(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤02¤¤ . ¤Wannan Sadaukar wa ce zuwa ga..... Boss dina, Yaya na, Dan uwa na, Bappa na, wanda adomin sa na ke nan, Allah ya ba shi sa'a da nasara a komai nasa da sauran en uwa musulmai gabaki daya... (MARABAS DAN ANTY) jinjina gare ka.¤ . Ci gaban labari... . Yace; Me zan taho miki dashi? Tana murmushi tace; ''Goba'' Yayi dariya yace; Kedai kam ina ga sai kin haifi da mai kalar goba...Shikenan sai na iso. Ya kashe wayar ya dauki makullin motarsa. Yana shirin fita ke nan Basiru masinja ya shigo ofishin rike da zungureren fayil(file) a hannunsa suka yi kici6us ya rusuna yace: Yalla6ai ga takardun injinan nan da akayi bonanza daga ofishin peter yace akawo maka kasa hannu. Ya kar6i fayil din ya dora akan tebur ya dauki biro yasa hannu(signing) sannan ya mikawa Basiru. Yana fita yaci karo da Alh. Sammani Sabo. Don haka dole suka koma cikin ofishin, suka gaisa Alh. Sagir yana dan fara'a yace; Alh. Sammani jiya nake tunanin na kira ka ban samu sarari ba. Alh. Sammani yayi murmushi yace; kada ka damu ni gani nazo da kaina. Alh. Sagir ya dan yi shiru na wani lokaci sannan yace; Gaskiya nayi tunani mai zurfi naga hakan bazata samu ba, musamman idan nace zan 6ullo da hakan a kungiya baza a aminta ba, don haka kawai nake ganin mu hakura...... Alh. Sammani ya bugi teburin da hannunsa yana dan murmushi yace; Kada ka damu Abokina,Aminina ni na san kai masoyi nane ko bayan ba raina zaka iya taimakon iyalina. Nagode da bayaninka yanzu yaushe ne za a dauka? Alh. Sagir yace; Eh, to kamar yadda aka soma fada tun can baya. Alh. Sammani ya yunkura yace; shikenan aminina ba matsala, amma ni zan yi tafiya zuwa Dubai har sai bayan komai ya kammala zan dawo. Don haka ina neman afuwa ga kowa-da kowa, a kuma kula da ci gaba da abubuwan da ake yi yadda ya kamata. Alh. Sagir yace; Yauwa aminina nagode kwarai da yadda ka hakura ka sadaukar. Babu komai. Ya rako shi har bakin kofa, sannan shi kuma ya koma cikin ofis din ya dauko makullunshi daya ajiye cike da farin ciki ya fito ya tunkari inda suke ajiye motoci. Ya kusa karasawa kenan yayi tuntu6e da wani 'Kashi ya kife kasa, bisa tsautsayi ya kama aman jini. Mutanen dake shawagi a gurin suka ankara da abinda ya faru don haka da sauri suka tunkaro shi, don kawo masa dauki. Aman jinin yake kashir6an saboda haka sai ba a tsaya 6ata lokaci ba aka kwashe shi aka nufi Asibiti dashi. Ko kafin a isa Asibitin ya gala baita sosai, da gaggawa aka shiga dashi Emergency room. Alh. Saminu wanda ya jagoranci zuwa Asubitin yayi amfani da wayar Alh. Sagir ya lalubo lambar Alh. Ahmad ya kira shi. Bugu daya wayar ta shiga. Yana dauka yace; Yane Baban gobe? Ko an sauka ne? Alh. Saminu yace; Bashi bane Daya daga cikin ma aikatan gidan gonarsa ne, don Allah ka same mu a NAJNOOR HOSPITAL, Saboda oga yazo hawa mota yayi tuntu6e ya kama aman jini. Shine muka kawo shi Asibiti. Cikin tashin hankali Alh. Ahmad yace; To gani nan zuwa. Mintin sha biyar a tsakani Alh. Ahmad ya iso Asibitin. A lokacin suna da damar shiga inda yake saboda an samu aman jinin ya tsagaita. Suna shiga suka tarar dashi dik ya yamutse kamanninsa dik sun sauya,tamkar wanda yayi ciwon shekara. Alh. Ahmad ya matsa kusa dashi yaga idanunsa sunyi jajur kamar jan gauta. Wani irin siririn haske ne acikin idonshi,sai kace yana saitin hasken kwan lantarki. Cikin tausayawa Alh. Ahmad yace; sannu Alh. Sagir. Bai iya amsawa ba, sai dai idanu kawai da ya zuba masa,kai kace wannan shine karo na farko da yayi tozali da shi..... ada Hausa Book stories MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA) ¤¤03¤¤ Dama baka lafiya ne ko kuwa sanadin tuntu6en ne? Har yanzu bai iya tankawa ba sai Alh. Saminu ya amshi zancen da cewa; Gaskiya nima ina tunanin bashi da lafiya, domin yaui sukuku yake a gidan gona,tunda ya shiga ofis dinsa bai fito ba sai da wannan sanadin ya faru. Alh. Ahmad yace; To Allah ya bashi lafiya? Gaba daya suka amsa Ameen. Sun shafe mintuna goma babu wanda ya sake magana daga cikinsu. Sai zuwa can Alh. Sagir ya lumshe ido Alh. Saminu yace; Ina ga ma ya samu bacci. Alh. Ahmad ya dago kai ya dubi Alh. Sagir, sai ya ga ya bude ido, amma kwayar idon ta sauya launi ta koma KORE shar, sannan ta koma DORAWA, sai ta koma BAKI. Shikenan ya maida idon ya rufe. Gaban Alh. Ahmad ya fadi, bai fahimci abin da ya gani ba, ya dubi Alh. Saminu da sauri yace; Ku duba ku gani yadda kwayar idonsa ke sauya launi. Da sauri suka dubi Alh. Sagir amma sai suka ga kwayar idonsa a rufe Alh. Saminu yace ai bacci yake. Alh. Ahmad ya dunga tunanin anya kuwa bai ga wani al'amari ya faru da dan'uwansa ba? Amma jin amsar da suka bashi yasa ya share maganar. Alh. Saminu yace ya kamata a sanar da maidakinsa. Alh. Ahmad yace; Eh ba ma ita kadai ba harda mahaifanmu. Ya ciro waya yana niyyar doka kira kenan, Alh. Sagir ya mike a firgice ya dafe kansa da hannunsa guda da ba a dora masa ruwa ba? Alh. Ahmad ya maida wayar a aljihu ya matso da sauri kusa da dan'uwan shi yana tambayar; Ya jikin? Amma shiru bai tanka ba daga karshe sai ya koma yaraf! Akan gado. Gaba dayansu suka saka sallallami, daya daga cikinsu yayi saurin kirawo likita. Ya duba shi ya tabbatar musu da RAI YAYI HALINSA. Kwalla suka sirnanowa Alh. Ahmad cikin karfin hali ya kirawo mahaifinsu ya shaida masa halin da ake ciki. Sannan ya kira Alh. Sada shima ya bayyana masa abinda yake faruwa. Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankalinsu a tashe. Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankali a tashe, aka gama dik abinda ya dace sannan aka basu mota (Ambulance) da zata kai musu gawar a gida. Suka taho,kowannensu cike da wannan jimamin wannan BABBAN RASHIN da sukayi, Saboda rashin irinsu Alh. Sagir yana da matukar ta6a zuciya. Jan gwarzo jarumi wanda ya tsayu da kyautatawa na kasa dashi, zai yi wuya talaka ya kawo kukansa ga Alh. Sagir ba tare da an share masa hawaye ba. Amma duk wannan yakana tasa bata hana ya amsa kiran mahaliccinmu ba. Laillai Allah baya barin wani don wani yaji dadi!!! Kuma dik jarumtar rai da nuna hazikanci, dole ne ta dandani mutuwa. (Dacin mutuwa mai ta6a zuciyar wadanda aka yi wa komai, ma'ana juriya da jarumta basu isa su hana rai dandanar mutuwa ba, yayin da suka rasa wani nasu) mu samman ma Alh. Sagir da ya zamto tamkar shugaba a wannan tsatso, saboda yapi kowa kudi a cikinsu. . (ALLAH YA JIKAN MARUBUCIYAR WANNAN LITTAPIN YA GAFARTA MATA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA AMEEN) . Ci gaban labari... KADDARA TA RIGA FATA Haj. Karimatu tana zaune a falo Haj Asmo ta shigo dauke da faranti a hannunta, fuskarta kunshe da fara'a tace; Yau dai ina sauke hakkin da ya rataya a wuyana. Haj karima tayi murmushe tace; uhm kaji manyan masu gida, don anyi min sanwa shine ake koda kai? To dama kin bari domin ba gwaninta kikayi ba tunda ba ci zanyi ba shi dai na karfen ya dawo yaci. Haj Asmo ta zauna a gefenta tace ke kin isa? Ai bazan wahala a banza ba. Haj Karima tace ; Ko yanzu ba kiyi wahalar banza ba,tunda dan'uwanki zai dawo,kinga kin hutashshe dani. Tace wlh kuwa ke nifa yau tinda na tashi nake jin gabana na faduwa komai ba yayi min dadi,hatta yawun bakina daci yake min. Ga shi dan da yake cikina yana ta yamutsamin 'ya'yan hanji. Haj Asmo ta danyi murmushi tace; To ko dai haihuwar ta zone? Don dama naga cikin naki yayi kasa sosai. Haj Karima tayi murmushi ita ma tace; Wai ita mai tsohon ciki babu wani ciwo ko damuwa da zata shiga sai dole nakuda? Ni fa wallahi tsoro ma nake kada na zo haihuwar nan na wuce. Haj Asmo tace; Ai haihuwa ba mutuwa bace ke dai Allah ya sauke ki lapiya, amma ki daure kici abincin nan zama da yunwa yana azabtar da mai ciki. Haj Karima tace; Bazaki gane me nake nufi ba, sam ba na jin yunwa kuma bana iya kai komai a bakina. Ke dai kici kawai ba ra na shiga daga ciki. Haj Asmo ta dan harare ta, ta wutsiyar ido tace; Ke dai ko wayo kike so ki yi min ki shiga daki ki haihu sai dai na jiyo kukan jariri? Dariya Haj Karima tayi tace; A'a wallahi kinga ma na fasa shiga dakin shike nan? Za tayi magana suka ji karar tsayuwar mota Haj karima tace; Ina ga ma gashi nan ya iso. Haj Asmo tace mai yuwuwa bashi kadai bane naji kamar karar tsayuwar motoci ne ba daya ba. Tace kila shi da Abokanensa ne Kafin su gama tantancewa Alh. Sada ya danno kanshi cikin falon fuskarshi babu annuri suka amsa sallamarsa. Haj Asmo ta dora da cewa: Ai naje gidanka baka nan shine na wuto nan kafin anjima na koma. A takaice yace; Ai gwara ma da kika zo nan din. Ya dubi Haj Karima yace ina makullin sitroom? Kafin ta bashi amsa sai da suka kalli juna ita da Haj Asmo sannan daga bisani tace; Yana daki, yace kawo min. Zata tambayeshi ya daga mata hannu yace: Hanzarta ana jirana a waje. Haj Asmo jikinta yayi sanyi ta dubi Haj. Karima tace; Ko ki fada min inda yake sai na dauko, tace; yana kan dressing mirror. Haj Asmo ta nufi dakin a hanzarce ta dauko makullin sitroom ta kawo masa. Ya kar6a ya fice ba tare da yayi musu bayanin komai ba. Sai da aka shigo da gawar Alh Sagir tukunna Alh Rabi'u ya shigo falon. Ga ninshi da suka yi gabansu ya tsananta faduwa, tabbas ya nuna musu akwai wani al'amari da yake faruwa sai dai basu san ta ina abin yake ba. Suka durkushe su duka biyun suna gaishe da shi. Bayan ya daidaita zaman shi akan kujera ya amsa musu ya dubi Haj Karima murya a taushe irin ta dattako yace..... . . Gaskiya ban gane canzawar idanuwan sa ba!!! Se ku cigaba da biyo mu, dan jin yanda za a kaya....... Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA) ¤¤04¤¤ . ''Karima ina so ki sani Allah shiya halicce mu ba ya barin wani don wani kuma dikkan rai bata wuce wa'adinta. Allah yayi wa mijinki rasuwa!!!! Yana sitroom ki taso ki masa wanka don a sadar dashi da gidansa na gaskiya. Wasu taurari ta gani suna walainiya acikin idonta. Da sauri ta runtse idonta tana tunanin mafarki ne take amma koda ta bude idon sai ta ga dattijon surukin tsohon nata a zaune, wannan ke nuni da KADDARA TA RIGA FATA! Abinda kunnuwanta suka jiye mata tabbas haka yake babu tababa. Yayin da Haj Asmo ta fashe da wani irin rikitaccen kuka su duka biyun suka mike da sauri cikin faduwar gaba suka tinkari sitroom din. Suna isa suka ga gawar shi a shimfede a kasa an lullu6e shi da sauri Haj karima ta kai hannunta ta yaye mayafin da aka rufe mamacin idanuwanta suka yi tozali da jarumin mijinta ai bata san lokacin da ta kurma kara ba. Ta zube kasa sumammiya. Gaba dayansu hankalinsu ya dugunzuma ya tashi suka nufe ta suna sallallammi. Ba a jinkirta ba aka kwasheta zuwa asibiti ana tunanin ita ma rai yayi halinsa. Lokacin da ta farfado daga sumanta ta farka ne tana ambaton sunan mijinta. Haj Asmo dake gefenta ta shiga rarrashinta da tausasan kalamai. Ta rirrike zanin da yake shimfide a saman gadon da ta ke kwance tana wani irin madodawa, Likita ya shigo yana dubata yayi mata allura sannan ya dubi Haj Asmo yace; Haihuwace zata yi zamu kaita dakin masu haihuwa. Haj Asmo tace shikenan Allah ya raba su lafiya. Aka mayar da Haj Karima dakin 'yan haihuwa sai dai ta jigata sosai kafin ta haihu. Ta haifo 'yarta mace santaleliya son kowa kin wanda ya rasa. Haj Asmo tana zane da ita a dakin hutu rungume da jaririyar yayin da mai jegon take sharar baccin gajiya. Su Alh. Ahnad suka shigo ta sanar dasu an sauka suka yi godiya ga Allah da ya rabata da cikin lafiya. Haj Asmo tace har an rufo yayan? Alh. Sada yace Eh, Tace to Allah ya jikansa ya kuma raya bayansa. Su duka suka amsa da Ameen. Misalin karfe tara na dare Haj Karima ta farka da sauri Haj Asmo ta jawo kula ta zuba mata farfesu sannanb ta hada mata ruwan shayi mai kauri ta matso kusa da ita. Tashi kisha wannan don ki samu karfin jikinki. Tsananin yunwar data ke ji ne yasa ta kar6a tasha. Sai a lokacin ne ta lura babu cikin da ke jikinta. Sam hankalinta bai kai ga jinjirar dake rungume a hannun Haj Asmo ba ta soma kuka. Haj Asmo ta shiga rarrashinta Haj karima tace; Shima cikin nawa ya zube koh? Haj Asmo ta mika mata jinjirar dake hannun ta tace; Bai zubeba ga abinda kika haifa 'ya mace ce. Ta dubi jinjirar fara sol da ita kyakkyawa idanuwanta hancinta girarta dik na uwarta ne yankan bakinta da tsawon ga6a ne kawai na mahaifinta. Tsotasar hannu kawai take tamkar me shan nono Haj Asmo ta ga bata da niyyar kar6ar yar ta girgiza kai tace; Kar6eta ki bata nono muga zata kama saboda tin da ta zo duniya ambata madara taki sha sai tsotsar hannu take gasi kuma ga dukkan alamu yunwa take ji. Ai ta jigata da yawa Allah ma ya auna arziki da rabon zata rayu. A hankali ta miko hannu zata kar6eta amma sai ta kasa Haj Asmo tace; Bari na daura miki ita a jiki ki bata ta sha. Naga ba kya iya daukarta ma ko? Ta karashe maganar tana kokarin dora mata 'yar ajiki. Ana kuwa saka mata kan nonon a baki ta kama zuko shi? Haj Karima ta kama cije le6e saboda yadda jinjirar take jawo ruwan nonon da karfi. Ji take tamkar zata tsinke mata shi. Haj Asmo ta lura da hakan tace; Daure saboda yana sabo ne data saba ruwan nonon yazo sosai zaki daina jin zafin. Da kyar ta daure 'yar ta sha ya ishe ta ta 6ingire da bacci Haj Asmo ta dauke ta ta kwantar cikin gadonta sannan ta juyo kan Haj karima tana kuma lallaminta. Washe gari 'yan uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa ganin jaririya da yiwa Haj karima gaisuwar mijinta. Ita dai kallonsu kawai take zuciyarta cike da radadin rashin data yi. Hakika tayi babban rashi a tsawon shekaru shiddan da suka yi da maigidan nata dai-dai da rana daya basu ta6a samun sa6ani ba. Kullum cikin tattali da nuna mata kauna yake. Ya koyar da ita matsanancin sonsa ta yadda ko wata unguwa yaje wadda zai kwana take samun kanta cikin kadaici. To yau gashi mai rabawa ta raba(Mutuwa) dole ne tayi kuka kuka kuwa mai ciwo, wanda baya da magani illa HAKURI da DANGANA. Kwananta biyu a asibiti aka sallame ta an so a sallame ta a washe garin data haihu to amma kasancewar tana fama da rashin afuwar jiki dole tasa aka jinkirta sai data kwana biyu. Ana sallamar ta kai tsaye gidanta aka zarce da ita 'yan uwa sai rarrashinta ake yi ana dannar zuciyarta don haka ta dan samu saukin zafin rashin da tayi. Ranar daren suna Alh Sada yazo gidan da daddare ya same ta yana tambayarta tana da za6in sunan da za a sakawa yarinyar? Kuka ta kamayi sai da ya rarrashe ta tayi shiru sannan tace; Marigayi ya ta6a cewa idan mace na haifa SHUHUDA za a Saka mata . Idan kuma namiji ne JAMILU. Alh Sada yace Shikenan za a saka mata Shuhudan sannan munyanke shawarar zaki zauna anan gidan ki shayar da yarki har zuwa lokacin da Allah zai fito miki da miji ki yi Aure. Ba ta iya ce mishi komai ba amma ita a zuciyarta bata tunanin zata iya auren wani namiji anan gaba saboda da kyar ne ta samu wanda yake sonta kamar yadda mijinta yake sonta ba. An yi taron suna da sadakar bakwai sai dai taron sunan babu armashi kamar yadda suka ci buri idan an haihu za a yi. Sai dai wani abu daya daurewa kowa kai shine; TSOTSAR HANNU da Shuhuda ke yi. Idan tana kwance aikin kenan haka idan wani ya dauke ta abin dake raba ta da tsotsar hannu to kuwa sai idan mahgaifiyar ta tana bata nono ne. Ga shi yadda take tsotsar hannu abin ya wuce misali tsotsa take yi da karfi kamar me tsotsar nono. Goggo Zuwai kanwar mahaifiyar Haj Karima ita ta zauna a gidan kasancewar mijinta ya rasu kuma yayanta dik mata ne suna ma'auri. Tana matukar kokarinta wajen ganin ta korewa Haj Karima damuwa ba laifi ana samun yadda ake so Haj karima ta rungumi kaddararta hannu biyu tana yawaita aikawa mijinta addu'o'in samun haske da rahamar Ubangiji a kabarinsa. . Tafiya sannu-sannu kwana nesa har aka samu tsayin shekar guda shuhuda tayi wayo sosai har tafiya ma tana dan ta6awa saboda ta tashi da kazarniya. Zuwa wannan lokacin zawarawa sun yiwa Haj Karima caa yawancinsu duk abokanan mijinta ne sai dai babu wanda ta ke kulawa har yanzu tana kewar mijinta. Dangin mijinta sun yi maya halacci domin suna matukar kula da ita babu mai son ya ganta cikin damuwa sun rungume ta tamkar ita ce tasu ba mai rasuwar ba. Tana matukar jindadin haka ko dama can farko aurensu da mai rasuwar sun nuna mata kauna kaunar ce ma har yanzu take bibiyarta. Ranar laraba da daddare misalin karfe takwas Haj karima da Goggo zuwai suna zaune a falo bayan sun gama sallar isha'i suna kallon labaran duniya.: Inna Yaduwa( mahaifiyar mijinta) suka yi sallama ita da ISAH (dan Alh Sada mai kimanin shekaru bakwai). Bayan sun zauna an gaisa Haj karima ta kawo musu abinci suka dan ci kadan saboda a koshe suke. Inna yaduwa ta dubi Haj karima tace; Karimatu musamman zuwan nan ba yi shi dominki. Gaban Haj karima ya fadi tsoroi ya kamata ta tuna ranar da Alh Rabi'u yazo mata da bakin labari tana gudu kada ace ita ma Inna yaduwan ta zo mata da bakin labarin mutuwar mahaifanta ne(Ance idan maciji ya sare ka tsumma ka gani sai ka ruga. Inna Yaduwa ta lura da halin da Haj karima ta shiga sai tayi murmushi tace; Kwantar da hankalin ki shawara ce zamuyi dake. Ta sauke gwauron nunfashi yayin da Inna yaduwa ta ci gaba da cewa. Shuhuda yanzu ta samu shekara daya sai dai duk wanda zai ganta zai dauka ta wuce haka saboda girman jikinta ga wayo tana da shi. To sai nake ganin me zai hana wata uku masu zuwa a cire ta daga nono tunda dama ba damuwa tayi da shi sosai ba?? Shiru Haj karima ta yi bata tanka ba saboda alkunya da yakana irin ta mutan da. Sai gwaggo Zuwai ce tayi magana; ............................................................ ................. Nima nayi wannan tunanin tunda a yini bai fi tasha nono sau biyu ko sau uku ba musamman ma yadda zawarawa suka fito suna son aurenta sai na ga cire Shuhudan a nono tayi aure zai fi da cewa. Inna Yaduwa tace Sannan kuma mai zai hana Ahmad ya maye gurbin marigayi , tun da shima ya nuna yana bukata? Da sauri Haj karima ta mike tsaye tare da zaro ido waje sai dai bata iya cewa komai ba sai girgiza kai da take yi tana ja da baya. Inna Yaduwa tace Kinga zauna idan bai kwanta miki ba babu dole dama shawara ce saboda shi dan uwan sagir ne zai iya zaunawa dake da yarki amma a wannan zamanin da wuya ne samun mijin da zai rike agola. Koda ya riketa ma sai kinga bambanci,don haka na yi miki sha'awar auren Ahmad to amma tunda bai kwanta miki ba , kada ki damu Allah Ubangiji ya za6a miki miji nagari. Idan lokacin yayen yayi zan zo na kar6e ta na yaye miki ita. Tana karashe fadar haka ta dubi Isah tace; Kai tashi Muje. Yace Kai Inna mun fa yi dake a nan zaki bar ni gurin 'yar uwata. Ta yi dariya Idan na barka makaranta fa? Yace; Ba sai direban ya zo nan ya dauke ni ba? Tace; kai ni taso mu ta fi, ka ta6a ganin maigida na gudun matarsa? Ba don yaso ba dole ya mike, Inna Yaduwa ta dubi Haj karima tace; Mu mun tafi. Jiki a sa6ule Haj karima tace; Shikenan Inna na gode Allah ya sauke ku lafiya. Inna Yaduwa ta amsa da 'Amin' sannan suka fice daga cikin gidan. Bayan tafiyarsu Goggo Zuwai ta dubi Haj Karima tace: Ke kuwa 'yar nan meye aibun Alh Ahmad da kika razana don an yi miki sha'awar aurensa? Idon Haj karima ya kawo kwalla a idonta tace; Kin gane Goggo ba zan iya rayuwar Aure da Alh Ahmad ba, ba wai don baya da kyawawan halaye ba sai dai don idan na dube shi zan dinga tunawa da kaninsa kuma ma dai gaskiya ina jin kunya da tsoron matanshi. Goggo zuwai tace; Hakane to amma ai wanda ya rasu ya riga ya rasu, su kuma matanshi ai sun san akwai aure a tsakanin ku. Tsoron me zaki ji nasu? A kansu zaki zauna ko kuwa? Kowa zaman kansa zai yi don haka ina ganin shi ya dace ki aura. Girgiza kanta tayi tace: Bazan iya aurenshi ba gwaggo. Tace To idan baki aure shi ba wa zaki aura? Kin dai san dole ne ki yi aure ko? Sai tayi shiri ta rasa abinda zata ce Tana da zawarawa da yawa wadanda sun fito ne domin su aure ta, kuma duk wanda ta za6a tana da yakinin zai kyautata mata sai dai ba zai kai ya mijinta ba. Don haka babu wanda ya kwanta mata. To amma tunda an 6illo da wannan maganar dole ne ta yo wani abu akai ko don tsallake wannan suradin. Maganar Gwaggo zuwai ta katse mata tunani tace; '' Aure a musulunci sunna ne daga cikin sunnonin Manzon Allah Muhammad(S.A.W) dama sauran manzanni da suka gabace shi Allah (S.W.T) Yace; Hakika mun aiki manzanni gabanka kuma mun sanya matan aure garesu da zuriyya(Ra'ad:38). Manzon Allah (S.A.W) yace ' Aure sunnata ce duk wanda yayi kyama ga sunnata to baya tare dani. Allah (S.W.T) yace '' ku auri abinda yayi muku dadi daga mata(Nisa'i:3). Akwai samun nutsuwa da kwanciyar hankali a 6angaren mata da miji. Allah (SWT) Yace 'Daga cikin ayoyinsa ya halitta muku mataye daga kawunan ku don ku natsu zuwa garesu? Ya kuma sanya soyayya da jin kai tsakaninku tabbas a cikin wannan akwai abubuwan lura ga mutane masu tunani kawai.(Rum:21). Manzon Allah yace (S.A.W) yace; '' Muna cewa duk namijin da bai yi aure ba to miskini ne komai yake da dukiya. Haka matar da bata yi aure ba miskiniya ce komai take da wadata''. A 6angare daya kuma duk wanda ya yi aure toya sami rabin addininsa,haka kuma al'umma suna mutunta da kuma fifita mai aure bisa ga wanda ba ya da aure. Idan kika tattara duk wannan bayanan da nayi miki ya isa ki san girma da darajar aure ga al'umma don haka kada ki bari zuciyarki tayi rauni ga gujewa abinda ya wajaba a gareki. Ita ZUCIYA MUGUN NAMA ce ko da yaushe anaso bawa ya dinga neman tsari da sharrinta domin idan ta gyaru gangar jiki ya gyaru,idan ta 6aci gangar jii ma ta 6aci''. ( ALLAHUMMA YA MU SARRIFAL QULUB SABBIT QULUBANA ALA DA'A TIKA) { YA UBANGIJI MAI SARRAFA ZUKATA KA SANYA ZUCIYARMU AKAN DA'ARKA) . Tayi shiru daga bayanin data ke yi yayin da Haj Karima ta kai hannu ta share kwallan dake zubowa daga idonta muryarta a raunane tace; Gwaggo zan yi aure ba zan ta6a gufunsa ba Inshaa Allah zan fitar da miji amma bazan iya auren Alh. Ahmad ba. Gwaggo zuwai tace Eh hakan ma yayi domin ba zamu tursasa ki auren da bai kwanta miki a rai ba kece zaki zauna da shi don haka idan zuciyarki bata aminta da shi ba ba zaki samu kwanciyar hankali ba Allah Ubangiji ya za6a na gari. Can kasan makoshi Haj karima ta amsa ''Amin'' ***** ***** ***** An shirya ranar juma'a da safe Inna Yaduwa zata zi ta kar6i Shuhuda don yaye ta kamar yadda aka tsara tun farko cewa idan tayi shekara daya da wata uku za a yaye ta. To tun ranar talata da aka yi maganar yarinyar tayaye kanta anyi-anyi ta kama nono amma taki sai dai tsotson hannun kawai take . Hankalin Haj Karima yayi matukar tashi ganin har yammaci yayi amma shuhuda taki tasha nono abincin ma dan kadan taci kuma babu kuka babu fitina sai ma bacci da take yawan yi. To a ranar anyu katari Gwaggo zuwai bata nan taje gidan yarta data haihu don haka gidan Haj karima ce kadai. Ta rasa yadda zata yu ita bata ta6a yaye ba hasalima bata ta6a ganin yadda ake yinsa ba saboda mace ce mai matukar tausayi bata son ganin yaro yana kuka yanzu ita ma ta kama kuka. Ganoin yadda shuhuda taki kama nono sai ta dinga tunani ko dama haka ake yayen kafin ranar tazo yaro ya daina shan nono? An gama sallar magrib Gwaggo zuwai ta dawo gidan Haj karima ta kora mata bayanin duk abin da ya faru. Dariya tayi tace; Ai sai ki gode Allah dama haka wasu suke idan suka ji za a yaye su to sai su yi fushi da shan nono wasu kuwa lokacin ma zaki ga sun tsananta shan nonon. Saukinmu daya daurin nan ya huda mata jiki don haka idan Allah ya kaimu safiya lafiya sai a kaiwa surukar taki ita.. da Hausa Book stories MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA) ¤¤05¤¤ Haka kuwa aka yi gari na wayewa Gwaggo zuwai ta goye shuihuda a bayanta ta nufi gidan Inna Yaduwa da ita. Tun bayan tafiyarsu Haj karima shigewa daki tayi ta kama rusar kuka ta tabbata sai wani ikon Allah Shuhuda ta rayu a hannunta saboda ta lura da take-taken surukar tata so kawai take taga ta kar6e shuhudan tunda ai tana gidan mai rasuwar inna yaduwa ta kar6o Isah dan Alh Sada ya dawo hannunta tun daga yaye. Kwana biyu yarinya sai harkokinta take bata kuka sam! Sai dai tana da yawan bacci idan ta farka kuma shiru zaka ji tayi tamkar kurma,haka Isah zai zauna a kusa da ita yayi ta mata wasa. Idan yaje makaranta makaranta yayi mata siye-siyen kayan kwalam da ragowar kudin da ake bashi na tara(break). Shuhuda ta samu wata shida da yaye Allah ya fitowa Haj karimatu miji duk da ba wani kwanta mata arai yayi sosai ba,ta daure ta amince dashi saboda yadda mahaifanta da danginta suka dame ta da maganar aure dadin-dadawa kuma gashi Alh Ahmad na yawan zuwa gidan. Ita kuma ta gama karantarshi tsaf fuskace dai bata ba bashi ba shi yasa bai yi mata maganar ba. Alh Jamilu Ahmad Karare, dan asalin karamar hukuimar Batsari ne a wani kauye mai suna karare cikin jihar katsina Dan kasuwa ne sosai yana da mata biyu da yaya shidda maza da mata. Haj karima ta aminta da aurenn Alh Jamilu ne kawai don ba yadda zata yi ya fito ne 6angaren mahaifinta amma ba tursasata yayi ba, ya dai nuna mata idan ta auri Alh Jamilun zai ji dadi zai yi farin ciki yana da yakinin zata samu zaman lafiya a gidan aurenta. Duka-duka haduwarsu da komai bai fi wata daya ba aka daura aure sati daya zata tare. Ta shiga tunanin yadda za ayi ta kar6o shuhuda daga hannun Inna Yaduwa. Ranar Alh Jamilu yazo gurinta suna zaune a falo ta ke cewa dashi. Alh. Wata alfarma nake roko gurinka. Yana murmushi yace mata. Fada ai kin wuce haka a gurina. Tace Dama so nake na kar6o Shuhuda na riketa a gurina. Yayi jim na wani lokaci sannan yace; Babu komai ai da na kowa ne musamman ma rikon maraya lada ne da shi. Sai dai inda gizo yake sakar da ta nemi a bata shuhuda sam kin amincewa suka yi suka ce ba su yarda Shuhuda tayi zaman agolanci ba dole a hannun Inna Yaduwa zata zauna. Haj karima bata iya musu iya musu ba don haka ta sanyawa zuciyarta dangana ta bar musu Shuhuda. Amma a yadda ta so, ta so ace ta rayu da Shuhuda a inuwa daya domin ta dinga debe mata kewar mijinta data rasa sai dai ba yadda zata yi ita mace ce mai kawaici da hakuri don haka a nan din ma dole hakurin ta sakawa ranta. A haka har ranar tarewa tazo aka shiryata aka mikata gidan mijinta can cikin jihar katsina cikin karamar hukumar Batsari a karare inda gidan Alh Jamilu yake. Tun durar yan rakiyar amarya da ita kanta amaryar suka soma cin karo da cin mutunci saboda matan Alh Jamilu irin matan nan ne na kauye wadanda suka dauki kishi da zafi ,amma kowaccensu baka raina haduwarta ba.don kana ganin uwargidan kaga barumayar asali ita ma ta tsakiyar barumayar ce farare tas dasu illa rashin iya zama da miji da kyautata masa kadai dake dawainiya dasu. Sai uwa-uba kazanta ga rashin iya girki mai dandano ba. Tun daga yan rakiyar har ita Hajiya kariman ba wanda ya kula da cin kashin da kishiyoyin suke yi haka suka gama komai suka ba wa Haj karima hakuri akan ta jure duk abin da zata gani ga matan nan idan ta yi haka sai ta ga komai ba komai ba. Suka yi mata sallama aka kwashe su cikin motocin da aka kawo su aka koma da su. ***** ****** ****** BABI NA DAYA IDAN AJALI YAYI KIRA........ Shuhuda ta tashi da wata irin bahaguwar rayuwa. Idan tana tsotsar hannun ko abincin bata cika ci ba . Inna yaduwa tayi fadan har ta gaji amma ba abinda ya ragu. Wata irin shakuwa ce tsakanin Shuhuda da dan' uwanta Isah ya kasance komai zai yi yana tare da Shuhuda makaranta ce kadai idan zai tafi yake rabuwa da ita. Har Inna Yaduwa na tsokanarshi tana cewa: Ka gama wayon naka amma baka isa kayi min kishiya da wannan bagidajiyar mai tsotsan hannu ba. Sai dai yayi murmushi kawai wani lokaci kuma yace; Kece bagidajiya amma shuhuda ba bagidajiya bace. Shuhuda tana da shekaru shidda aka sakata a makarantar islamiyya yarinyar tana da kwalwa sosai sai dai matsalar dake damunta tsorsar hannun nan nata. Yan ajinsu su yi ta tsokanarta wai ta girma tana tsotsar hannu bata damuwa don bata yi wayon da zata fahimci me suke nufi da hakan ba. Jarabawarsu ta farko sai ga shi Shuhudan ce tayi na daya har kyautuka aka yi mata a makarantar. Inna Yaduwa ta sanyata a gaba tana cewa: ' Kinga Shuhuda da zaki daina tsotsar hannu da sai kin fi haka kokari saboda mata masu tsotsar hannu ba sa da kokai. Don haka ki daina tsotsar hannu kin ji?? Tayi Shiru kawai ba tare da ta ce komai ba kuma ba ta daina tsotsar hannun ba. Shuhuda tana da kwalwa da kaifin basira ba ta yadda za a yi a koya mata abu ba ta dauke shi a kanta ba. Alh Sada suna matukar kulawa da ita tare da dukiyarta da mahaifinta ya rasu ya bari duk wata kadara tasa tun daga nan gida Nigeria zuwa kasashen waje babu abin da ba a kiblatasu ba kuma an ci gaba da tafiyar da harkokin kasuwancin yadda aka saba tun can baya. Yau ya kama ranar lahadi Shuhuda tana zaune ita da yayanta yana koya mata karatun Islamiyya a lokacin ba ta fi mintina sha biyar daga tashi a bacci ba. Inna Yaduwa na zaune gefensu tana kallonsu Ta gaza hakuri saboda yadda taga ana koyawa Shuhuda karatu amma ta zurmuka ya tsanta a baki sai tsotsa take yi. Ta mike tsaye da sauri cike da 6acin rai ta karasa inda Shuhuda take ta sa hannu ta gwa6e yatsan da take tsotsa. Ke kam kin ji haushin kanki kullum a yi ta abu daya dake sai kace mai kwalwar tumaki to na ga kin kara tsotsar hannun a gidan nan. Isah yace; Ke Shuhuda ki daina tsotsar hannu kin ji ko? Ta yi shiru hannunta na ajiye a kasa Inna Yaduwa ta koma ta zauna akan kujera tana bambamin fadanta. Ai kuwa tana zama Shuhuda ta maida yatsan a cikin baki tana tsotsa Inna Yaduwa ta sake harzuka tace; Wai ni uban me kike tsotsa a yatsan nan ne da ba zaki dai na ba? Dai-dai lokacin Salmai mai haja ta yi sallama a cikin falon Sam Inna yaduwa ba ta tsinkayo muryarta ba saboda tana rigima da Shuhuda tana son cire mata yatsan daga baki ita kuma Shuhuda ta kiya sai kakaniya suke. Salmai tace Haba Yaduwa ni da me ye haka? Inna yaduwa tace Bar ni da yar nan Salmai ta raina ni ne, kullum sai nayi fama da ita akan tsotsar hannu amma kamar mai kunnen kashi ta ki ta daina ta maidani mahaukaciya. Salmai tace Ayyah! Ai laifinki ne idan yaro yana tsotsar yatsa aka yi-akayi da shi ya ki dainawa mai dungurugum ake yi masa sai a samu zaman lafiya. Inna Yaduwa ta yamutsa fuska cikin rashin fahimta tace. Ban gane mai dungurugum ba? Salmai ta yi dariya dai-dai lokacin da ta ajiye jakar hajarta kasa tace. Tsarga hannun ake a saka masa borkono gobe ko cewa aka yi ya tsotsi hannun ba zai fara ba. Inna Yaduwa ta ce Ai ni tausayi nake ji bana iya tsarga hannunta da tuni na yi maganin abun.Salmai tace aikuwa idan ba ayi maganin abun da wuri ba haka zata mike har girmanta... Ke har ma ta haihu tana tsotsar hannu ga 'ya'ya a gabanta suna kallo wannan kuwa kuwa ai ba karamin faduwa bane. Inna Yaduwa ta jinjina kanta tace ; Lallai kam to ni yanzu ban san ya zan yi da wannan 'ya ba taurin kanta har mamaki yake bani ga ta 'yar karama yarinya amma idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya tankwarata. Ai haka dama wasu yaran suke akan tsotsar hannu ka rasa me suke tsotsa. Haka kawai yaro ya sanyawa kansa fitina ko abinci sai ki ga sai an yi da gaske yaro ke ci. To ni zan yi miki maganin abun dauko min dakakken barkono da sabuwar reza kiga ikon Allah. Isah ya yi sauri yace: Don Allah Inna kada ku tsaga mata hannu wannan zalunci ne!...... Inna Yaduwa ta kai mishi bugu. Kai ni rufe min baki sai a bar yarinya ta yi ta tsotsar hannu? Ta mike a zafafe ta dauko barkono da sabuwar reza ta kawo wa Salmai, amma ta kasa rike Shuhuda wai bata iya ganin tsarga hannun saboda tausayi. Ita kuwa Salmai ta kama Shuhuda take ta kokarun kwacewa, amma ina aikin gama ya gama. Tuni Salmai ta tsarge mata yatsa.!!!! Tashin hankali wanda ba a saka masa rana ai ko da tsarge yatsan sai RUWAN NONO fari kal ya dinga ambaliya maimakon JINI!!!!! Yau mun shiga uku! Yayin da Isah duk ya kidime ita kam wadda abin ya faru gare ta babu alamar tsoro ko razana a tare da ita sai ma daga yatsan tayi sama tana gyarawa nonon gurin zuba. Inna Yaduwa tana ganin abin da ya faru ga Shuhuda ita ma kidimewa tayi ta matso gurin tana sallallami. Isah yace; Inna kin ga abin da ake gudu ya faru. Ta juyo da dubanta gare shi tare da cewa : Yi sauri ka kira min mahaifinka a waya. Jikinsa na mazari ya kira lambar Alh Sada kara daya ya dauka yace: Ya dai Isamanu dan maryama? A figice Isah yace Abba kazi inji Inna za a kai Shuhuda asibiti Alh Sada yace Me ya samu Shuhudab ne??? . Isah yace Rauni ne a hannunta. Yace To gani nan zuwa. Inna Yaduwa ta dubi hannun Shuhuda har yanzu nonon ne yake tarara iya rudewa kam ta rude da wannan murdadden al'amari. Ita kuwa Salmai tsuru-tsuru ta yi hankalinta a matukar tashe ta rasa yadda aka yi hakan ta faru ita dai a saninta jini ne a jikin kowanne dan Adan, to ya akayi ita Shuhuda aka samu akasin haka? Gaba daya jikinta nono ko kuwa a yatsan nata kadai ne ke da nonon a maimakon jini? Idan a yatsan kadai ne ke da nonon shi ta ke tsotsa maimakon kiwo(feeding) nata? Wannan wani bakon al'amari ne mai rudani da daure kai. Su dukkansu aka rasa mai abin cewa kowa yayi shiru da abin da yake sakawa a cikin ransa. Ba a fi mintina goma sha uku ba Alh Sada ya dura a gidan Ko da ganin abin da yake faruwa hankalinsa ba karamin tashi ya yi ba ya dubi Inna Yaduwa yace; Inna ta ya aka yi haka ta faru. Inna Yaduwa tace To tsautsayi ne da ba ya wuce ranarsa Ba musan hikimar tsotsar hannun da Shuhuda take ba na sa aka tsarga hannun ashe nono ne take sha a jikin yatsan? Alh sada ya jimanta lamarin sannan yace; To shikenan Allah ya kyauta gaba ku taso muje clinic a dinke mata yatsan. Inna Yaduwa Isah gami da Shuhuda suka mike tsaye yayin da salmai take zaune a guri guda ta yi tsuru-tsuru da ita sai kace kazar da aka tsamo a cikin ruwa. Kai tsaye suka nufi kofar fita sai a sannan Salmai ta samu damar matsawa ita ma tabi bayansu suna fita mota suka shiga ita kuwa Salmai ficewa tayi daga gidan da jakar kayanta tana tafiya sukuku kamar mai tsoron taka kasa. FABCY CLINIC suka je Dr Ya'u ya jagorancui dinke yatsan /huhuda wanda har suka iso asibitin bai dai na ambaliyar da ruwan nono ba. Abin mamaki duk inda aka sa allura don dinkewa a jikin yatsan sai gurin ya 6ule nono yayi ta tarara. Shi kanshi Dr Ya'u ba karamin firgici ya shiga ba da ganin yadda lamarin ke gudana. . . Toh pa, ni ma se da na rude har waya ta ta pada ruwan jikin shuhuda... Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA) ¤¤06¤¤ Da ya ga haka sai ya dauko wani garin allura ya zuba a cikin raunin ya kawo bandeji ya lika mata sannan yayi mata allura. Yana cire tsinken allurar daga jikin Shuhuda zance ya sake shan bam-bam domin tsinken allurar ya karye a jikinta. Da sauri aka shiga theater room da ita aka samu da kyar aka tsinke allurar daga jikinta koda yake ita dakanta ta cire. Daidai lokacin ruwan nonon ya daina tarara sai wani irin nannauyan bacci ya sure ta. Dr Ya'u ya fito daga dakin tiyatar ya dubi Alh sada yace Alhaji dole sai ta kwana saboda gaskiya yanayin jikin yana bukatar kyakkyawar kulawa. Kaga bayan an samu an yi mata tiyata an cire tsinken allurar sai wani zazzafan zazza6i ya rufe ta. Yanzu dai ta samu bacci don haka ku yi hakuri ta kwana zuwa washegari sai a sallame ta idan komai ya dai-daita. Alh Sada ya sauke gauron numfashi cikin matukar jimami yace: 8abu komai Allah ya kaimu goben lafiya ya kuma bata sauki. Gaba daya suka amsa da ameen. Alh sada ya dubi Inna yaduwa yace Bari naje na kawo miki abubuwan da zaki bukata na amfani. A'ah bara mu je tare ai bacci take har maje mui dawo. Yace To. Suka shiga dakin da shuhuda take tana kwance tana ta sharar baccinta don haka suka fito su duka ukun suka nufi gida. Sun isa gidan Inna yaduwa ta shiga ciki ke nan wani yaro ya shigo yace; Inna wai ance a fada maki SALMAI MAI HAJA ta RASU. Inna yaduwa ta zabura tare da doka sallallami ido waje tace Salman ce ta rasu? Yanzu fa muka rabu da ita? Yaron yace Eh mota ce ta kade ta take wuyanta ya KARYE, Yanzu ma za arufo ta. Inna yaduwa ta sake jan sallallami ta dure tace; IDAN AJALI YA YI KIRA koba ciwo sai an tafi. Yanzun nan fa tabar gidan nan? Ta karashe magana tana nuna matukar alhininta. Yaron dai ya yi shiru yana sauraren ta. Alh sada ya shigo cikin gidan ganin ta jima bata fito ba. Ya tarar da ita cikin halin jimami yace; Inna ya baku fito ba? Kada fa ta farka babu kowa a kusa da ita. Tace. Tace Mhm kai dai bari wai Salmai ce ta rasu!! Yace wace Salmai? Tace salmai mai haja mana yanzun nan fa ta bar gidan nan bayan ta tsaga hannun Shuhuda wai mota ta kade ta. Ya ce Allah sarki kila tsabar rudewa ce ta sa ko gabanta ba ta gani har hakan ta faru. Allah dai ya jikanta ya rahamsheta. Tace Amin jiki ba kuzari ta hada kayan da zata hada suka nufi asibitin. Har lokacin Shuhuda bata farka ba bacci kawai take yi. Alh sada ya yiwa Inna yaduwa sallama ya tafi tare da Isah suka barta a nan. Sai a washegari ne misalin shida da rabi na safe shuhuda ta farka. Karfe takwas yan uwa da mutanen arziki aka yi ta zuwa ganinta da yi mata sannu da jiki. Misalin sha biyu na rana aka sallame su suka dunguma gida. ******** ********* ****** Zaman gidan Alh jamilu dai babu dadi domin sam karima ba ta da sukuni matansa ba sa sonra sun tsane ta musamman yadda suka ga yana riritata yana kulawa da ita. A ganinsu ya bam-banta su shi kuwa duk abin da yake yiwa karima ya na yi ne don mantar da ita alhinin rashin tsohon mijinta saboda a zahirin gaskiya karima ta yi rashi babba wanda take bukatar samun wanda zai maye mata gurbinsa. Alh jamilu adalin namiji ne kuma jarumi gwarzo yasan duk wani salo na soyayya don haka ya yi amfani da wannan damar ya mantar da karima bakin cikin da matansa ke kunsa mata. Koda yake a wani 6angaren ba ya da masaniyar irin zaman doya da manjan da ake yi a cikin gidan nasa. Saboda ya kasance mutum ba mazauni ba dan kasuwa ne da ke kewaya kasashen duniya. Ta 6angarenshi kam karima bata da matsalar komai domin ta samu nagartacciyar kulawa daga gare shi matsalarta ga matansa take su ma yayan nasu basu kyalle ba ne domin sam yaran basu da yarbiyyar to su ma ba ta ishe su ba bare su baiwa wasu. Rashin kunya kamar sa doke ta duj ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga yi mata korafi kenan. Rashin kunya kamar sa doketa duk ranar girkinta yaran da iyayensu sun dinga korafi kenan wai tana rage kudin cefane. Bayan komai akwai shi a cikin gidan tsakanin mai gidan da matan alheri ne ba ya baiwa mace kudin cefane amma don rashin adalci sai suke cewa tana rage kudin cefane. Wannan dalilin ya sa karima ba ta zama a falo koda yaushe tana cikin dakinta. Idan ka ganta a waje to kicin ko bandaki zata shiga kasancewar bandaki daya ne a tsakar gida wanda kowa yake amfani dashi sai kuma na shi mai gidan shi kuma idan ba mace ke da girki ba ba ta da damar shiga. Duk cikin yaran babu wanda yake kulata da maganar arziki ko gaishe da ita ba sayi to bata damu da hakan ba domin ba zamansu take yi ba. Zaman aure take shi kam zaman aure dan hakuri ne dama da mijin ta ke samun matsala wannan da da ciwo. Duk da wannan din ma da ciwo saboda zaman tare wani babban al'amari ne mai girma yana bukatar shakuwa da juna kyautatawa juna gami da taimakekeniya. To su lamarin matan Alh jamilu ba haka bane irin wannan banzan kishin ne suke na kauyanci kai yanzu ko a kauye a daina irin wannan kishin na hauka. Sam babu ragayya ba ta da ikon ta kwanta ta huta muddin aka ce ranar girkin ta ne. Habaici ko da yada bakaken maganganu abin ba a cewa komai har ma ta saba. Karima na kicin tana dafuwar miya ta gama kwashe tuwo miyar ce take son kadawa. Binta uwargidan Alh jamilu ta shigo kicin din tana bangaje karima ta dauko roba. Karima ta ja da baya sam batayi mamaki ba idan da sabo ta saba da irin wannan cin kashin da ake yi mata a gidan. Sai dai a ganinta izuwa yanzu yaci ace sun tsaya sun gina rayuwa mai kyau a tsakaninsu wannan zafin kishin babu inda zai kai su illa halaka. To amma ba yadda za a yi matan ne gasu nan dai kurum. Binta har ta kai kofa zata fita sai ta juyo tace; Allah wadaran naka ya lalace jakin dawa ya gana birni, Mace ba kyau ba ba siga ba amma sai shegen kilibibi da karfar baka to ni dai wallahi karyar duk wata juya bata isa ta fitar da ni a gidan mijina ba kowacce shegiya nan tazo ta tarar da ni don haka idan ban fidda mace ba ta yi kadan ta fidda ni. Karima tace Me ya kawo wannan maganar kuma? Binta tace Ban sani ba sai na ji makara don na lura kwanan nan wani karfi karfi kike ji idan kina magana tamkar zaki daki mutum. To idan kin isa kina ganin kanki ke wata abace ki kwa6e mu daku, kiga idan akwai kutumar da zaki diba a jikina. Karima ta girgiza kanta tace Ni kam bazan iya fada da ke ba ba ma ke ba ni a rayuwata ba na fada kowa kika ganni da shi burina na zauna da shi lafiya. Binta ta daka mata tsawa tace Rufe min baki bakar munafuka baki fada da kowa amma kin iya karfar baka ko? Kin iya ki kalallame miji ki raba shi da matansa ki raba shi da 'yayansa? To wallahi kin ji na rantse miki kin yi kadan kin yi tsururu a gidan nan muddin kika ce wannan mummunar dabi'ar zaki tsuro a gidan nan. Karima tace: Allah ya baki hakuri? Wannan kalami ya sake tunzura Binta tace Kin sa Alhaji ya bugi Mas'ud to idan dai ni na haifi Mas'ud har aban abada ba zai ta6a gayar da ke ba. Duk wani ahali nawa ba zai ta6a yin wata mu amala da ke ba, idan kina so ki burge ni kisa Alhaji ya sa wuka ya yanke kawunan duk wani ahali nawa akan ba sa gaishe ki sannan zan tabbatar da sunanki karima matar so. Ta ja wani dogon tsaki tace Shi kuma Alhajin yayi na farko ya yi na karshe don bashi ya sha min wahalar daukar cikin ba bare ya kama min 'yaya da duka akan wata banzar bazara ruwan kaka, juya wadda tun da ta shigo gidannan komai ya ta6ar6are. Tana karashe maganar ta sa kai ta fice daga kicin din ta bar karima nan tsaye sororo cike da takaici don halayen Binta ba su ba ta mamaki, sai dai tsoro. Ta tabbatar da ace za a bata umarni ta kashe ta ko jinkiri Binta ba zata yi ba zata iya kashe ta saboda wannan zafin kishin nata yayi yawa. Cikin rashin sukuni ta kammala miyar ta dawo daki da nufin ta huta kafin a dawo daga sallar azahar ta zubawa kowa nashi. Tana nan zaune ta jiyo sallama a falonta ta shaida muryar dattijuwa ce mai YAKANAH wadda ta nuna mata halacci ta sota a lokacin da take tare da ita wato Inna Yaduwa. Ai kuwa da sauri ta fito falon ta na lale marhabun da zuwanta. Bayan Inna yaduwa Shuhuda da Isah sun zauna Karima ta je ta zubo musu tuwon shinkafa miyar agushi ta kawo musu gami da ruwan sanyi. Ta zauna suna cin abincin suna gaisawa har suka kammala Inna yaduwa tace: Karimatu ki yi hakuri don Allah da jinkirin da aka samu na kawo miki Shuhuda tsayin watanni tara. Kinsan lamarin zaman gidan wani wuya gare shi musamman ma yadda na lura halayen abokanan zamanki ba ya da kyau. Karima tacr Lah! Wallahi Inna ba komai ai ana kawota don wannan karon an samu jinkiri sai ya zama wani abu? Wallahi ba komai. Shuhuda ta mike tsaye Inna yaduwa tace Ina zaki? Tace Fitsari zan yo? Ta fita Inna yaduwa ta dawo da dubanta ga karima ta ce; Ga fa danki kin san dul cikin satin nan ba zancen da yake sai naki yau dai ya takura sai na zo. Karima ta yi murmushi tace Isah ke nan? Ai shi kam da Mamansa sai Allah. Inna yaduwa ta dan saka nutsuwa tace. A nan zamu bar Shuhuda za ta yi miki sati biyu saboda mako mai kamawa zata soma zuwa Makarantar boko kuma kin san yaro idan ya na karatu baya da wani sukuni bare ga kuma Islamiyya. Karima taji dadi har cikin ranta da jin wannan batu saboda a yau zata kwana da gudan jininta 'ya daya tilo ta mallaka a duniya. Wadda in baci ita da sai ta aminta da maganar su Binta ke fada akanta cewar ita din juya ce to amma kasancewar ta san ta ta6a haihuwa sai zancen na su bai dauke ta ya nana da kasa ba. Ta san cewa tsawon shekaru biyar data shafe a gidan Alh jamilu Allah ne bai hukunto haihuwar da shi ba idan lokaci yayi zata haifa din. Kukan Shuhuda da suka jiyo ne a tsakar gida ya sa gaba daya suka mike tsaye a zabure suka nufo tsakar gidan. Mas'ud yaro dan shekaru sha tara suka hango ya kama Shuhuda yana jibga kamar wata tsaran shi. Sai dai suka ja tunga suka tsaya, Inna yaduwa ta dubi karima cike da tsananin mamaki ita karimar Inna yaduwan take kallo. Isah kam tuni ya kaiwa 'yar uwarshi dauki ya cakumi wuyan rigarshi ya yi wurgi da shi tare da kai mishi wani irin wawan naushi. Rigima ta raku6e tsakaninsu Shuhuda kuwa tana kwance. Karima ta yi saurin shiga tsakanin su ta raba su amma Mas'ud ya tattakura ya kaima ta naushi a gefen cikinta ba arziki kuwa ta ja baya. Inna yaduwa ita ta raba fadan yayin da Binta ta fito daga dakinta dama duk abinda yake faruwa akan idonta ne abinda yasa tun dazun ba ta fito ba tasan Mas'ud yana da taurin rai mawuyaci ne ayi fada da shi bai samu galaba ba amma yau sai ga shi zance ya sha bam-bam. Duk girman jiki irin na Mas'ud amma Isah ya fi shi zafin nama da karfi domoin ba don Inna yaduwa ta raba fadan ba wata kila sai dai a dauki Mas'udin ranga-ranga. Binta na fitowa daga dakinta ta balbale Inna yaduwa da masifa har tana kiranta tsohuwar akwala wai tana shiga fadan yara. Inna yaduwa ta rike ha6a kawai tana karewa Binta kallo mamaki take yi 'yar da ta haife ta a cikinta amma ita ce take yi mata wadannan munanan furucin. Binta jin ba wanda ya tanka mata sai ta kama hannun Mas'ud tace: Mu je ciki Alhajin ya dawo Ni na gaji da wannan masifa mata kin zame min ciwon ido mai wuyar magani a gida? To wallahi ba zata sa6u ba bindiga a ruwa yau alo tsiya alo danja sai an san mai yiwyuwa. Inna yaduwa suka karasa inda Shuhuda take kwance duk ya farfasa mata jiki, amma a madadin a ga JINI a gurin da ya farfasa mata sai suka ga RUWAN NONO fari kal yana zuba. Wannan lamari ya hargitsa tunanin karima don bata da masaniyar wancan al'amari da ya ta6a faruwa. To ita kanta Inna Yaduwan da Isah abin ya kara hautsina masu kwanya shin ita Shuhuda wacce irin halitta ce da gaba daya jikinta babu jini sai Ruwan nono? Dama akwai mutumin da jikinsa yake dauke da ruwan nono sa6anin jini kuma yana rayuwa? Amsar data yi musu wuya kenan suka taitaye ta zuwa daki. Kwallah ne kawai ke zuba a idon karima yayin da Inna yaduwa tace. Karima shin dama baki zaman lafiya da matan gidan nan ne? Sam ta kasa magana zubar hawaye kawai take. Inna yaduwa ta jinjina kai tace; To Allah ya sauwake tunda abin haka ne bazamu bar shuhuda a gidan nan ba. ada Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA) ¤¤07¤¤ Karima ta girgiza kai da sauri amma ba ta iya cewa komai ba Inna yaduwa tace; A'a ba za mu barta ba ba zan so sanadinta ki sake samun rashin jituwa tsakiniki da abokan zamanki ba har yayi sanadin mutuwar aurenki. Idan dai an kwana biyu za a dinga kawota ta yinar miki a koma da ita amma don Allah kici gaba da halinki na hakuri, shi dama zaman aure gaba dayansa hakuri ne jigonsa, da zarar aka ce babu hakuri to babu zaman aure. Ba yadda yi haka ta hakura sai dai abin na damunta a rai ganin ruwan nonon da ya zuba a raunikan Shuhuda amma ta yi alkunya ba ta tanka ba saboda kasancewa Shuhuda 'yar fari ce. Ita din ma Inna yaduwa ba ta maida kai kan al'amarin ba ta sa ruwa ta wanke wa Shuhuda raunukan. Da yammaci su kayi bankwana suka ta fi cike da alhinin abinda ya faru. Bayan sallar magruba Alh Jamilu ya dawo gida a gajiye saboda aiki da yayi masa yawa. Kai tsaye bandaki ya shiga yayi wanka. Yana fitowa ya tarar da Binta zaune akan kujera sai huci take tamkar kububuwa. Yana ganin yanayin ta ya san korafi ne ya kawota dakin don haka ya gumtse fuskarsa ya zauna gefen gado yana murza mai a jikinsa. Binta ta kara kulewa ganin yadda ya banzantar da ita cikin 6acin rai tace: Gaskiya Alhaji na gaji wannan matar ko 'yar gwal ce sai haka bare kuma ba abinda ta fi wani cikin gidan nan. Ya dago kai ya dube ta. Mai kuma ya faru? Cikin isa-isa tace; Kawai ta gayyato gayyar danginta sunzo sun kama Mas'ud da duka ba don na fito ba kila da kashe shi za su yi. Domin na lura wannan tsohuwar kwararon so tayi ta shake masa wuya ya mutu? Yace Shikenan a saurare ni zan bincika lamarin. Tace Ni fa gaskiya duk laifinka ne domin kai ka nuna iyalanka ba su da gata a gurinka.... Ya daga mata hannu ransa a dan 6ace yace: Kinga ya isa haka, kin fada min nace zan bincika ba shikenan ba? Ta mike tsaye. Ai don ka sani ne bazan lamunta da dik wani iya shege ba. Duk wanda ya ta6a min 'yaya sai na ji dalili. Ta karashe maganar tana kokarin fita. Ya bita da kallo kawai batare da ya tanka ba su dai korafi shine abin yin su inda yake jin dadin karima kenan. Sam bata kawo mishi korafin wani, duk abin da zata yi wanda zai sanya shi farin ciki shi take yi. Yana kokarin saka jallabiya ne karima ta shigo hannunta dauke da kofin ruwa a hannunta. Fuskarta dauke da fara'a amma idonta kadai zaka kalla kasan ta sha kuka. Tayi sallama ya dago kai ya dube ta shima fuskar tashi dauke da fara'a ya amsa mata. Don Allah ka yi hakuri na tsaya yin sallah ne. Yace Kada ki damu nima sallar zan yi. Ya gama zura rigar ya hau sallaya ya gabatar da sallah. Sai da ya gama tsaf ya zauna yana murmushi. Me aka tanadar min ne? Ta tsiyaya mishi ruwa a kofi tace: Ga ruwa dai ka fara jika makoshi, ai sai kayi Isha'i zaka ci abinci ko? Ya daga mata gira yayin da ya kai kofin ruwa a bakinsa. Ya sauke kofin yace; Yauwa yau su waye suka zo gidan? Sai taji gabanta fadi ya fadi tana da tabbacin an sanar dashi abinda ya faru. Tace: Su Inna ne suka zo kawo wagga mu gaisa. Ya gane wadda take nufi saboda ba zaka ta6a jin bakinta ya ambaci sunan Shuhuda ba. Yace Okay har sun koma ne? Tace Eh. Yace Mai yasa ba a bar mana Shuhudan ta yi mana ko dan kwana biyu ba? Sai tayi shiru, a ganinta idan ta fada masa kamar ta rura wuta ne do haka ta za6i yin shirun. Yace; Binta ta ce min an dan samu rashin fahimta don Allah karima ku zauna lafiya da junanku ku daina daga min habkali. Rashin zaman lafiyarku yana dagula min lissafi da hana min sukuni, ko fita na yi kullum da fargaba nake dawo wa. Cikin kwantacciyar murya tace; Inshaa Allahu komai ya wuce. Yace: Na gode na sanki mace ce mai biyayya idan don take za a yi tashin hankali to an dade ba a yi ba. To amma halin su Binta yana iya sauya miki hali don haka don Allah kada ki yi koyi da halayensu, ki dinga kawar da kanki garesu. Tace: To amma ni ma ina rokon alfarma. Don Allah kada ka kara yiwa wani iyalinka wani abu daga gare ni. Idan sun gaishe ni kan su ba kara min lafiya gaisuwar tasu zata yi ba haka rashinta ma ba zai rage ni da komai ba. Yace; Shikenan Allah yayi miki albarka. Tace Ameeen. Karfe Uku na dare wani irin mummunan ciwon ciki ya murde MAS'UD ihu kawai ya ke zabgawa. Sunusi kaninsa da yake kwance yana bacci shine mutumin da ya fara jin ihun yayansa. Cikin tashin hankali ya tashi ganin halin da dan'uwansa yake ciki ya daga masa hankali. Da sauri ya nufi cikin gida yana kwankwasa kofar mahaifinsu. Alh jamilu da yake bacci ya tashi a firgice yazo bakin kofa yana tambayar; Waye ne? Sunusi yace; Abba ni ne. Yace; Sunusi lafiya? Kafin ya bude kofar Sunusi yace;; Abba ya Mas'ud ne bashi da lafiya. Da sauri Alh Jamilu ya bude kofar suka nufi dakin. Kwance shame-shame suka tarar da sunusi jini yana madodawa. Iya tashin hankali Alh Jamilu ya shige shi ya rasa abinda zai yi. Yanzu wane asibiti za su nufa? Dare ne karfe uku na dare da wuya a samu asibitinb da za a tarar da likita. Ya tuna yana da wani aboki likita don haka da sauri ya dubi sunusi yace; Maza je ka dakina ka dauko min wayata. Sanusi ya nufi dakin, tare suka dawo da karima wadda a lokacin ta farka saboda girkinta ne tana dakin Alh jamilun. Sunusi ya mikawa mahaifinsa wayar ya kar6a ya soma lalubar lambar yayin da karima take sallallami ganin halin da mas'ud yake ciki. Bugun farko dr Musbahu ya dauja saboda a lokacin yana kan na'ura mai kwalwa(computer) yana binciken wasu cututtuka. Suka gaisa Alh jamlu ya sanar da shi halin da ake ciki. Dr musbahu yace; ga shi nan zuwa. Amma kafin dr. Musbahu ya karaso gidan tuni Mas'ud yace Ga garinku nan. Anin da ya daga hankalin Binta ke nan ta dinga kwarara ihu cikin daren shi kam Alh jamilu daukar gawar Mas'ud yayu ya kai dakinsa zuwa safiya a suturce shi don sadar da shi makwancinsa. ****** ***** ******** BABI NA UKU ------------- ------------ ------------- AL'AJAB --------------- -------------------------- Shuda ta soma zuwa makaranta inda ta ke a firamare(primary) Yarinyar Allah ya zuba mata kwalwa da fahimtar gane abu zai yi wuya a fada mata abu ba ta hardace shi ba. Matsalarta daya wani lokaci kamar gidi-gidi(marar hankali) take. Tana samun kulawa ga dan'uwanta Isah wata irin shakuwa ce a tsakaninsu ta yadda idan daya ya yini ba tare da daya ba to lallai zaka samu dayan cikin rashin sukuni. Tun lokacin da abin nan ya faru wato dukan da mas'ud ya yi mata ba a sake kaita gidan mahaifiyarta karima ba, to ita ma yarinyar sai Allah ya sa ba wani damuwa ta yi da akai ta gidan ba. Sai dai ita kariman ta kan zo duba ta shima ba sosai ba, don ma dai hakkin uwa. A haka ta shiga aji shidda na firamare a lokacin ne kuma Isah ya kammala karatun sakandire(secondry) dinsa don ma ya samu matsala ne a sanadiyyar wata rshin lafiya da yayi kamar ba zai rai ba. Sai da ya share wata daya a kwance sannan ya warke don haka aka maido shi baya tinda bai zana J.S.C.E ba. Mahaifinsa Alh sada ya sama masa gurbin karatu a kasar senegal san Isah bai si hakan ba domin yaso ace a nan gida Nigeria ya yi karatu saboda ya dinga ganin gudan jininsa Shuhuda, amma ina! Hakabsa ba zata cimma ruwa ba lokacin da ake shurye-shiryen tafiyarsa, ba shi kadai ba ita kanta Shuhudan hankalinta a tashe yake duk ta zabge ta ramr sau an yi da gaske take iya cin abinci. Suna zaune su uku a falo Inna yaduwa ta dubi Isah tace: Ni fa wannan rama da kuke tana ba ni tsoro daga zuwa karatu duk zaju bu ku tayar da hankalinku haka. Isah yae Wallahi Innada za a bi tawa ni dai a fasa tafiyar ma sam bana sonra. Ta dube shi cike da mamaki tace; Ko akwai dalili? Yace Eh Inna kinga na farko a ra'ayina na fi son ba yi karatu a kasarmu Nigeria, sannan abu na biyu...... Ya dubi Shuhuda tare da nunata da dan yatsansa. Ina so na zauna jusa da 'yar uwata. Inna yaduwa tayi dariya tace; Ka kai su dai in kaya ne. Idan ma don wannan kwailar yarinyar ne zaka damu kanka ka bari domin ko kana nan ba zan bari ka aure ta ba, gwara ma ka tafi kayi karatunka. Shima ya dan yi takaitacciyar dariya yace. Haba dai aike ma ba kya fara ba. Kuma bari ganin zan bar kasar nan ni na tabbatar har naje na dawo ina nan cikin zuciyar Shuhuda ko ya kika ce tawan? Shuhuda da ba tasan inda maganarsu ta dosa ba ta gyada kai. Isah yayi dariya yace: Aha ni dama nasan ba mai shiga tsakanina da tawan. Inna yaduwa tace To na ji amma don Allah ku sabya hakuri da nutsuwa a zukatanku ka dai ga inda zaka je kuma ba don komai zaka je ba sai don karatun nab don haka ka mayar da hankali ga abin da ya kai ka. Isah yace: Inshaa Allahu Inna zan yi karatu har sai na ga karshen biro da mai jan kunne. Ya karashe maganar yana dariya ita ma dariyar ta yi tukunna tace: Sannan kuma don Allah ban da kula masu jajayen kunne don ba ma zamu bari ka dauko mana jikanyar paparoma ba. Dariya ya sake yi ya mike tsaye: Mhm kaji Inna tana tsoron mai jan kunne ta kwace mata miji, ke shuhuda tashi muje gida Baba na kirana. Suka fice suka bar Inna Yaduwa tana tunanin yaran sun hada kansu Allah yasa su dore a haka har zuwa girmansu. Tayi musu kwadayin zama ma'aurata. A ranar da Isah zai tafi Senegak da kyar aka 6am6ari Shuhuda daga jikinsa yana kuka ya hau jirgu dole aka sakata a mota aka juya zuwa gida ba tare da sun ga dai-daituwar jirgin a sararin samaniya kamar yadda suka sa tsara ba, Tun bayan tafiyar Isah kasar Senegal Shuhuda ba ta da sukun sai anyi da gaske ta ke cin abinci. Sai da aka samu ta saka dangana a ranta, ta dinga cin abinci da walwalarta, sai dai wannan matsalar ta rashin wadatuwar hankali na nan har yanzu a tare da ita. Yadda abin nata yake idan ka dube ta ba zaka ce tana da wata matsala ba saboda a hutse ta ke, amma wani lokaci da ta yi magana zaka fahimci akwai shirmr a cikinta. Jarrabawarsu ta fito ta ci makarantar kwana ta shekara. Amma sam Alh Sada yaki don haka ya samo mata gurbin karatu a makarantar kudi mai suna AJURI MEMORIAL SCHOOL. Ta fara karatun ka'in da na'in dama can dai Shuhuda yarinya ce mai kwanya, to har yanzu din ma dai tana ta6ukawa. Mace ce mai nacin tambaya shi yasa malamai suke sonta saboda nagartar yaro makaranta ya kasance mai yawan tambaya da naci akan komai. Hutunsu na farko Shuhuda ita ta yi na goma cikin su talatin da biyar dake ajin. Kasancewarta bahaushiya kuma wadda bata da cikakken hankali kamar yadda 'yan ajin nasu suke gani, sun sha mamaki matuka ganin cewa wannan karamar yarinyar ce tayi na goma. Ba su sake samun wani mamakin ba, sai da aka sake yin jarabawa, a wannan karon na uku Shuhuda ta dauka. Kwalwar Shuhuda tana da ban mamaki joda yake babu mamaki ga lamarin Allah. ********** ******** ********** Haj. Karima tana ci gaba da zaman hakuri a gidan mijinta amma dai abinn da sauki don ma sai da Alh Jamilu ya tsawatar sosai. Binta cewa tayi Karima mayya ce ita da 'yarta sun lashe mata kurwar da. Da farko habaice-habaice ne take yi har dai daga baya ta fito fili ta bayyana manufarta. Ai kuwa duk yadda Karima ta ke da hakuri sai da maganar ta kai ta bango ta shiga daki ta soma hada kayanta, a dai-dai lokacin ne Alh Jamilu ya dawo gidan. Tambayarta yake abinda ya faru ya ga tana kuka ga kaya kuma tana hadawa amma ta kasa magana kukan kuma ya ki tsayuwa yi kawai take zuciyarta na kuna. Da yaga bata da niyyar tanka masa sai ya samu gefen gadonta ya zauna ya zuba mata ido har ta kammala shirya kayan ta saka hijabinta ta janyo jakar zata fice daga dakin. To a lokacin ne ya yi zumbur ya mike ya sha gabanta yana kallonta ido cikin ido yayi karfin hali yace: karimatu tun da na aure ki ban ta6a samun ki mai yin wani abu ba tare da izinina ba. Shin ina zaki da kika hada kaya wani ne ya rasu? Ta girgiza masa kai Yace; To mai yasa kika za6i datse zamanki a gidana? Wani laifi na yi miki? Ta sake girgiza kai yace: Ki fada min damuwar ki ta dai yi shiru ta kasa cewa komai ya ja hannunta ya zaunar da ita akan gado yace; Jirani ina zuwa. Ya fice zuwa dakin Hassu matarsa ta biyu. Tana zaune a dakinta tana zaune a dakinta tana karatun wani littafin Hausa yayi sallama ya shigo yace: Hassu me ya faru a cikin gidan nan bayan ba ni nan? Ta tashi zaune daga kwancen da take akan doguwar kujera ta yatsina duska tace: Eh rigima ce ake yi wai Binta ce tace: Karima mayya ce, su suka lashe mata kurwar Mas'ud. Yace Subhanallahi. Sai ya mike tsaye ya nufi dakin Binta. Kwance take akan gado yace. Binta kin kyauta shi dai jaki duk yadda aka yi da shi sai yaci kara. Ta yunkura ta tashi zaune fuskarta a daure tace: Kana nufin ni ce jaka? Yace Eh ai abin da kika yi ko jakar ma ba zata yi ba. Banda jahilci da duhun kai ta ya Allah ya amshi ran Mas'ud zaki ce Karima mayya ce sun lashe miki da? To bari ki ji wallahi na gaji da munanan halayenki baki isa ki ja min surutu da bakin jini ga al'ummar gari ba. Ta watsa mishi wani mugun kallo tace: Dole ka zoi ka yi ta yi min hargowa tunda an ta6a 'yar gwal mowar mata. Karya ake mata ba mayyar ba ce? Idan kai ba ka sani ba ni na samo cikakken tarihinta karima mayya ce ita ta lashe mijinta haka wata mata daga ta tsarga hannun 'yarta ta lashe ta saboda muguwar maita, don bakin cikin zata yi mata lahani a jininta, sannan ta lashe Mas'ud. Sai a hana ni fada? To na fada karima mayya ce a yi yadda za ayi da ni....' Ba tasan ya aka yi ba sai dai ganin wasu taurari ta yi suna walainiya a cikin idanunta sakamakon kyakkyawan marin da Alh jamilu ya dauke ta da shi. Yana huci ya cigaa da cewa; Maza ki fice min daga gida, zama da ke annoba ne har kullum ba za a ta6a jin alkhairi a bakin ki ba dai sharri. Ba tayi mamaki ba domin ta lura mijin nata ya zauce akan wannan afiruwar matar tasa. Ita kam ba inda zata kuma ba zata ta6a barin jinin danta ya tafi a banza ba. Alh jamilu ya cigaba da cewa; Kuma wallahi kika sake furta maganar nan ga wani sai na sa an kulle ki, mutumiyar banza marar hankali. Cikin dakewa tace da shi: Idan kasa an daure ni ka jefa mukullin cikin kogin maliya zama daram kuma a cikin gidan nan ban ga 'yar isakar macen da ta isa ta fitar dani ba. Yaja wani dogon tsaki ya fice daga dakin ya barta tana kananan maganganu. Ya tarar da Haj karima har lokacim kuka ta ke. Ya zauna kusa da ita ya soma share mata hawayenta yace: Don Allah ki yi hakuri karima an fada mim duk abin da ya faru. Ta yi shiru bata tanka ba. Zaman gidansa ya fice mata a rai saboda tunda ta shigo gidan ba ta da kwanciyar hankali. Yau dai hakurinta ya kai gaci a ganinta gwara ta kauce masa ko matansa sa samu sarar tunda dama tunda ta zo gidan ba ta nasa ko kwai ba bare dan adam. MAITA? Ai kalmar ta yi mata nauyi ba ko a kai ba. A'a a dukkan sassan jiki da ma rayuwarta gaba daya. Ta matse hawaye tace dashi; Alhaji ka yi hakuri amma na hakura da zama gidanka ka yi hakuri. Ya tsura mata ido cikin tsananin tausayi yace: A'a karima kar mu yi haka dake. Ki fahimce ni, ni nake aurenki , zamana kike..... Karo na farko yana magana ta katse masa hanzari tunda take da shi. Zamanka nake amma kuma zaman matanka tunda suna juya ni kamar waina a tanda. Yace: Hakane ban ce kin yi karya ba amma ki yi hakuri komai yazo karshe tunda na sauwakewa Binta. Dama ita ce matsalar gidana don ta Hassu za a iya zama da ita. Da sauri karima ta mike tsaye maganarshi ta dakar mata zuciya sosai ta soma girgiza kai. A'a Alhaji ka maido Binta, tare na tarar da ku ni na fi dacewa da wannan hukuncin domin zuwana ne ke neman hargitsa zamanku. Yace Ba zuwanki bane karima dama can Binta 'yar butsu ce hakuri kawai nake da ita. Karima tace Yanzu din ma hakurin zaka ci gaba da ita. Yace Hakurina ya kare. Tace Ni ma nawa ya kare don haka ina so ka maido matarka. Ya cika da mamakin yadda yau karima ta ke sa'insa da shi. Matar da ta kasance magana daya zai yi ta zauna, babu jayayya ko rashin amincewa amma yau sai ga akasin haka a tsakaninsu? Yace Wallahi kinji na rantse Binta ba zata zauna min a gida ba ke kuma dole ki zauna. Ya karashe maganar cijin bayar da umarni. Sai ta duke ta sunne kai a kasa tana rusar kuka shi kuma yayi am fani da kaifin basisararsa a matsayinsa na jangwarzo ya rarrashe ta da tausar zuciyata. Mata har kullum rauni garemu don haka zuciyarta ta yi rauni ta aminta da ci gaba da zaman gidan mijinta. Wannan ke nan!!!! *************** ************** A kwana a tashi Shuhuda ta shiga aji hudu na sakandire karatu ba kama hannun yaro kowanne malami yana alfahari da ita saboda kwazonta da mayar da hankali akan karatu. Ranar litinin bayan an gama assembly kowanne dalibi ya shiga aji don daukar darasi. Shuhuda na zaune a mazauninta a kujerar karshe ita da abokiyar zamanta mai suna Sa'adatu. Kowanne dalibi ka duba karatu yake kafin malami ya shigo dama haka al'adarsu ta ke ba ka ta6a ji dalibai suna hayaniya irin na sauran makarantu. Amma banda Shuhuda da ta yi tagumi ga dukkan alamu tana cikin yanayin nata. Wani malami ya shigo gaba daya daliban suka mike tsaye don girmamawa a gare shi banda Shuhuda wadda ba tasan da shigowarsa ba. Ya amsa gaisuwarsu ba tare da ya lura da rashin mikewar Shuhuda ba Ya ba su umarni da su zauna. Bayan kowa ya zauna ya gabatar da kanshi a gare su a matsayinsa na sabon malamin da zai dinga daukarsu darasin chemistry. Ya duba littafan wata daliba da ke kujerar gaba ya ga inda suka tsaya a karatunsu sai ya dora da yi musu karin bayani. Ya ji dadin yadda ya same su dalibai masu fahimta suna da rike abu a kansu. Yana cikin bayanin nasa ne ya jefo musu tambaya mai stauri yace; Cikinku wa zai min bayani akan Radioactivity? A cikin harshen Turanci ne ya yi musu tambayar don ka'idar makarantar ne haka ba a baiwa malami damar yiwa dalibai tambaya da wani harshe ba idan ba Turanci ba, sai dai idan Islamic studie ne wanda shi harshen larabci tsagwaronsa ake gabatar da shi ga musulman dalibai kenan. Gaba daya ajin aka yi tsit, wuta ta dauke musu saboda ba a ba su darasin a cikin ayyukan da zasu yi a aji hudu ba su kuma hankalinsu bai kai ga bincikar 6angaren ayyukan da ke gaba ba. ( Dalibai anan tsanyi tsokaci idan kuka shiga makaranta ba dole sai syllabos din da aka ba ku zaku duba ba a'a ana son dalibi ya kasance mai kutse-kutse yana binciko abubuwa da dama a harkar karatunsa yadda idan kun zo gurin komai zaizo da saukiza kuga kamar maimaici ne ma kuke yi). Uncle Hamza ya yi murmushi ganin cewa an rasa wandazai iya yi a gare su bai ce komai ba sai ya koma kan kujera ya zauna yana baza idanu ya ga ta inda zai samu amsarsa. Aka dauki tsayin mintina huudu a haka babu wanda ya ko motsa sai ya girgiza kai yace: Yanzu duk taron yawanku babu wanda zai iya ba ni amsar Radioactivity? Karaf sai ji aka yi daga kujerar baya an soma bayanin cikin zazzakar murya mai natsuwa. Kyam! Ya tsaya tare da tsura mata idanu yarinya karama 'yar fara mai kyawun sura tana ta bayani cikin hadadden turancin ta(Latent English) na kasar Amurka babu tuntu6en harshe ko gwamutsawa da gur6ataccen turanci(Broken English) kuma bayani take akan Radioactivity da tsurar saninta wanda kowanne malami zai saurara sai ya jinjina mata. Haka ma idan a jarrabawa ne babu tantama zata sami maki(scores)mai yawa. Su kuwa dalibai 'yan uwanta ba su yi mamaki ba domin duk wanda ya kwana ya hantse a makarantar nan yasan shuhuda da kaifin kwalwa zai yi wuya a tuntu6eta sanin wani abu a rasa amsa daga gare ta. Shuhuda ke nan mai abin AL'AJAB! Haka dalibai suke mata lakabi. Tana kammala jawabinta ta koma mazauninta ta zauna ta mayar da tagumin alamar ta nutsa tunani. Uncle Hamza ya rasa abin da zai ce wace jinjina zai yiwa yarinyar nan. Wace irin kyauta zai bata wadda zata nuna jin dadin da ya samu kansa a ciki. Lallai ya yarda ya kuma aminta wannan yarinyar 'yar baiwa ce kuma ga dukkan alamu gidansu ana dagewa akan karatun yaro. ada Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)¤¤08¤¤ Kai ko da ma dagewar to akwai BAIWA ta musamman dake tare da ita, aiki ne wanda ake yi a aji biyar ya tambaye su akai don kawai ya kafa harsashinsa ga dalibai su san cewa zai iya daukarsu darasin da aka damka masa ba kamar yadda suka yi kuka da wancan malamin ba wai ba su gane darasinsa sosai saboda sauri da yake a dukkan abin da zai koyar da su a takaice yake yi musu. Don haka shugabar ajin ta kai korafi gurin shugabar makaranta aka yi katari da sababbin malamai da suka samu sauyawa(transfer) daga wasu rassan makarantar. To shi ne aka turo shi ajin ya taho da azamar ba su mamaki sa6anin haka sau ga shi daya daga cikin mafi karantar daliban ta ba shi mamaki ba kuwa karami ba mamaki ne cike da AL'JAB da ace dukkan daliban da ke ajin haka suke da budaddiyar kwalwa to tabbas da zai ji dadin kasancewarsa malami a ajin. Uncle Hamza ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye daga inda yake zaune ya fito tsakiyar ajin yana duban inda Shuhuda take yace: Ke! Mike tsaye? Shuhuda ta dago da kai ta dube shi duba na rashin fahimta wanda ke nuni tamkar ba ta ji abin da ya fada ba. Ya sake maimata maganarsa, sai ta mike tsaye ta rusunar da idanunta kasa. Yace ya sunanki? Ta maimaita maganarsa kamar wadda ke koyon magana amma ita cikin yanayin tambaya da kuma jinjinawa ta yi maganar. Sai ya samu kansa cikin 6acin rai wannan wane irin rainin hankali ne zai tambaye ta sunanta ta maimaita tambayar da ya yi mata, sai kace tana magana da sa'anta? Duk fara'ar da ke fuskarsa ta kau a lokaci daya, yace; Tambayarki nake ya sunanki? Kanta na duke a kas ta ce: Sunana IZRA'EL!!!!! Ya cika da al'ajabin jin amsar da ta ba shi Izra'el? A yanayinta bai yi tsammanin zai ji sunan da ya dangantata da wata kabila wanda ba bahaushe ba. Saboda akwai hijabi karami a jikinta kamar yadda yake duk musulmin da ke ajin zaka samu bambancin kayansa da na sauran kabilu. To ba ma wannan ne al'ajabin ba shi ai sunanta ya tambaye ta mai yasa zata fada masa sunan mahaifinta? Lallai wannan yarinya ta raina shi, in baya da raini ta ya zata ba shi akasin tambayar da ya yi mata? Ya fito da ido waje sosai cikin barazanarwa yace: Sunanki na tambaya ba na mahaifinki ba. Na ce ya sunanki? Ta yi shiru bata ko motsa ba bare ta ba shi amsa. Abokiyar zamanta Sa'adatu ta mike tace: Uncle ka yu hakuri haka take tana da matsala a kanta. Matsala? Ya maiaita kalmar ta ya za a ce wannan yarinyar tana da matsala a kanta? Matsala ko rainin arziki? Idan ba haka ba ta ya yarinyar da ta ba shi amsar da bai ta6a tsammanin samu a ajin ba za a ce tana da matsala? Wato maganar da aka fada masa cewa 'yan ajin suna da rainin arziki abin ya zo kansa? Idan kuwa haka ne shi zai yi maganin abun domin shi ba ya daukar raini ga kowane dalbi. Ya dubi Shuhuda cike da 6acin ran rainin hankalin da ta zo masa da shi yace: Fita waje kika ma kunnan ki. Tayi tsaye tamkar ba da ita yake magana ba. Suka ce; Uncle ka yi mata hakuri haka ta ke tana da ta6in hankali. Ransa ya kuma 6aci ko kadan ba ya son wannan kalmar rainin hankalin wai tana da ta6in hankali Sai kawai ya ja dogon tsaki ya dauki dan littafinsa ya ficce daga ajin ba tare da lokacinsa ya karasa cika ba. Kowa yayi tsit cike da al'jabi shi ke nan akan mace daya sun yu asarar ragowar lokacin da ya ragewa Uncle Hamza? A take wadanda ke jin haushin Shuhuda a ajin suka kara jin tsanarta a ransu ta zame musu GOBARAR TEKU. Washegari bayan an koma tara(break fast) Uncle Hamza yake da period a ajin su Shuhuda don haka lokacin na cika ya nufo ajin, sai dai yau sam bai shigo da fara'a ba wannan yana daga cikin matakan da ya tsara game da 'yan ajin saboda ya lura wani lokaci sakarwa dalibin fuska yana kawo raini matuka. Abin da Shuhuda ta yi masa a jiya ya zauna masa a rai koda ya koma gida kasa sukuni ya yi yana ta tunanin yadda lamarin yake yarinyar mai kwalwa da hazaka wadda ta bayar da amsar da matsala a kwalwa? Dama ana saun irin wadannan mutanen? Da tunanin ya yi masa yawa akwai wani abokinsa Dr Ishak da ke Ibadan sai ya kira shi a waya ya yi masa tambaya akan kwalwa shin dama a cikin kashe-kashen kwalwa akwai wadda mutu yake kasancewa haziki duk abin da aka tambaye shi ya bayar da amsa sai kuma daga baya a same shi kamar wanda ba shi da hankali? Dr Ishak ya yi kwan-kwance yana yi masa bayani cewa ' ana iya samun mutanen da idan suna da fasaha da hikima wani lokaci ka gansu a hargitse. Uncle Hamza bai gamsu da bayanin Dr Ishak ba sai yake ganin kamar bai gane tambayar bane saboda haka sai ya share ya yi kwance tare da nutsawa tunanin don samun mafita shi dai kam yarinyar ta kwanta masa a rai, rayuwarsa yana son mace 'yar fara mai matsakaicin jiki kamar dai yadda ya ga Shuhuda matsalar dai ita ce fuskanta da ya yi 'yar rainin hankali ce. Wai tun tana karamarta ke nan ina kuma ga ta girma ta zama babbar mace? Da wannan takaicin ya kwana. Washegarin ne ya yanke hukuncin 6illo da sabbin matakai don tsirar da kansa daga rainin dalibai. Daga cikin matakan da ya tsara har da daure fuska da kuma hukunta duk wanda ya kawo masa raini komai girman dalibi ko daliba. Kamar jiya yau ma yana shigowa ajin dukkansu suka mike don girmamawa a gare shi. Yau har da Shuhuda cikin masu isar da gaisuwarsu. Hannu kawai ya daga musu alamar su zauna ba tare da yayi magana ba. Dukkansu suka zauna ya soma yi musu darasi akan Nitrogen it's compound ba laifi suna fahimta domin Turancinsa mai kyau ne kuma a nutse yake musu bayanin yana yi yana nuna musu a aikace. Inda Shuhuda take ma sam bai duba ba bayaninsa kawai yake . Ita din ma ba ta damu da kulata ba ko akasin hakan tana dai saurare da duban bakinsa. Yana kare yi musu bayanin yasa kai ya ficce daga ajin. Haka suka wanzu idan ya shiga ajin ba ya duban inda Shuhuda take har zuwa ranar juma'a wato karshen mako(weekend). Ranar second period yake da ita kuma double period ne don haka ya yi musu bayani sosai game da aiki da ya yi musu bayani sosai game da aikin da ya yi musu. Daga karshe ya ba su aikin aji(class work) ya umarce su yi maza su gama ya tafi da littafansu. Ba musu duk da tambayoyin masu tsauri ne haka suka kukata suka gama. Shugabar daliban ajin (monitor) ta daukar masa zuwa dakin malamai (staffroom). Uncle Hamza ya zauna akan teburinsa ya dauko littafan daliban yana gyarawa yawancinsu duk gajerun bayanai ne(short note) suke yi game da tambayoyin da ya yi musu sai dai ya yaba musu hakan na nuna suna fahimtar abin da yake koyar dasu. Dama haka ne burinsa domin aikin(subject) dinsa babban aiki ne da ake son dalibai da ke fannin ilimin kimiyya(science department) su sanshi sosai saboda Chemistry yana da muhimmanci sosai gare su. Yana gyaran cikin nishadi, wani malami mai suna Uncle Joseph shi ma yana zaune a teburinsa yana gyara takardun gwaji(test) da ya yi a ajin su Shuhuda a jiya, Shine yake daukansu darasin lissafi(maths) kowannensu gyaran yake yana murmushi saboda irin hazakar daliban. Uncle Hamza yana cikin gyaran ya zo kan wani littafin tun daga tsarin rubutun ya isa mai littafin ya samu maki to bare kuma dogon sharhi(long note) da aka yi. Da sauri ya juya bangon littafin ya tsurawa sunan da ya gani akai ido. SHUHUDA SAGIR RABI'U ya gani an rubuta. Ya sanya kan biro a bakinsa yana jinjina kai wace yarinya ce wannan mai kwalwa da hazaka irin haka? Bayananta sun fi na kowane dalibi tsaruwa ina ta samu wannan BAIWA? Daga Allah! Abin da wani 6angare na zuciyarsa ya fada masa ke nan. Lallai kam Allah mai baiwa ne ga wanda yaso lamarinsa ya wuce gaban mamaki domin idan bawa zai tsaya yana mamaki ga lamarin Allah to ba shakka yana iya fita daga musulunci tauhidinsa ya yi rauni. Shi kuwa tauhidi shine babban jigon musulunci. Mikewa tsaye ya yi hannunsa dauke da littafan ya nufi inda Uncle Joseph yale ya dube shi cikin harshen turanci ya yi masa magana. Joseph ko kasan wannan sunan a cikin daliban aji hudu 'yan ilimin kimiyya? Uncle Joseph ya kar6i littafin ya duba sunan sai ya yi murmushi ya zaro wata takarda daga cikin takardun da ya gyara ya mikawa Uncle Hamza. Eh ina jin wannan ma takardarta ce na gama gyarawa ko? Uncle Hamza ya kar6i takardar ya duba da kyau tabbas ita ce tun daga tsarin rubutun zuwa sunannata duk babu tababa a ciki. Kuma a nan din ma babu inda ta fadi har kyautar maki daya da rabi Uncle joseph ya yi mata. Wannan na nuni ke nan shi ma Uncle joseph ya yaba da kwalwar yarinyar? Ya jinjina kansa cikin gamsuwa yace: Lallai yarinyar nan tana da kokari? Uncle joseph ya fadada murmushinsa. Shuhuda? Ai a tarihin makarantar nan ba a ta6a samun mai kwalwa irin ta ba zai fi kyau ace wannan yarinyar jami'a ta ke ba wai sakandire aji hudu. Uncle Hamza yace; Ni ma abinda nake gani ke nan saboda banyi tsammanin samun bayanan da na gani a cikin littafinta da takardar dake hannuka ba. Ya juya ya koma akan teburinsa cike da AL'AJAB ya kasa ci gaba da yin gyaran ya fada duniyar tunani. Tabbas duk yadda aka juya wannan 'yar rainin hankalin yarinyar ce mai wannan littafin saboda babbar hujjar da yake da ita a ajin ya yi musu tambaya mai tsauri aka rasa wanda zai amsa masa sai ita ta yi bayani gamasasshe. Idan kuwa haka ne zai yi wuya ya kasance yanzu ma a samu wani da zai yi bayanin gamsasshe kamar nata. Lokaci daya ya soma jin zuciyarsa na sanyi akan tsanarta da ya fara yi a kuma lokacin ne ya soma aminta da bayanin abokinsa Dr Ishak cewar akwai irin yaran da idan baiwa ta yi musu yawa sukan koma kamar marasa hankali. Wani sashi na zuciyarshi yana karyata yiyuwar hakan domin masu irin wannan yanayin akan same su cikin rashin shiga mai ta kamala kana ganinsu ba sai an fada maka ba zaka san cewa suna da karancin hankali a tare da su. Ita kuwa Shuhuda kana ganinta ka ga cikakkiyar mai hankali ta yanayin shigarta gami da nutsuwarta . Duk macen da ta samu kanta a irin yanayin da Shuhuda ta ke ciki to tabbas za a iya kiranta cikakkiyar mai hankali amma abin tambayar a nan mai yasa 'yan ajin nasu suke ikirarin tana da matsala a kanta bayan duk ta fi su kwalwa? Ko kuwa hassada ce? Ai idan hassada ce da ya samu akasin haka daga gare su to amma wannan a bayyane yake akawai SHIRME? Cikin kalamanta in banda shirme ta ya mace ke juyewa zuwa jinsin namiji? Ma'ana ta kira kanta da sunan namiji bayan ta kasance mace? Idan ita ce yarinyar da ake magana mamallakiyar littafin dake hannunsa ai ya ga cikakken sunanta Shuhuda Sagir Rabi'u. To me ye hadin sunanta da Izara'el? Waye Izra'el din? Amsar da yake bukata ke nan a yanzu amma bai san ta ya zai same ta ba. Lamarin shuhuda ya daure masa kai matuka tunda yake rayuwarsa bai ta6a samun kansa a cikin dogon tunani akan lamarin wata diya mace ba, sai akan Shuhuda. Me yasa ne ya soma a kanta? Wani 6oyayyen al'amari!! A ranar bai samu komawa ajin na su ba, saboda kwalwarsa da ta dau caji, eh mana ai ko inji ne wannan aiki ya kamata ya huta, bare kuma kwalwa da ke jikin dan Adam wadda a kowane lokaci ake so bawa ya kasance yana saukaka mata wajen yawaita sanya mata abubuwa masu nauyi.=========- =============== ===========- =======BABI NA HUDU========- --------------- --------------------------- ======MAFARKI KO GASKE======- RANAR litinin kamar yadda a tsarin shigar malamai ya ke a ajujuwa yau ma Uncle Hamza ya shiga nashi ajin a dai-dai lokacinsa(period). Sanye da kananun kaya bakake wuluk da yake fari ne sai kayan suka amshi fatarsa. Idonsa sanye da karamin bakin tabarau shi din ma ya kara masa kyau ainun saboda matashi ne mai jini a jika. Ya aje kasumba a fuskarsa wadda ta sha gyara ta yi luf ba ya da haka ma kana dubansa kasan ya fito daga tsatson RUMAWA don akwai ma tsagen biyu-biyu a gefen fuskarsa. Bayan ya gama kar6ar gaisuwa daga dalibansa sai ya nemi guri ya zauna akan mazauninsa. Can karshen bango inda kujerar su Shuhuda ta ke ya tsurawa ido yana nazarinta. Amma farat daya baza ka ce ita yake kallo ba. Kanta na sunkuye kasa ta tallabe ha6arta da hannayenta. Akwai abinda ya lura da shi sai ya ga kamar lokacin da dalibai suka mike suna gaishe da shi ita ba ta tashi ba, kuma ba ta dago kai ba har kowa ya zauna. Amma abin ya tsaya masa a rai mai yasa ita ba ta mike don gaishe shi ba? Shin ita wani ne ta fi a ajin da ba za ta iya girmama malamanta ba. Eh to zai iya cewa tafi sauran 'yan ajin kokari to amma kokari babu ladabi ai shirme ne duk nagartar kokarin mutum idan ya kasance bashi da ladabi to ya kan zama FANKO. Ya kyale ta ne bai nemi ba'asin rashin da'ar da ta nuna masa ba saboda mikin farin cikin da ya shigo da shi ajin na samun gamsassun bayanai na amsoshim da ta bayar. 'Yan ajin suka shiga damuwa ganin Uncle Hamza ya shigo ajin har tsayin mintina sun fi goma amma bai fara yi musu darasi ba sai suka dinga tunanin ko don ba su ta6uka wani abin kirki ba ne a cikin aikin da ya ba su ranar juma'a. Suka tattara komai suka tsura masa idanu don jin hukunci ko wani abu da zai iya yi. Uncle Hamza ya yi huci tare da mikewa tsaye ya isa gaban allo (Black board) hannunsa rike da alli(chalk) ya rubuta sunan darasi Chemistry sannan ya rubta kwanan wata da aikin da zasu yi yau akan MAGNETIC FIELD sai da ya rubuta sannan ya juyo zai fara bayani sai ya tuna littafansu na hannunsa. Yace Ku yi hakuri na manta littafanku na hannuna. Ya dubi shugabar ajin yace Je ki kwaso. Ta fita shi kuma ya cigaba da cewa. A yau zamu yi darasinmu ne akan maganet to amma tunda lokaci ya kure zamu tattauna game da aikin ajin(class work)da ya gabata in yaso gobe sai mu dora wannan. Yana rufe baki shugabar ajin ta dawo dauke da littafan ta dora akan teburinsa ya soma kiran sunaye yana damkawa kowacce daliba nata har sai da ya zo kan na karshe sai ya ajiye shi a gefe. Yace An bawa kowa nasa? Suka ce Eh. Saboda ba wanda ya lura Shuhuda ba ta kar6i nata ba sai Sa'adatu ita kuma tayi nauyin bakin cewa Shuhuda ba ta amshi nata ba. Yayin da Shuhudar bata ma san abinda ke faruwa ba. Uncle Hamza ya ci gaba da yi musu bayani game da amsoshin da suka bayar ya dora da basu shawarwari don ganin sun zama Zakaru a kowanne darasi ba lallai sai na sa ba. A haka ya cinye lokacinsa sai da yaga wani malami a waje yana jiransa sannan ya dauki littafin da ya a jiye a gefe yace; Wace ce Shuhuda Sagir Rabi'u a cikin ajin nan? Kowa ya mayar da dubanshi can layin karshe inda Shuhuda ta ke zaune kanta rusune a kasa Sa'adatu ce ta yi saurin cewa. Ga ta nan. Yayin da ta zunguri Shuhuda. Zumbur Shuhuda ta mike tsaye ta nufo gaban allo ta durkusa(kneel down). Uncle Hamza ya cika da mamakin wannan yarinya daga tambayar wace ce ita sai kawai ta fito gaban allo ta durkusa sai ka ce yace ta yi hakan? Ganin rashin isashen lokaci tunda ga wani malamin a waje yana jiransa sai ya mika mata littafin ya girgiza kai ya ficce ba tare da ya iya cewa wani abu ba. Uncle Hamza yana zaune akan teburinsa cikin dakin malamai ta tagar dake ku sa dashi ya hango dalibai na shawagi a farfajiyar makarantar alamar an fito tara (break fast)ke nan dama ya kosa lokacin ya cika saboda yana son ganawa da Shuhuda akwai tambayoyin da yake son ta amsa masa su. Da sauri ya mike tsaye ya nufi ajin su Shuhuda kamar yasan tana can. Ya tarar da ita tana duba littafanta sai ya ja ya yi tsaye daga bakin kofa ba tare da ya karasa ciki ba. Ya tsura mata ido wato dama shi yasa ta kasance mai hazaka tunda idan an yi break ma ba ta fita daga aji karatu ta ke yi? Kamar ance dago kanki ana kallonki sai kuwa ta yi tozali da Uncle Hamza a tsaye yana kallonta. Da yake bai sako bakin tabarau dinsa ba don haka tana kallon kwayar idanunsa. Shi kuwa ganin ta dago ta dube shi sai ya tako sannu a hankali zuwa inda take ya zauna a kujerar da ke gabanta. Yace Shuhuda Sagir Rabi'u. Kanta na sunkuye ta amsa Na'am. Ya yi gajeran murmushi yace Mai yasa baki fita break ba bayan kowa ya fita? Muryarta a nutse cikin zakin nan nata yaji tace: Bana fita break idan na ciyo abinci daga gida bana karaci cin wani sai na koma. Yace amma ko ruwa kin bukata. Sai ta janyo lokar kujerarta ta fito da robar ruwa Swan water ta nuna masa ba tare da ta yi magana ba. Ya jinjina kai yace: Ki ce tafe kike da gidanki? Ba ta ba shi amsa ba haka kuma ba ta dago ta dube shi ba. Ya ci gaba da cewa yana kallonta. Dama wasu tambayoyi nake son yi miki. A wannan karon ba ta iya jurewa ba sai ta dago kai ta dube shi tace: Tambayoyi? Ya tabbatar mata da hakan ta hanyar daga mata gira sama ya ci gaba da cewa. Ke musulmace kuma bahaushiya? Fuskarta ta nuna yanayi na mamakin jin tambayarsa. Ta ce Eh. Yace Na ji ai cewa kika yi Eh ita kuwa kalmar Eh tana nufin DUKA ban san wane matsayi zan ajiye amsar eh dinki ba. Ta yi shiru ba ta tanka ba. Yace: To misali ma ace na ajiye ki a matsayin musulma shin mai ya hada sunanki Shuhuda da Izra'el? Ta dago kai da suri tace; Izara'el? Yace Eh. Ta girgiza kai tace: Ni ban san Izra'el ba ban hada komai da shi ba. Ya cika kwarai da tsananin mamakin jin maganarta amma sai ya daure yace: Idan baki san Izra'el ba sannan ba ki da wata alaka da shi mai yasa idan an tambayi sunanki kike cewa Izra'el? Ta kara fito da ido alamun dai nuna ba tasan zancen ba idan aka dubi kwayar idonta za a tabbatar da haka. Ta ce Ni din kuwa? Ya kara cika da mamaki wai wannan wacce irin yarinya ce mai wadannan halaye? Ya aminta idan ma kwalwa ce ta yi mata yawa to har da raini tsagwaronsa. Yace to na ji bake bace amma mai yasa idan malami na cikin aji ba ki mayar da hankali gare shi? Maimakon ta amsa masa tambayarsa sai cewa tayi......... ¤ ¤ ko me ta ce, oho!!! Sai ku biyo ni dan jin saura.......... da Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤09¤¤ uncle mu dawo kan maganarmu domin gaba daya ka daure min kai ina son gamsasshen bayani daga gare ka. Ya kara cika da tsananin mamaki wannan wace irin yarinya ce da take neman juyar masa da tunani? Bai gaza amsa mata alfarmar da ta nema ba ko ba komai a cikin bayanin da za su tattauna zai iya fuskantar kowace ce ita. Don haka cikin natsuwa yace: Abu ne mai matukar mamaki ga irin yadda kike wasu abubuwa. Ta katse shi da cewa: Uncle am sorry kamar wadanne abubuwa? Kasan komai yana da dalili zai iya yiyuwa idan ka fada min misalin abubuwan da nake yi na gamsu da zargin da nakewa kaina. Ya dube ta cikin ido yace: Kinga kina kiran kanki da sunan namiji alhalin kina mace. Kuma namijin ba wanda ya haife ki ko dan'uwanki ba. Ta yi murmushi tace: Auho! Ai uncle a tunanina ko wane suna mutum zai iya amfani da shi wata kila akwai wata Hoyayyar ALAKA da ta sanya haka. Cike da rudani yace 6oyayyar alaka? Ban gane ba. Tace Ka tuhume ni akan abun da ko a mafarki ba zaka samu amsarsa ba bisa wani 6oyayyen SIRRI mai wata irin YANAH mai duhuwa wadda idan za z kunna dukkan hasken kwan lantarki dake fadin duniya ba zasu haske DUHUN da ke tattare da ni ba. Illa wani muhimmin ABU wanda ko a mafarki bana tunanin kai zaka iya canko shi. Ya rasa yadda zai yi ya fahimci wace ce wannan yarinyar da ke zaune a gabanshi. Ko a kalamanta na yanzu kamar zai iya ajiye ta a sahun marasa cikakken hankali domin da farko kamar akwai hankali a tare da ita amma koda ta kai tsakiyar maganar tata sai sokana da shirme suka ida mamaye hankalin nata. To yanzu me ma zai furta mata? Kafin ya karasa lalubo abin yi ta cike gurbin shirun da maganarta. Uncle wai waye MUTUM? Ni fa har yanzu ban san waye mutum ba ban san mai ya alakanta shi da wasu jinsina ba. Maganarta wani tsani ne har wa yau da ya kara hauhawar da rudaninsa cikin rudanin da rikitarwa ya lalubo abin cewa. Halittar MUTUM halitta ce wadda Allah(S.W.T) Ya yi ta a doron kasa mai girma da daraja domin duk halittun da ke duniya kama daga shi kansa mutum, jinnu dabbobi tsuntsaye da tsirrai to babu ya mutum . Ana kiran mutum 'Yan Adam a jam'insu ma'ana idan za a tara mutane da suka zarce mutum daya, idan mutum dayan ne ana kiranshi dan Adam saboda asalin halittar mutum daga shugaban halitta ne Annabi Adamu (A.S) don haka duk mutum ake kiransa DAN ADAM mutane kuma ake kiransu Bil'adama ko 'Yan Adam. Idan muka koma ga sauran halittun idan kika tsaya kika lura zaki ga dukkan sauran halittu samuwarsu cikar farin cikin dan Adam ne. Ina fatan wannan bayanin nawa ya gamsar dake sanin ko waye mutum? Ta jinjina kai tace: Haka ne, bana son shiga hakki idan na yi tambaya aka amsa min ko na gamsu ko ban gamsu ba to na gamsu din ne, ba kuma don na gamsu ba. Shin uncle, Ni da kai din nan mene ne a cikin halittu? Ko kuma nace ni ko ka fahimci ni eace halitta ve a cikin halittu? Wadanne dabi'o'i ne mutane suke yi???? Yace Ni mutum ne dan Adam ke ma a yanzu kallon halittar dan Adam nake yi miki saboda kina da suffa da tsari irin na halittar dan Adam. Sannan Bil'adama suna dabi'u na tafiya da kafafu biyu yin ayyuka da hannaye biyu gani da idanu biyu shakar kamshi ko wari da hancina biyu. Bil'adama suna dabi'o'i na tunani da fahimta suna da dabi'ar yin karatu ina tunanin haka ma ya gamsar dake? Tace na fada maka kona gamsu ko ban gamsu ba na gamsu din ne. Yace Ai so nake na sani. Tace Watakila na gamsu wata kila ban gamsu ba ko kuma zan gamsu.... Amma dai na gamsu din tabbas. Dole unle Hamza ya shiga rudani domin gabaki daya maganganun Shuhuda ababen rudani ne. Idan banda rudani ta ya mutum zai ce koya gamsu ko bai gamsu ba amma ya gamsu din? Me ye MANUFAR hakan? Ba a gamsu ba ko an gamsu ya zama lallai an gamsu? Wannan tatsuniya ce ko soki burutsu? Yace: Idan kin gamsu ko ba ki gamsu ba zai zama hujjar gamsuwarki. To maimata min abin da na fada domin hakan shi zai ba ni kwarin gwiwar baki amsoshinki. Tayo dariya. Uncle sai ka ce ni yarinya ce 'yar shekaru hudu a duniya? Shekaruna fa sha bakwai ajina hudu a matakin sakandire ke nan zan iya rike duk abin da aka fada min har ma na yi masa fashin baki? Shi ma dariyar ya yi amma tashi gajeruwa ce mau kunshe da takaicin maganganun yace; Na ji maimaita idan da gaske kin riken. Ta kuwa maimaita har ma da karin bayani. Da ta karashe yace; A maganarki kin ce ba kisan ke mece ce a cikin halittu ba to amma na yi mamakin karin bayanin da kika yi min akan halittar dan Adam, me ne gaskiyar lamari? Kai tsaye tace dashi. Idan har ka yi mamaki akan faruwar hakan to kuwa zaka yi mamaki akan yadda dalibi ke fin malaminsa ililmi. Saboda shi dalibi makoyi ne kwalwa kuwa takan taimaka wa wanda aka fadawa ya kara sanin abun da aka sanarda shi. Ya baki zai kara magana ke nan dodon kunnensa suka jiyo masa karar kada kararrawar komawa aji don haka maganar tashi ta katse ya mike tsaye gudun kada dalibai su tarar da shi. Shuhuda akawai sauran tambayoyin da zan miki amma lokaci ya kure don haka sai idan mun sake samun dama. Tac ce; To uncle ammaka shirya min tambayoyi da suka shafu wasu halittu ba bil'adama ba domin shi ne dama ta karshe da zaka yi magana da ni. Ya daina mamakin maganganunta ya ce; Ke ma ki shirya amsa min korafin da kika sjigar na yi miki tambayoyi akan wasu halittu ba bil'adama ba. Ya karashe maganar yana kokarin ficewa daga ajin amma kafin ya kai ga ficewar sai kunnuwansa suka jiyo masa furinta tana cewa. Wannan hirar da muka yi yasa nasan kai MATA'UL HAYAT ne gare ni dama zan budi ido na ganni cikin yalwataccen guri kwatankwacin dokar daji da na samu MATA'UL HAYAT wanda ba ya ta6a yankewa a gare ni. Sai dai abu ne mai wahala na samu MATA'UL HAYAT a wagga Sai dai abu ne mai wahala na samu MATA'UL HAYAT a wagga........ Bai karasa jin furucin nata ba saboda samun nasarar ficewa da ya yi amma kalmarta ta karshe ta zauna daram a kwanyarsa hakan ne ma ya sa lokacin da ya koma dakin malamai ya shiga kogin tunani. Sam ya manta ma'anar kalmar daga ji dai kalma ce ta Larabci musamman idan ya yi la'akari da HAYAT da ta sako cikin jam'in kalmomin wadda ta sako cikin jam'in kalmomin wadda take nufin RAYUWA. To me MATA'UL ke nu fi? Amsar ta gaza samuwa sai da ya dangano ga uncle Tukur Ahmad Sada wanda shi ne H.O.D na Arabic ya isar da bukatarsa ta neman sanin ma'anar kalmar MATA'UL HAYAT ko ya tantance me Shuhuda ke nu fi? Uncle Tukur ya yi murmushi yana duban uncle Hamza yace; Kalmar MATA'UL HAYAT kalma ce da aka samo daga harshen larabci ma'anar gundarin kalmar tana nufin JIN DADIN RAYUWA. To amma wani lokaci ana alakantata da kayan dadin rayuwa. Uncle Hamza ya yi jinjina kai cikin gamsuwa. Uncle Tukur ya ci gaba da cewa. Wani bincike kake yi ne da ya hado da kalmar? Uncle Hamza ya yi takaitaccen murmushi ya ce Eh. Yana kokarin mikewa; Na gode . Ya koma teburinsa ya zauna. Wani tunanin ya bijiro masa idan kalmar MATA'UL HAYAT na nufin JIN DADIN RAYUWA me Shuhuda ke nufi da ta ce shi MATA'UL HAYAT ne gare ta? Wai kuma da zata samu kanta a cikin dokar daji to da ta samu MATA'UL HAYAT wanda ba ya yankewa. Ke nan ta kasance mai son yin rayuwa a cikin dokar daji? Me yasa ta ke da wannan burin? Wannan ma idan aka auna shi a mizani za a tarar da soki-burutsu ne a cikin maganganun nata kamar yadda ta saba abubuwanta a cikin soki-burutsu. To wai duk me ya yi sanadin hakan? Kwalwar ce ta yiwa Shuhuda yawa yasa ta ke wasu rudaddun al'amura ko kuwa tana daga cikin jinsin mutane masu raunin hankali? A'a gaba daya ma ba ta daga cikin jinsin halittun mutane? Aljana ce? Tabbas Aljana ce! Ya ji zuciyarsa na son gasgata masa hakan bisa kwararan hujjoji. To amma ta ya zai aminta cewar Shuhuda aljana ce? Idan ya alakantata da suffofin mutane ma'ana ba ta da kofato a kafarta idan ba ta daga cikin jinsin mutane ko na jinnu a wane jinsi za a ajiye ta? Bai sani ba! Babu wanda zai yi gajen yanke hukunci akan haka! Babu wanda zai iya cewa ga matsayin Shuhuda a rayuwa illa dai Shuhuda wata halitta ce da ke yawo bisa doron kasa don haka yanzu abu mafi rinjaye a tare da shi sanin nasabarta ma'ana asalinta iyayenta da ma sauran wasu al'amura da suka shafe ta! Zuciyarsa ta kalubalance shi mai yasa zai damu kansa a cikin lamarin Shuhuda a matsayinsa na malami wanda alakar karatu ta gada su? Da gaske ke nan abin da yake ji na masa yawo a rai ya zama gaskiya? Ya kamu da son Shuhuda? Ta ya zai kamu da son abin da bai da tartibin sanin ko mene ne shi? Lokaci daya ya kalubalanci wannan hasashen na shi kawai abin da ya dace dashi ya share ta. Ya manta da wanzuwarta a makarantar bare ta dinga caza masa kwalwa a karin banza. ANYA UNCLE HAMZA? DUBA DAI!!! Shuhuda na kwance a saman gado, inna yadywa ta shigo dakin tana cewa. Ke burkakkiya tashi ga wannan fitinannen yaron ya hanani sukuni wai sai ya yi waya dake. Shuhuda ta dago kai ta dubi inna yaduwa da wani irin kallo mai rikitarwa ta ja dogon tsaki ta mayar da kanta ta kife a filo. Ran inna yaduwa ya 6aci ta janyo Shuhuda tana cewa: Ke ni kike yiwa tsaki don gidanku? Shuhuda ta daga mata hannu tace: Kada ki kara ta6a ni idan ina wanka ki fita ki bar kallona.... Nace ki fita idan ba so kike na yi miki wanka ba? Inna yaduwa ta ture Shuhuda tace: Ja can burkakkiya kawai. Tana karashe maganar ta fita daga dakin. Isah da yake jiyo hayaniyarsu ta cikin wayar yace: Haba Inna bai kamata kina yiwa Shuhuda irin wannan tsawar ba ya kamata ace kina rarrashinta domin wannan matsalar da ta ke fama da ita ba karamar matsala ba ce: Ta katse shi da cewa: Bayan matsalar ma har da shakiyanci don kawai tana ganin ni kakarta ce sai ta dinga raina min hankali. Wai na shiga dakinta amma sai tace wai tana wanka na fita... Oh ni Yaduwa yau na gamu da gamona!! Isah yace: Wane irin wanka? Inna yaduwa ta ce; Shi ne abin da ke ba ni takaici, kwance fa ta ke akan gado sanye da doguwar riga baka amma don tsabar ta dauke ni wata karabiti shine zata ce tana wanka? Isah ya jinjina maganar yace: To don Allah Inna ki dinga hakuri da Shuhuda kuma ya kamata fa ace ya zuwa yanzu an san wane irin ciwo ne da ita. Saboda barinta cikin wannan matsalar ba karamin cutarwa ba ne a gare ta? Inna yaduwa tace To ai magana ba hannuna take ba wannan sai ka tuntu6i mahaifinku. Yace Shi ke nan zan yi masa maganar idan ma ba a samu kwararriyar asibitin da za a magance mata matsalara nan gida Nigeria ba ko nan Senegal sai a kawo ta tunda ba laifi suna da kwararrun likitoci. Inna yaduwa tace: Dada dai ai ni kuma na gama magana kai ni kyale ni haka yara kun zame min karfen kafa. Daga wannan ya yi watandaririya da ni sai wannan ya juyo ni sai ka ce masa a tanda? Tana karashe fadar haka ba ta bari ya tanka ba ta datse kiran. Washegari Alh Ahmad ya zo gidan ya tarar da inna yaduwa a falo tana matse lemon tsami a kofi ya zauna yana gaishe ta. Ta amsa masa cikin sakin fuska. Yace: Me zaku yi da lemon tsami? Ta ce: Sha zan yi kasan yana wanke dattin ciki. Shi yasa yake son zama da tsaffi ko banza zaka samu magungunan gargajiya. Yayi murmushi yace; To ina Shuhuda da ba ku ba ta ta matse muku ba? Ta kya6e baki tace: Wannan burkakkiyar yarinyar wani abu ta iya? Ya ce Kai inna rannan fa na ji kina yabonta akan dambun da ta yi muku? Ta sake kya6e baki ta ce: Ai ranar ma sa'a aka ci. Amma Shuhuda ba tasan komai ba daga kwanciya sai karatu, haka kawai yarinya ta tsiri wata tsurfa ana magana da ita sai ta yi shiru idan an matsa mata ta shige daki ta kudundune cikin bargo sai ka ce mai fama da lalurin basir saboda yawan kasala. Alh. Ahmad ya girgiza kai yace: Yau ma ke nan baccin ta ke? Tace: Ba fa bacci take ba. Kwance kawai take koda yake dazun tace min wai kanta na yi mata ciwo sannan cikinta na yamutsawa na ce ta dauko lemun tsami ta sha ta ce min. Wai ita rabonta da shan lemun tsami tun tana ciki kafin a haife ta don haka yanzu ba za ta sha ba. Wanda ta sha ma a dole ta sha ba don haka ba babu abin da ya hadata da lemon tsami wai ko ganinshi ta yi zuciyarta tashi ta ke ta jita kamar ba mutum ba. Don tsiya ma har da ce min ita ba tasan wace ce ita ba wai tana jin kanta kamar ba mutum ba. Alh Ahmad ya kwashe da dariya. Ya ce: Cewa zaku yi kuna shan durama a gidan nan? Tace Ba wata durama illa tsabar rainin hankali. Ya sauya fuskarsa daga yanayin fara'a ya nutsu yana cewa. Yauwa. Dama maganarta ce ta kawo ni mun yi shawara da yaya za a kaita asibiti a binciki lafiyar kwalwarta saboda mu ma abin yana damunmu. Cikin rashin kula inna yaduwa tace: Da dai ya fi domin ni na gaji da wulakancin yarinyar nan har ma na soma tunanin ta tattara kayanta ta koma can gidanku tunda ni ta rainani. Alh Ahmad ya yunkura ya mike tare da cewa. Bari na dubuta. Ba ta tanka ba. Ya nufi dakin Shuhuda tarar da ita ya yi zaune akan abin sallah tana lazimi shigowarsa yasa ta tsinke lazimin tace: Baba barka da zuwa. Yace yauwa 'yar baba. Bayan ya zauna saman gadonta ya dora da cewa; Akace baki jin jin dadi? Ta dube shi cikin yanayin rashin fahimta, ta ce: Ni? Kai ni yau garas nake, shekaru sha takwas ne dai na dan yi rashin lafiya, ita ma ban wani jima ba na samu sauki sai dai ko a mafarki ne na ji kamar ba ni lafiya? Fuskarta ta bayyanar da yanayi na tuhumar kanta da kanta. Kafin ya yi magana ta dora da cewa. Amma dai lafiya na ke, jina na ke ma kamar ingarman doki saboda karfi bari ma ka gani. Kawai sai ta mike ta kama tsalle. Bai yi yukurin dakatar da ita ba, tabbas Shuhuda tana da ta6in hankali. Abin da ya ayyana a ransa ke nan. Bayan ta yi tsallen ta koma saman gadon ta zauna tana wata irin dariya ya tsura mata idanu can yace; Ki shirya zamu je Asibiti. Tace: Asibiti? Eh, Ya tabbatar mata. Bata musa ba tac: To. Ya tashi ya fita. A falo ya zauna suna hira da inna yaduwa can Shuhuda ta fito daga dakinta. Inna yaduwa ta wurga mata sakon harara, Shuhuda ta ja tunga turus ta tsaya. Ni fa ki daina hararata idan kina hararata sai na dinga ganinki kin koma min kamar wata dodanniya. Dubi yadda idanuwanki suka yi kulu-kulu kamar kuruga, ina jin sai na rage miki girmansu. Inna yaduwa ta ja tsaki. Sai ki maida hankali tunda ke ce sarauniyar wauta. Shuhuda tace: Au ba ki san ni sarauniya ba ce? To wallahi ki sani an bani sarauta tu lokacin da ya shude, yanzu haka idan fadawana suka ganki sai sun hukunta ki. Alh Ahmad yana so ya yi dariya amma ya gumtse don shi abin na su ma dariya ya soma ba shi. Yace Inna zamu je Asibiti. Tace: Sai kun dawo, ya dubi Shuhuda yace: Wuce mu ta fi. Yana gaba tana binsa a baya har inda ya ajiye motarshi. Sun isa asibitin Fancy Clinic Alh Ahmad ya bukaci ganin Dr Ya'u likitan da ya yiwa Shuhuda tiyata shekarun baya. Anan ne ake sanar da shi ai ya jima da rasuwa. Gaban Alh Ahmad ya fadi yaushe Dr Ya'u ya rasu bai sani ba? Koda yake sun jima ba su zo asibitin ba. Dr Ya'u kwararren likitane da ake ji da shi a wannan asibiti. Ya yi musu aiki lokacin da Shuhuda ta ke tsotsar hannu aka tsaga wanda daga lokacin ne ba ta kuma tsotsar hannu ba. (((( Sai dai abin da Alh Ahmad bai sani ba shine; tun bayan sallamar Shuhuda daga asibitin ya yi ta fama da rashin lafiya wadda bata jin magani daga karshe ya rasu. Sanadin ya faru ne sakamakon allurar da yayi a jikin Shuhudan. wanda idan muka duba tun baya mutum biyu Salmai ta rasu bayan ta tsarga hannun Shuhuda da ta yi. Mas'ud shi ma ya rasa ransa sanadin jinin(ruwan nono) da ya fito daga jikin Shuhuda. Don haka zamu iya tantancewa duk wanda ya yi sanadin fitar jini(ruwan nono) a jikin Shuhuda yakan rasa ransa ne. Me ye sanadin haka?)))). Dole sai wani likitan suka samu ganawa da shi ya yi aune-aunensa da gwaje-gwajensa ga Shuhuda daga karshe ya tura su asibitin mahaukata da ke garin Dawanau don yace yana ganin matsalar tata sai an dangano da can. YAT (JIN DADIN RAYUWA) ¤¤10¤¤ koda suka fito daga wannan asibitin kai tsaye Dawanau suka nufa. A cikin motar Alh Ahmad har lokacin jimamin rasuwar Dr Ya'u yake yi yayin da Shuhuda ta yi lum kamar mai bacci. Suna isa asibitin Dr Ibrahim m Sani suka gani ya yi gwaje-gwaje ga Shuhuda ya dubi Alh Ahmad yace: Na gama bincike ga yarinyar nan abin da binciken nawa ya ba ni, lafiyarta kalau ba ta da wata cuta da ta shafi kwalwarta. Illa iyaka ta kasance daga cikin yara masu kaifin kwalwa (Gifted) don haka za a ga tana bada himma a karatu da sauran al'amura domin ita kwalwar tata ontop ce da an saka mata abu ta ke daukewa. Alh Ahmad yace; Likita ba wai ban aminta da bayaninka ba ne. Ina so ka gane ita wannan yarinyar ba a 6angaren karatu kawai ne ya samu zargin tana da ta6in hankali ba a'a wani lokaci fa idan ana zaune da ita sai ta yi ta sakin maganganu na shirme. Dr ibrahim yayi murmushi; yace: Irin wadannan yara ba su fadar abu na shirme sai dai idan a gaza fahimtarsu amma idan aka nutsu aka yi wa maganganunsu kyakkyawar fahimta za a ga komai suka fada yana akan turba. Alh Ahmad ya jinjina kai cikin sarewa yace; Shi ke nan likita, mun gode. Koda suka taho a hanya Alh Ahmad bai aminta da bayanin da Dr ibrahim ya yi masa ba. Gani yake bai da kwarewa ne akan aikinsa don haka ya yanke shawarar zaije ya fadawa dan uwansa abin da ya wakana inyaso idan ta kama su fita da ita wajen sai a fita da ita don gaskiya duk wanda ya ga abubuwan da Shuhuda ta ke yi yasan tana da ta6uwa a kwalwarta. Baba wai kuna zargin ni mahaukaciya ce? Muryar Shuhuda ta katse masa tunaninsa. Bai bata amsa ba taci gaba da cewa. Ina mamakin yadda ake kallona a matsayin mahaukaciya, shin idan ni mahaukaciya ce da ba a ganni ina shiga bola ba? Ku daina yi min kallon mahaukaciya ni na fi kowa hankali, ko kun manta daga MISRA na fito? Ko kuwa so kuke na koma inda na fito? Ko a yanzu ma ta yi shirmen da zai tabbatar da tana da ta6uwar kwalwa to amma a yanayin da take ciki ba zai nuna hakan ba, gudun kada ya sa ta a wata damuwar. Haka ya kyale ta tana ta zuba surutai na rashin kan-gado har suka isa gida ya sauke ta. Ko shiga cikin gidan bai yi ba ya juya. Yayin da ita kuma ta shiga gida tana gunjin kuka, wai an mayar da ita mahaukaciya bayan kuma an san ta fi kowa hankali. Inna yaduwa tana jinta ta yi kunnen uwar shegun da ita har dai bacci ya dauke ta. Inna yaduwa tana jinta ta yi kunnen uwar shegu da ita har dai bacci ya dauke ta. Ta leko dakin ta ga Shuhuda na sharar bacci ta yi murmushi rac: Ja'irar kawai waye zai ganki yace ba mahaukaciya ba, bayan kina abubuwa na mahukata? Ai ni ba su burge ni ba da ba su sanya igiya sun daure ki ba. Tsalam! Shuhuda ta mike daga kwance idanunta jajur tace: Sai kizo ki daure ni din. Inna yaduwa tace: Au! Ashe ba baccin kike ba? To koma ki kwanta kin fi kowa hankali. Ta karashe maganar tana kokarin juyawa. Idan ke ba ki daure ni ba, ni zan daure ki domin na ga alama kin soma shiga bola kina tsin-tsince dubi yarga6a66un kayan jikinki kin wani daura dankwalin kaya ..... Hahaha mahaukaciya 'yar larai ku yi mata yeho. Ta saka dariya. Inna yaduwa ta tabbatar dai akwai haukan a tare da Shuhuda ta sa kai ta ficce ba ta kuma saurararta ba, don idan ta biye mata shirme zata yi ta zuba mata. ==========================---- --------------------------------------- ========BABI NA BIYAR=======*** *******BARA DA BANA******* Ina da hujjoji da ya sanya nake tababa da zamantowata cikin irin halittunka na mutane. Wadanda idan ka dube su da kyau zaka gasgata hakan. kaga kamar misali: Ni idan dare yayi nakan samu kaina a wata daula ana kidan kalangu ina rawa tamkar mazari. Sannan nakan sha ruwa a cikin koko har ma na watsa a jikina ana zagaye da ni wasu na hidima a gare ni. Da zarar sanyin asuba ya ratsa gangar jikina sai kuma na tsinci kaina a cikin kasar Misra ina ta ibadu..... Da safe kuwa sai na dinga jina wata iri bana tantance halin da nake ciki na farin ciki ko bakin ciki? Haka nan nake jina sakayau, kuma nannauya har ma na rasa a ina nake......... Shuhuda ke nan da ta ke fadawa Uncle Hamza lokacin da ya sake rutsata a cikin ajin nasu, bayan dalibai sun fita break. Ta daina ba shi mamaki, sai dai maganganunta babu tababa za a ajiye su a matsayin BARA DA BANA idan akayi duba wai tana jinta SAKAYAU kuma NANNAIYA wannan anyi ba ayi ba ke nan. Tunda tana samun kanta a wannan yanayin. Ya kawar da shirunsu da cewa: Kin san me nake so da ke? Girgiza kai ta yi ba tare da tayi magana ba. Yac: Gidanku nake son sani. Ta fito da idanu waje. Gidanmu? Ya daga mata gura alamun tabbatarwa. Tace ; Ayya ka MAKARO domin gidanmu yana da nisa. Yace Eh, duk nisan sa ina son sani. Tace Misra fa? Kasan kuwa nisan da ke da akwai daga nan zuwa Misra? Ya girgiza kai. Tace; Nisa ne mai tarin yawa. Yace: Ke ta ya kike zuwa kina kuma dawowa makaranta? Ta yi dariya tac: Ai ni akan wani keken doki nake zuwa. Yace; Kinga ni ma sai na hau keken dokin naki ko? Ta sake yin dariya har tana tuntsirawa tac: Ai ba ka iya hawa. Yace: Saboda me? Saboda ba ka da guri, kuma iska zai yi maka lahani tunda ba ka saba ba. Yace; Ke mai yasa bai yi miki lahani ba kafin ki saba? Tace: Ni? Ai babu abin da ke min lahani irin iska, kullum fa na koma gida sai na suma, mamata ta yi ta kwara min ruwa sannan na ke farfadowa. Wannan yarinya ta gama raina masa hankali, abin da ya ayyana ke nan a ransa. Koda yake ya shiga tababa shi ma na zamantowarta mutum kamar yadda ita kanta ta ke tababa. Shi kam yaci alwashi ko ma aljana ce zai ci gaba da bibiyarta har ya gano ko wace ce ita. Da farko ya so sharewa da lamarinta amma a cikin kwanaki hudun da bai kulata ba, zuciyarsa ce ke azalzalarsa, ya shiga wani irin bahagon, yanayi na mararinta daurewa kawai ya yi yana kawar da kai ga duk abin da zai alakanta shi da ita, amma hakan ya ci tura. Ya dai yarda ya kuma amince ya kamu da matsanancin son halittar da bai san tartibin daga cikin halittun da ta fito ba. Ya ja gauron numfashi kafin yace: Kinga ni ma idan iskan ya yi min lahani sai maman taki ta kwara min ruwa na farfado. Wannan karon ma sai da ta kuma yin dariyarta, sannan tace; Gaskiya mamana ba ta bari na je mata gida da wani, wai ba ta son ganin bakuwar fuska a gidanta. Ta fi son kullum ta ga fuskar da ta sani. Ko me ye dalilin hakan? Ya bukata yana tsare ta da idanu. Nima ban san dalili ba. Ta bashi amsa cikin yanayin damuwa. Na dai lura baki son naje gidanku. To ai ban san me yasa kake son zuwa gidanmu ba. Ta fada. Ina son na gaishe da mahaifinki. Inji shi. Ba zato ba tsammani yaga hawaye sha-shar na zuba daga idanuwanta, kafin yace wani abu ta ci gaba da cew: Mahaifina Allah yayi masa rasuwa a gidan gonarsa, sanadin tuntu6e da ya yi da kahon LIBHAS, ya dinga aman jini daga karshe aka dangana shi izuwa asibit acan ya rasu, kuma a ranar aka haife ni. Cikin yanayin tausayi da rudani yace: Me ye LIBHAS? Tace; Nima ban sani ba, kawai dai an fada min da shi ne yayi tuntu6e. Wa ya fada miki? Ya bukata. Ta daga kanta sama kamar mai tunani can tace. Ni ko shi mahaifin nawa ne ya fada min? Ko kuwa YAKUB ne? Inna Yaduwa? Kai ni na manta, ban ma dai sani ba. Amma kuma kamar da KAHON LIBHAS ya yi tuntu6en....... Akwai alamar tambaya mai karfi na zamantowar Shuhuda mutum, saboda ya za a yi mutum da ta ce a ranar da ya rasu ta zo duniya kuma har ya samu damar fada mata da ya yi tuntu6e da shi? Kaddara ma shi din ne ya fada, sai dai ga waninsa da ta yi wayo kuma aka sanar mata. Waye Yakub da Inna Yaduwa? Duk yadda aka yi tana da alaka da su kuma zai iya yiwuwa cikinsu din ne wani ya fada mata. Idan haka ne me ye gaskiyar lamarin MTUMCE ITA KO ALJANA? . Mu taru littafi na biyu. . . MATA UL HAYAT BOOK 2 ......... Yadda TSAUTSAYI ya hada mu yanzu a gaba KADDARA zata hada mu...... ....... Kafin hannun ya isa jikin Shuhuda sai ya sandare Inna yaduwa ta ji gaba daya jijiyar hannunta sun daskare kamar babu jini a tare da hannun. ..... An fada miki ana dukana? Ko don kinga ina raga miki? To sauke hannun.... ...... Ai dik yawona ban kai TANZIF ba, wanda yana iya zuwa kasa goma a kwana goma..... ...... Na fada maka bana iya amsa tambaya don ni kaina ina da tambayoyin da zan yiwa kaina, to amma saboda wannan dalili yasa na kan ajiye tambayoyina har zuwa ranar da zan samu MATA'UL HAYAT...... ...... Amma cikinta na juyawa kamar ana wana wani abu, kwatankwacin yadda idan an harba kwallo take....... ....... Wannan Shuhudar itace muka hadu fa da ita a birnin....... Wadannan tare da wasu zallan chakwakiya dik zaku samu amsar su sinqi-sinqi a sassanqame a cikin wannan gida me Albarka. . . Taku har kullum Zahra'aru Baba yakasai Maman Shureim. . Allah ya jikanta ya gafarta mata Ameen . Ta ku a kullum kuma a koda yaushe me muku posting Sadiq Halima (Sadin Mama) er mutan NIGER. Hada Hausa Book stories ====MATA'UL HAYAT BOOK 2====- ==========¤¤11¤¤==========- Katse masa tunani ta yi da cewa. Mahaifina na sona amma sai Allah bai nufa za a haife ni a lokacin da yake da rai ba. Bayan mahaifina mutum daya ne yaso ni kamar mahaifin nawa, shi kuma ya ta fi kasar Senegal karatu. Uncle Hamza yace: Da gaske kike? Ta yamutsa fuska sannan tace: Ban gane ba? Yace: Mahaifinki ya rasu? Tace; Tabbas! To ina mahaifiyarki? Ko ita ce Inna Yaduwa? Ta girgiza kai, Ba ita ba ce Inna yaduwa, mahaifiyata ta yi aure. Ina zaune ne a hannun Inna yaduwa wadda ta haifi mahaifina. Yace: Allah ya jikan mahaifinki........ Ba ta amsa ba, sai suka yi shiru su duka can ya dago kai yana dubanta, yace; Rannan kin shigar da korafin kada na yi miki tambaya wadda ta shafi bil'adama ko me ye sanadi? Tayi murmushi tace: Saboda ka yi min bayanin waye dan Adam kuma na gamsu. A matsayinka na malamina nasan kana son dorani akan abubuwan da ban sani ba. To shi yasa na ce maka haka. Ka ga sai ka yi min tambaya a wasu halittun wata kila kai ba ka sani ba, ni kuma na sani sai na ba ka haske kamar yadda ka yi a gaske. Zai yi magana ke nan 'yan ajin wajen su goma suka danno kai, sakamakon lokacin da ya kare don haka ya fasa maganarsa. Ya mike tsaye ya koma gaban allo a inda kujerar malamai ta ke, don dama shi ne da darasi da zarar an dawo. Ya yi zaune yana tunanin maganganun da suka yi da Shuhuda ya dinga auna su a mizanin da ya dace ya ajiye su, amma dai ya gaza gane inda suka fi cancanta ya dora maganganun nata. A haka dalibai suka dawo gaba daya ya ci gaba da gabatar musu da darasi. ******** ********* ******* Tun daga wannan rana Uncle Hamza bai kuma samun sararin tsayawa da Shuhuda ba kasancewar ana cikin lokacin karatu ka'in da na'in sakamakon jarrabawar da ke tunkarowa. Gaba daya ya tattara al'amarinta ya kyale idan ma ya shiga ajin ba ya bari ko kwayar idanunsa ta gani koda yaushe cikin bakin gilashi ya ke. A haka suka cinye wannan zangon karatun aka yi musu hutu. Wata ranar laraba Shuhuda na kicin danwake ta ke yi. Yau tunda ta shi ta ke mitar a yi dan waken. Ita kuma Inna yaduwa ta tace ba zata yi ba, idan tana bukata ta shiga kicin din ai ita ma mace ce. Dariya Shuhuda ta yi ta nufi kicin tana cewa: Kin dai san zan iya girkawa ko? Shi ne ta shigo kicin tana hakilon yin danwaken. Inna yaduwa na falo tana kallon yadda Shuhuda ta ke shige da fice daga kicin zuwa falo. Ta gama danwaken ta zo falon ta zauna ta yanka tumatiri, Inna yaduwa ta kawar da kai gefe guda ta nuna kamar ba tasan da shigowar Shuhuda ba. Ana haka ne wani yaro ya yi sallama Inna yaduwa ta amsa? Yaron yace:: Wai an ce Shuhuda ta zo ana kira a waje. Shuhuda ta dago kai da sauri ta dubi yaron, tare da cewa: Ni din ake kira a waje? Yaron ya daga mata kai alamun tabbatarwa. Tace: Ka je kace nan gidan babu Shuhuda. Yaron ya juya zai fita Inna yaduwa ta tsayar da shi. Kai tsaya. Ta aikawa Shuhuda sakon harara. Don tsiya an aiko kiranki za ki ce babu Shuhuda a gidan nan? Shuhuda ta juyo ga Inna yaduwa idanunta jajur tace: To ina Shuhudan? Ina ce ni sunana YAKUB? Inna yaduwa ta sake kulewa, ta kaiwa Shuhuda bugu da hannu. Amma kafin hannun ya isa jikin Shuhuda sai ya sandare, Inna Yaduwa ta ji gaba daya jijiyar hannunta sun daskare kamar babu jini a tare da hannun. Shuhuda tace: an fada miki ana dukana? Ko don kinga ina raga miki? To sauke hannun. Bisa ga tsanani al'ajabi sai hannun ya koma Shafal, Inna yaduwa ta tsorata ainun ga wannan lamari, shi kuwa yaron dariya ya kama yi, don bai da isasshen wayo. Shuhuda ta dubi yaron tace: Ka je ka cewa wanda ya aiko ka nan gidan babu Shuhuda. Yaron ya juya yana dariya, ita kam Inna yaduwa gaba daya tsurewa ya yi. An ya kuwa wannan yarinyar ba aljana bace? Jikinta na 6ari ta mike ta nufi dakinta. Waya ta dauka domin kiran 'ya'yanta ta sanar da su abin da yake faruwa. Amma wani rudanin da ta lalubo lambar da zata kira, tana kira sai kawai wayar ta kashe kanta, kuma ga cikakken caji, amma kiran ya ki yiyuwa. Ta yi jigum tana mamaki, wannan aikin jinnu ne, babu tababa Shuhuda aljana ce, idan ta yi la'akari da kwararan hujjoji. Misali: An tsarga yatsanta an ga nono na zuba. Anje asibiti allurar da aka yi mata ta karye, daga baya labari yazo likitan ya rasu. Mas'ud ya ji mata rauni an ga nono maimakon jini, sannan tana wasu dabi'u wadanda sun zarce ace lalurin ta6uwar kwalwa ce. Anya kuwa lokacin da za a haifi Shuhuda jinnu ba su yi musayarta da diyarsu ba? Ba shakka wannan haka yake, jinnu sun dauke diyar Karimatu a ciki ko bayan ta haihu suka sauya mata wata 'yar da tasu. Idan haka ne me ye abin yi? Zuciyarta ta ci gaba da bugawa ta rasa abin da ke yi mata dadi a rai. Tana cikin wannan hali Shuhuda ta shigo dakin a rude tana cewa: Wayyo zai kashe ni Inna, ki taimake ni. Wallahi mugu ne! Ga shi can an hana shi shigowa , kashe ni zai yi! Kafin Inna yaduwa ta samu damar tofawa tuni Shuhuda ta 6uya a bayan Inna yaduwan. Sai kuka ta ke tana kiran taimako. Kan Inna yaduwa ya daure sosai, tsoro ya sake shigarta ba tasan lokacin da ta rukunkume Shuhuda ba tana cewa.: Waye? Shuhuda ta kasa magana kuka kawai ta ke yi kamar zata shide a gurin. Cikin jarumta Inna yaduwa ta 6am6are jikinta daga na Shuhuda ta nufi falo. Ba ta ga kowa ba, tana tafiyar sanda ta fito harabar gidan. Nan ma ba ta ga kowa ba, hatta maigadi babu shi babu alamarshi, sai dai a kofar gida ta jiyo hayaniya, don haka kai tsaye can ta nufa. Ta tarar da kofar gidan dankam da mutane, wai wani 6arawo ne aka kama ya shiga wani gida a layin yayi sayar Generator. Da ta dawo gidan iske Shuhuda ta yi kwance dai-dai akan gado yadda kasan ta dauki lokaci tana bacci. Inna yaduwa ta kai hannu tana bubbuga kafafun Shuhuda alamun tayar da ita. Shuhuda ta bude idanunta sun yi jawur saboda bacci ta ke kashir6an. Inna yaduwa tana hada ido da Shuhuda sai ta rasa me zata ce mata, hasalima duk sai ta ji ta manta abubuwan da suka faru a dazun. Cikim muryar bacci Shuhuda tace: Inna lafiya kika tashe ni? Inna yaduwa tace: Kin gama cin danwaken ne? Ta girgiza kai. Ai na fada miki ya lalace, ba shi yasa na shigo daki ba don takaici? Inna yaduwa ba ta san ya aka yi ba, sai cewa tayi. Af! Anyi haka fa! Amma duk da haka ki tashi baccin nan, ki dora mana girkin dare, kinga har uku ta gota. Shuhuda tace: Wallahi Inna ba zan iya kuma shiga kicin ba, har yanzu raina bai gama yin sanyi ba. Inna yaduwa ta yi murmushi tace: Ai dama kallonki kawai nake amma yaushe zaka yi danwake ka zuba gishiri a cikin kwa6in? Shuhuda ta koma ta kwanta. Ai na gama yin danwake har abada, ni sam ya fice min daga rai. Ta karashe maganar tare da lumshe idanu alamun zata koma bacci. Inna yaduwa ta koma falo ta zauna akan kujera tunaninta ya dan dawo, ta tuna abubuwan da suka faru ko kuwa a mafarki ne? Ta shiga tababar yadda abubuwan suka faru kamar gaske, kamar kuma a mafarki? Mikewa tsaye ta yi a lokacin da zuciyarta ta gama yanke mata yanke mata duk abin da ya faru a bayyane ne don haka zaman gidan bai ganta ba, zama da aljana? Sai dai me? Tana mikewa da wannan kudirin sai ta ji wata irin kasala ta zo mata ta ji kamar ta manta yanda abubuwan suka faru. Bayan sallar magriba Inna yaduwa da Shuhuda suna zaune a falo tamkar kurame haka suke. Babu wadda ke yiwa wata magana, kowacce da abin da yake yi mata yawo a rai. Alh Sada ya yi sallama tare da shigowa. Ya gaishe da Inna yaduwa. Shuhuda ta gaishe shi, sai suka yi shiru. Inna yaduwa na son sanar da shi abin da ya faru amma ta gaza daga harshenta bare ta furta.Wani irin nauyi ta ke ji harshen nata ya yi mata. Shirun ya dauke su wani wani lokaci kafin daga bisani Alh. Sada ya katse musu shirun da cewa:: Inna jiya angonki yana tambayata ku wai ba ya samun wayarki. Inna yaduwa ta yi gajeran murmushi tace: Bar ja'iri bai neme ni ba. Amma ni da wayata kullum ta ke da caji? Shima Alh Sadan murmushi yayi. Yace; Ni ma abinda nace kenan. Tace: Yaushe zai kare karatun na shi ya dawo ne? Alh Sada yace: Saura Shekara biyu ya fada min kila ma a can zai yi aiki. Saboda tun yanzun gwamnatin kasar ta fara kyarkyararshi. Kin san angon naki akwai himma. Tace: Dama haka ake so. Alh. Sada ya dubi Shuhuda yace: Ke ya 6angaren naki karatun? Na ji an ce ba ki mayar da hankali. Wani malaminki ya same ni yace idan kin je makaranta babu abin da kike sai wasa, haka ne? Ya karashe maganar cikin yanayi na zolaya. An ta6owa Inna yaduwa inda yake mata kaikayi, amma koda ta hada idanu da Shuhuda sai ta ga kamar tana yi mata gargadi kada ta yi magana. Ta daure cikin jarumta da niyyar furta abinda ke ranta, amma sai sa6anin hakan ya fito daga bakinta. Ai kuwa ba a ce Shuhuda ba ta karatu ba, yarinyar da kullum ba ta da wani aiki sai na karatu? Kawai dai ina ganin irin wadannan malaman ne da suke da kyashi akan kwalwar da dalibansu suke da ita. Alh Sada ya fadada murmushinsa yace: Gaskiya shi ma shaidar kirki ya yi mata yace duk cikin dalibansa babu wadda ya yaba da kwalwarta kamar Shuhuda, kawai na yi hakan ne don na tabbatar da abin da ya fada. Inna yaduwa ta rasa me yasa ta kasa fada masa cewar: Shuhuda aljana ce, babu abinda ta sani sai shirmen aljanu! Shuhuda kam rusunar da kanta ta yi kasa kawai ta yi. Nan ya dan ja Inna yaduwa da labari yana sanar da i2a abinda malamin ya fada masa. Daga karshe yace: Yaron yana da nutsuwa da maida hankali game da dalibansa. Yace min shi dan asalin katsina ne, sunansa Hamza. To yadda ya ga yarinyar na da kokari ne yasa ya biyo sawu ya yi tambaya ya gano ko su waye iyayenta, shi ne yazo. Da a ce za a dinga samun malamai irinsa lallai da iyayen yara sun ji dadi, don gaskiya ba karamin dadi na ji ba da har wani malami ya wanko kafafunsa ya zo musamman don ya yaba irin kojarin da Shuhuda take da shi ba. Inna yaduwa dai ta yi shiru, don ta kasa furta abin da ya faru din, Da ta yi yunkurin hakan sai ta ji harshenta ya yi mata nauyi. Don haka har Alh Sada ya gama maganganunsa ya yi musu bankwana ba ta iya furta abin da ya faru ba. Hutun 'yan makaranta ya kare, don haka daliibai da ke makarantar kwana suka soma komawa tun a ranar lahadin farko, Shuhuda kuwa da ke jeka-ka dawo ta wanke kayanta har ma da sabbin kayan makaranta da Alh Sada ya dinka mata. Ta hada komai na komawa makaranta gari kawai ta ke jira ya waye ta ganta a cikin makaranta. A cikin satin nan gaba daya Shuhuda ta sauya ta koma wata irin yarinya mai tsananin natsuwa hankali da kula da addini. Inna yaduwa tana ta tsananin mamakin yadda Shuhuda ta sauya kamar ba ita ba. Sam babu wannan shirmen nata, koda yake har yanzu Inna yaduwa ba ta aminta Shuhuda mutum ce ba. Sai dai ta rasa yadda aka yi ta kasa bayyanar da hakan ga wani, ko shuhudan ma ta kasa yi mata magana bare ta sake tabbatarwa aljana ce. Washegari ranar litinin Shuhuda ta tafi makaranta, kasancewar makarantar ta kudi ce, shi yasa dukkan dalibai sun dawo gudun kada a hukunta su. Sa'adatu wadda suke kujera daya da shuhuda ita ta fara lura da sauyin da aka samu a tare da shuhuda, sannan sauran dalibai ma suka fahimta. Kowa yayi murnar yadda Shuhuda ta samu lafiya, domin sun dauka cutar tata ta ta6in hankali ce, to yanzu kuma gashi ta warke. A ranar unlce hamza bai shigo ajin nasu ba, duk ma tsayin makon bai shigo ajin ba har sai da wani makon ya shigo. da Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤12¤¤ Da ya shigo ajin ya yi darasi yaga sauyin da aka samu a tare da shuhuda anin ya ba shi mamaki, shin da gaske dama ta6uwar kwalwar ce gare ta? Ko kuwa kaifin kwalwarta ne ya soma da kushewa? Da aka fita break fast ya shigo ajin amma bai tarar da ita ba kamar yadda ta saba zama a ajin idan an fita break. Sai da aka kusa komawa ya hangota tana tafiya. Ya yi wuf ya fito daga dakin malamai ya sha gabanta. Ta rusuna ta gayar da shi, ya amsa tare da cewa: Yau ya aka yi kika fita tara ke da kika ce daga gida kije ciwo abinci? Tace: Yau ban ci komai ba doki nake na zo makaranta. Yace: Wata kila don kina son ganin malaminki ne mai shisshigi ko? Ta yamutsa fuska cikin rashin fahimta, amma ba ta iya cewa komai ba, ya daga gira sama kafin yace: Eh mana, ko ba a fada miki na je can gidanku Misra ba? Ya karashe maganar cikin yanayin zolaya. Kanta na sunkuye kasa ba ta dago ba. Ya ci gaba da kallonta, yace: Har ma muka gaisa da dan'uwanki YAKUB? ya karramani, ashe dai gidanku babban gida ne? Har yanzu ba ta ba shi amsa ba. Ya gyara tsayuwa yana murmushi yace: Ai na fadawa Yakub ina so ya ba ni aurenki, kuma da yake da ne mai karamci da yakana, sai ya ya bani har yace zai shige min gaba a gurin neman aurenki. : Ta dago kai da sauri alamar ta razana amma ba ta tanka ba Shi kuwa Uncle hamza murnushi ya kuma yi, yace: Ko ba ki sona nw? Bata amsa ba sai kawai ta yi gaba , bai yi yunkurin dakatar da ita ba, saboda a ganinsa kunya ce ta hana ta tsaya. Sai ya cizi la66ansa ya koma dakin malamai ya zauna. Wani irin nishadi yake ji a zuciyarsa. A da ya dauka shuhuda ba mutum bace, to amma tunda ya je gidan yayan mahaifinta ( Alh sada) ya tabbatar mutum ce sai kuma da ya je gidan Inna yaduwa. Dan'uwanta yakub ya fito ya karrama shi, shike nan ya sake sakankancewa, ya kuma yadda lallai ya kamu da son Shuhudan. Hakan ne ma yasa ya gaza 6oyewa har sai da ya tunyu6i yakub din. Kuma sai ya samu hadin kan Yakub inda har ma yake yi masa bayanin Shuhuda lafiyarta kalau. Kwalwa ce ta yi mata yawa, amma zai sha mamaki ranar da zai ganta a makaranta da sauyawar abubuwa da dama. Don ya hanata yawan karatun nan na kure rai da ta ke yi da rana. Kuma sai ga shi din ya sha mamakin tunda ya ga sauyawar abubuwa da dama a tare da Shuhuda. A ranar yana da darasi da su, har kosawa yayi lokacin ya yi ya shiga ajin ko don ya ji muryar Shuhuda cikin tsadadden turancin nan nata wanda ko dan kasar Amurka sai haka. Lokacin na cika cije da doki ya nufi ajin nasu shigar da ya saba wadda ta ke kar6ar fatar jikinsa, wato shigar dogayen kaya, na danyar shadda ta tsadaddiyar hula gami da takalmi 'yan asalin kasar spain sai agogonsa kirar kasar Germany. Duk wanda zai ga uncle hamza zai yaba da tsananin kyawun da ya yi don shi din mai kyau ne. Ga kuma dorinar ado da yake da ita. Zai yi wuya ya yi shiga ba a ga zahirin kyansa ba. Yana shiga ajin ya dora idanunsa a kujerar da Shuhuda ta saba zama. Yau din ma tana zaune kanta na sunkuye ga dukkan alamu littafin da ke gabanta ta ke dubawa. Amma jin hayaniyar gaishe da uncle hamza da daliban ajin ke yi yasa ita ma ta bi sahunsu ta gaushe shi. Ya ba su umarni da su zauna . Kowacce ta zauna a hankali ya fara yanyara turanci yana yi musu bayani game da Equalibrium? Kowacce ta nutsu tana saurarensa har ya kai ga yi musu tambayoyi ana ba shi amsa. Amma sai bai ji Shuhuda ta yi magana ba, shi kuma abinda yake so yaji muryarta. Don haka kawai sai ya jefo musu tambaya akan Wave wanda ya shafi darasin physics kuma yana da yakinin ba su kai gurin ba. Ya dai san Shuhuda ce zata iya amsa wannan tambaya. Sa6anin hasashensa sai ya ji ajin ya yi tsit! Babu wanda ya koda motsa da nufin amsawa. Ya sake saurarawa Shiru, sai ya yi murmushi yana duban Shuhuda yace: Ke ya baki bamu amsa ba? Ita ma murmushin tayi tace: Ban sani ba uncle. A kalla ya dai samu abinda ya ke so tunda ya ji kalma daga bakinta. Ya zakuda kafada. Yace: Shike nan ya zama aikin gida(home work) zan kar6a gobe idan Allah ya kaimu. Yana karashe fada ya sa kai ya fice daga ajin. Washegari gaba daya Shuhuda ta hana kadaituwarsu, don lokacin da aka fita break fast ya shigo ajin bai ganta ba. Bata kuma komawa ajin ba har sai da aka shiga. Babu sararin kadaicewa da ita. Da aka tashi kuwa yana hangota tana tafiya zuwa inda direban da ke kawota makarantar yake tsayuwar jiranta. Da saurinsa ya fito daga dakin malamai amma koda fitowarsa sai ya ga tuni har motar ma ta tashi. Yaja turus ya tsaya yana cizon la66ansa. Ya yi tunanin ya bita har gidansu. Amma sai ya tuna maganar Alh Sada inda yake ce masa, ya ji dadin yadda ya zo har gida don yaba kwalwarta, amma ba su bukatar wata doguwar alaka tuinda Shuhuda yarinya ce, karatu ne yanzu a gabanta. A lokacin uncle hamza ya yi matukar mamakin yadda farat daya Alh sada ya fahimci abin da yake cikin kwayoyin idanunsa, har ya yi masa irin wannan gugar zanan. Wannan tunani da ya yi shi ya hana shi bin bayan Shuhuda ya yanke shawarar idan ya koma gida zai kira lam;bar da yayan Shuhuda(yakub) ya bashi don dama tunda ya kar6i lambar bai kirashi ba. Kullum yana son ya kira sai ya yi tunanin abin da zaice da shi shi yasa bai kira shi ba tun can baya. To amma yana ganin yau yana da cikakkiyar dama ko don ya ji muryarta. Hakana kuwa ce ta faru, bayan ya koma gida ya yi wanka ya ci abinci tare da sallah. Yana zaune a falo ya dauki wayarsa ya lalubo lambar yakub. Ya kira: Mamaki ya kama shi lokacin da yaji sautin kiran maimakon trin-trin sautin da ake ji idan an kira layin MTN ko ZAIN, sai yaji Triiiiiiin! Kamar ya kira layin GLO ko ETISALAT. Shi dai yasan layin da layin da YAKUB ya ba shi MTN ne mai 0803, to amma sai ya ci gaba da kasa kunnuwa yana saurare. Har wayar ta ganma kara ba a daga ba, bai hakura ba sake nema ya yi a karo na biyu. Nan ma ba a daga ba, sai ya ajiye wayar a gefensa ya janyo laptop dinsa yana dube-dube. Kira ya shigo a wayarsa, ya dauka ya duba, bakuwar lamba ce kuma ga dukkan alamu daga kasar waje ne, saboda yadda CODE din lambar ya fara da +2011. Cikin rashin sanin wanda ya kirashi ya kara wayar a kunne bayan ya latsa malatsin O.K. Sallama aka yi masa wadda kana ji kasan mai sallamar harshensa ya karye da larabci. Uncle yace cikin Harshen Hausa. Waye akan layi? Daga can 6angaren aka ce: ABUBAKAR IBN KHADDAB ne, an kira wayata ba ni kusa da wayar na gani kamar a kasar Najeriya ne, wa ke magana? Uncle hamza ya zabura saboda shi sam duk yau bai kira wata lamba ba idan ba yanzu da ya kira Yakub ba. Yana girgiza kai kamar Abubukar din na ganinsa yace: A'a gaskiya ban kiraka ba, domin duk yinin yau wayata a kashe ta ke. Abubakar ibn khaddab yana dariya ta cikin wayar yace: Amma na yi mamaki, saboda na dauka ko su Yusufa ne suke son magaba da ni. Don Allah kada ka zolaye ni ka fada min waye? Uncle hamza ya kara cika da tsananin mamaki yace: Abin da na fada haka ya ke, ni ban sanka ba. Babu wani da na sani a wata kasa da ta tsallake Najeriya bare na zolaye ka.: Abubakar yace: Ni ma cikin makon nan zan dawo Najeriyar idan ma ka 6oye min shike nan na gode. Ka gaishe min da su Alh BABBA. Yana gama fadar haka wayar ta katse, tsoro da fargaba suka cika zuciyar uncle hamza tabbas duk yadda aka yi akwai SANAYYA tsakaninsa da wanda ya kira kansa da Abubukar. Idan ya yi la'akari da maganarsa ta karshe, wai ya gaishe masa da ALH. BABBA. Mahaifinsa shi suke kira da Alh Babba, idan haka ne akwai alakar, ta ina? Waye Abubakar ibn khaddab? Yaushe ya kira lambarsa? Tambayoyin da suka damu kansa ke nan. Suka hautsina masa tunani ya rasa sukuni sat! Washegarin ma bai samu kadaicewa da Shuhuda a makaranta ba, ana tashi ya neme ta ya rasa, ko motar da ake daukarta bai ga lokacin da ta tsaya har Shuhuda ta shiga ba, bayan tun kafin a tashi ya ke zubawa kofar ajin nasu idanu har ya soma hango dalibai na fitowa daga ajin suna tafiya bai ganota ba. Wannan dalili ne ya sa shi yanke shawarar zuwa gidan su Shuhudan. Kamar yadda ya shirya zuwa gidan nasu haka ya dauki hanya yana tafe cike da tunanin abin da zuwan nashi zai haifar. Yayin da ya isa gidan kafin ya tsaya a kofar gidan ya hango Yakub ya fito daga cikin gidan ga dukkan alamu wani guri za shi. Sai uncle hamza ya bishi yana yi masa hon, sai da suka koma can karshen lungun sannan Yakub ya tsaya, ya juyo yana duban uncle hamza da ke kokarin fitowa daga cikin mota. Don Allah ka yi hakuri, wallahi ban san dani kake ba. Uncle hamza yace: Kada ka damu ab yini lafiya? Yakub yace: Kalau, jiya ina ta magana bana jinka. Dif! Wuta ta daukewa uncle hamza ya rasa mai zai ce dashi. Yakub yace: Shi yasa nbake tunanin sauya layi saboda matsalar network da MTN suke fama da shi a kasar nan, kullum daga wannan matsala sai wannan matsala. Kwanakin ba ya ma don wukakanci da mutum ya saka kudi sai su wafce masa, suka 6illo da wani tsari Magic number na yaudara. Shi dai uncle hamza shiru kawai ya yi yana kallon Yakub da hakikance yana magana ba ya jinsa. Bayab shi yasan da ya kira lambar Yakub din ba shi ya samu ba, kuma ma ai kiransa aka yi bayan ya gama kira ba a dauka ba. Watakila gaskiyar Yakub din ne matsalar daga network ne, lambarshi ta shiga wayar wani daga kasar waje. Yakub ya yi murmushi, tukunna yace: Hala mutumiyar taka ka biyo? Don tace min kwana biyu ba ku gaisa ba. Murmushin karfin hali uncle hamza ya kirkiro yana shafa kasumbarshi yace: Hakika an yi haka. Yakub yace: Ai matsalar ba daga gare ta ba ne. Daga gida ne, an yi mata shamaki da kula saurayi, har sai ta kammala sakandire dinta don haka idan ka ga ba ta kulaka ba kada kaga laifinta. Ina sauri zamuje taron matasan unguwa da muke yi duk karshen wata. Sai ga ni na biyu. Mun gode da kaunar da ka nunawa tsatsonmu. Ya karashe maganar yana kokarin barin gurin. Uncle Hamza ya yi saurin zura hannayensa cikin aljihu ya fiddo kudi yana cewa: Ga wannan ka sha ruwa. Yakub ya tsaya yana duban uncle hamza tare da kudin sannan yace: Ayya na gode amma mu ba ma amfani da irin wadannan kudaden. Yana karashe fadar haka ya yi gaba abinsa. Mamakin uncle hamza ya sake hauhawa, sam bai gamsu da maganganun yakub ba, me yasa su ba su amfani da irin wadannan kudaden bayan kuma a kasar Nijeria suke rayuwa? Lokaci daya maganar Shuhuda ta dawo masa a rai, lokacin da ya bukaci sanin gidan su. " Gidan mu?.... Gidanmu da nisa.... Misra fa.... Akan wani keken doki nake zuwa.... Kullum fa na koma gida sai na suma, mamata ta yi ta kwara min ruwan sanyi, sannan nake farfadowa...." Idan ya tattara maganganun Shuhuda da kuma maganganun da suka gudana tsakaninsa da yakub sun isa su zame masa hujja na cewar yana mu'amala da ALJANU a matsayin MUTANE. Wani kunci da takaici suka lullu6e masa zuciya kawai ya rufawa kansa asiri ya rabu da lamarin Shuhuda ya sa wa kansa salama ya cire sonta daga ransa shine kawai abin da zai sama masa nutsuwa. Idan ba haka ba kuwa zai yiwa rayuwarsa BARA DA BANA, ma'ana ya hana zuciyarsa samun matar da zai rayu da ita akan son da yake wa Shuhuda, wanda a bayyane yake babu aure tsakanin jinsin mutane da aljannu. Ko da ma ace zai iya auren aljana, ma'ana an halasta aure a tsakanin jinsin bil'adama da jinsin jinnu, to ba zai auri Shuhuda ba. Tunda bai san manufar da ta ke so da shi ba. Bai san me ye shirinta na kulle zuciyarsa da sonta ba. a Hausa Book stories MATAUl HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤13¤¤ Abubuwa da dama sun faru wanda sai yanzu ya samu kakkarfar hujja da zai saka Shuhuda a jinsin jinnu. Alh sada, shi ma ya kasance daga jinsin jinnu, an rike shi ne don kawar da tunaninsa ya aminta shuhuda mutum ce don ya aure ta a kaddamar da shirin da aka shirya. Tana karatu a makarantar ne don an samu tabbacin zai shigo makarantar koyarwa. Ta ko'ina dai babu hanyar da za a layance masa yace Shuhuda mutum ce ba aljana ba! Idan an bar zuciya da tabo ba a yi mata magani ba. Lallai za a samu rudani. Komawa ubangiji a dukkan tsanani da rudani, ko ma jin dadi shi yake haifar da nagartacciyar rayuwa. A duba. ****** ****** ***** BABI NA SHIDA ANA ZATON WUTA A MAKERA...... Tun daga wannan rana uncle hamza bai kara shiga shirgin shuhuda ba, sam ya nuna kamar bai san da wanzuwarta a cikin makarantar ba. Ko aiki ya ba su ya ga ta yi kokari ba ya nuna ya damu bare ya yaba mata kamar yadda yake yi a da. Sai ma ya koma duk lokacin da zai shiga ajin nasu idanunsa rufe da bakin tabarau, wai duk don kada ta ga wallensa bare ta raina shi. Tunda ya gane aljana ce yta ke rayuwa acikin mutane. Shi ba zai iya tona mata asiri ba, haka kuma ba zai kulata ba. Idan ma tana tunanin zata cimma wani buri ne a gare shi, to ta sha karya, ba zata ta6a samun wannan damar ba. Idan ya tuna yadda ta dinga yi masa yawo da hankali, sai ya ji haushin kansa. Ai tuni ya kamata ace ya gane shuhudan aljana ce idan ba haka ba ta ya mutum zai ce bai san waye bil'adama ba, bai san shi wane irin jinsin halitta ba ne? Ai daga ji ma kasan wata kullalliya ce kawai ake kullawa. An murda an tufka murdaddun al'amura don jefa shi a cikin tarkon da ba zai iya fitar da kansa ba. To amma da yake shi Allah mai taimakon bawansa ne, duk da ratar dake tsakanin jinsin bil'adama da jinnu hakan bai hana yayewar yanar da aka dankara a idanuwansa ba. Ya gane ko wace ce ita. Wannan ma abin godiya ne ga Allah da ya ni'imta shi da wannan ni'ima, tunda har ya kare shi daga kaidin jinnu. Ya sani ba hikimarsa ko kwarewarsa da dabarunsa ba ne ya ku6utar da shi ba. Illa wata BAIWA da HIKIMA ta Ubangiji. Wannan hukunci da ya dauka ya dan rage masa zafin da yake hada wa kansa, yanzu sam ba ya irin wannan zaman na dogon tunanin ya ya lamarin shuhuda ya ke? Saboda yasan yadda aka yi masa alayen irin na mutan 6oye (Jinnu). To kuma ga shi an yi walkiya ya ga komai, saura da me? Tabbas dole ne ya samu nutsuwa, a da kam ya susuce komai ya kunce masa, ba shi da wani tunani sai na yadda al'amuran shuhuda suke har wani kira yake kwalwa ce ta yi mata yawa. Ashe ba kwalwa ba ce tsabar rainin hankali ne da yaudara irin na shiryayyen lamarin da bai san dalilin shiryuwarsa ba. WAYE UNCLE HAMZA? """""""""""""""""""""""""""""" HAMZA A. Babba shine asalin sunan nasa dan asalin jihar katsina a karamar hukumar Batsari. Mahaifina Alh Babba mai lakabin sunan Abdullahi sananne ne a fadin birnin katsina. Domin ma aikacin gwamnatin tarayyar birnin katsina ne. Ya rike mukamai da dama a ganiyar kuruciyarsa kafin daga bisani ya ajiye aiki saboda girma da ya kamashi. Matansa hudu na aure, ko wacce kuma ta hayayyafa da shi. A takaice dai mutum ne mai yawan iyali saboda yana koyi da sunnar ma'aiki. Yawan 'ya'yansa bai sa aka samu nakasu ga tarbiyyarsu ba, tsaye yake tsayin daka gurin kulawa da tarbiyyar yaran nasa. Hamza yayi karatunsa na firamare a nan cikin kauyensu karare da ke cikin karamar hukumar Batsari. Da ya gama ya tafi Technical Mashi, inda ya fito da takardu masu kyau, bugun farko na Jamb dinsa ya samu 258point. Don haka bai samu matsala ba lokacin da ya nemi gurbin karatu a A.B.U ZARIA. Tunda hamza ya fara karatunsa ba shi da wata matsala har ya kammala lokacin da ya dawo gida yana hutun jiran aiki. Akawai wata yarinya zuwairiyyah diyar kanin mahaifinsa da ta so shi tun can baya, to amma sai aka samu akasi, zuwairiyya irin shagwa6a66un yaran nan ne, ba ta iya komai ba ga ta katuwar bagidajiya irin dai yaran nan da ake cewa: GIRMA YA RIGA WAYO. Hakan ne ma ya sa koda ya nunawa mahaifinsa rashin amincewarsa ga lamarin ba su zafafafa ba, amma daya daga cikin kannen mahaifinsa mai suna Binta ta zafafa abin, wai ita don me zuwairiyya zata ce tana son hamza zai ce ba ya sonta. Kuma a biye masa? Wannan salon gur6ata zumunci ne. Rigima aka yi sosai, dama can hamza ba ya shiri da Gwaggo binta, wata irin masifaffiyar mace ce, haka nan ta bushi iska ta zo gidan ma ta yi ta ruwan masifa. Da yake Alh Babba mutum ne mai tsananin hakuri da son zumunci ba ya damuwa da halayyar 'yar uwarsa. Ba ma ita kadai ba duk cikin sauran 'yan uwansa shi daban yake bai dauki rayuwa da zafi ba. Duk hutun da hamza yake dawowa yana zuwa gaishe da dangin mahaifinsa amma ba ya zuwa gidan Gwaggo binta saboda muguwar tsanar da ta yi masa tun yana yaro, har cewa take wai hamza kamar musaya aka yi aka ba wa Alh Babba shi, amma sam bai yi shige da tsatson gidansu ba. Idan 'ya'yanta sun zo gidan, misali ace an yi katari lokacin hamza ya zo hutu ba ya kula su. Saboda yaran sam ba su da kunya wannan ya sake hura wutar kiyayyar Gwaggo binta da hamza. A lokacin da yake aji uku a sakandire dinsa wani zuwa ziyarar dalibai da mahaifinsa ya je yake sanar masa dan Goggo Binta ya rasu, ko a kwalar rigarsa bai damu ba. Don haka da ya dawo hutun ma bai je yi mata gaisuwa ba. Ana haka kuma auren Goggo binta ya mutu, tace: zata dawo gidan Alh BABBA kin amincewa ya yi. Don yasan zama da Binta tashin hankali ne ba karami ba. Sai dai gidan wani dan'uwan ta koma. Ta yi zaman zawarci na shekaru hudu sannan ta yi aure. A lokacin hamza ya tafi ZARIA. Shi ma auren ba wani dadewa ta yi ba ta fito saboda rashin hakuri da munanan halayenta ba kowane namiji ne zai iya zama da irinsu Binta ba. Ta koma zaman zawarci har hamza ya gamo karatunsa ya dawo ya fara aiki a nan cikin jahar katsina. A wata makaranta MARIAMA AJURI MEMORIAL SCHOOOL Goggon tasa ba ta yi aure ba. Albashinsa na farko da na biyu zuwa na uku ya sayi tamfatsetsen filoti a nan cikin katsina unguwar kanada. Tafiya ta tafi ya gina gidansa ya sayi mota sai kuma maganar zuwairiyya ta kuma danno kai don har lokacin ba tayi aure ba. A wannan karon an so fin karfinsa, to amma sai ya roki alfarma a makarantar da yake koyarwa a mayar da shi wani reshen, tunda makarantar ta kafu tana da rassa da dama a garuruwa daban-daban. Yayi wannan hikimar ne don ya yiwa su zuwairiyya nisan zango. Idan aka ga ba ya kusa an gaji a bata wani mijin ta yi aure. Da farko za6i aka ba shi cikin Kaduna, Jos da kuma Bauchi. Ya duba duk cikin wadannan garuruwan babu wanda ya kwanta masa a rai, ya dauki lokaci yana tunanin garin da zai za6a. Kwatsam aka ce an turo shi Kano dama suna bukatar karin malamai. Ya yi farin ciki da hakan ko ba komai kano gari ne na cibiyar kasuwanci idan yaje kanon zai iya samun wani kasuwancin da zai yi ko ya saka hannun jari a wani kamfanin. Hakan ko akayi, yana zuwa birnin kano ya fara aiki, a hankali kuma ya fada harkar kasuwanci ya ba wa wani abokinsa kudi masu yawa yana yi musu kasuwanci a nan kasuwar kwari. A kuma makarantar ne ya hadu da ALJANA! Kamar yadda ya kira SHUHUDA. WANNAN KE NAN!!! ****** ****** ***** Rashin kulawar da uncle hamza ba ya yiwa Shuhuda ya sama masa nutsuwa na gajeran lokaci ne kawai. Domin lokacin da su shuhuda suka shiga aji shida suna gab da soma jarabawa tsumin abin nan ya taso masa haikan. Ya dinga jin a duniya babu macen da yake son ya aura sama da Shuhuda. Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta. Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu). To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa. Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba. Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba. Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda. Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta. Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu). To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa. Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba. Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba. Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda. Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Zuciyarsa ta jagule, yana son furtawa yana tsoron abin da zai biyo baya. Shin zai amince ya sake saka rayuwarsa a tarkon aljana? So wani irin makahon abu ne, duhu ne da shi wanda yake makantar da zuciya gami da idanu tsinkaye da tarin kalubale. Idan haka ne so ya taka muhimmin rawa ga uncle hamza tunda ya hana ganin duhun son da zai fada. Cikin rashin walwala ya mike tsaye ya shiga bandaki ya yi wanka, sannan ya dawo falon, ya dauki wayarsa yaga yana da kiran da aka rasa(missed call) guda sha uku, ya duba duk lamba daya ne aka kirashi da ita. Kuma babu suna ma'ana bakuwar lamba (New number) ce. Sannan yana da rubutaccen sako guda biyu baki wanda bai karanta ba. Ya buda daya daga ciki ya soma karantawa kamar haka:- " Wata rana mai dumbin tarihi wadda ta kasance LITININ an yi kullaliya mai kulle kwalwa da tunani. Ranar litinin an rasa an kuma samu . Ranar litinin anyi katari da wani shamaki, bayan wasu al'amura masu murdiya da murde kwalwa. Shin mai yasa wannan rana ta kafu da murdaddun abubuwa? Tambayar ke nan!" kuma a zahiri karshen sakon ke nan. Yanayin uncle hamza ya bayyanar da matsananciyar damuwa, rudani gami da razana. Bai san ina sakon ya sa a gaba ba, bai san wanda ya turo sakon ba, bai san me yasa aka turo sakon gare shi ba...... Da sauri ya buda dayan sakon don karasa tantance abin rudanin , shin shi aka aikowa ko kuwa dai halin network ne kamar yadda ya dauki lambar Najeriya ya kaita Misra? " Rayuka cikin kunci ba karamin tashin hankali ba ne, ace dan Adam ya rayu a gurbin da ba wanda ya sani anbin a tausaya masa ne. Shi yasa ta ke ba ni tausayi, nakan ji alhini game da lamarinta. Amma babu komai akwai Allah, shi ne maganin komai. Amma zaluncin ya yi yawa....." Iya rudewa uncle hamza ya shiga, ya rasa ma yadda zai fassara wannan cukurkudadden al'amari, hakika ko tantama babu halin network ne. Amma saboda ya fita daga wasu-wasin da yake ciki, sai ya kira lambar. a Hausa Book stories MATAUl HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤13¤¤ Abubuwa da dama sun faru wanda sai yanzu ya samu kakkarfar hujja da zai saka Shuhuda a jinsin jinnu. Alh sada, shi ma ya kasance daga jinsin jinnu, an rike shi ne don kawar da tunaninsa ya aminta shuhuda mutum ce don ya aure ta a kaddamar da shirin da aka shirya. Tana karatu a makarantar ne don an samu tabbacin zai shigo makarantar koyarwa. Ta ko'ina dai babu hanyar da za a layance masa yace Shuhuda mutum ce ba aljana ba! Idan an bar zuciya da tabo ba a yi mata magani ba. Lallai za a samu rudani. Komawa ubangiji a dukkan tsanani da rudani, ko ma jin dadi shi yake haifar da nagartacciyar rayuwa. A duba. ****** ****** ***** BABI NA SHIDA ANA ZATON WUTA A MAKERA...... Tun daga wannan rana uncle hamza bai kara shiga shirgin shuhuda ba, sam ya nuna kamar bai san da wanzuwarta a cikin makarantar ba. Ko aiki ya ba su ya ga ta yi kokari ba ya nuna ya damu bare ya yaba mata kamar yadda yake yi a da. Sai ma ya koma duk lokacin da zai shiga ajin nasu idanunsa rufe da bakin tabarau, wai duk don kada ta ga wallensa bare ta raina shi. Tunda ya gane aljana ce yta ke rayuwa acikin mutane. Shi ba zai iya tona mata asiri ba, haka kuma ba zai kulata ba. Idan ma tana tunanin zata cimma wani buri ne a gare shi, to ta sha karya, ba zata ta6a samun wannan damar ba. Idan ya tuna yadda ta dinga yi masa yawo da hankali, sai ya ji haushin kansa. Ai tuni ya kamata ace ya gane shuhudan aljana ce idan ba haka ba ta ya mutum zai ce bai san waye bil'adama ba, bai san shi wane irin jinsin halitta ba ne? Ai daga ji ma kasan wata kullalliya ce kawai ake kullawa. An murda an tufka murdaddun al'amura don jefa shi a cikin tarkon da ba zai iya fitar da kansa ba. To amma da yake shi Allah mai taimakon bawansa ne, duk da ratar dake tsakanin jinsin bil'adama da jinnu hakan bai hana yayewar yanar da aka dankara a idanuwansa ba. Ya gane ko wace ce ita. Wannan ma abin godiya ne ga Allah da ya ni'imta shi da wannan ni'ima, tunda har ya kare shi daga kaidin jinnu. Ya sani ba hikimarsa ko kwarewarsa da dabarunsa ba ne ya ku6utar da shi ba. Illa wata BAIWA da HIKIMA ta Ubangiji. Wannan hukunci da ya dauka ya dan rage masa zafin da yake hada wa kansa, yanzu sam ba ya irin wannan zaman na dogon tunanin ya ya lamarin shuhuda ya ke? Saboda yasan yadda aka yi masa alayen irin na mutan 6oye (Jinnu). To kuma ga shi an yi walkiya ya ga komai, saura da me? Tabbas dole ne ya samu nutsuwa, a da kam ya susuce komai ya kunce masa, ba shi da wani tunani sai na yadda al'amuran shuhuda suke har wani kira yake kwalwa ce ta yi mata yawa. Ashe ba kwalwa ba ce tsabar rainin hankali ne da yaudara irin na shiryayyen lamarin da bai san dalilin shiryuwarsa ba. WAYE UNCLE HAMZA? """""""""""""""""""""""""""""" HAMZA A. Babba shine asalin sunan nasa dan asalin jihar katsina a karamar hukumar Batsari. Mahaifina Alh Babba mai lakabin sunan Abdullahi sananne ne a fadin birnin katsina. Domin ma aikacin gwamnatin tarayyar birnin katsina ne. Ya rike mukamai da dama a ganiyar kuruciyarsa kafin daga bisani ya ajiye aiki saboda girma da ya kamashi. Matansa hudu na aure, ko wacce kuma ta hayayyafa da shi. A takaice dai mutum ne mai yawan iyali saboda yana koyi da sunnar ma'aiki. Yawan 'ya'yansa bai sa aka samu nakasu ga tarbiyyarsu ba, tsaye yake tsayin daka gurin kulawa da tarbiyyar yaran nasa. Hamza yayi karatunsa na firamare a nan cikin kauyensu karare da ke cikin karamar hukumar Batsari. Da ya gama ya tafi Technical Mashi, inda ya fito da takardu masu kyau, bugun farko na Jamb dinsa ya samu 258point. Don haka bai samu matsala ba lokacin da ya nemi gurbin karatu a A.B.U ZARIA. Tunda hamza ya fara karatunsa ba shi da wata matsala har ya kammala lokacin da ya dawo gida yana hutun jiran aiki. Akawai wata yarinya zuwairiyyah diyar kanin mahaifinsa da ta so shi tun can baya, to amma sai aka samu akasi, zuwairiyya irin shagwa6a66un yaran nan ne, ba ta iya komai ba ga ta katuwar bagidajiya irin dai yaran nan da ake cewa: GIRMA YA RIGA WAYO. Hakan ne ma ya sa koda ya nunawa mahaifinsa rashin amincewarsa ga lamarin ba su zafafafa ba, amma daya daga cikin kannen mahaifinsa mai suna Binta ta zafafa abin, wai ita don me zuwairiyya zata ce tana son hamza zai ce ba ya sonta. Kuma a biye masa? Wannan salon gur6ata zumunci ne. Rigima aka yi sosai, dama can hamza ba ya shiri da Gwaggo binta, wata irin masifaffiyar mace ce, haka nan ta bushi iska ta zo gidan ma ta yi ta ruwan masifa. Da yake Alh Babba mutum ne mai tsananin hakuri da son zumunci ba ya damuwa da halayyar 'yar uwarsa. Ba ma ita kadai ba duk cikin sauran 'yan uwansa shi daban yake bai dauki rayuwa da zafi ba. Duk hutun da hamza yake dawowa yana zuwa gaishe da dangin mahaifinsa amma ba ya zuwa gidan Gwaggo binta saboda muguwar tsanar da ta yi masa tun yana yaro, har cewa take wai hamza kamar musaya aka yi aka ba wa Alh Babba shi, amma sam bai yi shige da tsatson gidansu ba. Idan 'ya'yanta sun zo gidan, misali ace an yi katari lokacin hamza ya zo hutu ba ya kula su. Saboda yaran sam ba su da kunya wannan ya sake hura wutar kiyayyar Gwaggo binta da hamza. A lokacin da yake aji uku a sakandire dinsa wani zuwa ziyarar dalibai da mahaifinsa ya je yake sanar masa dan Goggo Binta ya rasu, ko a kwalar rigarsa bai damu ba. Don haka da ya dawo hutun ma bai je yi mata gaisuwa ba. Ana haka kuma auren Goggo binta ya mutu, tace: zata dawo gidan Alh BABBA kin amincewa ya yi. Don yasan zama da Binta tashin hankali ne ba karami ba. Sai dai gidan wani dan'uwan ta koma. Ta yi zaman zawarci na shekaru hudu sannan ta yi aure. A lokacin hamza ya tafi ZARIA. Shi ma auren ba wani dadewa ta yi ba ta fito saboda rashin hakuri da munanan halayenta ba kowane namiji ne zai iya zama da irinsu Binta ba. Ta koma zaman zawarci har hamza ya gamo karatunsa ya dawo ya fara aiki a nan cikin jahar katsina. A wata makaranta MARIAMA AJURI MEMORIAL SCHOOOL Goggon tasa ba ta yi aure ba. Albashinsa na farko da na biyu zuwa na uku ya sayi tamfatsetsen filoti a nan cikin katsina unguwar kanada. Tafiya ta tafi ya gina gidansa ya sayi mota sai kuma maganar zuwairiyya ta kuma danno kai don har lokacin ba tayi aure ba. A wannan karon an so fin karfinsa, to amma sai ya roki alfarma a makarantar da yake koyarwa a mayar da shi wani reshen, tunda makarantar ta kafu tana da rassa da dama a garuruwa daban-daban. Yayi wannan hikimar ne don ya yiwa su zuwairiyya nisan zango. Idan aka ga ba ya kusa an gaji a bata wani mijin ta yi aure. Da farko za6i aka ba shi cikin Kaduna, Jos da kuma Bauchi. Ya duba duk cikin wadannan garuruwan babu wanda ya kwanta masa a rai, ya dauki lokaci yana tunanin garin da zai za6a. Kwatsam aka ce an turo shi Kano dama suna bukatar karin malamai. Ya yi farin ciki da hakan ko ba komai kano gari ne na cibiyar kasuwanci idan yaje kanon zai iya samun wani kasuwancin da zai yi ko ya saka hannun jari a wani kamfanin. Hakan ko akayi, yana zuwa birnin kano ya fara aiki, a hankali kuma ya fada harkar kasuwanci ya ba wa wani abokinsa kudi masu yawa yana yi musu kasuwanci a nan kasuwar kwari. A kuma makarantar ne ya hadu da ALJANA! Kamar yadda ya kira SHUHUDA. WANNAN KE NAN!!! ****** ****** ***** Rashin kulawar da uncle hamza ba ya yiwa Shuhuda ya sama masa nutsuwa na gajeran lokaci ne kawai. Domin lokacin da su shuhuda suka shiga aji shida suna gab da soma jarabawa tsumin abin nan ya taso masa haikan. Ya dinga jin a duniya babu macen da yake son ya aura sama da Shuhuda. Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta. Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu). To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa. Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba. Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba. Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda. Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Ta kowane 6angare jinta yake kainarta na yi masa yawa, duk kuwa da a lokacin ya fara tunanin ya komawa zuwairiyya. Saboda hakuri da juriyar jiran tsammanin da ta ke yi dominsa. Tunda har lokacin zuwairiyya ta ki aure ita a cewarta akwai ranar da mafarkinta zai zamo gaskiya. Wato ranar da hamza zai aure ta. Da farko an so takura mata sai ta tsiro da karatu, tace lallai sai tayi karatu mai zurfi tukunna za su yi aure, wai haka uncle hamza ya sanar da mata, don haka aka zuba mata na mujiya(idanu). To lokacin da uncle hamza ya daina kula shuhudan sai ya ji kamar ya komawa zuwairiyya saboda shi ma a lokacin Alh Babba ya soma korafin rashin aurensa. Allah ya sa bai yi saurin jefa kansa a ragaya ba sai kuma ga shi ya koma ruwa tsundum! Akan kaunar Shuhuda, yarinyar da yake da hujjojin kiranta Aljana. Wannan shi ne kwan-gaba-kwan baya, ma'ana yasan abu amma ya kasa aminta da sanin sa. Hujjoji dai sun bayyana a gare shi Shuhuda aljana ce, ba ita kadai ba duk wani wanda ya ra6eta shi ma jinnu ne, to amma kuma ya kasa amincewa kin yin mu'amala da ita. Mu'amalat ma irin wadda yake sa ran zata zamo uwar 'ya'yansa. Da zarar ya dora idonsa akanta wani irin abu ne yake ji yana fizgarsa, idan ya so sharewa sai ya ji idan ba tsura mata ido ya yi ba, ba zai samu sassauci ba. Don haka ba ya iya hassalawa kansa komai idan ba ya yi kokarin kawar da idonsa daga gare ta ba. Hasalima gaba daya gangar jikinsa yake ji ta yi masa nauyi, tamkar an daura masa gungumemen dutse, sai dai kuma ya kasa tunkararta, domin a duk lokacin da ya dauki damarar zuwa inda take da maganganun soyayya sai ya dinga jin faduwar gaba. Yanzu kam shuhuda ta gama rikita masa zuciya da kalbinsa, yanzu haka ma da yake zaune a falonsa, yana tunanin hanyar da zai soma bi domin sake bayyanar da soyayyarsa ga shuhuda. Uncle hamza ya sauke doguwar ajiyar zuciya. Ya sa hannu ya dauki hankici ya goge gumin da ya jike shi sharkaf Zuciyarsa ta jagule, yana son furtawa yana tsoron abin da zai biyo baya. Shin zai amince ya sake saka rayuwarsa a tarkon aljana? So wani irin makahon abu ne, duhu ne da shi wanda yake makantar da zuciya gami da idanu tsinkaye da tarin kalubale. Idan haka ne so ya taka muhimmin rawa ga uncle hamza tunda ya hana ganin duhun son da zai fada. Cikin rashin walwala ya mike tsaye ya shiga bandaki ya yi wanka, sannan ya dawo falon, ya dauki wayarsa yaga yana da kiran da aka rasa(missed call) guda sha uku, ya duba duk lamba daya ne aka kirashi da ita. Kuma babu suna ma'ana bakuwar lamba (New number) ce. Sannan yana da rubutaccen sako guda biyu baki wanda bai karanta ba. Ya buda daya daga ciki ya soma karantawa kamar haka:- " Wata rana mai dumbin tarihi wadda ta kasance LITININ an yi kullaliya mai kulle kwalwa da tunani. Ranar litinin an rasa an kuma samu . Ranar litinin anyi katari da wani shamaki, bayan wasu al'amura masu murdiya da murde kwalwa. Shin mai yasa wannan rana ta kafu da murdaddun abubuwa? Tambayar ke nan!" kuma a zahiri karshen sakon ke nan. Yanayin uncle hamza ya bayyanar da matsananciyar damuwa, rudani gami da razana. Bai san ina sakon ya sa a gaba ba, bai san wanda ya turo sakon ba, bai san me yasa aka turo sakon gare shi ba...... Da sauri ya buda dayan sakon don karasa tantance abin rudanin , shin shi aka aikowa ko kuwa dai halin network ne kamar yadda ya dauki lambar Najeriya ya kaita Misra? " Rayuka cikin kunci ba karamin tashin hankali ba ne, ace dan Adam ya rayu a gurbin da ba wanda ya sani anbin a tausaya masa ne. Shi yasa ta ke ba ni tausayi, nakan ji alhini game da lamarinta. Amma babu komai akwai Allah, shi ne maganin komai. Amma zaluncin ya yi yawa....." Iya rudewa uncle hamza ya shiga, ya rasa ma yadda zai fassara wannan cukurkudadden al'amari, hakika ko tantama babu halin network ne. Amma saboda ya fita daga wasu-wasin da yake ciki, sai ya kira lambar. da Hausa Book stories MATA UL hAYAT ¤¤14¤¤ Bugu daya kuwa ta shiga amma har sai da ta gama ringin ba a daga ba, ya sake kira a karo na biyu shi ma ba a dauka ba. Kamar ya share, sai da aka dauki tsawon lokaci sannan ya sake kira. A wannan karon an dauka, muryar mace ce ya ji: kuma kamar ya ta6a jin muryar. Bayan ta gaishe shi yace: Yauwa don Allah wa ke magana? Cike da tsananin mamaki aka amsa masa. Wake magana fa ka ce? Amma wallahi Yah hamza ban san me ka dauke ni ba. Wai don Allah me ye aibuna da ba ka damu da ni ba? Ya ji tsau! A dukkan sassan jikinsa, idan dai idanunsa biyu ne yana a farke to zai iya cankar sunan wadda ke magana, amman ta yaya hakan ta faru? Ko dai mafarki ne? Da ta ji ya yi shiru bai tanka ba, sai ta ci gaba da cewa: Ace wai ko arzikin ajiye lambata a wayarka ba ni da shi a gurinka? Haba don Allah, aiko ba ka so ni don kyauna ba, ka so ni don arzikin alakar da ke tsakanin mu ta 'YAN UWANTAKA. Idan ba ka so ni don haka ba, ka so ni ko don saboda shekarun da na share ina jiranka. Ka dai san ba rasa samari na yi ba, amma na jure ina zaman jiranka, karshe sai ka saka min da haka? Har yanzu bai tanka ba, har sai da ta dure da maganganun nata ta kuma sanya masa kuka, sannan ya samu karfin gwiwar cewa: Na ji dai na kukan ki nutsu ki min bayanin wadannan sakonnin naki, don kwata-kwata ban fahimci inda kika dosa ba. Ta tsagaita da kukan tana cewa:: Kawai na turo maka ne ganin cewa ba ka damu da ni ba, ka manta da babina a rayuwarka, ko dan kiran da kake yi min a da muna gaisawa yanzu sam ka daina. Yace: To layin waye wannan? Tace: Wai da gaske da ba kada lambata din ke nan? Shi kansa sai yaji ba dadi kuma ta ya aka yi ya rasa lambarta a wayarsa bayan yasan yana da ita? Bai sani ba! Don haka sai yace mata : Wayar ce ta samu matsala shi ne cire layin na saka a wata wayar. Lambar ki tana a cikin waccan wayar, don a waya (phone) nake ajiye lambobi. Sai ta dan washe kadan tace: Sai ta dan washe kadan tace: Shi ke nan, amma don Allah Yah hamza ka daina yi min abin da kake min, ka tuna irin dumbin son da nake maka...... Ya katse ta, kada ki damu..... Ita ma ta katse shi, Ya zaka ce kada na damu bayan kai baka damu da ni ba? Yace: Duk da haka, ai nace kada ki damu ko? Ki bari karshen watan nan zan zo, tunda 'yan jarrabawa sun kusa kammalawa. Tace: Shike nan Yah hamza sai ka zo. Ya kashe wayar yana kallon fuskar wayar(screen). Zabura ya yi ya mike tsaye sakamakon sunan ZUWAIRY da ke yawo akan madubin wayar, lambar da ya kira ce ta koma haka. Ko kuwa dai bai sani ba hannunsa ya lulubo lambar zuwairiyya har ya kirata. Sai ya shiga neman lambar har kundin ajiyar rubutaccen sako(inbox) sai da ya shiga, amma dai sunan ZUWAIRY ya gani dauke da wannan sako. To ya haka? A da yana zargin shuhuda ce aljana to yanzu ma ya dora alamar tambaya ga Zuwairiyya, domin yadda al'amuran suka faru ba su da maraba da aikin jinnu, ko kuwa shine ma aljanin bai sani ba? Ya shiga tuhumar kansa. Cikin kwana biyu uncle hamza ya rame, ya susuce saboda tsananin damuwa da tunani da ya sakawa kansa. Sam ba ya cikin nutsuwarsa, ko abinci ba sosai yake ci ba. Illa kayan gwangwani ko na kwali. Hatta abokinsa zaharaddeen Lawan ya fahimci halin da yake ciki. Sai dai ko da ya tambaye shi amsar da ya ba shi ita ce. " Ba ni cikin nutsuwa, ban san kuma yadda zan kwatanta damuwata ba". Don haka zaharaddeen ya tsura masa idanu, dama yasan hamza mutum ne mai zurfin ciki, sai ka ce bafulatani. An fito daga jarrabawar Biology, daliban ilimin kimiyya(science) sun taru a lab. Saboda malamin Biology yace za su yi hotuna, tunda wannan shine karo na karshe na shigarsu lab din Biology. Uncle hamza yana daga cikin malaman da suka tsaya kai da fata gurin gudanar da jarrabawar, don haka shi ma yana cikin jerin malaman da suka nufo lab din daukar hotunan. An shirya kowa aka soma dauka, kowane dalibi cike yake da farin ciki, suna ganin darajarsu ga malamai, tunda har suka bukaci yin hotuna da su. A 6angaren uncle hamza zan iya cewa ya fi kowa farin cikin daukar wadannan hotuna ko ba komai akwai HASKEN ZUCIYARSA a ciki. Tunda dama yana son mallakar hotonta, amma ya rasa ta ina zai fara, sai ga dama ta zo masa, don haka cikin doki ya kosa a dauki hotunan, wanda ya tsaya a bayan Shuhuda yana murmushi. Bayan an gama daukan hotunan bai samu yin magana da shuhuda ba, sakamakon aikin hada takardun da ya tsare shi. Lokacin da ya samu sarari sai nemanta ruwa a jallo bai gan ta ba. Yana da tabbacin tuni ta dade da komawa gida. Don wannan al'adarta ce, tun ma kafin soma jarrabawar da zarar an tashi ba ta tsayawa jinkirin komai ta ke tafiya, to dama ita ba kawaye ba bare ace sun tsare ta. Yayi takaitaccen murmushi, tare da lasar busassun la66ansa tukunna ya wuce izuwa mota. Ko a cikin motar ma kafin ya tafi ya dauki wani lokaci yana jin dadin daukar hoton. Wannan dama ce da zai yi amfani da ita gurin kwantarwa da Alh Babba hankali, zai nuna masa hoton shuhuda a matsayin matar da zai aura. Inyaso an shafa masa lafiya akan zuwairiyyah, tun da shi dai Allah bai saka masa sonta ko kadan a cikin ruhinsa ba. Shi kuwa ingancin zaman aure yana ta'allaka ne da ingantacciyar kauna. Da zarar aka ce anyi aure daya ba ya so, dayan ma musamman namiji to kuwa za a yi katari da abubuwa marasa dadi, to bare kuma shi da zuwairiyya wanda akwai karfaffen zumunci a tsakaninsu. Da wannan tunani ya tayar da motar ya nufi gida. Washegari aka wanko hotunan, a ranar kuma bau jarabawa, Mr philips ya kira shi a waya ya sanar masa an wanko hotunan. Don dama tunda aka gama dauka yace a wanko masa duk wanda shuhuda ta ke ciki. Har Mr. Philips yana dariya yana cewa: " ko dai ita ce Lobi din ne?" ¤¤¤ . A lokacin da wayar ta same shi yana kauwar kwari inda zaharaddeen yake gudanar da kasuwancinsu, kaya ne aka kawo daga MALAYSIA, don sun jefa hannun jarinsu da wani kamfanin Material da ke Malaysia shi yasa suke kawo musu kaya akai-akai. Babu laifi kuma wannan ya kara janyo musu daukaka, don ba karamin abin mamaki ba ne daga fara kasuwancinsu a kasuwar kwari duka-duka shekaru biyu da watanni, amma suin shahara irin haka. Wanda ga wadanda suka share shekaru aru-aru amma ba su yi irin wannan shaharar ba. To shi da ma kasuwanci ribarsa saukaka abu, da zarar mutum ya yi hakuri da riba kadan, sai ya tarar da tarin alkhairai. Amma muddin za a tsauwala to kuwa akwai ragee kwarjini da kuma dakusar da kasuwancin. ( Don Allah 'yan kasuwa mu duba wannan lamari, barin ma idan Sallah ta zo ko Maulidi sai ka ga an dauki dogon buri an dora a lokacin. Wanda babu wanda ake cuta sai talaka. Shi kuwa talaka abin tausayi ne akan komai na rayuwarsa). Zaharaddeen ya dago kai ya dube shi da yaga ya mike tsaye yace: Ina kuma zaka je? Uncle hamza ya juyo da kansa yana dubansa, yace: Zan je na dawo ne, ba dadewa zan yi ba. Yana karashe fadar haka bai jira amsar zaharaddeen ba ya sa kai. Sauri-sauri, gudu-gudu har ya isa inda ya ajiye motarsa ya shiga ya tayar da ita. Nan da nan ya isa gidan hoton Mr. Philips, suka gaisa, mr philips yana dariya ya dauko hotunan yana cewa: Gaskiya yarinyar nan tana da kyau duba ka ga yadda tayi kyau a dukkan hotunan nan, duk fa ta fi kowa yin kyau. Cikin harshen turanci yake maganar uncle hamza ya kai hannu ya kar6a. Idanunsa suka kai ga abin al'ajab! Tashin hankali aka ce wanda ba a saka masa rana. Ya gigice ya kuma razane duk a sanadin abin da ya gani a jikin hoton. Maimakon ganin shuhuda sai ya ga taswirar zuwairiyya. Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤15¤¤ Mr. Philips ya dube shi cike da tsananin mamakin yanayin da ya gani a tare da hamza, yace: Lafiya? Uncle hamza sam wuta ta dauke masa. Abin da yake damunsa shine: ta ya aka yi zuwairiyya ta shigo a cikin hotunannan da suka dauka a makaranta? Ina inuwar shuhuda ta shiga a cikin hotunan da bai ganta ba? Shuhuda ce ta yi wannan kullalliyar tunda ta kasance aljana. Su kuwa jinnu sukan yi fiye da hakan! Abin da zuciyarsa ta ayyana masa ke nan. Bai san yadda zai yiwa Mr. Philips bayani ya gamsu ba, don haka sai wayancewa ya yi da yin murmushi yace: Kyawun da ta yi ne ya firgita ni. Mr. Philips ya dan daki kafadarsa yace: Kai mutumina zaka fa more idan ka mallaki wannan zukekiyar yarinyar. Murmushi kawai uncle hamza ya yi ya dauko kudinsa ya bashi, tukunna ya masa bankwana ya tafi. Travelling bag dinsa ya saka hotunan bai kuma bin ta kansu ba. Haka bai kuma bi ta kan shuhuda ba, don ko da suka dawo yin jarrabawa yana kallonta amma ba ya kulata. Wannan yana daga cikin matakan da ya dauka na kauracewa abin da zai saka shi da-na-sani. Ranar asabar yana zaune a falonsa yana lissafa wasu kudi da zaharaddeen ya kawo masa na ribar da suka samu a wasu kaya da suka shigo dasu. Wayarsa ta yi kara, yana dubawa lambar yayansa Alh Mukhtar ya gani akai. Cikin girmamawa ya dauki wayar suka gaisa, Alh Mukhtar yace: Dama Abba ne ba shi da lafiya yana asibiti, sun ba shi gado shine na ce bara na sanar maka. Hankalin uncle hamza ya tashi, cikin rudani yace: Mai yake damunshi? Alh Mukhtar yace: Ciwon hanta ne, mu ba mu san yana da shi ba, wai ashe dama ya dade yana fama da shi yana zuwa ganin likita a 6oye. Uncle hamza yace: Allah ya ba shi lafiya, ina nan tafe anjima. Suka yi sallama ya tashi ya soma shiri. Karfe uku na yammaci ya isa birnin katsina, a gidansu ya fara sauka ya tarar da su Goggo binta duk suna gidan har zywairiyyah. Suka gaisa ya ajiye jakarsa ya nufi asibiti. Ya tarar jikin da sauki, don har ma ya samu bacci, saboda haka ya dawo gida. Ya tarar da tashin hankalin da ya hautsina masa kwalwa a lokacin da ya shigo gidan. Goggo binta ce rike da hotunansa da ya saka a jakarsa, tana kururuwa wai hamza zai janyo musu MUGUN IRI a zuri'a, tunda yake yawo da hotunan MAYYA a jakarsa! Zuwairiyya kuwa sai kuka take ana rarrashinta, tana kuma rusa ihu barin ma da ta ga uncle hamza ya shigo gidan. Cikin sanyin jiki da takaicin binciken da aka yi masa ya karasa ya kar6i hotunan ya ga ba ZUWAIRIYYA? to ya haka? Ko kuwa dama idanuwansa ne a wancan lokacin suka yi masa gizo, suka nuna zuwairiyya a maimakon shuhuda? Muryar Goggo binta ce ta katse masa tunani, inda ta ke cewa: Wallahi ita ce ta lashe MAS'UD, diyar fa KARIMA kishiyata ce, wadda ta yi sanadin mutuwar aurena! Yarinyar nan muhun iri ce, domin ta lashe ma wata mata daga ta tsarga yatsanta. Gadon mugun abu ta yi, kuma na tabbata tunda na ga hotunanta a tare da hamza shi ma so take ta lashe kurwarsa....... Haj Mardiyya ta katse surutun da cewa: Ya isa haka binta, ya kamata mutuna halin da muke ciki. Uncle hamza bai ce komai ba, ya saka hotunan a jakarsa ya fice zuwa dakin kaninsa salisu. Koda ya shiga dakin tunani ya sha masa kai, ya auna maganganun Goggo binta, sannan ya daura al'amuran da suka faru gare shi, shin da gaske mayyar ce? Ko kuwa aljana dai? A'a wata halitta ce daban! Ya rasa inda zai dorata a matsayi, mutum-mayya ko kuwa aljana-hatsabib iya? . ****** ******* ***** . BABI NA BAKWAI . . TSAUTSAYI KO KADDARA? . Daya ga watan satumba, wanda ya kasance ranar litinin jirgin Egypt air ya sauka a birnin Egypt bayan da ya taso daga senegal don sauke wasu fasinjoji(pasingers)kafin daga bisani ya yi hutun awa daya da rabi, sannan ya dage zuwa birnin kano. Kamar yadda yake a bayyane masu Transit visa wucewa zasu yi, idan jirgin nasu ya huta ba tare da ko airpot din sun fita ba. bare ganin yanayin gari, ko yin wasu mu'amaloli nasu abinsu. Da yawan mutanen da ke cikin jirgin dalibai ne, wadanda suka kammalo digiri dinsu a kasar senegal, wasu kuwa 'yan kasuwa ne da ke zuwa siyayya, don haka mafiya yawan mutanen ciki kabilu ne farare, dai-daiku ne bajkaken wadanda sauyin gari, cima, yanayi da kuma kwanciyar hankali ya sanya suka saje da fararen fatan, amma dai kana kallonsu kasan asalinsu bakar fata ne. Bayan jirgin ya sauka, fasinjoji suka soma saukowa, ISAH SADA RABI'U yana daya daga cikin masu saukowa daga jirgin. Amma shi zai shiga cikin gari ne saboda yana son ganawa da wani malaminsa da yake mazauni a kasar Misra, aiki ne ya jai shi can kasar senegal daga baya kuma ya dawo kasarsa ta haihuwa. To sun yi da Isah idan zai koma Nigeria zai biyo ta nan Misra, hikimar hakan gurin malamin mai suna Dr. Outhman Ibn Abdulfatah shi ne, yana so ya samawa Isah aiki a ma'aikatar karafa da ya bude ta kashin kansa mai suna KHAIR METAL, saboda tun yana koyarwa a makarantar ya aminta da kaifin kwalwa irin na Isah, ba duka dan Nigeria ne ake samunsa da yin karatu idan ya shallake kasarsa ba. Mafi yawancinsu sun fi mayar da hankali ne ga shashanci wajen kula mata da shaye-shaye, amma shi Isah ko kawance ba ya yi da mata, abin da ya kai shi kasar shi yake yi. Hakan kuwa ya kara masa kwarjini da cikar HAIBA a idanun malaman makarantar. Yana saukowar daga jirgi tafiya kadan ya yi ya isa inda ake bincike, aka gama yi masa duk wani bincike da ya kamata a yi masa a matsayinsa na bakon kasar. A lokacin ne kuma ya samu layin da ake amfani da shi a kasar ya kira layin Dr Outhman ya sanar da shi ya kammala komai shi kawai yake jira.: Bayan gama wayar akwai wani guri inda ake zama musamman don irinsa. Wadanda za a zo taryensu, ya zauna yana nazarin wani littafi SHOCK TREATMENT. Kamar an ce ya dago kansa, sai ya yi sai ya yi TOZALI da wata kyakkyawar mace, fara tas. Ma-abociyar cikar zati, idanuwanta narai-narai da kwalli radau a cikinsu. Tana cikin shiga ta bakar jallabia ta yafa gyalen rigar a kafadarta, sannan ta nade kanta da wani yalolon dan kwali, wanda ya kara fitowa da kyawunta a sarari. Kana ganinta kasan balarabita ce, amma bisa ga tsanin al'ajabi, kai tsaye gurin da yake zaune ta tukaro, kuma koda isowarta cikin harshen Hausa ta yi masa sallama, tun kafin ma ya amsa ta soma jero masa gaisuwa. Mamaki ya cika shi don bai yi tsammanin jin harshen Hausa a bakin wannan Balarabiyar da ke gabansa ba. Baya da haka kuma yana mamakin saukin kai irin nata wanda har ya sa ta zo inda yake ta gaishe shi ba tare da shi ya yi hakan ba a matsayinsa na namiji wanda ya ga mace yana so zai tunkara. Duk da ba ya mu'amala da mata, ya sha jin yadda aka tsayar da suke da girman kai musamman idan aka tsayar da su. To amma ita wannan mai sanyin hali ce, ko kuwa ita ma daga senegal din ta baro, sun yi tarayya a makaranta daya? Murmushi ya sakar mata cikin harshen Hausa yace: Kai duk ni kadai wannan gaisuwan? Ita ma murmushin ta yi masa, tukunna tace: Ai ka isa ne, gani na yi kamar na sanka, don Allah kai dan Najeriya ne, a birnin Kano ko? Bai yi mamaki ba, don ya sha jin ana cewa duk inda DAN KANO ya shiga ba ya 6uya, wata kila hakan ne ya sa ta canki wannan tambayar. (Ta6! Ai ba ma hakan bane. Ni dai ban yadda ba. In dai ba mayintan san kudi ba, kanawa ba su san komai ba, sai shirme. Da ma dai 'yan zaria ne sune suka fita zakka a fagen gogewa da komai. Lolx) Gira ya daga mata ba tare da ya yi magana ba. Tace; Haba, kofa naji, unguwar SALLARI ko? Yanzu kam ya sha mamaki, don jin ta ambaci sunan unguwar su kakansa, yana dubanta yace: Hala ke ma 'yar can unguwar ce a kano, kuma Najeriya? Ta girgiza kai tace: ....... . 1- Abubakar Ibn Khaddab 2- Shuhuda Ibn Khaddab 3- Yusuf Ibn Khaddab Uncle hamza ya hadu da Abubakar ibn khaddab. Isah kuma ya hadu da Shuhuda ibn khaddab To ni kuma bari na arce watakil nine zan hadu da Yusuf ibn khaddab. ada Hausa Book stories MATAUL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤16¤¤ Ta girgiza kai tace: A'a, Ai ni 'yar wannan kasar ta Misra ce, na dai sanka, ko ba kai ne YAYAN SHUHUDA SAGIR RABI'U ba? To yanzu fa mamakinsa ya kuma hau-hawa akan na dazun. Ya dube ta da kyau, yace: Kin ce ba a Najeriya kike ba, ya aka yi kika san garinmu, unguwarmu, dama kanwata? Tayi murmushi, sannan ta ce dashi. " Ai sunanmu daya da kanwarka, ni kuwa duk inda mai sunana ta ke sai nasan wace ce ita. Murmushi ya yi mata, saboda ya fahimci wasa ta ke, ita ma din 'yar Najeriya ce. Yace: Kina nufin ki ce min saboda sunanku daya dakanwata shi yasa kika santa, har kuma kika san ina da alaka da ita. Yadda duk inda kika ganni za ki iya shaida hakan? Ta daga masa kai cikin tabbatarwa, ita ma fuskarta dauke da murmushi. Yace: Ban yarda wannan zai zama karfaffiyar hujja ba, don haka kada ki wahalar da kanki gurin zolayata ta wannan hanyar, don ba ni kadai ba, duk wanda ya ji ma ba zai gasgata ba. Tace: Wallahi rantsuwar dan musulmi ke nan ko? Na sanka, na san kai kuma yayan Shuhuda ne, da Babanta mai rasuwa da Babanka mai rai uwa daya uba daya suke. Shi kam dariya ta ba shi matuka, yana daritar yace: Eh, ai ba cewa nayi ba ki sanni ba, na aminta kin san duk wadannan alakar da ke tsakanina da shuhuda, amma hujjar da kika bayar cewar saboda sunanku daya da shuhuda kanwata kika san haka ba mai kar6uwa ba ce. Idan ma har zata kar6un to cikin dayan biyu. Ko dai kin hadu da shuhuda ko wani da yake da alaka da tsatsonmu, ko kuma kacokam a kasarmu, jaharmu kuma unguwarmu kike. Idan ba ta wadannan hanyoyin ba bazan ta6a yarda da abin da zaki ce ba. Tace: Ni asalina 'yar wannan kasar ce, ban ta6a zuwa Najeriya ba, amma nasan kanwarka shuhuda sagir Rabi'u ta hanyar tsananin bincike da KAIFIYYA irin tawa...... Ba ma kanwarka kadai ba, a kasarku kuma jiharku, na san masu sunana SHUHUDA sama da trilliom, saboda haka kada ka yi mamaki. Ya jinjina kai alamar jinjinawa, yace: Lallai kam kina da kokari tunda har kika yi wannan bincike, amma dai duk da haka kin san wani abu? Ya nemi kawar da wancan zancen tunda ya lura 'yar barkwanci ce. Ta girgiza kai, tare da fadar: Sai ka fada. Yace: Kin burge ni, har na ji ina son mu-amala da ke. Ta yi murmushi, wanda ya bayyanar da siririyar wushiryarta, ba ta yi magana ba don haka ya ci gaba cewa. Da gaske sunanki shuhuda, kuma wannan kasar kike? Ta jinjina kai. Tabbas sunana Shuhuda Ibn Khaddab, mu uku ne gurin mahaifinmu, ni da 'yan uwana Abubakar da Yusufa, iyaye da kakanni dukkansu 'yan kasar nan ne, sai me bayan haka? Yana murmushi, yace: da ita: Lambar wayarki, da adireshin gidanku. Tace: Tabdijan, lambar waya? Yanayinsa ya nuna tuhuma, yace: Ban gane mamakin da kika yi ba? Tace: Eh, to ni da ba zama kasa daya nake yi ba, wace lamba zan baka idan ba so kake ka yi ta nemana ba ka samu ba? Yanzu ma fa kasar sudan zan je, kuma daga can wata kasar zan je? Yanayinsa ya sake nuna damuwa yace: Ke kam duk me ya janyo miki wannan yawo haka sai ka ce 'yar kasuwa? Ta yi dariya, tace: Haba dai? Ai duk yawona ban kai TANZIF ba, wanda yana iya zuwa kasa goma a kwana goma. Bare ni da idan na je kasa nakan samu kwana goma ban barta ba. Isah yace: Waye kuma TANZIF? Tace: Ba ka sanshi ba. Yace: To amsa min tambayata me kike zuwa yi kasashe? Tace: Yawanci ina zuwa majalisi ne na malamai. Sannan nakan ta6a kasuwanci. Ya jinjina kai. Cewa zaki yi Ustaziya ce? Don haka ma daga yau haka zan dinga kiranki USTAZIYA SHUHUDA. Ta duba agogon da ke daure hannunta tace: Ka ga har mun ci lokaci da yawa, sai nace sai gani na biyu ke nan? Ya yamutsa fuska yace: To idan kin ce sai gani na biyu ta ya zamu sake haduwa, ba ki bani adireshinki ba? Tace: Haka ne, amma....... yadda TSAUTSAYI ya hada mu yanzu, a gaba KADDARA zata hada mu. Yace: TSAUTSAYI KO KADDARA? Ban gane ba. Ta yi dariya wadda ga dukkan alamu dabi'arta ce, dariya ba ta mata wuya. Tace: Idan na ce TSAUTSAYI, ina nufin tsautsayin haduwarmu bayan kuma zamu dade ba mu sake haduwa ba, wata kila kuma har abada. Sannan idan na ce KADDARA ina nufin KADDARAR ALLAH ta hadamu sanadin mai sunana, idan na biyota har kasarta don........ Karar maganar da ke fita daga abin maganar da ke kafe a gurin ta soma bayar umarni ana neman wadanda zasu SUDAN don yin setting dinsu ta katse maganar da shuhuda ke yi. Tana dan hanzari tace da shi. SAI WATA RANA! Ya yi sauri yace: Dan tsaya na ba ki lambata........ Tace: A'a kada ka damu, sai ka jini. Ba ta jira abin da zai kuma fada ba, ta yi gaba ta barshi galala da baki cike da alhini, wannan yarinya da barkwanci ta ke. Lokaci daya ya ji wani nishadi na kwarara a zuciyarsa, tunda yake a rayuwarsa bai ta6a yin soyayya ba. Don haka ya kira abin da yake ji game da yarinyar SOYAYYA. ( Kai wannan gayen akwai shirme, yanzu dai naga ya nuna halin kanawa. Lolx) Farad daya maganarta ta fado masa a rai, wai haduwarsu tsautsayi, abin da kuwa zai sake hada su kaddarra, ke nan zata je Najeriya? Mhm! Lamarinta gaba dayansa na barkwanci ne, don haka zuciyarsa ba ta aminta ita din 'yar kasar Misra ba ce, ya fi kyautata zaton Najeriya ta ke, birnin kano, unguwar sallari tunda har tasan sirrin ALAKA da ke tsakaninsa da Shuhuda, kuma ta yi ikirarin a sanadin kaddarar sunan Shuhuda zata je Najeria unguwar Sallari wadda ta ke mu'amala da kanwarsa. Ba don haka ba, me ya hana ta kar6i lambar wayarsa tunda ita ba ta ba shi tata ba? Ai maganar ji ma daban ta ke, kawai dai ita irin mutanan ce masu barkwanci da zolayar wanda Allah ya hada su zama da su. Yana nan zaune Dr. Outhman Ibn Abdulfatah ya iso airpot din, ba su wani tsaya ba suka rangaya gidansa. Duk yadda Dr Outhman ya so da Isah domin ya tsaya ya yi masa aiki, ya tubere sai dai ya ce zai je Najeriya in yaso daga bisani idan mahaifansa sun aminta sai ya dawo. Kwanansa hudu, Dr. Outhman ya sake masa visa ta zuwa Najeriya bayan sun je babbar kasuwar garin wadda ita ce cibiyar kasuwar kasuwancin kasar, Isah ya duba zobe mai kyau na zallar azurfa ya sayawa shuhuda a cewarsa wannan zobe shi ne babbar tsarabar da zai ba ta, tunda kullum suka yi waya da ita ya tambaye ta abin da zai kawo mata tsaraba da shi, sai ta ce zobe. Wai ita a rayuwarta babu abin da yake burge ta irin zobe, shi yasa ta ke matukar son a yo mata tsaraba da shi. Burin Isah ya ganshi a birnin kano, ya ga yadda shuhuda ta koma. Yasan ta kara girma, kyau da komai ma, tunda lokacin da ya bar kasar tana yarinya. Yana zaune a kujerar jirgin max air ya tuna ranar da ya baro kasar shuhuda kuka ta ke kamar ranta zai fita, shi din ma har ya isa kasar senegal kukan yake. Ya yi murmushi, rayuwa ke nan, komai mai cewa ne ban da ikon Allah! Yau ga shi a cikin farin ciki saboda zai koma kasarsa ta haihuwa, zai koma cikin dangi, 'yan uwa, yarensa, addininsa gami da mu'amalolinsa da ya rasa su na tsayin wani lokaci, yau duk zai cike wannan gurbin da ya samu gi6insu. Karfe bakwai na dare jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu kano, babu 6ata lokacin fasinjoji suka soma saukowa. Alh sada, Alh Ahmad, Haj Asibi, Inna yaduwa da shuhuda su ne suka zo taryen Isah, saboda haka yana fitowa daga cikin jirgin da su ya soma tozali. Wani yalwataccen murmushi ya saki, yayin da shuhuda ta rugo da gudu ba zato ba tsammani Isah yaji ta rungumeshi. Wani irin tsau! Ya ji a gaba daya sassan jikinsa, tsikar jikinsa ta tashi, amma ya kasa cire ta daga jikin nasa, shi ma sai ya rungume ta tsam yana tuna tsananin shakuwarsu, yana tuna wannan rana da ta ki goguwa a idanunsa da ma zuciyarsa gaba daya, wato ranar tafiyarsa Senegal. Sai da suka dauki lokaci a haka, sannan Inna Yaduwa ta 6an6are shuhuda daga jikin Isah tana cew: Ke sakar min miji kada ki karya min shi. Bayan an gama duk abin da ya dace, kai tsaye gidan Inna yaduwa suka nufa don ta ce ita ce mai masaukin bako, shi ma dama gidan nata ya fi sha'awa tunda a nan ya yi rayuwarsa kafin tafiyarsa Senegal. BAYAN WATA UKU Har su Shuhuda suka kammala jarrabawarsu uncle hamza bai kulata ba, saboda a lokacin ya gama amanna ita din aljana ce, amma duk da haka ya kasa samun sukuni, kullum tunaninta ne ke nukurkusar zuciyarsa. Sai dai da yake shi din jarumin namiji ne haka ya daure yana ji yana gani har suka kammala jarrabawarsu suka bar makarantar. Wanda hakan ke nufin rabuwarsu ta har abada musamman wannan lokaci da abin al'ajabin ya faru. Lokacin da Goggo binta ta ce shuhuda mayya ce, wanda shi kuma ya karyata hakan ya fi alakantata da aljana, to tunda dama makarantar ce ta hada su yanzu kuma ta raba su. A 6angaren su shuhuda kuwa, shakuwar da aka ginata a 6angaren su shuhuda kuwa, shakuwa da aka ginata a wancan tubalin na aminta da kuma kuruciya an sabuntata ta dawo sabuwa dal! Don yanzu kam shakuwar da ke tsakanin shuhuda da Isah har ta zarta ta wancan lokacin. Kullum suna tare, hira suke yi yana ba ta labaran abubuwan da suka faru da shi a kasar senegal har tuhumarta ya yi ko tasan wata shuhuda ibn khaddab, amma tace ita sam ba tasan wata shuhuda ba, ita ba tama ta6a jin mai sunanta ba, don wani lokaci ma har tana tababan ingancin sunanta. To shi ma sai bai tsawaita bincike ba, don dama shi mutum ne mara son shiga harkar da ba tashi ba. Ana gama sallar isha'i ne yake shigowa dakin Inna yaduwa ya ci abinci tare da shuhuda, sannan ya zauna da su hira har sai karfe tara da rabi sannan yake yi musu addu'a ya ja musu kofa ya nufi 6angarensa. Wannan dabi'a ce da yake gudanarwa tun ranar da ya dawo, saboda haka babu wani guri da yake zuwa da daddare. A 6angaren maganar aikinsa kuwa Alh Rabi'u yace:o sam bai amince Isah ya koma wata kasa ba, shi ma ya tsaya ya amfanawa kasarsa, tunda ana bukatarsa. Bai damu ba, don tunda ya dawo ya dora idanunsa ga shuhuda sai ya ji sam baya bukatar abin da zai kuma janyo masa ya yi nisa da ita. Saboda haka aka soma nema masa aiki a kamfanoni da dama, duk da an yi tunanin bude masa kamfani na kashin kansa, to amma sai aka dakatar da wannan yunkuri saboda halin da ake ciki na karyewar tattalin arziki na al'umma. A haka har ya samu watanni uku da dawowa, izuwa wannan lokacin yana cikin wani hali wanda shi kansa ba zai iya kwatanta shi ba, domin dai ji yake kamar yana son ya auri shuhuda, kullum ta kawo masa abin karin kumallo ko na rana ko kuma idan suna hirar dare, wani irin nishadi yake ji na kwaranya masa. Idan ya gama yi musu hira ya koma dakinsa kafin bacci ya dauke shi, tunaninta ne ke bijiro masa ya dinga ganin kamar tana yi masa gizo. Da gaske babu tababa yana sonta, kuma yana son aurenta, amma ya kasa fada mata koda kuwa Inna yaduwa ya kasa fadawa, hatta da Alh Rabi'u wanda duk bayan, ya kasa 6usa masa maganar. Daga shi sai zuciyarsa, sai kuma Masanin halin da zukata ke ciki(Allah) BABI NA TAKWAS .......... RUWAN ZUMA Inna yaduwa tana zaune a falo ita da dattijon mijinta tana 6are masa gyada mai 6awo yana taunawa a bakinsa, shuhuda ta shigo falon cike da murna kira ta ke. Inna! Inna kina ina? Tayi tsalle ta haye kan cinyoyin kakar tata, yayin da Isah ya shigo shi ma fuskarsa dauke da fara'a. Inna yaduwa tana kokarin tureta daga jikinta, tace: Ke ni daga ni shagwa6a66iya kawai, zaki wani shigowa mutane gida ba ko sallama. Alh Rabi'u ya dubi Isah yace: Abokina ya dai na ga amaryar tawa tana murna tamkar ranar sallah? Isah yace: Wallahi Baba takardunta ne suka yi kyau shine ta ke ta murna, tun fa a mota ta ke ta wannan murnar. Gaba dayansu sai farin ciki ya kamasu. a Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤17¤¤ Alh. Rabi'u yace: Nima ba na shakka akan kwalwar amaryata, Allah ya sanya alkhairi. Shuhuda ta washe baki tace: Amin Baba. Ta ci gaba da zuba shagwa6ar farin ciki, Isah yana kallonta, yau hakurinsa ya kare, yana ganin rana ce da ya kamata ya yi amfani da ita ya sanar da shuhuda matsananciyar kaunar da yake mata. Ko ba komai ranar za ta zamo ta kafuwar tarihi masu dama a kundin rayuwarsa. Misali: Yau ranar ta kasance ta LITININ takardar shaidar tabbatuwar aikinsa da kamfanin NUEFI'A IRONIC METAL da ke jihar Ibadan ta same shi. Ranar LITININ shuhuda ta dubo jarrabawarta Waec da Neco duka ta cinye, tana A1 a wasu darussan B3 a wasu. Sannan ranar LITININ zata zamo cikin jerin abubuwan tarihi idan ya furta mata KALMAR SO. Shuhuda ce ta katse masa tunani lokacin da ta mike tsaye. Inna bara na yi wanka tukunna na ci abinci ko? Ba ta jira amsa ba ta nufi hanyar daki don sauya kayan wanka. Isah ya bita da kallo, tafiyarta ma dagwas-dagwas gwanin sha'awa. Shi ma sai yace: Bara na je daki na huta. Alh Rabi'u yace: Anjima idan an gama sallar magriba ka zo zan aike ka gurin mahaifinka ka kai masa wasu kaya da a ka kai masa aikin hannu. Isah yace: To. Sannan ya koma dakinsa yana ta kissima yadda zai tunkari shuhuda da bukatarsa ta soyayya, shin ko za ta amince ko ba zata amince ba? Karfe hudu da rabi na yammacin ranar ya tarar da shuhuda zaune akan farar kujerar roba tana sanye da dorawar shadda shar da ita, dinkin fitted, rigar ta matse ta sai dai ba yadda al'aurarta zata bayyana ba, sannan zani ce aka yi mata don haka kwalliyar tata dai babu makusa. Fuskarta narai-narai, har yanzu da akwai wannan murnar ta cinye jarabawa a tare da ita tana makale a fuskarta. Kafin ya karasa gare ta ya yi tsaye yana kallonta, lallai idan ya sami nasarar auren shuhuda ya dace da kyalkyawar mace, wadda zata haifa masa kyawawan 'ya'ya. Sannan kamilar mace ce idan aka yi la'akari da yanayin shigarta. Dubi dai yanzu yadda ta ci ado ta kame akan kujera, yadda kasan wata babbar mace ce ita, bayan duka-duka shekarunta sha takwas. Kamar an ce daga kai! Ta dago kanta saboda kamshin turaransa da ya buwaye ilahirin gurin, suka yi tozali da juna. Sai ta sakar masa murmushi. Ya tako a hankali ya ja kujera ya yiwa kansa mazauni, ta gayar da shi sai duk suka yi shiru shi da ita bayan gaisuwar, kanta na rusune a kasa yayin da shi kuma gaba daya ya dauki idanu ya daura mata. Shirun dai ya dauki 'yan mintoci kafin Isah ya katse musu shirun da yin gyaran murya yace: Shuhuda!. Ta dan dago kanta kadan tana satar kallonsa. Yace: Kin san me? Tayi shiru ba ta ba shi amsa ba. Ya ci gaba da cewa: Wata magana ce mai muhimmanci nake son mu yi da ke, amma ina bukatar ki tattaro hankalinki da nutsuwarki zuwa gare ni. Kuma ina son ki fadan gaskiyar abinda ke cikin ranki. Ba ta dai tanka ba, amma yanzu gaba daya ne ta ke kallonsa sa6anin dazun da kadan ta daga kai. Ya kuma saka nutsuwa a tare da shi sannan muryarsa kasa-kasa kamar ba ya son wani ya ji. Yace: Ko kin san me ye SO? Yanayinta gaba daya ya sauya, 6acin rai ya bayyana a fuskarta, ta yi shiru ba ta tanka ba, kuma ba ta dauke idonta akan kwayar idonsa ba. Ya lura ba tasan so ba, wata kila ma ba ta ta6a yin katari da wanda yace yana sonta ba. Shi kam hakan ya yi masa dadi sosai, saboda hakan zai ba shi damar kafa soyayyarsa a zuciyarta. Sai yayi murmushi mai kayatarwa ga wanda ya san sirrin murmushi, sannan yace da ita. So wata kwaya ce da ke kafuwa a zuciya ta sababin wasu abubuwa masu muhimmanci, na farko KYAU, Idan mace ko namiji na da kyau, yana iya haduwa da masu sonsa ta sanadin wannan kyawun da Allah ya yi masa baiwa da shi. ADDINI:- Idan mace ko namiji suna da addini ana iya sonsu saboda addinin da suke da shi. Ma'ana sun kasance masu yawan yin sallah akan lokacinta, kyautata addininsu da sauransu. NUTSUWA:- Ita ma tana kawo a so mutum saboda ita. KWARJINI:- Akwai mutanen da kwarjini ke sa a so su, ba don kyau ko addini ba, kwarjininsu zai sanya kawai idan aka gansu aji ana sonsu. ASALI:- Nagartaccen asali yana sa a so mutum saboda an san asalinsa, tun daga nasabarsa zuwa mu'amalolinsa. SHA'AWA:- Akwai mutanen da Allah ya yi su da raunin sha'awa, ma'ana idan za su ga mace ta yi shiga ko tafiya mai kyan tsari zasu kasance cikin sha'awar yin tarayya da ita, ba don asalin son ko kauna, illa sha'awar ce ta yi jagoranci. A mafi yawan mutanen da suke soyayya sha'awar ce ke yi musu jagoranci, shi yasa ake yawan samun ma....... Maganarsa ta katse sakamakon kwalla da ya gani shar a idanuwan shuhuda. Hankalinsa ya tashi, cikin rawar murya yace: Sh....u.....hu......da........? Ta rusunar da kanta kasa, ya matso kusa da ita cikin tausasawa yace: Me ye na kuka? Ki fada min maganganuna ne suka 6ata miki rai? Ta yi shiru tana shesshekar kuka, hankalinsa ya sake dagulewa, sai yake tunanin wata kila ta ta6a yin soyayyar, ko saurayin ya sota ne akan turbar SHA'AWA. Yanzu da yayi mata wadannan bayanan ta samu tabbacin sha'awar ce tsakaninta da shi. Ko kuma ta yi soyayya da wani saurayi da yakan zaunar da ita ya yi mata kwatankwacin wannan bayanai, daga bisani Allah ya yi masa rasuwa. Idan kuwa wannan zargin ya zama gaskiya, yana da yakinin ba karamar wahala zai sha ba kafin ya rushe wancan tubalin ya kafa nasa tubalin soyayyar ba. SO RUWAN ZUMA, dole ne sai ya yi amfani da sanyayyen kalamai masu nutsar da zuciya gurin kawar mata da tunanin duk wani da namiji a rayuwarta, saboda haka ya ciro hankici daga aljihun rigarsa da nufin goge mata hawayenta. Amma koda ya nufo fuskarta da nufin hakan, sai ta yi sauri ta kawar da kai gefe guda. Ya yi murmushi yace: To ki daina kukan idan ba kya son na goge miki hawayen. Ta sa hannu ta goge hawayen, yana kallon kanta don fuskarta na rusune, yace: Shuhuda ina sonki! Mikewa tsaye ta yi da sauri tana girgiza kai, muryarta na fitar da wani irin yanayi. Bana soyayya saboda hatsarinta a gare ni. Bata bari ya yi magana ba ta ci gaba da cewa: Bana soyayya saboda amsa tambaya, ita kuwa soyayya tana tafiya ne da amsa tambaya. Bana soyayya saboda ban cancanta da ita ba. Bana soyayya soyayya saboda ba zata sama min MATA'UL HAYAT ba, illa bankado da TASHIN HANKALI, wanda zai iya shafar duk wanda ya shafe ni. Wani hautsinannen kallo yake mata na tuhuma, amma ba ya son tuhumarta tunda ya ga akwai mikin tabon soyayyar wani a zuciyarta, hanyoyin kafuwar tashi soyayyar ita ce a gaban shi. Na ji, amma na tambayeki mana? Ta daga masa hannu. Na fada maka bana iya amsa tambaya, don ni kaina, ina da tambayoyin da zan yiwa kaina, to amma saboda wannan dalilin yasa na kan ajiye tambayoyina har zuwa ranar da zan samu MATA'UL HAYAT. To wannan fa nasan zan iya soyayya har na samu damar amsa tambayoyi, nawa da na wasu ma gaba daya. Ta daure masa kai matuka. Ya girgiza kansa, ya ce: Shike nan, ni kuma zan jiraci wannan rana domin nasan ni ma zan samu MATA'UL HAYAT idan har na samu rasarar auren ki....... Ta sake daga masa hannu. Yah Isah kada ka jefa rayuwarka a hatsari, kada ka yi gaggawar sanya SOYAYYA a tsakaninmu, domin tana da mayukar hatsari. Gargadi ne nake yi maka, ba shawara ko izina ba, idan ka ce zaka sanya soyayya a tsakaninmu hakan zai iya haifar da TASHIN HANKALI, RUDANI, TAKAICI da kuma NADAMA marar amfani. Tana kammala zancenta ta yi gaba yana kwala mata kira amma sam ta ki tsayawa. Ya dade zaune a gurin yana murmushi, yasan ba komai ne ke ta6a mata zuciya ba illa zafi da radadi ko na ganowa da ta yi, can baya ta yi soyayya da wani a tubalin sha'awa, ko kuma mutuwa ta gitta ta raba su. Wadannan kuwa ababe ne masu radadi. Ya mike tsaye ya nufi cikin gidan. Don tarar da shuhuda ya sanyayar mata da zuciya, sai dai yana shiga falon ya tarar da Inna yaduwa zaune akan kujera ya nufi dakin shuhuda. Ta sanya baki ta kira shi, ya dawo ya zauna a dayar kujerar tace: Kada ka shiga gurin shuhuda, domin kana shiga zaka sanya ta tayar da hankalin mutane. Haka ta tsiri wannan dabi'ar tun bayan kammala sakandiri dinta, da zarar an 6ata mata rai sai ta shige daki ta yi ta kuka. Ai ka gani abin da ya faru kwanaki ko? Don haka kyale ta, me ya faru ne a tsakaninku? Yace: Daga na ce ina sonta shine ta shiga wannan yanayin. Inna yaduwa tace: Kyale ja'ira kawai ci gaba da son nata, inshaa Allah idan rabonka ce zaka aure ta. Bayan an gama sallar magriba Isah bai samu komawa gida ba, saboda tun kafin su shiga sallah Alh Rabi'u ya ba shi sakon da zai kaiwa Alh sada(Mahaifinsa) ya saka a mota, saboda haka ana gama sallar kai tsaye can gidan mahaifin nasa ya nufa. '''''''''''' ''''''''''''' ''''''''''' '''''' Duk yadda ya so ya koma gida da wuri hakan ya ci tura, saboda kannesa da suka saka masa shagwa6a lallai sai ya zauna sun sha hira tunda tun bayan dawowarsa bai zauna da su ba. Dole ba don ya so ba ya zauna. Tun yana duba agogo yana tunanin i wannan lokacin yana tare da su shuhuda a dakinsu yana yi musu hira, har tara da rabi ta yi ya tuna dai-dai lokacin yake tofe musu dakinsu da addu'a ya koma dakinsa. Goma dai-dai ya kissima yanzu su shuhuda sun dade da yin bacci, saboda dama a daddafe ake yin hirar da ita zuwa karfe tara da rabi. Saboda haka sai ya sare, gwiyoyinsa suka yi sanyi, ya tabbatar ya yi rashin wannan daddadan hira da suke yi musamman ma da yake dokin ta yau zata fi kowacce hira armashi, tunda har ya samu damar furzar da abin da yake cikin ransa. Sam ba shi da niyyar tafiya, har sai da Hajiya Safiyya tace: Wai kai ba zaka yi harama ka koma gida ba? Ta dubi su Asma'u tace: Ku tashi ku je ku kwanta. Haka ya mike ya yi musu sallama ya hawo motarsa ya nufo gida. Lokacin da ya iso gida sha daya saura kwata. Kai tsaye 6angarensa ya shiga don yana da tabbacin sun dade da yin bacci. Bayan ya gama duk abubuwan da suka zamo al'adarsa misalin karfe sha biyu da mintina takwas bacci ya yi awon gaba da shi. ******* ******* ***** Shuhuda ina son! Nasan haka'' Shuhuda ina kaunarki. Na fi kowa sanin haka. Shuhuda tunanina ya zan yi da raina. Shine abin da ke nukurkusar min da zuciya, yake saka ni damuwa, amma kada ka damu mafita ta zo gare ka. Ta ya ya? Mikewa ta yi daga inda suka yi tsugunnon su duka biyun, ta soma taku yana kallonta hat ta isa inda garken kananun dabbobi suke, irin su kaji, Agwagwa, Talo-talo da tantabaru. Yana kallo ta zama ZAKANYA ta soma taune kananun dabbobi, yana so ya daga baki ya yi magana ya kasa, yana so ya yi amfani da kafafuwansa ya zura da gudu ya kasa. Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤18¤¤ Yana nan tsayen ta gama taune kananun dabbobin nan tas! Sannan ta koma halittar mutum, ta yi murmushi, tace: Yadda ka ga na taune dabbobin nan haka zan yiwa 'YA'YAN CIKINKA, HANTA, KODA da ma ZUCIYARKA. Wannan ita ce kadai mafita, idan ba haka ba babu wata mafita da zamu yi amfani da ita, mun riga mun yi SAKACI wanda 'yan magana ke cewa: TUN RAN GINI RAN ZANE! Firgigit Isah ya yi ya farka daga baccinsa mai kunshe da wannan hargitsattsen mafarki. Ya duba agogon da ke dakin, amma bai iya ganin komai ba, saboda duhun da ke da akwai. Sai da ya yi amfani da malatsin kunna fitila, sannan haske ya gauraye dakin. Karfe daya da mintina shidda, tabbas tun ran gini ran zane na fadar shuhuda a mafarkinsa. Ai tunda ya dawo ya saba kullum sai ya yi musu hira kafin daga bisani ya yi musu addu'a ya ja musu kofa ya koma nasa dakin. Idan haka ne an tunatar da shi yau bai yi musu addu'ar ba kamar yadda ya sabar musu. Saboda haka cikin mutuwar jiki da kuma sauran baccin da ke tare da shi ya mike don nufar dakin nasu ya yi musu addu'a tukunna ya dawo ya dora nasa baccin. Mamaki ya kamashi na hango haske da ya yi ta tagar(window) dakin bayan ya shigo falo, shin me yasa ba su kashe kwai ba kafin su kwanta? Tagar ya fara nufa, ya kai hannu ya yaye labulen tagar a hankali. Das! Zuciyarsa ta buga sakamakon abin al'ajabin da ya gani, Inna yaduwa na kwance tana ta sharar bacci cikin nutsuwa, ya yin da shuhuda ke gefenta ita ma baccin take. Amma cikinta na juyawa kamar ana wana wani abu, kwatankwacin yadda idan an harba kwallo ta ke juyawa kafin ta isa ga inda ake so. Tambayar da ta fara darsuwa a zuciyarshi ita ce, shin dama haka shuhuda ta ke bacci, ko kuwa ba ta da lafiya ne? Amsar ta gaza samuwa a gare shi ya kuma dauki tsawon lokaci a wannan hali kafin daga bisani ya bar jikin tagar ya nufi kofar shiga dakin. A nan ma ya dauki lokaci yana ma ya dauki lokaci yana kallon abin al'ajabi, ga shi dai dare ne, kuma a yanayin da shuhuda take kwance zai tabbatarwa dik wanda ya ganta lallai bacci ta ke, hakan ke nan yana nufin haka ta ke baccinta, cikinta na juyawa kamar kwallo? Tunda da ace ba ta da lafiya ne, hakika da ba a haka za a ganta tana baccin ba hankali kwamce. Ya karasa kusa da ita cikin tafiyar sanda don kada karar takunsa ya tayar da su daga baccinsu, ya sani za su tuhume shi me ya kawo shi dakinsu a irin wannan lokacin wanda ya ke da yakinin idan zai kwana dubu yana fada musu addu'a ya zo ya yi musu ba zasu aminta da hujjarsa ba. Idanuwanta a lumshe suke tabbacin dai baccin ta ke yi. Zuciyarsa ta dinga ayyana masa abubuwa da dama, ganin Inna yaduwa ta gyra kwanciya tsoro ya kama shi, kada ta bude ido ta ganshi. Don haka ya yi sauri ya durkushe har sai da ya ji motsinta ya gushe sannan ya mike cikin tafiyar sanda ya koma bakin kofa ya yi musu addu'o'in da ya saba tukunna ya fice ya ja musu kofar a hankali bayan ya kashe musu wutar. Koda ya koma dakinsa kasa kwanciya ya yi, zaune ya yi a gefen gado yana tunani, shin idan haka shuhuda ta ke bacci ya ya ke nan idan ya aure ta? Amsar da ta gaza samuwa ke nan, amma lallai yana cikin zullumin tabbatuwar hakan, domin yana da tabbacin ba zai samu sakewar da yake son samu ga matar aurensa ba matsawar aka ce haka shuhuda ta ke bacci. Har gabatowar asubah Isah bai samu ya runtsa ba, karshe ma sai da ya sallaci sallan asubah sannan ya koma kan gado ya nade. Bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi. ***** ****** ***** Shuhuda! Isah ya kirayi sunanta lokacin da ta ajiye masa abin karin kumallo. Ta juya zata fita ba tare da ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu ba. Turus ta tsaya ba tare da ta juya ta kalle shi ba, fuskarta a daure sam babu alamat fara'a, sake cira baki ya yi ya ambaci sunanta, sannan ya dora da cewa: Dawo ina son magana da ke. Ba ta juyo ba, tace: Idan dai akan maganar jiya ce babu amfanin dawowata, tinda na fada maka ra'ayina. Ya yi murmushi, yace da ita: No, ba wannan maganar ba ce, dawo ki zauna. Ta juyo idonta a rusune ta samu kasan kafet ta zauna ta yi shiru. Yace: Dago idonki ki dube ni, sannan na isar da korafin da nake son isarwa gare ki. Babu musu ta dago ido ta dube shi, duban da ya haifar da abubuwan al'ajabi, daga ciki ya ji wani irin tsoronta ya shiga zuciyarshi, ta yi mishi wani irin kwarjini, tambayar da yake son ya yi mata na abin da ya faru a daren jiya bayan mafarkin da ya yi ta koma zakanya ta cinye dabbobi ya shiga dakibsu ya ga cikinta na juyawa kamar kwallo. Ya ji tambayar ta yi masa nauyi a baki, ba zai iya furtawa ba, sam! Da sauri ya rusunar da kansa kasa ba tare da ya iya isar da korafin rashin gaishe shi da ba ta yi ba. Ita kuma ta kasa cire idonta a kansa, kallonsa ta ke, kuma sauraron abin da zai fada ta ke, amma har tsayin lokaci:- Can tace: Ka tsayar da ni, kuma ka ki yin magana. Bayan ina da abubuwan yi. Da kyar ya cafko abin da zai ce, bayan ya yi takaitaccen murmushi, yace: Dama cewa zan yi ya kamata mu je katsina. Saboda me? Ta bukata a takaice. Saboda mu gaishe da Goggo Asma'u da kuma mama karima. Tace: Sai ka fidda lokaci. Ya ji dadin hadin kan da ta bashi, yace: Ina ganin kafin na tafi Ibadan ya kamata mu je ko? Tace: Duk yadda ka gani. Yace: Sai muje karshen satin nan. Tace: Ba matsala..... Shi ke nan? Ya daga mata gira. Tace: Allah ya kaimu lafiya. Ta karashe maganar tana yunkurin tashi, ya ambaci sunanta cikin jarumta, yanason ya yi mata maganar abin al'ajabin, amma ko da ta juyo suka hada ido ya sake jin wani nauyinta ya kama shi. Yana tunanin ta yadda zai furta maganar a gare ta, ai da kunya. Jin ya yi shiru bai ce komai ba ya sa tace: Yah Isah ka cika matsala, ka ce ka gama magana na mike zan ta fi kuma ka tsayar da ni, to me kake son na yi maka? Yace: Dama cewa zan yi ki ba ni lambar wayarki? Tace: Waya? Ka manta ba ni da waya? Fuskarshi ta nuna yanayin mamaki, don a zahiran bai san ba ta da waya ba. Yace: Kina nufin ki ce sam ba ki da waya? Faduwa ta yi ko sacewa aka yi?: Ta girgiza kai tace: Ko daya, ni ban ta6a rike waya ba. Yace: Saboda me? Tace: Haka nan! Yace: To zan saya miki. Ta girgiza kai a karo na biyu. A'a ka barta. Ko akwai dalili? Ya bukata. Eh-to, Ni ban iya rike waya. Yanayinsa ya sake bayyanar da damuwa. Me ya samu hannun naki? Maimakon ta amsa, sai ta jefo masa tambaya. Kai me yasa kake son dole na yi amfani da waya? Ya yi murmushi, yace: Saboda a yanayinki na budurwa zaki bukaci rike waya ko don saurayinki ya kiraki. Ta hade rai, tace: Me ye kuma haka? Jan aji irin na mata. Abin da ya ayyana a ransa ke nan, zahiran kuwa cewa ya yi. Kamar yadda na bukaci yin mu'amala ta soyayya tsakanina da ke, har ta kaimu ga yin aure. Tace: Bana soyayya. Kuma wannan yana daga cikin sharuddan haduwarmu da kai, muddin wannan jigon ne zai dinga hada mu lallai zan kaurace maka don tsirar da rayuwar mu....." Tana karashe fadar hakan ba ta jira cewarsa ba ta fice daga dakin, amma ya hango lokacin da kwalla suka zubo daga cikin idanunta. Sai ya yi murmushi, ya ci alwashi ko ta ya sai ya ja hankalin shuhuda zuwa gareshi, sai ya dandana mata zakin soyayya a ruhinta. Da daddare da ya shigo dakin nasu domin yi musu hira, shuhuda nadewa ta yi a gado ta lumshe idanunta alamun ba ta bukatar a yi hirar da ita ba wai don tana jin baccin ba. Ta yi bakam tana saurarensu, mafi yawancin hirar duk akan zuwa katsina ne, Inna yaduwa tana cewa ita ma lallai sai an je da ita. Yayin da isa ya jajurce babu inda za a da ita tunda tafiya ce ta matasa sabbin jini ba zasu kwashi kayan tsufa su tafi ana musu wani gani-gani ba. A haka dai suka yi hirar ba tare da shuhuda ba, karshe ya mike ya yi musu addu'a ya kashe musu wuta ya nufi dakinsa. Ya yi duk abin da ya saba, ya kwanta bacci ya sure shi. Tarihi ya maimaita kansa, domin abin da ya faru a daren jiya yau ma shi ne ya faru, mafarkin ya yi shuhuda ta koma zakanya ta shiga daji tana cinye kananun dabbobi. Tana kammalawa da dabbobin ta dawo suffarta ta asali ta tsaya a gabansa tana mai jifarsa da wani yalwataccen murmushi, tace: Kana son hawa keken shanu don zuwa bigirena? Ya buda baki da nufin amsa mata ke nan, firgigi ya farka daga baccin nasa yana raba idanu, yau dai bai baro dakin su shuhuda ba sai da ya tabbatar da ya tofe su da addu'a, da ya dawo daki ya yi duk abin da ya saba yi. Illa abu daya wanda bai san ta yadda aka yi ya manta bai yi ba, wato ADDU'A, shi dai yasan lokacin da ya yi wanka ya saka kayan bacci(pyjames), sannan ya shiga duniyar gizo(internet) ta Lap-top dinsa. Da ya kammala da wannan ya rufe lap-top din ya mayar da ita ma'ajiyarta, sai ya kishingida ya shiga tunanin yadda shuhuda ta yi masa. Daga nan bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba. Hakika rashin addu'a ga rayuwar dan Adam wani babban gi6i ne, idan ya yi la'akari da jiya bai yiwa su shuhuda addu'ar da ya saba yi musu ba, ya yi mafarki mai firgitarwa, wanda yake nufin tunasarwa a gare shi na rashin yi musu addu'ar. Yau kuma ya sake mummunan mafarkinsa duk a sanadin rashin addu'a don haka wannan IZNA ce gare shi da ma duk wani wanda ba ya addu'a ga lamuran rayuwarshi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa a sarari. Alhamdulillah! Sannan ya mike tsaye bayan zuciyarsa ta ayyana masa ya je dakinsu shuhuda ya kara tofe su da addu'a don nema musu tsari daga shaidanun dare. Daram! Gabanshi ya yanke ya fadi lokacin da ya karasa a cikin falon, ta taga ya hango hasken kwan lantarki. Ya dai san bayan ya yi musu addu'a sai da ya kashe musu wuta sannan ya nufi dakinsa. Abu na farko da ya fara zuwa ranshi shi ne, Inna yaduwa ko shuhuda daya daga cikinsu ya farka daga bacci ya kunna kwan lantarki watakila don yin ibada ko kuma wani uzurin na daban. Cikin dakiya ya karasa bakin kofa, yana tura kofar sai ya ji ta a bude ba a rufe ba. Yaye labulen da zai yi idonsa ya yi masa tozali da al'amarin da ya faru a daren jiya a irin wannan lokacin, wato cikin shuhuda yana juyawa kamar kwallo. Mamaki, tsoro, fargaba dukka suka durar masa a lokaci daya, wai wannan wane irin rudadden al'amari ne ace mutum yana bacci cikinsa yana juyawa kamar kwallo irin haka? Lallai ko tababa babu shuhuda ba ta sa lafiya, akwai cutar da ke damunta, tunda haka nan ba zai yiwu cikinta ya dinga irin wannan juyawar ba, ko dai tana da cutar kyambon ciki? Cikin sanda kamar yadda ya yi a daren jiya don gudun tayar da Inna yaduwa, gaba daya jikinsa kyarma yake, ji yake kamar wani abu na fizgarshi karasawa inda shuhuda ta ke, duk da cewar ya sani muddin daya daga cikinsu ta farka ba shi da hujja ko kalaman da za su kare shi. Idan jiya yana da hujjar ya zo yi musu addu'ar da bai samu damar yi musu ba, yau kuma mece ce hujjarsa? Zai ce ya yi mafarki shuhuda ta koma zakanya tana cinye dabbobi shi ya sa ya shigo musu daki a dai-dai wannan lokaci? Hujjar ba mai kar6uwa ba ce, illa ya sani tsautsayi ne ke fizgarsa. Idanu ya tsurawa cikin shuhuda har yanzu juyawa yake yi kamar ana juya kwallo. Cikin shakku da rashin sanin fa'idar yin abin da yake yunkurin yi ya daga hannu zai ta6a cikin, har ya kusa kai hannun ya yi saurin daukewa, sakamakon buhum kirjinsa da ya tsananta. A karo na biyu ya sake kai hannunsa da nufin ta6a cikin, saboda zuciyarsa da ta ke azalzalarsa ya ta6a cikin ya ji me ye yake juyawa haka? Wannan karon duk kokarin da ya yi na hana hannun nasa isa ga cikin shuhuda sai da ya isa. Bisa ga tsananin mamaki, hannun na isa cikin ya tsaya cak! Ma'ana ya daina juyawa kamar ace talabijin ce take aiki aka sa hannu aka kashe ta. Da sauri ya dauke hannunsa yana ci gaba da tsura mata idanu, har tsayin wani lokaci babu abin da ya kuma faruwa, cikin bai sake juyawa ba, haka kuma shuhuda ba ta farka daga baccin nata ba. An shafe ya fi mintina takwas babu wani abu da ya faru, don haka ya fice daga dakin ya nufi dakinsa cike da al'ajabin yadda abin ya faru. Washegari da yammaci misalin karfe biyar, rana ta yi sanyi, Isah yana kokarin bude murfin motarsa don shiga zai je cikin gari wajen abokinsa da suka yi za su hadu. Da sauri shuhuda ta karaso gurinsa tana cewa. Yah Isah! Don Allah tsaya!! Ya dakata da bude murfin motar tare da juyawa yana kallonta. Ta tsaya a gabansa tana sanye da doguwar riga ta atamfa mai gajeran hannu, ta daura dan karamin bakin gyale a kanta, kafarta da silifas. Ta sunkuyar da kanta kasa ta kasa magana. Yace: Ya aka yi ne shuhuda? Muryarta a raunane tace: Yah don Allah ka yi hakuri na tsayar da kai ko? Ya girgiza kai. Kada ki damu, me ye matsalarki? Ta sake rusunar da kai kasa. Ni ma ban san abin da ya sa na tsayar da kai ba. Mamaki ya bayyana a fuskarsa, yace: Aha! Ban gane ba kui san abin da ya sa kika tsayar da ni ba? ada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤19¤¤ . Tace: eh yaya, shin hakuri zan baka, ko kuwa albishir zan yi maka? Ya yi murmushi, ya jingina da mota yace: Duka. Sai ki fada ina saurarenki. Tace: Ka yi hakuri akan kin kar6ar soyayyarka da na yi, hakan ya faru ne bisa tunanin da na yi kamar ban cancanta da zamowa abokiyar rayuwarka ba a matsayinka na wayayyen mutum, wanda ya rayu a cikin masu jajeyen kunne, ni kuma BAGIDAJIYA, bakar fata, wadda ta rayu cikin 'yan uwanta bakaken fata! Sai na ga yin soyayyar akwai matsala. Tana karashe fadar hakan ta yi shiru, shi kuwa murmushin ya sake saki, sannan yace: Sai kuma aka yi rashin sa'a duk da kasancewar na rayu a cikin masu jajayen kunne, sai Allah bai sa na ga wata daga cikinsu da zuciyata ta aminta ta zamo uwar tuwona ba kamar ke. Hasalima tunda nake mace daya ce na ta6a gani, wadda zan ce ta burge ni. Wato SHUHUDA IBN KHADDAB, wadda na fada miki mun hadu da ita a birnin misra, ita ma burgeni ne kawai ta yi ba wai ina son ta zamo mata a gare ni ba. Saboda haka ke din dai ke ce wadda asalin sona yake a tare da ita, wannan tsinkayen naki raunanna ne, bai isa ya zamo jigon da zai hana soyayyarmu ba. Ya yi shiry yana sauraren ya ji daga gare ta, amma ba ta tanka ba, ya ci gaba da cewa: Wani albishir ne zaki yi min? Ta dan dago kai ta dube shi, suka hada idanu ta mayar da idanunta ta rusunar kasa, murya a sanyaye tace: Na amince da soy....... Maganar ta makale a kasan makoshinta, yayin da farin ciki ya cika masa zuciya, ya daga hannu sama yana cewa: Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin Talikai, masani akan dukkan SIRRIN 6OYE da na BAYYANE. Ya sake dubanta, yace: Idan na ce na fi kowa farin ciki a wannan rana ban yi laifi ba, saboda na tabbata duk wanda ya dace da mace irinki, lallai ya yi dace da uwar 'ya'ya ta gari, irin wadda ake son samu, wadda aka yi hasashen idan mutum ya same ta lallai zai yi katari da madauwamin farin ciki. lokaci daya fara'ar dake fuskarshi ta raunana, sakamakon abin da ya faru SHERAN JIYA, da kuma JIYA na ganin cikin shuhuda yana juyawa kamar kwallo. Ya so ya yi mata magana akan haka, amma suna hada idanu da ita sai ya ji nauyinta ya kama shi, tabbas wannan ba muhallin da zai furta abin ba ne, domin gudun kada ta zarge shi akan yana son fakaitar idanu ya 6ata mata rayuwa...... Shuhuda ta katse shirun da cewa: Yauwa, Yar Isah, wai don Allah ya kamannun shuhudan da kuka hadu da ita yake, ina ganin kamar na ta6a ganinta. Ya girgiza kai, yace: Bana tunani, tunda ta ce ba ta ta6a zuwa Najeriya ba. Ko ke kin ta6a zuwa Misra bayan tafiyata? Tace: A'a amma ba ta ta6a zuwa Najeriya ba ya aka yi ta sanni? Yace: Eh, ni ma abin da nake mamaki kenan, tace: wai bincikenta ne ta sanki, wata 'yar fara doguwa, irin matan Misran nan dai. Shuhuda ta yi dariya, tace: Kai Yaya, su matan Misra har kala daban gare su? Yace: Sosai ma kuwa, domin kina ganinsu kin san su 'yan asalin kasar Misran ne. Ta jinjina kai, tace: Ni kam zan so na ga wannan shuhuda mai bincike haka. Yace: Nima zan so hakan....... Ya kawar da maganar da cewa: Jibi ne tafiyarmu katsina ko? Tace: Haka ne. Yace: Ya kamata ki shirya gobe dai mu yo tsaraba ko? Ta narke idanu cikin shagwa6a, tace: Kai Yah Isah ni fa bana son zuwa super market. Yace: Ko akwai dalili? A'a, haka kawai bana sha'awar zuwa super market. Cewarta. Yanzu ya kamata ki koyawa kanki sha'awar zuwa tunda ra'ayina ne. Shi ma ya fada yana kallonta. Sai tayi shiru ba ta ce komai ba. Yace: Yanzu ma ba don mun yi alkawari da Salman Alparis zamu hadu ba, ai da yau zamu je, amma yau da gobe duk kayan Allah ne. Tace: Haka ne, bara na koma tunda fita zaka yi...... Ya katse ta, idn babu takura mu je ki raka ni mana? Tace: Anya? Akwai wani nazari da na ke yi. Yace: Shike nan, sai na dawo. Ai ba jimawa zan yi ba. Tace: To Allah ya dawo da kai lafiya. Ya amsa, Amin. Yana kokarin shiga mota, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. A ranar da dare hira suka sha mai tarin yawa, da amfani ga Isah, domin a cikin hirar ne ya kara tabbatarwa kansa lallai ya yi sa'ar samun mata mai kaifin hankali da basira. Wadda ta san makamar rayuwa, ta kuma san yadda zata farantawa wanda ke tare da shi rai. Saboda dik hirar ta su ta ta'allaka ne akan yanayin da ma'aurata suke kasancewa idan sun sami matsala. Ya dinga dangantawa da su. Misali: Ace ya aureta matsala ta shigo ta karin aure ba tare da ya sanar mata ba, sai ranar daurin auren ko kuma ana gobe daurin auren. To idan irin wannan matsalar ta shigo ta ya ya zata magance ta? Murmushi ta yi, tace: Yah Isah ai ita soyayya ta gaskiya wadda ta zamo jigon aure mutumtata ake yi, kuma a yi uzuri tsakanin juna, tare da kar6ar uzuri. Zata iya yiwuwa saboda tsananin kaunar da kake yi min ne yasa ka kasa sanar da ni zaka yi nin kishiya. Kasan a rayuwar aure nagartacciyar kauna da fahimtar juna ake nema, muddin aka samu haka to kuwa dole ne a samu uzuri. Kuma duk macen da ka gani ko jin mijinta zai kara aure ta tayar da kayar baya, da tasa rayuwar auren na su ta samu tangarda. To ka tuhumi asalin tushen kafuwar tubalin auren. Mai yiwuwa ne dama can ba kaunar mijin ta ke ba, sha'awa ko burgewa ce ta sa ta aure shi. Ko kuma ta kasance daga cikin jinsin mata wadanda suka dauki KISHI dabi'a mai kyau a gare su. Wannan dogon bayanin da ta yi masa ya sama masa nutsuwa da gamsuwar cewar, lallai ya yi dace da samun mace ta gari. Inna yaduwada yake babbar mace ce, tuni ta fassara maganganun nasa, ta yi dariya tace: Isah kenan, ga dukkan alamu kana daga cikin mazan da ke sha'awar tara mata fiye da daya..... Ya yi saurin katse ta da cewa: Ko daya Inna. Ai samun sahihiyar mace guda daya ya fi ka tara mata hudu da suke tayar maka da hankali. Ni kam a ra'ayina mace daya nake son aure, musamman don na samu zaman lafiya tsakanina da iyalina. Inna yaduwa ta sake murmusawa tace: Sai aka ce maka idan mutum ya auri mace fiye da daya ba zai samu kwanciyar hankali ba? Yace: A'a, amma ni dai ra'ayina mace daya ne, saboda nasan idan na auri biyu daya ta fi kayutata min, sai na nuna rashin adalci a tsakaninsu. Shuhuda ta shiga cikin zancen tace: Ni kuwa a nawa ra'ayin ina son zama da kishiya, domin 'yar uwa ce, akawai matan da suke mantawa da girman amfanin zama da kishiya, suka dauki kishiya a marsayin abokiyar gabarsu. Wasu sun iya KISHIN BIRNI su 6oye kishinsu a zahiri, sai dai karfar baka, ko kuma KISAN MUMMUKE, yayin da wasu kishin na su ke gaza 6oyuwa zaka ga ma wasu har buge-buge da yage-yage suke yi a junansu. An sani dukkan mace an halicce ta da kishi, to amma babu mafi dacewa a yi kishin na nuna kyautatawa ga miji, a ririta shi, a mantar da shi damuwa ba wai a saka masa wata damuwar ba. Tun da ta fara wannan bayanin ya ke kallonta, mamakin yadda tasan wannan mas'ala yake, a matsayinta na karamar yarinya wadda ba ta ta6a yin aure ba bare zama da kishiya, kuma ta rayu a gidan da babu kishiya. Hakan ya tabbar masa ko wane mutum da irin NASIBINSA, ita kam ta samu nasibi mai kyau, sai fatan Allah ya sa ta dore da wannan halayya nata. Inna yaduwa tace: Ke duk ya aka yi kika san haka? Shuhuda ta yi dariya, tace: Haba Inna, kada ki ba ni kunya mana? A tunanina kinsan mace tana da sani game da lamuran kishi ko da kuwa ba ta shiga fagen ba, sai dai wata idan tana da raunin tunani ba zata gane hakan ba har sai ta shiga fagen. Ni kuwa na sani, kuma ina da ALAKAR da zan sani. Inna yaduwa tace: Saboda kin zauna da kishiya ko? Shuhuda tace: Ko ban zauna da ita ba, zan iya sani, saboda ALAKAR na sanin. Inna yaduwa tace: Lallai kam tunda ubanki yana da mata biyu(Alh Sada take nufi) dole ki sani. Sai duk suka yi shiru saboda girman maganar. Inna yaduwa tace: Ja'iran kawai, ni ka tashi ka bamu wuri haka nan zamu kwanta. Shuhuda dai ce, idan ba ka manta ba tun kafin ka je kasar masu jajayen kunne na sanar da kai ba zan ba ka aurenta ba. Shuhuda ta yi tsagal tace: Haba dai! Ai ko ba ki ba shi aurena ba, ni sai na aurasa masa kaina. Inna yaduwa ta daga hannu zata kaiwa shuhuda duka, sai ta tuna da abin da ya ta6a faruwa lokacin da ta yi yunkurin dukan nata, don haka ta yi saurin sauke hannunta, tana cewa: Rufe min baki rasa kunya 6eran tanka. Isah yace: Yauwa amaryas, fada mata ta ji da kyau. An fada mata har yanzu kambun nata yana tasiri? Ya karashe maganar yana kokarin mikewa. Inna yaduwa ta aika masa sakon harara, tace: Na ce ka wuce ina so mu kwanta. Yace: Ba sai kin kore ni ba, ni ma baccin nake ji. Ya soma tofa musu addu'o'i yace: Mu kwana lafiya. Bai jira amsarsu ba ya ficce. A ranar bai yi mummunan mafarkinsa ba, tunda ya kwanta ko motsawa bai yi ba sai gabanin sallar asuba. Lallai addu'a makami ce ga dan Adam, dubi dai kwanaki biyu matsalolin da ya samu akan rashin addu'a, amma yau da yake ya yi addu'ar sai ga shi da yin bacci cikin nishadi. Koda ya gama sallar asuba dakinsu ya nufa, sai dai ya tarar da shuhuda zaune akan sallaya tana Azkar din safe, yayin da Inna yaduwa ta ke kujiba-kujibar dama koko, don ita Allah ya yi ta ba mai ganda ba ce, don haka ma ko 'yar aiki ta ki aminta a ajiye mata. Zaunawa yayi a gefen gadon ya na jiran ta kammala lazimin su gaisa, amma har tsayin lokaci ba ta dakata ba, shi kuma yana son ta datse su gaisa ya koma daki don yin sababben baccinsa, hakan ta gaza samuwa. Da ya ga ba ta da niyyar tsayar da lazimin nata su gaisa, sai ya mike tsaye ya fice daga dakin. Yana fitowa falo suka yi kici6us da Inna yaduwa ta fito daga kicin. Ya rusunar da kai yana kokarin shigewa sashensa, Inna yaduwa ta ambaci sunansa, ya juyo yana kallonta. Ita kuma ta zauna akan kujera fuskarta a dan daure. Ganin ta zauna ya tabbatar magana ta ke son yi da shi, sai ya dawo falon ya zauna ya yi shiru yana sauraren abin da zata fada. Ta sauke gwauron numfashi, sannan ta dora da cewa: Isah magana zamu yi da kai ta fahimta, kuma shawara da gargadi ne a gare ka. Ka ga wannan yarinyar shuhuda da kake gani ko, bana son abin da zai ta6a ranta ko sakata a damuwa. Abin da yasa ka ji na fadi wannan maganar wani abu ne yake yi min ciwo a rai, na rasa wanda zan kama na sanar da shi abin. Yanayinta ya sauya gaba daya, ta koma kalar tausayi, hakan ya sa shi ma Isah yanayinsa ya sauya, ya dai kasa kunnuwa yana saurarenta. Zata ci gaba da magana ke nan, shuhuda ta shigo falon, Inna yaduwa ra dago kai suka hada idanu, sai ta ga kamar launin idanuwanta sun sauya daga fari da baki zuwa wata WALKIYA, don haka da sauri ta rusunar da kwayar idanunta kasa. Isah kuwa da ya dago bai ga komai ba, illa ya ga shuhuda tsaye a bakin kofa sanye da hijabin sallarta. Shuhuda tace: Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi idan ina azkar ba na son tsinkewa saboda idan na koma ba zan iya yin adadin da nake yi a kowacce rana ba. Yana murmushi yace mata. Kada ki damu. Tana kokarin zama, tace: Hala wannan tsohuwar ta zaunar da kai zata yi maka shirme ko?. Babu wanda ya tanka mata. Bayan ta zauna tace: Yaya barka da kwana. Yace: Min tashi lafiya?. Tace: Kalau, don na fi wannan tsohuwar, tunda na lura yau tunda ta tashi a suku-suku ta ke, ko kuwa neman rigima ta ke? Ba shakka don mun ce ba zamu je katsina da ita ba ne ta ke neman ayi rigima da ita. Inna yaduwa ta yi murmushin karfin hali, tace: Sha kuruminki idan dai ni ce ko da kunce ba zaku je da ni ba, ba zan damu ba. Shuhuda tace: Ke dai ki ce kin yi abin nan da Hausawa sukan ce, Wai abin da baka samu gama shi da baka so, ko kuwa yaya? Ya girgiza kai yace: Kwarai kuwa. Inna yaduwa ta mike tsaye, tace: Isah bai so tashin Inna yaduwa ba, ya so ta sanar da shi abin da yake damunta har ya ji tausayin 'yar tsohuwar ya kama shi. Wata kila ba ta jin dadin zama da shuhuda. shi kam a yadda yake ganin shuhuda ba ya tunanin tana da wani mugun hali da wanda yake zaune da ita zai koka. Domin ta kasance kamilar budurwa, da ace irin 'yan matan yanzu ne yadda ta ke zaune da kakarta, da kullum sai ta sakata kuka, amma sam shuhuda ba ta da wannan hali, ba ta son ma yin irin wannan haramtaccen wasan na JIKA da KAK , don da yawa wasu wasanni da ake yi jika da kaka ya haramta. Wasa na rashin ganin girma da nuna kuruciya a zahiran. Bayan tafiyar Inna yaduwa shuhuda ta dubi Isah tace: Yauwa Yah Isah, wai kana da Umdatul Ahkam? Yace: Me zaki yi da shi? Tace: Karatu. Yace: A'a ba ni da shi, amma anjima idan mun fita siyayyar tsaraba sai mu nemo ko? Tace: Allah ya kaimu. Yace: Amin, amma kafin nan bari idan na shiga daki zan fito miki da wani littafin addini, don na lura kina son karance-karance. Tace: Sosai ma kuwa, don littafan da na karanta na addini suna da yawa, ka ga kamar littafin Fikhul Wadii na ji dadinsa sosai, yadda aka yi bayani game da yadda al'adar mata ta ke zuwa, da kuma yadda take daukewa, har ma idan ta zowa mutum da matsala. Kasan mafi akasarin mata ba su san jinin haila ba, ba su san rabe-rabensa ba, da kuma yadda idan sun dauki lokaci ba su yi ba, ba su san me ya haddasa hakan ba, su ba ruwansu kawai sun san cewa, idan wata ya zo karshe suna fitar da jini, babu maganar akwai matsala ko akasin ta idan ba gani sukayi sun kwanta ba...... Isah ya katse ta da cewa: Me ye matsalar matan? Sai ta yi murmushi tace: Au, na fa manta kai namiji ne ko?. Ta mike tsaye cike da jin kunya ta koma daki. Bai yi yunkurin tsayar da ita ba, ya yi mata uzuri, sai ya tashi ya koma dakinsa, don dama bacci ne ke cinsa. Da yammacin ranar suka je Sahad store da Alh. Shehu super market suka yo siyayyar abubuwan da zasu yi tsaraba da shi, sannan suka wuce kasuwar kurmi shuhuda ta za6o littafan addini, daga bisani suka dawo Gida. Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤20¤¤ Duk yadda ya so kadaicewa da Inna yaduwa don jin damuwarta hakan bai yiyuwa ba, saboda duk lokacin da ya shigo falon sai ya tarar da ita tare da shuhuda. Washegari ma tun da safe ya nufo falon bai ga Inna yaduwa ba, ya leka kicin wai ko ya tarar da ita kamar yadda tayi jiya, amma sai ya tarar da shuhuda. Bai wani jata da labari ba, saboda yana ganin dama ce ta samu, kawai ya je daki ya tarar da Inna yaduwa ya ji matsalarta tunda shuhuda na kicin. Yana zuwa dakin ya tarar da ita kwance akan gado, idanunta a lumshe, yace: Matar bacci kike? Sai ta bude ido ta kalle shi tace: A'a jikina ne yake ciwo. Yace: Ayya, Allah kawo sauki. Tace: Amin, ai da saukin, kawai surutu ne ban so, ga shi ina so na dama koko. Yace; Ai ga shuhuda can na yi. Sai suka yi shiru na wani lokaci, kafin daga bisani ya katse shirun da cewa: Jiya muna magana ba mu karasa ba shuhuda ta shigo?. Tace: Eh wallahi, ga shi kuma na manta abin da nake son sanar da kai. Ya dube ta cikin tuhuma, sai ta jinjina kai alamun tabbatarwa. Sannan tacce: Karfe nawa zaku tafi katsinan? Yace: Sai sha daya. Tace: Allah ya kaimu. Ya amsa da, Amin. BABI NA TARA RUDANI Babu mai magana a cikin su biyun, tafiya kawai suke tamkar kurame, kowanne da abin da yake sakawa a cikin ransa. Ga karar kira'ar Sheik Ahamad Sudeis na tashi cikin tausasshiyar muryarsa, SURATUL MUHAMMAD ce ke tashi, wadda ta ke magana akan Manzon Rahama, Manzon tsira, Manzon da babu kamarsa duk cikin Manzanni. Dan Amina baban fadima, Angon nana khadija da nana A'isha, suruki ga sayyidina Aliyu(A.S) kaka ga Hassan da Hussain, wato Annabin Annabawa, amintaccen Allah, Yardajjen Allah, Annabi Muhammad(S.A.W). Surah ce wadda ta ke da muhimmanci akan kowanne musulmi yasanta, duk da cewa babu surar da ba ta da muhimmanci ga kowanne musulmi ya sani a cikin littafi mai tsarki(Alkur'arni mai girma). Littafin da ya shafe kowanne littafi, tun daga kan Injila, Attaura, gami da zabura. Domin littafin alkur'ani ya tattaro dukkan bayani kama daga kan asalin halittar dan Adam, abin da ke da akwai a aljanna da wuta. Bayani na kissoshiin Annabawa, bayani akan ranar tashin alkiyama da yadda aka halicci duniya da lahira, gami da abubuwan da Allah ya yi rantsuwa da su. Lallai Allah(S.W.A) gwanin HIKIMA ne, Arrahim ke nan mai saukar da rahma, Arrahim(mai jinkan bayinsa). Arrazzaku(mai azurta bayinsa), Alfahatu(mai budawa bawa kofofin budi). " An kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar, manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda ya karanta suratul GASHIYA, to Allah zai yi masa hisabi mai sauki. Kuma wanda ya karantata akan rumbun abincinsa to ya aminta daga cutarwarsa. Haka kuma an kar6o daga ubayyu dan ka'ab(R.A) cewar; Manzon Allah(S.A.W) yace: Wanda ya karanta suratul BALAD har zuwa karshen surar, to Allah zai amintar da shi daga fushinsa ranar alakiyama. Manzon Allah(S.AW) yace: Wanda ya karanta suratul LAIL, to Allah zai tseratar da shi daga duhu guda biyu, duhun zunubi da kuma duhun kabari. Wanda ya lazimci karanta suratul Lail sau dari har tsawon kwana arba'in tare da yin azumi da Riyadh(wato nisantar sa6o) to Allah zai yi masa khasafi(wato zai samar da shi 6oyayyun ilmi). Wata rana Annabi(S.AW) ya cewa sahabbansa, shin ko kuna son Allah ya yi muku katanga daga shaidan kamar yadda ya katange Yajuju da Majuju? Sai suka ce: Eh, Sai yace: To ku karanta suratul QADR bayan sallar magriba, da bayan sallar asuba sau uku-uku kafin ku tashi daga wajen da kuka yi sallar. Sannan sai kace: " Ya Allahu, Ya sahibul kadri farraji auni hammi wakarbii"(ma'an a:- Ya Allah, Ya mai iko, ka yaye min bakin ciki da 6acin rai). Wannan duk daga cikin falalar alkur'ani ne, don haka alkur'ani rahma ne ga dukkan musulmi, karanta shi na saka nishadi, sauraren kira'arsa na gusar da bakin ciki. Har suka isa birnin katsina babu wanda ya yi magana daga cikinsu. Sai da suka zo Welcome to katsina(sabon garin Dandagoro) a sannan ne Isah ya dago kai ya dubi shuhuda tare da rage sautin karatun alkur'anin da ke tashi, yace: Zamu biya NNPC mu sha mai, don na ga man ba zai ishe mu zuwa karare ba. Tace: To. Yaci gaba da sulalawa da motarsa har ya shiga gidan man, ya jera layi a bayan motoci hudu da suke gabanshi. Shuhuda ta yi wata irin zabura tare da cewa: Subhanallah!! Da sauri Isah ya dago kai ya dube ta, kokarin fita take daga cikin motar, ya riko gefen hijabin da ke jikinta, yace: Me ya faru? Ina zaki?? Fuskarta cike da fara'a da kuma doki, tace: Wata kawata ce na gani, ga ta can, fita zata yi daga gidan man. Ta karashe maganar tana nuna masa budurwar da ke kokarin shiga motarta kirar hummer jeep da aka gama zubawa mai. Kafin ya yi magana tuni har ta fita, ta karasa inda ta ke tana cewa. Shuhuda dama kina raye? Wadda aka kira da suna shuhuda ta juyo cike da farin ciki suka rungume juna suna masu murnar haduwa. Isah da yake cikin mota yana hango su, ya ga kamar ya ta6a ganin fuskar. Da farko da zai share, amma zargin da ya ke na kamar wata FUSKA da ya ta6a haduwa da ita watanni hudu da suka shude a birnin MISRA ya sa ya gaza hakuri, ya yi fit! Ya bude mota ya tunkare su. Yana isa ya soma nuna bakuwar fuskar da dan yatsansa yana cewa: SHUHUDA IBN KHADDAB? Ta dube shi cikin yanayin tuhuma gami da mamaki. Ita kanta shuhuda mamakin ne bayyane a fuskarta, tace: Yaya ina kasan Shuhuda? Bai amsa mata tambayarta ba, yace da dayar shuhudan. Yaushe kika zi Najeriya? Ko kuwa dama dai maganata ce ta zama gaskiya ke 'yar Najeriyar ce tunda har kika san kanwata? Mamaki ya sake bayyana a fuskar shuhuda Ibn Khaddab. Ta mayar da kallonta ga shuhuda Sagir Rabi'u tace: wannan kuma waye a gare ki? Shuhuda ta dubi Isah, tukunna ta maido da duban nata ga dayar shuhudar tace: Yaya na ne Isah, wanda nake fada miki? Shuhuda ibn khaddab tace: Auhi, Allah sarki yayanmu, barka da yini? Kin amsawa ya yi, saboda ya ga ta raina masa hankali zahiran, in bacin rainin hankali su hadu da ita sannan yanzu ta nuna masa ba ta ta6a saninsa ba? Shuhudan ma ya dauke ta a wadda ta raina masa hankali, kuma MAKARYACIYA, ya tambaye ta shuhuda ibn khaddab ta nuna masa ba ta ta6a sanin mai sunan ba, sannan shuhuda ibn khaddab ta nuna masa shuhuda kanwarsa ba ta santa ba, hasalima ba su ta6a haduwa ba. To ta ya kuma suka san juna bayan ya ji shuhuda kanwarsa ta yi ikirarin shuhuda ibn khaddab kawarta ce? Wannan salon rainin hankali ne da yawo da tunaninsa, abin da kuwa ba su sani ba shi ne, hankalinsa ya wuce nasu bare su sa shi a RUDANI, sa6anin haka ma sai dai shi ya saka su. Shuhuda ibn khaddab tace gaba da cewa: Na yi ta neman yadda za a yi mu hadu na sanar da ke auren Sa'adatu ban samu ba. Shuhuda tace: Ayyah, ashe anyi auren Sa'adatu? Makaranta? Ta fasa ci gaba? Isah ya ga za su dauke shi shawaragi sun share da shi sun ci gaba da hirarsu, saboda haka ransa ya sake 6aci, yace: Shuhuda ina yayanki Abdallah ibn khaddab? Ta juyo da sauri alamun mamaki, sai ba tace komai ba, ta dubi shuhuda, tace: Takwara wai don Allah ina yayanki ya sanni hat yasan Ya Abdallah? Shuhuda tace: Ni ma mamakin da nake yi ke nan, saboda ba a nan ya yi rayuwarsa ba, kuma lokacin da ya dawo muna jarabawa har muka gama bai je makarantarmu ba, bare na ce ko a can ya sanki, yasan kuma yayanki da yake kawo ki makaranta. Isah ya shiga RUDANI matsananci da wannan bayani da ya ji suna yi, anya kuwa shuhudan da ya hadu da ita ce a Misra yanzu a gabansa? Idan ba ita ba ce me ye alakar sunanta da sunan yayanta da waccan shuhuda? Idan ita ce me yasa ta ke son yawo da hankalinsa? Tun ranar da ya soma ganinta da salon yawo da hankalinsa ta fara, tunda ita ta soma yi masa magana cewar ta ganshi kamar yayan Shuhuda Sagir Rabi'u, wannan kuwa idan ba kana da alaka da sanin hakan ba babu yadda za ayi ace bincike na sanadin suna ya kasance idan sun hadu ta shaida shi. . Ci gaban labari. . Bayan basu ta6a haduwa ba. Abin tambayar a nan shine me yasa suka yi amfani da wannan salon gare shi? Shin kowaccensu sonsa ta ke yi ne shi yasa suke son juyar masa da kwalwa? A'a ba sonsa suke ba, so suke su juya shi kai-kai ce, su rikita shi, su sanya shi cikin RUDANI, Su kuma tsotse ruwan kansa bisa jagorancin shuhuda kanwarsa, don ita din ma ta nuna masa abubuwan RUDANI da yawa, saboda ranar da ya ce yana sonta kin amincewa tayi, daga baya kuma ta zo masa da amincewarta. Tunda ya gane manufarsu kamata ya yi ya bi su da yadda suka zo masa. Murya a taushe kuma yana murmurshin da yake kara masa kwarjini, murmushin da yake fito da cikar HAIBARsa( Asalin sunan littafin) Yace: Kada ki damu shuhuda ibn khaddab, haka nake na kasance mai binciken duk wata mace mai sunan kanwata, don haka ne ma zan iya cewa na sanki, na san yayanki Abdallah Ibn Khaddab. Yanayinta ya nuna bata gamsu da bin da ya fada ba, amma jin karar hon din da ake ta doka mata wanda ke nuni ta tsarewa na bayanta hanyar fita, sai ba ta samu damar tankawa ba. Ta dubi shuhuda, tace: Don Allah minti daya na dai-daita tsayuwar motata. Kafin ta amsa mata tuni har ta shige mota, Isah ya lura da zoben da ke yatsanta, wanda iri daya ne sak da wanda ya sa yowa shuhuda kanwarsa da shi lokacin da ya tsaya a kasar Misra. Da sauri ya dubi yatsan shuhuda kanwarsa inda ya saka mata zoben, yana nan daram, saboda haka kama ce, ita ma ta sayi irinsa. Sai ya koma motarsa ya matso da ita, ya kasance motoci biyu ne yanzu a gabansa. Kafin ya baro jikin motar har an sanyawa daya daga cikin motoci biyun da ke gabansa mai, saboda haka sai bai yi garajen barin gurin ba, ya tsaya. Cikin sa'a kuwa ita ma motar dake gaban tasa ba wani mai yawa aka zuba mata ba, sai shi. Ya fadi adadin yawan da yake so, aka zuba masa sannan ya iso gurinsu da motarsa. Yana isowa shuhuda ibn khaddab ta cewa shuhuda. To takwara sai gani na biyu, da fatan zaki cika alkawari idan bikin ya tashi ki kawo mana katin gayyata, da dai nace bazan kara zuwa bikin class mate dinmu ba, amma tunda ke ce da yayanmu ba ji, zan zo. Shuhuda ta rusunar da kanta kasa saboda kunya, tunda Isah na tsaye a kanta. Shuhuda ibn khaddab ta dubi Isah tana murmushi tace: Yayanmu Allah ya sa yadda ka binciko ni saboda ina da sunan kanwarka, idan lokacin aurenku ya yi ka iya binciko ni ka kawo min katin gayyata. Kuma idan na koma gida zan sanarwa Yah Abdallah na hadu da abokinsa ISAH SADA RABI'U. Tana kammala fadar haka ta bude murfin mota ta shige. Isah tsaye ya yi sararo yana kallonta, ya kasa koda motsin kirki ne, ambatar cikakken sunansa da ta yi ya kara jefa shi cikin rudani. Koda yake a wani 6angare bai kamata ya yi mamakin jin haka ba tunda ya ba su dama wata kila a cikin lokacin shuhuda ta samu sararin fayyace mata cikakken sunansa, ko kuma dama ta dade da saninsa,idan ya yi la'akari da maganganun da suka tattauna, wai makaranta daya suka yi. Ta gabansa ta zo ta wuce yana kallonta tana kallonsa, tamkar tana son fada masa wani abu amma ba ta tanka ba, illa murmushin da ya ki 6acewa daga fuskarta.Shuhuda tace: Yaya mu tafi ko? Ajiyar zuciya ya soma yi, kafin daga bisani ya girgiza kai ya nufi mota.Ta bi bayansa, duk suka shiga cikin motar ya soma jansu zuciyarsa ta gaza nutsuwa, haka kuma ya kasa daurewa, yana son cikakken bayani game da alakar da ke tsakanin shuhuda kanwarsa da shuhuda Ibn Khaddab, don haka yace Amma kun sakani a RUDANI sosai. Ta dube shi tace: Wane irin rudani kuma yaya? Yace: Wannan shuhudar ita ce muka hadu fa da ita a birnin Misra na tambaye ki kika ce baki santa ba, ita ma ta ce ba ki santa ba, amma ita ta sanki ta hanyar bincike a dalilin sunanku ya zamto daya, sai ga shi na ganta a Najeriya wanda a can ta tabbatar in ba ta ta6a zuwa Najeriya ba, a yadda na lura na kuma fahimta a cikin kalamanku kun dade da sanin juna, kamar ma a makaranta daya kuka yi, to mutumin da yace bai ta6a zuwa Najeriya ba ta ya kuma ya yi karatu a Najeriya har yasan wasu mutane da ke rayuwa a cikinta? Thats my question (wannan ita ce tambayata) Shuhuda tace: Kai yaya anya kuwa ita ce wadda kuka hadu kuwa? Ita fa wannan a nan katsina ta ke, karatu ya kaita kano ta zauna gidan yayan mahafinta. Da farko ba ma shiri, saboda lokacin da na yi karatu ina rayuwa da hankali ne na awa biyu, sai gab da zamu soma jarabawa muka soma shiri har ma muke zama mu yi hira. A nan ne ma ta sanar da ni ita 'yar katsina ce, su uku mahaifanta suka haifa, daga ita sai yayanta Abdallah wanda yake karatu a Misra, sai kaninta Yusufa su ke nan mahaifinsu suka haifa. Mafarin ke nan suke samun ingantacciyar kulawa daga mahaifan nasu... Har muka gama makaranta ba tasan gidanmu ba, ni ma haka dama kuma ba zuwa bikin kawaye nake ba, shi yasa tun da muka gama makaranta ba mu sake haduwa ba sai yau. Ya gama sauraronta ne kawai, amma bai gama fahimtar inda kalaman nata suka sa gaba ba, shi dai ya yarda ya kuma amintar ma kansa, wannan shuhudar da suka hadu a Misra ce, wadda ke bin kasashe yawon majalisin malamai, shuhudan da ta sanar da shi iyaye da kakanninta dukkansu 'yan asalin Misra ne. Ya fi amincewa lokacin da suka hadu a Misra wani sanadi ne ya kaita, amma ta 6oye masa saboda sun shirya hakan da kanwarsa shuhuda, wannan shi ne hakikanin abin yarda. Tammat bihamdillah Gare ku fa makaranta? Kun yarda? Anya kuwa? Kai ko ni ban yarda ba, akwai dai yadda akayi. Shin ina Uncle Hamza da zuwairiyyarsa? Kada fa a yi danyen kasko mana? Ai kun fahimci labarin MATA'UL HAYAT ko? Idan ma ba ku fahimta ba, zaku fahimta ne idan kuka ji muhimmin sakon da ya kunsa. Kada dai ku manta da tarin abubuwan da suka faru tun daga littafi na farko zuwa na biyu. Musamman rayuka uku da aka rasa saboda shuhuda, da sauran abubuwan da suka biyo baya? Izra'el,Libhas,Tanzif me ye alakarsu da shuhuda? Ina aka samo keken doki da ta ke zuwa Misra kamar yadda ta fawa uncle Hamza? Yakub, Abdallah ibn khaddab, da shuhuda ibn khaddab duk me ye alakarsu da shuhuda. Kai-kai-kai!!! Akwai fa yawa abubuwan, amma dai mu yi hakuri,juriya zuwa MATA'UL HAYAT-3 don jin yadda zata kaya. Shin Hamza ko Isah? Akwai dai sadaukarwa, waye mai sadaukarwar? Kuma ta ya ya? ada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA)Book 3 ¤¤21¤¤ . KUSKURE. . Idan aka duba littafi na biyu page na 150 sakin layi na karshe an yi amfani da sunan Abdallah Ibn Khaddab a maimakon Abubakar Ibn Khaddab har zuwa karshen littafin a haka ya kare. Matsalar ta faru ne daga gare ni ne, da parko Abdallah shi ne asalin sunan, bisa wani dalili na maida Abubakar, na ci gaba da bi ina replace da Abubakar, tuun daga page din da aka samu matsalar gaskiya ban duba ba, lokacin ba ni da lafiya, kuma har aka gama aikin ban ga kuskuren ba, sai da na yi nisa a 3 sannan ma na fuskanta. . A gafarceni bisa wannan kuskure. Zahra u Baba Yakasai. . Allah ya jin kanta da rahama ya saka mata da Aljannah.....ameen. . Ci gaban labari.. . Shuhuda ta dan dube shi a kai kaice, tukunna ta ci gaba da cewa. 'Shuhuda tana da mutumci, ta na da kaifiyya da bincike akan abin da ya shafi harkar taimako. Ka ganta dai yarinya ko, amma wallahi idan ka ji irin mutanen da ta binciko ta taimaka musu abin sai ya ba ka mamaki matuka. Shi yasa a rayuwa duk wanda ya kasance yana da kaifiyya ya ji dadi'. Wannan kalma ce da Shuhuda Misra ta yi amfani da ita a lokacin da ta ke sanar da shi yadda aka yi tasan kanwarsa Shuhuda, ta ce tana amfani da bincike ne gami da kaifiyya. Wannan ma kadai ya isa ya zamo hujja agare shi, Shuhudan Misra ce ya yi tazali da ita a Nigeria. Ya so ta ba shi lambarta, gami da adireshin gidansu a can Misra ta goce masa, kuma babu amfanin da ba shi lambarta don gudun kada idan sun hadu a Nigeria ta nuna ba ta sanshi ba ya kira wayarta ta yi kara a gabansu asirinsu ya tonu, shirin da suka yi ya ruguje. Lallai idan haka ne ya ci a jinjinawa wannan kaifin hankali nasu, tunda har suka iya wannan tufkar ba tare da an samu rauninsu ba kasancewarsu MATA masu tarin rauni, da kuma kuruciya. Domin mace mai shekaru sittin a duniya ba ta kai namiji mai shekaru ashirin kaifin hankali ba, su dama mata haka suke, rauni ne da su. Abin da suke tunanin idan sun yi dai-dai ne, amma idan maza suka tace sai aga abin ba dai-dai ba. . (Sadin Mama yar Anty, ni dai na ce what a man can do, woman can do far much better ) . Ku yi hakuri yan uwa na mata, kada kuce na yanke mu, gaskiya ce idan kuwa gaskiya ta zo ana son fadarta komai dacinta. . Shiru ya yi bai kuma tanka mata ba domin ta gama yawo da hankalinsa, ta gama kunce masa duk wata jijiya ta tufka da warwarashi. . BABI NA GOMA TABDIJAN! Shagari low-cost nan ne unguwar da Haj Asmo ta ke, a kofar gidan suka tsaya suna jiran maigadi ya bude musu get. Koda ya bude Isah ya sulala da motar cikin harabar gidan, Shuhuda ta bude kofa ta fita ta nufi hanyar shiga cikin gidan. Isah ya sanya baki ya kirayi sunanata. Ta juyo tana dubanshi ba tare da ta tako ba. Ya ce, "ki tsaya mu shiga da tsarabarsu mana". Cikin shagwaba ta ce masa, "mu tara shiga mana, ba sai a samu wadanda zasu shiga da tsarabar ba?" Yana kyabe baki ya ce da ita. "Shi ke nan". Yara kusan su shida suka tarar a falon suna kallo, da ya ke sun san Shuhuda don haka suna ganinta suka mike da sauri suna mata oyoyo-oyoyo. Ta dauki Sajida 'yar shakara hudu ta saba a kafadarta. Hayaniyar yaran ce ta fito da Haj.Asmo daga dakinta. Ita ma tana ganinsu ta washe fuska. "Ni kam na yi fushi, yanzu saboda Allah Isah sai yau kake zuwar min?" Yana sosa keya irin na maza, ya ce, "Ayi hakuri Goggo". Ta ce "idan ban yi hakurin ba ai da ba zaku ma gane gidan ba, duk da kuwa ka dauko wannan marar son zumuncin. Ta hana min 'ya zaman lafiya, kullum kuka wai ita akaita gurin Aunty Shuhuda". Su duka suka yi murmushi, Shuhuda ta dora da cewa. "Ki yi hakuri Goggo, dama karatu ne yake hana ni zuwa, to yanzu kuma an gama kafin a tafi wata". Haj.Asmo ta ce. "Idan an daura aure ko? Ai ni an fada min kun hada kanku....." Kunya ta lullube Shuhuda har shi kansa Isah, aka rasa wanda zai ce wani abu. Haj.Asmo ta lura da hakan, sai ba ta ja zancen ba, ta dubi Sajida da har lokacin ta ke makale a kafadar Shuhuda ta ce. "To a sauka a bar Aunty ta zauna ko?" Ba musu yarinyar ta soma kokarin sauka, Shuhuda ta sauke ta, ta zauna akan kujera. Haj. Asmo ta ce da daya daga cikin matasan matan. "Nafisa a kawo musu abinci da ruwa ko?". Nafisa ta nufi kicin don hado musu abinci. Isah ya dubi sauran yan matan, ya ce. "Ku taso mu je ku kwaso tsarabarku". Sun kwaso kayan tsarabar wanda suka ware na gidan, sauran kuma suka barshi a mota. Sai da suka soma gaisawa sannan suka ci binci, aka shiga hira. Karfe shida na yamma, Isah da Shuhuda suna zaune a falon Haj. Asmo da ita kanta Haj. Asmon suna hira, Musabahu ya shigo falon hannunsa rike da waya yana murmushi ya ce. "Afuwa, wani uzuri ne ya tsayar da ni". Isah ya kawar da kai, ya ce. "Ba ni zaka bawa hakuri ba, kanka zaka baiwa, domin yiwa wani yiwa kai ne, kuma duk wanda ya gyara ya sani". Musbahu yana kokarin zama akan kujera ya ce. "Kin ji shi ko Sister?" Shuhuda ta kawar da kai, ta ce. "Ni kyale ni, bani da lokacinka. Bayan tunda muka zo aka sanar maka isowarmu, amma ba ka tashi zuwa ba sai yanzu da ka ga dare ya yi, don kada mu fita zaga gari ko?" Musbahu ya saka dariya, ya ce. "Shi yasa ina shigowa na soma neman afuwa, kuma sha kuruminki tunda dai kwana zaku yi ai magana ta kare, gobe idan muka dinga yawo sai kin ce kin gaji". Haj. Asmo ta saka musu baki. "Ai sun ce da safe zasu wuce. saboda zasu karare. Kuma a goben zasu koma kano". Ya ce "shi ke nan, sai a yi min uzuri". Bayan sallar magariba Isah da Musbahu su ka fito daga masallaci. Wayar Musbahu tayi kar. Yana dubawa ya ga wande ke kiransa, kafin ya duba ya dubi Isah ya ce. "Ina ji se ka rakani wani guri saboda wannan kiran da aka yi min nasan mafita". Kafin Isah ya magantu, Musbahu ya kara wayar a kunnansa, yana cewa. "Ya aka yi ne Malami?" Ya dan saurara kadan don jin abinda ake fada masa, sannan ya ja fasali ya ce. "Malami ni a ganina ka baiwa Allah zabi idan Zuwai din ce alkhairi. Allah Ya tabbatar, idan kuma Dodoridon ne.... Don Allah tsaya.... Na daina.. Kana jina? Ba na son ka sanya kanka a cikin taskun rayuwa, ka yi hakuri...." Ya sake saurarawa na wani lokaci, sannan ya ce. "Kai kasan yadda ta ke, mu kam ba ka taba nuna mana hotonta ba, don haka maganar musun kyawunta ko kwarjininta bai taso ba.... Kuma yarinyar da aka tabbatar maka da MAYYA ce na me zaka....... No! Wallahi na fi kowa son ka, son da nake maka din ne ma yasa nake nusar da kai tarin kalubalen da kake neman fadawa.... Shi ke nan, zan shigo, baki muka yi ma ai da tuni ka ganni.... To sai na shigo din". Ya kashe wayar cike da alhini. Isah a tun soma wayar ya tsurawa Musbahu ido, mamakin kalaman da suka tattauna yake, don haka Musbahu na kashe wayar ya ce. "Me ya ke faruwa?" Musbahu ya yarfar da kai, ya ce. "Wallahi wani aboki na ne yake cikin rudani. Wata yarinya ce Allah Ya hada su da ita, yana matukar sonta amma matsalar ne barkatai, ka ga dai na farko wani yayanta Yakub ya same shi ya fada masa auren zumunci za a yi mata, amma shi ya kasa hakura da ita, kuma fa akwai wata kanwar mahaifinsa da ta ce yarinyar mayya ce, shi kansa yana tunanin kasantuwarta jinsin mutane, saboda kana kallonta zaka ga tsabar kyau kamar aljana. Amma sonta ya makantar da shi kana ji yanzu har an kai fagen da yake tunanin tuburburewa lallai sai ya aure ta". Isah ya girgiza kai cikin tausayawa.ya ce. "So ke nan! Kasan idan mutum ya na son abu hankalinsa ba zai taba kwanciya ba har sai ya ga ya mallaki abin".. Musbahu ya ce. "Ai ko dai, amma wani lokacin yana da kyau mutum ya dinga ragewa kansa kaifin son abu idan har ya soma katari da matsalolin da abin zai saka shi". A dai-dai lokacin suka karaso gidan. Sun gama cin abinci, Isah da Musbahu suka mike zasu fita. Tsam! Shuhuda ita ma ta mike tana cewa. "Ina zaku?" Musbahu ya yi murmushi, tukunna ya ce. "Zamu je wani guri ne mu dawo". Ta ce, "Ai kafarku kafata". Nusaiba kanwar Musbahu wadda zasu iya zuwa kai daya da Shuhuda, ta ce. "Yaya ai wannan cingam ce, don haka kada ka damu tunda dai ka dauke mai jan kunne ai ita ma sai ka dauka". Sukayi murmushi, Isah ya ce. "Idan dai da ita za a fita, to ke ma sai ki taso mu tafi tare, don ba zamu tafi da mace daya tsikau ba ace maza biyu mace daya". Musbahu ya dubi Nusaiba ta gafen ido, ya ce. "Dama abin da ta ke so ke nan, don tasan ni ba zan fita wani guri da ita ba, Amma kin ci arzikin su". Nusaiba tana dariya, ta ce. "Na dai ji, komai zaka ce ka fada". Haj. Asmo dai ba ta tanka ba, haka suka tafi su hudu. Musbahu da Isah a gaban mota, Shuhuda da Nusaiba a kujeraa baya. Suna tafe suna hira irin ta abokan wasa(Dan mace da dan namiji). Sun isa Kanada Quaters inda gidan Malami yake, Musbahu yayi hon maigadi ya bude kofa suka shiga. Su duka hudun suka fito daga cikin motar, Musbahu a gaba, Isah a bayansa, sannan Shuhuda da Nusaiba. Yana zaune akan kujera cikin falonsa, sanye da wando (3quater) baki, sai karamar riga(roundneck) ja. Kayan sun kara fito da kyawunsa, duk da dama shi din kyakkyawa ne, don da wahalar gaske ka ga dan asalin Ruma mummuna, yawancinsu farare ne dogaye masu cikar haiba. Sai da Musbahu ya shigo sosai sannan yayi tozali da wadanda ke bayan Musbahu. Zumbur! Ya mike cikin RUDANI, ya ambaci sunanata. "SHUHUDA!" Ita ma cike da rudanin ta ambaci sunansa. "UNCLE HAMZA!" Musbahu, Isah gami da Nusaiba suka kama kallonsu cike da tsananin mamaki, ina suka san juna? . Sadin Mama 'yar Anty na ce "WAI! Ni ma na rasa inda su ka san juna". ausa Book stories Kyan Alkawari........ . MATAUL HAYAT ¤¤22¤¤ Saboda yadda suka ambaci sunan juna yanayi ne da ke bayyana sun dade da sanin juna kuma sun dade basu hadu ba. Shuhuda ta sake dubanshi, tace. "Uncle Hamza dama zan sake ganinka? Dama kana raye a duniya ka manta da dalibarka, kuma kanwar ka?" Wannan batu da ya fito daga bakin Shuhuda ya baiwa su Musbahu amsar tambayarsu ta inda suka san juna, kuma kalaman dai ne suka haskowa Musabahu wannan ita ce yarinyar da Malami ya ke so, wadda kuma yake cikin tashin hankali a game da ita. Shi kam ya san Shuhuda mutum ce tunda a tsatsonsu ta fito, mahaifiyarsa da mahaifinta uwa daya uba daya, sannan ya sani duk cikin tsatsonsu babu MAYE, don haka wannan ma wata hujja ce da zai kafawa Malami, sai dai kash! An makaro. Domin an sanar masa Isah zai auri Shuhuda a yadda ma suka zo Katsina tare shaida ce ta cewa sun aminta su zamo ma aurata. Abinda ya ke bashi mamaki ma ta yadda akayi duk labarin da ya bashi game da yarinyar da ya ke son suka faru akan kanwarsa Shuhuda. Uncle Hamza ya kama mustuke idanu, gani yake kamar abinda ya saba faruwa da shi ne na gizon da take masa, yau din ma gizon take masa, ba don haka ba, ta ya zai ganta da Musbahu mutuminda ya kasance abokinsa tun kuruciya, kuma suka san juna sosai? Isah ya kashe shirun da kuma al'ajabin ta hanyar zaunawa ragwab! Kan kujera yana cewa. "Ya kamata ku zauna sannan a tattauna duk abinda ya dace". Ba su bijirewa tayin sa ba, dukkansu suka zazzauna, amma al'ajabin ya ki boyuwa ko wanne ka dubi fuskarsa ka san yana cike da rudanin yadda aka yi hakan ta faru. Shiru na 'yan mintoci suka gilma kafin daga bisani Uncle Hamza ya dubi Musbahu ya ce. "Wai Musbahu da gaske ko kuwa a mafarki ne ka zo min da Shuhuda don ka sani a rudani? Idan da gaske ne, taya ka samo Shuhuda har ka kawo min ita a cikin gidana? Ka yi min gamsasshen bayani da zai fitar da ni daga rudanin da nake ciki, don na gaza fahimtar a matsayin da zan dora wannan rudadden al'amari". Musbahu ya matsa kusa da Uncle Hamza, ya ruko hannunsa yace . “Ina tunanin ruko hannunka da na yi ka ji dumin hannuna ya is ya tabbatar maka a ido biyu muka bayyana gabanka. Sai dai kamar yadda ka samu kanka cikin rudani mu ma ka saka mu a rudani. Amsa day ace wadda zata warware tambayoyi masu yawa a lokaci guda. Shin mai ye alakarka da Shuhuda. Itace yarinyar da kake so a makarantar da ka ke koyarwa can jihar kano? Ita ce yarinyar da kake zrgin aljana ce, wadda kanwar mahaifinka ta kira MAYYA? Wadda kake kokarin yi………..” Uncle Hamza ya daga masa hannu cikin sarewa, y ace. “Tsiyar dan Nigeria kenan. Ya ce zai maka tambaya daya,amma saiya jero fiye da goma ba tare day a bari ka amsa masa daya ba”. Isah yace, “ina ganin manufar hakan warwarar lamari ne ko?” Ba tare da Uncle Hamza ya bari Musbahu yayi Magana bay a ce, “Shuhuda it ace dalibata wadda na koyar daita karatu a MARIAMA AJURI reshen jihar Kano. Maganar ina zargin aljana ce bat a taso ba.domin ina da tabbacin mutum ce kamar kowa. Haka maganar cewa ita mayya ce har tayi sanadiyyar mutuwar wasu bayin Allah ban yarda ba,saboda kwararrun hujjoji na. Da ace Shuhuda zata zamto mayya ba zamu shafe shekaru uku da ita ba tare da ta lashe kurwata ko wani a gabana ba. Na yarda na amince dukkan wanda ya rasu ake zargin Shuhuda ce sanadi mutuwa ce ta Allah da Annabi. Wadda ko wane bawa yak e hawa siradinta da zarar lokacin amsa kira yayi.” Bayan karshen bayaninsa, Shuhuda ta fito da idanu waje, ta ce. “Uncle n ice za ka aura?” ta dafe kirji, ta ce. “Na shiga uku ni Shuhuda, aure kan aure? Aure da ci……” maganar ta makale sakamakon tangadi da suka ga ta na yi alamar za ta fadi. Nusaiba tayi saurin tallafar ta, idanta biyu tangaram babu alamar suma ko mutuwa a tare da ita, amma tan a cikin yanayi na fitan hayyaci. Su din ma hankalinsu ya tashi matuka. Sai dai Musbahu ya dauki maganarta akan labarin day a sani na cewar Isah zai aure ta. Su ma Isah da Nusaiba duk haka su ka fahimta, amma shi Uncle Hamza sam shi bai fahimta ba, abin daya dauka shi ne, har yanzu Shuhuda na nan da SHIRMENTA! Nusaiba ta soma girgizata tana cewa. “Shuhuda! Shuhud!!” Ta bude ido fayat tana kallon Nusaiba, hakan ya tabbatar wa Nusaiba ba suma tayi ba, don haka ta sauke ajiyan zuciya tare da jin wani sanyin dadi. Musbahu ya dubi Uncle Hamza murya a sarke cikin tsananin sarewa y ace. “Malam ina me baka hakuri ka taushi zuciyarka, ka sa lumana a dukkan komai, ka yi hakuri ka karbi Zuwairiyyah a matsayin matar da Allah ya zaba maka ka rabu da soyayyar Shuhuda tunda a halin yanzu an bada ita ga Yayanta!” Cikin firgici Uncle Hamza yace. “Ga wa aka bayar da ita? Yayanta Yakubu? Shi yasa dama y ace min auren zumunci za a mata , ashe shi ne mugun?” Musbahu ya nuna masa Isah yace. “Ka ga wannan, shi ne aka bai wa ita, sunansa Isah, bata da wani yaya Yakub”. Uncle Hamza y ace. “Ya za a ce min bat a da yaya Yakub, bayan shi ya fara burbusamin ba za a bani aurenta ba, saboda yasan anyi min katobara?” Isah da Musbahu suka dubi juna, su dai sun san duk cikin family din su ciki da bai basu da mai suna Yakub, amma ya cije akan wai wani yayanta Yakub ya sanar da shi ba za a ba shi aurenta ba. Shuhuda t ace. “Uncle Hamza da gaske kake za ka iya………” Nusaiba ta yi saurin rufe mata baki, tana gudun kada ayi abin kunya, tun da ta fuskanci tan a son ta aminta da soyayyar Uncle Hamza bayan ga Isah wanda ke sonta tun tana jinjira. GIDA BE KOSHI BA. Ai bai kamata a bai wa DAWA ba. Kuma ko banza Isah shi ne wanda zai riketa bias gaskiya ba tare da ta fuskanci tsangwamar dangin miji ba. Sabanin Uncle Hamza da tun kafin ya aure ta an soma kiran Shuhuda da MAYYA. Duk mutumin da aka kira nasa maye ba karamin bakin ciki zai samu kansa a ciki ba. Wannan babban cin zarafi ne. dan haka koda Shuhuda na son Uncle Hamza kuma tana da burin auren sa, in shaa Allahu zasu ruguza abun, ba zasu bari taje inda za a dinga jifarta da miyagun kalamai ba. Uncle Hamza ya ji wani takaici ya tokare masa a makoshi, wannan wane salon rainin hankali ne su Musbahu suka zo masa da shi? Sai ya dinga zargin mafarkin dai ne yake yi, hakika duk abinda ke faruwa a mafarki ne, yanzunnan zai bude idanunsa ya ga komai ya koma a matsayin mafarki. Don karfin hali hard a rufe idanunsa, ya bude cike da fatan hakan ya zamo a mafarki, amma hakan bai samu ba, domin suna zaune a gabansa kamar yadda ya barsu a lokacin da zai rufe idanunsa. Wannan al’amari da me yayi kama? Shuhudan da yasha mafarki ta zama matarsa har m da ‘ya’ya a tsakaninsu it ace ake ikirarin an baiwa wani ita? Shin meye ribar wahalar sonta da yake sha? Shike nan ya tashi a tutar babu? Ya watsawa Nusaiba harara cike da takaici, y ace. “Ki barta ta fadi abunda zata fada mana”. . Ko me zata pada, oho! Sai ku canka!!!!!!! Taku har kullum Sadiq Halima(Sadin Mama) 'yar Anty lol.... ausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤23¤¤ Isah ma ya harzuka, shi ma ya san Shuhuda niyyar maida masa zance ya kwana take, shi dama tuni yasan ta taba yin soyayya, dama ya yi has ashen wani dalili ne ya sad a yayi mata bayanin soyayyar ta kama yi masa kuka, har tana ikirarin ba zata iya soyayya ba. To yau dai an yi walkiya ya ga komai tangaram! Babu inda za alayance masa, hakan ma ne ya darsar da kishin nasa wanda yak e da shi na halitta, a harzuke ya dubi Musbahu y ace. “Ya kamata ka tashi mu koma, don ko da ace ba ni zan auri Shuhuda ba, ba azan bari ta yi aure a inda za a wulakanta tab a. Shuhuda amanita ce, b azan saurarawa duk wanda zaici zarafinta ba”. Uncle Hamza ya dubi Isah ido tsakar kai yana mamakin yadda Isan ya yake yana wannan cika da batsewa, ya tuna lokacin yaje wurin Alh. Sada ya karbe shi hannu biyu, amma bai ba shi dammar kadaicewa da Shuhuda ba har sai ta kamala sakandire dinta. Haka Yayanta Yakub ya amince masa aurenta da farko. Sai yanzu da kaunarta t agama mamaye masa zuciya sannan za a nemi a tarwatsa masa rayuwa? Ina! Ba zai lamunta ba. Ya dai fahimta Shuhuda na sonsa, wanda dama hakan shi ne ribarsa, saboda haka zai nuna KWANJINSA don karbo soyayyarsa da ke barazana kubucewa. Muryarsa babu kyawun amon sauti y ace, “Malam ka taka a sannu, don kana neman aurenta ba wai ka aureta ban e. Shuhuda tana da dammar da zata zabe ni ko kai, don haka ka sanyawa ranka mun yi gamayya akan son abu daya, kowa tasa ce zata fisshe shi, amma b azan juri cin zarafi ba, don ban ma sanka ba, ba zaka ci mutunci nab a, ok?” Maganar ta batawa Isah rai, y ace, “Duk abinda ya samu kuda shi ya jaw a kansa, idan kuma hankaka yana yin dan kansa ga fili ga mai doki”. Hankalin Musbahu ya tashi, saboda yadda ya ga kowanne yana muzurai tamkar zasu rukume da kokawa, da sauri ya mike tsaye ya dubi Shuhuda. Yace, “Ku tashi mu tafi”. Ya maida kallonsa ga Uncle Hamza, y ace, “Malami ka yi hakuri, mu bakinka ne kada kayi fushi dam u”. Isah ya ja wani dogon tsaki y ace, “Hkurin me za ka bashi? Kai baka san muna da hakki a gurinsa ba? Ko yanzu bari ganin yana abokin ka idan yakama mu nemi hakkin mu, waLlahi sai mun nema sai muji ta yadda aka yi Shuhuda ta zama mayya”. To a nan Uncle Hamza bai iya tankawa ba, illa wani mugun kallo day a ke watsawa Isah, ji yake a duniya babu wanda ya tsana sama da Isah, da ace za a bawa wani dammar kashe wani ba tare da zunubi akan wanda yayi kisan ba, hakika da zai iya dauke Isah, saboda shigar hanci da kudundunen daya soma yi masa.Gaba dayansu suka mike tsaye, Shuhuda idanunta taf da hawaye, suka fice daga gidan. A cikin mota Isah n eke ta yarfa uwar masifa, yana kyamar tsatson Uncle Hamza tunda har suke jifar Shuhuda da miyagun kalamai irin wannan. Musbahu ne kawai yake tausarsa, a haka har suka isa gida. BABI NA GOMA SHA DAYA ANYA KUWA? Misalin karfe goma da rabi na safiya su Isah sun gama shirinsu, Haj. Asmo da iyalenta su ka rakosu har bakin mota, Musbahu na tsokanar Shuhuda. “Ke bakauya sai ki shirya ina nan zuwa Kano neman aurenki, tunda nag a kowane tsuntsu ma hawa bishiyar yake”. Isah ya auna masa sakon harara, y ace. “Sai ka maida niyya, albishir daya zanyi maka, kafarda ta kaika Kano neman auren Shuhuda, ba ita zata maido ka ba”. Nusaiba tana dariya, t ace. “Kai ma yaya Musbahu da taya dora bari kake, ina kai ina wannan yariyar mai shanyayyar kafa? Ai ka wuce ajinta, kana ganin ko iya daura zani bata iya ba”. “Musbahu ya fashe da dariya, y ace, “Ai dama ba neman mai saye ake ba”. Haj. Asmo t ace, “Kai idan zaku tafi ku tafi, kada ku tsaya yi min shirme”. Ta mayar da dubanta ga Shuhuda t ace. “Idan kun isa kya gaishe min da Haj. Karimar Allah Ya sauke ku lafiya”. Su ka amsa mata da ”amen”. Yayinda suka shige cikin motar suka tafi. Suna tafiya a motar da farko babu wanda yake Magana, sai daga baya da tunanin ya yiwa Isah yawa, yasan kuma Shuhudan ce kadai zata iya amsa masa tambayoyin da yake da su, don haka ya dago kai ya dube ta. Kanta a rusune yake a kasa, tana kallon yatsun kafarta. Yace. “Shuhuda!” Ta dago kai kadan tana dubansa. Ya ci gaba da cewa. “Waye Yakub?” Ya daga mata kai. “Eh, domin a maganganun malaminki ya ambaci wani yayanki Yakub, ni kuma a sani na duk tsatsonmu bamu da Yakub, sai nake tunanin ko daga dangin mahaifiyarki ne?” Ta girgiza kai, tukunna t ace, “A’a, ni sam ban san waqni Yakub ba, ni ma nayi mamaki da na ji y ace waqi wani yayana Yakub”. Yadda ta yi maganar akwai alamun gamsarwa a ciki, don haka ya yarda haka din ne, soki-burutsu ne da zafin rabuwa da masoyi ya sa Uncle Hamza ambatar sunan Yakubu a cikin maganganunsa. To amma fa akwai alamar tambaya, kuma akwai aiki ja agabansa, saboda ya lura kamar Shuhudan tana son Uncle Hamza. “Shuhuda wai da gasket kin san Hamza yana sonki? Ya jefa mata wannan tambayar a ba zata. Ta girgiza kai, t ace . “Eh, ya taba fada min wai ya je gidanmu bayan ya je gurin Babanku ya zo namu gidan ya hadu da wani yayana Yakub ya sanar da shi yana son aure na. Sai dai ni ban dauki maganar da muhimmanci ba, saboda nasan duk gidanmu bam u da Yakub, watakila gidan su wata Shuhudar ce ya je ba niba”. Ya dan samu nutsuwa kadan a zuciyarsa, ya ci gaba da cewa da ita. “To ya ni kuma fa?” Ta ce “ban gane ba?” Ya dan juyo kadan yana kallonta, yace, “Ma’ana soyayyata a gareki”. Ya karashe maganar yana mai langwabar da kai. Tayi murmushi, t ace, “Ai kai ne masoyina, me kake tantama?” y ace. “Na sani ko za a so wani bare akan na gida?” Sai ta kama dariya, t ace. “Yaya Isah kenan, wani lokaci RANAR NAKA………. Sai naka, wani lokacin kuma BARE ke zama NAKA”. Ya dubeta cikin rashin fahimtar inda ta dosa da maganarta, y ace. “Ban gamsu ba” . . Toh pa, ni dai nace na gamsu, don Shuhuda sai bare wato MAI JAR KOMA! Lol . Ta ce, abin da nake nufi a nan shine, wani lokaci zaka ga bare shi yake SADAUKAR da komai na rayuwarsa akan abin da yake so, amma sai ka gad an uwa ya kwanta rashin lafiya wadda yak e bukatar jinni amma duk cikin ‘yan uwa sai a rasa wanda zai iya sadaukarwa ya bayar da jininsa. Ka gamsu?” Yayi murmushi, y ace,..... da Hausa Book stories MATA’UL-HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤24¤¤ Ya yi murmushi, y ace. “Na gamsu, sai dai ki sani bana daga cikin wadannan mutanen……….” Ta katse shi da cewa. “Kash! Ba ba nufi na ken an ba, kuma ai ba a san mai cin tuwo ba……….” Yana dariya ya karshe mata Karin maganar cewa. “Sai miya ta kare , amman kin san hasashe da tsinkaye na sa makeri yunkurin narka karfe ba tare da yana da tabbacin hakansa zata cinma ruwa ba ko?” Ta ce, “A’a, dutsen day a ke cikin ruwa ai bai san ana rana ba, don haka ka daina ma tunanin akwai wani babban shamaki a cikin soyayyarmu”. Ya girgiza kai cike da jin dadin yadda yadda ta karfafa masa gwiwa, y ace,. “To Allah Ya shige mana gaba”. Ta amsa masa da . “Ameen”. Y ace, Yadace a samara min kyauta ta musamman wadda zan gain na rinka jin dadi”. Ta yi dariya t ace masa”. “Kyauta? Sha kuruminka, zan maka kyauta ta bajinta mai matukar muhimmanci”. Yace, “Wace kyauta ce haka mai muhimmanci?” Tace Dan mutum! Ko ba ka so na samara maka da?” Ya juyo dube ta, wani sanyin dadi ta ratsa zuciyarsa tunda har tana yi musu fatan samun sanyi idaniya. Y ace, “Allah Ya kaimu lokacin”. Bata amsa ba, sai tayi hamma. “Y ace ya dai? Bacci ne, ko yunwa?” Ta ce, “Ina jin bacci ne, don jiya ban samu bacci ba”. “Yace mai ya hana ki yin bacci?” Yayi tambayar zuciyarsa akuntace, don yayi has ashen tunanin Uncle Hamza ne ya hanata bacci. Tce, “Naje wani taro ne”. Ya juyo ya dube ta, y ace. “Taro? Wane irin taro, kuma a ina? Ta ce, “Ni ma ban san wane irin taro ba, kuma ban san gurin ba”. Ta ce, “Eh kasan akwai abin da za ka yi kai kanka ba kasan me ka yi din ba”. Ya girgiza kai, y ace.”A’a, na fi aminta cewar, kin yi mafarki ne, ko ba haka ba?” Ta ce, “Ina tunanin mafarki amma ni da nasan ban kwanta bacci bay a zan aminta mafarki na yi?” ya ce, “Hakan yana iya faruwa, wata kila saboda gajiyar hanya yasa kika fita hayyacinki har bacci ya sace ki baki sani ba, a cikin baccin kuma kika yi mafarki ana gudanar da wani taro da ke. Sai muyi fatan Allah Ya sa taron alkhairi ne”. Ya karashe maganar yana kallon hanya, yau ji shiru ba tanka ba, sai ya dan waigo, ya yi katari da ita tana sharer bacci. Murmushi kawai ya yi, yasan har yanzu akwai gajiya a tare da ita, ya ci gaba da tafiya akan titi cikin nutsuwa da kwarewa. Suna isa Karare ya juyo ya dubeta, har lokacin bacci take yi, ya ambaci sunanta, ba ta farka ba sai ya kai hannu ya dan bugi cinyarta. Da sauri ta bude ido kamar ta tsorata. Ya yi murmushi y ace,”Sha bacci ko?” Sai ta kuma dube-dube kamar ba ta yarda da kanta ba. Ta ce. “Ya na ganmu a nan?” Y ace, “To a ina dama za ki ganmu? Ko so kika yi ki tashi daga baccin ki ganki cikin gida?” Sai ta yi gum da bakinta. Ya ce, “Nuna min hanyar gidan”. Ta dinga nuna masa yana shiga lungu har suka isa kofar gidan Alh. Jamilu, ya tsayar da motar Shuhuda ta fito fuskarta ba yabo ba fallasa ta taryi yaranda suka fito da ga gidan suna yi mata sannu da zuwa. Ta kama hannun Amira zuwa cikin gidan, Isah ya dade a cikin motar bai fito ba yana kallonta har ta shige cikin gidan. Sannan ya sauke ajiyar zuciya yana auna matsanancin son da yake mata. Lokaci daya haduwarsa da Shuhuda Ibn khaddab a birnin Misra da kuma jiya da suka hadu a gidan mai ta nuna bata sanshi ba sam. Abin duk ya dawo ya zauna masa a ransa daram! Yaran suna da salon barkwanci a cikin lamarinsu, abinda ya ayyan ke nan a ransa. Sannan zuwansu gidan Uncle Hamza da abinda ya faru shi ma ya dawo masa. A bayyane ya ce. "Zan sadaukar da komai na rayuwata don ganin na kwalaka a kasa, domin ni na sha wahalar sonta tun tana cikin tsumma, tun bata mallaki hankalin kanta ba, har zamana cikin jajayen kunne bai sauya zuciyata daga alkiblar sonta ba...." Shuhuda ta katse masa zancensa yayinda ta sunno kanta a tagar motar tana murmushi ta ce, "Yaya, ka shigo mana ka tsaya a mota?" Bai ce komai ba ya bude motar ya fito ya bi bayanta zuwa cikin gidan. Haj. Karimatu ta karbe su hannu bibbiyu, kuma taji dadin yadda ta ga Shuhuda da Isah sun hada kansu, sika shigo mata da tsarabar da suka zo da ita. Alh. Jamilu ya dawo cin abincin rana ya tarar da bakin nasu. Ya dubi Shuhuda ya ce. "Ni kam bana marhabin da zuwanki tunda kinki zama da mu". Shuhuda tayi murmushi kawai, shi kam yana son ace Shuhuda ta dawo gurinsu da zama ko don yadda ya ke ga Haj. Karima na bukatar hakan, musamman tunda ya aure ta bata taba haihuwa ba. Amma da ya ke ita mace ce ta gari, sai ta rungumi 'ya'yan da Binta ta fita ta bari tamkar 'ya'yanta. Haj Karima ta ji dadin karar da ya nuna mata, ai a so naka ma wata martabace. Isah ya karbe zance da cewam "Ai yanzuma sai da na tursasa mata ta zo". Shuhuda ta juyo da sauri, ta ce. "Kai Yaya kar muyi haka da kai, ni fa na ce maka mu zo nan din". Shima sai ya auna mata harara cikin sigar wasa ya ce. "Kun ji ta da son kai". Alh. Jamilu ya ce. "To na ji ko ma ta ya akayi kuka zo munji dadi, kuma mun gode". Ya soma nufar dakinsa, Haj Karima ta bishi a baya. Sun sha yini a kauyen karare, sannan daga bisani suka yi haramar tafiya kano, Alh Jamilu ya ce. "Ai na dauka zaku yi mana sati". Isah ya girgiza kai, ya ce. A'a, dama cewa muka yi bari mu zo mu gaisheku". Ya ce, "To madaLlah". Ya dauko kudi zai ba su, sai Shuhuda tayi saurin cewa. "A'a Baba ka barsu, ai ga kudi can mun ba Umma ta baka sako daga Alh". Isah ya cika da mamaki, da yaushe Alh ya bawa Shuhuda kudi shi bai sani ba? Amma sai ya basar, shi kuwa Alh Jamilun sai zuba godiya yake yana cewa. "Allah ya kara girma, ai kyautar dattijai ba a mayarwa". Haka suka yi musu sallama suka tashi. Sun soma tafiya a motar, Isah ya ce. "Wai ke na tambayeki". Tayi shiru bata tanka mishi ba. Ya ci gaba da cew. "Yaushe Alhaji ya ba ki sakon kudi da kika bayar?" Ya ji shiru ba ta tanka ba. Sai ya dago kai ya kalleta, ya ce. "Kina ji ina yi miki magana amman za kiyi shiru ki kyaleni?" Har yanzu ba ta tanka ba, ranshi ya sake baci, sai ya faka motar a gefen hanya ya juyo gaba daya yana kallontta. Fuskarta a daure ta ke tamau kamar ma bata damu da shi ba. Ransa idan ya yi dubu ya baci, cikin kakkausar murya ya ce mata. "Shuhuda ba magana nake yi miki ba ki ka yi banza da ni?" Ta dago kai ta ce. "Me ka ce?" Ya hasala da maganarta, ya ce. "Wannan wane salon rashin kunya ne haka?" Ta ce "kai ka ji ni dai Isah, me nayi na rashin kunya?" Baki ya hangame yana kallonta cike da mamakin abin da ya fito daga bakinta, sam ba ta damu da abin da ta fada ba ko ya bata masa rai ko bai bata masa ba, ita dai ba ta damu ba. Ya ce. "Tambayarki nake, yaushe Alhaji ya baki sako ban sani ba?" Ta murguda baki ta ce. "Kuma lallai idan zai aikeni sai ka sani tunda kai kadai ne jikansa mai 'yanci?" Ya kara hawa sama ya ce. "Ko ba ni kadai ne jikansa ba, ai naga tare muka fito da ke ko? Ya akayi ban ga lokacinda ya baki kudin ba?" Ta ce, "Idan zai bani wani abu ne? Me kake nufi? Ni fa ban son shiga sharo ba shanu, ina ruwanka?" Ya jinjina kai yana kallonta, ya ma kasa tofawa, sai kawai ya ja motar suka tafi ko wanne na hura hanci. . BABI NA GOMA SHA BIYU GA KOSHI GA KWANAN YUNWA Alhaji Rabi u yana zaune a dakinsa rike da carbi yana lazimi, Isah yayi Sallama ya shigo fuskarsa a daure. Zaunawa yayi akan kujera, yayinda Alhaji Rabi u ya dago kai yana murmushi, ya ce. "Ya akayi ne mazajen? Na jiyo muryarku kuna shigo wa". Isah ya dan saki fuska kadan, ya ce. "Barka da yini". Alhaji Rabi u ya amsa masa. "Yauwa, an dawo lafiya?" Ya ce "lafiya, suna gaishe ku". Alhaji Rabi u ya ce, "Muma muna amsawa". Isah ya gyara zama sannan ya ce. "Alhaji Jamilu ya ce ayi maka godiyar kudin da ka aika masa dasu ta hannun Shuhuda". Alhaji Rabi u yayi murmushi ya ce. "Babu komai ai shi magidanci komai kudinsa yana bukatar taimako, bare kuma irin Alhaji Jamilu, Ni kam bani da bakinda zan yi masa godiya akan rikon da yayiwa Karimatu, tunda ya aure ta dai-dai da kwana daya bai tab kawo min korafinta ba, haka itama, ba kuma taba jin ance anje gidansu da yaji ba". Ya karashe maganar yana alhinin rabuwa da Karima a cikin ahlin gidansa. Isah ya gaza yin hakuri, ya ce. "Wai Alhaji yaushe ka bawa Shuhuda sakon kudin? Kuma mai yasa baka bani ba a matsayina na miji?" Alhaji Rabi u ya dube shi da yanayin rashin fahimta, ya ce. A a, don zan bada sako dole sai a gabanka, ko kuwa kai kadai ne dan sakona? Jin yadda Alh. Rabi u yayi maganar kamar acikin hasala ne, sai bai ji dadi ba, kuma dai gaskiyar Shuhuda ne, ai ba shi kadai ba ne jika ga Alh. Rabi u, to don me zai damu kansa akan an bawa Shuhuda sako ba shi ba? Ko da yake ai wani bangare dole ne ransa ya sosu, ai shi na miji ne, dama gaba ya ke da Shuhuda, zai di kyautuwa ace shi aka damkawa duk wani sako, ko don ta girmama shi, a'a duk ba ta wannan ba, me yasa lokacinda za a bada sakon ba a bayar a gabansa ba, kuma ba a sanar da shi an bata ba, sai dai kawai yaji ta bada sakon, me hakan ke nufi? Muryar Alh. Rabi u ta katse masa tunanin da yake. "Isah kada dai ka ce min kana daga cikin mutane masu kyashi ga 'yan uwansu? Ai ko kana daga cikin irinsu bao dace ka nuna kyashinka ga Shuhuda ba. Musamman idan kayi la akari nan gaba kadan zata zamto mata a gareka, ka ga kuwa,wannan hali bai dace da kai ba sam". Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤25¤¤ Da sauri Isah ya girgiza ka, ya ce. "Ba haka nake ba Alh, sam ban kyashi akan ka nunawa Shuhuda soyayya, ai ita ma jika ce gare ka, kuma marainiya. Shi kam maraya ana son a na son a nuna masa kauna a sarari ko don kada maraici ya dameshi". Alh. Rabi u ya saukar da ajiyar zuciya ya ce, "Ko da naji, kasan zamanin ne ya lalace, sai ka ga dan uwa yana kyashin dan uwansa ya samu ci gaba, Musamman ga mata da miji, idan ya kasance matar ta fi mijin samun hanyoyi alkhairi, sai ka ga mijin na nuna mata tsana duk saboda haka, baya tunanin ko wane Dan Adam da hanyar arzikinsa". Alh. Rabi u ya kawar da wannan hirar, ya dora da cewa. "Ya maganar tafiyarka Ibadan?" Isah ya ce, "Tana nan, mako mai zuwa zan tafi". Alh. Rabi u ya ce, "To sai a kula, a san mutumcin kai da kiyaye addini. Nasan san ka mutum ne mai yawan ibada, saboda haka sai ka dage kada kayi watsi da addu a domin addu a takobin mumini ce, duk wanda ya juri yin addu a a rayuwarsa ba zai tabe ba". Nasiha mai ratsa bargon jiki Alh. Rabi u ya yi wa Isah, sannan daga bisani sukayi sallama, isah ya fice daga dakin. Kwana hudu sam Isah Isah ya rasa kan Shuhuda, ba ta kulashi, idan tana zaune a falo da zarar ya shigo sai ta tashi ta shige kuryar daki. Shi bai ga abin fushi da bata rai ba akan wannan dan sabanin da suka samu ba. A ganinsa tunda har rashin fahimta ne ya kamata ta tsaya ta saurare shi, amma ta kiya, ta ki yi masa uzuri a matsayinsa na dan Adam wanda yake da yawan ajizanci. To sai bai nuna mata ya damu da wannan hali da ta kirkiro musu ba, amma ya damun fushin nata na nukurkusar mai zuciya. . KUNGA MAZAN KIRKI, BA IRIN SU 'O'O BA! lol.... (Sadin mama) . Ana yau gobe zai tafi Ibadan yana zaune a falo shi da Inna Yaduwa suna hira wani yaro ya shigo. "Wai ance ana sallama da Shuhuda" Isah da Inna Yaduwa suka dubi juna duba na mamaki isah ya dago kai ya dubi yaron ya ce. "Waye ke nimanta?" Yaron yace. "Wai inji Hamza ne". Isah ya bata rai ya ce da inna yaduwa. "Wani malamin makarantarsu ne yake neman ya shigar min hanci a kudundune, haka fa da muka je Katsina ya nemi tarwatsa mana farin ciki". Inna Yaduwa tayi shiru bata ce komai ba, yayinda Isah ya dubi yaron ya ce. "Ka je ka ce bata nan". Har yaron ya juya zai fita, tsallam! Shuhuda ta fito daga daki tana tsayar da yaron. "Ka ce masa ga ni nan zuwa". Inna Yaduwa da Isah suka sake kallon juna, yaron ya fice yayinda Shuhuda ta koma daki ta dauko gyale ta fito falo, ta nufi hanyar fita. Inna Yaduwa ta ce. "Ke Shuhuda ina zaki je? Ca na ke ance baki nan? Shuhuda ta juyo tana kallon Inna Yaduwa fuskarta a daure ta ce. "Yo mutum ya zo nemana sai ace masa bani nan, bayn kuma ina cikin gidan don kawai a raba hanta da jiji?" Inna Yaduwa ta ce "Amma tunda an bayar da ke, maiye amfanin tsayawa da wani?" Shuhuda ta ce, Ni fa ba zan auri mutuminda yake da tsattsauran ra ayi ba, mutuminda komai sai ya tuhumi mutum". Isah ya langwabe kai, yasan har yanzu fushin ne bai sauka ba. Inna Yaduwa ta ce, "Ai shi zaman tare haka ya gada, dole sai anyi hakuri da juna, kuma ina amfanin mace ta auri mijin da baya tuhumarta akn abubuwan da suka shafe ta? Idan ba ta haka ba ta ya zata samu ingatacciyar rayuwa?" Bata tsaya sake tofawa ba, ta sa kai ta fice abinta. Inna yaduwa tace da Isah. "Wai me yake faruwa ne haka?" Shiru Isah ya yi gabadaya wutarsa ta dauke, kada fa abin ya zama da gaske, Shuhuda ta daina sonsa,tana son mutuminda bai dace da rayuwarta ba, mutuminda zai kai ta cikin tsatson da za a dinga aibatata. Tsayin lokaci shi da Inna Yaduwa suna yanayin shiru, daga bisani kamar wanda aka tsikara da tsinken allura, firit ya mike tsaye ya nufi kofa, Inna Yaduwa ta ce. "Ina zaka je?" Ba tare da ya juyo da dubansa gareta ba ya ce. "Ina zuwa". Ya fice. Tun daga nesa ya hango Shuhuda da Uncle Hamza sai faman dariya suke alamu da ke nuni suna jin dadin hirar da suke. Wani abu mai kaifi (kishi) ya soki zuciyarsa, ya tsaya kamar ba zai karasa ba, sai kuma ya ci gaba da takawa cikin kasaitaccen takunsa wanda duk wanda zai yi tozali da shi zai tabbatar nagartaccen namiji ne, domin Isah namiji ne mai kyakkawar shiga game da cikar haiba. Cikin takunnasa ya isa inda suke zaune akan fararen kujerun roba, a gabansu akwai yalwar korayen ciyayi (grass carpet) don haka gurin sai tashin kamshin ciyayin yake. Lokacin da ya isa, su duka biyun sai suka gumtse fuska, dariyrsu ta dauke a lokaci daya. Isah ya mikawa Uncle Hamza hannu da nufin suyi musabaha a matsayinsu na Musulmai su duka. Uncle haamza bai tsallake tayin ladar da aka masa ba, ya mika masa hannu suka yi musabiha, daga bisani Isah ya dora da cewa. "Ban so ka kasance cikin mutane masu taurin zuciya ba, ta hanyar yin nema cikin nema, wanda ko a musulunci ya haramta". Uncle Hamza ya ce kamar yadda ban so kai ma ka kasance cikin mutane marasa yiwa soyayyar gaskiya uzuri ba" Isah ya ce. "Ai babu uzuri ga abin da aka san haramtacce ne". Uncle Haza ya dan yi malalacin murmushi, ya dora da cewa. "Idan haka ne sai na ce ni aka yiwa hawan kawara, aka naushe ni kuma ake son a hanani zubar hawaye". Cikin takaicin maganarsa Isah ya ce, "ita ZUCIYA MUGUN NAMA ce, idan mutum bai dace da zuciya ta kwarai ba sai ta hada masa ZAFI BIYU, na radadin zuciya da kuma na kaskanci, don haka sai a yi ta ganin mutum yana abubuwa wanda basu dace ba, amma shi da yake bai dace da zuciyar ta kwarai ba sai ya ga duk abin da yayi dai-dai din ne a gareshi". Maganganun Isah masu shiga zuciya ne, da kuma zafafata, to amma sai Uncle Hamza ya bude baki da nufin mayar masa da martani cikin sanyayan kalamai, kafin yiwuwar hakan Shuhuda ta riga shi da cewa. "Yah Isah amatsayinka na yayana bai kamata kayi min wannan rashin adalcin ba, ina hira da wanda na ke so ka zo kana jifarsa da gugar zana. Ai ai ita mace uzuri ake yi mata, musamman da ya kasance na fada maka, ba zan iya auren mijin da zai jefa rayuwata cikin takura ba. Dona haka ka saurara mana, ka daina shigar min rayuwa".Gaba daya jijiyoyin sadar da magana da suke aiki a jikin Isah suka tsinke saboda jin maganganun da Shuhuda ke amayarwa a gare shi. Ba shi da abin da zai iya fada mata, saboda haka ya juya ya koma cikin gida cike da kuncin zuciya. Bayan tafiyar Isah daga gurin, Uncle Hamza ya dago kai ya dubi Shuhuda, ya ce. "Yayan nan naki yana da tsananin kishi, wanda kuwa bai dace da shi ba, domin mace idan tana budurwa, ma'ana tana a gidansu ba ta yi aure ba, kakarin da zaka yi ka kimtsa soyayyarka gare ta, wannan shine babban kishi mai amfani. Idan ka aure ta kuma sai ka nuna kishinka ta hanya wadatata da dul abin da yake hakki gare ka. Ka yarda da ita don gudun zargi kada ka ganta da dan uwanta ka zari wani abu". . TOH PA MAZAN WANNAN GROUP! Da patan kun ilmantu!!! . Shuhuda ta jinjina kai, hirar da ba a karasheta cikin dadin rai ba ke nan. Suka yi sallama ta koma cikin gida. Inna Yaduwa ta watsa mata wani mugun kallo, yayin da Isah yake zaune kansa a sunkuye, gabaki daya ba shi da sukuni . Shuhuda ta ce. "Kinga ni ban san harara ba sai kwayar ido ta fado. Haka kawai a takurawa rayuwata, in bacin tausayi da kuma shakuwa da tuni ba a kaddamar da mutum ba, amma sai a takurawa mutum a hana shi rawa gaban hantsi? Wallahi ba zata sabu ba bindiga a ruwa, ba zan juri wannan matsin ba, don ba da ni za a yi gamin gambizar nan ba". Inna Yaduwa bata tanka mata ba, Shuhudan ta shige daki. Isah ya mike tsaye ya dawo kusa da Inna Yaduwa, murya a raunane ya ce. "Inna ki taimaki rayuwata, wallahi Shuhuda ita ce zabina, matsawar na rasata hakika na rasa wani bangare na daga farin cikina. Ina son Shuhuda Inna, itace burin rayuwata, ki taimake ni kada na rasa ta!" Yanayinsa gaba daya ya sauya zuwa launin tausayi kallo daya zaka yi masa ka fahimci tsananin son da yake yiwa Shuhuda, wanda dama shi so na gaskiya ba ya buya, a cikin farin ciki ko akasin haka kake. So na gaskiya ba zai taba boyuwa ba. . Hmm, Isah da badan sunan ka ba, sai ince Sadin Mama zata yi da kai, amman ba laipi idan zaka canza zuwa sunan larabawa.... Lol . Isah kam yana son Shuhuda har cikin kalbinsa, ta zame masa NURUL KALBI, ta zame masa tauraruwa mai haske da kyalli, ta zame masa mahadin rayuwarsa idan kuwa ya rasa soyayyarta tabbas ba karamin rashi ba ne a gareshii. Cikin tausayawa inna Yaduwa ta ce. "Isah shawara zann baka ka yi hakuri da Shuhuda ka nemi wata". Tar! Tar!! Kwalla suka suka zubo masa, cikin sanyin jiki yana girgiza kai ya ce. "Bazan iya ba Inna, ba zan iya rabuwa da Shuhuda ba idan kuwa har zan iya rabuwa da ita, to hakika ba ta a doron kasa ne". Tausayinsa ya kara narkar wa Inna Yaduwa zuciya, ta ce. "Ba ka lura da abin da na ke so ka lura da shi game da yarinyar nan ba. Akwai abubuwa da yawa da suke faruwa wanda yasa nake tababa.........." "Eh, ai ni mahaukaciya ce! Ba sai kin maimaita ba!" Muryar Shuhuda suka tsinkayo daga bakin kofa. Su duka biyun suka mayar da kallonsu gareta, fuskarta a daure babu ko digon fara'a. Sannan idanunta jajur sai ka ce jan gauta, babu wanda ya tanka mata, ta ci gaba da cewa. "Wallahi kuyi hankali da ni a cikin gidannan, ina nuna muku ni mai tausayinku ce, amma kun kasa fahimta. Duk ranar da na cire imani a kanku zaku sha mamaki.." Kausasan kalaman nata sunyiwa Isah tsauri, ya kasa jurewa ya mike tsaye tare da daka mata tsawa. "Don ubanki waye sa'anki a cikinmu da har zaki zo kina fada mana wadannan kalaman, ko don kinga ana kyaleki shi ne za ki juya mutane? To bari ki ji don na ce ina sonki ba yana nufin bani iya hukunta ki ba ne". . Su Isah MAZA!!! . Dariya ta fashe da ita. "Allah ko? To ga fili ga mai doki, idan har ka isa ka sanya hannu ka buge ni. Idan kuwa ka kasa baka haifu ba, ku....." Ya yunkura sai kai mata duka, inna Yaduwa ta yi saurin tare shi. "Kada ka dake ta, kyale ta da halinta". Ta juya ga Shuhuda, ta ce. "Ke kam ba ki ji dadin halinki ba, ace ba ki ganin mutumcin kowa a idanunki, rashin kunya da fitsara su kika sa agaba?" Kai tsaye Shuhuda ta ce. "Gadon gidanmu ne!" Inna Yaduwa ta ce. "Karya kike wallahi, duk gidan nan babu fitsararre, amma ke....." "To ya fa isa, kuma fitsara da rashin kunya yanzu na soma". Isah ransa ya kuma baci ga shi Inna Yaduwa ta hana shi dukan Shuhuda, sai kawai ya ficce daga falon. . Da kuwa Isah anga sarkewar hannu. (Sadin Mama). . Shuhuda ta ce. “Idan hark u masu zuciya ne kada wanda ya kara kulani a cikin gidan nan, kowa yayi abin da yake so ban hana ba”. Inna Yaduwa t ace da ita. “Ai mu ba kafurai ban e, bare mu zamo masu zuciyar kafurawa. Ke dai da kika ji zaki iya yin gaba dam u sai ki yi. Sai dai ina me tunatar da ke cewa, gaba dad an uwanka Musulmi haramun ce, bare kuma ga wanda suka zamo tsatsonki”. Shuhuda ta murguda baki t ace, “Sai ki yi, ni dai na fi karfin dauk wani mai hankali”. Tana karashe maganarta ta sanya kai cikin daki. Inna Yaduwa ta bi tad a kallo tana girgiza kai, halin Shuhuda yana bat a mamaki, da daure mata kai, wani lokaci ta fassarata zuwa mara hankali, wani lokaci kam gaba daya ta fi dangantata da aljana ba mutum ba. Wannan ke nan! BABI NA GOMA SHA UKU MURDADDIYA Isah ya tafi Ibadan cike da takaicin Shuhuda, a lokacin da zai tafi ma ko fitowa daga daki bata yi ba bare suyi sallama, shi ma bai damu da hakan ba don t agama kaishi bango, kiris ya rage ya fashe don haushi da takaicinta. Mamaki yake wai yarinya karama kamar Shuhuda ta iya wannan fitsara da cin fuska. Ba don Inna Yaduwa ta yi masa togaciya ba, da sai ya nada mata shegen duka inyaso gobe ma ta kiyaye harshenta. Shi yanzu baa bin da ta yi masa na juyawa soyayyarsa baya yafi damunsa ba, a’a mummunana halin da ta tsira. Ya sauka Ibadan cikin rashin walwalar zuciya, dama komai ya kammala na muhallinsa, da makullan ofis dinsa, don haka kai tsaye gidan da aka mallaka masa ya nufa, a unguwar Shasha, a layinda yak e gidaje ne jeer masu kyau da kayatarwa, komai na layin a shirye yake gwanin ban sha awa, haka cikin gidajen ma an saka duk wani abu na jin dadin rayuwa. Idan da akwai abin da zaka nema ka rasa a cikin gidajen, to ba zai wuce na abin da zaka ci ba, wanna hakkin duk mazaunan gidajen ne, kasancewa gidaje ne da masa’antu suka gina, kowace masa’anta idan ta dauki ma’aikaci sai tab a shi gida daya inda zai zauna. To shi Isah tun kafin zuwansa ma’aikatar da ta dauke shi aiki tuni t agama tanadar masa komai kan abinci, musamman da suka samu tabbacin a kasar da yayi karatu sun san cimar da ta dace da shi. Yana shiga ciki ya tarar da ma’aikatan da aka sanar da shi suna jiransa, ma’ana wadanda zasu yi masa hidima, wanki, dafuwar abinci da sauransu. Duk da basu sanshi a sarari ba, sai taswirarasa da suka sani a hoto, amma suna ganinsa suka gane shi. Gaba daya suka mike tsaye cike da girmamawa, gaisuwa da kawo kayan sha duk suka yi masa, sannan aka kai masa rowan wanka bandaki. Ya fito ya shiga bedroom ya tarar da duk abin da yake bukata na jin dadin rayuwarsa. Sai dai kash! Baya da jin dadin, hasalima jin kansa yake kamar ba shi ba. Washe gari ya soma fita gurin aiki, ofis kam yayi kyau, ya kuma matukar dacewa da shi. Kwana biyu yana cikin ayyuka na ofis, ranar na uku da daddare misalign karfe takwas na dare yana tsaye a barandar gidansa, sanye da pyjamas jajaye, don yana gama sallar Isha’I yayi shirin bacci ba don yana da tabbacin baccin zai yi ba, kawai yayi hakan ne don ya san babu inda zai kuma zuwa musamman a matsayinsa na bako, bai da wani wanda ya saba da shi. Kamar an ce ya daga kansa, sai kuwa idanunsa suka hango masa kyakkyawar fuskar dab a zai manta da ita ba, ta fito daga mota har tana kokarin bude wani gida daga cikin jerin gidajen da ke layin. Daram! Gabansa ya yanke ya fadi. “SHUHUDA IBN KHADDAB!” Ya fada a sarari cike da tsananin mamakin yadda aka fara ya ganta a nan. Lallai wannan yarinya shu’umar gasket ce, ba don haka bay a ganta a birnin Misra, ta zo masa a bakuwar fuskar da ta san kanwarsa ba tare da ita kanwar tasa ta sanshi ba. Ya ganta a Katsina ta nuna bata taba saninsa ba, yanzu kuma aiki ya kawo shi Ibadan ta biyo shi, dama ‘yar Ibadan ce? Wani burin e gare ta game da shi? Abin da bai sani ba kenan, amma mamaki kam ya nunka hauhawa a zuciyarsa. Kafin yayi wani yunkuri hart a shige cikin gidan, zuciyarsa ta ayyana masa yabi ta zuwa cikin gidan don jera mata gwanon tambayoyin da suka cike masa ruhi, amma kuma sai ya fasa wannan yunkurin nashi, sakamakon tunowa day a yi hakan da yake son yi haramun ne ka shigarwa mutum gida bad a izininsa ba. Wata tambayar ma ta sake zuwar masa, ta dade a gidan tana zaune, ko kuwa ma dai gidan wasu ‘yan uwanta ne? idan gidan wasu ‘yan uwanta ne ai makulli ya ga ta saka ta bude gidan, hakan yana nufin ba kowa, ita dai ce yazu ta bude ta shiga. Tabbas haka ne, sai dai ko iada masu gidan suna da tsarin rufe gidansu a kowane lokaci, idan mutum zai shiga sai yayi amfani da makulli. Wannan tsari ne na wasu mutane da ke kasasjen Turai, amma mu kam a Nigeriar mu ba mu san wannan tsari ba, to ya abin yake? Tsayuwar waata bakar mota kirara Odessy a kofar gidan da Shuhuda Ibn Khaddab ta shiga ta dau hankalinsa. Wani Balaraben matashi ne ya gani ya fito daga cikin motar,sanye da Fakistan a jikinsa, fuskarsa da karamin tabarau. Isah yana kallo shi ma Balaraben ya sanya makulli ya bude gidan ya shiga, haka dai ya tabbatar masa duk wanda zai shiga gidan da makulli yake amfani. Waye shi wannan matashin Balarabe da ya shiga gidan? Babu amsa gumi ya gama jike shi sharkaf! Duk wata nutsuwarsa tayi kaura ta rabu da gangar jikinsa. Kanwarsa Shuhuda ta tabbatar masa Shuhuda Khaddab 'yar asalin jihar Katsina ce, kuma mazauniyar jihar Katsina, wadda ta yi karatun sakandire dinta a jihar Kano. Wane sanadi ne ya kawo ta birnin Ibadan? Ga shi ba ya shiri da kanwarsa Shuhuda da ya tuntubeta shin ko dama Shuhuda Ibn Khaddab tana zuwa Ibadan ko ta taba zama a can ne? Komawa yayi cikin gida, ya zauna a gefen gadonsa yana tunanin abin yi, shin ko dai ba Shuhuda ibn Khaddab bace ya gani ba? Ta ya ma zai ce ba ita ce ya gani ba? Lallai ita ce to tababa babu. juyawa yayi ya dauko wayarsa da ke kan bedside(gefen gado) wata zuciyar ta shawarce shi kawai ya kira Shuhuda yayi mata tambayoyinsa. Har ya laluba lambar Inna Yaduwa, sai kuma ya fasa sakamakon wani kunci da ya ji ya mamaye masa zuciya. Abin da ta yi masa akan Hamza ya yi masa ciwo, wai har ta iya son bare akan na gida? Karar kwankwasa kofa yaji, a hankali yace. Alwaye ne?" Daga bakin kofar dakin nasa ya jiyo muryar Beka (daya daga cikin masu yi masa hidima) ya ce. "Ni ne yallabai". Cikin harshen turanci yayi maganar. Isah ya bashi umarni ya shigo, ya ce "Yallabai an kawo wuta za a sauya". "Ok, ba matsala". Isah ya mayar masa da amsa. Beka ya fice daaga dakin. Isah ya maida kai ya kwanta, tunanin ma aka rufe babinsa, amma damuwa da rudani sun kaura daga zuciyar sa. Da yaga abin zai masa tarnakinda zai iya haddasa masa matsala, sai ya janye wani littafi 'lobe sick' ya soma karantawa. Washegari sai misalin karfe takwas da mintina arba'in ya tafi gurin aiki. Bai dawo ba sai yammaci sosai, yau ma a barandar ya tsaya har lokacin magaruba ya yi, da yake akwai masallaci a layin,sai ya fito ya samu jam'I. Ana gamawa ya dawo, bai shiga cikin gida ba, a harabar ya tsaya. Yana kallon motar ta tsaya, Shuhuda ibn Khaddab ta fito, yau sanye ta ke da material mai ruwan sararin samaniya (sky blue) sabanin jiya da take sanye da leshi ja. Da ta fito daga motar ba ta bar gurin ba, jingina tayi da motar tana dube-dube tamkar mai neman wani abu. Zuciyarsa ta ayyana masa kawai ya isa inda take, sai dai yana yunkurawa da nufin haka, sai yaga ta rabo jikinta daga motar ta soma taku tana nufan gidan da ta shiga jiya. Fasa zuwa wurin nata yayi, don yana da tabbacin kafin ya zagaya ya fita tuni ta dade da shigewa gidan. Har tsayin mintina ashirin da uku da shigarta cikin gidan bai ga matashin Balaraben ya shiga kamar yadda ya faru a jiya ba. Kamar walkiya ya hangota ta fito a sukwane gurinsa ta nufo. Kallo daya zaka yi mata kasan a rude ta ke, sam ba ta cikin nutsuwarta. Sai da ta karaso daf da barandar maimakon ta zagayo ta get ta shigo ciki sai ta tsaya daga nesa musryarta da dan sauti mai karfi ta ce. "Don Allah yah Isah ka taimaka min, mijina ne ba shi da lafiya, ba zan iya tuki ba, ka taimaka min don Allah". Ta karashe maganar cikin raunanniyar murya, kwalla suncika gurbin idanunta. Maganarta ta hargitsa masa tunani tabbas dai Shuhuda ibn Khaddab ce, tunda har ta iya ambatr sunanasa kai tsaye haka. Amma abin tambayar shi ne, dama tana ta aure? Ba mamaki hakan ne tafuya ta kamata ita da mijin nata zuwa birnin Misra, asalinta 'yar Katsina ce, zaman aure ya kawo ta Ibadan. A haduwarsu ta Katsina ta nuna sam ba tasan shi ba, yanzu kuma ta zo ta ambaci sunansa har tana neman taimako, wannan rainin hankali da yawa ya....... "Ka taimaka min, wallahi zai iya mutuwa!" . . Wata sabuwa........!idan kai/ke ,ne/ce, zaka/ki taimaka? Hanya, Isah zai taimaka??? da Hausa Book stories MATA UL HAYAT ¤¤26¤¤ Ta katse masa tunani da fadar haka, hankalinta yayi kololuwar tashi. A matsayinsa na Musulmu, wanda yake son ya kasance mai karfin imani da tausayawa halin da dan uwansa muslmi ya shiga, sai ya ji zuciyarsa ta kare har ma yana kwadayin samun wannan gugguben ladar. Kawai sai ya zagaya ya bi bayanta yana jefa kafafu tamkar wadda zata tashi sama. Ta bude gidan ta zura kai, shi ma ya bi ta bayanta. Yana kwance a falo, magashiyan yake. Usah ya karsa gurinsa da sauri yana taba jikinsa. "Subhan Allah". Ya dago kai ya dube tan ya ce, "Tun yanshe ne bashi da lafiyar?" Cikin yanayi na rashin sukuni ta ce, "Yanzu ne na dawo na tarar da shi a haka, amma lafiya lau ya baro ni gurin aiki". Ya ce, "bari na dauko mota". Ta katse shi, tana mika masa makulli. "Ga tawa, mu je kawai". Ya kama shi suka fito harabar gidan, Ta yi sauri ta bude masa gidan baya ya shiga da mara lafiyan, sannan ya zagaya mazaunin direba ya shiga, itta kuma ta shiga gidan baya, Ya ja suka tafi. Ba a bata lokaci ba aka karbe su, wani daki na musamman aka saka marar lafiyan, su kuma aka bar su a bakin kofa. Isah yana zaune saman kujera, yayin da ita kuma ta ke zarya daga bakin kofar dakin da mara lahiyan yake ciki zuwa tsakar falon da suke, tana takun tana buga hannunta cikin daya hannun. Shi dai kallonta yake a nazarce don tantance shin da gaske ita din dai ce ko kuwa kama ce? Amma iya duba da nazarinsa bai ga wata alama da ta banbanta da Shuhudar da ya gani Misra da Katsina ba, har yanzu zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa a lamarin, idan ya kamo wannan zare kafin ya tufke shi, sai ya gudu, ya sake kamo wani, shi din ma babu nasara. Sun yi shiru su duka na tsayin lokaci babu wanda ya tankawa dan uwansa. Can Isah ya dago kai yana sake dubanta, ya ce. "Ya kamata ki zauna, in shaa Allahu zai samu sauki". Ta dan juyo a kaikaice ta ce masa. "Ina son mijina! Ina mararin zama da shi, kada ya mutu idan na rasa shi ban san da wane namiji zan rayu ba. Wayyo yah Abubakar kada ka mutu ka barni da maraici, kasan kai ne NURUL KALBI dina, kai kadai ne wanda zan kalla na ji sanyi a kalbina". Idanunta suka soma zubar da hawaye. Sai ya ji zuciyarsa ta karaya ya soma rarrashinta da sanyayen kalamai masu kwantar da zuciya da saka nutsuwa. A hankali ta nemi guri a gafensa ta zauna tare da sanya hankici tana share hawayenta. Murya a raunane ta soma cewa da shi. "A rayuwa idan mutum ya dace da masoyi na kwarai, wanda sai iya sadaukar da rayuwarsa don sama maka farin ciki, ya yi tawaya akan komai don kai, ai ka gama samun komai a rayuwa. Irin su Yah Abubakar Ibn Khaddab suna da karanci a duniya, duk macen da ta yi sa'ar samunsa a matsayin miji to ta godewa Allah, domin ba karamin rabo ne ta samu ba". Isah ya tuna sunayen 'yan gidan su Shuhudar Misra da ta lissafo masa a haduwarsu can Misran, daga cikin lissafin nata tace su uku ne mahaifansu suka haifa. Ita kanta Shuhudan, Yayanta Abubakar sai kaninsu Yusif, kuma dukkansu suna lakabi da sunan mahaifinsu IBN KHADDAB. Yanzu wannan Shuhuda da ke gabansa ta ce sunan mijinta ABUBAKAR IBN KHADDAB ke nan ba iata ce Shuhudan da ya tab sani a Misra da Katsina ba, tunda a bayyane yake babu aya ko hadisin da suka halatta auren JINI DAYA.... Ta katse masa tunaninsa da cew. "Akwai wadda nake zargi da ciwon mijina!" Ta mike zunbur kamar wadda aka tsirawa allura, ta ce, "Tabbas na gano sanadin rashin lafiyar mijina!" Ta daga yatsanta sama kamar zata yi masa nini da wadda ta ke nufi, shi dai ya tsura mata idanu kawai yana kallonta da sauraren maganganun da suke fitowa daga bakinta. "SHUHUDA SAGIR RABI'U ce! Ita ce ta bakunce mu a ofis ta ba wa mijina wani lemo. Da farko bai karba ba, sai da na matsa masa a matsayinta na bakuwarsa bai kamata ta yi masa kyauta ya ki karba ba. Ina tunanin lokacinda ya dawo gidan ne ya sha lemon, shi ne ya haddasa masa rashin lahiya, wata kila wani mugun abu ne ta sanya masa..." Tun lokacin da ta ambaci cikakken sunan kanwarsa ya mike tsaye cikin rudani, musamman da ya ji karashen maganarta. Yaushe Shuhuda kanwarsa ta zo ibadan? Me ye alakarta da garin? Ba ta zo ba, kuma ba ta da alaka da birnin Ibadan, to amman me maganganun wannan Shuhudar ke nufi? Sharri za ta jawa kanwar ta, aminiyarta? Ko kuwa rainin hankalin da suka saba yi masa ne za ta yi masa don dilmiyar da shi cikin rudani? Idan haka ne ba ta yi masa adalci ba, ta zoleye shi da yiwa kanwarsa sharri irin wannan, rai ai ba abin wasa ba ne. Ba tare da ta damu da shi ba, ta ci gaba da maganarta. "Dama tunda na ga kwayar idanunta na zargi wani abu, na dauka ko irin kishin nan ne namu na mata yasa na zargi wani abu, ashe dai akwai wata kullalliyar da ta kullo mana?" Isah ya ske tsintar kansa cikin wani rudanin jin tana tabbatar da zarginta akan Shuhudarsa. Amma sai ya maze ya boye damuwarsa ya ce, "ki yi hakuri, kada zuciya ta sanya ki yi hasashe mara kyau gudun saka rayuwarki cikin rudu".. Wani murmushin takaici ta yi masa tukunna ta ce, "Mhm! Kai dai ayi sha'ani, maye ya ci dansa. Amma mutum? Mutum?" Ta sake maimaitawa cikin jinjinawa. "Mugun icce ke nan, mutum dan masara kana goyonsa yana fidda kai. Kana kallonsa sumi-sumi amma mugun nifinsa ya wuce misali. Shi ya sa na tsani mutumin da zan dinga kallonsa kamar salihi, na fi son kawai ka zo min a tsayenka sai na fi aminta da nutsuwarka, amma sai su nuna su na gari ne, suna wani sunnar da kai alhalin KATTIN MUGAYE ne!" Daga haka su duka suka yi shiru, Isah yana tunanin hanyar da zai bi ya fitar da maganganun da ke cikinsa, amma yana tuna hakkin aure, bai kamata ya tsawaita zance da matar da ba muharramarsa ba. Bai. San yadda aka yi ba, ya kasa hakuri ya magantu. "Yauwa, don Allah a ina kika san sunana don na ki lokacin da kika zoneman taimako a gurin kin ambaci sunana?" Ta dube shi fuskarta da dan yalwa, ta ce. "Ba mamaki, ai duk mutumin da yake cikin unguwar nan musamman layin nan, mijina ya sanar da ni wanzuwarsa gami da sunansa, don haka nake kiran kowa YAYA saboda na tabbata kowa ya mirme ni". Bai gamsu da amsar da ta ba shi ba, ya buda baki zai kuma magana ke nan, likita ya fito. Da sauri ta mtsa inda yake, ta ce. "Likita ya mutu? Wayyo ta kashe min miji!" Ta soma kuka, liktan ya ce. "Saurara madam bai mutu ba, yana nan da ransa". Isah ya matsa shi ma kusa da likitan ya ce da shi. "Ok, muna iya shiga gurinsa?" Likitan ya girgiza kai, ya ce. "Bacci yake, idan har ba zaku yi masa kwarabniya ba za ku iya shiga, saboda yana bukatar hutu, ciwon ciki ne yake damunsa". Isah ne kadai ya karasa sauraren maganganun likitan, ita kuwa tuni ta shige dakin. Likitan ya wuce, yayin da Isah yayi tsaye yana mamakin wannan MURDADDIYA, ko ta ina zai warware ta? "Mhm! Hanya mai sauki!" Wata zuciya ta ayyana masa. "Idan ka danganta Shuhudan Misra, da ta Katsina da kuma wannan ka samu warwarar labarinka". Zuciyar tasa ta kuma ayyana masa. Da sauri ya ciro wayarsa, ya lalubi lambar Inna Yaduwa ya kira, ta yi kara sau daya, biyu, ana uku aka dauka. Shuhuda ce ta dauka, ko bari ba ta yi ya yi magana ba ta soma magana cikin doki da murna. "Haba Yah Isah, yanzu haka rayuwa ta ke? Zunmunci sai ya yi wuya?" Mamaki ya hana shi magana, yayinda ita kuma ta dora da cewa. "Ai na yi tsammanin ko ba wani abu a tsakaninmu wanda ya danganci JINI, aka nuna maka ni aka ce 'YAR UWARKA ce, ka dinga kirana muna gaisawa, amma saboda Allah tunda ka tafi ka taba tunawa da ni? Yanzu ma ba don wayar Innar na hannuna ba, na tabbata ba zaka ce a baka ni mu gaisa ba". Cikin kasalalliyar murya ya ce da ita "Kuna lafiya?" Ta ce, "kalau waLlahi, ya birnin Ibadan? Don Allah Yah Isah me da me ke da akwai a ibadan wanda babu a kano, wai akwai sanyi, ana barin wuta, matansu farare ne sol, wai ko ina cikin Ibadan akwai cinkoso kamar nan K....." Ya katse ta da cewa. "Ya isa haka, ina Inna Yaduwa?" Muryarta a raunane kamar wadda zata yi kuka, ta ce. "Kayi hakuri Yah Isah, ban san zan takura maka har na bata maka rai ba, ka yi hakuri don Allah.... Inna Yaduwa ta fita unguwa, ni ma Shuhuda Ibn Khaddab ce ta kawo min ziyara daga Katsina shi yasa ban bita ba, ita kuma ta manta wayar".kamar zai tuhume ta abin da yake son tuhumarta, amma jin abin da ta fada sai ya kasa magana ya katse wayar. Komawa ya yi akan kujerar da ya tashi ya zauna. Wani tunani ya darsu a zuciyarsa, wai bakuwa ta yi... Shuhuda ibn Khddab ta kawo mata ziyara daga Katsina... Ke nan wannan ta gabnsa ba ita ce wadda yake nufin ba, wata ce can daban? Lokacin da yana Senegal suna yawan yin waya da kanwarsa Shuhuda a wayar Inna Yaduwa, da ya dawo ya bukaci ya siya mata waya ta kawo masa kabli da ba'adi wai hannunta ba ya iya rike waya, yanzu da wane hannun ta yi amfani ta rike wayar da suka yi magana? Da can da wane hannun ma ta ke rike waya suna gaisawa? Gaba daya yaran nan sun gama raina masa hanka li, fita a sha'aninsu shi ne mafitar MURDADDIYAR da suke saka shi! Sai dai zuciyarsa ta kasa wannan yunkurin, Allah Ya jarabce shi da abu mafi tsauri, wato KINAYAR MATA, abin da ya fi ba shi mamaki kasancewar yaran kanana, amma sai juya shi bai-bai suke kamar waina a tanda. Ya dokantu ya ga an zo karshen wannan wasarere da hankalinsa da ake yi. * * * * ********* . Kwana hudu tsakani tun bayan rabuwar Isah da wadda yake ganin Shuhuda Ibn Khaddab ce bai sakata a idanunsa ba, sakamakon aiki da ya rufe masa kofa, sam ba shi da sukuni, idan ya fita tun safe ba shi yake dawowa gida ba, sain gama sallar magruba. Lokacin da zai dawo a gajiye yake, don haka a daddafe ya ke samu ya salaci jam'in isha'I ya shige gida ya yi wanka, sai kuma maganar bacci. Yau ya kama ranar lahadi ce, baya zuwa aiki, tun asuba da ya yi sallah ya koma bacci bai farka ba sai karfe sha daya. Kafin ya fito wanka Beka ya gama hada masa abin karin kumallo. Yana gama karin ya fito barandar gidansa ya tsaya, sanye yake da kananun kaya blue jeanz da red T shirt wadda daga bayan rigar aka rubuta Onlu for you. Rashin sukunin da yake da shi ya sa ya dan rame, amma ramar sai ta kara masa kyau dama ga shi kyakkyawan.. Yana tsaye a gurin tunanin abubuwan da suka faru suka dinga dawo masa a rai. Wato tunani ma lokaci gareshi, hakika ba don aikin da ya sha masa kai ba da damuwar da zai shiga Allah ne Ya yi yawa da ita, amma yanzu dan takaitaccen lokaci da ya samu na hutu tunanin har ya bijiro masa. Sai dai bai yi nisa a tunanin ba ya hango Abubakar yana fitowa da jakunkuna yana zubawa a mota. Mamaki ya kama Isah, lafiya? Ya tambayi kansa. Kafin ya samu amsar tambayar tasa ya ga Shuhuda ita ma tana fitowa da wasu kayan, sannan tana share kwalla da hannayenta. Hakan da ya gani ya tabbatar masa da lallai ba lafiya ba, akwai wani muhimmin al'amari a tare da su. Da farko ya so ya shere da su, amman zuciyarsa ta ki amincewa, makoci ba wasa ba, hakkin da yake kan makoci ba karamin ba ne, shi mutum ne da yasan darajar makocinsa. Idan ya kyale su suka tafi bai san damuwarsu ba, abin zai dame shi, wata kila ma rasuwa ce aka yi musu. Cikin karfin gwiwa ya soma takawa don isa inda suke. Daga can nesa da su kadan ya tsay saboda Shuhuda na kusa da mijinta, yasan ko yaya ne mijin nata ba zai ji dadi wani ya kusanta da ita ba. Ya dan daga murya, ya ce. "Malam Abubakar lafiya dai na ga kuna loda kaya a mota kamar za ku yi doguwar tafiya?" Abubakar yana kallonsa ya ce. "A'aha Haji isah karaso mana, ka toge daga nan?" Cikin karkarfan takunsa ya karasa gurin yana kuma maimaita tambayarsa. Abubakar ya ce masa. "Eh, gida Kaduna zamu je, wata yarinya ce ta yaudareni daga ta zo min bakunta ta zuba min magani a lemo shi ne na sanya aka kamata tana yunkurin guduwa da dalolina, don haka zamu je. Sai munyi tsayin wata daya kafin mu dao shi ne mai dakin nawa ke kuka. A rayuwarta ba ta son zama Kaduna. Ta fi sha'awar nan ibadan ni kuma ina duba kadaicin da zata shiga kafin na dawo. Isah ya ce da shi. "Akkah Sarki, ashe dai abin da gaske ne? An samu nasarar kamata ke nan?" Shuhuda ta tsoma musu baki, ta ce. "Ai idona idon Shuhuda Sagir Rabi'u sai ta raina kanta, muguwa, azzaluma kawai". Abubaakar ya dube ta, ya ce. "Ai sai ki yi hakuri tunda dai. Ba ta kassara miki rayuwa ta raba ki da ni ba, ba ga shi ba da yake Alla ba Ya barin hakkin wani akan wani ba, tun aduniya Ya toni asirinta ba?" Shuhuda ta ce, "Wallahi Yah Abubakar ba komai nake ji da tafiyar nan ba. Illa dadewar da zamu yi ba ma nan, gida babu kowa akwai matsala, musamman yadda bata-gari suka yi yawa a gari yanzu. Wannan shi ne damuwata kawai ba wani abu ba". Abubakar ya yi dan takaitaccen murmushi, ya ce. "Ka ji hasashen matan ko? Sai ka ce wadda ta tsauna dukiyar Nigeria gaba dayanta". Isah ya ce, "A'a kada ka ga laifinta, ai ko naira biyar aka sace wa mutum dole ya ji zafi, ba satar ke da ciwo ba, abu mai muhimmancin da aka sace shi ne ciwon". Abubabakar ya ce. "Haka ne, amma an fi so mutum ya saka karsashi a zuciyarsa, babu abin da zai same shi face rubutaccen al'amari ne daga Allah". Isah ya ce. "Idan haka ne, kada ku damu in sha Allah zan saka a dinga kular muku, ni ma idan ina gida zan dinga kula". Abubakar ya ce. "Ai kuwa mun gode da wannan taimako da ka yi mana". Ya dubi Shuhuda ya ce. "Ina makulli? Kawo mu ba shi daya ko da wani abu zai taso na bukatar shiga ciki". Isah ya yi saurin cewa. "A'a ba ma sai na karbi makullin ba, zan dinga kula, inshaa Allahu babu abin da zai faru har ku dawo". Abubakar ya girgiza kai, ya ce. "Idan dai har ka amince zaka yi mana wannan taimakon, to karbar makullin yana da amfani". Bai tsawaita jayayya da su ba, ya karbi makullin tunda ya ga sun aminta da shi, bai kamata shi ya ki aminta da kansa ba. Yana kallo suka ja mota suka tafi suna daga masa hannu, shi ma yana daga musu nasa hannun. Har yanzu dai kwakwalwarsa ba ta gama wartsakewa da yadda lamarin ya gudana a tsakaninsu ba. A yadda dai suka nuna masa su din wadansu mutane ne na daban wadanda ba su da alaka da wadancan da yake hasashen su ne. Abu daya ne ya fi aminta da shi, wannan Shuhudar ko tantama babu Shuhuda Ibn Khaddab ce, amma ta ya ta ke auren dan uwanta na jini? Ko kuwa zakin soyayya ce ta sanya ta alakanta sunanata da sunan mahaifin mijinta (surukinta), ko shi mijin nata ya alakanta nasa sunan da sunan mahaifin matarsa (surukinsa)? Lamarin dai akwai matukar rikitarwa da juyar da hankali har ma mutum ya soma lalubar hanyar WARWARA! An samu tsayin makonni biyu da tafiyar su Abubakar Kaduna kamar yadda suka sanar da Isah, a tsugin babu wata damuwa da ke tare da Isah, ya kawar da kai da kokarin cusa harkokin ofis a cikin ransa a kowanne lokaci don samawa kansa zaman lafiya da nutsuwar zuciya. Yau ya taso aiki da wuri, ya kuma iso gidan nasaa da wuri. Ya fito harabar gadan yana shan iska, haka kawai zuciyarsa ta ayyana masa ya je gidan su Abubakar don kewaya. Bai yi kasa a gwiwa ba kuwa ya tunkari gidan, ya kewaye shi tsaf ya ga komai lahiya, tukunna ya koma gidansa ya dauko makulli ya zo ya bude gidan.yan zura kafarsa cikin falon gidan yayi katari da wata farar takarda, mai dauke da rubutu. Ya durkusa tare da kai hannu ya dauka. Abu na farko da ya fara gani an rubuta shi ne:- "BUDADDIYAR WASIKA Daga Shuhuda Ibn Khaddab Zuwa ga Isah Sada Rabi'u.". . Gabansa ya yi wani irin yankewa ya fadi, ya shiga matsanancin rudani, anya kuwa sunansa ne a jikin wasikar? Idan dominsa aka rubutata me yasa ba a damkata a hannunsa ba? Me ma wasikar ta kunsa wanda har aka sanya mata suna da "budaddiyr wasika"? Ya kalli rubutun da kyau kananan rubutu ne matuka wanda kana gani ka san da biro mai karamin kai aka yi rubutun,kuma falle biyu kowanne gaba da baya an cika shi. Cab! Aiki ja, sai ya soma dube-dube cikin falon. Shirye yake da manyan kujeru sabanin nasa kala ce kawai, amma yanayin tsarinsu iri daya ne. Sannan akwai kayan kallo nau'in duk da ke da akwai a nasa gidan, sai dan karamin firij daga can gefen kusuruwar yamma. Center table a gaban kujerun. Ya jijuna kai, sannan ya nemi daya daga cikin kujerun ya zauna ya tsurawa takardar idanu, tare da soma karanta abin da ta kunsa a sarari..... . . BABI NA GOMA SHA HUDU Budaddiyar Wasika "Na san lokacin da zaka sami wannan wasika tawa hankalinka zai tashi, ranka zai dagule, zuciyarka zata shiga kissama maka abubuwa da dama. Misali, me yasa na zabi rubuta maka abin da nake son sanar da kai a wasika sabanin na same ka kai tsaye na yi maka maganar da nake son yi maka? To akwai dalili mai karfi, ida kuwa aka ce dalili ana nufin abu mai girma da muhimmanci. Dalilin kuwa shi ne, ba zamu samu isasshen lokaci ba, tunda nasan idan na fada maka maganganun zaka so na amsa wadansu tambayoyi daga gareka. Ture wannan gefe daya, mu dora akan makasudin wasikar, don sji ne abu mai muhimmanci a gare ka da gare ni. Wasu matsaloli sun faru da tsatsonku wadanda suka rudar da tunanin duk wanda yasan kanwarka Shuhuda. Musamman hasashe da mafi yawancin ku suke yi na cewar, ALJANA ce, ko kuma MAHAUKACIYA ce! A cikin jinsin bil'adama akwai wadanda Allah ya horewa kaifiyya gami da yakana ta fahimtar abubuwa da dama. Akwai kuma wadanda a rayuwarsu MATA UL HAYAT (Jin dadin rayuwa ko ince kyale kyalen rayuwa) ke rudarsu har yasa su assasa wani gagarumin laifi wanda zai buwayi al'umma ba tare da tsinkaye da sakamako ba. Baya da haka akwai wadanda laifin wasu ke shafar wasu ba tare da su suka aikata laifin ba. A cikin wani boyayyen sirri ne kadai za a iya fahimtar badinin Shuhuda, har a iya kawo tallafin samun jin dadi da nutsuwar zuciya a gareta. . (Allah Sarki Shuhuda) Sadin Mama. . Yi hakuri Isah, na rasa hanyar da ya dace na yi mak maganganun da nake son sanar da kai, illa wannan da nake ganin zata fi cancanta. Sai dai idan ka bini sannu a hankali ne kadai zai sa ka fahimtar, idan kuwa ka rudar da tunaninka ba zaka tab fahimtar tawa ba. Shuhuda tana cikin wani hali na rashi tun wani lakaci da ya shude, don ko lojacinda muka yi karatu da ita a makaranta ba ta da nutsuwa, awa biyu ta ke da hankali, idan hankalinta ya gushe kahin ta dawo dai-dai sai ta samu awa biyu, ke nan gaba daya rayuwarta ta makaranta yini cur tan yinsu na awanni uku da hankali, wanda in bacin da Allah Ya sa ita din mai kaifin kwalwa ce babu inda iliminta zai kai. Kada ka yi mamaki akan duk abin da nake zayyana maka, domin nasan sirrikan Shuhuda da dama wanda babu wani mahaluki da ya sani. Ba Shuhuda kanwarka kadai ba, idan ba ka manta ba a haduwar mu Misra na ce maka nasan adadin Shuhuda da ke da akwai a birnin Kano ciki da wajenta, saboda bincike na mai sunana. A haduwarmu da kai Misra na ji dadin samunka da saukin kai, har na yi tunanin kai ne mutumin da DUHu zai yaye ta sanadinsa, sai aka samu akasin haka. Munhadu da kai a birnin Katsina na nuna maka ban sanka ba, ba wai don ban gane ka din ba ne, a'a saboda wani dalili wanda idan da a lokacin na bayyana maka kaina Shuhuda zata Shiga rudani matsananci, watakila ma har numfashinta zai iya fita daga gangar jikinta. Ka ga kuwa amatsayina na musulma bai dace na yi abin da zan firgita dan uwana Musulmu har ya rasa ransa ta sanadina ba. Shuhuda ba tasa na je Misra ba, ba tsan kuma ina zaman aure a garin nan ibadan ba, hasalima akwai abubuwa da yawa da suka shafe ni wanda ita ba ta sani ba. Amma duk wani motsi nata na sani, nasan da a gabanka nake zaka tambaye ni ta ya na sani? Kamar dai yadda na fada maka a Misra na kasance mai zurfin bincike akan mai sunana, duka da wannan bai isa ya zamo hujja a gareka ba, illa kawai ka share duk yadda zuciyarka ta kissama maka game da yadda aka yi na sani ka dauke shi a hakan. Maanufar dai itace ka fahimci RUFAFFEN SIRRIN da na ke so ka gane. Lokacin da Shuhuda ta shiga aji hudu a makarantar sakandare an yi wani zama na sirri aka shirya wani shiryayyen sirri mai MURDADDIYA da daure kai. Matsayi mai girma ya wanzu a gare ta, ta kuma zama hazika a wani bangare bisa wani boyayyen sirri kamar yadda wasu rayuka suka shude bisa boyayyen sirri. Abin tambayar anan shi ne, wannan wane irin boyayyen sirri ne haka? To sirrin yana tattre da sirrantaccen sirri kwatakwacin sirrin haduwarmu. Kwatankwacin sirrin tsotsar hannun da Shuhuda ta ke yi. Kwatankwacin sirrin fitar ruwan nono a jikin Shuhuda sabanin jini. Kwatankwacin wani abu mai kama da almara da ya faru a tsakaninku bisa wani boyayyen sirri. Isah zan so matka ka saita kwalwarka da tunaninka wajen fahimtar maganganuna duk da dai kai tsaye ban fito fili na sanar maka ba, gudun dai abin da na fada maka, 'MATSAYINA NA MUSULMA bai dace nayi wani abu da zai razana dan uwana musulmi ba har ya rasa numfashinsa". Idan aka ambaci kalmar SILA tana nufin SANADI, Shi kuma sanadi yana nufin faruwar abu ta dalilinta wani...... (Shin WAYE MUSABBABI na padawar Shuhuda cikin wannan boyayyen lamari?) Ku biyo ni dan jin karshen BUDADDIYAR WASIKA. Sadin Mama. Hada Hausa Book stories MATA UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) 27 . CI GABAN BUDADDIYAR WASIKA……………… Zan iya ce maka dukkan rudadden al’amarin day a rudaka da ma duk wanda yasan Shuhuda ya faru ne sanadin ABOKI, shi ya sa ake so mutum yasan abokan da zai yi mu’amala da su, koda yake faruwar sanadin ma rubutacce ne da ga Lillahi, duk hikima da wayon zillewa ba zasu yi tasiri ba, duk gudun Rago ba zai hana a dora masa wuka don yin layya da shi ba. Hamza yana son Shuhuda har cikin ransa, sai dai ba shi da kwanjin zamowa miji a gareta, idan aka yi la’akari da kasancewarsa akan matsalolinta. Haka kai ma akwai kasawarka, shin wa ya dace da wannan muhallinta? Amsar it ace ZABIN ALLAH domin Shi Yake da SANIN GOBE. Daga karshe zan diga DANBA akan tunatarwa. ‘a duk lokacin da aka manta da mayar da lamari ga Ubangiji akwai tarin da na sani.Addu’a aba ce ga duk musulmi ya dimanci yenta ba wai sai wata matsala ta faru ba. Sannan akwai cutuka wadanda likita bai isa gano makasudin samuwarsu ba bare yasan magungunansu. Shawarar d azan baka, ka kasance mai yin addu’a ba dare ba rana, ko me kake ka yawaita neman tsari daga:- MIYAGUN MUTANE MIYAGUN SHAIDANU. Allah Ya taimakeka ka tsallake siradin da kake a kai, Allah Ya taimakeka ka zamo mutum mai himma wajen SADAUKARWAR da rayuwa akan tafarkin addinin musulnci. Akwai zobenka da yake hannuna wanda ka ba wa Shuhuda lokacin da ka dawo daga Senegal, watakila kaga irinsa a yatsana a haduwarmu burnin Katsina? To na hannunta ma ya dawo hannuna bias wani boyayyen sirri. Wassala! Sai Allah Ya yi mana dawowa idan da rabon ganawa! Tun kafin ya karasa karanta wannan zungureriyar takarda mai taken ‘Budaddiyar wasika’ gumi ya jike Isah, ya yi sharkaf, idanunsa sun sauya launi, zuciyarsa ta jagule. Bat a yi karya ba kamar yadda ta fada, dole ne ya shiga rudani akan wannan takardar, ba ma shi kadai ba dak wanda zai karanta takardar dole ne ya shiga rudani. Idan zai iya tace abubuwan day a karanta a cikin wasikar to abu na farko da zai kissima, wannan wani labari ne day a fito daga hannun AJJANA SHUHUDA IBN KHADDAB, bias hujjojin sanin wasu abubuwa da ta ked a su, wanda ya fi karfin sanin bil’adama, koda ace ma wani bil’adama zai zansu, to sai dai ya kasance mai yawan shekaru, kuma wanda yake da alaka da wanda abin yake faruwa akansa. Ita kuwa wannan a yadda ta ke din nan ba zata wuce shekaru ashirin ba, idan ma ta kai ken an. Kuma ba ta zaune da Shuhuda koda yaushe bayan makaranta da ta hada su, bare tasan komai na rayuwarta wanda ita kuma Shuhudan ba tasan wasu abubuwa da suka shafeta ba. Isah mutum ne mai kwanji, amma bai ga alamar yana da kwanjin da zai iya jure wannan sha’ani ba. Nadama ta zo masa a karo na biyu na dawowars kasarsa ta haihuwa, wato Najeria tunda tun lokacin day a dawo bai samu nutsuwar zuciya ba. Abin day a lura da shi matsawar yana bukatar zaman lafiya da fita daga tarin rudanin da yake ciki game da wannan murdaddiyar al’amari to kawai ya yi kaura da Najeria ya koma Misra ya yi aiki a karkashin kamfanin da malaminsa Dr. Outhman Ibn Abdulfatah ya so ya yi tun da farko. Sai dai inda yake hangen matsalar bay a wuce ta bangaren mahaifinsa, tunda a farko ma ya so hakan amma mahaifin nasa ya kiya masa, yanzu day a fara aiki a Nigeri zai kuwa yiwu ya amince masa aiki a Misra? Shirme, hauka gami da tsabar rainin hankali shi ne muraran abin da yake ganin su Shuhuda na yi masa. Tunda yasan kauracewa zamansa Nigeria ba abu ne mai yiyuwaba, to kawai ya dauki matakin fatattakar duk wani lamari da zai sada shi da Shuhuda tundabai ga wani abun anfanu a hakan ba. Ya ja wani dogon tsaki yana yarfe gumin day a jike shi, tukunna ya mike tsaye ya tunkari kafar fita daga falon. Tsau! Yaji wani abu ya ratsa ta dukkan sassan jikinsa, kamar tsoro n eke dirar masa. Cak! Ya ja tunga ya tsaya tare da waigawa da sauri, ya duba ko’ina bai ga wani abun da zai tsoratar da shi ba, illa dai haka nan ya samu jininsa da tsinkewa ya yi tsururu tamkar ruwa. Ya dau mintina biyu a haka, sai ya ji kamar zuciyarsa na yin shakulaton bangaro (sharewa) da lamarin Shuhuda, musamman la’akari da abinda budaddiyar wasika ta kunsa. Sai dai a wani bangaren yana karfafawa kansa sharewa da Shuhudan, domin budaddiyar wasika babu abin da ta kuma sanya shi illa wani firgici. Sam bai hango wata hanya da zai shawo kan matsalar rudanin da yake ciki ba. Da azamarsa ya sake ‘yunkurin ficcewa daga falon, amma kamar an daure shi, domin ji ya yi gaba daya babu wata gaba da ke iya motsi a jikinsa. Hatta kansa ya kasa juyawa zuwa bayansa, illa gabansa kawai da yake kallo. A bayan nasa kuwa yana jiyo kamar ana motsi, kamar ma taku yake jiyowa. Da sauri ya ambaci….. ‘INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN, LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH……’ Kafin ya karasa ma tuni ya ji wani irin kuzari ya zo masa, ya kuma fice daga falon yana mai takaicin shigowarsa hurumin dab a nasa ba. Cikin rudanin ya yi saurin rufe gidan da makulli ya koma gidansa, ya zube a falo tare da rafka tagumi. Hakika duk abin day a faru da shi a cikin gidan su Abubakar lamari ne na sihiri, ko kuma gaba daya ma y ace jinnu idan haka ne kuwa daga Shuhuda Ibn Khaddab har mijinnata Abubakar Ibn Khaddab duk jinnu ne? idan hasashensa ya zama gaskiya ta ya suka samu wannan gida da suke ciki? A matsayinsu na jinnu zasu iya zama a gidan, to amma ina asalin mutanen da ke zaune a gidan? Ko kuwa sun z one a sigar mutane an dauke su aiki har aka bas u muhalli kamar yadda shi ma kamfanin da yake aiki suka yi masa wannan gatanci? Hakika akwai boyayyen al’amari mai matukar rudani da daure zuciyar tunanin duk mai tunani. (nima n ace, Isah ba kasan dawn garin ba, Shuhuda Ibn Khaddab ta baka haske sosai ta yadda zaka warware lamarin cikin saukakar hanya, (sadin mama)). BABI NA GOMA SHA BIYAR TARIHI YA MAIMAITA KANSA An wayi gari yau laraba, Inna Yaduwa na kishingide a falo idanunta a rufe, ta kara ‘yar karamar radiyo (kachbo) a kunnenta tan a sauraren wani shiri ‘Ku karkade kunnuwanku’ wanda Aisha Bello Mahmud ke gabatarwa a tashar FREEDOM RADIO wanda suke karanta wani littafi mai suna MACE BAIWA na jinjirar marubuciya mai tasowa Naja’atu Haruna Sale. Tana jin dadi labarin, saboda yadda aka dauko rayuwar da mata suke a karkara aka rubuta, duk wasu tarin matsalolin mata sun kunshi wannan hadaden labari. Da yake yau din it ace rana ta farko da aka soma karanta littafin, sai Inna Yaduwa ta ke ji, ina ma kada lokacin da aka dibarwa shirin ya cika ba tare da an kamala karanta littafin ba? Kusan da gudu-gudu, sauri-sauri Shuhuda ta fito daga daki da nufin isa bandaki, sai dai kafin ta isa tuni ta soma kyelaya amai, wanda yunkuri da karar sautin zubar aman ne ya farkar da Inna Yaduwa abin da ke faruwa, hart a hanzarta mikewa zaune daga kishingiden da ta ke tana ambaton. “lafiya” Amma Shuhuda shiru ta kasa Magana illa ci gaba da kyelaya aman da take yi kamar zata amayar da duk abin da ke cikinta. Hankalin Inna Yaduwa ya tashi matuka, ta isa gaban Shuhuda a rude tana tambayarta abin day a same ta tare da tattaba jikinta. Sai da kyar aman ya tsagaita, amma duk ta galabaita ta fita hayyacinta. Inna Yaduwa ta kamata zuwa bandaki, tab a ta ruwa ta kurkure bakinta, sannan suka dawo falon, Shuhuda ta kwanta akan doguwar kujera, yayin da Inna Yaduwa ta goge gurin da aman ya bata ta dubi Shuhuda cikin tausayawa, t ace “sannu” bat a amsa ba, Inna Yaduwa ta mike ta nufi kan dan karamin firij da wayarta ke ajiye a kai, ta dauko ta duba lambar Alh. Sada wadda ta sanya wa alamar mota, don duk wanda ke cikin wayar akwai alamar da ta ke gane lambarsa da ita. Kasancewar ba ilimin book ta yi ba. Tana kiran wayar yayin da take dawowa don zaunawa kan kujera. Ya dauki wayar cikin ladabi ya isar da sakon gaisuwarsa tukunna t ace masa. ”Shuhuda ce ba lafiya, tana ta amai, idan kana da hali ka zo a kai ta asibiti” y ace “ina direban gidan ne?” t ace, “sun fita da Alhaji”, y ace, “to ni yanzu na yi nisa sosai, amma bari na turo Nuruddeen sai ya kai ku” t ace, “ba damuwa”, Ta kasha wayar tare da tsurawa Shuhuda idanu cike da jin tausayinta. Ba jima sosai ba Nuraddeen ya shigo gidan yana kada makullin mota, fuskarsa a sake y ace,”yar tsohuwa ke bakin cikin shan gumba zaki yi mana, an ce na zo na kai ki asibiti?” ya fadi maganarsa cikin sigar wasa na kaka da jika, fuskarta a daure t ace,” da yake ba ka da idanu shi yasa ka gaza gane ba nice ba ni da lafiya ba…………. Yayarka ce Shuhuda gat a nan bat a da lafiya, it ace za mu kai asibiti”. Sai lokacin ya lura da Shuhuda da ke kwance akan doguwar kujera y ace,”A’a Aunty Shuhuda me ya same ki”? Inna Yaduwa t ace masa. “ka ga muje asibitin tunda ka ganta a kwance ai kasan akwai matsala”. Ta fada tana kokarin tallafa Shuhuda, suka fita su ukun zuwa inda ya yi fakin, ya bude musu gidan baya ta saka Shuhuda. Nuraddeen ya ja motar cikin azama suka isa ZAHTY MEMORIAL HOSPITAL, aka shiga da ita emergency, Tashin farko likitan day a dubata ya bukaci fitsarinta, aka shiga da ita wani ban daki tayi, sannan ya basu magungunan taimakon gaggawa tare da cewa a dawo anjima a karbi sakamako. Bayan sun dawo daga asibitin gidan ya dinga daukar harami, nan da nan ya cika da ‘yan dubiya. Karfe hudu da rabi Alh. Ahmad da Nuruddeen suka je karbo sakamako. Likitan ya tsayar da su kafin ya basu sakamakon, ya dubi Alh. Ahmad fuskarsa cike da fara’a y ace. “Alhaji ina taya ku murna, da fatan Allah ya raba su lafiya. Amma zan so nab a ku sahwara, duk macen da take da farkon ciki kafin ya yi kwari ana bukatar ta rage yin ayyukan da za su wahalar da ita gudn zubewar cikin…………………..” Zai ci gaba da dogon sharhin nasa Alh. Ahmad ya daga masa hannu fuskarsa a turbine yana cewa, “Dakata don Allah doctor! Ban fahimci mai kake nufi ba fa?” Ran likitan ya dan baci sai ka ce bad a yaren Hausa yake masa bayani ba? Yanzu haka irin mutanen nan ne da suke auren yara kanana amma bas a son haihuwa. Don haka sai ya dauki sakamakon gwajin ya mika masa. Alh. Ahmad ya sa hannu ya karba cikin zumudi, ya duba abin da takardar sakamakon ta kunsa. Ba wani abu ba ne face Shuhuda tana dauke da danyen ciki na wata daya da kwanaki biyar. “INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN!” Alh. Ahmad ya ji gabansa ya soma faduwa, idanunsa suka sauya launi, cikin wata rikitacciyar murya y ace. “Shuhudan ce da ciki? Mun shuga uku! Ina zamu kai wannan tarin abin kunyar?” Jin kalaman da ke fitowa daga bakin Alh. Ahmad ya sa jikin likitan yayi sanyi, da farko ya dauka Shuhuda mat ace ga shi Alh .Ahmad din, amma yanzu ya fahimci ‘ya ce a gareshi. Sai ya shiga kwantar masa da hankali cikin sanyayan kalamai. Alh. Ahmad y ace cikin dafe kai. “Likita anya ba a samu akasi an sauya sakamakon Shuhuda da na wata ba? Wallahi budurwa ce ba matar aure ba, ta ya kuma za a ce tana da ciki?” Likitan y ace cikin nuna tausayawa. “Wallahi ba wani akasi da aka samu, hasalima duk yau ita kadai aka yiwa awon ciki a asibitin nan, shi ma dalilin da yasa aka yi mata, lokacin da aka kawo ta yanayi na mai shigar ciki duk sun bayyanar da kansu a tare da ita, hakan ce ta san a bada umurnin a yi mata awon cikin, sai kuma shi hakan ya tabbata”. Nuruddeen wanda tun fadr cikin ya sandare, sai yanzu y ace. “Abba idan dai har cikin ne da mamaki, saboda kowa yasan tarbiyya ta gidanmu”. Alh. Ahmad ya dafe kansa, ya nutsa tunanin yadda abin ya faru, iya tunaninsa bai hango wata baraka da zata sa Shuhuda fadawa wannan rayuwar banzar ba. Lokaci daya ya ayyana a ransa, duk yadda aka yi Isah ne yayi mata cikin, musamman idan ya yi la’akari daga kasar waje ya dawo, wata kila dama abinda yake aikatawa ke nana tun zuwansa kasar. Likitan ya girgiza kai, y ace, “Alhaji wannan duk baa bin damuwa ban e, kawai ku kawo ta sai a zubar da cikin asiri a rufe”. Nuradden ya yi saurin cewa. “Haka kawai ma ya dace”. Alh. Ahmad y ace da Nuraddeen, “muje”. Suka yi sallama da likitan suka nufo gida kowanne zuciyarsa cike da kunci, wai Shuhuda da ciki na wata daya da kwanaki biyar? Kafin su isa gidan Alh. Ahmad ya kira yayansa Alh. Sada ya ce su hadu can gida. Suna isa harabar gidan shi ma Alh Sadan ya karaso gidan. Gaba daya suka karaso falo. A cike falon yake, don haka aka wuce dakin mahaifinsu Alh. Rabiu. Dattijon yana zaune akan sallaya yana lazimi, suka zube a gabansa suka kwashi gaisuwa. Alh. Rabi'u ya dubi dansa Alh. Ahmad ya ce. "Ahmadu ya aka yi na ga duk kun shigo gaba daya?" Yayi shiru yana tunanin ta inda zai yanko maganar abin kunyar da Shuhuda ta tafka muusu. Alh. Sada ya magantu ganin shirun ya yi yawa, ya ce. "Ahmadu kai muke saurare, ka kirani a waya ka ce mu hadu nan, kuma ka yi shiru". Ya dago kai cikin dauriya da shanye damuwarsa, ya ce, "Sakamako ne bai yi kyau ba, domin Shuhuda ciki ne da ita na wata daya da kwanaki biyar!" Gaba daya dakin suka dauki sallalami har shi kansa Alh. Amad din. Bayan sun dure sallalamin, Alh. Rabiu ya dora da cewa "Lallai yarinyar nan ba ta kyauta mana ba". Alh. Sada mutum ne mai zafi, idan aka bata masa rai bai iya daukar hukun ba. Yanzu ma cikin matsanancin bacin rai ya nufi falo, kira yake, "Ina Shuhuda???" Ganin yadda ransa yake a bace yasa Inna Yaduwa tasan da walakin, akwai gagarumin laifin da Shuhuda ta yi wanda yake nemanta, a yadda kuwa ta gani a kwayar idanunsa idan ya damku Shuhuda watakila shi ne sanadin ajalinta. Ta ce. "Tana daki, lafiya?" Bai tsaya bata amsa ba, yana huhhutai ya nufi dakin. Da sauri Inna Yaduwa ta bi bayansam. Yana shiga Shuhuda na kwance akan gado ya wani damko wuyanta, ya daga hannu ke nan zai kifa mata mari Inna Yaduwa ta buda muraya da karfi ta ca, "Idan har ka sake ka daki yarinyar nan ban yafe maka ba!al Cak! Jininsa ya tsaya, Inna yaduwa. Ta ci gaba da cewa. "Abin da nutsuwa bata yi shi ba, daga jijiyar wuya ma ba zai yi shi ba. Komai ta yi maka yadda bata da lafiyan nan karbar hukunci ba nata ba ne". Dalilin Inna Yaduwa kuwa na dakatar da shi daga dukan Shuhudan bai rasa nasaba da tuna halin da ta riski kanta a ciki lokacin da ta jaraba dukan Shuhudan din ba, hannunta ya sankare, abin da har yanzu kuwa babu wanda yasan da faruwarsa. Sai ya saki wuyan Shuhudan ya fice, ita ma Inna yaduwa ta bi bayansa. Ya shiga dakin mahaifinsa ya kifa kai a bango kwallan da ke makale a gurbin idanunsa suka samu damar zubowa. Inna Yaduwa da ta shigo dakin ta gansu sun yi jugum-jugum ta shiga tambayar abin da ya faru, Alh Ahmad ne ya yi karfin halin fada mata komai.m Itama kukan ta fashe da shi, Alh. Rabi'u ya ce. "Kinga daina kukan haka,ku nutstu mu tunkari kalubalen da ke gabanmu". Duk suka yi shiru zuwa wani loka ci, sai can daga bisani Alh, Sada ya dago kai ya ce. "Cikin mutane biyun nan dole a samu daya wanda ya yi mana wannan muguwar ta'asar, don haka a kira yaron nan a tambaye shi ko shi yayi mata ciki". Alh Rabi'u ya dube shi, ya ce, "Wane yaro ke nan?" Ya ce, "Malaminta, wanda ya same ni da maganar yana son aurenta. Hamza sunanasa, shi ma Isah zan kira shi a waya duk abinda yake ya bar shi ya zo domin sanin gaskiyar lamari". Alh. Rabi'u ya girgiza kai, ya ce, "Ba haka za a yi ba, kuu bar min komai. Zan tuhumi yarinyar idan yiwuwar kiransu ya kama sai dai a bari sai lahadi don kada abin ya shafi aikinsu". Inna Yaduwa ta sharce kwalla, sannan ta ce, "Malam ni a ganina kawai a zubar da cikinnan asiri a rufe ba sai wasu sun ji ba". Alh. Rabi'u ya girgiza kai ya ce. "Ko day ban yarda da wannan gurguwar dabarar ba, mutane suna daukar zubar da ciki wani abin rufin asiri, bayan kuma babban tonon asiri ne, kuma budewa yaro kofar shiga bariki ne. Ciki dai an sameshi, kuma ko mun so ko mun ki dale ne mu yarda da kaddarar da ta fada manam Saboda haka maganar ma zubar da ciki ba ta taso ba, ku dai saurareni". Da wannan shawarar suka tashi, Alh. Ahmad da Alh. Sada kowa ya kwashi zugar iyalinsa da suka zo dubiyar suka koma gida bayan gargadin da suka yiwa Nura ddeen akan kar ya sake ya fasa zancen ko da ga mahaifiyarsa ce. Alh.Rabi'u bai samu ganawa da Shuhusa a ranan ba, sai washegari da safe ya sa Inna Yaduwa ta yi masa kiranta. Shuhuda ta shigo dakin ta durkushe. A agabansa, kanta asunkuye ta gaishe da shi, ya amsa. Shiru na wani lokaci ya biyoo bayan gaisuwar, can ya daga harshe ya ce, "Shuhuda wani mummunan labari ne ya zo min game da rashin lafiyar ki, wanda ya daga min hankali, shin me ye gaskiyar lamarin? Da gaske wai kin siyar da mutmcinki har kin samu ciki ba tare da aure ba?" Ba ta dago kai ba bare yaga wani yanayi na tsorata ko razani game da jin furucinsa ba. Ta dai yi bakam kamar an dasa dutse. Ransa ya baci ya dan daga murya cikin barazanarwa ya ce. "Magana nake miki, ki ba ni amsa". Har yanzu dai ba ta tanka ba, sai shi ma ya yi shirun yana ci gaba da tsare ta da idanunsa. Ganin ba ta da niyyar tanka masa ya sa ya ci gaba da cewa. "Shuhuda ba ki kyauta ba, kin kuma zubar mana da mutumci duk da cewa kkanki kika yiwa illa. A matsayinki na marainiya maimakon ki rungumi maraicinki da kyau, amma sai kika yi watsi da kyakkayawar rayuwa. Shin wane rudin soyayya ne ya kai ki ga aikata wannan mummunan abu wanda ko a fada ma akwai muni?" Har yanzu dai bat tanka ba, duk yadda ya so ta tanka amma dai shiru. Ya kwantar da murya cikin tausayawa ya ce. "Isah ne?" Ta yi shiru, ya ce. "Ko Hamza ne?" Nan ma tayi shiru, ya ci gaba. "Shi ke nan,Tashi ki je, amma na baki daga nan zuwa gobe duk abin da ake ciki ki sanar min da wanda yayi miki wannan aika-aika”. Tayi shiru bat a mike ba, kuma bata da alamar tashin, y ace, “Cewa nayi ki tashi ki tafi”. Kamar bad a ita yake Magana ba, a’ah sai ya dan leka kansa ga fuskarta ya ga idanunta a rufe. Ya yi tsammanin kuka ta ke, nan take tausayin maraicinta ya tsirga masa jiki. Inna Yaduwa ta shigo dakin hannunta rike da kofin ruwa, ta ajiye a gabansa tana cewa, “Ta fada maka?” Y ace “A’a amma abi a hankali, kamata ku tafi”. Inna Yaduwa ta nufeta zata kamata da sauri Shuhuda tad ago kai tare da daga hannu. “Kada ki taba ni, za ki kone idan kika taba jikina!” Inna Yaduwa ta dubi mijinta, shi ma ya dube ta cike da mamaki, sai ta ja tsaki t ace. “Wallahi ba hauka ba, kowace irin burkewa ce ba ki isa ki bata mana suna ba”. Murmushi Shuhuda ta yi tun kafin ni tuni sunanku ya baci ko dan abu yana boye? Mhm, kuma ku sani nib a tsatsonku b ace, ban hada komai da ku ba, taimako ne yasa na shigo cikinku, kuma kun ki fuskanta. To amma masha Allahu tunda har wannan matakin ya sosa ranku har kuka yi tunanin taron gangami, abin d azan muku matashiya da shi anan shi ne, tarkonku da zaku yi don gano wanda ya yi min ciki said a taimakona don gudanar da taron a cikin sirri, gudun idanuwan masu sirri kar su fuskanci sirri har su yi wani abu a cikin sirri kwatan-kwacin yadda suka aiwatar da wani sirri a cikin sirri mai murdaddiya da tsuke tunanin duk wani mai tunani. A rayuwa ana so komai a yi shi cikin sirri, domin sirri abu ne mai matukar amfani” Gaba daya daga cikin maganganunta babu daya na kamawa, illa tsabar rainin hankali da rashin kunya da suke ganinta da su. Alh. Rabi’u ransa y abaci, sai ya nuna musu hannu cikin daure fuska, y ace, “Na ce ku fice min ko?” Idanuwan Shuhuda suka kawo kwalla rau-rau, ta durkushe a gabansa tana cewa, “Alhaji don Allah, don Annabi ka yafe min idan maganganuna sun bata maka. Wallahi ni mai taimakonku ce, ba kuma zaku yi nadamar taimakon da na ke muku ba”.Ta mike cikin azama ta nufi kuskurawar dakinsa inda gadonsa yake, ta durkusa daga shi har Inna Yaduwan idanu suka bita da su. Jim kadan tad ago tare da juyowa gaba dayanta dauke da wata roba wadda su duka sun yi mamakin samuwar tata. Ta durkusa a gaban Alh. Rabi’u t ace, “Ka ga wannan robar na tabbata ba kasan da ita ne a cikin sirri, saboda kawar da idanun masu sirri. Wannan kadai zai iya zama shaida a gareku da zaku aminta zamowata a cikinku RAHAMA ne, kuma taimakon rayuwarku ne”. Har yanzu ba wanda ya fuskanci abin da ta ke nufi, illa zargin da suka dade suna yi akanta ya bijiro musu, wato dai lokacin da aka haifeta jinnu sun yi musaya sun dauke asalin wadda aka Haifa sun ajiye musu tasu ‘yar jinsun jinnu! Shuhuda ta ci gaba da cewa, “Zan mayar da robar nan a inda ta ke don ci gaba da zama cikin sirri gudun idanun masu sirri, sai dai ku sani duk iya duba idanunku ba zasu taba hango muku inda take ba, tunda ita din an samara da ita ne a cikin sirri. Tunda ya kasance kun tsayar da ranar taron gangami, ina ji it ace RANAR NADAMA! RANAR YAMMA! Wato ranar da kasuwa t agama ci, wadanda ke cikin kasuwar zasu waste!” Su duka suna son yi mata Magana, amma sun kasa. Mamaki, tsoro, firgici, rudani gami da damuwa duk sun mamaye sansanin zukatansu. Haka suna gain Shuhuda ta maida wannan rufaffar roba inda ta daukota tukunna tga sa kai ta ficce daga dakin tana sharer kwalla a gurbin idanunta. Bayan fitar Shuhuda sai aka shiga kallon-kallo tsakanin Alh. Rabi’u da Inna Yaduwa, kowannensu da abin da yake son cewa dad an uwansa, amma sun kasa furtawa, sai dai kallon. An kira Isah a waya cewar duk abinda yake ya tabbatar ya zo Kano karshen mako, hankalinsa ya tashi ya shiga kiraye-kirayen lambobin kannansa don jin abin da yake faruwa, amma ba labari. Nuraddeen ne dama yasan labarin shi kuma an gargade shi, don haka Isah ya kosa matuka karshen makon ya zo ko ya je Kanon ya ji abin da kiran ya kunsa, yana addu’a kada ace sanar masa za a yi an ba wa wani auren Shuhuda ba shi ba. Shi kuma Uncle Hamza takanas Alh. Sada ya je har makarantar da nufin saduwa da shi, amma bai tarar da shi ba, domin an ba shi labarin mahaifin Uncle Hamza wato Alh Babba ne ciwonsa ya tashi a lokacin ma suna birnin Misra don nema masa magani. Haka ya baro makarantar jiki a sanyaye ya dawo gida jiran zuwan karshen mako. The end . To bari mu gani me karshen makon zai haifar, da gasket din ne ranar taron zata zamo RANAR NADAMA? RANAR YAMMA? . Ina shirye-shiryen makaranta, shi isa ban cika samun chance din typing ba, da patar zaku cigaba da hakuri. . Sai ku biyo ni don jin karshen yadda zata kaya, taku har kullum Sadin Mama me kaunarku har kullum Ainihin marubuciyar wannan littapi Allah ya jink anta da rahama ya kara mata hasken kabari, (ZAHRA’U BABA YAKASAI) Hada Hausa Book stories MATAU’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) BOOK 4 ¤¤28¤¤ BABI NA SHA SHIDA Tunda Isah ya shigo gidan ya ga wani sauyi, amma dai bai magantu ba, ya gaishe da Inna Yaduwa ta amsa masa ba kamar yadda ta saba amsa gaisuwarsa ba. Sai yayi tsammanin ko itace bata da lafiya aka yi masa wannan kiran gaggawan. Yayi murmushi yana dubanta y ace “Yar tsohuwa mai ran karfe, hala hala lokaci ya yi ki ke neman yin gardama?” Ta yi masa shiru illa wani irin kallo da take auna masa. Sam bai ji dadin hakan ba, y ace. “Wai don Allah Inna mai yake faruwa ne/. ni fat un da Abba ya kirani hankalinaya gaza kwanciya, ga shi na iso na tarar da sauyi atare da ke. Shin wani ne ba shi da lafiya? Ko kuwa na yi laifi ne b an sani ba? Idan ma akan rashin zuwana net un bayan tafiyata Ibadan, wannan ai bai isa zama laifi ba, idan aka yi duba ni sabon ma’aikaci ne”. Cikin kufula t ace da shi. “Idan don rashin zuwanka new a zai damu? Je ka ma hakan dinne, asabar da lahadi suma ranakun aiki ne?..... Ture wannan, laifi kam ai ka fi kowa sani tunda ka nemi tarwatsa farin cikin mu”. Hankalinsa ya kuma tashi, idanunsa a waje y ace, “Ni din Inna? Me ya yi zafi haka shi ba wuta ba?” sai tag a kamar ma ya raina mata hankali, ta ja baki ta tsuke bat a ko kara kallon inda yake ba. Shi kuma abin day a sa shi shakku ken an, can ya nisa y ace, “Ina Shuhuda?” Ta ce “ban sani ba, mugu kawai wanda ba shi da tausayi bare tsinkaye da maraici”. Wannan gugar zana ce ta yi masa, atunanintsa ken an, duk yadda aka yi akan Shuhuda ne aka yi masa wannan kiran gaggawan, yanzu haka akan ya katse mata waya ne duk ta bi ta tayar da hankalin mutane, ashe dai tana sonsa, yawo da hankali ne yasa ta wulakanta shi a gaban wani bare? Ganin yadda Inna Yaduwa ta ke amsa masa maganganunsa sai bai kara cewa da ita kanzil ba, ya nufi sashensa, don lokacin Alh Rabi’u baya gidan. Amma zuciyarsa fal ta ked a damuwa na rashin sanin tartibin kiransa. Da daddare bayan sallar Isha’I Alh. Rabi’u ya kira Isah adakinsa, sai dai ya rasa ta inda zai kamo zancen. Isah ya shiga laluben laifinsa da har yasa dattijon ma ya kasa cew da shi komai, anya kuwa laifin na katse waya ne? suka yi shiru tamkar kurame, can da Isah ya ga shirun bai zai haifar dad a mai ido ba, sai ya magantu. “Baba ko shakka bana yi, wani gagarumin laifi ne na aikata mafi muni tunda har kai ma ka gaza ce min komai, amma don Allah ina rokon ku afuwa akan aikata laifi bias kuskure”. Alh. Rabi’u ya jinjina kai y ace, “Lifi kam ka aikata, sai dai na kasa furta abin da na ke son furtawa duk da cewar ga abin a raina, bakin ne yaki furtawa. Amma gobe idan Allah Ya kaimu lafiya za a yi wani taro akan laifin da ka aikata da misalign karfe tara na safe”. Isah ya dube shi a kai-kaice y ace “Allah Ya kaimu lafiya”. Alh. Rabi’u ya kawar da hirar da cewa, “ya gurin aikin naka, da fatan dai babu wata matsala?” DANKARI! Ya ayyana a ransa, matsala kam akwai ta, sai dai ba zai so fadar wannan labari na al’ajab din day a faru a zuwansa birnin Ibadan, don bai ga fa’idar fadar ba. Suka dan zanta tukunna ya koma sashinsa. Tun day a dawo bas u hadu da Shuhuda ba, hakan kuma bai dame shi ba. . Karfe takwas da mintina sha uku na safiya, Alh. Ahmad da Alh. Sada sun hahllara a gidan, yayin da su Inna Yaduwama duk sun gama shirin day a dace na Karin kumallo. Shuhuda sai wani irin farin ciki ta ke, sai ka ce ranar sallah, abin day a bai wa kowa mamaki kenan. Au shidda suna a dakin Alh Rabi’u an ci an sha, ana shirin soma maganganun da suka assasa tarin, maigadi ya doka sallama daga bakin kofar dakin. Alh .Ahmad ya leka yana lekawa yana amsa sallamar, maigadi y ace, “Wani ne ya zo ya ce a fada muku Hamza A. Babba ne ya iso”. Ya bi maigadin zuwa harabar gidan, Uncle Hamza yana jingine a jikin motarsa, sanye da farin boyel day a sha dakakken aiki, fuskarsa na fitar da annuri. Alh. Ahmad ya ba shi hannu suka yi musabiha, tukunna y ace. “Mu shiga daga ciki”. Ya yi gaba, Uncle Hamza na binsa a baya, zuciyarsa na cike da farin ciki. Tunda ya samu sakon nemansa da ake gidan su Shuhuda ya samu kansa cikin farin ciki, saboda tunaninsa magar aurensu ce ta taso, don haka ya zabi zuwa gidan cikin farar shiga. Koda suka shiga dakin, kowa ya bishi da kallo, gaban Isah ya soma dukan tara-tara ba ma uku-uku ba, shi ken an zargin da yake ya zamo gaskiya, yasan an bawa Uncle Hamza auren Shuhuda tunda yaga fuskarsa cike da annuri an kira shi ne domin a ba shi hakuri, a kuma kunsa masa bakin cikin dab a zai gushe gare shi bs abadan abidina. Wato shi kadai ne yake cikin kuncin zuciya, tunda ga Shuhudar ma sai washe baki ta ke tana jin dadin za a aura masa wanda take so. Take ya ji kamar ya tashi ya fice kada a hauda jininsa. Yayinda shi kuma Uncle Hamza ya sake jin wani nishadi ya mamaye masa zuciya, musamman ma ganin yadda aka tara mutane da yawa, ciki kuwa hard a Alh .Sada mutuminda ya san alakr Shuhuda shi wato mahaifi gareta, ganin Isah yana hada rai ma yasa shi jin nishadi ko babu komai yasan yayi masa kub daya, ma’ana ya kasa shi. Bayan Uncle Hamza ya gaisheda su Alh.Sada y dube shi tare da cewa. “Na je makarantarku nemanka an ce min kun fita Misra kai Mahaifinka asibiti, ya jikin nasa?” kansa na sunkuye a kasa y ace ”da sauki, sun ma wuce Saudi-Arabia shi da yayana”. Alh. Sada yace. “Allah Ya kara masa lafiya, amma ta ya ka samu labarin neman da ake maka?” a wannan karon said a ya dago kai cike da mamaki, y ace. Yakub ne ya je har asibitin da muke ya duba mahaifina, sannan ya sanar min sakonku”. Sai aka shiga kallon-kallo tsakanin iyayen, Alh Rabi u ya ce "wane Yakub ke nan?" Mamakin Uncle Hamza ya sake bayyana, ya ce. "Yayan Shuhuda!" Alh Sada ya maimaiita maganar, tukunna yace. "Ai mu nan gidan ba mu da mai irin wannan sunan ma Yakub". Jin wanna batu, sai Uncle Hamza ya yi tsuru tsuru, ya tuna can baya da ya fadawa Shuhuda ya je gidansu har ya hadu da Yayanta ta nuna mamaki, to ya lamarin yake? Alh Ahmada ya ce. "Yaya kawai agabatar da abinda ya assasa taron". Alh Sada ya dubi Shuhuda ya ce, "Ga Isah, ga Hamza dukkan su suna ikirarin samarinke ne, don haka sai ki fada mana wanda yayi miki ciki a cikinsu idan kumma babu daya sai ki fada mana wanda ya aikata wannan aika-aikar" da ga Isah har Hamza ko wanne ya zabura ya mike tsaye cikin kaduwa, suna girgiza kai Alh Sada ya daka musu tsawa yace. "Kun ga ku zauna". Suka zauna jiki a sabule, Isah ya ce "Wallahi ba ni ba ne". Shi ma Uncle Hamza ya ce. "Na rantse da girman zatin Ubangiji ba ni ba ne". Kafin wani ya yi magana a cikinsu, Shuhuda ta mike tana murmushi ta ce "Baba ku yi min afuwa, zan je na shigo da baki gasu can harabar gida". Ran kowa ya baci, wato su zata mayar abokan wasanta, yaushe aka aiko ga bakin bare ta ce haka? Sai dai kafin wani ya tanka tuni ta kai bakin kofa. Alh Sada ya biyota da hanzari yana kira, har sai da suka fito harabar gidan. Lalle kuwa ya ga baki su uku, mace daya maza biyu, turus! Ya ja tunga ya tsaya cike da tsorota ya Shuhuda tasan da zuwan bakin? Bai ga lokacinda aka kira a waya bare kuma turo mata sako ta duba ba. Yayin da ita kuma Shuhudar ta rungume macen suna fara'a. Daya daga cikin mazan ya mika wa Alh Sada hannu ya ce, "Baki ne daga Misra akan zaman da kuke yanzuu muka iso, kada ku damu, ku aminta da mu". Alh Sada ya tsayar da zuciyarsa ganin yadda suka zo musu cikin salama, ya ce. "Ba damuwa". Ya yi musu jagoranci zuwa cikin dakin. Uncle Hamza ya mike tsaye da sauri yana nuna daya daga cikin bakin, ya ce. "Yauwa ga Yakub din". Shima Isah ya mikke yana nuna sauran bakin biyu, ya ce. "Abubakar, Shuhuda me ya kawo ku nan?" Alh Rabi u, Alh Ahmad, Alh Sada da Inna Yaduwa suka dinga kallon juna cikin mamaki. a Hada Hausa Book stories MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) 29 Yakub y ace, “ku kwantar da hankulanku, sannu a hankali” Yana fadar haka suka zauna, sannan su Isah ma suka zauna, sai dai gaba dayansu suna cikin rudani. Bayan sun zauna Yakub din ne ya soma Magana.”Dan Allah ku yi hakuri da bakuncin da muka kawo muku katsaham, akwai babban dalili na yin haka, dalilin kuwa ba zai rasa nasaba da boyayyen sirri ba wanda muke bukatar nutsuwa daga gare ku. Da fatan fahimtarmu bias kyakkyawar fahimta”. Ya mayar da dubansa ga Inna Yaduwa, y ace. “Inna ke mace ce, muna bukatar idan ba zaki damu ba ki fita domin gudun razani a gareki. Idan kuma har zaki dake, ki yi hakuri da kaddarar da ta faru, ba matsala”. Inna Yaduwa ta dubi Yakub cikin takaici, a ganinta ya raina ta, yaushe a matsayinta na babbar mace yaron da a haife ta haife shi zai ce ba zata iya dauke dafin da zai fada ba? Ta ce, “Shekaruna sittin da uku, a haife na haifeka, kuma dukkan zafin kalma ba zata wuce ta rashin ba, ni kuwa na rasa mahaifana da dana Sagir, kuma na yi hakuri, sai sanadin gurbata rayuwar jikata ne b azan dauke dafin ba?” Yakub ya yi malalacin murmushibtukunna y ace. “ki yi hakuri Inna, ba nufi na ke nana ba, amma babu komai tunda nag a alamar zaki nuna juriya ai shi kenan”. Ba ta tanka ba shi kumja ya ci gaba da cewa. “wani labari ne za mu baku bias yarjejeniya, da kuma alkawari”. Alh. Sada gwanin zuciya, y ace. “kun ga don Allah su waye ku? Kada ku zo kukawao mana raini”. Alh Rbi’u y ace, “ka ga Sada saurara”. Ya dubi Yakub ya ce “muna saurarena”. Yakub ya gyara zama, sannan ya dora da cewa, “Ni sunana Yakub, wannan kuma Abubakar, macen it ace Shuhuda. Mun kasance tare da ku tsayin lokaci….. koda yake ba wannan ke gabanmu ba, muna a gabar sanin wani sirri da ke lillube a cikin sirri”. Ya dora idanunsa akan Alh Rabi’u y ace. “Alhaji yarjejeniyar da zamu yi da ku it ace, ku amince zaku sauraremu har sai mun gama ba ku labarin da zamu ba ku tukunna zaku tambaye mu abin day a shige muku duhu. Sannan alkawarin, za ku yafewa wanda ya assasa komai laifinsa”. Alh Rabi’u y ace, “zamu amince da yar jejeniya, amma maganar alkawari babu ita, tunda bam u san mai laifin ba…….. Hasalima dai babu yafiya ga mutumin day a kunsa mana bakin ciki ba tare da yayi nadama ba”. Abubakar ne wannankaron ya magantu, inda y ace. “Tunda harm u muka nemi hakan kun san akwai babban dalili. Na farko dai shi mai laifin bay a cikin duniyar nan bare ya iya neman afuwa, kuma a matsayinku na iyaye dole zai kasance kun e mutane na farko da zasu yi fatan ‘ya’yansu su sadu da rahamar Ubangiji”. Babu wanda ya fahimci inda maganganun suka dosa, kuma gaba daya yanayinsu ya nuna rashin fahimtar. Yakub ya ci gaba da Magana da cewa muna rokarwa Marigayi Alh Sagir gafara a gurinku iyayensa bisa wani boyayyen sirri da ya assasa”. Inna Yaduwa tayi tsagal t ace, 2wani ne y ace muku muna fushi da shi? Ko salon ku bata masa gawa ne? kai ni fa ban yarda da ku ba”. Alh .Rabi’u ya girgiza kai y ace, “Yaduwa idan ba zaki iya saurara ba kina iya fita”. Ya kareshe maganar yana nuna mata hanyar fita daga dakin. Sai ta yi mucus! Alh. Rabi’u y ace, “mun yafe masa, Allah Ya yafe mana baki daya. Suka ce “Amin” Yakub y ace, “ina so hakan ya zamo alkawari ne, kada daga baya dokin zuciya ya sa ku sauya shawara”. Alh. Rabi’u y ace. Mun yi alkawarin”. Yakub ya dubi Abubakar y ace, “wannan shi zai fara ba ku labarin, saboda labarin ya kasu kashi uku, kowanne mud a bangaren da yake jagoranta, Abubakar bismiLlah”. Abubakar ya gyara zama ya soma da cewa. BABI NA SHA BAKWAI MAFARI MATA’UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA KO KYALE-KYALEN RAYUWA) “Kamar yadda kuka sani Sagir ya taso da hazaka, uwa uba nutsuwa da yake da ita, wanda hakan ne ya ja masa farin jin a gurin al’umma. Da yake labarin a takaice ne zan baku shi, kun san lokacin da yake aji hudu a sakandire kun sauya masa makaranta zuwa ta kudi, to a can ne Allah Ya hada Sagir da wani aboki IZRA’EL, wanda tasu ta zo daya sosai don gurin zamansu daya ma, haka idan ana maganar kokarin daya to za a sanya dayan. Wannan shakuwa tasu da hazakarsu ya sa malamansu ke kiransu 2 Effect, duk da wannan tarayya tasu Izra’rl bai taba taka kafarsa gidansu Sagir ba, hakan kuwa daga Sagirun ne don yana tsoron mahaifansa, sanin Musulmai ne shi kuma Izra’el Krista, yana ganin kamarbza a kalubalanci tarayyarsu. Sai dai shi Sagir ya je gidan su Izra’el wanda zuwan nasa ya tayar da hankalin mahaifansa har said a suka hukuntashi akan don me zai yi mu’amala da musulmi, dalilin haka yasa abotarsu ta soma ja baya, amma dai bas u rabu ba. Lokacin da suka gama sakandire, sai ya kasance, suna haduwa a cikin gari. Tsutsayi mahaifan Izra’el suka gano har wannan lokacin bas u rabu ba, don haka suka tura dansu karatu, can kudancin Najeria. Wannan ya sa suka daina ganin juna, kuskure na farko da aka soma samu a rayuwar Sagir shi ne, gidannan ba a tsaya sosai ga ilimin addinin musulunci ba, ita kuwa duki rayuwar da aka bar ilimin addini akwai nakasu a tattare da ita. Shigar Sagir poly ta sauya masa rayuwa, ta hanyar yin mu’amala da mutane daban-daban, na banbanta addinai, daga cikin mutanen day a yi mu’amala da su akwai wata yarinya mai suna Akkina, wadda ta kasance daga addinin Yahudawa. Akkina ta so Sagir, shi ma ya so ta it ace ma mace ta farko da aka soma SADAUKARWA da ita, a wani bangare na sirri………..” Inna Yaduwa ta katse Abubakar cikin daukar zafi. “ka ga malam dukkan mu nan ba yara ban e, idan kun z one domin ku ci zarafinmu ku bata mana gawar da, to ku fice ku bam u guri”. Alh.Rabi’u y ace, “kafin a soma bada labarin said a aka nemi shawarar idan ba zaki iya saurare ba ki fita, don haka yanzu ma kofa a bude ta ke”. Jin abin da ya fada yasa ta yi shiru amma tacika fam! Abubakar ya jinjina kai yana kallonta tukunna ya dora da cewa, har Sagir ya kamala diplomarsa suna tare da Akkina, yana ta neman aiki bai samu ba, rannan da yammaci ya je gidan zoo shi da Akkina, wadda ta kasa komawa mahaifnta tun kamala karatunta, saboda tunaninta idan ta koma Sagir ba zai bi bayanta ba, ita kuwa a rayuwarta babu wanda ta ke so irin Sagir, don haka ta ki komawa ta zauna a gidan abokin mahaifinta inda ta soma zama ganiyar karatunta. Suna ta yawon kallon dabbobi, kowanne a cikinsu yana nuna abin da ke burge shi na daga dangin dabbobi. Sun zo layin da ked a akwai zakuna, sun tsaya a dai-dai kejin wani zaki suna kallo, kawai sai sager ya ji an ambaci sunansa. Dago kan da yake suka yi tozali da Izra’el, nan take suka rungume juna cike da jin dadi. Sun dau lokaci a wannan hali kafin daga bisani sun saki juna suna kallo-kallo a tsakaninsu.Sagir ya ga sauyi sosai a tare da Izra’el mamakinsa bai boyu ba, saboda shigar day a yi ba karamar shiga ba ce, shiga ce irin ta wadanda ke jin dadi, duk da dama mahaifan Izra’el masu kudi ne, to amma ga dukkan alamu yanzu sun fi kudi. Izra’el y ace, “mutumina yanzu wane aiki ka ke?” Sagir ya girgiza kai, y ace”bana aiki, na dai gama karatu ina ta neman aiki ban samu ba”. Murmushi Izra’el ya yi y ace “aiki a kasar nan ai wahala ne, idan bad an wane kake ba baza a taba baka aiki ba”. Ya ciro wani kati(comlementory card) daga aljihunsa, yace. “yanzu dai babu isasshen lokaci, amma ka same ni a gida sai mu tattauna”. Ya karashe maganar yana mika masa katin Sagir ya sa hannu ya karba, a haka suka rabu. Kwana biyu a tsakani day a shirya ya yi amfani da adireshin da ke jikin katin ya je gidan Izra’el, gida na alfarma wanda ya kunshi duk wani nau’in abu na shagalta, ko kafin Izra’el ya fito daga daki, said a Sagir ya yi kauyanci. Yana fitowa, tsoron ma hada hannu da shi ya yi don gaisawa, sai zubewa ya yi a kasa yana gaishe shi. Dariya Izra’el ya dinga yi, sannan ya tayarda Sagir ya zaunar da shi saman kujera, su kadai ne a falon, sai mai aiki da t agama zube nau’o’in ababen cid a na sha, ta fice. Sagir ya gaza hakuri y ace. “kai mutumina, yaushe Bos dinka ya zama hamshakin mai kudi ne haka?” Izra’el y ace. “a’a duk abin da ka gain a gidan nan mallakina ne, ni na hada komai da kudina da kuma gumuna, domin bayan tafiyata karatu mahaifina ya rasu, yanzu haka ni ke rike da duk dawainiyar gidanmu ba kuma da gadon mahaifina ba”. Mamaki ya sake mamaye zuciyar Sagir, ya dinga dube-dube, fuskarsa na nuna matukar kauyancinsa. Izra’el ya yi murmushi, y ace “to yanzu dai fara cin abinda da aka ajiye maka kafin mu shiga tattaunawa”. Hka ya ci abubuwan da aka jera masa shi kuma Izra’el ya koma cikin wani daki, jim kadan ya dawo hannunsa dauke da wata ‘yar karamar jaka, ya ajiye ta a gafe, ya zauna akan kujera yana kallon Sagir har ya kamala. Sannan suka gaisa tare da tambayar juna bayan rabuwa. Izra’el y ace, 2Sagir na tausaya maka matuka, acebsaurayi kamarka babu ‘yan cnji ko aikin yi akwai fargaba, amma kada ka damu, ni zan taimakeka saboda shakuwar da muka yi da kai, zan sama maka aikin yi ko don abotar da ke tsakaninmu tun kuruciya, sai dai akwai sharadin d azan gindaya maka muddin ka amince shi ken an”. Cikin zakuwa Sagir y ace da shi “wani sharadi ne?” Izra’el ya yi murmushi tukunna y ace masa yana kallon kwayar iadanunsa. ‘”a’a ba yanzu zan fada maka ba, ka dai bi ni sannu a hankali”. Haka suka ajiye Magana, da zai tafi Izra’el ya damka masa wannan jaka day a fito da ita, wadda ke dauke da manyan agoguna guda hudu kowacce daya zata kai dubu goma, sai tsabar kudihar na dubu talatin. Sagir ya rude, ya rasa inda zai saka kansa don dadi, ya shiga zabga masa godiya tamkar an ba shi kyautar aljanna. A takaice sun ci gaba da haduwa a lokuta mabanbanta, da haka har yawon dare suke zuwa, tukunna Izra'el ya bullowa Sagir maganar aiki. Iya kaduwa ya kadu da ya ji irin aikin da Izra'el din yake ikirarin ya samar masa, wannan shi ne dalilin dauke kafarsa ga gidan Izra'el, amma ko da aka dauki lokaci ba su hadu ba, sai ya ji zuciyarsa ta karaya, har ya amincewa kansa zama daya daga cikin 'ya'yan kungiyar safara da shan jinin mutane...." Ko da Abubakar ya zo nan a labarinsa, gaba daya sai gurin aka dauki salati. Inna Yaduwa kam fashewa ta yi da kuka. Abubakar ya ci gaba da cewa, "Tun Sagir yana dari-dari har ya bada kai bori ya hau, ya je ya samu Izra'el ya sanar masa ya amince. Gudun kada a gano shi tunda ba aiku yake ba, kada a ganshi da manyan kudade a zarge shi da wani abu, sai daya daga cikin 'y'yan kungiyar ya sama masa aiki a ma'aikatar kula da tsirrai na jihar Kano. Tashin farko abin da dodon tsafi ya fara bukata ga sagir shi ne jinin Akkina a matsayinsa na wadda ya fi so fiye da kowace mace. A ranar sam bai samu yin bacci ba saboda yana tunanin yadda zai iya sadaukar da Akkina ga dodon tsafi bayan dumbin son da yake yi mata. Sai da ya dauki tsayin kwanaki hudu a halin damuwa da rashin sukuni, sannan ya amince. Ya tsarata akan zasu je Abuja holewa kamar yadda sukan yi, amma ba ya son kowa yasan da tafiyar, don haka ta yi karya a gidan da ta ke zaune cewar zata je can gidan su mahifarta. Wannan shi ne dalilin da ya sa har yau iyayenta ba su san yadda aka yi da gawarta ba. Bayar da Akkina ga dodn tsafi ya kara samarwa Sagir daukaka a kungiyarsu, sannan hakan ne ya sa ba wanda yayi zargin ta ya ya samu wadannan dukiyoyin nasa. A kungiyar tasu akwai Hausawa da yawa a ciki, irinsu Alh. Badaru mataimakin shugaba, Alh. Nuraini da dai sauransu. Alh. Sammani shi ne mutumin da kusan suka shiga kungiyar a tare, shi mutumin jihar Jigawa ne, a shekaru ma za su kusan sa'annin juna. Bisa ga yadda shugabancin kungiyar yake shugaba wanda yake akan karagar mulki shi ne mai alhakin zabar wanda zai maye gurbinsa a lokacin da wani sanadi ya taso, ko mutuwa ko kuma rashin cika ka'idojin shugabancin kungiyar. To tun kafin daya daga cikin wadannan abubuwa biyu su taso yake zabar magaji wanda zai gaje shi. Wanda yake shugabancin kungiyar a lokacin wani inyamuri ne mai suna John, tun lakacin da Sagir ya shiga kungiyar ya kasance yanna kaunarsa, don haka shi ne ya kasance yana kaunarsa, don haka shi ne ya zaba a matsayin MAGAJINSA, wanda hakan bai yiwa da yawa 'ya'yan kungiyar dadi ba, ganin cewa akwai waganda suka shafe Sagir a shekaru, kuma akwai wadanda suka fi shi dadewa a kungiyar, bugu da kari ma akwai wadanda sunfi shi gogewa a harkar tsafin nasu, amma ace Sagir shi ne zai shugabance su? Wannan dalilin ne ya sa aka yi ta cece ku ce a tsakaninsu,sun manta da cewar muddin shugaba ya fidda Magaji shi ke nan maganar ta zauna, ko da shi shugaban ne ba zai iya kankare abin ba. Wannan tsari ne na abin tsafinsu, don haka ya koma gefe yana kallonsu sai da daya daga cikinsu ya samu nutsuwa ya tuna da wannan tsari, tukunna ya tunatar da sauran. Dole ba don sun so ba suka amince da wannan zabin magaji. Ana ta gudanar da rayuwa ne cikin jin dadi da shagaltar MATA'UL HAYAT (kyale kyalen rayuwa), babu mai tunawa da wani imani a zukatansu. Sagir ya samu sararin bude gidan gona kamar yadda wannan buri ya jima aransa, don shi kam yana sha'awar tsirrai. Shekarar da zai yi aure ne john ya mutu shugaban kungiya, don haka aka hada hidimar aurensa da nadinsa shugaban kungiyar. Isan ba zaku manta ba, akwai mutanen da suka halarci bikin da dorayin kaya ajikinsu a gurin partyn auren, harma aka so yin rigima da wani daga cikinsu shi da wata budurwa da ta nemi cin zarafinsa, wadda ita kuma ta kasance dama yarinyarsa ce, ta gano matsafi ne, ta rabu da shi, da kyar aka samu aka fitar da ita tana cewa jininta ya fi karfinsa. Ina tunanin a lokacin ba wanda ya gane abinda ta ke nufi, shi yasa ba azurfafa bincike ba aka fitar da ita, karshe kuma jinin nata bai fi karfinsu ba, domin sai da aka mikata ga dodon tsafi ya sha jininta. An samu tsayin shekaru uku da auren Sagir, Amma ko batan wata Karima matarsa bata taba yi ba, hakan bai dame shi ba, sai dai ita Karimar ce ta ke cikin damuwa akan rashin haihuwarta. Duk kawaicin da ta ke da shi, sai da wata rana ta shawarce shi da suje asibiti a auna su a gano wanda ba shi haihuwa a cikinsu, ya yi biris da ita, sai ta saka masa kuka tana cewa, ita ta amince idan shi ne ba ya haihuwa zata ci gaba da zama da shi muddin ranta. Yayinda idan aka samu akasin haka tana shawartar shi da ya kara aure, saboda a duk lokacin da aka kawo Isah (lokacin yana dan yaye) gidan hankalinta tashi yake, ta dinga fatan Allah Ya ba ta hauhuwa. Ya yi shakulaton bangari da zancen natam saboda shi bai ga wani abin doki ga haihuwar ba, duka shekaru uku da aure har an isa a soma karafinn rashin haihuwa? Ganin yadda bai damu da damuwarta ta rashin haihuwar tasu ba, ga kuma fuskanta da ta yi a duk lokacin da ta yi maganar ransa na matukar baci sai ta daina yi masa maganar, ta rungumi hakuri tare da rokon Allah ba dare ba rana akan Ya bata haihuwa. An samu shekaru biyar cur da yin auren Sagir babu wani bayani na game da haihuwa, don haka su duka ma sun fitar da rai da samun haihuwa a gare su, suna ganin dama can su din ba masu kwan haihuwar ba ne. Wata ranar litinin ce aka yi zama cikin sirri irin nasu na masu sirri, 'yan kungiya suka taru kamar yadda akasari suke gudanar da taronsu a ranakun littinin domin ta fi kowacce rana muhimmanci a gurinsu, kasancewar a ranar ta littinin ne aka kafa kungiyar, kuma airin ranakun littinin din ne shuwagabannin da suka shude suka hau kujerunsu, don haka sun fi yin taro a wannan rana. Sai dai idan wata bukata ce ta taso musu ta gaggawwa, wannan za a iya gudanar da taron a kowace rana ta kama. Taron na wannan ranar ba shi da armashi, domin sun taru ne akan korafin tun da Sagir ya hau karagar mulki bai fitar da Magaji ba, ga shi har ya shafe shekaru biyar, wanda azahirin fitar da Magaji, domin yadda yake jin dadin Mulkin nasa, yana ganin kamar idan ya fitar da Magaji to wa'adi na iya riskarsa a kowane lokaci. Amma a ranar 'yan kungiya suka uzzura masa har suna ikirarin ya karya doka daga cikin dokokin da kudin shugabancin nasu ya tanadar, wanda bijirewa hakan akwai hukuncin da aka tanadar. Cikin bacin rai ya yi SUBUL-DA-BAKA ya ce. "Tunda kun matsa lallai sai na fitar da Magaji kamar yadda kuka sani, Shugaba ne kadai yake da damar zabar magajinsa, idan kuwa ya zba ko shi bai isa ya ce ya sauya da wani ba. Don haka ni ma a yau zan bi jerin takwarorina, zan fitar muku abin da kuke so, zan fitar muku da Magaji yanzu-yanzun nan. Magajin kuwa shi ne, duk abinda na haifa, ma'ana dan cikina shi ne magajina, shine wanda zai ci gaba da mulki bayan gushewata daga doron kasa". Dukkansu sai suka kama kallon-kallon, domin dai sun san Sagir bai taba haihuwa ba, amma wai dan da ya haifa shi ne magajinsa. Alh. Sammani shi ne ya soma magana, ya ce. "Honourable, dama kana da da ba mu sani ba?" Sagir ya girgiza kai, ya ce. "Ba ni da ko kwai, amma hakan da na fada shi ne hukunci fakat!" . (Wato bai son sauka daga KAZAMAR MULKI!, ni kuma na ce da kyakkyawar mulkin ma ai, MUTUWA BATTA KYALE WANI DAN WANI........(Sadin Mama)) . Alh. Nuraini ya ce. "Isan kuma ka gushe ba ka haihu ba fa?" Bai ba shi amsa akan hakan ba, sai ya ce. "Na sallami kowa bana bukatar jin wani cece ku ce daga gare ku". Shi a tunaninsa wannan karamin al'amari ne, sam bai taba nadama akan wannan hukunci da ya yanke ba. Sai da aka wayi gari Karima ta samu ciki, wannan rana ita ce ta zamo RANAR NADAMA agare shi, ya shiga kuncin zuciya, ya shiga damuwa ainun har Karima ta rasa gane kansa. Yayin da ya kai labarin a kungiya ba karamin dadi suka ji ba, musamman mutanen da suke adawa da shi, dalili kuwa shi ne, suna ganin Sagir ya gina ramin mugunta ne ta zabar abinda ya haifa ya zamo magajinsa a tunaninsa ba zai samu haihuwa ba, sai ga shi ramin ya burma da shi tsulum! Babu wanda ya jajanta masa bare ya ba shi wata shawara don gujewa faruwar subul-da-bakan da ya yi, shi da kansa ya shiga laluben hanyar da zai magance matsalar abin ya ci tura. Ya yi tunanin ya fita daga kungiyar, amma gudun abin da zai biyo baya shi ya hana shi fita, daga baya ya yi na'am da wannan BAHAGON HUKUNCI da ya yiwa kansa, ganin cewar ai da bai taba haihuwar ba, hasalima bai yi tunanin zai haihu ba. Tunda kuwa yanzu za a soma akwai alamar za a ci gaba da haihuwar agidansa, shi ba komai yake jiwa tashin hankali ba, sai ganin shi da kansa ya kai abinda ya haifa kungiyar shan jinin mutane, ina zai kai wannan abin kunyar yayin da kwai ya fashe? Dole dai ya hakure rayuwa taci gaba da tafiya har aka samu watanni takwas rannan abib tsafinsu ya bukaci jinin dan Alh Sammani, ai kuwa duk ya rude ya kidime ganin cewa da daya yake da shi, amma yana gani zai rasa shi? Ga shi yana yiwa dan matsanancin so, yayi juyin duniya akan a hakura da jinin dansa, amma ba wanda ya kula shi saboda sanin ka'idojin kungiya. Daga karshe ma wani da ke kira Madu ya harzuko masa da ruwan masifa cewar, lokacin da dodon tsafi ya bukaci jinin mahaifin Madun waye ya hana? Alh Sammani wani irin bahagon mutum ne, yana da bakar zuciya, sannan ba ya hakuri da daukar fansa. A dalilin bukatar jinin dansa da dodon tsafi ya yi ya sa shi shiga cikin rudu da tunanin hanyar daukar fansa ta ayyana masa ya bi duk hanyar da zai bi ya kawar da Sagir in ya so daga bisani ko ta halin kaka shi sai ya hau karagar mulkin yadda zai fanshe jinin dansa, ya dinga yiwa 'ya'yan kungiyar dauki dai-dai da iyalansu. Saboda haka shige da ficensa ya yi yawa wurin ma shahuran bokaye duk da kasancewarsa gogaggen matsafi masani sosai a harkar, hakan bai sanya ya san wasu hanyoyi da zai assasa mutuwar Sagir cikin sauki ba, don haka bin bokaye shi ne abin da ya ke dacewa a gareshi. ada Hausa Book stories MATA’UL HAYAT(JINDADIN RAYUWA) ¤¤30¤¤ Kafin a samu nasarar abin da yake so, said a aka yi wani gagarumin aiki, wanda ya boye duk wani shiri da Sammanin ke yi bare har Sagir ya gane ya dauki mataki, shi ma shirin kafin yinsa said a aka halakar da mutane uku, don wani shahararren boka ne mai gain har hanji ya yi aikin. Bayan ya tabbatarwa Alh. Sammani cewar, matsawar ana son kawar da Sagir sai an yi wannan shirin. A cikin wannan shiri da aka yi akwai wasu bayin Allah guda uku da suka so tarwatsa shirin, to suma said a bokan ya daure, daurin talala cikin boyeyyen sirri da surkulle irin na mushirikai wadanda Allah ne kadai yake iya karya shirinsu, tunda yasan shi bai isa ya kawar da su daga doron kasa ba. An samu nasarar kowanne shiri da aka yi, wanda ana gobe rasuwar Sagir aka zo gidan gona cikin sirri aka kafa tarkon a dai dai inda yak e ajiye motarasa. Washegari da safe shaukin abin ne ya dinga fizgarsa har yah an masa sukuni, yana son yin kiran gaggawa a kungiya don tattaunawa, amma kasala ta hana shi. A lokacin ne Haj. Karima ta kira shi a waya ta sahida masa Haj. Asmo ta zo daga Katsina. A lokacin kuma ne da zai tafi gida Alh. Sammani ya zo a ofis dinsa, wanda y agama bulbule jikinsa da turarukan da bokan ya ba shi. Ma’anar turaren shi ne, matsawar ya yi tozali da Sagir ya ji kamshin turaren kafin mai afkuwar ta afku, to ba shakka shi ne zai hau karagar mulki sabanin abin da matar Sagir zata Haifa akasin da aka samu bokan y ace kada ya yarda ya yi Magana da wani yayin day a saka turaren, har sai ya je gurin Sagir. To amma day a shigo gidan gonar akwai wadanda suka gaishe shi ya amsa musu, wannan shi ne sanadin day a sa Sagir bai ji kamshin turaren ba. Bayan sun gama tattaunawa game da batun daukar dan Alh. Sammani da za a yi abai wa dodon tsafi, suka rabu lokacin ne Sagir ya fada tarkon da aka kafa masa, ya yi tuntube da kahon LIBHAS wanda aka samo daga kasar Sin, cikin surkullen bokan Alh. Sammani, ya dinga aman jinni har zuwa asibiti…” Ko da Abubakar ya zo nan alabrinsa sai ya ja baki ya yi shiru, yayin da su kuma duk kasala, damuwa, firgici da komai ma suka lillube musu jiki. Inna Yaduwa kuka ta ke kamar ranta zai fita, shi kansaAlh. Rabi’u kwallan ne a idanunsa, Alh. Sada yace, “Subhan Allahi, tabbasa biri ya yi kam da mutum, akwai lokuta da dama da na dinga mamakin irin dukiyar da Sagir yake da ita, ashe akwai sanadin samuwarta?” Yakub ya karbi zancen da cewa, “wannan shi ne sanadin duk wata matsala da ta faru, abin al’ajab ko rudani da kuka ga sun faru da Shuhuda duk sanadin hakan ne.kamar yadda na fada muku labarin yana dauke da bangare uku, kuma kowane a cikinmu yana da bangaren da zai bayar, to kun ji bangare daya, sannan muna rokonku da kada ku yi fushi ku yafewa da uwanku, kuma danku abin day a aikata, ko don ya samu sassauci”. Babu wanda ya tanka, shi kuma ya ci gaba da cewa.”kafin wani daga cikin mu biyun nan y ace wani abu zan sanar da ku wani abu day a faru, yayin da Sagir ya zo rasuwa Alh. Ahmad ya ga idanuwansa sun sauya launi daga fari da baki kamar yadda idanunsa suke, zuwa launin KORE, DORAWA da BAKI. Tabbasa hakan yana da nasaba da sirrin tsafinsu duk wanda zai mutu dan kungiyar ko kuma aka sha jininsa ta wannan hanyar to sai anga wadannan launuka a idanunsu” ya karashe maganarsa yana duban Uncle Hamza, ya dora da cewa. “nasan daga kai Hamza har Isah kun yi tozali da abubuwan al’ajab daga ciki hard a sirrin NETWARK, sirrin sauya suffa dama dai sauransu. Tun da zare daya na labarin ya kamala, Shuhuda ita zata kamo zare na biyu wanda ke dauke da sirrin NETWORK da wasu abubuwa da suka faru su ma cikin sirri”. Ya yi furucin yan duban Shuhuda Ibn Khaddab. Ita kuwa ta gyara zama sosai tana fuskantar mutanen da ked akin, sannan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ta soma fadin cewa:- BABI NA SHA TAKWAS SAKAKKIYA Yayin da aka haifi Shuhuda ‘ian kungiya sun ji dadi matuka, koda yake akwai alhinin rasuwar shugabansu a tare da su da suka wayi gari bakatantan, to amma wannan bai hana su farin ciki ba. Idan an cire Alh. Sammani wanda tunda ya bar gidan gonar bai zame ko ina ba sai gurin bokansa ya sanar masa ya aikata duk abinda y ace ya aikata. Bokan ya fashe da dariya, sannan y ace. “sammani ka yi kuskure gurin aikata abubuwan da an ace maka tun a gida lokacin da zaka fito ka yi amfani da ruwa, wanda n ace maka kada ka kusanci ruwa yayinda ka fesa turaren. Sannan da ka je gidan gona kafin ka isa gurin Alh. Sager ma’aikata sun gayar da kai, kuma ka amsa musu, ko mantawa ka yi, ko kuwa duk girma da isr ce suka janyo maka? Don haka aiki bai yi kyau ba sam-sam. A bangare daya ne aka sami nasarar wato mutuwar Sagir, domin tabbas ya yi tuntube da kahon dama ka’idarsa na muddin mutum zai yi tuntube dakahon libhas shi lallai babu makawa sai ya tattara inda ba a dawowa. Sai dai an haifi ‘ya mace wadda it ace magajinsa a kungiyarku kamar yadda tsarin kungiyar ta ke, samun galabrka kuwa zai yi wuya”. Tun day a ji wannan bakin labarin hankalinsa ya dugunzuma ya tashi, sun rabu da bokan akan idan wata bukata ta tashi zai dawo masa. A lokacin da aka haifi Shuhuda an ganta tana tsotsar hannu wanda aka yi tunanin sanadin bakunta ne ko kuma tana jin yunwa, wanda a zahiri ba haka ban e, babban makasudin tsotsar hannun Shuhuda shi ne, don nusar da ku akwai wani boyayyen al’amari a tare da ita mai bukatar tallafi, amma ba wanda ya yi tsinkaye da hakan. Idan ba ku manta ba a labarin da Abubakar ya bayar yanzu ya sanar da ku cewa, akwai wasu bayin Allah guda uku da aka daure yayin hada tarkon kawar da Sagir daga doron kasa, hakika su wadannan bayin Allah ba mutane ban e , ALJANNU ne masu alaka da KHASHIM TSAGEM, ai kun gane ko wan a ke nufi ko?” cikin mamakin yadda yarinya karama ke ta lailayo labari Alh. Rabi’u y ace. “Idan na fahimce ki, kina nifin kakana wanda ya haifi mahaifina?” t ace, “Tabbas shi nake nufi, wadannan bayin Allah sun kasance masu yiwa Khashi Tsagem hidima tun zamanin yana mahaifarsa (Tsagem) lokacin da yake haziki kuma hafizi don a gurinsa bayin Allah suke daukar karatu, har ya baro Tsagem suna yi masa hidima. Sun ci gaba da bin tsatson Khashi Tsagem suns bas u kariya daga miyagun aljannu, bas u taba sarewa ba, to lokacin da aka daure su aka gudanar da wannan aiki na kafa kahon libhas, Sagir na mutuwa aka kunce su, iya kuka sun koka, duk da dama can suna kuka akan shigar Sagir kungiyar matsafa. To lamari ne wanda yake rubutacce wanda babu wani mahalukin daga bil’adama zuwa jinnu da suka isa su hana ikon Allah tabbatuwa, don haka suna ji suna gain babu yadda suka iya Sagir ya fada wannan kungiya ta matsafa. Damuwar da suka shiga ta ta’azzara, haka ya sa daya daga cikinsu yayi kaura daga kasar Nigeria ya koma can Misra.daya daga ciki kuma ya assasa tsotsar hannun da Shuhuda ke yi, sannan da ta soma girma wata rana da aka yi yunkurin tsaga hannunta ya samara da rowan nono maimakon jinni, don dai a fahimci matsalar da ke tattare da ita, amma ba a fahimatar ba. A can kungiyar matsafa kuwa sun ci gab da kulawa da karagar mulki, domin bayan Alh. Sammani ya bar gurin boka bai hakura da son hawa karagar mulkin ba, don haka da aka samu shekara daya wata rana kawai yah aye karagar a zuwan ya zama shugabansu kamar yadda burinsa, amma nan take ya daskare suka ga naman jikinsa na zagwanyewa har ya zube kaf sai kasusuwansa. Bayan shi ma Izra’el da kwadayin mulkin ya shiga ransa ya jaraba hawa karagar mulkin ya daskare naman jikinsa ya zagwanye. Hakan ya daga musu hankali matuka, amma da dodon tsafin nasu ya sanar musu babu mai iya hawa karagar mulkin a zauna lafiya face wanda aka zaba ya zama magaji sai hankalinsu ya kwanta, sun san akwai wanda zai shugabance su a gaba. A sirrance suna zuwa ganin Shuhuda amma ba a taba bat a wani abu day a danganci naman mutane ko jinni ba, suna dai zuwa dubata a matsayinta na Mgajiya wadda zata zamo shugabarsu nan gaba. Lokacin da Slmai mai haja ta tsaga hannun Shuhudan ‘yan kungiya ne suka kasha Slmai, saboda ta raunata magajiyarsu su kuma ka’idarsu ken an, ba a taba musu shugsba a zauna lafiya. Maganar kwalwa da Shuhuda ta ked a ita, hakan Allah Ya yita ita din mai kwakwalwa ce, sai dai akwai abubuwan da ta yi wanda daya daga cikin bayin Allah nan guda uku ne ya yi jagorancin yinsu. Misali lokacinda tana aji hudu ranar da aka kawo wannan………” Ta nuna Uncle Hamza ta cigaba da cewa. a Hada Hausa Book stories MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤31¤¤ “a matsayin sabon malami, ya yi musu tambaya akan RADIOACTIVITY ta bayar da amsa, amma a zahiri ba it ace ta bayar da amsar ba, saboda a duk lokacin da hankalinta ya gushe bat a ma inda ake tsammaninta. Sannan irin haka tta sha faruwa da Shuhudan, a dauketa a samara da wata. Mas’ud ya bugi Shuhuda a lokacinda suka je Katsina har ya ji mata rauni don huce haushin dukan da mahaifinsa ya yi masa saboda mahaifiyarta Karima, shi ma yan kungiyane suka halaka shi. Dr Ya’u ma ya rasa ransa net a sanadin kungiya saboda su a ka’idarsu shugabansu bay a rashin lafiya ya je asibiti kai tsaye,suna da likitocin da ke kula da wannan bangaren, kai yawa ne fa da su ta kowanne bangaren ma’aikata da ke Nigeriyar nan, abin kunya ne matuka a garesu ace wani ya fitar da jinni ga shugabansu, sun bar shi da rai Shuhuda ta yi amfani da sunan Izra’el a wajen Uncle Hamza, da nufin sunanta ken an a lokacin ba it ace ta furta hakan ba,BAWAN ALLAH ne ya furta kamar yadda na fada muku a duk lokacin da hankalinta ya gushe bat a a muhallin, sai an samara da wata, shi yasa lokacin da Uncle Hamza ya sake tambayarta me yasa take amsa sunan Izra’el a matsayin sunanta ta nuna bat a san ta yi hakan ba, tabbas din bat a da masaniya. Hikimar yin hakan shi ne, tun lokacin da bawan Allah ya lura da Uncle Hamza ya shigo rayuwar Shuhuda sai ya yi tunanin ta hanyarsa za a samu a gano matsalar da Shuhudan ked a ita, shi yasa Hamza ya dinga katari da abubuwan rudani game da Shuhudan. Amma sai ya dauki abin kwalwa ce ya yi mata yawa kamar yadda wani abokinsa Dr Ishak ya sanar masa ana samun irin yaranda ked a kwalwa irin tata su kuma kasance da irin abubuwanda yake ganinta da su. Ko kuma yana dubanta a matsayin burkakka mara hankalibkamar yadda Inna Yaduwa itama ta ke ganinta a hakan. Wata rana Inna Yaduwa ta zo dukan Shuhuda hannunta ya srke, bawan Allah ne da alohakin hakan, duk dai akan turbar haska mata akwai babban al’amari a tare da Sahuhuda……….” Alh .Ahmad ya katse Shuhuda Ibn Khaddab da cewa. “wai shin duk a ina kukasami wadannan labaran? Idan dai kun kasance mutane ne ku, to muna bukatar Karin bayanin ta yadda aka yi kuke da sani na abubuwanda zai yi wuya ku iya sani kai tsaye sakamakon karancin shekarunku”. Yakub ya yi murmushi, y ace. “ai cikin sharadinmu da ku, ba zaku yi mana tambaya ba har sai mun gama sanar da ku labaran da muke son sanar da ku. Idan kuma kunce lallai sai mun sanar da ku yadda aka yi muka samu wannan labaran, hakika abin da ake gudu zai faru, zaku rasa Shuhuda ‘yar ku, rasawa ta har abada, wanda hakan ba karamin barazana ban e a gareku ba, domin laifin wani ne ya shafeta”. Sai aka yi shiru, Shuhuda Ibn Khaddab ta ci gaba da cewa bayan ta fasali. ***** “idan dare ya yi maji dadin kungiyar mai suna Mandus yakan zo ya dauki Shuhuda ya kai ta guraren da ake shakatawa ake casu don girmamawa a gareta. Wannan tsarinsu ne ma ji dadi shi ked a wannanaikin. Wani lokaci Shuhuda ta taba fadawa Hamza takan ganta a wata daula tana rawa tana shan ruwa a cikin koko, bawan Allah ne ya yi hakan duk a cikin abin da yake faruwan na gushewar hankalinta a samara da wata, ya yi hakan ne domin haskawa Hamzan, amma bai gane ba sai ma ya dauki abin a BARA-DA-BANA, saboda an yi amfani da kalmomin sakayau da kuma nannauya. Mu koma sirrin Network wato sabis ken an, lokacin da Inna Yaduwa ta so dukan Shuhuda hannunta ya sake, ta shiga daki ta dauki waya don ta kira wani ta sanar masa halin da ake ciki, amma sai wayar ta mutu. Abin day a faru shi ne, idan har Inna Yaduwa zata yi tunani daga ta zo dukan Shuhuda sai hannunta ya sake haka kawai? Ai dole akwai sanadi, ita ba sanadin ta ke tuhuma ba, a’a burinta ta sanar a zo a dauke mata Shuhuda daga gidanata ba jikanyarta b ace. Wata rana tunani ya yiwa Hamza yawa game da Shuhuda, ya kira lambar da mutumin day a kira kansa da Yayanta ya ba shi, ya kira maimakon ya ji sautin tiring-tirin irin na Mtn, sai ya ji tiring sau daya wanda hakan ke nuna wani layin ne ya kira bayan shi kuma yasan MTN ne. ba a dauka ba, har sau biyu yana kira ba a amsa kiran ba. Can aka kira shi da bakuwar lamba, daga kasar waje aka sanar masa Abubakar Ibn Khaddab ne daga Misra, wai ya kira lambar ne shi a tunanin Hamza matsalar network ne, wanda duk kadan ne daga cikin hikimomin bayin Allah da za a gane akwai wani sirri dangane da Shuhuda”. Ta dan saurara da bayar da labarin tana kallon Uncle Hamza fuskarta cike da murmushi. Y zuwa yanzu ko ba a fada musu ba sun gano ko su waye wadannan bayin Allah wato dais u ukun nana sun e aljanun! * (kun sani typing cikin dare ina yi ina hawaye :’( :’( :’( ……………) Ko da yake J ALLAH na tare da ni don addu’a it ace takobin mumini ALHAMDULILLAH Sadin Mama) * Dukkansu matsanancin tsoro ne ya dirar musu, domin bas u taba tunanin hakan ba, Shuhuda= Ibn Khaddab ta ci gaba da cewa “Hamza an turo maka rudadden sako wand azan iya cewa ya juyar da tunanika, da ka kira lambar kuma sai ka yi katari da samun kanwarka kuma wadda ta ke son ka aureta ZUWAIRIYYA. Alal hakika Zuwairiyya ta fi ka gaskiya, domin itama ta turo maka sako a lokacin tana Magana game da irin son da take yi maka kai kuma ka yi watsi da hakan, shi yasa ta yi mamaki da ka nemi juyar da tunaninta. Ranar littinin ne suke yawaita yin taron kungiya. An hasasa maka Shuhuda tana rayuwa cikin kunci saboda azal din day a fada mata shi yasa wanda ya turo maka sakon yake jin tausayinta. Hikimar juye suffer Shuhuda a hotoin da kuka dauka a library lokacin yin candy dinsu, don ka gane akwai boyayyen sirri, matsalar kasancewarka mai zurfin ilimin addini. Amma sai hakan ya sanya ka rudani, ka rasa wace ce aljana a cikin su biyun, Shuhudan ko Zuwairiyya? Karshe kai kanka said a ka dinga tabbatar zamowarka bil’adama”. Shuhuda Ibn Khaddab ta mayar da dubanta ga Isah, sannan ta ci gaba da cewa tana dai murmushi. “mun hadu da kai a birnin Misra ranar da ka baro Senegal, sannan mun hadu da kai a Katsina, mun sake haduwa da kai a Ibadan har ka samu budaddiyar wasika, koda yake kafin haduwarmu da kai a Katsina da Ibdadan, wasu murdaddun abubuwa sun faru, masu SARKAKKIYA, misali, furtawa Shuhuda da ka yi kana sonta ta ki amincewa, a ranar ne ka yi mafarki Shuhuda ta kima Zakanya tana cinye kananan dabbobi. Da ka je dakinsu ka tarar cikinta na juyawa kamar kwallo wannan duk aikin bawan Allah ne. washegari kan son yi mata maganar amma ka rasa yadda zaka furta a haka har kwanaki biyu, ka taba cikin a cikon kwanaki na biyun, wanda daga lokacin ne ba ka kuma mafarki da Shuhuda ba, kuma a washe garin ta amsa soyayyarka. Dalilan da suka sa Inna Yaduwa ta dinga jin tsoron Shuhuda a dukblokacin da ta so furta wani al’amari shi ne, an shirya kasha Inna Yaduwa a can kungiya, saboda dodon tsai ya bukaci hakan, har aka bai wa Shuhudan wani kaho wanda zata zuki jinin Inna Yaduwar hakan bai samu ba.wannan shi ne sanadin da bawan Allah yayi kafi a gidan hatta Shuhuda said a aka neme ta a kungiya sama ko kasa bas a ganinta muddin dai a gidan za a zo daukarta to ba za a ganta ba. Wannan mataki da bawan Allah ya dauka ya samo shi ne daga sarakunan fararen aljannu na lardin kasar Misra. Shekara da shekaru bawan Allah na neman hanyar da zai kubutar da Shuhuda daga halaka, amma bai samu ba, sai wannan lokaci day a soma samun nasara ta batar da gidan nan daga idanun masu sirri, wannan rufaffiyar robar it ace sirrin batar da gidan. Wannan shi ne karshen labarina wanda ya hattama zare na biyu”. Yakub ya yi saurin magantuwa tun kafin wani ya tanka, y ace. “zare na biyu ya kamala, ni zan ba ku labari na karshe”. Kowa dai ya zuba masa ido ya ci gaba da cewa. BABI NA SHA TARA WARWARA “ba wasu ban e bayin Allah da ke hidima da Khashim Tsagem illa mu ukun nan!!!!!!! Tabbas mun kasance daga cikin jinsin jinnu, kada ku tsorarta domin lamarin yanzu ya wuce matakin tsoro, idan kuka yi la’akari da sanin sirrin da muka yi, kai tsaye dama bai kamata ku danganta mud a bani ‘adama ba”. Alh. Sada mai dakakkiyar zuciya y ace. ”idan ba zaku damu ba, zan so kai tsaye ku fada mana yanzu abin da ke tare da Shuhuda, da kumja abinda za a yi a cireta dag kungiyar matsafa, tunda kun ce ku masu taimako ne a gare mu, kuma kuna da sani na sirrin masu sirri, sai nag a mafita kawai ya kamata ku kawo mana!” yakub yayi gajeren murmushi, sannan y ace. “tunda kuka yi hakurin sauraren labarin da aka ba ku a baya, yanzu ma hakurin ya kamata ku sake yi, garaje ba shi da amfani, musamman kasancewar saura zare daya ne labarin ya kamala. Sannan mu kai matakin WARWARA. Rashin hakurin sauraren karshen labarin ba zai kawo samun WARWARAr labarin ba. Don haka ku yi hakuri da juriya a karasa”. Alh. Rabi’u ya magantu. “Babu matsala, kuna iya ci gaba da labari”. Inna Yaduwa kam ta yi duru-duru, tsoron su Ykub ya ci gaba da tsirga mata jiki. Yakub ya dora da cewa. “Rashin ganin Shuhuda a kungiya ba karamin damuwa suka shiga ba, koda yake sun dauki mataki akan haka duk lokacin da Shuhuda ta fita zuwa wani guri suna samun nasarar dauketa su kai ta kungiyar. Sun yi iya bincikensu don gano sanadin da yasa bas a samun nasarar ganin Shuhuda yayin da take gida, hakan ya ci tura, sun kasa gano komai, babu abin da suke gain a cikin madubin tsafinsu face DUHU dun-dum! Idan sun kai ta kungiya suna tuhumarta abubuwa da dama, sai dai ta kan manta abubuwan da ta sani yayin dab a ta cikin kungiya, don haka bat a iya bas u amsa game da tambayoyin da suke yi mata. Ganin wannan yanayi da suka samu kansu ya sa Alh. Nuraini wanda yak e da mukamin kujerar SANIN SIRRIN KUNGIYA wato DANMASANIN KUNGIYA ya yi gagarumin shiri na daukar mataki…….. Koda ya ke ku yi hakuri ban gabatar muku da zaren d azan kama ba, hakan ya faru sakamakon dokantuwa da na yin a karashe muku labarin tun kafin ya gundure ku kamaryadda na gain a kwayoyin idanun wasunku labarin ya soma gimsarku. Ni zan ba ku labari game da kungiya da abin da shafi Shuhuda a zamanta na kungiya, zuwa samuwar ciki da halin da Shuhuda ta ke ciki a halin yanzu, da yadda za a bi a warware matsalar idan Allah Ya nufa hakan mai yiwuwa n eke nan”. Babu wanda ya tanka, ya ci gaba da cewa “ Alh. Nuraini ya dauki matakin sanin sirrin day a sa ba a ganin Shuhuda akai-akai a kungiya, matakin day a dauka kuwa shi ne. yana da wani kaskon wuta, wanda babu komai a cikinsa sai garwashi yana sirrin wuta, ya samu wannan kaskon wata ne bayan shekaru shidda da mutuwar Sagir wani kasurgumin matsafi ne dan wata kungiya da suke abota ya ba shi kaskon wutan a wani zama da suka yin a gamayyar wasu ‘yan kungiyoyi don kare kansu daga kalubalen da suke fuskanta na barazanar wasu mutanen.Dama sukan yi irin wannan zama ta hakan ne yasa wasu ‘ya’yan kungiyoyin suka hadu da wasu ‘ya’yan kungiyoyin suna mu’amala. To a irin wannan zama da suke yin e Alh Nuraini ya fadawa abokinsa halin da kungiyarsu take ciki, shi ne ya bashi wannan kasko, ya umurce shi day a dinga kadaita a daki shi kadai ya sanya wani garin magani day a ba shi a cikin kaskon wutar, zai ga komai. Hakan kuwa ya yi, sai dai bai iya ganin sirrin da zai faru a gobe ba, tunda a lokacin Shuhuda na zuwa kungiya, kuma ana komai yadda ya kamata da ita. Duk wasu shirye-shirye danake yi bana tunanin ko sau daya Alh Nuraini ya sani,harzuwa lokacin da aka daina ganinta a kungiya, sai idan ta fita daga gidan kawai ake samun nasarar daukarta. Shima saboda a wajen babu magungunan da muka saka a cikin gidan.wata ranar liyyinin suka sami nasarar daukar Shuhuda lokacin suna cikin mota a hanyar su ta zuwa Katsina………….” Da ya zo nan, sai ya tsaya ya dubi Isah, y ace masa. “Zka iya tuna hirarrakin da suka gudana a tsakaninku?” Isah day a kasa kunna yana sauraren rudadden al’amarin nan ya gyada kai, tukunna ya labarta musu hirar da suka yi da Shuhuda tun daga lokacin da suka bar gida garin Kano har zuwa Katsina, da kuma lokacin da suka tafi Karare,kauyen karamar hukumar Btsari gurin Hajiya Karima. Yana karashewa Yakub ya yi murmushi, ya ci gaba da cewa. “watakila zaka yi mamaki idan n ace ba Shuhudar da ka sani a matsayin kanwaraka b ace kayi hira da ita hart a ce zata yi maka kyautar dan mutum, wadda kuna karashe hirar ka juyo ka gat a bingire da bacci”. Mamakin said a ya bayyana karara a fuskar Isah, Yakub bai bari Isah ya tanka ba, ya ci gab da cewa. “to Shuhudar da kuka yi hira ba it ace Shuhdan da ka sani ba, wata ce aka samara musamman, ita Shuhudar ku tun lokacin da kuka fito waje aka dauke ta zuwa kungiya, wanda kafin ranar an kwashi tsayin kwanaki buyar ana son samun wannan dammar bat a samu ba. Shi yasa ana samun dammar aka dauke ta, wanda dai-dai lokacin lira ne ba ka yi ba babu ita har muka kawo wata a zuwan it ace. A ranar an tattauna matsaloli da suka shafi kungiya na rashin halattar Shuhuda a kungiya, wanda suka yi ta bincike, amma bas u samu dammar sanin wani abu ba. Hakan yasa aka yanke hukuncin ba zata koma gida bat a dawo kungiya ken an. Sai dai maji dadin kungiya ya karya wannan batu bias karanto dokokin kungiya day a yi, babu shafin day a nuna cewa a tsare shugaba a hana shi harkokinsa nay au da kullum koda kuwa hakan na nufin zai bar kungiya ne. sannan ya kuma karanto dokokin kungiya ga wanda ya yi yunkurin barinta, aka yanke hukuncin cewa, za a dinga daukarta a duk lokacin da ta fita daga gida. Haka kuwa suka ci gaba da yi, a ranar da Isah zai tafi Ibadan Shuhudar da ke cikin daki ba ita b ace, saboda ta fita da safe bias kaddara zata siyo sabulun wanki aka dauketa, a lokacin dukkanmu muna wani taro na bita akan addini can kasar Saudiyya, shi yasa ma bat a fito sun yi bankwana ba. Duk abin day a faru da Shuhuda izina ce ga wanda ya dauki kyale-kyalen rayuwa ya gane cewar bayan kura ta lafa akwai daru, ma’ana bayan shuka sharran zai iya bibiyar bayanka(iyalinka). Yau kwanaki takwas ken a Shuhuda bat a cikin gidan nan, tana can wani tsuburi da ke Sokoto an daure sakamakon wani laifi da ta yi, kamar yadda na fada muku an taba bat a wani kaho wanda za ta zuki jinin Inna Yaduwa bat a yi hakan ba, shi ne aka kuma son ta zuko jinin saboda abarakar da muka saki suka yi tunanin su ne suke hana shuhuda halartar kungiya, shi yasa suka yanke shawarar kawar da inna yaduwa da Isah daga doron kasa. A matsayin Shuhuda na shugaba ta nuna bat a amince da hakan ba, shi ne aka yi mata caa! Daga cikinsu akawai wanda ya nuna dama bai dace ace Shuhuda ce shugabarsu ba, tunda bat a taba shan jini ba a iya tsawon zamanta a kungiyar. Don haka aka kai ta tsuburin aka duare ta ana azabtar da ita bisa laifin karya dokar shugabanci da ta yin a son bada wasu ga abin tsafi da ta nuna rahsin amincewarta, a shafi na tare cikin kundin tsarin mulkinsu ya bayyanar da wannan hukunci a gare ta . Sannan an yanke shawarar ranar da aka gama hukuntata wato bayan kwanaki goma sha hudu ke nan za a bata jini ta soma sha, don tabbatuwarta shugaba a gare su. Shuhudar da ke tare da ku wannan……. Ya nuna daya Shuhuda da yatsa, ya ci gaba da cewa. “Ba asalin Shuhudarku b ace, wata ce muka samar. Cikin da kuke zargin tana da shi ba ciki ba ne, anyi haka ne bisa mataki na karshe da muke ganin zamu iya bullo muku da shi ku gane cewa Shuhudarku na bukatar tallafi daga gare ku. Wannan shi ne cikamakon zaruruwan labarin da muke son ba ku Yanzu kuma sai a ba ku zabi da shawar akan lamarin. Da farko dai Shuhuda tan a da matukar amfani a tare da ku kasancewarta tsatsonku, zabin da zamu ba ku shi ne, kuna sonta a cikinku ko ba kwa so . ba ruwanmu ba ne mu tursasaku ku so ta, sai dai zamu karfafa muku gwiwa akan ku so ta. Shawara kuwa, idan har kuna son ta ci gaba da zama da ku, dole sai kun kawar da komai na abin da ya faru, kun rungumi kaddara bisa azal din da ya fadawa shuhuda tunda ba don ra’ayin kanta ta shiga kungiyar matsafa ba. Sannan ko da ta ke a kungiyar har yau ba ta sha jinin wani dan adam ba, bare nata. jinin mutum yana halatta ne yayin da kasace mushiriki mai shan jinin yan uwansa mutane (ALLAH SHI NE MASANI). Idan muka yi amfani da wannan batu za mu ga cewa, wanda yak e shirka don Karin kansa, yak e kuma shan jini shi ne jininsa ya halatta , idan kuma ya tuba ya daina jininsa bai halatta ba. Kun ga ke nan har yanzu akwai sauran dama a grace ku ta yin jihadi ku ceto tsatsonku daga halakar da ta ke ciki I dan kuka yi watsi da lamarinta hakika kuna da hakki, Allah (SWT ) sai ya tuhume ku a ranar gobe kiyama Yakub yana zuwa nan a labarinsa ya yi shiru, kowa da abin da yake kissimawa a ransa Alhaji Rabi’u ne ya kawar da shirun nasu da cewa . “ lallahi mun tafka kuskure da muka dauki kowace cuta akwai maganinta a asibiti mun manta cewar duk inda aka bar Alkur’an i sai an samu ba dai -dai ba, domin shi Alkur ‘ani shi ne zuciyar kowace irin ciwo. Amma mun gode wa Allah da ya kawo mana ku cikinm rayuwarmu , shin yanzu ta wace hanya zamu kubutar da Shuhuda? Yakub y a ce, “ gaskiya kubutar Shuhuda daga tarkon da ta ke ciki yana da matukar wahala, amma da yake Allah yana tare da mu, da izininsa zamu samu nasara. Shuhuda kam na cikin wani mawuyacin hali na azabtarwa, idan har ana son kwatota daga hannun matsafa akwai SADAUKARWA, ma’ana a fita da zummar za a dawo da rai ko akasin haka Kuma ba lallai ne a samun nasara ba, sai dai addu’a bat a bar komai ba, rubutaccen al’ amari kuma ba wanda ya isa ya kankare shi Tsuburin da Shuhuda ta ke yana can jihar sokoto a can kungurmin daji, dole sai an yi tattaki daga nan Kano zuwa Sokoto sannan za a sadu da inda ta ke , kuma tafiya ce da za a yi a cikin sirri ba tare da idanun masu sirri sun san da ita ba. Daga ban garenmu za mu dauke nauyin tafiyar har kusa da tsuburin , sannamn za mu bada wata addu’a ta makantar da makiya daga ganika Mu ba zamu iya tunkarar tsuburin bas hi yasa tun tuni ba mu kwatota daga hannun masu sirri ba, hakan kuwa ya biyo baya ne akan wani sinadari da saka a tsuburin da zarar jinsin jinnu ya ratsa gurin to kuwa zai soye ne rumus` Karmar yadda na fada muku a baya masu sirri suna tunnanin isah da inna yaduwa suke hana shuhuda zuwa kungiya, shi ne suke ganin a kowane lokaci su isah za su iya sanya malamai su tura jinsinmu (jinnu) a dauko ta, don haka suka yi wanna surkulle amman bani’adam yana iya keta tsubrin har ya isa inda shuhuda ke duare ba tare da wani abu ya same shi ba. Matsawar idanun masu sirri bas u san da zuwan bani’adamu din ba, ma’ana bas u ga wanda yatunkara guri ba Idan an samu nassar isa inda ta ke , hannu ba zai iya kunce daurin talalar da aka yi mata ba, akwai surar WAKI’A, karantata a koda yaushe yana kawo tsari, ita za a karanta a dai-dai inda shuhudan ta ke, idan Allah ya yarda daurin zai kunce hart a dawo hayyacinta da ta rasa tun lokacin da aka daureta a tsuburin. Ina mai tabbatar muku da cewa, daga lokacin da daurin ya kunce, dukkan wadandan ke kungiya sai sun ji a jikinsu, don haka za su yi saurin zaburowa domin sun dauki matakin gaggawa. To a wannan lokacin Allah ne masanin yadda zata kasance, ko a mutu ko a yi rai, fatan ma dai a yi ran ga godiyarmu. Idan har aka samu nasarar fitowa da shuhuda daga tsaburin komai zai iya faruwa ga kungiyar, imam ta tarwatse ko kuma ta ci gaba da wanzuwa ana farautar rayuwar shuhuda da duk wanda ya shafe ta. Idan bat a fito daga tsuburin ba, shi ma wanda ya yi jarumtar zuwa tsuburi ba zai fito ba, kuma dukkan su zasu zamo kyautarwa fa abin tsafi. Fitowar su daga tsuburin na tafiya bisa kalubalen tarwatsewa kungiya ko akasin haka!” Yakub ya yi shiru da ya karashe maganarsa. Alh. Ahmed ya karbe da cewa. “Idan aka samu nasarar fitowarta daga tsuburin kungiya bat a tarwatse ba, wane irin taimako za ku ba wa lamarin?” Abubakar ya magantu. “Allah shi ne masanin yau da gobe, don haka shi ya bar wa kansa sani. Shi yasa aka ambaci SADAUKARWA a cikin lamari. Ma’anar da muke nufi da sadaukarwa shi ne, ku sadaukar da rayuwarku don yin jidadi. Amma ki sani mu ba mu isa mu ba ku kariya ba facea bin da Ubangiji ya tsara, idan ya nufe mu da ci gaba da ba ku kariya za mu ba ku kamar yadda ya nufe mu da sanin sirrin da wayonmu ko kasantuwaru jinsin jinnu ba mu isa mu sani ba. Tun a nan za ku gane shi (Allah) gwani ne, mai hikima ne a dukkan lamuransa, kamar yadda suratul Ikhlas ta bayyana tsarkin Ubangiji. Abin da muke so ku sani shi ne rayuwar dan Adam da dukkan abin da yake bisa doron kasa na sarari da na boye, da abin da yake a kiyama duk Allah (S.W.T) ne ya yi su, kuma Annabi Muhammadu (S.A.W) dan gatansa ne! Idan kun yarda da hakan babu tababa a cikin duk rokon da zaku yi, shi roko ana son yinsa da tsarkakkiyar zuciya, madamar ana son Ubangiji Ya karba, don shi (Allah) mai tsarki ne, ba ya karbar ibadar marar tsarki. A cikin suratul Bakara aya ta 186 an bayyana yadda bawa ya kamata ya yi roko da tsarkin zuciya. Duk zuciyar da ta kasance cikin wasi-wasi akan tabbatuwar Ubangiji, ko kin amincewa da Annabi Manzon Allah ne, lallai ba za a taba amsa rokon mai zuciyar ba”. Shahuda Ibn Khaddab ta dora da cewa. “An karbo daga Abi Hamzata anas bn Malik (R.A) hadisi na sha uku, manzon Allah (S.A.W) y ace, “ka so wad an uwanka abin da ka so wa kanka”. Dukkan mu nan ababen halitta ne, banbancin jinsi shi ke tsakanimun, amma mu duka wajibinmu ne mu bautawa Allah. Tun da kuwa mun yi tarayya akan abu daya (bautar Ubangiji) sai mu yi amfani da wannan hadisi mu sowa ‘yan uwanmu a musulunci abin da muke so wa kanmu. Kiran da zan yi a gare ku, ba ku kadai ba duk wata al’umma da wannan labara zai kai gare su shi ne, kada mu yi sakaci da neman kariya daga shidan mai kawata mana MATA’UL-HAYAT (Kyale-kyalen rayuwa) a zukatanmu. Iyaye su tsaya tsayin daka gurin sauke nauyin da Ubangiji ya dora musu na tarbiyyantar da ‘ya yan dashi (Allah) ya bas u amana. Idan yaro ya samu dukiya a bincika cikin hikima a ga ta ya ya sameta? Wane irin aiki yake da dukiyar? Su waye mutanen da yake mu’amala da su? Hakika idan iyaye suka bi wadannan hanyoyin ‘ya’ yansu za su kasance tsakanin Katanga daga shaidan, Allah zai kare ‘ya’ yan nasu daga fadawa halaka ba domin saka idanunsu ba, a’a shi (Allah) Yana kare bawansa a duk lokacin da ya so, amma wanna ma hakki ne da ya rataya a wuyan iyaye na kula da yadda ‘ya‘yansu ke a rayuwa. Allah Ya yi mana jagoranci a bisa aikin a gari, Ya kare mu daga sahrrin shaidan (La’ananne), Ya shiryar da zukatan mu bisa tafarki na gaskiya alfarmar Sayyidul sadati”. Gaba daya gurin aka amsa mata da. “Amin”. Uncle Hamza ya dago kansa da ke rusune a kasa, y ace. “ni na sadaukar da rayuwata, zan je tsuburin domin kubutar da Shuhuda”. Jin abin da ya fada ya harzuka Isah, wato ma Uncle Hamza har ya fi shi son Shuhuda ken an da zai sadaukar da rayuwarsa a kanta? Lallai ba zai amince da hakan ba, domin shi ne mutumin da yafi cancanta ya yi komai akan Shuhuda, shi ya fi dacewa da wannan sadaukarwar ko da ace ita zata rayu shi ya mutu, yasan har karshen rayuwarta ba zata manta da sadaukarwarsa ba. Amma kuma idan ya mutu a gurin sadaukarwa Shuhuda ta rayu, shi ken an sai ta auri Uncle Hamza, ya same ta a sanga? Zuciyarsa ta karaya, ya ji wani kunci ya dirar masa a zuciya, karo na farko tsanar marigayi Alh. Sagir ta tsira masa dukkan bargon jikinsa domin bas hi ba hakan da ta faru ba. Ga shi ya tafi ya bar su da azal mai razanarwa da rudar da hankali! Wani bangare na zuciyara kuma ya shawarceshi, kawai ya sadaukar, ko da ya mutun Uncle Hamza ya auri Shuhuda haka Allah Ya tsaro, kuma bas hi doron kasar bare abin ya dame shi. Wannan shawara da zuciyarsa tab a shi ya sa yayi saurin cewa. “ni ne zan sadaukar da rayuwata don ceto ‘yaruwata Shuhuda , tunda daman can ni din na sadaukar da rayuwata a gareta saboda a dalilin Shuhuda tsayin zamana a kasar Senegal ban taba mu’amala da wata ‘ya mace ba, itace na ba wa zuciyata tun kuruciya, don haka yanzu ma zan bata rayuwata don inganta rayuwarta”. Uncle Hamza yaji gaban say a yanke ya fadi, tsoro mai tsanani ya shige shi, a yadda ya ga fuskar Isah ya ayyana zai yi bakin naci kuma ga alama yanzu ma nacin zai yi! Shi kam yana son Shuhuda kuma yana son nuna bajinta,ko don duniya ta shaida irin son da ye mata tsayin lokacin da ya soma ganinta (RIYA) Kafin ya tanka Yakub y ace. “Dukkanku za ku iya jarraba sa’a domin mai nema yana tare da samu, kuma ba a san maci tuwo b sai miya ta kare. Sai dai ina so dukkanku ku nutsu ku san cewa Allah (swt) Ya haramta riya (yi don wani) a cikin littafin Ahlari an bayyana hakan. Idan kun san zaku yi aiki don riya ku sani aikin naku haramtacciya ce. Su duka biyun wuta ta dauke musu, domin kowannensu ya gano kuskurensa akan abin da zuciyoyinsu suka kissima musu, wato zasu sadaukar da rayuwarsu domin duniya ta sahaida irin son da suke yiwa Shuhuda. A bangaren Uncle Hamza sai ya ga abin da zuciyarsa ta kissima masa bai isa ya zamo riya ba, tunda dai hark ace ta ceto masoyi daga halaka. Yayinda bangaren Isah ya gano lallai idan ya sadaukar da rayuwarsa akan ceto Shuhuda don duniya ko ita Shuhudan su san irin dumbin son da yake mata, babu “Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un, La haula wala kuwwata illa billahil aliyul azim, subhanaka inni kuntu minaz alimeen”. A cikin zuciyarsa, sai ya ji ya samu nutsuwa, ya kuma tabbatar zai sadaukar ne domin Allah makagin duniya da lahira da dukkan abin da suke cikinsu. Yakub ya yi murmushi , tukkunna y ace , ”Dukkanku kun amince wa zukatanku zaku iya sadaukar da rayuwarku domin ceto rayuwar Shuhuda Alhamdulillah kamar yadda na fada muku mu zamu dauke muku nisan tafiyar, ba gudu ba ja da baya kuma har kullum kamar yadda muka fara hidima Khashim Tsagem zuwa tsatson sa insha Allah zamu ci gaba da yi har karshen rayuwarmu”. Alh. Rabi’u ya jinjina kai y ace, “mun godewa Allah mun gode muku, Allah Yayi mana jagoranci akan komai”. Shuhuda Ibn Khaddab ta dubi inda matasan samarin suke, t ace, “Isah da Hamza ina so na baku shawara, ku zamo mutane masu hankali da nutsuwa, idan n ace hankali ina nufin masau amfani da baiwa da Ubangiji Ya yi musu, masu jajurcewa da mayar da lamari ga Ubangiji, wadanda bas u dauki rayuwar da zafi ba. Masu so wa dan uwansu abin da suke so. Iadan kuma n ace ku kasance masu nutsuwa ina nufin, kada ku yi sakaci wani abu kalilan ya hargitsa ku, ya juyar muku da tunani hark u diga wasu-wasi wajen mayar da lamari ga Ubangiji. Idan kuka kasance masu hankali da nutsuwa, hakika bau wani abu da ba zaku cimma nasara ba insha Allah”. Abubakar ma ya dora da cewa. “hakkun ‘yar uwa, idan mutum ya kasance mai wadannan dabi’o’in lallai y agama dacewa, shi yasa ma ake so bayan mutum ya mallaki hankali da nutsuwa ya kasance kuma maizurfin ilimi, don su hankali da nutsuwa sun a samuwa ne ga bawa musamman baiwa daga Allah. Amma samun ilimin sai yakarawa bawa kwarjini a idanun wadanda ke kallonsa”. Uncle Hamza ya kasa hakuri ya boye kishinsa, fuskarsa ta nuna hakan muraran, amma bakinsa bai furta ba. Shi kam Isah ya kosa ya je sadaukarwa, yana son ganin Shuhuda, yana kuma jin tausayin halin da ta samu kanta a ciki , ashe duk wannan rudaddun al’amuran da ke faruwa game da ita akwai boyayyen sirri? Hakika ba don Allah Ya so su da rahma ba Ya kawo su Yakub a cikin rayuwarsu lallai da sun yi BABBAN RASHI na tsatson su. . To 'yan uwa masoya Shuhuda, wa zai sadaukar??? ada Hada Hausa Book stories MATA’UL HAYAT(JIN DADIN RAYUWA) ¤¤32¤¤ . WANNAN PAGE IN, SADAUKARWA CE GA DUKKAN MASOYA NA WANNAN GROUP MAI ALBARKA . Wannan ma abin godiya ne matuka ga makagin sammai da kasai. Shuhuda Ibn Khaddab ta kai dubanta ga Isah fuskarta da yalwa ta ce. “A cikin budaddiyar wasika na fada maka zoben da ka ba wa shuhuda yana hannuna bisa wani dalili, kuma a cikin labarinmu ba mu yi maganarsa ba, to ka sani dalilin da yasa na dauke zoben shi ne, za a yi amfani da shacin yatsanka ta jikin zoben a shaye jininka, shi yasa ni ban ga amfanin zobe ba, wannan shi ne dalilin da yasa na dauke zoben”. Isah ya yi godiya da wannan karamci da aka yi masa. Dakin ya dauki shiru na wani lokaci, kowanne da abin da yake cikin ransa. Sai zuwa can Yakub ya buda baki, y ace. “Gobe idan Allah ya tashe mu lafiya ya kamata a yi tafiyar zuwa sokoto, saboda wasu dalilai da nake ganin alamun nasara ta hanyarsu. Na farko dai, goben ta kasance lahadi, ranar jajibirin kafuwar kungiyar EROSU mai tambarin kwalwar kai, kuma a irin ranar yan kungiya sukan huta hasalima ba sa shan jinni a irin wannan ranaku. Kum a irin wannan ranar ma ko da ace za a tarwatsa kungiyar ne to za a iya samun nasara, wata kila kuma akasin haka. Don idanun masu sirri kaifin haske gare su na sirri, amma da ya kasance an samu kaifin haske na ALKUR’ANI to la shakka kaifin haske na masu sirri zai koma DUHU. Saboda haka lahadi it ace ta cancanta a yi wannan tafiyar, sai ku zamo cikin shiri karfe bakwai na safiya Insha Allah zamu tafiyar. BABI NA ASHIRIN GA FILI GA MAI DOKI… Tun bayan da Uncle Hamza ya baro Gidan su shuhuda ya shigo dakinsa ya yi zugum, zuciyarsa na ayyana masa abubuwa masu yawa. Hakikanin gaskiya shuhuda it ace mace ta farko da ya soma so a rayuwarsa, so kuwa ban a was ba, bayan ita bai taba son wata ‘ya mace ba’. Zuwairiyya ita ke haukan sonsa, shi kuma ko a kwalar rigarsa, bai ga inda zai dasa wata kwayar son Zuwairiyya a zuciyarsa ba bare hart a yi tsirran da sonta zai samu muhalli a tare da shi. Kallon da ya yi wa kwayar idanun Isah sai da zuciyarsa ta harba, domin ya ga sirrikan so masu tarin yawa a cikinsu, so irin wanda ya jima datsirga jinin jiki. Ke nan zai sha fama da zogin zuciya ko da ya auri shuhuda tunda akwai alaka tsakaninta da Isah, dole wata rana za su hadu, idan sun hadu wane irin kallo Isah zai yiwa shuhudan? Irin wanda ya gano a cikin kwayoyin madarar idanunsa? Cab! Ashe shi ma dai yana a nasa salon kishin bai sani ba? Ya yi juyi akan gado tare da rungumar filo, ya tuna yadda murdaddun al’amuran suka dinga faruwa har kawo wannan lokaci, hakika akwai so mai karfi da yake yiwa shuhuda. Sai ya soma ayyana yanayin da ta ke ciki a yanzu, wai gat a can a tsakiyar jeji daure cikin sasari irin wanda ake daure dawakai, numfashinta na fita sama-sama. Zumbur! Ya mike tsaye cike da tsoron abin da ka iya samun shuhuda. Hannayensa ya soma bugawa a hankali, tare da cizon lebensa na kasa yana tattaki, wata zuciyar ta yi masa matashiya me yasa tun farko bai jajurce don gano sahihin abin da ke damun shuhuda tun kafin a kai ga wannan matsayi Tabbas ko a zantukanta ya kamata ya gane wani abu makamancin haka, sannan kuma daukar hoto da suka yi da shuhuhan ya yi sabaninta da kiran waya wadannan duk sunyan jigogi ne da ya kamata ya gano abin da ke faruwa da shuhuda. Ta tab ace masa ita sarauniya ce, ashe da gaske sarauniyar c eta matsafa? Wa’iyazubillah, rayuwa mai kunci ken an, yarinya karama bat a san hawa ba bare sauka amma azal ta fada mata. Shin ya matsayin mutanen da aka hallakar ta sanadinta? Hakkin kisan akan way a rataya? Bai sani ba, amma yana da yakinin shuhuda bat a da kamasho, saboda baita ke yin kisan ba, ana yi ne saboda ita. Kuma ba ita ta kai kanta kungiyar matsafan ba, an kai ta ne tun kafin hankali ya shige ta. Shin zai iya sadaukarwar ma don ceto rayuwarta? Idan su duka biyun suka yi nasara suka dawo da ita ba tare da wani ya hallaka ba, ya za a yi? Wa zata zaba cikin su biyin biyin shi ko Isah? Tunda dai dole namiji daya ne zata aura, ba duka biyun ba. Har dare dai bai samu kwanciyar hankali ba, akwai son shuhuda a ransa, haka kuma akwai tsoron abin da zai biyo baya idan shuhuda ta kubuta ta zabi dan uwanta sama da shi! Shi din ma bangaren Isah bai samu nutsuwar ba, tunaninsa bai wuce ta ya zai yiwa Uncle Hamza kub daya ba. Lallai so marurun zuciya, duk irin son da Uncle Hamza ke yiwa shuhuda a hasashe ba za a kwatanta shi da wanda Isah ke yi mata ba, domin salon son Isah daban ne mai tafiya ne a jinin jiki, wanda yak e tsittsinka jijiyoyin jiki, ya makantar da kurumtar. Dai-dai lokacin da y agama gyara makwancinsa, ya kishingida akan katifar yana tuno abuburwan da suka faru tun haduwarsa da shuhudan Misra har kawo yau, ashe boyayyen al’amuri ne zai fito fili? Ya tuna lokacin da suka je Katsina, Shuhuda ta ce zata yi masa kyautar dan mutum har tana tambayarsa ko ba ya so, ken an dama manufar furucin ke nan? Ya dai shiga rudani da shi da kansa ya saka kansa, domin da ya yi la’akari da labarin da aka bas u da bai ja ba, lamari da aka saka jinnu a ciki zasu aika. Yanzu abin da yake cikin zuciyarsa shi ne, addu’a Allah ya bas hi juriya da jarumtar da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda Allah ba don wani ba, ya sanya a ransa idan ya samu nasara ta sanadinsa, shuhuda ta kubuta falillahi hamdihi, ya yi hakan ne domin Allah ba don shuhuda ko wani nata su yaba masa ba, domin shi a rayuwarsa ya tsani abin da zai yi don wani ya yaba. Shi yasa ko lokacin da yana Senegal idan suna group discussion ya kawo idea da zarar ya ji wani ya fara yi masa godiya zai bar gurin, haka ko irin assignment din nan aka bas u ya taimakawa wani bay a bukatar a yi masa godiya, har ma wasu suka yi masa lakabi mai sadakatul jariya musulmai ken an! Isah yana da kyakkyawar zuciya abar so da koyi ga kowa, don da ace matasa zasu yi koyi da irin halayya ta Isah, ko shakka babu rayiwarsu zata inganta, ta zamo abar kwantance. Daren ranar asabar Isah da Uncle Hamza bas u runtsa ba, kowanne da yanayin da yake ciki. Kusan a tare zan ce sun sami bacci, bayan sallar asuba ken an, wanda sun farka ne sun gansu a wari daya su duka biyun a cikin kungurmin daji bisa wasu buzaye. Mamaki ya cika su ta yadda lamarin ya faru har suka soma tunanin ko a mafarki ne suka samu kansu a muhalli daya. Isah ne ya soma yin Magana bayan dogon lokacin da suka dauka suna duban juna, inda yake cewa. “Ta ya na ganni a wannan guri, ko mafarki nake yi ne?” Shi ma Uncle Hamza hakan ya furta, su duka biyun suka rasa amsar da za sub a wa inna, sai dube-dube da waige-waige suke a tsakaninsu, babu gida a gaba bare a baya ko gefensu. Daji ne sosai ga manyan bishiyoyi suna ta rangaji fiska na kada rassansu. Duba da yanayin da gurin ya nuna zai iya shaida musu rana bat a yi sosai ba, hasalima za a iya kiran lokacin hantsi ya daga gari ya shaaa, saboda ransar ba ta da kaifi. Suna cikin wannan yanayi na tababar gaske ne ko mafarki suka hango Yakub na saukowa daga wata bishiyar Rimi, fuskarsa dauke da fara’a. Babu wanda ya samu dammar furta wata kalma har ya karasa saukowa ya iso gabansu. Tare da mika musu hannu don yin musabiha,bayan sallama da ya yi musu. Babu wandan ya noke suka ba shi hannayensu suka yi musabihar, don sun yardarm wa kawunnansu yakub ba mai cutar da su ba ne,kuma ganinsa ya tabbar Musu da duk yadda aka yi shi ne sanadin wanzuwar su a gurin. lle-kuwa bayan gama musabihar yakub ya dora da cewa. ‘’kada ku wahalar da zukatanku wajen tunanin wanzuwarku a wanna bigire, domin ni ne na kawo ku bisa alkwarin da na dauka na yanke muku nisan tafiyar da ke tsakanin kano da sokoto. A halin yanzu kuna cikin jejin da shuhuda ta ke a daure, tafiya kadan ce zaku karasa tsuburin. Kamar yadda na fada muku jiya cewar idan kun isa tsubum bannu ba zai iya kunce shuhuda ba, tabbasa haka abin yake. Suratul waki’a ita za ku kalanta a yayin da kuka isa inda shuhuda ke daure, da yardar.Assamadu za ku kasance masu nasara. Sai dai abin da nake so da ku shi ne, ku zamo masui sadaukarwa, ma’ana ku yi rai ko akasin haka’’. Ya dan saurara yana dubansu daya bayan daya, su din ma dubansa suke yi a nazaree Tsayin mintina ba tare da wani ya tanka ba,sai can daga bisani yakub ya ci gaba da eewa. “masu sirri wasu irin hatsabiban mutane ne, dole sai kun kasance cikin neman tallafi daga basani yakub ya ci gaba da cewa “masu sirri wasu irin hatasabiban mutane ne , dole sai kun kasance cikin neman tallafi daga lillahi , ko da yaushe ku yi ta rook don shi mai rook ga mahalicci bay a zama kaskantancen bawa . kuma mahalicci yana son bawan da yake rokonsa ba don rokon yana amfanar da shi (Allah) kamai ba, face shi bawan da ya mayar da lamiri gare shi (Allah ) don haka abin da zan ce, GA FILI GA MAI DOKI , Allah ya ba wa mai rabo sa’a, yak are ku daga hatabibancin masu sirri, ya makanatar da su daga ganiku. Ya kawo tallafi da zaku zamo sila ta rushewar majalisin da ake farautar bayin Allah . Majalisin da kafuwarsu bai zamo riba ga addinin musulunci ba, sai dauki dai- dai da ake yiwa bayin da ba su jiba ba su gani ba Gaba dayansu suka amsa masa da Amin Yakub ya nuna hanyar da ta yi arewa ya ce I dan kuka bi wannan hanyar tafiya kadan zaku yi ku tarar da wani fili daga nan sai tsuburin Allah Ya bada sa’a Yana karashe fadar hakan suka neme kallon –kollo a tsakaninsu , kowanne fuskarsa turbine babu almar fara’a ko kadan Uncle hamza ya dan ja gajeran tsaki ya soma taku da nufin tunkarar hanyar da yakub ya sanar musu zata sada su da tsuburin da shuhuda ta ke Ganin uncle hamza ya nufi gurin sais hi ma isah ya yunkura da karkarfan takunsa ya tunkari hanyatr, su duka biyan sauri da azama suke ba tare da wani ya kula wani ba, a kasan zukatansu kuma suna ta yiwa kawunnasu addua Wani ma keken fili suka yi tozali da shi fari fat da shimfidadden yashi ya yi shamal tsaye suka yi suna fuskantar juna, domin iya hangensu ba su iya hango karshen wannan fili ba, alhalin kuma an ce tafiya kadan ce za su yi su ruski inda shuhuda ke zaue Ga su dukkansu sun kasance masu son abu daya bare us tambayi juna shawara Yanayi fuskokisun kadai zaka kalla ka gane karayar da zukatansu suka yi muraran . “ akwai matsala “ Isah ya ambata a ransa wannan yanayi da suka sami kansu ciki kadai ya is is aya sanar musu babu nasara a wannan yunkuri nasu Tsayin mintina babu wanda ya mostsa, dace kuma wanda ya iya lalubo abin da ya dace ya yi a cikinsu Isa shi ya yi jarumatar daga kafa ya soma tafiya yayin da uncle ya yi isah idanu yana yaba jaruntarsa, bai sani ina ya nufa ba. Duk yadda yake ganin zai iya sadaukarwa don ceto shuhuda yanzu ya samu karaya ., koda yake a gurinsa bai ga laifinsa ba, iyakacinta ba, kwatan –kwacin a ajiye ka dakin da babu digon haske ace ana so ka lalubo kofa Isah kuwa tafiya yake cikin rashin tsammani , yana kuma karanto duk adduar da ta zo bai san , abin da ya sanyanwa ranshi koda ace zai karashe rayuw a ta tsayin shekaru goma a wannan fili yana da fadi ba tare da ya san inda shuhuda ta ke ba, lallai ba zai yi kasa a gwiwa ba zai ci gaba da wanzuwa a gurin Kamar yadda cikin littafin alhlari aka ce, wanda ya yi hijira domin Allah da Manzonsa, hijirarsa nag a abin da ya yi niyya, ya riga ya sanyawa ransa zai yi komai don ceto shuhuda mastsawar bai kaucewa addini ba, domin Allah Ya yi nisa sosai a tafiyar tasa, har ya kasance nisan da ke tsakaninsa da uncle hamza zai kai na kilo mita ba zato ba tsammainni ya hango wani katon dutse a samansa turun hayaki ne yake tashi karmar an hura wuta. Gabansa ya yanke ya fadi , koda ya yi rayuwa a senagal inda suke zuwa gurin duwatsu don yin nazari bai taba jin faduwar gaba ba idan ya ga hayaki sai da ya samu kansa a cikin firgici Watakila hakan bay a rasa nasaba da lokacin da suka soma hango filin ba su ga karshiensa ba karmar yadda sam bas u hango wannan katon dusten ba , tunda tunda kuwa yanzu dutsen ya bayyana baa bin wahalar da kai ba ne , don an yi mamaki . Samum saukin raguwar faduwar gaban nasa ya biyo bayan saurin lalubo aduo I da ya yi sai ya samu nutsuwa, har ya ji wani karfi ya zo masa. Ckikin azama ya tunkari katon dutsen ,ya matsen masa sosai , sai ya hango shuhda daure cikin sasari, irin wanda ake daure dawaki da su Ta yi ligib idanunta a rufe ruf da alamas ko baccie ta ke, ko kuma babu numfshi a jikinta Kusan rikicewa ya yi , har ya manta da yin tsinkaye da gargdin da yakub ya yi masa ya ruga da gudu da nufin isa gurin, zuci yar sa na harbawa kamari zata tsago kirjinsa ta fito . Bisa tsautssay I kafaluwansa suka harde ya fadi a cikin yashi . ya jima kafin ya dago kai yana hango shuhuda , ga ta kamar a kusa da shi, amma akwai tazara sosai kafin ya isah inda take Cikin rashin kuzari ya mike tsaye , wannan karon nutusuwa t a zo masa , ya yi saurin ambaton . “ innallahi wa inna illahi raju un “ Tukunna ya soma taku bisa diga -digan kafarsa babu ko takalmi , hasalima bai san ta ya ya watsar da sub a Ya isa gab da inda ta ke ya yi tsaye yana kare mata kallo , sannan ya soma karanto suraturl wikia daga farkonta zuwa karshe Yana dire aya , duk igiyoyin da jke daure da shuhuda suka tsinke, ta bude idanunta da sauri kamar wadda ta farka daga nannauyan bacci, ta ambaci “ subhannaallah” Cikin attausan lafazi , sannan ta soma akarewa gurin kallo Ganin a inda ta ke da kuma isah da ke gabantan ya daga mata hankali , ta fashe da kuka tana cewa Yah isah me yasa zaka yi min haka ? me na yi maka zaka kawo ni a cikin wannan bakar dajin? Ina rokonka alfarma kada ka keta min haddi , kayi min hakuari kada ka bata min rayuwa Jin kalaman da ke fitowa daga bakinta ya tabbatar masa ba tasan duk wainar da ake toyawa ba . maganar yakub ta fado masa a rai inda yak e cewa , da zarar igiyoyin suka tsinke a yi kokarin barin jejin , domin a lokacin komai zia iya faruwa, masu sirri za su ji kubutar shuhuda a jikinsu Sai ya ji wani karfi y a zo masa ya samu karfin gwiwar fizgar hannaunta yana mai karantao audo’iI ya soma gudu da ita Yayin da ita kuma ta ke ta tsala kuka tana rokonsa kada ya bata mata rayuwa Kamar hadari suka hanga a gabnasu iska mai matukar karfi ta taso wanda har ba su iya bude idanunsu illa yana ambaton Allah akan harshensa. Ya kuma rike hannun shuhuda gam, iskar ta raba su kamar daukewa wutar lantraki, sai ya ga komari ya yaye Shuhuda ce a hannun wasu irin mutane sun kai mutun shida , kowance da shuhuda a hannunsa tana kuka, tana cewa . “ yah isah . wyyo yah isah za su kase ni, za su sha jinina , ka taimake ni haya isha “ Kansa ya daure hankalinsa ya tashi , ya rasa wa zai kwata, wace ce shuhuda ta gaskiya a cikin su shiddan da ke hannun miyagun mutanen Cikin dakiyar zuciya ya yi kabbara yana kiran sunan shuhuda , gaba daya dajin amsawa ya yake “yayana ka zo gare ni, n ice shuhuda ka taimake ni ” A fusace ya yi kan wani mutm wanda shi ne mataimakin shugaban kungiya , shi ke rike da shuhuda ta gaskiya , ya ce . “mhm , kifi na ganinka mai jar koma (ANTY RAISAT KINDE JI lol….) , ko ka dauka duk yunkurin da kake na fita da shugabar mu a wannan guri ba ma ganinka ? bude kunnuwanka da kyau ka ji, kmar yadda basarake ba zai satu ga barawo ba saboda dogarawa , haka muma ba ma wasa da shugabar mu , don haka kan sani aa mu sha jinin shuhuda don ya halatta ga abin tsafinmu , kamar yada muka sha jinin dr ya’u, Kamar yadda muka sha jinin masa’ud da zarar mun sha jinin shuhuda za mu jinin wannan jemammiyar tsohuwar sannan mu sha naka mai yi mana karamabani Dama mun dade muna burin shan jininka , tunda kuwa ka kawo kanka faduwa ta zo dai –dai da zama . sannan za mu hada da tsoho rabi’u don kun ci kuin jini, kun sha kudin jinni, kun ji dadi da kudin jinni dole mu kaddamar da ku jiniku ya yi kuka Cikin tsananin jarumata isah y ace “ allah ya fi ku , do domin kuidn jinni ba mu da masaniya a kansu , allahi bay a kama bawa akan lain da bai sani ba . Ina rokon allah kariya a bisa sharrinku, saboda ku mushirikai ne, ina mai tabbatar muku da ku tuba ga allah , don ka sha jini domin samun kyalen rayuwa me ka yi ? me kuka dauki rayuwa ne ? Akwai fa tsufa, idan hisabi” A fusace mataimakin shugaba ya yiwa Isah wata razananniyar tsawa bakinsa na fidda yahaki, idanusa na awalkiya suna sauya kaloli KORE, DORAWA zuwa BAKI. Isah dai ya budi idan ya ganshi a daure, sun zagaye shi yayin da shuhuda ke faman rabsar kuka tana ba su hakuri, tana fada musu matsayin Isah da muhimmancinsa a rayuwarta. Sun tabbatar mata cewa, yau za su sha jinin Isaha yanzu kuma ita zata yi jagorancin kisan nasa kasancewarta shugaba kuma sarauniyar matsafa. A hankali ta tako gaban Isah idanunta dauke da wasu sirrika, amma zuciyarta na kuka akan abin da tasan yanzu ya zamar mata dole ta kasha Isah, anya zata iya bayar da jinin Isah wasu can su sha? Isah da ke kallonta a ci kin zuciyarsa yana karanto ayoyi daga cikin alkur’ani bakinsa ya furta. “Allah ga bawanka kada ka bar wadannan bayin naka su halaka ni, Ya Allah, Ya Ubanjigin Jibrilu da Mika’ilu da Israfilu, mai kaga halittar sammai da kassai, masanin fake da sarari. Kai ne kake hunkunci tsakanin bayinka cikin abin da suka kasance suna sabawa a gare ka na gaskiya. Ina rokonka ka shiryar da su don su kasance masu saba maka, Allah idan ka so kai ne mai shiryarwa, Allah ka shiryar da su izuwa tafarki madaidaici. Idan kuma ba masu shiryuwa ba ne, Allah bayinka ne na barka da su, ka tsare ni daga sharrinsu, ka kuma kwato min baiwarka shuhuda wadda azal ta fadawa ba ta ji ba ta gani ba, tunda tun tuna da kuruciya suka sanyata hanyar halaka. Allah ka tserar da mu daga sharrinsu”. Ya yi kabbara mai karfi, y ace. “Allahu akbar! Allahu akbar!! Allahu akbar!!! Walhamdu lillahi kasiran! Walhamdu lillahi kasiran!! Walhamdu lillahi kasiran!!!. Take ya sake karanta suratul Waki’a sai ga daurin jikinsa duk ya zube. Cikin zafin nama ya janyo hannum shuhuda, amma sai ta soma togewa. Ya sake yin kabbara, ya kuma maimaitawa sai kawai ya ji ita ma ta dauka, suka soma gudu. Ba su dade suna gudun ba sai suka tarar da miyagun mutanen a gabansu. A yanzu zuciyar Isah ta soye bay a shakka, kuma bay a fargaba bakinsa dauke da Ayatul Kursiyyu yana karantunta a fili yana karanto surorin karshe na Suratyl Bakara a fili. Tsoro tare da firgici ya shiga cikin zuciyoyin matsafan, don suna mamakin irin barnar da Isah ya yi musu, suna kuma ji suna gani gas hi yana neman samun galaba a kansu. Cikin tsirkewar zuciya mataimakin shugaba ya kwo hannu da niyya shaker Isah, sai hannun ya kama da wuta, ganin haka sai gurin ya yi tsit, babu su duk sun bace. Isah da shuhuda gudu suke bas u yi aune ba ga su jikin dutsen nan na kasar Sokoto, wato Dutsen Kwatarkwashi, suka fadi yaraf. Shuhuda ta zabura ta kankame inna yaduwa ta ce. “Don Allah kada ku bari su sake tafiya da ni, suna wahalar da rayuwata, sun takura min, ni dai wallahi ban yafe masa ba, cuce ni!” Inna yaduwa tana kuka tana rika da shuhuda tana tuno rayuwar da ta yi, lallai akwai sakayya, shi yasa Hausawa suke cewa wata shari’ar sai dai Allah. Ita ma addu’a aka ci gaba da tofa mata har bacci ya yi awon gaba da ita. Zuri’ar Alh. Rabiu sun shiga fargaba da tarin tsoro saboda halin da suka tsinci kansu na samun jinisu cikin matsafa. “Ina zargin kaina a bisa lalacewar Sagir, saboda tun farko shi yaro ne mai son kyale-kyalen rayuwa, a gaskiya na taka rawa wajen shigarsa kungiyar matsafa”. Gaba daya suka zubawa tsohon ido, ya ci gaba da cewa. “Abin da yasa na fadi haka shi ne, me yasa lokacin da Sagir ya soma tashen kudi farad daya ya zam mai arzikin gaske ban bincike shit a ya ya same su ba, wannan yan faruwa bag a ni kadai ba, al’umma baki daya. Me yasa ba zamu ringa bibiyar rayuwar ‘ya’ yanmu ba tare da sun sani ba mu gano su waye abokansu, ko a ofis ko kasuwar, amma idan yaro ya taka matakin balaga shi ken an sai mu zuba masa ido ba zamu san me rayuwarsa ta ke ciki ba. Anya mun son samawa rayuwar iyalanmu jin dadi? Wai me muka dauki MATA’UL-HAYAT (kyale-kyalen rayuwa) ne a wannan zamani? Me muka dauki rayuwar kanta ma? Mu yi gida, mu sanya suture na alfarma, mu shiga motoci na gani a fada, mu auri mataye, me yasa kyale-kyalen rayuwa ya fi tasiri a cikin al’umane?” Kuka sosai Alh. Rabi’u yake yi yana jin ciwon abin da dansa ya aikata. Ya dago idanunsa fal da hawaye, ya ci gaba da cewa. “misali akan Sagir, ya dauki shuhuda ya bayar da ita cikin matsafa, tun farkon rayuwarta cikin kunci ta taso, cikin maraici, ana yi mata wasarere da hankali, da muna yin kafi a gidajenmu irin wadannan shu’uman mutane da bas u shigo ba. Ita shuhuda ya addinta ya ke? Ya karatunta ya ke? Amsar it ace, an birkita rayuwarta, an hanata jin dadin rayuwarta, an hana ta zam mutum. Ni abin da ya fi daure min kais hi ne, su matsafan bas a tsoron yadda rayuwa ta ke juyawa, ma’ana shin suna ta salwantar da jinin al’umma ya rayuwar bayansu zata kasance a lokacin da su suka mutu? Ba sa tsoron abokan huldarsu su yi ta dauki dai-dai cikin iyalansu? Lallai wannan toshewar basira ne babba, kuma ba su tsoron Allah sun tabbatar ko tsafinsu bai kasha sub a lallai ne za su mutu tunda kuwa fadar Allah ce, kowance rai sai ya dandani mutuwa. Saboda haka ya zamar wa iyaye dole su gano su wa ‘ya’ yansu ke abota da su, idan danka ya yi kudi ka sanya idanu ka gona ta ya ya same su, a kuma sanya tsoron Allah a zuciyar iyali, a bas u ilimi musamman ilimin islama, don tsoron Allah ya shigi mutum, ya gano tsafi abu ne na SHIRKA, ka yi arziki ta hanrtar halal, kuma idan Allah ya rubuto kai mai arzikin ne dole zaka yi shi, amma iyaye su ne mafi’ala su gano inda dansu ko ‘yarsu ta sa a gaba, domin ‘ya’ yanka ababen kiwo ne a gare ka. Da ace ma mu iyaye muna kokarin samawa yaro sana’ar yi, misali ko a kasuwa zai yi kasuwanci ya kasance mune jagoransa, ko aiki ne mu zamu nema masa, lallai da an samu ragowar bara gurbi, saboda wasu yaran daga neman abin yin ne ake batar da su, ake jefa rayuwar cikin gurgataccewa duk saboda MATA’UL-HAYAT (kyale-kyalen rayuwa)”. Alh. Rabi’u ya saurara yana sharer hawaye da gefen babbar rigarsa. Inna yaduwa ta ce. “Ni kam Sagir ya cuce mu, haihuwarsa bat a yi mana komai ba sai bakin ciki”. Alh. Rabi’u ya daga mata hannu, y ace. “Kuskuren da wasu iyayen ke yi ken an akan yaransu, ba ma iya dannar zuciyarmu dan ‘ya’ yanmu suka yi mana wa, ni abu, bakin iyaye ko masifa ne ga yaro”. Ta ce, “to ina ranar haihuwarsa, ya mutu ya bar baya da kura?” Alh. Sada ya ce. “Ku yi hakuri, mun sha jin jita-jita game da hakan, to amma kun san yanzu rayuwa ta lalace, yawamnci hassada ta shiga zukatan al’umma , daga an ga mutum ya fara samun kudi ma sai ku ji an ce dan mafiya ne” Alh. Ahmed shi ma ya magantu, ya ce. “wannan abu dai ya riga ya faru, addu’a zamu dinga sanyawa ana yi masa, mu ma mu ringa aika Masada tamu don nema masa rahmar Ubangiji” Shuhuda ta yi tsagal cikin bacin rai ta ce. “B azan yafe masa ba, ya cuce ni, ya shafa min bakin fenti, na yi wata bahaguwar rayuwar, kullum tambayar da name yiwa kaina, wai ni mutum ce ko aljana, ko wata dabba ce daban. Amsar da na kasa ganewa ke nan” Gaba daya shiru ya bakunci falon, Isah ya ce. “shuhuda dukkan mai rai yana kuskure a rayuwarsa, ki yafewa mahaifinki, ki yarda da kaddara domin ke kika fi cancanta da ki yafe masa” Ta ce, “To ko na yafe masa jinin al’umma da ya sha fa? Kun san abin da nake ji ace ka kasance dan matsafi, kuma ya sanya ka a hanyar tsafi, shi ke nan ni mai son MATA’UL-HAYAT ce? Shi ke nan…” Sai ta sanya kuka. . Allah Sarki Shuhuda, hakuri ya zama dole... Hada Hausa Book stories MATA'UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA) ¤¤33¤¤ . Karshe.... BABI NA ASHIRIN DA DAYA GARIN BANZA.. Washegarin da abin ya faru, alh. Ahmad ya samu waya ake sanar masa gidan gonar alh. Sagir ya kama da wuta. Inaalillahi wa’inna ilaihi raju’un kawai yake karewa” Wani irinci ciwon shuhuda ta kwanta bahu ci babu sha, kuma iyayenta bas u son su fita da ita zuma asibiti saboda tsoron azzaluman da ke bibiyarta. Yakub ne ya zo da wani mani malami, don tunda suka dawo das u isa gida ya wucw zuwa birnin g taron fararen aljannu da sukan gudannar a irin wanna lokaci. Har dakin da shuhuda ta ke kwance ma Islamic, masu bayer da magani na gargajiya don kauceuwa tarkon jinn. Ya dubi isah bayan ya gama duba shuhuda ya ce. “ga wasu magunguna nan da zata dinga amfani da su, sunnan ga addu’o’ in da idan tashi zata ringa yi ba ita bag a duk wanda matsafa ko aljannun suka dame shi, idan dai zai bi ka’. Ida zai raba das u. Ayutul kursiyyu 30 bayan kowace sallah, amma sallar ish’I 40. La’ilaha illallahu wahadahu lasharikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa ala kulli shai’in kadeer, kafa 100 bayan sallar asuba da sallar isha’i. idan ta zo kwanciya bayan adduo’in yau da gob eta karanta Ayatul kursiyyu 1 ta hura daya a damanta, daya a hagunta, daya a kafarta, daya a kanta. Sai ta hada hanneyenta ta karanta surorin farko aya biyar na Bakara, da Ayatul kusiyyu da ayoyi guda na karshe na Bakara amanar rasulu, sai ata sha ajikinta ta kwanta.kada ta tashi ta je ko’ina idan tasan da wata bukatar da zata yi, to kafin ta yi bukatar zata yi, in shaa Allahu ta fi karfin abin sharri mutum ko aljan. DOKOKIN DA ZATA BI DON KAUCEWA MATSAFA DA SHAIDANUN ALJANNU. Ta dinga yawan zama da alwala. Ta dinga yin bismillah akan duk abin da zata yi. Ta kaura da kallon finafinai hart a warke. Ta daina jin kide-kide. Ta daina zama babu riga ko dankwali. Idan da hoto a dakin a cire ko na tsuntsaye ne. ta dinga yawaita zikiri, irin wanda ya tabbata bakin manzon Allah (S.A.W). MAGANI Man habbatus sauda dan saudiya,itiliti garin babbar roba guda daya, shayin shaidanu guda 12, jan miski. Wadannan su ne magungunan da zata yi amfani das u, ga ga ita kadai ba har ga wanda shaidanu suka dame shi, irin masu yin aljannu”. Bayan sun tafi ne, sako ya iso gidan ganar ya karasa kamawa da wuta, yak one kurmus, duk abin da yake ciki ya zama toka. Sam Shuhuda bat a damu ba, amma dangin mahaifiyarta sun fi damuwa kwarai saboda sub a su san wainar da aka toya ba, su Alh. Sada su dama sun yi has ashen hakan. ********* Uncle Hamza tun day a ga Isah ya juyo zuciyarsa ta karaye, ya sani yana son Shuhuda amma ba zai iya kassara rayuwarsa ba, (IRI DAYA DA OGA MUHSEEN )ya sha jin labarin shu’umancin matsafa ko jinnu, tabbas ba zai iya ba, dole ya turje ya dawo baya. Suka hadu da Yakub, ya kale shi yana murmushi, y ace. “haba Hamza, kada ka zama ragon maza mana, ko ba kasan mace ta fi son namiji sadauki, gwarzo a? mace bat a son namiji soko, hakika duk da haka na yaba da kwazonka, kasancewarka malamin makaranta sai nag a kana da iya mu’amalada kowa, kasan cewar malamin makaranta babban mutum ne a cikin a’umma mai iya mu’amala da kowa, malamin makaranta mutun ne mai juriya mai kwazo, mai himma amma duk da tarin baiwar da Allah ya yi maka sai gas hi ka karaya. Dama haka rayuwa ta ke, komai himmarka akan abu idan ba ka da rabo akansa sai ka samu sarewa” Uncle Hamza ya yi shiru dai bai iya cewa komai ba, ya san dai zuciyarsa ba zai iya ba, kuma dama komai na rayuwa bay a tabbata said a niyya, idan har ka samu karfi a zuciyarka to kana saka ran samun nasara, shi kam ba zai iya ba. Haka Yakub ya dauke shi ya dawo das hi inda ya dauke shi, ya yi alwala ya yi sallah ya fuskanci alkibla yana addu’o’ in da suka sauwaka a gare shi don samun sauki, yana rokon Allah ya karbi uzurinsa ya cire masa son shuhuda, tunda alamonin su nuna ba zai same ta ba har abada, koda Isah yana son shuhuda ba sai iya barwa wani ita ba. Labarin da Uncle Hamza ya samu na rashin lafiyar shuhuda shi ya sanya ya nufo gidan su don ya je ya yi mata sannu da jiki. Ya same ta a zaune a falo, amma tana kishingide jikin inna Yaduwa, ya ce. “tun yaushe ne bat a da lafiya” Ta yi murmushi, ta ce. “Ai Hamza ta kwana biyu, yanzu kam sai ta samu sauki ma kwarai” Ya kada kansa alamar gamsuwar, muryar Isah suka jiyo yana sallama, suka amsa masa ya shigo. Uncle Hamza ya ji wata matsananciyar kunya ta kama shi, amma sai ya mazance saboda kada ya bayar da kansa. Isah ya dube shi, ya ce. “Ai ta ji sauki”. Hamza yana son ya tambayi Isah yadda aka yi ya kwaci shuhuda, amma bai sami fuska ba, ya dake ya ce. “Ina godiya ta Allah day a baka nasarar kwato marainiyar Allha. Ina yaba maka bias kokarinsa na amince ka fini juriya, ka fini karfin hali. Saboda haka Isah kai ka fi cancanta ka zamo abokin rayuwar shuhuda. Kai ka fi cancanta ka zam miji a gar eta saboda haka ni na janye na bar maka ita. Ina rokon Allah barku tare har karshen rayuwarku” Inna yaduwa cikin zolaya, ta ce. “Kai Hamza ya zak yi saurin karaya? Kasan ba a san mace tuwo ba sai miya ta kare” Ya ce. “Inna, Isah ya fi ni cancanta”. Ta yi murmushi, ta ce. “Mun gode da kaunar da ka nunawa shuhuda duk da kasancewar ta cikin wani yanayi lallai soyayyarka gar eta ba kadan ba ce. Ina fatan zumuntarmu zata dore” Ya ce, “Insha Allah” Isah da Hamza sun zam abokai tunda har sukan kaiwa juna ziyara, shuhuda ta samu sauki kwarai tana fita tana yawo, duk inda ta ga dama babu yadda matsafa zasu yi da ita, saboda ko inda ta ke bas a iya karasowa. Shi ma Isah ya fi karfinsu saboda mutum ne ABIDI, ma’ana mai yawan ibada. Cikin dare shagunan shuhuda da ke cikin kasuwar kwari suka kama da wuta, hankalin Alh. Rabi’u ya tashi kwarai, amma ita shuhuda ko a jikinta, don da zasu bi shawararta ma da an sadaukar da dukiyar gaba dayanta tasan kuma dole zata kare, domin kyalkyal banza ce, kuma dama GARIN BANZA a farau-farau banza yake karewa. Mabiya kungiya sun tashi da tashin hankalin mutuwar mataimakin shugaba, sun damu tun daga nan wasu suka soma yiwa kungiyar tawaye tunda dama babu wanda ke gundanar da mulki kamar mataimakin shugaba, sai suke gudu wasu kuma suka yi gamayya da wata kungiyar saboda sama akwai abota a tsakaninsu. Wannan dalilin ya tashi hankalin tsafinsu inda ya bas u tabbacin jinin shuhuda da Isah ya zam dole a sha shi, amma an rasa ta inda za a kama su, hakan ya sa Yakub da ke kallonsu ya sanar da Isah da shuhuda suka nufi kasa mai tsarki don yin umra, suka yi dawai don samun rinjaye akai. Allah ya bas u nasara gaskiya ta fi karya, alkur’ani waraka ne, sun ce gaba da karantun alkur’ani a masallacin Makka, sanna suka ziyarci Manzon mu a can Madinatul Munawwara. Cikion kudirar Ubangiji dakin tsafin nasu ya kama da wuta, duk wasu manyan bokayensu da suka yiwa biyayya Allah ya karya su, duk abin da suke tinkaho das hi ya lalace, wasu daga cikinsu Allah ya ganar da su, sun shirya, wasu sun mutu, wasu sun samu tawaya ta rasa wani bangare na jikinsu, wasu kuwa hauka tuburan suka dinga yi, haka komai ya lalace musu. Shuhuda ta kubuta daga sharrinsu, ta samu lafiya, ta samu jin dadin da ta rasa. BABIN KARSHE RAI DA RABO Jin dadin rayuwa ya samu ga shuhuda Sagir Rabi’u, yanzu ta gano Isah Sada abi’u shi ya sama mata jin dadin rayuwar da ta rasa. Yanzu shuhuda ta zam mutum kamar kowa. Dama can ita yarinya ce mai nutsuwa ga kaifiyya, a yanzu ma abin haka ya ke, ta samu gurbin karatu a B.U.K Kano, yayin da ta tsunduma neman ilimi ka’in da na’in, a yanzu ta dawo baya saboda samun waraka ma’ana tun farko ta soma karatun alkur’ani ta dantsama a sira don sanin tarihin manzannin Allah, kawa ‘idi, Ahlari, Ishmawi, Izziya duk cikin kankanin lokaci ta yi nisa, dama can ita yarinya ce mai kwalwa. Idan ta samu hutu tana kai wa mahaifiyarta Haj. Karima ziyara can karare. Dama an bat a dama ne saboda ta samu ilimi cikakke domin a da tana rayuwa ne ga ta nan ga ta nan, shi kuma Isah yana can Ibadan a ma’ikatar da yake aiki, yana samun dudi sosai a rayuwa, domin Allah ya yi masa nasibi. Ya samu dauka kwarai da gaske, ya kuma fantsama harkar kasuwanci, samun kudin Isah ya tada hankalin Alh. Rabi’u ta inda ya yi kiran mahaifin Isah Sada ya fada masa abin da ke cikin zuciyarsa. Hausawa sun ce, idan maciji ya sare ka to idan ka ga bakin tsumma zak tsorata. Sun sanya masa ido sun bi komai daki-daki, kuma bas u same shi da wata badala ba, hakika dukiyarsa wankakkiya ce, a yanzu an maida shi Abuja kuma ana ta shirye-shiryen yi masa biki da shuhuda. Shuhuda kwance idanunta na zubar da hawaye. Inna yaduwa ta shigo ta samu gefenta ta zauna, ta ce. “Anya shuhuda rayuwa zata samu haka?” Ta daga idanunta dubi inna yaduwa ta ce mata. “dole ne na yi kuka inna, da ban san komai a rayuwarta ba, duk abin da ya faru gare ni wai-wai nake ji, nasan dai ina rayuwa ne tare da matsafa, ina kuka ne don ina jin tsoron haduwata da Allah” Inna yaduwa ta ce. “haka ne shuhuda, amma ina so ki sani Allah ba ya kama bawa da laifin da bai aikata ba, sun juyar miki da tunani ne tun kuruciya” Sallamar Haj. Karima ta katse ta, ta shigo Inna yaduwa ta yi mata lale marhabin, bayan ta zauna inna yaduwa ta ce. “Gwanda da Allah ya kawo ki, yarinyar nan taki ta dauki abin nan da ya faru ta saka a zuciyarta, kowane mai raid a irin kaddararsa, ki yi hakuri kinji shuhuda”. Ta sanya hannu tana goge idanunta da suka yi jijir saboda kuka. “Ni ina jin haushin Baban ne, ina ji a raina ban yi sa’ar mahaifi ba, in jin haushin Ummata da aure shi, saboda kila don yana da kudi ne ta aure shi, me yasa bat a nema min uba na gari ba?” Murmushi kawai Haj. Karima ta yi, tana jin radadin kalaman ‘yar tata, tasan auren soyayya suka yi da Sagir duk cewar lakacin da ta aure shi yana da abin hannunsa, amma dukiyarsa ba ta rufe mata idanu ta so shi ba, kuma har yanzu tana jin soyayyarsa a ranta, ba don Alh. Jamilu ya yi mata rukon mutumci ba, kila da har abada ba kuma wani auren ba, tana kuma yi masa addu’ar Allah ya yafe masa kura-kuranse. Ba karamin rudewa ta yi ba a lokacin da inna yaduwa da Isah suke kora mata bayanin abin day a faru ba, saboda sam Sagir a mu’amala mutumin kirki ne, kila da ya yi TSAWON RAI za ta iya gano illar halin day a sanya kansa. Hawaye na bin kumatunta ta dubi shuhuda, ta ce. “shuhuda ke yanzu ba yarinya karama ba ce, domin aure ne a gabanki, ke yanzu kina shirin zam uwa, shin kina irin wannan halin wace tarbiyya za ki ba wa ‘ya’ yanki? Kin san kaddara kuwa? Kin san me ake nufi da kaddara? Shin kin yi imani da Allah kuwa? Ina da ja a kan ki shuhuda, ni mahaifiyarki ce zan sanar da ke abubuwan da har yanzu nag a tunaninki bai zo kai ba. Kin yi imani da Allah kuwa, ko har yanzu tsafin na cikin kwanyarki ne? ko har yanzu ba ki zam cikakkiyarki mutum kamar mu ba? Bari ki ji abin da ake nufi da imani. IMANI DA ALLAH Abin da ake nufi da imani da Allah shi ne, ki yi imani da Allah da kyakkyawar zuciyar, ki shaida cewa akwai Allah, kuma Shi ne mai kowa mai komai, Shi ne wanda Ya kagi duniya da lahira da duk abin da suke a cikinsu. Idan hakan ta samu, toh lallai za ki so Allah, domin son Allah wajibi ne, idan kin so Shi za ki girmama Shi Zuciyarki. Ya zamar wad an adam wajibi ya so Allah, ya kuma girmama Shi, idan mutum ya kasance haka zai guji sabawa Allah da manzanSa, zai kuma nisanci abin da Allah Ya hana idan haka ta samu mutum zai samu jin dadin rayuwa a nan duniya da lahira, kamar fadin Allah (S.W.T) a cikin alkur’ani mai girma. “wadna ya aikata aiki na gari mace ko namiji a halin yana mumini wallahi zamu rayarda shi rayuwa mai kyau, kuma wallahi zamu saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa”. IMANI DA MALA’IKU Kuma idan kana son zama cikakken mai imani dole ka yi imani da Mala’ikun Allah (S.W.T), Shi Ya halicce su, Ya sanya su su dinga gadinka a matsayinka na dan gatan bawanSa. Idan mai imani ya tuna haka zai dada son Ubangiji har ya ji yana da GIRMA sosai, saoda kulawar da Yake bas hi, hakan kuma zai sad an Adam ya godewa Allah. IMANI DA LITTATTAFAI Amfanin imani a zuciyar dan Adam zai sa kasan HIKIMAR ALLAH da kulawarsa ga bayinsa dalilin littattafan da Ya saukar wa kowace al’umma. Hakan zai samu gane hikimar Allah cikin abubuwan da Ya shr’antawa kowace al’umma, domin su fuskanci littattafan da suka dace da zamaninsu, sai Ubangiji Ya maida karshen wadannan littattafai shi ne ALKUR’ANIL KAREEM, wanda ya dace da halukan kowa kamar yadda kuma ya dace da kowanne zamani, kuma kowanne bigiri har ya zuwa ranar kiyama. Kai mun godewa Allah da Ya yi mana ni’ima da saukar mana wannan littafi mai tsarki. IMANI DA MANZANNI Dole ne mu so manzannin Allah (SWT) domin Allah Ya aiko mana da Annabawa masu daraja da girma don su zama shirya a gare mu, ya kuma aiko mana da fiyayyen halitta don ya zama cikimakin Annabawa. Hakan zai sa mana son Annabawa ya sa kuma mu girmama su, mu yaba musu domin su ne Manzannin Allah, su ne kebabbun bayinSa da suka tsaya akan bautar Allah da isar da sakonsu da yiwa bayin Allah nasiha suka yi matukar hakuri abisa duk wata cuta da ta su a cikin wannan aiki nasu. IMANI DA RANAR LAHIRA Dole ka yi imani dar ranar lahira hakan zai kwadaita wa mutum bautar Allah Ta’ala t inda zaka yi kwadayin samun ladan lahira, zai kuma sa mutum ya nisanci sabawa Allah a cikin ranar lahira ne wadda ya guji MATA’ULHAYAT (kyale-kyalen rayuwa) zai shakata da ni’imar Allah, ya ji dadin ladan aikinsa” Shuhuda jikinta ya yi sanyi da jin bayanin haifiyarta, ta yi sa’ar uwa wacce ta ked a ilimi, sai dai ba ta yi sa’ar uba ba, da ace yana da ilimi kila da bai shiga kungiyar matsafa ba. Kamar mahaifiyarta ta karci zuciyarta, ta ce. “Zan miki bayani akan IMANI DA KADDARA, domin na sanar da ke kowanne rai bay a tsallakewa akan abin da Allah ya kaddara masa. IMANI DA KADDARA Idan kin dauki kaddara kin yi imani da Annabawansa, dole ki yi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau. Idan ka yi imani da kaddara hakalinka zai kwanta, don zaka samu hutun zuciya, in dai ka yi imani da ita duk wani tunani zaka daina shi, domin duk lokacin da mutum ya fahimci duk abin day a same shi hukuncin Allah ne babu shakka idan ya yarda da hakan zai samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, ya kuma yarda da hukuncin Allah a kansa.. Babu wanda ya kai mai imani da kaddara samun nutsuwa da hutun zuciya, domin idan ka yi imani da haka, sai ranka ya nutsu, ka sakankance ka rungumi kaddara zuciyarka ta saki. Haka kuma zai korewa mutum duk wani ji ji da kai, inda wani alheri ko wata ni’aima ta same shi sai ka gay a gode Allah, ba zai yi mamaki ba, kuma ba zai kawo wayonsa ko dabararsa c eta ba shi ko iliminsa ba. Yarda da kaddar zai korewa mutum bacin rai, sai mutum ya yi hakuri da abin day a same shi sai Allah ya bas hi ladan hakurin. Wannan shi ne manufar Allah (S.W.T) da yake cewa a cikin alkur’ani mai girma. “Wata masifa bat a taba samuwa ba ko a ban kasa ko kuma cikin kawunanku face duk yana cikin littafin lauhulmahafus, kafin mu halicceta, wato ita wannan kasar da wannan ran lallai wannan abu ne mai sauki ga Allah, domin kada ku bata ranku da abin fa ya kubuce muku, kuma kar ku yi fariya da abin da Allah ya ba ku. Allah bay a son mai yawan takama, mai yawan alfahari. Shuhuda ta fashe da kuka, yanzu ta fahimci Ummanta, ta gano kuskurenta ta yarda da kaddara. Ta dubi mahaifiyar tata, ta ce. “A da na yi alkawarin har na bar duniya b azan taba yiwa babana addu’a ba. Amma yanzu kin karya lagona, zan kasance mai roka masa rahmar Ubangiji” Inna yaduwa ta dubi Haj. Karima, ta ce. “Shi yasa na ke sonki, har yanzu in bakin cikin rabuwarmu da ke a tsatsonmu” Haj. Karima ta ce. “Inna ya zamu yi da hukuncin Ubangiji? Haka Allah ya tsara mana, sai na yi aure a wani gurbin” Ta yi murmushi, tukunna ta ce. “Muna zaune lafiya, ni da zai yarda da na ba shi shawara ya dawo da uwar ‘ya’yansa tunda ta fi mu gaskiya akan zargin mutumwar danta” Jin hirar da suke shuhuda ta mike ta fice a falon, inna yaduwa ta ce. “A’a. kada ki soma wannan dayen hukuncin, yanzu gas hi kin yi kyau, kin yi kibarki, kin san fa su jarababbun mata daban suke, kuma mai hali ba ya fasa halinsa sai dai ya yi sauki ku dai yi zamanku lafiya, Allah ya bata wani mijin” Bakin Uncle Hamza da Zuwairiyya ya tashi, kamar ba a yi ba, haka nan dai ya daure ya amince zai aureta ko don jiran da ta yi masa. Isah da shuhuda sun halarci bakin, sun kuma yi masa gudunmawa wacece tat say masa a zuciya. Sanye ta ke da doguwar riga ta yi daurin daidai da zamani, flat shoe ne a kafarta ta sanya dankunne da awarwaro hard a zobe, duk macin hannynta dauke da ledar tana tafiya kamshin turarensa kawai ta shaka don kanta a kasa yak e, tad ago fuska tana murmushi. Isah ya ce. “Sai ina haka ‘yanmatan?” Ta ce, “Wajen su Hajiya zan zaga” Ya ce, “Bari na yi rakiya” Ya ce sanya hannu ya karbi ledar hannunta, tad an tsaya ta marairaice cikin shagwaba ta ce. “Ni a’a ba sai mun je da kai ba” Ya ce, “kin san dama mu tun muna yara tif da taya ne, raba mu sai Allah, ko bah aka ba ‘yar amaryata? Yarinya day a fada ya ba ta dariya. Sun jera cikin gida kananan yara suka tso da gudu, “Aunty Shuhuda oyoyo” Ta samu gefe ta zauna suna gaisawa da matan gidan, yaran suka ringa lekenta sai suka sake gaishe ta, sun gaishe ta ya fi sau uku said a Isah ya kore su, sai ta farga alewar da ta saba raba musu ce bat a bas u ba, shi ne suke ta gaishe ta, ta amshi ledar hannun Isah ta ce. “Gas hi ku je ku sha, mantawa na yi” Su Haj. Asibi suka ringa dariya akan kuruciyar su Hadiza auta. Komai aka saw a rana wa’adi gare shi, kuma saurin zuwa yake, aka ce RAI DA RABO, yau Allah kawo ranar bikin Isah da shuhuda, an sakata a lalle mahaifiyarta tun ana gobe kamu tai so garin tare da ‘yan uwanta suka kawo kayan daki rantsattsu hard a furniture wanda Alh. Jamilu ne ya yi komai da uba yake yi. A nan ma iyayenta sun yi mata kaya na gani na fada, dayya aka shirya gidan shuhuda tamkar ba za a mutu ba. An shirya gagarumin biki na ‘yargata, Inna yaduwa ta godewa Allah akan TSAWON RAI da ta yi har ta ga auren Isah da shuhuda, ta dinga tuna kurunciyarsu. Manyan malamai sun yi laccar aure, sun kuma tunar da iyaye akan sanya ido ga rayuwar ‘ya’ yansu, domin rayuwar yanzu rayuwa ce mai cike da hadari a cikinta. Gidansa da ke shagari Quarter a nan cikin jihar Kano aka kai ta. Satinta daya suka wuce honey moon, sun zagaya kasashe shida, a China ne suka hadu da Zuhran ya Deen (KANIN MAJINA) wadda ita ta ji ta aminta da ita domin ita dama bat a yi wasu kawaye ba, Isah ne mijinta kuma amininta. Shuhuda ta samu gata a bangaren mijinta, yana riritata, domin ita ma mace ce wacce tasan kanta, ma’ana tana kula da jikinta ta fannin gyara, sannan tana ba wa duk wani abu na mijinta muhimmanci ta fannin abinci saban wasu matan da ba su mayar da hankali akan abin da majinsu yake so ba. Tana ba shi kulawa ta musamman, sai ta kosar da shi, hakan ba ta taba barinsa da wata bukata har sai ta kosar da bukatunsa, tana tattilin mijinta kamar yadda yake riritata. Da safe idan ta tashi sai ta yi kwalliyar da zata tsaya masa a rai, bat a barin kofar da mijinta zai hango kyawun wata macen a waje. Kamshin jikinta kamshi ne na musamman duk mecen da tasan sirrin kanshi, kuma tasan kanta dile ne ta kula da kikinta ta hanyar kamshe yadda zai wadata jikinta, domin mu mata jikinmu lunguna-lunguna ne das hi, idan har za ki bari miji ya ji wani wari a jikinki, lallar za ki gundure shi har idan kina da kishiya ki ringa zargin ta raba ki da mijinki, alhalin ke kika raba kanki das hi. Dole ne mata mu kula da kamshi a jikinmu, domin shi kansa kamshi yana motsa sha’awa, baki yana da muhimmance a kula da shi, domin idan har zaki yi Magana a ji tashin wari lallai zaki ga ko mata ne za su ringa kawar da kai bare kuma mijinki. Hamata ita ma a kula da gyaranta, kada a barta da gashi domin tsafta tana taka muhimmiyar rawa wajen zaman takewar aure, kada ki ce, to ni dab a ni da shi, da me zan sanya turare? ‘Yan uwanna mata akwai turaruka masu kamshi da saukin kudi ba lallai sai kin yi amfani da mai matukar tsada ba. Sai uwa-uba ma kwanciya, lallai mace tasan salo-salon wasanni da zata zo wa majinta da shi don ta gamsar da shi, Muddin za ki kosar da shi babu yadda zai yi ya yi kwadayi a waje balle ya fada hannayen kurayen dawa (karuwar). A gaskiya wasu matan su ke sakaci wajen sanya mazansu bin matan banza, komai sai ka ji mace ta ce, sai ka ce wata ‘yar iska, ni ba zan iya ba, abin da mu matan gida ba mu gano ba shi ne, su matan wajen da me suka fi mu? Mun fi su komai namiji zai fi samun nutsuwa akan ta waje, amma sai mu sau bakin zare idan an aure mana yarinya ki ji an ce ‘yar yarinya c e, amma idonta a bushe yake, saboda me ke ba zaki bude idonki ba ki ba wa mijinki kulawa ta musamman don ki kwato shi daga hannunn kuraye? Shuhuda kwance ta yi filo da cinyar Isah, shi kuma hankalinsa na kan labaran da yake kallo, ta ga ya sauya tasha ta tabbarta y agama jin labaran, ta ce. “yah Isah?” Ya maida dubansa a gare ta ya ce. “Ya aka yi ne matar?” Ta ce “kasan na yiwa zuhura alkawarin idan mun shigo kano zamu kai mata ziyara. Ya ce allah ya kaimu za mu je ne. Sun je gidan zuhuran Deen ta kira wayarta ta bata adresse sosai suka iso gidan suna shigowa get din gidan a lokacin suka hango deeni sun yi fakin kusa da su, ya dubi Isah ya gane shi suka gaisa, ya ce. “A’a ashe kun iso kano? Ya Abujan ne? Suka gaisa da wasu yara, ya ce. “A’a duk naku ne wadannan yaran? Isah y ace “Eh, wai za su je gidanmu ne su gaida baffa su yi masa week end. Isah ya ce “A’a, kai dai ka ce kun kori yara zakuji dadinku” Deeni ya yi dariya, ya ce. “kada mu yi dariya, ya ce. Zuhura ta yi murnar ganin shuhuda don ba ta yi tsanmmanin za su sake haduwa ba. don ita duk zancen shuhuda ta sanya su a shirme. Ta hidima da su, sun san sun shigo gidan girma. Shuhud na kallon hotona suna hira, zuhura ta ce. “Oh shuhuda, labarinki yana matukar damuna a rai, har na sanr da maman shureim wata marubuciya da muke mu’amala, mun yi alkawari da ita idan dai mun hadu zan sanar mata” Sai ta jawo way ta soma neman wayar maman shureim, sai aka yi rashin sa’a ta tafi makaranta ta bar wayar a goda, sai ‘yarta ce Nusaiba ta dauka ta sanar musu. Sun yi hira sosai da zuhura labarin rayuwarta, har zuhura ta yi mamakin labarin, sun kuma shirya ranar da zasu samu maman shureim don mata da wannan labara don ta fesawa duniya kila ko mutane sun farga da sharrin MATA’UL-HAYAT. Rayuwa ta mika cikin shuhuda ya girma, suna zaune a falon inna yaduwa don ta rigima sai an dawo mata da shuhuda wait a haihu a gabanta. Isah yana zaune, innar na gefensu tana lazimi, ya dubi shuhuda ya ce. “kullum addu’ata a Haifa min ‘ya mace” “mace kuma? Kai ko saboda me?” “na ga mafi yawancin maza sun fi son ‘ya’ ya maza. Ya ce, “To ni na sha banban das u, kinga ‘ya mace ta fi tausayin iyaye, ta fi imani saboda rauninta, kuma ta fi zumunci, ni da za ki gaji wata kakata aid a na yi murna” Ta yi murmushi, ta ce. “Wai kana nufin Hajiya ‘yar Gandu? Don nasan dai ba inna yaduwa ba” Ya ce, “Ita mana, kinga haihuwa ta tara duk ‘ya’ya mata, ki duba ki ga dadin da ta ke ciki, ga iyalai masu hadin kai da zamunta, kwadayin haka ke sanya ni son ‘ya’ya mata? Inna yaduwa ta shafa addu’a ta ce. “ku dai Allah ya bada na gari, da mace da mijin du kana masu zumunci, masu tausayin”. Suka ce, “Eh, haka ne”. Watan haihuwa ya tsaya, ranar juma’a Allah ya sauki shuhuda, ta Haifa danta namiji, ‘yan uwa da abokan arziki sun halarci sunan, an ci an sha, yaro ya ci suna Muhammad Sagir wato sunan mahaifinta, sai ake kiransa SADAUKI. To Allah ya sa cikon addini ne, amin. . TAMMAT BI HAMDU LILLAHI Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maka, muna neman taimakonka, muna rokon afuwarka akan kuskuren da muka yi. . Marubuciyar wannan littapin mai cike da ILMANTARWA, PADAKARWA tare da NISHADANTARWA (Zahra'u Baba Yakasai, Maman Shauriem) Ya Allah Ya jin kanta da Rahama, Ya sanya Haske a kabarinta, Ya saka mata da gidan Aljanna, mu kuma Ya kyautata tamu karshen.....ameen. . Ashe sabo ya na da dadi, amman rabuwa da zapi, 'yan uwa na, ku tausaya idan nayi muku laipi cikin gan-ganci ko a kuskure, kuce kun yape, ni kuma daman baku min laipi ba! Allah (SWT) Ya gaparcemu baki daya.