*BAYA DA ƘURA* FitattuBiyar2025               ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 _Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bamu aron rai da lafiya har muka kawo wannan lokaci. Ina yiwa kowa barka da shiga sabuwar shekara, ina roƙon Allah ya sada mu da alkhairin da yake cikin ta, ya kiyaye mu daga sharrin da yake cikin ta. Ya zaunar mana da ƙasar mu lafiya, ya kare mu daga duk wata fitina Amin. Ina roƙon Allah ya bani lafiya da numfashin ganin ƙarshen labarin nan kamar yadda na fara lafiya cikin aminci amin._ _Labarin BAYA DA ƘURA ƙirƙirarre ne, ban yi shi dan wani ko wata ba, in yayi kama da labarin wani ko wata ayi haƙuri rashin sani ne._ _Ban amince a canja min labari zuwa wata siga daban ba!._ https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp *BOOK 1* *Page 001.* Madaidaicin gida ne mai kyau a unguwar tudun maliki dake cikin ƙwayar birnin Kano, kai tsaye kana kallon sa baza kace wanda suke ciki takalawa bane irin sosai ɗin nan, haka baza kace musu suna da kuɗi ba sosai. Zasu shiga cikin masu rufin asiri wanda suka fi ƙarfin abubuwan yau da kullum. Yana da babban tsakar gida mai tsaho mai ɗauke da bishiyar mangwaro wacce ta mamaye ko ina baka ganin hudowar rana ko kaɗan sai iska da take kaɗawa busassun ganyaye suna faɗowa kan tiles ɗin da yake ƙasa. A share gidan yake tasss sai ganye da yake faɗowa bayan wannan babu ko tsinke a tsakar gidan komai yana mahallin sa. Mata ne guda biyu masu matuƙar kama da juna sosai, kana kallon su zaka fahimci uwa da ƴa ne duba da yanayin shekarun su. Yarinyar wacce baza ta wuce shekara ashirin da huɗu zuwa da biyar fara ce tass irin farin nan mai kamar madara, tana da haske sosai wanda a kallo ɗaya kawai zai ɗauki hankalin mutum. Tana da idanu masu kyau da gashin gira yalwatacce, ga bakin ƙarami mai ɗaukar hankali. Kallon farko zaka fassara ta a kyakkyawa don ta cancanci ta amsa wannan sunan musamman hasken ta da yake da ɗaukar hankali, suna zaune a kan tabarma ciki inuwar bishiyar suna cin kwaɗon zogale a cikin kwano ɗaya, yadda suke ci suna hira sai ka ɗauka yaya da ƙanwa ne saboda yadda suka shaƙu da junan su. "Mama!." Yarinyar ta faɗa tana kallon ta. Wacce aka kira da Mama ta haɗɗiye ganyen da yake bakin ta tace, "Na'am." Tace, "Maganin ki ya ƙare, ya kamata mu koma asibiti muga likita kar a samu matsala."Mama ta sauke numfashi tace, "Manal nawa ya ƙare saboda takura min da kike yi da shan sa amma ke bakya shan naki. Ko yaushe tunanin ki akan nawa yake bakya tunanin kanki, ciwon nan kina dashi ina dashi, amma bakya maganar kan ki sai ni." Manal tayi shiru ta sunkuyar da kanta tana murmushi Mama tace, "Manal koda bana gani da idanuna zuciyata tana nuna min duk abinda yake faruwa, nasan bakya shan magani a ko yaushe ni kike siyawa ke kuma ki zauna da ciwo bayan kina kallon illlar da ciwon yayi min, bakya tsoron yayi miki ke?." Manal tace, "Allah Mama ina mantawa ina da wani ciwon sugar indai ba maganar kika yi ba, in kika samu lafiya kamar na samu ne. Wallahi koda na sha maganin indai baki samu lafiya ba bazan samu tawa lafiyar ba Mama." Mama ta janye hannun ta daga cikin kwanon zogalen ace, "Meyasa haka? Lafiya fa lafiya ce Manal, babu abinda ya kaita mahimmaci a duniya. Ni na girma har na haife ku keda ƴar uwar ki ke kuwa fa? Kwata-kwata shekarun ki nawa a duniyar? Ko aure baki yi ba balle a kai ga batun haihuwa, rayuwar ki tafi tawa mahimmaci Manal." Manal tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Mama taki rayuwar tafi tawa wallahi, da na samu lafiya gwara ace kece kika samu. Shiyasa bana tambayar Baba kuɗin magani na, indai ba shine ya siyo ba bana faɗa masa." Mama ta girgiza kai tana murmushi tace, "Manal ɗin Mama kenan, to ban amince da abinda kika ce ba, da kaina zan sanar da Baban naku bakya shan magani." Manal bata amsa ba Mama ta kuma cewa, "Wannan karon ki tambayi Baban kuɗin naki maganim, bana so wani abu ya same ki Manal. Kin san waccan Yayar ta ki ba hankali ne da ita ba, ta ɗauki rayuwar da tafi ƙarfin ta ɗora a zuciyarta, ta raina ni bata jin maganata saboda tana da kyau, ke kaɗai ce dani Manal, shiyasa bana so wani abu ya same ki." Manal zata yi magana kenan suka jiyo muryar Mubeena tana faɗin, "Wallahi bazan ci ganye ba, na gaji ai ni ba akuya bace da za'a dinga yanka tsinannen salad ɗin na naira hamsin ana cewa shi zamu ci safe da rana a gidan nan wallahi bazai yu ba. In ku kuna da ciwo ni ai lafiya nake. Haka kawai a dinga tauye ni? Ina! bazata saɓu ba." Mama ta girgiza kai Manal tace, "Kar kici mana, Yay Mubeena cikin ki ai." "Daman bance zanci ba ai, zan fita na nemo abinda zanci ne yanzu" ta ƙarewa gidan kallo tayi tsaki tace, "Wallahi ni ba kalar gidan nan bace gabaɗaya, ban cancanci zama a gidan nan ba. Tsausayi ne kawai ya saka aka haifo ni a gidan nan, amma ni kalar babban gida ce wallahi." Manal ta kalli Mubeena sannan ta kalli Mama taga tana girgiza kanta kawai sai ta miƙe ta ƙarasa kusa da Mubeena tace, "Baki da hankali ne wai ke? Yaushe zaki nutsu ki fuskanci rayuwa don Allah?. Ke a ganin ki wannan banzar rayuwar itace wayewa?." Hararar ta tayi tace, "ni kike cewa bani da hankali dan ma kin raina ni?" Ta kalli Mama tace, "Mama yarinyar nan bata san ni Yayar tace ba ko me?" Ta sake kallon Manal tace, "bazan zauna a gidan nan ba, ban cancanci zama a cikin sa ba domin kuwa ni ba kalar wacce za'a ce a nan na rayu bace." Manal tace, "bazan girmama ki ba domin baki cancanci hakan ba, a gaban Mama kike cewa baki cancani zama a gidan na ba?, wallahi baki da kunya." "ki ƙyale ni wallahi bazan zauna a nan ba talauci ya kashe ni, common abinci irin wanda nake so naci ace ya gagare ni wallahi bazai yu ba. Ke da kika ga zaki iya sai ki zauna ni kam bazan iya zama a gidan nan ba, kinga tafiya ta" kafin Manal tace wani abun Mubeena ta fita da sauri kawai ta bita da kallo zuciyar ta babu daɗi ko kaɗan. Allah ya sani bata son wannan ɗabi'ar da Yayar ta take yi, bata son wannan rawar kan da take ji dashi kamar itace tafi kowa kyau a faɗin duniya. "Ƙyale ta Manal, zo ki cigaba da cin abincin ki, Mubeena Itace ajalina ita zata ga bayana" ta faɗa murya na rawa alamun kuka zata yi. Da sauri Manal ta koma kusa da ita ta zauna ta riƙe ta tace, "Don Allah Mama ki daina faɗar haka addu'a zaki mata." "Manal na rasa wacce irin yarinya ce, gabaɗaya bata jin magana abinda taga dama shi take yi. Ita a ganin ta raina ni da tayi shine daidai?, a ko yaushe bata ganin ƙima ta saboda na kasance ni ba irin uwar da take so ace itace mahaifiyar ta ba. Hmmm! Taje tayi ai duniya ce ga ishe ta duk abinda take so tayi. Wanda suka fita ma ya duniya ta bi dasu balle ita ƙaramar alhaki." Manal tace, "Ki yi haƙuri Mama, ki mata addu'a zata daina in sha Allah." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Manal tace, "Mama Ina zuwa." Mama tace, "Karfa ki bi bayan ta." "Ɗaki zan shiga Mama" ta faɗa tana shiga ɗakin da sauri. Babu komai a falon sai carpet amma a share yake tass sai fridge ƙarami a gefe a ajjiye, ta shiga wata ƙofar da take falon ta ƙarasa wajan akwatin kayan ta tana bincika inda ta ajjiye kuɗin taji babu su alamun Mubeena ta kwashe. Zama tayi a wajan dan daman ta san za'a yi haka a bayyane tace, "Innalillahi, na shiga uku Yaya Mubeena ta kashe ni" ta faɗa tana dafe kanta tana shirin yin hawaye saboda halin da ta jefa ta. Wayar ta ɗauka tecno andriod wacce bata da girma sosai dan ko a hannu ba babba bace, hannun ta har rawa yake ta kira lambar Muneeba tana ɗauka tace, "Yaya kin san da yadda Baba ya samu kuɗin nan ya bani kuwa?, Mama zan kai asibiti dasu fa, meyasa zaki kwashe?." Daga can ɓangare tace, "Shi Baban zaki komawa ya sake baki, ai kowa ya siyi rariya ya san zata zubar da ruwa, tunda har zai iya riƙe mu matsayin ƴaƴan sa dan yayi asarar wannan kuɗin ba komai bane. Kar ki manta kuma ƙanin ɗan uwan baban mu ne, ko babu aure tsakanin sa da Mama zai sake biya. kije ki tambaye shi in ba haka ba ki nemo kawai ni na kashe su ma" tana faɗa ta yanke wayar. Manal ta dafe kanta zuciyar ta na harbawa cike da ɓacin rai, dan da ace Mubeena ɗin tana kusa da ita a wannan lokacin wallahi zasu iya yin dambe dan kowa yasan halin ɗan uwan sa. Da ya aka samu kuɗin ma bata sani ba kawai burin ta taje tayi ƙarya ita a lallai ga mai kuɗi. Numfashi ta sauke ta kalli agogom wayar taga huɗu na yamma tayi ta share idon ta ta fito ta tarar har Mama ta tayar da sallar la'asar itama tayi alwala tazo kusa da ita tayi sallar, bayan ta idar ta kalli Mama tace, "Mama zanje wajan Surayya yanzu zan dawo, babu abinda kike so?." Mama tace, "kin daina zuwa islamiyya dai Manal." "Ba daina zuwa nayi ba Mama, bana so na tafi na barki ke kaɗai ne shiyass kawai. Kuma mun sauke har sau biyu na samu abinda na samu ai." Mama tace, "to haka zaki zauna kina tauye kan ki saboda ni Manal?, kin ƙi cigaba da karatun boko tunda idanuna suka rufe, islamiyyar ma gashi kin ajjiye. Ita waccan da bata da amfani a gidan sai ita take zuwa kuma ta raina mai biya mata ƙudin makarantar, ko yaushe a banza take kallon sa saboda bashi da kuɗi kuma ba shine ya haife ta ba." Manal tace, "Wallahi Mama babu inda zan iya zuwa na barki, ko naje bazan yi karatun ba tunanin ki zan dinga yi. Kuma ni culinary school nake so, na zama fitacciya a fannin girki." Mama tace, "to ai ko ita ɗin kin ƙi Manal." Tayi murmushi tace, "Zan yi Mama amma ba yanzu ba, zan tafi Mama akwai sabon girkin da na gano mana nake so naje mu gwada da Surayya." Mama tayi dariya tace, "shiyasa kika iya saboda in dai kin gani zaki ce zaki gwada. Jeki babu abinda nake so Manal sai kin dawo, Allah yayi miki albarka ya baki abokin zama na gari, ya haɗa ki da masu taimaka miki kamar yadda kike taimakona." Murmushi tayi tace, "Amin Mamana, sai na dawo" ta faɗa tana tashi ta fita zuciyar ta gabaɗaya babu daɗi akan lamarin Yaya Mubeena. Da sallama Mubeena ta shiga falon gidan babba mai kyau kai da kaga falon kasan mazaunan falon ma ƙananun masu kuɗi bane ba saboda yadda ta tsaru sosai, babar macen da take zaune sanye da glasses a idanun ta tana duba waya ta ɗago ta kalle ta tayi murmushi tace, "Mubeena kece." Murmushi tayi ta ƙarasa ta zauna kusa da ita tana murmushi tace, "Mummy ina wuni?." Wacce ta kira da Mummy tace, "how was your day?, Ya Maman ki?." "She's fine Mummy. Tace tana gaishe ki." "Ina amsawa" ta faɗa tana kallon mai aikin ta tace, "ina so ki dafa min couscous amma baki iya ba." Tayi shiru bata amsa ba Mubeena tace, "mummy ki kawo na dafa miki." Mummy tayi murmushi tace, "noo! Bilkisu tana ciki jeki" da sauri Mubeena ta tashi ta shiga cikin ɗakin ta samu Bily a zaune tana waya ta bita da kallo kafin ta tsaya jikin mudubi tana kallon kanta cikin burgewa. Ita kanta tasan tana da kyau ko ba'a faɗa ba, tana da kyaun da lokaci ɗaya zai ɗauki hankalin ka in ka kalle ta sai ka sake. Sake kallon kanta take yi kafin tace, "Allah bai yi za'a haife ni a irin wannan gidan ba, da a wannan gidan nake ai sai nafi haka kyaun gani, da wannan gidan na dace ba waccan ba." Bily ta katse kiran tace, "ke kullum kika zo gidan nan sai kin maimaita maganar nan, dallah ki shiga kiyi wanka mu wuce bana son ɓata lokaci." Bata ce komai ba ta shiga banɗakim tayi wanka ta fito ta zauna tana shafa mai Bily ta kalle ta tace, "Gaskiya Mubeena dole ki dinga baƙin cikin haihuwar ki da aka yi a gidan ku, ke kin ganki kuwa?, kina da kyau sosai, kawai farin Manal da yake mai haske ne yafi burge ni, dan kin ga ita babu masu wannan hasken da yawa a cikin nigeria. Ke kuwa haske dai wanda kowa ya sani ki ke dashi, amma kina da kyau." Mubeena tace, "bari kawai, bayan talauci ma ga uwa makauniya, ga mai riƙon namu ma talaka, ga ƙanwa soloɓiyo babu abinda ta iya kullum cikin kiyi haƙuri da duniya take faɗa min. Shiyasa ko a school ban taɓa bari na nuna ta matsayin ƙanwa balle kuma na nuna babar ta mu balle kuma gidan namu gabɗaya." Dariya Bily tayi tace, "Shege talauci. Amma bai kamata ki cewa Mama haka ba, kuma a ko ina zaki iya nuna Mama saboda ta fi ki kyau. Kawai dai da ace ke ƴar Alhaji ce da an gama magana." Itama dariyar tayi tace, "Ina jin daɗin haɗuwar mu dake, ke kan ki farkon haɗuwar mu kin ɗauka irin wata shegiyar nan ce ni baki san ganye na baro su suna ci ba." A tare suka sake yin dariya Bily tace, "Wallahi baki da kirki, ke baki bar kowa ba har Mama." Mubeena ta tashi ta buɗe kayan Bily ta ɗauki kayan da take so ta saka ta tsaya tana kallon kanta a mudubi dan ita kanta tasan tayi kyau ba kaɗan ba. Bily ta bita da kallo tace, "Gab nake da daina baki kayana domin in kika saka sai naga sun fi miki kyau a kaina." Dariya Mubeena tayi ta shirya tsaf tayi kyau sosai suka dauƙi jaka suka fita ko mummy basu yiwa sallama ba dan su ƴan boko ne babu ruwan su basa tauyewa Bily haƙƙin ta, Bily taja mota suka fita daga gidan. ***** A yadda ya shigo falon zai tabbatar maka da ransa a ɓace yake, cikin fuskar sa da bata da alamun walwala a ko yaushe dan kana kallon sa  zaka fassara shi a mutum mara fara'a, kuma baza'a rasa faɗa a wajan sa ba. Kyakykyawa ne mai duhun fata da madaidaicin jikin, yana da ido da dogon hanci siriri, fuskar sa ɗauke da zagayayyen gashin da ya kewaya ko ina. Cikin glasess ɗin da yake idanun sa ya kalle ta tana zaune kafin yayi magana cikin fusata tace, "wai kai waye gaba tsakani na dakai ne? Yayar ka ma Farida gaba nake da ita balle kai da zaka dinga min shishshigi a cikin lamarin rayuwata, ina ruwan ka da abinda na zaɓarwa kaina?, har nawa aka ke da zaka dinga nuna min daidai da ba daidai ba?." Wanda take yiwa maganar yana tsaye yana jin ta ya kalle ta yace, "ba yaya ta ba, ko kece kika haife ni baki isa kina yi abu ba daidai ba na zuba miki idanu ina kallon ki. Yasan yana son ki meyasa ya rabu da ke? Ya san zai dinga bibiyar ki har ki dinga shiga motar sa meyasa ya miki sakin da bazai iya mayar dake na?." "Ina ruwan ka dani?, haka na zaɓa baka isa ka hana ni ba wallahi." "Ai kuwa zaki ja masa, na rantse da Allah na sake ganin sa ƙofar gidan nan sai na saka n kulle shi ya kwana biyu a cell, in kina musu ki sake gayyato shi kiga nida ke waye zaiyi nasara." Anty Maryam ta harzuƙa matuƙa kamar zata kifa masa mari tace, "baka isa ba walalhi, ƙarya ka ke Bebi baka isa ka hana ni abinda nayi niya a cikin gidan nan ba. gidan ubana ne kamar yadda yake gida uban ka, ina da iko kana da iko, baka iya ka hana ni abinda nake so ba. In kana hana ƙanen ka ni Yayar kace." Ganin Mamy tazo wajan sai baice komai ba ya juya ya fita ransa a ɓace sosai. Yana fita ta kalli Mamy tace, "yaron nan yana neman raina min hankali, Mamy kiyi mana tsakani dashi, ni yayar sace babu ruwan sa da abinda zanyi." Mamy ta kalle ta tace, "Gaskiya yake faɗa miki ai, kishin ki yake matsayin ki na yayar sa shiyasa yake tsaye akan lamarin ki. Ke kuma banza shashasha mara kamun kai miji ya sake ki amma ya dinga bibiyar ki kina masa dariya saboda baki san abinda yake miki ciwo ba. Ya san yana son ki ya miki saki har uku?." "Mamy su Nabila da Nabil na duba fa." "Zaki min shiru ko sai na tsinke ki da mari?, babu mota a gidan nan da baza ki hau kije wajan yaran naki ba? Ki aika a ɗauko miki su ko lallai sai kinje inda suke?." Anty maryam ta sauke numfashi tace, "kenan yanzu Mamy shine mai gaskiya ni mara gaskiya?." Mamy ta Harare ta tace, "ki cigaba da abinda kike yi nan gaba zaki dana sani, sai a lokacin zaki fahimci Bebi gaskiya yake faɗa miki. Bebi gata yake miki wanda uban ki bai miki shi ba." Tana gama faɗa mata haka ta shige ta barta a wajan. Kai tsaye Bebi ɓangaren mahaifiyar sa Mama ya shiga wacce shi kaɗai yake kiran ta da Mummy kowa Mama yake cewa, amma shi tun yana yaro yake cewa Mummy har girman sa. Yana shiga  ya same ta a zaune ita ƙanwar sa Mimi ya ce, "yanzu Mummy abinda yarinyar nan Maryam take yi daidai ne? Miji ya rabu da ita ya sake ta amma ya dinga bibiyar ta har yana ɗaukafr ta a mota? Akan wanne dalili?." Mama tace, "to Bebi ni me zance? Ina ruwana tasan daidai ai sannan tasan ba daidai ba." Ya kulle idanun sa bala'i kishi yake ji yana addabar zuciyar sa ya kalli Mama yace, "shikenan sai a zuba mata ido kenan?." "To maganar taka me ta canja? Su mazan yayyen ta akwai wanda ya damu da yayi maganar ne?, kai kaɗai ka ke tayar da jijiyar wuya akan lamarin Maryam da Lubna." Bebi ya girgiza kai kawai yace, "bazan bari ba kin san da hakan Mummy." Mama tayi dariya tace, "shikenan Bebi, zaka dinga asarar maganar ka kuwa dan ba ji zatayi ba ita da kanwar ta." Kallon Mimi yayi kamar zai yi magana sai ya fasa ya fita ya shiga mota kai tsaye ya bar gidan. Nana Haleema. *BAYA DA ƘURA* FitattuBiyar2025     ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp *BOOK 1* *Page 002.* Getting better specialist hospital ya nufa, babban private hospital da ya samu lambar yabo a fannin abubuwa da yawa, asibitin shine private hospital na farko da aka fara dashen zuciya a cikin sa arewancin nigeria, asibitin ya haɗa manyan likitoci masu ƙwarewa a kan aikin su. Asibitin gabaɗaya sa an gina shi ne zuciya, da abinda ya shafi cututtukan jini, da abinda ya shafi ɓangaren mata, sauran abinda bai shafi wannan ba ana yi ne kawai amma ba dan saboda haka aka gina shi ba sa. Asibitin mutane huɗu ne suka cure waje guda suka samar dashi, kuma suna matuƙar kula dashi sosai, shiyasa ya zama asibiti mafi ƙolowar masu zuwa da kuma tsada, a duk shekara suna yin aikin kyauta ga masu buƙata ta musamman, wannan dalilin ya saka sunan asibitin Getting Better ya zaga ko ina. Bebi ya faka motar a babar harabar asibitin ya shiga cikin asibitin da babu mutane sosai ya hau sama ya buɗe wata ƙofa ya shiga office ɗin da ya kasance mallakin sa. Kafin ya zauna maza guda wanda baza su wuce sa'anin sa ba suka shigo ɗaya ya ce, "Haba Bebi kasan kai ake jira tun ɗazu kace min gaka nan sai yanzu?." Bai kalle shi ba ya nemi waje ya zauna suka kalli juna Huzaifa yace, "yau kuma waye ya taɓo ka haka?." Hamza yace, "naga sai tiriri yake yi shi kaɗai. Kasan da yake shi ɓacin ran sa baya ɓuya." Baice komai ba ya buɗe laptop sai kuma ya rufe ya dafe kansa baice komai ba har lokacin. Huzaifa yace, "ko zancen Rumana ne?." Daman ƙiris yake jira ayi masa magana ya ɗago a fusace yace, "wacece ita? Me take dashi da zancen ta zai dame ni har ya ɓata min rai?." Huzaifa yayi dariya yace, "masoyiyar kace wacce kaso kamar ka mutu, dan kayi tunanin ta har ya saka ka wannan damuwar ai ba wani abun bane." "Mtswwww!" Ya ja tsaki yana miƙewa tsaye. Hamza yace, "Bebi ni banga abin ɓacin rai akan batun Rumana ba, yarinyar nan tun asali ita ka ke so tayi aure ta barka yanzu kuma  ta fito tana bibiyar ka meyasa baza ka amince ba?. Ka sani na sani kana son ta meye na damuwar." Juyowa yayi ya kalle shi ransa na sake ɓaci  yace, "nayi maka kama da wanda zai auri bazawara? Nayi maka kama da wanda zai auri ragowar wani?. Look Hamza!  Kasan bana son wannan maganar, ka bar maganar kawai, kai ka san ba ko wanne ɓacin rai nake iya jurewa ba." Huzaifa yayi dariya yace, "to waye ya ɓata maka rai haka?." "Waccan yarinyar Maryam mana, mijin ya ya sake ta amma a dinga bibiyar ta har tana bashi fuska suna fita, ina suke zuwa? Meye alaƙar su? Meye rage a tsakanin su yanzu?." Huzaifa yace, "wai Yayarka Maryam ka ke cewa waccan yarinyar?." Bai samu damar bashi amsa bama Hamza yace, "wannan ɓacin ran ai ba shine mafita ba, samun sa zaka yi ki yi magana ya daina zuwa wajan ta in ba haka ba ka ɗau mataki." "Ƙyale shi, wallahi in yayi wasa dani I'll take him to court over this matter. Bai san waye ni bane shiyasa." Hamza yayi dariya yace, "a nutse zaka same shi kunyi magana,in bai fahimta ba sai ka ɗauki matakin da ka ke ganin ya dace. Amma ita Maryam ɗin itace mai laifi, da ita zaka fara dan da bata bashi fuska na da hakan bai kasance ba." Ajiyar zuciya Bebi yayi Huzaifa yace, "A rayuwata kaf ban taɓa ganin namiji mai kishin ƴan uwan sa kamar ka ba, shiyasa nake so nayi ko yi da kai amma Allah ba haka ya halicce ni ba, ina son ƴan uwana ina kishin su amma ba kamar kai ba." Dawowa yayi a zauna ya lumshe idanun sa kafin ya buɗe ya kalle su kamar zaiyi magana sai ya fasa a saka buɗe laptop yana aikin dannawa. Hamza yace, "ni na wuce gida naga kai kana da baƙi anjima ni kam na tashi." "Nima haka, Bebi sai mun yi magana" yana faɗa suka fita duk barshi yana aikin sauke Ajiyar zuciya. Bai jima sosai ba shima dan mutane biyu kawai ya gani a kulle ya fita ya hau mota ya nufi gida a lokacin magriba tana daf da yi. Babban falo ne mai kyau da tsari tana zaune a ciki da budurwa guda ɗaya a gefen ta tana turaren wuta yana tashi a hankali, kallon yarinyar tayi tace, "Mimi ki dakata da yin wannan turaren wutar na, kin san Yayan ku yana hanya ko?." Wacce aka kira da Mimi ta ɓata rai tace, "Wai shikenan Mama saboda shi sai mu daina turaren wuta saboda Allah?." Mama tace, "to ai ke kin san baya so ko?." "To Mama dan baya so ai ba gidan sa bane." Kafin Mama tayi magana wata ta fito daga ɗaki ta kalle ta tace, "Yaya Farida kin kina jin abinda Mama take faɗa, yanzu don Allah saboda Yaya Bebi shikenan sai mu daina turaren wuta a falon nan? Komai in baya so Mama baza'a yi ba kuma yana da nasa ɗakin fa." Anty Farida ta zauna tana dariya tace, "gaskiya dai Mama maganar Kausar da Mimi gaskiya ce, akan sa sai a daina turaren wuta don Allah?." Mama tace, "sanin kan ki ne baya son turare, da ya shigo zai sarƙe shi yayi ta tari akan me za'a yi abinda za'a cutar dashi?." Mimi ta taɓe baki Yaya Farida tace, "ya kusa ma ai yayi aure ya tarkata ya bar magana gidan kowa ma ya huta. Ban taɓa jin mutumin da baya son turare kamar sa ba, shi ko kusa dashi zaki je to kar ki saka turare mai ƙarfi. Matar sa ta shiga uku." Mama tayi murmushi tace, "shida Rumana ba, in sha Allah hakan ya kusa tabbata. Rumana ai ta san halin sa tun ba yau ba." Mimi da Farida suka haɗa ido basu ce komai ba. Fita Kausar tayi karɓowa Mama saƙo wajan masu kawowa lokacin da ta shigo take cewa, "Mimi kin san ga motar Yaya Bebi tana nufo gidan nan ga kuma Lubna can a zaune tana zance ko mayafi babu, kin san babu abinda zai hana shi magana wallahi." Da sauri Mimi ta tashi ta leƙa taga ta hango Lubna a zaune tana hira da saurayin ko mayafi babu a jikin ta, gashi fitted gown ta saka dakyar ta iya zama a akan kujerar saboda ta matse ta. Sakin labulen tayi tace, "ni da Yaya Adnan zai ji wallahi ya daina shiga harkar Lubna da Anti Maryam, ɗazu akan ya yi magana akan tsohon mijin Anti Maryam ke baki ji yadda suka dinga magana a gidan nan ba." Anty Farida tace, "akan me zai daina shiga harkar su?, dan Maryam ta kasance Yayar sa Lubna ai ƙanwar sa ce, kuma shine ido a gidan nan tunda sauran mazan duk sun yi aure sai shi kawai namiji babba a gidan nan. Duk abinda kuka yi hukunci ya hau kan ku abinda ya kamata ya dinga yi kenan." Jin an buɗe gate ya aka Mimi da Kausar saurin buɗe taga suna kallon Bebi ya shigo ya faka motar ya fito ya tsaya cak yana kallon ƴar rumfar da take harabar gidan su wacce Lubna take zaune ya hango suka haɗa ido da ita Lubna ɗin. Da sauri suka ga ta tashi a guje tayi cikin gida ɓangaren Mamy Mimi tayi dariya tace, "ashe rashin kunyar ta ƙarya ce." Kausar tace, "Yaya da jawowa kai magana yake, kalli ya nufi wajan saurayin nata ko me zaice masa oho." Anti Farida tace, "maza yazo ya same ku kuna leƙe ya haɗa har ku." Ganin ya juyo falon sai suka bar wajan a guje suka dawo suka zauna Anti Farida tayi dariya Mama ma tayi tsaki kawai bata ce komai ba.      Da sallama ya shigo sai yayi turus yana yamutsa fuska, sam sam baya son ƙhamshin turaren wutar nan ko kusa, baya son turare mai ƙarfi yafi son turare mai sanyin khamshi baya son turaren da zai ji shi ya dabaibaiye shi lokaci ɗaya. Kansa sarawa yake a duk lokacin da ya ji hakan, lokaci ɗaya jiri sai ya fara ƙoƙarin kayar dashi. Mama ta kalle shi tace, "Adnan ƙaraso mana ka tsaya." Ya tako ya ƙaraso bayan ya cire takalmin sa yace, "ƙhamshin falon ya canja." Yaya Farida tace, "kai ka cika iyayi wallahi, yanzu ina khamshin yake da zaka fara ɓatawa mutane fuska?. Kai haka za'a kai matar ka baza ka bari tana turaren wuta ba?." Ya kalle ta fuskar sa kamar ko yaushe ba yabo babu fallasa yace, "bana so, sai aka ce sai an yi min dole?." "Kar kaso" ta faɗa tana hararar sa. Sai taga yayi murmushi wanda ba ko yaushe ake ganin sa a kan fuskar sa ba sai mai sa'ar gaske ne yake ganin Murmushin sa tace, "lallai akwai abinda ya saka ka farin ciki, Tunda har Bebi yayi murmushi akwai abinda zai faru." Mama tayi dariya tace, "kamar wasa kin saka masa suna Bebi ya bishi tun kuna yara. Adnan ne baki iya cewa ba sai Abban ku yace kawai ki ce masa Baby ke kuma sai ki ke cewa Bebi. Gashi yanzu Adnan ya ɓace a gidan na sai Bebi, da gaskiyar sa da yace sai yaci tarar ki."  Anti Farida tayi dariya tace, "Bebi kuwa har jikokin sa, a katin ɗaurin auren sa ma sai an rubuta Bebi.” Baice komai ba ya kalli Mama yace, "Mummy barka da yamma." Tayi murmushi tace, "barka dai Adnan. Ya aikin naka?." "Alhamdulillah" ya kalli su Mimi yace, "ina islamiyyar?." Kafin su yi magana Mama tace, "sun ce sun daina zuwa ai, wai tunda sunyi sauka an basu allo zuwan ne zasu cigaba da yi sun gaji." Kallon su yayi baice komai ba sai girgiza kai akwai da yayi dukkan su sun tsure ba kamar Kausar da tafi Mimi tsoro sun san me shirun yake nufi ko bai furta ba. "Mummy haka za'a bar yarinyar nan tana abinda take so a gidan nan?, yau ta kawo wannan namijin gobe ta kawo wancan?. Da ita da Yayar ta me yake damun su?." Mama tace, "to ka isa kace wani abun Adnan? Sai muyi shiru mu zubawa sarauta Allah ido." Anty Farida tace, "Adnan hukunci zaka yi mata tsauri dan wallahi kanta rawa yake yi, daga ita har maryam ɗin sai kana musu jan ido, kaine ido yanzu dukkan mazan gidan basa nan sai kai kaina Abba." Jin ta ambaci Abba sai ya kalli Mummy yaga tayi murmushi kawai ya ɗauke kai zuciyar sa nayi masa mugun ciwo, halin mahaifin sa yafi damun sa akan komai, sam iyalan sa basa gaban harkar neman kuɗi ta fiye masa zama a gidan, ya girgiza kai ya rasa ya zaiyi da Abba in ka ɓullo masa ta nan sai ya sauke karkacewa. "Salam" aka faɗa daga bakin ƙofa ana shigowa duk suka kalli wacce ta shigo Yaya Farida tace, "Rumana meye kuma salam? Sallama kenan?." Tayi dariyar ta ƙarasa tace, "ai saboda taƙaitawa, babar Yaya ashe kina nan" ta faɗa tana ƙarasawa ta zauna a kusa da ita tace, "ina nan, ya Ammi tana Lafiya?." "Lafiya lau. Mama ina wuni" Mama ta amsa tana murmushi tana kallon ta. Rumana ta kalli Adnan tace, "Beb ina wuni." "Lafiya" ya amsa a taƙaice ba tare da ya kalle ta ba ya miƙe tsaye yace, "Mummy zan je ɗaki, duk da ma an kusa sallah" ya faɗa yana kallon agogon hannun sa. Mama tace, "to ɗan Mummy, Rumana sai ta kawo maka abinci." Ya girgiza kai yace, "zan shigo naci a nan" yana faɗa ya fita daga falon, sam baya son zama a inda turare ya yi yawa ga Rumana dab'iar ta kenan bulbula turare kamar ba mace ba shi kuma hakan yana ɓata masa rai. Wajan Mamy yaso shiga sai kuma ya fasa dan yasan ransa ne zai ɓaci wani lokacin ita take goyan bayan duk abinda suke yi, ya wuce ɗakim sa. Babban falo ne mai ɗauke da ɗakuna wanda ya kasance na su kafin yayen sa suyi aure su bar masa wajan gabaɗaya. Zama yayi akan kujera ya rufe ido ya buɗe sai kuma ya tashi ya shiga ɗaki ya shiga banɗaki yayi alwala yana fitowa Rumana na shigowa. Kallon ta yayi yace, "amma nayi miki warning akan shigo min ɗaki without notice ko?." Murmushi tayi tace, "Banda abinda ka Beb meye laifi dan na shigo ɗakin ka? Auren ka fa zanyi. Kuma ai ba yau aka sqbq ba." "Mtsww!" Yayi tsaki kawai baice komai ba tayi murmushi tace, "Beb ya kamata ka manta da baya don Allah, na karɓi laifina na tuba ina so rayuwar mu ta koma kamar baya dan Allah. Kar ka manta nice Rumanan ka wacce kaso a baya kuma kayi niyar auren ta, nasan har yanzu kana sona meyasa kake min irin wannan abun?." Fita yayi daga ɗakin ya barta ta biyo bayan sa ta sha gaban sa tace, "nasan kana sona har yanzu, dan Allah ka tsaya mu fahimci juna mu yafewa juna abin daya wuce dan Allah." "Ruman!" Ya faɗa yana kallon ta ta lumshe ido cike da jin daɗi, shine kawai yake cire harafin A ɗin gaban sunan ta, in yace Ruman ɗin na daɗi take ji sosai yace, "you should stop thinking that I still have feellings for you, what happened is already in the past as you said, everythings between us is truly over" ya faɗa yana kallon ta tana kallon sa. Ta marairaice tace, "My love!, I know I hurt you, but my heart still beat for you Beb. I see the love we shared hidden beneath the pain. Please, don't deny it, I know me just as much as I love you." Kallon ta yayi yace, "absolutely not!." "Don't do that Beb." Wani kallo ya yi mata Baice komai ba ya wuce ta zuwa masallaci dan ya gaji da saurare ta. Da kallo ta bishi ta sauke numfashi tana kallon sa tace, "Wallahi Bebi sai na aure ka, ko kana so ko baka so sai na aure ka. ina son ka a yanzu dole ka manta da abinda ya wuce ka aure ni ko da baka so. Baka ka tuna da baya ba, haka zaka haƙura ko baka so" ta faɗa tana fita zuwa falon Mama  ranta a ɓace sosai dan Mama ce kawai maganin sa. Nana Haleema❤️🥂 *BAYA DA ƘURA* FitattuBiyar2025     ©️ *Nana Haleema.* https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp *BOOK 1* *Page 003* Rumana na fita daga ɓangaren Bebi wajan Mama ta wuce tana matsar kwalla ta same ta tana sallah ta zauna kusa da ita har ta idar ta kalle ta tace, "Ruma Lafiya?." Rumana hawaye ya zubo daga idanun ta ta kalli Mama tace, "Mama ina son Adnan amma shi yanzu baya sona, yaƙi manta baya, na amince da abinda ya faru a baya laifina ne meyasa bazai amince ya yafe min ba?." Mama ganin tana kuka ya saka tace, "Ruma yanzu akan Adnan kike kuka haka?." "Mama I love him so much, bana son sake rasa shi a wannan lokacin, gabaɗaya ya canja kamar ba wanda na sani a baya ba, ki yi wani abun Mama....!" Ta faɗa tana sake zubar da hawaye. Mama  ta girgiza kai tana murmushi domin kuwa ita hakan daidai ya yi mata, ta tashi daga kan sallaya ta zauna kusa da ita tace, "Haba Rumana, ai indai ina da rai ina numfashi Adnan bashi da mata sai ke kawai. Ki daina asarar hawayen ki kece matar sa in sha Allah." Ta sake komawa kalar tausayi muryar ta tayi rauni tace, "Amma Mama yanzu baya sona, gabaɗaya ya canja ko hira dani baya yi kwata-kwata. Kinga a baya ba haka yake min ba, sai na wuni muna hira dashi amma yanzu ya daina." Mama tayi murmushi tace, "ki kwantar da hankalin ki wannan ba abinda zaki hawaye a kai bane. Ke kin san Adnan bashi da magana sai kun saba sosai, kuma bashi da fara'a ko kusa shima sai kun saba zaki ga murmushin sa, kin san hali ba komai ake yi a burge shi ba hatta ni ba gwanin ta nake masa ba wani lokacin. Ki yi haƙuri yana son ki har gobe, kawai sabon da ku ka yi da ne ya ja baya amma zai aure ki."  Murmushi ya suɓuce mata ciki farin ciki da gamsuwa da maganar Mama tace, "Haka ne Mama, yanzu baya sakewa dani, shaƙuwar mu duk ta gushe. Amma tunda kina tsakani naji daɗi bana son rasa shi." Mama tayi dariya cikin jin daɗi tace, "baza ki rasa ba in sha Allah. Adnan naki ne ke kaɗai, duk wannan zille-zillen da yake yi zai daina." Tayi dariya zatayi magana kenan suka ji anyi sallama. "Assalamu alaikum" ya faɗa yana shigowa ɗakin Mama ta amsa tana kallon sa yace, "Mummy me aka dafa?." "Tuwo nayi." "Tuwo! A daren nan?" Ya maimaita yana kallon Mama. Mama tace, "eh shi, ba kai naji kana cewa kana son cin tuwon semovita ba? Shine nayi maka." Ya girgiza kai yace, "A'a Mummy gaskiya bazan iya ci ba. Tuwo a daren nan, inaa!." Mama ta harare shi tace, "daman ai ba'a iya maka, sai kaje ka san abinda zaka ci ai." Rumana tayi caraf tace, "Beb ko na dafa maka taliya?." "Bana so" ya faɗa yana fita ba tare da ya kalle ta ba. Sai ta ɓata fuska kamar zata yi kuka Mama ta kalle ta tace, "meye na jin haushi bayan kin san halin sa?, dan ya gwale ki ba komai bane a wajan sa, ki yi abu yace bai masa ba duk kin san da wannan, meye na jin fushi to?" Ta faɗa tana tashi ta fito falon ta tarar dashi a kitchen ɗin a tsaye yana zuba kunu a kofi kafin ya fito ya zuba madara a kunun ya zauna a falon. Mimi da Kausar sun fito ya bisu da kallo ganin kayan jikin su na bacci ne marasa nauyi masu kama jiki, ba kamar Mimi da take da jiki ya kamata kayan sosai yace, "baku da hankali ku ka yi wannan shigar a wannan lokacin?." Mimi bata san yana nan ba da bazata fito ba saboda indai ya gani sai yayi magana, tace, "Yaya dare ne fa." "Na fiki sani ai, Ku koma ku saka hijjab, ku ka san wanda zai zo yanzu?." Ran su bai so ba suka saka hijjabi suka dawo suka zauna sai mita suke a zuciyar su dan Allah ya sani yana takura musu, ga shegen saka aiki. Mama tayi murmushi, tana jin daɗin yadda yake kula da tarbiyyar ƴan uwan sa, ko ya ya yaga sun karkace zai dawo dasu daidai kuma dole su hau layi. Kallon da Rumana take masa ne gabaɗaya ya dame shi hakan ya saka ya miƙe ya kalli Mimi  yace, "in an idar da sallar i'sha dake da Kausar da Lubna kuzo ku same ni" yana faɗa ya fita daga falon Rumana ta bishi da kallo kamar ta jawo shi ta rungume haka take ji. Murmushi Mama tayi dan tana ganin irin kallon da take masa, shima tana lura dashi kallon ne ya saka ya gudu amma zata yi maganin sa dan ita kam tana son haɗa auren su duk da sai turjewa yake yi bayan a baya yaso Rumana fiye da ko wacce mace. Rumana tace, "Mama nima bara na koma gida gobe na dawo." Mama tace, "to ki gaida Sumayya" ta amsa to ta ɗauki key ɗin motar ta fita.      Mimi ta kalli Kausar bayan fitar sa tace, "ke me muka yi yake neman mu?." Kausar tace, "me muka yi kuwa? Laifin Lubna ne ya shafe mu. Tsoron wannan faɗan nasa nake  yi da in ya fara babu full stop, gashi abokan sa in sun kai dubu a falon sa dan ya miki faɗa a gaban su ba komai bane. Shine abinda yake haɗa ni dashi, bana son faɗa a cikin mutane." Mimi tace, "haka ya yi min ranar juma'a, ke kin ji faɗa a gaban Huzaifa wai fita da ƙaramin mayafi?,  kuma wai ina magana da maza, Kausar da fa Huzaifa ɗin kawai na gaisa, ai ya bani haushi wallahi." "Kema ke kika ja, shifa Yaya yafi so in kika ganshi a waje cikin mutane kar ki nuna kin san kowa ki wuce, wannan magana da mutanen ma laifi ne. Balle yaga kina yiwa wani namiji magana da dariya ki sha harara." "Matar sa ta shiga uku, ɗan mayafin zamanin nan bazai bari ta saka ba. Faɗa a cikin mutane wannan bai ɗauke shi komai ba." Mama na jin su bata ce komai ba suna zaune har akayi kiran i'sha suka tashi da nufin sallah. Kamar yadda yace ana idar da sallah suka nufin ɓangaren Mamy suka tarar da Mamy da Maryam da kuma Lubna suka shiga da sallama Mamy ta amsa suka zauna tare da kallon Lubna Mimi tace, "to ki tashi boss yana neman mu yace muje." Lubna ta bata fuska tace, "me kuma muka yi?." "Ke zamu tambaya ai, in ma faɗan zai mana ai ke ki ka ja mana," "Mtsw! Gaskiya ni Yaya Bebi yana takura min wallahi, haba shi komai bazai barka kayi yadda kake so ba, ni na gaji da wannam rayuwar." Mimi tace, "in baza ki je ba sai ki faɗa mu kama gaban mu, Kausar muje in ya tambaya muce tce ya takura mata." Tare suka fita, Mimi haushin Mamy take ji ganin a gaban take wannan maganar ta amma bata ce komai ba. Basu san ya abin ya faru  ba sai gano Lubna ɗin sukayi  ta fito. Suna shiga falon nasa suka same shi a zaune yana sanye da glasses a idanun sa fari wanda yake taimaka masa wajan kallon takarda da wani document a hannun sa yana dubawa. Sallama da suka yi ya saka ya kalle su ya amsa tare da ajjiye littafin yana kallon su suka ƙaraso suka zauna akan kan carpet Mimi tace, "Yaya gamu." Kai ya girgiza alamun na gan ku kafin ya ce, "tambayar ku nake so nayi, ina so ko wacce ta faɗa min asalin abinda yake zuciyar ta. Bana son ƙarya ku faɗa kai tsaye kar a ɓoye min." Basu ce komai ba ya kalli Mimi yace, "me kika shiryawa rayuwar ki a yanzu? Aure ki ke so?." Yadda yayi tambayar ya saka ta kalle shi suka haɗa ido dan bata kawo abinda zai ce ba kenan ya ɗaga mata kai yace, "asalin abinda yake zuciyar ki nake son ki,aure kike so?." Mimi ta sauke kai ƙasa tace, "ni Yaya abinda Allah ya tsara min shine daidai." "Kowa ma haka Mimi, but there's something on your mind that you wish to happen in your life, maybe aure maybe kuma karatun kike so ki gama har ki fara aiki." Mimi tace, "Yaya ina so, amma nafi so na kammala karatun tunda kaga ina final year." "Are you sure?." Ta girgiza kai alamun eh. Kallon Kausar yayi yace, "sai ke what's your plan about yourself?." Kausar tce, "ni Yaya ina karatu, in auren yazo zan karɓa. Amma kaga yanzu ko saurayi ma bani dashi, karatun shine a kan gaba." Ya girgiza kai ya kalli Lubna yace, "ke dai daman nasan auren ki ke so ko?." Ta girgiza kai alamun a'a yace, "then what?." Tayi shiru bata amsa ba yace, "in ba haka bane a ranki meyasa kike tara samari? Yau in na ganki da wannan, gobe da wannan an ganki. Kuma dukkan su babu wanda zai aure ki a cikin su duk ƴan ɓata lokaci ne, wannan wanda na ganku ɗazu nayi miki warning a kan sa amma baki ji ba. Taƙamar ki shima ai abokina ne, na fiki sanin abokina ne, shiyasa nace ki barshi sboda na san shi din amma baka jin magana Lubna." Lubna tayi shiru bata amsa ba yace, "duk wacce take ji a zuciyar ta she's ready to get married please let me know zan tabbatar ta samu abinda yake so. Abu ɗaya ne bana so ku dinga hiding abinda ku ke yi ko ku ke so a gare ni, baku san duk wani motsin ku akan idona kuke yin shi ba shiyasa. Ke Kausar ai baki nasan na san kinje Sufi mart ba Jiya. Mimi ɗazu kinje biki baki sanar dani ba." Shiru sukayi dukkan su ya kalle su yace, "zan muku duk abinda kike so amma ku tsayar da hankalin ku waje ɗaya, bana son kula samari barkai musamman ke Lubna" ya faɗa yan nuna ta da yatsa. "Kece Babba a cikin su amma kin fi kowa wannan rawar kan, ki dawo hankalin ki kafin ranki ya ɓaci,  na sake kama ki da makamancin wannan zan baki mamaki.  duk wanda yace yana son magana dake invite him to come over and talk to me, sai muyi magana akan ki na san waye shi da komai na shi, I'll only let him to talk to you if i trust him, otherwise l'll reject to him. Bama ke kaɗai ba dukkan ku, in na samu wata da akasin haka gaskiya ranku zai ɓaci" ya faɗa yana nuna su gabaɗayan su. Mimi tace, "To Yaya in sha Allah zamu yi abinda kace." Ya sauke numfashi yana kallon su yace, "good. Akwai abinda kuke so?." Mimi da Kausar aka kalli juna kafin Mimi tace, "daman Yaya gobe akwai get together na class mate ɗin mu tun na secondary ina so naje." Ya kalli Mimi yace, "which time?." "Around 4pm." "Where?." "Green pack." Yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "okay zan saka a kai ki." Tayi murmushi tace, "na gode." "Baku da abin cewa?" Ya faɗa yana kallon su suka ce babu yace, "okay zamu iya tafi, zan tura muku kuɗin kati."Suka yi murmushi dan sun san kyautar sa a gare su akai daɗi suka fita ya bisu da kallo. Allah ya sani baya so wani abun ya samu ɗaya daga cikin ƙannen sa mata, yana tattalin su sosai musamman yanzu da duniyar ta gama lalacewa kowa ba abin yarda bane, baya son yaga wani abun da zai ɓata musu rayuwa shiyasa bai basu fuskar sauraren ko wanne namiji ba, sannan bai basu fuskar karɓar komai a hannun ko wanne namiji ba. duk da iyayen su suna da halin da zasu basu kuɗi amma yana yawan basu kuɗi da canja musu waya saboda kar rashin basu yasa su tambayi saurayi. Gabaɗaya aikin da mahaifin su ya kamata a ce yayi ya dawo kansa bashi, tunda yayyen sa maza guda biyu kowa yana gidan sa shine tamkar uba a wannan lokacin, shiyasa bashi da nutsuwa sai yaji sun kwana lafiya sun tashi lafiya wani abun bai sake su ba. Gashi Allah ya yi shi a mutum mai kishin ƴan uwan sa, baya so yaga suna kula ko waye balle saurayi. Ajiyar zuciya yayi a bayyane yace, "Abba!." Kai ya girgiza kawai yana jin haushin halin mahaifin su amma ya zaiyi ba'a canja uba dolen sa dai shine mahaifi a gare shi. Tashi yayi da niyar shiga ɗaki sai yaji ana buɗe  gate ya ƙarasa wajan window yana kallo sai yaga motar mahaifin su ta shigo kawai ya saki labulen dan bai ga amfanin dawowar tasa ba dan da safe zai ce zai koma. Yana zaune yana cigaba da duba takardun hannun sa yaga wayar sa na haske ganin sunan Abba ya saka shi kulle ido ya buɗe ya ɗauka da sallama yayi shiru alamun ana amsawa kafin ya tashi ya fita waje. Kai tsaye ɓangaren Abba ya nufa ya same shi a zaune a kan kujera ya shiga da sallama ya amsa ya ƙarasa ya zauna a kasa yace, "barka da dawowa Abba, ina fatan an dawo Lafiya." "Lafiya lau Adna, ya aikin naka?." "Alhamdulillah" ya amsa a taƙaice daga nan bai sake cewa komai ba. Abba yace, "sai haƙuri aiki ne suke min yawa ga shirye-shiryen zaɓe mai xuwa shiyasa abubuwan sai a hankali." Adnan yace, "amma Abba duk mahimmacin abinda ka saka a gaba bai kai mahimmacin iyalan ka ba." "To iyalai na me suka rasa Adnan? Babu abinda babu a gidan nan koda babu ni na tabbata baza ka bar wani yayi kukan babu ba. Yadda kake kula da iyayen ka da ƴan uwan ka ko ni bana kula dasu, indai kana da rai ragamar gıdana tana hannun ka dan na yi shekara bana gida bazan damu ba." Adnan ya kalle shi ɗan daman shi ne kawai mai iya faɗa masa gaskiya yace, "Amma Abba ko mu yaran ka  ace babu haƙƙin mu a kan ka akwai iyayen mu mata, dukkanin suna buƙatar kulawar ka wacce a wajan ka kawai zasu samu, ni da ka bar min komai a hannuna bazan iya samar musu da kulawar da zasu samu a wajan ka ba. Idan zan iya kula da ƴan uwana su kuma fa Abba?." Alhaji Mu'azzam Alhassan ya kulle ido ya buɗe yace, "Haba Adnan! Iyayen naka bafa yara bane da kake wannan zancen a kansu, dukkan su babu wacce bata aurar da yara a cikin su ba har da jikoki, to me suke nema a wajena kuma?." "Kulawar ka suke so Abba domin matan ka ne, na tabbatar ka san suna buƙatar hakan." Yayi murmushi yace, "gashi ai na dawo, zan kuma yi sati a nan duk kulawar da suke so zasu iya samu a cikin kwanakin da zanyi." Kallon sa Adnan yake yi zuciyar sa gabaɗaya babu daɗi yaja bakin sa yayi shiru bai ce komai ba kafin Abba yayi magana Mamy da Mama suka shigo da sallama ya amsa sai Adnan ya miƙe yace, "Abba sai da safe." "Allah ya tashe my Lafiya, da safe kafin ka fita kazo nan Ina son ganin ka, koda ina bacci ka jira ni. Maganar da na kira ka muyi bamu samu ba zamu yi daga baya."  Ya amsa da to ya fita. Kallon Mamy da Mama yayi da suke zaune ko wacce fuskar sa babu yabo babu fallasa yace, "ko wacce ta shigo tana shan kunu kamar wanda aka yiwa dole." Mama tayi murmushi kawai bata ce komai ba ta miƙe tace, "barka da zuwa muka zo muyi maka daman, da fatan an dawo Lafiya." Yabi Mama da kallo ita kuma ba shi take  kallo ba yace, "Sannu da zuwan ce sai an tashi tsaye?." Mama tace, "Ina sauri ne zan je na kwanta, sai da safe" ta faɗa tana hanyar fita Mamy ma ta miƙe tace, "jira ni mu koma yadda kuka shigo tare" ta faɗa tana tashi tsaye itama. Mama ta kalle ta tace, "baza ki zauna a nan ba?." "Lissafina ya kwace min bazan iya banbance wacece ma ya kamata ace ta kwana a nan ɗin ba, ga dai abinci nan Maryam zata kawo yanzu" ta faɗa tana fita ta bar Mama a tsaye dan har ta riga taficewa. Mama na shirin fita tace, "kar ki fita Hauwa, dawo ki zauna muyi magana." Ta juyo ta kalle shi tace, "ko meye ma tattauna da safe in Allah ya nuna mana, ka kwana lafiya" ta faɗa tana fita ya bita da kallo yana murmushi. Shi kam mamaki matan nan masa suke bashi ko wacce ta girma a cikin su amma basu daina mararin neman wani abuna wajan sa ba, shi ɗauka yake gabaɗaya ma an ɗauke musu wata sha'awar sa tunda ko wacce har jikoki tana dasu. Har gwara ma Mama tafi Mamy ƙarancin shekaru amma Mamy tafi Maman nunawa. Shafa fuskar sa yayi dan shi kam yana da ɗanye jini a waje bai ga abinda zai nema a wajan wannan tsofaffin matan nasa ba, shiyasa ko a jikin sa in suna wannan abubuwan, duk wacce ta kawo kanta ita ta sani, shi ban damu ba. Nana Haleema❤️🥂 *BAYA DA ƘURA* FitattuBiyar2025 Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11     ©️ *Nana Haleema.* https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp *BOOK 1* *Page 004* A daren Manal suna zaune da Mama a falo cikin hasken fitilar da ya haske falon nasu Manal tace, "Mama gobe da safe zamu koma Asibiti." Mama tace, "Manal ni ba sai mun je ba lafiya lau nake jina, in mun je goben wani maganin zasu sake bayarwa kuma ba wani kuɗi ne a hannun Baban naku ba yanzu." Manal tayi dariya tace, "za'a samu Mama, Allah dai ya nuna mana goben. Kuma kin ga wajan Dr Huzaifa ne." "Eh gaskiya, yana da kirki ya ɗauke ki kamar ƙanwa, sai a ɗauka ma ya jima da sanin mu." "Auu na manta fa wajan likitan zuciya yace muje a kai masa wannan result ɗin, Allah ya kaimu goben da wuri zan fita dan ance ba wani kirki ne da likitan goben ba." Mama tayi murmushi tace, "to Allah ya nuna mana. Yadda kike kula dani Allah ya baki mai kula dake Manal ɗin Mama." Tayi murmushi ta amsa da amin Mama tace, "Ya sayyadi bai yi waya ba?." Manal tayi dariya tace, "Mama kina bani kunya, ni nace miki Ya Sayyadi ba sauryina bane kawai muna gaisawa ne." "Nima ai baki ji nace saurayin ki bane ba ai, Yayan ki ne." Tayi dariya kamar yadda Maman take yi Manal ta kalle ta tace, "Wallahi Mamana kina da kyau sosai." Mama tayi murmushi sosai tace, "duk kyauna bai kai na Manalin Mama ba." Manal tayi dariya kawai Mama tace, "Allah ya kawo miki miji na gari wanda zai kula min dake ya inganta rayuwar ki ya cika miki burin ki na zama shararriyar mai dafa abinci ta duniya ma gabaɗaya." Manal tayi dake ya tace, "Mama ta duniya fa kika ce?." "Ko baza ki iya bane?." "Zan iya mana, amma ta duniya yayi girma." "Kina wasa da ikon Allah?." "A'a Mama." "To kice amin kawai." "Amin Mamana. Amma ni bazan yi aure ba." Mama tayi dariya tace, "wannan kalma ta baza ki yi aure ba na faɗa miki bana  son ji." Cikin sha'agwaɓa tace, "ni dake zan rayu Mamana, indai kuma zanyi aura sai dai mijin yazo nan mu zauna ko mu tafi dake." Mama tayi dariya sosai tace, "Allah ko Manal?." "Allah Mama. In na tafi waye zai kula min dake?" Ta faɗa jikin ta nayi  tunawa fa da gaske wata rana zata yi auren ta bar Maman ta. Jin yadda Manal ɗin tayi magana sai Mama tace, "ki cigaba da addu'a kawai, duk inda alkhairi yake Allah ya kawo miki shi." Ta amsa da amin bata ce komai ba. "Ashe yau da arzuƙin nepa a unguwar" aka faɗa ana shigowa cikin falon. ko ba'a ce sun san wacce ta shigo. Manal ta kalle ta tace, "Yaya ko sallama baki yi ba fa." Hararar ta tayi tace, "bazan yi sallamar ba, bana son iyayi." Ta kalli Mama da take zaune daga gefe tace, "Mama ki shiga tsakanin a da yarinyar nan ta daina shiga harkata." Mama bata ce komai ba Mubeena ta wuce ɗaki sai gata ta fito tace, "ke Manal wai babu abinda aka dafa a gidannan ne?." "Inda kika je basu baki abincin ba?" Mama ta faɗa tana daga inda take zaune. Mubeena tace, "in baza'a bani ba ai sai a faɗa min kawai, daman nima karanbani na ne ya saka na tambaya, ina za'a samu irin abincin da nake so a cikin gidan nan?." "Wallahi Yaya baki da hankali." Wara ido tayi tana kallon Manal tace, "ni ki ke cewa bani da hankali Manal?." Manal tace, "na faɗa akwai abinda zaki min ne?." Kafin Mubeena tayi magann Manal tace, "Mai hankali bazai aikata irin abinda kike aikatawa ba, ke a ganin ki wayewa ce raina iyaye, baki san hauka ne da rashin sanin ciwon kai ba. Sai girmama iyayen wasu saboda neman suna bakya girmama naki, tirrr! Kin ji kunya wallahi." "Salamu alaikum wai Nusaiba tazo!." Wani yaro ya faɗa yana shigowa, abinda ya dakatar da Mubeena ga yiwa Manal masifa ta juya kan yaron tace, "sai naci kaza kazan wanda ya sake kira na da Nusaiba, sai na zage shi duk girman sa na rantse da Allah. Kar a kuma kira na da Nusaiba ba sunana bane, in baza'a ce Mubeena na ba a kira ni da baiwar Allah. Meye wani Nusaiba ana zaune Lafiya? Ni an cuce ni ma da aka samin Nusaiba wallahi." Yaron da take yiwa masifa tace, "Baba ne yace kizo in baza ki zo ba sai naje na faɗa masa" ya faɗa yana fita daman dan ya tunzura ta yace Nusaiba. Mubeena tace, "ko ne zan masa da zai aiko nazo oho, ni bana son takura da saka ido wallahi. Tunda ba shi ya haife ni ba meye nasa na takura min?" ta faɗa tan figaat mayafi ta fita daga gidan. Manal ta kalli Mama dan tasan bata so taji Mubeena tana ambatar sunan mahaifiyar ta tana cewa bata so, ranta yana ɓaci sosai har hakan sai ya nuna a fuskar ta. Manal tace, "Kiyi haƙuri Mama, ki cigaba da yiwa Yaya addu'a wata ran zata daina duk abinda yake yi." Mama bata ce komai ba tayi shiru kawai Manal sai ta tashi ta ɗauke kwanon da suka gama cin abinci ta fita dashi ta dawo ta ɗauko kayan shimfiɗa Mama ta shimfiɗa musu tace, "Mama nayi shimfiɗa in zaki kwanta." Kafin Mama tayi magana Mubeena ta shigo tana cewa, "ni wallahi babu wanda zai takura min, sai nayi abinda nake so bazan kuma auri talaka ba wallahi. Ni Mubeena nafi ƙarfin ɗan mai kuɗi,  sai dai mai kuɗin kan sa ba ɗan sa ba. Bazai yu ace sai uban miji ya bawa mijina sannan shima ya bani ba, na fi so daga hannun mijina sai wajena. Babu wanda zan aure gwara ma Baban ya sani, dan yana ƙanin mahaifin mu kuma yana auren Mama ai mahaifin mu bane. Bana son takura a bar ni na sake" ta faɗa tana shigewa ɗaki Manal zata bita Mama tace, "kar ki bita Manali, zo ki bani ruwa na sha." Manal ta canja hanya ta kawowa Mama ruwa ta sha tace, "kashe min hasken falon ki kwanta, in kuma kin kashe shikenan." Kamar yadda tace haka tayi ta kashe hasken Mama ta kwanta ita kuma ta ɗauki alqur'ani ta koma tsakar gida ta zauna tana karantawa zuciyar ta babu daɗi.  Bata son halin da Mubeena take nunawa Maman su ko kusa ko alama, tana jin haushin hakan domin yana daga cikin dalilin da ya saka ciwon zuciyar Mama yaƙi sauƙi saboda damuwar Mubeena. Da sassafe Manal ta tashi tayi abubuwan da ta saba dan zasu je asibiti da Mama kuma bata so su makara, dan sau biyu suna son ganin likitan makara take hana su ganin sa. Ɗorawa Mama ruwan wanka bayan ta fito ta juye mata a bokiti ta kai mata banɗaki sannan taje ta tarar da maman a zaune ta dafe kanta tace, "Sannu Mama, har yanzu ciwon kan ne?." Mama tace, "kece da sannu Manal, har yanzu bai sake ni ba ciwon nan kaina yayi nauyi sosai." Manal tace, "har na juye miki ruwa saboda zuwa asibitin, Anya zaki iya zuwa ma kuwa?." Mana tace, "gaskiya bana tunanin zan iya fita, kaina ciwo yake min sosai ba kaɗan ba Manal." Manal tayi shiru ta kalli ƙaramin agogo falon su tace, "gashi har bakwai ta kusa, ance likitan tun shida yake zuwa. Bara na shirya naje kawai na kai result ɗin zuciyar sai ya bani maganin na ki." Mana tace, "Anya zai saurare ki?." "Zan gwada Mama, tun yaushe ake saka mana ran zamu ganshi bamu ganshi ba, ga dama mun samu baza mu yi wasa da ita ba. Bara na saka kayana nayi sauri naje na dawo" ta faɗa tana shiga ɗaki a lokacin Mubeena bacci take sosai ko alamun tashi bata yi ba, ta shirya ta saka hijjabi ta ɗauki katin Mama da kuɗin mota ta fito ta samu Maman ta koma ta kwanta tace, "Mama zan tafi babu abinda kike so?." Mana tace, "babu komai Manal, sai kin dawo Allah ya kiyaye yayi miki albarka." Ta amsa da amin ta fita daga cikin gidan. Napep ta hau zuwa asibitin murtala ta sauka ta shiga ciki inda aka yi mata kwancen likitan yana zuwa nan ta hango dandazon mutane mata da maza a zaune a cikin wata rumfa da alama duk likitan zasu gani. Ƙarasowa tayi wajen wanda yake tsaye da katina a hannun sa tace, "sannu da aiki." Ya kalle ta yace, "Yauwa." "Dan Allah nan ne wajan likitan zuciya?." "Eh nan ne, kawo katin naki." Miƙa masa katin tayi ta koma ta zauna akan abinda ake zama tana jiran azo kanta. Ta jima sosai sama da awa ɗaya tana zaune kafin a kira sunan Mama jin hakan ya saka ta tashi da sauri ta karɓi katin ta shiga office ɗin. Bebi yana zaune a kan kujera cikin manyan kaya ya sunkuyar da kai yana rubutu ta zauna ya miƙa mata hannu yace, "bani katin." Ba musu ta bashi katin ya karɓa tace, "ga sakamakon gwajin zuciyar da akayi." Karɓa shima yayi ya buɗe takardar yana kallon ta sai ya ɗago suka haɗa ido da Manal ya sake kallon age din jikin katin ya sake kallon ta yace, "Zahra'u Muhammad, are you?." Manal tana kallon sa tace, "Mamana ce, bata da lafiya baza ta iya zuwa ba shine nazo na kawo da kaina. Bana son rasa damar ganin ka ne, sau uku ana saka ran zamu ganka bamu ganka ba shiyasa na karɓo nazo a madadin ta." Kallon fuskar ta yake yi jin yadda take magana da sanyi ya jingina da kujera yace, "Maman kice babu lafiya kuma kece kika zo ganin Dr?." Manal ido ya ciko da ƙwalla tana kallon sa tace, "eh." Wani irin kallo na ta raina masa hankali ma yake mata, yanzu banda ma raini shi zata zo ta cewa wai katin babar ta ne amma itace tazo ganin likitan?. Tsaki yaja ya ajjiye mata katin zaiyi magana tace, "don girman Allah ka bani maganin kwana biyu har bacci kasawa take saboda ciwon ƙirji, yanzu haka bata da lafiya na fito na barta dan Allah ka taimaka ka rubuta maganin dan Allah." Sai hawaye ya sakko daga idanun ta yayi shiru yana kallon ta, yana girmama mace a rayuwar sa duk ƙarancin shekarun ta amma baya so azo masa da rainin hankali, in ba rainin hankali ba tazo tace ya bada magani bayan bai ga mata lafiya ba sannan ba'a faɗa masa ya ake jin ciwon ba kawai sai ya ɗauka ya bayar, wani abun na faruwa kuma sai dai yaji sunan sa a gidan radio ana cewa bai san aikin sa ba. Ta saka shi a gaba tana masa kuka kamar wacce ya daka, baya son shagwaɓa ta banza da wofi, in zaka yi ma kayi akan hujja. "Zaki iya fita daga nan?. Ta ɗago idanun ta da suka koma ja tace, "ka taimaka dan Allah." "ki je, duk sanda Maman naki ta samu lafiya sai kuzo." Ta girgiza kai tace, "wahala ake sha kafin a sake samun ka, dan Allah ka amince ka bani maganin." Shiru yayi yana kallon ta ya lura baza ta fahimta ba. "Out!" Ya faɗa yana nuna mata ƙofa. Jikin ta a sanyaye ta tashi ta ɗauki katin da takardar ta fita bata sake cewa komai ba a lokacin wata mara lafiyar ta shigo. Tsaki yayi bai sani ba ya kalli sabuwar da ta shigo ya karɓi katin ta ya fara rubutu a kai. Manal tana tafe tana kuka, wannan shine taga samu taga rashi, ga likitan da suke son gani kwana da kwanaki amma ta ganshi ganin nasa babu amfanin da yayi mata. A haka ta shiga gida tun daga soro take jin muryar Mubeena tana mita kamar yadda ta saba. Kai ta girgiza kawai ta shiga a lokacin Mubeena yake cewa, "Yauwa gwara da kika dawo, sai ki ɗauki hanya ki fita bayan kin kulle kitchen da kika bar mu uban me zamu ci?." Manal da fuskar ta tayi ja sosai tace, "kin san inda nake ajjiyewa" tana faɗar hakan ta ƙarasa falon ta tarar da Mama a zaune har tayi wanka amma kayan shimfiɗat suna nan ba'a kwashe ba. Ajjiye katin tayi tace, "Mama na dawo" ta faɗa tana kwashe kayan ta kai ɗaki ta dawo Mama tace, "sannu, ya bada maganin?." "Bai bayar ba Mama, wani fusatacce ne ba irin roƙon da ban masa ba amma mutumin nan da yake bashi da mutunci ko ya kalle ni ma, wai tunda babu ke babu amfanin bada magani ba. Amma a haka Dr Huzaifa yake cewa yana da kirki." "Sai bayan kin tafi nayi tunanin hakan Manal, zuwan babu ni a kamar gwara ba'a je bane dan kin San likitoci basa son ka saka musu baki ko tambaya suka yi balle kuma ace kinje babu ni. Kin ga ai bai san ya nake jin ciwon ba balle ya bani magani." "Amma Mama tunda na faɗa masa uzurin rashin lafiya ne ai yaci ya saurare ni." Mama tayi dariya tace, "shine ki ka sha kuka kenan?." Manal tace, "Mama ya akayi kika san nayi kuka?." "Manali kenan, ni nasan abun kuka baya miki wahala, sannan ga muryar ki nan ta canja." "Wallahi Mama ina tafiya ina kuka." Mana tace, "Kiyi haƙuri, Allah ya kaimu wani lokacin sai mu koma nida ke din." "Amma Mama ciwon nan yana damun ki sosai, bana so abin yazo yayi miki yawa ne." "Babu abinda zai yi yawa, kar ki damu." Manal ta tashi tace, "ya bani haushi sosai wallahi, daman fuskar sa a tamke kamar mala'ikan mutuwa ko annuri babu, da gani bazai yi kirki ba." Mama tayi dariya tace, "ke kin taɓa ganin mala'ikan mutuwan ne?." Manal tayi dariya tace, "bara na kawo miki kunun ki" ta faɗa tana fita a nan ta tarar da Mubeena ta fito daga wanka bata tanka mata ba ita ma haka ta wuce zuwa ɗaki. Da kofin kunun ta dawo a hannun ta tace, "Mama gashi." Mama ta karɓa tace, "gaskiya yau ma sai na saka sikari Manali." Manal tace, "kai Mama! Jiya ma kin sha sugar shekaran jiya ma fa haka." "Zuciyata tana so Manal, mutuwa dai ake gudu kuma dole mu mutu. Bani sikarin na zuba." "Dan Allah Mama kar ki sha." "Allah sai na sha Manal, Haba kai kenan cikin hana ni abinda zuciyar ka take so, bani ki gani." Manal ta kwance ledar ta zuba mata kaɗan jin tace Allah tace, "gashi nan na zuba miki." Mama ta juya tace, "bai ji ba, ƙara min." "Haba Mama dan Allah, ki daina sha sugar kwana biyu kina sha sosai kar yayi miki illa." "Ke ƙara min daga yau bazan sake ba." Manal ta ƙara mata kaɗan Mama ta juya tace, "shiyasa naso bakya nan zan sha sikari son raina, da bakya nan ai gashi har biredin da Baban ku ya rage jiya na cinye ba wanda ya sani," Manal kamar zatayi kuka tace, "amma Mama kin san hakan zai cutar dake sosai ko?." Mama bata ce komai ba ta shanye kunun ta tsaf Manal na zaune a gefen ta tana kallon kafin Mubeena ta fito cikin hijjabi mai kyau baƙi dogo wanda ya amshi fuskar ta tace, "ke Manal zan tafi makaranta, ina kud'in mota?." "Bani dasu kuma Baba bai bani ba, in zaki je ki tambayi Baba kije, in baza ki ba sai ki tafi a ƙafa." Mubeena tace, "nice zan tafi a ƙafa?." Mama tace, "kin wuce kije da ƙafar ne?." Jin mama tayi magana sai tayi shiru kawai ta wuce ta fita Mama ta girgiza kai tace, "Mubeena na da rai ba dole zuciya ta dinga min ciwo ba." Manal bata ce komai ba ta tashi ta fita ta sha mata kunun babu sikari ta fara gyara gidan kamar yadda ta saba. Nana Haleema🥂❤️ *BAYA DA ƘURA* FitattuBiyar2025 Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11              ©️ *Nana Haleema.* https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp *BOOK 1* *Page 006* Adnan suna zaune shida su Huzaifa bayan sun idar da sallar magriba wayar sa ta fara ƙara, ya duba ganin mai kiran sai ya ɗauka ya saka a kunne a bayyane yace, "kun koma gida?."  Yayi jim alamun ana bashi amsa kafin yace, "okay, thanks you." Daga haka ya yanke wayar ya kalli Huzaifa da yake kallon sa yayi murmushi yace, "Bebi kana takurawa ƙannen ka da yawa, wannan takura musu ɗin da ke yi bazai haifar da ɗa mai ido ba." Adnan ya zauna sosai yace, "kai a wajan ka takura ce, ni a wajena kariya ce." Hamza yace, "Gaskiya ne, amma yawan saka musu Idon da kake kamar yayi yawa, duk inda suke je sai ka sani hatta hoto sai an ɗauka an turo maka. Ko irin saurayin nan na sirri basu isa su yi ba, ga wayar su kullum a binciken ta kake." "Ban taɓa karɓar wayar wata ta duba ba, saboda nasan waya kamar sirri ce, wannan baya gabana abinda na sani duk inda ƙannena zasu je haƙƙina ne a kaina na san da fitar su da dawowar su. Bama su ba har iyayena." Huzaifa yace, "Gaskiya ne, masu irin wannan zuciyar a cikin mutane baku da yawa gaskiya." Hamza yace, "ƙanne ma fa kenan, wannan ina ga matar ka Bebi?." Bebi ya kalli wani wajan daban yace, "iyayena sai dai ace iyayen mu, yayyena sai dai nace yayyen mu, ƙannena sai dai ace ƙannen mu" ya kalli Huzaifa yace, "Matata fa? Za'a ce matar mu?." Jin abinda yace suka yi dariya shida Hamza banda Bebin da darıya ba dabi'ar bace ba Hamza yace, "kace Rumana zata sha tsaro." Bebi ya sauke numfashi yace, "wai waye ya faɗa muku wannan yarinyar zan aura ne?." "Babu wanda ya faɗa mana, mu muka ga hakan saboda ka so Rumana sosai kai ka sani." Bebi ya taɓe baki yace, "Na so ta a da amma banda yanzu.” “First love ɗin kace fa, har yanzu akwai sauran son ta a zuciyar ka” Hamza ya faɗa yana dariya. Bebi yace, “ba dai a zuciyar Adnan ba, ni ba irin wannan soyayyar nake ba, in nace bana son abu to bana so ɗin ne. Yeah I know a baya naso Ruman sosai, but by now babu wannan soyayyar a zuciyata. Shiyasa bana saka soyayyar da zan cutu a zuciya ta, in na samu fine in ban samu bana zan rayu babu tashin hankali." Hamza yayi dariya sosai yace, "Dr Adnan kenan, kawai kayi addu'a Allah kar ya ɗora maka wacce tafi ƙarfin ka, domin kuwa soyayya ita take yin kanta a zuciya a lokacin da baka shirya ba. Kar kaga ka daina son Rumana lokaci ɗaya ta fita a ranka, akwai wacce zaka iya so nan gaba in ka rabu da ita sai dai kaji ana likitan zuciya yana ganin likitan zuciya." Bebi ya kalle shi yace, "har abada wallahi, Tunda ban samu ciwon zuciya akan soyayyar family na ba babu wata yarinya da zata saka min ciwon kai. Kai ni fa ba ɗan wahalar soyayya bane ba, in na samu fine in ban samu ba kowa ya kama gaban sa." Huzaifa yayi dariya yace, "Shikenan dai Bebi, zamu gani." Ya tashi tsaye ya kalli agogo yace, "ni kam zan wuce." "Gobe zaka shiga asibitin ne?." "Naje yau, bana tunanin zan koma. Ta ƙarfin tsiya aiki da asibitin gwamnati ya fita a raina saboda rashin gani nayi shiru.” "Ka koma don Allah." Ya kalli Huzaifa da yake maganar yace, "sai nayi niya, kasan ba'a sani ba'a hana ni" yana faɗa yayi gaba abin sa ya barsu a zaune kafin suma su tashi sunyi gaba.           Anty Maryam tana zaune a motar tsohon mijin ta suna daga waje a bayan wani gini ba sosai ake hango su ba ta kalle shi tace, "ka faɗi abinda kace zaka faɗa min kasan yanzu Bebi yana hanyar dawowa, yanzu in yazo sai ran mu ya ɓaci.” Tsohon mijin ta ya bita da kallo har ta tsargu tace, "wai wannan kallon da kake yi min na meye? Bana son iri wannan kallon." Ya sauke numfashi yace, "wani abu nake tunawa ne matata, kin manta lokacin da muke gidan mu in nayi miki wannan kallon abinda nake nufi?." Anty Maryam tayi murmushi kafin tayi magana ya riƙe hannun ta yace, "ni nasan baza ki manta da irin yanayin da muke kasancewa ba, musamman in kika bani abinda nafi so a jikin ki, Wato nan" ya faɗa yana kai hannun sa ƙirjin ta, bata hana shi ba amma ta dan doke hannun tace, "Kamal ya kamata ka tuna yanzu fa ni ba matar ka bace, kace kin zakayi magana dani akan su Nabil shiyasa na fito." "Abban Nabil ɗin ne yake son magana dake ba akan su Nabil ba." "To ka faɗi abinda zaka ce min bana so Bebi ya dawo." "Wai bebin nan ba kece gaba dashi ba?." "Nice gaba dashi amma magana ce bana so." Yayi tsaki yace, "Ko mu bar wajan na?." Maryam tace, "A'a, ka faɗi abinda yake tafe da kai kawai." "Ai ban gaji da kallon ki bane." Ta furzar da iska tace, "Meyasa baza mu nemi hanyar gyara auren mu ba?, bisa kuskure muka rabu ba son ran mu ba.” Ya ɗan sosa kai kafin ya basar yace, "Matata ƙaddarar da ta raba mu ita zata mayar damu, a baya nasan ban kyauta miki ba amma zan gyara kuskure na." Bata ce komai ba ta sauke numfashi ganin hakan sai ya ɗauko wayar sa yace, "kin ga wani abu" ya faɗa yana nuna mata fuskar wayar. Gaban ta ya faɗi matuƙa ganin abinda ta manta ta tura masa a zaman auren su, ta runtse idanu cikin kunya da sanyin jiki tace, "Haba Kamal, wannan ba abinda zai zauna a wayar ka bane, kar ka manta bafa matar ka bace ba ni, ganin wannan abun haram kake gani ka goge dan Allah." Yayi murmushi ya sake kallon screen ɗin wayar ya kalle ta ya ajjiye wayar yace, "in na goge me zan dinga gani yana tuna min ke?." "Zaka iya kira na ko yaushe, amma kallon wannan ai tsaraice ne bai kamata ba." "To meye baƙona?." "Na san babu, amma yana dakyau ace ka goge yanzu ni ba matar ka bace ba. Wallahi tunda muka rabu na goge naka a wayata saboda ba abu ne mai kyau ba.”Yayi murmushi ya kalli wayar ya goge ya nuna mata yace, "shikenan na goge." Tayi murmushi zatayi magana ta kallo kan titin nan ta hango motar Bebi na shiga gida. Sai da ta gama shiga ta kalle shi tace, "kaini ƙofar gida." Ba  musu ya kai ta bata ce komai ba ta buɗe ta fita ta shiga gidan a lokacin Bebi na tsaye jikin motar sa ya bita da kallo yace, “ki faɗa masa in na sake ganin ƙafar sa a ƙofar gidan nan wallahi sai na saka an kama shi, Tunda baki da hankalin da zaki hana tsohon mijin ki zuwa gare ki ni zan koya masa hankali, har ke zan koya miki tunda naga hankalin ki ya gushe.” A fusace ta jiyo tace, "ni kake cewa bani da hankali Bebi?." Baice mata komai ya juya ya fita daga gidan zuciyar sa nayi masa zafi sosai baya son wannan banzar ɗabi'ar ta yayar sa. Miji ya sake ka har saki uku ammaya dawo ki dinga kula shi, Bebi ya shiga ɓangaren Mama ya tarar da Mimi a zaune kawai a falon gani sa sai tace, "Yaya Sannu da zuwa." Har ya wuce sai ya tsaya ya kalle ta yace, "Yawwa." "Naje na dawo daga get together na gode sosai." Kai ya girgiza alamun amsawa yayi shiru akwai abinda yake so yaji ta faɗa ganin tayi shiru sai ya ɗaga ƙafa zai tafi tace, "Yaya!." Sai kuma tayi shiru ganin hakan sai ya kalle ta yace, "ina Jin ki." "Daman wani ne ya biyo ni wai yana sona, tun a can ban kula shi ba ka tambayi Saminu kaji, har ƙofar gidan nan yazo da ya takura min sai nace Saminu ya bashi number wayar ka kawai, ya bashi yanzu.” Kallon ta yake yi daman abinda yake so yaji kenan bata san yasan komai ba ya mata shiru ne ko zata faɗa masa, ya kawar da kai gefe tace, "shikenan abinda zaki ce?." Ta ɗaga kai tace, "eh Yaya, daman kar ya kira ka ne kayi min faɗa." Ya kalle ta yace, "ba shine wannan ba?" Ya faɗa yana nuna mata fuskar sa, sai kuwa taga lokacin da Saminu yake bashi lambar, ta kalli fuskar Bebi tana nan kamar kullum babu fara'a amma sai taga ya saki fuskar yayi murmushi ya dafa kafaɗar ta yace, "na san komai, ina so naji kin faɗa ne shiyasa ban miki magan ba. Kar ki damu indai ya kai yadda nake so ya kai zan bashi number ki da kaina” ya faɗa yana yin gaba kafin taji yace, "in bai kai ba zaki ji shiru" ya faɗa yana shiga ɗakin mummy. Ita mamaki ya daskarar da ita a wajan, kenan dai Yaya Bebi duk wani motsin su yana gani, ya riga ya saka musu matakan tsaron da su kansu basu san dashi ba, duk wani motsin su ya sani shiyasa da zarar kin saɓa lamba zaki ji waya. Girgiza kai take yi sai kuma tayi murmushi a bayyans tace, "wani lokacin naga kamar takura ce, wani lokacin in na nutsu dai naga mutunci ne." Tana nan tsaye yazo ya wuce ta tayi murmushi ta zauna sosai take alfahari dashi a wannan lokacin.            "Nayi sabuwar baby ina faɗa maka, da ganin ta kuma kai kasan sabuwa ce dal yadda na dama haka zan sha" Alhaji Mu'azzam yake faɗawa wani abokin da da yake zaune a kusa dashi yana kallon sa. Sukayi dariya a tare suka tafa yace, "shegen, kace ka samo ƴar shawalwala." Alhaji Mu'azzam ya cire hular kansa yace, "Tayi ta ko ina mutumina, kyau kamar ita tayi kanta, da farko har fargabar yi mata magana nayi saboda kyau. In tana magana kamar mage saboda sirantar muryar ta, daƙyar na iya riƙe kaina walalhi." Alhaji Magaji yayi dariya yace, "wato Alhaji Mu'azzam kana abinda kgaa dama wallahi, ka bar mata a guda biyu a gida kana nan mana sheƙe ayar ka." "To sun tsufa ai, har wani fushi suka yi dani basu san ni hakan nake so ba, ta haka zan yi abinda nake so da hujja." Alhaji Magaji yayi dariya yace, "yanzu su kuma yaran naka fa? Baka Tunanin wani mai irin halin ka ya lallaɓa musu?." Alhaji Mu'azzam yayi dariya yace, "Bebi fa yana da rai, ai Bebi shine katangar da take kare gidana. Ko tafiya zanyi naje nayi shekara goma bana nan Bebi zai kula da komai bazai bar wata yarinya ta wulaƙanta ba. Kai shi wani irin mutum ne da Allah ya masa kishin iyaye da ƴan uwan sa, yadda yake son family sa ko kansa baya so, kana iyalan gidan nan zai iya yin komai ganin ya basu kariya. Haka Allah yayi zuciyar sa, in kaji yadda yake kishin ƙannen sa mata sai ka ɗauka matan sane, ko kusa baya so yaga wani ya raɓe su musamman wanda suka kasance na banza." Alhaji Magaji yace, "irin ka kenan." Alhaji Mu'azzam yayi tsaki yace, "ya ishe ka malam, ni ai na banza bane saboda biya nake ba kyauta ake bani ba.” Yayi dariya yace, "Wato shiyasa hankalin ka kwance saboda kasan Adnan yana kular maka da iyalan ka." "Babu abinda zai dame ni, na san kuma Adnan zai yi iyakar yin sa dan killace ƙannen sa dama iyaye nasa, dan haka bani da wata fargaba akan wannan." Alhaji Magaji ya bashi hannu suka tafa yace, "Gaskiya ne mutumina, kana basu wuta wallahi." Suka sake yin dariya a tare Abba yace, "sai ma kaga Mubeena, a nan zaka tabbatar da ni din bana wasa bane ba, ni ɗin mai sa’a ne. A hankalin zan jawo ta jikina daga nan kuma" ya fad'a yana masa alama da hannu suka sake yin dariya mai sauti suka sake tafawa. Alhaji Magaji yace, “da yake naga kana son mai kyau har na hango wata yarinya, fara ce ƙal wannan iya kallon fatar ta ma ya isa a ci kuɗin ka wallahi.” “Allah mutumin?.” “Wallahi, da gani sabuwa ce dal kuma. Daman kai nake so a ɗaukowa ita ni kasan sababbin na basa gabana, nafi son ƴar hannu wacce zata kawo kanta.” Alhaji Mu’azzam yace, “yanzu ya za’a yi?.” “Ka jira ni kawai, zan saka a kawo maka ita daga nan sai ka san abinda zaka yi.” Abba yayi dariya yace, “ayi da gaggawa, kasan in naji labarin mace tsigar jikina tashi take wallahi.” Alhaji Magaji yace, “saboda tsabar jaraba ko?.” Sukayi dariya a tare. "Hello Yaya Mubeena bakya kina ne?, koma ina dare yayi baki dawo ba?." Manal ta faɗa a waya na kunnen ta." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta sauke wayar ta kalli Mama da Baba tace, "wai tace a gidan su Bily zata kwana." Mama tayi tsaki tace, "kuma waye yace ki bibiyi wannam yarinyar? Yau ta saba kwana a waje ne?." Baba ya ɗauki waya ya kira Mubeena amma ta kashe wayar ya kalli Manal yace, "daman akwai lokacin da bata kwana a gidan nan?." "Eh Baba." "Amma Meyasa baki taɓa faɗa min ba?." Mama tace, "Meya amfanin faɗar? Mubeena ai ta riga ta zama abinda ta zama, babban baƙin cikina da na saka mata sunan mahaifiyata, da Manali na sakawa duk da nafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali.." Manal yace, "don Allah Mama kiyi haƙuri kinga baki da lafiya." Baba ya kalle su yace, "amma dai gobe zata dawo ko?." Manal tace, "eh zata dawo zuwa gobe." Baba yayi shiru gabaɗaya baya jin daɗin abinda yake faruwa yace, "kin san gidan su wacce tace tana can ɗin?.” “Ban sani ba Baba.” Baba yayi shiru kafin yace, “tafiya zanyi gobe da safe shiyasa na shigo yanzu, amma n fasa sai naga dawowar Mubeena gobe." "Kayi tafiyar ka kar ka jira dawowar ta domin kuwa babu abinda zaka tsinka a ciki sai baƙin ciki da takaici, indai Mubeena ce sai ta saka maka ciwo kamar yadda nake fama dashi nima." "A'a ba haka ya kamata ko dinga faɗa ba, addu'a itace abinda ya kamata y dinga fitowa daga bakin ki a kanta." Mama bata ce komai ba ta kawar da kai Baba ya saka hannu aljihu ya ɗauko kuɗi ya bawa Manal yace, "duk abinda kike da buƙata a siya koda na tafi.” Manal tace, "to Baba, Allah ya kiyaye." Ya amsa da amin Mama ma tayi addu'a ya amsa ya fita. Manal dan ta kawar da maganar Mubeena sai tace, "Baba kamar shine ya haife mu, ba dan na san mahaifin mu ya rasu ba da nace Baba shine ya haife mu.” Mama bata cekomai ba ta kawar da kanta gefe abubuwa na dawo mata cikin kanta tayi murmushi tace, "albasa bata yi halin ruwa ba, koda yake barewa baza tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba." Manal tace, "Mama me kike nufi?." Shiru bata amsa ba dole Manal din tayi shiru itama, amma tana mamakin wannan karin maganar da Mama take yawan ji ta faɗa akan Mubeena, me hakan yake nufi kenan?....... *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025 ©️ *Nana Haleema.* Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp *BOOK 1* *Page 007* Tun asuba Manal ta lura da yanayin Mama babu daɗi, bata mata magana ba amma idanun ta na kanta sai da taga yanayin ta ya canja gabaɗaya ta birkice hankalin Manal ya tashi tayi kanta a guje tana faɗinn, "Mama! Mama! Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Mama ki tashi don Allah." Sai ta fita a guje zuwa gidan Baba, ta samu matan sa guda biyu a tsakar gida ɗaya tana dama kunu ɗaya tana aikin wanke waken ƙosai tace, "Umma, Inna, Mama na bata numfashi, ku taimaka min don Allah na kaita asibiti.” Wacce take amsa sunan Umma ta galla mata harara tace, "bazan taimaka ba, kaji min yarinya da sakarci, ni zan taimaki uwar taki dan bata da lafiya?. To ni ce na ɗora mata ciwon da zan taimake ta?.” Wacce take wanke waken tace, "ke kika saurare ta ma ai, wanda yake goya mata bayan baya nan sai a canja wani sarkin." Manal tana kuka tace, "don girman Allah ku taimaka min, Mama bata numfashi ban san ya zanyi ba." Ganin sun ma ƙi sauraren sai ta miƙe ta fita a guje ta sake komawa wajan Mama ta tarar da ita yadda ta barta daƙyar take numfashi, ta saka fita a guje ta shiga gidan su ƙawar ta Surayya a guje. Maman su Surayya tana zaune ita da Surayya ɗin suna ta shirin haɗa abin karyawa Manal ta faɗo tana kuka Maman su Surayya tace, "Subahanallahi Manal Lafiya?." Manal tana kuka tace, "Mama ce bata numfashi sosai, ki taimaka min don Allah, na rasa ya zanyo.” A firgice tace, "Subahanallahi, Surayya tashi kuje maza bara na faɗawa baban ku sai na biyo bayan ku" ta faɗa tana shiga wani ɗaki, suka fita ita da Surayya suka shiga gidan. Surayya ta tsorata da ganin yanayin Mam tace, "kina ji Manal, asibiti zamu je bara na nemo mai napep mu tafi" ta faɗa tana fita a guje ba jimawa sai ga Maman tasu ta shigo Manal na zaune kusa da Mama tana ta kuka. A guje Surayya ta dawo tace, "ga mai adaidaita sahun na samu." Maman su Surayya tace, "to yanzu ai ɗaukar ta wahala zai mana" ta kalli Manal da take kika tace, "a gidan Baban ki babu wanda zai taimaka mana mu fita da ita?." Manal girgiza kai kawai take kafin tace, "Zamu iya Mama, mu gwada kar Mamana ta mutu." Haka suka ɗauki Mama suka fita aka saka ta a daidaita sahu Manal da Surayya suka shiga suka tafi asibitin Murtala. A safiyar Adnan da kasala ya tashi kamar bazai je wajan aikin ba, tunawa da akwai masu jiran sa ya saka shi ya tashi dole yayi wanka ya shirya ya fito zuwa ɓangaren Mamy. A falon Mamy ya tarar da ita da Maryam da kuma Lubna a zaune ya shiga da sallama Mamy ta amsa tana faɗin, "Har an fito Bebi?." Ya ƙarasa ciki yace, "eh wallahi Mamy, zan shiga babban asibiti ne shiyasa. Barka da safiya" ya faɗa yana kallon ta amsa fuska a sake tare da faɗin, "Allah ya taimaka ya kiyaye hanya." "Amin ya Allah" ya kalli Maryam da take zaune fuska a haɗe ya kalli Lubna da take kallon sa sai tace, "Ina kwana Yaya." "Lafiya lau, baki tafi school ba?." "Bani da lecture yau." Ya kalli Maryam yace, "ina kwana." Kallon sa tayi tace, “Lafiya lau." Daga haka bai bata sake cewa komai ya tashi yace, "Mamy sai na dawo" ta masa fatan alkhairi shi kuma ya fita. Wajan Mama ya shiga ya same ta a tsaye kitchen tana yankan albasa yace, "ina Mimi da Kausar suke da zasu barki kina aiki?" Ya faɗa yana niyar juyawa zai je ya kira su Mama tace, "ƙyale su, ba wani abun bane nice nace su huta." "Amma Mummy kina aiki su suna kwance suna bacci meye amfanin su?." "Ƙyale su kawai. Baka fita ba kenan?." "Yanzu zan tafi. Ina kwana" ya faɗa yana durƙusawa har ƙasa ya gaishe ta amsa tare da faɗin, "Lafiya lau. Yau me ya hana ka fitowa da wuri?." Ya tashi tsaye yace, "gabaɗaya da bazan ma fita ba bana son jin daɗi ne" ya faɗa yana shiga kitchen ɗim ka karɓi albasar hannun ta wacce ta gama yankawa yaga kwai guda uku a ajjiye da alama shi zata soya, ya ɗaulp bowl ƙamari ya fasa kwan ya zuba albasar ya kunna gas cooker ɗin dan ta ɗota fan a kai, da kallo take bishi tana murmushi kafin tayi magana yace, "Abba bai kwana a gida ba kenan?." "Hmmm kai ka damu wannnan ai an saba, ƙiris nake jira da mahaifin ku wallahi." Jin abinda tace sai yayi shiru baice komai ba kafin ta kawar da maganar  tace, "yaushe zaka yi aure ne Bebi?." Baice komai ba ya zuba mai a kaskon ya juye ƙwan a kai tayi dariya tace, "haka zanci ba gishiri ba maggi?." Ya dan dafe kai yace, "na manta" ya faɗa yan ɗaukar abinda yasan tana ajjiye gishiri ya zuba mata ta sake cewa, "yaushe zaka yi aure ina tambayar ka." "Mummy sai ranar da Allah yayi." "Komai akwai niya ai Bebi, ya kamata zuwa yanzu kana da iyali kaima." "To Mummy zan fara neman matar aure in sha Allah" ya faɗa a lokacin yana juya ƙwan sama ya dawo ƙasa. Mummy tace, "Rumana ai a shirye take ko yau kace zaka aure ta zata shirya." Ya ɗan sauke numfashi ya kashe gas ɗin baice komai ba tace, "kayi shiru." Ya kalli Mummy yace, "Wallahi Mummy babu Ruman a raina a ya kamata ku fahimci hakan, Tunda daga lokacin da tace na barta shikenan na barta har raina, bana tunanin zan sake dawo da ita yanzu ko nan gaba." Mummy ta ta kalle shi shi kuma ya ɗauke ƙwan daga cikin fan ɗin ya saka a plate ya fito mata dashi ta zauna tace, "ya kamata ace ka mayar da ita kam Adnan, tana sonka kaima kana sonta, kawai abinda tayi maka ne ya saka ka kasa mantawa, amma da ka kawar da komai shikenan. Ai soyayya bata fita duka, tana nan a zuciyar ka na tabbatar da hakan.” Shiru yayi baice komai ba kafin ya kalli agogo yace, "zan tafi." "Allah ya kiyaye in ka dawo zamu tattauna akan maganar dan baka da matar da ta wuce ta indai ina da rai, Rumana itace matar ka in sha Allah.” Baice komai ba ya fita hau mota ya fita daga gidan gabaɗaya baya jin daɗin maganar Rumana da ake masa ko kusa, dan shi kam ko meye zai faru bazai aure ta ba, yadda ta barshi tayi aure shima haka zai barta yayi auren sa.           Ɓangaren Manal suna yashe a ƙofar shiga A&E an hana shiga da Mama ance babu gado, hankalin Manal ya tashi ta fita daga hankalin ta saboda gigicewa musamman in taga idanun Mama suna yin harrrr kamar zasu kulle sai hankalin ta ya saka tashi matuƙa. Babu irin magiyar da bata yi musu ba amma sun ƙi sun ce babu gadon da za'a ɗora Mama,  sai kuka take tana zaune kusa da Mama Bata da tsuntsu bata da tarko. Wani mutum ta gani ya fito daga cikin A&E din ta tashi a guje taje wajan sa tace, “Don Allah ka taimaka min Mamana bata da lafiya, don Allah ka taimaka min sunce babu gado ban san ha zanyi ba. Mamana zata mutu anki karbar ta ance Wai babu gado. Na rasa abinda zanyi dan Allah ka taimaka min."  Kallon ta yayi ya murmusa a zuciyar sa dan ya tabbatar itace yace, “Subahanallahi! Maman ce babu lafiya tana ina?." Da sauri ta nuna masa inda Mama take ya wuce ta zuwa wajan ya kalli Mama ganin da gaske fa Mama babu lafiya ya bar wajan zuwa wajan mai gadin shiga ciki ya tabbatar masa da babu gado a ciki ko ina ya cika, ya kalli ciki yaga mata da maza nan a ajjiye a kasa.. Da baya ya dawo ya kalli su Manal da Surayya da dukkan su kuka suke ya kalli Manal yace, "tana buƙatar taimakon gaggawa ina zuwa" ya faɗa yana shiga ciki bai jima ba ya dawo tare da wani nurse ya tsuguna kusa da Mama, ya kalli Manal yace, “me yake damun ta?.” Manal tana kuka sosai tace, “ban sani ba.” Surayya tace, “amma dai tana da ciwon sugar.” Kai ya girgiza ya tashi ya shiga ciki ba jimawa ya dawo ya sake tsugunawa yana auna sugar ta kafin ya ya buɗe bakin ta ya saka wani tablet a ƙasan harshen ta ya kalli mutumin yace, "ku canja asibiti kawai zai fi." Surayya tace, "bamu san inda zamu je ba, ko kuɗin mota babu a hannun mu." Mutumin Ya sauke numfashi ya kalli Manal yace, “kar ki damu zan taimaka miki in sha Allah.” Kuka take kamar zai sake magana sai ya fasa ya kalli wani namiji da yake tsaye ya taimaka masa suka fita da Mama su kuma suka bi bayan sa da gudu aka saka mama A mota suma yace su shiga suka tafi. Sai da suka tafi ya kalli Manal da take baya tana kuka yace, "kar ki damu zata samu sauki in sha Allah. Akwai asibitin da zamu je yanzu za’a kula da iya sosai.” Duk da yanayin garin a cike yake amma haka yake gudu dan ya isa asibitin, nan da nan suka isa ya faka motar ya budɗe ya fito da sauri ya shiga ciki sai gashi an fito da gado aka ɗora mana a kai suka shiga su kuka suka bi bayan sa. Wani ɗaki aka shiga da Maman tsabar ruɗewa zasu shi shiga aka dakatar dasu suka tsaya bai jima sosai ba ya dawo yana nan tsaye wani nurse ya fito ya kalle su yace, "Ya akayi aka bari sugar ɗin ta ya hau da yawa haka? Magani ta daina sha ko me?." Manal hawaye ya zubo mata tace, "Tunda maganin ya ƙare ta daina sha, kuma kwana biyu tana yawan sham shayi da sugar." Ya girgiza kai yace, "sugar tane ya hau sosai, sai kuma zuciyar ta da bata bugawa yadda ya kamata.” Mutumin ya kalli nurse din yace, “yanzu ya ake ciki likita? Ya jikin Maman?.” Ya sauke numfashi yace, “yanzu dai mun samu komai ya daidaita, Amma akwai likitan da zai zo anjima zai duba yanayin zuciyar ta ta in sha Allah komai zai zo da sauƙi. Tayi wani gwaji ne na zuciya cikin kwanakin nan?.” Manal ta daga kai tace, “eh tayi.” Nurse din tace, “yana ina?.” “Wallahi Mun bar shi a gida.” “To a kawo kafin zuwan likitan.” Manal ta girgiza kai tana kallon Surayya da wanda ya taimake su. Ta kalli Surayya tace, "ƙawata ko zaki je ki ɗauko? Wallahi hankalina bazai kwanta na bar Mama a nan bana wajan ba." Surayya tace, "kar ki damu Milky, zanje na ɗauko, a ina suke?." "Suna nan cikin jakata ta islamiyya." "Shikenan zan je, kinga ko kulle gidan ma bamu yi ba Allah yasa Mama ta kulle. Amma bani da ƙudim motar tafiya Manal." Manal tace, "kuma akwai kuɗi a jakar Baba ya bani jiya suna ki ɗauko su.” Wanda ya taimake su yana jin ta sai yayi murmushi yadda take kuka saboda mahaifiyar ta abin burge shi, da alama duk abinda ya nema saboda babar ta zata yi. yace, "ga dubu biyu kije ki dawo da sauri, kin ga lokacin sallar juma’a ya kusa.” Surayya ta kalli kuɗin da yake miƙa mata ta kalli Manal sai Manal ta girgiza mata kai yayi murmushi yace, "karɓi kar ki damu." Hannun a rawa ta karɓa tace, “mun gode, Milky sai na dawo” ta faɗa tana yim gaba. Manal ta kalli mutumin da bata san shi ba, bata taɓa ganin sa ba balle sunan sa tace, "bawan Allah na gode Allah yasa maka da alkhairi ya baka abinda ka ke so.” yayi murmushi yace, "bani zaki godewa ba, akwai wanda ya saka nayi miki shi zaki yiwa godiya. Shine yace duk abinda ake buƙata nayi miki, yana tausayin ki sosai.” Manal tace, "yana ina?." Yayi murmushi yace, "anjima zan zo na kai ki wajan sa, yanzu ya tafi saboda sallar juma’a, amma zuwa yamma zai dawo sai ki masa godia har gida.” Kai ta girgiza tace, “to sai kazo ɗin.” Yayi murmushi ya tafi ta samu waje ta zauna. Ba jimawa ya dawo da ledar abinci ya bata ta sake yin godiya ya tafi. Sai kuma gaban ta ya faɗi sosai tsoro ya mamaye mata zuciya, a zabure ta miƙe ta leƙa ɗakin da Mama take ta tagar dake wajan ta hango Mama a kwance tana bacci cikin ɗakin mai a.c. "Mai na aikata ne ni Manal? Waye wannan? Meyasa ma na amince dashi har aka kawo ni nan?. Waye shi? In Mama ta tambaye ni nace mata meye?.” Ta wara ido waje tace, "in aka cutar dani ko Mama fa?." "Manal!." A firgoce ta juya jin an kira sunan ta kuma muryar namiji sai hakan ya bata mamaki ta kalli wajan, Dr Huzaifa ta gani a tsaye yana mata murmushi yace, “me kike yi a nan?." Manal ta juya tana kallon sa tace, "ina kwana?." "Lafiya lau, ohhh! Mana ce aka kawo yanzu ko?. Haba nidai ina ta tunanin nasan fuskar ashe Maman ki ce. Ya akayi kika bari sugar ta ya hau sosai haka?." "Bata Shan magani kuma kwana biyu har sugar take sha." "Zata samu sauƙi in sha Allah, ki daina kuka." Ta goge idanun ta yace, "waye ya kawo ku nan asibitin?." Manal ta kalle shi tace, "wani ne ya taimaka mana wallahi, ban san ma nan zai kawo mu ba a can Emergency ance babu gado aka ƙi kula Mama" ta faɗa tana kuka sosai. Dr Huzaifa yace, "kar ki damu zata samu lafiya in sha Allah. Ki zauna nace aje a kawo gwajin zuciyar zuwa anjima likitan da zai ga sakamakon zai zo." Kafin tayi magana ya kuma cewa, "Jiya da nace kije wajan sa baku je ba kenan?." "Naje, tun jiyan Mama babu lafiya sai naje na kai masa dan ya rubuta magani shine ya kore ni." Yayi murmushi yace, "dole ya kore ki ai, kin taɓa ganin anje ganin likita babu mai jin ciwon?." Tayi shiru bata ce komai ya sake cewa, "zata samu lafiya in sha Allah." Yana faɗa ya bar wajan ta koma ta zauna, sai a lokacin taji sanyi a ranta ganin likitan da ta sani wanda suke wasa da dariya kamar ba likita ba in suka je wajan sa. Ba jimawa sosai Surayya ta dawo amma tayi wanka ta canja kaya a nan suka yi sallar azahar suna zaune suna jiran tsammani. Ba jimawa Dr Adnan yazo asibitin kai tsaye office ya wuce yana zama Huzaifa ya shiga yace masa, "daman kai nake jira wallahi, duba min wannan result ɗin" ya faɗa yana bashi takardar, bai musu ba ya karɓa yana dubawa ya kalle shi yace, "ina patient ɗin?." "Anyi admitting ɗin ta, tana nan emergency." Adnan yace, "ciwon ya ɗan yi ƙarfi kaɗan gaskiya, tana buƙatar magani masu kyau sosai. Wanne magani take sha?.” Huzaifa yace, “bani dasu a yanzu.” “Okay, tana da buƙatar kula dai sosai, in aka cigaba da haka ciwon wuce yanzu.” Huzaifa yace, "patient ɗina ce duk two weeks suke zuwa wajena itace ƴarta, itama ƴat ciwon ne da ita amma na uwar yafi yin worst tunda kaga ya taɓa mata ido yanzu ko gani bata yi sosai, ga zuciya ma." "Subahanallahi, haka ciwon naku yake ɓarna?." "Yanzu kazo muje ka ganta don Allah, ni kaina ya kulle wallahi na rasa ma abinda zan mata.." "To kai da kake endologisy baka iya komai ba ina ga ni cardiologist? Me zan iya?." "Experience ɗinka akan zuciya ne kana da abinda zaka iya." "To kai kuma akan ciwon ne gabaɗaya, kamar ka fini sanin aikin ka." Huzaifa yace, "Nidai kazo muje ka ganta kawai don Allah." Ba musu ya tashi suka fita bai ma kula da Manal ba ya wuce zuwa ɗakin ba jimawa suka fito Huzaifa ya tsaya ya kalli Manal tace, "kar ki damu Manal, ga wanda zai kula da lamarin zuciyar Mama nan, kar ki damu." Kallon Adnan tayi suka haɗa ido ta glasses ɗin Idon sa, ita ta gane shi amma shi bai gane ta ba sai ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba, shi kuma a zuciyar sa yana ayyana ita kuma ko gaisuwa bata iya ba. Ya wuce ya shiga office ya samu Hamza a zaune a ciki bai kula shi ba ya kalli Huzaifa Adnan yace, "Huzaifa meye alaƙar ka dasu?." Huzaifa da yake bayan sa yace, "babu komai wallahi, patients ɗina ne kawai kamar yadda nace maka." "To yayi, tana buƙatar hutu a ƙalla one week to ten days a nan, sannan akwai abinda yake damun ta wanda yake jawo mata ciwon, in aka yi bincike sosai babu lallai diabetes ya kawo shi.” Hamza cikin tsokana yace, "taya ka gane?." Ya Harare shi yace, "iya pulse ɗin ka zan riƙe zan fahimci yanayin heart beat ɗin ka, in stress ne ya saka ta bugawar zan gane, in gudu kayi zan gane, in damuwa ce zan gane ka fahimta?. Nan ba office ɗin kallon matan mutane bane, i am cardiologist.” Hamza yayi dake shi yace, "wallahi zan baka amsa a lokacin da matar ka zata haihu a hannuna." Bebi ya taɓe baki yace, "Allah ya kiyaye, ni matata ta haihu a wajan ka…? ai har abada wallahi." Suka yi dariya a tare banda Bebi da yake sake kallon sakamakon gwajin Maman Manal. Sai ya ajjiye takardar ya furzar da iska yace, "wa kuka sani a police station? Akwai wanda na ke so a kama min." Huzaifa ya ce, "to me yayi maka kuma?." "Mijin Maryam nake so a kama, in ba kama shi nayi ba bazai daina bibiyar ta ba." Hamza yace, "wannan matsalar fa daga Maryam take ba daga shi ba Bebi, da bata bashi dama da fuskar zuwa wajan ta bayan ya sake ta ba wallahi da bazai zo ba." Huzaifa yace, "wannan gaskiya ne abinda kake faɗa, itace ta bayar da dama tun farkon rabuwar su da bata bada dama ba da hakan bata kasance ba.” "Shiyasa nake so ayi mana iyaka dashi, tunda babu ragowar igiyar auren sa a kanta a kan me zai dinga bibiyar ta? Tunda dai babu damar mayar da ita wallahi kar ya sake sauraron ta. Jiya da daddare bayan na koma na ganshi da ita mota, me ake a motar? Meye alaƙar su da har zata dinga shiga motar sa?." Hamza yace, "wannan ita zaka tambaya, kuma ira zaka jawa kunne ba wani ba." Ya girgiza kai kawai baice komai ba suma basu sake ce masa komai ba suka fita shima ya fita. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp *BOOK 1* *Page 008* A ɓangaren su Manal yunwa Surayya take ji gashi a zaune basu ci komai ba ta kalli Manal tace, "Milky Yunwa nake ji sosai." Manal tace, "a kuɗin da kika ɗauko kije ki siyi wani abun Kkici." "Kefe Milky? Baki karya bafa." "Bazan iya cin komai ba in Mama bata farka ba." Wayar Surayya tayi ƙara ganin sunan Maman ta sai tace, "bara naje na shigo da Mama." Fita tayi ba jimawa siai gasu da Mama har da abinci ta kawo musu Mama tace, "ya jikin Maman taki Manal?." Manal tace, "tana nan dai kwance." "Kin san wanda ya kawo ku nan ne? Surayya ta faɗa min komai." "Wallahi Mama ban san shi ba, ni kaina gabana faɗuwa yake yi sosai. A lokacin a ruɗe nake sai yanzu na nutsu na fahimci nayi kuskure.” "Hankalin ki baya jikin ki a lokacin ne shiyasa Manal, amma babu komai Allah yana gani dan mahaifiyar ki kika yi bazai bari ki cutu ba." Ta ɗaga kai alamun haka ne Mama tace, "Mubeena bata zo ba?." Manal ta taɓe baki kawai bata ce komai ba dan ita ta manta ma da wata Mubeena. Ganin haka dai Mama tace, "ga abinci nan ki ci bana son musu dan nasan yunwa kike ji. Akwai salad a ciki sai ki zuba ki ci.” Jin abinda tace ya saka dole ta karɓi abincin da Surayya ta zuba mata tana ci daƙyar. Manal tace, “ni na manta, wanda ya kawo mu ya kawo mana abinci” ta faɗa tana jawo ledar ta buɗe. Mama na wajan har akayi magriba ta kalli Manal tace, "ki kira Mubeena a waya tazo ta taya ki zama a nan." Da to kawai ta amsa dan ba yi zatayi ba dan ɓata lokacin ta zatayi indai Mubeena ce ba zuwa zatayi ba. Ba jimawa suka tafi Manal tana ta godiya harda kuka suka tafi ta dawo ta zauna tare da yin shiru. "Sannu Manal." Ta ɗago ganin wanda ya taimaka mata sai tayi murmushin tace, "Yauwa." "Ya jikin Maman?." "Da sauƙi, bacci ma take." "Haka ake so sosai Allah ya bata Lafiya." "Amin. Na gode sosai." Yayi murmushi yace, "ki kula da ita zuwa gobe zan zo sai muje wajan wanda ya taimaka miki." Manal ta ɗaga kai tace, "to Allah ya kaimu, na gode sosai." Murmushi yayi ya tashi ya bar wajan ya tsaya bayan ya bar wajan tare da ɗaukar waya ya saka a kunne yace, "Ranka ya daɗe tana hannu yanzu, zuwa nan da gobe duk abinda nace tayi zatayi domin akwai target ɗina a kan ta, shiyasa na zaɓi wannan asibitin saboda yana da tsada sosai." Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, "zuwa gobe zan kawo ta." Shiru ya sake yi kafin yace, "Allah ya taimaki uban gıdana, wannan ai abu ne mai sauƙi, Tunda ka ganta kaji tayi maka ai an wuce wajan. Ba da ƙarfi zamu yi amfani ba da kanta zata amince saboda bata da mafita, in taƙi ta kwana a hannun yan sanda." Dariya yayi mai sauti kafin ya kashe wayar ya juya yana hango Manal da ke zaune ya girgiza kai yace, "ba ƙarya yarinyar akwai kyau, iya wannna farin nata ko shi kaɗai ya ɗauki hankalin mai gida balle in tayi magana. Ta haɗu ba ƙarya wallahi, zata yi abinda ake so. Sorry yarinya kin zo hannu” yana gama faɗar hakan ya tafi yana dariya mai kama da dariyar mugun ta. Manal tana nan zaune har akayi i'sha a nan tayi sallah dan wajan yana da tsafta sosai, tana idar da sallah Bebi yazo wajan ya kalle ta yana mamakin yadda bata gajiya da kuka, ta idar da sallah amma sai kuka take yi jikin ta har rawa yake yi sosai, har ya wuce ta sai ya tsaya yana kallon ta yace, "Kina ji? Ki shiga wajan maman ki zauna." Jin magana a kanta sai ta ɗagp suka haɗa ido yace, "tashi kije ciki." Jikin ta a sanyaye ta tashi fuskar ta jiƙe da hawaye ta shiga ciki yabi bayan ta har lokacin Mmaa bacci take. Bugun zuciyar ta ya sake dubawa ya rage gudun ruwan da yake shiga jikin ta ya sake yi mata allura sannan yace, "anytime zata iya farkawa, in ta farka zaki iya zuwa reception ki sanar da nurse." Ta ɗaga kai alamun to har lokacin kuka yake yi ya bita da kallo yana tunanim ita wannan yarinyar kuka baya mata wahala ne ko kuwa me?. Huzaifa ne ya shigo ɗakin yana cewa, "kai nake ta nema ashe ka shigo nan" ya kalle ta yace, "Manal kar ki damu zata ki sauƙi, ki daina wannan kukan kar ya cutar da ke.” Ta ɗaga kai alamun to yace, "ina Yayyen ki suke?." Ta kalle shi tace, "Bana da yayye, Yayata guda ɗaya ce kuma tana makaranta." "Ke kaɗai zaki kwana a nan?." "Eh" ta faɗa a sanyaye tana kallon sa. Yace, "shikenan to zuwa da safe duk zamu dawo, in akwai abinda kika ga Mama nayi in ta farka kije ki sanar a reception." "To" ta fadɗa muryar ta na rawaHuzaifa yana kallon ta Allah ya sani yana jin tausayin Manal sosai har zuciyar sa bai san dalilin hakn ba. Shi kansa Bebi kallon ta yake yi kafin ya kalli Huzaifa ya wuce ya fita shima ya biyo bayan sa. A wajan ajjiye mota ya samu Bebi yana niyar shiga mota Huzaifa yace, "yarinyar nan tana bani tausayi Bebi, har zuciyata nake jin tausayin ta wallahi ban san meyasa hakan ba." Bebi yace, "Akwai tausayi kam, sai da safe" ya faɗa yana shiga mota ya fita daga asibitin. Shima Huzaifa shiga motar yayi ya tafi. Yana komawa gida ya tarar da ɓacin rai a harabar gidan nasu domin kuwa Lubna ce tana zaune da saurayin da ya hana ta kulawa suna hira. Ransa yayi mugun ɓaci ya rasa ya zaiyi da yarinyar nan duk abinda yace sai ta tsallake, in yace kar tayi sai tayi bata san abinda yake ji a zuciyar ba in hakan ta kasance. Lubna tana ganin sa ta tashi ta shiga gida da sauri shi kuka saurayin nata sai ya tashi ya nufo inda Bebi yake a lokacin ya fito daga mota ya miƙa masa hannu yace, "Barka da dare Yaya Adnan." Kallon hannun nasa yake yana kallon fuskar sa kafin yace, "Mujahid wannan abinda kake yi bai kamata ba, dani kake faɗa banga dalilin da zai saka ka sako ƙanwata a ciki ba." Wanda aka kira da Mujahid yayi dariya yana kallon sa yace, "Neman aure nake fa Yaya Adnan, ba da wani abun nazo gidan nan ba auren ta nake so nayi in an bani dama." Adnan ya gyara tsayawa yace, "zan maka last warning akan Lubna, babu kai babu ita ka fita daga cikin rayuwar ta in ba haka ba.." kafin ya kai ƙarshe Mujahid yace, "in ba haka ba zaka saka a ɗauki raina?" Sai yayi dariya ya ce, "naga Lubna ina so kuma auren ta zanyi, baka isa ka hana ni neman auren ta ba, domin kuwa ba kaine mai gidan ba kuma ba kaine riƙe da gidan ba. dan haka zan nemi auren Lubna sai kuma na aure ta sai naga iya abinda zaka iya yi." Juyowa yayi zai tafi sai kuma ya dawo ya saka kallon sa yace, "in ma ban aure ta ba zata faɗa cikin soyayya ta wacce zata kasa sarrafa ta, daga nan duk abinda nake so zanyi da ita baka isa ka hana ni ba, sai dai kaji ance likitan zuciya Dr Adnan Mu'azzam yana kwance yana jinyar zuciya saboda saurayin ƙanwar sa. Wannan fagen nawa ne Adnan, ba wajan ƙwace leinses bane” ya faɗa yana murmushi tare da barin wajan ya fita daga gate ɗin gidan dan motar sa ma a waje ya barta. Ransa ya ɓace sosai ya nufi cikin gidan ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga ɗaki ya zauna a kan kujera yana tunani. Shi yasan da biyu Mujahid yake zuwa wajan Lubna, yasan saboda wani nufin da yake zuciyar sa ne yake zuwa ba don Allah da annabi ba. Waya ya ɗauka hannu na rawa ya kira Lubna tana ɗauka yace ta zo ta same shi ya yanke wayar ya ajjiye. Ba jimawa ta shigo jiki a sanyaye ta zauna tace, "gani." "Ban miki warning akan kula Mujahid ba?, bance kar n saka ganin ki dashi bane yasa kike haka ne Lubna?." Tayi shiru bata ce komai ba amma a zuciyar ta mamaki yake bata, to wai shi ina ruwan sa da samarin tane?. Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa, "magana nake miki fa, in baki amsa ba sai na taso na fasa miki baki." Jin yadda yayi magana sai tace, "To ni ina son sa." Wani iri yaji a zuciyar sa ya kulle ido ya buɗe cikin takaicin abinda tace ya fuzar da iska yayi shiru baice komai ba. "Allah Yaua ina son sa, kuma daman kace na zaɓa aure ko karatu ko?, to ni aure nake son yi kuma shi zan aura." A fusace yace, "ba sonki yake ba shi, yana amfani dake ne saboda wani nufi masa amma ba dan yana son ki ba. Ki dawo hankalin ki malama, wannan tunanin da kike bashi da amfani domin kuwa baza ki aure shi ba.” Tayi shiru ganin yana zare mata idanu, ido ya cika da hawaye sai ya dafe kai yace, "look Lubna! Mujahid ba irin mazan da zaki saurara bane a matsayin wanda zaki aure kin gane?." Magana take so tayi amma ta kasa yace, "faɗi abinda yake bakin ki ina jin ki." Tace, "Yaya naga abokin kane fa, meyasa baka so yake zuwa wajena? kuma ni nace auren sa zanyi ina son ..."'yadda ya taso kamar zai mare ta shine ya hana ta k'arasa maganar yace, "shut up your mouth, stupid girl ina miki magana kina sake maimaita min kina son sa? Ni zaki faɗawa kina son sa don kin raina min hankali..? Ina magaa kina maganq? baza ki aure shi ba ki rubuta wannan ki ajjiye. Indai Adnan yana da rai baza ki auri Mujahid ba, ya kamata ki san da wannan. Kuma na sake ganin ki dashi sai nayi miki dukan da ba'a taɓa yi miki irin sa ba tunda kika zo duniya, sai na miki dukan da shi Mujahid ɗin bazai gane ki ba, daga ranar zaki shaida waye Adnan.” Cikin tsawa yake magana hakan ya saka ta shiga hankalin ta sosai, ya sake cewa, “Tashi ki bani waje." Da sauri ta zabura ta miƙe ta fita da sauri ya daki kujera cikin takaici da baƙin ciki. Mujahid yayi nasara a kansa tunda har Lubna ta fara son sa shikenan ya gama karya masa lagon Lubna, amma yasan abinda zai masa bazai sake waiwayon Lubna ba itama dole ta haƙura dashi domin bai dace da ita ba, ba irin sane ake kira da mijin aure ba. Mujahid da murmushi ya bar gidan ya shiga mota ya zauna ya samu abokin sa a zaune yana jiran sa yace, "tunda naga kana murmushi nasan akwai abinda ka shirya wanda kake gab da samun nasara." Yayi dariya kaɗan yace, "burina na baƙantawa Adnan kamar yadda ya baƙanta min, badai ƙannen nasa yake tattali kamar ƙwai ba? To ni kuma sai na saka ƙafa na take wannan riritawar da yake musu dan wallahi sai na saka masa baƙim ciki a zuciyar sa." Wanda yake sanarwa ya shigo a kai yace, "kar ka manta Adnan abokin nake fa Mujahid, da sunan ka aka buɗe asibitin getting better kana daga cikin ma'aikatan sa kafin ka daina aiki." "Kafin yayi silar daina aiki na dai, har abada bazan manta da abinda Adnan yayi min ba, kuma wallahi sai na rama akan ƙanwar sa Lubna. Bashi da weakness point a duniya kamar familyn sa, musamman ƙannen sa mata guda uku, tabbas zan yi amfani da Lubna na saka masa baƙin cikin da na ɗanɗana a zuciyata nima." "Kenan baka son Lubna?." Yayi tsaki yace, "bana ce ba" ya faɗa yana jan motar suka bar wajan yana aiyana irin abinda zai yiwa Lubna, dan walalhi sai ya saka Adnan kuka in ba haka ba bazai daina jin da daɗin abinda yayi masa a zuciyar sa ba. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* Page 009 Washe gari Bebi ya jima yana bacci bai tashi ba sai zuwa ƙarfe goma na safe sannan ya fito bayan ya shirya, motar Abba ya gani a ajjiye alamun ya dawo kenan sai ya nufi ɓangaren sa da niyar gaishe shi.  A nan ya tarar da yayyen sa maza a zaune da alama sun shigo gaishe shi, suka gaisa ya samu waje ya zauna baice komai ba shima saboda sun ce ya zauna ne. A lokacin Abba yace, "kuna gani dai gashi tun ɗazu na kira iyayen ku gashi sun ƙi zuwa, ni ban san me suka ɗauke ni a cikin gidan nan ba, basa jin maganata a ko yaushe so suke suga raina ya kai maƙura wajan ɓaci." Bebi ya kalli Abba yace, "kayi haƙuri Abba, ban san me ku ka tatttauna a farko ba kafin shigowa ta nan, amma Abba gaskiya matsalar gidan nan daga ɓangaren ka take. Dan iyayen mu sunyi fushi ba laifi bane duba da kwanakin da ka ɗauka baka gidan nan, da ka dawo kwanan ka ɗaya ka sake fita sai yau da safe ka dawo." Abba ya kalle shi yace, "Daman ai Adnan na jima da sanin kai kake son maye gurbin ubana Alhassan da ya mutu, kama kunne na ka faɗa min kamar zan fi ganewa sosai." Bebi yace, "Allah ya wuce zuciyar ka, ba haka nake nufi ba." Sai kuwa abba ya fusata yace, "me kake nufi to? Haihuwar ka nayi ko haihuwata kayi da zaka zo gabana kana faɗa min wai dole su yi fushi da ni?. Akwai abinda na rage su dashi a cikin gidan nan ne? Akwai abinda ban ajjiye kafin na bar gidan ba?, Meya damuwar su dan naje nayi kwanaki a wata ƙasar ko wani garin? Meye abinda zai shafe su?." Dukkan su sunyi shiru ganin ya fusata sosai babu wanda ya sake magana. A lokacin Mama ta shigo jin yana faɗa sai taja ta tsaya bata zauna ba ya kalle ta yace, "ita babar taka abinda take yi daidai ne?, Dana dawo gidan akwai wacce ta nuna taji daɗin zuwa na? Akwai wacce ta bani abinci?. Dukkan su bana gaban su shiyasa nima na ajjiye su a gefe tunda basu damu da tawa rayuwar ba nima ban damu da tasu rayuwar ba." Mamy ma na tsaye a baya tana jin duk abinda yake cewa. Ya sake kallon yaran nasa yace, "indai iyayen ku basu gyara ba kar wanda ya sake zuwar min da maganar abinda nake ba daidai bane, in kuma ba haka ba wallahi ransa ya ɓaci dan sai na saɓa masa fiye da tunanin ku. Kai Adnan kaine daman mai bakin magana, ko magana aka kasa faɗa min kaine mai iya faɗa to ahir, ka jawa iyayen ka kunne in ba haka ba kuma ranka ne zai ɓaco matuƙa." Ya girgiza kai yace, “kayi haƙuri Abba.” Abba bai kuma magana ba ya tashi ya shige ɗaki ya barsu a zaune a  wajan. Mamy da Mama basu ce komai ba ko wacce ta fi daman basu zauna ba. Adnan ya kalli babban yayan su yace, "yanzu tsakani da Allah a haka za'a tayi a gidan nan?." Yaya Bilal yayi masa alama da su tashi su fita. Dukkan su tare suka fito suka tsaya a rumfar ajjiye motocin gidan Bebi yace, "na rasa abinda zai mu yiwa abba, yanzu tsakani da Allah ina amfanin maganar nan da yake yi a gaban idanun mu?, a ganina wannan saɓani ne da ya shafi zaman auren sa da matan sa meyasa baya jin kunyar faɗawa iyayen mu magana a gaban mu ne? Meyasa Abba bai san lokacin wannan ya wuce ba?." Yaya Bilal yace, "Bebi su kansu iyayen mu suna kuka da wannan halin, in suka masa laifi a gaban yaran su zai faɗa musu maganar da zata saka su hawaye bai damu ba." Yaya isma'il yace, "ni ban san abinda zance bama wallahi, amma iyayen mu suna cikin damuwa sosai." "Ni na gama yanke hukuncin zan samu wani babban malamin da nasan Abba yana da alaqa dashi na kai masa maganar yayi masa nasiha" Bebi ya faɗa cikin yanayin damuwa. "Hakan ma mafita ce" Yaya Bilal ya faɗa yana kallon sa. Bebi ya furzar da iska daga bakin sa yace, "zamu san abinda za'a yi, duk da baza mu canja shi ba ya riga ya saba zama ba'a gida ba, amma zamu yi addu'a ba dan mu ba, ko dan ƙannen mu da suke gidan." Yaya Ismail yace, "kana ƙoƙari akan kowa a gidan nan Adnan, Allah ya cigaba da baka ikon sauke haƙƙin da ya hau kanka tunda kaine kamar mahaifi a gidan namu." Ya amsa da amin kafin ya wuce zuwa wajan Mama. A zaune ya same ta kamar komai bai faru ba ita dasu Mimi suka gaishe shi ya amsa ya zauna yana kallon Mmaan kafin yace, "Mummy barka da safiya." Ta kalle shi tace, "Barka dai Bebi, yau ma kasha bacci."  Kafin yayi magana tace, "yaushe zaka je ka gaida Hajiya ne? Yanzu da muka yi waya muka gaisa sai da tace ina Adnanu basarake, shi baya zuwa inda mutane suke, tace a gaishe da sarkin sarakuna. nace yana nan." Ya ɗan saki fuska kaɗan yace, "zanje ko anjima ne ko gobe in sha Allah.” "Nima anjima nake so na leƙa na kwana biyu bamu gaisa ba, gashi Sumayya tace min zata zo in tazo muje tare ko kuma naje zuwa dare ko gobe." Jin tace Sumayya yasan Maman su Rumana take nufi ƙanwar ta kenan sai ya girgiza kai yace, "Allah ya nuna mana." Ya amsa da amin ya kalli Mimi yace, "kawo min abinci naci." "Akwai ragowar shinkafar nan ta jiya na ajjiye maka ayi warming sai a kawo maka naga kana son ta." Ya kalli Mummy da mamaki jin tace wai warming yace, “ta jiya dai Mummy?.” “Eh, naji kace ta maka daɗi ne ai.” “Ai Mummy a barta kawai, ina ni ina cin abincin jiya?. Na sha tea, Mimi kawo min.” Sai kuwa Mimi tayi dariya ita da Kausar Mama ta kalle su tace, "daman sai da suka ce kar na ajjiye ba ci zakayi ba amma na ƙi ji, gashi yanzu maganar tasu ta tabbata shine suke darıya." Mimi ta tashi ta kawo masa tea da kuma soyayyen dankalin hausa dana turawa a haɗe sai ketchup a gefe dan tasan ko bata saka ba sai ta koma. Karɓa yayi yana ci dan shi tea bai dame shi ba sam, ya rasa me zai cewa Mama akan maganar Abba shiyasa yayi shiru bai ce komai ba. Har ya gama ci baice komai ba ya cinye dankalin amma bai shanye tea ɗin ba dan tea ba wani abokin sa bane. Sai Mama tace, "Yauwa bebi Kausar tace min tana son zuwa asibitin ku wajan Hamza, Wai marar ta ke ciwo haka kawai kuma gefe ɗaya ya riƙe sosai." Ya kalli Kausar ɗin sai yaga ta sunkuyar da kai ya kalli Mama yace, "Hamza yana asibiti ina jin yanzu ma." "To tazo sai ku tafi gwara taje ta san matsalar ta kar azo abin yafi haka." "In na tafi da ita waye zai dawo da ita?." "Sai ta dawo ita kaɗai, kai wai kallon su kake kamar yara ƙananu, daga asibitin naku zuwa nan wani nisa ne dashi?.” Yace, "ba haka bane Mummy, Yawon su kaɗai ne bana so" ya kalli Kausar yace, "muje." Ya miƙe tsaye ya kalli inda Mimi take ya kalli Mama yace, "mun gama magana da wanda yace yana son Mimi, ban bashi damar zuwa ba banyi binciken da nake so nayi ba, zuwa nan da jibi dai haka." Mama tayi murmushi tace, "To Baban Yaya, Allah ya taimaka." Ya amsa da amin ya wuce ya fita Kausar tabi bayan sa. Sai da yaje wajan mota ya lura da ita a bayan sa ya bita da kallo up and down yace, "wannan wanne irin mayafi ne? Koma malama ki canja." Da sauri ta juya shi kuma ya shiga motar ba jima ta dawo ta saka abaya akan kayan ta shiga gaba ya fita daga gidan.  A hanya ya kalle ta yace, "bakwa yiwa yayar ku Lubna faɗa ko?." Tace, "Wallahi Yaya muna yi bata jin magana ne, sai tace wai takura mata ake ita da Yaya Maryam." Ya girgiza kai yace, "bata jin magana." Bata ce komai ba ya cigaba da tafiya kafin yace, "tun yaushe kike ciwon?." "Kusan sati kenan." "Kuma kin tabbatar ba period bane?." Ta ɗaga kai ta amsa da eh baice komai ba ya cigaba da tafiya har suka je asibitin ya faka motar ya fito itama ta fito suka shiga ciki.  Office ɗin sa suka shiga da ita akwai patient guda biyar da suke jiran sa tana zaune duk suka shigo ba jimawa suke fita har ya gama dasu sai ga Hamza da Huzaifa ɗin sun shigo. Huzaifa ya kalli Kausar yace, "Kausar yau ke kika yiwa Yayan naki rakiya?." Tayi dariya ta gaishe su suka amsa ya kalli Hamza yace, "wajan ka tazo." Hamza yace, "to Allah yasa Lafiya." Huzaifa yace, "Kuje office ai kowa yana son sirri." Ba musu ya fita ita kuma bata tashi ba tana jira Bebi ya bata umarnin tafiya. Lura da hakan sai Huzaifa yayi dariya yace, "Kausar tashi kije na baki umarni a madadin sa." Sai a sannan ya ɗago dan shi ya ɗauka ma ta fita a lokacin ta fita ya cigaba da abinda yake yi. Ba jimawa ta dawo da sallama suka amsa tace, "Yaya an gama." Ya ɗago ya kalle ta yace, "to yanzu ya za'ayi? Tafiya zaiyi ko zaki jira na gama?." "A'a zan tafi dai." "Allah ya kiyaye" ya faɗa yana cigaba da rubutun sa. Sai tace, "babu kuɗi a hannuna ai." Huzaifa ne ya bata dubu biyu ta karɓa tace, “An gode, Yaya na tafi.” “Allah ya kiyaye, ki kula.” Ta amsa da to ta fita, Huzaifa yace, "wani lokacin kana burge ni akan yaran nan, wani lokacin kana bani haushi." Baice komai ba ya cigaba da abinda yake yi. Huzaifa yace, "Yauwa, wanne magani kake ganin za'a bawa matar nan ta jiya?." "Wacce mata?." "Mahaifiyar yarinyar nan mana da suka kwana a nan." "Ohh! Sai naje naji yanayin bugawar zuciyar sannan nasan abinda za'ayi." Bai jima ba ya tashi zuwa ɗakin ya samu Maman a zaune Manal ɗin na gefen ta tana bata apple da ta yanka mata ƙananu. Ƙarasawayayi yace, "Sannu Mama." Mama duk da ba gani take ba sosai tace, "Yauwa sannu likita." "Ya jiki?." "Da sauƙi" ta faɗa a wahala kana ganin ta kasan tana jin ciwo har lokacin. Hannun ta ya riƙe yana sauraren bugun zuciyar ta kafin ya saki yace, "Mama saka damuwa a zuciya ba komai yake kawowa ba sai ciwo, ki kawar da abinda yake damun ki kodan Lafiyar ki." Mama tayi murmushi kawai tana girgiza kai bata ce komai ba ya kalli Manal kamar zai magana sai ya fasa ya fita. Ba jimawa ya dawo ya bawa Manal takarda yace, "babu wannan allurar a nan sai gobe za'a kawo, zuwa dare ki bawa yayan ki a siyo ta.” Karɓa tayi ya fita ita kuma ta ajjiye takardar a kusa da ita. Mama tace, "Manal wanne Yaya yake nufi?." Manal tace, "Mma ki yi shiru kina wahala in kina magana." "Mubeena bata zo ba ko?." Manal tace, "eh bata zo ba." Mama ta girgiza kai kawai bata sake cewa komai ba. Sai da Mama tayi bacci Manal ta fito neman wannan mutumi bata ganshi ba haka ta koma a lokacin Surayya da Maman ta sun sauke zuwa suka ɗauke mata kewa har magariba sannan suka tafi. Suna tafiya yazo bai shiga inda Mama take ba ya tsaya a inda ya ganta Manal tace, "sannu da zuwa." "Yauwa Sannun ki. Ya jikin Maman?." "Da sauƙi sosai. Tun ɗazu nake neman ka an bani wata takardar magani ance a siyo allurar, da kuɗi a a hannuna amma ban saninda za'a siyo ba ko zaka taimaka min." Yayi murmushi yace, "siyan allura da magani duk aikin wanda ya ɗauki nauyin Mama ne, abinda zai faru yanzu tunda tana bacci Mama kizo muje ki masa godiya daga nan sai a baki allurar. Kin San godiya tana daɗi, sai yafi jin daɗin sake miki wani alkhairi musamman in akace kin taka kin je har inda yake.” Manal cikin faɗuwar gaba tace, "amma bi kaɗai ce a wajan Mama, in na tafi waye zai zauna?." "Ai ba jimawa zaki ba, amma in kina ganin basai kin gode masa ba shikenan." Manal murya a sanyaye tace, "ina ne inda zamu je?." "Nan ne gidan sa babu nisa, da mu je zaki ga mata ma wanda ya taimakawa kamar ki." "Da zamu bari sai da safe maje ko?." "To ya za'ayi da allurar?." Manal tace, "zan siya da kuɗina." Yayi murmushi yace, "kuɗim ki baza su iya ba, wannan allurar da kike gani a ƙalla zatayi dubu hamsin, kizo muje a siyo a yi mata dare yana yi." Manal tayi shiru tana tunani yace, “ko kina da dubu hamsin ɗin?.” Ta girgiza kai alamun a’a yace, “muje.” Gaban Manal dai faɗuwa yake sosai ta ɗaga kai alamun to ta biyo bayan sa. Mota ya shiga itama ta shiga suka fita daga asibitin, sai salati take a zuciyar ta dan ta san ba daidai take aikatawa ba. Babu nisa da asibitin sosai ya tsaya aka buɗe masa gate suka shiga ya faka motar yace, "kinga masu neman taimakon ko?." Ya faɗa yana nuna mata wasu mata da suke tsaye da hijjabai su biyu. Kai ta ɗaga tana kallon su jikin sanyi jiki, murmushi yayi yana aiyana ai kin zo hannu yarinya ya buɗe motar ya fito yace, “muje ko?.” Manal jikin ta har yayi ɗumi saboda tashin hankali ta fito tana kallon gidan, yana da girma sosai ga haske ko ina kamar rana, gaba yayi ganin hakan sai ta sauke numfashi suka nufi ciki kai tsaye. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* *Page 010* Suna daga cikin falon a tsaye a bakin window suna hango masu shigowa da masu fita, ganin Manal ta fito daga mota sun doso ciki sai Alhaji Magaji yace, "to kaga yarinyar nan an kawo maka ita, ɗanya sharaf ga shegen kyau, yadda kaga fuskar ta na tabbatar ka san daga ciki ma zata yi kyau ai ka gane, ni na tabbatar ko ita wacce kake zance bata kai wannan ba. Kalle ta fa, komai yaji da gani zata yi sauƙin kai, kayi abinda ka ke so kai kaɗai babu mai takura maka.” Alhaji Mu'azzam yayi murmushi yace, "akwai haske kam kamar yar india, kasan ko a can ba’a samun masu wannan hasken kamar madara. Hasken ta akwai ɗaukar hankali tun daga nesa na tabbatar. Amma ni wallahi hankalina yana ga Mubeena. Ina son yarinyar, ina kuma ƙaunar ganin ta ko yaushe, saboda Mubeena ta haɗu daidai gwargwado.” Ganin zasu shigo sai suka koma suka zauna a lokacin suka shigo da sallama. Suka amsa yana binta da kallo duk da kanta yana ƙasa, ta tsuguna kamar yadda wanda ya rako ta ya tsuguna yace, "Alhaji gata itace mai mara lafiyar, tazo tayi maka godiya ne." Jin haka sai tace, "ina wuni." Alhaji Mu'azzam ya amsa fuska a sake yana so yaga fuskar ta sosai amma taƙi bada damar hakan, taee, "Na gode Alhaji, Allah ya saka da alkhairi ya biya buƙata." "Haba ai yiwa kai ne ƴan mata. Kamar ku bai kamata ace kuna neman abu ku rasa ba, mu kuma in muka ga haka dole sai mun taimaka.” Wanda ya rako ta yace, "gashi takardar allura ce za'a siya, na tambayi kuɗin allurar ance duba ɗari ce shine nace tazo in tayi maka godiya sai ka bada kuɗin." Murmushi yayi masa alamun ya tashi ya tafi, ya kalli Alhaji Magaji sai ya miƙe yace, "Nidai zan wuce sai gobe." Ya ɗaga masa kai kawai, falon ya rage daga ita sai shi sai ihun a.c. Ya fito da kuɗi daga aljihu sa ya ajjiye yace, "zo ki karɓa aje a siyo.” ya faɗa yana mika mata kuɗin, ta taso ta ƙarasa zata karɓa sai ya haɗa da hannun ta ya riƙe, da ssuri ta kalle shi gaban ta ya faɗi suka haɗa ido sai yayi murmushi yace, "kar ki damu ba komai bane wannan." Hannun ta ta zame ba ta karɓi kuɗin ba ta matsa baya yana kallon ta yace, "bakya son kuɗin?." "Bana so indai sai ka riƙe hannuna." Yayi murmushi yace, "kin amince kar a yiwa Maman ki allurar kenan?." Tayi shiru bata amsa amma tsoro ya gama mamaye ta, dana sanin zuwa kuwa kamar ta cakawa kanta wuƙa saboda takaici yace, "kar ki manta ba'a biya kuɗin asibitin ba sai za'a sallama ku, kinga kenan ke zaki biya duka abinda aka kashe in ba haka ba su kama ki. Wannan ai ba komai bane ki amince na baki kuɗin ki tafi. Kamar baki waye ba ƴan mata? Wannan ai ya zama normal ba wani abin damuwa bane.” Gaban Manal faɗuwa yake sosai ta kalle shi suka haɗa ido, haka kawai gaban sa ua faɗi dan tayi yanayi kaɗan da wata da ya sani a baya tace, "na gode ka riƙe kayan ka, bana so na amince a kama ni ɗin indai sai ka riƙe ni ne. Kuma Allah sai ya saka min abinda kayi min, Allah bazai barka ba, indai haka ne taimakon Allah ya wadaran sa wallahi. kuma abinda ka yiwa ɗan wani sai an yiwa naka ɗan ko yanzu ko nan gaba” ta faɗa tayi tsaki ta fita a guje tana hawaye da dana sani, tashin hankali, rawar jikin duk sun tarar mata. Lokacin da taje fita an buɗe gate mota zata shigo sai ta sake kwasa da gudu ta fice tana kuka sosai. Babu nisa sosai daga gidan zuwa asibitin tana kuka sosai ta isa asibitin, a ƙasa lokacin har duhu yayi tana shiga ta zauna inda take zama ta dafe kai tana kuka sosai, jikin ta har lokacin rawa yake saboda gani take kamar zai biyo ta. Sai kalle-kalle take yi saboda tsoro da tashin hankali, hakan bai taɓa faruwa da ita ba sai yanzu, hakan ya saka ta firgita sosai bata ɗauka ita wannan halin bazayen mazan zai zo kan ta ba. Babban tashin hankalin ta bai wuce yanzu abinda ya kamata tayi ba akan kuɗin asibitin da kuma kuɗin allurar da akace ana so da gagawa, gaban ta ya tsananta faɗuwa kana kallon ta zaka hango tashin hankali ƙarara akan fuskar ta. _yanzu ya zakayi Manal? Da wanne kuɗin zaki biya kuɗin asibitin nan da a ƙalla ya kai dubu dari biyu? Ga kuɗin allurar da akace za'a yiwa Mama, ya zanyi ni Manal me zanyi na samu wannan kuɗin?._ Hawaye take yi sosai cikin zullumi da tsoro, ƙirjin ta sai bugawa yake yi sosai hankalin ta ya tashi saboda tsoro da tashin hankali. "Ashe daman amfani aka yi da rashin lafiyar Mama dan a keta min haddi? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! yanzu ba’a taimakon mace sai dai ayi amfani da ita?. Babban baƙin cikin ma babbba dashi, ya kusa jika dani amma ba kunya ba tsoron Allah. Duk laifina ne, nice na jawowa kaina” ta faɗa tana kuka sosai. "Manal!” Huzaifa ya faɗa yana zuwa inda take ganin tana kuka sosai sai ya tsorata yace, "jikin Maman ne ya tashi?" Ya fadɗa leƙa Maman yaga bacci take ya dawo yana kallon ta yace, "Meya faru kike wannan kukan? Me ya faru? Wani ne ya rasu a gida?.” Manal kukan take yi sosai muryar ta har sarƙewa take, so take tayi magaar amma ta kasa. Ganin hakan sai yace, “nutsu, nutsu ki faɗa min abinda yake faruwa..” Manal tace, "Bani da kuɗin da zan biya kuɗin asibitin nan, ni zan ɗauke Mama mu tafi gida kawai. Tsoro nake ji, tafiya zamu yi.” "Me kike cewa haka? Ina shi Yayan naki da kika ce ya kawo ki nan?." Ta girgiza kai tana hawaye wani yana bin wani tace, "Ba Yayana bane, wallahi ban sa shi ba, kawai yayi amfani da ciwon Mama da ruɗewar da nayi ne a can babban asibiti ya kawo mu nan. Nidai tafiya zamu yi, baza mu zauna ba.” Daidai a lokacin Bebi yazo wajan yana kallon su Huzaifa yace, "to yanzu yana ina? Ina allurar da likita ya baki yace a kawo kafin dare?." "Tana hannun sa" sai ta sake fashewa da kuka mai cin rai tana rufe fuska da hannun ta duka biyun. Ya kalli Bebi da yake tsaye ya sake kallon Manal yace, "yana ina shi? Ki yi bayani lokacin allurar yana yi.” Sai da ta tsagaita kukan yace, "ban sani ba, nidai na bashi sai yace sai mun je na yiwa wanda ya saka aka kawo ni nan godiya…..!” Sai muryar ta tsay tana kuka kafin tace, “Nidai a can na barsu na gudo nan bazan iya abinda suke so ba, wallahi tsoro nake ji sunce za'a kama ni tunda bani da kuɗin biyan asibitin nan, Nidai ka taimaka min Mama ta samu lafiya koda za'a kama ni ɗin, na yarda naje prison indai har Mama zata warke na tabbata zata dinga min addu'a. Amma bazan iya abinda suke so ba, wallahi bazan iya ba” ta faɗa tana kuka sosai. Huzaifa ya kalli Bebi da suka fahimci maganar ta, yadda take maganar ya nuna musu kenan dai sai ta bayar da kanta za’a taimaka mata shine abinda take cewa baza ta iya ba. Huzaifa ya sauke Ajiyar zuciya yace,” ki kwantar da hankalin ki babu wanda zai kama ki, kuma kuɗin asibiti dana magani duk kar ki damu za'a yi Mama komai in sha Allah. Kin amince bazan cuce ki ba?.” Ta ɗaga kai alamun eh yace, “to ki daina kuka, za’a yiwa Mama komai har sai ta samu lafiya in sha Allah” Ya kalli Bebi yace, "don Allah ka sake bani allurar sai naje a samo ayi mata, lokaci na tafiya kace kafin dare.” Taɓe baki Bebi yayi yace, “Done!” yana faɗa ya bar wajan shima yabi bayan sa. Office ya koma yana tattara kayan sa zai tafi gida Huzaifa yace, "ka duba rashin imani irin na mutanen mu, baza'a taimake ta ba kenan sai ta bada kanta?. Anyi amfani da rashin wayo da kuma ruɗewar da tayi ana neman lalata mata rayuwa. Na tsani irin wannan mutanen wallahi. Yarinyar nan yadda take son Maman ta abin a taimaka mata ce, amma mutanen mu an lalace ba’a taimako tsakani da Allah.” Bebi baice komai ba amma har zuciyar sa ta bashi tausayi ya sauke numfashi ya ɗauki wayar sa yana kallon huzaifa kana yace, "haka duniyar ta koma, itama kuma bata da hankali ne. Tun farko ma bai kamata a barta a wajan nan ba, ina Baban ta? Ina ƴan uwanta?, duk baza su zo ba sai a barta ita kaɗai yau kwana biyu?. Tun farko meyasa ma ta amince dashi har aka kawo ya nan? da ace komai ma ya faru da ita tace ta jawowa kanta." "Bebi yarinya ce fa, kuma tana cikin ruɗewa in ka duba. A yadda na san yarinyar nan akan Maman ta wallahi zata iya yin komai, in akace yau diabeties ɗin Maman ta yyai high yadda hankalin ta yake tashi ko Maman nata baya tashi, tsaf za’a cuce ta akan Maman ta.” Bebi ya taɓe baki yace, “waƙila ma ƙarya take, daman bata da abin biya tazo na, wannan duk cikin plan ne.” “Na faɗa maka na san ta, baza ta yi haka ba wallahi.” "Shikenan shugaban masu sanin mutane, Allah yayi tana daga cikin wanda za'a yiwa komai for free, ta huta. Ni gida zan wuce" yana faɗa ya wuce shi shima ya fita ya samu ta koma ciki wajan Mama amma har lokacin kuka take. Daƙyar ya lallaɓa ta ta daina kuka ta kuma amince baza'a kamata ba sannan ya tafi shima. Sai a sannan Manal ta ɗauki wayar ta wacce Surayya ta kawo mata ta kunna ta kira lambar Baba amma a kashe ake cewa ta ajjiye wayar kawai tayi tagumi tana kallon Mama har lokacin zuciyar ta rawa yake saboda tsoro. "Da yake baki da mutunci ki ko ki kira ni ki faɗa min Mama babu lafiya" Mubeena ta faɗa tana shigowa cikin ɗakin. Ganin ta sai Manal taji daɗi sosai ta tashi da sauri ta rungume ta sai kuwa ta janye ta tace, "ke bana son sabon salon iskanci, da yake kina so a dinga yi dani a baki a unguwa ana cewa ban damu da uwata ba sai kika ƙi faɗa min kina nan, Sai Surayya muka haɗu da ita takr cemin ai kuna wanna asibitin. A taƙaice ma ubanwa ya baki kuɗin asibitin nan?." Manal kallon ta kawai take yi ta kasa magans, ita kuma ta isa wajan Mama da take bacci ta sake kallon Manal tace, "ni zan koma bacci nake ji sosai gaskiya, waye ya kawo ku nan?." Manal kallon ta kawai take yi bata ce komai ba ta ɗauki apple guda ɗaya a wacce take ajjiye tace, "ashe daɗi ma kike ci, ni na wuce" ta faɗa tana hanyar fita Manal tace, "Yaya tun jiya Mama take tambayar ki, ki dakata ta farka ta ganki don Allah." "Manal na faɗa miki bacci nake ji, ina so na huta sosai zan dawo da safe." "Hutun yafi zama a wajan Maman ne?." "Ke bana son iyayi, baga ki nan ba ai dani dake duka ɗaya ne ko?." Wayar tace tayi ƙara sai bata sake magana ba kawai ta fita Manal ta bita da kallo. Tafiya take tana waya har ta ɗan yi tafiya mai nisa kafin taga motar wanda take nema ya sauke baƙin glass ɗin sa, ganin hakan sai ta shiga tace, "meyasa baka je bakin gate ɗin ba ka barni Ina takawa a ƙasa?." "Sorry Baby, akwai wanda bana son haɗuwa dasu ne shiyasa." Cikin shagwaɓa tace, "to ba sai ka turo a ɗauko ni ba, ni duk ƙafana ya gaji." Murmushi yayi yace, "sorry na tuba, in kina so zan iya miki tausa." Ya faɗa yana jan motar suka tafi. Tayi dariya bata ce komai ba yace, "Tunanin ki kawai nake yi sai naga kina waya, in ba ke ba babu wanda zai saka ni na fito daga gida yanzu, sai ke ɗin kawai." Tayi farrr da ido cikin jin daɗi kafin tayi magana yace, "amma wa kika zo dubawa a nan?." "Wata course mate ɗina ce." "Kin taɓa zuwa asibitin ne?." "Ban taɓa zuwa ba sai yau. Yana da kyau a ido gaskiya.” Yayi murmushi yace, "akwai kyau a ido amma ba wani aiki suka iya ba, kar ki sake zuwa ma saboda kar ki ɗauko ciwo." Tayi dariyar jin daɗi tace, "an gama Baby." Yayi murmushi sai ya kai hannun sa cinyar ta inda hannun ta yake ajjiye ya riƙe bai kalle ta ba yaga dai ta kalle shi reaction ɗin ta ya canja amma bata nuna ba yace, "ina sonki Baby, in muna tare Ina kasa riƙe kaina sai na rasa nutsuwa ta gabaɗaya Baby." Murmushi tayi har lokacin hannun sa yana kan nata ya riƙe yana matsawa a hankali yace, "Baki ce komai ba Baby." "Me zance?." "Komai ma kice." Tayi murmushi kawai bata sake magana ba har akazo ƙofar gidan su Bily. Ta kalle shi tace, "zan shiga gida kar Daddy yayi min faɗa.” Ƙare mata kallo yake irin kallon ƴan bariki yake mata har ta tsargu da irin kallon da yake mata ta gyara zama kaɗan ganin haka sai yace, “kike so?." Jin abinda yace sai tace, "waya nake so a canja min." "Iphone ko android?." "Iphone." Kai ya girgiza yace, "gobe zaki ga sabuwar waya Baby, in kina so muje yanzu ki zaɓi wacce kike so." Mubeena tace, "A'a, Allah ya kaimu gobe ɗin." "Amin Baby. Sai sauri kike ki gudu ki barni ko? Bayan ni kewar ki nake ji kamar na jawo ki jikina haka nake ji." Ganin babba dashi yana wani abu kamar yaro sai ya bata dariya tayi murmushi shima sai yayi y shafa fuskar ta yace, "kina da kyau Baby" ya faɗa yana matsowa kusa da fuskar ta. Ta saka hannun ta akan masa ta cire hannun sa a fuskar ta yace, "ya kike haka Baby? Wannan fa ba komai bane soyayya ce, kar ki zama wanda basu waye ba mana, ina kallon ki wayayyiya meyasa zaki bayar da kan ki baya?." "Ina sauri ne kawai." "Okay, hug me before you leave." Ta kalle shi zata yi magana ya riga ta yace, "please baby" kafin tayi magana ma ya rungume ta, sai taji wani iri domin duk rawar kanta wannan shine karo na farko da aka rungume ta, har gwara dai riƙe hannu amma ruguma bata taɓa yi ba. Kam ya riƙe ta sosai ga turaren da ta saka mai ƙarfi da sanyi yana sake tasiri wajan sake riƙe ta sai lumshe ido yake daƙyar ta iya janye jikin ta tace, "sai da safe." Muryar a sarƙr yace, "okay Baby." Tana faɗa ta fita ta shiga gidan jikin ta yayi sanyi shima ya ja motar ya tafi. Bebi yana tsaye daga baya yana kallon mace ta shiga motar Abban nasa amma bai ga wacece ba, yaga dai an shiga dan lokacin ya karya kwana yaje ya siyawa Mama wani zabo gashashe da take so shigar macen ya gani da kuma wucewar motar dan yasan lambar motar mahaifin sa. Zuciyar sa sai bugawa take yi ji yake kamar yabi bayan sa amma zuciyar sa na hana shi hakan dole yaja motar ya tafi yana hana zuciyar sa tunanin da yake kai kawo a zuciyar sa akan Abba. A haka ya shiga gida ya shiga wajan Mama ya same ta zaune ta ajjiye abinda ya kawo mata ya kalli Kausar da take zaune ya bata leda ɗaya yace, "kaiwa Mamy wannan.” ba musu ta karɓa ta fita ya zauna yayi shiru zuciyar sa dai harbawa take. Mama tace, "Zabon ne? Allah yayi albarka. Amma lafiya kake?." "Babu komai Mummy, na gaji ne." "Ga abinci nan in zaka ci." "Me aka dafa?." "Fried rice ce" Mimi ta bashi amsa tana zaune. Ya sauke numfashi yace, "bani kaɗan naci." Mimi ta tashi ta zubo masa ya karɓa yana ci amma hankalin sa baya tare dasu gabaɗaya. Mama tace, "Sumayya tazo, tana ta zancen ka sai jiran ka take baka dawo ba. Ban ɗauka ma a gida zaka kwana ba yau.” Yace, "zan je na gaishe ta in sha Allah." "Da ka kyauta, daman ina so kaje gidsan kodan ku tsayar da lokacin auren ku da Rumana." Ya kalli Mama ta san kallon na meye sai tace, "haka za'ayi da Bebi, kana sonta tana sonka meyasa kake son zillewa ne?." Ajjiye bowl ɗin abincin yayi ya tashi yace, "na ƙoshi, sai da safe" ya faɗa zai fita Mama tace, “don nayi maka maganar Rumana shine ka bar abincin? Da yake ga wacce ka tsana ko?.” Bebi yace, “A’a ba haka bane, na tuna ina da aiki anjima ne shiyasa zan je na kwanta” ya faɗa yana fita. Yana fita Mimi da Kausar ma suka shige ɗaki dan basa son zancen Rumana nan amma Mama qaunar abin take yi. Misalin ƙarfe ɗaya na dare Mam ta farka tana jan numfashi daƙyar idanun ta sun fito waje sai wani ɗaga ƙirjin ta sama take da alama ya dame ta da ciwo. Motsin da yake yi ne ya tashi Manal ta kalle ta da sauri ta isa wajan tana faɗin, "Mama! Mama!!" Sai ta fashe da kuka ta fita a guje isa zuwa reception ta sanar da nurse suka tawo a guje zuwa kan Mama amma ina abin yafi ƙarfin su dole sai Bebi yazo. Iya abinda zasu iya suka yiwa Maman kafin su fita su biyun suka kira Bebi a lokacin kwanciyar sa kenan. Ganin kiran daga asibiti ya saka shi ya ɗauka yana sakawa a kunne akace, "Sir it's ugently emergency." Ya furzar da iska baice komai ba ya yanke wayar ya tashi ya saka riga doguwa ya ɗauki makulin mota ya fita. Tun daga ƙofar ɗakin da ya nufa yake jin kukan Manal mai sauti, ya shiga da sauri Nurses maza biyu suna biye dashi a baya, ganin yadda lamarin Maman yake ya saka yace a canja mata ɗaki da sauri aka ja gadon aka fita dashi zuwa wani ɗaki daban Manal tana bayan su dole ta tsaya a bakin ɗaki tana kuka kamar ranta zai fita. Sun jima sosai a ciki kamar bazu fito ba, tana zaune a kasan tiles tana kuka mai ratsa zuciya ya fito tana jin an buɗe ƙofa ta zabura tana kallon sa ta zube guiwa biyu yace, "ka ceci ran mahaifiyata, ita kaɗai nake da ita bani da mahaifi bani da yaya namiji, itace kawai gatana a duniya, Allah ne gatana Mama itace gatana, ka taimaka min kar Mama ta mutuuuuu!. In Mama mutu nima mutuwa zan yi.” Sosai ta bashi matuƙat tausayi ya bita da kallo kafin yace, "ki nutsu babu abinda zai same ta in sha Allah, ki daina kuka zata samu Lafiya ki mata addu’a.” Biyu biyu take gani itama kanta ciwo yake yi sosai, yanayin ta ya canja lokaci ɗaya tayi baya kawai ta kwanta tana dafe kanta. Nurses biyu ya kira aka ɗauke ta aka shiga da ita ɗaki itama aka kwantar yana tsaye a kanta. tunawa yayi Huzaifa ya ce masa tana da diabetes ya kalli nurses din yace, "ku bani glucometer da sauri." Da sauri suka bashi ya riƙe hannun ta ya samu sabon syring ya fasa yatsan ta ya jini ya fito ya auna. Abin daya gani ya saka shi wata ido yace, "Subahanallahi, yayi ƙasa sosai!." Jin abinda yace suka gane mai yake nufi da gaggawa aka kawo ruwa kala biyu lokaci ɗaya, da kansa ya saka mata cannula ya fara zuba mata ruwan a jikin ta dan a samu sugar ɗin jikin ta ta dawo daidai dan yayi ƙasa sosai. Suna ɗura mata ruwan ma tayi bacci ya kalle ta ya kalle su yace, "take care of her, duk abinda ya faru a sanar dani.” Suka amsa da okay Dr ya fita dan shi yaji daɗi ma da take a kwance, dan bai san taya zai faɗa mata halin da Maman ta yake ciki ba. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025                   ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* *Page 011* Da safe kasancewar monday ce da wuri ya tashi ya shirya bai shiga wajan Mummy bama ya hau mota ya fita. Kai tsaye asibitin ya wuce sanin yana da appointment da wasu patients ɗin yana zuwa kuwa ya tarar da mutane da yawa suna jiran zuwan sa. Zaman sa babu jimawa ya fara duba mutane wasu ya basu magani wasu ya basu test, wsu a kawo masa kafin wani lokaci ya gama dasu sai ya shiga ɗakin da ya ajjiye Mama jiya. Kallon ta yayi yana sake kallon bugawar zuciyar a na'ura sai kuma ya ɗauki abin gwada bugun zuciya dan so yake yaji da kansa ya auna bugun zuciyar ta ba laifi ta dawo daidai amma ba wani sosai ba, allura ya sake mata sannan ya fita zuwa inda Manal din take. Tana zaune ta dafe kanta idanun ta biyu tana zubar da hawaye ya shiga da sallama ta ɗago ta kalle shi, yadda fuskar ta tayi ja abin ya bashi mamaki sosai tace, "ina kwana Dr, ya jikin Mama? Tun ɗazu nake so na ganta ance sai kazo dan Allah ka nuna min Mamana" tana faɗa tana hawaye. Matuƙar tausayi ta bashi ya tausasa murya yace, "Maman ki tana nan lafiya." "Ina so na ganta don Allah." Numfashi ya sauke a yanayin da maman ta take ciki bazai so ta ganta ba sai yace, "zaki ganta." Abinda yace kenan ya juya zai fita tace, "don Allah ka taimaka min naga Mama." Baice komai ba ya fita dan bai san abinda zaice mata ba. Da nurses ya haɗu yana musu tambaya akan Manal yace, "an mata Fbs?." "A'a ba'a yi ba." Da mamaki yace, "meyasa?." Wanda yake tambaya yayi shiru sai yayi tsaki ya koma inda Manal ya take yaga ta kwanta har lokacin kuka take. Ganin yanayin ta sai yace, "zo." Abinda yace kenan a taƙaice ta kalle shi fuskar sa tana nan kamar kullum babu annuri ita kuma hakan ne yake bata tsoro dan kana ganin sa take wanda bashi da mutunci. A tsorace ta tashi zaune ganin zai fita sai itama ta tashi tsaye kanta na ciwo sosai amma saboda kar ciwon ya hana ta ganin Mama sai ta biyo shi duk da jiri take ji sosai. Ɗakin da ya shiga ta shiga itama ta hango Mama a kwance an saka mata ruwa ga oxgen a hancin ta da wani abu a yatsan hannun ta. Da sauri ta ƙarasa wajan Mama tana kallon ta tana hawaye amma bata ce komai ba ta riƙe hannun Maman amma ta kasa magana yadda kanta yake ciwo bata tunanin zata iya magana a wannan lokacin. Kallon ta kawai yake yi tausayin ta yake ji a ransa, yadda take yi ya tabbatar masa da tana qaunar Mamn ta sosai sai yake ji ko shine Mummy take wannan yanayin bai san  ya zai yi ba. "Muje ko?." Jin abinda yace bata yi  musu ba ta saki hannu Mama ta fito yana binta a baya har ta koma ɗakin da take ta zauna, shima bai fita ba ya duba gefe ya sauke ɗaukar glucometer ya sake auna sugar ta har lokacin bai yi yadda ake so ba ya kalle ta har lokacin tsayan ta yana hannun sa yace, "kin ci abinci?." Kai ya girgiza alamun A'a yace, "ina ƴa  uwan ki?." Murya a shake tace, "basu zo ba." Kai ya girgiza ya saki hannun ta ya fita. Tana nan zaune ba jimawa sai ga nurse mace da abinci ta shigo dashi tace, "Sannu, ga abinci Dr yace a kawo miki." Ajjiyewa tayi abincin a pack anyi selling ɗin sa da cleamfim. Kai kawai Manal ta ɗaga amma baza ta iya ci ba nurse ɗin ta fita. Tana kwace ta sake gwada kiran Baba amma har lokacin wayar a kashe, take ta ajjiye wayar tana juya kanta har ta kawo bata gani ma sosai komai guda biyu yake ganin sa. Bebi koda ya koma office aiki kawai yake na ganin marasa lafiya dan yasan Huzaifa da Hamza suna babban asibiti sai azahar zasu je. Abubuwa sun masa yawa yana nan yana can duk da akwai taimakon nurses ga kuma sauran likitocin da suke aiki tare. Glucometer ya koma ɗakin Manal dan ya ɗauka ya gwadawa wata mara lafiya nata jinin ya ganta kamar a sume take. Da hanzari ƙarasa inda take yaga idom ta kulle. Hannun sa ya kai wuyan ta yaji zafi sosai yace, "Subahanallahi." Abincin ya kalla yaga da alama ba'a ci bama, da gaggawa ya fara taimaka mata saboda yanayin jikin yayi weak sosai kuma ya tabbatar sugar tane yayi ƙasa da yawa. Ganin ya saita komai sai ya fita ya kira nurse ɗin da ya tura ta bata abinci ta shiga office ɗin da sallama kafin tayi magana yace, "aikin nurse ne kula da mara lafiya ko ba aikin sa bane?." Jin hakan sai tayi shiru tasan tayi wani abun yace, "na baki abinci ki kaiwa patient sai ki ajjiye baza ki tabbatar taci ba? Wanne irin aiki ku ke yi wannan? Kin manta duk wata kulawa ta mara lafiya a kan ku take?, meyasa baku san aikin ku bane wani lokacin?." "I'm sorry Sir!." "Sorry for what? Sorry for your mistake?." Shiru tayi bata amsa ba daman in aka taɓo shi yan faɗa baya tsayawa. Shigowa office ɗin akayi Huzaifa ya kalli nurse ɗim da take tsaye ya kalli Bebi kafin yayi magana a Bebi yace, "In baku canja ba gabaɗayan ku zan ajjiye ma ɗauki wasu, wannan ai shirme ne da rashin hankali. Ku shiga medication baza ku yiwa patient fbs ba kawai sai bashi magan kun san diabities patient ne?." Shiru bata ce komai ba yayi tsaki yace, "out!." Ta juya ya fita jiki a sanyaye. Huzaifa yace, "laifin ta sake yi?." Tsaki yayi kawai baice komai ba kafin ya kalle shi yace, "har ka gama da can?." Zama Huzaifa yayi yace, "A'a, nazo nan ne naga jikin Manal then na koma. Hankalina yana nan gabaɗaya." Wani irin kallo Bebi yayi masa har sai da Huzaifa yace, "wannan kallon da kake min na meye?." Bebi ya ɗage gira yace, "saboda ita ka baro wanda suke jiran ka kazo nan?." "Yes, but I will go back now." "What kind of relationship do you have with her?. Wacece ita ɗin ka?." Huzaifa yayi murmushi yac, "nothing is going on between us, i simply adore her." Bebi ya jingina a jikin kujerar yana kallon sa yace, "ƙarya ka ke, akwai wani abun a ranka akan ta." Huzaifa yayi murmushi yace, "babu komai a tsakanin mu ina mata kallo kamar ƙanwata ne, mun saba da ita sosai tunda ni suke gani duk sanda suka je asibiti. Tana kula da Mama ta sosai shiyasa nake mata kallon kamar ƙanwata. Baka ji itama Yaya take cemin?." Bebi yace, "hmmm! kai dai ka sani." Huzaifa yace, "na shiga ɗakin sai naga itace kawai a kwance, any problems?." Bebi yace, "jiya an samu problem akanMaman ta, a yanzu ma Maman ta tana kwance babu lafiya sosai. Itama ƙanwar taka blood sugar ɗin ta is very hypo, shine dalilin faɗan da kaji ina yiwa wannan yarinyar." Huzaifa yace, "mostly daman ita blood sugar ɗin ta bai cika zama so hyper ba gaskiya, yana tafiya daidai tana ƙoƙari wajan kiyayewa that's why ban ɗorata akan magani ba, iya diet ɗin is okay dan bai fi sau biyu naga sugar ta yayi high ba, shima tace min cake  taci." "Okay" abinda Bebi ya faɗa kenan dan shi bai ga amfanin bashi wannan labarin ba. Huzaifa yace, "kuma har yanzu babu wanda yazo daga gidan su?." "Ni zaka tambaya ko kai zan tambaya? Ƙanwar ka ko ƙanwata?." "Kai ma ƙanwar kace tunda kana da kamar ta." Bebi ya yi shiru baice komai ba, Huzaifa ya girgiza kai shima  baice komai ba kafin Bebi ya tashi ya fita shima ya biyo bayan sa. Hanyar ɗakin sukayi a tare suka hango Surayya a tsaye a wajan ganin Huzaifa sai ta ƙaraso wajan su tace, "ina kwana?." Huzaifa ya amsa dan suna yawan zuwa asibiti da ita da Manal  tace, "Dan Allah milky beauty ma bata da lafiya? Naga banga Mama ba kuma naga itama an saka mata ruwa." Huzaifa yace, "wacece Milky Beauty?." "Manal nake nufi." Huzaifa yace, "eh, kin san tna da ciwon sugar ko?." "Eh na sani." "Shine yayi ƙasa, in ta farka ki tabbatar kin bata abinci taci." Surayya tace, "to, Maman fa ya jikin ta?." Huzaifa ya kalli Inda Bebi yake yaga baya wajan ya kalle ta yace, "da sauƙi, kar ki damu zata dawo daidai." Kai kawai Surayya ta ɗaga ta shiga inda Manal take, gani tayi  ta bud'e ido sai ta koma ta fita dan ta faɗawa Huzaifa amma baya wajan sai Bebi. "Likita ta farka." Jin haka sai ya juyo ganin fuskar sa sai taji wani iri domin baiyi kama da mai mutunci ba gabaɗaya. Baice komai ba ya wuce zuwa ɗakin ya kalli Manal da take kwance idanun ta a buɗe ya kalli ita Surayya ɗin yace, "abinci zaki bata taci." Zatayi magana yace, "kar ki damu ki bata ko wanne ma." "Amma Milky bata cin abinci in bata sha tea ba, in taci bata sha ba amai take yi. Gashi ban zo da ruwan zafi ba." Ya kalle ta jin tana kiran ta da wani suna wai milky, shi baya son iyayi a rayuwar sa yafi son mace sak komai za'a yi ayi shi kai tsaye, yayi tsaki ya nuna mata inda kettle take baice komai ba kawai ya fita. Da kallo ta bishi kafin ta ɗauke ido Huzaifa ya shigo yace, "ta farka?." "Eh ta farka, na faɗawa wannan likitan wanda na ganku ɗazu." Baice komai ba yaje inda Manal ɗin take ya kalli Surayya tace, "abinci zaki bata taci, in da dama a bata ko wanne ma." "Na faɗawa wancan likitan bata cin abinci sai ta sha tea wallahi, amma sai yayi tsaki yana nuna min can wajan kuma ban gane ne yake nufi ba. Ka fishi mutunci walalhi." Huzaifa yayi murmushi yace, "kar ki damu yana nufin ga abin dafa ruwan zafi nan, ina da tea leave da sugar a office zan aiko a kawo miki sai ki haɗa mata tasha, amma sugar din kaɗan zaki saka mata ba mai yawa ba. Amfanin sa dan ya farfaɗo da blood sugar ɗin ta da ya sauka sosai." Surayya ta amsa ya fita yana darıya, wato  in baka san Bebi ba nan take zaka tabbatar da bashi da kirki da fuskar sa batayi kama da ta masu kirki ba ko kusa. Amma da ka san waye shi kun saba a nan zaka tabbatar da kirki ma a wajan sa ya samu mafaka, musamman ma ace ke mace ce, Allah ya saka masa tausayin mace da kishin ta. Mubeena a safiyar suna cikin makarantar Yusuf mai tama sule ta ƙofar nasarawa, fitowar su daga class kenan Bily ta kalle ta tayi dariya tace, "ke dai Mubeena wani lokacin kin yi asara wallahi, an kore ki daga school amma baki daina zuwa kina zaman lectures na banza da wofi ba." Mubeena tayi dariya tace, "zaman gidan mu ne bana so ke kin sani, kuma ni ko Manal bata san an kore ni ba." Bily tace, "wataran zata sani ai." Waya ta ɗauka tana dannawa Bily tace, "dawa kike magana ne kina tafiya?." "Baby ne, zai aiko a ɗauke ni kin san yau zai canja min waya." Bily da mamaki tace, "ke  wai baza ki hankali dashi ba? Ke kika faɗa min kallon da yake miki da yadda ya riƙe ki bakya jin tsoro ne wai ke?. Kuma in ya canja miki waya ki cewa Mama waye ya baki?. Ni wallahi duk ya sire min." "Meye na tsoron? Falaqi da nasi kawai zan karanta ta zama makami akan ko wanne shege, dan ya riƙe ni wannan kin san normal ne ai ba wani abun bane, kawai na tsorata ne kasancewar hakan shine na farko amma bayan nan ai bai min komai ba ko?." Bilkisu tace, "ki dai yi a hankali wallahi, domin somi somin hauka zubar da yawu." Mubeena tace, "kar ki yi min baki, aurena zaiyi in sha Alalh." Bily tace, "Allah yasa, zan fi kowa murna indai da gaske auren naki zaiyi. Yauwa yanzu mu je mu duba Mama daga nan sai mu wuce gida" ta faɗa a lokacin da suke zuwa wajan motar Bily. Mubeena tace, "ai ni ba bin ki zan yi ba, na faɗa miki zai aiko a ɗauke ni, ke kije kawai ai na baki address ɗin wajan." Bily da mamaki tace, "kee Mubeena kiji tsoron Allah, yanzu baza ki koma wajan Mama ba?." Mubeena tace, "to naje nayi me dan Allah? Naje jiya ban samu ta ganni ba to me zan koma nayi?, in naje bama ba lafiya zan bata ba kuma Manal zata yi mata komai." Girgiza kai Bily tayi tace, "lallai rashin jin ki ya wuce inda nake tunani, ni na wuce" ta faɗa tana shiga mota taja motar ta barta a wajan. ba jimawa aka zo da ƙatuwar mota aka ɗauke ta suka bar cikin makarantar. Suna cikin tafiya drivern ya kalle ta ta madubi yace, "ranki ya daɗe akwai saƙon da Alhaji ya bayar yace na baki" ya faɗa yana nuna mata wata leda a kusa da ita. Ledar ta ɗauka ta buɗe, kwalin iPhone ne a ciki da hanzari ta buɗe taga wayar sabuwa dal a ciki, ta duba takardar jiki taga an rubuta iPhone 16 pro max. Farin ciki taji yana mamaye mata zuciya ta cigaba da juya wayar bayan ta kunna tana ji kamar tayi ihu saboda murna. Wayar tace tayi ƙara ganin Babyn tane sai ta ɗauka cikin yanga da shagwaba tace, "Baby!." Daga can ɓangaren yace, "Babyna, an baki saƙon ki?." "An bani Baby, na gode sosai." "Kar ki damu Baby, kin cancanci fiye da hakan a wajan. Anjima kaɗan jirgina zai tashi zuwa lagos ina so na ganki." Mubeena tace, "to ai kaine baka zo ɗaukana ba." "Ina da baƙi ne Baby, amma yanzu in kina so ya kawo ki nan inda nake daga nan sai ku wuce gida, minti biyu kawai ganin ki zanyi ki koma." Mubeena tace, "Kar Mummy tayi min faɗa fa Baby." "Baza tayi miki faɗa ba, baza ki jima ba ai." "To gamu nan." "Thanks you Baby, sai kun zo" ya faɗa tana yanke wayar ta faɗawa driver suka wuce gidan alhaji Mu'azzam. Har gidan aka shiga da ita a motar ya fito aka nuna mata inda zata bi ta shiga cikin gidan ta same shi a zaune akan kujera yana danna waya ganin t sai ya miƙe cikin nuna farin ciki yace, "Welcome my Baby." Murmushi yayi ganin harda buɗe mata hannu alamun runguma sai ta basar ta nuna kamar ba gani ba yayi murmushi yace, "Zauna Baby, ya school?." "Alhamdulillah." Kallon ido cikin ido yake mata yace, "a kawo miki ruwa?." Kai ta girgiza alamun A'a kafin tace, "Ashe ma baka shirya tafiyar ba kasa nazo" ta faɗa da shagwaɓa wacce ta shige shi lokaci ɗaya ya kwance ya kasa gane kansa. Daƙyar ya danne abinda yake ji yace, "Yanzu zan fita ke kawai na tsaya na gani." Bata ce komai ba y sake cewa, "Dama zaki raka ni da nayi farin ciki." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta miƙe tace, "zan koma gida Baby, sai ka dawo a kawo min tsarabar lagos." Ya miƙe tsaye yace, "kar ki damu, in ma lagos ɗin kike so a ɗauko miki zan kawo miki" ya faɗa yana matsowa kusa da ita kafin yace, "in na tafi zanyi kwana biyu ban ganki ba, baby please ki bani hug guda ɗaya wanda zan tuna dashi in bana nan." Jin abinda yace sai ta kalle shi kamar wani yaro har marairaicewa yake sai tayi murmushi dan wallahi dariya yake bata tace, "A'a ni dai." "Yanzu bazan samu ba kenan? Ni ki bani dama to." Ƙafa take bugawa cikin son sake burge shi tace, "A'a nidai." Hakan da tayi bai san lokacin da ya jawo ta jikin sa ya rungume ba yana furta, "ina sonki Baby." Sacanni bai wuce goma ba ta janye jikin ta tana turo masa baki gaba wanda yake jin wani abun na fizagar sa akan bakin tace, "to zan tafi." Cikin taushin murya yace, "bana so ki tafi, ki tsaya a nan kin ji baby" ya faɗa yana riƙe hannun ta. Bata ƙwace hannun ba tace, "A'a ni dai tafiya zanyi." Ya sauke numfashi yace, "shikenan Baby tunda bakya son kasancewa dani." Bata ce komai ba bai saki hannun ta ba ya ɗauki wayar sa yana dannawa da hannu ɗaya kafin ya kalle ta yace, "na tura miki kuɗin shan ice cream." Murmushi tayi tace, "thanks you Baby." "I love you Baby." "I love you so much" ta faɗa da wata murya mai ɗaukar hankali. Ɗakyar yake iya riƙe kansa, amma ji yake kamar ya fizgo ta ya kama bakin ta ya tsotse shi ya haɗe kirjin sa da mata  yana jin buguwar zuciyar shine abinda yake buƙata a wannan lokacin, amma baya son yi mata shigar sauri dan sabuwa ce shiyasa yake bin ta a hankali, ya san lagon mata irin ta sababbi. Har ƙofar falon ya tako ta kafin ya koma ciki ta shiga mota su ɗauki hanyar gidan su Bily. Shima gidan ya shirya ya bari ya tafi gidan sa ya ajjiye motar sa ya shiga ɓangaren sa kai tsaye. Mama daman jiran zuwan sa take tunda ta san yana garin, tana ganin ya dawo ta nufi ɓangaren nasa ta same shi a tsaye a falon yana amsa waya yana murmushi a lokacin da yake cewa, "zanyi kewar ki sosai Baby, kamar na fasa tafiyar nan." Taji abinda yake cewa sai bata nuna ta ji ba ta shiga da sallama ya amsa yana yanke wayar bai kalle ta ba tace, "sannu d zuwa." Sai da ya kalle ta sannan ya cigaba da abinda yake yi yace, "Yauwa." Mama tace, "ina so zanje na gaida Hajiya an jima." Fuskar sa a ɗaure matuƙa yace, "sai kin dawo." Ta juya zata tafi yace, "zanyi tafiya zuwa lagos yau, ki faɗawa  ƴar uwar ki." Mama ta kalle shi tace, "ai mu ko yaushe a baka nan muke ɗaukar ka a gidan nan, ko baka faɗa mana ba, hakan ba sabon abu bane a wajan mu Alhaji." Kallon ta yayi kamar zai magana sai ya fasa tayi dariyar takaici tace, "Su baby sune suke ganin ka ko yaushe, amma matan gidan ka sune basa ganin ka sai lokacin da ka so, sai lokacin da su Baby suka sallame ka ka ke zuwar mana." Ya kalle ta yace, "me kike nufi?." Kai tsaye tace, "ƴan matan ka nake nufi, sune suke ganin ka ko yaushe available amma matan ka na gida ko yaushe baka nan a wajan su, Allah ya kiyaye hanya. Sannan ina yawan faɗa maka ka dinga sara kana duban bakin gatari, kar ka bar baya da ƙura" tana faɗa ta fice ya bita da kallo sai ya share dan kar maganar tayi tasiri a zuciyar sa. Abinda yazo ɗauka kawai ya ɗauka ya fito y sake gida mota driver ya ja suka fita. Zuwa yamma Manal taji faɗin jikin ta sosai, wanka take so tayi ya canja kaya gashi Surayya ta tafi. Tashi tayi ta fita zuwa ɗakin da Mama take tana kallo duk da bata ganin ta a wajan ta kallon ɗakin ma kawai hankalin ta kwanciya yake yi. Tana zaune tayi tagumi tana hawaye Bebi ya fito daga ɗakin ya kalle ta dan bata ji fitowar sa ba. Wucewa sa ta gani ta gaban ta ta kalle shi taga dai shine sai taji tsoron tambayar sa halin da Mama take ciki dan babu wannan fuskar a tare dashi. Miƙewa tayi kawai tabi bayan sa duk da bata jin dadi amma haka ta tashi ta bishi zuwa office ɗin da ya shiga, ƙwanƙwasawa tayi ya amsa daga ciki ta shiga da sallama ta same shi a tsaye shan ruwa, ya kalle ta ta kalle shi ya sauke jarkar ruwan daga bakin sa ya amsa sallamar sannan tace, "Likita don Allah ya jikin Mamana?." Kallon ya yayi yaga kamar jiri take a tsayen sai yace, "zauna" ya faɗa yana nuna mata wajan zama ta zauna ya ajjiye ruwan ya ƙarasa inda take ya zauna akan kujerar da yake zama ko yaushe yace, "jikin ta da sauƙi zata samu lafiya." Ta goge idanun ta tace, "yaushe zata tashi?." "Nan kusa!" Ya bata amsa a taƙaice. Kafin tayi magana yace, "meye sunan ki?." Murya na rawa tace, "Manal." Ya maimaita sunan a zuciyar sa kafin yace, "Ina Baban ku?." "Baya nan yayi tafiya ina ta kiran wayar sa a kashe take." "Baki da Yaya namiji?." Ta girgiza kai tace, "bani dashi, sai dai ɗan Baban mu kuma baya ƙasar nan yna Qatar." Yayi shiru kafin yace, "yaushe Mama ku ta samu ciwon rashin gani?." Manal tace, "ba'a fi shekara uku ba, kuma da tana gani da rana da daddare ne ganin yake raguwa sosai." Ya girgiza kai kafin yace, "zuciyar fa?." "Ta riga samun zuciya akan idanun, ciwon baiyi yawa bane sai yanzu." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "zata samu lafiya in sha Allah. Kar ki damu, kwantar da hankalin ki." "Allah yasa" ta faɗa a raunane hawaye na zubo mata. Sosai yaji ta burge shi da alama tana son Mama ta sosai, shi kuma duk wanda yasan darajar iyayen sa yana samun matsayi babba a wajan sa yace, "zaki din shan wannan magani kema shine  zai dinga daidaita sugar jikin ki, but na iya lokaci kawai ba ko yaushe ba" ya faɗa yana tura mata maganin gaban ta yace, "ki buɗe yanzu ki sha kafin ki tashi." Da to ta amsa ta buɗe  maganin ta riƙe a hannu tana kallon inda taga yasha ruwa, tana niyar tashi ya dakatar da ita ya ɗauko mata ya ajjiye tayi murmushi tace, "Na gode." Maganin ta sha ya kalle ta yace, "zaki iya tafiya." Manal tace, "don Allah zan iya zuwa gida na dawo? Har na dawo Mama bata farka ba?." Ya ɗaga  mata kai ta tashi ta fita ya sauke numfashi yayi shiru cikin tunani. ganin macen da yayi a motar mahaifin sa yana sake dawo masa cikin zuciyar sa da idanun sa. Manal daga nan ɗakin da take kwance ya koma ta saka takalmi ta fito zuwa bakin titi. Titin kamar anyi shara babu abin hawa ko kaɗan  shiru, kasancewar asibitin a cikin gra ne ba'a samun mota sosai a hanyar sai kayi sa'a. Tana nan tsaye sai taji tsayuwar baza ta yu ba sai ya zauna akan wani ƙaramin dutse da yake gefen wajan. Wanda ya kai ta wajan Alhaji Mu'azzam ta gani gaban ta yayi mugun faɗuwa ta tashi tsaye tana kallon sa, ganin kamar ita yake nufowa tana ja da baya bata san ta shiga kan titi ba ga mota ta tawo sai jin ta tayi a ƙasa tayi ƙara. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* Page 012 Da sauri ya fito daga motar yana kallon ta da take zaune a ƙasa a da alama ya taɓa ta da motar, kallon ta yake maimaita sunan ta yaga sai waige-waige take yi a ransa yana mamakin har lokacin bata tafi ba kenan, "kina lafiya?." Ya faɗa yana kallon ta.  Da sauri ta kalle shi tace, "shi na gani yana kallona, tsoro nake ji dom Allah ka taimake ni." Kallon inda take kallo yayi yaga babu kowa yace, "waye?."  Ganin a ruɗe take sai yace, "tashi." Yunƙurin tashi take amma ta kasa dan ta ɗan bugu a ƙafar ta ya riƙe hannun ta ta tashi tsaye tana ɗingishi ta shiga motar shima ya shiga motar har lokacin a tsorace take.  “Nidai na shiga uku da wannan mutum, wallahi shi na gani yana zuwa inda nake" ta faɗa tana kuka. Kallon ta yayi yace, "waye?." "Wani ne wanda ya taimaka min ya kawo ni nan shine daga baya ya kaini wani gida na gudu, yanzu ma shi na sake gani yana zuwa inda nake." Tunawa yayi da abinda ya faru a wancan lokacin yayi tsaki dan shi tun a lokacin laifin ta ya gani sam-sam bai san meyasa matan yanzu basa kishin kan su ba. Ƙafar yaga ya riƙe tana cize baki yace, "Kina Jin ciwo?." Kai ta girgiza kafin tace, "kaɗan ne." "Kin tabbatar?." Ta daga kai alamun eh. "Ina zaki je?." "Gidan mu zanje." Unguwar ta faɗa masa ya kaita har bakin layin tace ya isa ya tsaya ta kalle shi taga titi yake kallo tace, "na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi." Da Amin ya amsa ya kalle ta yace, "a gidan zaki kwana?." Ta girgiza kai tace, "A'a yanzu zan koma, bazan iya kwana Mama na asibiti ba." "Okay" ya faɗa a taƙaice ta fita daga motar shi kuma ya juya motar ya tafi. Ƙafar na mata ciwo amma haka ta taka zuwa gıda ta shiga gidan su Surayya ta karɓi makulli suka fito da Surayya suka shiga gidan. Yana nan yadda ta barshi wanka ta shiga tayi ta fito Surayya na zaune taga tana tafiya daƙyar tace, "Meya same ki?." Manal ta zauna tace, "ƙafata ciwo talemin, bige ni akayi da mota." "Yaushe?” Ta faɗa da tashin hamkali. "Yanzun nan, wannan likitan mai haɗe fuskar nan ne ya buge ni tsoron sa nake ji shiyasa ma bance masa ina jin ciwo ba kuma shine ya kawo ni." Surayya tayi dariya ta ce, "ke nima tsoro yake bani, da kina kwance nan fa da nayi abu sai yayi tsaki, ai wannan sam bai kamata ya zama likita ba.” Manal tayi dariya tace, "Dr Huzaifa ya fishi kirki, bara na shirya na koma. Baba bai dawo ba ko Surayya?." "Bai dawo ba gashi naji ana zancen ba'a samun sa waya." Manal tace, "Allah yasa lafiya" ta faɗa tana shiga ɗaki ta jiyo Surayya na cewa, "ɗazu Mubeena tazo gidan nan ai." Manal bata ce komai b dan lamarin Mubeena yanzu tsoro yake bata ba iya mamaki ba. Shiryawa tayi cikin doguwar riga kusan ko yaushe kayan ta kenan, doguwar riga musamman abaya ta ɗauki wasu a leda harda sabulun wanka ta ɗauka da humrar da turare duk ta saka a leda ta fito tace, "Surayya zan koma." Suka fito tare da Surayya tana cewa, "Milky dare yayi baza ki bari sai gobe ba?." Manal tace, "bazan iya ba wallahi, gwara na koma hankalina zai fi kwanciya, in ina na bazan iya bacci Mama na can ba, to in ta farka ma fa?" ta faɗa tana kulle gidan ta bawa Surayya makullin kafin tace, "tafi dashi ina shiga Mama han ni tafiya zata yi, bara na shiga na gaida su Umma." Surayya tace, "to nima bara na kawo miki abinci kafin ki fito." Ta amsa da to ta shiga gidan Baba da sallama jin muryar ta aka amsa a daqile tace, "Umma ina wunin ku?." Wacce ta kira da Umma tace, "da ban wuni ba ai baza ki ganni ba, ana can ana yawon banza an fake da uwa babu lafiya, a haka dai za'a ƙare uwa yawon banza ya haka ƙanwa ma haka. To haka ne mana tunda a hanya aka tsinto uwar, waye ya sani ma ko duk a yawon banzan aka samar daku?.” Ajiyar zuciya Manal tayi bata ce komai ba saboda darajar Baba, amma badan Baba ba wallahi sai tayi mata tas nan gaba ta kiyaye bakin ta, to ko babu komai Baba uba ne a wajan ta. T fito ta shiga gidan su Surayya dan bata fito ba Maman su take cewa ta zauna taci abincin sai ta tafi haka kuwa akayi taci ta ƙoshi, a nan take faɗawa Mama wanda ya kawo ta Mama tace, “An gode masa, Amma Manal kar fa ganin Mama na kwance ya saka ki dinga yin abinda ba halin ki ba, wancan lokacin na san ruɗewa ce ta saka ki shiga motar wanda ya kai ku asibitin wannan lokacin fa?.” Manal tayi shiru Mama tace, “ba halin ki bane kar ki fara yanzu, duniyar babu yarda a ciki masu zuciyar taimako kaɗan ne Manal.” Manal tace, “zan kiyaye in sha Allah Mama.” “Allah ya tsare, sharrin mutum da aljan yasa ku fi ƙarfin su.” Suka amsa da amin sannan ta fita zuwa kan titi ita da Surayya zuwa lokaci har anyi sallar i'sha. Bebi kuwa koda yayi gaba ja yayi ya tsaya haka nan yaji bazai iya tafiya ya bar Manal ɗin ba bayan tace masa asibiti zata koma ba, in Kausar ce ko Mimi ko Lubna bazai tafi ba, kuma shi duk wata mace a duniya indai ta riƙe mutuncin ta yana matuƙar kishin ta, baya so yaga ta wulaƙanta haka nan Allah ya halicce shi shiyasa in ba Allah ne ya kiyaye ba mace zatayi saurin cutar sa saboda raunin da yae dashi a kanta. Tunawa yayi da abinda ya faru da wanda tace ta gani a bayyane yace, “in wani abun ya same ta kamar ina da alhakin hakan.” Yana hango su madubi akan titin sai taɓa ƙafar ta take yi ya ƙaraso da motar ya tsaya ya sauke glass ya kalle ta itama ta kalle shi tana son yin magana amma babu wannan fuskar hakan a tare dashi, ganin tayi shiru bata ce komai yace, "shiga na mayar dake.” Ta kalli Surayya itama ta kalle ta, da ido Surayya tayi mata alama da ta shiga hakan ya saka tace, "Sury sai kin zo, na gode." "To Milky Allah ya ƙara lafiya" ta faɗa tana juyawa ita kuma ta shiga motar haka nan take jin gaban ta na faɗuwa. Bata taɓa shiga motar wani ba tunda take, ita adaidaita sahu ta saba hawa shiyasa take a takure ga faɗan da Mama tayi mata sai yawo yake mata. Gata ga namiji dai a mota bata taɓa yi ba sai yanzu, gabaɗaya a takure take sai addu’a take dan ɗazu a ruɗe take. Tana shiga khamshin turare ne ta ya kai masa ziyara, ya kulle ido ya buɗe a duniya baya son khamshi mai ƙarfi yanzu sai ya ɓata masa rai ko ya saka shi ciwon kai, hakan ya saka baice komai ba ya kunna a.c sosai a motar yaja suka tafi. Baice komai ba bata ce komai ba sai wayar sa da aka kira ya ɗauka yace, "Na’am Mummy." Shiru yayi alamun ana magana kafin yace, "Yanzu zan dawo, bazan wuce mintina goma ba in sha Allah.” Yanke wayar yayi ya cigaba da tafiya har bakin asibitin ya kai ta ya faka daga gefe ta kalle shi kamar ɗazu ba ita yake kallo ba tace, "na gode, Allah ya saka maka da alkhairi." Da amin ya amsa kawai ta fita ta shiga shi kuma ya wuce gida yana tsaki bai san meyasa mata suke son saka turare ba bayan sun san haramcin da yake cikin hakan. Inda Mimi ce ko wata cikin ƙannen sa ta isa ta shigar masa mota tana wannan khamshin? Itama kawai saboda taimako ne. Yana gab da gidan yaga an sauke Maryam a mota ya girgiza kai zuciyar sa na zafi a bayyane tace, "zanyi maganin abun" ya faɗa yana shiga da motar gida ya shiga wajan Mama. Mama na tsaye da hijjabin tace, "au ka dawo?, shirin tafiya nake ai daman gidan Hajiya zani na jira ka shiru shine zamu tafi da Mimi." "A daren na Mimi zata ja mota Mummy? Muje na kai ki." "Daga dawowar ka baka ci abinci ba, baka huta ba kace zaka kaini?.” "Bana jin yunwa naci abinci da yamma" ya faɗa yana fita Mama ta fito ita da Mimi ya buɗewa Mama baya ta shiga ya shiga shima Mimi ta shiga. Tsaki taji yayi gaban Mimi ya faɗi dan tasan da ita yake yace, "Mummy meyasa basa jin magana ne? Meya amfanin saka wannan banzan turaren da daddaren nan?. In ma turaren yana da daɗi da sauƙi, amma wannan turare kamar na aljanu?.” Mama tayi dariya tace, "ikon Allah, ni na jima banga mutumin da baya son turare ba sai kai, kamar mai aljanu? Baza’a yi na hayaƙi kana nan ba, baza’a saka a jiki ba. Ke Mimi koma ki canja rigar kizo mu tafi in ba haka ba kafin muje aljanun sa zasu iya tashi." Mimi ta fice tana ƙunƙuni haka kawai ya hana su saka turaren da suke so dan kawai shi baya son yaji khamshi na tashi sosai, shi wai daga dry spary sai body mint kawai zakayi amfani dashi, ko yaya ka saka mai ƙarfi in kazo inda yake yaji yayi ta bala'i kamar a jikin sa aka saka. Kuma Mummy ce take goya masa baya shiyasa ya samu damar ham turaren wuta a falo ko su saka turare. Mimi na mita ta canja kaya ta dawo ta shiga motar suka tafi dan tasan badan Mama ba bazai jira ta ba.        A can gidan Hajiya tana tayi masa wasa yana mayar mata da amsa dan baya ƙyale ta tayi dariya tace, ka dai ki ƙi aure sai na mutu ko?." Ya ɗan murmusa yace, "kar ki damu na kusa in sha Allah." Mama tayi caraf tace, "kin san da yake takwarar taki ce dai da ita za'a yi." Nan take fuskar da ta koma yadda take yayi shiru Hajiya tace, "da gaske? Kai amma nayi murna wallahi sosai, na jima ina burin hakan ya faru tsakanin yaran ku. ina son auren zumunci dan kar ace na takura ne yasaka nake yin shiru amma da hakan ya faru naji daɗi. Ni in tani ne yaran nan mata da maza babu wanda zai fita waje yayi aure, nafi so kowa ya zaɓa cikin ƴan uwan sa. Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Mama ce kawai ta amsa Hajiya ta kalle shi tace, "shugaban masu ɗaure fuska, ka dinga dariya don Allah Adnanu wannan rashin fara'ar taka yayi yawa wani lokacin.” Baice komai ba akayi sallama duk suka amsa suka kalli mai shigowa sai ga Rumana ta shigo da kwano a hannun ta Hajiya tace, "ga amarya, ga kuma angon a zaune." Ganin su Adnan sai zuciyar Rumana tayi fari karr ta ƙaraso ta zauna kusa dashi tace, "Hajiya Ina wuni." "Lafiya lau Rumana, ya Umman taki?." "Lafiya lau. Mummy ina wuni?." Mummy ta masa tana murmushi ta kalli Adnan da yayi kamar bai ganta batace, "Beb ina wuni." Kamar abinda yake jira tace kenan sai yayi sauri ya miƙe bayan ya amsa yace, "Mama in kin gama ina mota" ya saka hannu aljihu ya ɗauko kuɗi ya baya Hajiya yana cewa, "duk da nasan kuɗi ne dake, amma a saka mana albarka." Tayi dariya ta karɓa tana godiya tare da addu’a ya fita. Rumana ta miƙawa Hajiya kwanon tace, "Hajiya gashi inji Ammi." Hajiya ta karɓa ta buɗe tace, "dambun kaza muka samu, kai Allah yayi albarka. Ga so yayyen nama ma Hauwa’u ta kawo." Rumana ta kalli Mama tace, "Mama ke zan bi a can zan kwana, bara na faɗawa mai kuɗi ya wuce gida kawai" ta faɗa tana ɗaukar waya ta faɗawa wanda ya kawo ta . Hajiya tace, “banda abin babar ki ma ai bai kamata ta ɗauke ki ba, ga wacce ta riƙe ki tun kina shekara biyu har kika girma, amma da tgaa kin zama mutum sai ta ƙwace ki.” Suka yi dariya suka yi sallama da Hajiya suka tafi.      Rumana ce ta shiga gaban motar Adnan yana zaune yana danna wayar sa Mama da Mimi suka shiga baya yaja motar suka tafi. Tsaki Mama taji yayi sai tayi dariya tace, "Ke Rumana ban san me yake damun ki ba, har yanzu kin kasa gane Adnan baya son turare mai ƙarfi, amma ke duk sanda zaku haɗu sai hakan ta faru, wannan tsakin da yake na turaren ki ne." Rumana tace, "to ni Mama ban san ya yake so nayi masa ba, shi ace baya so a saka turare haka zaka zauna babu turare?" Ta faɗa tana kallon sa, bai kalle ta ba bai kuma ce komai ba tuƙa motar kawai yake yi. Har suka je gida baice komai ba yana faka motar duk suka fita shima ya fita ya shiga ciki kai tsaye banɗaku ya wuce ya jima ciki sannan ya fito bayan yayi wanka ya saka doguwar riga ya fito ya zauna a lokacin Rumana ta shigo da abinci a hannun ta ta ajjiye masa tace, "Gashi inji Mama." Baice komai ba ya ja abincin ya fara ci ta zauna kusa dashi ya tsayar da cin abincin yace, "in kina son zaman lafiya ki daina zuwa inda nake da irin wannan turaren, bana son oil perfume." Rumana ta jingina da kujera tace, "nasan wannan tun a baya Beb, amma ni mamaki kake bani har yanzu meyasa baka son turare?. Da na ɗauka zaka daina zuwa yanzu sai gashi yanzu abin yafi na baya ma, kuma kai ai ana jin ƙhamshin a jikin ka.” Bai bata amsa ba ya cigaba da cin abincin sa tace, "Ko dai yana saka ka cikin feeling ɗin mace ne?." Kallon ta yayi sai ta rufe baki tana kallon sa baice mata komai ba ya cigaba da cin abincin ta tashi zaune tace, "ni ina son turare kai ma ka sani, tun a wancan lokacin na faɗa maka amma in mun yi aure zan rage." Ta sake cewa, "Beb wa na gani ɗazu a motar ka? Na ganka kai da mace wacece ita?." Cikin salon tura mata haushi kai tsaye yace, "Wacce zan aura ce." Tayi dariyar rainin hankali tace, "ai kasan baka da matar da ta wuce ni a duniya." "A aya aka faɗa ko a hadisi?." "Babu ɗaya, amma dole ya tabbata." Ta sake yin dariya tace, "gwara ka faɗa mata tun wuri ta nemi mijin aure wannan mijin na Rumana ne kawai." Ya ajjiye abincin ya sha ruwa ya kalle ta sosai yace, "kina ji, ni banza auri ragowar wani namijin ba, komai nawa sabo nake amfani dashi ko meye kuwa. You have to know that, I'm not your type. Banyi kama  da wanda zai auri ragowar wani banza ba kin gane?. Ya kamata ki daina hauka a kaina Ruman, na riga na rufe shafin rayuwar ki bazan sake buɗe shi ba har abada. Mummy baza tayi min dole ba dan nasan duk wani hope din ki akan Mummy yake, nobody can force into married you, ki daina wannan rawar kanAdnan na sabuwar mace ne ba na wacce aka rage ba" ya faɗa yan kallon ta ido cikin ido, ya lura maganar ta kashe ta dan tunda auren ta ya mutu ta dawo tana wannan rawar kan bai taɓa faɗa mata magana kamar haka ba. Murya a sanyaye tace, "Adnan ni ka ke cewa ragowar wani?." Ya jingina da kujera yace, "to meye in ba ragowar wani ba? Ke ba ragowar bace?. Kuma wacce ke da bazan faɗa miki haka ba Ruman?." Ta girgiza kai tace, "ni Ruman wacce ka ke so." "Point of correction! Ruman wacce Adnan yaso a duniyar yarinta ba wacce Adnan yake so ba. Adnan mace ɗaya yake so yanzu tak a duniya itace wacce kika gan mu tare, ya kamata ki ƙyale mata mijin ta ki daina wahalar da kanki akan abinda baza ki samu ba.” “Adnan har yanzu kana sona." Yayi Murmushin da yake masa kyau a duk sanda ya bayyana a tare dashi yace, "this is your failure Ruman, kina tunanin har yanzu Adnan yana son ki wannan shine abinda yake cutar dake, Baki san Adnan ya manta da wata mace mai suna Ruman a duniyar soyayya ba. Yana mata kallon ƴar uwa ne kawai kuma wacce suka tashi tare bayan nan babu wani abu. Inda zaki kwantar da hankalin ki ke ƴar uwata ce, kina da wannan matsayin a wajena amma batun soyayya babu” ya faɗa yana wara idanun sa yana girgiza mata kai. Ta kasa magana sai kallon sa da take yi, ya lura da ya kulle mata baki shi kuma yana sane ya mata haka dan ta san bata isa ta barshi taje tayi aure ba bayan ta fito kuma tace sai ya aure ta ba, beside shi babu soyayyar ta a zuciyar sa Allah ya sani. Ana cewa ba’a mantawa da first love shi kam ya mata da ita. Ya sake kallon ta yace, "Kina ji, na farko turaren ki ya dame ni, na biyu bana son magana dake ki tashi ki bani waje." Kai take girgizawa cikin ɓacin rai tace, "wallahi sai ka aure ni Bebi, ko sama da ƙasa zata haɗe sai na zama matar ka." Ya taɓe baki ya tashi yace, "babu abinda zai saka sama da ƙasa ta haɗe a kan ki Ruman, aure ne bazan yi dake ba tunda ba’a dole you have to give me some space please, kina ta insisting akan abinda bazai faru ba." Tashi tayi tsaye tana kallon sa tace, "dole ya faru ko bak so. Ko dan wannan cika bakin naka sai na tabbatar da ka zama mallakina, wallahi sai ka aure ni, a ranar zan mayar maka da martanin ba ko yaushe ake samun abu sabo ba, ni da ka ke kira ragowar wani sai an kira ni da suna matar Bebi.” "Okay! we shall see" ya faɗa yana kallon ta ta fita ya bita da kallo sannan yayi tsaki. A bayyane yace, "na gode Allah da ya cire min son wannan yarinyar da ban san ya zanyi ba, ina ni ina auren ta? Ga rashin kunya sannan gata bazawara?. A baya ma tsautsayi ne da ƙuruciya ya kai ni” ya faɗa yana tashi ya shiga ɗaki. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 Book one Page 013 A fusace Rumana ta fita kalaman sa sun mata ciwo sosai ta nufi wajan Mama dan abinda ta faɗa masa so take ya tabbata taga ya zai yi. tana shiga ɗakin Mama ta wuce ta same ta a zaune da ƴan matam tace, "Mama meyasa yanzu Bebi baya sona? Meyasa yake wulaƙanta ni dan Allah ya ɗora min ƙaunar sa?. Na san nayi kuskure a baya da na auri wani bashi ba, wannan dalilin ne ya saka yake min haka? Kuma na gane nayi kuskure kuma na nemi yafiyar sa meyasa bazai sake bani dama ba?." Mama da take kallon ta tace, "me ya faru kike kuma haka? Zauna ki faɗa min ne Bebin yayi miki kuma?." Rumana ta zauna tace, "Mama ni yake kallo yana cewa ragowar wani ce bazai aure ni ba, Mama in wani zai ce min haka bai kamata shi yace ba, amma shine yau yake cemin bazawara wai yafi ƙarfina.  Kuma Mama ko babu komai ni ƙanwar sa ce tare dashi muka tashi a gidan nan, ko dan wannan alaƙa ɗin bai kamata yace min haka ba, auren nan da nayi ƙaddara ce ta kaini tunda ko shekara ban yi ba na dawo. Wallahi Mama ina son Bebi in na rasa shi zan iya mutuwa." "Ƙaryar banza" Kausar ta faɗa tana daga gefe Mama ta harare ta ta dawo da kallon ta ga Rumana tace, "Haba uwata, na faɗa miki baki da wani miji na gaba a duniya in ba Adnan ba, meyasa kike son zubar da hawayen kina banza a wofi?." Ta share hawaye tace, "Mama bai yana faɗa min magana kamar yau ba, har cewa yake nice na nace amma shi yanzu baya sona, ni kuma ina son sa Mama." Mama tace, "ya isa ki daina min kuka. Duk duniya in akwai wanda Adnan yake jin maganar sa to nice, meyasa kika kasa amincewa da nace miki shine mijin ki?. Ko kina kokwanto akan umarnina ne?." "Mama ba naƙi amincewa bane ba, Ina jin tsoron yadda ya dage kan maganar ne." "Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki sai Adnan ya aure ki in sha Allah." Ta goge idanun ta tana jan numfashi tace, "Kuma Mama har wata na gani a motar sa ɗazu, dana tambaye shi sai yace wai wacce zai aura akwai abinda zanyi ne." Mama da mamaki tace, "mace a motar Bebi?." "Eh wallahi Mama na gansu." Mama ta girgiza kai tace, "wannan ba komai bane kar ki damu, ya faɗa miki haka ne dan ya ɓata miki rai amma bashi da wata budurwa. Saboda son da yake miki tunda kuka rabu bai sake yin wata budurwar ba." Mimi da take kallon Rumana tace, "to wai Yaya Rumana tun da kin san kina son sa kika rabu dashi kika auri wani?. Tun tashin mu tare muka san ku, ko da baya nan yana karatu kowa ya san Yaya Bebi ke yake so, amma lokaci ɗaya kika juya baya kika ce ke sam baza ki aure shi ba kuma aka ƙyale ki, dan yanzu yace baya son ki sai a takura shi?." Mama ta harare ta tace, "ya ishe ki malama, tashi ku bani waje." Duk tashi sukayi suka fita dukkan su basa fatan ya aure ta dan lokacin da ya nuna son auren nata wulaƙanta shi tayi ta nuna bai kai wannan matsayin ba saboda ta samu wanda yake da mahaukacin kuɗin ya ɗauke ta suka koma Dubai da zama, sai gashi auren bai je ko ina ba ya mutu. Rarrashin ta Mama ta dinga yi har taga ta daina fushi ta daina kukan sannan tace taje ta kwanta ta fita ita kuma ya kira Bebi a waya. Yana zaune a lokacin ya rasa wanne irin tunani ma zaiyi komai ya tsaya masa ya tsani zancen auren Rumana da ake masa wallahi, baya qaunar hakan in badan Mama bace babu wanda zai dinga yi masa zancen nan ya zauna lafiya. Wayar yaga tana haske ganin sunan Mama sai ya ɗauka sai kuma ya sauke waye ya tashi daga inda yake ya fito zuwa wajan Mama. Falon mata babu kowa y shigo ɗakin ya same ta a zaune ya zauna shima yace, "Gani Mama." Ta kalle shi rai a ɓace tace, "Yanzu tsakani da Allah ka kyauta abinda akayi?." Da mamaki ya kalle ta yace, "Me nayi Mummy?." "Kai yanzu na ɗauka in wani zai cewa Rumana ragowar wani kaini zaka kare ta sai inda ƙarfin ka ya ƙare saboda shaƙuwar ku da kasancewar ta ƴar uwar ka, sai gashi kaine kake faɗa da kanka Bebi, hakan daidai ne?." Numfashi ya sauke haushin ta ya ninku a zuciyar aa yace, "Mummy ƙarata ta kawo kenan?." Mama ta fusata cikin faɗa tace, "ita ta kawo, ko kana ganin bata kawo kuka gidan magani ba?." Ya girgiza kai alamun jin abinda ta faɗa cikin faɗa yace, "A'a, ki yi haƙuri." tace, "meye laifin yarinyar nan ne wai? Laifin ta abinda tayi kuma ta gane kuskuren ta tace ka yafe mata,  kar ka manta daman Allah yayi ba kaini mijin ta na farko ba, babu wanda zai canja ƙaddarar meyasa ka ke wannan fushin bayan har yanzu kana sonta?." "Wallahi Mama bana sonta, Soyayyar da nake mata kamar ta sauran ƴan uwa ne amma waccan soyayyar ta jima da gushewa." Mama tayi mamakin abinda yace amma bata nuna masa ba tace, "ƙarya ne Adnan, ita ka fara so a rayuwar ka, soyayyar farko da wahalar mantawa take, domin tana da tasiri a zuciyar wanda yayi ta. tana nan a cikin zuciyar ka inda zaka bincika sosai zaka gani har yanzu kana son Bebi." Shiru yayi baice komai ba yasan Mama baza ta taɓa fahimta ba  gashi baya son mata musu tace, "ka adana kalaman ka akan ta domin matar kace wacce zaka aura, ku fara daidaita kan ku kafin maganar nan taje gaba." Nan ma baice komai ba amma mamaki abinda yake bashi, ita lokacin da ta guje shi babu wanda ya mata dole amma shi yanzu ana so ayi masa dole a kai dan babu yadda zaiyi. "Tace min taga wata a motar ka da gaske ka ɗauki wata yau?." Lumshe ido yayi ya buɗe gabaɗaya haushin ta ya sake cika masa zuciya tunda gashi har ta fara haɗa shi da mahaifiyar sa tun kafin auren yace, "eh Mummy haka." "Wacece ita?." "Wacce nake so!" Ya faɗa ba tare da ya shirya ba yana kallon Mummy ɗin dan so yake yaga yanyin ta,  itama tana kallon sa da mamakin abinda yace Mama tace, "har ka samu wacce kake so babu labari?." Adnan yace, "ina son sanar miki sai yanzu na samu dama." Mama ta kalle shi kallon baka isa ba tace, "amma kasan kayi  gangancin fara son wata bayan Rumana tana da rai ko?." Ya kalli Mama yace, "Mummy yanzu saboda Ruman sai a hana ni abinda nake so?." Mama ya ɗaga  kai tace, "ƙwarai kuwa, ai bama za'a hana ka ba, an ma hana ka ɗin Adnan. Sannan kayi gaggawar bawa zuciyar ka haƙuri akan wacece ka gayyato soyayyar ta Rumana ta maye gurbin ta  domin gida bai ƙoshi ba baza a kai wa dawa ba Adnan." Shiru kawai yayi baice komai ba dan bai san abinda zai ce ba  Mama tace, "kaje kayi abinda nace, sannan cikin satin nan ku shirya kan ku kai da ita wata mai zuwa ayi auren ku a huta. Ita kuma waccan ka faɗa mata an yi maka mata a gida." Kamar ana zuba masa ruwan zafi haka yake ji a zuciyar sa in ana zancen auren Rumana,  baya so ko kusa ko alama, har mamakin Mama yake wai yace an masa mata kamar wani mace. Mama ta kalle shi tace, "zaka iya tafiya ka kwanta, ka kashe min hasken ɗakin." Da to ya amsa ya tashi ya fita itama ta kwanta. A haka ya koma ɗaki yana mamakin wannan abu da ake son yi masa mai kama da auren dole, zama yayi yana tunani gaskiya baya son auren Rumana badan baya son yiwa Mama abinda take so bane sai dai in ya auro Rumana kamar ma maganar ta tayitasiri a kansa kenan, dolen da take cewa ta tabbata a kan sa kenan, ya bɗe ido yace, "Allah kada ka ƙaddara min auren ta, Allah ka kawo min abinda zanyi da gaggawa na gujewa auren ta" ya faɗa yana sake kulle idanun sa domin samo mafita ya zamar masa dole kafin ayi masa auren dole. iPhone ɗin Bily take kallo tana  kallon Mubeena tace, "iPhone 16 pro max, kuɗin ta ya kuwa five millions a yanzu, Sannan ga kuɗi  har naira dubu ɗari bakwai just for ice cream. Wow! Mubeena you have to me very careful akan wannan tsohon. Kamar ba da aure yake son ki ba akwai wani abun a zuciyar sa." Mubeena tace, "Bily ke kike cemin ya kamata na samu wayar da zan riƙe saboda a dinga ganina big girl, i've finallay fulfilled my dreams. Meyasa bakya murna?." Bily tace, "ban amince dashi bane Mubeena, dan nace ki samu waya ai bance kiyi komai ki samu waya ba, beside bance ki biyewa kowa ba." "İn ba ta haka ba da wanne kuɗin zan siyi waya? Nifa na faɗa miki babu wani zance na banza da ya taɓa min, In dai ba ina kewar ki ba dama kina kusa dani, shikenan fa." "Kissing naki da yayi fa, shima hugging ɗin ba komai bane?." Mubeena tabi Bily da kallo tace, "Bill wallahi mamaki kike bani, Meye a cikin kiss da hug dan Allah? It's normal abu da yake faruwa tun a secondary school. Maza nawa kika yi hugging da Muna school?." Bily tace, "wannan ya wuce ak Mubeena, lokacin ba wani hankali ne damu ba ai. Muna maganar yanzu ne ba wani abun ba." Mubeena tace, "abinda kayi da dan ka yi shi yanzu ai ba komai bane Bily." Bily tace, "okay naji, in Mama ya warke taga wayar nan a hannun ki me zaki ce mata?." "Da wanne idon zata gani?." "Shine ƙarfin guiwar ki? To Baba fa?. "Shine ya haifan? Ubana ƙasa ta jima da rufe idon sa babu wani mijin mahaifiyata da yana auren uwata da zai latsa ni." Bilkisu ta girgiza kai tana kallon ta tace, "kin yi nisa bakya jin kira" ta faɗa  tana shiga toilet ta barta a wajan ita kuma tan sake kallon sabuwar wayar ta.            Washe gari ma da wuri Bebi ya fita koda yaje asibiti theater sukayi bai samu yaje inda su Manal suke bama sai kusan sha ɗaya na safe sannan ya shiga inda Maman take ya samu zuciyar ta t dawo bugawa normal sai jiran tashin ta. Yana fitowa daga ɗakin suka haɗa ido da Manal ta saka black ɗin hijjab yayi mata wani mahaukacin kyau, ganin sa sai tayi murmushi ta ƙaraso tana jan ƙafa tace, "ina kwana, tun ɗazu nake jira kazo ka faɗa min ya jikin Mamana, Yaya Dr Huzaifa bai zo ba balle ya faɗa min a madadin ka." Kallon ta kawai yake yi, na farko tayi amsa kyau sosai bazai ƙaryata zuciyar sa ba, na biyu ya fuskanci yarinyar akwai surutun kafin ya amsa gaisuwa ta faɗi ma abinda yake ranta. Ɗauke kai yayi daga kallon ta yace, "tana lafiya kar ki damu." "Ko yaushe haka ka ke cemin, dan Allah ina son na ganta." Hanyar ya bata alamun ta shiga tayi hanzari zata wuce sai ta taya tace, "Wayyo." sai kuka ta cigaba da jan ƙaafar ta shiga ɗakin. Bata jima sosai ba ta fito tan darıya da kuka tace, "naji daɗin ganin Mama da aka cire mata oxygen, na gode da kulawar da kake bawa Mama. Duk da baka darıya amma kana da mutunci." Dariya yayi a zuciyar sa ya kalli ƙafar ta yace, "Jiya kika ce ƙafar ki bata ciwo." "Yau ta fara." "Ki biyo ni" ya faɗa yana yin gaba tabi bayan sa har office ɗin sa ya nuna mata kujeara babba a gefen office ɗin alamun ta zauna, ta zauna ya tsuguna yana kallon ƙafar daga wajan idn sahun ta ga wajan nan har ya kumbara sosai. Hannu ya saka ya shafa wajan a hankali tayi shiru dan taji ba da ƙarfi ya riƙe ba, sai da ya shammace ta ya tashi ya ɗauko wani cream ya saka safa ya dawo ya shafa a wajan ya fara matsa ƙafar da ƙarfi. Da hanzari ta riƙe hannun sa tana kuka tace, "don Allah ka bari ƙafata zata cire da zafi sosai, don girman Allah ka dakata na haƙura na cigaba da zama a haka." Ido cikin ido ya kalle ta sai ta janye hannun ta tayi shiru ya janye idon sa daga kanta ya cigaba da abinda yake yi sai kuka take. Bai jima ba ya tashi ya zare safar da ya saka ya kalle ta sai kuka take yi sosai yayi tsaki a bayyane yace, "kamar wacce aka karya." Sai da taci kukan ta sosai ta kalli inda yake yana zaune kamar bai ma san  da zaman ta ba tace, "ina ganin yana da kirki ashe ba haka bane ba" ta faɗa a bayyane ba tare da ta sani ba, ya jita amma bashi da lokacin kallon ta. Yatsun sa biyu ya murza suka bada sauti ta kalle shi ya nuna mata ƙofa. Daƙyar ta tashi amma taji daɗi babu laifi, ta fita tana waigen sa. tana fita ya ajjiye pen ɗin hannun sa yayi murmushi ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya san murmushin na meye ba. Bai jima ba ya tashi ya nufi office ɗin Huzaifa ya same shi a zaune shida Hamza suna magana shima ya zauna yace, "me ake cewa da baza'a kira ni ba?." Huzaifa yace, "yanzu nake niyar yi maka waya, zance ne akan meeting ɗin da za'ayi." "Oh!" Shine abinda yace kawai yayi shiru kafin yace, "ba wannan ba, ya zanyi da damuwar Ruman ne? Abin har ya kai Mummy tana cewa Hajiyar ta wai mun daidaita da Ruman yanzu aure zamu yi, jiya haka tazo har ɗakina tana cewa sai na aure ta ko bana so, bayan ta fita taje ta samu Mummy duk abinda na faɗa mata sai da ta faɗawa Mummy. Babban tashin hankalina da na cewa Mummy ina  da wacce nake so amma Mummy ta nuna na ajjiye soyayyar ta na dawo da ta Ruman." Huzaifa yace, "İkon Allah, Mummy ta riƙe wuta akan Rumana gaskiya. Amma kai meyasa baza ka amince ba ko dan Mummy ɗin?." "Wallahi Huzaifa bazan iya ba, ina so ayi kodan Ita amma zuciyata ta kasa amincewa da ita a karo na biyu, haushin kaina nake ji in na tuna cewa na sota a lokacin baya. In na amince da auren ta gaskiya zan cuci kaina ne kuma zan cuce ta." Hamza yace, "amma a baya ka sota, ya kamata ka jure saboda Mama ba bawai dan ita ba." Bebi yace, "baza ku gane abinda nake ji bane akan ta shiyasa." Huzaifa yace, "to kai wa kake so ɗin? Da gaske kuma ta ganku a motar?." Bebi yace, "wannan yarinyar ce da Manal take kowa oho, na ganta akan titi kun san I can't leave her alone, because I took every woman as my sister. In na barta a akan titi a tsaye nima wani bazai taimaki su Mimi ba in matsala ta same su, that's why na ɗauuke ta na kaita har gıda, har buge ta nayi da motar ma ban sani ba." Huzaifa yace, "ita Rumana ya akayi ta ga Manal a motar ka?." "Oho mata, shegen munafurci a cikin ta mana. Ni kuma nayi amfani da damar ne nace ai itace wacce nake so ɗin  dan Mummy tayi sanyi ta ta janye maganar ta amma sai ta sake yin zafi." Hamza yace, "shawara ɗaya a nan Bebi, ko ka amince da auren Rumana ko kuma duk yadda za'ayi ka samo wacce kake sona cikin kwanakin nan. İn Mama ta tabbatar da gaske akwai wacce ka ke so zata iya baka dama guda biyu, na farko ko tace ka aure su dukkan su, na biyu ko tace ka fara auren wacce ka ke so ɗin kamar yadda aka bawa Rumana dama sannan ka aure ta daga baya." Ya dafe kai yace, "kun  kasa fahimtar bazan iya zaman aure da Rumana ba kwata kwata." Huzaifa yace, "ajjiye wannan maganar zakayi, zancen Hamza shine abinda ya kamata ayi." Ya kalle su ta cikin glasses ɗin idon yace, "a ina zan samu wata mace a yanzu?, ban shiryawa hakan ba wallahi." Hamza yace, "ga mata nan da yawa, ko yanzu kaso zaka iya haɗuwa guda ɗari na tabbatar a cikin ɗarin nan casa'in zasu karɓe ka hannu biyu ma kuwa." "Nema matar babu wahala samun wacce zance zan so shine shine mai wahala." "Ba lallai sai kana son ta ba ai, in ka aure ta nan gaba zaka so ta." Ya girgiza kai yace, "har abada bazan auri wacce bana so ba, in kunga nayi aure to auren soyayya ne,  bazan auri wacce bana qaunar ta ba," Hamza yace, "ka mayar da hankali akan neman matar, ka saurari zuciyar ka a duk lokacin da idanun ka suka shiga cikin na wata mace, kasan meye so kasan yadda bugawar zuciya take canjawa a duk lokacin da idanu ya kalli abinda yake so ko yake maradin fara so." Bebi yace, "nifa soyayyar ƙurucuya nayi bazan wani gane sosai," Huzaifa yayi dariya yace, "zaka gane, so sunan sa so, balle kai da kayi shi a matsayin na farko. Zaka tabbatar kamar yadda ya faɗa maka hakan shine mafita a wajan ka." Ya sauke numfashi ya kulle ido ya buɗe yace, "Yanzu Ina zan fara nemo wacce zan so ni Adnan?. Wannan yarinyar Ruman sai Allah ya saka min wahalar da ta saka ni."  Dariya sukayi ya kalle su ya sauke numfashi yace, "baza ku gane abinda nake ji bane shiyasa kuke dariya" yana faɗa sai ya miƙe dan ya tuna da abinda zai yi a wannan lokacin hakan ya saka ahi ya fita daga office din. Sai da yayi sallah a masallaci sannan ya hau mota ya bar cikin asibitin. A ƙofar wani gida ya faka ya tsallaka ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan aka buɗe mai gadi ya kalle shi suka gaisa yace, "mai gidan yana nan?." Mai gadin yace, "eh yana nan." "Dan Allah ka sanar dashi Adnan yana son ganin sa, in yace wanne Adnan kace masa Adnan ƙanin Maryam." Ya amsa da to ya kulle ƙofar ya juya shi kuma ya koma mota zauna. Ba jimawa sai gaahi ya fito ganin sai ya fito daga motar ya tsallako yace, "yace ace ka shiga ciki."  "Na gode, ga wannan ka sha ruwa" ya faɗa yaana bashi kuɗiya karɓa yana godiya shi kuma ya shiga gidan. A wata ƙaramar rumfa ya hango shida yaran sa a zaune, yara biyu mace da namiji su naganin Adnan suka taso a tuje suka rungume shi ya kalle su yace, "ba wani Uncle baya bakwa ma zuwa inda nake?" Ya faɗa yana zama a kan kujera kamar yadda yake shima. "Uncle muna zuwa sai ace kaje aiki." Ya basu chocolate da kuɗi yace da Nabila ta raba musu yaran suka wuce ciki ana murya. Kallon Kamal yayi mijin Yayar tasa yace, "nasan kayi mamakin gani na." Kamal yace, "sosai ma kuwa, da farko na ɗauka kazo ganin yaran yayar kane sai naga ba haka abin yake ba." Ya ɗan murmusa ta gefen baki kafin yace, "warning  nazo maka na ƙarshe akan Maryam, babu aure tsakanin ku ya kamata ka daina bibiyar ta, ina so na tuna maka saki uku ne a tsakanin ku, babu maganar dawowa gidan nan sai tayi wani auren ta fito. Na faɗa ka ƙi, shiyasa nazo da kaina nayi maka warning da babbar murya." Kamal yayi dariya yace, "Allah sarki yaro man kaza in ji hausawa, yo kai baka san ita yayar taka ya kamata ka jawa kunne ba ni ba? Ita take nema na bani nake neman ta ba." "Wannan kuma kai ne ka sani Kamal bai dame ni ba, abinda nake so ka sani ka ja mutuncin ka ko dan yaran ka, in ba haka ba zan jawo mutuncin ka kan titi nayi wasa dashi son raina har sai naga ya gushe daga gare ka," Kamal yayi dariya yace, "ni ne nake da wannan makamin ba kai ba." Bebi ya girgiza kai yace, "in kana ganin bazai yu ba na sake ganin ka da maryam don Allah." Kamal ya kalle shi yace, "Ko gobe ma zamu haɗu da ita zan so naga abinda zakayi." Bebi ya miƙe ya kalle shi ya girgiza kai yace, "Allah ya kai mu goben" yana faɗa ya fice ya bishi da kallo yana darıya domin kuwa Bebi bai isa ya hana shi bibiyar tsohuwar matar sa ba duk da babu kome a tsakanin su. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025                  ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* Page 014 Yana barin gidan asibiti ya koma yana zama a office Hamza ya shigo yace, "Yauwa Bebi barka da zuwa." Bebi ya miƙa masa hannu suka gaisa kafin Hamza yace, Ga baban su yarinyar nan yazo yana so kayi masa bayani akan yanayin babar ta." Kai kawai ya ɗaga Hamza ya fita sai gashi sun shigo tare da Baba ya ƙaraso ya zauna Bebi yace, "Baba barka da rana." "Barka dai likita, ya aiki?." "Alhamdulillah. Ciwon sugar ta ne yayi yawa sosai, sugar ya hau sosai, da alama ta kwana biyu bata bin ƙa'idar sa kamar yadda aka saba, amma yanzu Alhamdulillah yayi yadda ake so. Sai batu akan ciwon zuciyar ta." Baba ya gyara zama Bebi yace, "Ko zaka iya tuna lokacin da ta kamu da wannan ciwon?." Baba yace, "za'a iya kaiwa shekara biyar ko shida." Ya girgiza kai yace, "ya taɓa kwantar da ita haka?." "A'a gaskiya, sai dai wani lokacin in ya tashi tana shan wahala matuƙa musamman in ranta ya ɓaci da yawa a cikin sati ɗaya, to kafin satin zata iya kwanciya ciwo sosai." Bebi yace, "ciwon idanun fa?." "Shi bai fi shekara biyu ba, kuma a lokacin baya tan gani amma ba sosai ba. Lokaci ɗaya ya ɗauke ganin, ana shan magani amma bai dawo ba, sai dai wani lokaci tace tana gani dashi amma kaɗan." Bebi ya girgiza kai yace, "in sha Allah ganin zai dawo ko da ba sosai ba, ko iya da rana ne zata iya dinga gani indai za'a bi dokar da zamu saka in ta warware. Rashin shan magani mai ƙarfi ne ya saka ciwon idon yazo wannan mataki, amma in sha Allah zata samu sauƙi." Baba yace, "Alhamdulillah, Allah ya sa hakan." Bebi yace, "Amin. Sai maganar ƙaramar, ita kuma nata bai hau ba sai dai ya ƙone, ina nufin sugar yayi ƙaranci a jinin ta sosai. Abinda mutane basa ganewa shi wannan ciwon ya fi wa masu ƙarancin shekaru kamar ta illa, yanzu Illar da zai mata ba zai yiwa Maman ta ba." Baba yace, "bata jin magana ne, indai akan mahaifiyar ta ne ta amince taƙi ci taƙi sha indai Maman ta zata sha. To wani lokacin in aka kawo takardar maganin in ta tabbatar babu kuɗi sosai a hannuna sai ta bada na uwar kawai sai ta hana na ta. Duk da dai daman ita ba'a ɗora ta kan magani ba gaskiya, iya kula da cima ake bata amma wani lokacin a kan bata magani." Bebi yayi murmushi kaɗan yace, "Allah Sarki! Ayi ƙoƙarin ganin tana zuwa asibiti kamar duk sati biyu ana gwada jinin ta, tunda ita babu magani ya kamata a dinga lura ta yadda za'a fahimci a wanne mataki ciwon yake. Sannan su dinga yawaita cin cucumber, in baza su iya ci ba su dinga markaɗe ta suna shan ruwan, tana taimakawa sosai wajan daidaita sugar jikin mutum." Baba yace, "in sha Allah." "Shikenan Baba, daman bayanin da nake so nayi maka kenan." Baba ya amsa yayi masa sallama ya tafi ya koma inda ya bar Manal a zaune ya zauna yana kallon ta yace, "kin fara bani labari aka kira ni, ina jin ki, ya akayi kika tsinci kan ki a asibitin nan? A ina kika samu kuɗin da kika kawo ta nan Manal?." Manal ido ya ciko da ruwa ta kalle shi tace, "wallahi Baba banyi komai ba, ka tambayi Surayya da ita muka zo babu abinda nayi." Baba yace, "ai bance nima kin yi wani abun ba Manal, faɗa min abinda yake faruwa." Manal ta bashi labarin abinda ya faru kafin tace, "ban san hakan zata faru ba Baba, na ɗauka tsakano da Allah ya taimaka mana ganin yana ta taimakawa mutane a wajan, ban yi tunanin hakan ne zai faru ba Baba." Baba y sauke numfashi yace, "kin yi kurkure Manal, abinda kika yi ba ƙaramin shirme da rashin hankali bane, yanzu da ya cutar dake fa ki cewa Maman ki meye in ta farka?." Manal tana kuka tace, "bazan sake ne, na ruɗe ne sosai Baba, a lokcin ina tsoron kar na rasa Mama." Baba yace, "Dan kin ruɗe bai kamata hankalin ki ya gushe ba, ina ke ina bin wanda baki sani ba? Babban abin haushin ma da ya sake ɗaukar ki kuka fita kuma kika bishi, da mai satar mutane ne fa Manal?." Manal ta goge hawaye tayi shiru Baba yace, "da wasa kar ki sake wannna kuskuren, daga haka wata ran zaki tsinci kan ki a inda baki tunani ba, ba ko wanne mutum ne mai kyakykyawar zuciya ba, na banza sun danne na kirin, ki kula kar rashin lafiyar Babar ki y saka ki fara abinda ba halin ki ba." Manal ta ɗaga kai tace, "bazan kuma ba, ka yi haƙuri." "Shikenan, Yanzu nawa ne bill ɗin asibitin? Sun faɗa miki?." Manal ta girgiza kia tace, "tun lokacin nace zamu tafi sai likitan da muke ganin a babban asibiti yace kar na damu shine aka cigaba da yin komai." Baba yace, "Kar ki damu kamar ya?." "Ban sani ba Baba, haka yace." "Bara naje na same shi naji abinda ake nufi." Har ya tashi sai ya kalle ta yace, "Mubeena bata zo ba?." Manal ta sauke numfashi tace, "Tunda tazo da daddare nayi nayi ta zauna taƙi, koMaman bata san tazo ba tayi tafiyar ta, ko waya bata min." Baba ya girgiza kai yace, "kar ki sanar da mahaifiyar ki in ta nemi sani, kice mata Mubeena kullum tana zuwa tana barin wajan ne saboda makaranta." Ta ɗaga kai alamun to Baba yace, "zan je na dawo yanzu" ta amsa Baba ya fita ta zauna tayi shiru alamun tunani take yi. Washe gari Mama ta farfaɗo jikin ta yayi kyau sosai har abinci taci tana kwance Manal na kusa da ita ta riƙe hannun ta, Maman kallon ta take yi tace, "Manali Yayar ki bata zo ba ko?." Manal tace, "tazo Mama, tana ma zuwa makaranta ce ta saka baki ganta ba." Mama tayi dariya tace, "ƙarha kike" ta faɗa tnaa kallon ta kafin tace, "Allah yayi miki albarka Manal, yadda kike kula dani Allah ya kula dake kema." Manal ta amsa da amin Mama tayi shiru tana jin zafin halayen Mubeena a zuciyar ta ko ba'a faɗa ba tasan yana daga cikin abinda ya saka ciwon zuciyar ta yaƙi warkewa kenan.   *****Kamal ne a zaune a mota shida Maryam tana kallon ta cikin ɓacin rai shima kallon ta yake yi kafin yace, "Wai Adnan ba ƙanin ki bane ba?." Maryam tace, "tunda naji kace kana so mu haɗu nasan bazai wuce zancen Baebi ba, ƙanina ne me ya faru?." "Yaron nan da tsabar wulaƙanci har gida ya bini ya shiga har cikin gıdana ya zauna yana cemin wai in ban fita harkar ki ba sai ya bani mamaki, ke kin ji wulaƙanci da cin fuskar da yaron nan yayi min akan ki?." Maryam ranta ya ɓaci tace, "na rasa abinda yake damun wannan yaron wallahi, ya takura min kamar shine ya haife ni ko kuma shine babban yaya a gidan gabaɗaya. Nima fa yanzu cewa yayi wai kar a barni na fito." Kamal yace, "kar a barki ki fito?." "Wallahi haka yace." "Lallai ma yaron nan ya fara wuce gona da iri. Dan ina son ki hakan ba yana nufin zan ɗauki wulaƙanci daga wajan ƙanin ki ba Maryam, bazai yu yazo har gida yaci min fuska ba, darajar ki akwai yaci matsayin sa na jinin ki amma wallahi da yanzu ba wannan magana ake ba ke kin san waye ni." Maryam tace, "ka barni dashi zan yiwa tufkar hanci, bazai sake aikata abinda ya aikata ba in sha Allah." Kamal yayi shiru baice komai ba tace, "kayi haƙuri, bazai sake faruwa ba in sha Allah."  Ya kalle ta yace, "soyayyar da nake miki shine ya saka nake bibiyar ki bayan wannan kin san babu komai, amma yaron nan yazo har cikin gida ya ci min mutunci. Da farko da yaje nayi tunanin wajan su Nabil yaje ashe ba haka bane." Maryam tace, "kayi haƙuri don Allah." "Ya zanyi, ai dole nayi haƙurim." "To kayi dariya mana." Ya kalle ta ya kawar da kai bai yi murmushi ba sai ta tuna lokacin da take gidan sa in yayi irin haka, ta kalle shi suka haɗa ido sai tayi murmushi yasan abinda ta tuna shima kuma shi ya tuna a lokacin amma shi baiyi Murmushin ba so yake sai ta aikata abinda ta tuna ɗin dan yasan zatayi bata jurewa fushin sa ko kaɗan. Hannun ta ya riƙe sai ta kalle shi ya ɗaga mata gira yace, "ina kewar ki." Murmushi tayi tace, "har nayi farin ciki da ka wuce." "Na mayar dake gida ko akwai inda zaki je?." "Eh, Mamy ta aike ni kasuwa akwai atamfar da zan siyo mata." Bai ce komai ba ya kunna motar har lokacin yana riƙe da hannun ya fara tafiya sannan ya kalle ta yace, "ina tuna yanayin da muke kasancewa dake, yanayi mai daɗi da yake gusar mana da hankali ni dake, haƙiƙa kin yi matuƙat iya sarrafa...." Sai yayi shiru ya kalle ta sai ta kawar da kai tana darıya amma bata ce komai ba. Shima dariyar yayi suka cigaba da tafiya ya kai ta kasuwar ya jira ta shiga ta fito ya dawo da ita gida sannan ya wuce inda zai je. Tana shiga gida wajan Mamy ta ajjiye ledar tace, "Yanzu Mamy abinda Bebi yake a gidan nan ya kyauta? Ya dinga yin abu kamar shine Yaya komai cikin gadara. Kamal fa yaje ya samu har gida yaci masa mutunci kawai dan yana kawo min yarana ina ganin su, yanzu me ya aikata don Allah?." Lubna da ke gefe tace, "haka kawai ya hana ni kula Mujahid, ina son shi yana sona yana son rabu mu kawai dan baya son sa, shine nima bazan so shi ba. Wallahi Yaya zanje na samu da maganar nan na gaji, a gida yake so nai ta zama duk wanda yazo yace ya tafi." Mamy da take jin su tace, "to meye na zuwa wajan Kamal kuma?." Maryam ta zauna tace, "wulaƙanci mana." Mamy tace, "gaskiya bai kyauta ba, ko babu komai akwai yara tsakanin ku da Kamal dan an gaisa ai ba wani abun bane. Maganar Mujahid nima yana bani mamaki ya hana Lubna kula shi a gidan nan gabaɗaya, kuma in kika tambayi dalili babu, akan ra'ayin sa kawai yake son danne mata haƙƙi." Maryam tace, "to kuwa wallahi bai isa ba, sai ta aure shi dan ni ban ga aibun da yake dashi ba." Mamy ta girgiza kai tace, "abin da mamaki." Maryam ta girgiza kai domin kuwa ta ɗaura ɗamarar cigaba da kula Kamal ko dan taga abinda zai yi. Kamar yadda ya saba bai dawo ba sai dare ya faka motar sa a gidan ya shiga wajan Mama dan da yunwa ya dawo sosai, yana shiga ya tarar da ita a zaune ita da Rumana ne kawai dan su Mimi basa wajan. Zama yayi yace, "Sannu da hutawa, Mummy yunwa nake ji." Mama ta kalli Rumana tace, "kawo masa abinci." Ta tashi ta wuce kitchen ba jimawa ta kawo abincin ta bashi ya karɓa ya fara ci yana zaune kafin yace, "Ina Mimi take?." Mimi da yake fitowa daga daki tace, "Gani Yaya, Sannu da zuwa." Zama tayi sannan yace, "Yauwa. Wannan saurayin naki" sai yayi shiru yana shan ruwa kafin yace, "mun gama magana dashi zai zo gobe, da yau ne ma zai zo sai da ya kira ni nake sanar dashi na manta ban sanar dake ba amma gobe yana nan zuwa" ya faɗa yana kallon ta. Da to ta amsa Mama ta kalle shi tace, "ka gama yi masa interview ɗin kenan ko?." Yayi murmushi baice komai Mama tace, "wataƙila a haɗa auren naku kai da ita ai, in Allah yayi shine mijin ta shikenan faɗuwa tazo daidai da zama sai ayi auren naku a wuce wajan." Shi dai baice komai ba yana cin abinci Mama tace, "ko ba haka ba Rumana?." Rumana tayi ƴar dariya tace, "Haka ne Mama." Sai da yaci abincin sosai sannan ya tashi yace, "yau ban shiga wajan Mamy ba, zanje mu gaisa daga nan bazan fito ba sai gobe." Mama tace, "Allah ya tashe mu Lafiya" ya amsa da amin ya juya zai fita Rumana tace, "Gud night Beb." Bai amsa ba bai kuma juyo ba ya fice daga falon haushin ta yake ji sosai a zuciyar sa, ita ko kunyar Mummy bata ji ta dinga abu kamar mara hankali. Wajan Mamy y shiga da sallama ta amsa a ciki bai ma lura da yanayin ta ba ya zauna yace, "Mamy barka da dare, yau ban shigo mun gaisa ba gabaɗaya." "Barka, ya aikin?." Sai da ya kalle ta jin a yadda ta amsa kamar bata so, amma sai bai nuna ba yace, "Alhamdulillah." Maryam da take gefe tace, "wai Bebi meye damuwar ka da Kamal ne? Dan rashin kunya da rashin mutunci har cikin gidan sa kije ka ci masa mutunci? Meya tare mata wai? In ma bibiyar tawa yake ina ruwan ka ba rayuwa ta bace ba?." Kafin yayi magana ta sake cewa, "dan tsabar wulaƙanci da raini shine ɗazu kace wai kar a barni na fita da yake ga wacce ka haifa ko?, ko kuma ga gidan da ka gina ubana?." Bebi yace, "Duk abinda nake yi ina yi ne saboda rayuwar ki, badan son raina ba ko kuma dan ra'ayina ba....." a fusace ta katse shi tace, "Ina ruwan ka da rayuwar tawa? Ka cire hannun ka daga cikin rayuwar tawa mana sai me?." Ya kalli Mamy tace, "Mamy nasan ke kin fahimci abinda nake nufi, ya kamata ki mata faɗa abinda take yi ba daidai bane nan gaba zai jawo mata dana sanin da har ta mutu baza ta daina ba. Meye amfanin kula mijin da ya rabu da kai har da zama dashi a mota ko ina a kulle da sunan gaisawa?. Ko ɗazu shine ya ajjiye ta a ƙofar gidan nan, meye amfanin aikata hakan a wajan ta don Allah?." Mamy tace, "A'a Bebi, ɗazu nice na aike ta kasuwa, kuma dan sun gaisa da tsohon mijin ta kamar ba laifi bane ba ai ko?." Jin abinda Mamy tace sai ya kalle ta da mamaki sosai yace, "Mamy kina goyan bayan hakan kenan?." "Ai babu wanda zai ƙi hakan sai kai, ka hana Lubna sauraren Mujahid kawai dan bai maka ba, ko kuma dan ta samu miji su Mimi basu samu ba shine damuwar ka?." Maryam tace, "ba dole ba, kishin ƴan ubancin ne ya tashi shiyasa yake so ya korar mata shi, yadda nasa basu samu ba itama ta zauna haka." A fusace ya kalle ta yace, "Kul kar ki sake faɗar haka in ba haka ba zaki nadama. Mimi, Lubna, Kausar, Maryam da Farida duka ɗaya ne a wajena basu da wani banbanci sai na halitta. Kuma bara kiji, ko me zai faru sai na tabbatar na raba alaƙar ki da Kamal wallahi, haka itama Lubna indai ina da rai bata isa ta auri Mujahid ba, duk abinda zaku ce kuce wannan kamar umarnina ne babu wanda ya isa ya canja shi koda Abba ne, dan ni kaɗai nasan hatsarin da yake cikin abinda kuke son yi. Sam baki San abinda kike yi ba, miji ya sake ki saki uku amma kice kike biye masa har ake zama a mota ana tuna rayuwar da ta wuce ana dariya, hakan a wajan ki daidai ne ko kuma wayewa. Rashin sanin darajar kai ne, da kuma rashin sanin ciwon kan ki da bakya yi, ki gyara rayuwar ki ko dan yaran ki" ya faɗa cikin faɗa dan tasan daman dole zaiyi haka baya jurewa tension, kuma in ransa ya ɓacı kome yazo bakin sa faɗa yake kuma a gaban kowa. Maryam ta kalli Mamy tace, "Mamy kina jin abinda yake cewa ko?" Ta sake kallon shi tace, "ni kuma wallahi sai Lubna ta auri Mujahid sai dai duk abinda akayi kayi" ta faɗa shi lokacin ma yayi  nisa da barin falon. ta sake kalli Mamy tace, "Daman Mamy ke kike goya masa baya, gashi yanzu a gaban ki yake zazzaga min rashin kunya kamar ba gaba nake dashi ba, ko da yake har ke ya yiwa bama ni kaɗai ba." Mamy na zaune dai kawai bata ce komai ba amma ya bata mamaki kam sosai. Rai a ɓace Bebi ya shiga ɗakin sa ya rasa abinda yake damun Maryam gabaɗaya bata da girma sai na jikin ta, in badan haka ba da hankalin ka da tunanin ka ka dinga sauraren tsohon mijin da ya sake ka har ka dinga yi masa darıya kuna zama waje daya?. Yayi tsaki ya zauna, dole ya yiwa tufkar hanci kar abinda yake gudu yazo ya faru. Nana Haleema❤️🥂 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 015.* Washe gari bai fita da wuri ba tunda yaje ya gaida su Mama da asuba, sai da ya tashi ya shiga wajan Mamy  ya gaishe ta ta amsa daƙyar bai yi wata magana ba ya wuce wajan Mama ya same ta a zaune ita kaɗai babu kowa ya zauna yace, "Mummy basa nan ne?." Mama ta kalle shi tace, "Basa nan, sai ka tashi kaje ka haɗa tea ɗin da kanka tunda kai komai sai an maka, Rumana ta shiga uku da yawan saka aikin ka wallahi." Baice komai ba shi dai, ya tashi ya haɗa tea ya dawo yana cewa, "Wai Mummy baki wannan kunun ba?, ni tea ba damuna yayi ba, shan sa sai dole." "Ai tunda nayi kace babu daɗi bazan sake maka kunu ba Bebi, na hana idona bacci na dama maka amma sai kace wai kamar ba'a dama ba." Yayi ƴar dariya yace, "Allah Mummy ranar tuntuɓen hannu kika yi, ni na ɗauka ma fa Mimi ce ta haɗa ashe wai kece da kan ki." Ta harare shi tace, "Yanzu ai sai ka samu mai yi maka." "Tuba nake Mummy." Kausar ce ta shigo falon da sallama suka amsa ya kalle ta yace, "me ya dawo dake?." "Test muka yi, kuma daman yau bani da class." "To ɗauko min sugar" ya faɗa yana ajjiye tea ɗin. Shiga kitchen tayi ta kawo har zata tafi yace, "baki ɗauko tea spoon ba." Ta juya ta sake kawo masa sai ya kalle ta  bayan ya karɓa yace, "haka zan sha babu madara?." Kausar kamar ta zubar da hawaye ta sake kawo masa tan ajjiyewa tayi ciki gab da zata shiga ɗaki yace, "Kausar bani ruwa, ki buɗe flaks in akwai wani abun ki kawo min." Ta juyo ta ɗauko ta kawo masa tare da doya da kwai a plate ta wuce ciki a guje dan kar ya sake aiken ta. Mama ta kalle shi tace, "kai dai saka aikin ka yayi maka yawa wallahi, indai kana waje shikenan baza su huta ba? Ɗauko min wannan ɗauko min wancan?. Yamzu ba sai kace mata ɗauko min sugar da madara, ki haɗo min tea spoon da ruwa, in akwai wani abun a flaks ki kawo min, shikenan zuwa ɗaya taje ta dawo amma sai da ka mayar da ita sau huɗu." Baice komai ba ya shanye tea ɗin da yake sha Mama ta kalle shi tace, "Adnan ka cire hannun ka daga batun Maryam da Lubna don girman Allah." Jin magiyar da Mummy tayi masa sai ya kalle ta yace, "me ya faru?." "Jiya Maryam tazo har nan bayan ka fita tace nace maka babu ruwan ka da lamarin su, in ma tana kula Kamal ɗin rayuwar tace ba taka ko ta Farida ba. Sannan ko ƙanin far'auna ne Mujahid saboda baƙin halin babu ruwan ka, ka cire lissafin Lubna baza ta aure shi ba a ran ka don Allah. Komai kayi ba gani ake ba, a kullum a ɗan kishiya ake kallon ka." "Ke tazo ta faɗawa haka?" Ya faɗa  alamun bai ji daɗi ba tace, "kaga kwantar da hankalin ka, bada rashin kunya ta faɗa ba cikin lallami ta faɗa,  domin kasan ita ko yaushe ƴan ɗakin su sune ƴan uwan ta, ku kuma ƴan ɗakin nan daban ku ke a wajan ta." Bebi ya ajjiye kofin tea ɗin Mama tace, "dan haka ka ƙyale su babu ruwan ka ko me ya faru kayi iya bakin ƙoƙarin ka amma basu gani ba, ƴan uwan ka basa son abinda kake musu tunda su basa ganin sa matsayin gyara, su suna jin abinda Lubna take faɗa a kan ka, suna jin ciwo domin kai nasu ne kamar yadda su suke ɗauka ƴan ɗ'akin su sune ƴan uwan su. Mimi da Kausar ko kara ka ajjiye baza su tsallake maka ba zasu yi maka biyayya domin  sun san baza ka cutar dasu ba, yadda ka ke kishin rayuwar su kake tarairaiyar su ko mahaifin su baya yi. Tunda su basa gani a dakatar da wannan abun haka, ka ƙyale su suyi abinda suke so dom Allah." Bebi ya kalli Mama bayan ya gama jin abinda tavr yace, "Mummy inda zan iya ƙyale su dana ƙyale su  ɗin amma bazan iya ba." Mama tace, "zaka iya Bebi, ka kawar da kan ka daga  duk abinda zasu aikata tunda haka suka zaɓa." "Wallahi Mummy bazan iya ba, zafi nake ji a zuciyata a duk wanda naga suna sauraren waɗannan mutane guda biyun. Mummy Allah ya saka min kishin ƴan uwana dukkan su ji nake kamar ana tafasa min zuciya lokacin da na gansu da wani namiji wanda na tabbatar ba mutumin kirki bane. Mummy ban sani ba ko kowa haka yake ji akan iyalan gidan su, ni yadda nake jin  iyalan gidan nan zan iya sadaukar da raina saboda farin cikin ku gabaɗaya. Da naga wani abun ya cutar da ɗayan ku gwara ni ya cuce ni. Aka cigaba da tafiya haka wallahil azim Mummy nan gaba sai sunyi hawaye domin Mujahid ba sonta yake ba, yana amfani da ita ne dan ya ɓata min rai, shi kuma Kamal yana amfani da son da take masa ne yana cigaba da bibiyar ta duk da babu aure tsakanin su, in aka zuba musu ido me zai faru?. Taya zan iya barin wannan ɗanyen aikin Mummy?." Mama tace, "Na sani Bebi, nasan kana yi da zuciya ɗaya amma su basa gani ne." "Kar su gani mana ai Allah yana gani, babu abinda zai dakatar dani ga daidaita musu zama a gidan nan ko meye zai faru kuwa, don Allah ki cire bakin ki Mummy, ki ƙyale ni nayi abinda nake ganin shine daidai." "Zaka sake yin baƙin jini a wajan su, dmaan suna cewa mahaifin ku yafi son ka." "Na amince, baƙin jinin na ɗan lokaci ne, daga sanda suka fahimci ni ne a kan daidai shikenan zai gushe." Mama tace, "ai shikenan Allah ya bada lada." Ya amsa da amin ya tashi tsaye tace, "nasan abinci kuma ya fita daga ranka, ɓacin rai ya daina saka ka ƙin cin abinci kan ka zaka cuta." Yace, "Zanje na shirya zan wuce aiki." "Allah ya kiyaye." "Amin" ya faɗa yana fita zuciyar sa cike da ɓacin rai ya kuma yi alqawarin ki ne zai faru bazai bar Lubna da Mujahid ba, haka bazai bar Kamal da Maryam ba. Da wannan tunani da ɓacin ran ya shirya ya fita zuwa asibiti, yana zuwa kai tsaye office ya buɗe ya shiga yayi zaman sa a ciki dan baya cikin yanayin da zai iya zuwa yaga wani mara Lafiya. A can ɗakin su Mama tana zaune sosai ta samu lafiya dan shayi ta gama sha Manal na zaune sai Baba shima da yake zaune a ɗakin. Huzaifa ne a ɗakin a tsaye yana kallon Mama yace, "Mama sugar ki ne ya hau sosai ya kamata a gujewa shan abubuwa masu zaƙi, sannan kuma a dinga yawan shan magani kar a dinga bari sai ya ƙare." Mama tace, "likita rai ne da buri, kuma yau da gobe sai Allah." "Haka ne Mama, amma lafiya tafi komai, yanzu gashi shan da kika yi na kwanaki shine ya jawo miki wannan ciwon gashi yau satin ki ɗaya a kwance." Mama tace, "za'a kiyaye in sha Allah. Manal fa?." "Ita kuma nata ƙonewa yayi alamun tana gushewa cin abubuwa sosai, duk da na bata magani zuwan ta na ƙarshe amma da alama bata sha yadda ya kamata ba." Mama ta kalli inda take jin motsin Manal tace, "bata sha kam wallahi, nayi mata faɗa sai tace in na sha kamar ya sha ne." Huzaifa yayi murmushi yace, "zata dinga sha yanzu in sha Allah duk da bana son ɗora ta a magani, amma za'a san yadda za'a yi. so nake likitan da yake kula da yazo in yaga kin samu Lafiya za'a iya sallamar ki." Mama tace, "Allah ya saka da alkhairi yayi albrarka." "Amin. Sannan yace akwai maganin da za'a baki cikin ikon Allah in ana sha ganin ki zai dawo duk da ba duka ba amma za'a dinga ganin ko yaya ne, sannan za'a haɗa da glasses shima don ya taimakawa ganin naki." Mama tayi murmushi tace, "Allah ya sa hakan." Huzaifa ya amsa da amin ya fita dan ya duba office ɗin Bebi dan ya ji shi shiru. Yana tura ƙofar ta buɗe alamun yazo kenan Bebi ya ɗago ya kalle shi suka haɗa ido sai Bebi ya cire glasses ɗin sa ya ajjiye Huzaifa ya shigo yace, "yau lafiya har azahar?." Ya faɗa yana zama yana kallon sa. Bebi yayi ƙaramin tsaki yace, "raina ne a ɓace wallahi, zan iya ɓatawa kowa rai shiyasa ban fito ba." "Akan Rumana ne?." "Nata mai sauƙi ne akan wannan. Kasan Mujahid yana can yana neman Lubna wai auren ta yake so yayi." Huzaifa da mamaki ya kalle shi yace, "Mujahid ɗin?." Ƙaramin tsaki Bebi yayi yace, "ban sani ba, ina faɗa maka kana sake tambaya ta, bashi ba." Huzaifa yace, "abin ne ya bani mamaki, da wacce manufa kenan yake son Lubna?." "Da wacce manufa kuwa wacce ta wuce saboda ya ɓata min? Kai ka manta abinda yace min a cikin office ɗin nan?." "Ban manta ba Bebi, shine abin ya bani tsoro tabbas ba son Lubna yake ba da wani abun a zuciyar sa. Abinda ya kamata ka raba su ta ɓangaren Lubna ɗin tunda ita kana da iko da ita." Bebi ya kulle ido kawai bai ce komai ba dan Huzaifa bazai gane abinda yake ji a zuciyar sa ba Huzaifa yace, "Bebi ka bi komai a sannu babu abinda zai faru in sha Allah." Numfashi ya sauke ya mayar da glasses ɗin sa kafin Huzaifa yace, "kana ganin za'a iya discharging ɗin su Maman su Manal yau?." Ya ɗan wara hannun sa kafin yace, "taya zan sani bayan kai ne suke ƙarƙarshin ka? Duk abinda nake musu karanbani ne aikin ka ne" ya faɗa a fusace. Huzaifa yayi dariya dan daman yasan bazai amsa masa ba tunda ransa a ɓace yake, kuma shi bai iya sarrafa ɓacin rai kowa ma yasan hakan. Kuma in ran sa ya ɓaci na kowa ma sai ya ɓaci, kana yi masa abinda bai masa ba zai aikata maka abinda kai ma sai ranka ya ɓaci. Dukan table ɗin yayi Huzaifa ya kalle shi sai kawai yaga ya tashi ya ɗauki key ɗin mota ya fita. Yana fita ya fara tafiya bai ma kula da bayan sa ba yaji ance, "Dr." juyowa yayi sai suka haɗa ido da Manal da take tsaye a bayan sa, yau kuma jan Hijjabai ne a jikin ta jalbab har ƙasa tana murmushi tana kallon sa fuskar nan a haɗe sosai fiye da kullum." "What?." Ya faɗa yana kallon ta. Sai jikin ta yayi sanyi godiya take son yi masa amma sai taga babu fuskar hakan. Ƙaramin tsaki yayi yace, "me ya sa kika tsayar dani? What do you want?" a fusace yake maganar kai da ka ganshi kasan ransa a ɓace yake sosai. Huzaifa ne ya fito yana jin abinda yake faɗa mata kafin ma tayi magana ya bar wajan har ya ɓace. Kawai sai Manal ta fara hawaye Huzaifa ya kalle ya yace, "lafiya me ya faru?." Manal tace, "magana nayi masa kawai ina so mu gaisa na masa godiya akan abinda yayi mana, kuma Mama ce ta turo ni amma ina magana ya fara faɗa yayi tafiyar sa." Yayi murmushi a ransa yana girmama shagwaɓar yarinyar yace, "shine abin kuka?." "Bana son faɗa, kuma ya wulaƙanta ni." "Kiyi haƙuri ran sane a ɓace shiyasa kika ga haka." "Daman shi ai kullum haka yake, na gode" ta faɗa tana juyawa ta koma. Huzaifa yana dariya dan halin Bebi sai shi, bai san wani abu sarrafa ɓacin rai ba, ko ba kai ka ɓata masa rai ba to zai shafe ka. Kai tsaye Bebi babban ofishin Hisba ya wuce, bai taɓa zuwa ba hakan ya saka koda ya faka motar sai da yayi tambaya aka raka shi har ciki yace shi da babban su yake son magana, akace malam baya nan amma mataimakin sa yana nan aka raka shi har wajan sa yana zaune a office ya shiga. Bayan sun gaisa da girmamawa Bebi yake cewa, "Suna na Adnan Mu'azzam na kawo ƙorafi akan wani Kamal tsohon mijin Yayata da suka rabu da yara biyu, babu aure a tsakanin su saboda saki uku ya yi mata amma kuma yana bibiyar ta. Ina so a kira shi ayi tsakani a tsakanin su." Wanda yake faɗawa yace, "meye dalilin da ya saka yake bibiyar ta?." Bebi ya masa bayanın komai nan take yace a bada number Kamal aka kira shi aka bada umarnin yazo ofishin in yana da dama. Nana Haleema🥂🫶🏻 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025    ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 016* A nan yayi sallar la'asar yana idawar Kamal yana zuwa, tare suka koma ciki dashi da shugaban da kuma Kamal dɗin. Kamal sai kallon Bebi yake domin ya tabbatar shine ya kawo ƙarar sa baice masa ba shima baice ba a haka suka shiga ciki suka zauna, aka gaisa da Kamal da Malam kafin yace, "Kaine Kamal?." Kamal yace, "ƙwarai ni ne." "Kasan wannan?" Ya faɗa yana nuna masa Bebi ya kalli Bebi yace, "na san shi, ƙanin tsohuwar matata ne." Yace, "kaima kace tsohuwar matar ka amma yace kana bibiyar ta, kana so ka mayar da ita ne?." Kamal ya sauke numfashi cikin takaici yace, "A'a babu wannan a zuciyata. Saboda saki uku ne a tsakanina da ita." Malam yace, "to meyasa ka ke bibiyar ta?." Kamal yace, "in dai naje wajan ta saboda yaran ta ne, wani lokacin maganar makarantar su ce, wani lokacin maganar rashin lafiya ko abinda yayi kama da haka. bayan wannan babu komai." "Yara zaka iya haɗa su da ita koda a waya ne, sannan zaka iya kai mata su ba lallai sai kun haɗu ba. Haɗuwar ma inda ba ko yaushe bace dan an haɗu an gaisa ba komai tunda akwai zuri'a a tsakani, amma ko yaushe ba daidai bane, shaiɗan zai iya shiga tsakanin ku a aikata abinda za'a yi dana sani." Kamal yayi shiru Malam yace, "Gashi da kan ka kace baka da ra'ayin mayar da ita, to meyasa kuma ka kasa rabuwa da ita?." Kamal yace, "kamar yadda na faɗa da farko maganar yara ce take kaini wajan ta." "In maganar yara ce kaje har cikin gidan su a gaban kowa kayi mata maganar yaran ta wannan ba wani abun bane, ko ka kira ta a waya ko ka kira wani nata kamar shi Adnan ɗin. Keɓewar ku ku biyu illa ce a gare ku, zaku dinga tuna rayuwar ku ya baya ne daga wannan lokaci kuma shaiɗan zai ratso ta tsakiya sai wani abun kuma ya afku, ga saɓon Allah ga dana sani." Kamal yace, "za'a gyara in sha Allah." Adnan ya tari numfashi Malam  da yake niyar magana yace, "Malam ayi musu tsakani da ita, tunda babu aure a tsakani to ya jira in akwai rabon zata dawo wajan sa zata koma, ya daina bibiyar ta." Malam yayi murmushi tace, "kar ka damu, duk da itama naso ace tana wajan nan dan itace babbar mai laifi, da bata bada fuskar hakan ba da bai faru ba." "In bai je inda take ba bazata saurare shi ba" Bebi ya faɗa yana kallon Manal. Malam yace, "A kiyaye Kamal, kodan saboda gujewa aikin dana sani." Kamal yace, "Gaskiya ne, na gode zan iya tafiya?." Ya amsa masa ya tashi ya fita shi kam Adnan godiya yayi masa sannan ya tashi ya fito. Yana zuwa gaban motar sa yana niyar shiga yaji Kamal yace, "Wai kai me ka ɗauki kan ka ne? Mahaifin Maryam?." Bebi ya juyo yana kallon sa yace, "zaka iya kira na da hakan ba laifi bane." "Kana ganin wai hakan da ka yi  shikenan ka raba ni da Maryam?." "Ai hukuma gaba take da kowa, in kana ganin kai kana gaba da ita ne ka sake maimaita abinda kayi. Wallahi nan gaba sojoji zan saka su yi maka dukan da zaka kasa tashi." Kamal yayi murmushi yace, "ni ka wulaƙanta Bebi har ka kawo ƙarata wajan nan. Ka jira abinda zai faru sai na tartarsa maka zuciya wallahi, badan kai mai kishin ƴan uwan ka ba? Na tabbatar Maryam zata baka kunya wacce baka yi tunanin jin ta nan kusa ba. Kuma ina so ka sani bazan nemi wata hanyar da zan gyara auren mu da ita ba, kuma bazan rabu da ita ba kayi abinda zaka yi." Adnan yace, "zaka ga abinda zan yi kuwa, domin ba'a shiga gona ta a zauna lafiya, abinda nake so shi nake aikatawa kuma shi nake aiwatarwa akan kowa koda shi baya so. Nafi ƙarfin ka tarwatsa min zuciya Kamal, sai dai ni na tsarwata taka. Rashin ilimin addini ne yake sakawa namiji ya bibiyi wacce ba matar  sa ba, ina baka shawara ka koma islamiyya domin yaƙi da jahilci domin yana damun ka sosai. Shine ya ke saka ka aikata hakan kan ganin hakan daidai ne, baka san tsabar jahilici da rashin sanin addini ne ya saka ka ke aikata hakan ba" ya faɗa yana nuna shi da key na mota kafin ya juya ya buɗe motar ya shiga yana ya fita daga cikin wajan. Da kallo Kamal ya bishi zuciyar sa na zafin kiran sa jahili da yayi, yayi ƙwafa shima ya shiga mota lokaci yayi da zai tabbatarwa da Bebi shi zai tarwatsa masa zuciya, zai ga aikin jahilai kuwa, zai yi dana sanin kiran sa jahili da ya yi. Mubeena ce ta fito daga banɗaki Bily ta kalle ta taga ta zauna tana cigaba da danna waya tans murmushi  Bily tace, "Wai da wa kike chart da kika kasa tashi kiyi sallah?." Ta kalle ta tace, "my future husband mana." Ta faɗa tana ɗaga wayar ta yiwa kanta hoto ta kalli hoton tayi murmushi ta cigaba da danna wayar. Bily tace, "yanzu kuma kin fara jin daɗin zancen banzan da yake miki kema kenan?." "Na fahimci soyayya ce hakan, yanzu ma hoton sa ya tura min babu riga amma view once ne" ta faɗa  tana dariya alamun abin bai dame ta ba. Bily tayi dariya tace, "Mubeena ki kiyayi wannan tashon fa, wallahi zai iya saka ki dana sani." Mubeena  ta kalle ta da mamaki tace, "na rasa yaushe kika canja Bily, Wai duk meye wannan ɗin? Bafa wani abun yake min ba kawai chart ne, kuma kin san wayewa ce ba wani abun ba." "Sexy chart din ne wayewa?." "Ya akayi kika san sexy chart ne?." "Saboda naga abinda ya rubuto miki a notifications yanzu, shi ko kunya baya ji da ƴaƴan sa da jikokin sa ya tsaya yana wannan shirmen dom Allah?." Mubeena tace, "kinga Bily don Allah ya isa haka." Bily tace, "bai isa ba Mubeena, sai na faɗa miki gaskiya. Dan ina biye miki ina cewa baki dace da haihuwar gidan ku ba hakan yana nufin na biye miki ki fara iskanci ba." Da sauri ta kalle ta tace, "ni kike ceawa ƴar iska Bily?." "Ita kike ƙoƙarin komawa ai Mubeena." Mubeena tunawa a gidan su Bily take sai tayi sanyi tace, "kinga ki ƙyale ni kawai ni yunwa ma nake ji" ta faɗa tana fita ta bar mata ɗakin, Bily ta bita da kallo tana tunanin lokaci yayi da zata raba garo da Mubeena domin tafi ƙ'arfin ta a yanzu. Bebi yana komawa asibiti baban Yayan su yayi masa yace in ya tashi daga aiki yazo gida ya same shi ya amsa ya kashe wayar ya ajjiye ya cigaba da abinda yake yi. Huzaifa ne ya masa waya ya ɗauka ya saka a speaker yace, "ina ji." "Nayi discharging Maman Manal suna so su ganka su yi maka godiya abubuwan da suka faru, ka dawo ne?." "Godiyar me za'a yi min? Me nayi kuma?." "Kaga Bebi don Allah ka nutsu, Wai kai ɓacin ranka kowa sai ya shafa? Meye haka ne wai?." "Mtsww! To me nayi musu ne? Naga aikina ne ko? Dan na yi aikina sai an yi min godiya?. Bana son takura suj je kawai ai nasan sun gode." Huzaifa yace, "sun ce baza su tafi ba sai sun ganka, sannan akwai maganin da kace min zaka rubuta musu, meyasa kake haka ne wai?." Ya sake jin takaici a fusace yace, "indai magani ne zan turo maka yanzu kaje ka siya musu. Bana son magana ka sani in raina yana a ɓace, domin duk abinda yazo baki na zan faɗa musu ne, don Allah ka ƙyale ni kawai bana son haɗuwa da kowa." Knocking ake yi hakan ya saka shi datse kiran yace, "yes." Aka buɗe ƙofar aka shiga ya hango Manal ta shigo ya dauke kai daga kallon dan ji yayi kan sa ya sara haka kawai bai san dalili ba, ta kalle shi a nutse tace, "Dr zamu tafi, Allah ya saka da alkhairi Mun gode." "Amin" ya amsa a taƙaice ya cigaba da abinda yake yi. A tsorace take itama tace, "Dr Huzaifa yace zaka bani takardar magani...." A fusace ya katse ta yace, "kije ki same shi zai naki, bana son magana bana son takura kije kawai!" Ya faɗa yana nuna mata hanyar fita. Sai da ta tsorata jin irin tsawar da yayi mata tayi baya tana kallon sa tace, "Allah ya baka haƙuri, baza mu iya tafiya bane ban maka godiya ba ka ceci ran mahaifiyarta wacce bani da kamar ta, koda dukana zaka yi bazan tafi ba sai na tabbatar na gode maka." Shiru yayi baice mata komai ba, amma ji yake kamar ya tashi ya tsinke ta da marin da zata daina gani, ya lura shegiyar maganar ta inda waje ɗaya suke zai iya sakawa ya mata dukan tsiya, ta juya tana tafiya ido ya ciko da hawaye. Da wata likita mace suka haɗu  tana fitowa tana shiga ita kuma ta wuce wajan Dr Huzaifa ta shiga da sallama ya amsa yana murmushi domin nutsuwar ta na burge shi sosai yace, "Manal zaku tafi ko?." Ta goge idon ta  zata yi magana yace, "ya dai? Ko jikin Maman ne?." "A'a babu komai." "Faɗa min mana, me ya faru kike goge hawaye?." "naje wajan Dr nan abokin ka mai glasses na yi masa godiya shine yake ya faɗa kamar zai dake ni." Yayi murmushi yace, "Kar ki damu ransa ne a ɓace na faɗa miki,  haka yake in ransa ya ɓaci baya son magana. Ga maganin ya bani duk zan baki in har tana sha komai bata zai dawo daidai hatta idanun ta zasu iya gani wani lokacin. Kema kuma zan baki naki ki tabbatar kina sha saboda ya daidai miki sugar jikin ki." Ido ta goge ta amsa yayi murmushi sai ya kalli maganin ya kalle ta yace, "ki jira ni a inda kuke zama zan je na kawo miki kafin ku tafi." Kafin tayi magana aka shigo taga likitan da suka haɗu  da ita a wancan office ɗin tace, "Huzaifa meyake damun Adnan yau?." "Kema ya koro ki ɗin ko?" Ya faɗa yana dariya. "Inda kaga zai min duka ma kuwa" ta faɗa  tana dariya  itama yace, "ran sane a ɓace kawai shiyasa." Ta girgiza kai tace, "lallai kam naga alama" ta faɗa tana fita shi kuma yacewa Manal su je suka fito ta koma ɗakin su shi kuma ya fita. Da maganin ya dawo ya shiga har ciki ya basu suka dinga masa godiya har Baba yace babu komai ai yiwa kaine. Bayan ya fita suma suka fita Manal na riƙe da hannun Mama Baba ya riƙe kayan suka fita harabar asibitin. Bebi yana tsaye yana kallon su ta window sai a lokacin ya tuna abinda ma yayi mata. Yayi tsaki yana kallon su har suka fita daga harabar asibitin daga nan ya daina ganin su. Yana nan tsaye Huzaifa ya shigo ganin ya juya baya yana kallon taga yace, "abinda kake yi ba daidai bane ba Bebi, bai kamata ɓacin ranka ya dinga shafar wanda bashi ne ya maka ba. Meye laifin yarinyar nan da tazo maka godiya? Don Allah?." Bebi ya juyo yana kallon sa da mamaki yace, "wai na tambaye ka, Yarinyar nan aure ta zakayi ne?." "In ma auren nata zanyi ai ba laifi bane ba ko?, bata isa na aure ta ɗin ba ko kuma ni ban kai matsayin auren ba?." Kallon sa yake yi kafin ya taɓe baki yace, "Ba laifi kam" ya faɗa yana sake juya masa baya. "Kai kasan ina da wacce zan aura bikina bai wuce kwanaki kaɗan ba, ina mata kallon ƙanwata ne har a jikina haka nake ji saboda yarinyar ta san abinda take yi, ina son naga wanda ya san mahimmacin mahaifiyar sa." Bebi ya sauke numfashi baice komai ba ya juyo ya kalli Huzaifa yace, "to naji mai tausayi, zaka iya bani waje?." Nan da nan ya hasala Huzaifa yace, "bazan fita ba ka fitar dani." Murmushi yayi ganin ya fusata baice komai ba ya zauna, lokaci ya tafi har magriba ta kusa sanin babu abinda zaiyi kawai ya tashi ya ya kalli Huzaifa yace, "in ka gama ka bada key ɗin a ajjiye min" ya faɗa ya fita ya barshi a tsaye cike da jin haushin sa. Mota ya hau ya fita abin mamaki sai ya hango su Manal a tsaye Maman su kuma tana zaune da alama babu abin hawa, har zai canja hanya sai ya fasa, ya ƙarasowa inda suke  ya tsayar da motar ya sauke glass daidai inda Baba yake yace, "Baba ku shigo na kai ku gida, wajan nan ba'a samun motar haya sosai daman." Baba ganin sa sai yayi murmushi yace, "ai kam ka kyauta likita, mun gode Allah yyi albarka. Manal riƙe Maman ki mu shiga?." Manal ta buɗe baya Mama ta shiga itama ta shiga Baba ya shiga gaba suka tafi. Jan motar yayi suka tafi Bebi yace, "hanyar babu jama'a sosai." Mama da take baya tace, "Likita Allah ya saka da alkhairi, Mun gode da taimakon da ku ka yi mana Allah ya biya ku." Ya amsa da amin Manal dai tayi shiru bata ce komai ba kafin Bebi yace, "Ku dinga zuwa asibiti duk bayan sati biyu ana gwada jinin ku sannan ana duba ki saboda matsalar zuciyar ki, sannan Mama sai kin daina ajjiye damuwa in ba haka ba ciwon ki bazai yi sauƙi ba." Mama tayi murmushi tace, "to likita na gode. Manali kina ji a dinga shan magani, likita itace bata son magani ko kaɗan, dana matsa mata sai ta fara min kuka dole na ƙyale ta." Baba yace, "da yake bakya son kukan ta ba." Mama ta sake murmusawa ta riƙe hannun Manal tace, "To nima ai bata son nawa kukan ne shiyasa bana son nata." Ɗago ido Bebi yayi ya kalle ta ta mirror sai yaga tana sake goge ido alamun kukan sannan gashi face ɗinta yayi ja alamun tayi kuka. Ɗago ido itama tayi sai suka haɗa ido ya janye idanun sa daga kanta dan yaga alama ta cika sangarta da yawa. Da yake Manal ta basu labarin har gıda ya kai ta basu yi mamakin ganin ya tsaya a bakin layin ba sai kuma ya kalli layin yace, "mota tana shiga?." "Ƙyale mu nan ma, Mun gode sosai" Baba ya faɗa yana kallon sa. "A'a muje ciki" ya faɗa yana shiga da motar daidai gidan Baba yace, "nan ma yayi likita, Allah ya saka da alkhairi yayi albarka ya raya zur'ia." Bebi yace, "Amin. Babu komai." Mama tace, "Gashi zamu fita ban san sunan ka ba, muryar ka kawai na sani." Bebi yayi murmushi yace, "Adnan." Mama tace, "mun gode sosai Allah biya" ya sake amsawa da Amin har lokacin Manal bata ce komai ba domin tsawar da yayi mata tana cikin kanta sosai, bata son sake masa magana ya wulaƙanta ta dan ba jurewa zata yi ba. Suka fita daga motar bayan juya motar yaga Manal ta shiga wani gida su kuma sun isa ƙofar gidan da yake a kulle da alama nan ne gidan, gama juya motar yayi amma ya kasa tafiya kawai so yake ta fito ya sake ganin ta dan yaga kukan take yi. Sai gata kuwa ta fito tana murmushi tana kuma magana ta isa ƙofar gidan ta buɗe suka shiga, ita kuma ta kwashe kayan ta shiga dasu. Kallon ta yake a bayyane yace, "shegen surutun tsiya ne da ita, ga shagwaɓa kamar wata auta." sai yaji babu daɗi akan abinda ya mata ɗazu, duk da ba laifin sa bane laifin tane, yayi ƙaramin tsaki yaja motar ya tafi. Nana Haleema🫶🏻🥂 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025   ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 Masu nema daga farko ku shiga wannan link din https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 017.*         Kai tsaye gidan Yayan sa ya wuce kamar yadda yace yana neman sa, kafin ya shiga sai da yayi sallar magriba sannan ya shiga cikin gidan ya samu matar sa da suke kira Anty Khadija tana zaune a falo, ya shiga da sallama sai ga yara guda uku sun tawo a guje ana masa oyoyo. Shi fuska babu fara'a sannan ga ɓacin rai hakan ya saka ɗan yayi murmushin da babu wanda ya lura ya riƙe  hannayen su yace, "baku zo gida ba ba ko?." Zama yayi sai ya kalli matar Yayan nasa suka gaisa tace, "wato dai Bebi ba'a ganin ka a gidan nan ko da ziyara sai da dalili." Yace, "kin san aikin namu, ko yaushe tasowa yake babu excuse." "Haka ne kam, Allah ya taimaka ya bada nasara. Ai tunda yaran nan suka ji zaka zo shikenan ake murnar ganin ka." Yayi dariya yana kallon su yace, "gashi yau ban zo da chocolate ba ko?." Babbar ciki tace, "zamu je a siyo ko?." Ya ɗan saka sakin fuska yace, "to sai a siyo." Matar Yayan nawa ya sake kallo yace, "Ina Ummi?." "Tana ciki tana aikin karatu wai debate zasu yi Monday a school tun yau take ta practice." "Ta kyauta." "Khalifa kira Yaya" ta faɗa tana kallon ɗaya daga cikim yaran, ai kuwa ya shiga a guje sai gasu tare da matashiyar budurwa wacce zatayi shekara sha huɗu zuwa sha biyar sun fito tace, "Lah Yaya Adnan." Kallon ta yayi tace, "ina wuni." "Lafiya lau, ya school?." "Lafiya lau yaya." "Yayi kyau" ya amsa kawai tana tsaye a wajan mahaifin nasu ya shigo. Ganin Bebi sai yace, "A'a Alhaji Adnan ko nace Bebin Mummy, ashe kazo?." Anty Maimuna tace, "ya kamata ku ajjiye Bebim nan don Allah, haka zai aure kuna ce masa Bebi kamar wata ƴar tsana?" Ta faɗa tana dariya. Bebi yace, "sun kasa ajjiye suna, tun ina jin haushi har na gaji da magana." Yaya yayi dariya yace, "zo muje mu tattauna. A kawo mana abinci." Tare suka fita zuwa nasa falon suka zauna ya kalli Bebi yace, "yarinyar nan ce tazo min da maganar wani yaro Mujahid ɗazu, sai nace ai kai zata samu da maganar sai take cemin wai kace baza ta aure shi ba bayan ita kuma tana son sa. Nasan kana da hujja shiyasa nace bara na kira ka naji meye dalilin ka." Bebi yace, "Yaya in wanda muka haɗa kai dashi aka buɗe asibitin nan namu dashi?." Yaya yace, "wanda ku ka raba hanya daga baya kenan." "Yauwa, shine to yake sonta. Ba kuma dan komai ba sai dan ya ɓata min rai kamar yadda yake ganin nayi masa." Yaya yace, "Wai wannan wanda yaso ɓata muku sunan asibitin?." "Shifa Yaya, inda da gaske yana son tane sai a bashi auren ta amma wallahi ba sonta yake ba, ya nemi Mimi taƙi sauraron sa shine ya dawo kan Lubna kawai dan ya samu damar da zai rama abinda na saka aka yi masa." Yaya yace, "Ai ko yana sonta ai ba mijin aure bane, wanda aka kama yana neman marasa lafiya ta hanyar banza meye amfanin bashi aure?." Bebi baice komai ba Yaya yace, "ai an soke wannan maganar gaskiya, abinda akayi kayi daidai in ka sake ganin su tare kayi mata dukan tsiya." A lokacin Ummi ta kawo musu abinci ta ajjiye ta fita Bebi yace, "ni na kai Kamal ƙara hisba fa Yaya, yaƙi rabuwa da Maryam ko yaushe yana zuwa wajan ta da rashin dalili, taƙi fahimta, yaƙi fahimta. Na kai shi hisba anyi mana iyaka dashi, abin mamakin a gabana yake cewa shi babu niyar mayar da ita auren ta koda an samu damar hakan." Yaya ya girgiza kai yace, "Wannan fa laifin maryam ne Adnan itace ta bashi dama wallahi, da bata bashi dama ba da bazai yi ba itace take biye masa har yake zuwa wajan ta. Da yazo ta kore shi, ya sake zuwa bata je ba, bazai sake zuwa ba saboda ta riƙe mutuncin ta, amma da yake bata da hankali wai har shiga motar sa take yi.  Hakan da kayi shima daidai ne Adnan Allah ya cigaba da baka ikon yin abinda kake yi." Ya amsa da amin yace, "Daman ɓacin rai bai barni naci abinci ba" ya yana buɗe abincin yaga dambun shinkafa ne sai farfesun nama a gefe. Rufe naman yayi ya zuba dambun ya fara ci Yaya ya kalle shi yace, "ashe fa kai baka cin nama, gaskiya ka bar daɗi." Murmushi yayi kaɗan yaci dambun sosai, dan  ya masa daɗi suna hira da Yayan nasa kafin ya gama ya fita yaje mota ya tafi gida dan ya gaji sosai.        ****** Su Manal bayan sun shiga gidan ana ta kiran sallah hakan ya saka Mama zama a tsakar gidan tace, "bani ruwa nayi alwala Manal." Manal tace, "Mama tsakar gidan yayi dauɗa kika zauna." "Ke bani ni, abinda a cikin ƙasar za'a saka mu wata rana." Manal ta ɗauko buta zuba ruwan ta kaiwa Mama ta fara alwala Baba yace, "nima zanje sallah na dawo" ya faɗa yana fita Manal ma ta fara alwala duk da tana jin ciwon kai. Bayan Mama ta kammala tace, "ɗauko min sallaya nayi a nan kawai, babu wuta ciki zafi zaiyi." Da to ta amsa ta ɗauko ta shimfiɗa mata ta itama ta saka tata ta yayar da sallar. Bayan ta idar Maman ma ta idar Manal tace, "Mama me za'a dafa miki?." Mama tace, "basai muna da abincin ba, duba ki gani in akwai ɗin dan yunwa nake ji kamar ban ci abinci ba ɗazu." Tana niyar tashi Baba ya shigo bai ƙarasa shigowa ba sai ga Maman Surayya a bayan sa da Surayyan riƙe da babban kula suka shigo. Maman Surayya tace, "Maman Manal Sannu, kin sha jiki." Mama jin muryar ta sai tace, "bari kawai, sai dai muce alhamdulillah." Manal tace, "Mama, Baba, kullum Mama ce take bawa Surayya abinci kai mun mai yawa. Wani lokacin in Surayya ta tafi makaranta aika min take dashi, abincin na dinga ci har kawo yanzu." Baba sai yaji wani iri cikin takaicin halin mata sa yana da abinci ba babu ba amma matar sa na kwance asibiti babu wanda ya je inda take balle yayi tunanin basu abinci yace, "Allah ya saka da alkhairi." Mama tace, "Haba dai, babu komai wallahi da Manal da Surayya duk ɗaya ne a wajena." Mama da take zaune tace, "Godiya ta zama dole ai, Allah ya saka da alkhairi. Ni daman na san ko babu raina Manal tana uwa." Maman Surayya tace, "haba don Allah ki bari, Kamar yadda kika ce ni uwa ce a wajan Manal, babu godiya a tsakanin mu ya kamata ace mun wuce wajan nan tun ba yau ba." Surayya ta ajjiye abincin tace, "Milky ga abinci nan kin huta girki." Manal zatayi magana Maman Surayya tace, "ke bana son ki ce min komai. Surayya tashi muje Allah ya ƙara lafiya yasa kaffara ce." Mama ta amsa da amin tana mata godiya sosai sanma suka fita. Manal ta tashi ta ɗauko plate ta buɗe abincin sai kuwa taga tuwon alkama ne da miyar ganye ta zubawa Maana tace, "Mama kinga tuwon alkama suka kawo mana, kuma kin san Mama daman ko za'a kai min abincin a can har salad sai an saka saboda lalura ta." Mama tace, "Ai Balaraba mutum ce wallahi, tun kuna yara muke tare har yanzu bata ƴar dani ba. Kaf unguwar nan bani da kamar ta, jin ta nake kamar Yayata komai abu ya taso min ita nake faɗawa." Manal ta fara cin na Maman tace, "kuma Mama akwai wani ma, Baba ma zai iya ci har mu ajjiye da safe mu ci." Mama tace, "Allah Sarki, da yawa haka suka kawo?." "Wallahi" ta faɗa tana cin tuwon itama Maman tana ci. Ganin duhu yayi sai Manal ta tashi ta ɗauko  fitili ta kunna a tsakar gidan ta dawo suka cigaba da ci har suka gama suka wanke hannu suna nan zaune har akayi i'sha. Bayan i'sha ne sauro ya dame su a tsakar gidan dole suka koma cikin falon a lokaci. matan Baba suka shigo da sallanma,  a ciki Mama da Manal suka amsa suka zauna Umma tace, "Ya jikin?." Mama tace, "da sauƙi." "Allah ya ƙara Lafiya" Inna ta faɗa Manal ta amsa da amin daga haka suka tashi suka fita. Mama tayi murmushi bayan ta fita bata ce komai ba Manal da take kallon ta tace, "Umma da Inna basa son mu Mama. Ranar da baki da lafiya da naje wajan su na faɗa baki ga abinda suka min ba, ni wallahi duk na tsane su." Mama bata ce komai ba Baba ya shigo da sallama Manal ta amsa bayan ya zauna tace, "Mama akwai tuwo da aka kawo na ɗauko maka?." Baba yace, "A'a kuci, su Umman ki sun shigo?." Manal tace, "eh sun zo." "Su suka kawo tuwon?." "A'a maman Surayya ce." Yayi tsaki zai tashi Mama tace, "Alhaji ka ƙyale su don Allah, mu mun ƙoshi ma munci  tuwon alkama da aka kawo mana ka barsu kar rai ya ɓacı." Kafin ya bada amsa Mama ta ace, "Mubeena a ina take kwana ne?." Baba yace, "dana dawo nayi mata waya bana samun ta, Manal ke kina samun ta?." Manal ta girgiza kai alamun a'a Mama tace, "me yarinyar nan take son zama ne? Ko asibiti bata je bafa inda nake, me take so ta zama? kashe ni take so tayi?." Baba yace, "kiyi haƙuri, ƙuruciya ce amma ki cigaba da mata addu'a." "Yayar Manal ce fa, meyasa ita bata yi abinda take yi?. Wallahi na mutu a yanzu na tabbatar da baƙin cikin ta na tafi lahira. Yarinya kamar mai kunnen ƙashi? Tsakani da Allah a ina take kwana? Tana da inda ya wuce gidan ka ko gidan su Surayya ne?." Baba yace, "Haba Zahra! Wannan maganar bata kamace ki ba, addu'ar  da kike mata ko yaushe ita zaki sake dagewa a kai, wannan kalaman da kike babu abinda zasu gyara sai dai su ɓata, don Allah ki kwantar da hankalin ki kina jin abinda likita yace akan saka damuwa a zuciyar ki. In dai kina yi mata addu'a nan da lokaci kaɗan zaki ga canji a rayuwar ta." "Damuwa da ita zan mutu ai indai akan Mubeena ne, yanzu tana ina? A ina take kwana don girman Allah?." Baba ya kalli Manal da ta fara hawaye yace, "kira wayar ta." Manal hannu na rawa ya ɗauki wayar ta sai kuma tace, "bani da kati" ta faɗa murya na rawa. Baba ya ɗauko naira ɗari biyu ya bata yace, "siyo a kanti Bala kizo ki saka, in baya nan kar kije ko ina ki dawo wayata na bayar chaji." Karɓa tayi ta ɗauki Hijjabai ta fita. Ba jimawa ta dawo ta shiga da sallama tace, "Baba na saka katin." "To maza ki kira ta." Ba Musu ta kira ta amma bata ɗauka ba ta sake kira ba'a ɗauka ba sai tace, "bata ɗauka, gashi bani da number Bily ƙawar ta na tabbatar daƙyar in basa tare." Mama ta girgiza kai tace, "kace kuma kar na damu?, in ban damu ba me zanyi?. Sati ɗaya bana gida ban san a inda yarinya take kwana ba ba dole na damu ba. Mubeena! Mubeena!! Hmmmm" ta faɗa kawa bata ce komai ba ganin hakan sao Manal tace, "Baba bara naje gidan su Surayya na dawo" ya amsa mata ta fita dan tana so ta basu waje ne ya rarrashi Mama. Tana fita Baba yace, "Kiyi haƙuri  mana, ki cigaa dayi mata addu'a zata yi hankali in sha Allah." "Halin uban ta tayi ne kawai, bazata taɓa gyaruwa ba kamar yadda nasan bai gyara ba har kawo gobe in dai yana da rai. Ya cuce ni, ya saka ƴata tayi gadon halin sa tsiya." "Wai ba magana nake miki ba? ina miki magana kina sake karkacewa, Meyasa baza ki haƙuri kiyi abinda nace ba?, yanzu wannan maganar itace zata gyara Mubeena ko ita zata saka ta dawo? Meyasa baza kice Allah ya shirye ta bane?." Mama tace, "Allah ya shirye ta." Ta faɗa tana Jan numfashi Baba ya dinga rarrashin ya har ya samu ta ɗan sauka amma shi Kansa zuciyar sa cike yake da son sanin inda Mubeena take.        Manal a gidan su Surayya ta zauna suna hira sai da tara na dare tayi sannan ta dawo gida ta tarar Mama har tayi bacci Baba ma yana falon sa na tsakar gida. Zama tayi bayan ta cire kaya ta ɗauki wayar ta tana sake kiran number Mubeena amma bata ɗauka. Katin da Baba ya saka mata ta siyi datar naira ɗari ta shiga WhatsApp rabon ta dashi har ta manta kasancewar babu wani abu a kai babu messages ɗin kirki duk yawanci groups ɗin makaranta ne, duba lambar Mubeena ta ganta online. Magana tayi mata ta zauna jiran amsa shiru bata amsa ba kuma tana ganin ta online sai ta tura mata voice note tana cewa, "Duk abinda ya samu Mama akan tunanin ki Yaya Allah bazai barki  ba nima bazan yafe miki ba wallahi, kwanan Mama bakwai a asibiti amma sau ɗaya kika je, inda babar su Bily ce da kullum kina can dan ki faranta mata rai. Bakya kwana ma a gida baki san halin da take ciki ba, wallahi ki kiyayi duniya domin tana gab da kai ki ta baro ki" tana gama faɗa ta tura mata ta kashe datar tayi lamooo tana tunani. Mama na jin ta duk abinda take cewa tayi murmushi ta share hawayen idanun ta cikin so da ƙaunar ta, babu yadda zata iya haɗa matsayim Manal da Mubeena a zuciyar ta, ta ko wanne ɓangare ita ɗin ta daban ce. Abinda yake tayar mata da hankali yanzu a ina Mubeena take kwana?. Mubeena kuwa duk kiran da ake mata tana gani kawai bata yi niyar ɗauka bane, lokacin da Manal take mata message tana kan yin waya da Baby shiyasa ma bata bi ta kanta ba hankalin ya yana ga soyayyar sa da ta gama mamaye mata jikin ta cikin lokaci kaɗan. Bata iya tsallake duk abinda tace saboda kar ransa ya ɓaci kamar yadda shima a nasa ɓangaren yake jin ta a jikin sa har ya ƙagu ya dawo kawai saboda ya ganta. Daga can ɓangaren yace, "Baby." Ta amsa da cewa, "Na'am Baby." "Gobe zan dawo me zaki tanadar min?." Tayi murmushi tace, "abinda ka ke sl." Yana kallon ta tana kallon sa kasancewa video call yace, "ni ke kawai nake so." "Ni ai taka ce Baby." "Ina so goben ya kasance na musamman, da fatan a ɓangaren ki hakan zai kasance ko?." Tayi murmushi tace, "sosai ma kuwa." Murmushi ya mata tace, "Wai kuwa Baby matan ka nawa? A ina kake da zama?." Yayi ƴar dariya yace, "sai yau kika tambaya?." "Sai yau naji ina so na sani." "Mata na biyu, yarana takwas. Maza uku mata biyar." "A ina suke zaune?." Yace, "mu bar zancen nan Baby, ni yanzu ki ji dani kawai." Tayi dariya tace, "to me kake so?." "Ke mana. Da zan zamu abinda nake so gobe ina sauka daga lagos na ganki a gidana a zaune da nayi farin ciki." "Kar ka damu zanyi abinda ka ke so." "Da gaske zaki zo?." Ta amsa masa da Uhum ya dinga murna yana farin ciki a haka suka raba dare suna waya kafin ta kashe ta tashi daga falon ta koma ɗakin Bily tana zaune tana karatu, ta wuce ta kwanta bata ce mata komai ba itama bata ce mata ba. Nana Haleema❤️🫶🏻 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025   ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 Masu nema daga farko ku shiga wannan link din https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 018.* Da safe Mubeena da wuri ta shirya ta taho zuwa gida, lokacin da ta shiga gidan Mama da Manal suna zaune kamar ko yaushe suna cin abinci a kwano ɗaya da alama sai lokacin suke karyawa. Yatsine fuska tayi ganin tuwo ma suke ci abinda ta tsana gabaɗaya  a duniya, ta ƙarasa da sallama Mama na jin maganar ta taji hankalin ta kwanta amma bata nuna ba har ta ƙaraso ta zauna tcae, "Mama ina kwana, ya jikin ki?. Naje asibitin lokacin kina kwance kina bacci gashi muna da jarabawa a makaranta shiyasa ban dawo ba." Mama kamar tana kallon ta tace, "ki dinga jin tsoron Allah Nusaiba, ba haka mahaifiyata take ba, a ko yaushe in na tuna sunan ta kika ci ina dana sanin saka miki sunan ta a rayuwata." Mubeena ya zauna tana zunburo baki tace, "Mama nace makaranta naje fa, kuma me nake yi don Allah?." Mama tace, "babu abinda kike yi Mubeena, komai kike yi daidai ne." Ta kalli Manal da take kallon ta itama ta zabga mata harara Manal ta taɓe  baki bata ce komai ba. Baba ne ya shigo ya shirya da alamun tafiya wajan nema ganin Mubeena sai yace, "A'a Mubeena." "Na'am Baba, Ina kwana" ta faɗa tana gaishe shi ya amsa yana faɗin, "ina kika shiga?." "Baba makaranta ce fa ta ɓoye ni, kuma ina nan zoo road gidan su Bilkisu ƙawata a can nake kwana saboda tare muke karatu." Baba yace, "Allah ya taimaka, zo ina son ganin ki" ya faɗa  yana yin cikin gidan ta tashi rai a ɓace ta bishi ta zauna yace, "Mubeena shi wannan rawar kan da kika saka a gaba ba komai zai amfana miki a rayuwa ba face dana sani, mu da kike rainawa kina ganin baki dace ace iyaye ki bane saboda kina da kyau mune gatan ki yanzu da nan gaba. Ɓacın ran da kike sakawa mahaifiyar ki kema ganin ki shine burgew?kin san da ɓacin ranki a ciwon zuciyar babar ki? Kin sani?." Mubeena tayi shiru batayi magana ba yace, "Ki bi duniya a sannu, shi kuɗi da kike gani ba komai bane face takardar, ba kowa Allah yake bawa ikon amfanar ba sai wanda y zaɓa. In kina ganin mahaifiyar ki bata dace dake ba saboda tana da lalaurar ido da kuma tana aurena saboda bani da kuɗi kuma sannan itama bata da kuɗi kin yi kuskure, baki san wacece mahaifiyar ki ba, in zancen kuɗi ake kafin a lisaafo wanda kike bi saboda kuɗi za'a lissafa ta a jerin su. Koda yake ke ba wannan lissafin kike ba, baza kuma ki gane inda na nufi  a yanzu ba wataƙika sai nan gaba. Abinda nake so dake Mubeena ki nutsu kiyi hankali ki tabbatar da abinda kike aikawa ba burge bace ko kuma darajar ki bane, babu inda wannan hali zai kai sai tashar dana sani." Mubeena bata ce komai ba tayi shiru ya miƙe yace, "nasiha nake miki matsayin uba a wajan ki, in kin ɗauka Mubeena ke zata amfana, in baki ɗ'auka ba shima ke zata cuta. Allah yana gani ina iya bakin ƙoƙarina wajan na miki tarbiyya mai kyau, na barwa Allah lamarin ki ina kuma faɗa masa kullum. Ki sani haƙƙin mahaifiyar ki ba zai bar ki ki zauna lafiya ba, ba kuma zai bari ki samu abinda ki ke so ba. In ma yawo ki ka fara ki sani kafin ke anyi irin ki dubu, babu wacce tayi riba a yawon banza, a ƙarshe da ciwo suke ƙarasa rayuwar su a wulaƙance" ya faɗa yana fita. Baki ta turo bayan ya fita ta fito tsakar gidan ta zauna tana kallon su kamar basu san tana wajan ba saboda babu wanda ya tanka mata. "Assalamu alaikum" aka faɗa ana shigowa duk suka juya a tare ita da Mubeena. Manal ganin wanda ya shigo sai tayi dariya tace, "Laaa Yaya Harun." Dariya yayi shima ya ƙaraso yace, "Manal." Mama jin muryar haruna sai tayi murmushi tace, "Mutanen ƙasar Riyad ne a tafe kenan." Yayi dariya ya zauna kusa da Mama yace, "mu ne wallahi Mama, ina kwana." "Lafiya lau Haron, saukar yaushe?." "Ɗazu da safe nazo, ashe bBaba bai faɗa miki ba." "Ya sha'afa. Ya hanya?." "Alhamdulillah Mama, ya ƙarfin jikin? Baba yace jiya kika dawo gida daga asibiti." Mama tace, "Da sauƙi Haruna, naji sauƙi sosai." "Allah ya ƙara Lafiya" ta amsa da amin ya kalli Manal yace, "nifa fushi nake dake ko kiran wayar nan ma bakya yi ki nemi." Tayi dariya tace, "wayar tawa ce sai a hankali Yaya, ba wani damuna tayi ba ko datar na saka na shiga na kalli video abinci na kashe shine aikina." "Daman ke ai babbar mai dafa mana abinci ce." Sukayi dariya a tare ya kalli Mubeena da bata ma san ya shigo ba kamar zai mata magana sai ya share ta ganin ta kawar da kanta gefe. Ji tayi yana kallon ta a jikin ta sai tace, "Sannu da zuwa" ya amsa bai kalle ta ba ya saka hannu aljihu ya ɗauko waya ya miƙawa Manal yace, "ga waya na tawo miki da ita a cigaba da kallon abinci, shiyasa na bayar a gaban Mama nasan zaki ce Mama baza ta bari ba" ya faɗa yana kwaikwayon muryar ta sai sukayi dariya har Maman. Mama tace, "Haruna harda hidima haka? Waccan wayar ma kai ne ka bata fa." "Babu komai Mama, Manal ai ƙanwata ce da nake ji da ita." Manal ta karɓi wayar tana duba ta cikin murna tana kallon jikin wayar, baƙa ce ta gabaɗayan baya an saka Samsung S10. "Na gode sosai Yaya,Allah ya saka da alkhairi ya kai mu bikin ka mu sha biki." Yayi dariya yace, "Amin Manalin Mama, sannan duk sanda datar ki ya ƙare ki faɗa min zan saka miki ki cigaba da kallon abinci, dan so nake ki iya sosai nan gaba ki zama shararriya a duniya." "To Allah ya biye bakin ka Yaya." "Amin ƙanwa, zan saka a duba makarantar koyar da girki ma ki fara shiga tun yanzu. Akwai wacce na biiya miki online ma wajan wata Leemars_Delicious, ta iya girki ina ganin ta a Ig shiyasa da naga zatayi online classes sai na tura mata kuɗin, zata saka ki a group ki koya da kyau ƙanwata." Mama tace, "A'a Haroun kar hidimar tayi yawa kuma." "Haba Mama, Manal da ƙanwata ce dan nayi mata ai ba komai bane." Mama tace, "haka ne, Allah ya saka da alkhairi." Ya amsa da amin. Wayar Mubeena aka kira ta ɗauka wayar ta duba ganin mai kiran sai bata ɗauka ba, hanyar fecewa kawai take so ta samu amma babu dama. Haroun ne ya kalli wayar hannun ta amma sai bai yi magana ba  fa tashi ta shiga falo shi kuma yau sallama ya fita. Haka ta kai bayan azahar a gidan gabaɗaya a takura take gashi tana ta kiran Baby bai ɗauka ba duk ya damu. Sai da akayi sallar la'asar sannan taga message ɗin sa an saka, _Sorry baby, kina ta jira na ko? Na dawo ina gida a kwance bana jin daɗi sosai Baby. Kizo ki ganni._ hankalin ta ya tashi sosai ta kira shi a lokacin ya ɗauka tace, "Baby me yake damun ka?." Murya can ƙasa yace, "Zazzaɓi ne Baby, gashi ina gida ni kaɗai ko abinci bansamu naci ba." "To baby ka saka ayi maka take away mana." "Babu kowa Baby, ban san ya zanyi ba ji nake kamar zan mutu." Cikin tashin hankali tace, "to yanzu ya za'a yi?." "Ki zo ki ganni Baby, ganin ki kawai zai saka naji daɗii." Shiru tayi bata amsa ba yace, "amma in baza ki iya zuwa ba ki damu babu komai." Mubeena tace, "A'a zan zo, sai dai bazan jima sosai ba kaga yamma tayi." "Okay Baby, gashi babu kowa balle ma turo a ɗauke ki. Bara na kira driver na duk inda yake yazo ya ɗauko min ke." Ta amsa da to ta kashe wayar tana tunanin ta wacce hanya zata bar gidan su.      Mubeena da ta fito daga ɗaki ta ga Mama ita kaɗai zaune da alama Manal  gidan su Surayya sai tace, "Mama an yi mana  kiran gaggawa daga makaranta zanje na dawo." Mama tayi tsaki tace, "tambaya ta kike daman in zaki fita Mubeena? Wacece ni da zaki nemi izinina?." Mubeena tace, "Mama kiyi haƙuri in dan na kwana a gidan su ƙawata ne kike fushi dani." Mama bata ce komai ba tayi mata banza Mubeena tasan bazata cs komai ba hakan ya saka tace, "Mama zanje na dawo yanzu" tana faɗa ta fice bata ma jira mai Maman zata ce dan driver ya fara yimata waya. Tana fita ta ɗauki wayar ta sakaa kunne tana yin titi da sauri. A lokacin Manal da Haruon suna tsaye suna kallon ta yace, "Manal waye ya bawa Mubeena wannan wayar ta hanun ta?." Manal tace, "Wallahi ban ma kula da wayar hannun ta ba." Haroun ya girgiza kai yace, "babar waya ce sosai fa, a hannun yaran masu kuɗi ma bata da yawa saboda bata jima da fitowa ba, kuɗin ta yayi miliyan uku da wani abun wallahi." Gaban Manal ya faɗi tace, "Yaya miliyan fa? A ina Yaya ta samo ta? Ko dai sata tayi ko kuma ta ƙawar ta Bily ce?." Ya girgiza kai yace, "bama ce ba, amma zan faɗawa Baba maganar dan wannan ba abinda za'a bari bane, shi ya tambaye ta a ina ta samu wayar." Manal cikin tsoro tace, "ni na fara jin tsoro." "Kar ki damu, kar ki sanar da Mama wannan ki bari na faɗawa Baba." Jiki a sanyaye ta amsa yace, "jeki gida na tsayar dake" ta amsa da to ta juya ta tafi tana tunanin waye ya bawa Mubeena wayar fin naira miliyan 3?. Bebi kuwa ranar bai samu ya fita da wuri ba dan daren jiya sai dare ya dawo gida saboda theater da suka yi a babban asibitin Murtala. Bayan ya tashi daga Murtala asibitin su ya wuce, yana shiga kawai sai Manal ta faɗo masa a zuciya musamman inda take tsaye tana yi masa murmushi a lokacin da ransa yake ɓace bai tsaya ya saurare ta ba ya wuce. Numfashi ya sauke yana inda yake tsaye yace, "gabaɗaya taƙi barin tunanina." "Wacece taƙi barin tunanin maka?" Hamza ya faɗa yana kallon sa ya juya ya kalle shi yace, "har ka fito kenan?." "Mun fito, sai yanzu ka shigo?." "Uhum, na jima a can ne kuma kasan jiya muna team work shiyasa ban samu ma na fita da wuri ba." "Wacce taƙi barin tunanin naka naji kana maganar? Kodai an samu madadin Rumana ne?." Bebi ya girgiza kai yace, "bana ce ba, haka kawai na kasa mantawa da ita musamman....." sai kuma yayi shiru yace, "forget it kawai. Ina Huzaifa?." Huzaifa da yake tunkaro wajan yace, "gani, da labari ne?." Hamza yace, "akwai labari, da alama wata ta kama zuciyar Bebi fa." Huzaifa yace, "haba don Allah, da gaske?." "Wallahi da gaske, shi kaɗai naji yana zancen ya kasa mantawa da ita kuma shima ya faɗa min." Huzaifa yayi dariya yace, "Wacece wannan Bebi?." Kallon Huzaifa yayi kafin yayi magana ya riga shi yace, "kamata yayi kayi hanzarin ko wacece a yi a wuce wajan saboda damuwar Rumana." Bebi yace, "nifa bance son ta nake ba, kawai dai na kasa mantawa da ita ne, nasan kuma saboda abinda nayi mata ne bayan wannan babu komai" ya faɗa yana barin wajan ya ƙarasa inda office ɗin sa yake ya shiga duk suka biyo bayan sa. Bebi ya kalle su yace, "ina da wanda zasu zo nan fa meye na biyo ni?." "Sanar damu zaka yi wacce wannan ta kamo zuciyar ka haka?." Bebi yace, "ku bari na tabbatar sai na faɗa muku amma yanzu ban tabbatar ba." Buɗe ƙofar akayi aka shigo da takardu Bebi yace, "kun gani ko? Patients ɗina sun zo sai anjima" ya faɗa yana karɓa ya zauna suka fita ya fara duba mutane. Sai bayan ya kammala sannan yayi shiru yana tunani zuciyar sa na bugawa a hankali da ya rufe ido fuskar Manal yake gani musamman ranar da ta saka black hijab tana dariya. Numfashi ya fesar daga bakin sa yace, "wai me hakan yake nufi ne? Daga ɗan sabawa da ganin ta sai na fara tunanin ta? Meyasa na kasa mantawa ne?." Glasses ɗin idon sa ya cire ya ajjiye amma bai daina jin wannan bugun zuciyar ba yayi shiru ya zubawa waje ɗaya ido yana kallon inda ta zauna ya saka mata magani a ƙafar ta. "Oh my god!" Ya furta a hankali ya rasa ma tunanin da zaiyi yaji daɗi. A cikin asibitin yayi sallar magriba ya tashi ya buɗe window yana kallon masu shigowa da fita iska na shigowa kaɗan da khamshin ganyayyaki. "To wai har magana sau nawa muka yi ne da zan saba da ita haka? Adnan me kake yi ne?" Ya faɗa yana sake kulle ido ya buɗe sai ya kulle window ɗin ya ɗauki key na mota ya fito ya shiga ya tafi gida. **** Mubeena tayi mugun tsorata tana zaune tana kuka da shima yana kusa da ita yace, "Haba Baby, meye na wannan damuwar haka? Kawai hug ne da kiss ba wani abun kika yi ba, kuma gashi kin taimaka min na samu Lafiya amma meye na shiga damuwa haka?." Mubeena tsoron ta ya riga ya gama bayyana ƙ'arara tace, "Ba abinda kace zanyi ba kenan, ni dai gaskiya banji daɗin hakan ba, bamu yi hakan da kai ba. "Nima ban san hakan zata faru ba ai Baby, shauƙin son ki ne ya warkar min da rashin Lafiya, da kuma murnar maganin ki kusa dani shine har hakan ya faru. Amma babu komai kar ki damu, baza'a saka ba wannan ɗin ma kuskure ne." Mubeena jikin ta gabaɗaya ya gama yin sanyi ta kalli danƙwalin ta da yake gefe da mayafin da ta sako yace, "muje kiyi wanka ko?." Ta girgiza kai tace, "A'a sai naje gida." "Kiyi a nan, in kika bari sai a gida za'a ce wankan me kika yi kina dawowa daga unguwa, nan yafi kwanciyar hankali tashi muje" ya faɗa yana riƙo hannun ta suka ƙarasa inda banɗaki yake yace, "ki shiga kiyi wanka da kin fito sai a kai ki." Kai ta daga ta shiga ciki yayi murmushi bayan ta shiga yana shafa fuskar sa a bayyane yace, "Yarinyar nan tayi, laushi jikin ta kamar mage, ga wani daddaɗan khamshi da take yi, zaƙin bakin ta kuwa kamar alawa. Wow komai yaji akwai halitta kam a tare da ita, Ta ya zan bari wannan ta kubce min?" Ya faɗa yana murmushi tuna yanayin da ya shiga ina kuma ga anyi mai gabaɗaya. Yana zaune ta fito kamar ma bata yi komai ba dan ta mayar da kayan ta tun a banɗakin ya kalle ta yayi dariya yace, "muje a sauke ki." Ya ƙaaraso kusa da ita ya riƙe kafaɗunta yace, "bana son wannan damuwar da nake gani a fuskar ki, Haba mana Baby ba fa wani abin muka aikata ba na faɗa miki, da nayi miki wani abun da yanzu kin ji a jikin ki kema. Ki kwantar da hankalin ki wannan ma soyayya ce ba laifi bane dan kin nuna min yadda kike shauƙin sona. Kefa wayayyiya ce Baby ban ɗauka wannan zai dame ki ba, ina ganin ki big girl ya kike so ki mayar da kan ki baya?." Mubeena tace, "Nidai bana so kawai, kar a sake maimaitawa." "An gama ranki ya daɗe" ya faɗa yana mata jinjina suka fito tare ya saka a kaita har gida shi kuma yana jin farin ciki sosai a zuciyar sa. Sai bayan ta tafi sannan ya hau mota shima ya nufi gidan iyalan sa, yana fakawa kai tsaye ɓangaren sa ya wuce bai nemi ko wacce a cikin su ba har garin Allah ya  waye. Bebi da wuri ya tashi ya yi wanka ya fito zuwa ɓangaren Mama bai ma san Abba ya dawo ba sai a lokacin yaga motar sa ya shiga wajan Mama yana cewa, "Mummy yaushe Abba ya dawo?." Mama da take zaune ta kalle shi tace, "au ya dawo?." "Yanzu naga motar sa a ajjiye." "Ban ma sani ba" ta faɗa ban tare da ta kalle shi ba. Ya zauna ta kalle shi tace, "Ka tashi ka ɗauko abinda zaka ci babu mai yi maka jeka ka dawo bacci suke yau." Yayi dariya kaɗan baice komai ba Mama tace, "Murmushi yana yi maka kyau Adnan amma gaba kake yi dashi, kai kullum fuska a haɗe kamar mala'ikan mutuwa. Shiyasa ake fassara ka a mutum mara kirki, dariyar ma sai ka saba da mutum ka ke yi." Yayi dariya yace, "to Mummy kawai sai na dinga dariya kamar wani mara hankali?." "Lallai, mu da mu ke yi duk bamu da hankalin kenan ko?." Ya wara ido yacec "Ni na isa?." "Sak Alhajin mu kayi, shima bashi da fara'a sai kun saba zaka ga dariyar sa, amma in baku saba ba kallo ɗaya zaka ce bashi da kiri. Allah ya jiƙan sa." Ya amsa da amin. Tashi yayi ya shiga kitchen ɗin sai gashi ya fito da kofi a hannun sa yace, "Mummy ashe anyi min kunu." "Eh gashi nan nayi karanbani nayi maka, Allah yasa kar a sake bani kunya ace babu daɗi." Ya zauna yana dariya yace, "ai yayi daɗi matuƙa." Tayi dariya bata ce komai ba shi kam kallon ta yake gabaɗaya tausayi suke bashi saboda halin da mijin su ya saka su a ciki. Mama ta katse masa tunani tace, "Da alama Mimi saurayin nan mata dai yayi mata Bebi." Yace, "na tura shi wajan Yaya ni maganar ya bar hannun kuma ai." Mama tayi shiru kafin tace, "ya zancen Lubna ɗin?." Yace, "na sanar da Yaya komai akan waye wanda take so ɗin ya tabbatar da bazai bari ta aure shi ba." Mama tace, "Bebi kana da saurin fushi amma na rasa meyasa ka kasa fushi akan lamarin su Lubna." Yace, "Mummy ai ba dan su nake yi bane shiyasa" ya faɗa yan ajjiye kofin ya tashi yace, "zan tafi Mummy." "Shikenan har ka ƙoshi?." "Eh, in naje zanci abinci." "To sai ka dawo, kofin an barni a ɗauke ko?." Ɗaukar kofin yayi yace, "Tuba nake." Ta Harare shi tace, "yau ka saba?, a ɗauko maka kuma a ɗauke maka, dan gata. Shiyasa in na tura ɗakin ka plate ɗin da na manta dashi ma zan ganshi." yana ji murmushi yayi kawai ya fita daga falon. Wajan Abba ya shiga amma bai ji motsin sa falon ba hakan ya saka shi fitowa ya hau mota ya tafi. Nana Haleema🫶🏻 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025   ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 019* Mubeena haka ta kwana a gida gabaɗaya babu walwala, Manal na lura da ita ta share ta kawai dan haushin ta take ji sosai. Sai da safe Baba ya shigo sun gaisa ya kalle ta tana zaune da wayar a hannun ta yace, "Mubeena zo ɗakina ki same ni yanzun nan." Haushi taji a zuciyar ta tana tunanin yanzu to me kuma tayi, haka ta tashi rai ɓace ta shiga inda ya shiga, ba tsammani taji ya karɓi wayar hannun ta gaban ta ya faɗi sosai yace, "a ina kika samu kuɗin wannan wayar? Waye ya siya miki ita?." Mubeena ta fara kame-kame cikin rashin gaskiya tace, "ba tawa bace, ta ƙawata Bily ce ta ara min." Yadda take maganar kana ji kasan ƙarya take yi ya girgiza ki ya saka ta a aljihu tace, "to shikenan kice mata tazo ta karɓa a wajena tunda ba taki bace ba, sannan daga yau ɗin nan kar ki sake fita baki tambaye ni ba, duk inda zaki koda bana nan ki faɗawa Manal ta baki waya ki kira ni. Ko makarantar ce kar ki sake zuwa sai na sani." Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Bab yace, "kin ɓata wayon ki indai wannan hanyar da kika ɗauka kike ganin itace daidai da rayuwar ki Mubeena, zaki yi dan sani a lokacin da baza tayi miki amfanin komai ba." Mubeena tace, "wallahi ni babu abinda nayi Baba." "Waye ya sauke ki jiya da magariba a mota?." Gaban ta ya faɗi sosai tayi shiru, ya sakar mata tsawar da sai da ta firgita ta kusa faɗuwa daga zaune yace, "tambayar ki nake waye ya sauke ki a mota jiya?" Ya faɗa da tsawar da bai taɓa yi mata irin ta ba. Tace, "Drivern gidan su ƙawata ne." Baba yace, "ƙarya kike wallahi, ki cigaba da abinda ki ke yi, ke a ganin ki hakan shine wayewa ko? Hmmm Mubeena zaki dana sani indai wannan banzar rayuwar kika zaɓarwa kan ki, kin ga ina bin ki ta lallami shine kike abinda kike so kina ganin babu mai hana ki ko?, daga yau mun saka ƙafar wando ɗaya dake, zamu ga waye mai nasara ni ko ke." ya faɗa yana tashi ya fita ta bishi da kallo babban tashin hankalin ta itace wayar ta. Yana fitowa tsakar gidan yaga Mama a zaune da alama taji komai tace, "Wayar mai tsada ce a hannun ta ko Baban Manal? Sannan jiya waye sauke ta a mota?. Ai shikenan Mubeena sai ta kashe ni zata huta." Baba bai so taji ba yace, "Kar ki saka wannan a zuciyar ki, ta tabbatar min da motar gidan su ƙawar tace na kuma amince da haka, wayar ma ba ta ta bace ta ƙawar tace." Mama tayi murmushi tace, "Ko Manal baza ta amince da abinda kace ba balle ni Baban Manal, ni fa na haife ta. Shikenan ai duk wanda yayi daidai ya sani, wanda bai yi daidai bama ya sani." Baba yace, "bance ki saka wannan abin a zuciyar ki ba, addu'a zaki mata itace maganin komai." Mama bata ce komai ba Baba ya kalli Manal yace, "ki kula da ita kin ji." Ta ɗaha kai alamun to har ta fara kuka ya fita. Mubeena ta wuce zuwa ɗakin jiki a sanyaye Manal ta tashi tabi bayan ta tana shiga tace, "in wani abun ya samu Mama ta dalilin ki Allah ya isa ban yafe miki ba Yaya, sannan har abada kar ki tuna ni matsayin ƴar uwar ki daga ranar bazan sake kallon ki matsayin jinina ba, daga ranar bazan sake miki kallon ƴar uwata ba wallahi. Babu ni babu ke kamar yadda kika ɗauki hakan a yanzu.  ke bakya son mahaifiyar mu ni ina sonta, in ke kin raina ta ni ina girmama ta, in ke kunya kike ji ace itace ta haife ki ni alfahari nake na nuna ta matsayin wacce ta haife ni." Mubeena da take kallon ta tace, "ni kike faɗawa wannan maganar?." "An faɗa miki, in kinga dama ki dake ni kuma wallahi sai na rama. Meye a duniyar in baka girmama mahaifiyar ka ba? Me zaka tsinka a cikin ta in baka yi biyayya ga iyayen ka ba?, Ke a ganin ki wannan wayewa ce ai ko? To kije ki tayi Allah ya bada nasara. Amma ki tuna daga lokacin da kika saka wani abun ya same ta babu ni babu ke" tana faɗa mata ta fita ta barta a tsaye. Taji kunya sossi amma wayar ta kawai take ji domin ko wanne lokaci za'a iya yi mata waya. Haka Manal ta wuni kusa da Mama, duk da Maman tayi shiru bata cewa komai kai da ka ganta kasan tana cikin damuwa sosai amma bata nunawa. Kwanan Mubeena biyu bata fita ba saboda babu fuska wajan Mama gashi Baba ya saka mata ido ko ya ta motsa yana kallon ta ko kuma ya saka ana kallon ta gabaɗaya ta damu zaman gidan ya ishe ta sosai. Ranar laraba a safiyar Mama na zaune suna hira da Manal kamar yadda suka saba tace, "Manal kin ji yadda nake jin idona ya ɗaure ya daina wallahi, a hankali nake ji yana saki, da alama dai abinda likitan nan ya faɗa zai tabbata." Manal cikin farin ciki tace, "Da gaske Mama?." "Da gaske mana." "Allah ya tabbatar Mama." Mubeena tazo ta zauna a kan tabarmar da suke tace, "Mama zanje makaranta na dawo." Mama tayi mata banza kamar bata ji me take cewa ba tace, "kiyi haƙuri ni duk abinda ake zargina a kai ba haka bane ba wallahi." Mama tace, "in ma haka ne Mubeena rayuwar ki ce ba tawa ba, Dana sani ke zata bibiya ai bani ba domin kowa yayi daidai ya sani. Tashi ki bani waje ai ba tambaya ta kike ba in zaki fita." Mubeena tayi shiru ta kalli Manal da ba ita take kallo ba sai ta tashi ta fita. Mama ta girgiza kai tace, "Mubeena hmmm!." Abinda tace kenan bata sake magana ba Manal ma bata dawo da zancen ba ta ɗaukewa Mam hankali da hira dan ta kawar da batun Mubeena.         A cikin kwana biyun Bebi ya tabbatar da son Manal yake so na gaske ba na wasa ba, duk yadda yaso ƙaryata zuciyar sa ta dage akan hakan domin duk wata alama ta soyayya ta gama shiga zuciyar sa ta kuma bayyana a ganganar jikin sa. Kewar ta yake ji sosai, burin sa ya ganta amma ya rasa ta wacce hanya zai bi hakan ta kasance. Ranar bai ma fita ba yana gida tunani yayi masa yawa akan Manal, da ya kulle ido ita yake gani zuciyar sa na harbawa sosai alamun soyayyar da yake mata mai ƙarfin gaske ce. Duk ya damu, tunanin kar yaje an mata miji gashi soyayya ta gama kama shi, hakan ya hana shi nutsuwa gabaɗaya shine dalilin da ya hana shi fita. Yana zaune yana wannan tunani Huzaifa ya kira shi ya ɗauka Huzaifa yace, "Bebi baza ka fito bane har rana tayi?." Bebi ya sauke numfashi yace, "gaskiya ba zan shigo ba sai zuwa yamma." "Amma akwai mutanen da suke jiran ka, akwai wanda aka kawo ma yanzu kuma matsalar zuciya ne. Da zaka daure da kazo ɗin ka san David da Yasir  suna off." Ajiyar zuciya yayi yace, "gani nan" ya faɗa yana yanke wayar ya tashi daga inda yake ya saka kaya ya fito. Ganin motar Abba tana nan sai ya shiga wajan sa ya same shi a zaune da alama bai san ya shigo ba duk da yayi sallama, Abban yana zaune yana magana shi kaɗai yana cewa, "Wai me yake damun wayar yarinyar nan ne? Kwana biyu a kashe Allah yasa ba fushi tayi ba." Girgiza kai yayi domin kuwa ya fara tabbatar da Abban su yana harka da ƴan mata a waje, duk da bai san alaƙar su ba amma a yadda ya damu hakan ya nuna ya damu da yarinyar sosai. "Asslaamu alaikum". Bebi ya sake faɗa yana kallon sa, sai a sannan ya juya ya ajjiye wayar yace, "Wa'alaika salam, Bebi yau ba'a fita ba?." Ya ƙarasa ya zauna a ƙasa yace, "barka da rana." "Barka dai, ya aiki?." "Alhamdulillah. Yanzu zan fita sai naga motar ka na shigo mu gaisa." "Ka kyauta sosai, Allah ya taimaka." Ya sauke numfashi sannan yace, "Amin" ya miƙe yace, "a tashi lafiya" ya faɗa yana fita. Yana fitowa compound na gidan Lubna na shigowa, haka nan bai amince da ita ba duk da hankalin sa ya kwanta kwana biyu baya ganin Kamal baya ganin Mujahid amma yanayin yadda take murmushi ita kaɗai kamar bata da gaskiya. Ganin yana kallon ta sai ta tsargu ta ƙaraso inda yake tace, "ina wuni." "Daga ina kike?." "Mamy ce ta aike ni?." "Shine sai ki fita ke kaɗai?." Lubna tace, "ita tace naje." Baice komai ba ya wuce ta bishi da harara ta wuce ɓangaren su itama. Yana shiga wajan Mama bata falo ya wuce ɗaki ta ya samu tana ɗaura ɗankwali ya zauna tace, "kace min yau babu inda zaka je gashi naga ka shirya." Bebi yace, "ana nema na ne a asibiti shiyasa zan tafi." Ya sake kallon ta yace, "Mummy Abba ya dawo." Mama tace, "na sani, sai me?." "Mummy gaskiya a rashin zaman da Abba baya yi a gida nan wallahi da saka hannun ku ciki." Mama ta kalle shi tace, "Bebi akwai abinda baza ka gane bane shiyasa, mahaifi ne a wajan ka shiyasa bana son buɗe bakina a gaban ka, amma in kana yi min irin haka wata ran zan faɗi  kalmar da zaka kwana baka manta ba." Bebi yace, "shikenan yanzu haka za'a zauna kenan? Kamar ba mijin ku ba don Allah?." Mama bata ce komai ba sai ta canja maganar tace, "da alama dai wannan yaron saurayin Mimi shine mijin ta, dan Yayan ku yace yaje ya samu Daddyn ku a kan maganar da." Bebi ya gigita kai yace, "Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta amsa da amin ya miƙe yace, "sauri nake Mummy sai na dawo." "Allah ya kiyaye, dole ka gudu ai saboda kar nayi zancen Rumana, daɗin ta a nan zan kwana ai." Baice komai ba ya wuce dan kuwa haka ɗin ne, yanzu zata masa zancen yaje ya samu Yayan mahaifin sa da suke kira Daddy da maganar Rumana shi kuma baya so. Bebi koda ya fita sai ya samu kansa da bin unguwar su Manal, umarnin zuciyar sa kawai yake  bi a lokacin ban da son ganin ta babu abinda yake so.  a daidai layin ya faka motar yana kallon layin zuciyar sa na wani irin bugawa tana tura shi akan yaje gidan nasu amma ya kasa. Kamar ance ya juya ya ganta riƙe da leda a hannun ta ita da Haroun tana murmushi shima haka sun jera sun shiga layin gidan. Gaban sa ya faɗi sosai saboda abubuwa biyu da suka haɗar masa a lokacin wanda yake gudun faruwar sa, na farko ganin da yayi mata ya saka gaban sa ya faɗi haka kawai, na biyu kuma ganin ta da Haroun ya saka zuciyar sa a ruɗani, domin bai san alaƙar su da shi ba duba da murmushin da yaga tana yi masa. Numfashi ya sauke ya kwantar da kansa a kan sitiyarin motar yace, "kaiii! Meyasa zan faɗa soyayya cikin ƙaramin lokaci haka? Meyasa?!." Ya jima a haka kafin ya miƙe zaune ya kunna motar ya ja ya tafi jiki a sanyaye gabaɗaya bashi da kuzari. Bai je office ba sai da ya fara ganin wanda aka kawo ɗin tun a ƙasa kafin ya wuce office yaga mutanen da suke gaban sa. Tashi yayi ya fito suka haɗu  da Dr Hadiza tace, "Dr akwai meeting yanzu." Ya kalle ta yace, "kuje ku yi bazan iya attending." "But why?." "Please!" Ya faɗa kawai yana barin wajan a lokacin Huzaifa yazo ta kalle shi tace, "yace bazai attending meeting ɗin ba." Huzaifa yace, "share shi muje muyi abinda yake gaban mu kawai." Cikin mota kawai ya koma ya zauna ya rasa abinda yake damun zuciyar sa a wannan lokacin, ji yake kamar ya fashe da kuka saboda abinda yake ji yayi masa nauyi a cikin zuciyar sa.  Ya rasa yadda zai sarrafa kansa, nauyi yake ji a ƙirjin sa ya rasa inda zai saka kansa yaji daɗi. Har suka fito daga meeting ɗin yana cikin mota a zaune sai waya ake masa amma ya kasa kallon wayar ma balle ya ɗauka dan baya cikin nutsuwar sa. Kulle motar yayi kawai ya kunna ya ja motar ya fita daga gidan. Babban asibiti ya wuce bai jima ba ya sake wucewa gida ko wajan Mummy bai shiga ba ya shiga ɗakin sa yana ji kamar ya zubar da hawaye saboda kaifin soyayyar da take sukar zuciyar sa. Bayan sallar magriba Huzaifa da Hamza suka zo gidan wajan Bebi, har wajan Mummy suka je suka gaishe ta take cewa, "mutumin naku ma da ya dawo bai shigo min ba, na lura tun ɗazu kamar bashi da lafiya." Hamza yace, "Mun ga hakan, yau ko damu bai haɗu ba ya dawo gida." Huzaifa yace, "bara muje wajan sa Mama." Ta amsa suka fita suka shiga wajan Bebi suka same shi a kan kujera ya harɗe hannayen sa waje ɗaya yana kallon ƙasa. Hamza ya zauna kusa dashi yace, "Me yake faruwa ne ka koma haka Bebi?." Ɗago kai yayi ya kalle su ya sauke numfashi yace, "ni kaina ban sani ba, wani iri nake ji a zuciyata kamar nayi kuka. Zuciyata tayi min nauyi sosai, na rasa gane kaina nima." Huzaifa yace, "me ya kawo hakan?." Tsaki yayi a bayyane kafin yace, "Wata yarinya ce, haka nan na kasa daina tunanin ta." Hamza yayi dariyar shaƙiyanci yace, "shine ka shiga wannan damuwar Bebi?, Kamata yayi kayi murna ai ka samu wacce kake so ko babu komai ka samu mafita akan lamarin Rumana." Huzaifa yace, "Yanzu akan wannan ne duk ka tayar mana da hankali?, wallahi na ɗauka wani babban abu ne yake shirin faruwa ko ya faru." Bebi yace, "ni ba ɗaga hankalina nayi ba, na tabbatar ina sonta na amince tun ban amince ba na yarda yanzu, amma abin ne yayi min yawa a zuciyata, kwata-kwata magana sau biyar bana tunanin ta shiga tsakanina da ita, amma yadda nake ji zuciyata na bugawa soyyayar ta tayi yawa." Hamza yace, "tsakanin so ɗin kenan Bebi. Kuma shi so ina ruwan sa da baku yi doguwar magana ba? Daga kallo ɗaya ana faɗawa soyayya." Bebi a raunane yace, "tun yanzu?, Tun kafin mu saba ina jin haka a kanta ina ga nan gaba?. Wallahi bana son soyayyar da zata wahalar dani Allah ya sani, bana son soyayyar da zata hanani sukuni. Can you imagine ɗazu kafin na tafi office sai da naje bakin layin su kawai ko zan ganta?. Na kuwa ganta ɗin, amma ita da wani namiji da ban san alaƙar su ba. Yanzu wannan soyayyar da na sakawa zuciyata in an yi mata miji fa ya zan yi?." Huzaifa ya girgiza kai yana murmushi, Allah ne ya kama shi ko yaushe gani yake shi zai saka soyayya a zuciyar sa dan haka sai yadda yaso, Gashi Allah ya nuna masa iyakar sa, ya nuna masa shi ke saka soyayya a zuciyar bayin sa. Huzaifa yace, "Wannan ba abin damuwa bane, kayi addu'a akan lamarin ta?." "Nayi, tunda na fara tunanin ta na fara addu'a, sai bayan nayi addu'ar nake ji tana sake shiga raina sosai." Hamza yace, "magana ta ƙare kawai, kaje ka nemi izinin ganin ta wajan iyayen ta, kaga in kaje in ma da maganar auren a kan ta zaka ji." Ya girgiza kai yana kallom su da manyan idanun sa yace, "ina niyar hakan, amma zuciyata baza ta jure ace na yi mata miji ba Hamza, a yadda nake ji in akace an yi mata miji zan...." Sai kuma yayi shiru yana girgiza kai. Hamza yayi dariya yace, "kar ka damu khairan in sha Allah, mallakin ka ce  wannan yarinyar da izinin Allah." Huzaifa dariya yake yi sosai yana kallon Bebi kafin yace, "Bebin Mummy manya, Wai wacece yarinyar ma?." Hararar sa yayi dan kuwa bazai faɗa musu ba sai ya tabbatar komai ya tabbata sannan zasu san wacece. Hamza ma dariyar yake yi yace, "ka share batun Huzaifa, kaje gobe ka samu iyayen ta akan maganar." Bebi ya wara ido yace, "har sai gobe? Meye amfanin yau?." Hamza da mamakin gaggawar Bebi yace, "kana da theater amma kace yau ko?." "Eh amma sai goma na dare ai, in banje ba bazan samu nutsuwar yin aikin yadda ya kamata ba, so nake naji an tabbatar min babu maganar aure a kanta." Hamza yace, "to maza ka shirya kaje yanzu mutumina, Allah ya bada sa'a." Kamar mai jiran umarni sai kuwa ya miƙe ya shiga ɗaki. Hamza da Huzaifa suka ƙyalƙyale da dariya har suna tafawa. Sun ji daɗin yadda Allah ya kama shi tun ba a je ko ina ba, cika baki akan soyayya ya ƙare tunda ya samu wacce yake yiwa son da bai yi zato ba. Nana Haleema🥂🫶🏻 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025                  ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu. https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 020* Adnan dariyar su ya jiyo daga ɗaki sai ya fasa abinda yayi niya ya fito yana kallon su Huzaifa ya kalle shi yace, "ka fasa tafiyar ne ɗan soyayya?." Sai shima ya samu kansa da yin murmushi ya kama ƙugu yace, "abin mamaki ko? Wai ni Adnan da son wata mace bayan soyayyyar yarinta." Hamza yace, "ba abin amma ki bane ba, ka kai kayi ɗin ne. Ka koma ka shirya ka ƙyale wannan yana da wacce zai aura a hannun sa." Huzaifa ya tashi yace, "tafiya zanyi ma ni." Hamza yace, "jira ni" ya kalli Bebi bayan ya tashi tsaye yace, "kar kayi wasa mutumina, kaje da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, Allah ya daidai ku. Na san baza ka zaɓo ta banza, duk yadda aka yu tarbiyya da kyau ka gano, dan na san ka akwai son abu mai kyau." Bayan su ya biyo zuwa harabar gidan suna hira, lokacin sallah yayi Adnan yace, "amin, in ma da biyu ka yi addu'ar in sha Allah zamu daidaita." Suna dariya su biyun shi kuma yana tsakiyar su. Suna nan tsaye Mimi ta fito cikin riga da siket ƴan kanti sun kama ta musamman rigar, ita da ƙawar ta suka fito suna hira sai da suka zo kusa dasu Bebi suka gaisa suka wuce, ta raka ta har bakin gate ta fita sannan ta juya ta koma ciki. A lokacin su Huzaifa suka hau mota suka tafi shi kuma ya wuce ciki rai a ɓace saboda abinda Mimi tayi. Yana shiga yace, "Ke Kausar ina Mimi?." Mimi ta fito da plate a hannu tace, "Gani." "Wanne irin rashin hankali ne zaki dinga fita waje a haka? Kalli kayan jikin ki, don baki da hankali a haka kike yawo daman?." Ta kalli kanta ta kalle shi tace, "Yaya a cikin gida nake fa." "Zan tsinke ki da mari in kika sake min magana, kin fini sanin a cikin gidan ki ke?. Wannan wanne irin hauka da shirme ne da kuma rashin hankali?. Kin fito ko mayafi babu kina ganina da ɓaki maimakon ki dawo ki saka mayafi sai kika wuce ke ga ƴar gayu ko?." Tayi shiru tana kallon wani wajan Mama ta fito daga ɗaki taji duk abinda yake faɗa tace, "Mimi jeki ki sauke min naman can a kan gas." Hakan ya saka ta wuce Kausar ta tashi ta bita dan wallahi Bebi haushi yake basu wani lokacin dan babu yadda zasu yi dashi ne. Mama ta kalle sji tace, "Bebi yanzu dan ta fita harabar nan a haka meye laifi don Allah da zaka zo kana mata wannan faɗan?, Ka dinga sassautawa yaran nan wani lokacin takurar tana yawa sosai." Bebi yace, "Mummy tana ganina da baƙi fa, ai sai ta dawo ta saka mayafi sannan taje su gaisa. Sun kasa gane bana son abinda suke yi ne kwata-kwata." "Sai kayi haƙuri, aure zasu yi su bar maka gidan." Ya juya ya fita bai ce komai.        Sallah yaje yayi ya dawo yana tunanin abinda zai yi saboda da ya keɓe kansa tunanin Manal ke zuwa zuciyar sa. Kamar an bashi umarni sai ya tashi shiga ɗaki ya shirya cikin manyan kaya da suka yi kyau sosai harda hula, kallon kansa yake a madubi yana jin ƙarfin guiwar zuwan, zuciyar sa na sake bashi shawarar Tafiya gidan su Manal. Ya sauke numfashi ya fita ya hau mota ya tafi gidan su Manal kai tsaye. Sai da ya tsaya a ƙofar gidan sai kuma ya rasa abinda zai yi, yana zaune a mota yana kallon gidan kasancewar akwai haske a layin dan da wutar nepa ko ina da haske har ƙofar gidan su. Baba ne zai shiga gidan suna tsaye da Haroun suna magana a ƙofar gidan, ganin hakan sai Bebi ya fito daga motar ya ƙaarasa inda suke yana zuwa yayi sallama Baba ya amsa masa sai ya saki murmushi yace, "A'a dr Adnan, barka da zuwa." Adnan yayi murmushi yace, "barka da dare Baba." "Barka dai likita, ya aiki?." "Alhamdulillah, ya masu jiki?." "Da sauƙi sosai duk sun samu lafiya. Haruna wannan shine likitan da suka taimaka lokacin da su Manal basu da lafiya, shine wanda na baka labari ko naira biyar basu ƙarba ba." Suka gaisa da Haroun yace, "Allah ya saka da alkhairi, ɗazu ma Manal tayi min wannann zancen, taji daɗi sosai, Allah ya biya."  Ya amsa da amin. Baba yace, "ya kamata ka shiga ku gaisa in da damar hakan." Bebi yace, "babu damuwa Baba, daman wajan ka nazo Baba." Baba yace, "wajena kuma? To mu shiga ciki" ya faɗa yana shiga cikin gidan Adnan ya biyo bayan sa yana mamakin kansa wai shine yazo tambayar izinin neman wata yarinya. Tun daga soron gidan yake jiyo muryar ta tana bada labari tana dariya da alamun tana cikin nishaɗi, sai daga baya yaji muryar Mama tana cewa, "Manali Allah ya shirye ki, kice kin yi samari duk babu labari sai yanzu da Allah ya matsa bakin ki." Sai tayi dariya tace, "Amin Mama. Sosai ma kuwa, kawai bana faɗa miki ne, amma yanzu zaki sani." Sallamar Baba ya saka suka yi shiru suka kalli Baban sai Baba ya juya yaga Adnan bai shigo ba yace, "Dr shigo mana." Dr Adnan ya shigo da sallama yana kallon tsakar gidan, kai tsaye suka haɗa ido da Manal da take zaune da doguwar riga a jikin ta ta saka huta a kanta wacce ta ja ta baya gashin ta ya ɗan fito ta gaba. Suna haɗa ido abinda yazo mata kawai wulaƙancin da yayi mata amma sai bata nuna ba dan ya taimaki Mama hakan ya saka tace, "Dr! Sannu da zuwa." Ta kalli Mama tace, "Mama Dr da ya kula dake ne fa." Mama tayi murmushi tace, "ai daga jin sallamar na gane ɗauki murya, kuma naji kin ce Dr. Sannu da zuwa." Sai yayi murmushi ya kalli Manal sai yaga ta wara idanu waje tana kallon sa dan ita mamaki take daman yana sakin fuskar har a ga haƙorin sa?. Har kan tabarmar da suke kai ya ƙarasa ya gaida Mama ta amsa da fara'a tace, "Ya aiki?." "Alhamdulillah, ya jikin?." "Jiki da sauƙi, ɗazu nake cewa Manal kinga ina jin sauƙin Idon nan da alama dai abinda ka faɗa zai tabbata." Yace, "indai za'a dinga shan maganin ana ganin likita babu abinda zai faru sai alkhairi." "Allah yasa, sai dai ga Manal nan bata shan nata maganin da aka bata wallahi." Manal da take gefe ta turo baki tace, Allah Mama ina sha, maganin ne daɗi fa." Kallon ta yayi yana jin wata irin kewa a zuciyar sa kamar baya tare da ita, Allah ya saka masa son ta farar ɗaya a lokacin da bai shiryawa hakan ba. Wani abu yake ji yana jan sa zuwa gare ta musamman yanzu da take magana, hakan ya saka shi zuba mata ido kawai yana kallo har sai da yaji Mama tace, "ƙarya kike Manal, bakya sha ni nasan halin ki fa, kuma magani ai ba dan daɗi ake sha ba." Manal ta kalle shi suka haɗa ido sai ya janye idon sa tace, "ina sha, kawai Mama ce take cewa bana sha." Baba yace, "kun barshi a durƙushe sai magana kuke yi, Dr taso mu shiga ciki." Adnan baiyi musu ba ya tashi suka shiga falon Baban yana jiyo maganar Manal cikin shagwaɓa Maman na sake gwale ta kamar dai kawaye baza kace uwa da ƴa bane ba. Baba ya zauna Adnan ya zauna a ƙasa Baba yace, "Haba Dr, tashi ka dawo sama don Allah." Adnan yace, "Babu komai Baba, nan ma yayi." Baba yace, "Allah yasa Lafiya." "Lafiya lau Baba." "To ina jin ka." Bebi yayi shiru yana tunanin ta ina zai fara kafin ya aro jarumta yace, "Baba nazo ne akan maganar Manal." Baba yace, "To wani abun ne ya faru? Ko a kan ciwon nata ne?." Bebi ya girgiza kai yace, "Ba akan ciwon ta bane Baba." "To ina jin ka." "Baba nazo ne daman akan in ba'a yi mata miji ba ina so a bani dama da izinin magana da ita." Nan da nan Baba ya saki fara'a yace, "Ikon Allah, Manal dai tawa?." Adnan ya ɗaga kai Baba yace, "Ba'a yi mata miji ba Adnan, dan kullum cikin rigima ake da ita akan ita baza tayi aure ta bar Mama ba, ka ganta nan kamar yarinya ƙ'arama haka take. Adnan naji daɗi sosai wallahi, ace Manal ta samu kamar ka ya furta yana neman izinin zuwa wajan ta babban abin farin ciki ne, dan mutum nagari ba ya neman wacce bata gari ba, naji daɗi sosai musamman yadda baka je gare ta kai tsaye ba kazo ka same ni." Baba ya sake cewa, "naji daɗi sosai Adnan, nayi farin ciki wallahi. Amma sunan ka kawai na sani ko sunan mahaifin ka ba ban sani." Bebi yace, "Adnan Mu'azzam Alhassan, mahaifina shine tshon minister na harkar noma. Kamar yadda ka sani Baba ni likitan zuciya ne, asibitin da muke aiki dashi na mu ne wanda muka wallafa shi da kan mu." Baba ya girgiza kai yace, "ma sha Allah, ƙwarai nasan sunan mahaifin ka a kafafan sada labarai, Allah ya bada nasara. Shikenan Adnan, Gobe in Allah ya kaimu sai kazo ku tattauna da ita Manal ɗin, abinda ya sa bazan ce yanzu ba ina so na sanar da mahaifiyar ta in muna da rai gobe sai a baka damar magana da ita." Adnan ya girgiza kai yace, "Na gode Baba, Allah ya ƙara lafiya." Ya amsa da amin yana murmushi kafin yace, "ai ni naji daɗi sosai, iya zuwan nan da kayi neman izini wajena baka fara tunkarar ta kai tsaye ba ya tabbatar min da nagartar ka da kuma tarbiyyar da ka damu a wajan magabatan ka, Allah ya tabbatar da alkhairi yasa kai ne rabon ta." Sosai yaji daɗin wannan addu'ar yayi murmushi ya amsa da amin kafin ya saka hannu a aljihu ya ɗauko kuɗi ya ajjiyewa baba yace, "Baba a rabawa yara." Baba yace, "harda hidima?." "Babu komai." "To Allah yayi albarka." Ya amsa da amin yayi masa sallama ya taso ya fito tsakar gidan da son sake ganin ta amma bata nan sai maganar ta da yake ji tana dariya, yayi murmushi ya fita zuciyar sa kamar an wanke masa haka yake ji saboda farin ciki. Falon Baba ya shiga ya kalli Manal yace, "Mubeena bata nan ne?." Manal tace, "Tunda ta fita tace taje makaranta har yanzu bata dawo ba." Baba ya girgiza kai ya zauna ganin hakan sai Manal ta tashi ta koma tsakar gida bayan ta ɗauki sabuwar wayar ta daman kallon wani American series da take kalla, dan tana a son su tana ƙaruwa a fannin ingilishi sosai. Baba ya kalli Mama yace, "Kin san abinda ya kawo Adnan gidan nan?." Ta girgiza kai tace, "ban sani ba, amma nasan bazai wuce zance akan ciwo na ba ko?." Ya girgiza kai alamun a'a yayi murmushi yace, "addu'ar da kike yiwa Manal a ko yaushe itace take bibiyar ta, shiyasa nake faɗa miki ki dinga haɗawa da Mubeena saboda bakin ki akwai kaifi kasancewar ki mahaifiya. Addu'ar ki bata da hijjabi a wajan Allah, da kin yi addu'a a kan yaran ki da Allah ya amsa, ko yaushe zaki ce Manal Allah yayi miki albarka amma sai ita Mubeena bakya faɗar hakan a kanta. Inda kina faɗa kina fatan Allah ya shirya miki ita da yanzu wataƙila ta shiryu, ki dinga haɗawa da ita domin ta samu itama alkhairin bibiye ta." Mama tace, "ka lasa min zuma a baki, ka sanar dani abinda yake faruwa don Allah." "Yazo ne akan yana so a bashi izinin zuwa wajan Manal a matsayin wanda yake neman auren ta." Mama da mamaki tace, "auren Manal kuma? Shine yake son auren ta?." Baba yace, "shine abinda ya kawo shi, naji daɗi kuma da ya fara tambayar izini bai fara magana da ita ba hakan ya nuna yasan abinda yake yi yana kuma da tarbiyya da sanin ya kamata." Mama sai tayi murmushi da farin ciki tace, "ikon Allah! Yanzu shi likitan da kansa ne yake son Manali ta? Kai alhamdulillah Allah na gode maka, ko yanzu Allah ya karɓi raina nasan addu'ata na bibiyar Manal." Baba yayi murmushi ganin tana farin ciki sai tace, "to a ina ya santa? Ko kuma zaman asibitin ne ya saka har ya fara sonta?." "Shi so a lokaci ɗaya ma ai shiga zuciya yake balle kuma anyi kwanaki." "Kaji ikon Allah, Allah Alhakim, daman silar haɗuwar sa da ita ne ta kaimu wannan asibitin. Naji daɗi sosai wallahi, Baban Manal tun daga kan taimakon da ya yi mata ya kawo ta gida bai barta a titi ba, ganin dare yayi ya jira ta ya mayar da ita asibitin, tunda ta bani labarin nan na tabbatar yasan darajar ɗan adam yana kuma girmama mace." Baba yace, "ɗan gidan tsohon minister noma ne Alhaji Mu'azzam Alhassan, baban sa babban mai kuɗi ne sosai kuma ya shiga siyasa a yanzu."  Sai Mama tayi shiru tace, "to, sai kuma jikina yayi sanyi, anya kuma bai fi ƙarfin Manal ba Baban Manal? Minister fa?." Sai Baba yayi murmushi yace, "in Manal bata fi ƙarfin sa ba bana tunanin zai fi ƙarfin ta, kin manta wacece mahaifiyar Manal ne? Kin manta wacece ke ne?." Mama ta sauke numfashi tace, "wannan duk ya wuce ai, babu wanda yasan da shi in ba kai ba, ka manta da waccan da aka sani ta yanzu ake magana a ka." Baba yayi murmushi yace, "ai ba'a canjawa tuwo suna." "In aka yayyanka shi aka saka mai da yaji ya zama kwaɗo." Yayi dariya yace, "bai fi ƙarfin Manal ba Fatima shine daidai ita, kuma har zuciyata na amince dashi ina so ta amince dashi itama domin ya shiga raina sosai." Mama tace, "nima zan so hakan, amma Allah kaɗai yasan abinda ya shirya mana baki ɗaya." "Haka ne, yanzu na bashi dama yazo gobe su gaisa da ita, kafin nan ni kuma da safe zan saka ayi min ƙaramin bincike akan sa da kuma halayen sa." Mama tace, "hakan yayi, Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya amsa da amin kafin ya ɗaga murya yace, "Manal!." Daga tsakar gida ta jiyo kiran ta amsa ta shigo tace, "Gani Baba." Baba yace, "Wannan likitan da yazo yanzu yazo ne akan ki." Manal ta kalli Baba tana jira ya cigaba taji akan me yazo kuma sai Bab yace, "Yazo ne akan yana sonki yana kuma son a bashi dama ku yi magana dake dashi a matsayin mai neman auren ki." Gaban Manal ya yanke ya faɗi,ta zauna daga tsugunen da take ta kalli Mama taga sai murmushi take yi da alama abin ya mata daɗi shima Baban murmushin yake yi ya cewa, "na bashi dama gobe yazo ya ganki ku tattauna abubuwa a tsakanin ku. Sai ki shirya zuwa goben nasan bazai wuce da yamma ko da daddare zai zo ba." Manal dai ta kasa magana kallon Baba take yi abin mamaki yake bata, yaushe hakan ta faru bayan ita wulaƙanci ne ya raba su?, Yaushe ya fara son ta har ya samu ƙarfin guiwar zuwa gidan su?, Har yaushe ma ya santa suka yi sabon da soyayya zata shigo tsakani?. Ashe daman zai iya sonta? Daman kallon da yake mata ɗazu na so ne?. Katse mata tunani Baba yayi yace, "tashi kije" ta miƙe jiki a sanyaye ta fita tana tunanin lamarin kamar a mafarki, wai Dr Adnan ne yake sonta. Nana Haleema🥂❤️ *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025   ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 Masu tambaya daga farko zaku samu a wannan link din https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 021.* Mubeena kuwa a daren suna zaune a falon gidan su Bily su Mummyn sun je wata dubiya su dawo Mubeena sai ƙunci take yi Bily tace, "wai duk akan an ƙwace miki waya shine kike wannan ƙuncin? Ni Baba yayi min daidai domin kuwa wannan shegen mutumin iskanta ki zaiyi wallahi." Mubeena bata ce komai ba mai gadi ya shigo da sallama Bily ta amsa yace, "akwai wanda yazo yace ayi masa magana da Mubeena shine nazo na sanar da ku." Mubeena ta kalle shi tace, "waye?." Mai gadin yace, "ban san shi ba, amma babban mutum ne."  Kafin yace wani abun Mubeena ta miƙe ta yafa mayafi ta fita Bily ta bita da kallo tana girgiza kai cike da jin haushin ta. Waje ta fita taga motar tasa ta buɗe gaban motar ta shiga ya kalle ta yace, "kin wahalar dani Baby, yau kwana biyu wayar ki a kashe baki neme ki ba, wallahi ko abinci bana iya ci. Duk akan abinda ya faru ne kike min wanna horon? To kiyi haƙuri bazan sake ba." Mubeena itama kewar sa take yi sosai a zuciyar ta sai ta fara kuka ta gigita shi lokaciyace, "Haba Baby, me kuma don Allah? Kina so nima nayi kukan ne?." Bata amsa ba yace, "Don Allah ki faɗa min abinda ya faru, in akan abinda nayi ne nace ayi min afuwa ko?." Mubeena ta goge idanun ta tace, "wayata ce ta faɗi kuma bani da lafiya." "Me ya same ki Baby? Wani abun yana damun ki?." "Ciwon kai ne, amma naji sauƙi sosai." "Yaushe wayar taki ta faɗi?." "Tun washe garin da muka rabu." "Amma da sai ki saka Gmail ɗin ki a wata wayar ki ɗauki number ta ki kira ki sanar dani, na damu sosai baby." Ta share idanun ta tace, "ban yi wannan tunanin ba." Yayi murmushi yace, "to shikenan, indai waya ce za'a sake siya miki wata dan ma dare yayi ne da yanzu za'a kawo miki amma gobe da safe ki shirya karɓar waya. Sim card ɗin fa?." Mubeena tace, "zan canja wani kawai, daman bana son wancan damuna ake da waya." Yayi murmushi yace, "an gama ranki ya daɗe, zan aiko ayi miki register har gida ba sai kinje kin bi layi ba." Tayi murmushi tana turo baki ya bita da kallo kurilla yace, "Ina kewar ko baby." Ta kalle shi itama tace, "Nima haka" ta faɗa tana kallon sa tana tuna abinda yayi mata sai tsigar jikin ta ta tashi. Hannun ta ya riƙe yace, "yaushe zaki raka ni Abuja? Ina so naje na gana da president kinga sai muje ko?." Mubeena Jin ance president sai ta kalle shi tace, "Mummy baza ta barni ba, faɗa zata yi min." Yayi murmushi yace, "to yanzu ya za'ayi? Ina so kiyi min rakiya muje mu dawo a ranar." Mubeena tayi shiru tace, "a ranar muje Abuja mu dawo?." Yayi dariya yace, "sosai, jirgi zamu hau kuma private get ne sai lokacin da naso muje mu dawo." Jin haka sai ta sake jin daɗi tayi dariya tace, "to zan duba na gani in zanje." "Zaki je ma kawai Baby." Tayi murmushi shima yayi tare da yiwa hannun ta kiss yace, "hankalina ya tashi akan rashin magana dake, yanzu dana ganki sai na samu nutsuwa." Tayi dariya bata ce komai ba yace, "in badan ke ba bana driving da kaina, amma bazan iya zuwa da wani wajan ki ba Baby" ya faɗa yana ɗauko leda a bayan motar ya ajjiye akan cinyar ta. Buɗe ledar tayi taga kayan ciye-ciye ne kawai a ciki, tayi murmushi tana kallon ledar sai ji tayi ya mata kiss a kumatu ta kalle shi ya ɗaga mata gira sai suka yi dariya a tare.  A haka suka rabu ta koma ciki shi kuma ya ja motar domin baya so Maubeena ta guje masa bai samu abinda yake so ba, in hakan ta faru yayi babbar asara. Mubeena bata dawo ba sai goma na dare Baba yana zaune a ƙofar gida yana jiran yaga ta inda zata ɓullo dan lamarin ta ya lura sai ana mata yi jan ido,  ai kuwa ya hango ta shigo layin, baiyi magana ba har ta shiga cikin gidan sannan yabi bayan ta ya kulle gidan dan a wajan Mama yake ya shiga ciki. "Daga gidan uban wa kike?." Jin abinda Baba yace sai da gaban ta ya faɗi ta juyo tana kame-kame,  ya ɗauke ta da mari mai zafi kafin ta dawo hankalin ta ya sake marin ta sai ta zube a wajan tana gani biyu-biyu dan rabon da a mare ta har ta manta yace, "ni zaki mayar ɗan iska? Dan kinga ina bin ki a hankali sai ki mayar sa'an wasan ki? Daga ina kike a cikin daren nan?." Baya yayi ya ɗauki  igiyar shanya yace, "Wallahi ko ki faɗa min ko yau na zane miki jikin ki, daga gidan uwan ban wa ki ke a daren nan?." Mubeena ta tsorata sosai karo na farko da Baba yayi mata haka,jiki na rawa ta rasa abinda zata ce kawai taji ya fara dukan ta dan ta gama ɓata masa rai. A guje Manal ta fito jin maganar Baba da ƙarfi ganin ana dukan ta sai jikin ta yayi sanyi ta fara kuka tana daga tsaye Baba yace, "baza ki faɗa min ina kike zuwa ba?." "Makaranta naje, sune suka tura mu wani aiki sai yanzu na dawo." "Ƙarya kike, har makarantar taku na saka an duba bakya nan, ko faɗa min inda kikaje ko yau sai na lahira ya fiki jin daɗi, ko ki faɗa min uban da yake goya miki baya yake zuga ki ko yau na karya ki." Ganin Baba dukan nata zai sake yi da sauri tace, "Wallahi Ina can, ina can babu inda naje" ta faɗa tan kuka sosai dan ta daku. Baba yace, "duk abinda kike ganin daidai ne a wajan ki Mubeena ki yi, ki cigaba da ɗurawa babar ki baƙin ciki, ki cigaba da bari tana zubar da hawaye a kan ki. Daga lokacin da kika yi sake tayi miki baki daga wannan lokacin zaki gane kuskauren da kika tafka a rayuwar ki wanda baza ki gyara ba. Ina so ki sani, daga yau babu ke babu zuwa makarantar na soke, sannan daga yau kar na sake gani kin fita ko da gidan su Surayya ne. wallahil azim kika sa ke aikata wani abun sai nayi miki illa, sai na karya ki gida biyu" ya faɗa yana cillar da igiyar ya shiga ɗakin sa cikin ɓacin rai sosai. Manal da take kallon ta tana kuka tace, "Ko yaushe burin ki ran Mama ya ɓaci, bakya damuwa da wanne hali zata shiga saboda son zuciya da son kuɗi ya riga ya rufe miki ido. Ki yi abinda kike ganin ya dace, abinda baki sani ba nasan ba makaranta kike zuwa ba Yaya akwai inda kike zuwa in kika fita, bana zargin ki a baya, amma yanzu ina zargin kin fara wata ɗabi'ar da baki da ita. Kije ki yi ke zaki dana sani, ke zaki nadama a lokacin da bata da amfani, ke abin zai bibiya har mutuwar ki" tana faɗa ta shige ciki ta barta a wajan tan kuka sosai. Mama duk tana jin abinda yake faruwa tayi kamar tayi bacci nan kuwa idon ta biyu babu wanda ya kai ta jin baƙin ciki a zuciyar ta. Tana jin wucewar Mubeena ɗin tana kuka bata ma ɗaga kai ta kalle ta ba balle tayi mata magana. A haka suka kwana kowa rai a ɓace. Da ciwon ƙirji Mama ta tashi sai da Manal ta bata magani sannan ta ɗan ji daɗi. Mubeena na ɗaki taƙi fitowa ko cin abinci balle wanka babu wanda ya neme ta duk suka share ta. Gab da sallar azahar Bily tazo gidan Baba yana nan dan bai fita ba saboda case ɗin Mubeena, Bily ta gaishe da Mama suka gaisa da Manal kafin tace, "Manal Baba yana nan?." Manal tace, "eh yana nan, amma yana wancan gidan." Bily tace, "muje ki raka ni wajan sa na zo" Ta amsa da to ta tashi ta saka mayafi suka fita. A lokacin zai fito daga gidan suka  haɗu a soron gidan, Bily ta gaishe shi ya amsa kafin Manal tace, "ƙawar Yaya ce Baba, tace tana son ganin ka." Baba yace, "Allah yasa Lafiya." "Ba Lafiya ba Baba, magana ce akan Mubeena." Baba ya nutsu yana kallon ta yace, "Ina jin ki." "Baba tun shekarar mu ta farko aka kori Mubeena daga makaranta saboda bata maida hankali akn karatun, duk wata ƙarya da take yi akan makaranta ƙarya take wallahi bata da register babu sunan ta a jerin ƴan makaranta, tana dai taya ni zama mu dawo. To yanzu ta daina zuwan ma saboda akwai wani Alhaji da yake wure mata kunne da sunan zai aure ta, baban mai kuɗi ne sosai a garin nan, har waya ya siya mata mai tsadar gaske. Nayi shiru da ban faɗa ba, amma yanzu rawar kan nata yafi na baya, shiyasa naga in nayi shiru naci amanar ku dalilin da ya saka nazo na faɗa a saka mata ido domin a kansa babu abinda baza tayi ba." Baba ya girgiza kai cikin mamakin Mubeena yace, "Ya sunan ki?." "Bilkisu." Baba yace, "Na gode Bilkisu, Allah yayi miki albarka, Allah ya saka miki albarka a rayuwar ki." Bily tace, "Amin Baba. Nayi anyi da ita akan ta bari taƙi shiyasa na yanke hukunci nazo na same ka, kuma daman gidan mu shine mafakar ta, a nan take wuni har dare sannan ta tawo." Baba yace, "kin kyauta da kika faɗa ɓin, na gode sosai Allah yayi miki albarka" ta amsa da amin tayi musu sallama ta wuce. Manal ta koma ciki jikin ta duk babu daɗi jin abinda akace Mubeena ɗin nayi. Manal da ta shiga gida kai tsaye inda Mubeena take ta wuce ta shiga ta zauna kusa da ita tace, "ni kaɗai ce ƴar uwar kuma wacce zan faɗa miki gaskiya Yaya, ni kaɗai kike da ita ko kina so ko bakya so. Rayuwar da kika ɗauka ba komai bace face watsewa da kuma lalacewa, in kina ganin hakan da kike yi shine daidai kuma shine wayewa wallahi rashin hankali ne da kuma rashin wayo da lalacewa. Zai jawo miki dana sanin da har ki mutu baza ki daina ba a lokacin da bazai miki amfanin komai ba, ita wannan duniyar kayi daidai ma ya ka cika balle baki yi daidai ba?. Kabi iyayen ka ya ka zauna balle ka raina iyayen ka?." "A ko yaushe burin ki ɓatawa Mama rai, bakya ganin girman ta bakya darajata dan ta kasance a wannan gidan da kika raina kuma bata gani, ke a ganin ki Allah bai miki daidai ba da ya yo ki a gidan nan. Ba ƙarya kowa yasan kina da kyau amma meye amfanin kyau babu kyaun zuciya? Meye amfanin kyaun da zai kai ki wuta da ƙafar ki?. Ke a tunani ki wannan ɓacin rai da kike saka Mama bazai iya kai wuta ba? Ko hawayen da kike saka ta a kulluɓ ruwa ne yake zubewa daga idanun ta Yaya?." Mubeena tayi shiru bata ce komai ba Manal tace, "duk abinda kike aikatawa in ya kamata kin sani wallahi, kome kike yi ki na sane domin kuwa da hankalin da kuma ilimin ki, ki sauke tunanin da ya shiga kan ki, ki yi rayuwa mai kyau in ba haka ba dana sani zata riske ki a lokacin da hakan bazai miki amfani ba. Na faɗa miki haka ne a matsayin ki na ƴar uwata ta jini, bani da kamar ki shiyasa na faɗa miki gaskiya, in kin ga zaki gyara kanki, in baza ki gyara ba kan ki" tana gama faɗa mata haka ta tashi ta fita dan in tana zaune kusa da ita ji take kamar ta mare ta. Ɓangaren Bebi haka ya kwana ya yini cikin karsashi  da farin ciki da annushuwa, koda yaje asibiti sun lura da yadda yake komai da kazar-kazar kai da ka ganshi kasan akwai wani abu mai daɗi da ya same shi. Lokacin da yake asibitin su na getting better babu wani conjunction na marasa lafiya in ma akwai ba ɓangaren da bane da yawa ɓangaren su Hamza ne da ƴan team ɗin sa, hakan ya saka shi zama kawai yana tunanin Manal da abinda zaice mata in yaje wajan ta a ranar. Bai jima sosai ba ya tashi zai tafi sai a sannan suka haɗu da mutanen nasa Hamza ya kalle shi yace, "Ahha Bebi wannan yanayin da na ganka a ciki duk soyayyar ce?." Ɗaure fuska yayi gudun kar su jawo masa raini ganin basu kaɗai bane a wajan, hararar su yayi yace, "ku kuka sani" yana faɗa  yayi gaba suka yi dariya suka cigaba da abinda suke yi shi kuma yayi gida. Yana shiga gidan Maryam tana shigowa itama ya bita da kallo, gabaɗaya baya amincewa da yawan fitar da yake gani suna yi ita da Lubna su kaɗai,  amma da yake idanun sa basa ganin abinda baya so a tare dasu bai wani damu ba. Ciki ya wuce ya shiga wajan Mama ya samu Yayar sa Farida a zaune ita kaɗai tana danna waya. Ya zauna yace, "saukar yaushe?." "Na jima a nan, ya aikin?." "Alhamdulillah. Ina Mummy?." "Tana ciki. Ya batun Rumana ne?, Mama ta matsa a kai fa, yanzu ma kafin ta tashi maganar take yi min, maganar ta taso da gaske ne?." Ya kalli hanyar da Mama zata ɓillo yaga bata nan yace, "zan zo gida mu tattauna a kai." "Ya dai kamata, ni sam-sam bana so yanzu wallahi, da dai naso ka aure ta amma yanzu abin ya fita a kaina haka kawai." "Hmm! Kema dai kya faɗa." Mama ce ta fito tana cewa, "A'a Bebi an dawo?." Yayi murmushi yace, "eh Mummy, na dawo" ta ƙaraso ta zauna tana kallon sa tace, "to Sannun ka." "Ina su Mimi?." "Sun je gidan Yayan ku." "Me ake yi?." Mama ta kalle shi da mamaki tace, "Sai ana wani abun zasu je gidan Yayan su? Meyasa ka ke haka ne wai?." Baice komai ba yayi shiru ya tashi ya shiga kitchen sai gashi da abinci yana yamutsa fuska san baya son macaroni amma gashi an dafa kuma jellop duk tayi sanyi ba yadda yake so ba. Mama ta kalle shi yana ci yana taɓa baki yace, "Bana son wannan abar Mummy." "Sai ka ajjiye ai." Baice da yawa ba kuwa ya ajjiye ya kalli Farida yace, "dama zaki min girki da naji daɗi." Hararar sa tayi tace, "ashe zaka kwana baka ci ba wallahi." Ya taɓe baki Mama tayi dariya tace, "Kema dai , ai da sai kice ya jira ki zaki dafa masa, in kana son girki na kira Rumana nace ta kawo maka." Ya girgiza kai yace, "A'a Mummy ƙyale ta, zan san abinda zan ci" ya faɗa yana tashi ya fita. Mama tayi dariya bayan ya fita tace, "duk zilliyar ka sai ka auri Rumana Adnan." Farida bata ce komai ba dan itama ba so take yi ba. Sai bayan sallar magriba sannan yayi wanka yayi kyau cikin manyan kaya kamar jiya, yana ta ƙhamshi mai sanyi dan shi baya ƙhamshi mai ɗaukar hankali, baya son turare mai ƙarfi kowa ya san da wannan indai kuna tare. Falon ya shiga ya tarar da Mama da Farida dasu Mimi duk sun na nan ganin sa sai suka tsaya kallon sa dan ya yi musu kyau sosai. Farida tace, "Sai ina?." Mimi ƙasa-ƙasa tace, "Kamar dai mai zuwa zance" ta faɗa tana kulle bakin ta tana dariya. Mama ta kalle shi tace, "ma sha Allah Bebin Mummy, kayi kyau sosai, ina zaka je haka?." Yayi murmushi Yace, "zanje wani waje mai mahimmaci Mummy, kiyi min fatan samun nasara" ya faɗa yana ƙarasowa inda take ya cire hular kansa ya tsiguna a gaban ta ɗora hannun ta a kana tace, "Allah ya bada nasara, ko ina kaje kai ne mai nasara ai Adnan." Ya mayar da hular ya tashi ya kalli Farida da suke gulmar sa ita da su Kausar yace, "me kuke cewa?." "Cewa nayi yanzu wataƙila dan wata kayi wannan kwaliyyar ko?, Ko da yake Kausar tace ko wacece bata san wanda zata ɗauko bane shiyasa". Yayi ƴar ƙaramar dariya yana kallon su yace, "munafukai." Ganin har darıya yayi sai suka suka yi  dariya suka samu ƙarfin guiwa Mimi tace, "wallahi kayi kyau Yaya, kuma yau naji kana khamshi kuma naga baka son turaren." "Na gode. ƙaryata ni ki keso kiyi kice daman dai ina sakawa ko?." Ta girgiza kai tace, "A'a, kawai dai nayi mamaki ne da na ji ƙhamshin yanzu, ban taɓa jin khamshin mai yawa haka a jikin ka ba, nasan ana ji amma sai anzo inda ka ke sosai." "Ke dai munafuka ce, to dan kin ji turare a jikina sai ki cigaba da sakawa kizo inda nake" sai ya faɗa cikin wasa suka yi dariya. Mama dai kallon sa take tace, "wannan kwaliyyar kamata yayi ace ta Rumana ce, ina zaka je haka ne?." "Zan sanar dake Mummy sai na dawo" yana faɗa ya fice suka cigaba da gulmar sa suna dariya. Nana Haleema🫶🏻🥂 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025   ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 Masu nema daga farko ku shiga wannan link din zaku samu. https://whatsapp.com/channel/0029VaLsFSiGZNCrecIWUc36 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 022* Bebi sai da yayi sallar i'sha sannan ya ƙarasa ƙofar gidan su Manal, Baba ya gani ya fito daga masallacin da yake farkon layin yana shigowa a ƙasa yana jan charbi, ganin sa sai ya fito daga motar Baba da ya hango shi sai yayi murmushi ya ƙaraso yace, "Adnan ka ƙaraso?." "E Baba, barka da dare" ya faɗa yana duƙawa ya amsa yana cewa, "barka dai likita, ya aikin naku?." "Alhamdulillah." "To ma sha Allah. Muje ciki" Baba yayi gaba yana bin sa a baya. Sai da suka shiga soron gidan su Manal ɗin sannan yace, "anyi sa'a ma yau ma da wuta, kasan da yake ni ban amince da wani taɗi a soro ko a mota ba gaskiya, nafi gane a shigo har cikin gida in ta kama a tsakar gida ma a zauna hakan yafi min kwanciyar hankali." Bebi ya girgiza kai cikin jin daɗi da gamsuwa yace, "haka ne Baba." Tare suka shiga gidan babu kowa a tsakar gidan a share tiles ɗin yayi tass sai ganyen bishiya da ya faɗo ƙasa, gidan shiru kamar babu kowa. Ƙaramin falon da suka shiga jiya nan suka sake shiga an gyara shi sai khamshi yake kaɗan kaɗn Baba yace, "ka zauna a nan zan turo maka ita yanzu nan." Bebi yayi godiya ya zauna Baba ya fita dan ya kiran Manal. Yana zaune yana danna wayar sa yaji sallamar ta ya amsa yana ɗago kai ya ganta cikin baƙin hijjabin da ya ganta a asibiti, shine lokacin da ya kasa mantawa ko yaushe tunawa fuskar ta yake a wannan lokacin. Shaf ya manta kallon ta yake yi, yaso yayi controlling emotion ɗin sa a kanta amma ya kasa ashe har ta ƙaraso ta zauna daga gefe a kan carpet ɗin da yake falon sai ji yayi tace, "ina yini." A lokacin ya dawo hankalin sa ya dake kamar bashi ba dan ya shagala da kallon ta shi kansa ya sani yace, "kin yini Lafiya? Ya jikin ki?, I hope kin samu Lafiya sosai?." Jin tambaya har uku da yayi mata lokaci ɗaya sai ta kalle shi suka haɗa ido ta shagwaɓe fuska tace, "to wacce zan fara amsawa?. Na yini Lafiya, naji sauƙi, eh sosai a samu Lafiya." Jin ta amsa masa duka a tare yadda ya tambaya sai yayi murmushi sosai yana jin wani nishaɗ a zuciyar sa, ya gama lura shagwaɓa a jinin ta take kowa ma yi amsa take yi. Ganin yana murmushi abin ya bata mamaki tana kallon sa a ranta tana ayyana daman ya iya murmushi yake kullum fuska a ɗaure fuska. Ya girgiza kai yace, "Adnan Mu'azzam shine sunana, nasan kin san aikina ni likitan zuciya ne." Ta girgiza kai bata ce komai ba ya kalle ta yace, "Baba ya sanar dake dalilin zuwana nasan da hakan, haka kawai Allah ya saka min ke a zuciyata na kasa mantawa dake har sai da nazo gidan nan jiya na samu Lafiya." Bata ce komai ba yace, "Manal bana son ƙarya, duk wani abu da kika sani ya shafe ki ki sanar dani kar ki yi min ƙarya kat ki ɓoye min wani abu. Manal ƙarya tana sakawa naji mutum ya fita daga raina lokaci ɗaya, dan haka kar ki ɓoye min komai a kan ki. Bazan ce lallai sai kin so ni ba, in kina da ra'ayina daman haka nake fata, in bakya yi haka Allah yayi daman." Yayi shiru yana kallon ta dan yaga yanayin ta amma bai fahimci komai ba yadda take haka take yace, "meye a zuciyar ki?." Ta girgiza kai tace, "babu komai. Amma ni masu aikin ku basa burge ni, likita bai taɓa burge ni ba, so bana tunanin...." Sai tayi shiru bata ƙarasa ba. Yayi murmushi yace, "Kina da wanda kike so?." Ta kalle shi ya ɗaga mata kai yace, "na faɗa miki bana son ƙarya ko ɓoye-ɓoye, ina son magana kai tsaye." Tayi ƴar dariya tace, "ƙarya ba halina bane, bazan kuma fara daga yau ba." "Okay Answer me." "Ni bana dashi, dan bani da wannan lokacin, kula da Mamana shi na saka a gaba."  Ya girgiza kai cikin jin daɗin hakan yace, "Zaki iya saka Adnan zuciyar ki?." "Sai na duba naga yuwar hakan" ta faɗa bata kalle shi ba. Yayi murmushi yace, "haka ne, amma nasan you most love him." Sai tayi dariya tace, "really? For what reason?." "Saboda na yarda da kaina." Tayi murmushi bata sake magana ba yana kallon ta, Allah ya sani yana sonta matuƙar so, daga lokacin da ya fara sonta soyayyar ta tayi masa kamu sosai musamman yanzu da take gashi gata tana kuma murmushi tare da magana mai sanyi cikin muryar ta mai zaƙi. Haɗa ido suka yi sai yace, "Ki bani phone number ki." Ta kalle shi ido cikin ido kamar zata yi magana sai ta fasa ya miƙa mata waya ta karɓa tana saaka number kira yana shigowa taga an rubuta Rumana. Miƙa masa wayar tayi ya karɓa ganin wace take kiran sai ya ajjiye bai ɗauka ba suka yi shiru babu mai magana a cikin su. Kallon ta yake yi yana ji farin ciki sosai a zuciyar sa, Allah ya sani yana son Manal so mai yawa. Ƙara wayar ta yi ganin mai kiran sai ta ɗauka tace, "Yaya." Bai ji me akace mata ba sai yaji tace, "subscription din ya ƙare." Cikin shagwaɓa yaji ta kuma cewa, "nidai Yaya kawai ka shigo yanzu, in kace sai gobe ni bana so na kai gobe ban gama ba" ta faɗa kamar zatayi kuka. Sai yaga tayi murmushi tace, "to ina jira." Ta yanke wayar ta ajjiye tana murmushi yana kallon ta sai suka haɗa ido ta sake faɗaɗa murmushin tace, "na tafi?." Wani irin abu yake ji a zuciyar sa na tasowa yana game ilahirin jikin sa, ko ba'a faɗa ba yasan kishi ne hakan ya saka shi zuba mata ido kawai yana kallon ta. Allah ya sani yana da kishi shi kansa ya sani. Ya sauke numfashi domin ya san kishin Manal sosai, zuciyar sa zafi take yi jin tana waya da wani. Ya sauke numfashi yace, "Manal you have to be careful ba komai nake iya controlling a kai ba lokacin. Kina waya a gabana hakan zai bai min daɗi ba." Manal ita mamaki ma yake bata daga zuwa zance zuwan farko sai a dinga kafa mata sharaɗi kamar mijin ta?. Sai magana yake yi dan ita bata ɗauka ma yana da magana haka ba, wai ba komai yake controlling ba kamar wanda yake auren ta. Ta kalle tace, "Yayana ne." Bai bata amsa ba sai kallon ta da yake yi tana kallon sa kafin ya janye Idon sa yace, "Ban san kina da Yaya ba." "Ynzu na sanar da kai." Ya kalli gefe ya kulle ido ya buɗe, in ba soyayya ba taya wannan yarinyar zata zauna a gaban sa yana faɗa tana faɗa?. Ya tabbatar ko Mimi zata iya girmar ta, amma itace yana faɗa tana mayar masa inda sune da yanzu zanen yatsun sa sun bayyana a fuskar su. Sake kallon ta yayi ta sauke kai ƙasa tana wasa da wayar ta yace, "sai da safe." "Allah ya tashe mu Lafiya" ya faɗa tana tashi itama ya ajjiye kuɗi a inda ya tashi baice komai ba ya fita ta bishi da kallo, ita dariya ma ya bata wallahi da mamaki, daga zuwa zance sai a fara mata zancen bana son kaza ba'a son kaza. A haka ta koma cikin gidan Mama tace, "Manal ina fatan kin amince dashi?." "Wanne irin na amince Mama? Kina ji yana kafa min sharaɗi daga zuwan farko?, shi baya son ƙarya kuma yana da kishi kamar wanda ya haife ni ko yake aurena." Mama tayi dariya tasan halin Manal ɗin ta bata son rainin hankali sannan akwai faɗa duk da kuma akwai surutu kamar aku tace, "ai ya faɗa miki gaskiya ne Manal, gwara ku saba tun yanzu." "Yaya Haroun ne fa kawai yayi min waya dan na ɗauka muna waya shine ya dinga kallona irin zai zane ɗin nan fa Mama, shine aka fara cemin ana da kishi" ta faɗa tana dariya. Mama ma dariyar tayi tace, "kema da laifin ki meye na ɗaukar waya a gaban sa?." "To Mama Yaya Haroun ne fa?." "Na sani ai, amma ai baƙo ne dake sai ki bari ai kin fito sai ku gaisa." Manal tayi dariya Mama tace, "kina jin a zuciyar ki zaki iya amincewa dashi?." Manal tace, "gashi nan dai Mama, bashi da fara'a ko kusa ni sai jiya da yau naga dariya, sannan yana da shariya da faɗa." Mama tayi dariya sosai tace, "Manali ta kenan, Nidai ina miki sha'awar aure sa duk da bana ganin rashin fara'ar tasa." Tayi dariya itama tace, "to Mama zamu gani dai" ta faɗa tana tashi ta shiga ɗakin su ita da Mubeena tana dariya dan bata ɓoyewa Mama komai. Shi kuwa farin ciki farin ciki, ɓacin rai ɓacin rai haka ya koma gida, bai yi niyar shiga wajan Mama bama ta window ta gano shi ta kira shi ya shiga ta bi shi da kallon tuhuma tace, "zance kaje ne Bebi?." Ya kalli Maman alamun bashi da gaskiya zaiyi magana tace, "in ma can kaje na faɗa maka kayi ganganci, kana ɓatawa ko wacece lokaci ne domin kuwa kai mallakin Rumana ne, ya kamata ka san da wannan tun ba yanzu ba, babu wata mace da zata zama mallakin ta matuƙar Rumana tana da rai. Sannan gobe ba jibi, kaje ka samu Yayan mahaifin ka aje gidan su Rumana a nemo maka auren ta, kar kayi min bayani akan wata mace na riga na faɗa maka tun ba yau ba. Indai ina raye baka da mata sai Rumana ka jingine ko wacece a gefe, in kuma ban isa da kai ba dai zan gani" tana gama faɗa masa haka ta koma ciki. jikin sa yayi sanyi sosai, gashi soyayyar Manal tayi masa kamun da bazai iya haƙura da ita ba, gashi kuma dole yayi abinda Mama take so, to ya zai yi?. Yana shiga ɗaki zama yayi a kan kujera ya zubawa waje ɗaya ido cikin rashin sanin abinda zai yi, tashi yayi ya shiga ɗaki ya canja kaya zuwa ƙananu ya fito ya hau mota ya wuce asibiti. Yana shiga da Dr Hadiza suka haɗu zata fita tace, "barka da zuwa Dr." kai ya ɗaga mata kawai ya wuce ciki a reception ya tarar da Huzaifa yana niyar tafiya ganin ya wuce shi sai yabi bayan sa daman akwai abinda zai faɗa masa. Haɗuwa suka yi da Hamza ya fito daga maternity yace, "Ga Bebi ɗin can yazo, muje muyi masa zancen ko?." Ya amsa suka wuce suka same shi a tsaye ya juya baya ya harɗe hannayen sa a ƙirji Hamza yace, "Yauwa Bebi kana ji, akwai machine ɗin nan da aka siyo to custom sun kama shi a jirgin ruwa, don Allah ka yiwa Abba magana bazai rasa sanin wani ba a sake su don Allah. In machine ɗin nan yazo mune asibitin farko da muka fara mallakar sa a kaf nigeria." Huzaifa yace, "Akwai sabbin ma'aikata da muke tunanin ɗauka this year, shima yana da kyau ka nutsu mu duba cv ɗin su mu gani, ni nan da wasu kwanaki zan je Qatar Daddy yana son ganina, kaima kace min akwai contract ɗin ku da india." Sai a sannan Bebi ya juyo ya kalle su yace, "kuyi abinda ya dace kawai, zan samu Abba na sanar dashi zancen machine ɗin. Amma batun wani members kawai ku yi." Huzaifa ya kalle shi yace, "akwai damuwa ne?." Kamar jira yake yace, "Na rasa ya zanyi, Mummy tana cewa in ma akwai wacce nake so na ajjiye ta a gefe indai tana raye bani da mata kamar Rumana. Na shiga tashin hankali sosai, na farko bazan iya tsallake maganar ta ba, na biyu bana son Rumana a yanzu, na uku yarinyar da nake faɗa muku Allah ya ɗora min ƙaunar ta fiye da tunanin ku. Gabaɗaya komai baya min daɗi." Hamza yace, "to kayi haƙuri ka aure su duka su biyun." Ya kalle shi yace, "wallahi bana son Rumana, in na aure ta kamar tayi nasara a kaina ne, kullum gadarar ta sai na aure ta ko bana so." "Haka zaka yi haƙuri kayi na dan ita na dan saboda Mama, ita kuma waccan ɗin ka haƙura da ita in da hali." Ya girgiza kai yace, "bazan iya ba wallahi, baku san abinda nake ji a kanta ba shiyasa ku ke cewa haka. Ban taɓa son wani abu lokaci ɗaya kamar yadda nake son ta ba, bana so na rasa ta. Bana son ɓatawa Mummy rai, in akwai mai son farin cikin Mummy ni ne, amma....!" Sai bai ƙarasa ba yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya. Sun lura yayi rauni sosai, da alama abin ya taɓa shi har zuciyar sa yake maganar. Huzaifa yace, "Ka cigaba da addu'a kawai, kar ka daina sauraren ita sabuwar saboda kana sonta, in duka matan kane sai ka aure su. Ni a shawara ta in Mama ta matsa ka samu kuyi magana kace mata zaka auri Rumana amma ta bari ka fara auren ita wacce ka ke so ɗin daga baya sai ka aure ta, zata iya amincewa saboda tasan baka yi mata ƙarya sannan kuma itama Rumana an bata dama ta farko har ta auri wani bakai ba, duk da lokacin kana sonta ba'a matsa mata ba aka bari ta auri wani ba kai ba, kaima ya kamata a baka wannan damar." "Anya Mummy zata amince kuwa? Bata da burin da ya wuce na auri Rumana." "Zata iya amincewa mana ai ba ƙin auren nata kayi ba ka fahimta?." Ya kalli Huzaifa yace, "to ƙarya nayi mata kenan ko da gasken zan aure ta ɗin?." "Zaka aure ta mana, kaima ai baza yi mata ƙarya ba?." Ya girgiza kai yace, "wai kasan yadda na tsani batun aure akan yarinyar nan?." Hamza yace, '"mafita kake nema, zancen ka tsana duk bai tashi ba ai Bebi. Dan Mama zaka yi ba don ita ba." Ya sauke numfashi yayi shiru baice komai ba dan bai san abinda zaiyi din ba. Mujahid yana tsaye a bayan su yana jin duk abinda suke faɗa,yazo ya yi masa albishir akan yayi nasarar fara soyayya da ƙanwar sa sai yaji abinda yafi soyayya da ƙanwar sa ma dadi, yana tsaye yana girgiza kai a zuciyar sa tana faɗa masa ba mutuncin ƙanwar sa ya kamata ya taɓa ba, wacce yake so ya kamata ya fara da ita domin shima abinda yake so ya raba shi dashi. Murmushi yayi daga bayan su yace, "Ina da Shawara...." Duk a tare suka juya suna kallon sa cike da mamaki. Nana Haleema🥂🫶🏻 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025                 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* *Page 023* Haɗa idanu suka yi da Mujahid yana tsaye yana aiko musu murmushin da ya saba na yaudara yace, "Ya naga dukkan ku kuna kallona?, Kun manta Mujahid abokin ku ne?." Hamza  ya kalle shi yace, "Yaushe ka shigo nan?." "Ban wani jima ba, daman wajan Bebi nazo." Ya tako ya ƙaraso zuwa inda suke ya kalli Bebi da shima shi yake kallo tace, "Yayan mu barka da dare, nasan da cewa Yayan mu bai san da cewa soyayya ta da Lubna tayi nisa ba ko?." Sai yayi dariya yace, "kai a ganin ka wai zaka iya raba mu da Lubna ne? Ai na riga na shiga zuciyar Lubna mai raba mu a wannan lokacin babu shi, in kaga Lubna ta bar ni tabbas lokacin hakan ne ya yi a wajena." Huzaifa yace, "Mujahid ka faɗi abinda ya kawo ka bama son maganar banza da wofi." Yayi ƴar dariya yana kallon hotunan Adnan da suke manne a bangon office ɗin wanda ya samu awards a ƙasar india da saudia da sauran wurare, ya kalli hoton su su huɗu ranar da aka buɗe asibitin yayi murmushi yace, "cardiologist Adnan, ya kamata ka duba zuciyar ƙanwar ka tunda aikin ka ne zaka cire mata Mujahid in ka isa. Kana ganin kamar kwana biyu bama haɗuwa saboda baka ganina ko?" Ya faɗa yana ɗauko wayar sa ya nuna masa yace, "to kalli wannan Kaga Yaya." Kallon fuskar wayar Adnan yayi yaga hoton su ne da kayan da ya ganta ta ta shigo gidan ya kalle shi yayi dariya yace, "Lubna na sona, ko yanzu nace Lubna tazo gıdana ta same ni zata zo zan kuma zan iya yin duk abinda nake so da ita baka isa ka hanani ba, sai naga bayan license ɗina me zaka sake a karɓa. But I found something important better than this, so maybe I'll get it twice, nayi alƙawarin sai na saka ka rasa farin cikin ka kamar yadda ka saka na rasa nawa." Bebi ya kalle shi yace, "Baka isa kayi nasara a kaina ba Mujahid, na fika ƙarfin ikon samun nasara a ko yaushe saboda zuciyata a tsarkake take, baka isa ka yiwa Lubna komai ba in kuma ka iya kayi ɗin." Ya ƙyalƙyale da dariya yana kallon su yace, "kun ji abinda yace ko?" Ya kalli Bebi yace, "Wallahil azim sai nayi nasara a kan ka Bebi, ko yanzu ko nan gaba sai na saka maka ƙuna a zuciyar ka kamar yadda ka saka min." Bebi ya gyara tsayawa yace, "go ahead." Huzaifa ya kalle shi yace, "babu nasarar da zaka iya yi Mujahid, domin kuwa komai ya faru kaine ka jawowa kanka ba wani ba, kuma ko yaushe gaskiya ce take nasara ba ƙarya ba." Mujahid ya girgiza kai yace, "mu zuba dai mu gani" yana faɗa ya juya ya fice suka bishi da kallo har ya ɓace. Bebi ya kalle su yace, "Kun gani ko? Yarinyar nan Lubna daman nasan baza ta rabu da Mujahid ba, sun yi min shiru suna ganin kamar bana kula da komai amma nasan suna haɗuwa har ita Maryam suna haɗuwa da Kamal, so suke su kashe ni su huta kawai." Hamza ya sauke ajiyar zuciya yace, "Kayi haƙuri Bebi, babu abinda zai faru in sha Allah. Amma laifi na Maryam ne wallahi, ita Lubna ka ture maganar ta yarinya ce dole zai yi galaba akan zuciyar ta, ka sani na sani ko da muna karatu Mujahid ya iya tsara ƴan mata, lokaci ɗaya yake yake galaba a kansu, amma Maryam fa?. Miji ya sake ki kuna da yara biyu shi bai mayar dake ba kuma ya dinga bibiyar ki kina biye masa?. Ko me ya faru ita ta jawo." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "haka wasu matan suke yanzu ai, miji zai sake ki amma rashin hankali da sanin ciwon kai sai ya saka ya dinga bibiyar ki kuma kina sauraren sa, nida Kamal a office ɗin hisba yace ko da akwai ragowar igiya bazai mayar da ita ba, amma da yake bata san abinda take yi take zuwa inda yake wai da sunan tattaunawa akan batun yara." Huzaifa yace, "Abba ne zai maganin lamarin Maryam fa, kai tana ganin ƙanin tane baka isa ka hana ta ta hanu ba." Ya kalle shi cikin ƙunar rai yace, "Abba! Hmm." Abinda yace kawai kenan. Knocking ƙofar aka yi aka shigo wata nurse tace, "Dr akwai wanda aka kawo yanzu ƙarfe ya soke shi a zuciyar sa, "it's emergency." "Bebi yace, "They come with police?." "Yes sir." "Okay I'm coming" ya faɗa ya kalle su yace, "Zamu ƙarasa maganar, ina zuwa." Dukkan su fita suka yi ya ƙarasa wajan mara lafiyaa, a nan yaga ƙarfe ne dogo aka soka masa dan a sume ma yake,  ya kalle shi yana karanta yanayin shigar ƙarfen sukayi handling case ɗin da police ya kalli wanda ya kawo shi yace, "garin ya hakan ta kasance?" ya faɗa a lokacin ana ɗaukar sa aka shiga dashi theatre room. "Matar sace ta soke shi." Bebi da mamaki yace, "matar shi?." "Eh wallahi likita." Ya girgiza kai kawai ya wuce zuwa ɗakin, nan da nan aka shiga aikin cire masa ƙarfin Allah ya taimaka ma a gefen zuciyar ne da a tsakiya ne da yanzu ba labarin ake ba. Kusan mintina arba'in aka kwashe a ciki kafin ya fito zuwa lokacin ƴan uwan sa sun ƙaru a wajan ya kalle su yace, "kar ku damu zai samu Lafiya." Suka amsa a tare ya wuce su ya zauna akan kujera yayi shiru. Raba dare yayi ranar a babban asibiti yana aiki yaso tafiya gıda ma sai ya fasa kawai ya kwana a ciki, da asuba  ya koma gida a nan ya samu yayi bacci sosai sai azahar ya farka. Da ya shiga wajan Mama bata nan ya fita suka gaisa da Mamy ya koma ya zauna. Wayar sa ya ɗauka yana kallon lambar Manal da ta bashi jiya yana tunanin ya kira ko kuma kar ya kira, "in na kira nace mata meye?." Ya kifa wayar bai san ya kira ɗin ba yana can yana kallon wani wajan yaji ance, "Hello." Da sauri ya kalli wayar yaga seconds suna tafiya alamun ya kira har an ɗauka yace, "Hello." Manal daga can ɓangaren ta gane maganar sa amma sai taso raina masa hankali sai tace, "ina ji, da wa nake magana?." Shiru yayi bai bata amsa ba jin wai da take magana ta raina masa hankali Manal tace, "na kashe kenan?." "Kina so kice baki gane mai magana ba?." "Inda na gane bazan tambaya ba." Yayi murmushi domin haka nan yaji a jikin sa ƙarya take yi yace, "okay, basai kin san waye ba zaki iya cewa Mama ina gaishe ta." "Sai nace Mama wani ya kira ban san shi ba yace yana gaishe ki?." "Yeah you can." Murmushi yaji tayi yasan daman ta gane shi rainin hankali ne kawai sai yace, "Adnan ke magana, duk da na san kin sani." Yayi murmushi tace, "ina yini." "Lafiya lau, ya jikin?." "Alhadulillah, na samu lafiya." Bebi yace, "Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin yace, "kina cin cucumber ɗin?." Manal tace, "eh." "Ki daure zai daidai miki blood sugar ɗin." Bata amsa ba yace, "meye real name ɗin ki?." "Fatima." "A ina kika tsaya a karatu?." "Secondary school." "Baki da burin cigaba da karatun?." "Ina so, amma nafi son culinary school." Shiru ya biyo baya daman ya jima da fahimtar tana da magana sosai sai yace, "You're so good in kitchen?." Yaji tayi murmushi tace, "i think so." Daɗin waya da ita yake ji sosai komai tana bashi amsa in ya tambaya kamar kar su daina sai yaji waya na zuwa ya kalla ganin daga asibiti ne sai yace mata, "Kashe kiran it's emergency." Datse kiran tayi ya ɗauki waccan yayi shiru ana faɗa masa kafin ya tashi ya fita. Cikin kwanaki biyu Manal da Adnan sun saba sosai duk da babu wani kalaman soyayya da yake yi mata in ya kira ta, hira ce akan abinda ya shafe ta sai yanayin jikin ta dana Mama bayan wannan babu wani abun da yake ce mata. Shi a wajan sa kalaman soyayya kamar sai yara, shi kawai sai ya tsaya yana wani tsara kalamai, ai tunda yaje gidan su da niyar aure zancen soyayya ya ƙare. Tunda yaje zuwan farko bai sake zuwa ba sai dai suna waya sun saba har tana mamakin dama yana magana kuma yana da kirki haka.        A ranar litinin yayi nufin zuwa gidan nasu bayan sallar i'sha kamar wancan lokacin yaje ya haɗu da Haroun a waje  suka gaisa ya raka shi har inda suka zauna a wancan lokacin. Bai jima sosai da zama ba ta shigo ɗakin da haske wutar solar amma ba sosai ba kasancewar babu wuta ta zauna bayan tayi sallama tace, "ina yini." Khamshin turaren ta yayi masa yawa sosai hakan ya saka shi kulle ido ya buɗe, ya dafe kansa da lokaci ɗaya ya harbawa. Shiru yayi na wani lokaci kafin ya kalle ta yace, "Manal i forgot to tell you that bana son khamshin turare da yawa, wannan turaren na ki yayi min yawa sosai, yana bani ciwon kai sometimes it cause dizziness." Manal tace, "Ayya nan sani ba, kuma ni ban saka ma turare ba ɗauko hijjabin nayi kawai." "So please duk lokacin kika san zamu haɗu dake ki daina amfani da irin wannan, zaki iya amfani dashi a cikin gida amma in zaki fita ma ki daina please." Tayi murmushi tace, "in sha Allah." Ya ɗan dafe kansa kafin yace, "I don't like it!" Ya faɗa a ƙasan murya kansa har ya fara ciwo. Ganin da gaske fa baya son ɗin sai tace, "I'm sorry, let me change it." "No, is okay." Ya ɗago ya kalle ta suka haɗa ido ya sauke ajiyar zuciya, "Manal I'm here to ask you what's on your mind about me. Kina ganin zaki iya aurena?." Manal tayi ajiyar zuciya ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba yace, "please kar ki min ƙarya, na faɗa miki bana son ƙarya. Duk son da nake miki ƙarya zata iya rage kaso mai yawa a ciki." Ta kalle sho ya ɗaga kai yace, "eh ina sonki, sonki shine ya kawo ni gidan ku. Bana son ɓata lokaci da jan lokaci a soyayar baki, ki sanar dani gaskiya bana son auren wacce bata sona." Tayi ajiyar zuciya tace, "ina da ciwon sugar, ina da fushi, ina da yawan magana in ji Mama. Ina son Mamana, ina da ƴar uwa guda ɗaya." "I know all this, ina magana a kaina ne Manal." Ta sauke ajiyar zuciya tace, "zan faɗa maka." "Why now?." "No, not now, zanyi shawara da Mama." "Baki da buƙatar shawara, abinda yake ranki shi zaki faɗa." Tayi murmushi tace, "akan abinda yake ran nawa ai zamu yi shawara da ita, I'm sorry komai sai Mama ta sani sai kuma tace nayi shiyasa nace haka." Ya girgiza kai yace, "good! Zuwa nan da yaushe?." Manal tace, "maybe gobe." "Okay, I'm waiting, saboda bana son ɓata lokaci." Bata ce komai ba tayi shiru tana kallon sa yana kallon ta sai yaga tayi murmushi tace, "meyasa kake son kallona?." Yayi murmushin shima baice mata komai ba yace, "ina so mu gaisa da Mama." Ta miƙe tsaye tace, "to bara na faɗa mata." Zata wuce shi ya kalle ta yace, "ji mana." Ta jiyo ta kalle shi yace, "Meyasa ko yaushe kike murmushi?." Sai ta sake yin murmushi mai kyau mai bayyanar da asalin kyan ta tace, "it's my nature" Tana faɗar hakan ta fita ya bita d kallo cikin tsananin farin ciki da soyayya. Ba jimawa ta dawo ta tsaya daga bakin ƙofar tace, "tace kazo." Tashi yayi ya fito yana sako ƙafa tsakar gidan aka kawo wuta, haske ya gauraye ko ina fiye da ɗazu.  ya kalle ta a hasken ya rasa meyasa hijab yake mata kyau har haka ko dan tana da gaske ne bai sani ba. Ita ta fara shiga wajan Mama tana zaune akan carpet ta saka hijjaba ya shiga da sallama Mama ta amsa ya zauna yace, "Barka da dare Mama." Tayi murmushi tace, "Barka dai Adnan, ya aiki da mutanen gidan?." "Alhamdulillah, ya jikin?." "Jiki da sauki, ɗazu kamar almara naga haske a idona daga nan dai ban sake gani ba, amma tabbas ɗazu idona ya buɗe. Ko manali ban faɗawa ba." Manal ta wara ido tace, "da gaske mama?." Mama tace, "A'a da ƙarya." Sai Manal ta haɗe fuska tace, "tambaya fa nayi, kuma naga baki faɗa min ɗazun ba." Mama tace, "nima ai amsa na baki." Murmushin da Adnan yayi ne ya saka Mama ta tuna waye Adnan a wajan ta yanzu sai taji yace, "in sha Allah a hankali idanun zasu buɗe koda ba duka ba tunda anyi sakaci a baya, amma ganin zai dawo in sha Alalh ciwon bai kai ace idanun sun rufe duka ba." Mama tace, "ai naga alamun hakan kuwa, na gode sosai Allah ya yi albarka." "Amin Mama" ya faɗa yana saka hannu aljihu ya ajjiyewa Mama kuɗi sannan yace, "sai anjima." Mama tace, "a gaida mutanen gidan, na gode." Ya amsa ya fita Mama bata ji motsin Manal ba alamun bata fita ba tace, "baza kije ki raka shi ba?." Manal tace, "ɓata zaiyi ne Mama?." Girgiza kai taga Maman ta ɗaga sai tayi kamar zata ta tashi alamun zata dake ta kenan ta fito tana dariya a lokacin har ya fita. Wajan Maman ta koma ta ajjiye hijjabin tace, "Mama ga kuɗi nan fa ya ajjiye miki." Mama tace, "na ji su yanzu, kuma nawa ne?." "Dubu ɗari ce." Mama tace, "na gode Allah ya saka da alkhairi." "Amin" ta faɗa tare da yin shiru. Mama tace, "To ya ake ciki yanzu? Kina jin zaki iya auren sa Manal?." Manal tayi dariya tace, "Allah Mama kina bani kunya, ki ta tambayata a kansa." Mama tayi dariya tace, "baki da ƙawa sai ni, faɗa min abinda yake ranki a kansa na baki shawara." Manal tace, "zan iya Mama, na fahimci yana da mu'amala mai kyau, sai ka mu'amalance shi zaka gane waye shi, a haka zaka masa fassarar bashi da kirki lokaci ɗaya." Mama tayi dariya tace, "shiyasa hausawa suke cewa ba'a yankewa littafi hukunci da bangon sa. Naji daɗi sosai tunda kika ga haka to Allah yayi shine mijin ki. Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Manal ɗina zata yi aure." Manal ta dawo jikin Mama ta kwanta tace, "Mama kunya nake ji." Mama tayi dariya tace, "Zamu fara shirin biki da wuri, zan faɗawa Maman ki Balaraba a fara shiri." Bata ce komai ba sai dariya da tayi Mama na tsokanar ta. Mubeena ta fito da yake ma sun saba bata zama sun mata da ita a gidan. Gabaɗaya ta rame  ko fitowa bata yi ita lallai an yi mata ba daidai ba, Jim kaɗan  ta dawo ta sake wucewa Mama bata ce mata komai ba haka Manal. *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025    ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 024.* A daren babyn Mubeena ya faka a ƙofar gidan su Bily yana shirin yiwa mai gadi magana sai ga Bily zata shiga gidan ya sauke glass yace, "Sannun ki." Kallon sa tayi ta matso kusa da motar tace, "Yauwa sannu." Yace, "ina neman Mubeena ne, Tana ina kwana biyu shiru haka?." Bily tace, "Ayya ai sun bar Kano sun koma garin su." Gaban sa ya faɗi sosai ya kalle ta yace, "me kika ce?, dama ba a Kano suke ba?." "Eh, a Adamawa suke fulanin can ne, daman ai da kaga Mubeena kaga bafulatana. Sun tafi shiyasa da ka aiko da waya ma nace ace bata nan." Yace, "Adamawa! Ya maimaita cike da mamaki da tsoro kafin ya sake cewa, "kenan nan ba gidan su bane ba?." Bily tace, "eh, gidan mu ne nan, Mubeena ƙawata ce mun zama kamar ƴan uwa a nan take zaune kamar gidan nasu yake." Ya girgiza kai yace, "ki bani lambar ta." "Kasan ai babu waya hannun ta, a haka ta tafi bata yi sabon sim card ba." Yayi shiru alamun damuwa Biky ta Harare shi ta gefen ido tace, "da yake aure ma zasu yi mata shiyasa suka yi tafiyar gaggawa." Da sauri ya kalle ta da faɗuwar gaba yace, "aure kuma?." Ya faɗa da mamaki zuciyar sa na bugawa sosai domin haka kawai yake ji gaban sa na faɗuwa. "Eh aure, ina jin in ba'a yi bama an kusa. Sai anjima" ta faɗa tana wuce ta barshi a bayyane tana cewa, "sai na raba ku ai wallahi, haka kawai zaka lalata yarinyar mutane kai ka bar naka a gida" ta faɗa tana shiga gida shi kuma yana motar ya tafi cike da damuwa mai yawan gaske. Maryam na zaune a motar Kamal tana kallon sa da mamaki tace, "amma kace min ka goge hotunan, meye na dawo dashi kuma?." Yayi dariya yace, "meye na dawo dasu kuma? Gani nake ina tunawa dake." Maryam tayi tsaki kaɗan yace, "wannan ba abinda zaka dinga gani kana tunawa bane ba, don Allah ka goge. Tsaraicina ne fa, kuma yanzu ni ba matar ka bace." Wani kallo yake mata na bama ki da hankali kafin yace, "zan goge, yanzu gida zan kai ki ko muje nawa gidan?." Kallon sa tayi suka haɗa ido tace, "muje gida, amma nafi son don Allah ka goge hoton nan." "Wai meye abin damuwar ne? Naga lokacin da aurena a kan ki akayi hoton nan ko? Kuma kema kina da nawa meye na damuwar?." "Ni bani da naka, auren mu na mutuwa na goge dukkan hotunan dan basu da amfani tunda ba kai ba mijina bane ba." "Saboda bakya kewata ne, ni da nake kewar ki ai ban goge ba." Maryam tace, "Gaskiya zamu yi yin faɗa akan hoton nan." Ya sake yin dariya yace, "zan goge kar ki damu my love" ya faɗa yana jan motar sai fushi take yana dariyasuna tafiya. A bakin bakin su ya sauke ta ta fita yace, "gwara mu tsaya a nan kafin yayan ki ya gani mu." Bata ce komai ba yaja motar yana dariya yace, "da wannan hotunan tsaraicin naki zanyi amfani na samu abinda nake so a wajan ki, sai na saka Bebi kuka domin sai na tabbatar da kin yi ciki Maryam" ya faɗa yana ƙwafa.       Tana shiga gidan yana ajjiye mota shima bata kalle shi ba ta wuce shima bai mata magana ba ya fito ya shiga wajan Mama tana zaune kamar ko yaushe a inda ta saba zama tana cin abinci. Ya shiga ciki da sallama ya zauna ta kalle shi tace, "ina kake zuwa ne ka ke kwalliya haka?." Kafin yayi magana Mama tace, "baka je ka samu Daddy akan maganar Rumana ɗin ba ko?." "Aiki ne yayi min yawa shiyasa, amma zanje." "In baka je bama ni zanje na same shi na sanar dashi." Mimi ya kalla yace, "Mimi bani abinci naci." Ba musu ta tashi ta kawo masa bata dawo ba sai da ta haɗo da ruwa da lemo gudun kar ya mayar da ita amma ta ajjiyewa yace, "baki ɗauko kofin ruwan ba, koma ki ɗauko ki haɗo min da ketchup kin san bana son cin doya sai dashi ai." Juya tayi ta koma ta kawo masa ta ajjiye ya fara jin doyar bai sake magana ba haka Mama ma. Sai daga baya yace, "Mummy Tahir mai son Mimi, su Daddy sun gama bincike a kansa har sun bada dama ya turo tunda tana son sa." Mummy tace, "Abban ku ya faɗa min ɗazu, shiyasa ai nake so kayi abinda ya kamata a haɗa bikin naku." "Ni Mummy ai ban shirya ba, ko gini ba'a ba ina ni ina aure yanzu?." "In an saka ranar auren zaka mayar da hankali ka gama ai, kana da kuɗin yi ai, in babu baban ka na dasu. Balle ai ba kai ka ke yi ba, Abban ku ne yake maka." Shiru yayi bai kuma magana ba ya gama ci. Yana shirin tashi yaji tace, "Adnan ka jini da kyau, wallahi babu wata mace da zaka aura in ba Rumana ba kaji nace wallahi, wannan kwaliyyar da kake kwana biyu na lura zance ka ke zuwa to ka fita daga idona na rufe, ko wacece ita ka dakatar na faɗa maka domin kana da mata a ƙasa tun baka kai haka ba." Jikin sa ne yayi sanyi jin Mama har da rantsewa, bata taɓa rantsuwa haka ba sai yau shiyasa jikin sa yayi sanyi sosai. baice komai ba ya tashi ya fita shi ya rasa wannan wanne irin abu ne da Mama take masa akan Rumana. Ɗaki ya shiga ya rasa ma tunanin da zaiyi kawai sai ya kira Farida, tana ɗauka tace, "Bebi ya akayi ne?." "Ya zanyi da Mummy ne?." "Me ya faru?." "Mummy yanzun nan ta rantse akan bazan auri kowa ba sai Rumana." Farida tace, "Mummy na son Rumana ita dai kam, kana ji gobe kazo mu tatttauna nasan abinda za'ayi in sha Allah." Bai ce komai ba ya yanke wayar ya sauke numfashi ya shiga banɗaki bai jima ba ya fito ya saka kayan bacci riga da wando masu kyau ya kwanta. Da safe da wuri ya shirya da ya shiga wajan su Mama ma bacci suke ya fita kai tsaye gidan Farida ya wuce a lokacin ƙarfe bakwai na safe. Mai gadin gidan ta ya buɗe masa ya shiga yana zaune a motar ya kira ta amma bata ɗauka ba kawai ya fito ya shiga cikin gidan. A babban falon ta yara ne guda biyu suna ta shirin makaranta sai mijin ta da yake zaune yana breakfast ya shiga da sallama. Mijin nata ya amsa yana kallon sa yace, "Adnan yau kai ne a gidan namu?." Ya ƙarasa inda yake suka yi musabaha Bebi yana yamutsa fuska saboda khamshin falon da alama bata jima da gama turaren wuta ba ya zauna yace, "na shigo da sassafe kamar gidan rasuwa, in ba yanzu ba bani da lokaci." "Haka ne kam, ai kuma ƙoƙari ma sosai Allah ya taimaka." Bebi ya amsa ya kalli babar ƴar ta yace, "ina Mama naki?." "Tana sama" ya dafe kansa jijiyoyin kansa har sun fara harbawa yace, "kice mata nazo, jeki da sauri" ya faɗa yana tashi mijin mata ya kalle shi yace, " ka hau saman mana." Bebi yace, "zan jira ta ba sai na hau ba" ya faɗa yana ɗaukar waya sa ya fita daga falon. Bai jima da fita ba ta sauko tace, "A'a ina bebin?." "Ya fita waje." "Ohh shifa baya son turare, wannan khamshin ne ya dame shi shiyasa ya fita. Kasan yanzu sai ya saka shi ciwon ko ya fara jiri." Yayi dariya yace, "kowa dai da yadda Allah yayi shi, mu muna so shi baya so." Tayi dariya ta fita ta hango shi a kan kujerar ƙarfen da take ajjiye a harabar gidan ta ƙarasa ta zauna kusa dashi tace, "Kai dai ka saba zuwa gidan mutane da farar safiya, badan yara zasu makaranta ba ka sanai ban tashi ba." Ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Lokacin da nake dashi kenan. Duk kin lalata gidan ki da wannan khamshin mai sakawa mutane ciwo." Tayi dariya tace, "mijina yana so nima ina so." Ya taɓe yace, "ina jin ki, ya zamuyi da Mummy?." Tace, "kai da gaske akwai wacce ka ke so ɗin?." Kallon ta yayi kafin ya girgiza kai yace, "da gaske, lokaci nake jira aje ayi magana a gidan su." Yaya Farida tace, "kasan meye mafita a lamarin nan?." Ya girgiza kai alamun a'a tace, "Hajiya kawai zaka je ka samu kayi mata bayanin abinda yake faruwa, itace gaba da Mama ita kaɗai ce zata ne a bar maganar nan kuma dai an barta." "Nayi tunanin hakan, amma bakya ganin in na samu Hajiya da maganar ran Mummy bazai ɓaci ba? Zata yi fushi dani sosai." Farida tace, "da wannan gaskiya, Tunda dole zata san kai ne kaje ka faɗa mata zata ga ka tsallake abinda take so ne." Bebi yace, "kin fahimta. Abinda ya kamata ayi ke kije wajan Hajiyar, ki yi mata bayanin komai don wallahi in na aure Rumana na cutar da ita na cuci kanta, bazan iya kallon ta matsayin mata a wajena ba saboda ta riga ta fita daga raina gabaɗaya. Zuwan ki zai fi nawa sauƙi a wajan Mummy, in ni naje sai tafi fusata." Farida tace, "Anjima in na dawo daga aiki zan biya wajan Hajiyar. Nima bana goyan bayan auren ka da ita wallahi, da farko ai kowa yana so, da taga ɗan hamshaƙin mai kuɗi ai guduwa tayi ta aure shi ko shekara auren bai ba ya sako ta. Amma ban san meyasa Maman ta dage a kai ba, bata ganin itace ta guje ka da farko." Ya sauke numfashi yace, "Yanzu dai kije kiyi magana da Hajiya yadda ku ka yi ki sanar dani" ya faɗa yana tashi tsaye itama ta tashi tace, "ji mana, baka faɗa min a ina aka samo matar ba." Ya kalle ta yace, "mu gama da wannan case ɗin tukunna, sai mun yi waya" yana faɗa ya wuce ya shiga mota tayi dariya ta koma ciki. Nana Haleema❤️🥂 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025      ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 025* Koda ya fita kai tsaye unguwar su Manal ya huce, yana zuwa daf da layin su yayi murmushi shi kaɗai ya tsaya daga nesa yana hangen layin ya sake yin murmushi kamar mai kallon wani abun. Kamar a mafarki ya hango ta da leda a hannun ta ita da Haroun suna tafiya suna hira shima hannun sa da leda sun shiga cikin layin.  Ransa yaji ya ɓaci sosai, ya rasa meyasa take son yawo da wannan saurayin, sau biyu kenan yana ganin su, da sassafiyar nan me ya fito ma da ita har da zai ganta da wani?. Dana sanin zuwa wajan ta dabaibaiye masa zuciya ya ja motar ya tafi ba tare da ya sake kallon inda suke ba amma zuciyar shi zafi take masa sosai. Haka yayi wunin ranar bai kira ta ba itama bata kira shi ba, sai bayan sallar azahar ta kira shi sai bai ɗauka ba ta sake kira yana kallo ya sake yin banza daga nan bata kuma kira ba. Tsaki yayi ya ɗauki wayar ya kira ta kafin yayi magana yaji maganar ta hankali tashe tace, "Dr Mama ƙirjin ta ciwo yake, wanne magani zan bata tasha bata da lafiya sosai?." A ruɗe take masa magana hakan ya saka shi ya nutsu yana sauraron ta yace, "nutsu ki saurare ni." Ina ta kasa nutsuwa tace, "sosai yake ciwon, ko magana sosai bata yi ka taimaka min kar wani abun ya samu Mama." "Ki nutsu nace, ki saurara da wannan kukan ki tsaya kiji abinda zance miki." Ta kasa magana kuka kawai take da alama bata nutsuwar ta, sai ya yanke wayar ya tashi yana tunanin abinda ya kamata yayi, fita yayi da sauri zai shiga mota kenan nurse ta fito a guje tace, "Dr patient ɗin da aka yiwa theater jiya yana bleeding,kazo muje zubar jinin yayi yawa." Rasa abinda ya kamata yayi a wannan lokacin dole ya bi bayan ta da sauri amma hankalin sa baya wajan ya shiga kusan mintina talatin kafin ya fito. Turus yayi ganin Baba da kuma ita Manal ɗin a reception tana ta kuka fuskar ta tayi ja sosai. Ganin sa sai Baba ya miƙe tsaye Bebi ya ƙaraso yace, "Baba ya jikin nata? Ina aka kai ta?." Baba yace, "Dr Huzaifa ne ya karɓe ta." Da sauri ya juya suka haɗu da Huzaifa ya nuna masa ɗakin ya shiga don ganim abinda ya kamata ayi. Nan da nan ta samu bacci ciwon ya lafa, ya fito daga ɗakin ya koma reception ya tarar dasu har lokacin suna zaune sai dai ta daina kukan sai jan numfashi da take yi. Ya kalli yace, "Baba muje ciki." Ba musu Baba ya taso suka tafi cikin har Manal ɗin ya zaunar dasu a wani personal room. Sai a sannan yace, "Baba bamu gaisa ba." Baba yayi dariya yace, "Manal ta ruɗa ni, ta ruɗa kowa taya zamu iya gaisawa?." "Barka da rana." "Barka dai Adnan, ya aikin?." "Alhamdulillah. Jikin nata da sauƙi, akwai damuwa ko ɓacin ran da ya haifar da ciwon, amma yanzu zai daina mata ciwon in sha Allah." Baba ya girgiza kai yace, "Ban san me yake damun Fatima haka ba da zata dinga saka damuwa a ranta bayan tasan ba lafiyar kirki ce da ita ba." Baba ya sake cewa yace, "zamu iya zuwa mu ganta?." Adnan yace, "sosai, muje na raka ka" tare suka fita aka bar Manal a zaune bata dawo daidai ba har lokacin tayi shiru kawai. Sai bayan sun fita tabi bayan su zuwa ɗakin Mama na kwance tana bacci Manal ta tsaya kusa da ita Baba yace, "Hankalin ki ya kwanta ko Manal? Ga Mama nan ta samu lafiya, to sai ki nutsu don Allah." Bata iya cewa komai ba sai daga baya murya a sarƙe tace, "Baba kaje ka baro kasuwar babu kowa zan zauna da ita a nan." Baba yace, "A'a bazan barki a nan babu kowa ba, mu zauna duka ai yamma ta kusa daman." "Yaya Haroun zai zo, kaje kawai Baba." "To bara yazo ɗin na tafi." Adnan yace, "babu damuwa Baba zaka iya tafiya duk muna nan tare." Jin haka sai Baba ya amsa gudun kar ya gwale shi yaji babu daɗi ya fita bayan sun yi sallama. Kallon ta yayi amma ita Mama take kallo yace, "ki barta ta huta a nan, muje ko?." Gaba tayi tana tafiya a hankali kamar bata so suka fita. "Manal jikin nata yayi sauƙi ko?." Kai ta ɗagawa Huzaifa da yake tsaye a bakin ƙofar. Yayi dariya yace, "Tunda naga kin daina kuka nasan jiki Alhamdulillah, ki shiga wannan ɗ'akin ki zauna ki huta kema." Ɗakin da ya nuna mata da hannun ta kalla taga wanda suka zauna da Baba ne, ta nufi ɗakin shi kuma ya kalli Huzaifa yace, "Ya akayi suka zo nan?." "Kirana tayi hankali a tashe, da yake ina kusa da gidan na su sai naje kawai muka taho nan." Gaban Adnan yayi mugun faɗuwa cikin fargaba da kishi mai tsanani yace, "kana da number ta kenan, kuma har ka san gidan su ma?." Yayi dariya yace, "eh mana, kasan da yake yanzu da ita za'ayi na fasa da waccan" ya faɗa cikin wasa ba tare da yasan alaƙar su da Adnan ba ya tafi ya barshi a wajan kamar an dasa shi a tsaye shi kuma bai lura da yanayin sa ba. Gaban sa ne yake faɗuwa sosai tashin hankali ya dabaibaye shi, zuciyar sa na bugawa da ƙarfin gaske saboda kishi. kallon inda Huzaifa ya shiga yayi ya kalli inda Manal ta shiga nan da nan ransa ya kai ƙarshe wajan ɓaci, yayi ƙoƙarin sarrafa kishin sa da ɓacin ran ya huce zuwa office bai ma sake waiwayar ta ba. "Amma na faɗa mata bana son ƙarya meyasa bata sanar dani wannan ba?, Meyasa bata ce min Huzaifa yana son ta ba?" Ya faɗa shi kaɗai yana dukan kujera yana jin zuciyar sa har wuya ya tsaya gabaɗaya ya rasa ma abinda ya kamata yayi. Ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zagaye yake daga nan yaje nan, daƙyar dai ya samu ya zauna yayi shiru baice komai ba ya zubawa waje ɗaya idanu zuciyar sa na bugawa a guje. Kishi ne yake addabar sa, baya so a ɓoye masa komai shiyasa ya faɗa mata tun farko, meyasa bata faɗa masa Huzaifa ya san ta har haka ba?. Huzaifan ne ya shigo da sallama yace, "Bebi ya ka yiwa Abba maganar machine ɗin nan?." Lumshe ido yayi ya haɗɗiye yawu ya buɗe idanun nasa ya kalli Huzaifa da shima shi yake kallo tace, "lafiya kake idon ka yayi ja haka?, Meyasa cikin kwanakin nan baka zama daidai ne?. Idanun ka sunyi ja, akwai wani abu ne?" Ya faɗa dan shi ya manta da katoɓarar da ya aikata. "Huzaifa kasan bana son ɓoye-ɓoye, bana son ƙarya kuma, meyasa baka faɗa min kuma soyayya da Manal ba?." Huzaifa mamaki ya dabaibaiye zuciyar sa yace, "ikon Allah, meya kawo wannan maganar kuma?. Ban da abin ka in ma ina soyayya da ita ai kamar ba sai na faɗa maka ba ko?, kai ma baka faɗa mana da wa ka ke soyayya ba, dan na ɓoye maka ai ban yi laifi ba." Baice komai ba amma ya zuba masa idanu yana kallon sa Huzaifa yace, "wannan shine silar ɓacin ran naka?, To meye na ɓacin ran? Akwai aibu a ciki in ma son nata nake?. Kai ko Lubna ce nake soyayya da ita ai bana tunanin ranka zai ɓaci haka balle ita da baka da alaƙa da ita. Ba kai ka ke cewa daman sonta nake ba?, meye na damuwa kuma?." "Ya isa! Ya isa Huzaifa!. Don girman Allah bani waje bana son magana ma dakai gabaɗaya." Mamakin sa Huzaifa yake yi yayi shiru ya tafi tunani na wani lokaci kafin ya sake kallon sa baice komai ba sai ya fice. Wajan Hamza yaje ya jawo hannun sa suka fito daga ɗakin da yake cewa, "Meya faru?." Huzaifa yace, "Adnan ya faɗa maka akwai alaƙa tsananin sa da Manal ne?." "Wace ma Manal?." "Wata yarinya kwanaki da suka kwanta a nan da Maman ta?. Duk suna da ciwon sugar ka gane ta?." "Ohh na gane, bai faɗa min ba meye ya faru?." Huzaifa yace, "Wasa nayi masa nace yanzu da ita za'ayi na fasa auren waccan kaga yadda ya canja?, da naje na same shi a office ya tsare ni da ido yana cemin baya son ɓoye-ɓoye na faɗa masa yaushe na fara son ta." Hamza yayi dariya yana kama baki da mamaki yace, "kar dai itace yarinyar da yake faɗa mana?." Huzaifa yace, "nima nayi wannan tunanin, kai kaga yadda ya tashin hankalin sa sosai? Fuskar sa ta kaza ɓoye abinda yake zuciyar sa, kai da ka gani kasan akwai kishi a lamarin." Hamza yayi dariya harda tafa hannu yace, "Shege Bebi yana son mata masu kyau. yanzu dai naga kuna mutunci sosai da ita, muje ka tambayar mana, ka san gulma akwai daɗi." Huzaifa yayi dariya shima yace, "jira ni ina zuwa" ya faɗa yana wucewa ya bar Hamza yana dariya kafin ya cigaba da abinda yake yi. Wajan Manal ɗin yayi niyar zuwa amma sai ya fasa tunawa da aikin da ya bari an office amma yaso yaje yaji kwakwaf dan ya ƙure Adnan. Bebi bai sake ganin Manal ba itama bata kuma ganin sa bar bayan la'asar, a lokacin Maman ta farka kuma ance shi zata sanarwa, sai a sannan ta ƙwanƙwansa office ɗin ya amsa daga ciki ta shiga da sallama ya amsa bayan ya ɗaure fuska sosai tace, "Dr Mamana ta farka." Ba tare da ya kalle ta ba yace, "reception ake zuwa a faɗa." jin abinda yace ta kalle shi sai tace, "Okay, thanks." Ta faɗa zata fita sai taji yace, "wait." Ta kalle shi yace, "ina zuwa." Bata sake magana ba ta juya tana mamakin hali irin nasa, gabaɗaya ya canja kamar ba shi ne suke hira a waya da zahiri ba. Takun sa taji a bayan ta kafin ta shiga ɗakin ma ya riga ta ya saamu Mama ta farka tana kwance ya ƙarasa yace, "Sannu Mama." Mama tace, "Adnan ne?." "Shine Mama, ya jikin?." "A asibiti muke kenan. Da sauƙi, ciwon yayi sauƙi sai kaɗan da nake ji." Adnan yace, "Zaki daina shima in sha Allah, damuwa ce ta miki yawa shine ya haifar da wannan ciwon. Sai Ana haƙuri ana kawar dakai a kan dukkan lamura, ina ance komai sai an damu a kansa zuciyata baza ta zauna lafiya ba. Kuma shi wannan ciwo ko ya ɓacin rai yake baya iya ɓuya sai ya bayyana." Mama ta girgiza kai tace, "Haka ne Adnan, na gode. Ina Manali?." "Gani Mama" ta faɗa murya na rawa. Mama tace, "Manal meye na kukan gashi ai na tashi ko? Kina ina?" Ta faɗa tana miƙa mata hannu Manal ta ƙaraso ta riƙe hannun Maman tana kuka. Mama tace, "meye na kukan kuma Manal? Ai naji sauƙi yanzu ciwon kaɗan nake ji." "Mama ɗazu ko magana bakya yi, hankalina ya tashi na rasa ya zanyi." "To ki yi haƙuri na samu sauƙi, ki gode Allah da ya haɗa mu da su Adnan." Murmushi yake yana kallon su suna burge shi sosai domin akwai soyayya da shaƙuwa a tsakanin su sai ya fita dan yaga sun manta ma dashi. Bai jima da komawa office ba ta sake dawowa da sallama ya amsa a lokacin yana zaune da laptop yana dannawa ya kalle ta bayan ta shigo tace, "sorry na kuma dawowa, Mama tace zamu iya tafiya gida?." Kallon ta yake yi kafin yace, "zauna." Bata musu ta zauna ya tashi ya ɗauki ruwa da kansa ya bata yace, "sha." Ta karɓa tasha kaɗan ta ajjiye yace, "ki dawo nutsuwar ki." Manal tace, "a nutse nake." "Mama ta samu lafiya kar ki damu, ki dinga ƙoƙarin ganin bata shiga damuwa ba ko tunani, duk abinda kika san zai saka ta a damuwa ko tunani kiyi ƙoƙarin ki ga bai faru ba kina ji?." Ta ɗaga kai alamun eh yace, "anytime, anywhere wani abun ya faru just call me, in banyi picking ba ki ta kira na har sai kin tabbatar na ɗauka, kin gane?." Ta ɗaga kai alamun eh. "Mama zata zauna a nan har sai gobe da safe, saboda ta sake samu sauƙi sosai sai ku koma." Kai ta ɗaga kai ta yunƙura zata tashi yace, "ki koma ki zauna." "Zan faɗawa Mama sai gobe ne." "İn kin koma tayi bacci." Ta kalle shi tace, "ya akayi ka sani?." Ya kalli agogon hannun sa yace, "Lokacin tayi baccin ne yayi." Ganin bata amince ba sai yace, "kije ki duba, in kin tabbatar tayi baccin ki dawo." Fita tayi taga Maman tayi bacci kuwa sai bata koma ba saboda kiran sallar magriba da ake yi, sallah tayi tana zaune kusa da Maman Baba ya dawo ya shigo ɗakin suka cigaba da zama kafin ya fita lokacin i'sha tayi sallah itama Bab ya dawo yace, "Manal baki ci abinci ba, gashi Dr Adnan ya faɗa min zata kwana a nan saboda ta sake warwarewa gobe sai mu koma gida." Manal tace, "Bana jin yunwa ma Baba." "Zaki ki yunwa Manal, zan saka nemo miki abinda zaki ci." "Allah bana jin yunwa." "Ai kwana zaki ko kin manta ne?." Ta girgiza kai tace, "Ban manta ba, basai naci komai ba." Baba yace, "To shikenan." Suna nan zaune har tara na dare sannan Baba ya tafi ya barta bayan ya tabbatar da Haroun ya tawo. Ita kuma ta fito ta zauna a kofar ɗakin tayi tagumi kamar wata marainiya. Huzaifa da yake niyar tafiya gida ya gano ta ya ƙaraso yace, "Manal ba dai jikin Maman bane?." Tayi murmushi tace, "A'a Dr, bacci ma take sosai." "Haka ake so, zan wuce ni gida amma Bebi yana nan nasan zai kula da komai." "Allah ya saka da alkhairi." "Kar ki damu an zama ɗaya ai." So yake ya tambaye ta maganar Bebi amma sai ya kasa sai daga baya yace, "kin san waye Bebi ɗin?." Ta ɗaga kai alamun eh yace, "Yauwa, duk abinda yake damun ki ki sanar dashi." Ta amsa da to yayj mata sallama ya tafi badan haka yaso ba yaso yaji meye alaƙar su da shi. Tana nan zaune sai ga message a wayar ta ya shigo ta buɗe taga Adnan ne yace, _ki tashi daga nan ki shiga ɗakin da kika zauna ɗazu, sai zuwa sha ɗaya Mama zata farka._ kallon wajan tayi taga baya nan, abin bai bata mamaki ba ta san bazai wuce ta camera ya ganta ba, tashi ɗin tayi ta shiga dan ta gaji da zaman. Tana shiga ta zauna akan kujera babba ta jingina, buɗe ƙofar akayi aka shigo sai ga wata nurse da abinci tace, "Dr Adnan yace a kawo miki." Murmushi tayi ta karɓa tayi godiya ita kuma ta koma. Buɗe pack din abincin tayi shinkafa ce basmati fara tass ga miya a wani pack ɗin sannan ga salad mai yawan gaske yaji uban cucumber. Fara ci tayi a hankali taci rabi ta tashi ta sha ruwa a water dispenser ta dawo ta zauna tana murmushi a zuciyar ta. Knocking ƙofar aka yi ta amsa ya buɗe ya shigo ta kalle shi ya kalli abincin yace, "baki ci ba?." "Naci, ya ishe ni, na gode." "Ɗazu kafin nazo waye ya kawo ku nan?." "Dr Huzaifa ne, shi na kira na sanar dashi, na ruɗe na manta ma ba faɗa maka." Ya girgiza kai yana kallon ta yace, "baki taɓa bani labarin kina da number Huzaifa ba, bayan nace miki bana so kiyi min hiding komai." Manal da mamaki tace, "ban ɗauka ya shiga ciki abinda kake nufi bane, beside na jima ina da number shi tun muna zuwa babban asibiti, ina kiran shi a waya in yana nan muje in baya nan sai mu fasa zuwa." Ya girgiza kai yace, "Baki bani labarin alaƙar ku tayi girma haka ba ai." Manal tace, "yana da kirki sosai har yaso ya fika, yana ɗauka na kamar ƙanwar sa nima ina ɗaukar shi Yayana. Kai tsaye zan iya kiran shi kafin na kira ka." Ran Bebi ya sosu sosai bai magana ba ta kuma cewa, "Saboda wani lokacin kai sai aga kamar baka son ma ayi maka magana." Ya sauke numfashi yana kallon ta ta ƙasan ido cikin ƙunar rai yace, "shi kuma wanda ma gan ku da safe tare fa? Sau biyu ina ganin ki dashi akan titi kuna hira, shi kuma waye ɗin ki? Shi ma yafi ni ɗin ko?." Nana Haleema🥂❤️ *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025      ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 _Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da Mandi rice, chicken biryani, funkaso, alelen gwangwani, bread pocket da sauran su._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ call/whatsapp 09030398006 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida. *BOOK 1* *Page 26.* Manal ta kalle shi cikin mamakin abinda yace tace, "ka gan mu da safe? A ina to?." Ya jingina da kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya yace, "ki bani amsa." Manal ta yatsine fuska tace, "Yaya Haroun ne, Yayana ne, kuma ka san shi." "Baki bani labarin kina da Yaya ba."  Kallon sa tayi tace, "komai sai na faɗa maka?, kuma ranar da kazo gidan mu ya kira ni a waya ai na faɗa maka ko?." Da ido ya bata amsa ya kulle shi ya buɗe alamun eh ta kawar da kai tace, "kai ba komai ka faɗa min ba ai" ta faɗa tana kallon agogo kafin tace, "Lokacin tashin Mama yayi kamar yadda kace, zan koma wajan ta." Baice mata komai ba ya ta fita yayi murmushi bayan ta fita, Allah kaɗai yasan yadda yake matuƙar farin ciki in yana zaune gashi gata. Sau uku kawai suka zauna tare amma bazai manta da wannan ranakun ba gaskiya. Kamar almara tana shiga taga Mama ta farka dan tana zaune ma ta ƙarasa tace, "Mama kin tashi?." "Eh Manal, ina kika je?." "Ina zaune a wani ɗaki a can ma naci abinci." "To zo ki taimaka min nayi sallah, dare yayi ko?." "Eh Mama, har ta wuce tayi." Mama tace, "Subahanallahi." Taimaka mata tayi ta sauka tayi alwala ta tayar da sallah. Sai bayan ta idar Manal na zaune Mama tace, "Manal ina ganin hasken ɗakin nan da kaɗan-kaɗan." Manal tace, "da gaske Mama? Kina iya ganin ɗakin nan?" Ta tambaya a ruɗe da farin ciki.  Mama tayi murmushi tace, "ina iya ganin hasken ɗakin amma ba sosai ba." "Bara naje na faɗawa Dr ko akwai abinda za'a yi." Mama tace, "yi zaman ki ki huta, Mubeena bata zo ba ko?." Manal tace, "tare muka zo sai Baba yace ta koma gida." Mama bata ce komai ba tayi shiru Manal tace, "Mama abinci fa?." "Bar shi Manal naci da safe." "Safe kuma Mama? Bafa kici abinci ba kwata-kwata." "Yanzu in nace zanci a ina zaki samo? Sai dai ki faɗawa Adnan a kawo min kuma ni bana so. Yaron nan bai fa aure ki ba har yanzu, kin ce baki gama tunani akan zaki iya auren sa ba ko baza ki iya ba, tun yanzu muna ɗora masa wahalar rashin lafiyata?, ko ya aure ki kula dani ba a kansa yake ba balle bai aure ki ba. Da na san ma shi zaki kira da ban faɗa miki bani da lafiya ba. Matsayin sirikina yake a yanzu, bai aure ki ba baza'a dinga ɗora masa wahala ba. Ko ya aure ki haƙƙin kula dani ba a kansa yake ba." "Assalamu alaikum." Aka faɗa daga bakin ƙofa mai share-share na asibitin ya shigo da leda a hannun sa yace, "Barka da dare, ya mai jikin?." Manal ta amsa ya miƙa mata yace, "Gashi in ji Dr Adnan." Manal ta karɓa tayi godiya ya fita ta kalli Mama tana buɗe abincin tace, "gashi ya aiko dashi." Mama ta girgiza kai tace, "Bana jin daɗin haka Manal, nauyin sa nake ji wallahi." "To Mama bani nace masa ya kawo ba ai." "To sai ki bani naci." Manal tayi murmushi ta koma kusa da ita ta buɗe mata tana ci. Sai bayan ta gama cin abincin Adnan ya shigo da sallama ya kalli Mama yace, "Mama ya jikin?." "Da sauƙi sosai Adnan, har ciwon ma na daina ji." Manal tace, "Mama tace tana ganin hasken ɗakin nan." Mama ta taɓa ta tace, "Manal!." Manal tace, "Mama bazan iya shiru ba, kiyi haƙuri." "Daman ke ai bakya iya shiru." Manal tayi murmushi Bebi yace, "Ana samun cigaba sosai, zan aiko da magani yanzu ki saka mata a idon ta, sannan akwai glasses da zan baki tana amfani dashi." Manal tayi murmushi tace, "To" sai ta kalli Mama tace, "Mama kin ji ko? Kar kice na takura miki da magani wani sabo za'a bayar." Mama tayi murmushi ita nauyin ma Adnan ɗin take ji, Bebi ya fita ba jimawa aka aiko da maganin ta sakawa Maman suna ta hira sama-sama. Adnan ya gama komai amma bazai iya tafiya ba haka ya kwana a asibitin, har bakwai na safe yana asibitin a lokacin ake medication nurses suna bi ɗaki-ɗaki suna bawa a marasa lafiya magani. A lokacin Huzaifa yazo da mamaki yake kallon motar Bebi ganin inda ya barta jiya, ya shiga ciki yaga dai yana nan kuma gashi da kayan jiya da alana kwana yayi, ya bishi da kallo yace, "Daman kwana kayi?."  Idanun sa lumshewa suke saboda bacci Adnan yace, "Uhum! Yanzu zan tafi." "Wai saboda Manal ɗin ka kwana ka yini kana aiki?." Kallon sa yayi bai ce komai ba Huzaifa yace, "ai na gama fahimtar itace wacce ka ke so ɗin, daga yi maka wasa jiya ka canja." "To ka fahimta kuma kake tambaya ta? Kasan dai babu inda zan iya zuwa ko?." Huzaifa yayi dariya yace, "lallai soyayya tana wahalar da kai." Baice komai ba ya fita ya barshi ya shiga inda su Manal ɗin suke a lokacin ma Baba yazo suka gaisa ya bawa Baba glasses ɗin yace, "Wannan zata dinga amfani dashi, zai taimaka mata wajan gani in sha Allah." Baba yace, "mun gode sosai Adnan, Allah yayi albarka." Yayi murmushi kaɗan ya kalli Manal a lokacin ta kalle shi sai tayi masa murmushi ya ɗauke kansa yace, "zan wuce gida yanzu, akwai wanda zai kai ku gida in kun gama shiryawa zai zo ku tafi." Mama tace, "ai mun gama ma mu tafi kawai." Adnan ya girgiza kai ya fita. Jim kaɗan sai gashi tare da wani suka fita gabaɗaya suka shiga mota ya tafi kai su shima ya hau mota ya tafi gida dan bacci yake ji matuƙa. Koda ya koma gida ko wajan Mama bai iya zuwa ba kai tsaye ɗaki ya wuce ya cire kayan jikin sa ya kwanta nan da nan bacci ya ɗauke shi. Sha biyu na rana wayar sa ta tashe shi ya kalla yaga daga asibiti ne, kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauke abinda akace masa ya saka shi sauke wayar ya miƙe daƙyar ya shiga wanka. Da sauri da sauri yake shiryawa ya gama ya fita ya gaisa da Mamy ya shiga wajan Mama Mimi tace bata nan ya hau mota ya koma asibitin, kansa har ciwo yake saboda bai samu bacci ba.       Mama tayi wanka taji daɗin jikin ta sosai suna zaune da Manal Maman su Surayya ta fita a lokacin Mubeena tazo ta zauna tace, "Mama ya jikin?." Mama tace, "da sauƙi." "Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin kafin Mama ta kalli Manal tace, "Baki faɗa min ya kike ji a zuciyar ki akan maganar Adnan ba, har yanzu baki yanke hukunci ba?." Manal tayi shiru jin shirun Mama tace, "Ni dai ina miki sha'awar auren sa, duk ke zaki yanke abinda kike ganin daidai dake ne, amma ni kam ina so ki aure shi. Duk da ban san ya kammanin sa suke ba, amma yanayin maganar sa zai baka tabbacin nustuwar sa a zahirance." Manal tayi murmushi a zuciyar ta tana ayyana daman ai shi zan aura in sha Allah, a zahiri sai tace, "Na yanke hukuncin ai Mama." Mama tace, "faɗa min to mana." Manal tayi dariya tana ɓoye fuska tace, "To Mama ki gane abinda nake nufi mana." Mama tayi dariya dan ta fahimta tace, "to na gane, Allah yasa shine mijin ki, Allah ya sa ya zamar miki na gari Manal. Burina daman ki samu mijin da zai kula min dake kuma na tabbatar kin samu." Tayi murmushi tana jin daɗi a zuciyar ta. Manal tace, "Mama bara naje wajan Surayya kin ji Mama tace bata da lafiya." Mama tace, "to yi sauri, duk da nasan zaki je ki bata labarin Adnan ne." Tayi dariya ta saka mayafi da takalmi ta fita. Gidan su Surayya ɗin ta shiga ta samu Mama zata aike ta farkon layi kawai suka fito tare suka jera suna hira. A hanyar su ta dawowa da yake rana ce babu mutane sosai suna ta hira Manal taji an kira sunan ta daga baya, ta juya ta kalli wanda ya kira ta dan bata san shi ba hakan ya saka ta mamakin a ina ya santa. Ya ƙaraso yace, "Barkan ki, nasan baki sanni ba ko?." Bata yi magana ba yace, "Abokin Adnan ne ni, sunana Mujahid." "To sai akayi me?" Ta faɗa tana kallon sa. Yayi murmushi yana kallon ta yana kuma yaba kyaun ta yace, "in kina tantama zan nuna miki shaida" ya faɗa yana ɗauko wayar sa ya nuna mata hoton su ta kalli screen ɗin wayar yace, "abokin sa ne ni sosai, in kika tambaye shi zai faɗa miki.." Manal ta ɗaga ƙafa zata tafi yace, "Nazo na sanar dake wata gaskiya akan Adnan. Manal Tsakani da Allah ba wai yana son ki bane, Adnan ƴar masu kuɗi yake burin aure daidai shi, yana amafani dake ne saboda kina da kyau daga zarar ya samu abinda yake so shikenan zai mama gaban sa. Zan iya cewa kece mace ta goma da Adnan zai yaudara domin wannan halin sane, kar kiyi mamaki ko tunani akan wani abu kiyi tunani akan rayuwar ki." Ya sake cewa, "na zaɓi na sanar dake ne saboda naga ke marainiya ce mai kula da mahaifiyar ta, kiyi baya da Adnan kar ki amince da duk wani daɗin bakin sa in ba haka ba nan gaba kaɗan zaki dana sani" yana gama faɗar hakan ya shiga mota ya tafi ya bar Manal tana kallon motar. Kallon Surayya tayi Surayya itama ita take kallo tace, "kar wannan yayi tasiri a zuciyar ji, irin mutanen nan ne masu so lallai sai sun raba mutum da wanda yake so. Ni ban ɗauka ana korarwa maza wacce suke so ba, na zata mata ake yiwa suma kuma daga na jikin ka yake faruwa. Don Allah ki share kawai mu wuce, da ganin wannan bana kirki bane, in haka halin Adnan ɗin yake da yanzu Baba ya raba ku." Manal ta share maganar a lokacin suka tafi suna sake tattaunawa akan maganar Mujahid ɗin har suka je gida ta shiga gıda itama ta shiga gida zuciyar ta cike da saƙe saƙe. Tana shiga Mama tace, "har kin dawo?." "Eh Mama na dawo." Mama tace, "Yanzun Baba ya fita nake sanar dashi kin amince da auren Adnan ayi musu magana manya su shiga maganar." Manal ta yi shiru jin hakan sai Mama tace, "Lafiya kike?." "Lafiya lau Mama, bacci nake ji" ta faɗa tana tashi ta wuce ciki Mama ta girgiza kai kawai dan tasan akwai abinda yake damun ta. Manal duniyar tunani ta tafi a wannan lokacin, in hakan da gaske ne ya zata yi kenan? In hakan da gaske ne kenan yazo ya lalata mata rayuwa ne ya gudu?. Dafe kanta tayi ta bayyane tace, "da gaske fa nayi mamaki, meyasa kaf matan garin nan ƴan gayu masu wayewa da ilimi bai nemo wata ba sai ni?. Kuma tabbas a office ɗin sa akwai hoton su da wannan mutumin, kenan da gaske abokin sa ne?." Shiru ta sake yi a lokacin Mubeena tazo ta zauna a inda take ta kalle ta dan tana buƙatar a bata shawara amma ba daga Mubeena ba, gabaɗaya haushin Mubeena take ji hakan ya saka ta tashi ta bata waje ta koma daƙin Mama ta kwanta ba dan tana jin baccin ba. Tashi zaune tayi ta ɗauki waya tana tunanin ko ta tambayi Huzaifa ne?. Shiru tayi ta ajjiye wayar ta koma ta kwanta ba tare da ta nemowa kanta mafita ba kuma bata kira Huzaifa ba.       Bebi bai dawo gida ba sai magriba yana tsayawa yaga motar Kamal ta wuce sai kawai ya fasa shiga gidan ya karkata motar kai tsaye ya ɗauki hanyar gidan iyayen su Kamal ɗin dan abin nasa yaga ya fara yawa. A ƙofar gidan ya tsaya kasancewar gidan ba gate bane ya rasa yadda zaiyi ayi masa magana da mai gidan. Yaro ya gani zai wuce ya tsayar dashi ya aika gidan jim kaɗan sai ga mahaifin nasa ya fito Adnan ya ƙaraa suka gaisa da girmamawa sannan yace, "Alhaji nasan baka sanni ba, sunana Adnan ni ƙani ne ga tsohuwar matar Kamal Maryam." Sai fuskar sa ta washe yace, "to na gane ka yanzu, kana magana sai naga kama da Alhaji Mu'azzam Alhassan. Ya mahaifin naka da masu gidan?." "Alhamdulillah." "Mu shiga ciki." Adnan yace, "A'a nan ma yayi, ƙorafi na kawo akan Kamal." Mahaifin sa yace, "wani abu ya faru ne?." "Yana faruwa ma Alhaji, Kamal yana cigaba da bibiyar Maryam bayan babu aure a tsakanin su. Nasan itace ta bada fuska ita ya kamata na fara yiwa magana, nayi mata wanda suke gaba da ita ma sunyi,  shima Kanal ɗin na same shi nace indai akan yara ne babu damuwa duk sanda take son ganin yaran zan je na ɗauko su shima in yana sona dawo dasu zan dawo masa dasu. Abin yayi yawa Alhaji, har maganar na kai gaban babban malamin hukumar hisba amma Kamal bai ji ba." Adnan ya sake cewa, "Shiyasa nazo da maganar gaban ka, tunda babu aure babu amfanin bibiyar da suke yiwa juna, in Allah ya rubuta zai sake zama da ita matsayin mata zai sake nan gaba in muna da rai, amma bibiyar bata da amfani wani ma sai yayi musu fasssarar da bata kamata ba. Wannan tambari da nake guje musu zai bibiye su har yaran su." Girgiza kai yake yi cike da gamsuwa da maganar Adnan a bayyane yace, "Na jima ina ji ana labarina kawai yaron da yafi babba hankali da hangen nesa da iya kalamai ban amince ba sai yanzu, gaskiya kayi tunani mai kyau da kuma hangen da mu iyaye a mu yi ba. Tunda babu aure a tsakani babu amfanin bibiyar ta da yake yi kamar yadda yace. Zan yiwa tufkar hanci in sha Allah, na kuma gode sosai da ka same ni da maganar kai tsaye dan wannan gyaran babbar ɓarna ce." Jin ya fahimce shi sai yayi murmushi yayi godiya shima ya gode suka yi sallama ya hau mota ya tafi gida. Nana Haleema❤️🥂 *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025                 ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* *Page 027.* Sai da yayi sallar i'sha sannan ya shiga gida, yunwa yake ji matuƙa domin tun da yaci abinci da safe a office bai sake ci ba. Yana shiga wajan Mama ya same ta a zaune ranta a ɓace matuƙa amma bai kula da yanayin ta ba ya wuce kitchen yana cewa, "Mummy yau bamu gaisa ba, na dawo kuna bacci zan fita bakya nan sai yanzu." Jin tayi masa banza yasan akwai wani abun ya dawo da abinci a hannun sa ya zauna yace, "Barka da dare Mummy." Bata amsa ba bata kuma kalle shi ba,  sai ya kalli Mimi ta masa magana da ido ya kalli kausar itama ta masa alama nan ya fahimci akwai damuwa. Ya kalli Mimi yace, "Akwai abinda ya faru ne?." Kafin Mimi tayi magana cikin fusata Mama tace, "tambaya ka ke bayan kasan abinda ka aikata?." Yayi sak yana tunani kafin yace, "Wallahi Mummy ban san abinda yake faruwa ba, a asibiti na kwana da na dawo ko baccin five hours ban samu ba na koma ban dawo ba sai yanzu." "Amma da haɗin bakin ka aka je aka samu Hajiya akan maganar Rumana ko?." Gaban sa ya faɗi dan shi ya manta ma sunyi haka da Farida dan ko waya basu yi da ita ba shiyasa bai tuna ba. Ganin yayi shiru sai ta sake fusata sosai tace, "Tunda aka yi maganar nan ban sake ganin ka ba sai yanzu da yake kasan kayi laifi, ai ka kyauta Adnan ni zaka haɗa da mahaifiyata ko?." Bebi yayi shiru kansa yan ƙasa tace, "ni zaka tura a kai ƙara wajan wacce ta haife ni saboda ina so ka auri Rumana kai baka so?, duk da na nuna maka ina so hakan bai saka kabi ra'ayina ba sai da ka tabbatar kabi hanyar da za'a dakatar da hakan duk da burina ne, ka zaɓi wata daban a kan farin cikina." Bebi a raunane ya sakko daga kan kujera ya zauna kusa da ƙafar ta yace, "Don girman Allah ki yi haƙuri Mummy, wallahi ba haka nake nufi ba. Allah ya sani bana......" Mam ta fusata sosai  tace, "Wallahi bakin ka ya furta baka son Rumana sai na tsinke fuskar ka da mari, in kana musu kuma ka cemin baka son ta kaga aiki da cikawa Adnan." Tsitt yayi ya sunkuyar da kai ƙasa Mama tace, "ni zaka dinga kallon ido kana cewa baka son jinin ƴar uwata wacce muke uwa ɗaya uba ɗaya Adnan?, ni ka ke kallo kana ce min baka son yarinyar da na raina a cikin gidan nan?, ashe ko da gaske baka son nata baza ka iya yi kin kara ba taci albarkacina ka aure ta?. Inda ina da wani ɗa namijin ba kai ba zan saurare ka ne Adnan?. Kai kasan bazan bi ta kanta ba, dan kai duk yadda mutum ya kai ga yi maka abin kirki baka gani." "Ku ka haɗa kai da ƴan uwan ka aka je aka a samu mahaifiyata akace wai baka son Rumana na tilasta maka sai ka aure ta kai kuma baka so, sannan wai ita lokacin da tace bata son ka an ƙyale ta amma kai yanzu an kasa ƙyale ka. Ashe zaman namu da rashin darajar da bani da ita a wajan ka har ya kai haka Bebi?." "Ki yi haƙuri" ya furta a hankali zuciyar sa tayi rauni sosai. tayi tsaki tana girgiza kai tace, "haƙuri ai ya zaunar min dole saboda ka haɗa ni da wacce ta isa dani, Tunda ni ina jin maganar ta dole nayi abinda tace. Kai da baka jin tawa ai tsallake abinda nake so kayi ka kai ƙarata wajan uwata. Kaga nima da bana jin maganar ta irin ka da baka jin ta uwar ka sai naje na samu na sama da ita na faɗa masa shima yaje ya yi mata magana." Shi wallahi gabaɗaya ma komai ya fita daga ransa jin Mama tana faɗa tana cewa bata isa dashi ba, duk sai yaji nadamar abinda yayi ga dabaibaiye shi, ji yake ina ma bai kai kansa wajan Manal ba, ina ma ya tsaya akan Rumana ɗin kamar yadda Mama take so?. nan take yaji zai iya auren Rumana duk da baya so. "Hajiya tace kar na sake yi maka maganar auren Rumana na barka ka auri wacce ka ke so kamar yadda aka bata dama, zanyi hakan saboda bin umarnin wacce ta haife ni. Sannan zan baka umarni a matsayina na mahaifiyar ka nima, in zaka bi kanka in baka bi bana kan ka, sai kaje ka zauna da wacce ka ke so ɗin tunda ka zaɓi soyayyar ta akan farin ciki na." Da sauri yace, "kiyi haƙuri Mummy, ki yafe min don Allah, ko me kike so zanyi." "Baka da adalci wallahi, ka san irin kukan da Rumana tayi da maganar nan taje kunnen ta? Kaga yadda ta shiga tashin hankali saboda kai?. Duk wannan bai nuna maka tayi nadamar auren wani da tayi ba kai ba Bebi?, Kai kaɗai ake yiwa laifi ne a duniya? Meyasa baza ka haƙura ba?, meyasa baza ka yi tunanin daman Allah yayi sai ta auri Jawad ba kafin kai? Baka san ƙaddara ba?." Yayi shiru bai amsa ba dan Mama tayi zafi sosai shirun yafi alkhairi. Mama ta sake cewa, "tunda haka ka zaɓa na amince ka auri wacce ka ke so kamar yadda uwata tace, tace na saka maka albarka a auren zan kuma yi hakan. Amma ina so ka sani sai dai ka auri mata biyu a rana ɗaya." Da sauri ya kalli Maman suka haɗa ido ya sake sauke kai ƙasa tace, "in kuma ba haka ba, naji ka fara auren wacce kake so ɗin tunda umarnin Hajiya ne, amma ina so ka sani shekara ɗaya na baka kai da ita ku gama zaman ku, da zarar ranar da aka ɗaura auren ku ya dawo anyi shekara ɗaya a wannan ranar Rumana zata shigo gidan ka matsayin amaryar ka. Ko ka yarda, ko kar ka yarda haka za'ayi, in ba haka ba kaje ka auri wacce kake so ba da albarka ta ba, sannan bazan taɓa kaɓar ta matsayin sirikata ba." Da sauri ya kalle ta yace, "na amince Mummy, Allah ya wuce zuciyar ki, ki yafe min ɓata miki ran da nayi. Na amince da hakan Alalh ya nuna mana lokacin, Allah ya sa muna da rai da lafiya." "Kar ma ka amince mana Adnan, kar ka amince ka nuna min budurwar ka ta fi ni." "Har abada, ki yi haƙuri, ki yafe min tuba nake." Ta harare shi cikin ɓacin rai tace, "Tashi ka bani waje." Ya miƙe a sanyaye yana sake bata haƙuri zai fita tace, "Daga yau duk wani shiri da zaka fara na aure ka dinga yin guda biyu, in lefe ne ka siyi na mata biyu, in ma ginin gidan naka ne ka saka a rushe ya dawo baya ayi ginin mata biyu, in baka da ra'ayin hakan ka tabbatar kana gina inda Rumana zata zauna. In kana ganin hakan bai maka ba Hajiya tana raye." Juyowa yayi ya duƙa yace, "hakan za'a yi in sha Allah. Ki yi haƙuri." Tsaki tayi ta tashi ta wuce ciki ta barshi a wajan,  ya fita jikin sa gabaɗaya yayi sanyi ya rasa abinda yake masa daɗi. Bebi ya kasa nutsuwa gabaɗaya, a haka ya koma ɗaki yayi wanka ya kwanta dan ya huta. Sai dai ya kasa baccin tunanin abinda Mama tace kawai yake yi, tsakani da Allah ta ina zai iya wani aure bayan yayi aure da shekara?, shekarar yanzu da ba'a wani jimawa sai kaga ta dawo, har yaushe ya saba da matar tashi da zai ɗauko wata ya kawo?. Bashi da abinda zai ce dan bazai ce ba a masa adalci ba Mama ce haka ya dinga saƙa da warwara har yayi bacci. ******* "Wai yanzu akan yarinyar can ka damu haka? Mata nawa ka rabu dasu kafin ita hankalin ka bai tashi ba sai a kanta?." Alhaji Mu'azzam Alhassan ya kalli abokin sa yace, "baza ka gane yadda na ƙwallafa rai akan yarinyar bane, Taya akayi hakan ta faru?, meyasa bata faɗa min aure zata yi ba?." "Ta gama neman abinda zata samu ta samu ba dole ka neme ta ka rasa ba?." "Bata yi wannan wayewar ba, ban amince da kalaman ƙawar ta ba dole akwai wani abun wallahi. Ya zama dole kuma na saka a nemo min ko meye yake faruwa." Alhaji Magaji yace, "ya kamata ka dinga taka tsantsan fa, sunan ka sannen ne a kunnen al'uma, kana da yara da kuma jikoki da mata a gıda. Ka dinga ɗaga ƙafa kodan su." Alhaji Alhassan ya kalle shi yace, "yarinyar bata san waye ni ba, in fact ban faɗa mata asalin sunana ba a fuska ta kawai ta sanni,duk abinda nake yi ina sane bazan yi abinda zai lalatawa iyalan suna ba." Alhaji Magaji yace, "in tayi maka video fa?." "Na faɗa maka bata yi wannan wayewar ba, bata san komai ba ni ne nake ƙoƙarin sanar da ita. Sabuwa ce dal babu abinda ta sani ni nake so na sanar da ita. Taya za'a ce lokaci ɗaya sun bar gari bayan mu haɗu da ita tace min wayar ce ta faɗ? Akwai lauje cikin naɗi a maganar nan." Alhaji Magaji yace, "ka daina bibiyar yarinyar nan, ka koma harkar Abuja kamar yadda aka saba. Iyalan ka a kano suke, ka daina bin mutane Kano kar ka bar baya da ƙura." Ya kalle shi yace, "zan daina da zarar na samu Mubeena, hankalina bazai kwanta ba in ban same ta ba, ya zama dole na saka ayi min bincike a kanta" yana faɗa ya tashi da sauri ya ɗauki waya ya fito ya shiga mota driverm sa yaja suka fita daga gidan. A ɓangaren Manal haka ta kwana babu walwala saboda tunanin maganar Mujahid. da safe bayan ta idar da sallar walha wacce ta zamar mata jiki Mama na gefe duk da bata gani amma ta fahimci canji a tare da ita, hakan ya saka tace, "Manal zo nan." Ba musu taje inda take Mama ta riƙe hannun ta tace, "faɗa min abinda yake ranki, bakya ɓoye min komai Manal, sanar dani abinda ya faru kika canja haka." Manal tace, "Mama dama jiya ne da naje gidan su Surayya sai Maman su ta aike mu, a hanyar mu ta dawowa shine muka haɗu wani ya min magana sai na tsaya shine yake cemin shi abokin Dr Adnan ne, kuma wai wallahi Dr Adnan ɗin ba sona yake ba, zai yaudare ni ne daga ƙarshe ya gudu. Kuma Mama na taɓa ganin hoton shi abokin a office ɗin Dr tare dashi dasu Huzaifa. Na rasa tunanin da zanyi Mama, zuciyata tana ganin kamar da gaske ne hakan." Mama tayi ƙaramjn tsaki tace, "kawai dan kinga mutumin da baki sani yace miki wanda yake son ki ba mutumin kirki bane sai ki amince?." "Mama har hoton su tare na gani, shiyasa ma na amince da hakan a zuciya ta." Mama tace, "wani lokacin ai baki da wayo Manal, meye abin amincewa da wannan maganar?. Ke kin san inda halin sane baban ku bazai barki har yanzu tare dashi ba?, yayi bincike a kan sa sosai an tabbatar masa da nagartar sa da kuma girmama mace da yake yi a duniya, a cikin labarin da aka bawa mahaifin ki babu zancen yaudara, ance ya taɓa yin wata budurwa amma tayi aure bayan ita babu wata da aka san su tare. Wajan aikin sa da ko ina an tambaya an tabbatar ba'a ganin sa da mace in dai ba mara lafiya ba. Ke kina ganin da yana da wannan halin zai ɓuya ne? In wani bai sani ba wani tabbas zai sani." Manal ta girgiza kai tace, "Haka ne Mama." "Kar wani ya sake kawo miki irin wannan tunanin ki amince Manal, akwai mutanen da suke faɗar gaskiya akwai saboda kar ka faɗa halaka, akwai wanda suke faɗar ƙarya dan su cutar dake ko su cutar dashi. Barin wannan yayi tasiri a zuciyar ki ba abu bane mai amfani, kamar ma baki yarda da Adnan ɗin ba duk tarin girmama ki ɗin da yake yi tun kafin yace zai aure ki." Manal ta sauke numfashi tace, "Haka ma Surayya tace ban yarda, amma yanzu na amince da batun ki Mama bazan sake ba." "Yafi miki dai. Ashe da kin fasa auren nasa ban sani ba ko?." Manal tace, "ina tunani dai." Mama tace, "baki da wayo ne Manal, bazan amince a aurar dake babu bincike ba domin naga illar hakan, ko ni da kaina zan fita na bincika Adnan balle da baban ku a raye. Abinda baki sani ba akan Adnan yanzu ya sani shiyasa ya amince dashi ɗari bisa ɗari dan ya tabbatar zai kula dake kula mai kyau. Shiyasa kika ga na amince nima, bai wa dan yana da kuɓi ba sai dan kawai ya cancanci a zaɓe shi. Ni kuɗi ba baƙona bane Manal, babu wani mai kuɗi da zai zo ban amince dashi na bashi ke." Sai a sannan tayi murmushi tace, "haka ne Mama." Mama tace, "ko kefa, da kina ta yin tunanin banza da wofi. Ina Mubeena?." "Tana kwance." Mama bata sake magana ba tayi shiru Manal ta tashi tace, "Mama bara na siyo mana kayan cefane, yau dambu zan mana." Mama tayi murmushi tace, "sai kin dawo" ta faɗa tan fita. Tana fita gidan ta ɗauki waya ta kira Dr Huzaifa akayi sa'a ya ɗauka ta saka a kunne tace, "Dr ina kwana?." "Lafiya lau Manal, ya jikin Mama?." "Taji sauƙi sosai." "To haka ake so, Allah ya ƙara Lafiya." "Amin. Daman tambayar ka nake so nayi don Allah in babu damuwa." Yayi dariya yace, "Ina jin ki amaryar Adnan." Sai tayi murmushi tace, "Don Allah a cikin abokan ku akwai Mujahid?." Da sauri yace, "a ina kika san shi?." "Dama jiya ne yazo ya same ni yana min magana akan wai in na amince da auren Dr yaudara ta zaiyi ba aure na zaiyi ba, ya saba yiwa mata haka ba nice ta farko ba Magana dai kala-kala, hankalina ya kasa kwanciya shiyasa na kira ka." Huzaifa yace, "Innalillahi! Wai kina nufin har gidan ku yazo?." Manal ta amsa Huzaifa yace, "kar ki damu da abinda yace, yana yi ne dan ya raba Adnan da abinda yake so, duk wani farin cikin Bebi baya so, so yake yaga ya jefa zuciyar sa cikin ƙunci baya ƙaunar yaga Bebi yana murmushi a duniya. Wallahi ba ina faɗa miki dan na kare Bebi bane, ina faɗa miki gaskiya ne domin ke kanwata ce bazan miki ƙarya akan abinda yake gaskiya ba, in na cutar da rayuwar ki kaina na cuta. Mujahid da abokin mu ne kafin mu rabu dashi saboda wata ɗabi'a tasa ta banza, Bebi shine yayi silar da aka kwace lasisin sa na zama likita, shikenan ya tsani Bebi yake so ya raba shi duk wani abun da yaga yana so. Bebi yana sonki Manal, babu macen da yake so in ba ke ba na tabbatar da hakan, Mujahid yaga haka ne shine yazo dan ya raba ku Allah bai bashi nasara ba." Manal ta girgiza kai cikin gamsuwa da abinda yace tace, "na gode sosai, na kuma fahimta." "Yauwa ko kefa, ko da zai sake dawowa kar ma ki saurare shi." "In sha Allah, Amma don Allah kar ka faɗa masa, kar kayi masa zancen gabaɗaya don Allah." Huzaifa yace, "kar ki damu, bazan faɗa masa ba." "To na gode." Daga nan suka yi sallama ta kashe sai a sannan hankalin ta ya kwanta dan tana son Bebi itama. Nana Haleema❤️ *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025                  ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* *Page 028* Bebi kuwa yana kwance a gida baya son fita a ranar kwata-kwata, ya jawo wayar sa ya kira Huzaifa bayan ya ɗauka yace, "Yau bazan shigo ba, in akwai wani abun ku yi kar ku jira ni." Huzaifa yace, "Lafiya?." "Baba jin daɗi ne." "Sannu, Allah ya ƙara Lafiya." Ya amsa da amin kafin yace, "Mama ta amince da maganar aurena da Manal, amma tace da sharaɗin in na auri Manal da shekara ɗaya zan auri Rumana." Huzaifa yace, "kuma dai!." Bebi bai iya magana ba jin haka Huzaifa yace, "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, kar ka sake mata musu a wannan lokacin kawai ka amince  tunda tana so." "Na amince ma ai Huzaifa, na amince har zuciyata ta saboda ita." "Hakan yayi, Allah ya kai mu lokacin" ya amsa da amin ya yanke wayar ya koma ya jingina da kujera. Manal ya kira bata ɗauka ba ya sake kira a lokacin ta ɗauka tayi sallama yayi shiru na wani lokacin idanun sa a kulle kafin ya amsa tace, "an tashi lafiya?." "Lafiya lau, ya jikin Mama? Ina fatan ta samu Lafiya?." "Da sauƙi sosai, yau ma tace min tana ganin hasken rana." "Ma sha Allah, a hankali komai zai dawo in sha Allah. Ki gaishe ta." Manal tace, "zata ji in sha Allah." Yayi shiru baice komai ba itama bata ce ba na wani lokaci, sai da ya sauke ajiyar zuciya ya katse shirun yace, "kin cemin kina da Yaya, ban taɓa ji kin min maganar ta ba ban kuma taɓa ganin ta ba. Bakya so na santa?." Tayi murmushi tace, "Yaya Mubeena wai? Tana school, cikin kwanakin nan ne ta dawo gida kuma bata jin daɗi shiyasa baka ganin ta." "Ohhh" Abinda ya furta kenan kafin yace, "ita tana zuwa makaranta amma ke bakya zuwa, meyasa bakya so?." "Ina so sosai, kawai dalili ne ya hana ni zuwa." "Meye shi?." "Mama, bazan iya tafiya school na dinga barin Mama  ita kaɗai ba gaskiya. Shiyasa na ajjiye duk wani burina a gefe, tana da lalurar ido in muka tafi duka waye zai kula da ita?." Lumshe ido yayi yana jin wani irin bugun zuciya a lokaci ɗaya, Allah ya sani yadda take son mahaifiyar ta yana daga cikin abinda yake jan hankalin sa zuwa gare ta, soyayyar ta yake ji sosai a zuciyar sa fiye da yadda yake tunani, bai taɓa tunanin zai so wata mace kamar haka ba, shi ko a yaushe burin sa kar soyayya tayi masa mugun kamu, sai gashi a lokacin da bai yi tunani ba ya faɗa tarkon ƙaunar ta, ƙauna mai tsanani ma kuwa. Har bugun zuciyar sa yake ji a kunnen sa saboda soyayya,  bai san lokacin da yace, "ina sonki Manal" ya faɗa cikin shauƙin so da kuma ƙauna. Murmushi yaji tayi jin abinda yace, yadda yake furta kalmar ma abin jin daɗi ne balle yadda kalmar take ratsa ta sosai, tace, "Nima haka Dr." "Kema me?." Tayi murmushi ta kulle fuska kamar tana ganin sa bata ce komai ba yacw, "ina jin ki, kema me?." Tayi dariya tace, "nima i love you." Ƙaramin tsaki yayi yace, "Da hausa zaki faɗa min." Manal cikin shagwaɓa tace, "kunya nake ji." Ya gyara zama sosai shagwaɓar ta na ratsa shi sosai yace, "shiyasa nace ki faɗa." Manal tace, "to ba na faɗa ba?." "Ban amince da wanda kika ce ba, da hausa nake so ki faɗa." "Ina son ka." Ƴar dariya yayi cikin farin ciki  ya wara idanu yace, "wow! Finally yau dai kin ce." Tayi murmushi shima shi yake yi yace, "sake faɗa naji pls." Ƙi tayi sai ta canja maganar tace, "meyasa ake ce maka Bebi?." "Sunan gida ne" Ya faɗa a taƙaice kafin yace, "bakya zuwa makaranta saboda Mama, amma yanzu zaki aure ki bar Mama." Tayi shiru na wani lokacin muryar ta ta raunana kafin tace, "tuna hakan yana saka ni ciki damuwa" ta faɗa murnar ta na rawa sosai alamun kuka zata yi. Da sauri yace "wasa nake miki, meye na kuka Manal?." "Da gaske ne ko baka ce ba itama tana faɗa min, don Allah babu ta yadda za'ayi na zauna a wajan Mama? Wallahi bazan iya zama a  ko ina in bata nan ba, ko Ina zanje bazan ji daɗi sa kamar wajan ta ba." Kuka take sosai nan take yayi dana sanin faɗa mata haka yace, "Manal relax please, ki daina kuka ki tsaya kiji abinda zance miki." Bata yi magana ba hakan ya saka yace, "Manal kina tare da Mama a ko yaushe in sha Allah kar ki damu, aure ai ba mutuwa bace." Manal bata ce komai ba jin tayi shiru yace, "ki nutsu ni da wasa nake faɗa miki ba da wani abun ba, naga alama kina son kuka baya miki wahala ke kam." Manal tace, "duk yadda zan faɗa baza ka gane ba, Mama na kira na" Tana faɗa ta yanke wayar shi kuma yabi wayar da kallo yana jin wani iri a zuciyar sa da ya saka ta kuka. Ba jimawa ya kuma kira amma bata ɗauka ba, ya sake kira ba'a ɗauka ba, babu daɗi zuciyar sa haka ya ƙyale ta ya cigaba da harkokin sa. A ranar Bebi ya samu kiran Baba akan Manal  ta sanar dashi ta amince da auren sa ya turo iyayen sa, da yamma yaje ya samu Yaya ya faɗa masa yayi masa  bayanin gidan su Manal da komai, shi kuma yace in sha Allah da safe zai je ya samu Yayan mahaifin su  y sanar dashi a saka rana su je.         Rumana hankalin ta ya tashi ta gigice jin labarin da yazo kunnen ta na auren da Bebi zai yi kuma ba ita zai aura ba. Ammi tana zaune kusa da ita tana rarrashi tace, "Haba Rumana, wai akan Adnan kike wannan koke-koken?. "Ammi ina son sa sosai, inaa son Adnan" ta faɗa tana kuka. Ammi tace, "nasan kina son sa, kuma yanzu ma ai ba fasa auren ki yayi ba zai aure ki amma ba yanzu ba." Ta girgiza kai tace, "Wallahi da zarar yayi aure bazai aure ni ba, ni kawai ya fara aurena kafin ya auri waccan ɗin. In ya fara auren wata bani ba mutuwa zanyi." Ammi tace, "kin cika rigima wallahi, ke ba auren ki ka yi ki ka barshi ba ne wai? A lokacin wanne irin so ne Adnan bai nuna miki ba?, Amma kika saka ƙafa kika yi fatali dashi kika ce ke Jawad kike so aka aura miki shi, to shi yanzu dan yace a bashi dama ya auri wacce yake so shikenan sai ya zama laifi?." Rumana ta goge idon ta tace, "Rabuwa ta dashi tsautsayi ne, kuma yanzu Ina son sa fiye da baya, don Allah ki taimaka min." Ammi tace, "taimakon naki ne ya saka zai aure ki nan gaba ai." Rumana ta tashi tace, "wajan Maman zanje ni gaskiya a canja shawara, matuƙar ya auri wacce yake so shikenan na gama yawo wallahi, bazai aure ni ba kamar yadda yace. In ya auri wata ba ni ba kafin lokacin da aka bashi na aurena yayi na mutu." tana faɗa ta ɗauki mayafi da key ɗin mota Ammi na mata magana amma ina bata ji ba ta fita. Kaii tsaye gidan su Adnan ta wuce ta shiga wajan Mama ta same ta ita kaɗai kuwa tana zuwa ta zube a cinyar ta tana tace, "Mama don Allah kar ace Adnan bazai aure ni ba, in bai aure ni mutuwa zan yi" ta faɗa tana kuka sosai. Hankalin Mama ya tashi  cikin rarrashi tace, "Haba Rumana, zai aura ki mana, waye yace bazai aure ki ba?." Bata ce komai ba sai kuka da take yi a jikin Maman, Mama tace, "ki nutsu ki daina zubar da hawaye muyi magana." Hawayen ta goge tana jan numfashi Mama tace, "in dai ina da rai kina da rai sai kin zama mallakin Adnan in sha Allah, ki daina wannan kukan, ɗan lokaci ne kawai na bashi damar ya auri waccan ne saboda haka hajiya tace, amma na tabbatar miki da zai aure ki kuma matsayin ki zai wuce matsayin waccan saboda kece wacce ya fara so tun bai girman haka ba, a duniya abinda ka fara so yafi tasiri a zuciya." "Mama ni nake so ya fara aura, in ya auri waccan shikenan bazai aure ni ba Mama." Mama tace, "nace ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru, zai aure ki in sha Allah ke matar Adnan ce amma sai kin daina tayar da hankali. Ki fara shirin zama matar sa daga yanzu dan shekara kwana ce." Ta kwantar da kanta jikin Mama tace, "Mama..." Mama ta dakatar da ita tace, "kiyi haƙuri a bashi dama kamar yadda aka baki taki damar, ke mace ce bazai yu ki auri maza biyu ba amma shi namiji ne zai auri mata biyu har sama da haka. Ki yi haƙuri ayi hakan yafi kwanciyar hankali." Rumana ta girgiza kai bata ce komai ba, ba haka taso ba, ba kuma haka take so ba amma hakan za'a yi babu yadda zata yi. Taso ace ita ya fara aure domin ta ƙure cika bakin sa amma hakan bai samu ba dole ya fara zama da wata kafin ita. Numfashi ta saukar zuciyar ta nayi mata zafi tana tunani kala-kala. Hankalin Maryam ya tashi sosai tunda sukayi waya da Kamal ya shaida mata bashi da lafiya yana kwace ta rasa nutsuwa so take kawai taje inda yake, sai bayan ta fita da mota sannan ta kira shi tace, "Kana ina gani nan zan zo?." Daga can ɓangaren yace, "ina gidan mu dake." Kashe wayar tayi ta nufi gidan da ta zauna dashi matsayin mata da miji. Gidan babu mai gadi dan ba'a ciki matar sa take ba, a ƙofar gida ta ajjiye motar ta fito ta tura gate ɗin ya buɗe ta rufe ta shiga ciki da sauri. Baya falon hakan ya saka ta masa waya tace, "ka sakko gani a falon, Sauri nake zan koma." "Bazan iya sakkowa kowa ba, ki hau saman kawai ina ɗakin ki" Daga haka ya yanke wayar ta sauke ajiyar zuciya ta hau saman jikin ta yayi sanyi rayuwar ta ta cikin gidan yana dawo mata hankalin ta. Ɗakin ta buɗe ta shiga an saka sabon furniture yana kwance a kan gado jin ta shigo sai ya miƙe daƙyar ya zauna yana kallon ta yace, "Barka da zuwa my love." Da sauri ta ƙaraso gab da kan gadon tace, "ya jikin naka?." "Gani nan dai kawai." "Meyasa ka zauna kai kaɗai a nan? ba ga gidan matar ka ba?." "Nan ma gidan matata ne." Tayi shiru ya tashi tsaye sai tayi saurin kawar da kai daga kallon sa domin daga shi sai gajeren wando ko riga babu a jikin sa. "Maryam ƙaddara ce ta jawo na furta saki a kan ki, amma wallahi Ina son ki ina ƙaunar zama dake, wannan damuwar itace ta haifar da zazzzaɓi, ina so mu sake zama matsayin mata da miji" Ya matso daf da ita yana magana a hankali yana kallon ta. tace, "ƙaddarar kenan, babu wanda zai canja ta tsakanina da kai. In Allah ya yi nida kai zamu sake zama tare zamu zauna ko bayan shekara nawa ne." "Ina son kasancewa dake, babu macen da nake kwaɗayi sai ke Maryam" ya faɗa yana komawa da baya ya zauna ya dafe kai yace, "Na rasa abinda yake min daɗi, kiyi wani abun dom Allah Maryam." Maryam tana tsaye jikin ta yayi sanyi ta kalle shi kafin tayi magana yace, "Maryam ya zanyi?." Kallon sa tayi tace, "haƙuri" ta faɗa a taƙaice zuciyar ta na bugawa. Da azama ya taso ya riƙe kafaɗun ta ƙirjin ta yana gugar nasa yace, "Haƙuri Maryam? Wallahi zan iya mutuwa yanzu in ban same ki ba" ya faɗa yana jan ta da ƙarfi zuwa jikin sa ya rungume ta sosai yana sauke ajiyar zuciya. Ƙoƙarin kwacewa tayi amma ta kasa  saboda ya riƙe ta sosai a kunnen ta yana cewa, "ki bari Maryam, nasan kina son kasancewa dani kema don Allah ki bari mu ji ɗumin juna." Yadda yake maganar ya saukar mata da kasala sosai ta daina ƙoƙarin ƙwace kan ta tayi shiru tana ji yana sake matse ta a jikin sa. "Ina son ki Maryam, ƙaddara ce ta raba mu da ban  muna so ba, ina son ki Maryam kema na san kina sona, bana marmarin ko wacce mace in ba ke ba" ya faɗa yana sake matse ta sosai a jikin sa. Ita dai taji ɗumin bakin sa a wuyan ta daga nan baza ta sake cewa ga abinda ya faru ba ta tsinci kanta ne kawai a kan gado a kwance ita dashi a cikin bargo guda ɗaya tamkar ma'aaurata. A firgice ta miƙe tunawa da abinda ya faru ta cure a waje ɗaya hankalin ta ya tashi sosai ta gigice, ganin hakan sai ya ƙaraso inda take yace, "Haba maryam meye haka?." Kuka take yi sosai yana rarrashi amma taƙi bada damar hakan, yayi yayi tayi shiru amma abin yaci tura shi kansa hankalin sa ya tashi bai ɗ'auka zata ruɗe haka ba. Ya san tana son sa sosai bai ɗauka dan wannan abun ya faru tsakanin su hankalin ta zai tashi sosai har haka ba. Haƙuri yake bata amma taƙi sauraren sa kallon doguwar rigar ta tayi a gefe a ajjiye, tana kuka ta zira hannu ta ɗauka ba tare da ta cire abinda rufe jikin ta ba ta saka rigar tana daga zaune ta miƙe tsaye ta saka da takalmi da mayafi ta ɗauki key da wayar ta fita a guje. Bin bayan ta yake yana mata magana amma inaa ta shiga mota ta bar unguwar da gudun gaske. Da sauri ya koma gidan ya ɗauko nasa key ɗin ya hau mota yabi bayan ta, saboda gudun da take yi bai iya tarar da ita a hanya ba sai da yaje har gidan mai gadin gidan ya tabbatar masa da ta shiga sannan hankalin sa ya kwanta ya koma. bashi damuwa akan abinda ya faru dan yasan zata yafe zai kuma wuce, wataƙila ma a sake maimaitawa in soyayyar ta sa ta motsa a zuciyar ta. Bayan kwana biyu. Nana Haleema🥂❤️ *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025      ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* *Page 029* Adnan yana zaune a gaban babban Yayan sa yana masa bayanin abin da ya faru a gidan su Manal da suka je nema masa auren ta, yace, "Ai suna da kirki sosai wallahi, na yaba da su sosai. Sun karɓe mu hannu biyu, na ji daɗin yadda suka yaba da kai sosai, nima na yaba da yarinyar. Duk wanda na tambaya wani abu game da gidan su babu wanda ya faɗi wata kalma mara daɗi, kowa yace in dai aure ne zai haɗa ku da mutanen gidan ku je kan ku tsaye." Adnan yayi murmushi jin daɗin Yayan yace, "Kuma wanda yake riƙon nasu yana da faɗar gaskiya ya san mahimmacin faɗar gaskiya a ɓangaren neman aure, kasan harkar neman aure ba a so a ɓoye komai gaskiya ake faɗa. Shi ne yake sanar damu ma shi bashi da alaƙa dasu yarinyar, mijin mahaifiyar ta kawai amma shi ba ƙanin mahaifin su bane, ana faɗar cewa shi ƙanin mahaifin su ne kawai saboda wani dalili." Adnan ya kalle shi tace, "Kamar ya kenan Yaya?." "Eh, yace mana mahaifin ita yarinyar da babar ta rabuwa suka yi ba mutuwa yayi ba kamar yadda ake faɗa, kuma basu da tabbacin ya mutu kawai tana faɗar ya mutu ne saboda bata son ma tuna musu mahaifin su. Shi bashi da alaƙa dasu mijin mahaifiyar su ne kawai, sannan ya shaida mana yarinyar tana da ciwo diabetics wanda ka san dashi." Adnan yayi shiru baice komai Yaya yace, "wannan ai ba wani abun damuwa bane ba, an tsayar da rana kamar yadda kace a saka. Itama Mimi an tsayar da lokaci daidai da naka lokacin, abinda muke jira su daga can gidan su matar taka sun ce zasu yi waya in sun yanke hukunci. in yanke hukunci daidai da lokacin mu shikenan, in sun ƙara ko sun rage duk ɗaya ne." Kafin yayi magana Yayan ce, "mun je da gwajin jinin ka yadda ka ke lafiya haka ta ke, genotype ɗin ku kai AA itama AA. Blood group ɗin ka kai O positive, ita kuma B positive. Sai dai naga tana da diabetics ai ka san dashi ko?." Bebi ya ɗaga kai yace, "eh na sani Yaya, Huzaifa ne likitan da take gani." Yaya ce, "ma sha Allah, sai mu jira lokaci." Bebi yace, "haka ne, Allah ya kai mu lokacin." Yayan sa ya amsa da amin Bebi ya tashi ya fita zuciyar sa cike da tunanin meyasa Manal bata faɗa masa abinda yaji yanzu ba?. Mota ya shiga zai ja kenan sai aka masa waya sai ya tsaya ya ɗauki wayar daga can ɓangaren aka ce, "Bebi kamar yadda ka ce na nemo maka na nemo, Yayar Manal Mubeena an jima da korar ta daga makaranta, yarinyar bata jin magana zan iya ce maka ma tana ɗan taɓa yawon banza. Sannan Haruna ɗan wanda yake riƙon su son Manal ɗin yake." Ajiyar zuciya yayi yace, "na gode." Yana faɗa ya sauke wayar zuciyar da masa zafi akan ƙaryar da Manal tayi masa, meye in ta faɗa masa gaskiya ai ba wani abun bane tunda ba itace take yawon ba. A haka yaja motar zuwa asibiti ransa a ɓace sosai auren ma yana fitar masa daga rai.           Mama tana zaune da glasses ɗin ta a ido tana gani amma ba sosai ba Baba yana zaune ya ajjiye mata kuɗin da aka kawo na aure da kuma na saka rana a haɗe yace, "Baki ce komai ba, ga kuɗi an kawo har naira dubu ɗari biyar na aure da na saka rana, kuma su suna so ayi auren ne nan da wata huɗu masu zuwa in Allah ya nuna mana." Mama tace, "to ai shine ya saka na kasa magana, wata huɗu ai yayi kusa Baban Manal, ina laifin ma shekara ɗaya?." "Ban da abin ki Fatima ko shekarar aka saka zai zo fa." "Eh haka ne, amma wata huɗu me muka shirya?. Akwai aiki sosai fa, ko da kayan kitchen aka bar mu aiki ne mai yawa balle gasu gado da manyan abubuwa." Baba yace, "iya abinda za'a iya shi za'a yi ai, kuma kin manta akwai kuɗin ki a hannuna wanda ake juyawa?, sannan nima akwai nawa matsayina na mahaifi?." Mama tace, "ban manta ba, amma duka kuɗin zamu kashe muyi amfani dasu?." Baba yace, "A'a da wasu za'a yi amfani, kar ki damu wallahi Allah zai rufa asiri ayi komai a gama. Bikin ƴar gata za'a yi in sha Allah, ke kan ki sai bayan komai ya lafa zaki dinga tunanin a ina aka samu kuɗin da aka yi wannan aka yi wancan, ki miƙa lamarin ki ga Allah kawai." Mama tace, "haka ne wallahi, Allah ya nuna mana lokacin. Gwara a bar shi a hakan ma ayi a gama." "Amin. Ina Mubeena take?." A lokacin Mubeena ta shigo tace, "gani." Baba ya kalle ta sai da zauna yace, "kin mayar da kan ki wata shiru-shiru saboda kawai an miki faɗa gaskiya Mubeena? So kike mu barkı kina abinda kike so da sunan wayewa?." Tayi shiru baba yace, "tunda haka kika zaɓarwa kan ki daidai ne, Tunda kin zaɓi ki janye jikin ki daga cikin mu saboda akwai an miki faɗa akan abinda kike yi ke kika sani. Kina gani an kawo kuɗin auren ƙanwar ki har an saka rana, ki yi ƙoƙari kawo naki mijin a haɗa ku duka biyun a aurar a huta." Mubeena tace, "to." Baba yace, "tashi ki shiga ciki." Ba musu ta tashi ta shiga Mama ta kalle ta dan tana iya ganin ta bayan ta wuce tace, "Ni tunda idona ma ya buɗe nake mata wani kallo, wallahi gani nake kamar an canja ta, wayewa ta tayi yawa idanun ta cikin na mutane take magana bata jin kunya. Kaii!" Ta faɗa tana dafe kai akwai abinda ta tuna. Baba yace, "ki cigaba da yi mata addu'a." Mama tace, "Allah ya shirya. Kuɗin fa, ka barsu a nan?." "Ki bar su a hannun ki, ki fara siyan kayan kitchen Mama tace, "to bara a na tura ta wajan Balaraba su yi lissafin abubuwan da zasu siyo." Baba ya amsa ya fita Mama tace, "Manal." Ta amsa tana fitowa ta zauna kusa da ita Mama tace, "ga kuɗin auren ki da na saka rana, abinda za'a yi kije ki samu Balaraba ku rubuta abubuwan da zaku siyo in yaso sai ku shiga kasuwa keda Surayya ku siyo a ajjiye a gidan su." Manal kallon kuɗin take yi abin mamaki yake bata wai kuɗin auren ta, har yaushe suka haɗu da shi gashi ana maganar aure har an kawo kuɗi, lallai in akace lokaci to tabbas in yazo baya jira. Mama da take ganin ta dishi-dishi ta kalli ta tace, "ya naga kin yi shiru?." "Mama da gaske wata huɗun za'a bari?." "Eh mana Manal, ko shekara huɗu aka saka ai zata zo, gwara ayi a gama kawai a huta." Idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Mama wata huɗu yayi kaɗan, kwata-kwata yaushe muka haɗu dashi da za'a ce za'a yi biki nan da wata huɗu?." Mama tayi murmushi tace, "ƙarya kike, ki faɗi asalin abinda yake zuciyar ki Manal. Kina son Adnan, dan haka kina son kasancewa matar sa nan kusa, abinda yake ran ki na san bai huce zaki yi aure ki bar gidan nan ba." Sai kuwa ta fashe da kuka ta kwanta a cinyar Mama tana kuka kamar wacce akace gobe ne auren, Mama tana shafa bayan ta tace, "Manal aure ai ba mutuwa bane, zaki dinga zuwa kina gani na indai ina da rai, kuma bakya ganin yanzu na samu lafiyar idanu? Har girki zan iya yi da kaina ai ba abin damuwa bane wannan Manal." "Nidai Mama a'a, a bar shi nan da shekara don Allah." "Baza'a ɗaga bafa Manal, aure ne sai anyi shi in sha Allah. Da kike wannan koke-koken wata rana mutuwa zanyi na bar ki." Manal tace, "ai sai na riga ki mutuwa Mama." Mama tayi dariya tace, "ni dai bana son wannan kukan naki Manali, aure fa zaki bautar Allah zaki je ki yi to meye na kuka?." Zatayi magana ta hana ta tace, "Kiyi addu'a kice Allah yasa hakan shine alkhairi a rayuwar ki." Shiru tayi Mama ta ɗago ta ta share mata hawaye tace, "amarya! amarya!." Dariya ta bata ta ɗora kanta a kafaɗar Maman tana dariya Maman ma tayi dariya tace, "Ko kefa fa Manali na, yanzu kije wajan Maman su Surayya ki faɗa mata sai ku zauna ku rubuta duk abinda kike so, ko me kike so ki siya indai ya burge ki, daman ke mai son harkar kitchen. in kun gama rubutawa gobe sai ku shiga kasuwar ke da Surayya ku siyo duk abinda kika rubuta." Manal tace, "har da Yaya Mubeena ko?." Mama ta kalli Mubeena da take zaune daga cikin ɗaki tana kallo su tace, "baza taje ba, ki ƙyale ta gaba take yi da mutanen gidan gabaɗaya." Mubeena da take gefe tace, "zan je." Mama tace, "babu ruwana sai kin tambayi baban ku, in ya barki to." Ta kalli Manal tace, "tashi kije ki same ta, baki da wata uwa kamar ta bayan ni." Ta amsa da to ta tashi zata fita Mama tace, "zo ki kai mata kuɗin ta ajjiye a wajan ta." Manal ta turo baki tace, "to kawai sai na kai mata kuɗi nace na kuɗin aurena na ne?." Mama ta kalle ta tace, "kunyar ta ki ke ji?." Manal tace, "eh." Mama tayi dariya tace, "ƙarya kike, yadda bakya jin kunya ta itama bakya kunyar ta." Manal tana dariya tace, "To Mama ai ke aminiya ta ce, ita kuma Maman su Surayya ce fa." Mama tana dariya tace, "zo ki ɗauka ki wuce, ina wata kunya a wajan ƴan matan yanzu?. Sai dai gulma da munafurci." Manal ta ɗauka ta fita tana dariya tana son dramar su da mahaifiyar ta sosai.           ** Suna zaune a cikin mota ita dashi, gabaɗaya ya gama kashe mata jiki yadda yake faɗa mata yana sonta abin yana sake jefa zuciyar ta cikin kogon soyayyar sa. Ya iya kalmai, ya san ta kan iya tsara ƴan mata, yanzu zai miki murmushin da zai rikita zuciyar ki. Ya kalle ta ya ce, "yanzu Lubna haka zamu zauna kenan? Meye aibu na? Na taɓa ƙoƙarin koda taɓa jikin ki?." Ta girgiza kai alamun a'a kamar zaiyi kuka yace, "to meyasa baya so na Lubna?, meyasa yake so lallai sai ya raba mu dake?." Kamar zata yi kuka saboda rauni tace, "ban sani ba, ni na rasa me na yiwa Yaya baya sona ma gabaɗaya." ya sauke numfashi yace, "ga Mimi an kawo kuɗin ta ko?." "Har an saka rana ma, shima an kai kuɗi sa har an saka rana amma ni ya hana." Da sauri ya kalle ta kamar bai sani ba yace, "an saka rana?." "Eh an saka ranar sa, kuma wata huɗu aka saka." Girgiza kai yake yi lallai Manal ta shammace shi, shi a tunanin sa tunda bata da wani ilimi mai zurfi ba wani wayo ne da ita ba, kasancewar ba wata babba bace zata yi sauri yarda da abinda zai ce sai gashi tayi watsi da abinda yace mata. Nan da nan ransa ya ɓaci, Bebi bai isa ya cigaba da yin nasara yana barin sa ba, ya zama dole yayi nasara a kansa ya cusa masa baƙin ciki da takaici kamar yadda yake ji a zuciyar sa. "Tunanin me kake yi?." Kallon Lubna ɗin yayi yace, "ina tunanin yadda baya qauna ta ne, ina so na samo mana mafitar da zai amince dani." Tayi shiru cikin damuwa ya kuma yace, "Ko Abba na samu da maganar bazai kawo mana mafita ba?." Tace, "Abba sai ya kira Bebi ya faɗa masa kuma bazai amince ba tunda baya son ka." Ya kalle ta sosai cikin taushin murya yace, "Sweetheart!." Ta kalle shi itama yace, "Kina sona?." Ta kalle shi tace, "Wannan wacce irin tambaya ce?." "Ki amsa min kawai." Ta girgiza kai tace, "ina son ka." Yayi ajiyar zuciya yace, "kin amince bazan cutar dake ba?." Tana kallon sa cikin soyayya da shauƙin da yake gani a idanun ta tace, "na amince baza ka cuce ni ba." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "Alhamdulillah! Sweetheart bazan cutar dake ba saboda ina son ki, mafita nake nemar mana da zamu kasance a inuwa ɗaya matsayin ma'aurata." Ya gyara sosai yana kallon ta yace, "shawara zan kawo ko nace mafita, ban sani ba ko zaki amince ko baza ki amimce ba, sannan ban san da wacce fuska zaki kalle ta ba." Ta kalle shi a raunane tace, "na amince ka faɗi ko meye zan amince da kai, na tabbatar baza ka cutar dani ba." Ya sauke numfashi yayi shiru yana kallon ta kamar ba zai magana ba kafin yace, "ban san ta ya zaki ɗauki abun ba, amma dai ina so na taimaki junan mu ne dan na tabbatar in muka rasa junan mu zamu faɗa wani hali." Lubna tace, "ka faɗa kawai, ni na amince da kai nasan baza ka taɓa cutar dani ba." Ya girgiza kai cikin gamsuwa a zuciyar sa kuwa tausayin ta yake ji amma ya zaiyi bazai bari tausayi ya rinjaye shi akan fansar sa ba, saboda fansar sa yake komai har soyayyar da yake nuna mata duk ta ƙarya ce. yace, "ina so ki bani dama ki amince dani har zuciyar ki, ki yarda bazan cuce ki ba, ina so mu kusanci junan mu...." Kafin ya kai ƙarshe ta kalle shi da sauri, sai ya tari numfashin ta yace, "ki jira na gama faɗar abinda yake bakina kafin ki yanke min hukunci please." Kallon sa take yi hakan ya saka yace, "so nake hakan ya faru,in ya faru babu wanda zai hana ni auren ki. Wallahi Lubna zamu yi hakan ne saboda a bani ke na aura ba dan wani abun ba Allah ya sani kema kin sani. Amma in kina ganin hakan bai dace ba shikenan sai mu haƙura da junan mu tunda Bebi bazai bari mu auri juna ba." Shiru tayi alamun tunani, shi kuma yana sake karyar da murya yana yi mata bayanin yadda abin zai kasance har yaga ta fara aminta da maganar sa ta kalle shi tace, "in na amince baza ka guje ni ba? Baza ka manta dani ba in hakan ta kasance?. Kaga ni ba ƴar iska bace ba, wallahi ko hugging wani namiji ban taɓa yi ba har yanzu, zan amince da abinda kace ne saboda ina sonka, na amince da kai baza ka cutar dani ba domin kana sona kuma kamar ƙanwar ka nake. Kayi min alqawarin baza ka guje ni ba?." Kalaman ta sun saka yaji wani iri a zuciyar sa ya sauke numfashi yace, "bazan guje ki ba Lubna, ina son ki bazan taɓa abinda zai cutar da ke ko rayuwar ki ba." Ta sauke numfashi tace, "Allah yana kallon ka in ka cutar dani, Allah bazai bar ka ba domin kaci amanar ƙaunar da nake maka." "Lubna ina wannan abun ne dan neman mafita ba dan ina so na kasance dake ba, inda ni mutumin banza ne da yanzu kin fi kowa fahimtar hakan Lubna." Ta girgiza kai cikin amincewa da maganar sa tace, "nima ban ce kai na banza bane, kawai ina so ka riƙe min alƙawari ne kar ka guje ni bayan ka raba ni da abinda nake dashi." Mujahid yace, "indai alƙawari ne nayi miki." "Shikenan, na amince da abinda kace" tana faɗa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa daga idon ta. sai jikin sa yayi bala'in sanyi ya kalle ta murya a raunane yace, "meye na kukan?." Murya na rawa tace, "Daga zuciyata yake zuwa, ban san dalilin zuwan sa ba." Yayi murmushi yace, "kar ki damu, zan nema mana wata mafitar in bamu samu ba sai muyi amfani da wannan ɗin. Hakan yafi miki ko?." Ta sauke Ajiyar zuciya ta ɗaga kai tace, "to." Ya kalle ta yace, "to ki yi murmushi mana, haba Sweetheart." Murmushi tayi shima yayi yana kallon ta kafin yaja motar su tafi zuciyar sa nayi masa saƙa da warwara akan lamarin Lubna, Anya yayi mata adalci? Anya in yayi hakan bai cuce ta ba?. Amma Itace hanyar da yake da ita wacce zai sakawa Bebi baƙin ciki a zuciyar sa, babu yadda zaiyi dole yaci amanar qaunar da take masa. Nana Haleema.🥂❤️ *BAYA DA ƘURA.* Fitattubiyar2025      ©️Nana Haleema. Wattpad@Nanahaleema Arewabooks@nanahaleema11 *BOOK 1* *Page 30* Abban su Bebi lokacin da ya shiga gida Mama ya kira a waya yace tazo da yake yamma tayi sai ta tafi da abinci ta kai masa ta ajjiye ta zauna kamar yadda yake a zaune shi da Mamy tace, "sannu da zuwa." "Yauwa sannu, ya gida?." "Lafiya lau." "Ayyuka sun mana yawa shiyasa kwana biyu komai ya sake lalacewa, ku yi haƙuri komai zai wuce da zarar komai ya dawo daidai." Mamy tace, "Allah Sarki."  Abba yace, "nasan bana kyautawa amma ayi haƙuri, cikin kwanakin nan zan jima a gidan nan in sha Allah." Mamy tace, "hakan yayi kyau, Allah ya daɗa gyara komai." Ya amsa da amin Mamy ta miƙe tace, "ina da baƙi zan je na sallame su, in kuma ban dawo ba sai da safe" ta faɗa tana fita. Mama ya kalla ganin wani wajan take kallo yace, "ran ku nasan a ɓace yake dani, ayi haƙuri kawai." Mama tayi murmushi tace, "Sai yanzu zaka ce ayi haƙuri?. Kudin ƴar ka ta cikin ka aka kawo aka saka rana baka san anyi ba, aka kai kuɗin Bebi aka saka rana shima baka sani ba. Wanne irin uba ne kai?, Hakan yana nufin kana sauke haƙƙin da yake kan ka wanda Allah ya rayata ya maka kenan?. Yanzu da babu ƴan uwan naka haka yaran zasu zauna basu da wanda zai shige musu gaba a lamuran su?." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "duk na ɗauki laifin, kuma za a gyara in sha Allah." Tayi murmushi na takaici tace, "sai da lokaci ya ƙure za'a gyara kenan?. To ina so ka tunda duk abinda ka ke yi mana sai an yiwa yaran ka wallahi, mu ma ƴaƴan ne kamar yadda naka suke ƴaƴa mu ma haifar mu akayi. Ko me ka ke aikatawa a waje wallahi sai an yiwa yaran ka a suke cikin gida koda kuwa ka saka ƙarafuna kayi musu katanga ne, wallahi sai an samu wani ya ɓalle wannan katangar ko da kuwa mai gadin gidan nan ne." Kallon ta yayi hakan ya saka ta sake yin murmushi tace, "ƴan matan ka na waje, in soyayya ka ke dasu ba don ka aure su ba kana da ƴan mata a gidan nan ai, in ma lalata su ka ke dasu kaima kana da ƴan...." "Hauwa wacce irin magana ki ke yi haka? Kina cikin hankalin ki kuwa?" Ya faɗa yana kallon ta a fusace. Mama tayi Murmushin takaici tace, "Da hankalina nake maganar kamar yadda ka fahimci abinda nake nufi. Mu matan ka mun zama banza saboda kana da wasu a waje shiyasa ka raina mu kana ganin kamar mu ɗin ba komai bane face wanda suka tsufa, kana da sabon jini a waje wacce tsiyar zamu yi maka?. Kar Ka ga dai ina da jikoki a gidan nan ko?, to hakan bazai hana na bar gidan nan ba walalhi, tura ta fara kaiwa bango ƙiris nake jira, lokaci kaɗan kawai" tana gama faɗar hakan ta miƙe ta fita ya bita da kallo hankalin sa ya tashi sosai. Kenan duk sun fahimci yana da ƴan mata a waje ko me? Kenan da gaske maganar ta zata tabbata na wani zai nemi ya lalata masa yara?.  Ya firgita sosai da abinda tace hakan ya saka shi saurin kawar da tunanin amma zuciyar sa bugawa take matuƙa.           **** Maryam kuwa tun bayan abinda ya faru tsakanin ta da Kamal ta shiga damuwa sosai ko wayar sa bata ɗauka, babban tashin hankalin ta bai wuce abinda ya wakana tsakanin su ba in ta tuna hankalin ta tashi yake yi sosai. Yana kiran ta bata ɗauka, yayi message bata reply domin kuwa bata ga amfanin cigaba da kula shi ba, tayi nadamar abinda tayi sosai haushin kanta take ji. A ranar yayi mata message sama da goma tayi banza bata bada amsa ba, kawai taga an turo mata hoto a ƙasan hoton an rubuta, _Ko dan saboda wannan ki amsa wayata Maryam._ gaban ta yayi mugun haɗuwa ganin hoton ta babu suttura irin wanda take tura masa a lokacin da take gidan sa matsayin soyayya. Jikin ta rawa yake sosai, hankalin ta ya kai ƙarshe wajan tashi kallon hotun take yi cikin kiɗima da nadama mara amfani. yana kiran wayar hannu na rawa ta ɗauka daga can ɓangaren yace, "har ni ina miki waya ki daina ɗauka? Na baki haƙuri meyasa baza ki haƙura ba Maryam?." Maryam tace, "Kamal kace min ka goge hotunan nan." "Akan me za'a goge bayan gashi yayi min amfani yanzu?." "Kamal ya kamata ace ka goge shi saboda ni ba matar ka bace ba. Barin tsairicina a wayar ka haram ne." "Zan goge, amma Ina so ki fito anjima ina so mu yi magana." "Bazan sake zuwa inda kake ba, na daina zuwa inda ka ke, baza ka kuma ganina ba ko me zai faru." Yayi dariya yace, "Maryam kenan, kina so kice kin daina ganina?." "Na daina ganin ka, na kuma daina zuwa inda ka ke, kuma ka fita daga rayuwata." "Ni kuma wallahi yanzu na fara jin daɗin rayuwa dake, a baya ji nake kamar ma ban taɓa wata mu'amala dake ba kamar yadda ya faru yanzu. Maryam ki fito mu haɗu yanzu in ba haka ba wallahil azim zan ɗora hoton nan na ki a Facebook da tiktok." Gaban ta ya faɗi matuƙa, ta wara idanu hannun ta yana kan ƙirjin ta saboda rashin hankali. Murya a sarƙe tace, "me ka ce?." Yayi dariya yace, "ai kin ji abinda nace, ko ban saka hoton fuskar ki ba zan saka na jikin ki, ke kina gani kin san jikin ki ne. Kuma zai zaga ko Ina babu inda bazai je ba ke kin san yadda hoton tsaraici yake zaga ko ina, Balle ma da fuskar ki zan ɗora dan babu amfanin kullewa." Kasa magana tayi shiru hankalin ta ya tashi sosai ta rasa ma abinda zata ce, gaban ta faɗuwa yake yi nadama ta mamaye ta lokaci ɗaya har zazzaɓi take ji. Kamal ya katse mata tunani yace, "in kin shirya ganin hoton ki a social media kar ki fito Maryam, in kuma baki shirya ba zan miki text na inda zamu haɗu ki tabbatar kin je wajan. in ba haka ba wallahi!, wallahi!!, wallahi!!, kin ji uku ko?, sai na watsa hoton nan media, ke kin san ba iya hoto nake dasu ba har videos ina dasu. Videos ɗin ma sun fi komai kyaun gani, saboda....." sai kuma yayi dariya yace, "Na san ma kin sani, Sai na jiki" yana faɗa ya katse wayar. Faɗuwa tayi a wajan jagwab hankalin ta ya kai maatuƙa wajan tashi, me hakan yake nufi...? kenan blackmailing ɗin ta Kamal yake da hotunan tsaraicin ta wanda take tura masa a zaman auren su ko kuma me? Yanzu ya zata yi? Dama zata ɗauka ko haggu?. Zina zata je ta aikata dashi saboda kar ya watsa hotunan ta?, in kuma bata je ba ya watsa hotunan ta da wanne ido zata kalli yaran ta guda biyu?, da wanne ido zata kalli duniya ma gabaɗaya. Ta daki katifar gado ta dafe kai a bayyane tace, "ya zan yi ni Maryam, ya zanyi?. Aikata zina ko kuma yaɗa hotunan tsaraicina?."           Bebi ya fito daga cikin asibiti yana shiga mota Huzaifa ya buɗe gaba ya shiga, Bebi ya kalle shi Huzaifa yace, "ka ajjiye ni a gida please, motata na kai ta gyara sai gobe zan ɗauko." Kana kallon fuskar Bebi kansa ransa a ɓace yake sosai yace, "sai akace maka kuma hanyar da zaka yi zan yi ni?." "Ko ba nan zaka yi ba kaje duk inda zaka je ka sauke ni." Ƙaramin tsaki yayi ya ja motar ya bar asibitin zuciyar da zafi take akan ƙaryar da Manal tayi masa. Suna zuwa bakin layin gidan su Manal ya tsaya ya ɗauki waya yana kiran ta, Huzaifa yayi dariya yace, "sai kace min zance kazo ai, daman kana zuwa da ƙananun kaya ne?." Bai kula shi ba ya kira ta a lokacin tana kwance ciwon marar da take fama dashi duk wata ya dame ta sai kuka take, gashi ita in bata da lafiya dole sai ta ji ta a jikin Mama take samun sauƙi-sauƙi, amma bata son damu Mama saboda bata da lafiya sai ta fito tsakar gıda ta zauna. Tana wannan kukan kiran sa ya shigo ta duba kamar baza ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta saka a kunnen yace, "Kizo Ina bakin layin ki saƙo zan baki." Yana gama faɗa ya kashe wayar bai jira yaji abinda zata ce masa ba. Manaltabi wayar da kallo tana mamaki, bai taɓa cewa tazo bakin layin su ba sai yau, hakan ya saka ta daure ta tashi tunda ciwon bai yi zafi ba ta shiga wajan Mama tace, "Mama wai Dr Adnan ne ya kira ni nazo bakin layin nan zai bani saƙo." "Saƙo kuma Manal? Meyasa bazai shigo ba?." "Ban sani ba wallahi." "To jeki, amma kar ki jima dai kinga dare yayi sallar i'sha za'a yi" ta amsa da to ta saka Hijjabai ta fita zuwa bakin layin. Hango ta Huzaifa yayi sai ya kalle shi yace, "Wai daman a mota ku ke zance ne Bebi?, gaskiya hakan ba daidai bane tunda kai ma baka so a yi haka da ƙannen ka. Ban taɓa ganin ka bar su suna zance a mota ba, kaima bai kamata ka yi ba." Bebi ya gaji da maganar Huzaifa a ƙufule yace, "ya ishe ka Malam, in baza ka zauna ba ka fita ban nemi zaman ka ba ko?." Kallon sa Huzaifa yayi ganin da gaske ransa a ɓace yake sai yace, "bazan fita ba sai mun gaisa da ƙanwata. Kuma haka zata ƙaraso ka wani ci magani kamar wani boss?." Banza yayi masa ta ƙaraso gaban motar ta gane motar sa ce amma bata ganshi a tsaye a bakin motar ba. Sai da ta ƙaraso sannan ya sauke glass ya kalle yace, "zaki iya shigowa?." Ta girgiza kai alamun A'a ya buɗe motar ya fito yana kallon wajan da babu jama'a sosai daman layin nasu bashi da mutane. A jikin motar ya tsaya yana kallon ta itama haka yadda fuskar sa take haka ta ta fuskar take dan ciwon da yake damun ta ba kaɗan bane, jira take taji me zai ce ko mai zai bata amma yayi shiru. Ya kalle ta sosai yace, "abinda kika yi kin kyauta kenan Manal?." Ta kalle shi alamun me tayi yace, "na faɗa miki tun farko bana son ƙarya meyasa kika min ƙarya?." "Wacce ƙarya nayi maka?" Ta faɗa tana kallon sa da mamaki. "Meyasa baki faɗa min Baba ba ƙanin mahaifin ki bane?, meyasa baki faɗa min mahaifin ki bai rasu ba?, meyasa baki faɗa min aura ne kawai tsakanin Mama da Baba amma babu alaƙa ta jini a tsakanin ku?." Gaban Manal ya faɗi sosai ya kalle shi tace, "me kake nufi?." "Kin san me nake nufi, meye amfanin ɓoyewar?." "Dakata mana, ni ban fahimci akan abinda kake magana ba" ta faɗa dan taga da faɗa yake mata magana kamar wanda ya haife ta. "Kin san dukkan abinda yake faruwa, na faɗa miki ƙarya tana sakawa mutum ya fita daga raina lokaci ɗaya amma baki ji ba. Sannan meyasa baki faɗa min yayar ki ba makaranta take zuwa yawo take tafiya?." Da sauri Manal ta kalle shi dan ta gane me yake nufi da kalmar yawo ɗin da ya ce, Ya wara ido aka fuskar ta yace, "eh!. Shi kuma wanda kika ce min yayan ki ne ashe saurayin ki ne, ke a ganin ki wannan daidai ne?, a ganin ki kin kyauta?." Ran Manal itama ya ɓaci sosai musamman kiran Mubeena da yayi wai tana yawo, kalmar tafi komai ƙina mata rai hakan ya saka a fusace tace, "duk wannan maganar da ka ke akan ban faɗa maka abinda ban sani ba shine ka ke yi?." "Amma na faɗa miki ai bana son ƙarya,ƙarya tana sakawa naji mutum ya fita daga raina na faɗa miki wannan tun farko ba yanzu ba" ya faɗa cikin fusata sosai yana kallon ta kamar zai dake ta. A wuya itama take jin ta, daman ga ciwo ga kuwa ɓacin ran da yake faɗa mata ya sake tunzura zuciyar ta, katse ta yace, "I'm higly disappointed, banyi wannan tunanin daga wajan ki ba." "Duk wannan maganar da kake yi kana so kace ka fasa aurena kenan?, gashi kana maimaita min ƙarya tana sakawa abu ya fita daga raina kenan na fita. To ka fasa mana Adnan sai meye in ka fasa?, fasawar ka bazai hana wani yazo yace zai aure ni ba. sannan kar ka sake kuskuren cewa Yayata tana yawo, Yayata bata yawo duk wanda ya faɗa maka ƙarya yake yi. Dan kawai kana son ka ce ka fasa aurena ka faɗa kan ka tsaye ba sai kazo kana min maganganun da babu su a cikin rayuwata ba. Ka fasa auren sai me? Waye ya ragu ni ko kai?." katse ta yayi ta hanyar cewa, "Ai bazan tsaya a gaban ki ina miki ƙaya ba dan na burge ki ko dan wani dalili nawa, ya kamata ki san waye ni." Ganin mutane suna wucewa ana tafiya masallaci ya saka Manal danne ciwon da take ji tace, "ka furta ka fasa aurena sai me waii? Daman ai an gargaɗe ni naƙi ji nace ba haka ka ke ba, ka fasa auren nawa wannan ba komai bane. Wallahi ban da kai ɗin ne ina ganin girman ka saboda abinda ka yiwa mahaifiyata wallahi da yanzu ka fara dana sanin sanin wacece Manal a duniya, ka turo a karɓar maka kuɗin auren ka da ka kawo, ko kai baka fasa ba ni Fatima bazan aure ka ba!. Adnan ka je ka ssmu shugabar masu gaskiya ka aura, ka bar maƙaryaciya mai ɓoye maka abubuwan da ya kamata ace ka sani. Ko baka furta ba na fahimce ka, to na hutar da kai furtawar, ni Fatima Manal na fasa auren ka, ba shikenan ba?" tana faɗar hakan ta juya ta bar shi a wajen dan ciwon marar ya dame ta sosai. Da kallo ya bita zuciyar sa na bugawa sosai, ɓacin ransa ya ninka na baya sau babu adadi. kamar shi tayi masa laifi yazo yana faɗa ta dinga yi masa wannan faɗan har da tafiya ta bar shi kamar wani sa'an ta?. Tsaki yayi yana ji a zuciyar sa dole ma ya fasa auren nata!. End of book 1. _Tofa ana dara ga dare yayi, ya ku ke ganin salon zai kasance nan gaba?. Shin mahaifin Adnan zai samu galaba akan Mubeena?, to in hakan ya faru wanne irin abun kunya za'a tafka?. Hmm da gaske auren Manal da Adnan babu shi ko kuwa zasu shirya nan gaba?, ya matsayin Maryam da Kamal?, zata amince ta sake aikata zina daahi saboda hotunan tsaraicin ta ko kuwa zata ƙi amince shi kuma yayi posting?. Ya batun Lubna, shin Mujahid zai aure ta  bayan ya raba ta da budurcin ta?, anya lubna bata yi gangancin amincewa da Mujahid ba?. To wai wacece Maman Manal ne?, ina mahaifin su Manal yake?, Waye shi?, yana da rai ko ya mutu?. Ya batun Rumana da Adnan? Auren nasu zai yu ko kuwa zai sake bijirewa Mama?. Hmmm kwamachala ɗin kenan._💃🏼😃 _Duka amsoshin wannan tambayoyi suna cikin book 2&3, akwai soyayya, akwai taɓa zuciya, akwwi nadama, akwai dan sani, akwai zallan kishi a cikin littafin BAYA DA ƘURA BOOK 2&3. Zai fara zuwa 20/1/2025 in sha Allah. promo is over za'a biya asalin kuɗin littafin. an fara yin payment tuni na book 2&3 regular akan naira 500 kacal. Akwai vip group shi kuma naira 1000 ne. Ga masu buƙata zasu yi min magana a kan wannan number 09030398006 but only on whatsapp. Kuɗi kawai zamu karɓa banda katin waya!._ Nana Haleema🥂❤️