[23/11, 21:00] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA ƊAYA DAULAR JABAL Shekara Ɗari Biyu Baya (1825) Daular Jabal ta kasance ƙasaitacciyar daula, da ke ɗauke da dubban al'umma. Sunan Jabal ya samo asali daga yawan tsaunikan da yankin yake da su, mafi yawa suna zagaye da daular bakidaya. Daular Jabal tana kewaye da tekun Farjum, wanda yake da tsofaffin tarihi mabambamta masu cike da ban tsoro zuwa almara. Yankin yana ɗauke da tarin ƙabilu, waɗanda suke da bambamcin harshe a ƙalla sama da ɗari. Kuma yanki ne da yake da tarin arziƙin noma, kiwo da kasuwanci. Tsaunin Jaddum shi ne katafaren tsaunin da ya fi kowanne tsauni girma a Daular Jabal, kuma tsauni ne mai matuƙar tsoratarwa da munanan al'amura suke faruwa a kansa. A labarin kunne ya girmi kaka, an ce a shekarun da suka gabata. Tsaunin matattarar wata ƙabila ce ta Gussum, wasu kuma suka ce sunan ƙabilar Hadira. Waɗannan ƙabilu da ake tantama a kansu, an ce sukan yanka duk jaririya macen da aka haifa ranar Alhamis, su shayar da jininta ga abin bautarsu da ke jingine a jikin tsaunin. Da matar shugabansu ta haihu a ranar Alhamis, sai suka nemi da a yanka jaririyar. Shi kuma Shugaban ya yi tsalle ya dire a kan hakan ba za ta kasance a kan jininsa ba, kuma da yake ya fi su ƙarfin dukiya da iko sai suka haƙura. Tun daga ranar, duk wanda ya hau kan tsaunin sai dai a ga ƙoƙon kansa ya gangaro ƙasa ya faɗi, kuma ba za a sake ganin gangar jikinsa ba. Wasu kuma suka ce, bayan da aka yi wa shugabansu haihuwar mace ranar Alhamis. Da labarin ya bayyana, bai yi sallama da kowa ba ya tattara iyalinsa da jaririyar da aka haifa suka bar garin. Tun daga wannan ranar suke fuskantar mummunan hukunci ga duk wanda ya hau kan tsaunin da sunan bauta, domin abin bauta ya yi mummunan fushi da su. Sai dai duk yawan tarin addininan da ke cikin daular, manyan addinai uku ne suke da tasiri a cikinta. Addinin Musulumci, addinin Kiristanci da kuma addinin gargajiya. Addinin Musulumci Addinin Musulumci addini ne da Musulmai suke bauta wa Allah Shi kaɗai, ba tare da waninSa ba. Wanda musulmai suke bin doron koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W), wacca take ƙunshe cikin littafi mai tsarki (Alƙur'ani) da Allah (S.W.T) Ya yi wa Annabi Muhammad (S.A.W) wahayi, ta hanyar Mala'ika Jibrilu. Tare da bin Hadisansa, waɗanda suke tafe da sunnar yin aiki kyakkyawa da guje wa saɓon Allah. Addinin Kiristanci Addinin Kiristanci, addini ne na kiristoci da suke bautar Yesu Almasihu. Wanda mabiyansa suka ce yana koyar da ƙauna, gafara da aminci. Kuma sun yi imani da an gicciye Yesu, har ya tashi daga cikin matattu bayan kwana uku sannan ya hau sama. Kiristoci suna amfani da littafin Bible, daga rubutu daban-daban a cikin harsuna kamar Ibrananci, Aramaic da Girkanci. Addinin Gargajiya Addinin gargajiya, addini ne da mabiyansa suke amfani da koyarwar abubuwan bauta tun daga kan iyaye da kakkanni. Sun yi imani da tsafi, bokanci, sihiri da camfe-camfe, musamman a wasu ƙayyadaddun abubuwa kamar wurare, ranaku da sauransu. Addinin gargajiya, yana da bambamci da addinin Musulumci da na kiristanci. Saboda mabiyansa suna da abubuwan bauta kala-kala, wasu sukan bautawa ruwa, wuta, dutse, gumaka, rana, bishiya, kabari da sauransu. Kuma sun yi imani da taimakon aljanu, tare da ruhin kanninsu da suka gabata. Haka zalika ba su da littafin da suka amfani da shi a wurin bauta. Sai dai kuma a Daular Jabal an samu dubban mabiya addinan gargajiya, sun yi haɗuwar tsintsiya wurin samar da littafi guda. Wanda aka sassaƙa bangon jikinsa da fatar wata tsohuwar damisa, wanda suka ajiye sirrikan kiran aljanu da kirarinsu. A silar haka ne aka samar da kundi ukun da mabiya addininan yankin suke amfani da shi. Sai dai kuma wani al'amari da ya faru a waɗansu shekaru ya sa bayyanar Kundin ke barazana, cimma buri da jefa kokonto a zuciyoyin Sarakuna ukun da ke rayuwa a cikin Daular. Masarautar Kajjura (Sarki Gambo) Masarautar Judala (Sarki Giɗaɗo) Masarautar Zulwara (Sarki Dikko) Sune masarautu da sarakunan da ke kewaye da Daular Jabal, kowannensu yana shimfiɗa mulki cike da isa, ƙasaita da izzar mulki. Domin gabaɗaya duka sarakunan babu wanda yake ga maciji da ɗan'uwansa, ba don komai ba. Sai don wasu munanan al'amura da suka gifta a tsakaninsu a lokautan da suka shuɗe. MASARAUTAR KAJJURA Zaune yake a kan lallausar kujerar da ta ƙayatu da kayan alatun gidan sarauta, fadawan da ke zagaye da shi gabaɗaya kawunansu a sunkuye yake suna jiran umarninsa. Daga gefe Shamaki ne ya sake russunar da kai, har zai fara magana. Daga jikin bangon gabas, suka ga fatar zakin da ta sha ado mai ɗauke da rubutun tsafin masarauta ta dare gida biyu. Kakkaifan takobi, kuma tsafaffan da ke saƙale a jikin fatar ta fitar da kanta daga cikin gidanta. Kamar walƙiya haka ya yi tsalle ta dira a daidai maƙoshin Sarki Gambo, duk yadda ya so matsawa sai ji ya yi ya manne da jikin kujerar da yake zaune. Da ido ya dubi fadawansa domin su kawo masa ɗauki, amma ga mamakinsa sai ya ga sun bushe da dariyar ƙeta. Yana cikin wannan yanayin ya ga farin dattijon ya ratso daga bangon da ya dare. Ya ƙaraso gabansa yana sakin murmushi, kafin Sarki Gambo ya yi wani yunƙuri tsohon ya saka wannan takobin ya datse kansa ƙasa. Firgigit! Sarki Gambo ya tashi zaune a razane daga mummunan mafarkin da ya yi yana shafa wuyansa, gumi ya shiga keto masa cikin tashin hankali. "Allah Ya taimake ka, Allah Ya ba ka yawan rai..." "Fulani akwai abin da yake shirin faruwa." Sarki Gambo ya katse matarsa cikin damuwa, ajiyar zuciya Fulani Sadiya ta sauke ta ce. "Ina fatan wannan ya kasance tuntuɓen fahimtarka ne ranka shi daɗe." Bai amsa mata ba, ya miƙe jiki babu ƙwari. Don haka ita ma ta miƙe fuska ɗauke da damuwa ta ce. "Ranka shi daɗe ina za ka je a tsohon daren nan?" "Zan je na ga Malami!" Ya furta mata yana naɗe fuskarsa da baƙin ƙyalle, cikin shigar ɓatar da sahu. Ganin har ya je bakin ƙofa ya sa ta bi shi da sauri ta ce. "Amma ranka shi daɗe me zai hana ka bari zuwa safiy..." "Idan har muka kai wannan lokacin, mummunan abu zai iya faruwa da mu. Kin san Bahaushe ya ce, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe." Ya furta yana fita, ba tare da ya waiwayo ta ba. Ta ɓoyayyar ƙofar da ke cikin ɗakin ajiyar kayan sirrinsa ya shiga, yana tafe cikin duhu yana haskawa da itacen da yake ci da wuta har ya ƙarasa. A bakin bukkarsa ya tsaya, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kutsa kansa cikin bukkar. Kamar bai ji motsinsa ba, haka Malami ya cigaba da shafa yashin da ke kan faifan gabansa. A gefensa Sarki Gambo ya zauna, bayan da Malami ya ƙarasa sannan ya dube shi ya ce. "Tun da na ganka da kanka ba aike ba, na san banza ba ta kai zomo kasuwa." Sarki Gambo ya warware rawanin fuskarsa sannan ya ce. "To ai zuwa da kai ya fi saƙo ne Malami, kuma tun da kuka gan mu yanzu ai kun san akwai gagarumar matsala." "Ita na kwana ina duba maka, domin niyyata zuwa safiya na zo har ɗaki na same ka da maganar." Malami ya furta yana tsare Sarki Gambo da ido, cikin ƙaguwa ya ce. "Amma me yake faruwa malami? Haka kuma muna fatan wankin hula ba zai kai mu dare ba." "Najibullah Bn Muhammad Bn Najibullah Dogaran bulukiya!" Jin sunan da Malami ya ambata ya sa Sarki Gambo miƙewa zumbur! Nan take jikinsa ya shiga karkarwa kamar wanda ya ji kiɗan gangi. "A wayewar garin gobe jinin Najibullah wato Najibullah zai shigo masarautar nan, kuma idan har ba ka dakatar da shi ba shukar da ka jima da binnewa za ta bayyana. Domin zuri'arsa za ta bankaɗa maka labulen sirrin da babu wanda ya san da shi daga ni sai kai sai amintacciyarka." Malami ya ƙarasa maganar yana kallon Sarki Gambo, kamar zai yi kuka sarki ya dafa gwiwoyin Malami ya ce. "Don girman Allah, da matsayin abin bautar da na fi aminta da ita ka taimaka mini Malami." Murmushi ya yi masa ya ce. "Zan taimaka maka Gambo, kamar yadda na rife sirrin addinin da kake bautawa, saɓanin na Musulumci da kake yaudarar talakawanka da shi." A fili Sarki Gambo ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido, Malami ya cigaba da cewa. "Lokacin tashin alƙiyamarka ya zo Gambo, matuƙar ba ka hallaka jinin Najibullah ba. Kuma lokacin mallakar Kundi ukunka ya bayyana, domin kuwa Za a kawo Najibullah tare da aminin kakansa tsoho Sulaimanu. Wanda a shekarun baya na ce maka duk duniya daga marigayi Najibullah, sai tsoho Sulaimanu ne suka san maɓoyar ragowar kundi biyun cikin masarautun nan. Ɗaya dai na san yana cikin masarautar nan, amma a ina? Ban sani ba, kuma duk shaiɗanun aljanun da ke yi mini aiki ba za su iya bayyana inda suke ba..." "Yaya kamannin Najibullah yake? Haka shi ma tsoho Sulaimanu?" Murmushi Malami ya yi ya ce, "Amma me kake ci na baka yana zuba Gambo? Ai duk gaggawarar amarya ta bari a kai ta ɗaki." "Sanin a bari ya huce shi ke kawo da rabon wani, ya sa nake son ka yi gaggawar warware mini zare da abawa. Domin ko babu komai za mu aika Dogarai su bincika mana inda suke." Da yake murmushi ya zama ɗabi'arsa, a wannan karon ma murmushi Malami ya yi ya ce. "Ka gode wa Dogaran da suke farmaki yankin Baɗiya, domin a wani ƙasurgumin dajin da tsoho Sulaimanu ya ɓoye su a can suka farmake su. Idan da hali ma ka ƙara musu matsayi, ungo wannan turaren." Malami ya miƙa masa wani garin baƙin magani, sannan ya cigaba da cewa. "Ka yi shelar dakatar da bayin da za a shigo da su, sannan ka saka garwashi ka turara ɗakin da za ka killace su. Wannan aikinka ne ba na bayi ba, abu biyu zuwa uku ne zai faru a wannan lokacin." Sarki Gambo ya damƙe maganin kamar wani zai ƙwace masa, ya shiga gyaɗa kai kamar na ƙosasshan ƙadangare. "Na farko idan har jinin Najibullah yana wurin take zai fara haɓo ya bayyana kansa, daidai wurin da suke tsaye ƙasar wurin za ta yi ja kamar wuta. Har da za ka saka hannu za ta iya babbake ka, sai dai kuma na bincika Najibullah ne kaɗai ragowar jinin zuri'arsa a doron ƙasa, amma kuma zuciyata tana yi mini wasu-wasi. Yana tafe da iyalinsa mai ɗauke da tsohon ciki, ka tabbatar da ka kashe shi. Ka killace matarsa har zuwa lokacin da za ta haihu, shi ma ɗa ko 'yar da za a haifa ka kashe su..." "Dole sai mun jira ta haihu? Me zai hana mu hallaka su lokaci ɗaya?" Sarki Gambo ya furta a harzuƙe, Malami ya girgiza kai ya ce. "Matarsa za ta yi mana amfani, ko ba ka san jininsa da ya gauraya da nata zai zame maka takin da kowanne manomi yake burin samu ba? Idan har ka kashe ɗan da ta haifa ka kawo mini ita nan, ragowar bayanin zan yi maka daga baya." Godiya Sarki Gambo ya yi masa, Malami ya cigaba da karanta masa bayanin duk abin da ya dace ya yi. Sai gabannin asuba, sannan ya yi masa sallama ya koma turakarsa. A yadda ya bar Fulani Sadiya a haka ya koma tana zaune jigum, har ya koma ya same ta ba ta koma bacci ba. Dafe kai ta ga ya yi, cike da kulawa ta dafa jikinsa ta ce. "Tun bayan fitarka zuciyata ke ɗamfare da tarin damuwa da tashin hankali." Sai da ya janyo ta jikinsa, sannan ya sumbaci goshinta ya ce. "Tarin alkairai ne suke ƙwanƙwaso mana ƙofa Fulani, dangane da tsofaffin kundun da na taɓa baki labari. Sai komai ya tabbata zan sanar da ke yadda aka haihu a ragaya." Dam! Ƙirjinta ya buga, amma sai ta kawar da damuwar fuskarta. 'Na yi alƙawarin bankaɗa maka labulen kowanne irin sirrin Sarki Gambo, kada wani abu ya dame ka. Na tabbata yana yi mini kallon kitse, ina yi masa na rogo ne.' Fulani Sadiya ta tuna kalaman da ta furta wa Sarki Giɗaɗo, a lokacin da suka yi wata ɓoyayyar tattaunawar sirri. Amma a fili sai ta saki murmushi ta ce. "Ina tare da kai Sadaukina, haƙiƙa kai ɗin mai sa'a ne." Sarki Gambo ya saki murmushi, jin ana ƙoƙarin shiga sallar Asuba ya sa shi fita ya ɗaura alwala ya nufi masallaci. Asubar fari Sarki Gambo ya sanar wa da Shamaki, da a kulle duk ƙofofi huɗun da ke cikin masarautar. Sannan ya ce a tsaurara tsaro a ƙofar Yamma, domin ta nan ne ya bada umarnin idan Dogaran da suka tafi farautar bayi sun dawo za su shiga. Har sai da rana ta fara fitowa sannan labari iso wa Mai martaba, kan dawowar babban dogari Sale. Don haka zuciyarsa fal farinciki, ya shirya cikin baƙar alkyabba mai rashin jajayen duwatsu. Daga saman kansa akwai wata hular azurfa, ya ɗaga kansa yana kallon zabgegiyar takobin da ya yi mafarkin an datse kansa da ita. "Da ita zan datse kanka Najibullah." Ya furta cikin izza, isa da ƙasaita. Sannan ya ɗauko ta ya saƙala a wuyansa, kai tsaye fadawa suka ba shi hanya. Nan take aka fara busa sarewa da algaita, fadawa suka shiga zabga masa kirari. Yayin da maroƙa suka fara bambaɗanci suna wasa shi tamkar babu gobe. Duk da bai furta musu koda kalma ɗaya ba, amma irin murmushin da yake yi ya sa suka fahimci yana cikin tsananin farinciki. Sai dai kuma a ɓangare ɗaya, suna mamakin wannan umarni da Sarki ya bayar. Domin ba ya daga cikin hali ko ɗabi'arsa, duba bayi a duk lokacin da aka kawo su masarauta. Tun da aka killace su ƙirjin Najibullah yake dukan uku-uku, gumi ya shiga karyo masa. Ganin yanayin da yake ciki ya sa tsoho Sulaimanu ya girgiza masa kai, duk da hannu da ƙafafuwansu a ɗaure suke hakan bai hana ya yi masa inkiya da ya lulluɓa wa kansa mayafin jarumta ba. "Tsoho Sulaimanu, haƙiƙa zuciyata ta gama tsinkewa. Tun da nake numfashi a doron ƙasa, ban taɓa jin yanayin da yake kassara ƙwarin gwiwar gangar jikina ba sai yau." Tsoho Sulaimanu ya yi ƙasa da murya ya ce. "Ƙwarin gwiwarka ita za ta assasa tawa ƙwarin gwiwa Najibullah. In Shaa Allahu sai mun cimma nasara, domin Ubangiji ba ya zalinci." "Kai kaɗai ka rage daga cikin zuri'armu Najibullah, kuma a kanka nake saka ran za ka dawo da ƙima da martabar gidanmu. Haƙiƙa a baya an riga da an ci mu da yaƙi, amma ina son na nuna wa zuri'ar jininmu ba za ta ƙare a banza ba. Don haka nake umartarka da ka yi aure a cikin kwanaki ƙalilan, domin ta haka ne za mu cigaba da yaɗuwa a doron ƙasa." Najibullah ya tuna kalaman mahaifinsa na baya, a lokacin da yake yi masa wasiyyar bankwana. Hawaye masu ɗumi suka zubo masa, sakamakon ido biyu da ya yi da matarsa Zainaba mai ɗauke da tsohon ciki. Yana shirin yin magana, ƙaurin turaren da ke hannun Sarki Gambo ya daki hancinsa. Lokaci ɗaya ya ji kansa ya sara, daga gefen hagunsa ya ji an ce. "Ka gafarce ni Najibullah, a wannan karon na gagara ba ka kariyar da ta dace." Juyawa dattijuwar matar ya ga ta yi, sai ta ratsa ta jikin bango ta fita tana zubar da hawaye. Lokaci ɗaya ya ji abu mai ɗumi yana fita daga hancinsa, yana sauke idonsa ya ga jini yana zuba. Ɗago idon da zai yi suka haɗa ido da sarki Gambo, da yake jifansa da murmushin ƙeta mai cike da zallar rashin imani. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [23/11, 21:33] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA BIYU https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t 🛍️Assalamu Alaikum – Hafsat Collection ce! Kinason kayan masu inganci masu kyau kuma cikin sauƙin farashi? To ba ki da matsala! 🥳💃 📌 HAFSAT COLLECTION ta kawo muku: ✨ Kayan gyaran gida ✨ Kayan ado da kyalliya ✨ Kayan mata da maza masu kwalisa ✨ Kayan kitchen masu kyau da karko 🔥 Duk a cikin farashi mai sauƙi! 📦 Muna a Kano, amma muna aikawa zuwa ko ina cikin amincin Ubangiji! 🙏 Maza ki shiga group ɗinmu yanzu: 👉 📌 Kasance da Hafsat Collection – Sayan daidai, ko sari! https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t Kamar yadda ƙirjin Najibullah yake dakan lugude, haka tsoho Sulaimanu ya shiga matsanancin tashin hankali. Najibullah ya runtse idonsa cikin sarewa, da wata irin raunanniyar murya ya fara yi wa tsoho Sulaimanu magana mai kamar wasiyya. "Haƙiƙa ajalina ya gabato tsoho Sulaimanu, don haka zan damƙa ragamar duka wannan yaƙin a hannunka, duk da a yanzu shekaru sun cimma maka. Don Allah ka kula da Zainaba idan har ka samu damar haka, ina mai bar maka wasiyya a kan muradin mahaifina." Zafafan hawaye suka shiga sintiri a saman dakalin fuskar tsoho Sulaimanu, cikin murya tsufa da kuka ya sunne kai ƙasa a hankali. Ta yadda ba za a ankara da abin da yake faɗa ba ya ce. "Allah Shi ne masanin daidai Najibullah, amma duk alƙawuran da ka damƙa mini zan rungume su hannu bibbiyu, domin ko babu komai idan Allah Ya ja kwanana zan tabbatar da gaskiya tana iya danne ƙarya." Duk tattaunawar da suke yi Sarki Gambo yana kula da su, ya saki murmushin gefen baki. Sannan ya fara takawa cikin isa da ƙasaita, kafin ya ƙarasa gaban Najibullah ƙasar da yake tsaye iya daidai saitin ƙafafuwansa ta yi jajir, kamar ƙarfen maƙerar da ya shekara a wuta. Daga dogarawa, fadawa zuwa bayin da ke ɗaure maza da mata. Gabaɗaya kallo ne ya koma wurin Sarki Gambo da ke tsaye a gaban Najibullah. Babban ɗakin tsit ya yi kamar babu masu numfashi, a karo na biyu Sarki Gambo ya saki murmushin gefen baki. Cikin wulaƙantacciyar murya ya ce. "Najibullah!" A razane tsoho Sulaimanu da Najibullah suka ɗago, zuciyarsu ta shiga tsalle kamar za ta yi tsuntsuwa ta hudo ƙirjinsu Sannan ya nuna dogari Ɗanjuma, ya ba shi umarnin fitowa da Najibullah, ganin haka ya sa wani abu ya tsarga wa Zainaba. Dogari Ɗanjuma irin ƙarfafan mutanen nan masu siffar samudawa ne, kusan indai Sarki Gambo zai zartar da mummunan hukunci shi yake kira. Da ido ya yi masa nuni, tun bai yi magana ba. Ɗanjuma ya shiga kiciniyar kunce Najibullah, nan take ƙananan maganganu suka fara tashi. Sarkin Zagi ne ya dubi mutanen ya buga musa tsawa, nan take kowa ya ja bakinsa ya tsuke. Jikin Najibullah ban da karkarwa babu abin da yake yi, Ɗanjuma yana fito da shi ya dankwafar da shi a gaban Mai martaba. Shi ma ya zube ƙasa cikin girmamawa ya ce. "Ina neman izini wurin adalin Sarki, da ya ba ni dama na datse kan wannan ƙasƙantaccan bawan." Murmushi Sarki Gambo ya yi, ya saka hannu ya ɗago haɓar Najibullah sai ya dubi Ɗanjuma ya ce. "Wannan hukuncin namu ne, mu za mu zartar da shi." A wannan karon ma hatsaniya ce ta ɗan fara tashi, domin kusan a saninsu da Takawa. Wannna ce rana ta farko da zai taɓa zartar da mummunan hukunci da hannunsa a gaban jama'a, dogari Ɗanjuma ya sake russunawa ya ce. "An gama ranka shi daɗe, idan an ba ni izini zan iya komawa mazaunina na tsaya." Da ido Sarki Gambo ya yi masa magana, nan take Ɗanjuma ya ɗaure hannun Najibullah ta baya. Sannan ya koma inda yake ya tsaya, wurin ya yi tsit kowa da abin da yake saƙawa a zuciyarsa. A hankali Sarki Gambo ya fara zaro sihirtacciyar takobin hannunsa, nan take tsoro ya ƙara mamaye bayin da suke ɗaure. Don a tunaninsu ɗaya bayan ɗaya haka za a hukunta su, Zainaba tana ganin haka ta durƙushe a wurin. Ba tare da ta damu da tsohon cikin jikinta ba, cikin magiya, roƙo da ƙasƙantarwa ta furta. "Allah Ya taimake ka, Ubangiji Ya ba ka yawan rai. Kai sarki mai adalci ne, ka yi wa mijina afuwa idan har akwai kuskuren da ya aika..." "A shekarun da suka gabata, an ce mahaifiyata ta yi irin wannan roƙon da bai amfane ta da komai ba. Zainaba! A matsayina na mijinki, kuma shugabanki. Ina umartarki da kada na sake jin bakinki a wurin nan." Najibullah ya furta cike da ɗacin zuciya, jin haka ya sa Zainaba ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Ajiyar zuciya Sarki Gambo ya sauke, yana jin ɗaci a zuciyarsa. Ya ɗan russunar da kansa kaɗan, ta yadda ba kowa zai ji tattaunawarsu ba ya ce. "Haƙiƙa tarihi yana ƙoƙarin maimaita kansa kenan Najibullah, sai dai ka sani. Idan har kai ka rayu, abin cikin iyalinka zai zama matacce, iyalinka kuma..." Sai Sarki Gambo ya saki murmushi, sannan ya ɗago. Sai da ya dubi ilahirin mutanen da ke wurin, sannan ya ɗaga takobin hannunsa yana sakin dariyar ƙeta ya datse kan Najibullah da shi. A razane Zainaba ta ƙwallah wata irin gigitacciyar ƙara, lokaci ɗaya ta faɗi a wurin babu numfashi. Tsoho Sulaimanu ya sunkuyar da kai ƙasa yana zubar da hawaye, jin abu ya gangaro jikin ƙafarsa ya sa shi buɗe idonsa. A nan ya ci karo da kan Najibullah, a razane ya janye ƙafarsa. Sarki Gambo ya sake kallon Ɗanjuma, ganin haka ya sa Ɗanjuma ya ƙarasa ya kunce tsoho Sulaimanu. "A umarce shi da ya kawo mana kan wannan ƙasƙantaccan ɗakin gabas, ita kuma matarsa muna buƙatar a bata kulawa har zuwa lokacin da za ta haife cikinta. A tabbatar da an kawo mana jariri ko jaririyar da za ta haifa, ita kuma a killace mana ita." Sarki Gambo ya furta, sai ya fara takawa cikin izza fadawa suka rufa masa baya haɗe da yi masa kirari. Lokacin da Sarki Gambo ya ƙarasa ɗakin gabas, a zaune ya samu Malami yana duba wata fatar ɓauna wacce take cike da ƙananan rubuce-rubuce. Zama ya yi a kujerar da take kallon ta Malami, Sarki Gambo fuskarsa ɗauke da annushuwa ya ce. "Komai ya tafi daidai yadda muke muradi." "Amma kuma tsugunne ba ta ƙare maka ba." Malami ya furta yana cigaba da karatun ba tare da ya ɗago ba, da mamaki Sarki Gambo ya ce. "Ai na ɗauka na yarda ƙwallon mango zan huta da ƙuda? Malami ina son ka fitar da ni daga duhu." Malami ya ninke fatar hannunsa, sannan ya ce. "Kana neman ka yi kitso da kwarkwarta Sarki Gambo." Cike da damuwa Takawa ya ce. "Ban fahimce ka ba Malami, na fi so ka warware mini zare da abawa." Miƙa masa fatar hannunsa ya yi ya ce, "Akwai wanda ya san duka tanadin da kake yi a cikin masarautar nan, domin kuwa a yau da safe na tsinci wasiƙar sirri zuwa ga abokan adawarka." Hannun Sarki Gambo yana rawa ya karɓi fatar ya duba, sai ya ci karo da cewar. _Kada shirun da ka ji ya sa ka dakata da shirinka, akwai sauran rina a kaba. Domin kuwa ƙoƙofi ukun da kake muradin buɗewa ana shirin haramta maka su. Ba sai ka damu da sanin fatar dabbar da aka yi rubutun ba, kawai ka yi abin da ya dace._ Da mamaki Sarki Gambo ya ce, "Malami ban fahimci komai ba, shin mene ne amfanin wannan rubutun?" Karɓar fatar Malami ya yi ya ajiye ta a gefe, sannan ya dubi Takawa ya ce. "A ziyarar da ka kawo mini jiya, akwai wanda ya ji tattaunawarmu. Wannan wasiƙar za a tura ta zuwa ga ɗaya daga cikin sarakuna biyun da baƙin layi ya shata a tsakaninku. Ana sanar da su ka kusa mallakar kundi ukun da na maka bayani, shi ya sa aka siffanta su da ƙofa. Da aka ce kada a damu da sanin fatar dabbar da aka yi rubutu, ana nufin marubucin ba sai ya bayyana kansa ba." Malami ya miƙe ya fara takawa, yana cikin haka suka ji an nemi izinin shiga ɗakin. Da kansa ya ƙarasa ya buɗe ƙofar, sai ga tsoho Sulaimanu hannunsa ɗauke da kan Najibullah. Kallon-kallo suka tsaya yi wa juna, tsoho Sulaimanu ya kafe shi da ido yana nazartar fuskar Malami da tsantsar cin amanar da ya yi masa. A gaban Sarki Gambo aka dankwafar da shi, har zai fara magana Malami ya ce. "Gambo sai ka sake miƙewa tsaye, domin na fahimci idon masarauta har yanzu yana kanka." Jinjina kai Sarki Gambo ya yi sannan ya dubi tsoho Sulaimanu ya ce. "Duk wata tambaya da zan yi maka ka riga da ka san amsarta. Najibullah ya san maɓoyar kundi ɗaya, kai kuma kana da sani a kan ragowar. Idan ka sanar da ni, za ka tsira da rayuwarka. Idan kuma ka ƙi, za ka ƙare rayuwarka a kurkuku." Murmushin takaici tsoho Sulaimanu ya yi ya ce, "Idan na sanar da kai ba tsira zan yi ba, don haka ni ba maci amana ba ne. Ba zan taɓa bayyana sirrin nan ba, kuma ina mai tabbatar maka. Lokaci zai zo da za a ɗauki kanka a hannu kamar yadda ka aiwatar wa Najibullah." A fusace Sarki Gambo ya miƙe ya yi kan tsoho Sulaimanu, cikin zafin nama Malami ya shiga tsakiya. Sannan ya kai bakinsa saitin kunnensa ya yi masa raɗa, jinjina kai Takawa ya yi. Sannan ya koma mazauninsa, Malami ne ya leƙa ya kira sarkin ƙofa. Bayan ya shiga ya zube a gaban Sarki Gambo ya ce. "Allah Ya taimake ka ranka shi daɗe." "A ɗauki wannan tsohon a kai shi kurkukun ƙarƙashin ƙasa, ɗakin da Kursum take rayuwa." Sarki Gambo ya furta cikin taƙama. "An gama ranka shi daɗe, Aljanna mai masoya da yawa. Sikari ba ka yi farin banza ba, ina gwanin wani ga nawa. Kabari mai ƙulla sabuwar abota, mutuwa mai sa a tuna barzahu. Gaba salamun bayanka salamun ubangidana maganin kukana, ka yi shekaran jiya, ka yi jiya kuma gobe ma da kai za a yi In Shaa Allahu." Sarkin ƙofa yana gama yi masa kirarin ya tasa ƙeyar tsoho Sulaimanu, suna fita Malami ya saki murmushi sannan ya ce. "Ka gama da wannan babin, idan har gumi ta yi gumi. Da ka tuntuɓe shi zai bada kai bori ya hau." "Ai dole gyaɗa ta yi mai idan ta ƙi ta sha matsa." Sarki Gambo ya furta yana sakin murmushi, shi da Malami sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama. ZAINABA Sarki Gambo yana fita, Dogari Nalami ya sallami ragowar mutanan. Ya bayar da umarni aka yayyafa wa Zainaba ruwa a fuska, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara bin tsirarun mutanen da ke tsaye a kanta. Uwar bayi ce ta shiga ɗakin ta riƙo ta suka nufi can sashensu na bayi, Zainaba tafiya kawai take yi kamar wacce aka zarewa laka a jiki. A wani ɗaki aka ajiye ta mai ɗauke da mutane biyar, wata mai ciki ɗaya ta gani sai ragowa mata da yara. A gefe ta zauna, tana tuna al'amarin da ya faru da mijinta a kan idonta. Sannu a hankali ta fara jin mara da bayanta suna yi mata ciwo, ta shiga yarfe hannu tana cije baki saboda a zaba. "Ki tabbatar kin saka wa matar nan ido, Mai martaba ya ce tana haihuwa a kai masa abin da ta haifa ita kuma a killace ta. Kin san fa a yadda na ji an ce mijinta yana da tsohuwar tsattsamar alaƙa da Takawa, wai shi ya sa ya kashe shi. Kuma an ce kashe jaririn ma zai yi." Ta ji muryar matan da suke tattaunawa daga wajen ɗakin, tagar ɗakin ta kalla ta ganta 'yar mitsitsiya. Ta ga ƙofar ɗakin a rufe ballantana ta nemi mafakar guduwa, tana cikin haka naƙuda ta ciyo ta gadan-gadan. Tun tana daurewa har ta fara kiran sunan Allah ƙasa-ƙasa, ɗaya daga cikin matan da ke ɗakin ce ta leƙa ta tagar ta ce. "Wannan matar fa naƙuda take yi." Dam! Ƙirjinta ya buga, tana nan zaune ta ga uwar bayi ta shiga ɗakin sannan ta sa aka fitar da ƙananan yaran. Yanayin da Zainaba take ciki ne ya tabbatar mata da ta galbaita, kuma har lokacin haihuwa shiru sai jinin da take zubarwa. Uwar bayi ce ta fita, domin ta sanarwa da Takawa abin da yake faruwa. Don ba ta fatan abin da zai sa ta ɓata wa Sarki Gambo rai, musamman da ta fahimci Zainaba na da matuƙar muhimmanci a wurinsa. Bayan da aka shafe lokaci mai tsayi, Zainab ta haifo jaririnta namiji ƙato. Shigowar uwar bayi ɗakin tare da unguwar zoma ya sa ta ƙarasa wurinta da sauri, jaririn ta yi saurin ɗauka. Sai dai ganin ba ya numfashi ya sa jikinta ya yi sanyi. A ɗarare ta nufi wurin Sarki Gambo, ta zube a gabansa tana sanar da shi abin da ya faru. A tsammaninta ba ƙaramin faɗa zai yi mata ba, amma sai ta ga ko ajikinsa. Ya karɓi jaririn ya ajiye, sannan ya ce a yi gaggawar kawo masa Zainab. Uwar bayi tana fita, Sarki Gambo ya shiga uwar ɗakinsa. Daga ƙarƙashin gadonsa a kwai wani tsohon kabari, ya yashe ƙasar da hannunsa kamar yadda Malami ya ba shi umarni sannan ya tura jaririn ciki ya binne shi. A daidai lokacin da aka kawo Zainaba dare ya fara yi, kuma a sannan Malami ya sake dawo wa wurin Sarki Gambo. Ta galabaita sosai, hatta idanunta da ƙyar take iya buɗe su. Ƙuri Malami ya yi mata da ido, sannan ya zura hannu a ƙasanta. Duk da yanayin da take ciki hakan bai hana ta kare kanta ba, cikin zafin nama ta bige hannunsa. Ta ɗago shayayyun idanunta tana jifansa da mugun kallo. "Idan kin ba ni haɗin kai, ba zan wahalar da ke ba. Amma matuƙar za ki yi mini gardama, sai na wahalar da ke sannan kuma na gudanar da binciken da yake gabana." Malami ya furta a ɗan fusace, Sarki Gambo ne ya take hannunwanta biyun. Duk yadda ta so ƙwacewa fir ta gagara, don haka Malami ya saka hannu ya dangwalo jinin ƙasanta. Ya shafe a jikin farin ƙyallen da aka shafe da shi da turaren jan Burhum, sannan ya dubi Sarki Gambo ya matsa ya fara yi masa raɗa a kunne. Wata mahaukaciyar dariya ya ƙyaƙyace da ita, sannan Malami cigaba da cewa. "Ka tabbatar da ka bi kowacce hanya da kake ganin za ka bi, wacce al'umma ba za su yi saurin fahimtarka ba. Ka dakatar da masallatai biyun da ake gudanar da ibada a ciki, idan ba haka ba. Akwai miyagun al'amuran da za su cigaba da biyo baya." Cikin damuwa Sarki Gambo ya ce. "Mene ne dalilin yin haka?" "Idan ka aiwatar zan yi maka bayani daga baya." Malami ya furta. Har yana gab da fita Sarki Gambo ya ce. "Bayan waɗannan matsalolin, sai kuma rashin haihuwa da muke fama da ita Malami. Abin yana damunmu, domin a ƙallah mun doshi shekara goma babu haihuwa ni da Fulani Sadiya." "Idan har ina numfashi za ka haihu Gambo, sai dai ba da Sadiya za ka haihu ba. Yarinyar da za ka aura jinin musulmai ce, wato Khadija. 'Ya a wurin Malam Ubaidu, limamin masallacin yamma. Iya bayanin da zan iya yi maka kenan, zan bincika maka yanayin gamuwar hallitar burujin tauraronku. Idan ban manta ba tauraronka kamar Aƙrabu ne, amma kuma a binciken da na yi kwanaki kamar Jadyu ne ɗabi'a nari. Kada na ja da nisa, ina buƙatar ganin tafin hannun yarinyar domin na karancin ilimin tafin hannunta, ina fatan dai ɗabi'arta ba za ta kasance Nari ba." Malami ya furta yana shirin fita, har Sarki Gambo zai sake magana sai ya ɗaga masa hannu ya ce. "A yau jawabin da zan yi maka kenan, ita kuma wannan ta gabanka ka aiwatar da abin da na sanar da kai tun lokaci bai ƙure ba." Yana gama maganar ya fita. Malami yana zuwa bukkarsa ya samu Fulani Sadiya a tsaye, murmushi ya sakar mata sai ya ga ta sake haɗe fuska tamau. Kafin ya fara magana ta katse shi da cewa. "Zuwa yanzu na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba." Malami sai da ya zauna a kan buzunsa sannan ya ce, "Me kike ci na baka na zuba Fulani?" "Lokaci yana tafiya, kwanakin Gambo suna ƙara tsayi, har yanzu ba ka hallaka shi ba. Ni kuma a kullum ruhin mahaifina yana sake azabtuwa, idan ba za ka iya ba zan aiwatar da kaina." Ta furta a fusace. Malami ya furzar da iskar bakinsa ya ce. "Idan Gambo ya mutu yanzu babu ribar da za ki tsinta, rayuwar Gambo a tafin hannuna take. Amma ki sani, gaggawa ba za ta haifar miki da samun ɗa mai ido ba." *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [23/11, 22:02] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA UKU https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t 🛍️Assalamu Alaikum – Hafsat Collection ce! Kinason kayan masu inganci masu kyau kuma cikin sauƙin farashi? To ba ki da matsala! 🥳💃 📌 HAFSAT COLLECTION ta kawo muku: ✨ Kayan gyaran gida ✨ Kayan ado da kyalliya ✨ Kayan mata da maza masu kwalisa ✨ Kayan kitchen masu kyau da karko 🔥 Duk a cikin farashi mai sauƙi! 📦 Muna a Kano, amma muna aikawa zuwa ko ina cikin amincin Ubangiji! 🙏 Maza ki shiga group ɗinmu yanzu: 👉 📌 Kasance da Hafsat Collection – Sayan daidai, ko sari! https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t Jim Fulani Sadiya ta yi kamar mai nazari, sai ta kafe Malami da wani irin kallo tana nazartarsa sannan ta ce. "Ba na son na fara dasa zargi a kanka Malami, domin ka san duk duniya babu mutumin da na ba wa yarda kamar kai. Ina gudun na sakankance da kai, a kai gaɓar da za ka fara gasa mini gyaɗa a hannu." Malami ya saki dariya sannan ya ce, "Tun da na binne sirrinki na wurin marigayya mahaifiyar Sarki Gambo. Ya kamata a ce kin watsar da duk wasu-wasin da ke ɗamfare a cikin zuciyarki, Fulani Sadiya ki sa a zuciyarki ni mai lulluɓa wa ruhinki rumfar kariya da binne sirrinki ne. Babu yadda za a yi na ci amanarki, kin sani na sani. Ni da ke muna amfani da Gambo domin mu cikar muradinmu ne, da zarar mun kai gaɓar da muke muradi za mu yasar da ƙwallon mangoro mu huta da ƙuda." A fili Fulani Sadiya ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya, sannan ta ɗora da cewa. "Tun da haka ne, ina son haihuwa da Takawa. Ko babu komai zan bar magaji a masarautar Kajjura, masarautar da babu mai fahimtar gabanta da bayan har sai wanda ya gane sirrinta." "Ba za ki haihu a masarautar nan ba." Malami ya katse ta, ya cigaba da cewa. "Haka kuma har yanzu ba ki san sirrin masarautar nan ba." "Me ya sa ba zan haihu ba? Kuma wanne sirri ne ya rage da ban gama saninsa ba?" Fulani Sadiya ta furta cikin damuwa, Malami ya saki murmushi ya ce. "Saboda mahaifarki tana soke a dutsen Jaddum, haka kuma sirrin Masarautar nan ba za ki taɓa gane shi ba." Malami ya furta yana buɗe ƙur'anin da ke gefensa, har za ta sake yin magana. Ya ɗaga mata hannu yana cewa. "A yanzu ina da uzuri Fulani, kina iya dawowa bayan wani lokaci. Domin a daren nan zan sayi rauhanai biyar da za su yi mini wani aiki." Sam ba haka Fulani Sadiya ta so ba, tana tafiya Malami ya saki murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa. Sai da ya tabbatar da ta yi nisa, sannan ya ɗebi ƙasar sawun ƙafarta. Ya haɗe ta a cikin fatar farin maciji, sannan ya shiga bukkarsa ya ɗora a kan ƙaton shurin da ke tsakiyar gidajen tururwan da ke zagaye da shi. SARKI GAMBO Lokacin da Fulani Sadiya ta shiga ɗakinta, ta jima tana kaiwa da kawowa. Kamar wacce aka tsikara, sai ta ƙwala wa baiwarta kira. Cikin girmamawa ta zube ƙasa tana faɗin. "Hutawarki lafiya uwar gijiyata, Allah Ya ja zamanin giwar sarki. Da yardar Allah Yarima yana bisa hanya, Aljanna mai masoya da yawa. Sikari ba ki yi farin banza..." "A sanar da Jakadiya ta nemar mini izinin ganin mai martaba." Fulani Sadiya ta furta a daƙile, jin haka ya sa Baiwa Indo ta sake zubewa ƙasa ta ce. "An gama ranki shi daɗe, hutawarki lafjya mai farar zuciya." Miƙewa ta yi ta fita kai tsaye ta sanar wa da Jakadiya saƙon Fulani Sadiya, babu jimawa Jakadiya ta nemi izinin shiga ɗakin Fulani Sadiya. A gaggauce ta amsa mata, don a ɗokance take da son ganinsa a wannan lokacin. "Allah Ya taimake ki, Allah Ya tsare gabanki da bayanki. Takawa bai amsa goron gayyatarki ba, a yi mini afuwa ranki daɗe." Jakadiya ta furta tana sunne kai ƙasa, rai a matuƙar ɓace Fulani Sadiya ta ce. "Saboda me Takawa zai yi mini haka?" Jakadiya ta waiga hagu da dama, sannan ta sunne kai ƙasa ta ce. "Allah Ya taimake ki, ki gafarce ni da abin da zan faɗa." Kallon tsaf Fulani ta yi mata ta ce, "Tafi kanki tsaye." Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya ta ce. "Allah Ya taimake ki wannan maganar ba za ta faɗu ba, sai dai na raɗa miki a kunnenki." Kamar Fulani ta dakatar da ita, sai ta gyaɗa mata kai. Jikin Jakadiya har rawa yake yi, ta matsa saitin kunnen Fulani Sadiya ta fara yi mata raɗa a kunne. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, amma sai ta kawar da damuwar fuskarta ta ce. "Jakadiya an jima zan aiko mini da kyautar alkaki, domin ba zan bar wannan albishir ɗin ya tashi a banza ba." Jikin Jakadiya har rawa yake yi ta zube a ƙasa ta ce. "Godiya nake ranki shi daɗe, an gaida farar mace alkyabbar mata. Allah Ya taimake ki ina neman alfarmar da a taimaka a rufa mini asiri." Fulani Sadiya ta saki murmushi ta ce, "Kada wannan ya dame ki Jakadiya, ina mai yi miki albashir da yanzu ma muka fara." Jakadiya ta sake zubewa a ƙasa tana godiya sannan ta fita. TSOHO SULAIMANU Lokacin da sarkin ƙofa ya tasa ƙeyar tsoho Sulaimau tafiya mai nisa suka yi a cikin masarautar, sai da suka je bakin wata katanga sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo da ke tsaye fuska babu ɗigon fara'a. Kallo ɗaya tsoho Sulaimu ya yi masa, ya fahimci rashin imani da ƙeƙashewar zuciya ya samu gurbin zama a zuciyarsa. "Mai martaba ya bayar da umarnin a killace shi a kurkusun ƙasa, a tabbatar da a saka shi a ɗakin Kursum." Sarkin ƙofa ya furta, sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo. Kai kawai ya gyaɗa masa, ya dubi tsoho Sulaimanu da jajayen idanunsa masu kama da sabon borkono. Wanda suka sa cikinsa ya kaɗa saboda tashin hankali, da ƙarfi ya hankaɗa tsoho Sulaimanu. Suka bi ta wata siriiriryar hanya, sannan suka ɓulla gaban wata ƙatuwar ƙofa wacce aka sassaƙa ta da farin ƙarfe. Ilahirin saman wurin a zagaye yake da ƙarfe, sai wasu dogarai da ya ci karo da su fuska a murtuke babu alamar fara'a. A nan ma tafiya suka yi mai ɗan nisa, sannan suka ƙarasa wani wuri mai duhun gaske, harshen wuta ya ga an miƙe wa Sarkin horo. Ya karɓi itacen yana haska musu, a nan tsoho Sulaimanu ya ci karo da waɗansu ƙananun ɗakuna. Numfarfashin mutane ya dinga ji sama-sama, wasu kuma ya ji suna roƙon a taimaka a ba su ruwa. Tsoro ne ya mamaye shi, har yana jin ƙafafuwansa sun yi wani irin sanyi kamar ba na shi ba. Wata mai tsohon ciki ya hango a zaune, cikin galabaita tana cewa. "Ku taimaka mini da abinci, yau ne ranar da za a ba ni na ci. Wayyo Allah cikina, ku taimaka mini da ruwa ko cikin tafin hannu ne." Cikin tsawa ya ji Sarki horo ya ce. "Idan kika sake magana, sai kin maimaita kwanakin karɓar abincinki kafin a ba ki ki ci." Ba ita kaɗai ba, lokaci ɗaya tsoho Sulaimanu ya ji hatta mutanen da ke numfarfashi sun yi tsit kamar an yi ruwa an ɗauke. Jikinsa a sanyaye suka ƙarasa bakin wata ƙatuwar rijiya, wacce aka sassaƙa murfinta da dalmar baƙin ƙarfe. Mukulli Sarkin horo ya saka ya buɗe, ya dubi tsoho Sulaimanu ya ce. "Wuce mu je." Cikin tsoro, firgici da tashin hankali tsoho Sulaimanu ya ce. "Ina?" Tass! Ya sauke masa mari a fuskarsa, nan take ya ji kunnensa ya yi dum! Kansa ya yi masa nauyi, juwa ta fara yunƙurun taɗe ƙafarsa. Bakinsa da hancinsa ne yake zubar da jini, don tun da ya zo duniya bai taɓa jin marin da ya gigita kwanyarsa kamar wannan ba. "Mu je na ce!" Sarkin horo ya sake buga masa tsawa, tun bai rufe baki ba tsoho Sulaimanu ya yi sauri zura ƙafarsa, sai a lokacin ya lura da marattakalar benen ciki. A haka Sarkin horo ya tasa ƙeyarsa har suka kai ƙarshen matattakalar benen, sai dai suna gama shiga ya ga tsananin duhun wurin har ya ninka na baya da suka baro. Ƙananun ɗakuna ne ƙuntatattu, gaban tsoho Sulaimanu yana bugawa bai yi aune ba ya ji Sarkin horo ya buɗe wani ɗaki ya hankaɗa shi ciki. Ji ya yi ya ci karo da abu mai gashi, nan take hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi. Harshen wutar ya ziro musu, sai a lokacin ya lura da hallitar mai zubin mutum kuma mace ce a gefensa. Sai dai gashin da ya lulluɓe kanta zuwa jikinta ya sake hautsina hanjin cikinsa. Cikin muryarsa marar daɗi ya ji Sarkin horo ya ce. "Shawara ɗaya zan ba ka, idan har wani abu Mai martaba yake nema a wurinka, yana da kyau ka ba shi haɗin kai domin amfanar gobenka. Idan ba haka ba, sai ka fi Kursum lalacewa. Domin ita kai tsaye ɗakin horo aka fara kai ta, taurin kanta ne ya kawo ta zuwa ga wannan matsayin. Kai kuwa tashin farko ɗakin ƙasa Mai martaba ya ce a saka ka, na tabbata hukuncinka sai ya fi naka muni matuƙar ba ka bayar da kai bori ya hau ba." Sarkin horo yana gama faɗa ya fice daga wurin, sannan ya rufe rijiyar da mukulli kamar yadda ya same ta da farko. Wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyar tsoho Sulaimanu, gabansa yana faɗuwa ya ce. "Sannu malama kursum." Shiru ya ji ta yi masa, bai daddara ba ya sake maimaitawa. Bai yi tsammani ba sai ji ya yi ta karce shi da farcenta, wanda hakan ne ya sa shi jin ɗumin da ya tabbatar masa da jini ne yake zuba. A ɗarare ya ja gefe, duk da ba ya iya ganin koda tafin hannunsa. Sai kawai ya fashe da kuka, sannan ya ɗaga hannuwa sama yana roƙon Ubangiji Ya kawo masa ɗauki. SASHEN BAYI Tun sassafe da gari ya waye kowacce Baiwa ta kama gabanta, domin gudanar da aikin da ya zame musu ta kamar sallar farilla. Ɗakin shiru babu kowa sai Baiwa Sakina da ke rungume da jaririn hannunta, kallon fuskarta yake ƙir kamar yana tantance surarta. Murmushi ta sakar masa, ta kai hannu ta lakuci kumatunsa ta ce. "Allah Ya raya mini kai Ridwan, sai dai ina jimamin yadda za ka taso a ƙasƙantacciyar rayuwar bautar da muke kai." Kamar ya san me ta faɗa, sai ta ga hawaye yana zuba daga idonsa. Nan take gabanta ya faɗi, tana shirin sake magana Uwar bayi ta ɗaga labulen ɗakin cikin faɗa ta ce. "Sakina kin san duk wani adalci da zan yi na yi miki ko? Yau kwananki nawa da haihuwa, ina ce kin doshi kwana hamsim. Ko kuma don ba ki san zuru ba me shi ya sa za ki cigaba da laƙewa a ɗakina kina rungumar ɗa kina yi masa rawa. Ki fito ku tafi casar gero tun lokaci bai ƙure ba." Jiki yana rawa Sakina ta zame Ridwan da ke cinyarta ta ce. "Bari na goya shi, tuba nake Uwar bayi." Uwar bayi ta saki dogon tsaki ta yi gaba tana cewa. "Daɗina da ku ba ku san harkar mutumci ba, ina laifi adalcin da na yi miki za ki shantake a ɗaki. Ai hutu ba na ki ba ne, tun da Allah Ya ƙaddaro miki rayuwar bauta a gidan nan." Kwantar da Ridwan Baiwa Sakina ta yi, ta shiga uwar ɗaki domin ɗauko zanen goyonsa. Tana fitowa ta hango shi a kwance yana kallon kusurwar bango yana ƙyalƙayala dariya, da mamaki take kallon wurin sai dai ganin babu komai ya sa ta miƙa hannu za ta ɗauke shi. Da sauri ta ja baya, ganin yatsarsa sanye da da wata azurfa mai ɗauke da wani zanen da ba ta fahimce shi ba. A sanyaye ta miƙa hannu tana taɓa azurfar, sai dai jin ta da zafi zau kamar an ciro daga cikin wuta ya sa ta yi saurin yarfe hannunta gefe. "Wallahi idan na sake magana Sakina sai kin yi aikin wata guda babu mataimaki. Iskancin banza da wofi wannan wanne irin wulaƙanci ne?" Uwar bari ta katse mata nazarin da take yi, game da baƙon lamarin da ya faru da Ridwan bayan shigarta ɗaki. Jiki yana rawa ta ɗauke shi ta saka shi a baya, sannan ta fito daga ɗakin zuciyarta fal wasu-wasi. Koda ta je wurin aiki hatta ragowar bayin da suke aiki sun lura da sanyin jikin Sakina, don duk yawan hirar da ake yi sai sun sako ta za ta jefa kalma ɗaya zuwa biyu. Sai da ta ji ya fara mutsu-mutsu alamar yana jin yunwa, sai ta koma can gefen wata bishiyar kuka ta sauko shi tana ƙare masa kallo. Da yake wurin ya yi nesa kaɗan da wurin da suke surfen, ba ta yi aune ba ta ji wata tsohuwa ta yi mata sallama. A ɗan razane ta waiga, don har lokacin zuciyarta ba ta daina rawa ba. Kallon mamaki take yi wa tsohuwar don ba ta taɓa ganinta a gidan ba, amma abin da ya ba ta mamaki ganinta sanye da irin kayansu na bayi. Sai da ta amsa mata sallamar sannan tsohuwar ta ce. "Ɗazu muna filin sassaƙa na ga kin yar da ɗan kunnenki, ban samu damar miƙo miki ba saboda uwar bayi tana wurin." A sanyaye Baiwa Sakina ta shafa kunnenta ta ji babu wari ɗaya, ta miƙa hannu ta karɓa sannan ta yi mata godiya. Sai ta ga tsohuwar tana kallon Ridwan, tana shirin yin magana tsohuwar ta cigaba da cewa. "Allah Ya yi miki babbar kyautar da ba kowa yake yi wa ba, saboda haihuwa babbar ni'ima ce. Idan kika cigaba da riƙe wannan amanar ta hannunki, haƙiƙa za ki rabauta da lada mai yawa. Tabbas wannan yaron ba kamar sauran yara ba ne, ki riƙe shi hannu bibbiyu Sakina." Tana gama faɗar haka ta saki murmushi ta wuce, da sauri Baiwa Sakina ta bi bayanta. Sai dai tana shan lungun da tsohuwar ta yi ta neme ta sama da ƙasa ta rasa. Kallon ɗan kunnen hannunta ta yi, sai a lokacin ta ga kamar ba nata ba. Ƙura masa ido ta yi, ta sake kallon zoben hannun Ridwan sai ta ga yana ɗauke da irin rubutun zoben hannunta. "Zainaba! Wace ce Zainana?" Ta samu kanta da furta haka, tana cigaba da kallon Ridwan da ke ta tsotsar hannunsa. BAYAN SHEKARA GOMA (1835) Tun daga bakin ƙofar ɗakin za ka fara jin salatinta, cikin galabaita ta dubi Unguwar zoma ta ce. "Lami! Ki taimaka ki karɓo mini tofi a wurin takawa." Cikin girmamawa Unguwar zoman ta ce, "Allah Ya taimake ki, yanzu haka Jakadiya ta tafi wurin Shamaki ta sanar da shi, domin ya faɗa wa Sarki Gambo halin da kike ciki." Cike da zafin naƙuda, Fulani Khadija ta ce, "Ki bi ta Lami, ni na san abin da nake ji. Wayyo Allahna! Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ganin Fulani Khadija ta fara fita hayyacinta ya sa Unguwar zoma Lami ta fita da sauri, da fitarta babu jimawa Fulani Khadija ta ga an shigo ɗakin. Fuskarta a naɗe take cikin shigar kayan bayi, a daidai kanta aka tsaya ta ɗan ja da baya ta ce. "Wace ce?" Ba a tanka mata ba, aka yarfa mata wani baƙin ruwa a fuska. Ji ta yi kamar an zare mata laƙa, ta faɗi baya yaraf. A daidai lokacin ta saki nishi, nan take tagwayen jariranta mata suka faɗo. Murmushi ta yi tana ƙare wa matar tsugunnen da kallo, sai kawai ta saki wata irin dariya. Cikin shammata ta saka hannunta biyu a saman kawunan jaririn nata, ta fara motsa baki ba tare da ana fahimtar abin da ta furta ba. Ganin ana ɓata mata lokaci matar da ke tsugunne, ta zaro kaifaffan ƙahon da aka wasa ya yi tsini. Ta burma a saitin zuciyar Fulani Khadija, nan take idanunta suka lumshe tana fara motsa bakinta cikin azabar fitar rai. Cikin zafin nama, matar ta zaro zuciyarta wace ta haɗa da mabiyyar jariran ta ɗauka ta fice daga ɗakin. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [23/11, 22:41] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA HUƊU https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=ems_copy_t Masarautar Judala (1835) Fulani Zannira tana ƙarasawa turakar Sarki Giɗaɗo, bayin da ke biye da ita suna riƙe da alkyabbarta ta baya suka dakata. Cikin girmamawa suka zube ƙasa suna faɗin. "A fito lafiya ranki shi daɗe, Allah Ya ƙara miki lafiya mai zuciyar zinare." Ba ta tanka musu ba, ta tura ƙofar da shiga, sassanyan ƙamshin rumfar Takawa ta daki hancinta har sai da ta lumshe idonta. Cikin takunta na isa da jan hankali ta fara takawa har zuwa turakarsa, sallama ɗauke a bakinta ta shiga tana faɗaɗa fara'arta. A jingine ta hango shi kan ƙasaitacciyar shimfiɗarsa ta alfarma, sai dai ta lura har ta ƙarasa gabansa bai fahimci ruhinta ya wanzu a wurin ba. "Barka da hutawa sarkin sarakai." Ta furta cikin salo mai jan hankali, wuri ɗaya ta ga yana kallo don haka ta zauna daga ƙasansa. Sannan ta kai hannu ta shafa sajensa da ke kwance luf a zagaye da fuskarsa. Murmushi ta ga ya sakar mata, ya fara ƙoƙarin kawar da damuwar da ke kwance a saman fuskarsa. "Barka da shigowa sarauniya." "Damuwa ba ta dace da gwarzon mazaje ba, nannauyan tunani bai cancanci samun sukuni a tare da kai ba jarumina." Ta furta tana zuba masa idanu, sannan ta ɗora da cewa. "Idan ban takura Mai martaba ba, ina son sanin damuwar da yake ciki domin na samu sukunin kawar masa da ita." Janyo ta ya yi jikinsa yana jin tsananin soyayyarta tana mamaye zuciyarsa, haka kawai yake jin soyayar Zannira ta doke duk ragowar matan da ya aura a baya. Nan take ƙirjinsa ya buga, tausayinta da shi ya mamaye shi. Amma gudun kada ya ɗarsa mata damuwa ya sa shi kawar da damuwar zuciyarsa ya ce. "Akwai baƙin al'amuran da ke shirin faruwa Fulani, kun san jan ragamar sarauta ba abu mai sauƙi ba ne." Kwanciya ta yi a jikinsa, ta janyo hannunsa ta shiga wasa da shi sannan ta ce. "Ni san mijina gwarzo ne, don haka babu gwagwarmayar da za ta dagula masa lissafi. Kai ɗin jarumin namiji ne, zuciyarka tamkar ta dakarun jarumai dubu ce." Yadda a ɗan kwanakin da suka yi da Zannira take ba shi ƙwarin gwiwa abin ba ƙaramin birge shi yake ba, ta kai hannunsa saman cikinta sannan ta ce. "Allah Ya taimake ka wani babban albishir gare ni, ban san da wanne irin tukwici za a saka mini ba." Cikin zumuɗi Sarki Giɗaɗo ya ce, "Duk abin da Fulani take muradi za mu mallaka mata, matuƙar bai saɓa da tsarin masarautarmu ba." "A yau da muka cika kwana talatin da biyar da aure, tun wasu kwanaki da suka wuce na yi ɓatan baƙon watana..." A zabure Sarki Giɗaɗo ya miƙe, cikin zallar farinciki mai haɗe da tashin hankali ya ce. "Da gaske Zannirata?" A ɗan kunyace ta sunne kai ƙasa, ta saki murmushi sannan ta gyaɗa masa kai. Rungume ta ya yi tsam a jikinsa, nan take idanunsa suka fara zubar da ƙwalla. Hawayen fuskarsa ta saka hannu ta share, sannan ta ce. "Ranka shi daɗe, ban yi tsammani har farincikin rabon jikina zai sa ka hawayen farinciki ba." Sarki Giɗaɗo ya ɗago murya a ɗan dashe ya ce, "Dole mu yi hawayen farinciki Zannira, kyauta ce da tun muka zo duniya ba mu taɓa samun irinta ba. Sai dai kuma kash..." Jin ya yi shiru ya sa ta ce, "Sai dai me ranka shi daɗe?" Ya ƙaƙalo murmushin yaƙe ya ce. "Babu komai Fulani, za ku iya tafiya don akwai muhimman abubuwan da za mu duba yanzu." Kallon tsaf ta yi masa tana karantar yanayinsa, cikin damuwa ta ce. "Ranka shi daɗe!" Kallonta ya yi ta cigaba da cewa. "Tun a tsirarun kwanakin da suka gabata, na fahimci sauyinka. Na fahimci kana cikin matsananciyar damuwa, don Allah ranka shi daɗe ka warware mini zare da abawar halin da kake ciki." 'Tabbas ba ki yi ƙarya ba Fulani, a kullum na wayi gari zuciyata cike take da fargabar makomar miyagun al'amuran da ke bibiyar rayuwata. ' Amma a fili sai ya ce. "Idan har akwai abin da yake damunmu kune mutanen farko, da za su fara fuskantar damuwar da muke ciki. Muna buƙatar hutawa Fulani, zuwa wayewar gari akwai kyakkyawan albishir da za mu yi wa mahaifiyar yarima." Murmushi ta yi, don haka ta miƙe tana gyara alkyabbar jikinta. Janyo ta jikinsa ya yi, ya sumbaci goshinta sannan ya sake ta ta fita daga ɗakin. Zama ya yi a gefen gado, ya dafe kansa da hannuwa biyu. Yana ayyana ga ƙoshi ga kwanan yunwar da ke tun karo shi, kamar wanda aka tsikara da allura haka ya miƙe zumbur ya fita. Yana zuwa ya samu Dogari Isiya da ke kula da ƙofar turakar Takawa, Sarki Giɗaɗo ya ce. "A gaggauta kira mana Galadima." Cikin girmamawa dogari Isiya ya ce. "An gama ranka shi daɗe, Allah Ya tsare gabanka da bayanka ɗan toron giwa. Gaba salamun baya salamun uban kowa mai taimakon talakawa." Ɗaki Sarki Giɗaɗo ya shiga, ba a ɗauki lokaci ba Galadima ya ƙaraso yana neman iso. Nan take Sarki ya ba shi izinin shiga, yana zama ya dubi Sarki Giɗaɗo ya ce. "Allah Ya taimake ka, an aiko kana nemanmu. Ina fatan ba wani laifin muka aikatawa mai martaba ba." "Akwai gagarumar matsala Lurwanu, wannan wani sirrina ne da za mu bankaɗa maka. Wanda babu wani mahaluki da ya san da shi. Don haka muke son mu yi magana da akai a matsayinmu na ɗan'uwanka ba sarkin masarautar Judala ba." Jinjina kai Galadima ya yi ya ce. "Ina sauraronka ɗan'uwana, In Shaa Allahu zan ba ka gudunmawa matuƙar abin bai fi ƙarfina ba. Kuma ni mai lulluɓe maka bargon sutura ne, ba tare da na bayyana sirrinka ba." "Duk matan da na aura a baya, waɗanda nake kai wa kurkukun zauren horo. Ba gaskiya ba ne laifin da nake laƙaba musu, kowaccensu mutuwa take yi." A razane Galadima ya ɗago yana kallonsa ya ce, "Ban fahimce ka ba yaya Giɗaɗo." Ajiyar zuciya Sarki Giɗaɗo ya sauke ya ce. "Daga kan marigayya Fulani Karima, kun san mun auri mata masu yawa." Galadima ya jinjina kai, Sarki Giɗaɗo ya cigaba da cewa. "To tun bayan mutuwar Karima, duk matar da muka aura bayan kwana arba'in take mutuwa." A wannan karon Galadima baki da hanci ya saki yana bin sa da kallon mamaki, Sarki Gidaɗo ya miƙe tsaye yana zagaya ɗakin cikin damuwa ya ce. "Babban abin ya girgiza duniyarmu, ya dagula mana lissafi bai wuce Fulani Zannira ba." Kallonsa Galadima ya yi yana son jin ƙarin bayani, Sarki Giɗaɗo ya koma kusa da shi ya zaune murya a raunane ya cigaba da cewa. "Tun da muke aure, babu macen da muka fi so muka fi ƙauna har cikin jikinmu face Fulani Zannira. Kuma a yanzu maganar da muke yi maka, Fulani tana ɗauke da cikin Yarima ko Sarauniya." A fili Galadima ya faɗaɗa fara'arsa, ya ɗaga hannu cikin jin daɗi ya ce. "Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, haƙiƙa na yi matuƙar farinciki. Domin idan lissafi ba ƙwace mini ya yi ba, ka doshi shekara kusan ashirin da auren fari ba tare da Allah Ya kawo rabo ba." Ajiyar zuciya Sarki Gidaɗo ya yi, ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu yana girgiza kai. Murya ɗauke da damuwa ya ce. "Ba a nan gizo yake saƙar ba, domin a yau kwanan Fulani Zannira talatin da bakwai. A ƙiyasin mummunan al'amarin da yake bibiyar matan da na aura, saura kwana uku ta yi bankwana da duniya." Hankali a tashe Galadima ya miƙe, ya matsa kusa da ɗan'uwansa sannan ya ce. "Ya zama dole mu nemi mafita, domin haka kawai nake ji a jikina banza ba ta kai zomo kasuwa." "Shi ya sa muka kira ka, domin ku nemar mana mafita. Mun sha zuwa wurin malaman soro a sirrance, amma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba. Don haka muke son ku nemo mini hatsabibin bokan da zai magance mana damuwarmu. Don mun tabbata, ba zai wuce kaidi da makircin wancan la'annan Sarkin ba." Galadima ya gyaɗa kai cike da gamsuwa sannan ya ce, "Tabbas biri ya yi kama da mutum, amma wani hanzari ba gudu ba. Zuwa wurin boka sauka daga doron addinin musulumci da saɓa wa Allah ne." "Idan mun saɓa masa Ubangiji mai gafara ne, idan buƙatarmu ta biya sai mu ɗaga hannu mu nemi yafiyarSa." Galadima ya jinjina kai, sannan ya yi wa Sarki Giɗaɗo alƙawarin nemo masa hatsabibin bokan da zai warware masa matsalarsa. MASARAUTAR KAJJURA Baki ɗauke da sallama Jakadiya da Unguwar zoma suka shiga ɗakin Fulani Khadija. Jakadiya da ke riƙe da ƙoƙon tofi ta ce. "Allah Ya taimake ki, Allah Ya buɗe ido lafiya. Ranki shi daɗe ga tofin Shamaki ya karɓo a wurin Mai marta..." Jin kukan ɗaya daga cikin jariran ya sa ta yi saurin ajiye ƙoƙon ta ce. "Lami maza duba kamar fa ta sauka." Da sauri suka ƙarasa wurin Fulani Khadija, a nan suka ci karo da jarirai guda biyu suna wutsul-wutsul a ƙasa. Unguwar zoma Lami ta shiga kiciniyar yanke musu cibiya, Jakadiya kuma ta tallafo Fulani a nan ta ci karo da jinin da ke tsartuwa daga ƙirjinta. "Fulani! Fulani! Innalillahi Fulani me nake gani haka? Lami taya ni gani ko idanuna ne." Jakadiya ta furta cikin tsananin kaɗuwa da tashin hankali. Lami tana ɗagowa ta yi tozali da yanayin Fulani, nan take jikinta ya shiga karkarwa ta ce. "Na shiga uku ni Lami, yau wacce irin baƙar rana nake gani." "Maza-maza ɗaurewa tagwayen cibiya kada su mutu mu sake shiga uku." Jakadiya ta furta a hargitse. Hannun Lami ban da karkarwa babu abin da yake yi, a haka ta samu ta ɗaure musu cibi. Kafin ta ƙarasa Jakadiya ta fita da gudu cikin kururwa ta sanar da abin da ya faru. Kafin wani lokaci tuni labari ya zagaye cikin masarautar, Bayi, Dogarai da masu sarautar masarautar lokaci ɗaya jikinsu ya yi sanyi. Saboda kowa ya shaidi Fulani Khadija mutuniyar kirkice, don haka mutuwarta ta zo musu a bazata musamman da ya kasance kisan rashin imani aka yi mata. Sarki Gambo yana zaune a turakarsa, Shamaki ya faɗa ɗakin babu ko neman izini kamar wanda aka jefo daga sama. Jiki da muryarsa suna rawa ya zube a ƙasa ya ce. "A gafarce ni ranka shi daɗe, a yi mini aikin gafara. Tuba nake uban talakawa, tuba nake damo sarkin haƙuri. Tuba nake jarumin sarki mai dakakkiyar zuciya, a yi mini afuwa bisa mummunan furucin da zai fito daga bakina." Kallon da Sarki Gambo yake yi wa Shamaki ya sa shi fahimtar yana cikin tashin hankali, Shamaki yana shirin yin magana Jakadiya ta faɗa ɗakin a hargitse ta ce. "Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Kaina bisa wuyana ubangidana, tuba nake ranka shi daɗe. Ina neman afuwa abisa miyagun kalaman da zan yi, na mummunan kisan wulaƙancin da aka yi wa Fulani Khadija a yanayin da take naƙuda." A razane Sarki Gambo ya miƙe, nan take jijiyon kansa suka fito. Da wata irin murya ya buga musu tsawa da cewa, "Wacce irin maganar banza ake sanar da mu?" Gabaɗaya suka russunar da kai ƙasa, hawaye yana zuba Jakadiya ta sanar masa da duk abin da ya faru. Gani suka yi ya zauna a kujera daɓar, ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin ɗacin zuciya. Ganin haka ya sa suka nemi izinin fita, don sun fahimci Sarki Gambo yana cikin kiɗima da tashin hankali. Fulani Sadiya da kawo kanta kenan turakar Sarki Gambo, ta saki murmushi zuciyarta fes ta tura ɗakin ta shiga. "Barka da hutawa Sadaukina!" Bai tanka mata ba, don haka ta matsa gabansa ta dafa kafaɗarsa ta ce. "Ina yi maka ta'aziyya Sarkina." "Ke ce kika kashe ta ko?" Ya wurga mata tambaya, Fulani Sadiya ta fara takawa tana murmushi sannan ta ce. "Eh." Ta yi furucin tana kashe masa ido ɗaya. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 [23/11, 23:14] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA BIYAR Masarautar Zulwara Kasancewar duk ranar asabar ita ce ranar bikin gaida abin bautarsu, ya sa iyalai da dama suke shirya ƙwai da kwarkwarta domin halartar wurin bauta. Kusan tun asuba ilahirin mutanen ƙauyen suke zuwa bakin kogin, saboda kowa burinsa ya isar da bukatarsa domin Allahnsu da suke bautawa ya yi gaggawar amsa musu. Kogin Sutturu shi ne kogi ɗaya tal da yankin Zulwara suke bautawa, kasancewar akwai wata murgujejiyar bishiyar kukar da ke gaban kogin. Dalilin da ya sa suke bautawa kogin da kuma bishiyar kukar, kasancewar a shekaru masu tsayi da suka gabata. Ita wannan bishiyar an wayi gari da ta faɗi a cikin ruwan, da mutanen yankin suka yi yunƙurin tsamo ta daga ciki saboda wucewa a kwale-kwale, sai ya zamana duk wanda ya shiga kogin ba zai fito ba sai da wata nakasa. Ko dai idanunsa su makance, ko ƙafa ta shanye da hannu, wasu ma sai dai a tsame gawarsu daga ciki. Tun daga lokacin mutane suka daina shiga wannan kogin, a hankali sai kuma ruwan cikinsa ya dinga janyewa. Har ta kai ga ruwan kogin ya ƙafe tas. Bishiyar kukar da ke kwance ta ƙone ƙurmus, sai aka wayi gari shuri da gidajen turuwawa sun kewaye wannan bishiyar kukar. Ana cikin haka sai Boka Ɗan Asabe ya yi mafarki, a cikin mafarkin an ce ya je ya ɗebi ƙasar wannan kogin ya yi wa wani ɗansa mai nakasa magani. Idan ya warke sai ya cigaba da bayar da magani, da farko ya ji tsoro. Amma da ya tuna a mafarkin nasa an ce za a ɗaukaka shi, kuma za a ba shi ƙarin ilimin bokanci sai ya yi ta maza. Ya tara mutanen gari ya sanar da su abin da ya faru, mutane da dama ba su amince da kalamansa ba. Saboda suna ganin kamar yawo da hankali ne a ce su bar bautar rana su koma bautar ƙonanniyar bishiyar kuka. Boka Ɗan Asabe cikin fargaba ya tunkarin ƙonannan kogin ya ɗebo ƙasa, ga mamakinsa sai ya ji ƙasar ta yi sanyi sosai kamar ya ɗebo ta daga cikin kogi mai ruwa. Bayan ya ɗiba ya karyi itacen bishiyar, ya fito daga ciki ya haɗa wa ɗansa magani ya shafe masa ƙafafuwansa. Ko sa'a guda ba ta shuɗe ba, ɗansa ya miƙe garau ya samu lafiya. Wannan dalilin ya sa mutane suka fara gasgata maganar Boka Ɗan Asabe, musamman da wasu nakasasun suka dinga zuwa yana warkar da su. Sai ya zamana duk umarnin da bokan ya ba su tamkar wahayi haka suke amfani da shi, na zartarwa su zartar na aikatawa su aikata. Ana cikin haka Boka Ɗan Asabe ya ce kowanne magidanci ya ɗauki dabba ɗaya daga cikin gidansa ya kaita wannan ƙonannan kogin, da sunan godiya ga sabon abin bautarsu bisa ni'imar da ya fara yi musu. Jin yadda boka Ɗan Asabe yake ƙara samun ƙwarin gwiwa, maganarsa take karɓuwa. Ɗaukakarsa ta tumbatsa ya sa sarkin wancan lokacin ya aika har gida aka hallaka shi, saboda yana ganin idan aka cigaba da tafiya a haka al'ummarsa za ta daina ba shi girma da matsayin da yake kai. Tun da sai abin da Bokan ya faɗa ake zartarwa, saɓanin idan shi da yake sarki ya bada umarni ake tantama a kai. A ranar da Boka Ɗan Asabe ya mutu, a daren ranar Sarki Nomau ya makance. Tun ana nema masa magani har abin ya ci tura aka haƙura, daga ƙarshe aka naɗa ɗansa ya zama sarki. A ranar da Sarki Isa ya hau kan karagar mulki, a ranar kuma ƙoramar da suke bautawa ta fara tsattsafowa, bishiyar kukan da ta shafe sama da shekaru masu yawa ta miƙe. Haka mutane suka dinga turuwa suna ganin abin al'ajabi, ana cikin haka sai Damina ɗan Boka Ɗan Asabe ya gaji mahaifinsa a fannin bokanci. Sanin abin da ya faru ga tsohon sarki ya sa sarki mai ci bai yi yunƙurin kashe shi ko illata shi ba. Haka suka cigaba da tafiya ana zaman doya da manja tsakanin Sarki Najume da Boka Damina. A haka har girma ya cin musu, ajali ya riski sarki Najume bayan mutuwarsa aka naɗa ɗansa Sarki Dikko. Abu na farko da Sarki Dikko ya fara yi a ranar da ya hau kan karaga shi ne rushe tsibirin Boka Damina. Ya sa aka kawo masa shi a gabansa a fada, ya zare takobi a gaban jama'a. Sannan ya bayar da umarnin daga ranar babu wanda zai sake bayar da wani umarni idan ba shi ba, ganin abin da ya faru da Boka Damina ya sa jikin mutane ya yi sanyi. Tsoro ya mamaye su, sai dai a ɓangare ɗaya suka shiga dakon ganin mummunan yanayin da zai faru da Sarki Dikko kamar yadda ya faru da kakansa tsohon Sarki Nomau. Abin da ya sake ba su mamaki da tsoro jin shiru babu wani al'amari da shi, don dama tun hawansa mulki suke jin raɗe-raɗin ana cewa shi ma Dikko hatsabibin kansa ne. Tun daga wannan lokacin suka bayar da kai bori ya hau, suka zame masa tamkar raƙuma da akala saboda yadda suke yi masa biyayya sau da ƙafa. Shi kuma Diko ya cigaba da murza kambumsa yana yin sarauta yadda ya ga dama, saboda hatta dattawan ciki fada shakkarsa suke yi. Babban tashin hankalin da Sarki Dikko ya fara fuskanta akan haihuwa ne, ba don ba ya haihuwa ko iyalinsa ba sa haihuwa ba. A lokacin da uwar gidansa ta fara haihuwa sai ya zama duk yaran da take haifa masu nakasa ne, daga makafi sai masu shanyewar ƙafa da hannu. Waɗansu kuma masu taɓin ƙwaƙwalwa ta yadda ba za su mori ba. Da farko sai ya yi tsammanin daga ɓangaren uwargidansa ne, don haka ya ƙara aure sai dai ita ma tana zuwa ta haifo masa jariri mai shanyewar jiki. Amma duk waɗannan al'amarun da suke faruwa, Sarki Dikko bai taɓa bari labarin haihuwar masu nakasar da yake yi ya fita ba. Saboda killace yaran yake sa wa ayi, tare da yi wa masu tsaronsu bazaranar matuƙar zancan ya fita sai ya hallaka su. Da al'amarin ya fara ci masa tuwo a ƙwarya, sai ya sa amintaccansa wato Waziri. Da ya nemo masa hatsabiban bokayen da su iya warware masa matsalarsa, kuma duk ƙiyayyarsa da addinin kiristanci sai ya amince da a kira malaman addinin a sirrance domin su kawo masa ɗauki. Amma kowanne da ya jarraba maganinsa sai ya ga aikin bai ci ba, don haka ya cigaba da bada ƙarfi a ɓangaren addininsa na gargajiya. Aka cigaba da nemo masa bokayen da ke aiki da ruhin magabata, amma sai lamarin ya girme wa tunaninsa. Sarki Dikko (1835) Cikin damuwa yake duƙurshe a gaban tsohuwar bukkar da aƙalla za ta kai shekara hamsim, Waziri da ke gefe ya sunkuyar da kai cikin damuwa. Hatsabibin bokan ne ya ratso ta jikin dutsen da ke kallon bukkar, sannan ya ƙarasa gabansu ya zaune a kan shurin da ke fuskantarsu. Waziri ya ɗan russuna ya ce, "Ran boka ya daɗe, fatan shekaru masu yawa irin na dabino. Ina mai ja da aikinka ya zo a nuna masa ƙarshensa, ba don ka hana a bauta maka ba da babu mahalukin da ya isa ya hana mu fara bauta maka ya kai boka Tsumbur." Jin irin kirarin da Waziri yake yi wa Boka Tsumbir ya Takawa jin ɗaci a zuciyarsa, saboda shi mutum ne mai tsananin kishi. Don ba ya san ko kaɗan ya ga al'umarsa na fifita wani fiye da shi. "Ya kai shugabana, a yau tare nake da Sarkin masarautar Zulwara..." "Sarkin da yake ƙyashin fifikon wani a kansa, sarkin da yake gabana amma yake jin ban isa a ba ni matsayin da ka ba ni ba. Sarki da yake fama da matsalar haihuwar masu nakasa, kuma a yanzu ma kun zo gabana domin na taimaka muku a kan haihuwar masu nakasar da aka yi masa da asubar yau." Boko Tsumbur ya furta yana ƙura wa Sarki Dikko idanu, a sanyaye Sarkin ya sunkuyar da kai ƙasa. Duk sai ya ji kunya ta kama shi, don duk a kalaman bokan babu wanda ya yi ƙarya a ciki. Saboda lokacin da Waziri yake masa kirari ji yake kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi, Waziri ya katse masa tunanin da cewa. "Tuba yake uban kowa, tuba yake mai taimakon kowa." Boka Tsumbur bai tanka masa ba, ya miƙe a gabansu ya saki fitsari a saman shurin da yake zaune. Sai kuma ya mayar da ganyen jikinsa ba tare ya yi tsarki ba, ya ya ɗebi kasar shurin da ta jike da fitsarin ya miƙa wa Sarki Dikko. A tsantsance Sarkin yake kallonsa, Boka Tsumbur ya zuba masa daƙwa-daƙwa idanunsa sannan ya ce. "Ka yi imani da wannan ƙasar shurin ita ce mai rayawa kuma mai kashewa. Sannan ita za ta sa na taimaka wa duk matsalar da kake ciki, kuma sai ka yi imani da wannan shurin ya fi abin bautar da kake bautawa." Jim Sarki Dikko ya yi, cikin sauri Waziri ya ce. "Ya amince tabbatacan boka." Sarki Dikko kallon Waziri ya yi, ya fakaici idon Boka Tsumbur ya matsa hannunsa alamar ya ce ya amince. Cikin muryar takaici da ganin gazawarsa Sarki Dikko ya ce. "Mun amince." Wata mahaukaciyar dariya Bokan ya saki sannan ya fara yi wa kansa kirari, "Sai ni bokan da har gobe babu wanda ya kai ni, sai ni Tsumbur jikan maguzawa masu abin mamaki. Sai ni waraka ga duk wanda ya raɓe ni, sai ni mai abin bautar da babu wanda ya kai ni." Sai ya waigo ya dubi Sarki Dikko ya cigaba da cewa. "Matsalar 'ya'yanka ba daga matsalar iyalinka ba ne, wannan matsalar tana da alaƙa da kisan da ka yi wa Boka Damina. Don haka ko yanzu matanka suka tara da wani namijin za su haifi lafiyayyun yara." "Zafin kishina ba zai bari na saki mace ta yi wani auren ba, babu wanda ya isa ya aikata wannan mummunan aikin a kan macen da na santa." Sarki Dikko ya furta a fusace, murmushi Boka Tsumbur ya yi ya ce. "Ƙarfin zuciyarka yana matuƙar birge ni Dikko. Sai dai ka sani daga nan har ka mutu ba za ka taɓa haihuwar lafiyayyun 'ya'ya ba." A razane Sarki Dikko yake kallonsa, Boka Tsumbur ya cigaba da cewa. "Sai dai waɗannan jariran da aka haifa maka za mu iya warkar da su." "Ka taimaka mini Boka Tsumbur, wallahi ina cikin tashin hankali domin a yanzu babu ɗa ɗaya ƙwaƙƙwara da zan ɗaga wanda zai gaji karagata." Boka Tsumbur ya ɗebi ƙasar shurin ya watsa a wutar da ke ci a gabansa, sannan ya ce. "Za su warke matuƙar ka lamunce da sharaɗin da za mu kafa maka." Cike da rashin dogon nazari Sarki Giɗaɗo ya ce. "Kowanne irin sharaɗi ne a shirye nake da na tunkare shi. Na amince da sharaɗinka Boka Tsumbur." "An haifa wa Sarki Gambo tagwayen mata, adaidai gaɓar da iyalinka ta haife maka tagwayen yaranka mace da namiji. Macen da aka haifa maka makauniya ce, shi kuma namijin ƙafafuwa da hannuwansa a shanye suke." Sarki Dikko ya sunkuyar da kai ƙasa cikin takaici, boka Tsumbur ya cigaba da cigaba da cewa. "Don haka za mu musanya lalurar 'ya'yanka zuwa kan 'yan tagwayen da Sarki Gambo ya haifa." "Amma me ya sa sai Sarki Gambo? Boka Tsumbur ko ka san ni da Sarki Gambo kamar wuta da ruwa muke, idan har sarki Gambo yana ƙaunata. Ko kuma idan ina ƙaunar Sarki Gambo to zan ƙaunaci mutuwata, ta yaya 'ya'yana za su yi amfani da surar 'ya'yan maƙiyina?" Boka Tsumbur ya yi saurin katse Sarki Dikko da cewar. "Saboda ba ka san jinin wace ce a jikin 'ya'yan Gambo ba, da ace ka san wace ce mahaifiyar yaran nan. Na tabbata da ka zabarce ta cikin rayuwarka tun kafin mutuwarta, kamar yadda wani ƙudurin Sarki Gambo ya sa shi aurenta ba don yana sonta ba." Ajiyar zuciya Waziri ya sauke, ya yi ƙasa da murya yana yi wa Sarki Giɗaɗo raɗa. "Ranka shi daɗe ka ajiye batun gabarku a gefe, ka fuskanci abin da yake gabanka. Wannan wata dama ce ta idan ta kuɓuce ba lallai mu sake samun ta ba, kada ka manta ranka shi daɗe. A ƙalla yau shekara biyar kenan ina bibiyar Boka Tsumbur a kan ya ba mu damar ganinsa, amma sai yau ya ba mu wannan damar." Shiru Sarki Giɗaɗo ya yi yana nazari, cikin zafin nama ya ce. "Mun amince Boka Tsumbur." Dariya Bokan ya saki marar daɗin sauraro, sai ya saka hannunsa a cikin wutar gabansa. Ya ɗauko wani allon farin ƙarfe, ya soka a jikin shirun sannan ya fara biya ɗalasiman tsafi, yana kiran sunayen manyan aljanun da suke yi masa aiki. Wani ruwa mai kamar jini da ke tafasa ya ɗiba ya watsa a kan allon, nan take hoton jariran Sarki Gambo da ke kwance Unguwar zoma tana yanke musu cibi suka bayyana. Daga gefe kuma jariran Sarki Dikko ne kwance a saman gadon mahaifiiyarsu, ruwan ya sake watsa musu lokaci ɗaya jarirai huɗun suka fashe da kuka jikinsu yana wata irin karkarwa. Har sai da Sarki Dikko ya tsorata da ganin abin da yake faruwa da su, Boka Tsumbur ya ɗago ya dube su ya ce. "A yanzu haka duk irin tawaya da nakasar da ke jikin jariranka, sun koma yaran Sarki Gambo. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba." Da sauri Sarki Dikko ya dube shi yana shirin yin magana suka ji tsibirin ya yi wata irin tsawa mai razanarwa. *Ummmou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [24/11, 15:59] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA SHIDA Masarautar Kajjura A haukace Sarki Gambo ya ƙarasa cikin zafin rai, ya maƙure wuyan Fulani Sadiya har sai da ta fara kakari. Murya a kausashe ya ce. "Saboda me za ku kashe mana iyali? Saboda me za ku raba mu da uwar 'ya'yanmu?" Fulani Sadiya ta tattara ƙarfinta ta fisge hannunta da ƙyar, sannan ta gyara zaman rigarta ta ce. "Saboda har yanzu ba ka gama karantata ba, saboda har yanzu ba ka tantance maƙiyin ɓoye da na zahiri ba." Ta yi jim tana shafa wuyanta da har lokacin yake yi mata raɗaɗi sannan ta cigaba da cewa. "Ranka shi daɗe! Kana tsammanin zan kashe Fulani Khadija sannan na bar 'ya'yan da ta haifa? Me ya sa ban haɗa har su na hallaka ba? Mai martaba! Yana da kyau ka nutsu domin ka san wanɗanda suke zagaye da kai. Amma Allah Ya taimake ka, ka san ba zan taɓa cutar da kai ba." Fulani Sadiya tana zuwa nan sai ta fara zubar da hawaye, jikinsa ne ya yi sanyi. Ya riƙo ta a jikinsa, sai Fulani Sadiya ta sake fashewa da kuka ta ce. "Na yi mamaki da har kake tsammanin zan iya cutar da Fulani Khadija, a duk tsawon shekarun da muka ɗauka. Ban taɓa tsammanin za ka yi mini mummunar shaida ba, ko don ban haihu ba kake yi mini haka oho?" Ta sake fashewa da kukan kissa, nan take tausayinta ya kama shi. Cikin tattausan lafazi ya ce. "Ku yi haƙuri Fulani, mutuwar Fulani Khadija ta gigita mu." "Ina yi maka ta'aziyya ranka shi daɗe." Fulani Sadiya ta sake furtawa tana kwantar da kai. A gaggauce Sarki Gambo ya fita daga ɗakinsa, ya koma rumfar ya zauna. Abin duniya goma da ashirin ya haɗe masa, dafe kansa ya yi da hannuwa biyu yana nazarin al'amuran baya da suka shiga tsakaninsa da Fulani Khadija. Unguwar Zoma Lami tana zaune tana yankewa tagwayen Sarki Gambo cibi, ta ga jikinsu ya fara wata irin karkarwa. A ɗan tsorace ta ajiye su tana kallo, tana cikin haka Jakadiya ta shiga ɗakin tana wurga mata tambaya. "Me ya faru Lami? Me ya samu jariran nan? Lami kada ki jefa mu a masifa mu shiga uku, kin ga dai uwarsu a hannunmu ta mutu. Yanzu idan wani abin ya samu yaran nan me za mu cewa Mai martaba?" Jikin Unguwar zoma nan take ya cigaba da karkarwa, bakinta yana rawa ta ce. "Wallahi ban san me ya faru da su ba Jakadiya, ki yadda da ni haka na ga suna karkarwa ba tare da komai ba." Unguwar zoma ba ta gama rufe baki ba, suka ga ɗaya daga cikin jariran ta fara jijjiga kai. Nan take wani ruwa mai kamar na ɗaurayar nama ya fara zuba daga idonta a madadin hawaye. Ɗayar kuma ƙafafuwnata suka shiga karkarwa, irin ruwan da ke fita daga idanun ɗayar shi ma ya fara tsattsafowa daga jikin ƙafafuwanta. Jakadiya da Unguwar zoma kallon juna suka yi cike da tsoro, Jakadiya ta yi ƙasa da murya ta ce. "Lami kina ganin abin da idanuna suke gani?" "Ina gani Jakadiya, magana ta Allah na jima ban ga haihuwar da ta zo mini da al'ajabi kamar wannan ba." Lami za ta yi magana, suka ji muryar Shamaki daga dokin ƙofa. A daidai lokacin uwar Bayi ta shiga ɗakin, duk suka yi carko-carko. Daɗin da suka ji a lokacin jariran sun dakata da kukan da suke yi, kuma ruwa da karkarwar da suke yi duk sun daina. A ɗan ɗarara Lami ta ɗauke ta ta cigaba gaba da gyara su, sannan Jakadiya ta ɗauke su ta fita da su. Dangin Fulani Khadija ne suka yi wa gidan sarautar tsinke, mahaifiyarta ban da kuka babu abin da take yi. Koda aka nuna musu jariran ba su bi ta kansu ba, suna shiga da suka ga irin kisan da aka yi mata duk sai jikinsu ya sake yin sanyi. Mahaifiyarta ta dubi mahaifin Fulani ta ce. "Malam dama sai da na ce maka ba na son auren nan na Hadiza a gidan sarauta amma ka ƙi ka ji, dubi yadda makircin masarautar nan ya sa aka hallaka mana ita." "Fatima! Ke musulma ce, kuma kin sani da Khadija ta yi aure a nan da mu aurar da ita a wani wurin ba nan ba. Duk abin da Allah Ya ƙaddara a cikin rayuwarta sai ya faru, abin da za ki yi mata a yanzu addu'a ce. Idan har 'yata Khadija ba ta da haƙƙi a wannan kisan da aka yi mata, na tabbata sai Ubangiji Ya yi mata sakayya." Mahaifin Fulani Kgadija ya furta yana ɓoye hawayen da ke gangarowa daga idonsa. Fulani Sadiya Fulani Sadiya tana fita daga ɗakin Takawa kai tsaye ɗakinta ta nufa zuciyarta fes, sai da ta shiga ɗakinta sannan ta fara kai kawo cikin farinciki ta ce. "Fulani Zainaba ke kaɗai kika rage mini. Tun da har Fulani Khadija ta tafi, na tabbata kema ta ki tana hanya. Sai na tabbatar da na aiwatar da ƙudurina, a kan duk wanda zai ba ni matsala a doron ƙasa koda kuwa Sarki Gambo ne." Motsi ta ji daga cikin ɗakinta, da sauri ta ɗaga labule ta shiga. Cikin girmamawa Baiwa Sakina ta zube a ƙasa ta ce, "Barka da shigowa ranki shi daɗe." "Tun yaushe kike a nan?" Fulani Sadiya ta furta da sauri, saboda ba ta yi tsammanin akwai wani a ɗakin ba. "Allah Ya taimake ki kafin fitarki kin manta kin saka ni gyaran ɗaki. Amma idan na yi laifi ki gafarta mini ranki shi daɗe." Baiwa Sakina ta furta tana sake russunar da kai ƙasa, saboda yadda gabanta yake faɗuwa. Domin wani irin tsoron Fulani Sadiya ne ya mamaye ta. "Sakina!" Fulani Sadiya ta kira ta da wata irin murya, a sanyaye Baiwa Sakina ta amsa. Sannan Fulani ta cigaba da cewa. "Ki ji kamar ba ki ji ba, idan kika yi yunƙurin furta kalma ɗaya daga cikin abin da kika ji. Na rantse da girman Yesu mai ceto, sai na sa an yi miki azabar da ba a taɓa yi wa wani mai numfashi a cikin gidan nan ba, sai na wulaƙanta ruhinki ta yadda za ki dinga yagar naman jikinki kina ci da haƙoranki." A razane Baiwa Sakina ta ɗago, sai ta rarrafa a guje zuwa gaban Fulani ta ce. "Ki yi mini afuwa Fulani, Na tuba wallahi ba zan taɓa aikata miki wannan kuskure ba." Fulani Sadiya ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce. "Daga yau idan kika sake kika ɓoye mini wani abu, wallahi ranki zai yi mummunan ɓaci. Idan kika bari na gano wata manaƙisar da kike ɓoye mini za ki yaba wa aya zaƙinta. Kuma daga yau, za ki fara shiga cikin wasu al'amuran da nake gudanarwa a bayan fage." A wannan karon ma cikin tsoro haɗe da girmamawa Sakina ta amsa mata, daga ƙarshe Fulani Sadiya ta sallame ta. Jikin Baiwa Sakina yana rawa ta nufi sashen bayi, tana mamakin jin miyagun abubuwan Fulani Sadiya take aikatawa. A ɓangare ɗaya ta shiga fargabar rantsuwar da ta yi da Yesu mai ceto, saɓanin Allah Ta'ala da ta san gabaɗaya cikin masarautar suna bautawa. Baiwa Sakina tana shiga harabarsu ta hangi Ridwan zaune a gefe, daga can nesa tsirarun yaran bayi ne suke ta wasanninsu. Ƙarasawa ta yi wurinsa ta ce, "Ridwan!" Ɗagowa ya yi ya kalle ta, nan take ta ga idanunsa sun kaɗa jajir kamar sabon borkono. Gabanta ne ya faɗi, don haka ta matsa kusa da shi ta ce. "Me yake damunka Ridwan?" "Wallahi sai na kashe ta." Ridwan ya furta cike da ɓacin rai, Baiwa Sakina tana shirin sake magana ta ga ya furzar da wani gudan jini daga bakinsa. Tana nan tsaye ta ga ƙasar wurin da jinin ya ɗiga ta rauzaye ta faɗa ciki. Tsoro ne ya sake mamaye ta, duk da ba a wannan lokacin Ridwan ya saba baƙin al'amura masu ɗaure kai ba. Amma na wannan lokacin ya tsorata ta, don jin kalmar kisa da ta yi ya firgita hanjin cikinta. "Ridwan me kake faɗa haka? Duka shekararka goma amma har kake furta kalmar kisa, wa za ka kashe? Kuma a ina ka ji wannan kalmar?" Baiwa Sakina ta kawar da tsoron da ke kwance a saman ƙirjinta, ta furta masa tana kallon yanayinsa. Manyan idanunsa ya ɗago ya zuba mata, har sai da ta ji tsoro ya mamaye ta. Sai ya kawar da kai cike da rashin damuwa ya ce. "Ba ki santa ba." "Kai a ina ka santa?" Baiwa Sakina ta furta cikin sauri, Ridwan ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Tana masarautar Judala, masarautar Sarki Giɗa..." "Kul." Baiwa Sakina ta furta tana toshe masa baki da hannunta, jikinta yana rawa ta ja hannun Ridwan ɗaki. Sai da ta zaunar da shi a kan gado sannan ta ce. "Kul Ridwan, koda wasa kada na sake jin Masarautar Judala a bakinka. A ina ka ji sunan? Ko kana son wani ya kai wa Mai martaba tsegumi a hallaka mini kai? Ba ka san furta sunan masarautar a cikin wannan masarautar kusan daidai yake da hukuncin kisa ba?" Kawar da kansa ya yi gefe yana taɓe baki sannan ya ce, "Haka kawai na ji ba na sonta, shi ya sa nake son kashe ta. Kuma Masarautar Judala ai masarautarmu ce, mahaifata ce..." "Me kake faɗa ne Ridwan? Wa yake faɗa maka waɗannan maganganun?" Baiwa Sakina da ta gama firgicewa ta katse Ridwan, Ridwan ya washe baki cikin rashin damuwa ya ce. "Wallahi Inna wata tsohuwa ce take faɗa mini, kuma duk dare ma a can nake kwana. Ta ce za ta sanar da ni maɓoyar Kundi ukun da sarakuna uku suke son mallaka, amma wai ai sai na ƙara girma." Kusan mutuwar zaune Baiwa Sakina ta yi, tana son sake tambayarsa amma tsoro ya mamaye ta. "Kuma a can na ga an haifi Batul! Ni kuma ba na sonta shi ya sa nake son kashe ta." Ridwan ya sake faɗa cikin damuwa, Sakina ta kamo hannunsa ta ce. "Kana son ka daina ganina Ridwan? Ko kana son na dinga yi kuka?" Da sauri ya girgiza mata kai, Sakina ta cigaba da cewa. "To ka daina faɗar irin maganganun nan, idan ba haka ba waɗannan maganganun za su kai mu har gaban Mai martaba. Kuma zai iya zartar mana da hukuncin kisa." "Shi ma Sarki Gambon ba na sonsa, ta ce mini na kashe s..." A wannan karon da sauri Sakina ta sake toshe masa baki gabanta yana faɗuwa. 'Na shiga uku ni Sakina, me Ridwan yake neman janyo mana?' Ta raya a ranta tana zubar da ƙwallah. "Inna kin ga can fa." Ridwan ya furta cikin murmushi yana nuna mata kusurwar bangon ɗakin. SARKI GAMBO Sarki Gambo yana zaune aka kai masa tagwayen jariransa duka mata, waɗanda ya yi wa laƙabin Hasana da Usaina. Kowaccensu ta saka hannu a baki tana tsotsa. Jiki a sanyaye dogaransa suka sunkuyar da kansu ƙasa, Sarki Gambo ya fara zubar da hawayen tausayin halin da jariransa suke ciki. Ya jima a haka, sannan aka iso aka sanar da shi an gama haɗa gawar Fulani Khadija za a sallace ta. Da ƙyar Sarki Gambo ya iya miƙa wa Shamaki su, ya bayar da umarnin a kai su ɓangaren Fulani Sadiya domin ta kula da su. Sannan ya ce a tabbatar da an tatsi nonon awaki an ba su don gudun kada yunwa ta illata su. Cikin ƙanƙanin lokaci mutane da dama suka sallaci gawar Fulani Khadija, don mahaifinta ne ya jagoranci sallar gawarta. Bayan da aka kai ta gidanta na gaskiya, mahaifiyar Fulani ta nemi da a bata jariran domin ta kula da su. Amma fir Sarki Gambo ya ƙi amincewa, saboda tsananin soyayyarsu da yake ji a cikin zuciyarsa. Kusan wuni guda Sarki Gambo ya yi yana karɓar gaisuwar Fulani Khadija, sai yamma liƙis ya shiga turakarsa. Da shigarsa babu jimawa, Jakadiya ta zo nema wa Fulani Zainaba iso wurinsa. Ya yi matuƙar mamaki, don haka kai tsaye ya amsa wa baƙuntarta. Sallama ɗauke a bakinta ta shiga, sai dai kamar kullum fuskarta a cunkushe take babu ɗigon fara'a. Sai da ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta ji ya ce. "Mun yi matuƙar mamakin ganinku Fulani Zainaba, yau kusan shekara goma kenan da shigowarku rayuwarmu. Sai dai ba ku taɓa neman izinin ganinmu a turaka ba, idan ba mu muka nemi ƙeɓewa da ku ba." "Saboda babu buƙatar hakan a tattare da ni, a yanzu ma akwai dalilin da ya kawo ni turakarka." Fulani Zainaba ta furta cikin tsana, Sarki Gambo ya saki murmushi ya ce. "Zainaba ba za ki taɓa sauyawa ba." "Zan sauya Sarki Gambo, amma lokaci alƙali ne yana nan tafe." Ta ba shi amsa kai tsaye, sai kuwa ya ƙura mata ido. Ita ma ba ta janye idonta ba, ta cigaban da kallonsa har sai da ya matso gabanta ya ce. "Dalilainmu masu muhimmanci ne suka sa muka bar ku a raye Zainaba, tun da kun san ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba." Fulani Zainaba ta saki murmushin takaici ta ce, "Ni kuma Ubangiji Ya ja da kwana ne, domin na fahimtar da kai kuskuren da ka tafka a baya." A fusace Sarki Gambo ya ɗago, Fulani Zainaba ta girgiza kai cike da takaici ta ce. "Na zo na ji ya aka yi Fulani Khadija ta mutu? Don ina zargin wani abu a mutuwar baiwar Allahr nan. Sanar da ni, ya aka yi aka haihu a ragaya? Domin a sanin mugun halin da na yi maka tun daga shigowata gidan nan, na tabbata babu abin da ba za ka iya aiwatarwa ba." Da sauri Sarki Gambo ya dube ta, cikin zafin rai ya ƙarasa ya maƙure wuyanta. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [24/11, 17:29] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA BAKWAI ADVERT *MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR* 'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki. zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp. Location: Kano Sai kun zo💃🏻 Masarautar Judala Ayarin rukunin bayi ne suke tafe cikin gajiyawa saboda irin doguwar tafiyar da suka yi, ba su ƙarasa cikin masarautar Judala ba sai kusan lokacin da dare ya tsala. A sashen bayi aka zuba su tamkar wasu kayan wanki, a galabaice suke saboda yunwa da ƙishirwa. Don haka suna zuwa a kan ruwa suka fara dira kamar waɗanda suka shekara ba su gan shi ba, bayan da suka sha suka yi ƙat sai ya zamana cikkunansu ya ƙulle saboda rashin abinci. Ƙanan yara maza da mata suka shiga kukan yunwa, da yake ba lokacin abinci ba ne a kan dole iyayensu suka lallashe su don su haƙure wa zuwa wayewar gari. A lokacin da dare ya tsala sosai, a ƙalla kusan ƙarfe biyu da rabi na dare. Fitsari ne ya tashi Indo, don haka ta dubi katafaren filin da suke kwance. Da tarin bushiyoyin da ke zagaye da su, haka kawai ta ji tsoro ya kama ta. Saboda ko a garinsu babban dalili ne yake fitar da ita waje da daddare, don haka a hankali ta miƙa hannu ta tashi Zinaru tana yin ƙasa da murya ta ce. "Zinaru! Zinaru!" Cikin gajiya da magagin bacci Zinaru ta ce, "Tuba muke don Allah ku yi haƙuri ku bar mu a ƙauyukanmu, kada ku kai mu masarautarku mu zame muku bayi." Sake taɓa ta Indo ta yi don ta fahimci firgicin da suka shiga a lokacin da za a kamo su, daga garinsu ne ya sa Zinaru take surutai har a cikin bacci. "Zinaru Indo ce, don Allah ki raka ni na yi fitsari." Sai a lokacin Zinaru ta sake wartsakewa, ta miƙe tana hamma tare da murza idanu tana kalle-kalle. "Yanzu Indo a wannan dokar dajin za mu tafi fitsari, ni fa wallahi tsoro nake ji." Indo da fitsari ya gama matsarta ta ce, "Wallahi ni ma tsoron nake ji Zinaru, amma ko ɗan gabancan ki taimaka ki raka ni." A hankali suka fara takawa zuwa bayan ɗakunan Bayin da suke jere, kasancewar duk mutane ne a warwatse ya sa suka ƙara tafiyar da ɗan nisa. Musamman da ya kasance akwai hasken farin wata, sai tsoron da suke ciki ya ragu sosai. A bakin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya Indo da Zinaru suka tsugunna ba tare da addu'a ba, sai da suka gama sannan suka rasa abin da za su yi tsarki da shi. Don haka suka laluba suka ɗauki duwatsu suka shafa a madadain ruwan da ba su samu ba. Miƙewa suka yi suna waigowa suka ganta jingine, a jikin wani ƙaton shuri da ke kallon bishiyar tsamiyar da suke tsaye. Gaban Indo da Zinaru ya yi mummunan bugawa, har sai da kusan lokaci ɗaya suka saka hannuwa biyu suka dafe ƙirjinsu. "Wash! Wayyo cikina da marata, ku taimaka ku zo ku agaza mini." Matar ta furta tana yarfe hannu alamar tana cikin tsananin ciwo, sai a lokacin suka lura da tsohon cikin jikinta. Zinaru ce ta yi ta maza ta ce. "Da me za mu taimaka miki?" "Naƙuda nake yi wash!" Ta furta gumi yana sake tsattsafo mata, kallon juna suka yi, jikin Indo ne ya shiga rawa. Ganin haka ya sa Zinaru ta ja hannunta don su yi gaba, cikin galabaita matar ta ce. "Ku ma mata ne, watarana ba ku san inda za ku tsinci kanku ba, don Allah ku taimaka mini." Sosai kalamanta suka tausasa zuciyar Indo, ta tsaya cak wuri ɗaya. Da sauri Zinaru ta kalle ta, Indo ta ƙarasa gaban matar cike da tausayawa ta ce. "Kema kina daga cikin tawagar bayin da aka kawo ne?" Kai matar ta gyaɗa mata a daidai wannan lokaci suka ji ta saki nishi, nan take jaririyar 'yarta ta faɗo. Tsoro ne ya kama Indo, kasancewar bata taɓa ganin an yi haihuwa a gabanta ba. Da sauri ta ƙarasa wurin Zinaru da ke tsaye har lokacin tana kallonsu, cikin sauri ta ce. "Zinaru don Allah ki zo ki taimaka mata ke ce kika taɓa haihuwa." Wani mugun kallo ta watsa mata, cikin masifa ta ce. "Saboda ni ma ba ni da hankali kamar ke ko? Wai Indo ba za ki zo mu tafi ba?" Shiru Indo ta yi, ta waiga tana kallon matar tana yankewa jaririyar cibi. Wani ƙaton ganyen ayaba ta ga tana ƙoƙarin cirowa, da sauri Indo ta ciro ta miƙa mata. Sai ta ga ta ɗora jaririyar akansa, ta dubi Indo tana sakin murmushi a galabaice ta ce. "Sunana Karima kuma a cikin masarautar nan nake, sunan da zan saka wa wannan Jaririyar Batul. Don Allah ki taimaka ki yi mini wata alfarma, ki riƙe mini yariyar nan akwai kayana a bayan shingen can da zan ɗauko." Kamar Indo ba za ta yi magana ba, jiki a sanyaye ta miƙa hannu ta karɓi jaririyar. Zinaru da ke can gefe tana ganin haka ta saki ƙwafa haɗe da yin tsaki ta yi gaba, tana sake jaddada rashin hankalin da Indo take yi. Daidai wurin da Karima ta tashi nan ta nuna wa Indo, sai a lokacin ta lura da mazaunin matar a kan ƙaton gidan tururuwa ta yi shi. Ya jiƙe sharkaf da jini, ga waɗansu manyan tururuwai da ba ta taɓa ganin irinsu ba sun zagaye jinin suna ta tsotsa. "Baiwar Allah zuciyata a cike take da fargaba da ruɗa ni, don Allah kada ki cutar da ni." Indo ta furta zuciyarta tana rawa kamar za ta saka kuka, kama hannunta Karima ta yi, nan take Indo ta ji wani yarr tsigar jikinta ta fara tashi. Ga wani irin sanyi da ta ji hannunta kamar ta tsamo daga cikin ƙanƙara, ta sakar wa da Indo murmushi ta ce. "Ba zan cutar da ke ba, ungo riƙe wannan." Karima ta furta tana miƙa mata abu kamar wacce take shirin ba ta abu. Zuciya ɗaya Indo ta miƙa hannunta, Karima ta zuba mata ido har sai da tsoro ya sake mamaye Indo sannan ta ce. "A duk inda kike zan cigaba da bibiyar rayuwarki, ina son ki riƙe mini Batul tamkar 'yar cikinki. Akwai tarin ƙalulaben da za su afko cikin rayuwarki, sai dai duk abin da ya sha miki duhu. Ki zo bakin shurin nan za ki samu mafita, duk adadin shekarun da zan ɗauko zan dawo gare ki Indo..." "Don Allah me kike faɗa ne? Ban fahimce ki ba." Karima ba ta tanka mata ba, ta tsugunna ta damƙi ƙasar gjdan turuwar, sannan ta damƙi ta saman shurin. Ta shafa a fuskar Indo, sannan ta shafa a fuskar jaririyarta Batul da ke hannun Indo. Nan take Indo ta ji wata irin juwa tana yunƙurin ɗaukarta, tun tana ganin Karima har ta fara yi mata dishi-dishi. Ba ta yi tsammani ba, ta ji Karima ta matso wurinta ta fara yi mata raɗa a kunne mai kama da barin wasiyya.Tana buɗe idonta ta ji jariraiya Batul ta tsanyare da matsanancin kuka, sai dai ba kukan ne ya fi ɗaga mata hankali ba. Rashin ganin mahaifiyar Batul ya fi hautsina hanjin cikinta, tana fara waige-waige ta ji Zinaru ta ce. "Indo ba za ki ajiye 'yar nan ki zo mu tafi ba?" Cikin sauri Indo ta ce, "Ban ganta ba Zinaru, na shiga uku wallahi ban ganta ba." Kafin Zinaru ta bata amsa suka ga Dogaran sun ƙaraso da sauri suna cewa. "Kai baƙaƙen munafukai, wato da guduwa za ku yi? Allah Ya tona muku asirinku ku wuce mu je." Daga Zinaru har Indo rasa mai bakin magana aka yi, Dogarin da ke gaba sai a lokacin ya lura da jaririyar da ke hannun Indo tana kuka. Cikin mamaki ya ce. "Ke! Dama haihuwa kika yi shi ne har za ki gudu?" Indo da ta rasa bakin magana sai ta fashe da kuka, saboda gabaɗaya tsoro ya kamata ita da ko auren fari ba ta yi ba ya za ta yi da jaririya sabuwar haihuwa. "Ko ba magana nake yi miki ba?" Dogarin ya sake buga mata tsawa, Indo da ta rasa mafita cikin kuka ta ce, "A'a ba guduwa zan yi ba." "To ku wuce mu koma, ƙananan munafukai. An faɗa muku duk girman masarautar nan idan kun shigo za ku iya fita ne?" Zinaru da Indo suka yi carko-carko musamman Indo da damuwa ta cunkushe mata kai. "Indo kin ga irin abin da nake gudu ko? Wai ina uwar jaririyar nan? An ya kuwa ba gamo muka yi da aljana ba?" Kamar Indo tana jira ta ce, "Wallahi Zinaru ban san inda ta yi ba, kamar ƙiftawar ido tana gama yi mini siddabaru na neme ta na rasa. Ni yau na shiga uku." Duk maganganun da suke yi ƙasa-ƙasa suke yin su, shi ya sa ma Dogaran ba su san wainar da suke toyawa ba. "Indo ki faɗa musu gaskiya kawai." Zinaru ta faɗa tana satar waigensu. Indo ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Yanzu wannan labarin mai kama da almara waye ya zai yarda da shi? Idan aljana ce me ya sa 'yarta ta kasance mutum, wallahi ina cikin tashin hankali Zinaru." Indo ta ƙarasa maganar cikin kuka, musamman da ya kasance ita ma jaririyar ban da kuka babu abin da take tsalawa. Sarki Giɗaɗo Tun bayan fitar Galadima abin duniya ya haɗu ya haɗe masa, dafe kansa ya yi cike da damuwa. Ganin ba shi da mafita ya sa ya miƙe ya haye kan gadonsa ya kwanta yana tunanin makomar rayuwarsa, da yadda duniya take neman yi masa atishawar tsaki ba tare da ya shirya ba. Abu ɗaya ya sani yana da gawurtattun maƙiya guda biyu, Sarki Dikko da Sarki Gambo. Wanda zuciyarsa ta fi karkata da kaso casa'in da tara a kan su suke yunƙurin dakushe tarihin zuri'arsa daga masarautar Judala. Kusan duka wunin da ya yi haka ya ƙarasa shi sukuku, jiki babu ƙwari. Sai zuwa washegari ya ɗan saki jikinsa, ganin Fulani Zannira ta shiga matsananciyar damuwa. Da daddare bayan sallar Isha'i, Fulani Zannira da Sarki Giɗaɗo suna zaune suna hira a turakarsa. Shamaki ya doka sallama a bakin ƙofar, yana nema wa Galadima izinin shiga. A ɗabi'ar Sarki Giɗaɗo matuƙar aka yi sallar Isha'i ya rufe ganin kowanne irin baƙo. Amma ga mamakin Fulani Zannira sai ta ga jikinsa yana rawa ya amsa wa Shamaki, sannan ya dube ta ya ce. "Fulani kuna iya shiga daga ciki, domin akwai muhimmiyar tattaunawar da za mu yi da Galadima." Duk da ta yi mamaki, da yake Zannira mace ce mai kawar da kai, amma sai ta saki murmushi ta ce. "Ni mai bin umarninka ce ranka shi daɗe." Martanin murmushi ya mayar mata, ya taka mata har bakin ƙofa cike da ɗokantuwar ganin Galadima. A rumfar (Falo) da Sarki Giɗaɗo yake ganawa da baƙi suka zauna shi da Galadima. Cikin girmamawa Galadima ya ce. "Allah Ya taimake ka, Ubangiji ya ba ka yawan rai ina fatan na same ka lafiya ranka shi daɗe." Sarki Giɗaɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Kun same mu kafiya Galadima, tun da muka ji labarin neman isonku muka tabbatar akwai alkairi a tattare da zuwanku." Galadima ya russunar da kai ya ce, "Wannan haka yake ranka shi daɗe, akwai wata ƙasaitacciyar bokanya da muka samu nasarar gano ta. Sai dai ta kasance ƙungurmar kafira, mai bin addinin kiristanci. Sunan da ake kiranta Bokanya Kande, ta kasance hatsabibiya kuma makira. Babban abin farincikin kuma har kawo yanzu, ba kowanne basarake ne ya san da zamanta ba." Nan take Sarki Giɗaɗo ya faɗaɗa fara'arsa, cikin zaƙuwa ya ce. "Galadima a tafi kai tsaye." Galadima ya saki murmushi ya ce, "Allah Ya taimake ka na samu izinin ganawa da hadimanta, sai dai sun sanar da ni babban sharaɗinta ba ta taɓa ganin mutum ido da ido har sai ya yi imani da Allahn da take bautawa, sannan kuma ya amince Allahnta shi ne mai gaskiya, kuma mai zartar da kowanne hukunci. A taƙaice dai, kusan ridda take sa mutum ya yi." Shiru Sarki Giɗaɗo ya yi, yana cikin nazari Galadima ya ce. "Amma fa an tabbatar mini da aikinta tamkar yankan wuƙa haka take yin sa. Kuma tana aiki da mabambamtan jinsin aljanu kala-kala, a taƙaice dai buƙatarka za ta biya ranka shi daɗe." A fili Sarki Giɗaɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Mun amince Galadima." Galadima ya jinjina kai ya ce, "Amma kuma yana da kyau mu yi fitar sirri ranka shi daɗe." "Yanzu haka a shirye muke Galadima, idan babu damuwa za mu iya tafiya. Sai dai ba ma son masarauta ta fahimci ba mu kwana a gida ba." A fili Galadima ya saki murmushi mai sauti ya ce. "Ranka shi daɗe, Bokanya Kande sha'aninta fa ya shallake duk tunanin mai tunani. Saboda a ziyarar da na kai, hadimanta sun ba ni wuridin da zan furta a zuciya wanda za mu buɗe ido mu gan mu a tsibirinta." Daɗi sosai Sarki Giɗaɗo ya ji, nan take ya shiga Turakarsa ya sauya kayan jikinsa. Yana fitowa ba su ɗauki lokaci ba, Galadima ya dafa tsakiyar kan Sarki Giɗaɗo. Ya saka shi suka rufe ido, sannan ya fara biya wuridin tsafin da zai kai su tsibirin da take rayuwa. Wata irin sassanyar murya suka ji tana raira waƙar mai matuƙar daɗi, hakan ne ya alamtawa Galadima sun ƙarasa tsibirin Bokanya Kande. Suna buɗe ido suka ga ƙaton cross a gabansu, Galadima ya dubi Sarki Giɗaɗo ya ce. "Ranka shi daɗe, ni iya hurumin da aka lamunce mini kenan. Kai ne za ka runtse idonka, idan ka dafa wancan gicciyen (Cross) za a biya maka kalmaman imani da Allahn Bokanya Kande. Kamar Sarki Giɗaɗo yana jira, cikin sauri ya matsa gaban cross ɗin ya dafa shi haɗe da runtse ido. Murya da suka ji a farko, ita ta sake karaɗe kunnensa tana biya masa kamar haka. "Ya Ubangiji Yesu, na yarda cewa kai .... Na furta cewa ni mai zunubi ne, kuma yanzu haka ga ni a gabanka ina neman gafararka. Na karɓe ka a matsayin Ubangijina, mai ceton rayuwata. Na buɗe maka zuciyata ka shiga ciki ka ceci rayuwata. Na gode maka da ka ceci rayuwata daga ɓata, Amin." Muryar tana gama biya wa Sarki Giɗaɗo, ya ga ya sake tsintar kansa a wani babban kogon dutse. Ilahirin cikin dutse cike yake da cross manya da ƙanana, wata gajeriyar farar mace ya gani. Daga ita sai ganye a ƙirji da ƙasanta. Sarki Giɗaɗo yana shirin yin magana ya ji ta katse shi da cewar. "Barka da shigowa sabon addini sabuwar rayuwa. Jikinsa yana rawa ya amsa mata. "Barka dai Bokanya Kande." Yana shirin yin bayanin abin da yake tafe da shi ya ji ta ce. "Duk matsalolinka na gama saninsu. Matanka suna mutuwa duk bayan kwana arba'in da aurensu, a yanzu haka kuma iyalinka tana ɗauke da juna biyu, kai kuma ba ka son ka rasa ta." Gyaɗa kai Sarki Giɗaɗo ya yi ta cigaba da cewa. "Mafitarka ɗaya ce ka nemo mini tsohuwar matarka Karima, ko kuma ka kawo mini jininta wato 'yarta." A firgice Sarki Giɗaɗo ya ɗago ya ce. "Ya shugabata Fulani Karima ta shafe lokaci mai tsayi da mutuwa. Babu yadda za a yi na iya kawo miki ita, kuma a iya sanina da ita ni ne mijin da ta taɓa aure. Kuma a ɗakina ta mutu, aka binne ta a masarautata." "Ba ta mutu ba!" Bokanya Kande ta furta tana zuba masa manyan idanunta farare tas da sha kwalli ya ƙara musu kyau, ji ya yi ba zai iya cigaba da kallon ƙwayar idonta ba. Ta saki murmushi sannan ta cigaba da cewa. "Har yanzu Karima tana doran ƙasa, domin binciken da na yi tauraron rayuwarta yana nan har yanzu. Amma ban gama tabbatar da shin ainihin ruhinta ne, ko kuma akwai wani ƙulumboto da aka aikata ba. Kuma ta haifi jininta a cikin masarautarka, domin tauraron jaririyar daga tsagin tauraron Karima yake, sai dai har kawo yanzu bincikena bai bayyana mini ainahin fuskar jaririyar ba. Sai dai yana kyau, ka binciki masarautarka. Duk sababbin jariran da aka haifa a ciki, ka shafa musu wannan jan garin maganin da zan damƙa maka. Idan har ka ga jini daga al'aurarsa, wala mace ko namiji ko kuma sauran alamomin da zan raɗa maka a kunne, to tabbas jinin Fulani Karima ne." *Ummou Aslam Bint Adam* 07062062624 [25/11, 21:38] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA TAKWAS *MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR* 'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki. zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp. Location: Kano Sai kun zo💃🏻 Masarautar Kajjura Yadda Sarki Gambo ya maƙure wuyan Fulani Zainaba, abin ba ƙaramin tsoro ya ba ta ba. Don har sai da numfashinta ya nemi ɗaukewa, idanunta suka firfito ta fara fita hayyacinta. Wurgi ya yi da ita ta faɗi ƙasa, nan take tari ya turnuƙe ta. Zuwa ya yi ya tsiyayo mata ruwa a tulunsa, ya ƙarasa gabanta ya miƙa mata. A galabaice ta karɓa ta kai bakinta, sai da ta sha mai isarta sannan ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya. Kafe ta ya yi da ido yana kallo, ita ma ta zuba masa idanu tana sake jadadda ƙarfin rashin imaninsa. Sarki Gambo ya ɗago haɓarta, yana bin ta da wani rin kallo mai wuyar fassarawa. "Zainaba ba yanzu zan kashe ki ba." Ya furta a kausashe, kamar ta yi masa shiru. Sai kuma zuciya ta ɗebe ta, tana ayyana mata idan har ta yi shiru zai ga kamar ta fara jin tsoronsa ne. Cikin dakiya da taurin zuciya ta ce. "Rashin kisana da ka yi, yana da nasaba da ganin gawarka da zan yi Sarki Gambo." Ya ji ɗacin maganarta, don haka ya furzar da isa mai zafi ya ce. "Lokaci kawai nake jira, amma mu koma maganarmu ta baya. Me ya sa kike son ɗora alhakin kisan Fulani Khadija a kaina, duk da kina da masaniyar a wurin haihuwa mummunan al'amarin ya faru da ita?" "Saboda na san babu abin da ba za ka iya aikatawa ba saboda buƙatar kanka." Fulani Zainaba ta ba shi amsa kai tsaye. Miƙewa ya yi ya fara zagaye ɗakin yana girgiza kai, sai da ya yi zagayen kamar sau uku sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna suna cigaba da kallon juna ya ce. "Tabbas ba ki yi ƙarya ba Zainaba, zan iya aikata komai kuma a kan kowa matuƙar buƙatata za ta biya. Domin dalilin haka ne ya sa na hallaka mijinki Najibullah da jaririn ɗanki." Runtse idonta ta yi da sauri, tana jin wani irin ɗaci a ranka. Saboda duk lokacin da ta tuna irin kisan wulaƙancin da Sarki Gambo ya yi wa Najibullah sai ta ji abin ya dawo mata sabo. Murmushi mai sauti ta ji ya saki, sai a lokacin ta buɗe idonta sannan ta ce. "Abin da ba ka sani ba Sarki Gambo, babban kuskuren da ka aikata a rayuwa shi ne rashin kashe ni a daidai lokacin da ka kashe mijina. Za ka maimaita waɗannan kalaman naka a gaba, kuma ina mai sake tabbatar maka da kamar yadda kake tare da ni saboda biyan buƙatar kanka. Na rantse maka da zatin Allah, ni kaina na jinkirta hallaka ka ne saboda manufar da ke ɗamfare a cikin zuciyata." "Taurin kai, kafita da ƙarfin zuciyarki suna birge ni Zainaba. Sai dai abin da ba ki sani ba, tun da har zan iya juya wa Fulani Sadiya baya. Babu macen da za ta sha a wurina, idan kika tsame tagwayen 'ya'yana da abar bauta rana da ta ba ni." Da sauri Fulani Zainaba ta dube shi saboda jin furucin da ya yi. "Me kake faɗa haka?" Jin tambayarta ya sa shi ɗaga mata gira ya ce. "Kamar yadda kika ji a kunnuwanki." Fulani Zainaba ta miƙe a hankali, sai da ta ƙarasa kan faffaɗar shimfiɗarsa ta zauna sannan ta ce. "Wannan wani salon ne? Ko kuma kana son nuna mini hatta Ubangiji sai ka haɗa shi da waninSa?" Sarki Gambo ya girgiza kai haɗe da cewa, "Ko kaɗan ba yadda kike tsammani ba ne, na kasance ɗaya daga cikin masu bin addinin gargajiya tun asalin iyaye da kakanni. Akwai dalili mai ƙwari da mahaifina ya ɗora ni a turbar nuna wa al'umma ni mai bin addinin Musulumci ne. Wannan furucin da na yi miki, kada ki yi tsammanin zai zame miki hujja da za ki nemi tarwatsa ni, domin har abada ba za ki iya da ni ba Zainaba." "Ai ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma Sarki Gambo." Fulani Zainaba ta furta tana nufar bakin ƙofar fita, sai da ta gyara zaman alkaybbarta sannan ta waigo ta ce. "Ni daga yau nawa aikin zai fara, domin duk kalma ɗaya da kake furta mini ina ajiye ta a mizanin da ta dace." Murmushi Sarki Gambo ya yi ya ce. "Ina yi muku fatan samun nasara Zainabata, haka kuma a wannan daren muna buƙatar raya shi tare da ke. Sai dai zan ba ku dama domin ku je ku huta, ko za ku samu sukunin nazaratar abin da yake ranku." Ta fahimci sarai abin da yake nufi, amma sai ta kawar da zancan da cewa. "Hankalina bai kwanta da zaman su Hasana a hannun Fulani Sadiya ba." Jim ya yi kamar mai nazari, don haka kawai shi ma yake jin zaman tagwayensa bai samu gurbi mai kyau ba. Amma kuma a yadda ya san Fulani Zainaba ta yi masa mummunar tsana, ba ya jin zai iya damƙa raganar rayuwar 'ya'yansa a hannunta. Don ya tabbata ko ta ɓangarensu ne za ta iya yin galaba a kansa, hakan ne ya sa a fili ya ce. "Ko da su ba jininmu ba ne, mun tabbata Fulani Sadiya ba za ta cutar da su ba. Mun aminta da Fulani fiye da yadda kuke tsammani, idan kuna mummunan tunani a kanta ya kama ku janye." Murmushi Fulani Zainaba ta yi kamar za ta tanka masa, sai kuma ta girgiza kai ta yi gaba. Tun da ta fita hadimai da dogarawa suke zubewa suna jera mata kirari, ba ta iya tanka musu ba. Sai ta wuce sashenta a gaggauce, don kanta ba ƙaramin cushe mata ya yi ba. Ta jima tana kai wa da kawowa, har ta zauna tana nazari kamar wacce aka tsikara sai ta miƙe ta fita ta kira Baiwa Lawisa ta ce mata ta gaggauta kira mata Jakadiya. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba, Jakadiya ta ƙarasa jiki a sanyaye. Don tun bayan mutuwar Fulani Khadija, zuciyarta a cike take da zullumin yadda makomarta za ta kasance. "Allah Ya taimaki Fulani, Ubangiji Ya tsare gabanki da bayanki. Ke kaɗai ce zarah a cikin taurari, hutawarki lafiya ranki shi daɗe." Jakadiya ta furta tana sake dunƙule hannunta cikin jinjina, A ɗan gaggauce Fulani Zainaba ta ce. "Jakadiya ina son sanin asalin tarihin Sarki Gambo, tarihin masarautar nan da kafuwarta." A ɗan razane Jakadiya ta ɗago, cikin in'ina ta ce. "Amm... amma... ranki shi daɗe me... yake faruwa haka?" "Ba na buƙatar tambayoyinki, amsa kawai nake buƙata." Jin furucin Fulani Zainaba ya sa Jakadiya ta sauke gwaruwar ajiyar zuciya ta ce. "Allah Ya taimake ki tarihi ne mai cike da tarin al'ajabi da ƙalubale, ki gafarce ni ranki shi daɗe. Amma duk abin da zan sanar da ke harsashe ne, ko kuma labaran su kasance masu haɗe da rashin cikakkiyar gaskiya ko tabbacin waɗansu abubuwa. Amma akwai wani kundi guda ɗaya, wanda aka buga hatiminsa da rubutun ajami, bangon jikinsa da fatar tsohon zaki Guzugu, sai dai a yadda na ji labari. Mutum ɗaya ce ta san maɓoyar wannan kundin, kuma ta san mafi yawa daga cikin sirrin masarautar nan." "Wace ce ita?" Fulani Zainaba ta furta kai tsaye cike da zaƙuwa, Jakadiya ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige. Sai da ta ƙara matsawa gaban Fulani Zainaba, ta yadda wani ba zai iya jin abin da suke tattaunawa ba sannan ta ce. "Sunanta Kursum!" "Kursum!" Fulani Zainaba ta maimata sunan tana nazari, ta sake duban Jakadiya ta ce. "Wace ce ita? Kuma a ina take? Mene ne alaƙarta da masarautar nan? Kuma a ina zan same ta?" Jakadiya ta sake russunawa cike da girmamawa ta ce, "Allah Ya huci zuciyar Fulani, tuba nake abisa kalaman da zan furta. Amma kalamar ban sani ba, ita ce kalamar da duk wani mahalukin da ke zaune a cikin masarautar nan zai sanar da ke." "Saboda me?" Fulani Zainaba ta jefa mata tambaya, Jakadiya ta ce. "Saboda babu wanda ya san yadda aka haihu a ragaya, amma a wani labari da na taɓa ji, na ji an ce akwai wasu ɓoyayyun wasiƙu da Mai martaba yake da su a turakar sirrinsa." Wannan karon a bayyane Fulani Zainaba ta sauke gwauron numfashi, haɗe da jinjina kai saboda yadda take jin baƙin al'amura daga bakin Jakadiya. Fulani ta sake kallon Jakadiya ta ce. "A ina turakar sirrin nasa take?" FULANI SADIYA Tun lokacin da aka aikawa Fulani Sadiya tagwayen marigayya Fulani Khadija, ta ji kamar ta shaƙe musu wuya su ma su mace har lahira. Amma gudun zargi ya sa ta haƙura, ta cigaba da nuna musu kulawar yaudara don tun dangin Fulani Khadija suna ɗari-ɗari har suka saki jiki da ita. Amintattun bayin Sarki Gambo biyu aka ware masu yi musu hidima da kulawa da su, don haka yaran ba su cika rigima ba tun da gari yana wayewa ake tatsar musu nonon akuya su sha. SARKI GAMBO Sarki Gambo ya jima a yana jiran Malami ya ƙarasa surukullen da ke gabansa, sai da ya kammala tsaf sannan ya dubi Sarki Gambo ya ce. "Ban yi tsammanin ganinka a daidai wannan lokacin ba." Sarki Gambo ya sharce gumin goshinsa ya ce. "Dalilin hakan ne ya kawo ni ya kai babban matsafin da nake aifahari da shi." Malami ya saki murmushin jindaɗi, don yana matuƙar son a fasa masa kai. Ya kalli Sarki Gambo alamun ya faɗi abin da yake tafe da shi, sai da ya gyara zama sannan ya ce. "Mun zo ne domin mun san wanda ya kashe mana Fulani, kisa mafi muni da wulaƙanci." "Sanin makashin ba shi zai fisshe ka ba Sarki Gambo, a yanzu babban ƙalubalen da ke gabanka ya ninka mutuwar Fulani Khadija, domin kuwa ita tuni ta mutu. Sai dai mu jira yi ruhinta tun da ya kasance mai tsarki, amma a yanzu tagwayenka sune manyan ƙaddarorin da za su taɗe duk wani burin rayuwarka." A hargitse Sarki Gambo ya ce. "Ban fahimce ka ba Malami, mene ne zai faru da tagwayen da nake fatan su zame mini sanyin idaniya?" "Ba matsalar ce za ta same mu ba, idan har kana tunanin haka ka dakata. Domin idan har matsalar a gaba take za mu iya cimma mata har mu magance ta, ina son Sarki Gambo ya sani. A halin yanzu Hassana da Husainarka sun kasance nakasassun da ba za su amfane ka ko su amfani masarautar nan ba. A taƙaice dai, kai da wanda ba shi da magaji a ɓangaren sarauta ɗaya kuke, ɗaya tana ɗauke da shanyewar ƙafa da hannuwa. Yayin da ɗaya ta samu matsalar makanta da ta ƙwaƙwala, wannan wani mummunan al'amari da zai iya daƙile komai na rayuwarka." *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [25/11, 22:11] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA TARA *MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR* 'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki. zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp. Location: Kano Sai kun zo💃🏻 Masarautar Zulwara Sai da Boka tsumbur ya gama sauraron tsawar da kogon dutsen yake yi, sannan ya dubi Sarki Dikko ya ce. "Haƙiƙa akwai sabon al'amarin da zai faru a wannan zuwan naka Sarki Dikko, ta wani fannin nakan iya ce maka kai mai nasara ne. Sai dai kuma akwai duhun da na hango yana mamaye da tauroronka, tauraronka ya kasance Himlu don haka nake..." "Amma mun jima da sanin tauraronmu Surdanu ne Boka tsumbur. Kuma wanne irin duhu aka hango mana, shin yana iya cutar da mu ko akasin haka?" Sarki Dikko ya katse boka Tsumbur, bai tanka masa ba ya cigaba da shafa ƙasar shurin gabansa yana wani zane a kanta sannan ya ce. "Tauraronka Himlu ne kuma ɗabi'ar nari, sannan duk wani bincikena bai bankaɗo mini ainahin abin da yake ƙunshe a cikin duhun ba." Ajiyar zuciya Sarki Dikko ya sauke cikin damuwa, yana shirin yin magana boka tsumbur ya katse shi da cewar. "Sarki Dikko kuna iya ba mu wuri, domin a yanzu haka muna da babban baƙo, shugaban rauhanai na ƙarƙashin ƙasa ya ziyarce mu. Matso kusa mu sanar da kai sharuɗɗanmu, da dokokin da za mu gindaya maka." Sarki Dikko kamar yana jira, ya yi saurin matsawa kusa da boka tsumbur. Ya jima yana yi masa raɗa, sai dai tun bai kammala ba gumi ya jiƙe shi sharkaf saboda tsananin fargaba da tashin hankali. Har ya buɗe bakinsa zai yi magana boka tsumbur ya ɗaga masa hannu da cewar. "Mun riga da mun gama zartar da hukunci Sarki Dikko, don haka dabara ta ragewa mai shiga rijiya. Amma muna iya baka shawara, idan har buƙatar hakan ta kama." Jiki a sanyaye Sarki Dikko ya miƙe, suka fita da Waziri yana fargabar sharuɗɗan da boka ya gindaya masa. Sarki Dikko yana komawa gida kai tsaye turakarsa ya shiga, kai kawo ya dinga yi a cikin ɗaki cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali. 'Shin kana ganin za ka iya fita a kan muradin boka Tsumbur? Ta ina za ka fara?' 'Kada ka manta duk abin da ka yi, za ka yi shi ne domin kyawun goben 'ya'yanka. Idan har ka gagara yin haka, sannu a hankali watarana za a shafe tarihinka da irin sarautar da ka shimfiɗa a doron ƙasa.' 'Buƙatar boka ba abu mai sauƙi ba ce, ya zame maka wajibi ka zage damtse domin gujewa kuskure masa.' Ire-iren kalaman da zuciyar Sarki Dikko ta dinga wassafa masa kenan, cikin tsananin damuwa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. "Ya zama dole mu nemo wa kanmu mafita." Cikin sauri ya buɗe wata ƙaramar ƙofa da ke bangon Yamma na cikin ɗakinsa, wani tsoho ne tukuf a zaune. Sai da Sarki Dikko ya zaune a gefensa sannan ya ce. "Muhimmiyar magana ce ta kawo ni wurinka Babagana." "Na riga da na san haka, domin banza ba ta kai zomo kasuwa." Tsohon ya furta muryarsa tana rawa, Sarki Dikko ya ce. "Ina mai cigaba da ba ka haƙuri bisa killace ka da na yi a nan na tsahon shekaru, duk da na tabbata duniya ta jima da binne shafin rayuwarka." Babagana ya saki murmushin takaici sannan ya ce. "Lokaci zai zo da zan bayyana a idon al'umma, a wannan gaɓar da za ta zo kuwa ina matuƙar tausayinka Sarki Dikko." Sarki Dikko ya zuba masa manyan idanunsa da suka kaɗa jajir, ya dafa kafaɗar Babagana ya ce. "Kafin lokacin mun gama samun biyan buƙatun kanmu har mun hallaka ka." "Lokaci ne zai nuna, don yana gab da zuwa a daidai wannan gaɓar." Babagana ya furta yana sakin murmushi, duk tsahon shekarun da Babagana ya ɗauka a wannan ɗakin bai taɓa jin Babagana ya furta doguwar magana haka ba. Don haka tsoro ya so mamaye zuciyarsa, amma gudun kada ya nuna a gabansa ya sa shi cewa. "Babagana ban san abin da kuka taka ba har kuke ƙoƙarin nuna mana ƙwarin gwiwarku? Shin mene ne abin da kuka taka?" Kamar yadda yake yi akai-akai, haka yanzun Babagana ya fara tari sama-sama. Sai da Sarki Dikko ya miƙa masa ruwa ya sha, sannan ya ce. "Ƙwarin gwiwata tana gab da zuwa, sai dai a wanne lokaci? Ni kaina ban sani ba, amma na sani ba za ta taɓa bari gangar jikina ta mace a hannunka ba." Ajiyar zuciyar Sarki Dikko ya yi sannan ya ce. "Mu ajiye tattaunawarmu a gefe, za mu ajiye mata lokaci domin mu samu tattaunawa." Jinjina kai Babagana ya yi ya ce, "Ina sauraronka, wataƙila ina da masaniya a game da damuwarka." Gyara zama Sarki Dikko ya yi ya ce, "Bayan Waziri babu wanda ya san da wannan sirrin namu Babagana." "Ba iya Waziri ba, har waɗanda ba ka taɓa tsammani ba sun san da wannan matsalar taka, kai dai ka saka ido mutanen da ke kewaye da kai. Hatta shi kansa Waziri ban gama aminta da shi ba, amma wannan ra'ayinka ne ka ɗauki shawarata ko ka watsar da ita." Shiru Sarki Dikko ya yi da jin kalaman Babagana, ya ƙura masa ido yana kallo tare da sake jinjina baiwa da hikimar da yake da ita. Sai da ya gyara zamansa sannan ya ce. "Dattijo Babagana, shin kuna nufin bayan Waziri akwai waɗanda suka san ina haifar yara masu nakasa?" Gyaɗa masa kai Babagana ya yi ya ce. "Ba ka yi mamakin yadda aka yi ni da nake kulle a ƙarƙashin ikonka a tsawon shekaru na sani ba, sai waɗanda suke rayuwar 'yanci a doron ƙasa? Shi ya sa na ce ka cigaba da kula da hagunka da damanka, domin za ka sha mamaki idan ka ji masu son bankaɗa labulen sirrinka." "Sautari muna mamakin da tambayar kanmu, shin kuna taimakonmu ne ko kuwa mu maƙiyan juna ne Babagana?" Sarki Dikko ya furta yana kallon Babagana, shi ma kallonsa yake sai kuwa ya saki murmushi ya ce. "Kada ka saki jiki ɗari bisa ɗari da ni Sarki Dikko, domin murmushin maƙiyi ba abin yarda ba ne. Duk wani taimako da za ka ga na yi maka, ina yi ne domin na haskawa mai shirin fitar da ni hanya." "Wace ce ita?" Sarki Dikko ya wurga masa tambaya a kausashe, a madadin Babagana ya ba shi amsa sai ya saki murmushi ya ce. "Bari na saukaka maka bincikenka, mace wacce ta kasance tana yawo a cikin rayuwarka. Amma ka rubuta ka ajiye, duk daren daɗewa za ta zo har cikin nan sannan ta tono duk wani ƙulli da ka binne kuma ta bayyana a idon duniya." Haɗiye yawu mai ɗaci Sarki Dikko ya yi ya ce, "Mun ji duk kalamanku, ita ma wannan maganar mu ajiye ta a gefe. A ina zan samu Kursum? Kuma a wannen yanki zan haɗu da ɗan'uwanka tsoho Sulaimanu? Domin Boka Tsumbur yana buƙatarsu a cikin aikin da ya yi mana." "Ba ni zan baka wannn amsar ba, amsarka tana cikin littafin 'Ruwa A Wuta' wanda ka binne shi tare da gawar Sarauniya Humaira." A hargitse Sarki Dikko ya ɗago yana kallonsa, Babagana ya gyaɗa masa kai ya ce. "Domin kuwa ga dukkan alamu tarihi ne yake yunƙurin maimaita kansa." Ajiyar zuciya suka saki su duka biyun, daga haka Sarki Dikko ya miƙe ya ce. "Na bar ka lafiya Babagana, ina fatan za ka cigaba da hutawa cikin aminci." Yana gama faɗa bai jira cewar Babagana ba ya fice daga ɗakin. Sai da ya tabbatar ya rufe ƙofar, sannan ya cire kubar ya wuce maɓoyarsa ta sirri sannan ya zauna ya zabga tagumi. Yana nan zaune babu jimawa, ya ji sallamar Jakadiya daga bakin ƙofa. Sai da ya ba ta izinin shigowa sannan ta shiga cikin girmamawa ta zube a ƙasa tana faɗin. "Allah Ya taimake ka, Ubangiji Ya ƙara maka lafiya. Allah Ya sauki Fulani Hauwa kulu lafiya, sai dai a gafarce ni abin da ta haifa Allah Ya yi masa rasuwa." Sarki Dikko ko a jikinsa, saboda ya san ko babu komai yana da waɗanda za su gaje shi su ɓangaren sarauta a wannan lokacin. Don haka ya ce, "A cewa Shamaki su yi duk abin da ya dace, idan an kintsa Fulani muna buƙatar ganawa da su." Godiya Jakadiya ta yi masa ta fice, sannan ta ƙarasa ɗakin Fulani Hauwa kulu. Sai dai tana zuwa ta same ta a bakin ƙofa, ta zube a ƙasa ta ce. "Allah Ya taimake ki ranka shi daɗe ya ce a sanar da Shamaki ya yi abin da ya dace." Gyaɗa kai Fulani Hauwa kulu ta yi, ta ce. "Ki je kawai Jakadiya, duk abin da ya dace zan aiwatar wa abin cikina, daga haka kuma zan binne shi a ɗakina domin hankalina zai fi kwanciya." Jakadiya tana son sake magana, ganin babu fuska ya sa ita yi godiya sannan ta fice daga sashen Fulani Hauwa kulu. Bayan fitarta Fulanin ta shige ɗakinta, ta shafa cikinta tana sakin murmushi sannan ta ce. "Tun da na gama da wannan shafin, a yanzu ne zan dawo Fulani Karima kamar yadda nake a baya, ba Fulani Hauwa kulun da aka sanni ba." Masarautar Judala Kukan da jaririya Batul take tsalawa shi ya tashi mafi yawan bayin da ke kwance suna bacci, jiki a sanyaye Indo ta ƙarasa cikinsu hannunta rungume da jaririyar. Sai da dogaran suka ga su Indo sun zauna, sannan suka wuce suna cigaba da faɗan kamar yadda suke yi a baya. Ɗaya bayan ɗaya haka suka dinga bin ta da kallon tuhuma, wasu suka fara mamakin yadda ƙaramar yarinya ta haihu lafiya ƙalau ba tare da sun ji nishinta ba. Wasu kuma ganin yadda take raɓe-raɓe, ta sake birkicewa ya sa suka fara zargin ko ba 'ya ce ta halaliya ba. Kallon Zinaru ta yi idonta yana cigaba da zubar da hawaye, Zinaru ta kawar da kai gefe alamar can ta matse miki tana sakin guntun tsaki. "Ke yarinya ki ba ta ta sha mana, wannan ai ɗaukan hakki ne. Ba kya ganin yadda take tsala kuka?" Wata dattijuwa da aka kamo su tare da su Indo ta furta, birkicewa ta sake yi ta shiga inda-inda ganin haka ya sa suka sake tabbatar da lallai haihuwar fari ce Indo ta yi. Saboda sun lura da yadda take jin nauyin shayar da ita, murmushi Dattijuwar ta saki ta ce. "Ƙuruci dangin hauka, yarinya ai kowa kika gani da haka ya fara. Bari ki gani, idan aka ce za a bi ta kunya ai da ke ma ba ki kawo haka ba." Dattijuwa ta sake furtawa, sannan ta miƙe ta isa gaban Indo. Sakata ta yi ta gyara zamanta, ta saka hannu tana ƙoƙarin ciro maman Indo. Wata mata daga gefe ta ce. "To ko ruwan maman ne bai zo ba? Kin san wasu fa dama sai zuwa wani lokaci yake sauka." Kamar Indo ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ta, bakinta har rawa yake ta ce. "Eh bai zo ba." "To 'yar nan ai ba shiru za ki yi ba, yanzu kin ga mu baƙi ne a wurin nan. Ballantana a tatsar mata nonon akuya." A daidai lokacin da dattijuwar ta furta haka Uwar bayi ta ƙarasa cikin gadara ta ce. "Kai! Ba ma son shashancin banza da wofi, lafiya kuka cika mutane da surutu tun asuba ba ta yi ba? Jaririyar wace da ba za ta kula da ita, sai ta hana mutane bacci?" Gabaɗaya shiru suka yi, sai dattijuwar ce ta sake cewa. "Tuba muke yi, dama yarinyar nan ce ta haihu. To kuma yanzu haka jaririyar sai kuka take ga babu ruwa a maman." A wulaƙance Uwar bayi ta dubi Indo da ke raɓe tana zare ido, ta taɓe baki ta dube su ta ce. "Kuma duk cikinku babu mai shayarwa? Ba za a samu wata ta ba ta kafin nata ya zo ba?" Shiru suka yi babu wanda ya iya magana, sai wata busasshiyar mata ce ta ɗaga hannu ta ce. "Allah Ya taimake ki yanzu haka shayarwa nake, idan mahaifiyar jaririyar ta lamunce sai na shayar da ita." A sheƙe Uwar bayi ta dubi Indo ta ce, "Kin ji ai abin da ta faɗa, idan kuma ba za ki ba ta ba sai ki bar ta ta yi ta tsala kuka." Tana gama maganar ta yi gaba, har ta fara tafiya ta waigo ta ce. "Idan na sake jin hayaniya har na sake fitowa, to kuwa za ku yaba wa aya zaƙinta." Tsuru-tsuru suka yi duk tsoro ya sake mamaye su, a hankali Indo ta ƙarasa wurin matar da ta ce za ta shayar da jaririya Batul. Ta miƙa mata ita cikin sanyin jiki ta yi mata godiya, zuciya ɗaya matar ta karɓi Batul ta zauna sannan ta saka mata mama a baki. Batul tana kai bakinta jikin matar sai gani suka yi matar ta yanke jiki ta faɗi. Ummou Aslam Bint Adam🌚 [26/11, 21:49] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA GOMA *AF'S DATA PLUG* _MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_ Monthly data — valid for 30 days _📶MTN DATA_ • 500MB — 450 • 1GB — 700 • 1.5GB — 1000 • 2GB — 1,300 • 3GB — 1,900 • 5GB — 2,100 _📶AIRTEL DATA_ • 1GB — 750 • 2GB — 1,400 • 3GB — 2,150 • 3.5GB — 1,800 • 5GB — 2,850 • 6GB — 2,900 • 10GB — 5,600 𝙋𝙖𝙮𝙢𝙚𝙣𝙩 : Opay — 7049439332 AFNAN ADAM 𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027 _Thank you❤_ Masarautar Kajjura Shiru Jakadiya ta yi kamar mai nazari, saboda sai a lokacin take ganin girman wautar da ta aikata na sakin bakin da ta yi a wurin Fulani Zainaba. Cikin inda-inda ta ce. "Na'am... ranki... shi daɗe, dam... dama na ce a yi mini afuwa ban san wurin da turakar sirrin take ba." Kallon tsaf Fulani Zainaba ta yi mata, ta ƙarasa gabanta murya a kausashe ta ce. "Idan har kika ɓoye mini wani abu, to tabbas sai na haɗa miki tuggun da ba za ki taɓa fita ba. Ko a kan mutuwar Fulani Khadija, ina iya zarge wuyanki har gaban Mai martaba. Don haka ina son ki feɗe mini biri har wutsiyarsa, idan ba haka ba za ki gane ba ki da wayo." Cikin Jakadiya ne ya kaɗa, cike da tsoro ta ce. "Don Allah ki yi mini rai, ki yi mini aikin gafara ranki shi daɗe." Gyaɗa mata kai Fulani Zainaba ta yi ta ce, "Ina sauraronki." Sai da Jakadiya ta waiga, ta ƙara matsawa gaban Fulani har sai da ya kasance suna jin numfashin juna sannan ta ce. "Ranki shi daɗe, wani ɓoyayyan sirrin ɗakinsa ne da ke cikin turakarsa. Idan kika shiga rumfar (Falo) ki tsaya a daidai tsakiyarsa, idan kika ɗaga kanki sama daga jikin azarar za ki hangi wata gajeriyar aska a saƙale a sama, ita wannan askar ta tsafi ce. Ita ce za ki ɗauka, ki shafa jinin sarki gambo a jiki. Saboda a yadda na taɓa jin labari, an ce duk shigar da zai yi ɗakin sai ya yanki jikinsa da wannan askar. Jininsa ya taɓa jikin askar, a haka zai zo saitin tsakiyar rumfar ya fara haskawa da ita. A nan za ki ga daidai ƙofar da take shimfiɗar wurin tana yayewa, da zarar kin soka askar ƙasar wurin za ta dare. Idan za ki shiga ki tabbatar askar tana hannunki na hagu, kuma da ita za ki shiga har cikin ɗakin. To da zarar kin shiga, shimfiɗar wurin za ta haɗe ta koma yadda take." A fili Fulani Zainaba ta sauke ajiyar zuciya, tare da sharce gumin da yake saman goshinta. Cikin damuwa ta ce. "Jakadiya dole sai ta wannan hanyar?" Gyaɗa kai Jakadiyanta yi ta ce, "Ai ba a nan ma gizo yake saƙar ba ranki shi daɗe!" "A ina ne?" Fulani Zainaba ta yi saurin wurga mata tambaya, gyara zama Jakadiya ta yi ta ce. "A wurin fitowar ne, don a yadda na ji labari an ce a yadda Sarki Gambo ya sihirce ɗakin ba ya fitowa a take a lokacin da ya shiga, har sai doshin magriba. Sai dai ina jiye miki tsoron kada Sarki Gambo ya gano ki ranki shi daɗe, domin na tabbata sai ya zartar miki da mummunan hukunci, don an ce ya taɓa hallaka ƙaninsa Galadima wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya saboda wannan ɗakin. To da yake dai jita-jita ce, amma zancan da nake yi miki Galadima ya yi ɓatan dabo har yau ba a sake ganinsa ba. Dalilin haka ya sa ake yi masa wannan zargin, amma Allah Shi ya bar wa kansa sani." Jakadiya ta numfasa sannan ta cigaba da cewa. "Saboda an ce ba iya waɗannan takardun ne a cikin ɗakin ba, ɗakin ya haɗa duk wani babban sirri da ƙudurin Sarki Gambo. Don a wata majiya da na ji, an ce akwai wata doguwar hanya idan aka bi ta har maɓoyar da Kursum take rayuwa. Don har kawo yanzu, babu wanda ya tabbatar da ainahin abin da ke ƙunshe a cikin ɗakin. Saboda babu wanda ya taɓa shiga cikinsa ya fito har ya cigaba da rayuwa, sakamakon kisan wulaƙancin da yake sa wa ayi wa mutum. Saboda a zargin da ake yi, mutane kusan uku ne suka taɓa gangancin shiga." Kan Fulani Zainaba ne ya cunkushe, ta miƙe ta fara zagaye tana nazartar kalaman Jakadiya. Duk sai ta ji gwiwarta ta yi sanyi, don gani take ba za ta iya cimma alƙawarin da ta ɗaukar wa marigayin mijinta Najibullah ba. "Ke da tsoho Sulaimanu kaɗai, kuka rage waɗanda za ku cika muradin ahalina. Sai kuma jinina da ke jikinki idan kin sauka lafiya, Zainaba ina ji a jikina za ki yi tsawon rai har ki cika mini burina." Fulani Zainaba ta tuna kalaman marigayi Najibullah, nan take ta hau girgiza kai ta ce. "In Shaa Allahu zan iya, zan cika maka burinka matuƙar ina numfashi. Idan har ni da tsoho Sulaimanu mun gagara cika muradinka, jininmu da ke rayuwa a masarautar nan zai kawo ƙarshen komai In Shaa Allah Najibullah. Na zaɓi ya yi ɓoyayyar rayuwa ne, har zuwa lokacin da zai ɗauki fansar zuri'arku." Jakadiya tana daga zaune ta yi kasaƙe, tana nazari da mamakin yadda aka yi Fulani Zainaba take da ɗa a cikin masarautar ba tare da kowa ya sani ba. Gyaran muryar da Fulani Zainaba ta yi ya sa Jakadiya ta sake russunar da kai ƙasa ta ce. "Amma Allah Ya taimake ki, idan kin lamunce zan sanar da ke wata maganar." Cikin sauri Fulani Zainaba ta waiga ta ce, "Je ki kanki tsaye Jakadiya." Jakadiya ta yi gyaran murya sannan ta ce, "Allah Ya taimake ki akwai abin da ban sanar da ke ba, amma don girman Allah ki dubi darajar Allah ki rufa mini asiri ranki shi daɗe." Shiru Fulani ta yi don ta fahimci maganar Jakadiya tana da matuƙar muhimmanci, don haka ta zauna a kujerar da ke fuskantarta ta ce. "Na yi miki alƙawari Jakadiya, tsakanina da Allah babu mahaulikin da zai san da wannan tattaunawar tamu." Jinjina kai Jakadiya ta yi ta yi ƙasa da murya ta ce, "Allah Ya taimake ki, bayan ke fa akwai wacce take dakon bankaɗa labulen sirrin Sarki Gambo. Wato Fulani Sadiya, don ta jima tana son ta samu irin wannan damar da kike son samu. Kuma ni na san Fulani hatsabibiya ce, matuƙar ta samu labarin kin ziyarci ɗakin sirrin Sarki Gambo, na tabata za ta iya aikata komai domin cikar muradinta." Ajiyar zuciya Fulani Zainaba ta sauke ta ce, "Na fahimci komai Jakadiya, tun ranar da Sarki Gambo ya kawo ni sashen matansa a matsayina na matarsa. Na fara nazartar hali da ɗabi'ar Fulani Sadiya, don haka har yanzu nake kan binciken yadda aka yi Fulani Khadija ta mutu, da irin kisan cin zarafin da aka yi mata. Don abin da ya sa na gagara nutsuwa an tabbatar da an cire zuciyarta, wanda hakan yake alamta mini akwai dalilin yin hakan." Jakadiya da ta shiga nazarin yadda suka dawo, suka samu Fulani Khadija a daidai gaɓar da take gargarar mutuwa ta ce. "Allah Ya taimake ki duka zancanki a hanya yake, Allah Ya bayyana gaskiya duk ɗacinta." Fulani Zainaba ta amsa mata sannan ta sallame ta, tare da ba ta kayan sha tara ta arziki. Don tana buƙatar ta huta, domin ta san ta yadda za ta tunkari turakar sarki Gambo. Saboda ta ci alwashin duk rintsi, ba za ta shafe mako guda ba tare da ta tunkari turakar sirrinsa ba. Don ta haka ne za ta samu sukunin karanta wasiƙun da za su yi mata iso zuwa ga wurin da aka killace Kursum kamar yadda Jakadiya ta sanar da ita, cewar ita ce ta san kowanne irin sirrin da ke cikin masarautar. Fulani Sadiya Jakadiya tana fita daga sashen Fulani Zainaba kai tsaye sashen Fulani Sadiya ta nufa. A lokacin da ta ƙarasa Baiwa Sakina tana zaune tana matsa wa Fulanin ƙafa, kamar an jefo ta daga sama haka Jakadiya ta faɗa ɗakin tana sauke numfashi ta ce. "Barka da hutawa ranki shi daɗe, barka da wannan lokaci gatan marar gata. Shugabar kowa mai tausayin talakawa, Allah Ya taimaki tauraruwa mai haske sasarin samaniya. Hutawarki lafiya giwar sarki kuma 'yar gaban goshinsa." Kafin Jakadiya ta gama bambaɗanci, tuni Fulani Sadiya ta gama karantar akwai wata muhimmiyar maganar da ke tafe da ita. Don haka cikin isa da ƙasaita ta ce, "Jakadiya muna saurarenki." Satar kallon Baiwa Sakina ta yi ta ce. "Allah Ya taimake ki maganar tana buƙatar sirri." Fulani Sadiya ta dubi Baiwa Sakina, don ta fahimci abin da take nufi amma sai ta ce. "Tafi kanki tsaye Jakadiya babu wata damuwa." Baiwa Sakina ta cigaba da matsa mata ƙafa, kanta a sunkuye tamkar ba ta san wainar da ake toyawa ba. Jakadiya ta gyara zama sannan ta zayyane wa Fulani Sadiya duk yadda suka yi da Fulani Zainaba, sannan ta ɗora da cewa. "Ranki shi daɗe babban abin da ya ba ni mamaki, da na ji Fulani tana cewa koda ta mutu ɓoyayyan ɗanta da ke cikin masarautar nan zai maye gurbin muradinta domin jini ba wasa ba ne." A hargitse Baiwa Sakina ta ɗago, saboda tashin hankali har sai da ta ƙware da tari. Amma da yake maganar Jakadiya ta girgiza Fulani Sadiya sai ba ta lura da yanayin da Sakina take ciki ba, cikin tsananin mamaki Fulani ta ce. "Jakadiya kina nufin ita Zainaba ce take da ɗa a cikin masarautar nan?" Cikin son gwaninta da neman suna Jakadiya ta gyaɗa kai ta ce. "Na rantse da Ubangiji mai girma abin da ta faɗa kenan ranki shi daɗe." Shiru Fulani ta yi tana nazari, sai kuwa ta ce. "Idan kuwa da gaske ɗan Zainaba yana raye to waye Sarki Gambo ya kashe? Domin kuwa duka duniya kowa ya shaida an kai masa jariri, kuma Zainaba ta haihu a wannan lokacin." Jakadiya ta zuba tagumi cikin nazari ta ce, "Abin da ya ɗaure mini kai kenan ranki shi daɗe, domin kuwa uwar bayi ce ta karɓi haihuwar Zainaba, idan kuwa haka ne ya zama wajibi ta amsa duka waɗannan tambayoyin." Da sauri Fulani Sadiya ta jinjina kai ta saki murmushi mai ɗauke da ma'anoni sannan ta ce. "Jakadiya!" Yadda Fulani ta ambaci sunan Jakadiya ya sa ta ɗago gabanta yana faɗuwa, sai ta ga Fulani ta dubi Baiwa Sakina ta ce. "Kin yi mini mai wuya da har kika binciko mini wannan maganar Jakadiya, sai dai akwai yuwuwar ki sake zuba mini ido a kanta sosai domin akwai muhimman bayanan da zan samu daga gare ki." Jakadiya ta jinjina kai, sai Fulani Sadiya ta sake duban Baiwa Sakina ta ce. "Ke kuma Sakina! Ina son damƙa miki kaso mafi girma na bincikena a hannunki." A ɗan hargitse Baiwa Sakina ta ce, "Na'am... iye ranki shi daɗe." Fulani Sadiya ta yi mata kallon tsaf sannan ta ce. "Ina son ki nutsu, domin tun a wancan lokacin na ce miki ƙofa a buɗe take da za ki cigaba da sanin waɗansu sirrikana." Gumi ya shiga karyo wa Sakina, ta shiga gyaɗa kai gabanta yana cigaba da faɗuwa. "Don haka, na ɗora miki alhakin binciko mini yadda wannan yanayin ya kasance, zan kira Uwar Bayi na ji daga gare ta. Ke kuma daga yau ne za ki fara shiga jikin Zainaba, domin ki gano mini a wurin da ɗanta yake a cikin masarautar nan. Haka kuma, ina son ki kasance mata lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi, ta yadda zan dinga samun bayanan sirri daga gare ki. Idan ta kama ma..." Sai kuma Fulani ta yi shiru kamar mai nazari sai ta cigaba, "Wannan wata magana ce daban zan neme ki." Haɗiye yawu Sakina ta yi cikin tsananin tashin hankali ta ce. "An gama ranki shi daɗe." "Koda wasa, idan har kuka kuskura kuka munafunce ni, ko kuka ci amana. Ko kuma na gano wani abu da kaina, na rantse da girman Yesu mai ceto sai na shayar da ku ruwan mamakin da har gawarku ta ɓace a ƙarƙashin ƙasa ba za ku taɓa mantawa da ni ba." Baiwa Sakina ba, hatta Jakadiya sai da ta razana da jin furucin Fulani Sadiya da kalaman rantsuwarta na ƙarshe. Sai kuma suka ji ta saki dariya ta ce. "Ita kuma Fulani Zainaba ku bar ni da ita, sai na shirya mata tuggun da za ta da gwammaci mutuwarta a kan rayuwarta. Domin sai ta yi danasanin shiga ɗakin sirrin Sarki Gambo da za ta yi, ba zan sa ya kashe ta ba. Zan bar ta ne har zuwa lokacin da zan gano wanne jinin nata ne yake numfashi a doron ƙasa da take cin alwashinsa." Duk jikinsu ne ya yi sanyi, tsoron Fulani Sadiya da kaidinta ya mamaye zuciyoyinsu. Ban da gyaɗa kai babu abin da suke yi, Fulani ta dube su ta ce. "Za ku iya tafiya, zuwa an jima kowaccenku zan aiko mata da da turmin zani da kallabi. Idan Allah Ya kai mu gobe da safe, ku zo zan shirya liyafa tare da ku. Wannan somin taɓi ne daga irin manyan darajojin da zan ɗaga ku a gidan, matuƙar kuka cigaba da yi mini biyayya." Duk da sun ji daɗi amma har lokacin zuƙatansu cike suke da fargaba da tashin hankali, cikin yaƙe suka russuna suka ce. "Godiya muke ranki shi daɗe." Umarnin fita ta ba su, bayan sun fita ta cigaba da zagayen ɗakin tana nazari sannan ta ce. "Lokaci ya yi da zan yi amfani da ku, da zarar na gama cin moriyar ganga sai kuma na yasar da kwauronta." Fulani Sadiya ta ƙarasa maganar tana sakin murmushin ƙeta. Sarki Gambo A hargitse Sarki Gambo ya miƙe tsaye cikin ƙaɗuwa da tashin hankali. Jikinsa har yawa yake idanunsa suka ƙanƙance, wata sharɓeɓiyar takobin da ke rataye a jikin bango ya zaro ya saita daidai wuyan Malami ya ce. "Ka sanar da mu gaskiyar abin da kuka faɗa, idan ba haka ba za mu datse kanku." A madadin Malami ya razana, sai ya saki murmushi ya ce. "Ba za ka iya kashe ni ba Sarki Gambo koda kuwa a sume nake, kai ko ina gargarar mutuwa na fi ƙarfinka!" Kalaman Malami suka ƙara harzuƙa Sarki Gambo, da sauri ya wurgar da takobin ya cakumi wuyan Malami ya shaƙe ya ce. "Kada ku sake furta munanan kalamai akan jininmu, kun yi sa'a kune Malami. Da mun rantse da ubangiji haske sai mun azabatar da ku." Duk da jikin Malami yana rawa irin na tsufa, amma hakan bai hana shi tattara ƙarfinsa ya hankaɗe Sarki Gambo ba. Ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce. "Da za ka ajiye zafin ranka a gefe, da na taimaka maka har ka samu ka ga hasken da zai haska maka hanya. Idan kuma kana tunanin hanyar da ka bi ita ce mafita, ga fili nan ga doki sukuwa kawai ya rage maka." Jikin Sarki Gambo ya yi sanyi, don haka ya zauna daɓar, kamar wanda aka zarewa laka a jiki. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. "Malami zuciyarmu ta gagara aminta da mummunan labarin da kuka sanar da mu. Ta yaya aka haihu a ragaya? Me ya sa sai tagwayenmu? Wane ne ya aikata mana haka?" "Tambayar da ni kaina nake wurga wa kaina kenan, sai dai har kawo yanzu da nake yi maka wannan maganar ban hangi wata alama, haske ko tauraron wanda ya aikata wannan mummunan sihirin ba." Malami ya furta cikin damuwa, jin haka ya sa Sarki Gambo ya fashe da kuka. Cikin mamaki Malami ya girgiza kai, ya dafa kafaɗarsa ya ce. "Haƙiƙa na haɗu da jajirtattun sarakuna, na yi mu'amala da sadaukai kuma jaruman mazaje. Amma ban taɓa cin karo da ingarman namiji mai dakakkiyar zuciya kamar kai ba Sarki Gambo, tabbas wannan hawayen naka na tabbata ba zai tashi a banza ba. Don na tabbata ƙashin gwiwar kura har abada ya gagari fiƙar gawurtattun karnuka." Lokaci ɗaya Sarki Gambo ya goge hawayen idanunsa, ya dubi malami cikin cin alwashi, zafin zuciya da kalaman ɗaukar fansa ya ce. "Mun yi rantsu da fatalwar iyayenmu, mun yi rantsuwa da abar bauta tsumbutuwa. Mun rantse da abar bautar da kakannin kakaninmu suka mutu a wurin bautarsu, haka kuma mun yi rantse da duk wani kaifin tsini da rashin imaninmu. Duk wanda ya aikata mana wannan mummunan al'amarin, sai mun azabtar da ruhinsa azaba mai raɗaɗi. Sai mum shayar da shi ruwan dalmar da har a ƙare danginsu za su dawwama a ƙarƙashin uƙubarmu. Malami!" Ya kira sunan Malami da wata irin murya, yadda idanun Sarki Gambo suka kaɗa jajir ya sa tsoro ya ɗarsu a zuciyar Malami, don bai taɓa ganin mummunan yanayin haka a tatare da shi ba. Jiki a sanyaye Malami ya amsa, Sarki Gambo ya cigaba da ce. "Ko numfashi da arzkinmu za su ƙare, ko bayi da sarautarmu za su ƙare ko lafiya da jininmu duka mutanen yankin nan zai ƙare, mun rantse da hasken rana sai mun ɗauki mummuna mataki a kan duk wani mahaluki da yake da saka hannu a wannan mummunan al'amarin." Malami ya dafa hannunsa ya ce, "Ina tare da kai ɗari bisa ɗari sadaukin sadaukai, ni mai haska maka kowacce hanya ce da za ta bayyana gaskiya. Musamman da ya kasance waɗannan yara su kaɗai za ka iya mallaka har ƙarshen rayuwarka..." "Mene ne mafita malami? Kuma ta ina za mu fara?" Sarki Gambo ya katse shi, wani kan ƙwarangwal Malami ya ɗauka ya rubuta wata aya da alƙalami da tawada a tsakiyar kansa. Sai ya kafe shi a kan allon farin ƙarfe, ya hura masa wuta yana kiran waɗansu sunayen aljanu. Ya jima yana abu ɗaya sannan ya ɗago fuskarsa da ta haɗa gumi sharkaf ya ce. "Na hango mafita guda biyu, wacce idan muka bi su za mu samu sukunin kamo bakin zaren." Tsoho Sulaimanu Kamar yadda ya kasance duk sati a kan buɗe ɗakin da tsoho Sulaimanu, shi da Kursum suke rayuwa ake ba su ruwa haka a wannan ranar ma ta kasance. Sai a gabannin wannan ranakun ba su dalilin da ya sa ake kawo musu abinci akai-akai ba, hakan ne ya rage musu raɗaɗin zaman ƙuncin da suke ciki. Kamar yadda yake a bisa al'adarta, a yanzun ma tana zaune tana rubuce-rubuce a jikin bango duk da ba ta iya tantance abin da take rubutawa a kuma daidai wurin da take rubutawa saboda tsananin duhu. A wannan ranar tsoho Salaimanu ya ci alawashin sake tunkararta da tambayoyin da ya sha jifanta da su, duk da a duk lokacin da ya yi mata ba sa wanyewa lafiya ƙalau shi da ita. Saboda idan ya yi mata tambayoyin haka za ta dinga kartar jikinsa cikin huci da ɓacin rai, har sai da ya yi tunanin ko ba ta magana saboda tun da ya shiga ɗakin bai taɓa jin kalma ɗaya daga bakinta ta amsa masa ba. Ta yadda ya tabbatar da tana magana, da yake yawan jin tana zikiri da istigifari. Sai kuma idan ta tashi sallah ya ji tana karatun sallah, wani lokacin kuma haka za ta wuni tana kuka ko ta wuni tana karatun alƙur'ani. Tsoho Sulaimanu a daidai wannan gaɓar shi kansa ya saddaƙar da rayuwarsa za ta ƙare a cikin wannan baƙin ɗakin, domin tun bai ɗauki shekaru a gidan ba Sarki Gambo ya sha turowa a tafi da shi, domin ya bada kai bori ya hau. Amma a kullum aka kai shi furucin da yake faɗa shi yake sake maimaitawa, don haka Sarki Gambo ya ce a ajiye shi su cigaba da zama da Kursum har ƙarshen rayuwarsu. "A tsawon shekara sama da goma da muka shafe tare a ɗakin nan, ya kamata a ce zuwa yanzu kin watsar da duk wani kallo da zargi da kike yi mini Kursum. Na sha faɗa miki ni ba na daga cikin mutanen Sarki Gambo, amma a kullum gani kike lulluɓe kura nake yi miki da fatar akuya. Wallahi-tallahi ni ma zalincinsa ne ya kawo ni wurin nan, saboda na cika burin marigayi Najibullahi." Tsoho Sulaimanu ya ƙarasa maganar cikin kuka, ƙashin da take rubutun a jikin bango ta wurgar. A tsorace tsoho Sulaimanu ya ja da baya, don ya yi tsammaninsa a wannan karon ma za ta fara yagar namansa kamar yadda ta saba yi a baya. Ya ji sautin tafiyarta ta ƙaraso wurinsa, cikin dakusasshiyar muryarta mai haɗe da tsufa ya ji ta ce. "Wane ne kai? Me ya sa ka damu da sanin dalilin zuwana? Mene ne dalilinka na ambatar sunan Najibullah? Ya aka yi ka san shi? Yaushe Najibullah ya mutu?" Da mamaki tsoho Sulaimau yake bin wurin da yake jin sautinta, cikin tsananin farin ciki ya gyara zama domin ya ba ta amsa, don ya fahimci haƙarsa za ta cimma ruwa ba har ya san wace ce ita. *Ummou Aslam Bint Adam* 07062062624 [29/11, 23:41] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA SHA ƊAYA Masarautar Zulwara Bayan fitar Jakadiya da ta isar masa da saƙon mutuwar jaririn Fulani Hauwa Kulu Sarki Dikko shiru ya yi yana nazari, ta wani fannin zuciyarsa ta fara ɗaci game da takunkumin da boka Tsumbur ya saka masa. "Ba ni zan ba ka amsar wurin da Kursum tare da ɗan'uwana Sulaimanu suke ba, amsoshinka suna cikin littafin 'Ruwa A Wuta' wanda aka binne tare da gawar Sarauniya Humaira a cikin tsohuwar Fada." Sarki Dikko ya tuna kalaman da tsoho Babagana ya furta masa, furzar da iska mai zafi ya yi a fili ya ce. "Dole za mu ziyarci kabarin sarauniya Humaira, domin ranar biyan buƙata rai a ba a bakin komai yake ba." Yana gama faɗar haka ya buɗe wata ƙatuwar randar ruwa, hannu ya zira ya ɗauko kuba a ƙasan ruwan. Har ya nufi ƙofar fita sai kuma ya yi turus, sakamakon tuna wasu sharuɗɗa shiga cikin kabarin nata. Shiru ya sake yi cikin damuwa, kamar wanda ya tuna wani abu sai kuma ya fita da sauri. Yana zuwa harabar sashensa ya sallami masu tsaron ƙofarsa, ko kaɗan ba ya son aikata abin da idanun masarauta za su hau kansa, duk da ya san yana da ikon aikata fiye da haka. Amma sanin kansa ne, haramun ne kuma kuskure ne sannan zunubi ne halartar kabarin sarauniya Humaira tun shekarun baya. Sakamakon camfin da suka yi a kan waɗansu miyagun al'amura da suke faruwa da su, tun yana ƙarami baya mantawa ya ji an ce mahaifin kakansa ya zartar da dokar hana shiga cikin kabarin ana ajiye kayan tsafe-tsafe, ko kuma ɗiban waɗansu kayan tarihi a fita da shi domin biyan buƙata. Kabarin Sarauniya Humaira, tsohon kabari ne da ya ɗauki tsahon shekaru masu yawa. Asali an ce adaidai wurin da gawarta take, a nan ne aka gudanar da wani mummunan cin amana tsakanin wasu sarakuna da suka gabata har aka hallaka ta. Wasu kuma suka ce a wurin ne aka gudanar da yaƙin Durr, wanda shi ne silar tsaga masarautu ukun da su sarki Gambo suke jagoranta. Don a wani labarin kunne ya girmi kaka, an ce a da masarauta ɗaya ce a cikin daular. Wani hargitsi da ya gifta ne ya kawo musababbin rabuwarta gida uku, har ya zama akwai wata daɗaɗɗiyar gaba a tsakanin gidaje ukun. Sai dai kuma a labari mafi shahara, wanda har su Sarki Dikko suka samu labari kuma suka yi na'am da shi. An ce Sarauniya Humaira wata jajirtacciyar sarauniya aka yi a lokacin, mara tsoro ga dakiya da ƙarfin zuciya. Uwa-uba baiwar da aka ce tana da ita, domin duk abin da ya shige maka duhu, ko dai game da sha'anin kasuwanci, aure ko mu'amalar abin da ya shafi mulki. Matuƙar ka kai kukanka wurinta, da zarar ta ɗebi wani ruwan ta zuba a wata 'yar ƙorama da ke tsakiyar fadarta. Nan take za ta samu ilimin duk abin da ya shige maka duhu, kuma ta samu sani a game da tarin tambayoyin da aka yi mata. Asalin wannan ƙoramar an ce ta hada tushe daga babban kogin ƙasar misira, wasu kuma suka ce tushiyarsa tana da mahaɗa da babban kogin maliya. Sai dai kuma mafi yawa daga cikin masana da masu bincike, sun tabbatar da cewa wannan 'yar ƙoramar ta haɗa tushe da dukka kogunan guda biyu, daga na Maliya har na babban ƙasar Misira. Sai kuma wani shu'umin wani ƙanƙanin kogi da yake cikin dajin Buhul, wanda aka ce daji ne da manyan aljanu da rauhanai suke rayuwa. Wasu sun ce Kakan Sarauniyar Humaira yana da kyakkayawar alaƙa da aljanun wannan yankin, domin har yana da wani babban amini rauhani yake da shi. A saboda haka tun Sarauniya Humaira tana ƙarama kakanta ya kan je wannan dajin da ita, idan ya kai ta sai ta shiga cikin ƙoramar nan ta yi ta wasa tare da sa'anninta 'ya'yan aljanun wancan lokacin. Amma da labari ya faɗaɗa sai wasu suka ce wata lalura ce ta shigo da wani tsohon rauhani ta masarautarsu Sarauniya Humaira, a nan mahaifinta ya taimaka masa da maganin jinya har ya warke. Saboda mahaifinta tun yana ƙarami yake da baiwar sanin itatuwa da ganyaye domin warkar da masu lalura, kuma tun da rauhanin nan ya warke sai ya bayyana masa kansa, suka cigaba da abota har mahaifinta yake kai ta wannan dajin suna wasa da yaransa. Akwai tarin mabambamtan bayanai dangane da zuwan ƙoramar cikin fadar Sarauniya Humaira, wasu masana binciken tarihi suka ce a ziyarar da take zuwa dajin ne wani hatsabibin aljani ya ce yana sonta. Wasu kuma suka ce ba sonta yake ba, sadaukar da jininta zai yi ga wani boka da yake yi wa tsafi a wancan lokacin. Dalilin haka ya sa rauhanin nan amini mahaifinta, ya samar mata da haɗakar koguna ukun nan a cikin fadar mahaifinta. Wasu kuma suka ce ba haka ba ne domin dalilin yana ƙunshe cikin littafin 'Ruwa A Wuta' Wanda aka binne ta da shi, dalilin mutuwarta, da wasu abubuwan almara da take gudanarwa. Tare da tarin bayanan wasu al'amura na duba da ta yi kuma ta rubuta da za su faru a shekaru masu zuwa bayan mutuwarta. Sai dai shi kansa rubutun littafin an samu rarrabuwar kai game da shi, wasu suka ce Sarauniya Humaira ce ta rubuta littafin da hannunta. Yayin da wasu suka ce ta yaya za ta rubuta labarin mutuwarta? Bayan kuma tana raye, tun da an ce har dalilin mutuwarta da ƙalubalen da za a fuskanta a game da zuwa kabarinta duk ta rubuta. Waɗanda kuma suka yarda da cewar ita ta yi rubutun, sun ce ba abin mamaki ba ne tun da tana rayen ai tana da baiwar faɗar abin da zai faru a gaba kuma ya tabbata. Sunan littafin 'Ruwa A Wuta' Yana da nasaba da ƙoramar fadar Sarauniya Humaira, a lokacin da Sarauniya Humaira tana raye idan ta so yin duba ko nishaɗi ta kansa a ɗebar mata wani ruwan daban na cikin masarautar ta zuba a cikin ƙoramar, tana zubawa sai nan take tsakiyar ƙoramar ta kama da wuta, kuma a zagaye da ita ruwan da ke cikin ƙoramar bai fasa kaɗawa ba. Haka kuma duk wanda ya yi ganganci taɓa wannan ruwan a nan take jikinsa yake sandarewa, daga nan numfashinsa ya ɗauke gabaɗaya. Kuma tun da wannan al'amarin yake faruwa, ba a taɓa jin Sarauniya Humaira ta furta kalma ɗaya game da hakan ba, kuma ba ta taɓa gargaɗi ko jan hankali ga mutane a kan su kiyaye wannan ƙoramar. Tun daga ranar da aka tsinci gawar Sarauniya Humaira, sai aka ga ƙoramar tana ci da wuta. Sai ruwan ya fara kwarara daga cikin raminsa, haka ita ma wutar ta fara ƙaruwa. Ana tsaka da tsoron halin da aka tsinci kai, sai aka ji irin muryar Sarauniya Humaira daga sama tana shela da bayar da umarnin da a haƙa babban ɗaki mai girma, a kuma sassaƙa mafi gajartar bishiyar kukar da ke Masarautar, kamar yadda ake sassaƙar jirgin ruwa a fafe cikinsa. Sai a saka gawarta a ciki, akai ta ɗakin da ke tsakiyar ƙoramar a binne, tare da wannam littafin da suka gani. A cikin kaso casa'in da labaran da ake kawowa, an ce Sarauniya Humaira musulma ce. Yayin da mahaifinta ya kasance ƙungurmin kafiri mai bin addinin gargajiya. Wasu kuma suka ce, ita ma tana bin addinin gargajiya saboda a ra'ayinta tana ganin don mutum ya yi haɗakar addinan da yake so ba kuskure ba ne. A lokacin da aka binne ta an ce mutanen da suka yi wannan aikin babu wanda ya rayu, tun daga wannan ranar duk wanda ya shiga ɗakin sai dai a nemi gangar jikinsa a rasa ba tare da an sake ganin wulgar ko mai kama da shi ba. Tun daga nan sai malamai, bokaye da 'yan tsibbu suka shiga fagen binciken abin da yake haddasa haka. Sai da ƙyar suka gano mafitar da za ta sa a kamo bakin zaren ga duk wanda yake da buƙatar shiga ɗakin gawarta, shi ya sa a duk lokacin da mutum zai shiga domin neman biyan buƙatar kansa, ya zama wajibi ya tafi da wanda zai sadaukar da jininsa, ma'ana suna zuwa ɗakin ya fara hankaɗa shi sai daga baya shi kuma ya shiga ya yi abin da zai yi. Tun da aka binne Sarauniya Humaira, ba a taɓa samun mahalukin da ya yi gangancin buɗe cikin kabarin ba. Saboda yadda kowa ya san hatsabibancin ɗakin, da mummunan al'amarin da zai biyo baya. Duk da a hakan ma yawan shigar da ake yi ya haddasa musu abubuwan masu yawa, daga ciki har da ambaliyar ruwa, mutuwar jarirai akai-akai da gurɓatar ruwan kogunan yankin. Tun daga lokacin ne aka haramta wa mutane shiga ɗakin, da niyyar neman biyan buƙata ko yin wani abu. Sarki Dikko Sarki Dikko yana nan tsaye yana nazari, ya ga bawa Bukar ya shiga hannunsa ɗauke da daron abincin dakawansa. Sai da ya russuna har ƙasa sannan ya ce, "Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Barka da hutawa uban gidana maganin kukana, Allah Ya ja da kwana ya raya mana Yarima da Sarauniya lafiya." Farincikin Sarki Dikko ya faɗaɗa har a fili, cikin murya ƙasaita ya ce. "Bukar a kai daron nan a dawo muna buƙatar ganinku." Cike da girmamawa bawan ya sake zubewa a ƙasa ya ce. "An gama ranka shi daɗe, ni mai bin umarninka ne." Murmushin cimma nasara Sarki Dikko ya saki, yana nan tsaye babu jimawa bawan ya dawo yana jiran umarninsa. Itace ya ce ya kunna, sannan ya nuna masa hanyar nufa tsohuwar fada, gaban bawan ne ya faɗi amma sai ya dake ya cigaba da bin umarnin uban gidansa har suka ƙarasa jikin siririyar hanya mai duhun gaske, wacce za ta sada su da tsohuwar ƙofar fadar. "Rarr... ranka shi...daɗe... tsohuwar fada za mu shiga?" Bawan ya furta bakinsa yana rawa cike da tsoro, kallo ɗaya Sarki Dikko ya yi masa ba tare da ya tanka masa ba. Nan take ya haɗiye kalamansa, yana jin zuciyarsa tana harbawa kamar za ta ɓullo daga ƙirjinsa. Ƙofar jikin tsohuwar fadar ta yi ƙura sosai, har yana ta yanyame ta gabaɗaya tare da ƙananna ƙwari. Kallon bawan ya yi, da yake ya fahimci abin da yake nufi nan take bawan ya saka hannu ya fara cire yanar da hannunsa, sai dai kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci kwanciyar hankali ta yi bankwana da gangar jikinsa. Sai da ya gama cire yanar, sannan Sarki Dikko ya zura kuba ya fara cire sakatar ciki, wata irin guɗa suka ji cikin zazzaƙar murya mai daɗin sauraro. Sai dai ƙara da kauɗinta yana addabar kunne kamar zai tarwatsa shi, hakan ne ya sa daga Sarki Dikko har bawa Bukar suka toshe kunnuwansu. Sai da suka ji guɗar ta tsagaita, sannan ya cigaba da buɗewa, duk da zuciyarsa tana harbawa sama-sama. Yana jin ƙofar ta buɗu ya tura ƙauren, nan take wata walƙiya ta haske idanunsu wacce ta sa suka hangi wata mace a tsaye sanye da alkyabba kanta yana kallon sama. Ganin haka ya sa hantar cikin Bawa Bukar ta kaɗa, cikin shammata Sarki Dikko ya hankaɗa shi cikin ɗakin. A karo na farko Sarki Dikko ya ji wata tsawa da ta nemi hargitsa kwanyarsa, duk taurin zuciyarsa sai da ya ji tsoro ya ɗarsar masa. Amma da ya tuna abin da yake tafe da shi, sai ya furzar da iska daga bakinsa wata sabuwar ƙwarin gwiwa ta mamaye shi. Tun lokacin da Sarki Dikko ya hankaɗa Bawa Bukar bai sake jin motsi ba, cikin sanɗa ya dinga takawa yana haske ɗakin da itacen ɗakinsa. Ɗakin ya yi ƙura sosai, duk inda ya taka sai ya ji sautinsa tare da tashin ƙura da yanar da yake cin karo da ita. Sannu a hankali ya fara jin tashin busar sarewa, sai kuma yake jin motsi daga cikin kowacca kusurwar ɗakin. Ajiyar zuciya ya sauke a ɗan tsorace, ganin baƙin al'amuran suna neman zautar da shi ya sa shi tunkarar ɗakin da aka saka gawar Sarauniya Humaira. Sai dai yana ƙarasawa wurin ya ga wutar cikin ɗakin kabarin ta kama, take ƙoramar da ke zagaye da ita ta bayyana. Kamar yadda ya samu labarin yanayin yadda aka ajiye sassaƙaƙƙiyar bishiyar kukar da aka saka gawar Sarauniya Humaira, haka ya gan ta har lokacin da yake komai na ɗakin ana hangowa daga waje. Sai kuma ya hango littafin da ya shigo ɗauka yana kallon kabarin, a lokacin ya faɗaɗa fara'arsa ya cigaba da kusa kai cikin ɗakin har ya ƙarasa wurin bakin ƙofar shiga ɗakin kabarin. Hannunsa ya kai kan ƙofar, lokaci ɗaya ya ji wani zum! Tamkar yadda wayar wuta take jan mutum, yarfe hannu ya gama yi ya sake miƙa hannunsa. Sai dai ga mamakinsa a lokacin babu abin da ya ji, kansa tsaye ya shiga cikin ɗakin da zummar ɗaukar wannan littafin. Bai yi tsammani ba ya ji jiri yana ɗaukarsa, yana shirin dafa bango sai gani ya yi ƙofar ɗakin da ya shigo ta shafe. Harshen wutar da ke gefen kabarin ta yi tsayi zuwa gabansa, a razane ya ja da baya yana sauke ajiyar zuciya. Yana cikin wannan yanayin sai gani ya yi hasken wutar ya ɗauke, daga wurin ƙafafuwansa ya ji wani irin ruwa mai sanyi yana kwararowa jikinsa har zuwa saitin maƙogaronsa. Masarautar Judala Ba iya Indo ba hatta ragowar bayin da ke tsaitsaye sai da tsoro ya mamaye su, cikin sauri wasu mata suka yi ta maza suka ƙarasa kan matar. Ɗaya ce ta shiga kiciniyar cire jaririya Batul, sai dai jin yadda jaririyar take shan maman cikin kwanciyar hankali ya sa ta dubi ɗayar ta ce. "Allah sarki, dubi yarinyar nan ashe yunwa ce. Yanzu yaya za mu yi da ita?" Cikin sauri ɗayar matar da ke shafawa matar da ke kwance ruwa ta ce. "Maza cire ta Dago, ba ki ga halin da take ciki ba?" Da sauri wacce aka kira da Dago ta shiga kiciniyar cire jaririya Batul daga jikinta, sai dai ita kanta abin ya ba ta mamaki yadda jaririya ƙarama take yunƙurin fin ƙarfinta. Ta ɗago tana shirin sanar da su halin da ake ciki, sai ta ji ta yi nasarar raba jaririya Batul da matar. Sai dai babban abin da ya sake ɗaga hankalinsu ganin bakin jaririyar kace-kace da jini, a razane duk suka ja baya. Cikin rawar muryar Dago ta ce. "Ku taimaka ku raba ni yarinyar nan don Allah." Ta ƙarasa maganar hawaye yana zuba. "Don Allah ki kula mini da Batul, tamkar yadda za ki kula da 'yar cikinki. Na damƙa miki amanarta, don Allah kada ki ci amanata." Indo ta tuna kalaman Karima, jiki a sanyaye ta matsa gaban matar ta ce. "Kawo ta." Dago tana miƙa wa Indo jariraya Batul suka ga matar da ke kwance a ƙasa ta ɗago, gumi ne ya shiga keto mata tana sauke ajiyar zuciya. "Wannan wacce irin irin yarinya ce saboda Allah, ku dubi yadda jini yake fita ko dai idanuna ne? Ke yarinya an ya kuwa ba ki da haɗi da maita?" Wata gajeriyar mata ta faɗa a tsorace tana sake leƙa fuskar Batul da ke mamular baki, amma da yake hankulan mutane yana kan matar sai ba su bi ta kan Batul ba. "Wallahi tun wuri ki koma wurin can ki ajiye musu 'yarsu, don wallahi yarinyar nan ba mutum ba ce. Idan kuma ba haka ba, wallahi za ki kuka da kanki." Zinaru ta furta wa Indo cike da jan kunne, idanun Indo suka ciko da ƙwalla. Zuciya ta shiga raya mata a kan ta je ta mayar da jaririya Batul, tana cikin wannan nazarin ta ji ana yi wa matar sannu. "Oh ni jikar mutum huɗu, sannu Zuwaira kin ji." Wata 'yar uwar matar ta furta, Zuwaira da ta ɗago a galabaice ta ce. "Ku kawo mini jaririyar nan, don Allah ku ba ni ita. Wallahi ita ɗin ta dabance, don Allah kada ku nisanta ni da ita." Da mamaki suka dinga bin ta da kallo, Indo da Batul ke hannunta ta sake ƙanƙame ta. "Ke yanzu ba ki dubi halin da kika shiga ba, amma kike ƙoƙarin gayyato wa kanki mutuwa? An ya kina cikin hankalinki kuwa Zuwaira? Ko da ma can haka kike shayarwa?" Wata mata ta yi caraf ya karɓe zancan, Zuwaira ta dube su sai ta saki murmushi ta ce. "Da kun san wace ce ita..." Sai kuma ta yi shiru, ta gyaɗa kai ta ce. "Eh haka nake goyo na, wani lokacin idan ina shayarwa yana jini, idan hakan ta kasance har suma nake yi. Na taɓa tambayar wani mai magani, ya ce mini cuta ce. Ina gab da komawa karɓar magani aka kamo mu." Lokaci ɗaya jikin mutanen wurin ya yi sanyi, tausayin Zuwaira ya mamaye su. Sai suka ɗauke mummunan zargin da ke zuciyoyinsu a kam Batul, jin Batul ta fara motsi ya sa Zuwaira ta dubi Indo ta ce. "Miƙo mini ita yarinya na shayar da ita." Girgiza kai Indo ta yi, don haka kawai ta ji ba ta gamsu da amsar da Zuwaira ta bayar ba. Cikin muryar kuka ta ce. "A'a ina tsoron kada wani abu ya sake samunki." Suna cikin haka, wata mace ta yi ƙasa da murya ta ce. "Amma can kamar garken awaki ne, me zai hana mu tatso mata nonon akuya ta sha." Kallon kallo aka shiga yi wa juna saboda tsoron kashedin uwar bayi, ganin haka ya sa Indo ta nufi wurin Dogarawan da ke can nesa da su. Tun ba ta buɗi baki ba, wani Dogari ya buga mata tsawa da cewa. "Ke wanne irin kunnen tsiya gare ki, ba cewa aka yi ki zauna a cikin 'yan'uwanki ba?" Baki yana rawa Indo ta ce, "Don girma Allah ku lamunce mini na tatsi nonon akuya zan shayar da jaririyat..." Tun ba ta rufe baki ba, Dogarin ya zuba mata dorina a bayanta. Azaba da gigicewa suka sa ta yi baya ta faɗi, don kaɗan ya rage jaririya Batul ba ta bugu da ƙasa ba. Da ƙarfinsa ya ƙarasa gabanta ya sake ɗaga hannu ya zuba wa Indo dorinar dukan dokin, ta yi saurin sunkuya don kada ya samu Batul da buguwar da suka yi, ta sa ta yin shiru kamar ta san abin da yake faruwa. "Au tare mata za ki yi? Shi ne kika zagayo ta bayana? Ai kuwa wallahi za ki gane ba ki da wayo." Indo da sauran Dogaran suka ji ya faɗa yana waigen bayansa, ko kaɗan babu wanda ya ga kowa. Don haka ɗaya daga cikinsu ya ce, "Kai Mamman, wai lafiyarka kake magana kai kaɗai?" Tun bai gama maganar ba, suka ga Dogari Mamman ya fara kai duka yana nausar iska. Tun suna ganin abin kamar wasa, sai suka rufa masa baya suna kiran sunansa. Daga haka suka ji ya saki wata gigitacciyar ƙara ya faɗi ƙasa yana shure-shure. Ganin hankalinsu ya tafi kan wurin da Mamman yake, ya sa Indo ta yi saurin rarrafawa cikin garken awakin. A cinyarta ta zaunar da Batul, da saka hannu ɗaya tana tatsar nonon wata ƙatuwar akuya tana tara da ɗayan hannunta. A hankali take ɗisa mata a baki, nan da nan Batul ta shiga tsotsa tana ba ta har ta lura da ta ƙoshi, tana gama shayar da ita babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya Indo ta yi, ta zuba wa fuskar Batul ido, ta ɗaga hannu cikin muryar karaya da kai kuka wurin Ubangiji ta ce. "Ya Allah ka ga kyakkyawar niyyata, Allah ka taya ni rainon wannan baiwa taka. Idan ma ba mutum ba ce kamar yadda zuciya take raya mini, Allah kada ba wa ahalinta ikon cutar da ni." A hankali ta shafa a fuska, sannan ta miƙe ta fito daga cikin garken awakin. Ta ƙarasa wurin ragowar bayin ta zauna, sai dai kallon da Zinaru take yi mata ya sake sanyaya mata jikinta. Haka suka ci gaba da zaman jigum-jigum har aka fara kiran sallar asuba, kuma a daidai wannan gaɓar labarin kisan wulaƙancin da aka yi wa gawar Dogari Mamman ta riske su. Indo ba ƙaramin kaɗuwa ta yi da jin irin kisan da aka yi masa ba, tana cikin wannan jimamin Uwar Bayi ta ƙarasa ta ingiza ƙeyarta da jaririya Batul ba tare da ta san dalili ba. _MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_ Monthly data — valid for 30 days _📶MTN DATA_ • 500MB — 450 • 1GB — 700 • 1.5GB — 1000 • 2GB — 1,300 • 3GB — 1,900 • 5GB — 2,100 _📶AIRTEL DATA_ • 1GB — 750 • 2GB — 1,400 • 3GB — 2,150 • 3.5GB — 1,800 • 5GB — 2,850 • 6GB — 2,900 • 10GB — 5,600 𝙋𝙖𝙮𝙢𝙚𝙣𝙩 : Opay — 7049439332 AFNAN ADAM 𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027 _Thank you❤_ Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [30/11, 20:57] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA SHA BIYU Tamkar raƙuma da akala haka Indo ta cigaba da bin Uwar bayi, sai da suka wuce soro uku ganin tafiyar ta fara nisa ya sa Indo ta ce. "Don Allah ina za mu je?" A yatsine Uwar bayi ta waigo ta dube ta, sheƙeƙe ta ce. "Idan mun je za ki gani." Haɗiye yawu Indo ta yi cike da damuwa, ta sauke ajiyar zuciya tana kalle-kallen yanayin tsarin gidan sarauta, da zane-zanen da aka ƙawata na fari da ja ba ƙaramin birge ta ya yi ba. Wurin wani babban fili suka ɓulla, daga nesa ta hangi dandazon maza a tsaitsaye waɗanda take tsammanin Dogarai ne. A ɗan tsorace Indo ta ƙarasa saboda yadda ƙirjinta yake dakan lugude. "Sarkin tsaro shin wannan ce yarinyar da kuke magana a kai?" Ƙuri suka yi wa Indo suna nazari, saboda lokacin da ta same su da dare hasken farin wata ne. "Ƙwarai ita ce, ke zo nan!" Nan take Indo ta sake rungume Batul, ta fara takawa a tsorace. A tsammaninta saukar duka za ta ji a jikinta, amma ga mamakinta sai ta ji ya sunkuyo daidai fuskarta ya yi ƙasa da murya ya ce. "Yarinya ki faɗa mana tsakaninki da Allah, me kika yi wa ɗan'uwanmu har muka tsinci gawarsa a tsakiyar dajin da muka bi shi." Ajiyar zuciya Indo ta sake saukewa ta ce. "Wallahi-tallahi ban yi masa komai ba, tsakanina da Allah nake wannan maganar." Indo ta ƙarasa maganar tana goge hawayenta, shiru suka yi suna nazari sai ɗaya daga ciki ya ce. "Ka san fa dama hanyar ɗorawar can ba ta da kyau, ko dai wani abin ya takawa mazauna wurin suka huce fushinsu a kansa?" Cike da ɗaurewar kai Dogarin ya ɗago yana dafe kai cikin jimami ya ce, "Na shiga ruɗani wallahi, to amma fa tun kafin ya shiga dajin ya fara surutai kamar mai magana da iskokai." Duka shiru suka yi cikin jimami, Uwar bayi ta ja bawan da ya gama magana suka ɗan yi gaba. Sai da ta tabbatar da ta yi nesa da su ta ce. "Bala an ya ba za ku bar wannan maganar ba, don idan Mai martaba ya ji wannan zancan ina ganin kamar da matsala." Cikin sauri Dogari Bala ya riƙe baki ya ce, "Uwar bayi me ya kai mu aikata wannan ɗanyen aikin? Ni fa gabaɗaya tsoron yarinyar nake yi, don wallahi ganin idona Mamman yana gama dukanta ya fara wannan haukar, ai kawai ki ja ta ku koma ciki." Jinjina kai Uwar bayi ta yi ta ce, "To shi kenan, mu kuma da muke tare da ita Allah Ya kiyaye mu." Kusan lokaci ɗaya suka saki dariya. Indo tana zaune cikin zullumi Uwar bayi ta riƙo hannunta tana washe baki kamar ba ita ba ta ce, "Yarinya mu je kin ji, wai ya sunanki ne?" Da yake har lokacin Indo a tsorace take, jiki a sanyaye ta ce. "Sunana Indo." Cikin bugar ciki Uwar bayi ta ce, "Indo tsohuwa, wai kuwa tare da mijinki aka kawo ki gidan nan?" Ras! Gaban Indo ya faɗi, cikin in'ina ta ce. "Na'am... ai... a'a... ba tare muke ba, mijina ya mutu tun kwanaki." Ƙuri Uwar bayi ta yi mata tana son gano wani abu daga kalaman Indo, sai ta ɗan kalle ta daga sama zuwa ƙasa ta ce. "Amma kuma na ga garau kike tafiyarki jiya-jiya da haihuwa, kodayake ai kowacce mace da yanayin jikinta." Ita dai Indo shiru ta yi, a haka har suka ƙarasa sashensu na bayi. Indo tana shiga ta ga mutane suna bin ta da kallo, duk sai ta ƙara tsarguwa. Hakan ya sa ta raɓe can a gefe, zamanta babu jimawa Batul ta fara kukan yunwa. Da sauri Zuwaira ta matso kusa da ita ta ce, "Kawo ta na bata..." "A'a zan nemo mata nonon akuya, saboda na ga jiya ta ji daɗinsa sosai." Indo ta katse ta, tana miƙewa tsaye. Murmushi Zuwaira ta yi, Zinaru da ke gefe ta saki guntun tsaki ta ce. "Ke dai wahala ta gan ki wallahi Indo, amma a juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe." Duka mutanen ɗakin kallon Zinaru suka yi, jikin Indo a sanyaye ta fita. Sai dai Indo tana fita ƙananan maganganu suka fara tashi, wasu suka shiga kare Indo yayin da wasu suka fara tsegumi a kan ƙanƙantar Indo a matsayinta na mahaifiyar Batul. A wannan lokacin babu wanda ya hana Indo tatsar nonon akuyar, don haka ta cika cikin Batul taf sannan ta taso ta dawo sashen bayi. Duk jin ta take babu daɗi, saboda ta lura zuwa wannan lokacin Batul a gajiye take tuɓus, don har kawo lokacin ko ruwan zafi jikinta bai gani ba. Hatta sutura babu a jikinta sai zanin da mahaifiyarta Karima ta naɗe ta da shi. Tana komawa ta tarar da an kai musu abinci, kallon miyar kukar ta yi sau ɗaya ta ɗauke kanta saboda yadda ta ji zuciyarta tana tashi. Amma jin yunwa za ta illatata ya sa ta matsa kusa da su, har za ta saka hannu Zuwaira ta ce. "Indo ga abincinki na ajiye miki, cikin jego ne da ke bai kamata ki shiga cikinmu ki ci abinci ba." Cikin jin daɗi Indo ta yi mata murmushi haɗe da godiya, suna cikin cin abinci uwar bayi ta ƙarasa kansu daga bakin ƙofa ta ce idan sun gama su fito, kowacce za a bata aikin da za ta dinga gudanarwa. Amsawa suka yi, sai da suka gama cin abinci, sannan Zuwaira ta dubi Indo ta ce. "Akwai ruwan da na roƙi alfarma a wurin uwar tuwo na ɗora, idan kin gama zan yi mata wanka." Gyaɗa kai Indo ta yi, sai dai kuma har kawo lokacin zuciyarta ba ta gama nutsuwa da Zuwaira ba. Cikin ƙanƙanin lokaci bayin ɗakin duka suka watse, Zuwaira ta ɗauko ruwa ta surka a wata ƙatuwar kwarya sannan ta karɓi Batul ta fara yi mata wanka. Shiru Indo ta yi tana kallon yadda ake wankan, don dama ko kaɗan ba ta san yadda ake yi ba. Sai da mutanen ɗakin gabaɗaya suka fita sannan Zuwaira ta dubi Indo ta ce. "Indo wace ce ke?" Da mamaki Indo ta yamutsa fuska ta ce, "Ni kuma? Me kika gani?" Zuwaira ta gyara riƙon Batul ta naɗe ta da ɗankwalinta ta ce. "Batul ba kowacce irin yarinya ba ce, haƙiƙa wannan yarinyar Suryu ce." "Suryu! Me hakan yake nufi?" Indo ta tambaya, Zuwaira ta sake ƙura wa Batul ido, ita ma Indo kallon Batul ta yi lokaci ɗaya suka ga idonta ya fara fitar da farin hayaƙi. Cikin sauri Indo ta ja baya ta ce, "Mene ne a idonta?" Zuwaira ta sake jinjina kai ta ce, "Wallahi yarinyar nan Suryu ce, ita ce wacce tsoho Baushe ya sanar da ni." Sake kallonta Indo ta yi, Zuwaira ta gyaɗa kai ta cigaba da cewa. "Akwai manyan cutukan da suke addabar rayuwata, lokacin da na je wurin Baushe sai ya ce mini laƙanin makarin lalurar jikina sai na shayar da jaririya Suryu, wacce ta fito daga wani irin tsatso mai rikitarwa." Zaro ido Indo ta yi, Zuwaira ta cigaba da cewa. "Sai dai ina jin tsoro, tun lokacin da na ga alamunta sun bayyana." "Tsoro kuma? Tsoron me?" Indo ta tambaya, Zuwaira ta sauya fuska cikin damuwa, sai ta gyaɗa mata kai ta cigaba da cewa. Sarki Giɗaɗo Tamkar wanda ruwa ya shanye haka Sarki Giɗaɗo ya yi tsuru yana sauraron bokanya Kande, sai da ya ji ta kammala jawabinta sannan ya ce. "Ki gafarce ni yake mai cetona..." "Yesu Almasihu shi ne mai ceto ba ni ba." Bokanya kande ta katse shi a harzuƙe. Russunar da kai ƙasa ya yi ya ce. "Tuba nake yi bisa aikata saɓo." Gyaɗa masa kai ta yi, Sarki Giɗaɗo ya yi godiya sannan ya cigaba da cewa. "Ki yi mini afuwa yake hatsabibiya bokanya Kande, haƙiƙa ina cike da ruɗu tare da tashin hankalin jin matata Karima tana raye." "Wurin nan ba wurin ja'inja ba ne Sarki Giɗaɗo, idan har kuna tantama game da abin da muka faɗa, kuna iya zuwa ku duba kabarinta domin ku tabbatar da abin da muke faɗa." Bokanya Kande ta furta fuska a haɗe, russunar da kai ƙasa ya yi alamar ban haƙuri, Sarki Giɗaɗo ya ce. "Yanzu ta ina za mu fara wannan aikin yake Bokanya Kande?" "Ba ma faɗar mafitarmu kai tsaye gabaɗaya, za mu sanar da ku ta cikin baccinku yau da dare idan kun kwanta. Duk abin da kuka gani ko muka bada umarni to hakan za ku zartar da shi, amma kada ku manta muna sake jan hankalinku da ku binciko Karima a duk inda take ko jininta, domin kuwa ita ce maganin matsalarku. Ragowar jawabin zan yi muku a cikin mafarki, kuna iya tashi ku ba mu wuri. Yesu Mai ceto zai yi alfahari da kai, matuƙar ka tabbata a kan addinin gaskiya ba na ɓata ba." Jiki yana rawa Sarki Giɗaɗo ya russuna ya ce, "Ina godiya bokanya, sai dai ba a sanar da ni tukwicin da zan bayar ba." "Tukuwinmu shi ma zai zo a cikin baccinka, domin daga jikinka za mu ɗauki abin da muke muradi." A razane Sarki Giɗaɗo ya ɗago jin furucin Bokanya Kande ya ce, " A jikinmu kuma?" "Kada wannan ya razana ka, ba za mu cutar da kai ba. Za mu ɗebi gumin jikinka, tare da duk wani gashi na jikinka, idan ka kuskure wa aljani Ɓugun, kai da sake samun gashi a jikinka har abada. Wannan ita ce magana ta ƙarshe da za mu faɗa." Daga haka sai ya ga Bokanya Kande ta miƙe ta bi ta jikin tafkeken cross ɗin da ke fuskantarsu, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miƙe ya fita harabar wurin da ya bar Galadima. Yana zuwa wurin Galadima ba su ɓata lokaci ba, sakamakon kalaman tsubbun da Galadima ya furta wanda bokanya Kande ta koya masa. Sarki Giɗaɗo ya jima yana zarya a ɗakinsa, haka kawai ya ji soyayyar Zannira tana sake addabar zuciyarsa, ta yadda ba zai iya jure rashinta ba. Musamman da ya tuna tana ɗauke ciki a jikinta. "Ka tabbatar da ka nemo duk wani jariri da aka haifa a cikin masarautarka, ka shafa masa wannan jan garin maganin nan. Matuƙar ka ga jini ya fito daga al'aurarsu mace ko namiji, to tabbas jinin Karima ne." Sarki Giɗaɗo ya tuna kalaman bokanya Kande, cikin sauri ya miƙe ya nufi ƙofa. Har zai fita, sai kuma ya tsaya cak. Tunowa ya yi da Kabarin Karima, don haka ya yi saurin canja hanya ta ƙofar baya. Ya nufi ɗakin kushewa, babban ɗakin da ake binne duk wani ahali da ya dangancin masarautar. Mukulli ya saka ya buɗe, ya shiga ɗakin cikin sanyin jiki. Sai dai rana ta farko kenan da ya ji gabansa yana tsanannin bugawa, a bakin ƙaton kabarin Karima ya tsaya. Har ya kai hannu, sai kuma ya yi saurin komawa ya tura ƙofar ya rufe. Tamkar ba Sarki Giɗaɗo ba, haka ya zage ya dinga haƙar ƙasar kabarin har sai da ya yashe ta tas. Yana kwashe itacan kan kabarin ya cigaba da dubawa, sai dai sama da ƙasa ya neme ta ba tare da ya ganta ba. Hatta ƙashin da ya ji labarin an ce yana saura a jikin mutum, da likkafani duk bai gani ba. Wata ƙaramar fata ya gani, wacce aka yi rubutu a jikinta. Jikinsa yana rawa ya yi saurin kai hannu ya ɗauka. "Ka yi kuskure da kake tsammanin za ka hallaka Karima. Sarki Giɗaɗo abin da ka guda shi ne zai faru a daidai gaɓar da ba ka yi tsammani ba, lokaci zai zo da zan yi ajiya mai muhimmanci a cikin fadarka. Sai dai ka sani, yadda ka dakushe mini farincikina, har bada ka yi bankwana da shi. Domin kuwa yadda ka zartar da miyagun al'amura a kaina da mahaifina tsawon kwana arba'in, daga lokacin da na mace a idanun al'umma, kowacce kwana arba'in za ta zame maka mafi masifa da uƙuba a cikin rayuwarka. Ragowar amsoshin da kake buƙata, za ka same su daga bakina a lokacin da ka fahimci Karima ba ta mutu ba. Sai dai ba za ka fahimci hakan ba, har sai lokaci ya ƙure maka. Ba za ka iya ja da ni ba Sarki Giɗaɗo, don a yanzu ba ka da tabbacin mutum ce ko wani jinsin daban." Sarki Giɗaɗo yana gama karantawa ya yi wurgi da takardar, ko ƙasar kabarin bai mayar ba ya fita daga ɗakin a fusace ya nufi ɗakinsa. A lokacin dare ya tsala sosai, don haka ya haƙurewa washegari gudun kada Zannira ta fahimci wani abin ko ta tada hankalinta. Sai dai yadda ya ga rana, haka ya ƙarasa ganin darensa. Sai da gari ya waye garau, sannan Sarki Giɗaɗo ya sa aka kira masa Jakadiya, uwar bayi da mai soron baƙi. Kallon fuskarsa kaɗai suka yi, suka fahimci ransa a matuƙar ɓace yake. "Mun tara ku ne ba don dogon bayani ba, sai don mu sanar da ku. Muna son ku kawo mana duk wani jariri da yake rayuwa a cikin masarautar nan, muna nufin tun daga ɗan shekara biyu zuwa jaririn da aka haifa yanzu. Idan har kuka yi gangancin saɓa mana, mun yi rantsuwa da sarkin da ya busa mana numfashi sai mun azabtar da ruhinku." Jin kalaman Sarki Giɗaɗo ya sa Uwar bayi ta yi saurin ɗaga hannu jiki yana rawa ta ce, "Allah Ya taimake ka akwai wacce ta haihu a masarautar nan jiya da dare, ɗaya daga cikin bayin da aka kawo ce." Jin kalaman Uwar bayi ya sa Sarki Giɗaɗo ya miƙe zumbur, cikin kausasshiyar murya ya ce. "A gaggauta kawo mana ita yanzun nan." Masarautar Kajjura A hargitse Baiwa Sakina ta fita daga sashen Fulani Sadiya, duk wanda ya ga irin tafiyar da take yi sai ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. A haka ta ƙarasa sashensu na bayi, tana shiga ɗaki ta hangi Ridwan a zaune yana biya karatunsa na allo. A fili ta sauke ajiyar zuciya har sai da ya waigo ya kalle ta, murmushi ya sakar mata ta ƙarasa kusa da shi ta zauna ta ce. "Ridwan karatu kake yi?" Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi, ta zuba masa ido tana kallon yadda tsantsar kyawun yaron yake sake bayyana. Dara-daran idanunsa ta kalla, sai ta ga kamar ƙwayar idonsa ta sauya zuwa irin ta maciji, gabanta ne ya faɗi amma sai ta kawar da damuwar abin da ta gani ta ce. "Kada ka dinga fita waje ka ji Ridwan." Riƙe bakinsa ya yi, yana yi mata alamar ya aikata wani laifin. Ɗan zaro ido ta yi, tun ba ta tambaye shi ba ya ce. "Inna ban daɗe da dawowa masarautar nan ba, wai dama Inna ba ke kika haife ni ba?" Da sauri Sakina ta zaro ido waje bakinta yana rawa ta ce, "A ina ka ji? Kuma ina ka je? Ridwan kana son ka saka mu a matsala ne?" Kamar ba laifi ya yi ba ya saki murmushi ya ce. "Allah ba ke ba ce, an ce mini mamana tana gidan nan." Sai kuma ya yi fuskar tausayi ya ce, "To ko tana ina oho? Amma dai an ce min wai tana sona, kuma babana ma kafin a kashe shi yana sona." Sakina da ƙirjinta yake bugawa ta rasa mafita sai kawai ta fashe da kuka, ganin tana kuka sai jikinsa ya yi sanyi. Ya matsa kusa da ita ya goge mata hawaye, riƙe hannunsa ta yi ta ce. "Don Allah ka daina irin wannan maganar Ridwan, za ka saka mu a matsala. Ni da na ga yau kana cikin farinciki na ɗauka ma abokan wasa ka samu." Wata dariyar ya sake yi, ya ajiye allonsa a gefe sannan ya ce. "Inna ni ba na wasa da kowa a gidan nan, sai wasu mutane masu muhimmanci." Za ta tambaye shi su waye, sai ta ji ya cigaba da cewa. "Kin san me ya sa yau nake cikin farinciki?" Girgiza masa kai ta yi, ya miƙe tsaye yana 'yan tsalle-tsalle ya ce. "Na ji daɗi yau Batul za ta mutu, ni dama ba na ƙaunarta." A hargitse Sakina ta sake kallonsa, sai gani ta yi ya sake washe mata baki cikin murna. Book 1 yana gab da ƙarewa, ga masu sha'awar karanta book 2&3 za su iya turo kuɗinsu. 700 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lamabar 07062062624 idan ya kammala zuwa document 1k ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 07062062624 [30/11, 21:05] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA SHA UKU Sarki Gambo Ƙuri Sarki Gambo ya yi wa Malami yana sauraronsa, kamar wanda yake nazari sai ya ɗago ya ce. "Malami waɗanne irin mafita kuka hango mana? Muna fatan ba za ta ɓata mana lokacin da za a fuskanci 'yan biyunmu suna da tawaya ba?" Cigaba da binciken tsubbunsa Malami ya yi, sai da ya sake ɗaukar lokacin sannan ya ɗago ya ce. "Mafitar guda biyu ce kamar yadda na faɗa maka da farko, kuma a karo na biyu haka binciken ya sake maimaita mana. Mafita ta farko, zan yi aiki da idanun mikiya, kan baƙin maciji da kuma ƙoƙan kan ɗan'uwan wancan tsohon." Cikin sauri Sarki Gambo ya ce. "Wanne tsoho kenan?" "Tsoho Sulaimanu!" Malami ya furta yana kallon Sarki Gambo, cikin mamaki Sarki Gambo ya ce. "Malami ban fahimci abin da kuke nufi ba, shin shi tsoho Sulaimanu yana da ɗan'uwa ne? Ko kuwa shi kansa tsoho Sulaimanu kuke nufi?" Malami ya girgiza kai ya ce. "Tsoho Sulaimanu yana da ɗan'uwa Babagana, kuma su ɗin tagwaye ne. Sai dai wannan wani sirri ne da ba kowa ne ya san da shi ba, kuma kaifin ƙwaƙwalwa da hangen nesan Babagana ya zarce tunanin mai tunani. Domin zan iya ce maka ya fi mikiya hangen nesa, don haka zan haɗa wannan aikin da ƙoƙon kansa. Idan na haɗa idon mikiya da ƙoƙon kansa, za su haska mini duk wani duhun sihirin da aka gudanar a kan tagwayenka, shi kuma kan maciji zan yi amafani da shi ne domin ka san duk duniya babu dabbar da ta kai maciji jin motsi ko magana duk ƙanƙantarta. Ragowar mahaɗin kuwa ruwan ƙoramar fadar sarauniya Humaira ne, amma wannan mai sauƙi ne. Domin ina da kyakkyawar alaƙa da Aljani Dakkum, na tabbata shi zai ɗeɓo mini shi." Ajiyar zuciya Sarki Gambo ya sauke, cikin damuwa ya ce. "Amma ya aka yi a duk binciken da kuke yi mana ba ku taɓa sanar da mu haka ba? Ya aka yi ba mu san da zancan Babagana ba?" "Saboda komai yana da sila Sarki Gambo, a yanzu ma mafitarka ce ta sa muka binciki maka wannan maganar." Malami ya numfasa sai ya cigaba da cewa. "Mafita ta biyu kuma, sai dai ka ziyarki kogin Sutturu, wanda yake ɗauke da hatsabibiyar bishiyar kukar nan da ake bautawa. Amma wannan ziyarar taka za ta kasance mafi hatsarin gaske, domin kuwa akwai tarun ƙalubale a cikinta, za ka iya dawowa a raye za ka kuma iya haɗuwa da ajalinka. Domin ba iya ziyarar za ka kai ba, akwai waɗansu abubuwa da za ka gudanar a cikin wannan bishiyar kukar. Sai dai kuma, tunkarar mutuwarka sai ya fiye maka sauƙi a kan ka tunkari wannan bishiyar kukar." "Mun fi aminta da zaɓin farko! Shin a ina za mu samu shi wannan tsohon Babagana? Don shi kaɗai ne abin da zai nemi wahalar da mu, tun da mikiya da maciji ba za su yi wahalar samu ba." Sarki Gambo ya furta yana kallon Malami. Murmushi Malami ya yi ya ce. "A yanzu haka Babagana yana ɓoye a fadar sarki Dikko, kuma wannan fadar ta kasance hatsabibiyar da sihiri bai cika tasiri ba. Da ace mutum ɗaya tana raye, ita ce za ka iya samun shiga salin-alin ba tare da wani mummunan al'amari ya faru da ita ba." "Wace ce ita?" Sarki Gambo ya tambaya bakinsa yana rawa. Malami ya ajiye bangon ƙur'anin hannunsa ya ce. "Fulani Karima! Sai dai kuma koda ace tana raye, zai yi wuya ta karɓi buƙatarka hannu bibbiyu. " A wannan karon damuwar Sarki Gambo ta sake yawa, cikin sanyin jiki ya ce. "Mene ne mafita tun da ba ta raye?" "Mafita ɗaya ce ka nemi amintacciyar baiwarka, ko wata makusanciyarka. Ka aikata masarautar Sarki Dikko, domin ta san duk wani shige da fican makircin da za ta yi ta samu nasarar auren Sarki Dikko." Malami yana gama faɗa Sarki Gambo ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Idan har wannan ce mafita an gama Malami, domin a kan tagwayena babu abin da ba zan iya aikatawa ba." Malami ya jinjina kai ya ce. "Za ka iya tafiya Sarki Gambo, ragowar tattaunawar za mu yi ta daga baya." Da yake zuciyar Sarki Gambo a cunkushe take da damuwa, miƙewa ya yi ya fice ba tare da ya yi wa Malami sallama ba. Sarki Gambo yana zuwa turakarsa ya aika aka kira masa Fulani Sadiya, sai da ta sheƙa kwalliya sannan ta ƙarasa cikin takun isa da ƙasaita. "Barka da hutawa sadaukina!" Fulani Sadiya ta furta tana sakin shu'umin murmushi, don kallo ɗaya ta yi masa ta fahimci yana cikin matsananciyar damuwa. "Barka dai Fulani!" Ya amsa mata murya babu yabo babu fallasa, Fulani Sadiya ta sake narke murya cike da kissa ta ce. "Ina kewar Sarki na tsawon kwanaki, sai dai damuwar da ta cunshe shi tana yunƙurin shata layi tsakanina da shi." Shi kansa ya san ya yi kewarta, don haka cikin shauƙin so ya ƙarasa kusa da ita ya riƙo hannunta. Da ɗayan hannunsa ya tallafo kanta, suka fuskanci juna kowannensu yana sauke ajiyar zuciya. Zame alƙyabbar jikinta ta yi, ta lumshe ido cike da jan hankali ta ce. "A kullum na kan tuhumi zuciyata, ko na jefa mata tarin tambayoyin dalilin da ya sa ta afka da'irar ƙaunarka." Kalamanta ne suka fara tasiri a kansa, don haka a kasalance ya ɗago haɓarta ya haɗe bakinsu wuri ɗaya. Fulani Sadiya ƙwararriyar ce wurin gogewa a kissa da kisisina, don haka duk irin fushin da Sarki Gambo yake ciki matuƙar zai gayyato ta makwancinsa, to tabbas za ta yaye masa kaso mafi yawa daga cikin damuwar da yake ciki. Cikin salonta, ta shiga sarrafa shi har sai da ta lura saƙon da take isar masa ya gama mamaye ilahirin jikinsa. Zare jikinta ta yi daga na shi, cikin wani irin yanayi ta ce. "Gwarzona!" "Me ya sa kika dakatar da mu? Alhalin kin san jikinku ya zame mana madogarar da ke yaye duk damuwar da muke ciki." Tallafo fuskarsa ta yi, ta sa bakinta ta sakar masa sumba a saman laɓɓansa. Tabbas idan ta ce Sarki Gambo mummuna ta san ta sharara ƙaryar da duk wanda ya ji zai ƙaryatata, tana yunƙurin janye fuskarta ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam kamar wani zai ƙwace fa. Ɗago idanunta ta yi ta dube shi, kamar mai raɗa cikin sauyin yanayin da ya shiga ya ce. "Muna cikin damuwa Fulani." "Dalilin da ya kawo ni turakarka kenan ranka shi daɗe, domin damuwar da nake ciki ta ninke taka." Ɗan ɗagowa ya yi ya zuba mata ido cike da kulawa. Book 1 ya kusa ƙarewa, masu son cigaban book 2&3 za tura 700 ta acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta nan 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa doc 1k ne. _MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_ Monthly data — valid for 30 days _📶MTN DATA_ • 500MB — 450 • 1GB — 700 • 1.5GB — 1000 • 2GB — 1,300 • 3GB — 1,900 • 5GB — 2,100 _📶AIRTEL DATA_ • 1GB — 750 • 2GB — 1,400 • 3GB — 2,150 • 3.5GB — 1,800 • 5GB — 2,850 • 6GB — 2,900 • 10GB — 5,600 𝙋𝙖𝙮𝙢𝙚𝙣𝙩 : Opay — 7049439332 AFNAN ADAM 𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027 _Thank you❤_ Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [30/11, 21:36] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA SHA HUƊU Masarautar Judala Sai da Zuwaira ta gyaɗa wa Indo kai, sannan ta cigaba da cewa. "Tun ranar da Baushe mai magani ya sanar da ni wace ce yarinyar nan, da irin al'amuran da ke tattare da ita. Ya bayyana mini miyagun ƙaddarorin da za su afka wa rayuwarta, don babban abin da ya fi ba ni tsoro yadda na ga ya jiƙe sharkaf da gumi a lokacin da yake yi binciken tauraronta." Zuwaira ta ɗan yi jim sai kuma ta cigaba. "Na san za ki yi mamaki a lokacin da na shayar da Batul har na yanke jiki na faɗi, tun kusan shekarun baya nake fama da wannan lalurar. Kuma Baushe da kansa ya sanar da ni sammu ne aka yi mini wanda ba zan samu warkewa ba har sai na haɗu da ita. Kuma na san za ki yi mamaki idan na ce miki ni mayya ce." Cikin alamun tsoro Indo ta ja da baya, ƙirjinta yana bugawa ta cigaba da kallon Zuwaira. Ganin haka ya sa Zuwaira ta saki murmushi haɗe da gyaɗa mata kai ta ce. "Ƙwarai kuwa ni 'yar sarkin mayun yankinmu ce, maita gadon gidonmu ce gaba da baya. Kakata da ta haifi mahaifina an ce saboda yadda maita ta huda ɓargon jikinta, ko tsuntsu ne ya zo giftawa ta saman gidanmu sai dai gawarsa ba shi ba. Wani zubin kuwa idan abin ya ciyo ta, ta rasa dabbar da za ta ci. Sai ta je kasuwar mahauta, ta sayi ɗanyen nama ta shige ɗaki ta cinye. Amma kuma duk wannan maitar ta kakata, ba ta taɓa cin ɗan mutum ba har ta ƙare rayuwarta." Indo a tsorace ta sauke ajiyar zuciya tana gyaɗa kai, don wasu kalaman na Zuwaira jin su take ba tare da tana fahimtarta ba. Ita kanta Zuwaira ta lura da haka, ta dafa kafaɗarta ta ce. "Kada kalamaina su tsorata ki Indo, ni ba mai cutarwa ba ce. Kawai ina sanar da ke wani sirri ne, domin tun da na fahimci kina tare da Suryu hankalina ya kwanta da ke. Duk da wani tsagin na zuciyata yana tantamar kasancewarki mahaifiyarta, domin ban ga alamun da Baushe ya ce mahaifiyarta tana da shi a jikinki ba. Ya ce mini mahaifiyarta zuciyar zaki gare ta na rashin tsoro, ke kuma na ga tsoro ƙarara a saman fuskarki. Sai dai kuma na tabbata ko da ba ke ce mahaifiyarta ba, tabbas zuciyarki mai kyau ce Indo." Sai a lokacin hankalin Indo ya ɗan kwanta, Zuwaira ta kawar da ƙwaryar da ta yi wa Batul wanka gefe sannan ta cigaba da faɗin. "Daga mahaifina har mahaifiyata ƙungurman mayu ne, har sai da ta kai mahaifina ya ci mutum ɗari ba ɗaya wanda silar haka ne ta sa a ka naɗa shi sarkin mayun yankinmu. Duk da dama can mahaifinsa shi yake riƙe da wannan sarautar, amma kasancewar mahaifina yana da tarin 'yan'uwa daga waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya zuwa 'yan uba. Sai suka taso shi a gaba saboda kowa so yake ya gaji sarautar mahaifinsu, sai dai duk miyagun sihirin da suke yi na jifan mahaifina bai yi tasiri a kansa ba. Da suka lura mahaifina yana son damƙa mini ragamar sarautar hannunsa, sai suke shiga jifana da asiri kala-kala. Kuma ni abin da ba su sani ba, ko kaɗan ban taɓa sha'awar riƙe kambun da mahaifina yake kai ba. Don mun sha kai ruwa rana da mahaifina, a kan sai na ci adadin mutanen da ake ci kafin a damƙa maka ragamar sarautar maita. Me zai sa na cutar da 'yan'uwana Indo? Bayan kuma Ubangiji bai hallice mu don mu cutar da kowa ba, kuma me zai hana mu dinga taimakon bayar da magani a madadin cutarwa?" Indo ta jinjina kai ta ce, "Haka ne kam Inna Zuwaira." Zuwaira ta ji daɗin sunan da Indo ta faɗa mata, don ta tabbata a haife kam za ta haifi Indo. "To don na nuna wa mahaifina haka, sai ƙilu ta ja bau. Mahaifina ya sako ni a gaba, haka dangin mahaifina da suke zargin za a damƙa mini sarauta suka sako ni a gaba. A taƙaice dai har sai da mahaifina ya so bayar da kurwata a bikin bada kurwa da ake yi a yankinmu duk shekara, amma sai mahaifiyata ta tsaya kai da fata don ganin hakan ba ta tabbata ba. In taƙaice miki labari, ban san hawa da sauka ba sai kawai na wayi gari da wasu baƙin cututtuka. Yau da lafiya gobe babu, hatta mijin da na aura mun haɗu ne a wurin neman magani. Da Innata ta kai ni shi kuma ya nuna yana sona, amma duk sanin sirrin maganinsa sai ya gagara gano ainahin abin da yake damuna. A haka na fara haihuwar yara suna mutuwa, abin da ban sani ba ashe dangin mahaifina ne suke kashe mini su suna cinyewa. Wannan ɗan da kika ga na zo da shi masarautar nan, shi kaɗai ne ya rayu a cikin yara goma da na haifa. Shi ma tun cikinsa yana ƙarami na fara zuwa wurin Baushe mai magani, a nan ya dinga ba ni taimakon magunguna har Allah Ya sa na haife shi lafiya. Ranar da na fara shayar da shi, a ranar na ga abin al'ajabi. A madadin ruwan mama ya zuba, sai ya zamana wani baƙin jini ne yake fita. Jaririna ya ƙi karɓa, bayan da na koma wurin Baushe ya ba ni magani sai na samu lafiya. A nan ya sake sanar da ni duk irin cutukan da ke jikina, tare da makarinsu da kuma yadda za a yi na samu lafiya." Buɗe baki Zuwaira ta yi, ta zaro wani abu fari mai tsayi kamar zare. Ita dai Indo tana takure a gefe sai raba idanuwa take yi, kama hannun Batul ta yi za ta saka mata. Da sauri Indo ta janye Batul gabanta yana faɗuwa ta ce. "Don Allah kada ki sa ta zama mayya ita ma, don Allah ki ƙyale ta haka." Murmushi Zuwaira ta yi, busasshiyar fuskarta da babu tsokar kirki ta sake yamutsewa. Da yake Indo ta gama tsora ta da ita, har gani ta yi fuskar Zuwaira tana neman razana ta. Tana cikin haka ta ji Zuwaira ta ce. "Ba ƙanƙarar maita ba ce Indo, ina tunanin har yanzu ba ki san wace ce Batul ba. Shi ya sa kike tsammanin zan iya cutar da ita, wannan dalilin ne ya sa na sake tabbatar da ba ke ce mahaifiyarta ba." Indo ta waiga tana kalle-kalle don kada wani ya ji tattaunawarsu, ta yi ƙasa da murya ta ce. "Don girman Allah kada ki furta wannan maganar a cikin mutane, tabbas Batul ba 'yata ba ce. Ba ni na haife ta ba, amma ƙaddara ta haifar mini ita kuma zan riƙe ta hannu bibbiyu." Nan take Indo ta kwashe duk abin da ya faru tsakaninta da Karima ta sanar da ita, Zuwaira ta jinjina kai ta ce. "Shi ya sa na ce zuciyarki mai kyau ce Indo, kuma In Shaa Allahu zan cigaba da nuna wa duniya ke ɗin mahaifiyarta ce. Kuma na ɗauke ki tamkar 'yar cikina, haka kuma Batul kamar jika ta. Sai dai ni ma ina neman alfarma a wurinki." Idanu Indo ta zuba mata alamar tama sauraronta, Zuwaira ta ce. "Ki yi mini alƙawarin ba za ki taɓa sanarwa da kowa cewa ni mayya ba ce, haka kuma ba za ka dinga wasu-wasin zan cutar da ku ke da Batul ba. Sannan duk halin da kike ciki, ki mini alƙawarin ba za ki ɓoye mini ba." Gyaɗa kai Indo ta yi ta ce, "Zan faɗa miki amfanin wannan zaren da zan saka mata, kema kuma idan ba za ki damu ba. Zan saka miki shi a dantsen hannunki, idan kuma ba ki da muradi shi kenan ba zan tilasta miki ba." Zuwaira tana gama maganar ta naɗa zare ya zama kamar awarwaro, sai ta kamo hannun Batul ta zura mata shi, wani irin haske suka gani a jikin hannun nata. Nan take zaren ya fara kwanciya a fatar hannunta, daga ƙarshe ya shige cikin jikinta gabaɗaya tamkar wani abu bai taɓa wanzuwa ba. Daga Indo har Zuwaira kallon juna suka yi, bakin Indo yana rawa ta ce. "Ya... ya... aka yi ne Inna Zuwaira?" Zuwaira da ta gama tsora ta ta ce, "Wallahi ban san yadda aka haihu a ragaya na, ni a iya sanin da na yi wannan zaren yana zama a jikin hannu ne ba tare da ya ɓace ba. Amma ita nata ki duba ki ga har wata wuta ya yi kafin ya ɗauke." Kamar Indo za ta yi kuka ta miƙe tana jijjiga Batul da ta fara mutsu-mutsu za ta yi kuka. Suna cikin haka sai suka ga daidai wurin tsintaiyar hannun nata ya yi ja kamar an saka awarwaro a wuta an ciro an saka mata a wurin, wanda hakan ne ya tabbatar wa Zuwaira shatin zaren da ta saka mata a hannun ne. Uwar Bayi Uwar bayi sai da ta fito daga fadar sarki Giɗaɗo sannan ta ankara da irin katoɓara da kuma suɓutar bakin da ta yi. Musamman da ta tuna abin da ya faru da Dogari Mamma, gabanta ne ya shiga faɗuwa sai kuma ta tuna wane ne Sarki Gidaɗo da hatsabibancinsa. Da wannan ta ɗan ji faɗuwar gaban ta ragar mata, tana shiga soron farko ta ji kamar an hankaɗa ta har sai da ta kusa faɗuwa. Waigawa ta yi ba ta ga kowa ba, tana juyo da kanta don ta cigaba da tafiya sai ta hangi wata dattijuwa a gabanta. Da sauri ta ja baya tana sauke ajiyar zuciya, tsohuwar ta fara matsawa gabanta cikin muryar tsufa ta ce. "Uwar bayi sannu da ƙoƙari, ko babu komai za ki taka muhimmiyar rawa a wannan tafiyar..." Daga haka sai tsohuwar ta wuce soro na biyu, cikin sauri Uwar bayi ta bi ta. Sai dai tana zuwa soron ba ta ji koda takun tafiyar tsohuwar ba. Juya kalaman tsohuwar ta fara yi ba tare da ta fahimci inda suka dosa ba, don haka jiki a sanyaye ta cigaba da tafiya har ta fita daga soron ƙarshe. Zaniru ta hango suna surfe, ta yafito ta da hannu alamar ta zo. Jiki yana rawa Zinaru ta ƙarasa ta ce. "Barka da fitowa uwar bayi." Uwar bayi ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Mene ne ma sunaki?" Cikin sauri Zinaru ta ce, "Sunana Zinaru!" "Yarinyar jiya da ta haihu fa?" Uwar bayi ta tambaya tana zuba wa Zinaru idanu, shiru Zinaru ta yi tana nazari, cikin son gwaninta da neman samun wurin zama a wurin Uwar bayi ta yi ƙasa da murya ta ce. "Uwar bayi Indo fa ba ita ta haifi jaririyar nan ba, hasali ma Indo budurwa ce ko auren fari ba ta yi ba." Da sauri Uwar bayi ta dube ta ta ce, "Ke Zinaru ki fito ki yi mini bayani dalla-dalla, domin zancan da nake yi miki yanzu haka Takawa ne ya turo ni na kai ta wurinsa ita da jaririyarta. Kin ga kuwa tun da kin zo da ƙarin haske, za mu tafi da ke domin ki yi bayanin komai a wurinsa." Ƙuuu! Cikin Zinaru ya bayar da sautin mai ƙarfi, hankali a matuƙar tashe ta ce. "Don girman Allah don zatinSa ki yi mini rai Uwar bayi, wallahi tallahi abin da na faɗa gaskiya ne ba sai an kai ni gaban mai martaba ba." Da wani irin kallo Uwar bayi ta dube ta, sai kuma ta haɗe fuska ta ce. "Ke Zinaru ki shiga hankalinki, ni da kika gani ban taɓa faɗar magana an musa mini a wannan ɓangaren namu na bayi ba. Saboda haka dole ki wuce mu je har da ke gaban Takawa ki yi masa jawabin abin da kika sani, idan ba haka ba kuwa wani hukuncin daban zai iya biyo wa ta kanki." Uwar Bayi tana gama maganar ta yi gaba, wasu gajerun zafafan hawaye ne suka siraro daga ƙwayar idon Zinaru. Lokaci ɗaya ta ji nadama ta mamaye ta, tana danasanin ɓarin zancan da ta yi don ba ta yi tsammanin wankin hula zai kai ta dare ba. Zuwaira da Indo suna tsaka da tattaunawa, ba su yi aune ba suka ga Uwar bayi ta bankaɗa labulen ɗakin. Da sauri duka suka dube ta, kusan lokaci ɗaya gabansu ya yanke ya faɗi. Saboda ganin yanayin da Uwar bayi take ciki, fuska babu walwala ta ce. "Ke Indo! Ki ɗauko jaririyarki Mai martaba yana son ganinki cikin gaggawa." A hargitse Indo ta ɗago, nan take jikinta ya ɗauki karkarwa har ta matsa gaban Uwar bayi ba tare da ta sani ba. "Na'am... Uwar bayi... zuwa zan yi?" Cikin masifa Uwar bayi ta ce. "Kin ji abin da na faɗa tsabar iskanci ne ya sa kike sake tambayata." Kamar Indo ta san abin da yake faruwa, nan take hawaye ya cika idonta. Tana waigawa suka haɗa ido Zuwaira, alamar ta kawo mata ɗauki. Amma sai ta ga ita ma Zuwairar ta sunkuyar fa kai ƙasa cikin sanyin jiki. Babu yadda Indo ta iya, haka ta rungumi Batul ta ja sagaggun ƙafafuwanta ta bi bayan Uwar bayi suka nufi sashen Sarki Gidaɗo. Indo ta yi mamaki da ta ga har da Zinaru aka nufi sashen Takawa, sai dai ko kaɗan ba ta kawo komai ba. Sai ta yi tsammanin ko an gano sun tsinci jaririya a masarautar ne ba tare da sun sanar ba. Su uwar bayi ne a kan gaba wurin shiga ɗakin, sai Indo da take ƙarshen shiga. Tana tsoma ƙafarta ta ji baƙuwar murya a kunnenta ta ce, "Kada ki shiga, za a salwantar mini da ita. Kada ki manta Indo, amana ce na damƙa miki." Cak! Indo ta tsaya tana nazari. Kuma ta tabbata muryar Karima mahaifiyar Batul ce, tana nan tsaye kamar an daskarar da ita ta ji muryar Uwar bayi cikin tsawa tana faɗin. "Hattara Indo, kina gaban Mai martaba." Ajiyar zuciya ta sauke, ta fara takawa a hankali kamar wacce aka zare wa laka a jiki. Tana shiga ɗakin ta ji Batul da ke rungume a hannunta ta tsanyare da kuka, a duburburce ta shiga jijjiiga ta gabanta yana cigaba da faɗuwa, sai dai har ta zauna Batul ba ta daina tsanyara kuka ba. "Allah Ya taimake ka, wannan ita ce wacce na ce maka ta haihu jiya a masarautar nan. Sai dai kuma a yanzu maganar ta sha bambam da tawa ranka shi daɗe, domin wannan sunanta Zinaru ita kuma ta tabbatar mini da Indo ba ita ce mahaifiyar jaririyar ba. Amma idan ka lamunce mini ranka shi daɗe, zan gabatar da Zinaru ta warware mana zare da abawa." Uwar bayi ta yi maganar cikin girmamawa, fuskar Sarki Giɗaɗo a murtuke take. Don haka murya babu walwala ya ce. "Muna sauraren Zinaru." Indo ce ta ɗan zunguri Zinaru, Zinaru da ta gama yin fiƙi-fiƙi da idanu ta kawar da kai gefe daga kallon Indo ta ce. "Allah Ya taimake ka, abin da na faɗa haka yake. Indo ba ita ce mahaifiyarta ba, hasali ma Indo budurwa ce ko auren fari ba ta yi ba. Jiya da daddare mun fita na raka ta fitsari..." Zinaru ta kwashe duk iya abin da ta sani ta sanar wa da Sarki Giɗaɗo, ƙuri ya yi wa Indo yana kallo. Cikin rashin imani ya zaro wata sihirtacciya kuma kaifaffiyar askarsa da ke walwali da sheƙi ya ajiye a gefen cinyarsa. Sannan ya dubi Indo cikin wata irin murya ya ce. "A kawo mana jaririyar nan." Kalaman Sarki Gidaɗo ya yi daidai da faɗuwar gaban Indo a karo na barkatai, idanuwansa ne suka yi mata kwarjini. Jikinta ya shiga karkarwa kamar mazari, don haka jiki babu ƙwari ta miƙe ta fara takawa har gaban Sarki Gidaɗo. Babu yadda ta iya, haka ta ɗora masa Batul a saman hannunsa, wani irin zummm ya ji, haka ita ma daga ɓangaren Indo. Tana nan durƙushe a gabansa ya ce. "Wace ce ke? Wace ce ta damƙa muku jaririyar nan? Muna nufin wace ce mahaifiyarta." Tun sarki Gidaɗo bai rufe baki ba, daga can bakin ƙofa ya ji muryarta ta ƙarade kunnensa da cewar. "Ni ce mahaifiyarta." Ba iya sarki Gidaɗo ba, hatta su Jakadiya mutuwar zaune suka yi suna bin ta da kallo. Masarautar Kajjura Jin Tsoho Sulaimanu ya yi shiru ya sake fusata Kursum, don haka a harzuƙe ta matsa wurin da take jin hucinsa. Cikin fusata ta kai hannu ta shaƙo shi, sai ta yi nasarar shaƙar daidai wuyansa. Nan take ya fara kakari tamkar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa, sai da ta ji ya fara fita daga hayyacinsa sannan ta yi wurgi da shi ya faɗi ƙasa yana mayar da numfashi. "Na ce wane ne kai? Mene ne haɗinka da Najibullah? Kuma yaushe ne ya mutu?" Tsoho Sulaimanu ya furzar da iska yana sauke ajiyar zuciya a galabaice ya ce. "Sunana Tsoho Sulaimanu, kuma marigayi Najibullah tamkar ɗa yake a wurina." Sai ya haɗiyi yawu mai ɗaci, yana jin ɓacin rai da kewar Najibullah tamkar a lokacin sarki Gambo ya hallaka shi. "Sarki Gambo ne ya hallaka Najibullah da kisa mai muni, kuma ya sa aka killa ce matarsa Zainaba da zummar idan ta haihu a kashe abin da ta haifa. Idan har kunnuwana ba gizo suke yi mini ba, na ji ya ce zai auri Zainaba idan ta haife cikinta." Kuka ya fara cin ƙarfin Tsoho Sulaimu, sai da ya share hawayensa sannan ya cigaba. "Ni kaina ya kawo ni wurin nan me saboda na gagara bayyana masa maɓoyar kundin da yake kwana ya tashi da su. Kuma na san a tsawon waɗannan shekarun ya hallaka abin cikin Zainaba. Kaico! Da ban samu nasarar cika burin Najibullah ba." Tsoho Sulaimanu yana gama maganar ya fashe da kuka, yaraf! Ya ji alamar zamanta a ƙasa. Yana nan zaune bai yi tsammani ba sai ji ya yi ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Jikinsa ne ya sake yin sanyi, don tun daga ranar da ya shiga ɗakin har ya shafe waɗannan shekarun masu tsayi a tare da ita. Bai taɓa jin ta yi kukan da yake jin zafinsa har a cikin zuciyarsa ba. Don haka bai hana ta ba, haka kuma bai san dalilin kukan nata ba. Sai da ta yi mai isarta sannan ya ce. "Na jima ina jin sautin kukanki, sai dai ban taɓa jin makamancin irin wannan ba. Haƙiƙa akwai wata ɓoyayyar alaƙa tsakaninki da Najibullah, domin yanayinki ya sauya tun a lokacin da na ambaci sunansa." "Tabbas kalamanka haka suke, domin hawayen mahaifiya ya sha bambam da kowanne irin hawaye a faɗin duniya. Wannan kukan da nake yi yana tuna mini tarun abubuwan da suka cunkushe rayuwata. Na farko rashin mijina, mahaifi a wurin ɗana. Na biyu killace ni da azzalumin wancan bawan ya yi tsawon shekaru, ba tare da na cimma muradin mijina ba. Na uku rashin ɗana Najibullah, wanda na ɗora amincewa ta ɗungurungum zai iya dawo da martabar ahalinsa." Kursum ta share hawayenta sannan ta ce. "A baya zuciyata tamkar dutse take, sai dai a yanzu ta yi laushi tuɓus domin Sarki Gambo ya gama ruguza duk wata ƙwarin gwiwar da ke tattare da ni. Domin ya riga da ya hallaka duk wani..." "Har yanzu Sarki Gambo bai yi nasara ba, domin bai san wurin da kundi ukun nan suke ɓoye ba. Najibullah ya san da ɗaya, ni kuma na san maɓoyar biyu." Tsoho Sulaimanu ya katse Kursum, sautin murmushinta ya ji wanda ya alamta masa murmushin takaici ne take yi. Yana shirin yin magana ya ji ta ce. "A naka tunanin da binciken duk wani mai tsafi ko binciken sirihi ne, ake tsammanin kai ne mutumin da ya san maɓoyar kundi biyun da na hannun Najibullah. Alhalin a zahiri kuma ba haka ba ne, domin kundi biyun da ake tsammanin kana da masaniyar maɓoyarsu ba su ne ainahin kundin da ake muradin mallaka ba." Cikin tsananin mamaki Tsoho Sulaimanu ya ce, "Me kike nufi Kursum? Shin kina nufin kundi biyun da na sani, da wanda Najibullah ya sani ba su ba ne? Bayan har bokaye da 'yan tsubbu idan suka yi bincike kundin da muka sani suke faɗa." Takunta ya ji ta fara tafiya, sai kuma ya ji ta tsaya cak! A karo na biyu ya sake jin murmushinta sannan ta ce. "Kundin da ka sani da na Najibullah duka na jabu ne!" Zumbur Tsoho Sulaimanu ya miƙe yana sake juya kalamanta a zahiri. Yanzu ne wasan ya fara ɗaukar zafi😆 kada ku manta na faɗa muku shi fa wannan littafin kowa ba abin yarda ba ne. Don Allah waɗanda suka yi payment su yi mini salam saboda gobe zan buɗe group, saƙonni wasu sun yi ƙasa zan iya manta wasu. In Shaa Allahu saura shafi ɗaya mu kammala book 1 mai son cigaban 2&3 zai biya 700 ta wannan Acc ɗin Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 1k ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [30/11, 21:57] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA SHA BIYAR Masarautar Zulwara Tun Sarki Dikko yana jin ruwa mai sanyi yana mamaye shi, har ya ji yanayin ruwan ya fara sauyawa zuwa mai ɗumi-ɗumi. Wata irin tsawa ya ji ta tashi a cikin kabarin Sarauniya Humaira, ɗakin kabarin ya fara girgiza tamkar ƙasarsa za ta rushe ta haɗiye shi. Duk taurin zuciya irin ta Sarki Dikko, sai da ya ji wani matsanancin tsoro ya kama shi. Har ya fara saddaƙar da shi kansa tasa rayuwar ta zo ƙarshe, saboda ji ya yi ruwan da ya shanye shi ya daskare ta yadda ba zai iya motsa koda ɗan yatsansa. Yana cikin wannan yanayin, sai ya ji ruwan ya fara yin ƙasa. Wutar cikin ɗakin ta dawo kamar yadda take ci da farko, sai dai a ɓangare ɗaya ji ya yi jikinsa ya yi lakwas har da ƙyar yake iya motsa ƙafarsa. Ganin ya samu kansa, Sai Sarki Dikko bai daddara ba. Ya fara jan jiki a sanyaye ya tunkari wurin da littafin yake, yana miƙa hannu ya ji gabansa ya yanke ya faɗi. Amma haka ya yi ta maza ya miƙa hannunsa na hagu da zummar ya ɗauka. Wani irin sagewa mai haɗe da yin sanyi ya yi masa, ya janye hannunsa da ƙyar ya miƙa hannun dama a nan ya samu nasarar ɗauko littafin. Sai dai yana duba littafin ya ji daga bayansa an ce. "Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai." Da sauri ya waiga, sai dai bai ga komai ba, cike da mamaki ya sake maimaitawa. "Mutuwa, Rayuwa, Hatsari da Rai. Me hakan yake nufi?" Ya wurga wa kansa tambaya ba tare da hango wurin da amsar take ba. Cikin ɗakin ne ya cigaba da girgiza tamkar ƙasar ciki za ta faɗa ciki, don haka cikin sauri Sarki Dikko ya fice daga ɗakin sannan ya sake biyo siriryar doguwar hanyar da ya shigo. Sai da ya ƙasara cikin turakarsa, sannan ya rungume littafin a ƙirjinsa ya runtse ido cike da tsananin farinciki. "Haƙiƙa na yarda rayuwa kasada ce, cimma buri jajircewa ce. Duk wanda ya yi tseren agali tilas ɗayan biyu zai faru, kodai ya mace murus kuma ya kai ga hawa turbar tudun tsira." Sarki Dikko ya furta cike da farinciki yana sake ƙanƙame littafin kamar wani zai ƙwace masa. Har ya kai hannu zai buɗe littafin, sai kuma ya saki murmushi ya nufi ɗakin da tsoho Babagana yake zaune. Sai da ya zauna a kujerar da ke fuskantarsa, cikin izza, isa da ƙasaita ya ɗago masa littafin. Cikin tsananin mamaki Babagana ya ɗago a hargitse yana kallonsa, Sarki Dikko ya saki malalacin murmushi mai ɗauke da manufa da izgilanci ya ce. "Babagana na sha sanar da kai ni mai nasara ne! Duk wani abu da na saka a gaba sai na same shi." Babagana ya kawar da mamakin fuskarsa, don kada Sarki Dikko ya fahimci lagonsa ya ce. "Kana da nasara a wurin da nasarar da ma can taka ce, Sarki Dikko kada wannan nasarar da ka samu ta sa ka fara jin ka a matsayin mai nasara." A ɗan harzuƙe Sarki Dikko ya ce. "Me kake nufi?" "Ina nufin kai ba komai ba ne, domin wannan abin da ka yi kowanne mai numfashi ma zai iya." Babagana ya furta, duk waɗannan maganganun yana yin su ne don ya dasa wa Sarki Dikko wasu-wasi a zuciyarsa. Domin har a cikin ransa yake jin tsoro da shakkun makirci da taurin zuciya irin ta Sarki Dikko. Miƙewa tsaye Takawa ya yi, ya kalli Babagana ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, wacce ta sake kaɗa hanjin cikin Babagana. "Matuƙar wannan littafin shi ne zai ja mini gora zuwa ga ɗan uwanka Tsoho Sulaimanu da Dattijuwa Kursum. Ina mai tabbatar maka da nesa ta kusa zuwar mini kusa, haka zalika ina gab da mallakar manyan kundin da kowanne basarake yake fatan samu musamman Sarki Gambo da Sarki Giɗaɗo." Sarki Dikko ya yi furucinsa yana sake sakin dariyar ƙeta, duk da kalamansa sun sayaya jikin Babagana hakan bai dakushe masa ƙwarin gwawa ba. Cikin yanayin jikin tsufa ya dafa bangon ɗakin ya miƙe, sai da ya yi taku biyu ya matsa gaban Sarki Dikko sannan ya ce. "Na ji daɗi da rashin sani ya zama babban duhu ga kowanne mai numfashi. Ba zan ce maka uffan a kan maɓoyar Kundi uku ba, haka kuma ba zan dakatar da kai daga bulayin nemansa ba. Sai dai zan ce maka ga wani abu a kan matar sarki da ace da ido da tuni ta gani. Ko kuma na ce maka da magani a gonar yaro, amma rashin sani ya sashi bai sani ba." Babagana ya saki dariyar mugunta. Da sauri Sarki Dikko ya waigo ya ce. "Akwai abin da ka sani Babagana, ka hanzarta sanar da ni tun ban ɗauki mummunan mataki a kanka ba. Babagana ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas ina da masaniya, ina da sani mai zurfi game da wannan Kundin. Amma ba a yanzu ne lokacin ya dace na motsa ba, hukuncinka kuma a shirye nake da na karɓe shi kowanne iri ne. Amma ka sani, koda ka kashe ni na rantse da sarkin da ya busa mini numfashi. Ba za ka dakatar da wacce take ƙoƙarin ceton rayuwata daga nakasa taka rayuwar ba. Abu ɗaya zan ce maka Sarki Dikko, ita ɗin ta jima da yi maka illa, don ta kowacce fuska ta shammace ka. Ba za ka fuskanci haka ba sai a nan gaba, na tabbata ko ba na raye za ka tuna da kalamaina." Shiru Sarki Dikko ya yi yana nazari, cike da sanyin jiki ya ce. "Wace ce ita? A ina take? Me ya sa ban santa ba? Ko a binciken bokayena me ya sa ba su hango mini ita ba?" "Saboda ita ma ba ta fito ba sai da ta shirya, ta kasance tamkar ingarman dokin da ke gudu a dokar dajin sahara. Ta kasance wuta mai laƙume duk wani makamashi, ita ɗin zakanya ce mai ɗauke da zuciyar gawurtattun zakuna dubu..." "Ya isa!" Sarki Diko ya katse Babagana daga maganar da yake yi, cikin ƙufula ya ce. "Duk hatsabibancinta sai na tsamo ta da hannu." Babagana ya saki murmushi ya ce. "Ina maka fatan alheri." Daga haka Sarki Dikko ya fice daga ɗakin cikin takaici. Sarki Dikko zama ya yi a kan ƙasaitacciyar kujerarsa, ya ɗago littafin da aka buga bangonsa da fatar tsohon jemage. Daga ƙasan litttafin akwai wani gashi, wanda duk wanda ya san gashin ɗawaisu yana gani zai gane shi ne. Daga sama kuma wani gashi ne, wanda duk wani maharbi yana gani zai san gashin jelar zaki ce. Daga tsakiyar bangon littafin cikin rubutun ajami an rubuta 'RUWA A WUTA' Sai waɗansu ƙananan rubuce-rubucen ajami, wanda sai ka ƙura ido sosai za ka gane abin da aka rubuta. Ganin zai wahalar da kansa, ya sa shi buɗe shafin farko ba tare da ya karanta ba. "Duk kalma ɗaya da ka tsallake daga cikin littafin nan, daidai take da gayyato masifar da ba ka yi tsammani ba a kundin rayuwarka." Ya ji an furta da wata irin murya, wacce yaka jin kamar ya taɓa saninta. Yana sauke idonsa don ya cigaba da karatu ya ji sallamar Shamaki a bakin ƙofa, da sauri ya rufe littafin. Ya ƙarasa can ƙarƙashin gado ya zaro wata tsohuwar akwati ya zura a ciki. Sai da ya koma mazauninsa, sannan ya ba wa Shamaki izinin shiga. "Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Jakadiya ce take neman iso idan ka lamunce mata ranka shi daɗe." Shamaki ya furta yana sunkuyar da kai ƙasa. "A ba su dama." Sarki Dikko ya furta a taƙaice. Cikin girmamawa Shamaki ya ce. "A huta lafiya ranka shi daɗe." Miƙewa ya yi ya fita bayan Takawa ya ba shi izini, yana fita Jakadiya ta shiga. Sai da ta zube ta kwashi gaisuwa bayan ya amsa mata ta ce. "Allah Ya taimake ka, Fulani Asiya ce take son ganawa da kai ranka shi daɗe." Murmushi ta ga ya suɓuce masa, cike da annushuwa ya ce. "A cewa Fulani muna nan zuwa gare ta, mun hutar da ita da zuwa wurinmu." "Allah Ya ja zamanin amale, Allah Ya taimaki fari mai farar aniya. Garnaƙaƙin dutse kake, kowa ya yi faɗa da kai shi zai faɗi. Hadari mai zubar da ruwa, ƙasa mai karɓar shuka idan an gume ki rumbu ya kwana da yunwa. Ina gwanin wani ga nawa, ina wanda yake iƙirarin shi sarki ne ya zo ga ubangidansa. Sai ka yi gajimare mai ɓoye wata, sai ka yi damuna mai zubar da ruwan alheri. Sai ka yi ko da tsiya ko da ƙarfin ikon Allah." Murmushi Sarki Dikko ya yi ya ce, "Kulawa da yabawa Jakadiya." Cike da jin daɗi Jakadiya ta yi masa jinjina ta ce. "Idan mai martaba ya lamunce zan iya tafiya?" Amsa mata ya yi sannan ta yi masa godiya ta fita. Da fitar Jakafiya babu jimawa Sarki Dikko ya kira Shamaki, ya sanar da shi zai ziyarci sashen matansa wurin Fulani Asiya. Sai da ya koma ya shirya cikin shigar ƙasaita, ya yi kyau sosai sai baza ƙamshi yake yi. Sabuwar alƙyabba ce ya saka ta, wacce ta sha adon jajayen duwatsu. Fitowa ya yi yana dogara sandarsa, fadawa da Dogarai suka shiga yi masa kirari suna take masa baya. Har sai da suka je sashen matansa, sannan ya dakatar da su. Ya tura ƙofar ya shiga, sashen Fulani Aisha ne a farko, sai sashen Fulani Halima, Sashen Fulani Hauwa kulu na ƙarshe shi ne sashen Fulani Asiya. Da yake a jere kamar yadda suke uwargida da mabiyarta har zuwa amaryarsa Fulani Asiya. Duk a tsammaninsu zai leƙa sashensu ya fara ganim lafiyarsu, amma ga mamakinsu sai suka ga ya wuce wurin Fulani Asiya. Fulani Hauwa kulu tana daga ɗaki ta ga giftawarsa, mamaki da takaici ya kamata. Tana nan zaune ta ga ya fito har zai fita ta yunƙura ta fita wurinsa. "Ranka shi daɗe barka da hutawa." "Barka!" Ya amsa mata a daƙile, duk da bata ji daɗin abin da ya yi mata ba. Amma sai ta saki murmushi ta ce. "Ranka shi daɗe idan ba za ka damu ba mu shiga daga ciki..." "Duk abin da za ku faɗa, muna sauraronku ba sai mun shiga ba." Ya furta fuska a haɗe, ajiyar zuciya ta sauke tana haɗiyar yawu mai ɗaci ta ce. "Ranka shi daɗe haihuwa fa na yi, na aika Jakadiya ta sanar da kai ɗan babu rai, amma har aka binne shi ba ka zo ba. Kuma ba ka ga jaririn ba, sannan yanzu ka shigo ba ka leƙo ka ga lafiyata ba. Amma idan na yi kuskure ka yi haƙuri ranka shi daɗe." "Tun da muka ji shiru ai kuna cikin ƙoshin lafiya, haihuwa kuma tun da babu rai mene ne amfanin ganinsa? Muna da magada masu yawa, don haka ku yi haƙuri idan ma kun haifa sun mutu. Domin tun asali mun fi son jinin Fulani Asiya ya gaje mu, kuma hakan ce ta faru tun da kwalliya ta biya kuɗin sabulu." Cikin murmushi mai ɗauke da manufa ta ce, "Amma muna fatan waɗannan tagwayen su lafiyayyu ne da za su iya kula da sha'anin mulki?" Da mamaki Sarki Dikko ya dube ta, sai Fulani Hauwa kulu ta cigaba da cewa. "Amma kada ka sa a ranka su ne kaɗai za su iya zartar da mulkin masarautar nan. Wataƙila akwai wani jinin naka da zai shammaci magadan da ake tsammani." Tana gama faɗar haka ta faɗa ɗaki, cikin ƙasa da murya ta ce. "Sarki Dikko ka yi kuskure da kake tsammanin ni Karima zan lamumce maka, kuma ka yi ganganci da kake tsammanin tagwayenka za su mulki masarautar nan. Batul! Ita kaɗai ce za ta gaji karagar nan, ni kuma zan cigaba da yaƙi har na samu nasarar fitar da Babagana daga ƙangim bautarka." Tana rufe baki Sarki Dikko ya ɗaga labulen ɗakin ya ce, "Me kuke faɗa haka?" Fulani Hauwa kulu ta saki murmushin ƙeta ta ce. "A sauka lafiya ranka shi daɗe." Masarautar Kajjura Ɗan ɗagowa Sarki Gambo ya yi, ya zuba wa Fulani Sadiya idanu ya ce. "Matsalar da zan sanar da ke a kan su Hasana ne." "Ni ma matsalarsu ce take tafe da ni, Sarkina akwai gagarumar matsala. Ka gafarce ni ranka shi daɗe, amma a yadda na lura da su Hasana kamar ba su da wadatacciyar lafiya." "Ba kama ba ce Fulani..." Nan take Sarki Gambo ya zayyane mata duk abin da ya faru, Fulani Sadiya ta kawar da kai gefe tana sakin murmushim ƙeta. Amma sai ta danne ta ce. "Mene ne mafita Sakina, domin ba na son magauta su fahimci rauninmu. Ko kuma Malami ya kawo maka wata mafitar?" Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya sanar mata da bayanin Malami, sun jima suna tattaunawa. Sai da Fulani Sadiya ta kwantar da kai ta gama jin sirrin Sarki Gambo, sannan ta shiga nuna masa kulawa cike da soyayya. Fulani Zainaba A bayan ɗakunan bayi suka keɓe suna tattauna, cikin shigar ɓadda kama ta ce. "Wanzam na kira ka ne domin na sanar da kai na san duk wani tuggu da kuke kitsa wa kai da Ciroma, kuma kai ka sani idan har na buɗe baki a wurin Takawa taka ta ƙare." Wanzam da cikinsa yake kaɗawa ya ce, "Tuba nake ranki shi daɗe." Murmushin cin nasara ta yi ta ce, "Idan ka ga wannan maganar ta mutu, to tabbas ka samar mini da jinin Sarki Gambo a gobe Alhamis idan za ka yi masa aski. Idan ba haka ba kuwa, tabbas zan bankaɗa masa sirrinka. Sannan na sanar da shi tuggun da kuka binne a cikin turakarsa." Cikin sauri ya zube a ƙasa ya ce. "Tuba make uwar ɗakina, zan yi duk abin da kike buƙata." 'A Gobe war haka na tabbata na samu nasarar ganawa da tsoro Sulaimanu tare da Kursum.' Zainaba ta raya a ranta, daga can bayan bishiya Jakadiya da ke laɓe ta gyaɗa kai ta ce. "Ƙarshenki ya zo Fulani Zainaba, na rantse da girman Allah sai na yi sanadin da Sarki Gambo zai tarfa ki a ɗakin." A nan na zo ƙarshen book 1 na KUNDI UKU mai son karanta 2&3 zai tura 700 zuwa ga Aisha Adam 3090957579 shaidar biya ta nan 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa doc 1k Sarki Giɗaɗo ga shi da jaririya Batul, Sarki Gambo da Fulani Zainaba ga Jakadiya a gefe. Sarki Dikko ga Babagan ga Fulani Hauwa kulu/ Karima. Ba sai na ce komai ba, kun san dai akwai ƙura.👌🏻 Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624