*SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION                      *001* Lumshe idanunshi yake yana shaƙar sassanyar iskar dake kaɗawa a harabar ƙaton gidan a hankali yake jan tsaki ƙasa ƙasa yana sake duba agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannun  shi ya kai mintina goma a zaune babu alamun zata zo, tsaki yaja a karo na barka tai gaba ɗaya ranshi ya gama ɓaci a duniya idan da abin da ya tsana shine jira Kasancewar shi mutum mai kazar kazar da zafin nama, marar haƙuri da ɗaukar raini Zuciyarshi ce take zafi nan da nan idanunshi yayi jajir Gumi na yanko masa daga saman goshin sa ƙurawa hanyarta idanu yayi har ya tashi ze bar wajan ƙamshin turarenta yayi masa sallama tun kafin ta ƙaraso wajan ƙamshin haɗaɗɗan turarenta ya gama cika wajan. Tafiya take kamar ba zata taka ƙasa ba, cikakkiyar Budurwa ce Ƴar Gajera  baƙa mai jiki, baƙinta irin mai ƙyallin nan ne dan irin sune ko man saka haske suka shafa ba lallai ya amshi fatar suba amman da yake akwai hutu da jin daɗi a tare da ita se Baƙin nata ya murje ya ƙara mata ɗan karan kyau. Babu wani abu a fuskarta mai haske se fararen idanunta waɗanda baƙa ƙirin ɗin ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata idanun nata Zanan idanun nata kuma se yayi kamar ta shafa kwalli daga saman hancinta kuma gumi ne wanda ze tabbatar maka da ita ɗin babu sauƙi mafaɗaciya ce bata wasa ba, tana tafe tana huci harta ƙaraso inda yake.         Ƙerere ta tsaya a saman kanshi tana karkaɗa jikinta ta saka hannu ta kama ƙugunta, Nuna wa yayi kamar bai san da wanzuwarta a wajan ba, wanda hakan seya ƙara tunzura zuciyarta wannan wani irin ƙasƙanci Abbanta yake son yayi mata duk faɗin samarin ta babu wanda Abbanta zece ta aura se wannan gajan kuma yaro ƙarami wanda bai fi sa'an haihuwar ta ba dan bata jin zai girme mata, tun jiya take son fahimtar da Abban ta cewar ita fa tana da wanda take so yake son ta amman yaƙi sauraren ta akan wannan kucakin, Tun da take da Abbah bai taɓa Yi mata faɗa kamar na jiya ba kuma duk silar zuwan wannan yaron da Baban Chiranchi Ya turo wai ya aure ta Tsaki taja acikin zuciyarta tana kau da tunanin Ɓacin ran da suka kwasa jiya ita da Momi Mahaifiyarta akan zuwan wannan ƙolon. Jitai zuciyarta na ingizata akan ta gargasa masa baƙaƙen maganganun da zai ji haushi Ya ƙi dawowa. Saadik wayar shi ya ciro ya kunna data ya shiga facebook ya na duba posting ɗin jama'a gaba ɗaya ya shagala ya ma mance da ƴar rainin hankalin yarinyar dake gabanshi wadda taci albarkacin Mahaifin shi wanda umarnin shi ma yabi har yazo wajanta dan shi ne ya tursasa shi akan sai lallai yazo ya nemi auren ƴar ƙanin nashi ko Allah yasa ta silar hakan zumuncin su ya ƙara ƙarfi. Bai taɓa zuwa gidan Kawun  nashi da girman shi ba, se yau hasalima ita yarinyar da aka turo shi wajanta bai ko taɓa saninta ba bare yasan sunanta duka se yau ɗin da yazo gidan bisa tirsasawa da bin umarnin mahaifan shi. Takaicin yarfin daya mata ne ya fusata ta cikin zafin zuciya ta miƙa hannu ta warce wayar hannun nashi tai wurgi da ita jikin ginin dake kallon su kafin ta soma magana a zafafe! "Aikin banza aikin wofi an gaya maka talaka yana da alfarmar wulaƙanta mai kuɗi kai ɗan gidan uban waye! da zaka....... Bata ƙarasa faɗin maganar ba tai saurin faɗuwa a wajan tai zaman ƴan bori hannu biyu ta sa tana dafe kuncin ta sabida azababbiyar gilmawar wutar data gani a cikin idanunta. Ba kuma wutar bace zafin Hannun Saadik! Ne ya gigita ta, Akanta ya tsaya yana huci bayan ya ƙarasa sauke mata marika har guda uku a jere Huci ya saki mai zafi yana Naushin Iska Allah ya bashi zafin rai na masifa sam baya ɗaukar raini baya son wasa shiyasa ko acikin gidansu Yara na shiga hankalin su in suka jiyo muryar shi kai babban ma idan Saadik ya rikice masa shiga hankalin sa yake. Cikin dakakkiyar Muryar shi wadda ta ratsa dodon kunnenta ta kuma hautsina mata ƴaƴan hanjinta yace mata. "Wuce kije ki tattara min wayata banza shasha sha ballagazar mace"! Kuka take Tuni Kuncinta ya haye kuma taƙi koda motsi a wajan sabida masifar kafiyar ta. Tsaki yaja cike da fushi ya wuce fuww yabar mata wayar batare daya haɗa wayar tashi ba,bare ya ɗauka, sabida yana jin idan har ya tsaya a wajan ze ɓallata ɓallin masifa wannan tasa yayi gaggawar barin Gidan. Ta ka ƙasa yake kamar ze tsaga ta tsananin zafin zuciyarsa tasa har numfashinsa na ƙoƙarin barin gangar Jikinsa. Daga gadon ƙaya zuwa ɗorayi Chiranchi da ƙafa yaje gida Yana shiga Ɗakinsa dake soron gidan ya shige tare da faɗawa saman katifa yana lumshe ido hoton fuskarta yake gani acikin idanunshi gaba ɗaya haushi da tsanarta na mamaye zuciyar sa, sam baya son mutum mai izgili da girman kai, baya son mutum mai wulaƙanta mutane, domin baka san baiwar da Allah yayi wa kowa ba. Anya zai iya bin umarnin Baba? shi kam yana jin yafi ƙarfin mace ta wulaƙanta shi duk kuɗinta duk mulkinta domin bai nema daga wajanta ba, Shi talaka ne amman mai zuciyar nema domin ta ko ina Allah bai kassara shiba ya bashi rai da lafiya da dakakkiyar zuciyar neman halak ɗinsa uwa uba wadatar zuci wadda yake jin in mace huɗu ya aura zai iya ciyar da ita da halalin sa. Mirginawa yayi tare da miƙewa, ya fita cikin gidansu bakin Rijiya ya tsaya zai ɗebi ruwa a bokitin daya riƙo don ya watsa a jikinsa sabida Zafin ranar da ake tsulawa a garin. "Kawu Saadik kawo na zuba maka ruwan" Inji Khadija ɗaya daga cikin Jikokin gidan nasu waɗanda Innar shi ke riƙewa a wajanta. Fuska babu walwala ya miƙa mata Bokitin ta cika masa shi da ruwa ya ɗauka ya koma cikin ɗakin shi ya shigar banɗaki ya watsa a jikinshi ya fito Farin yadi marar nauyi ya saka ya fesa turare mai sanyin ƙamshi ya fita zuwa cikin Gidansu sai Lokacin yaji zuciyar shi na masa sassauci na daga Ƙuncin daya kwaso Innah na tsige zogale Zarah na gefenta nashan Koko. Da gudu ta aje kofin tazo Jikin shi ta ɗane shi ta hau yi mashi surutu. "Kawu Saadik Innah tace dambu zatai mana, Kuma Ɗazu Baba yace kaje wajan Matarka wai aure zaka yi?" Murmushi ya yi kaɗan tare da shafa kanta. "Zarahh Sarkin surutu mai shan koko da rana" Sai Lokacin Innah tayi magana. "To ya za'ai kasan Rigimar Mutuniyar taka nayi ranar abincin ne yau wai Ummi na aika kai ɓarzar tsakin masara Wallahi tafi awa biyu nace Nanah ta bita itama shuru, Ita kuma wannan sarkin cin se kuka take yi shiyasa na bata sauran Kokon Babanku" Matsowa yayi ya zira hannu cikin zogalan yana tayata Aikin zagewa. Batare daya ce komai ba. "Wai yaya kukai da Gidan Kawun naka?" Cewar Innah. Cikin son ya basar da maganar dan tina wa ma ɓata Masa rai yake, Ya ɗan langwaɓe kaɗan tare da cewa. "Innah nima fa yunwar nake ji, amman zan fita shago In kika gama ki bawa wani ya kawo Min" Sarai tasan dan ya basar da maganar ne, Setai murmushi ta shiga yi masa fatan dawowa lafiya zarah na bashi saƙon abin da zai tawo mata dashi yana Murmushi yana amsawa har ya bar Gidan. Ido jajir ta faɗa cikin katafaren falon gidan nasu wanda ya kusa girman wani gidan ihun ta har cikin ɗakin baccin momi wadda ta fito a guje dan masifar sauri zaninta har kunce wa yake yi a gigice ta nufi wajan Yarinyar tata Ƴa ɗaya tamkar da Goma kenan Ƴar gata dangin kitse a barka a inuwa ka daskare a saka ka a rana ka narke, Cikin tattali da Riritawa tamkar tsoka ɗaya a miya ta Rungumeta duk a kiɗime take mata magana. "Babyn momi waya taɓa min ke kika shigo kina kuka kin san yadda kukan ki yake ɗaga min hankalina wallahi kaina har juya mini yake sabida azabar faɗuwar gaban da kukan ki ya haifa mini" Shure ƙafafunta take tana ƙara sautin kukan tana janyo hannun Momi zuwa fuskarta Jikin Momi ne ya hau rawa sakamakon shatin yatsun data gani kwance a kunci shalelen tata a zabure tace. "Kan uba waya miki wannan illar lallai ya tafka ganganci domin zanyi shari'a da kowa ye sannan kuma zan ɗaure kaf ahalin su har igiya tayi rata dan uban sa!" Sangartaccen kuka ta kuma saki lokacin Momi ta zauna ta ɗorata a kan cinyarta In kaga yadda sukai zaman seka yi dariya sabida ita aba ƙatuwa an tashi an ɗora ki a saman cinya ko Kunyar hawa ita kuma bata jiba. Cikin siririyar muryarta wadda in kaji ta seka rantse bata ta bace domin muryar irin ta ƙananun yara ce, Tace. "Ba wannan gaulan da Abbah ya turo bane ya mare ni dan cin zali ban masa komai ba" Tunkuɗe ta momi tayi ta tashi a zabure tana sintiri a falon Fuskarta fal bala'i wanda ta hau surfashi har seda muryarta ta dashe. "Dama nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, Mai talaka ya sani akan mace face ya mai da ita baiwar sa wato shi dan ubansa har wuyan sa yayi kaurin da zai mareki an gaya masa bakin rijiya wajan wasan makahone to aikuwa zan tauna tsakuwa don aya taji tsoro sabida wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa" Gaba ɗaya kalamin Momi sun sanyata acikin duhu don waɗannan karin maganar bata sansu ba bata iya suba seta zubawa Momi idanunta da suka kumbura suka ƙara girma sabida kuka. A sassauce momi ta dawo gareta ta sunkuya gabanta haɗi da dafa gwiwowin ta kana tace mata. "Shalele na kwantar da hankalin ki babu wani ɗan iska faƙirin talakan da za'a aura Miki ni za'a wa tawaye rabu dani da Abban ki yadda Allah ya bani ke ƙwaya ɗaya tal wallahi ba zan yadda rayuwarki ta salwance, a gidan talaka ba, ai se duniya ma tai min dariya ƴaƴan aminaina daga mai auren Ƙusan gwamnati sai mai auren ɗan kasuwa shahararre sannan ni tawa ta auri ɗan jagaliya talakan banza ina sam sai dai in ba ni maryam bace na haife ki" Kwantar da kanta tayi a cinyar momi tana jan ajiyar zuciya. kafin tace. "Momi in kika min haka zan ƙara alfahari dake, wallahi Ina da wanda nake so Habib yana sona ina sonshi Ɗan ajinmu ne tare muke lecture da shi baban shi mai kuɗi ne Tun tuni yake son na bashi dama amman naƙi gashi nan Abbah yayi min shigar sauri kuma ba kowa bane zai zuga Abba se Baban Chiranchi dama kince ba ƙaunarki yake yi ba" Hura hanci Hajiya Maryam take tana kaɗa ƙafafu ita kaɗai tasan tawayen da zata wa Alhaji Amadu Mijinta in ya dawo Jira kawai take ya shigo gidan ba zata tsaya ayi mata sakiyar da babu ruwa ba. Tashi tayi daga jikin Momi ta nufi bedroom ɗinta Yadda ta bincike Wardrobe ɗinta ɗazu haka tazo ta tarar da ita bayan kafin ta fita seda ta cewa Maimuna Mai aikinta wadda aikinta agidan shine gyara mata ɗakinta da kuma bata abinci da kai mata ruwan wanka ta gyara mata kayan kafin ta dawo amman shine bata gyara ba, Sabida haka Rigar jikinta ta cire ta janyo zani ta ɗaura ta fito falo tana kwaɗawa maimuna kira Lokacin Momi bata falon ta shige room ɗinta. Cikin tsumar Jiki maimuna ta ƙaraso gabanta ta zube tana cewa. "Ai mini afuwa uwar ɗakina banji kiran bane se yanzu" Tsaki taja mai ƙarfi tana zabgawa maimuna harara kafin tace mata. "Ai ba zaki ji kirana ba, Munafuka kina can kina kallo kamar wadda ta warke a makanta dan Ubanki ni zan gyara Miki ɗakin?" Nan da nan jikin maimuna ya hau rawa abin tausayi ta soma bata haƙuri, Tsaki taja ta wuce saman seater ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya. "Na baki Minti Biyar kije ki gyara Mini ɗakina sakarai" Da sauri maimuna ta wuce bedroom ɗin nata, Ita kuma zama tayi a falon tana karkaɗa ƙafa tana Ayyana Zafin shigar marin daya mata ɗazu Tsintar bakinta tayi da furta Allah Ya Isa! Muryar maimuna ce ta dawo da ita daga tunanin data faɗa. "Uwar ɗakina na kammala Allah ya huci zuciyarki" Bata ko kalli Maimunan ba ta miƙe ta shiga ɗakin kwanciya tayi akan gado tana janyo wayarta dake gefenta tarin Kira daga Saurayin ta Habib harda ɗan guntun saƙon shi Ƙorafi ne akan Yana ta kira bata ɗauka ba. Mayar da wayar tayi ta aje sam ita soyayya bata gabanta, duk da tana da masu sonta samari da masu aure masu kuɗin gaske kawai bata sauraron sune ta ɗan fi kula Habib shima tsananin nacin sa gare ta ne yasa take ɗan kula shi a waya da kuma in sun haɗu a school. Kiran nashi ne ya katse mata tunaninta. A hankali ta ɗauka kamar bata so. "Amincin Allah ya tabbata a gareki sabihata hasken idanuna my madarata" Haɗe ranta tayi sam kalamin bai wani ratsata ba meye wani madara dan iskanci itafa bata son irin haka ta lura yawanci maza jikinta suka fi so ba ita ba, dama Allah baya haɗa maka duka duk yadda takai da halinta ita ɗin ba mutuniyar banza bace tana da taka tsantsan wajan kare mutuncinta ta wannan fagen za'a iya bata lambar yabo ta ɗaya. "Sweet ina maki magana kin min shuru haba mana" Tashi tayi zaune tare da cewa. "Look Habibu nifa bana son wannan kashe murya da kake yi min ni ban maka shagwaɓa ba sai kai zaka yi min goɗai goɗai dakai haba mana" Daga ɓarin shi yaɗan zare ido Gabanshi ya faɗi, shifa wani bin har shakkar yarinyar yake ita ko ɗan feeling ɗinnan bata ji kamar wata dutse, Amman ba ze sare ba zai cigaba da lallaɓata har haƙon shi ya cimma ruwa dan shi kam ya kwaɗaitu da Yarinyar daga ganinta zatai ɗanɗano a matsayin sa na shahararran ɗan Duniya wanda yasan mace ciki da bai sabida yana da kuɗi mahaifinsa na sakar masa kuma yana da ɗaurin gindi wajan tsohon nasa shiyasa yake facakar sa yake hurɗa da duk maccen daya ke so. Ita kaɗai ce tai masa zarra duk wannan kwanton da yake mata Kansa yake wa tanadi amman yasha gwadata ta hanyoyi da dama ya gano zafin kai kawai gareta amman bata biyar mazan banza. Cikin ƙwarewa da harkar bariki yace. "To yi mini naji please zumana" Yadda ya fitar da sautin seda ya rikita ta matse Jiki tayi kamar mai jin sanyi kasancewarta mace mai tsananin buƙata wannan dalilin yasa take nesanta kanta da maza domin ta gano ba son ta suke ba Jikinta suke maitar so shiyasa take ƙaurace wa masu sonta domin ta kare martabarta. Muryarta a shaƙe tace. "Zanyi sallah Habib sai anjima" Murmushi ya saki daga jin muryar tata yasan ta kamu seya kuma jefa mata wata maganar wadda ta sanya ta saurin kashe wayar gaba ɗaya ta wurgata can ƙarshen gadonta, ta kama Lips ɗinta tana cijewa Idanunta lumshe tana Sakin zazzafan Numfashi kafin a hankali ta Miƙe ta shige toilet wanka tayi ta ɗauro alwala sai Lokacin ta sami damar sallar azahar ta haɗe da la'asar babu ko kunyar Ubangiji na haɗe sallolin data yi. Kallo ta kunna ko zai ɗebe mata kewa sabida jiyo sautin maganganu daga Room ɗin Momi tasan ƙawayen nata ne ƴan gado da suka saba cika masu gida kusan koda yaushe suna hanyar gidan nasu. Ko wacce matar wani ce don a ƴan group ɗin su momi babu matar talaka, dukkan su matan masu da shi ne. A wannan kallon ta lalace har akai magariba da ƙyar tai sallah ta cigaba da kallon nata, bata damu da karatu ba duk da suna exams sabida akwai wata ƙawarsu mai ƙoƙari da take taimakonsu. Su kuma suke bata kuɗi don ita ba ƴar masu kuɗi bace bayan sallar isha'i ta kashe kallon ta kunna wayarta ta kunna data ta shiga grp ɗinsu suka hau Hira da ƙawayenta. Kiran Abba ne ya shigo wayarta ya bata umarnin ta fito yana falo Hijabi ta sanya akan kayan baccin data saka ta fita falo  inda ta tarar da Momi da Abbah a zaune Momi se kaɗa ƙafa take tana hura hanci Shima Abbah babu walwala a fuskar shi kallo ɗaya tayi masa tai ƙasa da kanta domin yau babu wannan sassaucin da riritawar da yake yi mata. A ƙasa ta zauna tai ƙasa sosai da kanta kafin tace. "Abbah barka da dawowa gani" Da hannu ya amsa mata kafin ya gyara murya yace mata. "Rabi'ah ni wanene a wajan ki?" Jikinta ya hau rawa kirjinta yana bugawa ta ɗago tama kasa furta koda kalma guda ɗaya sabida tsananin ta shin hankalin daya ziyarce ta. Ya buga mata tsawar data sa ta ɗimauce wa. "Nace ni waye a wajanki?" Da sauri tace. "Ba.ba.na" Muryarta na rawa. "Idan har ni Ahmadu nina haifeki to baki da miji sai ɗan Yayana sabida haka ki fara shiri a ko wani Lokaci zan iya ɗaura Miki Aure da ABUBAKAR" Wani irin tsalle tayi sai gata a gaban Abba... 09022260850 ​    *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *002* Ta sa hannu ta kama ƙafafun Abba tana wani irin kuka mai cin rai wanda yake bayyana tsananin ƙiyayyarta ga auren da ya ke shirin yi matan. "Abba kaiwa girman Allah kada ka min auren dole, Abba bana son shi bana ƙaunar shi ba kalata bane ta ko ina nafi ƙarfin shi Abba shifa talaka ne ni kuma Mai kuɗi ta yaya zaka haɗani da ƙasƙantaccen mutum........ Gigitaccen mari Abba ya sharara mata abin da bai taɓa yi mata ba kenan tunda tazo duniya shine duka koda wasa bai taɓa dukan Adaah, ba, sabida soyayyar da yake yi mata amman a yau furucinta ya saka ya mareta Cikin ɓacin rai yace. "Ni zaki watsa wa ƙasa a ido wani bambanci ne tsakanin ki da shi yana ɗan Yayana cikin mu ɗaya da mahaifin sa to bari Kiji Komai zaki sai dai kiyi amman Muddin Nine mahaifin ki auren nan babu fashi" Yana gama faɗin haka ya wuce fuww yabar falon. Adawiyyah, ta zube a wajan tana wani irin kuka, Momi tsananin baƙin ciki ya hanata yin magana sai faman huci take yi kafin ta yunƙura ta kamo Adah tayi cikin Room ɗinta da ita. Zaunar da ita tayi a saman Gado tana rarrashinta. "Nina san asiri sukai wa Abbanki domin nasan a duniya bai da wani farin ciki sama dana ki amman a yau bana hango soyayyarki a idanun shi sai tsananin tarin rikici" Ido shaɓe shaɓe da hawaye ta kalli Momi. "Shikenan ni yanzu aura min shi zaku yi momi bakwa sona in dai kuka aura min mai suffar samudawan can wallahi bai da imani ko kaɗan gashi talaka ƙawayena ma suka san Shina aura wallahi kashina ya bushe" Momi ta rungumeta tana ta rarrashinta tare da bata ƙarfin gwiwa akan lallai lallai zata san yadda zata yi auren nan ya lalace. Anan ɗakin momi tayi sallar isha'i ranar Ko abincin dare bata iya ciba itama momi bata je ɗakin Abbah ba domin fushi ta ɗauka dashi sosai. Se bayan Adaah tabar ɗakin ne momi ta ɗauki waya ta kira ƙawarta. Bayan ƙawar tata ta ɗauki wayar tare da cewa. "Hajiya maryam yaya naga wayarki da wannan dare ina fatan dai lafiya?" Momi cikin damuwa tace. Hajiya lubna dole kiji wayata a wannan lokaci domin Alhaji ke son ɓallo min ruwa ɗazu nake son gaya miki to naga bamu kaɗai bane shiyasa. Hajiya lubna tace. "Ina sauraron ki Hajiya maryam" Momi ta karkace tana zayyanewa Hajiya Lubna abin da yake faruwa sabida akaf duniya babu wadda momi ta yarda da ita kamar Lubna ƙawarta ce Aminiyarta. Seda Hajiya lubna ta gama jin komai sannan taja tsaki! tana cewa. "Akan wannan ƙaramar maganar har zaki ɗagawa kanki hankali, mai akai da auren talaka, in kika kuskura ƴarki ta aure shi to se kin siyar da akuya ta dawo tana ci miki danga, sabida haka ni a ganina wannan matsalar ƙarama ce kota ƙarƙashin ƙasa kibi ki lalata abin" Momi ta yarfe zufa! A raunane tace. "Lubna kin san halin mahaifiyata  ba son biye biye take yi ba, har baki tai min muddin nabi wata hanya don biyan buƙatar kaina" Lubna taja tsaki! "To Iyah tasan sanda zaki To shikenan ni dai iya shawarata dake kenan in zaki yi kiyi in ba zaki yi ba shikenan su waya san abin da suka banko suka ruɗa miki Mijin naki" Momi da damuwa tace. "Ni ban san me nayi wa Baban chiranchi ba, baya ƙaunata ko kaɗan haka kwanakin baya yace se lallai Alhaji ya ƙara aure da ƙyar maganar ta mutu mai nayi Musu da zafi" Ta faɗa tana kuka don lokacin zuciyarta ta karye. Da wannan damar Lubna ta zugeta tas nan suka ɗaura alƙawarin gobe zasu yi sammakon zuwa wani ƙauye, duk akan su rusa maganar Auren Adaah. Lubna hatsabibiya ce ta gasken gaske ita ce sitiyarin momi a bin malamai kaɗai suka banbanta Ita Momi tana tsoron bakin da mahaifiyarta tai matane shiyasa bata biyewa lubna ta nan ɓarin ba, Amman a duniya Momi bata da aminiya kamar Lubnah. Da shirin fita momi ta kwana a iya zamanta da Abbah bata taɓa bin wata hanya don cikar burinta ba amman akan auren da yake son ƙaƙabawa ƴarta tana jin sai inda ƙarfinta ya ƙare. Tun asubah datai sallah bata koma bacci ba wanka tayi ta zauna jiran drivern Hajiya Lubna da zaizo ya ɗauketa bata jin ko Abba ma zata gayawa inda zata je tunda tasan a fushi yake ba lallai yabi ta kanta ba, Sedai wajan ƙarfe Bakwai na safiya wayar ƙaninta Abbas ta sameta akan lallai tazo gida Jikin mahaifiyarsu Iyah ya rikice haka ta ɗauki jakarta a gigice ta fice Ɗakin Abbah Yana bacci dan haka ta wuce parking space Ta kira driver suka wuce Gida. A hanya taga wayar Lubna wadda tace mata ta fito, ta bata amsa da tana hanyar hotoro Iyah ce babu lafiya badan Lubna ta yarda da maganar ba tayi mata Allah sawaƙe ta kashe wayar. Cikin Kiɗima Momi ta shiga gidansu wanda ta gyarawa mahaifiyarta ta zuba mata komai na alatun rayuwa domin Morewa da jin daɗin Rayuwar Duniya a falon Iyah Likita na zaune a gabanta inda take kwance a saman katifa Yana Ɗaura mata ruwa Abbas ƙaninta da Mariya Ƙanwarta mai aure itama data ƙaraso Gidan, Suke zaune a gefen Iyah Momi ta ƙarasa cikin fargaba ta zauna a kusa da iyah tana ta jera mata sannu. Bayan Likita ya saka mata ruwan ya dube su cikin son kwantar Musu da hankali yace musu ɗan zazzaɓi ne ke damunta dama jikin girma ya gaji haka sallama yayi musu tunda Mariya ƙanwarta Nurse ce in ruwan ya ƙare zata cire wa Iyar. Seda ruwan ya ƙare Mariya ta cire mata sannan Iyah ta buɗe ido tana kallon Momi. "Maryama waya taso ki?" Momi ta kama Hannun Iyah kana tace. "Abbas ne ya kirani dama na shirya zani anguwa dana ji wayar shi shine kawai na tawo nan" Iyah bata kuma cewa komai ba ta juya ta koma baccinta Mariya ganin Jikin da sauƙi tai musu sallama ta tafi gidanta dama Ƴaƴan Iya daga Momi ne se Abbas se mariya su uku ne, Mariya nada ƴaƴa uku Abbas bai aure ba Momi ce Babba Nada Ƴa ɗaya Adaah, da yake ba wani shiri suka fiya yi da Mariya da Momi ba sakamakon ita momi Ƴar ƙarya ce bata fiye jan Mariya ajiki ba sabida ta raina ajinta Mijin mariya malamin makaranta ne Ita kuma Nurse se Mariya ma ta shekara bata je wajan Momi ba duk da cikinsu guda dan Momi tafi bawa Ƙawaye mahimmanci fiye da ƴan uwanta dan ma Inda Allah ya tarfota tana jin tsoron Iyah mahaifiyarta kamar me da wannan aka ɗan sami sauƙin ta. Dan ko abu taiwa Iyah se Iyah taƙi amsa tace seta ba Mariya, Shi dama Abbas Ba anan yake aiki ba bai fiye zaman kano ba se ya ɗanzo week end. Bayan fitar Mariya Abbas ma yace mata bari yaje ya dawo falon daga iyah sai Momi. Iyah ta yunƙura domin tashi Momi ta taimaka mata, Bayan ta tashi ta haɗo mata tea mai kauri ta kawo mata. Bayan tasha Ta dubi Momi tace mata. "Maryama kamar naganki acikin damuwa meke damunki?" Momi tai ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. "Babu komai Iya kawai bacci ne akaina" Iyah tai mata wani kallo kafin tace. "Jiya ai Amadu yazo nan ashe Rabi tayi miji shine nace kin sake dangi ne dani baki gayan ba?" Jikin Momi yayi sanyi nan da nan, domin batai zaton Abbah yazo wajan mahaifiyarta ba, lallai duk inda tai zaton lamarin yaso ya wuce zaton ta. A hankali tace. "Iyah Bata son shi wallahi Auren dole yake son yayi mata" Iyah ta watsa mata kallon banza kana tace. "Sabida shi wanda zata aura ɗin talaka ne?" Da sauri momi ta zaro ido iyah ta kuma cewa. "Eh mana ai nasan baki son talaka maryam domin ke rayuwarki da faɗi, bayan mu ɗin ba kowa bane amman kin haɗu da Ƴan duniya sun sauya Miki rayuwa" Momi ta fashe da kuka mai sauti tana cewa. "Iyah kema zargin da kike mini kenan fisabilillahi Iyah Alhaji yayi daidai zai ɗauki ƴarsa mai ilimi ya bawa sakaran talaka marar galihu nidai an cuceni" Iya ta ɗauki Kofin shayi ta jefowa momi wadda tai saurin gocewa tana kuka cikin zafin rai tace. "Ashe Duk abin da ake faɗa ba ƙarya bane, Maryam ina shi wanda Uban Rabin ya zaɓa mata Musulmi ne, Ina jiye Miki duniya maryam bam miki baki ba amman wallahi ki guji duniya da uban yaron nan da Uban Rabi uwarsu ɗaya uban su ɗaya meye naki aciki da talaka da mai kuɗi duk Allah ne yayi su Ina baki shawara ki ɗauke kanki daga batun auren nan babu ruwanki" Da kuka Momi tace. "Iyah ita ma fa bata so wallahi" Iyah ta zaburo kana tace. "Ai dole taƙi tunda kin zugeta Rabi dai batai sa'ar uwa ba shiyasa duk baƙin halinki ta kwafe yarinyar da ko cikin mutane bata son shiga Kin rabata da dangin mahaifinta Kin cusa mata aƙidar raini da girman kai da izzah tun wuri ki sauya hali maryam nidai Allah ya sani baki gado halina ba wallahi acan duniya kika samo halin ki" Bakin momi ya mutu don a duniya Mahaifiyarta ita kaɗai ke taka mata burki sabida duk rashin mutuncin da take shukawa labarin na zuwar wa Iyah shiyasa iyah takanas tasa aka kira mata Baban Chiranchi ta Nuna goyon bayanta ga auren da zasu haɗa Ko hakan yasa Maryam ta saduda kawai dan dangin Mijinka talakawa ne seka ƙyamace su ko taron su bata zuwa a cewarta tafi ƙarfin ajin su ba kuma komai bane yaja mata hakan face Yawan ƙawaye waɗanda suke hure mata kunne. Tass iyah tayi mata sannan ta zabga mata Allah ya isa idan har tabi malamai ta rusa auren, Ranar Momi da kuka ta baro gidan Iyah da ta dawo kuma ta tarar da tijarar Abbah dan da cewa yayi seta koma inda ta fito seda tai wa Abbas ƙaninta waya ya kira Abban yace shiya kirata Iyah ce babu lafiya, Sannan ta bawa Abban haƙuri ta shige ɗaki. Ita kuwa dama Adaah data tashi daga bacci shirin school tayi bayan ta kammala ta leƙa room ɗin momi a rufe tai zaton tana wajan Abba sabida haka setai ficewarta a motar ta fara mai kyau kai tsaye Bayero University ta shiga sabida anan take karatu tana matakin lavel 2 ne yanzu haka exams suke yi wadda in suka kammala zasu tafi hutu. Bayan sun fito daga exams suka haɗu da Habeeb wanda yake zaune saman motarta yana jiranta koda ta iso daga nesa da shi ta tsaya tana harɗe hannayenta a saman ƙirjinta yanayin kallon ƙurullar da yake aika mata shiya bawa gangar Jikinta damar Mutuwa. Saukowa yayi daga motar yana wasa da keyn hannun sa ya ƙaraso gabanta. Iska ya hura mata a saman fuskarta idanunta Lumshe taɗan saki ajiyar zuciya. A hankali yace. "Muje" Ba musu tayi gaba yana binta a baya motarta ta shiga ta zauna shima ya buɗe emty seat ya zauna yana facing ɗinta. A hankali yake gaya mata daɗaɗan kalamai waɗanda ya kashe mata Jiki dasu shima akaran kansa yasan a yau ta bashi damar da bai taɓa samu ba domin ta saurare shi. "Zaki aure ni Baby karki damu da ina karatu, wallahi ina zuwa kasuwa Ina da halin da zan riƙe ki" Ya faɗa Cikin kashe Murya. Zuciyarta ce tai rauni, tabbas Inda da dama gwara ta auri Habeeb akan ta auri wancan garan da Abbah yake son Liƙa mata. Cikin Nutsuwa tace. "Zanyi tunani akan maganarka Habeeb ka ɗan bani lokaci" Daɗi yaji har cikin zuciyarsa. Da kansa yaja Motar tata seda ya kaita har ƙofar Gidansu sannan ya fita ya bata Key ɗin yana ɗaga mata hannu. Lumshe idanunta tayi tana Jin wani irin yanayi mai kama da amsuwar tayin soyayyar Habeeb acikin zuciyarta. Gidan nasu yayi shuru, alamun ya nuna kamar babu kowa room ɗinta ta shiga tayi wanka ta saka doguwar riga marar nauyi ajikinta sannan ta nufi Room ɗin Momi ************ A gajiye liss ya shiga Gida Lokacin ana Kiran sallar Magarib seda ya wanke jikinsa damma yana amfani da safar hannu wajan awon ƙarafan amman duk da haka seya yi wanka in ya dawo Gida. Yayi shiri cikin Farar shirt da Baƙin jeans, Ya fesa turare mai sauƙin kuɗi. Masallaci yaje yayi sallah tare da Baba suka jero zuwa gida yana ƙoƙarin shiga ɗaki Baba ya kira shi. "Sadauki,Muje muci tuwon dare tare mana" Ya shafa kanshi kana yabi bayan Baba. A rumfar Baba suka zauna tare suka ci tuwon da Mahaifin sa bayan sun kammala ya ɗauke kwanikan yakai Kicin. Daga nan fita yayi dan yasan Ba komai bane yasa Baba Yi masa hakan face yana son yaji yadda sukai da waccan yarinyar shi kuma bai san me ze cewa Baban Ba. Karo suka ci da juna goshin su ya gwaru waje ɗaya, dafe goshin nasa yayi........09022260850 [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *004* Zama tayi a gefen gadon Momi tana jiran ta sabida ta jiyo alamun saukar ruwa wanda ya bata tabbacin wanka momi take yi. Babu jimawa Momi ta fito daga cikin toilet Jikinta rufe da Ƙaton Hijabi ganin haka yasa Adaah fita falo domin ta bawa Momi damar shiryawa kusan awa Guda da fitar tata Momi ta biyo bayanta. A kusa da ita ta zauna tana jan tsaki. "Shalele Mahaifin ki yayi min shigar sauri a lamarin auren ki sai dai ni kuma zan nuna masa Nina haifeki wallahi Koda kin Auri yaron nan ba zaki Zauna lafiya a gidan ba har sai Kin kaso wannan ƙaddararren aure na kwaɗayi sabida anga ke ɗaya ya haifa shine za'a ƙaƙaba maki auren dangi" Taɓe baki Adaah tayi tana Jin zafin furucin kalmar auren nata da Momi ta faɗi kafin tace. "Yanzu Momy ke kina tunanin zanyi rayuwa da shi? Haba Momy kimin Fatan alheri mana dan wallahi dana aure shi gwara na auri Habib duk da Habib ɗin ba wani shigemin rai na yayi ba" Da tarin takaici Momi tace mata. "Inda dama mahaifinki ya bayar akan ki fidda Miji ni kaina dana haɗaki da Yaron Hajiya Lubna Maheer amman kina kallo fa umarni ya bamu bawai dama ba wannan makircin Na rasa daga ina ya fito hatta Mahaifiyata anje an faɗa mata ƙarya da gaskiya" Zaro ido Adaah tayi haɗi da saurin cewa. "Iyah aka faɗama maganar auren nawa? Wayyo! Shikenan yanzu zata ce in baki bari ba Bata yafe ba Haba Abbah yaya zeyi min haka ya rasa da wa zai haɗani sai Ƙasƙantaccen Mutum ɗan talakawa" Kuka Adaah take mai cike da tsananin ƙiyayyar Auren da za'ayi mata Tin Momy na rarrashinta Har abin ya faskara sai ta zuba mata ido tana kallonta domin duk yanda take zato Adaah ta fita Ƙiyayyar Auren har akai sallar Magarib tana zaune batare data Miƙe Domin gabatar da sallah ba tana ta kuka a wurin Gajiya Momi tayi ta Tashi ta nufi Bedroom Domin gabatar da sallah. Ana idar da sallah Abbah ya shigo Jin Shashsheƙar Kukanta yasa shi ƙarasowa wajanta ya fasa hawa saman dayay niyya Gyaran Murya yayi tare da Zama a kusa da ita Wanda Itan kuma tai saurin Zamewa ta zauna a ƙasa tana Goge hawayenta. Da sassauci acikin Muryar Abbah ya dube ta. "Rabi'atuna kukan mai kike Ɗiyar Abbanta kome Kike so ki faɗa min Kinji bana son damuwarki" Jin wannan kalmar daya ambata sai taji zuciyarta tayi sanyi ta ƙara Goge sauran hawayenta tare da cewa. "Abba dan Allah karka aura Min shi wallahi har cikin raina bana son shi" Tsira mata ido Abba yayi tare da kamewa sosai ya kalleta na wani Lokaci sannan yace. "Ko kina da dalilin Ƙin Yi mini Biyayya wadda bata saɓawa Allah ba? Ni  Mahaifin ki na zaɓa maki Mijin Aure Kice zaɓina bai maki ba Ko kina da zaɓin ki? sannan Ki bani dalilin Ƙin wannan aure da Kike?" Daburcewa tayi seda ta aro jarumta wurin furta kalmar. "Abbah ka duba Gidannan ka duba tsarin shi sannan ka duba tarin dukiyar dake gareka sannan ka duba yanda na taso Sannan Abbah kace zan auri wanda Da ƙyar In yayi karatun Boko ma daga ganin shi yafi kama da ƴan jagaliyar anguwa Abbah na roƙeka karka aurawa Ƴarka tilo ɗaya tal wanda ba tsaranta ba kuma ba ajinta ba" Ɗaga mata hannu yayi tare da dafe saitin zuciyar sa. "Innalillahi wa'innah Ilaihirraju'un" Ya furta a fili yaushe Rabi'ah ta ɓaci haka yaushe ne ta zama mai raini da ƙasƙanci ga mutane tabbas ba laifin kowa bane face na Mahaifiyarta shiba zama yake a gari ba yawanci In yazo baya daɗewa yake tafiya dalilin daya sa harya ƙauracewa zuwa gidan Yayan nasa kenan sedai ya aika masa da kayan abinci da kuɗi wanda takanas Shi Kuma Baban Chiranci ya aiko masa da cewar Ya daina amsa shiba wannan yake soba Zumunci yake so Yanayin kasuwanci yau ya fita ƙasa kaza gobe ya fita ƙasa Kaza shine silar tarwatsewar Komai, Gudun kar Ƴarsa ta Koyi Wata Tarbiyar yasa ya hanata Karatu a ƙasar waje ashe Gudun Gara yayi domin ya mance yawanci Ƴaƴa suna samun tarbiya ne daga wajan Iyayensu mata. A fusace ya shiga Kiranta. "Maryam! Maryam!!Maryam!!! Da tsananin zafi ita kuma da tsananin sauri ta ƙaraso Falon. "Alhaji sallah na idar ina addu'a kana kirana da ƙyar na shafa wallahi ka ɗagamin hankali" "Dole na ɗaga miki hankali Maryama Kin kyauta da tarin tarbiyar da Kika bawa Ƴarki Amman Ina so a daren nan Ki shaida mata waye Abubakar a wajena waye mahaifinsa wacce Irin Rawa mahaifinshi ya taka a rayuwata Kuma ki sanar mata In Mutuwa tayi zan kaita Gidan Mijinta daga nan a suturtata akaita makwancinta Amman Auren ta da Abubakar Babu fashi In har Nine mahaifinta" Fuww Ya tashi yabar wajan Tagumi Momi ta zabga wato duk yadda take zaton lamarin so yake ya fi ƙarfinta, Mijinta mai son ta da ƙaunarta Ko magana zai mata baya mata ita cikin faɗa sai a hankali sabida Gudun Ɓacin Ranta kasancewarta mai kirsa yanda take wa Alhaji ba zaka ce Wannan matsala zata zo ta shiga tsakanin suba duk yadda takai da kirsarta a Lamarin Auren nan ta kasa dannewa jita ke ba zata iya Gani talaka yazo ya aurar mata ƴaba kuma Ama rasa daga ina zai fito sai daga gidan maƙiyanta dan Momi a duniya bata Ƙaunar Baba da Innah domin sai da takai ga har Gida taje ta Yiwa Innah gargaɗi akan mijinta ada sanda Yake Musu Hidima sosai kafin ta janye shi da Kinibibinta. Duk da sanyin falon Momi zufa take Adaah kuma na kuka wayarta dake Gefen Kujera ta janyo ta shiga Kiran Ƙawarta Lubnah. Hajiya Lubna dake zaune Tare da Ɗanta Maheer suna tattaunawa taga wayar Ƙawarta Murmushi tayi tare da cewa. 'Kaga ƴar halak kamar tasan zancenta Muke" Da sauri Maheer yace. "Mama ki ɗaga mana Kiji" Gyara zama tayi tare da ɗaukar wayar daga ɓarin Momi a gigice ta shiga zayyanewa Hajiya Lubnah Halin data ke ciki. Tsaki Hajiya Lubnah tayi. "Ga Hanya mafi sauƙi na faɗa Miki kizo mu fita da tuni wata maganar ake Keni In ba zaki bi malamai akan wannan matsalar ba dan Allah karki sake Kirana" Tana Ƙoƙarin kashe wayar Momi tace. "Zani wallahi dole ma naje inya so saina nemi gafarar Iyah In komai ya daidaita Amman ba zan ga wannan abun na bari ba wato in suka aura masa Ita shikenan Komai Namu ya koma Gindinsu Daga ƙarshema su gaje Dukiyarmu tinda Ƴar tawa dana Ke tutiya da ita ta koma cikinsu wallahi Hafsatu ba zata ci galaba akaina ba" Dariya Hajiya Lubnah ta saki gami da cewa. "To ai tuni nake faɗa maki karki ga kin sami daula dole sai kin Miƙe tsaye to gashi nan dai Kirsar da kike cewa kina da Ita bata hana Mijinki Botsare miki ba" Momy ta ɓata rai. "Keni kada ki faɗa min magana mafita kawai nake Nema Amman Ni nasan Kirsata tai Min maganin waɗancan tsinannun" Taɓe baki Lubnah tayi tare da cewa. "Yanzu dai turo min wani abun Da zan turawa malam ya fara Bincika mana Halin da ake ciki" Da sauri Momy tace. "Baki da matsala bari na sako Miki Kuɗin nan ƙawata Aminiyata ta duk duniya dan wallahi Kinfi min ƴan uwana don basa damuwa dani kamar Ke" Lubnah tai dariya tare da cewa. "Karki damu Komai nai miki kaina nayi wa Kin manta taren fa bata yanzu bace, Nima Kin min Komai a rayuwata duk da Mijinki yafi nawa arziƙi Amman baki taɓa yada ni ba Komai naki sai kin saka dani Allah dai yabar mu tare" Bayan sun kashe wayar Momi ta rarrashi Adaah Ta nufi ɗaki domin sallah, Ita kuma Momi ta zauna tana turawa Hajiya Lubnah kuɗin data Buƙata Bayan Awa Biyu Hajiya Lubnah ta Kira Momi tare da ce mata Lamari fa ya wuce nan dole seta zo sunje tare dan bayani a waya ba zai yuwu ba. Tashin hankalin ƙaryar da zatai wa Abbah ta shiga domin tasan Ba zai barta Ta fita cikin sauƙi ba Koda kuwa da Jikin Iyah tayi ƙarya A haka ta kwana tana Juyi tare da saƙe saƙen yanda zatai Cikin Ikon Allah ma washe gari da asubah Abbah ya zo mata sallama akan zashi lagos sati ɗaya zai yi wato rashin Jituwar da basa yine bai faɗa mata ba, Itama babu wata walwala tai masa fatan dawowa Lafiya ta Juya ta cigaba da uzirin gabanta. Sai da taji fitar shi sannan ta kira Hajiya Lubnah Akan fitar tasu da magagin Bacci Lubnah ta miƙe se Lokacin ma tasan Asubah tayi Ta shiga Toilet dan ta kintsa domin a cewarta fitar wuri zasu yi. Itama Momi Kintsawa ta shiga yi tasan Adaah inta farka taga bata nan ba damuwa zatai ba dan haka data kammala shirin sai ta zauna tana Jiran isowar Aminiyar tata. Abbah Har ya nufi Airport Sai ya cewa driver ya koma da baya suje Chiranchi tinda akwai sauran Lokaci kafin tashin Jirginsu Suna tafe yana duba hanya don ya kwana Biyu bai zo wajan Ɗan uwan nashi ba sanda Motar su ta shiga Layin Baba yana Addu'ar fita daga gida sabida sammako zaiyi Abbatuwa wajan sarin nama domin Idan kana son Nama mai Arha sai kayi Asubanci. Da sauri Abbah ya Ɓalle Murfin Motar ya fita ya ƙarasa gaban Baba ya tsugunna har ƙasa tare da cewa. "Yaya barka da Asuba" Baba ya miƙawa Abba Hannu cikin so da ƙauna irin ta Jini Abba ya kama Hannun Baba ya miƙe suka shiga Cikin Gidan. Da Saadik suka ci karo wanda yake zaune a bakin Rijiya yana Brush cikin sakin fuska Abba yace. "Malam Abubakar ashe yau zamu haɗu barka da asubah" Sai da ya wanke baki sannan ya shiga gaida Abba wanda yaketa Kallon Saadik cike da son Ƙulla Alaƙar Aure tsakanin shi da Ƴarsa shiko Saadik ɗaki ya wuce ba wata cikakkiyar walwala a tare dashi domin shi Mutum ne mai gudun ƙasƙanci. Abba yabi bayan ɗan uwanshi yana waigen Saadik aranshi yana Jin amintar bashi Ƴarshi domin Irin Yaron da wiya mace ta raina shi, Har Saadik ya shige Abba na waigen shi Tare da Jin rashin daɗin yanda baya sakewa dashi daga gaisuwa shikenan kwanakin baya babu yanda bai da shi ba akan ya dinga zuwa kasuwa wajan shi Amman fafur Yaƙi Yace shi  Gwangwan ɗin shi ta fiye mishi zuwa kasuwa. Innah dake fitowa daga Kitchen hannunta Riƙe da Ludayin Miya wanda take Juya Miyar da zatai Ɗumaman tuwon Ƴammakaranta ta saki fuska sosai tana amsa gaisuwar Abbah "Dama Amadu kana duniya yaushe rabon duniya da ayyaraye rabon dana ganka har na mance fa" Abbah ya sosa kai Zai bata amsa Baba ya ɗaga Murya yana cewa. "Amadu Rabu da Hafsa yau wasan ƙanin Miji take maka zo mu gaisa Ina sauri" Jiki a sanyaye Abbah ya shiga Rumfar da Baba ke zaune a nutse suka gaisa dan tsananin Kunya Abbah yama kasa ɗagowa ya kalli Baba shiko Baba sai jan Abba yake da Hira koda wasa bai masa maganar komai ba. Tuwon dawa miyar kuka sai tashin ƙamshi daddawa yake Innah ta shigo masu da shi tare da Koko mai zafi. "Wato Amadu yasa dole sena karya zan tafi kasuwa, Kin san Hafsatu fa da tuni nakai Titi Amadu wanke hannu a silba Muci tuwo". Abbah ya ɗauki ruwa ya na wanke hannun shi tare da cewa. "Wato na jima banci tuwon Innah ba kuma ina marmarin tuwon innah kasan Yaya yawanci matan yanzu ba ko wacce bace ta iya tuwon dawa kamar na Innah" Aiko mai innah zatai In ba dariya ba ta fice tana cewa. "Kai Amadu kodai zolaya ta kake yi nikam ba zan tsaya jin daɗin bakin kaba nayi nan" Daga shi har Abba dariya suke Suka saka hannu tare da Bismillah suka fara cin tuwon Abbah ya zage yaci sosai yasha Kokon Shi kam Baba bai ma ci da yawa ba Ya tashi ya wanko Hannu Abbah ne yakai kwanukan bakin Rijiya ya wanko hannu shima ya dawo. Bayan sun zauna Abbah yace. "Dama Yayah batun auren yaran nanne Ina ganin idan na dawo daga wannan tafiyar sai a ɗaura musu Auren, Batun Hidimar Aure dama nace maka bana buƙatar Komai sai sadaki Zan basu gida sannan don Allah maganar Kasuwa har yanzu Ina Barar yazo wajena Ya nemi abincin shi na bawa wasu ma waje bare kuma nawa" Baba ya nisa kana yace. "Haƙiƙa Amadu a baya nayi Fushi dakai sabida yadda ka ƙaurace mini ka daina zuwa inda nake, Amman yanzu na huce sabida haka Bari na kira Sadauki! inya Aminta da tayin naka sai ayi komai a nutse dama bai fara Ginin Gidanshi ba kasan yadda lamarin yake yadai sayi fili anan bayan Gidannan" Baba ya fita yasa Ummi tayi Kiran Saadik wadda tai shirin makaranta Cikin Blue Ɗin Uniform ɗinta. "Ke Ummi in kika fita ki kira min kawun ku a ɗakin soro" Ummi ta amsa wa Baba tana nufar soron sai dai ta ga Khadija a raɓe tana share hawaye Ummi tai saurin cewa. "Ke kuma keda wa kike faman share hawaye?" Cikin ƙasa da Murya Khadija tace. "Kibi a hankali kayan kari Innah ta bani na kaiwa kawu Saadik wallahi bakiji ranƙwashin daya Min ba wai banyi sallama ba kuma nayi fa" Dariya Ummi tayi tana cewa. "Ba lallai Kinyi ba kuma kinsan halin Kawu su Ya Umar ma shakkarshi suke bare mu" Ummi ta wuce A bakin Ƙofa tayi sallama sai da yaja aji kafin yace. "Waye ne?" Ummi tace. "Kawu dama baba ne" Bata ƙarasa ba jin yayi shuru sai can yace. "Ni kike faɗawa ko ƴan Ƙofar Gida?" Fahimtar mai yake Nufi yasa taja Labulan ɗakin nashi Ƙamshi da wani Irin sanyi ne suka bugeta daga Nesa dashi ta durƙusa duk Girmansa ya cika ɗakin. Murya a hankali tace "Dama Baba ne yace kazo" Ta faɗa tana Raba ido sabida yadda yayi mata masifar kwarjini. Batare daya kalleta ba yace. "Kice gani nan" Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa daga bakin katifar. Da. "To" Ummi ta amsa tana miƙewa ta fita daga ɗakin taje ta sanar da Baba Saƙon sannan suka tafi makaranta Lokacin ƙarfe bakwai da rabin safiya tayi. 09022260850 [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *003* Ita kuma tayi saurin taɓe baki tayi raurau da manyan idanunta waɗanda suka ciko da hawaye ta ƙura masa idanun nata duka tana kallon shi. Murmushi yake yi har Lokacin hannunsa yana dafe da goshinsa. "Ni da kika bugawa wannan ƙaton Goshin naki banyi hawaye ba sai ke?" Hannu tasa ta kare fuskarta tana Murmushi ga hawaye kuma na ƙara zubowa. Ya ƙara matsowa gabanta ya fita tsayi nesa ba kusa ba hakan ya sa ta ƙara komawa ƴar ƙarama a gabansa. "To ni yaufa naga takaina Kinga dan Allah zoki rama Duk da nima dai naji zafi" Dariya ta saki tana cewa. "Kai kawu Saadik tsokanar kafa nake yi wai ina zaka je Sai ƙamshin turare kakeyi?" Ta faɗa cikin sigar tsokana Ya tsuke fuska kaɗan. "Dama bana saka turare sai zan fita Hawwa'u?" Saurin dafe baki tayi tana wara ido. "Wasa nake maka fa" Ya ɗan kalleta. "Wai bana ce na soke kawun nan ba su in sun cemin kawu kema sai kice min kawu maza sai wata tazo tana cemin my love ke kina faɗin wani kawu" Ƙafafu ta hau dirawa ta fara Kukan ƙarya Raɓeta yayi zai shiga ɗakin shi dake soro da sauri ta bishi Ya tsaya a bakin ƙofar ya kare hanyar da zata shiga ɗakin ya tsareta da ido. "Abinchi na kawo maka na miƙo maka?" Ta faɗa tana Waigawa bayanta tare da ɗaukar Kular data zubo masa Abinchin. Cikin tsananin so da tausayi ya dubeta. "Bana hanaki kawo abincin nan ba yanzun nan muka kammala cin tuwon innah nida Baba" Turo baki tayi kaɗan. "Nima Gas ɗinmu ne ya ƙare  seda ummah tayi wa Yayah Fa'izu waya ya kawo mana shiyasa ban kawo maka abincin da wuri ba" Yadda take maganar Jiki a sanyaye ta ɗan bashi tausayi shikam ya rasa wani irin so yarinyar take mishi wanda yake ganin son da take mishi kamar yafi nashi duk da shima yana sonta. Ya zira hannunshi ɗaya ajikin aljihun wandon shi. "To ni yanzu yaya zanyi da wannan abincin tinda nidai cikina ya ƙoshi" Yanda yayi maganar ta bata haushi sai kawai ta juya tare da ficewa daga soron. Beyi gigin bin bayanta ba dan yasan rigima ce zata kaure musu ƙarshe inta saka mai rigima ya karɓi abincin ba iya ci zai yiba inya bayar kuma taji haushi. Sai kawai ya shiga ɗaki cikin hukuncin Allah yana shiga ana kawo Nepa ya jona cajin ƙaramar wayarsa. Yana ƙoƙarin cire shirt ɗin jikinsa ƙaramar wayar tasa ta shiga Ƙara alamun kira yana shigowa Bayan ya ɗaga Muryar Abokin shi Nura saiti ta cika masa cikin kunnen shi. "Wai dan Allah dagiya ina ka shiga ne?" Saadik ya ɗan ja tsaki kaɗan. "Yanzu dai meke tafe dakai ko tambayata ka kirani kayi? kaje shagona baka ganni bane koka zo gida bani nan?" Saiti yayi dariya tare da cewa. "To sarkin fushi nai maka magana ne naji shuru, ko baka kunna Data bane yau?" Takaicin ɗazu ne ya faɗo masa ya fesar da huci mai zafi. "Bari kawai Nura wayar ma bata wurina Allah yasa sim ɗin yana wannan wayar" Da sauri Nurah yace. "Garin yaya matsala ta samu?" Cikin son kauda zancen sabida shi gwanin zurfin ciki ne yace. "Ya ake ciki ne kana shagone koka shigo?" Nura yace. "Yau na sami cinkoso ne a wajan IBB Road kasan hanyar tamu sai a hankali, Amman gani nan dama Najika shuru ne nace bari na taɓaka kako san yau Za'a Buga wani zazzafan wasa?" Duk yanda Saadik ke son kallon Boll sam yau ya mance zasu je kallo kwata kwata sabida haka tsaki yaja dan baida karsashin fitar ma gaba ɗaya Nafila zai yi kawai ya kwanta yasan Baba zai fita waje shan iska bayan ya gama jin Labaran sha ɗayan dare ya rufo gida shiyasa zeyi kwanciyar sa. "Nura Kuje kawai kaida su Babu danni gaskiya yau ɗinnan ba zan iya zuwa gidan kallo ba" Daga haka ya kashe wayarsa gaba ɗaya ya mayar chaging ya koma ya kwanta ya zurfafa acikin tunanin wannan lamari mai girma daya faɗo masa ko a kanshi bai taɓa tunanin Baba zai masa auren dole ba, dan shi kam wannan aure na dole ne yana zaman shi lafiya Baba ya bashi Umarnin zuwa inda za a ɓata mishi rai. Maganganun Baba na jiya da daddare ne suka soma dawo masa cikin kansa. "Sadauki!Waye mahaifinka?" A lokacin sun kammala cin abincin dare ne duk suna zaune a Rumfar Baba shida Baban da Innah wadda take cin Gyaɗa marau marau. Ya Nutsu sosai tare da cewa. "Baba duk duniya ban san wani a wannan matsayin na uba ba face kai" Baba yaji daɗin kalamin shi duba da yanda yayi Murmushi a lokacin haɗi da samai albarka kafin ya fara dirar mashi da maganar data haifa masa ɗaukewar Numfashin wucin gadi. "Sadauki jiya mahaifin Wannan yarinya Hauwa'u mai haƙuri da kawaici ya kirani akan maganar auren ku sabida karatunta daya kusan zuwa ƙarshe, Bayan nai masa na'amm da maganar sai na ɗauki wayata na Kira ɗan uwana wanda duk duniya bani da kamarshi Amadu uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya nina saki Nono ya kama na shaida masa batun Auren ka" Baba yaja fasali. Saadik yaji wani irin farin ciki a zuciyarshi. Innah ma sai ta hau murmushi sabida Jiddah ta cancanta ta zama surukarta duba da yanda yarinyar ke son ɗan nata tilo tal namiji aduniya kuma auta acikin ƴaƴanta waɗanda dukka mata ne Allah ya bata shi kaɗai ne namiji acikin su kuma shine auta. Maganar baba wadda ta katse Murnar Innah da Saadik ita ce ta cika Kunnuwan su. "Sai dai Amadu ya katsen hanzari, ya mini kyauta kuma na amsa tinda bahaushe yace yaba kyauta tukwici dik da kyautar dama bata yanzu bace amman Lamarin daya zo ya cuɗe a tsakanina da shi yasa na fidda rai akan kyautar ta shi Sadauki Amadu yace kaje ka Nemi auren ƴarsa RABI'AH duk da maganar ba sabuwa bace a wajena nida Hafsatu mahaifiyarka Tin ranar da Aka haifeka da Amadu ya ɗaga ka yace In har Matar sa ta haifi ƴa mace yayi ALƘAWARIN ba tada Miji sai kai to yanayin yadda Zumuncin mu ya lalace da shine yasa Ban ɗauka zai cika wannan Alƙawarin ba sai kuma gashi ya cika don yace sadaki kaɗai zaka bada Rabi'atu dai ƙanwarka ce da ubanta dani cikinmu guda dan haka In har ni na haifeka kamin alfarma kaje ku sasanta In yaso ita Hauwa'u sai ka aure ta inta kammala karatunta ba zan hanaka auren wadda kake so ba Amman Nima ka auri wadda Mukai Alƙawari Nida ɗan uwana ko Allah yasa silar auren ku zumuncin mu ya daidaita" A lokacin jikin Saadik babu abin da yake sai rawa hatta bakin shi Gumi ya jiƙa masa rigar shi, Dama ga zafin ɗaki dan lokacin babu wutar Lantarki. Inna zatai magana Baba ya ɗaga mata hannu alamun baya buƙatar cewarta, Sai taja baki tayi shuru. Numfashi ya dinga ja yana ambaton sunan Allah kafin ya samu Nutsuwar Furtawa Baba Kalmar. "Amman Baba hakan ba zai jawo mana ƙasƙanci ba, Mutumin da baya neman ka Yana matsayin ƙaninka amman ya nuna yanzu Shi mai Kuɗi ne ya janye zumuncin dake tsakanin ku, Baba ka rabu da shi Ka Nema min Auren Hawwa'u ita ce wadda take matiƙar sona domin Allah Nima Kuma nake sonta Amman ita waccan da ban santa ba bata sanni ba Ko sunanta ban sani ba tayaya zan aureta Baba?" Baba yayi murmushi irin nasu na manya kana yace. "Ka bar batun Amadu Yaro ne ɗan halak Shu'umar macce kawai Ya haɗu da ita Ina son ka auri Rabi'ah ne Ko ta sanadin auren ku Allah zai sa Zumuncin mu yayi ƙarfi nida ɗan uwana, Fanni zamantakewa kuwa nasan Autana Ba ragon namiji bane in mace Huɗu ya aura zai iya ɗaukar Nauyi ci da shanta Hauwa'u Kuma In Allah ya yarda bata da Miji Sai Kai Kodan karamcin Mahaifanta garemu" Yayi Biyayyar Amsawa Baba tare da amsar Auren ne badan komai ba sai dan tsan [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *005* Da sassarfa yake tafiya cikin gidan nasu harya ƙarasa cikin rumfar da mahaifin nashi tare da ɗan uwan shi, suke zaune da sallama a bakin shi Ya Nemi Gurin zama daga Nesa dasu yaɗan Sunkuyar da kanshi a ƙasa. "Sadauki! dama Babanka Amadu ne yazo min da magana shi ne nace a kira ka Amadu ga ɗan naka nan sai kuyi maganar" Har Lokacin bai ɗago kanshi ba Abbah ya gyara Murya tare da cewa. "Kwanakin baya na taɓa zuwa da maganar ka fara zuwa Inda nake a kasuwa amman ka nuna baka ra'ayi shine nace yanzu meze hana kazo wajan nawa Kodan Iyalin da zaka fara riƙewa kasan yadda rayuwar ta koma, Batun auren ka da ƴar uwarka Ina son daga na dawo ai maganar auren ku sadaki kaɗai nake buƙata zan baka Gidan zama da Mota sannan kuma ga kasuwa duka Allah ubangiji yasa wa auren ku albarka Amin" Baba ne kaɗai ya taya Abbah amsawa da Amin amman gogan naku ko gezau bai yi ba sai da Baba ya kuma cewa. "Wai Sadauki! ba kaji maganar Kawun naka bane?" A hankali ya ɗago fuskar shi wadda tai jajir abin ka da fari yawanci in yana cikin damuwa Fuskarshi ja take Musamman saman Hancin shi. Murya a shaƙe kamar an masa dole yace. "Abba nagode da karamcin auren da kabani ma kaɗai ya wadatar sauran duk na yafe, da farko ina da sana'ata duk da a wajan wasu kamar ta ƙasƙanci ce amman ni a wajena sana'ata tana da Muhimmanci a gareni domin da ita na dogara har na tsaya da ƙafafuna, Gwangwan nake kamar yanda ka sani ina Auna ƙarafa ina siya nima na siyar na sami abinci, Sannan Batun Auren gaggawa dan Allah Abbah ayi min uziri kaɗan zan ƙarasa shirina sabida Kutsen da aka min son samu na zauna agidan kaina amman hakan baze samu ba dan haka zan kama haya Kuma zan mata lefe daidai ƙarfina son samu ta saka kayan Da Mijinta ya ɗinka mata sabida haka ayi min uziri har na kammala komai sena yi magana" Gaba ɗaya Abbah shagala yayi da kallon Saadik a ranshi kuma yana jin wannan shine Mijin da ya cancata Ƴarsa ta aura sabida ta Ko'ina jarumi ne, Baba kuwa baiji mamakin furucin ɗan nasa ba Yasan shi sarai shiyasa yaƙi amsawa Abbah tayin daya masa Sabida yasan da wiya Saadik ya amsa aikuwa gashi nan ba'a je ko ina ba yaƙi. "Shikenan Abubakar! Allah yasa albarka a lamarin Na gamsu da bayananka, Kuma Ina fatan Zaka riƙe ƴar uwarka da amana" Bai Motsa ba, bai kuma tankawa ƙanin mahaifin na shiba. "Zaka iya tafiya" Cewar Baba. Da sauri Abba yace. "A,a dan Allah Abubakar, ka ƙara komawa wajanta Ku sake tattaunawa sabida Ku fahimci Juna don zaman lafiyar auren ku shine kwanciyar hankalin mu" Tausayi Abba ya bawa Saadik da ɗan sassauci yace. "In sha Allah" Yana danne takaicin ta na jiya dan shi ba soko bane baya jin zai iya kai ƙarar mace bada ban haka ba da yace ya mata faɗa ta gyara kalamanta dan gudun kumburin baki. Kafin Saadik ya kai da ficewa Abbah ya dakatar dashi tare da ɗauko waya ya shiga Kiran Adaah Ƴar Mulkin anci sa'a tai tashin wuri tana bakin gado taga Kiran Abban ta ɗauka Magana ɗaya yayi mata ya kashe wayar Umarni ya bata kamar haka: "Ki shirya Anjima kaɗan Ɗan uwanki zai ƙara zuwa Ku tattauna Saura naji Kin masa Shirme" Tana shirin magana ya kashe wayar ƙafa ta fara dirawa tana ita Babu inda zata kuma fita Seta tafi wajan Momi sai dai koda taje Room ɗin Momi bata sameta ba. Juyawa tayi cikin Rooom Ɗinta tana gunguni. Tashi Abba yayi bayan ya direwa Baba damin Kuɗi Amman fafur Baba yaƙi amsa Da damuwa Abba ya maida kuɗin gaba ɗaya Yanayi Baba baiwa Abba daɗi ba wato shi horo wani bin base an maka faɗa ko an maka magana ba. In har kana da hankali in ka ɓatawa Mutum rai zaka gane a mu'amalance kuma cikin sauƙi. Sanda Saadik ya fito daga Rumfar Baba ɗakin sa yayi Niyyar wuce wa sabida yana son yau yakai wasu ƙarafa daya siya can ƙofar ruwa shine yasa ma har yayi tashin wuri. Innah ce ta tare shi da Kofi fal koko aciki. "Dan Allah karka fita baka sa komai cikin kaba zoka sha kokon nan yaji sugar na sanka gwanin shan zaƙi" Murmushin daya kasa yi a rumfar Baba ya sakar mata yana ƙarasowa gabanta. "Innah akwai abin kari a ɗakina fa Naga ni baki sako min tuwo ba Ƙosai kika zubon da Kunu" Ya faɗa cikin tausayin mahaifiyar shi wato shi ta bambanta a wajan karin kumallon ta soya mai Ƙosai tai masa Kunu gida Kuma tuwo ɗumame da koko. Bai bata zarafin magana ba ya karɓi Kofin yana ɗan Kurɓar Kokon adaidai nan Abba da Baba suka fito Fuskokin su ƙunshe da Murmushi wanda zai nuna maka girman soyayyar Junansu a fili. Har gaban innah Abbah yazo tare da aje mata kuɗi yana cewa. "Gashi innah babu yawa ban san laifin dana wa yaya ba samsam yaƙi amsar kuɗina, wallahi ason samuna Yaya ya daina fita saida naman nan" Baba yayi dariya kana yace. "Wato so kake zuciyata ta mutu kenan ai in kaga na dena saida naman nan Ciwo ne ko Mutuwa amman ba zan zauna na kashe zuciyata ba" Sai Lokacin Saadik yayi wani basaraken Murmushi tare da cewa. "Haba Baba in sha Allahu cikin farin ciki da lafiya zaka daina wannan saida naman nan kusa" Yana faɗa yaja baki yayi shuru shidai Abbah Murmushi yake wani farin ciki yana ƙara baibaye masa zuciyar sa. Rabon daya sami farin ciki irin wannan harya manta dama haka kasancewa Cikin ƴan uwa yake yasha auna zuwa sai Hajiya maryam ta tare shi da zantuka a haka yake shagala sai yau Allah ya ƙaddara zai shigo wanda rabon daya zo ɗin ya jima ada kuwa Kullum ne in zai fita sai yazo wajan ɗan uwan nashi. Sallama sukai, Da Innah Da shi da Baba suka fita sai dai Ko a ƙofar Gidan ma Baba yaƙi shiga motar Abbah babu yanda Abba bai da shi akan yazo su aje shiba Amman yaƙi Jikin Abbah ne Yayi sanyi tabbas yasan ɗan uwan nashi ya janye masa ne sosai tinda har yaƙi amsar Dukkan ta yin daya mashi. Bayan motar su Alhaji Amadu ta tafi Baba ya fita titi ya tari abin hawa zuwa kasuwa yana jin hakan yafi masa Mutunci duk da shi ba zai ce ga wani abu da Amadu yayi mishi ba, Amman Gorin da matarshi tazo har Gida tayi musu shida Innah yasa suka tattare lamarin Amadu suka aje Kuma Allah ne ma ya rufawa Matar Amadun asiri data zo harta tafi Saadik baya gida domin ba zai ɗauki ƙasƙanta Iyayen shi ba Shiyasa daga Innah har Baba basu faɗawa kowa a ƴaƴan suba hatta shi Amadun bai sani ba kawai dai sun kama kansu ne. Daga cikin gida Saadik ya tokare a gefen katanga. Ya cigaba da sauraron innah wadda take miƙo masa kuɗin da Abbah ya aje mata. "Auta ungo waɗannan kuɗaɗen kai da kake da hidima a gabanka Ko wani abun ka rage danni babu abin da zanyi dasu hidimar gabanka tafi tawa" "Haba innah dan rashin imani a baki kuɗi na saka hannu na karɓa, In da dai ina da Dama da tin yana nan zance kada ki amsa masa kuɗin sa to kin riga da kin karɓa lokaci ya ƙure" Innah ta zuba masa ido kafin ta janye kuɗin ta aje a gefenta kana ta dube shi a nutse. "Zauna muyi magana Sadauki" Da yake ita da Baba ba kasafai suke faɗin Saadik ɗin ba sunfi kiran shi da Sadauki! Ya nemi guri a bakin ƙofar Kitchen ya zauna. "Mai yasa kake da sa abu aranka ya kamata zuwa wannan Lokacin , ka rabu da ƙullin ƙanin mahaifin ka a zuciyarka, Wallahi Ba laifin shi bane a rayuwa babu abin da Amadu baiwa mahaifinka ba macece Allah ya bashi marar mutunci a tarihi ban taɓa ganin mace marar kirkin Maryam ba Amman shi ka duba kodaga mu'amalar shi damu kasan akwai ƙauna mai girma" Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace. "Nifa innah ba ƙullin shi nayi ba, meze sa na ƙulle shi a raina bayan alhakin kulawa daku ba a kanshi ya rataya ba, kawai Innah bana son ka cika zaƙewa ne a lamarin mai kuɗi, Banyi niyyar bayyana wa kowa ba" Sai yaja bakin shi yayi shuru ya kasa ƙarasa maganar da yake son faɗi. Ta zuba masa ido tana son jin sauran ƙarin bayanin. Ya fesar da zazzafan Huci yana shirin yin magana. Suka jiyo muryar Faridah tana kiran Sajjad Sai dai tuni shi Sajjad ɗin ya biyo ƙanwar sa Sajidah sun shigo tsakar gidan Innah. Har rige rigen hayewa cinyar innah suke suna dariya Faridah ma dariyar take bayan tai sallama tana cewa. "Karfa ku ɓallamin cinyar uwata wallahi sena zane yaro" Innah tana dariya tace. "Baki isa kin taɓa yaran nan a gabana ba, keda Hajjo ƴaƴan ku basu da sakewa sam sam bini bini kun daki yaro ku haka nai rainon ku" Dariya faridah ta saki tana kawowa Saadik dukan wasa kasancewar shine sakon ta. "Dagiya ba magana ne ka wani cinno baki ko shagwaɓar autan ce ta tashi yau?" Harara ya ɓalla mata da sauri tai masa gwalo ta shige ɗakin Innah ita kuwa Innah me zatai In ba dariya ba Dama indai Faridah ta zo se sunyi faɗa da Saadik, Kuma dama sun saba tin kan tai aure ita tsokana shi fushi datai masa zai kamata ya zane wani bin sai Baba ya kawo musu ɗauki to ko datai auren bata daina tsokanar shiba shiyasa basa wani shiri yafi shiri da Marigayya Mai sunan Innah Aunty uwani ita ce Mahaifiyar su Ummi wadda ta rasu a garin haihuwar zara shine Yaran nata suke hannun Innah da Baba, Kasancewar Aunty Uwani akwai haƙuri ita ce mai ɗaukar Rigimar Saadik, akaf ƴan uwan nashi. Farida ce keta ƙwalowa Innah Kira daga cikin ɗaki tana cewa. "Innah wannan sabon Hijabin naki ne ina so wannan Sabuwar Doguwar Rigar ma ina so" Tsaki yaja yana cewa. "Kedai Kinji Kunya wallahi nan gaba kaɗan zan soma rufe ɗakin Innah duk sanda Kika zo sekin Rabata da kayanta" Dariya ta saki tana cewa. "Allah ma dai yasa kafin kazo duniya nazo" Wannan kalma tana ƙona masa rai tsaki yaja wanda Innah ta fara magana. "Kinga fito ki tsincen shinkafa tinda Allah ya kawo ki, Dama su Khadija sai ƙarfe Biyu suke shigowa gida sabida makarantar tasu akwai tazara" Daga ciki farida tace "Innah yau base kinyi girki ba, Abban Sajjad zai koma Gida Anjima kafin nan Mai aikina ta gama abinci zata zubo mana na faɗa masa ma yace zai kawo" Innah salati tahau yi tana tafa hannu. "Faridah wannan wani irin sakarci ne Ban hanaki dafo mana abinci in zaki zo ba to ni wannan abin kunyar bada ni ba" "Innah wallahi shine yake sawa Ko gidansu In zani sai yasa an wa Mama Girki kuma yace dake da mama duk iyayensa ne yau ma Na shirya a makare ne shi kuma yana sauri zai ajeni da senai girkin zan tawo se kawai na barwa mai aiki nace tayi" Innah tace. "To madalla zan tuntuɓi shi Mijin naki na kuma haneshi, dammu ma Allah bai hanamu abinci ba" Dariya faridah tayi sosai kafin ta furta. "Innah shima ba raina mana yayi ba kawai kyautatawa ce, kuma Innah idan yazo ɗin ki tambayeshi wallahi Innah babu yadda za'ai na ɗauki abincin Mijina ko wani abun daya kawo Gida nayi kyauta dashi batare daya sani ba Komai zanyi tare da sanin sane da amincewar shi. Murmushi Innah tayi. "Na sani faridah Ina dai ƙara gargaɗin ki karki yarda Ki bada Kome ye na mijinki batare da sanin shiba, Kuskuren da yawanci mata suke kenan Kyautar kayan abinci komai ma suna iya badawa dan sunga na mijin sune wannan Kuskurene babba ba'a hana ka bada ba Amman ya zama ka bayar da Amintar sa da yardar sa wannan In kayi hakan babu laifi" Saadik ne ya katse maganar tata yana cewa bari ya tashi fita zaiyi Ƙofar Ruwa yabar su Umar a shago in an gama Girki a miƙa Musu. "Dagiya zona aike ka Ƙarshen waya ka siyo min Gurji" Seda ya taka bakin Ƙofar ya hangota kwance a gadon Innah sannan yace. "Inda kina da Biyayya da Har mai Gurjin zan kawo Miki amman Ji bakin ki wai Dagiya mtss" Farida dariya innah dariya Shidai kama Hanya yayi ya fice daga tsakar Gidan waya kaɗai ya ɗauka ya rufe ɗakin shi ya fita Titi  seda ya biya ta ƙaton shagon shi wanda ya cika da ƙarafe buhunna robobi kala kala gasu nan Umar yana ta auna ƙarfe a kilo Usman yana bawa wasu Yara canji. Sallamar shi yasa suka Jiyo suna masa barka da shigowa ya sami saman Banci ya zauna. "Kawu Saadik! dama tin ɗazu muke Jiranka masu ƙarfan Motar nan sun zo wai ba zasu siyar Dubu Goma ba" Ya ɗan kalli Umar yace. "Sai nawa suka ce?" Umar yace "Sun ce sai dubu sha uku" Ya ɗan murza kanshi tare da cewa. "Ba matsala, Usman haɗa min ƙarafan can, Ka kira min Babur a titi" Ya juya yana kallon waje Inda shi kuma Usman ɗin ya fita da sauri. "Ina salman ne?" Ya furta. "Kawu Saadik wallahi sai ka zane Shi sannan zai Nutsu ɗazun nan naganshi da Tawagar ƴan Goburawa wai sun tafi Boll ko makaranta yau bai je ba" Ya ɗan kalli Umar kafin yace. "Kana kallon shi ba zaka Hukunta shi ba ni kake jira na zane shi kome?" Umar ya sada kai ƙasa bai kuma magana ba Usman ya zo ya kama kayan suka soma fitarwa wajan Baburin ɗan sahun da Usman ya kira seda suka cikata tab sannan Saadik ya hau gefen Drivern suka tafi. Ya jima a kasuwar kafin ya kammala komai Lokacin Ƙarfe Huɗun Yamma Sallar la'asar yayi sannan ya tari abin hawa. "Gadon ƙaya" Ya faɗa a dake sabida son ya cika alƙawarin daya ɗauka. Domin yana jin Yadda ya gajin nan baze iya Komawa Gida sannan ya kuma fita wani Gurin ba da kwatancen da yakewa mai ɗan sahun suka ƙarasa Har bakin Gidan kawun nashi ya fito ya bawa mai Ɗan sahun kuɗin shi ya taka har bakin gate ɗin gidan Tarin takaicin Jiya ya shiga Faɗo masa aranshi kawai dan karya ma Kawun shi gardama ne yasa zai ƙara zuwa wajanta Amman da baya  jin zai ƙara komawa inda take. Mai gadi ya leƙo ta ƙaramar Ƙofa yana tambayar waye? Ya gyara tsaiwa kafin yace. "Baƙo ne" Mai gadin yace. "Alhaji baya nan Hajiya babba bata nan sai Hajiya ƙarama" Tsaki Saadik yaja kafin ya koma da baya yana ƙoƙarin tafiya mai gadin yace. "Bismillah ai na gane ka kaine wanda ka zo jiya" Bai tanka masa ba, sabida shi wani bin baya son yawan magana yana tafiya iska tana kaɗa shi sabida yalwatuwar ganye da bishiyun dake cikin gidan. Zama yayi a ɗaya daga cikin ƙayatattun Kujerun dake zagaye da Farfajiyar gidan da sauri mai gadin ya wuce shi ya ƙarasa Bakin Ƙofar falo ya shiga Kiran Maimuna, Wadda takewa Adaah Hidima maimuna ta fito daga Kitchen tana amsa Kiran mai gadin wanda ya sanar da ita ga baƙo nan yazo da alama wanda jiya yazo wajan Hajiya ƙarama ne ya dawo. Maimuna ta koma ciki Ƴar Mulkin tana zaune a falo na biyu ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya tana waya da Habib Ganin Maimuna bai sa ta katse wayar ba maimuna ta tsugunna har sai da ta kammala wayar sannan Maimuna cikin ladabi tace. "Ranki ya daɗe kinyi baƙo yana waje" Taɓe baki tayi sam tama mance da sharaɗin Abbah na wayar daya mata akan zuwan wancan Ƙolon bata Motsa daga inda take zaunan ba kamar an mata dole tace. "Kice masa ya shigo ciki in ya shigo kuzo tare ki tawo Min da Ruwa a cup da Moper" Daga haka ta koma ta kwantar da kanta ajikin kujerar da take kai. Maimuna cikin ladabi ta ƙarasa wajan Saadik, yadda yake a zaune seta daburce sabida masifar kwarjinin daya mata da ƙyar ta iya haɗa kalmar ya ƙaraso Ciki ta miƙe. Kamar baze tashi ba se kuma ya miƙe ɗin shima suka ƙarasa Ciki seda Maimuna ta ɗauko mata ruwan da Moper ɗin sannan suka ƙarasa shiga Ciki yana biye da maimuna. Wadda ta aje saƙon ta juya da sauri shiko daga bakin Ƙofa ya tsaya cak ya tokare shibe shiga ba shibe koma ba........ 09022260850. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *006* Kallo ɗaya yayi mata yayi saurin kawar da kanshi, Gaba ɗaya shigar da take jikinta bata kamata ace ɗa namiji ya sameta a cikinta ba, Juya masa Baya tayi ta cigaba da danna wayarta bata jin zata masa magana idan zasu shekara a haka. Shima daga ɓarin shi gefe ɗaya ya zubawa ido sabida Gudun kar Idanunshi su ƙara mugun gani, Sai dai daga cikin zuciyar shi tafasa take kamar zata tsaga masa ƙirji ta fito wannan wace irin Yarinya ce wadda bata da Kunya bata da Tarbiya ko kaɗan sam baiji sha'awar auren ta ya kawota gidan shiba, Inda yana da dama da ya warware maganar auren su saidai Iyayensu sun riga da sun yi Alƙawari babu yanda za'ai yayi silar Rusa wannan Alƙawarin. A fusace ta yunƙura daga kwanciyar ta nufo ƙofa zata fita Jikinta sanye da Doguwar riga mai hannun shimi wadda tai matiƙar kama mata jikin nata surarta mai ɗaukar Hankali ta bayyana kanta babu ɗankwali Siririyar kalaban dake kanta duk ta Miƙe tsaye sabida ita bamai yawan gashin ka bace. Ƙoƙari take ta raɓe shi sai dai hakan ba ze yuwu ba sabida Ya riga ya tokare ƙofar. "Malam zan fita ka wani zo ka cika mana wuri sai kace gidanku" Har ga Allah shi bema san ta ƙaraso ba hankalin shi ya tafi tunanin neman mafitar zamewa auren ta sai jin dirin muryarta yayi a gab dashi cike da rashin kunya. Yana ɗago kanshi da nufin ya kalleta tana mai juyawa ita kuma da sauri wannan ruwan da Maimuna ta kawo mata ta ɗauko babu tunanin komai tayo kanshi da ruwan mai yawa a cup ga ɗan karen sanyi ta juye masa shi tas a jikinsa damma tsayinta bai kai ko kafaɗar shiba da tindaga saman kanshi zata zuba Ruwan. Tsayawa yayi yana kallonta ruwan na ɗiga daga jikin rigar shi Adaah dariya ta sa tana Nuna shi da yatsa. "In banda kai sakarai ne ta yaya zaka yarda da maganar aure na kalleni" Ta faɗa tana juya jikinta sannan ta nuna shi. "Kalleka dan Allah kayi kama da kalata jiba kayan jikinka wani ƙazami dakai wawa Mtsss" Ta faɗa tana Ƙoƙarin Nufo shi. Ƙura mata ido yayi wanda yayi jajir har wani ruwan bala'i ne ya kwanta Jijiyar dake kanshi ta Miƙe babu abin da jikin sa yake sai rawa yana mazari kamar wanda yasha maganin tauri Ƙafarsa ke takawa tana wa gangar Jikinsa linzamin Isa gabanta, wanda ita kuma Adaah keja da baya gaba ɗaya idanun shi ya tsoratata ga gida babu kowa yana binta tana yin baya tana yarfe hannu. Cikin Hukuncin Allah sai da yakai ga sunje ƙarshen Falon ta raɓe da bango ta ɗora hannunta duka a fuskarta ta rufe gaba ɗaya yanayin sa ya firgitata sai tace ita bata taɓa ganin Namiji mai Irin suffar shiba Ingarman namiji ne kamar wanda yake cin ƙarfe. Hucin Numfashin sa mai zafine ya daki fuskarta hannu yasa ya tokare bangon data raɓe ɗin wanda Sauran kaɗan fitsari ya biyo ta jikinta sabida kaɗuwa. "Dani da ke waye sakarai?" Ya nisa kafin ya cigaba. "Sakarai shine mai cusa kanshi inda ba'a neman shi, tallanki aka min aka liƙamin ke yau ɗinnan sai da Ubanki ya biya gidanmu ya ƙara roƙata akan nazo wurin ki To bari Kiji bakya Birgeni baki min ba cutar dani akai da Biyayya zan karɓeki danni bana Bijirewa mahaifina Amman wallahi ban taɓa ganin halittar dana tsana na ƙyamata Lokaci ɗaya ba kamar ki, Kisa a ranki zanyi auren cikon Umarni ne dake ba domin soyayya ba ƙazama wadda bata san Ciwon kanta ba bata san martabar Jikinta ba shasha sha" Ya faɗa tare da jan wani irin tsaki mai ƙarfi ya juya da sauri yabar falon Da wani irin yanayi Adaah ta zame daga tsaye ta zauna ta ɗora hannu aka tana rusa Kuka. Ba'a taɓa Yarfata kamar yanzu ba  ya cuceta ya danƙara mata maganar data fi marin daya mata Jiya illah. Tashi tayi tana watsi da kayan falon tana kuka tana ihu tana Jin dama Allah zai karɓi ranta kafin Lokacin auren su yayi. Da sauri yake fita daga gidan Ko ina na jikinsa Rawa yake har Lokacin idanunshi a juye suke  kamar ya sha ƙwaya Allah ne kaɗai ya kaishi Titi Lafiya ya tari abin hawa zuwa gida. Ya ci alwashin Ba zai ƙara komawa wajanta ba, Kuma Yana fatan Allah yayi gaggawar Watsa lamarin auren su baitaɓa ganin Mace irin ta ba wai dame taƙe taƙama ne haka? Gumi ne ya cigaba da yanko masa ta ko ina Kirjinshi na masa zafi da taimakon Allah ya ƙarasa Gida yana shiga ya faɗa ɗakin shi ya rufe kanshi. Babu abin da yake se mayar da Numfashin Bacin rai, a haka ya zauna har Lokacin magariba yayi lokacin yaji zuciyar shi tayi sanyi sai yayi alwala ya fita masallaci. Tin suna tafiya mai daɗi har sai da Momi ta ƙosa ta dubi Lubna wadda take ta Hira da Drivern ta da alamun sun saba irin tafiyar. "Waini Lubna ina zaki kaini ne har yanzu bamu ƙarasa ba duk sammakon da Mukayi" Lubna tayi dariya tare da cewa. "Cinikin kanki zanyi don Kin san Kanki zeyi kuɗi" Dariya sukai Driver yana karkata kan motar suka nausa Cikin Jeji Momi ido kawai take zarewa Ko yaya Motar ta Bugu Momi seta hau salati Gaba ɗaya tsoro ya kamata haka sukaita tafiya har sanda suka shiga ƙauyen. Tafiya kaɗan sukai suka ƙarasa Ƙofar Gidan Mai Rumfar Kwano mata ne zazzaune ga masu awara nan da masu wainar Gero ga masu Nama driver yayi parking Suka fito Ƙafafun Momi duk sun kumbura sabida zama Hajiya Lubna wajan mai nama taje ta siyo Musu Ita kuma Momi wajan zama ta samu don ta gaji sosai. Bayan Lubnah ta miƙawa Driver Ƙullin Nashi ta iso wajan Momi suka fara ci batare da tunanin Yin sallah ba. Seda akai la'asar layi yazo kansu Lubnah ta dakatar da Momi ta fara shiga sannan daga baya ta Kira Momi. Babban mutum ne zaune akan farin Buzu ya sha manyan kaya ɗakin sa babu wata alama da zata Nuna wa Mutane yana Tsubbu Irin sune masu ci da Buguzun Suna tsubbu ta ƙarƙashin ƙasa a fili Kuma suna Nuna wa jama'a su Na Allah ne. Seda ya cewa Lubna ta rufe ƙofa sannan ya janyo kwanon sha ya zuba ruwa ya ɗora hannu akai ya tura gaban Momi. Zaro idanu Momi tayi tare da cewa. "Ranka ya daɗe wannan Ƴata ce Adawiyyah da Mijina a cikin Ruwa" Dariya yayi tare da shafe saman Ruwan Hoton su Adaah ya baje. Kafin yace. "Kinzo da Buƙata Biyu ta farko a Juya kan Mijinki akan auren Ƴarki Na biyu Kuma a raba shi da Ɗan uwan shi kwata kwata" Momi ta Gyara zamanta sosai Cike da mamaki tace. "Ƙwarai Ranka ya daɗe, Ƙawata ta jima tana gayan yadda ka shahara a fannin aiki amman naƙi zuwa sai yau Allah yayi, wallahi yayan Mijina ne ya sakoni a gaba na samu ada na rabasu da Kisisina, To yanzu kuma kwatsam suka Bullo da Maganar haɗin gida da ɗan shi da yarinyata Kuma wallahi ba dan Allah suka shirya hakan ba sedon kwaɗayi da son cin dukiyar Mijina" Ɗaga mata hannu yayi tare da ƙara janyo kwanan sha ya Ɗora Hannu. Akai ya kuma tura mata gabanta. Zare ido tayi ganin Hoton Mahir Ɗan Hajiya Lubna na yawo akan Ruwan. Ya kuma janye Ruwan ya maida kwanon sha ɗin yace. "Waye kika gani a ruwan?" Da sauri tace. "Yaron wajan Hajiya Lubnah ne Mahir" Yayi dariya sannan yace mata. "Kinga wannan yaron shine mafitarki da ƴarki Sabida haka zan baki maganin da zaki zubawa Mijinki a ruwa in ya sha zai baku damar Fito da zaɓinku Ina so bada ɗaukar Lokaci ba Ki zaɓa mata wannan yaro domin Shi aljanu suka Nunan a matsayin Hasken Ƴarki" Cike da ɗunbin mamaki Momi tace. "Jiya ma sai da nayi maganar Mahir da Adaah take cewa ita Inda Abban ta ya bata zaɓi data Fito da wani saurayin ta shine nace mata Ga Mahir Nan Ɗan aminiyata ashe kaga na faɗa akan Gaɓa Ni wallahi da wancan auren ƙaddarar gwara Mahir Ɗari Bisa Ɗari" Fuskar Hajiya Lubna ta Bayyana da tsantsar farin ciki bata zaci Komai zaizo da sauƙi haka ba. Maganin daya bawa Momi Ta ɗauka ta bata tasa ajaka, Kuɗi masu kauri Momi ta Kuma dire masa ta fita tabar Lubna aciki domin suyi sallama. Zuciya ɗaya Momi ta ƙarasa Mota. Bayan fitar Momi Hajiya Lubnah ta Matsa gaban Malamin tare da cewa. "Wallahi ban zaci abin zaizo da sauƙi ba, Ita ce ƙawar tawa dana so na kawo maka ita amman da yake tana da wata Irin Uwa Mai Kafiya ita ce ta hanata Bin malamai wanda Nina fahimci kamar mahaifiyar tata ta gano Wasu al'amurane ko zaka duban?" Ya janyo ƙasa yayi abin da zaiyi sannan yace. "Kawai macece mai ibada amman bayan nan babu komai, Kuma Ƙawar nan taki zata baki haɗin kai sosai akan haɗin auren ƴaƴanku sai dai banyi zaton wannan lamarin zai kunno ba da takan Mijin nata zamu fara bi, Sabida mutanan suna da ƙarfin Ibada aikin zaiyi wahalar shiga Jikinsu sai dai ita Yarinyar zamu tura mata nata aikin duk da tana da kafiya da taurin kai" Hajiya lubna tace. "Nima bata gaya min ba sai da taga abin yafi ƙarfinta kasan a hankali nake so mubi abin sabida bana son wata Ƙofa da zata nuna cewar da wata manufa Mahir zai Auri Ƴarta, Malam Mijinta Ƴarta kaɗai ya haifa kaga Idan ɗana ya auri yarinyar zamu sami dama sosai tinda Ni yanzu mai gidana ba kamar daba abin kawai fafa ce nake Musu dan bana son ƙawayena suga gazawa ta amman wallahi ranar da Maryam tace min Yayan Mijinta ya turo ɗansa Auren Ƴarta ban Rintsa ba Ni ina nan ina faman yadda zanyi na Ɓullo mata da Maganar su kuma suna can sun Min shigar sauri" Dariya yayi tare da cewa. "Aiko furucin data wa ƴarta na Auren ɗan naki aikin dana sa a gabane mai zafi ƙawarki ta fiki son duniya fa Lubna Amman zaku sami alheri sosai In Auren nan ya haɗu sabida naga dukiya sosai" Shirya yadda zata kasance suka yi har ta Miƙe sukai sallama ta ɗauki Jakarta ta fita. Jiki a sanyaye ta shiga motar Momi tai mata Murmushi. "Wato Lubna naji daɗin maganganun Malam se naji kamar nayi tsuntsu naga wannan aure ya tabbata" Lubnah tace "Kayya Maryam baki gani Mahaifin Mahir bai kai mahaifin Adaah ba?" TsakiMomi tayi. "Haba Lubna ta yaya zaki faɗi haka bayan Kuma kuna da shi daidai gwargwado ai dama ƙwarya tabi ƙwarya ne wallahi da Adaah ta auri wancan gwara Mahir ɗin sau dubu mayi tuwo na mai na nida ke" A zuciyar Lubnah Murna take tana fatan haƙonta ya cimma ruwa batun yau take kwaɗayin ɗanta ya Auri Adaah ba sabida su Gaje arziƙin mahaifin Adaah ganinta ta Hanyar auren ne kaɗai zata Iya haɗa kafaɗa da Maryam wadda ta fita jin daɗi ta ko ina. Momi keta jan Hajiya Lubna da Hira Amman ita Lubna gaba ɗaya bata tare da Nutsuwarta Idanunta ya rufe akan tunanin cikar Burinta tana Jin Kozata rasa Komi nata seta san yadda akai Mahir ya aure Adaah Domin da arziƙi a garin wasu gwara a nasu garin, Don ba tin yau Ni'imar Maryam take tsone mata idanu ba. Basu ne suka shigo gari ba sai bayan Isha'i a ƙofar Gida suka sauke Momi wadda Hajiya Lubna take ƙara gargaɗinta akan tafa yi amfani da maganin nan kartayi wasa dashi. Da shigar Momy Gida Room ta wuce tai wanka sannan ta zauna rama sallolin kanta babu tunanin komai ta kwanta a saman gado sai bacci. Wajan taran dare wayarta dake yashe acan gefe ta soma ƙara ɗauka tai ganin Kiran Abbah Sama sama suka gaisa ya shiga tambayarta Abbakar yazo wajan Adaah rasa yadda zatai tayi seta Amsa masa da yazo kashe wayar yayi ita kuma ta Miƙe da hanzari ta nufi ɗakin Adaah sabida gajiya bata barta taga halin da ƴar tata ta wuni ba......................... Bayan idar da sallar Isha'i Jidda ta fito daga cikin Gidansu Hannunta ɗauke da Jug wanda ta ciko shi da Kunun aya Shi take son kaiwa sabida yau azumi tayi bata gama abincin dare ba. Tana Ƙoƙarin saka ƙafa a soron Gidan shima yana Ƙoƙarin Shiga Yana kallonta ya ƙaraso Ita kuma ta dakata tana Juya masa Baya........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *008* A hankali yayi tattaki zuwa gabanta ya jingina da jikin bango yana kallonta ya harɗe hannunshi a saman ƙirjinshi ita kuma sai kuka take babu ƙaƙƙautawa gaba ɗaya ta cika mishi kunne Rintse ido yake yana faman hura iska daga cikin bakin shi, bai san ta inda zai fara da Rigimarta ba, Kuma bai shirya rarrashin Rikincinta ba domin yana jin makaman yaƙin shi sunyi kaɗan wajan tunkarar Rigimar Jiddah. Sai da tayi kukan mai isar ta sannan ta shiga mai da Numfashi kamar wadda tai wasan ƴar tsere a hankali ya Kusanci dab da ita Cikin Nutsuwa Muryarshi tayi Mugun sanyi yace. "Wai mai aka yi maki ban san waya taɓa min ke ba shiyasa na barki kiyi kukan ko zuciyarki zatai sanyi seki faɗa mini damuwar ki?" Wani kallo ta watsa mai da dukkan Girman idanunta waɗanda sukai jajir kafin tace. "Ina fatan Allah yasa kunnuwa na ke min gizo daga abin da naji Baba yana faɗa maka, In kuma gaskiya suka ji ina fatan nice ba wata ba" Cikin dake wa ya dube ta. "To tinda kinji ai shikenan Kinga bakina ya huta da surutu maganin mai laɓe" Juya wa yake Ƙoƙarin yayi Cike da Jarumta. Da sauri tai tsalle ta Cakumo shi ta riƙe masa Riga gam tana Huci kamar ba ita ba. "Wallahi baka isa ba sai ka faɗamin manufarka Dole ne kayi min ƙarin bayanin abin da Kunnuwa na suka ji" Da kallo yabi hannunta dake Riƙe da rigar shi cije gefen baki yayi yana girgiza kai kallo ɗaya yayi mata tak tai saurin Sakin Rigar tashi yaja tsaki Mai ƙarfi cikin Fushi yace. "Tin da kema kin soma zama mara kunya zan saita ki kwanan nan karki ga ina sakar miki ki nemi raina ni wallahi ranki zai yi mugun ɓaci, Maganar da kika ji Baba yana min kuma aure ne zasu mini na zumunci sauran ƙarin bayanin Kuma laɓen da kikai sai ya ƙarasa maki shi" Da sauri ya fice daga gidan gaba ɗaya ya barta a wajan. Idanunta ne suka soma juyawa wani irin Mugun jiri ya kwasheta. Baba dake fitowa daga cikin gida ne yaci karo da Jiddan kwance kamar marar rai cikin tsumar Jiki Baba ya koma gida ya shiga Kiran Innah yadda Baba ke Kiran innah ne ya jawo hankalin su Khadija duk suka Biyo Baba wanda yake Cewa Innah. "Hafsatu zo ki gani tawo da ruwa Yarinyar mutane mai ya sameta" Innah har zaninta na kuncewa garin sauri haka take bin bayan Baba itama yadda taga Jidda abin ya bata tsoro haka Ummi ta Ebo ruwa a kofi Innah ta shiga zubawa Jidda a jiki da shafa mata a fuska amman ko gezau da Ummi da khadija ne suka kama Jidda kamar gawa suka shiga gida da ita bisa umarnin Baba  a rumfar Innah aka shinfiɗe ta, a tabarma Baba ya ce da Innah ta cigaba da shafa mata ruwa In bata farfaɗo ba su tafi asibiti Kusan Minti Goma innah na shafa wa Jiddah Ruwa a fuska tana hura mata Iska gaba ɗaya duk sun firgita dan Khadija ma kuka take yi sosai, Sabida Jiddah Aminiyarta ce. Sai can taja wani ƙaƙƙarfan Numfashi kafin ta tashi a firgice ta Rungume Innah se kuka mai ƙarfi ya tawo mata cikin kukan take cewa. "Innah don Allah karki bari kawu Saadik! ya auri wata ba ni ba, Innah wai aure zakuyi mashi da wata?" Baba ya kalli su Ummi waɗan da suka yi saurin ta shi suka bar wajan. Rumfar tayi shuru babu abin da yake ta shi acikin ta sai sautin Kukan Jiddah. Daɗa rungumeta Innah tayi gaba ɗaya abin duniya ya taru yayi mata yawa ga tausayin Jiddah na ratsa mata zuciyarta. "Hafsatu sake ta dawo nan Hauwa'u zo kusa dani ki zauna muyi magana" Baba ya faɗa a hankali shima jikinsa yayi sanyi matiƙa duk yadda yake zaton lamarin ya wuce Zaton sa. Innah ta saki Jiddah wadda take ta faman share hawayenta Gaba daya wannan kunyar da take wa Iyayen Saadik ta kau idanunta ya rufe bata hango komi sai tina abin da kunnuwanta suka ji. Baba ya kalleta Yana ƙara jin ƙimarta da girmanta a zuciyarshi duk wannan suman da kukan akan son ɗansu ne take yi lallai wannan yarinya ta cancanci komai na kyautatawa a wajan su. "Hauwa'u ki nutsu kar shaiɗan ya saka ki ji wani abu acikin zuciyarki, Aure dai nufi ne na Allah shima kanshi sadauki! bai san da wannan aure ba, sabida magana ce ta ALƘAWARI! Wanda muka ɗaura nida ɗan uwana ga Hafsatu shaida ce abin da nake so dake shine ki kwantar da hankalin ki, wannan kukan ki daina auren ki da Sadauki babu fashi yadda yayi mana biyayya ya karɓi auren nan kema ba zamu hana ya aureki ba da zarar kin kammala karatun ki" Har baba ya kammala maganganun shi Jiddah bata ce komi ba sai hawayen da take sharewa nasiha sosai Baba yayi mata kafin ya kira Khadija yace ta rakata Gidansu. Bayan fitarsu Jiddah Innah ta kalli Baba ranta a jagule tace. "Gaskiya Babansu ya kamata a duba yaran nan shi kanshi Sadauki ba auren yake soba dan Allah karku cutar da su" Ya ɗaga mata hannu tare da cewa. "Don Allah Hafsatu kibi yadda nake so bana son ƙananun maganganu Sadauki fa Namiji ne yana da damar auren mace har huɗu sabida haka muyi wa lamarin fatan alheri" Ba don ran Innah yaso ba sai don tsananin Biyayyar Mijin nata yasa taja baki tai shuru Baba ya saka takalman shi yabar gidan Itama fita tayi wajan daka daddawarta bayan ta gama daka wa ta ɗora sanwar tuwon dare. Sai dai ƙasan ranta damuwa ce fal. Nana tana zaune a tabarma tana tankaɗe, Innah ta dube ta. "Nana ɗauko min wayata ki kiramin Babar su Hassan" Da yake bata kiran sunan Aunty Aminah Babbar Ƴarta sai dai tace mata Babarsu Hassan, ko wannan yarinyar. Nana ta ɗauko wayar ta kirata mata Aunty Aminar ta miƙa mata. Wayar tana Ringing! Innah ta kwaɗawa Ummi kira wadda take ɗaki tace mata taje wajan tukunyar tuwo taga in ruwan ya tafasa tayi ruɗe. Aunty Amina ta ɗauki wayar tana sallama. Inna ta amsa a nutse. "Innarmu barka da yammaci yanzun nan fa maganarki muke da Saadik bai jima da shigowa ba" Inna tai murmushi tana cewa. "Au dama gidan ki ya tawo to ki faɗa masa ga Jidda can tana suma" Aunty Amina ta hau salati tana cewa. "Subhanallahi Innah Jiddan Saadik ɗin to garin yaya haka ta faru?" Cikin damuwa Innah take faɗawa Aunty Amina abin da yake faruwa Shuru Aunty Amina tayi tana sauraron Mahaifiyar tasu har ta gama maganganun nata, dama kuma hirar da suke da Saadik kenan daya zo mata da maganar don duk basu sani ba. Nisawa Aunty Aminah tayi tare da cewa. "Innah karki tashi hankalin ki Addu'ar dai da ake ita za a cigaba Yanzun nan Kawu Saadik yake faɗa min ashe aura masa Rabi'atu za ai to mudai bamu da ja don aure nufin Allah ne kuma muna fatan Allah yasa albarka a lamarin, ita kuma jidda haƙuri zatai tinda dai aure halal ne ba haramun ba" Innah ta sauke ajiyar zuciya tana cewa. "Hakane yarinyar ta bani tausayi ne shiyasa naji duk hankalina ya tashi da lamarin to bari na barku ku tattauna ɗin amman kice mai ya tawo gida da wuri dan ban ganewa Hauwa'u ba" Dariya Aunty Aminah tayi tana cewa. "Wato abin cikin ƙwan yafi ƙwan daɗi innah kada fa Rabi'ah tazo ai mana ƴan ubanci" Itama innar dariya tayi tana katse wayar. Saadik ya shiga murza goshin sa cikin damuwa yace wa Aunty Aminah. "Kinga sakarcin ko don Allah menene abin suma daga maganar aure nifa bana son damuwa Allah in batai wasa ba sai na fasa auren nata ma gaba ɗaya duk wannan damuwar don wa nakeyi in ba domin taba, ba zata tayani kwantar da hankalina ba sai ɗagamin" Aunty Amina dariya ta saki tana kiran Hussaina ƴarta. "Hussaina kawo wa kawu saadik ruwa mai sanyi dan naga sai gumi yake" "Haba Yaya dole nai zufa nama rasa inda zan saka kaina ne" Hussaina ta kawo masa ruwan a plate ɗin roba ya ɗauki guda ya shanye Ganin ya sami Nutsuwa Aunty Amina ta fara masa magana. "Kabi komai cikin nutsuwa mu dama mata an sammu da kishi sai dai kowacce kalar nata daban Dan Allah kada kaiwa Jiddah magana marar daɗi kayi mata uziri ka rarrasheta, sannan batun lefen da kake min shima ba ka da matsala Abban su yana kawo min kayayyaki daga kasuwa ina siyarwa ina ɗora nawa, sabida haka zan daukar maka duk abin da kake so in yaso a hankali ni sai mu ƙarƙare" Zuba mata ido yayi harta ƙare maganar. "Yaya niko wani irin rashin imani  zai saka na amshe kayanki na saidawa nakai lefe" Yayi ɗan shuru sannan ya cigaba. "Yanzu dai ki bani account number ɗinki na saka abin da ya samu zuwa jibi in sha Allah zan ƙara sai ku sissiyo ko keda Yaya Hajjo ne" Ta kalle shi. "In banda abin ka ba daɗin nakan kenan ba, karka takura kanka akwai kuɗi a wajena kasan Bikin Hussaina yana ta ƙaratowa to na ɗau dashin dazan ƙarasa siyayyar kayan kitchen in baka son na ɗauki kayan Abban nasu saina baka kuɗin daga baya ko yaushe ka samu sai ka biyani" Murmushi yayi. "Kai Yaya nifa bashin ne bana so" Ta kalle shi. "Auta na baka kyauta tunda baka son bashi" Da sauri yace. "Wallahi ba zan amshi kuɗin kuba kowa yana fama da kanshi da ɗanshi akan me" "Saadik kenan ni na rasa irin zuciyarka Ubangiji ya sa kafi haka duk hidimar da kake mana kace kai taka tazo ba zamu taimaka maka ba, Bani manta Bikin jawahir kaifa kai mana kayan kitchen sannan Abbansu kasuwar bata garawa don Allah ka amshi kuɗin nan Saadik nasan rayuwar ana fama amman Allah zai warware" Cikin son kauda maganar yace. "Ki bani account ɗin sauri nake yi in yaso sai ki ma Yaya Hajjo waya ku tattauna nidai bana son ƙananun atamfofi gwara ko ba yawa a sayi masu aminci" Duk yadda taso su sasanta ya amshi bashin kayan kona kuɗin yaƙi Sabida acewarsa kowa yana fama da kanshi ba zaka ɗora mai wahala ba. Ya amshi Account Number ɗin nata ya saka mata Kuɗin da suka rage mai yayi mata sallama ya tafi gida duk da taso ya tsaya yaci abinci tinda an kusa gamawa amman fafur yaƙi tsayawa. A bakin titi ya sauka ya shiga shagon mai fura da nono ya siyawa innah sanin tana son surki sannan ya saiwa Zarah alewa ya nufi lungun su. Bai iya ɗakin shi dake soro ba sai da ya ƙarasa cikin gida ya sami su innah suna ƙoƙarin ɗaura alwalar sallar magariba da ake ƙoƙarin kira. Ya miƙawa zarah alewarta wadda tazo ta ɗane shi yana kallon innah wadda ta zabga mai harara. "Wai innah nikam mai nayi daga zuwana ga furarki na sayo" Sai da ta ɗaura alwalarta sannan tace. "Ka kyauta ka bar ƴar mutane cikin wani hali kai tafiyarka" Ya wani zaro ido waje. "Inna itan ce tace nai mata wani abun nifa kawai biyoni tayi da kuka shiyasa na bar mata wurin" "Oho ca nake kasan sanda ta faɗin, yanzu kayi sallah sai ka leƙa gidan nasu kaji yadda take nima danai sallar zan shiga" Ya miƙa mata ledar furar tare da amsa mata da cewa. "To" Yana juyawa ya nufi ɗakin shi da fitilar ƙaramar wayarshi yayi amfani wajan haska banɗaki yayi uzirin gabanshi tare da ɗaura alwala, ya fita masallaci. Bayan ya idar da sallar magariba, ya dawo ɗaki yayi wanka Nura saiti ya kira a waya yana tambayar shi akan koya dawo Nurah yace mishi yana bakin titi yanzu zai shigo lungun da sauri yace masa inya shigo ɗin ya biyo don Allah zai rakashi Gidansu Jiddah. Zama yayi yana jiran Nuran bayan ya katse wayar jim kaɗan nurah ya shigo tashi kawai yayi suka fita. A ƙofar gidan su Jiddah suka dakata yana tunanin ta yadda zai sami yaron da zai musu iso zuwa gidan dan shi yana jin nauyin kiran Umma a waya yace yazo. Ana haka Fa'izu yayanta ya ƙaraso ƙofar gidan yana ƙoƙarin kashe babur ɗinsa ya ga su Saadik waɗanda suka ƙarasa gaban shi suna miƙa mai hannu. Cikin mutuntawa suka gaisa yace. "Kuma kunzo basa gidan kenan? nima sai da na zo bakin layin ummah ke faɗa min, suna asibiti Jikin Jidda babu daɗi" Da sauri Saadik ya kalli fa'izun gabanshi ya faɗi tofa abin yayi zafi kenan harya kai da zuwa asibiti. Cikin sanyi yace. "Okay wane asibitin kenan bari mu ƙarasa" Fa'izu yace. "Nan asibitin Charity na bakin titi  ko wani acikin ku zai hau bayan babur ɗin muje tare?" Saadik ya kalli nurah wanda shima ya kalli saadik ɗin kafin Nuran yace. "A,a bari mu tafi bibbiyun tafi daɗi" Fa'izu yaja babur ɗin nashi ya tafi su kuma su nufi bakin titi. Gaba ɗaya Saadik ji yayi garin yayi masa zafi fargaba ta cika zuciyarsa sai dai da yake akwai shi da dauriya yasa fargaban bata fito fili ba. Duk Hirar da Saiti ke yi masa kawai jinsa yake a haka suka ƙarasa titi suka sami napep tafiyar kaɗan ce ta kaisu asibitin wanda yake ɗan ƙarami ne na kuɗi. Suka sauka tare da bawa mai ɗan sahun kuɗin shi, suka shiga cikin asibitin. Suna shiga shima fa'izu na ƙarasowa sabida haka a tare suka ƙarasa cikin ƙaramin ɗakin da aka kwantar da jiddan bakin su dauke da sallama. SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *007* Kwantaccen murmushi ya saki yana shafa saman kanshi da hannun shi guda ɗaya, haka nan ya ƙarasa gefen data mayar da kanta ya zuba mata ido tamkar ranar ya fara ganinta, Har Lokacin murmushin kuma bai gushe daga saman fuskar shiba. Turo baki tayi gaba tana ƙoƙarin sake juya masa baya yayi saurin jan gefen Hijabin ta ya wani marairaice kamar wanda yake roƙar ta gafara tare da cewa. "Haba ƴar aljannah, ban sanki da fushi ba haba Hauwa'na mai jiddana" Yadda yayi maganar ba ƙaramar dariya ya bata ba, Seta sa hannu ta rufe baki tana dariya ƙasa ƙasa, ya wani gyara tsaiwa ya ɗan tsira mata ido kaɗan sannan ya kauda idon nashi. "Yanzu dai ki wuce muje cikin gida Innah tace bakya zuwa kwana biyu sabida kin zama surukarta tace ko kin ganta guduwa kike yi" Zaro ido tayi kaɗan cikin sanyin halinta tace. "Wallahi ina zuwa kawai kwana biyun nan ne, Bana zama kaima ai kasani sauka ta sakoni gaba sai munyi zan sami sukunin zama" Yadda tai maganar ya kwaikwaiya sai ta kawo masa dukan wasa tana shura ƙafafunta da gudu yayi soron gidansu ta bi bayan shi da wayo ya jata har Rumfar Innah wadda duk suna zazzaune an kunna Fitila mai farin ƙwai sabida babu nepa. Su kansu su Ummi zuba masa ido sukai ganin yadda ya faɗo Rumfar yana dariya wadda tai mugun yi masa kyau don shi ba ma'abocin yin ta bane. Inna ce tace. "Lafiyar ka kaikam ka faɗo min ɗaki kana faman dariya" Muryar shi ce ta katse maganar Innah inda yake wa Jiddah magana yana waigowa wajan innah. "Ki shigo mana kin wani raɓe to wai gidan baƙon kine?" Sai lokacin Innah ta fahimci silar dariyar tashi wato tare da Jiddah suke. Sai ta kada baki cike da Murnar Ganin Jiddan tace mata. "Maza shigo Hauwa'u ni na rasa kwana biyu kunyar da kike ji tawa Ko a waje bana ganin ki ko wajan ƙawar taki bakya shigowa duk sabida Sadauki?" Duk su Ummi dariya suka saka Banda Saadik daya ɗaure fuska aiko ba shiri su Ummi suka kama kansu kowacce ta yi ɗaki sim sim gudun Karsu jawa kansu masga. Da sanyin ta tashigo ciki ta raɓe a gefe shiko ba kunya ya matsa wajanta Jug ɗin dake hannunta ya karɓa. Yana ƙwalawa Khadija kira da sauri tazo gaban shi. "Kawu gani?" Umarni ya bata akan taje Kitchen ta ɗauko masa Kofi ƙarami ba jimawa ta kawo masa ya fara tsiyaya Kunun ayar aciki ya ɗagawa ya kurɓa ya wani Lumshe ido yana Murmushi. Jiddah ta ɗan saci kallon shi tare da cewa. "Nifa ba kai na zowa da shi ba" Sannan ta kalli Innah tace. "Innah kinga ya shamin abuna ko?" Me Innah zatai In ba dariya ba kafin ta Miƙe tana cewa. "Nikam babu ruwana da sha'anin ku kunfi Kusa ba ina jinki watarana Kina kawo masa ɗan Girke Girken kuba Ni wallahi gwarama anyi auren nan mun huta" Ƙunshe fuska Jiddah tayi tana Murmushi shiko Saadik kallon Innah yayi yana cewa. "Innah ko nayi aure ina tare dake babu mai rabani dake" Innah data kai bakin Ƙofar fita tace. "Kaji dashi dai ni ba za a min daɗin baki ba" Innah tana fita ya matsa gabanta ya Miƙa mata Kofin Hannunshi. "Kema ki shiga kiji gaskiya yayi daɗi nayi dacen mata komai fa Kin iya" Juya fuska tayi tana ce masa. "Dan Allah ka matsa baya kar Innah ta shigo" Da taga yaƙi matsawar sai ta Miƙe tsaye ta fice daga ɗakin, Binta yayi da kallon So da ƙauna Tsananin kunyarta tana ƙara Jefa zuciyar shi a tafkin sonta da ƙaunarta. Da sauri yabi bayanta kafin ya fita harta kai waje dama yasan ba zata tsaya ba. Yaji daɗin Kunun Ayar sabida haka da shi ya wuce Ɗakin shi. Yana shirin zama. Nurah saiti da Abubakar Babu suka kutso cikin ɗakin nashi Saiti da Babu abokan shi ne tin na ƙuruciya da ihu suka faɗo ɗakin nashi suna rige rigen zama a saman katifa. Aje Jug ɗin yayi tare da shiga Cikin banɗaki kafin ya fito har sun shanye Kunun ayar yayi tsaki tare da cewa. "Ku dalla meye haka? daga ganin abun mutum kawai ku ɗauka Ku sha babu izini?" Babu ne ya yi dariya tare da cewa. "Dallah ware mu kaje wajan Hajiya Innah ka samo mana abinci yau ba kanta" A fusace yace "Ni ba maganar abinci nake muku ba ina ruwana da yunwarku ko gidan baƙon kune Kunun ayar da Kuka shamin zaku biyani" Nura saiti me zeyi inba dariya ba. "Haba Dagiya don Tafisu tayo maka kunu mun sha shine kake wannan masifar, Ko shima kunun nata Kishin sa kake tinda naga ƙiri Ƙiri ka hana Tafisu saka mayafi sai Hijabi" Babu ne ya tare Numfashin saiti da cewa. "In ma bita zaizai aka zubo maka to sai mu bita tare" Juya musu baya yayi tare da kwanciya a can ƙarshen katifa bai Kuma yi musu magana ba. Babu ya miƙe jim kaɗan ya kawo musu tuwon daya je Innah ta zubo musu suka ci suka Ƙoshi suka bar masa kwanukan a wajan sukai tafiyar su dama inda sabo sun riga sun saba da Halin shi abin masifa da ƙunci baya masa wahala. Uban ƴan tsaftan suna fita ya share ɗakin ya kira salmanu ya fitar da kwanukan harda sawa a samo mai garwashi ya zuba turaren wuta nan da nan ɗakin ya cika da Ƙamshi. Da yake babbar yaya Aunty Aminah Irin sana'arta kenan turaren wuta take tana aikawa gari gari. to shi kuma mayen ƙamshi ne duk sanda tayi sabo ta aikowa da Innah seta ware nashi daban tace a bawa Auta. Cire kayan Jikin sa yayi ya ɗaura ƙaramin Tawul ya shiga wanka mayen wanka ne innah har faɗa take masa akan ya rage yawan watsawa Jikinsa ruwa, to da yake shi Mutum ne mai Jin zafi Bini bini ya yi wanka hakan yasa baya rabuwa da Mura wadda inta tayar masa kamar zai Mutu domin tana Matiƙar bashi wahala. Seda ya kintsa komai sannan ya kwanta. Yadda Momi ta sami Adaah Hankalinta yayi Mugun tashi kwance ta tarar da ita sai Nishi take sabida tana da matsalar Ciwon Ƙirji Muddin tai kuka Ko ranta ya ɓaci yanzu Ƙirjin nata zai sarƙe numfashinta yayi ta kaiwa da kawowa kamar mai Asma, yawan ciwon Ƙirjinta yasa Ba kasafai take sa kaya masu matse Jiki ba musamman riga domin in har zata sa rigar data Matseta yanzu zaki ganta tana Haƙi tana nishi. Da sauri momi ta janyota Jikinta. "Haba Shalelena meze sa ki ɗagawa kanki hankali kita Kuka so kike bayan matsalar Ciwon ki wata damuwar ta Kunno kai In maganar aure ce an gama rusa ta Nan da kwanaki kaɗan zakiji labari mai daɗi ai alƙawari nai miki wannan aure bamai tabbata bane" Kwanciya tayi akan cinyar Momy hawaye na zuba kamar famfo a idanunta muryarta a dashe tace. "Baki ga maganganun daya gaya min ɗazu daya zo ba, Mai yasa Abbah na zai kaini Gidan halaka yadda nake hango idanunshi Momy baya da imani Momy don Allah karki bar wannan auren ya tabbata" Girgiza ƙafa Momy take Iya ɓacin rai Ranta ya ɓaci matiƙa Musamman yadda Adaah ke bata labarin har cikin falon su ya shigo ya gargasa mata magana son ranshi ya tafi. Wata irin tsuma jikin Momi yake Ture Adaah tayi daga Jikinta tabar Ɗakin domin ba zata Iya zama ta cigaba da sauraron wannan Ɓacin ran ba. Ranar sai ɓacci ɓarawo Amman Momi kwana tayi tana saƙa yadda zata kasance In burin su ya cika na Rusa batun auren Adaan Washe gari wajan taran safiya Abbas ƙanin Momi ya kirata a waya bayan sun gaisa yace. "Yaya maryam dama Iyah ce tace na kiraki gata zakuyi magana" Jikin Momy a sanyaye ta fara gaishe da mahaifiyarta. Cikin dattijantaka Iyah tace. "Maryam ya shirye shiryen aurem Rabin?" Momi ciki ciki ta amsa da Sai Godiya Innah bata jira cewar Momi ba ta cigaba da yi mata magana kamar haka "Amadu yace daya dawo za'a ɗaura aure, sabida haka nake son Ki turo Min Rabi tunda Ni ban isa an kawota wajena a matsayina na kakarta ba, To nina na roƙa Ki kawon Ita ta Koyi wasu abubuwan Kona kwanaki Ne kafin tariyarta Kin san Dole sai Ƴarki ta sake halinta ta Koyi tarbiyar Gidan Miji sannan zamanta zai yi daidai" Ajiyar zuciya mai ƙarfi Momi ta sauke kafin tace. "Iyah don Allah Kiyi haƙuri wallahi Nasan Adaah ba zata zo gidan kiba, kinga da nan da wajanki akwai bambanci sannan maganar Aure kuma Iyah babu Ita in sha Allahu Adaah ba zata Auri Wannan Baƙin Mugun ba" Momy ta ƙarasa maganar tana Haɗe ranta, sabida tasan koda wasa Adaah ba zata zauna wajan Iyah ba duk da ta ƙere Gidan Iyah amman ba wani babba bane tasan ƴar tata akwai Tsurfa kwata kwata bata ma saba da Zuwa gidan Iyah ɗin ba tafi zuwa gidan Ƙawayen ta masu cewa tazo ta kwana haka zata haɗa kayanta taje can Shiyasa sai daga baya ta ganar da Adan cewar bafa ƴan uwanta bane waɗancan Ƙawayene. To yanzu ma kwata kwata bata zuwa ko ina tinda ta ƙara Girma Daga makaranta sai Gida Ko sunce taje bata zuwa. Ba tare da mamaki ba Iyah tace "Nasan zaki faɗi fin haka Maryam tinda Allah ya ara miki dama har Kike ganin dan Ƴarki tazo wajena Ƙasƙanci ne, Nima ina ga bada ban albarkacin haihuwa ba da tuni Kin sakeni Kin ɗauki Duniya da ƴan duniya Kin maidasu dangi Ai shikenan Maryama duk yadda kika gani Kiyi duniya ce" Iyah ta kashe wayar Jikin Momi na rawa take sake Kira amman ba'a ɗaga ba Inda dane da hankalinta baze kwanta ba har sai tabi Iyah gida ta bata haƙuri amman yanzu da yake hankalinta baya Tare da ita yana can wajan son cikar Burinta bata sake Bi takan Iyah ba ta shiga Kiran Lubnah. Bayan Lubna ta ɗauka tattaunawa sukai akan zuwan Mahir wajan Adaah.Wanda suka bari akan yau zai shigo da Yammah tana gama wayar Kiran ƙawarta Hajiya Sa'a ya kuma shigowa akan yau ake kawo Lefen ƴar ta, wadda zata auri ɗan sarkin Yola. Momi dabur cewa ta kuma yi a daddafe sukai sallama da wannan ƙawar tata ta shiga sintiri kai ai bama zata bari Adaah ta auri wannan yaro ba ina sam ai hakan babban Ci bayane a agare ta. Cikin shirin Makaranta Adaah ta fito doguwar Rigar Material mai mayafi ce ajikinta har Lokacin Fuskarta bata saɓe daga Kumburin kuka ba ta ƙaraso ɗakin Momy domin tai mata sallama Momy ta zubawa Ƴar tata ido kafin tace. "Kai Allah ya isa! wallahi duk wanda yayi silar Jefaki a damuwa Allah ya saka miki Jibi Yadda kika Koma don Allah Kije ki saka kwalli ki gyara anjima Maheer zaizo wajanki Ɗan Babarki Lubnah in kuka daidaita Kawai auren ki zeyi mu huta da wancan auren tsiyar" Dafe gefen kanta tayi,tana rintsa ido tana so taiwa Momi magana amman ta kasa saboda yadda kan nata Ke faman sarawa Se zama tai a bakin gado da tausayi momi tace mata In bata Jin daɗi ta haƙura da zuwa makarantar. Kwanciya tayi a gefen gado tai lamo tana Tuna waye ma Mahir Ita yaushe rabonta da shi Waya tayi wa ƙawarta Husnah akan yau ba zata iya shiga School ba bata jin daɗi Husnah tai mata ya jiki sukai sallama a ɗakin Momy taita Birgima har bacci yayi awon gaba da ita dama rashin baccine yasa mata ciwon kan. Bayan sallar la'asar tayi wanka tayi sallah tana zaune Mahir ɗin ya faɗo falon yana faman Kiran Momi kallo ɗaya Adaah tai masa ta shaida shi kauda kanta tayi ko kaɗan bai mata ba, bama kalar Namijin data ke so bane. Ita ko Momi Sai Murna take suruki yazo se sawa take ana kawo masa kayan Motsa baki shiko ya wani kafe Adaah da kallo tsaki taja ta bar Mishi falon  kuma duk yadda Momi ta Bita ta rarrasheta akan tazo su gaisa da mahir taƙi daga ƙarshe ma seta sa kuka tana cewa. "Yaya zanyi ne Abbah ya kawon ɗan jagaliya ke kin kawon mai kama da fefe tsakani da Allah wazan zaɓa wallahi Momy bai Yi min ba Koni fa na fisa tsayi Ga shegen rawar kan tsiya gaskiya Momy ki sake shawara Nidai abar min Habib yafi min su dukan su" Ran Momi ya ɓaci tana gudun kar tirjiyar Adaah ya basu matsala da ƙawarta fita tayi ta bawa Mahir haƙuri akan Cewa Adan bata da lafiya ne ta kwanta. Da rawar Jiki yace amata sannu zai dawo domin shi kam yaga waje dan baya jin zai iya haƙura da Neman aurenta koda in ya auren ta zata kashe kanta ne sabida wannan Dukiya daya hanga a gidan yasan in ya auri Adaah Kakarshi ta yanke saƙa ai shi du yadda Mamanshi ke kwaɗaita masa abin Bai tabbatar ba seda yazo dan shi bai taɓa shiga Cikin Gidan ba sai yau ko kawo mamarsu yayi to daga waje yake Juyawa. Tare suka jero da Baba shi ya dawo daga shago baba kuma ya dawo daga kasuwa, Hannun Saadik riƙe da manyan ledojin daya yo  musu siyayyar gida. Har tsakar gida suka ƙarasa Innah tana daka daddawa Saadik ya mata sannu da aiki ya aje Ledojin yana ƙoƙarin ya juya Baba ya kira shi. Ya dawo gaban baba ya tsugunna Baba yace. "Sadauki nikam banji kana yin shirin bikin kaba, kaga jiya Amadu ya min waya yana ƙara tabbatar Min da ɗaurin auren ku bayan ya dawo" Cije yatsa yayi sam ya manta da maganar gaba ɗaya Tunanin shi bama ya kan batun "Baba akwai wasu kuɗaɗe dana aje akan fara ginina In sha Allah zan kaiwa Aunty Amina a fara haɗa lefe sannan batun wajan zama wannan Gidan da yake kallon mu naga masu gidan sun tashi zan wa mai gidan magana in babu wanda ya kama ni Ina so" Baba ya faɗaɗa far'a tare da cewa. "To Allah yayi jagora Ubangiji ya sawa abin albarka yanzu naji batu" Innah kam dakanta ta cigaba dayi dan ba zata tabbatar da Murna ko takaicin auren ɗan nata ba tana dai yin addu'ar zaɓin alheri kawai. Tashi yayi tare da nufar ɗakin shi. Har ji yayi kansa na juyawa sabida Tada maganar da Baba yayi. Ya zira Key a jikin Ƙofa Yaji alamun Kuka a bayan shi da sauri ya juya sukai idanu Huɗu da Jiddah Kwanon abinci ne ta kawo masa tazo Baya ɗaki zata Miƙawa Innah ta aje masa ta kuma gaida Innar wadda tace bata shigo wa kwana biyu tana shirin shiga Gidan taji maganar Baba wadda yake wa Saadik kuma tasan ba akan ta bane to wacece wannan wadda zata aure shi in ba ita ba inko itan ce ai ba shirin yanzu bane tinda taji Baffa yace seta gama makaranta. Tana ƙara kallon shi sai taji zuciyarta ta karye wani Irin ƙaƙƙarfan kuka na ƙara tawo mata....... SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹 *NA* *AUTAR MANYA* *009* Yana sa ƙafafun sa a ɗakin sukai idanu huɗu da ita kallon juna suka shiga yi kafin da sauri ta janye idanunta daga cikin nashi tana mai juya kanta gefe bata sake kallon shiba. Saiti da Fa'izu suka sami gurin zama suna gaida ummah saɓanin Shi daya ƙarasa gaban gadon yana zubawa inda ta juya idanu. Tsananin kunyar Umma tasa ya nemi gefe ya jingina kafin yaɗan rissuna ya shiga gaisheta. Ba yabo ba fallasa umman take amsawa fuskarta ɗauke da damuwa. Maganar fa'izu ce ta katse shurun ɗakin sabida tinda suka gaisa babu wanda ya kuma yin wata magana. "Ummah wai me ya sameta har kuka zo asibiti?" Shuru ummah tayi kafin ta furta. "Shirme ne kawai irin na Jidda da yarinya yo Allah na tuba namiji goma uba goma ne ni wallahi tin kafin ayi auren nan lamarin nan ya fitar min da ga rai" Saadik ya rintse ido ya shiga furzar da iska mai zafi, yaji ɗacin maganganun ummah domin tana Babba bai dace tana faɗin irin haka ba, in rai ya ɓaci zuciya ake dannewa bare ma shi bai ga wani abun zafi daya ma ƴarta ba. "Umma wani abunne ya faru da Jiddan ni duk kin sakani a duhu na kasa fahimtar abin da kike nufi wallahi" Ƙaramin tsaki taja. "Wai dan mahaifan Abbakar sunce zasu aura masa ƴar uwarsa shikenan ta faɗi a soron gidansu ta suma yana kallon ƴar tawa ya tsallake ya tafi ya barta a haka ba da ban Allah yasa mutan gidan sun ganta ba da ko mutuwa zatai babu wanda ya sani ni wallahi Jiddah batai zuciyata ba sam danni inda nice da yanzu wata maganar ake ta daban banda abin ta menene na ɗaga hankali akan namiji" Murmushi fa'izu yayi gaba ɗaya kunyar abin da mahaifiyar shi tayi yanzu ta gama kamashi inya fahimta ummah tana cikin zafin kishin ƴarta ne shiyasa take faɗin duk maganar data zo bakinta. "Ummah bai kamata ki dinga faɗin irin haka ba shi aure nufin Allah ne karku bar shaiɗan ya raba alkairi don Allah ku dinga sauƙaƙa zuciyarku" Ɗaga masa hannu tayi da sauri Saadik ya fita daga ɗakin yana jin ba zai iya jure cin fuskar da mahaifiyar Jiddah ke masa ba kuma baya jin zai iya tanka abin da take faɗa sabida yana ganin girmanta. Nura da kansa ya kulle da lamarin shiya iya musu sallama ya baro ɗakin a titi ya hango Saadik yana tafiya sabida saurin da yake har yayi wa Nura nisan da bai tunani ba sai da Nura ya ƙarasa da gudu sannan ya cimmasa. Tafe suke babu wani wanda yace wa ɗan uwan shi wani abun, sanin halin Saadik da Nura yayi in yana cikin damuwa baya magana har sai ya huce damuwar ta tafi sannan yake samun damar yin maganar. Da ƙafa suka ƙarasa gida a ɗakin Saadik suka yada zango Nura ya zauna a gefen katifa shi kuma Saadik ya shiga banɗaki ya jima aciki sannan ya fito ya ɗauki Jallabiya ya koma banɗakin ya saka sannan ya dawo ya zauna. "Wai Dagiya meya ke faruwa ne?, gaba ɗaya kaina ya kulle kaifa kana da matsala wato mu semu faɗa maka duk abin da yake damun mu amman kai zurfin cikin tsiya baka bari a tattauna damuwarka" Yaja ajiyar zuciya mai ƙarfi saman hancinsa kamar kullum yayi jajir sabida ɓacin rai da damuwa idanunsa ya kaɗa yayi ja ya kalli Saiti tare da cewa. "Aure baba zai mini, auren dole shine ita kuma take wannan shirmen har take kwanciya a asibiti" Da mamaki saiti yace. "Aure kuma kai ban fahimta ba aure da wa kuma?" Ya lumshe ido kafin ya buɗe a wahalce yace. "Wata yarinya ce ƴar ƙaninshi da sukai alƙawari zasu haɗa auren mu, to abin nima kaina da ka ya zo mini" Saiti me zeyi in ba dariya ba harda kifawa ganin Yadda Saadik ya haɗe ranshi yana cewa auren dole baba zai mashi. "To kai kam kaji daɗin ka ina ma nine aure a wannan ƙadamin ai sai ka shirya, Allah ya tabbatar da alheri inna fahimta Maman Tafisu taya ƴarta kishi take yi har taso tai abin kunya a gabanmu" Jingina kanshi yayi da jikin bango ya rintse ido maganganun Ummah sun ƙona masa ranshi, inya fahimta Jiddah ce ta haɗa masa ƙarya da gaskiya a wurinta shine ita kuma ta hau ta zauna ta goyi bayan ƴarta in ko haka rayuwarsu zata tafi akwai matsala babba tabbas! Nura ya tashi yana masa sallama tare da ce masa gobe zasu haɗu dasu Babu a tattauna akan bikin shidai bai cewa Saiti komi ba har ya bar masa ɗakin. Dama ya ɗaura alwala a banɗaki sabida haka sallar isha'i yayi har ya cire jallabiyar jikinsa zai kwanta ya tina bai leƙa wajan innah ba yasan ko yayi bacci sai ta tashe shi yaci abincin dare, sabida haka rigar ya maida a jikinsa ya saka takalmi ya fita cikin gidan. Da umar suka ci karo zai shiga cikin gidan shima, umar yaja baya yana bawa Saadik wuri don ya wuce, sai da ya shiga sannan umar yabi bayan shi yana cewa. "Dama Kawu Saadik neman ka nake naje ɗakin ka na ganshi a kulle lissafin kuɗin ƙarfan motar nan ne" A hankali yace. "Umar kaje ka huta mu barwa safiya mana sai kace zaka gudu" Dariya umar yayi yana cewa. "Gobe ina da Exams a school zan fita da wuri sabida karatu" Ya ɗan juyo yace. "Ban gane sabida karatu ba, da me kake yi da baka yi karatun jarrabawar ba?" Umar ya shafa kai tare da cewa. "Kasan yanayin shagon yanzu anfi ciniki sabida masu cire rodin aikin titi, shiyasa bana son na motsa ko ina, kasan su Usman ba kamar niba in aka ga sune a shagon raina musu hankali ake su tsula kuɗi suyi tsada" Saadik yaɗan ja ƙaramin tsaki. "Wannan ba dalili bane, kada ka kuma sake jarrabawa tazo bakai karatu ba, ka miƙo makullin shagon ni sai na zauna kai kuma ka dinga zama a gida kana karatun ka har ku gama jarrabawar Allah ya bada nasara, in da wani abun da zasu siya kuma ka sanar dani koka ɗauka kawai" Umar ya rissuna cikin ladabi yana masa godiya su kam tsakanin su da kawun nasu sai dai addu'a amman abin da yake musu a rayuwa na kyautatawa yafi gaban baki ya furta. Shiga ɗakin Innah yayi shi kuma Umar ya shiga nasu ɗakin da yake kusa dana Baba. Da sallama a bakin sa ya zauna a gefen gadon innah kafin ya jingina kansa ajikin gadon ya zuba mata ido tana lazumi ne carbi mai dubu a gabanta. Har ya soma bacci sama sama yaji muryarta tana tashin sa. "Sadauki! sadauki!! bawan Allah wato har yayi bacci" Ya Mitsika idanun shi waɗanda suka ƙanƙance sabida bacci yana kallonta. "Innah wai sai yanzu kika kammala kenan na dawo ne shine nace bara na zo muyi sallama sai da safe kuma" Ya faɗa yana miƙewa yana saka hannu a baki yana hamma. "A,a sadauki ka daure kaci tuwo mana kada ka kwana da yunwa" Ya wani zaro ido ya saki ƙaramar dariya. "Haba Innah so kike dole dai na zama ɗan gargajiya, tuwon darannan kumbura min cikina yake amman ke dole sai naci" Dariyar itama ta saki. "Dama kai tin kana yaro baka son cin abinci sosai to yanzu bara na dafa maka ruwan shayi kasha sai ka kwanta, Yaya jikin Jiddan?" Ya lumshe ido ya buɗe tare da cewa. "Da sauki tana ma gaishe ki" Ya ɓoye mata zuwa asibitin da kuma maganganun ummah sabida su iyaye ba komi ake son faɗa musu na ɓacin rai ba. "Innah kibar shayin nan zan fita na sayi kankana da lemo na sha na kwanta" Ta zuba masa ido cikin so da kauna tace. "To kadai kafe amman mai kankana zata maka maza jeka ka siyo ɗin kada dare yayi" Ya fita yana dariya ƙasa ƙasa tin yana yaro innah ta saba masa da zaman gida in baya gida yana wajan neman kuɗi ko makaranta, bata son yawo ko kaɗan kuma bata son yawan abokai ko su Nurah ma don abokan shine tin na ƙuruciya shiyasa ta barsu tare amman innah macece mai saka ido sosai akan lamarin ƴaƴanta ta gwammace in yana gida ya zauna suyi hira ko girki tare, to hakama ƴan jikokin nan nata Motsi kaɗan tace a duba mata wane takan ce Allah shike da rayuwa dai amman kaima ka kula sosai ka kuma haɗa da yin addu'a. Sai da ya je ya siyo kankanar ɗauri uku aka masa ya kai tasa ɗaki ya miƙawa Innah leda biyun aiko tana tsakar gida da fitila a hannunta. "Yawwa dama kai nake jira ka shigo to sai da safe" Ta karɓa ta juya ɗakinta. Shima nashi ɗakin ya ƙarasa yayi duk abin da zai ya sha kankanar ya yi brush haɗi da ɗaura alwala sannan ya kwanta nan da nan bacci mai daɗi ya ɗebe shi. *** Sai da Momi taga fitar Mahir sannan taja ajiyar zuciya ta shiga sintiri a falo kanta ya ɗau zafi gaba ɗaya lamarin Adaah nason bata matsala tana ganin kawo Mahir shine mafi sauƙi da kuma mafita a garesu amman Adaah zata ce beyi mata ba. Da sauri ta koma cikin ɗakin Adaah wadda take zaune ta zabga tagumi Motsin Momi yasa ta ɗago ta zubawa momi idanu har momi ta ƙaraso bakin gadon ta zauna jiki a sanyaye. Ta dubi Adaah kafin tace mata. "Ki nutsu zamuyi magana" Cikin sanyin jiki tace. "Ina sauraron ki Momy" Momi ta gyara zama tare da tattara hankalinta ga Adaah kafin tace. "Ni ban gane miki ba fa Adawiyyah jiya kinsan wahalar dana sha kuma duk akanki, tafiya mukai tamkar zamu bar garin muka je wajan wani shahararren malami shiya ce mana dole auren ki da Mahir shine mafita sauran bayanan kanki bazai ɗauka ba, amman dai don Allah kada ki watsa min ƙasa a ido duk wannan wahalar dan wa nakeyin ta hatta mahaifiyata fushi take dani duk akanki" Adaah ta nisa kafin tace. "Momy nifa fahimtata ce baki ba, wallahi gaba ɗaya Mahir ɗinne bai yi mini ba kar nazo na aure shi ku sami matsala da aminiyarki" Momi ta kwantar da murya ganin yadda jikin Adaah yayi sanyi tace. "Ki haƙuri ki min biyayya, Adaah ki auri mahir kodan mu bawa marar ɗa kunya kinji ƴar albarkar momynta in sha Allah wannan haɗi namu alheri ne abin da nake so dake da zarar abbanki ya dawo ki kafe kice ke Mahir kike so kinga daya bamu dama mu dama a shirye muke" Adaah cikin rashin madafa tace. "To Momy zan yi yadda kike so ɗin amman nikam bai mini ba" Momi tayi murmushin cin nasara kafin tace. "Zai miki ne da zarar kun zauna waje ɗaya Allah dai ya maki albarka" Kwanciya Adaah tayi a cinyar Momy idanunta suka cicciko da ruwan hawaye don dai kawai bata son ta zubawa momin ƙasa a ido ne sannan kuma ta bata tausayi na wahalar data ce mata ta sha shiyasa zata karɓi auren Mahir ɗin. Sai dare sosai Momi tabaro ɗakin Adaah har sai da ta tabbatar ta saki jikinta damuwar da ke tattare da ita ta kau sannan tai mata sallama ta baro ɗakin ta koma nata waya tayi wa Hajiya Lubna akan gobe mahir ɗin zai iya dawowa su gana da Adaah dama ɗazu ciwon kaine ya saka bata fito ba. Makirin murmushi lubnah tayi tare da cewa. "Kai haba Maryam wajan jibi ya dawo abarta ta ƙara hutawa shima kin ganshi tinda ya dawo ya ɗagamin hankalina akan ciwon kan nata" Daɗi ne ya rufe momi cikin farin ciki tace. "Ga wanda ya dace ƴata ta aura wanda ya san darajarta yasan damuwarta harya ji ya damu da damuwarta ba wancan shegen baƙin mugun ba, daya zo ya gargasa mata baƙaƙen maganganu ba, ta mutu ko tai rai shi babu ruwan sa tinda su in da zata mutu ba so zasuyi domin suci gado" Hajiya lubna mai zatai in ba dariya ba. "Kai ƙawata baki da dama wallahi" sallama sukai suka kashe wayar ranar Momi taji iska mai sanyi na shigarta domin tana jin ta gama da Kaso Hamsin cikin ɗari sauran yaƙin gabanta kuma na Abbah ne don tana jin sai dai duk abin da zeyi yayi amman bafa zata bar wannan aure ba muddin tana da numfashi! tinda har ta sami nasarar shawo kan Adaah sannan shima Mahir ya karɓi abin hannu biyu to fa tana jin sauran yaƙin gabanta ba komai bane. ** Washe gari wajan ƙarfe goma na safiya Iyah na zaune a falonta gabanta kuma Alkur'ani ne mai girma ta karanta shi, ta shafa ta aje shi a gefe ɗaya, sannan ta juya ta kalli Abbas dake zaune a gefenta yana waya, bayan ya kammala tace masa. "Abbas kira min Amadu Mijin maryam jiya nayi mafarki marar daɗi ina fatan Allah ya tsare Maryam daga sharrin dukkan abin ƙi" Abbas ya shiga kiran Abban Adaah a waya wanda sai da wayar ta katse sannan Abbah ya kira. Cikin girmamawa suka gaisa da Abbas sannan ya miƙawa Iyah. Abbah ya shiga gaisar da iyah cikin mutunci da sanin ya kamata. Iyah ta gyara murya kafin tace. "Amadu yaya batun auren Rabi ne naji kwana biyu baka bugo munyi magana akai ba" Daga wajan Abbah cikin farin ciki yace. "Alhamdulillahi Iyah dama yaron namu ne ya nemi da a ƙara masa lokaci sabida ya gama shirye shiryensa, shiyasa ma maganar ta ɗan kwanta" Cikin dattijantaka iya tace. "Haba Amadu shifa irin wannan aikin alherin ba a jinkiri wajan aiwatar da shi sabida magauta wannan abu fa duk na cikin gida ne sabida haka, ni zan sa akira min Ɗan uwan naka ai da lambarshi a wayar Abbas, se muyi maganar data kamata ayi a ɗaura auren nan sabida ina gudun kar maganar ta lalace" Abbah yayi murmushi cikin ƙarfin zuciya yace. "Da ikon Allah maganar ba zata lalace ba iya" Sallama sukai cikin mutunci kafin ta umarci Abbas daya kira mata lambar baba, wanda Lokacin yana kasuwa kiran ya shigo sama sama suka gaisa dan bai ɗauki murya ba, sai da ta masa bayani sannan ya gane nan suka kuma gaisawa a mutunce sannan ta shiga yi masa maganar data sa ta kira shi a wayar. Baba ya nisa kafin yace. "Ni bana gida ne, ina wajan nema amman bari na sa a sako miki lambar wayar sadaukin sai ki masa waya kuyi maganar, kinsan yaranmu sai haƙuri shi yace yafi son yayi komai kamar yadda ake yi a yayin aure to kuma abin ka da marar ƙarfi fafutukar ake yi" Cikin Nutsuwa Iyah tace. "Haba haba malam kamar ba gida ba nifa yadda na ɗaukaki wannan aure abin sai ya baka mamaki maza turon lambar mijin nawa muyi magana" Baba ya sa dariya yana cewa. "To to iya angode da karamci" Ya kashe wayar tare da miƙawa wani yaro dake gefen shi yace ya turawa lambar data kirashi lambar wayar Sadauki. Baba yana ta murmushin karamcin iyah wato albasa ce batai halin ruwa ba, inda tayo ruwan da batai yaji ba. Minti kaɗan lambar ta shigo wayar Abbas shi kuma ya kira wa Iyah lambar wadda taita ringing ba a ɗauka ba. Da yake fita zai yi sai ya aje mata wayar yace koda za a kira seta ɗauka suyi maganar. Tai mashi fatan alheri ya fita. ****** An sallamo Jiddah daga asibiti sai dai har zuwa lokacin Ko waya Saadik bai sake yi mata ba, kuma dama bai faɗawa Innah suna asibitin ba bare suje dubiya, Gaba ɗaya ran ummah ya gama ɓaci mita take tana cewa ga baki ga hanci ai ko iyayensa ne sa zo dubiya bare shi. Duk Jidda tabi ta damu ta ƙara komawa ƴar firit sabida Mitar umma da kuma damuwar rashin Jin Saadik.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma,9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *10* Zaune yake a bakin rijiya hannun shi riƙe da kofin da Innah ta cika masa shi da koko gefen shi kuma ƙosai ne wanda yake dangwala da yaji yana ci yana korawa da kokon. "Haba kokai fa nina fi son ka dinga cin abinci sosai koka yi ƙiba kaike nan sai tsayi babu kauri" Saadik ya ƙunshe dariyar shi sabida gudun kada ya ƙware sai da ya kammala sannan ya ɗago idanun shi ya kalli innah tare da ce mata. "Haba hajjaju kullum fa sai na fita filin ball na ɗan motsa sabida naga har tumbi ya fara zamarmin ni kuma bana son shi, ni banga rashin ƙibata ba" Innah tayi murmushi. "Sanda kana yaro kafi haka fa yanzu duk ka rame sai tsayi ma sha Allah, nidai Sadauki ka dinga zama kana cin abincin ka sosai" Tashi yayi da kofin da plate ɗin Ƙosan daya kammale ya miƙa gaban kayan wanke wanke wanda Khadija ke zaune tana yi sannan ya ƙarasa wajan Innah ya mata sallama sabida shago zai fita addu'ar alkairi ta dinga yi masa har bakin ƙofa ta raka shi Ɗakin shi ya shiga ya ɗauki wayar shi da makullin shagon da Umar ya bashi ɗazu da Asubah da suka fita masallaci ya rufo ɗakin ya fita. Yana fita suka haɗu da Baffa mahaifin Jidda shima da alamun fita zaiyi da ɗan sauri ya ƙarasa wurin Baffan suka gaisa ya ƙara masa ya mai jiki. Saadik na durƙushe baffa yace. "Malam Abubakar kafa yi haƙuri da halin mata naji duk abin da Saratu tayi maka a asibiti kuma nai mata faɗa ai wannan shashancine dama ina son ma na gana da mahaifinka gwara ko kuɗin auren ne ku kawo asan inda magana ta dosa in yaso ta na kammala karatun nata sai ayi biki ina ga abin da zamuyi kenan Amman kayi haƙuri don Allah" Saadik ya shafa kai tare da cewa. "Haba Baffa karka sa damuwa acikin ranka, Ni ban riƙe abun ba ina ga ita Ummah fahimta ce batai ba Allah dai ya shiga lamuranmu gaba ɗaya" Baffa ya ansa da "Amin" Saadik ya miƙe yayi hanyar fita daga lungun shi kuma Baffa ya ƙarasa wajan Babur ɗinshi da zai hau ya fita. Sai da yaje shagon ya zauna sannan ya ga kira da sabuwar lamba a wayar shi, ya ɗan shiga mamaki sai da ya sallami matasan da suka kawo masa wani Fayif sannan yabi kiran. Cikin kamilalliyar muryarshi Yayi sallama, daga ɓarin Iyah ma ta Amsa cikin Nutsuwa. "Dama naga kira ne ɗazu" Ya faɗa kafin yayi shuru yana sauraron abin da za'a faɗa. "Eh nice nasa a kira min mijin da bai kawo min kayan faɗar kishiya ba" Yadda ta faɗi maganar yasa yayi murmushi mai sauti duk da bai fahimci abin da take nufi ba. "Kakar Rabi ce in babu damuwa ko zaka zo muyi magana" Ya shiga tunanin wace rabin wace kakar rabin maganar iya ta kuma katse masa tunanin shi. "Rabi wadda zaka aura mana ƴar ƙanin mahaifin ka amadu" Sai lokacin ya tina Iyah bata bari ya shiga dogon nazari ba ta ce masa. "Hotoro zaka zo tsamiyar boka anan gidana yake inda hali ina neman ka yau, In kazo seka min waya Abbas ya ƙaraso dakai" Jin muryarta da alamun girma ya kamata yasa ya ƙanƙantar dakai tare da cewa. "In sha Allah zanzo idan anyi sallar la'asar" Iyah tayi masa godiya ta kashe wayar. Yaɗan nisa yana tunanin kiran data ke masa kafin ya watsar da abun ya shiga sallamar mutane bashi ya sami kanshi ba sai dab da magariba kawai bari yayi idan anyi magaribar ya je don yadda ya gaji ma bada ban ya mata alƙawari ba da baze iya zuwa ba. A masallacin da yake kallon shagon shi yayi sallar magariba da yake yau basuyi awon ƙarafe da robobi ba jikin sa tsaf yake sabida haka titi ya ƙarasa ya tari Napep zuwa hotoron da yake akwai go slow saboda magariba ce ƴan kasuwa da ma'aikatan gwamnati na tashi daga aiki bai ƙarasa ba sai wajan sallar Isha'i koda ya sauka ma sai da yayi sallah sannan ya shiga layin da Abbas yayi masa kwatance a bakin layin ya dakata ya kira Abbas wanda ya ƙaraso suka shiga Gidan Iyah. Cikin mutunci suka gaisa da Abbas sannan ya shigar da shi falon iyah tana zaune a ƙasan Carfet gabanta kuma kwanon tuwo ne da alamun ta kammala cine. Saadik ya ƙarasa gabanta a nutse ya shiga gaishe da ita. Iyah ta miƙe da sauri ta shiga wani lungu jim kaɗan sai gata da ƙaton tire wanda ta zubo masa Ruwa da lemo da Fulas ɗin Abinci a gefe. Zata aje yayi saurin tashi ya karɓa ya aje Dattijuwa ce sai dai Jikinta irin na fulani ne a murje yake babu gigita bare rakwarkwaɓe wa a tare da ita. Samun gurin zama tayi ta zauna cikin sakewa tace. "Ango na ga kayan sanyi nan ka sha na sanku sarai da son sanyi ga tuwon amaryarka nan kaci nan gida ne karka ƙi ci dan Allah" Ruwan ya ɗauka ya sha kaɗan ya aje. Tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cikin rashin sakewa. Iyah ta gyara sosai ta fuskance shi tare da cewa. "Wato zaka ji wani iri ne nasan sanda na maka waya, dama ba komai bane yasa na kiraka sai maganar auren ku da Rabi, Ni na haifi maryam mahaifiyar Rabi" Da sauri Saadik ya kalli Iyah ko kaɗan daga kammani har hali ba iri ɗaya bane da waɗancan sabida Ita wannan Tsohuwar akwai ta da mutunta ɗan adam da sanin ƙimar shi saɓanin su. Ta nisa kafin ta cigaba da magana. "Munyi magana da mahaifin ka ɗazu yace kace masa sai ka kammala shirin ka kafin ayi batun aure ban da abin ka naga duk gida ne mene zai saka ka ɗaga hankalin ka, kaga duk abin da kake da shi kayi fatana Allah yasa inga wannan aure da raina da lafiya domin shine babban burina" Saadik ya shiga mamakin furuncin nata kafin ya maida ajiyar zuciya yace. "Haka ne Baba, amman kin san lamarin yadda ya zo minne duk da bai zo min cikin shiri ba dama abin da Allah ya hore min shi zanyi kuma na gode da karamci" Iya ta kalle shi wani farin ciki na ƙara ninkuwa a zuciyarta tabbas Jikarta tai sa'ar miji. "Kayi haƙuri da duk abin da zaka gani ko kaji nina haifi Maryam nafi kowa sanin halinta, Kuma dukkan wani hali nata ƴarta rabi shita kwafe sabida haka don Allah don Annabi ka zama namiji ka tsaya sosai akan tarbiyar Rabi domin daɗin dana ji da Allah yasa jininta zata aura ba bare ba, sabida haka kayi haƙuri ka rungumi wannan aure ina da yaƙinin alheri ne in sha Allahu" Ƙasa yayi da kanshi yana jin ninkin sassaucin zuciyarsa na game da damuwar auren kafin yace mata. "In Allah ya yarda Babah Nagode Allah ya ƙara girma" Iyah ta miƙe tare da cewa. "Ɗan ci tuwon tsofi bari na baka guri" Ruwan kaɗai ya ƙara sha ya saka hannu ya rafka tagumi, Minti kusan goma Iyah ta dawo wurin yana ganin ta dawo ya miƙe yana mata sallama Dubu biyu ya zaro ya aje mata tare da cewa taci goro har bakin ƙofa ta bishi tana masa tsiyar baici tuwon ta ba shidai Murmushi kurum yake harya fita daga gidan. Wani irin ƙima da darajar tsohuwar na ninkuwa a ranshi tabbas! ya ga karamci da mutunci a tattare da ita kuma daga gani macece data san karamci. Ya jima a titi kafin ya sami abin hawa aiko kira ne rututu Innah ke masa. Sai da ya shiga abin hawan ya zauna sannan ya ɗauki wayar tata tambayar shi take a ina ya tsaya ta aika shago akai masa abinci baya nan. "Innah ina abin hawa ganinan In sha Allahu" Ya kashe wayar ya jingina da ƙarfen napep ɗin yana nazarin maganganun tsohuwar can wato sudai mutan da suna da kirki da karamci bai taɓa ganinta ba sai yau amman jinta yake kamar mahaifiyar Innah sabida abin da tai masa. Har ya ƙaraso gida yana ta Murmushi shi kaɗai a babban titi ya tsaya yayi siyayyar kayan shayi sabida Ya gaji da cin ƙosai da Kunu koda koko gaskiya gobe shayi za'ayi. Yasai Liptom yasai madara da su sugar ya tsaya yasai ƙwai tare da ƙaton burodi. Sauran canjin daya rage ya sayawa Innah kifi karfasa yasan tana son karfashe musamman wanda ya kwana domin maggi yafi ratsa shi idan ya tsumu. Sai daya kammala siyayyar sannan ya ƙarasa gida ya shigo lungu suka haɗu da Babu, wanda shima dawowar shi kenan gaisawa sukai babu ya shiga gida shima ya ƙarasa gida sabida su Babu a farkon Lungu gidan su yake gidajen su na kallon na juna dana su Nura saiti su kuma su Saadik nasu gidan a ƙarshen lungun yake akwai tazara a tsakanin su. Yana ƙoƙarin shiga gida yaganta a raɓe a bakin ƙofa yi yayi kamar bai ganta ba. "Kawu Saadik" Ta faɗa murya a shaƙe. Juyar da kai yayi zai shiga soro tayi saurin tare gaban shi. "Don Allah karka shiga ka bari muyi magana" Cak ya tsaya tare da zuba mata ido. "Dan Allah kawu Saadik kayi haƙuri da abin da ummah ta gaya maka nasan shiya ɓata maka ranka" Shuru yayi mata. "Allah fa nace" Ta faɗa tana yin ƙasa da kanta gaba ɗaya jikinta yayi sanyi na yanayin shi data gani. "Kin gama zan shiga gida kin tare min hanyata" Ta langwaɓar da kanta. "Kawu Saadik Allah fa nace maka" Shuru yayi mata. "Kawo kayan na riƙe maka mu shiga gidan" Nan ma yayi mata banza. "Lahh kawu saadik ledar burodin ta fashe, kawo na riƙe kada ya faɗo" Shuru yayi mata ganin hakan yasa ta fashe da kuka ta durƙushe a wurin ta dinga zunduma masa ihu! ganin zata jawo hankalin mutane kansu yasan ya yayi gyaran murya tare da cewa. "Kinga in magana zaki ƙara jawo min dan Allah jeki bana neman duk wata magana mai zafi a yanzu ki barni da abin da yake damuna" Share hawayen take tana cewa. "Kawu saadik yaya zanyi na cire soyayyarka a zuciyata duk yadda naso na rabu dakai kamar yadda Umma ta faɗa min na kasa duk rufe idon da zanyi hotonka ke yawo a idanuna" Ya jingina da bango. "To kibi maganarta mana, ai shawara ta baki kinga tin kafin ki mutu azo ana nine sila gwara kin kama kanki" Sai ta ɗago ta kalle shi da kyau. "Nike nan nake haukana ka dena sona sabida ka sami wadda ta fini ka sami ƴar masu kuɗi ko?" Maganar data faɗa ta ƙarshen nan ita ta karya masa zuciya wato ko yayi niyyar yi mata ƙaura inta masa laifi akwai abubuwan da in tayi kota faɗa masa yake sawa yayi saurin janyewa daga ƙaurace matan. "Hauwa waye yace maki ƴar masu kuɗi ce?" Ta tashi tsaye ta na turo baki. "Zancen duniya yana ɓuya ne" Yayi murmushi mai ciwo. "Baya ɓuya kam amma nayi mamaki kuma in tunanin ki haka ne to kinyi tunanin ƙarya domin ni har yanzu banga kuɗin da zai sa na auri mace ba kawai shi aure nufi ne na Allah" Hawaye ta goge. "To yanzu ka daina fushin dani?" Ya tsira mata ido. "Ki nutsu Hawwa wannan shirmen naki ki daina ta yaya zaki je wurin ummah ki haɗa min sharri ni yaushe na tsallake na barki a sume?" Ya faɗa yana zuba mata girman idanun shi. Ƙunshe fuska tai a cikin hannayenta. "Kayi wa mai so uziri man kawu" Murmushi yayi. "Shine aka ce shi mai son yayi ma masoyin sa sharri yanzu fisabilillahi haka mukai dake" Ta tura ƙaramin bakinta gaba kaɗan tare da cewa. "Bana baka haƙuri ba ni ya kamata ma a rarrasa da aka ma kishiya amman ni na zo biko Nikam wannan mallaka da kama zuciyata har tai yawa" Bai niyyar dariya ba amman seda ta sa ya dara. Da sauri ya faɗa soro yana ta dariya shirmen jidda wani bin mamaki yake bashi in tai wani abun kamar ƴar fari koda yake akwai ƙuruciya a tare da ita. Juyawa Jidda tayi don ba zata iya binshi gidansu ba tana jin kunyar suman data yi da abin da ta dinga faɗa akan shi a gaban Innah da baba sai yanzu abin ke bata kunya ita ɗaya inta tina seta rufe fuska tana murmushi. Saɗaf saɗaf ta shiga gida ta faɗa ɗaki domin umma bata san ta fita ba sai dai duk abin da tayi umma na kallonta ta window ɗaga murya umma tayi tare da cewa. "wallahi jidda kin bani kunya na dena shiga tsakanin ki da Abbakar in sha Allah duk abin nan da kukai amman saida kika tare shi ai da fitarki da shigowarki duk ina lura" Ƙunshewa tai a ɗaki kamar ruwa ya cinyeta har umma ta gama ɓaɓatunta daga ƙarshema baccine ya ɗauketa. Cikin gida ya shiga har lokacin dariyar yake sai da ya ƙarasa tsakar gidan sannan ya daidai kansa duk su innah na baje a tsakar gida suna shan iska. Yayi sallama su ummi suka shiga yi masa sannu da zuwa. Ya kalli salmanu dake kan rijiya yana cin tuwo. "Kai yau ina ka shiga?" Fuska a ɗaure yayi maganar. Salman ya shafa kanshi. "Kawu munje kallon kilisa ne" Girgiza kanshi yayi bai ce komi ba ya ƙarasa kusa da Innah sai dai jikin salman yayi sanyi sanin shuru Kawu Saadik ba alheri bane ƙarshe zane shi zai sa Umar ko Usman suyi da safe sabida ya hana shi zuwa kallon Kilisa abin da yasa ya faɗa yasan inya masa ƙarya zai bibiya shiyasa kai tsaye yace masa ga inda yaje. "Ai salmanu kamar mai kunnen ƙashi yake Allah dai ya shirya mana zuri'a sam baya jin magana" Inji innah. Saadik bai ce komi ba ya aje ledojin hannun shi tare da ma innah sai da safe. Gaba ɗaya agajiye yake ne. Yana shiga ɗakin sa,salman ya biyo shi da kwanikan abinci ya aje daga bakin ƙofa sannan ya tsugunna yace. "Kawu don girman Allah kayi haƙuri" A hankali yace "Jeka salman Bording ɗin maza kawai zan nema maka wallahi na gaji da jamin magana da kake yi" Sum sum salman ya miƙe jiki a sanyaye yabar gun yasan kawun nasu baya son naci. Sai da yayi wanka sannan yaci abincin taliya ce jallof mai ruwa ruwa yasan innah shi kaɗai taima sabida sanin aminin taliyar ne. Ya jima bai bacci ba dan sai da yayi nafila ya daɗe yana addu'a akan lamarin auren nashi sannan ya kwanta. ********* Yau gidan na Momi ya kacame Maimuna sai shiga take tana fita tsakanin Kitchen da dining ana shiryawa Mahir abinci momi sai nan nan take da Adaah gudun kada ta Botsare anci sa'a tai wanka ta shirya ta zauna zaman Jiranshi wajan Magariba ya ƙaraso gidan a babban falon da maimuna ta shirya masa abinci Momi ta sauke shi sai da Ya cika cikin shi da ci da sha sannan Adaah ta miƙe ta isa wurin shi yana zaune a saman Kujera ya wani harɗe ƙafa........ SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *11* A lokacin da take zama a saman kujerar, lokacin yayi daidai da sanda gabanta yayi mugun faɗuwa hannu ta ɗora a ƙirjinta wanda ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi a hankali ta lumshe idanunta ta buɗa akan shi wanda shi sai murmushi yake yi mata tsintar kanta tayi itama da sakar masa murmushin tana jin wani abu na fusgarta mai kama da so! Ya matso kusa da ita ya zauna ƙamshin su ya gauraya wuri ɗaya. A hankali ya miƙo hannu zai taɓa nata hannun sai tai maza ta zame tana yin ƙasa da kanta. "Yaya jikin naki?" A hankali ta furta. "Da sauƙi Alhamdu lillahi" Cikin ƙwarewa da iya hira da ƴammata yace mata. "Baby tin jiya ban kwana cikin daɗin rai ba, sabida tinanin ciwon kanki" Cikin sanyin murya tace. "Ai naji sauƙi fa" Bata da wani saurayi sai Habib duka shima sau ɗaya ta bashi dama sukai hira ranar daya kawota gida sabida haka sam bata da ƙwarewa a hira da Saurayi tinda ba zancen takeyi ba, sabida haka Mahir ne ya dinga hirar tana amsawa da "Eh" Ko ta ɗaga masa kai bai tafi ba sai bayan magariba har bakin Motarshi ta rakashi. Ita dai koman ta ya tsaya tin sanda sukai ido huɗu da shi bata sake samun sukuni ba, Wani irin sonsa ne taji yana fisgarta. Sam wannan aibun nashi data dinga gani jiya ya gushe a guje ta faɗa falo tana kiran Momi. Cikin sauri Momi ta fito gabanta na faɗuwa zatonta ko wani abun ne sai dai ga mamakinta ganin Adaah tayi tana murna tana tsalle cikin farin ciki tace. "Momy wallahi yayi min ashe Jiya ban zauna da shi bane, Nikam Ina sonshi Momy har yafi Min Habib sau dubu" Momi ta rungumeta itama tana murnar tare da cewa. "Barka Ƴar albarkata" Nan suka shantake suna hirar yadda zata kaya ba tare da tinanin ayi sallah ba bare azo kan Azkar! Da maɗaukakin farin ciki Mahir yake tuƙi ya matsu yaje gida ya faɗawa Hajiyarsa yadda sukai da Adaah sabida haka da farin ciki yakai gida shima tindaga bakin Ƙofar falo yake kiran Hajiyar tasa, Wadda itama ta taso tana cewa. "Me ya faru ne wannan kira haka?" Kamota yayi suka zauna ya shiga bata labarin yadda sukai da Adaah sosai tai farin ciki da jin yadda komai yazo cikin sauƙi. Jin hankalinta take yayi mugun kwanciya kuma ta shaida alƙawarin aikin malam daya mata akan lallai sai ya juya hankalin Adaah ya dawo kan Mahir wanda ga shi kuwa tin kafin aje ko ina aikin yaci kwalliya ta biya kuɗin sabulu ƙarashen ne ya rage mata. ****** Washe gari da safe Saadik ya shiga cikin gida wajan Baba yaje suka gaisa wanda yayi shirin fita kasuwa. Shima bai wani zauna ba ya fita Ƙofar ruwa yaje wajan wani mutumin sa wanda suke harkar Ƙarafe dashi cikon kuɗin da ya biyo mutumin ya karɓa daga Ƙofar ruwa kawai Gidan Aunty Aminah ya wuce rana gatsal a garin haka ya shiga gidan duk Gumi ya gama rufe shi. A falonta ya zauna suka gaisa Miƙewa tayi ta shiga cikin ɗaki Sai gata da manyan ledoji har guda uku ta aje a gaban shi. Sannan ta fita kitchen ta haɗo masa abinci da ruwa mai sanyi ta kawo masa gaban shi tana zama a kusa da shi tare da cewa. "Auta sha ruwan sanyi kaci mutuniyar taka shinkafa da wake sai muyi lissafi" Ya sha saman kanshi tare da yunƙurawa ya fita bakin famfon tsakar gida yaje yayi alwala ya fita masallacin dake layin yayi sallar azahar, sannan ya dawo Sanda ya shiga gidan an kawo nepa saboda haka a falon ya zauna yaɗan tsakuri abincin ya sha ruwa ita kuma Aunty Aminta tana gefen shi tana Gyaran Turaren wutar data zuzzuba a kwalba da yake tana yin su na siyarwa. Ture plate din abincin yayi gefe yana Jan ledojin data aje masa a gabanshi tsala tsalan atamfofi ne a babbar ledar ta biyun kuma Laces ne ɗayar kuma material ne da mayafai atamfofin zasu kai Turmi Biyar Laces kuma uku material Biyu mayafai Uku. Cikin mamaki ya ɗago yana cewa. "Yaya minau gaskiya kuɗina ba su kai asai waɗannan kayan ba shiyasa na biyo na kawo maki sauran cikon" Murmushi tai tare da cewa. "Ai kaga ma magana ta sauya na kira Hajjo da farida tin ranar da kazo nan mun tattauna shine suka ce kabar kuɗin ka kagan su a gefena na fito maka da shi du wannan kayan Hajjoh ce ta bada kuɗin aka siyo farida tace zata sai akwatina ni kuma zan ƙarasa sauran har kayan kwalliya wannan shine gudun mawar mu dakai auta" Amaimakon ya yi farin ciki sai ya ɓata fuska yayi kicin kicin tare da cewa. "Gaskiya ni baku kyauta min ba tayaya ko wacce tana fama da kanta a wannan rayuwar tare da ƴaƴanta sannan kuce zaku Min lefe salon ma a zageni" Me Aunty Amina zatai in ba dariya ba harda ƙwalla. "Kai Saadik matsala ta dakai kafiya wannan kaci sunan naka Dagiyar wato kai ba za'a maka komai ba abikinka mu muke hidima kake mana duk da ba'a biki da ɗan uwa amman ai kamanci kamata mu haihu kai mana kai mana abikin ƴaƴanmu Kai kaɗai Allah ya bamu Namiji acikinmu In bamu yi maka ba wa za muyi wa?" Bai ce komai ba sai Miko mata kudin daya ke har lokacin dariya take kafin ta kwantar da murya sanin halin shi in har batai masa dubara ba wallahi ba zai amshi kayan ba sai dai su aje. "Haba kawu saadik Innah fa tace bayan ka auri Adawiyya zaka auri Jiddah kaga akwai sauran Hidima akanka tinda wannan tamu ce mu mun maka ita kuma Jidda sai kai abin ka da kanka yanzu wannan kudin ka aje ka sai kayan abinci tinda Baba yace Hayar ma har ka fidda kuɗin Biyanta to wannan kasai kayan abinci dasu" Ya mayar da ajiyar zuciya tare da furta. "Allah ya saka da alheri" Itama murmushi tai tare da cewa. "Yauwa ko kai fa yanzu cikin wannan satin zamu kawo kayan Gidan ku in yaso ƴan uwa suka gama gani sai akai" "Kinga Ya Minau nifa ko taro Innah baza tai ba karma ku faɗawa kowa dan babu wani abu da za'ai a bari in zan auri Jiddah sai ayi taron ƴan uwa" Ita dai dariyar rikicin Saadik take  har ya ƙare maganar shi ya Miƙe yana mata sallama zai tafi har waje ta raka shi da yake Gidan nata ba kowa acikin yaran nata ya zaro dubu Uku yace ta bawa yara ta sa hannu ta amsa tana godiya don tasan in bata ansa ba fushi zaiyi ya tafi. Daga gidan ya minau shago ya wuce aiko ya sami masu jiran shi sabida gaba ɗaya bai buɗe shagon ba yau sakamakon Umar na hutun karatun jarrabawa Shiyasa ya dakatar da Usman yace Shima ya huta a gida sabida umar ya fisu Hankali In suka zauna za'a iya samin matsala. Bayan buɗe shagon ya shiga sallamar Cincirindon matasan dake jiran shi wasu sun kawo rodi ne wasu ƙarfe wasu Robobi bai sami kan shi ba sai da akai la'asar ya kulle shagon ya tafi sallah bayan ya dawo ma sallamar mutane yake har akai magariba sannan ya kulle ya nufi gida. Ya dakata a bakin wani shagon awo dake gab da layin su ya sai shinkafar tuwo da garin tuwo aka zuba masa a ƙatuwar leda ya ƙarasa gida. Bai shiga ciki ba a ɗakin shi ya aje kayan daya sayo yayi alwala ya tafi masallaci da yake jikinsa babu datti domin idan zai awon ƙarafe yana amfani da safar hannu ne ta leda sannan kuma yawanci ma yana aje ƙananun kayan da yake sakewa in yana shago duk da yau yaje amakare kuma bai amfani da kayan da yake sawa ba hakan bai saka ya ɓata na jikinshi ba. Daya dawo daga masallaci wanka yayi ya saka jallabiya Mai ruwan toka ya fesa turare mai sauƙin ƙamshi ya ɗauki ledar Shinkafar tuwon da gari ya ƙarasa Cikin gidan. Muryar Aunty Hajjoh yaji tana cewa innah. "To Innah ga autan naki nan hankalin ki sai ya kwanta" Da sauri innah ta fito daga rumfarta tana cewa. "Kaiko sadauki ina ka shiga aikena tara da abinci shagon ka baka nan" Kamo hannunta yayi suka zauna a saman tabarmar rumfar tare da cewa. "Ki kwantar da hankalin ki innah ba zan ɓata ba ina gidan Ya Minau muna lissafi bayan naje kasuwa na karɓi kuɗi can na wuce" Innah ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da furta. "Alhamdulillahi ina ta kiran wayarka sai wannan baturiyar taita yarika kala kala" Sayyidah mai zatai in ba dariya ba Khadija nayi ummi nayi Juyawar daya yi ne suka daidaita kansu. Aunty Hajjo itama dariyar take tare da cewa. "Wato shiyasa sayyidah tace Min Ummi don Allah kije dani gidan Innah naci dariyar soyayyarta da kawu saadik wai niko Hajiya Innarmu zaki bar ɗanki ya tare a wani gun wannan ƙauna haka" Haɗe rai saadik yayi tare da tashi zai fita dama ya saba jin tsiyar Yaya Hajarah duk sanda tazo gidan sai yaji haushin tsiyar data ke mai ya fita ya bata gu Da sauri Innah ta riƙo hannun shi. "Kinga Hajara ki fita daga idanuna zoki haɗa ƴarki ku bar min gida wallahi bamai ɓata min ran sadauki" Ƙunshe sauran dariyarta ta yi tare da miƙewa ta basu guri domin tasan akan saadik zasu iya rabuwar faɗa da innah. Tashi tayi bayan barin gun da su Aunty Hajjo sukai. Ta shiga kitchen ta ɗauko masa abinci harda ruwan shayi a fulas "Innah nikam a ƙoshe nake naci abinci gidan ya minau sai dai Ruwan shayin zan amfani da shi anjima" Ta ɗan ɓata fuska. "Kaiko kaci dambu ne na tsaki mai daɗi irin namu na mutan da" Ya kalleta dama duk sanda taga ba zai ci abinci ba sai tai masa wannan dabarar yake ci. Aiko janyo kwanon yayi ya sa cokali ya hau ci duk da ya ƙoshi amman haka yake cusawa a cikin sa don hankalinta ya kwanta ta ga dai ya ci ɗin. Kaɗan ya rage yayi Hamdala sannan ya kira Ummi yace takai kwanon kitchen tare da Ledar Daya shigo da ita. "Kinji innah su Ya minau sun min lefe" Innah tai murmushi tare da cewa. "Yanzu muke maganar da Hajjo faɗa take tayi wai akan mai yasa ba'a faɗa musu da wuri ba da sunyi shirin daya fi haka" Ya lumshe ido wato ada yana jin takaicin tasowar shi, shi ɗaya acikin mata kuma shine ƙaramin su amman daga baya sai ya dinga ganin Cewar Matan suna da matiƙar jin ƙai da tausayi uwa uba kuma suna son shi sosai. "Ni kam innah faɗa ma nahau yi don me zasu ɗorawa kan su nauyi" Innah tai murmushin jin daɗi tare da cewa. "Haba sadauki in su Hajjo ba su maka ba wai wa za su ma duk duniya ka ma daina maganar nan Ni dama burina Allah ya haɗa min kanku yau daɗin dana ji ko yanzu Allah ya ɗau raina babu abin da zan ƙara masa sai Godiya domin nasan zaka zame musu uba su kuma su zame maka iyaye" Buɗa Aunty Hajjoh take daga cikin ɗakin Innah kafin ta fito tana cewa. "Wai innah dole muyi ƙara'i a bikin ɗan auta, ranar kawai nake fata tazo nasha rawa son raina" Innah ta hau salati. "Haba Hajjo da ƴaƴanki har kina shirin karɓar jika kiyi rawa wannan son rawa taki naga ranar denawa" Da sauri Saadik yace. "Innah kima faɗa musu babu taro in taro za su yi su bari sai bikina da Jiddah don wannan auren dole ne" "Kai da kata bafa zaka hanamu sakewa ba kaji da gulmarka kuma duk ranar dana ga kana kuka akan soyayyar adawiyya sai na maka tunin wannan maganar kuma abin da nake so dakai shine tin yanzu ka koyi adalci duk matan kane in ma kana son wata to ka barshi a ranka amman batun auren dole duk bai taso ba, Adawiyya ƙanwar ka ce daga baba sai kawu Amadu duk duniya bamu da kamar mahaifinta a cire maganar mahaifiyarta da ita kanta a kalli Zumuncin Allah duk wanda ya ɗauki ɗansa ya baka wallahi ya gama yi maka ƙarshen ƙauna" Innah ta zubawa Hajarah ido tana kallon yadda take zabgawa Saadik faɗa shi kuma yay ƙasa da kanshi domin ba zai iya musu ba dama duk ƴaƴan nata Hajarah ce tsayayya bata ɗaukar raini sannan akwai tsage gaskiya shiyasa suke shakkarta dama gata ma sha Allah duk tafi su ya minau girma in ka dubeta sai kace ita ce ma babba acikin su. Sosai Aunty Hajjoh tai masa faɗa mai haɗe da Nasiha sannan ta cewa ƴarta ta haɗa musu kaya zasu tafi gida shiya raka su titi har suka je babban titi tana ƙara Yi masa nasiha da koya masa dubarun zama da iyali. Shiya biya mata na Mota sannan ya wuce shagon su Nura Saiti. SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma,9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan  dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *12* Sadiq Babu, Nura saiti, babawo duk suna cikin shagon Nuran suna Buga lido ga kofunan shayi nan irin ƙananun nan na buzaye a gefen su ihun su ya cika shagon, duk sallamar da Dagiya yake yi basu ji shiba tsaki yaja kaɗan ya nemi gefen katifar saiti ya zauna. Babu ne ya kula da shigowar Saadik sabida haka ya dakata da Buga lidon hannun shi ya zabga ihu tare da cewa. "Sai angon mata biyu na rabi da hauwa mai abin mamaki" Saadik ya haɗe fuska ya sha kunu ya na lalubar wayar shi da ke ringing, Nurah ya ƙunshe dariyar sa ganin rabin hararar akan shi take sauka. "Haba Dagiya auren ka guda ya tashi amman ka kasa faɗa mana sai a bakin Nurah muke ji?" Cewar Babawo daya juyo yana kallon Saadik, Shidai bai tan ka suba kuma bama shi da niyyar ya tanka sun sai ma hararar da yake sakarwa Nurah wato bin da yay masa rakiyar dubiyar Jidda shine ya zo yana tsaigunta wa su Babawo lamarin auren nashi daya jiyo, ƙwafa yayi tare da tashi yana ƙoƙarin fita daga shagon da sauri Babu ya tare mai hanya yana cewa. "Mu zaka mayar marasa hankali mu kome muka yi sai mun faɗa maka amman auren ka guda ka kasa faɗa mana bada ban Saiti ya bika duba tafisu ba da bama zamu ji ba" Saiti ya cafke da cewa. "Ai kasan dana ji a wurin maman tafisu wajan Baba naje shiya faɗan komai na auren nashi, wallahi kai dai Dagiya ka daina haka zurfin cikin nan naka har ya fara isata, to me kake nufi da sai dai muji auren naka daga sama ko yaya, ka fa tina mu yanzu mun wuce Abokai wallahi mun zama ƴan uwa in ma kai a abokai ka ɗauke mu to mu a ɗan uwa muka ɗauke ka" Ganin duk sun masa caa sai jikin shi yayi sanyi sanin kan shine ya san bai kyauta ba, ko yace ma baya kyauta wa su suna faɗa masa duk wata damuwar su hasalima shike kawo musu masalaha in wani abun ya taso musu amman shi da wiya suji lamarin shi haka tsarin shi yake kuma hakan halitta ce daga Allah wani bin ko innah baya faɗawa damuwar shi sai dai abin yayta cin ranshi. Komawa da baya yayi ya zauna a saman kafitar Saiti ya dafe kan shi da hannu biyu, Ya jima a haka kafin ya ɗago idanun shi ya sauya kala ya koma ja, alamar damuwa ta bayyanar masa. Gyaran murya yayi kamar kullum cikin ƙasa da murya kasancewar sa mutum marar son hayaniyya ko ɗaga murya. "To babawo yanzu mai kuke son nace muku? so kuke na fito fili na bayyana muku cewar Baba auren dole zai mini ko yaya?" Mai su Babawo za suyi in ba dariya ba Babu harda ƙwarewa ganin yanda Saadik ya taƙarƙare yana cewa auren dole. Ganin zasu mai da shi sakarai yasa ya ƙara miƙewa a fusace ya bangaje saiti ya fice daga cikin shagon. Saiti ya tsagaita dariyar tashi yana cewa. "Kunga ku zo mu bishi dole ai zama akan auren nan, Domin Dagiya ɗan halak ne ba zamu bar shi da ɗawainiya shi kaɗai ba kuma don Allah kubar dariyar haka ai maganar hankali, Kun san halin shi kamar kuturu yake zuciya da fushi ba sabon abu bane wurin shi" Ta shi sukai suka rufo shagon suka bi bayan Saadik da yake basu da nisa tuni suka shiga gidan su saadik ɗakin shi dake soro suka shiga baya ciki da alamun yana banɗaki Nura ya zauna a saman kujerar roba su babawo kuma suka zauna a saman carfet ya kusa minti goma a bayin kafin ya fito shige su yayi ya nufi hanyar ƙaramar wardrobe ɗin shi, ya ɗauki abin da zai ɗauka ya koma bayin Minti kaɗan ya fito cikin farin wandon polo da farar rigar polo marasa nauyi da alamun na baccin sa ne, ya ɗauki turare ya fesa sannan ya shinfiɗa darduma yayi sallar isha'i ganin yayi sallama yana kokarin mai da ta nafila Nura yayi gyaran murya. "Kaga muma fa musulmai ne na ƙwarai tinda kayi sallar Isha'i ka bari muyi magana muma muje muyi tamu in mun fita sai kayi Nafilar" Dan dai kawai ɗakin shi suka zo ne bai son suji ba daɗi shiyasa kawai ya juyo yana fuskantar su. "Mu yanzu a matsayin mu na abokanka zamu ɗauki nauyin wasu abubuwan kama daga kayan abinci zuwa sauran hidimar tura motoci zuwa gidansu amarya" Sai da ya ɗauki lokaci bai magana ba sannan yace. "To nagode" a taƙaice. "To ya batun mazauni fa?" Cewar babu. Ya shafa kanshi yana cewa. "Nan gidan dake kallomu na kama kasan masu gidan zasu tashi shine ni zan shiga" Babawo yace. "Kai gaskiya yayi maka kaɗan kuts ni kaf arear nan ma akwai ƙaramin gida kamar wannan kuma har mata biyu zaka saka aciki" A zafafe ya ce. "To daidai ƙarfina kenan uban wa yace maka duk su biyun zan aura lokaci ɗaya ina zan kaisu Jiddah sai ta gama karatu kafin nan na fara ginina In sha Allah ko ɗaki biyu nayi saisu koma su duka mu zauna a muhallina" Nurah yace. "Eh to tinda mace ɗaya ce ai ya isa sai ai maganar gyare gyare zan saka Mizambilun gidanmu yaje yaga gidan tinda ya iya painti sai yaje yayi maka shafen ɗakuna dana tsakar gida" Saadik yace. "Wasu ɗakuna ɗaki ɗayane ciki da falo sai kicin da bayi amman bakaji kuɗin da suka sawa gidan ba haka dai zan biya tinda nina fi son kusa da innah gaskiya" Nurah yace. "Okay ba matsala sai batun lefe kuma?" Ya ɗan haɗe rai. "Nikam titsiye ni kuka zo yine to ban yi ba" Babawo yayi dariya tare da cewa. "Kaifa ka zama ɗan alallaɓa yanzu Angon Rabi in ma bakai lefe ba mu sai muyi karo karo" Wani kallo ya watsama Babawon tare da cewa. "Kasan dai ni ba rago bane babu abin da yake firgitani, Lefen yana gidan Yaya Minau kun san gidan sai kuje ku gani" Saiti yace. "Baka isa ba dole a kawo min kayan madam nai mata ɗinkuna masu fisgar hankali tasan ta auri abokin telan mata" Ta shi yayi cak ya tada sallar shi sukam maganganun su suka cigaba dayi akan bikin kafin su miƙe su fita. Shikam ya jima a sujjadar shi yana ƙara jaddada neman zaɓin Allah akan lamarin auren wanda dama wannan addu'ar yake ba dare ba rana in har yayi sallah sai ya miƙa koken shi wurin Allah akan lamarin auren nashi. Bayan ya sallame ya na ɗe abin sallar ya kashe ƙwan ɗakin yayi kwanciyar shi. Da asubahi suka haɗu da baba a masallaci wanda baban yake masa magana akan shirin auren bayanin yadda ake ciki yayi ma baba cikin ladabi, baba ya ƙara da cewa, mahaifin jiddah ma yay masa magana jiya akan wai sukai kuɗin aure in yaso in ta kammala karatun sai ayi bikin. "Baba ka basu haƙuri kaga duk ƴan kuɗaɗen hannun nawa na haɗa zan kai kuɗin gidan can su min alfarma bayan biki sai na bada akai" Baba ya murmusa tare da cewa. "Hakane sadauki, amman tinda suka nemi akai to akai ɗin ni zan bada kuɗin akai musu kaga sanda zamu kai kuɗin Amadu yazo min da batun auren ka da rabi'ah to kar suga kamar ba zaka auri ƴarsu bane mutanan nan babu abin da zamu ce musu sai godiya da irin ƙaunar da suke nuna mana sabida haka Amadu yace jibi zai dawo kano in ya dawo zan bada Kuɗi suje su kai gidan su jiddan shida sauran ƴan uwan mu na ƙauye" Saadik ya rissunar da kai ƙasa tare da cewa. "A,a Baba Kana ta kanka ka ɗorawa kanka wahala ka bari bazai gagaraba in sha Allah, Burina akai lefen sannan na bawa masu gidan can kuɗin su sai hankalina ya kwanta" Baba yace. "Banda abin ka Sadauki In da ni mai hali ne ai da na ɗauke maka komai na hidimar aure, to ni babu mahaifiyarka babu sai kai kaɗai da Allah ya bawa ƙarfin zuciyar nema ga shi yanzu Nauyi zai ƙara ninkuwa akanka bayan namu Allah ya maka albarka kuma zan cire kuɗin auren akai Musu In sha Allahu" Daɗa rissunawa yayi yana wa baba godiya sannan suka ƙarasa gida. Ɗaki ya koma ya sake kaya dan ko wanka bai yi ba, a gurguje yaje suka gaisa da Innah ya fice shago tin sassafen don abin kari ma sai Usman ne yakai masa dole yabar Usman a shagon Shi kuma ya wuce Ƙofar ruwa. Wajan ƙarfe Sha ɗayan safiya gaba ɗaya iyalan na Innah suka hallara agidan Aunty Amina da Ƴaƴanta jawahir wadda ba a jima da bikinta ba sai Hussaina wadda za'a ma biki kwanakin nan, Aunty hajjo da Fatima ƴarta wadda ke dauke da tsohon ciki sai Sayyidah, Sai faridah data zo tare da Sajidah da Sajjad ga kuma su Ummi nan don bama suje Makaranta ba ranar shiyasa gaba ɗaya gidan na Innah ya gama cika da Ƴaƴanta da Jikokinta ƙatuwar tukunya Khadija ta wanke aka ɗora wake da shinkafa a tsakar gida wadda za a ci da rana. Babu komai da yake ta shi sai hayaniyar su, ta surutun su kuma duk akan bikin auta ne suke ta faman maganganu na yadda bikin zai tafi. Shigowar Sayyid da Hassan ce ta sa surutun ya ɗan lafa, Sayyid ɗan Aunty Hajjo Hassan ɗan Aunty Amina, Suka shigo da akwatina niki niki da alamun daga kasuwa suke sai da suka shigo da akwatina saiti Biyar cif da ƙatuwar gana Hassan yay miƙa yana cewa "Washh Allah Ummah ba ƙaramar wahala muka sha a kasuwa ba, da ƙyar Abba ya samo ɗaya atamfar nan fa" Aunty amina ta fara janyo akwatinan tana cewa. "Allah dai yay muku albarka dama nasan za a ci wahalar kafin a samo, da kuka amso ne kuka je gida kuka ɗauko akwatinan? to kun sallami mai ɗan sahun daya kawo ku?" Sayyid yace. "Eh mun sallame shi yama tafi Ummi nina wuce school" Ya faɗa yana kallon Aunty Hajjo. Innah da bakin ta ya ƙi rufuwa cewa take. "A,a ku bari kuci abinci mana Allah ya maku albarka kuma ya ninka musu abin da kukai" Matasan dai fita sukai sunawa Innah murmushi, tare da amsa addu'ar da tai musu suko su Ya Minau kayayyakin sukaita ɗagawa don an karo wasu kayan akan na da faridah ce mai shirya kayan ko wanne tana haɗe shi a inda ya dace. Kafin Ya Minau ta cewa su Ummi suje maƙota su farfaɗa azo aga lefen kawun su saadik aiko Su Ummi fita sukai gida gida sukaita faɗa kafin kice kwabo gidan Innah ya cika da mutane ƴan kallon Lefe. Sai dai mahaifiyar Jiddah furr taƙi zuwa ta kuma kafawa Jiddah takarar ko kallon saadik karta ƙara yi ranar Jiddah taci kuka ta godewa Allah, domin Wata irin ƙaunar Saadik ce ke ƙara ninka mata ruhinta. Maƙota kowa yazo sai ya tambaya gidan su Jidda za'a kai sai Faridah ke musu bayanin Ai ƴar ƙanwar Baba zai aura Jiddah kuma sai ta kammala karatun ta wasu suyi fatan alheri wasu kuma su tafi suna ƙus ƙus ranar har dare ana shigowa kallon Lefen wanda kowa ya gani sai ya yaba shi kan sa Baba yayi mamakin rawar ganin da ƴaƴan nashi sukaiwa ƙanin nashi aiko sai saka Musu albarka yake. Saadik bai shigo gida ba sai bayan Isha'i shima wayar innah ce ta saka ya tawo sabida a kwanakin nan cikin taskar Allah yana samun ciniki ne fiye da yadda yake yi ada shiyasa yake jimawa a shagon. Tin daga bakin layi yaji mutane na masa Allah ya sanya alheri wani maƙocin su ne ya tare shi sanda zai shiga gida yana ce masa. "Malam saadik ashe lokaci yayi to Allah ya sa alheri" Dama da mamakin yadda ake masa Allah sanya alheri ya ƙaraso sai kuma ga wannan maƙocin nasu shima ya tare shi yana masan. Ƙaƙalo murmushin dole yayi tare da cewa. "Amin ya rabb! nagode" Ya faɗa yana ƙoƙarin shiga gidansu. "Amman Saadik kaji tsoron Allah naji ance ba Waccan yarinyar jiddah zaka aura ba, ƴar ƙanin mahaifinka zaka aura mai kuɗi shiyasa ma kuka haɗa lefen ƙarya, amman gaskiya bai ci kaiwa Jiddah haka ba kowa yasan yadda kake da yarinyar nan amman ka yaudare ta" Da sauri ya ɗagawa maƙocin nasu hannu tare da faɗawa soron gidansu da sauri......... SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma, 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *14* Ya lumshe idanunsa yana fesar da Numfashi ƙasa ƙasa Sautin Kukan Ya Minau na ratsa dodon Kunnen shi, Kafin ya ɗago da idanun nashi ya dire kallon shi akan Innah wadda tai tagumi tare da zubawa Ya Minau Ido takaici da tarin damuwa ne bayyane a saman fuskarta. Tsaki Aunty Nafi taja tana cewa. "Haba Yaya gaskiya a sake tunani danni kam banga alfanun wannan aure ba, kowa ni ɗa namiji yana fatan samun macen ƙwarai wadda ta fito daga gidan martaba amman wannan kam mahaifiyar yarinyar nan ba ƴar mafuta bace" Cikin damuwa Innah ta dubi Ya Minau tana cewa. "To yaya zamuyi wannan ƴar, Babanku ya kafe akan ayi auren nan ni kaina ba so nake ba sabida Maryam ba ƙaunata take ba to abin ne yafi ƙarfina dole na tattara na zubawa sarautar Allah ido duk abin da Allah yayi akai daidai ne" Faridah ma mita take Aunty Hajjo kam ta kasa magana sai faman Jijjiga ƙafa take duk irin wahalar da suka sha wajan haɗa lefen nan amman wannan cin zarafin ne zai biyo baya. In kujerar daya ke kai tai motsi to Saadik yayi motsi acikin maganar su, sai dai zuciyar shi ƙunci ne tare da tarin damuwa haka ya cigaba da wanke takalmin shi ya kaɗe ruwan ciki ya jingine a jikin bango ya miƙe yabar Musu tsakar Gidan to shi mai zai ce, bayan duk Babane yaja musu da bai karɓi tayin ubanta ba da wannan tozarcin bai faru a gare suba. Ɗaki yaje ya shirya cikin Jc jajaye wandon iya gwiwar shi sai farar safar ƙafa sai farin takalmin Ball ya fito bai ma shiga gidan ba ya wuce filin ball cikin son kau da damuwar daya bar ƴan uwan shi suka fara buga ƙwallo. Da ƙyar innah ta rarrashi ya minau sabida dama itace babba amman tafi ƴan uwan sanyin zuciya da rauni har magariba suna gida suna jira shigowar Baba ganin bai shigo ba har bayan sallar yasa suka tattara suka wuce gidajen su duk rai babu daɗi. Sai bayan sallar isha'i baba ya shigo gida sam innah batai masa maganar ba har sai da yaci abinci ya zauna a tsakar gida yana sauraron labarai a Radio. Innah ta aje masa kofin Furar data damo masa. Ya dube ta tare da cewa. "Hafsatu mai yake damunki ne? gaba ɗaya tinda na shigo gidan nan na fuskanci yanayin ki ba daɗi" Innah ta rausayar da kanta gefe cike da zurfin ciki tare da danne abin da ke cin ƙasan ranta tace. "Babu komai Babansu ga furar nan ko sai anjima zaka sha?" Baba ya fuskance ta. "Haba Hafsatu bafa yau na sanki ba, wallahi shiyasa inna ga Sadauki ya ɓoyen abin da ke damun shi nakan ce barewa batai gudu ɗanta yayi rarrafe ba, yanzu dai faɗa mini mai ke damun ki?" Ya faɗa yana maida hankalin shi kaco kam izuwa gareta. "To inda hali Babansu ina neman alfarma da abar batun haɗa sadauki da wannan yarinya ƴar wajan Amadu wallahi abin babu arziƙi sam kai kaga cin zarafin da maryam taiwa yaran nan yau haba talauci hauka ne shima baya so nima bana so dama dannewa nake kuma nike tausar shi akan auren" Ta faɗa tana haɗe fuska. Baba yayi dariya. "Ikon Allah wato ku dai mata bakwa rabo da cece kuce, To yanzu so kike na zama ƙaramin Mutum ɗan uwana ya bani kyauta nace bana so kome?" Innah ta kuma haɗe fuska cikin rashin sukuni tace. "Tinda abin ba daraja ba martaba a haƙura kawai" Baba ya kama haɓa. "Haba Hafsatu shifa shaiɗan baya son ƙulla alheri gaba ɗaya bamu san mai ke tattare da wannan aure nasu ba" Cikin zafin da bai santa da shi ba tace,,, "Meye acikin auren in ba ta shin hankali ba........ Da sauri yace. "Kefa uwa ce Hafsatu kada kiwa auren nan mugun baki" Lokacin hawaye ya fara sauka daga saman fuskar Innah abin da yayi matiƙar ɗagawa Baba hankali kenan cikin kuka! tace. "Shekaru Kusan Arba'in muna tare da kai Muhammadu baka taɓa saka doka na karya maka ba baka taɓa zuwa da abu na musa maka ba amman don Allah ka janye auren Sadauki da wannan yarinya tinda shima ba sonta yake yi ba kawai biyayya ce yake yi maka" A ɗan fusace Baba yace. "Sabida bakya ƙaunar Jinina Haɗin zumuncin ne bakya so shikenan zan gani tsakanin ni da ke waye zaifi rinjaye akan wannan lamari" Da sauri tace. "Kai ne zakai rinjaye" Ta faɗa tana goge hawayenta. Lokacin Saadik ya shigo gidan wanda sauran ƙarashen maganar ta sauka a cikin kunnen shi. Ya nemi guri a bakin Ƙofar Kitchen ya zauna ya tsirawa Innah ido wanda idan idon nashi bai masa gizo ba hawaye yake gani a saman fuskar Mahaifiyar tashi. Baba miƙewa yayi cikin fushi yama fice daga gidan gaba ɗaya. A hankali Innah ta ɗago tana cewa. "Kaga ni ko sadauki wallahi bana son auren nan bana so bana so! Kalmar data firgita Saadik ta hargitsa masa zuciyar shi kenan. Hannun shi biyu ya saka ya rufe fuskar shi yana jan numfashi gaba ɗaya Jikinsa rawa yake hankalin shi yayi mugun tashi. Ya kai minti goma a haka kafin ya ɗago manyan idanunshi waɗanda suka sauya launi zuwa jajir ya zubawa Innah yana fesar da Huci zazzafa. Muryar shi a raunane ya ce mata. "Haƙiƙa innah nafiki tsanar wannan aure wallahi innah nima bana son shi bana ƙaunar shi ban san meye yasa Baba ya kafe ba" Sauran maganar ta maƙale masa sabida Jin muryar Baba akan shi. "Idan ka auri Rabi'atu ka saka wuƙa ka yankanta Abubakar Saadik! daga nan zan san kai cikakken maƙiyinta ne kuma zanyi maganin ku daga kai har uwar taka tinda naga abin babu arziƙi" Gaba ɗaya Baba ya birkice musu kamar ba shiba faɗa yake ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba seda yayi wa Innah da Saadik kaca kaca sannan ya sa kai ya shige ɗaki. Innah ta zabga tagumi shiko Saadik ta shi yayi yana rangaji yabar tsakar gidan. Ya shiga cikin yanayi marar daɗi ranar sai bacci ɓarawo a idanunshi amman duk juyi fushin mahaifin shi da ɓacin ran mahaifiyar shi akan auren yake haskowa. Shi baba idanunshi ya rufe ne akan haɗin zumunci ita kuma innah cin zarafin da akaiwa ƴaƴanta ke cin ranta har taji ta tsani auren. Zaɓin wa zaibi? Daya gaji da juyi, sai ya miƙe ya shiga toilet ya ɗaura alwala ya shiga jera sallah yana faɗawa ALLAH damuwar shi yaji daɗin zuciyar shi yaci kashi casa'in da tara na daga cikin damuwar shi ta kau dalilin daya sa har ya sami bacci mai nauyi wanda ya kusan makara a sallar asubahi agurguje yayi wanka yayi alwala ya fita masallaci yana idar da raka'atul fijir liman ya tada Iƙamar sallah ya maida ajiyar zuciya Allah ya taimakeshi ya samu raka'atul fijir ɗin, ba a tada ba hakan yabi sahun sallar bayan sun idar ya zauna yayi azkar sannan ya fito cikin gida ya shiga ya gaida Baba wanda ya amsa mai gaisuwar da ƙyar sannan ya ƙarasa wajan Innah dake damun koko a kitchen ya tsugunna ya gaishe da ita. Yana saka hannu yana tura mata wutar ɗumamen tuwon data ɗora. Cikin kwantar da murya yace. "Don Allah don Annabi Innah ki bar sanya damuwar auren nan aranki nina barwa Allah komai kuma wallahi tinda na barwa Allah in har auren nan babu alkairi rushewa zai yi" Innah ta maida ajiyar zuciya. "Sadauki haƙiƙa cin zarafin da maryam taiwa yarannan ya ɗagan hankali da shi na kwana ga ɓacin ran mahaifinka amman tinda ka ambaci Allah magana ta ƙare nima zan cigaba da addu'a akai" Ya lumshe idon shi dayay masa nauyi ya warasu akanta yana cin tsananin damuwar daya gani a tare da ita. A hankali yake kwantar mata da hankali harta sake. Don ya ƙara kwantar da hankalinta yasha kokon yaci ɗumamen tuwon da farar safiyar duk da bai kari a wannan lokacin. Sannan yayi mata sallama ya tafi ɗaki agurguje ya shirya ya fita kasuwar ƙofar ruwa. Don kai kaya. *********** Momi ta sheƙe da dariya tana cewa. "Tsinannu gayyar tsiya ai nice maganin ku" Ko kallon kayan batai ba ta barsu a wurin. Ita kam adaah bata ma san wainar da ake toyawa ba tana can ɗakinta tana kukan takaici. Abbah da magariba ya shigo gida yadda yaga kayan ne ya bashi tabbacin masu kawo kayan basu sami tarbar arziƙi ba. Aiko tindaga parlour yake kiran Momi ranar taga tijara domin cewa yayi akan auren zai iya sakinta. Data ga ba haza shine tahau bashi haƙuri. Ranar Abbah yayi kwanan takaici washe gari wajan ƙarfe goma ya dira agidan Baba. Lokacin Baba yana ƙoƙarin fita kasuwa Abba ya ƙaraso haka suka juya cikin gidan haƙuri Abba ya dinga bawa Baba duk da bai da tabbas na abin da Momi taiwa masu kawo lefen amman ya tabbata bata shuka abin kirki ba musamman daya kira Iyah mahaifiyarta tace sam Momi bata faɗa musu maganar kawo kayan lefen ba. Baba ya dubi Abba yace. "Amadu wannan ban haƙuri da kake kamar nace maka Sadauki ba zai auri adawiyya ba ka kwantar da hankalin ka akan wannan lamari komai zai tafi yadda bakai zato ba cikin alheri" Cikin sanyin Jiki Abba yace. "Hankali na ya tashi da lamarin Maryam haƙiƙa banyi dace da mace ta gari ba, gaba ɗaya Halin Rabi'ah na uwarta ne, In har ta auri bare ba zasu zauna lafiya ba Ina ji ajikina auren rabi'ah kamar wani nauyi ne da zan sauke kafin fitar Numfashi na" Da sauri baba yace. "Ka bar faɗin haka amadu ni ban da kamar ka, duk shirme suke itama hafsatu ta damu ko wacce bata son auren mu toshe kunnuwan mu alheri muka nufa kuma shi zai ƙullu Sadauki yayanta ne koba aure shi mai tsaya mata ne da ikon Allah" Da ire iren wannan Baba ya samu hankalin ɗan uwanshi ya kwanta koda suka fito innah da ƙyar taiwa Abbah sallama muryarta a shaƙe ranar anci sa'a domin a motar Abba suka fita Abba ya aje baba a kasuwa shi ma ya wuce tasa. Iyaye mazan sun toshe kunnuwan su daga cece kucen matansu domin ita ma innah ta riƙe wuta sosai akan lamarin musamman da Anty nafi ƙanwarta ke ƙara rura mata wutar ƙin auren sai dai Baba da yake yafi ƙarfin gidan shi tara ƴaƴanshi yayi kaf yace bai lamunta wani ya ƙara sukar auren ba da wannan aka samu sauƙi. Shiko Abba komai na shawarar biki baya tinkarar momi Iyah yake faɗawa hatta kayan lefen ma ya ɗebe su ya kai gidan iyah sabida haka koda biki yayi saura kwanaki bakwai iya ta sayi goron rabo ta saka Mariya ta kakkai gidan danginta sabida ganin take taken matan yasa Baba yace wa Abba ya tsaida ranar biki domin ko Saadik ɗin ma baba bai faɗawa ba, sai da Bikin yayi saura kwanaki bakwai. Baba ya kira saadik ɗin ya shaida masa duk yadda saadik yaso baba ya ɗaga masa ƙafa amman baba yaƙi yace ko bukka ce ya saka matar shi. Da damuwa saadik ke shaidawa Innah wadda sam baba bai shawara da ita ba, cewa tai kada ya ɗaga hankalin shi abin da Allah ya hore mishi yayi ita kam ba taro zatai ba tinda abin yazo a ƙure iya ƴan uwanta kaɗai zata faɗawa. Gaba ɗaya saadik ya shiga busy gidan daya kama suka shiga gyara shida su Nura ƙanin Nura yayi paint a gidan wanda Falo ne guda ɗaya sai ɗaki aciki sai banɗaki da Kitchen duk a falon. Ɗan ƙarami ne gidan irin na zaman mutum ɗaya. Bai sami nutsuwa ba sai ana saura kwana biyu daurin aure su Nura ne suka bugo katin ɗaurin aure suka shiga rabo Babawo yayi musu ɗinki shaddar ɗaurin aure duk su huɗun. Ana gobe ɗaurin aure Iya ta saka Abbas ya kaita gidan Momi wadda ta saki jikinta sam batai zaton da bikin bama sabida Abbah baya bibiyar ta akan lamarin shiyasa ta saki jiki akan aikin malam yaci maganar aure ta mutu zasu yi son ransu ita da lubna shiyasa suke ta ƙulla yanda za'ai Mahir ya turo manyan shi. Ƙaramin hauka momi ta shiga yi sanda iya ke sanar da ita tazo tafiya da Rabi'ane sabida gobe za'a daura aure a wuce da ita gidanta. Momi kuka Adaah kuka sai da Abba yayi jan ido sannan Adaah tabi iya domin ko kayanta ma bata haɗa ba, Abba yace a kai mata su daga baya. Komai na momi ya tsaya cak sai faman zage zage take kuma tace ba zata taka ƙafarta gidan bikin ba Hajiya lubna tafi momi shiga tashin hankali data ji maganar amman data tina zagon ƙasan datai sai taji bata damu da auren ba tasan dole adaah zata fito ɗanta ya aure ta, domin ba burin ta auren adaah ba burinta dukiya.SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank ko kuma 9022260850 Opay bank, Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. [12/16, 10:27] Autar Manya: *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *13* Da tsananin ɓacin rai yake shiga cikin gidan nasu, yadda ya tarar da mutane a tsakar gidan nasu suna ta ɗaga kayan cikin akwatinan abin ya bashi mamaki ba kaɗan ba. Ya tokare a bakin rijiya tare da zuba hannayen shi a saman ƙirjin shi sabida yadda ranshi ke ɓace baya tinanin ma na tsakar gidan sun ji sallamar da yayi. Innah ce ta farga da tsaiwar ta shi ta taso ta iso inda yake tana cewa. "Sadauki! lafiya na ganka a tsaye ka ƙaraso mana, Allah ya sa ƴan uwan naka basu tafi ba dama kai suke jira" Ya ɗago tare da zuba mata jajayen idanunshi murya a raunane yace. "Yanzu innah sai da kuka aika azo aga lefen nan fisabilillahi mai iyayen jiddah zasu ɗauke ni?" Sai ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana cije bakin shi, sauran maganar ta tokare a maƙoshin sa. Innah ta zuba mai ido tana ƙara jinjina son da yake wa jiddah tinda har yana gudun ɓacin ranta da kuma na iyayen ta. "To sadauki ya za'ayi da ƙaddarar Allah tinda Ubangiji ya ƙadarta ba Jiddah bace matarka a farko ba, yaya zamuyi gaba ɗaya haƙuri zamu yi tare da addu'ar alheri acikin lamarin" Jinjina kanshi yayi tare da cewa. "Tin da kika ce Allah magana ta ƙare" Bai iya faɗa mata maganar da maƙocin nasu ya tare shi da ita ba sabida masifar zurfin ciki. Ya na ƙoƙarin juyawa ya koma ɗakin shi su Ya minau suka ƙaraso wajan da shirin tafiya gida faridah sai tsokanar shi take yayi mata banza ya wuce ya barsu a wajan. Innah tai murmushi tana kallon Aunty Hajjo tare da cewa. "Yanzu goben ƙarfe nawa za a kai kayan? sai na kira Nafi kuje da ita amman ban da abinku da kun bari maza sun kai yanzu yaushe rabon da ku ga mata sun kai lefe?" Da sauri faridah tace. "Ban da abin Innah mazan su waye zasu kai? abu duk ɗaya Mu dai ki bari Muje mukai" Ba yadda Innah ta iya ta amsa musu kamar yadda suka buƙata Ya Minau ce tace. "Innah ni naga Saadik na haɗe rai wai meke faruwa ne?" Innah cikin basarwa tace. "Ke rabu da shi ya ƙarata da Ƙuncin sa" Har soro innah ta raka iyalan nata tana musu addu'ar fatan gamawa da duniya Lafiya suka fita titi ko wacce ta hau motar gida. Ba jimawa da fitar tasu Baba shima ya shigo gida lokacin mutanen dake ganin kayan lefen duk sun tafi sai su Khadija dake tattare tsakar gidan. Baba ya zauna a saman tabarma a rumfa Hasken farin ƙwan tsakar gida ya hasko har cikin rumfar da yake zaune yabi akwatinan da kallo Fuskar shi dauke da maɗaukakin farin cikin haɗin zumuntar da zasuyi da ɗan uwan shi ya dubi Innah dake haɗa masa abinci yace. "Haƙiƙa Hafsatu naji daɗin wannan aure ina fatan Ubangiji yasa sai mutuwa ce zata raba su, tabbas Amadu ya wanke duk wani laifi da ya min abaya domin duk duniya ba wanda zai iya riƙe Ƴar amadu kamar Sadauki kinga munyi tuwo na mai na" Ya faɗa yana sakin ƙayataccen Murmushi, Itama Innah Murmushi tayi tana cewa. "Allah dai yasa ayi lafiya a gama lafiya niko burina na goya ƴaƴan ɗan auta tin da ƙwarina Kuma Allah ya cika min, sai batun kai Lefe kunyi magana da shi Amadun ne? waɗan nan yara fa sun kafe sun ce sai sune zasu miƙa kayan" Baba ya ɗaga kofin da innah ta cika mai shi da ruwan sanyin randa mai daɗi yace. "Munyi waya ɗazu yace min Gobe da safe zai sauka kano Wajan yamma sai su miƙa abu duk na gida nida ma niyata ma a bata kayanta ranar ɗaurin aure, to tinda sunce zasu kai kar a katse su duk cikin murna ne" Ire iren hirar bikin suka cigaba dayi har zuwa Lokacin kwanciya bacci. ******* Adaah bata san waya bawa Mahir Numbern wayarta ba amman tafi zaton Momi ce ta tura masa shiyasa sanda taga kiran shi cikin dare batai mamaki ba hira mai cike da so da kulawa yake mata har sai da ya tabbatar ya dasa mata son sa acikin zuciyarta sannan ya barta aiko daren bata rintsa ba duk juyi shi take tunani abin ka da farin shiga. Washe gari sai wajan taran safiya tayi sallar asubah sabida wayar da suka sha da Mahir ta makara ne tasha baccinta ta gode Allah wanka tayo ta shirya cikin Riga da skirt na Jar Atamfa Java bata ɗaura ɗankwaliba a haka ta fito Parlour tana kiran Maimuna da sauri maimuna ta ƙaraso ta rissuna tana cewa. "Gani uwar ɗakina Barka da asubah" Cikin halin ko in kula tace. "Kije ki wanken toilet ki gyaran ɗakina ki kunnan turare akwai undies ɗina da zaki wanken washing machine ɗin toilet ɗina ya lalace" Har lokacin maimuna bata ɗaga kanta ba har sai da Adaah taja aya sannan maimuna tace. "An gama uwar ɗakina ga break ɗin ki can na haɗa komai kawai ci zaki yi" A ya tsine ta amsa wa maimuna da. "Ok" Sannan ta wuce dining ta zauna ta haɗa tea ta ɗauki bread tana haɗawa da soyayyen ƙwai tana ci da yake Allah ya ɗora mata ci kamar gara ita Ko irin rashin cin nan ma na ƴaƴan masu kuɗi bata da shi. Sai da ta share wannan bread da ƙwai tas sannan ta goge bakin ta da tissue ta ƙarasa cikin parlour ta kwanta tana canza channel. Momi ce ta fito sai baza ƙamshi take. Ta ƙaraso gaban Adaah tare da cewa. "Tashin ki kenan na lalleƙa ki naga baki farka ba, Nima fita zanyi yanzun nan zan dawo" Adaah tabi momi da kallo kafin ta kawar da kanta, ba tare da gaishe da mahaifiyar tata ba. Momi tana ƙoƙarin fita daga Parlourn Sukai Kiciɓus da Abbah wanda shigowar sa gidan kenan hannun shi riƙe da ƙaramar jaka ta matafiya. Momi zamewa tai a wayance ta zauna a saman kujera tana aje ƙaramar jakar hannunta dama lefen ƴar ƙawarta zata je gani sam bata kawo Abba zai dawo yau ba shiyasa zatai gaban kanta sabida ana faɗin irin dukiyar da aka laftawa ƴar ƙawar tasu. "Sannu da shigowa Alhaji, amman dawowa babu sanarwa" Ta faɗa tana sosa kai alamun rashin gaskiya. Bai kulata ba sai Neman gurin zama da yayi da sauri Adaah ta diro tana sauka ƙasa har tana ƙwarewa wajan yiwa mahaifin nata barka da zuwa sabida shi tana shakkar shi ba kamar Momi ba. Abbah ya bita da kallo ba tare daya amsa gaisuwar tata ba. "Rabi'atu mai kike agida yau baki je makaranta ba?" Sai ta hau kame kame sabida sarai tana da lecture ranar amman taƙi zuwa. "Wato asarar kuɗina nake a banza ba karatun kike soba ko da yake ai magana ta ƙare dama abin da yasa na rabu dake na zaci zaki dage ki karatu ne, amman tinda baki son makaranta zan faɗawa Mijin naki ko bayan aure karya barki Fita ki haƙura haka abin da kika samu Allah yasa mai albarka" Haɗe rai tayi nan da nan ruwan hawaye ya fara firfitowa daga idanunta ta jefa kallon ta ga Momi wadda ta kafe Abbah da ido tana jijjiga ƙafa. "Wannan wace irin magana kake Alhaji wai shi wannan auren dole ne? haba yarinya bata so nida na haifeta bana so gaskiya ba zan lamunci a cusawa ƴata ƙatoton jahili ba, ce maka akai bata son karatu bayan ita kaɗai Allah ya bamu Tarin dukiyar da Allah ya baka in baka barta tai karatun ba waye zai riƙe mana ita nan gaba" Abbah ya zubawa Momi ido cike da ɓacin rai, sam tinda lamarin auren nan ya tashi momi bata saurara mai bata masa ta sauƙi hatta ga kalamanta kawai yana kai zuciyar shi nesa ne yana duba wasu abubuwan jiba yanzu yadda take masa magana agaban ƴarta ba ladabin harshe ko tauna magana. "Maryam sai fa Rabi'a ta auri Saadik koda gawarta ce wallahi zan kai gidan ƙarewar ƙiyayya in an aura masa ita tasa Ashana ta kunnawa kanta ta Ƙone ta mutu Ki sanar da ƴan uwanki anjima Za a kawo lefe" Daga haka ya miƙe yabar Parlourn zamewa momi tayi daga saman Kujerar tana yarfe Zufa. Da sauri ta ɗaga waya tana Kiran Hajiya Lubna. Daga ɓarin Lubnah dake kwance domin har Lokacin bata tashi daga baccin safe ba. Ta ɗaga wayar tana jan ƙaramin tsaki. "Maryam yaya akai wannan wayar da farar safiya?" Momi ta yarfe zufa a karo na barkatai kafin tace. "Kinji wata sabuwa anjima zasu kawo lefen Adah ni kaina ma ya kulle" Da sauri Lubna tace. "Kamar yaya dama baki zuba masa magani a ruwan ya sha ba har ya sami zarafin maganar auren?" Momi ta juya tana kallon hanyar da Abbah yabi taga ya ƙullewa ganinta sai tace. "Yau fa ya dawo gari yanzun nan ya sauka yake wannan bayani wallahi bai ma bani fuskar na bashi ruwan ba bare akai ga na saka ke nifa gani nake suma aiki suke akan Alhaji duk yabi ya birkice min kamar ba shi ba" Ƙaramin tsaki Lubna taja ido rufe da son biyan buƙatar kanta tace. "Duk yadda za'ai karki yarda da wannan aure nima zanyi ƙoƙari na ta nan, Nifa ko ba Mahir ba wallahi nafi son Adaah ta auri Miji na kece sa'a irin yadda ƴaƴan ƙawayen mu suke aura haba ƙiri ƙiri za'a tauyeki ƴa ɗaya da Allah ya baki za'a cutar da ke a bata Ɗan jagaliya talaka faƙiri marar ilimi wanda ba lallai yasan darajar mace ba Niba burina Adaah ta auri ɗana ba Burina ta sami Mijin nuna sa'a mijin da zamu nunawa duniya cewa ƴarmu ta auri Namiji, wallahi inda ina da ƴa mace Budurwa Maryam kota halin ƙaƙa sai na shiga na fita na nemo mata wani ƙusa a ƙasar nan Ina zan yarda ƴata ta auri talaka" Kalaman Lubna suka ƙara Raunana momi suka kuma ƙara bata ƙarfin gwiwar Tsanar auren da za'ai wa Adaah a raunane tace. "Lubnah wallahi bada ban kar nai ƙarya ba sai nace kinfi kowa sona da damuwa dani, Tinda lamarin nan ya kunno ke kaɗai kike bani ƙarfin gwiwa duk da malam yace Adaah ta auri mahir amman ke ba burin ki ma ta aure shin ba ke burin ki ta tsallake ta sami miji na kere sa'a ya zanyi yanzu yau fa zasu kawo lefe?" Ta faɗa tana kuka! Lubnah ta cije baki ita kaɗai tasan meke ƙasan zuciyarta sai kuma Allah kafin tace. "Karki musun zuwan su wannan ma wata dama ce da zaki ci musu mutunci karma ki gayyaci kowa daga dangin ki ke kaɗai zaki zauna su zo ki ci zarafin su tass kwaɗayayyun banza kinga daga nan suma in suka ji haushi zasu koma da ɓacin ranki nan ma wata damar ce da zaki wargaza auren" Da sauri momi tace. "Haka ne lubna dama wa zan faɗawa a dangina Allah na tuba Ai wallahi dama ni burina in Adaah ta sami miji ku zaku yi komai cikin girma ba tare da kun bani kunya ba" Sai da suka gama tattauna komai sannan sukai sallama momi ba abin da take sai girgiza ƙafafu Adaah ta ja jiki ta ƙaraso wurin Momi. Murya cikin rauni tace. "Allah momi ina son ya Mahir ɗin Momy lubna yanzu bani jin zan iya rayuwa da wani idan ba shi ba momi kada ki bari Abba yayi mini auren dole" Momi ta janyo Adaah jikinta tana rarrashinta Har ta samu ta saki ranta. Cikin shiri Abbah ya sakko sabida zai fita kasuwa zasu gana da wani mutum dake jiran shi duk da yana buƙatar hutu amman hakan ba zai samu ba. Har lokacin bai da sukuni a fuskar shi ya ce. "Maryam sai ki sanar da Ƴan uwanki nan da lokaci kaɗan zasu kawo kayan lefen akwai Lemuka da ruwa dana sa akawo sai ki sa masu aiki suyi musu Girki ki ɗauki kuɗi a ɗakina ki sallame su duk da ƴan gida ne amman yaba kyauta tukwici" Idan kujerar data ke kai ta tanka to ta tanka wa Abbah har ya ƙare ya fita itama Adaah da ƙyar tai masa Adawo lafiya aiko yana fita tai ɗaki aguje tana kuka. Momi da takaici ya hanata motsi a nan ta cigaba da zama koda mai kawo ruwa da lemuka ya turo mai gadi cewar ya ƙaraso cewa tai ace ya mayar dasu basa buƙata haka ya juya har akai azahar tana zaune sai da ta gaji dan kanta sannan ta miƙe ta shiga ɗaki tayi sallah ta ƙara dawowa parlourn jira kawai take masu kawo lefen su zo. Ƙarfe ukun yammaci daidai Maimuna tai wa su Ya minau Iso babban parlourn gidan ƙanin mahaifin nasu wanda in za a kashe su ba zasu iya cewa ga yanayin gidan kawun nasu ba sabida ba zuwa suke yi ba. Ya minau ce, sai Aunty hajjo, da Faridah da Aunty Nafi ƙanwar Innah sabida innah tace karsu faɗawa kowa daga cikin danginta domin basu san kalar tarar da zasu samu ba gudun abin kunya, gwara Aunty nafi ƙanwar Innah ce cikinsu ɗaya bazzawara ce take zaman gida. Su Ya minau suka nemi guri suka zauna Umar ne ya dinga shigo da akwati nan ya jere su reras a parlourn. Momi tana kallon su batare data amsa sallamar su bare akai ga batun ta amsa gaisuwar da suke mata ba. Aunty nafi ta ce. "Ina mutan gidan ne muna ta sallama kamar babu kowa" Tsaki mai ƙarfi Momi ta saka tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙaro Ƙarfin Tv. Aunty Hajjo ce tace. "Innah Maryam barka da rana ga abin arziƙi mun kawo kuma mun zo kamar baku shirya zuwan namu ba naga babu ƴan ɗaga kaya koda yake abune duk gida ina amaryar tamu?" A fusace Momi ta ɗago tana watsa musu harara kafin ta taso har gabansu. "Ku wasu irin mayu ne? wai ba'a faɗa muku bama ra'ayin haɗin auren nan ba kwaɗayi ne yasa Za'a ɗauki ƴata a bawa Ɗan uwanku to ni dana haifeta bana so Itama bata so don Allah ku ɗauki gayyar tsiyarku kuje kucewa Ubanku bama........ Da sauri Anty Nafi tace. "Kai kai baiwar Allah ya kike abu irin na Mutane marasa kan gado Shin ba mijin kine ya kawowa Baba tallan ƴarki ba har kike kiran kayanmu da gayyar tsiya wallahi ke kam baki gaji arziƙi ba duk inda kika fito daga tsiya kika fito Yau inda ina da iko sai na hana Saadik ya auri ƴarki sai kace autar mata kije kiga yadda ƴammata suke tururuwa akan shi ke an samu an liƙa masa jarabar ƴarki har kina da bakin magana" Anty nafi ta kai maganar cikin Ƙunar rai. Tabbas yadda su Farida suke jin zuciyoyin su bada ban taci darajar Baba Amadu ba da babu abin da zai hana su gargasa mata baƙaƙen maganganu amman wata fuskar tafi gaban mari taci arziƙin auren ƙanin mahaifin su sabida haka da sauri suke ficewa daga parlourn. Momi dan izzah da ƙasƙanci takan akwatinan ta dinga bi tana takawa tana tafiya zuciyar Aunty Nafi tai zafi ji take kamar Ranta zai fita dan ɓacin rai bata taɓa ganin mace mai izza da wulaƙanci da rashin sanin darajar mutum irin matar nan ba. Sai a titi suka haɗu da junan su Ya minau mai rauni tuni ta soma kuka. Umar ya samo musu ɗan sahu suka hau duk cikin su babu wanda ya iya magana, har suka ƙarasa Gida. Yanayin da suka shigo gidan kaɗai shiya fahimtar da innah abin da ke zuciyoyin su. Saadik yana zaune saman kujera ƴar tsugunno yana wanke takalmin training ɗinshi. Farida randa ta nufa tana shan ruwa. Su kuma suka zauna saman tabarma. Kukan ya Minau ne ya cika kunnuwan su. "Don Allah Innah ki cewa Baba yabar batun auren Saadik da Ƴar gidan Baba Amadu haba talauci hauka ne duk wahalar da muka sha ganin munyi komai cikin tsari abin ya kasa yiwuwa matar nan takan akwatinan da muka kai ta dinga bi tana takawa bayan cin mutunci da muzancin data mana.........SO DA ALƘAWARI....! littafin kuɗi ne 500 Naira zuwa asusun bankin 0078174806 sterling bank, ko kuma 9022260850 Opay bank,Shaidar Biyan kuɗi zuwa 09022260850, Ƴan Private waɗan da ba sai nayi adding ɗinsu a grp ba ta Private kawai zan dinga tura musu 1000 Naira ne in sha Allah. *SO DA ALƘAWARI..!*🌹                   *NA* *AUTAR MANYA*                      *15* Idanunta yayi burɗun burɗun yayi wani irin ja, fuskarta ta kumbura sabida tsananin kuka wanda take yin sa cike da tsana da ƙiyayya. Daga ita sai ɗaurin ƙirji daga dokin wiyanta zuwa cinyoyinta duk dilka ce Aunty Mariya ta sa wata mai gyaran jiki ta shafa mata gefe guda kuma ga haɗi na musamman a kofi wanda zuma ce da sauran ingantattun magunguna na gyaran jiki Aka zuba mata zata sha. "Rabi ba zaki ɗauki kofin nan ki kafa a bakin ki ba sai ranki ya ɓaci?" Cewar iyah wadda take zaune ta saka Adan a gaba. Hawaye ta share babu damar musu ta ɗauki kofin tana sha tana yatsine fuska. "Ina tausaya miki Rabi zaki je ki rayuwa wadda ba iri ɗaya data gidan ku ba, dama shiyasa ake son iyaye mata su horar da ƴaƴan su akan ayyukan gida da tarbiya sabida baka san ina ɗanka zai je yayi rayuwa ba, zaman aure zama ne na har abada sabida haka ki daure ki koyi tarbiyar zama da miji da kuma ƴan uwan shi sannan ki tina mijinki nada uwa nan ma sai kin koyi tarbiyar zama da ita" Duk abin da iya take faɗa tana jinsa ne ta bayan kunnenta domin tabbas bata shirya zaman auren ba babu wanda zata bi babu abin da zatai musu tinda har ya kafe sai ya aure ta, to ta ɗaura ɗamarar gasa shi  sai ya gwammace kiɗa da karatu tinda har ya nace sai ya aure ta. Tana kuka tana komi ta shanye maganin aka kammala mata gyaran jikin Aunty Mariya tace ta shiga wanka ga ruwan ɗumi can a toilet yana jiranta. Sai kallon banza take watsa wa dangin mahaifiyar tata waɗanda suka zo biki don wasu ma sai ranar ta sansu don ba shiga cikin su take yiba, ta tashi a wulaƙance ta shiga wankan. Wai inda aka ci sa'a ma tana shakkar Iyah don tsohuwar batai mata da daɗi shiyasa har ta ke yin abun da Aunty mariyar ta sakata. Koda tayi wankan ma zamanta tayi a ɗakin Iyah taƙi fitowa tana jin ƴan uwan iyah nata tsokanarta amman taƙi magana dama iyah ta kashe bakin kowa duk wanda ya tambayi bai ga Maryam ba sai tace maryam kam Kunya ta hanata zuwa wajan biki tana can gidanta tace gasu Mariya nan sune iyaye, tinda duk tsiya naka nakane baka bada fuska a wajan wani don ya ɓaci duk baƙin halin Maryam ƴarta ce, abin da yasa ma ta ɗauko Adaah tasan ba za'a wanye lafiya bane da Maryam shiyasa Abbah yace tayi taron a gidanta a ɗauki amarya agidanta dama ɗaurin aure a Ƙofar Gidan Baba za'a ɗaura tinda shine maɗaurin auren dama. Wajan magariba wasu daga cikin Dangin su Iyah suka dawo daga gidan Amarya sai dai motar data ɗauki kayan ɗaki ta dawo da fin Rabin kayan ɗakin a cewar wata daga cikin ƴan uwan iya ai kujera ma guda ɗaya ce doguwa kaɗai ta shiga falon, Uwar ɗaka kuma sun saka katifa don gadon ma yaƙi shiga sai akwatinan da aka sa don su madubi ma duk sun ƙi shiga sabida kayan ba ƙananu bane. Ataƙaice dai yadda suka sanar da Iyah falon ya sami carfet sai doguwar kujera guda ɗaya sai labulaye suma ba duka ba uwar ɗakan kuma katifa da akwatinan Adaah, Kitchen ma Gas yaƙi shiga sai tukwane da ƴan tarkacen ƙananun kaya ne suka sami zama sabida rashin wadataccen faɗi a gidan Iyah ta maida ajiyar zuciya tace. "Ai babu damuwa Allah ya sa albarka hakan, bari naiwa mahaifinta magana in yaso sai a maida kayan kawai" Sabgar haɗa miyar taushen biki aka cigaba da yi. Adaah na ɗaki tuni zazzaɓin takaici yayi awon gaba da ita ***** "Yanzu saratu duk yadda Jiddah tayi wa Saadik halacci haka zai mata kawai sai ganin katin ɗaurin aure mukai ana rabo?" Cewar wata maƙociyar su Jidda mai suna talatu. Umma ta kama haɓa tayi tagumi Cikin damuwa tace. "Ni duk ba wannan ba, na samu wannan uwar nacin ta rabu da shi gaba ɗaya ta fitar da shi daga zuciyarta ta nuna da shi da babu duk ɗaya amman taƙi kullum kuka wallahi jiya daga ni har mahaifinta bamu rintsa ba ni yaya zanyi ne" Ummah ta faɗa duk damuwa ta bayyana a saman fuskarta. "Hmm saratu ai tashi tsaye zaki ki samawa ƴarki farin cikinta, wannan aure ai na kwaɗayi ne naji ance ƴar ƙanin mahaifin sace mai kuɗi kuma ita kaɗai ubanta ya haifa kinga da zarar ta haihu ai dukiya ta su ce sabida haka idan har kina buƙatar taimako akwai wani da zan haɗaki da shi a jawo hankalin Saadik ya birkice muku" Umma tai jimm kafin tace. "A iya ganin idanuna ai kamar soyayyar da yake wa Jiddah ma ta wadatar in muka ce zamu haɗa da bin malamai zamu shiga haƙƙin sa, Ni kin san talatu bana harkar biyar malaman nan nafi gane tsaiwar dare, Nidai barni in raina ya ɓaci zanyi faɗana sosai amman bana raba imanina biyu in har Allah yace jidda matar Saadik ce zasu yi aure amman in har Allah bai ƙaddara ba babu wanda ya isa ya basu junansu" Cikin rashin samun nasara talatu tace. "Haka ne saratu to Allah ya daidata lamarin bari na ƙarasa gida" Ummah ta raka talatu har bakin ƙofa ta tafi. Ɗakin jiddah umma ta shiga ta sameta kwance da rigar baccin jiya a jikinta, ummah ta sami guri ta zauna a gefenta tare da kamota zuwa jikinta. "Kinga har yanzu jikin ki akwai zazzaɓi don Allah jiddah ki bar wannan damuwa nina fiki shiga tashin hankali amman yaya zamuyi mahaifin ki ya baki haƙuri nina baki haƙuri amman kinƙi daina kukan nan" Muryarta sanyi ƙalau tace. "Ummah kawu Saadik fa aure zaiyi gobe, duk yadda nake son shi ya kasa aure na a karon farko sai wata haba umma ta yaya zan sami Nutsuwa umma ki taɓa zuciyata kiji yadda take harbawa" Cikin faɗa ummah tace. "Zaki kashe kanki, ne a banza kinga sun kasa bikin su? ko kinga sun dena shirin su ina ba har lefe ya haɗa mata ba to in zaki gane karatun ɗa namiji ki gane, ni inda kinyi zuciyata da shi da babu duk ɗaya ki tattare su har mahaifiyar tashi ki watsar itama banda munafurci meye a auren da bakwa so harda gayawa maƙota su zo suga lefe in zaki buɗe idanunki ki kalli gaskiya ki buɗe, don Allah ko yayi miki magana karki kulashi ki gasa mai maganar da zatai mai ciwo" Jidda ta juya tare da lumshe idanunta tana jin son shi aduk kan gaɓɓan jikinta soyayyar shi na motsa mata kamar yanda Numfashinta ke fita sam bata jin maganganun umma zuciyarta ta tafi tunanin shi har umma ta gama faɗanta ta fita. A hankali ta jawo wayar umma data ɓoye a ƙasan pillow ta miƙe tare da rufo ƙofarta gudun dawowar umma. Ta kunna wayar tare da zuba wa wayar ido can kuma ta shiga Jera lambobin sa data haddace su akanta ta shiga kira. Saadik dake kwance don har lokacin bai ji daidai a zuciyar shiba, tinda ya dawo daga sallar asubah yake juyi a katifa yana jiyo sautin share sharen tsakar gida da yara keyi sai haɗa kayan gidan suke sabida shirin ɗaurin auren gobe. Baida niyyar tashi bare akai ga batun yayi wanka, gaba ɗaya jikinsa yayi masa nauyi dama abinka da jikin wahala an saba fafutukar nema. Wayar shi  ta shiga ƙara alamun kira na shigowa, a hankali ya lalubi wayar ganin lambar dake yawo a saman screen ɗin wayar yasa shi sakin murmushi har kiran ya katse sannan ya shiga kira yaushe rabon daya ji muryarta yaushe rabon da su haɗu gaba ɗaya ta yi masa yaji ta ɗauke masa wuta tinda maganar auren shi ta fasu shi kuma yana jin nauyin zuwa inda take duk da akwai shirin kai kuɗin auren shi gurin ta kamar yadda baba ya sanar da shi. Bayan ta ɗaga wayar shuru tayi masa. Cikin tattausar murya yace. "Ƴammatana an dena fushin dani kenan?" Turo bakin ta tayi kaɗan kamar yana kallonta kafin ta share hawaye. "Sabida kaga ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba ya sa ka zaɓi yi min haka?" Ya saki murmushin takaici. "Hawwa yaya kike so nayi ne mu duka bamu isa mu ja dayin Allah ba" Sai ta saka kuka. "Dama haka zaka ce daga nai magana sai ka faɗi haka amman ai wani abin ma akwai son zuciya acikin sa" Ta faɗa har lokacin tana kuka! "Kinga idan kin san ɓacin rai kika kira ki sa min zan kashe wayata haba ke wace mutum ce yaya kike so nayi ne kin san abin da yake damuna kin san meke zuciyata so kike na bujirewa mahaifina ne sabida farin cikin ki ko yaya?" Ya faɗa yana hucin ɓacin rai. Cikin sanyin murya tace. "Kayi haƙuri nima bani na ɗorawa kaina soyayyarka ba ka tayani da addu'a Allah ya yaye min" Sai ta saka masa rauni a zuciyarsa muryar shi a kwance ya shiga rarrashinta. Sai ga shi ta ware tana dariya, sam ta mance ma da damuwar data shiga cikin kwanakin nan ta kuma yi watsi da huɗu bar umma ta saka aranta Saadik ne farin cikin rayuwarta. Lokaci mai tsayi suka ɗauka suna hira kafin suyi sallama shima yaji wani sashi na zuciyar shi ya sami nutsuwa jin tana cikin farin ciki. Innah ce ta turo ƙofar ɗakin nashi ta shigo bakin ta dauke da sallama. Da sauri ya tashi daga kwanciyar da yake. Ya shiga gaishe da ita cikin ladabi "Sadauki ina ta zuba idanun ɓullowar ka gidan shuru, shiyasa nace bari naji ko lafiya?" Ya sauka daga katifa ya miƙe ƙafafun sa ya zube su a ƙasa yana cewa. "Lafiya lau, innah zan shigo sai nayi wanka yau na tashi da nauyin jiki ne" Ta kalle shi da kulawa "To  kayi hanzarin fitowa ciki ka sa wani abun acikin ka kaga rana harta fito" Cikin kulawa yace. "In sha Allahu" Innah ta fita shi kuma wata wayar ya ɗaga wani mutumin sa ne dake siyan ƙarafan shi a kasuwa suka gaisa mutumin yace. "Malam Saadik ashe lokaci yayi Allah yasa akhairi jiya Yaron ka ke faɗa min nazo shagon naka baka nan yace kuna shirin biki ne amman abin alkairi yazo ba labari" Yayi ɗan murmushi kaɗan. "Wallahi abin ne yazo babu shiri amman kayi haƙuri" Mutumin yace. "Ba damuwa ba zan sami damar zuwa ba, amman ga saƙo nan ba yawa na sa maka ta account Allah yasa albarka" Saadik yace. "Harda hidima to Allah ya sa ka da alkairi na gode ƙwarai" Sukai sallama daya duba kuwa dubu ashirin ne mutumin ya tura mishi. Wanka yayi ya shirya cikin ƙananun kaya ya fita cikin gida A bakin ƙofar kitchen ya sha shayi da biredin da innah ta haɗa masa Atm ɗin shi ya bawa Umar yaje P.o.s ya ciro masa dubu ashirin ɗin da mutumin ya turo masa gaba ɗaya ya bawa Innah yace ayi cefane anjima zai kawo shinkafa zai je janguza domin tafi sauƙi acan. Inna ta karɓi kuɗin ta ƙirgi dubu goma ta miƙa masa sauran. "Dubu goma ta isa sadauki ina da shinkafa ta ba sai ka siya ba, ka bar kuɗin ka ni ba wani taro zanyi ba idan ƴan uwana sun zo sai ƴan uwanku na makoɗa shikenan sai waɗannan yaran" Ya ɓata fuska. "Innah me kike siyarwa da zaki ce zaki hidimar ƴan biki nifa innah ban so ki ɗaga hankalin ki Allah ya rufan asiri komai zanyi" Fafur taƙi amsar kuɗin nashi. Sabida tausaya masa take nauyin yayi masa yawa yayi nasu yayi na marayun gabansu sannan ga na gidan shi zai fara. Haka ya fita ba dan yaso nauyin data ɗora wa kanta ba, zuwa rana ƴaƴan innah sun hallatara sai matar ƙaninta da matar yayanta sai Yayarta da Anty nafi sai wasu daga cikin dangin su Baba na makoɗa da suka zo miya su Aunty hajjo suka ɗora a ranar dai kwanan hira akai damma burin da suka ci abikin bai cika ba sabida ɓacin ran da suka kwaso washe gari maƙota suka shigo tayin kwasar tuwo wajan takwas an haɗa komai na ɗaurin aure. Tin ƙarfe goma su nura suka ishi Saadik daya shirya sufa sun kintsa sabida goma da rabi za'ai ɗaurin auren. Cikin farar shadda ɗinkin babbar riga da ƴar ciki ya shirya kansa da hula da agogon silver fari a tsintsiyar hannun shi sai baza ƙamshi yake da ka ganshi kaga ango ya fita ƙofar gida abokan shi suma duk farar shaddar suka sanya irin tashi suka sanya shi a tsakiya suka shiga cikin gida Innah ta saka sabuwar atamfa sai gaisawa take da ƴan uwa ta waya waɗanda basu sami damar zuwa bikin ba. Tana ganin tawagar su saadik ta saki Murmushi tana kawo hannu ta rungume shi bayan ta kashe wayar, sai ta hau kuka! Saadik ya sa hannu yana share mata hawayen nata su Ya Minau mai za  suyi  inba dariya ba gaba ɗaya yadda Innah tai ya bayyana tsantsar soyayyar da take wa Saadik da ƙyar ya cireta daga jikin shi suka fita wajan ɗaurin auren Ƙofar gidan sune wanda tuni ya cika da mutane sabida Abba yayi gayya Baba ma yayi gayya. Ƙarfe goma da rabin safiya alƙawarin Allah ya tabbata Aka ɗaura auren. Abubakar Muhammad Makoɗa.                        Da Rabi'atu Ahmad Makoɗa. Akan sadaki mai daraja shaidu suka shaida,bayan anyi addu'a tare da fatan alkairi ga amarya da ango Baba da Abbah kowa ya shiga gaisawa da mutanan shi. Duk yadda saadik yaƙi faɗin ɗaurin auren nashi hakan bai hana jama'a tururuwar zuwa ba haka kowa ya dinga janshi ana hoto sai dai fuskar shi sam babu sukuni musamman daya ga yayyen jidda da mahaifinta sun tawo wajan shi suna yi masa Allah ya sanya alkairi. Ƙwarya ƙwaryar walima suka yi ba wani waje suka jeba anan ƙofar gida su Babawo suka dinga raba abinci a ledar takeaway wa abokansu wanda shi sam bai da labarin wannan hidima sai yanzu daya ga suna yi. Sai wajan ƙarfe ɗayan rana jama'ar suka rarragu sannan ya sami keɓancewa da Abbah da baba da wasu daga cikin ƴan uwan su na makoɗa Su babawo na waje suna jiran shi, shi kuma yana tsugunne a soron wajan mahaifan shi. Abbah ya dube shi. "Abubakar Ga amanar Rabi'atu na sabida yau ina jin na sauke nauyin dana ɗaukarwa kaina ko yanzu Allah ya karɓi raina burina ya gama cika don Allah don Annabi ka riƙe min ita amana" Muryar Abba tai rauni sosai wanda hakan yasa jikin Saadik yin sanyi shima baba nasiha ya dinga masa kafin ya bashi umarnin zuwa gidan iyah shida abokan shi domin su gaisa da ƴan uwan amarya. Ba don yaso ba yabi umarnin mahaifin nashi. Mota suka hau ta wani abokin su zuwa hotoro sabida Baba ya sanar mai acan ake taron da yake yasan gidan kakar tata shiyasa suka tafi can kai tsaye Da yake motar gida ce sunyi saurin ƙarasawa gidan Iyah nan ɗin ma akwai taron mutane. Ƴan uwan iya suna ganin tawagar angwaye suka hau buɗa harda masu fesa turare har falon Iyah akai wa su Saadik iso wadda ta cika da farin ciki maɗaukaki. Suka zazzauna a saman kujerun falon masu tsokana nayi masu hotuna nayi. Daga ɗaki Aunty mariya taitai da Adaah ta fito wajan angon nata taƙi sai ma kifa ciki datai a kan gado tana rusa kuka. Da ɓacin rai Aunty mariya take sanar da iya batare da kowa ya kula ba. Cikin hikima iya ta dubi saadik. "Kasan kishiyar tawa da kunya taƙi fitowa tin safe ko zaka shiga ku gaisa ne?" Kanshi a ƙasa yace. "A,a dama mun leƙo ne mu gaida ku nan ma ya isa" Ƴan uwan iya ne sukai masa caa akan sai ya shiga sun gaisa da amaryar tashi ba dan yaso ba ya miƙe Aunty mariya tai masa iso zuwa ɗakin Iya. Ya dakata a bakin kofa batare daya ƙarasa cikin ɗakin ba. Sautin kukan ta ya cika ɗakin da ƙyar ma idan tasan da shigowar shi. Miƙewa tai tana rangaji zata shiga toilet sabida fitsarin daya ciyota, haɗa ido sukai da juna atare gaban su ya faɗi. Kasa taka ƙafarta tai sabida nauyin data mata. Shi kuma ya tsinci kanshi da kafeta da ido yana hango ramar datai ta ƙara baki idanunta ya faɗa lallai ba ƙaramar tsana taiwa auren shiba kamar yadda shima ya tsani auren nata. Ƙaramin tsaki taja kafin ta juya da sauri ta shige toilet ɗin ta banko ƙofar. Murmushin gefen baki ya saki tare da juyawa yabar ɗakin. Sallama sukai dasu iya suka fita zuwa mota suka nufi gida. Sabida yawan mutane yasa yayi kwanciyar shi a shagon Nura duk da abokan su nata shigowa suna masa Allah sanya alheri. sallah kaɗai ke tada shi don bai shirya tinkarar gida yanzu ba sabida mutane. Ƙarfe Shiddan yamma motocin dasu saiti suka nema dan ɗauko amarya suka jeru a ƙofar gidan Innah ƴan uwansu na makoɗa ne mutum biyu suka shiga motar don ɗauko amarya. Cikin mutunci su Aunty mariya suka karɓi masu ɗaukar amarya wadda sai da akai da gaske sannan ta shirya aka fito da ita tana kuka kamar ranta zai fita. Har motar ta tsaya a ƙofar gidan Innha Adaah tana kuka Aunty Mariya da wata ƴar uwarsu suka kamata kanta a lulluɓe suka shigar da ita gidan Innah wanda wannan shine zuwanta na farko gidan a  tun  tasowar ta da girman acire ƙuruciya bata sani ba ko an kawo ta amman dai da girmanta wannan ne karon ta na farkon zuwa gidan. A rumfar innah suka zaunar da ita duk yadda aka so innah tai magana taƙi kanta yana ƙasa ba zaka fahimci abin da yake ranta ba ganin lokaci naja ne yasa suka miƙar da Adaah suka nufi gidanta da ita. A ƙaramin falon ta saman doguwar kujerar da aka saka guda ɗaya suka zaunar da ita Lokacin daga ita sai Aunty mariya sauran mutanan sun fita a hankali Aunty mariya ta yaye mata mayafin. Tare da ce mata. "Rabi'atu kinga dai yadda Allah ya tsara miki rayuwarki ko ba a faɗa miki ba kin san gidan da kika shigo sabida haka ki cire duk wata izza da taƙama ki biyayyar aure in sha Allah zaki alfahari da wannan auren naki" Ita dai kuka take har Aunty mariya ta gama mata nasihar tabar gidan falon ya rage da ga ita sai halinta. Idanunta ta buɗe tana bin falon da kallo duhu ne sosai acikin sa don hasken fitilar dake kunne ya fara mutuwa alamun batir ɗinta yay sanyi, ga uban sauro wani irin zafi ke shiga jikinta ware idanunta tai wannan wani irin gida ne acikin wannan gidan zatai rayuwa ita da ko wanki bata taɓa yi a rayuwarta ba amman shine za a kawota wannan gidan wanda ko kitchen ɗinsu na gida bai kai girma ba. Dunƙulewa tai guri ɗaya ta daddage ta zunduma ihu mai cike da tashin hankali fargaba ɗimuwa damuwa.......... SHIN WACE IRIN RAYUWA ADAAH ZATAI A GIDAN SAADIK? SHIN WANI IRIN ZAMA ZATAI A TSAKANIN UWAR MIJI? DA KUMA BUDURWAR MIJI WADDA SUKE TSANANIN SON JUNA? SHIN ZATA RABU DA MAHIR? WANI IRIN SHIRI HAJIYA LUBNA ZATAI AKAN CIKAR BURINTA? WANI IRIN MATAKI MOMI ZATA ƊAUKA AKAN AUREN? SHIN AUREN JIDDAH DA SAADIK ZAI YUWU? SHIN ZAMAN ADAAH DA SAADIK ZAI YUWU WANI IRIN ZAMA ZA SUYI WACE IRIN RAYUWA ZA SUYI ZATA SO SHI? KO SHI ZAI SOTA? GA DAI ADAAH A GIDAN TALAKA ƊAN GWANGWAN MAI CINIKIN ƘARFE DA ROBOBI YA ZATA SHIN FIƊA RAYUWARTA AGIDAN SHI WADDA ITA TA TASO GIDAN HUTU GIDAN JIN DAƊI WANDA KO WANKI BATA IYA BA BARE SHARA BARE ƊORA ABINCI SHIN YAYA ZATAI DA RAYUWAR GIDAN TALAUCI? AKWAI TARIN ABUBUWAN DA BAN ZAYYANO BA. SOYAYYA ƘAUNA SADAUKARWA YAUDARA CIN AMANA DUK ACIKIN LITTAFIN SO DA ALƘWARI TABBAS IDAN GANGA TA CIKA ZAƘI FASHE WA ZATAI BAN CE NA KAI BA AMMAN ZAN ƘAYATAR DA IKON ALLAH. DUK WANDA YA SAKA KUƊI YA SAI RABO YA RANTSE BAƘON LAMARI AI BAI NADAMA BA, BARE KUMA WANNAN DA AKA ƊAUKI TSAYIN LOKACI ANA SHIRYA SHI DUK DOMIN JIN DAƊI DA FAƊAKAR DA MASOYA KU SHIRYA BIYONI CIKIN TAFIYAR SO DA ALƘAWARI LABARIN SAADIK DA ADAAH DA JIDDAH YANZU MA AKA FARA WASAN DUK SHINFIƊA MUKAI A FREE PAGE YANZU LITTAFIN ZAI FARA RAYUWAR ƳAR MAI KUƊI MAI IZZAH DA TAƘAMA AGIDAN ƊAN JARI BOLA. WANNAN SHINE ƘARSHEN SHAFIN KYAUTA MA'ANA LAST FREEE PAGE BIYA........ 500 NAIRA A SAKAKI A PAID GROUP ZUWA ASUSUN BANKIN 0078174806 STERLING BANK KO KUMA 9022260850 OPAY BANK, GA MASU SON A SAKA SU A GRP KENAN WAƊAN DA SUKE SON NAKE BASU A PRIVATE KUMA BA SAI NA SAKA SU A CIKIN GROUP BA SU 1000 NAIRA ZA SU SAKA A BANKIN SAMA, A TURO SHAIDAR BIYA ZUWA WANNAN LAMBAR 09022260850. NOTE! Idan na kammala littafin nan complt ɗin sa zai koma 1000 naira ne kamar koda yaushe idan ina rubuta littafi farashin sa 500 naira ne idan na gama shi kuma complt 1000 naira ne. WANNAN KARON BEST IN REALITY MUKA TAƁO. AUTAR MANYA.🌹 Marubuciyar..... *RABON WANI* *BAƘON LAMARI* *RABO YA RANTSE* *FITAR RABO* *ƊAN MAJALISSA* *HASKE* *KOBA SO* *ZUMA A BAKI* *BAƘAR FATA* *ƁOYAYYAR ƘAUNA* *BA SONTA NAKE BA* *AUREN BARE* *DA IZZATA* *YANKAN ƘAUNA*