: WATA RANA DA DADDARE.🖤 🖤 (horror story)☠️ Writing by Aishat Abdul-falalu. (Rimin k'aura). (Mmn Humaira.) Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una Kullu napsin za'ikatul,maut (Ya Allah ka jik'an Humaira da rahama,'Ya Allah kasa Chan tafiye mata Nan,'yata Humaira ina sanki Amma Wanda ya bani ya amsa,Ina sanki Wanda ya k'ago ki ya k'arb'a. Ubangiji ka k'ara danganar min da zuciya ya Allah Kai ka bani Kai ka k'arba. Ina barar addu'a ga duk Wanda ya karanta wannan Page d'in.) WATA RANA DADDARE LABARINE DA AKA ƘAGOSHI CIKIN SIRRIN DARE, AKWAI ABUBUWAN AL-AJABI DA MAMAKI WANI IRIN BAHAGON SIRRI NE ME CIKE DA CHAKWALKWALI DA CHAKWAKIYA SAI AN KARANTA. DOGON LABARINE AKWA 1, 2, 3,4 NA FARKO ZAI ZAMA FREE NE SAURAN PAID. Daga marubuciyar ISHARA. SO KO HAUKA. SHAGALTATTUN DUNIYA. WATA RANA DA DADDARE. Page 1-2 A kullum tambayar da Muhijjinatu kewa mahaifinta, wanda take kira Abbu itace . ''Abbu me yasa muke rayuwa a daji, Ina mahaifiyata, Abbu ina danginmu, kai ma ina naka iyayen? A duk lokacin da ta jefo mishi wa'innan tambayoyin zai gigice zai fita hayyacinsa numfashin sa zai dinga fat, fat. baƙin ciki zai tsaye ya tokare mishi ƙahon zuciya. idonsa zai kaɗa yai jawur, wani lokacin har suma yake. Ita kuma bata damuwa zata zauna ta tsare shi da ido bata ko ƙyaftawa amsa kurum take jira ya bata. Yau da hantsi suna zaune ita dashi, kifi ne yake gasa musu irin manyan nan mai ƙashi da tsoka. Kammala gasa kifin keda wuya ya miƙo mata cikin wani ɗan ƙoƙo. karɓa tayi ta ajiye gefe tana jira ya ɗauko gishirin da yake ḅarbaɗawa. Ba jima wa ya dawo da gishirin shima cikin ƙoƙon zama yai ya ɗauki kifin da ke ajiye a gaban muhijjina cire ƙayar ya soma yi yana bata a baki tana ci cikin nishaɗi. harta ƙoshi, saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya soma ci. Bayan kowa ya ƙoshi kana Muhijjinatu ta zuba mishi ido bata ko ƙyaftawa. ''Abbu'' ta kirasa. ''Na'am ''ƴar lele. dubansa tayi ta ƙura mishi ƙyawawan idanununta tace ''Abbu me yasa muke rayuwa daga ni sai kai, sannan me yasa bama cin hatsi, alhali kace mutane suna cin hatsi, shin mu mutane ne koko, sannan yaya kasan akwai labarin mutane a cikin gari? Muhijjinatu ta fashe da matsanancin kuka bayan ta gama jerowa Abbunta wa'innan tambayoyi. Miƙewa tayi tsaye tsam tare da zuwa gab dashi ta durƙusa ta riƙe hannayensa tsam, har a wannan lokacin idonta bai daina tsiyayar da ruwan hawaye ba. ''Abbu kullum sai na tambayeka amman baka bani amsa ka ƙi ka sanar min da ko muɗin su waye.. . . . . . ka bani amsata Abbu ta faɗa da ƙarfi. Shiru ba amsa ''Abbu! "Abbu!! ta faɗa da ƙarfi tare da girgizashi. Sam Abbu ya suma baya koda motsi, kuka ta kuma fashewa dashi da ƙarfi, da gudu ta ruga kogi da yake a tsakaninsu da kogin ba nisa ta ruga ta ɗibo ruwa ta soma shafa mishi. Dogowar ajiyar zuciya yaja ya kirata ''Muhijjinatu! shiru tayi bata amsa ba, wai a dole tayi fushi da Abbun nata Allah sarki ƙuruciya na aiki a nan. Abbu dai ya washe tangarangan yana ƙoƙari ya kawar ma Muhijjinatu tunani ita kuma a ɓangarenta ɓacin rai ya linku sosai. Miƙewa tayi tsam dagudu ta ruga ta nufi tafkeken kogon, sai da taje gaf dashi ta dubi Abbu dake nesa da ita ya zuba mata ido, azatonsa ruwa zata sha. bai ankara ba yaji kalaman Muhijjinatu wai'nda koda cikin barci bai taɓa zaton ƴar lelensa Muhijjinatu zata faɗa mishi wa'innan maganganu ba. ''Abbu'' nayi nayi dakai ka faɗa mini koni waccece ''Shin mu wanne halitta ne , me yasa muke rayuwa a DOKAR DAJI kaƙi ka sanar dani, kullum innayi tambaya sai ka faɗi ka suma, to zan faɗa kogon nan ruwa ya jani, in yaso sai ka huta da gani na. . . . . . . . . . kafin ta ƙarasa jikinsa ya katse da ƙyarma bakinsa ya soma ƙyaf, ƙyaf. ''Karki aikata haka Muhijjinatu'' ki ceci rayuwata kece farinciki na dawo gareni koda zan mutu to zan sanar dake komi dawo gare ni Muhijjinata. . . . . ''Da gaske kake zaka bani sirrin komai? gwaɗa kai yai alamar farin ciki. da gudu ta dawo kusa dashi ta rungumoshi ta baya tace ''Ina jinka Abbuna'' juyo da hannayenta duka biyun yai ta gabanshi ya zaunar da ita ƙaunarta da soyayyar ɗa da mahaifi na daɗa lunkuwa a kowanne saƙo na jikinsa. ''Abbu bani amsar tambayata'' ta faɗa tana goge ƙwallah. ''Muhijjinatu share hawayenki. Zan amsa miki tambayarki a yanzu. Cikin mamaki ta ɗago ta dubeshi tace''Abbu da gaske? karon farko a rayuwarsu da yai mata magana mai daɗi a duk lokacin da ta tsare shi da tambayoyinshi. Yace nutsu Muhijjinatu ''Zan amsa miki kaɗan daga tambayoyin da kikai min. Waro ido tayi farin ciki ya gaza ɓoyuwa. ''Da gaske kake Abbu?" gwaɗa kai yai alamar ''Ehy. kafin ya ɗora da faɗar. Idonsa ya kaɗa yai jawur sosai yace wa'inda zan amsa miki su nake da amsar su wa'inda ban amsa miki kuwa bani da amsarsu. . . . . . . . . . Abbu ina jinka. . . . . To be nex page. Da sannu zaku ci chakwakiyar da ke ciki. Ku ci gaba da kasancewa da Mmn Humaira a domin jin ci gaban labarin. 07049138863. Call 07012329134. [12/25, 11:21 AM] Rip my dauther: WATA RANA DADDARE.🖤 🖤 (horror story)☠️ Writing by Aishat Abdul-falalu. (Rimin k'aura). (Mmn Humaira) from the writer of Ishara. So ko hauka. Shagaltattun duniya. Page 3-4. Abbu yace ''Muhijjinatu tambayar farko da zan amsa miki ita ce. "Labarin mutane da nake baki a mafarki nake gani. . . . . ''Abbu ta katseshi. Dakatar da ita yai ta hanyar cewa''Ba sai kin kuma jefo ni da wata tambayar ba tsaya. Banaso na fara ƙarya iya abinda na sani shi zan sanar miki. . Tambaya ta biyu dalilin da yasa muke rayuwa a dokar daji shine, tabbas mutane suna rayuwa a cikin gari, to amma mu me yasa muke zaune muna rayuwa a daji? Kinga kenan amsar a bayyane take mu ba mutane bane, ina ji a jikina muɗin wani jinsi ne cikin halittu. . . . Shiru Muhijjina tayi ta zubawa Abbu ido, da alama dai bata gamsu da amsar da ya bata ba, sai wani maƙoƙon baƙin ciki ya kuma tokare mata ƙahon zuciya ''Me ma yasa ta tsaya ɓata lokacin ta najin wa'innan bahagon amsar daga bakin mahaifinta? shi kuma ta ɓangarensa yana cikin zullumin ƙar ta kuma jefo masa wata tambayar da ta shallake tunaninsa. ''Abbu idan ya kasance muɗin wasu nau'in halittun ne to ina 'yan uwanmmu? kowacce halitta da take rayuwa a DOKAR DAJIN NAN tana da ƴan uwa to mu ina namu? ''Kai waccece ta haifeka? "Sannan Nima Ina mahaifiyata? tirƙash! chakwakiya. dafe kai yai wani irin tashin hankali marar misaltuwa ya ziyarci dukkanin wata gaɓa da sashe dake jikinsa. ''Me yasa a duk lokacin da Muhijjinatu ta tuskeshi da tambayar dangi yake shiga ruɗani? wani mugun bala'i da musifa da tashin hankali ke riskarsa a lokacin. Abu na farko zaiji tamkar an ɗauki dutse an guma mishi aka, abu na biyu bakinsa zai mutu murus! "ABBU ta kirasa. Firgigit ya juyo ya zuba mata ido kafin tace wani abu yai saurin katseta ta hanyar faɗar ''Muhijjinatu muddin kina a raye Akwai WATA RANA DADDARE da zan bayyana miki komai ina jin lamarin ya kasance sirri ne domin DADDAREN komai ya faru sau ɗaya tak WATA RANA DADDARE nakan tuna waye ni. kema waccece ke ki jira lokacin yazo da zarar yazo to zan tashe ki komin NISAN DARE na fayyace miki SIRRIN. Gaba ɗaya kan Muhijjina ya toshe kwalwar ta ta shiga chakwakiya, lissafinta duka ya kwance sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda ya kuma cewa uffan, Muhijjina dai Abbu ya ida jefa ta cikin wata rikita rikitar ya ida chaƙuɗata ya ida damalmala mata lissafi. Miƙewar Abbu ya katse shiru, dubanta yai yace''Muhijjinatu zan tafi daji na ƙutsa na nemo mana naman dabba domin na gaji da cin kifi hakanan. Kema nasan ya gundure ki ko Muhijjinata? Ya faɗa fuskarshi cike da annuri. ba yabo ba fallasa ta dube shi tace''Abbu banasa so kana yin nesa dani, wata rana idan ka daɗe sai naga tamkar ba zaka dawo ba Abbu bana son rabuwa dakai ko kaɗan rashinka a tare dani yana rikita ni da jefani cikin matsananciyar damuwa. Sannan bana san wani abu ta cutar min dakai daka bari mun ci gaba da cin kifin mu tinda shima abunci ne. dafa ta yai ya soma bubbuga kafaɗarta yace''Muhijjinatu kece bugun numfashina idan na rasaki rayuwata bata da amfani kamar yadda kike jin niɗin rayuwarki ne nima haka nake ji a jikina. Don haka kar ki damu zan dawo kinji. Cimak ya ɗagata ya tafi da ita a saman gadon da suke kwana wanda shi ya sassaƙa shi da itace. Kwantar da ita yai kana ya ɗauki baka da wuƙaƙensa ya rataya ya luluƙa cikin daji ''Sai na dawo Muhijjinatu. To Abbu karka daɗe. Murmushi yai ya juya ya tafi yana kallonta. Ita kuma ta sarda kai ƙasa hawaye na tsiyaya. Share don girman Allah. 07049138863. Call 07012329134 ƙahon zuciya ''Me ma yasa ta tsaya ɓata lokacin ta najin wa'innan bahagon amsar daga bakin mahaifinta? shi kuma ta ɓangarensa yana cikin zullumin ƙar ta kuma jefo masa wata tambayar da ta shallake tunaninsa. ''Abbu idan ya kasance muɗin wasu nau'in halittun ne to ina 'yan uwanmmu? kowacce halitta da take rayuwa a DOKAR DAJIN NAN tana da ƴan uwa to mu ina namu? ''Kai waccece ta haifeka? "Sannan Nima Ina mahaifiyata? tirƙash! chakwakiya. dafe kai yai wani irin tashin hankali marar misaltuwa ya ziyarci dukkanin wata gaɓa da sashe dake jikinsa. ''Me yasa a duk lokacin da Muhijjinatu ta tuskeshi da tambayar dangi yake shiga ruɗani? wani mugun bala'i da musifa da tashin hankali ke riskarsa a lokacin. Abu na farko zaiji tamkar an ɗauki dutse an guma mishi aka, abu na biyu bakinsa zai mutu murus! "ABBU ta kirasa. Firgigit ya juyo ya zuba mata ido kafin tace wani abu yai saurin katseta ta hanyar faɗar ''Muhijjinatu muddin kina a raye Akwai WATA RANA DADDARE da zan bayyana miki komai ina jin lamarin ya kasance sirri ne domin DADDAREN komai ya faru sau ɗaya tak WATA RANA DADDARE nakan tuna waye ni. kema waccece ke ki jira lokacin yazo da zarar yazo to zan tashe ki komin NISAN DARE na fayyace miki SIRRIN. Gaba ɗaya kan Muhijjina ya toshe kwalwar ta ta shiga chakwakiya, lissafinta duka ya kwance sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda ya kuma cewa uffan, Muhijjina dai Abbu ya ida jefa ta cikin wata rikita rikitar ya ida chaƙuɗata ya ida damalmala mata lissafi. Miƙewar Abbu ya katse shiru, dubanta yai yace''Muhijjinatu zan tafi daji na ƙutsa na nemo mana naman dabba domin na gaji da cin kifi hakanan. Kema nasan ya gundure ki ko Muhijjinata? Ya faɗa fuskarshi cike da annuri. ba yabo ba fallasa ta dube shi tace''Abbu banasa so kana yin nesa dani, wata rana idan ka daɗe sai naga tamkar ba zaka dawo ba Abbu bana son rabuwa dakai ko kaɗan rashinka a tare dani yana rikita ni da jefani cikin matsananciyar damuwa. Sannan bana san wani abu ta cutar min dakai daka bari mun ci gaba da cin kifin mu tinda shima abunci ne. dafa ta yai ya soma bubbuga kafaɗarta yace''Muhijjinatu kece bugun numfashina idan na rasaki rayuwata bata da amfani kamar yadda kike jin niɗin rayuwarki ne nima haka nake ji a jikina. Don haka kar ki damu zan dawo kinji. Cimak ya ɗagata ya tafi da ita a saman gadon da suke kwana wanda shi ya sassaƙa shi da itace. Kwantar da ita yai kana ya ɗauki baka da wuƙaƙensa ya rataya ya luluƙa cikin daji ''Sai na dawo Muhijjinatu. To Abbu karka daɗe. Murmushi yai ya juya ya tafi yana kallonta. Ita kuma ta sarda kai ƙasa hawaye na tsiyaya. Share don girman Allah. 0704913886 page 5-6 Kwance take tana ta safa da marwa har rana ta take Abbu bai dawo ba. Zuciyartavta cunkushi da tarin tambayoyi ta rasa me bata amsa cikin shekara uku da suka shuɗe ta fara sanin abubuwa na tambayar tushen asalinsu da jinsinsu. Amma wanda ya kasance shine jigo kan lamarin ya kasa bata amsa akan komi to ita yanzu yaya zatayi da rayuwarta? Sud'in wa'inne kalar jinsun halittane? "Me yasa suke rayuwa a DOKAR DAJI.? dukkanin dabbobin dake rayuwa a dajin nan su da yawa ne, amma me yasa suke rayuwa su su kaɗai? wannan bahaggon al-amari ya gaza misaltuwa tabbas abune me cike da chakwakiya waye zai warware mata shi *** b*** Rana ta ƙwalle ƙwal, farkawar Muhijjinatu kenan daga barcin ranar da ta daɗe tanayi wanda bata san sa'adda ya saceta ba. Jikinta ya soma karkarwa ''Shin ina mahaifinta? Tin safe Abbu har yanzu shiru'' gabanta ya dinga dukan tara tara zuciyarta ta dinga safa da marwa. Duk wannan matsananciyar yunwar dake addabarta sam bata ji tunaninta kawai ina Abbunta yake. Lallai ba abinci kaɗai ke magance yunwa ba tashin hankali ma yakan gusar da ita. fargaba zullumi duka sun taru sun cukurkuɗewa baiwar Allah ita kaɗai. Chan da taga ba sarki sai Allah ta dawo wajen bukkarsu ta zauna dirshan ta dinga dirzar kuka yi take ba ƙaƙƙauta wa zuciyarta tana tafarfasa. . . Kuka take sosai bilhaƙƙi da gaskiya. *** Tana tsaka da yin kukan ne taji an dafa mata kafaɗa ''Muhijjinatu ''Meke damunki?. . . Kafin ya rufe baki ta tashi cikin farin ciki ta maƙalƙaleshi sai kuma ta fashe da kuka tana share hawaye. Shima dariyar yai yana ƙoƙarin ajiye ƙatuwar dabbar da ya kaso musu ko meye ?oho! gefe ya ajiye kafaƙin dabbar kana ya kamo Muhijjinatu yai yace ''Ƴar lelen Abbu meke damunki, me yasa min ke kuka? murmushi tayi kana tace''Abbu ba kaine ba ka daɗe sai, naga kamar ba zaka kuma dawowa ba. Murmushi shima yai ya ɗora da faɗar ''Shikenan don na daɗe sai aka ce miki bazan dawo ba. Sinne fuskarta tayi ƙasa alamar kunya. Chan kuma tace''Abbu bana san kana nesa dani, bana san rasaka, bansan kowa ba, banda komai sai kai, kai kaɗai nake gani inji daɗi a rayuwata duk ranar da ya kasance na rasaka bansan yadda zanyi da rayuwata ba. . . . . . . Katseta yai yace''Ƙwarai Muhijjinatu akullum abinda kemin yawo a rayuwata kenan idan kika rigani tafiya yaya zanyi? lokacin da muke rayuwa nida mahaifiyarki haka mutuwa tazo ta ɗauke min ita tabarni ƙwallin ƙwal, to sauƙin tabarmin sanyin idaniya ƙeɗinnnan ya nunata, to yanzu zullumina ranar da za'a wayi gari niko ke babu ɗaya wayyo Allah! Wannan ita ce kaɗai damuwata bani da damuwa face wannan.. . . . . . Ya faɗa tare da goge hawaye masu zafi. . . . Muhijjinatu ta miƙe ta goge mishi ƙwallar da suka tarar masa a kwarin ido tace''Abbu nasan mutuwa tana da tausayi babu yadda za'ayi ta ɗauke ɗaya tsakanin ni ko kai tabar ɗaya duk tare zata ɗauke mu Abbu. . . Kawar mata da damuwar yai ta hanyar cewa''Maza tashi ɗauko wuƙa a gyara naman kinji? a zuciyarsa kuwa yana sane da damuwarsa yasan dole ranar zata zo ranar da mutuwa zata ɗauke shi koshi ko Muhijjinatu. . . . . Tunaninsa ya tsaya lokacinda ta miƙa masa wuƙar mai kaifin tsiya. Kamo kafaƙin yai ta riƙe yana yankawa suna labari. har yai dubarar da yai ta haɗa dutse da dutse wuta ta kama ya ɗora naman saman wutar. 07049138863. Call 07012329134 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ page 7-8 Cikin ƙanƙanin lokaci naman ya gasu. Muhijjinatu ta ɗauki tsoka ta cusa baki kana tace''Abbu cikin naman dawa meye ka kaso mana? Murmushi yai batare da ya bata amsa ba yace ''Kedai ci ƴar lelena. ''Abbu da alama ba ƙaramin fafatawa kayi da dabbar nan ba ko? a wannan karon ma bai bata amsa ba murmushi ya kuma yi sosai da alama dai murmushi al-adar Abbu ce. bata damu da rashin bata amsar da bai ba, sai tace''Gaskiya Abbu kai jarumine wannan katotuwar abu haka. A wannan karon fashewa yai da dariya yai tayi ba ƙaƙƙautawa. ''Muhijjinatu tambayarki tayi yawa. *** **ABUJA STATE** ''Haba Daddy yanzu naji gari ba matse ba takura. Amma a kano talakawa sunyi yawa kullun gida baya rabo da ƴan maula, musamman dangin Mommy na ƙauyen nan ga ɗauɗa ga talauci, kokai yanzu ai ka huta Daddy. Farida ce me wannan magana tanayi tana kallon mahaifinta Alh. Bashir wanda ya kwashe da dariya, dama halayensa sak sune Farida ta biyo. Haj. Zainab dake jinsu ta zuba ma Farida ido jira kurun take su haɗa ido ta harareta amma Farida ta kasa haɗa ido da ita. Alh. Bashir yace ''Ai Farida komi kike so a duniyar nan nima shi nake so babban burina shine inga kin zama babbar ƴar boko ki zama professioir. Farida ta kwashe da dariya tace, Daddy dole nayi karatu kodon kai a duniya kai kaɗai ke sona Daddy. suna cikin taɗin friend ɗin Farida suka shigo ba ko sallama, kallo ɗaya zakayi musu ka tabbatar da su duka sun ƙoshi da rashin tarbiya. Alh. Bashir ya zauna ya bararraje cikinsu yana dariya harda ƙyaƙyatawa. Da zai tafi taransfer 1 miloin yai musu a account, bayan fitarsu wata daga ciki ke cewa. ''Amma Farry Dad ɗinki wayayyen mutum ne sosai kekam kin caɓa. DAma ni. Farida tace. ''Shi kaɗai ke wayayye Allah ya tsimake ku ya kori Mommy da tuni ta kwafsa mana, kunsan ita rainon ƙyauye ce. baki ɗaya suka saka dariya. Shigowar Mariya ya katse su ta ajiye musu ababan ciye, ciye da shaye shaye, ƴarta Azkafiya tana biye da ita. Tsawar da Farida ta dakawa Mariya ya katse Azkafiyya daga kallon da take bin ƙawayen Farida dashi. ''Ke wacce iriyar jahilar ƙyauye ce iye? Uban meye nan kika ƙwaɓa min? shiru Mariya tayi, ran Azkafiyya idan yai dubu ya ɓaci, kwashe kayan haukanki muje restaurant a chan munyi lunch ɗin. jikin Mariya na ɓari ta kwashe kayan, ran Azkfiya ya dugunzuma sosai. na irin wulaƙancin da farida kewa mahaifiyarta. . **DOKAR DAJI** Gari ya waye rana ta ƙwalle ƙwall yau Abbu baya zuwa ko ina zamansa zaiyi da Muhujjinarsa susha fira. Tashi tayi daga kishingiɗar da take tace. ''Abbu! "Na'am ya Amsa yana kallonta. Kace Mahaifiyata ta rasu ko?" gyaɗa kai yai alamar ''Ehy, ta rasu wajen haifarki, kuma ni na binneta da hannuna. ''Abbu ina ne wajen, kuma me yasa baka ziyartattta? Ya kamata ace nima ka nuna min wajen in dinga zuwa ina ziyartatta, zataji daɗin ganin ƴarta. ''Na tabbata da ace mahaifiyata zata dawo wannan duniyar to zata yi fushi dakai, na mantawa da ita da kayi baka zuwa inda take. Koko dama bakwa san juna kaida ita, ba soyayyah da ƙauna tsakaninku? " "Abbu baka kyauta ma mahaifiyata ba "Ina so da k'auna da shak'uwa? Shiru yai batare da yace uffan ba,illah hawaye kawai dake zirarowa a kwarin idonsa. ''Abbu ta kirasa. bai amsa ba. Hawayen da ta hango a fusksrsa yasata fashewa da matsanancin kuka me zafi, tausayinsu ita da Abbun ya kamata. Sai taji me yasa take yawan takura mishi da tambaya? shi a kullum burinshi ya sadar da ita farinciki ya kyautata mata kullum shine burinshi. tayi zurfi wajen dogon tunani shima ta ɓangarensa tsananin tausayin zuƙeƙiyar budurwa kamar Muhijjinatu RAINON DAJI. ita kwata, kwata batasan jin daɗin duniya ba, basan farinciki da baƙin ciki ba ba ilimi an tauye mata rayuwa. (nikam nace meye sanadi) gata duniya amma ita da dabba kusan lissafin su ɗaya ne banbancin ita takasance mutum ƴar Adam, tun da ta tashi tare da dabbobi take rayuwa sune abokanta, an hanata jin daɗin duniya. . . Kullum takure waje ɗaya. . . . . Muhijjinatu!" Firgice ta waigo,tare da zuba mishi ido ''Tabbas ban kyautawa mahaifiyarki ba, , ban kyauta ba yadace ace ina zuwa ina ziyartata amma ba laifi na bane. Ina da hujja. . Ɗan jan nunfashi yai kafin yaci gaba da cewa ''Zan baki labarin rashin zitarta ta da banayi amma kiyi haƙuri akwai RANAR DA ZATA zo WATA RANA DADDARE zan baki labarin zan kuma amsa miki dukkanin tambayoyinki DADDAREN sai dai kafin nan yau ɗaya tashi muje kabarin mamanki in sadaki da ita. Kiga inda na binneta. Tsantsar farinciki Muhijjinatu bata san lokacin da ta daka tsalle ba ta ta rungushi, kamo hannunta yai suka jera. **BAƘAR MASARAUTA. ** Jejjere suke kowacensu mazansu da matansu, sanye cikin baƙin unifan baƙi kallo ɗaya zakayi musu ka tabbatar da cewa dukkaninsu bayi ne. Saɓanin da da ya kasance a tarihin masarautar unifoam ɗin bayi kore ne shar amma dai muje zuwa muji dalililn da ya sa yanzu ya kasance baƙi wuluƙ! Mukashifiyya dake zaune taji an dafa kafaɗarta. Ta juyo don ganin waccece. Jamila ta dubeta ''Mukasshifiyya tunanin me kike? ''Ba komai Mukashifiyya ta faɗa batare da ta juyo ta dubi Jamila ba. ''Jamila tace ''Kin cika girman kai''Shi yasa kowa ya fita harkar ki. nikaɗai na damu dake kowa sai yace kin cika girman kai. bakya sakewa da mutane. Mukashifiyya bata ce uffan ba illah miƙewa da tayi ta miƙa kwano aka zuba mata shinkafa da wake dafa duka, wacce fara ce ƙal, ba mai ko ɗis, haka zalika ba kayan miya. Sannan ita suke ci DARE DA RANA. . bayan an zuba mata kamo hannun Jamila tayi suka zauna saman ɗan damalin dake wajen. Su biyu suna zaune Mukasshifiyya tace ''Jamila bawai bana san sanar miki damuwata bane Aa''ni bani da girman kai daga yau zan dinga sakewa da kowa a gidannan bakusan ni bani, shi yasa kuke ganin kmar ina da girman kai. Tausayinn kai na da ku nake na ƙuncin rayuwar da aka saka mu a ciki. Yanzu damuwar da tafi damuna ita ce Ƙarshen shekara yazo, lokacin SADAUKARWA DODO da jinin wasu daga cikin mu yayi damuwata da fargabata. ''Shin wa za'a ba Dodo? ''Fata na ya kasance nice na gaji da ganin baƙin ciki kullum ana kashemu kamar dabbobi. Ina tausayawa duk wacce ya kasance ace ta zama rabon DODON TSAFI. Wannan rashin imani na SARKI SAFWAN ya ishe ni. Shiru Jamila tayi. kafin ta jero mata tambayoyi. ''Don me zakiyi wa kanki fatan mutuwa? "Shin bakya fatan ki sake saduwa da iyayenki? "Don me Zaki zab'i mutuwa a yanzu,alhali dukkaninmu muna fatan kawo k'arshen sarki safwan. Mukashifiyya ta fashe da kuka. Kuka haiƙan me cin rai kafin ta dubi Jamila tace. ''Jamila ku kuna fatan sake saduwa da iyaye a wannan duniyar saɓanin ni da na banbanta daku fatana shine nabi iyayena a inda suka tafi. Bani da uwa da uba bani da kowa a wannan duniyar. . . . . . ''Bangane ba ''Shin daga sama kika faɗo. A''a nidai nasan an ɗauko ni a wani DARE,tsintar kaina nayi na ganni nan. A wannan BAƘAR MASARAUTAR a wani lokaci DADDARE. Jamila tace gaskiya maganarki ta rikitani ta damalmala min lissafi ''Amma dai muci abinci tukunna. Kowaccensu kwanon shinkafa ta j awo suka soma ci hannu baka hannu kwarya domin sai sun galabaita da yunwa ake basu abinci. **DOKAR DAJI** ''MUHIJJINATU wannan shine kabarin mahaifiyarki'' anan na binne ta. Matata BINTA. Abar sona, abar ƙaunata DARE DA RANA. . . . . . . ƙaryane baka santa, baka ƙaunarta, da kanasanta da ka ɗaukar mata fansa. . . . ''Kaasheeta akaayii'' jikin Muhijjinatu ya soma rawa. ''Abbu Waye? be bi takan tambayarba yace ''Abbu mubar wajen nan. ''hhhhhhhhhhhh!!!" ''Abbu kana faji ance Mamata kasheta akayi, kuma za'a ɗaukar mana fansa'' "Abbu meye haɗinka da wannan Baƙar guguwar? "Wacce ce mahaifiyata,Kaima waye Kai nima waccece? ka amsa min karon farko a rayuwarsu da ita. Ya daka mata tsawa da ƙarfi. ''Ki wuce muje nace''...... 07049138863. https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ 9-10. ''Babu inda zamuje, mu tsaya a ɗaukar mana fansa. ''Me magana ka bayyana kanka. Wata muguwar dariya me haɗe da baƙin sauti ta bayyana. "Muhijjinaaa!!!" me maganar ya faɗa. Abbu ya ɗaga hannu ya shararawa Muhijjinatu mari. dafe wajen tayi saboda zafi. Fisgota yai yace muje. ruƙota yai gam yajata keeyyy!!! Suka bar wajen. *** "Farida kinyi ƙyau sosai wannan wanka sai ina? kamar zaki gasar kyawawa ''Allah ko Mommy?" ƙwarai da gaske'' Washe baki tayi sosai take farin cikin yabon da Mommyn tayi mata. ina ma yadda kike kyakkyawa haka ma zuciyarki'' turɓune fuska tayi. ''Kai Mommy mi kuma nayi? "Jiji dakai da wulaƙanta ɗan adam. ki bar wannan halin farida, da talaka da mai kuɗi duka Allah yai su, kuma duka matsayinsu ɗaya illah wanda yafi tsoron Allah. Dudu nawa duniyar take.* (duniyar da za'a barta me ya kawo* haɗama???* *Rayuwar da zata ƙare ina farin ciki*?? *jikin da zai zama gawa me ya kawo ɗagawa?*) "Don haka kisan abinda kikeyi Farida duniya bata da tabbas, wata kil talakan da kake wulaƙanta wa a duniya ranar gobe shine zai fara shiga aljanna. Duk wannan zantukan da Haj. Zainab keyi Farida najinta har yanzu bata ce uffanba. dubai abaya ta saka kalar sikyblue a gaban Haj. Zainab tabar ɗakin fuskarta sam ba annuri. A tsiyace taja motar a gaban wani shararren shagon alawowi ta parking ɗin motar ta ta shiga. Ta jima tana jibgo alawowi da chaculate kala, kala masu daɗin dandano. Kana daga ƙarshe ta hau mota, tana direving tana taunar chachulate, tana lumshe ido irin tana cikin nishaɗin nan. Koda ƙarasowarta gida bakin get, tai hon, tai hon, amma maigadi barci kurum yake da ƴar radionsa tana ta yi. A fusace Farida ta fito daidai inda yake zaune yana barci. A zabire Farida ta ɗaga bencin ta maka da ƙasa, Mal. Kabir yai wata irin super ƙasa bakinsa ya dafji ƙasa, haƙorinsa na gaba ya tsalle ya faɗi, jini yai tsartuwa. Cikin fushi tace ''Uban me kake? ''Saboda gaka matsiyacin banza da wofi har lokacin barci gareka, har hutu ke akwai ga mutum talaka? talaka baya da yanci baya da galihu idan ba zaka iya ba akwai matsiya ta da yawa irinka. Tana gama faɗar hakan ta kama gabanta. 'Mariya matarsa ta fito ranta a matuƙar dagule tace. ''Malan yanzu haka zamu ci gaba da zama da wa'innan mutanen cikin wulaƙanci haka , dubi yadda ta zubda maka haƙori ƴar cikinka. Azzkafiyyah ta fashe da kuka tace ''Wallahi mun gaji da wannan wulaƙancin kuma sai mun ɗauki fansa. mu tashi mu bar musu gidanan mu huta. Mal. Kabir ya ruƙota yace. ''Nutsu Azzakafiyyah a domin ki muke zaune a gidannan badon keba da tuni nabar nan mutunci na yafi haka. . Inaso ki ɗauki fansa Azkkafiyyah. Ki jira lokaci zaki san komai yau da gobe. Azkafiyya tace Baba Me kake nufi? dafe kai yai yace. ''Wash! ruƙoshi sukayi suka bar wajen abin gwanin tausayi. **DOKAR DAJI. ** ''Abbu kayi haƙuri dole ne ka bani amsar tambayata. ''Me yasa baka ziyartar kabarin Mamata?. Shiru yai ita kanta ta fitar da ran zai bata amsa chan ya ɗago yace. ''Wannan mummunar maganar da kika ji ita ce amsar maganar. . . A naso a saka ni cikin harkar TSAFI ne inba haka ba ba'a mutuwa a dawo. Dukkanin wanda ya mutun ya tafi kenan har abada. Suna so su tursasani na bisu na dawo da gawar mahaifiyarki a wannan duniya. Anaso a sarrafata ta miƙe ta ɗauki FANSA akan wa'inda suka aikata mana haka. Amma ina so ki DUNƘULE maganar waje ɗaya ki jira ranar tazo, wato WATA RANA DADDARE. zan warware miki komai. Kan Muhijjinatu ya toshe waje ɗaya ta dubi Abbu tace ''Meye amsar WATA RANA DADDARE? ''Yaushe ne zata zo? "Yaushe zata zo?" "Yaushe zata zo?" ta faɗa game da fashewa da kuka. da gudu Abbu ya ruga ya ɗauko sharɓeɓiyar wuƙa ya dasa a maƙogwaronsa yace. ''Muhijjinatu na lura ni ɗaya nake kiɗa na inyi rawata, ni kaɗai na damu da farin cikinki, ke bakyasan dukkan abinda nake so, dukkan abinda kike so a doron duniya ƙoƙari nake naga na samar miki shi. Da kinsan irin ƙunci da ƙuna da raɗaɗin da nake ji da zarar kinyi min maganar jin muɗin su waye, nace kiyi haƙuri akwai RANAR da zata zo DADDARE, zan sanar miki zakiji komai har ma abunda baki tambayeni ba. ina san dukkan abinda kike so amma tinda kikaga banbaki labarin nan ba da akwai dalili, to amma tinda kin gaji dani da rayuwata kin gwammaci ki kashe ni da kanki domin da kiyi min wannan tambayar gara ki ḍaɓa min wuƙa a maƙogwaro in huta. Ya ɗan ja numfashi kafin yaci gaba da cewa ''Nasan ba zaki iya kashe ni ba mafarin na yanke shawarar gara ni na kashe kaina da kaina tinda kin gaji dani A YAU ZAN BAR MIKI DUNIYAR. ''Zan kashe kaina Muhijjinatu'' da gudu ta miƙe ta ruƙo shi da ƙarfi. ''Abbu na tuba, na tuba Abbu!!!" ''Ka yafe min kayi min afuwa. ''Bazan kuma ba! sai kuma ta fashe da kuka. tausayinta ya kamashi. Shima sai ya fashe da matsanancin kuka me ɗaci me ciwo me tafe da baƙin ciki, su duka biyu sai suka rungume juna suna kuka sosai. bai san lokacin da yai jifa da wuƙar ba. Kuka suke wiwi su duka ba mai rarrashin wani daga bisani shi ya koma rarrashin muhijjinatu. Ɗauƙarta yai cimak ya shiga ɗaki da ita ya ɗauƙo kayan marmari dangin Apple da banana da kankana ya yanyanka da baki ya dinga bata tana ci yana mata labari mai daɗi sai gashi ta murmure. . . Sun koma tamkar basu ne ke kuka a yanzu ba. Kwanciya tayi ya jawo bargon fattar dabba ya lulluɓeta yace- ''Muhijjinatu zanje na kamo mana kifi. ''To Abbu ka dawo lafiya'' ƙyaren katakon ya jawo ya rufe ƙofar ya tafi kogon kamun kifi. Tafiyarsa babu daɗewa ta soma barci, barci ne me tattare da miyagun mafarkai barkatai, mafarki ne dai akan mutumin nan mai mummunar murya, me tsoratarwa da razana shine ya dawo mata. Cikin barcin ta ganshi yana cewa ''Muhijjinatu ki bamu haɗin kai zamu dawo miki da mamanki ku ci gaba da rayuwa. ''kar ki biyewa mahaifinki domin shi bai damu da ita ba ke kuma mamanki ce ki bamu haɗin kai. ''kin amince koko? Kafin ta bud'a Baki ta Bashi amsa ta farka a firgice. tambayoyi daƙare a cikin zuciyarta tabbas akwai lauje cikin naɗi. Duk yadda akayi da akwai abinda Abbu ya ɓoye mata tanasan tasan koma meye. *****DOKAR DAJI. **** Lallai ya zama dole ta koma kabarin mahaifiyarta, dole ne taje ta binciko me ke wakana a wajen. Tinda Abbu yaƙi bata labarin dole taje wannan sheɗanin aljanin ko ma fatalwa ne shi ya bata labarin, to Amma ta wacce hanya? Murmushi tayi da ta tuna mafita ta tuna *hanyar da zata bi don gano gaskiya. * 07049138863. https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ PAGE 11-12. ''Shin meye alaƙar Abbunta da wannan baƙar guguwar? dole ne na bi ƙwaƙƙwaf na gano gaskiya. Muhijjinatu dai tana daga kwancen nan dai zuciysrta nata saƙa mata abubuwa da masu ƙyau da akasin haka. ''Dole ne naje ga ko waye, dole ne na amince da ko waye. Muddin zai dawo min da mahaifiyata na rayu da ita in rayu da ita da mahaifina a waje ɗaya. Sannan nayi alƙawari sai na ɗauki fansar duk wanda ya kashe min mahaifiyata. Ahalin yanzu na fahinci muɗin mutane ne ƴan adam bamu kasance ɗaya daga wata halittar ba. To Amma meye dalilin mu na keɓancewa a dokar daji? wannan amsa sai Abbu. Dole na jira sai WATA RANA DADDARE kamar yadda yake faɗamin. ******** Gudu take falfalawa sosai kamar wacce zata tashi sama. Ba zato ba tsammani taga tsohuwar a gabanta. Ƙuuuu! Cikin hukuncin Allah tasa giya motar ta tsaya. Cikin musifa da bala'i ta fito fuskarta ko kaɗan ba annuri bala'i kawai ke cinta. ''Ke wacce iriyar tsohuwa ce mai karanbanin tsiya salon kija na taka kiki ki ɓata min tayar mota. Ki jazamin azumin ba gaira ba dalili. ''Na rantse bacin ina tsoron lafiyata data bisa kanki zanbi in wuce. gobe sai inga kin fito, don haka tsohuwa aje gida a koyo wayo da hankali. duk wai'nnan zantukan da Farida keyi tsohuwar nan bata ce uffan ba. Ido kurum ta zubawa Farida. Farida tace. ''Ki matsa zan wuce. . . . . Shiru bata tanka ba hakan ya fusata Farida ta juyo a fusace da nufin ta zo ta jefar da tsohuwar. Kwatsam!!! ta nemi tsohuwa ta rasa. Hakan ko kaɗan bai tsorata Farida ba bai kuma girgizata ba illah dariya da ta fashe da ita a ranta tace. ''Tsohuwar banza ko mutum ce ke ko aljana duk zan iya dake ni zakiyiwa siddabaru. Nikam MmnHummy nace anya Farida kina da hankali kuwa. **BAƘAR MASARAUTA. ** A ƙallah zasu kai kimanin mutum ɗari biyu mata da maza, bayi kowacce sanye cikin uniofoam baƙi wuluƙ! Abinda ke ɗaure min kai ni Aishat shine har yau banga wannan sarki mai baƙar masarauta ba. Jamila da Mukasshifiyya suna zaune, lokacin hantsi ne, dukkanin bayin mata da maza kowacce na al-amurran gabanta. Wani gajeren bawa baƙi yazo yana sanar dasu cewar ''Sarki yace a sanar musu gobe i war haka yana nan tafe. Koda ya gama jawabinsa sai ya bar wajen dama shi ba ya ɗaya daga cikinsu. Mukashifiyya ta dubi Jamila tace- ''Mugun baƙin ɗan saƙo kenan baki ga duk bayin dake wajen nan ba kowa ya sha jinin jikinsa ba? Jamila ta ɗaga kai ta kalli bayin gaba ɗaya kowa yai saranda. Ǧyaɗa kai tai tare da zubawa Mukasshifiyya ido tace. ''Me hakan ke nufi? Tabbas naga wasunsu ma kuka sukeyi. Mukashifiyya tace. ''Ai mun shiga uku! ''Zuwan sarki ba alkhairi bane. Domin kowa anan cikin fargaba yake. Zuwan Rabiya ya katsesu da kukanta tazo. Jamila ta duba tace ''Jamila kece baƙuwa gobe war haka mun bani. Zuwan Sarki Safwan bala'i ne da musifa. Bai da imani ko misƙala zarratin sannan zuwan shi abune me nuni da sabon Ʌeq́s da zai kunno. Sai ya gama azabtar damu matanmu da mazanmmu sannan ya ɓullo da mugunwe ƙuḍirin dake danƙare a zuciyarsa Lokaci yayi da zamu sami yancin kai. Tin ina ƴar shekara 10yrs aka ɗauƙoni. A ƙallah na share shekara 20yr anan ḄAƘAR MASARAUTA har na fitar da rai da rayuwar ƴanci na fitar da rai da sake farinciki nasan ada ina cikin gata ina da uwa da uba, amma a halin yanzu ko na fita bansan taya zan sake tozali da iyayena ba, bansan hanyar da zanbi in gano su ba. Kullum zaluncin srki Safwan ƙara ƙamari yake. Mukasshifiyya tace. ''Rabiya kenan duk wannan zantukan nasan dasu, kawai dai ina nuna muku bansan komai ba yanzu dai duk ba wannan ba, wacce hanya zamu bi mu gudu kafin gobe? Zaro ido Rabiya tayi tana kallon Mukasshifiyya. sassauta murya tayi ta dafe baki tace. ''Mukasshifiyya ki ma daina wannan maganar sam. Ki duba girma da tsayin katangar masarautar nan ki gani ta ya, ta ina mutum zai iya guduwa? ke kanki in kika duba tsayin katangar kanki bazai hango tsayinta ba. Sau ɗaya tak! wani ya taɓa gigin guduwa Sarki yasa aka kamo shi aka yanke mishi ƙafa da hannu kana aka fille mishi kai, kafin a fille mishi kai sai da aka gana mishi azaba kala daban-daban. . . . . ******* Da sanyi safiya kowacce ta kwaɗa wanka ta cire uniopom ɗinta ta wanke tas, domin al-adar sarki kenan kowacce sai ta wanke kayanta tas kana domin shi ba'a ganinshi da ɗauɗa. Domin ita kanta ɗauɗar muddin aka kamaka da ita, to hukuncinta dabanne. Ƙaton kafet ne aka malala tundaga inda Sarki Safwan ya safko daga mota har zuwa inda bayi suke. Gefe ɗaya kujera ce haɗaɗɗiya nidai Mom Hummy da na ruɗe cewa nayi kujearar zinari ce🙊🙊🙊 Cikin tafiyar ƙasaita, izzah girman ƙai ƙasaita dik ya tara waje guda. sannan ga , zalunci cuta ƙeta, da sannu dai zakuji waye Sarki Safwan. Bayi biyar ne gefe, da gefensa, wato dama da hagunsa. Ɓangare ɗaya kuwa ga wani nan tsaye baya um, baya UmUmm ba laifi shima shiga ce ta sarakai a jikinsa. Fuskarsa ɗaɗɗaaure domin dama shi baya dariya, wato Sarki Safwan. Kayan jikinsa da rawaninsa duka baƙine kalar tambarin sarautarsa. Shi wannan bawan Allah fusakrasa cike take da yalwa , nidai na dasa mishi ayar(????)nayi mamaki da sarki safwan ya iya haɗa wajen zama da wani domin duk sarakunan Nigeria ƙarƙashin ikon S. Safwan suke to shi waye?" SARKI, SAFWAN ɗaya bayan ɗaya yake bin bayin da kallo kowa ya sarda ƙanshi ƙasa alamar girmamawa. Wannan bawan da yazo sanar musu saƙon zowar Sarki jiya shine ya miƙe ya soma magana kamar haka. *Sarki yace ya gaisheku* *kana yace a gaya muku cikin shekarar nan anyi asarar bayi* *A ƙallah guda 50 don haka daga yau ya yarjewa kowanne bawa ya nemi* *baiwa ƴar uwarsa domin ta haka ne zakuyi ta hayyayyafa* *sannan duk wacce tayi gardama akwai hukunci mai tsauri da za'ayi mata* *baya ga haka yace bayan mace da namiji to zaku iya neman jinsi* *wato mace da mace, namiji da namiji* *sannan akwai horo da azaba ga duk* *baiwa ko bawan da yai wa gwaninsa* *gardama. * 07049138863. ̈̃̈̃Call 07012329134 WATA RANA DADDARE.🖤 🖤 (horror story)☠️ Writing by Aishat Abdul-falalu. (Rimin k'aura). (Mmn Humaira) from the writer of *Ishara. * *So ko hauka. * *Shagaltattun duniya* *And new book WATA RANA DADDARE https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ page 13-14. **BAYIN ALLAH** Gaba ɗaya sun shiga mummunan tashin hankalin wannan baƙin zalunci na Sarki Safwan. Sukan mazan gaba ɗaya farin ciki ne marar misaltuwa a zukatansu na ganin zasu samu abinda suke nema a kyauta. **DOKAR DAJI** **MUHIJJINATU** Zaune ta zafga uban tagumi. A halin yanzu ta gane cewar ita da Abbunta mutane ne ba dabbobi ba,ko kuma wasu launin halittu daban ba tamkar dai yadda ada take zato. Tsanar Wanda yai silar jefasu a wannan halin yai mata tsaye a ƙoƙon ranta aranta ji take ina ace yanzu tai arangama da ɗaya daga cikinsu wayyo Allah! ai da a take zata kashe su har lahira.''shin su waye ma ɗin ? dole ne ta ɗau fansar ran mamanta da kuma ƙasƙantacciyar rayuwar da aka jefata ita da Abbunta. to amma ta yaya? "Shin waye ummul-aba'isin jefasu cikin ƙasƙantaccen halin nan? A gaskiya dolene ta koma ƙabarin mahaifiyarta a domin ganawa da wannan sheɗanin baƙin al-janin a domin ya fayyace mata komai. Dole tana buƙatar jin babban sirrin nan a domin tinkarar koma waye yai musu haka ita da Abbunta. Zuciyarta taji ta ƙeƙashe a fusace ta miƙe tsaye ta doshi wajen. Koda isarta tsayawa tayi fuskarta babu alamar tsoro ko razani da ƙarfi ta furta. ''Shin kana ina kana ina baƙin aljani ka bayyana min kanka ''Shin meye ka ɓoye min gani nazo na shirya a shirye nake da ɗaukar koma meya kai nake jira. Ka fito da sauri bana so na jima kar Abbu yazo ya tarar bana nan zai shiga damuwa. ''hhhhhhhh! hhhhhhh!!hhhhhhhhhh!!! wata muguwar dariya me mugun sauti ta bayyana. Dariyar ta karaɗe dajin baki ɗaya abin gwanin tsoro. A halnkali sautin ya rage amo ya dinga fita sannu,sannu. A hankali wani baƙin hayaki ya dinga tuɗaɗowa wanda saboda ƙarfinsa Muhijjinatu har rufe ido tayi ya zamana bata ganin komai face hayakin a hankali ya tsaya cak! hayakin ya dunƙule waje ɗaya kan kwarangwal ya bayyana haɗe da wata baƙar guguwa. Muhijjinatu ta tsaya cak! babu alamar tsoro ko razana a tare da ita (to meye abin tsoro ga mutumin da tin buḍewar idonsa a daji yake rayuwa?) ''Muuhhijjjnnatuuuu!!! bata ammsa ba illah zuba ma baƙinshi ido da tayi a inda yaci gaba da cewa''Mahaifinki ya faye taurin kai,munso mu taimakeshi mu tayashi ɗaukar fansa amma mugun taurin kai ya hanashi. Ƴan'uwanshi sune silar jefa ku a wannan ƙangin da kuke ciki SARKI SSAFWAN da kuma ALH.BASHIR. Yan'uwanshi ne na jini Uwa ɗaya uba ɗaya. Jikin Muhijjinatu na ƙyarma tace''Waye SARKI SAFWAN,WAYE ALH.BASHIR? ''Kamar yaddaukayi miki bayani sune suka rugaza mishi rayuwa su suka ƙasƙantar da rayuwarku A DOKAR DAJI. Kana nufin Abbu yana da dangi UWA ƊAYA UBA ƊAYA.....? kafin ya bata amsa wata guguwar ta taso da ƙarfi wannan bame tsoratarwa bace........ **Assalamu'alaiki ya Muhijjinatu. Sunana Mal.Abdurrahman ni cikakken musulmine kuma rauhanin aljani. ''karki sake ki bishi sheɗani ne yaudarrki zaiyi kansu haɗe yake..cutardake da Abbunki zaiyi kuyi hakuri Allah (S.W.A)shi ya halicceku yana sane da halin da kuke ciki zai kawo muku agaji kinji..Harda sauran ƴan'uwanki duk Allah zai saka muku kinji.... Muhijjinatu ta shiga ruɗani bakinta na kyaf,kyaf ta dubi wanda ya kira kanshi Malan Abdurrahman tace. ''ƴan'uwa kuma,dama ina da ƴan'uwa?......... kafin ya bata amsa baƙin aljani yaɗora da cewar ka gudu in baka gudu ba zan kira.... Ai kafin ya ƙarasa Mal.Abdurrahm ya ɓace bat. Baƙin Aljani ya kwashe da dariya yace ƙyaleshi maƙaryacin banza. ''Ni ne zan taimakeki Muhijjinatu asiri sai asiri tsafe sai tasafi hhhhhhhhhh! "Meye asiri meye tsafi? Muhijjinatu ta fad'a Akwai sauran sirrika ma Amma kijira sai WATA RANA DADDARE IDAn tazo mahaifinki ya faɗa miki sirrikan duka to daga ranar zan ɗora miki nawa kije ki jira tazo. Yana gama faɗar hakan ya ɓace Muhijjinatu tai kira tai kira a domin yazo ya amsa mata jerin tambayoyinta da suke naniƙe a ranta,an kuma ƙara birkita mata lissafi . jikinta ba laka tabar wajen. ********** Koda Abbu ya dawo ya sameta salalaf. Shikanshi yasan akwai damuwa a tattare da Muhijjinatu. Bawan Allah duk ya kiɗime hankalinsa kacokam ya koma kanta. Babban burinshi yaji abida ke damun ƴar tilon ƴarsa da ya mallaka a DOKAR DAJI. damuwar Muhijinatu ɗaya kar Abbu ya fahince ta ina taje kar ya gano ta haɗa kai da sheɗanin da kullum yake gargaɗinta da kar ta sake ta tinkari inda yake. Sai dai abunda bai sani ba shine zuciyar Muhijjinatu ta ƙeƙashe a halin yanzu bata ji bata gani. Bayan Abbu ya gasa nama taci ta ƙoshi ta dube shi kana tace''Abbu wai dagaske akwai abun bauta da zai kawo mana agaji ya taimakemu ya saka mana akan cutardamu da akayi,dama akwai shi amma me yasa baka taɓa sanar minba? koda Abbu yaji haka a take ya faɗi ya soma.ƙirjinsa yai ta fat,fat. . https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ PAGE 15-16. KAGA dole ne ka nemo mafita, a halin yanzu yaron nan Haidar kaɗai yasan *securityn*shiga ƙofar get ɗin da dukiyr nan take. to wai tukun shi boka Zaƙawanu me yace game da rashin maganar Haidar? Sarki Safwan yace''cewa yai wai bazai taɓa magana ba sai ranar da yai tozali da mahaifinsa Abdullahi. . . . . . . What? Alh. Bashir ya faɗa a kwai gagarumar mstsala kenan, to ashe bazai warke ba, domin Abdullahi dai baya raye. ƙyal-ƙyalewa da wata muguwar dariyar ƙeta Sarki Safwan yai yace''banda ƙarya da jahilci irin na Boka zaƙawanu ina Abbdullahi yake a raye wanda ya daɗe da sheƙawa. . . . . Cigaba yai da dariyarsa tamkar bashi ne cikin baƙin ciki yanzun ba. Alh. Bashir yace wallahi nafika baƙin ciki rashin samun kuɗin nan domin dalilin kuɗin na sadaukar da lahirata na zaɓi duniya amma never ace ba nan ba chan a sake lalubo mafita. . . . . Ai ni na fi chanchanta da na mallaki dukiyar nan kaifa shuwagabannin ƙasashe su baka, kamafa raina arziƙin govnoni amma duk da haka mugun son abun duniya yai maka katutu ga sarautarka,, Yaya ga zaluntar dukiyar masu kuɗi,haƙƙin ƙasa ka taushe duk sarakuna tsorn zaluncinka suke . . . . . . . . ''Kai Bashir hattara banda kana ɗan'uwana ka isa ka tsaya a gabana kana faɗa min wa'innan maganganun? ina sarki. . . . . . dariya Bashir ya kwashe yace''Yaya Safwan kenan sarautar da ka ƙwace da tsiya. . . Yana gama faɗar haka yabar wajenḷ ************** Jamila ta dubi Muƙashifiya tace''wayyo mun shiga ukuḷ yanzu haka rayuwarmu zata ƙare kamar dabbobi ? Haka banza wofi zai zo ya cuɗanya damu kamar marassa gata? Muksfy tace. ''Wallahi summa tallahi babu wanda ya isa ya kusance ni banda mijin aurena, Domin. . duk namijin da yai gigin shiga gonata to tabbas ajalinsa ne ke kiransa. Kuka Jamila ta fashe dashi da ƙarfi, tace Mukassfy inkinsan waccece ni sai kin tausaya min, ga gata ga bayi ina su amma wai ayau nice baiwa marar gata, an sato ni an raboni da mahaifina mai sona NI ƳAR SARKIN GARIN GABAS CE. . Sannan nice ƴa mace duka yayuna maza ne. Kuka Jamila take wiwi. . Kukan ta ya karaɗe ɗakin baki ɗaya, don haka sukayo caaa Farisa ta basu labarinta tace NIMA ƳAR SARKIN KANO CE. Ruƙayya tace ƴar sarkin Katsina gaba ɗaya sai suka gane cewar ashe baƙi ɗayansu duka ƴaƴan sarakain ne. TO abin tambayar anan shine meye dalilin tara ƴaƴan sarakai da Sarki Safwan yai? Koda kowa ya gama bada labarinsa tsaf Muƙashifiyyah tace. Ni nawa labarin yafi na kowa al-ajabi da bugun zuciya da girgiza da razana da kuma ruɗani kunsan koni waccece? baƙi ɗaya kowa yace''dama mun daɗe munasan sanin labarinki Muksfyyh. Murmushi tayi kafin tace kunsan wanda ya tara mu anan? gaba ɗaya kowa ya girgiza kai Alamar ''Ey. ''Waye shi ? ta tambaye su "Azzalumi Sarki Safwan. Uhum'' to ƙanen Mahsifinanene uwa ɗaya uba ɗaya asali ma sarautar ta mahaifina ce ya ƙwata da ƙarfi ya salwantar da rayuwar mahaifina. . . . . . . Cije yatsa Mksfy tayi ta fashe da kuka. Baki ɗaya kowa ya ɗago yana dubanta a razane har Jamilar ma tana mata kallon ko kin zare? kuyi manage banda charge ne. . . . . 07049138863. 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ PAGE 17-18. Share hawayen fuskarta tayi tare da yin wani ɗan taƙaitaccen murmushi tace''Nasan zaku ce ko na zare ko? Garau nake. Murmshi Mksfy ta yi tace ''Kunsan ban taɓa muku ƙarya ba ko? Kuma bazan Fara daga yau ba. Ni Mukasshifiyya bana ƙarya hasalima mun gaji gaskiya a wajen mahaifinmu mai tsoron Allah. Dalilin da zaku gaskata ni shine''Nasan kunsan Sarki Safwan ko? Kowa yace ''Ehy'' Kowa yasan shi. Mukasshifyyah tace ku hararo kamanninshi ku gwada da nawa baku ga kama ba? Sannan ku hararo kamannina da wannan saurayin Yayana nane Haidar UWA ƊAYA, UBA ƊAYA. Baki d'aya wajen ya kaure da hayaniya kowa yana faɗar Albarkacin bakinsa. Sadiya tace''Tabbas hatta hasken fatarku kala ɗaya ne. Ruƙayya tace tabbas saurayin nan kowa ya ganku dashi yasan kamarku tamkar an tsaga kara. To amma me ya kawo haka? Jamila ce mai faɗar hakan ta gyara zama tana mai fuskantar Mkshfyy. ''Kina nufin Sarki Safwan bayan rasuwar mahainki ya gaji sarautar, to amma me yasa yabarki matsayin baiwa matsayinki na ƴar'ɗan uwansa ba. don Allah Mkshfyy muna san sanin labarinki . Ɗagowa tayi ta dubesu tace. ''Zan baku labarina, amma labarin masarautar nan bazai yuwu ba da rana, ko da safe ko da yammaci. To sai Yaushe? Jamila ta fad'a Sai DADDARE domin masarautar nan tana da wani BABBAN SIRRI wanda bazai faɗu ba da rana, amma ku jira lokaci yana zuwa, amma yanzu ba zs bane abinji wannan iftila'in da ya faru shine abin ji wajen mu. *****DOKAR DAJI**** MUhijjinatu tsaye daodai inda guguwarnan take idonta ƙur akanta tace. ''Kai waye? Kuma me yasa ba'a bada labarin SAI DADDARE? "hhhhhhhhhh!!! Kamar dai koda yaushe wannan mummunar dariyar ƙwarangwal ɗin ya fashe da ita. Yace "Muhhiijjjinnahhh!!!"" zan taimakeke, amma na faɗa miki dole ne sai ya baki labarinnan sannan zan dasa miki daga inda na tsaya. kije ya faɗa miki sirrin DARE. Zan taimakeke. ''Kayi alƙawari muddin babana ya faɗa min zaka taimake ni ka dawo min da Mamana? ''Ehyyyy nayi Alƙawari muddin kema kika bi sharuɗɗan mu. Kuma ba zaki ɗauki fansa ba saida izinin mahaifinki. Zaro ido Muhijjina tayi tace''Mahaifina bazai taɓa amincewa dakai ba hasalima ya tsaneka!!! "Nasan da haka ai akwai dubarar da za'ayi mishi. ''Wacce dubara ce?" Dole ki mutu ki dawo In MUTU, kuma INDAWO, kaman ya? "Hhhhhhhhhhhhhhh!!!! Nifa sheɗanin aljanine bana tsoron Allah, uwata ta tsinee mini ubana ya tsine mini, sheɗanci babu kalar da ban iya ba. Da zarar kin mutu, to zai fusata sosai sabida a halin yanzu duk duniyar nan kece kaɗai sanyin idaniyarsa kece kaɗai yake gani yaji daɗi to kinga muddin yaga gawarki to zai yadda yabi mu mu tsafa shi domin ɗaukar fansa. ''Kin amince? Ehy'' Na amince da sharad'i Muhijjinatu ta faɗa fuskarta ba tsoro ba razana. ** Cikin gaggawa ta baro wajen baƙin aljani ta doso sansaninsu. Cikin fargaba ta iso, tsoronta kar Abbu yazo ya tarar bata nan bata san wacce amsa zata bashi ba. Tin tashinta bai taɓa zuwa wani waje ya dawo ya tarar bata nan ba. Aikam gabanta yaci gaba da bugawa ganin yadda taganshi tsaye ya zuba mata ido. ''Muhijjinatu daga ina? Ammm! Umm! Baiwar Allah bakinta bai saba da ƙarya ba duk ta gigice. Katseta ya kuma yi. "Daga Ina Muhijjinatu? "Abbu naje ganin tsuntsaye ne. Dama kina zuwa dubo tsintsaye? "Ki sani cewar tuni tunin duniya ake mutuwa, kuma duk wanda ya mutu bazai taɓa tashi ba sai ranar tashin alƙiyama. Mutuwa ɗaya ce tak! Kuma shikenan bazai dawo ba,Kuma kowa zai mutu,kowa Sai ya mutu Kuma duk Wanda ya mutu bazai dawo ba. Kef, kef jikinta ya katse da ƙyarma shikenan Abbu ya gano ta. ****** A yau ma kamar kullum Farida ta fito cikin shiga ta al-farma ta shiga motar Daddynta. Sunyi hon, hon, shiru ba me gadi ba alamarsa. Zaune yake yanata barci. . . . Cikin fushi Farida tazo ta ɗaga hannu ta sharara mishi mari. A zabire ya miƙe firgigit. fitowar Azkafiyya kenan daga cikin gida. Gaba ɗaya gigicewa tayi ta saki wata iriyar ƙara. . Aikam batai wata wata ba isa tayi daidai inda Alh. Bashir yake tsaye ta kam daddage iya ƙarfi, bai zata ba Farida ma bata zata ba AZKAFIYYA ta kwasheshi da mari. wayyoḷ Bala'i Farida ta gaza cewa uffan, Alh. Bashir ya gaxa cewa uffan. Azkafiyya ta ruga da gudu bayan Mal. Kabir. Ruƙota yai yajata suka nufi boysqeaters. Da gudu ya isa ya iske Mariya zaune tsna cin ɗumame yace Mariya ''Mun shiga ukuḷ Azkafiyya ta mari me gidannan Alh. Bashir. Gwalalo ido Mariya tai warwaje. ɓangaren Farida kuwa mamaki Al-ajabi ta cije yatsa wai ko barci take? Amma da zarar ta farka Alh.Bashir mahaifinta tsaye mamaki ya kasheshi. wai ƴar matsiyata ce ta dallara wa mutum me kuɗi irin ubanta mari. Tiƙashḷ ''Na rantse da girman Allah a yau sai kin gwammaci mutuwa da rayuwa dagake har matsiyatan iyayenki kuma sai hannunki ya rabu da gangar jikinki. ''Wallahiḷ Wallahiḷḷḷ. Yau zaki shiga musifar da bala'i na gidan duniya. . . kKafin kace me sojoji sun cika gidan sun zagaye ko ina. Farida tsaye tana ba sojoji Umarni. ''Ina so da Uwar da uban ku yi musu ligif. Ita kuma ƴar ina so ku tsinko min hannunta. . . . . Zama tayi ta kame akan kujera tana jiran a tsinko mata hannun Azkfiyyh a yau sai taga ubanda ya ɗaure mata gindi. Zamanta ba jimawa sojan yazo yake sanar mata an duba boysqeaters ba kowa,ba komai hasalima tamkar biladama bai taɓa wanzuba a wajen. ''Babusu kaman wasu Aljanu? ''Ranki ya daɗe zaki iya dubawa. To ta ina suka bi? Duk fa an kukkule ko ina kai never ,,Hannu ta ɗora akai ta fasa kururuwa,sojan ne yazo yake bata haƙuri akan karta damu suwaye su? da har zasu gagaresu gano wa a wannan duniyar. Tofa duk wata social media an ɗora hoton Azkafiyyah M.Kabir da kuma kyautar maƙuḍan kuɗaɗe ga duk wanda ya gansu ko ya san inda suke. tofa. . . . . . . . . duk group ɗin da basa commts wannan ne last page ɗinmu. 07049138863. ̈̃̈̃Call 07012329134 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ PAGE 19-20. **A DOƘAR DAJI ** **TOFA** ' DARE ya raba sosai MUHIJJINATU na tsaka da barci me daɗi. ABBU Ya taso ya yaye bargon da ta lulluɓa dashi . Yace Muhijjinatu tashi ! Tashi! Yau Zan baki labari, A DAREN YAU ta tabbata duk amsar da kike buqata tana cikin wannan DAREN. Cikin magagin barci tace''Abbu wannan wanne kalar labarine da ba'a ba dashi sai DADDARE.?" Toshe mata baki yai yace''Idan kika bari wannan damar ta wuce sai kuma nan da shekara A WANI DAREN kar ki kuma cewa komai amsar da kuma sirrin duka suna cikin wannan DAREN. Yanzu kunnuwanki sun shirya sauraren wannan cukurkuɗaɗɗen labarin? Muhijjinatu ta miƙe daga kwancen da take idanuwanta tsaf suka washe. ''Abbu kai nake saurare. **WATA RANA DADDARE** **LABARIN ABBUN MUHIJJINATU** To Abbu ina sauraranka Muhijjinatu ta faɗa tana me duban Abbunta. Ƙasar AMSAD babbar ƙasa ce dake Chan yankin gabas,kuma babbar ƙasa ce da duk sauran ƙasashe a ƙarƙashinta suke. Sunana Sarki Abdullahi bn AbuSufiyan bn Abdulfatta bn Nuhu Bn Abdulƙadir........Kuma nine Sarkin ƙasar nan ta AMSAD............ Abbu dama kai sarki ne? Bai tsaya bata amsa ba yaci gaba da cewa. Mahaifina AbuSufiyan Adalin Sarkine mai tsausayi kuma duk sarakunan sauran ƙasashe suna mishi biyayyah sannan babu mai ƙarfin arziƙi irin nasa. ya daɗe bai samu haihuwa ba matansa huɗu a duniya. Gimbiya Rahima Mai babbanɗaki,sai Gimbiya Baraka Mai ɗakin gabas,sai Gimbiya Balaraba,sai mahaifiyata Gimbiya Habibata.... Abbu ya ɗago ya dubi Muhijjinatu yace. ''Ina fatan kin fahinci inda labarin ya dosa? Muhijjina ta ɗago ta dube shi tace. Ehy Abbu na fahinta,hakan na nufin amsar tambayata da nake yawan cewar muɗin ƴan Adam ne tabbas yanzu na fahinci mu mutane ne ba wasu naui'n dabbobi ba tamkar yadda na saba cewa. Murmushi yai yace''Dama nace da sannu zakiji duka amsar tambayoyinki. ''To Abbu ci gaba labarin akwai daɗi. bai ce uffanba yaci gaba da cewa. ''Duk yadda matan mahaifina suka so su haihu,abu ya gagara,domin dukka su uku babu wacce ta taɓa koda batan wata. Mahaifiyata shekararta biyar Allah ya ƙaddare ta da samun cikina kar kaso kaga murna wajen sarki,tsabar murna saida ya saka aka tara masa sarakunan duka ƙasashe saboda taya sa murna. Wata tara daidai ta haifo ƙaton ɗanta namiji kyakkyawa ni ne nan balarabe na biyota sak domin ita ƴar sarkin Makkace. Haka akai ta murna da shagalin haifata,tofa shekarata 1 daidai akayo min ƙane Safwan,shima shekararsa ɗaya tayo masa ƙane Bashir. Wayyoḷ Ina wuta kishiyoyinta su jefata? anyi tsafin an kwace hanyar to amma da yake iyayenta sun shirya mata babu abinda ya sameta. Tun tashin mu Safwan ya tashi irin yaran nnan marasa tausayi. Shi kuma Bashir ya tashi irin ƴan ƙaryar nan me mugun son kuɗi.... Tin yana ɗan shekara 16yrsold ya soma neman matan banza da shaye,shaye. Da dama dangi sun ta'allaƙa kan cewa dangi kishiyoyin mahaifiyarmu suka yi ma ƴaƴanta 2 asiri Safwan da Bashir,dama ni bana shiga harkar su. To ita dai ta barwa Allah ikon sa. **** Lokacin da tsufa ya kama mahaifinmmu yana so yai murabus. daga kan karagar mulki,kowa yasan babban ɗa shine magajin uba. To ɓangaren Safwan kuwa ya haukace shi lallai shi zai gaji sarautar Sarki. Abin baƙin ciki matan babanmmu suke daɗa zugashi ya haukace sam bayaji baya gani. Mahaifiyarmu da Sarki soyayyar da suke gwada mishi ta hana su tanƙwarashi. da naga abu zai zama tashin hankali haukan Safwan kullum ƙaruwa yake yasa nace a ƙyaleshi. Indai Sarauta ce ni na haƙura nabar mishi. Sarki ma bai ja ba ya ƙyale ni nan ya sake tabbatar da cewar nafi safwan hankali. Wani abin al-ajabi ranar da Safwan ya hau karaga ma'ana aka rantsar dashi da ya hau kujera da an wulloshi da qasa an rasa meye musabbabin abun. Sau uku ana haka cikon na huɗun ne ni na hau.Koda na hau sai na zauna daram ba abinda ya faru. sai bushe bushe algaitu wanda ba'asan daga ina yake fitowa ba. A dole Safwan na kallo na na zama sarki.̇ Ransa ya dugunzuma sosai sai ya soma sakin maganganu yace''Dama munafurcu yasa nace na haƙura saboda ina da abinda na ƙudurwa a zuciyata tofa. Shekara ta ɗaya akan karaga mahaifinmmu AbuSufyn adalin sarki yace''gagarinku nan'' Allah Sarkiḷ mutuwar sarki ta dugunguza ƙasashe da dama a duniya musamman mu ƴaƴansa saboda ni duk yafi shaƙuwa dani fiye da kowa a yaransa. Mutane sun san sarki ya tafi yabar copy wato ni domin duka halayensa babu wanda na baro. Abbu ya ɗanja numfashi yana goge hawaye,tamkar a yanzu mahaifin nasa ya mutu. ya zuba mata ido kana yace''Muhijjinatu NI MUSULMI NE CIKAKKKE!!! a mamakance ta ɗago tace Abbu meye hakan meye musulmi????" 07049138863. ̈̃̈̃Call 07012329134 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ PAGE 20- 21 Bai dubeta ba ya soma da bata amsa. Addinin musulunci shine addinin gaskiya. Addinin da manzon Allah( S.A.W) ya koyarvdamu. Addinin.Musulunci shine addinin da zaka san mahaliccinka kuma ka bauta mishi. Addinin musulunci shine addini me tsafta. Cikar musulunci shine. kalmar shahada. Ka ƙiyasta babu abun bautamawa da gaskiya face Allah ,(S.W.A) sannan ka shaida Annabi muh'd bawan Allah ne kuma manzonsa ne. Inkai haka ka zama cikakken musulmi. Sannan sai sauran.Sannan kayi imani ......... 1Imani da Allah. 2kayi imani da manzonsa. 3Imani da mala'iku. 4IMANI da Littafansa. 5kayi imani da ranar tashin alqiyama 6Kayi imani da ƙAddara alkhaiei. 7kayi imani da ƙaddarar sharri. 1Sallah 2Azumi 3zakka 4Hajji daga cikinsu babu wanda banayi. Ada ina sallah,ina azumi ,ina fitar da zakka daga cikin ɗumbin dukiyar da Allah( s.w.a.)ya azurtani da ita. Abbu sallah,amma yaya akayi ban taɓa ganin kayi ɗaya daga ciki ba Kuma nima baka taɓa koya min ba? Murmushi yayi yace karkiyi sauri Muhijjinatu da sannu zaki ji duk dalilin da yasa. ******* Ranar da Sarki ya cikia sati da rasuwa aka ɗaura min aure da mata 4. Akuma ranar aka nemi ƙanena Safwan aka rasa. Sati na zagayowa ɗaya ta mutu mutuwar farat. Anyi sadakar uku ɗaya ta kwanta ciwo kwana 2 ita ma tace gagarinku nan. cikin wata 1 kaf matan nan saida suka mutu. Na shiga tashin hankali yadda baki zato kuma duk auren soyayyah mukayi dasu,kuma duka ƴaƴan sarakuna ne. Ke in taƙaice miki cikin shekara mata 10 suka mutu,duk an chanfani cewar tsafi nake,mutane sun soma tsoron ince ina son ƴaƴan su. Don haka sai na haƙura da aure na fawwalawa ubangiji al-amarina. Na yi shekara ɗaya ba mata. Kwatsam ina zaune wani shararren Malamin addinin musulunci Shekh,Ibrahim ya zo tare da ƴar sa ina zaune fada duk abin duniya ya dame ni. Maganar da yazo da ita bani ba hatta fadawa sun girgiza,har wasu na ganin kwaɗayi da son abin duniya yasa zai jefa ƴarsa hallaka. Abinda yace min shine. Shi yayi imani da Allah ke kashewa kuma shike rayawa,rayuwa da mutuwa duka suna wajen Allah don haka muddin ina san ƴarsa Sayyada Binta to zai bani aurenta. Mun daɗe muna jayayya nace mishi nifa da na auri mace mutuwa take yace indai ina san Binta to ya bani. Kuma itama ta amince,don haka amincewa ta kaɗai yake buqata yanzu a ɗaura aure,in bashi sadaki kaɗai yake buqata. Ba yadda na iya haka na haqura na rungumi ƙaddara. Ni da mutanena tun mun̵'a qirga kwanakin mutuwar Binta har mukaji shiru. Shekara guda ta sulluɓo ɗanta namiji aka saka mishi suna Haidar. Yana shekara ɗaya ta watanni ta haifo mace wacce taci suna Mukasshifiyah. Bayan an yaye Mukasshifiyya ta haifi Azzkafiyah. To na haqura da aure tinda Binta ita Allah ya hukunta ta zama matata. Muna zamanmmu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali.......... Kartseshi Muhijjinatu tayi idonta taf da ƙwalla tace''Abbu ashe bayan ni kana da wasu yaran? gyaɗa kai yai alamar ''Ehy'' to mu yaya akayi ka nisantamu dasu,Me yasa ka zaɓi rayuwar DAWA? sannan su sauran ƴan'uwan nawa suna a raye koko? Kuka sosai Abbu ya fashe dashi yace SAFWAN,SAFWAN ɗan'uwanane Amma Allah ya isa tsakaninni dashi. To Abbu har yau banji ka ambaci komai game da Safwan ba amma sai kiran sunansa kake. yanzu zaki ji komai saurara............ Tun tsawon shikarun da na kwashe ina mulki wajen shekara 5 kenan yarana uku,sai qaramin cikin da Binta ke ɗauke dashi a halin yanzu. Al-umma najin daɗin mulkina tamkar dai yadda mahaifina ke mulkinasa. duk tsawon shekarunnan babu wanda yasan inda Safwan yake harni kaina. Ashe Safwan ya nutsa duniya yabar matarsa da ƴaƴansa ya nutsa duniya neman duniya bokaye ya shiga nan ya fita nan a dole sai ya wulaqantani. Nida ba laifin da nayi masa. Cikin shekara 5 ɗinnan ya haɗu da shararrenn bokan da duk duniya anyi ittikafin babu wani boka shaharre matsafi kamarsa boka zaƙawanu kenan,duk wani sheɗanin al-jani to dashi yake aiki duk wani bil-adam ɗin da ya ziyarci boka Zaƙawanu to sunan sa A SAIDA LAHIRA A A SIYO DUNIYA(wa'iyazu billah)/ Safwan ya sami nasarar haɗuwa da boka Zaƙawanu,tinkan Safwan ya faɗi buqatarsa shi shi bokan ne ya faɗi masa abinda ke tafe dashi. Boka ZAƘAWANU yace ni sharaɗina kurum zan faɗa maka. ''Safwan sharuɗɗan sune kamar haka- Dole ne kabar sallah kwata,kwata a rayuwarka, sannan zakayi zina da ƴarka kuma a cikin azumi. Sannan zaka sadaukarwa mahaifiyarka dodon tsafi ya zuƙe jininta. Sannan idan buqatarka ta zama sarki ta cika to zaka mayar da bayinka ƴaƴan sarakuna, ma'ana zaka sato ƴaƴan sarakai su zama bayinka. kuma duk shekara za'a ba dodo jinin ɗaya daga cikinsu ya shanye. Idan duk ka cike wa'innan sharuɗɗa za'a nemi sarki Abbdullahi a rasa rashi na har abada. Zai shiga daji shida matar sa a inda namun daji zasu cinye naman su. Kuma duk duniya babu wanda zai ƙara tuna Sarki Abdullahi hatta fadawan sa. sannan abu na gaba da zarar ka zama Sarki zaka maye gurbin masarautar da bakin zane komai zai zama baqi ne,sannan hatta da rawanin ka baqi get ɗin da za'a buɗe a shiga baqi unipoam ɗin bayi baqi sittirarka kullum baqa. Fadawan ka ma komai nasu baqi. Kuma ka kori wa'innan a chanza wasu. To ina me tabbatarmaka Sarki Abbdullahi da matarsa Gimbiya Binta zasu bar ƙasar nan gaba ɗaya Abbdullahi da matarsa zasu mance kowa kai hatta kansu sai sun mance Abbdullahi zai mance da sarauta sau ɗaya a duniya zai dinga tuna shi waye. kuma cikin DARE.Ko ya tuna yayi gigin ɗaukar mataki kafin gari ya waye zai manta. Sannan duk Wa'innan abubuwan ya kasance DADDARE za'a aikata kar ayi komai da safe ko da rana ko da yamma. Abbu yaɗanja numfashi yana duban Muhijjina. Hawaye suka zubo mishi babu wacce akafi cutarwa kamarta zarkaɗɗiyar budurwa kamar wannan ace ta kasance RAINON DAJI.̀ ba ilimin addini ba na zamani har gara ƴan'uwanta su sun rayu cikin gata,kuma suna da ilimi sosai kuma sunsan su ko su waye ita kam bata san kowa ba sai dabbobin daji...... Abbu kenan banda Bashir cikin aika aikar? Safwan shi kaɗai ne ya aikata. murmushi Abbu yai yace. ''Bashir shine Impomer na Safwan duk abinda nakeyi akan idon Bashir shike sanarwa da Safwan duk halinda nake ciki. Sai dai shi Bashir ba mulki yake so ba shi dukiyar ce kurum a gabansa duk da dumbin dukiyar da mahaifinmmu ya bar mana gado wacce inda zamuyi ta cinta har ɗiyan,ɗaiyammu bazai talauci ba,ke mubar juya kuɗi kwata,kwata har abada bamuyin talauci.... ***** BOƘA ZAƘAWANU ya ci gaba da gindiyawa Sarki safwan sharuɗɗa kamar haka .........Da zarar matar Abdullahi tazo haihuwa dodo na buqatar jinin naƙudarta. Safwan yace''Nama bada jinin uwata bare na wata banza uwata ita kaɗai ta ragemin amma na bada jininta saboda in sami duniya. Uwata ita taci kashi da fitsari na. Ya matse ƙwallah karon farko da yaji tausayi a rayuwarsa..... To balle jinin matar maqiyina. Boka yace sharaɗin qarshe shine zaka duka kayiwa DODO SUJADA,shin ka amince? 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ 22-23. ''NA Amince da wannan sharaɗi,kuma zanbiduk wata doka dake ciki, nama amince da sharaɗin barin sallah kwata,kwata a rayuwa bare wannan don haka na amince ni a halin yanzu buƙatata ce kurum a gaba na. ''hhhhhhhhhhhhhh!!! Boka Zaƙawnu ya kwashe da mummunar dariya. Kafin Safwan yace uffan tsintar kan sa kurum yai a gaban DODO. Baƙar halitta ce mummuna bakinsa sai dalalar da baqin Jini yake,kuma gulama gulama,wannan halitta ita Safwan ya faɗi yaiwa sujada(wa'iyazubillah) Kafin kace me sai algaitu da bushe,bushen sarauta suka dinga watsuwa a ko ina na cikin ɗakin. Ana busa ana SAFWAN BAƘIN SARKI, ME BAƘAR MASARAUTA, DAGA YAU KAINE SARKI KAINE ME BAƘIN MULKI. Koda aka gama wanka aka mishi da jini. ya daɗe ana mishi wanka da jini tsira haihuwar uwarsa. Gaba ɗaya yalwataccen farin ciki zaka hango a fuskarsa a yau mummunar buƙatarsa ta biya. Daga baya Boka yace ya rufe idonsa. Koda rufe idonsa ya buɗe tsintar kansa yai ɗakinsa. Matarsa tayi mamakin ganinsa amma kuma ba yau ta saba ganin makaman cin hakan ba, duk da cewa tayi mamakin ganin ya koma matsafin qarfi da yaji. ******* DARE ya raba A lokacin ukun dare ne Sumayya na kwance a saman katafaren gadonta barci take cike da nishaɗi da farin ciki zuciyarta fes bata da damuwar komai. Sumayya ita kaɗai ce ƴa a wajen Safwan tana kwance cikin daɗin barci ta tsinci kanta cikin baƙon al-amari shin mafarki ne ko gaske,zafi da zogi da raɗaɗin da taji yasata fasa gigitacciyar qara wacce tasa ba arziƙi mahaifiyarta fitowa. Tirƙash! ai ba Sumayya ba hatta mahaifiyar ta daskarewa tayi daga tsayen da take ganin Safwan mahaifi ga Sumayya kwance saman ta yai mata kaca,kaca,reaping na wulaƙanci. Cikin kuka Sumayya ke faɗar ''Daddy nice,nice Daddy Sumayya fa ce. Maman Sumayya,Wacce ta faɗo ɗakin fujajan daskarwa tayi, daga tsayen da take.hannu aka ta fashe da kuka ta soma cewa ''Alh.Me yassmeka? Sumayyace fa ƴa ƙwal da ka mallaka a doron duniya. ita ce kayi mata fyaɗe? Safwan ya miƙe fuskarsa ko alamar razana da ruɗani babu babu alamar nadama ko da nasani a tare dashi fuskar sa sam ba tsoron Allah. Buƙatar sa ta duniya kurum ke gaban sa. Cikin kuka mahaifiyar Sumayya tace. Ka sake ni a yau ɗin nan a kuma yanzu. ''Bazan tona maka asiri ba,saboda innna tona maka asiri Sumayya na tozarta,amma ka sani zama na da kai ya qare,wallahi,kuma Allah ya isaḷ tsakanin ni dakai ka jira yaumatubulasra'i insha Allah Allah zai bi mana haƙƙinmmu. Safwan ya kwashe da dariya yace idan ana saki dubu nayi miki,kuma rufin asiri kar ki rufa min ki sane duk duniyar nan banga ubanda zanji wa kunya ba babu shi,ke ko me martaba zai dawo duniya yaga wannan aika,aikar bazan taɓa damuwa ba. Sumayya ta safko daga saman gado tana tafiya tamkar ƴar kaciya,tace ''Mommy don Allah zan biki. Safwan ya tillata saman gado,har goshinta ya dafji qasa. Yace ''Babu inda zaki dake tazo? Mahaifiyar Summayya ta dube ta idonta na sharar da hawaye tace''Sumayyah ki tuna Allah yana tare dake!!! daga haka ta juya.Sumayya ta kifa kanta ƙasa tana kuka wiwi. ******** Kwana biyu da faruwar hakan Mahaifiyarmu ta mutu sakamakon aman jini. Daga rashin lapiyar mahaifiyarmu kuwa ni kaina na kwanta jiyya.Rashin lapiya sosai. Duk wata qasa da kika sani an kaini domin sanin ciwo na amma ina. A shefa duk ciwo na ya danganci sheɗancin Safwan,ko mata na da sukaita mutuwa shike bada jininsu wa dodon tsafi ita ma Binta kafin na aureta mahaifinta babban malamin addinin musulunci ya shiryata tsaf. Da ayoyin Allah kuma anyi anyi asha jininta yafi qarfinsU. Haka ma yaranta sunfi qarfin dodo. Safwan yabar sallah kwata,kwata a rayuwarsa ya zaɓi duniya fiye da lahirarsa wa'iyazibillah. A ɓangarn Bashir kuwa duk wani asiri naci shike bani shi sai ya fake da yana bani kulawa dangane da ciwona kana kuma duk wani duk wani asiri na bisnewa Safwan ke bashi sai yazo ya bisne. Koda wasa Safwan bai taɓa zuwa dubani ba. Wai mutane me yasa muka ɗauki dogon buri muka ba duniya al-hali rayuwar qanqanuwa ce. Shi Bashir munafinkin ɓoye ne bai taɓa nuna min ƙiyayyah a gabana ba Safwan shi ke nuna min ƙiyayyah da gaba da hassada. MASARAUTAR ASAD. Babbar masarauta ce kuma duk wani sarki dake duniyar nan Yasan da zamanta,kuma ƙarƙashinta yake masarauta ce me dumbin tarihi kuma a tarihinta ba'a taɓa sarkin da aka sha wahalarsa ba duk sarakunan da suka shuɗe a dalai ne masu tausayin talaka. SAFWAN. Yaiwa ƴarsa fyaɗe. Safwan ÿaiwa ƴar cikinsa fyaɗe. Safwan ya baiwa dodon tsafi jininn mahaifiyarsa. Safwan yabar sallah kwata,kwata a rayuwarsa. ******** Yau wata na 2 da kwanciyata jiyya kuma ayau ne na warke tangaram. Abin mamaki ba kuma wani yazo ya bani magani ba ba kuma likita ya duba ni ba ikon Allah kenanḷ ko fadawa duka sunyi mamakin wannan al-amari sauqi kwatsamḷ da yamma ina ɗaki naji sallama. ''Assalamu'alaikum. Mamaki ya kamani nasan dai ni ni kaɗai ne to sallama daga ina? ni da ƙofa take garƙame da jamlock. Ido na ne yai min arba da farin mutum dogo,sanye yake da farin tufafi. Kafin ince uffan yace''Sunana Mal.Abdurrahan. Ni rauhanine cikakken musulmi. ...Nazo ne na sanar maka cewa ka yarda da ƙaddara wannan jarabawace tana daga cikin ƙaddarorin da ubangiji ya aiko zasu sameka ka sani cewar cikakken musulmi shine wanda Allah ke jarabta,Manzon Allah S.A.W yace duniya sijinil.Muminin wa jannatul kafeeroon. ... Ayau sabuwar sauyi zai riskeka zaka rabuda ƴaƴanka sarautarkan wannan duk ƙaddararka ce domin kafin Allah ya halicce mu ya halitta annabawa kuma duk ya jarabcebsu to mu su waye da Allah bazai jarabce mu ba? nan Mal.Abdurrahman ya kwashe labarinnan kaf ya faɗa min game da ƙullin da Safwan da Bashir kemin yaci gaba da cewa na para bibiysrsu don na tsimake ka to mahaifiya ta tace Muddin na sake taimakon musulmi Allah ya isa bata yafe min ba,ita ba musulma bace mahaifin musulmi ne kuma ya mutu. Ina mata biyyah ina gudun fushinta Yarona Bilal ilimin shi bai kai na yaƙi da sheɗanun aljanun da aka haɗaka dasu ba,amma zansa ya dinga bibiyarka sannan zai shiga duniya neman ilimin addinin musulunci a domin ya tayaka yaƙi dasu. .........Yana gama faɗar hakan ya ɓace. Mal.Abdurrahman,Mal.Abdurraham.........Naso ma ƙwalla mishi kira amma inq....Bazan iya tafiya nabar ka ba idan na tafi wajen wa zani? ban san kowa ba sai kai Abbu.. Amma Abbu idan mutuwar tazo me zai hana ka lallashe ta ka faɗa mata da gani sai kaine muke rayuwa, don haka ta ɗauke mu rana ɗaya nasan zata tausaya mana......Shiru yai ransa yana ƙissima rashin ilimi da jahilcin muhijjinatu sai tausayinta ya ɗaɗa ka mashi. yana jin a ransa a kowwanne hali zai shiga sai Muhijjinatu tayi ilimi ta san kanta. Dubanta yai yace. Mutuwa saƙone daga ubangijin musulunci ke aiko mala'ika a azara'ilu ba magana yake ba bakuma a ganin lokacin da yake zowa sai dai kawai ya zare rai ya tafi,kuma baya ƙetare maganar ubangiji. gyaɗa kai tayi kurum batar da ta gamsu da maganarsa ba tace. To Abbu ci gaba da bani labarin yaya akai da sauran ƴanu'uwana kuma ta yaya kukayi rayuwa da mamana a DOKARDAJIN NAN?.... Daga wannan page ɗin a page na gaba za'a dawo labarin ma'ana labarin Abbun Muhijjinstu zai ƙare zamu dasa daga inda muka tsaya. Idannnaga commts over zamu takarkare labarin zuwa anjima zan kara page 1 in mai kowa mai komai ya kaimu gobe zamu ci gaba da dawowa labari. Kuma book 1.ya kusa ƙarewa.A page 49-50.Shine book 1 sauran page ɗin har zuwa page 200 shine paid.Allah ya bada iko. karku manta yawan page zai saka mu ƙara page ɗaya da yamma insha Allah. 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ page 26-27. ABBU yace kinga wancen kogin? Muhijjinatu ta gyaɗa kai tace ''Ehy'' yace to kullum chan nake zuwa ina kamo mana kifi tamkar dai yadda nake yi dake. Wata rana kuwa nakan kutsa dawa na kamo mana naman daji. haka dai muka ci gaba da rayuwa a baibai.Kwananmmu arbai'n Mal.Abdurrahman ya kawo mana ziyara. A lokacin ina ɗan tuna yara na na tambayeshi ina Haidar da Mukasshifiyya da Azkafiyyah? yaya labarin sarauta ta anan yake labarta min komai. Mal.Abdurrahman yace ''Abdullahi bayan ɓacewarka Safwan ya haye akan karagarka.Sannan sun kwashi dukiyarka shida Bashir wacce har ɗiyan ɗiyansu bazaiyi talauci ba. Abbdullahi nasan jin daɗin duniya baya gabanka. Labari mafi muni shine ƴarka Azkafiyya tana wajen me gadi.Mal.Kabir,ita kuwa Mukasshifiyyah ta na gidan Safwan a matsayin ƙasƙantacciyar Baiwa.Haidar kuwa ni da kaina na kurumtar dashi baya magana a gabansu.Yanzu halin da ake ciki babban burin Safwan shine Haidar ya sami lafiya yazo ya buɗe wannan kogon saboda sun san dokar cewa duk duniya babu mai iya buɗe kogon face ƴaƴanka sun haɗu su duka nasan security ɗin shine ............MUKSSHIFIYYA AZKAFIYYAH HAIDAR.to sunan farkon ne babu wanda ya sani daga Allah sai kai sai kuma Haidar da ka faɗa mawa.Na dubi Mal.Abdurrahman nace wannan zance haka yake,babu wanda yasan sunan kuma sunan farko sunan ƴar da Binta zata haifa ne,sannan koda Haidar yana magana a dole sai yara na sun haɗu waje ɗaya kana kogon ya buɗe dukiya ce tunda daga zinari lu'lu'lu yakutu daimon goal da sauransu kuma kuma halak malak ɗina ce ba dukiyar talakawa bace kuma ba gado bace kasuwanci na ne ya tara min...sunan farko shine MUHIJJINATU. Kaga kenan security ɗin shine Muhijjinatul,Mukasshifiyyah,Azkafiyyah,Haidar da sun haɗu suka faɗi kalmar zai buɗe nine kaɗai zanje in buɗe ya buɗu kuma sihirrin su Safwan bazai iya buɗe wajen ba. Company ne me zaman kansa nasaka ya haɗa min ƙofa me wannan sirrin me kama da sihiri kuma ba sihiri bane ni Sarki Abdullahi ban taɓa tsafi ba. Mal.Abdurrahm ya miƙa mishi wani abu cikin leda yace''wannan tsari ne dakai da iyalinka Insha Allah babu abinda zai sameka. Kuma daga yau bazaka kuma ganina ba domin mahaifiyata tana gab da dawowa.Daga tafiyar da tayi,har na samin sararin ganawa dakai amma na tura yaro na Bilal saudiyyah neman ilimin addini a domin yazo ya taimakeka a ksrya sihirin dake tare dakai. Abbu ya ce ''nagode sosai Mal.Saidai dakayi haƙuri domin ni nafiso na qarasa rayuwata anan dani da Safwan da Bashir kowa zai mutu babu wanda zai dawwama a wannan duniyar kowa zai mutu mu koma zuwa ga Allah... Akwai ranar tsayuwa Mal.Abdurraham yace haka ne amma rabuwa da sihirin shima abu ne mai kyau...Sannan ka sani DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI: 1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka. 2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka. 3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka. 4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa. 5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake. 6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin). 7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka... wannan bayani da Mal.Abdurrahn yai min yasa jikina yai sanyi na fashe da kuka ganin bazai iya jure kuka na ba ya sa ya bavce shima kukan yake kashirɓan. A kuma lokacin Binta ta soma yunƙurin naƙuda zata haifoki...... Cikin sauri na isa gareta. cikin hukuncin ubangiji Binta bata sha wahala ba ta sulliɓo ƴarta kyakkyawa wato ke ɗinnan. Kina zowa duniya nayi miki huɗuba da Suna Muhijjinatu. Aljanin dake tsare yana jiran a haihu yaji sunan domin buɗe kogo a take yabar wajen domin jinkinsa duk ya sale saboda bazai iya tsayawa a wajen ba saboda tsarin da Mal.Abdurrahmn ya saka a wajen. Dalilin da yasa bana zuwa wajen kabarin mahaifiyarki to achan madaddalar sheɗanun yake daga chan tsarin ya kare. Ranar da na fara kai ziyara to aranar suka ɓatar min da tunanina suka mantar dani ƴaƴana da baro Mukashifiyya Azkafiyyah Haidar. Ke hatta sallah da ibaduna azmi duk daga lokacin na manta komai hatta waye ni daga ke sai mamanki nake tunawa a rayuwata. Daga lokacin na gaza gane shin ni mutum ne koko dabbar daji? daga haka Abbu ya tsaya ya fashe da kuka me ɗaci. A wannan karon tausayin mahaifinta ya kasheta,rungumshi tayi ta fashe da matsanancin kuka,su duka an rasa me rarrashin wani...... Abbu yaci gaba da ba Muhijjinatu labari. Safwan shine ya sadaukar da jinin mahaifiyarki ga DODON TSAFI. A domin cikar sa shekara daya akan karagar mulki. Tin daga lokacin ta kwanta jiyyar ciwo baci basha jinyar da baci basha sai aman jini hanci da baki. Kwatsamḷ wata rana na shiga daji nemo magani na dawo na tarar da ita ta fita hayyacinta sai amai take hanci da baki ga ƴar jinjira gefe sai aman jini take. Da sauri na isa garena nace''Gimbiya Bintaḷ magaganunta su suka daskarar dani na rasa yaya zanyi,alokacin na shiga wani mugun ruɗani. Daƙyar maganar ke fita. ''Abdullahiḷ Karon farko a rayuwarmu da naji ta ambaci sunana. Duk yadda zan fasalta miki mummunan tashin hankalin da na shiga a wannan yanayin abin zai baki mamaki. Maganar ta ta sa na sandare shin suma nayi,Ina a raye? Allah ya barwa kansa sani. ''Ina so ka rike min Muhijjinatu amana kuma bana fatan Muhijjinatu ta ƙare rayuwarta a DOKAR DAJI,ina so komin daren daɗewa a sadata da yan'uwanta. Na kuma rokarka banaso Muhijjinatu ta qare rayuwarta A MUGUN DAJIN NAN. La'ilahaillahu muhammdurrasulli............Banji ƙarashen maganar ba na faɗi somamme a wajen. ban farkaba saida garen Allah ya waye sannan na buɗe idona alokacin harta sandare ita kuwa ƴar taci kuka har tayi barcin dole. Koda buɗe idona madarar jarirai na tarar a jiye gefe anba yar harda fita irin madarar nan me suna NAN basai na tambayaba aikin Mal.Abdurrahman ne. Na sake fashewa da kukan rashin Binta wai nida Matata Gimbiya Binta sai ranar lahira(Allah sarki Abbu ka tuna min da Humairata shikenan sai ranar lahira😭😭😭😭) Mal.Abdurrahmn shi ya aiko min da likkafani nayi mata wanka irin na musulunci na ɗauketa na ɗanyi nesa da wajen. Haka naje bakin kabarin na zauna bayan na tona na zauna tun safe har rana ta take kuka nake ba mai rarrashina,danaga babu sarki sai Allah haka zalika Binta tatafi tafiyar da bazata dawo ba yasa na tashi na saka ta gidanta na gaskiya nayi kuka me cin rai mussammn sa'adda ɗibar ƙasa ina zubawa wayyo Allah na!!!😭😭😭 kukan Muhijjnatu ya farkar dani na miƙe na ɗauketa na juya da nufin barin wajen wannann baqar guguwar tataso. Dakan ƙwarangwal. Sarki Abdullah! naji ankirani da wata baƙar murya me amo. Arazane na juyo da matuqar mamaki zatona Mal.Abdurrahmn kaɗai yasan inda nake. Hhhhhhhhhhh!!!!!! wannan mugunyar dariyar ta katseni. Sarki Abdullahi Safwan ya cuceka ya ƙwace maka sarauta Bashir ya kwashe dukiyar dake gidanka,sun ƙasƙantar da rayuwar ƴaƴanka. Tun sa'arda Safwan ya haye karagar mulkinka har yau babu wanda ya tambayi kana ina,koda mutuwa kayi ai ɗanka zai gajeka to ɗannaka magajinka yana chan qasqaskance. Hatta matarka su suka kasheta suka ƙasƙastar da rayuwarka A DOKAR DAJI. Idan harka amince da dokokina zan tsaya maka zan ɗaukar maka fansa zaka dawo rayuwarka kamar da da iyalinka ƴaƴanka zasu dawo sarautarka zata dawo Gimbiya Binta ma zamu dawo maka da ita,kana da damar ɗaukar fansa badon komai ba sai don ƴar jinjinrannan da bata cutar da kowa ba. Koko kafiso ta qare rayuwa A DAJI cikin DABBOBIN DAJI? na ɗago na dubi shi meye sharaɗin? hhhhhhhhhhhhhhh ba wani abu me wahalarwa bane illah kayiwa DODON TSAFI SUJADA...... MATARKA Gimbiya Binta zata dawo sarautarka zata dawo..... zaka fita daga ƙangin musifar nan ƴaƴanka da ka baro zaka ruske su........ ''Ni bazan iya yiwa wata halitta sujada ba,haka zalika tun wanzuwar duniya ake mutuwa har yau babu wanda ya taɓa dawowa..... Tin daga lokacin duk sa'arda naje wajen kabarin mamanki haka nake karo da sheɗanu nnan suna bijiro min da wannan buqatar,daga lokacin ban kuma zuwa ba haka naita rainonki har kawowa iyanzu da nake baki labarin nnan ƴaƴana sarauta duk ɗan uwana Safwan ya kwace da ƙarfin bokayen da yai imani dasu wannan shine ƙarshen labarin......... (wayyo da dama makaranta na sun tausayawa abbu da dama sun tausaya wa rashin sallar da Abbu ya kwqshe bayayi ku tuna cewa duk zunubin y a rataya akan sarki safwan kuma kar ku manta ƙiƙiƙrarren labari ne me kuke ci na baka na zuba kunsan rayuwar Abbu bazata qare a haka ba akwai fa Allah. Sannan labarin Mallah Abdurrahn da gaske akwaishi kuma labarinsa gaskiya ne .karku gaji ku jirabkaɗan.) ) 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ page 28-29. **ANDAWO LABARI** Muhijjinatu ta ɗago ido ta dubi mahaifinta,wanda ya dage iya san ransa yanata kuka haiƙan. Muhijjinatu tace''Abbu ni idan ina kuka kaine me rarrashina,kai kuma kukan ka yana sakani kuka,shin kai kayi kuka ni kuka waye zai rarrashi wani? Abbu ka daure kayi jarumta kayi haƙuri Abbu. Share hawayen fuskarsa yai da gefen hannunsa yace.''Dole nayi kuka Muhijjinatu kuka ya zamar min dole,duk DAREN DA na tuna wannan labarin kwana nake kuka sosai kamar zan haɗiye raina da zarar gari ya waye zan manta kowa da komai da ya shafeni.̇.. Abbu ya kamo hannun Muhijjinatu ya haɗa da nashi yace''Muhijjinatu ina neman alfarma a wajenki. ''Tame fa Abbu? ta faɗa fuskarta ɗauke da mamaki. ''Duk abinda kake so Abbu koda raina ne zan mallaka maka. Cikin tsananin tausayi yace. ''Gobe idan rana ta fito ina so zan ɗoraki a hanya ki shiga gari. Da izinin ubangijin musulunci zaki haɗu da mutanen kirki,da zasu riƙeki tamkar ƴarda suka haifa,Muhijjnitu kina buƙatar abubuwa da dama a rayuwarki kina buƙatar ilimi kina buƙatar kisan kanki matsayin ki na ƴa mace.Daɗin daɗawa kina buƙatar abokin rayuwar da zaku rayu ku tara zuri'a ke idan da raboma zaki iya haɗuwa da ƴan'uwanki Mukasshifiyya Azkafiyya Haidar. Muhijjinatu kina buƙatar farinciki kina buƙatar kiji daɗin duniya ni rayuwata ta kusa ƙarewa rayuwata dake ba dawwamammiya bace.dole wata rana za'a wayi gari babu ni a duniyarnan. saboda kullum rana girma yana ɗaɗa ruskata ranarda aka wayi gari babu ni yaya zakiyi,Waye zai ci gaba da nemo miki abinda Zaki ci? duk ranar da babu ni to daga ranar zski zama bebiya alhali da kunnenki zaki zama makauniya me duniya,duniya zata juye miki,sannan daga ranar kin gaman jin daɗin duniya,amma idan kika shiga gari kinga zaki haɗu da 'yan'uwanki mutane zaki ga abun mamaki iri-iri zaki ga jarafta wacce ma tafi taki amma yanzu ma ke kanki baki san ƙadddara me kyua ba ko akasinta. Idan na barki a haka na cuceki ranar lahirabAllah zai tuhume ni.̧kuma kinga idan na ƙyaleki ban cika ma mahaifiyarki wasiyyarta ba. ni ina ji a jikina keɗinnan zaki zama wani haske a rayuwa. Amma idan rayuwarki ta ƙare a dokar daji na cutar dake muguwar cutarwa ma ranar lahira Allah (S.W.A.) zai tuhume ni bazan so hakan ya kasance ba...... Yanzu me kika zaɓa? ya ƙarasa dogayen zantukansa da kafe ta da ido baya ko ƙyaftawa. Duk dogayen zantukannan idanuwanta a ƙasa suke sarde bata ɗago ta dubeshi ba. ''Ke nake saurare Muhijjinatu! firgigit ta ɗago ta zuba mishi ido. Hawaye share,share a fuskarta abin gwanin tausayi. Bakinta na kyarma tace. ''Bazan iya ba! "Bazan iya ba!!! A lissafinka kace shekaruna sha takwas a duniya,tin tashi na ban san kowa ba sai kai ban rayu da Uwa ba haka zalika dangina duk ka maye min gurbin su kawai rana ɗaya sai ace in tashi in barka in tafi ina? Duniya???? Duniya meye jin dad'in duniyar Nan? Nifa sam bansan jin daɗin duniya ba balle ya birgeni kuma koda zanji daɗi a duniyar nan to muddin ya kasance batare da kai ba nikam na yafe bana buƙatarsa Abbu na roke ka ka daina yimin maganar rabuwa dakai bana buƙatar hakan.Abbu ina tare dakai duk tsanani duk wuya baza mu rabu ba. ''Na yafe jin daɗin duniya,yanzun dai ka tashi mu kwanta ina jin gari ya kusa haske ko. Batare da yace uffan ba ita ta jawo bargon fatar dabbar da suke rufa ta lulluɓa musu. Kafin kace me barci me daɗi yai awon gaba dasu. Asuba ta gari Abbun Muhijjinatu. *** Farida cikin tsananin ƙuna da ɗacin rai take duban Alh.Bashir ranta ya dugunguza tace. ''Daddy yanzu duk wata social media an tura hotunan matsiyatan nan amma shiru ba labari. Alh.Bashir ya ƙuta yace. ''Ni kaina abun ya ɗaure min kai duk wata state dake nigeria na aika jami'an tsaro amma shiru kaman an aika bawa garinsu. ''To Daddy meye abin yi yanzu?.... 🖤WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari]_ Page 30-31- ALH.Bashir yace tun tashina a duniya babu wanda ya taɓa wulaƙantani,shiyasa ma ban zauna waje ɗaya da ɗan'uwana Safwan ba saboda wulaƙancinsa babu wanda ya ragawa. Farida ta cije leɓen ƙasa. zuciyarta na turiri tace''Kema abin baƙin ciki ƴar matsiyata ma.......Alh.Bashir yace''Waye ya faɗa miki ƴar matsiyata ce? Sai Kuma yai shiru....To Daddy ubanwa ya haifeta bnda tsohon me gadin nan.....Inji wa Azkafiyya ba ƴar matsiyaci bace,ubanta yafi ubanki komai banda zalunci ke da baki isa ki nuna Azkafiya da yatsa ba........Ya ishiki Haj.Alh.Bashier ya katse matarsa dake saukowa saman Upstar juyawa tayi fuskarta ɗauke da murmushi mayalwaci. Fareeda ta zubawa mahaifin nata ido tana jiran ƙarin bayani akan maganar Mommynta. ''Daddy da gaske ne maganar Mommy? ''Ke ƙyaleta kin dai santa da tausayin talaka. Karki sake ki biyewa maganarta bare ta dà̀me ki. Farida ta gyaɗa kai alamar gamsuwa. *** Mariya Mal.Kabir Azkafiyya,tsintar kansu sukayi cikin wani ƙyauye na fulani. Mariya tace ''Nashiga uku Mal.Tsafi ka koma..Taya ka iya yin layar ɓata Mallam kardai tsubbu kake? Saboda Azkafiyya zaka kauce hanya? karfa ka manta Alh.Bashir babu abinda zai iya yi mana saboda Azkafiyya tunda yasan bamu muka haifeta ba,to don me za'a hukunta mu da laifin da bamu muka yi ba haka zalika ba ƴarmu tayi ba? Wani irin tari ya sarƙi Azkafiyya ta zaro ido warwaje tace''Mama dama baku kuka haife ni ba na shiga uku! ''Karki kuma kira na da Mama ni ba uwarki bace,Mal.Ba ubanki bane mu bamu taɓa haihu......... Toshe mata baki Mal.Kabir yai.. ''Haba Mariya duk aikin alkharin da kikai rana ɗaya ki toshe ladarki.....Kuma ni ban taɓa tsafi ba kuma bana shirka,nima tsintar kaina nayi nanɗin tamkar yadda kika tsinci kanki a nan. Mariya tace A gaskiya Mal.Sai dai ka zaɓa ko ni ko Azkafiyya domin bazan iya tafiya da yarinyar da ban san asalinta ba da tushenta kaima ma fa cewa kayi tsintar ta kayi,ƙir,ƙiri muna gidan kuɗi cima me daɗi makwanci me daɗi amma ƙiri,ƙiri dalilin ta mun dawo ƙauyen da bamu san makomarmu ba. Don haka muddin kana san ci gaba da zama dani sai dai ka zaɓa koni ko Azkafiyyah. Kuma karka manta mahaifinka yace muddin ka rabu dani bai yafe maka ba,kuma ya rigada yabar duniya bare kaje ka nemi Affuwarsa. Kuka me ƙarfi Azkafiyya ta fashe dashi tace.Mama Dama duk kallon da nike muku,Baba daman ba kaine ka haife ni ba? wani mugun tausayinta ya kama Mallam Kabir yace,Aa Azkafiiya karki ce haka nine Babanki........ Yaushe ka haife tan sai dai idan ciki kayiwa wata ta haifo maka ita,ka dubi wannan tsaleliyar budurwar kamar balarabiya kana baƙi kace ƴarka ce..... ''Kai Mallam lokaci yayi da zaka faɗawa yarinya gaskiya. ''Ke ta kira sunan Azzkafiiyah. Tsintarki mukayi,kuma tunda kin zame mana bala'i gara mu jefar da ƙwallon mangwaro.... Kuka sosai Azkfiyyah keyi gwanin tausayi idonta ya kaɗa yai jajir. Mal.Kabir ya saukar da Ajiyyar zuciya yace. ''Ina neman Alfarma wajenki Mariya duk naji uzirinki. Gatsina baki tayi tace''Tame fa? ''Kin ce sai mun rabu da Azkaffiyh ko? ''Ehy ƙwarai ince ai da hausa nayi magana bada wani yare ba. ''Ajiyar zuciyar takaici yai yace''To ina so mu samu mutsugunni,kafi nnnan ina so kafin na sallami Azkafiyyh zan sanar da ita ko ita ɗin waccece. ''Am don wannan ba damuwa muje a sami matsugunniN. Suna tafiya Mariya nata bala'i ''Banda musifa da fitina yarinya kina banza a wofi ki saka hannu ki dallarawa me gidan da muke ci ƙarƙashinsa mari. Ni abin tambaya ta ma waye ya jefo mu nan muda ke tsakiyar ɗaki. Mal.Kabir ya girgiza kai yace amman ni da aka maran baki ji zafi ba ko? Tinda bakisan daraja ta ta mijinki ba. ***** **DOKAR DAJI** **DA SAFE** Wannan barci da su Muhijjinatu da Abbu keyi barci kaman na mutuwa har kusan ƙarfen biyun rana. to ai ba'a bun mamaki bane in ku kayi duba da a DAREN jiya sun raba DARE suna hira. Sai da rana ta iskosu dai dai wajen taga sannan Abbu ya farka yana tashin Muhijjinatu. Tangaram ta miƙe daga barcin da shike idon nata ya ƙoshi da barci bai sha wahalar washewa ba. Ki tashi ki wanke baki da fuska ki ɗauko sauran naman jiya ki cinye ni kuma zan shiga daji na samo mana wani naman. Farin ciki ya washe a fuskarta babban burinta shine Abbunta yabar wajen taje wajen baƙin Al-jani ya ɗorata hanyar da zata yaƙi Sarki Safwan da Alh.Bashir. WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari] page 32-33. **DOKAR DAJI** Haka ta zauna cikin tsantar farin cikin Don son ganin Abbu ya bar wajen domin ta tafi ta aiwatar da buƙatarta a wajen Baƙin al-jani. ''Washi! Abbu ya faɗa. Cikin sauri tace. ''Abbu Lfy? dafe kai yai. ''Muhijjinatu,ina jin matsanancin ciwon kai bazan iya gwagwarmaya da dabba,babba ba Amman bara na tsaya nan kusa kusa ko ƙarama sai na samo mana. Bakinta na ƙyarma tace. ''To Abbu. Amman a zuciyarta ba hakan taso ba. Kwanciya tayi saman gado,bayan fitarsa . Zuciyarta ta luluƙa cikin mugun tunani. Labarin da Abbunta ya bata jiya DADDARE,shine abinda kurum ke mata yawo a cikin zuciyarta. Tabbas a halin yanzu duk ta fahinci amsar tambayoyinta duka,da kullum take tsare Abbunta dasu. ***Sarki safwan*..*mayen mulki* *Alh.Bashir mayen kuɗi* *''Na rantse da ubangijin musulunci,wanda Abbu na ke faɗar ana rantsuwa dashi,sai na ɗau fansa akan ku,sai na kassara muku rayuwa tamkar yadda kuka kassara rayuwar Abbu.* *''Nayi alƙawarin zan bi duk sharuɗɗan da baƙin al-jani ya gindiya min a domin ɗaukar fansa akan ku.* *kun hana mu jin daɗin duniya duk da ni * *bansan jin daɗin duniya ba,amma kun ƙuntata wa Abbuna ƙun salwantar mishi da rayuwar ahali.* **Meye Abbu yai muku a wannan duniyar? me yayi da kuka hana shi jin daɗin duniya,kun rabashi da sarautarsa kunyi silar jefa shi a ƙasƙantacciyar rayuwa. Meye ribar ku,zaku gani,zaku gani,ni Muhijjinatu sai na ɗau fansa. yinin ranar bata ci komai ba zuciysrta tana cikin tuƙuƙi da baƙin ciki,shikam bawan Allah Abbu ya manta komai da ya shafe rayuwarsa bashi da burin komai illah ya farantawa Muhijjinatu. A cikin labarin da Abbu ya bata ta gane waye,Mallam Abdurrahmn kuma waye baƙin al-jani. To a ciki waye zata bi? meye hikimar baƙin al-jani da san taimakonta? Sannan shi Mallam Abdurahmn yace da sannu ubangijin musulinci zai saka mata. To sai ysushe ubsngijin msuluncin zai saka mata. ''Shin tsakanin Mallam Abdurrahmn da baƙin al-jani waye zata bi? idan tabi baƙin all-jani cikin ƙanƙanin lokaci zata ga bayan Sarki Safwan da Alh.Bashir. Shi kuma Mallan Abdurrahn bashi zai taimaketa ba,yce da sannu ubangijin musulunci zai saka mata ita da Abbunta hakan yana nufin ba yanzu ba kenan? to yaushe ne zai saka matan?(karfa ku manta bata san komai ba.Game da addini) gaskiya baƙin al-jani ya dace tabi,to Amma a labarin da Abbu ya bata yace mata mallam Abdurrahn mai taimako ne,yayin da baƙin al-jani ya kasance azzalumi. bayan haka shi Mallam Abdrhn yace da Akwai ɗansa da zai zo ya taimake su... Chakwakiya. **BAƘAR MASARAUTA.** Dare ya tsala duk bayin Sarki Safwan sun kwakkwanta a saman gadajen su barci suke haiƙan. A hankali duk suka ji ana lalubar sul lokaci ɗaya duk suka zabura gaba ɗaya kowaccen su ta wartsake. ''Waye,Waye,? kowacce ke ambata. ga wajen duhu ɗiff. Kuma basu san dalilin kashe sololin ɗakin ba. Mukashifiya wacce ita ma taji ana lalubarta don haka cikin sauri ta miƙe ta isa inda mukunnin solar yake. Ta kunna. Koda kunnawarta maza yanyame da kowanne gado ta tarar duk sun cika gaba ɗaya ɗakin. Kowacce ta duru,duru ,kuka suke da daman su,domin kuwa da yawa daga cikin su,sun sami nasarar haƙewa matan a yayin da ake ta gumurzu da wasu. Muksfyyh ta dawo gadon ta,gardi ta gani tsaye ƙerere yana ta haɗiyar miyau muƙut,muƙut. Muksfyyh ta ƙare masa kallo daga sama har ƙasa sannan tace, Mal.Lafiya?kazo ka tsaya a gaba na ƙaton gardi da kai,kai ni ba matarka ba ba ba ƴar ka ba ba wani ɗan uwana ba why not da ba zaka tafi wajen jinsin ka ba? Murmushi yai ya dubi Mkshfyy yace ''To da farko dai sunana Sadik ba Mal.Ba ni ɗane wajen Sarkin zazzau. Amma a halin yanzu ni Bawa ne a BAƘAR MASARAUTA tamkar dai yacce kema kike baiwa. A halin yanzu dai ke baiwa ce a Bakar masarauta tamkar yadda nake bawa. Kuma baki da yanci,tamkar yadda ban da yanci,saboda haka nazo ne a domin aiwatar da buƙatar sarki safwan. Ma'a na nazo da nufin yi miki ciki domin mu haifi ɗa a baiwa dodo tamkar dai yadda Sarki Safwan ya buƙata. Dafe kai Muksfyy tayi ta dubi shi . ''Ni? "Yes of course. Hawan gadon yai ya na ƙoƙarin ɗora hannunsa jikin Mkshfyyh. A ɓangaren su Jamila ma hakan ce ke faruwa ɗakin duk ya kaure da hayani ,da koke koke tofa. WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari] page 34-35. Zaro ido Mukashifyyah tayi tare da jawo kwalar rigar sadik,abunka da kodaɗɗitar riga ta daɗe da tsofewa, tuni ta yage. ƙarfinta tasa duka, ta ɗaga shi sama ta wulwula shi ƙasa. bata ƙyalesa ba,duka ta dinga kai mishi ta ko ina, dik inda ta samu duka take baji ba gani,har sai da ta fitar mishi da jini tukunnan ta ƙyalesa ya tashi daƙyar yabar wajen. A ƙule Mukashifiyyah take ranta yai mugun ɓaci da wannan al-amari. Jamila kuwa ƙarfe ta samu ta soke nata ƙwarton a ido,wata iriyar razananniyar ƙara ya saki da ƙarfi. Da dama daga cikinsu kwankwance suke cikin jini an musu fyaɗe na wulaƙanci,Allah sarki duk ƴaƴan sarakuna masu gata. ***** Washe gari dattaijan dake girki,a wajen sun girka,su kuma duk dattijiyar da ke wajen Matan sarakuna ne sarki Safwan ke satowa kowacce da aikinta,anya kuwa kun taɓa jin labari irin na sarki Safwan? me mulki makamancin na fir'auna. Ka'idar kunun ko suga babu haka suke shansa shekara da shekaru. To washe garin da Abun ya faru babu wacce ta iya shan kunun domin kuwa ba abincine kaɗai maganin yunwa ba. Ɓacin rai da damuwa na magance matsalar yunwa. + *** Da Jamila da Mukashifiyya ne zaune suna tattauna ysdda suka wanzu a daren jiya. Jamila tace,Mukashifiya wai kamata ƴar sarki me gata me bayi,aikin komai a gida yau nice Sarki,Safwan ya mayar ƙasƙantaciyyar baiwa? Yanzu haka zamu ci gaba da wannan baƙar rayuwar? ''Ni shawara ta ita ce mu nemo hanyar guduwa daga wannan muguwar rayuwar. Mukashifiyya ta zaro ido,Jamila anya kina da hankali kuwa,kinsan waye Sarki safwan? ''To bara kiji gidan nan kewaye yake da baƙaƙen,sheɗanun al-janu. Duk duniya bamu da gata sai Allahn da ya halicce mu,shine gatanmu kuma shine kaɗai zai iya cire mu daga wannan ƙuncin da muke ciki. Mutum bazai iya kawar da zaluncinsa ba face Allah domin shine mamallakin kowa. Jamila tace duk zaluncinsa yakai fir'auna? Mukashifiyya tace. Ko kwatarsa bai kai ba,amma kinga lokaci ɗaya Annabi musa ya gama dashi. Wannan haka ne kamar wasa yake ganin Annabi musa an haifeshi a tafin hannunsa amma gashi,shi Allah ya aiko ya kawo ƙarshen zaluncinsa. Mukashifiyya ta dubi Jamila tana murmushi tace.Kin ganni nan ko? Insha Allah nice zan kawo ƙarshen sarki safwan. Zaro ido Jamila tayi kana tace. Kamar yaya,ta wacce hanya? Mukashifiyya kin ƙi kiban labarin ki,kaman baki yarda dani ba? murmushi ta kuma yi kafin tace''Kin dai san duk gidan nan bani da aminiya kamarki ki, jira lokaci insha Allahu WATA RANA DA DADDARE Zan sanar miki ko ni wacce ce, UKUN DARE zaki san sirrin Sarki Safwan. **** Kusan ko wanne DARE hakan ce ke faruwa haka ake wannan gumurzu. tsakanin MATA DA KUMA MAZA. kuma kullum wa'inda akewa fyaḍe daɗa yawa suke.abin babu ƙyawun gani. Sati ɗaya da fara wannan mugun baƙin zalunci,aka kuma sake sanarwa Sarki yanan tafe. Kowa yasan ka'idar sarki baya zuwa ɓangaren bayi,amma da yake Safwan ɗan iskan sarki ne shi yana zuwa,musamman idan zai aiwatar da baƙin zaluncinsa. Jejjere bayin suke kowacce ta sunkuyar da kai ƙasa, kuma babbar dokarsa duk baiwar da ta sake ta haɗa ido dashi,to hukuncinta shine za'a ƙwaƙwle mata,ido ba kuma za'a kashe ta ba,da dama maxa da mata akwai makafi badon Allah yayo su haka ba, mugun baƙin zaluncin Sarki Safwan ya maida su makafin ƙarfi da yaji. a halin ynzu suna zaune a matsayin mkafi. Cikin fushi ya ɗaga murya,yau da kanshe yake bayani a fusace. Daga cikin ku wacce ce taƙi bin umarni na? Juyowa yai wajen mazan yace. Kowanne ya tashi ya fito min da duk wacce taƙi bashi haɗin kai. Kowa yasan doka da nasa maza da mata domin ina buƙatar jarirai ƙanana domin a baiwa dodon tsafi. Kowa a cikin ku yasanni. Nine Sarki Safwan wanda na SIYAR DA LAHIRA NA SIYO DUNIYA. To idan banyi yarda naga dama ba a duniya me zanyi? dole nayi yadda naga dama a duniyata,kunsan banda tausayi,kuma bansanshi ba,banda ɗigon imani (waiyazubillah ) don haka duk cikinn ku babu wacce nake tausayi. don haka zan yanke hukunci a bisa zalunci na,hukuncin duk wacce taƙi bada haɗin kai shine za'a yanke mata matancinta. Ma'ana gaban za'a yanke sai ta zama marar amfani,karkuma wacce tayi min magiya,duk wacce ta buɗe baki tayi magana kuwa hukuncin ta za'a datse mata harshe. Mazan ku fito ku zaƙulosu. Ɗaya bayan ɗaya suka dinga fitowa suna nuna ana ɗaukowa a gaban sarki Safwan wanda ke zaune hakimce dariya kurum yake ƙyaƙyatawa....... Sai da aka zaƙulo mace takwas. sannan Sarki Safwan yace to a yanzu ni zanyi muku fyaɗe kuma bayan na gama a yanke muku gaba. Hakan ce kuwa ta faru duk sai da yai musu fyaɗe ɗaya bayan ɗaya kowacce ya yanke mata gaba,kuma gaba ɗsya kowaccensu a some suke,babu wacce ke motsi. Cikion ta tara Jamila ce koda Mukashifiyya taga an kira Jamila a ta tara ita kuma Mukashifiyya ita ce ta goma. Amma taga Sadik bai nunata ba. ''Shin meye dalilin sa na ƙin kiran Ta? har an kwantar da Jamila za'a yanke mata matancin ta, tunanin Mukashifiyya ya dawo jikinta.... .....Anya kuwa akwai azzalumin sarki irin Safwan. Mu haɗu a nex page. WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari] page 36-37. An an zindire Jamila za'a yanke ta Tunanin Mukashifiyyh ya dawo jikinta. An ɗora kaifaffiyar wuƙa ana shirin kashe mata rayuwa. Mukashifiyya tazo gabansa ta tsaya tace. Tace ''Ran Sarki ya daɗe! ''Azzalumin sarki me cikakken iko,wanda baida tausayi bare imani. Sai kayi Sarkin da babu irinsa,sai kayi sarkin da mulkinsa zallar zaluncine. ''Ranka ya daɗe zanyi tuni matsayina na wulaƙantacciyar baiwa. Da farko kace Jinsi ma zai iya kusantar jinsinsa. To ni da wannn baiwa taka kullum muna biyawa junanmu buƙata. a matsayin mu da mace da mace.. Hhhhhhhhhhh ɓgɓgɓgɓgɓgɓg. Haka ya saki baki yai da babbaƙar inda yake cewa ''Ke wannan wulaƙantaccitar baiwa a ina kika san kirarin nan mai daɗi,wanda ya saka ni jin shauƙi,da annushuwa gaskiya kece baiwar farko a wanzuwar mulkinmu da kika taɓa faranta wa Sarki Safwan rai. Ɗago ido ki dube ni. Mukashifiyya ta ɗago ta kallesa, amma a zahiri bashi ne wanda take kallo ba,Haidar ɗan'uwanta take kallo shima sai taga ita yake kallo. Bawan Allah ɗan'uwa kenan rabin jiki,ƙwallah ta hango a idon Haidar,wanda ita ma hawayen ne,suka zubo mata sai tayi ƙoƙarin gogewa don kar Azzalumin sarki yaji. Ku saki ƴaruwar tata abokiyar masha'arta. ''Naji daɗi sosai da kuka kasance bayi masu son faranta mini masu biyyah da bin umarni na,saboda haka daga yau bana so kowaccen ku ta kuma aikata abu me kyau a masarautata. Na yarda da ZINA LASS tsakanin mace da mace.LUWAƊI tsakanin namiji da namiji. (wai'yazu billah) duk wani abu na saɓo shi nake son ku da ku aikata,banaso kowannen ku ya aikata abu me kyuau. Wannan zai sa sheɗanun Al-jannu su ƙara haska sarautata,mulkina zai yaɗu duk duniya sai na zama gawurtaccen sarkin da babu kamata a doron duniya. Sai na zama gagara badau a wannan duniya. Ku sake wannan Baiwa. Jamila ta sauke wata gawurtacciyar ajiyar zuciya me ƙarfi. idon ta duk ya ɗashe saboda kuka. Wata zazzaƙar murya yaji ta karaɗe tana mishi kirari. *Sai kayi azzalumin sarki me mulkin baƙar masarauta.* *Ka zama ƙarfen ƙafa me wuyar cirewa.* *murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya* *kabewar kan kabari baƙin cikin me taushe* *dakalin majina a hauka a silɓe ka hau mutum ka zauna daidai* *baƙin sarki, mugun sarki, kai baƙi, mulkinka baƙi,zuciya baƙa,sarautarka baƙa,gidanka baƙi,tambarin sarauta baƙi* *baƙi,baƙi,fentin Allah fentin da ba'a sawa burish* *duniya aka zaɓa kuma an samu kai yadda kake so duniya taka ce* *An ƙwaci mulki da ƙarfin zalunci* Wata iriyar muguwar dariya sarki safwan ke ƙyaƙyatawa tamkar bazai daina ba. Sai da yai ta ishe shi. Kana ya dubi Mukashifiyya yace. ''Ke wannan baiwa ina kikasan kirarina? gaskiya kin faranta min. Don haka zan kai ki ɗaki na musamman kiɗan huta na wucin gadi kiji daɗin duniya na wucin gadi. Sannan zan ƴanta ki daga baiwa,amma na ɗan lokaci. To daga nan labarinki zai soma wata kil bayan babu ke,albarkacin wannan kirarin zansa a sassaƙa gunki me siffarki matsayinki na baiwar da ta taɓa faranta ran Sarki. To bayan haka kinsan ni bana saka Al-khari da Al-khari haka doka ta take duk wanda yai min sharri,to zan linka mishi sharrinshi,wanda yai min all'khari zan saka mishi da sharri. Saboda haka saka makon ki shine shekarar da zata zo kece wacce DODON TSAFI ZAI SHA JININTA,a matsayinki na wacce kika faranta mini. Wannan shine sakamako na na MULKIN ZALUNCI Irin nawa. Daram! dam! ƙirjin Mukashifiyya da duk wani mai sonta ya bada. Tofa. ***** Kai tsaye gidan mai gari Mal.Kabir ya dosa. cigiyar gida ya bayar. Ba jimawa a ka samar musu gida lafiyyayye. Da yake akwai wadatatattun kuɗi a jikinsu. Duk sallamar aikin ce domin kuwa babu abunda suke siye a gidan Alh.Bashir komai ya wadace su. Ta ɓangaren Mariya kam sai cika take tana batsewa,da zarar ta haɗa ido da Azlafiyyah zata gaura mata harara. Azkfyyh bata ce uffan ba,tana da zafin zuciya sosai bata san raini. Amma dole ta zubawa Mariya ido domin kuwa har yau da wannan sirri ya fallasu kallon uwa takewa Mariya. Bayan sunci sun ƙoshi Mariya tace. To ka bamu labarin Waccece Azkfyyh? Mal.Kabir yace labarinta ba zai faɗu ba sai DARE ya raba. ''Wannan wanne kalar mugin baƙin labarine da bazai faɗu ba sai DA DADDARE? **** DARE YA raba Mal.Kabir ya tashi Mariya da Azkafiyya. A zabire Mariya ta miƙe tana rarraba ido tace. ''Tun ɗazun nake tambayar ka wannan wanne mugun labari ne da baza'a faɗe shi ba sai DARE ya raba,daga ji dai wannan yarinyar irin aljanu ce ko kuma wasu miyagun daban? Mal.Kabir yace yanzu kam zan amsa miki,dalilin da yasa ba'a ambatar Labarin sai DADDARE,miyagun mutane da suka yi wa labarin dabaibayi,ba Azkafiyya ba ko wani nata, Ba'a ambatar su da rana saboda da rana idon su suna jin me ake cewa amma idan DARE,YA raba suna chan suna aikata mugun aikin da ba ta wane suke ba,koda ka ambace su ba zasu ji ba saboda ba takai suke ba. TSAKIYAR DARE shine ranar su rana Tsaka kuma shine DAREN SU. WATA RANA DA DADDARE🖤* _(horror story)☠️_ Written by Aishat Abdul-falalu Rimin k'aura (Mmn Humaira) The writer of: *Ishara.* *So ko hauka.* *Shagaltattun duniya* *And now WATA RANA DA DADDARE* *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amala tagari] page 38-39. free page na gab...... wannan ne qarshen free page. Yanzu zamu shiga kaɗan daga paid booK. Kuka Abbu ya fashe dashi,kana ya ɗora kansa a jikin gawar Muhijjinatu yace. ''Dole ne nima na kashe kaina,banga amfanin rayuwata ba muddin babu ke Muhijjinatu. Dariyar bakin al-jani ta katse sa,ɗagowa yai ya zubawa bakin al-jani ido kana yace. ''Meye ya kawo ka wajena,kunyi silar rabani da dukkan farin cikin rayuwa ta,na haƙura da duk wani jin daɗi banda kowa banda komai sai Muhijjinatu to ita ma ɗin kun kashe min ita.Yanzu ni kaɗai na rage banda kowa banda komai to ku kashe ni nima. Muddin baku kashe ni ba ni zan kashe kaina. Baƙin al-jani yace ''Ba cutar da kai nazo yi ba,nazo a domin na taimaka maka,domin Sarki Safwan yaci amana ta shi yasa nake so na rama,na duba naga babu ta hanyar da zan rama sai na ga ta hanyar ka kaɗai ne,nazo na taimake ka akan ƴarka Muhijjinatu da Safwan ya kashe. ''Kai munafuki ne bazan yarda da kai ba. Baƙin al-jani ya fashe da kuka sosai,yana duban Abbu. Yace Abdullahi ka yarda dani,Abbu yace tayaya? Baƙin aljani yace Muddin ka yarda da sharaɗina to ni kuma zan taimake ka. Zuciyar Abbu ta soma tafarfasa ya duba yaga Muhijjinatu rungume a matsayin gawa to me zaiyi baya ga ya yarda kawai. Tabbas Safwan shine ya kashe Muhijjinatu,domin koda tazo mutuwa sunanshi ta ambata. Ya kasheta ya kashe mahaifiyarta shi kaɗai ya rage a wannan duniyar.... Muhijjinatu ta mutu!" kodai mafarkine. Meye sharaɗin.? ********** MALLAM Abdurahn ya ciga da cewa yana duban Azkafiyyah. Ba zaku iya cin galaba akan Safwan da sheɗanun aljanu shi ba,sai kun nemi ilimi Al-qur'ani,ALQur'ani shi kaɗai zai iya yaƙar Safwan. Kuma babbar matsalar ma sai kun haɗu ku duka ƴaƴan Sarki Abdullah. Mukashifiyya tana da ilimi sosai,Haidar ma haka,ke kuma kina cikin nema,ƙatotuwar matsalar ita ce ƴar ƙaramar ƙanwarku MUHIJJINATU,baƙaƙen sheɗanu sun yaudareta da nufin taimako ahalin yanzu ta zama babbar SHEƊANIYA KUMA HORRANYA* **** ABBU ka daina sona ne? Abbu domme zaka ɗaɗɗaure ni kamar wata .dabba ko ka daina sona? sai ta fashe da kuka wiwi. Tausayinta ya kamashi,kuma yaji farin cikin samun Muhijjinatun shi a hayyacinta. Abinda bai taɓa gani ba tinda lalurar ta sameta. Kukanta yana damunshi,aransa yana jin wani maƙoƙo. To Amma kuma wannan hukuncin na ɗaureta a keji shine dai-dai da ita. Ko dai ya buɗeta,wata kil ma ta samu lafiya. To Amma kuma yasan yaudara irinta BAƘIN SHEƊANI,tamkar dai yadda ita ma suka mayarda ita BAƘAR SHEƊANIYAR. domin a halin yanzu tana cikin sarrafawar Sarki Safwan da kuma baƙin al-jani. Zama yai kusa da kejin ya kira sunanta ''MUHIJJINATU! har yanzu kukan take batare da ta amsa kiran da yai mata ba. Ki ɗago kanki ki dube ni,ya faɗa cikin rarrashi. ɗagowa tayi a hankali ta zuba mishi idonta wanda ya ɗashe da kuka yai ficifici.. Ƙur! ya zuba mata ido yana me binta da kallo sai yaga idonta lafiyar Allah sak! kalar na Muhijjinatunshi,ba na HORANYA BA! ''Yace Muhijjinatu ban daina sonki ba,duk duniya babu wanda nake so da ƙauna kamarki,ki sani cewa A duniya Soyyaayyahr gaskiya biyu daga iyaye sai ƴaƴa a halin yanzu banda uwa da uba,bani da wani ɗa a duniya da ya ragemin face ke. Don haka soyyayyah ta duka duniya na sadaukar da ita kacakon gareki Muhijjinatu. ''Wannan hali da muka riski kammu a ciki ni dake jarabtarmu ce a haka domin kafin mu Allah ya jarrabi Annabawan da sahabbai. Kiyi haƙuri da sannu Allah (s.w.a)zai dube mu ya kawo.Mana mafita. Kuka tasa da ƙarfi tana birgima. To nidai Abbu ka daina sona kwata kwata inda kana sona bazaka kawoni wulaƙantaccen wuri irin wannan ba. ''A duniya wanne uba ne zai wa ɗan cikinsa haka? "Abbu wanne laifin na aikata da na chanchanci wannan hukuncin?" ido ya zuba mata. ''Muhijjinatu kalli ƙwayar ido na. Bata dubeshi ba yaci gaba da cewa. ''Ina sonki Muhijjinatu wannan abu da nayi miki gata ne. Yanzu karɓi kifinnan kici kinji. To idan baki karɓa ba zan haƙura dake Muhijjinatu. Haƙuri na har abada tunda yanzu kin daina yarda dani,bakyajin maganata. Cikin fushi ya juya yabar wajen. ''Abbu ta kirasa da ƙarfi. Cak! ya tsaya batare da yace uffan ba. ''Abbu nasan ba zaka cutar dani ba. Hannu ta miƙa tana nufin ya miƙo mata gasasshen kifin. Wani daɗi yaji aransa ya juya. Ɗurƙusawa yai ya zira hannu ta ƙofar kejin tare da miƙa mata. yana hawaye saboda tausayin halin da Ƴar tasa take ciki. ''Koke fa Muhijinatu,karɓi kici....... Bai ƙarasa ba sakamakon wani mugun zafi da raɗaɗi da ƙuna da yaji ya soke shi tin daga tsakiyar kansa har ƙafarsa. Muhijjinatu ce ta cafko mishi hannu da zureren hannuta da ya kusa kai tsayin fall waya,ba ma wannan ke abin jin ba,illah zaƙo,zaƙon faracenta musu mugun kaifi kaman reza. A wannan karon idonta kala biyu ya koma jajawur da kuma kore shar! ''Zaka fito damu koko? wata mummunar murya,tamkar ba muryar Muhijjinatunshi ba,wannan ai muryar SHEƊANUN ALJANUN DAKE sarrafata ne. To Amma kuma daga gareta maganar ke fitowa. Ka fito damu,aka kuma faɗa a karo na biyu. Shi dai mugun raɗaɗin da yake ji daga kowanne sashe na jikinsa ya ishe shi. Cikin sauri Abbu ya soma addu'a. ''A uzu bikalimatillahi tahmati min sharri ma kalaqa. Wassafati ƙafa 5 baqara ƙafa 5. yana cikin rera karatun duk ta saki wata muguwar ƙara ihu take,sosai kukanta duk ya gareme dajin gaba ɗaya. Hannunta ya koma yadda yake ada ta saki hannun Abbu. Sharaf ta kwanta cikin kejin ta soma barci. Dafe kai yai yana karanta Allahumma ajirnifimusibati wakhalifnii khairan minha. ********** TSAKAR DARE. Abbu yana ɗurkushe gaban ubangiji yana ta nafilfilinsa. Wata iriyar baƙar guguwa ta taso. Irin baƙar guguwar da ta saba tasowa a Duk DAREN da Sarki Safwan ya aiko a tafiyan mishi da Muhijjinatu. Salamce sallar keda wuya. Abbu yace yau dai komi zai faru sai dai ya faru domin bazai bari a tafiyan mishi da Muhijjinatu ba. Tsaye yake saman iska da ƙaton kanshi kwarangwal. Zureren hannunshi ya zira a jkin kejin da Muhijjinatu take. Cikin sauri Abbbu ya ɗauko koko da ruwa a ciki,wanda addu'oi' ne wa'inda ya karanta ya tottofa kafin ya soma sallah. Koda zura hannunshi da nufin ɗauko Muhijjinatu wacce ke kwance tana ta faman barci, Abbu ya watsa masa ruwan tofin a zureren hannun da ya zira. Wata iriyar mummunar ƙara ya ƙwartsa. Hatta namun dajin dake cikin dajin da gudu suka sheƙa dawa suna iface,iface. Abbu ya matsa kusa da ita ya shafa kwantaccen gashinta da yai luf,barci kurum take sosai. Hannu ya ɗaga ya soma yiwa ubangiji godiya da sunayen da yafi so. ''Ya Allahu,Ya rahmanu. ''Ya hayyu ya ƙayyumu bi rahmati ka astagisu. ''Ya badi'ussamawati,walardi ya zulzulalu wal ikiram..... ''Shin Abbu da Muhijjinatu zasu dawo rayuwa cikin gari koko, zasu dawwama A DOKAR DAJI har k'arshen rayuwarsu. ''Yaushe Bilal zai bayyaha? ''INA LABARIN SARKI SAFWAN. Ina labarin Mukasshifiyyah Azkafiyyh Haidar??? "Shin sarki Abdullahi zai sake had'uwa da ƴaƴansa ? Mallan Abdurrahmsn yace Qarshen zaluncin sfwan bazai zo ƙarshe ba har sai yaran sarki Abbullahi sun haɗu su huɗu. Ɗaya tana DOKAR DAJI,MATSAYIN BAƘR SHEƊANIYA,KUMA HORANYA. Ɗaya TANA WANI ƘAUYE TARE DA ME GADIN GIDAN ALH.Bashir. ƊAYA TANA GIDAN SARKI SAFWAN A MATSAYIN BAIWA ƘASƘNTACCIYA. Namijin kuma ya kamu da lalurar rashin magana,shin yaya za'ai su haɗu???? Ina labarin Farida Alh.bashir??? wannan duk amsar na cikin paid book. 2-3-4. ga duk wanda ya shirYa biya zamu buḍe paid group inda zamu dinga tura page 2 a rana kuma dogon shafi. 400kacal👌👌👌 ta wannan Account ɗin. Aisha Abdullahi fcmb. Shedar biya. 9187153012 07049138863. a domin jin badaklar da ke cikin wannan chskwalkwalallen labarin da kuma hanyar warwareshi. Nagode da bibiyata da kukayi har na kawo qarshen book1 Allah y bada ikon biya.