga cikin matan da na lissafa maka, shashasha kawai mara tunani" mum ta fada cikin tsananin ɓacin rai ta baro masa part ɗinsa. Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara turab ya dunkule hannun sa na hagu yakaiwa bangon ɗakin wawan naushi har saida yayi hakan sau uku kafin ya koma ya jingina da bango, ya furzarda iska mai zafi daga cikin bakinsa. Idanunsa kuwa sun kaɗa sunyi jajir kamar garwashi saboda ɓacin rai. Domin kuwa kalaman mum na ƙarshe sunyi matukar ƙona masa rai. Fita yayi daga ɗakin, ba abunda ke yi masa daɗi a yanzu, hanyar garden ɗin sa ya nufa saboda a can kaɗai zai iya zuwa ya zauna hankalinsa ya kwanta a halinda yake ciki yanzu. Tunda ya shigo wurin ya kejin ƙarar sautin piano na tashi daga can inda yake ajiye kayan kiɗansa. Nan take ransa ya kuma yin baki ƙirin, duk tafiyar da yake da saurin da yakeyi sai yakeji kamar ana mayardashi baya ne domin gani ma yake wurin na ƙara yimasa nisa. A ransa kuma yana auna irin dukanda zaiyiwa khulud "da alamu jikinta ƙaiƙayi yake yimata shiyasa har ta shigo wurin nan kuma ta rasa inda zata je ta zauna sai........" Maganar ce ta maƙalemasa sakamakon arba da yayi da leeyana a wurin zaune. Razananniyar tsawa ya daka mata muryarsa har tana crack saboda ɓacin rai, "me ya kawoki a wurin nan, kuma ya akayi kikasan da wannan wurin a cikin gidan nan gayamin ko nayi miki dukan tsiya anan ba wanda kika gani balle ya kwace ki a hannuna wallahi" "Wayyo Allah, na shiga uku dan Allah ya-Turab kayi hakuri, wallahi kaddara ce tasa na shigo nan Ni ban masan kana nan ba wallahi da bazan shigo ba" leeya ta faɗa tana shirin rushe wa da kuka. "Wallahi idan kika sake kika min kuka saina ɓaɓɓalaki, me aka yimiki da har zakiyi kuka this is the last, last warning, billahil azeem idan na ƙara ganin kafar ki a wurin nan sai na miki dukan da sai ance accident kikayi, kinga tun shigowar ki gidan nan ban taɓa dukanki ba kho, ba dan komai ba saboda ke marainiya ce wallahi da badan haka ba ko hanyarda nabi bazaki ƙara kalla ba" "Wallahi ko yanzu ma bazan kalla ba, dan Allah kayi hakuri" "Fita kiban wuri" ya faɗa yana nuna mata Kofar fita. Raɓewa ta farayi tana tafiyar sanɗa kamar wata ɓarauniya "Wallahi idan na buɗe idanuna naganki wurin nan....." Tun bai ƙara saba yaji ta wuce a guje gabansa kamar bullet. Sharafff kakeji leeya ta zube kan gadonta sai maida numfarfashi take da sauri da sauri. Tashi tayi zaune tana leƙa ƙofar ɗakin ta a hankali, ta dafe ƙirjinta tana sauke nannauyan ajiyar zuciya "wai Allah Nagode maka, ya Allah ka ƙara tsareni daga dukan ya-Turab, Allah ka ciremin kaunar garden ɗin ya-Turab ya Allah" Ta faɗa a fili tana ɗaga hannayenta alamar roƙo. "Leeya garden ɗin turab kikaje?" Ta jiyo Muryar mum da take shigowa ɗakin. "Wallahi kuwa mum ƙaddara ce takaini wallahi, amma in Allah yaso ba ƙaddarar da zata kuma kaini wurin nan ko hanyar wurin ma bazan ƙara kalla ba" "Ai kho daya fimiki alƙairi, yau khulud zata fara zuwa School kuma gashi bata tashi da wuri ba shine nazo ki taimaka mata dan Allah kije ki gyara ɗakin Turab, domin shi bayada uzuri kinsani duk da yasan zataje school idan bata gyara ba bazasu wanye lafiya ba". "Mum yanzu gyara ɗaki shine abun taimako ai ba komai bane wallahi, Ni tun farko ma naso na dinga gyarawa shine ya dage kan ita dai zata riƙa yi" "Eh Nima nasan da haka, kuma Ni na bada shawarar a barta tayi da kanta domin kina ganin khulud duk girman nan nata ba ko wane aiki ta iya yiba, idan mu munyi haƙuri da ita a hakan wanda zai ɗauke ta nan gaba shi bazai yi hakuri ba komai sonda yake yi mata. Koda yayi na marmari zaiyi amma daga randa ya lura sosai to zai fara yin magana daga nan kuma matsala zata fara shigowa, kinga daga haka abun sai ya taɓa zamansu" "Gaskiya kuma fa hakane mum, ba Kowa zai iya haƙuri da wannan ba gskiya, Bara naje na gyara kafin ya kammala shan iska nima kinsan ina cikin laifi banaso ya tarar dani ɗakin" "Okay tau kije kiyi sauri kuma, kinga idan kika yi sauri kika kammala da wuri kika fito ko ya dawo baisan wa yayi aikin ba a tsakanin ke da kuma Khulud. "Eh wallahi mum ai shiyasa nake so nayi sauri na isa" "Okay muje to" Cewar mum tana wuce wa gaba ita kuma tana bayanta. Suna fita kowa ya kama gabansa, mum ta tafi sashen ta, yayinda leeya kuma ta tafi sashen turab sai addu'a take a Zuciyar ta. Ji take kamar idan ta shiga zata ganshi, amma kuma tasan ba kowa a ciki tunda tasan inda ta baro shi. Da sallama a bakinta ta shiga parlourn duk da tasan ba wanda zata tarar amma hakan bai hanata yin sallama ba domin shiga wuri da sallama nadaga cikin ɗabi'un ta. Kwata kwata ba datti ko kura parlourn kamar ma ba'a zama cikinsa domin komai tsatsaf. Amma duk da haka bai hanata yin shara da mopping ba. Bayan ta kammala tayi goge-gogen da zatayi sannan ta saka air freshener da kuma turaren tsintsiya. Bedroom ɗin sa ta wuce shima tsaf-tsaf kamar yanda ta tararda parlour gadon ne kawai a chakude da alama ya kwanta a kan gadon. Shareshi tayi sosai shima kaana tayi mopping ta saka turare shima. Duk inda yakeda glass a ɗakin sai da ta gogeshi yafito tsaf dashi. Gaban wata HANGER CABINET taje ta tsaya tana kallon soldier's uniform ɗin da ya sarƙafe, wanda zasu iya kai kala goma, kuma ko wane kallar uniform da sunan ƙasarsa, ɗaya daga cikinsu ta ƙurawa idanu masu kalar maroon and green. Uniform ɗin sun ɗauki idanun ta matuƙa, a hankali ta saka abun ciro wa ta ciro jacket ɗin kayan "maroko" abunda taga an rubuta kenan a kan bottom ɗin da ke kan maroon jacket ɗinsa. "Kenan wannan uniform sune uniform ɗin sojawan maroko" Ta faɗa a cikin ranta. Lokacin da take shaƙar kamshin da ke fitowa daga cikin jacket din. Haka kawai taji sha'awar saka rigar, batare da wata shawara ba kuwa ta ɗora ta kan kayan da ke jikinta. Hular kayan ta ɗakko ta saka a kanta. Komawa tayi da baya inda yake ajiye takalmansa ta ɗakko waɗanda taga sun dace sosai ta uniform ɗin ta saka ƙafarta. "Hmmm, ashe ya turab kana da ƙafa da yawa takalman nan ai ko kafata biyu zata iya shiga cikin su, amma dai ɗaɗɗaya zan saka ma ko wace ƙafa" Bangaren da yake ajiye glasses ɗin sa tayi, bayan takalmansa da jacket ɗinsa dake jikinta, wani farin glasses sol ta ɗakko wanda shi yafi ɗaukar idonta duk a cikinsu, da yake niqab ɗin da ke fuskarta ya bayyanarda ƙwayar idanunta, yasa ta saka glasses ɗin ba tsoron komai. Hannu ta saka ta janyo agogon hannusa baƙi wulll ta saka shima dai yayi mata yawa sosai. Ƴar siririyar dariya tayi tana faɗin "ikon Allah, Ni ban taɓa tunani ya-Turab nada jiki kamar haka ba, agogon nan fa ya kasa tsayawa a hannuna hmmmm, yanzu sai me ma" ta faɗa a fili tana ɗan taga kanta sama kamar mai tunani. Sake ja da baya tayi tana gyara tsayinta sosai kai kace itace turab ɗin "mum na tafi maroko, idan na kammala musu aikin su kuma ba dawowa zanyi ba zanwuce Argentina, nan ma idan na kammala Austrelia zanje zan dai iya ɗaukar 2/3 weeks na tafi ku tayani da addu'a" leeya ta faɗa tana gyara agogon da ke hannunta kamar dai yanda turab yakeyi idan zai yi tafiya. Tafi taji amfara yimata daga bayanta"BRAVO" DR.TURAB K. WAASIB kinyi ƙoƙari sosai. Kamar sauƙar aradu haka taji muryar turab ta dira a kunnuwanta, suman tsaye tayi daga inda take tsayen domin kafafuwanta ma ji tayi sun kasa ɗaukar ta, ta bashi bayane tana jira yazo yayi mata abunda zai yi mata kawai domin tasan yau tata taƙare saidai buzunta.............✍🏽😌 BAYAN WUYA....... By RUMANA M DIGGI EP.27 ______________"kinyi ƙoƙari fa sosai leeya, ashe haka kike actress bansani ba" cewar turab yana tsaye daga bayanta kawai domin shi mamakinta da tsaurin idonta ya hanashi tantance kalar hukunci da zai yi mata. Zubewa tayi kan gwuiwoyinta ƙasa tun kafin ta juyo gareshi, domin a yanda takejin nan bata tunanin zata iya kallonsa. "Dan Allah ya-Turab na roƙeka dan Allah kayi hakuri, wallahi indai na ƙara shiga gonar ka kaymin duka duka sai ance nayi accident a jirgin sama, amma dan Allah na yanzu kayi hakuri" "Hakurin me kuma Dr. Turab, kamar ka Chief military health service zaka durƙusa gaban mace kana bata haƙuri" "Nidai yaya don Allah da alfarmar annabi kayi hakuri wallahi nidai, nidai in nice wallahi bazan ƙaraba" ta faɗa cikin muryar kuka. Cikin muryarda ke nuna alamar ba wasa turab yace"idan kika ga na hakura to sai dai idan kin juyo da kanki nan, kin aikata duk abunda kikayi bayan idanuna, ki aikatashi a gaban idanuna yanzu" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Ni yau na shiga uku, wallahi yaya sharrin shaidan ne. Wallahi bazan kuma yiba dan Allah kayi hakuri" "Yanzu sharrin shaidan ne ko" Da sauri ta daga masa kai tana faɗin "eh wallahi, dan Allah kayi hakuri kawai" Komawa yayi kan sopa ya zauna yana fuskantar ta" lokacin ki ya fara tafiya, ki tashi ki fara ko kuma na naɗa miki dukan jakai a ɗakin nan" Sosai leeya ta tsorata, danasani kam tafi dubu da takeyi a ranta, "ke nake jira" taji muryar sa ta ƙara shigowa cikin dodon kunnenta. "Dan Allah ya-Turab kayi hakuri wallahi bazan iya ba" "Ashe kuwa kinada rabon shan duka" "Duka kuma yaya, wallahi na rantse da Allah bazan ƙaraba, dan Allah kayi hakuri" Miƙewa yayi fuskar sa na sauyawa zuwa yanayin fushi sosai, a hankali leeya ta miƙe itama tana zame kayan daga jikinta. Tana duƙawa da nufin ta cire takalman sa dake ƙafarta taji saukar wani abu a jikinta kamar dai belt. da sauri ta miƙe ta fara zagayen ɗakin tana roƙon shi cikin tsoro da tashin hankali. "Yau na shiga uku na janyowa kaina, ya-Turab kayiwa Allah kayi hakuri wallahi nidai nace idan na kumayi kaymin fitinannen duka" Turab kam bata ma gabansa, surutanta kawai take domin shi tama fara damunsa, yana bakin ƙofar ɗakin ne yana jira ta gama zagayen da take ta tsaya wuri ɗaya, domin baya tunanin zai iya ƙyaleta da wannan uban laifin data aika ta masa. "Zo ki wuce" ya faɗa har idanunsa na rufewa saboda tsananin ɓacin rai da hasala. "Dan Allah ya-Turab kar..." "Zo ki wuce nace" da mugun gudu ta biyo ta gabansa zata wuce. Da sauri ya cafkota ya watsa mata belt ɗin da ke hannunsa har sau biyu, kafin ta wuce. Kuka kam ba kalar wanda leeya bata sha ba kuma ta kasa gayawa kowa labarin. RONY COLLEGE OF SCIENCE AND INNOVATION UNIVERSITY SULEJA. wata baƙar mota ƙirar Ferrari f8, ta faka a harabar makarantar. Dalibai sai kai kawo suke a harabar makarantar kowa na sha'anin gabansa. Parking driver yayi inda aka sharɗan ta yin parking a compound ɗin makarantar wato parking space. Yana parker motar ya fito tare da Zagayawa back sit ya buɗe kofar da faɗin "hajia mun ƙaraso" Ƙafarta ɗaya ta fara fitarwa, kana ta fito gaba ɗayan ta tana hura hanci. Sanye take da wando pallazo kalar, baƙi sai wata rigar kuma mai ɗauke da falmara. Rigar a iya cinyoyinta ta tsaya, ta cikin ce fara yayinda ta falmarar kuma ta kasance baƙa ce kamar wandon ta. jessy veil fari sol tayi rolling akanta, yayinda takalman da ke sanye a ƙafarta suka kasance farare suma Hill masu matukar tsawo. Wani glasses ne sanye a fuskar ta irin fashion ɗin nan daya kusa cinye rabin fuskarta. Hannunta ɗaya kuma handback kalar Black. Sai kuma ɗayan hannunta na riƙe da wata karamar takarda wacce da alamu wani abun take dubawa a ciki. Tafiya ta farayi, kamar batason taka ƙasa domin a hankali take takawa, tana ɗaga kai tana hura hanci. Saida ta kawo daf da wasu hanyoyi da suka rabu uku, kuma ko wace hanya da inda ta nufa. Ƴar ƙaramar dakardan da ke dunƙule a hannunta ta ɗago tare da walwaleta ta ƙalla, sosai tayi nazarin wurin kafin ta juya ta koma hanyar da ke nufar gabas a makarantar. Bangaren ANATOMY classes ta nufa tare da duba number class ɗinta, da taimakon wannan takarda da aka yimata jotting yanda tsarin ginin makarantar yake ta gano ajinda take. Ƙara gyara zaman glasses ɗin ta tayi kafin ta shiga ajin. Ajin cike yake maƙil da mata da maza kowa nata sha'anin sa. Shigowa tayi ajin batare da ta kula kowa ba domin ba wanda ta sani. Wani bangaren na cikin ajin ta nufa inda ta hango wata kujera da ba kowa taje ta zauna, waya ta ƙara akunnunta da alama kira taji tace "shikenan, ka tafi na gane class ɗin kuma ka kula da lokacin tashi karka makara, idan kuma kaƙi ji kasan sauran" ta fada bata jira cewar wanda tayi wayan dashi ba ta yanke wayar. Kamar jira ake kuwa tana zama, malamin da zai yi musu lactures ya shigo. Nan ya gabatarda lactures dinsa har yayi ya gama ya tafi. Da haka time by time malamai suka shigo suna yin lactures. har lokacin tashi daga School ɗin yayi. Yunkurawa tayi da nufin zata tashi, kwatsam taji an dafa kafaɗarta, da mugun fushi ta waiwayo domin ganin wanene ita da ba wanda ta sani a makarantar. Wasu ƴammata tagani su uku da sukaci ado sukayi kyau sosai, kana ganin su zaka tabbatar nera da kanta na magana a jikinsu. "Malama lafiya dai? kinzo kin riƙeni ko wani abun nayi miki" khulud ta faɗa cike da tsiwa. Murmushi yarinyar tayi kaana tace"lafiya ƙalau, kuma lafiyar ce ma ta janyo hakan. Munga kamar ke ɓakuwace a makarantar nan kuma idan bazaki damuba munaso mu ƙulla ƙawance dake. Nidai sunan AMRAH RAFEEQ TIMIA. Mahaifina ne mai kamfanin NBC na ƘASAR nan gaba ɗaya har kuma da ƘASAR Japan" Dan waro idanu khulud tayi cikin mamaki domin ba wanda baisan NIGERIA BOTTLING COMPANY ba (NBC) Indai a garin suleja yakai. Bata gama mamaki ba taji ɗaya daga cikinsu tace"nikuma sunana REEMAH RABEEL mahaifina ne commissioner of police na kasar nan". Ta ukun kuma tace; "Nikuma sunana RAUDHA MAHEER YASAR mahaifina ne current governor na yanzu"ta faɗa tana kaɗa carkeys dake hannunta. "Wow nice to meet you, I khulud Khattab waasib mahaifina ne current minister of judiciary. Chief Khattab waasib SAN, kuma babban dan kasuwa ne a kasashen ketare" khulud ta faɗa tana fitar da siririyar iska daga bakinta. Wani irin tsalle suka daka su duka huɗun suka rungume juna, cikin farin ciki. Raudha, da amrah duk halinsu ɗaya kamar dai khulud, kwata kwata basa ƙaunar talaka ko kaɗan, ga girman kai da son a nuna su wasu ne, a kaff makarantar basa shiga lamarin kowa sai idan sun fahimci kunada mahaukatan kuɗi, kuma idan suka san mahaifinka sanannene. Sunjima zaune su biyu kaɗai ba wani wanda yake ɗalibi a makarantar Rooney da bai san raudha da amrah ba saidai idan new commer ne, kuma ko new commer aka samu bazai wuce kwana biyu zuwa uku ba zai sansu a makarantar yanda suke fantamawa da kuɗi da manyan motoci. Samari kuwa sai chahhh suke musu, amma kuma duk wanda yaje sau ɗaya bazai ƙara kwatanta zuwa ya samesu da wata maganar soyayya ba, domin ko mutum bai furtamusu kalmar soyayya ba sun wulaƙanta shi balle ma ace ya nuna musu. A cewarsu babu irin tsarin samarin da suke so a Rooney ko akwai kuma basu shigo ba tukunna, Rooney school of science babbar jami'ah ce a garin suleja, kuma shigarta sai ɗan wane da wane, duk wanda kagani a cikinta to mahaifinsa yayi fice domin kuwa ba talaka bane. Haka amrah da raudha suke rayuwarsu iya su biyu kadai a Rooney basa kula kowa, kuma kowa baya kulasu. Haka suke duk lokacin da aka kawo new commer idan mace ce zasuje su gabatar mata da kansu da kuma nasabarsu. Itama kuma sai ta faɗa musu, idan sukaji nasabar ta kuma suka gano mahaifinta ba wani sananne bane shikenan suyi gabansu itama tayi gabanta ba ruwan kowa da kowa. Idan kuma sukaji sunan mahaifinta sannanne ne shikenan sai su kulla ƙawance. Hakace ta faru lokacin da aka kawo REEMAH RABEEL makarantar, da suka gabatar mata da kansu, itama ta gabatar musu da kanta shikenan sai suka ƙullla ƙawance da ita. Saboda mahaifin REEMAH ma sananne ne sosai a ƙasar, kuma gata da cikakkiyar gata domin ita kaɗai Allah ya bawa iyayenta. Sai dai wani abu ɗaya REEMAH da RAUDHA da kuma AMRAH basa jituwa sosai a tsakanin su, saboda halinsu ya bambanta da nata. Ko kaɗan REEMAH bata ƙyamar talaka, kuma bata wulaƙanta mutane kamar yanda su amrah sukeyi. Amma kuma batajin zata iya rabuwa dasu kan wannan, saidai suyi faɗa su shirya, haka suke koda yaushe. Shiyasa REEMAH tayi farin ciki sosai ganin khulud tana tunani wata ƙila halin khulud daban dasu amrah shikenan sun zama su biyu a bangaren ta, suma su amrahn su zama su biyu ke nan tunda ba zasu sauya halayensu ba. "Shikenan ku fito mu tafi kho, wata ƙila ma anzo ɗaukar wasu daga cikinmu" REEMAH tayi maganar tana wucewa gaba. Su kuwa su amrah sai jan khulud surutu suke, ita kuwa ta sake sai basu labari take kamar da can sun saba. Fitowa sukayi harabar makarantar suna tafiya su huɗu sunsha kyau sosai da gayu, mutane kuwa sai kallon su suke duk inda suka gifta musamman ma khulud da take baƙuwa fuska bakowa yasanta ba. "REEMAH kinga fa ke nake nema tun ɗazu" wani farin matashin saurayi ya faɗa yana murmushi. "Lahhh wallahi Sayyid muna class tun ɗazu, baƙuwa mukayi shiyasa kaga mun jima bamu fito ba, ince dai lafiya". "Lafiya ƙalau fa, kawai inaso nayi tambayane amma muje daga can" ya faɗa yana nuna mata wasu plastic chair's dake ɗan nesa dasu. "What!?, ba inda zataje idan bazaka iya yin tambayar anan ba ka ƙara gaba, ko kaje can wurin wanda yayi lacturing ɗin kaje kayi tambayar ka ai ita ba lactures take yiba" cewar raudha tana hararar matashin saurayin da ya tsayarda reemah rabeel. "Raudha kenan, nasan ba lacturing take ba. Na zaɓi nayi tambayar wurin tane saboda ita tasan abunda take, inaga ga mutane nan da yawa sai ita na zaɓa ta gayamin saboda ita tasan mutumcin jama'a" Raudha na shirin yin magana khulud ta daga mata hannu alamar tayi shiru. Tafiya ta farayi ɗaɗɗaya har ta ƙaraso gaban sayyid. Sayyid kuwa ganin haka yasa ya gyara tsayuwar sa, tare ta mayarda hannayensa gaba ɗaya cikin aljihunsa yana jira yaji dame tazo. "Kai Sayyid naji an kiraka ko wah, Please ka fita sha'anin mu a School ɗin nan gaba ɗaya, naga kamar kanka yana ɗan rawa. So it's better for you to maintain yourself. If not kasan sauran" khulud ta faɗa tare da juyawa ta fara tafiya. "Hmmm, idan kika tambayi labarin Sayyid Turaki bana shiga lamarin ƙananun yara, musamman yaranda basu san abunda suke ba. Kuma Ni idan kika duba bana kula jahilai kamar ke ɗin nan dama sauran tumakin abokan nan naki raudha da amrah. Idan kika ganni a wuri to nasan inda na kawo kaina, REEMAH RABEEL tasan mutumcin mutane kuma wurinta nazo, inace ma danazo wurin nan bankira sunan ko waje akuya a cikinku ba kho, so kuma ku kama kanku Sayyid baya lamarinsa da dabbobi" cewar Sayyid yana wani shu'umin murmushi. Kalamansa sun ƙona zuciyar khulud matuƙa, hakama amrah da raudha, saidai nasu duk mai sauƙine tunda su ba yau suka saba ba. Khulud ce ya fara yiwa yanzu, ba ranarda Sayyid zai haɗu dasu AMRAH ba'a sha daga ba, wani lokacin kuma REEMAH ce ke tarewa tun kan a fara. Khulud na shirin magana, REEMAH ta dafe mata baki da hannayenta tana shirin kuka "dan Allah khulud kiyi haƙuri karki ƙara faɗar komai dan Allah na roƙeƙi, Sayyid kaima ka tafi dan Allah zanzo kaji kayi haƙuri Please " ta faɗa cikin matukar damuwa tana rangwaɓarda kanta kamar zata fashe da kuka. "Shikenan REEMAH zan tafi saboda ke, wallahi da badan keba bazan je ko'ina ba sainaji ina rashin kunyar wadannan yara ta tsaya" cewar Sayyid yana barin wajen tare da jefawa su amra wani wulaƙantaccen kallo. Cikin matukar zafin zuciya da ɓacin rai khulud ta bige hannayen REEMAH daga kan fuskar ta"dan Allah tsaya Malama, ashe ke matsoraciya ce, gskiya Ni banason mutane irinki REEMAH na rantse da girman Allah ni banason mutane irinki, kum naga su AMRAH ba wannan tsoron a idanun su ke kaɗai ce, to wallahi Ni bazan iya da wannan abun kunya ba. Duba kiga yanda wani ɗan iska yazo ya cimana mutunci ya tafi ba abunda muka iya yi masa" "Kedai kibarta kawai khulud, wallahi reemah bakyajin magana kece kike janyo anayimana kallon ƙananun mutane, yanzu ki duba wannan dan iskan Sayyid ɗin da yazo yana cimana mutunci harda kiranmu wai awakai, wallahi da ace munsan yanda zamuyi da Sayyid da tuni mun saka an fitar dashi daga Rooney" cewar amrah cike da masifa. "Saboda me baza'a iya fitarda shi ba, Ni wallahi zan iya samun mahaifina da maganar nan kuma in sha Allah zai iya saka a sallameshi daga School ɗin nan" "Hmmmm, kedai khulud rufa mana asiri, Sayyid bazai iya fitardamu a Rooney ba, haka muma baza mu iya fitardashi ba. Sayyid ya zamarmana ƙadangaren bakin tulu ba yanda muka iya dashi ya riga da ya rainamu duk fadin Rooney sayyid ne kaɗai baya shakkun faɗa mana magana" Ƙwafa khulud tayi kawai tare da barin wurin bata cewa kowa ƙala ba, saboda ranta yayi matuƙar ɓaci............✍🏽 BAYAN WUYA........ By RUMANA M DIGGI EP.28 _________________________________________K. WAASIB MANSION. "mum na kammala" "Kije kiyi wanka ki shirya, fita zakuyi" "Fita kuma mum?" "Eh, kije ki shirya turab zai kaiki shopping, saƙo nakeso na Baki. "Ok mum, yanzu zanje na shirya, amma dai mum da so samu da sai driver ya kaini ya-Turab yayi zamansa" "Turab nakeso yaje ya kaiki, kiyi sauri kuma karki ɓata masa lokaci domin shima na faɗa masa ba ruwana idan kika ɓata masa lokaci". Juyawa leeya tayi gwiwarta duk tayi sanyi, domin rabon da ta saka turab a idanun ta tun ranar da tayi masa laifin a dakinsa. Daga ranar ne kuma ta toshe duk wata ƙofa dazai dinga ganinta, sun kwashe kusan sati uku basa ganin juna. Dayake shi bai cika zama a gida ba, ita kuwa leeya duk ranarda yana gidan bata taba fitowa ko cin abinci, idan ta fito da sanɗa zata fito tayi duk abunda zatayi sannan tayi tafiyar ta batare da sunga juna ba. Da sanyin jiki ta ƙarasa ɗakinta, tana isa kuwa wayarta ta fara ɗauka tare da dannawa zohal kira, Bugu ɗaya ta ɗaga. "Bestie" aka faɗa daga cikin wayar. "Na'am, zohal barka kina lafiya" "Lafiya ƙalau, yasu mum" "Mum tana nan lafiya" "Masha Allah, bestie kina lafiya kuwa, naji muryarki ta sauya" "Wallahi zohal da dama dai za'a ce, kinsan tunda na baki labarin laifin da nayiwa ya-Turab koh" "Eh masani, bestie badai laifi kika ƙara yimasa ba kuma" "Ah, ah, banyi masa laifi ba amma tsawon wannan lokacin bamu ƙara haɗuwa dashi ba, na kiyaye duk wata hanya dazata sake haɗamu, sai yanzu ne mum takirani tace naje na shirya tanaso ta aikeni nayimata shopping kuma ya-Turab ne zai kaini" "Tabbb, lallai kam dole hankalinki ya tashi, ke mene ma wani abun tashin hankali. Kedai kawai ki tashi kije ki shirya ki fita kar kuma ki sake masa laifi, amma kuma shawarar da zan baki ki kama kanki karkiyimasa ba daidai ba duk yanda yace kiyi, koda bai miki daɗi ba kiyi don ku rabu lafiya. Naga kamar zaifi da wani tsoro-tsoro da kikeji" "Tau shikenan zohal, in sha Allah ba wani abu dazai faru indai ta bangarena ne, amma Ni wallahi tsoronsa nakeji" "Hmmm, yafi ma zaki cire tsoron sa a ranki, idan yaga kin cika tsoransa da yawa wallahi zai ta kura miki ne da yawa shima" "Shikenan bara naje nayi wanka, sai na dawo" "Allah ya tsare hanya" "Ameen thumma Ameen" Leeya ta faɗa tare da katse wayar. Ajiye wayar ta tayi a inda take zaune daga nan kuma sai ta shiga toilet da nufin yin wanka. Bayan mintuna kaɗan kuma sai gata ta fito, Dressing mirror ta nufa tare da shiryawa tsaff cikin riga da skirt na atamfa ruwan shuɗi mai ɗan haske. Kayan sunyi matukar yi mata kyau, duk da ba'a ganin fuskar ta amma hakan bazai hana mutum ya fahimci irin kyawun da kayan suka yimata ba. niƙab ɗinta ta ɗauko kalar blue mai duhu, sai kuma ta yafa gyale kalar blue mai duhu shima. Sannan ta juya da nufin ɗaukar wayanta, Lokacin da takai hannunta ga wayar da nufin ta ɗauka, babban abunda ya ɗaure mata kai shine shigowar sakkoni uku lokaci ɗaya, kuma ko wane saƙo da lambar da aka turoshi daban. Amma kuma duk abunda saƙon yake isarwa ɗayane da kowace lamba. Lamba ta farko abunda aka turo da ita shine, "AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GAREKI MY DREAM GIRL, INA FATA KINA LAFIYA, ALLAH YASA HAKA. NASAN KINA CIKE DA MAƊAUKAKIN MAMAKI KHO? KO KAƊAN KADA KIYI MAMAKI LEEYANA, NI MASOYINKI NE NA HAƘIƘA WANDA BANA TUNANIN KINADA KAMARSA A HALIN NAN DA MUKE CIKI YANZU, NASAN KINA MATUƘAR BUKATAR NA BAKI DAMA KIYIM TAMBAYA KHO, HMMM, KARKI DAMU WATA RANA IDO DA IDO ZAKI GANNI KINJI. BYE KI KULA DA KANKI, SAI ANJIMA". Number ta biyu kuma sai aka turo sakon kamar haka"SORRY MY DREAM GIRL, NACE MAKI SAI ANJIMA KUMA GASHI BAMU KAMMALA MAGANA BA, YANZU NA SAMI LABARIN WAI ZAKI FITA SHOPPING KHO, AMMA KUMA SHINE BAKI GAYAMIN BA, KO DA YAKE MA AI BAKIDA WATA ƘOFAR DA ZAKI IYA SANARMIN DA KOMAI SAI DAI IDAN NI NA ƁUKATA, WELL SAI DAI KIN DAWO ALLAH YA KAREKI DA KARIYAR SA". Number ta uku kuma saƙonta shine"YAWWA MY DREAM GIRL, BAN GAYAMIKI ABUNDA ZAKI SIYOMIN BA IDAN KIN FITA SHOPPING ƊIN, DAN ALLAH INASO KI SIYOMIN KYAKKYAWAN AGOGON HANNU DOMIN YANA DAGA CIKIN ABUNDA NAKE BUƘATA. KUMA NAJI ANGAYAMIN BAKE KAƊAI ZAKIJE BA, DAN ALLAH KI KULAMIN DA KANKI. KINSAN INADA MATUƘAR KISHINKI. KARKI DAMU KANKI DA SANIN WANDA YA GAYAMIN ZAKI FITA BA, KEDAI KAWAI KISAKA A RANKI INA KAUNARKI KUMA INA KULA DA DUK WANI MOTSI NAKI DREAM GIRL ƊINA. NASAN ZAKI ZARGI KO ZOHAL CE TA GAYAMIN KHO, HMMMM. MAGANATA TA ƘARSHE ITACE BASAI KIN WAHALAR DA KANKI DA TAMBAYAR ZOHAL BA DOMIN WALLAHI KO ITA ZAKI TAMBAYA BATA SANNI BA KAWAI DAI TASAN INA SONKI DA ƘAUNARKI SAI ANJIMA". Leeya nakai nan a karatun da take sai ta sauke wani ƙaƙƙarfan numfashi tare da zaunawa kan royal chair, ta ɗauki lokaci a haka daga bisani kuma ta kira number zohal. Kwata kwata bata kawo kiran number ko ɗaya daga cikin numbers ɗinda aka yimata saƙo ba, domin kuwa tasan abu ne mawuyawaci ta sami number a kunne, kuma idan ma tayi reply ba respond saboda andaina aiki da number. A Yanzu kam abunda takeji yafi gaban mamaki domin kuwa wannan bashi bane na farko, kuma bashi bane ba biyu. Domin idan zata lissafa, wannan abun yakai tsawon wata bakwai. Kuma ko sau ɗaya ba'a taba turamata sako da number iri ɗaya ba. Kuma wanda yake turo saƙonnin bai taɓa barin alama ko ɗaya da zata gane shi ba. Yasha faɗa mata abubuwa yace daga bakin zohal yake samu, sai dai kuma ita zohal tace batasan da labarin ba sam. Ko yanzu ta kira zohal ne kawai badan tanada tabbacin samun abunda takeso ba. "Hello, zohal" "bestie kun fitane" "Zamu fita yanzu" "Lafiya, ko wata matsalar ta faru ne?" Zohal ta tambaya da mamaki. "Zohal maganar mutumin nan ne da yake turamin saƙo a kowace safiya ta Allah, yau ma yace wai ke kika faɗa masa zamu fita shopping, har yace wai na siyomasa agogon hannu" "Hmmm, bestie bazaki gane bane, abunnan akwai ɗaure kai wallahi. Amma kiyi hakuri yanzu kije ki dawo idan kika dawo mayi magana in sha Allah ki kwantarda hankalinki kawai Allah ya kai ku lafiya" daga haka zohal bata jira cewartaba ta yanke wayar. *A bangaren turab kuma yana zaune a parlourn sashen sa, sai faman waya yake yana murmushi cikin natsuwa. Mum ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, ta zauna a kusa dashi kaɗan. Shi kuwa turab ganin mum yasa shi faɗin "shikenan fahad zankiraka in anjima, ga mum ta shigo yanzu" Daga cikin wayar kuma aka amsa masa da faɗi"well ba damuwa ka kirani ɗin idan kun gama, kuma kacewa mum ina gaida ita" "Zataji in sha Allah, sai na kiraka ɗin" Sallama sukayi kafin su katse wayar, turab ya dubi mum da fara'a "mum, barka da warhaka" "Yawwa, ya aikin ya gajiyar hanya?" "Hanya alhmdullillah mum, ai bazanyi tafiya a watan nan ba" "Saboda me!?" Mum ta tambaya da mamaki "ince dai lafiya" "Lafiya ƙalau mum, Alex zaiyi aiki dasu a wannan watan domin ni na ɗauki hutu, duk da bai taɓa aiki dasu ba. Amma yanzu na sakashi ya wakilceni" "To Allah ya taimaka, ya tsare ya bada Sa'a" "Ameen ya rabbil ibaddd mum" "Dawa kake waya danashigo ne" "Mum, da angonmu nake waya" "Yanzu ya kaji da kace ango turab, bakaji kamar kai ake kira da sunan nan ba dan Allah. Wallahi ni dana shigo na ɗauka da wata kake waya har naji sanyi ashe da fahad ne" "Eh shine mum muna tattauna maganar auren ne" Taɓe baki mum tayi tana faɗin "katashi ka shirya zaka kai leeya tayi shopping" Cikin mamaki ya ɗago da faɗin "leeya kuma, ni zan kaita shopping, duk ina driver's ɗin gidan nan mum. Dan Allah mum kinsan banason raini kho, please karkija yaran nan su rainani nine zan kaita shopping wallahi ni har na manta da wata leeya a gidan nan" "Har ka manta kho? To na tuna maka yanzu saboda haka ka tashi kaje ka shirya idan kuwa haka zaka fita sai ka tashi muje" "Mum please kije ki haɗata da driver dan Allah" "Kai nakeso ka kaita turab, idan kuma bazakaje ba sai ka faɗa min kagah idan zan ƙara maka maganar" mum ta faɗa da bayyanannen ɓaci rai. "Kiyi hakuri zanje" ya faɗa fuskar sa ba annuri ko kaɗan. (ROONEY) Zaune suke su huɗu cikin wata ƴar qaramar rumfa da iyakacin ta mutum huɗu sune abunda take iya dauka domin tayi ƙanƙanta ga Mutanen da suka haura huɗu. Rumfa ce ƙarama wacce akayita domin ɗalibai su ɗinga zama suna shan iska ko kuma suyi karatun su a ciki. Amrah ta kalli khulud tace "khulud ya akayi jiya naga wata ta tsayardake tana tambayarki, Ni kuma a wannan lokacin driver na yazo shiyasa banzo naji abunda kuke tattaunawa ba, amma dai kinsa ita ba kowa bace kho. Wallahi babanta custom yake yiwa aiki bama shine custom ba yaronsa ne" Taɓe baki khulud tayi cikin jin haushi tace "ke rabuta shashashar yarinya, wai gayamin take na fita harakar ku a makarantar nan domin ba wanda kuke gani da mutunci" "Hmmm, ke kuwa me kika cemata" raudha ta tambaya cike da masifa. "Ai kema kinsan bazan rangwanta mata ba wallahi, nayi mata wankin babban bargo. Tun a wurin saida tayi danasanin tarona da maganar" cewar khulud tana wani makirin murmushi. "Wama take da suna" cewar raudha cikin sigar tambaya. "Ni ko menene sunan ta, inaga kamar sunan ta hibbah basheer" Cewar amrah da tabbacin abunda take faɗa. "Haaaaa, hibbah basheer kho, ina ga fa Physics class take zata gane ta shigo gonar mu wallahi, ita menene damuwar ta damu to, tunda bamu taɓa yimata komai ba yanzu zatasan ta taɓomu wallahi dan sai tayi nadama" Da sauri reemah ta ɗago kanta da faɗin "me zakiyi mata raudha dan Allah karki saka a koreta a makarantar nan kamar yanda kikayiwa husnah, da kubrah. Kinsan har yanzu wasu suna wannan maganar kuma har yanzu wasu suna dubinmu da wannan zaluncin, kinga hibbah ma bamusan yanda mahaifinta ke fadi tashi yana samun kuɗinda yake kawowa ba, ki wama Allah da Manzonsa karki saka a koreta a makarantar nan" Wawan kallo amrah da raudha suka jefamata yayinda khulud ta daka mata tsawa da faɗin "wai kekam reemah menene matsalar ki ne dan Allah, Allah ya bambanta tsakanin mu da talakawa amma ke kin kasa gane haka, ita hibbah da ake magana a kanta ita kaɗai ce a Rooney? Ko kuma wani abu ya taɓa shiga tsakanin mu ne. Bata duba bama ragawa kowa ba sai tayi mana kutse kho, kuma ta rasa wanda zata gayawa sai Ni wallahi batayi a banza ba kuma idan kikaga taci gaba da karatu a makarantar nan, saidai idan Bama nan cikinta" Khulud ta faɗa tare da janye su amrah daga wurin. Suna nufin fita daga rumfar ne sukaji muryar Sayyid na faɗin "idan kun rabata da School ɗin nan ai ba da ranta kuka rabata ba kho, to wallahi kun rago tunda bazaku iya fitar da rai daga gangar jikin taba, kuma duk irin zaluncin da kuke tafkawa kuda azzaluman iyayenku, Allah yana gani. Kuma ba mantawa yayi dakuba a hadisin Manzo Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa; "(IN-NALLAHA LAH-YUMLIE LIZZALIMIN, HATTA IZAA AKAZAHU LAM-YUFLIT-HU)", [Ma'ana] "Allah yana jingitarwa azzalumai, har sai ranarda suka shigo hannunsa. "wallahi kuyi gaggawan komawa ga Allah domin cin zalinda kuke yiwa mutane yayi yawa" Sayyid na gama faɗin haka, ya janye reemah daga wajen. yabar su amrah na binshi da ido baki sake kamar wanda basu saba ganin sa ba. A zafafe khulud ta kalli amrah da faɗin"amrah wai sayyid ɗin nan dan gidan uban waye dayake yimana yanda yaga dama a Rooney?" Murmushi irin najin haushi amrah tayi tare da faɗin "Sanin ko ɗan gidan waye bazai yi mana maganin komai ba, domin tun kafin yau raudha da mahaifinta ba yanda basuyiba kan su fitarda sayyid makarantar nan amma abu ya faskara. Koda suke Wannan mahaifin raudha bai san waye mahaifin sayyid ba, sai daga baya ne daya gane mahaifinsa komai ya tsaya domin idan har bai kiyaye ba raudha ce za'a fitar a Rooney ba sayyid ba" "Saboda me za'a fitarda raudha alhali ko waye mahaifinsa mahaifin raudha ya fishi matsayi" "Mahaifin raudha bai fi mahaifin sayyid matsayi ba" "Hmmm, amrah kenan nadai san mahaifin sayyid bashi bane shugaban ƙasa ba, domin kaff ƴaƴan shugaban ƙasa na yanzu ba wanda ban sani ba, saboda suma familyn mune" "Eh, mahaifin sayyid ba shugaban ƙasa bane" "To waye Sayyid" khulud ta tambaya cikin ƙuluwa. "Yarima sayyid ɗan sarki maleek al-shams" "What!!?". Khulud ta faɗa cikin mamaki da kuma tsoro. Amrah cikin tabbacin abunda take faɗa ta maimaita da faɗin "ehh sayyid ɗan sarki maleek al-shams ne wallahi, shine babban dansa namiji, Sayyid maleek al-shams" "Aww dama wannan shine Sayyid maleek, amma kuma ba a dubai yake karatuba" "Eh, dubai yake karatu nima bansan abunda ya mayar dashi nan ba" "To kuma shine dan yana ɗan sarauta zai hana mana yin yanda mukaga dama, wallahi bai isa ba takun saƙa tsakanin mu dashi kuma yanzu aka fara, wallahi tsakanin mu dashi ba gudu ba ja da baya" "Kwarai kuwa khulud domin kowa ya gaji bai saba ba, kuma haka nake gayawa mahaifina kullum, muddin Sayyid bai fita harakarmu a Rooney ba wallahi muma bazamu kyaleshi ba. Yanda yake taƙama da mahaifinsa muma haka muke taƙama da namu" raudha tayi maganar tare da ɗaukar hand bag ɗinta tabar wajen. Suma suka bita a baya suna faɗin albarkacin bakinsu akan Sayyid da mahaifinsa wato maleek al-shams mai Mulkin garin suleja. * A Chan gida kuwa leeya ce zaune a parlour tana jiran fitowar turab, ta kai tsawon mintuna goma da fitowa amma babu shi babu alamarsa. Mum ce ta fito hannun ta ɗauke da jotting paper ta miƙawa leeya. Ki jirashi ko kuma kije ki kirashi a part ɗinsa. "Wah Ni na isa, nida sashen ya-Turab kuma sai mai rabon ganin baɗi, kema kanki mum dan bakisan mazgan da nasha bane da kin sani bazaki yarda na ƙara zuwa ba" a zuciyar ta tayi maganar amma a zahiri cewa tayi "ah mum ai ban jima da fitowa ba bara na jirashi kawai" Mum tace "to shikenan, idan kinga zaki iya zaman amma idan kikaga ya jima bai fitoba kije ki kirashi kinji" "In sha Allah mum" "Sai kun dawo" mum ta faɗa tana hayewa sama. Bayan tafiyar mum kaɗan ba jimawa sai ga Turab ya sako. Bataji takun tafiyarsa ba, amma kamshinsa ne ya tabbatar mata da isowarsa. Juyawa tayi da ƙarfi ta kalleshi sosai, kafin ta ɗauke idonta daga gareshi. Sun kuyarda kanta tayi kaɗan kaana ta gaidashi "ya-Turab, Barka da fitowa" Ko kallon ta baiyiba yayi tafiyar sa. Ita kuma sam abunda yayi mata baisaka taji haushi ba ko kaɗan. Haka ta bishi a baya tana tafiya ta a nutse. Koda suka iso compound ɗin gidan har an fito musu da motarda zasu fita da ita. Driver side ya buɗe ya shiga baicewa leeya komai ba. Itama bata cemasa uffan ba ta buɗe back side na motar ta shiga. "Ke! Ni drivern kine da zaki shiga back side ki zauna" ya faɗi maganar kamar dai kullum fuskar sa babu annuri ko kaɗan. A hankali ta buɗe kofar motar kamar mai jin tsoron ta fito, sannan ta shiga front side ta zauna. Kunna motar yayi, aka wangale masa gate ɗin gidan ya tura hancin motarsa waje..............✍🏽 BAYAN WUYA...... By RUMANA M DIGGI EP.29 ______________________ROONEY UNIVERSITY, ANATOMY CLASS. zaune suke a babban class ɗinsu da a ƙalla zai iya ɗaukar mutum ɗari biyu a ƙiyasi, saidai su basu kai dari biyun ba domin Private School ce ba sosai aka cika takurawa ɗalibai ba, wani lactura mai suna Dr. Nicole sami ne a tsaye da mic a hannunsa yana lactures. Sai da yakai inda aka sanya alamar tsayi a lactures ɗinda yake kafin ya dakata. Sakamakon shigowar wani matashin saurayi. "Me kake nema, ko a class ɗin nan kake" Dr Nicole sami, yayi tambayar da harshen turanci yana kafe saurayin da idanuwa. "Sunana IDRAK MANAF" saurayin ya faɗa da yaren turancin yana miƙa masa wata nannadaddiyar takarda. Karɓar takardar Dr Nicole sami yayi kafin ya ɗan dubata kaɗan. "IDRAK MANAF kho" "Eh" saurayin matashin ya faɗa yana ɗaga masa kai alamar tabbatar wa. "Kaine ka sami free scholarship kenan" "Eh nine" "Amma akace waɗanda gwamnati zata ɗauki nauyin karatun su mutum uku ne ya akayi ba ganka kai kaɗai" "Eh Nima haka naji, amma Ni kaɗai sunana ya fito gaskiya" "Ok Allah ya taimaka". Cewar Dr.necole sami. Jin an ambaci free scholarship yasa wasu dayawa daga cikin ajin ɗaga kai suga ko waye. Saidai su raudha tun kafin su ɗaga kan nasu suka kwashe da dariya Raudha ta dubi Amrah tace "AMRAH har yanzu akwai waɗanda gwamnati ke ɗaukar nauyin karatun su?" "Akwai mana gashi nan kin gani" AMRAH na kai nan a zancenta suka sake kwashewa da dariya gaba ɗaya su uku suka ɗago kansu domin ganin wane talakan ne wannan da yafi kowa talauci. Duk su duka suka saki baki suna kallon shi, yayinda khulud ta shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa, domin tana kallonsa zuciyarta ta fara bugawa da sauri dasauri, kamar da can akwai wani abu daya taɓa haɗasu. Mayar da kanta tayi ƙasa, saidai zuciyarta ta kasa haƙura da kallonsa. Sai a lokacin ya ɗago da kansa yana karewa class ɗin kallo yana murmushi. Sake kai dubanta tayi kansa tayi masa kurieee kamar mai son gano wani abu a tattare da shi. Dubana na kai kan matashin saurayin da ke tsaye, yayinda Dr Nicole sami ke yimasa ƴan tambayoyi. A nan ne na karewa fuskar sa da kuma zubin halittarsa kallo, siriri ne amma yanada ɗan kauri, tare da cikakkiyar fuska, kyakkyane sosai mai hasken fata, amma ba irin hasken nan sosai ba kuma baza'a kirashi da baƙi ba, gashin gemunsa da ƙasumbarsa ma baƙi ne siɗik, da alama yana basu kulawa sosai sai wani kyalli suke suna fitarda wani farin haske. Izinin zama Dr Nicole sami yayi masa, kafin shima ya ci gaba da lactures ɗinsa. * A chan ɓangaren su leeya kuwa tunda suka fita gidan ba wanda ya kuma cewa komai tsakanin ta da turab, saidai shi turab yana shiga motar ya ɗakko wayarsa ya dannawa zafaran kira sai wayarsu sukeyi abunsu. "ya-Turab samad store zamuje inaga can za'a fi samun kayayyakin nan" Leeya ta faɗa gabanta na duka Saboda tsoro. "Bazamuje samad ɗin ba dan ubanki, ke zaki biya kuɗin ne balle ki faɗi inda kikeso muje, ko aka gayamiki dan ke na fito shopping ɗin nan. Wallahi idan baki kiyayeba sai na ɓaɓɓalaki" cewar turab yana kaimata wawan ranƙwashi. Wasu irin zafafan hawaye taji sun gangaromata sakamakon zafin da taji a kanta. "Ke kuka kikeyi dan uwarki, menayimiki wallahi idan kika sake naga hawaye a niƙab ɗin nan sai kin gane kuskuren ki" Da sauri leeya ta toshe bakin ta, domin tanajin kukan da take rikewa zai iya suɓucemata idan yaci gaba da yimata magana irin haka. "Wallahi, billahi, na rantse da Allah idan kika sake naji Muryarki da nufin kina yin kuka saina raunata ki" Tsit tayi kamar wacce ruwa suka cinye har suka isa classic shopping mall, kuma can yakeda ra'ayin zuwa tun a farko. Parking motar yayi yana fitowa daga ciki, ita kuwa leeya tana gudun ta fito bai bata izni ba kuma abun ya zama laifi. Domin ita tana gani a yanzu komai tayi masa laifi ne. "Ke malama idan baki tashi ba ki fitarmin daga mota ki kama gabanki" "Kayi hakuri ya-Turab, ina jira kaban izni na fito ne, kar kuma na fito ba tare da iznin ka ba ya zamo nayi maka laifi" "Mtswww, yayi tsaki tare da barin wurin ko kallon arziki baiyimata ba balle yaji maganar da take masa. Binsa tayi baya har suka isa cikin mall ɗin. Saƙon da mum ta bata ta shiga duddubawa inda take gano komai a hankali, bayan ta kammala yiwa mum siyayyarta ne sai ta fara dudduba abubuwan da take buƙata itama. Saida ta kammala komai ne ta juya zata bar wajen idanun ta suka sauka akan wani kyakkyawan farin agogon hannu na maza Kuma na fata. Agogon na mazane mai tsananin kyau da tsari gashi da kala mai ɗaukar ido. Haka kawai taji agogon ya birgeta sosai, inda aka ajiye agogon ta nufa tare da kai hannun ta taɗauki agogon. "Kada ki manta ki SIYOMIN KYAKKYAWAN AGOGON HANNU DOMIN YANA DAGA CIKIN ABUNDA NAKE SO" Taji saƙonda aka turo mata ɗazun ya dawo mata kamar yanzu take karantawa. Daukar AGOGON tayi ta sakashi a siyayyarda tayi, duk da tasan ba amfanin da zai yi mata domin kuwa ba ganin wanda ya bata saƙon zatayi ba, hasali ma batasan ko waye ba, gashi kuma ita ba namiji ba balle ta saka sanin agogon na mazane ba mata ba. Turab kuwa tunda suka isa yayi wani ɓangaren daban domin yayi shopping ɗinsa shima. Dawowa tayi receptionist ɗin domin ita ta kammala abunda tazo yi, ɗan dudduba shi tayi harabar wurin bata ganshi ba, harta juya zata tafi nemansa sai ta hango shi ɗan nesa kaɗan daga inda take. Jiransa tayi tsawon mintuna huɗu zuwa biyar sai gashi ya ƙaraso, ɗaya Bayan ɗaya ya fitarda kayanda yayi shopping aka lissafa nasa. "Ke!! Sai ance ki bada kayan a lissafa miki" Da saurin ta ɗora kayan itama, aka dinga fito dasu ɗaya bayan ɗaya, sai da aka kawo ga AGOGON ne turab ya kalleta da mamaki "uban wa kika siyawa agogon maza" Inda-inda ta fara yi har muryarta na sarƙewa tace "ya Wallahi ba kowa na siyawa ba Nima ya birgeni ne kawai yasa na ɗauki shi" "Duk agogon da suke na mata a mall ɗin nan ba wanda ya birgeki sai Wannan, saboda ba ke kike nemo kuɗin ba ko" ya faɗa yana kafeta da ido. "Daina kallona da Waɗan nan idanun naki maso kamada aljannu" Da sauri na mayarda kaina kasa ina kallon tiles ɗin wurin, yayinda idanuna suka sake cikowa da ƙwallah. "Ki ɗauki kayan mu wuce munafuka ko ni kike jira na ɗaukar miki" Da sauri na tsuguna na ɗauki kayan muka bar shopping mall ɗin. gaba ɗaya zuciyata batayimin daɗi, na rasa menayiwa wannan bawan Allah. Daga nan direct gida muka wuce ba wanda ya ƙara kula wani a cikin mu har muka ƙara so gidan. Ba kowa a parlourn koda muka shigo, ledojin da na shigo dasu na ajiye tare da nufar sashen mum domin sanarda ita dawowarmu. Knocking nayi kafin shigata, sai naji tayimin alama da sallah take. Shiga nayi ɗakin na sami wuri ɗaya na zauna tare da kifa kaina a ƙasa, na lula duniyar tunani. "Leeyanah!" Naji muryar mum na kiran sunana da karfi. Kamar wacce ta farka daga bacci haka na ɗaga kai na kalleta. "Tunanin me kike haka, ko wani abu turab yayi miki" Da sauri na jijjiga mata kai alamar bakomai "Mum, ba tunani nake ba kuma ya-Turab bai min komai ba sai tarin alƙairi kinga siyayyarda yamin gata can a parlour" Na faɗa ina ƙaƙaro murmushin dole. "Masha Allah, kice kunyo shopping da yawa kenan" "Eh, wallahi mum" na faɗa ina faɗaɗa fara'a a fuskata duk da nasan ba ganina take ba amma zata fahimci haka daga yanda sound ɗina ke fitowa. "Okay, Tau ki tashi kije kiyi wanka, kiyi sallah kizo daining abincinku na nan yana jiranku" "Ummmm, mum da dai kin barshi Ni bana jin yunwa gaskiya" "Bakyajin yunwa to me kikaci" "Mum, muda muka fito daga shopping zakije menaci kuma, a inda nukaje shoprite akwai restaurant ai" "Hmm, kice yau abincin waje akaci kho" Dariya na ɗan yi wacce iya bakina ta tsaya nace"eh mum amma baza'a sake ba in sha Allah" "Shikenan kije ki ɗauki shopping ɗin da kikayiwa kanki kije ki huta kinji" Godiya sosai nayiwa mum, sannan na bar sashen. Parlourn na sauka na dakko siyayyarda nayi gaba ɗaya na koma sashen mu. Ina zuwa nayi wanka, sannan nayi sallah. Rigar yadi mara nauyi na ɗakko na sanya sannan na saka after dress gown a saman kayan domin rigar tayi sharara, hijab ɗina na dakko na saka sannan na fito da siyayyarda nayi na jerasu gaban mirror. Shafff na manta da agogon hannun da na siyo, ina ganin shi kuwa na yi sauri na lalubo wayana tare da dialing number zohal. "Hello, bestie" "Na'am bestie zohal, kina lafiya yasu umma" "Su umma duk ƙalau, ya mum da papu" "Wallahi duk sai Godiyar Allah" "Har kun dawo da shopping ɗin kenan" "Eh, mun dawo. Wallahi karkiso kiga irin abunda ya turab yamin" leeya ta faɗa da raunananniyar murya. "Allah sarki bestie me yayi miki haka" Kwashe labarin abunda ya faru gaba ɗaya nayi na faɗa mata, har ma da labarin siyo AGOGON HANNU danayi. "Haba dai, amma gskiya wannan turab ɗin bashida kirki wallahi, ya cika masifa shi ba'a yimasa abun girma" "Hmm, kedai bari kawai Allah dai ya sauwaqe" "Ameen bestie, kici gaba da haƙuri kinji, tunda haka yake, haka halinsa yake kinga ko wannan shegiyar ƙanwar tashi ma bai ragamata ba" "Ke kuwa dai zohal, me khulud tayi miki da zaki kirata shegiya" "Kedai bari kawai wallahi halayen yarinyar naban haushi" "Allah dai ya sauwaqe" "Ameen leeyana, mu koma waccan maganar agogo, ya zakiyi dashi ne" "Nima bansaniba bestie, amma zan ajiye agogon har sai lokacin da ya bayyana, tunda nayi niyyar haka" "To Allah ya baki ikon cikawa" "Ameen ya rabbil alameen" Fira muka ɗan taɓa da ita mai tsayi kafin mukayi sallama da ita. Kiran mum naga ya shigo wayana da sauri na miƙe na fita daga sashen na nufi sashen ta domin nasan akwai abunda take buƙata. "Mum, naga kin kirani ne" "Eh, turab ne yace akai masa abincinsa sa a sashensa, shine na kiraki kije ki kaimasa saboda khulud bata dawo school ba har yanzu". "Tau" kawai na faɗa tare da barin wajen, domin har ga Allah banso naje sashen sa ba. Saboda tsoron haɗuwar mu dashi ne ma yasa nace bana jin yunwa amma a zahirin gaskiya ba haka bane. Yanzu gashi kuma zanje dakaina sashensa na kaimasa abinci. Faranti madaidaici na samu wanda zai iya ɗaukar kayayyakin da zan ɗora a kansa. Duk abunda nasan za'a buƙata saida na haɗa masa shi a farantin kafin na wuce part ɗinsa. Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na fara tafiya har na isa sashensa, a hankali na tura ƙofar tare da yin sallama. "salamu alaikum" "Ameen" turab ya faɗa a takaice yana zaune kan fabric chair dake can gefe a ɗakin, inda yake gudanarda duk wani aiki da zaiyi a wurin, duk wasu takardunsa da computers ɗinsa duk suna wurin. Bancemasa ƙala ba na ajiye masa abincin kan Centre table ɗin da ke tsakiyar parlourn, na juya da nufin tafiya. "Ke zo nan" Da sauri na juyo na dawo har inda yake zaune tare da dan rusnawa nace"gani ya-Turab" "Da aka aikoki haka akace kizo kibani abinci kamar wani almajira zakizo ki ajiyemin abinci ba maganar komai" "Dan Allah ya-Turab kayi haƙuri" "Rufemin baki dakeda hakurin kunci gidan ku, ƴar rainin hankali zaki wani zo ki ajiye abinci ki juya kamar wani sa'an ki. Wane irin abinci ne" "Jollof rice, sai kuma yam-porridge and fried chicken" "Basu nake so ba,,,,spaghetti Bolognese nake so, sai kuma bitterleaf soup, sannan ki haɗo min da bruschetta. Sai kuma ki haɗomin da pimm's juice, kuma ki dafa abincin na kimanin mutum uku domin zanyi baƙi" Cikin ladabi ta ƙara sunkui da kanta kasa ta amsa da "toh" Sannan ta tashi tabar sashen. Sashensu ta koma ta zabga uban dagumi tana tunanin ta inda zata fara "spaghetti Bolognese, bitterleaf soup, bruschetta, pimm's juice. Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un Wannan abun dame yayi kama" Na faɗa a raina ina ƙara takure jikina. Wayana na janyo dake yashe akan gado na buɗe da zummar kiran zohal na sanar da ita abunda ke faruwa domin ta ban shawara. Kamar dai kullum saƙonsa na gani ya bayyana kan screen ɗin wayana. Ni abun yama daina ban mamaki yanzu, saidai nace tsoro. Buɗe saƙon nayi domin ganin abunda aka rubuta "Assalamu alaikum warahmatullah my dream girl, barkanki da warhaka, barkanki da Wannan lokaci. Ina fata kun dawo lafiya kho. To ya kike yasu mum, yawwa nace ina so na tuna miki batun tsarabar da nace kiyimin idan kinje shopping, Allah sarki ashe kema kinasona kaɗan, daga yanda nake sonki kho, saboda labari ya sameni cewa kin siyamin. Gskiya ba ƙaramin farin ciki ya ziyarce niba da aka gayamin, kuma Nagode sosai Allah ya barmu tare ya mallaka min ke dream girl. Kuma ina rokon wata alfarma a gareki dan Allah ki ajiye agogon nan a wurin ki har lokacin da zamu haɗu dake sai kiban, kiyi alƙawari a cikin zuciyar ki kinji. Bye bye I love you so much dream girl, na barki lafiya" Wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya na sauke tare da runtse idanuna da ƙarfi, "mai baka kulawa ƙaunarsa daban take a ranka, ko ba komai bawan Allahn nan yana kula da ita. Ba ranar Allah dazata fito ta faɗi bai turamata saƙo ba, kuma ba saƙon da zai yi mata bai furta yana ƙaunarta ba, ko a iya Wannan ai ya cancanci ƙauna daga gareta ko kaɗan ce. Duk da ba sanin sa tayi ba, amma ya kamata ta ajiye ahi a sahun mutane masu daraja a wurinta" "In sha Allah, kuwa" ta furta a fili tana danna wa number kira, duk da tasan ba samunta zatayi ba. Cikin ikon Allah kuma sai ta sami number a kunne, da mugun mamaki tayi zumbur tare da miƙewa tsaya tana zubawa wayar blue eyes ɗin ta. Sai da wayar tayi ringing har ta yanke ba'a ɗaga ba, sake kiran wayar tayi nan ma ba'a ɗaga ba. Kiran number ta kumayi sau ba adadi saidai ba respond. Wani tunani ya faɗo mata, nan take kuwa ta shiga cikin messages ɗinta ta laluba number sannan ta tura sako Kamar haka; "dan Allah waye kai da kake bibiyar rayuwata tsawon shekara ɗaya, kagayamin dan Allah i need to know please". Bayan ta tura sakon ne tsawon mintuna biyu ba alamar za'a yi reply, nan da nan kuwa ta kira zohal suka ɗan gaisa, daga nan kuma ta gaya mata duk abunda ke faruwa, har girkin da ya-Turab ya sakata da kuma samun number bawan Allahn da yake turamata da kuma sakon Da ta turamasa itama, saidai kuma ta gaya mata ba'a ɗaga kiran ba, kuma ba'a mayarda sakon ba. "Gskiya wannan ya-Turab ɗin ya fara takuramiki bestie, meyasa bazaki gayawa mum ba, ina zaki iya da girka wani abincin ƙarti har uku, hmmm kedai kika ɗauka wallahi. Ni ba wani shashashan namijin da zan ɗaukarwa wannan, meye ma wani bitterleaf soup?" Zohal ta faɗa cike taf da jin haushin turab. Murmushi mai sauti leeya ta ɗan yi, amma kanajin sautin fitowar murmushin kasan na yaƙe ne "ummm, wallahi kuwa bestie lamarin ya-Turab sai haƙuri, bitterleaf soup miyar ganye ce da aka fiye samunta cikin igbo, kuma Ni na jima da iyata" "Cikin igbo kuma besty kina nufin bama miyar hausawa bace, lallai ma. To ke kuwa ya akayi kika iya abincin igbo kuma keda ba Igbo ba" "Na iya mana, kuma waya gayamiki ni ba Igbo bace, mahaifiyata ai yarenta igbo ne" "Da gaske bestie, yanzu mum Igbo ce" zohal ta faɗi haka ne domin ita duk a zatonta mum ce asalin mahaifiyar leeya. "Kedai kibari kawai, idan na dawo zan kiraki, Bara na tashi naje na fara aikina tun kafin yazo ya naɗamin na jakai" "Tau yayi, Allah ya taimaka sai kin dawo ɗin" cewar zohal tana yanke wayar. Miƙewa leeya tayi tare da nufar kitchen area. Aikinta ta farayi hankali kwance, domin kuwa aikin yana bukatar nutsuwa. Saida ta kammala komai, kafin ta zube ko wanne a wurinda ya dace. "Leeya me kike dafawa haka naji ƙamshi nata fita a ko'ina" Cikin mamaki na waiwayo, idan ba mafarki nake ba to Muryar khulud naji tana yimin Magana. Mamaki bai ƙarasa shigata ba saidai na waiwaya naga fuskar ta ɗauke da murmushi. "Bazaki amsa min ba leeya, kiyi haƙuri da duk abunda ya faru a baya kinji, ki zo mu zauna lafiya kinji komai ya wuce dan Allah" khulud ta faɗa tana dafa kafaɗuna. Saboda tsananin mamaki, maganar ma kasa fitowa tayi daga bakina, sai da kyar na samu nace mata "ya-Turab ya sakani nayi masa girki". "Uhhm khulud tayi murmushi kaɗan "kaga ƴan CATERING SCHOOL gidan namu sai ƙamshi yake, Bara na barki kiyi aikinki saboda nasan halin ya-Turab yanzu zaice kin ɓata masa lokaci" Ko amsa mata banyiba, ta juya ta fita daga kitchen ɗin. Jikina gaba ɗaya ya mutu da ganin sauyin khulud domin ina tunanin kamar wani abun take shiryawa.......✍🏽 BAYAN WUYA...... By RUMANA M DIGGI EP.30 _________________da kyar na samu na kammala sauran aikin da ya rage bayan na haɗa masa pimm's juice. Jido kayan na farayi daga kitchen zuwa sashensa, sai dai har na kusa kammala kai kayan ban ganshiba. sosai hakan yamin daɗi, na koma kitchen da nufin dakko juice ɗin da na hada masa, ina fitowa sashen nasa sai nayi karo da khulud itama ta fito da system a hannu tana tafiya tana ɗan dudduba wa, da alamu wani abun mai muhimmanci take dubawa. "Leeya har kin kammala aikin" "Ah ah juice kawai ya rage na kaimasa shikenan na kammala sannan nayi wanka nayi sallahr la'asar" "Okay dan Allah idan kin kammala duk abunda zakiyi kizo ki tayani yin assignment saboda naga kin iya mathematics sosai lokacin da muna BUSY BRAIN" "Okay ba damuwa ki jirani kaɗan yanzu zan kammala" na faɗa ina wujewa batare danaji abunda zata faɗa ba. Juice jug ɗin da na haɗa masa na ɗakko tare da komawa sashen nasa, kamar yanda nayi tsammani kuwa ban tarar dashi a parlourn nasa ba kuma hakan yamin daɗi sosai, na juya da nufin na fita muka kusa cin karo dashi, da sauri na ja baya da ƙarfi ina toshe bakina gudun kar kuka ya suɓucemin nayi wani laifin kuma. "Ke! Dan ubanki wari nake da zaki wani toshe baki da hanci" Jijjiga kai na farayi kukan da nake riƙewa ya suɓucemin "dan Allah ya-Turab kayi hakuri, wallahi ba warinka nakeji ba, ina jin tsorone kar kuka yazo min kuma nayi maka laifi shine na rufe bakina, amma wallahi bada niyyar komai nayi ba" "Me zai sakaki kukan, dukanki akayi da zakizo daga shigowar ki nan sai ki fara kuka, daina kallona da waɗannan mayun idanun naki ko yanzu ki gansu a ƙasa, shegiya mai siffar aljanu. Fita daga nan kiban wuri ko yanzu na karyaki wallahi" Da sauri na raɓe ta gabansa zan wuce, wawan rankwashi ya sakarmin akai naji kamar dutse ne ya dakeni dashi. "Wayyo ya dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan sake kallon ka ba" na faɗa cikin matsanancin kuka. "Bar nan nace" Da sauri na fito part ɗin nasa ina cigaba da tafiyata ina share hawayen da ke zubowa, jinayi an dafa kafaɗata ta baya. Ban wani razana ba saboda sanin cewa mum ce, juyowa nayi a hankali na kalleta da sauri ta jaa baya da ƙarfi. "Khulud lafiya naga kin jaa baya kamar wacce taga wani abun tsoro" Na faɗa cikin sassanyar murya irin ta wanda yayi kuka ina ƙara tsureta da idanuwa na. "Ke zanyi wa wannan tambayar leeya meyasameki kike kuka, ya-Turab ne kho" Da sauri na ɗaga mata kai ina ƙare rushewa da kuka. Cikin tausayawa khulud tace "kiyi hakuri kinji, wallahi lamarin ya-Tk sai shi, kinga Ni na huta bana ma wuni a gidan ina school, kuma idan na dawo yamma tayi bana ganinsa sosai sai idan an fito cin abinci, da safe kuma koda nakeyin break fast ɗina bai fito ba, idan na tafiyata bana dawowa sai yamma, kinga ba yanda za'a yi mu dinga haɗuwa". "Khulud dan Allah wani abun kikeso kiyimin ne" Dan murmushi khulud tayi domin ta fahimci abunda nake nufi "me kika gani ne leeya, ko saboda kinga nayi miki magana, wallahi dama can rashin fahimtar rayuwane yasa nake miki irin haka, yanzu dana faɗa tarkone yasa nake ganin nayi babban kuskure a can baya, saboda haka ina neman gafararki kinji" Khulud ta faɗa har iyakar gskiyarta tana haɗe hannayenta biyu wuri ɗaya alamar roƙo. "Leeya, wallahi na faɗa ƙaddarar soyayya ne da wani bawan Allah, wanda nasan samun sa zaiyi matuƙar wuya a gareni sakamakon abokinsa" "Abokinsa kuma" na tambaya da mamaki, "abokinsa ne zai hanaki mallakeshi" na kuma tambayarta. "Eh, abokinsa zai hana na mallakeshi domin id wani Mutum ne da yake saurin yarda da mutane musamman ma abokinsa, shi kaɗai ne amininsa a kaf faɗin makarantar mu, kuma duk abunda ya sakashi shi zai aikata, idan kuma ya hanashi ya hanu kenan. Haka shima idan ya umurce shi da yin abu koda bayaso sai yayi saboda ya faranta masa rai kuna idan ya haneshi ya hanu kenan" Khulud ta faɗa kwalla na gangaro mata. Taci gaba da faɗin "zakiji cikakken labarin in sha Allah, kibari duk ranar da kika nutsu kizo ɗakina muyi magana ko kuma ni na sameki a ɗakin naki" Tausayinta ne ya kamani sosai ganin yanda take zubarda hawaye akan ɗa namiji, "kiyi haƙuri kinji, in sha Allah zamu shawo kan matsalar, kuma zan tayaki da addu'a idan hakan alƙairine Allah ya tabbatar miki. Kuma zan kira ƙawata zohal in sha Allah, itama zata bada idea" "Nagode sosai kinji, dan Allah ki yafemin gaba ɗaya. Wallahi har kunyarki nakeji" Cewar khulud. "Allah sarki, wallahi khulud Allah ne shaidata ni tun farko ban taɓa riƙeki a rai ba, saboda haka komai ya wuce kinji" "Yawwa Nagode, sai kin fito kho gani nan a parlour ina jiran ki" "Okay" leeya ta faɗa tana barin wajen. Haƙiƙa khulud taji tsoron ganin leeya a yau, tunda take da leeya bata taɓa haɗa idanu da ita ba balle tasan yanda idanunta suke, asalin pure blue. Da suka haɗa ido da ita, ta tsorata matuka har takai ga ta jaa baya da ƙarfi, amma kuma sai ta nuna mata ba komai. Saboda karta fahimta. *** A can ɓangaren leeya kuwa tana komawa part ɗin ta tayi wanka tare dayin sallah, Sannan ta shirya cikin riga da skirt na jumper cotton silk. Ɗan ƙaramin mayafi ta ɗakko ta yafa, sannan ta saka niƙab ɗin ta. Wayarta dake a jiye a gefe ta gaban dressing mirror ta ɗakko, number zohal ta lalubo tare dayin dialing number. Bayan ta ɗaga wayan ne sun ɗan gaisa, da yake ba wata gaisuwar kirki sukayi ba domin basu jima da gama wayar ba. Leeya kuwa ta fara koro mata bayanan dalilin da yasa ta kirata. Murmushi mai sauti ZOHAL tayi tare da faɗin "baza'a bata shawarar ba taje can ta ƙarata, wallahi wannan yarinya ta raina wayon mutane, sai yanzu tasan kinada muhimmanci da zata nemi shawarar ki, taje can wurin masu kuɗi irinta ta nema, wallahi amanar ki ce kawai ke fita a kanta, saboda haka mu bamuda abunda zamucemata sai dai Allah ya kyauta, ya kuma bata ƴan uwanta masu kuɗi da zasu bata shawarar abunda ya dace" "No zohal, wannan ba reason bane kawai kisamu abunda zakice kinji Please. Ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba kuma Ni wallahi ban taɓa riƙeta a raina ba kinga ko yanzu ita ta kawo kanta gareni, wannan alamace daga wurin Allah da yakeso ya jarraba iyakar hakurina, kinga tun muna yara tayi min abubuwa da dama da bana tunanin mantawa dasu, har kuma muka girma bata daina ba ni kuma ban daina abunda nake ba tun a farko wato haƙuri, yanzu kuma ta kawo kanta tana nunamin kuskuren nata ne, kuma bata fahimci rayuwa ba a can baya. Ai kuwa kinga dole nayi mata uzuri kho, ko dan mahaifin ta da mahaifiyar ta zan mata komai Zohal" Jikin zohal yayi sanyi sosai da jin kalaman leeya saboda haka ne tace "to shikenan yanzu ki tambaye ta idan har wani abu ya taɓa shiga tsakanin ta da abokin shi wanda takeso ɗin, idan kuma ba abunda ya taɓa shiga tsakanin su nan ma zamu fahimci wani abu" "Yawwa bestie na haka nakeso naji kin faɗa Nagode sosai" "Ya batun Private lover ɗin ki" "Hmm kedai bari kawai, har yanzu ba reply" "Okay to kiɗan kara haƙuri kadan, ki bada lokaci muga. Ko ki kara kiran number" "Ke nifa har na gaji da kiran wayarsa domin kona kira ba'a ɗagawa, banaso kuma na cika yawan kiran kuma yazo kashe wayar alhali na tura masa saƙo kuma bai yi reply ba, kar garin neman gira a rasa ido" "Haka ne kuma fa, to kijira mugani" "Okay" ta yanke wayar da faɗin wannan. ***** A can ɓangaren turab kuma; Tunda leeya tabar sashen gaba ɗaya ya dauki daddaɗan kamshin girkin ta, juice jug ɗin da ta haɗa masa ya ɗaga tare da tsiyayawa kaɗan yasha, yana isa cikin maƙoshinsa kuwa ya lumshe idanun sa ya ƙara buɗewa, ƙara tsiyaya wa yayi yayi fiye da rabin cup ya kuma kai bakinsa ya shanye. Sosai yayi mamakin yanda ta iya haɗa pimm's juice lafiya ƙalau haka, domin rabonsa da shan daddaɗan juice irin wannan tun a Mexico. Ƙarar wayarsa yaji Alamar kira ya shigo, a nutse yakai hannu ya ɗauki wayar yayi gyaran murya. "Hello man fahad ango ya akayi kun ƙaraso" "Eh gamu a gate" "Okay ganinan tafe" Ajiya wayar yayi tare da nufar hanyar fita. **** Leeya kuma bayan ta gama waya da zohal ta tashi ta fita waje, a parlour ta sameta sai faman aiki take a system. "Leeya kin fito" "Eh, na fito wallahi kinga har na kammala nayi wanka shine na fito muyi assignment ɗin idan mun kammala kuma sai naje na ɗora girkin dare" "Tau shikenan, kiyi sauri mu kammala sai muje nima na tayaki girkin kho" Cikin mamaki na ɗago zanyi magana ta takatardani da faɗin "Leeyana ya kamata ki daina mamaki a duk al'amurana, kinsani ba abunda yakeda wuya a wurin Allah, kuma wani iko na Allah ya wuce gaban mamaki" Ban furta komai ba na mayarda kaina kan system ɗinta muka fara aiki. "Kinsan me" khulud ta faɗa tana kallona. "Ah ah sai kin faɗa" "Ki tashi muje Library room ɗin mu muyi assignment ɗin nan, NASAN yanzu ya turab zai shigo kuma naji fakawar motoci ina tunani yayi baƙi ne, dan har waya naji yana yi yanacewa "ku shigo mana ko gidan baƙon kune. Kuma naga kina tsoron sa sosai shiyasa nace kizo mu bar nan kar ya shigo, NASAN su ya fahad da ya Zafaran ne sukazo kinga ba kunyarsu yakeji ba ko a gabansu zai iya cimana uba". Tunawa leeya tayi da ya cemata tayi girkin mutum uku, nan da nan kuwa ta gaskata abunda khulud ta faɗa mata. da azama suka miƙe suka bar parlourn. Suna shigewa kuwa sai gasu turab sun ƙara so parlourn sai sheƙa dariya suke abunsu, Zafaran kam kamardai ko yaushe idan ya shigo suleja, dafe yake da saitin zuciyar sa, sai kiran sunayen Allah yake a bakinsa. Turab ne ya ɗan dubeshi kaɗan cikin sigar zolaya yace " lewa ta motsa kho" "Hmm, bari kawai man turab, wallahi duk inda lewa take a yanzu motsin ta yana tafiya da motsina da kuma kowane harbawa da zuciyata takeyi a halin yanzu" "Iyyeee kaji majnoon a gaskiya wannan yarinyar ta wahalar damu, ina tabbatar maka idan Allah ya ƙaddara saduwarmu da ita saita biyamu ladar wahalar da mukesha wallahi, ko ya ka gani man Fahad" cewar turab yana mayarda kallonsa ga Fahad. "Eh mana ai shima kansa yasan sai ta fanshe wahalarda mukayi akanta kota hanyar girka mana abinci mai daɗi ne" Tattausan murmushi Zafaran yayi sannan yace"lallai kuwa zata fansar da kanta har kuma ta fanshe Ni Nima indai ta hanyar abinci ne, domin a ta Wannan ɓangaren kan ta wuce boss" "Ae dai zamu gani" Fahad ya faɗa daidai lokacin da suka ƙara so sashen nasa. Zama sukayi a ɗan madaidaicin Centre carpet ɗin da ke tsakiyar parlourn, inda turab ya fara jido musu abincin da yasa aka girka musu, sosai suka ƙagu da su fara cin abincin domin ƙamshin sa ya kaimusu ko'ina. Bayan ya buɗe abinci ne kowa ya ɗiba wanda yasan zai iya cin yewa, cooler da aka saka bitterleaf soup Zafaran ya buɗe, cikin matuƙar farin ciki ya kalli Turab yace"wannan ai miyar igbo ce, kuma igbo kaɗai suka iya haɗa miyar nan ta fito sharrr da ita kamar haka, dama mum igbo ce ba bafulatana ba" "Uhmm--hmmm, ba mum ta dafa ba" "Kunada House-maid igbo ne" "Ah ah" "Waya dafa to" Zafaran ya kuma tambaya. "Wata yarinya ta dafa, nima na faɗa ne kawai wallahi banyi tunanin zata iya dafawa ba, kuma dana sakata ba musu ta tashi taje tayi kaga alamar ta iya kenan" "Ita yarinyar igbo ce" fahad ya tambaya yana kai bruschetta bakinsa. "Wallahi nima bansanshiba, ƴar ƙawar mum ce data rasu shekarun baya, kuma bana tunanin mahaifiyarta igbo ce gskiya, saidai ko mahaifinta duk da bansanshi ba". "Ikon Allah amma tayi ƙoƙari gaskiya" Zafaran ya faɗa cike da al'ajabi. Cin abincin su suka farayi cikin kwanciyar hankali har suka kammala gaba ɗaya, aka kira sallahr magariba sannan suka bar gidan bayan sun shiga sashen mum sun gaida ita. Dayake papu baya ƙasar yasa basu jira dawowarsa ba suka yi tafiyarsu. ***** A can ɓangaren su khulud kuwa bayan sun kammala assignment ɗin da aka bata, sai suka nufi kitchen domin girka abincin dare. Khulud ce ta kalli leeya cikin kulawa tace; "Sis-leeya me ya kamata mu girka" Ɗan ɗaga kaina nayi kaɗan ina tunanin abunda ya kamata mu girka da daren nan kafin nace "mu dafa jollof rice da fried potatoes kho, sai kuma muyi fried plantains" "Wow gud ideas wallahi kamar kinsan ina kwadayin fried plantains, fara aikin ko mr. Chief kinsan ba komai na iya yi ba" khulud ta faɗa tare da laƙato hancin leeya. Itama leeya ta rama abunda tayi mata, cikin nishadi. A can kofar kitchen ɗin kuma mum ce tsaye, farin cikin ta ya kasa ɓoyuwa na ganin yaran sun haɗa kansu. "Allah yasa ku ɗore haka ƴaƴana" ta faɗa a zuciyarta tana barin kitchen area ɗin. Saboda ta taso ne ta taya leeya aiki kar ta barta da aikin ita kadai yayi mata yawa, ganin khulud na tayata yasa ta koma domin tayi wani aikin duk da ba wani aiki daya rage domin kuwa gaba ɗayan gidan ba inda basu tsaftace ba. Sai kusan karfe bakwai da rabi na yamma suka kammala aikin komai da komai kaana suka wuce sashensu, ko wacce ta nufi ɗakinta domin su huta. Leeya na shiga ɗakin nata tayi sauri takai hannu ta ɗauko wayanta jin ƙarar shigowar saƙo. Sai dai wani abun ban haushin koda ta buɗe saƙon na MTN ne bawai sakon da takeso ta gani ba. Ajiye wayar tayi tare da nufar ban daki tayi wanka, tayi alwala kaana ta fito ta saka kayanta, ta zumɓula babban hijab ɗin ta ta tayarda sallah. Tana cikin sallar ne taji ƙarar buɗe kofa, khulud ce ganin leeya na sallah yasa ta juya ta koma bedroom ɗin ta. Leeya kuwa tana sallame sallar tayi addu'o in da zatayi sannan ta ninke sallaryar ta maida ta inda take ajiyeta tabar ɗakin nata. Bedroom ɗin khulud ta nufa bakin ta ɗauke da sallama cikin siririyar muryarta. "Khulud ya dai, ya kike, ya gajiyar aiki kuma" "Gajiya kam tana nan wallahi, ai naje bedroom ɗin ki kina sallah" "Eh, wallahi shine na kammala nazo ai" "Ok tau muje daining, dama shine naje na faɗa miki kuma na tarar kina sallah" "Da kin bari anyi sallar isha ai tunda kinga saura kaɗan". "Okay tau ai ba damuwa mu Bari idan aka yi sallar sai muje" Cewar khulud. "Yawwa, na kira zohal munyi magana da Ita, kinji yanda tace min" leeya ta kwashe kaff yanda sukayi da zohal ta gayamata. "Eh, a gaskiya zohal bata faɗi karya ba, wannan shine abunda yakamata na fara dubawa tun a farko, Sayyid maleek al-shams shine cikakken sunansa, kuma shine babban abokinsa na hakiƙa. tun ranarda muka fara haɗuwa da sayyid jininmu bai haɗu dashi ba, kuma babu rana ta Allah da zata fito idan mun haɗu da sayyid bamuyi faɗa ba, bama ƙaunar Sayyid ko kaɗan haka zalika shima baya ƙaunarmu, mu huɗu ne kawayenmu kuma tare muke komai duk halayenmu ɗaya ba abunda ya banbanta , sai ɗaya daga cikinmu ce da ake kira reemah rabeel, ita kaɗaice ta banbanta damu kuma ita kadaice take shiri da Sayyid duk a cikinmu. leeyana zakiyi mamaki sosai idan nace miki Sayyid shine babban abokin wanda zuciyata take bege dare da rana, kuma shi wannan danake ƙauna wato IDRAK MANAF, sabon ɗalibi da aka kawo mana a School ɗin mu ne, amma babban abunda ya kamata kiyi mamaki akansa shine shi Wannan mutumin da nake ƙauna wallahi talakane sosai kuma bashida mahaifi mahaifiyarsa ita take ɗauke da nauyi su da taimakon sa shima, da sana'ar faci da yake yiwa babura da motoci. da Farko da muka ganshi munyi tunani shima mai kuɗi ne kamar Sayyid, ashe ba haka bane yanda mukayi zato domin kuwa wata rana da muka fita ranar weekend nida ƙawayena motarmu tayi faci, da muka tambaya aka nuna mana inda akeyin faci bamu tsaya ko ina ba sai gaban rumfarsa dayakeyin faci, a razane na kara daga kaina na kura masa idanu domin tabbatarda shine koba shi bane, ban gama tantance wa ba naji raudha ta daki kafaɗa ta da ƙarfi "ke id nake gani ko idanuna ne" "Wallahi shine, raudha duba fa kingani" cewar amrah tana ƙara kafeshi da idanu. Murya na rawa na kira sunan shi "id, ina mai wurin nan" Miƙewa Id yayi da murmushinsa yazo har gabanmu da kuma abun yin faci a hannun sa. "Id tambayar ka nake ina mai wurin nan" "Wa kika gani anan Hajiya, faci za'a muku?" Idrak ya faɗa yana durƙusawa gaban tayar motar mu. Da sauri raudha ta banko ƙofar motar ta fito ta nufeshi ta cewa "kai wai da gaske kaine anan, faci kake yi kuma kake karatu a Rooney" Ta faɗa cike da cikin tsiwa da masifa. "Hmmm" kawai idrak ya faɗa yana ƙoƙarin fara aikinsa. Da sauri amrah ta fizge abunda yakeyin faci dashi tayi cilli dashi gefe ɗaya "malam magana ake maka kayi banza da mutane, ko dai bakai bane IDRAK MANAF ba na Rooney. Cikin tsananin ɓacin rai id ya kalli amrah da raudha yace.............................✍🏽 BAYAN WUYA........ By RUMANA M DIGGI EP.31 _______________"malamai idan kun tashi ku ɗaga nayi muku aikin ku, idan kuma ba aikin kukeso ba dan Allah ku tafi daga nan" Dariya amrah da raudha suka sheƙe da ita harda yin tafi,duk abunda su raudha da amrah keyi a zamanmu dasu ban taɓa yin haushin su ba sai a yau ɗin nan da sukayiwa id, kuma bansan dalilin da yasa haka ba. "Amrah Dan Allah a taimaka masa da abunda zai ja jari" Raudha ta faɗa cikin izgilanci. "Gaskiya ya kamata a bashi jari kuma fa tunda kin ga sana'ar faci ba sana'a bace" Dawowa raudha tayi mota ta ɗauki hand bag ɗinta, nidai inata kallonsu ban cemusu uffan ba. Domin kuwa jikina yayi sanyi likiss kuma bansan dalilin haka ba. Komawa tayi inda id ke tsaye, tare da buɗe handbag ɗin ta taciro bandir uku na ƴan dubu dubu, ta ɗan juyasu kaɗan a hannun ta. "Amrah ai kuɗin nan zasu ishi mai faci ya ja jari kho" "Sosai kuwa raudha, har jarin wankin mota ma zai samu, kinga ya haɗa biyu kenan da faci da wankin mota" Sake sheƙewa sukayi da dariya ita kuwa raudha ta watsa masa kuɗin da ke hannunta "gashi nan, ka dauka kaje ka....." Tassss taji saukar mari a fuskar ta, tun kafin ta gama tantance ko waye taji an sake saukar mata da wanda yafi na farko zafi . Da kyar ta ɗaga idanunta ta iya furta "id! sayyid ku kuka mareni, to wallahi baku mari banzaba musamman kai idrak na rantse daidai da wannan rumfar taka sai tayi maka wuyar zama balle makarantar Rooney kuma kajira ka gani" raudha ta ƙarashe maganar tana sakin kuka. Da sauri na fito daga cikin motar ganin id da Sayyid sun mari raudha lokaci ɗaya, babban abunda yaban mamaki shine ganin sayyid a wurin alhali kuma koda mukazo wurin bayanan. Cikin matsifa na ƙarasa gabansa da sauri na ɗaga hannu na mareshi nima domin na ramawa raudha marinda yayi mata. Caraffff naji an riƙe hannunta. Ba kowa bane ya riƙemin hannu face id. "Wallahi karki sake wannan ƙazamin hannun naki ya taɓa fuskar Sayyid, idan kuma kikayi kuskuren aikata haka wallahi sai dai kici gaba da ganinta yashe a ƙasa domin san na rabata da gangar jikin ki" Cikin mamaki naji na kasa mayar masa da martanin abunda yayi min, sayyid kuma inda yake shiga ba nan yake fita, amrah da raudha har ma Ni ba wanda ya ƙyaleshi, haka mukaci gaba da ɗauki ba daɗi tsakanin mu dasu, hardai wasu dattijawan da ke sana'a a wurin sukazo suka rabamu dasu ko wa ya kama gabansa, yanzu kwana biyu kenan da mukayi abun nan. Kuma tunda muka samu misunderstanding dasu nidai ban ƙara sakasu a idona ba, kuma tun a wannan lokacin soyayyar id ta kamani ta hanini sukuni, wallahi leeya bana ganin kowa sai shi. Khulud ta faɗa tana saka yatsa tare da goge hawayen da suka zubo mata taci gaba da cewa "Babban abunda yake bani tsoro taya zan tunkareshi da maganar, kuma ya su raudha da amrah zasu ɗauki maganar. Wallahi akwai kunya gskiya ace kamar ni na rasa wazan faɗa a soyayyar sa sai talaka mai faci a titi" Khulud ta ƙarasa labarin nata cikin rauni da gazawa. "Khulud kenan, kin manta da Allahn da yayi ki mai kuɗi shi yayi id talaka mai faci a titi, ko kuma kin manta da Allahn da yayi ki ƴar ministan shari'a shi ya saka soyayyar mai faci a zuciyarki wanda ba kowa ba, ba kuma ɗan kowa ba, sannan kuma.kisani ita soyayya bata shawara balle ta zaɓi mai dukiya ta hadashi da mai dukiya, ko kuma ta zabi talaka ta hadashi da talaka dan uwansa,. soyayya ikon ta take ba shawara take ba" "Duk nasan da wannan leeya amma wallahi Allah bai ƙaddarceni da gane hakan ba saidai na faɗa soyayya" "Haka Allah yake al'amuran sa khulud, dama a rayuwa kana naka ne Allah na nasa, kinga ke ko kaɗan a rayuwarki baki taɓa tunanin akwai rana ɗaya da zatazo ki haɗa inuwa da talaka ba, kuma rayuwarki ma ta baya ba abunda kika fi tsanar gani da kuma ji kamar talaka, sai gashi Allah ya nuna miki ƙudurar sa cikin sauƙi ya saka kin faɗa soyayyar talaka, a maimakon ace talakan ne ya faɗa soyayyarki. Amma yanzu duk ba wannan ba, dha nayi tunanin lamarin nan mai sauƙine ashe yafi gaban tunanina, domin kuwa ba babban kuskuren da kika aikata kamar yunkurin marin Sayyid da kikayi a gaban id, kuma ta dalilin sa sayyid yaje wurin, da yazo kuma yaga ana cimasa zarafi har gaban kasuwancinsa sai ya shiga maganar domin kare abokinsa da wulaqanci da kuka yi niyyar yi masa. Kinga tun a farko dama baki fito motar ba, tunda kinga ko da sayyid yazo baiyi tunanin ku uku bane saboda su biyu kadai yagani ke bai ganki ba, sai kuma kika fito da abunda yafi wanda su raudha sukayi, domin su basuyi yunƙurin bugun kowa ba, ke kuma kinyi. Babban abun haushin ma kuma wanda kikeso ɗin shi ya riƙe miki hannu har yana ikirarin zai rabata da gangar jikin ki. Kinga kuwa ba yanda za'a yi kije masa da maganar soyayya yanzu kuma ya amsa miki, amma dai kuma baza'a fasa ba saboda ba'a fitar da rai daga Rahmar Allah" leeya ta faɗa cikin tausayawa halin da khulud ta tsinci kanta. "Wallahi nima wannan ne tashin hankali na, domin nasan ba yanda za'a yi id ya karɓi soyayya ta, koda ya karɓa kuma sayyid bazai barshi ya zauna dani ba nasani, duk a cikin mu sayyid yafi tsanata da yawa. Nima kamar yanda yake nuna ya tsaneni haka nake nuna masa harma nawa yafi nashi" Dafata nayi cikin son kwantar mata da hankali, domin kuwa duk wanda ya tsinci kansa cikin halin da take ciki abun tausayawa ne, duba da yanda hawaye ke faman tartsuwa a idanunta. "Ki kwantarda hankalinki kinji, in sha Allah zamu sami mafita zan kirawo zohal tazo gidan nan sai muyi Magana baki daya. Kuma abun da nakeso dake kibar wannan zancen a matsayin sirri tsakanin ki da zuciyar ki, karki bari amrah ko raudha suji har ma ita kanta reemah domin hakan zai iya janyo wata matsalar daban, kuma kiyi saurin dakatar da raudha cikin hikima da matakin da takeso ta ɗauka game da Id, domin kuwa idan kika kuskura kika bari ta ɗauki matakin sanya mahaifin ta ya koreshi daga Rooney wallahi kinyi Babban kuskure kuma kin rasashi, domin kuwa a kullum zai dinga dubin harda saka hannun iyayenku a ciki, saboda haka kisan yanda zakiyi ki hanata aikatawa" "Hakane leeya, zanyi ƙoƙari daga yau zuwa gobe nayi tunanin abunda zan sanar da ita". "Tau shikenan yanzu ki tashi kiyi alwala muyi sallah, sai mu tafi daining kho". "Ke dai kije kiyi sallah nikam ina cikin jar mota" Siriyar dariyar ta tayi domin ta fahimci abunda khulud ke nufi. Bedroom ɗin ta ta koma sannan tayi alwala tayi sallahr isha kaana ta fito suka haɗu da khulud suka wuce daining. Sosai mum ta nuna farin cikin ta da wannan sasanci da aka samu tsakanin leeya da khulud, haka suka ci abincin su cikin nishaɗi da wasa da dariya. Su uku ne kacal a gidan domin kuwa dad yaje ƙasar NAYAH tun wancan sati, shi kuma turab ya fita dasu ya-fahad baya nan. Bayan mun kammala cin abincine muka koma parlour, sosai mukasha fira da mum da khulud, haka mukayi firar mu cikin farin ciki da nishaɗi har sai ƙarfe goma da kwata kafin mum ta sallami kowa, bayan mun koma sashen mu saida muka tattauna batun id, dayake kuma da muka koma sashen namu sai da nakira zohal na sanya speaker tare da bata labarin duk abunda yake faruwa tsakanin khulud da sayyid da kuma id. Sosai zohal ta tausayawa khulud kuma ta bada shawarwarin da khulud zatayi amfani da su wajen janyo hankalin id, da kuma yanda zata kyautata zamanta da sayyid koda yana wulaƙanta ta karta daina hakan zai janyo id yayi magana koda baya sonta ɗin zai iya yin magana kan Sayyid yadaina abunda yake, daga nan kuma ta samu wata hanyar shiga rayuwarsa. Haka dai muka dinga bata wasu shawarwari da muke gani za'a sami nasara idan akayi amfani dasu. Miƙewa nayi da nufin in tafi, khulud kuwa ta riƙeni wai na kwana a ɗakinta ta sami abokiyar fira. nayi nayi tace ba inda zanje sai dai idan ɗakina zamuje mu kwana, haka muka fita muka koma ɗakina a can muka kwana. Can cikin dare misalin ƙarfe sha biyu na dare, naji ƙarar shigowar saƙo a wayana, Khulud kam tuni tayi nisa a baccin ta da alama. miƙewa nayi da kyar domin baccine a idona, dan gefen pillown da nake kai na ɗaga na fito da wayar. Da sauri ta miƙe zaune ganin number nan ce da ake tura mata saƙo da ita, cikin matukar ƙaguwa ta bude saƙon da aka turomata da shi kamar haka; Barkan ki dai my dream girl, ina fata kina cikin ƙoshin lafiya kho, wallahi ina kewarki sosai na kasa bacci da nutsuwa ne, ina so injiki koda kaɗan ne, a game da tambayar ki kuma, sanin waye ni a yanzu bayada wani amfani. Zaifi kyau abi tafiyar a hankali yanda tazo kar ayimata garaje, domin kuwa idan muka saka sauri mun tafka babban kuskure, kuma zaki gane amfanin hakan nan gaba kaɗan. Nidai abunda nake roƙonki don Allah ki taimaka ki dinga bani lokacinki mu dinga magana dake anan a kuma Hakan nan, idan nace a nan ina nufin nan, wato ta hanyar turamin da saƙo, nima kuma na turamiki, banda tsananta bincike dan girman Allah. bazai yiwu na kiraki ba ko kuma ke kinkirani, ah ah duk wannan zai faru ne idan komai ya tashi bayyana. Wallahi ko contacts ɗin ki kawai na tsurawa ido zuciyata na samun sauƙin raɗaɗi da azabar wutar sonki da ƙaunarki da take daɗa ruruwa a duk wani lungu da saƙo na rayuwata baƙi ɗaya, idan kikayimin wannan kin taimake Ni sosai, kuma kin ceci zuciya ta daga faɗawa hallaka, bye bye I love you more than words can describe wallahi daga zuciya ta komai ke fitowa Leeyana ina sonki da ƙaunarki da muradin ganin kin zama Uwar ƴaƴana, sai da safe ki huta lafiya. Amma kuma dan Allah inaso zuwa gobe da safe ki yanke shawarar da zata zama mafita ga ko wannen mu. yarda Dani, ko akasin haka. Duk wanda yayi miki a ranki zaɓinkine, kuma ra'ayin ki ne, kuma bazan hanaki ba, tunda ke kika ɗauka. amma ki tuna da girman so da masoyi a duk tsawon lokacin da zaki ɗauka kina tunanin mafita". Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke a fili tare da miƙewa ta tashi daga kan gado, wayar ta fara jujjuyawa a hannunta cikin wani yanayi da ita kanta batasan wane yanayi bane domin kuwa zuciyarta ta tsaya chakkk!! ba komai dake aiki a cikinta hakan kuma ya bada gudunmawa sosai wajen dakatarda duk Wani abu da zatayi tunani a cikin ƙwaƙwalwar ta. A daren ranar kasa runtsawa tayi domin kuwa tunanin wannan bawan Allah ya hanata saƙat, ko wane second da minti shi take tunawa da kuma saƙonsa da ta karanta ba adadi. Domin kuwa idan tambayar ta za'a yi ba abunda zata manta a cikin massage ɗin kamar wacce aka ce mata hardace shi zatayi. Haka tanaji tana gani idon ta ya ƙeƙashe kyam ba alamar bacci sai saƙawa take da kuncewa take a ranta har akayi assalatu. ɗan hasken screen ɗinta ta kunna sannan tayi amfani da shi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito. Kayan baccin da ke jikinta ta sauya zuwa doguwar rigar jalabbiya ta mata, tare ta janyo ƙatoton hijab ɗin ta Ta zura. Batayi ƙoƙarin tada khulud ba Domin ta faɗa mata period takeyi a kwanakin Nan. Sallahyarta ta ɗakko tare da shimfiɗata, Sannan kuma ta juya ta ɗakko Al-qur'ani tare da hisnul-muslim ɗinta ta ayije. Raka'a biyu ta farayi kafin a tayarda sallar asuba wato raka'atanil-fajhr, bayan ta sallame ne ta ɗakko qur'ani ta fara karantawa a nutse cikin sanyin muryarta. Ta ɗauki lokaci kadan tana karatun kafin taji an tayarda sallah, miƙewa tayi tabi jam'in Sallar domin tanajin duk abunda ake faɗa har aka kammala, tasbihi ta soma yi, bayan ta yi iya gwargwadon abunda zata iya ta ajiye, kaana ta ɗauko qur'ani shima ta kammala ayoyin da suka rage mata saura ta ƙarasa karatun suratul-ahzab. Tana kammala karatun ne ta ɗakko hisnul-muslim shima ta ɗan dubbuba kafin ta mayarda hankalin ta wajen azkar. Saida ta kammala tsaff kaana ta roƙi Allah ya tsare ta ya kuma bata kariya da kuma sauƙin duk abunda zai tunkaro ta Indai na cutarwa ne, daga Nan kuma tayi addu'a tare da neman zaɓin Allah kan lamarin mutumin nan da bata san ko shi waye ba. Tana gama addu'ar ta tofe ta shafe Sannan ta tashi daga wurin, duk abunda tayi amfani da shi ta mayardashi muhallinsa kamar darduma da kuma ƙur'ani. Komawa tayi ta zauna tare da zabga uban tagumin tana neman abunda ya kamata tayi, domin harga Allah ita tanajin wannan bawan Allah a ranta, amma ita a ganin ta bazata iya miƙamasa yardar taba tunda ko saninsa ba tayiba kar tayi abunda zai saka tayi dana sani daga baya. "Leeya, me yake damunkine tun ɗazu kin tsurawa wuri ɗaya idanu" Sai da ta dan bugi kafaɗarta tana kuma maimaita abunda ta faɗa. Kamar wacce ta farka daga bacci haka ta kalli khulud dake tsaye akanta tace"ulud yaushe kika tashi?" "Nima bansaniba amma ba yanzu natashi ba na ɗan jima da tashi amma tun sanda na tashi na ganki a haka har na shiga toilet na fito kuma kina a haka, me ya ke damunki ne" "Ba komai kawai" "Haba sis-leeya taya zaki ce ba komai Alhali duk wanda yaga yanayinki yasan akwai abun da ke damunki" "Uhmm--hmmm, ba komai ke damuna ba" "Hmmm, a tunani na daidaiton da muka samu zai iya mayarda mu kamar yaya ta ƙanwarta ko kuma ƙawaye ko kuma ƴan uwa, kuma waɗan da zasu dinga faɗawa juna sirrinsu ko kuma wani abu dayake damunsu, sai yanzu na gane sha-sha-shan tunani ne yake bani haka ba gskiya bane, kiyi haƙuri Kinji nina shiga lamarin da ba nawa ba" Ta faɗa lokacin da take miƙewa zata tafi cikin yanayin ta mai kamada fushi. Da sauri leeya ta riƙo hannun ta da lafazin mai taushi tace "zauna muyi magana ƴar uwata, kiyi min uzuri Please wallahi abun nan yanada mamaki ne bansaniba ko zaki iya fahimtar abunda zan faɗa miki, amma kiyi hakuri kinji wallahi ba haka bane duk abunda tunanin ki ya baki gaskiya ne munzama ɗaya yanzu, kuma zamu dinga faɗawa juna matsalar mu" Zama khulud tayi jin kalaman da leeya tayi amfani da su wajen bata haƙuri. Leeya kuwa ta kwashe labarin komai ta faɗa mata kan batun wannan mutumin da ke turamata sakonni kuma bata sanshi ba, da kuma tsawon lokacin da ya ɗauka yana turomata da sakonni tsawon shekara ɗaya kenan kuma harda ƴan satuttuka kuma duk tsawon wannan lokaci ba rana ta Ubangiji da zai gaza da turamata sako ba, kuma kullum safiya zai zai turamata saƙo fiye da uku, har tsawon shekara ɗaya kuma ko tayi masa reply ko kar tayi masa bai damuba hasali ma bai damu da reply ɗin ba domin yana turawa yake fitarda sim ɗin a wayarsa idan ta kira bata samu kuma ko da tayi reply baya tafiya sabida layin baya aiki. Komai da komai dai ta kwashe ta gayamata harda batun saƙon na jiya da kuma abunda ya ce mata a cikin sakon. "Hmmm, gaskiya wannan lamarin akwai ban al'ajabi, amma kuma ke baki taɓa tambayar wani bayani daga gareshi ba, kamar a ina ya sami number ki, ko kuma inda ya taɓa ganinki" "Khulud kin manta a cikin bayanin da nayi miki na faɗa miki bai taɓa ban wata dama da zan iya yimasa tambaya ko kuma nasan wani abu daga gareshi ba. Sai a wannan karon kuma jiya-jiya, a saƙonsa da yayi min ya sanarmin da kar na damu da komai zan sani daga baya, kuma ya ce karna tsananta bincike" "Yanzu wace shawara kika yanke kan batunsa da yace ki yarda da soyayyar gaskiya yake yimiki" "Wallahi khulud shine sillar tunanin nan da kika sameni inayi saboda Ni bansan ma mezanyi ba" "Nidai gskiya a ganina ya kamata ki yarda ki amince domin kuwa a labarin da kika bani tsawon shekara ɗaya kenan yana bibiyar rayuwarki, idan da wani abu yake nema da ya wuce soyayya tsawon wannan lokaci ya kamata ace ya samu. Nidai ina gani kamar soyayyarsa gaskiya ce a gareki dan haka kisan abunda zakiyi idan kinji zuciyar ki ta amince masa" "Alamar hakan nakeji khulud domin tun bana kula saƙonsa har nazo na fara duddubawa ina karanta wa, har takai ina ɗan shiga wani yanayi mai kamada damuwa idan naga saƙonsa ɗaya takk zuwa biyu a wuni, sai inga kamar wani abu ya sameshi ne ko kuma bayada lafiya domin kuwa abune mawuyaci ya turamin saƙo daya ko biyu a wuni" "Uhmm--hmmm, sis-leeya albishirin ki" khulud ta faɗa da wani shu'umin murmushi a fuskar ta. Cikin matukar mamaki leeya ta ƙara ɗago kanta ta kalli khulud tsaff har kallon ya bayyanarda mamakin ta. Haka kawai ta tsinci kanta da faɗin "goro fari" "Bana son goro, goro yanada ɗaci sosai ki sauya da kishiyarsa" Kaɗan leeya ta ɗaga kanta sama kamar tana tunani kafin tace "to zuma" "Yawwa na karɓi zuma, kinsan me" "Ah ah" ta faɗa tana ƙara dalleta da idanunta masu kamar kwan fitila saboda girma da faɗi. "Kin faɗa soyayya, ki yarda Dani kawai wallahi kin faɗa soyayya" "Taya zakice na faɗa soyayya da Wanda ban taɓa gani ba kuma bansan shi mutum bane ko aljan. Bansan ko cutar dani zaiyi ba, bansan daga ina ya fito ba, bansan, bansan....." "Ya isa haka sis-leeya wallahi ko ki yarda dani ko karki yarda kin faɗa soyayya, ina da dalilina na faɗar haka, ki duba kiga tsawon wannan lokacin da ya ɗauka yana turamiki saƙo baki taɓajin ya takuramiki ba balle ki ɗauki mataki, kuma kina da damarda zaki sauya sim card amma bakiyiba, a duk lokacin da ya turamiki saƙo sai kinyi yunkurin kiran numbern da ya turamiki saƙo da ita amma bakya samu, kuma zaki bibiyi number domin mayar masa da martani, sannan kuma jiya daya turamiki saƙo har ya baki damar yin magana dashi abu ɗaya kika fara tambayar sa waye shi, saboda shine a ranki. Da baya ranki wani abun zaki tambaya ba wannan ba, sannan kuma jiya kasa bacci kikayi saboda ya baki zaɓi biyu da zaki yi domin jagoranci zuciyar ki, kuma Sannan yanzun nan tunaninsa ya hanaki magana ma balle a je ga batun wani abun daban. Gayamin duk wadannan alamomi basu baki cewa kina sonsa ba, da bakya sonsa duk wannan zai faru ko kuma idan bakya sonsa zaki barshi ya ci gaba da kutsowa cikin rayuwarki, da bakya sonsa duk wannan bazaki bari ya faruwa ba domin kinsan duk yanda zakiyi ki yakiceshi daga cikin rayuwarki"..................✍🏽 BAYAN WUYA........ By RUMANA M DIGGI EP.32 _______________khulud ta ƙarashe maganar cike nutsuwa da tunanina. Leeya kuwa jin abunda khulud ta faɗa yasa ta fara ji kamar da gaske ne ta kamu da soyayyarsa to waye shi?. "Khulud kinga fa bansan ko waye ba to taya zan yi SOYAYYA da wanda bansaniba" "Duk da haka ai, idan kin fahimci bayaninsa cewa yayi zaki sani idan lokacin sanin yayi kiyi hakuri ki jinkirta kiga iya abunda zai iya yi" Haka dai khulud ta dinga ba Leeyana shawarwari da kuma bata haske kan wannan lamarin har takai leeyana ta amince ɗari bisa ɗari ta faɗa soyayyarsa ne, domin kuwa duk wanda yaji bayaninda khulud keyi a wannan lokacin yasan gaskiya take faɗa. Kuma ba yanda zatayi dole ta aminta da ta faɗa soyayya. "Yanzu abunda za'a yi ki rubuta masa sakon barka da safiya da tattausan lafazi kinji" "Ni wallahi khulud tsoro nake ji" "Ki aiwatar da abun da zuciya ɗaya kawai ki fitar da tsoron komai a ranki, rubuta kawai" "Okay" Zama tayi dakyau tare da yin guntun tunani kafin ta tsara masa morning text massage. Cikin mintuna ƙalilan aka mai da mata da reply ɗin saƙon da ta aika kamar yanda tayi nata cikin tattausan lafazi, da kuma godiya mara adadi, domin duk bayan layi ɗaya na saƙon sai ya gode mata. Khulud kuwa tana ganin haka ta saka shewa da tafi tana faɗin "shikenan ƴar uwata ta faɗa soyayya to Allah yasa kin shiga a Sa'a ta" ta faɗa cikin sigar zolaya. Pillow ta dauka tare da jefa mata, da gudu khulud ta fita ɗakin tanata dariya. Bayan sati biyu. Haka al'amura sukaci gaba da tafiya, khulud da leeya sun haɗa kansu sosai Tamkar ba su ba. Domin a Yanzu kam khulud ta canja halayenta sosai ba wanda zaiyi tunanin khulud ɗin yanzu itace ta baya can farko. A ɓangaren leeya da masoyinta kuwa soyayyar su tayi ƙarfi sosai har mamaki ma takeji yanda akayi wannan lamarin ya faru farat ɗaya, sosai suke bawa junansu kulawa da muhimmanci tare da tsaftatacciyar soyayya mai ma'ana. Saidai duk wannan a rubutun sakonni kawai ya tsaya bawai fili da fili ba. A can gefe kuwa tsakanin kulud da idrak sai abunda ya ƙaru a soyayyar da khulud ke yimasa. Sosai sayyid yake yiwa khulud son ransa kuma ba abunda zata iya yi domin ita ta nema. Shima id ba'a barshi a baya ba wajen nunawa khulud ita ba kowa bace, kuma ko a gaban kowa zasu iya yimata duk abunda suka ga dama. Sosai su raudha da amrah suke damuwa akan wannan, domin kuwa a shawarwarin da zohal ta bata ta gayamata ta faɗawa abokanta ko suma zasu rage faɗan da sukeyi dasu sayyid, amma a duk lokacin da amrah ko raudha suka ga an yiwa khulud wani abu mara daɗi to sai sun mayar da martani ga su sayyid hakan kuma zai janyo wata masifar daban. Cikin ma Sayyid yana ragawa mutuncin da ke tsakanin sa da reemah ne da abunda zai yimusu har ma baza'a iya faɗa ba. Bangaren turab kuwa ba abunda ya ragu saidai ma abunda ya ƙaru domin ya tsananta musu sosai ga kuma dokokin masu tsauri daya kafa musu, domin kuwa basuda ikon amfani da wayoyin su idan yana gidan ko sunyi da ɓoye ta yanda bazai gani ba. Yau juma'a 24 ga watan nan kuma hakan yayi daidai da saura sati ɗaya kacal ayi bikin auren ZOHAL KHALIL GIRAH da angonta FAHAD GAHEES WAASIB. Yaune kuma familyn su mum suka hallara na nesa dana kusa Domin gudanar da taron da sukeyi duk lokacin da za'a yiwa wani ko wata daga familyn aure dama haka Al'adar familyn take. Sosai mutane suke taruwa domin kuwa Ni abun har mamaki yake bani, Mutanen nan da suke zuwa sun ninka waɗanda suka zo walimar ya turab sau uku, domin a wannan karon har mahaifiyar su papu, da ƴaƴanta mata da suke zaune a garin barno sai da suka zo, haka ma ƴan uwan mum da dama sun zo taron. Khulud kuwa sai nan-nan take yi da ƴan uwanta musamman ma Sa'aninta da waɗanda suka ɗan girme mata a shekaru kamar dai ni. Ko ƴan uwanta da sauran iyayenta sunyi farin cikin sauya warta domin a can baya basa zuwa gidan nan idan ba irin haka ta taso ba, shiyasa ko walimar da akayiwa ya-Turab basuyi irin wannan yawan ba saboda kowa yana gudun wulaqanci ne daga khulud. Zaune muke a parlour inda dangin su mum suketa nishaɗinsu sai ɗaukar photo suke, Ni kuma ina zaune a gefe kusa da su khulud sai fira sukeyi cikin nishaɗi ita da ƴan uwanta su kusan huɗu itace cikon ta biyar sai ni danake zaune kusa dasu. Daga can gefe kuma wasu mutane ne zaune daban amma duk a cikin su ɗayace ta fara tsufa sosai irin tsufan nan, amma dayake masu kuɗi ne sai tsufan bai wani bayyana yanda za'a fahimci komai da komai. Wasu matane kusan su uku suma suna kewaye da ita sai fira suke yi ankawomata abubuwan fruit a gabanta sai ɗauka take ɗaɗɗaya tana gutsurawa a hankali, bayanta jingine da wani ƙatoton sofa pillow mai taushin gaske. Nikuma sai kallonsu nake ina mamakin wace matace wannan domin har mum naga sai bata kulawa take sosai. Daga can naji muryar matar tana cewa"ke baiwar Allah bakya magana ne kinyi shiru sai kallon mutane kawai" matar ta faɗa Muryar cike da Dattaku. Murmushi nayi kaɗan wanda nasan bazata gani ba, nayi ne kawai saboda hakan ɗabi'a a tace. Saina sunkui da kaina ƙasa bance mata komai ba. "Zo nan" na ƙara jin muryarta tana yimin alama da hannu danazo wurin ta. Da sauri na miƙe na zo gabanta tare da durkusa har ƙasa nace "barka da yamma anzo Lafiya" "Ah lafiya ƙalau ya maigidanki" Ƙara ƙasa dakaina nayi daga can kuma naji muryar khulud cikin muryarta tana dariya tace hajiya babba wannan fa batayi aure ba, sa'ar su meenal ce" "Aww, ba matar aure bace nikam na ganta da niqab ai nayi tunanin matar aure ce" "Tohm haji kidaina tunanin haka domin ita ba matar aure bace" "To ke kuwa shine kikayi shiru cikin sa'an ninki bakya magana kije can ki shiga cikinsu kuyi fira mana" "Kedai haji rabuda ita batason zama a familyn mu ne tun ɗazu Aneesa da Badar ke yi mata magana tazo ayi fira da ita taƙi har meenal ma tayi magana amma taƙi ta zo tayi magana" "Khulud naji baki sakani a sahun mutanen da sukace tazo muyi fira ba karta riƙeni a rai tace nikaɗae ce bana so ta zauna cikin familyn mu". Wata kyakkyawar matashiyar yarinya ta faɗa daga cikin ƴanmatan da ke zaune tare da khulud su biyar. "Haji har Airah ma ta faɗa tace leeya tazo muyi fira" khulud ta faɗa tana ƴar dariyar da ta bayyanar da fararen haƙoranta tare da kallon budurwar da tayi maganar. Leeya kuwa jin yanda ƴan matan suka yita magana kan tazo cikinsu yasa ta miƙe ta koma wurinsu. "Yawa ko kefa, yanzu ai zaki fi sakewa kho" "Hmmm, kedai badar ki barta kawai wallahi surutu ne da ita amma kinga nan tayi shiru kamar ba ita ba" "Ai irin wannan kana ganin su kasan basuda yawan magana" cewar wata budurwa dake daman leeya. Haka sukaci gaba da firrarkinsu, da dariye-dariye har aka kira sallahr la'asar. "Ku tashi muje muyi sallah kho" "Wai su meenal an musulunta yanzu an fara sallah" "Da can ba musulma bace" "Ah wace ni baza'a ji mutuwar sarki a bakina ba" cewar khulud cikin tsokana. Miƙewa sukayi Dukansu leeya ta kalli khulud tace "khulud wacece matar nan data tashi yanzu" ta faɗa tana nuna datijjuwar matar da ta kirata ɗazu. "Ah bakisan haji bane hala ke ba a familyn nan kike ba?" Aneesa tayi tambayar da mamaki. Leeya zatayi magana caraffff khulud ta karɓe da faɗin "ƴar ƙawar mum ce, amma mahaifiyarta ta rasu" "Allah sarki, ƴan matan suka haɗa baki wajen faɗin haka, fuskar su na Bayyanarda tsantsar tausayi. "Menene sunanki hala, Ni sunana meenal" "Leeyana sunana" "Sannu leeyana, Allah yayi mata Rahma kinji, Allah yasa ta huta" "Ameen, Nagode sosai" "Karki damu anzama ɗaya, tambayar da kikayi waccan matar da kika gani kakarmu ce itace mahaifiyar papu, da dadyn Kaduna, kuma duk nan jikokin tane banda waccan" ta faɗa tana nuna Airah. "Okay, to ita menene sunanta?" "Wake nan?" meenal ta faɗa ta sigar tambaya. "Wannan" "Okay wannan Airah sunanta, kuma mahaifiyarta ce jikar haji ba ita ba, duk nan da kika ganmu ƙanen mahaifiyarta ne" "Ok Allah sarki, Allah ya ƙara haɗa kanku" "Ameen" suka faɗa baki ɗaya, yayinda Airah ke faman hararar meenal. "Wallahi Airah bakida kunya kingani bake bace sa'ar yina, ya-safiyyah ce Sa'a ta" "Hummm, wallahi shine matsalar ƙaramin yaro ya haifeka, Ni kunga tafiyata idan baku tashi ba sister kekam zo muje kinji bar waɗannan dama ba damuwa sukayi da sallah ba" Airah ta faɗa tana jan hannun leeya. "Kambala'i mu zaki gayawa haka bin na gaba dai bin Allah" khulud ta faɗa tana bin Airah da gudu sauran ma suka rufamata baya kamar ba ƴan mata ba. Ko bayan shigar su ɗakin saida suka taɓa fira kafin wasunsu sukaje sukayi alwala, aneesa da Airah ɗakin leeya suka bita. Inda meenal da badar kuma sukaje ɗakin khulud. Bayan sun kammala sallarh ne suka haɗu gaba ɗaya ɗakin leeya, sosai sukaji daɗin haɗuwar su inda wata mata ta zagayo ɗakin tace kowa ya shirya karfe uku daidai za'a fara meeting ɗin, ba jimawa da fitar ta sai suka jiyo murya ta waje kamar Muryar Mayah ce tana kiran sunan meenal. Isowarta kenan sai taga maman su meenal ɗin ta tambaye ta ina meenal take sai aka gayamata suna part ɗin nan. Ita kuwa bata da haƙurin wulaqanci shiyasa ta tsaya bata ƙarasa ciki ba domin bataso su tada masifar da suka sabayi ita da khulud, idan sau goma zasu haɗu sai sunyi faɗa sau goma mayah kenan, amma idan fannah ce ba ruwanta da duk abunda khulud keyi domin ba saboda ita take zuwa gidan ba. Itama Rukhshanah batada haƙuri ko kaɗan a wannan bangaren duk FANNAH ta fisu sanyin hali. "Meenal ke nake kira fa rainin wayo kuma kinyi banza kamar bakya jina" mayah ta faɗa cike da masifa. Tana shirin juyawa sai taga khulud tafe tana tunkaro ta, gyara tsayuwar ta tayi dakyau tana jira taga dame yazo, domin ta ƙudurta a ranta ko mummy zata daketa a gaban mutane indai khulud tayi mata maganar banza ko raini sai ta wanke mata fuska da maruka. Fuska ɗauke da murmushi khulud ta karaso wurin tana faɗin "twins saukar yaushe" Duk da ganin yanayin da khulud ke ciki bai saka mayah ta murmusa ba, ƙara tamke fuska tayi tace "khulud meenal nake nema, ko sunanki kikaji na ambata" "Ah ah baki ambaci sunana ba amma nake gani da Ni da meenal duk ɗayane a wurinki kho" "Kowa daban a cikin ku kuma kowa da halinsa" mayah ta faɗa tana juyawa zata tafi. Hannunta khulud ta riƙo tare da faɗin "ya kamata ki ajiye duk abunda kikeji a ranki mayah, ki daina ƙullatata a ranki domin kuwa hakan bashida wani amfani, nasan kinyi mamaki kwarai da gaske da kika zo kika sameni tare da ƴan uwana kho, Badar, Aneesa, Airah, da kuma meenal, sai kuma baƙuwar gidan nan namu wato Leeyana wacce yanzu ta wuce baƙuwa ma saidai a kirata da ƴar gida, duk muna tare sai nishaɗi mukeyi. Nasan nayi miki kuskure a can baya bama ke kaɗai ba da ma sauran mutane da dama amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafemin na gane kuskurena, domin wannan ɗabi'un nawa da halaye mara kyau su suke neman jefani tsaka mai wuya, dan Allah ki yakemin na tuba kinji ƴar uwata". Sosai jikin Mayah yayi sanyi nan da nan ta rungume khulud tace; "na yafemiki ƴar uwata nima dan Allah ki yafemin a can baya kuruciya ce ke damun mu amma a yanzu munsan ciwon kanmu ba abunda zai ƙara shiga tsakanin mu in sha Allah, Allah Ubangiji ya ƙara haɗa kanmu" "Ameen" khulud ta faɗa kwalla na kwance a idanunta. "Muje ciki" ta sake faɗa hannunta na riƙe dana mayah. ******* Hajiya mainah waasib wato (haji-mainah) yanda mafiya yawan ƴaƴanta da jikokin ta ke yawan kiran ta da haka ko kuma su kirata da (hajia babba). mahaifiyar papu da dadyn Kaduna wato maihaifin twins da Fahad, suka ɗaina ƴaƴa maza da Allah ya bata, Khattab waasib shine babban ɗanta wato mahaifin TURAB da KHULUD. inda gahees waasib ya zamo ɗa na biyu a gareta kuma shine yake biyema Khattab a shekaru. Daga kansu Allah bai ƙara bata ƴaƴa maza ba, sai ƴaƴanta mata su uku, saknah waasib, itace mai biyewa mahaifinsu fannah tanada ƴaƴa huɗu ɗaya mace uku maza, macen itace Safiyyah wato mahaifiyar Airah, sai kuma fawzan, sha'aran, da kuma fideer shine auta. Sai kuma rafa'at waasib kanwa ce a wurin Saknah waasib ita ce sherunsu suka kusa da juna domin a haihuwa daga saknah sai ita tanada ƴaƴa biyu mata Badar da Aneesa sune sha'anin ulud, sai kuma ƴar autar haji mainah wato ubaidah, itace ƙanwarsu gaba ɗaya, ƴa ɗaya gareta mace sannan sai namiji ɗaya macen itace meenal (Ameenah) kuma itace babba sa'ar Leeyana, sun girmewa su ulud shekaru biyu zuwa uku, sai kuma ƙaninta waasib wanda aka mayarda sunan mahaifinsu kuma kakansu alhaji waasib sai ake kiransa da suna Little. *Mahaifinsu Alhaji waasib kabeel, dan asalin jahar barno ne kuma a can yake zaune da iyalansa aiki ne ya mayarda Khattab a Abuja, daga nan kuma ya samawa ƙaninsa gahees aiki a Companyn da yake aiki da takardunsa na karatu cikin nasara kuwa ya samu aikin domin takardunsa nada kyau sosai, a ƙa'idar Companyn duk shekara ana tsintar mutane daga cikin ma'aikatan Companyn suje su wakilci Companyn a ƙasashe da dama domin tattauna dasu game ta yanda tsarin Companyn ke tafiya, haka ta kasance a shekarar aka zaɓi mutanen da zasuje harda gahees waasib, kuma a india ne za'ayi taron, ba'a wuce sati ɗaya da maganar ba ya koma gida barno ya sanarwa da iyayensa, amma a zahirin gaskiya yaji tsoron yanda ya sami mahifinsu waasib kabeel cikin matsananciyar jinyar da ta kamashi a kwana biyu kaɗai duk ya sauya kamanni, sosai hankalinsa ya tashi gaba ɗaya gwuiwoyin sa sunyi sanyi da ganin halinda mahaifinsa ke ciki har yace ya fasa tafiyar, da kyar aka samu aka rarrasheshi da magana mai dadi aka shaida masa Khattab zai ɗauki hutu yazo yayi jinyar mahaifinsu, ta hakan ya yarda yayi tafiyar, Khattab babban ɗan kasuwane har a ƙasashen waje gashi kuma cikakken alƙali kuma minister of judiciary. Bayan tafiyar gahees kullum sai yakira gida yana tambayar jikin mahaifinsa ana gayamasa yaji sauƙi, ba rana da Ubangiji da zata fito ta faɗi ba tare da yakira yaji halin da mahaifinsa yake ciki ba. Da kalaman da yake samu ne suka saka ya kwantar da hankalinsa ya fara aikin da ya kawoshi a nan India, a kuma wajen aikin ne ya hadu da neesa wato mahaifiyar twins asalin ƙabilar ta urdu ce saidai su musulmai ne basa bautar gumaka daga nan kuma ya kira gida ya sanar musu da cewa ya sami matar aure, sosai sukayi masa farin ciki da fatar alƙairi, ba jimawa ya aureta lokacin da suka kammala aikin da ya kawoshi India. Kwana uku tsakani suka dawo gida NIGERIA, sosai yayiwa iyayensa da ƙannesa da yayansa tsaraba, bayan haka kuma ga tsarabar mata ba-india daya kawo musu. ƴan uwansa sunyi murna sosai kuma sun karɓi neesah hannu bibbiyu, sai dai wani tashin hankali da gahees ya tarar gida aka gaya masa tun bayan tafiyarsa da kwana ɗaya mahaifinsu waasib ya rasu, kuma an zaɓi a ɓoyewa masa ne saboda aikin da yake yi sunsan idan suka gaya masa bazai zauna ba balle yayi aikinda yakai shi. Ranar gahees yayi kuka sosai kamar wani mace, rarrashi kuwa ba kalar wanda ba'a yimasa ba sai da yaci kukansa ya ƙoshi sannan yayi shiru. Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu, sosai suke kula da mahaifiyarsu duk da suna nesa da ita amma hakan bai saka ta saka tunani a ranta ba domin iya gwargwado suna kula da ita. Bada jiwa ba gahees ya koma kaduna da iyalansa domin yaci gaba da kula da harkokin Companyn su na Kaduna. Shikuma papu a lokacin yana zaune a Abuja, sai daga bayane khulud ta ƙeƙashe kan itafa garin suleja takeso su koma da zama tun ana ɗaukar maganar ta matsayin wasa saboda a wannan lokacin ƙaramar yarinya ce sosai har sukaga abun nata ya wuce gaban tunanin su, domin haɗa kayanta tayi wuri ɗaya kan zata bar gidan idan basu koma garin da takeso su zauna ba. Anyi rarrashi har aka gaji batayiba, papu kuma baya ƙaunar ganin abunda zai taɓa khulud domin sosai yake sonta yake kuma jin tausayinta sakamakon larurar da take fama da ita, tanada ciwon zuciya wanda dashi aka haifeta. Ciwon zuciyan mai tsanani idan ya tashi sai an fita da ita waje domin baya barinta a Nigeria saboda tana zubarda jini sosai hanci da baki harma kunne, tana cika shekaru tara ne alamomin ciwon asthma suka bayyana gareta, domin kuwa sosai numfashi keyi mata wahala a duk lokacin da ciwon ya tashi, kuma ciwukan biyu zasu iya tashi a lokaci ɗaya. Da wannan dalilin ne yasa papu ya sangar tata sosai baya taɓa bari ayi mata wani abu da zai ɓata mata rai, ko kuma ta nuna tanason abu bata samu ba a kasa yimata duk baya bari hakan ta faru Domin gujewa tasowar wani abu. Wannan shine takaitaccen bayani kan su haji mainah da ƴaƴanta da jikokinta. A ɓangaren su leeya kuwa..........✍🏽 BAYAN WUYA....... By RUMANA M DIGGI EP.33 ____________zaune suke gaba ɗayansu a ɗaki ɗaya daga part dinsu khulud, ba sosai aka cika zama a cikinsa ba sai idan anyi baki haka, a kafff part ɗin ɗakin yafi ko wanne girma da faɗi domin gado huɗu ne a Cikin Dakin royal bed. Zaune suke gaba ɗayansu a kasan Centre carpet, kowa ya sami abokin da yake fira dashi kuma sunayi a tsakanin su gaba ɗaya. Airah ce ta ɗaga murya tace "Mayah wai ina fannah da Rukhsha" "Wallahi kamar kinsan abunda zan tambaya kenan wata sabgar ta ɗaukemin hankali" "Tau badariyyah uwar ƙarya sai yanzun dana tambaya ne kuma sabgar ta dawomiki da hankalin ki kho" "Wallahi Airah bakida mutunci muna nan dai matsayin mu ba'a chanjawa tuwo suna mune dai ƙannen iyayenki" "Mtswww, ƙannensu kikace ai ba ƙanne na ba" "Tau iyayen masifa kun tambayeni twiney da Rukhsha amma kuna nan kuna zabga ruwan bala'i ku baku zaman lafiya ne" "To malama mayah mun zauna lafiya, meya hana fannah zuwa" "Hmm kedai bari banji daɗi ba ai rashin zuwan su, Ni banmasan Allah ya shirya khulud ba nacewa mummy wallahi idan nazo ban tararda ku ba bazan tsaya ba domin nasan bazamu wanye ƙalau da khulud ba ashe ma ta shiryu" "Ai ke bari wallahi dah can baya ina cikin duhu ashe mutane rahma ne baramma ƴan uwanka, nidai ku ƙara yafemin. Ke kuma ana tambayarki sai surutan banza kikeyiwa mutane" "Tau na daina surutan, kinsan ba skul ɗaya mukayi apply dasuba, su suna zuwa har yanzu basu kammala exams ba, mu kuma munyi tun wancan sati, shiya hana suka zo" "Okay tau Allah ya basu Sa'a" "Ameen kudai ƴan uwana muna godiya sosai" "Ke ƙarfe uku da Aunty beelkisu tace za'a fara meeting, kunga saura mintuna bakwai uku tayi fa" Miƙewa wasunsu suka yi da sauri suna fara shirya wa domin family meeting ɗin nasu nada dokoki masu tsauri sosai, kuma a dokar meeting ɗin nasu abune da kowa ya sani idan baka cikin familyn baza'a je zaman da kai ba, idan ma kayo rakiya ne saida kajira wanda ka rako kafin a kammala taron. Haka ne ta faru ga leeya domin itama tasan da dokar tun kafin yau. "Leeyana ki tashi muje ai kema kinzama familyn mu yanzu" "Kuje kawai sis-khulud sai kun dawo, kinga Ni bacci ma nakeji idan kuka dawo ku ta dani" leeya ta faɗa tana hayewa kan ɗaya daga cikin gadajen da ke ɗakin. Ba yanda basuyi da ita ba kan ta tashi ta bisu amma taƙi, har meenal ma da tunda suka shigo ɗakin suke ta surutu da ita tayi tayi amma furrrr tace bazata je ba. Suna cikin hakane kuma sukaji ƙarar wayar leeya daga can gefe inda ta tashi, da sauri khulud ta miƙa hannunta ta ɗauko wayar tare da dubawa. "Oga ya turo saƙo" ta faɗa cikin sigar zolaya. Ƴar harara leeya ta jefamata da idanuwanta masu tsoratarwa khulud na kaɗuwa tace "ahhh rufamin asiri karɓi wayarki, kidaina harara ta kar idanun nan su cinyeni, kunga kuzo mu tafi wannan ba zuwa zatayiba kunga ma masoyinta ya zo suyi fira" "Yana ina" Aneesa ta faɗa a ɗan tsorace. "Gaskiya Aneesa ke doll ce ana maganar ya turomata saƙo kina wani maganar yana ina" Wawan duka Aneesa ta sakarwa Airah a bayanta "shegiya mara kunya badan Aunty Safiyyah yayarmu bace danace ita ce doll, mara mutunci kawai" Da sauri Airah ta daga hannu zata rama dukanta Aneesa ta yima ita kuma Aneesar ta fita da gudu, Airah ta bita a baya tana kukan shagwaɓa sai ta rama dukanta. "Leeya mudai mun tafi sai mun dawo, karkiyi bacci kinji idan na dawo sai muci gaba da fira" "Tau meenal sai kun dawo, Allah ya tsare" "Okay be safe, muna gaida mijinmu" Cikin jin kunya ta rufe fuskarta da pillow tana dariya a hankali, su kuma suka juya suka fita. Suna fita kuwa taci gaba da firarta da masoyinta, ta sake sosai dashi kuma harga Allah tana so da ƙaunar sa domin Allah. Itama tanaji a ranta ko shi wanene yana sonta kwatankwacin yanda take sonsa wata ƙila ma ƙaunarda yake mata tafi wacce take yi masa. ★ A can ɓangaren su mum kuwa anyi taron ne a farfajiyar gidan kuma an tattauna kan abubuwa da dama da kuma amfanin sada zumunci, an kuma faɗakarda sauran waɗanda suke tasowa kan su riƙe ƴan uwansu da kuma zumunci sosai, domin zumunta ibadace, kuma al'umma rahmace. Bayan haka anyi musu nasihohi da dama kan komai, musamman fahad da nauyi ke shirin rataya akanshi. Sosai taron ya tafi yanda akeso, kuma aka watse lafiya ba wata rigima ko sa in sa ko kuma tashin hankali. Iyayen yara kuwa sai faman haɗa kan iyalansu sukeyi domin komawa gida, inda meenal da badar sukacewa mahaifiyarsu su ba inda zasuje suna nan sai anyi biki, Aneesa kuwa tana ganin haka itama ta sanarda tata mahaifiyar, Airah ma haka, sannan mayah itama taje ta samu mummy da maganarnan. Ba abinda iyayensu suka iya cewa domin kuwa duk dangine kuma duk an riga anzama ɗaya. Sosai khulud tayi farin ciki da haka sai tsalle tsallen murna suke suna gani tare zasu shirya komai na bikin. Da murna suka koma cikin gidan inda suka tarar da leeya tayi aiki tuƙuru wajen ganin ta tsaftace gidan gaba ɗaya, kana shigowa kanshin turaren tsintsiya mai tsada ne zaya fara tarbarka, sai kuma daddaɗan kamshin girkin da suka ƙara banbance wane kalar abincine. Da sauri suka isa part ɗin ta domin ba ƙaramar yunwa sukeji ba, kuma hakan ya saka wasu daga cikinsu suka ƙara jin leeya ta kwanta musu sosai a rai. Haka ma su mum da suka shigo suka tararda wannan ƙoƙari da leeya tayi, sosai ta birge wasu daga iyayen saboda ko wace uwa tana buƙatar ganin hakan ga ƴarta. Bama wanda yakai mum farin ciki domin tun sa'adda aka kammala family meeting ɗin take ta tunanin abunda zata samarwa haji da sauran ƴan uwa da suka rage basu tafi ba. Sai kuma ta dawo gidan ta tarar leeya ta girka isasshen abinci. "Fanaya, dama kunada ƴar aiki ne amma banganta a gidan ba tun jiya danazo" "Ah ah haji wallahi bamuda ƴar aiki, wannan yarinyar da tayi aikin nan ƴa tace ƴar ƙawata data rasu" "Allah sarki, wacece yarinyar nan amma bangantaba kho" "Itace wannan mai saka niqab idan kin kula a tare suke dasu khulud da Aneesa" "Ahhh, itace Wannan yariyar mara son hayaniya kho, ɗazu naganta sai fama muke da ita kan ta shiga cikin su meenal suyi fira amma taƙi, sai daga baya nagane hayaniyarce bataso" "Eh wallahi haka take amma wani lokacin kam tana magana haka tayi farkon zuwan ta gidan nan mun jima da ita kafin ta sake da mutane" "Allah sarki tanada hankali gaskiya tayi ƙoƙarin yin aikin nan haka, ita dai bata jin wuyar yin aiki ɗazu ma naga ita ta girka mana abincin rana, kuma yanzu gashi ta girka na yamma Allah yayi albarka" "Ameen haji, muje sashenki na zuba miki ruwa kiyi wanka idan kin fito sai na zuba miki abinci" "Kedai ki barshi kawai zan iya wallahi, je kiji da su sahiya wato (Safiyyah) ki zuba mata taci abincin kinga mahaifinsu samirah wato (Airah) yana waje yana jiransu. "Ni gaskiya kaka-haji kidaina kirana sahiya ni ba haka bane sunana idan baki iya faɗin sunan mutum ba kidaina mana ki bari a koyamiki" "Ni bazan iya lankwashe harshe ba da wani game leɓe wajen faɗin sunankun nan na zamani" "Haji Safiyyah ne sunan zamani kuma" "Eh mana mu sahiya muka sani kuma shi zamu faɗa Ni kinga tafiyata ma" Haji mainah ta faɗa tana wuce sashen ta cikin tafiyar ta ta tsofaffi. duka gidajen ƴaƴan nata maza an ware mata sashenta inda zata riƙa zama duk sa'adda tazo gidan ɗaya daga cikin su, ko suleja ko kuma Kaduna, ko Abuja. Washe gari su khulud suka haɗa karfi su duka shida sukayi aikin gidan tun kafin su mum da papu su tashi. Dayake gidan ma ba wani aiki sosai domin duk mafi yawan ayyukan leeya tayi tun jiya. "Tau Mr. Chief, yanzu ke zaki shiga kitchen ki mana girki kho wallahi jiya girkin ki yamin daɗi sosai har sarauyina saida na bashi labarin abincin kuma yace idan kika tashi shiga kitchen na je nagani idan munyi aure nadinga yi masa" badar ta faɗa cike da rashin kunya. "Bazata jeba dan bakida tausayi jiya tayi mana abinci har sau biyu kuma yau tayi kamar wata baiwa, leeya kije ki huta Bara na shiga kitchen na girka mana" "Nop Aneesa ki bari naje kawai ai ni bana gajiya da yin girki, saboda haka kowa a cikin ku ta faɗi kalar abincin da takeso a girko mata" Har badar ta buɗi baki da nufin faɗin abunda takeso meenal tace"muje na tayaki muyi tuwon doya da miyar cabbage da crayfish kawai, duk wanda zai ci yaci wanda bazai ciba kuma ba wanda ya tare masa hanyar kitchen" bata jira cewar kowa ba ta janye leeya daga wurin suka koma kitchen area. Mintuna kaɗan suka gama haɗa komai da komai dai-dai lokacin da papu da mum suka sakko. "Ahhh ɗiyan albarka sannunku da aiki, Allah dai yayi albarka" "Ameen papu, barkanku da safiya" Haka su meenal suka gaida su mum da papu cikin farin ciki da nishaɗi tare da gabatar musu da girkin da sukayi musu. Daga nan kuma aka zubawa haji nata girkin leeya da meenal sukaje suka kaimata, koda suka tarar da ita ma tana shirin zuwa sashen nasu sai ta fasa zuwan sakamakon Abincin ta da aka kawo mata har nan. A mutunce leeya da meenal suka gaida haji bayan ƴar guntuwar fira da sukayi sannan suka tafi suka barta Domin taci abinci. Da suka fito basu tsaya ko ina ba sai hanyar da zata sadasu da sashen su khulud, abun mamaki koda meenal da leeya suka iso sashen Sai suka tarar da su Mayah gaba ɗayan su sun dawo sashen. "Badar har kunci abincin ne" ta faɗa cikin sanyi ta. "No sis-leeya mum da papu muke jira idan sun gama sai muje parlorn domin cashewa zamuyi, wai Aneesa ce take faɗin ta fini iya rawa, shine Airah ta aza mana competition mayah da khulud suka ce su zasu bayarda kyauta ga duk wanda yafi iyawa. To shine muka dawo domin musaka kayan yin rawa" "Hummm, to Allah ya kyauta muje kho meenal" "Badar wai yaushe zakuyi hankali dan Allah, ita rawar ce zaku fita har parlour bazaku tsaya a nan ba in ma rashin kunya kuke ji" "Aunty meenal kidai ki yi shirunki ba abunda zai hana mana rawar nan saboda haka kiyi shirunki kawai, kuma ma ai speakers ɗin ɗakin nan basuda ƙara na parlour sunfi ƙara" "Tau Allah ya taimaka" daga haka meenal bata ƙara cewa komai ba. "Khulud muje muci Abincin Please wallahi yunwa nake ji" "Muje nasan ai su mum sun isa kammala wa" Tare suka fita parlourn gaba ɗaya kowa na faɗin albarkacin bakinsa game da competition ɗinda zasuyi tsakanin Aneesa da Badar. Koda suka sauka parlourn sai suka ga ashe su mum bama parlorn suka ci abinci ba, ta yu sun koma bedroom ne ko kuma suna main parlour. Hakan kuwa yayi musu daɗi sosai, nan kowa ya ɗiba Abincin da zai iya ci har ya ƙoshi. Bayan sun gama cin abincin ne sai suka kunna tv kuma suka ƙure volume a speaker, sabuwar waƙar joeboy mai suna just for you aka saka musu tare da ƙure volume ɗin kowace speaker dake parlourn bakajin ƙarar komai sai sautin waƙar dake tashi. sukuma sai ihu suke da shewa tare da yin tafi, badar da Aneesa kuwa sai tiƙar rawa suke suna bin waƙar da salon rawar su. Meenal kam Abincin ta takeci hankalinta akanta, domin ita daɗin abincin ma ya hanata ko ɗaga kai ta kalli shirmen da suke. Leeya kuwa tana ɗan gefe dasu kaɗan, wayarta a hannunta daga yanayin zaman da tayi ta ƙurawa wayar idanu zaka fahimci abu mai muhimmanci take dubawa a wayar. Shigowa yayi parlourn fuskar sa a haɗe kamar ko yaushe, sanye yake da uniform ɗin sojoji fuskar sa kuma tasha baƙin glasses wanda ya ƙarawa fuskar tasa kwarjini sosai. Kafin ya shigo parlourn yayi sallama kusan sau biyu, ta ukun ce ta maƙale masa a baki sakamakon arba da yayi da ƙannensa suna kwasar rawa haka ba sauƙi, ga babban abun haushin ma sun ƙure volume sosai ta yanda ko anyi magana baza'a ji me ake faɗa ba kamar wani sabon club ɗin chasewa da ake tallatawa. Da sauri ta ɗaga kanta tana kai dubanta a kofar parlourn sakamakon jin ƙamshin turarensa data yi ya ziyarci hancinta, karaff idanunsa suka sauka a kanta itama lokacin da ta sauke nata akansa, wata mummunar faɗuwar gaba ta dira a zuciyar ta sakamakon wani mugun kallo haɗe da muguwar harara daya jefa mata. Da sauri ta mayarda kanta ƙasa zuciyarta na tsalle saboda tsananin tsoro, tanaso tayiwa su badar magana amma ba dama kuma kaf a cikin su ita kaɗai da ke zaune a gefe ta lura dashi. "Ai ya kamata koda khulud ce taji kamshinsa kho? tunda tasan ƙamshin turarensa itama, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un allah ka takaita mana" leeya ta faɗi maganar a zuciyarta yayinda tsoro da fargabar ya-Turab suka cika taff a lungu da saƙo na zuciyarta. Shikuma tunda suka haɗa ido ya ɗauke kansa daga gareta domin bayason kallonta kwata kwata, shi a ganinsa ma idanun ta canja kala suke bai taɓa kallonta yaga idanun ta da kala ɗaya ba. Kittt sukaji an danna remote ɗin tv dana speakers ɗin gaba ɗaya. Da sauri Airah ta juyo cikin matsifa domin ganin waye, ai kuwa tana juyowa taga turab ne ta zube gwuiwoyin ta gaba daya a ƙasa, "itadai ta Banu ta shiga uku, ba ranarda zatazo gidan nan ta fita lafiya batare da ya-Turab ya mata dukan jakai ba, ita tana gani ma ko bata yimasa laifi ba sai ya ci ubanta balle da laifin, ya lafiyar kura bale taga nama" Airah tayi maganar a ranta tana matsar ƙwallah samm taki bari su haɗa ido. Sosai gaba ɗayansu suka shiga tashin hankali ganin ya kafesu da idanunsa masu matukar ƙaɗa ƴaƴan cikin waɗanda sukayi masa laifi ba mazan, ba matan ba. Baramma Yanzu da yake sanye cikin uniform ɗin soja, ita kuwa Aneesa ba abunda take tsoro ta kuma tsani gani kamar bindiga, sai kuma gata a fili a gefen ƙafar wandonsa na hagu. Duk sun sanshi, kuma sunsan halinsa idan aka yimasa laifi aka cika bashi haƙuri to bazai haƙura ba koda yayi niyyar yin haƙurin saboda hakane yasa sukayi tsitt ko wacce a cikinsu kanta a ƙasa tana saƙawa da kuncewa har leeya da meenal ma da suke gefe yanzu sun dawo gabansa. "Ku!" Ya faɗa da kakkausar murya "dan uwayenku wannan tarbiyyar aka baku a gida kuzo kuna shan kiɗa kuna rawa kamar wasu arna, kuma abin haushin ma kun kure Volume kamar wani club, idan rawa kuke so kuyi ga hanyar gate nan, duk wace take so kuma taga takai ta isa to ta tafi gidan rawa mana, wallahi summah tallahi, na rantse da Allah wannan shine First and last nazo na sameku a haka, billahil azeem kunji rantsuwar da nake ko wallahi idan na kara ganin ɗaya daga cikin a haka saina kakkarya ƙasusuwan jikinsa" ya faɗa yana nuna alamar karyawa da hannayen sa cikin matuƙar ɓacin rai. "Kunci albarkacin gajia da kuma ɓacin rai danake ji wallahi da badan haka ba ku da kanku zakuyi bayani shashashu kawai, ku tafi kubani wuri" ya faɗa cikin Tsawa. Da sauri suka tashi wasu harda haɗawa da gudu ita kuwa leeya har harɗewa take tambakar zata faɗi saboda tsananin tsoro su ka koma sashen su. Hanyar da zata sadashi da part ɗin haji ya nufa domin koba komai zaifi samun nutsuwa a can, wata ƙila ma fushin da yake ciki ya wanke idan yaje wurinta, domin kuwa tasan abunda yakeso tsaff idan ranshi na ɓace yafiso ayita bashi labarin dariya, to da zarar labarin yanada dariya shikuma idan yaji yayi dariya shikenan ba wani sauran fushi ko ɓacin rai za'a buɗe sabon fejin fira. "Assalamu alaikum haji, haji!" "Na'am Abu manyan ƙasa, yaushe gari irin saukar ba zata haka" Haji ta faɗa tana fitowa daga bedroom ɗin ta. "Haji dan Allah ba sunana Abu ba sunana abu-turab idan zaki iya faɗar haka, idan bazaki iyaba ki dinga kirana da turab kawai ko kuma tk (turab Khattab) kenan. "Ungo wannan, nace karɓi wannan ɗan damtsen uwa ba abu aka saka maka ba, kune dai ƴaƴan zamani kuke yiwa suna wani kwaskwarima, nifa bazan iyaba wallahi, tun da aka haifeka nake ina kiran Abu har yanzu, sai yanzu dakaga ka tara ƙasumba ne da gashin baki kake so na kiraka da sunan da ba naka ba" "Mtwsss", yaja guntun tsaki can ƙasan zuciyar sa. "nidai haji ba wannan ba so nake naji dalilin da yasa aka yimin kiran gaugawa bayan kuma ansan aikinda nake kuma bana ƙasarnan" "Awww, baka masan dalilin kiran naka ba kenan" "Haji wallahi kinada abun mamaki danasani dazan tambaye ki ne" turab ya faɗa kamar a ƙule. "Kajimin Abu da iya shege, kai ba'a yimaka Maganar lalama ne, to je ka tambayi ubanka" "Haba hajiyarmu babba, Allah dai ya ƙara Lafiya da wadata da nisan kwana, kiyi haƙuri mana" "To kaje kawai, ai ko bakazo nan ba za'a kiraka tunda har ka dawo ka bari mahaifin ka yazo kawai, za'a gaya maka ko menene. Yanzu kaje ka huta kafin ya dawo" "Haji lafiya dai?" "Lafiya lau kaje ka huta karka saka komai a ranka ba komai ba ne kawai magana za'a faɗa maka. Kaje kayi wanka ka ci abinci ni kwanciya zanyi bacci nakeji sai mahaifin ku yadawo zakuzo har nan kusanar dani" "Okay ba damuwa amma me aka dafa a gidan haji?" "Tuwon doya da miyar ganyen cabbage da bushasshen kifi" Dan yatsune fuska yayi kafin yace; "haji anya kuwa abincin nan bazai ɓata wa mutane ciki ba, kinga ni ko a Mexico danayi rayuwa ba kowane irin abinci nake ci ba balle a nan" Wani kallo haji ta wurga masa tare da yin ƙofa tace; "sannu jikan Elizabeth turawan duniya, to ni kaga tafiya ta baccin nan naso yafi ƙarfina" "Haji da gaske ne kenan da'akace idan mutum ya cika tsufa sai bacci yayita yimasa yawa a kullum kamar dai yan da jarirai suke" "Uhmm--hmmm nikam banida masaniya amma kaje ka tambayi wanda kaji suna faɗin maganar" daga haka ta koma kan sopa tare da yin kwanciyar ta ƙyaleshi, sai dariya yake ganin yanda tayi da fuskarta..................✍🏽 BAYAN WUYA......... By RUMANA M DIGGI EP.34 ______________miƙewa yayi yabar ɗaƙin bayan yayi cokali biyu na abincinda yagani kan Centre table, dayake ba yunwar yake ji sosai ba shiyasa bai tsaya yaci da yawa ba. A ɓangaren su Airah kuwa suna faɗawa ɗakin ko wacce su ta zube kan gado tana maida numfashi da ƙarfi saboda gudun da sukayi ga kuma tsananin tsoro take cike falll a ransu. "Gaskiya uncle turab bashida mutunci wallahi matarsa kam ta shiga uku dan sai taga ta kanta" "Ke Airah ki rufawa kanki asiri, turab kawunki ne fa gwanda muma idan yaji muna zafinsa zai iya mana da sauƙi ba kamar ke da yake ƙanin mahaiyarki ba dukan Kawo wuka zai yimiki" "Wallahi Badar sai an faɗi gaskiya, ai ko iyayena sukejin rashin gaskiya sai an faɗa balle shi dayake ƙanin mahaifiyata" "Menene rashin gskiya a ciki Airah, sabida yaga kuna rawa yayi muku magana shine yayi rashin gaskiya" "Tau Aunty meenal nadaina tunda kinyi magana amma ko gobe yayi irin haka sai na maganta nikam, tun sa'adda nayi wayo ba ranarda nasan nazo gidan nan na tafi ba tare da uncle turab yaci ubana ba, ina ga wannan ne na fari wallahi" Haka dai sukaci gaba da maganganun su kowa na sabgar gabansa. Turab a ɗakinsa da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare papu ya kira wayarsa, da mamakinsa ya ɗaga wayar domin tunda yayi tafiyar nan papu bai taɓa kiransa ba, kuma a duk lokacin da aka zauna family meeting duk wanda baya kusa sai ankirashi video call a ajiye wayar inda zaiga komai har ayi a gama yana ji kuma yana gani. Amma a wannan karon kam papu baiyi masa hakaba, kuma ya hana kowa ya kirashi, tun tafiyarsa yake ganin wani abu mai kamada fushi daga mahaifinsa, haka ma jiya kamar wannan lokacin yana ƙasar Europe sai saƙon Aunty Safiyyah yagani wai papu na yi masa kiran na gaggawa a Nigeria. Daya tambayeta ko lafiya, jiki a sanyaye sai tace masa "wallahi turab nima bansan dalilin kiran ba, kuma na tambayeshi ko lafiya yace ba yanzu zan san maganar ba sai komai ya kammala, Allah dai yasa lafiya" "Ameen aunty Safiyyah, amma wallahi abun nan yaban mamaki to saboda me papu bai kirani da kansa ba saidai yakiraki kigayamin saƙon" "Allah masani turab, kaidai kashirya gobe kazo gida, irin wannan kiran ba'a sanya domin bakasan abunda zakaje ka tarar ba" "Haka ne Aunty Safiyyah Nagode, Bara naje nayi Booking flight gobe da sassafe zan dawo in sha Allah". Sake sauke ajiyar zuciya yayi tunawa da yayi da maganar da sukayi jiya da shi da Aunty Safiyyah, saidai kafin ya kai ƙarshe a tunanin sa har wayar ta ƙatse. Da sauri ya maida kiran amma tuni ba papu ya riga shigowa "Assalamu alaikum" "Turab kazo ina neman ka a sashena yanzu" "In sha Allah gani nan zuwa papu" Kittt papu ya kashe wayar batare da ya ƙara cewa komai ba, wannan ne ya ƙara tabbatar masa da cewa papu fushi yake dashi. "To menayi masa, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" "Wazaka tambaya amsar tana wurin sa ai tun da kai bakasan kayi masa laifi ba" wani ɓangare na zuciyar sa ya faɗi haka. Miƙewa yayi da sauri cikin tashin hankali ya nufi part ɗin papu, domin har ga Allah shi bayason fushin mahaifansa, a garesa hakan babban asara ce a wurin yin ibadarsa domin wani hadisi na Manzo Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "ridallahu fiii ridal-walidi, sakhɗullahi fiii sakhɗul-walidi" ma'ana (yardar Allah tana tare da yardar mahaifa, hakama fushin Allah yana tare da fushin mahaifa" idan kuwa mahaifanka sukayi fushi dakai babu shakka Allah zaiyi fushi dakai, idan kuwa Allah yayi fushi dakai kana cikin azaba. A nutse ya shiga ɗakin tare dayin sallama, a fuska idan ka kalleshi kuwa kamar ba abunda ke damunsa, saidai a karkashin zuciyar sa kuwa damuwace fall ransa domin baisan abuda yake faruwa ba. Shiga yayi ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, su uku ya tarar a ɗakin haji, mum sai kuma papu. A gaban haji yaje ya zauna amma a ƙasa saiti da ƙafarta, gaidasu yayi baki ɗaya duk suka amsa masa, saidai papu kam yana amsawa ya ɗauke kai fuskar nan tasa a haɗe. "Haji, don Allah laifin me nayiwa papu wanda bansani ba" turab ya faɗa ɗauke da damuwa. "Waƙa a bakin mai ita tafi dadi shi zaka tambaya ai tunda gaka nan ga shi" Miƙewa yayi cikin nutsuwa ya taka har gaban papu ya durkusa "papu, babanah, dan Allah idan nayi maka laifi ina neman afuwa da gafara a gareka, dan Allah ka yafemin duk da nasan Ni banyi maka laifi ba, amma kayi hakuri idan wani abu nayi kake dubin shi matsayin laifi na roƙeka da sunayen Allah tsarkakakku mahaifina" "Abu turab!" Papu ya kira Asalin sunansa a tsanake, yana kuma kifeshi da idanuwa. "Na'am papu" "Kasan anyi family meeting" "Nasani, kuma naga anyi sanarwa a group tun Kafin ayi" "Good, kasan me aka tattauna kuwa" "Eh nasani, kan maganar auren fahad ne" "Nice, but shi kaɗai kasami!?" "Eh, shikaɗai nasani gaskiya, kuma NASAN kaso chasa'in daga cikin ɗari na taron dan wannan maganar akayi shi" "Sauran kason fa" "Gskiya bansan sauran ba" "Turab ka saurareni sosai kaji abunda zan faɗa maka, jiya anyi maganganu da dama a wurin taron da akayi, kuma mafi yawa daga cikin maganar anyita ne saboda kai" "Saboda Ni ku....." "Dakata" papu ya katseshi ta hanyar ɗaga masa hannu. Da sauri kuwa yayi shiru kamar bashiba, papu ya ci gaba da faɗin; "mafi yawa daga cikin family sunyi korafi kan zamanka a haka har yanzu ba aure, ƙannenka da ƙannen ƙannenka duk sunyi aure, da aka lissafa ku, ku biyu ne zuwa uku kuka rage da ya kamata ace yanzu duk kunada iyalai, kuma duk a cikin waɗan nan da suka rage gaba ɗayan su ka girmemusu. Duk sa'anin ka wasu suna ƴaƴa biyu wasu kuma uku, amma kai gaka nan zaune ba aure. Wasu zasu iya tunani rayuwar banza kakeyi da wasu ƴammatan waje tunda kakai lokacin da Yakamata ace kaima kazama magidanci amma kuma hakan bata kasance. Na rantse da girman rabbi bakasan iya kunyarda naji a wurin ba, domin kuwa dole sai wani yayi zarginka da aikata mummunan abu a waje, wasu kuma zasu dubi da saka hannun mu a ciki. Babban abunda ya baƙatamin rai wai ashe mahaifiyarka ta taɓa kiranka da batun auren nan amma sam kaƙi yarda, akace maka meenal kace bakaso, akace Aneesa itama kace ah ah, ga fannah, ga mayah, duk kaƙi yarda, da ma wasu daga cikin ƴan uwanka. Turab so kake ka shafa min baƙin fenti a idon iyayen wadannan yara, kuma ina matsayin babba a garesu. Turab!!!!?" Papu ya ƙarashe maganar tasa ta karshe cike da sanyi. "A yi hakuri papu in sha Allah wani abu nakeda nufin naƙarasa da yarda Allah idan na ƙara sa zan fito da matar aure, kuyi hakuri ku ƙara bani lokaci" "Ba wani lokaci da zamu kuma baka turab wannan shine lokaci na ƙarshe saboda haka mun riga mun yanke hukunci" "Hukuncin me kuma mum!?" Turab ya tambaya cike da tashin hankali. "Mun zaɓa maka matar da zaka aura turab, kuma ba shawara muke baka ba umurni ne, inma kaso ko karkaso ruwan kane, idan kuwa kaƙi wallahi saidai ka changer wata uwar bani ba" "Nima saidai ka canja wani uban bani ba, zan iya yimaka alfarma ɗaya idan kanaso kaje ka auro matarda ka zaɓarwa kanka daga baya idan ka kammala abunda zaka yi, amma wannan kam sai anyi in sha Allah Indai ba gawata ke magana" "Subhanallah" ya faɗa a fili. Papu kar Allah ya nunamin wata rana da zaku shata min layi na ketare, wallahi na yi na'am da zafinku koma wacece, na amince ɗari bisa ɗari duk abunda kukayi akaina kunyi daidai kuma na gode sosai Allah ya saka muku da alƙairi Allah yasa ku ganmu yanda kukeso" A can cikin ransa kuwa tsoro ne da fargaba fal, "wannan shine dalilin da yaran nan suka dawo gidan nan saboda a haɗa aure, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Allah ka sanya wannan zabin ya zamo alƙairi a gareni. Ya rabbbb, wa nake da tabbacin itace aka zaɓarmin meenal banason meenal ban taɓa sonta ba, hakama mayah tayimin ƙanƙanuwa banasonta, Badar ma ƙaramar yarinyace Sa'ar ulud, Aneesa kuma batada tarbiyya, Airah ƴar Aunty Safiyyah ce ba aure tsakanin mu, khulud ƙanwatace bama zan sakota ba to wacece a cikinsu ya Allah!" Ya faɗa a zuciyarsa tare da dafe kansa dake yimasa azabar ciwo kamar zai tsage. Muryar haji ce ta dawo dashi hayyacin sa, sakamako tambayar da tayi masa "Abu Lafiya dai kho, anata yimaka magana kamar wanda ke bacci" A hankali ya ɗago rinannun idanuwansa da sukayi masa nauyi sosai ya kalleta, "bakomai haji, ba abun da ya sameni na ɗan shiga tunani ne kawai banji kuna yimin magana ba" "Ka shiga tunanin matarda aka haɗaka da ita kho" "Eh haji dan Allah wacece aka haɗani da ita" ya faɗa muryarsa na karkarwa. Shafff ya manta da mum da papu dake zaune a ɗakin domin kuwa shi kaɗai yasan abun da yakeji a zuciyarsa. "Karka damu kaji, kar ka saka komai a ranka domin kuwa iyayenka sunyi namijin ƙoƙari wajen yin tunanin haɗaka da yarinya mai hankali da nutsuwa, ga tarbiyya ga kunya, ga ilimin addini sosai, wallahi ka ƙara godewa Allah da ya saka iyayenka sukayi tunanin haɗaka da Leeyanah a matsayin matar da zaka aura" "What!!???, haji kinsan me kike faɗa kuwa wannan yarinyar ce aka haɗa ni da ita, Itace mum da papu sukeda muradin na aura?, impossible haji, wannan bazai taɓa yiwu ba" "Kamar yanda bazai taɓa yiwu mu kuma sakaka a jerin wanda muka haifa ba" Sai a lokacin ya tuna duk abun nan dake faruwa mum da papu na zaune basu fita ""ya subhanallah, na rantse da Ubangijin talikai na karɓi zaɓinku mum, wallahi ku yarda Dani" "Ka tafi" papu ya faɗa yana dafa kafaɗarsa, domin kuwa ya hango abun nan dayake hangowa a cikin idanunsa a duk lokacin da yake cikin halin tashin hankali" ( karku manta fa turab soja ne, kuma cikakken likitan Sojojin ƙasashen waje, saboda haka ana iya fahimtar abubuwa da dama a cikin ƙwayar idanun su, musamman ma idan suka faɗa wani hali). Juyawa yayi kawai baice uffan ba har ya fita ɗakin, tafiya kawai yake baya ma kallon gabansa duk inda ya samu jefa kafarsa kawai yake, idanunsa ma ba sosai yake iya bude su ba saboda sunyi masa nauyi sosai, ikon Allah ne kawai ya ƙaishi sashensa. A ɓangaren su khulud kuwa tunda suka shigo sashen ba wanda ya kuma fita, har aka kira sallahr ishah suna nan, sai bayan an idarda sallahr ne meenal ta fita da nufin ta zubowa leeya abinci taci, dalilin haka kuwa tun kafin ma turab ya gansu suna rawa ita leeya bata jin daɗin jikinta, saidai bata nuna ba sai yanzu ne da yaci ƙarfinta har ya kaita kwance. Duk jikinsu yayi sanyi, sunyi zugum suna zagaye da gadonda take kwance duk sun zuba mata idanu ganin yanda take makerketar sanyi, kuma bayan sun rufa mata blanket har biyu, amma ba abunda ya rage. "Badar kije ki dubo dan Allah idan su mum sun gama Maganar da suke ki gayamusu leeyanah batada lafiya" "Bara naje na duba, amma yanzun nan naga Aneesa ta fita bansan ko can zatajeba" "Okay tau ɗan jira, inaga can zataje domin duk ta fimu shiga damuwa" cewar MAYAH "Haka ne, kinsan Aneesa tanajin tsoron mara lafiya gani take kamar mutuwa zai yi a gabanta" badariyyah ta faɗa tana kafe kofar ɗakin da ido. "Allah sarki, in sha Allah leeya bazataje ko'ina ba" "Allah ya ƙaddara haka" "Ameen suka faɗa baki ɗaya har khulud daketa faman hawaye tun ɗazu. Da ƙarfi suka waiwayo domin ganin wanda ya banko ƙofar ɗakin. "Aneesa lafiya kike kuwa, saboda me zaki shigo bedroom a haka kamar wacce aka biyo za'a kasheta" cewar badar cikin jin haushin abunsa aneesar tayi. Muryar Aneesa na cracking tace"kunsan me, yanzu zan shiga sashen papu najiyo maganarsu daga ciki, har haji da mum duk suna cikin ɗakin" "Me kikaji suna faɗa a cikin ɗakin?" "Khulud, ji nayi haji nata faɗar ya-Turab yayi dace sosai ya sami mata mai hankali ga nutsuwa ga...." "Mata kuma Aneesa kodai bakiji da kyau ba, yaushe ya-Turab yayi budurwa har ana maganar mata bamuda labari" "Mtswww yanzu Aneesa kan wannan ne zaki shigo haka duk kinbi kin tada mana da hankali" "Hmmm, Mayah kenan ya zakiyi idan akace kece matar ya-Turab" "Nop Aneesa banason irin maganar nan kinji, turab yayana ne kawai kuma ɗan uwana, Saboda haka ba wani mata ko aure" "A misali ne fa kawai, kuma tambaya nayi miki kuma mu ƙaddara yana sonki fa, bawai baya sonki ba" "Kidaina misalin dani domin koda a mafarki hakan ta faru sai na ƙaryata mafarkin duk da nasan mafarki ba gaskiya bane amma sai na ƙara karya tashi domin haka bazata taɓa faruwa" "Tau mu kaddara bake bace wata ce ya kike gani zaman nasu zai yi" "Tabb, ai koda yana sonta ɗin dole sai tayi hakuri dashi sosai, domin ya-Turab zuma ne ga zaƙi ga harbi. A ganina kawai macen soja ce zamansu zai yi daidai idan allurarsa ta sojawa ta motsa itama ta motso da tata shikenan saidai acee Allah ya sauwaqe" "Idan yana sonta kenan koh, idan suna soyayya" Aneesa ta faɗa. "Ehmana, ai dama sai anason juna ake aure" sukaji muryar Airah tana faɗar haka. "Yawwa, to ya zakuji idan akace muku matar da aka bama ya-Turab basu taɓa soyayya ba, hasali ma bai santa ba, kuma koda yasanta bai taɓa ganin ta ba, basu taɓayin maganar da ta haura mintuna biyu ba" "Saidai addu'a kawai amma wannan lamarin zai yi mata wuya sosai wallahi, amma Hausawa sukace bayan wuya sai daɗi maybe tasha wahala wajen gane kansa daga baya kuma ya dawo kamar bawanta, wata ƙila kuma mukadaine bama samun sauqi a wajensa zai iya yuwa matar ta samo kansa sosai" "Hmmm, wallahi khulud bana tunanin haka, ki duba kiga yanda ya wulaƙanta meenal a gaban kowa saboda ta nuna masa so, shin meenal ta cancanci hakan a wajensa koda ba ɗan uwanta bane ai akwai hakkin masoyi, domin mai ƙaunarka ya gama maka komai a rayuwa" "Hakane Aneesa, mudai muna fatar wannan da aka zaba masa tayi dauriya da taurin zuciya domin idan ba haka ba zaman bazai yi daɗi ba" "Kunsan wacece za'a haɗa da ya-Turab kuwa" "Ah ha sai kin faɗa" cewar Badar. "Leeyana" Aneesa ta faɗa tana nuna leeya dake kanan naɗe a kan bed ko ina na jikinta sai rawa yake. "What" suka faɗa a tare kamar haɗin baki. Meenal ce tazo ta gaban Aneesa ta wuce dauke da farantin da ta sako wa leeya abinci. Kan side drawer ta ajiye farantin. Kaff a cikinsu ba wanda ya iya cewa komai, kowa da abunda yake saƙawa a ransa. Leeya kuwa numfashin ta ne ya tsaya chakkk, halin ciwo ne kawai yasa batayi wani ƙwaƙƙwaran motsi ba, domin duk firarsu tun daga farko har ƙarshe ba abunda bata jiba sai abunda suke faɗa yanzu, yanzu kam duk hankalin ta yabar jikinta. Addu'ar ta kawai Allah yasa mafarki take duk abunda taji ba gaskiya bane, tana fatar haka a ranta. Komawa sukayi suka zauna gaba ɗaya domin kuwa al'amarin yafi gaban wasa ba wacce ta iya cewa komai daga cikin su, sun rasa me zasuyi tsakanin murna da jimami, leeyana ƙawarsuce koba komai zasuyi farin ciki idan abun farin ciki ya samu, koda ba ƴar uwarsu bace ai akwai haƙƙin zama wuri ɗaya. Turab kuma yayansu ne dole suyi murna a duk lokacin da wani abun alƙairi ya sameshi, kuma suyi baƙin ciki a duk lokacin da abun baƙin ciki yasameshi, wannan kam saidai su kirashi abun alƙairi domin aure rahmace mai lulluɓe da alƙairi, amma ba halin yin murnar a yanzu saidai ko daga baya. Meenal ce ta kalli leeyana cikin tausayawa halin da take ciki tace "Leeyana tashi ga abinci kici kinji" Cikin Muryar da take nuna alamun mai ita na dauke da zazzaɓi mai zafi tace "meenal da gaske ya-Turab aka bani a matsayin mijin da zan aura" Meenal da ta fahimci idan tagayawa leeya gaskiya komai zai iya faruwa a yanayin nan da take ciki na mara lafiya yasa tace "ah ah ba gskiya bane kinji, wasa ne suke kawai suna zolayarki ne kawai, ina zaki iya da soja kuma litana sojoji leeya, wannan ai sai irinsa kinga ƙwarya tabi ƙwarya kenan" meenal da faɗa cikin ƴar dariyar da kanaji kasan iya laɓɓanta ne. Miƙewa leeya tayi zaune meenal na taimaka mata har ta jingina ta ga kan gadon ta yaye mata blanket din da ta rufa dashi ta barmata shi iya gwiwoyinta. Haƙiƙa duk wanda ya kalli leeya zai fahimci tsananin tsoron da ke cikin zuciyarta sakamakon wannan maganar da taji su Aneesa nayi, meenal dake kusa da ita sosai takejin ƙarar bugun zuciyarta ta karfi kamar ganga. Meenal ta fara bata abincin tare da yimata kalamanda zasu kwantar mata da hankali koba komai tana bukatar su domin batada lafiya, a hankali har ta fara ƙoshi. Sannan ta gayawa meenal cewa ta ƙoshi, magani meenal ta ɗakko a can parlon ƙasa ta dawo tare da ɓallawa ta bata, bako gardama ta karɓi maganin tasha, ta maida kwanciyar ta. Su kuwa khulud suna fira jefi-jefi suna yimata ya jiki kuma, mum ce ta shigo ɗakin tare da yimusu sallama duk suka amsa mata suna gaida ita. "Ina leeyanah" ta faɗa tana rarraba ido a tsakanin su. "Mum leeyana na kwance batada lafiya tun safe" khulud ta faɗa tana nuna leeya dake kwance kan bed bacci ya fara kwasarta sai dai wannan karon ba rufe dake ba. Da sauri mum ta isa gareta tare da dagota "leeya bakida lafiya har haka, meenal meyasa bakuzo kun gayamin batada lafiya ba, za'a bar mutum haka da ciwo ne" Meenal ta kalli mum cikin damuwa da halin da leeya ke ciki tace "Wallahi mum, mun aike Airah taje ta sanar miki amma ba'a sameki a part ɗinki ba, sai dai tasha magani yanzun nan.................✍🏽 BAYAN WUYA........ By RUMANA M DIGGI EP.35 _______________mum ta kalli leeya cikin kulawa tace" ko muje asibiti?" "Ah ah mum kinsan banason zuwa asibiti dan Allah wallahi yanzu ma nasha magani kho meenal, ke kika bani maganin da hannunki nasha" Mum ganin hankalin leeya ya tashi yasa tace mata"shikenan kiyi kwanciyar ki kinji ba inda zamuje, amma da sharaɗin idan baki walwale daga zazzaɓin nan ba gobe ba abunda zai hanaki zuwa hospital" "Tau mum, in sha Allah zanje idan bansamu sauqi ba" Daga haka mum bata ƙara cewa leeya komai ba, ita kuma tayi kwanciyar ta har bacci ya ɗauketa. A ɓangaren turab kuma tunda ya shiga ɗakin sa ya zube kan gado ko wani dogon motsi bayayi, domin tun da aka faɗa masa maganar kansa ke bala'in ciwo, hannusa ya saka ya fara lalubo wayarsa, ɗaga idanunsa yayi da kyar waɗan da suka rine suka jajir saboda azaba, number fahad ya lalubo tare da danna masa kira ringing ɗaya ɗaga. Banji abunda ya faɗa daga cikin wayar ba saidai shi turab ya buɗi baki da kyar yace "ka fasa kenan", shikenan goben ku shigo kawai sai muyi magana" Daga haka bai jira cewar fahad ba ya kashe wayar. Ya jima kwance a wurin ko motsin kirki baya yi, sai kamar Bayan mintuna arba'in tsakani ya miƙe hannun sa dafe da kansa yana tafiya a hankali yana cije gefen lips ɗinsa na ƙasa tare da runtse idanun sa duk taku ɗaya da zaiyi. Har gaban akwatin da yake saka magunguna ya isa tare da buɗe a akwatin yafito da wani magani nannade a farar yana, sannan ya kuma ɗauko wani daban a cikin kwalli ya ɓalla ɗaya, daga nan kuma ya ɗauko wani syrup yasha marufi ɗaya, tashi yayi da sauran a hannunsa ya isa har gaban fridge ya buɗe Sannan ya ɗakko robar ruwa ya haɗiye magungunan da ke hannunsa. Komawa yayi kan bed ya kishin giɗa, har kuma lokacin kansa bai sassauta ba. ★ Washe gari tunda asuba meenal ta farka daga bacci, ganin kamar lokacin sallah ya kusa yasa bata maida kwanciyar ba, Waya ta janyo tare da kunna ɗan hasken screen ɗin wayar, ganin saura mintuna goma sha ɗaya akira sallah yasa tayi niyyar tada su khulud suyi sallah, side lamp ta kunna daga nan kuma ta kai hannu kan wuyan leeya dake kwance ta taɓa, Sosai tayi mamaki jin jikin nata raɗau kamar abunda aka zubawa ruwan zafi "Allah sarki leeya har yanzu ana ta fama da ciwo Allah ya baki lapiya" Airah kuwa jin ana magana ne yasakata buɗe idanunta a hankali domin batada nauyin bacci ko kaɗan "meenal lafiya!?" Ta faɗa a ɗan tsorace ganin leeya kwance ita kuma meenal ta sakata a gaba tana haske ta da touch. "Da dama dai Airah" Da sauri Airah ta sakko kan gado ta nufo gadonda su leeya suke tace; "meenal zazzaɓin ne har yanzu" "Eh wallahi Airah, ki taɓa jikinta kiji yanda yakeda zafi sosai" Hannu Airah takai tare da taɓa wuyanta "Ah'uzubillah, meenal kinji yanda jikinta yayi zafi, gaskiya meenal zanje na gayawa mum tazo Wallahi tsoro nake ji kar ƴar mutane ta mutu a hannun mu" "Bazamu gayawa mum a Yanzu ba, mu bari idan safiya ta waye sosai sai muje mu sanar musu, kuma nasan mum zatazo part ɗin nan domin ta dubamu idan mun samu Sallar asubu, ko batazo dan haka ba zatazo dan tabar mara lafiya jiya, saboda haka muyi hakuri tazo kawai, daga nan ma sai suje asibiti gaba ɗaya, amma yanzu idan muka gayamata zamu tada mata hankali ne kawai, kuma zatace sai anje asibiti kuma koda anje asibitin kinsani ba likitoci saidai masu shara" "Haka ne meenal, amma haka zamu zuba mata ido har sai mum tazo ai abun da tausayi wallahi" "Yanzu darena Airah da kinje parlourn ƙasa kin ɗauko min maganin rage zafin jiki, dana sani jiya da nah ɗauko sachet ɗin gaba ɗaya" "Bara naje na dauko kawai meenal, bani fitilar wayanki wayana ba chaji" "Ah ah karki fita yanzu kinji Airah, kije toilet ki jiƙa towel da ruwa masu sanyi sosai ki kawomin saina rage mata zafin jiki da shi" "Okay tau jiran mintuna biyu gani nan zuwa" Airah ta faɗa ta ficewa ɗakin da sauri. Haka kuwa akayi da taimakon towel ɗin zafin jikinta ya ragu, kuma ba abunda ya rage na game da ciwon saidai ma abunda yayi gaba domin jiya Bata yin amai, amma daga wayewar gari zuwa yanzu tayi amai yakai sau huɗu. KhUlud na zaune a gefen ta, ita kuma tana daga kwance. Sai meenal, badar, Airah da mayah duk suna zaune kan gadon, Aneesa kuma tana daga gefen damanta ta riƙe hannunta cikin tausayi, "Ki tashi muje sashen haji idan zaki iya ta aiko tace kizo kiyi breakfast sannan kuje asibiti" Miƙewa tayi da kyar suka taimaka mata har ta tashi gaba ɗaya, miƙewar ta keda wuya amai kuwa ya bijiromata da gudu ta isa toilet ta nufi sink, "Yau ta wahala wallahi Ni har tausayi ma take bani" "Gaskiya kam ko wannan aman wahala ne balle kuma ga zazzaɓi, Allah dai ya bata lafiya" "Ameen" khulud ta faɗa daidai lokacin da leeya ke fitowa daga toilet. Hannunta meenal ta rike har sashen haji, da kyar leeya ta iya ƙarasawa da kanta duk da tana tsayawa ta hutawa, da yake ba wata tazara tsakanin sashensu dana haji, suna sashen meenal ta wuce bedroom ɗin haji, ita kuwa leeya ta kwanta kan sopa duk da ba daɗin kwanciyar tayi ba amma zafin ciwon ya sakata kwanciya bata damu da rashin jin dadin ba. Haji ta fito daga bedroom tare da meenal har suka ƙara so inda leeya ke kwance. "Leeyanatu ashe bakyajin daɗi mu bamu sani ba" "Haji ina kwana" "Lafiya lau leeyanatu ya jikinki" "Naji sauƙi haji zazzaɓi ne kawai" "Allah sarki Tau Allah ya baki lafiya, Bara na zubomiki koko mai zafi danayi yanzu sai kisha, kafin na kira Abu turab yakaiki asibiti" Gabanta ne ya yanke ya faɗi sakamakon sunan turab da taji haji ta furta "Nagode sosai" ta faɗa da dusashshiyar murya. Koko mai zafi haji ta ɗebo ta har gabanta ta kawo mata, ita kuma meenal tunda ta rako leeya ta fice daga sashen domin tayi aikace aikacen da ya kamata ace tayi. Haji kuma ta fita zuwa sashen turab domin gayamasa, tana fita sukaci karo da papu shi kuma yazo ya gaida ta da safiya "Haji ina za'aje haka" "Wallahi zanje sashen Abu ne na gayamasa yazo yakai leeyanatu asibiti aduba ta" "Leeya batada lafiya ne" "Eh wallahi tun jiya akace batada lafiya ta kwana tanayin amai" "Subhanallah, amma da ciwo a jikin mutum tun jiya ba'a faɗi ba, ai da ankira ko dr.jif ne yazo ya dubata" "Wallahi Nima bansaniba sai daren jiya nakejin fanaya na sanardani" "To Allah ya sauwaqe" "Ameen ya rabbil ibaddd" Haji ta faɗa daidai lokacin da suka ƙara so part ɗin turab. zaune yake kan darduma ya kammala Sallar walha yana tazbihi yaji ƙarar kwankwasa kofa, miƙewa yayi yaje har gaban ƙofar ɗakin ya buɗe ba tare da yace komai ba, ganin haji harda papu yasa ya faɗaɗa fuskar sa da murmushi "haji yau ziyara aka kawomin kenan, pa barka da safiya" ya faɗa yana ɗan rusnawa a gabansu. Shafa kansa papu yayi shima fuskar sa ɗauke da murmushi yace"son barka dai, ka tashi lafiya" "Eh pa lafiya ƙalau nake stress kaɗai ke damuna" "Uhmm--hmmm tau ayita hakuri kaji, Allah yayi maka albarka ya kuma baka ladar biyayya" "Ameen pa" turab ya faɗa har haji ma ta amsa da faɗin ameeen. "Ku shigo daga ciki" "Ba shigowa zamuyi ba nabar mara lafiya a sashena kuma ba kowa a tare da ita" "Subhanallah, waye ba lafiya kuma" "Leeyanatu" haji ta faɗa. Wani abu yaji ya tsargamasa tun daga tsakiyar kansa har tafin ƙafarsa"Allah ya bata lafiya" "Ameeen, kazo muje ka fara sauke nauyin ta dake kanka" "Muje nayi mata me haji" ya faɗa fuskar nan tasa babu yabo ba fallasa. "Ka kaita asibiti" "Haji dr.jif fa" "Baya gari" "Okay gani nan tafe idan nayi wanka" "Turab karka jima kaji, kasan ciwo ba daɗi tun jiya take fama wallahi" "In sha Allah bazan jima na papu zanyi ƙoƙari naga na kammala komai yanzu" "Yauwa Allah yayi albarka" "Ameeen pa" Komawa yayi cikin ɗakinsa haji da papu kuma suka koma sashen mum. Yana shiga ɗakin nasa ya mayarda ƙofa ya rufe, wayansa ya ɗakko ya ɗan dudduba kafin ya ajiyeta a gefe ya shiga toilet. Ba jimawa yayi wanka ya fito, a nutse ya yi shirinsa cikin plain cotton yard, violet Ash color. Kalar yadin yayi masa kyau sosai ga dinkin da ya zauna tsaf dashi a jikinsa. Farin gilashin da ya ƙarawa fuskar sa cika da Haiba ya ɗakko ya saka sannan ya saka hularsa plat cap dark ash ya zura takalmansa ya fita ɗakin. A can ɓangaren leeya kuma, tana kwance har yanzu kamar yanda haji ta barta, bata sake dawowa ɗakin ba domin a tunanin ta turab ɗin yazo dan bataga dauɗa a jikinsa ba balle tayi tunanin ko sai ya ƙara yin wanka. Leeya kwance a kan Centre carpet ɗin tsakar parlorn duk ta jeme da ita, ba abunda yake tada ita daga kwancen sai idan taji amai na batun kwace mata. Ƙamshin turarensa ne ya bugi hancinta yayinda yake shigowa parlourn, sallama yayi da tunanin ko haji na parlourn. Daidai lokacin da ya shigo tsakiyar parlourn, leeya ta zabura da ƙarfi ta dafe saitin bakin ta daga cikin niqab, da gudu ta biyo ta gabansa zata wuce take ya kara mata ƙafarsa tayi tuntuɓe da kafarsa har saida ta faɗi ƙasa. Ƙara miƙewa tayi da nufin ta tashi ya damƙo gashin kanta ta gabansa yana fuskantar ta kuma babu wata tazara sosai a tsakanin su, juya kanta tayi gefe still hannayenta na rufe da bakinta sai zare idanu take tana wani yunkuri tun daga ƙasan maƙoshi. "Ke! Dan ubanki shine zaki ganni ki nemi guduwa harda wani toshe hanci da baki ga dodo ko, wai wace irin mai kunnen ƙashi ce ke? Ban faɗamiki karki ƙara yin irin haka idan kika ganni ba, shine zakije ki liƙewa mum da papu har haji kin asirce su da wadannan mayun idanun naki kika saka aka tauyeni ko, wai za'a haɗamu, Ni in aureki, hmmm, God forbid bazan taɓa haɗa inuwa dakeba leeyana, kuma kada ki saka ranki zan aureki domin hakan bazai taɓa faruwa" rufe bakinsa keda wuya yaji saukar amai da ya fito da karfi daga bakinta zuwa jikinsa. Suman tsaye tayi ba abunda zaka gani a idanun ta face zallar tsoro da fargaba, tunani take kan maganganun da ya gama faɗa mata yanzu, me yake nufi da aure kuma, me asirin da ya faɗa yake nufi wai nayiwa mum, da papu da haji asiri da idanuna, idanuna kuma, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un bazamu taɓa zama inuwa ɗaya ba, ya-Turab duk ina kalaman nan naka suka dosa. Tayi nisa a cikin tunanin da take domin ita bama aman data lalata masa jiki dashi ne damuwarta ba, sarƙaƙƙun maganganun da yayine keyita dawo mata arai haƙiƙa da zai bata dama da ta nemi ƙarin sani daga waɗannan maganganun nasa. Saukar wani kafirtaccen bahagon mari ne da taji ya sauka a fuskar ta ya dawo da ita hankalinta "dan kinga an nuna ki a matsayin wacce zan aura bashi yake nuna cewa Ni sa'an ki bane wallahi idan baki shiga hankalin ki ba sai na nuna miki na wuce da saninki kuma wallahi rigarnan da kika ɓata sai kin gyarata. Gata nan kije ki wanketa ki busarda ita da dryer sannan ki gugeta ki kawomin gani nan ina jiranki, kuma da hannu zaki wanketa banason wankin machine na baki mintuna goma sha biyar kije ki dawo idan kuma ba haka ba jikinki ne Zai gaya miki wallahi" Turab saboda fitina irin tashi ya ma manta da batada lafiya, ya rufe ido rufff yana zabga mata rashin mutunci. Duƙawa tayi da kyar ta dauki rigar da ya cillo mata, a hankali take iya ɗaga ƙafarta tana takawa har ta shiga toilet. Tana shiga kuwa ta durkushe tare da sakin wani marayen kuka mai cike da ban tausayi, sai da tayi kukanta ta gaji ba mai rarrashi daga nan ta wanke fuskar ta ta koma laundry room ta wanke masa rigarsa da daddafe ta fita, tana fita ta sakata dryer ta bushe sannan ta goge masa ita kamar yanda ya buƙata. Sosai tayi ƙoƙarin yin aikin domin ta galaɓaita. Fitowa tayi da rigar a hannun ta tana dafa bango a hankali tana tafiya har ta shigo parlourn, babban abunda ya bata mamaki shine ganinsa a zaune har ya canjo kaya ya saka wasu kayan daban. Har gabansa ta ƙara so tare da durkusawa har ƙasa, bata iya ɗaga kanta ta kallesa ba domin ita a ko yaushe tsoron sa da takeji yana ƙara ninkuwa a zuciyarta. "Allah sarki ya jikin naki da sauƙi ko, kinga Ni harma na chanja kaya ki ajiye waɗannan a wurinki kinji, Allah dai ya baki lafiya ki tashi muje kar muyi letting muje da wuri a dubaki, sannu kho" Turab ya faɗa da sassanyar muryarsa mai cike da kwarjini. Mamaki ne ya kusa kasheta da mugun sauri ta ɗago kanta domin ta ganewa idonta shine ko kunnuwanta ne suka fara samun matsala. Tana ɗago kanta kuwa sai taga mum da haji da sukayi turusss a bakin ƙofar shigowa ɗakin su a zatonsu duk soyayyarce haka. "Ki tashi muje kinji, ko na ɗagaki ne" Da sauri na zabura ganin da gaske yake "ki ajiya rigar har mu dawo mana, ke duk da bakida lafiya bazaki huta ba gaskiya sai naje na sami su mum a daina wahalarda ke wallahi zai iya yiwa ma gajiyace ke sakaki zazzaɓin nan" ya faɗa yana karɓar rigar daga hannunta cike da kulawa. "Muje" ya faɗa yana juyawa, "lahhh, mum yaushe kuka shigo ne" "Ina zakasan mun shigo kana ta shan soyayyarka" "Wane soyayya kuma haji, ana soyayya ba lafiya" "Ko ba'a yi kaikam gashi nan kanayi" "Ah ah nikam ba wata soyayya wallahi" "Dallah wuce ka bamu wuri mu bama son shashanci mara kunya kawai" "Mum har da su kora lallai ma, idan bakya buƙata akwai masu bukata indai nine'' cewar turab Yana rufe fuskar sa da tafin hannun sa tare da fita parlorn da sauri yana dariya. Sai yanzu na fahimci duk wannan abun da yayi saboda yaga su mum ne, Allah ne ya tausayamin ya kawo su mum domin da badan su ba bansan wane kalar hukunci zai yimin na sakamakon na haura lokacin da ya ɗiba kansa zan gama aikin da ya sakani. Muna fita ɗakin ya ɗaure fuskarsa tamau kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa, parking space ya nufa Ni kuma na tsaya gefe ina kallon sa kafin ya fito da motar. Sake matsawa nayi kusa sosai domin har ya fito da ita fili, gaban motar na buɗe na shiga na zauna, wata Uwar tsawa ya dakamin "ke dan uwarki baki iya sallama bane da zaki shigo wuri ba sallama" Baki na rawa nace masa"kayi hakuri dan Allah, wallahi na zata nayi sallama ne kayi hakuri wallahi zafin ciwo ne ya sakani" "Sannu asibiti, ciwo kho? Nace sannu asibiti wallahi kika sake shigowa wuri idan ina nan baki yi sallama ba sai na saɓamiki wawuya kawai daƙiƙiya" Kamar saukar tafasasshen ruwan zafi naji a zuciyata irin munanan kalaman da ya-Turab ke min. Da sauri na ɗago kaina domin in gayamasa Ni ba ɗakikiya bace kuma Ni ba wawuya bace, amma sai na kasa mayar masa domin rashin kunya ba halina bane kuma bansaba yi akan kowa ba balle nayi akansa. Mayarda kaina nayi ƙasa bance masa komai ba, sai hawayen dake faman zuba a idanuna kamar ana izosu da karfi. Hannun sa ya saka ƙasan wuyanta tare da ɗago haɓarta ya saka tissue ya fara goge mata idanunta da hawaye ke zuba, a hankali yake goge mata idanunta kamar yana tsoron tissuen ya taɓa ta "kiyi hakuri kinji Yanzun nan zamu ƙarasa, ki daina kuka kinji Allah ya sauwaqe, ya baki lapiya" Dosƙarewa tayi tana kallonsa saidai ba shi take kallo ba idanun ta ne kawai a kansa ko kaɗan bata iya kallonsa na seconds biyar domin yana yimata kwarjini sosai a duk lokacin da ta kalleshi sai tsoronsa ya ƙara nikuwa a cikin ranta. Bai gushe ba har yanzu yana goge mata hawayen tare da kalamai masu kwantarda hankali. Daga can wajen motar naji muryar papu da fara'a yana faɗin "turab har kun fito" Shima ya kalli papu da alamun jin kunya yana ɓoye tissuen da ke hannunsa yace "lahhh papu har ka fito, Ni bankula dakai na ma ashe har ka fito, ga ƴarku nan sai kuka take wai batason allura". "Leeyana my daughter kiyi hakuri kinji, ciwo sai anyi haƙuri kinji. Kuma ciwo ne yake shiga da sauri Lafiya a hankali take shiga saboda haka kiyi haƙuri kuje Allah ya kai lafiya kuma ya baki lapiya kinji". "Ameen" ya Turab ya faɗa nikuma na ɗaga kaina kawai hawaye na ci gaba da fitowa a idanuna ina mamakin ya-Turab a ƴan mintunan nan tsakanin sa da mum, da haji da kuma papu. To meyake nufi..........................✍🏻 BAYAN WUYA..... By RUMANA M DIGGI Ep.36 ____________har muka fita gidan bai ko kalli inda nake ba balle yayi min magana, a haƙiƙanin gaskiya na kasa gane manufar ya-Turab kan wannan abun da yakeyi. Cikin nutsuwa yake tuƙinsa yayinda ya saka karatun Alkur'ani mai girma a speakers ɗin motar, duk da zafin ciwon da nake ji bai hanani bin karatun a zuciyata ba. Har muka ƙaraso asibitin bai cemin komai ba, muinda ake packing ɗin mota muka iso ya buɗe kofar ya fito nima na buɗe na fito. Office ɗin likitan da yakeda duty muka shiga bayan yayi tambaya angayamasa wanda zamu gani, bai nunamin komai ba a asibitin shiya tsaya yayi komai har aka kammala yimin abunda za'a yimin. Allurai aka yimin, kuma aka aka sakamin drip gora ɗaya, bai je ko ina ba har ruwan ya ƙare domin ni bacci ma nayi bansan abunda ake ba. Ina farkawa na ganshi a ɗan gefe dani yana danna wayarsa ba abunda ke damunsa, cikin raunananniyar muryata dana keyi a duk lokacin da yake zaune kusa dani ko kuma idan na ganshi nace "ya-Turab dan Allah ka kiramin zohal inaso nayi magana da ita na bar wayana a gida" "Ki bari idan kin koma gida ki kirata amma bazan baki wayana ba" ya faɗa ko kallon inda nake baiyiba kuma bai fasa danna wayarsa dake hannunsa ba. "Dan Allah ya-Turab......" Cikin tsawa da ɗaga murya yace"nace bazan bada ba kho, idan kuma ke kika siyamin wayar kizo ki karɓa" ya faɗa yana miƙa wayar Alamar ta karɓa. Kamar dai kullum hawayene ya cika mata idanu bata sake cewa komai ba ta mayarda kanta zata kwanta taji yace"kinajin yunwa ne, ko akwai abunda kike buƙata ki faɗa fita zanyi yanzu, kuma ga su mum da haji da sauran ƴan uwanki nan tafe, saura idan sukazo ki faɗa musu wani abu, kindai san hausawa sunce "nuna sani a kasuwar jahillai, wautane" idan kuma kina musu ki faɗa musu kigani" "Bana buƙatar komai" . na samu kaina da faɗar haka batare da na kalli gefen da yake ba. "Hmmm" kawai ya ya faɗa yana barin ɗakin. Fitarsa ba jimawa kamar da mintuna biyar zuwa shida ya dawo, tun daga ƙofar ɗakin na fara jiyo hayaniyar ƴan gidan mu, sosai raina ya cika da farin ciki koba komai zan sha iska yanzu. Domin zaman ya-Turab a tare da Ni ba abunda yake ƙaramin sai wulaƙanci da tozarci. Tana tsaka da tunanin tane taji muryar zohal na kwala sallama lunch bag a hannun ta. Sosai farin ciki ya cika ranta samakon ganin abokiyar ta ɗaya tilo, Da sauri ta ƙaraso inda leeya ke kwance hankalinta duk a tashe. "Besty Leeya bakida lafiya har haka kuma baki sanarda ni ba, dan Allah zama yace haka" Cikin sanyin jiki irin na marasa lafiya leeya ta tashi zaune sosai tana fuskantar zohal tace"zohal kiyi haƙuri Kinji, wallahi nima bansan ciwon zai kai har haka ba. Jiya ne fa da safe kuma wallahi tun lokacin ban ƙara amfani da waya ba balle na kiraki na gayamiki amma kiyi hakuri kinji" "Ba komai fa, kawai dai banji daɗi bane wallahi, Allah ya baki lafiya". "To amma waya gayamiki banada lafiya ne" "Wallahi gobe mukayi niyar mu rubuta invitation kuma kinsan dole sai dake za'ayi komai, shiyasa na kiraki ɗazu da safe na gayamiki ki shirya gobe za'a rubuta, sai kawai naji khulud tana gayamin wai bakida lafiya tun jiya har ma ankai ki asibiti" "Ina su khulud ɗin suke" "Tare muke dasu da kuma ya-Turab amma Ni na rigasu isowa gaskiya bansan meya tsayardasu ba" Leeya na shirin yin magana sai sukaji an buɗo kofar. Airah ce sai kuma mayah dake bayanta. Da sallama suka shigo dakin suma suna ɗauke basket food. "Leeyana ya jikinki" "Jiki alhmdullillah Airah, ya gida" "Lafiya lau munata kewarki" "Ai naji sauƙi wata ƙila ma za'a sallame mu yau" "Tau Allah yasa, amma inaga kamar hakan zaiyi wuya, dan naga ya-Turab yakai papu wurin likitan da ya dubaki, har likitan ya bashi takardar da za'a shiyo magungunan da allurai". Airah na gama faɗin haka sai ga mum, haji, meenal, badar da kuma khulud sun turo ƙofar gaba ɗaya suka shigo. Sosai suka nuna damuwarsu yanda suka ganta duk tayi wani iri kamar ba ciwon kwana biyu ba. KhUlud ce ta matso kusa da ita sosai bayan tayi mata ya jiki tace "leeya waya gayawa saurayin ki bakida lafiya" Sai da gabanta ya faɗi ta ɗaga idanuwanta da duk suka jeme har colour ɗinsu ta blue ta ƙara fitowa abun tsoro tace"kamar ya bangane ba, waye saurayin nawa?" "Samari nawa ne dake?" KhUlud ta faɗa "Ko ɗaya" leeya ta faɗa a takaice sai dai har yanzu muryarta bata dawo nml ba. "Hmmm, menene Matsayin Wanda kuke tare dashi a koda yaushe ta hanyar turamasa da saƙo a duk lokacin da kikaga saƙonsa" "Wannan ba saurayina bane, amma kuma ina jin sa a zuciyata fiye da idan yana saurayina. Sai dai ko za'a tambayeni a Yanzu bazance ga matsayinsa a wurina ba" "Hmmm, wannan ma wata babbar alamace leeya, yanzu bakida lafiya bamuda lokacin da zamuyi maganar nan har sai kin warke hankalin ki ya tsayu wuri ɗaya, daga nan ne nakeso ki zauna kiyi tunani kan abunda zai fisshe ki, kinga wannan bawan Allah dayake turamiki saƙo a koda yaushe?" Leeya ta ɗaga kanta alamar "ehhh" KhUlud ta gyara zama taci gaba da faɗin "wallahi na tabbatar da soyayyarsa gareki gaskiya ce, a yanda yake kula dake hakan nan ba kowane namiji bane zai iya yin haka, wallahi daga jiya da aka kawo ki asibitin nan ya turamin sakonni sunfi a kirga da wayanki dake hannuna, kuma ba saƙo ɗaya da ya turamin da number iri ɗaya, kin ma san menene? Wallahi wancan box da kika gani daga gareshi ta fito, kuma sakonsa ne zuwa gareki". Khulud ta faɗa tana nuna wata ƴar qaramar kyakkyawar akwati wacce da alamu abinci ne a ciki, sai kuma wani gefe daban da akayi wasu ƙananan abubuwan daga gefen akwatin, kamar dai wurin saka ruwa ko wani Abu mai kamada haka. Da mamakin da ya Bayyana ga leeya ƙarara ta kalli khulud irin kallon nan na bangane abunda ki ke nufi ba. Kamar khulud ta karanto abunda ke zuciyar leeya tace "baki gane ba kho?" Cikin son jin ƙarashen zancen leeya tace "eh wallahi ban gane ba, dan Allah kice min kinganshi kuma kin sanshi Please, wallahi ina so na san waye a tsawon lokacin nan." "Uhmm--hmmm, ki kwantarda hankalinki nayi miki bayani" "Ina saurarenki khulud nasan kin sanshi kho!?" "Ah ah wallahi ko kaɗan Ni bansanshiba, hasali ma ba waya mukayi dashi ba, kamar yanda kuke magana dashi ta hanyar turo da sakonni, haka nayi magana dashi har wannan sakon ya shigo hannuna, da taimakon wayarnan taki. Yayi min bayani inda zan sameshi da kuma kalar kayan da ya saka a jikinsa, sannan kuma ya gayamin yanda zan sami saƙon da kuma kalar saƙon wato box ɗin nan dake gabanki, nayi iya ƙoƙarina wajen ganin ba'a sami mistake ba, haka kuwa bamu samu mistake ko ɗaya ba wajen kwatancen da yayi min da kuma yanda nayi saurin ganewa. Sai dai abun mamakin shine koda naje wurin sakon kaɗai na tarar babu shi mutumin, ina shirin tura masa saƙo ne naji shigowar saƙonsa "khUlud k-waasib kho, bravo kinyi ƙoƙari sosai da kikayi saurin gano wurin nan, nasan zakisha mamaki sosai idan kika zo wurin nan baki ganni ba, amma kuma hakan shine daidai domin bamuyi dake zaki ganni ba saƙo kawai nace zan bada kuma ga sakon nan a gabanki ki ɗauka ki wuce, na roƙeki da girma Allah ki kaiwa dream girl saƙon nan kuma kigayamata ya fito daga babban masoyinta mai burin zama da ita har abada ki dauka ki kaimata please kema ina yimiki godiyan ki ta musamman sai anjima". Wannan shine sakon da ya turomin lokacin da na iso wurin da yace mu haɗu, Ni kuwa ina gama karanta saƙon na tsaya shawarar ɗaukar box ɗin ko na ƙyaleta domin na fara zargin wani abu, bankai ga karasa zancen zuci na ba naki shigowar wani saƙon, "khulud me kike jira naga har yanzu baki ɗauka ba ko kina tunanin Ni mai cutarwarne zan Cutar da ke kho?, to ki daina wannan tunanin domin ko wata bakeba bazan iya cutar ta ba balle ke, idan na cuta muku wallahi amanar so da haƙƙi bazasu barni ba kidaina wani kokonto kinji kho" maganarsa kenan a cikin saƙon kamar mai gargaɗi. Mamaki ya kamani sosai domin bansan yanda akayi ya gane ban ɗauki saƙo ba, babban abunda yaban mamaki shine yanda akayi yasan sunana har da na papu, "mamakin me kike wata ƙila leeyana ta gayamasa tunda kinga soyayya suke ai" wani bangare na zuciyata ya faɗi haka. A fili na furta "to ya akayi yasan ban ɗauki saƙon ba, me hakan yake nufi? Kenan yana nan. Dube-dube ta farayi hagun ta da dama domin taga ko zata hango wani da hankalinsa ke kanta saidai bata iya gane komai ba. Durƙusawa tayi ta ɗauki box ɗin ta miƙe zata wuce sai kuma taji an sake turomata da sako "yawwa ko kefa, amma fa ki daina tunani zaki ganni, bazaki ganni ba saɓanin Ni da nake kallonki a yanzu haka duk abunda kike ina gani, hannunki ɗaya akwai shopping leather, ɗayan kuma saƙon da na baki ne da kuma wayanki sai kuma ke kanki da kike rataye da handbag fara da hijab ɗin ki light-blue ko ba ke bace". "Nice" na faɗa a fili saboda tsananin ruɗewar da nayi domin Ni a nawa ganin wannan mutumin ba mutum bane duk yanda akayi aljanine. Amma kuma zuciya ta bata karfafa ni wajen cewa shi aljanine domin ko aljanine bai cutarda keba a iya tsawon zamanku, kuma Nima ya ƙara jaddada min bazai cutardani ba saboda haka dan Allah ki kwantarda hankalinki kinji, ki taimakamin na sauke wani nauyi dana ɗaukarwa kaina" "Wane nauyi kika ɗaukar wa kanki khulud?" "Nayi masa alqawarin zaki karɓi wannan kyauta tasa da hannu biyu, kuma zaki ci, nasan kin yarda dashi kuma ma ai shi ɗin masoyinki ne akwai soyayyarsa mai girma a zuciyarki nasan da haka saboda haka bama sai nace kici ba nasan zakije". "Amma kafin nan kibani wayar nayi magana dashi, sannan kuma nayi masa godiya da kyautarsa gareni, haƙiƙa naji daɗin kyautar nan ko ba komai nasan ina ransa tunda har ya binciki lapiya ta kuma ya damu dani har ya kawomin kyauta duk da bansan meye a ciki ba" "Karɓi to ki yi masa saqon bara na buɗe naga abinda ke cikin box ɗin nan" khulud ta faɗa tana miƙawa leeya wayar da ke hannunta a lokaci ɗaya kuma tana janyo box ɗin da ke gabanta. Karɓar wayar tayi ta rubuta masa zanzamammen sako mai cike da sanyi da kwanciyar hankali tare da tsaftatacciyar godiya. "Wow, Masha Allah" khulud ta faɗa lokacin da take buɗe box ɗin nan, daidai lokacin da meenal da airah suka matso kusa da su. Wani ɗan ƙaramin bowl ne mai marufi fari sol sai sheƙi yake kamar wanda aka shafawa mai, daga gefen box ɗin kuma kyakkyawan cofi ne madaidaici kamar bowl ɗin nan kalarsu da sheƙin su daya, saidai an warewa ko wanne wurin zamansa a cikin box ɗin, a jikin bowl da mug cup ɗin kuma anyi wani tsararren rubuta da aka rubuta sunan Leeyanah cikin salo da kwarewa, sosai abubuwan sukayi kyau kamar ka sace ka gudu. A tare suka furta "Masha Allah, gaskiya abubuwan nan sunyi kyau sosai" KhUlud da murmushi tace " ai Ni bazance komai ba idan ana sallah ba'a Magana bari dai mu buɗe muga abunda yake ciki. Bowl cooler ɗin ta fara ɗauka ta buɗe marufinsa "sweetness" Airah ta faɗa tana lumshe idanun, snaks ne a ciki masu matukar ɗaukar ido ga wani shahararren ƙamshi daya garwaye ɗakin hatta su mum sai da suka kalli inda su leeya ke zaune, jin wannan kamshin ya saka badar da Aneesa tasowa sukazo wurin. Saida kowa ya gama faɗin abunda zai faɗa kan snaks ɗin sannan suka dauko mug cup, shima marufinsa suka bude nan take ƙamshin fruit ya haɗe wurin da yake akwai air-conditioner yasa fitar ƙamshi ba wuya. dama can Mayah ce kawai bata ƙara so ba itama ganin duk sun haɗe kai waje ɗaya kamar masu kallon wani abun mamaki ya sakata ta zo itama, domin Ganin abunda ke faruwa. "Menene a ciki" cewar meenal "Niƙakken fruit ne gskiya yaji haɗi sosai sai kamshi yake bugawa" cewar khulud tana saka cokali cikin mug ɗin fruit dake hannunta. "Lallai ma wannan massager din shi har yanzu bai haƙura ba akwai bala'i kenan tsakaninsa da ya-Turab" Aneesa ta faɗa lokaci ɗaya kuma tana rufe bakinta data tuna cewa leeya batasan da zancen ba. "Me kike cewa haka Aneesa, mezai haɗasa da ya-Turab balle suyi bala'i ba wanda yasan wani a tsakanin su bala'in me zasuyi" Aneesa duk ta daburce ta rasa abunda zatace, sai cewa tayi "leeya kin manta kenan ya-Turab yana faɗamana duk wacce ya kama a cikinmu tana kula samari sai ya karyata, kinga ke gashi dan tsaurin ido har a Asibitin nan saurayinki ya kawomiki kyauta, duk wanda yaga kayan nan yasan abun masoyane wallahi. Shi yasa nake gudun kar ya-Turab ya ganki ko kuma wata rana kuna tare da messengern saurayinki ya turomiki massage ki shiga uku" Aneesa ta sauya zancen da haka. Duk suka amince da maganar ta ana neman yanda za'a ɓoye kayan domin kar ya gani ya karyasu musamman ma ita uwar gayyar da aka kawowa. KhUlud ce ta bada shawarar zube snacks da fruit wani wurin daban sai a ɓoye kayan idan zasu tafi su wuce da su. Da wannan shawarar sukayi amfani, nan suka haɗa hannu kowa da kowa banda mum da haji mainah, dama basu san abun da ake ba. Suka ci suka sha smoothie fruit dinda messanger ya kawo, sosai khulud ta Bama leeya fruit ɗin nan tasha musamman ma da taga yayi mata daɗi sosai. Fira sosai sukasha har zuwa yamma sallah kaɗai take tada wasu daga cikinsu da suke yinta. Har sai da aka kira sallahr magariba ko wannensu ya hau shirin tafiya, papu da kansa yazo shima ya qara duba jikin leeya sannan ya haɗa kansu gaba ɗaya suka tafi, haji kaɗai aka bari ta zauna ta kula da leeya kafin taji sauqi. Leeyana taji daɗin hakan amma ba sosai ba taso duk a barmata ƴan uwanta koba komai zata fi sakewa, domin tana jin nauyin haji sosai bazata iya dogon surutu da ita ba. Ƙarfe goma da mintuna huɗu na dare leeya ta ɗan motsa da alama ma ta farka. "Leeyanatu ya jikin kin tashi kenan" "Eh haji na tashi, jiki alhmdullillah naji sauƙi" "Allah ya ƙara afuwa" "Abu-turab yazo kina bacci ya jima kafin ya tafi, amma yazo miki da ferfesu yace ke kikace a zo miki dashi" Bata tsaya shawarar komai ba ta amsawa Haji da "ehh ninace ina son ferfesu Tun ɗazu ne ma kafin kuzo da zai fita" "Amma Abu bayada tausayi yanzu tun da rana kika gayamasa amma bai kawoba sai yanzu ƙarfe goman dare, da nasan haka ne ai bazan karɓa ba wallahi saidai ya koma dashi na kira fanaya akawomiki daga gida wannan rashin tausayin har ina ko yanzu ma idan zai dawo da ya koma da abunsa ɗan rainin hankali kawai" Haji ta ƙarashe maganar da faɗa kamar turab ɗin yana gabanta. "Kiyi hakuri haji, wata ƙila ya manta ne ko kuma wani uzurin ya riƙe shi shiyasa bai zo da wuri ba". "Zaizo ya sameni ai sai naji dalilinsa nayin haka, yanzu ki tashi kici kinji" Badan inaso ba na tashi naci kaɗan, ko shi ma dan haji tayi Magana ne da ba dan haka ba Ni ba abunda zanyi da kayansa. Kwana biyu tsakanin kullum sai mutanen gidan mu sunzo sun wuni su koma, kuma haka zamuyita fira dasu har su tafi. Washe garin rana ta uku da sukazo ne da yamma aka sallame mu a asibitin domin naji sauƙi sosai na warke kamar ma bani nayi ciwon ba, sosai haji da mum sukayi dawainiya dani kamar nice khulud ko meenal ko wata daga jikokinsu na cikinsu. Tun ranarda akace ya-Turab ya kawomin ferfesu ban ƙara sakashi a ido ba sai ranar da za'a sallamemu, nida mayah da mum muka shiga motarsa. Haji da Badar, da Aneesa da meenal kuma suka shiga motar driver, ita kuma Airah suka shiga motar da khulud tazo da ita. Kusan tare suka iso gaba ɗaya, sashen haji suka wuce gaba ɗayan su, a can leeya tayi wanka aka ɗauko mata kaya ta saka sannan sukaci abinci. Sun jima a sashen daga nan kuma khulud da mayah, Badar meenal, Aneesa da Airah suka koma part ɗinsu leeya kuma suka barta a sashen haji domin ita tace suje Magana zatayi da leeya. Tana zaune a parlourn turab ya shigo da sallamar sa, ko kaɗan bai lura da tana zaune a parlourn ba yasa yayi zamansa a ciki, zamansa ba jimawa mum da papu suka shigo a tare, bayan ya gaidasu yaci gaba da abunda yake cikin laptop dinsa, sannu suka yiwa leeya, ta amsa musu cike da nutsuwa. Sai a lokacin ya lura da ita, nan ya kare daure fuskar sa sosai kamar wanda bai taɓa yin dariya ba a Rayuwar sa. Suna zaune a haka sai ga haji ta fito daga bedroom itama "ahhh kuce kun haɗu gaba ɗayan ku kenan" "Eh haji mun fito, amma ai bamu jima da fitowar ba" "Tau shikenan sai muyi abunda ya kawomu kowa ya kama gabansa kho". Ita dai leeya tana zaune a wurin kanta a ƙasa gabanta sai duka yake, tana Addu'a a zuciyarta "Allah dai yasa Lafiya" haka take ta nanatawa. "Leeyanatu!" Ta tsinci muryar haji na kiranta cikin muryarta mai cike da Dattaku. "Na'am Haji" "Leeyanatu menene matsayin fanaya wurinki, domin duk sun bani labarin yanda zamanki gidan nan ya kasance dama sauran wani labari na daga rayuwar ki" Da mugun ƙarfi turab ya ɗago ya kalli haji da ke Maganar amma yayi saurin mayar da kansa ƙasa domin kar a fahimta. "Haji da zaki sanardani idan na tambayeki wani abu daga abunda kike faɗa da kin rage min nisan tafiya" Turab ya faɗa a zuciyarsa yana kara gefawa leeya wani mugun kallo da ta rasa menene ma'anar sa. Leeyana ta dago kanta a hankali ta kalli mum, sannan kuma ta mayarda kallonta ga haji tace "mum uwace a gareni, a kaffff faɗin duniyar nan banida uwa kamar mum, kuma mum ce matar da Allah ya wakilta ta zamo gatana a Duniyar Nan. Idan akwai wani matsayi da daraja daya take mahaifiya to na kira mum da wannan sunan saboda ta wuce haka a wurina, tayi min abunda ba kowace mace bace zata iya yinsa, mum ta kauna ceni lokacinda kowa yake guduna, mum ta soni lokacin da ba wanda zai yarda a kirasa masoyina, mum ta fito dani daga kunci ta saka na zama mutum kamar kowa. haƙiƙa babu kalaman da zanyi amfani dasu wajen fassara matsayin wannan baiwar Allah a wurina, amma kiyi hakuri da wannan dana bata saboda ta wuce haka a wurina" Leeya ta karashe magana da hawaye a fuskar ta har ga niqab ɗin ta. Kan Turab na laptop dinsa sai dai ba aiki yake da ita ba, ya.kofa kansa ga laptop din ne kawai saboda bayason yana kallon ko inuwar leeya idan ta fito ɗakin balle ita kanta. Maganar da tayi ne ya sake jefashi wani yanayi "me wannan sha-sha-shar yarinya take faɗa, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Allah ka taimakeni ka saka peace of mind a zuciyata kada kalaman mum, da haji, da kuma wannan munafukar yarinya su tarwatsa min kwanya" ya faɗa a zuciyarsa da ta ke yawan wani suya mai Kanada ɓacin rai. Allah sarki!. Cewar haji cikin tausayawa. Duk wanda yake zaune wurin saida jikinsa yayi sanyi sosai da ji furucin leeya, ga kuma kukanda take mai ban tausayi shima. Mum dai kallonta kawai take tana ƙarajin soyayyar ta ta daban a cikin ranta. Ita dai tana kallon ta kamar ƴar cikinta. "To menene matsayin Khattab a wurin ki?" "Haji matsayin papu dana mum duk ɗayane a wurina, kamar yanda na ɗauki mum shima haka na ɗaukesa, wallahi haji kunyi min komai a rayuwa banada abunda zance muku, ladarku tana wajen mai duka. Ina rokonsa ya saka muku da mafificin alƙairi" "Ameen thumma Ameen leeyanatu, ba komai Allah yayi albarka kinji". "Ameen ya rabbil ibaddd" "Kenan zaki iya yin komai saboda ki faranta musu" "Wallahi haji a kullum tunanina mezanyi na farantawa mum da papu" "Shikenan, kwanan baya kafin zuwanku asibiti mun zauna munyi tunanin, kuma fanaya ta bada shawarar haɗa aurenki da yayanki gashi nan zaune abu turab, kuma mahaifinsa ma ya bada goyon bayansa ɗari bisa ɗari, sanna shima abu-turab ɗin anyi Magana dashi kuma ya amince, ke kaɗai ake sauraro munyi alƙawari bazamu taɓa miki dole ba, idan bakyaso wallahi baza'a baki ba sai kin kawo wanda kikeso saboda haka ki faɗi gaskiyarki ba wanda zai miki dole sai kin yarda". Wani abu mai Kanada tsoro da fargaba taji ya dira a zuciyar ta, daga nan kuma taji wani ƙololo ya tokaremata maƙoshi wanda ya hanata cewa uffan sai bin haji take da idanu kamar bata taɓa sanin ta ba. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" ta furta a hankali cikin zuciyarta, nan taji komai ya tafi kamar ma ba maganar akayi ba. "Wallahi haji kar Allah ya nuna min ranarda mum da papu zasuyi iko akaina na ɗaga murya, nasan gata sukayi min kuma a yanzu na ƙara tabbatar da soyayyarsu gareni gaskiya ce kuma ta tsakani da Allah tunda har suka ɗauki ɗan su na cikinsu suka haɗani dashi a matsayin wanda zan aura, papu mum Nagode Allah ya bani ikon yimasa biyayya, Allah ya sanya alƙairi a tarayyar mu, ya kuma bamu ikon hakuri da junanmu, Allah yasa hakan shine mafi alƙairi a cikin Rayuwar mu, Allah ya baku ladar haɗin zama da kukayi, Nagode sosai" har ta gama Magana hawaye bai daina gudu a fuskar ta ba, ita kanta bata san ma'anar hawayen nan dake fuskar ta ba. ko tambayarta za'a yi akansu batada amsa. "Allah yayi muku albarka LEEYANA" " Turab!" Papu ya kira sunansa yana kafe shi da ido, sai yanzu ya ajiye laptop din da ke hannunsa ya mayarda hankalinsa gaba ɗaya kansu, domin duk rabin abunda ake hankalinsa baya kansu. "Na'am pa" ya amsa kiranda akayimasa. "Kaji abunda ƙanwarka kuma matarka nan Gaba kaɗan ta faɗa kho" Sai da ya runtse idonsa da karfi yana cije bakinsa yace "naji pa,. Ameen Allah ya bamu zaman lafiya" "Yawwa, haka akeso Allah yayi muku albarka baki ɗayanku" Nasiha papu da mum harma haji suka yi musu kafin daga bisani ya sallamesu suka fita ɗakin tare. Bai cemata komai ba, ita ma haka har suka kawo inda zai bi ya shiga sashen sa, yayi tafiyar sa itama ta shigewarta, ikon Allah ne kawai yasakata ƙarasa sashen su domin kukanda yaci karfin ta, Sa'arta ɗaya mum na sashen haji. Da karfi ta banko kofar ɗakin nasu tare da zubewa kan gado ta saki kuka. Dayake duk sun san abunda take yiwa kuka yasa hankalinsu bai wani tashi ba sai dai sun rarrasheta sosai, har suka samu kukan ya ɗan tsaya. "Haba matar yaya dan Allah kidaina haka mana, yanzu yasu haji zasuji idan ɗayansu yasameki kina irin wannan kukan, Ni shawarar da zan baki idan bakya sonsa kije kawai ki faɗa" "Haba badar ya zakice haka, kindai san ya-Turab ɗan mum ne kho, wallahi duk yanda kike gani mum bata damuwa dashi sosai ba, ba hakan yake nuna idan anyi masa abu bazataji haushi ba ɗanta ne na cikin ta fa, kawai dai kunyar nan ne ta fulani da suke nuna rashin kula ga ƴaƴansu na fari, wallahi idan leeya tace bata son ya-Turab mum bazata taɓa mantawa da itaba kan wannan abun, kuma wallahi mum sai ta kalli tsantsar butulci ne leeya tayi mata" "Gaskiya meenal kinada kyakkyawar zuciya, wallahi da wata ce kamar ke yanda kikeson ya-Turab yaƙi amince wa dake, da dabakinki zakice leeya taje tace bata sonsa Allah dai ya baki mafi alƙairi a rayuwarki" Dago d blue eyes ɗin tayi da sukayi wulu-wulu saboda kukanda tasha ga kuma colour ɗinsu ta blue ta sake fitowa gwanin ban tsoro ta kalli meenal tace "Allah sarki ke kinaso Allah bai baki ba, sai ni da bamtaɓa kawo hakan a raina ba" "Kedai leeya kidaina faɗin haka, kici gaba da addu'a kawai idan hakan ne alƙairi Allah ya tabbatar, kuma da kikaga haka Allah ya fiki sanin dalilin sa nayin haka" "Wallahi ni duk ba wannan bane araina, a rayuwata naso sanin bawan Allahn nan daya damu dani ina mafarkin zama dashi, amma kaddara ta riga fata, in sha Allah zan gaya masa komai, amma wallahi naso nasan wani abu daga gareshi har sunansa ma ban sani ba balle nasan garin da yake dama Asalin fuskar sa gaba ɗaya" "Leeyana kina nufin kice ko sunansa baki sani na" "Kwarai kuwa khulud bansan sunansa ba a kullum idan na tambayeshi sunansa sai yace na kirashi da komai nakeso, domin ba abunda zan iya sani akansa sai lokaci yayi, wallahi Nima bansan na damu dashi ba kuma ina qaunar sa sai yau danaji zancen nan, yaa Allah ka taƙaitamin wahala" Da faɗa da Muryar kuka. "Ameen" duk suka faɗa suna ci gaba da rarrashin ta..............✍🏻 BAYAN WUYA..... EP.37 ___________________tayi shiru kamar ba abunda ya faru har fira mai daɗi ta ɓarke a tsakanin su, sai tsokanarta suke matar yaya ko matar soja, ko kuma sucemata matar likita. tun tana yimusu magana bataso har ta ƙyale su ko sun faɗa sai dai ta murmusa bata ko kulawa. Yau Monday yau kuma khulud zataje duba result ɗinta kafin ayi closing ceremony na karshen kowace shekara da akeyi a Rooney. Sosai suka bata shawarwari yanda zata tunkari id da Sayyid da kuma yanda zata ƙanƙan da kanta ƙasa wajen nuna nadama kan abunda tayi musu, cikin shawarar da suka bata kuma harda nuna mata tayi masa ƙayatacciyar kyauta. Gaba ɗayan su suka shirya suka rakata tayi masa shopping, sosai suka kashe kuɗi kamar me, duk abunda suka gani indai maza na amfani dashi sai da suka siyawa id. KADUNA STATE. "Mum yaushe zamuje dan Allah? Tun wancan satin fa twiney ta tafi har yanzu ko leƙe bata leƙomuba, kinsan wallahi dai ta jima da yawa kuma gashi maganar tafiyarmu ba'a ce komai ba" "Gaskiya mum ya kamata muje muma musha suleja kafin a tashi bikin, zama wuri ɗaya ba daɗi tun da nan ko fita bamayi" "Ko can kukaje bazaku fita ba Rukhshanah, nasan halin dadynku Babba bazai bari ku fita ba. Amma kuyi hakuri tun da saura kwana takwas, idan muka tashi zuwa sai muje ba dole sai munbi tafiyar mayah ba tunda kho tunawa da mutane batayi" "Eh wallahi mummy kinga idan mukaje muce a saukemu bisa quarter tunda ba kowa a ciki idan zamuyi wani abu zamu yishi har mu gama ba wanda zai ganmu a cikinsu kar mu fito mu bari sai idan an fara programme ɗin bikin sannan muyi shiri mu fito, kinga ma a lokacin zata gane kuskurenta domin sai ta yita kiran number ki don a aikomata da kayan da zata saka na fitar biki. To a lokacin da ta kiraki tana tambayar kayan a lokacin zamu rama abunda tayi mana mu daina ɗaukar wayanta itama taji idan da daɗi" "Yes!!, gskiya kin kawo shawara Sweet fannah haka za'a yi amma dai nasan mum bazata bari ba gaskiya" "Mum wai bazaki bari mu rama abunda tayi mana ba?" FANNAH ta faɗa da alamar tambaya. "Zan bari mana, me zai hana ai harda ni aka yiwa kinga kho nima dani za'a yi mata". "Mummy ana kiranki a waya amma kin saka wayar silent shiyasa bakiji ba" cewar Rukhshanah tana miƙawa mummy-neesah wayar. Karɓar wayar mummy-neesah tayi tare da picking call ta kara wayar a kunnen ta "okay ku shigo kawai, kuma ki turo account number na turomiki sauran two millions ɗin, gobe kikace za'a kawo sauran kayan kho, ok gani zuwa bara nazo na buɗe muku Ni banji knocking ba ai da bazan barku tsaye a waje ba kuma da kaya" cewar mummy tana katse wayar. "Rukhshanah" "Na'am mummy" "Waya rufe sashen nan su hajiya Aƙeesah sunzo sun tararda kofar a rufe" "Wallahi mummy bani bace sai dai kho fannah" "Tunda ni kika raina kho, to bani bace junior ne daya dawo daga islamiyya ya rufe na jishi lokacin da yake saka key wallahi" fannah ta faɗa tana nufar kofar sashen. "Rukhsha ki tashi ku taya su shigo da kayan". "Wane kaya mummy, yanzun nan fa muka dawo nidai na gaji gaskiyar Allah". "Ki tashi bana son ragwanta, Rukhshanah bakyason aiki kho wallahi ina guje miki ne baki san inda Allah zai kaɗa ki ba nan gaba kadan". "Bansaniba mummy amma kiyi min fatan inda zanje na huta" . "Ita ake yimuku kullum Safiya" faɗar mum yayin da mutane suka fara shigowa da wasu manyan akwatuna masu matukar ɗaukar ido. Ihun murna Rukhshanah ta farayi, da gudu ta nufi kofar parlourn taje itama a jido akwatunan da ita, domin ita da aka ce kaya bata yi tunanin akwatunan lefen ya-fahad bane. Masu gadin gidan su uku aka kira sai kuma hajiya Barira da ƙawarta hajiya Aƙeesah wanda su suka haɗa lefen har Dubai sai FANNAH da kuma Rukhshanah su suka shigo da kayan gaba ɗaya akwatin sets biyu ko wane set yanada akwatuna takwas sai kuma hand bag ɗaya da travelling bag itama. Sosai aka cika akwatunan da kaya kala-kala kamar kayan zasuyi magana da kansu, ba jaka ko akwati da ba'a zubamata kaya ba a cikin akwatuna, sosai naira ta koka ba sauqi. "Gaskiya kayan nan sunyi kyau sosai, kuma qualities ne daga gani". "Kedai bari kawai hajiya neesah, ai indai mune wallahi zaki samu kayan ki yanda ma bakiyi tunani ba, domin mu tsakanin mu da Allah muke kasuwancin mu ba cuta ba cutuwa". "Hakane hajiya Aƙeesah ai naga alama wallahi, kuma muna godia sosai domin kaya sunyi kyau Masha Allah, yanzu ku bada account number na cika muku alkawari" Account number ɗin su suka bata ta tura musu 2 millions ɗin da suka rage harda ƙarin dubu ɗari biyar sama na godiya da alkawarin da suka cika mata da kuma gaskiyar da suka yi mata. Sosai hajiya Aƙeesah da Hajiya Barira suka ji daɗin haɗuwar su da Hajiya neesah wato mummy, sun ɗan jima a gidan bayan sun ci sun ƙoshi suka wuce. Fannah da Rukhsha kuwa sai videon kayan suke suna haɗa pics ɗin zohal da Fahad suna ɗorawa a status. Kayan sunsha Magana sosai inda kowa yake yabawa, sai sakawa kayan albarka ake, kan kace me magana duk ta karaɗe families sai zuwa suke suna dubawa aka saka ranarda za'a kai kayan gidan su amarya. *SULEJA STATE* ROONEY. sanye take cikin hijab abaya har suna ja ƙasa kalar maroon da powder colour. Wasu daga mutanen dake harabar makarantar sai kallon ta sukeyi cike da mamaki ganin ta da hijab. Hango motar AMRAH tayi tana tahowa, wuri ta samu ta raɓe har motar ta karaso kusa da ita. "KhUlud kece haka da wannan shigar kamar wata ƙasaitacciyar Malama" Sosai khulud ta Haɗe fuska tace "bansaba yin shigar bane da zakice haka" "Maida wuƙar mutuniyar bani na kar zomon ba rataya aka bani" "Kanki dai ake ji amrah, ina raudha?" "Raudha suna capteria tun ɗazu ita da reemah" "Okay muje musamesu nayi missing ɗinku" Fitowa AMRAH tayi daga motar taci ado cikin blue T-shirt ta mata mai adon kore, sai black Tony skirt da kuma ƙaramin mayafi iya kafaɗarta kamar dai yanda suka saba fitarsu. Tare suka jera har suka isa, sosai mutane suka cika a wurin da yake safiya ce mafi yawan mutane basu fara lactures ba. Basu wani sha wahalar ganin su ba domin raudha ma data gansu ta kira wayar khulud ta gaya mata gefen da suke, suna isa wurin khulud ta zaune kujerar da ke kusa da ta reemah. Har khulud ta buɗi baki zatayi magana aka kira reemah rabeel da waya "sallamu alaikum, Yawwa barka da safiya, Okay har kun shigo kenan, Kuna wane gefe, Eh na gane jirani kaɗan gani nan tafe" Reemah ta faɗa tare da yanke wayar, handouts ɗin ta ta ɗauka da handbag da carkeys ɗinta "friend's kujirani ina zuwa yanzu zan dawo abu nakeso naje a nuna min" "Okay sai kin dawo" amrah ta faɗa hankalinta na kan wayarta da take Street a Snapchat. "Ina zakije reemah" "Baya zanje yanzu zan dawo jirana ake naga kamar kinada magana kho khulud, ki bari idan na dawo sai muyi maganar kinji" "Okay sai kin dawo, kar ki manta saura 30mns mushiga lactures kiyi sauri karki ɓata lokaci, kuma kinsan result ya fito kho" "Eh nasani idan na dawo sai muje mu duba" cewar REEMAH tana barin wurin. Bayan mintuna goma sha biyar da tafiyar reemah su khulud sukayi order din abinci, suna kammala cin abincin basu jira komai a capterian ba suka koma ANATOMY. Har zata saka waya ta kira reemah sai ta hango ta zaune a class. Bayan wasu awanni, block ɗin da ke kallon ANATOMY suka nufa cikin fara'a kowa yana fata a ransa result ɗinsa yayi kyau, khulud sai rarraba ido take a harabar wurin ko zata hango id domin ko a class bata samu ganin shi ba kyau. Numfashin ta ne yayi ƙoƙarin tsayawa sakamakon hango shi da tayi gaban notice board inda aka liƙa result ɗin, wani irin fitinannen kyau yayi mata baƙar shaddace a jikinsa da aka yiwa adon kwaɗo ruwan zuma, sosai kayan suka yimasa kyau inda kwantaccen sajensa ya kara kwanciya lif a fuskar sai wani sheƙi fuskarsa take ga hasken fatarsa ya fito daidai misali. "Masha Allah" ta furta a zuciyarta "ina ma inada damar da zan faɗa maka kayi kyau" ta faɗa ƙwallah na cikowa a idanun ta. Wayarta ta fito da ita ta fara ɗaukarsa hoto ta yanda ba wanda zai gane photo take yimasa, tuni su AMRAH da REEMAH da RAUDHA sunyi gaba basu san ma me take ba. Sai da tayi masa hotuna masu isarta sannan ta mayarda wayarta jaka ta ƙarasa wurin, bata nemesu ba ta fara duba sunanta, sai da tayi godiya sosai ga Allah bayan ta ga sunanta kuma taga result ɗinta daga nan tayi snapping shima domin ta nuna idan taje gida. Sai yanzu ta lura da su amrah basa wajen, kuma da taje inda suka ajiye motocin su taga motar AMRAH bata nan ita raudha driver ne yake kaita shiyasa bata gane tana school ba ko kuma ta wuce gida. Sai dai reemah ita motar ta na nan alamar tana nan kenan, Boot ɗin motarta ta buɗe tare da fito da manyan ledojin da tayiwa id siyayya guda biyu ta nufi cikin makarantar dasu, domin ta ɗauki alwashin yau sai anyi duk wacce za'a yi tagaji da dakon soyayyarsa a ranta tana wahalarda ita. Dayake reemah tasan da batun kuma duk a cikinsu ita kaɗai khulud ta labartawa kan soyayyar da take cinta a zuciya, number ɗin reemah tayi dialing ringing biyu ta ɗaga wayar "hello khulud, kin duba result ɗin" "Eh wallahi na duba kuma alhmdullillah ba abunda zance saidai in ƙara godewa Allah". "Kice anci baza kenan". "Meye banza reemah?" "Uhmm--hmmm kaidai bari kawai wallahi result ɗin nan yayi banza da yawa wasu mutanen kam basu ma je dubawa ba saboda sunsan sun cinye". "Wallahi kuwa, kina ina haka" "Yanzu haka ina hango ki amma ki biyo hanyarda kike strect idan kikaci gaba da tafiyi zaki ganmu" "Okay" khUlud ta faɗa wayar na kunnenta. Cigaba sukayi da maganar har ta fara hangosu daga nesa, saida ta hangesu sannan ta kashe wayar ta ƙarasa wajenda suke zaune Sallama tayi lokacin da ta iso wurin, su uku ne a zaune a wajen reemah da sayyid suna zaune wuri ɗaya, sai kuma id dake zaune gefe dasu kaɗan amma duk cikin rumfa ɗaya suke zaune. Reemah kawai ta amsa sallamar id da Sayyid kam kamar badasu take ba damar ma shi id ya amsa sallamar amma a yanda ya amsa ko da kana kusa dashi bazakaji ba balle kuna nesa da juna. "Ina wunin ku, sayyid ya karatu" Nan ma bai amsa ba. Cikin jin ɗacin abunda ya faru reemah ta kalli sayyid tace "sayyid bakaji khulud ba gaida ku ba" Fuskar sa a tamke bai ko dago da kansa ba muryarsa a dakile yace "sorry banjibane, lapiya alhmdullillah" ya faɗa bai ko kalli inda take tsaye ba. "Kizo ki zauna idan na kammala sai mu wuce kinji, kiyi haƙuri sayyid yace baiji kin gaida shiba" "Uhmm--hmmm bakomai" cewar khulud tana ƙaƙaro murmushin. "Zauna" reemah ta maimaita mata. "Okay" khulud ta faɗa tare da zagayawa inda ɗayan kujerar da ta rage wurin take, kuma kuma kusa da ita ne id ke zaune. Yana ganinta ta nufo wurin ya hau haɗa kayansa dake baje kan plastic table ɗin da ke tsakanin kujerun biyu zai tashi. "Idrak me kake shirin yi, Saboda ka ganni ne zaka tashi" "Mtswww" yayi tsaki sannan yaci gaba da abunda yake. "Id Yakamata kagane adadin ƙaunar da nake yimaka a raina, dan Allah kaji tausayina wallahi ina sonka, duk abunda ya faru a can baya tsausayine kuma ƙaddara ce wacce Allah ya riga ya tsara saita faru, kuma Wannan ya riga ya wuce dan Allah kayi haƙuri ka soni idrak wallahi ina sonka da ƙaunarka so na tsakani da Allah, kuma ba ranar dainawa muddin ina numfashi a wannan duniyar" ta faɗa tana haɗe hannayenta wuri ɗaya idanun ta duk sunyi jajir ga kuma hawaye kwance a cikinsu. Bai kalleta ba kuma bai cemata komai ba, yabi ta gabanta zai wuce. Gefen rigarsa ta riƙe tare da durkusawa gabansa "dan girman Allah id kaymin Magana dan Allah Wallahi idan bansamu soyayyarka ba rayuwata na cikin haɗari ka taimakamin wallahi ina sonka" Cikin zallar ɓacin rai ya fizge hannunta daga riƙon da tayi masa yayi gaba zuwa wurin da su Sayyid ke zaune. Duk abun nan da suke Sayyid da reemah basu sani ba domin sun juya musu bayane. Miƙewa tayi tana share hawaye ta ɗauki kayan da ta siyomasa ta bishi har inda yake, yana magana da sayyid da alama dai yana gayamasa ne gida yakeso ya tafi. "Ga wannan dan Allah karkace bazaka karɓa ba" khulud ta faɗa zuciyarta na bugawa bataso yaƙi karɓa duk da tasan zai yi wahala ya karɓi kayan. Miƙewa Sayyid yayi da sauri gaban kayan ya ɗauki ledojin biyu ya zubarda su a ƙasa ya fara ball dasu ko wanne yana yin gefensa kwalin waya sabuwa kirar Apple 15 yake ball dashi har gaban ta. Cikin kasaita irin ta jinin sarauta ya fara magana"Ya faɗa miki yana buƙatar kayanki ne, ko angayamiki shi matsiyaci ne irinka, this is the first and last, wallahi idan kika ƙara siyo wani abu kika kawo masa saina wulaƙantaki daga ke har kayanda kika zo dasu" Har ya tafi ya dawo kamar mai raɗa yaje kusa da kunnenta"fool" Ya faɗa yana yimata murmushin tsana. KhUlud da ta rasa abunda zatayi sai kawai ta durkushe ƙasa tare da riƙe kanta ta fashe da matsanancin kuka. Cikin wani irin ɓacin rai reemah tazo gaban sayyid "sayyid me ka aikata haka, me khulud tayi muku da ta cancanci haka daga gareku kalla! Kalla kaga yanda kuka maida ita, idrak kalla kaga yanda tunanin ka ya sauya mata kamanni, idan bakwa buƙatar kyautar da tayi muke it's fyn ku mayar mata da abunta a mutunce kamar yanda ta yi muku, duk abun nan da ka gani a nan da kuɗi aka siyeshi. Wallahi tallahi sayyid kaban mamaki ban taɓa zaton haka daga gareka ba ko a wajen wata ba khulud ba balle ita kanta khulud ƙawata, dan Allah bakaji kunyar idanuna ba ? kome ta maka yakamata taci albarkacina a wurinka sayyid, alhmdullillah, alhmdullillah Sayyid na godewa Allah daya fara bayyana min yanda halayenka suke tun a yanzu. wanda yayi wa mace haka a gaban wacce yakeda burin aura to karta fitarda tsammanin itama wata rana zai iya yimata haka ko a gaban kowa, shikenan mungode" ta faɗa cikin wani yanayi da sayyid da idrak har ma ita kanta khulud basusan reemah nada irin wannan zuciya ba domin idanunta har rufewa suke saboda tsananin masifa. Sayyid kam kamar dasashi akayi wurin sai bin reemah yake da kallo domin yama manta da tana wurin kuma bai taɓa ganinta a yanayin nan ba wannan abun ne ya kara bashi tsoro da mamaki. Inda khulud ke durkushe taje ta tada ita ta riƙe hannunta ta kaita har inda tayi parking motar ta ta buɗe mata mota "ki zauna ki jirani naje na kwaso kayanda suka watsar kinji kiyi haƙuri kuma dan Allah". KhUlud bata ce komai ba ta kifa kanta kan steering motar tana hawaye a hankali, ita duk wannan abun da sayyid yayi mata bata ji soyayyar id ta fita daga zuciyar ta ba saima abunda ya ƙaru. Reemah kuma tana zuwa wurin bata cemusu komai ba ta fara haɗa kayan da suka watsar "sayyid karka taɓa kayan nan idan ba so kake na nuna maka asalin kalata ba wallahi" reemah ta faɗa lokacin da Sayyid ke ƙoƙarin tayata haɗa kayan. Bayan ta gama haɗa kayan zata tafi sayyid ya tareta ta raɓa gefensa ta wuce, da sauri idrak yasha gabanta "karkace min komai id wallahi kunban mamaki, da kanku kuke wulaƙanta mutane wannan halin ne fa yasa kuka ɗauki karan tsana kuka ɗorawa ƙawayena ashe duk halin ku ɗaya dasu kaicona, kaicona danayi tunanin ku daban ne da kowa musamman kai*" ta fada tana nuna Sayyid. "Dan Allah reemah ki tsaya ki saurareni, banyi tunanin haka sayyid zaiyi ba, da farko ya birgeni da yayi mata haka koba komai zataji yanda akeji idan idan tayiwa wani ko wata haka, harga Allah abun nan da yayi mata yamin daɗi, saidai abunda baimin daɗi ba da wannan tunkiyar yarinya ta kasance daga cikin ƙawayenki, reemah gaba ɗaya ƙawayenki basu dace dake ba, amma kuyi hakuri mun tuba" cewar id. "Hmmm" kawai ta iya yie kafin tayi tafiyar ta. Suna gani, motar Sayyid ta fita makarantar, har ta fita daga Rooney khulud na kallon motar. Ji take kamar ita da id ɗinta ne a ciki zasuje gida bayan sunyi aure. "KhUlud zaki iya zuwa gida ko na kira drivern gidanmu yazo ya kaiki". Murmushi mai ciwo khulud tayi tana kallon reemah tace"zan iya karki damu kinji kije gida kar a nemeki". "KhUlud dan Allah na roƙeki kicire soyayyar id a zuciyarki, wallahi id baya sonki domin duk wanda yakesonka bazai jure ganin ana wulakantaka ba" "Reemah da akwai yanda zanyi na cire zuciya ta gaba ɗaya, dana cireta ko zan huta na sami bacci cikin kwanciyar hankali kamar yanda kowa yake yi, fitar da soyayyar id a zuciyata babban abune wanda banmasan ta inda zan fara ba amma zan gwada na gani ko zan iya duk da nasan ba lallai ba" "Shikenan Allah ya sauwaqe kinji, kuma kiyi haƙuri" "Ameen Ya rabbil alameen, kuma don Allah abunda nake roƙonki kada ki kama sayyid da laifi domin bashi bane mai laifi nice babbar mai laifi da halayena basu kasance haka ba da baza'a min ba. dama hausawa sukace alhaki kuikuyo mai shi yake bi, kuma abunda ka shuka shi zaka girba, kije gida reemah Nagode". Sallama sukayi reemah bata gushe ba tana bata haƙuri itama tana bawa reemah haƙuri kan abunda yafaru tsakanin ta da Sayyid. Anan reemah ta fita daga motar ta khulud ta nufi inda ta ajiye tata, itakuma KhUlud ta fara tuki. Tana cikin tafiya ne ta hango motar sayyid tayi parking gaban wani babban mall. Wuri ta samu inda take hangosu sosai daga inda take, saidai su basa ganinta kamar yanda take ganinsu. Fitowa tayi ta jingina da motarta tana fata a ranta Allah ya bata Sa'ar abunda take kuɗuri a ranta yanzu. Wayar ta ta kashe gaba ɗaya domin kar a dameta da kira daga gida tanaso sai tayi solution ɗin matsalarda ke gabanta kafin ta koma gida. Tana jinginen ne ta ga fitowar su da sauri tayi locking motar ta ta tare taxi. "Hajiya ina zamuje" "Dan Allah so nake ka bi waccan motar, kuma cikin dubara nakeso kayi yanda bazasu gane su muke bi ba" "Bakida matsala hajiya shigo muje" Da hanzarin ta shiga motar drivern taxi ɗin ya fara bibiyar motarsu sayyid cikin kwarewa da ɓoyon sahu, sosai sukayi tafiya, da zarar direban ya fahimci hanyarda zasubi sai yayi short cut ya taresu a gaba, haka sukayi har suka iso unguwar ta su idrak. Sosai khulud tayi mamakin ganin wai mutane ke rayuwa a wannan wurin, ita harga Allah idan da motarta taje bazata iya shiga wannan unguwar ba domin a ganin ido bazace akwai hanyar da mota zata bi ta wuce ba. Mamaki bai gama tafiya da imanin ta ba sai da taga inda motar sayyid tayi parking, bakin wani ɗan ƙaramin gidane wanda bulon da aka ginin dashi ya gaji da duniya har wani baki-baki ginar gidan tayi, gata guntuwa sosai wani wuri ne da tsawo sauran duk ya faɗin saida aka saka laka aka tada ginin, kofar gidan sai dai aka saka wani tsohon turmi aka tangaleta dan karta faɗi. "Allah yasa ba gidan bane gidansu id" Ganin sa ya fito waje ya saka kansa a motar kamar yana magana ne da Sayyid yasa ta ƙara gasgata nanne gidansu, tana kallonsu har suka gama maganar ya juya ya shiga gidan, shi kuma sayyid ya tada motar ya bar unguwar. Nannauyan ajiyar zuciya ta saki ta kalli drivern taxi ɗin tace "menene sunan arear nan?" "Tsohuwar bariki" Drivern ya bata amsa. "Ikon Allah, amma Ni bantaɓa sanin unguwar nan ba" "Aikuwa unguwar nan a sane take Hajiya, kuma wasu mutanen sunfi sanin ta da suna layin ƴan haya, domin kaf faɗin unguwar nan ba wanda yakeda gidan kansa duk na hayane". "Kana nufin har wancan gidan" ta faɗa tana nuna masa gidan da taga id ya shiga. "Ehh sosai hajiya ina yimiki maganar layin nan ne gaba ɗayansa" "Kana nufin gidajen da ke layin nan na haya ne kuma mutanen da ke ciki suna biyan haya". "To idan basu biya ba ya zasuyi, ai dolensune su biya, da babu ai gwara ba daɗi". "Haka ne to muje ka mayardani inda ka ɗaukoni" "Okay hajiya" cewar drivern yana tayarda taxi ɗinsa. Saidai ya kaita har gaban mall ɗinda ya ɗauke ta sannan yayi packing ta fita, kuɗi ta ciro wanda bata san ma adadin suba ta miƙawa Drivern taxi ɗin. baki buɗe yabi kuɗin da ke hannusa da kallo wanda ko a cikin sati ɗaya bazai sami irinsu ba "hajiya na wah ne gaba ɗaya?" Ya faɗa yana washe baki. Bata bi ta kanshi ba ta buɗe motarta ta shiga sai gida. Babban abun da ya ɗaga mata hankali shine hango cincirindon mutane da tayi a ƙofar gidansu harda police da kuma dss, "innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" ta furta a tsorace zuciyarta na matsanancin bugawa "me yake faruwa a gidan ya rabbi kasa naji alƙairi" ta faɗi maganar a fili dai-dai lokacin da motar ta ta Parker bakin gate ɗin gidan. da gudu meenal da Aneesa sukayo kanta, basu jira komai ba suka rungumeta meenal ta saki kuka, nan zuciyar khulud ta daɗa tsinke wa tuni ruwan hawaye sun cika mata idanu itama tana tsoron jin abunda ke faruwar a zuciyarta. Kallonta takai ga kofar gidansu inda taga mutane suna fitowa suna nufota, papu tagani ta sauri kamar ya kifa har tuntuɓe yayi saboda tsananin tashin hankali, kana gani fuskar sa zaka san akwai babbar matsala a ransa. "La-ila-ha illa antah subhanakah inni kuntu minaz-zalumin" ta kuma maimaita wa a Zuciyar ta domin ganin papu yasaka ta manta da tambayar da takeson yiwa su Aneesa, da sauri ta fizge kanta daga garesu ta isa ga papu cikin tashin hankali tace "papu meya faru a gidan nan" "KhUlud ina kika shiga, alhmdullillah Allah" papu ya faɗa yana lumshe idanu, ya kuma maimaita mata tambayar da yayi mata"ina kika fito?" "Unguwar tsohuwar bariki layin ƴan haya" "KhUlud yaushe kika fara min karya ki gayamin abunda ke faruwa" "Wallahi pa can naje, wani abu na dubo na dawo kuma ina sane na kashe wayata dan kar na tada muku hankali" "Kashe wayar da kikayi shine zai hana hankalin namu tashi, mum ɗinki da turab tun ɗazu suna abuja domin bada jigiyarki, leeya da haji da badar ma driver ya kaisu gidan television dana Radio, yanzu haka an rufe school ɗin ku sai an gama bincike, haka da kikayi kin kyauta mutum nawa kika tadawa hankali yau ɗin nan KhUlud, karfe biyar na yamma fa keda kika fita gida tun karfe takwas na safe ina hankali zai kwanta tunda baki kira kin sanarba, kindaisan duk inda zakije ba hanaki za'a yi ba dan Allah karki ƙara irin haka kinji" "In sha Allah pa bazan kuma yin haka ba nayi kuskure na tuba, kuyi haƙuri kuma ku yafemin da haƙƙin ku dana ɗauka" " ba komai Allah ya ƙara tsarewa, kuma a kiyaye. Amma kamar naga idanunki sun kumbura kuka kikayi?" "Ah ah pah Nima haka kawai nagani bansan me yake faruwa ba ina kyautata zaton ciwon ido ne keson kamani" "Subhanallah, to muje gida idan kinci abinci kin yi wanka sai muje asibiti a duba idanun" "Okay pa muje" khulud ta faɗa tana tafiya. "Yallaɓae idan kun gama tattaunawa da ita munaso muyi mata wasu tambayoyi" police ɗinda ke tsaye kusa da wurin suka faɗa. "Ohh sorry, inspector fargab raji, kuyi haƙuri harna sha'afa inaso nazo nayi muku bayani, yarinya dai gata can tana tafiya Allah ya dawo mana da ita duk da ba ɓata tayi ba", papu ya faɗa yana nunawa inspector fargab raji khulud dake tafiya. Yaci gaba da faɗin "amma mu a zaton mu ta ɓata ne tunda anje school bata nan, ankira wayanta kashe kuma an tambayi abokan ta gaba ɗaya sunce sun barta School, ɗayan kuma tace a gabanta ta fita da motar ta, kaga kho dole ne hankalinmu ya tashi tunda lokacin dawowarta gida yayi har ya wuce amma bata dawo ba. Ashe ta biya wata unguwar ne daban kuma bata sanarwa kowa ba, idan kunje kuyiwa inspector Agu Clement bayanin komai" "Okay ba matsala yallaɓae za'a gaya masa in Allah yaso, Allah ya ƙara tsare gaba" "Ameeen, Ameeen mungode sosai" papu ya faɗa yana ciro kuɗi aljihunsa, no yallaɓae, sir Agu yace kar mu sake mu karɓi ko kwandala taka, mu mun tafi" godia sosai yayi musu sannan ya rakasu har inda sukayi packin mota daga nan ya dawo gida, ya kira kowa ya sanar masa yanda akayi. Dama su mum kam suna hanya har sunje an fara aiki. Hakama su haji har sun bada nasu suma. Bayan shigarta gida ba jimawa su haji suka dawo sunyi farin cikin ganin ta da ganin tana lafiya sosai, sai a lokacin aka fara ƙoƙarin shirya abincin dare domin basa cikin kwanciyar hankali da tuni an kammala komai, ana kiran sallar magariba ne su mum da turab suka ƙara so sai sam barka ake. Daren ranar khulud batayi bacci ba saida ta labartamusu abunda ya faru tsakanin ta da Sayyid harshi kansa id da yanda suka yimata wulaƙanci. Airah kamar zuciyar ta zata fashe dan haushi da bakin cikin kyalesu da khulud tayi sukayimata haka, da yawansu sunga dacewar abunda khulud tayi domin ta hakane id zai gane tana danasani da abunda tayi musu. Duk wannan bai saka Airah taji a ranta ya kamata khulud ta basu dama suyi mata abunda ransu keso ba "kenan da babu reemah dukanki zasuyi" "Badai duka ba Airah ai ko zan shanye komai bazan taɓa bari id ko Sayyid yakai hannusa jikina da sunan duka ba, kuma ni duk abun nan da sukayi min gaba ɗayansu koda dama aka bani banaji zan iya mayar musu da martani, shiyasa ma na ƙyalesu sukamin abunda sukaga dama mai so baya fushi". Taɓe baki Airah tayi tace "Allah dai ya kiyayemu da faɗawa kaddararren so irin naki ɗin nan" "Ameen" suka amsa gaba ɗayansu daga nan kowa ya nufi makwancinsa. ********** Washe gari kuwa tun karfe tara na safe zafaran ya kira wayar turab ya sanar masa da zuwansa, kuma ya gayamasa idan yazo bazai tafi ba har sai an gama bikin fahad da zohal. Shima turab ya kuɗuri niyar barin gidan su koma can kaduna inda gidan Fahad ɗin yake. Domin bayason hayaniyar jama'a kuma yasan danginsu na kusa dole zasuzo gidansu tun a yanzu ma mutane sun fara yawa gidan koba komai ga ƙannensa nan su meenal su kusan biyar ko shida, shima kansa zafaran ɗin bazaiji daɗin zama gidan ba idan da mutane sosai domin shi kwata-kwata ma baya son zama cikin mutane saboda bai saba da hakan ba yana dubin hakan babbar takura. Ɗan murmushin turab yayi wanda ya bayyanar da fararen haƙoransa lokacin da ya tuna da maganar da zafaran yayi "yawwa man-turab albishirinka" "Goro" turab ya amsa masa da son jin abunda zaice, domin harga Allah shi abunda ya faɗo masa a rai daidai wannan lokacin shine zafaran ya haɗu da lewa ko yaji labarin inda take. "Fari ko ja?" Cewar Zafaran. "Fari sol mutumina, me ya faru gayamin naji" "Da yunwa zanzo gidanku yau" "Ban,,,,,,,gane ba me hakan ke nufi" turab yayi Maganar a rarrabe. "Ina nufin tun taga yanzu har nazo suleja bazan ci komai ba har sai nazo gidanku, dan Allah ina so ka saka wannan yarinyar da ta taɓa yimana abinci ta sake yi magana ko yanzu ina missing ɗin girkinta". "Wace yarinya?" "Wannan yarinyar daka ce ƴar ƙawar mum ce mai rasuwa, wacce ta taɓa yimana girkin nan na igbo kwanakin baya" "Uhmm--hmmm, okay nagane wane kalar abincin kake so?" "Egwusi and okazi soup, sai kuma oha crayfish soup, sannan da yam and ginger juice ba mai kauri ba sannan kar a saka yajiiii yawa" "Mutumina duk kai kaɗai zaka ci wannan" "Nida kai da ango dai" "Wah, Allah ya kiyaye Ni bazan iya cin jagwalgwalen abincin nan naku ba ya rikitamin ciki bara na kirata na gayamata ta haɗa maka kafin ka ƙaraso" "Godiya nake man turab sai na karaso" Daga haka sukayi sallama ya katse wayar ya zauna, gaban television duk da ba ita yake kallo ba tunanin da yake daban, shine tunanin maganar da sukayi da zafaran ya faɗo masa arai har ta sakashi yin murmushi. Number mum yakira bugu ɗaya ta ɗauka "Assalamu alaikum" "Wa'alaikasalam" mum ta karɓa masa sallama. "Mum ki turomin wannan yarinyar inaso na bata saqo, yanzu fa!" Bata cemasa komai ba ta kashe wayar domin tasan wacce yake magana a kanta, "wannan yaron ya raina mutane dayawa wai "wannan yarinyar" hmmm, Allah dai ya sauwaqe" mum ta faɗa tana murmushi. Har part ɗinsu taje ta tarar dasu kowa yana sha'anin gabansa, meenal tayiwa alama tazo da hannu domin ba wanda ya lura da shigowarta ɗakin sai ita. Miƙewa tayi ta ƙaraso gaban mum "mum lafiya dai naganki haka" "Lafiya ƙalau meenal ina leeyanah" "Ta shiga toilet wanke takeyi" "Okay idan ta fito ki gayamata yayanku na nemanta sashensu" "In sha Allah za'a gayamata da zarar ta fito mum" "Okay Allah yayi muku albarka" "Ameeen ya rabbi mum" Fitar mum ba jimawa leeya ta fito meenal kuwa tagayamata saƙon mum, sosai taji tsoro tana fata a ranta ba laifi tayi masa ba. Saida da shirya tsafff cikin doguwar rigar ta ruwan azurfa, wacce papu ya siyomusu dawowarsa Saudiyya, rigar tayi kyau sosai irin wacce larabawa ke sakawa, rigar batada yawan ado sai dai tanada ɗaukar idanu kalar rigar ma haka sai wani shining take. Gashinta data gyara ta sako gaba ɗaya ya zubomata har gadon bata ya kwanta lifff a kafaɗarta, sai nigab ɗinda ta ɗaura kusan kalar rigar saidai shi baya walƙiya kamar yanda rigar take amma shima yayi mata kyau, ya ƙara fito da daradaran idanunta data shafa musu baƙin kwallin da ya ƙara fito da ainihin kalarsu blue da ɗan sirkin fari-fari. Mayafin rigar ta ɗakko ta yafa sannan ta fita daga ɗakin. gabanta na faɗuwa ta Kwankwasa Kofar dakin. "Waye" ya faɗa muryarsa a dakile kamar wanda ya tashi daga bacci. "Ni ce, mum tace kana nemana" ta faɗa Muryar ta na rawa saboda tsananin tsoronsa daya fara ziyarar tar zuciyar ta tun kafin su ga juna. "Mtswww" yayi tsakin da yakai har kunnenta saidai bata ɗauki wannan komai ba taci gaba da tsawuyar jiransa. Mintuna Takwas bayan kwankwasa kofar da tayi kuma har yanzu bai fito ba ko motsin sa bataji ba kuma tana nan tsaye kofar ɗakin, Shikuma yana zaune abinsa kamar bai san da mutum a waje yana jiransa ba, da saninsa yabarta a tsaye tsawon lokaci tana jiransa. Miƙewa yayi ya fara tafiya kamar bayason taka kasa har ya isa kofar ɗakin, mirɗa handle ɗin Kofar yayi ya fara buɗeta a hankali, buɗewar kofar gaba daya yayi daidai da leeya ta juya zata bar wurin. "Imagine!, ke dan kin kai isashiyar mara kunya har ni zan aika kiranki kizo ki tafi ba tare da na sanarda ke dalilin kiran ba" Addu'a ta fara karantawa a zuciyarta ko zata rage jin abunda takeji a duk lokacin da ya-Turab ke kusa da ita. "Wallahi nayi tunanin kana toilet ne saboda na jima nan a tsaye shiyasa nace bara naje parlour na jiraka kafin ka fito" "Bazaki iya jiran nawa a nan ba sai kinje parlour, uban me zakiyi a can" "Ah ah bakomai zanyi ba, zanje na zauna na jirakane kawai kafin ka fito" "Duk wurin nan bazai isheki zama ki huta ba sai kin fita parlor dan munafunci" "Kayi hakuri dan Allah, naga babu wurin zama a nan ne" "Kin fi karfin ki zauna kasan tales ne" Bata amsashiba sai jijjiga masa kanta da tayi tana kara soke kan nata ƙasa. Wani wawan rankwashi ya sakarmata aka saida ta rasa abunda zatayi saboda tsananin firgici. "Ban sanardake idan ina magana da mutum banaso a dinga ansamin dakai ba" "Kayi hakuri Wallahi na manta ne" ta faɗa tana rufe bakinta da hannayenta dan kuka ke ƙoƙarin suɓucemata. "Wallahi kika sake kikayi kukan nan sai na miki dukan gaske da zai sakaki kuka da dalili babba". Ƙara danne bakinta tayi domin kar kukan da take ya fito. Dan guntun tsaki ja ya ɗauke kai daga gareta yace "ke bashi yasa na nemoki ba da zakizo ki sakani gaba kina kuka kamar kinga wani matacce, girki nake so kiyi yanzu-yanzu kuma nakeson aikin ya fara, egwusi and okazi soup, sai kuma oha crayfish soup, sannan kuma ki haɗa min yam and ginger juice karki saka yajiiii da yawa, sannan kiyishi ba mai kauri ba, bani account number ɗin ki na saka miki kuɗin da zakiyi siyayyar kayan girki" Amsa masa tayi da bakinta dan dole, duk da ba wata maganar tayi ba amma kuma bata kyale shi ba saboda tana gudun yayi mata wani dukan, account number ɗin ta tagayamasa nan taji alert ɗin shigowar kuɗi, dubawa tayi taga ya tura mata da kuɗi har dubu ɗari uku. "Kuɗin nan sunyi yawa indai siyayyar kayan girki ne 20k ma zasu isa" "Idan kinyi siyayyar ki zubar da sauran kuɗin" yana gama faɗin haka ya juya tare da banko kofar ya rufe ta rufff. Komawa tayi part ɗin su babu bata lokaci tayiwa meenal bayanin komai ba abunda ta ɓoyemata har zancen yawan kuɗin da ya turomata. "Bara na ɗakko gyalena nazo na rakaki siyayyar idan mun dawo sai na tayiki aikin, muyi saurin kammala wa kho, amma taya zamu girka wannan kalolin abincin, na yi searching a YouTube amma bangane komai ba wallahi". Cewar meenal. "Karki damu girkawa ba Matsala bane muje kawai bana so na kuma yin wani laifin". Da sauri meenal ta buɗe closet drawer ta dakko gyalenta, sannan suka shiga part ɗin Mum leeya tayi mata bayanin komai. Suna fita gate suka kira drivern gidan yazo suka zaɓa motar da zasu fita da ita kaana suka ɗau hanya. Babbar kasuwar kayan miya masu kyau da kamshi suka nufa, inda suka yi siyayyar komai da komai harma abunda zasuyi amfanin kansu ba iya na ya-Turab ba. Sa'ar da sukayi ba abunda suka nema suka rasa daga ingredients ɗin girkin da zasuyi, sun ɗauki tsawon mintuna talatin kafin su dawo gida. Tare suka haɗu kitchen ita da meenal ta fara nunawa meenal duk abubuwan da take buƙatar ta taimaka mata dasu wajen haɗa girkin, ita kuma ta fara aikinta matsayin ita zata girka komai, Sosai sukayi saurin kammala aikin, tun kan a ƙarasa meenal ke faman sonti, har tana faɗin Igbo sunyiwa hausawa wayo domin abincinsu yafi na hausawa daɗi. "Hmmm, haka dai kikace amma ai abincin su bazaifi na hausawa ɗadi ba domin su mafi yawan abincinsu ganyayyaki ne kuma su zasu yi matsayin tuwo da miya namu na hausawa". "Me kike nufi leeyana kina nufin Igbo sunayin tuwon ganye" meenal ta faɗa tana gwalalo idanunta waje alamun mamaki. Dariya ce ta suɓucewa leeya har saida ta gama tiƙar dariyar ta sannan tace"wallahi meenal kinban dariya sosai taya za'a yi tuwon ganye, nace miki mafi yawan abincinsu ganye ne kuma wani lokacin shi zasu haɗa su girka su ci Matsayin tuwo da miya na mu na Hausawa". "Okay, sai yanzu na fahimta ai, da zance taya za'a iya yin tuwon ganye ki koyamin nima na gwada nagani". "Ah ah ba haka nake nufi ba, yawwa meenal nace cikin wace cooler ya kamata mu zuba Abincin nan". Saidai ta ɗan niiisa kaɗan sannan ta kurawa wata cooler dake jerin kulolin da ke jera a kitchen idanu sannan tace "mu ɗauki ash ɗin can mai glitter kuma set biyar ne kinga zata isa mu saka komai da komai, har Babban jug ma sai a zuba juice a ciki." "Gaskiya kam kular nan ta dace da girkin nan kinga komai zai samu muhallin sa, yanzu ki miƙomin su gaba ɗaya ki mu fara zuba waɗannan da muka kammala" Da hanzari meenal taje ta ɗauko kuloli ta kawo mata, nan suka fara zuba Abinci sannan suka rage wanda zasu ci da sauran ƴan uwan nasu da zasu iya cin girkin. Bayan sun kammala kwashe abincin leeya ta ɗauki Babban farantin da ta jera komai ta juya da nufin taje ta kai masa. Da sauri meenal ta dafa kafaɗarta tace "me zakiyi?" "Abincinsa zan kaimasa" "A haka zakije, ɗazun fa ya ganki da kayan nan na jikin ki kuma yanzu zaki koma masa dasu bayan kinyi girki ga ki nan sai kamshin spices kike kamar an baɗa miki su a jikinki. Gaskiya ki ajiye muje kiyi wanka ki canja kaya sannan ki tafi". Cikin damuwa leeya ta kalleta da blue eyes ɗin ta masu tsorata wanda duk yayi tozali dasu tace; "kinga meenal barni naje, yayi min kashedi karna jima fa, kuma tsakanin mu yanzu awa kusan uku ne bansan adadin abunda zai min ba". "Leeyana!" Meenal ta kira sunanta da kausa-sasshiyar murya, bata jira amsawarta ba tace "Dole sai kin fitar da tsoron ya-Turab a ranki, domin kuwa wannan ɗabi'ar ba inda zata kaiki wallahi. Rayuwa da zakuyi, wata sabuwar rayuwace wacce daga ke harshi sababbi ne a wannan rayuwa, saboda ke baki taɓa yin aure ba shima haka, dole sai kin neman wa kanki girma tun a gidan nan domin bakisan inda zaije dake ba idan kunyi aure, idan kikace komai yayi ya zama abun tsoro wallahi bazakici ribar zama ba, kwata-kwata ma bazakiji daɗin zaman dashi ba. Na rokeƙi leeya dan Allah ki rage tsoron ya-Turab a ranki kinga baya wani kulaki sosai kinsan saboda me?" Jijjiga mata kai leeya tayi alamar bata sani ba, meenal kuma taci gaba da magana; "saboda kina tsoronsa sosai yasan bazai shata miki layi ki ƙetare ba shiyasa ko a gaban kowa zai iya yimiki son ransa, yana gani duk ranarda ya bukaceki a rayuwarsa zaki shigo ki manta da komai da yake miki Saboda kina tsananin tsoransa, bawai nace kiyi masa rashin kunya bane, ko ɗaya kawai dai ina gayamiki ne dan kisan irin zaman da zakuyi bayan aure. Ajiye farantin muje ki sake shiri" Meenal ta faɗa tana karɓar farantin daga hannun ta ta ajiye sannan suka fice daga kitchen suka koma bedroom ɗin su. Suna isa ta shige toilet tayi wanka, koda ta fito har meenal ta zaɓa mata kayanda zata saka, bata ɗauki lokaci wajen shirya jikin ta ba ta janyo doguwar rigar atamfar da aka fito mata da ita ta saka, sosai rigar tayi mata kyau ga kuma adon da akayiwa rigar na bead and stone work kamar ba nigeria akayi dinkin ba. Juyawa tayi zata fita bayan ta gama shafa turarukan da take amfani dasu Airah tayi saurin tarota "sis-leeya kinga yanda kika haɗu kiyiwa Allah kibari nayi miki hoto". "Nima Bara naɗauko wayata nayi miki wallahi kinyi kyau sosai matar yaya" cewar badar. "Ai kuwa idan kika bari Airah da badariyyah suka ɗaukeki Nima sai na ɗauka wallahi" mayah ta faɗa tana daidaita wayar a fuskar leeyana duk da tana rufe rufff sai ƙwayar idanun ta ake iya gani. Haka suka sakata dole ta tsaya badan ta soba sukayimata hotuna kala-kala kafin suka barta ta tafi, da gudu-gudu ta shiga kitchen ta ɗauko faranti ta isa part ɗin sa gabanta na faɗuwa tana tsoron abunda zata tarar sakamakon ɓata lokaci da tayi.......................✍🏻 BAYAN WUYA........ By RUMANA M DIGGI EP.38 _____________________A buɗe ta tarar da kofar bata tsaya shawarar komai ba ta kutsa kai ciki, sallama takeyi a tsorace har muryar ta naɗan sarƙewa. Daining ta nufa ta ajiyemasa abincin har ta juya zata tafi tajiyo motsinsa, da sauri ta sauko daga step ɗin daining tanaso ta fita kafin ya sameta a ɗakin. Turusss sukayi lokacin da ta iso tsakiyar parlourn. "zo nan" ya faɗa fuskar sa a murtuƙe. Har ta buɗi baki zatayi magana ya kuma faɗin"dan uwarki sai yanzu zaki kawo....." Dakata ya-Turab, ta tari numfashin sa tana ɗaga masa hannu alamar ya dakata ɗin, da ci gaba da faɗin"ka zageni, kaci mutuncina, kaci mutuncin iyayena duk dan Ni. Wai baka san Ni marainiya bace banada uwa banada uba, duk sun mutu shekaru Bakwai da suka gabata, ko dan daɗewarda sukayi a ƙasa bazaka raga ba, ko dan mutuncin su musulmai ne kamarka bazaka raga ba, ko dan tausaya min da tunamin da mutuwar Iyaye na bazaka daina ambaton su da mummunan kalami ba, ko dan ni da akeda burin auramaka bazaka ragamusu ba, iyayena sunyi maka komai ya-Turab domin Allah ya basu kyautar haihuwata har iyayenka sukaga dacewar mu dakai suke so su haɗamu, ya-Turab kodan mutuncin wannan bazaka raga ba, ai koda iyayena suna raye bai kamata ace bakada abun zagi da kaskanci ba sai iyayena, Wallahi bakasan yanda nake jinka a zuciyata ba aduk lokacin da ka ambato sunan mahaifiyata ko mahaifina a bakinka da niyyar ka zagesu, bazan iya misilta yanda nakejiba na kasa banbance tsana da ƙiyayya wannene zuciyata take yimaka. Bawai ina nufin Ni na tsaneka bane zuciya ta ce ta kasa aminta dakai ya-Turab, domin kuwa ita ce takeda haƙƙin yarda da duk wani abu da yanzi idan dai ya shigo rayuwata, domin duk zuciya tana son mai kyautata mata, haka kuma tanaƙin mai munana mata ko ya yake" ta ƙarashe maganar da wani irin kuka da kuma karfin halin tsayawa a gabansa harta amayar da abunda ke ranta. Sosai mamaki ya kashe turab a tsaye domin tsawon rayuwar bai taɓa sanin leeya zata iya tsawa tayi masa Magana kamar haka ba, bai taɓa tunanin tanada taurin zuciya har haka ba, mamaki bai gama kasheshiba sai da yajiyo karar buɗe kofa da sauri kamar wanda yake gudun ceton rai ne yazo yaga kofa a rufe kuma ba'a saka makulli ba. ya kuke tunanin zai buɗe kofar? To kamar haka ne leeya tayi lokacin da kukan da take yaci ƙarfinta, sai gani yayi kawai babu ita a inda take tsaye kuma baiji fitarta ba domin mamaki ya hanashi faɗar komai, sai guntun tsakin da jaa tare da kowa bedroom ɗin sa dafe da kansa. Da gudu ta shiga ɗakin nasu tana gunjin kuka ta zube kan gado taci gaba da rera abunta, mayah, Aneesa da badariyyah na zaune suna kwasar abincinda leeya da meenal suka dafa. Meenal da airah da khulud kuma suna zaune wuri ɗaya, sai dai su ba abincin sukeciba firarsu suke kawai domin sun kammala cin nasu abincin. "Subhanallah, leeyana me ya faru" cewar Airah tana nufar leeya dake zube kan gado. "Hummm, ya-Turab ne ko leeya, wallahi ya-Turab ya shiga uku shi ba'a taɓa yimasa abun alƙairi, yanzu kar ayi mamakin dukanta yayi fa" khUlud ta faɗa tana jin babu daɗi. Miƙewa sukayi gaba ɗayansu sukaje inda take, sosai suka rarrasheta har sai da ta daina kukan, sannan ta sanar musu duk abunda ya faru tsakanin ta dashi bata ɓoye komai ba na game da abunda ya wakana tsakanin su. Sosai suka bata gaskiya bawai don ganin idanunta ba, domin kuwa duk wanda yakesonka da gaskiya, kai koda ma baya sonka bai kamata gana zagin iyayenka ba koda suna raye balle ma ace basa raye. "KhUlud da karfe nawa zaki fita" cewar Aneesa. "Sai karfe huɗu zan fita domin nafiso sai pa yana nan, dan kar mum ta hanani zuwa" "KhUlud ina baki shawara kada kije gidansu id ya lafiyar kura balle taga nama" "Hmm, Aneesa kenan wallahi ba ƙaramin abu bane zai hanani zuwa gidansu id ba sai dai wani ikon mahalicci kuma, kamar yanda kikaga saura sunyi kema kiyi haka, kimin addua da fatar alƙairi kawai kinsan ba wanda zai wuce ƙaddararsa Ni id ne ƙaddarata kuma soyayyar sa ce jarabtata in sha Allah sai na cinye jarraba wa" "Ina yimiki addu'a da fatar alƙairi ƴar uwata, Allah yasa hakan da kikayi shine alƙairi" Aneesa ta faɗa tana dafa kafaɗarta. Daga haka kowa ya kama gabansa wasunsu suka fita wasu kuma suna zaune, leeya kuma tana zaune duk abun duniya ya isheta gaba ɗaya ta rasa sukuninta tana zaune zugummm kamar ba ita ba. Da yamma likiss khulud ta shirya da ita da badariyyah da fannah suka fita, sai dai su badar da fannah shopping zasuje ba hanyar su ɗaya ba, sai an ajiyesu zai wuce da khulud gidansu idrak. "Driver saraki mall zaka ajiye su fannah, nikuma layin ƴan haya unguwar tsohon barikin sojoji" "Tau yayi hajiya ba damuwa yanzu zamu isa in sha Allah". Saraki mall yakaisu badar da fannah ya ajiye su, sannan ya wuce da khulud layin ƴan haya. Ba jimawa suka iso unguwar, kuma cikin ikon Allah ta gane gidan domin tun ranarda sukazo da mai taxi ta hardace hanyar tsaf. Sai da ta ɗan tsaya bakin kofar gidan tsawon mintuna biyar kafin daga bisani ta shiga, da sallama cike da bakinta ta ƙarasa har tsakiyar gidan nasu, saida ta karewa gidan kallo tsaff kafin ta ƙarasa bakin kofar tilon ɗakin da ta gani na cement ɗaya jal a gidan, sai kuma ɗan wani ƙaramin daki da akayi da langa-langa, sai kuma daga gefe banɗaki ne da kuma rijiya. Sallama ta kuma ko zasuji su fito, saidai sallamar ta maƙale sakamakon arba da tayi da matar da ke tsaye gabanta. Duk da tsufa da girma sun bayyana a jikin matar bai hanata shaida ko ita wacece ba. Numfashin ta yayi barazanar ɗauke wa har wani fesoshi take da karfi kamar wacce za'a zarewa shi. "Dayam-mmah aiki ki-ke a gidan nan" khulud ta faɗa Muryar ta na rarrabewa saboda tsanin razana da tayi da matar. Sai da tayi maganar ne ta tuna da girman gidan bai isa a ɗauki ƴar aiki ba. Da sauri ta rufe bakinta da hannayenta, sannan ta kuma buɗewa sai faman zare idanu take "dayammah nan gidan kine". Murmushin dole matar ta ɗauko ta yaɓawa fuskar ta sannan ta ce "hajiya ƙarama yau a gidan nan, ko kinyi ɓatan kai ne ko wani gidan kike nema?" "Ah ah gidan nazo dayammah, dan Allah ki yafemin duk abubuwan da nayi miki a baya wallahi yarunta ne kuma lokacin bangane gaskiya ba sai a yanzu Allah ya Bayyana min gaskiya, wallahi na gyara halayena dayammah dan Allah ki taimaka ki yafemin" khulud ta faɗa hawaye na wanke mata fuska. Juyawa matar tayi batare da ta cemata komai ba har saida ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa daga nan ta dawo wurinta "hajiya ƙarama muje ki zauna, nasan ba ƙaramin abu bane ya kawoki gidan nan ba amma nayi mamaki sosai dana ganki wallahi dan banyi tunanin zaki iya shigowa unguwar nan tamu ba". "Dan Allah dayammah ki daina faɗin haka, wallahi na yi rantsuwa da mahalicci na ba khulud ɗin da kika sani a can baya bace, wallahi duk na canja daga munanan halayen da kika sanni dasu". "Shikenan dai Yanzu muje ki zauna zaifi tsayuwar nan" Ba musu ta bi bayanta har suka zauna kan shimfida, gaisawa sukayi sosai inda khulud ta kasa nutsuwa saboda kunya da kuma tsoron abunda zai biyo baya, tana tuna munanan kalamai da zagi da cin mutunci wanda tayiwa baiwar Allahr nan. Ita a yanzu ma ji take kamar idan tayi maganar id dayammah ta cemata ba gidan yake ba ko kuma tace mata ba ɗan ta bane. "Tunanin me kike haka Hajiya ƙarama inata magana bakiji ba" Firgigit ta zabura kamar wacce ta tashi daga nannauyan bacci ta sauke tagumin da tayi tare da ajiye numfashi mai tsawo sannan tace "dayammah kinsan abunda ya kawoni gidan nan?" "Shi nake so na sani hajia ƙarama" "Wallahi bansan ke zan tarar a gidan nan ba, har ga Allah Ni bansan nan kuke zaune ba, dan Allah inaso na roƙeki wata alfarma ɗaya kafin nakai ga faɗin buƙata ta" "Ki faɗi ko menene hajiya ƙarama, muddin zan iya yi to sai na aikata miki ita" "Dan Allah dayammah na roƙeki ki dubi girman Allah da Manzonsa ki yafemin duk wani laifi dana taɓa yimiki a rayuwar nan wallahi kinji na rantse wallahi na canja hali ki yafemin" tun kan ta ƙarasa dayammah ta tari numfashin ta da faɗin "duk wannan Maganar ta riga ta wuce yanzu hajiya ƙarama, kuma abunda ya wuce bai kamata ana taso dashi ba kiyi maganarki kawai karki damu da wannan, kuma wallahi indai ni kika yiwa laifi na yafemiki duk wani abu da kika yiman duniya da lahira. Allah Ubangiji ya yafe mana ga baki ɗaya". "Ameeen ya ilahi" khulud ta faɗa a sanyaye sannan taci gaba da faɗin "Nan ne gidansu idrak?" "Idrak!!" Dayammah ta faɗa kamar a tsorace. "Eh, idrak manaf nake magana nan ne gidansu" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Hajiya ƙarama dan Allah karkice fréri laifi yayi miki, dan Allah ki sassauta masa Wallahi baisan Matsayin ki bane da bazai......" "Ba abunda kike nufi bane dayammah, na kamu da sonsa ne kuma matsananciyar soyayyarsa sosai, sai dai shi idrak bani bace gabansa, wallahi babu rokon da banyimasa ba amma ya ƙi amincewa da soyayyata dayammah zaki yarda idan nace miki na durƙusawa idrak da gwiwoyina saboda ya soni. Ni nasan amanar ki ce ke bina, nasan duk abunda nayi muku ne da sauran ma'aikata amanarku ke bina ku yafemin dan Allah kice idrak yasoni dan girman Allah" ta faɗa tana wani irin kuka mai ban tausayi kamar ba ita ba. "Shine kika biyoni har gida, kikazo ki haɗani da mahaifiya ta, Annah dan Allah na roƙeƙi ki fitar da bakinki cikin wannan maganar, wallahi khUlud bata cikin tsarin matan da nakeson aura kwata kwata batada halayen kwarai, Annah khulud batada mutunci bata mutunta kowa hatta malamai bata mutuntawa balle ɗalibai, Annah ta, dalilinsu ne saboda sunga iyayensu manya ne agari aka koreni inda nake faci kuma su sukazo har wurina suka cimin mutunci suka wulaƙanta sana'a ta, daga baya kuma suka saka iyayensu suka tada ni daga rumfar da nake samun abincin da muke sakawa a bakinmu Annah. Shin kina farin ciki da wannan yarinyar ta zama surukarki Annah, inajinki Annah ki faɗamin, Tun Sa'adda kuka fara magana da ita ina jinku ina nan bakin kofa tsaye ina jinku idan na fahimta wannan itace KhULUD K. WAASIB wacce kikayi aikatau gidan su shekarun da suka shuɗe, Annah wannan yarinyar ita ta ruguza farin cikin ki, ita ta tarwatsa plain ɗin da kika jima kina haɗawa har nazo na samu kinyi nisa, Annah ta dalilin wannan yarinyar ne muke zaune cikin matsanancin talauci da Rashin hujja mai ƙarfi, annnah ta dalilinta ne muke zanune cikin tauyewar rayuwa, daba dan itaba da yanzu komai yana zuwa daidai yanda aka tsara, da badan ita ba da yanzu mun haɗa karfi da karfe da mahaifinta mun ruguza shirin da fairozha ke shiryawa, da mahaifinta ba azzalumi bane da yanzu......" "Dakata id, ya isa haka, mahaifina ba azzalumi bane baya zaluntar kowa" khulud ta tare shi a tsawace cikin kukan da yaci ƙarfinta, sai da ta ɗan daidaita numfashin ta dake ƙoƙarin tsayawa sakamakon ciwon ta na asthma da ke kokarin tashi sannan taci gaba da faɗin, "kayimin adalci id, nace kayi min adalci. saboda inasonka, kai kuma baka sona bashi zai saka na zamo sillar waɗan nan abubuwan ba, sannan ka tuna shekaru sunja yanzu. Kuma nayi imani da yanzu ne bazan taɓa aikatawa dayammah wannan ba nasani! Ka gayamin menene farin ciki a cikin Rayuwarku dana tarwatsa, menene plain ɗin ku dana ruguza, menene?, wallahi duk wannan abun da kake magana akai bansan dashi ba, abunda nasani kawai na saka an kori dayammah a gidan mu tare da karyar ta mareni alhali bata mareni ba, kuma nayi hakane kawai saboda banasonta a cikin gidan mu a wannan lokacin, kuma bayan haka ba'a barta ta tafi haka ba sai da aka biyata ladar aikin da tayi shin menene laifina a cikin wadannan abubuwa daka lissafa" "Kinaso ki sani khulud!?, na ce kinaso ki sani" ya faɗa cikin tsawa da fushi "to kije ki tambayi mahaifinki dan wannan maganar ba taki bace ta mahai....." "Idrak!!!!" Dayammah mahaifiyar sa ta kira sunansa ƙwallah na cika mata idanun. "Annah dan Allah ki dakata na faɗa mata, har sai yaushe abun zai tsaya Annah, kinada shaidodi da yawa da zasu tabbatar da haka, meyasa? Me yasa bazakije ki sameshi kuyi magana ta fahimta ba Annah, tsoro kikeji" ya faɗa yana takowa gaban mahaifiyar tasa, "bakyaso yasan laifin mu ne ya shafi mahaifinsa Khattab har fairozha ta kasheshi, bakyaso yasani, bawai ina kwaɗayi bane Annah ta. nima inaso ki samu farin ciki da kwanciyar hankali kamar yanda mahaifiyarta ke ciki, duba kiga Annah har bauta kikayi musu tsawon shekaru duk baki aikata komai akai ba, kin kasa yimusu bayanin komai dan Allah a tsayarda abun haka kinji mahaifiyata dan Allah nake rokarki akawo ƙarshen komai". Da sauri khulud ta zube kasa kan gwiwoyinta gaban dayammah domin ita gaba ɗaya kanta ya rufe, maganar kisa, me idrak da mahaifiyarsa suke boyewa, dama akwai sanayya tsakanin mahaifin ta da mahaifiyar idrak, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un meyake Mala'ikun faruwa. A gaban Annah dayammah ta durkusa tana kuka tace "dan Allah ku taimaka ku fitar dani duhu dayammah menene tsakanin ku da pa, me ya aikata muka. Nasan mahaifina baya cuta kuma bayason a cuceshi, wallahi inada tabbacin idan ma cutar ku yayi bada saninsa bane, yakamata kuje ku sameshi ku yi masa Magana domin a Tsawon shekarunda naji kuna faɗa Maganar ba karama bace dan Allah kije kiyi Magana dashi, wallahi nasan ko mum bata san da wannan ɓoyayyen al'amari ba, koda bazaku gayamin ba shi kuje ku gaya masa ku daina kallonsa da laifin da baisan ya aikata ba". Juyowa tayi ga id ta kallesa da rinannun idanuwanta da sukasha kuka tace "id kayarda Dani wallahi bansan su amrah sun saka an tadakai rumfar da kake aiki ba na rantse maka da Allah, kuma wallahi ko ranarda mukaje inda kake aiki ɗin nan Ni ban saka bakina ba, bamu taɓa samun saɓanin da Raudha da Amrah ba sai ranarda suka yimaka wannan abun, kuma tun daga ranar na daina sakar musu fuska, wallahi danasan an tada kai bazan zuba ido ba, dan Allah kayi haƙuri kaji in sha Allah zanyi Magana da papu ya samamaka wani aiki". Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata har saida kayan cikin ta suka motsa "fitar muna daga gida!" Ki tashi ki fita nace ko gidan kune nan". Da sauri mahaifiyarsa ta kalleshi tun kan tayi magana yace "Annah kiyi shiru". "KhUlud! Ki fita daga gidan nan tun muna shaida juna wallahi" yana faɗin haka yayo kanta da sauri ta miƙe ta fita daga gidan ranta na mata ƙuna. Motar ta ta koma domin tun zuwansu kofar gidan ta bama driver kuɗin adaidaita tace masa ya tafi kawai zata jima a gidan. Tana shiga motar ta ɗan jingina bayanta a sit ɗin motar, ta ɗaga kanta sama wasu zafafan hawaye na gangarowa a fuskar ta. Ji tayi ambuɗe motar an shigo sai dai bata buɗe idanun ta ba kuma bata motsa daga yanda take ba. "Meya sameki kike kuka?" Taji sanyayar muryarsa ta dira a dodon kunnenta. Da sauri ta ɗago kanta sai dai tana ido huɗu dashi ta sake fashewa da matsanancin kukan da tayi a baya. Da sauri ya dafe kansa, saboda tsorata da yayi da ganin yanda take kuka, kuma shi a Duniya ba abunda yafi tsana kamar sautin kuka musamman ma na mace, a can baya kullum da dare sai annahnsa tayi kuka sosai sannan take iya kwanciya, kuma baisan Dalilin haka ba, idan ya tambayeta dalili kuma tace masa zai sani ko ba yau ba. "KhUlud ki dakata dan Allah, nine fa idrak ki faɗamin menene dalilin kuka har haka, bayan kuma gani" "Id nasan abunda ya zo dakai nan, kazo ne ka bini gidan mu kaga mahaifina ko, dan Allah menayimaka da ka tsaneni haka id" "Shhhhh" ya faɗa tare da saka ɗan yatsansa a bakinsa alamar tayi shiru "karki sake faɗin na tsaneki khulud ni ba wanda na tsana, ban iya ƙiyayya ba kuma bansan yanda ake ba, ban iya tsanar mutum ba balle na tsaneki, ki kwantar da hankalinki kinji in sha Allah komai yayi fine, yanzu kije gida zanzo na sameki muyi magana kinji, kiyi shiru ki daina kuka banason kukan mace yana sakani ciwon kai mai tsanani" "Ah ah Id, idan har da gaske kake abunda kake faɗa sai dai kazo muje gidan yanzu, domin idan kace zakazo, ka faɗa ne kawai banada tabbas kaga ko gidanmu baka sani ba, kuma gashi banada number ka ma dan Allah ka biyoni muje" Murmushi yaƙe ya danyi wanda ta gaza gane ma'anar sa yace "nidai kije kawai ai ni nace zanzo kho, kinga ban shirya zuwa gidanku ba yanzu amma dai zanzo kinji kar ki damu" "Kar na damu! Kar na damu fa kace id, Dan Allah gayamin yanda zan hana damuwa yin tasiri a raina bayan bana cikin zuciyarka da Rayuwarka" "Ni na faɗa miki bakya raina da zuciyata, na gargaɗeki a karo na Farko ki daina amfani da Maganar da kikeji ranki na raya miki, kije gida sai nazo" "Dan Allah to ka bani number ɗinka" ta faɗa tana zaro dalleliyar wayanta daga cikin jakarta" "Banida khulud, da inada wayan da na baki number na saboda a halin yanzu danasan komai nafiki bukatar number ɗin wani da yake gidanku" "Ina wayanka take?" "Na gayamiki banida, kwana biyu kenan da suka shuɗe, Annah batada lafiya na siyarda wayan nayi mata magani, domin inda nake samun kuɗin maganin kun saka an toshe min" "Dan Allah id kayi hakuri, wallahi banida masaniya, ka karfi wayan nan tawa bara na cire sim card dina idan naje gida zan saka a wata wayar kayi amfani da wannan, duk ranar da kaje gidan mu sai na baka wata sabuwa" Sosai ya haɗe fuska kamar bashi ba, yace "kinaso muyi faɗa" Hannu ta saka ta dafe bakinta tana zare idanu tace "banaso sai dai idan kai kakeso zuciyata ta buga shikenan" "Taya zan so zuciyar ki ta buga tun yanzu bayan ban gana da mahaifinki ba, idan zuciyar ki ta buga wazai min iso" "Babu" ta faɗa ba tare da ta gane takamammen abunda yake nufi ba. "Tau kije gida sainazo" Daga haka ya buɗe kofar motar ya fita, da ido kawai ta bishi har ya shiga gida sannan ta tayar da motar ta ta tafi ranta yana washewa a hankali. Bayan ya shiga gidan ya karaso kusa da mahaifiyar shi ya zauna sannan ya ɗora kansa kan cinyoyinta yace; "Annah naje kuma nayi mata magana na rarrasheta har ma na gayamata zanje gidan su kinji Annah ta, in sha Allah bazan zama butulu mai Rama alƙairi da sharri ba, wallahi tun farko da nasan ita ƴar gidan hajiya fanaya ce bazan yi mata haka ba, ki yiwa Allah karki ƙara zubarda hawayenki a kan wannan kinji" "Allah yayi maka albarka fréri, haƙiƙa ko dan mahaifiyarta taci muyi mata ragowa". "Amma Annah dan Allah idan bazaki damuba inaso in tambayeki" "Ina jinka frére faɗi tambayar ka idan na sani zan gaya maka" "Annah" ya kira sunanta da nutsuwa sannan yaci gaba da faɗin "Annah ya akayi hajiya fanaya ta dawo rayuwar ki bayan sun koreki daga aikin gidan batare da sunga ne wa idanun su laifin da kika aikataba, taya ta dawo rayuwar ki har ta taimakawa karatuna nakai har haka?"....................✍🏻 Ep. 39 ______________________sai da Annah ta ɗan niiisa sannan ta kalli idrak ta fara bashi labarin yanda komai ya wakana a lokacin da khulud ta saka aka koreta a gidan. "Bayan na fito da kayan da nasan nawane a gidan kamar yanda Alhaji wato mahaifin khulud ya umurce Ni, na fito dasu wajen gate din gidan na tsaya, sai sharar hawaye nake saboda bansan inda zanje ba, tun farkon zuwana garin suleja lokacin kana yaro karami sosai baka wuce shekaru biyar ba a duniya, a hanya na haɗu dasu hajiya fanaya kazo tsallaka titi suka buge ka da mota, su suka daukeka harma ni mukaje asibiti, ita hajiya ita ta biya kuɗin da aka yimaka magani har sai da ka warke gaba ɗaya sannan suka daina yimana hidima bayan kudin da suka bamu masu dan yawa. An sallamemu a asibitin suka saka mu a motarsu muka nufo cikin gari. A cikin motar take tambaya ta inda zasu saukeni, sai nake gayamata labarina cewa Ni bakuwace bansan kowa ba, kuma bana da miji rana ɗaya aka nemeshi aka rasa, ta tausaya min matuƙa inda take tambayata zan iya yin aikatau. Na amsa mata cewar zan iya, tace min ba damuwa muje gidansu sai tayi magana da mijinta itama, da wannan maganar muka tsaya, sai dai abunda ya bani mamaki shine da mukaje gidan mai gidan shima ya tarbemu hannu bibbiyu kuma ya amince amma da sharadin idan ƴarsa bata yarda da zamanmu a gidan ba bazamu zauna ba, na yarda akan hakan nima sai addu'a nake Allah ya sa kar yarinyarnan ta ƙi amincewa, Cikin ikon Allah yarinyar na zuwa aka tambaye ta ta amince amma da qyar da sudin goshi, sai da aka haɗa da rarrashi da komai kafin ta yarda na fara aiki a gidan, wulaqanci yau daban, na gobe daban a hannun yarinyar. Bata sonka ko kadan a lokaci, ta Dalilin hakane yasa na mayarda kai makarantar kwana kaci gaba da karatunka, a kwana a tashi har wannan kaddara ta faru yarinyar nan khulud ta saka a ka koreni a gidan, dana fito na rasa inda zanje, dama can bansan kowa ba, ina zaune dan nesa da gate din gidan najiyo karar wayata da alamu kirana ake, nayi mamaki sosai ganin hajiya fanaya ce mai kiran nawa na daga ina goge hawaye, kuma ina saurar abunda zatace "hello, dayammah kina jina" "Eh ina jinki hajiya, wallahi Ni ban mari khulud ba, hasali ma ban taɓa nufin dukanta ba, tun zamana a gidan, ko magana da tsawa ban taba yimata balle musu, balle har nakai ga d'aga hannu na mareta" "Nasani dayammah, nasan baki aikataba kuma ki kwantar da hankalinki kinji, justice ya d'auki zafi sosai kuma ya riga yayi rantsuwar cewa bazaki koma gidan da sunan aiki ba" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" na fada ina ƙara sakin kuka. "Yi hakuri ki daina kuka, yanzu kina ina?" "Ina Wurin bishiyar nan ta lim wacce ke kallon gidan naku" "Okay karki damu, kiyi zamanki anan zan aiko da shuraihu driver yazo yakaiki gidan da zaki zauna, na saka ya binciko karamin gidan haya unguwar tsohon bariki inda zakici gaba da zama amma sai kinyi hakuri, saboda unguwar tsohuwa ce gaskiya, kuma cikin nasara ansamu gidan, sannan ki karɓi number ɗinsa idan yazo, duk abunda kike bukata ki kirani a waya ki sanardani, idan kuma bazaki iya ba shi ki kirashi ki gayamasa sai ya faɗamin, koda bakyayin aiki a gidan mu idan wa ta yayi lokacin da ake biyan ma'aikatan gidan nan za'a dinga fitar miki da kasonki kamar yanda ake miki lokacin kina nan, kuma zan dauki nauyin karatun yaronki harya kammala baki daya, kuma zanyi masa tsaye ya sami aikin da zai dogara da kansa bayan ya kammala karatun karki damu, sannan kuma na saka muku abinci a boot din motarda shuraihu zaizo da ita, kiyi hakuri kinji Allah ya sauwaqe sai anjima" Doskarewa nayi da wayar a kunnena domin na rasa da wane baki zanyiwa hajiya fanaya godiya, ban ankara ba sai ji nayi an katse wayar, sake danna wa nayi da nufin in mayarda kiran tare da kokarin tattaro ƴan sauran kalamaina wajen yimata godiya, sai ganin mota nayi a agabana. Shuraihu ne ya fito yayimin bayanin komai nikuma na shiga motar, duk abunda Hajiya fanaya ta faɗa ta cika, kuma har free scholarship din da kake gani kamar ka samu wallahi saida da tayi ruwa da tsaki kafin daga bisani ka samu". Dayammah ta faɗa tana kallonsa. "Gaskiya Annah wannan hajiya fanaya tanada kirki sosai, wallahi Allah danasan itace ke dauke da nauyin mu tsawon waɗan nan shekaru da ban kwatanta yiwa khulud haka hakaba, duk wani jinin Hajiya fanaya bai cancanci tozarci daga garemu ba, amma meyasa fairozha ke ƙoƙarin ganin bayan ahalin waasib kabil?" "Ba yanzu yakamata kasan labarin fairozha da mahaifinka ba idrak, amma ka kara hakuri lokaci yana nan tafe" "Annah, har sai yaushe zamu tsaya jiran lokacin, a yau ba gobe ba Annah, zanje na sanarwa da Khattab waasib asalin mu* "Ban amince ba idrak, wallahi ban amince kaje gidansu ba yau da nufin bayyanar da ko mu su waye, domin kafin waasibudden mahaifin Khattab ya rasu ya gayamusu ko wacece ta yi masa asiri, mainah matar waasibudden tana gidan Khattab yanzu haka kuma tasan da labarin fairozha, kana tunanin idan munje bazasu kamamu a matsayin munsan abunda fairozha ta aikata ba". "Shikenan, amma banaso ki saka kanki cikin damuwa ko ɓacin rai saboda wannan abun danayi, kinji dan Allah" ya faɗa ya na yin fuskar tausayi. Shafa kansa tayi kaɗan tace"shikenan, bazan saka ba Allah yayi maka albarka kaji" "Ameeen ya rabbi annah bara na fara aikin girkin dare kho" "Kullll, karka sake ka shiga madafah na gayamaka, duba kaganka fa wai a ce kana girki da girman nan naka" "Haba Annah, idan banyi ba waye zai yimiki, ai banace zan dinga yi kullum bane idan jikinki ya warware gaba ɗaya shikenan ai bazan ƙara aikin ba" Yana shirin miƙewa ya shiga ɗan ƙaramin kitchen ɗin nasu ne suka jiyo sallamar Sayyid yana shigowa gidan. Har gaban Annah Sayyid ya durkusa ya gaida ita cikin tarbiyya "Annah to ya jikin?" "Jiki alhmdullillah Sayyid, ya gidan naku" "Lafiya qlau, ga wannan a ci da hakuri annah" Sayyid ya faɗa yana ajiye wata babbar leda daya cikota da abubuwa. "Har da dawainiya haka sayyid, tho an gode Allah bada lada" Miƙewa sayyid yayi yaje inda idrak ke tsaye sukayi musabaha, daga nan ya janyeshi suka fita gidan. "Jiya da safe nazo gida ban tarar dakai ba, sai Annah na tarar ba Lafiya, dana tambayi inda kaje tace baka nan, na gayamata lafiya kake tun jiya ina kiran number din ka bana samu tace min ai ka siyarda wayanka, na ce mata meya sami wayan taka tace min wai magani ka siyamata da kuɗin" Sayyid ya faɗa lokacin da suke zama cikin motar Sayyid ɗin. "Eh hakane wallahi mutumina, jiya Annah ta tashi ba lafiya, kuma ba kudi a hannuna shine na saka wayar kasuwa na siya mata magani" "Amma wallahi idrak bakay min adalci ba, kuma ka bani mamaki, aka daiyiwa wasu mutanen da ba'a sani ba balle kai id, wallahi banyi tunanin haka daga gareka ba. Wai ace muna tare koda yaushe har Annah zatayi zazzaɓi bansaniba sai kaje ka siyarda wayanka ne za'a sami kudin magani" Id na shirin yin magana, Sayyid ya tare shi rai a matukar 'bace "wallahi nidai na gayamaka idan ka kuma min haka ranka in yayi dubu sai ya ɓaci" "Tuba nake ur highness" Id ya faɗa yana langwabar ta kai gefe tare da haɗe hannayensa biyu. Kwalin waya sabuwa filll Sayyid ya miƙe masa "ga wayarda ka siyar, dan Allah ajima naji ance ka siyarda ita". Id ya rasa abunda zaiyi kawai sai ya rungume Sayyid cikin tsananin farin ciki "Nagode sosai Sayyid, Allah ya ƙara buɗi na alƙairi, ya sa ku gama lafiya da duniya" "Ameen abokina, kadaina.....! babu godiya tsakanin mu, and kuma dan Allah anjima da yamma ka shirya, mai martaba na nemanka domin na bashi labarin ka da mahaifiyar ka" "Okay ba damuwa Allah ya kaimu anjima ɗin" "Ameen" "Yawwa Sayyid yau khulud tazo gidan mu" "Gidan ku kuma, yin me?" Sayyid ya faɗa yana dan gyara zaman sa dai-dai. "Wallahi kuwa ashe tasan Annah sosai, kuma iyayenta ma sun sanmu" Nan id ya kwashe labarin ta kafff da suka sani da kuma yanda mahaifiyarta ke taimakon su. "Aikuwa dai wallahi da badan mahaifiyar ta ba banga abunda zaka nema a wajen ta ba, kenan ita ɗabi'ar ta ce tun a gidansu kho, wulaƙanta talaka, shiyasa tayiwa Annah sharri har aka koreta" "Eh wallahi mutumna, ai wannan yarinyar da badan ta tuba ba da tayi asara wallahi" "Kai manta da ita kawai Allah ne ya nuna mata abunta tunda talakan da take gani ba komai ba shine kuma ya zamarmata komai yanzu" "Hmmm, Allah dai yayi jagora" Ameen Sayyid ya faɗa daga nan sukaci gaba da labarunsu. K.WAASIB MANSION. Tunda wannan abu ya shiga tsakanin leeya da turab ba wanda ya kuma kula wani a tsakanin su, leeya ta zage sai soyayyar ta take sha da messengern ta, kullum tana maƙale da waya har mum ma ta fahimta yanzu, sai dai bata san soyayya take a wayar ba tunanin ta kawai yanzu leeya ta shaku da wayar ne. "Mum yau inaso naje gidansu zohal, kuma inaso meenal ta rakani" "Tau ba damuwa ki shirya kuje, lefe zakuje gani kho" "Eh mum ta kirani ta sanardani ankawo lefen jiya da rana, amma kuma bashi kaɗai bane zanje mu tsara yanda bikin zai kasance" "Okay nagane, tau idan kin shirya ki sanardani wata ƙila tafiyarku zatayi dai-dai da turab sai ya ajiye ku, domin kaduna zai koma sai an fara programme ɗin shima zai dawo" "Uhmm--hmmm tau shikenan mum, amma fa mu munshirya meenal ma Ni kaɗai take jira idan nayi wanka nayi sallah sai mu wuce" "Okay tau sae kun dawo" "Yawwa mum mun gode" "Ki gaida ummansu Zohal" "Zataji mum" Daga haka leeya ta mike ta shiga part dinsu ta sanarwa da meenal yanda sukayi da mum, ita kuma ta fara shirin tafiyar. Sai da suka shirya tsaff kaana sukayi sallama da sauran ƴan uwan nasu suka tafi. Suna fitowa harabar gidan suka haɗu da turab shima ya fito da trollynsa janye kana gani kasan tafiya zai yi. Jingine yake yana jira a fito masa da motarda zai fita da ita su kuma su meenal suka karaso wajen. Ta gabansa suka bi zasu wuce meenal ta gaidashi "ya-Turab ina yini" Cikin sakin fuska wanda bata taɓa gani a tattare dashi ba ya amsa mata "Lafiya lau meenal fita za'a yi" "Eh zamuje gidansu Zohal ne mu duba lefen da aka kawo" Sai a lokacin leeya tace masa "ina yini" ko kadan kuma bata d'aga kai ta kalleshi ba hannun ta na kan wayanta tana dannawa duk da ba komai takeyi da ita ba. "Lafiya lau" ya amsa cikin halin ko in Kula. Gaba sukayi suka barshi a wajen bayan sunyi sallama dashi yayi tafiyarsa shima. "Amma gaskiya ya-Turab ya changer kamar ba shiba, ko dai magana akayi masa" Ɗan murmushi leeya tayi......, meenal kuma na ci gaba da tuƙa mota tace "wa zai yi masa Magana tunda haka tsarin rayuwarsa take, wata kila dai yana cikin mood na farin ciki ne shiyasa kika ga haka, amma Nima nayi mamaki sosai gaskiya" "Ai da haka yake tun farko da an huta, wallahi banyi tunanin haka daga gareshi ba, sai naji yau kin birgeni da baki nuna masa tsoronsa da kikeyi a fili ba" "Meenal kenan, ya-Turab yana samun damata da yawa shiyasa yake min komai dayaga dama, amma yanzu gaba ɗaya banajin akwai sauran wani abu mai suna tsoro da ya rage a cikin raina indai na ya-Turab ne, kuma bana tunanin akwai Ranar da wannan zai dawo" "Lallai kam gaskiya wannan da kika dauka yayi, bawai ina zugaki kiyimasa rashin kunya bane amma a dinga jan girma kawai" meenal ta faɗa lokacin da suke karasowa kofar gidan su zohal. Mai gadi ya buɗe musu gate suka shigo da motar har cikin gidan, mai gadin ya san leeya sosai kuma yanajin sunanta a bakin mutanen gidan. Fitowa sukayi sukazo har wurin da yake tsaye suka gaidashi, ya shaidar musu zohal tana nan bata fita ba. Suna shiga gidan kuma suka tarar da mutane sosai, gidan ya cika da mutane masu duba lefe, ummah mahaifiyar su zohal tayi maraba da leeya da kuma meenal, an karrama su a gidan sakamakon zamansu familyn fahad kuma ga leeya kawar amarya, sai da aka buɗe musu kayan lefen gaba ɗaya suka gani kafin leeya taje inda Aunty zainab yayar Zohal babba tace mata"Aunty zainab ina zohal tunda mukazo bamu ganta ba" "Lahhh leeya ba'a gayamiki tana dakinta ba, ai na zata kinje wallahi, faruk nace ya gayamiki fa kiyi hakuri karkuga kamar mun barku ne wallahi tana d'akinta ita da sultanah" "Bakomai Aunty bara naje dakin nata, su sultanah sun zo kenan" "Eh yau sukazo sai bayan biki zaku koma, maman numrah tazo sai faɗa take wai baku rubuta invitations da wuri ba har gashi saura kwana biyar, sauran families sai ganin laifin mutane suke wai ba'a turamusu invitations ba, da akayi mata Magana akan ta rubuta sai tace sai ranar da kikazo saboda bakida lafiya har asibiti aka kaiki kwana biyu" "Eh wallahi Aunty banajin daɗi kwana biyu zazzaɓi nake fama dashi, amma naji sauƙi. Aunty ai da kun rubuta tunda gaku nan ba sai ta jirani ba" "Eh haka mutane suka ce amma furrrrr taƙi yarda wai sai kinzo" "Tana dakinta kikace kho" cewar leeya. "Eh fah, tana dakinta ita da sultanah ne a ciki inaga" "Muje meenal" leeya ta faɗa tana yiwa meenal alama da su tafi. ZOHAL a dakinta, sai leka window take ko yaya Imran zai fita ta samu suyi satar hanya ta bayan gidan su ta tafi gidan su leeyana, domin ya imran babban yayansu namiji ya hanata fita tun shigowar satin nan indai ba fitar ta gida bace wacce za'a fita da motar gida. "Yawwa sulteey kinga yafito Gashi chan Allah kasa tafiyar ce" ta faɗa tana daga hannunta alamar roko. Sultanah dake kwance kan bed tace "zohal ki kirata a waya don Allah, Wallahi Nima ba wani fitar nan nakeso ba kin matsa ne kawai amma ga hanyar sauqi kice bazaki bi ba" "Ina hanyar sauƙin?" Sultanah na shirin magana sai ga leeya ta faɗo dakin baƙinta dauke da sallama. Da gudu Zohal ta dago tsalle daga kan gado ta rungume leeya "besty ashe kina tafe, wallahi gani nan ina shirin zuwa gidan ku yaya Imran kawai nake jira ya fita nabi ta hanyar baya naje gidan ku" "Satar fita kuma zohal amarya da akace tsausayine da ita" "Ke wane tsautsayi, wallahi ba wasa ba da bakizo ba binki nakeda niyyar yi yanzun nan, mutane duk sun azomin baki wai ban rubuta invitations ba har yanzu, kullum sai anyi magana" "Tau ai gani nazo" leeya ta faɗa tana kokarin zama. "Ina yini" cewar meenal tana kallon Zohal. "Lahhh meenal, tare kuke kenan har naji kunya, wallahi Allah Bankula dakeba yi hakuri kinji yasu mum" "Duk suna Lafiya, ya haƙuri" "Alhmdullillah, mungode Allah" "Ya shirye-shirye kuma" "Uhmm--hmmm yana nan kunayi meenal" Dan murmushi meenal tayi sannan ta gaida Sultanah itama. Sultanah da Zohal mahaifinsu ɗaya, kuma kusan girman shekarunsu ma daya, amma ba'a garin suleja suke ba. Tunda mahaifin su Zohal ya rasu mahaifiyar sultana ta koma gaban iyayenta a Katsina, sai idan biki ya taso ko kuma aure sannan suke zuwa, ko kuma idan sallah tayi sai suzo. "Lafiya qlau, meenal naji zohal ta kiraki kho? Ykk" "Lafiya lau alhmdullillah" "Masha Allah, leeyana kema sannunki, muna shan labarin ko a bakin Zohal" "Yawwa sulteey sannu, Nima ina shan labarin ki sosai ashe kin iso" "Eh na iso wallahi tun jiya ma, sai da nazo nake samun labarin wai baku shirya invitations ba har yanzu, amma Yanzu tunda gaki nan kinzo sai muyi sauri a tsara a turawa wanda zai yi printing" Zama sukayi gaba ɗayansu suka fara tsara yanda events din zasu kasance. Leeya tace "rubutawa za'a yi ko kuma dai ayi typing a waya a turawa mai printing din" "Gaskiya yafi, gwanda ayi typing ayi bayani dallah-dallah yanda shi wanda zaiyi printing invitation din zai gane" "Okay programme nawa za'a yi?" "Uku" sultanah ta faɗa tana kallon zohal koda an changer tsarin domin ita a yanda ta sani a gidan nasu ba'a yin wata bidi'ah sosai. "Uku kadai za'a yi dame-dame kenan?" "Kamu, sai kuma dinner, sannan sai waleemah da akeyi ranar daurin aure da Yamma" cewar sultanah dan ita zohal bata cewa komai. Meenal ma haka suna kallonsu ne kawai da kuma sauraro. "Okay ina za'a saka venue din wurin day one, kamu kenan kho" Sultanah tace "Eh kamu ne za'a day one, kuma a gidan nan za'a yi ki saka yanda za'a gane kawai kiyi summarize Kar zancen ya tsawaita" "Na saka day one:kamu; Venue: resident of Alh Khalil Adam girah. Time: 4pm" Haka dai leeya tayi masu bayani dallah-dallah yanda tayi komai, har akazo kan dinner da waleemah shima tayi kamar yanda tayi day one ɗin. "Shikenan bara a tura masa tayi wallahi" cewar sultanah da meenal bayan sun gama karanta wa a wayar zohal da aka rubuta. Miƙa mata wayar akayi itama ta karanta kafin daga bisani aka turawa wanda zaiyi printing invitation din. Bayan haka kuma sunsha labari sosai inda zohal take gayamata batun fitarda zasuyi gobe su raba katin gayyata idan an kammala aikin zuwa gobe. Sai Yamma sosai leeya da meenal sukayi shirin tafiya, meenal ma ita ta kuma tukasu da mota har gida domin ita leeya bata iya tuki ba, kuma hakan bai taɓa damunta ba balle tayi tunanin koya. A bangaren Turab kam tun da ya fita gidan ya dau hanyar kaduna, ya ɗauki tsawon awanni yana tafiya kafin ya iso. Wayar sa ya laluba lokacin da yayi parking gaban wani babban supermarket. Number ɗin zafaran yayi dialing ringing ɗaya ya dauka. "Turab ya akayi ka karaso ne?" "Yanzu na shigo, na tsaya supermarket ne na siye abu gani nan karasowa" "Okay, a estate ɗin fahad muke ba gidansu ba" "Aikuwa gwara da ka sanardani gidansu nayi niyyar zan tafi wallahi, amma dai ko da haka zanje na gaida mommy munjima bamu ga juna ba, idan na gama sada zumunta zaku ganni" "Okay no wander, sai ka shigo" Daga haka turab ya kashe wayar sannan ya shiga supermarket din yayi abunda zaiyi kaana ya fito. Gidan su fahad ya fara zuwa bayan sun gaisa da mutanen gidan ne ya nufi estate ɗin da su zafaran da fahad suke. Zaune ya tarar dasu a balcony din da ke wurin, kamar shi ake jira kuwa yana zuwa suka tambeshi, bayan sun gabatar masa da abinci yaci ya koshi ya kalli fahad yace "up going groom, yau ba wani deal ne sai shan iska kawai" Fahad ya dan yi murmushi mai sauti sannan yace "mutumina mukuwa mukeda deal babba wallahi" "Masha Allah, ina saurarenku ya akayi" "Batun lewa ne" fahad ya faɗa yana ɗan satar kallon zafaran da hankalinsa yafi karkata da wayansa dake ajiye a gabansa. "Lewa kuma" turab ya faɗa da mamaki. "Eh, wallahi batun lewa ya dan sakamu attention shiyasa ka ganmu a haka munyi jugum-jugum" Har a lokacin zafaran bai kallesu ba kuma bai ce uffan ba, har turab ma ya lura da haka. "Ya akayi, me ya faru ne kuma" "An samu labarin Yan bindigan da suka aika aikan basu kashe mata ba, kuma tun a farko munsan da haka" "Eh dama basu kashe mata ba ayanda muma muka sami labarin, sai dai abun tambaya anan shine ina suka kai matan" "Basu kaisu ko'ina ba hasali ma duk matan da suka kwaso wasunsu sun tsira" "Taya???" "Accident 'yan harin suka samu, kuma da sukayi accident din wasu sunyi kokarin ceton rayukansu, wasu kuma sun mutu, kuma labarin accident ya isarwa jami'an tsaro, har Allah yasa aka cafko wasu daga maharan, sannan kuma aka taimakawa wadanda sukaji rauni daga cikin matanda aka kama, sai kuma wasu da suka rasa rayukansu" "Allah sarki, yanzu to mecece standard Magana kan lewa" "Babu" fahad ya faɗa yana Tafa hannayensa biyu alamar babu ɗin. "Ina kuka sami wannan labarin, kunyi wata tafiyar ne bada ni ba?" "Ina zamuje bada kai ba seniorman?, kawai dai labarin bincikoshi akayi" "Waya binciko?" "Har ma sai ka tambaya man turab" cewar Fahad yana nuna zafaran alamar shi yayi binciken. "Allah sarki, Ni wallahi zafaran tausayi ma kake bani, gashi Allah ya jarabceka da ƙaunar wacce bakada tabbaci kan tana raye ko ta mutu, ina rokon Allah ya takaita maka wahala idan tana raye ya bayyana maka ita, idan kuma ta mutu Allah ya musanya ta da wata matar daban ya Allah" Turab ya faɗa a zuciyarsa, a zahiri kuma yace"zafaran a wannan zaka kare ai, Ni ko yaushe idan ka zauna da waya hannunka, kana nan kana search din labaran yan bindiga, Allah dai ya bayyana lewa mu huta" "Ameen suka faɗa baki ɗaya. K. WAASIB MANSION. "Mum ba sai driver ya kaimu ba dan Allah, wallahi zan iya tukin da kaina kinsani" "Justice yace a daina barinku kuna fita ba tare da driver ba" "Saboda me mum" khulud ta faɗa kamar zatayi kuka "mum tun dazu fa nake rokonki ki barni muje da yanzu fa na dawo, kunga ma wallahi ilyass sai kirana yake wata ƙila fita zaiyi daga shagon nasa" ta fada tana dagowa mum wayanta dake ta faman ruri. "Okay shikenan, keda wa zaku fita?" "Da badariyyah zamu fita, ita kadaice bai auna size dinta ba lokacin da yazo tana bacci" "Fito da kayan" Mikewa khulud tayi ta koma bedroom ɗin mum ta fito da kaya niƙi-niƙi a trolly. Kayane na sakawa wadanda ba dunkakku ba, duk anko ne da kuma sauran kayan fitar biki da papu ya saka aka fita da yaran gaba daya kowa ya zabi abunda yakeso. Shine ake shirin kai dinki, khulud kuma ta dage kan ita zata fita kai kayan saboda yanzu ba sosai ake bari tana fita gidan ba tunda ba skul an yi hutu. Dalilinta na son fita kuwa tanaso ta je unguwar tsohon bariki ne ta haɗu da id tun ranar bai nemeta ba gashi kuma batada contact dinsa balle ta nema shi, shine ta yanke shawarar fita yanzu zuwa wurin mai dinki. Da saninta ta saka badariyyah tayi bacci lokacin da mai dinkin yazo har gida zai aunasu, shiyasa ko yanzu ma mum batayi gardamar fitar ba saboda kar a tauye wa badar haƙƙin ta.....................✍🏻 EP.40 ___________________"badar kama mu fita da trollyn nan" Miƙewa badar tayi suka d'aga trollyn, ita ta riƙa hannu ɗaya khulud ma ta riƙa ɗaya har suka isa mota. "Nidai bazan iya driving ba wallahi ke zakiyi tunda kika cewa mum zaki iya" "Driving kam ai bazai haɗa faɗa ba muje" khUlud ta faɗa tana nufar mota. Centre ɗin mai ɗinki suka fara zuwa suka kaimasa kayan daga nan kuma suka wuce layin ƴan haya. Bangaren su id. "Gaskiya Mutanen nan suna da karamci, kamar ba gidan sarauta ba" "Annah nifa inaga jinin su sayyid basa wulaƙanta mutane tun haduwar mu da shi na fahimci haka, Ashe abun daga gida ya gani" Annah zatayi magana sukaji sallamar khulud. "Annah ina yini" khulud ta faɗa lokacin da ta karaso inda suke zaune id kuma yana yimata tausa. "Hajiya ƙarama yanzu ake tafe" Cikin dan jin kunyar abunda Annah tace khulud ta ɗan soke kai ƙasa ba tare da tace komai ba. "Barkanku da wuni"Badar ta faɗa tana satar kallon akulkin gidan da khulud ke mutuwar son ɗan cikinsa. "Yawwa Barkanmu dai, ya hanya?" "Alhmdullillah sai godia" "Idrak kaje ka dauko tabarma ka shimfida musu mana ah bar mutum tsaye haka kawai" Sai a lokacin id ya dago kansa sannan ya furta "sannunku" can a kasan zuciyarsa, domin ko badariyyah dake gefensa bataji abunda yace ba, amma ita khulud ta ji maganar. kamar shi kaɗai take jira yayi maganar kuwa ta karɓa masa. Gaisuwa sukayi sama-sama sannan ya wuce tilon dakin ginin siminti da ke gidan ya dauko musu tabarma ya shimfiɗa masu duk suna tsaye. Idrak badai ɗa'a da ladabi da tausayi ba, domin kuwa yana taimakawa mahaifiyarsa sosai ta fannoni da dama musamman ma bangaren aikin gida, shara, girki, wanke-wanke, wani lokacin har tufafi yake wanke mata domin ita kaɗai ce ta ragemasa a duniyar nan, kuma shikadai ne ɗa daya tilo a wajen ta. Idan bai mata ba wazai yiwa, kalmar da yake yawan faɗa kenan a duk lokacin da ya ke wani aiki daya kamata ace mace ce take yinsa bawai namiji ba. Bayan sun zauna ya juya da nufin fita gidan "ina zakaje?" Ya jiyo Muryar khulud na tambayar sa ba tare da ta kalleshi ba. "Fita zanyi" "Munzo duba jikin Annah kuma nazo nayi Magana dakai" "Ina waje idan kin gama abunda kikazo yi" "Okay" ta faɗa tana mayar da hankalinta ga Annah. "Annah Allah ya baki lafiya ga wannan" ta faɗa tana fitowa da kudi masu dan yawa daga cikin jakarta. "Hajiya ƙarama harda dawainiya haka, to angode Allah ya sanya alƙairi" "Amin Annah, Allah ya baki lafiya" Daga haka suka miƙe gaba ɗayan su suka fita, mota badar ta wuce ita kuma Khulud ta zauna kan wani yankakken ice dake kofar gidan inda taga id zaune a yanzu. "Na dauka kayi tafiyar ka kabarmu ai" cewar khulud tana kallon idrak dake zaune. "Kin taɓa ganin inda mutum yayi bako ya gudu ya barshi" "Idan mutumin ya zama mara cika alkawari ai zai iya yin haka" Haɗe hannayensa yayi wuri ɗaya ya langwabar da kansa ƙasa kamar mai roko yace "dan Allah hajiya ƙarama kiyi haƙuri da alkawarin da nayi bancika ba, idan kin bani dama sai na tashi na miki bayanin abunda ya hanani zuwa" Wani abu ne taji ya tsarga mata a hankali ta furta; "idrak.........!" "Nifa bazan taso ba Hajiya ƙarama har sai kin yarda kin yafe min laifin Sa'ba alƙawari danayi" "Tun kafin kayi laifi indai a wurina ne ka ɗauka an yafe maka saboda bakayin laifi" "Kina wasa kenan" Ya faɗa yana kara kasa da kansa. "Na yafe maka ka taso muyi magana ka gayamin abunda ya saka ka karya alkawarin mu" Mikewa yayi ya zauna daidai sannan ya kalleta yace "jiya ne fa kikazo nace miki ina nan tafe gidanku, naga kamar kinyi gajen hakuri, jiya da Yamma bayan kin tafi sayyid yazo duba Annah daga nan ya sanar mana da mai martaba nason ganin mu, shine yau muka shirya mukaje, yamana kyauta sosai bayan sayyid yayi masa bayani akanmu shine ya bamu kyautar gida a wata unguwar daban kuma yace zai sama min wata sana'a idan an duba" Fuskar khulud dauke da murmushi tace"gaskiya wannan abun murna ne kuma Sayyid ya cika aboki yayi kokari kwarai, Allah ya saka masa da alƙairi gaskiya na tayaku murna" "Muna godiya, wannan shine dalilin da ya hanani zuwa gaskiya, kuma gobe zamuje duba gidan amma in sha Allah zanzo banda gobe karki damu" Karar kiran waya da taji yana fitowa ne ya sakata shiru bata ce komai ba har saida id ya fito da wayar tana binsa da idanu ya daga wayar ya kara a kunne. Mintuna uku yayi wayar ya gama, sannan ya kalli khulud yace "sorry ma" Ita wallahi har mamaki ma yake bata yanda taga yana wani lallabata kamar ba shiba. "Kodai a kwai wani abu ne" ta faɗa a zuciyarta. Tunanin tane ya katse lokacin da taji yace "kinyi shiru bakiyi hakuri bane" "Ah ah ba komai, amma ka gayamin bakada waya kho" "Eh jiya sayyid ya siyamin wannan" "Hummm, kyautar Sayyid kawai kakeso ko idrak" "No ba haka bane naga ba dadi ne kinzo da waya haka kawai na karfe inaaa.............! abun bazai yiwu ba ai" "Amma kuma Ni na baka ko?" "Duk da haka ai, amma kiyi hakuri wannan maganar ta wuce. Yawwa nace dan Allah idan nazo gidan ku zaki bani dama na yi Magana da mahaifinki" "Sosai, me zai hana, ai mahaifina yasan Labarin ka sosai a bakina, mahaifiyata ce kawai ta fara sani yanzu, yan gidan mu ma gaba ɗaya ba wanda bai san labarin ja a wajena ba" "Tau shikenan na gode da kauna" "Uhmm--hmmm, bani number din ka tunda sai na roka" "Roko kuma, ai ba roko bane kawo na saka miki koda baki tambaya ba inada niyyar na baki ai" "Amma kuma sai da na yi tambaya ne niyyar tazo maka" "Ah ah tun dazu surutun da muke ne ya hana in fada, idan bakyason number dina to ga wayana ki saka min taki" Zatayi magana yayi saurin cewa"dan Allah" Karɓar wayar tayi ta saka number ɗinta sannan sukayi sallama ya rakata har mota suka tafi. "Wallahi kinci arziki banyi niyar tuki ba har na koma gida da ji kawai zakiyi na tuka motar nan na yi tafiya ta" badar ta faɗa a kufule. "I'm so sorry sweet badariyyah wallahi bada niya na jima wurinsa ba kiyi haƙuri wani abu ya dan tsayar da mu amma yanzu mun kammala kiyi hakuri dan Allah, muje gida mum ta fara calling" *________ A can bangaren su leeya kuma yau tunda sassafe sukayi duk aikin da zasuyi suka gama sannan suka shirya tsaff suka tafi gidan su zohal ita da meenal. Misalin ƙarfe goma sha daya suka isa gidan su Zohal a parlour suka sauka duk da mafi yawan bakin da ke gidan suna parlourn, nan su leeya suka tsaya suka gaida su. Sultanah ce ta taso tazo inda suke domin su basu ma lura da ita ba. "Meenal yanzu ake tafe" ta faɗa tana zama inda suke "Lahhhhh sultanah ai bamu lura dake ba ma wlh yanzu muka karaso" "Eh ai na kula baku san dani ba, Zohal na ciki bata gama shiryawa ba inaga kaya take sakawa yanzu ta fito wanka tun dazu muna zaman jira baku zo ba har munyi tunanin zuwa gida mu sameku" "Sai kuma Gashi Allah ya kawo mu, muje cikin to" cewar leeya tana shigewa dakin zohal su kuma sultanah da meenal suka rufa mata baya. "Besty sai yanzu, mu nan har munyi Magana da driver idan mun fita gidan ku zamu fara zuwa" "Kaiiiiii, aikuwa da bazaku samemu ba dan muma tun dazu muka fito biya ta shagon mai tela ne" "Okay tau ba damuwa, sannunku da zuwa meenal zo ki zauna ga invitations nan ki d'ibai wacce zata ishi su mum da kuma su fannah" Zama meenal tayi ta fara duba invitation din yanda akayita cikin tsari aka bi komai dalla-dallah gwanin ban sha'awa, bayan ta gama dubawa ne ta cire adadin waɗanda za'a buqata a bangaren gidan maza wato su fahad kenan. "Leeyana inaga waɗan nan zasu isa kho" cewar meenal tana nuna mata yawan invitations din da ke hannun ta. "Eh mana ai zasu ishesu in sha Allah, ki ajiyesu hannunki idan mun koma gida sai a isar da saqo" "Muje" sultanah ta faɗa lokacin taga Zohal din ta kammala shirin da take. Fita dakin sukayi sannan suka shiga inda umma take mahaifiyar zohal sukayi mata sallama sannan suka wuce da driver. Sai misalin ƙarfe takwas na dare suka dawo gidan su Zohal bayan su gama raba katin gayyatar, sosai suka d'ebo gajiya kuma sunsha yawo. Sallar magariba da isha sukayi gaba daya domin basu samu sunyi ba, daga Nan kuma suka ci abinci sannan leeya da meenal suka dauki hanyar komawa gida. Sultanah da Zohal kuma kowa ya nufi bed dan rage gajiya. Washe gari ya kama ranar talata, kuma yayi daidai da ranar da za'a kamu wanda muka sanshi a al'adance shine saka amarya lalle. Da yake familyn gidan maza wato angwaye basu cika zuwa wurin kamu ba saidai waleemah ko dinner party, shiyasa ƴan gidan su mum basa wani d'oki, meenal da leeya ne kawai suma kuma don suna kawayen amarya ne. Kasancewar mummy neesah da kuma su twins da dad ƙarami basuda wasu dangi a garin Kaduna hasali ma aiki ne kawai ya mayar dashi garin yasaka suka tattaro wasu kayayyakin su da zasu bukata suka dawo suleja gidan dad babba wato papu, kuma a chan Bhopal India ma an wakilta wasu familyn su mummy-neesah suzo daura auren fahad yasaka akazo dasu su kusan shida a gidan yau. Sosai gidan su mom ya fara cika da dangi domin a ka'ida duk wanda yake babba gidan sa za'a yi komai dad'in dad'awa kuma har haji-mainah na gidan mahaifiyar kowa a familyn. Yau saura kwanaki uku kacal ayi komai a gama har daurin aure, domin yau talata kuma ranar juma'a ne za'a daura auren. Karfe huɗu saura kwata yaran da ke gidan suka shirya zuwa saloon da kuma gyaran jiki. mayah, khulud, badariyyah, da kuma Airah. Leeya da meenal kuma suka wuce gidan su zohal suyi attending programme ɗin da za'a fara yau. Da shirin su suka fita gidan da kuma anko da za'a saka yau ranar kamu, zani da dan-kwali iri ɗaya, sai kuma riga ta roba karama mai dogon hannu kalar baki. Koda suka isa gidan su zohal din sunyi mamakin ganin mutane rututu har haka, sunsan dai a gayyatar da sukayi basu yi inviting mutane har haka ba. Har inda aka warewa Amarya wurin zama leeya da meenal suka nufa, Zohal yau ba damar a rugo da gudu a tarbi leeya yasa ta sake mata murmushi mai sauti tana washe haƙora, daga can nesa kuma sukaji muryar Sultanah tana kwala musu kira cikin jin dadin ganinsu tana tare da wasu yan mata kimamin mutum hudu itace cikon ta biyar. Gaisawa sukayi sosai cikin mutunta juna bayan ta ƙaraso wurin, pictures suka fara dauka bayan wasu mutane sun dauka kafin wasu suzo kuma. "Besty yau meya sameki dan Allah na ganki sanyi-sanyi kamar akwai wani abu dake damunki" Murmushi leeya tayi wanda tasan zohal zataji tace"besty ina tunanin yanda zan zauna idan an kammala bikin nan naki Ni kadai, meenal tafiya zatayi can yobe kinsani ke kuma kinyi aurenki su badar duk tafiya zasuyi, khulud kuma kinsan makaranta take itama" Jikin zohal ne yayi sanyi sosai domin itama tanajin abunda leeya keji a game da haka kusan ma tace tafi leeya jin d'acin haka "karki damu in sha Allah komai zai daidaita ai kema ba dadewa zakiyi ba, fahad yace min da yanzu lokaci daya za'a yi auren mu daku amma kuma aka daga naku domin ba'a saka rana ba ma har yanzu, kuma kinga ai estates daya fahad da ya-Turab suke ai koda aure kukayi wuri ɗaya zamu zauna dan Allah ki kwantarda hankalinki ki daina saka damuwa a ranki" Duk da ƙarar sautin kidan kwarya dake tashi wurin bai hana leeya jin meeting din wayarta ba alamar shigowar saƙo. Dan dago da wayar tayi ta duba ko ba'a faɗa mata ba tasan wanda ya turo mata saqo messenger dinta ne sunan da su khulud suka sakamasa. "Me yace?" Zohal ta tambaya lokacin ta fahimci leeya ta isa kammala karanta saqon da aka turo mata. Mika mata wayar leeya tayi tana shirin dubawa sai ga wasu mutane da alamu dai duk familyn nasu ne. Da murna suka gaisa gaba daya hade da yimata pic's ita kadai, sannan suka fara dauka a tare, leeya na tsaye jikinta duk a sanyaye ta rasa meyasa kuma tunda taga messengern ta ya turomata sako taji gaba ɗaya yanayinta ya chanja. Bayan sun tafi ne zohal ta janyo hannun leeya suka zauna, dago da wayar tayi ta karanta sakon da taga antura mata. Cikin matuƙar farin ciki zohal tace "congratulations bestie komai zaizo karshe in sha Allah, kinga a nan ne zaki sami duk wata dama da kika rasa akansa a baya, wallahi nayi matukar farin cikin ji da ganin wannan saƙo" Cikin madaukakiyar karaya leeya tace "hmmm, bestie kinsan na kamu da matsananciyar soyayyar bawan Allahn nan? wallahi besty har ina rasa abunda ke damuna a wasu lokutan idan na tuna irin yanda nakeji akansa, besty koma waye wannan mutumin na kamu da sonsa a lokacin da babu wani amfani da hakan zaimin, domin an katangeni da kula duk wani saurayi, a yanzu banida yanda zanyi kuma" "Allah sarki karki damu da wannan kinji, idan abu rabon ka ne ko mai wuya da rintsi zaka sameshi, kuma idan ke rabonsa ce zai samu. Idan kuma rabon ya-Turab ce ke babu abunda za'a iya yi domin haka Allah ya tsaro tun kan a halicci duniya da abunda yake cikin ta" Sosai gaban leeya ke duka jin an ambaci sunan ya-Turab ita harga Allah mantawa take da bawan Allahn nan, hasali ma babu shi a lissafin ta na komai. "Dan Allah zohal kidaina faɗin haka, Ni ba rabon ya-Turab bace in sha Allah" "Kiyi sauri ki tuba besty" "Astagfirullah, Allah na tuba" cewar leeya a sanyaye. "Dan Allah karki kara kwatanta fadin haka, Allah ba ruwansa da komai, kuma ikon kowa bazai hana Allah nashi ba saboda haka ki roki abun da yafi alƙairi kawai kinji" "Allah kayi mana mafi alƙairi" "Ameen besty ki tashi muje kiyi rawa yau" "Rawa! Hmmmm, kin ta'ba gani" "Bantaɓa gani ba amma ki tashi muje Ni zanyi idan bazaki min ba" "Zohal bakida dama wallahi, Amarya ba kunya gasu Sultanah can sai bajewa suke amma ke duk bai miki ba" "Rawar su bata min ba gskiya" zohal ta fada kamar mai rad'a suka kwashe da dariya baki daya. Haka akayi komai yanda aka tsara da kuma yanda abun yake a al'ada, sai karfe bakwai na yamma aka kammala taron bikin kamu da akayi, meenal da leeya suka dawo gida bayan sunyi sallama da sauran kawayensu. KADUNA. CLASSIC ESTATES. "Zafaran kayi sauri karka jima dan Allah yau nakeso mu tafi, kuma ina so mu kwana suleja yau domin gobe ne za'a yi dinner, kuma na sanarwa duk friends dinmu na Abuja dana nan kaduna harma 'yan suleja ɗin" "Sorry our groom, gani hanya fa na kusa na karaso saura kadan, ina turab" "Yana sama yana shirya mana kaya a trolly" "Soja da kansa, lallai yau sunanka Sa'adatu fahad, turab ne yake shirya kaya a trolly yau" "Wallahi idan ka zagesa saina gaya masa bazan rufeka ba" "In rufe kaina mana idan baka rufeni ba ko banada blanket" "Kanada, ka zaga ka gani" "Na zaga" "Bakasan na zama munafiki ba yanzu, muna gama wayarnan zanje na sanar masa" "Ai mun gama" Zafaran ya faɗa yana dariya. Fahad zaune a parlour ya ajiye wayar kan table bayan ya gama waya da zafaran, knocking kofa yaji anayi daga waje. "Waye?" Ya tambaye da mamaki. "Bude kagani" aka bashi amsa daga waje. "Lahhhhh, Zafaran dama kana kusa kenan" "Malam ka bude min kofa dan Allah idan na shigo kayi duk tambayar da zakayi" "Kofa a bude take ko kai ka rufe ta da zaka fita" Mirɗa handle din kofar zafaran yayi yajita a buɗe, cikin haɗe fuska ya karaso gaban fahad yace "ina abincina" Dariya ta kwace wa fahad ganin yanda zafaran yayi kamar da gaske, dama haka suke ta wasa tsakanin su kullum da shi zafaran, suna iya kokarinsu wajen ganin sun mantarda shi soyayyar lewa da ta zamo masa ciwo a zuciya. "Sorry rankayadade sir, abincinka na daining" "Allah ya ceceku wallahi da sai kunyi frog jump" "Soja kenan" fahad ya faɗa yana toshe bakinsa da dariyar da yake. "Kuyi duk abunda zakuyi idan na kammala cin abinci mu wuce suleja" cewar zafaran yana wucewa daining. SULEJA STATE. K. WAASIB MANSION. "Mun gode sosai ilyass, shiyasa muke sonka da son aikinka Kanada alƙawari wallahi ba kamar sauran madinka ba" "Nima na gode hajiya khulud, inason yimuku aiki nima Allah ya kara bamu hakurin zama da juna" "Ameen, jirani na hau sama na sanar wa da mum zuwanka domin batasan kazo ba" "Ahh, ai da kin barta kawai wata kila tana tare da baki ne tunda kinga gidan nan mutane ne ta ko'ina" "No, karka damu bari na kirata kawai dan Allah" "Okay ba damuwa, ina jira" Miƙewa tayi ta shiga part din mum ta sanar mata da zuwan ilyass wanda shine yake musu dinki, ko yanzu ma ya kawo musu dinkin da suka bashi ne gaba daya. "Malam ilyass yanzu ake tafe" cewar mum tana sakkowa da ga step. "Hajiya barka da dare ina wuni ya jama'a" "Alhmdullillah ilyass komai lafiya Ƙalau, khulud tace an kammala aiki kho" "Ehh in sha Allah Hajiya, an gama komai ba abunda ya rage" "Masha Allah, Allah ya saka maka da alƙairi sannu da kokari mun gode sosai" "Ni ke da godiya hajia Allah ya sa a more Ni zan wuce" "Okay ba damuwa, Allah ya kai lafiya ga wannan a sha mai kho" karɓar kudin yayi yana qara yimata godiya, ya fita daga gidan. Zama mum tayi ta zube kayan ta fara dubawa daya bayan daya, kayan iri daya ne kuma dinkin da akayi ma iri daya ne sai dai anyi alamar suna a jikin ko wace leda, nan hajiya ta kira kowa, leeya, meenal, mayah, Airah, khulud, da kuma badar kowa ya dauki nashi suka tafi bayan sun da d'a yin godiya. Tafiyar su ba jimawa mum ta kuma kiran meenal, ita da leeya suka fito suka sami Mum a parlor. "Yawwa ai gwanda da kukazo ku biyu, kun ragemin tafiya wallahi yau duk na gaji. Leeya je kitchen ki sakawa haji abincin ta ki kaimata sashenta, sannan ki diba wani daban a babban wuri ki je dashi domin akwai baki a bangaren nata" Miƙewa leeya tayi ta nufi hanyar kitchen tayi abunda aka sakata. "Meenal ke kuma kije daining abinci na nan a basket ki dauka kije boss quarter maman twins suna nan ki basu, kuma kar inji kin gayawa mayah sunzo" Cikin mamaki meenal tace "mum meya sa suka zauna boss quarter su kuma?" "Wallahi su fannah ne suka dage akan haka wai sai sun rama abunda mayah tayi musu tunda tazo har tsowon sati biyu bata taba kira ba ko a wayane ta gaida su, wai ta manta dasu shine sukace idan sunzo bazasu bari ta gansu ba sai dai idan sun hadu wurin dinner" Tashi tayi batace komai ba taje daining ta ɗakko abunda aka gayamata sannan ta wuce boss quarter. Ba jimawa ta dawo tuni leeya ta dawo itama, a can bedroom ɗin su kuma sai fira suke, kowa na ayyana irin kyawun da zai yi a wurin dinner gobe, ganin yanda aka kashesu da dinki na ji da gani. "Kowa yaje ya kwanta dare yayi muryoyinku kadai suke tashi a gidan nan har wajen gate ana jiyoku" Murmushi mai sauti Airah tayi sannan tace"kunji mamana nayi muku magana kowa yaje ya kwanta, wallahi yanzu nake shirin gaya musu haka sai gaki kinzo" "Sameerah bana son karya wallahi ai muryarki tafi ta kowa tashi duk a wurin nan" Shagwaɓe fuska Airah tayi jin mamanta ta kirata da asalin sunanta sameerah "mama Ni kullum bana abu kice gaskiya ne komai dai karya, ai sai kisa su badariyyah su raina ni tunda ke kika fara" Wani mugun kallo badar ta jefa wa aira tace"Aunty zainab ki yiwa Allah ki tafi zamu kwanta, kuma idan kin fita ki ja kofar dakin nan kiyi locking, yau sai naga wane irin raini ne ya shiga tsakani na da wannan yar taki wallahi. Mu fa kannen ki ne, ita kuma yar ki amma sam bata bamu girman mu da Allah ya bamu" "Zanyi duk abunda kika ce domin ko ni da nake mahaifiyar sameerah ta raina ni balle ku da kuke qannena amma yanzu ku taru ku mata bugun hatsi ko zata dinga baku girman naku" "Kamar kina kusa Aunty zainab yi tafiyarki kawai kar ki damu" Badar na gama faɗin haka Aunty zainab mahaifiyar Airah ta fice dakin ta janyo kofar ta rufe ta saka padlock. Dariya suka fara yi ƙasa-kasa, suma sun kagu bata tafi ba tana tafiya kuwa suka dora inda suka tsaya. Da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare mai gadi yaji ana kwankwasa kofa kamar a mafarki. da karfi ya zabura yana kara murza idanu. "Waye anan yanzu?" Ya faɗa cikin murya irin ta masu jin bacci. "Turab ne". Mai gadin yaji ambashi amsa daga waje. Tsoro, sauri, mamaki, duk suka zowa mai gadin a lokaci ɗaya Yana taku a hankali yana kara dallara hasken fitilar sa bayan duk hasken da yake wurin na electric bai hanashi saka hasken fitilar sa ba. Dan leqa wajen yayi kafin ya fara zare luck din a hankali. "Baba wai tsoro kakeji mune fa, ai dare bai yi ba sosai har ta yanda zakaji tsoro" fahad ya faɗa daga wajen gidan domin ya gane nufin mai gadin. Zare key mai gadi yayi ya buɗe karamar kofa "Alhaji karami lafiya cikin daren nan" "Lafiya qlau, nazo ganin mum ne" "Allah sarki to shigo" mai gadin ya faɗa yana hamma. Turab ya fara wucewa sannan zafaran, da Fahad suka rufa masa baya. Ba kowa a parlour kuma bakajin motsin komai sai na agogo. "Man ka duba yanda muka zo muka sami gidan nan zaka iya rantsuwa da Allah karfe ukun dare ne" "Eh wallahi kuma fa yanzu ne 11:50 amma babu wani mahaluki mai matsi a gidan nan sai cikin bacci" "Ikon Allah to kaje ka fito zamu jiraka a parlour" fahad ya faɗa. Juyawa turab yayi inda zafaran ke zaune ya jingine kansan ga sofa idanunsa a lumshe ya dafe saitin zuciyar sa kamar dai kullum abunda yakeji idan ya shigo suleja. Girgiza kai kawai turab yayi bai ce komai ba sannan ya wuce part ɗin mum, knocking ya farayi a hankali. Kuma a daidai lokacin mum na zaune kan sallayah tana tazbihi taji knocking. Alama tayi kamar tana sallah, shikuma yana jin haka ya gane sai ya dan dakata da knocking din mintuna uku tsakani yaji tace "waye?" "Mum turab ne ki buɗe kofar" "Turab kuma lafiya daga ina kake yanzu?" Mum ta faɗa a dan tsorace. "Mum ki buɗe Please, Kamar yanzu na fara shigowa gidan nan da dare" Mikewa tayi taje ta bude masa kofar, da ido take binsa har ya isa ya zauna. "Mum nazo ganinki ne daga kaduna muka zo, motar mu ta tsaya hanya sai da muka kira gida can kaduna aka kawo mana ita sannan aka kira bakanike yazo ya tafi da dayar data lalace. Yanzu kuma Abuja zamu wuce cikin daren nan kuma inada abunda zan dauka a cikin dakina shiyasa na biyu ta gidan nan da sai gobe zamu zo, yanzu haka ana jirana a parlour badai kuna lafiya ba?" "Lafiya qlau muke, amma dan Allah ka daina tafiyar dare turab wallahi tanada had'ari sosai baramma yanzu da duniyar ta zama sai a hankali" "Mum kiyi mana addu'a Allah ya tsare kawai, Bara na tafi sai da safenku" "Allah ya tashe mu lafiya, Allah ya tsare hanya" "Ameen" ya faɗa yana barin dakin. Hanyar da zata sadashi da part dinsa ya nufa, wani mugun tsoro ne yaji ganin mutum ya wulga ta gefensa, amma a ɗan nesa dashi. Da sauri yabi bayan mutumin domin bai iya tantance mace bace ko namiji. Sai da ya kusa isa daff sannan ya gane mace ce kuma ya ganeta leeyana ce domin kayan bacci ne a jikinta masu nauyi riga da wando. Mayafin da ya hango ne lokacin da ta juya domin itama taji alamar kamar ana biye da ita, sai dai bai bari ta ganshi ba, ta juya taci gaba da tafiyarta. "Me kika fito yi cikin daren nan" ya faɗa muryarsa wasai kamar yanda yake magana da kowa. Juyowa tayi a tsorace zata gudu ya cafko hannunta, a fusace ya kuma faɗin "tambayar ki nayi amma kike kokarin guduwa, me kika fito yi nace" Bata wani ji tsoronsa sosai ba kamar yanda take a baya domin tayi imani da can baya ne da yanzu hawaye sun wanke mata fuska. "Ko bazaki yi magana ba ne" "Zanyi, ba komai na fito yi ba na kasa bacci ne yasa na fito kuma bana jin dadin zama wuri daya kar tunani yamin yawa" "Meya hanaki bacci?" "nima bansani ba baccin ne dai nasan bana ji" "Shine kuma bazaki iya zama a part ɗin ku ba harsai kin fito nan ko ba mutane a can" "Akwai, bazan iya zama bane domin su duk sunyi bacci nikuma bazan iya zama ni kadai ba" "Saboda me?" "Tunani zai iya min yawa" "Tunanin me?" Kallonta ta mayar kan hannunta da kuma nasa dake riqe da juna, shima ganin tana kallon hannunsa ya saka ya kalla. Da sauri ya saki hannun nata, yana yarfe nashi. "Ki koma sashen ku" Tana shirin magana ya kuma daka mata tsawa, da sauri har tana haɗawa da gudu ta bar wurin ta koma part dinsu. Part dinsa ya wuce shima yayi abunda zaiyi sannan ya koma parlour suka dau hanyar Abuja cikin daren nan. Washe gari tunda asuba kowa ya tashi aka fara gyara gida tukunna bayan sunyi sallah, sannan aka fara shirin girke girken snacks da kuma juice wanda za'a bukata a wurin dinner. Leeya kam kiran wasu tayi daga cikin daliban catering dinsu Domin su tayata hada wasu abubuwan domin ita ta zama mr.chief a gidan gaba daya, sai da gari ya fara wayewa wadanda leeya ta kira suka iso suka hadu suka fara aikin. Sosai yanayin gidan ya sauya sai kamshi ta ko'ina. Mafi yawan ahalin ango idan zasuje biki a gidansu Amarya suna zuwa da abincin su ne wanda zasu rabawa baƙin da suka zo dasu, da kuma wanda zasuci su kansu basai sun jira an basu abinci a gidansu amarya ba. shiyasa su mum sukayi komai nasu a gida. Koda karfe goma sha daya na safe ta buga duk sun kammala aikin abincin da zasuyi, suka fara shirya wani abun daban kuma. A boss quarter na gidan kuma mum neesah ce zaune tana shirya wa. "Mummy Dan Allah nima zan fita" "Fannah kina gani ga Rukhshanah nan bata jin dadin jikinta idan kika fita dawa zaki barta" "Mum muje da ita nima bazan iya fita na barta ba" "Rukhsha zaki iya fita?" "Mum kuje kawai idan nu'aim ya tashi da bacci zan gayamasa kuma cikin gida, zan iya zama nikadai, bana son hayaniya ne da zan biku ai ina so na sami relief ne da maganin da nasha idan na walwale zaku ganni, idan kuma ban fito ba sai idan za'a je dinner zan fita" "Okay Allah ya baki lafiya" "Ameen, sweet fannah ki gaidamin da mayah kinji" "Zataji sweet rukhsha Allah ya baki lafiya" "Ameen sai kun dawo" Daga haka rukhsha da mayarda kwanciyar ta su kuma suka fita. Koda Lokacin sallahr azahar yayi mutane a gidan ko magana ba'ayi aka sanar musu da zarar anyi sallahr la'asar kowa ya shirya motoci zasuzo. Su khulud kam har sun shirya, meenal da leeya tuni suka wuce gidan su zohal, bayan kowa yayi sallahr la'asar ne aka fara shigar da kaya Boot, basu wani dauki lokaci ba suka kammala kowa ya tafi, har haji da sauran mutane ba wanda aka bari hatta rukhsha da batada lafiya. "Ina ne venue din?" "Royal elegant center, idan kunzo ku kirani ko ku kira zafaran wayan fahad ma na hannun sa" "Ok sai kunzo, Allah ya kawoku lafiya" Daga haka turab ya katse wayar, sannan yaci gaba da shirin sa. Angwayen sunyi kyau sosai kamar su ukun ne ake daurawa aure, wankan farar shadda sol sukayi wacce akayiwa aikin hannu cikin tsari, kayan iri dayane su duka uku turab zafaran da kuma fahad, tsarin yanda aka dinka kayan nasu ne kawai ya bambanta. Pics sukayi kafin daga bisani suka dau hanyar Royal elegant event center inda a nan ne ake gudanar da taron dinner party din. A bangaren su leeya suma sunyi kyau sosai, musamman leeya da zohal, farin material suka dinka suma, dinkin ne kawai ya bambanta amma koman su iri ɗaya itace babbar qawar amarya. Sultanah kuma da sauran familyn su zohal sunyi kalar ankonsu daban. Suma su meenal da sauran familyn su fahad sunyi nasu daban. Wurin yayi tsari sosai sai dai amarya bata iso ba tukunna, suna can an killacesu wuri daya har sai ango ya fara zuwa ya zauna. Shigowar mc kamar da minti ashirin sai ga angwayen sun iso sai kamshi suke bazawa, mc ya fara kirari aka saka waqar aure yana binta ana yimasa liki har angon yazo ya zauna sannan su turab da zafaran da sauran abokansu suka juya suka tafi. Bayan haka kadan sai ga zohal itama ta shigo da kawayenta, itama haka mc ya mata ya saka waqar auta waziri ta amarya ya fara bin waqar, qawayen amarya kuma suna yimasa liqi harda dollers, ganin haka ya saka aka fara ihu da tafi kan amare sun fara buge angwaye tun kan a fara. Leeya na shirin isa wurin sai mum ta kirata da waya, da sauri ta janyo Sultanah tace "sulteey ki isa da ita ta zauna mum na kirana ina zuwa yanzu" Fita tayi fili inda babu surutu sosai sannan ta amsa wayar. "Okay, suna waje yanzu, tho bara na shigo dasu" Daga yanayin yanda take waya na tabbatar wasu akeso ta shigo dasu hall din. Fita tayi ba jimawa ta dawo da ba'ki, an fara gudanar da taron cikin tsari kuma anabin komai daki-daki. Amarya da ango kadai ne zaune a can saman step, mc kuma a down. Mc ya fara magana cikin d'aga murya yace. "Bayan dogon jawabi da muka saurara a bangarori biyu na dangin Amarya dana ango, yanzu kuma zamu fara kiran babban yaya kuma aboki ga ango wato Turab k. Waasib dan Allah ku bashi hannu" Nan family ɗin sa suka fara tafi da ihu wasunsu kuma suna video din fitowar sa, wasu kuma suna bin waqar da aka saka da muryoyinsu. Fitowa yayi shima ya tsaya inda yaga kowa yana tsayi idan zai yi magana ya fara magana yanda ya kamata, sai da ya yaba halayen abokin sa daga karshe ya godewa Allah da kuma adadin mutanen da zukazo taron, ya kuma yiwa Amarya da ango addu'a da fatar alƙairi. Sosai mutane ke murna har ya sauka wurin sannan zohal ta fara wurga idanu domin bataga leeya a wurin ba, leeya kuma tana tare da mum tun dazu itama mum bata zauna ba sai fama da 'baki suke. Mc ya dora da cewa "yallaɓae turab k. Waasib mun gode sosai, munji bayanin ka kuma muna fatar Allah ya amshi addu'ar ka, yanzu kuma zamu kira babbar kawar amarya, amintacciyar ta, kuma yar uwarta wato leeyana Hamraz Awais, dan Allah ku bata hannu" Wani mugun zabura da zafaran yayi har sai da ya bawa turab da sauran abokansa tsora, miƙewa yayi tsaye hannu na makyarkyata bakinsa na rawa yake nuna musu da yatsansa ya kasa furta komai sai rawa jikinsa yake sosai har kafafunsa suka fara gazawa dashi, tuni mutanen da ke wurin suka fahimta zaka iya faduwa ko yaushe, akayi saurin zaunardashi amma ya kasa zama sai nunawa yake bakinsa na rawa idanunsa kuwa tuni ruwan hawaye suka fara ambaliya, makoshinsa na sama da kasa da alama dai magana yakeso yayi amma ya kasa. "Le!!!_ _ _le!, ita_ _ _ce!" Ganin yahaka ya saka suka zaunar dashi da karfin su suka daddafeshi. Rukhsha na zaune ta d'ora kanta a cinyar mummy-neesah taji ankira wani suna, "Leeyana hamraz Awais, wannan wane irin suna ne kamar na taɓa jinsa" "A ina?" Mummy-neesah ta tambaya Rukhshanah. "Wallahi mummy ji nake kamar nasan sunan nan" ta faɗa tana miƙewa zaune. Ganin leeya ta hau step din da ake tsayawa ayi magana ya saka rukhsha fizgewa daga rikon da mummy tayiwa hanneyenta ta mike tsaye tana nuna leeya baki na rawa ta furta "Yahyah-leeya" daga haka ta sulele kasa idanunta suka kikkife kamar wata gawa ta daina motsi, su fannah da sukaga abunda ya faru da gudu suka iso burin ko kallon gabansu basayi sai buge abubuwan da ke gabansu suke sunata kuka da ihu har suka iso wurin, Da sauri suka dafata suna kuka, mayah tace "innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un mummy me akayiwa sweet rukhsha meya sameta, mutuwa tayi mun shiga uku mummy" Tuni wurin ya hargitse domin kuwa zafaran ma an kasa gane makarinsa da kyar aka samu mutane kimanin goma suka fita dashi hall din, aka sakashi a mota turab ya tafi dashi. Leeya ma da sauri ta janyo zohal ta fita da ita wasu daga dangin zohal din suka sakata mota suka tafi da ita domin mutane cewa sukayi anyi kisan kai yanzu-yanzu a hall din nan, Gaba ɗaya hankalin kowa a tashe yake wasu harda guntayen hawaye, Fahad ma da sauri yayo kan rukhsha suka kinki meta suka sakata mota aka wuce asibiti da ita, mum kuma da leeya da badar suka shiga wata motar khUlud tayi driving dinsu suka bi bayan su mum neesah a asibiti. Tuni labari ya isarwa su papu da dad ƙarami suma suka dauko hanyar zuwa abuja domin su a gida aka barsu. Suna isa asibitin aka karbesu emergency don ganin halin da rukhsha ke cikin twins kam sai kuka suke kamar ransu zai fita duk a tunaninsu mutuwa tayi. Mummy-neesah da fahad sai rarrashin su suke amma suka ƙi yin shiru, Mum fanaya da badar da kuma leeya na isowa asibitin suka ci karo da turab. "Mum Lafiya, meya kawo ku asibiti waye ba lafiya?" "Kai zamuyi wa wannan tambayar turab" "Mum zafaran ne wallahi ya dan samu shock tun dazu bai farfaɗo ba" "Subhanallah, a wane room yake" "Male side room 27 akwai abunda zan karbo Chemist, wa kuka kawo" "Wallahi kanwar fahad din nan Rukhshanah, itace ba lafiya itama haka kawai akaga ta fadi ta daina motsi" "Subhanallah tana da aljanu ne?" "Wallahi muma bamu sani ba inaso inkira maman twins ne ta kwatantamin inda suke" "Shikenan mum Allah ya bata lafiya, bara na yi sauri na dawo zanzo in Allah ya yarda.............................✍🏼 EP. 41 _____________________kiran mummy-neesah mum tayi ta kwatanta mata dakin da suke. "Mum kuje ciki wata ƙila gida zan koma ko kuma na kira meenal tazo muje gidan su zohal" "Saboda me bazaki shiga ba leeya?" "Mum tsoro nakeji bana son shiga asibiti wallahi" leeya ta faɗa kamar zatayi kuka. "Okay tau karki damu kajirani na duba jikinta nazo mu koma gida yanzu nima inaso naje naga ko su haji sun koma gida, amma ke wa zaki bi ki koma suleja yanzu ana shirin yin magariba" "Shikenan mum kije ina nan ina jiranki, badar zaki iya shiga kho?" "Ehh Nima zan shiga in dubata" Khulud batace komai ba suka shige gaba daya ita kuma leeya ta koma ta jingina da motarda suka zo. Bata jima da tsayuwa wurin ba ta hango turab yana zuwa idan take fuskar sa ɗauke damuwa. "Leeyana, me kike a nan" Karo na farko a rayuwarta da wannan bawan Allah yayi mata Magana cikin kwanciyar hankali. "Bana iya shiga asibiti tsoro nakeji" Yasan ana samun irin haka dama, akwai wasu mutanen da basa son shiga asibiti ko kadan idan ba dole Ba. "Zo muje na bude miki mota ta ki shiga ciki ki zauna kafin su mum su fito tun da naga motar nan a rufe take kuma baki amshi key ba" "Ah ah ya-Turab kaje kawai Nagode zan tsaya anan na jirasu" "Okay normal, idan kin fi son haka, zan shiga nima na kaiwa abokina magani ana jirana" "Sai ka fito" ta faɗa bata ko kalleshi ba, shima bai kara kallonta ba yayi tafiyar sa. Shigar mum fanaya ɗakin yayi daidai da farfaɗowar rukhsha taga sumanda tayi. Da sauri su mummy-neesah da fahad da sauran likitoci sukayo kanta. "Nnene! Yahyah-leeya nagani itace wallahi" Rukhshanah ta faɗa murya a dakile idanunta rufe hawaye na bin gefen kuncinta. Da sauri mummy-neesah ta kara kunnewanta saitin bakin ta ko zataji abunda take faɗa. "Leeya! Yahyah-leeya leeya kece" rukhsha ta faɗa tana riko mummy-neesah. Da sauri mummy-neesah ta dago ta kalli fahad tace da karfi "fahad Rukhsha ta sami lafiya, wallahi taga wani abu da ta taba sani kayi sauri kaje mota ka dauko allura nan da aka bamu a Bhopal ka kaiwa likita yazo ya mata" Da sauri fahad ya fita dakin ya nufi inda suka aje motarsu da sukazo asibitin. *_________ Idan baku manta ba a can baya na gaya muku an fita da rukhsha waje can Bhopal India, sunje anyi mata magani kuma sun gana da likitan qwaqwalwa har ya bata magunguna da allura daya tak, wacce ya shaida musu duk lokacin da taga wani abu da ta taɓa sani gabanin ciwon ya sameta idan har taga wannan abun kuma ta taɓa saninsa, da zarar ta farfaɗo da sunan abun a bakinta a yi mata allurar nan. Tun daga lokacin duk inda mummy-neesah zata tafi da allurar take zuwa. tayi mata kyakkyawan wuri a cikin motarsu kuma ba wanda baisan inda allurar take ba don gudun bacin rana shine yanzu take gayawa fahad kan yake ya dauko. *___________ Mum fanaya kuma jin Rukhsha na surutai wanda mafi yawan abunda take fadi a cikin maganganun da take sunan leeya ne yasa ta matso kusa sosai domin ita kanta ya rufe gaba daya. "Hajiya fanaya dan Allah wacece leeyana danaji ankira sunanta dazu a wurin dinner, haƙiƙa tana da alaqa da wannan yarinyar Rukhshanah" "Nima nayi mamaki sosai maman twins, amma bana tunanin leeya tasan Rukhshanah din nan gskiya, bazan ki ta taki ba bara naje na kirata tazo muji, amma kin gayamin yanda akayi kuka sami yarinyarnan meye zai hadata da leeya itafa leeya Lagos ta fito" "Wallahi nima shine abunda yake bani mamaki, duk dai yanzu ba wannan ba dan Allah idan leeya din nan tana kusa ki kira mana ita musan wani abu daga wannan yarinyar" "Tau shikenan Bara na kirata tana waje" Fita daga dakin mum fanaya tayi, har kuma lokacin rukhsha bata daina magana ba idanunta a rufe sai hawaye suke sosai. Mum fanaya na fita sai ga fahad ya shigo, ya mikawa mummy-neesah allurar da ya ɗakko. Karba tayi sannan ta umurce shi daya kira likita, likatan na zuwa tayi masa bayanin komai nan take ya karbi allurar yayi wa Rukhsha, ko cire allurar bai yi daga jikinta ba tayi bacci. A bangaren mum fanaya kuma tana fita tayi dialing number din leeya domin bata ganta a inda ta barta ba. Ita kuma leeya tana tsaye jikin motar har wannan lokaci sai taji kiran mum ya shigo wayanta, ta dauka wucewa zasuyi yasa ta sauke ajiyar zuciya da karfi. Sannan ta daga wayar "Na'am, ina wurin da mukayi packing ɗin mota,,,,,, ok tau gani nan zuwa yanzu" Tana gama faɗin haka ta mayarda wayan cikin jakarta ta juya zata bar wurin. sai ganin mum tayi har ta kusa karasowa. "Lahh mum da kin bari nazo ai" "Ba komai ai Ni gani nan nazo, yauwa nace kin taɓa sanin wata yarinya Rukhshanah sunanta" "Rukhshanah?" Ta maimaita sunan a bakinta, "bansantaba gaskiya, amma inajin sunan a bakin mayah, amma lafiya meyasame ta?" "Wallahi itace batada lafiya, kuma itace ta suma a hall, yanzu ta farfaɗo tana ta kiran sunan ki" "Ni kuma!?" Ta faɗa tana nuna kanta. "Muje to" Sun juya zasu tafi kenan sukaji horn din mota a bayansu. "Mum su papu ne" leeya ta fada domin ta gane motar. Bin motar sukayi baya sai da tayi packing sannan papu da dad ƙarami suka fito suka gaisa da juna. "Ya me jiki?" Cewar dad ƙarami. "Alhmdullillah me jiki da sauƙi" "Ta farfaɗo?" "Eh ta farfaɗo amma abun akwai ban mamaki tunda ta tashi take kiran sunan wannan yarinyar" Cikin mamaki shima dad ƙarami ya kalli leeya yace"kinsan ta ne leeyana?" "Ah ah dad wallahi ban taɓa ganin ta ba amma wata kila ita ta sanni nice bansan ta ba" "Ah to mu shiga ciki mana" Papu ya fada yana wucewa su kuma suka rufamasa baya. A bangaren Fahad gaba ɗaya komai ya shafe a tunanisa. "Turab" ya furta a ransa. Miƙewa yayi da sauri zai fita mummy tace "fahad ina zakaje" "Mummy zanje na kira wayan turab ne, wallahi na manta gaba ɗaya bansan inda suke ba yanzu, inaga ma koda wannan abun ya faru basa cikin hall din nan" "Allah sarki ya kamata gaskiya kaje ka kirashi" Yana fita yayi ta wata hanyar daban, wayarsa ya ciro yayi dialing number ɗin turab. "Subhanallah, meya faru? Meya same shi" Fahad ya faɗa lokacin da turab ya daga wayar. "Shock kuma, akan me? Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un yanzu kuna ina" "Okay wane asibitin, gayamin gani nan tafe yanzu" "Ahhh ikon Allah muma muna asibitin wallahi, wane room ne?" "Okay gani nan zuwa" Tun bai kammala wayar ba ya nufi sashen da aka gaya masa nan aka kwantar da zafaran. Da sallama dauke a bakinsa ya shigo dakin, zafaran ya farfaɗo yana jingine da gadon da mug a hannusa yana kurfa tea a hankali. "Sannu zafaran ya jikin?" Fahad ya tambaya yana daddafa goshin sa. "Da sauki fa, Ni lafiya kalau nake tun dazu ina ta so kazo na sanar maka" "Me zaka sanar dani?" A can bangaren su leeya kuma suna shigowa dakin da Rukhsha take mummy-neesah ta tarbesu da murmushi kwance a fuskar ta. "Sannunku da zuwa anzo Lafiya?" Ta fada tana kallon su Papu da suka shigo Abuja yanzu. "Hanya alhmdullillah, ya me jiki?" "Me Jiki da sauki alhmdullillah sai godiyar Allah, gata can tana bacci" Mummy-neesah ta fada tana nuna gadon da Rukhsha take, sai dai basa ganin fuskar ta domin ta juya kanta ta bangon dakin su kuma suna daga bayanta. Wuri suka samu suka dan zauna, minti biyar tsakani ba wanda ya kuma cewa komai. Fannah da mayah, khulud da badariyyah tuni aka kira driver yazo ya mayar dasu gida domin fannah da mayah sun kasa daina kuka hankalin su ya kasa kwanciya shiyasa aka mayar dasu gida. Miƙewa suka ga leeya tayi da karfi tana toshe bakinta tare da ja baya lokacin da Rukhsha ta dan motsa har ana iya ganin rabin fuskarta. "A...A...Aleena, mum wannan Aleena ce ba Rukhshanah ba, ba itabace Rukhshanah Aleena ce ƙanwata mum, mahaifi da mahaifiyar mu daya wallahi itace kuzo ku gani" Leeya ta fada tana jan hannu mum fanaya zuwa gadon da Rukhsha ke kwance kamar wata zautacciya. Mummy-neesah da dad kam suka doskare a tsaye sai bin leeya suke da idanu duk abunda take. Papu ma kallonta yake cike da madaukakin mamaki, suna isa gadon leeya ta saka hannu ta sake juyo da fuskarta yanda kowa zai ganta. Sake ja da baya tayi kamar mai jin tsoro ta kuma cewa "Aleena, kece dan Allah ku taimaka ku tadani idan bacci nake aleena ta riga ta mutu wanda ya mutu kuma baya dawowa ai" cikin matsanancin kuka take fadin haka ta juya zata bar dakin da gudu taji an riko hannuta ta baya. "Yahyah-leeya ina zaki tafi ki kuma barina, wallahi nice Aleena ban mutu ba, mu ke muka d'orawa mutuwa tun a farko" Aleena ta fada itama cikin hawaye. Da gudu leeya ta yo kanta ta rungume ta suka sake fashewa da kuka. Buɗe kofar dakin akayi kanajin sautin bude dakin kasan wanda ya bude ta baya cikin kwanciyar hankali. Turab ne farko, sai kuma fahad ya biyo baya sannan sai zafaran. Cirko-cirko sukayi suna kallonsu leeya dake ta sheka kuka har tsawon wani lokaci. Miƙewa Rukhshanah wato (Aleena) tayi da karfi tana kokarin gasgata abunda idanunta ke gane mata, fizge drip dinda ke daure a hannunta tayi tana kokarin kara gudun hawayenta. A kafff dakin ita kadai ta lura da shigowar su turab. "Bro O, kai ne yaushe ka dawo meke shirin faruwa? Daga ina kake ina Nnene da uchie na" Kamar wani zaki haka zafaran ya tsallako inda suke domin shi harga Allah har yanzu bai gasgata leeya yake gani a gabansa ba, wai harda budurwa. "Leewa, leeyana! Ina kika shiga tsawon lokacin nan" zafaran ya faɗa yana riko hannayenta, ruɗanin da ya shiga ya saka shi mantawa da inda yake kuma a gaban su wa yake har ya riqa hannun leeya a gaban kowa. Kamar wanda aka zubawa ruwan dalma haka turab yaji lokacin da zafaran ya rike hannayen leeyanah, da sauri ya rumtse idanunsa yana jin d'aci da radadi a zuciyarsa. Dunkule hannayensa yayi da sauri ya kaiwa iska naushi yana jaa da baya idanunsa a rufe. Fahad kuma ganin haka ya sakashi rike turab da sauri ya zaunar dashi. Da sauri dad ƙarami da mummy-neesah da kuma papu suka yo kan turab da yake neman fita hayyacinsa. "Papu leeya ce, mum meyasa tun a farko kika ki gayamin gaskiyar asalin inda kuka sami leeyana meyasa mum? Kince min ƴar aminiyarki ce mai rasuwa, alhali a bincinken da nayi babu wata alaqa tsakanin leeyanah da ita ƴar Aminiyar taki, gashi yanzu mum, ga abunda wannan abun ya janyo" "Me kake nufi turab, kwata kwata ban fahimci inda zancenka ya dosa ba, wai menene haka ya kukeso kwakwalenmu su dauki wannan abun, wallahi gaba daya kaina ya rufe na rasa gano bakin zaren" cewar mum tana matsowa inda suke. A bangaren zafaran kuma lokacin da ya riko leeyana har razana tayi da ganinsa sosai domin tafin hannunta ta saka ta dafe fuskar ta da kwayar idanunta da suka bayyana a cikin mayafin da ta sako. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Okene kaine dan Allah ku tadani daga mafarkin da nake, ku maida ni duniyarmu ta asali, meke shirin faruwa damu" Bata idar da fadin abunda take shirin faɗa ba kamar wacce ta tuna wani abu ta wafce hannayenta daga rikon da zafaran wato okene yayi mata ta koma inda Aleena ke tsaye hankalinsu duk a tashe tambayoyi ne falll a ran duk wani mahaluki mai numfashi a cikin mutanen da ke dakin. "Budurwa nasan an kashe uchie tun a gabana ina Nnene take?" Kamar wata zararriya kafin rukhsha ta bude baki tayi magana tuni leeya ta sake dira gaban zafaran. "Taya iyayenka suka bar ka ka musulunta okene, dama karya kayi mana da kace kasar waje zaku koma, meye amfanin kin gayamana gaskiya dakayi" "ki Zauna a nan leeyana, Fahad miko min mug da ruwa masu sanyi, karɓi kisha" Karɓar mug din tayi kamar yanda aka umurceta tasha, sannan ta kuma zabura zata tashi, "ki zauna nace" mum ta kuma daka mata tsawa. "Ki bita a hankali hajiya fanaya, kina ganin lamarin nan kinsan ya girmewa tunaninta, maganar kisa fa ake, babban abunda nakeso na sani shine alaqarsu su ukunnan. Amma duk wannan ba maganar da zamuyi anan bane muje gida yanzun nan" "Turab baya cikin nutsuwa mum inaga kamar ma ya daina motsi wallahi" Sukaji muryar fahad daga bayansu yana magana. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, wai meyake shirin faruwa damune, kaje ka kira likita yanzun nan" Da gudu fahad ya fita har yana tuntuɓe. "Hajiya ku tafi da yaran nan suleja yanzu, mu zamu zauna da turab din, kuje waje driver yana nan wanda ya kawomu, mu idan muka tashi sai fahad ya dawo damu" Mummy-neesah da mum fanaya, da kuma leeya da Rukhsha suka dauki hanyar komawa suleja tare da driver, amma har a wannan lokacin leeya bata dawo cikin hayyacinta ba komai take ganinshi kamar a mafarki, a back sit ta zauna ta ta haɗe kai da gwiwa har suka isa gidan batayi magana da kowa ba. Ita kuma Rukhsha tana jikin mummy-neesah tana bacci har suka karasa domin itama allurar da aka yimata bata ida saketa ba, a ƙa'idar allurar ma ba'a tambayar mutum komai ko ayi masa magana har sai yayi 24hr allurar na zaga jikinsa. A asibiti kuma papu ne da dad ƙarami sai kuma fahad, zafaran, da turab dake kwance a yanzu ya farfaɗo. Dad ƙarami ne ya kalli turab da murmushi kwance a fuskar sa yace "son meke damunka haka wanda mu kanmu bamu sani ba kana neman sake tada mana hankali bayan wanda muke ciki?" "Dad nasan kuna matukar son farin ciki na, kuma kunaso kuga na rayu dad, amma wallahi bana tunanin rayuwata zatayi tsawo idan babu leeyana a ciki, wallahi ina matukar sonta, na rantse da girman Allah idan leeya bata aureni ba zan iya mutuwa, dan Allah ku taimaka kuji tausayina" turab ya faɗa gwanin ban tausayi. Wani irin azababben faduwa gaban zafaran yayi da sauri ya kalli inda turab ke kwance jin abunda yake faɗa, kamar a Sa'a kuwa idanunsu suka sarke. Mikewa turab yayi hade da fizge drip dinda ke daure a damtsensa ya karaso gaban zafaran idanunsa duk sun firfito waje saboda tsananin tashin hankali da yake ciki. A gabansa ya durƙusawa tare da riko hannayen sa gaba ɗaya. "Abokina wallahi ina sonka so na tsakani da Allah wanda Allah ya yarda abokai su yiwa junansu, kuma kaima nasan kana sona, wallahi a rayuwata ban taɓa tunanin akwai Ranar da zatazo na zautu dalilin soyayya ba, zafaran wallahi summah tallahi ina son leeyana na kasa yarda da cewa yarinyar da kake so muke neman ta tare dakai ita zata hana zuciya ta sukuni, alal haqiqa nasan soyayyar ta na zuciyar ka, kuma nasan abu ne mawuyaci ka fitar da ita a ranka, banso kaina ba Muhammad zafaran Areyola amma wallahi na tabbatar da na Fika bukatar leeyana a rayuwata, infact itace Yarinyar da iyayena suka zabamin matsayin matar aure. na rokeka da girman Allah da darajar fiyayyen halitta kayi hakuri ka fitarda Leeya a ranka, wallahi duk tsawon wannan lokacin da muka ɗauka muna Neman leeya banyi tunanin ita ce yarinyar da kake nema ba saboda baka taɓa furtamana Asalin sunanta ba, ko Ranar da mum ta fara gayamin sunanta saida nayi dogon tunani ko zan iya tuna inda naji sunan amma na kasa, I'm so sorry to say Zafaran wallahil Azeem ina son leeya har cikin rainah" turab ya karasa maganar yana durkushe gabansa. Jiki a sanyaye zafaran ya miƙe daga zaunen da yake idanunsa sun sauya kala zuwa jaaa jajir hawaye kwance zaiyi magana fahad yayi saurin shiga tsakaninsu hannunsa ɗaya rike da turab daya rike da zafaran yace; "Dad kuzo muje gida please, wallahi sam wannan maganar bata dace da ko'ina ba sai a gida, dan Allah kuzo muje gida gaba ɗaya ayi komai a gama" "Shikenan muje gida kawai" cewar papu. Dad ƙarami ne yazo ya riqa hannun Zafaran shi kuma fahad yana riqe da na turab kamar wasu kananun yara har suka isa mota gaba dayansu suka dauki hanyar komawa suleja tare. fahad ne kan gaba, kuma shi yake tuka motar. SULEJA STATE. K. WAASIB MANSION. Zaune take a tsakiyar gado ta nannade kafafuwanta ta cusa kanta tsakan ka nin cinyoyinta tana fitar da sautin kukanta a hankali cikin dusasshiyar murya wacce bata fita sosai saboda tsananin kuka da kuma shakewa da muryar tayi. A gefenta kuma meenal ce da kuma Khulud sauran yaran duk basa dakin iya su biyun ne kawai. ""Leeyana kiyiwa Allah ki daina kukan nan haka, wallahi kuka ba shi bane maganin matsalar, domin da kuka yanada mafita da tun awa uku da suka gabata ansamu mafita don Allah kiyi haƙuri ki daina kuka haka" "Meenal ya zanyi da rayuwata? Daga na fita wannan sai wannan meyasa ya-Turab bayada adalci a rayuwarsa, da tun farko ya karbi zabin da aka yimasa da ba haka ba, inason Okene da dukkan zuciyata, wallahi tun kafin ya musulunta ina mafarkin zama da shi, me yasa bai Bayyana ba sai a wannan lokaci, Meyasa ya-Turab bai furta yana so da qaunata ba saida yaga asalin masoyina na gaskiya ya fito, bazan taba yarda ba meenal, kuma bazan taba butulcewa alkairin da iyayensa sukai min ba" "Gaskiya wannan lamari Akwai daure kai, to shi ya-Turab yana sonki tun farko ko kuwa dai sai yanzu ne dayaga asalin masoyinki ya fito yasa yake nuna kamar yana sonki" "Wallahi meenal Ni har banason tunawa da wasu abubuwa na baya da ya-Turab yayimin, amma Ni ban taɓa rike shi a rai ba, kawai dai yarda da shi ne bazanyi ba" "Ki dinga hakuri kawai kinji, Allah ya sauwake yanzu ki tashi muje parlour abincin ki na can tun dazu, kuma har yanzu hankalin mum da haji bai dawo akanmu ba domin wannan yarinyar rukhsha na bacci tun da suka dawo nan, kuma ya-Turab da ya-zafaran duk suna kwance a asibiti" Cikin zallar tsoro leeya ta dago kanta daga jinginashi da kan gado da tayi ta kalli meenal tace "me ya samesu?" "Tho wallahi muma dai bamu sani ba, amma dai ankira haji an sanar mata suna hanya, dha niyyar ta ma taje abuja yanzun nan har sun shirya zuwan kuma aka gayamata ba sai tazo ba domin suna hanya" "Allah ya qara tsare gaba" "Ameen" Meenal da khulud suka faɗa. Tun zamansu a wurin khulud bata ce komai ba saboda bataso tayi magana cikin wannan lamarin domin abun ya fi karfin ta, duk yanda tayi Magana za'a ce tayi son kai tayi. "Ku tashi muje parlour" khUlud ta faɗa tana miƙewa tsaye. Miƙewa sukayi suma har leeya suka wuce parlour. A parlourn kuma haji ce zaune da shirinta sai kuma mum da kuma mummy-neesah. Shigowar su leeya yasa suka dago gaba ɗaya. "Leeya kizo idan kin kammala cin abinci" cewar haji mainah. Daga mata kai tayi cikin nuna alamun maganar ma tana yimata wahalar fita. Daining suka wuce su biyu kaɗai ita da meenal. Zama sukayi meenal tayi serving dinta, amma har tayi ta gama leeya bata sani ba saboda ta na zaune ne kawai hankalinta baya wurin ta zabga uban tagumi ta zubawa wuri daya idanu. "Leeya ga abinci nan ki ci don Allah kar ki sakawa kanki tunani da damuwa kinji Please" Kamar wacce ta farka daga nannauyan bacci haka leeya ta mike tsaye "meenal ina kanwata Aleena, wallahi na manta da tana gidan nan tun shigowar da muka yi ban ganta ba" Dafa kafaɗarta meenal tayi sannan ta mayar da ita zaune tace cikin tausasan kalamai "ki zauna kici abinci kawai, leeya rabonki da abinci tun karfe goman safe fa, kici idan kin gama zamuje ki ganta bacci take yanzu" "Meenal waye ya mayarwa Aleena da suna Rukhshanah, alhali Abbinmu Aleena ya saka mata?" "Sai idan kin gama cin abincin ne zamuje muyi magana dasu kinga yanzu bazai yiwu muje inda suke ba tare da kinci abinci ba" "Shikenan zanci, amma wallahi bana ma jin yunwa kuma saboda ke zanci" "Tau kici koda bakyajin yunwa hakan ma ba laifi" Zama tayi ta fara kai spoon din abinci a hankali kamar bata son ci, a zahirin gaskiya cin abincin kawai take batasan ya tasting din abinci yake ba turashi kawai take ya zamarmata kamar dole. "Na ƙoshi" ta faɗa tana sake mikewa tsaye. "Karɓi ruwa kisha" "Na koshi" ta kuma fadi murya a sanyaye. "Muje ki kaini in ganta don Allah, wallahi inada tarin tambayoyi danake so nayi mata" Parlour suka koma sai dai basu tarar da kowa a parlourn ba. "Su mum basa nan, kuzo muje dakinmu ki kwanta ki huta idan suka dawo zan kiraki kizo muje ki gana da kanwar taki" "No meenal, ba nada gajiyar da nake bukatar hutu yanzu i need to meet her please" "Okay muje part ɗin mum, bansan takamammen inda zan ganta ba gaskiya, amma kinga idan muka tambayi mum zata gaya mana" Part ɗin mum fanaya suka shiga sai dai basu tarar da ita a dakin ba, sake dawowa master parlour sukayi amma kuma har yanzu ba wanda suka samu a parlour. Parloun kasa suka sauka shima basu tarar da kowa ba, suna shirin fita part din ne sai ga mum da papu sun kunno kai, da sauri leeya ta dan tattaro yar sauran nutsuwarta ta gaida shi tayi masa ya hanya kuma ta yi masa ya masu jiki" "Meenal kuje part din haji ki raka leeya yanzu a can zata kwana" "Okay mum, muje leeyana" meenal ta fada tana riko leeya suka fice daga part din. Sashen haji suka wuce direct, mugun faduwa gabanta yayi ganin turab da zafaran da kuma fahad suma zasu shiga sashen na haji-mainah. Da sauri ta soke kanta kasa sosai har tana hardewa da tafiyarda take tanaso tayi saurin barin wurin. "Leeyana!?" Ya kira sunanta da kausa sasshiyar murya. Kamar wacce akeyiwa lugude haka ta keji gabanta na da ka da karfi. Ci gaba tayi da tafiya bata tsaya ba kuma bata wai wayo ba, meenal ma na iya kokarinta taga ta tsayarda ita, daga karshe ma fizge hannunta tayi ta ci gaba da tafiyarta ita kaɗai. "Leeyana ki tsaya magana zanyi dake". still bata tsaya ba taci gaba da tafiyarta. "Don girman Allah ki tsaya" Chakkk ta tsaya bata kara ko taku daya ba har ya iso daf da ita meenal na ɗan nesa dasu, zafaran da fahad ma suna biye da su da ƴar tazara kaɗan. Tsayuwar sa ya gyara sosai tare da zuba hannayensa gaba ɗaya a cikin aljihu, yaci gaba da kallon ta a yanda ta tsaya ma'ana ta bashi baya kenan baya ganin fuskarta, bayanta kawai yake iya gani. Magana ya fara yi, kuma a yanda yake magana ba wanda baya jin abunda yake faɗa, har meenal da zafaran, da kuma fahad. "Leeyana, nasan zakiyi mamaki sosai idan na gayamiki sirrin zuciyata akanki, wallahi tun ranar da na fara ganinki na kamu da matsananciyar kaunarki, wanda hakan ya haifar min da illa sosai a rayuwa ta, wallahi leeyana da a ce bana shan magani akai-akai da yanzu ba wannan maganar ake ba, ina bada abun sadaka a masallaci, ina kuma rabawa mabukata domin komai ya zomin da sauki, ina pretending sosai akan komai na rayuwata domin ba wanda ya san da haka, ina cikin addu'ar samun mafita ne iyayenmu suka kiramu suka hada aurenmu, a zahirin gaskiya na nuna rashin amincewata amma a badini naji farin ciki da sauyin da bantaba ji ba, wallahi leeyana da zaki sami lokaci ki tambayeni zan iya sanar dake dalilin da yasa na ke nuna miki tsana, kuma har ga Allah bazaki kamani da laifi ba idan kikaji dalilina, ki yarda dani leeya zan iya gayamiki komai idan kin bukata" Cikin muryar kuka leeyana ta waiwayo gareshi tace da karfi "bana sonka turab, ba kuma zan taba sonka ba, meyasa bakada adalci a rayuwarka, Meyasa? Sai da kaga masoyina mai sona da gaskiya mai jin tausayina ya fito, shine kake so ka yaudareni da kalaman banzan ka, bazan taba yarda dakai ba kuma wallahi bazan aure ka ba turab, okene shi nakeso! Soyayyar sa ce kadai a zuciyata a halin yanzu" "To amma meyasa kika yaudari zuciyata kikace kina sona, kin yi min alqawari da dama leeyana, meyasa kika kasa cika ko daya, wallahi banyi tunanin wannan daga gareki ba" Wani irin kakkarfan numfashi ta saki a wahalce har idanunta na rufewa suna budewa, baki da hannunta dake nuna shi duk suna rawa ta furta "da....da...kai...!...nake chattinga.....kuma muke magana ta messages, dama kaine?... innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" leeya ta faɗa tare da durkushewa kasa tana gunjin kuka. Wani abu zafaran yaji ya tokaremasa a makoshi, sai dai baiyi yunkurin aikata komai ba, sai meenal ce taje tana rarrashi, turab kuma bai kara fadar komai ba ya juya ya tafi, kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka zafaran yabi bayan turab shima fahad haka. Haka leeya ta Karachi darenta babu komai a ciki sai kuka da tarin bakin ciki da nadama, bata taɓa sanin ta tsani turab ba sai ayau, ko sunansa bata so taji an ambata, kalmar sunansa ma idan ta tuna wani abu ne yake tokaremata makoshi. Har akayi assalatu idanunta biyu bata runtsa ba sai faman zubarda hawaye take kamar wacce akayi wa babbar mutuwa, meenal ma tayi aikin ban hakuri da rarrashi har ta gaji amma leeya taki. Bubbuga gadon leeya ta farayi da karfi meenal ta mike zaune; "Leeya, lafiya dai kho" "Lokacin sallah yayi" leeya ta fada da muryar da tayi kamada mai mura saboda tsananin azaba da muryar tasha. "Leeya kina nufin har anyi asuba baki daina kukan nan ba, na gayamiki wallahi kuka ba ya maganin komai, dan Allah yanzu ki tashi muyi alwala kiyi sallah, sannan ki samu abinda kika karanta daga cikin Alkur'ani mai girma" "Bazan iya komai ba a yanzu meenal" "Don darajar fiyayyen halitta ki tashi kiyi abunda nace leeyana,. wallahi bana kaunar ganinki cikin damuwa" "Zanyi meenal, kuma Nagode da kokarin da kikeyi akaina" Mikewa su kayi gaba daya, leeya ta fara shiga toilet tayi wanka sannan ta dauro alwala ta fito ta tada sallah, tana kammalawa ta d'akko Kur'ani ta fara karantawa. Sai misalin ƙarfe bakwai na safe ta rufe Kur'anin, hakan kuma yayi daidai da shigowar haji ta tada su suyi sallah. "Haji barka da safiya, antashi lafiya ya tsufa kuma" meenal ta faɗa da sigar wasa. "Lafiya qlau Amiiina, jiya baku shigo da wuri ba har nayi bacci ban san shigowar ku ba" "Eh, wallahi mun dan tsaya waje ne kafin mu shigo nan" "Ah to babu damuwa ba dai kun tashi lafiya ba" "Lafiya qlau faa alhmdullillah" Miƙewa leeya tayi ta ninke sallahyar tana gaida haji da kwana itama. Bayan ta amsa mata tace, "koko nayi da kosai idan zakuci, kunsan ni ba wani son kayan turawa nake irin yanda kuke so ba, idan zakuci muje na saka muku idan kuma bazaku ci ba sai ku kira a kawo muku abin karyawar ku daga can gida" "Zamuci mu sha kuma basai an kira gida ba muje kawai" Fita sukayi gaba ɗaya suka koma parlon haji suka zauna, koko da kosan ta zubo musu suka fara ci, sallama sukaji an turo kofar parlon, fahad ne ya shigo bakinsa dauke da sallama. Gefen haji ya zauna yana gaida ita mu kuma muka gaida shi, "Fahad ya maganar auren?" Haji ta tambaya domin yau ne aka saka date din daura auren, sai dai rikitattun al'amurran da suka ɓullo ne ya saka ake ganin auren kila-wa kala. "Aure yana nan in sha Allah haji, amma inaga sai idan an taahi sallar juma'a ne za'a daura" "To Allah ya kaimu lokacin" "Ameen" Fahad da meenal suka fada daidai lokacin da turab da zafaran suka shigo parlon. Wani mugun faduwa naji gaba na yayi nan take naji na koshi da komai da nake ci, mikewa nayi zan tafi naji haji ta min magana. "Leeyana ina zakije" Jin wannan tambayar yasa na bata amsa ba tare dana shirya ba nace "haji ba nisa zanyi ba, ina so naje na gyara dakin da muka kwana ne" "Da kin barshi ma idan na tashi zan gyara da kaina" "Haji mu kuwa mene amfanin mu idan muka bari kina yin aiki da kanki, Bara naje na gyara kawai" "Ohhh 'yar nan, Allah ya miki albarka ya baki 'ya'ya na gari masu albarka wanda zasu yi miki kema" "Ameeen ya rabbil izzati haji" daga haka na wuce da sauri ban jira cewar kowa ba, sai da na kusa shigewa sai naji muryar haji tana cewa; "Idan kin gama da wuri kizo mahaifinku naso yayi Magana da ku" Ban kawo komai ba domin nasan maganar bazata wuce na gayamusu alaqata da Aleena, wanda rud'u da tashin hankalin da nake ciki sun hanani zumud'in ganin ta. Ban jima ba na kammala aikin da nake,,,,, na fito, ban samesu a parlourn ba, haji ce zaune akan sopa sai kuma meenal a kasa tana yimata tausa, zama nayi mina na kama muka ci gaba da yimata, ba jimawa da zaman da nayi sai ga mutane sun shigo parlon, Papu, dad ƙarami, mum, mummy-neesah, Aleena, ya-Turab Fahad sai kuma zafaran da yayi shigowar karshe. Tsoro ne ya kamani ganin har su ya-Turab a ciki, a raina ina fatar Allah ya sa ace an fasa bawa turab ni sai dai zafaran domin shi ne ya cancanci zama dani. Bayan sun zauna aka gaisa da kowa papu ya kira sunana. Amsa masa nayi ina kara yin kasa da kaina "leeyana kinsan meya tara mu anan" Na amsa masa da faɗin "ah ah" "To kaso chasa'in na taron nan saboda mu gana da ke ne, kuma kema mu baki damar sanin abunda ya shige miki duhu" "Wacece wannan a wurinki" papu ya faɗa yana nuna Aleena. "Kanwatace, mahaifi da mahaifiyar mu daya da ita" "Masha Allah, amma ita labarin da ta bamu yanada banbanci da wanda kika bamu a farko, amma a karshe labarin ku ya zama daya da ita, amma ita har yanzu bata gaya mana asalin sunan iyayenku ba, kawai dai tace mana Abbi da Ammi" "Eh hakane papu, na zabi boyemuku labarina ne kawai dan kar ya tsawaita kuma bana son tuna irin wuya da kuncin rayuwarda na shiga" "Ai koda haka ba laifi tunda baki yi mana karya ba, kuma mun gode da haka wallahi kin cika har halak a shekarun da mukayi dake baki taɓa cutarda mu da komai ba" "Ni ce da godiya papu, Nagode sosai Allah ya baku ladar kyautatawa Maraya" "Ameen ya rabbi" "Amma papu, inaso in san yanda Aleena ta tsira daga mugayen mutanen can, kuma ina so nasan inda mahaifiyar mu ta biyu take" "Nasan da haka leeya amma ga dan uwana GAHEES WAASIB shi zai bada labarin komai yanda akayi Kanwarki Aleena tazo hannunsa........................✍🏼 42. _____________shiru ya ratsa na wani seconds kafin dad ƙarami ya fara magana; "Shekaru shida zuwa bakwai da suka shuɗe wata rana da nida iyalaina baki daya mun dawo ziyara daga Maiduguri zamuje kaduna, anyi ruwa sosai masu karfi har bama iya hango abunda ke gaban mu duba da yanda ruwan ke sauka kasa da mugun karfi. Packing ɗin mota mukayi kafin ruwan su tsagaita, munfi awa uku muna jiran ruwan suyi sauki amma sai abunda ya karu, ganin haka ya saka matata Neesah taimin magana akan mu tafi mu lalla' ba kawai domin muna cikin daji kuma gashi dare ne sosai bamusan abunda zaizo ya samemu a inda muke ba duba da yanda tsaro yayi karanci. Na karbi shawarar da sosai haka muka ci gaba da tafiya gab da zamu shigo garin lere ne a cikin dajin muka kusa cin karo da mutum yana nufomu da gudu har sai da ya shiga gabanmu ya giftamana muka bige shi da mota, babban abunda ya tayar mana da hankali shine bayan mun bige mutumin motar bata tsaya ba har saida muka jingina shi da wani katoton iccen bishiya mutumin ya fadi a rigingine kansa ya daku da iccen, mummunar buguwa yayi domin har mu da muke zaune a mota sai da mukaji karar buguwar. Da gudu na fito motar na nufi mutumin da ke kwance a kasa kamar gawa, ganin haka yasa matata da 'ya'yana gaba ɗaya suka fito. Wani irin tausayi ne ya kamani ganin karamar yarinya kwance cikin jini, karamace sosai domin bazata wuce Sa'ar Fannah da Mayah ba, sai dai ko tafisu jiki da tsawo kaɗan. Ruwa duk ya jikata. Da zallar tausayi Neesah ta dauketa amma bazata iya dagata ita kadai ba Saboda tayi mata nauyi yasa na kama mata muka shigarda Yarinyar mota muka dauki hanyar Kaduna da sauri. fahimtar yarinyar tana cikin mawuyacin hali tsakanin rai da mutuwa yasa nake gudun fitar hankali da motar har bana tunanin abunda zai faru gaba. Direct asibitin kudi muka wuce bayan shigowarmu Kaduna, inda nakeda tabbacin za'a sami kwararrun likitoci a tsakar daren nan domin kuwa karfe biyun dare ta gota. Karɓar ta likitocin sukayi aka wuce da ita emergency, a lokacin tuni 'ya'yana sunyi bacci, a mota muka barsu muka shiga asibitin. In takaice muke zance daren da abun ya faru tsakanin Ni da Neesah ba wanda ya rumtsa har asuba kuma duk yarana suna mota a can sukayi bacci gaba dayansu, har kuma wannan lokacin yarinyar da muka bige bata farfaɗo ba. Sai kusan karfe hudu na yammacin rana ta biyu da abun ya faru sannan yarinyar ta farka, a lokacin ma Ni bana nan amma na bar Neesah tana kula da ita. Tashin hankali da tausayi ya shigeni sosai lokacin da labarin abunda ya faru da yarinyar ya sameni, Likita ya gaya mana buguwa da yarinyar tayi da wani abu mai karfi ya haddasa mata matsala a kwakwalwar ta har tayi loosing memory dinta komai ya goge a kwakwalwar ta babu abunda zata iya tunawa, haka kuma an gaya mana cewa buguwar ta taba wata jijiya ta idanunta sosai har bata iya ganin komai a halin yanzu. Nayi bakin ciki sosai da jin haka domin kuwa yarinyar ko sunanta bata iya tunawa bata cewa ummmm bale umm-umm, mu kwashi tsawon sati uku a haka kuma ana yimata magani sosai kafin aka sallamemu tare da bamu shawarar sosai game da lafiyar ta, ta samu saukin idanunta a hankali domin tana iya gani kadan kadan da rana amma idan dare yayi bata ganin komai. Likitan da muke karɓar magani wurinsa ya kwatanta mana wani likitan daban saidai shi bangaren idanu ne kawai, haka mukaje muka sami likitan aka yimata wankin idanu aka yanka mata glasses, a lokacin ne ta fara ganin komai tarrrr idan ta saka glasses din, amma daga zarar ta cire shikenan bazata kara ganin komai ba har sai ta mayar da shi a fuskar ta. Wannan shine dalilin da kuka ga tana sanya glasses ko yaushe kuma yana fuskarta a kullum" Dad ƙarami ya faɗa yana mayarda kallonsa inda Rukhshanah ke zaune, haka ma sauran mutane suka kalleta cikin tausayawa Leeya kam har da kukanta. Dad ƙarami yaci gaba da faɗin; "haka muka kwashi tsawon shekara daya da watanni tare da ita, a nan ne muka sauya mata suna zuwa Rukhshanah domin babu wanda yasan abunda zai kira sunanta dashi tunda ba wanda ya santa a cikinmu kuma itama kanta bata san wacece ita ba. A bangaren ciwonta daya kuma muna iya kokarin mu aƙalla mun kaita asibitoci sunfi a kirga amma maganar daya ce. Mun dauki Rukhshanah kamar yar da muka haifa da cikinmu domin bama taba nuna wani bambanci a tsakaninta da 'ya'yamu ba, su harma suna gani munfi sonta amma duba da larurar da take ciki yasa basa wani damuwa har dai sukazo suka girma suma suka daina damuwa da wannan. A kwana a tashi girma yana zuwa shekaru suna shuɗewa har mukaje da ita India akayi mata magani aka kuma bamu wannan allura da akayi mata yanzu, a nan ne kuma Allah ya kawo mata karshen wahalar ta kunga yanzu ta warke ta sami lafiya har muka gana da ita, ta shaidar mana da asalin sunanta da kuma labarin ta gaba daya" dad ƙarami ya karashe maganar sa da faɗin haka. Cikin Muryar kuka Aleena ta taso tazo gabansa baki na rawa ta fara yimasa godiya, haƙiƙa sun yi mata namijin kokari, kuma samun mutum kamar dad ƙarami a halin yanzu ba karamin aiki bane. Tayi masa godiya kwarai da gaske haka ma Mom Neesah har suka rungume juna da ita, sannan ta mike taje ga yayarta itama suka rungume juna tare da sakin kuka mai ban tausayi. "Aleena ya akayi kika tsira daga yan bindigan da suka tafi daku" Leeyana ta tambayeta. "Kamar yanda dad ya fada muna a bangaren mu ruwa akeyi sosai. Amma hakan bai saka sun dakata gudu da motar ba. Ina cikin tashin hankali sosai matuka ganin yanda Nnene ke wani abu tana gu kamar mai aljanu har tana yagar kayan jikinta, sai kuka nake ina kokarin dakatar da ita daga abunda take. muna cikin hakane naji motar mu ta daku da wani abu mai karfi kamar dutse, take motar ta birkice da kowa dayake cikinta. Nnene tayi kukan kura ta fito daga motar tana kokarin guduwa, da sauri na riko hannunta ta janyoni nima na fito, amma ina fita daga motar ta fizge hannayenta daga gareni ta shiga daji da gudu tana ihu, ganin haka ya tsoratani sosai har nayi kokarin na bita, amma ganin tamin nisa sosai ya sakani hawa titi da gudu ina kuka da kiran sunan mutane koda akwai wani akusa yazo ya ceceni, wani haske naga ya fara tunkaroni gadan-gadan nima na tunkareshi ina d'aga hannayena domin ruwan da ake basu bani damar ganin abunda ya shigo gabana ba, ji na nayi na bugu da wani abu mai mugun tauri da karfi. Daga haka ban qara tunawa da komai ba sai daren jiya" Sai a lokacin Zafaran yayi magana yace "Allah sarki kenan Nnene hauka tayi?" "Ba mamaki domin a gabanta aka kashe mijinta" cewar Leeya batare da kalleshi. "Ya zama dole na nemo ta idan tana raye, domin tayi min hallaci kuma ta rike amana, a wannan lokacin ne ya kamata na nuna mata godiya ta da abunda tayi min" "Nima inada fatar haka okene, domin kuwa Nnene ta rikemu kamar ya'yan ta bata taba nuna mana kyama ko bambanci ba saboda mu ba Christian bane" "Ba Okene bane sunana Lewa, yanzu ni ba Christian bane na musulunta sunana Muhammad Zafaran" "Lewa!" Ta maimata sunan a bakinta. Tunawa tayi da lokutan baya idan zai rakasu unguwa ko kuma islamiyya ko idan taje gidan su zata dawo, sau dayawa yana kiranta da wannan sunan. Mafi yawanci ma yafi kiranta da haka ko kuma ya kirata Ifunanya, idan kuma ta tambaye shi sai yace mata zata san meye fassarar haka idan ta girma, bata iya ganewa ba sai da ta koma Makoko gidan kawunsa da ta fara jin yaren igbo sannan ta fahimci"lewa" yana nufin masoyi ko wacce aka bawa wani matsayi na daban, "Ifunanya" kuma yana nufin matar da ake da burin aure. Tun daga wannan lokacin ne taji a duniya ba wanda take so da kauna kamar Okene, amma kaddara ta riga fata domin kuwa shekaru shida kenan rabon da ta sakashi a idanun ta, sai dai yana nan a zuciyarta koda bata ganinsa. Turab ma wani abu yaji ya tokaremasa makoshi, a hankali ya fara kiran sunayen Allah domin bayaso yaji sauyi game da zamansa da abokinsa saboda mace, yayi imani da zai iya kyaleta wallahi da ya barta da Zafaran ko zai samu peace of mind, sanin yanda yake fama da soyayyarta a zuciyarsa tsawon lokaci. Dan gyaran murya papu yayi sai kuma hankalin Leeya da sauran mutane suka dawo kansa, tun kafin papu yayi magana Leeya tayi saurin yiwa Zafaran tambaya. "Ya akayi ka musulunta Alhali nasan ku katafawa ne bakwason addinin Musulunci ko kaɗan, kuma ko a Cristian ku na daban ne?" "Lewa wallahi kin bani mamaki da kike maganar ki kuma kike sakawa hardani, wallahi sanin kanki ne banada wani buri da ya wuce na musulunta, da inada akidar katafawa da bazan taba zama musulmi ba. Ke kanki zaki karyata idan aka ce miki banason musulunci da musulmi amma ba komai tunda kince haka na d'auka" "Kayi hakuri" ta furta a sanyaye, "nasan iyayenka ba sa so ne shiyasa, amma inada tarin tambayoyi akan haka" "Tambayar ki itace ya akayi na tsinci kaina a musulunci kho?, to zan gayamiki yanzu kuwa. Bayan barina garin Ikeja sai mukazo Abuja, mun kwashi tsawon watanni tara muna Abuja kafin akayi mana biza muka wuce kasar Mexico, a can ma na dauki lokaci kafin na fara karatu sakamakon halin jinya da mahaifiyata ta tsinci kanta a ciki, in takaice miki banshiga makaranta karin karatu ba har sai da komai yazo karshe ma'ana mahaifiyata ta mutu, daga nan kuma mahaifina ya dauki hutu a wajen aikinsa muka dawo Nigeria kasarmu wato Delta akayi bikin binne ta aka gama muka koma Mexico kuma. Guntun lokaci da faruwar wannan mahaifina ya dauki soyayyar duniya ya ɗora min har baya iya yimin musu da abunda nakeso saboda tsanin so da kuma tausayina da yake, anan ya bani damar za'bar makarantar da nakeso nayi karatu, nikuma na shiga binciken makarantar da Musulmai suka fi yawa a 'kasar , bayan dogon binciken da nayi kuma na samu sai na sanar dashi makarantar da nakeso. Ya gane makarantar mafi akasarin ɗaliban da ke ciki Musulmai ne amma bai nuna min damuwarsa akan haka ba, bayan nayi register da komai na fara zuwa, ranar zan fara shiga school din na hadu da Turab kuma muka k'ulla abota mai ƙarfi da shi, bayan wasu lokaci kuma na nuna masa ra'ayina akan addininsu, wannan kuma bai wani bani matsala tsakanina da mahaifina saboda abunda nakeso shi akeyi, ya yarda na shiga addinin Musulunci bisa son raina amma kar nayi tunanin shi zai fita addininsa ya shiga wanda na shiga, naji bakin ciki sosai da furicinsa kuma na nuna rashin jin dadi na akan rashin shiga da yayi addinin musulunci. Shikenan na shiga Musulunci kuma amana da yarda sosai ta kara shiga tsakanin mu da turab har nake jinsa kamar dan uwa na jini, shima yake jina haka. Mahaifina ma yana matuƙar kaunar turab, shima iyayensa na matukar kauna ta, ta dalilin hakane muka sada mahaifanmu domin su san juna, kuma ba dan albarka cin turab ba ko kusa mahaifina bazai yarda na zo Nigeria ba. Wallahi lewah saboda ke na dawo kasarnan, Saboda nasan abunda ya faru da ke tun kafin mu tafi Allah ne bai kaddara zan fara bincike ba tare da naje Mexico ba, Wallahi kaso chasa'in na dawowa ta Nigeria saboda kene lewah kisani ina sonki, ina kaunarki, soyayyar ki ta zamo jini da numfashina, ba wanda zai fita batare da nabar duniya ba, tun Ranar da nadawo shekaru biyu kenan, wallahi ba rana ta Allah da zata fito ta fadi ba tare da nayi bincike akan maharan da suka kawo muku hari ba, Dan Allah ki saka wannan a ranki leeyana wallahi billahi bantaba son wani abu a duniya daya wuceki ba, idan har kika cire iyayena, leeyana bana ganin yuwar mallakarki, amma wallahi nasan da soyayyarki zan mutu a cikin raina, ina ji a jikina bazan sameki ba leeyana, narasa yanda zan misilta sonki a zuciyata, inda ace zaiyu zaki ga gaskiyar sonki a jinina ina kaunarki na fad'a na nanata." Zafaran ya faɗa hawaye na gangarowa a kumatunsa. Ba leeya ba hatta turab da kuma su Papu sai da sukaji tausayinsa sosai. Mikewa turab yayi a sanyaye yaje har gaban Zafaran ya tadashi tsaye, muryar sa na rawa ya kalleshi yace; "Abokina hakika na cika babban azzalumi idan na rabaka da leeya wallahi nasan hakkinku bazai barni ba, amma inaso kasani kamar yanda kake jin sonta haka nima nakeji wata kila ma nawan zai zarce naka, nayi alkawari koda soyayyar ta zata zamo ajalina bazan rabaku ba, dan Allah ka yafemin abisa kuskuren rashin sani da kuma kamuwa da soyayyarta danayi" Yana gama fadin haka ya juya ga leeyana itama har gabanta ya d'ingisa domin ji yake kamar zai fadi saboda nauyin da jikinsa yayi masa. "Leeya na rokeki da kiyi haƙuri ki yafemin iya abubuwan da namiki a rayuwarki da wanda kika sani harma da wanda baki sani ba, wallahi ki sani duk abunda nake soyayyarki ce ta janyo ba wani abu ba. amma nan gaba zaki gane nufina akan duk wani abu da nayi miki" Yana gama fadin haka ya juya zai fita sai dafe kansa yake saboda tsakanin ciwo da yake masa. Da mugun sauri dad ƙarami da zafaran suka isa gareshi tare da rike shi suka zaunar dashi ganin kamar zai fadi. Duk irin alkunya da kawaicin da mum fanaya take hankalin ta yayi mugun tashi ganin yanda kamannin sa suka sauya, ga kuma alamomin tashin ciwonsa sun fara bayyana. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, justice muje asibiti don Allah kar ya rasa ransa" Da sauri mummy-neesah da haji suka kamata itama suka zaunarda ita, "kwantar da hankalinki hajiya fanaya, a yanzu hankalinsa bai gushe ba kuma ciwon nasa bai tashi ba koh, muna da damar da zamuyi masa magana yanzu kuma abashi abunda yake bukata, hakan ne kawai zai dakatar da damuwa da tashin hankalin da ke tunkaroshi" Tun kafin wani yayi magana a cikinsu da sauri zafaran ya riko hannun leeyana ya haɗa dana turab ya durkusa a gabanta idanunsa na zubarda kwallah yace; "Leeyana don Allah kar muyi sanadin rai!, wallahi turab ma yana sonki, da alama yafini sonki Allah ne kawai ya sani, I'm so sorry to say leeyana kije ki zauna da turab na barmasa ke" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me kake fada haka zafaran kana nufin ka sadaukarda da soyayya ta ga waninka, kenan kamin adalci kake gani, meyasa ka fiye son kai? Ka sadaukarwa abokin ka da soyayya ta ne saboda kanason farin cikin sa nikuma ina nawa farin cikin?" Tun kafin ta karasa fadar abunda zata fada Papu ya katse maganar ta cikin bacin rai yace; "Ka gani ko turab, kaga abunda ka janyo wa kanka kho? Tun a farko da muka baka wannan yarinyar a matsayin matar da zaka aura da ace ka nuna mata so saɓanin tsana da bazata nuna rashin so a gareka kiri-kiri ba, wallahi Ni kaina nasha ganin kana azabtar da wannan yarinyar amma nayi shiru saboda gudun abunda zaije ya dawo, idan baka sonta an baka zabi a cikin yan uwanka na gidan nan kuma kannen ka, amma ka qie haka kake so ayita zuba maka idanu, wallahil Azeem yau ba gobe ba zan daura maka aure da duk wanda naga dama" "Zafaran!" "Na'am Papu" "Kaima ka shirya yau zan daura maka aure" "Ba damuwa Papu Allah yasa hakan yafi zama alƙairi, amma Papu don Allah...." "Karka sake kace komai Zafaran na gama yanke hukunci kuma yanzu zan kira mahaifinka na gaya masa" "Leeyana my daughter, kiyi hakuri kinji, don't confuse yourself, kuma kiyi haƙuri a yau ba sai gobe ba kema zan daura miki Aure" Leeyana bata iya cewa komai ba, ta daga kai kawai alamar taji kuma tayi biyayya, hawaye na kwararowa a idanunta. "Na sallami kowa" papu ya faɗa yana shirin barin part din rai a matukar 'bace. Daga gefensa yaji muryar dad ƙarami yana cewa; "Idan har na isa dake, kuma kina kallona Matsayin mahaifinki da kike yiwa biyayya da d'a'ah yau zan daura miki aure Rukhshanah, kuma yanzun nan zan biya sadaki" Da sauri Rukhshanah dake rike da kafadar leeya ta dago kanta ta kalleshi tace"kafi da nan dad, wallahi bana fata Allah ya kawomin ranar da zaka yi hukunci akaina na nuna baiyi min ba koda a fuska ne balle a zuciyata, nasan bazakaymin zaben tumun dare ba, kuma nasan bazaka zabamin mijin da bai dace dani ba, koda kayi hakan wallahi dad nayi maka alkawarin zama dashi har mai rabawa ta raba, kuma nayi maka alkawarin baza'a sami matsala a ta bangarena ba in sha Allah" "Kin cika 'yar halak Rukhshanah, Allah ya saka miki da alƙairi, ya biyaki ladar biyayya" Daga haka suka fice gaba daya har turab dinda hankalinsa ya fita daga jikinsa, domin bai san ma wane matsayi zai daura kansa ba tsakanin mai hankali da marar hankali. "Leeya kije kiyi wanka ki fito ki sameni a parlour" cewar mum. "Nayi wanka da asuba mum, da dai wani abu zanyi miki sai muje" "Ina meenal?" Mum ta kuma tambaya. "Meenal ta fita waje tun lokacin da ciwon ya-Turab ya soma tashi" "Okay zo muje" Fita sukayi sashen gaba dayansu, sai bayan fitowar su ne suka lura ba kowa a cikin yan gidan. Zama sukayi a parlourn ƙasa har mum ta buɗi baki tayi magana sai ga khulud ta shigo da waya kare a kunne ta. Sai da ta kammala wayar ne ta gaishe da mum domin basu gaisa ba tun da safe. "Mum ba'ki mukayi, kuma suna so su gana da ke da kuma papu. Amma naga fitar sa da su dad ƙarami nasan ba nisa zasuyi ba" "Eh ba nisa zasuyi ba, sunje sanarda daurin aure ne babban masallacin juma'a" "Wallahi mum abubuwan da suka faru sun saka duk na sha'afa da batun daurin auren nan na ya-fahad" "Ai ba fahad kadai za'a daurawa aure ba a gidan nan" "Ban...gane ba" khUlud ta faɗa tana 'yar i'kina "Eh, har turab da kuma zafaran sannan da leeya da shi fahad din da kuma kanwar leeya Aleena" "Wallahi mum bangane nufin kiba taya haka zata faru, wa ye zai auri Aleena kuma" "Fahad ne kadai yakeda tabbacin wacce zai aura, amma duk sauran ba wanda yasan wanda zai aura" "Gaskiya akwai gyara a cikin lamarin nan mum, duk meya janyo wannan?" Mum na shirin yin magana a karo na biyu wayar khulud tayi kara alamar kira. Da sauri ta dago wayar tana dubawa "mum ba'kin suna waje pah" "Su waye wai??" "Zaki gansu idan sun shigo mum, Bara na je na shigo da su yanzu" Mum bata furta komai ba haka ma leeya da kuma mummy-neesah domin su kadaina a parlourn Yanzu. Fitar khUlud ba jimawa ta dawo tare da baki biyu mace da namiji, macen ta ɗan manyanta shi kuma namijin saurayi ne matashi fuskar sa Fal da annuri. Da sallama suka shigo parlon gaba ɗaya har khUlud din dake biye dasu, saurayin na bayanta sannan sai matar ta shigo da karshe. Fuskar mum cike da mabayyanin mamaki take bin matar da kallo kafin ta iya karfin halin hade kalmomin da ta samu damar yimata Magana dasu. "Dayammah!, kece ko mafarki nake?" "Ni ce hajiya barka da yau, ya gidan, ya dawainiya" "Alhmdullillah dayammah, yaushe gari dan nasan bakya nan tsawon wannan shekaru duk baki waiwayo muba" "Ina nan ba inda naje hajiya, kawai na dan ja baya daku ne na wani lokaci yanzu kuma gashi na kara dawowa rayuwarku" Cikin rashin fahimtar inda zance dayammah ya dosa mum tayi mata tayin wurin zama ta kuwa zauna. Gaisheda mum da kuma sauran mutanen da ke parloun id yayi, khulud kuma hakan yayi mata dadi sosai ganin bai yi girman kai ba, zama sukayi anata firar yaushe gamo tsakanin dayammah da mum, har mum ke tambayar dayammah a inda ta kuma haduwa da khulud a karo na biyu. Labarin duk abunda ya faru tsakanin su da khulud ta gayawa mum, inda suke firarsu su biyu kadai, sannan ba kowa yakejin abunda suke fadi ba. Girgiza kai kawai mum tayi tana kallon khUlud tana dan murmushi, "yaran zamani sai a hankali, kalleta kamar bazata iya haka ba" "Mena yi kuma mum" khUlud ta faɗa a dan shagwaɓe. "Ungo nan" mum ta fada tana ware mata hannu. Kara zum'buro baki tayi, cikin rashin Sa'a idanun su suka sarke dana idrak, hararar wasa ya sakarmata da sauri ta washe baki tare da kashe masa ido ɗaya. Mum da ta lura da su murmushi mai sauti kawai ta sake ba tare da ta kalli inda suke ba. Fannah da Rukhsha ne suka shigo parlon bakinsu dauke da sallama, wucewa rukhsha tayi inda leeya ke zaune tayi mata Rad'a a kunne. "Yahyah wallahi yau ina cikin madaukakin farin ciki" "Farin ciki kuma budurwa tho farin cikin me? Ko don saboda za'a daura miki aure" "Ohh, wallahi fa kinga Ni har mantawa nake da batun auren nan ina ganin komai kamar wasa" "Hmmmm, wallahi nafi ganin sa kamar wasa budurwa, to amma gamu nan mun zubawa sarautar Allah idanu" "Tau Allah ya yi mana jagora yayata, Bara na gaida bakuwar mum" "Dan tsaya!" Leeya ta faɗa lokacin rukhsha ta tashi zataje ta gaishe da su mum. Dakatawa tayi daga tafiyar da take, dayake kuma ba wata tazara a tsakanin su tace "ya akayi" "Baki bani amsar tambayar da na miki ba" "Wace tambaya kuma?" "Farin cikin da kikeji a yau, menene dalilin haka?" "Yayatah, kin manta yau aka shaidar mana da za'a daura miki aure kho" "Ban manta ba Aleena, amma ko ya ne inason ganin ki cikin farin ciki" "To zaki ganni cikinsa a yau kinji" " menene silla" cewar leeya. "Yahyah-leeyana, alqawarin ku da mum ya cika yayata, yau ne ranar da zata fito miki da darajar ki, ta kuma bayyanar dake a idanun mutanen da ke kallonki ba komai ba" "Bangane nufin ki ba qanwata" "Ina nufin yau, a yau din nan zaki buɗe fuskar ki, ki kuma bayyanar da asalin halittarki ga ko waye da aka aura miki" Da dan karfi Rukhshanah ke maganar saboda haka ne yasa sauran mutanen suka mayarda hankalin su kansu. "Baki gane nufina ba, so kike inyaye hijabin da nayiwa maganar lullubi dashi, yahyah-leeyana ina nufin a yau ce rana mafi daraja a gareni, domin a yau ne zaki yaye mayafin da ke fuskarki ki bayyanar da fuskar ki ga kowa dayake kokwanto a kanki" Gaban leeya ya yanke ya fadi, haƙiƙa Aleena ta fadi gskiya. Sai dai taya gaskiyar ta zatayi amfani alhali ita kanta tafi jin dadin haka, duk da tana kwadayin ganin fuskar ta amma hakan bai sakata jin cewa zata iya cire mayafin da take amfani da shi shekara da shekaru ba. "Kin manta ko, na tuna miki idan mantawa kika yi. Saboda haka ki shirya tarbar sabuwar rayuwa" cewar Rukhsha ta wuce kawai ba tare da ta saurari abunda zai fito Daga bakin leeya ba. Tunda ta doso inda su mum ke zaune Annah dayammah ta kafeta da idanu kamar zasu fado kasa saboda tsanin mamaki, ba mum dake kusa da ita ba hatta ita kanta rukhsha da kuma meenal, da fannah, da mummy-neesah dake shigowa yanzu sun lura da irin kallon da dayammah ke yiwa Rukhshanah. Idrak ma da ya lura a yanzu da sauri ya karaso gaban mahaifiyar tashi ya duka saitin kunnuwanta yace "Annah menene haka dan Allah ki nutsu mana, duk mutanen da ke parlourn nan idanunsu akanmu yake, munzo yin abu mai muhimmanci a gidan nan, dan Allah ki daina kallo irin haka wallahi wani bangaren irin wannan kallo haram ne" Saurarensa kawai take, ko motsi batayi idanun ta kawai ke dan yawo a hankali kan rukhsha na, dan ta'bata yayi kad'an, da sauri ta zabura kamar wacce ta farka da nannauyan bacci. "Annah Lafiya?" Id ya tambaya a tsorace saboda yaga kamar mood dinta ya changer. Da mamaki itama mum ke binta da kallo kafin ta furta "lafiya dai?" "Hajiya dan Allah wannan yarinyar su waye iyayen ta?" "Ban gane me kike nufi ba" cewar mum. "Eh ina nufin su waye suka haifeta?" Jin wannan tambaya da annah tayi ya saka leeyana kureta da idanu sosai ita kuma Rukhsha ta dan ja baya tana kara shigewa jikin mum, harga Allah ta fara tsoron wannan matar, ita bata ma yarda da ita ba kwata kwata. "Ga mahaifiyar ta can kina gani, mahaifinta kuma on ready nasan kin sanshi tunda a gidan nan kike can baya, gahees ne mahaifin da kanin justice" "Allah sarki, ai kuwa basuda yanayi da wannan matar gaskiya, sai dai ko dadyn twins din ta biyo" "Eh shi ta biyo, dashi take kama ai" mum ta fada a fili, a zuciyarta kuma tunani take, batasan iyayen waɗan nan yaran ba me zata dinga cewa a game da haka, "ina ga lokaci yayi da ya kamata nasan wani abu" "Me zai hana ki tambayi dayammah dalilin yin tambayar da tayi" Wani sashe na zuciyarta ta faɗi haka. Kallonta ta mai da ga dayammah da har yanzu bata daina kallon Rukhshanah ba kamar zata cinyeta tace "to amma dayammah meyasa kika min wannan tambayer" "Wallahil Azeem hajiya ban taba ganin asalin kama ba kamar yanda nagani ga wannan yarinyar" "Kama kuma, to da wa" "Da wani bawan Allah dan uwan mijina, mahaifin wannan yaro idrak" "Ikon Allah, to ai kama ce kawai, menene sunan wanda take kama dashi din, zai iya yiwa sun haɗa jini shi" "Sunansa HAMRAZ, 'yan biyu ne shida mijina MAHARAZ" Wani mugun wuntsilowa Aleena tayi da sauri ta dira gaban dayammah bata san lokacin da ta riko hannun ta ba, kusan lokaci daya suka iso gaban ta tare da leeyana........................✍🏼 EP.43 _____________________"Rukhshanah kunsan wanda take magana?" Mum ta faɗa da mamakin ganin yanda suka iso wurin. Murya na cracking ta daga baki da kyar ta furta "mun sanshi mum" Sai a lokacin mum ta tuna da sunan HAMRAZ idan ba mantawa zatayi ba ai kamar da sunan leeyana ke amfani har a makaranta, kenan mahaifinsu ne kanin mijin dayammah. "Dayammah kinsan wani abu game da shi?" Ita kuma dayammah ta kure yaran da idanu kawai ƙwallah na zubowa a cikin kurmin idanunta. "Hakika an ci amanarku, an zalunci ku, da mahaifin ku gaba ɗaya, wallahil Azeem hakkin ku dana sauran mutane ba zai taba barin fairozha ba" "Fairozha!, dan Allah wacece fairozha?" Sukaji muryar haji ta fada tana karasowa wurin da sauri. Murmushin fuska kawai dayammah tayi domin tasan wannan rana zatazo a cikin zanen rayuwarta. "Nasan zaki so sanin wacece fairozha hajiya mainah, amma kisani sanin fairozha a bakina babban bala'i ne a wurina, amma nayi alqawarin duk ranarda Allah ya bayyana min wani daga dangin ta, zan sanar masa da komai in ya so nima ta tsafaceni kamar yanda take tsafi da sauran mutane" Matsowa sosai haji mainah tayi, har wata zufar tashin hankali ke keto mata. Idan bazata manta ba, ranar da waasibudden mijinta wato kakansu khulud namiji kenan, ranar da zai mutu da sunan wannan baiwar Allah ya mutu a bakinsa wacce basusan ko wacece ba. Ba iya sunan ta yake fad'i ba, ya fad'i abubuwa da dama dayasani a game da ita Kamar kuma yana ganinta kusa dashi, haka ya koma kamar wani mai rauhanai, abun sai ya baka tausayi, sai ji kake yana fadin; "Fairozha kiji tsoron Allah, dan Allah ki tuba ki koma ga Allah. Wallahi Allah ba azzalumin kowa bane kuma yana ganin duk irin zunuban da kike tafkawa saboda son duniya kawai, kin sadaukarka da rayuka da dama saboda rayuwarki kadai, Allah Allah ba zai barki ba" wani wahalallen numfashi ya ajiye zufa sai karyo masa take yana hakiiii kamar wanda yayi mugun gudu. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, wallahi fairozha hakkina bazai barki kici gaba da rayuwa a doron kasa ba, jinina fa kike zukewa, kuma kina katsar min 'ya'yan hanci" "Fairozhaaaaaa!!!!!" Ya furta da karfi daga haka bai kara motsi ba, idanunsa suka kafe, ya sandare wuri komai nasa ya daina motsi. Koda hajiya mainah tazo nan a tunanin ta sai ta dago kai idanunta duk sun cika da hawaye ta kalli dayammah tace "dan Allah menene tsakanin ta da marigayi waasibudden" Daga inda Aleena ke zaune itama sukaji tace "muna muna son sanin wani abu daga ahalin mahaifin mu ko ya yake dan Allah" Kallonsu tayi gaba ɗaya ba tare da ta furta komai, ganin haka ya saka ba wanda ya kuma cewa komai tsakanin su, duk suka tattara hankalin su wajenta suna sauraron abunda zatace. Cikin juriya da yarda dakai ta furta a zuciyarta "fairozha yau zan bude asirin da na dade ina boyewa domin tsira da Rayuwa ta, amma a yau gashi zan bayyanarda shi ga wadansu domin suma su tseratarda rayukansu, nasan babu wani abu dazai sameni fa ce yana rubuce cikin kaddarata. Idan kika ga kin cutardani to da yardar Allah, bakida wani karfi ko iko batare da Allah ya baki ba" Tana gama fadin haka a zuciyarta, sai taji kanta kamar a mafarki ta daina ji da ganin komai, ganin kanta take zaune a parlourn, amma kuma mutanen da ke cikin parlourn kafin ta kwatanta bada labari, ba su bane yanzu da ta gama tunanin ta. Ji take kamar an daureta bata iya motsa ko dan yatsan ta, babban abunda ya bata mamaki ganin waɗannan mutane. Bata san su ba, kuma bata tunanin ta taɓa saninsu duba da yanda yanayin suturar jikinsu take. Wata doguwar bakar riga ce wacce takai har kasa sosai tana sharar kasa, baka iya hango komai na jikinsu face fuska, kuma ko fuskar mutanen a wannan lokacin tana kasa ba wanda ya daga kansa ya kalleta a cikinsu balle ta gane su waye. Rigar tanada dogon hannu mai fadi wanda ya rufe har yatsun hannayensu, kuma a gaba da bayan rugar anyi wani tambarin kan bakar mage da jini. Hakika mutanen nan sunada ban tsoro sosai duba da yanayin da suke ciki, duk suna durkushe ne sun sunkuyar da kansu gaban wata matar daban. Sun dauki tsawon mintuna biyar a haka. Matar ta fara daga kanta, daga nan kuma suka fara dagowa suma daya bayan daya. nidai ina zaune ina kallon ikon Allah, domin kuwa bana iya ta'buka komai ina jina zaune ne kawai ba tare da na san abunda ke faruwa ba. Gabana ne yayi mugun faduwa ganin fuskar da na taba sani shekaru talatin da biyar baya, duk da ba ganin ta nake ba amma hakan bai hana na gane ta ba domin tana zuwar min a duk lokacin da mummunan mafarki zai riskeni a cikin baccina. Ina so na furta sunan ko iya fatar bakina ne amma na kasa, ji nake kamar an dauremin harshe. Mikewa tayi ta fara tafiya har sai da takai gaban matar da nake gani a kujera ita kadai, kuma nake kyautata zaton itace babba a cikinsu. Naji tsoro sosai lokacin da naji matar da ke zaune ta budi baki tayi magana, cikin tsawa da daga murya tace da karfi. "Fairozha!, ya zama dole ki ja kunnenta sosai ki gargadeta akan abunda take nufin yi, domin idan kika kuskura kika barta ta idar da nufinta rayuwarki da ta sauran ƴan kungiya na cikin haɗari, ya zama dole ta manta da maganar bada labarinki, labarin maharaz da hamraz da kuma waasibudden, da sauran mutanen da jininsu ya gushe akan dodon tsafi Black cat, idan kuwa kikayi sake ta bayyana babu abunda ya shafeni bayan hukuncin da zaki dauka daga wurin black cat, kuma zan miki nawa sannan yan kungiya suyi miki nasu tunda kika yi sake asirinsu ya fita. gata na kawo miki ita kija kunnenta naga tana shirin warga za mana shiri" Cikin ladabi da biyayya irin tasu ta matsafa ta kara sunkui da kanta kasa tace "kiyi hakuri the Queen, ki yarda DAYAMMAH tanada kafiya sosai, na rasa me zan yi domin naci galaba akanta, kinsani mai girma black cat ya hana mu tsaface jininta da tuni ba wannan maganar ake ba amma zamu gargadeta a karo na karshe" "Ya rage naki, nidai kinji abunda na fada miki". "Naji the Queen, kuma nabi nayi biyayya" Banajin komai da suke fadi, bawai dan suna nesa dani ba. Kuma Nima ban san dalilin da yasa banajin komai daga maganar da suke ba, gani nake bakunan su na motsi kawai amma bana jin ko d'iif. Kamar yanda sautin aradu ke shiga a kunnuwan mutane haka naji murya mai kara da amsa amo tana min magana a lokacin da na daina ganin komai a dakin saboda tsananin duhu ko tafin hannuna bana iya gani. "Dayammah ya zama dole ki janya kudurinki nason to na mana asiri, idan har kinaso kici gaba da rayuwa to dole ki manta da fairozha, dole ki manta dani dayammah, Ni fairozha naci dubu sai ceto, ja dani ba karamin aiki ba ne a wajenku, na gargadeki sau ba adadi amma kin kasa fita rayuwata, wallahi da badan Black cat bai bani damar shan jininki ba da tuni ba wannan maganar akeba. Amma duk da haka bazan barki ki ki tafi a banza ba" Muryar ta faɗa tare da daukewa d'iif. Muni mugun zugi taji a cikin tafin hannayenta da kafarta har sai da ta kurma uban ihu. "Dayammah lafiya?" Taji Muryar hajiya fanaya na tambayar ta. Da karfi ta buɗe idanunta ta kallesu duk tayi sharkafff da gumi. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, meke faruwa dani yanzu fa naga fai........" Bata karasa faɗar abunda zata faɗa ba ta manta da komai. "Ke kawai muke sauraro dayammah" "Wallahi hajiya banada nutsuwar da zan iya bada labarin komai yanzu, amma idan za'a sami Kur'ani a kusa inada bukatarsa don Allah ko zan sami nutsuwar zuciya" "Leeyana je dauko mata Kur'ani" hajiya fanaya ta fada tana kallon leeya. Ita kuma dayammah ta mike da nufin tayi alwala, da mugun sauri ta zauna tana kallon kafafunta da tafukan hannunta. Sosai hankalin ta ya tashi ganin yanda aka raunana ta, sake yunkurin mikewa tayi amma ta kasa gaba ɗaya, ganin haka ya saka suka tambaye ta ko lafiya. "Lafiya ƙalau" ta fada da karfin hali. Miƙewa id yayi ya tako gabanta shima tare da rike kafafuwanta yana duddubawa, "Annah meke faruwa?" "Ciwo naji idrak, kagani kamar yankan wuka kho?" "Ban ga komai ba Annah, me kikeji a wurin" ya faɗa yana shafa tafin kafafuwan nata. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, idrak ka daina tabawa baka gani yanda kake taba ciwo" ta fada kamar zatayi kuka saboda tsananin azabar da takeji. Hakan kuma yayi daidai da ƙarasor leeya wurin da Kur'ani a hannunta. Karbar Kur'anin dayammah tayi daga hannun leeyana, duk da bata da tabbacin cewa zata iya rika Kur'anin da hannunta yanda takeji. Cikin ikon Allah kuwa tana rika Kur'anin da hannunta taji ta daina jin komai daga azabar da hannun ke yimata. Sake gyara zaman ta tayi ta bude Kur'anin da ke hannunta ta fara karantawa dallah dallah, duk shiru sukayi ba wanda ya kuma cewa komai har sai da ta kammala karanta surar da ta bude. Anan taji komai ya dawo mata yanda takeso, amma tambayar ta anan shine ya akayi taga wasu abubuwa kamada mafarki, ko kuma almara. Cikin mintuna kalilan komai nata ya changer kamar ba ita ba, to me hakan yake nufi, shin fairozha ta gani ko kuma mafarki take, idan fairozha ce ya akayi su mum basu ganta ba? Idan da gaske komai ya faru meyasa idrak baiga yankan wuka da fairozha ta yimata ba, idan kuma mafarki ne yaushe tayi baccin??? "Ya Allah ka fitardani cikin wannan sarkakiya" Ta fada a zuciyarta. Tun kafin wani ya sakeyin magana dayammah ta ci gaba da faɗin. "Tun ranar da na baro asalin mahaifata nakeda buri da addu'ar Allah ya hadani daku" ta faɗa tana kallon hajiya fanaya ido cikin ido. "Allah yaga zuciyata kuma yaga abunda nake nufi a cikinta, yasaka ina sauka garin nan daku na fara cin karo, cikin isarsa da ikonsa ya kawo qaddara a tsakanin mu ya saka kuka kadeni da mota, har na dawo ina aiki a gidan ku, duk da a farko bansan cewa ku nake nema ba sai daga baya na gane hakan bayan naji Asalin sunan alhaji. Anan na gane kune mutanen da nazo nema cikin garin nan, domin in samu bayyana wa Alhaji wani bakon al'amari, kuma shi kansa alhajin yanzu idan aka tambaye shi yana da matsananciyar bukatar son ya sauke nauyin dake kansa" "Dayammah wallahi ban fahimce ki ba, me kike so ki sanardani game da maganar nan da kike fad'a Yanzu" Dan murmushi tayi kafin tace"ba damuwa zaki gane komai in sha Allah, ki bari idan Alhaji ya dawo kawai zaku fahimci komai" "Tau shikenan, Allah ya mai da shi lafiya, kuma Allah yasa muji alqairi" Ameen suka fada gaba daya, dayammah kuma ta dora da fadin; "Nasan baku san wanene mahaifinku ba kho, kuma nasan babban abunda ke cikin ranku a yanzu bai wuce ake kunsan asalin wanene mahaifinku ba, to karku damu domin mahaifinku mutumin kirki ne, kuma bai baro danginsa da mahaifarsa don ra'ayin kansa ba, wallahi sakashi akayi bayin kansa bane. Asalin garin da mahaifinku yake shine calaba, kuma can yake zaune da iyayensa da sauran danginsa. Ni matar dan uwansa ce wato maharaz domin na gayamuku mahaifinku ba shi kad'ai aka haifa ba su tagwaye ne, sune na fari, sannan sai kanwarsu dake biye musu a haihuwa sunanta fairozha, a gidansu na tashi nake rayuwa tun kafin auren mu da maharaz. Mahaifiyarsu wato neela kanwace a wurin tawa mahaifiyar, kuma akwai zumunta mai karfi tsakanin mu dasu. Ganin haka ne ya saka mahaifiyar su maharaz wato neela ta nemi mahaifiyata ta mayar Dani gidan nasu naci gaba da karatuna tare da yar wajenta fairozha. Mahaifiyata bata nuna rashin amincewarta ba, kuma ta nuna mata wannan ba komai bane. Ba jimawa nayi shiri na koma gidansu maharaz naci gaba da zama gidan da bayada bambanci da gidanmu, saboda komai zan yi a gidan mu, zan iya yinsa a gidansu. Mahaifinsu hilwah mutum ne mai karamcin da alkunya Dattijo ne mai kamala, gashi kuma mutum ne wanda Allah ya azurta da dumbin dukiya sakamakon sana'o'in da yake dasu a gida Nigeria da kuma kasashen ketare, bai gaza da karatun mu ba kuma yana kwatanta adalci a tsakanin mu domin bazan fitarda kaina a cikin 'ya'yan gidan ba saboda komai yake musu nima yana yimin. wani lokacin ma sai ayi min abu su ba'a yimusu. A lokacin fairozha bazata wuce shekaru goma sha hudu zuwa sha biyar ba, babban abun ban haushi game da rayuwar fairozha shine rashin godiyar Allah da kuma tsagwaron hasada da kyashi da kuma bakin cikin ganin wani ya ci gaba, kullum idan aka kwatanta yiwa wani alqairi a gabanta ko waye bazata bari ba, fairozha bata alqairi, kuma bata yarda ayi alkairin a gabanta. hamraz da maharaz kuma sunada kusan shekaru 17 zuwa sama. A lokacin ne suka kammala karatun su har ana shirya yanda zasu ci gaba da wani karatu. Batare da hilwah ya nemi shawarar d'aya daga cikinsu ba ya yanke shawarar turasu kasar DENMARK suci gaba da karatunsu a can. Fairozha bataji dadin wannan lamari ba ko kadan, duk da suma basu so aka rabasu da qasarsu ta gado ba. Sunso a barsu cikin danginsu suci gaba da karatunsu amma hilwah ya ki amincewa da batun su. Cikin 'yan kwanaki aka shirya komai na batun tafiyar su, hakika fairozha bataji dadin wannan lamarin ba, kuma ba yanda batayi ba akan ta hana tafiyar amma Allah yaso faruwar haka , har ita kanta ta dage kan da ita za'a yi tafiyar amma abun yaci tura tunda bata kammala karatunta na secondary ba. An shirya musu komai na batun tafiyar su washe gari zasu wuce denmark din. Ita kuma fairozha ta rasa abunda ke yimata dadi Saboda tana ganin taci baya idan ta bari wannan lamarin ya faru. Me zatayi domin domin ta hana tafiyarsu?? Maganar da take faman nanatawa kenan tun daga fitowar alfijir din yau har yanzu da muke kusan karfe uku na rana. Mikewa tayi cikin mutuwar jiki da kasala domin ita abun ya zamo mata kamar jinya. Sai da ta lura sosai da hilwah baya nan dakinsa, sannan ta shiga cikin d'akin da sand'a cikin ikon Allah ba wanda ya ganta har ta shiga ta rufo kofar. Bedroom ɗin hilwah ta wuce kai tsaye tana shiga bedroom din ta nufi inda yake ajiye takardunsa masu muhimmanci, 'yar karamar kit ce ta akwati kuma an sakamata key, wani irin mugun haushi ya turnuketa ganin an sakawa kit din makulli. Juyawa tayi da nufin ta fita, wata zuciya ta ce mata "meyasa zaki fita bayan kinsan inda yake ajiye makullan sa" Da sauri ta juya bayanta,,,,,,, idon ta kuwa suka sauka kan wata 'yar karamar jakar da hilwah ke saka makullan sa. Bata san da wane makulli zatayi amfani ba domin bude kit din da aka saka takardun da take nema, duba da haka ne ya saka ta je da makullan gaba daya, kuma da d'ad'd'aya ta dinga gwada makullan har dai ta samu wani daga cikin makullan ya bude kit din akwatin da takardun komai suke ciki a gidan . Murmushin mugunta tayi lokacin da ta bude kit din idanunta suka sauka akan takardun da take nema. Ba tare da shakka ko tunanin komai ba ta d'ebi takardun gaba ɗaya waɗan da tasan zata bukata ta 'boye su sosai a jikinta sannan ta mayarda komai inda ta dauko kamar ba'a ta'ba ba. Fita dakin tayi cikin tsananin farin cikin samun nasara da tayi sannan ta nufi bayan d'akunan gidan gaba ɗaya. Ajiye takardun tayi gefe daya, sannan ta kuma dawowa cikin gida ta shiga kitchen ta dauko ashana ta fita. Bata zarce ko'ina ba sai gaban takardun nan, tana zuwa ba wata-wata ta kestawa takardun wuta, nan da nan kuma wutar ta cinye takardun gaba d'aya kamar basu taba wanzuwa ba. Tsinsiya ta d'akko ta tsaftace wurin har da zuba ruwa ta wanke tass kamar ba'a yi komai a wurin ba, sannan ta koma cikin gida hankalinta kwance, zuciyar ta fal da farin ciki. Bayan dawowar hilwa gidan tare da maharaz da hamraz ya kaisu sunyi bankwana da yan uwa da abokan arziki sannan suka dawo gida, tun lokacin da hilwah ya shiga dakinsa ya tabbatar da akwai abunda ba daidai ba a dakin. Kiran maharaz da hamraz yayi domin suzo su fara hada kayayyakin da zasu bukata a tafiyarsu. Sai da suka nutsu sosai kafin suka hada kayan ba wata rigima, kuma suka kwantarda hankalinsu duk abunda zasu bukata idan sunje suka sakashi a cikin trollyn su. Washe gari tun da sassafe suka tashi suka dora daga inda suka tsaya domin tafiyar tasu karfe tara da minti sha biyar na safe zata kasance. 'yar karamar jakar da hilwah ke saka makullan sa ya d'akko tare da fito da wani karamin mabudi da yafi kowanne karanta. Direct inda ya ajiye kit ya nufa tare da zare mata padlock bayan ya saka mabudi. Ido ya zaro cikin mamaki ya kalli hamraz da maharaz yace "ku kuka ɗauki takardun da na saka anan" Suma ɗin kallon mamaki suka bishi dashi domin maharaz ma bai gane nufinsa ba hamraz ne kawai ya sami damar amsa masa. Inda ya samu damar gayamasa basu suka dauka ba, sosai abun ya bashi mamaki domin shi dai a saninsa nan ya sakasu, kuma ya tabbatar nan ya sakasu tunda shi ya saka da hannunsa harma ya rufe da kansa. "Ikon Allah" ya fada tare da talla'be ha'ba. "Hilwah ka kira neela ka tambaye ko sun gani" maharaz ya fada yana dakatawa da aikin saka kaya trolly da yake. Mikewa hilwa yayi ya fita dakin ba jimawa suka dawo tare da ni da neela da kuma fairozha. Sai da muka shigo dakin hilwah sannan aka sanar mana da dalilin kiran. "Bayan fitar mu gidan nan akwai wanda ya shigo dakin nan?" Hilwah ya tambaya. Jin kowa yayi shiru yasa na kalli gefen da fairozha ke zaune domin yau gaba daya ita naga ta shigo ta bangaren nan hatta neela ma ban ganta ba. "Hilwah fairozha ta shigo dakin nan yau gskiya" na fada ba tare da tunanin komai ba. "Me kika dauka a nan fairozha?" Hilwa ya tambayeta yana kafeta da idanu. Murya na rawa cikin tsantsar rashin gaskiya tace "hilwah nazo ne naga ko kana ciki na kara jaddada maka magana ta akan nima zan bi maharaz da hamraz denmark" "Amma kuma mahaifiyar ki ta riga ta gayamiki ba inda zakije kho, Ni dama kin kammala secondary ne da zan iya hadawa har ke ma ku tafi Ni wannan ba wata matsala bace, Amma kiyi hakuri zuwa wata shekara kinji" "Shikenan hilwah ba damuwa zamu hakura har wata shekaran domin ba ni kadai zan hakura ba" "Hummm fairozha kenan, to idan dayammah kike dubi ai ita bata da sha'awar yin nisa da gida" "Ba dayammah kadai ba, hatta su Hamraz da maharaz din da aka fifitasu akanmu sai sun hakura domin na 'kona takardun su gaba daya dana gani cikin wanchan akwati" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me kikayi haka fairozha, Ashe baki da hankali? Yanzu toshewar kwakwalwarki da hankalinki har sun kai ki aikata irin haka?" Neela ta fada cikin tsananin bacin rai mara misali. Kafin hilwah da sauran mutanen da ke dakin suyi wani yunkuri tuni neela ta dira kan fairozha, dukan ta kawai take ta ko'ina batare da tunanin abunda hakan zai janyo nan gaba ba. Da kyar suka 'ban'bare neela daga jikin fairozha bayan tayi likiss har bata iya yin kuka. Sosai hilwah ya rufe neela da fad'a inda ya nuna mata illar yin haka, kuma ya shaida wa su maharaz da hamraz su kwantar da hankalinsu tafiya ba fashi domin takardun da ta kona basu bane original duk copies ne. Sunyi farin ciki sosai da jin haka, fairozha kuma kamar ta hadiye zuciya ta mutu, Babban abunda ya hanata tasha maganin kwarin jiki shine son daukar fansa"............... "Fansa kuma? Wurin wa zata dauki fansa?????" Aleena ta tambayi dayammah lokacin da ta kai daidai nan a bayanin ta. "Wurin mahaifiyar ta neela?" "Taya zata dauki fansa......? saboda ta daketa akan laifin da tasan ta aikata, kuma ma ita ta faɗa da kanta" "Ki saurara kiji yanda komai yazo karshe" "Okay ina sauraren ki" cewar Aleena, wato (Rukhshanah) "Bayan sati biyu da faruwar wannan komai ya dawo daidai domin su Hamraz da maharaz sun jima da tafiya karatunsu can denmark, shekara hudu zasuyi kafin su dawo, kuma har wannan shekara hudun su kare ba zasu zo gida ba sai dai aje musu. Komai ya ci gaba da tafiya kamar yanda ake dha, fairozha ma duk ta manta da komai kamar ba'a yi ba. Amma wani babban al'amari dake dauremin kai dangane da ita, d'aki daya muke kwana, kuma a gado d'aya, a duk lokacin da zan farka cikin dare bana ganinta a dakin. Tun abun baya damuna har yazo ya fara damuna. Idan nayi yunkurin sanar da wani sai naji harshena yayi nauyi sai kawai nabar abun a zuciyata. A wata rana cikin ranakun da bazan manta ba, Ko da muka tashi da safiya sai muka tashi da jimami a zukatan mu, neela ce ta tashi da zazzabi mai zafi, tunda sassafe kuma hilwah ya dauketa suka tafi asibiti, wuni daya a asibitin suka dawo gida. Taji sauki sosai kamar ba itace aka fita da ita gidan ba ko motsin kirki bata iya yi yanda akeso. Hatta aikin gida neela ta ki bari nayi Ni kadai, sai da ta tayani a wunin ranar, dama can ita fairozha bata cika yin aikin gida ba. Sai da muka kammala komai da komai har abinci dare da komai mukaci sannan ta koma sashen ta nima na shigo namu sashen. Bada fairozha mukaci abincin dare ba, dama can bata wani damu da abincin ba sai idan hilwah da neela sun takuramata. Nayi mamaki kwarai da gaske dana dawo dakinmu bansameta ba, "to ina fairozha taje yanzu?" Na tambayi kaina ba tare da na ajiye mai bani amsa ba. Saida da nayi addu'a sosai kafin nan na kwanta bacci barawo bansan lokacin da ya saceni ba. Can cikin baccina kamar a mafarki naji muryar hilwah na kiran sunana, a firgice na tashi zaune ina murza idanuna ko da mafarki nake, sunan fairozha naji ya sake kira cikin tashin hankali na bud'e kofar na fita ban ma kula da fairozha na gidan ko bata nan ba. Ban sameshi a kofar dakin ba, sai alamar tafiyar danaji ya wuce sashensa, da sauri na bishi har ina hadawa da gudu. Turussss nayi lokacin da na isa tsakiyar dakin hilwah, bakinsa kawai naga yana motsi amma duniyar da nake a halin Yanzu bansan wani abu mai motsi da zai yi magana na ji ba. Neelah yayar mahaifiyata ce kuma uwa d'aya uba daya, ita kadai na sani a garin calaba. Da kyar na sami zarafin magana da sarka-kakkiyar murya nace "hilwah me ya sa sami neela, itace kwance haka? Mutuwa tayi? Hilwah neela ta rasu ne? Naga sai matattu ake rufewa har fuska, ko sanyi takeji hilwah?, ko kuma zazzaɓn ta ne ya tash......?" Bansan a wane yanayi hilwah ke ciki ba nidai naji sautin Muryar sa kamar nesa dani sosai yana fadin. "Dayammah sai kunyi hakuri kinga illar Rayuwa kho, ga yanda rayuwa tayiwa neelar ku, yanzu shikenan babu ita a wannan duniyar mai cike da tarin rud'ani, yanzu gashi mun kwana da ita amma bamu tashi da ita ba, Dayammah na kira mahaifiyarki da sauran danginku na gayamusu abunda ke faruwa, sannan kuma na gayawa wasu daga cikin makwotanmu, kiyi hakuri kinji rayuwar kenan muda muke tsaye akan gawarta yanzu, wata rana wasu ne zasu tsaya akan tamu" Daga haka hilwah bai qara fad'ar komai ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito yayi sallah raka'a biyu sannan ya dauki chazbi ya fara salati gaban gawar neela. Ina mamaki sosai yanda koda wasa banji hilwa ya tambaye ni fairozha ba, nikuma ganin bai tambayeni ba bai saka na ce masa komai ba game da haka, ina zaune a wurin sai kuka nake mai sauti da marar sauti duk wanda yazo yinsa kawai nake. Lokacin da aka kira sallahr asuba hilwah yamin umurni akan naje nayi sallah, fita nayi na d'auro alwala nima na dawo dakin, har a wannan lokacin hawaye basu daina zuba a idanuna ba, ina tunanin yanda su maharaz da hamraz zasuji labarin mahaifiyarsu mafi soyuwa a cikin zuciyoyin su ta rasu ba'a gabansu ba. Shigowa nayi da sallama dauke a bakina na nufi sallahya na tayarda sallah, bayan na kammala nayiwa neela Addu'oin neman gafara da afuwa wurin sarkin da ke kashewa da rayawa, tun kafin na tashi daga inda nayi sallah mutane suka fara shigowa gidan rututu, kafin kace me mutane sun cika gidan, nayita rarraba idanu ko zanga fairozha, amma ko mai kamada ita banganiba. Har aka suturta neela za'a kaita makwancinta babu Ita babu alamar ta, kirana akayi domin nayi mata addu'a, kuka yaci karfina sosai har bansan abunda nake ba. Sai riko mutanen da suka dauki gawar neela nake ina kuka wai ko zasuji tausayina su fasa tafiya da ita, amma sai aka sami waɗan da suka fini karfi suma suka rikeni har aka fita da gawar cikin gida. Durkushe wa nayi ina kuka sosai, duk da zamana 'yar fari a wurin mahaifiyata bai hanata rarrashina a agaban mutane ba. Sai da akayi kwanaki biyar da rasuwar neela sannan kowa ya watse a gidan, mahaifina da mahaifiyata sunyi duk yanda zasuyi akan na dawo gida muci gaba da zaman mu tunda neela bata nan yanzu, nikuma nace bazan iya ba, ni su barni a nan zan yi zamana. Da dai suka dage akan sai mun tafi sai na saka kuka, hilwah kuwa yana ganin haka yace su tafi zai maidani da hannunsa. ko yaushe mamaki na bai wuce na yanda ya manta da 'yar sa ta cikinsa ba. Ina tsoro ace wani mummunan abu ya faru da ita, kuma bana jin dadin ganin yanda hilwah ke nuna halin ko in kula akan lamarin nan. Ba yanda iyayena suka iya tunda hilwah yayi magana, haka suka hada kayansu suka tafi ba tare dani ba. Ni kadai na kwana a dakinmu yau, sakamakon duk bakin da nake kwana da su da sukazo gaisuwa sun tafi. Wani abun ban tsoro da mamaki shine koda na tashi na tarar da fairozha a gefena tana kwanciyar ta hankali kwance. Cikin matukar tsoro da shakku na ja baya daga kusa da ita, a hankali na sauka daga kan gadon na dawo gefen ta, sai da nayi shawara da zuciyata kafin na fara ta da ita ina kiran sunanta. "Fairozha ki tashi, ina kika shiga? Meyake faruwa da ke ne, kuma yaushe kika shigo gidan nan? Fairozha kin san neela ta rasu kuwa, neela ta tafi ta barmu fairozha?" Na faɗa kuka na kufcemin. Miqewa tayi zaune tana yamutsa fuska da alama ma baccin dadi yake mata "dayammah,,,,,,,,,,kikace neela ta rasu kho? Hmmmm nasan da rasuwar dayammah! da ma baki wahalar da bakinka wajen gayamin wannan ba" cewar fairozha. "Amma kinsan da mutuwar fairozha kika bari har aka fita da gawarta gidan nan baki ganta ganin karshe ba, dan Allah me ya faru dake kika koma haka fairozha?" Maimakon tayi magana sai kawai naga tayi murmushi sosai har haƙoranta suka bayyana, sake juyar da murmushin tayi izuwa kuka, nan ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta ta fara kuka kamar ranta zai fita. Banyi yunkurin hanata ba sai ma qara ci gaba nayi da kukan nawa, sai da mukayi mai isarmu kafin fairozha ta fita daga dakin. Ni kuma na shiga toilet din dakin namu nayi alwala na fito na tayarda sallah ta, fitarta dakin bansan ya sukayi da hilwah ba domin na tabbatar wurin sa taje. Bata sanar dani inda taje ba haka hilwah bai sanardani ba, kuma bansan abunda ta gayamasa ba dayasa banji ya taso da maganar ba. Sati biyu tsakani gidan ya dawo kamar bashi ba, komai na gidan ya sauya abubuwa a wurin fairozha kam sai abunda ya k'aru, zata iya wata daya, biyu........ bata gida. Sosai hilwah ke kula dani da karatuna, kuma yana kula da kasuwancinsa, hatta su Hamraz da maharaz dake denmark yana kula dasu iya gwargwadon iyawarsa. Amma duk wannan da ake ko da wasa banji yana ambatar fairozha ba, sau ba adadi idan nayi nufin yimasa maganar ta sai naji kamar an dauremin harshe duk sai naji na kasa fad'in komai a kanta kamar aikin asiri ko tsafi, ni hankalina ma yafi karkata da haka. Kamar da wasa kuma sai gashi muna lissafa ranakun da suka ragewa su maharaz da hamraz a chan kasar denmark. kwanaki sai zuwa suke suna shud'ewa har muka cimma ranar da aka diba musu zasu dawo Nigeria. Da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana jirgin su ya iso, a lokacin kuma na gama shirya komai na gidan nan. Tsawon shekaru hud'u ne da tafiyar su, kuma idan za'a auna yayi daidai da lokacin da neela ta rasu kenan. Kunga kenan basu san da mutuwar ba, na gyara komai na gidan tsafff, kuma na girka musu abinci har kuma sashensu duk na gyara dah ma can ban cika barin shi da datti ba ko dan gudun irin ranar nan. Ina zaune tsakar gidan nikadai ina jiran dawowarsu naji an kwala sallama da karfi. Fuskata dauke da walwala na fita da dan saurina domin na tarbesu, maharaz kawai ya tsaya shi kuma hamraz muna gaisawa kadan ya wuce ciki yana kiran sunan neela cikin d'aukin ganinta. Jin haka ya saka idanuna suka ciko da kwallah har ta zubo, da sauri maharaz ya iso gareni tare da rike kafaduna yana jijjigani; "Kanwata Lafiya? Meya sameki ko dai bakiji dadin ganinmu ba ne kike kuka?" Jijjiga masa kai nayi alamar ba abunda yake nufi bane, domin a yanda nakeji kukan yanaso ya ci karfina. Yana shirin sake tambayata sai ga hilwah ya shigo gidan, "Maharaz meya faru ne?" "Wallahi hilwah bansani ba nima na shigo ne yanzun nan tazo ta tarbemu, sai kuma naga ta fashe da kuka haka kawai shine nake tambayarta ko lafiya?" Juyawa hilwa yayi gareni ya fara tambaya ta abunda ke faruwa, nikuma bansan yanda zan yi masa bayani ba domin ga dukkan alamu ma bai sanar da su mutuwar ba tunda naga haka daga garesu. "Muje ciki maharaz" hilwah ya fada yana nuna masa kofa alamar mu wuce. Shigewa mukayi har a lokacin maharaz bai saki hannun na ba, kuma bai daina tambayar abunda ya sameni ba. Gab da zamu shiga parloun hilwah ne muka ci karo da hamraz yana fitowa. "Hilwah neela bata san mun dawo bane naji gidan shiru ko sun fita ne?" "Muje ciki hamraz" cewar hilwah damuwa shimfid'e a fuskar sa Shiga sukayi gaba ɗayansu, hilwah bai bawa kowa damar magana ba har sai da sukayi wanka sukaci abinci sannan suka dawo parloun suka zauna. Bai 'boye musu komai ba na duk abunda ya faru game da mutuwar mahaifiyar su, sunyi kuka sosai kamar ransu zai fita domin shi hamraz kusan zaucewa ma yayi. sake tambayar sa fairozha sukayi, sai ya shaida musu cewa tana nan cikin koshin lafiya, kuma itama zai sanar dasu labarin ta nan gaba. Basu kawo komai ba, domin suna tunanin kamar tana hannun wasu daga cikin danginsu ne, duba da tayi rashin mahaifiya. Haka mukaci gaba da zama a gidan cikin kwanciyar hankali, shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin mu da maharaz har kuma ta juya ta zama soyayya, mun fahimci junanmu sosai inda yaje da kansa ya sanarwa da hilwah abunda ke zuciyoyin mu, hilwah yaji dadin zancen nan sosai babu 'bata Lokaci yaje ya sami iyayena ya gayamusu, suma sunyi farin ciki matuqa. inda aka umurci hamraz daya nemo matar aure ayi aurenmu lokaci daya dashi, amma ya nuna cewa shi bai tashi yin aure ba akwai abubuwa da dama a gaban sa da yakeso ya kammala. Ba'a tilasta masa ba, kuma babu wani 'bata Lokaci akayi bikin mu da maharaz aka gama. Sashen mahaifiyar sa neela mai rasuwa aka gyaramin na tare, kuma sashen yana kusa da na hilwah sosai, kusan ma duk gini daya ne kofofi ne kawai a rarrabe. Hilwa ma Ya so ya tashi ya koma wani sashen amma maharaz yace masa idan har ya tashi saboda mu, to muma zamu tashi mu bar wurin ba koma tunda ya ki yarda ya zauna a kusa damu. Da kyar dai muka samu yayi zamansa a sashen. Bayan wata shida da aurenmu, abubuwa sun chanja sosai yanda ba'a misali. Rayuwa ta tsanan ta mana sosai, sai mutuwar ban al'ajabi ake a cikin danginmu yau idan kaji an dauki wannan, gobe sai kaji ta wancan mun rasa wace irin annoba ce ta fado mana. Gashi yau mun wayi gari da 'batar hamraz , dashi muka kwanta bacci, amma gashi mun wayi gari an nemeshi an rasa. Hilwa kuma tsawon sati shida kenan yana fama da jinya, anje asibiti anyi magani har an gaji ko hagu babu ballantana dama. Wani babban abokin kasuwancin sa da ake kira WAASIBUDDEN KABEEL shi yake jinyarsa, shikuma maharaz yana can yana fama da neman d'an uwansa gidan television da na Radio. Ina zaune a parlour abun duniya duk ya isheni na jiyo murya daga can dakin hilwah yana kirana cikin muryarsa irin ta majinyata. Da azama na mike na shigo dakin da sallama a bakina, mijina maharaz na gani zaune a gefensa ya zabga tagumi da alama bai ma san zuwana wurin ba. Abokin hilwah waasibudden ne ya tsayarda tunaninsa ta hanyar kiran sunan sa. "Maharaz" "Na'am Abba" "Dayammah kho" abokin hilwah waasibudden ya fada yana tsureni da ido. "Eh,,,eh" na fada murya na rawa. "Kunsan dalilin da yasa mahaifinku ya taraku anan" "Shi muke so sani Abba" "Yawwa, kunga waɗan nan takardu" ya fada yana nuna wasu takardu dake ajiye a gefe daya. 'Daga kai mukayi alamar mun gani. Yaci gaba da fadin "ku sani na kiraku ne dan ku zama shaida,,,,,, wadan nan takardun sune kadarar mahaifinku da dukiyarsa gaba d'aya. duk wasu kamfanoni nashi da masana'antunsa da kuka sani da wanda baku sani ba akwai su a wurin nan, kuma ya bani sune amana na ci gaba da juya masa su har zuwa lokacin da 'ya'yansa zaku buqaci komai ya dawo hannunsu. Kuma Ni waasibudden kabeel ina rantsuwa da girman Allah zan rike alƙawari, bazan yarda naci hakkinku ba koda kwayar zarra wannan alqawarin tsakanina ne da Allah, da kuma ku da zaku tsaya shaidata a ranar gobe kiyama idan naci amarku" abokin hilwah waasibudden ya fadi haka idanunsa na tsiyayo da ruwan hawaye. Ba wanda bai zubarda hawaye ba a wurin hatta shi hilwah dake halin jinya sai an kwantar a tayar. "Maharaz nasan kana cikin rudani da tashin hankali yanzu ganin yanda matsala ta taru tayi maka yawa, ga mahaifinka kwance cikin matsananciyar jinya, ga kuma dan uwanka da aka nema aka rasa, nayi tafiya mai nisa daga barno zuwa nan calaba, kuma nasan baka sanni ba, koh da ka sanni nasan ka manta dani tsawon shekarun da ku ka d'auka bakwa nan bakasan inda nake rayuwa ba. saboda haka gobe ka shirya muje can na gabatar da kai ga iyalaina da kuma nauyin ku dake kaina, dan Allah karka ce baza je ba domin jinkirin mu a wannan lokacin shine babban tashin hankalinmu. Da kasan abinda ke faruwa bazakaso mu kara kwana ɗaya ba tare da munje barno ba. Amma ka ci gaba da addu'a kaji, Allah ya kaimu gobe lafiya" Daga haka ya sallamemu muka tafi, rayukan mu duk ba dadi kowa da abunda ya dameshi, washe gari tun da sassafe abokin hilwah da mijina maharaz suka d'au hanyar zuwa barno, nayi kuka tuburan ji nake kamar bazan sake ganinsu ba, ko su su mutu kokuma Ni mutu. Komawa nayi sashenmu zuciya ta na min zafi, zama nayi na rasa makama da abun yi, na rasa wane tununi zanyi da haka har bacci ya ɗaukeni....................... A can cikin ɗakin hilwah kuma kwance yake kamar yanda ya saba kullum sai kiran sunayen Allah yake a zuciyarsa domin baya magana a fili tun lokacin da ciwon ya sameshi. Yana cikin hakane yaji wani sauti mai qarfi ya ratso cikin dakin, sekonni biyar da faruwar haka yaji dirar wani abu mai nauyi ta gefensa. Baiyi niyar ya juya ba haka kawai yaji zuciyarsa na matsa masa akan sai ya juya, juyawar da zaiyi ne idanunsa suka sauka akanta. Cikin matukar tashin hankali yake kokarin yin magana duk da yasan abune mai matukar wahala taji abunda zai faɗa amma yayi karfin halin kiran sunanta. "Fairozha ina kika shiga tsawon wannan shekaru?" Bai yi zaton taji abunda ya fad'a ba, shi kansa masani ne akan baya magana tsawon watanni domin ko yayi ba jinsa ake ba shiyasa ya daina yi gaba ɗaya, ko yanzu bai sani ba ko fairozha taji abunda ya ke cewa. Da sassarfa ta fara tafiya har ta zo inda yake, zama tayi kusa dashi ba tare da ta kalli inda yake ba. "Hilwah ka yafemin da abunda zan fada maka, nasan wa'adin ka ya kusa. yanzu hakan nan shi yasa nazo in sanarda kai abunda ke faruwa wanda nasan ba ku san dashi ba" sai da ta ɗan sauke ajiyar zuciya a hankali kafin ta d'ago kai ta kalleshi tarrr tace "hilwah na shiga kungiyar asiri!, kuma Ni na kashe neela, itace sadaukar wa ta ta fari a kungiya, kuma Sannan duk mace-macen da ake a cikin danginmu ni nake bada su, sannan kuma ni na 'batarda hamraz saboda ba yanzu bane lokacin da zamuyi amfani dashi ba, hilwah kasani wannan ciwon da kake nice silar sa amma lafiya Ƙalau kake gabanin wannan" fairozha ta fada babu tsoron komai, kuma babu wata alama ta nadama a tattare da ita. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, fairo,,,,,,zha dan,,,, Allah me kika ra,,,sa da zaki,,,,,,,shi,,,gga kungiyar asiri" ya fada kalmomin na neman kufcemasa. Murmushi mai sauti tayi wanda ya bayyanar da duk hakoranta tace "hilwah sai yanzu kake tambayar me na rasa dha can da kake daukar 'ya'yan ka maza kake kaisu kasar waje suyi karatu ka taba tambaya ta abunda na rasa? Sai yanzu dana daukesu ne kake tambaya ta" Fairozha dan Allah me mukayi miki a wannan duniyar da muka cancanci irin wannan sakayyar, fairozha mu muka haifeki fa karki manta wallahi hakkin mu na iyaye a wurinki da kuma hakkin mutanen da kika kashe basu ji ba basu gani wallahi bazai barki ba" "Wallahi hilwah ko a yanzu na mutu banada takaici ko haushin mutuwata, babbar fansa ta akanku ne kuma na riga na dauka hmmmm amma Ni kaina nasan lokacin mutuwata bai yi ba sai na karasa aikina, kasan menene aikina?" Bata jira cewar sa ba taci gaba da faɗin, d'an ka maharaz da ka aika da babban amininka waasibudden suje barno sun isa lafiya hanyarsu ta zuwa, amma ina maka rantsuwa da gunkin tsafinmu abun dogaronmu d'an ka maharaz bazai dawo garin calaba da rayuwa ba, sannan shima waasib da ya shiga gonata wallahi bazai girbeta da dad'i ba........." Tun kafin kafin ta kai ga karasa fadin abunda zata fad'a wani mugun tari ya turnike hilwah, har idanunsa na rufewa suna budewa, cikin matukar karfin hali yayi kalmar shahada shikenan yace ga duniyarna. "Dama nasan ko ciwon nan bai kasheka ba maganganun da na gayamaka zasu karasaka, ki shigo ki shafe gawarsa domin babu wannan hilwah sai dai wani" fairozha ta fada tana mayarda hankalin ta ga kofar shigowa dakin. Wani irin rawa da mazari jikina ya fara yi domin banyi zaton ta san dani a wurin ba, tun lokacin da ta shigo dakin ina la'be ina sauraren ta duk a zatona bata ganina. Wata tsawa ta qara dakamin har sai da 'ya'yan cikina suka yamutsa da gudu na shigo dakin ba shiri, babban abinda yabani mamaki shine babu fairozha babu alamar ta a cikin dakin iya gawar hilwah ce kawai. Cikin kuka na isa wajen gawar sai dai tsoro ya hanani aikata komai, naji tsoro sosai rayuwa kenan wai hilwah ne kwance matsayin gawa innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un. Na dade akan gawarsa ina kuka mara sauti nayi har sai da nayi mai isata, wayata na laluba tare da dannawa maharaz kira, saidai tana nunamin inda yake ba network, nayi iya kokarina inga nasamu wayarsa amma abu d'aya ake fad'a tun dazu. Mutanen unguwar mu suna gudun mu, tsoron mu sukeji gani suke kamar akwai Mayu a cikin mu sakamakon yawan mace-macen da akeyi a cikin danginmu, fairozha ta ja an shafa mana bakin fenti, ta dalilinta ne komai yake faruwa har haka. Hankalina yayi mugun tashi, bansan yanda zanyi da gawar hilwah ba. nasan abu ne mawuyaci su yarda da suturta hilwah su kai shi makwancinsa. Mikewa nayi da sauri na fita gidan, duk inda nasan akwai majalisa da ake zama a unguwar tamu sai da naje na rokesu, wasunsu ma ba bari suke in karaso inda suke ba, daga sun ganni sai kaga suna gudu. Inda naje na karshe kuwa harda jifana sukayi da duwatsu, kuka mai kara na fashe dashi da gudu na nufi cikin masallacin unguwar tamu ban tsaya ba har sai da nakai gab da mutanen zasuyi sallahr azahar, ban zarce a ko'ina ba, kuma babu wanda yayi yunkurin tsayardani har sai da na isa gaban limamin yana shirin kaffara sallah a dan tsorace ya juyo gareni yace; "Malama lafiya, meyake faruwa dake?" Cikin Muryar kuka da damuwa nace "malam dan Allah ka taimakamin mahaifina ne ya rasu, 'yan unguwar nan suna zargin mu da maita wai dan ana yawan mace-mace a cikin danginmu, shine yau Allah yayiwa mahaifina rasuwa kuma nika dai ce a tare dashi, diyansa biyu maza an nemi d'aya an rasa yau kwanaki hud'u kenan, dayan kuma yayi tafiya zuwa barno ina ta kiran number ɗin sa bata tafiya. Gashi mahaifinmu ya rasu ban san yanda zanyi da gawarsa ba, duk Inda naje korata akeyi shine na yanke shawarar na shigo nan na sanar muku da abunda ke faruwa. Dan Allah ku taimaka min wallahi bamu da alaka da maita" Cikin matukar tausayin da ya bayyana har fuska limamin yace; "Allah sarki karki damu kinji in sha Allah mu zamuje muyi masa sallah mu tsaftace shi mu suturceshi mu kaishi makwancinsa na gaskiya, kiyi hakuri Allah ya jikansa ya yi masa rahma. Allah ya bashi masauki mai girma" "Ameen malam Nagode sosai Allah ya biyaka, Allah ya jikanka yanda ka jikanmu malam" "Ameen ya rabbi" suka fada har sauran mamun da zasu bi limamin sallah. "Kije wancan dutsen ki zauna ki jiramu kafin mu idar da sallah sai muje gidan ki nuna mana" limamin ya kuma fada yana nuna mata wani dutse dake gefen masallacin daga waje. Fita daga cikin masallacin tayi sannan taje wurin dutsen ta jirasu har suka kammala sallah. Yanda limamin ya fad'a haka ta kasance wato su sukayiwa hilwah wanka, suka yimasa sallah Sannan suka binneshi a makwancinsa na gaskiya. Nasha kuka sosai lokacin da za'a fita da shi gidan, na zama ni kadai ke nan innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me muka aikatawa fairozha da zafi haka, shikenan na rasa kowa. Idan har da gaske ne abunda fairozha ta gayawa hilwah gabanin mutuwar sa, duk kisan da akeyi itace, hakan yana nuna kenan har iyayena ita ta kashe su. Wunin ranar ba wani aiki da nayi da ya wuce kuka, sai idan lokacin sallah yayi ne nake tashi nayi, kuma daga zarar nayi sallahr nake ci gaba da kukana. Na dauki tsawon kwanaki uku a haka, kuma kullum ta Allah sai na kira wayar maharaz amma bana samu, yau ma haka ne ina zaune tsakar gida ni kadai abun duniya duk ya isheni na rasa inda zan saka kaina. Wayata naji tayi qara, ganin baƙuwar number ya sakani d'an shakku, kuma ban d'aga wayar ba har sai da akayi kira kusan biyar. Ganin karar wayar na so ya fara takuramin sai ya saka na dauki waya na kara a kunnena. "Kece dayammah" naji an fada da wata baƙuwar murya da bazan iya shaidawa ba. "Ninni........Ni....ni ce" na fada muryata na rawa. "Yawwa masha Allah, sunana inspector Bukar Elyass, dayammah ki kwantar da hankalinki ki saurareni. Wata mota da ta taso daga garin barno ta samu accident yau da safe, amma ba wanda ya rasa ransa a lokacin da aka samu accident din, sai bayan anje asibiti ne dayan da yafi kowa rauni a cikinsu Allah ya karbe shi, kuma shine muka dauki wayarsa muka fara binciken contact dinsa, a yanda muka ga yayi miki saving ya tabbatar mana da ke matarsa ce, kiyi hakuri dan Allah mijinki ya rasu Allah ya karbi abunsa sai hakuri" 'kitttt mutumin ya kashe wayar. Dayammah ta sake kallon mutanen da ke zaune a parlourn idanunta sharkafff da hawaye tace "Wallahi Hajiya bazan iya kwatanta muku irin kunci, da bakin ciki da tashin hankalin da na shiga ba a wannan lokacin" dayammah ta kare Magana wasu zafafan hawaye na gangaro mata. Sai a wannan lokacin id yayi magana shima idanunsa sun kad'a sunyi jajir jin irin yanda rayuwar ahalinsa ke tauye. "Annah kenan maganar fairozha da ta gayawa marigayi hilwah zata kashe Affana gskiya ce? Shine ta kasheshi ta hanyar saka su had'arin mota kuma taji masa rauni da yawa, sannan ta kasheshi ki kaɗai. 'yar uwarsa ce fa, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya labarin dan uwan affana maharaz, sannan kuma ya akayi kika baro garin calaba bata hanaki ba?" "Wallahi nima duk wadannan tambayoyi ne ke min yawo a kwakwalwa" hajiya fanaya ta fada cikin tausayawa. Murmushin da yafi kuka ciwo tayi sannan tace "bayan sati biyu na maida komai kamar ba komai ba, naci gaba da nemawa iyayena da mijina da kuma sauran mutanen da suka riga mu gidan gaskiya gafara, ba wanda nake ra'ba kuma babu mai ra'ba ta. Haka naci gaba da zaman kadaici, wani abu kawai nake tunawa naji sanyi shine cikin maharaz dake jikina, a duk lokacin da na kalli cikin sai naji tsakanin farin ciki naji kamar maharaz nake kallo, naji kamar na fito da abunda ke cikina na ganshi. Cikina na cika wata tara da kwana biyu na haifi d'ana namiji, cikin taimakon Allah nayi nakuda na gama, akwai dukiya sosai a gidan, kuma akwai dabbobi, a ciki na zabi biyu naje na kai masallaci aka yanka akayiwa yaro suna. Nayi matukar farin ciki sai dai yaron baya kamada mahaifinsa ko kaɗan, a komai na fuskarsa ni ya biyo hakama yanayin tsarin jikinsa. Ina rainon d'ana hankali kwance cikin tarbiyyar da naga mahaifinsa na da burin bashi idan yazo duniya, sai kuma Allah bai qaddara zaizo yana raye ba. Wata Rana da dare Misalin karfe takwas na dare, idrak na zaune tsakiyar parlour ba yanda banyi ba akan yayi bacci amma yaki, a lokacin kuma ya fara girma domin yanada shekaru biyu da watanni. Kwatsam naji an bude kofar dakin anshigo, a razane na tashi ganin fairozha fuskarta a hade babu alamar rahama a cikinta. Hannu na d'ora a ka ina kokarin rokonta akan kar ta cutarda mu da d'ana. Kunsan me tace?" Dayammah ta tambayi su mum dake zaune jugum-jugum suna saurarenta.......................✍🏻 44. _____________Bata jira cewar su ba taci gaba da fadin; "Sosai nake kuka kamar hawayena zasu qare saboda ina tunanin shikenan ranar rabuwata da yarona tazo, idan ta rabani dashi ina zan saka kaina, nasan ba raina take da buqata ba, domin dah rai na ne da tuni tayi yanda takeso dani. Wata gigitacciyar tsawa ta dakamin har sai da hanjin cikina suka motsa, shikuma idrak ya kwallah kara yana shirin fadowa daga kan gado da yake zaune. Kafin nayi wani yunkuri tuni fairozha ta chafe kafafunsa tayi sama dasu ta mayarda kansa ƙasa, wani kuka na sake ina neman karasawa gabanta na ceci rayuwar yarona, domin yanda nake ji a lokacin zan iya bayar da kaina fansa akansa. "Bazan cutarda yaronki ba, haka zalika kema bazan cutar da ke ba,,,,,,,Face kin kasa cika sharadin da zan gindaya miki. dayammah! Kinada sanin nasan kinsan da duk asirina dana jima ina 'boyewa kho, kuma nasan kin san komai, a yanzu duk burinki bai wuce ki tona min asiri ba kho, to bara kiji wallahi wannan shine mafi girman kuskure da zakiyi a rayuwarki idan kikace tona min asiri zakiyi. Zan ida fadamiki wani abu da baki sani ba, a wannan ƙungiya tamu muna da sirruka sosai wanda ba kowa ya sani ba, kuma ba'a fadin koda kalma daya tak ga wani mai rai da motsi da lafiya ba tare da wa'adinsa ya cika ba. Hilwah da kikaga nazo na sanarmasa, nasan lokacin sa ya riga yayi saboda nayi sacrifice din sa wa kungiya. Ke kadai kika san wannan, bayyanuwar wani al'amari ko kuma sanarda wannan labarin ga wasu to daidai yake lalacewar kungiya, idan kuma kungiya ta lalace ta dalilina to hukunci zai hau kaina, nikuma idan har hukunci ya hau kaina na rantse miki da Allah bazan barku a rayeba keda wannan d'a naki. Sannan abu na gaba dayammah ki saurareni, inaso ki tattara komanki kiyi nisa da garin nan, har abada bana bukatar sake ganinki a gidan nan daga ke har yaronki. Kuma karkiyi tunanin kamar na fita rayuwarki, ah ah....... Ina nan ciki, kuma ina bibiyar duk wani motsi naki, kamar yanda na 'batar da hamraz sannan na kashe maharaz to kema haka. da wannan d'an naki kasheku yafimin sauqi bisa ga ko wane aiki da zanyi, saboda haka ki kama kanki. Wallahi kwana daya jal na baki idan na dawo na sameki sai dai wata bake ba" Tana gama faɗin haka ta juya, kamar walqiya na nemeta na rasa, tun daga wannan lokacin na tattara komai nawa na baro garin calaba, sannan tun daga lokacin Sai dai naga fairozha a mafarki tana qara min gargadi akan kada na Bayyana labarin su ga kowa kamar dai yanda nayi wannan. Tho kunji, wannan shine takaitaccen Labarin da na sani game da iyayenku" dayammah ta fad'a a sanyaye. Kamar daga sama sukaji muryar dad ƙarami yana cewa"haqiqa akwai qamshin gskiya a labarin nan na dayammah, domin kuwa mahaifin mu yazo mana da wani baqo, kuma har ya shaida mana cewa d'an amininsa ne dake zaune garin calaba, sannan ya gayamana dashi da dukiyarsa amana ce a wurinsa, bayan haka kuma yace mana koda bayan ransa mu nemi waɗan nan mutane mu Mallaka masu dukiyarsa, Wallahil Azeem da kunsan yanda muke neman bayin Allahn nan da sai mamaki ya rufeku gaba ɗaya, ashe bamu sani ba muna tare da su har a cikin gida" "Yaushe ka shigo dad?" Khulud ta faɗa cikin sigar tambaya. 'Dan murmushi irin na Dattaku yayi sannan yace"tun lokacin da ta fara bada labari ina tsaye jikin kofa ina saurarenta, haqiqa anci amanarku, kuma an zalunceku, amma Allah baya barin azzalumi da haqqi, Wallahi indai fairozha ce bazata gama da duniya lafiya ba, ta dalilin dukiyar maharaz da dan uwansa hamraz da mahaifina ya karba amana shine dalilin da ya saka fairozha ta kashe shi har lahira". "Yanzu kina nufin kice ku dangin mu ne? Dan Allah ki amsamin kice wancan saurayin da nake gani ahalinmu ne jinin mu daya" leeyana ta fada tana fashewa da kuka. Itama Dayammah kuka take Aleena ma haka, idrak ne kadai mai taurin zuciya, amma hatta su mum dake zaune da dad ƙarami sai da sukayi hawaye. Da sauri Leeya ta miqe ta nufo Dayammah ta rungume ta tana kuka, itama Aleena ta rungume su gaba daya tana kukan. "Leeyana, indai har da gaske kike da kika bamu labarin kinyiwa mahaifiyar ki alqawarin bazaki bude fuskar ki ba har sai ranar da aka daura miki aure, to ki bude fuskar ki yanzu, domin yau andauramiki aure da yardar Ubangiji" Chak kowa ya tsaya da abunda yake kafin duk suka waiwayo suka kai dubansu ga papu dake shigowa dakin rike da wani farin bowl sabo cike damtsam da dabino da kuma alawa, har gabansu yazo ya ajiye tare da basu umurnin kowa yaci goron daurin aure ne. Ba wanda yayi wani kwakkwaran motsi a cikinsu, baramma leeya dake tsaye kamar gunki sai zanje take da zuciyar ta. Tana ji cewa bazata iya cire mayafin ta ba domin ta riga ta saba dashi tsawon shekaru. Tanaji a ranta koda ta cire to bazata iya zama babu shi a fuskar ta ba kwata kwata. Maganar da ta jiyo Papu nayi ne ta qara dawo da ita hankalinta. "Amma idan kinji baza ki iya cirewa ba shikenan kiyi zamanki da abunki, wannan ba matsala bane" Kafin wani yayi magana a cikinsu papu ya kuma kallon gahees cikin tsananin bacin rai yace"gahees kunsan kuskuren da kuka aikata kuwa, kunsan abunda kukayi tauye haqqine? Wallahi kunso kanku da yawa, akan d'a d'aya jal, zuciyoyin mutane nawa za'a 'bata a gyara ta mutum d'aya kawai......" "Wallahi da kasan Dalilin mu na yin haka da bakayi wannan furuci ba justice Khattab, amma kayi haƙuri idan komai ya dai-dai ta zanyimaka bayani, abi komai a sannu justice please" dad ƙarami ya katse papu da fadin haka. "Ba wani bayani da zan saurara daga bakinku, amma kusani komai zai zo karshe bazan lamunci wannan ba" "Justice kanada masaniyar wannan matar dake tsaye....." "Wacece?, meye had'ina da ita, banada wata alaqa da ita a yanzu, a baya alaqarmu ta aikace-aikacen gida ne kawai da take taya hajiya fanaya sunayi, daga baya kuma tazo ta nuna ta gaji da aikin har ta fara dukan 'yata har cikin bedroom ɗin ta, wannan ne ya saka na koreta domin bazan yarda da hakan ba gskiya" cewar Papu cikin matukar bacin rai. Mum ce ta kalli dad ƙarami cikin nutsuwa ta tambaye shi "baban twins, Dan Allah me akayiwa justice da zafi haka, wallahi na jima rabon da naga ya shiga yanayi irin wannan" "Hajiya kiyi hakuri, wallahi wannan maganar ba yanzu Yakamata ayita ba domin ba qaramar magana bace sanin abunda ya faru, amma kiyi hakuri idan mun gama wannan case na Dayammah sai na yimiki bayani" "Wane case ne ke tsakanin ku da ita Dayammah?" Cewar Papu a kufule. Jin tambayar nan ya saka dad qarami kallon Papu cikin nutsuwa da son tattaro magana mai ma'ana yace "Justice Khattab waasib, ka mayarda hankalin ka sosai ka saurareni. wancan matashin saurayin da ke zaune d'ane wurin maharaz, waccan yarinyar da kuka riqa tsawon shekaru wato Leeyana ita da qanwarta Aleena 'yar wajena, 'ya'yane wurin hamraz, wannan kuma da kake gani Dayammah mata ce a wurin maharaz mutanen calaba, 'ya'ya wurin aminin abbanmu mai rasuwa" "Whattt??!" Papu ya fada fuskar sa dauke da madaukakin mamaki, 'yan amana?" ya kuma fad'a kamar zai yi kuka, Allah sarki ashe muna da rabon haduwa da ahalinku, Wallahi munsha wahala sosai, a kullum addu'ar da nake bata wuce allah ya bayyana muna ku ba a duk inda kuke........" "Justice me kake nufi Ni fa bangane ba, kana nufin abunda ta fada na batun dukiya gaskiya ne?" Mum ta fad'a da kokonto a ranta. ""Hajiya, haqiqa wannan labarin da ta baki gaskiya ne, domin kuwa dukiyar su na hannun mu.......! ki sani duk kamfanonin da kika san ina ziyarta kasashen waje to ba nawa bane, na leeyana, ne da kuma qanwarta Aleena, da idrak gashi nan zaune. Sannan kuma kamfanonin jiragen sama gudu shida dake Abuja suma ba nawa bane, sai kuma kasar Kuwait da jordan suma kamfanonin masarufin da ke kasar ba nawa bane nasu ne" papu ya karashe maganar da tabbacin abunda yake cewa. A rud'e khulud ta miqe sakamakon jin abunda mahaifinta ke fad'a"papu are you serious?" "Yes Khulud my daughter, kina mamakine kho? Ko kuma kin fara jin kunyar leeya ne irin cin zarafin da kika yimata akan bata da dukiya ita yar talakawa ce, to ki sani leeyanah ba yar talakawa bace, domin dukiyar da suka mallaka a yanzu ta kasa tamu uku, kinga yanzu mune qasa, su kuma suna sama" Wani kuka ne ya kwacewa Khulud, tana tuna yanda ta dinga wulaqanta leeya, da kuma irin baqaqen maganganu da take mata. ta bangare d'aya kuwa ta qasa had'a idanu da idrak shima yanda ta dinga masa prouding a skul. Ji tayi an rungumota ta bayanta, jiki a sanyaye ta waiwayo. Sake fashewa tayi da kuka lokacin da taga leeyana ce, itama leeyanar kuka takeyi. Sake neman gafarar juna sukayi a karo na biyu, inda leeyana ta sake jaddada mata cewa bata taɓa riqeta a rai ba, kuma tun a wancan lokacin ta yafe mata domin kuwa da gaske ta changer halayenta. Karasowa tayi har gaban idrak ta durkusa cikin matsanancin kuka tace "dan Allah karka gujeni idrak, Wallahi idan baka soni ba mutuwa zanyi. Zuciya ta bata da kwari da dauriyar da zata iya hakurin rashin ka, dan Allah karka barni idrak Wallahi inasonka, karka gujeni saboda kaji kunfimu dukiya" Ba zato ba tsammani, taji yace "ban ta'ba son wata yarinya ba a rayuwata sai ke, tun ranar da kuka zo inda nake kasuwanci na fahimci halayenki sun sauya, kuma na fahimci kina sona domin kuwa na tabbatar wa kaina ke kika dakatar da Amrah da raudha wajen saka iyayensu su koreni a Rooney. Bazan gujeki ba Khulud k. Waasib, kisani idrak Manaf maharaz nakine ke kadai in Sha Allah" idrak yayi maganar murmushi kwance a fuskar sa. Miƙewa tayi tana murmushin itama while hawaye na zubowa daga idanunta, "ina sonka sosai id, Allah ya mallaka min......" "Uhmm, uhmm" badar tayi gyaran murya tun kafin Khulud ta karasa fadin abunda takeda niyyar fad'a. Ba id ba har ita khulud din sai da taji kunya, shafff ta manta a inda suke. Sake komawa tayi inda leeya ke zaune ta zabga tagumi Allah kad'ai yasan abunda take tunanowa. Dai dai lokacin da Aleena ta karaso inda leeyana ke zaune. Janye hannayen leeyana tayi daga tagumin da take tace "Yahya leeya tagumi bai dace dake ba a dai-dai wannan lokacin, ina fata zabin da akayi mana su zama alqairi a garemu, kisani mun fita daga sahun da kika sanmu a baya mun shigo wani sahun da sai mai qarfin hakuri zaici ribar zama a ciki. Kisani gata wadan nan mutane suka yimana,,,,, gata kuma wacce ba kowane mutum ne zai iya yimana ita ba, ba su sanmu ba, ba kuma su san ina muka fito ba, sun yarda da imaninsu ne kawai suka taimakemu, sun zauna damu tsakanin su da Allah, sun saka mu makaranta, sun ciyar damu, sun shayarda mu, sun tufatar damu, muka girma suka nemo 'ya'yayensu suka had'amu aure dasu. Menene abunda ya rage suyi mana Yahya leeya? Bamuda kamar mutanen nan a duniya sai kuma matar yayan Abbinmu. Yahya wallahi na rasa kalmomin da zanyi amfani dasu wajen godewa waɗan nan bayin Allah, dan Allah ki tashi muje gaban su, ki tashi muje mu nuna godiyar mu a bisa wannan dinbin alkairi da suka yi mana" Aleena ta fada kwallah na kwararomata. Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka leeya ta mike ta fara takowa gaban su mum, Papu, dad ƙarami, mummy-neesah, Khulud, badariyyah, meenal, Aneesa, twins, Dayammah da kuma Idrak duk suna zaune a parlourn. Kowa ya kasa idanu yana kallon leeya ba wanda yace uffan. Aleena kuma ganin kowa ya kife leeyana da idanu yasa ta waiwayota. Daidai lokacin da leeyana ta karasa cire mayafin da ke fuskarta gaba ɗaya. Wata irin bugawa zuciyar Aleena tayi lokacin da idanunta suka sauka cikin asalin fuskar leeyana. Su mummy-neesah da su papu kuwa suka ja da baya sosai,. khulud da su meenal kuma har sun kusa fita parloun da gudun su saboda tsanin tsorata da sukayi. Fahad, turab da zafaran kuma da shigowar su kenan suka rasa me zasuyi. Ba makawa yau tasu ta qare, dama shi wallahi yana zaton leeyanar nan ba mutum bace. Yanzu ya zasuyi kenan?" Fahad ke maganar a ransa, hanjin cikinsa kuwa sai wani yamutsawa suke da qarfinsu. Lokacin da mum ta haɗa fuska da leeya kuma wasu abubuwan suka shiga dawo mata. Mum kamar mai shafar aljanu ta kalli leeya cikin tsawa da daga murya tace "leeyana, ki gayamin asalin mahaifiyarki. Wacece ke leeyana? Ki gayamin" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Aleena kizo dan Allah. Wallahi nasan ko kowa zai gujeni ke bazaki gujeni ba, dan Allah menene a fuskata da ya saka kowa yayi nesa dani ki gayamin kinji kanwata" leeyana ta fad'a cikin kuka tana qarasowa inda Aleena take. Ganin haka sauran mutanen da basuda taurin zuciya suka qara zurawa da gudu kamar wadan da sukaga dodo ko wata halitta mai ban tsoro. Sake dakamata tsawa mum tayi kamar zata rikota tace "leeyana ba tambayarki nake ba! Wacece mahaifiyarki nace?" Kallonta leeyana tayi ido cikin ido, a yanzu ta rasa mezatayi lissafin ta gaba ɗaya ya kufcemata har bata iya yin controlling kanta tace "me kike so ki sani?" "Ina so nasan wacece mahaifiyarki, haqiqa kama ma qarya take ace mahaifiyarku daya da wannan yarinyar Aleena, zan iya yarda da mahaifiyartace a makoko wacce aka sacesu tare, amma wallahi Indai kece ban yarda da cewa wannan da kika bada labari itace mahaifiyar ki ba. Gayamin asalin gaskiyar da kike boyewa leeyana, ke mutum ce ko aljan?" Kuka mai tsanani ta fashe dashi kafin ta iya furta"Ni mutum ce wallahi, banada da hadi da wasu aljannu, don girman Allah kuyimin bayanin abunda nakeso na sani menene a fuskata dan Allah?" "Ba komai a fuskar ki yayata, kuma koda kowa ya yarda da cewa ke ba mutum bace Wallahi bazan ta'ba yarda ba. ki kwantarda hankalinki, muje mirror ki kalli kanki" "Kafin nan Aleena!, nace kafin naje mirror ki gayamin dan Allah" "Yahya ta, wallahil Azeem kyawunki ya yi yawa, ya yi yawan da ba'a iya fahimtar mutum ce ke ko bil'adama, wallahi da ace bakya saka mayafi da yanzu sai wata bake ba, abune mawuyaci a sami mai irin halittar nan taki, kwata kwata ba halittar mutane bace dake, kinfi shiga da jinsin aljanu shiyasa mutane suke gudu, kowa da kika gani a wajen nan a rikece yake yana gani kamar cutardashi zakiyi idan kika karaso inda yake" Zaman dirshem tayi a kasa ta dafe kanta dake neman tarwatse wa. "Leeyana dan Allah ki gayamin asalin gaskiyar wacece mahaifiyarki, wallahi na fara wani tunani a kanki" taji Muryar mum a sanyeye kamar zata fashe da kuka. "Bansan wacece mahaifiyata ba, bansan asalinta ba, ban san dangintaba, wallahi ita kadai na sani sai abbina da kuma qanwata Aleena" "Menene cikakken sunan mahaifiyarki??" "Faheema Rawaan Hahmeed". "Whattt??????" Mum ta fad'a baki na rawa. A lokacin da sunan nan yaje kunnen papu da turab basu san lokacin da suka qaraso gaban leeya ba su duka ukun mum, turab, da kuma Papu. "Leeyanah zo gareni, kizo gareni leeyanah nice mahaifiyarki, kuzo 'ya'yana" mum ta fad'a cikin Muryar kuka tana ware musu hannayenta biyu alamar suzo. Kamar kuwa jira suke suka fad'o jikinta sai kuka suke su duka ukun gwanin ban tausayi. Turab da Papu ma suna tsaye suna kallon ikon Allah da dimbin mamaki, hatta mommy neesah da dad qarami da suka san asalin sunan hajiya fanaya sai da suka kwashi taslimah jin suna nan da leeya ta fada. Basu san ko wacece ita ba, ba kuma susan ina ta fito ba, amma sun tabbatar da koma wacece tanada alaqa da mahaifiyarsu. Janye jikinta tayi daga nasu tana shafa fuskar leeya, a hankali ta furta "Masha Allahu fi ahsanil kaliqiin" kinada kama sosai da mahaifiyarki, sai dai ke kinfita kyau nesa ba kusa ba, amma kuma duk wanda yasan ta farin sani daga zarar ya ganki zai fahimci kinada alaqa sosai da ita. Ba banza ba danaji ina qaunarki tun ranarda na fara ganinki a bakin hanya, Allah ya sakamin qaunarki da tausayinki, a she soyayyar jini ce leeyanah ke ƴa tace" "Mum, Nagode sosai da duk wata qauna da kuka nunamin. Kuma ina roqon Allah yasa ku jera kafad'a da annabi wajen shiga aljanna akan wannan, Amma mum har wannan da kike gani qanwatace, mahaifi da mahaiyarmu d'aya da ita" leeya ta fad'a tana kallon Aleena dake tsaye. Ita bata gane komai ba, wannan matar tana fadin mahaifiyarsu ce, amma kuma bata san alaqarsu da ita ba, a yanda take nunawa ma kamar itace ta haifi leeyanah, taya haka zata faru? Riko hannun Aleena mum tayi tana shafa kanta cikin tsanin so da qaunar su tace " Allah yayi muku albarka, nasan labarin da zaku bani akan faheema bai wuce kuce ta rasu ba. Tunda naga kunyi fama da rayuwa har haka nasan bata raye, Allah ya jikanta yayi mata rahama, Allah yasa ta huta, Allah ya yafemata kurakuranta dan darajar fiyayyen halitta" Tun kafin su leeyana suce wani abu Dayammah ta tari numfashin mum cikin tsananin mamaki da rashin gane makamar zancen ta tace "hajiya kema kinsan wani abu game da yaran nan ko kuma mahaifiyar su?" Sai da mum ta isa kan sofa ta zauna tare da d'aga kanta sama kadan kamar mai wani tunanin hawaye na zubowa a hankali daga cikin idanunta tace "nasan mahaifiyarsu, mahaifi da mahaiyarmu d'aya da ita, mu biyu ne kacal Allah ya bawa iyayenmu, mahaifiyarsu faheema itace yahyah a wurina nikuma ina matsayin qanwarta. Mahaifinmu ya kasance mutum ne mai tsanani akan abunda ya saka gaba, kuma babu abunda ya tsana kamar cin amana da kuma karya alqawari, mahaifinmu Rawaan Hahmeed mutum ne mai saurin fahimta da sauqin kai, sai dai kuma baya so ya nuna ya isa dakai kai kuma ka nuna masa bai isaba, mu ba masu kudi bane amma muna da rufin asirin Allah sosai. Domin za'a iya sakamu tsaka tsakiya. Sana'ar mahaifinmu itace ya sauke masuyin cirani ya basu masauki, a kwai wurare da dama da aka ke'be a wajen gidan mu inda ake sauke mutane komai yawansu. Mahaifinmu nada wani yardajen amininsa dake daura jahar katsina, wata rana aminin mahaifinmu yazo kawo mana ziyara da babban d'an sa su biyu, sun jima a gidan mu kafin su tafi bayan mahaifinmu ya gabatar da mu wajen Aminin nasa har kuma babban d'ansa da yazo dashi ya nuna yana son faheema mahaifiyar ku. Abu kamar wasa soyayya mai karfi ta kullu tsakanin su harda maganar aure. Ana cikin hakane kuma wata qaddara ta afku akan faheema, ba kowace qaddara bace face ta soyayya. faheema ta kamu da matsananciyar soyayyar wani bako da ya sauka gidanmu cikin yan ciranin da ke zaune tare damu, mutane da yawa sun tabbatar da cewa babu wanda ya sanshi, kuma babu wanda ya taba ganinshi ko a wani wurin, hasali ma mu'amalarsa ta bambanta da ta sauran mutanen da ke wurin, kuma sannan baiyi kamada ya'yan hausawa ba ko kadan, duba da yanayin maganarsa. Abu kamar wasa magana tayi karfi tsakanin mahaifin mu da faheema, ita ta tubure akan bazata auri wanchan ba wannan takeso, kuma mahaifinmu ya riga ya karbi sadaki har ansaka rana sati biyu masu zuwa. Wani Abun bakin cikin ma da aka kira shi wannan da takeso aka tambaye shi wani abu game dashi ba wata gamsasshiyar amsa da ya bayar, amma kuma shima ya nuna mana irin tsananin qaunarta da yakeyi, a lokacin kuma nima inada manemi domin kusan ma lokaci daya aka shirya dauramana aure da ita. Mahaifinmu ya gargademu akan bayason wannan Magana ta fita domin bayaso a dinga yimasa kallon mutumin banza, in takaice muku ma hatta su iyayen angon basu san da wannan matsalar ba, shidai kawai yaga sauyine a tattare da ita ba kadan ba, amma dayake mai hakuri da yawan uzuri bai taba kawo kararta wurin iyayenmu ba. Anyimata iyaka sosai da wannan bakon mutumin, kuma mahaifinmu mutum ne mai gaskiya cikin al'amurran sa, shiyasa bai kori bakon mutumin a gidanmu domin yawan kudin da ya bada ko rabin su bai ci ba. Ana washe gari za'a dauramana aure ne cikin dare faheema ta kasa bacci sai kuka take da tunani, mikewa nayi zaune na rarrasheta hadi da ban baki domin tayi shiru ta daina kuka ta yarda komai nufin Allah ne. "Dan Allah karki manta dani fanaya, inaji kamar bazamu sake haduwa ba. Ko ba komai zanyi nisa dake sosai" "Haba dai, ki daina wannan maganar kinji. aure zakiyi fa, in Sha Allah babu abunda zai faru dake yar uwata" "Inaso ki bani wannan zoben na hannunki ko zan dinga kallonsa naji kamar muna tare dake" Murmushi na mata lokaci daya kuma hawaye na zuba daga cikin idanuna, hakika ba wanda ya siyamin zoben da ke hannunta, amma wallahi ina matukar kaunar zoben da ta nemi na bata. Idan za'a ce in lissafa abubuwanda nafi qauna a rayuwata Wallahi nasan zoben nan zai shigo a cikin abunda zan fada. Ganin da gaske ne nisan zatayi dani ya sa na cire zoben na saka mata "yar uwata dan Allah kiyimin alqawarin zaki riqe zoben nan da amana, sannan kuma ki dinga tunawa dani a duk lokacin da kike tare da zoben nan, idan kinyi aure kinzo gida ganin mu bazan fara tambayar komai ba sai shi idan kuma kika gayamin wani abu sabanin abunda nakeson ji, shikenan ba ruwana dake tunda nasan kin manta dani ne kawai" "In Sha Allah komai nisan da nayi zan kula da zoben nan fiye da komai fanaya, ki saka wannan a ranki" Mahaifiyarku faheema ta fadi haka tana qara daidaita zoben a yatsanta. Da haka dai har bacci ya daukemu gaba daya. Koda safiya ta waye ban ganta a dakin ba domin kuwa ban tashi da wuri ba yau ko sallahr asuba banyi cikin lokaci ba, dubana na kai kan shinfidar ta nayi murmushi kawai ina tuna yanda mukayi da ita jiya tana wasu maganganu kamar mai shirin barin duniya. Ban nemeta ba domin nasan tana dakin mahaifiyarmu ko kuma tsakar gidan duk da yawan jama'a yan bikin daura aure da suke faman tururuwa. Munsha kitso da lalle ga kuma gyara irin wanda akeyiwa amare kana gani ba sai an cemaka komai ba. Nasha mamaki sosai danaga har rana ta hudo ban ganta ba, kuma bata tsakar gidan, dakin iyayenmu ne kawai banshiga ba saboda ina jin kunyar wasu mutanen da ke zaune a dakin. Sai dai wani abun tsoro da mamaki ina zaune a dakinmu nida qawayena da sukazo tayani zama sai ga wata mata ta shigo da sallamar ta tace wai ummanmu na neman faheema. Da mamakina na kalleta na kuma tambayar ta faheema ko kuma ni, domin ita faheema bata nan tunda na tashi daga bacci bansakata a idanuna ba. Wannan dalilin ne ya saka nayi tunanin ko tana wurin umantamu. Abu kamar wasa har magana ta fito fili akayi neman duniya a gidan babu ita babu labarin ta. Dawowa nayi cikin dakin mu domin ni ban gasgata abunda yake faruwa ba cewar wai an nemi ta a ko'ina ba'a ganta ba. Duk wani lungu da saqo da ke cikin dakinmu dubawa nake ko Allah zai saka na ganta amma banganta ba, gadonda take bacci na nufa tare ta fatar Allah yasa in ganta idan na daga bargonda nake hangowa daga nan inda nake. Duk da nasan abune mawuyaci a sameta akan gado yanzu. Ina zuwa na d'aga bargon da karfi banga komai ba sai wata nadaddiyar takarda ta fado daga cikinsa. Hannu na rawa kamar mazari na buɗe takarda na karanta, abunda na gani a ciki ne ya saka na zube wurin bansan wane hali nake ciki ba sai jina nayi a ɗakin ummanmu. A hankali na fara buɗe idanuna ina kallon kowa dake zaune a dakin anyi cirko-cirko. Sake murtsika idanuna nayi cikin Muryar kuka nace "dan Allah umma kada ku gasgata mafarkina, dan Allah kuce banga wasiqar da faheema ta ajiyeba duk mafarki nake kinji ummana" Dan guntun hawaye ummanmu ta share sannan tace "kwantar da hankalinki fanaya, Allah ba azzalumin kowa bane idan faheema ta zaluncemu Allah bazai bartaba, babban tashin hankalina shine dangin mijinta duk suna nan suna jira. Baramma mahaifinku dake can waje yana jira lokacin daura aure yayi a daura. Maganar nan da muke yanzu saura mintuna Takwas ne a daura aurenku, taya zan gayawa Rawaan faheema ta gudu da bakon mutumin nan, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un Allahummah ajirnee fiii musibatii, wa'akhlifnii khairan min ha" mahaifiyarmu ta karashe maganar da kuka mara sauti. Tausayin ta ya kamani sosai ganin yanda muka tara jama'a dangi da wad'anda ba dangi ba. "Ummah me zai hana ki kira yaya arman (babban d'an yayan mahaifinmu kenan) sannan kuma ki kira uncle Bahar da kuma uncle Dawud ki sanar musu da komai tun kafin a daura auren tunda kinga lokaci kurewa yakeyi" Nima na fada cikin karayar zuciya. Da shawarar nan mahaifiyata da kuma babbar amintacciyar ta sannan kuma da qanwarta da suke uba d'aya mukayi amfani wajen sanarwa da kanin mahaifinmu da kuma yayansa sannan da babban d'a a cikin familyn mu. Koda aka sanarmusu sunyi Allah wadai da halin faheema sosai, kuma sun jinjina rashin hankali da kuma rashin wayonta da har zata dauki kafa ta gudu da wani saurayi. Saurayin ma ba'ko wanda ba'a san asalin sa ba. Koda suka sami mahaifinmu da wannan maganar zuciyar sa kusan bugawa tayi domin sai da aka tafi dashi asibiti aka bar komai hannun uncle Dawud. Shikuma uncle Dawud da yazo ya sami mahaifin angon da faheema zata aura da kuma shi angon ya gayamasu gaskiyar komai bai boyemusu ba anan kuma ya shaidarwa da ango baza'a a fasa daura auren ba za'a Daura. Saidai ba da faheema da 'yar wajensa idan ya yarda, ango kuwa bai watsa musu qasa a ido ba ya nuna amincewarsa ɗari bisa dari akan hadin da sukayi. Lokaci na cika kuwa aka daura aurena da angona, shikuma angon da akayi niyyar daura aurensa da faheema aka fasa aka daura masa aure da 'yar wajen uncle Dawud Babba a cikin 'ya'yans. Har muka sami wata d'aya da aure ana ta jinyar mahaifinmu da ciwon da ya shigeshi rana daya. Mun kwashe tsawon watanni takwas babu wani sauqi kullum abu gaba yake zuwa. Mu ba masu kudi bane, amma kuma akwai manyan masu kudi da 'yan kasuwa sosai a cikin danginmu, shiyasa sukayi shawarar fita dashi waje a duba lafiyarsa. Ana washe gari za'a yi tafiyar ne kusan asuba ciwon mahaifinmu yayi tsanani, kafin akai ga kiran sallahr Asuba Allah ya karbi ransa. Amma wallahi bai mutu ba sai da ya furta kalmar yafiya ga faheema, yace ya yafemata ta dawo ta ci gaba da rayuwa cikin danginta, sannan kuma ya yarda ya amince da aurensu Allah ya saka masa albarka. Da wadannan maganganu a cikin bakinsa har ya bar duniya Munsha kuka sosai, dangi dana kusa da na nesa sai Allah ya isa akeyiwa faheema musamman ma dangin da suka fito daga bangaren mahaifin mu suna ta munanan furuci akanta. Dana ji munanan kalaman da suke akan yar uwata sun isheni na tashi da kausa-sasshiyar murya nace "ya isa haka dan Allah, menene amfanin munanata da kukeyi, ita qaddara idan zata zo bata shawara da kowa take zuwa, haka zalika ba wanda yasan dame zatazo, kuna ta fadar faheema ta kasha Abba taya ta kasheshi wacce a halin yanzu bata ma san abinda ke faruwa ba, qaddara ce tazo. Kuma a kanta ta fad'a. komai yanada sanadi a duniyarnan, Allah yayi sana'ar mahaifinmu ce zata yi sanadin komai na chanjawar rayuwarsa. Da a ce bayayin sana'ar sauke ba'kin mutanen cirani, bansan inda faheema zata ganshi ba har ta bishi su gudu ba. A wannan maganar idan akayi tunani cikin aikin nutsuwa da hankali to faheema ba ita bace sanadin mutuwar Abba ba, shine da kansa sanadin mutuwar ke hannunsa. Saboda haka na rokeku dan girman Allah kudaina zaginta. Kuma abbanmu bai rasu ba sai da ya furtamata kalmar yafiya, saboda haka ko kun tsinemata ba inda tsinuwar zataje tunda mahaifin ta ya riga da ya yafe mata" Duk jikinsu yayi sanyi likiss da abunda na fad'a daga nan kuma kowa ya ja baki yayi shiru ba wanda ya qara magana akan haka. Lokaci ya jaaa sosai abunda zai faru dai ya riga ya faru, mun rasa mutane biyu daga cikinmu, muka saka salama a cikin ranmu muka manta da komai kamar ba'a yi ba. Bayan watanni kuma wani iftila'i ya afku akanmu, cikin tsakiyar hantsi Yan boko haram suka sauka a Maiduguri sukayi kan mai uwa da wabi. Mun samu nasarar tserewa ba tare da wani ya cutu tsakanina da mahaiyarmu, muna fita Maiduguri kuma muka dauki hanyar Bauchi domin a can ma munada wasu dangi da dama, koda muka je Bauchi ma mun tarar da wasu danginmu dake Maiduguri anata sam barka, anan muka sake kafa wata sabuwar zumunta. Yanzu maganar nan da nake miki gaba dayan danginmu suna bauchi d'ai-d'ai ku daga cikinsu ne Bama tare dasu. Nan mukaci gaba da rayuwa da dangina, saidai Ni tuni mijina ya daukeni muka koma abuja da zama bayan anyi masa qarin matsayi a wurin aiki. Sai bayan an haifi khulud ne muka dawo suleja da zama. Amma yanzu duk dangin namu sun koma gida, mafi akasarin su duk sun koma Maiduguri. Babban albishir ɗin da nake yimuku leeyanah shine ummanmu tana raye, kuma itama ta yafewa faheema, sannan da yawa daga cikin danginmu duk sun yafemata domin suna ganin kamar duk inda taje zata dawo, wasu kuma suna ganin ta dawo amma ta tarar da an tarwatsa mutanen Maiduguri. Alhmdullillah ya Allah ina qara jaddada godia ta agareka, kaine sarki ɗaya tak, kaine muke nufa da buqatun mu ya Allah na gode maka da ka qarfi addu'a ta. Allah kabani ikon yiwa marayun nan naka gata wacce iyaye suke yiwa 'yayansu" Mum fanaya ta fad'a hawaye na sakkomata amma a fuskar ta murmushi ne kwance. Rungume su tayi tsamm a jikinta tanajin qaunar su na qara ratsata. Wata sabuwar qauna takeji game da yar uwarta faheema sai dai ba halin nuna qauna gareta tunda bata nan. Saboda hakane yasa takejin qaunar leeya da Aleena na Ratsa ko'ina na sassan jikin ta. Ba wanda baya hawaye a Dakin bayan mazan da suke tsaye, musamman ma Khulud hawayenta yafi na kowa ita har ranta kunya takeji wai ashe ma yar uwarta ce ta jini ta dinga wulaqantawa da tozarci. Zuwa tayi gabansu itama ta rungumesu tana hawaye, turab da papu kuma suka qaraso suka zauna. Fahad, da zafaran da kuma dad qarami suka zauna kan sofa's dinda ke farkon shigowa parlourn. Turab kam inda mum take ya nufa shima ya zauna kusa da ita sosai, ya kwantar da kansa a kafadar ta ya lumshe idanun sa. Juyowa tayi gareshi lokacin da ya kwantar da kan nasa taji shi rad'au, da alama bashida lafiya ne akwai abunda ke damunsa. Sake godiya da tazbihi tayi acikin ranta tana qara godewa Allah daya albarka ceta da wadannan yara. "Allah ya kara shiryamin ku, Allah ya raya ku bisa tafarki madaidaici" ta fad'a a fili duk suka amsa da "Ameeen" "Fanaya Rawaan Hahmeed, ina miki murna da samun 'ya'yan 'yar uwarki cikin koshin lafiya, Allah ya rayasu ya qara hadin kanku, Allah Ubangiji ya jikanta ya yafe mata kurakuranta yakai haske kabarinta" cewar papu yana kallon fanaya. "Ameen ya rabbi justice, godiya maras adadi. Allah ya jikan faheema da kuma sauran muminan da suka rigamu gidan gskiya" Kowa ya amsa addu'ar mum sai papu ne kadai da ya yi zurfi a cikin tunanin da yake. Magana mum ta fara yimasa sai dai hankalinsa baya wurinta. Kallon ta ta mayar ga baban twins wato dad qarami fuskar ta dauke da damuwa tace "baban twins dan Allah kabani labarin abinda da yake faruwa da justice na kasa gane masa tunda ya dawo gidan nan sanin ba haka muka saba ba, kana ganinsa kasan yana dauke da damuwa, meyake faruwa" ~Awanni biyu da suka gabata~ Tafe suke su biyu kadai sai kuma driver a cikin wata rantsatstsiyar farar mota sai kyalli take kamar madubi idan ka tsaya kusa da ita. Sunci ado dakyau komai nasu iri daya ba abunda ya banbanta kama daga kalar shigarda sukayi. Motar tasu tayi packing ne a harabar babban central mosque dinda yake gaba da unguwar su kad'an, duk wanda ya gansu yasan suna cikin farin ciki da nishadi. Fitowa sukayi lokacin da motar ta yi packing suka nufi cikin masallacin juma'a mutane ma sai tururuwa suke ganin lokacin sallah ya gabato. Dad qarami ne ya kalli papu fuska dauke da fara'a yace "Justice meyasaka ka hana yaran nan zuwa masallacin nan?" Shima papu da murmushi a fuskar sa ya bashi amsa "Nafiso ayi komai yanda na tsara, bana so a sami kuskure shiyasa na dakadardasu daga zuwa masallacin nan suje na gaba da nan idan aka daura auren sai a sanar musu" "To amma justice abokansu fa da suka gayyato" "Kowa ya zauna a daura auren a gabansa mana, ai wannan ba matsala bane in yaso idan an gama sai su kirasu a waya, kuma ma duk abokansu da suka gayyato idan suka ganmu ba wata magana ai" "Tau shikenan Allah ya sanya alƙairi ya sa hakan da muka yi shine daidai" "Ameen ya rabbi" papu ya fad'a daidai lokacin da suka qaraso kofar shiga Masallacin. Fara gaisawa sukayi da mutane har suka isa inda zasuyi sallahr, basu jima da zama ba aka tayarda sallar juma'a, bayan an idar ne kuma aka fara gabatar da adadin auren d za'a daura. Nan limamin ya fara karanto sunan yaran da za'a daurawa aure da kuma mazajen da zasu auresu ciki harda su leeyanah. Sunan da aka d'aura na karshe ne da kuma wanda aka ambata a matsayin ango ne ya saka papu mikewa ba shiri ya fita Masallacin kamar wani zararre. Duk irin iskar da ke faman kad'awa sakamakon bishiyoyin lim dake zagaye da masallacin bai hana papu jin zufa da zafi na kwararo masa ta ko'ina a sassan jikinsa ba, sai sharce zufa yake yana fifita da hularda ke kansa fad'i yake yana cewa; "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, taya wannan auren zai yiwu. Taya wannan babban al'amari ya faru. Idan na aikata haka na so kaina, meyasa zan 'bata farin cikin mutanen dayawa akan na farantawa kaina Ni d'aya tak ya subhanallah. Allah ka sanya wannan lamarin yazo da sauki ya rabbi kana gani bani na aikata haka, taya duk wannan zai faru alhali ba haka na bayar ba......" Yana cikin yin zancen ne a fili yaji an dafa kafad'arsa ta baya. Juyowar da zaiyi ne yayi ido biyu da gahees dafe da kafad'arsa, tun kafin gahees yayi magana papu ya tare shi da fadin "wallahi ba Ni na aikata ba, to wa zaiyi haka gahees, dan Allah ka sanardani zuciyata gaf take da sarewa domin kunya ce danqare a ciki, don girman Allah ka sanar dani wani abu" Murmushi dad ƙarami yayi yana bubbuga kafad'ar papu a hankali yace "kwantar da hankalin ka justice, kanaso mu kashe kan mu da kanmu ne, idan har ina da abu kuma samun abun bai fi qarfi na ba wallahi zan iya sadaukarda shi ga yarona saboda yayi farin ciki. Ina tunani kamar ka manta d'ana yana dauke da wannan cutar kho, kasan Ni likita ne, kuma a bakina kuka fara jin cutar da yake dauke da ita, shin saboda na boye ban gayamuku illar abunda kuke shirin yi bane yasa ku bazakuyi tunani da kanku ba, kasani danmu yana dauke da cutar (BPD) borderline personality disorder, wannan cutar cutace mai hadarin gaske Justice. Nasan duk yanda zanyi maka bayani bazaka gane ba, amma zan takaitamaka ko da zaka iya fahimta, borderline personality disorder the mental health disorder marked by intense emotions and unstable relationships. People with BPD often fear abandonment and have difficulty managing their feelings. They may struggle with self-image, impulsive behavior, and mood swings. requires professional help like therapy to manage symptoms and improve quality of life. Wannan ma'anar cutar kawai na baka, lokacin da kuka fara kawoshi kaga wasu alamomi a tattare dashi kho, tun a lokacin naso sanar maka da illolin cutar nan ganin hankalin ka baya kwance yasa nayi shiru har zuwa lokacin da wani abun zai taso. This disorder makes a person very sensitive emotionally. They need constant care and can get very upset if things don’t go their way. Stress and negative feelings can seriously affect their mental health. Justice d'a namiji ɗaya tak Allah ya baku, kuma yana dauke da wannan babbar larura shin bazaku tausayamasa ku nema masa farin ciki da kanku ba, kwantar da hankalin ka muje gida yanzu" Dad ƙarami ya fad'a yana rike hannunsa zuwa mota, jikin papu yayi sanyi sosai da jin abunda dad qarami ya fad'a, yasan gaskiya ce ya fad'a, to ya zaiyi shi kansa yasan yaso kansa da yawa duk da ba shi ya sauya komai ba, amma ga Dukkan alama aikin dad qarami ne. *Wannan shine abunda ya faru a masallaci wurin daura aure, kuma ana kammala wa dad qarami ya kira yaran gaba ɗaya ya sanar musu an daura aure, tsakanin zafaran da kuma turab ba wanda yayi gigin tambayar matar da aka aura masa domin sun fahimci kamar ran dad qarami 'bace yake. "Allah sarki, to Allah ya sanya alƙairi a auren nan, kuma Allah ya bada zaman lafiya. Dan Allah ina neman wata alfarma guda d'aya rak" cewar mum tana shafa kan Aleena dake kwance a cinyarta. Dad qarami da ya harbo jirgin ta yayi saurin cewa "yawwa, iyayen zohal sun tuntuɓeni maganar daukar amarya. Na yanke shawarar a abuja zasu zauna gaba ɗaya, kuma a sababbin gidajena dana gina kwanakin nan, na saka an gyara ko'ina kuma an Na saka furnitures sun sa komai a ciki, ga address din gidajen kowa a cikin ku ya dauki arear da yakeso ya zauna da iyalansa idan kun gama dubawa sai ku sanarda ni a fara shirin tafiya" cewar dad ƙarami yana miqawa Fahad da zafaran da kuma Turab wasu takardu, da alama sune takardun address din. Dubansa ya kuma kai ga yaran yace, "Rukhshanah, ko kuma dai nace Aleena, my sweet daughter ki tashi kije ki fara shirin tafiya gidan mijinki kinji yar albarka" dad qarami ya fad'a da shigar rarrashi. Da kuka sosai ta tashi da gudu ta nufi mummy-neesah ta rungume ta tana faɗin "mummy dan Allah kice na fasa auren, Wallahi bazan iya tafiya na barku ba Please mummy kicewa dad a fasa dan Allah, fannah mayah kuna gani za'a rabamu banason tafiya dan Allah" da gudu suma fannah da mayah suka nufo inda take suka rungumeta suna kuka da magiya akan afasa da auren. Dariya ma suka bawa kowa dake wurin "aure kam an riga an daura ai" cewar dad qarami cikin ransa. "Dad kace ya saketa har ta girma, wallahi munyi alqawarin idan ta girma zamu kai ta da hannunmu ba ma sai ya zo ba" A wannan karon kam papu ya kasa riqe dariyar sa har sai da yayi sannan yace"to ai ba anan garin yake ba, bakiji ance Abuja zasu zauna ba, means mijin d'an Abuja ne kho?" "Ehh" twins suka fada kamar wasu qananun yara. "To sai munje da ita rukhsha, idan mukaje sai mu nuna masa qarama ce bata girma ba, a saketa sai ta isa aure zaku kawota da kanku" "Eh papu, wallahi a gayamasa haka munyi alqawari, kuma damu za'a je muyi masa alqawari da kanmu" "No my twins basai anje daku ba, in sha Allah yanda mukaje da ita lafiya haka zata dawo lafiya. Kunga lalla'ba shi za'a yi yayi sakin, wata qila idan mukaje da ku zai iya qin yarda da abunda mukazo masa dashi, zai yi tunanin kamar mun tara masa mutane ne". Ba dan sun so ba suka amince ayi tafiyar ba tare da su ba, amma a tabbatar cewa an dawo musu da rukhshan su gida yau. Da kyar da sudin goshi suka amince har ita Rukhshanah din, inda aka umurci leeya itama taje ta shirya babu 'bata Lokaci, kuma a cikin tsatstsauran hukuncin dad qarami yace ba wanda zaije abuja acikin yaran, iyayen yaran kawai aka kira suyi rakiya. Aunty saknah da kuma aunty Rafa'at qannen su papu mata kenan. Aunty saknah aka had'a ta da Rukhshanah da kuma Mummy-neesah domin rukhsha taki yarda su rabu da mummy ko nan da chan. Ita kuma leeya aka had'a ta da aunty Rafa'at kad'ai, domin mum bazai yiwu taje ba tunda da ita za'a je daukar matar fahad wato zohal. Sai a lokacin da aka gama tsara komai dad qarami ya kalli mum yace fadi alfarmar da kikace kina so ayi miki. Cikin d'an jin haushi mum tayi murmushi kawai tace "baban twins kenan kuci gaba da aikinku kawai daga baya mayi Magana" Murmushi shima yayi kaana ya umurci Aunty saknah da kuma Aunty Rafa'at suje su taya yaran had'a kayayyakin su. Leeya kam sosai take kuka kamar ranta zai fita ga Khulud itama da take jin leeya kamar wani bangare na jikinta a yanzun nan, take ji ina ma ace yanzu ne zasu fara rayuwa, sai gashi lokacin da komai ya bayyana, a lokacin kuma aka rabasu. Id ganin Khulud na kuka Sosai gwanin ban tausayi ya sakashi fita daga parlorn, haka kurum yake ji bazai iya jure ganin hawayenta ba. Yana fita parloun ya nufi wani bangare na gidan ya sami wuri ya zauna, kiran number din ta ya fara bugu hudu ta dauka. Tun a cikin wayar ya fara rarrashinta har sai da yaji tayi shiru ta daina kuka. Awanni kad'an aka gama hada musu komai nasu, sannan su haji-mainah da mum da kuma maman twins da su Aunty saknah suka zaunar da su sukayi musu nasiha sosai akan hakuri da kuma juriya a zaman aure, nasiha sosai sukayi musu mai ratsa jiki, tun lokacin da aka fara yimusu nasihar suke zubarda hawaye har aka gama ana shirin tafiya. Da gudu leeya taje ga mum fanaya ta rungume ta tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. mum kuma hawaye take kawai murmushi kwance a fuskar ta tana yimata magana a hankali yanda ba kowa yake iya jiyota ba, "kiyi hakuri kinji, in sha Allah nan da sati ɗaya komai zai daidai ta. Naso a d'aga wannan tafiyar kafin a shiryaku, a gyara ku. Amma kuma naga kamar baban twins baya son hakan yanzu shiyasa nayi shiru kawai, amma nan da sati ɗaya in sha Allah komai zai daidaita zamuje har Maiduguri da ku kusan dangi, suma su sanku kinji 'yar albarka, Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa da mijinki, Allah ya baku hakurin zaman aure ya albarka ce ku samu tsaftatacciyar zuri'a" Leeya da kuka yaci qarfin ta qasa cewa komai tayi sai kuka take yi har Aunty Rafa'at tazo ta ja hannunta tana rarrashinta suka wuce mota. tana tafiya tana waigen su mum da su meenal, khulud, fannah, da mayah, Aneesa da kuma badariyyah. Suma suna tsaya sunyi cirko-cirko abin murna ya dawo kamar na kuka. Misalin ƙarfe shida na yamma suka dauki hanyar Abuja, leeyanah kaɗai Sai aunty Rafa'at sai kuma driver da zai kaisu. A hanya ma leeya bata daina kuka ba abun ka da farar fata fuskar ta tayi jajir kamar gauta, aunty Rafa'at kam sai d'ari-d'ari take, domin da ba'a gabanta mum ta rungume ta ba babu abunda zai saka ta shigo mota d'aya da ita ba, taso tayi tambaya amma kuma ganin ana uzurce yasa tayi gummm da bakinta, hatta driver kallo ɗaya yayi wa fuskar leeya ya rud'e domin ya haqiqance aljana ya dauko shiyasa yaketa sheqa gudu babu daddaukawa domin ya tserar da ransa. Itama aunty Rafa'at sai zancen zuci take domin ko leeya da kanta zata faɗa mata cewar ita ba aljana bace bazata yarda don tasan babu inda za'a sami halittar dan Adam mai kyau da tsari haka kuma a kirata da mutum. "Idan mutum ce wane irin kyawu Allah ya bata haka". Da misalin ƙarfe bakwai na yamma suka karaso, da yake an kwatantawa drivern estate ɗin yasa bai wani sha wahalar ganewa ba. Wani tangamemen gida ne da ya amsa sunansa gida, tsayi fadar kyau da tsari irin na gidan bata lokaci ne domin bazai fad'u ba sai wanda ya gani da idanunsa. Packing yayi a madaicin packing space din gidan, da drivern da mai gadi suka shiga da kayan da su leeya sukazo dasu. Leeya kuma tana bacci bata ma san sun iso ba sai ji tayi ana kiran sunanta a hankali. 'Dago jajayen idanunta tayi ta kalli aunty Rafa'at tace "Aunty mun qaraso ne?" "Eh mun qaraso leeyanah, kinata bacci" "Wallahi aunty bansan zuwan baccin ba ina ta tunanin mum" "Allah sarki, aikuwa mun qaraso fito kiga gidan ki leeyana, gidan da muke miki fatar kasancewa har qarshen rayuwarku" Jiki a sanyaye ta zuro qafarta waje gabanta na duka uku-uku, kasa d'aga 'kafar tayi nan take ta fashe da kuka mai sauti. Tana tunani barkatai a zuciyarta, shikenan yanzu nan zata ci gaba da rayuwa, ba mum, ba zohal ba papu, ba Aleena kuma. Ga sabuwar amintacciyar ta meenal itama babu ita. Haka taci gaba da zance a zuciyarta sai kuka take. Abunda leeya ta manta shine Aleena da zohal duk a abuja suke domin suma anan aka basu estate. Tunowa da hakan da tayi ya saka ta d'an tsagaita kukanta sai matsar ƙwallah kawai. Aunty Rafa'at kuma sai ban baki take tana bata hakuri da guntayen nasihohin manzo Sallallahu alaihi Wasallama. Miƙewa tayi ta fito daga motar jikinta duk ba kwari ta fara takawa sannu a hankali tana kallon yanayin tsarin gidan a fakaice. Har suka isa Tsakiyar kasaitaccen parlorn ta ba wanda yayi magana a tsakanin su. Sai dai kafin ta shiga Aunty Rafa'at ta umurce ta da yin Addu'o'i daban daban wadanda manzon Rahma yayi umurni dasu a daidai wannan yanayin na sabuwar rayuwa. Aunty Rafa'at ta sha mamaki sosai ta kuma ji dadi ganin yanda leeya ta dinga karanto Addu'oin neman tsari da kariya da kuma samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aurenta. Nan aunty Rafa'at taji leeya ta qara shiga ranta, kuma ta qara yaba hankalin ta da nutsuwarta. Komai na parlourn tsaf-tsaf gwanin ban sha'awa, kuma tsarin parlourn yayi dai-dai da mace mai tsafta kamar leeya domin komai na parlorn adon fari ne sol da ratsin golden ba sosai ba. Zama sukayi cikin daya daga kujerun furnitures din da akayi order daga Saudiyya gwanin kyau kamar ka sace ka gudu. Leeya na zaune ta kasa d'aga kanta, sai 'kullawa da kuncewa take cikin zuciyar ta. Aunty Rafa'at kuma tana zama ta shiga kitchen ta d'akko cup da ruwa masu sanyi ta bawa leeya. "Bana sha, na qoshi aunty" leeya ta fad'a cikin sanyinta. "Leeyanah Please dan Allah karki saka damuwa cikin ranki, wallahi da nice ke babu wani abu da zai baqantamin rai a fad'in wannan duniyar yanzu, kinga na farko sama da shekaru goma kuna gararamba baki San dangin mahaifiyarki ba balle na mahaifinki, sai gashi yau da rana tsaka Allah ya bayyana miki su cikin tsatso mafi albarka da asali da Dattaku. Sannan abu na biyu yau Allah ya d'aga darajar ki, burin ko wace mace ganin wannan rana, ke kuma gata nan kingani. To me zai hana ki nunawa Allah farin cikin ki a fili da kuma 'boye leeyanah?. Please karki zama mai butulcewa da ni'imominsa ki zamo mai yawan godiya a gareshi kinji" "In sha Allah Aunty zan kasance mai yawan godiya da ni'imominda Allah ya yimin". "Nice gurl, haka nakeso naji kin fad'a, ga ruwan kisha kinji" cewar Aunty Rafa'at tana miqamata mug din ruwan sanyi. Karɓar ruwan tayi ta dan sha kadan sannan ta ajiye. "Muje na nuna miki bedroom dinki" Aunty Rafa'at ta faɗa. Mikewa tayi tana binta a baya har suka isa wani tangamemen bedroom kyakkyawan gaske kamar cartoons aka bawa yin decorations komai na dakin kyakkyawa ne. Kamar yanda parlour yake haka nan bedroom komai na cikinsa fari ne mai ratsin golden. Kan wawakeken farin royal bed din ta ta qarasa ta zaune gefe daya ta zabga uban tagumi. Har ga Allah idan tambayar ta za'a yi meya sakata cikin damuwa batada takamammiyar amsar da zata bayar. Qarar kiran waya ne ya shigo wayar aunty Rafa'at, sai a lokacin leeya ta tuna da wayanta. "Allah sarki, wallahi na manta wayana suleja" ta faɗa a zuciyarta. Sai da kiran ya kusa katsewa aunty Rafa'at ta daga kiran da sallama da kuma murmushin ta duk a lokaci daya. "Okay, kin kwatanta masa kenan,,,,,,,,,"Allah ya sa zai gane wurin. Dan Allah banda bata lokaci, kinsan ango ya kusa qarasowa yanzu,,,,,,,,"ok Nagode sai na iso,,,,,,,,, Ameeen ya rabbi" Aunty Rafa'at ta faɗa tana ajiye wayarda ke hannunta. Dubanta ta kai ga leeyanah dake zaune ta tsurawa wuri ɗaya idanu kamar ruwa ya chanyeta tace "leeyana zan tafi gidan aunty hajaarah, dayake ba'a sanar dake a gida ba kho? Zan tafi yanzu dan kinga dare ya soma yi har karfe tara ta gota, kinga kho ya kamata in tafi, kuma ma gidan da zan sauka suna nan suna jira nazo" Murya na rawa kamar wacce zata fashe da kuka tace "Aunty tafiya zakiyi ki barni dan Allah ki bari Zafaran yazo kinji, banzo da wayana ba kuma koda nazo da wayar banada number dinsa balle na san inda yake yanzu, dan Allah ki dan jira kadan ko Allah zai saka yanzu" Da mamaki lulluɓe a fuskar Aunty Rafa'at ta kalli leeya tace"waye kuma zafaran leeyanah" Cikin zuciyar leeya kuma cewa tayi "wanda aka d'aura mana aure dashi mana" a zahiri ma hakan ta so ta fad'a, amma gudun kar Aunty Rafa'at tace batada kunya yasa tace "wanda zamu zauna dashi a gidan nan" Ko kusa Aunty Rafa'at bata gane abunda leeya ke cewa ba tana shirin yin magana kuma sai ga kira new number ya shigo wayanta. Tana ɗaga wayar ta gane ashe drivern da aka turo ne yazo ya dauketa, Bayan sun d'an gaisa ya gayamata daidai inda yayi packing. "Zan tafi Leeyana, ki jira kaɗan kinji, ba laifina bane wallahi baban twins ne ya bada wannan umurnin. Amma zanzo gobe tun da sanyin safiya" "Ok Aunty ba damuwa sai kinzo goben, Allah ya bamu ikon taahi lafiya" leeya ta faɗa a sanyeye. Miƙewa Aunty Rafa'at tayi ta fice daga gidan bayan sunyi sallama da mai gadi. Leeya kuma bayan fitar Aunty Rafa'at da kamar mintuna goma tana zaune inda ta barta. Ta rasa abunda zatayi ga yunwar da ke addabar cikinta, ga kuma gajiya, sannan ga alama tana ji kamar zazzaɓi yakeso ya kamata. Tashi tayi daga parlorn ta shiga bedroom dinda zai ci gaba da amsa sunansa nata halakh malakh. Tana shiga ta cire dogon hijabin da ke jikinta da riga da zane na atamfa. Wurin da aka ajiyemata akwatunan kayanta da suka zo dasu ta nufa ta dakko riga da wando na yadi mara nauyi ta ajiye akan bedsofa, sannan ta ninke wadanda ta cire ta bude closet zata saka. Ido ta zaro waje ganin yanda aka zauna aka jera uban kaya na sakawa dunkakku, sake bude wuri na biyu tayi anan ta kuma cika da mamaki ganin wasu kayan daban da ba dunkakku ba. Da sauri ta bude ta gabanta, qananan kaya ne na bacci da kuma na shan iska na roba dana yadi mara nauyi colours kuma masu kyau da daukar idanu. Wata gown ta hango pitch mai matukar kyau, da sauri takai hannu ta janyota, abun ban sha'awa kuma tana janyo rigar cikin ledarta sai ta ganta har qasa kuma ga wani dan qaramin tsararren hijab da hula mai kyau. Murmushi ne ya subucemata babu shakka rigar nan ta shiga ranta, kuma ita zata saka yanzu. Ji tayi kamar tazo ta zube kayan gaba ɗaya taga yanda suke. Fitarda rigar tayi sannan ta mayarda riga da wandon da ta dakko bayan ta gyara kayan yanda ta samesu. Toilet ta wuce ba jimawa ta fito da wanka ta kuma yi alwala. Sai da tayi duk sallolin da tasan suna kanta kafin ta isa gaban mirror. Ta bata lokaci sosai gaban mirror domin cikakkiyar yar kauye ta zama lokacin da ta ganta gaban mirrorn da ke bedroom ɗin ta, kayane jere a wurin birjit wasu bata san yanda zatayi amfani dasu ba, wasu kam ko ganinsu bata taba yi ba hatta shi kanshi mirrorn abun kallo ne balle kayan da aka jera kamar babie bedroom. Zama tayi a wurin ta dan gyara jikinta ta shafa abunda zata shafa sannan ta saka kaya ta nufi inda ta hango perfume display, tana isa wurin ta bude cabinet din ta fito da wani turare mai sanyin qamshin furanni ta fesa ko ina ajikinta, sannan ta juya ga show glass shima ta buɗe ta dakko roses bottle shima ta shafa humrah kamar yanda tayi da turare. Nan take kuwa kamshi ya garwaye dakin kamar zai danwama a haka. Hular kayan ta saka bayan ta gama cumbing gashinta sannan ta sanya hijab. Shafff ta manta dare ne take irin wannan shiri kamar wacce zataje biki. Gaban mirror taje ta tsaya, tanaso ta kalli fuskar ta. Amma kuma tanajin tsoro ganin yanda halittar ta take sanin cewa har yanzu ba'a daina jin tsoron ta ba domin ko ɗazu da ta fara bude fuskar ta sai da aka gudu. Rumtse idanunta tayi sosai ta lalubi lamp side dinda ke gefen mirrorn ta kunna, nan take kuwa haske ya kuma bayyana tarrr kamar da Rana tsaka. A hankali take bude idanunta kamar batason amfani dasu har ta bude su tarrr akan fuskar ta dake zane kan tangamemen mirrorn ta. Gaban ta ne yayi wani azababben faduwa da sauri taja baya ta rufe fuskarta da tafin hannunta biyu tana mayarda numfashi. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me zan gani? Wazan iya yiwa wannan tambayer. Ni mutum ce ko kuma aljan? Idan Ni aljana ce ya akayi ban gane ba, idan kuma Ni mutum ce taya zan kasance haka" Saurin fadin "Astagfirullah" tayi sanin ba abunda zai gagareshi yasa tayi shiru ta zabga tagumi kawai tana jinjina Al'amarin a ranta. Duk abun zan gayamuku Dangane da halittar kyau da tsari da Allah yayiwa leeyanah dole sai na ragemata wasu abubuwan domin ba yanda za'a yi mutum ya iya siffanta ainihin kyawun da Allah ya bata. Babban dalilin mahaifiyar ta na sakata rufe fuska kuwa shine; tun ranar da aka haifeta mutane na cike da mamakin irin kyau da Allah ya bata, tun tana yarinya qaramarta, kamar hawainiya ce dake chanja kala, ba rana ta Allah da baza ka ganta kaji ta shiga ranka ba, sau shida ana yunkurin kashe iyayen ta domin a saceta a gudu da ita, da suka fahimci haka sai suka tattara nasu E nasu suka bar garin gaba ɗaya. Da suka dawo lagos kuma sai suka dinga boyeta sosai amma kuma hakan bai yiwu ba domin tuni mutane suka ankara da haka, abunda ke faruwa a nan kuma duk mai sauki ce bisa da inda suka baro domin nan iya hoto ne kawai ake zuwa ana yimata, har takai ta kawo anfara zuwa ana fita da ita unguwa ko wani biki ko taro. Ranar da wata mata tazo ta fita da ita har dare basu dawo ba, tun suna ganin abun kamar wasa har ya kasance abun ya fara damunsu sosai. Basu san inda zasuje su nemi matar ba Bayan gidansu, gidansu kuwa sunje yafi a qirga sai ganin suke gidan sanye da key. Sai misalin ƙarfe goma sha biyu har da mintuna arba'in na dare matar ta dawo gida hankalin ta duk tashe, leeyanah kam tayi kuka har ta gode Allah. Da sauri suka rungumeta suna kuka itama leeya kukan take a lokacin bazata wuce shekaru uku zuwa hudu ba. 'Dagata sama abbinta yayi ya d'orata akan kafadar sa yana qoqarin yiwa matar sallama su shiga gida, sai a wannan lokacin ya lura da ammi dake magana da matar gefenta kuma wasu jami'an tsaro ne su kusan hud'u. Da yayi tambaya kuma aka gayamasa wai abinda ya tsayarda matar shine a hanyarsu ta dawowa wasu mutane suka tare su da motoci guda biyar suka sakasu tsakiya, wai leeyanah suke nema ta basu ita ko kuma harbeta. Tasha kuka da roqo amma ko kallon ta basuyi ba, sai da ta ga kamar da gaske suke zasu iya harbe ta ya saka ta miqamusu leeyanah. Daga chan bayan su kuma qarar harbin bindiga suka fara jiyowa yana dumfarar wurin. da sauri barayin suka fara neman gudu amma inahhh sun makara domin jami'an tsaron ne sukayi musu qawanya. Karbar leeyanah sukayi daga hannun mutumin da ya dauketa, sannan suka yiwa matar magana aka wuce da ita office ayimata wasu tambayoyi. sukuma barayin aka tafi da su matsayin masu laifi. Sai da akayi musu tambayoyi kafin aka sakosu suka dawo gida. Wannan shine dalilin da yasa suka jima sosai basu dawo ba, Ammi tayi kuka har tarasa yanda zatayi. Anan ne suka yanke shawarar boye fuskar ta ga kowa har sai lokacin da zatayi aure domin idan tayi aure zata zama a qarqashin kulawar mijinta da kuma tsaron sa. Mayafi aka fara rufemata fuska dashi sannan sukayi nisa sosai da unguwar da suke suka koma IFE inda babu wanda suka sani kuma ba wanda ya sansu...............✍🏼 45. ______________Babban dalilin da yasa ake zargin leeyana da maita shine wata rana sun fito da amminta zata rakata islamiyya sai suka had'u da wani saurayi dan mai unguwar da suka da suke zaune. Tsayardasu yayi yace don dole sai ammi ta budewa leeyana fuskar ta ya gani, ammi na kuka ta ke rokonsa akan yayi hakuri da wannan quduri nashi domin tana gudun abunda zai sami leeya ko ya yake, qoqarin fizgar leeya yayi daga rikon da ammi tayi Mata, cikin Rashin Sa'a ya fizgo mayafinda ke lullube da fuskarta. Wani irin mugun ja da baya yayi yana qara kureta da idanu a hankali kuma idanun sa suna lumshewa har ya fadi qasa, ko motsi bai baiyiba lokacin da ya fadi shikenan rai yayi halinsa sakamakon bugawar tsoro da zuciyar sa tayi lokaci ɗaya. Haka aka tabbatar wa mahaifinsa bayan gwajin da aka yimasa asibiti, ga mutanen qabila ne basuda dangana yasa suka ce sai sun kashe leeyana da amminta tunda suka kashe babban yaron mai unguwa Abiola. Babbar sa'ar da sukayi shine gidan da suke ciki ba nasu bane da tun a ranar da abun ya faru zasu iya qona gidan gaba daya, da kyar da sudin goshi da sasancin ƴan sanda aka shiga tsakaninsu sukaci gaba da zama unguwar, amma kuma kowa tsoronsu yake yana gudunsu, qalilan ne suke mu'amala dasu. Ammi kuma bata fasa da horar da leeya akan saka mayafi ba domin hakan babbar kariyace a wurinta. Ammi ta hana leeyanah kallon madubi kuma. domin hakan zai iya zama illa a wurinta, ko kuma tayi amfani da kyawun da Allah ya bata ta lalata rayuwar ta. Shiyasa ammi ta hana leeya duk waɗan nan abubuwa tsawon shekara da shekaru. Wannan shine takaitaccen tarihin leeya da kuma babban dalilin da yasa take boyewa kowa fuskar ta. * Tun daga farkon shigowar sa parlourn wani sassayan kamshi turaren roses ya tarbeshi, a zahirin gaskiya da ace yana cikin asalin mood dinsa ne da babu abunda zai hana masa tsayawa ya shaqi qamshin domin ya tafi da imaninsa sosai. Bakinsa yayi masa nauyi sai tunanin abunda ya dameshi yake tun daga gate da yayi sallama bai qara yi ba sai da ya shigo tsakiyar parlourn kuma ko a parlourn sau daya yayi, idan ma mutum baya kusa da shi sosai bazaiji abunda yace ba sai dai yaga vakinsa na motsi kawai. Tana cikin baccin da ya shareta taji qarar ajiye wani abu mai nauyi dai-dai inda saitin kanta yake. Tun kafin tayi yunkurin wani abu ya fara magana da muryarsa mai kamada wanda ya tashi daga bacci yace "ko wacece ke to kisani ba dan ina sonki zan zauna da ke ba, kisani zama ne kawai zakiyi matsayin matarda aka dauramin aure da ita batare da sona ba, karki taba tunanin zan soki, domin zuciyata ba taki bace na riga na sadaukarda ita. Karkiyi tunanin wulaqanci ko tozarci daga gareni akanki, wallahi bazan taba wulaqantaki ba tunda akwai haqqinki akaina, kuma zan sauke miki duk wani haqqinki daya rataya akaine, ke kuma ruwanki ne ki sauke haqqina da yake kanki, ruwankine ki qie saukewa wannan tsakanin ki da wanda ya rataya miki haqqin ne, kuma wannan da nayi karkiyi tunanin so ne ko wani abu mai kamada haka, wallahi ko kadan ba digon sonki cikin rainah, kinji na gayamiki. Nasan kinyi wanka, kuma kinyi sallah. Good gara da kikayi haka domin kin haqiqance bazan yi wannan dake ba kho, kamar yanda ake kawowa ko wace mata abinci a first night kema ga naki nan ki tashi kici tsirai ne da fresh milk kuma ki tashi idan kinci ki kwanta sai da safe. Da wani matsananci kuka ta mike tsaye ta kunna electric LED din da ke kusa da ita domin hasken bedside lamp kawai ta bari saboda bata iya bacci cikin haske, ba tare da ta waiwayo gareshi ba take magana domin a iya qamshinsa da taji ta gama gane shi, balle kuma ga muryarsa da takeji na sauka a kunnuwanta. "Dama kai aka auramin! kaine aka auramin? Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Wallahi ba dole bane sai ka soni.....! kuma dama nasan ba sona din kake ba, menene soyayya ta zata amfane ka idan ka soni, koda baka faɗi da bakinkaba, na riga nasan baka sona, balle kuma gashi ka faɗi, kamar yanda kasan biyayya tasa ka aureni nima wallahi rashin sani ne da biyayya ta sa na aureka duk da bakai nayi zaton aura ba. Kaje kayi rayuwarka a Cikin gidan nan nima nayi tawa, duk da sanin da nayi cewa zamanmu zaiyi wahala tare a gidan nan domin bama zama inuwa d'aya hakan bazai saka na sare tun yanzu ba, na rokeka kaje kayi rayuwarka nayi tawa har zuwa lokacin da Allah ya iyakance mana" leeya ta faɗi maganar cikin gazawa da karayar zuciya. Turab da yayi suman tsaye ya kasa cewa uffan, ko a cikin zantukan ta ba komai yake iya fahimta ba. Ko kusa bai yi tunanin haka ba, bai taɓa kawowa a ransa wai leeyanah zata tsaya kusa dashi har haka ba balle ma ace ta zama matarsa, mallakinsa, muharramarsa. Sharaff yaji ta zube kan gado, qarar fad'awar ta kan gado ne ta mayar dashi hayyacinsa daga tsunduma kogon tunanin da yayi. Da sauri ya isa kan gadon ya fara jijjiga ta amma ko motsi batayi ba, sunanta ya fara kira da qarfi yana jijjiga ta amma har a lokacin tana nan yanda take. Da sauri yayi hanyar toilet ya ɗibo ruwa ya ajiye ruwan sannan ya kamata ya sauketa qasa ya fara zubamata ruwan da ke hannunsa, kusan sau uku yana dibo ruwa yana zubamata amma ko yatsarta bata motsa ba balle ita kanta. Addu'a ya fara yi a bakinsa yana tofamata hadi da shafa mata addu'ar kowane sashe na jikinta. Bakinsa ya kafa kan hancinta ya fara hura mata numfashi da qarfinsa. Ya kusa mintuna biyar a haka kafin yaji tayi ajiyar zuciya mai nauyi. Hamdala yayi yana godewa Allah a ransa, a fili kuma kiran sunan ta yake tun tana bude idanunta a hankali har ta budesu tarrr a kansa. Wani wawan zabura tayi lokacin da ta ganshi kusa da ita sosai, da azama da kuma sauran qarfin da takeda ta tureshi kusa da ita bayan ta tashi. "Sannu leeyana, bansan abunda ya sameki ba haka kawai naga kin faɗi, Allah yasa da sauqi" turab ya fada yana matsowa kusa da ita. Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara leeyanah ta daga idanunta da takeji kamar zasu fado qasa Saboda tsananin nauyi da zugin da suke mata Sakamakon kukan da tasha tace "na rokeka ya-Turab dan Allah ka fita rayuwata, wallahi kamar yanda kace baka sona nima bana sonka, kuma bazan taɓa sonka ba, kada ka yarda ruɗaɗɗiyar zuciyar ka ta vaka zan soka wata rana idan kuma kaji hakan kayi gaggawan cire shi a ranka domin bazai taba faruwa ba". Kamar ya fashe da kuka haka yake ji zuciyarsa nayi masa raɗaɗi, cikin kwantar da kai da nuna nadama yace "dan girman Allah leeyana ki tsaya ki saurareni, wallahi ba ina nufin abunda ke kike nufi bane. Kamar yanda kikasan baki san mijin da aka auramiki ba, Nima bansan matar da aka auramin ba. A tunanina wata matar daban ce aka auramin wacce ba ke ba, banjin zan iya rayuwa a wuri ɗaya da wata matar sabanin ke. duk a tunanina bake aka auramin ba domin banyi zaton na mallakeki har haka ba, shiyasa dana shigo gidan nan bankula da ke bace ko kuma bake ba har na fara magana kawai, amma wallahi ko cikin mafarki kika ji Ni nace bana sonki yakamata ki qara qaryata mafarkin har a zahiri domin kinsan wannan bazai ta'ba yiwuwa ba, dan Allah kiyi haƙuri, ki yafe min kura kurainah dana miki wanda kika sani da wanda baki sani ba, dan Allah kinji na roƙeki" turab ya faɗa yana durƙusawa kasa da gwiwoyinsa. Wani irin haushinsa take ji mara misali, ya bata tausayi sosai amma kuma zuciyarta taki bata hadin kai wajen nuna masa yafiyarta gareshi. Wani kallo ta jefa masa dana kasa gane nufinta. "Ya-turab inaso inyi bacci dan Allah ka fita ka koma parlour ko kuma Ni na fita na baka wuri, sorry kuma ka fita da wannan tarkacen naka domin ko yunwa zatayi sanadina bazanci wannan abun da ka kawo ba" Kamar turab ya dora hannunsa aka yayita rusa kuka yakeji, muryasa na cracking yace"dan Allah leeya.........." Katseshi tayi da faɗin "in fita in barmaka dakin ne?" Cikin taurin zuciya da juriya yace "shikenan zan tafi in baki wuri leeyanah, sai ki saka wani abu a space din da na tare miki, na miki alqawarin nisanta dake kamar yanda kika buqata, dole nasan wata rana ko babu raina ki tuna irin son da na ke miki, sannan ku tuna yanda kike wulaqantani, ki tuna yanda nake rokonki akan ki zauna dani, ki tuna komai da ya shiga tsakanin mu tun ganina dake na fari, dole nasan zaki tuna da haka idan kika juya idanunki gabas, da yamma. Kudu da Arewa na wannan duniyar bakiga mai kamada Ni ba balle ki gani. Nagode da sakayyarki gareni. Inaji kamar bazan sake kai gobe ei war haka da rayuwa ta ba, a yanda nake maganar nan sai naji kamar wasiyya ce kawai nake gayamiki. Leeyana ki dauka kamar da gawa kike magana yanzu domin bana tunanin zankai labari bayan babu ke a cikinsa. Nagode sosai ina fatar samun kwanciyar hankali da kyakkyawan dare a gareki dream gurl, Allah ya sada mu Da alƙairi" turab ya faɗa wasu zafafan hawaye na sauka daga cikin idanunsa. Juyawa yayi ya kalleta, ya kusa seconds talatin a haka kafin ya juya ya tafi ba tare daya sake kallonta ba. Zama tayi jagwabbb kan gado ta fashe da wani rikitaccen kuka. Kalamansa sun saka zuciyarta saqa sosai, ta rasa wane mizani zata ɗora zancensa wajen gane abunda yake nufi. Tausayinsa ya kamata sosai tanaji kamar ta bishi parlour ta bashi hakuri amma sai taji bazata iya yin hakan ba. Tunani kala-kala ta dinga yi a daren ko isasshen bacci bata samu ba har aka kira sallahr asuba. Miƙewa tayi jiki a sanyaye ta shiga toilet ta ɗora alwala ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta d'akko hisnul Muslim ta fara dubawa har sai ta alfijir ya keto. Fita tayi parlourn domin ta samu ta tsaftace shi duk da tasan Lafiya qalau yake. Tasha mamaki sosai na rashin ganinsa da tayi parlour. "Maybe ya biya wani wurin daban da aka tashi daga masallaci" ta faɗa a fili. Knocking taji anyi, bata ankara ba sai taji tayi murmushi, babbar tambayar da tayiwa kanta sanin dalilin murmushin ta daga jin knocking. "Saboda mijinki ya dawo mana" zuciyarta ta bata amsa da haka. Guntun tsaki tayi tana ture amsar da zuciyarta ta bata domin tasan hakan ba zai yiwu ba ace zatayi murnar ganin ya-Turab yanzu. Knocking taji an sake yi, cikin tafiyarta mai cike da nutsuwa ta isa qofar ta buɗe. Wata baquwar fuska taci karo da ita da ga kofar bayan ta wangaleta. "Barka da safiya" ta furta cikin muryarta tana kallon wani dattijo dake tsaye da kaya a cikin basket. Dattijon kuwa ya amsata da fadin "yawwa barka da safiya Hajiya, sunana ilu nine mai gadin gidan nan. Wannan kuma saqo ne wata mata ta bayar tace a kawomiki, sannan ga shi ta bayarda katin ta tace ki kirata idan na baki saqon zatayimiki bayani" "Okay Allah sarki, nikuwa bansan wace mata bace. Amma nasan bazai wuce Aunty Rafa'at ba tunda da ita mukayi zata dawo da safe, amma wallahi banida wayarda zan kirata da ita domin na manta wayana gida" Washe baki ilu mai gadi yayi yace "hajiya ga 'yar kwakuleta ta ki kira da ita nasan akwai sauran credit jiya da rana na saka bata isa qarewa ba yanzu" Leeyanah taji dadi har ranta domin kho badomin saqon kiran Aunty Rafa'at ba....tanaso tayi waya da mum Wallahi. Karɓar wayar tayi tana yimasa godiya, hannu ta saka zata karɓi basket yace ta barsu ya shigardasu gida. 'Kin amincewa tayi domin tana ganinsa dattijo dashi ta ya zata yarda ya shigar mata da kaya. Sai da kyar ya mika mata kayan ita kuma ta shige ciki harda wayar tasa. A daining ta dire basket din ta bud'e, yunwa takeji bil-haqqi domin rabon ta da saka wani abu abakinta tun jiya da la'asar. Babban flask din ruwan zafi ne sai kuma cooler mai biyu da kuma wani qaramin bowl mai murfi. Bowl din ta fara budewa sai ta tarar da soyayyen dankalin turawa da kwai da kuma toasted cheese. 'Daga bowl din tayi ta ajiye shi kan daining sannan ta bud'e cooler d'aya, taga tuwon semovita ne kulli uku. Murmushi tayi cikin jin dadi ta ajiye cooler din kan daining itama sannan ta bud'e qaramar. Miyar ganye ce sharrr da ita taji manshanu sai qamshi spices take. Tun kan leeya taci tuni yawunta ya tsinke. Flask kuma tea ne a ciki, sai kuma gefe daya na flask din cool water ne. Miƙewa tayi lokacin da ta gama duba abincin sannan ta nufi kitchen ɗin ta. Tasha wuya sosai kafin ta gane kitchen inda kitchen yake domin zagaye ta farayi da ta bud'e wannan kofar sai ta ganta anan, idan ta bud'e waccan sai ta ganta a wannan, ko kuma ta ganta inda ta baro. harta kusa sharewa sai kawai ta ga wata qaramar kofa, tana budewa kuwa taci karo da tsararren kitchen mai matukar fadi da daukar hankali. Ga kaya nan birjit kamar kanti, abunda tazo dauka ta dauka bayan ta gama baiwa idanun ta abinci, sai da ta gama kallon komai tare da duba duk abunda bata sani ba sannan ta fice daga cikin kitchen ɗin zuciyar ta na mata wasai. Haqiqa mum da papu sun gama mata komai a wannan rayuwa sun zama gatan ta a nan duniya, Allah ne kawai zai yi musu sakayyar alƙairi tsakaninsu. Fita tayi sashen bayan ta gama hardace hanyar da zata mayar da ita daining tsafff tayi zuwa da dawowa yakai uku kafin ta zauna. Tea ta zuba a cup d'aya, sannan ta zuba dankalin turawan da kuma toasted cheese ta fita ta miqawa ilu mai gadi, Godiya yayi mata sosai, ta dawo ciki ta zuba nata sannan ta ragewa ya-Turab nasa. Sai da taci ta qoshi Sannan ta adana tuwon domin batada space din da zata sakashi. "Maybe ya-Turab zai buqata idan ya dawo" tsaki ta jaaa a fili lokacin da tayi maganar a zuciyar ta, a fili kuma tace to meye damuwata yaci ko kar yaci. Sake jan wani tsaki tayi tana kunna wayar ilu mai gadi da ya aramata. Katin ta d'akko ta kwashe number din da ke jikin katin tayi calling. Bugu ɗaya da dauka da sallama a bakinta tace "barka da safiya" Daga cikin wayar kuma akace"Yawwa barka leeyanah kin tashi Lafiya" bata jira amsa ba taci gaba da fadin "sai kikaga saqo ga mai gadi kho, kiyi hakuri wallahi wani uzuri ne zai mayardani suleja yanzu. Baban Aamir ne ya kirani yake sanardani wai Arfah tana asibiti jiya dare wutar nepa ta jaa ta har sai da aka kaita asibiti, shine ya kirani ya sanardani. Amma kuyi hakuri kinji zamu dawo nida su mum fanaya soon" Leeya dake sauraren aunty Rafa'at tace "Allah sarki Aunty Wallahi babu komai, mun amshi saqo mun gode kuma Allah ya sanya albarka, Allah kuma ba bawa Arfah Lafiya ya tsare gaba" Tun kafin Aunty tayi magana katin wayar ya qare, kamar leeyanah ta rusa kuka taji lokacin da wayar ta datse da kanta. Mum ta so ta kira wallahi tayi missing ɗin ta, rasa yanda zatayi tayi dole ta miqawa ilu mai gadi wayarsa ta dawo parloun cikin bakin ciki. Bedroom ta wuce ta gyara tsafff kaana ta bude wata qaramar kit daga cikin sababbin akwatunan ta da papu ya siyo musu jiya. Turarukan daki ne a ciki birjit dana garwashi da kuma na tsinsiya. Fitowa tayi dana garwashin domin qamshinsa yafi tafiya da imaninta, sa'ar da taci itace ɗazu ta lura da kwalin sabuwar borner akan tv stand. Da ita tayi amfani wajen turara ɗakin gaba daya, bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka Sannan ta yi shirinta cikin doguwar rigar less mara nauyi mai matuqar kyau wanda yaji qanan Arab stones kamar anyi bari sai sheqi take kamar tauraruwa. Ta Rasa abunda zatayi kawai ta dawo parlour ta kunna kallo da remote a hannunta tana sarrafa shi har iskan A.C da fanker dake parlorn suka kad'ar da ita tayi bacci. Ba ita ta farka ba sai da aka kusa kiran sallahr azahar, wasu masallatan ma har an idar, miqewa tayi ta shiga bedroom ɗin ta. tayi mamaki Sosai ganin sa yanda ta barshi. "Kenan ba wanda ya shigo gidan nan?" Tayi tambayar a fili. "Wata qila kuma ya shigo ya tarar dake kina bacci ya sake fitarsa" Da wannan zancen zucin nata ta aminta, ya-Turab ya shigo ya tarar da ita tana bacci bai tayarda ita ba ya sake fita. Alwala tayi sannan ta tayarda sallah, bayan ta idar gaba ɗaya sai ta koma daining, Abincin da Aunty Rafa'at ta kawomata ta duba, tasha mamaki sosai ganin har breakfast din tea da kuma toasted cheese din da ta ajiye suna nan a yanda suke ba'a ta'basu ba. Tattara su tayi wuri daya sannan ta zuba kulli daya na tuwo da miya ta haɗa da tea din ta fita waje. Wurin da ilu ke kwance yana shan iska ta nufa fuskar ta wasai. Sallama tayi masa bakinsa har rawa yake wajen amsa mata, shidai yana tsoron hada idanu da wannan hajiyar mai kamada aljanu saboda tsanin kyawu, ko a hakan ma dauriya kawai yake yana yimata magana da amsa mata. Bakinsa a washe yace "Hajiya sannu faa, Nagode Allah ya qara budi" Itama murmushin ne a fuskar ta tace "Ameen baba ilu, yawwa nace ka saka credit ne wallahi banida kudi hannuna gashi mai gidan ya fita balle in yi masa Magana" Da mamaki ilu ya dan dago kad'an yace "hajiya wane mai gidan kuma, ai tun jiya da dare da ya shigo ba wanda ya qara fita, kinga ma motar da yazo da ita" ilu ya faɗa yana nunamata packing space. Motar ya-Turab wacce yafi so ta gani a pack ba ko alamar an ta'bata yau din nan. Cikin madaukakin mamaki ta jinjina kai sannan tace "toh shikenan baba ilu Nagode sosai ka saka credit din inaso na kira gida wallahi" "Allah sarki hajiya wallahi bansaka ba, amma bara in ranto bashi nasan zasu bani da yawa tunda ban taba rance ba kinga sai kiyi wayarki isasshiya" Leeya cikin farin ciki tace"Kai amma Nagode baba ilu...... in sha Allah idan nayi waya da gida zan saka a turamin kudin siyen waya da kuma kudin credit dinka dana saka ka ranta" Ilu mai gadi yace"haba hajiya, ai kinfi karfin nan wallahi. Ki karba sun bada rancen" Karɓar wayar tayi da hannu bibbiyu tana yimasa godiya ta wuce ciki, number mum ta fara trying on ready tanada number din da kanta. Sunyi gaisuwa sosai cikin kewar juna da so da qauna na tsakanin 'ya da uwa. Leeya kuwa harda d'an guntun kukanta da zasu gama wayar bayan ta gayawa mum duk matsalar ta, sai dai bata gayamata har yanzu bata sanya ya-Turab a ido ba. illah ma cewa da tayi yana lafiya, daga nan kuma mum ta gayamata zasuzo nan da kwanaki hudu masu zuwa. Daga karshe kuma tace mata "ki je ki kaiwa ilun waya kice yayi magana da mai p.o.s na tura masa kudin ki fadi kalar wayar da kikeso asiyamiki, sannan ayi miki sim nima na gaji da shirun nan tsakanin 'ya da uwa" leeyanah taji dadi sosai har farin cikinta ya kasa boyuwa har mum sai da ta gane hakan. Murmushi kawai tayi tana qarajin tsagwaron soyayyar 'yar uwarta na dawomata filll. Mum koda leeyanah takirata akan ta turamata kudin siyan waya bata kawo komai ba. "Leeya kenan maybe bataso mijinta ya siya mata Ni take buqatar na siyamata shiyasa ta gayamin" Haka mum ta fad'a lokacin da suka kammala wayar. Fita waje leeyanah tayi a karo na biyu taje ta sanarwa da ilu mai gadi abunda hajiyarta tace. "Aikuwa akwai wani shago da ake cire kudi gaba da gidan nan kaɗan bara naje yanzu" Leeyana dai tana yabawa da mutuncin baba ilu tace "Nagode baba ilu Allah ya yimaka yanda kaimin, kuma idan kaje shagon Dan Allah ka kira wannan lambar" ta faɗa tana nuna masa number din mum dake kan kira yanzu. Baba ilu yace "nagane hajiya zan kira idan naje in sha Allah, ki shiga ciki kafin in dawo, kuma ki rufe ko da yake ai Alhaji yana nan ko? Amma dai duk da haka ku rufe ko'ina saboda tsaro idan na dawo zan kwankwasa" Annurin fuskar ta ne ya ɗauke gaba daya lokacin da ilu ya ambaci sunansa, tasan bata kyauta masa ba. To Amma meyasa zai tafi tun jiya da dare ya kasa waiwayo ta har yau zuwa wannan lokaci, ai ko dabbobi ka ajiye ya kamata ka dinga waiwaye balle kuma mutum d'an adamu mai daraja. "Ki tuna irin wulaqancin da kika yimasa jiya, kuma fa ke ce kika koreshi da kanki" Wata zuciya ta fad'a mata haka lokacin da tunanin ya-Turab ya zagayo ta. Komawa tayi ciki jikinta sanyi kalau, yanzu ya zatayi ta fara nemansa, gashi bata san wane wuri aka ajiye kanwarta Rukhsha ba, da kuma bestin ta zohal, da ma ache d'ayar su tana kusa da ta kawo mata mafita... * A daren jiya kuma bangaren su Aleena. Su mummy-neesah ne da kuma Aunty zainab suka rakata. Gidan da aka ajiyeta da kuma inda aka ajiye leeyanah da zohal duk iri dayane, hatta tales da kuma painting gidan babu abunda ya banbanta. Furnitures din Aleena da leeyanah duk iri dayane, har kuma yanda aka yi tsarin ajiye kayan komai iri dayane. Mummy-neesah da Aunty zainab basu jima gidan ba domin drivern da yazo dasu shi ya koma da su garin suleja cikin umurnin da dad qarami ya bayar. Aleena ma tasha kuka sosai amma mummy-neesah tayi mata alqawarin kwanan nan zasu zo gaba daya, kuma za'a je da ita gidan leeyanah da kuma gidan matar yayansu wato fahad duk suga juna domin ba unguwar su daya ba, kowa da bangaren da aka bashi. Mummy-neesah da Aunty zainab basu jima da tafiya ba ango ya shigo, a lokacin kuma Aleena na zaune parlour tana game da wayarta domin ita bata manta da wayar ta ba da abunta tazo. Sallamar da taji ne ya sakata dagowa, da mamaki take binshi da kallo, shima haka. Muryarta na rawa saboda tsanin tsoro ta furta "broth O kaine ko idanuna ne" Matsowa yayi kusa da ita fuskar sa dauke da murmushi idanunsa kuma sunyi jajir har da kwanciyar ruwan hawaye a cikinsu. Har gabanta ya taka ya saka hannunsa d'aya ya shafa gefen fuskar ta "kinyarda nine ba mafarki kike ba kho" ya fada da murmushin da bai gushe masa ba. Miƙewa tayi tsaye itama tuni idanunta sun kawo ƙwallah tace "broth dan Allah kai aka auramin, ya kakeso yayata tayi da soyayyarka dake zuciyarta" Murmushi mai sanyi yayi mata sannan yace "budurwa, kinsan kuwa bawa baya wuce qaddararsa? To tun a farko Allah bai rubuta leeyanah a matsayin qaddarata ba, ke da banyi zato ba kuma banyi tsammani ba dake Allah ya tsara qaddarata. Duk abunda kaga ka saka rai kuma Allah bai baka shi ba, to ba shi bane daidai da rayuwar ka ba, domin kuwa ko ya shigo zai fita wata qila ma ba alqairi bane" Aleena kam tuni tasan zafaran da tawakkali tun kafin ya musulunta, balle ma yanzu Da ya musulunta, ai sai abun ya qaru "Hakane broth O, Allah ya zaba mana mafi alqairi, Allah ya sanya albarkarsa a cikin zaman mu" "Aleena kina sona?" Taji saukar muryarsa a kunnuwanta babu zato babu tsammani. Batare da tunanin komai ba tace"ina sonka broth O ina rokon Allah ya kawomana kwanciyar hankali da kyakkyawar fahimta a tsakanin mu, ina rokonsa ya azurtamu, ya rufamana asiri a zamantakewar mu" ta karasa maganar muryarta na rawa alamun kuka take qoqarin tayi. Ganin haka ya saka zafaran ya ware mata hannayensa biyu, da gudu tayo kansa ta rungume shi. Shima ya rungume ta tsamm a faffaɗan qirjinsa. Kamar mai rad'a yayi mata magana yace "karki bari hawayen nan su zuba dan Allah kinji budurwa d'iyan amminta. Allah sarki rayuwa........ naso ammi taga wannan rana, naso ammi ma ta saka mana albarka a aurenmu, amma ba haka Allah ya tsara ba Allah ya jikan Ammi da Abbi ya basu kyakkyawan masauki" "Amin ya rabbil alameen mijina" Aleena ta fad'a tana boye fuskar ta cikin qirjinsa. Ganin haka ya saka shi sakin lallausan murmushi yace"hummm sannu mai miji wai bakya jin kunyata kho" "Lahhhhh, dama akwai wata kunya tsananin miji da mata bansaniva broth O?" "Kinga idan baki daina kirana da wannan sunan ba sai na cire miki bakin nan" ya faɗa yana ɗan jan lips din ta na qasa. Cikin shagwaɓɓiyar murya tace "da zafi fa" Yace "dama ina so kiji zafin ai dan idan ban miki hakan ba bazaki daina kirana da sunan nan ba" Taɓe baki tayi zatayi kuka da sauri ya saketa ya kama kunnuwansa yace "tuba nake rankishidade a gafarceni bazan sake ba kinji, dan Allah kiyi haƙuri banason kukan nan" Kamar zatayi dariya sai ta kanne tace "Ni bacci nakeji" "Ok Madam, muje kiyi alwala sai muyi sallah sannan kici abinci sai kiyi baccin kinji" "Nidai sallah kawai zanyi bana jin yunwa" "Aikuwa baki isa ba dole sai kinci abinci wallahi ko in yimiki d'ure da qarfi da yaji" Yar dariyar farin ciki tayi sannan tace"To kafini qarfin ne hala?" "Sai an gwada ake sanin na kwarai malama" "to muje a gwada" Aleena ta fada tana wuce gaba shikuma yana binta a baya. Haka suka gudanar da daren su cikin farin ciki da nishadi, sai wasa da dariya suke kamar da can sun saba bayan tsawon shekarun da suka dauka ba sa tare. *** A bangaren leeyanah kuma baba ilu bai wani ɗauki lokaci ba ya dawo da uban kuɗaɗen da mum ta turawa leeyanah, bata tsaya lissafawa ta cire dubu ashirin ta bashi kyauta sannan ta gayamasa wayarda takeso ya siyo mata, baba ilu kamar ya kai kasa saboda godiya. Ko chan da ya je bai jima ba ya dawo mata da waya harda sim da credit mai yawa da ya saka aka yimata v.t.u Sosai take masa godiya shima godiyar yake mata da irin kyautatawar ta gareshi. Komawa tayi ciki ta fara shirin daura girkin dare, tunanin ta shine yanda zata saukewa turab kwandon rashin mutunci idan ya dawo, wato shi ga isasshe an kawomasa mata tun jiya ya tafi ya barta har gashi ana batun kwana daya babu shi ba labari. Ai ba sai ya nuna mata baya sonta ba domin shima yasan ba sonsa take ba biyayya ne kawai, balle har ya wani tafi ya barta ya manta da ita. Kitchen ta shiga ta dora girkin ta na dare tana ta mita har ta kammala kusan sallahr magrib, baba ilu ta kaiwa nasa sannan ta shiga tayi wanka ta dauro alwala ta fito, sai da ta jira aka tayarda sallah sannan taci abincin ta. Daidai lokacin kuma wayanta da aka siyomata tayi full, number ɗin mum ta kira har wajen kira hud'u amma ba respond. "Maybe wayan bata kusa da ita" ta fada a fili lokacin da take qoqarin kawo numbern bestin ta zohal. Ta kira number yafi a qirga amma abu daya ake gayamata not reachable. Kusan karfe goma da rabi ta rarraba idanunta ko'ina a gidan ko zataga ya-Turab amma bata ganshi ba, abun har ya fara bata tsoro. domin baba ilu mai gadi ya tabbatar mata da Turab bai fita gidan ba. "Hajiya ko akwai wata kofa daban da ake fita a gidan nan bayan wannan da nake tsaro?" Muryar a sanyeye leeya tace "wallahi Nima bansaniba baba ilu, amma dan Allah ka dan zagayamin a gidan nan ko zaka gano wata hanya, nikuma bara naje ciki in duba ko zanga wani wuri" "Shikenan hajiya, Bara naje na duba Allah yasa adace, to ko zaki kira number din sa kigani Hajiya?" "Banada number dinsa a kai na baba ilu, kuma na kira mum bata daga wayar ba" "To Allah yasa komai da sauki zaizo hajiya, amma ahce tun daren jiya babu mutum ba labarinsa" "Duk inda yaje da saninsa baba ilu domin shi ya fita da qafafunsa ba wanda ya fitar dashi" "Bara naje na dudduba mugani ko Allah zai saka adace" Daga haka ba wanda ya kuma cewa komai duk suka tafi. Baba ilu kam yayi zagayen da duk zai yi a faɗin gidan amma bai gano hanya ko ɗaya da ake fita cikin gidan ba bayan hanyar da gate yake. Yayi zagaye yakai biyar zuwa shida bai gane komai ba dole ta saka ya hakura ya nemi wuri ya tsaya yana jiran fitowar leeyana ya sanar da ita. Itama a bangaren ta haka ta kasance, domin tayi duk duban da zatayi a ɗakunan da ke gidan bata gane komai ba. sau biyu tana ɓata sai tasha wuya kafin ta mayarda kanta master parlour. Tayi duk iya qoqarin ta wajen fahimtar ɗakunan da ke gidan amma ta kasa, haka ta fito parloun jikinta duk ya mutu ta nufo baba ilu tana faɗin. "Baba ilu Wallahi na yi iya qoqarina amma abu dayane rashin Sa'a" "Subhanallah, wallahi Hajiya nima bangaren nan nawa hakane, babu wata hanya ta fita gidan nan da ta wuce gate, sai kuma idan katanga mutum zai tsallake" Leeya na shirin magana taji qarar waya, da sauri ta dago wayar don ganin wanda ke kira. Duk da tasan kiran bazai wuce mum ba. Hannu na rawa ta daga kiran. Gaisawa sukayi Sosai cikin farin ciki da kewa kamar kullum. Kamar zata gayawa mum abunda turab yayi mata sai kawai tayi shirunta. "Mum ina su meenal?" Daga dayan bangaren kuma mum tace "meenal ai sun wuce tun jiya, yanzu khulud ce kawai a gidan nan" "Allah sarki shikenan su meenal sun tafi....?" Murmushi mai sauti mum tayi tace "sun tafi amma zasu kawomuku ziyara in sha Allah kinji" "Yawwa mum dan Allah nace kinsan inda aka ajiye Aleena da zohal?" "Ehh to wallahi bansan address din gidan nasu ba, amma dai suma cikin garin ne saidai address ya bambanta, karki damu zan tambaya miki justice idan ya dawo" "Yawwa mum Nagode, ina gaida papu" "Zai ji, kuma kiyi haƙuri zamuzo zuwa ranar asabar kinji" "Tau amma mum ai yaune lahadi" "Eh sati mai zuwa nake magana" "Tau yayi mum Allah ya kaimu lokaci" "Ameen ya rabbi" "Mum Dan Allah idan khulud tana kusa ki bata wayan mu gaisa" "Okay bani mintuna biyu na kaimata wayar parlour ina kitchen" "Tau shikenan mum" leeya ta faɗa batare da ta yanke wayar ba. Mum na fita taci karo da Khulud zata shigo kitchen din ta domin taya mum aiki. "Mum ina zakije haka...? sai sauri kike" Mum na dariya tace "Khulud ke zanje na kaiwa waya leeyanah ke magana" Cikin matukar farin ciki Khulud ta daka tsalle ta karbi wayar sai murna take. Sallama tayi mata, itama ta amsa mata. "Khulud ki fita fili Magana zamuyi" Khulud kuma jin haka ya saka da fita daga kitchen ta sauka har parlon qasa. "Ina jinki sister me" Cewar khulud tana tattaro dukkan nutsuwarta wuri ɗaya. "Khulud dan Allah sirri nakeso muyi dake bana so ki gayawa kowa maganar nan kinji,,,,,dan Allah!" "Hummm, sister leeya me kike tunani, Wallahi bana tunanin Ni inyi magana dake kuma sannan inje in gayawa wani koh wata........! don Allah kar ki saka wannan a ranki kinji" "Nayarda dake, kuma na yarda da abunda kika fada, kinsan me??" "Sai kin fad'a" cewar Khulud. Leeyana kuma ta zage ta fara bawa Khulud labarin duk abunda ya faru tsakanin ta da turab bata rage mata komai ba har binciken da sukayi a cikin gidan ita da baba ilu. Bawai dan turab yana matsayin yaya ga Khulud ba, ko ba don haka ba wallahi ya bata tausayi matuqa. Har hawaye ta kusa yi domin tuni idanunta sun sauya kala. Mamaki sosai tasha wai turab ne yake durqusawa wata domin ta soshi, wanda 'yan mata 'yan gayu suke ribibinsa, wanda ko wace mace take burin ta sameshi amma ga leeyanah ta samu har take wasa da damarta. Khulud bata ji tsoron komai ba ta fara nunawa leeya kuskuren ta na qin karbarsa da tayi. "Ke zafaran yakeso, kuma kema shi kike so. Amma aka aura masa qanwarki, kuma yayi na'am da haka, yanzu suna nan zaune cikin aminci da kwanciyar hankali. Jiya sai da mukayi video call dasu, kingansu gwanin birgewa kamar masoyanda suka dauki lokaci mai tsawo a tare, a ransu komai ya wuce. zafaran ya riga ya dauki qaddararsa da Allah ya d'ora masa ta rashinki. Domin taimako da jihadi. Leeyanah wallahi idan ya-Turab ya rasaki mutuwa zaiyi! Kinsan ya-Turab yana dauke da ciwon zuciya mai tsanani, Wanda yakai limit dinda idan yaga abu ya kwallafa ransa gareshi bai samu ba komai yana iya faruwa dashi, ke turab yake so kuma ke ya saka ran samu. Koda akayi list din sunayen ku aka je masallaci inda za'a daura aure ba sunan ki keda turab aka sanya ba, fahad da zohal aka saka, Aleena kuma da ya-Turab aka sanya, ke kuma da zafaran. Amma sanin babbar matsalarda hakan zai haifar ya saka dad qarami ya bawa zafaran hakurin Rashin ki, ya kuma nuna masa irin mummunan halin da turab zai shiga idan ya rasaki ke, wata qila ma ya rasa ransa ta dalilin haka, kuma ya qara jaddada masa amintarda ke Tsakanin su, take hankalin zafaran ya tashi duk ya tsorata yana gani kamar duk abunda zai faru ya riga ya faru tunda an riga ankai sunayen masallaci. shikuma dad qarami da ya fahimci Zafaran ya tsorata ta kalaman sa ya sakashi fadin "wannan ba matsala bane zafaran ai zamu iya zuwa gaban limamin mu nemi da ya bamu takardar mu gyara. Haka dad qarami da zafaran suka koma masallaci suka sami limamin ba tare da sanin papu ba suka mayarda auren akan ke da kuma ya-Turab, shikuma ya karɓi Aleena matsayin matarsa, ko da kika ga papu ya shigo hargitse lokacin da aka daura aurenku ba don komai bane sai don yana ganin ba a yiwa zafaran adalci ba tunda aka hana masa aurenki. Kinji wannan shine silar sauyawar komai, wayasan inda ya-Turab ya tafi yanzu. Wata qila ma baya Nigeria Allah kadai yasani. Tun jiya mum na ta kiran wayarsa amma ba'a d'aga kiran. Kuma ma ai Da Baya cikin Nigeria number dinsa bazata je ba idan an kira" Leeyana da jikinta duk ya gama yin sanyi, tausayin ya-turab ya mamaye ko'ina a cikin jinin jikinta tace "Khulud dan Allah karki sanarwa da su mum da papu ki taimakamin kinji, wallahi na gane nice mai laifi dana kasa saurarensa, amma in sha Allah za'a gyara dan Allah ki turamin da number dinsa yanzu, kinji Please" ta fad'a kamar zatayi kuka. Khulud kam harda hawayenta tana jinjina girma da iko irin na sarkin sammai bakwai, wai ya-Turab ne da kansa yake duk wannan saboda mace. Leeyanah kuma tana zaune tayi zugummm, ta rasa me zatayi taji dadi duk ta rasa abunda ke damunta. Qarar shigowar saqo taji da sauri ta daga wayar, ganin number ce ya saka tayi copying, ta shiga gidan kira tayi dialing da sauri. Har kiran ya katse ba'a daga wayar ba, haka taci gaba da kiran har ta gaji amma ba'a dauka. Dole tasaka ta hakura ta dakatar da kiran. Washe gari ma haka ta wuni sukuku batada aiki banda kiran wayar amma kuma duk abu daya, ba amsa ba respond. Sosai leeyanah ta sauya,,,,,,,,,, tunani duk yayi mata yawa ko abinci bata iya ci, ta ma daina girka abinci gaba ɗaya balle taci. A safiyar kwana na uku ne misalin ƙarfe 2 na rana, leeyanah ce zaune a parlour ta gyara ko'ina na gidan, kwance take kan sofa ta kurawa wuri ɗaya idanu. Wayarta dake hannunta ta d'ago ta kira number ɗin turab amma a kashe take, a kwanakin nan bata da aiki banda kiran number din sa tun lokacin da aka tura mata numbar ɗin sa har yau bata bada tazarar minti d'aya ba wajen kiran number ɗin sa da aka bata, tun tana kiran numbar ba'a dagawa har takai yanzu idan ta kira tana jin ta kashe. Knocking taji anayi, amma bata ko kalli wurin ba taci gaba da abunda take, sosai ake kwankwasa gidan. Dan guntun tsaki tayi kafin ta miqe ta isa ga kofar dakin, a hankali ta fara bude kofar. Tsaye su biyu hannunsu sarqafe da juna fuskokin su dauke da yalwataccen murmushi. Leeyanah kuma ganin ƴar uwarta tsaye gabanta kamar a mafarki ta daka tsalle ta rungume ta cikin farinciki. Sosai taji dadin ganinsu gwanin birgewa. Janyota tayi suka shigo ciki, har zata rufe parlourn Aleena ta dan zaro idanun tace "kinbar mijina waje faa, haka zaki tarbemu kenan" Leeyana cikin mamaki ta kalli kofar parloun domin ita shaff ta manta tare suke da zafaran "kinga wallahi na manta fa, muje ki shigo dashi" Bud'e kofar leeyana ta kuma yi sai ga zafaran tsaye fuskar nan tasa a gimtse ya zuba hannayensa a aljihu. Leeyana ma tana dariya ta iso inda yake tsaye tace "in-low kayi haƙuri wallahi ganin yar uwata yasa na manta ka" Zafaran kam ko kallonta bai yi ba kuma bai kalli Aleena yace "to idan na yan uwane ni da nake bare sai in tafi kho, tunda ganin ƴar uwarki ya saka kin manta da mijinki, ke kuma ganin qanwarki ya saka kin manta da yayanki" ya fada yana mayarda kallonsa ga leeyanah. "Waye yayanah?" Cewar leeyanah. "Ni mana" zafaran ya bata amsa. "Uhmm--hmmm, bakaji ba dan Allah, qanwata fa kake aure, lallai ma" "Tau kice bangaren kika dauka, dan son girma" "Eh mana, waye bayason girma to" "Ni mana" zafaran ya fad'a yana nuna kansa. Dariya sukayi gaba ɗayansu suna shigewa cikin parlour. "Ikon Allah" Aleena ta faɗa lokacin da suka shigo parlon gaba daya. "Menene?" Zafaran ya tambayi Aleena. "Broth O duba kaga komai na parlorn nan da namu iri dayane, har komai fa" ta faɗa tana qara waro idanunta waje kamar wata qaramar yarinya. Dariya ta bashi sosai har sai da ya dara sannan yace mata "hakane wallahi beauty ki duba kiga can muka zauna mukaci abinci dazu koh, har kika bata min jiki da miya" "Ehh wallahi ugly nan ne, kaga ma ga sauran miyar can a qasa banyi mooping ba" "Ohh ni, beauty yaushe zaki daina qarya dan Allah" "Sai ka daina ugly" "Ni na ke qarya kho" zafaran ya faɗa yana jefamata pillown da ke hannunsa daidai lokacin da leeyanah ta shigo dauke da ruwa da drinks zata kawo musu. Ajiye musu tayi kan Centre table dinda ke tsakiyar parlourn ta juya zata koma bedroom. "Leeyanah!" Zafaran ya kira sunanta da asalin muryarsa wacce babu wasa a ciki. Jin haka ya saka ta mayarda hankalin ta gaba daya gareshi ta amsa masa "na'am" "Zoki zauna" ya faɗa yana nuna mata wurin zama. Komawa tayi ta zauna tsamm tana sauraren abunda zai fada. "Me yake damunki?" "Bakomai" leeyana ta faɗa muryarta na cracking. "Leeyanah saboda bani na aureki ba bazaki iya gayamin damuwarki ba, amma wannan ra'ayinkine ban taɓa tunanin akwai ranar da zaki iya boyemin damuwarki ba, wannan ba asalin leeyanahr okene bace, ba leeyanar ammi da abbi bace ba asalin leeyanahr da take kiran okene bace ta gayamasa damuwarta, ba leeyanar da bata qaunar ganin okene cikin damuwa bace, ba asalin leeyanahr da ke zuwa ta nemi okene domin ta gayamasa damuwarta bace. Aleena kitashi muje, muje kinji ba gidan nan bane gidan yar uwarmu wacce bazata iya boyemana sirrinta ba, ki tashi muje kinji" zafaran ya fad'a idanunsa duk sun kad'a sunyi jajir. Leeyana kuma da kuka ya kwace mata tayi saurin shan gabansu cikin kuka take fadin"hakika duk leeyanar ku ce wannan, kuma bakuda wata leeyana wacce ta wuce muku Ni, ya-zafaran kazo ka zauna na gayamaka damuwata, nasan zakayi ala wadai dani, zaka yi tirrrr da haleena, ban kasance mai fahimta da tunani ba, wallahi ya-zafaran ban kasance mai tausayi ba, dan Allah ina ya-Turab yake in roki yafiyarsa" Cikin tsananin tashin hankali ganin yanda leeya ke kuka kamar zata shid'e Zafaran yayi mata umurni da ta zauna, da kyar suka samu ta zauna ta daina kuka kuma. sai hawaye ne ke zubowa a hankali. Fuskar nan tata ta qara wani jaaa ga idanunta sun qara fito da asalin kalarsu ta blue mai dan haske. "Leeyana ki nutsu dakyau kimin bayanin abinda ya faru da turab, wallahi shine babban dalilinda ya kawomu gidan nan, domin tun washe garin ranar da kuka tare nake kiran wayarsa amma ba'a dauka, nayi tunanin nikadai ne yake yiwa haka, sai na kira fahad na sanar masa turab baya daukar wayana bansan laifin da na masa ba, amma shi ya gwada kiransa ya ga ko zai daga kiran. Kamar yanda yamin haka yayiwa fahad gashi bamu san address din gidan nan ba, kuma muna ta kiransa don ya sanar damu amma ya ki daukar kiran mu, ganin haka ya saka fahad ya ari wayar makwancinsa ya kira numbern dinsa da wayar amma duk abu ɗaya ake nunawa. Ba shi kadai ba har ni ma na kirashi da wata wayar amma bai dauka ba, tsakanin jiya da yau kuma muna ta kiran wayar a kashe. Shine muka yanke shawarar zuwa gidan nan mu duba ko lafiya, duk da muna da sanin abu ne mai wuya lafiyar ta kasance. Nayi shawarar sanarwa da mum wannan lamari sai Fahad ya dakatardani domin bamu da tabbacin lafiyar ce ko akasinta. Amma duk da haka sai da muka kira dad qarami ya bamu address din gidan nan, bani kadai ba har fahad ma zaizo nasan suna hanya yanzu haka. Meyake faruwa ne leeya, babban abunda ya tayar min da hankali shine da kika tambayeni ina turab, Ni a nawa ganin nine wanda ya kamata nayi miki wannan tambaya kho?" Leeya na sharar ƙwallah ta kwashe labarin duk abunda ya faru tsakanin ta da turab ta sanarwa da zafaran, hatta fahad da zohal da suke shigowa sai da jikinsu yayi sanyi, Allah ya gyarawa Fahad da Zafaran mutane ne masu dauriya da babu abunda zai hana su suyi kuka. Musamman ma kalamansa na karshe daya faɗa, sosai gaban zafaran ke duka idan ya auna maganganun turab a mizani tunani, kalmomine masu kamar wasiyya. "Allah ya kiyaye ka kar ka cutar da kanka turab, Allah ya bayyanaka, Allah ya tsareka a duk inda kake Allah yasa kada kayi yunkurin hallaka kanka" Zafaran ya fad'a a zuciyarsa da ta yimasa nauyi sosai, tausayin turab ne danqare a ciki..........................................✍🏼 46. __________________Sallamar fahad ce ta ratso wurin bayan shirun da ya gifta na dan lokaci. Sai zafaran ne yayi karfin halin amsa masa. Ko kaɗan zohal bataga rashin daidai da leeyana tayi ba idan ta tuna abubuwan da turab ya dinga aikatamata a can baya, hasali ma tayi mata dai-dai, babban abunda ya saka zohal taji ba dadi shine a can baya haqqoqin turab ba ko daya akan leeya, amma a yanzu kam sun rataya, a nan ne kawai zohal taga laifin leeyana da wautarta. "Kaji komai kho Fahad? Yanzu menene abun yi?" Zafaran ya fad'a yana sauke jajayen idanunsa akan fahad dake shirin zama. "Leeyana!" "Na'am ya-fahad" "Kiyi hakuri kinji, banga laifinki ba nima. Duba da yanda turab ya dinga aikatamaki abubuwa babu ko duba gaba, tun a farko yasan yana sonki amma zuciyarsa ta umurceshi da ya boye soyayyar har zuwa wannan lokaci...... yanzu gashi lokacin yazo kuma ba nasara kho, hmmm haka qaddarar take wallahi. Ki kwantarda hankalinki kinji, ki daina kuka. In Sha Allah komai zaizo ya wuce kamar ba'a yi ba. Leeyana bata amsa masa ba sai jijjiga masa kai da take alamar tana jinsa kenan. "Yawwa ina so in tambayeki kuma" 'dago da kanta tayi ta kura masa idanu alamar shi take sauraro. Fahad kam sai da ya tsorata lokacin da idanunsa da nata suka sar'ke. aikuwa da sauri ya janye nashi yana ci gaba da magana. "Leeyanah......! da misalin karfe nawa turab ya dawo gidan nan?" "Misalin karfe goma da ashirin" ta bashi amsa a dakile. "Gud, koda ya shigo kinji alamar yana tare da mutane ko wani motsi daga can wajen gidan?" "Gskiya banjiba, hasali ma Ni ban san shigowar sa ba. Sai dirar abu kawai naji a gabana yasa na tashi daga baccin da ya fara fizgata a lokacin" "Dirar abu kamar me kenan?" "Abunda ya dawo dashi a shopping leda, wallahi idan nace nasan ko meye qarya na maka domin ba ma wannan ne a gabana ba" "Okay, da zai fita dakin ya tsaya daukar wani abu misali takarda haka, ko kuma makulli ko waya ko wani abun daban" "Ah'ah ba abunda ya tsaya dauka, kuma tunda ya sanya kansa bai sake waiwayoba ya fita" "Da zai fita kinji qarar tashin mota ko kuma qarar bude kofar gate ko kuma wani abu makamancin haka" "Ah ah, amma dai naji qarar bude kofa, sai dai bansan ko wace qofa bace saboda ba qofa daya bace a gidan nan" "Bayan ya rufe kofar bedroom din kikaji qarar bude wata kofar" "Ehh" ta faɗa da tabbacin haka a fuskar ta. "koda kukazo gidan nan kun tarar da mai gadi" "Ehh akwai mai gadi tun kafin muzo ma, haka ya gayamin. Sannan kuma ya gayamin ba wanda ya fita a daren ranar tunda Aunty Rafa'at ta tafi, sannan ita Aunty Rafa'at tana tafiya ba jimawa motar sa ta shigo gidan. Mai gadin kuma ya gayamin tunda aka ajiye motar ba'a taɓa ta ba har yanzu" Ɗan murmushi fahad yayi domin a Duk lokacin da yake hango nasara a aikinsa yanayin irin wannan murmushin da yake gani kamar kwarin gwiwa ne gareshi. *Masu karatu karfa ku manta fahad babban lauya ne mai matsayi da dama, kuma lauyan gwamnati wanda ake damawa dashi. Bincike kuwa ba abu bane mai wuya a wurinsa" "Zafaran!" Fahad ya kira sunansa a tsanake. "Na'am fahad kai nake sauraro" "Nasan idan aka shigo da su mum cikin maganar nan dole zasu shigo da 'yan sanda domin bincike, nikuma a yanayin aikina idan aka shigo min da yan sanda aikin ba zaiyi yanda akeso ba" "Yanzu ya kake so ayi?" Cewar zafaran. So nake ka kira dad ƙarami ka tambaye shi su waye suka yi ginin gidan nan, nasan zai gaya maka ginannen sa ya siyeshi, to idan yace maka haka sai kace ya aramaka zanen gidan akwai abunda kakeso ka duba nasan ba zai maka musu ba domin kaima kayi masa hallarci. Yanzu fa hurry up please bamuda lokaci kaje suleja yanzu urgent please Allah ya tsare hanya" "Amma fahad meye alaqar zanen gidan nan da kuma 'batan turab" cewar zafaran da mamaki. Mikewa fahad yayi ya tattako har inda zafaran ke zaune ya dan bubbuga kafad'ar sa yace"zakasan amfanin haka abokina, yanzu ka tashi ka karbo mana zanen kawai" "Amma Meyasa sai naje har kaduna akan karbo zanen gidan nan, naga nima zan iya zana hoton gidan ko daga waje nake, balle ace ina kwana cikinsa ina tashi. Domin kasan ba abunda ya bambanta da gidan sa da kuma nawa gidan har kayan dakin ma. Sannan kuma wace irin mantuwa ce ta shiga kwakwalwar ka, kai da kanka da ka sanardani dad qarami yana nemana na fitar masa ta taswirar wani kamfani da yakeso ya gina a Imo" "Wallahi thummma tallahi na manta man zafaran, dan Allah kazo muje gida yanzun ka dauko instruments a fara fitar da zanen nan wallahi ina hangen wani abu amma abun bazai tabbata ba har sai an fitar da zanen gidan nan" Mikewa sukayi suka fita parloun ba tare da sunyi sallama da matayen nasu ba, suma su leeyana a ta bangarena su ba wata doguwar fira, jimami da tausayi duk ya cika zukatansu. A bangaren su zafaran kuma babu jimawa suka dawo dauke da duk wasu kayan amfani da zasu buqata a wurin zane. Sai da suka ware kyakkyawan wuri a cikin parlourn sannan suka ajiye kayayyakin. Zafaran kam wayarsa ya dauka suka fara zagawa lungu da saqo na gidan, video ya fara dauka da wayarsa har suka gama zaga ko'ina. Dawowa sukayi parlour, Zafaran ya zauna ya fara shirin sa, videon ya kunna ya mayarda hankalinsa cikin kwarewa da fasaha ya fara bin tsarin gidan dallah dallah yana zanawa. Sun dauki kusan awa daya har da mintuna arba'in zafaran na aikin zanen kafin ya fitar dashi tsafff, babu wani lungu ko wata kwana da take a cikin gidan wacce zafaran bai fitar ba. Fahad kuwa tunda zanen ya fara fitowa ya tsurawa wuri ɗaya idanu a cikin zanen tsawon lokaci har aka kammala fitar da komai dake wurin. Murmushin da ya zamo masa kamar dabi'a yayi yayinda yake tsaka da bincike a duk wani aiki da zai yi idan ya hango nasara. "Na kammala" zafaran ya fada yana qara gyara zaman allon da takardar zanen ke kai. "Good job mr. Zafaran me ka fahimta a wannan aikin namu" Tsawon sekonni zafaran shima yana kallon zanen tsappp "babu abunda na gane gaskiya, wallahi da wannan dama an gayawa jami'an bincike na farin kaya". "Hummm, man zafaran kenan. Kasan me?" Bai jira amsawar zafaran ba yaci gaba da faɗin "Turab fa yana gidan nan!" Ba zafaran ba!!! hatta su leeyana dake zaune jugum-jugum sai da suka girgiza da jin wannan zancen. "Taya turab yake zaune gidan nan tsawon kwanaki fahad?" "Gaskiya ya-Turab baya gidan nan ya-fahad, Wallahi Ni da kaina da kuma mai gadi ba inda Bamu bincika ba a gidan nan ciki da wajensa babu shi babu mafarin sa" "Akwai inda baku bincika ba leeyanah" "Ina ne wurin?" "Bani zanen zafaran" cewar Fahad yana miqawa zafaran hannunsa alamar ya bashi. Ciro zanen yayi ya miqa masa, shikuma ya mikawa leeya. "Nanne baku bincika ba" ya fada yana nunawa leeya dan wani guntun gini a cikin zanen kamar Piller, kamar kuma step. A cikin step din an fitarda wata ƴar qaramar shafaffiyar kofa wacce idan mutum bai kula ba ma zai iya rantsuwa bango ne. "Ya-fahad nan a bangon gefen bedroom ɗina ne" Ba bango bane muje ki nuna min wurin" Gaba ta shige su kuma suka rufamata baya, basu tsaya ko'ina ba sai gaban step din. "Ka gani bango ne fa" Murmushi kawai yayi yana shafa wallpaper da aka yi ado da ita a wurin. Daga cikin window bedroom ɗin ta ya saka hannu har can gefe sai da yaji hannunsa ya sauka akan handle. A hankali ya fara mirdashi har sai da ya buɗe, nan da nan kuwa kofa ta wangale sai ga wani daki ya bayyana daga cikin bangon step din. A wurin kuma saboda ba'a so aikin yayi two colour ne yasa aka shafe kofar kamar bango sannan aka saka wallpaper kalar bangon dakin gaba daya ya sajeh da ko wane bango. Daga ciki aka fitarda handle wanda sai ka saka hannunka ta windown bedroom dinda ke kusa da bangon sannan kake iya kamo handle din kofar, idan ka bude kuma kofa ce zata bayyana. Hakika duk wanda yake rayuwar Turai wannan ba baqon abu bane a wurin sa. sai dai idan baka sani bane zai zamo baqo a wurin ka. Sosai mamaki ya kusa kashe duk wanda yake wurin har zafaran da ya riga ya san irin haka, amma bai yi tunanin har Nigeria ana aiki da irin wannan gini ba. Wata kofa suka ga fahad ya nufa ita ma ya buɗe ta, madaidaicin daki ne da baza'a kirashi babba ba kai tsaye, haka kuma baza'a iya kiran dakin qarami ba domin gado biyu ne a dakin sai set daya na kujeru. Sai wardrobe da kuma toilet gefe. Shigarsu cikin dakin ya qara tabbatar musu da turab yana ciki domin kuwa da mayen qamshin turarensa suka fara cin karo. Wani madaidaicin Centre carpet mai taushin gske aka shimfida tsakiyar dakin, babu wata kwalliya ko ado a cikin dakin iya carpet din ne kawai sai kuma mirror. Shigowa sukayi gaba dayan su, babban abin mamaki kuwa dukansu wuri daya ne suka tsurawa idanu da alama wani abun suke kallo. Sallayah ce shimfiɗe a gefe sai cazbi da kuma waya dake kan sallayar da alama mamallakin kayan baije nesa ba. "Masha Allah, kagani ko zafaran na san akwai wani private part a gidan nan, Nima wallahi shekaran jiya na gano irin wurin nan a gidana. Nasan gidajen mu duk iri ɗayane amma wallahi banyi tunanin wuri daya aka ware aka fitarda private part ɗin nan ba, kaga ko a gidana daidai nan aka fitar dashi ba bambanci, shiyasa na buqaci kaimin zane ka fitarda gidan nan naga ko zan iya ganowa a wane bangare akayi dakin cikin ikon Allah kuma munyi nasarar ganowa ba tare da munsha wahala sosai ba, yanzu sai mu jirashi kawai nasan yana toilet" fahad ya faɗa yana zama kan daya daga cikin kujerun da ke dakin. Zafaran yayi murmushin jin dadi yace "gashinan kam Allah ya bayyana mana shi sai ya zo naci masa mutunci saboda me zai 'buya anan ba ci ba sha, sannan kuma baya ɗaga kiran kowa" cewar zafaran yana qoqarin kai hannunsa ga wayar da ke ajiye a gefe. Tsugunawar da zai yi ya dauki wayar ne karafff idanunsa suka sauka akan mutum kwance cikin jini, amma jinin ba mai yawa ba iya kansa ne a ciki da kuma wasu sauran sassa na jikinsa. "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, fahad kaga abunda na gani" zafaran ya fad'a yana nuna wurin da yatsarsa cike da tashin hankali. Da gudu suka isa kofar toilet inda suka hango wani mutum da suka kasa gane waye shi daga nesa. Sai da suka iso gaffff da shine suka fahimci ashe turab ne. Kamar fahad zai fashe da kuka saboda tsananin tausayi yace"ya subhanallah, zafaran yanzu turab ne ya dawo haka, ɗan gayu mara son kazanta, mutum cike da kyankyami. Yau shine a haka ji yanda gashin kansa ya hargitse, ga sajensa duk ya cika masa fuska, ba wanka, ba wanki. Jin yanda kayan jikinsa suka yi. Fuskar sa duk tayi baqi ta jeme a cikin kwanaki hudu kacal, yanzu da bamu zo ba bamu san iyakar abun da zai faru ba zafaran........" Zafaran yayi saurin katse fahad da faɗin; "Wallahi fahad turab baya numfashi!" Cikin Matukar tashin hankali suka rugo gare shi aguje har su leeyana dake gefe. Sunansa suka fara kira da karfi amma ko yatsunsa bai motsa ba balle su saka ran zai musu magana. "Fahad don girman Allah a kira mum a sanarmata uwa ce fa. Inada tabbacin yanda baya d'aga kiranmu itama baya d'aga kiranta, gashi yanzu chajin wayar ma ya qare ta dauke saboda yawan kiran da ake yimasa idan ta kira wayar ba samu zatayi ba ji kaga yanda turab dinmu ya dawo" zafaran ya fad'a cike da damuwa. "Ka kwantarda hankalinka zafaran ni yanzu tsorana kar turab ya rasa ransa a wannan yanayi da yake, kasan yanda za'a yi........?muje da shi asibiti tukunna idan muka kaishi asibiti sai mu kira su mum da papu mu sanarmusu, inaga yanzu ba amfanin saninda zasuyi tunda muma bamusan abunda yake damunsa ba" Garaff.....! sukaji qarar rufe kofa, da sauri kowa da yake wurin ya duba. "Leeyana ce!" "Fita tayi? "Wallahi nima bansan fitarta ba, sai bayan ta fita ne naji qarar kofa" Sosai zafaran da Fahad sukayi qoqarin fitar da turab daga dakin har suka sakashi cikin mota suka tafi dashi asibiti. Wani Asibitin kudi mafi kusa suka kaishi, cikin ikon Allah kuma suna isa aka karbeshi emergency domin duk wanda yayi tozali da turab dole sai ya tsorata ganin yanda yake ba ya da wani bambanci da gawa. Sai da suka gama cika ko wace takarda da za'a cika kafin suka kira gida suka sanardasu, cikin mintunan da basu haura hamsin ba su mum da kuma Khulud suka sauka asibitin. Duk irin karfin halin mum da kuma juriya da Alkunya irin ta tata sai da tayi kuka kamar ranta zai fita ganin halin da turab ya ke ciki. Bayan mintuna ashirin da zuwansu mum sai ga papu da dad qarami sun iso. Zaman jira suka fara yi domin tun zuwansu ba wani bayani game da turab, abu kamar wasa har aka shafe Awanni bakwai ba amo ba labari. Dad qarami kam kamar zai yi hauka, haka kawai yake bala'in son turab, sosai mutane suke jin mamakin wannan iri so da dad qarami ke yimasa saboda duk yanda yakeson ƴaƴansa na cikinsa baikai quarter na son da yake yiwa turab ba. Qaunace kawai da Allah ya sakawa dad qarami tun lokacin da turab ya fado duniya. Cikin matukar fushi dad qarami yace "Kagani ko justice Khattab, wannan shine babban kuskuren da nake gudu ya faru, Khattab kana sane da cewa ciwon turab ne ya tashi wanda muke matuqar kiyaye faruwar hakan tun yanada shekaru shida a duniya, wallahi idan turab ya rasa ransa bazan taba yafemuku ba daga kai har wannan yarinyar leeyana. Duk yanda akayi ta kasa fahimtarsa ne shiyasa abun ya zauna masa arai. Kuma da take muguwa sai taki sanarwa mutane da ciwon, Wallahil Azeem da tasan irin matsalar da ke tattare da hakan ta bata 'boye mana ba" Mum kuma hawaye na zuba daga idanunta ta amsawa dad qarami da fadin "baban twins kadaina aibatamin 'ya Wallahi leeyana ba muguwa bace, da ka san irin abubuwan da ya dinga mata a baya da bakaga laifinta ba saboda ta hukunta shi, kuma wannan da tayi shine daidai yanzu zai gane karatun ai, gobe ko cemasa akayi ya wulaqanta wata bazai yiba domin wannan abun daya faru......" "Dakata dan Allah hajiya fanaya" dad ya katse ta da tsawa ta hanyar daga mata hannu alamar ta tsaya din "d'anki ne fa na cikinki yake halin rayuwa ko mutuwa, amma har kike yaba wata banza wacce itace sanadiyyar fadawar sa halin da yake ciki, lallai. Kiyi abunki wallahi da ba dan a asibitina kika haifi yaron nan ba da na ce ba ke kika haifeshi ba" "Eh din ka fada mana baban twins, kace bani na haifi turab ba mana, kuma wallahi leeyana ba banza bace a wurina, uwa daya ta haifenu ta raine mu tare da uwarta. Kamar yanda nake jin Khulud haka nake jin leeyanah da turab, wallahi da za'a tona...... soyayyar leeyana tafi yawa a zuciyata bisa ga yaran nan" "Ba ke kika haifeta ba amma kike jin soyayyarta fiye da yaronda kika haifa da cikinki hummm....... tirrrr da ke wallahi" "Baban twins kanada bakin da zaka gayamin haka, kai ba d'an d'an uwanka kake yiwa wannan ba, ai kaima yanda kake son d'an d'an uwanka fiye da yaranda ka haifa haka nima nakeson ƴar ƴar uwata fiye da yaranda na haifa. Kaga anyi one one kenan sai dai ace tirrrr damu gaba ɗaya". "Mum, dad don Allah kudaina wannan gaban duniya.... gaban mu ƴaƴanku kuma. Wallahi wannan abun da kuke shine babban abun kunya domin yanzu ba lokacin yinsa bane. Wannan da kuke yaqi akansa da shine a kwance emergency fiye da awanni takwas. Da wannan cece kucen da kuke da ma ace addu'a kuka yimasa. Idan Mala'ikun karbar addu'a suna kusa kuma shikenan za'a karba, dan Allah ku daina wannan domin ko qananan yara bazasuyi irin abun nan da kuke ba haba dan Allah". Fahad ya faɗa cikin kuka. Dafa kafadarsa papu yayi yana masa murmushin karfin hali domin shi kadai yasan yanayin da yakeji agame da halin da babban d'ansa mafi soyuwa a ransa yake ciki. Yace"ka barsu fahad, idan basuyi hankali ba duniya ce zata saka suyi ba sai ance suyi ba, duk akan mutum daya ne ake wannan,.wata qila ma ya barmusu duniyar su huta, wata qila kuma yana shirin barin duniyar ne. domin halin da turab yake ciki ba wanda zai iya saka ransa da zai tashi yayi rayuwa kamar yanda yake dha" "In sha Allah turab zai tashi papu, kuma yaci gaba da tafiyarda rayuwar sa kamar dha ka saka ran haka" "Allah ya yarda fahad, Allah yayi muku albarka ya qara hada kanku" "Ameen" fahad ya faɗa yana qoqarin zama. Mum da dad ƙarami kuma jikinsu ne yayi sanyi sosai, duk suka fara jin kunyar abunda sukayi. Sallamar Aleena ce ta rasa wurin ita da zohal da kuma leeyana. Isowa sukayi suka gaisheda kowa dake wurin, zama Aleena tayi kusa ga dad qarami domin ita shine mahaifinta. Kuma shima yana jinta sosai kamar ƴar da ya haifa da cikinsa. Ita kuma leeyana ta isa ga mum ta rungume ta tare da fashewa da kuka. "Mum dan Allah ki yafe min amma wallahi bazan iya zama da....." Tun kafin ta qarasa mum tace "nasan bazaki iya ba leeyana kiyi hakuri kinji, wallahi idan na isa da shi dole sai ya sauwaqe miki kije ki auri wanda kikeso kema kiyi rayuwar ƴanci ,kwantar da hankalin ki idan har turab ya tashi an gama komai" mum ta fad'a idanunta na cikowa da ƙwallah. Dalili kuwa shine ta gayawa leeyana hakanne kawai ba dan tana da tabbacin zata iya saka turab ya sauwaqe mata ba, a iya qin yarda dashi da tayi ya sakashi wannan ciwon. idan aka sakashi ya saketa kuma wane hali sukeda tabbacin zai faɗa. Duk firar da suke ba wanda bai ji su ba kuma ba wanda bai ji kalaman da leeya ke fadi ba, haka zalika ba wanda bai ji abunda mum ta faɗa ba. Sosai mamakin leeya ya kashesu, musamman ma zohal da taga sauyawar leeyana lokaci ɗaya. Wanda ba a haka suka fito gida ba, tana ganin tsantsar butulci a cikin kwayar idon leeyana. Leeyana kuma cikin wani irin yanayi da suka kasa bambance farin ciki take ko bakin ciki ta buɗi baki zatayi magana. Sai ga likita ya karaso inda suke ba alamar fara'a a fuskar sa ko kaɗan yace "su waye suka kawo Turab k. waasib?" "Gamu nan" su fahad suka faɗa da sauri gaba dayansu duk suka miqe. "Ok good, Ina mahaifinsa?" Likitan ya kuma tambaya. "Gani nan" dad qarami ya fad'a yana qarasowa gaban likitan. "Dr. Mahad Barka da aiki, nine mahaifin turab. Koda muka iso kuna ciki da shi Allah yasa abun da sauqi, Saboda naga an dauki lokaci sosai" cewar dad qarami yana miqawa wanda ya kira da Dr. Mahad hannu. 'Dan sake fuska mutumin yayi shima ya miqa masa hannunsa sukayi musabaha yace "Dr gahees WAASIB ashe yaron ɗan mu ne kho ?" "Eh wallahi Dr. Ai nayi tunanin bazaka iya tuna ni ba domin anjima ba'a haɗu ba" "Haba dai, aikuwa babu abunda ka qara wanda ban sani ba ajikinka dr. Gahees, amma meyasa kuka bar yaron nan har ciwon nan yaci qarfinsa. Wallahi da ba'a yi gaggawan kawoshi asibiti ba da zai iya rasa ransa cikin mintuna talatin a wannan lokaci. Shin me kuka yimasa da zafi haka. Yanzu haka zuciyar sa ta kumbura sosai. Kuma ya zubarda jina. Sannan kuma hanyar da ke sada iska daga waje zuwa cikin hancinsa su fitarda numfashi ta toshe Saboda qaba da kumbura da zuciyarsa tayi. Ina tabbatar muku da yaronku bazai iya numfashi da kansa ba a yanzu. Sannan tunda muka shiga dashi emergency bai motsa ko yatsarsa ba balle yayi motsi. Munyi iyakar qoqarin mu amma abun yaso ya gagaremu. Akwai wata allura da akeyiwa masu irin ciwonsa a lokacin da suka kai limit din nan na halin rayuwa ko mutuwa cikin sekonni. Kuma munyi masa ita awa daya da rabi alurar take dauka zuwa qasa, bata haura haka face mutum bayada rayuwa gaba ɗaya. Amma idan akayi Sa'a cikin mintuna biyu ko uku allurar zata farkarda mara lafiya. Wani kuma mintuna talatin, wani awa daya, kai wani zata iya tayardashi a minti daya kacal. Wani kuma sai awa daya da mintuna talatin. Amma daga zarar ya haura hakan mutum bai motsa ba to he's no More! Ya mutu kenan kuma mun gwada wannan allurar ga danka turab" "Dr Yanzu turab ya mutu kenan!!?" Mum ta tambaya cikin matukar tashin hankali. Kamar yanda tayi haka dad qarami yayi shima, saidai nashi bai kai nata ba domin kuwa shi namiji ne sannan kuma babban Dr. Bazai yanke hukunci batare da yaji abunda likitan zai fadi ba. "Dr. Da aka gwada allurar wane sakamako ta bada" cewar papu. "Yawwa Alhaji, gaskiya sai dai mu godewa Allah domin kuwa da akayimasa allurar mintuna shida kawai ya dauka ta fara masa aiki kuma ya farfaɗo. A yanzu haka munyi masa allurorin da zasu saka zuciyarsa ta daidaita kuma ta sache da kumbura da tayi. Amma fa har yanzu baya iya controlling numfashin sa sai da muka saka masa oxygen. Sannan muka daura masa drip da zai hana shigar zazzaɓi bayan wannan, har kuma ya sami bacci. Saboda haka yanzu zaku iya shiga ku ganshi" Jikinsu duk yayi sanyi da jin halin da turab yake, wai turab. Wannan shine abunda yake faman yawo a kanunsu, ko a mafarki basu taɓa tunanin turab zai iya fadawa wannan hali ba hummm rayuwa kenan. Da sallama dauke a bakin wasu daga cikinsu suka shiga dakin, ganinsu kuma ya saka sauran likitocin da ke kansa suka fita suka basu wuri. Ga wurin zama amma ba wanda yayi yunkurin zaunawa ganin yanda turab ya ke. Jikinsa har wani yellow yayi saboda tsanin jigata da yayi. Leeyana kam zamanta tayi har da dora kafa daya akan daya, haqiqa leeyana ta sauya daga kawo Turab asibiti zuwa yanzu, domin lokacin da ya 'bata ba'a ganshiba kullum cikin damuwa da tunani take, amma kuma a yanzu sai saɓanin hakan take nunawa. Sun jima tsaye akansa mai addu'a yanayi, mai zubarmasa da ƙwallah nayi. A hankali ya fara bude idanunsa yana kallon kowa, ba wanda ya kula da ya buɗe idanunsa sai ita! Kuma idanunsa na haduwa da nata ta masa wani irin kallo da ya saka shi zabura kamar zai fado daga kan gadon. Hakan ne ya mayarda hankalinsu gareshi. Ganin ya farka ya saka dad qarami zuwa wurinsa da azama. Ya jiki ya fara masa, shikuma yana daga masa kansa alamar yaji sauki. Zafaran da fahad ne suka qaraso gareshi, zafaran kamar mace tuni kuka ya kwace masa yana shafa kan abokin nasa. Ganin haka ya saka turab ya lumshe idanunsa sannan ya juya kansa gefe ya daina kallon gefen da zafaran yake. "Nagane abokina, bakaso ina kuka ko to kayi hakuri ka juyo garemu na daina kukan kaji" zafaran ya fad'a still hawaye na tsiyayo wa daga idanunsa, shima ya fadi hakan ne kawai saboda turab din ya juyo. Shi kuma turab da yaji abunda zafaran yace a hankali Cikin rashin kwarin jiki ya mayarda fuskarsa wajen su yana qara matse hannun zafaran da fahad dake sarqafe da nasa hannun. Mum da khulud ne suka zo inda yake, mum ta shafa goshin sa hawayen ta na qara guda kamar fanfo tace"Allah ya baka Lafiya, Allah ya tada kafadun ka, ya saka ciwon nan ya zama kaffara a gareka". Hannunsa ya fara dagawa a hankali har saida yakai daidai idanunta ya shafe mata hawaye yana girgiza mata kansa. Khulud kam kamar jira take tana ganin haka itama kuka mai sauti ya kufcemata, da sauri Aleena tazo ta janyeta suka fita daga dakin. Papu yazo ya masa ya jiki shima, komai da papu yake yi sukuku yake yinsa domin tunanin halin da turab ya shiga ya hana masa gudanar da lamarinsa kamar yanda yake. Ta ido fahad yayi wa zohal alama, haka tazo itama tayi masa ya jiki sannan ta koma ta zauna, duk abunda suke leeyana na zaune ko motsawa batayiba, kuma tanajin duk abunda suke fad'a amma ko kallon wurin batayi. Aleena da khulud ne suka dawo dakin bayan Aleena ta rarrashi khulud akan ta daina kuka. Basu tsaya ko'ina ba sai gaban gadonda turab yake. Sannu da jiki suka yimasa, amma da kansa kaɗai yake iya amsa musu domin oxygen ne a hancinsa. Komawa sukayi suka zauna kowa na saqa abunda yake saqawa a ransa game da leeyana da kuma sauyawarta cikin ɗan qaramin lokaci. Zafaran kam har qaryata kansa yake wai leeyanahr ammice ta mayar da Rayuwar ta haka ba tausayi ko kadan kamar ba musulma ba, ai ko wanda ba Musulmi ba idan yaga ɗan uwansa a irin wannan yanayi dole ne ya tausaya masa balle turab da yake dan uwanta na jini, kuma yayanta da-ɗin daɗawa kuma mijinta. A rayuwar Fahad bai taba ji a ransa ya tsani mutum ba sai a wannan lokaci, kusan yanayi daya suka shiga da mahaifinsa dad ƙarami. Shi dad yana gani ta dalilin leeyana ne d'ansa ke kwace cikin matsananciyar jinya. Kowa da yanda yake kallon leeya a wannan lokaci. Shikuma turab yayi duk yanda zai yi domin su haɗa idanu amma taqi yarda samm. Mintuna biyu da suka wuce ba wanda ya qara fadin komai kuma ba wanda ya qara kula kowa a cikinsu, sai dad ƙarami ne yake tambayar turab jikinsa akai akai Har bacci ya daukeshi, saida dad ƙarami ya fahimci yayi bacci ne sannan ya daina masa sannu. Miƙewa leeyana tayi fuskar ta a hade kamar bata taba bud'e bakinta ba da nufin dariya. Tafiya ta fara yi d'ad'd'aya kamar wata basarakiya, kowa dake wurin ya zubamata na mujiya domin suga iya gudun ruwanta. durkusa tayi da gwiwoyinta gabansa har ya kai ba wata tazara sosai a tsakanin su, hannuta ta saka kan qirjinsa, sannan ta ɗora kanta saitin zuciyar sa ta kawarda kanta daga fuskar sa cikin muryar kuka take fadin "nasan bakajin lafazin bakina, saboda halin jinya da kake ciki. Amma hakan bazai saka in fasa furucin zuciya ta ba, saboda nasan ba kalamaina bane ba, zuciyata ce take kai sako ga zuciyarka" numfashi mai qarfi ta jaa saboda kukan da ke shirin zo mata taci gaba fadin "a gaskiya zuciyata tana sonka!!!! Kuma ta kasa daina sonka ya-turab" Huuuhhh ta furzarda wata iska mai zafi. "Ina fargabar zan iya tsintar kaina a cikin halin da kake ciki, koma fiye da haka idan har aka rabani dakai. Dan Allah....... Ina roqon alfarmarka, ka daukeni a matsayin abokiyar rayuwar ka, dan nima na rayu! Nayi qoqarin cireka araina ganin baka sona, amma abun ya gagara, ina fargabar abunda Zai faru dani idan na rasaka. Na kasa danne abunda ke zuciyata. Saboda kaine burin zuciyata Wallahi ina matukar kaunar ka ya-turab! Na rokeka ka qaunaceni koda quarter ne a cikin tarin qaunar da nake maka" Leeya ta qarashe maganar ta da wani kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, musamman Wanda akayi dominsa. Suman tsaye kafff mutanen da ke dakin sukayi, baramma fahad dake ji kamar ya shaqeta ta mutu. To a wane mizani zasu daura leeyana. Dama tana sonshi amma ta wahalarda kanta kuma ta wahalar da shi. Gsky lamarin nan nasu akwai ban tausayi da izza da al'ajabi, ga tarin jin kai. Miqewa tayi zata tafi while tana ci gaba da kukanta, ji tayi an qara kwantarda kanta a qirjin nasa. Hannunsa daya ya saka ya cire oxygen din da ke bakinsa, dayan hannun kuma ya kwantar da kan leeya lif a qirjinsa yana shafa gefen fuskar ta. Mamaki bai ida kashe su fahad da sauran mutane ba sai da suka ji turab yana magana da muryar nan tasa mai cike da kwarjini lafiya qalau take fita kamar ba shi bane ke ciwo. "Ko da zan sha wahala fiye da haka, zuciyata ba za ta taɓa janye miki ba. Kin cika rayuwata da haske da farin ciki a duk lokacin da wani zai ambaceki kusa dani, kuma burina na ƙarshe a duniyar nan bai wuce na kasance tare da ke ba, kasantuwa ta har abada. Ina son ki da zuciya ɗaya, so domin Allah ba don kyawunki ko dirinki ko wata sura ta jikinki ba, halattacciyar soyayyar ki da Allah ya sanyamin a zuciya. Na sha wahala sosai saboda ke, bana tunanin akwai kalmar da zanyi amfani da ita wajen sanardake leeyana wallahi kece komai nawa, kuma duk irin tashin hankali da tsanani dana shiga akanki ba zai hana ni faɗin yadda nake ji ba. Soyayyarki ta canza ni, ta sa na fahimci ma’anar rayuwa. INa roƙon Allah ya sanye miki halattacciyar soyayya a zuciyar ki akaina leeya. Ina sonki ina kuma qaunarki dan Allah kar ki qara nisanta kanki dani kinji Please" ya fada yana qara qanqameta jikinsa. Gyaran murya sukaji anyi daga bayansu, cikin sauri leeya ta miqe ya sake janyota, a wannan karon kusa dashi ya zaunarda ita kan gadon da yake kwance. "Sai dai su fita su bamu wuri ba ke zaki fita ba, idan kika fita wazai kula dani" turab ya fada yana daga muryarsa don suji abunda yake fadi. "Ga mum nan zata kula da kai, ga kuma ya-fahad nan da ya-zafaran" leeya ta faɗa tana ci gaba da qoqarin tashi kusa dashi, har ga Allah ita dai kunya takeji. "Mum zata kula dani kika ce? To idan mum ta kula dani wazai kula da pa? Zafaran da fahad kuma ina zan iya dasu waɗan nan gardawa, amma dan Allah karki gayamusu kinji, kinga sirri muke kho" Da sauri ta daga kanta ta kalli inda fahad da zafaran suke tsaye,.fahad kam sarkin zuciya ya cika fammm, domin yanaji duk firarsu. Kujera ya janyo yazo wurin da turab ke kwance ya ajiye sannan ya zauna. sheqeqe yake kallonsa yace"tho sabon mara kunya butulci zakayiwa mum, da can data kula dakai wata mai kular ka samowa pa, shine dan amarya ta karɓe ka zakazo kana mana surutai. Yanzu bakinka ya kere na kowa a wurin nan, amma mintuna goma da suka wuce iya kanka kake iya motsawa ko zarahin yin magana baka da sai yanzu ne zakazo kana cika mana kunne da surutai" Murmushi turab yayi yace " dad ku bazakuzo muyi firar ba sai dai ku koma gefe daya meyake faruwa" "Son, ai mune ya kamata mu tambayi abunda ke faruwa" cewar dad qarami. Murmushi turab yayi a karo na biyu kafin ya dafa gadon sosai ya miqe zaune ya jingina da bango, tari yayi a hankali sau biyu sannan yace "dad leeyanace duk ciwona, yanzu kuma ta dawo gareni. Wallahi kaso chasa'in na abunda nakeji ya ragu" "Ungo nan mara kunya, kai bakasan duk iyayenka ne ke wurin nan ba" mum ta faɗa tana watse masa hannu. "Na karbi zagin dear mum, amma ai kune kuka haɗa auren kunyar me zanji. Yawwa dan Allah mum kwananku nawa a asibitin nan?" A ganin mum kamar tambayar raini ce kawai turab yayi mata, amma shi bil-haqqi yayi mata tambayar harga Allah bai sani ba. Tunawa tayi koda aka kawoshi hospital din nan baya numfashi, ba kuma yanda za'a yi ya iya ganewa tunda yana halin ciwo. "Bamu kwana ba, yanzu ne zamu kwana in sha Allah" Zaro idanu yayi sosai ya d'an marairaice yace "mum ku koma gida Please gobe sai kuzo da safe, dan Allah ku tafi angode da jinya Allah ya biyaku na sallameku sai gobe da safe kuzo" Zafaran da Fahad kamar su naɗa masa duka sukeji, wato gayen nan yanaso ya musu wulaqanci kho, zai gane ai. Kuma Allah yasa bashi kaɗai akayiwa aure ba balle ya kurantamusu. Fira sukaci gaba cikin nishadi har aka kira sallahr isha, ana bashi kula sosai lokaci zuwa lokaci. Dad ƙarami da Papu daga fita sallah suka wuce suleja. Mum da Khulud kuma suka wuce gidansu dake nan cikin abuja. Idan baku manta ba a can baya na sanarmuku da su mum da papu abuja ne Asalin mazaunarsu, khulud ce ta saka suka dawo suleja da zama. Saboda haka basu zarce ko'ina ba sai a gidan nasu. Leeya da turab kuma sun sha fira sosai, har suka raba dare suna labaran nishadi kamar ba su ba. Tun suna saka ran dawowarsu mum har suka fitarda ran domin kuwa su mum sun dauki maganar turab da gaske sanin likitoci sun gargadesu a karo na karshe akan rayuwarsa. Shi yasa duk abunda ya faɗa jiki na rawa ake aikawata. Sai cahn dare gabanin asuba ya farka daga baccinsa, idanu ya tsuramata yana tunanin meye ma qarshen zancensu a daren jiya. Shidai yasan labari kawai take bashi shikenan sai yanzu da ya farka ya ganta a haka. Kenan bacci yayi lokacin da take bashi labarin, "Allah sarki" ya furta a fili ganin yanda take. "Kenan zaune ta kwana" ya faɗa yana shafa bayanta. "Ki yafemin kinji, Wallahi dana san wannan wahalallen bacci zakiyi da na baki gado na zauna kan kujera. Blanket din da ya rufa dashi ya sauke ya rufa mata domin sanyi ya fara sauka, yana rufa mata kuwa yaji ta sauke numfashi. Addu'a yayi sannan ya tofa mata shikuma ya tattakure jikinsa ya saka hannunsa tsakanin cinyoyinsa ya mayarda bacci.........................✍🏼 47. ____________sai da aka fara kiraye kirayen sallahr asuba ne Dr. Mahad ya shigo dakin, mamakin ne ya kusa kashe shi. "Kenan akan yarinya nan ne ya shiga wannan tashin hankali....?" Murmushi yayi a bayyane ganin yanda kwanciyar tasu take, kana gani kasan ba'a shirye suka kwanta ba. Abun ya birge Dr mahad sosai, wayarsa ya ciro ya fara yimusu video. Ganin yanda leeya ke zaune ta dora kanta kan gadon da yake kwance, shikuma ya cire blanket dinda yake rufe da shi ya sakamata. Kwance yake a takure duk ya du'kun'kugune wuri daya, kana ganinsa kasan matuqar sanyi yakeji. Sai da Dr ya gama yimusu video sannan yadan bubbuga gadon a hankali yanda iya leeyanah ce kawai zataji, baya ma so ya tada turab. Tashi tayi tana murza idanun ta har ta bud'e su gaba d'aya. "Lahhhhh wai bacci nayi da zaune" ta fada fuskar ta dauke da mamaki. "Soyayya tayi dadi har baki san kinyi bacci ba kho, wai dama ku kadai kuka kwana asibitin nan duk ina su Dr". Dad ƙarami kenan. "Wallahi mu kadai muka kwana su dad sun tafi gida ai, amma zasu zo da safiyar nan" Juyawa tayi ta kalli turab ta ga yanda yake kwance, cikin matuqar tausayinsa ta cire blanket dinda ya yafa mata ta saka masa. "Ki cire kawai nifa alwala zanyi inyi sallah nasan lokaci yayi" Cikin damuwa ta ce "ya turab Meyasa ka hana kanka blanket tsawon dare, kasan mura zata iya kamaka idan sanyinan ya maka yawa" "Kema idan na barki kika kwana murar ta kamaki fa, kinga Ni zaki daura wa aiki domin zan rama jinyarda kika min haka kk so koh?" "Ah ah ya-Turab Ni dan Allah nake zaune anan, da kuma kwadayin ladar da zan samu" "To Allah ya baki lada, ki tashi kiyi alwala. Nima zanyi sai nazo muyi sallah" Sosai farin ciki ya kama Dr mahad domin da tunanin halin da turab yake ciki ya kwana, shiyasa yayi sammako tun asuba yazo ya duba shi. Amma yayi mamaki kwarai da gaske ganin yanda jikinsa yayi kyau, kuma ba mamaki a cikin ikon Allah domin Mafi yawa masu irin ciwon nan komai neesan da yayi idan aka samarmusu da abunda suke buqata zasu iya warkewa sumul cikin mintuna qalilan. Bayan sunyi alwala sukayi sallah, bacci suka koma har sai da rana ta take. Fahad da matarsa suka fara zuwa, sannan dad ƙarami yazo da iyalansa gaba ɗaya. Sai da aka dan jima mum da Khulud suka qaraso, sannan papu yazo. Zuwan papu ba jimawa ga zafaran da Matarsa Aleena. Wata irin kulawa turab yake samu daga ɓangarorin musamman ma matarsa da basa rabuwa tare koda yaushe, sosai shaquwa ta shiga tsakanin su kamar da can sun saba. Kuma hakan yana birge kowa, kowa yana musu fatar zaman lafiya mai dorewa. Kwanan su uku a asibitin aka sallamesu domin yaji sauqi sosai, idan ka ganshi zaka iya rantsuwa ba shi bane mara lafiyan da ake jinya. Duk a zatonsa gidan su dashi da matarsa za'a fara kaisu a ajiye sai yaga an koma dasu suleja, bai musa ba domin baisan dalilin iyayen nasa nayin haka ba. Koda suka koma gida kuma mutane sai tururuwa suke wajen dubinsa musamman ma families. Kullum ba'a raba gidan da ƴan dubiya, babban abunda ya bawa turab mamaki shine tunda suka dawo yau kusan kwanaki hud'u kenann amma ko kusa bai saka leeyana a ido ba. Tawaga d'aya ta sojaji daga ko wane bangare na sassan duniya suka had'o zuga suka zo dubin turab. Duk da su mum basu san da zuwan su ba, ba qaramar tarba suka samu ba, wanda har ƴan gidan tv da jarida suka zo ganin waɗannan mutane. Turab kam bakinsa kamar gonar auduga, farin cikinsa ya kasa boyuwa har sai da ya tambaya a ina sukaji bashi da lafiya. Sai suka gayamasa a social media suka ga ana yad'awa shine suka kira sauran qasashe akayi meeting kuma aka za'bi 'bangarori da dama a kowane sashe har aka had'a tawaga akazo dubinsa. Sosai abun ya bawa mutane sha'awa had'e da mamaki, sun jima a gidan kafin sukayi sallama da mutane suka koma inda suka fito. Kwana biyu da faruwar haka kuma turab ya kasa hakuri har sai da yaje ya sami mum da maganar. "Mum, tambaya nazo nayi dan Allah" Murmushi mum tayi tace "nasan zakazo don yin tambayar ai" "Mum ina take Please?" "Me kake so?" "Matata nake so mum" ya fad'a in funny way. "Wai yaushe ka zama haka turab?" "Tun ranarda muka dawo hospital, Ni ina zargin likitan nan fah mum..... inaga shi yamin allura na zama haka yanda kika gani nan" Pillow ta dauka da niyar jefamasa ya hade hannunsa wuri ɗaya "I'm so sorry mum Wallahi ba shi nazo inyi ba, dan Allah ina leeyana" "Turab....!, ta kira sunansa babu wasa a fuskar ta. Ganin haka ya saka shima turab din ya shiga taitayinsa. "Na'am mum" "Kasan yanda yanayin daurin auren nan naku ya kasance ko?, hasali ma ba kowa yasan da shi ba. Hatta justice bai san kai aka aurawa leeyana ba sai daga bayan nan ya san haka, kuma kaga auren nan anyishi babu wani shiri kho? To yanzu Alhmdullillah tunda mun fahimci kuna son junanku za'a qara daura auren nan bayan sati daya, amma gskiya Ni sati daya yamin kadan saboda ina so in gyara 'ya'yana kamar yanda akeyiwa sauran 'ya'ya, da kyar justice ya yarda ya mayarda shi wata daya, kafin nan kuma munaso gobe zamu wuceh Maiduguri da ita da kuma qanwarta mu nunawa families dinmu su" Cikin tsananin bakin ciki yace"wata d'aya mum?" "Eh ko yayi kadan?" Wata irin zufa yaji tana karyomasa tun daga tsakiyar kansa har tafin kafafuwan sa "mum Dani za'a je?" "Ai yanzu haka ma kana can" "Haba mum meyakai ga wannan, dan Allah mum ku barni na ganta Please kafin ku wuce" "Idan mun dawo dai ka ganta, kuma ko mun dawo ba ranar ba sai ranarda aka kaimaka ita gidanka" "No mum....., Dan Allah karki yankewa d'an ki wannan hukunci haba dai mum" Ganin turab naso ya wargaje musu plain ya saka tace masa "tana gidan maman twins kaduna, na baka damar kaje gobe misalin ƙarfe sha daya na rana, idan ka wuce haka bazaka samemu ba" "Mum me zai hana naje yau" "Sai gobe nace maka! Idan kuma kaje yau wallahi zan gayawa maman twins kar ta barka ka ganta" "Na tuba mum, yanda kikace haka za'a yi" Washe gari tun karfe tara na safe ya fara shirin tafiya, ya kira zafaran da Fahad ya sanar musu. On ready su suna Abuja, saboda haka basu tsaya wani bata lokaci ba suka zo suleja gaba ɗaya harda matansu, fahad gidansu zohal ya kaita kafin su dawo. Shikuma zafaran ya ajiye Aleena gidan mum Saboda sanin da ita za'a yi tafiya zuwa Maiduguri yau. Sai da mum ta fahimci su turab sunyi nisa da tafiyarsu sannan suka dauki hanyar zuwa Maiduguri suma. * Bayan awanni biyu. turab, fahad da zafaran ne zaune a parlourn mummy-neesah suna cin abinci. Su fahad sai tsokanarsa suke. "Yanzu duk girman nan naka anyi maka wayo fa chief military health service" Tsaki yayi, bai kula ba yaci gaba da cin abincinsa. "Turab ka kira kaji ko sun sauka lafiya" "Bazan kira ba......!, ai kaima matarka tana cikin tafiyar me zai hana ka kira kaji kai da kake son ji" Dariya suka qara shekewa da ita fahad yace"mum dai ba ganin leeyana ta turo mu ba ganin abincin mummy ta turo mu" "Ehh wallahi ka fahimci karatun" Zafaran ya fad'a yana dariya. Haka sukaci gaba da tsokanarsa shikuma yaqie biyemusu har suka gaji sukayi shiru. Haqiqa mum bata sanarwa turab da gaskiyar inda leeyana take ba, domin da sukazo kaduna mummy-neesah ta tabbatar musu da ba wata leeyana da ke zaune a gidan. Mum ta fad'a musu haka ne kawai. **** A bangaren su leeyana kuma sai bayan la'asar liss rana na qoqarin shigewa suka iso Maiduguri, basu zarce ko'ina ba sai gidan ummansu mum fanaya. Su biyar ne a motar, mum da kuma Aunty Rafa'at sai Aleena da kuma leeyana. Sosai suka sami kyakkyawar tarba domin mum kam ƴar gidace ba wanda bai santa ba, sauran ne ba'a sani ba. Mahaifiyarsu su mum wacce suke kira da umma tace "fanaya da baki kuke tafe haka" "Eh wallahi umma baki ne kam, amma a gidan nan ba baqi bane gskiya" "Toh......,,,,, Aikuwa kema kanki baquwarce" "Ah Ni ba bakuwa bace umma, yawwa Umma inaso atara mutanen gidan nan namu gaba daya, akwai bayanin da nakeso nayi da kowannen su" "Lafiya dai koh fanaya?" Ummah ta tambaya. "Lafiya kalau wallahi ummah nidai na buqaci hakan ne kawai" "To shikenan bara na saka a gayawa kowa zuwa bayan sallar isha idan kowa ya kammala aikin da zaiyi sai yazo a haɗu anan" Haka kuwa akayi bayan sallahr isha duk mutanen gidan nasu suka hadu a Babban parlourn da ke gidan wanda shine parlourn mahaifinsu marigayi Hahmeed abbansu mum. Bayan gaisuwar mutumci da sukayi mum ta fara koro musu bayani akan leeyana da kuma qanwarta Aleena, mum ta kwashe labarin su kaff da kuma irin wahalar da sukayi da yanda ake nunawa leeyana kyama da kuma irin rayuwarda suka gudanar akan haka. Ba wanda bai zubarwa da labarin nasu hawaye ba, hatta aunty Rafa'at da take qanwar Papu sai da labarin su leeyana ya sanyaya jikinta. Hannu umma ta ware musu cikin muryar kuka tace "kuzo gareni jikokina, nice mahaifiyar faheema. Na yafe mata har lahira, Allah ya jiqanta ya sanyaya makwancinta" Da gudu suka faɗa jikin umma suka rungumeta suna sakin wani marayen kuka. Tun a cikin daren aka fara nunasu ga sauran families dinda ke kusa, har mum na sanar dasu cewa za'a yiwa leeya aure, domin ita Aleena da aurenta aka, itama dai keeyaba da auren nata sai dai za'a qara daurawane saboda ba kowa yasan da wancan ba, kuma nan da wata ɗaya mai zuwa ne auren. A gidan kuwa kowa so yake ace wurinsa su leeyana zasu kwana, cikin ɗan qanqanin lokaci yaran suka shiga ran mutane, domin wata irin kulawa suke samu daga dangin nasu, soyayya da qauna ake nuna musu ta kowane bangare. Hajiya ummasalima babbar aminiyar Ammi ce Lokacin suna 'yan mata, yarda ce mai qarfi a tsakanin su. Ko a lokacin da labarin guduwar Ammi da saurayinta suka sami ummasalima sai da tayi zazzaɓi na kwana da kwanaki, kullum bata da aiki sai kuka da tunani. Sai da abun ya dan lafa ne ta sami sauqi, tun daga lokacin bata qara jin wani labari daga Ammi ba. Sai kawai rana ɗaya aka je mata da Leeya da Aleena sune 'ya'yan fanaya. Hmmm zo kaga Gata, ummasalima ji take kamar ta hadiyesu saboda tsananin qaunar da take yiwa mahaifiyarsu. Da taji labarin auren da za'a yimusu tace "hmmm ina da rayuwa ina numfashi zan bar yaran nan a garin nan a gyarasu, hajiya fanaya ina so ki bani passport dinki da na yaran nan in sha Allah zuwa ranar lahadi zamu wuce Thailand ayi musu gyaran jiki mai kyau" Mum kam ta rasa da wane baki zatayiwa ummasalima Godiya baki har kunne ta isa gida ta gayawa umma, sannan ta kira gida ta sanarwa da mazajen yaran ta kuma sanarwa da papu da dad ƙarami. Ranar Lahadi kuwa suka dauki hanya sai kasar Thailand, mum fanaya da kuma ummasalima da leeyana da Aleena. Satinsu biyu a Thailand, suka dawo tare da uban siyayyar da ummasalima ta yimusu. Maiduguri suka dawo kwanan su daya suka tattara suka koma suleja. Ranar kamar turab yayi hauka, shidai zafaran a ranar da suka dawo a ranar aka mayar masa da matarsa. A wannan karon ma haka akayi domin turab ya kasa idanun sa ko zai yi tozali da ita amma inahhhh.....,,,,,. Duk ya shiga damuwar akan haka, itama leeyana tayi kewarsa sosai. Wani lokacin ma tanaso ta kirashi amma kuma sai ta fasa. tuno da gargadin mum. Yau kam ta kuduri aniyar kiransa tunda saura kwana biyar kacal a daura auren. Da dare Misalin ƙarfe goma ta kirashi, yana kwance bacci na fizgarsa a hankali yaji qarar kiran waya. Bai duba lambarba ya d'aga kiran. Lokacin da muryarta ta doki dodon kunnensa sai da ya zabura. "Mafarki nake ko gske leeyana kece, Allah sarki sama da wata daya bana ganin ki, kuma banajin wannan Muryar. Sai yau kika tuna dani" "Lahhh, haka ma zakace saboda na kiraka kho" "Awww gori kike min saboda kin kirani, to ki kashe wayarki bana buqatar kiran na ki" 'kitttt ta kashe wayar tana jin haushin kanta, on ready tasan mutumin nan d'an wulaqancine dama ta sani da bata kirashi ba wallahi. Tana cikin zancen zuci ne taji qarar ringing din waya, dago wayar tayi tana dubawa,.ganin baƙuwar number ya sakata ɗaukar kiran. "Kinga yanzu Ni na kira ki ba wani gori da zaki min" 'kayataccen murmushi tayi kamar yana kusa da ita tace "ni dama can ba gori na maka ba kawai naga kanaso ka dauramin laifi ne" "Ah ah na isa in dauramiki laifi, rufamin asiri kinji 'yar nan" ya fad'a cikin sigar wasa. Dariya sukayi gaba ɗaya cikin nishadi, daga nan fira ta 'barke a tsakanin su har ta manta da gargadin mum. Da kalamansa ya bugo cikinta ta gayamasa inda take zaune tsawon lokaci. Wanda mum ta gargadeta akan kada ta sanar masa, shafff ta manta sai bayan ta gayamasa ne ta tuna da haka. "Yanzu dama tsawon lokacin nan kina gidan Aunty Rafa'at, ance rashin sani yafi dare duhu amma wallahi ko yau nabi ta unguwar na shiga gari......! Shiru yayi bai idarda fadin abunda yakeson fad'a ba Sakamakon jin kiraye kirayen sallahr asuba ta aka farayi. "Wai kana nufin kiran sallahr asuba nake ji?" "Abun mamaki" turab ya faɗa yana dariya. Kuka ta fashe dashi ala dole ya hanata yin bacci. da kyar ya samu tayi shiru suka ci gaba da fira kafin lokacin zuwansa masallaci yayi. Idan ba farin sani kayiwa leeyana ba, ba lallai ka iya gane ta ba sakamakon gyaran da ta samu daga kwararrun turawa. Jikinta yayi sumul babu alamar 'kurji ko kuma tabo, tayi mugun fari tassss, fatarta sai shining take da wani 'kyalli mai daukar ido. Fuskar ta sai sheqi da walwali take tayi wani smooth gwanin kyau. Idanunta sun qara fito da ainihin asalin rikitacciyar colour dinsu mai matuqar daukar hankalin wanda yayi tozali dasu. Magungunan mata kam ba'a magana dan mum da ummasalima zage wa sukayi suka samarsu da komai na wannan bangare. Qamshi kuwa duk idan ta wuce sai ta barshi domin gyara suka samu sosai daga dangin nasu a Maiduguri, sosai aka tsumasu da humrah kala daban daban. Ita kanta dadin qamshinta take ji balle wanda yazo kusa da ita. Kwance akan makeken bed dinda ke amsa sunan nata a gidan aunty Rafa'at take, waye ce manne a kunnuwanta sai murmushi take ta rungume pillow a jikinta da alama tanajin dadin firar da take a waya. "Wallahi nidai na gaji da jiran rushewar katangar nan da mum ta saka mana tsakani" Narkarda muryar ta tayi cikin shagwa'ba tace "Allah nima na gaji da jiran ganin rushewar katangar nan ina son ganinka sosai" "Really......?" Yace yana murmushi mai sauti. Turo baki tayi kamar yana kusa da ita tace "not really, partially" Ta faɗa tana murgud'a baki. Sosai yake dariya har tana iya jin yanda yake dariyar "haba uwar gidan turab, ya da wannan maganar haka?" "nice uwar gida?" "Eh mana" "Awww kana shirin yin amarya kenan.....!?" "Ehhh, amma ba yanzu ba" yayi maganar cikin sigar wasa. "Allah nidai banaso ka daina" ta yi maganar a shagwa'be kamar zata fashe masa da kuka. "Tau naji kina ina haka......?" "Ina bedroom....." "Me kikeyi a bedroom....?" "Kwanciya kawai..!" "To ki sakko qasa" "Bazan sakko ba..! Akwai rana da zafi nikuma banason rana yanzu" "Bakyason rana? Ko mijinki zaki gani baza ki iya sakkowa ba" Miƙewa tayi da sauri cikin madaukakin farin ciki tace "da gaske dan Allah T-heart..!? "To kizo ki gani mana" Da sauri jiki na rawa ta ajiye wayar ta buɗe wardrobe ta fito da wata doguwar rigar abaya deep blue da mayafinta ta sanya. Light make up ta d'anyi abunka da baka saba ba, sosai kyawunta ya fito kamar 'yar sarkin aljanu saboda tsananin kyau. Plate shoe black ta saka ta fita kamar tayi fiffike ta isa inda yake. Zaune yake cikin motarsa a compound din gidan ya tsurawa kofar parlourn idanunu. Kusan dauke numfashinsa yayi lokacin da ya hango ta tana zuwa. Sai godiya da tazbihi yake yiwa Allah da zai mallakamasa wannan halitta mai daraja. Sai da ta kusa isowa inda motarsa take ya fito, fuskokin su dauke da yalwataccen murmushi. Leeyana kam ji tayi kamar ta tafi da gudu ta fad'a jikinsa, idanunsu sar'ke cikin na juna tayi hanyar parloun ba'ki kafin tayi masa alama da hannu ya biyota. Murmushi yayi yana kad'a key din motar sa ya bi bayanta. Cikin nutsuwa suka zauna, idanunsa akanta. Fridge ta nufa ta dauko masa drink ta miqa masa tana gaidashi. Kar'ba yayi ya sha sannan ya amsa mata gaisuwar da tayi masa. Lumshe idanunsa yayi yana fadin "Alhmdullillah, Allah ina godiya da ka bani dama da iko na ci gaba da rayuwa, yau nine a gaban leeyana a matsayin wanda zai aureta" Ganin yanayinsa ya chanja yana shirin kuka ya saka ta ɗora yatsarta akan lips dinsa"shhhhhhh" A hankali ya fara buɗe idanunsa ya dora cikin nata bugun zuciyoyinsu na tsananta. Cikin wata irin murya da bata ta'ba ji turab yayi amfani da ita ba saboda sanyinta yace "idanunki launin shudi mai haske, sai farin da ya zagayesu kamar sabuwar tatacciyar madarar shanu, sunada wani sirri a cikinsu wanda Ni kadai na iya fahimtar haka, ubangiji ya yi halittar sa dole na yaba" Murmushi mai sanyi tayi masa wanda sai da dimples din ta suka lo'ba sosai tace "adadin mata nawa ka gayawa haka....!?" "Tabbb aikuwa sai dai idan an sami calculator, domin bazasu lissafu ba haka kawai" 'dan basarwa tayi tace "okay yayi kyau, kayi qoqari ai" ta faɗa tana qoqarin mikewa. Da sauri ya riqo hannuta ya zaunar da ita kan cinyoyinsa yana dariya yace" I'm sorry my gurl, ke kadai na taba gayawa haka, kuma ke kadai ce na fara so a rayuwata. Da ke kadai na tsara rayuwata" Ya fad'a yana riqe kunnuwansa da hannayensa biyu. Murmushi mai sauti tayi, ta d'an jaa kumatunsa tace "baka laifi" "Da gaske kho my queen..? Nima fa bakya laifi a wurina wallahi. Ko da bana da lafiya da naji anaso a kamaki da laifi bazan iya yaqi da su bane da sai kinga jarumta" Dariya Sosai tayi tace "waye jarumi..?" Tayi tambayar cikin tsokana. Murmushi yayi shima yana shafa kwantaccen gashin kansa zuwa sajensa yace "Ni mana" "Kai waye to..?" Hannunsa ya daga yana d'ago kanta suna fuskantar juna yace "Ni angonki, masoyinki...!, mai qaunarki, mai burin zama dake har abada, mai qaunar ganin farin ciki da nishadinki, wanda zai hana hawayenki zuba muddin yana da rai da lafiya, kece a cikin zuciyata, rayuwa ta....! Ke kadai, ke dai leeyana.....!" Murmushi tayi hadi ta danna masa light kiss a kumatu"thanks for loving me T-heart" "Me too precious...!, ya maganar sadakin ki ne?" "Ka ga Ni ka bada abunda Allah ya hure maka kawai, da badan ba'a yafe sadaki ba da sai ince na yafe maka, ni burina kawai musami zaman lafiya da yarda da juna da kuma fahimtar juna, amma kuma Annabi ya fada cewa "koda tsalle mace tace kayi sau daya shine matsayin sadakin ta, to har a wurin Allah sadakin kar'ba'b'be, dan haka mafi qanqantar sadaki, mafi albarkacin aure" "Wallahi shiyasa nake qara jinki a raina precious, amma kuma akwai kyautatawa a tsamin mu kho....? Dan haka ga makullin mota nan na baki halak malak, motar kuma tana waje tun kafin isowa ta nan na saka aka kawota. Wannan kuma zoben diamond ne, sannan kuma akwai brief case a mota 20millions ne zan bada matsayin sadaki, Allah ya sa banyi rowa ba" Zatayi magana ya dora yatsarsa akan lips din ta yace "no argument......! Just obey Kinwuce ki ce komai a wannan da na yimiki precious,,,,,,kece burina, idan ban miki ba wazan yiwa....? dan Allah karki ce komai, just accept it" "I accepted, Nagode sosai yalla'bai..! Allah ya saka maka da alkairi, Ubangiji ya sanyawa aurenmu albarka ya bamu zuri'a dayyiba, Allah yasa ka gama duniya da iyayen mu lafiya" "Ameeen ya rabbi precious me, then gobe zanzo na amshi passport dinki domin ba'a qasarnan zamuyi first night ba" Ya fad'a cikin tsokana. Remote dinda ke hannunta ta d'an doka masa a gefen fuska ya goce yana dariya. "To yanzu me kaki shirya mana na bikin da zamuyi" "Kamar me fa....!?" Ta fad'a idanunta akansa. "Kamar su dinner, da lunch da sauransu" "My T nifa gskiya bana son bidi'ah" "Tabbb.... Chief military health service zai yi aure ba tare da Nigeria ta sani ba, impossible. Bama Nigeria ba hatta qasashen ketare zamuyi inviting, kinga da farko za'a daura aure anan suleja, sannan muyi waleemah a abuja. Zamuyi lunch a Greece, muyi dinner a Jordan, Arab woman's a Egypt, sai kuma muyi love show a London sannan mu wuce Spain muyi honeymoon muci amarcin mu" Baki ta turo gaba cikin shagwaɓɓiyar murya tace"Allah nidai banaso" "To naji bakyaso, mu fasa da love show din da za'a yi a London......amma gskiya sauran sai anyisu" Zatayi magana ya ɗora hannusa a bakinta yace "shhhhh mu komai namu cikin tsari da ilimi da wayewa zamuyi, Bazamu yi abu any how ba, zamuyi komai a nutse cikin kwanciyar hankali batare da munyi bidi'ah ko mun sa'bawa Allah ba in Sha Allah kinji...! Jiki a sanyaye ta d'aga masa kai. "That my precious gurl, I really love you" ya faɗa yana manna mata Peck a goshi. "Love you too my T-heart" "Yawwa kuma na bawa mum 5millions a hada miki kayan fitar biki, sauran kayan lefe kuma idan munje honeymoon za'a had'a. Godiya take masa sosai da hidimar da yake yi da ita, sun jima a tare suna fira cikin kwanciyar hankali da nutsuwa da kuma tattauna yanda bikin zai kasance. Sun ɗauki tsawon lokaci kaana suka rabu da tsananin kewar juna. Yana fita daga gidan ya fara neman layin mutanen da zasu yimasa komai a biranen da zasuyi programme sai da ya tabbatar angama komai sannan ya sanarwa dasu fahad da zafaran. Sosai suke murna da jin haka, lokaci yayi da zasu nunawa abokinsu qauna suma. Passport din yan gidansu ya kar'ba da kuma sauran families, dana zafaran da matarsa....... sannan fahad shima dana Matarsa. A can biranen kuma angama shirya musu komai hatta kayanda zasu saka, date kawai akejira. Shirye-shiryen biki kuma kullum anata yi, domin wasu manyan iyayen su leeyana a Maiduguri sun fara zuwa kamar su ummasalima da sauran mutane. Sosai k. Waasib families ke shirye-shiryen biki, sanin auren ne na fari a gidan, kuma shine babba, mafi soyuwa a wurin iyayensa. Dangi kuwa na nesa dana kusa duk suna halarta sai hidindimu ake. Mum kuwa da Papu sun saki bakin aljihu sai fitarda kudi ake yanda kasan gidan ake 'kerasu. Ummasalima kuma daga Niger republic ta d'akko wacce zatayiwa amarya 'kunshi, ai kuwa aka d'and'asamata jan lallen solatif wanda yafito maroon colour sharrr hasken fatarta ya qara fita kamar balarabiya. Gashinta kuwa yasha gyara sai wani qamshi da kyalli yake abunka da mai gashi. Aka yimata tsoraye guda biyu ta suka kusa ta'ba 'kugunta. Sai wani farin haske gashin ke fitarwa. Idan ka ga leeyana a wannan lokacin zakayi tunanin labaran asali ne. Wani bangaren kuma ta wuce balarabiya, don idan ganinka na fari ne da ita batada wani bambanci da aljana saboda tsantsar kyau da tayi, duk inda ta juya sai wal-wal take tana kyalli da d'aukar ido. Sosai daurin Auren TURAB KHATTAB WAASIB da matarsa LEEYANAH HAMRAZ AWAIS ya sami halarta manya mutane daga kasashe daban-daban na sassan duniya, kama daga presidents, commissioners, governor's, manyan lauyoyin kasa da manyan likitoci, da kuma manyan ƴan kasuwa 'yan nigeria da kuma wanda ba Nigeria ba. Manyan limamai da mukama manyan ma'aikatan tsaro na qasa. Sosai sojojin qasar Mexico sukayiwa turab kara musamman ma mutanen da ya yiwa aiki. Key holder suka yimasa mai zanen bindiga da kuma tambarin qasarsu, sai kuma can gefe suka saka hoton turab dana leeyana tare da sunayensu. Masu aikin jarida da gidan tv kam kamar su akayiwa taron domin duk motsin da mutum zaiyi zai ga ma'aikatan jarida ko na tv a bayansa suna qoqarin jin ta bakinsa. K'arfe biyu da rabi dai-dai, dubannan miliyoyin jama'a suka shaida daurin Auren DR.TURAB KHATTAB WAASIB da kuma sahibar Amaryarsa LEEYANA HAMRAZ AWAIS, akan sadakin zunzurutun kudi har millions ashirin da kuma dallelen makulin mota qirar Benz, da zoben diamond....................✍🏼 48. _____________da sauri ya rumtse idanunsa ya cije gefe daya na lips dinsa yana dafe saitin zuciyar sa. Wasu hawayene suka gangaro daga cikin idanunsa, lumsassun idanunsa ya fara bud'e wa yana jin abun kamar a mafarki. Hausawa sukace idan farin ciki yayi yawa yana saka hawaye, musamman lokacin da zuciya mai cike da buri ta sadu da muradinta........! irin wannan yanayi ne turab ya shiga lokacin da yaji an shafa fatihar daurin aurensa da leeyana. Sosai farin cikinsa ya kasa boyuwa har sai da hawaye ya gangaromasa. Mikewa yayi yana hamdala. Wata tawagace ta tunkaro shi tare da ma'aikatan gidajen rediyo da talabijin dai-dai lokacin da ya durkusa yayi sujudul-shukhur. Sosai mutane suka shiga mamaki da sha'awar abinda yayi, da wani irin sauri fahad da zafaran suka rungume shi. Shima zafaran hawayen yake tunda aka d'aura auren leeyana da turab kuma ya rasa dalilin yin hawayen gwanin tausayi. A can gida kuwa leeyana ce zaune a babban dakin da yafi ko wane daki girma a gidan papu. Zaune take gaban mirror tana saka sarqa. Wata farar basudaniyar matace tsaye akanta tana gyara mata gashinta, domin ba'a samu akayimata kitso ba saboda yanayin tsayin gashinta ba yanda za'a yi masa kitso. tsayinsa ta kuma santsinsa yayi yawa. Daga Sudan aka dauko wacce zata rinka yimata gyaran gashin da kuma kwalliya har a kammala bikin. Yanzu ma tana tsaye ne ta gama shiryata, ba wata kwalliya da aka mata saboda yanzu zasu wuce Abuja inda za'ayi waleemah. Meenal, Badar, Aleena, Aneesa, Airah da twins da kuma bestin ta zohal duk suna zaune a dakin wasunsu na cin abinci, wasu kuma suna shiryawa. Wasu kam pictures sukeyi abunsu. Leeyana na zaune an gama gyaramata gashin har dauri ma an yimata. Bakin less ne mai fulawas golden da red. Ɗinkin half boo-boo ne a jikinta wanda ya kwanta a jikinta Sosai ya fito da tsadaddiyar kalar fatarta. Tsayi fadar kyawunda leeyana tayi bata lokaci ne, wani jan net na amare basudaniyar matar ta yafa mata sai zuba kyalli yake. Hill shoe ta saka suma kalar ja ne, sosai takalman suka dauki qafarta da kyakkyawan red henna din da ke qafarta. a hankali take takawa domin bata iya yin tafiya dasu ba, idan mutum ya gani kuwa zai yi tunanin kamar salon tafiyar ne haka. Qamshinta kuwa sai da ya cika sashen gaba ɗaya tun kafin ta tashi gaban mirror. Qarar kiran waya ya shigo daidai lokacin da basudaniyar take daura mata tsadadden agogon hannu na mata. Cikin sanyin ta ta d'aga kiran ganin turab ne ya saka ta d'aga da sauri. "Kice alhmdullillah kinji matata, yau kinzama matata da gaske kuma duniya ta shaida haka, ina sonki leeyana dan Allah karki barni kinji...!" Ya fad'a muryarsa na cracking alamar kuka yakeso yayi. "Alhmdullillah,,,,,,,,alhmdullillah,,,,,,, Alhmdullillah" ta fad'a sau uku tana lumshe idanun ta, hawaye taji sun sakkomata itama, kamar an dauremata harshe haka taji domin ta kasa cemasa uffan sai shine ya katse shirun da faɗin "ki sauko down ina main parlor ina jiranki yanzu kinji" Baki ta bud'e cikin jin kunya da shagwa'ba tace "ya-turab akwai mutane da yawa fa.......! "Yes to meye..!? And ke ba matata bace....!?" Ya fad'a cikin halin Ko in kula. "Gaskiya nidai a a!" "Okay bara nazo Ni, ki jirani gani nan" Da sauri tace "no please, gani nan zuwa dan Allah karkazo.....!" Murmushi yayi yana yanke wayar bayan yaji abunda ta fad'a. Juyowa tayi da niyar neman ɗayan su ya rakata. Ba'ki sake suke binta da kallo tsantsar mamakin irin wannan kyau da Allah ya bata, a ransu suna qara jinjina wayo da dubara irin na ammin leeya, yanda ta baiwa 'yarta kariya cikin dubara. Domin da ba dan haka ba Allah kadai yasan halinda leeya take daidai wannan lokaci. Daga cikin tunanin da suke ne sukaji qarar camera da alama pictures ake yi mata, aikuwa khulud ce ta shigo dakin ganin duk sunyi suman tsaye yasa ta ciro wayarta ta fara yimata pic's wannan qara da camera keyi idan ana daukar hoto shine ya karkato hankalin su badariyyah da suka faɗa duniyar tunani. Har rige-rigen ciro wayayunsu suke wajen son daukar ta hoto....! Ba wacce bata yimata hoto ba a cikinsu, wasu su yimata su kadai wasu kuma su had'a da kansu suyi salfie. Ringing din wayar ta taji a karo biyu da sauri tayiwa zohal rad'a a kunne, alama sukayi wa meenal da ta matso kusa. Banji me suka gayamata ba sai gani nayi sun fita dakin su uku. A hankali suke sauka kan step gab da zasu shigo parlourn ne meenal da zohal suka juya suka tafi sakamakon ganin turab da sukayi shi kadai ba tare da abokansa ba kamar yanda sukayi zato. kenan ita ma leeya tazo ita kadai,,,,,! Haka yake nufi. Jiki a sanyaye ta zauna gujerar da ke fuskantar wacce yake zaune. Kansa na qasa yana daddana waya yayi kamar baisan da zuwanta ba. Sai da suka dauki tsawon mintuna biyu a haka kafin ya daga kansa ya fara magana kamar bayason yinta. "Ke yarinya kin shigo ba zaki iya gaida ni ba sannan bazakiyimin Allah ya kyauta aure ba kho.......? Bama wannan ba, yau za'a yi walima kinsani ko? To motocin da zasu dauke ku suna hanyar zuwa ba jimawa, ku shirya komai da wuri duk da ba wani shiri zakuyi ba domin na gayamuku akwai komai a can. And..........yarinya dan Allah shawara nazo muyi, duba da yanda kikayi kyau haka tubarkallah a hakan kike so muje walima kowa yana kallonki ....? ai sai bakin mutane ya kamaki aimin asara, shiyasa nake so mu yanke shawarar duk wani programme da za'a yi ki dinga saka mayafi kamar yanda kike dha.......! Ya kika ji shawarar tawa......?" Ya qarasa maganar cikin sigar tambaya. Numfashin ta ne ya tsaya chakkk ya daina tafiya.! Ko wace ga'ba ta jikinta ta daina aiki, motsi ma ta kasa yi lokacin da ta d'ago ta kalleshi da nufin tayi magana bayan da ya qarasa maganar da yake. Amma me...? Maganar ta ce ta maqale lokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskar sa da kuma shigarsa. Duk da bataga wannan tsadadden murmushin nasa ba domin kansa a soke yake da alama yana wani abu mai muhimmanci a cikin wayarsa da ya 'kura wa idanu. Wani irin fitinannen kyau yayi, shadda ce a jikinsa kalar sararin samaniya, ko makaho ya lalubi shaddar yasan an kashe mata maqudan kudi, balle mai idanu da yake ganin komai. Sumarsa ta kwanta luf, hakama sajensa da yaji gyara kamar yanda larabawa suke, qasa ne da d'an yawa sai saman da ya kasance kadan ya kwanta sosai Fuskar sa cike da annurin da ya qara bayyana tsantsar kyau da Allah ya bashi. “Tabarakallah fii ahsanul khaliqin, wa ja‘alahu min ibadika as-salihīn.” Ta fad'a a ranta kamar yanda Annabi ya umurta idan kaga mutum mafi kyau da tsari. A ranta tana ci gaba da fadin, "shin wai mutanen da suke gani inada kyau basu ta'ba ganin ya-turab bane, wallahi da mutane zasu ganshi da ba wanda zai qara kallona a matsayin mai kyau, ya-turab Allah ya sa ka more kyawunka........." Zancen zuciyan ta ne ya maqale lokacin da taji muryar sa ta daki kunnuwanta. "Ke yarinya ki daina kallona haka mana,,,,,, kin ga d'an kyakkyawa kho, kinaso ki qaremin kyau da wannan kallon naki......! To Ni fa ban gama aure ba kar kallon nan ya saka kyauna ya qare inje neman aure ace baza'a bani ba......" Ya yi maganar yana dariya. Taɓe baki tayi zatayi kuka yayi saurin isowa gaban ta "haba dai kyakkyawar ya-turab, dan Allah karkimin asarar ruwan hawayen nan naki masu tsada, taya zan jure ganin irin haka daga gareki. Kiyi hakuri kinji" Cikin muryar kuka tace "ba kai bane kace baka gama aure ba....!" "Ke rufamin asiri kinji" wanda yake da ke zaice bai gama aure ba, hmmmmm kiyi hakuri kinji wallahi turab mallakinkine ke kadai in sha Allah, wata bata isa ta sami gurbi a zuciyata ba, turab na kine ke kadai" ya fad'a tare da manna mata Peck saitin d'an qaramin bakinta. "Har a cikin gidanmu....?" Ta fad'a tana zare idanun "Har abun da yafi haka zamuyi a cikin gidanku idan kuma kina musu ki sake yin magana ki gani" Mikewa tayi da sauri ta fita parlourn tana dariya, shikuma ya saita muryarsa yanda zata iya jiyoshi yace "karki manta ku shirya da wuri wallahi motocin na hanya". Da qarfi ta amsa masa da"tho...." Shikuma ya juya ya fice daga parlorn. Fitarsa keda wuya Aunty Rafa'at da sauran mutane suka shigo Domin ganin amarya. A cikin 'yan kwanakin wata shaquwa ce sosai ta shiga tsakanin Aunty Rafa'at da leeyana, Leeyana jin Aunty Rafa'at take kamar yayarta wacce suka fito ciki ɗaya da ita. Itama Aunty Rafa'at a 'bangaren ta haka ne domin duk abunda mace zata buqata a wurin yayarta ta baiwa leeyana damar hakan. Zaune a bedroom leeyana ce tana feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi, sai Aunty Rafa'at kuma tana saka kayan su Arfah ta Aamir a trolly. "Aunty na gayamiki yace ba sai anzo da komai ba fa, yace an tanadi komai a can" "Ai kayan matarsa kawai ya sani bai san namu ba, sannan kayan nan ba nawa ba ne na Aamir da Arfah ne...., na kammala shiryawa kinga Mutane da dama sun tafi motarmu kawai ta rage, zohal da meenal duk suna parlour tun dazu" "Nima na gama shirin Aunty muje...." Leeyana ta fad'a tana saka takalma. Ba wani shiri tayi ba domin komai nata yana can a Abuja hatta kayan da zata saka idan lokacin walimar yayi. Fita sukayi suka tarar da drivern da zai daukesu yana jiransu. Suna isowa suka shiga gaba d'aya suka d'au hanya. Da misalin ƙarfe hudu na yamma aka fara gudanar da waleemar daurin aurensu. Sosai leeyanah tayi wanka na ji da gani, lifaya aka yafamata malt colour da kuma rigar roba ta ciki mai dogon hannu kalar golden da yafi yawa a cikin lifayar da ta saka. Fuskar ta kuwa tasha kwalliya mai tsananin kyau da tsari domin bazakace hannune ya zana ba, duk wanda yazo wurin walimar idan yayiwa leeya kallo daya sai ya qara fiye da haka, wasu har ba sa son dauke idanunsu daga kanta. Hotuna kuma ta sha su babu adadi kamar ba ranar dainawa. Ummasalima kam abu nasu, darduma, da chazbi da kuma Kur'anai ta raba, a cikin wata jaka madaidaiciya wacce ke dauke da hoton amarya da angonta a kyakkyawan yanayi. Ita kuma mum da qawayenta kamar su mummy-neesah suka raba turmin atamfa da kuma turaren tsintsiya da robar dabino, suma a cikin jakar su, jakarsu mum ta bambanta da irin wacce ummasalima ta raba, domin tasu mum bata da hoto sabanin tasu ummasalima da ta kasance mai hoto. Lapia qlw aka kammala taron walima, su mum da wasu tsirarun mutane suka dawo suleja. Leeyana da Aunty Rafa'at da sauran yaran gidan da suke tare kuwa suka wuce masaukinsu domin kuwa gobe idan Allah ya kaimu jirgin sassafe zasu bi zuwa Greece gudanar da lunch. Ba yanda turab bai yi ba akan aunty Rafa'at ta barsu su ga juna da leeyanah amma 'kememe ta hana hakan, duk da ya san address din gidan da aka saukesu a abuja hakan bai saka shi ya je ba domin yasan ba bari zatayi yaga matarsa ba tunda har ta gayamasa. Washe gari kuwa tun ƙarfe bakwai na safe suka dau hanya. Sai misalin ƙarfe biyar na yamma suka isa babban birnin Greece United State. Nan ma masaukinsu suka wuce babu 'bata lokaci domin qarfe takwas na dare akeso a fara taron. Direct wurin da aka tanadarwa leeya domin shiryata suka wuce. Da kanta ta zabi kalar kayan da take so. Ba su dauki tsawon dauki ba aka kammala komai, sai Aunty Rafa'at ce takira turab ta sanar masa. abokan turab dake ƙasar Greece su sukayimasa hidima sosai wajen zirga-zirga da amare domin shima yana can ana gyara shi. Leeyana tayi kyau sosai fiye da tunanin mai hasasowa, Ni a ganina alqalamin bazai iya fassara muku irin fitinannen kyau da tayi ba, ball gown ta saka fara sol irin wacce turawa suke sakawa idan sukazo shagalin aure. Fara ce sosai har tana dallare idanu. Qasan ta ya bude sosai inda aka ru'banya ta tayi wani irin cika daga qasa idan tana tafiya sai kaga tana wani bubbud'ewa kamar rafah, kama kuma fiffike. Samanta kuma d'an simple ba wani ado sosai bead kawai akayi adon dasu kalar maroon da suka qara fito da rigar ya zama kamar sarqa. Gashinta kuwa angyara mata shi sosai aka yi packing dinsa tsakiyar kanta, sannan aka saka roberline aka qara kwantarda shi. Farin net aka yafa mata har ya rufe fuskarta daga gaba, daga bayan ta kuwa ya sauka har qasa yana jaa da qasa idan tana tafiya ko tana tsaye. Hannuta da yaji kunshi kuma rige take da flowers masu matukar kyau da kamshi abun sai wanda yagani. Turab ma haka yasha wankansa cikin suit farare tasss kamar yanda nata yake, wankansa ba laifi gskiya. Kana gani kasan an narka nera ba kadan ba. Haka ma su zohal da sauran families da sukazo sunyi wanka naji da gani abun ma baya misiltuwa. Haka akayi wannan taron shima aka gama hankali kwance, turawan greece da suka halarta kam sunsha mamakin ganin waɗan nan mutane wai a Nigeria suke. Ko kusa basu kawo za'a iya samun kalar fatar leeyana a Nigeria ba, shikuma turab sun zata daga Arabian counties yake. Yauma kamar jiya ana kammala taron aunty Rafa'at ta tusa 'keyarta gaba, turab kamar yayi ihu domin a yanzu kam ya gane tsaff indai ba wurin programme suka had'u da leeya ba baya ganinta yanda yakeso, ko wurin programme ɗin kuma babu time da yawa sakamakon mutane. Washegari ma haka suka wuce Portugal inda suka gudanar da dinner dinsu cikin aji da wayewa, sosai qasar tuwara ta dauka, baramma Nigeria da kullum suna social media jiran ganin kyakkyawan ango da kyakkyawar amaryasa da ake ta posting kullum duk wani event da akeyi. Daga Portugal kuma babu 'bata lokacin suka wuce Egypt don su gudanar da taron Arabian nights da za'a yi. Hmmm abun sai ganin idanu, domin duk taron da akayi a baya bai kamo qafar wannan ba, duba da yanda larabawa, da turawa, da hausawa, da kuma manyan celebrities na fadin duniya suka halarci wannan taro. Sosai aka darje kudi, turab da abokansa sun saki bakin aljihu kudi kamar nan ake 'kera su, haqiqa duk talakawan da suka halarci taron kakarsu ta yanke saqa domin a cikin mintuna kadan za'a fara lissafinsu a sahun masu dukiya. Sunsha wanka har ba'a cewa komai, kunsan larabawa da ado,,,,, haka suka zage suka shirya leeya cikin adon farin zinari da jauhari, wallahi ganin farko zaka iya yin rantsuwa da Allah kace daga duniyar aljannu leeya ta fito duba da tsanin kyau da ado wanda ta sha. Mafi yawa daga wurin sai da suka dinga suma ana tada su idan sukayi tozali da ita. Tayi kyau sosai kamar watah d'an daren goma sha biyu, haka nan kake ji kamar ka sacheta ka gudu idan ka tsuramata idanu. Yanzu ma haka an kammala Arabian night kuma kowa ya dawo masaukinsa washe gari zasu koma nigeria gaba daya su sake shirin tafiya spain honeymoon. Leeya ce kwance kan sofa idanunta a lumshe tana murmushi, zakayi mamaki sosai idan ka kalli fuskar ta wani irin nishadi take fuskar tana kyalli kamar tauraruwa. Mamakin ka zai tsaya chakkk idan ka lura da yanda take sakin murmushi haqoranta na bayyana ga kuma wayarda ke ma'kale a kunnenta kana gani kasan fira take. "Please jarumata........! dan Allah kisan yanda zakiyi wallahi na kasa bacci ne ina matuqar son ganinki" "Kayi haquri T-heart, Wallahi ba yanda za'a yi kuma kaga gobe ne tafiyar mu idan bata bari muka haɗu anan ba ai dole mu haɗu Nigeria" Cikin kwantarda murya da rarrashi yace "dan Allah..........! My precious kinsan yanda zakiyi ki fito yanzu nan zanzo, koda bamuyi magana in ganki kawai ya wadatar da zuciyata, kinga zan sami peace of mind idan kuma na sami kwanciyar hankali shikenan zan iya yin bacci kinji Please matata" Yanda yayi maganar ya bata matuqar tausayi yasa tace "to shikenan bara na sanarwa da aunty zakazo yanzu" "Kinsan bazata bari ba wallahi" "Hummm zata bari in sha Allah, Nima zan saka baki sosai akan haka, kasan ba kai kadai kake so ka ganni ba. Nima ina so na ganka jarumina" "Tau shikenan my favorite Dan Allah kiyi qoqari idan ba so kike ki rasa angon ba" "Rufamin asiri idan na rasaka ai nima rasani za'a yi" "Tau Bama fata, ki je kinji my gurl" D'aga masa kai tayi kamar yana ganinta, da wayar a kunnen ta ta wuce ta shiga bedroom inda aunty Rafa'at ke zaune da su zohal, da Aleena, khulud, meenal da badariyyah da kuma su Airah da Aneesa da twins. 'ya'yan aunty Rafa'at Arfah da Aamir kuma suna bacci. Sukuma suna ta fira wasunsu na shirya kaya, gobe zasu koma nigeria. Shigowa tayi da sallama a bakinta, cike da nutsuwa ta zauna gaban aunty Rafa'at. "Amarsu har an gama firar" zohal ta fad'a tana gyara kwanciyarta itama yanzu suka rabu da fahad. "Ai ke zancewa haka, wai ta wace hanya kika shigo nan. Nidai nasan tare na barku da Fahad?" Zohal na dariya tace "ta hanyar da ake shigowa mana, ina zaki sani kina nan kina soyewa" Taɓe baki leeya tayi kawai tana kai dubanta ga Khulud domin yanzu sunfi kusa da Aleena ganin shekarun su zasu zo ɗaya tace "khulud ina Aleena ko sun tafi?" "Ba su jima da fita ba ai, amma bata kofarnan nan suka bi ba ta waccan hanya suka fita" Khulud ta fad'a tana nuna mata wata hanyar daban. Aleena tun da sukazo mijinta yake zuwa yana daukar ta idan sun dawo masaukinsu sai ya jira ta idan ta gama fira da 'yan uwanta sannan yazo, kusan wuri daya suke domin da gidan da aunty Rafa'at take da nasu gida biyu ne a tsakani, fahad da zafaran na turab shine ya zama cikon na uku, ba sa da wata tazara mai yawa tsakanin su. "Aunty ya-turab ne yakeso ya gaida ke ga wayar" cewar leeya tana miqawa Aunty Rafa'at waya. Cikin sanyin murya yayi mata sallama ta amsa suka ɗan gaisa sannan ya fara rokonta akan buqatarsa. Da kyar da sudin goshi ya samu ta amince da zuwan, aikuwa kamar jira yake yana ganin ta amince ya zuro jallabiya kawai ya fito. Da qafa ya karaso gidan domin basuda nisa ko kadan. Knocking suka fara jiyowa da sauri suka kalli juna suna dariya. Khulud da sautin dariyar ta yafi na kowa tashi da sauri ta gimtse bakinta cikin matuqar tsoro Sakamakon ganinsa da tayi fuskar sa daure tamau da alama ya gane shi sukeyi wa dariya. Wata gigitacciyar tsawa ya daka musu hatta aunty Rafa'at sai da ta ɗan ji tsoro. Leeyana kam ta tsorata matuqa domin yanzu ya fito asalin Turab din sa da ta sani a baya wannan mai tsanani da tsakura, mara tausayi, mara sakin fuska, mara sauqi da kuma rashin son raini. Har saida fuskar sa ta sake dawomata a baya lokacin da ya sami su Airah na rawa a parlor wanchan lokacin. "Dan uban ku wa kuke yiwa dariya?" Shiru ba wanda ya amsa sae wata zufa da karkarwar da suke saboda tsoro. "Ba magana nake ba kun wani zubamin ido kamar baku sanni ba" Baki na rawa meenal tace "dan Allah ya-turab kayi hakuri wallahi bazamu sake yin irin haka ba" Ko kallon ta baiyiba sai ma qoqarin qarasawa yake gaban khulud, ya shaqo wuyan ta ya sake dakamata uwar tsawa "bazaki gayamin abunda kk yiwa dariya ba koh, Ni sa'an wasankune da zan shigo wuri kuymin dariya? Ga mahaukaci kho?" Jijjiga kai kawai Khulud keyi hawaye na faman gudu tanaso tayi magana amma tsoro ya hanata faɗar komai, shikuma wannan ne babban abunda ya tsana wai yana tambayar mutum bazai bashi amsa da baki ba sai da kai. "Bazakiyi magana ba" ya fad'a a hasale yana shirin kaimata duka, da sauri leeya ta shiga tsakanin su tana kuka sosai. A rikice ya ajiye khulud ya janye leeyana amma ta turje. Cikin murya mai bayyanar da tsantsar fushi yace "zo muje...!" Itama da karfi take magana cikin muryar kuka tace "bazan je ba, ka haɗamu mu duka kayi mana abunda kaso..... Duk wadannan yara da ka gani saboda kai sukazo fa, ai koda wani zai quntata musu bana tunanin akwaika ciki. Nasan idan har zaka iya taba wata a cikinsu akan wannan karamin abu, to nima zaka iya taba Ni, idan har basu chanchanci ragowataba, to nima banason ragowar saboda haka ka barni na zauna a cikinsu ba inda zanje" Da ido ya jefa musu wani kallo aikuwa da saurinsu har suna hardewa suka fita bedroom din. Zaunar da ita yayi, sannan ya durqusawa kusa da ita. "Ki gafarceni rankishidade, bada niyya nayi hakan ba, wallahi nima inaso na yakice wannan halin amma na kasa zanyi qoqari naga na zama yanda kikeso kiyi hakuri kinji sarauniyata" Goge hawayenta tayi sannan ta ce "tom shikenan na hakura amma dan Allah kar ka sake irin haka" "Bazan sake ba in sha Allah, karki damu kinji" "To kuma menene na durkusawa" ta fad'a a shagwa'be. "Kin taɓa gani bawa yayiwa uban gidansa laifi kuma ya bashi hakuri a tsaye ai hakan bazai yiwu ba gskiya" "To kuma shine bazaka tashi ba" "Kin ce in tashi ne rankishidade" Hannu ta saka ta rufe fuskarta tana jin kunyar sa sosai wallahi, wani lokaci ma har bata iya boyemasa haka, shikuma yanaso ta daina kunyarsa shiyasa yake mata Irin haka. "Kice na tashi mana Please gimbiya ta" cewarsa yana d'an langwa'be kansa gefe daya yanda yayi maganar kamar da gaske bawa ne a gaban uban gidansa. "Tohm ka tashi kaji, ai dama ba Ni na saka ka ba" Mikewa yayi shima ya zauna sukaci gaba da firarsu ta masoya kamar ba abinda ya faru, sai da aunty Rafa'at ta fahimci dare ya soma yi sannan tazo ta sanarmasa, haka bayaso ya tashi ya koma zuciyarsa cike fal da tunanin Leeya ɗin sa. Washe gari haka suka shirya cikin farin ciki kowa yana mararin ganin ƴan gidan su. Haduwa sukayi wuri daya gaba dayansu bayan sunyi sallama da larabawan Egypt, sosai amarya da ango suka sami kyaututtuka domin kuwa ba inda ba'a san turab ba a qasahen nan da suka zauna kwana d'ad'd'aya. Misalin k'arfe biyu da kwata suka dauki hanyar shigowa Nigeria. A Nan gida Nigeria kuwa sai shirye-shiryen dawowarsu ake, families duk sun qara taruwa, sosai ake qaunar ahalin gidan Khattab waasib saboda tausayinsa da yawan kyautar sa da kuma saurin fahimtar mutane. Uwa uba ga kuma sanin darajar jama'a. Misalin ƙarfe hud'u da kwata daidai jirgin su yayi landing, nan aka tura drivers babu b'ata lokaci suka dawo da su. Sai da suka huta sosai kafin fahad da zafaran da kuma matan su harda shi turab din suka koma abuja. Bai saka ransa da ganin leeya a koda yaushe ba shiyasa bai damu da haka ba. Dawowarsu Nigeria da kwana biyu shirin su na tafiya spain ya kammala. Kusan motoci hud'u aka tafi dasu filin jirgi na ƴan rakiya kawai, bayan motocin su fahad da wacce su Khulud ke ciki. Tun a cikin mota leeyana ke kuka, turab kuwa jin kukanta yake har bangon zuciyarsa da 'bargo, dole tasa ya kyaleta don bashi da yanda zaiyi ne saboda yawan mutanen da ke tare dasu. Allah-Allah kawai yake su shiga jirgi....! Misalin ƙarfe 1:30 na rana aka kira sunansu, sosai ta rungume mum da Aleena tana kuka sai da kyar aka rabasu, mum ma kukan take yi. Gab da zasu shiga jirgi ne zafaran ya dagawa turab hannu alamar ya tsaya. Tare da fahad sukazo wajensa bayan sun gama bankwana suma, "afuwan Chief turab, na manta kyautarka ne ban baka ba. Amma dan Allah kar aje Kasar turawa a manta damu" Murmushi mara sauti yayi kafin yace "idan na mantaku na manta kaina zafaran, kune Ni a wannan rayuwar banada kamarku idan kuka cire mahaifana da matata, kaga ba yanda za'a yi na mantaku" "Kar ka damu muma munsan ba abu mai yuwa bane, yanzu dai ga wannan, karka bud'e anan sai kun isa inda zakusha soyayya" Sake fadada murmushin fuskar sa yayi yana qara gode musu tare da fatar alkairi. A bangare na musamman suke, iya sune sai kuma ƴan kayayyakin su duk da ba wasu kaya suke da su masu yawa ba. Inda aka ware musu a jirgin kuwa bambancinsa kaɗan da d'aki. Addu'a yayi sosai kafin su shiga, suna shiga kuwa ya zaunar ta ita ya kwanto da ita jikinsa ya matseta tsamm, tisue ya zaro yana goge mata hawaye ba tare da yace uffan ba yana ci-gaba da bubbuga bayanta alamar rarrashi. Ita kuma ganin jirgi na d'agawa yasa ta qara qanqameshi sosai sakamakon wannan shine shigarta na Farko" "Sorry dear..... kiyi hakuri kinji. Komai zai wuce zakiga kamar ba'a yi ba....! Ya fad'a cikin sanyin murya mai kamada rarrashi. A hankali ta daga kanta ta kalleshi suka hada idanu, da sauri ta mayarda nata idon qasa. Wani irin nauyi da kunyarsa takeji, ga wata faduwar gaba dake ziyarta ta akai akai, tsoro da kunya duk suka taru suka sami mafaka a cikin zuciyar ta. Lura da haka yasa ya shafa kanta kadan yana sauke ajiyar zuciya. Wani madanni ya danna akan kujerar da suke zaune, nan take kujerar ta juya ta zama makeken gado. Kwantar da ita yayi, sannan yayi mata pillow da cinyarsa yana shafa kanta. Kasancewar da gajiya a tattare dasu yasa Bacci yayi awon gaba dasu. k'arfe takwas da mintuna goma sha biyar na dare jirgin su ya sauka a Babban Birnin spain. Jin tsayuwar jirgi da kuma qarar na'urar da take shaidar haka ya saka turab ya gane sun iso. Ganin har yanzu tana bacci bata farka ba ya dan shafa gefen fuskar ta. A hankali ta buɗe idanun ta dake cike da bacci ta saka a cikin nashi "mun qaraso...?" Ta tambaya cikin sanyinta. Murmushi ya sakarmata da fadin "eh hajajju mun qaraso kinata bacci kho" "Da nikadai nayi baccin zakace haka, sau nawa ina farkawa ina ganinka kana baccin kaima" "Thom naji,... Amma dai yanzu na rigaki tashi" Murmushi tayi itama bata qara cemasa komai ba, hannunta ya riqo suka sauko a hankali cikin natsuwa. Suna fitowa aka fara watsa musu wasu fararen furanni masu matukar qamshi. ""Abun mamaki" ta faɗa a fili ganin mutane masu tsananin yawa, kuma duk kayansu iri dayane da alama kayan ma uniform ne. Murmushi ya sakarmata tare da kashe mata ido daya. Wani lallausan farin carpet aka shimfida musu sukabi ta kansa har suka isa gaban motocin da akayi packing. Mutanen da ke tsaye kusa da motar kuwa suna ganin sun qaraso daff dasu suka dinga bud'e wasu qananan Cage's sai ga tsuntsaye kala daban daban masu wani sauti mai dadi. Sai zagayasu suke suna wake-wakensu na tsuntsaye............ Ba leeya da ta fara shigowa ba, hatta turab daya jima a cikin wadannan mutanen sai da ya kamu da sha'awar irin wannan tarba da suka yi masa. Shikam me zaiyi ya biya waɗan nan bayin Allah. Ita kuma leeya mamakine fal ranta, ya akayi turab yayi suna har haka ta inda ko'ina ya tafi sai an ganeshi gashi da dimbin masoya. Ikon Allah, taci gaba da fad'a a zuciyarta. Har a Cikin motar anyi decorations da balloons gwanin birgewa, a bakin wani makeken gida suka yi packing. Wani Bature ne ya fito da kayansa na sojojin kasar ya bude musu gate suka shiga cikin compound din gidan. Gidan babba ne sosai irin gidajen nan ne turawa masu dogon gini da muke gani a film. Fitowa tayi tana murmushi tana kallon ginin gidan har ya shige gabanta yana tafiya bai kula da ya yi mata nisa ba. Ita kuma bata masan abunda ake ba ta saki baki tana kallon gidan, chak taji an d'aga ta sama....! bai direta a ko'ina ba saib a tsakiyar babban parlourn gidan gaba ɗaya. "Masha Allah" leeya ta furta a hankali tana sakkowa daga jikinsa kuma. "Gidan nan yayi kyau my King....." Tsadadden murmushin sa ya sakarmata tare da fadin "Nagode Allah tunda gidan nan yayi miki, muje kiga ko'ina" Cikin zumud'i ta bishi suka fara zagawa lungu da saqo na gidan 6 bedrooms ne a gidan kuma shahararru, babu wanda bayada kaya a cikin dakunan kuma duk kayan tsadaddu ne na turawa iyakar ganin idanunka. Sannan 4 parlours, sai kuma 3 kitchens da kuma 2 daining area's. 2 laundry rooms, and 6 bathrooms, sai swimming pool da garden, sai kuma 6 prayer-rooms. Gidan ya tsaru sosai domin tsayi faɗin tsaruwar gidan bata lokaci ne, babu abunda basu tarar a gidan ba, daidai ta tsinke akwai a gidan komai ya saka anshirya masa tun kafin yazo. 5 rooms gaba ɗaya kayan gyara da shafe shafe ne a ciki har kayayyakin make up. Wasu rooms guda hud'u kuma duk kayan sakawa ne manya da qanana kuma nata ita kaɗai. Shoes and bags kam ba'a magana kamar kaje Company. Babban abunda ya daurewa leeya kai shine komai da ta gani size dinta ne, kuma ita dai tasan basu ta'ba magana akan haka ba. Cike da mamaki ta kalle shi da faɗin "sadaukina..., ya akayi kasan sized dina haka....?" Murmushi mai sauti yayi yana laqato hancinta yace "taya bazan san sized din matata ba...." "Amma harda......" Kasah qarasawa tayi domin wata kunyarsa da ta lulluɓe ta. Shikuma daya gane abunda take son fad'a yace"har da su mana, ya ma za'a yi na kasa sani. Idan bansan naki ba nawa zan sani....?" Idanunta kam tuni sun chanza kala, hawaye duk sun taru tana murmushi take kallonsa; "duk domin ni kayi wannan sadaukina....?" A hankali ya d'ago fuskar ta suna kallon juna, hawayen yake shima yace "wallahi idan ina da ikon cire rayuwa dana cire tawa na baki leeyana, ina sonki Sosai Allah shaida haka, ina yimiki halattacciyar soyayya wacce nake fata Allah ya sanya mu a aljanna saboda ita, kamar yanda yayiwa laila da majnoon alqawari. Ya-turab loves you much Leeya" ya qarashe maganar sauran hawaye na gangaro masa. "Nagode, Nagode sosai jarumi nah, Allah ya sanya alqairi da albarka a zamanmu..." Ta fad'a kukan ta na qara tsananta. Shima kukan yake sosai ba mai rarrashin wani a cikinsu "yau nine a gabanki a matsayin mijinki leeyana! Ashe zanga wannan rana mai cike da albarka a cikin rayuwata, ashe dama zan mallakeki ki zama tawa, zama na har abada leeyana....?, dama zamu zama d'aya mu zauna a qarqashin inuwa daya, wallahi ban taɓa zaton haka ba, na riga na cire raina da samunki a cikin rayuwata leeyana.....!" Ya qarashe maganar cikin matsanancin kuka. Itama kukan take sosai tausayinsa kuma na qara shiga zuciyar ta, "damah ace baka yi zaton haka ba ya-Turab, wallahi nima inasonka, wanda ban tashi gane hakan ba sai lokacin da ka fad'a mummunan hali ta dalilinah, ka yarda soyayyata a gareka gsky ce, kuma wallahi bana fatar Ganin ranar da zamu rabu da idanuna ko mutuwa zamuyi ina fatar ta fara daukata domin Ni nasan bazan jure rashinka ba uban 'ya'yana" Rungume ta yayi tsammm ajikinsa yayi ajiyar zuciya, bubbuga bayanta ya farayi "sorry matar ya-turab guda ɗaya jal, kuka bai dace da kyakkyawan idanun Nan naki ba a daidai wannan lokaci, dan Allah kiyi hakuri kidaina zubarmin da wadannan hawayen naki masu daraja, wanda nayi alqawarin indai inada rai da lafiya bazan ta'ba bari su zuba ba, Dan Allah kiyi hakuri kinji, Yanzu ki tashi muje muyi wanka muyi sallah kinji" Goge hawayenta tayi tare da tashi tsaye, miqewa yayi shima yana shirin bin bayan ta. "Ina zakaje....? Kayi zamanka kawai nasan toilet ai ban manta hanyar ba" "Wanka zamuyi tare mana...." Ido ta zaro waje kamar zasu fado qasa tace "wanka da kai da wah....?" Yana dariya yace "dani da matata mana, Annabi yace hakan yana qara dankon qauna" A shagwa'be take kallonsa irin kallon nan da yake narkemasa zuciya kamar zatayi kuka tace "nidai a'a Please, ko zamuyi ba yau ba kabari wata rana kaji" ta fad'a tana kashe masa ido ɗaya. "Hummm,,,,,,tau shikenan kije kiyi ke ka d'ai idan kin fito sai nima nayi. Kinsan bana so na sakaki abunda baki niyyar yi ba" "Na sani my happiness, Yanzu zan dawo in sha Allah I love you" ta fad'a cikin 'kayataccen murmushinta tana yimasa alamar heart da yatsunta ta wuce toilet. zuciyar ta cike fal da farin ciki. Shigarta ba jimawa ta fito, koda ta fito parlourn bata tarar dashi ba, bedroom din da ke passing sosai da parlourn ta shiga domin tana tunani shima yana ciki. Tana shiga kuwa taji motsinsa a bathroom, wardrobe ta bud'e ta fito da wata doguwar rigar bacci mai dan kauri wacce ta kaimata har qasa, kuma ta bud'e sosai bata d'ameta ba. Babban hijab ta ciro shima har qasa ta sanya saman rigar, sannan ta shimfida sallahya tana jiran fitowarsa. Ganin har yanzu tana jin motsin ruwa da alama bai gama wankan ba ya saka ta bud'e wardrobe ɗin da ta kasance mallakinsa domin kaf kayansa dake parlorn a ciki suke ta fito masa da jallabiya, sannan ta fesa masa turare mai sanyin qamshi. Idan ba kusa kake Sosai dashi ba bazakasan ya saka turaren ba ta ajiye masa akan bed tana jiran fitowar sa. Sai da ya ɗauki mintuna uku bayan haka kafin ya fito. Yaji dadi sosai dayaga ta shirya sannan shima ta fito masa da nashi kayan. A gaggauce ya saka sannan yace "muje" yana nuna mata qofa. "Bakaga na shimfida sallahya ba" "Ni ba'a nan zamuyi sallah ba, zo ki ga" Ba musu ta bishi a baya suka fi ta bedroom ɗin, suka shiga wata 'yar siririyar kofa qofa sukagani gani zagaye da wani daki da akayi gininsa da gilashin azurfa. Babban zanen dakin kha'a, bah ne a kofar dakin, a samansa kuma anyi jera wasu qananan tasoshi guda biyu daya kan daya sannan akayi alamar wata da taurari a samansu. A harabar kuma lallausan grass carpet ne shimfid'e, sai wani haske mai kyalli da ya zagaye dakin gaba d'aya. Leeyana har sauri take ta isa cikin dakin domin ganin wane irin daki ne wannan. "My love! Wurin nan yayi kyau wallahi tun Kafin na shiga" Murmushi ya sakarmata hannunsa na cikin nata yace "mu shiga ki gani tukunna" Ba musu ta biye masa suka shiga dakin "Masha Allah, shine abunda take furtawa a fili da zuciyarta. "Mijinah Allah ya baka ladar kowace ibada da zamuyi a wurin nan" "Ameen ya rabbi matata, ke kuma Allah ya baki ladar ibadar da zakiyi a wurin nan" Lallausan Italian carpet ne mai alamar kha'ah'bah da aka saita ta a qeeblah leme a fadin dakin, kai tsaye zaka iya kiransa masallaci. Amma ganin irin tsarin da akayimasa yasa idan ka gani shiru zakayi da bakinka kawai. Bangare d'aya na dakin bayada wani banbanci da masallaci. Bangare d'aya kuwa decorations akayimasa sosai aka fitar da wurin saka litattafai. Inda ba komai a wurin sai tarin littafan addini da kuma Alqur'ani mai girma. Harda littatafan tarin annabawa. Ga kuma daddad'an kamshi dake fitowa wanda leeya bata san daga ina qamshin ke fitowa ba. "Masoyi, anan zamu dinga yin sallah kullum kho" "Eh, amma ba anan kadai ba, ko wane bedroom yana da irin wannan dakin. Kinsan anan ba musulmai sosai kuma babu masallatai. Shiyasa na gina wannan kinga kiran sallah ne kawai bazamuji ba, amma muna shigowa masallaci" Idonta akansa tana murmushi mai sauti tace"gsky mijina kai na daban ne, Allah ya qarawa zuciyar ka imani" "Ameen" ya fad'a yana dai-dai ta tsayuwarsa itama ta gyara tata tsayuwar. Sallolinsu sukayi cikin nutsuwa bayan sun gama ya dafa kanta yana kwararomata addu'ar da manzon Allah yayi umurni ayi. Bayan ya gama yimata addu'ar ya fara yimata tambayoyi akan addinin ta. Babu wani abu da ya tambayeta wanda bata bashi amsa ba. Cikin tsananin farin ciki da alfaharin samunta ya rumgeta yana yaba mata sosai akan riqo da addini da tayi, yaji dadin hakan sosai. "Yanzu kuma muje muci abinci kar in barki da yunwa mu koma Nigeria ace ban iya kiwo ba" Dariya ta yi sosai har haqoron ta suka bayyana, ba zato taji ta ajikinsa. D'aga ta yayi tsammm har suka iso daining area. Zama yayi tare da d'ora ta akan cinyarsa. Mamaki Sosai ya rufe leeya har ta kasa cewa komai ganin abinci kala-kala a jere har mamakinta ya kasa boyuwa. "Mamakin me kikeyi......!?" Ya fad'a cikin sanyi da nutsuwa. "Abinci...." ta fad'a tana nuna tari abincin da ke zube sama wawakeken daining table ɗin "waya dafa.......?" Ta kuma tambaya da mamaki. "Robot...! Akwai su da yawa a gidan nan kuma kowa da aikin da yake, waɗan da suka shirya abincin nan su biyu mace da namiji" Zatayi Magana ya ɗora hannunsa akan lips din ta "shhhhhhh,,,,,,,,kice Abincin tukunna, zaki san komai daga baya kinji. Wannan lokaci bana tambaya bane na abinci ne kawai" A baki ya dinga bata abincin har ta gayamasa ta qoshi, sannan shima yaci ya qoshi. Wani remote daga gefe ya dauka ya dannah wani wuri. Sautin na'ura suka faraji da alama magana take. Jimm yayi yana saurare kaana ya kuma dannawa. Robot biyu taga sun jero cikin tariyar su. Suna isowa suka tsaya har saida ya qara danna wa kaana suka fara aikin tattare kwanukan da aka 'bata. Leeya kam banda mamaki har tsoro ya shigeta sosai, sai da turab yayi mata bayani sannan ya bata remote din tayi amfani dashi, Sai a sannan tsoronta ya d'an ragu. Bayan sun gama komai ya kuma ɗaukar ta chakk ya rabata da qasa suka doshi wani daki ba wanda suka shiga da farko ba, wanine na daban. Cikin nutsuwa ya kwantar da ita kan gado ya juya ya fita batare da ɗayansu yace uffan ba. Tana daga kwance ta miqe a hankali ta kashe bulb din dakin ta kunna bedside lamp. Kafin kace me nannauyan bacci yayi awon gaba da ita abunka da wanda ya kwaso gajiya. Cikin baccinta kamar kuma a mafarki taji zafafan sak'onninsa na shigarta. Hakan yasa ta bud'e lumsassun idanunta dake cike da bacci. Ta dan tsorata da ganinsa domin ita dai tasan koda ta kwanta baya dakin, sai farkawa tayi ta ganshi. Da kyar cikin kasalalliyar murya ya furta "na katsemiki bacci kho, kiyi hakuri kinji" Tana shirin yin magana ya matsa kusa da ita sosai cikin ƴar nutsuwar da ta ragemasa ya hade bakinsu wuri daya ya fara kissing dinta. Sun dauki tsawon mintuna talatin suna abu ɗaya har ya janyo blanket ya rufe su, bayan ya karanta addu'ar da Annabi ya umurci kowane namiji da yayiwa matarsa a lokacin da suka hadu shimfiɗa daya. A daren ne turab ya sami nasarar mayarda leeyana cikakkiyar mace, kuma qima da darajar ta suka qaru a wajensa. Har aka kira sallahr asuba tana qanqame a jikinsa, ko wane motsi nata idan tayi zakaji ya kira sunanta yana sanya mata albarka. Da kanshi ya kaita toilet ya gasata sosai sannan yayi mata wanka, a daddafe tayi alwala ya nad'ota cikin towel ya dawo da ita kan bed. Leeyana kam jikinta yayi mata tsami sosai har wani zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Da kansa yayi mata komai, shi ya ciro mata kayan sawa ya sakamata sannan ya dauketa suka tafi prayer-room sukayi sallah ya dawo da ita. Saman bed ya ajiyeta sai sannu yake jeramata ita kuma kunyarsa duk ta rufeta. Matseta yayi gammm a jikinsa sannan ya ɗora bakinsa dai-dai kunnenta ya fara karanto mata surorin Alkur'ani cikin zagin muryarsa kamar Balarabe haka yake karatun. Itama a hankali ta fara bin karatun nasa har bacci ya dauketa, dama hakan yakeso yanaso tayi bacci ta samu ta huta. Aikuwa tanayin bacci ya janyeta daga jikinsa a hankali ya sauka kan bed din ko dogon motsi baiyiba gudun kar ya tasheta. Kayan da duk suka bata ya tattara gaba ɗaya ya tafi laundry ya wanke su tasss sannan ya saka a Drayer ya busardasu. Bayan ya gama kuma ya shiga ciki ya umurci robot dinsa da su hada musu lafiyayyen breakfast. Nan da nan kuwa suka fara aikin, parlour ya dawo ya zauna haka kawai yake jinsa wasai, zuciyarsa cike da farin ciki. system dinsa ya saka gaba ya fara aiki sakamakon yayi kwanaki bai ziyarci shafukansa ba. Fridge ya kalla yaga nisansa dashi kuma gashi yana buqatar ruwa. Murmushi yayi lokacin da ya tuna remote na hannusa. Ciro shi yayi daga cikin aljihunsa tare da dannah shi. Ba jimawa sai ga robot ya iso gabansa. Magana yayi mata take ta juya inda fridge din yake. Da ta dawo ma bai kula ba sai jin alamar na'ura yayi a gefensa. Hannu ya saka zai kar'ba sai kuma yaga kofuna biyu, cikin mamaki yakebinta da kallo fuskar sa ta kasa boye farin cikinsa yace "qalbie kinji sauqi, masha Allah. Alhmdullillah Allah ka qara bawa matata lafiya" Tana murmushi tace "to ka karbi ruwan mana" "Zo ki zauna ki qarasa ladarki" ya fad'a yana nuna mata cinyarsa tare da kashe mata ido daya. Janyota yayi ya zaunarda ita ya bude bakinsa ya rufe ido, ganin haka ya saka ta gane abunda yake nufi nan take kuma ta dinga bashi ruwan har ya qoshi. "Kamanta da robot fa" "Ba fa robot ne sunan wannan ba, kowanne a cikinsu yanada suna. Ita wannan sunanta Clara" Aikuwa yana fadin haka ta gyara tsayuwarta tana kallonsu. Leeyana ta maimaita fad'ar sunan "Clara....." Tana ji leeyana ta kira sunanta ta juya ta tafi gabanta tana miqamata kofin. A wannan karon leeyana bata ji tsoronta ba ta karbi kofin tana murmushi. Martanin murmushi ta mayarmata itama tare da juyawa tabar wurin. "Clara tana da saukin kai ba kamar sholeen ba" "Kana nufin kace har a cikinsu akwai masu sauqin kai akwai masu wuyar kai" Dariya ta bashi Sosai yanda tayi maganar "wai wuyar kai" hakan ya sakashi darawa tare da cewa "kwarai ma kuwa, yanda kikasan mutane haka suke" "Ikon Allah" ta fad'a tana tallafe ha'ba. "Babynah kinyi kyau sosai wallahi kin ganki, gskiya ina qara godewa Allah da yayimin ni'imar samunki leeyana, wallahi kayan nan sunyi kyau amma meyasa baki kirani na tayaki shiryawa ba" "Banyi tunanin kana kusa bane, abunda ya saka na jiyo alamun ka ma shine lokacin da zaka kira Clara" "Okay tau ki tashi muje ayi breakfast kho...?" "Yawwa sweet dan Allah ka kira min su mum na gaida su Wallahi har nayi kewarsu ina so naga mummah na" Baki ya taɓe tare da cewa"su kewa manya aikuwa bansan ranar da zaki gansu" Baki ta bud'e zatayi kuka da sauri ya rufe bakin"kin manta nayi alqawarin bazakiyi kuka ba indai inada rai da lafiya, dan Allah karki soma dan wallahi bazan jura ba" ''Yayana to ka kirasu na gansu yanzu'' "Yanzu kuma sweetheart kin manta yanayinsu da namu ba daya bane, mu yanzu safiya ta waye..... Su kuma Yanzu ne suke shiga bacci" "Eh, kuma fa haka ne........! Nidai wallahi sai ankirasu" ta fad'a cikin rigima irin Tata. "Naji zankira, amma dai zaki bari muyi breakfast Koo.......?" "Ni bana jin yunwa...." Cewar ta tana juya masa kai gefe....................✍🏼 49. _____________"haba dai uwargidan ya-turab, kiyi hakuri mana muyi breakfast just in minutes fa, wallahi zan kirasu koda karfe ukun dare ne a Nigeria yanzu....!" Jin yayi rantsuwa ya sakata d'an sake fuskarta kadan tace "promise....!" Tana d'aga yatsarta daya. Ganin haka yasa ya riqo hannun nata gaba daya yace "I promise you dear, can we go...!?" D'aga masa kai tayi alamar ehh. Tamke fuska yayi sosai yace "bana so ana daga min kai idan nayi magana" Ganin ransa ya soma ɓaci ya saka ta dan sunkuyar da kanta qasa tana qara shigarda kan nata cikin qirjinsa, "kayi hakuri na daina" "Hummm ni bakyamin laifi ai, koda kinayi ma na yafemiki tun Kafin kiyi, kuma ki tashi muje Yanzu. Nifa da nine banyi breakfast ba bazan damuba, amma wlh duk na damu da ya kasance kece bakiyi ba" "Allah sarki mijinah, to muje" ta fad'a tana qoqarin miƙewa. Jinta kawai tayi jikinsa ya d'aga ta sai daining area. Haka ya kira clara da sauran robot dinsa sukayi sarving dinsu. A baki ya dinga bata harta qoshi. duk yanda tayi yaci yace "a'a" sai ta qoshi tukunna. Tana qoshi itama ta fara bashi abaki har sai da ya qoshi shima. "Muje to akira mum dan Allah" "Oh ni jikan mainah na haɗu da rigimammiyar mata" ya fad'a yana talla'be ha'ba. Kukan shagwa'ba ta saki harda hawaye tana bubbuga qafa"nice ma rigimammiyar mata, to ai nima ina da wayar ba'a buqatar kiran naka bara naje na kirasu da wayana" Fizge jikinta tayi daga nashi ta tashi fusace zata wuce bata ankara ba taji bakinsa cikin nata. Kissing dinta ya farayi deeply har suka koma zaune gaba ɗaya yana romancing dinta cikin kwarewa. Tsawon mintuna sai qarar numfashinsu akeji. Murya a kasalance cikin yanayinsa da ya fara changerwa yace "Ni banyi komai dakeba, naga kinyi fushi ne, wannan ce hanya mafi sauqi da zan baki haƙuri saboda haka kiyi haƙuri kinji....ke ba rigimammiya bace my one..." A hankali ta d'aga kanta dake kirjinsa ta shafa sumar kansa tana murmushi tace "naji kuma banyi hakuri ba" "Subhanallah...dan Allah mana" ya fad'a yana marairaice fuska. "Bazanyiba gskiya.....!" "Saboda me qalbie...?" Kamar zatayi masa kuka tace"to bakai bane tun ɗazu fa ina roqon ka akan ka kiramin mahaifiyata amma ka qie, kuma kace can Nigeria yanzu dare ne so kake koda zaka kira sunyi bacci kho" "Lahh yanzu akan wannan. Ki tashi muje parlour na kirasu da system ma nasan zaki fi jin daɗin ganinsu a babban screen" "Muje to.....!" ta faɗa tana miqewa. Shima miqewa yayi da nufin ya bita, lokacin kuma har leeya ta fara tafiya. "Tho malama ki jirani kho..." "Ka sameni kawai bazan iya bin shiriritar tafiyar ka ba.." "Ikon Allah, Princess nine mai shiririta idan ina tafiya..? Wai ko kin manta soja ne ni, harfa yaqi ina yi, shine zakice ina shiririta idan ina tafiya. Nidai ki jira ni kawai" "Naqi bazan jira ba d'in..." "Shikenan kije, ynzu za'a mayarmin dake nan kinga remote ɗin su sholeen da Clara kho, derbesh ma zan saka ya d'akko min ke domin shine namiji acikinsu, kuma duk yafisu rashin mutunci" "Robot....!.." ta fad'a a fili tana dafe kirjinta. "Kwarai kuwa robot zan kira su dawomin dake har gabana" Tana tsaye ta kasa ko motsi Allah yasan tana tsoron wadannan robot bada wasa ba..... ita ko acikin film bata cika ganinsu ba ma balle su saba........" Tana cikin zancen a zuciyarta ne taji qarar na'ura alamar ya kirasu kenan. Aikuwa da mugun gudu ta isa ta fad'a jikinsa tana sauke numfashi "miji.....! dan Allah kayi hakuri dauke ni da kanka muje Please, Ni ko ganinsu bana so inyi yanzu dan Allah ka kirasu kuma kace basai sun zo ba" "Nayi hakuri, muje kar su mum suyi baccinsu" ya fad'a lokacin da yake direta bayan sun iso main parlor. Fita yayi daga wurin ya shiga wani d'aki ba tare da ya furta komai ba ya dawo inda take kusa da ita sosai ya zauna yana bude system dinsa. Ita kuwa ta zuba masa idanu tana jiran sakamakon. *NIGERIA* kwance take akan sofa ta lulluɓe rabin jikinta da blanket sakamakon yanayin sanyin da ya shigo. Murmushi take Sosai ta kafe wayarta da idanu tana daddanawa da hannayenta biyu cikin sauri da kwarewa a typing da alama dai chat take. Dariya sosai take harda 'kya'kyatawa. Mamakine ya rufeta sosai har sai da ta dakatar da dariyar da take. Ga qatoton screen ɗin wayarta ya bayyana video Call ake kiranta. "Rabeen jiki..." Shine abunda saving ɗin number ya numa lokacin shigowar kiran. Ido ta zaro waje da matuqar farin ciki har hannunta na rawa wajen picking call din sa. Da mugun d'oki ta amsa wayar ko sallama batayiba tace "ya-turab mutanen Spanish ashe dai baku manta damu ba" Dan murmushi yayi kawai yace "autar mum kin wuni lafiya? Dah na dauka kinyi bacci ai..., ashe kina nan baki kwanta ba har yanzu" Bakin khulud har kunne ganin ya-turab ya ɗan sake mata tace "ina nan ya-Turab banyi bacci ba tukunna ina amaryarmu" Kallon gefen da leeya take yayi yaga itama system din ta kurawa idanu sai washe baki take ganin Khulud a gabanta kamar su rungume juna ba qaramin dad'i hakan yyi mata ba. Juya kan system din yayi yanda leeya zataga komai dakyau. Cike da kewa da farin ciki suka gaisa gaba dayansu, sun dauki tsawon mintuna goma kafin leeya ta tambayi khulud. "Ina mum da papu, wallahi ina kewar su sosai" "Aikuwa dai sarkin kewa, su mum suna nan lafiya qalau wallahi. Ba'a jima ba da na ji motsinsu down stairs bara na duba idan suna nan sai na basu wayar kho" "da kinyi agaji wllh domin idan bangansu ba yau fiffike zanyi sai Nigeria kinga nan ko goman safiya batayiba balle dare yay min akan hanyata" Turab ya kalleta yana dariya yace "nifa har naga kin jima baki wuce Nigerian ba na ga iyakar kewa, ke mai iyaye kho" Taɓe baki tayi zatayi kuka, yanda tayi ta bakin idan ka gani zakayi tunanin yarinya ce ƴar shekara huduj, sosai abunda tayi ya birgeshi yana kallon dan qaramin lips dinta yana murmushi yace "menene kuma my princess, me akayimiki, gayamin naji kinji waya taɓa matar yaya guda" Kamar zata ɗan yi kuka tace"to ba kai bane ba yaya ina magana da 'yar uwata zaka sakamin baki" "To ba kai bane ba yaya ina magana da 'yar uwata zaka sakamin baki" ya kwaikwaya kamar yanda tayi maganar da qaramar murya yana dariya. D'an naushin nan ta masa irin na love tana shirin kuka ya shafa fuskarta yana qoqarin had'e bakinsu wuri ɗaya. "Ummmm, ummmm, ya-Turab baku katse kiran ba fa, naga kuna batun ku fara (L) a gabana" Khulud ta fad'a tana qoqarin kumshe dariyarta. "Ke banason raini ki kaiwa mum wayar ko na 'ba'b'ballaki wallahi" Turab ya fad'a kamar ba shi yake dariya ba yanzu nan. "A ina zaka ganni balle ka babballaki, Lallai ma ya-Turab kanada abun mamaki, daga abun arziki, ina naga abun alheri ya zama na tsiya, saboda kawai na tuna maka karka saki layi agabana shine abun wani babballawa" Khulud ta fad'a a zuciyar ta, a fili kuwa cewa take "yayan mu Allah ya baka hakuri, mum kam kamar an bata wayar angama kuyita kallon juna sai safe" 'kwafa yayi yana jijjiga kai kafin ya kawarda kansa daga kallonta. Leeya kam idanunta na kyam akan screen ɗin system din tana jiran ganin mum, cikin hakan ne bata ankara ba kuma sai dariyar mum da papu sukaji. Turab bai san yayi kewar iyayensa ba sai da yaji muryoyinsu suna dariya duk da ba wannan ne farkon tafiyarsa mai nisa ba amma yayi kewarsu sosai a wannan karon. Cikin murna da farin ciki suka gaisa da mum da papu gaba dayansu sai farin cikin ganin 'ya'yansu suke. Sosai hakan yayiwa su mum dad'i. "Tau nakira mum hankalin ki ya kwanta kho..?" Turab ya fad'a lokacin da suka kammala wayar gaba d'aya. Rungume shi tayi tana dariya tace "eh hankalina yayi rabin kwanciya, ka cika ya zama ya kwanta gaba d'aya Please" "To ya zanyi na cika hankalin ya kwanta gaba d'aya" "Ka kira ya-zafaran mu gaisa dasu suma..." "Ke wai baki san dare bane yanzu a wajensu ko dan kina ganin rana tarrr anan" "Nidai wallahi ba ruwana ka kira kawai idan kuma ba haka ba zanci gaba da barin hankalin nawa tsaye tsaff ko zama ba zai yi ba balle ya kwanta" Murmushi yayi kawai yana jijjiga kai, number din zafaran ya lalubo normal call ya kirashi, sai da wayar tayi ringing sai biyu ana ukun ya dauka, bai ma jira jin abunda zafaran zaice ba ya riga shi fadin, "idan matarka tayi bacci ka tayarda ita ku hau online gimbiya ta na buqatar yin waya da ita video call.....!" Bai jira cewar sa ba kuma ya katse wayar ya koma online. Zafaran kamar bazai zo online ba ba dan ya dauki mintuna kafin su ka ga saqonsa ya yi musu sallama "hi nice couples" ya tura musu da saqon wannan. Da sauri leeya ta bud'e sakon ta danna musu kira, cikin matuqar farin ciki leeya ke kallon qanwarta "budurwar ammi kin manta da yahyah leeya kho..?" Cewar leeya tana murmushi amma idanunta tapp suke da hawaye. "Yahyah-leeya taya zan manta dake Ni kuwa, wallahi ki tambayi broth O ma kiji yanzu muke zancenku, Ni ina ma tunanin da wuya idan 'yan Spanish basu mayardaku aljanu ba, da kukazo kuna leqon asirin mu, Domin fa yanzu muke zancenku wai sai ga kiran wayanku abun akwai mamaki gsky" Aleena ta fad'a tana washe baki. Leeyana ma bakin take washe wa suka gaisa kafin ta miqawa turab system, Aleena kuma ta miqawa zafaran suka gaisa. A cikin zancensu ne Zafaran yake bawa turab labarin kwanan nan zasuyi tafiya zuwa taraba wato asalin garin iyayensa. Da mamaki turab yace "taraba dai zafaran....?" "Eh wallahi, grandnee na ne sukace sai ankawomusu amarya sun ganta" "Allah yasa dai karsu nunawa qanwata wariyar launin fata" "Bazasu nuna ba ai, saboda muma muna da musulmai a familyn mu amma gskiya basu wuce hud'u ba, kuma tunda momynah ta rasu suka rage nunamin qiyayya akan nafita addininsu na shigo wannan. Suna gani sun quntatani idan suka ci gaba da nunamin qiyayya shiyasa suka sassauta. Yanzu ma sun sami labarin nayi aure shine suka takurani akan sai na kawo musu amarya sun ganta kuma itama na gayamusu musulmace kaga babu wata wariya da zasu nunamata in sha Allah" Cikin gamsuwa da maganar da zafaran yayi turab yace"okay, tau Allah ya kaiku lpia ya mayar daku lafiya" "Ameen ya rabbi, amma dawowa ba yanzu ba tun da na sanarmusu she's pregnant suka kafe akan saina kawota Ni ina tunanin ma bazasu bari ta haihu anan ba kasan yanda qabilar mu take fa" Turab da mamaki yace"waye mai ciki kuma" Zafaran ya ɗan shafa kansa yana dariya Yace"matata mana, me kake tunani nifa ba ragon namiji bane wallahi kaima ka matsa ka qara qaimi" Cikin jin kunya leeya ta tashi zata bar wurin turab ya riqota har tana fadowa kan jikinsa, ta zaune suka dinga sheqiyanchi ko kunyar matan nasu basa ji sukuma kamar su nutse saboda kunya. Haka sukayi sallama cike da kewar juna, "nasan yanzu zakice sai an kira Fahad kho" "Eh mana my love Wallahi nayi missing bestina Please ya-Turab dan Allah mana" tayi maganar tana marairaice fuska. Dan jan hancinta yayi "kinganki kho, tho bazan kira ba" "Haba yaya dan Allah.......!" ""To shikenan kinga ma baki kula ba harna kira ringing take ki shirya" Ko rufe bakin sa baiyiba yaji alamar sun daga kiran, fahad ne zaune sai zohal dake kwance ta dora kanta akan cinyoyinsa, suma da system suke aiki hakan yasa call din nasu yafito so well. Cike da nutsuwa suka fara gaisawa gaba dayansu, leeya da zohal kamar su rungume juna saboda murna sun jima suna wayar kafin sukayi sallama. Dare yayi sosai a Nigeria ba kamar spain da suke qarfe tara na safe ba yanzu. Rufe system din yayi yana cewa "my princess angama komai koh...?" "Eh honey, ina godiya sosai Nagode Allah ya barnin kai jarumina" "Ameen ya rabbil ibaddd, ki tashi muje na shiryaki zamu fita yawo yau" Har wani ihun murna take domin tun shigowar su garin ya qawatata matuqa, har Allah-Allah take taji ranar da zaice su fita yawo. Da hanzari ta shiga toilet tana qoqarin rufewa ta ganshi ya biyota. Zare idanu tayi tana shirin magana ya saka yatsarsa yana rufe mata baki tare da jijjiga mata kai. Zip din rigarta ya fara zugewa har ya kaishi qasa, ya rage kayanda ke jikinta basuda yawa, tafukan hannunta ta saka ta rufe fuskarta ta lokacin da taji ya mayarda da ita naked, shima yayi naked ya fad'a cikin koman wanka ya janyota itama ta fad'a kan jikinsa. Saida sukayi romance sosai kafin yayi mata wanka shima yayi wanka ya nad'ota cikin towel kamar wata baby ya ajiye ta akan bed. Tana kwance ta kasa ko motsawa harya shirya cikin qananun kayan da suka yimasa kyau matuqa. Blue armany jeans ya saka anyi layi uku na fari daidai gwuiwoyinsa. Sai kuma keymoni short fara tasss mai dogon hannu, sai wata arninyar top da ya saka saman kayan. Turarukan sa masu qamshi ya feshe jikinsa dasu, duk abunda yake tana jinsa tayi lamo kamar mai bacci. D'aga ta yayi zaune kafin yakaita gaban mirror, da kansa yayi mata make up so simple bayan ya shafeta da lotions. Irin kayanda ke jikinsa sak ya saka mata sai dai nata na mata ne daga yanayin sharp din kayan. Farin gyale jessy ya ajiyemata yace "my one rolling ne kadai ban iya ba kiyi da kanki nasan ke zaki iya yi" "Nidai bazan yi ba ai tunda kai ka fara ya kamata ace ka qarasa da kanka" Magiya yayita yimata akan ta daura Jessy din amma fur ta qie,,,,,! ganin suna cin lokaci ya saka shi janyo wata cabinet drawer ya fito da rolling pin kalar jessy din wato fari. "Ki gyara da kyau na daura naga ko zan iya" Juyomasa da kanta tayi sosai yanda zaiji daɗin roller ma ta gyalen. Sosai ya bada himma wajen ganin rolling din ya fita yanda yakeso. "Ki duba kiga ko yayi miki" cewarsa yana juya kujerar da take zaune gaban mirror. Baki sake takebin fuskar ta da kallo, ganin ko ita da take mace idan tayi wannan ai sai an yaba mata balle ma ace namiji yayi. Mamaki ya hanata faɗin komai sai tashi da tayi ta rumgumeshi tsamm ta manna masa kyakkyawan Peck a kumatu. "Kinyi kyau my angel" "Allah kaima kayi kyau sosai hub..., kar 'yan matan Spanish su kwace min baby.." ta fad'a tana dan langwa'be kai. "Humm, kar ma ki bari wannan yayi tasiri aranki domin turab nakine ke kadai" "Allah koh qalbie.....?" "Eh sosai nakine ni, Ni akayiwa ke, kema ke akayiwa ni. Mun hadu babu rabuwa" "Allah yasa haka Honey, muje" "Ina zamu fara zuwa....?" Cewar turab yana tuqa mota bayan sun fito gidan. "Inaso muje gidan namun daji first, daga nan kuma naje gidan tarihi da al'adu na qasarnan, sannan kuma inaso muje asibiti aqallah guda biyu muyi sadaqa, sannan muje gidan abinci.........." Tayi jimmm kamar mai tunani daga nan kuma bata qara cewa komai ba. "Umhumm, ina jinki sai ina" "sai muje mall" "And them...?" "Sai.....sai......sai mu dawo gida". Laquto kumatunta yayi yana dariya yace"naji nabi ya shugabata" Dariya sukayi gaba dayansu lokacin da suka qaraso bakin wata asibitin gwamnatin dake qasar. Kamar yanda leeya tace haka turab yayi, kuma duk inda ta fad'a sai da sukaje sosai ya kashe kuɗi kamar ba gobe. Haka suka tattaro suka dawo gida a gajiye. Damansu ɗaya duk sallahr da akayi suna tsayawa suyi har lokacin sallar isha da yayi suna waje basu dawo gida ba acan wurin yawon shan iskansu sukayi. A matukar gajiye sukadawo leeyana da jan qafafu ta shigo parlon gyalenta a hannu da kuma waya da handbag. sai turab ne ya shigo da kaya niqiqi bayan ya kira robot dinsa sun taimaka masa. Da taimakon sa tayi wanka shima yayi wankan suka shirya cikin kayansu na bacci masu masifar kyau suka kwanta. [{BAYAN WATANNI UKU}] *SPAIN*~~~~ _____Kwance take ta kanannad'e a cikin blanket, tunda zai je sallah yake tada ita amma ta kasa tashi. Yasan mafi yawan lokuta idan tana period haka take a maimakon ta bud'e baki ta gayamasa cewar bata sallah. Fita yayi daga bedroom din ya nufi prayer-room, ya dade sosai yana yimusu addu'ar qara samun farin ciki da zaman lafiya mai dorewa kafin ya dawo bedroom din da ya barta. Da mamaki yake bin ko'ina da kallo, shi dai yasani idan tayi irin haka, ya tabbatar koda zai dawo sallah zai tarar ta tsaftace jikinta, sannan ta gyara ko'ina a duk ɓangaren da suka kwana a gidan. A mamakinsa sai ya tarar tana nan yanda ya barta. Cikin sanyin murya irin tashi yake kiranta "wife ki tashi gari ya soma wayewa kinji, nasan kina period ne kho...? Toh nagane. ki daina jin kunya ki tashi ki tsaftace jikinki ki dawo kici gaba da kwanciyarki, zankira su sholeen su gyara komai in yaso muje wani bangare ki kwanta ki huta. Bata d'ago ba, haka zalika ko motsi baiga alamar tayi ba. Bubbuga gadon ya fara yi tun yanayi a sannu har ya fara bugawa da qarfi amma ko kezau batayiba, babu kuma wata alama da ta nuna taji bugun da yake. Bargon ya d'aga yana kiran sunan ta "wife wai meye haka ki tashi mana" ya fad'a lokacin da yake yaye bargon daga fuskar ta. Da mugun sauri ya d'aga bargon gaba ɗaya, hankalin sa a masifar tashe ganin yanda take. kwance take ta kanannad'e jikinta wuri ɗaya sai karkarwa take haqoranta na sama na karo da na qasa. A hankali ta dago idanunta da sukayi jajir saboda tsananin ciwo tace "ka gafarceni hub,,,, ban gayamaka ba wallahi kwanaki biyar kenan yau shine na shida ina fama da zazzabin nan, banyi niyar gayamaka ba nasan xakace sai munje asibiti, nikuma a duniya babu inda na qie jinin zuwa kamar asibiti shiyasa nayi shiru ban gayamaka ba. a zatona zan sami sauki da magungunan da nake sha. Amma yanzu inajin ciwon nan yaci qarfina da yawa" A fusace ya hau kan gadon ya ɗora kanta akan cinyarsa ya fara magana Cikin tsawa "ke wace irin mace ce haka leeyana, me yasa kike qoqarin yimin wasa da ranki da kuma lafiyar ki, duk da bakya buqatar zuwa asibiti ya kyautu ki zauna da ciwo a jikinki. Wannan shine abunda bazai taɓa yuwa ba saboda haka ki tashi muje na shiryaki yanzu mu tafi hospital. Idanu ta zazzaro. ganin bai bata damar musawa ba ta gimtse bakinta. Cikin azama ya kinkimeta sai toilet, a hankali ya sakata a koman wanka, shiya yimata wanka da kansa ya shiryata cikin wata doguwar riga mara nauyi, ko kadan rigar bata kama jikinta ba rigar ta zauna sosai yanda bazata takura mata ba. Ɗaukar ta yayi da kansa ya sakata a mota ya kira driver yazo ya tuqasu, shikuma ya zauna back sit yana tallafe da ita. Wata tsadaddiyar asibiti suka nufa wacce turawan koria suka bud'e ta, kuma kafff Birnin Spain itace babbar asibitin Kudi da aka fi sani lungu da saqo. Tun a gate na hospital din aka fara tarbar su, hannu bibbiyu aka karb'esu bayan shigarsu ciki. Wani qaramin gado aka kwantar da ita aka saka wasu labule aka killaceta kafin a kammala cika mata Form, wannan yana daga cikin wani abun birgewa da Asibitin ke yi. Basu dauki lokaci ba aka kammala komai kafin aka shiga da ita inda zasuga doctor. Tare suka shiga da turab ya zauna kusa da ita a kan wasu kujeru biyu da suke fuskantar likita. Cikin nutsuwa likitan ya fara tamabayarta da harshen turanci domin basa jin hausa ko kaɗan. "Me kike ji a jikinki, ma'ana menene abunda yake damunki wane yanayi kikeji.......?" Itama cikin harshen turanci ta fara masa bayanin abunda ke damunta tsawon kwanaki biyar. "Inajin ciwon kai mai tsanani, ina yawan jin qishi, kuma ina yawan ganin juwa wani lokacin ma sai na dafa bango nake iya yin tafiya" "Okay, kina yawan jin yunwa" "A'a" ta bashi amsa a ta'kaice. "Kinajin d'and'ano idan kika ci abinci" Jijjiga masa kai tayi alamar bata ji "ko kaɗan banajin dandanon komai ruwa kawai nakesha naji dad'i" Rufe file din da ke gabansa yayi bayan ta qarashe maganar. Wani belt ya d'an kad'a nan da nan sai ga wasu nurses mata biyu sun shigo office din. 'dayar ta janyo kujera mai kamar gado ta ajiye gaban leeya, d'ayar kuma tana murmushi tace "madam ki hau nan yanzu zamu dawo mintuna goma". Zama tayi kan gadon suka bi ta wata kofar daban suka faɗa wani daki. Turab kam sanin yanda tsarin manyan asibitocin suke ya saka yayi gum da bakinsa yana jiran sakamako. Cikin mintuna goma kuwa basu dad'a ba suka dawo, nurses d'aya ce ta fara shigowa da takardu a hannunta ta ajiye gaban doctor sannan ta juya inda ta fito. Hannu likitan ya miqa masa yana murmushi haɗe da takardun da nurse din ta shigo dasu. "Congratulations sir-turab, amarya tana dauke da juna biyu tsawon sati takwas" Wani irin wuntsilowa yayi daga kan kujerar da yake zaune, hakan kuma yayi daidai da shigowar leeya da kuma nurses din da ta fita dasu amma a wannan karon kam ba bisa gado suka dawo ba da qafafunta take. Da sauri ya rungume ta tsamm kamar wani zai kwacemasa ita. "You are pregnant my wife, Allah yayi miki albarka, ina matuqar sonki da qaunarki, Allah ya nunamin ranarda zaki haifi wannan cikin lafiya matata, Allah ya baki lafiya. Alhmdullillah ya Allah" Ya fad'a ƙwallah na taruwa a idanunsa har ya kasa kwatanta irin farin cikinda yake ciki a wannan lokaci. Likita da kuma nurses kam kallonsu kawai suke cike da sha'awa domin basa jin komai da yake fadi sakamakon da hausa yake magana. Dawo da hankalinsa yayi ga likitan bayana ya zaunarda leeya akan kujera. Bayani likitan ya masa da yanda ya kamata a kula da ita da kuma irin abincin da ya kamata ta dinga ci da wanda bai kamata ta ci ba a ka'idance. Cike da farin ciki suka koma gida turab kam hatta drivern da ya daukoshi sai da ya gayamasa wannan abun farinciki, ai kuwa kamar jira yake ya koma gida ya fara kiran mutane yana sanar musu. Leeya kam duk kunya ta kamata tana qara godewa Allah da yasa ba Nigeria suke ba da rufe kanta zatayi a d'aki. Mum ya kira ko kunya babu ya sanarmata, mum ta gayamasa ai tuni aka kirata aka gayamata. Yayi mamaki sosai amma mamakin nasa ya ragu tunawa da yayi ya sanarwa mutane da yawa kafin mum. Anan kuma ya sami labarin ai 'yan uwan nasa duk basa nigeria, zafaran da Aleena suna Mexico amma kuma 'yan uwan zafaran din sun nemi ya dawo taraba, idan cikin Aleena ya isa haihuwa nan suke so su ajiyeta har sai ta haihu sannan su rad'a wa yaro suna, idan anyi suna kuma sai 'yan uwanta suzo su dauketa sai anyi kwana arba'in sannan a mayarda ita gidan mijinta haka al'adar su take. Lokacin da turab ya gama jin zanjen mum yayi ajiyar numfashi sannan yace "ikon Allah, mum kowa da irin nasa amma ina na taɓa ganin anyi irin haka" Mum ta bashi amsa da faɗin "kasan kowace qabila tana da al'ada irin ta ta, to su kuma waɗan nan wannan shine al'adar su tunda har suka gayamana. Yanzu dai suna Mexico kuma nasan idan lokacin haihuwar yayi dole zasu koma chan taraba" "Mum kuma naji kince wai sai an rad'a wa yaro suna" "Eh sunan da sukeso su dinga kiran yaron, sunada damarda zasuyi haka ai, sannan kuma muma zamu sakawa yaro sunanda mukeso. Idan suka tashi su dinga kiransa yanda suke so, muma mu kirasa yanda muka saka masa" Cike da al'ajabi turab yace "shikenan mum, Allah ya sauke su lafiya, shima fahad ya gayamin sun je India. Kuma ya gayamin wata mai fita ne watan zohal. Ina tunanin shima bazai dawo ba sai ta sauka" "Saboda me?...." Mum ta tambaya da mamaki ganin yanda familyn zohal din suketa shirye-shiryen bikin ta idan ta haihu. "yana so su sami kwararrun likitocin karɓar haihuwa basai ta wahala da yawa ba. idan ta sauka Lafiya ko kwana ɗaya bazasu qara ba zasu biyo flight su dawo" "Ikon Allah, yaran nan kunada abun mamaki, da alama dai kaima irin haka kake so kayi" "Eh wallahi mum kamar kinsan abunda yake raina kenan" "To bara kaji, wallahi mamanta ummasalima bazata yarda ba, ko Aleena ma da kyar da sudin goshi aka samu tayarda shima dan yana al'adar su ne, saboda haka ka fitarda ranka tun wuri" "Naji, dama ban saka raina duka-duka ba, amma fa anan zamu yi rainon cikin sai idan ta shigo watanta sannan zamu dawo" "Ko ma dai menene idan ba so kake ta biyoku spain ba" "Bama zata biyomu ba mum zamu dawo, kedai kice kina kewar d'iyarki ne kuma bakyaso ki fad'a" Haka suka ci gaba da fira cikin raha har ya bawa leeya waya sukayi waya da mum sosai duk da suna yin wayar lokaci zuwa lokaci. _______*A bangare d'aya kuwa. Sayyid ya tsaya sosai ganin rayuwar id da mahaifiyar sa tatafi daidai. Inda ya dage sosai ya saka mahaifinsa ya basu gida, wani Makeken gida mai martaba sarkin suleja Muhammad Safwan al'adal ya bawa mahaifiyar turab. Sannan ya ginawa turab qatoton mall da babu kamarsa. Shikuma sayyid ya gina musu gida iri daya kuma a unguwa ɗaya, babu abunda ya bambanta gidajensu. Kuma ya saka mai martaba ya nema musu aure. Aka saka bikin nasu lokaci guda nan da shekara daya mai zuwa. Dalili kuwa shine zasuje aikin hajji sannan kuma sayyid zai wuce jidder ya wakilci mahaifinsa wani taron gaggawa da za'a yi kuma taron zai dauki tsawon watanni shida shiyasa aka saka auren a shekara ɗaya. Da reemah rabil akayi engaging din sayyid shikuma id da Khulud, kuma sosai suke qaunar junansu. ***** Bayan wasu kwanaki. SPAIN. Zaune take kan cinyarsa hannunsa riqe da rubber bowl yana bata abinci a baki. Ruwa ta d'akko zata sha da sauri ya ajiye bowl din ya d'akko ya bata. Cikinta ya girma sosai sai da kyar take iya tsugunawa. Kuma idan ta zauna bata iya tayarda kanta daga zaunen. "Inaso na kwanta" ta fad'a tana murmushi. "Muje na rakaki tho, cikin nan kam yana wahalar min da babynah Allah dai ya rabaku lafiya" "Ameen honey, amma ba dai baby ba sai dai maman baby kho" "A'a ni a wurina har yanzu baby ce" "Wallahi dear cikin nan yana bani tsoro ji girmansa fa....... kuma har yanzu akwai watanni biyu gaba" "May be basamude zaki haifa ma na, ko kuma mai qarfi sosai kamar jarumi hantaru" Kwa'be fuskarta tayi sosai.........! mai neman kuka an jefe shi da kashin tumaki. "Ɗan Allah kiyi hakuri karkimin kuka wasa nake ba kamar jarumi hantaru zaki haifa ba ai" Kukan ta saki a shagwa'be tana faɗin "ai gwara jarumi hantaru da basamude menene ma basamude irin mutanen nan masu tsawo kho...?" Daga Mata kai yayi yana gimtse dariyarsa sanin yanda takeji idan aka ce ɗan ta babba ne ko kuma dogo a cewar ta sai ta wahala wajen yin naquda. "Eh masu tsawon nan ne samudawa mana....... sosai fa, inagayaki shi basamude ko qaramar yatsar qafarsa ta fimu tsawo mu duka biyu idan aka hada" "Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, amma Lallai ya-turab bakada tausayi wallahi, shine kuma kake cewa na haifi basamude. Allah ya kiyayeni wallahi" Yana shirin magana yaji qarar wayarsa dake hannun leeya alamar kiransa ake. Miqamasa wayar tayi ba tare da ta duba mai kiran ba. Cike da farin ciki yayi accepting Call. "Alhmdullillah" ya faɗa bayan yayi sallama an amsa masa bayyannen farin cike ne cike da fuskarsa ya kuma faɗin "masha Allah, me aka samu.........! Allah ta'alah ya raya mana akan sunnah,,,,,,,,,,tho Allah ya kaimu muma zamuzo ayi biki damu in sha Allah..........., ba wasa ba zamuzo wallahi gudan bestinmu ta haihu kuma muqi attending suna, Ameeen ya rabbi" turab ya fada yana fadada murmushin fuskar sa zuwa dariya bayan ya katse wayar......................✍🏼 Ep.50_END.....🥳🥳🥳 ________________da murmushin da bai gama gushewa daga kan fuskarsa ba ya kalleta da faɗin "gskiya sai kin bani tukuici kafin na gayamiki wannan daddad'an labari" Ita kam tunzuro baki tayi.......! shi har ya manta da abunda tace masa. Bacci fa tace tana ji, har zai tsaya wani shiririta, alhali yasan tana jimawa baccin bai zo ba....... Shine yanzu ta samu yazo shine yakeso ya koreshi. "Wallahi idan na haihu bacci zan yi har sai an manta dani tunda wannan Babban cikin ne yake hanani bacci" "Ohh sorry my princess ai zakiyi bacci sai ma kin gaji wallahi, kuma ba wanda zan bari ya tadaki har sai kin gaji kin tashi da kanki....., yanzu dai kibani tukuici na gayamiki abunda nakeson gayamiki" Cikinta ta kalla tana shafawa tace "na baka tukuici wannan....!" "Wannan ai nawane tun tuni ma,,,,,,bani wani abun" "Na baka wannan........" Ta fad'a tana nuna masa ɗan mitsitsin bakinta. Dariya yayi sosai ya d'an ja bakin yace "na karɓa" "To gayamin.....!" "Zohal ta haihu fa yanzu nan fahad ya kirani ya sanardani ta sami 'yarta mace mai kamada ke" "Whattt......!!!!, bestie....." ta fad'a kamar zata kifa Saboda batada wani nauyi duk cikin ya karɓe komai. "A hankali dai madam kar ki min asara" cewar sa yana tallafo ta jikinsa. "Hub....Dan Allah mu koma Nigeria yau, can't wait to see my bestie with our precious baby gurl" "Yaushe zamu tafi Nigeria tho" "Yau mana babe..." Ta fad'a cikin shagwa'ba "Uhmm lallai kho, to suma su zohal din basa nigeria suna India sai nan da kwanaki biyu, nima ina tunanin komawarku a kwana na uku. Idan akayi biki damu sai mu dawo nan" "Muyi me anan ya-turab" "Ki haihu mana" "Tabbb wallahi bazan iya ba, nifa idan na koma Yanzu ba abunda zai mayardani idan ba haihuwa nayi ba, Ni kunya ma nakeji ana ganina da wannan tulelen ciki" Dariya mai sauti ya kece da ita yana qara jin soyayyar matarsa na ratsa jini da 'bargonsa. "Yanda kikeso haka za'a yi mai girma da daraja a fadar turab" Dariyar jin dadi tayi kafin tace"muje mu fara shirin tafiya kho, ai baccin ma ya tafi" "Inahhh.......! Ai baki isa ba wallahi sai munje kinyi" Rigima ta saka masa akan bazatayiba da kyar ya samu tayi baccin. Kwanan su biyu a haka, leeya kam kullum tana qara narkewa turab dinta shikuma sai faman biyemata yake, washegari ya kama laraba kuma a sannan ne suka shirya tafiya. Tun a daren yau ya shirya musu komai na tafiya da kuma sauran abubuwan da zasu buqata na haihuwa. kama daga kayan babies da kuma ita kanta wadanda basa tunanin a samesu a Nigeria. Tashin hankalin daya shine yanda zasu je gida Nigeria da leeya a haka, shi wallahi yana matuqar tausayinta yanda cikin nan ke wahalar da ita, idan ta jima zaune qafafunta su kumbura suntul, dha ɗin daɗawa kuma idan ta jima zaune bazata iya tashi da kanta ba har sai an tallafamata saboda nauyin cikin. A kan cinyoyinsa ta kwana a cewarta bazasu yi bacci ba kar suyi missing morning flight din da zai tashi karfe 7:45am agogonsu na can. Domin morning flight ne kawai zasubi su isa gida da wuri. Shine tace bazasu yi bacci ba suna nan zaune har sai lokacin tafiya yayi karsu makara. Amma gashinan a zaune wasai ba bacci, ita kuwa fara baccin ta zuwa yanzu taci mintuna fiye da arba'in. Dariya yayi yana shafa sumar kanta mai tsananin taushi da qamshi, wacce ta bajeta a kan cinyoyinsa. Magana ya fara mata a hankali cikin kunnuwanta "qalbie kinga kho, da wannan baccin naki kin saka munyi missing flights.....Tho kici gaba da baccinki tunda haka Allah ya qaddara ba yau zamuyi tafiyar ba" Yanayin yanda ta miqe zaune yasan da ace ita kadaice abun sai yafi haka, kafin ta gama tantance gaskiyarsa tuni idanunta sun kad'a sunyi jajir da kwanciyar ƙwallah a cikinsu. "Meyasa baka tasheni ba ya-Turab, wallahi na saka rai da tafiyarmu yau....! Har mafarki ma nayi mun tafi wallahi, Saboda me zaka barni ina yita bacci dan Allah. nidai baka min adalci ba gaskiya" ta fad'a har wata rawa muryarta keyi. Wayarsa ya nuna mata "qarfe biyar da kwata fa wasa nake miki garin ma bai idarda wayewa ba na miki haka ne kawai dan ki tashi muyi sallah idan mun idar mu fara shirin tafiya" Miqewa tayi da kyar ya taimaka mata suka shiga toilet tayi wanka tare da alwala, shima wankan yayi ya d'auro alwala sannan suka dawo bedroom. Kaya ya saka mata sannan ya zuro jallabiya ya tayarda sallah. Sosai sukayi Addu'oi bayan kammala sallarsu. "Ki kwanta ki huta kinji, Bara naje na fitar mana da kayayyakin mu sannan muyi breakfast" Wani lallausan murmushi ta sakarmasa tana gyada kai, har ya juya zai tafi ta kira sunansa. "Ya-turab....!" "Na'am" ya amsa mata da mamaki jin yanda ta kira sunansa da kuzari. "Ina sonka yayanah, dan Allah karka barni kaji Please, wallahi ina matukar kaunar ka, qauna irin wacce ban taɓa yiwa wani hallita makamanciyarta ba bayan mahaifana da Yar uwata sai kuma kai mijinah, qauna da soyayyarka daban suke a zuciyata, dan Allah kar ka manta dani da irin soyayya ta a gareka ko bayan babu ni" Sosai maganar ta tayi tasiri a zuciyarsa, cike da sanyi jiki ya dawo har kan bed din da take kwance ya shafa gefen fuskar ta. Ance sumbata a koshi tana nufin alqawari mai girma da babu abunda zai iya karyashi face wanda ya aikata ya cika alqawarin. Irin haka ce ta faru da leeya da kuma turab, kafin ya furta komai sai da ya sumbaceta a goshi sau biyu sannan ya fara magana. "Dan Allah qalbie ki daina irin wannan zantuka, taya zakiyi tunanin ni turab zan iya rabuwa dake kuma inada rai da lafiya, wallahi ko kusa haka bazata taɓa faruwa ba,,,,! ko a cikin mafarki naga haka wallahi da gudun jirgi zan qaryata domin nasan ba gskiya bane. Kuma bazan mata dake ba, ba kuma zaki mutu ba in Sha Allah muna tare, kuma tare zamuga tsufa in Allah ya yarda. Ina sonki irin sosai din nan more than words can describe....!" Lumshe idanunta tayi har ga Allah taji dadin kalamansa, har ta kasa samun kalma ɗaya tak da zata gayamasa da ita domin shima ta sakashi farin ciki kamar yanda ya sakata. "Ki yi bacci kin ji, amma fa na mintuna talatin kawai, suna cika zan ta da ke mu tafi" Rufe idanunta tayi kamar yanda yayi fatar gani sai kuwa baccin gskiya yazo. NIGERIA. K.WAASIB MANSION. Sosai aka shirya komai na tarbar su, musamman mum da ta qagu taga 'yarta. Komai an shirya mata na haihuwa ita da qanwarta duk da sanin haihuwar batazo ba, jiya har taraba mum ta tafi taga 'yarta Aleena kuma ta kaimata kayayyakin da aka had'a mata na shirin haihuwa, sosai qabilar su zafaran suka tarbi mum kamar ba kirista ba. sun saki jiki da ita Sosai har suka ta'ba fira kafin mum tayi musu sallama ta biyo flight ta dawo. * Mintuna kadan turab ya qara kira ya sanarmusu da isowarsu, bada jimawa ba mum ta haɗa tawaga harda su papu akaje tarbarsu. Mamakin kowa ya bayyana lokacin da sukaga yanda leeyana ta chanja, haqiqa ko da ka santa dole zakayi gardama akan ba ita bace. Duba da yanda ta sauya gaba daya, tayi wani irin sihirtaccen kyau. Babban abunda ya qara bawa mutane mamaki Ganin yanda cikin leeya yake, wasunsu ma zasu iya rantsuwa basu ta'ba ganin cikin irin nata ba. Gashi nan dai abun sai wanda yagani. Bayan kwanaki hud'u da zuwan su aka shirya gagarumin bikin sunan zohal da jaririjarta. Sosai farin ciki ya cika ahalin musamman mummy-neesah yanda mutanensu sukayi mata karah. takanas mutanen india sukazo bikin, kuma suka sakawa yarinya suna. A ranar da ake bikin Halloween na cika shekaru biyu da rasuwar nahaifiyar mummy-neesah, a kuma ranar ne aka haifi jaririyar zohal. Saboda haka yasaka mummy-neesah ta roqi fahad akan yayiwa mahaifiyarta wato kakarsa takwara da 'yarsa da aka haifa. Cike da tsantsar farin ciki ya amince domin shima shawarar hakan yake a ransa sai kuma Allah ya saka mummy-neesah ta fahimci tunaninsa. Ranar suna kuwa yarinya taci sunan babba a cikin familyn su fahad aka sakawa jaririyar suna (GULNAR) sannan fahad ya baiwa ahalin gidan Khalil girah damar zaɓen sunan da zasu sakawa yarinyar a matsayin nickname. "Ifrah.....!" Shine sunan da fahad ya maimaita a bakinsa lokacin da zohal ta gaya masa sunan da suka za'ba. "Masha Allah, Allah ya rayamana GULNAR mai sunan manya a india, a Nigeria kuma ifrah. Ina matuqar qaunarki ifrah. Ina godiya ga Allah da ya bani mahaifiyarki. Allah ya qara bani ikon kiyaye haqqoqin ku" "Ameen" zohal ta faɗa cike da jin dadin kalamansa. * A bangaren su Aleena kuma tun daren jiya take fama da naquda, sosai zafaran ya damu ganin yanda suka hanamasa kai ta asibiti. Duk wannan yana cikin qa'idodinsu, kuma hakan shine al'adar su kuma suna girmama al'ada matuq, ba qaramin abu bane yake sakasu su karya dokar al'ada. "Samanta, ya kamata ki saka baki a maganar nan, tunda nasan inne najin maganar ki. Kar 'yar mutane ta mutu a hannun mu" Zafaran ya fad'a yana durkushe gaban wata tsohuwa mata. Murmushi tayi kafin tace masa "kar ka damu, bazata mutu ba. Kaga ai anata kula da ita. Haihuwar ce batazo ba kawai amma bana fatar mutuwa agareta gaskiya, domin tanayin naqudar yanda akeso tanada dauriya sosai" "Haba samanta, taya mutum yana cikin matsanancin hali irin wannan zakice na kwantarda hankalina ina matsayin mijinta, wallahi idan ta mutu sai iyayenta sunyi Shari'a damu, kinga mahaifiyarta ɗaya ma da kyar ta barta gidan nan, kuma har da jaddada muku tayi komai ya sami yarinyarta sai ta yi Shari'a daku koda komai da ta mallaka zai qare" (Ummasalima yake nufi) Tsohuwar da yake kira da samanta na shirin magana sukaji kukan jarirai na fitowa daga cikin dakin da Aleena take. Tare suka tashi aguje suka nufi dakin, sai dai iya samanta ta sami shiga, zafaran na gab da zai shiga aka rufo qofar da sauri. Wani mugun duka ya kaiwa qofar cike da jin haushi. Sanin tunda suka rufe bazasu bude masa ba. Hakan ya saka ya koma gefe yana jiran fitowar su. Bayan tsawon mintuna arba'in sai gashi an bude masa kofar, aikuwa kamar za'a qara rufemasa ya shiga dakin da azama. Bakinsa ne ya kasa rufuwa ganin matarsa gatanan kwance an tsaftace ta har turare aka kunna a dakin da kuma yara biyu kwance cikin kyakkyawar shiga ta kayan jarirai masu kyau da mum fanaya ta sako a cikin kayayyakin da ta kawo musu. Bai isa inda yaran suke ba har sai da ya gama yiwa Allah kirari a zuciyarsa kafin yakai hannu ya d'akko daya daga cikin yaran. "Kagani kho, matarka tagwaye ta haifa mace da namiji kyawawa dasu" wata mata ta fad'a tana murmushi. Shima murmushin yake kafin yakai yaron saitin bakinsa yayita koro masa Addu'oin da manzo Sallallahu alaihi Wasallama ya umurta ayiwa jarirai idan aka haihu. Bayan ya gama ya d'akko mace ya yayi mata itama. sosai yarinyar ta shiga ransa lokacin da yayimata 'kuriiiiii.....!!!!! Yana kallon ta ganin yanda take cikakkiyar kama da ammi mahaifiyar Aleena. Batare da 'bata lokaci ba ya fara kiran mutane yana sanar musu, su mum kam baki har kunne baramma ummasalima da ta fi ji da Aleena. Aikuwa kwana uku da haihuwa suka dawo taraba sukaci gaba da kula da ita, saura kwana ɗaya jal ayi biki mutane suka fara yin tururuwa daga wurare daban-daban. Leeyana ma da kyar ta iya zuwa dha har turab yace suyi zamansu tunda yanzu tafiyar ma da kyar take saboda girman cikinta. Amma sai mum tace abarta tazo kawai bikin yar uwarta guda..! Yakamata ace ta halarta. Hakanan ta tafi cike da dauriya da kuma tarin gajiya, har zohal da ifrah sun zo, ifrah kam an fara wayo kamanninta da mahaifinta na fitowa sosai duk wanda ya ganta zai yi tunanin indiyawa ne iyayenta, har ta fi su fannah da mayah zama cikakkiyar ƴar india tun daga gashinta idan mutum ya kalla. Zafaran ya sami abokansa sukayi shawara kafin yaje ya sanarwa mum shawarar da ya yanke game da sunan da za'a sakawa yara, tayi na'am sosai ta qara martaba qimar zafaran a zuciyarta. Ranar suna sai ji sukayi ana sanarwa, a bangaren iyayen zafaran sun sakawa yara suna, haka ma bangaren zafaran da dangin uwar yara sun saka sunan su suma. Kuma duk sunyiwa yaran yanka. danginsu zafaran sukayi yankansu yanda yake a al'adar su, namijin yaci suna (DUBEM) macen kuma (CHIDINMA). a bangaren zafaran kuma ya sakawa yaransa suna da kansa macen sunansa (FAHEEMA) namijin kuma sunansa (HAMRAZ) wasu hawayen farin ciki ne suka zubowa Aleena tana qara jin soyayyar mijinta na rasa ko'ina a sassan jikin ta, Sosai mutane sukayi mamaki domin babu wanda yayi tunanin haka, leeyana ma taji daɗi sosai, tun lokacin da fara ganin yaran suka shiga ranta musamman ma macen dake kamada amminsu sak. A lokacin da taji an saka sunan kuma taji ta qara qaunar yaran fiye da tunanin mai hasasowa. Haka akayi biki lafiya aka qare kowa ya koma gida. bayan wata biyu leeyana ta shigo watan haihuwa a yanda aka basu IDD. Tun farkon shigowar wata leeyana ke fama da matsanancin zazzaɓi tanajin naquda akai akai kafin wani lokaci ta nemi naqudar ta rasa. Babu yanda turab baiyiba akan mum ta barshi ya fita da ita waje amma taqi yarda. Kwanaki uku da wannan wata ranar Alhamis leeyana ta tashi da naquda mai tsanani, tun da sassafe suka kinkimeta suka kaita wata private hospital. Kwanan su ɗaya da awanni ana abu daya, leeyana ta jigata sosai, haqiqa duk wanda ya ganta dole ya tausayamata. Allurorin tada naquda babu kalarda ba'a yimata ba amma abun yaci tura. Nan likitan ya sanarmasa ya zama dole ayi mata c's da gaggawa, idan kuma ba haka ba za'a iya rasa babyn ko kuma ita kanta. Jin haka ya saka turab ya saka hannu tare da yimusu transfer din kudin da za'a buqata bayan an gayamasa adadinsu. Likitan na shirin sanarda sauran likitocin da yake aikin c's tare dasu. wata nurse ce ta shigo office din da sauri. "Sir kazo, da alama haihuwar ce tazo, amma gskiya akwai matsala domin matar ta kusa kasawa" Wata mummunan faduwar gaba ta ziyarci turab lokacin da yaji kalaman nurse din na karshe, fuskar leeyana kawai ke fadowa aransa ya na qara nema mata sauqi wurin Ubangiji. Fita likitan yayi da sauri tare da yiwa turab magana akan suje dakin jira su jira. Haka nan jiki babu kwari suka koma dakin jira sukayi jugum jugum suna sauraren hukunci rabbil izzati. Bayan shigarsu dakin da kamar awa daya saiga nurse d'aya ta shigo dakin fuskar ta babu fara'a ta miqa masa baby boy din da ke lullube cikin tsadadden lallausan towel. Da sauri mummy-neesah ta taso domin mum fanaya da turab duk basu san shigowar matarba sunyi nisa a cikin tunani har sai da sukaji mummy-neesah na fadin "masha Allah tubarkallah hajiya fanaya leeyana ta sauka" Da sauri mum da turab suka miqa hannu lokaci daya su qarbi babyn, sai kuma ga nurse din nan ta dazu ta qara shigowa da yaro daya, qarbar wanda ke hannun mummy-neesah mum fanaya tayi, shi kuma turab ya nufi nurse din sam bakinsa ya kasa rufuwa, cikin madaukakin farin ciki ya furta "twins......?!" Ko rufe bakinsa bai yiba ga wata nurse ta shigo da wani baby a hannunta. Turab kamar ya nutse saboda farin ciki ya karbi yaron daya yana fadin "duk namu ne" Nurses din suka amsa masa da "kwarai kuwa, duk 'ya'yankune, Allah ya azurtaku da samun yara maza har uku a lokaci daya" Sosai idanunsa suka chanja launi jaaa ya maye gurbin fari. Miqawa nurses yaran yayi batare da 'bata Lokaci ba ya durkusa qasa hannunsa sama kamar mai addu'a kafin yayi sujudul-shukhur, ya dade a haka sannan ya d'ago ya karbi yaran yayi musu addu'a, car keys ya fitar guda biyar ya miqa musu da kuma katinsa da address dinsa. "Wannan tukuicinku ne, idan anjima ku kirani wannan kati nane kuyi sending account dinku, sannan wannan address dina ne inda zaku zo ku dauki motocin" Mamaki sosai ya rufe nurses din, ansha haihuwar yara uku a hospital din nan amma ba'a taɓa samun wanda ya karramasu kamar wannan mutumin ba. Su Mummy-neesah ba bakin magana ko wannensu ya ɗauki yaro daya sai kire kiren waya suke suna sanarwa. "Ya jikin matata" turab ya tambaya. "Jikinta da sauki, ta samu bacci tana resting room sai idan ta tashi sannan zaku ganta" Kafin kace me tuni mutane sun cika Asibitin sai tururuwa ake, har 'yan jarida da gidan talabijin. Yara kam son kowa qin wanda ya rasa, kyawu ne ya had'u da kyau, domin ko turab ba baya ba kyakkyawane na gaban kwatance mai zubin larabawa, leeyana kam ba'a magana. Tuni leeyana ta farka amma jikin bai sake yanda akeso ba, sai da yamma liqiss aka sallamesu suka koma gida, sosai Mutanen su na Maiduguri suka bada gudunmawa, baramma ummasalima tayi namijin qoqari, kamar yanda tayiwa Aleena. Haka tayiwa leeyana ko wane yaro sai da tayi masa set din akwatuna, ya zamana ta kawowa yara set uku kenan, mamansu ma haka. Mum fanaya har rasa bakin godiya take idan ta kalli abunda ummasalima tayi, baiwar Allah sai tace mata ba komai yiwa kaine ko bayan haka Leeya da qanwarta marayu ne kuma ga zamanda sukayi da mahaifiyar su. A bangaren turab fahad da zafaran sun dage sun hana masa siyan ko tsinke, duk wani abu da kukasan ana sakawa jarirai sai da suka saka shida ko wannensu bibiyu kenan, hatta akwatunan da ake kawowa su zafaran sukayi, da aka fara shigowa da kaya sai da kowa ya riqe baki ganin irin kayan da zafaran da Fahad suka kawowa yaran abokinsa kamar a kamfani. Mutanen da ke gidan basu qara shiga mamaki ba sai da suka ga anshiga da qosassun raguna guda uku da manyan shanu biyu masu matuqar girma da wani babban raqumi ɗaya wanda a nufin su a yankawa yara ranar suna. Turab kam harda kukansa domin bai taɓa tunanin haka ba, duk da shima yayiwa yaransu amma ko kusa baza'a had'a ba. A cikin kayan kuma aka gano makullin mota har uku a baiwa yara, Tuni gida ya dauki ihu da shewa. Turab kam ya rasa tayi domin wannan yafi qarfin ayi masa godiya, tunaninsa da wace kalma zai yi amfani wajen Bayyana musu farin cikin sa. Mum ta kirashi batun sunan da za'a sakawa yara amma yace ya riga ya sakamusu suna kawai ranar suna yake jira. Jin haka ya saka mum ta bar zancen domin tunda taga haka tasan baya so ta sani shi yasa tayi shiru da bakinta kawai. Su ma su fahad sun tambayeshi batun sunaye ya gayamusu ai leeyana ta riga ta sakawa yaran suna, kuma bazai iya musa mata ba. Zolayarsa suka fara yi cikin wasa, samm abun bai masa zafi ba domin sun saba da irin haka. Zafaran ya shaidar wa da mutanen da yakamata su san yau Aleena zatazo bikin suna. da kuma sauran families dinsa. Sanin ba wata matsala ya sanya mum ta saka aka gyara masu bangare d'aya a gidan. Sosai mutane suke gangaro domin anshirya gagarumar waleemah wacce za'a hade yaran wuri daya ayi musu waleemar duk da ba wata tazara a tsakanin su, banner turab ya saka aka yimasa a sirrance mai dauke da sunan jaririyar Fahad, da kuma yaran zafaran da kuma nasa yaran. Ranar suna kuwa tunda sassafe mutane suke kasa kunnuwa suji sunan da za'a sakawa yara. Sai misalin ƙarfe goma na safe maroqa suka fara kida da roqa. "Allah ya raya 'yan uku tagomashin albarka, yara masu halin Dattaku Da tausayi, yara jinin arziki da wadata. Yara qanana renon manya jikokin Khattab waasibudden ministan shari'ar uban turab, kakan turab. Ina gaisuwa gareka kakan 'yan uku jikokin albarka, gahees uban fahad kakan Fahad, mun kowa gaisuwar mu gareku qabilar chochawa, gaku da d'a zafaran gakuma farin jika zafaran kun samu Allah dai ya barma kowa nasa" Marokan suka faɗa suna nufar gaban families din zafaran, aikuwa suka fara zuba kudi har sai da aka riqesu, sun birge mutane sosai yanda suka fidda dan su kunya. Wani mutum yazo yayiwa maroqi ɗaya rad'a a kunne, gyaran murya yayi yana qara saita speaker a bakinsa ya fara da fadin. "An nemi mu ambaci sunan jikokin albarka, 'ya'ya uku chas maza. "na fari sunansa (zafaran, ambashi laqabi da Akhram) sannan na biyu sunansa (turab ambashi laqabi da Afeef) sai kuma na ukunsu, nasan kun sanshi. Amma kuma domin fitardaku kokonto yasa zangayamuku....! Na ukun sunansa (zafaran, amma laqabin sa shine Aslam). Yara dai sun ci sunanyen mahaifansu. Sosai wuri ya ɗauki ihu da shewa, zafaran da Fahad da kuma turab suna zaune a balcony sunsha dressing kamar sababbin angwaye, zaune suke suna cin kalaluwan abincin da aka had'a musu hatta su samanta iyayen zafaran sai da sukayi musu kalar girkinsu suna ci sai faman santi suke sukaji sanarwar da maroqan keyi. "Man Zafaran kaji abunda nake jiyowa kuwa.......?" Fahad ya yi maganar da alamun tambaya. Ka sah kunne Zafaran yayi yana jiyo yanda ake faman sakawa yaransu albarka. "Naji kamar sunayenmu mutanen ke fad'a kho.....?" "Eh nima haka naji wallahi" "Kenan sunayen mu aka sakawa yaran?" Fahad yayi magana yana kallon turab da son jin qarin bayani,,,,,, ko kallonsu baiyi ba ya miqe ya zura takalmansa yayi tafiyar da lokaci ɗaya. Miqewa sukayi suma suka bishi suna yimasa magana amma yaqi kulasu har suka iso filin da mutane suka yawaita kuma anan ne makid'an da maroqa suke. Ganinsu ya saka kidan ya kara tashi da qarfi ana yimusu kirari, hakan ya saka 'yan uwa da abokan arziki suka fara shigowa filin suna yimusu ruwan kudi. Meenal da Khulud da kuma zohal dauke da yaran uku ko wacce a cikin su tana riqe da ɗaya suka iso cikin filin" Fahad da ya kula dasu da sauri ya qaraso yana washe baki yace "ina little Fahad yake...?" Kallon kallo suka fara yi domin kamannin yaran daya ba mai iya bambancewa a cikinsun. Fahad da ya fahimci haka sai ya juya ya kira turab da zafaran sukazo. "Nunamin ina little Fahad a cikin su" Dariya turab yayi kafin yayiwa su meenal alama da hannu su zo. yatsun yaran ya fara dubawa ɗaya bayan ɗaya har ya gama dubasu tsaff. "Khulud je ki miqawa Fahad na hannunki shine Aslam little Fahad......... "Meenal ki miqawa zafaran shine Akhram little zafaran" "Kenan na hannuna ne Afeef Little Turab....?" Zohal ta tambaya da mamaki. "Eh, na hannunki Afeef ne" Sosai mamakin abun ya kamasu, Khulud kam da ta kasa shanye mamakinta sai da tayi magana tace "ya-Turab ya akayi ka gane yaran nan da wuri haka, har fa gardama muke nace na hannuna ne Afeef domin shi yafi kama da kai" "Ah ah na hannunki shine Aslam gskiya, wannan dake hannun zohal shine Afeef" "To Amma........ya akayi ka gane haka bayan babu wani banbanci tsakanin su....?" "Tun ranar da aka haifesu danaga kamarsu tayi yawa sosai na saka aka qeramusu zobunan azurfa, ko wanne zobe yana dauke da harafi daya na farkon kalmar sunansu, ba ma su kadai aka yiwaba har Ifrah da CHIDINMA da kuma duben duk anyimusu ban natsu bane da naje dakaina na kaimusu nasu suma" Zafaran na dariya yace "amma ba sunan nan ka saka ba kho...?" "No Ammi da Abbi na saka sai dai sunan nasu yanamin dad'i a baki shiyasa na zaɓi na dinga kiransu haka" Godiya fahad da zafaran sukayi masa sosai suna qara jin qaunar junansu. Kar'ba yaran su meenal sukayi suka koma cikin gida bayan anyi pictures. Lafiya qalau akayi waleemar yaran nasu baki daya, ifrah, CHIDINMA, duben sannan da 'yan uku Aslam da akhram da kuma Afeef. A banner da memo da calendar wacce turab ya raba duk haka aka sakawa yaran suna da kuma pictures dinsu matsu matuqar sha'awa da daukar hankali. Bayan shekara daya, komai na gidan ya dawo normal hankalin kowa ya kwanta domin kuwa har an aurarda yara da yawa a familyn kamar dai Khulud da meenal da kuma twins. fannah a gombe tayi aure. mayah a cikin garin kaduna, meenal ma a kaduna tayi aure. Idrak kam ya sami buɗi sosai arzikinsa ya ha'b'baka domin idan za'a zano sunan shahararrun matasa masu kuɗi a cikin garin suleja sunansa zaizo na uku koma ya fito na biyu. Sosai mum fanaya ta dinga rokon papu akan ya auri Dayammah ko ba komai sun zauna tare da ita sun santa da kyawawan halaye, kuma idan yayi hakan ya taimaka. Da kyar ta samu ta shawo kansa ya amince aka dauramasa aure da Dayammah. Hakan ma ya qara saka Papu yin kwakkwaran bincike akan fairozha, amma aka shaidamasa ai ta dade da mutuwa, kwatsam rana ɗaya akaga gidanta da suke tsafe-tsafensu ya kama da wuta ba'a fitarda komai dake numfashi ba a gidan, aka gayamasa yanzu shekara daya da wata biyu da kwana biyar kenan. domin wannan al'amari ba qaramin yawo yayi a jarida ba shiyasa aka kasa manta kwanan wata. Sosai Dayammah tayi mamaki domin idan ta auna da kyau kenan ranar da ta bayyana labarin su wurin mum da sauran mutane ne haka ta faru, aikuwa da tasan wannan shine had'arin da fairozha take magana akai da tuni ta dade ta fallasa asirin kungiyar. Leeyana, da Aleena, da kuma Idrak Papu ya tara gaba ɗaya tare ta alqalai domin ayi kasafin dukiyarsu da aka bashi amana amana tsawon shekara da shekaru. Bayan anyi bincike an kuma warware komai sai Papu ya miqawa kowa takardasa domin yayi signing. Sai da suka kammala leeyana ta tsayarda shaidun ta miqawa mum fanaya takardar tana hawaye tace "wallahi mum banada wata uwa a duniyarnan data wuce ki saboda haka na mallaka miki dukiyarnan halak malak idan dai inada haqqi da ita, kuma ina roqon kowa dake wurin nan yayi shaidata ko lahira" Kamar yanda tayi haka itama Aleena tayi saidai ita dad qarami ta baiwa domin ita shine matsayin mahaifin ta saboda yayi mata abunda ko mahaifinta ne iyakarsa haka. Haka shima Idrak ya mallakawa mahaifiyarsa dukiyar baki daya. Sosai hakan ya qara qauna da zumunci mai qarfi a tsakanin su. Su 'yan uku da twins da kuma ifrah tuni sukayi wayo wasunsu harsun fara tattakawa suna koyon tafiya, yaran sun shaqu da juna sosai, domin kuwa bayan iyayensu mata sun gama biqi sabon gida mai dauke da part uku da kuma d'akuna barkatai suka saye suka koma gaba ɗayansu. Wani lokacin yaran kaɗai ake barinsu su kwana a daki daya sai qalilan na ma'aikatan gidan da ake sakawa suje su kula dasu. amma gado daya ake shimfid'e su suduka shidan, wannan yasa sabo da shaquwa mai qarfi ta shiga tsakanin yaran da iyayensu daga abota suka zamo 'yan uwa na jini da hanta da babu rabuwa. ALHMDULLILLAH! ALHMDULLILLAH!! ALHMDULLILLAH!!!!! _GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAMALLAKIN MULKI DA DAUKAKA MAI KOWA MAI KOMAI MAI BAYARWA DA HANAWA MAI IKO AKAN KOMAI, TSIRA DA AMINCI SU 'KARA TABBATA A WURIN SHUGABA, JAGABA KUMA ƊAN GATA MANZON RAHMA ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM TARE DA AHALIN GIDANSA MASU ALBARKA. DA SAHABBAI DA ALAYENSA MASU TSANTSAR DARAJA. _ALHAMDULILLAH ALLAH INA KARA GODIYA A GAREKA DAKA BANI DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFIN DA RAINA DA KUMA LAFIYATA, KUSKURE NA A CIKI ALLAH INA MAI TUBA, ABUNDA NA FAD'A DAI-DAI ALLAH KA BADA IKO AYI AMFANI DASHI. _INA GODIYA GA DUK MASOYANA DA SUKAYI KOKARI DA HAKURI WAJEN BIBIYATA TUN DAGA FARKON LITTAFINA HAR IZUWA KARSHE ALLAH YA BAR ZUMUNCI DA KAUNA MASOYANA. BISSALAM, SAI KUMA IDAN ALLAH YA QARA HADAMU A WANI LITTAFIN NA GODE. *RUMANAH M. DIGGI.......✍🏼*