[2/2, 10:07 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫 🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÔLDÈÑ"S WRÎTÈRS_ _ÀSSÔÇÌÁTÎÒÑ_💥 Komai yayi farko zaiyi karshe Allah nagode maka daka nuna mun na kawo karshen littafina na RAYUWAR UMMIEY. Allah yasa kamar yadda naga farkon wannan littafin yasa naga karshen shi, Masoyana ina mika sakon godiyata zuwa gareku 🙏🙏🙏 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Page 1_2 mummy! mummy!!!Tun shigowarta take faman kwala wa mummynta kira, mummy dake cikin dakinta duk hankalinta ya tashi da jin irin kiran da Amatu_rahman keyimata da sauri ta fito tayi hanyar sauka palour Cin karo sukayi da ita cikin tsoro da firgici mummy tace Amatu meke faru dake?? Fadawa jikinta tayi tace wallahi mummy naga Abdul a waje yanxu yanxu nan kuma ina son iyi mashi magana sai bata karasa fadar abunda zata fada ba sakamakon tsawar da mummy daka mata aikuwa da hanzarinta ta daga kanta data dora saman kirjinta Tsuki mummy tayi tace amma dai Amatu kinyi asara yanxu akan wannan abun neh zakiyi ta faman kwala mun kira haka?? Ai na dauka ko wani abunne ya sameki Ashe akan wannan neh toh wallahi kibi a hankali karki zauce, tana gama fadar haka ta kara gaba Kuka Amatu tasa gami da haurawa sama, dakinta ta shiga ta fada saman gado tana zubar da hawaye ta rasa dalilin dayasa ta kasa cire Abdul a ranta. Tana cikin kukan neh wayanta ya hau ruri Dubawa tayi taga aunty hajara ce ke kiranta, ba bata lokaci ta amsa kiran daga bisani kuma ta tashi ta fita kodata fito palour mummy ta tarar sai data sanar da ita kafin ta wuce Tafiyar minti biyar tayi se gata a cikin wani Dan karamin flat mekyau, kai tsaye ta shiga cikin gidan, a palour ta tarar da aunty hajara tana cin abinci kallonta tayi tace Amatu lafiya naganki a haka? Dan jimmm kadan tayi sannan tace aunty yauma na sake ganin Abdul a banki amma kafin inyi mashi magana harya wuce shine dana fadawa mummy ta fara yimun fada Ohhhh Allah me iko gaskiya Amatu ya kamata ace kin rabu da Abdul hakanan kusan shekara biyu kenan babu labarinshi kuma ma idan yana sonki ai duk inda yaje ze iya nemanki amma kawai kinsawa ranki damuwa kila ma yayi aure ya manta dake Saurin isowa wurin aunty hajara tayi ta rufe mata baki da hannuwanta tace Allah aunty Abdul beyi aure ba saboda yayi mun alkawarin baze taba auran wata ya' mace idan bani ba kum......... Dakatar da ita aunty hajara tayi tace anya baki fara tabuwa ba kuwa ko an fadamaki kowani dan Adam neh keda tabbaci?? Nidai shawarata kawai ki manta dashi ko kya hutawa ranki Badan ta gamsu da maganar tata ba tace toh, zama tayi suka faracin abincin tare, bayan sun gama neh Aunty hajara tace tazo ta tayata gyara dakin baki kanwarta ameera ceh zatazo Ba karamin dadi Amatu taji ba tace aunty bari inyi sallah inzo Daga nan ta shige toilet tayi alawla tayi sallah bayan ta fito neh ta tarar da aunty harta fara kakkabe dakin. Hira suka shigayi inda aunty ke bata labarin ameerah duk da cewar Amatu ta Santa amma bata taba ganinta ba sai a hoto shiyasa take zumudin ganinta Suna cikin aikin neh sai ga mijin aunty hajara yazo, gaishe shi Amatu tayi taci gaba da aikinta aunty kuma jan mijinta tayi zuwa dakinshi. Bayan ta dawo neh sukaci gaba da aikinsu basu suka gama ba sai kusan magariba, suna gamawa Amatu tayiwa aunty sallama ta wuce Tafiya take a nutse cikin kwanciyar hankali nan kuwa ba'asan tunani neh fal cikin ranta ba Tunanin maganar da aunty hajara ta fadamata takeyi na cewar datayi kila ma ya manta da ita tana cikin haka neh taji an damkota da karfi ansa cikin mota, zata kurma ihu kenan taji an.................... Yawan comments yawan rubutu😎 [2/2, 4:29 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Wannan shafin sadaukarwa neh ga my real Momcy da kakata fatima, ina yinku irin ehhh dinnan, Allah yabar zumunci Page 3&4 Zata kurma ihu kenan taji an rufe mata baki da wani kyalle, haka tayi ta mutsu mutsun ta Har suka iso wani tangareren gida, ba shakkah duk inda ake neman gida mekyau da girma wannan yakai, a takaice dai gidan flat flat neh Guda uku duk iri daya kuma kowanne da girmansa Fitowa sukayi daga cikin motar, daya daga cikin su neh ya jawo hannunta zuwa daya daga cikin flat din, itako dake tun cikin mota sun rufe mata baki da fuska sai ya zamana bata ganin komai sai duhu Wani daki suka kaita suka aje ta sannan daya daga cikin su da gani shidin yana sama dasu, kallon su yayi batare da yayi magana ba yayi musu alama dasu kunceta kuma su fita Yadda ya umarce su haka ko sukayi shi kuma fuskar shi rufe take da bakin mask, ya karaso gab da ita yace keee bani number mahaifinki!! da sauri ta dago kanta dan jin muryar da bazata taba iya mantawa dashi a rayuwarta ba Shuru tayi masa tana kallonshi taji ko shine me muryar, shiko ya tsani kyaliya shiyasa a zafafe yace keee dan ubanki bada ke nake magana ba, cikin muryar kuka dan yanxu ta gama tabbatar da abunda take zargi tace Abdul kaineee murya na rawa ta karasa maganar Shiko kallon mamaki yakeyi mata dan beko taba ganinta amma ya akayi tasan sunan shi? Cire mask din dake fuskan shi yayi ya kare mata kallo dakyau yaga ehh din pah shi be taba ganinta ba Ita kuma a razane ta mike tsaye tana nuna shi da dan yatsa tace Abdul daman kana duniyar nan?? Ina ka shiga neh tsawon shekara biyu?? Kuma meeeeee Katse ta yayi ta hanyar daka mata tsawa yace what the hell are u?? Ke wacece da zaki dinga jero mun irin wa'annan tambayoyin?? Abdul nice pah amatu amatullahi masoyiyar ka, Abdul meyasa zakayi mun haka? Meyasa zaka tafi ka barni?? meyasa yanxu kuma zaka satoni?? dan Allah ka amsa mun tambayoyi na Gabadaya ta gama sashi a RUDANI duk ta rikita mishi tunani ga kuma kukan da takeyi wanda duk sadda hawaye ya gangaro mata sai yaji zafi a zuciyar shi kuma ya rasa dalilin dayasa hakan ke faruwa Matsowa yayi daf da ita, ya kalli cikin idanunta yaga duk fuskarta ta kumbura tayi ja saboda kuka, yace keee ni fah ban sanki ba kuma ban taba ganinki ba hasalima bani nasa a satoki ba baba nah ya nuna mun hotonki yace da komai naki yace naje duk inda zan sameki na kawo mashi ke maybe dai nayi miki kama da wani neh amma bani bane Cikin wata iriyar murya me ban tausayi ta kira sunan shi dan ita fah bata yadda bashi bane, tace plsss ka taimaka ka fitar dani daga cikin wannan rudanin Murmushin da yafi kuka ciwo ya saki yace wai kee wace irin yarinya ceh a ina kika sanni tell me?? Ya fada gami da fincikota, kuka ta sa tace wallahi Abdul Kaine idan ba kai bane meyasa kake amsa sunan Abdul idan nakira ka iyeee tambayar ka nake?? Haushi neh ya kamashi ya saketa gami da watsa mata mari a fuska sai data ga taurari guda dari bakwai da hamsin, saura kuma kuce karya neh 😏 Duk da cewar taji zafin marin da yayi mata amma daurewa tayi ta dago da fuskarta ta kalleshi ido cikin ido tace wallahi ka ban mamaki Ashe duk sonda kake yimun na banza neh?? Abdul me nayi maka da zaka hukunta ni ta hanyar kuntatawa zuciyata?? Toh bari kaji ko zaka shekara kana gana mun azaba bazan taba canza maka suna daga abdul din dana sani ba saboda Kaine ba wani ba Wannan karon tausayinta yaji sai yaji dama be mareta, juyawa yayi ze fita sai kuma ya dawo, gabanta ya iso zeyi magana sai aka fara knocking a bakin kofar Kyallen da aka rufe mata fuska dashi ya dauko ya rufa mata, tana kokarin hana shi yace shhhhhh duk abunda zakiji karki kuskura kice wani abu, idan ba haka ba u are on ur own Mikewa yayi yaje bude kofar, wani katon dattijo ne Wanda a kalla zai kai shekaru hamsin a duniya, murmushi ya saki gami da jinjina wa abdul yace aikin ka yayi kyau son yanzu abu na gama shine kayi amfani da layin dana baka ka amshi number mahafinta ka kirashi ka fada mashi duk yadda mukayi dakai kaji ko Amsawa Abdul yayi da toh kafin dattijon ya fita yana mai farincikin nasarar daya samu, shiko zuwa yayi ya bude mata fuska yace karki damu da abunda kikaji ya fada nidai abunda nakeso dake shine Ki dan bani takaitaccen labarin Abdul din da kika sani Kallon rainin wayo tayi mishi tace haba Abdul me kakeson na fadamaka cikin rayuwar da mukayi wanda kai baka sani ba? iska ya fuzar cikin nuna damuwa da tausayinta yace wallahi ban sanki ba amma sunana Abdul Jin yayi rantsuwa yasa ta dan Ji ta yadda dashi sai tayi tunanin toh kodai su yan biyu neh? Batare da tasan maganar da tayi ta fito fili ba sai jin tayi yace a'a ni kadai mahaifiyata ta haifa Shuru tayi tana kare mishi kallo lallai tabbas Abdul neh amma shi gashi ya musa yace bashi bane toh kodai mafarki nakeyi neh Kawar da tunanin tayi ta kalleshi tace tunda kace ba kai bane zan baka labarin Abdul dina amma kasani Allah yana kallon ka Girgiza kai yayi alamar ya yarda, nan ta fara bashi dan takaitaccen soyayyar da sukayi tsakaninta da Abdul kamar haka............... Ku biyoni dan jin yadda zata kasance [2/3, 9:29 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Masu bibiyar wannan littafin ina godiya kuma nima ina yinku kamar yadda kukeyi nah Wannan shafin SADAUKARWA neh ga duk mabiyan RUDANI Page 5-6 ASALIN SU Amatu, cikakken sunanta Amatullahi kuma ya' ce kwalli daya tak ga Alhaji Muhammad lemi da mahaifiyarta hajiya rukayya wadda take kira da mummy Alhaji Muhammad lemi shahararren dan kasuwa neh kuma su yan jahar kano neh, kasuwanci ya dawo dashi abuja, Amatu yarinya ceh kalar chakulati doguwa me kirar koka kola, shekarunta sha takwas a duniya, amatu ya'ce me hankali, da tarbiya da tunani ga kuma girmama na gaba da ita Iyayenta na matukar kaunarta kuma suna ji da ita sosai kasancewar ta ita kadai Allah ya basu, hatta da mota an koya mata amma bata fara tuki ba sai data karasa secondary schl dinta sun bata tarbiya da kulawa, tun tasowarta take cikin gata, komai na rayuwa amatu ta samu daga wurin iyayenta shiyasa a kullum idan tayi sallah take rokon Allah daya saka musu da gidan aljannah Amatu ta kammala secondary schl dinta a wannan shekaran amma taso taci gaba da karatu sai kuma Allah yasa bataci jamb ba shiyasa take zaune a gida amma duk da hakanan tana zuwa saloon dinda mahaifinta ya bude mata wanda tun tana ss1 ya bude mata amma saboda makarantar da take zuwa yasa bata da lokacin zama shagon sai dai inta samu hutu akwai wurin da take zuwa ana koya mata kwalliya da gyaran kai da dai sauran su Tun tasowarta take da son kwalliya ko shopping sukaje kayan saloon na roba take siyowa dasu baby tayi ta musu kwalliya a gida tun abun yana kamar wasa harta girma abun na ranta dake kuma iyayenta masu hali neh kuma duk abunda take so indai bai kaucewa addini ba sunayi mata shiyasa suka bude mata shagon saloon, Yanxu da take da lokaci kullum tana hanyar saloon idan kuma bataje ba toh tana gidan aunty hajara WACECE AUNTY HAJARA Aunty hajara makwabciyar su ceh, tun zuwanta anguwar suka hadu da ita Wanda a halin yanxu kowa na gidansu ya santa kuma sun matukar shaku da ita tamkar yan uwan juna CIGABAN LABARI Abdul dina na hadu dashi neh a shagon koyon kwalliya shima a lokacin ya kawo kanwar shi neh, bayan na fita neh sai na tuna da ban dauko wayana ba, toh na juya kenan sai na ganshi a gabana, wayata ya mikon nikuma na ansa ina mishi godiya Harna juya zan tafi sai kuma ya kirani na dawo nace gani, kallona yayi yace miye suna na sai na fada mishi, dan murmushi yayi yace toh tunda na fada mishi sunana na fanshi kaina daman ladan kawo mun waya zan bashi amma tunda na fada mishi sunana kuma ya wuce dariya nayi dan ya matukar shammata ta nace mishi toh nagode kaifa miye sunanka? Bata tare da wani daukan lokaci ba ya fada mun sunan shi, nan muka dan fara hira har zuwa lokacin da aka zo daukata, exchanging number mukayi dashi kafin na wuce ina mai jindadi a raina dan hankalina ya kwanta dashi Tun daga wannan rana Abdul yake kirana muna gaisawa kuma yana fadamin irin sonda yake yimun duk da cewar a lokacin ina da Karancin shekaru a haka nake zuba masa shirme na kuma shi din haka yake bina dan yasan akwai kuruciya a kaina Amma duk da kuruciyar dake kaina nasan yana matukar sona kamar yadda nima nake sonshi A haka muka dade dashi muna zuba soyayya duk wani kulawa da masoyi ze baiwa masoyiyar shi ina samun irinshi a wurin Abdul, hatta mummy na da aunty hajara sun San da zaman shi, Amma wata rana kwatsam sai aka wayi gari babu shi babu labarin shi, nata kiran number shi bata shiga kullum sai na fita bakin titi ko Allah zai sa in ganshi amma shuru gashi ni bansan kowa nashi ba balle naje nayi cigiyar shi Nayi kuka harda zazzabi akan rashin shi saboda ba karamar shakuwa mukayi ba, tun ina sa ran zan ganshi har aka kai wata daya, wata biyu, shekara daya yanzu kuma shekara biyu babu shi babu labarin sa Amma wani abu dayake bani mamaki kuma yake sani cikin RUDANI shine yan kwana biyun nan ina ganin shi amma duk yadda naso na tare shi muyi magana sai abun ya faskara, tun ina fadawa mummy na tana kwantar mun da hankali harta kai ga yanxu ma fada takeyi mun idan nace na ganshi Gashi ni kuma na kasa cire Abdul a cikin raina saboda ina yi mishi sonda ni kaina bansan iyakacin shi ba, kullum cikin addu'a nake Allah ya bayyanar mun dashi dan har yanzu ban fidda ran sake ganin shi ba, ta karasa maganar tana zubar da hawaye Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalleta cikin tausayawa yace kiyi hakuri amma Allah yana gani bani bane Abdul din da kike magana a kanshi ba amma kuma nine nayi ta bibiyar ki cikin kwana kinnan saboda inyi kidnapping dinki Kuma nima zanso inga wannan takwaran nawa wanda muke matukar kama dashi haka, Share hawayenta tayi tace toh ku meyasa kuka sato ni??? Dan jimmm kadan yayi sannan yace bazan boye miki komai saboda ko ban fada miki ba idan kika fita daga nan zakiji dalilin satoki da mukayi Abbana neh yasa a satoki saboda yana bin mahaifinki kudi masu yawa Wanda a kalla zasu kai million goma , abbana yayi iya kokarin shi kan mahafinki ya bashi amma yaki shiyasa ya yanke shawarar sato ki dan ya karbi kudin shi Amma kisani bawai na fada miki wannan maganar bane dan ki tayar da hankalinki a'a sam kawai dai saboda na fahimci ke mutuniyar kirki ceh kuma nasan hakan da abbana yayi ba abu bane mekyau Nikuma bani da halin da zan hanashi, amma nayi alkawarin ko an kawo kudinnan sai na mayar dasu kuma nasan yadda zanyi mahaifinki ya biya abbana kudin shi batare wata hargitsi ba Kuma kiyi hakuri da abunda abbana yasa akayi miki kinji? ko kala bata ceh ba sai tsura mashi ido datayi shiko sai faman surutu yakeyi Jin bata ansa shi ba sai yace ta kawo number mahaifinta yanzu ze kirashi, bata musa ba ta bashi, shi kuma mikewa tsaye yayi ya nuna mata toilet da hannun shi yace taje tayi sallah shima masallaci zashi kuma anjima ze dawo Dakyar ta samu ta mike tsaye Dan kakafuwanta sun mata nauyi sosai, shiga tayi ta dauro alawla, kodata fito dadduma taga an shimfida mata, hijabin dake jikinta ta gyara wa zama sannan ta fara sallah Shi kuma bayan ya fita masallaci ya nupa dan gabatar da sallar magriba data wuce shi, nan ya zauna har akayi isha'i sannan yaje ya siyo mata abinci, bayan ya dawo neh ya shiga part dinshi ya zauna sannan ya kira number mahaifinta Ko daya kira mummy da daddy suna nan zazzaune fuska babu annuri, harda aunty hajara na gidan dan hankalinta ba karamin tashi yayi ba, dan a lokacin da mummy ke fada mata Amatu bata dawo ba sai dataji tsoro kuma babbar tashin hankalinta shine an kira number ta ashe ta manta wayanta nan gidan aunty hajara Amsa wayar daddy yayi yana mai sauraron abunda aka ce mashi daga bisani kuma ya katse wayar yana......................... Muje zuwa👉🏿 [2/3, 1:44 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Page 7-8 Amsa wayar daddy yayi yana mai sauraron abunda aka ce mashi, daga bisani kuma ya katse wayar yana salati. a firgice mummy tayo kanshi tana sharar hawaye tace alhaji waye ya kira kuma meya faru?? Kallonta yayi da idanunshi da suka canza launi zuwa ja yace anyi kidnapping din amatu kuma wai se an bada naira million goma za'a saketa, salati mummy ta farayi tana kuka haka ma aunty hajara itama kukan take sosai. Wata nannauyar ajiyar zuciya daddy ya saki yace kuyi hakuri insha Allah zan kai kudin nan dan bazan bari su halaka mun da yarinya ba kuma wallahi duk Wanda ya aikata haka a gareni toh ya guji ranar haduwata dashi. Yana gama fadar haka a fusace ya haura sama. mummy kuma kallon aunty hajara tayi tace hajara kije gida kinga yanxu dare yayi zuwa da safe sai ki dawo kinji. Girgiza kai hajara tayi ta fice daga gidan mummy kuma dakin daddy ta wuce. ********* Bayan ya gama waya da daddy dakin da aka akai Amatu ya nupa. da shigar sa ya mika mata abinci gami da zama cikin daya daga cikin kujerun robar dake wurin. Kallonta yayi yaga yadda ta kawayar da abinci gabanta alamar bazata iya ci ba kenan. Wayar shi ya zaro daga aljihu ya kira number daddy ya mika mata. Bakinta har rawa yake tayi magana dan ta matsu ba'a dauka ba. Haka ta katse ba tare da an dauka ba. Ansar wayan Abdul zeyi sai kuma kira ya biyo baya. Da sauri ta amsa a rikice tana kiran daddynta tana cewa ina mummy. Sai da suka gaisa tukunnan yana kokarin mikawa mummynta Abdul ya anshe wayar gami da kashe ta gabadaya. Kuka ta saki tana rokonshi daya sake kira mata su amma fur yaki sai ma tashi da yayi yana kokarin fita dan kukan da takeyi ba karamin sa zuciyar shi zafi takeyi ba. Tashi tayi ta biyo shi tana kara rokon shi sai ya juyo ya kalleta ya kalli kuma abincin daya kawo mata yace indai kinason nakira maki mummy toh sai kin cinye abincin nan duka. Girgiza kai tayi alamar zataci sannan ta koma wurin abincin ta faraci. Duk cewar ba wani dadin shi takeji ba kawai dai tana ci neh dan ya kira mata mummynta. Haka yayi tsaye yana kallonta Har sai data gama ci sannan ta kalleshi tace ya kirasu. Murmushi yayi a cikin zuciyar shi yace lallai amatu baki da wayo yanzu idan na sake kiran iyayenki ai zasu iya ganoni. Amma a zahiri wata number yayi dailing wadda yasan bata shiga yasa a hands free yace kindai ji a kashe take ko?? Kwalla ceh ta fara taruwa a idanunta tace Abdul yaushe zaka kaini gida?? Tabe baki yayi yace Gobe. Wani sanyi taji a ranta tace kona fita Abdul bazan barka ba zan kasance tare dakai Har zuwa lokacin da zaka bayyana mun dalilin guduna dakayi. Niko nace Amatu har yanzu baki yadda ba Abdul dinki bane??🤔 Kee me kika ceh?? Saurin girgiza kanta tayi tace bance komai ba kawai nayi missing din yan gidan mu neh. Murmushi yayi mata a karo na farko kenan daya taba sakar mata murmushi yace ni fah zakiyi missing dina?? Rufe fuskarta tayi da hannuwanta tace a'a nikam bazan yi missing dinka ba. Waro idanunshi yayi yace Ashe kenan bazaki bar gidan nan ba. Bude fuskarta tayi ta dan marairaice fuska tace Allah wasa nakeyi maka zanyi missing dinka. Sosai?? Eh sosai mana ta bashi amsa a takaice. Toh yanxu ki cire duk wata damuwa ki kwanta kiyi bacci me dadi kinji ko?? Amsawa tayi da toh sannan ta kwanta saman dan karamin gadon dake dakin. Shima kashe mata wuta yayi sannan ya sawa dakin makulli ya wuce part dinshi. Yana shiga ruwa ya watsa ya shirya tsaf cikin kayan bacci sannan yabi lafiyar gado. Kwance yake amma sai faman sake sake yake tayi. Yana tunanin yadda zai mayarwa daddy kudin shi ba tare da ansamu matsala ba. Wata zuciyar shi ko cewa take kawai basai ka anso kudin shi ba ka mayar da ita inda ka daukota sai ka fadawa daddynta dalilin satota da akayi inyaso duk abunda zai faru ya faru. Tsuki ya ja da jin irin muguwar shawarar daya ba kanshi yana girgiza kanshi yace no no bazan yi haka ba idan nayi haka banyi wa abbana adalci ba kuma na raba zumuncin dake tsakanin su kuma bazan so hakan ta faru ta dalilina ba. Mirginawa yayi ta gefen daman shi jin wata shawarar daya yanke. A take murmushi ya bayyana a fuskar shi yace yesss haka zanyi dan bazan bari wannan damar ta wuceni ba. Yana cikin wannan sake saken neh bacci yayi a won gaba dashi. Bayan kwana biyu Haka daddy yayi ta fafucikan neman kudi dakyar ya samu ya hada kudin. har yaso ya dawo da kudin dayayi order motoci dasu sai kuma ya fasa saboda kudin sun kai. Mummy duk ta fita hayyacinta a cikin kwana biyun nan ko abinci bataci sai daddy ya tilasta mata. Haka ma bangaren aunty hajara duk ta shiga damuwa komai bata tabukawa hatta abinci sai ameera ke dafawa dake tun shekaran jiya ameera tazo kuma itama tayi kuka dataji labarin an sace Amatu. Amatu ko tun randa Abdul yace gobe zata gida bata kara sashi a idonta ba. Shiyasa duk tabi ta daga hankalinta. Ko abinci aiko mata akeyi kuma ba'a Bari tako iso bakin kofa balle tasa ran zata fita. haka take zama ta narki kukanta ita kadai babu me lallashinta. Zaune yake a gaban abban shi suna tattauna yadda zasuyi da kudin. Shi dai Abdul sauraron shi kawai yakeyi dan ya rigada ya gama shirin shi, duk yadda zeyi bazai taba bari kudin nan su shigo hannunshi ba sai dai in shine ya dawo masa da kudin sa da kansa yace gashi. Bayan ya gama magana neh Abdul ya kalleshi yace Abba wani hanzari ba gudu ba. daman ina son idan an kawo kudin ban kar'a tabasu saboda naga muna da isassun kudi anan kuma akwai wasu motoci da zasu shigo Nigeria nan bada dadewa ba shine naga ya dace a bar kudin sai ayi order motocin dasu in an kawo. Shafa kanshi Abba yayi yace gaskiya ka kawo shawara mekyau daman nima ba tabasu zanyi ba saboda akwai uzurin da zanyi dasu idan ya tashi kaga yanxu idan kun anso kudin sai ka rikesu a wajenka amma ka kula sosai fah. Farinciki neh ya mamaye Abdul yana gaf da samun nasara yace toh abbana insha Allah zan kula. Daga haka suka rabu. Yana fita dakinshi ya nupa ya kira daddy ya tabbatar mishi da su kawo kudin nan gobe idan ba haka ba kuma zasu kashe ta. Aikuwa sai da hanjin daddy suka kada yace ayi hakuri Dan Allah kada ku cutar mun da ya'ta wallahi mun samun kudin daman kiranku muke jira. Nan Abdul ya fada mishi inda zasu kai kudin da kuma lokaci. Washe gari Ko cikakken bacci daddy be samu ba shida mummy dan sun matsu safiya bata waye sunkai kudin nan ba. Haka daddy yayi zaune daram yana jiran kiransu. Da misalin sha daya na safe Abba ya aiko da wasu gardawan mutane dansu mayar da amatu su anso kudin. Abdul kuma tun wurin karfe goma ya shiga dakin da amatu take. tana ganinshi ta mike da sauri ta karaso kusa dashi tace ina ka shiga kwana biyu ka barni anan? Dan Allah ka mayar dani gida walla.................. Shhhhhh karbi wannan ki share hawayenki. Karba tayi tana share hawayenta dan gani tayi kamar babu annuri fuskar shi. Jawo kujera yayi ya dawo gabanta ya zauna yace zauna ki saurareni kiji abunda zan fada miki. Ba musu ta zauna bakin gado tana sauraron shi dan dataji abunda zai fada. Iyayenki sun taba ganin Abdul dinki?? Cikin mamakin jin irin tambayar dayayi mata tace a'a basu taba ganin shi ba amma sun San da zaman shi. Owk naji dadin haka. Toh ki bude kunnuwanki dakyau ki saurareni kiji abunda zan fada maki kuma idan.......................... Muje zuwa 👉🏿👉🏿👉🏿 [2/4, 11:25 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & Written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Page 9-10 "Toh ki bude kunnuwanki dakyau ki saurareni kiji abunda zan fada miki kuma idan kika kuskura ki kayi kunnen uwar shegu da abunda zan fada miki sai jikin ki ya gaya maki" "Abu na farko shine koda wasa kikayi subutar baki yan gidan ku ko kuma wata kawarki can tasan dalilin satoki fa to ki kuka da kanki" "Abu na biyu shine karki yadda ki sake ki fadawa daddynki ga wanda ya satoki ko kuma dai wani abu game damu dan nasan zai tambayeki" "Abu na uku shine duk abunda zakiji ko zaki gani daga gidanku karki yadda ki musa ko ki kawo korafi" "kina jina ko? Cikin rawar murya kamar me shirin yin kuka tace eh. "Abu na karshe yana cikin wannan takardar. Duk shawarar da kika yanke ki sanar dani. Ya karasa maganar gami da mika mata wata farar envelop. ''Karba tayi tana share hawayen da suka zuba mata. Cikin ranta ko haushi takeji da irin yadda ya tsareta kamar wani ubanta yana bata umarni. ''Shi kuma a bangaren shi ji yake kamar karta tafi dan yasan yanzu shi daya kara ganinta sai in gidansu yaje. Shuru sukayi na yan mintuna kafin ya dauko kyallen da aka rufe mata fuska ya karaso daf da ita cikin rada yace ba nayi hakan dan in bata maki rai bane kawai umarni ne daga abbana. ya fada yana mai rufe mata fuska da kyallen. ''Hannunta yaja zuwa farfajiyar gidan. Har sun kusa kai wurin shiga mota sai yajiyo muryar mahaifiyar shi dake daya bangaren saman bene tana magana da mai gadi. ''Dummm gaban shi ya fadi. Aikuwa da sauri ya jawo Amatu da karfi ta fado saman kirjin shi suka buya bayan flawoyin gidan. ''Haka suka tsaya manne da juna dan har suna jin hucin junan su. Sai daya tabbatar data koma cikin gida kafin suka fito ya jawo hannunta suka fita daga gidan. Ita kuwa sai binshi takeyi batare da tasan inda zasu ba kuma ta kasa tambayar shi. ''Bayan gidansu ya nupa da ita inda ya tarar da gardin mazan da Abba ya aiko dasu. Nan suka bude mota yasa ta aciki shima ya shiga da driver na tukawa. Dayan motan kuma sauran mazan ne suka shiga kuma Sune a gaba saboda tsoro. ************* ''Daddy ko cikin hanzari yake shiri dan sunce ya iso wurin kafin nan da minti talati. Bayan ya gama shiryawa ya dauki jakar kudin ya rataya a kafardar shi zai fita sai mummy tayi saurin shan gabanshi tace Alhaji ya zaka fita kai kadai ba yan tsaro?? Kallonta yayi yace haba Rukayya kina nan zaune fah suka ce idan na kuskura nazo da wani sai dai na samu gawar ya'ta. ''Shine kike son naje da wani? Rukayya nikam ban damu ba a halin yanxu saboda ya'ta tafi mun komai mahimmanci kedai kawai ki kwantar da hankalinki kiyi mana addu'a Allah ya tsare mu, sai na dawo. ''Tsaye tayi tana kallon mijinta dan harya bata tausayi. Cikin yan kwana biyun nan duk ya firgice. Hawayene ya gangaro mata a kumatu tayi saurin sharewa ta haura sama dan tayi alawla tayi nafila. ''Gudu yake tsalawa sosai sai daya kawo dai dai inda sukace ya paka motar sannan ya paka ya fito ya fara tafiya da kafa dan mota bata iya shiga wurin. Su kuma sun dade da isowa dan ta baya suka biyo shi kuma ta gaba sukayi mishi kwatance shiyasa yanxu duk taku daya yayi suna iya hangoshi. ''Abdul dake rike da waya a kunnen shi kuma yana hangoshi yace ya cigaba da tafiya sai ya kawo wurin wani jan kyalle da suka aza ya tsaya. ''Haka yaci gaba da tafiya sai daya kawo dai dai wurin kyallen ya ajiye jakar sannan ya koma wurin motar shi kamar yadda suka umarce shi. ''Bayan ya koma da kusan minti biyar sai Abdul yaja hannun Amatu zuwa wurin. Sannan ya dauki jakar ya mikawa wani gardi daya rakosu shi kuma ya kwance mata fuska yace tayi shuru kuma karta kara koda taku daya neh. Da haka suka juya suka shige mota. A matsiyacin gudu suka bar wurin. ''Sai da suka kawo bakin titi sannan suka tsaya suka kira daddy daya koma inda yakai kudin nan. Haka ko yayi yana zuwa ya iske Amatu a tsaye tana kuka. Aikuwa tana hangoshi tayi saurin zuwa ta rungume mahaifinta tana sharban kuka. Lallashinta ya shiga yi yace su shiga mota subar wurin dan akwai hadari zama cikin irin wannan dajin. ''Wuta ya karawa motar suka tafi. Direct gida suka nupa. Ko gyara parking beyi dakyau ba Amatu ta fito a guje sai cikin gida. Da shigarta ta tarar da mummy zaune duk ta tsure tana tunanin ko zasu dawo tare. Aikuwa kamar a mafarki taji an rungumeta ana kuka. ''Dagowa tayi da idonta caraf suka hade dana juna. Nan fa murna ya tashi mummy harda kukan farinciki. Karewa Amatu kallo tayi taga duk tayi baki ga wani dan bashi bashi da takeyi dan tun zuwanta bata taba yin wanka ba sai dai tayi alawla kawai tayi sallah. ''Daddy daya shigo yanxu shima ba karamin dadi yaji ba dan rabon da yaga mummy tayi dariya haka tun randa aka sace Amatu. ''Rungume suke da juna na kusan yan mintuna kalilan kafin mummy ta saki Amatu tace ga wayata ki kira hajara ki fada mata Allah ya kubtar dake ni zanje in hada miki ruwa kiyi wanka kinji? Amsawa da toh Amatu tayi ta karbi wayan ta kira aunty hajara. ''Ita kuma kamar jira take a kirata ta dauki wayan. Da jin muryar Amatu ko amsa sallamar batayi ba ta kwalawa ameerah kira tace tayi sauri ta fito Amatu ta dawo. ''Cikin minti uku sai gasu sun shigo gidan. Aikuwa Amatu da gudu ta rungume aunty hajara tana dariya ita kuma kukan farincikin dawowar take. ''Ameerah dake bayan aunty hajara tace Amatullahi niko murnar ganina ba'ayi ba kenan ko?? ''Sai a sannan ta lura da ita taje ta rungumeta dan ko ba'a fada mata ba tasan ameerah ce. Nan suka zazzauna ana hira. Mummy da yanxu ta fito murmushi tayi cikin zolaya tace to hajara yanxu sai a karbi girki tunda Amatu ta dawo. ''Waro idanu Amatu tayi tace girki kuma mummy to da wakeyi? Hararanta mummy tayi tace bansani ba kidai tashi zuwa wanka. Ameerah ko dariya tayi tace Amatullahi jeki ki dawo kisha labari. ''Amatu na dariya ta haura sama. Dakinta ta shiga taga tsaf yake kamar akwai mutum ciki, murmushi tayi dan tasan aikin mummynta neh.wardrobe ta bude nan ma taga kayanta tsaf a gogen su. ''Towel ta zaro sannan ta fara cire kayan ta sai farar envelop dinda Abdul ya bata ta fado. Ita harta manta dashi dauka tayi tasa a cikin handbag dinta kafin ta shige toilet. Ta dade tana zubama jikinta ruwa sai wani nishadi takeji gata a cikin gidansu. ''Takai kusan minti ashirin tana watsa ruwa daga bisani kuma ta fito. Gaban dressing mirror ta nupa dan goge danshin dake jikinta tayi sannan ta fara shafa mai ta kuma lailaye jikinta da turaruka masu kamshi. Yar simple make-up tayiwa fuskarta sannan ta tashi ta shirya cikin daguwar riga baka da ratsin ja. ''Flat shoe ta saka sannan ta fito zuwa kasa. Ameerah na ganinta tayi saurin karasa inda take tace wannan irin kyau haka sai kace me barin gari. Cunno dan karamin bakinta tayi tace a haka din?? Duba fa ki gani ko gira ban zana ba fa. ''Dariya ameerah tayi to naji kar kiyi kuka muje ga abinci can kici. Ta karasa maganar gami da jan hannunta zuwa dinning table. ''Dake Ameerah ma bataci abinci ba, zama tayi sunaci tare. Mummy da Aunty hajara sai kallonsu suke suna dariya daddy kuma yana can part dinshi. ''Bayan sun gama cin abincin suka kwashe plates din suka wanke, amatu yasa kwando tace suje su kai gida. Zaro ido ameerah tayi tace lallai Amatullahi ke yanxu baki ko tsoron fita? Murmushi tayi tace wani tsoro kuma ai Allah ne ke karewa kawai dai mu tafi nayi missing din gidan aunty neh. ''Hararanta ameerah tayi tace nidai bada yawu na ba kidai bari idan muka tashi zuwa gida sai mu tafi dashi kinji? Badan taso ba suka koma Palon ana ta hira dasu. ''Su ameerah sun dade a gidan kafin suka wuce. Amatu kuma mummy ta hanata fita tace kozata fita sai an kwana biyu. ''Da daddare Amatu na kwance sai tunanin maganganun da Abdul ya fada mata takeyi. Ita a niyar ta taso idan ta dawo gida ta fadawa daddynta wanda ya satota da kuma dalilin haka sai kuma Abdul yaja mata burki kuma ta rasa dalilin dayasa taki musa masa. ''Tunowa tayi da envelop din daya bata tayi saurin dauko handbag dinta ta cire envelop din. Sai data yi addu'a kafin ta bude ta fara karantawa kamar haka................... 👉🏿👉🏿👉🏿👉🏿 [2/5, 12:36 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Vote me on wattpad @lashminzy Email:bilkisualiyu248@gmail.com Page 11-12 "Amincin Allah ya tabbata a gareki ma'abociyar so da kauna da fatan kin isa gida lafiya" "AMATULLAH" nasan zakiyi mamakin jin abunda zan fada maki amma dan Allah karki barni da ciwon da kedai ce maganin shi! bazan iya boye miki abunda ke cikin zuciyata ba "a gaskiya tun ranar dana fara saki a kwayar idona naji na kamu da matsanacin sonki" "banso ace ta dalilina an satoki ba amma duk da haka nayi iyakacin kokari na wurin ganin ba'a saki a halin da kika tsinci kanki ba sai kuma Allah ya kaddari haka" "AMATULLAH Ni mutumin kirki neh tunda nake bantaba sata ba balle har inkai ga sato mutum, mutum ma irinki" Dan Allah kiyi hakuri da abunda muka aikata miki kuma na rokeki karki hukunta zuciyata ta hanyar kin karbar soyayya ta saboda idan hakan ta kasance komai yana iya faruwa dani kuma kece sila" "na barki lafiya masoyiyata" ''wata irin nannauyan ajiyar zuciya ta sauke kafin ta nade envelop din ta rungume a jikinta tana murmushi wanda ni kaina na kasa gane kona menene. **************** Kwance yake kamar wani mara lafiya in banda sake sake ta tunani abu abunda ke cikin ranshi. Yau kwana biyu kenan yana jiran reply dinta amma shuru shiyasa duk ya tashi jiki a mace ya kasa tabuka komai. Haka ya wuni cikin daki sai da ammie ta shigo neh ta ganshi can saman gado Ita ta dauka ma ko baida lafiya neh shiyasa baizo gaishe ta ba. Data tambaye shi lafiya yace lafiyan shi kalau kawai yayi aikine da yawa ya gaji dake shi din likita shiyasa bata damu ba ta koma part dinta ta aiko mashi da abinci. Tashi yayi ya wanke bakin shi ya zauna yana ci saboda gudun bacin ranta, bayan ya gama ci neh yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya sannan yaje bakin gado zai dauki wayar shi, daidai lokacin yaji sakon text ya shigo amma dake ba shine a gabanshi ba sai daukar wayar kawai yayi ya fice abunsa. Part din ammie ya nupa, da shigar shi hanan wacce bazata haura shekaru goma sha biyar ba tazo da gudunta ta rungumeshi tana murmushi, shima murmushin da bekai zuci ba ya sakar mata gami da jan hannunta suka zauna saman two seater Kallonshi tayi da manyan idanunta tace yauwa yaya daman kai nake jira ka dawo ka aramun wayanka. Ke fa ina naki da kikeson aran nawa?? Dan marairaice fuska tayi tace yaya ammie tayi seizing plsss ka aramun. Bata rai yayi yace waton ke bakya jin magana ko kusan kullum sai anyi seizing din wayar ki?? Toh wai ma me kikeyi da wayan neh har ammie ke seizing dinta? Kukan shagwaba tasa tace Allah yaya bakomai nake da ita ba kawai ina kiran friends dina neh fah. Nidai kar kiyi mun kuka gashi kuma ki kira anan ina gani, karban wayar tayi tana kunkuni. Dake tasan pin din wayar shi yana mika mata ta bude aiko sai taci karo da text message, mika mashi wayar tayi tana cewa yaya an turo maka sako ansa ka gani. Harara ya balla mata yace dalla kiyi abunda zakiyi ki mikon waya ta. Dariya tayi da yadda taga ya fusata tace to saina bude na gani kuma na ka ranta kaji. Ko kala bece mata ba sai jin yayi ta fara cewa barkan ka da war haka amintacce da............ da sauri ya fisge wayan ya banka mata harara sannan ya kara gaba. Ammie data fito yanzu murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace ke in banda abunki wake karanta sirrin wani? Shuru tayi tazo ta rungumeta tana cewa plsss ammie ki bani wayana nayi alkawari bazan sake ba. Kallonta ammie tayi tace to naji kije dakina cikin drower ki dauko. Cikin jindadi ta sumbaci ammie a kumatu ta wuce da gudu. Shiko yana fita part dinshi ya koma ya bude message din yana karantawa. Cikin tsantsar farinciki yayi saving number kafin ya shiga dailing din number amma sai dai kash a kashe take, haka yayi ta kira a kashe daga karshe kuma ya tashi ya fita amma yaji dadin ganin sakonta. Bangaren ta kuwa tunda ta tura mashi sakon ta kashe wayanta saboda ta dauki alkawarin tunda harya iya guje mata na tsawon shekara biyu toh itama sai ta rama ta hanyar wahalar da zuciyar shi shima ya dan dana irin zafin dataji Cikin ranta kuma take cewa toh idan bashi bane fah? Ya kenan? Tsuki tayi ta kawar da maganar dan ita har yanzu bata yadda ba Abdul dinta bane. Washe gari Da misalin karfe goma na safe ya kira daddyn amatu da ainihin number shi, nidai banji abunda aka ce ba sai dai daga gani maganar tayi mishi dadi. Da yamma ya shirya tsaf cikin shiga ta alfarma sai kanshi yake zubawa da ammie ta ganshi tace Allah yasa suruka za'aje samo min. Murmushi yayi yana Sosa keya ya fice daga gidan. Tafiya yake cikin annashuwa harya kawo dai dai gate din gidan, batare da bata lokaci ba megadi ya wangale mishi gate sai gashi cikin farfajiyar gidansu. Kiran daddy yayi sai gashi ya turo an shigo dashi palon baki. Cikin girmamawa ya gaida daddy kafin ya koma ya zauna, Kallonshi daddy yayi yace bari in dawo kaji yaro. Amsawa da toh Abdul yayi yana mai jindadin yadda daddy ya yarbe shi sai dai addu'ar shi daya Allah yasa ya amince da kudirin shi. Yana cikin haka sai gashi nan ya dawo, zama yayi kan kujerar dake facing dinshi yace ayi mun afuwa na bata maka lokaci ko. Murmushi Abdul yayi yace ai babu komai. Tau yaro ina saurarenka Daddy nasan baka sanni ba amma dan Allah ina rokonka daka amince da batu na. Shuru daddy yayi na seconds kafin yace indai bukatar ka bata kauce wa addini ba insha Allah zan biya maka ita Cikin dadi Abdul yace nagode daddy sunana Abdul........ Sai akayi sallama daga waje, dake daddy yasan da zuwanta babu wani bata lokaci ya bata izinin shigowa. Shigowa palon tayi dauke da paranti a hannunta duk da cewar tayi mamakin ganin shi amma haka ta daure ta karasa gabanshi ta ajiye mashi parantin, ji tayi ameerah dake bayanta ta gaishe shi shiyasa itama tayi kokarin saita kanta ta gaishe shi, shiko kamar ma bai taba ganinta ba dan kawar da kanshi yayi daga gareta yana fuskantar daddy. Suna fita Amatu ta sheka da gudu zuwa dakinta dan yadda taji gabanta na mugun faduwa Daddy kuma bayan fitar su kallon Abdul yayi yace toh yaro cigaba da maganar ka Muje zuwa 👉🏿 [2/5, 11:47 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Wannan shafin sadaukarwa neh ga my real Momcy (haleemah) ina sonki ina kaunarki fiye da yadda kike tunani, Allah yabar mu tare 💋💋 Vote me on wattpad @lashminzy Email; bilkisualiyu248 @gmail.com Page 13_14 "Sunana Abdulraheem Ibrahim kanta" cikin tsoro da mamaki daddy yace kana nupin kai dan gidan Ibrahim kanta neh aboki na kuma aminina?? Eh daddy. Ajiyar zuciya daddy ya sauke yace cigaba da maganar ka ina jinka. "Daddy duk da nasan cewar a kwanakin baya da suka wuce kun samu sabani da mahaifina inason karka fasa cika alkawarin daka dauka. Daddy bakomai ya kawoni wurinka face Yar gidanka dana gani kuma tayi mun shiyasa nazo neman izini a wurinka. Ya karasa maganar neh gami da sunkuyar da kanshi wai ala dole yaji kunya. A firgice daddy ya mike tsaye yace Abdul ka kuwa San abunda kake fada kuwa? Kasan irin rikicin da muka samu da mahaifinka a sakamakon abun duniya? Girgiza kai Daddy yayi yace kai ina bazai yiwu ba saboda koda ni na amince shi bazai taba amincewa ba. Amma kasani tunda nayi maka alkawari kayi hakuri ka jira zuwa karshen wata zan biya mahaifinka kudin shi kuma zamu sasanta kaga daga nan kai kuma sai ka bijiro da taka maganar ko? Eh daddy amma wani hanzari ba gudu ba. Dan Allah Inason kamun izinin zuwa gidanka. Murmushi daddy yayi ya dafa shi yace karka damu na maka izini kuma nagode maka da kokarin ka koba komai zumuncin mu zai karu. Cike da farinciki ya fara gode ma daddy. Daga nan suka fara hira, hira tayi hira daddy ke bawa Abdul labarin kidnapping din Amatu da akayi. Abdul ko kamar bashi ya aikata ba harda wani cewa Allah ya toni asirin su. Haka sukaci gaba da hira kamar wa'anda sukayi sabo, sai kusan magariba Abdul yabar gidan. Ko daya koma gida karfe goma na dare dan sai daya biya wurin abokan shi suka dan taba hira kafin ya dawo gida. Part dinsa ya nupa, da shigarsa ba bata lokaci ya watsa ruwa ya shirya cikin kayan bacci sannan ya kashe wuta ya kwanta. Wayar shi ya dauko da niyar ya kira Amatu sai ga sakonta ya shigo kamar haka "Slm Abdul me kazo yi gidan mu?? Tsuki yaja bayan ya karanta ya fara dailing number ta amma yaji ta a kashe. Ranshi neh ya baci yace wai me yarinyar nan ke nupi dani ne? Tace ta amince dani amma kuma take wulakanta ni? Toh wallahi bazai yiwu ba gobe goben nan zata ganni a gidansu kuwa. ************ Bangaren Amatu kuma tana aika sakon ta kashe wayanta amma da biyu. Na farko karya kirata ya balbaleta dan ta tuna da kashedin dayayi mata akan duk abunda ta gani tayi kamar bata gani ba. Na biyu kuma tanason ta wahalar da zuciyar shi har sai yagaji ya dawo ainihin Abdul dinshi. Niko nace Amatu kina da aiki kuwa Washe gari da maraice ya shirya tsaf cikin yadi me ruwan madara da bakin hula da bakin takalmi sai zuba kamshi yake kamar wani sabon ango. Part din ammie ya nupa, Kodaya shiga ammie na zaune saman one tana kallo hanan kuma tana aikin latsar waya Kallonshi ammie tayi cikin zolaya tace Abdul nipa kwana biyu na kasa kagane maka? Daga dawowarka daga aiki harka sake sabon wanka? Toh wai ma ina zakaje neh haka? Dan shafa sajenshi yayi yace ammie babu komai fa kawai zan raka abokina wani wuri neh. Toh Allah ya bada sa'a amma fah inka rakashi ka tabbatar kaima ya raka ka kaji ko? Dariya yayi dan ya fahimci inda maganar ta nupa ya fice daga palon gami da kwalawa hanan kira. Wurin motar shi ta sameshi yana latsar wayanshi. Kallonta yayi yace sis dauko gyalenki muje ki rakani wani wuri kinji? Ko amsawa batayi ba ta zura aguje taje ta dauko mayafinta ta dawo. Shiga motar sukayi ya kama hanya sai gudu yakeyi kamar wanda zai tashi sama. Ita kuma hanan sai faman tambayar shi ina zasu take amma ko kallonta beyi ba yace tasa ido ta gani. Hhhhh nima nace bari insa ido in gani hhhhh masu karatu kuma kusa ido ku gani. Daidai bakin kofar gidan ya tsaya dan ba shiga zeyi ba. Fitowa yayi daga cikin motar ya isa wurin me gadin gidan da niyar yayi mishi sallama da Amatu dan ya kira number ta switch off sai gasu nan sun iso ita da ameerah. Shan toka tayi zata shige sai yayi saurin shan gabanta yace ina da magana dake? Juyowa tayi suka hada ido sai taga alamar babu wasa attare dashi shiyasa bata musa ba ta bishi zuwa wurin motar shi. Ameerah kuma tun bayan ta gaishe shi ta shige gida. Tsaye tayi kamar wata gunki babu eh balle a'a. Shima murtuke fuska yayi kamar be taba dariya ba yace miye dalilinki na kashe waya? Shuru tayi bata ce kala ba sake maimaitawa yayi kafin ta kalleshi tace babu komai. Yar dariya ya saki ganin yadda ta cuno bakinta yace toh daga yau karki kara kashe wayanki indai har kina sona. Dago da kanta tayi ta kalleshi zatayi magana sai ya katse ta da cewa "AMATULLAH kar kiga kamar ina tauye miki haka, nop ba haka bane wani abu da ki kaga inayi akwai dalili wani kuma zuciyata ke sani aikatawa kamar yanzu danazo gidanku kunnuwana suna bukatar jin zazzakar muryarki kamar yadda idanuwana ke muradin ganin kakkyawar surarki ammai sedai ke kina mun rowa. Bansani ba ko kunyata kikeji ko kuma har yanxu kina tunanin wancan Abdul dinne oho amma dai kisani ni Abduraheem masoyinki neh na gaskiya ki saki jikin ki dani, ki manta da wancan Abdul din naki ki rungumeni hannu bibbiyu nayi alkawarin zan baki kulawa har karshen rayuwarki. Hawayene suka gangaro mata dajin irin kalaman da ya fada kamar na wacan Abdul din kusan komai nasu babu banbanci taya za'ayi bazata taba yadda bashi bane?? " AMATULLAH" zuciyarta ceh ta buga da karfi saboda yanayin yadda ya kira sunanta yace indai har zaki soni kuma zaki aureni toh kisa wannan a kwakwalwarki ni "ABDULRAHEEM" nayi miki alkawarin duk sadda Abdul dinki ya dawo zan sakeki ki koma gareshi koda kuwa yin hakan shi zai zamo ajalina. Da sauri ta dago da kanta suna kallon juna tace Abdul saboda me zakayi haka?? Saboda farincikin ki ya bata amsa. Hawayenta ta share tana mai jindadin kalaman shi tace nagode Abdul nima nayi maka alkawarin daga yau zaka fara jindadin zama tare dani. Murmushi ya sakar mata kafin ya zagaya ya budewa hanan kofa danta fito su gaisa da ita. Ja mata kunne yayi akan kada garin surutu ta sakar mishi layi dan hanan akwai iya surutu ga bakinta da kaifi kamar reza. Suna zuwa inda take hanan ta rungumeta tana cewa aunty ina wuni. Murmushi Amatu tayi karba mata tana kallon Abdul da fuskar shi dauke take da fara'a. Bayan sun gaisa neh kuma ya gabatar da matsayin hanan a wurin shi kafin suka wuce Koda suka isa gida ammie na kitchen tana dahuwar abinci, da gudu hanan ta karasa wurinta ta rungumota ta baya tace ammie mun dawo amma fah akwai labari. Abdul dake shigowa kitchen din yace toh sannu magulmaciya ki fada a gabana mana. Dariya tasa ta fice daga................... Pls share [2/7, 10:45 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Real Momcy and sweet janaf ina tayaku murnar kammala littafin ku Allah ya kara muku basira Allah yasa kufi haka Allah ya albarkaci rayuwarku Allah ya amfanar damu darussan dake ciki kurakurai kuma Allah ya yafe mana bakidaya Vote me on wattpad @lashminzy Email; bilkisualiyu248@gmail.com Page 15-16 Dariya tasa ta fice daga kitchen din. Abdul kuma taya ammie yayi abinci tana cewa ya bari amma fur yaki. Da hanan ta dawo dariya ta kamayi masa tana cewa dan daudu, ammie kuma murmushi kawai takeyi tana jin son yaranta na kara shigarta. ''Kwance take tana chatting ameerah da yanxu ta shigo kallonta tayi cikin dan bata rai tace Amatu wai bazaki shirya mu fita bane? Tashi tayi a kasalance ta dubi ameerah data bata rai, murmushi tayi tace sorry my meerah bari in shirya mu tafi. Mikewa ameerah tayi gami da cewa ki biyomin inkin shirya. Bayan fitar ameerah tashi tayi ta shige toilet ta watso ruwa babu wani bata lokaci ta shafa mai sannan ta lailaye jikinta da turaruka masu kamshin gaske. Batayi wata kwalliya me yawa ba tasa riga da skirt na atamfa da bakin hijabi. Handbag dinta dake rataye ta dauko gami dasa takalminta kafin ta fito. Dakin mummy ta nupa tayi mata sallama sannan ta fito waje, ta dauko wayanta kenan zatayi dailing number ta sai gata nan tazo. Murmushi suka sakarwa juna sannan suka nupi inda motar Amatu me kirar range rover kalar baka mai daukan ido. Batare da wani bata lokaci ba ta tayar da motar suka fita, sun kai kusan minti goma kafin suka isa bakin wani dan madaidaicin shàgo mekyau wanda daga sama an rubuta AMATULLAHI BEAUTY SALOON da manyan haruffa, pakawa sukayi ta gefen shagon sannan suka fito suka nupi shagon, mukulli amatu ta zaro daga jakarta ta bude shagon suka shiga. Dake shagon babu wasu kayaki da yawa saboda rashin zuwanta na kwana biyu kuma tunda akayi kidnapping dinta aka rufe shagon sai shekaranjiya suka fara zuwa. Dan kakkabe dan sauran kayan dake ciki suka farayi suna sharewa kafin titi ta dawo(wadda amatu ta aika ta anso mata kayan datayi order) kuma ta kama yau lahadi neh shiyasa babu yan aiki ciki dan duk ba hausawa bane su kadai neh musulmai sai wata Maryam amma yanxu tabar zuwa saboda tayi aure. Suna cikin aikin neh sai ga titi ta shigo da kaya niki niki a hannunta, ajiyewa tayi taje ta kwaso sauran kayan ta dawo. Zama tayi saman kujera da gurbataccen hausan ta wanda bata gwanance ba tace sannu aunty nageji sosai fah. Ruwan da amatu ta fito dashi daga mota ta mika mata tace gashi kisha ruwa kyafi jin dadin hutawan ko? Murmushi tayi ta amsa. Ameerah kuma dariya takeyi wa titi saboda yanayin yadda take magana kamar ansata yin hausan dole. Nan suka fara hira suna jera kayan da aka siyo wanda suka kare kuma a jefa fankwon shi cikin dustbin. Bayan awa biyu Abdul neh a bakin kofan shagon su dake maza basa shiga shiyasa daya zo ya yatsaya a bakin kofa yana jiran fitowarta. Ita kuma tana steaming kan wata neh shiyasa ta dan bata lokaci kafin ta fito. Kodata fito ya koma inda ya faka motar shi yana fuskantar shagon da hannunwan shi zube cikin aljihu. Murmushi ya sakar mata a daidai lokacin data iso wurinshi. Itama mayar masa da martani tayi gami da gaishe shi. Amsawa yayi cikin fara'a yana mai kura mata ido. Itako kunya taji ta rufe fuskanta da hannuwanta. Dan bata rai yayi yace to miye na rufe fuska kodai ba'aso naga kwalliyar neh?? Janye hannunta tayi ta dubeshi ta gefen ido tace laaaa ah'ah nida ko kwalliya ma banyi ba. Dan zaro ido yayi yace wannan hodar da janbakin fah ko haka Allah ya halicceki dasu?? Dariya ta kyalkyale dashi. Dan jim sukayi na dan mintuna kowa da abunda yake sakawa a ranshi. Ganin shurun yayi yawa sai amatu tace itakam zata koma shago sunada mutane da yawa. Bata rai yayi alamar beji dadin maganarta ba yace owk sai anjima. Itako ganin yanayin shi yasa jikinta yayi sanyi dan yadda yayi maganar kamar ranshi ya baci. Cikin sanyin murya tace Abdul... Sai kuma tayi shuru dan batasan abunda zatace ba. Juyowa yayi ya kalleta yace akwai wani abu neh?? Saurin bashi amsa tayi tace plsss am sorry nima banso mu rabu yanzu ba kawai dai babu yan aiki cikin shagon neh kuma ga customers na zuwa shine nake sauri in sallamesu. Tau naji baby ki kula da kanki and karki manta idan kin koma gida ki sanar dani. Amsawa tayi da toh gami da daga mishi hannu har sai daya bace ma ganinta. ************ Zaune yake a dakinshi yana cin abinci sai wayanshi tahau ruri, dubawa yayi yaga Abba neh kiranshi. Da sauri amsa daga bisani kuma naga ya tashi ya fita. Part din Abba ya nupa koda yaje ya tarar da Abba sai safa da marwa yakeyi a tsakiyar palonshi. Cikin tashin hankali Abdul yace Abba lafiya na ganka haka? Kallonshi Abba yayi da duk ya jike da zufa yace Abdul ina lafiya kuwa dazu Muhammad lemi (daddyn amatu) ya kawo mun kudina harda bani hakuri. Cikin nuna damuwa Abdul yace toh yanxu miye mafita? Ya zakayi ka mayar mishi da kudin shi? Haba Abdul nakira Kane fah dan ka bani shawara ni wallahi kaina ya kulle sai yanzu nake danasanin aikata abunda nayi. Ni yanzu ma da wani ido zan kalleshi idan yasan ni nasa akayi kidnapping din yar'sa? Kallonshi Abdul yayi yace hmmm abba kenan abunda nake nunar maka kenan ai gashi yanzu kayi danasani amma a zahiri cewa yayi abba abu mafi sauki kawai ka fada mashi, kaga tunda yana da saurin hakuri zai iya yafe maka. Wani banzan kallo Abba ya aikawa Abdul yace baka da hankali Abdul yanzu so kake naje har gabanshi ince ni na sace Yar shi? Ya kake tunanin ze kalleni? Wani matsayi zai daukeni ace yadda muke dashi na aikata mashi irin wannan akan abun duniya aiko waye bazai ji dadi ba. Eh hakane Abba amma ga shawara... Nace tunda ya dawo maka da kudin ka me zai hana ka mayar da zumuncin ku kamar na da sai kuma ka nema mun auren yar shi. Tswaya Abba ya daka mashi yace wai kai Abdul yau dinnan meke damun kwakwalwar Kane? Ya ina maka magana kana dauko mun wata magana can daban? Hakuri Abdul ya shiga bashi yace Abba ba wani Abu bane naga kamar idan na auri yar shi zumuncin ku zai karu kuma koda daga baya ka fada mashi haka zai iya yafe maka kodan albarkacin yar shi dake aurena kuma ma zai dubi girman zumuncin ku ya yafe maka. Kaga daga nan komai ya wuce. Murmushin da bekai zuci ba Abba ya saki yace kana ganin shawarar nan taka tayi kuwa?? Nima dai nace anya kuwa shawarar nan tayi?? Pls share [2/8, 10:53 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Vote me on wattpad@ lashminzy Email:bilkisualiyu248@gmail.com *سْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ* الرَّحِيْمِ _*May Allah (SWT) Bless you and your family with a restful mind, useful soul, peaceful home, commendable effort, acceptable worship, and a successful end. May He beautify your tongue with truth, heart with sincerity and count you among the dwellers of Jannatul Firdaus, Insha Allah. Juma'at Mubarak. Page 17-18 Abba kallon Abdul yayi yace jeka na yadda da shawarar ka kuma duk abunda ake ciki zan sanar dakai kuma wa'yannan kudin ka dawo su a jiye har zuwa lokacin da za'a bashi kaji ko? Amsawa da toh Abdul yayi sannan ya fita. Dakinshi ya nupa yana mai jindadin amincewar abba. Wayar shi ya dauko ya fita sai part din ammie, da shigarsa hanan taje da gudu ta rungume shi tana kukan shagwaba wai yaje wurin Amatu be fada mata ba. Murmushi yayi yace my hanan kukan me kikeyi haka. Dan hararar sa tayi tace ba kai bane kaje wurin aunty Amatu baka fada mun ba. Waro ido yayi yace injiwa? Tana dariya tace inji ammie mana bakai ka fada mata ba. Ammie dake shigowa cikin palo tace ke yar nan yaushe nace yaje wurinta nida nace miki yaje wani wuri? Dariya Abdul yayi yace toh dai ammie fada mata ni babu wata da nake zuwa wurin ta. Kura mishi ido hanan tayi tace aunty Amatu fah ko ita wurin ta ba wuri bane?? Dan shafo keyar shi yayi yaje wurin ammie ya zaune gami da dora kanshi saman cinyarta. Aikuwa kamar jira take ya hau tayi magana tace laaa dagani karka karyani ban shirya ba. Cikin sigar shagwaba yace ammie waton kinfi son hanan fiye dani ko? Toh miji ma zan samo mata ayi mata aure kowa ma ya huta. A million hanan ta dauko piloluwa guda biyu ta jefeshi dasu duk kuma a lokaci daya tace Allah yaya ban is aure ba sai na girma kuma kuma....Sai hawaye shar ta fada jikin ammie tace cewa ni ammie bazanyi aure ba ina nan tare dake kuma ji yaya ma daya fini girma sau goma ba'ace za'ayi mishi aure ba sai ni toh wallahi sai na fadawa Abba idan ya dawo. Kyalkyalewa yayi da dariya ita kuma taci gaba da kuka ammie kuma tasa bakinta tace baby na rabu dashi ai kwanan nan zamu koreshi duk ya cika mana gida da kashi. Dariya hanan tasa harda rike ciki. Aikuwa ya taso zaiyo cikinta ya bugeta ammie ta dakatar dashi. Bata rai yayi ya ficewarsa daga palon ma baki daya. Part dinshi ya shiga ya watsa ruwa kafin ya shirya cikin kayan bacci ya kwanta. Bangaren amatu kuma kwance take tana jiran kiranshi ga wani matsiyacin bacci da takeji dan yau tayi aiki da yawa kuma yanxu idan ya kira bai sameta ba ya hau wani shan kanshi shiyasa ta dauko wani littafi tana karantawa saboda hasken waya da daddare bacci yake sata shiyasa ma batayi yunkurin dauka wayar ba. Babu dadewa ya kirata daman jira take babu wani jan naji ta dauka. Cikin sassanyar muryarshi yace baby na ya kike? A hankali tace yadda kake. Murmushi yayi yace kinsan yadda nake neh kuma kinsan yadda nakeji neh? Girgiza kai tayi kamar yana kallonta tace a'a. Dan jim kafin yace toh kinason kiji yadda nake? Saurin amsa da eh tayi. Yace baby na lafiya kalau nake kamar yadda kike amma kuma soyayyar ki tayi mun illah ta hanani sukuni banaji bana gani indai akan soyayyar ki neh. AMATULLAH sonda nake maki baya misaltuwa bana samun nutsuwa idan har ban saurari muryarki ba kuma ki sani bazan iya rayuwa batare dake ba. Shuru tayi bata ceh komai sai wani abu da takeji yana mata yawo a jiki wanda ita kanta bazata iya fadin ko menene ba. Ganin shurun yayi yawa neh sai yace baby ina jinki nima ki fadamun yadda kikeji game da soyayyata. Aikuwa kashe wayar tayi dan batasan abunda da zata fada ba duk cewar itama tana jin wasu feelings a kanshi. Zaro wayar yayi daga kunnen shi yaga ta kashe sai ya fara kiranta amma bata dauka ba. Zai kara kira kenan yaga sakonta ya shigo. Karantawa yayi yana murmushi ya rungume wayar a kirjin shi a haka bacci barawo ya sace shi. Itama haka da tunanin shi tayi bacci. Washe gari tunda safe ta shirya zata shago sai wasu kawayenta na makaranta sukazo sunzo kawo invitation na auren daya daga cikin su mai suna maryam. Nan ta zauna sunata hira saboda an dade ba'a hadu ba. Kuma basu suka wuce ba sai da yamma. Dan haka suna fita itama ta wuce shago kuma dake ameerah ta tafi shiyasa kai tsaye ta nupi shagon. Bayan ta shiga neh suka fara gaisawa da mutanen dake cikin shagon. Ameerah tace Amatu sai yanzu kinsa mutane sai faman jiranki suke tayi, wata ma cewa tayi a fada miki sai gobe zatazo tunda bakya nan. Murmushi amatu tayi tace toh ayi afuwa gashi nan dai na iso yanzu waye akan layi. Wata cutomanta me suna hajiya Aisha tace amatu nice mana bakiga ma kujerar dana zauna ba? Murmushi Amatu tayi tace mummy kiyi hakuri na bata miki lokaci wallahi wani uzuri neh ya kamani. Murmushi hajiya Aisha tayi tace ai babu komai yanxu dai mu fara naga yamma tayi. Amsawa da toh tayi sannan ta kashe wayarta saboda kar Abdul ya kirata danshi ko aiki yakeyi haka yake kiranta suna hira kuma idan tayi magana yaga laifinta yace bata sonshi shiyasa bata damuwa ko bataji muryar shi ba. Nan ta fara da ita sunayi suna hira dan sun saba sosai shiyasa ma take kiranta da mummy kuma ba karamin dadi hajiya Aisha keji ba, dan tana matukar son yaro mai girmama na gaba dashi. Basu dade sunayi ba suka gama saboda ba wani abu me yawa akayi mata ba kawai wanke mata kai akayi da stretching. Bayan ta gama mata neh sai ga wata yarinya ta shigo wai ana sallama da amatu. Sai da gabanta ya fadi dan tasan Abdul neh haka yake idan ya kira wayarta a kashe sai yazo yagani ko lafiya ta kashe wayarta. Hajiya Aisha kuma zaune take tana kiran number driver amma switch off shiyasa kawai ta fara kiran number Abdul yazo ya mayar da ita gida. Daidai lokacin da amatu ta isa wurin shi wayar shi ta fara kara, dubawa yayi yaga ammie ce ke kiranshi sai yayi saurin dagawa. Daga cikin wayar naji ana cewa Abdul idan baka aikin komai kazo ka mayar dani gida na kira number musa ban sameshi ba. Har ga Allah beji dadin katse hirar su da ammie zatayi ba amma saboda ganin girma da darajar mahaifiya yace ammie kina wani wuri neh?? Ina maitama federal housing kusa da maitama store zakaga wani saloon a bakin titin nan nake. Amsawa yayi da toh kafin ya katse wayan. Kallon wurin da ammie tayi mishi kwatance yayi yaga ai shagon amatu take nupi. Ras gabanshi ya fadi dan bayason ammie ta fahimci wani abu tsakanin shi da amatu danshi yaso yakai mata ita har gida dasu hadu saman hanya, kuma ma akwai kunya tunda yanxu idan ta fito ta tarar dasu me zasu ceh? Amatu kuma satar kallon Abdul take a ranta tana cewa toh ko lafiya naga dazu yana murmushi yanzu kuma kamar me tunani. Ji tayi yace ki koma cikin shago anjima zan dawo ammie ce ta kirani. Zatayi magana ya daga mata hannu alamar ta tafi kawai. Juyawa tayi zata koma daidai kuma lokacin ammie ta fito.................. Yawan comment yawan typing😎 [2/8, 8:57 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÌÒÑ💥 Masoyana gsky babu kamar yau dan naji dadin comments dinku sosai, ina yinku irin ehh dinnan ku biyoni muci gaba da gashi Muje zuwa Page 19-20 Ammie na fitowa taci karo da amatu Wanda daga gani ko ba'a fada maka ba kasan daga wurin Abdul take. Amatu kuma zuwa tayi ta karbi jakanta tace mummy har kin fito kenan? Murmushi ammie tayi tace eh ga dana ma can ku gaisa. "Gaban Amatu neh yake dukan tara tara tana mamakin daman Abdul yaron mummy neh? "Katse ta ammie tayi da cewa tau amatu sai wani lokacin. "Itakuma ta lula duniyar tunanin sai da ammie tayi magana kafin ta tuno da cewar bata gaida Abdul ba kuma harya shige mota" Sallama tayi wa ammie ta koma shagon. ''Ammie kuma suna cikin mota take tambayar shi ko yasan amatu neh? Cikin rashin gaskiya yace am daman nazo neh sai na ganta shine nake tambayar ta ko kina ciki. Murmushi ammie tayi danta gano karya yakeyi sai tace owk ai na dauka akwai wani abu a tsakanin ku ne. Saurin girgiza kanshi yayi yace a'a ammie babu komai fah. Satar kallonshi ammie tayi taga kamar me wani nazari sai can tace gaskiya son yarinyar nan ta shiga raina ina ma ace zaka sota. "Jan burki yayi wanda sai da ammie ta danji tsoro tace Abdul miye haka? Ko dan nace haka shine zaka nemi ka shekeni" ''Dariya yayi harda dafe kai yace sorry ammie na ba haka bane kawai dai banyi zaton zaki ce haka bane. "Hmmm tau Abdul nidai gaskiya tayi mun dan tana da kirki sosai kuma kaga Har yanzu baka kawon yarinyar danaji kuna magana kaida hanan ba. Plsss son ka nemo mata kayi aure nima in samu yan jikoki na" Murmushi yayi yace karki damu ammie nah kiban nan da sati daya zan baki mamaki. Tau Allah ya kaimu son. ******* Bayan ta koma shago jan ameerah tayi suka koma gefe "cikin rada tace ke kinsam wani abu kuwa? Kallon ameerah tayi tace a'a sai kin fada. "Hmmm Ashe mummy itace mahaifiyar abdul bansani ba. Dan waro ido ameerah tayi tace wai da gaske kina nupin abdul dinki dan gidan hajiya Aisha neh?? Kwarai mai kuwa gaskiya nidai naji dadi" zan samu suruka mai mutunci. "Murmushi ameerah tayi tace gaskiya nima naji maki dadi Allah ya sanya alkhairi muma Allah yasa mu a sawun ku. Amsawa da ameen Amatu tayi kafin suka koma sukaci gaba da aikin su" Kusan magariba suka bar shagon suka nupi gida. Direct gidansu suka nupa, "bayan sun shiga ciki neh suka gaida mummy sannan sukayi sallah suka fita. Gidan aunty hajara suka shiga. Da shigar su aunty hajara dake wasa da danta mubaraka tace yauwa daman ku nake jira. Dazu abban mubarak yake fada mun wai an fara registration din JAMB shine nace sai ku shirya ku tafi ko zuwa gobe ne ko? Tau aunty nima dazu wata ta fada mun aza nayi karya ma takeyi shiyasa ban fadawa ameera ba amma yanxu zan fadawa daddy idan na koma gida. Dake ameerah ma tayi bataci ba shiyasa ma ta dawo gidan aunty hajara da zama " fatan samun nasara sukayi wa junan su kafin suka nemi wuri suka zauna. Amatu kam kitchen ta shiga dan jin yadda cikinta ke kugi kuma sai da mummy tace su tsaya suci abinci sukace a koshe suke. Kulolin dake kitchen din ta fara budewa tana dubawa ko zata ga abinci amma bataga komai ba. Nan ta fito ta wuce dinning inda ta tarar da best food dinta wato jollop din cous cous. Kamshi neh kawai ke tashi gashi yasha kayan lambu. ''aikuwa nan ta zauna tanawa ameerah gwalo dake ameerah batacin kifi kuma ansa kifi a ciki. Aunty hajara ko goyon bayan amatu take tana cewa "my amatu kici iya cinki sai kin koshi" Murmushi amatu tayi tace andai bar wata a baya. Shuru ameerah tayi mata dan tasan da ita takeyi. Tashi ma ameerah tayi ta sulala indomie, daidai lokacin kuma amatu harta gama cin abinci tana shirin zuga gida. Tsayar da ita ameerah tayi tace taje tayi sallah kafin ta gama cin abinci sai ta rakata. Nan ta wuce daki tayi sallar isha'i kafin tayi wa aunty hajara sallama suka fita. Wayarta ceh ta hau ruri, tana dubawa taga Abdul ne ke kiranta. Sai da taja aji kafin ta amsa kiran. "Cikin zazzakar muryar shi yace baby gani nan kofar gidanku kiyi sauri plsss akwai inda zani. Katse wayar tayi tana murmushi sannan tace my meerah ki koma gida ga Abdul can yazo. Harara ameerah ta banka mata tace to ina ruwana nidai har gida zan rakaki. Amatu dai batace komai ba sukaci gaba da tafiya. Bayan sun iso neh ameerah ta gaishe shi kafin ta koma gida. Ita kuma amatu tsaye tayi tana kallonshi kamar yadda shima kallon nata yakeyi. Kusan minti uku suka kwashe suna aikawa junan su sakon soyayya ta cikin ido daga bisani kuma yace my baby me matar nan tace miki dazu? Duk da ta gane wacce yake magana a kanta sai ta basar tace wace mata kenan?? Ina nupin wadda nakai gida dazu mana! Ohh ai sai kace mun mummy dan nafi ganewa ta haka. Murmushi yayi a ranshi yana cewa lallai sun saba da juna tunda naji tana ce mata mummy " amma a fili sai yace ina jinki me tace miki?? Dan murmusawa Amatu tayi tace kawai cewa tayi ga danta nan in gaida shi shine kaina ya kulle a lokacin bakaga banko gaishe ka ba? Murmushi yayi yace owk yayi kyau daman ita ta aikoni tace wai inzo in nemeki. Kallonshi tayi tace ni din? Eh mana kinsan fa batasan kece amatun danake fada mata ba ni kuma sai nayi mata wayo irin namu na yan zamani nace mata karta damu zan bada surprise a cikin satin nan. "murmushi amatu tayi naji dadi wanda sai da dimpul dinta suka lotsa tace naji dadi sosai my Abdul amma wane irin surprise zaka bata? "Hmmm ke zankai a matsayin surprise din nasan zataji dadi sosai idan kuma tace ina waccen amatun sai ince zabin mahaifiyata nakeso kinga zatayi farinciki da hakan" Murmushi amatu tayi na jindadi tace Allah sarki ammie (kamar yadda taji yace) tana sonka sosai nima gaskiya ina sonta saboda tana sona kuma naji dadi da zan zama surukarta fatana Allah ya kara mana son junan mu? "Amsawa da ameen yayi kafin ya bude motar shi ya miko mata wata leda yace gashi daga dan gidan ammien shi. Hararar wasa tayi mishi tana dariya tace hmmm wai dan gidan ammien shi toh nikuma fa? Hmmm kema yar'ta ceh ai kuma... Sai ga daddy yayi horn a bakin kofar gidan. Sai da daddy ya shiga kafin ya kalli amatu yace muje na gaida daddy nah. Bata ce komai ba suka shiga cikin gidan inda suka tarar da daddy har yayi pakin ya fito daga cikin mota. Karasawa yayi shi kadai dan amatu ta shige gida. Gaisawa sukayi har daddy ke fada mashi ai ya hadu da abban shi kuma yaso suyi magana saboda babu lokaci yace sai gobe zai zo har gida suyi maganar. Abdul ba karamin dadi yaji ba yace toh daddy nagode Allah ya saka da alkhairi ni natafi." Sallama sukayi wa juna kafin daddy ya shige cikin gida Abdul kuma ya wuce. Bayan daddy ya shiga ciki yaci abinci ya huta sai yasa mummy ta kira masa amatu dan akwai maganar da yakeson yayi da ita. Babu bata lokaci sai ga mummy tazo tare da amatu. Kallon daddynta tayi taga yadda ya nutsu yana kallonta alamar maganar nada mahimmanci kenan. Amatullah yaron nan dake zuwa wurinki kina sonshi?? Cikin jin kunya tace eh daddy. " tau masha Allah gobe za'a zo neman aurenki ina fatan kin amince dashi dan kinsan duk abunda kikeso shi nakeso bazan yi maki dole ba. Dan sunna da kanta kasa tayi tace daddy na amince. Tau naji dadi sosai Allah ya tabbatar da alkhairi, "amsawa da ameen sukayi dukansu har da mummy dan itama tana son abunda yar'ta keso. ********* Bayan kwana biyar, kwance yake yana waya da ita sai faman zuba love sukeyi. Duk wani kalaman soyayya sun sanshi, wani kalamin ma kai kace basu suka fada ba. Suna cikin hirar neh yace mata ta shirya gobe zai zo ya kaita ta gaida ammie. Cikin farinciki ta amsa masa da toh sannan sukaci gaba da hira. Yana gama waya da ita kiran abban shi ya shigo. Katsewa yayi ya nupi part din abba inda ya tarar dashi yana cin abinci. Gaida shi yayi kafin ya samu wuri kusa dashi ya zaune yace.............. Muje zuwa👉🏿 [2/9, 10:36 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Page 21-22 Gaida shi yayi kafin ya samu wuri kusa dashi ya zauna yace abba gani. Kallonshi Abba yayi sannan ya rufe abincin da yakeci yasha ruwa sannan yayi hamdala. Maida dubanshi yayi ga Abdul yace yauwa son daman maganar ka ce kuma an tsayar da magana dan kwana hudu da suka wuce naje mun tattauna da aminina Muhammad kuma ya amince da batun ka sai dai yace da sharadin zaka bari taci gaba da makaranta kuma nace mashi wannan ba matsala bane ina fatan ka amince?? Eh Abba na amince. Tau tau yayi kyau sai ka fara shirye dan mun tsayar da lokaci nan da wata uku. Murmushi neh ya bayayyana a fuskar Abdul yace Allah ya nuna mana lokacin "amsawa da ameen abba yayi Tashi yayi zai fita sai kuma ya dawo yace Abba ka fadawa ammie neh? "Girgiza kai Abba yayi alamar a'a" sai Abdul yace owk plsss Abba karka fada mata ka bari sai gobe da daddare."murmushi kawai Abba yayi batare da yace komai ba. Fita yayi ya koma part dinshi ya kwanta dan dare yayi kuma ya kira Amatu bata dauka ba dan yana son ya tambayeta ko meyasa bata fada mishi ansa lokacin auren su ba" sai wata zuciyar shi tace kila itama bata sani ba. "Wata duniyar tunani ya lula yana ayyana irin rayuwar da zasuyi shi da amatu. Niko nace Allah ya nuna mana lokaci musha biki💃 Washe gari tunda safe ya shirya zuwa asibiti dan ana neman shi da gaggawa shiyasa bayan ya shirya part din ammie ya shiga ya gaisheta sannan ya shige motar sa ya tafi. Bayan ya isa neh ya tarar da wasu mutane guda biyar wanda sukayi accident a daren jiya" abun dai ba'a cewa komai dan sunji ciwo sosai amma babu wanda ya rasu. Cikin tausayawa Abdul yace ya fara fada meyasa baza'ayi treaating dinsu ba har sai yazo? Nan yaci gaba da fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Sai daya gama fadan neh yasa aka kaisu wani special room, nan ya fara basu agajin gaggawa shida wasu nurses din. Bayan sun gama neh suka fita suka basu wuri dan anyi musu allurar bacci. Wani dan dattijo ne ya shigo office din abdul da kukan shi da komai yana rokon Abdul akan Dan Allah ya taimake shi karya bari su mutu. Kallonshi Abdul yayi yace baba kayi hakuri insha Allah zasu samu sauki amma kai miye hadin ka dasu?? Cikin muryar kuka yace wallahi dukan su yarana neh sai dana ceh karsu dawo su bari a yau amma sukaki yanzu kaga kaddarar data riske su ko?? Lallashin shi Abdul ya shiga yi yana bashi baki akan yayi hakuri nan bada dadewa ba zasu warke. Wata takarda ya mika mashi wacce ke dauke da sunayen magunguna yace yaje siyo ya kawo. Karban takarda dattijon yayi ya fice yana sharar kwalla. Abdul zugum yayi sai yaji mutumin ya bashi tausayi ace duka yaranka sunyi hatsari aiko kana cikin tashin hankali da '''rudani''' dan ma Allah ya takaita babu wanda ya rasu. Mikewa yayi ya fara bin dakunan marasa lafiya yana duba su wasu kuma sallamar su yakeyi wasu kuma kawosu ma akeyi. Haka ya zauna nan asibitin har kusan karfe biyu na rana gashi yau yakeson ya kai amatu wurin ammie amma ga abunda ya gitto masa. Dakin marasa lafiyan nan ya koma yaga duk sun farfado kowa sai kallon dan uwanshi yakeyi. Sannu yayi musu ya juya zai fita sai dattijon ya dawo da kulolin abinci da kuma magungunan da aka rubuta mashi. Karba Abdul yayi yace ya basu abinci shi zaije ya rubuto yadda zasu sha maganin. Daga nan ya fita ya koma office dinshi, wata nurse ya kira yace ta kula dasu kafin ya dawo. Amsawa da toh nurse din tayi kafin ta fita. Shima tashi yayi ya fita yana sauri ya koma gida ya shirya dan har uku ta gota. Bude motar shi yayi zai shiga sai ga Abokin shi Usman shima likita neh acikin asibitin yake aiki. gaisawa sukayi Abdul ya fada mishi akwai wasu patients ya kula dasu kafin ya dawo. Motar shi ya shige ya bata wuta sai gida, da Isar sa kayan jikinshi ya cire ya shiga toilet ya watsa ruwa. Daya fito gaban dressing mirror ya isa ya shafa mai ya fece gashin kanshi dayake walkiya kamar anyi barin mai😀 Wardrobe ya bude ya fiddo wani hadadden yadi kalar navy blue da ratsin sky blue ya saka" ya saka bakin agogo da bakin takalmi sai hula mai kalar kayan abun gwanin sha'awa dan gaskiya ya hadu sosai. Fitowa yayi ya nupi part din ammie sai zuba kamshi yakeyi kamar wani sabon ango. Haka harya karaso part din ammie lokacin tana zaune a palour tana kallo. Tunda ta ganshi take sakar mishi murmushi dan tasan wannan wankan da wala kin. Zuwa yayi ya mata peck a goshi yace ammie ki shirya nan da 30 minutes zan dawo. Beko tsaya jin abunda zata fada ba ya fice da sauri. Wayar shi ya dauko yayi dialing number Amatu sai data kutsan katsewa kafin ta dauka, cikin muryar ta na shagwaba tace my Abdul dazu ina ta kira baka dauka ba duk hankalina ya tashi... Katseta yayi dacewa sorry baby kinji amma ki shirya gani nan zuwa yanzu. Ko amsawa batayi ba ya katse wayar, bayan minti goma sai gashi a farfajiyar gidan su. Ita kuma tana can sai kyalle kyalle take tayi har mummy sai datayi mata fada akan tayi sauri ta fito dan tana daga palour tana jin wayanta na ringing kuma data leka ta window taga Abdul neh. Fitowa tayi cikin wani dakakken leshi me tsada da daukar hankali kalar ruwan kwai da digo digon ja" sai tasa jan gele da handbag ja ta fito sosai kamar a toilet. Mummy sai kallonta takeyi tana sakar mata murmushi dan ba karya yar'ta ta hadu sosai. Sallama tayi wa mummy kafin ta fita" tsaye ta ganshi a jikin mota ya nade hannuwan shi a kirjin shi, fuskar nan tashi kamar gonar auduga dan gaskiya yana cike da farinciki. Kura mata ido yayi har sai data karaso gaban shi kafin ya farfado daga duniyar kallonta ya bude dayan side din yace ta shiga. Ba musu ta shiga shima ya zagaya ya shiga ya tayar suka fita. Kallonta yayi yace Baby wallahi kin hadu kinfi kowace mace kyau. Murmushi tayi tace my Abdul ai ka fini kyau so dubu. Hmmm baby banason zolaya fah Kinsan dai duk inda akaje kin fini kyau shiyasa nake addu'a Allah yasa yaran da zamu Haifa duk suyi kama dake. Dariya tayi ta rufe fuskanta da gyalenta wai ala dole taji kunya. Murmushi yayi bece komai ba har suka iso gida. '''cyprus''' Wani hadadden matashi neh fari dogo wanda dagani bazai wuce shekaru ashirin da bakwai zuwa da takwas ba " sanye yake da kana nan kaya bakin wando da farar Riga daga gabanta an rubuta I'm cool. Kayan shi yake shiryawa cikin trolley, da ganin yadda yake shirya kayan kasan ya matsu bebar wurin ba kenan. Bayan ya gama shiryawa ya dauki agogo fari kal yasa da bakin hula sannan ya jawo trolley dinshi ya fito. Bodyguards dinshi dake bakin kofa sukayi saurin ansar trolley din suka nupi mota inda dayan guard din ya bude mashi gidan baya ya shiga, direct airport suka nupa inda guards din basu bar wurin ba sai da sukaga tashin shi. Da misalin karfe biyar na yamma ya iso ainihin kasar shi ta haihuwa waton nigeria, saukowa yake daga matakalan jirgi amma sai ka rantse ba kasa yake takawa ba saboda yanayin tafiyar shi a nutse yake yinta cikin kwanciyar hankali harya sauko ya karaso wurin................. 👉🏿👉🏿👉🏿 [2/9, 5:30 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Page 23-24 Karasowa yayi wurin Abokin shi ya bashi hannu suka gaisa sannan shiga mota suka wuce" Abokin shi me suna kabeer yace guy dinnan kana hutawa fah, jika kamar wani balarabe. Tabe baki yayi yace kabeer banson iskanci fah, kai kullum baka da aikin daya wuce zolaya? Murmushi Kabeer yayi yace babu wani zolaya ai gaskiya na fada. Banza dan saurayin yayi mishi har suka iso gida. A daidai kofar shiga Palo Kabeer ya ajiye wa saurayin trolley dinshi dan yana sauri shiyasa be shiga ba. Kwankwasa kofar yayi kafin wata kyakkyawar yarinya ta bude mashi kofar, ihu murna tasa tana kiran sauran yan uwanta. Suma da hanzarin su sukazo suka rungume shi, daya daga cikin su me suna lubna wadda bata karaso ba cikin tsananin mamaki take kallonshi dan ita kallon gizo takeyi mishi shiyasa batayi gaggawar zuwa ta rungume shi ba. Sai da Yar uwarta samha tazo kusa da ita tace aunty bakiga yaya Abdul bane?? Sai a sannan ta sheqo da gudu ta rungume shi tana cewa yaya abdul Kaine kuwa naga ka kara girma da kyau. Murmushin dole ya kirkiro yayi mata danshi har yanzu haushinta yakeji " duk wani abu da zatayi danya burgeshi baya taba burgeshi sai dai ma ya bashi haushi. Ganin taki cika shi ne sai ya janye ta daga jikinshi ya karasa wurin ammie da yanzu ta iso wurin dan jin hayaniya, zuwa yayi ya rungumeta yana murmushi. Kallonshi tayi tace son meyasa baka fada mana yau zaka dawo ba? Dan sosa kanshi yayi yace mummy wallahi na matsu ban dawo bane kuma nayi missing dinki shiyasa nace bari inyi muku zuwan bazata. Dariya mummy tayi tace aikam kayi zuwan bazata saidai kuma dakin naka ba share yake ba amma ka shiga dakinsu Umar ka watsa ruwa kafin a gyara naka. Amsawa yayi da toh sannan ya shige wani daki dake cikin palon, lubna kuma taja trolley dinshi zuwa dakin. ********* Tunda suka shiga gidan amatu taki sakin jikinta kamar irin ma bata saba da ammie ba, Abdul kuma sai faman tsokanarta yake tayi shiyasa ammie ta koreshi. Hanan kuma yanzu ta shigo gidan dan bata nan kuma batasan da zuwan Amatu ba shiyasa tana ganinta taje ta rungume ta tana cewa aunty yaushe kikazo?? Sai Amatu tace ban dade da zuwa ba. Murmushi hanan tayi tace aunty baki ci abinci ba? Ko baiyi dadi bane? Waro idanunta amatu tayi tace laaaa rufa min asiri nidai bance ba. Bari ma kigani in fara ci karki cewa ammie naki ci saboda beyi dadi ba. Dariya maganarta tabata ta mike tsaye gami dacewa bari in shiga ciki in dawo, amsawa da toh amatu tayi kafin ta fara cin abincin. Tana cikin ci sai ga Abdul ya shigo, tunda yaga an jere mata abinci yaji yanason," zuwa yayi ya zauna yasa hannu wai suci tare. Ita kuma kunya takeji kar ammie tazo taga suna cin abinci tare tace har rashin kunyar tasu takai suci abinci tare a gidanta kuma ma ba'a koyi auren ba? Nima dai nace wayaga zumudi😋 Mikewa tayi zata zauna saman kujera ya wani daure fuska yace karki kuskura ki zauna kuma kisa hannu muci. Zaro ido Amatu tayi cikin magiya tace plsss my Abdul ka rufa mun asiri yanzu kanason ammie tazo ta ganmu a haka? Eh mana to miye a ciki? Yatsine fuska tayi kamar wadda taga abun kyama tace nikam bazan iya ba nama koshi. Bata rai yayi ya mike zai wuce ita kuma da tsokana sai ta jawo pillow ta wullah mashi. Aikuwa cikin rashin sani ya fadi timmmmm a kasa. Cikin firgici tayo kanshi dan bata zaton zai iya faduwa ba shiko da gangan ya wani kara lafewa a kasa harda wani kukan karya yana kiran sunan ammie kasa kasa. A hankali ta furta mishi a daidai kunnenshi tace sorry my Abdul plsss ka tashi kaji? Cikin ranta sai faman dariya takeyi amma a zahiri sannu takeyi mashi harya mike tsaye. Daukan pillon tayi zata mayar gunda yake sai yayi saurin fisgewa yace ai kuwa baki isa ba dan sai na rama. Marairaicewa tayi tana bashi hakuri amma ina sai daya jefeta amma bai sameta ba dan kaucewa tayi sai pillon ya fada cikin plate din abincin da takeci. Salati kawai ta farayi tana kallonshi da shi dinma ita yake kallo tace Abdul kaga abunda kayi ko? "Allah babu ruwana idan ammie ta gani. Cire pillon tayi daga cikin abincin ta dora mishi a hannu sannan ta koma mazaunin ta ta zauna. Abdul kuma tsaye yayi yana kallonta. " jin kamar motsin ammie sai yayi sauri ya fice waje da pillon. Ammie kuma karasowa wurin amatu tayi tace amatu har yanzu dai banga kinci abinci da yawa ba kodai ta bakin hanan baiyi miki dadi ba. Saurin girgiza kanta tayi tace a'a wallahi ammie yayi dadi sosai kawai dai naci abinci neh kafin in fito. Murmushi ammie tayi ta fara kwashe plate din zata kai kitchen sai Amatu ma ta dauka zata tayata, aikuwa ammie ta hanata tace tayi zamaninta. Haka ko ta zauna badan ranta yaso ba. Abdul kuma part dinshi ya nupa ya wanke inda pillon ya baci sannan ya aza saman gadonshi dan ya bushe kafin zuwa anjima. Fitowa yayi ya dawo part din ammie inda ya tarar da bakowa palon. Haurawa sama yayi zuwa dakin ammie, "nan ya tarar dasu ammie tace ya koma gasu nan fitowa. Murmushi kawai yayi ya koma palour yana jiransu. Kusan minti goma sai gasu nan sun sauko harda hanan. Tasowa yayi ya ansa ledar dake hannun amatu yace bari in rike maki karki wahala" kunya taji ta wani sunna da kanta kasa hanan kuma murmushi tayi ganin yadda yayanta ke tarairayar mace. Har wajan mota sukayi mata rakiya daga bisani sukayi sallama suka wuce. Bangaren Abdul kuma wanka yayi ya shirya tsaf cikin yan kanti, fitowa palour yayi inda ya tarar an jera mashi abinci saman dinning. Zama yayi ya fara ci lubna kuma sai zuba mashi surutu takeyi shiko in bada eh da a'a su kadai neh abunda yake fada. Bayan ya gama cin abincin ko kallonta beyi ba ya tashi ya fita. Wurin Abokin shi Kabeer ya tafi, " be dawo gida ba sai wuraren tara na dare. Kodaya dawo har an gyara part dinshi dan haka can ya shiga, zama yayi gefen gadon shi yana ayyana yadda zasu kwashe da ita "wata zuciyar na cewa idan tayi aure kuma fah??tsuki yaja ya kawar da tunani ya tunanin yadda zai shawo kanta da ba abu mai sauki bane yayi tafiya tsawon shekaru biyu basu hadu ba Daga karshe dai ya yanke shawarar zuwa wurinta gobe dan yasan Amatullah da hakuri tunda tana tana matukar sonshi zata fahimce shi. '''waye abdul''' Asalin sunan shi............ 👉🏿👉🏿👉🏿 [2/10, 10:07 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Page 25_26 Asalin sunan shi "ABDULRAHMAN "da neh ga Alhaji Aliyu. Abdul yaro ne mai hankali da nutsuwa ga ilimin addini dana boko, tun yana karami yake sha'awar zama malamin makaranta shiyasa bayan ya girma yaci gaba da jajircewa akan sai ya cika burin shi. cikin ikon Allah ya samu abunda yakeso, dan yanxu haka ya gama degree dinsa a ABU Zaria inda ya karanci education computer daga bisani ya wuce Cyprus dan yayi masters kuma alhamdulillah yanzu ya kammala ya zama cikakken lecturer Abdul su uku neh a wurin iyayenshi, Abdul shine babba sai umar sai kuma autar su samha, lubna kuma Yar uwarsu ce tana mugun son abdul shiyasa ta dawo gidansu da zama Abdul kuma baya sonta ko sau daya be taba jin sonta ya darsu a ranshi ba, hasali ma ya tsane ta. Dan duk wani sakin fuska da take gani a wurin shi taci albarkacin mummy neh dan ita ke tsawartar masa saboda ta lura da yadda yake mata wulakanci" ita kuma ba abun ta tursasa masa sai ya sota dole ba. Cigaban labari Tsaye yake a bakin wardrobe dinshi yana duba irin kayan da zai saka, can ya hango wani yadi me shegen kyau kalar ruwan kasa. Daukowa yayi ya aje saman gadon shi. Murmushi yayi na jindadin tunowa da yayi Amatu tafi son ya sanya manyan kaya, rufe wardrobe din yayi ya dawo gefen gadon ya fara sanya tufafin. Sai daya gama shiryawa tsaf kafin ya dauki wayan shi da makullin motar shi ya fice daga dakin. Beko leka part din mummy ba yasa kai ya fice daga gidan. Direct gidansu amatu ya nupa, a hanya sai addu'a yake Allah yasa ta fahimce shi "harya iso daidai gate din gidansu addu'a yakeyi dan shima yasan be kyauta ba. Horn yayi a bakin kofar sai ga megadi ya fito dan ba kowa yake budewa gate kai tsaye ba. Tun kafin ya karaso Abdul ya sauke glashin motar shi. Hannu Abdul ya bashi suka gaisa shi kuma megadi sai wani wangale baki yakeyi duk a tunanin shi waccen Abdul dinne dan suna matukar kama da juna sosai. Abdul kuma ganin yadda megadin ya sakar mishi fuska bai kawo komai a ranshi ba, sai ma cewa yayi ya kira mashi Amatu. Dan murmushi megadi yayi yace yallabai ai hajiya yanxu ta fita amma gaskiya bansan inda taje ba. Haushi kamar ya kashe Abdul dan baiyi tunanin baza'a sameta a gida ba. Kallon megadi yayi ya zaro dubu biyu daga aljihun shi ya mika mashi. Godiya megadi ya shiga yi kafin ya tada mota yabar wajan. Bangaren Amatu kuwa yanzu ta iso shago dan kuwa yau ita kadai ta fita ameerah na gida wai bata da lafiya. Tun shekaran jiya aunty hajara ta fara ganin sauyi atattare da ita amma tayi tayi ta fada mata abunda ke damunta fur taki. Koda Amatu tazo gidan haka itama tayi ta tambayar ta tana lallaminta amma haka tayi burus taki fada mata. Ita kuwa ameerah tun lokacin da taga Abdul taji ya shiga ranta, tun tana ganin abun kamar wasa har ta fara gazgata kanta da cewa tanason Abdul. Danne abun tayi a ranta dan tasan yadda kawarta ke mutuwar son Abdul kuma abun kunya ne a gareta ace duk yadda suke ta furta Kalmar so ga wanda Yar uwarta keso. Abun haushi ma shine beko san tanayi ba shiyasa ta fara tunanin yadda zata cire shi acikin ranta ta karfi da yaji. Amatu kuma kawai dai taje shagon ne amma babu wani karfi a tattare da ita saboda yanayin yadda taga ameerah shiyasa taji jikinta ya mutu, yanxu haka ma wata takeson ta karasawa gyaran kai ta koma gida dan hankalinta yaki kwanciya. Abdul kuma tafiya yake yana yan sake sake dan yarasa abunda ke mashi dadi, Amatu kuma fitowar ta kenan daga shago ita da wata ma'aikaciyar shagon ta zata sauke ta saman hanya sai ta hango kamar Abdul ta cikin glass din motar ta. Sauke glass din motar tayi ta kare mashi kallo, daga dai fa Abdul dinta neh. Murmushi tayi ta budewa titi mota ta fita sannan ta juyo ta gefen data hango shi amma wayam babu ko alamar motar shi. Tsuki tayi taja motarta ta wuce, direct gidansu ameerah ta nupa, inda ta tarar da Aunty hajara a kitchen tana girki. Gaisawa sukayi kafin ta wuce dakin ameerah. Kwance ta tarar da ameerah kamar wata mara lafiya" da gudu Amatu ta karasa wurin ta gami da zama ta gefen ta tana kallonta har kwalla sun cika mata ido ganin ameerah na kuka ga jikinta yayi zafi sosai kamar garwashi. Hannunta tasa tana share mata hawayen da suka gangaro mata tace ameerah plsss na rokeki ki taimaka ki daina wannan kukan kuma ki dubi girman Allah ki fadamun abunda ke damunki. Rass rass taji gabanta ya fadi da jin irin yadda amatu ke hadata da Allah akan abunda ita karan kanta bazata so wani yaji ba ballantana ita Amatu. Share hawayenta tayi tasa hannuwan Amatu a cikin nata ta rike su gam tace my Amatu ki kwantar da hankalinki, duk wani abu da zai rusa maki farinciki bana fatan ya sameki kuma ki sani abunda ke damuna bazan taba bari ya hanaki sukuni ba shiyasa zan fada maki. Amatu saurayina aure zeyi nan bada dadewa ba kuma ni kinga gidan mu basu tashi yimun aure ba shiyasa na shiga damuwa dan nasan na rasa shi kenan kuma amatu zeyi wuya in samu kamar shi, " ta karasa maganar ne a yayin da hawaye ke kwaranya a idanunta. Share mata hawayen Amatu ta shiga yi tana lallashinta, dakyar ameerah tayi shuru dan kuwa tasan ta rasa Abdul ne da gaske. Haka Amatu tayi ta lallashinta inda daga karshe harta dan sake suna hira, da aunty hajara taga ameerah taji dadin yadda Amatu ta lallasheta amma tayi tambayar Amatu ta fada mata sai taki tace wai wannan sirri neh a tsakanin su Haka dai sukayi ta hira har zuwa magariba kafin Amatu ta wuce gida, a farfajiyar gidansu tayi parking din motar ta sannan ta fito, megadi ne ya karaso wurinta bayan sun gaisa yake shaida mata ai Abdul yazo har sau biyu bata nan, Dan waro idanunta tayi tace laaa yaushe kuma be kirani a waya ba?? Karasawa ciki tayi ta dauko wayarta sai a sannan taga wayar ta a kashe. Mummy ceh ta shigo dakinta tace Amatu ina kika sa wayanki ne dazu nayi ta kiran wayarki a kashe? Marairaice fuska tayi tace mummy nima bansan wayan a kashe take ba sai yanxu kuma wai Abdul yazo gidan nan?? Eh yazo har cikin palour yazo ya gaida ni, dan murmushi kawai tayi ta cire hijab dinta ta shige toilet, mummy kuma fita tayi daga dakin. Tana fitowa tayi sallar magariba, tana nan zaune har akayi isha'i, tana gama tasbihi ta linke sallayar ta maida ita ma'aji yinta sannan ta haye saman gado. Kunna wayarta tayi ta fara dialing number Abdul amma kusan kira biyar tayi mishi be dauka ba. Daman kamar ta sani dan ya hanata kashe waya kuma gashi yazo gidansu har sau biyu aikuwa yau ta shiga uku. Wayar ta dauko zata sake dialing sai gashi ya kira, cikin dan marairaicewa ta amsa kamar wadda zatayi kuka ta fara bashi hakuri tana kashe mashi jiki da kalamai masu dadi saboda karya farayi mata fada. Ba karamin tasiri kalaman sukayi a kanshi ba dan yama bar batun kashe wayarta datayi suka fara hira, suna cikin hirar take fada mashi ai dazu ta ganshi kuma taso tayi mashi magana sai kuma ya wuce. Murmushi yayi yace my baby ina kuma kika ganni haka?? My Abdul kusa da round about din shigowa shagon mu na ganka" shafo fuskar shi yayi yace ohh namanta, naje siyawa ammie fruits neh lokacin. Shagwaba ta farayi mashi tana wani narke murya tana suburbudo mashi kalaman soyayya. Shi kuma jiyake ina ma ace tare suke" haka sukayi ta hira suna fayyace wa junan su sirrin zuciyar su *********** Tsaye yake a daki sai kai kawo yake tayi kwata kwata ya kasa samun nutsuwa, gashi ya canza layi bale ya samu number ta. Laptop dinshi ya jawo yana dan wasu bincike daga karshe yayi addu'a ya kwanta amma sam ya kasa bacci sai tunaninta yakeyi. '''washe gari''' Abdul ne a asibiti acikin dakin marasa lafiyan da aka kawo kwana biyu da suka wuce. Su biyar neh, yammata guda biyu da maza uku sai baban su a gefe suna hira da Abdul dan har sun saba dan kwana biyun nan da sukayi. Wani namiji daga cikin su wanda duk sun fishi samun rauni da yawa yace yaya wai yaushe zaka kawo mana amatullahi din ne mu ganta naga kullum in muna hira sai kayi mana maganar ta. Murmushi Abdul yayi yace karka damu ai zaku ganta da zarar na sallameku har gida zan kawo muku ita. "Cikin zumudi fiddausi (kanwar shi) tace Allah yaya da gaske? Girgiza mata kai yayi alamar eh. Baba kuma sai kallon su yake yana jindadin yadda Abdul ya saki jiki dasu kamar wani dan uwansu na jini. Bangaren Abdul kuma kamar yadda yaci kwalliya jiya yazo gidansu Amatu haka yauma "amma wannan karon a farfajiyar gidansu ya paka motar shi dan kuwa megadi ya bude mashi gate. Tsaye yake ya jingina da motar shi ya nade hannuwan shi a kirjin shi yana kallon daidai saitin kofar da zata fito dan kuwa ya aika megadi yayi mashi sallama da ita..... ................ Plsss comments And share [2/11, 5:46 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Page 27-28 Fitowar ta kenan ta hangi motarshi ta wuce sakamakon kiran gaggawa da daddyn shi yayi mishi shiyasa ya wuce zuwa anjima ya dawo. Itako wayarta ta dauko tasa kiran Abdul taji ko lafiya ya wuce " sai kuma akayi rashin sa'a bai dauki kiran ba dan yana can asibiti a dakin tiyata. Abdulrahman direct office din daddyn shi ya nupa inda ya mika mashi wasu takardu na samun gurbin zama lecturer anan BASE UNIVERSITY dake cikin garin abuja. Karbar takardar yayi ya zauna daya daga cikin kujerun da'aka tanadar wa baki" kafin yasa hannu acikin takardar sannan ya mikawa daddy yana mai gode mashi kafin ya bar office din. Abdulraheem kuma sai yanxu ya fito daga dakin tiyata inda ya tarara da missed call din amatu kusan guda goma harda kuma sakonni dan ita a tunanin ko yagaji da jiranta ne yayi tafiyar sa shiyasa tayi ta kiransa harda tura masa sakon yayi hakuri. Kayan tiyata ya cire kafin ya bude dan karamin fridge din dake office din ya kwankwadi ruwa. Sai dayaji baya jin kishi sannan ya ajiye ragowar ruwan saman teburin shi ya zauna. Ammie ya fara kira dan itama tayi mashi kira biyu. Bayan ya kirata ne sai ya kira Amatu,"cikin yanayi na mamaki yace Amatu lafiya kuwa naga missed call dinki har goma ga kuma wani sakon hakuri duk na menene??? Shuru tayi kamar me tunani dan ta kasa fahimtar sa" toh miye yake nupi da hakan?? Katseta yayi da cewa baby ki daina damuwar kanki mana nasan dai akan jiya kin kashe wayarki ne kuma ai wannan ya wuce. My Abdul ba... Yace no stop it koma me kikayi mun na yafe saboda nasan bazaki bata mun rai da gangan ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace nagode my Abdul Allah yabar mu tare. Amsawa yayi da ameen daga bisani yayi mata sallama akan yana aiki zuwa anjima idan ya fito daga asibiti zai zo gidan su. Yana gama waya da ita ya tashi ya nupi dakin su fiddausi, baba ya tarar yana hada kayan su dan an basu katin sallama. Da fara'a a fuskar baba yace dana harka shigo kenan?? Eh baba ai tun dazu naso in shigo sai aka kawo wata mara lafiya yanxu haka tana dakin tiyata. Tagumi baba yayi yace Allah sarki kudai kuna ganin abubuwa iri iri "Allah ya saka muku da alkhairi akan taimakon jama'a da kukeyi, amsawa yayi da ameen kafin baba yace kaga waccen yarinyar burina ta zama likita amma rashin jinta ya hanata zama tayi karatu" baba ya fadi maganar yana nuna fiddausi da dan yatsar shi. Murmushi kawai Abdul yayi yana kallon fiddausi data wani tamke fuska jin baba yace bata jin magana. Sauran yan uwanta ko sai dariya suke mata. Baba na gama shiryawa suka fito zasu wuce, daya daga cikin su wanda ke dingishi kadan yace baba wai yanxu ina zamuje?? Ina fatan dai ba gidan mahaukaciyar matan nan zamu koma ba?? Wani irin kallo da baba ya gefeshi dashi neh yasa yin shuru be kara magana ba har suka iso inda baba ya paka yar 406 dinshi. Abdulraheem kuma yana biye dasu sai dai hankalin shi bekai kan maganar da sukeyi ba. Sallama yayi musu harda karban number baba yayi saboda sun rika gaisawa. Bayan sun wuce ne Abdulraheem ya koma office ya fara hada yan tarkacen shi dan dama baya dutyn dare sedai in wani abun gaggawa ya samu neh yake zuwa amma shi a asibiti baya wuce six yake dawowa gida sai kuma da safe. Yana gamawa yayi sallama da abokan aikin shi ya wuce gida " kodaya koma gida a gajiye yake shiyasa ya kira Amatu yace tayi hakuri bazai samu zuwa ba sai gobe. Ita kuwa bata damu ba saboda tasan yanayin aikin likita ako wani lokaci aiki kan iya gitto musu. Basu dade suna waya ba ya katse kiran sannan ya shiga bandaki ya watsa ruwa. Bayan ya fito ya sanya wasu kananan kaya masu kyau sannan ya nupi part din ammie. Palour ya sameta ita da hanan suna cin abinci, gaishe da ammie yayi sannan shima ya samu wuri ya zauna yasa hannu suna cin abincin tare kuma suna dan taba hira. '''Bayan sati biyu''' Abdulraheem neh tare da auntyn shi wato kanwar mahaifiyar shi maryam, suna tattaunawa neh akan bikin shi dan yanxu saura wata daya da sati biyu ayi bikinsu. Maryam kasuwanci takeyi inda take dauko kaya tsadaddi daga dubai" kama daga less, atampa, shadda, takalma da dai sauran su. Shine ammie ta kirata suna son ta hado musu kayan lefe masu kyau da tsada yadda duk wanda ya gani sai ya burge shi. Abdulraheem dake kusa da maryam yana fadar kalar kayakin da amatu tafi sawa da kuma kalolin su tace kai malam ya isa haka mana " ta fada a dan tsawace. Murmushi yayi yace haba aunty nifa sonake in bata mamaki" bakiga gidan da za'a kaita bama penti kalar da tafi so nasa akayi mata ba?? Hararan shi maryam tayi tace tau naji nidai yanxu ma wucewa zanyi dan ina ganin gobe ma zan wuce, duk wani abu daka tuna kayi mun waya kaji ko?? Amsawa yayi da toh sannan ya tashi ya basu wuri. Bayan ya fita ne ammie ta kalli kanwar tata tace maryam ki fita harkar yaron nan nidai duk wani kaya da kikasani na kece raini ki siyo sannan kuma akwatuna ki turo hotunan su a waya sai na zaba mashi, kinaji na ko?? Eh aunty. Haka sukaci gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da mijin maryam yazo daukarta suka wuce. A bangaren Abdulrahman kuma ji yake kamar zuciyar shi zata fashe, gabadaya kwana biyun nan duk ya shiga damuwa saboda rashin ganinta. Kusan kullum sai yaje gidansu sai ya tarar da bata nan, wani sa'in kuma sai ya kama hanyar zuwa gidansu wani uzuri ya gitto mashi. Ga kuma wannan jarababbiyar yarinyar data like mashi kamar cingum. Ita kota ganshi cikin damuwa bata iya tabuka komai sedai ma ta nemi kara bata mashi rai. Yauma zaune yake a gaban mirror sai kace wata mace, yana shiryawa da niyar zuwa gidansu Amatu dan yau ya kudurta wa ranshi duk yadda za'ayi sai ya ganta dan kuwa cewa yayi koda yaje gidansu bata nan zama zeyi har sai ta dawo tunda ta zama me kafar kaza. Niko nace a wurinka dai ta zama mai kafar agwagwa, dan rainin sense kawai😏😏 Lubna ce ta shigo dakin da fara'a a fuskarta, kusan minti biyar ta kwashe tana kallonshi dan ba karamin kyau ya mata ba, shi kuma gogan ko ajikin shi dan ya saba da halinta. Wani lokaci haka kawai sai tazo dakinshi tayi tsaye kamar wata gunki tana murmushi tana kallon shi yana kai kawo shi kadai. Kuma ko kala baya ce mata sai dai ta gaji ta wuce ko kuma shi yabar mata dakin. Yanxu ko zuwa tayi zata zauna bakin gadonshi ya daka mata tsawa sai data razana. Cikin huce takaici yace wai ke wace kalar yarinya ce?? Sau nawa zance karki kuskura ki kara taba wani abu daya shafeni??? Iyee dake nake. Shuru tayi batace komai ba dan tasaba da irin wannan wulakancin. Tsuki kawai yaja yadau key din motar shi zai bace ya fice ya barta a wurin. Ita kuma kuka tasa ta daura hannuwa saman kai 🙆 ta rasa ko wace irin narkakkiyar zuciya gareta ko tayi kokarin ta cire shi a ranta sai taji bazata iya ba. Kuka tayi sosai kafin ta shiga toilet dinshi ta wanke fuskar ta ta fito. Abdulraheem kuma yana wani mall yana ma Amatu shopping, kayan kwalama kawai ya siya mata kafin ya biya kudi ya fito. Wani Abokin shi ya gani a daidai shiga malla din, nan suka tsaya suka gaisa daga bisani kuma ya shige motarsa ya bata wuta Amatu kuma tana can gida tana hadawa Abdul dinta delious, bayan ta gama ne tayi wanka tayi kwalliya tasa wata doguwar riga mekyau kafin ta fito palour. Zama tayi saman kujera tana jiran isowar Abdul, aikuwa bada dadewa ba sai gashi ya kirata, yace ta fito kuma dai dai lokacin megadi yazo kiranta. Murmushi Amatu tayi dan taga Abdul ya kirata kuma abun ma be isa ba sai daya aiko megadi. Mayafinta ta dauko kafin ta fito sannan ta sanarwa mummy Abdul yazo. Gyara gyalenta tayi da murmushi a fuskarta ta nupi hanyar fita waje................................. Nan birona ya fadi saboda bansan yadda haduwar tasu zata kasance ba🤷🏻‍♀ Plsss share [2/12, 1:27 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Ina matukar jin dadin comments dinku, kamar yadda kuke bibiyar book dinnan haka nima nake bibiyar ku a cikin raina. I love u all gabadaya ❤      Page 29-30 Tun kafin ta karasa ta hangeshi jingine da motarsa, sai wani murmushi yake faman zuba mata, itama haka dan kuwa duk tunanin ta Abdulraheem neh. A hankali ta fara tafiya harta karaso kusa dashi. Ko kala bata ce mashi tayi mashi nuni da hannunta akan ya biyota. Shi kuwa sai mamakin yadda ta tarbeshi yakeyi dan kuwa beyi tsammanin zaiga koda murmushin ta ba balle har takai ga bashi masauki. Tana gaba yana biye da ita a baya har suka iso palon baki. Kujera ta nuna mashi ya zauna kafin ta fita, "bata jima ba ta dawo dauke da katon paranti a hannunta. Gabanshi takai ta ajiye sannan ta dauki ruwa ta zuba mashi a kofi ta mika mashi, kamar mazari haka ya karba da sauri ya fara shan ruwan, sai daya shanye ruwan tas ya ajiye kofi. Wani farinciki ne mara misaltuwa ya dabaibaye shi, daya bangaren zuciyar shi kuwa tausayinta yakeji yadda ko kala bata ce mashi ba saima sakin fuska daya gani daga gareta" hakan kuwa sai yasa yaji jikinshi yayi sanyi gashi yanason yayi mata bayani amma kuma ya gaza yana tsoron karya bata mata rai tunda yaga alamar tana cikin farinciki. Kawar da tunanin yayi ya mayar da kallonshi zuwa gareta yace my Amatu kina burgeni saboda ke mace dayace tamkar dubu,  kina da hankali da tarbiya ga kuma tunani, na bata maki rai a wasu yan lokuta da suka wuce, na sakaki a damuwa sai gashi ke daga karshe kin sanya ni a inuwar ki. My Amatu duk abunda zanyi maki bazai iya goge laifin dana aikata maki ba, amma kisani ni Abdul na dauki alkawarin yi maki duk wani abu da kike bukata a rayuwa kuma insha Allah zan kasance mai faranta maki har abada. Lumshe idanunta tayi ta kuma budesu ta dora akan nasa tace my Abdul plsss abunda ya wuce ya wuce mudai kawai mu roki Allah ya shige mana gaba duk wata maganar laifi kuma be taso ba" rayuwar mu kawai zamu fuskanta. Duk fa a tunanin ta saceta da Abdul yayi neh yake kara bata hakuri fah dan daman wani sa'in idan suna hira sai ya dinga bata hakuri yana cewa kaddara ce tasa ya satota, toh shine fah take cewa ya wuce. Amatu sai wani jindadi take gata ga Abdul dinta shima hakan ce ta kasance a wurin shi shiyasa yake ta wani kodata yana kashe mata jiki da kalamai masu dadi. Abdulraheem bawon Allah yana can asibiti an kirashi, yarinyar da akayi wa tiyata ta rasu shine ya koma asibitin da gaggawa. Kuma harya iso gidansu Amatu aka kirashi amma dake yana da son taimako da tausayi da kuma kula da aikin shi sai ya juya ya koma asibitin. Yanxu haka yana cikin asibiti tare da yan uwan yarinyar data rasu ana aunata kafin su bayar da ita. Su Amatu kam ana can ana soyewa da Abdulrahman "yanxu haka a tsaye suke bakin motar shi wanda sunyi kusan minti talatin a hakan kuma wai sallama zasuyi ya wuce amma shine sukaci gaba da soyewar su. Suna nan tsaye sai ga ameerah ta shigo, tunda taga Abdul ta fara danasanin shigowarta gidan, dan a cewarta datasan yana nan da bata shigo ba. Kuma ba abun ta koma ba tunda har sun ganta. Karasowa tayi ta gaida Abdul kafin ta wuce ciki, Amatu kuwa sai cewa take ta jirata amma ko kallonta batayi ba ta shige cikin gida kamar ta fasa ihu dan jin yadda zuciyar ta ke mata zafi. Basu dade ba yayi mata sallama ya wuce. Cikin gida ta dawo inda ta tarar da ameerah a dakinta, ameerah kuma duk damuwa ne fal ranta amma da jin shigowar Amatu sai ta kawar da duk wata damuwa dake fuskarta. Murmushi Amatu tayi ta hauro saman gadon tana kallon ameerah tace nace ki jirani shine kika wani wuce ko?? Hararan wasa ameerah ta aika mata tace toh sai in tsaya kuna soyewa a gabana kome?? Dariya amatu tayi ganin yadda ameerah ta bata rai kamar masu fada, " nan kuwa batasan duk zafin kishi bane. Kawar da hiran ameerah tayi suka shiga hirar abubuwan da za'ayi na bikin Amatu wanda duk ameerah ce ke fadin abunda za'ayi da kuma yadda za'ayi. Bayan sallar isha'i Abdulraheem neh ya kira amatu yana bata hakuri akan rashin zuwan shi, dake dazu Abdulrahman yace ze dawo ya kawo mata wani abu sai kawae tace ya daina bata hakuri ai sun zama daya itama ai watarana tana iya bata mashi laifi. Murmushi yayi yace baby na kenan ni wallahi na matsu ba'ayi auren nan ba nasan idan muna zaune a Inuwa daya komin daren dadewata a aiki kullum sai munga juna. Um um tace, shiko yace miye um um badai dan na ambaci aure ba zakice kunyata kikeji??  Saurin girgiza kai tayi kamar tana kallonshi tace nidai bance haka ba. Dariya yayi yace wallahi baby ji nake kamar a daura mana aure gobe. Laaaaa hmmm nidai banaso ta fada cikin tsokana, shi kuma har yaji babu dadi yace waton daman ni kadai ke kidina ko??  Sai tace a'a my Abdul ai nima ina so kawai dai bana zumudi ne saboda kar mutane suce wannan amayar da hazonta take. Dariya takeyi shi kuma ya bata rai yace waton ni ango ni nafi kowa zumudi ko?? Cikin dariya tace eh mana gashi sai wani murna kake kana jin kamar ma ace a kawo maka ni gobe! Kyacci yayi mata yace zaki gane kurenki neh dake da bakin ki me iya zaro zance idan kin shigo hannu. Shuru tayi masa dan tasan inda maganar tasa ta dosa yanzu tana biye masa zai fara wuce gona da iri shiyasa ma ta dauko wani labarin. ************ A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, yau saura sati daya bikin Amatu, gidansu harya fara cika da mutane sai shirye shirye ake tayi. Haka ma bangaren Abdulraheem suma suna can suna nasu shirye shiryen dan jiya suka kai lefe akwati saiti biyu da dubu dari. Masu kaiwa ma ba'a barsu a baya ba dan tukuicin dubu dari biyu aka basu bancin kuma gagarumin tarbar da sukayi musu dan abinci kala biyar sukayi kuma ko wanne da irin hade haden da akayi mashi. Abdulraheem harya buga invitation card ya aikawa Amatu danta rabawa kawayenta shima a nashi bangaren duk abokan shi sun sani "lokaci kawai suke jira. ********** Abdulrahman tun lokacin daya zo gidansu Amatu washe gari ya wuce Cyprus saboda wasu yan uxura, a lokacin da daddy ke fada mishi maganar tafiyan ba karamin tashin hankali ya shiga ba. Kuma wani abun haushi shine tun washe gari daddy yakai shi airport da kanshi, duk ranshi bace dan beso tafiyar ba amma haka ya wuce, Kwanan shi uku yaji bazai iya zama ba sai ya dawo gida, kwatsam sai ga daddy yazo Cyprus din, harda dan karamin zazzabi yayi saboda damuwa da tunanin ta kuma gashi shiba number ta balle ya kirata. Haka yayi hakuri har kusan wata daya, sai yau da Allah ya kaddari zai dawo. Duk wani abu me mahimmanci ko kuma wanda zai iya sashi ya dawo Cyprus sai daya dauko shi dan ya dau alwashin shi daya dawo Cyprus sai kuma wani ikon Allah dan a karamin tunanin shi duk wannan zuwa Cyprus dinne ya janyo mashi da yanxu kila ma anyi auren su. Toh masu karatu a nashi ganin fah 😁 Da saukar shi gida ko wani hutawa bai tsaya yi ba ya fice daga gidan baki daya, Direct gidansu Amatu ya nupa, kodaya je a bakin gate ya paka motar shi, yana shirin fitowa sai ga megadi ya fito. Cikin girmamawa megadi ya fara gaishe shi, gogan kuma dake ba gaisuwar ce a gabanshi ba ko amsawa beyi ba yace Amatullahi na gida kuwa??? Dan murmushi megadi yayi yace eh yallabai tana ciki sedai kuma hajiya tace kar a bari ta fita kuma duk wanda yazo nemanta ace bata na Cikin damuwa ya fara tunanin dalilin da zaisa ayi  mata irin wannan dokan sai can yaji megadi na cewa toh yallabai ka kirata a waya mana? Shuru yayi  Kamar mai tunani sai can yace a'a ai na kira wayanta a kashe shiyasa ma nazo gidan. Kallonshi megadi yayi yace toh toh yallabai kasan harkar mata in suna biki sai a hankali, ko nima da nake nan duk hayaniyar su ta isheni amma ba abun ayi magana ba dansu farinciki suke sosai dan zasu aurar da yar su kwalli daya tak wadda sukeji da ita kamar gwal ai abunda yafi hayaniya ma suna iya y.................................. Plsss share [2/12, 4:38 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''      Page 31-32 What??? Me kake fada haka? Kana cikin hankalinka kuwa?? Shuru megadi yayi yana kallonshi saboda tsananin mamaki,"shidai yasan babu wani wanda ke zuwa wurin Amatu in bashi ba kuma yasan cewa dashi za'ayi auren to miye kuma na damuwa?? Abdulrahman dake wani irin huci sai kace zakin daya ga nama, ya matso gaf da megadi rai bace yace wallahi ka kuskura ka kara ambaton Amatu gami da danganata da wani bani bai sai nayi maganinka! Banza kawai. Megadi ko sai hakuri yake bashi dan yaga kamar kishi ne ke dawainiya dashi shiyasa bai fahimci inda maganar tasa ta dosa ba. Wasu yammata neh guda biyu suka fito daga cikin wata mota zasu shiga gidan, sai nacikin motar, waton wanda ya kawosu ya leko kanshi ta window dan har sun kusan kai gate din shiga gidan yace ku gaida mun da amarya sai nazo ganinta. Murmushi sukayi dukansu kafin suka isa cikin gidan, Abdulrahman kuma yana tsaye kamar wani gunki yana kallon su. Karan wayar shine ya dawo dashi cikin hayyacin shi, yana ganin mummy ce ke kiran shi yayi saurin dagawa. Ko minti biyu basuyi ba ya katse wayar. Kallon megadi yayi yace wai bikin wa akeyi dan ni ban fahimta ba, washe baki megadi yayi "yace yallabai auren Amatullahi akeyi..........tas tas kakeji har sau biyu ya mare shi, dafe kumatu megadi yayi idanunwa duk sun zurmo waje ya fara ba Abdulrahman hakuri sai Abdul ya katse shi, zai yi magana kenan sai ga kiran mummy ya shigo, Amsawa yayi yace toh sai ya shige motar shi ya bata wuta kamar me shirin tashi sama hake yake ta faman tsala gudu  baji ba gani, duk ya burkice ga kuma mummy dake faman kiransa a waya. Garin ya dauki wayar ne motar ta kufce masa saura kadan ya bugi wata motar sai Allah ya takaita be bugeta ba dan me motar ya kauce. Fitowa yayi da sauri yana bawa mai motar hakuri amma mai motar sai faman zaginshi yakeyi yana mishi Allah ya isa. Tsuki kawai yaja ya shige motarsa dan a halin da yake ciki hankalin shi ba a jikinsa yake ba. Dakyar ya samu ya dawo gida dan a hanya sai kaucewa yake saman titi saboda irin gudun da yake tsalawa. Kodaya dawo gida ko rufe motar be samu damar yi ba, part dinshi ya nupa, yana shiga ya fada saman gado yana kurma ihu sai kace wani karamin yaro. Mikewa tsaye yayi ya nupi inda mirror yana kallon fuskar shi data kumbura ta koma ja saboda bacin rai ga jijiyoyin kanshi duk sun fito rado rado, tuno abunda megadin gidansu Amatu ya fada mishi yayi, aikuwa nan hauka ta tashi dan sambatu ya farayi gami da watsi da duk wani kaya dake saman mirron yana cewa wallahi baka isa ba, bazan taba bari ka auri farinciki na ba Kai waye wallahi sai naga bayan ka Yana magana yana huci kamar wani zaki Haka yayi ta surutai har na tsawon wani lokaci sai kuma naji ko'ina yayi dif Karasawa nayi daidai wurin da yake naganshi kwance a kasa bakin shi cike da bakin jini. Lubna da taga lokacin da Abdulrahman ya shigo taso ta biyoshi sai kuma tana tsoron wulakancin da zaiyi mata sai ta fasa zuwa. Tana tsaye a wurin sai takejin kamar hayaniya daga bangare shi, bata gasgata ba sai data ji karar wani abu ya fashe kamar glass, aikuwa da sauri ta nupi part dinshi, babu wani tsoro ko shakkar shi ta karasa cikin dakin. Ihu ta kurma ganin Abdulrahman a sume, da gudu ta fito daga dakin zataje wurin mummy ta fada mata sai kawai sukaci Karo, cikin rikicewa mummy tace lafiya lubna meya faru?? Lubna kasa magana tayi sai hannunta data daga tana yiwa mummy nuni data shiga dakin, da sauri mummy ta shiga dakin inda ta tarar da Abdul kwance kamar gawa. Salati mummy ta farayi tayi waje da gudu ta kira musa direba. Yana shigowa ya kama Abdulrahman sukasa shi a mota suka wuce asibiti, suna shiga babu wani bata lokaci akayi emergency room dashi aka fara bashi taimakon gaggawa, duk iya kokarin su akan ya farfafo, sunyi amma bai farfado ba.      After two hours Wani likita ne ya fito ya sami mummy a tsaye tayi tagumi sai hawaye ne ke fita daga idanunta, kallon inda take yayi yace hajiya kece mahaifiyar yaron nan?? Eh nice ya tashi??? A'a ki kwantar da hankalinki insha Allah zai tashi amma yanxu muje office dina. Yana gaba tana baya, kafarta har wani sarkewa take saboda ta matsu bataji abunda zai fada mata ba. Bayan sun shiga wuri ya bata ta zauna kafin ya maida duban shi zuwa gareta yace hajiya a gaskiya yaron ki na cikin matsala. Dumm taji gabanta ya fadi, tace likita meke damun dana dan Allah ka fada mun ta karasa maganar hawaye na zuba daga fuskarta. Dan Jim kadan yayi dan mummy ta bashi tausayi yadda yaga hankalinta ya tashi,   lallaminta ya farayi yana kwantar mata da hankali har daga karshe dai ya fada mata Abdul ya kamu da ciwon zuciya Kuma mafita daya neh shine duk wani abu dayake so ayi mashi kuma a guji bacin ranshi. Cikin tsantsar damuwa mummy tace likita tau yaushe ze farfado ne?? Nan bada dadewa ba zai farfado. wasu yan rubuce-rubuce yayi kafin ya mika mata wata takarda yace gashi kije banki ki biya Wannan kudin. Amma kafin ki fita ki tabbatar kin bar wani nashi kusa saboda karya farfado ya bukaci wani abu babu kowa kusa dashi. Amsawa tayi da toh sannan ta fita, daddy ta tarar sai kai kawo yakeyi, gabanshi taje ta mika mashi takaddar da likita ya bata, karba yayi yasa a aljihun shi kafin yace hajiya ta ya jikin nashi?? Fuskarta cike da damuwa tace Alhaji Abdulrahman yana cikin matsala sbd likita yace wai ya kamu da ciwon zuciya. Ciwon zuciya ya kara maimaitawa. Girgiza kai ya farayi cikin fada yace inaaa wannan ba gaskiya bane, yaron dake cikin jindadi, a koda yaushe? Ni ko damuwa ban taba gani a tare dashi balle ace yakai ga ciwon zuciya!! Ni ban yadda ba ina likita yake??? Likita da yanxu ya fito daga dakin da aka kwantar da Abdulrahman yace alhaji kayi hakuri da sakamakon da kaji amma wannan ba karya bane gama shaida nan, "ya mika masa takaddar gwadin da akayi mashi. Runtse ido daddy yayi dan ji yake kamar yayi kuka ko zaiji sassaucin zafin da yakeji a zuciyar shi." Shidai a iya sanin shi Abdulrahman be taba neman wani abu ya rasa ba kuma duk wani gata da kulawa yana samu daga garesu" to wace irin damuwace haka har tasa yakai ga kamuwa da heart attack basu sani ba?? Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya kalli inda likita yake yace zamu iya ganin shi?? Eh muje yayi musu iso har zuwa inda Abdulrahman ke kwance, kallon Abdulrahman daddy yayi yana mai jin tausayin shi. Mummy kuma sai kuka takeyi, haka lubna da suka shigo yanxu tare da umar da samha sai kuka sukeyi. Daddy neh yayi musu fada akan su daina kuka suyi mashi  addu'a Allah ya tashi kafadun shi. Nan suka zauna jugum jugum kamar Wanda akayi musu rasuwa. Suna nan zaune har dare amma Abdul be farfado ba, kowanne su yana cike da damuwar rashin farfadowar shi. Da karfe Tara na dare daddy yace su koma gida sai abar mummy ta kwana tare dashi su kuma zuwa da safe sai su dawo, duk ransu beso ba amma haka nan suka wuce. Har sunkai daidai shiga mota sai lubna ta tuno da wayar mummy na hannunta dan bayan wucewar su mummy asibiti cikin gida ta shiga ta dauko wayan mummy ta kira daddy, shiyasa ma ya rigasu zuwa. Bayan takai wa mummy wayar ne ta dawo suka wuce gida. Bangaren Amatu........ Pls share [2/13, 1:21 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' RUDANI fans grp ina yinku sosai dinnan👍🏻 Kuma ina kaunar ku sosai❤ '''wannan shafin na aunty na neh maryama a.i gital. Ina sonki kamar yadda nakeson raina, kisha zamanki ki huta Allah yaja zamaninki my best and sweetest aunty, I love u so much, Allah ya raya mana su beauties dinmu.'''          Page 33-34 Bangaren su Amatu kuwa sai hidimar biki sukeyi dan kuwa yanzu tabar zuwa shago, kai ko nan da can mummy bata bari ta taje saboda yan gyare-gyaren da ake mata. Ameerah kuwa sai zirga-zirga take bata nan bata can, duk wani shirye -shirye da rabon invitation card itace kan gaba, gashi gidansu Amatu harya fara cika da yan uwa tun kafin akai ga fara events. Abdulraheem kam ya matsu ba'a daura aure ba, su abokan shi har tsokanan shi sukeyi suna cewa ya fiye zumudi, shikuwa sedai ma yace eh din badai ya fita daga sahun gwauraye ba?? Haka zasuyi ta hira suna tsonkanar shi. ********* Bangaren Abdulrahman kuwa yau kwanan su uku a asibiti amma sai yau ya farfado, tun daya farfado sunan Amatu yake kira yana cewa tashi ce. Daddy neh ya matso kusa dashi ya rike shi yana lallashin shi, dakyar ya samu yayi shuru. Lubna kuma wani irin haushi neh ya kamata dan jin yace tashi ce"duk da cewar bata son ko wacece ba amma tasan dai akan macece. Bayan yan mintuna kadan, daddy neh ya kalli mummy yace hajiyata (hake yake kiranta) anya yaron nan ba zaucewa yayi ba kuwa dan naga sai sambatu yake tayi. Ajiye hannunta datayi tagumi tayi tace alhaji babu wani maganar zaucewa ina ganin dai ya fada tarkon soyayya neh dan yadda naji yana magana ya tabbatar mun da hakan. Ajiyar zuciya daddy ya sauke gami da cewa eh lallai ba shakka toh amma wacece wannan yarinyar da takeson taga bayan dana? Ya fada a dan tsawace. Kallon shi mummy tayi tace amsa tana gareshi  dan nima bazan iya cewa gata ba. Komai daddy baice ba ya kalli inda Abdulrahman yake kwance hawaye na zuba a idanunshi yace son meke damunka, ka fada mun koma menene indai har baifi karfina ba insha Allah zanyi maka. Share hawayenshi yayi yana mai fuskantar daddy yace daddy aure zatayi ta barni!! Daddy yace wacece ita?? AMATULLAHI aure zatayi kuma alhalin tasan ina sonta kuma itama tana sona. "Hannun daddy ya kamo yasa cikin nashi hawaye na zuba a fuskar shi yace daddy nah plsss ka taimakeni karka bari ayi auren nan auren dole za'ayi mata plsss wallahi idan na rasata mutuwa zanyi daddy! Ya karasa maganar yana mai langabar da kanshi jikin gado. Mummy ji take kamar ta taya shi kukan dan ya bata tausayi yadda yake kuka shida rabon da taga kukan shi tun yana yaro amma wai yau shine yake kuka," kukan ma akan mace. Lallashin shi daddy ya shigayi yana mai kwantar mashi da hankali. Saida yayi shuru tukunna daddy ya tambaye shi yace yarinyar yar' gidan waye? Cikin muryar shi data dishe saboda kuka yace yar gidan Alhaji Muhammad lemi. A dan razane daddy yace alhaji lemi dai wanda nasani dan kasuwan nan??? Girgiza kai Abdul yayi alamar eh. Nan daddy ya tashi yace yana zuwa ya fita. Mummy kuma tasowa tayi tazo bakin gadon da yake kwance ta zauna ta gefe tana kallonshi tace Abdul ka kwantar da hankalinka indai wannan ce damuwar ka an gama dan nasan daddynka yana son farincikin ka zaiyi iya kokarin shi wurin ganin an aura maka ita kaji?? Kayi hakuri. Amsawa yayi da toh. Mummy waigawa tayi zata yiwa lubna magana sai taga wayam bata nan Lubna ko tun sadda taji dalilin rashin lafiyar Abdul ta fita waje da gudu tana kuka, bayan asibiti taje ta samu wuri ta zauna ta kira  mummynta ta fada mata abunda ke faruwa. Duk da cewar mummy bataji dadi ba amma haka tayi ta bata hakuri tana mata fada akan ta rabu dashi tunda shi baya sonta ko an aura mata shi baza taji dadin zama dashi ba kawai tayi hakuri har Allah ya kawo mata nata. Kuka sosai lubna tayi dan tasan bazata iya daina son Abdul ba tunda tayi iya kokarin wurin cire soyayyar shi a ranta amma ta gaza. Bayan taci kukanta ta koshi neh taje wurin pampo ta wanke fuskar ta sannan ta nupi dakin. Tunda ta shigo ko kala batace ba, mummy kuma tsaf tana lure da ita dan ta gane cewar tayi kuka. Har ta danji tausayinta dan tasan yadda lubna ke masifar son Abdul din, ita kanta da badan batason ta takura mashi da tuni ta tilasta mashi ya aureta. Bayan daddy ya fita office dinshi ya nupa inda yasa aka samar mashi number Alhaji lemi, koda daddy ya kira lemi lokacin yana wani garden yana shan iska. Babu wani bata lokaci dan alhaji lemi ba irin mutanen nan bane masu wulakanta al'umma ba yace ya sameshi a garden inda yayi mashi kwatance, bada dadewa ba sai ga daddy ya iso wurin. Can ya hangoshi zaune da drinks a gabanshi, yana zuwa yayi mishi iso ya zauna kan daya daga cikin kujerun dake zagaye da teburin dake tsakiyar su. Bashi hannu yayi suka gaisa kafin daddy ya fara bashi labarin halin da danshi ke ciki. Alhaji lemi yace gaskiya dan tausayi na tausayawa danka sedai maganar gaskiya Amatullahi ba auren dole nayi mata ba kuma ma jibi za'a daura auren ta Abunda zance dakai shine kaba danka hakuri dan  yazo a kurarren lokaci, fatana Allah ya bashi wadda ta fita. Daddy kamar yayi kuka saboda haushi, shi yanzu ma matsalar shi besan ta ina zai fara yiwa Abdul bayani ba, yana tunanin haka Alhaji lemi yace amma kace danka yace tana sonshi ko?? Saurin amsa shi yayi yace eh eh tabbas kuwa yace tana sonshi.  Dan Jim kadan Alhaji lemi yayi yace tau Allah dai ya sauwaka nd ina kara baku hakuri, shi kuma danka Allah ya bashi lafiya. Jiki a mace daddy yayi wa Alhaji lemi sallama ya wuce. Direct asibiti ya nupa, lokacin Abdul yana cin abinci, da ganin daddy ya ajiye abincin yace daddy an fasa auren?? Fuskar daddy cike da damuwa yace son kayi hakuri kawa........ Be idaba yaga Abdul a sume. A razane yayo kansa, yana bubbuga shi mummy kuma da gudu ta ta fita ta kira likita, likita na zuwa yace su fita waje. Mummy bayan sun fito waje sai kuka take tana ma daddy mita akan meyasa zai fadawa Abdul magana mara dadi bayan yasan halin da yake ciki. Dago idanunshi da suka canza launi zuwa ja yayi dan shi a rayuwar shi be taba ganin wani ya kamu da masifaffen so kamar na Abdul ba. Kallon mummy yayi yace hajiyata dole in koma wurin Alhaji lemi dan kuwa bazan bari ina ji ina gani dana ya rasa ranshi akan abunda baifi karfina ba........ Tooo pah 🤔🤔🤔 Plsss kuyi hkr da wannan wlh dazu nayi typing me yawa ya goge😭😭 Ayi manaji da wannan For comments 09061103352 WhatsApp only [2/14, 9:33 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote and follow me on wattpad@lashminzy'''      Page 35-36 Waje ya fita ya dauko wayar shi ya kira Alhaji lemi, bayan sun gaisa yake fada mashi idan bazai damu ba yana bukatar ganin shi da gaggawa. Bayan ya gama wayar dashi neh ya sanar ma mummy ana neman shi a wani wuri yanxu zai dawo. Daga nan ya fita zuwa gidan shi dan harya koma gida. Koda daddy ya isa gidan akwai mutane da yawa sai zirga-zirga suke, nan ya kara tabbatar da cewar eh lallai fa bikin yar'shi ake. Har sai da yaji jikinshi yayi sanyi akan kudurin da yazo dashi, amma idan ya duba wani gefen sai ya ga ai rayuwar danshi yakeson ya ceto. Yana tsaye yana yan sake-sake sai ga Alhaji lemi yazo, nan ya mika masa hannu suka gaisa sannan yayi mishi iso zuwa palon baki. Bayan sun shiga abinci da ruwa Alhaji lemi yasa aka kawo mishi dan kuwa Alhaji lemi akwai iya tarban bako. Sun dan taba hira kadan kafin daddy ya sauka daga saman kujeran da yake ya matso gaban alhaji lemi, ya marairaice fuska yace Alhaji dan Allah ka taimakeni ka ceci rayuwar dana, wallahi yanzu haka yana asibiti bansan halin da yake ciki ba, "bayan na sanar dashi yadda mukayi dakai shikenan yaron nan ya sume, dan Allah Alhaji ka taimaka a daga aurrrr...... What??Alhaji lemi ya fada a tsawace, "yace me kake nupi in fasa wannan auren?? Inaaa bazai taba yuwuwa ba, "ka kuwa san iya adadin mutanen dana gayyata?? Bama Wannan ba mai kake tunanin zan fadawa baban yaron nan da kuma sauran mutane??? Murmushin da bekai zuci ba yayi yace nayi taimako da yawa, na ceci rayuwar mutane da yawa amma sedai wannan abu daya zan fadamaka shima taimako ne, ka dauki yaronnan kabar kasar nan dashi har zuwa wani lokaci. Zufa ce ta keto wa daddy jin irin maganar da alhaji lemi yayi "Cikin magiya daddy yace haba Alhaji wallahi dana yana iya mutuwa a kan akan haka kuma fah kasani a dalilin sonda yake wa yar'ka ne fa har samu wannan ciwon, "plsss kayi hakuri na roke ka da girman Allah ka daga auren nan har zuwa wani lokaci. Jikin Alhaji lemi ne yayi sanyi dan Allah yayi shi da tausayi, kallon daddy yayi fuska cike da damuwa dan har ga Allah beso fasa wannan auren ba, yace Alhaji na amince zan daga wannan auren har sai danka yaji sauki. Wani irin farinciki ne ya ziyarci daddy har besan sadda ya rungume Alhaji lemi ba yana murmushi. Ko hira basu tsaya yi ba daddy yayi mishi sallama dan zai koma asibiti yaga lafiyar danshi sannan kuma ya fada mashi wannan albishir din. Lokacin da daddy ya isa asibiti har Abdulrahman ya  dawo hayyacin shi, amma fah kuka yakeyi sosai, likita kuma saida yayi ta ma mummy fada akan su dinga kiyaye bacin ranshi idan ba haka ba zasu iya rasa shi. Bayan likita ya fita mummy sai rarrashin shi take, suna cikin haka sai ga daddy ya shigo da fara'a fuskarshi. Tunda mummy taga yanayin daddy ta tabbatar da sun samu nasara. Karasowa daddy yayi ya zauna kusa dashi ya dafa shi yace son ka kwantar da hankalinka wannan auren an fasa shi. Waro ido yayi yana murmushi yace daddy da gaske kakeyi?? Dukan wasa daddy yakai mishi yace toh da ina wasa dakai neh?? Murmushi yayi ya rungume pillow. Mummy ma taji dadin haka harda darinyan ta ta fara tsokanar shi. Bayan daddy ya fita, Alhaji lemi ya kira number mummy yace ta sameshi a palon baki yanzu yanzu. Bada dadewa ba sai gata tazo, wuri ya nuna mata da hannun shi yace ta zauna. Cikin yanayi na babu wasa yace rukayyatu ina son ki kasa kunnuwanki ki saurareni dakyau kuma kiyi aiki da basirar da Allah ya baki ki fahimceni "kina jina?? Cikin fargaba tace eh eh alhaji ina ji. To wannan auren na Amatullahi na daga shi saboda wani dalili nawa. A firgice ta mike tsaye tace Alhaji saboda me zaka daga wannan auren?? Duba fa kaga yadda gidan nan ya cika da mutane?? Me kakeson na fada musu?? Haba Alhaji ka canza tunani Dan Allah. Cikin fada fada yace rukayyatu ba nace ki fahimceni ina da dalilin yin hakan ba? Dan haka ba shawara na tambaye ki ba umarni nake baki a matsayina na mijinki kije ki sanarwa bakin gidan nan an dage wannan auren har zuwa wani lokaci. Amsawa tayi da toh sannan ta fita, da sauri ta nupi part dinta, dakinta ta shiga ta zauna tayi tagumi hawaye na zuba a fuskarta, kanwarta salma ce ta shigo dakin, ganin mummy na kuka da sauri ta karasa wurinta ta ta dafata tace aunty meya faru kike kuka haka?? Cikin muryar kuka tace salma an daga auren Amatullahi har zuwa wani lokaci! Cikin zaro ido salma tace injiwa yace miki haka?? Inji me gidan ta fada a takaice. Tagumi salma tayi tana dan tasan wannan ba karamin kalubale bane, dan yadda ma zasu tunkari bakin dake cikin gidan nan ma aiki ne. Cikin lallashi salma tace kiyi hakuri Allah ne bai kaddari za'ayi wannan auren jibi ba dan haka sai mu dauki kaddara kuma yanzu zanje na fara  sanar ma mutane. Nan ta fita ta nupi dakin su Amatullahi inda suke ta hira ita da kawayenta, kallonta salma tayi taga fuskar nan tata cike take da annashuwa ga kuma kawayenta da wasu tun fara biki suka dawo gidan da zama. Karasa shigowa tayi, ta tsaya a jikin wardrobe murya a sanyaye tace Amatullahi mummy na kiran ki amma kije tare da ameerah, nan suka tashi suka fita, salma kuma dakyar ta bude baki ta fada musu an daga auren. Aikuwa nan aka fara cece kuce ana Allah yasa shi yafi zama alkhairi Amatullahi kuwa tunda taga yanayin mummy tasan wani abu ya faru ga kuma aunty hajara dake zaune kusa da mummy da itama din yanayin ta ya sauya. Aunty hajara ce ta jawo hannun amatu ta zauna kusa da ita tace my amatu  dole mummy ta shiga wani hali amma dan Allah ke idan kikaji karki dauki abun da zafi, komai da kikaga gani mukaddari ne daga Allah dan haka ki dauki kaddara kinji ko?? Amsawa tayi da toh sannan aunty hajara tace daddyn ki ya daga bikin har zuwa wani lokaci. Amatullahi abun tausayi ko hawaye batayi ba tace Allah yasa shi yafi zama alkhairi. Suka amsa da ameen Cikin zuciyarta kuwa Allah ne kadai yasan irin damuwar data shiga amma daurewa kawai tayi saboda karta tada hankalinta ta kuma tada na mummy. Karasawa tayi kusa da mummynta tace mummy shine kike kuka?? Plsss ki daina kuka mu rungumi kaddara ai nasan ba karamin abu bane yasa da daddy ya daga wannan auren ba kuma mummy ai ba abun tada hankali bane tunda ba fasawa akayi ba dagawa akayi. Rungume ta mummy tayi tace Allah yayi miki albarka Amatullahi Insha Allah kina tare da cigaba a rayuwar ki. Ameerah kuma tana gefe tarasa farinciki take ko bakinciki. tana cikin wannan tunanin Amatu taja hannunta suka fita daga dakin. Suna fita sai ga mutane sun fara shigowa dakin mummy suna mata naje, wasu daman ba zuwan tsakani da Allah sukayi ba wasu ko harga Allah basuji dadi ba. Nan wa'yanda ke kusa suka fara shirye-shiryen tafiya wanda ke nesa kuma sai gobe dan yanzu yamma ta gabato. Haka Amatu ta tarar da kawayen ta suna shirin tafiya wasu kuma sai gobe, nan ta sallame su suka wuce, masu kidin kwaryar da aka gayyata suma an fada musu an daga bikin, hatta da malamar da zatayi wa'azi ranar daurin aure an fada mata an dage bikin. Zuwa wasu yan mintoci har an fara watsewa ba tare da wani fada ba amma fa masu bakinciki suna nan suna na zuci. A bangaren daddy kuma yanzu ya isa gidan Abba, amma basu tsaya maganar ba sai da sukayi sallar magariba dan yana isa ana kiran sallah. Bayan sun dawo daga masallaci part din abba suka nupa. Bayan sun zauna ne ya kwashe komai tun daga zuwan daddyn Abdul na farko zuwa na biyu ya fada mashi. Abba beji dadin daga auren da za'ayi ba amma tunda yaji dalilin haka sai  yace toh babu komai Allah yasa shi yafi zama alkhairi a garesu kuma ma yace zasuje asibiti dubiyar Abdulrahman. Nan suka dan taba hira kadan daga bisani kuma ya wuce. Abdulraheem kuma yana wani wuri inda zai kama hall din da za'ayi dinner sai ga abba ya kirashi, nan ya tafi ba tare da bata lokaci ba dan besan kiran da Abba keyi mashi ba. A part dinshi ya sameshi tare da ammie, da yanzu yake fadamata, haka nan taji babu dadi amma ya ta iya dole tayi hakuri. Shi kuma uban gayya yana zuwa ya wani fada jikin ammie yana shagwabe mata, a ranta tace hmmm yaro yaro ne da kasan abunda za'a fada maka da baka kwanto jikina kana shagwaba ba. Abba ne ya dubeshi yace Abdulraheem an dan samu wata matsala wanda a dalilin hakan yasa aka daga bikin ka har zuwa wani lokaci. Tashin hankali ba'a sa mashi rana😟 A firgice ya taso daga jikin mummy murya na rawa yace....................... Plsss share [2/15, 8:17 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' May Allah honour your knees when you bow in prayer and recognize your voice when you call upon Him,may you receive response from Him each time you asked.May the peace,blessing and mercies of Almighty Allah be upon you and your entire family. ᎪᎷᎬᎬΝ... JႮᎷᎷᎪ'ᎪͲ ᎷႮᏴᎪᎡᎪᏦ      Page 37-38 Abba...sab..boda me za'a daga bikin nan?? Abba yace Abdul bani nace a daga ba mahaifin yarinyar ne yace a daga kuma shima ba haka kawai ya daga ba yana da dalili. Batare da wani boye-boye ba Abba ya fayyace mishi komai, Abdulraheem kam wani haushi ne ya kamashi  yace Abba yanxu akan wanann abun za'a daga aurena?? Abba yace Abdulraheem dan Allah kayi hakuri, insha Allah komai zai daidai ta. Yanzu abunda nakeso dakai shine kaje ka huta Kuma banace kaje kayi ta sake sake bane ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai wuce kaji ko?? Amsawa yayi da toh kafin ya tashi ya fita. Dakinshi ya nufa, da shigar sa ya fada saman gado, yana tunanin maganganun Abba da yace saboda wani za'a daga bikinshi. Nan take yanayin shi ya sauya, fuskar shi ta koma kalar ja, idanunwanshi kamar garwashi suka koma saboda bacin rai. Wata irin zazzafar iska ya feso yace wallahi sai naga ko waye yake nema ya rabani da masoyiyata. Kuma ma idan har yana tunanin wannan ciwon nashi zaisa in hakura da Amatullahi toh ya farka dan mafarki yakeyi. Shi waye? A ina yake? Na rantse da Allah bazan taba bar maka ita ba, yadda kakejin zaka iya mutuwa akan sonta nima haka zan iya bada rayuwata saboda ita. Wani dogon tsuki yaja, ya zaro wayar shi daga cikin aljihu ya kira number ta akashe,. Wurgi yayi da wayar saman gado saboda haushi, "yana tunanin idan ya kirata zaiji dan sanyi a ranshi sai gashi tama kara bata mashi rai ta kashe wayar. Tashi yayi ya gyara kwanciyar sa yana mai jin bakin cikin faruwar wannan al'amarin, shi matsalar shi daya ma kar ace an fasa auren gabadaya saboda bakin mutumin nan da kuwa ya shiga cikin tashin hankali. Juye-juye kawai yake tayi saman gado yana surutu shi kadai kamar wani zautacce, wayar shi ce ta hau kuka amma saboda baya cikin jin dadi sai ya kashe wayar baki daya ba tare da yasan wanda ke kira ba. Saboda tsananin bacin rai ko kayan jikinshi be cire balle ma yayi tunanin wanka, haka bacci ya sace shi da niyar gobe zaije gidan su Amatu. Ammie kuma tana gaban Abba tana mashi mita akan cewa an tauye wa Abdulraheem "har a cewar ta wai bataga amfanin daga bikin da akayi ba tunda ko yaji sauki auren ba fasa shi za'ayi ba. Abba hakuri kawai yake bata yana cewa ta yadda da kaddara. Washe gari da misalin karfe goma sha daya na safe Abdulraheem yaje gidansu Amatu, koda megadi ya ganshi sai da hanjin shi suka kada, Abdul kuma beko bi ta kanshi ba ya paka motar shi bayan ya bude masa gate. Be jima da zuwa ba sai gata nan ta iso, kura ma juna ido sukayi, sai yaga ita kamar ma bata damu da daga bikin nan da akayi ba. Itakuma sai gani tayi duk idanuwan shi sun fada kuma ga fuskar shi ta nuna yana cikin damuwa. Kawar da idanunta tayi daga kallonshi ta gaishe shi, cikin dan sakin fuska ya amsa mata. Sai yace baby kinji abunda ya faru ko?? Eh wallahi jiya da daddare daddy keyi mun bayani "amma ni na shiga cikin ᎡႮᎠᎪΝᏆ fah saboda a iya sani na babu wani wanda nake soyayya dashi bayan kai amma daddy yace wai nima nace masa ina sonsa ji fa? Anya ba rabamu akeson yi ba? Kallonta yayi yace baby makiya sunyi mana yawa na tabbata bakin ciki kawai yakeyi dan yaga mun dace shine ya biyo ta wannan hanyar dan ya rabamu toh wallahi yayi karya, "Abdul ya karasa maganar a dan tsawace. Amatu tace my Abdul toh wai ma waye wannan yake son shiga tsakani na dakai neh?? Shuru yayi na yan muntuna yana yan sake-sake. Haka itama tunani takeyi, ita dai tasan babu wani wanda take soyayya dashi bayan Abdul dan ita shaf ma ta mance da wancan Abdul din dan har yanzu a tunanin ta shine Abdul dinta tun na farko shiyasa bata kawo komai a ranta ba. " haka shima beyi wannan tunanin ba dan ko lokacin data nuna shine Abdul dinta ba yadda yayi ba saboda a iya sanin shi shi kadai ammie ta haifa kuma be taba jin tace su biyu bane ko wani abu makamancin haka ba. Abdulraheem ne ya dawo daga duniyar tunanin daya fada yace baby ki kwantar da hankalinki idan har yayi nasara wurin ganin an daga bikin nan toh ya sani auren nan kamar an daura shine da izinin Allah kuma yau dinnan ba gobe ba zanbi abbana asibiti inga ko waye shi dan yanxu haka yana can asibiti yana ciwon zuciyar karya. Baby na shirya abubuwa da dama, na tanadi abubuwa masu tarin yawa, na tsara yadda bikin mu zai kasance amma wannan bakin azzalumin bawan Allah ya ruguza mana "toh ta Allah ba tashi ba. Amatullahi ko shuru tayi dan tana jinsa yana fadan shi, sai daya gama kafin ya dan yi kasa da muryar shi yace sorry na dameki da fada ko? Kiyi hakuri wallahi ina tsananin sonki da kishin ki ne shiyasa. Dan murmushi tayi batace komai ba sai yace baby zan tafi anjima zamuyi waya kinji? Amsawa tayi da toh shi kuma yayi mata sallama ya wuce. Ya fita kenan sai ga merry, da titi, da bola (ma'aikatan saloon dinta) sunzo, ko cikin palour bata kai ba ta tsinkayo muryar titi, dan kuwa titi muryar ta sama-sama take kamar na namiji, har gwanda ma in tana yarensu muryar tafi dadi. Iso tayi musu suka zauna a nan palour suna mata jaje dan sunji labarin a daga bikin ta. Daga nan suka fara hira sai ga ameerah ta fito daga dakin amatu, daman tana ciki. Zuwa tayi suka gaisa itama ta zauna ana hira da ita. Sai kusan la'asar suka ansa makullin shago suka wuce, daman tun lokacin da aka fara events din Amatu tasa aka rufe shagon tace kowa yaje hutu,. Toh shine yanxu da aka daga bikin sukazo ansa makullin dan suci gaba da aiki kafin Amatu ta dawo. Bayan sun wuce ne sai ga daddyn Amatullahi ya fito, nan yake fada musu zaije ganin Mara lafiya waton Abdulrahman. Gidan su Abdulraheem ya nupa dan tare zasuje, Abdulraheem ma yace zaije amma shi da biyu zaije dan yanason yaga ko waye, dan haka shike driving har suka iso asibitin. Da suka shiga ne ake sanar musu yanzu aka sallame su. Basuyi wata-wata ba daddy ya kira abban Abdulrahman ya fada mashi gasu sun iso asibiti wai an sallame su. Nan daddy ya fara basu hakuri kuma yayi musu kwatancen gidan shi. Basu sha wahala ba suka gano gidan dan gidan beda wuyar ganuwa. Koda suka shigo gidan Umar ne yazo yayi musu jagora zuwa part din Abdulrahman dan can aka kaishi amma shi hankalinshi bekai ga ganin Abdulraheem ba. Bayan sun shiga ne idon Abdulraheem ya sarke cikin idon Abdulrahman, cikin tsantsar tsoro da mamaki ya shiga ja da baya yana nuna Abdulrahman da shima ya mike tsaye yana nuna Abdulraheem. Nan yan dakin suka juyo suna ganin ikon Allah, Abba yace wai mafarki nake gani ko gizo? Daddyn Amatullahi yace wai kuna ganin abunda nake gani kuwa?? Daddyn Abdulrahman da mummy kam kwata-kwata basu mamaki domin kuwa sunsan wata rana hakan zata iya faruwa. Abdulraheem ya kalli abban shi yace abba kana ganin abunda nake gani kuwa?? Abba yace eh Abdul ina gani amma na shiga cikin ᎡႮᎠᎪΝᏆ dan ina bukatar a fitar dani daga cikin wannan ᎡႮᎠᎪΝᏆΝ Abdulrahman ya kalli daddyn shi yace daddy daman mu yan biyu neh??? Kowa ya zuba ido yana kallon daddy yaji abunda zai fada sai daddy ya....................... Plss comments And share Plss comments And share [2/15, 6:16 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 ```vote me on wattpad @lashminzy``` Page 39-40 sai daddy yace tabbas ku yan biyu ne ya bashi amsa, Kallon kallo suka shigayi a tsakanin su. abdulraheem kuma mamaki yakeyi yana cewa toh idan su yan biyu ne meyasa aka rabasu kuma ma abun tambayar anan itace be taba jin wani ko wata tace su yan biyu bane. Anya kuwa badai kawai kamanceceniya bace.... sai ya tsinkayo muryar daddy na cewa eh kwarai ku yan biyu ne kuma ni na haifu dukan ku. Kowa zaro ido yayi yana kallon daddyn abdulrahman. mummy kuma bataji dadin faruwar wannan lamarin ba dan gani take da zarar mahaifiyar su tazo tana iya tafiya dasu duka ita kuma ta shaku da abdulrahman bazata iya rabuwa dashi ba. Abba ne ya kalli daddy yace daman kaine mahaifin abdulraheem?? girgiza kai daddy yayi yace eh nine, wallahi sai yanzu nake danasanin raba ya'ya na danayi dan gaskiya na hakince su amma koda yake bani kadai keda laifi ba harda sa hannun mahaifiyar su tunda ita ta tilasta mun na rabu da ita. abba yace kana nupin aisha tana da hannu wurin raba yaran nan?? daddy yace wace aisha kenan? abba yace mahaifiyar abdulraheem mana. Cikin mamaki yace kana nupin aisha na raye? Abba yace eh tana raye, nan ya yaro wayar shi yayi dialing number ammie yayi mata kwatance inda yake yace tayi sauri ta iso, babu wani bata lokaci ammie ta shirya ta fito, yan mintoci kalilan sai gata a cikin harabar gidan ita da musa danshi yayi driving dinta. Tana nan tsaye sai ga umar nan yazo ya gaisheta sannan yayi mata jagora zuwa inda suke. koda ammie ta shiga gabanta ne yayi mummunar faduwa sakamakon abunda ta gani. Karasawa gaban abdulrahman dake tsaye kamar gunki ta dafashi hawaye na zuba a idanunta tace dana daman kana raye...... Abba ya katse da cewa daman abdulraheem yan biyu neh baki sanar dani ba?? juyowarta keda wuya zatayi magana da abba idanunta suka sarke cikin na daddyn abdulrahman. Ja da baya ta farayi tana nuna shi da dan yatsa, cikin rawar murya tace Aliyu da..man. kan..a raye?? shuru yayi mata dan shima tambayar da zeyi mata kenan ta riga shi. Alhaji lemi ne yayi magana yace dan Allah ku fitar damu daga cikin wannan ʀuɗɑɳiɳ. sai daddy yace alhaji mun tafka babban kuskure wallahi, amma ba'a son ranmu hakan ta faru ba kuma dalilin raba ya'yan mu da mukayi shine.... Shekarun baya da suka wuce aisha mata ta ce ina sonta tana sona dan auren soyayya mukayi, amma duk dangina basa kaunarta, mahaifiyata ce kawai ke sonta a cikin gidanmu sai kuma Allah ya dauki ranta. Bayan rasuwar tane yan uwana suka dinga musgunawa aisha, duk wani abu da zaisa ta farinciki sai sun ruguza shi haka duk wani hanya da zasubi dansu sakata cikin kunci sai sun bi. Daman mahaifiyata itace ke tsawatar musu toh bata nan nikuma konayi magana baji sukeyi ba kuma a lokacin bani da kudi balle mu kebe daga garesu. Haka rayuwar mu ke tafiya cikin gidan, idan har bana nan to fah aisha tana cikin kunci da damuwa, idan har kaga tana murmushi toh tana tare dani. nikuma ban fiye zama gida ba dan ina zuwa cikin garin kano ina dan kasuwanci na na saye da sayarwa shiyasa suke samun damar musguna mata. Akwai lokacin dana tsaya dakin daka nace duk wadda ta kara koda taka takalmin aisha sai nayi karar shi, amma duk a banza dan da zarar nasa kafa na fita zasu fara zaginta suna mata gori wai bata haihuwa. Kullum da sabon wulakancin da suke bullo mata, itakuma aisha akwai hakuri duk zagin da zasuyi mata bata taba ramawa sedai tabisu da Allah ya shirya. amma da suka kaita bango garinsu taje ba tare da sani na ba. ko dana dawo gida bata nan sai nayi tunnin kota shiga makwafata "sai ji nayi aisha shuru, su kuma yan gidan dake sun san abunda suka aikata babu wanda yace mun kala Haka na gaji da nemanta washe gari naje garinsu dake garinmu ba daya ba amma kusa muke. nan na tarar da ita sai kawunta yayi ta fada akan bazai bani ita ba dan baze bari yana ji yana gani a wulakanta amanar da aka bashi ba. dan aisha tun tasowarta batasan iyayenta ba ita da kanwarta maryam. a hannun kanin baban su suka taso kuma bai laifi yana kula dasu yadda ya kamata. Dakyar kawunta ya bani ita muka koma. Bayan wata daya da faruwar Haka sai aisha ta kamu da rashin lafiyar da har takai mu ga zuwa asibiti. nan aka tabbatar mun da cewa aisha nada biyu. Ba karamin farinciki mukayi ba dani da ita amma wani abun mamaki shine duk yan uwana babu wanda ya nuna jindadin shi. nikuma abun bai dameni ba daman tun tasowar mu sun tsaneni, bansani ba kodan ba uwa daya ta haifemu ba oho. Shine kiyayyar da suke mun ta shafi matata da kuma abunda ke cikin ta. Haka rayuwar mu ta kasance inda nake bawa aisha kulawa fiye dana da har Allah ya sauketa lafiya, inda Allah ya azurta ta da yara maza guda biyu. duk wani abu da mejego zata bukata nayi kokari wurin ganin na samar mata shi amma yan uwana komai basu bani ba hasalima ranar da ake suna basu ko gidan yan dangin aisha ne dakuma makwaftan mu suka halarci bikin. ************ Haihuwar su abdul ta zama kamar wata kofa ce ta kunno masifa dan kuwa duk wani wahala da aisha ta fuskanta a baya bekai na wanda take fuskanta a yanxu ba dan bata da ikon zama a tsakar gida, duk wani abu da aisha zatayi indai baya zame mata dole ba ko fitowa batayi saboda gudun matsalar su. Amma duk da wannan kaucewar da hakurin nata bata tsira ba dan kuwa yanxu kiri-kiri suke nuna mata bakincikin su. Akwai wata rana aisha bata nan ta shiga bandaki, sai tabar yaranta nan cikin daki ta rufesu saboda karsu fito suyi musu barna dan Allah ya azo ma yaran rashin ji da barna. Tana cikin wanka sai taji kamar abdulraheem na kuka, nan ta fito da sauri amma abunda ta gani ne yasata firgita, da sauri ta dauko muciya ta kwala matar yayana mai suna saude, bayan ta kwala mata ne ta dauke abdulraheem da take shirin jefawa cikin rijiya ta shige daki tana kuka. Ina dawowa aisha ta sanar dani, nan na shiga bata hakuri amma abunda aisha bata taba yimun ba shine musu amma a ranar saidata mun musu tace wallahi ta gaji hakurinta ya kare in sallameta ta wuce gidansu. Nikuma abun ya kona mun rai sosai ya za'ayi su takurawa mata ta tunda ba zamansu take ba ina ruwansu. nan na fito tsakar gida suna cin abinci na fara musu fada ina zaginsu, ta inda nake shiga ba tanan nake fita ba. haka na karaci babatu na babu wanda yace dani ko kala, abun ya bani haushi sai kawai na dauko wani icce na kwadawa auwal kanina dake zaune, nan jini ya fara zuba a goshinshi yan ihu haka na tafi na barshi. Washe gari bayan na fita ne matan gidan suka kama aisha suka kulle a daki suka mata dukan tsiya, kodana dawo gida na tarar duk sun kumbura mata jiki, na tashi zan fita inje wurin megari inyi kararsu ayi mana iyaka dasu dan lokacin raina yakai kololuwar baci, aisha tasha gabana. Tana kuka harda majina tace wallahi saina saketa kota kashe kanta dan ta gaji da zama cikin wahala dan itama tanada gata dan haka in sake ta, nan na shiga bata hakuri ina mata magiya amma kamar kara zugata nakeyi. Munyi kusan awa daya muna jayayya da ita, dana ga cewar da gaske takeyi sai na yanke shawarar inyi mata saki daya inyaso ta dan huta na kwana biyu kafinnan sai in samo mana wani gida koda na haya ne mu zauna. Haka na furta kalmar saki batare da zuciyata da gangar jikina sunso ba. ina kallonta ta shirya kayanta dana yaranta ta fito zasu wuce, sai nace mata nipa bazan bari taje da yaran ba tabar munsu in rike. Fur taki wai bazata barsu a dinga gana musu azaba ba, tun muna saisa saisa har abun ya dawo mana fada. ta fadi in fadi, daga karshe dai ta dauki abdulraheem ta wuce dashi. nikuma na rike abdulrahman yana ta kwalla ihu amma haka nayi ta rarrashin shi. Bayan kwana biyu da faruwar hakane sai na shirya zuwa garinsu aisha dan in kaimata abdulrahman ta rikesu har zuwa wani lokaci. Nan na tarar da mummunan labari, dan ba karamin firgita nayi ba dajin su aisha sunyi gobara kuma babu wanda aka fitar da rai. Haka na kwashi jiki na koma garin mu nan ma kamar wani hadin baki na tarar da gobara ta tashi kuma duk yan uwana sun kone saude ce kawai ta fita da rai amma itama ko sati batayi ba ta rasu. Na shiga damuwa da danasanin rabuwa da aisha danayi. kullum kuna ne sana'ata, abdulrahman kuma lokacin yana da shekara uku babu ruwanshi da abunda ke faruwa tunda ba wayo ke garesa ba. *********** Gidan wani abokina na koma da zama nida abdulrahman har zuwa wani lokaci da nayi ta fafutukan samun aiki, dakyar nasamu wani alhaji ya taimaka mun muna aiki tare dashi, inda har yaga na burgeshi ya hadani da yar'shi aure. A lokacin ban musa mashi ba dan ya zama kamar uba a gareni kuma ga abdulrahman yana fama da maraicin uwa shiyasa kawai na amince na aureta kuma Allah yasa muka fahimci juna da ita. Daga nan rayuwar mu taci gaba da tafiya inda kasuwancin alhaji yakara yelwaita, nima kuma yabani babban jari wanda shine silar zamana mai kudi. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya kalli ammie yace aishatu ina kika shiga ne a tsawon wannan lokacin kuma ma ya akayi kika kubuta daga gobarar data cinno muku?? ıŊAŦƐŘMıŞŞıƠŊ [2/16, 4:59 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' I love u so much ummu arpat, ngd da irin soyayyar da kike nuna mun amma karki manta nima fah ina kaunarki din kuma ina yinki 💯💘      Page 41-42 Kwalla ce ta zubo mata kafin ta share tace "bayan na koma gida washe gari gobara ta tashi a gidan mu a lokacin kuma nida maryam kanwata munje gidan halima matar kawunmu, toh muna can ne mukaji labarin gobara ta kama a gidan mu. Kuma duk mutanen gari sun aza harda mu dan tunda mukaji labarin haka bamu dawo ba sai mukayi zaman mu can daman kuma kawunmu kadai muke dashi shiyasa bayan wannan gobarar bamu dawo ba. Bayan sati d'aya da faruwar haka sai kawu bala wato mahaifin halima yace ni tunda mijina na nan kuma ga abunda ya samemu inyi mishi kwatancan garinsu yaje ya sameshi dan a mayar da auren mu. "batare da nayi wata jayayya ba na amince saboda ko nan da muke zama ba wani dadi mukeji ba danshi ma baida hali sosai. Bayan yaje garin ya dawo ne yake fada mana wai kun samu gobara kuma duk kun rasu wasu kuma sukace kabar gari. Daga nan nikuma na shiga damuwa, nayi kuka harna gaji daga karshe na dangana ga Allah. Bayan wasu lokaci da faruwar haka ne Allah ya hadani da Ibrahim waton mijina na yanzu, a lokacin ina yin panke ina kaiwa wani shago ana siyarwa sai Allah ya hadani dashi kuma tun daga lokacin daya bayyana mun yana sona na amince. Ba'a dauki lokaci me tsawo ba aka daura mana aure inda yace maryam ta dawo gidan mu da zama, dan yana da hali sosai dan ko lokacin bikin mu ya dauki nauyin abubuwa da dama. Haka rayuwar mu ta kasance inda muka dawo nan abuja da zama dan nan yake aiki, maryam kuma yasata a makaranta taci gaba da karatu nikuma yana kula dani yadda ya kamata. Abdulraheem kuma ko sau daya be taba nuna mashi bashi ya haifeshi ba dan haryanzu Abdulraheem besan Ibrahim bashi ya haife shi ba sai yanxu da wannan al'amarin ya faru. Ajiyar zuciya ta sauke tace Aliyu kaji yadda akayi muka tsira. Hamdala yayi ya kalli Abdulraheem yace dana zo kusa mana. A hankali Abdulraheem ya tako har zuwa inda yake ya zauna. Abba yace toh alhamdulillah munji dadi da Allah ya bayyana wannan lamarin, yanxu sai kowa ya gode ma Allah. Daddyn Amatu yace kwarai kuwa ai yanzu matsalar data kunno yanzu zamu kasheta tunda abun ya zama haka. Daddyn Abdulraheem yace eh kwarai kuwa amma yanxu wannan ya rage a tsakanin su tunda yan uwan juna ne yanzu sai daya yabar ma daya ko?? Gaban su ya fadi rassss a tare suka juyo suna kallon juna. "Cikin zuciyar  abdulraheem ko cewa yake lallai akwai chakwaki, amma nifa bazan taba bar mashi ita ba. Abdulrahman kuma dadi yakeji dan yasan duk yadda za'ayi shi za'a barma Amatu. Suna cikin zancen zucin su mummy ta katse su ta hanyar marairaicewa tana kallon ammie tace Aisha nasan cewa kina bukar duka ya'yanki a kusa dake amma dan Allah kiyi mun alfarma kibar Abdulrahman a wurina saboda na shaku dashi banason yayi nesa dani Dan Allah...... Ammie ta katse ta tace haba ke kuwa ai bazan rabaki dashi ba tunda haihuwar shi kawai nayi amma ke kika kula dashi tuna yana karami har zuwa girmanshi kinga ai kema danki ne dan haka kici gaba da zama dashi kuma kici gaba da bashi matsayin shi na danki. Murmushin jindadi mummy tayi ta karaso wurin ammie tana zuba mata godiya dan ba karamin dadi taji ba. Saboda ko ya'yan data haifa bata musu irin sonda takewa Abdulrahman ba" wani sa'in samha har kuka take tana shagwaba wai mummy tafi son Abdul. ********** Lubna ce ta shigo yanzu tare da samha dan duk abunda ke faruwa basu sani ba sai yanxu kuma dalilin zuwan su shine basu ga ammie da Umar ba kuma sunga motar daddy dana wasu shiyasa suka nupi part din ko suna ciki. Bayan sun shigane lubna taga Abdulraheem kusa da daddyn su duk a tunanin ta Abdulrahman ne, samha kuma gaishe dasu tayi kafin ta nemi wuri kusa da mummy zata zauna mummy ta kwabeta tace bakiga dan uwan Abdul bane?? Sai a sannan ta hango Abdulraheem dake zaune kusa da daddyn su. Lubna kuma jin maganar mummy ne yasata dawo daga duniyar tunanin data shiga dan ita kallon Abdulraheem kawai take ba kakkautawa sai yanxu ta kalli gefen gado, can ta hango Abdulrahman ya jingina da kan gado. Aikuwa cikin rudewa ta fara ja da baya, mummy ta taso ta jawota ta zauna tace lubna kwantar da hankalinki mana anjima zamuyi magana kinji ko? Gyada kai kawai tayi tana me kallon Abdulrahman da Abdulraheem dan babu wani banbanci a tsakanin su, hatta da yanayin askin Kansu yazo daya, "kayan da sukasa ne kawai ya banbanta dan Abdulraheem manyan kaya yasaka Abdulrahman kuma T-shirt ce baka da blue din jeans. Samha ma na daga gefen mummy tana kallon Abdulraheem, take sai taji ya shiga ranta dan yadda ya saki fuska sai taji ya burgeta ba kaman Abdulrahman daya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da manzon mutuwa. Daddyn Abdulrahman ne yafara magana cikin nutsuwa yace toh alhamdulillah komai yazo yadda ya kamata sedai wani hanzari ba gudu ba. Abdulrahman tunda ya kasance Abdulraheem dan uwanka ne ni a matsayina na mahaifin ku bazan iya cewa kai ko shi wanin ku ya hakura ba dan yin hakan ya zama tamkar tauye muku hakki ne amma shawara ta guda daya shine kuje ku sasanta kanku dan magance wannan matsalar. A tare suka kalli junan su Sai ammie ta karbe zancen da cewa alhaji kana ganin shawarar ka tayi kuwa? Bawai kar ace na nuna banbanci ba da sai ince Abdulrahman ya hakura tunda har anyi komai da sunan Abdulraheem kuma nake ganin kamar Amatullahi bazata amince da haka baa........ Sai daddyn amatu yace a'a hajiya shawarar shi tayi daidai dan kuwa Abdulrahman ya tabbatar ma Ibrahim da sun taba soyayya can a baya. Cikin dan mamaki ammie ta zaro ido tace kenan ta rigamu sanin shi?? Toh amma ya akayi tabar mu cikin RUDANI bata fada mana ba?? Sai Abdulraheem yace ammie itama bata sani ba dan a lokacin dana hadu da ita ta nuna ta sanni kuma harda cewa tayi munyi kusan shekara biyu muna soyayya da ita nikuma ban dauki maganar ta da gaskiya ba dan na dauka shirmenta ne kawai dai ina mata kama da wani ne Ashe da gaskiyar ta. Ammie tace tau Allah me iko🤔 indai kuwa hakane nima na yadda da shawarar daddyn ku, Allah ya baku sa'a Murmushi samha tayi dan ammie tace Allah ya basu sa'a sai kace wani jarabawa. Daddyn amatu ne yayi musu sallama musu yace duk shawarar da suka yanke a sanar dashi. Ammie da Abba suma tashi sukayi zasu wuce, sai Abdulraheem ya mike zai bisu, aikuwa ammie ta banka mashi harara tace toh bazaka tsaya ku gana da dan uwan naka ba! Bata rai yayi ya koma ya zauna. mummy da daddya kuma kallon juna sukayi kafin sukayi murmushi suka basu wuri, lubna kuma rai bace tabi bayan mummy tana yan sake sakenta dan a zuciyar ta cewa take tunda Abdul yan biyu ne ya zama dole ta samu daya daga cikin su. Niko nace kidai bi a hankali 😏 Umar ma fita yayi sai ya rage daga samha sai Abdulrahman da Abdulraheem. Zaune suke babu wanda yayi magana cikin su sai samha data ga shurun yayi yawa sai ta karasa wurin Abdulraheem cikin zolaya tace gaskiya yaya kafi yaya Abdul kyau ta fada tana murmushi, shima murmushin ya mayar mata yana tambayar sunanta. Cikin yanga tace baga yaya Abdul ba ka tambaye shi, " tana fadar haka ta fice. Dariya yayi a ranshi yana gani yanayin yarintar ta sak dana hanan dan itama haka take da surutu da shishigi. Dake Abdulrahman haka yake jin kanshi kamar wani sarki dan Allah yayi shi da son girma gashi kuma baya daukar raini shiyasa ya wani sha toka yana latsar wayanshi dan ko kallon inda Abdulraheem yake bayayi. Abdulraheem kuma gajiya yayi da zaman kuramen da sukeyi ya mike batare da yace kala ba ya ficewar sa daga dakin. Yana fita Abdulrahman ya ajiye wayar a fili yace wallahi baka isa kaso abunda nakeso ba gwara ma ka janye maganar baby ka dawo muyi zaman yan uwa. Abdulraheem kuwa yana fita yaga wayam su ammie sun tafi gashi daman bada motar gidansu sukazo ba, ammie kuma da zasu wuce motar datazo da ita ta shiga ita da abba suka wuce. Tsaye yayi yana yan kalle-kallenshi, yana kuma zancen zuci yace Abdulrahman kenan, bani ya kamata na hakura da Amatullahi ba kai ya kamata ka hakuri da ita dan haka idan ma kaki mun magana saboda ita ne to kayi gaggawar janye wannan hukuncin naka dan kuwa amatu kamar na aureta ne. Ni kuwa toh 😳 Samha ce tazo wurin shi ta katse mashi zancen da yake tace mummy na kiran shi, juyowa yayi suka nupi hanyar shiga palo tana gaba yana baya har suka shigo palon.............. Plsss share [2/17, 11:31 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Godiya mara iyaka, my fans ina sonku sosai da sosai, ina maku fatan alkhairi a duk inda kuke      Page 43-44 Mummy na zaune saman kujera tayi mishi nuni daya zauna, zama yayi kan two seater, mummy tace daman naga mummynka sun wuce da mota shine nace samha ta kira mun kai tunda magariba ta kusa kabari idan akayi sallah sai umar yakai ko? Da kamar zaice a'a sai yace toh mummy nagode. cikin jindadi tace yauwa bari a kawo maka ruwa kasha, ta fada gami da mikewa ta shiga kitchen. Samha kuma na nan palon tana kallon shi sai faman latsar waya yakeyi. Lubna dataji kamar magana sai ta fito palo, ganin abdulraheem yasa ta daskarewa a wurin tana kallon shi. Mummy ce ta fito daga kitchen dauke da faranti a hannunta sai lubna tayi saurin karbar farantin takai gaban abdulraheem ta ajiye. murmushi mummy tayi tace dana abdul gashi amma kayi sauri kaci dan lokacin ya sallah ya gabato. Da fara'ar shi ya amsa da toh sannan ya fara cin abincin dan dama yunwa yakeji, rabon da yaci abinci tun shayin safe, shiyasa yanzu ya mayar da hankalinshi kan abinci. Lubna ko sai kai kawo take kamar wata mayya, shiko abdul beko san tanayi ba dan dadin girkin mummy ya tafi da tunanin shi. Sai dayaci ya koshi kafin ya kalli samha data mayar da hankalinta kan wani season film a tashar bollywood. yanason yamata amma yarasa ta ina zai fara dan besan sunanta ba. Mikewa kawai yayi sai lubna ta taso ta karaso wurin shi tace yaya tafiya zakayi ne? kai ya gyada mata, sai tace tana zuwa bari ta sanar ma mummy. Bada jimawa ba sai ga mummy tazo, tana murmushi tace ahh har zaka tafi kenan? yace eh mummy. Kallon inda samha take tayi tace baby jeki kira umar kice yayanku ya tashi kinji? amsawa tayi da toh ta fita. Lubna kuma sai wani noke-noke takeyi tana murmushi batare da kowa ya kula da ita ba. Suna nan tsaye sai ga umar ya yazo, nan yayi musu sallama ya wuce. Suna fita ana kiran sallah sai suka tsaya nan wani masallaci dake unguwar su sukayi sallah sannan suka wuce. Tafiya kawai suke babu me magana cikin su dan umar ba ma'abocin hira bane dan harma gwara abdulraheem wannan abun ne yasashi zama silent amma idan jininku ya hadu dashi toh fah sai ka kaji dashi dan akwai barkwanci. Tafiyar su bata wuce minti goma sha biyar ba sai gasu sun iso gidan su abdulraheem. Sallama sukayi wa juna ya wuce. Abdulraheem na shiga gida part din ammie ya nupa, lokacin ammie kuma tana palo ita da hanan tana labarta mata abunda ya faru. Suna cikin hirar ne sai ga abdul ya shigo, da gudu hanan taje ta rungume shi tace laa yaya ashe ku yan biyu neh??? hmmm tau nidai ina bayan yaya abdulrahman kawai kabar masa aunty amat....... Wani irin damka yayi mata, kamar wani zaki yana huci, ammie tayi saurin zuwa wurinshi ta fisge hanan daga damkar da yayi mata. Cikin fada tace abdul kana da hankali kuwa? miye haka? akan dan tace haka shine zaka wani shaqo ta? ko so kake ka kashe mun ita? toh wallahi ka fita a idona kanaji na ko? Kamar yayi kuka dan har yanayin shi ya sauya yace ammie kiyi hakuri nima bansan nayi haka ba. Da fadar haka sai yayi shuru. ba'afi dakika talatin ba sai yace amm ammie plss ki taimakeni karki bari a rabani da amatullahi wallahi itace farinciki na kuma kinfi kowa sanin irin sonda nake mata "plss my ammie help me Cikin tausaya mashi tace abdul kenan dukan ku ya'ya na ne kuma ina sonku, da'ace wani ne can daban zan iya tsaya maka dakin daka, toh amma kaga yadda abun yake, yanxu shida yake fama da ciwon zuciya ya kake tunanin zan iya tunkarar shi da ince ya hakura yabar maka ita? haka kaima idan nace ka hakura kabar mashi ita zakayi tunanin ko nafison shi fiye da kaine shiyasa abbanku ma ya yanke hukunci yace ku sasanta kanku saboda karku ce yayi sonkai. Nidai abunda zance shine kayi hakuri, kaje ka zauna da dan uwanka zama na fahimta ku fahimci junan ku. kaga nima idan ina ganinku tare cikin farinciki da kwanciyar hankali nima zanji dadi. jikinshi ne yayi sanyi sai kawai yace insha Allah ammie zamu daidaita. Yana fadar haka ya fice. Ammie kuma waigawa tayi bata ga hanan ba, dan hanan tunda ammie ta kwaceta ta sheqa da gudu daki ta fada saman gado tana kuka dan ba karamin jin zafin rikon da yayi mata tayi ba. *********** Daddy ne zaune yana labartawa mummy da amatu abunda ya faru. Mummy kam ta hakikice tace ita kam bazata yadda da wata shawara ba. saboda me za'a ace sai sun yanke shawara bayan ansan cewa amatullahi nasan abdulraheem wace irin ace su sasanta kuma? Daddy yace haba rukayyatu wai ya ina baki kina roko? yanxu fa nace maki shekarun baya da suka wuce yaron nan da amatullahi ke soyayya dashi abdulrahman ba abdulraheem ba kuma shi abdulrahman ya tabbatar mun da cewa tana sonsa, koba haka ba ya fada yana kallon amatu data dukar da kanta kasa. Cikin rawar murya tace eh daddy. Mayar da kallon shi yayi wurin mummy yace to kingani, ko? yanxu haka yaron nan a dalilin soyayyarta harya kai ga kamuwa da ciwon zuciya kuma bayan haka ma abunda yasa muka yanke wannan shawarar dan munga yan uwan juna ne dan a samu sulhu a tsakanin su mukace su sasanta kansu. Dan sassautowa mummy tayi tace toh bakomai Allah ya zaba wanda yafi zama alkhairi a cikinsu. Cikin jindadi daddy yace ameen ko ke fah! murmushi tayi ta kalli gefen amatu tace amatullahi jeki daki ki kwanta. sum sum ta mike ta wuce dakin ta, tana shiga wayar ta na kara. Da kamar bazata dauka ba sai tayi tunanin ko abdul dinta ne shiyasa tayi gaggawar daukan wayar kafin ta tsinke. Cikin yanayi na damuwa yace baby ina cikin tashin hankali. Zai fara bata labarin abunda ya faru ta katse shi tace my abdul daddy ya fada mun komai, amma ni ban yarda da shawarar su ba saboda ni gaskiya banason abdul a yanxu. Duba fa kaga tsawon shekaru biyu ya gujeni sai yanzu da yaji labarin zan aureka shine zai wani dawo? toh nikam banason shi kai nake so. Plss my abdul kayi wani abu karka bari ya samu nasarar rabamu. Ta fada hawayene na zuba a kumatunta. Cikin lallashi da samun karfin gwiwar maganar data fada yace baby ki daina kuka insha Allah babu abunda zai rabamu. Kuma koda yazo gidan ku karki sake ki bashi fuska, ki nuna bakya sonshi, ki karyar mashi zuciya da barazana nasan zai hakura ya barmun ke kinji ko baby? tau my abdul. Sai yace tau yanzu ki share hawayenki ki kwanta kiyi bacci, insha Allah gobe idan na fito daga asibiti zan biyo gidanku. Toh tace daga nan sukayi sallam ya katse wayar ********** Bayan kwana biyu mummy ce a dakin abdulrahman tana mashi fada akan yaje ya gaida ammie dan tun jiya taketa mashi naci amma sam yaki zuwa. Ita gani tayi tunda yaji sauki ai ya kamata yaje ya gana da mahaifiyar shi amma kamar wata makiyiyar shi tayi-tayi yaki zuwa shiyasa yau dinnan cikin fada da bada umarni tace dole sai yaje ya ganta. Shima yanason ganawa da ammin shi kawai dae haushin abdulraheem yakeji dan bayason ganin shi dalilin dayasa kenan yaji bayason zuwa gidan. Ganin ran mummy ya baci sosai ne yasa yayi saurin isowa gabanta yana murmushi yace mummy nah kiyi hakuri ki dan saki fuskar ki yanzu zan wuce. Dukan wasa takai mishi hade da cewa sai dakaga nakai kololuwa zaka wani ce inyi hakuri? tayi kyacci tace zaka gamu dani ne ai. murmushi yayi ya dauki wayar shi daman a shirye yake sai yabi bayan ta suka nupi part dinta. Dan umar ne zai kaishi saboda besan gida ba. Samha kuma dagewa tayi akan saita bi abdul mummy tace bazata ba sai da abdul ya roki mummy sannan ta yadda zasuje. Da murnar ta taje tana yiwa labna gwalo sannan tasa kai ta fice. Lubna ko haushi kamar ya kasheta dan jitayi kamar ta bisu. Bayan sun fita umar ne driving, abdul na daga gefe yana yan kalle-kallen shi ta tagar mota. Samha kuma na baya suna hira da umar jefi jefi har suka iso gidan. Cikin farfajiyar gidan umar ya paka motar, suna fita ya tada motar ya wuce, dan akwai inda zashi. Samha ce ta fara kalle-kalle tana tunanin inda zasu bi dan plat uku ta gani kuma duk iri daya guda daya ne kawai ya bambanta a wurin penti. Abdul kuma tsaye yake yana waya. Bayan ya katse wayar neh ta nuna mashi plat din farko dan nan zuciyar ta raya mata dasu shiga tace yaya muje ko? ba musu ya bi bayanta dan da badan itaba komawa zeyi. Wani kofa ta gani wanda ya bata damar gane cewa nan ne hanyar shiga cikin gidan, dan handle din dake makale a jikin kofar ta hau bugawa. Tayi bugu daya, biyu, uku sai ta dan jinkirta. Jin basu bude bane gashi sunkai kusan minti biyar tsaye sai taji abdul yaja tsuki yace dalla mu wuce. Juyawar shi keda wuya yaci karo da abdulraheem har................ 👇🏽👇🏽👇🏽    Vote Comment And share [2/18, 6:00 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''      Page 45-46 Juyawar shi keda wuya sukaci karo da abdulraheem har wayar abdulrahman ta fadi a kasa,  a tare suka duka zasu dauki wayar sai abdulraheem ya riga shi dauka ya mika mashi yana cewa sorry plss shima daidai lokacin abdul-rahman ya dago kanshi yana ce mashi sorry. Samha ce tayi dariya ganin yadda suka duka a tare zasu dauki waya, yanzu kuma sun hada baki wurin bawa junan su hakuri. Hararanta abdulrahman yayi, sai ta gumtse dariyar ta. Abdulraheem kuma hannu ya mika mashi suka gaisa kafin yayi taku daya zuwa biyu ya kwankwasa kofar. Yana bugawa hanan ta bude kofar daman tun dazu taji ana buga kofar shiyasa bugu daya kawai yayi ta bude. Tamke fuskarta tayi dan har yanzu tana fushi dashi akan shaqar da yayi mata, tana budewa ta juya zata wuce, shi kuma yayi saurin tsayar da ita yace sis bakiga munyi baki bane?? Dawowa tayi bakin kofar sai idonta ya sarke cikin na samha. Cike da murna da mamakin ganinta taje ta rungume ta tana cewa besty waya kawoki gidan mu? Da fara'a a fuskar samha tace tare da yaya abdul nake. Juyawa hanan tayi danta ganshi sai bata ganshi ba dan tuni abdulraheem ya isar dashi cikin palo. Kallon samha, hanan tayi batare da tace mata wani abu ba taja hannunta suka shiga ciki. Lokacin har abdulraheem ya kirawo ammie. Gaishe da ammie samha tayi sannan suka haura sama ita da hanan. Ammie kuma zama tayi suka gaisa da abdulrahman sannan ta shiga kitchen ta kawo mashi drinks.  Bayan ta aje mashi parantin dake dauke da drinks din ne ta zauna saman kujerar dake fuskantar shi, tana dan murmushi dan ba karamin farincikin ganin ya'yan nata wuri daya tayi ba musamman ma da suka zauna saman kujera daya sai taji sun kara burgeta. Dan jan abdulrahman da hira ta farayi dan yaki sakin jikinshi kuma duk da haka nan ta lura shi din ba mutum bane mai son magana. Abdulraheem kuma tashi yayi zai fita sai ammie tace abdul ina zakaje bayan ga dan uwanka ya kawo mana ziyara?  Dan sosa keya ya farayi ya dawo ya zauna yana wani bata rai. Sai ammie tace toh tunda bakaji dadin ganin shi ba ai sai ka tafiyarka ko?  Kallon ammie yayi yace haba ammie ya zakice haka?  Ai nama fiki jindadin ganin shi, ya karasar maganar ne a yayinda yake kallon abdulrahman da shima jin maganar da ya fada ne yasashi dagowa suka hada ido. Cikin ran abdulrahman tsuki yayi yace ji kamar da gaske. A fili kuma sai kawai suka sakar ma junasu murmushin dani kaina bansan amanar shi ba. Tashi ammie tayi ta basu wuri wai ko kunyarta yakeji shiyasa yaki sakin jiki, hatta drinks din data kawo mishi bai sha ba shiyasa ta shige daki. Bayan ta wuce ne abdulraheem ya kalli abdulrahman yace dan uwa baka sha ruwa ba?   Abdulrahman yace a'a nagode. Fakon shi abdulraheem yayi ya harare shi yace waton kai dan iska ne ko? Dan ma kasamu nayi maka magana shine zaka wani dinga basarwa ko?  Toh inma dai akan amatu ne kake wani shan kamshi gwara ma ka daina dan bata lokacin ka kawai kakeyi, ya fada gami da kawar da kanshi gefe. Abdulrahman kuma baiji abunda ya fada ba dan kasa-kasa yayi maganar. Shuru sukayi babu wanda ya kara tanka ma wani. Sai dai yan sake-sake da ko wannen su keyi. Hanan ce da samha suka  zo palon suna dan kus-kus dinsu, dan tun daga saman staircase suka faro har suka nemi wuri suka zauna basu fasa ba. Samha ce talli hanan cikin yin kasa da murya tace Allah su twins abdul suna kama sosai, wallahi da badan nasan kayan da yaya abdulrahman yasa ba da bazan iya banbance su ba. Wallahi kuwa, hanan ta fada had'e da dauko wayarta zata kasta musu hoto. Samha ta waro ido tace keyyy hmmm ina ganin yaya abdulraheem ba masifaffe bane shiyasa kika ga fuskar da zaki daukeshi hoto. Hanan tace hmmm kedai ai naga alama dan kodana gaishe shi sama-sama ya amsa mun. kin gani kuma shine zaki dauka? Nidai kawai ki hakura da daukan hoton nan karki ja mana zagi, samha ta fada. Kallon uku saura hanan ta aika mata tace lallai toh wallahi sai na dauka, ammie fa nakeson in nuna ma. Dariyar mugunta samha tayi mata ta matsa daga gefenta koda zaiyi fadan sai dai yayi wa hanan ita kadai. Murmushi hanan din tayi tace ai duk masifar shi dole ya sarara mun tunda bakuwa nake a gurinshi kuma daman ance bakonka annabin ka. Kallon zaki sani ne samha da aika mata, sannan ta mayar da hamkalinta kan makeken TV dake palon. Hanan kam daukar wayanta tayi ta shiga camera ta danyi zooming camera din  saboda sun danyi nesa da ita. Aikuwa tana dauka wayar tayi kara gami da kawo flash. Abdulraheem da flash din  ya haska mashi ido sosai  yace hanan miye haka kin wani kunna touch din waya, dan baiji karar dauka ba saboda karar TV. Hanan tace sorry yaya hannu na ne yakai wurin. Komai bace mata ba ya mike yayi kwafa ya haura sama, dan ya kosa abdulrahman bai tafi ba. Samha kuma da hankalinta yake rabi kan kallo rabi kuma kan hanan, dan tayi tsammanin ko abdulrahman zai ce wani abu sai taji yayi shuru. Cikin jin haushi tace waton mu ka raina da ko bada gangan mukayi maka laifi ba sai ka hukunta mu ko? Allah sai na fadawa mummy. ta fada gami da yin qyaccin da batasan ya fito fili ba. Hanan na dariya tace samha wannan qyaccin fah? Injin dai lafiya? Harara samha ta watsa mata gami da cewa zamu hadu a school ai. Daman makarantar su daya kuma aji daya suke amma babu wanda yasan gidan wani. Mintuna kadan da tashin abdulraheem sai gashi tare da ammie, ammie tace abdul harka tashi wucewa Kenan? Cike da mamaki yake kallon abdulraheem dan yasan shine yacewa ammie ya tashi tafiya. Wayancewa kawai yayi ta hanyar gyada mata kai alamar eh. Ammie tace aina dauka sai dare zaka wuce. Sai abdulrahman yace eh ammie naso mukai dare amma ana nema nane shiyasa zan wuce amma insha Allah bada dadewa ba zan dawo. Ammie tace tau Allah ya kaimu Abdulraheem kuma ajiyar zuciyar ya sauke dan ya dauka ko abdulrahman zai ce be tashi bane. kuma shi gashi a matse yake da yabar gidan dan yanason yaje asibiti kuma inson samu ne ma ya biya ta gidansu amatu. Ammie ji tayi kamar karya tafi, amma bata nuna ba sai kawai tayi mashi sallama kuma ta bashi sako ya gaida yan gidan su. Nan suka musu rakiya har zuwa farfajiyar gidan. Inda abdulrahman ya tuna da baizo da mota ba. Aikuwa yayi tsuru gami da lalubo wayar shi zai kira umar kenan sai ya tsinkayo muryar samha na yacewa yaya tunda umar bai zoba basai mubi yaya abdul ba tunda shima fita zaiyi! Sai ammie tace tau kuje ya saukeku mana. Abdulraheem saboda haushi sai ya koma kamar wani wawa yana kallon abdulrahman dake shirin shiga gidan baya, samha kuma gaba ta shige tana washe ma hanan baki. Abdulrahman ko a jikinshi ya wani shige gidan baya ya babbaje kamar irin alhaji na jiran jireban shi. Sai wani murmushi kawai yakeyi wanda shi kadai ne kawai yasan manufar yinsa. Haka abdulraheem ya shiga mota yaja wani irin wawan reverse wanda yasa har saida kan samha ya dan bugu da dashboard. Sorry kawai yace mata yaci gaba da tukinshi. Bangaren su mummy................ Ayi manaji da wannan plss [2/19, 12:09 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''      Page 47-48 B'angaren su mummy, Abdulrahman na fita sai ga umma (yar'uwar mummy) tazo. Cike da fara'a mummy ta tarbeta, lubna kuma bataji dad'in zuwan ta ba dan tasan dalilin zuwan ta". Saboda jiya sunyi waya. 'Bayan sun gama gaisawa ne umma ke cewa ai tazo ta tafi da lubna ne" sai mummy tace lafiya zaki tafi da ita?  Umma tace eh lafiya kawai dai daman naga an kawota gidan ne saboda Abdulrahman. Toh babu wani canji da aka samu, shiyasa na yanke shawarar in mayar da ita gida. Fuskar mummy cike da damuwa tace umma wallahi da ace ni na haifi Abdulrahman da cikina da zan iya tilasta mashi ya auri lubna, amma sai aka samu akasin haka, dan kinga idan na tilasta mashi ya zamana kamar na tauye mashi hakki ne. "kuma kin dai ga abubuwan da suka faru, dan a dalilin kamuwa da ciwon shi ne yasa wannan abun ya faru. Kinga koda ina da niyar mashi magana ai baze yiyu ba tunda yana da wadda yakeso. Sai umma tace eh hakane gaskiya nima bazan so a takura mashi ba, shiyasa ma zan d'auketa tabar daga gidan nan tama bar ganin shi bakidaya nasan idan bata ganin shi zata manta dashi. Ni wallahi har mamakin irin sonda lubna kewa Abdulrahman nake, danni bantaba ganin irin haka ba. Umma ta fad'a. Mummy tace uhmmm tau Allah yasa tafiyarta shi yafi zama alkhairi. Umma ta amsa da ameen gami da cewa ina yaran gidan, dan tun shigowarta bata ga wulkitawar ko dayan su ba?  Nan mummy tace sun tafi rakiyar abdulrahman har tafara bata labarin yadda ta tilasta ma abdul zuwa wurin ammie. Murmushi umma tayi tana fad'in ai yarinta ce, dan inba yarinta ba tunda akace ga uwarka can ai zakayi zumud'in zuwa ganinta. Mummy tace kedai bari ai yaron nan sai a slow dan gabad'aya gidan nan dagani sai daddy ke iya tankwara shi yadda mukeso. Murmushi umma tayi game da cewa Allah dai ya shirya mana su. Mummy ta amsa da ameen had'e da fad'in zasuyi kewar lubna musamman ma samha da makaranta ce kawai ke rabasu amma komai tare sukeyi. Suna cikin hirar ne sai ga su Abdulrahman sun dawo. Samha ce tazo da gudu ta rungume umma tana dariya. Cikin jindadin yadda samha ke sonta tace baby na sannunku da dawowa. Samha na murmushi tace yauwa ummana yaushe kikazo?? Itama umma murmushin take yiwa samha tace ban dad'e da zuwa ba. Shigowar Abdulrahman kenan yanzu, ya duk'a har k'asa ya gaida umma. "Cike da fara'a umma ta amsa tana tambayar shi ya ayyuka. Kamar wani mara gaskiya ya fara sosa k'eyar shi gami da cewa lafiya kalau. Umma tace tau Allah ya taimaka. Ya amsa da ameen kafin ya mike yabar  falon. Samha na jikin umma sai surutu take faman zuba mata sai kace wata aku. Mummy tace wa samha taje ta kira lubna. Lubna ko tana d'aki sai faman kuka takeyi tana cewa umma batason farincikin ta, tana kuka ne a yayin da take kwashe kayanta tana zubawa cikin trolley. Samha ce ta shigo d'akin da sauri jin kamar ana shasheqan kuka, sai ta karaso gaban lubna ta dafa ta tace aunty lubna meya faru kike kuka? Lubna da fuskarta tayi shab'e-shab'e da hawaye tace samha gidan mu zan koma gabad'aya. Zaro ido samha tayi tace gida kuma? " toh saboda me zaki koma gida"? Lubna tace wai saboda yaya Abdul. Ji fah? "Sai kace ni na dorawa kaina sonshi" shine fa umma tazo d'aukana wai ta gaji da k'orafi na, tunda shi baya sona miye amfanin zamana a gidan nan? Kwalla ce cike da idonta na tausayinta dan itama tasan cewar lubna na bala'in son Abdulrahman. Sai samha ta dafata tace aunty kiyi hakuri kibar wa Allah komai kuma kibi umma ku tafi. Idan har Allah ya k'addari yaya Abdul mijinki ne insha Allah babu makawa duk nisar da kikayi dashi zai dawo gareki. Share hawayenta lubna tayi tace nagode yar'uwata da shawarar ki zanbi umma na amma kema ki tayani da addu'a Allah ya cire mun son yaya Abdul a raina kinji?? Samha ta amsa da toh had'e da rungumar junan su.   Kusan minti biyu suna a haka sai samha ta tuna da ance da kira lubna, aikuwa da sauri ta zame jikinta tace aunty na manta fa mummy na kiran ki. Murmushi lubna tayi tace kin ganki da mantuwa ko, ta fad'a had'e da ja mata karen hancinta. Itama murmushin tayi kafin suka fice a d'akin. Palour suka tarar da umma da mummy. Umma sai faman hararan lubna takeyi dan wani haushin takeji na yadda ta hak'ik'ice akan son wanda baiko damu da ita ba balle har tayi tunanin ko zai sota. Wata zuciyar umma tace toh ai ba ita ta d'aura wa kanta ba tunda gashi nan itama tanason ta cire shi ta k'arfi da yaji. Kawar da tunanin umma tayi dan jin mummy na cewa lubna su shiga daga ciki. Tsuki tayi ta kara jawo samha kusa da ita suna hira. Mummy kuma dariya taja hannun lubna suka haura sama.            Washe gari Abdulrahman ne sanye cikin wani yadi mekyau kalar bak'i da hula bak'a. Sai k'amshi yake zubawa yana murmushi sai kace wanda akayi wa albishir da aljanna. Fitowa yayi rik'e da makullin motar shi a hannu ya nufi part din mummy. Nan ya tarar da ita tana Lallashin samha dake kwance saman cinyarta tana kuka akan lubna da yanzu suka wuce. Gaishe da mummy yayi kafin yasa kai zai fice sai mummy tace Abdul ina zakaje ne haka? Komi bai ce ba ya dawo kusa da ita ya zauna, idanun shi na kan samha yace mummy wai kukan me takeyi ne haka duk ta cikawa mutane kunnuwa. Murmushi mummy tayi dan ta fahimci wayo wai yakeson yayi mata danta tambaye shi ina zashi shine ya kawar da zancen. Sai tace ai dole tayi kuka tunda yar'uwarta ta tafi. D'an bata rai yayi dan jin wai akan lubna take kuka haka sai kace wadda aka rabata da ranta. A fili sai kawai yace tau ayi hakuri gami da mik'ewa yana cewa mummy zan d'an fita wurin wani aboki na. murmushi mummy tayi irin nasu na manya tace a dawo lafiya. Amsawa yayi da ameen kafin yasa kai ya fice daga palon. Wurin motar shi nufa kirar Mercedes Benz ya shiga ya bata wuta. Yana duk'i ne a yayin da yake sauraron wata wak'ar wizkid ta I love my my baby dat's my baby....murmushi kawai yake yana bin wak'ar har ya iso gidansu Amatullahi. Horn yayi me gadi yayi sauri ya bud'e mashi amma baiyi yunk'urin zuwa inda yake ba dan har yanzu bai manta da marin da yasha ba. Bayan ya faka motar shi ne ya kira megadi dake shirin shiga d'an k'aramin dakin shi. "Gaban shi ne ya fara dukan uku, uku, cikin dauriya ya k'araso wurin Abdulrahman ya duk'a har kasa yace yallabai gani. Kallon shi Abdulrahman yayi yace dan Allah kayi mun sallama da Amatullahi. Ajiyar zuciya ya sauke gami da mik'ewa ya nufi cikin gida. Bada dad'ewa ba sai gashi ya fito ya sanar mashi da gata nan zuwa. Ko cikakken minti biyar ba'ayi ba sai gata nan ta fito. A hankali ta fara takowa har zuwa inda yake, murmushin dake fuskarta ya kara yalwaita, a yayin da shi kuma yana tsaye ya zubawa kyakyawar halittar ta ido. Bayan ta karaso gaban shi ne tasa hannuwanta biyu ta tafa wuri guda danta lura baiko san ta iso ba. Karan tafa hannuwanta ne ya dawo dashi daga duniyar daya shiga, yana sakar mata murmushi yace baby na kinyi kyau sosai. Cunno bakinta gaba tayi tace Allah Abdul bana son zolaya, ji fa ko kwalliya banyi ba ka wani ce nayi kyau, ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka. Duka hannuwan shi yasa ya rike kunnuwan shi had'e da marairaicewa yace a fuwan my baby amma ni kin fi mun kyau idan bakiyi kwalliyar bama. Hararan shi tayi ta gefen ido batare daya gani ba tace ya aiki? Abdulrahman yace alhamdulillah baby na ya mummyn mu? Hmmmm tana fushi dakai tunda bakazo ka gaishe ta ba. Cike da jindad'in maganar ta yace ai karki damu insha Allah zuwa na musamman zanyi dan in gaishe ta kuma in kin koma ciki ki isar mun da gaisauwa ta kinji? Amatu ta amsa da toh, daga nan suka shiga hirar soyayya kowannen su na fad'in sirrin zuciyar shi. Sunan har kusan k'arfe biyar na yamma kafin yayi mata sallama ya wuce. Yana fita wayar amatu ta fara ringing. Dubawa tayi taga Abdulraheem ne ke kiranta. Cike da mamaki tana tunanin kodai ya manta da wani abun ne? Kawar da tunanin tayi ta amsa wayar. Daga can yace baby ki fito gani k'ofar gidan ku. Batare da yaji amsarta ba ya katse wayar. Ita kuma tsayawa jiran shi tayi a wurin. Ya shawo kwanan gidan su kenan yaga wata mota ta taho a guje. Da yan dabaru irin nashi na kwararren matuk'i ya kauce mata sannan ya juyar da kan motar shi zuwa saitin gate d'in gidan su amatu...... Ku biyoni dan jin yadda zata kasance 😎 [2/19, 7:28 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''      Page 49-50 Abdulrahman kam ko ajikin shi dan beko yi kokarin ganin na cikin motar ba yaci gaba da tsala gudu kamar wanda zai tashi sama. Daman hake yake tuki, Allah ne dai kawai ke kare shi amma da yanzu ya dade da zuwa barzahu Abdulraheem na isa ya  danna horn da k'arfi me gadi ya bud'e mashi. Lokacin daya shigo Amatullahi na tsaye dan bata koma cikin gida ba. Cike da tsoro ta k'araso wurin shi tace Abdul ya naga ka canza kaya da mota?? Abdulraheem yace kamar ya na canza kaya da mota?? Amatullahi tace Abdul ba yanzu kabar gidan nan ba? Daf da ita ya matso yace kina nufin yanzu nabar gidan nan? Girgiza kai tayi alamar eh sai yace toh bani bane Abdulrahman ne. Zaro ido tayi muryar ta na rawa tace Abdul baa...kai... bane? Ko ansata beyi ba  rai a b'ace yace kina nupin kice mun bazaka iya banbance tsakanin na da Abdulrahman ba?? Hawaye ne ya fara ambaliya a fuskarta tace wallahi Abdul kuma matuk'ar kama sosai, kuma naga kullum cikin canza mota kake shiyasa da naga yazo da wannan motar banyi wani tunanin komai ba kuma bai nuna mun wata alama da zan gane bakai bane, sai ya kyaleni ina ta zuba surutu. Duk bacin ran da abdulraheem ke ciki saida yaji kamar yayi dariya saboda yadda tayi maganar. Sai yace daman ina kuwa zai fad'a maki ai basaja yayi maki amma kibar kukan nan ki saurareni kiji abunda zan fad'a maki. Cikin muryar kuka tace toh. Abdulraheem yace indai har kina sona to dole ki guji Abdulrahman kuma yadda zaki iya banbance mu shine ki dinga lura da zoben nan dake hannu na, yayi mata nuni da farin azurfan dake mak'ale a tsayar shi na tsaka sannan yace da yanayin kalaman mu da kuma d'abi'un mu. Kuma abu mafi saukin yadda zaki banbance mu shine, tunda bashi da number ki nasan dole aikowa zaiyi, kinga ko da haka kina iya ganewa. Dan haka sai ki lura karkije kiyi kwab'a. Ya fada yana murmushi. Bata rai tayi ta share hawayenta tace Allah sai naci mashi mutunci idan ya kara zuwa gidan mu, wai kaji irin hirar da mukayi dashi kuwa? Ya girgiza kai yace bana bukatar ji kawai a wuce wurin. Nan suka rufe wannan shafin suka dauko wata hirar daban. ***** Bayan wata biyu Daddyn Amatullahi ne tare da daddyn Abdulrahman da kuma abba suna tattaunawa akan maganar su Abdul dan har yanzu babu wata tsayayyar magana, shi kuma daddyn amatu yaji shurun yayi yawa ne kuma ga kaya da sadaki nan gida shiyasa ya tunkare su da maganar dan yaji inda bakin zaren yake. Abba ne ya fara magana yace dan Allah ya kara  hakuri insha Allah zasu tari yaran suji, indai har babu wata sulhu a tsakanin su za'a tuntub'i ita amatullahi da bakinta ta fad'i wanda takeso. Daddyn Abdulrahman yace eh wannan hakane dan Allah Alhaji kayi mana hakuri nan bada dadewa ba zakaji mu. Daddyn Amatullahi yace ai babu komai. Bangaren su Abdul kam ba'acewa komai dan yanzu wata shaquwa ce mai karfi  fiye dana da ta kara shiga tsakanin Amatullahi da Abdulraheem. Kullum cikin tattali da kyautatawa junan suke a inda Abdulrahman kuma tun lokacin da Abdulraheem yayi mata hudubar yadda zata banbance su ta farayi wa Abdulrahman wulakanci. Kuma duk wani wulakanci da batan ci da zatayi mashi bazai hana gobe ya dawo ba. Yanzu haka saboda nacin shi harya kai ga sanin shagon saloon d'inta saboda ranar dayazo gidan su yace ana kiranta kin fitowa tayi shi kuma yaki wucewa yana tsaye harta fito zataje shago. Nan ne ya fara binta harya fahimci cewa shagon ta ne. B'angaren Abdulrahman da Abdulraheem kam babu wata jituwa a tsakanin su, Kai suna ma dadewa basu ga juna ba, sai dan wani lokaci haka in Abdulrahman yazo ganin ammie shine in yayi daidai da Abdulraheem na nan zasu ga juna, ko gaisuwa wuya takeyi musu dan kowannensu da irin nashi Jan aji girman kai. Hatta da Abba da daddy sun tarasu akan su sulhunta kansu amma har yanzu abu yaci tura dan kowannensu gani yake idan ya fara magana ai kamar ya bayar da kanshi ne. ***** kamar kullum yauma, a hanyar shi ta zuwa wurin ta yake, amma ba gidan su ya nufa ba dan yasan a irin wannan lokacin tana shago. Da Isar sa ta gefen shagon ya paka motar shi yana daga ciki yana kallon daidai saitin kofar shagon. Kusan awa daya sai gata nan ta nufo wurin motar ta dake pake a gaban nashi. Batare da tayi tunanin komai ba ta karasa inda motar ta take. Ameerah dake gefenta suna dan hirarsu gwanin sha'awa sai tace laaa amatu na manta da wayata a shago bari inje in dauko. Amatu ta amsa da toh sannan ta karasa wurin motar ta tsaya, ameerah kuma ta koma shago dan dauko wayar ta. Abdulrahman kuma ganinta tsaye a jikin motar ne ya bashi daman fitowa, cikin takunshi na kasaita ya nufo ta. Lokacin tana latsar wayanta. Kanshi turaren shi ne ya bugi hancinta, sai lokaci daya kawai taji wani tsanar shi ya kara shigarta. Dan ko ba'a fad'i ko waye ba kamshin turarensa ya bayyana. Tsuki tayi, tayi kwafa zata shige motar ta yayi saurin shan gabanta, cikin marairaicewa yace Amatullahi ki taimake ni wallahi zan iya mutuwa idan na rasa ki plsss my Amatu help me..... A hasale ta dago kanta ta kalleshi idonta na cikin nashi tace wai kai wani irin nataccen mutum ne? Wace irin zuciya gareka ne da bakasan an kuntata mata ba?? Cikin daakiya da dauriya yace zuciyar kare gareni! Sakwakwa take kallonshi, a ranta tace anya yana da hankali kuwa? Sai ya katse ta ta hanyar kiran sunanta yace Amatullahi duk wani abu da zaki fada bazai taba sani in daina sonki ba saboda sonki a jini na yake kuma ki sani indai akan sonki ne sai da na mutu badai sonki ya fita daga zuciyata ba. Yana fadar haka ya wuce fuu ya shige motar sa ya barta nan tsaye. Ameerah ce ta karaso wurinta tace Amatullahi shiga muje ki rabu dashi kawai. Dake duk wani abu dake faruwa ameerah tasani shiyasa batayi mamakin ganin shi ba dan ba yau farau ba. Nan suka shiga mota Amatullahi taja suka wuce, wani dan cafe suka nupa inda zasu duba result dinsu na jamb dan har sun rubuta. Bayan sun shiga ne suka bada sunan su da kuma jamb slip dinsu. Nan aka duba musu kuma cikin ikon Allah duk sun samu makin da akeso dan amatu nada maki dari biyu da ashiri ameerah kuma nada maki dari biyu da uku. Nan suka fara murna suka bawa me shagon kudi suka wuce. Direct gidan aunty hajara suka nufa. Cike da murna suka isa palon. Lokacin aunty hajara na kitchen, aikuwa kitchen din suka nufa kowannensu da slip dinshi a hannu. Amatu ce ta fara mikawa aunty hajara slip dinta tana murmushi. Aunty hajara na gani ta rungume ta tana cewa Allah mungode maka, muga naki ameerah. Bata rai ameerah tayi ta fice daga gidan tana cewa tunda ba'a damu da ita ba mummy zataje ta nuna ma. Su kuma dariya sukayi, aunty hajara tace lallai yau daddyn ki zaiji dadi kuwa. Murmushi amatu tayi tace bari taje tabi bayan ameerah Gidansu ta tafi inda ta tarar da ameerah sai washe baki take mommy na zuba mata albarka. Da amatu ta shigo hararan ta mummy tayi tace me kuma ya kawo ki wurina? Cikin yanayi na shagwaba Amatullahi ta karaso wurinta ta daura mata slip din a cinyarta tace haba mummy duba fa ki gani maki na yama wuce na ameerah. Cikin wasa mummy tace toh sai me badai duk kun samu yadda akeso ba. Ameerah tace eh mana mummy, yanzu ma yaya Usman (mijin aunty hajara) nake jira ya dawo in nuna mashi. Amatullahi tace waton yaya kika sani banda daddy ko? Ameerah tayi saurin magana tace injiwa ai daddy shine kan gaba. Shi daya dau nauyin makaranta ta ai dole in nuna mashi dan yaji dadi. Ta karasa maganar gami da mikewa ta nupin kitchen dan jin yadda cikinta ke kugi saboda yunwa. Amatullahi kuma ansar slip d'in su tayi takai d'aki ta aje, akan in daddy ya dawo ta nuna mashi dan baya ma k'asar baki d'aya. Bayan ta dawo ne ta tarar da ameerah har ta zuba musu abinci. Nan ta zauna suka fara ci suna hira. ********** Abdulraheem ne tare da abba suna tattaunawa akan maganar sato Amatullahi da sukayi. Abba yace wa Abdul shi kullum cikin damuwa yake indai ba mayar da kudin nan yayi ba hankalalin shi bazai taba kwanciya ba. Sai Abdul ya fara dan lallashin Abba da kalamai masu dadi yana cewa ai yanzu idan ya fad'a mashi zai iya hanasu auren yar'shi kawai yayi hakuri ya bari bayan aure sai ya sanar dashi. Abba ya amsa da toh dan ya gamsu da shawarar shi. Nan suka dan tattaba hira daga bisani Abdul ya wuce. Bayan Abdul ya fita ne Amatullahi ta kira shi take fad'a mashi ai result dinsu ya fito tun shekaran jiya kuma Allah ya basu sa'a ita da ameerah. B'ata rai yayi kamar tana kallon shi yace shine baki fad'a mun ba sai yau ko?? Hakuri ta fara bashi harya hakura yace gashi nan zuwa gidan basu. A b'angaren Abdulrahman kuma yanzu ya fito daga lecture, duk yagaji ga wata yunwa da yakeji a d'ayan b'angaren zuciyar shi kuwa babu abunda idanuwan shi ke mararin gani kamar Amatullahi. Daidai zai shiga motar shi kenan wani sabon aboki da yayi mai suna fahad. Ya tare shi, shima lecturer ne a BASE UNIVERSITY dake cikin garin abuja, nan suka gaisa inda ya nemi Abdulrahman daya sauke shi saman hanya saboda motar shi tad'au zafi bata iya tashi. Badan yaso ba yace ya shiga ya sauke shi, nan suka fita inda suka kama hanya sai wuraren anguwar su Amatullahi ya ajiye shi. Shiko da yaga haka da yayi wahala biyu gwara kawai ya wuce gidan su Amatullahi tunda daman yayi niyar zuwa wurinta. Haka ya d'au hanyar zuwa gidan su amatu ba tare daya dubi halin da yake ciki na jin yunwa ba. A bakin gate din gidan su ya faka motar shi yana jiran yaga fitowarta, dan yasan koya aika a kirata ba fitowa zatayi ba. Abdulraheem kuma dake saman hanyar zuwa gidan su Amatullahi, ya kawo kusa da gidan su ya hangi wata had'addd'iyar mota ta paka a daidai gate din shiga gidan. Be kawo komai ba kawai ya karaso kafin yakai ga saita kan motar shi ta inda zai samu damar shiga kai tsaye sai ya yayi horn da k'arfi dan motar ta bashi hanya saboda ya lura akwai mutum a cikin motar. Abdulrahman kuma yi yayi kamar bada shi ake ba ya wani sha toka cikin mota yana cewa yau zamu gani ko ni ko kai. Abdulraheem ko wani haushi ne ya kamashi ya fito a fusace ya............ Plss share [2/20, 9:56 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''      Page 51-52 "Abdulraheem ko wani haushi ne ya kamashi ya fito a "fusace ya karaso wurin motar" Abdulrahman, ya d'an bubbuga motar saboda motar ansa mata tinted glass sai ya zamana baya iya ganin na ciki, "amma shi Abdulrahman sarai yana kallonshi, sai ma ya kawar da kanshi ya fara latsar wayanshi yana murmushi mugunta". "Abdulraheem dake waje,  fuskar nan tashi a murtuke, "yacika yayi taf, jira kawai yake a tab'o shi ya fashe". Wayar shi ya d'auko yayi dialing number Amatullahi. " ji kawai nayi yace am at d gate" sai ya katse kiran. "Baifi minti uku da kiranta ba sai gata nan ta fito harabar gidansu, "nan taga bata ganshi ba sai tasa kai ta fito waje". Tana fitowa ta ganshi a tsaye fuskar nan tashi babu walwala. "Saurin karasowa wurin shi tayi, " muryar ta kasa-kasa tace my Abdul". yana naga Abdulrahman ko tare kuka zo ne? Cikin ranshi yace gaske dai yaki matsa mun in wuce amma a fili wata uwa harara ya watsa mata yace kin tab'a gani da tare dashi ne?? Gyad'a kanta tayi alamar a'a. "Shi kuma dan ya batawa Abdulrahman rai kamar yadda shima ya b'ata mashi rai sai ya dan yalwata fuskar shi da murmushi yace "my baby tunda yaki bani babbar hanya in shiga bari mubi ta k'aramar k'ofa ko,"ya fad'a had'e da d'age girar sa sama". "Murmushin itama tayi suka jero zasu shiga ciki". aikuwa babu shiri Abdulraheem ya fito da hanzarin shi yasha gaban su gami da "shaqo kwalar rigar Abdulraheem ". " yana huci kamar wani zaki yakai hannu zai naushi Abdulraheem, abdulraheem ya kauce masa had'e da cire hannun da Abdulrahman ya shaqo kwalar rigan shi da k'arfi". "Yace what d hell are u? Waye kai dahar zaka shiga gona ta? To bari kaji kaja wa kafafunka kunne akan karsu kuskura su sake h'aduwa da nawa a k'ofar gidan". Idan kuma ba haka ba, " u shall see it. Abdulraheem ya fad'a a tsawace. "Tunkaro shi Abdulrahman yayi rai b'ace yace gidan ubanka ne da zaka gindaya  mun sharud'ad'a ko kuma kai uba na ne da zaka bani umarni in bi?? Toh let me tell u, "wallahi baka isa ba"..... Abdulraheem ya katse shi, yace karka kuskura kamun rashin kunya yanxu in fasa ma bakin nan. "Abdulrahman ya waro ido a zuciyar shi yace ya fasa mun baki? Shi a su wa?? Sai shed'an ya dunguza shi aikuwa ya kusanto shi har suna jin saukar numfashin junan su yace fasa mun bakin mana? Yana kara shigewa jikin shi had'e da cewa ai bansan ka cika ba sai naga baki na yana jini". "Yadda ya wani shige jikin shi ne ya kara bashi haushi", aikuwa yakai mashi naushi a gefen kuncinshi" Abdulrahman da yaji zafi sai kawai ya rama" nan suka fara kokawa Amatullahi na ihu tana ture Abdulrahman da dake faman kai ma Abdulraheem naushi duk da shima din ba baya ba. "Ganin fad'an yaki tsayawa ne yasa Amatullahi ta fasa wata irin "razananniyar kara" wanda ni kaina sai da biro na fad'i kasa. "Cikin rud'ewa kowannensu yayo kanta Abdulrahman yana haki kamar wanda yasha gudu yace baby meya faru?? Banza tayi mishi ta amsa Abdulraheem da yake kokarin jan hannunta su shiga cikin gida". Abdulrahman ya shawo gaban su yace ka saketa nace? Wata yar murmushi yayi saki wadda a iya leb'on shi kawai ta tsaya zai yi magana Amatullahi ta riga shi". " tace bazai sakeni ba! Wai kai Abdul yaushe zakayi zuciya ne iyee "to wallahi daga yau ka k'ara zuwa gidan mu sai nayi karar ka", ta karasar maganar a yayinda hawaye ke zuba a kumatun ta wanda batasan dalilin zubansa ba. "Abdulrahman yace Amatullahi ni zakiyi kara? Ni d'in yana magana ne tare da nuna kanshi yace baby yanzu akan wannan abun zakiyi karata?? Murmushin da bekai zuci ba ya saki yace hmmmm Amatullahi sedai ko kiyi karata amma kisani zuwa gidanku tamkar zuwa wurin kiwo ne. "Sannan ya juyo kan Abdulraheem yace kai kuma zamu sake had'uwa. Yana kai nan ya shige motar shi ya fece a tsiyace. Dariya Abdulraheem yayi yace banza kawai mara zuciya ai ina nan akan bakata.  Amatullahi ma Murmushin tayi tace su shiga cikin gida, " hannun su na sarke dana juna suka nupi kofar shiga cikin gidan, daidai lokacin ameerah ta fito daga cikin gidan zata wuce gida. "Wani kolo abu taji ya tsaya mata a makoshi wanda take jinshi tamkar an dasa mata karfen darma mai dan karan zafi. " dafe zuciyar ta tayi tana shirin komawa ciki dan  bazata iya jurar ganin su haka ba. "Amatullahi kuma ganin ameerah yasa tayi saurin zare hannunta daga na Abdul tana kiran sunan ameerah dat shige gida a guje. Batare data damu ba sukaci gaba da hirar su. Ameerah kuma cin karo tayi da mommy data fito daga daki" mummy tayi saurin tsayar da ita tace ameerah meya sameki kike kuka? Kuka kuma" ta shafo kumatunta taji eh lallai tabbas ga hawaye a fuskarta. Cikin son boye damuwarta tace mummy ba kuka nake ba ruwa ne. Mummy tace shine zuciyar ki ke bugawa haka da sauri? Ameera tace eh" mummy tace ameerah wai meke damunki ne, kinga yadda yanayin ki ya sauya kuwa? Kodai wani abun ne ya sameki da kika fita? Tuni ta fara tuno yadda taga hannuwan su sarke dana juna, take taji wani irin kishin Abdulraheem ya shige ta, "tama manta da mummy na wurin sai kawai ta fashe da kuka gami da dafe zuciyar ta dake faman zugi. "Rikon da mummy tayi mata ne yasa tayi saurin share hawayenta murya na rawa tace wallahi mummy babu abunda ke daa........... Bata karasa fad'a ba sakamakon tarin daya sarke ta, lokaci guda ta fad'i a kasa. Da sauri mummy ta sunkuya kasa tana bubbuga ta amma bata tashi ba, ruwa ta dauko ta yayyafa mata amma bata tashi ba. " nan mummy ta rude ta fita waje tana neman agaji" nan tarar da Abdul da Amatullahi a tsaye. "Suma babu shiri sukayo kan mummy dan yadda ta fito a rikice yasa suka gane babu lafiya". Batare da tayi magana ba tayi musu nuni da hanyar palour. Nan suka shiga palon inda suka tarar da ameerah kwance bata motsi. Abdul ne ya dauke ta da sauri yayi hanyar waje da ita. Nan suma suka bishi yasa ta a mota Amatullahi ta shiga gaban mota. "Mummy kuma ta zauna gidan baya tare da daura kan ameerah saman cinyarta. Direct asibitin su ya wuce dan yafi kusa daga inda suke. A harabar asibitin su ya paka mota sannan ya fita da sauri ya kirawo wasu nurses guda biyu. Da sauri suka iso suka ansa ameera suka shiga da ita emergency room. "Taimakon gaggawa suka fara bata "cikin ikon Allah sai gata ta farfado, ganin kanta a gadon asibiti ne kuma ga drip ansa mata yasa ta kwalla ihu. "Abdulraheem dake bakin kofar dakin yana magana da wata nurse sai jin ihunta yayi. Da sauri ya bude kofar ya shiga inda ya tarar da ameera na kokarin cire drip din da aka sama ta. Cikin kuzari ya isa gareta ya rike hannunta, yana kokarin........ Plsss share [2/21, 9:38 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''      Page 53-54 "Cikin kuzari ya isa gareta ya rike hannunta yana kokarin mayar da drip din a hannunta, ita kuma sai turjewa take tana nema ta fincike ta sauka daga gadon. "cikin yan dabaru irin nasu na likita yayi mata allurar bacci" sannan ya zare drip din ya gyara shi yadda ya kamata. Kare wa fuskarta kallo yayi sai yaji ta bashi tausayi "duk da cewar besan abunda ke damunta amma a iya gwajin da yayi mata ya gane damuwa ce tayi wa zuciyarta yawa". " kawar da fuskar shi yayi daga kallon da yake mata, ya kwashi wasu files daya shigo dasu ya fice daga dakin. "Yana fita sukaci karo da mummy da Amatullahi" "Cike da damuwa Amatu tace Abdul ya jikin ameera? "Abdul yace alhamdulillah yanzu haka ma ta samu bacci". Mummy dake tsaye a wurin cikin godewa Allah tace zan iya ganinta kuwa? Abdul ya amsa da eh. Nan suka shiga dakin, "Amatu tayi saurin karasawa wurin gadon da ameerah ke kwance" hawaye na zuba a fuskarta tace my ameera ki bude idonki ki kalleni......mummy tayi saurin katseta ta hanyar fad'in amatu miye haka? Keda zaki mata addu'ar samun sauki shine zaki wani tasata a gaba kina kuka, "miye amfanin kukan naki? 'Amatu ta juyo ta kalli mummy "tace mummy kukan tausayinta nakeji, bakiji abunda abdul yace ba wai damuwa ce tayi mata yawa, kuma mummy kin fa san halin ameerah da zurfin ciki" abu bekai abu ba zata iya mayar dashi abun damuwa and mummy ni nasan cewa akwai abunda ke damun ameera, "sau tari nasha jinta tana wasu yan maganganu ko kuma kiji tayi shuru tana tunani kuma kona tambaye ta sai tace babu komai". " idan baki manta ba watannin baya datayi ciwo dakyar da iya bud'ar baki ta fad'a mun abunda ke damunta" Ajiyar zuciya mummy ta sauke "tace hakane Amatullahi amma abunda nakeso dake shine kiyi mata addu'a Allah ya yaye mata damuwarta kinji ko? "Tau Amatullahi ta amsa dashi". "Kallonta mummy tayi tace ta zauna ita zataje gida ta sanar wa aunty hajara abunda ke faruwa" Amatullahi tace toh" daga nan tayi mata sallama ta wuce. "Bayan ta fita ne Abdulraheem ya shigo dakin lokacin amatullahi na shirin yin sallar magariba, shi kuma har yayi nashi sallar, ganin zata tada sallah ne yasa shi komawa. "Bayan yan mintuna kalilan sai ga mummy tare da aunty hajara da kuma mijinta. "Aunty hajara a kage take dataga halin da ameerah ke ciki dan hankalinta a tashe yake shiyasa bayan sun shigo asibitin ta rigasu shiga da sauri", wata nurse ce ta nuna mata dakin da a kwantar da ameerah. "Da hanzarinta ta shiga, cikin tashin hankali ta karasa wurin da ameera ke kwance. Kwallace taf a idonta tace ameerah sannu ya jikin ki? Ameerah da yanzu ta farka daga bacci, cikin kasalalliyar murya tace aunty lafiya ta kalau ki daina kuka."Cikin tausaya mata tace ameerah na daina kuka, ta fad'a gami da share hawayen daya zubo mata. Usman (mijin hajara) dake coge a bayan hajara yace ameerah ya jikin naki? Ameerah tace alhamdulillah naji sauki yaya. Tau Allah ya kara sauki, ameera ta amsa da ameen. Nan suka dan soma hira suna jan ameerah da hira dan su kawar mata da duk wata damuwa dake tare da ita. suna nan har kusan karfe goma na dare daga bisani suka mik'e zasu wuce, mummy tace ita zata kwana, aunty hajara tace a'a ita ya dace ta kwana. Sai Amatullahi tasa kukan shagwaba ala dole wai ita zata kwana. "Abdul da yanzu ya shigo nan yasa baki akan abar amatu ta kwana da ita tunda ma ameeran taji sauki ko zuwa gobe ana iya sallamar ta Kuma ma akwai nurse masu kwanan dare koda wani abu ya faru". Mummy "tace tau ai bakomai", nan suka fita har harabar asibitin sukayi musu rakiya, Abdulraheem ma wucewa yayi amma sai daya had'a amatullahi da wasu nurse guda biyu kafin ya wuce. "Bayan amatu ta dawo dakin ne ta tarar da ameera kan sallaya tana rama sallolin da suka wuceta, "bayan ta idar ne ta dawo bakin gado inda amatu ke zaune tana murmushi tace my amatu daman ina Allah Allah in idar da sallah in tambaye ki waya kawoni asibitin nan? Amatullahi tace Abdulraheem ne ya kawoki, Kinsan lokacin da abun ya faru muna cikin gidan shine mummy ta fada mana yayi sauri ya kawoki wannan asibitin. Murmushi ne ya bayyana a fuskar ameera tace Allah sarki gaskiya Abdul nada tausayi. "Cikin ranta ko jindadi take Abdul ya ceci ranta, "wani taci daji a lokacin data tuna cewar shi fa baiko san tanayi ba ita kadai ce ke haukarta, sai nan danan taji irin kololon dazu na shirin tokare mata makoshi, "da sauri ta kawar da tunanin saboda kar amatu ta gane. "Amatullahi kuma harta dan fara fuskantar wani abu sai ameerah ta katse ta da cewa suje kwanta dare yayi. Amatullahi batace komai ba illah fatan Allah yasa su wayi gari lafiya. Daga nan kowa ya kwanta makwancin shi.       Washe gari Tunda safe Abdul yayi saukon zuwa asibitin, dan harya rigasu mummy zuwa amma suma bada dadewa ba suka iso. Gaida junan su sukayi suna mai tambayar amatu yamai jiki, amatu "tace tau da dama dan jiya ameerah batayi wani baccin kirki ba, in banda sake-sake da tunani datayi tayi wanda a cikin daren ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani. "Koda asuba tayi Amatu hankali a tashe taje ta kirawo nurse din da Abdul ya hadata dasu, nan suka danyi mata allurori sannan jikin nata ya dan lafa. Abdulraheem kuma Amatullahi na fada mashi yayi saurin shiryawa yazo asibitin shiyasa ma ya riga su mummy zuwa. Abdulraheem dake kusa da Usman, cikin yanayi na damuwa yake tambayar kanshi toh wai meke damun ameerah ne?? Cikin son nemo mafita ya dubi dukan su dake cikin dakin yaga kowa damuwa ce shimfide a fuskar shi musamman ma hajara da Amatu. "Mummy ce tayi magana tacewa Abdul ko za'a iya bata abinci? Abdul yace eh, "nan mummy tasa Amatu ta zuba mata hadaddiyar jollof din taliya   da alayyahu da sauran kayan lambu. Bayan tasa ne mummy ta ansa plate din taje bakin gadon da "ameera ke kwance ta tayar da ita zaune ta mik'a mata ruwan gora tace taje ta wanke bakinta" Sukuku ameerah ta tashi dan babu wani k'arfi a tattare da ita, haka ta shiga dan karamin toilet din dake cikin dakin ta wanko bakinta ta dawo. "Zama tayi tana mai fuskantar mummy data debi abinci a spoon tana mika mata. "Bude bakinta tayi ta karba dan tasan halin mummy batason musu. Haka mummy ta dinga dura mata abinci sai da "ameerah ta fara rigima tana cewa cikinta zai fashe sannan mummy ta kyaleta". "Aunty hajara kuwa hararanta ameerah tayi tace ai gwara da kikayi mata dure, dan inba dan ke da bazata ci ba. Murmushi kawai mummy tayi batace komai ba. "Amatullahi dake gefen aunty hajara tasata tayi a gaba wai sai taci abinci, dan tun jiya bataci komai ba. "Usman ne yace shi zai wuce karya makara, sai aunty hajara tace ya jirata ya sauke su tare da Amatullahi. "Amatu tayi saurin dagowa ta kalli aunty hajara tace nidai aunty bazan je ba ina tare da ameerah. "Sai aunty tace a'a ki tashi muje kiyi wanka zuwa da rana sai mu dawo, "kinga yanzu ga mummy nan zata zauna da ita. Bata rai tayi,"ta fara bubbuga kafa a kasa" sai mummy ta harare ta had'e da cewa ta tashi su tafi. "saida Abdul ma yasa baki yace sannan ta hakura badan taso ba suka wuce. Tare suka fito Abdul na gefen Usman, suna magana, a haka har suka kai harabar asibitin, daga nan sukayi sallama suka wuce. "Abdulraheem ma kiranshi akayi a waya , sai dai banji abunda akace ba naga ya shige mota. "Gidan su ya nupa, inda daga fitowar shi wani abokin shi ya kirashi, "nan ya amsa wayar suna ta hira, sai dariyar Abdul kawai kakeji, rufe motar shi yayi ya nufi part din ammie still da wayar a kunnen shi. "Haka ya shiga cikin palon yana waya gami da dariya harya isa saman kujera "two seater yana ta wayar shi, kusan minti biyar yana waya kafin ya datse kiran". "Ajiye wayar yayi yana murmushi, ya mike kenan sukayi ido biyu da Abdulrahman dake zaune saman kujera. Aikawa junan su harara sukayi, kafin Abdulraheem ya mike zai haura sama sai yaji kamar motsin ammie a kitchen". "Fasa haurawa yayi ya dawo ya nufi kitchen din. Ta bayan ammie yaje da niyar ya bata "tsoro sai tun kafin ya bata tsoron" tayi saurin juyowa da taji kamar motsin tafiyar mutum. "Murmushi suka sakarwa junan su ammie tace likitan turai kenan kace harka iso?? Yace eh ammie nah "kinsan duk abunda nakeyi idan kika kirani ya zama dole ne in barshi in amsa kiran mahaifiyata". "Murmushin jindadi ammie tayi tana kallon Abdul tace ya jikin ameeran ne? "Abdul yace taji sauki sosai kila ma yau ya sallame ta. Ammie tace tau Allah ya kara sauki. "Ya amsa da ameen". "Abdulrahman kuma Abdulraheem" na shiga kitchen, "yayi saurin tashi yaje ya dauki wayar Abdulraheem yana addu'ar Allah yasa batada security, "aikuwa yaci sa'a batada. Nan ya washe baki yana cewa idan kunsan wata baku san wata ba. "Nan yayi sauri ya shiga contact dinshi yana dubawa, "can yagano wata number ansa my baby" take zuciyar ta bashi number amatu ne. Cikin gaggawa kwashe number, ya ajiye wayar yadda ya ganta sannan ya juya zai koma kujerar da yake zaune sai..................... 👇🏽👇🏽👇🏽     Follow     Vote   Comment @lashminzy (wattpad) [2/21, 1:58 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Яυ∂αиι fαиѕ gяρ 1&3 ιиα мιкα ѕαкσи gσ∂ιуαтα α gαяєкυ, α gαѕкιуα ιиα ʝιи∂α∂ιи ¢σммєитѕ ∂ιикυ, ιиα αℓfαнαяι ∂αкυ ❤❤❤❤      Page 55-56 "Sai yaji motsin su, da sauri har yana dan hadawa da gudu ya koma ya zauna, yana latsar waya s kamar bashi ba". "Fitowa sukayi ammie na rik'e da wata food flask mekyau. Bayan sun k'araso wurin shi ne ammie ta mik'a ma abdulrahman food flask din" tana cewa yayi sauri ya wuce karya makara. "Abdulraheem ya wani langab'ar da kanshi bisa kafad'ar ammie, cikin sigar shagwab'a "yace ammie waton shi kawai kika sani, shine harda wani sa mashi abinci ya tafi shi? "Ammie tace bakaga zai makara bane shiyasa nace ya tafi dashi yaci a can". "Abdulraheem ya bata rai yace Allah ammie inda ni ne ko makara" zanyi sai kin rikeni kin bani amma shi kika bari ya tafi dashi ko? "Ammie tace tau ba shine babba ba" "Gabadayan su suka kalli juna,"Abdulraheem ya kara shan toka, Abdulrahman kuma dadi yaji wai ance shine babba". Aiko da fara'ar shi yace cewa ammie sai ya dawo. "Ammie tace a dawo lafiya". "Sai daya kai bakin kofa sannan ya juyo ya kalli Abdulraheem yace kani babu ko rakiya?? "Abdulraheem ya wani washe baki saboda duk abun nan da sukeyi babu wanda ya sani, "dan in suna gaban daddy ko abba ko ammie far far suke wa junan su. "Sai ya waske kawai yace kaje bana son kayi lattin shiga makaranta anjima zamu hadu." Ficewa yayi batare da yace komai ba, Abdulraheem kuma da harara yayi mashi rakiya. "Zama ammie tayi saman kujera "tana mai fuskantar Abdulraheem tace" yauwa son jiya abbanku yace wai yau ku hadu gidan daddyn ku akwai maganar da zakuyi kaji ko? Abdul ya amsa da toh, gami da tambayar ta "wace magana zasuyi". "Ammie tace be fadamun ba amma nasan dai maganar bazata wuce akan naku ba, "dan jiya naji alhaji yana waya kuma da alama daddyn amatu ne dan naji sai hakuri yake ta bashi yana cewa "insha Allah yau zai jisu". "Ajiyar heart Abdul ya sauke yana tunanin yadda zata kaye, danshi yasan dai bazai iya hakura da Amatullahi ba..... Ammie ta katse shi ta hanyar "cewa Allah yasa a kwashe lafiya dan dai ita bataga wata alamu na cewa daya daga cikin su ya saduda ba". Abdul yace ameen ammie na insha Allah komai zai tafi yadda ake so. "Tashi ammie tayi ta shiga kitchen ta zubo ma Abdul, breakfast, ta kawo mashi, lokacin shi kuma yana shirin tashi ya wuce, "ammie ta dakatar dashi tace sai yaci abinci, haka ko ta zauna gaban shi saida yaci ya koshi kafin ya tashi ya fita, "ammie kuma na binshi da adawo lafiya. Motar shi ya shige, mai gadi yayi saurin bude gate ya fice, "a hankali yake tuki dan shi baya tsala gudu kamar Abdulrahman". Tuk'i yake hankali kwance duk da cewar yana tunanin yadda zasu kwashe dasu daddy hakan bai hanashi tafiya a hankali ba. Harya iso asibitin a slow yake tafiya. Direct wurin da yake paka mota yaje ya paka motar sannan ya fito yasa kai cikin asibitin, kodaya shiga dak'in da aka kwantar da ameera baiga kowa ba, ita kuma idanunta rufe suke kamar mai yin bacci. "Zuwa yayi can karshen gadon ya jawo plastic chair ya zauna yana facing dinta, "cikin sanyin murya ya kira sunanta, "zuciyar tace da buga a lokacin dataji ya kira sunanta dan yayi amfani da wata iriyar murya ce ya kira sunanta. Kara runtse idonta dake rufe tayi batare data kalle shi ba. "Shi kuma jin tayi shuru sai ya kara kiran sunan ta, "a hankali ta amsa shi gami da bude idonta ta watsa su akan nashi. Abdul yace ameerah damuwa bashi da amfani, ita karan kanta kalmar damuwa ba'a sonta saboda ba karamin illatar da dan adam take ba. Ameerah duk wani abu dazai zama damuwa ga zuciyar dan adam guje mashi akeyi saboda illolin shi, naga ke ba wata ma'abociya "kasuwanci ko hulda da jama'a bace" amma ace wai damuwa tayi maki yawa?? Gaskiya dai akwai wani abu. "Shuru yayi na yan dakika sai can "yace ameerah ki daure ki fada mun damuwarki saboda ayi gaggawar warware maki ita, "kinga auntyn ki da Amatullahi suna cikin damuwa sosai, "yanzu haka su suka sani in tambaye ki abunda ke damunki ko Allah zai sa ki fada mun". "Dan Allah ki fada mun nayi maki alkawarin bazan fadawa kowa ba kinji? Kamar bazata yi magana ba sai kawai ta daure tace "ni babu abunda ke damuna" Abdul yace akwai", shuru tayi bata sake cewa ko ufan ba. "Haka yayi ta shan cikinta wai ko zata fada mashi amma fur taki, "daga karshe wata dubara ta fad'o mashi, "ya kalleta sannan ya zaro wata allura daga cikin aljihun rigan shi na likita ya hada ta. "Yace ameerah tunda bazaki fada mun ba yanzu zanyi maki allura ki fita daga hayyacinki, "nasan idan nayi hakan duk abunda na tambaye ki zaki fada mun. '''A tsorace ta d'ago daga kwance da take ta zauna, gami da had'e hannuwanta duka biyu tana rokon shi tace dan Allah abdul kayi hakuri karka yi mun. Abdul "yace indai baki fada mun ba tamkar nayi maki ne. Ita kuma cike da tsoro da fargaba, "danta yadda cewa idan yayi mata allurar komai zata iya fad'a "sai kawai ta fara hawaye tana cewa karka yimun na rokeka zan fada maka. Murmushin zuci Abdul yayi yace ina jinki, "cikin muryar kuka tace ko ban fada maka ba kasan yadda "SO" yake, "Abdul miye amfani kaso mutumin da beko San kanayi ba?? "Abdul yace ban fahimta me kikeson kice?? Hawayen da suka zubo mata tayi saurin sharewa kafin tace, "ni naja wa kaina wannan damuwar saboda ina son abunda nasan har abada bazan taba samun shi ba". "Abdul yace ameera miye ne haka da kike cewa bazaki samu ba?? "Ameera tace "SO" Abdul ina son wani ne can daban wanda baiko San ina yi ba, yanxu haka shi kuma yancan zai auri kawata nan da dan wasu lukuta. "Abdul nikuma bazan iya tukarar shi da cewa ina sonshi ba. "Cike da jin tausayinta Abdul yace gaskiya naji dadi dabaki furta wannan Kalmar ba" saboda a matsayin ki na ya' mace mai hankali da tunani bai dace ace duk tsananin sonda kike wa d'a namiji kin furta Kalmar so a gareshi ba. Domin kuwa ba karamin rage kimar ya' mace yake a wurin namiji ba. "Kinyi kokari. Ameerah shawara daya ce zan baki shine kiyi hakuri ki cire shi a cikin ranki, "duk da nasan ba abu bane me sauki amma ki roki Allah ya kawo maki wanda ya fishi kuma dan Allah "kibar raina damuwa koda kuwa na dan cikin cokali ne" Kallonshi tayi da rinannun idanunta tace nagode Abdul Allah ya saka da alkhairi, hannu ya daga mata yace nop karki damu ai tamkar kanwata na dauke ki. "Murmushi tayi ta share hawayenta", har suka dan fara hira sai ga mummy ta shigo, "cikin dan jin kunya dan baiso mummy ta tarar dasu ba, 'ya fara sosa keya, sannan ya samu ya fice daga dakin". •••••• "Tun isar sa cikin makaranta yake zaune cikin mota, yana kiran number amatu bata dauka ba, "abincin da ammie ta bashi ya fara ci, "sai daya cinye tas yace alhamdulillah kafin ya sake trying number amatu duk da be tsammaci zata dauka ba sai kawai bugu daya yaji dauka". "Farinciki ne ya ziyarce shi, sai cikin zazzakar muryar shi yayi mata sallama. "Ita kuma tun daga jin sallamar shi ta gane mai magana" Tsaki tayi ta katse wayar. "Shi kuma be daddara ba sai ya kara kira sam taki dauka, "haka yayi ta kira yana tura mata sakonni da soyayya dana ban hakuri amma ba reply. "Gajiya yayi ya tada motar shi ya wuce class, lokacin har karfe tara yayi kuma tun karfe takwas ya kamata ya shiga. Tunda ya shiga class din babu annuri a fuskar shi, kamar yadda ya saba, sai dai na yau yafi ko wane lokaci dan hatta da sallamar da yakeyi idan zai shiga yau beyi ba". "Haka dai wani sukuku jiki ba kwari ya dan taba wani abu dasu ya fita tun ma kafin lokacin fitar shi bai yi ba". "Yana fita gida direct ya koma, dakinshi ya shiga kwanta yana jin zuciyar shi ba dadi". "Bayan la'asar" Abdulraheem ne tare dasu mummy dasu ameera a harabar asibiti yana musu sallama dan yanzu aka sallame su. "Amatullahi ta dan yi muryar ta kasa kasa ta kira abdul, "shi kuma dama idonshi na kanta shiyasa datayi mishi alamar yazo ya gane. "Matsowa yayi kusa da ita, cikin maganar kurame yace mene? cikin yin kasa kasa da murya tace Abdulrahman ya kirani dazu! waro ido yayi yana tunanin ina ya samu number ta sai Amatu ta katse ta hanyar cewa karka damu ko zai shekara yana kira kalmar nan da yake so bazai samu ba". "Murmushin jindadi yayi ya daga mata babbar yatsa 👍🏻alamar tayi daidai. Itama Murmushin tayi ta shige mota, tana daga mashi hannu. "Mummy ma zagayawa tayi ta shiga gidan baya ta zauna ita da ameera da aunty hajara. Musa direba yabawa mota wuta". "Bayan sun wuce ne shima ya shige tashi motar ya wuce gida. Part dinshi ya nupa direct inda yayi wanka yayi shigar kananan kaya, kuma ba karamin kyau sukayi masa ba. "Fitowa yayi da dan murmushi a fuskar sa dan yana tunanin yau za'a kai karshen komai kuma insha shi keda nasara tunda ko tambayar amatu akayi wa takeso shi zata zab'a. "Da wannan kwarin gwiwar ya nupi inda ya paka motar shi ya shige sai gidan su Abdulrahman. "Lokacin daya isa gidan yana paka motar shi sai ga daddy [2/21, 11:44 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' *سْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ* الرَّحِيْمِ _*May Allah (SWT) Bless you and your family with a restful mind, useful soul, peaceful home, commendable effort, acceptable worship, and a successful end. May He beautify your tongue with truth, heart with sincerity and count you among the dwellers of Jannatul Firdaus, Insha Allah. ʝυммα'т мυвαяαк тσ αℓℓ мυѕℓιмѕ.      Page 57-58 ''''A daki kuma Abdulrahman ne zaune a bakin gadon shi yana dialing number Amatullahi, "ita kuma amatu lokacin tana palour tana jin wayarta na ringing amma sanin ko waye ke kira yasa ta buga tsuki taci gaba da kallon ta". "Abdulrahman ko sai faman kiran ta yake, data gaji da jin karar wayar ne ta d'auka zata kashe ta gabadaya sai kawai taji tana son ta d'auka. Haka dai ta d'auka. "shi kuma cikin so da kaunar ta yace baby da fatan kina lafiya? Ita kuma cikin masifa tace lfya kalau nake "ka fad'i abunda zaka fad'a saboda ina da aikin yi" Murmushin jindadi yayi yace baby kiyi hakuri da abunda ya faru ki amince danii......cikin tsawa ta katse shi tace wallahi Abdul ban tab'a ganin mutum mara zuciya irinka ba, kai ko acikin dabbobi babu kamar ka, kuma ka rubuta ka aje, ni "AMATULLAHI MUHAMMAD LEMI", bana sonka, bana kaunar ka, "kai kasani koda duka mazan duniya zasu kare bazan taba aurenka ba because "I hate you!! "I hate you!!! Ta karasa maganar a tsawa ce. Sannan ta katse wayar. "Shi kuma a firgice ya mike tsaye da jin irin munanan kalaman da take fad'a dan duk wani zagi da barazanar da take mashi bata tab'a furta irin wa'yannan kalmomin ba shiyasa take yaji zuciyar shi ta dau zafi, duk jijiyoyin kanshi sun tashi sunyi rud'u-rud'u. Idonshi kuwa sun canza launi zuwa ja kamar garwashi. "sai ya fara tari gami da dafe zuciyar shi yana k'ok'arin ya kai zaune amma ya kasa". "Abdulraheem daya shigo kiran shi, jin kamar nishi da tari yasa yayi saurin k'arasawa wurin da Abdulrahman ke shirin zubewa k'asa.  "Taro shi yayi ya fad'o saman jikin shi. "Cikin tashin hankali Abdulraheem yace d'an uwa meya faru dakai?? meke damunka?? Waya yayi maka haka? Duk cikin rud'ewa yake mashi wannan tambayoyin. " Abdulrahman dake nishi sama-sama hawaye na zuba a idanunshi yace d'an uwa "mutuwa zanyi, "mutuwa zanyi". Abdulraheem yayi saurin rufe mashi baki da hannun shi, shima duk yanayin shi ya sauya yace insha Allah babu abunda zai sameka. "D'aura kanshi yayi saman pillow, yaje ya bud'e d'an k'aramin fridge d'in dake d'akin ya d'auko ruwan faro yazo wurin shi ya d'aga shi sannan ya bashi yasha. ''A hankali yake saukar da ajiyar heart bayan yasha ruwan, sai kuma wasu zafafan hawaye suka fara zubo mashi. "Cikin zubar da hawaye yace d'an uwa kaje nabar maka Amatullahi, "kaje a d'aura muku aure. Abdulraheem dake kallonshi kamar wani tababbe yace Abdul bakai ya kamata kabar mun amatu ba ni nafi cancanta dana bar maka ita, saboda bana son in rasa ka akan abunda baifi karfina ba "dan haka ni nabar maka ita badan komai ba sai dan Allah. "Abdulrahman yace a'a amatu bata sona, wallahi amatu bazata aureni ba....Abdulraheem ya katse shi yace ba haka bane Amatullahi na sonka, kawai tafiyar dakayi ne harna tsawon shekara biyu yasa ta fita batunka amma ina da tabbacin har yanzu tana sonka". Saboda a lokacin dana fara soyayya da ita na fahimci tana tsananin sonka sedai nikuma nayi k'okarin cire soyayyar ka a ranta na d'aura nawa. "Amma duk da haka na bar maka ita domin kuwa da tsohon zuma ake magani. "fashewa da kuka Abdulrahman yayi ya kara rungumo Abdulraheem jikin shi, cikin rawar murya yace d'an uwa bani da bakin gode maka, Allah ya saka maka da gidan aljannah kuma Allah ya.... "Abdulraheem da yake jin zuciyar shi kamar zata fashe, dan k'aramin jarumta yayi ba ya katse shi yace d'an uwa karka damu ko rayuwata zan iya sadaukarwa saboda farincikin ka". " kukan farinciki Abdulrahman yakeyi, yana kallon shi yana jin wani son d'an uwanshi na karuwa a zuciyar shi, daman can yana sonshi kawai wannan abun ne daya faru yasa shed'an yayi tasiri a zukatansu har yasa sukayi ta samun sab'ani. "D'aga shi Abdulraheem yayi yace yaje toilet ya wanko fuskar shi saboda su daddy na neman su. Ba musu ya shiga toilet ya wanko fuskar shi, sedai daga gani zaka gane yayi kuka. Abdulraheem ne ya ciro handkerchief daga cikin aljihun shi, ya goge wa Abdulrahman danshin dake kan fuskar shi sannan ta d'anyi dama-dama dan inba k'are mashi kallo kayi ba bazaka gane yayi kuka ba. "Murmushi suka sakarwa junan su a tare, kafin Abdulraheem yaja hannun shi suka nufi part din daddy".  "Da shigar su daddy ya fara musu fad'a yana cewa waton ku kun maida mu dattijan banza ko?? Yau kwana nawa da maganar da mukayi daku?? Kowannensu kanshi na duke basu ce kala ba. "Daddy yace tau bari kuji ko kuna so ko baku so na yanke hukunci, kuma "ba shawarar ku nake nema ba umarni na baku", dan haka kar wanda ya musa mun". "Abba kuma cikin sigar lallashin daddy yace alhaji kayi hakuri mana mu bisu a hankali! Daddy yace su kananan yara ne da zamu bisu a hankali?? Abba yace gaskiya ba kananan yara bane amma muji ta bakin su tukunna kafin ka zartar da hukuncin ka. Daddy baice komai ba. "Abdulraheem cikin sanyin murya yace Abba, daddy mun sulhunta kanmu. "Daddy yayi saurin kallon shi suka had'a ido, Abdul yaci gaba da cewa "a matsayina na d'an karami kuma d'an uwa ga Abdulrahman na hakura da Amatullahi har abada, "kuma nayi hakan badan komai bane sai dan gujewa halin da d'an uwana zai shiga. Kuma duk wani abu danayi na bikin Amatullahi nabar mashi kyauta "Abba yayi saurin kallon shi suna had'a ido Abdulraheem yayi saurin saukar da idonshi kasa. "Daddy daya taso da fad'a jin sun sulhunta Kansu sai ya sauko daga hawan da yayi yace Alhamdulillah Allah yayi muku Albarka, Allah yasa ku gama da duniya lafiya, kai kuma Allah ya had'a ka data mata ta gari. "Dukansu suka amsa da ameen, sai Abdulraheem yace amm wani hanzari ba gudu ba, dan Allah ina neman wata alfarma a wurinku. "Abba yace fad'i koma menene indai bai kauce wa addini ba zamu muyi maka Insha Allah. "Abdulraheem yace abba dan Allah banason a fadawa Amatullahi cewa bani zan aureta ba saboda wasu yan' dalilai nawa. "Daddy yace maganar banza maganar wofi, ya kake tunanin haka zata faru?? Abba ya katse shi yace alhaji hakan zata yiwu kuwa amma sai an fad'awa shi baban yarinya, idan ya amince da hakan tau komai zai tafi yadda akeso. " tunda kaga kamar su d'aya koni sai na kare musu kallo nake iya tantance su. Daddy yace tau shikenan tunda kace haka. "Allah yasa shi yafi zama alkhairi, suka amsa da ameen kafin daddy yayi musu izinin tafiya. " nan suka tashi suka fita, hannun su sarke dana juna, Abdulrahman yace d'an uwa bani da kamar ka, ka gama mun komai, bansan da wani baki zanyi amfani dashi wurin gode maka ba. "Abdulraheem yace karka damu u deserve it that's why, dan haka kaje ka huta ni zan wuce gida, insha Allah zuwa gobe zamuyi magana, "murmushi yayi ya mik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan ya shige motar shi ya wuce. "Bayan ya iso gida, ko cikin gida bai shiga ba ya paka motar shi ya wuce masallaci dan lokacin sallar magariba tayi, bayan an idar da sallar magariba, nan ya zauna har akayi isha'i kafin ya dawo gida. "Part din ammie ya nufa, lokacin ammie na palour ita da hanan suna kallo, jin bugun kofa yasa hanan tayi saurin zuwa ta bud'e, tana ganin shi ta rungume shi had'e da tambayar shi ina yaje dan tun dawowar ta makaranta bata ganshi ba. "Murmushi ya kakaro yace sis naje wani wuri ne shiyasa baki ganni ba. Ammie dake zaune tana kallon su tun kallo daya datayi mashi ta gane yana cikin damuwa. "Shiyasa ta dakatar da hanan dake ta faman zuba surutu dan taga baya cikin yanayin jindadi, "ita kuma hanan dake akwai yarinta saman kanta shiyasa bata wani lura da yanayin da yake ciki ba. "Tasowa ammie tayi ta jawo shi suka zauna tana kallon shi tace son meya faru?? Fad'awa yayi jikinta hawaye na zuba a fuskar shi yace ammie na rasata, na rasa Amatullahi. "Cikin rud'ewa tace Abdul fada mun abunda ya faru. Nan ya fara bata labarin tun daga halin da yaga Abdulrahman har zuwa zaman da sukayi dasu daddy. "Ammie ji tayi kamar tayi kuka dan ba karamin tausayin shi taji ba, dan ita kanta tasan yana matukar son Amatullahi, kuma da'ace ba Abdulrahman bane wani daban ne bazata taba bari Abdulraheem ya sadaukar da ita ga wani ba. "Cikin lallashin shi tace Abdul kayi hakuri ka mika lamuran ka ga Allah kuma ka dauki kaddara, saboda soyayyar dakayi da Amatu kaddara ce kuma ba matar ka bace dan kuwa wani baya auren matar wani. "Plsss karka sawa ranka damuwa wani abu ya sameka Kuma wannan sadaukarwan dakayi Allah yasa alkhairi ne kuma Allah ya saka maka da mafificin haka Allah ya baka wadda tafi Amatullahi. "Cikin zuciyar shi ko cewa yake ammie na bazan taba samun kamar Amatullahi ba domin kuwa komai nata na daban ne. A fili kuwa cewa yayi ameen ammie ki tayani da addu'a kinji?? Ammie ta amsa da toh. "Hanan dake zaune kusa da ammie wani irin tausayin yayan nata ne ya mamaye zuciyarta, duk da cewar batasan ko menene so ba amma tasan zafin idan mutum ya rasa abun shi. " kusa dashi tazo ta rungume shi ta baya, dan a duke yake ya d'aura kanshi saman cinyar ammie tace yaya kayi hakuri Allah zai baka wadda tafi aunty amatu. "Murmushi yayi wanda a iya leb'on sa kawai ya tsaya yace ameen sister nagode. Daga nan ya mike zai wuce part dinshi, ammie ta taro shi tace ya tsaya yaci abinci, amma fur yaki wai ya koshi. "Saboda karta takura mashi kawai ta rabu dashi ya wuce. Yana shiga dakinshi ya fad'a saman gado yana rusa kuka. "Yana cikin kukan ne yaji wayar shi na ringing. Plsss share [2/24, 7:53 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Wannan shafin kyauta ne ga duk mabiyin baba buhari, insha Allah sai kayi. Su oyy ban fada ba aje gida zuwa hutawa.      Page 59-60 "Dubawa yayi yaga Amatullahi ce ke kiranshi, "dumm yaji gaban shi ya fad'i, "sai kawai ya kifar da wayan, yayi mata wani irin damk'a kafin ya saketa had'e da zubar da wasu hawaye masu zafin gaske. "Cigaba da kiran shi Amatullahi tayi, shi kuma yana ji tana ringing amma ya kasa d'auka. "Tau idan ma ya d'auka yace me, tunda yanzu ba budurwar shi bace. "Gyara kwanciyar shi yayi ya kashe wayar gabad'aya dan bata bar kiran shi d'in ba. Haka yaci gaba da kukan shi yana jin wani irin zafi a zuciyar shi, "har baccin wahala ya d'auke shi.               Washe gari "Amatullahi ce a d'aki tana kiran number abdul but switched off. Duk hankalinta ya tashi dan bata tab'a kiran wayanshi taji ta kashe ba irin haka. "Cigaba da kiran nashi tayi tayi har taci sa'a ya bud'e wayar, wani farinciki ne ya ziyarce ta. Take kuma yanayin ta ya sauya sakamakon, rejecting d'inta da yayi. "Zata sake dialing kenan taji text d'inshi ya shigo. Cikin yatsine fuska ta duba ta gani, murmushi ta saki gami da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya "jin yace mata yana asibiti ne kuma daya fito zai kirata. "Tashi tayi da kwarin jiki  ta nupi toilet dan watsa ruwa. Bada jimawa ba sai gata nan ta fito, d'aure da towel. "Zama tayi gaban dressing mirror ta shafe jikinta da mai da kuma turarukka masu kamshin gaske. Simple make-up tayi wa fuskarta sannan ta shirya cikin doguwar riga light blue, "tayi rolling da gyelen shi, " sannan ta d'auko handbag d'inta dake rayate jikin gadonta, had'e da bude drawer ta d'auko wasu takardu. Fitowa tayi palour, nan ta tarar da mummy da daddy zaune suna hira. "Da murmushi a fuskarta ta karasa wurin su ta duka har kasa ta gaida su. "Cikin fara'a suka amsa mata". Daddy "yace yauwa daman ke nake jira ki kawo mun takardun. Dan murmushi tayi taje har gaban shi ta mika mashi. Daddy "yace gaskiya naji dadin ganin result dinku keda ameera, yanzu nan zanje can BASE UNIVERSITY nakai musu dan naji ance sun fara bada admission. Murmushi amatu tayi "tace eh daddy nima naji haka, daddy "yace karku damu insha Allah zaku dace Allah yayi muku albarka. "Suka amsa da ameen harda mummy dake wurin. "Sallama tayi musu, kafin ta fita, dan tana son ta leka saloon taga yadda abubuwan suke gudana dan tun ranar da aka kai ameera asibiti bata kara zuwa ba". Wurin hadaddiyar motar ta kiran range rover ta nupa, inda sai sheqi take dan kuwa tasha wanka. Shiga tayi ta tayar megadi ya wangale mata gate, " ta nupi gidan su ameerah dan tanason taga ya jikin nata yake duk da jiya taga jikin nata da sauki sosai. A bakin gate d'in gidan ta paka motar ta sannan ta fito ta nupi cikin gidan. Da shigar ta Mubarak d'an Aunty hajara wanda be wuci shekaru hudu ba yazo da gudu ya rungume ta yana cewa anci cuwit, da hausan shi wadda bai gama iyawa ba. Murmushi Amatullahi tayi ta d'agashi sama sannan ta dire shi, ta bud'e jakarta ta dauko sweet ta bashi. "Cike da murna ya ruga da gudu wurin aunty hajara da jin motsin su yasa ta fito. Murmushi ta sakarwa amatu sannan ta nemi wuri ta zauna. Itama amatu zama tayi suka gaisa sai ga ameerah ta fito. Mikewa amatu tayi taje ta tarbo ameerah suka zauna. Cikin kulawa "tace mata ya jiki. Ameerah "tace alhamdulillah besty ai naji sauki. Murmushin jindadi amatu tayi "tace yauwa daddy ya anshi takardun mu. Cikin jindadi ameerah "tace da gaske?? Amatu a'a da wasa. Dariya sukayi dukan su harda aunty hajara. Aunty hajara tace Allah sarki daddy, mukam babu abunda zamuce dashi sai Allah ya saka mashi da gidan Aljannah dan gaskiya ya kyautata mana da yawa". Ameerah ta amsa da "cewa wallahi kam aunty ai daddyn amatu ya maye gurbin abban mu. Allah sarki Allah yaji kan Abba, duk suka amsa da ameen. "Amatullahi kuwa sai murmushi take ana yabon daddy, ita kanta tasan daddyn ta mutumin kirki ne domin kuwa sau da yawa tasha jin ana yabonshi akan halayyar shi. Kuma ba shakka shi mutum ne mai tausayi, da hakuri da kuma tawakkali. Ameerah ce ta katse ta, "tace besty naga kinsha wanka ina zakije? Kai tsaye amatu tace saloon. Ameerah "tace tau bari in dauko hijabi na muje ko?? Cikin zaro ido amatu tace nikam rufa min asiri nima da kika ganni ba dadewa zanyi ba, zanje inga kayan da babu ne insa a kawo. Ameerah "tace koma dai mene sai naje, amatu "tace toh nama fasa zuwa. Ameerah "tace hmmm gaba takai ni bari ma ki gani, ta mik'e zata wuce dak'i, ta d'auko hijabi. Aikuwa Amatu tayi saurin rikota tace plsss my ameerah ki zauna ki huta kinga nima abu kawai zanyi na dawo. "Ameerah ta wani bata rai, alamun ita fa bazata zauna ba. Amatu "tace tau muje tunda kin matsa. Da sauri ta nupi dak'i ta d'auko hijabinta sukayi wa aunty hajara sallama suka fice. -------- B'angaren lubna kuwa tun sadda ta koma gida, kullum cikin kuka take,  umma kuwa dake bamai daurewa yara gindi bane sedai tayi ta mata fad'a kuma tana tayata da addu'a. Tun tana saran samu abdulrahman harta fitar da ran samun shi domin kuwa ko kiranshi tayi baya d'auka, wani abun haushi ma shine yasa number ta a blacklist, shiyasa data fahimci haka sai taji yama fita a ranta. " Kuma ga ummanta dake zaunar da ita tana mata nasiha sai hakan yasa jikinta yayi sanyi har tayi alkawarin bazata kara zubar da hawaye akanshi ba. "Umma kuwa dadi taji dan yar'ta ta fita daga damuwa da kunci. Yanxu haka ko hirar gidan su Abdulrahman batason anayi mata wai zai zama kamar ana tuna mata da Abdulrahman ne". Bari mu leka bangaren su abdul •••••••• "Abdulrahman ne tare da abdulraheem sunyi shigar kana nan kaya, duk iri daya, "sai wani sheki fuskar su keyi, kowannensu su yasa facing cap, kai ba karamin kyau sukayi ba". Masu karatu plsss ku kwatanta kyan yan biyun nan dan innace zan fayyace muku irin kyan da sukayi basira ta zata kare😜😜 Zaune suke a wani hadadden garden suna tattaunawa...abdulrahman "yace bro nifa gaskiya tsoro nakeji. Abdulraheem "yace haba dai kawai kayi yadda nace. Murmushi Abdulrahman yayi yace owk Allah yasa in dace. Abdul yace "insha Allah" zaka dace. Nan suke har kusan awa daya suna shan hira, inda  hira takai hira Abdul "yace shi kam ya matsu ba'ayi bikin su ya cashe ba. Abdulrahman yakai mashi dukan wasa "yace babu wani ai idan baka sani ba toh kasani, nidai bazanyi aure ba sai ka nemo mata ayi mana tare. Abdul "yace nikam ban yadda ba, kawai ayi naka inyaso daga baya ayi nawa. Abdulrahman "yace lallai ai ko za'ayi shekaru zakayi baka samu mata ba, ina tabbatar maka da nima bazanyi aure ba. Abdul "yace tau yayi dan uwa, Allah yasa duk wacce nace ina so taso ni. Abdulrahman ya waro ido yace haba dai sai kace wanda yayi kwantai?? "Hmmm aiko makaho ya sunsunaka yasan farashin ka mai tsada ne, bare kuma mai ido biyu, ya kake ganin zata kasance??? "Murmushi kawai yayi baice komai ba. Abdulrahman yace heyy bro ga lubna yar wajen mummy. Ya fada yana dariya. Bata rai Abdul yayi yace Allah ya sauwaka. Ni wallahi batayi mun ba. Abu sai kace fate.😍 Abdulrahman "ya kyalkyace da dariya harda dafe ciki. Hararan shi Abdul yayi ya mike zai wuce. "Da sauri Abdulrahman yaja hannun shi ya rike gam sannan suka bi hanyar fita daga garden din. Bayan sun fita Abdulraheem ne ke driving. Cikin yanayi na serious magana yace ya muje zuwa ko?? Abdulrahman yace yeah. Nan sukaci gaba da hirar su har suka iso wani dan karamin gida mai kyau. Fita Abdulraheem yayi da murmushi a fuskar shi yace bro sai na jika. "Abdulrahman daya fito ya zagayo ta bangaren shi hannu ya bashi suka sha sannan ya shiga mazaunin direba ya tadar motar. Tafiya yakeyi a hankali,( a karo na farko kenan da Abdulrahman yake tuki a slow) murmushi yakeyi wanda nikaina na rasa gane kona menene. Bayan ya iso gidansu "Amatullahi ne ya paka motar a daidai gate d'in shiga gidan sannan ya fito. Megadi daya fito da niyar bud'e mashi gate sai yaga harya paka motar nan waje sai ya fasa bud'ewa kawai ya dan rusuna ya gaida shi. Bayan sun gaisa ne Abdulrahman yace yayi mashi sallama da Amatullahi kuma ace macece ke neman ta. "Cike da mamaki megadi ke kallon Abdulrahman, sedai kuma  ba abun ya tambayi dalilin ba, "sai kawai ya amsa da toh sannan ya wuce. Bada jimawa ba sai gashi ya dawo. Lokacin har Abdulrahman ya shigo cikin harabar gidan. "Amatullahi kuwa tana ciki wai bazata fito ba, tunda dai mace ai ba haramun bane danta shigo. Mummy tace a'a kije dai kiga ko wacece. Dakyar ta yafa gyalenta tasha toka sai wani daddage kafa take har ta fita daga palour. "Dake hankalinta nakan can waje, "dan duk a tunanin ta wacce ke neman nata na can waje shiyasa bata lura da yana tsaye wurin parking space ba. Har tayi kusan kai gate d'in fita Abdulrahman yayi sauri har yana dan hadawa da gudu yasha gabanta. Cikin faduwar gaba tace Abdul miye haka zaka wani sha gabana??? Kuma banace karka kara zuwa gidan mu ba?? Abdulrahman ya amsa da eh. Tsaki tayi tabi ta gefen shi zata wuce, yayi saurin tsayar da ita, " yace Amatullahi nike nemanki. Zaro ido tayi had'e ta juyowa ta banka mashi harara, cikin ranta tace shine yace ace macece?? Qyatt tayi kyacci, ta nupi hanyar shiga ciki. "Cikin muryar shi mai d'an karan dad'i ya kiran sunan ta. Cak ta tsaya dan kuwa ba k'aramin shokin taji ba a yayinda ya kira sunanta sai taji kafarta ta sarke bazata iya koda taku d'aya ba. Cikin marairaicewa "yace Amatullahi nasan nayi maki laifi da yawa kuma duk wani hukunci da kika yanke ya dace dani, amma sedai abu d'aya nake rokon ki............... Plsss share [2/24, 6:41 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Masoyana ina alfahari daku a duk inda kuke, Allah ya kara mana kaunar junan mu ❤❤      Page 61-62 Amma sedai abu d'aya nake rokon ki, ki yafe mun lafin da nayi maki, ki nuna babu wani abu daya taba shiga tsakani na dake kuma kisawa ranki ni "Abdulrahman na cire sonki a raina kuma na rabu dake har abada". Dummm taji zuciyarta buga, "sai tunanin wulakancin da tayi ta mashi a baya ya dawo mata". Duk sai taji ta damu domin kuwa ai yaci ace duk nacin nan da yake mata ko bazata karbi soyayyar shi ba yaci ace ta yafe mashi. "Cikin rashin sanin abunda zatace hawaye ya fara zubowa daga idonta, "sai taji wani irin tausayin shi ya kamata. Hannunta tasa ta share hawayen da batasan ma'anar zubowar su ba.  Shi kuma yana tsaye yana kallon reaction d'inta, "sai tsinkayota yayi tana "cewa Abdulrahman na yafe maka nima dan Allah ka yafe mun. Har cikin ranshi yaji dad'i amma bai nuna ba sai kawai "yace nagode sannan ya ficewar sa daga gidan. "Fashewa tayi da kuka ta shige gida a guje, mummy dake palour tayi saurin tarota ta rungume ta gami da tambayar ta ko lafiya. "Cikin shasheqa kuka "tace mummy Abdulrahman ne yazo. Mummy ta maimaita kalamar cike da mamaki "Abdulrahman kuma??? Amatu ta gyada kai alamar eh. Mummy tace toh meya miki kike kuka?? Amatullahi "tace mummy kinsan jiya daddy yace sun sulhunta kansu, Abdulraheem na nan mazaunin shi kuma ya tambaye ni nace amince, kinsan daman abdulrahman yana zuwa wuri na shine yanzu yazo "wai in yafe mashi. Cikin d'an bata rai mummy tace toh shine abun kuka? Aina d'auka ko wani abun yayi maki. Amatullahi ta girgiza kai tace mummy beyi mun komai ba nima bansani dalilin kukan ba. Tsaki mummy tayi "tace amma dai Amatu da wawta kike, ai na zaci dad'i zakiji tunda ya rabu dake ko? Amatullahi tace eh mummy naji dad'i kawai irin maganganun da nayi ta fad'a mashi ne nake jin ban kyauta ba. "Mummy tai nisa tace tau kuskure kam ai an rigada anyi shi kuma tunda yazo ya rokeki gafara ai kam komai ya wuce tunda watakil kema kince ya yafe maki ko?? Amatu ta amsa da eh, mummy "tace tau "alhamdulillah Allah ya shige mana gaba. Amatu ta amsa da ameen. "Abdulrahman na fita direct gidan da ya ajiye Abdul yaje ya d'auko shi, bayan ya d'auko shi suna tafiya cikin mota, Abdulrahman yace kai wai kaga yadda tayi ne?? Hmmm harda kuka, Abdul yace kuka fah?? Abdulrahman yace wallahi ni nama rasa ko kukan me takeyi. "Abdulraheem yayi murmushi yace hmmmm ka gani ko, ai nasan yarinyar nan tana sonka, "kawai dai tana kaiwa kasuwa ne, kuma ni a tunani na gani nake kamar dan tana soyayya dani ne yasa bata amince dakai ba har take maka wulakanci". Abdulrahman "yace hmmm babu wani, kai dai ai aiki na gaba, "waton har naga tana cewa in bata takardar saki idan ta gane bakai bane. "Dariya Abdul yayi yace matsoraci kawai, kaida zaka koya mata sonka, ka koya mata yadda bazata iya rabuwa dakai ba?? Ai idan kayi haka toh ko daga baya ta gano gaskiya bazata taba "cewa ka saketa ba. Sedai tayi fushi dakai na kwana biyu, " kuma ai an wuce wurin. Abdulrahman ya shafo kanshi yana murmushi "yace kai d'an uwa kwakwalwar ka na mugun ja wallahi. Abdul baice komai ba yaci gaba da tuki danshi ya karbi tukin da Abdulrahman ya dawo d'aukan shi. "Sun kawo daidai tsakiyar hanya Abdul ya kalli gefen hagu da dama yace ya bro ina muka nufa? Abdulrahman ya kalli hagu ya kalli dama, yace kai muje gidan ammie dan nayi missing d'in girkin ta. Abdul ya harare shi had'e da "cewa babu wani nikam gidan mummy nakeson mu tafi, Abdulrahman yace babu matsala duk yadda kakeso haka za'ayi kaji d'an kani. "Abdul ya banka mashi harara kafin ya d'auke hanyar daman shi, gidan ammie kenan. Abdulrahman ko bai kara magana ba har suka isa. "Wurin parking space ya nupa sannan ya paka motar suka fito, hannun su sarke dana juna suka biyo hanya har suka iso bakin kofa. Abdulrahman ne yayi knocking, nan da nan ammie ta bud'e dan tana palon zaune tana kallo, duk kad'aici ya isheta dan hanan bata nan. "Murmushi ta sakar musu a lokacin da tayi arba ta kyawawan yan biyun ta. Suma suka mayar mata da martani had'e da shigewa cikin palourn suka zauna. "Cikin ladabi suka gaishe ta, Itama da fara'a ta amsa musu tana cewa daga ina haka wannan wankan? Abdulrahman yace amsa ta yana dan sosa keya yace ammie muje ganin wani abokin mu ne, "yayi saurin fad'a dan bayason Abdul yace wurin Amatullahi sukaje, dan kuwa ba karamin aikin shi bane. Ammie tace tau ai kun kyauta da ziyara, Abdul "yace ammie akwai abinci ne? Ammie tace eh, nan yace tasaka musu yunwa sukeji. Batare da bata lokaci ba ta zubo musu hadaddiyar shinkafa da miya da namomi, sannan ta hado musu da drinks ta dire a gaban su. "Cikin jindadin abincin suka fara hira suna santi ammie kuma kallonsu kawai take tana murmushi. Bayan sati d'aya "Komai na tafiya normal kamar yadda suka tsara", yanzu Abdulrahman shike zuwa wurin Amatullahi a matsayin Abdulraheem, kullum suna like a waya ga kuma nacin zuwa wurin ta. Ita har mamakin sauyin halin shi take, dan taga da ba kowani lokaci yake zuwa ba saboda yanayin aikin shi amma yanzu bai wuce kwana biyu bezo ganinta ba. "Abdulraheem kam yana nan shi kadai cikin kadai ci, sai kuma aikin shi daya mayar da hankali kai, kullum cikin addu'a yake Allah ya bashi wacce zata maye mashi gurbin "Amatullahi kuma Allah ya amsa domin kuwa, yau tunda ya wayi gari "yaji yana bala'in son ganinta". "Gashi ayyuka sunyi mashi yawa, dan asibitin nasu akwai marasa lafiya da dan yawa kuma babu halin ya tafi har sai ya basu isashen kulawa. Da misalin karfe shida da rabi na yamma yabaro asibitin, "lokacin duk a gajiye yake. Da isowar shi gida part d'in shi ya nufa, ya d'an huta na yan mintuna kafin ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin manyan kaya wanda suka amshi jikin shi. "Sai kamshi yake zubawa had'e da sakin murmushin daya kara fito da kyan fuskar shi. Wayan shi ya d'auka tare da makullin motar shi ya nupi part d'in ammie. "Bayan ya shiga palon ta hanan kawai ya tarar tana cin abinci. Da murmushi ta tarbe shi kafin ya k'araso wurin ta ya zauna gami da tankwashe kafafuwan shi, ya kalli fuskarta cikin zolaya yace ko kar nasa maki hannu?? "Murmushi tayi gami da waro idonta tace uhm uhm yaya ai nama koshi bari in karo mak..... Sai suka tsinkayo muryar ammie na cewa a'a zauna bari in kawo mashi. "Kitchen ammie ta shiga ta zubo mashi abinci ta kawo mashi nan inda yake zaune, a hankali ya faraci harya koshi kafin hanan ta kwashi plate d'in takai kitchen. "Shi kuma tashi yayi yace wa ammie zashi wani wuri sai ya dawo. Da murmushi a fuskar ammie tace ina zakaje? Cikin jin kunyar ta "yace ammie wani aboki na ke nema na. Ammie tace kullum dai aboki, aboki, tau Allah dai ya bada sa'a. "Murmushi ya saki a yayinda yake fita daga palon. "Wurin motar shi ya nupa, ya shiga ya bata wuta. Direct maitama store ya nupa, inda ya d'an sayi abubuwa da yawa sedai kuma bai bari naga abunda ya saya ba. Yana fitowa aka fara kiraye kirayen sallar magariba, nan ya shiga masallacin dake wurin yayi sallah har saida akayi isha'i kafin ya baro wurin. "Tsaye yake a bakin gate d'in gidan su yana jiran ta fito" dan yasa ayi mashi sallama da ita. Kallon daidai saitin kofar yake yana jiran zuwan ta. Ita kuma sanye take da gown mekyau ta yafa gyalen shi sedai fuskarta babu kwalliya amma duk da hakanan kyan ta ya fito domin kuwa Allah yayi ta da natural beauty. "Murmushi ta saki a lokacin data ganshi gami da karasowa wurin shi, suka gaisa, Bayan sun gaisa take.......... Masu karatu ga assignment kowa ta fad'i min ko wacece Abdulraheem yazo wurin ta 😎😎 Mu had'u a next page insha Allah [2/25, 9:42 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''        Page 63-64 'Bayan sun gaisa take tambayar shi ina Amatullahi, murmushi yayi "yace aike zan tambaya kuda kuke mak'wafta. D'an murmushi tayi "tace gaskiya kam amma dai kaima ai kamar mak'wafcin  ta kake, tunda ba'a dad'ewa babu had'u ba. "Hmmm kedai a wuce wurin, kallon shi tayi "tace a wuce wurin kamar ya? Kodai kazo wurinta bata gida ne?? Gyad'a mata kai yayi alamar a'a ayayin da idanuwanshi ke kallon d'an karamin bakinta da take motsawa a hankali. Kafin "yace kullum ina zuwa wurin Amatullahi amma yau ba wurinta nazo ba wurinki nazo. "Waro ido tayi cike da mamaki gami da pointing d'in kanta tana son tayi magana ya katse ta "yace karkiyi mamakin ganina saboda a halin yanzu ba Amatu ce a gabana ba kece a gabana. "Idonta taf da kwalla dan gani take kamar mafarki take ba gaskiya bane, cikin son ta gasgata kanta tace Abdul kaine kuwa? Kaine abdul d'in amatu?? "Murmushi yayi mai sauti ganin yadda ta rud'e "yace ameerah ki saurareni kiji abunda zan fad'a maki. Yi tayi kamar bata jishi ba ta juya zata koma cikin gida dan gani take kamar ba cikin hayyacin shi yake ba. "Cikin izza yace ameerah!! Cak ta tsaya tana jin wani zafi a zuciyar ta dan ta matsu bai wuce ba saboda ita duk wani abu dazai had'a ta dashi ba sonshi take ba saboda had'uwa dashi tamkar an fama mata wani ciwo ne. "Tsaye tayi ta kasa juyowa sai hawayen dake bin k'uncinta, shi kuma ganin bata da alamun dawowa yasa ya taka har zuwa inda take ya tsaya a gabanta yana kallonta yace share hawayen ki kiji abunda zan fad'a maki. Da sauri tasa gyalenta zata share, yayi saurin dakatar da ita had'e da zaro handkerchief daga cikin aljihun rigan shi ya mika mata. K'in karb'a tai cikin wasa "yace toh idan baki ansa ba zan share maki da kaina. Da sauri ta ansa ta share hawayenta ta mika mashi, sai ya girgiza kai alamar ta barshi kawai. K'ura mata ido yayi na yan mintuna ayayin da ita kuma ta rusunar da kanta kasa dan bazata iya jure irin kallon da yake mata ba. A hankali cikin sweet voice dinshi "yace nasan kinsan abunda ke faruwa tsakani na da d'an uwana da Kuma Amatu ko?? Ameera ta amsa da eh, can yayi nisa "yace toh a halin da ake ciki yanzu nabar wa Abdulrahman Amatullahi. "Da karfi tace me kace?? Ya bata amsa yace abunda kunnenki ya jiye maki. Sannan yace karki damu kanki fa saboda ko Amatu batasan Abdulrahman zata aura ba kuma ni nace kar a fad'a mata sai bayan aure, saboda banason a samu matsala. "Kuma kinfi kowa sanin yadda take wulakanta d'an uwana, alhalin shi yana masifar sonta, ta dalilin sonta komai yana iya faruwa dashi, shiyasa na hakura da ita. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tace yanzu shikenan Abdulrahman shi zai auri Amatu amtsayin kai?? Yace eh sai tace Abdul yanzu kana ganin an mata adalci kenan?? Abdul "yace meyasa kike fad'an haka bakiga halin da d'an uwana zai shiga bane? Ameerah meyasa d'an uwan zai nemi abun ya rasa al halin ina dashi?? Meyasa zan kasance cikin farinciki al halin d'an uwana yana cikin k'unci?? Ameerah kina ganin iyayen mu zasuyi farinciki da aure na nida Amatullahi bayan sunsan cewa akanta d'an uwana yake fama da ciwon da a kowane lokaci zai iya    tashi?? Hmmm na sadaukar da soyayyar amatu ne saboda farincikin shi da kuma samun zaman lafiya a tsakanin mu. "Iska ya fesar me zafi sannan ya kalli ameerah dake cikin tension yace plsss ameerah karki fad'a mata komai kinji ko? Ta amsa da toh. Juyawa yayi ya nupi inda motar shi take sai ya hangi hasken mota ta fito daga gidan su Amatullahi, murmushi yayi dan yasan ko waye, sai ya kira ameerah da tazo ta gani. Tana zuwa motar na wucewa. Murmushi ne ya subuce mata. Dan ganin rainin wayon da akayi wa amatu. Ledar da yazo da ita ya d'auko zai mika mata, tace a'a, cikin d'aure mata fuska yace shikenan tunda ba'a yadda dani ba zan wuce, ya juwa zai shiga motar shi. "Da sauri tasha gaban shi ta karbi ledar, murmushi yayi "yace ko kefa, itama murmushin ta mayar mashi. Sai yace mata zai tafi kar ace tayi dare, nan sukayi sallama ya wuce. "Yana wucewa ameerah ta saki murmushi tana mai jindadin hirar da sukayi. Cikin gida ta wuce lokacin aunty hajara na dakin mijinta, itama d'akinta ta shige ta fad'a saman gado had'e da d'aura handkerchief d'in daya bata bisa kirjinta, "tana mai shaqar kamshin shi  tana wani lumshe ido. Ta rasa dalilin da yasa takejin wani dad'i a zuciyar ta. "Sai ajiyar zuciya take ta saki tana murmushi, mikewa tayi ta rage kayan dake jikinta sannan ta d'auko ledar daya kawo mata ta bud'e. "Waro ido tayi ta fara firfito dasu tana dariya kamar wata zautacciya. Wani had'adden akwati ne d'an karami me d'auke da zobe me shegen kyau. Da kuma kayan maku lashe. Fito da zoben tayi ta lak'a a yatsar ta me bima manunin ta taga ya zauna cif, yayi mata kyau. Zare shi tayi tana jujjuya shi a hannunta tace toh me wannan yake nupi?? Hmmm nasan dai wannan zoben ba banza ba. Kodai mafarki na ne zai zama gaskiya? Uhmmm da nafi kowa farinciki. "Mayar da zoben tayi cikin akwatin shi dan cewa tayi baza tayi gaggawar sawa ba, wani chocolate ta gani me shape d'in heart sai taji ya burgeta, d'aya ta d'auka sannan ta mayar da sauran cikin leda ta ajiye can kasa a gefen gadonta, kafin ta dawo saman gadonta ta kwanta tana shan chocolate d'in cikin jindadi. Haka bacci ya sace ta kwance cikin farincikin dan rabon data kasance a haka an dad'e. B'angaren Abdul shima yana cikin farinciki, "dukda bai fad'a mata asalin abunda ya kawo shi ba amma yaga alamar nasara a tattare da ita".        Washe gari Tunda safe ameerah taje gidan su amatu, lokacin "amatu na bacci amma haka ta tashe ta ta fara bata labarin abunda ke faruwa, sedai bata ce mata Abdulraheem bane, cewa tayi Abdulrahman ne. Cikin zolaya amatu "tace hmmm kice kin shigo layin mu kenan? Ameerah tace babu wani ai baice yana sona ba kawai yacewa yayi yazo gaishe ni. Dariya Amatu tayi tace toh ai daga gaisuwa ake farawa kuma tunda kikaga ya tako kafa yazo wajenki to ba banza ba kawai ki saurari jin Kalmar so daga bakin shi. "Kuma shawara ta shine kawai ki amince dashi mu zauna a inuwa d'aya dake. Ameerah tace lallai Amatu waton bama in duba halayyar shi inga ko tayi mun ba zaki wani ce in amince babu koda Jan aji?? Amatu ta harare ta tace ohh Jan aji?? Hmmmmm bari kije garin jan aji ki rasa shi. Ameera tace gaskiya ne fah, nima na d'an fara pola mashi amma bazan nuna mashi hakan ba har sai ya furta mun da bakin shi. Amatu tace yes kina kawo light Allah ya sanya alkhairi. Ameera tayi murmushi had'e da barin dakin ta wuce gida. Wanka taje tayi ta shirya tazo ta sami Amatu lokacin itama ta shirya suka wuce saloon.. Bayan sati uku Plsss ayi hakuri da wannan [2/25, 9:03 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''          Page 65-66 Bayan sati uku, Abdulraheem ne tare da ameera suna hira, dan yanzu sun fahimci juna da ita, har gidan su an sani, kullum suna mak'ale da juna kamar yadda amatu da Abdulrahman suke. Yau asabar, kuma abdul yana hutu baije asibiti ba kuma kusan kwana uku baisa ameerah a idonshi ba, shiyasa yau ya shirya ya nupi gidan su. Bayan yaje ne ya kirata sai gata ta fito. Tun daga nesa ya fara aika mata da sakon daya saba, waton kallonta. Haka yaci gaba da kallonta har ta karaso wurin shi bai sani ba. Sai data huro mashi iskan bakinta a fuskar shi. Firgigit, ya dawo daga duniyar daya shiga yana mai sakar mata lallausan murmushin shi. Yace sweetheart yawo nazo muje. Ita kuma cikin shagwaba tace nikam ba inda zani, duba fa kaga kwanan ka nawa bakazo wuri na ba?? Cikin marairaicewa yace haba my sweet ameerah ayi mun hakuri kinji plsss ya karasa fad'a tare da kama kunnuwan shi. Murmushi tayi ganin yadda ya kama kunnuwan shi tace owk na hakura amma ba bazan je yawo ba. Nan ma ya sake bata hakuri yana rokonta kafin ya amince tace bari taje ta sanar da aunty hajara. Babu jimawa sai gata ta dawo. Nan ya bude mata gaban mota ta shiga sannan ya zagayo ta b'angaren direba ya zauna. Bayan ya shiga ne har sun fara tafiya tace sweet Abdul ina zamuje ne?? Yana kallon waje ta gefen windon shi yace zanje in sayar dake ne. Sai data kyalkyace da dariya mai isarta sannan tace sweet Abdul ai ko a mafarki kaga wani zai sayar dani bazaka bari ba ballantana kai da kanka ko?? D'an yatsine fuska yayi had'e da cewa inji waya fad'a maki?? Bata rai tayi ta banka mashi harara had'e murgud'a mashi baki ta juya kanta ta gefen window tana cewa Allah sai na fad'awa ammie. Kallon d'an karamin bakinta yayi wanda a duk lokacin da take shagwaba yake burge sa yayi nuni da kanshi yace ni kikei murgud'awa baki ko, qyatt Allah nayi kusan maganin bakin nan mai tsiwa da murgud'e murgud'e. Ita kuma ko kallon shi batayi ba taci gaba da lekenta ta window har suka iso "A CLASS PARK". Kud'in gate pass ya biya musu kafin suka nupi wurin parking ya paka motar sannan ya fito. Ita kuma sarauniya tana ciki tana jiran sai yazo ya fitar da ita saboda tsabar Jan aji irin nata. Shi kuma ko a jikinshi ya nupi inda take ya bude mata ta fito tana wani shan toka, wai a dole fushi take dashi akan maganar dazu. Murmushi yayi ya dawo gefenta yadda zasu samu damar tafiya tare, yana kallonta yana murmushi dan yadda take wani shan kanshi ma dariya take basa. Haka suka jera suna tafiya gwanin sha'awa sedai babu mai magana cikin su. Tsayawa Abdul yayi dan ya gaji da shurun nata yace sweet ameerah plsss kiyi magana mana, ai Kinsan wasa nake maki ko? Ta wani kawar da kai gefe, yace Allah idan bakiyi mun magana ba zan kurma maki ihu a wurin nan. Waro ido tayi tace a'a yi hakuri ka rufamin asiri. Yaso yayi dariya gudun kar asake komawa gidan jiya, yace toh, sannan suka fara hirar su na soyayya, ameerah sai kalle-kalle take, duk wani abu data gani wanda ya burgeta sai tayi magana a kanshi, ko kuma tace sai sunje ta gani. Haka sukayi ta zagaye a park d'in dan akwai shi da girma sosai kuma akwai kayan burgewa wanda zai sa ko baka cikin jindadi kaji shi. Wurin da ake sayar da ice-cream suka nupa, nan suka zauna saman kujerun dake wurin suna fuskantar juna yasa a kawo musu kayan mota baki. Babu bata lokaci sai gashi an kawo musu ice cream da pizza. Nan ta fara sha shi kuma sai kallonta kawai yake yana jin ina ma ace shike bata da kanshi. Ita kuma ko a jikinta dan ta mayar da hankalinta kan ice cream saboda ba karamin sonshi take ba. Bayan ta gama sha ne ta dubi robar shi taga ko alamun fara sha ba'ayi ba tace sweet Abdul ya baka sha ba? Sai yace a'a bana shan abu mai sanyi sosai. Mak'e kafad'a tayi irin ko ohon nan tajawo nashi zata sha, daidai shima yasa hannun shi zai d'auka. Wani irin yarrrrrrrr, sukaji a lokaci d'aya kuma a tare sukayi saurin janye hannuwan su suna kallon cikin kwayar idon junan su.  Ameerah ce ta fara kawar da kanta, cikin jin kunya ta rusunar da kanta kasa. Shima cikin jin kunya yace shida yace bazai sha ba kuma miye na d'auka, ya fad'a a cikin zuciyar shi?? Sai kawai ya tura mata gabanta yace gashi. Kallon junan su sukayi yayi mata sigina da girar shi a kan tasha, wani iri taji sai duk taji yama fita a ranta.  Sai tace su wuce gida ta gaji. Batare daya tambayi dalili ba yace su tafi, nan ta d'auki handbag d'inta ta rataya kafin suka jera a tare suna tafiya. Sun kawo wurin da sukayi parking kenan Abdul yaga motar Abdulrahman sedai bai gasgata ba sai daya hango shi tafe shi da Amatullahi. Cike da mamaki kallonsu yake kamar yadda suma da suke nesa suka hango shi. Cike da zumudi Amatu tafara sauri har tana d'an had'awa da gudu dan tayi saurin zuwa wurin da ameerah ke tsaye ta basu baya tana waya. Gama wayarta kenan ta juya cikin rashin sani wani mai mota da yazo da baya saura kad'an bugeta, Amatu data hango haka ta  kurma ihu, Abdul kuma dake can hankalin shi ya d'auke yana kallon Abdulrahman dake watso mashi hararan da besan ko na menene ba. Yayi saurin juyawa yaga saura kad'an motar ta buge ameera, da hanzarin shi yasa duka hannuwanshi biyu ya rikota kamar wata yar baby. Mai motar a tsorace ya fito dan ya aza koya bugeta ne. Hakuri ya fara basu akan bai lura da ita ba. Amatu kuwa har hanjin cikin ta sun kad'a. Abdul kuwa sai b'ab'atu yake tayi yana zagin shi wai da gangan ne, hhhhh kuji fa shirmen Abdulraheem. Abdulrahman yazo ya bashi hakuri yacewa mai motar yayi tafiyar sa. Bayan mai motar ya tafi ne Abdulrahman ya kalli ameerah datayi lamo a jikin Abdul tana faman haki kamar wacce tayi gudu. Abdulrahman yana dariya yace dalla malam cika ta, sai a sannan ya lura da rungume ta dayayi, yayi saurin sakinta, cikin jin kunyar su ameerah ta sunnar dakai kasa, shi kuma ko damuwa baiyi ba. Amatullahi ta karaso wurinta tana mata barka. Daga nan suka fara hira, Abdul yace subari har su koma gida saci gaba. Nan kowannensu ya d'auki tashi suka wuce, daman suma gidan zasu wuce.       Bayan wani lokaci Abubuwa da dama sun faru, ciki harda sa ranar auren su amatu da ameerah dan yanzu komai ya zama normal, iyayen ameerah sun amince data auri Abdulraheem, sai aka had'e bikin nasu lokaci daya. Amatullahi da ameerah sun samu admission a BASE UNIVERSITY sedai basu fara zuwa ba sai bayan auren su dan wani sati za'ayi bikin su. Yanzu haka duk gidajen nasu shirye-shirye kawai suke tayi, su amatu kamar wancan karon mummy ta d'auko me gyara na musamman dan a gyara amatu da ameera. Aunty hajara kam itama daginta dake kaduna wasun su sun fara zuwa. Su Abdulraheem kuma suma shirye-shiryen sukeyi, kamar yadda mummy itama ba'a barta a baya ba, dan itama shiri na musamman takeyi. Yau ta kama....... Plsss share [2/26, 8:46 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Wannan shafin nakune yan rudani fans grp 1&2 da beauty novels grp         Page 67-68 Yau ta kama laraba yau ake mother's day, ko'ina na gidan cike yake da mutane, "duk inda ka kutsa mutane ne a wurin. "Palon mummy na shiga, nan ma cike yake da mutane, gaishe da mutanen nayi kafin na kutsa dakin amarya, dan ita nakeson gani. Dak'yar na samu na shiga cikin d'akin, can karshen gado na hango amarya Amatullahi, fuskar nan tata sai sheqi takeyi, " sedai babu wata kwalliya a fuskarta, "da alama dai sai lokacin mother's day yayi za'ayi mata kwalliya. "Nan na samu wuri na zauna, ina jiran lokaci yayi, dan alkawari na d'auka sai na kawo wa Rudani fans GRP rahoto. "Ina nan zaune aka kawo mun abinci mai  rai da lafiya, sai danaci iya ci na kafin nayi gyashi na godewa Allah daya kawo ci da sha. "Bayan awa biyu akayi waje dani saboda za'a shirya amarya. Raina baiso ba amma haka na fita, da biro na da littafi na. Bayan awa biyu sai aka bud'e kofar, da sauri na shige gudun kar a rufe kofar. "Ko dana shiga baki sake nake kallon amarya, "tasha make-up mekyau, sedai kalar ta bata canza ba, "dana dubi kayan dake jikinta sai dana rufe ido na kara bud'esu dan in tantance kowane kala ne, sanye take da riga da skirt, shiba pink ba, kuma shiba purple ba, a takaice dai bansan kalar kayan ba.  idan baka lura da kayan nata ba zaka d'auka ko gown ce. Bayan an gama mata wanka da turare, "aka fito da ita waje, nan uwayen amarya suka bi layi suma sunsha anko, har cikin farfajiyar gidansu aka kaita. Inda shima yasha decoration d'in da sai ka rantse ba gida bane. Wani d'an kujera me kamar ta sarauniya, aka ajeta akai, lokacin har an kawo ameera, itama kalar kayan da amatullahi tasa akasa mata sedai kowa da kalar gyalen shi da purse. "Sun wanku sosai kuma daka fuskar su kasan suna cikin farinciki. "daga gefensu kuma uwaye ne kowacce da nata kalar wankan, amma anko suka dukansu harda uwayen ameera. Masu DJ kuwa duk sun hallara a wurin, uwar amarya tana cikin gida itama ana shiryata. Bayan kowa ya zauna ne aka fara jawabi, "bayan an gama aka kunna DJ, toh fah nan gidan ya dau wani irin duma wanda tun daga nesa zaka san ana wani abu a gidan. DJ ne ya umarci uwaye da su fito su nuna tasu farincikin, tunda dansu akayi taron. Nan kowacce ta fito da nata irin rangwadar suka sa amare a tsakiya suna zagaye su had'e dayi masu liki.    "Su amare na tsaka suma suna d'an takawa kad'an, Bayan sun gama cashewa ne aka nemi uwayen amare dasu fito, dakyar mummy ta fito wai kunya takeji, ameerah kuma kanwar mahaifiyarta ce ta maye gurbin ta dan fur taki shiga, kai tunda taji ana neman uwayen amarya ta sulale ta wuce. Nan mummy da aunty uwani suka fito suda su amare suna rawa suna liki, gabadaya gidan aka d'auki tafi dan ba karamin burgewa sukayi ba musamman aunty uwani data saki jiki tana rawa tana liki. DJ sai kara musu duma da katon kai yake su kuma suna dansewa. Haka akayi ta cashewa, daga baya kuwa kowa ya shiga ana nuna farincikin, nima na kutsa cikin mutane ina rawa, sedai banda kudin liki, sai kawai na fara yanka littafi na ina liki dashi 😍.sai kusan magariba sannan taron ya watse, nan kowa ta kama gabanta. Hmmmmm bari mu leko su Abdul mu gani😎 B'angaren su Abdul yau babu wani events da sukeyi, sedai suma ana ta shirye-shirye ammie duk ta rikice, ko magana kayi mata nan zata barshi ta wuce, dan kanta ya d'au zafi. Hanan uwayen biki tana gidan su samha suna nasu shirin dan gobe zasuyi wankin ango, inda suma b'angaren amare zasuyi wankin amarya. Duk ji nayi gidan babu dadi saboda ba casu sai wani hayaniya da mutane suke tayi. "Shiyasa kawai na fice daga part d'in na wuce part d'in Abdulraheem sedai kuma baya nan. Haka na jawo kafata nama fice daga gidan ina murmushi dan tunowa da nayi ko suna gidan mummy. "Nan na tari taxi, nayi mashi kwatancen gidan da zai kaini. Bayan mun isa gidan ne, na nemi kudi na rasa, nace toh fah masu hali sun nuna mun nasu halin, dan duk inda ake biki toh fah barawo yana nan. "Mai mota ko tsaye yayi mun wai sai na bashi kudin shi nikuma ina ta rokon shi amma fur yaki, muna nan sai ga Abdulrahman da Abdul sun, ganin kamar ana cecekuce yasa suka karaso wurin. Da fara'a ta tun kafin su nemi sanin ba'asi na fad'a musu, nan Abdul ya ciro 2k ya mikawa mai motar, duk da kudin shi beko kai rabin kudin ba. "Bayan me motar ya wuce ne, nima ya zaro 10k ya bani, "Abdulrahman kuwa ko murmushi baeyi mun ba, nikuma ko ajiki na daman Abdul nakeson gani kuma na ganshi. "Daga nan suka wuce nikuma na shige cikin gidan, "nan ma kodana shiga babu wani alamun akwai casu sedai cikin farfajiyar gidan nasu dana gaan fara decoration d'in wankin angon da za'ayi gobe. Dake gidan bekai cikar gidan ammie ba, a free na wuce, "ina tafiya had'e da yin yan kalle-kalle na har bansan sadda na bugi wani abu kamar mutum ba. Dagowar da zanyi inga ko mena buge keda wuya naji saukan mari a fuska ta. "Me zanyi inba dafe k'unci na ba. Bude idona nayi inga ko wace yar iskan ce ta mareni. Karaf idona ya sauka akan lubna da kwata-kwata fuskar nan tata babu annuri, "cike da haushin ta, cikin raina nace toh meya kawota?? Ina cikin wannan tunanin ne naji an bangajeni an wuce, "firgigit na dawo daga duniyar tunanin dana Lula, kafin na buga mata tsuki na shige gidan dan inga abunda ke faruwa a ciki. Bayan na shiga ne na tarar da umma sai fada take kamar zata tashi sama, "mummy kuma na gefe tayi tagumi. Tsaye nake har na tsawon minti goma umma na fad'a daga bisani ta sarara, mummy kuma ta shige dakin ta. Tsaye nayi ina rarraba ido, dan bansan ko wa zan tunkara inji dalilin fad'an ba. Haka na gaji da tsayuwa na juya zan wuce sai mummy data fito daga d'aki ta kirani. "Kafa ta na rawa na isa gabanta. Wata farar leda ta miko mun wanda bansan ko menene a ciki ba tace inkai wa umma. "Wani daki dana ga umma ta shiga nan nima na shiga, "a bakin kofar na tsaya dan ji danayi umma nata kuka ina tsoron karna shiga fad'an ya dawo kaina. Sai dana ga kukan nata ya lafa ne kafin naja kafata, jiki a mace na isa wurinta, hannu na rawa na mika mata. Ansa tayi ta ajiye nikuma na fice da sauri. Readers mu had'u a next page insha Allah dan jin yadda wannan al'amarin zai kasance. Plsss share [2/26, 6:49 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Readers plsss kuyi hakuri da rashin jina da zakuyi na kwana biyu sbd ina d'an da wani biki ne, kuma bazan iya cewa ga ranar da zaku jini ba amma Insha Allah da mun gama hidimar mu zaku jini. I love all my fans ❤❤        Page 69-70 Mummy ce ta shigo d'akin da umma take dan ta gaji da jin kukan nata, zuwa tayi ta zauna kusa da ita ta dafa ta, cikin sanyin murya tace,  umma wai dan Allah yaushe zaki bar kukan nan ne?  Duba fa ki gani tun da la'asar kike a haka kuma kinsan akwai baki masu shigowa ko so kike su fahimci akwai wani abu? Cikin shash'sheqar kuka umma tace "dole inyi kuka, wannan abun kunyar da yar isakan yarinyar nan tayi mun ai ya isa yasa nayi kuka. Kuma fisabilillahi yanzu ta kyauta mun kenan? Mummy da duk bataji dadi ba tace "umma kiyi shuru mana, wallahi nasan wannan d'anyan aikin da lubna tayi ba bayin kanta bane, kuma ai kuruciya ce ke damunta, plsss kiyi hakuri ki cire komai a ranki, kinsan banason kowa yaji wannan abun ko. "Umma tace nasani amma wallahi yarinyar nan ba karamin bata mun rai tayi ba, ji yadda nake nuna maki cewa ko maganar yaronnan sam batason ayi mata, ashe munafunta ta takeyi. Mummy tace umma, "kiyi hakuri mana, d'an yau fa ka haife shi ne baka haifi halin sa ba, "kuma tunda dai abunda taso ta aikata beyi ba ai sai mu gode ma Allah, "kinsan dai da ace Allah ya bata nasara ai da kashin mu ya bushe, daga ku har ni d'in. Tau Alhamdulillah Allah ya takaita, "share kwalla umma tayi tace yaya nagode da Allah yasa kece ba wata ba kuma insha Allah wani abu makamancin haka bazai sake faruwa ba. "Mummy tayi murmushi tace yauwa ko ke fah, yanzu sai ki tashi kiyi sallah muci gaba da aikin mu ko. "Itama da murmushi a fuskarta ta amsa da toh sannan ta tashi ta shiga toilet. "Mummy ma fita tayi daga d'akin.    ********  ********  ******** Lubna na fita daga gidan mummy, gidan wata kawarta dake aso drive ta nupa, bayan taje sun gama gaisawa ne kawarta ke tambayar ta lafiya ta ganta a haka? Nan lubna ta fara kuka tace wallahi Khadija na tafka b'arna da yawa, "cikin son jin abunda ta aikata tace lubna me kikayi ne haka? Lubna ta share hawayenta tace "duk abunda na aikata zee ce ta zuga ni, Khadija tace wace zee kenan? Lubna tace zee auwal mana. Khadija tace ina kika had'u da ita, ita dake kano meya had'a ta dake da kike nan abuja?? Lubna tai ajiyar zuciya tace, "ai yanzu na koma garin mu da zama saboda Abdulrahman, tun bayan komawa ta umma ta tace mun tunda shi baya sona nima kawai na hakura dashi. Sai nace mata toh kuma ni kwata-kwata na rabu dashi, wallahi ko maganar shi banason ayi mun, kinga umma harda dad'i taji saboda na cire wa kaina damuwa. "Wata rana na fita sai na had'u da zee, Kinsan kuma tasan ina son Abdul, data tambaye ni ina yake shine nake fad'a mata ai na rabu dashi, "shikenan fah ta fara cewa ai bai kamata in rabu dashi ba ai gashi gashi. Nan ta fara zugani harda cewa ai aure kamar anyi shi nw an gama. "Nikuma lokacin akwai d'an sauran sonshi a zuciyata shiyasa kawai na biye mata tace kar in damu yaushe zanje gidan su dan akwai abunda take son ta bani, " nace mata bansan lokacin da zanje ba, "sai kwatsam kawai naji labarin zai yi aure, sai na fake da haka nace ta bani. "Ni na d'auka wani abun ne zata bani sai gani nayi ta bani wani kullin magani, wai insa mashi a cikin abinci daya ci zai ce ya fasa auren waccen ni zai aura. "Da farin k'in ansa nayi saboda ina tsoro kar asiri na ya toni, "amma dake zee macuciya ce haka tayi ta Jana da dad'in baki har na yadda na amince. "Bayan munzo gidan su ne yau d'innan mummy tace in kaiwa Abdulrahman abinci can part d'inshi, "daman ina tunanin yadda zanyi ne sai kawai na amsa da fara'a ta na shiga kitchen na zuba mashi cikin plate sannan na d'auko kullin maganin zan zuba kenan sai ga umma da mummy sun shigo kawo kula. "Nikuma saboda tsoro na yarda maganin a kasa, umma nagani ta karaso kusa dani, ta d'auki maganin tace miye wannan?? Cikin rashin gaskiya nayi mata shuru dan bansan abunda zance ba kuma taga lokacin da maganin ya fad'o a hannu na. "Tayi ta tambaya ta miye wannan na fara inda, inda, mummy ta karaso wurin ta dafa ni tace miye wannan? Nan ma nayi shuru shine umma dataji haushin shurun danayi ta watsa mun mari, " nan da nan na fara zubar hawaye, still tana tambayata ko miye amma baki na yayi mun nauyi na kasa magana.    "Haka ta kara d'age hannu ta watsa mun mari, daga nan mummy ta rike ta tana cewa tabar mari na. Umma tace bazata bar marina ba Har sai na fad'a mata ko miye, "nan zuciyata ta raya mun kawai in fad'a mata dan nasan halin umma da zafi take, kuma tana da tsanani sosai. Nan na fad'a mata ko miye, "aikuwa tun kafin in gama fad'a mata ta dinga mari na a ko'ina na jiki na, mummy na tareta amma sai turjewa take. Haka ta gama jibaga ta sannan ta fara fad'a tana zagi na tace in fice daga gidan batason gani na. Mummy taja hannu na muka fito palour, inda mutane ke zazzaune sedai basu san taka maiman abunda ya faru ba amma suna iya jiyo fad'an da umma keyi. Daki mummy takai ni tace in wanke fuska in wuce koda gidan kawata ne tunda umma tace sai na bar gidan. Nan na wanke fuskata cike da jin kunyar mummy dan nasan tana ita ne amma da wata ce bazata taba rufa mun asiri ba. "Nan na share guntun hawayen daya zubo mun, "na fito daga d'akin mummy na biyo ta palour sum sum na wuce ina jin umma ta fito palour tana fad'ace fad'acen ta. Ajiyar zuciya Khadija ta sauke, "tace gaskiy lubna kinyi sakaci da kika bari zee taci galaba akan ki, "idan fa baki manta ba zee muguwa ce ajin karshe, yanxu gashi takai ki ta baro. Amma wallahi Allah ya wadar da mai hali irin na zee. "Uhmm lubna tashi kije kiyi sallah ki dawo, "nan lubna ta wuce toilet ta d'auro alawla dan gabatar da sallar magariba.      Washe gari Su amare na hango sanye da dogayen riguna masu kyau kalar ja da adon duwatsu agaban rigar su. Amatullahi na fara kare ma kallo naga iya wankuwa ta wanku, "dana leka mayafin ameerah naga itama ba karya ta wanku. Nan na juya, "na kare ma wajen kallo, sai naga fili ne amma an kawata shi da kayan alatu masu Jan hankali, "mutane na fara kallo, ina ganin kowa da irin wanka daya d'auka, can na hango, Habiba Usman, teema, hawwer, babyn MD, ummi baita, hassy, Ayeesha, swt aseeya da naima, sai faman kwasar rawa suke baji ba gani, dakyar na samu na tsayar da babyn MD nace ina sauran members suke?? Nan take fad'a mun wai sai gobe zasu zo dinner. Gaba na kara ina ta kallon mutane kowa sai rawa yake yana raha, "nikuma kutsawa kawai nake cikin mutane ina d'auko rahoto.      Wurin wankin ango😎 Hmmm can na hango wasu kyawawan mazaje su biyu masu kama da juna. tsaye suke abokan su sun zagaye su suna musu liki, "kare musu kallo nayi naga Abdulrahman ne da Abdulraheem, sanye suke cikin yadi kalar brown mai masifar sheqi da d'aukan eyes. Abdul rawa yake ba kunya ga uwaye nan da kannai suna kallon shi sai faman cashewa yake, "saboda jindadi da nuna farinciki yaje ya yawo hannun ammie da mummy yasu a tsakiyar su, "nan kowa ya basu fili ammie da yan biyun ta suna dansewa, "duk yadda taso kar tayi rawa amma saboda ta nuna farincikin ta ga ya'yan nata sai ta gyara mayafin ta had'e da ciro bandir d'in yan dubu dubu cikin purse ta fara musu liki tana takawa. "Mummy kam tuni ta fara rawa tana musu watsi da kud'i. Inaaa DJ saboda rikid'ewa  volume din wakar ya kure, MC kuwa sai wasa su yakeyi, "masu eyes kuwa kowa ya kara bud'e su yana kallo ana tafa musu had'e yin ihu, ammie kuwa ji take kamar ba ita ba, dan rawa ba damunta yayi ba, haka tayi ta rawa dasu har sai da wakar ta kare kafin suka tsaya. Ammie na fitowa mutane suka shi ga rungume ta ana dariya, hanan da tunda take bata taba ganin ammie na rawa ba ta karasa wurin ta tana dariya dan taji dad'i sosai. Su yan biyu kuwa ai duk farincikin mu bamu kaisu ba. Haka akayi ta raye raye har kusan magariba kafin taron ya watse.      Washe gari Plss comments And share [3/1, 4:42 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ" يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُون May Allah shower his Rahma & Salama  on you. Prevent any evil act from reaching you & decree you to  end with the most pious & beautiful acts. And May Allah uplift your value, forgive your past, grant you and your Family manifest Victory Fid-duniya Wal-Akhirat. Ameen. '''Jumma'at Mubarak.'''      Page 71-72     Washe gari Ko wane b'angare na gidajen yau babu wani hidima da ake illa shirye-shiryen zuwa dinner daga gefen amare har izuwa na ango.   Da misalin karfe takwas da rabi na dare. "Sanye suke cikin wani dakakken shadda riga da wando da babbar riga kalar baki mai sheqi da walk'iya, "daga gaban rigar anyi musu aiki da golden d'in zare. Kowannensu yasa agogo golden had'e da hula da takalmi golden. Wankan turare akayi musu a yayin da fuskar nan tasu cike take da annuri, "ga wani masifar kyau da haske da suka kara yi. "Domin kuwa kalar kayan ba karamin amsar jikinsu yayi ba. "abokan su kuma sanye suke da yadi milk mai sheqi. "Bayan an gama kammala shirya su ne aka fito dasu waje nan inda aka paka wasu sabbin motoci. "Motoci ne a kalla zasu kai ashirin, jere, "tun daga farfajiyar gidan har zuwa can wajen gida, "sedai guda biyun nan a tsakiya suke, kuma an kawata su da flawoyi masu d'aukar hankali. "Wasu daga cikin abokan ne suka ja hannuwan su Abdul suka sa kowanne cikin tashi motar. "Daga na suma suka shiga sauran motocin suka fice daga gida. Bayan fitar su direct gidan amare suka nupa. A lokacin amare sun sha kwalliya, "har baka iya ganesu saboda tsabar kwalliyar da akayi wa fuskar su, "sanye suke da wasu irin kaya masu kama da Arabian gown fari kal.  Ko waccen su rik'e take da d'an karamin purse golden colour da d'an uban su takalmi mai tsini shima kalar purse, "sai mayafin da aka yafa musu mai raga-raga, "wanda ya rufe duka ilahirin jikinsu. Ga doguwar rigar da suka sa sai jan kasa take sosai, dan lokacin da za'a fito dasu sai da kawayen su suka rirrik'e musu shi ta baya. "Haka aka fito dasu ana gud'a har akasa ko wacce cikin motar angonta, sauran kawaye dake sanye da dogayen riguna kalar ja da d'ankwali milk, suma suka take musu baya ta hanyar shiga sauran motocin da aka tana dar domin su. "Nan kowa ya tada tashi motar suka fara tafiya a Jere, "abun gwanin ban sha'awa. A cikin mota kuwa Abdul sai kallon ameerah yake tayi, "ji yake kamar ya rungume ta. Gashi duk yadda yaso su had'a ido taki ta bari. Abdulrahman tun daya ga Amatullahi yayi mutuwar zaune, "dan ba karamin kyau tayi masa ba, haka itama sai taga yafi ko wace rana kyau. Ba laifi Amatu ta saki jikinta suna hira da Abdulrahman sakamakon ameerah da gabadaya kunyar abdul ta lullub'e ta. Haka sukayi ta hira har sadda suka iso shahararren hall d'in da za'ayi event d'in. Koda suka iso mutane da dama sun hallara, a ciki, a bakin Hall d'in aka shirya yadda za'a shiga ciki. Samha da hanan dake sanye cikin dogayen riguna baki suma sun sha kyau su akasa a gaba a matsayin flower girls. Daga su sai Abdulrahman da Amatullahi wanda suma sun jeru da juna suna takowa a nutse, bayan su kuma, abokan Abdulrahman ne da kawayen amarya kowa da partner d'inshi. Daga su sai Abdulraheem da Amatullahi suma bayan su abokan shi ne da kawayen ameerah, "suna take musu baya. Tunda suka sa kai suka shigo hall d'in ya d'au wani irin duma, wanda ko a ina kaji shi, ko bakayi niyar rawa ba sai kayi. Haka sukaci gaba da tafiya masu d'aukar hoto sai haska su sukeyi da kuma masu wayoyi duk sun zageye su ana d'auka. Bayan sun kai mazaunin su ne kowa ya nemi wuri ya zauna, nan MC ya fara su jawaban shi daga nan aka fara su programs wanda daga ciki aka buk'aci amarya da ango su fito su nuna nasu farincikin. Nan aka basu fili, "kowanne ya rikon tashi amaryar suna d'an takawa, Abdul kuma sai fama yake da ameera yana mata magana a kunne akan tayi rawa fur taki koda motsa jiki ne, tsaye tayi kamar wata gunki. Abdul kuma ganin tana mishi taurin kai, "kawai baiyi wata, wata ba, ya saki hannuwan ta ya kama k'ugun ta yana girgiza wa a hankali, dan dole ta fara motsawa tana fakar mutane tana aika masa da harara. Abdulrahman kam ba laifi shima yana d'an takawa dashi da Amatullahi. Mutane sai liki suke ta musu, can na hango readers ko wacce da wayarta a hannu tana jan selfie 😎 saura kuma kuce karya ne 😏😏 Sai kusan karfe d'aya na dare taron ya watse. ************* Yau asabar wacce ta kama ranar da ake d'aurin auren ABDULRAHMAN ALIYU DA AMATULLAHI MUHAMMAD LEMI da kuma ABDULRAHEEM IBRAHIM DA AISHA USMAN (ameerah) akan sadaki duba dari, dari. Inda aka d'aura aure anan central mosque dake garin abuja, "d'aruruwan mutane sun halarci d'aurin auren su domin taya su murna. Bakin angwaye ko rufuwa bayayi saboda tsantsar farinciki, "haka ma su daddy suma sun matukar jin dadi da Allah ya nuna masu wannan rana, fatan su Allah ya nuna masu na y'an baya. Bayan an dawo gida ne, ammie ta kawo musu ferfesun kayan ciki da jallof din shinkafa da drinks ta ajiye musu. Dake gidan ta suka sauka bayan an dawo daga d'aurin aure. Saboda tasan ba lallai su samu wani isashen lokacin cin abinci ba yasa da aka kawo su ta rufe kofa ta kai musu abinci tace sai sun cinye duka. Kowannensu ya zaro ido yana kallonta, "Abdul yace ammie so kike cikin mu ya fashe ne?? Dan a kalla abinci data kawo ko mutum goma suna iya ci su koshi. Hararar sa tayi ta k'ara gyara tsayuwar ta tace wallahi idan basu ci ba babu me barin gidan nan yau. Abdulrahman yayi yar dariya yace ammie jeki wurin mutane ki dawo nan da 30mins zaki sha mamaki. Murmushi tayi ta fice daga d'akin. Abdul kuwa hararan Abdulrahman yayi yace Allah banda lokacin cin abinci yanzu saboda farincikin da nake ciki ya wadatar dani. Abdulrahman yace owk tunda baka son farincikin ammie ni bari naci ni kadai. Abdul yayi saurin matsowa wurin da Kulolin suke had'e da budewa, wani kamshin dad'i ne ya ziyarce shi, take yaji miyon shi ya tsinke. Nan ya zuba musu cikin plate d'aya suka fara ci suna hira har suka koshi. Bayan sun gama ci kenan sai sukaji hayaniyar abokan su nan Abdul yaje ya bud'e musu kofa. Aikuwa kamar jira suke ya bud'e kofar suka turo shi suka d'aga shi sama suna dariya, "dakyar ya samu suka saukar dashi. Nan suka nupi inda Abdulrahman yake da niyar shima su d'aga shi aikuwa ya banka musu harara nan take kowa ya canza ra'ayi. Sauran abincin da ammie ta kawo musu ne abokan su suka fara ci suna santi, da zolayar su wasu na cewa Allah ya nuna musu nasu wasu kuma na cewa Allah ya kawo su bikin haihuwa. Nan sukayi ta hira suna tsokanar su. B'angaren amare kuwa bayan an d'aura aure da misalin karfe hud'u na yamma akayi taron walima, wanda aka gayyato wata babbar malama ta gabatar da wa'azi inda tayi nasiha ta zamanta kewar aure mai ratsa jiki. ba'a watse taron ba sai karfe shida na yamma. Ko wacce amarya gidan su aka kaita domin samun albarka daga iyayenta. Plsss share [3/2, 7:44 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Wannan shafin naki ne ummu arpat, sai yadda kikaso yi dashi ina yinki sosai, Allah ya raya maki zuri'arki baki ɗaya, ngd da kulawar ki agareni. Kisa a ranki ni lashminzy ina sonki so na tsakani da Allah. Ana mugun tare 🤝🏿❤     Page 73-74 Amatullahi ce duƙe a gaban mummy da daddy suna mata nasiha mai ratsa jiki, "duk jikinta yayi sanyi saboda ba ƙaramin tasiri nasihar tayi a zuciyar ta da gangar jikinta ba. "sai faman rusa kuka take mummy na aikin lallashi.   ''''Bayan sun gama nasihar ne mummy ta jawo hannunta suka fito inda aunty salma ke tsaye ita da wasu ƙawayen amarya guda huɗu. Nan mummy ta damƙa ta a hannun su, "Amatu na kuka harda majina. "Bayan sun fita harabar gidan, wurin parking space suka nupa inda aka jera motoci kusan guda biyar.   "Ɗaya daga cikin motar aka sata ita da wasu ƙawayenta guda biyu, sauran ƙawayenta da aunty salma suka shiga mota ɗaya, sauran motocin kuma suka wuce empty.   Ɓangaren ameera kuwa indai ta fannin kuka ne ta tsare amatu domin kuwa tun bayan an tashi daga walima take ta kuka, ko abincin da aka kawo mata kasa ci tayi."Haka akayi ta rarrashinta har zuwa lokacin da umman su da sauran uwaye waƴanda sukazo biki tun daga kaduna suka sata a gaba suna mata nasiha. Ita ko sai kuka take wiwi, "tana tuna irin kewar ƴan uwanta da zatayi. "dan tasan tayi nisa dasu, indai ba wata matsala aka samu ba, kafin takai musu ziyara ai sai an ɗauki lokaci me tsawo.   Shiyasa idan ta tuna haka sai taji zuciyar ta karaya tayi ta kuka. Haka aka gama nasihar, "aunty uwani ƙanwar ummanta da ita da aunty hajara da da ƙanwar ta hafsa da wasu ƙawaƴenta guda uku suka riƙo hannunta har zuwa inda aka paka motoci. Nan suka sa amarya inda ya kamata sannan suma suka shiga tasu motar.   "Bayan sun fito ne suka tarar da motocin su amatu sun jera, "suma jerawa sukayi kamar yadda nasu amatu sukayi kafin suka take musu baya. Direct gidan ammie suka nupa, "inda ammie tayi musu tarba mekyau kuma ta nuna farincikin ta a gare su daga bisani tayi musu nasiha sosai sannan suka fito suka wuce gidan mummy itama sosai da fara'a a fuskar ta tarbe su haɗe dayi musu nasiha kamar yadda ammie tayi musu.    "Bayan sun fito ne suka ɗauke hanyar zuwa gidajen su dake cen gwarinpa wanda cikin wata ɗaya aka siye shi a ginan shi kuma part biyu ne a ciki duk iri ɗaya, sedai daddy da abba sun ƙara gyara shi yadda duk wanda ya ganshi sai yaji marmarin shiga.   "Haka ko akayi da ƴan kai amarya suka shiga gidan sai kalle-kalle suke tayi suna cews masha Allah. "nan suka sa kai suka shiga ɓangaren amatullahi. "baki sake suke kallon haɗaɗɗen palon ta daya sha kayan alatu, ga wani faskareren TV daya mamaye bangon palon," haka sukayi ta yaba kyan gidan kafin suka haura sama zuwa ɗakin amarya.    "Toilet suka shiga suka haɗa mata ruwa tayi wanka sannan suka shiryata cikin riga da skirt na atamfa, "suka feshe mata jiki da turarukka masu ƙamshi, sannan suka ɗaura ta can tsakiyar gado haɗe ta lulluɓa mata wani gyale mai raga raga wanda kai dake kallonta bazaka iya ganin fuskarta ba amma ita tana iya ganinka.   "Bayan sun kammala shirya ta ne aunty salma tayi musu sallama ta wuce tabar ƙawayen amarya tare da ita kafin ango ya iso.   Hakan ce ta kasance da ameera domin kuwa duk gidajen iri ɗaƴa ne, kala ce kawai ta bantanta, "ita ma haka suka sake mata wanka suka sa mata riga da skirt na atamfa sannan sukayi mata sallama zasu wuce. "nan fa ta botsare musu tana kuka kamar wacce akayi wa rasuwa, "haka suka tafi suka barta tare da ƙawayenta sai lallashin ta suke tayi.   "Fitowar su kenan sukaci karo da aunty salma, nan dukansu suka shiga mota suka wuce gida.   '''''Da misalin ƙarfe tara da rabi su ango suka iso, tun daga ɗaki su amatu kejin hayaniyar su, "su kuma suna farfajiyar gidan suna surrutan su da ƴan zolaye zolayen su. Abdulraheem kuma haushi ne ya kama shi dan bega amfanin tsayuwar su ba, "kabeer abokin abdulrahman dake duk cikin su shi kaɗai ne keda mata kuma goma harta kusa yace shi wallahi idan bazasu shiga ba tafiya zai yi saboda uwar gida na nan na jiran shi. Duk suka juyo haɗe da banka mashi harara, "banda abdul da har cikin ranshi yaji daɗin maganar sai ya waske saboda yasan halin abokan nasu da iya fassara abu yace gaskiya kam karta ce mu muka riƙe mata miji ba. ''''Usman yace kai gaskiya haka ne mu wuce, "kabeer yace toh fa shi sai ya shiga duka ɓangaren yaga amaren, "usman ya karɓa da cewa kamar ka shiga raina kuwa. Nura yace kai babu wani jayayya duka sai mun shiga kuma part ɗin abdulrahman zamu fara shiga. Nan suka sasanta kansu suka nupi ɓangaren abdulrahman harda abdulraheem. "bayan sun shigane ƙawayen amarya suka fito da amarya nan palour, "sukayi mata nasiha, sai nura da zolaya yace gaskiya ni fah zuwana yayi rana domin kuwa nan da wata ɗaya zanyi aure nima na huta da....... Usman yakai mishi daƙuwa haɗe da cewa wai kai wani irin mutum ne? Ko'ina kaje sai ka sayar da halinka neh?   Kabeer ya amsa da ina ruwanka kai kuma ɗan sa ido, faisal yace ku wallahi  baku da hankali yanzu nan ɗin ma sai kun nuna halin ku? Allah dai ya shirye ku. Usman yace tau sannu ustaz kai da baka raina laifi. Abdulrahman dan tun shigowar shi hankalin shi ke kan Amatu yace babu wani gaskiya ya faɗa idan ba haka ba nan ɗin ma miye na nuna hali, kodan asan daku a duniyar?? Abdul yayi tsakin jin haushi dan ya matsu basu wuce ba ya cika yayi taf har besan sadda tsakin ya fito fili ba. Kowa ya juyo yana kallon shi amma ko a jikin shi sai ma latsar wayar shi da yakeyi.   "suma basarwan kawai sukayi haɗe da miƙewa sukayi wa amarya sallama" nan ƙawayenta suka mayar da ita ɗaki, sai hawaye take suna lallashinta har ta ɗanyi shuru kafin suka fito nan palon. Nura sai kallon mufidah yake tayi ita ma haka sarai tana lure dashi sedai bata nuna ta ganshi ba. Nan suka fito abdulrahman ya juya zai rufe ƙofa aikuwa abokan suka bankaɗo mashi harara usman yace Allah baka isa ba sai ka rakamu. kabeer ya wani ɓata rai yace yama shiga ya gani.     Nida lokacin nawa wallahi har sha biyun dare suka kai saboda tsabar rashin mutunci. Abdulrahman yayi murmushi haɗe da jawo ƙofar ya rufe ya biyo su a baya yana tafiya yana tuna irin shaƙiyancin da sukayi wa kabeer lokacin auren shi. Part ɗin abdul suka nupa, nan ma haka sukayi musu nasiha sannan kuma suka nuna halayar su kafin suka fito. Bayan sun fito ne abokan ango suka kwashi ƙawayen amarya dan mayar dasu gida. Da suka wuce ne suma kowa ya kama gaban shi. Sai da suka iso daidai ƙofar shiga part ɗin su suka ɗaga ma junan su hannu haɗe da sakin murmushin da sukaɗai ne kawai suka san ma'anar shi. Hmmmmmm ɓangaren wa zamu fara leƙawa??? Lashminzy ceeee [3/2, 6:18 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''        Page 75-76 ''''Zaune take a tsakiyar gado, duk ta takure gu ɗaya, sai shasheƙar kukanta kawai kakeji, abdulraheem da shigowar shi kenan yaji duk hankalinshi ya tashi da jin kukanta. Daman tun kafin yaje rakiyar abokan nasu ya lura da kukan da takeyi. Saurin ƙarasowa wurinta yayi, haɗe da zama gefen gadon ya yaye mayafin da aka rufeta dashi. "Cikin nuna damuwa da kulawar shi yace sweet ameerah why crying? Ummm kukan me kikeyi? Shuru tayi taba ansa shi ba. Nan ya sake tambayar ta but still kanta na duƙe ta kasa ɗagowa ta kalleshi balle har yasa ran zata amsa shi.    "Tasowa yayi daga bakin gadon ya hauro sama daidai gabanta ya zauna yana fuskantar, a yayin da hannuwan shi ke sarƙe cikin nata, "yana ɗan murzasu a hankali, "yace wifey banason kukan nan da kike plzzz ki daina yana tayar mun da hankali.   ''''Ameera da duk jinta take wani iri  kamar ba ita ba yasa ta gaza magana dan yadda yake murza hannuwan ta cikin nashi sai takejin tsikar jikinta na tashi, "nan take hawayen dake zubo mata suka tsaya cak saboda baƙon yanayin data shiga, sai ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunwan ta amma inaa ya riƙe su gam. Abdul kuma ƙura mata ido kawai yayi yana kallonta and yanajin yadda take ƙoƙarin cire hannuwan ta daga nashi. "Sakar mata hannuwan ta yayi yasa hannun shi ya share mata hawayen da suka ɗan fara bushewa a fuskar ta kafin ya sauka daga kan gadon ya cire babbar rigan shi.   ''Bayan ya cire a hankali ya tako har zuwa inda take ya miƙa mata duka hannuwan shi biyu alamar tazo, "maƙe kafaɗa tayi tana wani sunne kai ƙasa. Shi kuma da yaga zata ɓata mashi lokaci sai kawai yasa hannu ya ɗauketa can cak ya direta a ƙasa yana kallon fuskarta datake ƙoƙarin karewa da mayafinta yayi saurin ansar mayafi ya wurga can tsakiyar gado.   ''''Daf da ita ya ƙaraso kamar mai shirin rungumar ta dan ita harta runtse ido tana jiran taji dumus sai kawai ta tsinkayo muryarshi daidai saitin kunnenta yana cewa matsoraciya kawai zoki zauna anan, "ya faɗa gami da jan hannunta ya zaunar da ita saman carpet ɗin dake malale a tsakiyar ɗakin. Shi kuma fita yayi yaje kitchen ya ɗauko plates da cup ɗin glass guda biyu ya kawo ya dire a gabanta sannan yaje wurin dressing mirror ya ɗauko ledar kazan daya shigo dashi ya aje sannan ya zauna suna fuskantar juna. Bayan ya zauna ne ya buɗe ledar nan take wata shirgegiyar kaza ta bayyana, tasha yaji da albasa sai maiƙon mai take fitarwa da ƙanshi. Wallahi har yawu na ya tsinke🙁😋 ku kuma da kuke kallona bazaku ci ba musamman baby md data fara tsilalo miyon kwaɗayi😍   "Buɗe marfin yoghurt yayi ya tsiyaya cikin kofi ya miƙa mata, "kallon shi kawai ta tsaya tana yi, shi kuma ɓata rai yayi yace karɓa nace!! Da sauri ta karɓa ganin babu wargi a fuskar shi. Daman yunwa takeji sai ta kafa kai tasha kusan rabin wanda ya zuba mata a cup ɗin kafin ta aje.   "Tana ajewa ya yago mata kaza yasa a bakinta, ba shiri ta fara cin dole, haka yayi ta tilasta mata yana bata a yayin da shi ko ɗanɗanawa baiyi ba. Duk ji tayi ya gundure ta gashi sai tura mata yakeyi yasa ta ɓarke da kuka, "da sauri ya ajiye wanda yayi niyar sa mata a baki yace wifey meya faru, faɗa mun. "Cikin sigar shagwaɓa tace bakai bane, "nace maka na ƙoshi amma kana ta tura mun. Haƙuri ya fara bata yana lallashinta kafin ya kwashe kayan yakai kitchen, ko daya dawo tana toilet, bakin ƙofar toilet ɗin yaje kamar mai yin raɗa yace kiyi alawla kafin ki fito. Yana faɗa ya juya wurin wardrope ya buɗe ya ciro mata doguwar rigar bacci mara nauyi wanda datasa da batasa ba duk ɗaya neh dan shara-shara take komai na jikinka ana iya hangowa.   "Bayan ya fitar ne ya ɗauko hijab babba ya haɗa da rigar ya ɗora mata saman gado sannan ya fice daga ɗakin. "Ɗakin shi ya shiga ya cire kayan ɗake jikin shi, ya shiga toilet ya watsa ruwa, "bayan ya fito ne ya tsane danshin jikin shi da towel, sannan ya nupi wurin dressing mirror ya shafe jikin shi da mai da kuma su body sprays. Bayan ya gama ne ya ɗauko wata farar jallabiya ya sanya. Nan ya kashe wutar ɗakin sannan ya fito ya nupi ɗakin ameera.    '''Ameera na fitowa daga toilet taga an ajiye mata kaya, duba yanayin su tayi haɗe da sakin murmushi ta nupi bakin ƙofar da niyar rufewa sai taga wayam babu makulli. Tsaki taja ta koma ta zauna tana wani cin magani. Ganin har kusan minti talatin bai dawo ba sai kawai da zura rigar haɗe da hijabi ta miƙe da niyar hawa kan gado sai taji ƙarar buɗe kofa.     "Take taji gabanta ya faɗi, amma sai ta fuske zata haura saman gado yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa kixo muyi sallah mu godewa Allah. Ba musu taje ta tsaya inda ya shimfiɗa musu sallaya yana gaba tana bayan shi. Nan yaja su raka'a biyu," bayan sun idar ne yayi musu addu'oin samu zaman lafiya sannan kuma yayi mata wasu ƴan tambayoyi da addini ya tsara kuma ba laifi duk ta ansa.   "Tashi sukayi ta naɗe sallayar duka biyu tasa cikin wardrope kafin ta iso bakin gado zata kwanta yace hijabin fah? Cak ta tsaya batare data juyo ba tace dashi zan kwanta. Ɗan jimm kaɗan yayi danshi ya gama ganota sai yace a'a ki cire hijabin ki aje tunda ga bargo can, kinga ni fita zanyi sai ki lulluɓe ke kaɗai ko? Cike da jindaɗin maganar shi tace eh eh dan duk a tunaninta da gaskiya yakeyi. Haka ta cire hijabin ta naɗe shi ta haura saman gado ta kwanta, shi kuma yana tsaye yana kallonta daga bisani ya ƙarasa wurin ƙofa yasa key ya rufe sannan ya kashe ƙwan wuta sai ya rage side bulb ɗin da hasken shi kaɗan ne dan ba komai kake iya gani ba.   "Ita kuma tana jin ya kashe wuta ta gyara kwanciyar ta dan duk a tunaninta fita zaiyi. Kwatsam bata zata ba sai jin mutum tayi a bayanta. Ƙoƙarin yin magana take yayi saurin rungumota jikin shi, muryar ta na rawa tace sweet ab..dul ba....cewaa....kai....fita..... Katse ta yayi ta hanyar ɗaura ɗan manunin shi akan laɓɓan shi yace shhhhh🤫 shuru tayi hawaye na zuba a idonta. Da sauri yace subahallah me kikeyi haka? Plsss ameera ki daina kukan nan kinsan banason zubar hawayenki ko? Shuru tayi masa yaci gaba da cewa tunda gudun mijinki kikeyi bari in fita in baki wuri ya faɗa yana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon.   "Jin irin maganar da yayi ne yasa ta fara tuno nasihar da aunty tayi mata na cewa kada ta kuskura ta ƙaurace wa mijinta, yasa da sauri tasa hannunta ta jawo jallabiyar sa tace am sorry plss amma ba haka nake nufi ba. Dawowa yayi ya kwanta gami da jawota jikinsa cikin raɗa yace karki damu kiyi baccin ki kinji. Toh tace amma cikin ranta tsoro takeji kar yayi mata wani abun da tanajin labarin abunda ke faruwa a first night.   "Abdul ƙara matsota yayi jikinsa sosai har yanajin saukar numfashin ta, "a hankali ya fara shafa jikinta tun daga kan fuskarta har abunda yayi zuwa ƙugunta. Ita kuma lafewa tayi a faffaɗan ƙirjin sa dajin baƙon yanayin daya shigeta. Cikin jindaɗin shafar ta da yakeyi har batasan lokacin da bacci ya ɗauke ta ba.   '''Ƙarewa fuskar ta kallo abdul yayi yana ɗan taba ɗan ƙaramin lips ɗinta da yake kalar ja sai sheƙi yakeyi, "take yaji yana sha'awar lasar su, "daman tun ba yau ba yakeson yaji yadda lips ɗin suke. Babu wani ɓata lokaci ya ɗora bakin shi akan nata yana musu tsotsar lollipop.   "Cikin baccin ta takejin kamar ana luguiguita bakin ta ga kuma wani abu me taushi da santsi da takeji yana mata yawo a cikin baki. Buɗe idonta tayi karaf suka sauka kan abdul dake faman tsotsar bakinta kamar anba ƙaramin yaro sweet.    "Zame bakinta tayi, "shi kuma sai huci yake, yana kallon cikin ƙwayar idonta yace na tashe ki ko? Cewa tayi eh sai yace am sorry kinji amma ki ɗan bari in ƙara tsotsar su kaɗan plss ya faɗa gami da haɗe hannunwan shi biyu. Ko ƙala batace ba sai ya kawai ya ƙara jawota jikinshi dan yadda yake mararin ƙara kissing ɗinsu yasan inya biye mata ba bari zatayi ba.   "matseta yayi a jikin sa yakai bakin shi kan nata, yaci gaba dayi mata wani irin salon tsotsa a yayin da ita kuma sai mutsu mutsun ƙwace kanta takeyi. Haka yaci gaba da kissing ɗinta yana shafar jikinta ta ko'ina, can ya saki bakin ta ya fara sunsuno wuyanta yana shafa wasu ababe masu taushi kamar auduga. Kallon inda hannuwan shi yayi yana ƙoƙarin zame mata riga tayi saurin riƙeshi. Dakatawa yayi ya ɗan faki idonta sai ya zame rigar.    "Nan take sha'awar shi ta motso dan yadda ya gansu ɓuluɓulu suna kallon shi, take yakai bakin shi kansu yana tsotsar su. Tunda ameera taji haka sai duk taji tsoro ya kamata, nan take ta fara hawaye, shi kuma duk ya rikice ya fita hayyacinsa, sai yamutsa ta yake tako ina.    Kuka tasa tana tureshi daga jikinta, amma yaƙi cikata, "da ƙarfi tasa hannuwanta duka biyu ta tureshi gefe sannan ta gyara rigar ta, "shi kuma gefe ya koma yana maida numfashi haɗe da tsura mata idonshi da suka ƙaɗa izuwa ja, "duk yanayin shi ya sauya, zuciyar shi sai zafi take mashi dan beso ta katse masa jindaɗin shi ba.   Cikin marairaicewa yace plssss my ameerah ina cikin matsala dan Allah karki gujeni wallahi mutuwa zanyi idan baki bani hakki na ba. Cike da tausayin shi da kuma tuno nasihar da akayi mata gashi duk ya fice a hayyacinsa kamar ba abdulraheem ba tace niba gudunka nakeyi ba.   Ajiyar zuciya ya sauke yace toh kibari inyi abunda nakeso, ya faɗa dan son jin amsar da zata bayar, "sedai komi batace ba ta kwanta haɗe da jawo blanket ta rufe duka jikinta. Ranshi ne yaɓaci dan ganin yadda tayi banza dashi ga marar shi da yakejin kamai zai fashe saboda zafi.    '''Kwantawa yayi cike da damuwa dan yasan dama hakan na iya faruwa kuma baiga lafinta ba tunda yasan wannan shine darenta na farko kuma dole zata dinga ɗari-ɗari  dashi. Kasa jurewa yayi ya mirgino zuwa inda take cikin lallashinta yace plsss ameerah idan bakya son wani abu ya faru dani ki amince kinji dan Allah.   "Juyowa tayi ta faɗa saman faɗeɗen kirjin shi, nan take ya gane manufarta aikuwa ba ɓata lokaci ya fara yi mata wasu salo wanda baki bazai iya faɗan su ba. Haka ya dinga murzata son ranshi daga bisani hajiya babba ta fara neman agaji. Babu ɓata lokaci naji ya fara adduar saduwa da iyali, daga nan na fice na basu wuri. Bari mu leƙa abdulrahman.    "Abdulrahman na shiga ɗakin amatullahi ya ƙarasa kusa da ita. kamar yadda dai aka saba, ya ciyar da ita sannan ya umarce ta data taso suyi nafila, "nan dukan su suka ɗoro alawla, ya shimfiɗa musu sallaya yana gaba tana baya yaja su raka'a biyu. Bayan sun idar ne yayi musu addu'a haɗe dayi mata ƴan tambayoyi kuma alhamdulillah an dace.    Bayan sun tashi ne ya nuna mata wuri data kwanta dan sam taƙi sakin jikin ta dashi duk wani abu da takeyi a takure takeyin shi. Shiyasa duk wata niyar shi ya aje a gefe dan bayason abunda zai takura mata.   "Can ƙarshen gado ta kwanta shi kuma ya cire jallabiyar dayasa lokacin da zasuyi sallah, "bayan ya cire ne ya kashe bulb ɗin ɗakin sannan ya hauro saman gadon ya kwanta haɗe da jawo amatu dake can ƙarshen gado ta duƙunƙune kanta. Cikin tsoro da fargaba ta fara addua a cikin zuciyar ta 😁 kuji wai? Hmmmm Shi kuma ganin yanayin ta yasa yace ki kwantar da hankalin ki babu abunda zanyi maki. Ya faɗa gami da ƙara jawota ya lulluɓe su da bargo. Hmmmmm asuba ta gari. Plssss share [3/3, 12:42 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''        Page 77-78 Washe gari da safe na leƙa ɓangaren abdul can ƙarshen gado na hango su shida ameera sai faman kuka take, shi kuma yana aikin lallashi. "Tun cikin dare take ta mashi koke-koke wanda har yanzu shi takeyi, duk ya ruɗe da jin kukan nata.   "Yanxu haka ma kwance take a jikinsa, tana shashsheqa, "duk ji yake babu daɗi, gashi duk wani kulawa da take buƙata ya bata amma still kukan take. Zameta yayi daga jikin sa ya nupi ɗakin shi. Wayar shi ya ɗauko yayi dialing number usman,"ba jimawa yayi picking.   ''Cikin muyar damuwa abdul yace guy plzzz kazo mun da tablets ɗin da zan turo maka yanzu, "daga can usman yai ƴar dariya yace haba dai kace har an shiga kenan, ya ƙarasa maganar haɗe da sheƙewa da dariya. Tsaki abdul yaja haɗe da kashe wayar dan kwakwata baya jin wargi yau saboda halin da sweet ameeran shi ke ciki. Bayan ya katse kiran ne ya tura mashi sunayen tablets ɗinda zai sayo mashi ta text message. Sannan ya koma ɗakin ameera. Ƙoƙarin tashi yaga tanayi amma ta kasa saboda wani irin zogi da takeji a ƙasar mararta. "Ƴar ƙara ta saki haɗe da komawa ta kwanta. Da sauri ya ƙaraso haɗe da zama a wurin ya rungumota jikinshi, "cikin jin tausayin ta yace wifey ina zakije? Hawaye na zuba a idonta tace fitsari zanyi. Batare daya amsa ta ba ya sureta sai cikin toilet ya direta sannan ya fito, bayan minti biyu ya koma toilet ɗin. Kamar yadda ya kaita haka ya dawo da ita sedai bakin gado ya ajeta yaje ya buɗe wardrope ya ɗauƙo mata doguwar riga mara nauyi. Daman tun sadda yayi mata wanka taƙi bari yasa mata kaya, ko underwears daƙyar tasaka su. Wurinta ya ƙaraso ya miƙar da ita tsaye, tana wash, wash amma haka yasa mata rigar da kuma hular daya gani tare da  rigar. Bayan yasa mata ne ya zaunar da ita, shima ya zauna ya fara dialing number ammie. Tana ɗauka suka gaisa sai yake tambayar ta breakfast, ɗan tsuki taja, tace kai baka da kunya ko, "shine zaka wani kirani wai breakfast? Murmushi yayi yace plzzz ammie ki aiko mana yanzu. Amsa shi tai tace ai mommyn kuce zata aiko muku ina ma tunanin yana kan hanya dan yanzu ta kirani tace basai na aika muku ba zatasa a kawo muku.    Murmushi yai yace Allah sarki mommy shiyasa nake sonta saboda akwai iya kula da mutum, ammie tace ai nima halayyarta na burgeni. Sallama yayi wa ammie dan jin kamar ana knocking. Da hanzarin sa ya isa bakin ƙofar, "nan yaga samha da umar riƙe da basket ɗin abinci. Gaisawa sukayi sannan samha ta miƙo mashi basket ɗin.    Bayan ya amsa ne yake cewa su shigo, umar yace a'a sauri sukeyi, nan suka wuce shi kuma ya ajiye basket ɗin a palour yana cewa ai gwara ku wuce dan karku takura mana. Kitchen ya shiga ya ɗauko musu plate da cup ya kawo wurin basket ɗin ya aje. Yana ajewa yaji ana buga ƙofa, tsoki yaja yayi kwafa ya nupi bakin ƙofar, yana buɗewa yaga usman. Murtuƙe fuska yai ya anshi maganin batare da yace wani abu ba yaja ƙofa ya rufe. Dariya usman yayi yana cewa zamu haɗu ne ai.    "Ɗakin ameerah ya shiga ya ɗaukota kamar waya ta baby ya direta a gaban abincin daya zuba musu, nan yasa spoon da niyar zai bata a baki tayi saurin tsayar dashi, cikin kasalalliyar muryar ta tace a'a kabari zan iya ci dakaina Ƙura mata ido yayi yaga duk ta zama wata iri, fuskarta harda ƴar rama tayi. Tsintar kanshi yayi da jin haushin abunda yayi mata, sai wani ɓangare na zuciyar shi ke cewa ai sunna kuka raya kuma ko wacece mace hakan ne yake faruwa da ita a first night d'inta. "Kawar da tunanin yayi ya tura mata abincin gabanta yana kallonta ta fara cin abincin harta gama, sedai ba wani cin kirki tayi ba. Ɗago kanta tayi ta kalleshi taga shima kallon nata yake, "tace my abdul kaci abinci mana, ta faɗa kamar zatayi kuka. Hannuta ya riƙe yace ameera bazan iya cin abinci ba alhalin kina cikin wannan yanayin. Duban shi tayi saboda ta kwantar mashi da hankali dan taga duk yana cikin damuwa tace nikam lafiya ƙalau nake, dan Allah kaci abinci. Matsota ya sakeyi jikinta yace kina nupin yanzu kinji sauƙi? Gyaɗa mashi kai tayi alamar eh sai yace owk amma duk da haka zan baki wasu tablets kisha saboda jikin ki ya rage zafi kinji ko? Amsawa tayi da toh gami da raba jikinta da nashi ta jawo kula zata zuba mashi abinci yace a'a sauran nata yakeso, ba musu ta ɗauki sauran nata ta matso dashi gabanta ta yadda zataji daɗin ɗiba tana bashi.    "Spoon ɗaya kawai ta bashi ya ansa ya faraci da kanshi wai bayason ta wahala. Nan ya cinye tass ya tattare ƴan plates ɗin yakai kitchen ya aje. Bayan ya dawo ne ya bata magani tasha sannan yace taje ta kwanta. Maƙe kaɗa tayi alamar ba inda zata. Murmushi yayi yaje ya kunna musu TV yace tazo suyi kallo tunda bazata kwanta ba. Nan ma ta maƙe ka faɗa alamar batazo ba. Zuwa yayi gabanta yana murmushi yace ameerah kin cika shagwaɓa, "yanzu me kikeso?? Cikin shagoɓa tace wurin amatullahi zanje. Waro ido yayi yace a'a kiyi zamanki zuwa anjima sai kije kinga yanxu ko sha ɗaya batayi ba yanxu haka bacci sukeyi. Kuka tasa mashi harda bubbuga ƙafa a ƙasa wai ala dole sai taje. Kinkimarta yayi yakai ta ɗaki yace toh tunda sai kinje nikuma sai na maimaita kafin in bari kije. Ihu tasa kamar wacce taga abun tsoro tace Allah bazan bari ba kuma sai na faɗawa mommy abunda kayi mun. Wayar shi ya zaro daga cikin aljihu yace gashi ki kira kice nace sai ma na kara maimaitawa.   "Buge wayar tayi ta fara dukan shi a ƙirji tana kuka, shi kuma cike da jin kasalar abunda take mashi ya haɗe bakin su wuri ɗaya, ɗip da ɗauke wuta, sai ajiyar zuciya take saukewa bayan ya zare bakin shi daga nata Murmushi yayi haɗe da kashe mata ido, ya fice da sauri da jin ana bugun kofar su. Murmushi ne ya bayyana a fusƙar shi a lokacin da idanun shi sukayi arba dana shi. Shima murmushin ya sakar mashi sannan ya miƙa mashi hannu suka gaisa.   Amatullahi ma gaishe shi tayi ta shige cikin palon. Wurin zama take nema abdul yace bazakije kiga kawar takii ba, murmushi tayi tabi hanyar da yake nuna mata da hannun shi, daman dan ameerah tazo toh kuma tana jin nauyin ta tambaye shi ina take shiyasa tayi shuru.   Tsaye taga ameerah, a bakin wardrope, aikuwa da sauri amatu ta ƙarasa ta rungumeta ta baya. Cike da murna ameera ta juyo dan ta hangeta ta jikin madubin dake liƙe da wardrope ɗin. Murmushi suka sakarwa junan su, amatu tace besty ya naganki haka, kamar wacce tayi rashin lafiya. Ameerah taja hannunta suka zauna saman gado tace kedai bari ai aikin gama ya gama. Amatu ta sheƙe da dariya tana cewa kice abdul da hazon shi yake. Ameerah ta ɓata rai gami da juya mata baya. Lallashin ta amatu tayi tana bata haƙuri kafin ta sauko tace suje palour. Nan ameerah ta gaida abdulrahman sannan suƙaci gaba da hirar su gwanin ban sha'awa Plsss ayi manage with dis page [3/4, 9:44 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''        Page 79-80 Bayan sati ɗaya,    ''''''Abdul ne tsaye a palour sanye cikin riga da wando na kanti masu kyau, "fuskar shi cike take da damuwar missing ɗin ameerah da zeyi. Ameerah ma tsaye take tana kallon shi idonta sun cicciko da ƙwalla. Hannuwanta kuwa sarƙe suke a cikin nashi, ta riƙe su gam.     "Cikin kakkausa murya yace "ameerah kiyi haƙuri nima ba'a son raina zan tafi in barki ba, "kuma nayi maki alƙawarin anjima da rana zan dawo in duba lafiyarki kinji ko? Ƙwallar data maƙale mata a ƙwayar ido ne ta zubo, cikin rawar murya tace toh ni fah tsoro nakeji, dan Allah ka tafi dani.   "Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "miye abun tsoro baga amatullahi ba sai kije part ɗinta kuyi ta hira ko, ya faɗa haɗe da ɗage girar sama. Cike da rigima irin nata ta sake hannuwan shi ta nupi hanyar shiga ɗaki. Da sauri ya jawo hannunta suka zauna saman kujera ya kalleta ido cikin ido yace tunda bakya son na taimaki jama'a na samu lada na fasa zuwa.   ''''Yayi maganar a yayinda yake ƙoƙarin cire takalmin dake ƙafarsa, "dakatar dashi tayi, haɗe da miƙewa tsaye ta jawo hannun shi tana girgiza kai tace a'a ka tafi kawai kaji. Ƙwace hannun shi yayi ya koma ya zauna yana cewa nikam ki ƙyaleni ba inda zani.   Kuka ta farayi tana jan hannuwan shi amma sam yaƙi tashi, "faɗawa jikinshi tayi tana ɗan bubbuga hannuwanta a jikinshi. Shi kuma daman abunda yakeso kenan, wai anba kura ajiyar nama😍 Nan ya rungumeta tsam a jikinshi yana shafa bayanta a hankali.   "Cike da jin kasala ta kalleshi tace my abdul ka wuce karka makara fah? Bakinta kawai ya tsurawa ido, yadda take magana tana motsa shi a hankali. Cigaba da magana tayi, gami da bubbuga ƙafafuwanta dake saman nashi.     ''''Take yaji wata irin kasala ta saukar mashi, rirriƙe hannunta yayi ya ɗago fuskarta cike da shauƙi ya fara kissing ɗinta, "Kamar yadda ya sabar mata a ƴan kwanakin nan da sukayi," sai itama ta fara mayar mashi da martani, a hankali suka fara mayar da numfashi bayan sun dakata. Tashi ameerah tayi daga jikinshi ta ɗauki jakar shi dake kusa dashi ta nupi hanyar fita waje, shima cike da kasala ya biyo bayanta.    "Can a harabar gidan suka tsaya inda motar shi ke sheƙi dan tasha wanka. Buɗe motar yayi ya shiga a yayinda yabar ƙafar shi ɗaya a waje yana kallonta.    Itama kallon nashi takeyi sai suka sakar wa junan su murmushi. Jakar shi tasa a gidan baya sannan ta dawo gefen shi tace tau...Allah ya tsare mun kai daga mugun nupi kuma Allah ya dawo mun dakai lafiya.    Lallausan murmushi ya sakar mata gami da fitowa ya sumbace ta a goshi ya koma saboda jindaɗin addu'ar datayi mashi. Hannu ta ɗaga mashi tana mashi bye-bye kamar yadda shima yake mata. bata bar wurin ba har sai daya ɓace wa ganin ta.   Ɓangaren amatullahi kuwa jiya suka sha amarci ita da abdulrahman ɗinta, domin duk kwanakin nan da sukayi be taɓa nemanta ba sai jiya da daddare, "ai kuwa tun ciki dare ta rikice mashi duk ta hanashi saƙat sai koke-koke take mashi, shi kuma bawan Allah kamar wani raƙumi da akala haka yake binta duk abunda tace ayi shi za'ayi.    Haka yayi ta faman rarrashinta har zuwa yanzu da safiya ta waye, yayi yayi da ita ta daure tasha tea daya haɗa mata amma fur taƙi sha. Sai ma tashi datayi tabar shi nan palour zaune. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwashe kayan yakai kitchen yana tafiya yana mita wai daman haka maza ke fama da matansu? Kwafa yayi ya shige ɗakin shi ya cire kayan dake jikinshi, "ya ɗaura towel ya faɗa toilet. Bada jimawa ba sai gashi ya fito, "jikinshi jiƙe da ruwa, ga gargasar dake kirjin shi ta kwanta luf gwanin burgewa. Ɗan ƙaramin towel ya ɗauko ya fara tsane jikin shi dashi kafin ya isa gaban dressing mirror ya fara shafa mai a hankali kamar wanda yake taɓa ciwo.    "A haka harya gama shafawa ya feshe jikinshi da turaruka masu ƙamshi sannan ya buɗe wardrope ɗinshi ya ɗauko wasu ƙananan kaya yasa. Bayan ya gama shiryawan sa ne ya fito daga ɗakin. Tsaye yayi yana kallonta yana jin wani irin sonta na ƙara shigar sa.   ,,,,,Itama dake bakin ƙofar ɗakinta tsaye tayi tana kallon shi dan ba ƙaramin kyau ya mata ba ga fuskar nan tashi daya ƙara yalwata ta da fara'a, daka ganshi kasan yana cikin jindaɗi da kwanciyar hankali. Takowa ya farayi har zuwa inda take ya tsaya cak yana kallonta.   Cikin son gano abunda take ɓoye mashi yasa kai zai shiga ɗakin sai hannun shi ya ɗan banko ƙofar, "ƴar ƙara ya saki haɗe da  dakatawa ya riƙe hannun yana washhhh, "cikin rikicewa tayi saurin aje kofin dake hannunta ta riƙe shi tana mashi sannu, sai kawai taga ya ɗago kanshi yana murmushi yace waton ni ne bakya son na baki ko.   Cike da jin kunya ta sunne kai ƙasa, "tana ɗan ɗingishi ta shige kitchen, bayan ta fito ne ta tarar dashi palour, nan taje ta zauna saman two seater tana kallon TV. Tasowa yayi yazo kusa da ita ya faki idonta, cak ya ɗauketa ya koma kan three seater da ita ya zauna ita kuma tana saman cinyar shi.   "Kiciniyar ƙwace kanta ta farayi ta kasa saboda riƙon da yayi mata bana wasa bane, "haka ta haƙura tayi zamanin ta daga ƙarshe dai bacci ne ya kwashe ta, "jin saukar numfashin ta yasa ya gane bacci tayi nan ya kwanta haɗe da janyo ta jikinshi ya rungume ta shima ya fara baccin.   Ameerah kuwa tana komawa cikin gida ta fara ƴan share-share duk da ba wani datti kega gidan ba. Bayan ta gama da ƙasa ne ta haura sama, nan ko datti babu dan basu fiye zama a nan ba, duk wani abu da zasuyi a ƙasa sukeyi, bacci ne kawai ke kaisu sama.    "Nan ma ɗan kakkaɓe dakunan tayi da falo, ta shiga toilet ta wanke. Bayan ta gama ne ta sauko ƙasa ta shiga kitchen tana tunanin abunda zata dafa musu da rana. Ɗaga kai tayi alamar tunani sai tayi murmushi ta buɗe fridge taga duk wani abu da zata buƙata akwai shi a ciki. Batare da ɓata lokaci ba ta ɗora tukunya kafin ta ɗauko sauran abubuwan da zata buƙata ta ajesu a gefenta. Nan ta shiga sarrafa su yadda ya kamata, take kuwa ƙamshi  ya gauraye kitchen ɗin. Tukunyar dake tafasa da ruwa ta zuba ɗanyen couscous a ciki, "cikin minti biyar ya dafu ta sauke ta sake ɗaura wata tukunyar dan haɗa musu farfesun kifi. Nan ta zuba ruwa dasu ingredients kafin ta fara kwashe couscous ɗin ta zuba cikin wasu haɗaɗɗun kuloli guda biyu.    ''Tana gama zubawa ta fito palour a gajiye ta zauna ta kunna TV tana kallo, bayan minti goma da zamanta ta shiga kitchen ta duba abunda ta ɗora, lokacin har yayi kusan dahuwa, nan ta ɗauki wayarta tayi dialing number mommy dan yau kwanan su biyu basu gaisa ba. Mommy na ɗauka ta fara zuba mata shagwaɓa, kamar yadda ta saba, "dan kullum  idan sukayi waya cewa take abdul yaƙi kawota gida. Mommy kam murmushi kawai takeyi tana cewa tayi haƙuri ai bada daɗewa ba zai kawota. Nan suka ɗan taɓa hira daga bisani ameerah ta katse kiran sakamakon abincin ta dake kan wuta tana gudun karya fara ƙauri.   Saukewa tayi ta kwashe cikin kula, sannan ta wanke pots ɗin da sauran kayan data ɓata sannan ta gyara kitchen ɗin komai ta mayar dashi mazaunin shi. Bayan ta gama ne ta wuce ɗaki danta watsa ruwa. Bada daɗewa ba ta shiga toilet tai wanka sannan ta fito ta isa gaban dressing mirror tayi ƴar simple make-up wa fuskarta sannan ta ɗauko wata atamfa kirar swiss kalar ja tasaka. Masha Allah kayan sunyi mata kyau sosai.   Flat shoes tasaka kafin ta fito daga ɗakin ta shiga kitchen, kulolin abinci ta ɗauka tasa a wani ɗan madaidai cin basket ta fito tayi hanyar fita waje. Tana buɗe kofa ta ganshi a tsaye riƙe da rigar shi irin na likitoci." Murmushi ne ya bayyana a fuskar su ita kuma har dana mamakin ganin shi dan duka duka yanzu sha biyu ne da rabi.   Hannuwan shi ya waro mata alamar tazo, aikuwa aje basket ɗin tayi ta faɗa jikinshi tana mai sakin murmushi kamar yadda shima murmushin yakeyi....... [3/5, 8:08 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Wannan shafin sadaukarwa ne ga Ruɗani fans grp 1,2&3 ina yinku sosai da sosai, Allah yabar kauna ❤       Page 81-82 Bayan ya cika ta neh tace zataje takaiwa Amatu abinci, "nan ya shige ita kuma ta isa part ɗinsu Amatu. A daidai ƙofar shiga ta tsaya ta fara knocking, "su amatu kuma lokacin suna bacci. Ƙara buga ƙofar tayi sai Amatu dake lafe jikin Abdulrahman cikin baccinta takejin kamar ana buga ƙofa.    """Da sauri ta buɗe idonta sai kawai ta zuba su akan Abdulrahman da yayi nisa a bacci, "ƙoƙarin tashi tayi sai yasa hannun shi ya ƙara jawota ya riƙe ta gam. Tsayawa kallon shi tayi taga ya ɗan sassauta riƙon da yayi mata sannan a hankali ta zare jikinta daga nashi sai tasa mashi pillow makwahinta.    "Ɗankwalinta daya faɗi a ƙasa wurin bacci ta ɗauka ta ɗoro sannan ta nupi bakin ƙofar, "tana buɗewa taga ameerah, "aikuwa rungumar junan su sukayi kafin suka ƙaraso ciki. Ameerah tace lallai yarinyar nan kina jindaɗin ki, waton ma bacci kike ko? Amatu tayi murmushi tace kedai bari wallahi banjin daɗi ne shiyasa na ɗan kwanta.    "Ameerah tace lallai kam. Ni kinga tashi mu shiga ɗaki karmu dami mijinki, ta faɗa haɗe dayin murmushi, "amatu kuma kallon basket ɗin dake hannun ameerah tayi gami da taɓa shi tace besty yau wani irin delicious kikayi mana? Ameerah tace favorite ɗinƙu keda mijinki. Amatullahi cike da murna ta ɗauki basket ɗin tace ameerah mu shiga daga ciki.     "Nan suka shiga kitchen amatu ta aje basket ɗin kafin suka shiga ɗaki, "ɗan hira kaɗan suka taɓa ameerah tace zata wuce saboda abdul na nan. Sallama tayi mata ta wuce.    ""Bayan ta tafi ne Amatu ta fito palour inda Abdulrahman haryanzu baccin sa kawai yake shirgawa, gashi lokacin sallar azahar yayi. Ƙarasawa wurin shi tayi haɗe da cire pillon data ɗora mashi, "aikuwa dajin ta cire yayi saurin jawo pillon haɗe da janyo hannunta data riƙe pillon. Sunkuyawa tayi ta ƙara zare pillon da hannunta a karo na biyu kenan, sedai a yanzu ya buɗe idonshi.    ,,,,,,A hankali ya saukesu akan Amatu, "murmushi ya sakar mata ya tashi zaune yana miƙa. Ita kuma miƙewa tsaye tayi ta zauna kusa dashi, cikin sweet voice ɗinta tace ummm kasha bacci gashi yanzu har ɗaya ta buga. Waro ido yayi ya duba agogon dake maƙale a hannunshi yaga ɗaya ma harta wuce, "aikuwa da sauri ya miƙe yaja hannunta suka haura sama. Direct ɗakin shi ya shiga da ita ya zaunar da ita saman gado sannan ya shige toilet. Ita kuwa binshi da kallo kawai take taga abunda zaiyi.     "Bada daɗewa ba sai gashi ya fito fusrkar shi da danshin ruwa, da alama dai alawla yayi. Kusa da ita yazo yaja hannunta ya shigar da ita toilet, "sannan a hankali yace kiyi alawla kiyi sallah anan kafin na dawo, "yana faɗar haka ya fice daga ɗakin. Ita kuma murmushi kawai tayi tace hmmmm Abdul kenan. Nan itama ta ɗoro alawla ta fito gami da shimfiɗa sallaya ta tada sallah.     Tsawon minti goma ta kwashe kafin ta sallame tayi ƴan addu'ointa sannan ta naɗe sallayar ta fita palon ƙasa. Direct kitchen ta shiga ta ɗauko su plates da cups da kuma basket ɗin abincin da Ameerah ta kawo musu.  Dinning area takai ta jera su sannan ta shige nan ɗakin ƙasa ta cire kayanta da niyar watsa ruwa sai ga Abdulrahman ya shigo.    "Aikuwa kamar wacce taga kwarto harda ƴar ƙara tayi haɗe da arcewa da gudu ta shige toilet, "murmushi yayi ya bita har bakin ƙofar. "Hannu ɗaya kawai yasa ya turo ƙofar a lokacin da ita kuma take kiciniyar sa key, sedai shi ya rigata. Cusa kanshi yayi ya shiga toilet ɗin. "mutuwar tsaye yayi a lokacin da idanunshi sukayi arba da kyakyawar surar ta, sanye take da towel wanda ko cinyarta bai ida rufewa ba. Hannuwanta tasa ta rungume kirjinta dashi wai duk dan karya gani. batasan kuwa hakan da tayi shiyasa nashanunta tasowa sama ba, har ana kallon burtsowar su ta saman towel ɗin.    Shi gabaɗaya hankalin shi ya tashi, dan ba ƙaramin sha'awar ta yaji ba musamman ma nashanunta da suke a waje. A tsorace ta fara ja da baya ganin yana kusanto ta. A hankali yake ƙara matsota har ta isa wurin bathtub wanda saura kaɗan ta faɗa ciki yayi saurin riƙo kugunta.    Ruƙo ƙugunta da yayi kuwa kamar ance towel kunce ne, towel ɗin ya suɓuce mata, "da sauri tasa hannunta ta gyara tana wani sunne kai ƙasa. Shi kuma duƙ ya wani susuce dan yadda ya gansu uwa an hura baloon, "ƙara matsowa yayi daf da ita yasa hannuwan shi duka biyu ya ɗago kanta.    Ƙura mata ido yayi yaga idanunta sun cicciko da ƙwalla, "Cikin tashin hankali ya tambaye ta yace baby kukan me kikeyi haka? Hannunta tasa tana goge ƙwallar data zubo mata muryar ta na rawa tanason tayi magana amma ta kasa saboda kukan da yaci ƙarfinta.    ?Cikin tashin hankali, ya rungumota jikinshi, cikin lallashi ya fara bubbuga bayanta at d sametime yana hura mata iska a kunne wanda hakan ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba. A hankali ya zareta daga jikinsa jin tayi shuru yace baby waton gudu na kikeyi ko?        Cikin sigar shagwaɓa da jan hankali tace toh ba wanka zanyi ba shine ka biyoni. Dariya maganarta tabasa yace toh shine abun kuka? Ta girgiza kai alamar a'a yace toh menene, "shuru tayi masa yace tau koma dai menene ya wuce yanzu dai bari in rage kayan jikina sai nazo na miki ko??   "Waro ido tayi haɗe da marairaice fuska tace plzzz yaya Abdul kayi haƙuri zanyi da kaina. Dariya yasa harda dafe ciki yace laaaa yaushe na zama yayanki?? Ƙafafunta ta fara bubbugawa a ƙasa tana cewa uhmmmm nikam ka fita da kaina zanyi. Murmushi yayi batare daya bata amsa ba ya fita.    Yana fita tasa key ta rufe ƙofar sannan ta zare towel ɗinta ta shige bathub ta fara waka, "fita nayi na bata wuri dan yadda naga ta ɓallo mun harara. Abdulrahman kuma  fita yai daga ɗakin ya nupi ɗakinta ya ɗauko mata wasu riga da wando da hular su me kyau. Sannan ya rufe ya buɗe ɗaya side ɗin ɗrowan ya ɗauko mata underwears kalar kayan waton pink colour ya aje saman gadon sannan ya fita.     Yana fita ɗakin ƙasa ya shiga ya zauna bakin gado yana jiran fitowarta, "bada daɗewa ba sai gata nan ta fito, aikuwa tana ganin shi tai saurin komawa dan kunyar fitowa take ya ganta babu kaya. Shi kuma ɓata rai yayi ya tashi a fusace yaje toilet ɗin, "tsaye ya ganta ta takure kanta. Batare da yayi tunanin komai ba ya isa wurinta ya jawo hannunta ya fito da ita ya zaunar da ita saman gado yace baby wai wannan kunyar fah?? Ni fah gaskiya wannan kunyar a daina ta saboda tana shiga hakki na.     Kuma ma daga yau tare zamu dinga wanka. A zabure ta ɗago idanunta ta watsa su akan nashi sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa zatayi magana ya dakatar da ita.... Yace a'a baby banason musu, yana faɗa ya fice daga ɗakin.     Cike da zulumi ta miƙe tsaye tana tunanin ko yayi fushi ne ya fita? Ganin bata da amsar da zataba kanta ta kawar da tunanin akan idan ta gama shiryawa zataje ta sameshi. Haka ko tayi bayan ta gama shafa mai tayi simple make-up ta haura sama zuwa ɗakinta.    Da shigarta ta hango kayan daya aje mata, murmushi tayi ta ƙarasa wurin ta ɗauki kayan ta fara sawa dan tasan shine ya fitar mata dasu. Woww kunga yadda kayan sukayi mata kyau kuwa?? Musamman rigar dan ita ta ƙara fito mata da surar ta waton kiran coca cola. Isa tayi bakin madubi ta ƙarewa kanta kallo tana ɗan jujjuyawa dan ita karan kanta tasan kayan sun amshe ta.     """"Yalwata fuskarta tayi da ƙayataccen murmushi ta fito daga ɗakinta ta nupi ɗakin shi. Tsaye ta hango shi a gaban madubi sedai da alama tsuwa kawai yayi. Ƙarasawa tayi inda yake ta tsaya ta bayan shi ta kira sunan shi, "shuru yai mata kuma yana jinta har tayi masa kira uku amma bai amsata ba.     Kukan shagoɓa tasa haɗe faɗawa bayan shi ta rungumo ta baya, a yayinda shi kuma wani irin yarrrr yaji sedai be nuna hakan ba sai ya juyo da ita ta gabanshi yana fuskantar ta yace baby rigimar ki tayi yawa, "nifa bakiyi mun laifin komai ba kawai nayi shuru ne inga yadda zakiyi. Sake shi tayi ta matsa baya tana share ɗan guntun hawayen data farayi ta nupi hanyar fita. Da sauri yabita yasha gabanta, ya riƙe ƙugunta da hannuwan shi cikin salon nuna soyayya da jan hankali haɗe ka kashe murya yace "baby wannan... [3/7, 5:22 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''            Page 83-84 Yace "baby wannan irin yanga haka fah, ai sai notin kaina ya kunce, ya faɗa yana murmushi. Da bataso kulashi ba amma maganar shi dariya ta bata kuma ita harga Allah tasan ba yanga tayi masa ba. Ɗan shan toka tayi ta cire hannunshi dake riƙe da ƙugunta ta fice daga ɗakin, "murmushi yayi ya bi bayanta har suka isa dinning area, nan ta zuba mashi abinci a plate ta tura gaban shi.     ''''''Yatsine fuska yayi kamar wanda yaga kashi kafin ya kalleta yace bazan ci ba! Waro ido tayi ta kalleshi suka haɗa ido taga duk ya murtuƙe fuskar nan tashi tace ayyah my Abdul plsss kayi haƙuri kaci, "idan bakaci ba nima fah bazan ci ba. Batare daya kalleta ba yace ya zanyi inci abinci bayan kina fushi dani?     "Ni fah ba fushi nake dakai ba ta faɗa a shagwaɓe, sai yace toh idan ba fushi kike dani ba miye neh? Babu komai ta bashi amsa a takaice. Komi baice mata ba ya tura plate ɗin gaban ta yace naji indai ba fushi kike dani ba toh ki bani a baki. Murmushi tayi wanda a iya laɓɓanta suka tsaya tasa spoon cikin couscous ɗin sai data cika cokali taf har yayi soro kafin ta ɗago ta kalle shi tace buɗe baki?     Waro ido yayi yace zaki  kashe mijinki neh??? Cike da shagwaɓa ta cunno bakinta gaba tace toh ni ban iya bama wani abinci a baki ba, "sai a naki bakin ko, ya ƙarasa faɗar maganar". Murmushi tayi tace uhmmm, "sai yace toh daga yau zaki fara kuma kullum a baki zaki dinga bani.    Kallonshi tayi har tana ɗan bubbuga kafarta dake sarƙe cikin nashi tace toh nifa ban iya ba, "murmushi yayi yace hmmm zaki iya ne ai ya faɗa haɗe da miƙewa tsaye ya isa wurin kujerar ta, "ta bayanta ya tsaya ya saƙalo hannuwan shi saman kafaɗunta ya saita bakin shi daidai kunnenta yace baby yaushe zamu maimaita ne ya ƙarashe maganar haɗe da shafo nashanunta??       """"Yi tayi kamar bata fahimce shi ba tace mene?? Shi kuma yasan sarai ta gane kawai jan magana ne sai yace toh bari in nuna maki ko, ya faɗa yana murmushin ƙeta. Aiko tayi saurin girgiza kanta, tace a'a nagane, dan tasan baƙar azabar datasha jiya kuma bata buƙatar sake jinta.      Ajiyar zuciya ya sauke ya koma mazaunin shi haɗe da janyota saman cinyar sa yace bari in koya maki yadda zaki dinga ciyar da mijinki. Ita dai komi batace ba sai gani tayi ya ɗebo abinci a spoon yafara bata, ba musu ta ƙarɓa.    Bayan ya bata spoon ɗaya ne ya juyota tana fuskantar shi yace saura ni, "cike da kunya ita ma ta bashi, haka sukayi tayi tana bashi yana bata and dsame time suna hirar su ta soyayya.     "After three weeks" Abubuwa da dama sun faru, Abdulrahman ya koma bakin aikin shi waton lecturing sedai kullum taka tsantsan yake da Amatu dan bayason ta fahimci wani abu dan shekaran jiya saura kaɗan ta gano shi dan mantawa yayi ya fito palour yana waya yana cewa shi bazai samu damar attending lecture.... Bai ida faɗa ba sai ya hangeta tafe, "aiko da sauri ya katse kiran. Shiyasa yanzu daya zo da takardun shi ɗakin shi yake kaiwa yasa cikin drower ya kulle, ko aiki zaiyi sai ya faketa yakeyi, "wani sa'in kuma sai tayi bacci yakeyi".    A ɓangaren soyayyar su kuwa sai abunda ya ƙaru, "kullum cikin kula da junan su suke, babu maison ɓata ma wani rai. Abdulrahman hatta da aikin gida indai yana nan tare sukeyi. Duk wani abu da amatullahi takeso shi yakeyi, ko kaɗan baya son ganin ɓacin ranta, inda itama hakane, duk wani hakki nashi bata taɓa tauye mashi, "a taƙaice dai zaune suke cikin zaman amana da kwanciyar hankali kullum suna liƙe da juna kamar cingum zuwa office ne kawai ke rabasu. Wannan tattalin da tarairayar da shagwaɓar  da abdulrahman ke nuna wa amatu ba ƙaramin tasiri yayi a jikinta ba dan yanzu ta koma tamkar ƴar autar mata, "duk wata hanya ta shagwaɓa da kissa da kisisina babu wanda bata sani ba.    Aikuwa kullum cikin rarrashinta yake, "da zarar yayi mata abu kaɗan zata sa masa kuka,    hatta da fita zaiyi kuka take sa mishi wai bata son ya fita ya barta ita kaɗai shi kuma haka zaiyi ta lallashinta harya samu yai mata wayo ya fita.   ''''''Yanzu abunda ma ke damun sa shine yadda gabaɗaya ta sauya, batason yana kusantar ta, "hatta da turare yasa cewa take ya daina sawa bata so, "ko abinci ba kowani iri takeci ba a yanxu, "sai kayan maƙu lashe wanda sune suka zama abincinta. Ɓangaren ameera da abdul suma hakance ta kasance dan kuwa kullum cikin kyautatawa junan su sukeyi, kuma soyayyar su ƙaruwa kawai take.   ,,,,,Kamar kullum, zaune suke suna hira Amatu na saman cinyar abdulrahman, dan yanzu indai suna tare nan ne mazaunin ta, "wani film suke kallo suna hira akan film ɗin. Sai wayar amatu tayi ringing, dubawa tayi taga mummy ce ke kiranta, da murmushi a fuskarta ta amsa kiran tana cewa "hello"   Daga can ɓangaren mummy ta amsa mata, bayan sun gaisa ne, mummy ke faɗa mata ai daddy yace su shirya ita da Ameerah ran monday zasu fara zuwa school, Cike da jindaɗi ko katse wayar batayi ba ta fice a guje, "daidai lokacin data isa bakin ƙofar part ɗin ameerah yayi daidai da  lokacin da Abdulraheemk ke shirin fitowa cikin shirin su na likitoci, "harya sa hannu zai murɗa handle ɗin ƙofar sai ya tuna daya manta da wani abu.    Sakin ƙofar yayi ya haura sama har yana ɗan haɗawa da gudu, ameerah dake bayanshi kuma ko ƙala batace ba dan yadda taga yanayinsa yasa ta gane cewar yayi mantuwa  ne. Zaman ta keda wuya amatu tayi knocking, nan ta tashi taje ta buɗe ƙofar lokacin amatu na tsaye riƙe da waya a hannunta. Murmushi suka sakarwa junan su amatu tace besty monday zamu fara zuwa school.    """Ameera tayi mata wani kallon up and down haɗe da yatsine fuska tace toh wa zaki faɗawa? Nida har ma na kira daddy nayi mashi godiyar kyautar motar daya bamu kuma Abdul yace cikin weekend ɗinnan zai fara koya mun mota. Amatu ta waro ido cike da mamaki tace mota? Yaushe? Wallahi jiya kuwa ina sa ran ma yau za'a kawo su harda naki. Amatullahi ta daka tsalle tana dariya tace wayyo Allah daddy, Allah ya saka maka da alkhairi, "ameera ta amsa ameen".     Abdulrahman daya biyo sahun amatu dan yaga abunda takewa murna, yayi saurin ƙarasowa wurinta ya riƙeta, yace baby miye haka? Ko so kike ki zubar mun da ajiya ta ne?? Sheƙeƙe take kallonsa ga kuma ƙunyar ameerah dataji sai ta kawar da zancen tace Abdul daddy ne ya siya mana mota nida ameerah kuma monday zamu fara zuwa school shiyasa nake jindaɗi. Dan murna kam ya tayasu sedai tunanin shi ɗaya yadda ƴan mazan jami'a zasu dinga kalle mishi mata, ga kuma cu ɗanya tsakanin maza da mata, take yaji wani irin kishinta ya dabaibaye masa zuciya kuma a take ya yanke hukuncin da zai ɗauka.......    Murmushi yayi yace gaskiya na tayaku murna Allah ya sanya alkhairi kuma Allah ya baku sa'a, duk suka amsa da ameen. Nan amatu ta koma part ɗinta ita da abdulrahman, ameerah kuma ɗaki ta wuce dan taga abunda ya tsayar da abdul dan kome   ya manta yaci ace ya ɗauko shi. [3/8, 8:16 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''                Page 85-86 ''''''''Kamar yadda kuka sani yau monday kuma yau su Amatu zasu fara zuwa school. Da misalin ƙarfe bakwai na safe na shiga part ɗin Amatu, WoW masha Allah kawai na iya furtawa saboda kyan datayi, "sanye take da dogon hijabi me hannu har ƙasa wanda ko kayan datasa ba'a gani, "hijab ɗin yasha guga sosai kuma kalar maroon ne kamar yadda safar ƙafarta ke kalar maroon a yayinda kafaɗarta ke saɓe da handbag baƙi mekyau."Fuskarta kuwa ko ban faɗawa me karatu ba ya san tana cikin tsantsar farinciki. A hankali Abdulrahman ke saukowa daga saman bene kamar wanda baison taka ƙasa shima ya shirya cikin manyan kaya wanda suka zauna dam a jikin shi, sai kuma baƙar jakar shi dake rataye a kafaɗar shi. Tun daga saman bene suke aikawa junan su da saƙon soyayya ta cikin ido har ya sauko ya ƙaraso wurinta. Murmushi ya sakar mata cikin zolaya yace iyee yau su baby za'a fara ɗauƙar lectures ya ƙarasa faɗar maganar yana mai yi mata dariya.       "Pillow ta ɗauko ta jefeshi dashi a yayinda ya kauce yana mata dariya, "cike da shagwaɓa ta faɗi zauna saman kujera tana bubbuga ƙafa a ƙasa wai sai ta faɗawa ammie. Cikin marairaice mata ya ƙaraso wurinta ya duƙa a gabanta yace sorry baby na kinga har kin ɓata kwalliyar taki ko, "ya faɗa yana mai shafo fuskarta.     Ita kuma harara ta banka mashi gami da cewa wace irin kwalliya nayi kai dama daƙyar kabari na shafa common powder?? Ɗan bata rai yayi yace toh so kike in bari kiyi kwalliya kowane ƙato ya kalle mun ke? Shuru tayi masa sai yace toh tashi mu tafi karmu makara. Nan ta miƙe tsaye yaja hannunta suka fito. A ɓangaren ameerah ma ta shirya tsaf itama sanye take da hijabi har ƙasa, "a bakin ƙofa suke tsaye ameerah na cewa ita fa ta gaji da ɓoye-ɓoyen da akewa amatu ya kamata a fito fili a faɗa mata. Abdul yace ameerah me kikeci na baka na zuba ne wai? Idan lokaci yayi zamu faɗa mata.     Ni yanxu matsala ta ita ce makarantar ku ɗaya da Abdulraman, "wallahi lokacin da nake faɗawa abdulrahman makarantar ku ɗaya da inda yake lecturing saida yayi kusa sakin fitsari saboda tsoro, kuma..... "Ameerah ta katse shi tace toh ku faɗa mata gaskiya mana kafin ta gane da kanta man. Abdul yace hmmm bazaki taɓa ganewa ba, "ameerah tace miye bazan gane ba??    """"Babu wata ɓoye-ɓoye Abdul yace muna zargin amatu nada juna biyu saboda yanayin ta da muka gani, "kuma abunda yasa muka jinkirta faɗa mata gaskiyar lamarin shine muna son sai mun tabbatar da in cikin ne da ita sai mu faɗa mata, kinga hakan da mukayi shine mafita dan nasan kodan albarkacin ɗan shi dake jikinta zata iya haƙura suci gaba da zaman su.    Ajiyar zuciya Ameerah tayi tace eh gaskiya wannan hakane toh amma yanzu wa zai kaimu school?? Murmushi yayi mai sauti haɗe da shafo kumatun ta yace sweet ameerah kenan kedai kawai mu tafi zaki ga abunda zai faru. Girgiza kanta kawai tayi tabi bayan shi.     A daidai parking slot suka tarar da Amatu da Abdulrahman, "suna ƙarasowa suka gaisa, Abdulrahman kuma ya ɗan matsa nesa dasu ya ƙara waya a kunne, sedai banji abunda yace ba kawai naga ya dawo wurin su, kallon su gabaɗayan su yayi sannan ya dawo da kallon shi zuwa ga Amatu yace ayi mun afuwa yanzu aka kirani wai an kawo emergency nan asibiti inyi sauri.    Duk da cewar taso ace shi zai fara kaita makaranta ranta bai ɓaci ba saboda tasan yanayin aikin su kuma aiki ne na samu lada, da fara'arta tace tau ai babu komai kayi sauri ka tafi. Toh yace yana kallon abdul yace hey bro ka kula mun da matas kaji ya ƙarasa faɗar maganar yana mai kashe mashi ido    "Shima abdul fakar su yayi ya ɗaga wa abdulraman babban yatsar shi 👍🏻 alamar yayi daidai kenan. Nan Abdulrahman ya shige motar shi ya wuce suma suka take mashi baya sedai ba hanya ɗaya sukabi ba. Suna tafe suna hira har suka iso cikin makarantar, "inda abdul bai wuce ba sai daya nuna wa kowaccen su department ɗinta da kuma hall ɗinda zasuyi lecture kan ya tafi.     "Zaune suke a wani haɗaɗɗen ƙaton hall wanda cike yake da ɗaruruwan mutane sedai abu mafi burgewa shine duk yawan jama'ar dake ciki baisa zafi ba saboda akwai AC dakuma fankoki masu bawa hall ɗin iska.    Wuri ɗaya suka zauna saboda bayan abdul ya siyo musu timetable sai yaga ai suna da lecture yanxu kuma duk wuri ɗaya zasuyi. Duk da ba abu ɗaya suke karanta ba amma yawaicin courses ɗin ma tare zasuyi shi.      "Zaune suke ko waccen su da joting note a gabanta sun mayar da hankalin su kan lecturer.    'Bayan abdul ya saukesu, zai fita kenan har ya kai gate sukaci karo da Abdulrahman na shirin shigowa, "saukar da glass dukan su sukayi haɗe da sakarwa junan su murmushi sannan kowa ya kama gaban shi.     "Da misalin ƙarfe huɗu na yamma su Amatu suka fito daga lectures, tsaye suke a bakin hall ɗin suna magana da wasu ƴan mata guda biyu, "ɗaya daga cikin su ce ke cewa gaskiya ya kamata suje su siyo handout dan haka akayi da koyarwa basu da shi suma ƴan matan yau suka fara zuwa.    Eh gaskiya dan ni wallahi banji daɗi ba kowa da handout a gaban shi mu kuma mun zuba na mujiya muna kallon malami, "ameerah ta faɗa cikin nuna damuwa, "Zaliha tace toh me kuke jira kawai mu tafi. Nan suka kama hanyar zuwa minimart dan siyan handout sedai sunayi suna tambaya har suka gano wurin.      Ko waccen su ta siya sannan suka bi hanyar dawowa, suna cikin tafiya ne Amatu ta hangi wata mota sak data abdulrahman, dan ita ta ɗauka ko shine sai ganin kawai tayi motar ta wuce su da gudu. Ameerah  kuma bata lura ba dan hankalinta na kan su zaliha da suke hira tana faɗa musu ai taga students handbook wasu rules and regulations idan ka gani sai kayi dariya, shine Ameerah ke cewa tana so "Amatu da sai yanxu hankalinta ya dawo kansu tace gaskiya nima ina so saboda karmu karya dokar makaranta, "sai nazifah tace ai su bari gobe tunda safe suje su anso, "Amatu tace daman ansowa akeyi ba siya ba?? Zaliha tace eh mana da zarar kinje da ID card ɗinki na school zasu baki.     Toh kawai Amatu tace tayi saurin ɗaukar wayar ta dake ringing, cikin sanyin murya tace ai na ɗauka ko Abdulrahman ne zai mayar damu gida shida ke cikin makarantar, "daga can ɓangaren da take waya yace a'a ai tun ɗazu nayi waya dashi yace idan na fito asibiti inzo in ɗauke ku inku tashi, "owk tau bakomai sai kazo ta faɗa haɗe katse kiran.     Ameerah da hankalinta ke kan Amatu tunda ta fara waya tace yaya dai? Amatu ta amsa ta tace cewa gashi nan zuwa ɗaukar mu. Ameerah ta amsa da toh.      Nan suka samu wuri suka zauna zaliha da hafsat kuma hostel suka wuce dansu kwana sukeyi. Basu wani daɗe a wurin ba sai ga Abdulrahman yazo da irin motar da amatu ta gani, "hakan kuwa ba ƙaramin damuwar tayi ba dan suna cikin mota sai datayi magana Abdulrahman da ameerah suka kalli juna ta madubi sai ameerah tace kin dai ga irin motar amma bashi bane, "Abdulrahman ya ƙara da cewa nida nake asibiti ina naga sararin zuwa makarantar ku? Shine ai ameerah ta faɗa.     "Nan suka kawar da zancen suka ɗauko hirar school ɗinsu suna bawa Abdulrahman labarin abubuwan da suka gani. Har suka iso gida.     A gajiye Amatu ta cire zumbulelen hijabin ta haɗe da faɗawa saman kujera, "ɗan hutawa kaɗan tayi ta shiga kitchen tasha ruwa, "Abdulrahman kuwa daman ɗaki ya wuce dan ajiye jakar shi. Bayan ya aje ne ya ɗauki wayar shi ya fara dialing number Abdul, "cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya ɗauka, yace ɗan uwa yane? Abdulrahman ya bashi labarin abunda Amatu tace na ta ganshi kuma da gaskiya shi ɗin ne dan shima ya gansu kuma babu halin ya koma shiyasa dayayi kusan isowa wurin su yabawa motar wuta duk cewar tana da tinted ba mai iya kallonshi.     Abdul yace gaskiya wata rana za'a iya samun matsala kawai ka ɗauƙeta ka kaita asibiti a aunata, idan harya tabbata da gaske tana da juna biyu tau shikenan idan ma bata dashi ya zama dole a faɗa mata gaskiya. Abdulrahman yace tana mun kallon likitan ne zan kaita asibiti a aunata?? Cike da damuwa abdul yace af hakane fah tau yanzu ya za'ayi kenan??    Abdulrahman yace nima kaina ya ƙulle amma bari idan ka dawo mayi magana, "abdul yace toh, daga nan ya katse kiran. Tashi yayi daga zaunen da yake ya shiga toilet ya watso ruwa sannan ya shafa vasilin, dan yanzu yabar shafa duk wani mai me kamshi ko turare saboda Amatu. Yana cikin zura ƴar farar jallabiyar sa kenan sai gata ta shigo sanye cikin doguwar rigar yadi mara nauyi........ Comment     Share [3/9, 4:43 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' Masoyana ina sonku da ƙaunar ku a duk inda kuke, kuma masu turo saƙonni ina jindaɗi sosai ngd, Allah yabar mu tare ❤ ONE LOVE               Page 87-88 """"Ƙarasowa tayi wurin shi ta taya shi sanya rigar sannan taja hannun shi suka fito palour, ta zaunar dashi a gaban abincin data jera musu nan tsakiyar palour. Shi kuma binta kawai yake da ido kan ta zauna ya janyota jikin shi yace baby kina ji dani wallahi. Ɗan murmushi tayi tace toh inban kula dakai ba wazai kula mun dakai, "ko so kake inyi banza dakai wata ta ƙwace mun kai??    Ƙyalƙyacewa da dariya yayi yace haba baby ai karki damu babu wacce ta isa ta ƙwace maki ni saboda zuciya ɗaya nake dashi kuma tuni na daɗe da mallaka wa matata farinciki na shi. "Murmushi tayi me sauti haɗe da rufe fuskarta da tafukan hannunta cikin zuciyarta tana jin wani irin son mijin  nata na ƙara shigar ta.     Shima murmushin yayi ya jaye hannunwan ta daga fuskarta ya riƙesu ya manna mata kiss a goshi kan ya saketa ya ɗan marairaice fuska yace "baby haƙuri na ya ƙare plsss ayi yau" ya ƙarasa faɗar maganar yana mai langaɓar da kai. Shuru tayi masa duk da tasan bata kyauta amma ita karan kanta batasan dalilin da yasa bata son ya kusance ta ba.     """Iskar bakin shi ya fesa mata a fuska dan yadda yaga ta faɗa duniyar tunani, duk da ba wasa yake mata ba dan ya kwantar mata da hankali yace "baby muci abinci wasa nake maki", sai a sannan ta ɗago kanta ta kalleshi cike da jin tausayin shi, "toh kawai tace ta fara serving ɗinshi, yana bata tana bashi har suka kammala cin abincin Kwashe plates ɗin tayi takai kitchen ta wanke su kan ta dawo palour kamar yadda ta saba, zama tayi saman cinyar shi haɗe da langwaɓar da kanta bisa ƙirjin shi '"Cikin sigar shagwaɓa harda wani ɗan shafa gemunsa tace plss ya Abdul ka kaini gidan ammie! dan tunda akayi auren su sau biyu kawai ta taɓa zuwa, na biyun ma baiko san taje ba, sai daya dawo gida ya tarar batanan.    Aikuwa na yahau dokin mulki yayu fushi da ita, haƙuri kam yasha harya gaji amma fur yaƙi, "abu kamar wasa da dare yayi rufe ƙofar dakinsa yayi, "da safiya tayi Amatullahi taje ta faɗawa Abdulraheem, nan ya tasata a gaba sukaje suka sameshi, yayi ta bashi haƙuri kafin ya haƙura. Kuma yajawa Amatu kunne akan ko nan da can zata tafi ta nemi izinin mijinta kafin taje idan ba haka ba mala'iku zasu dinga tsine mata.     Harda ɗan guntun hawayenta ta duƙa gaban Abdulrahman ta roƙeshi gafara yace ai babu komai ya wuce kawai yayi hakan ne danta gane kuskurenta. Daga nan sukaci gaba da zaman su kamar yadda suka saba. Kuma tun ranar bata ƙara cewa zata gidan ammie ba sai yau         "Cike da jin kasalar shafar shi da takeyi yace indai kina son na bari kije gidan ammie toh sai kin bani hakki na, idan kuma ba haka ba sai kiyi sha zamanki, "mutsu mutsu ta farayi a jikinshi wanda ba ƙaramin tayar mashi da hankali tayi ba. Cije lips inshi yayi na ƴan sakanni kan ya saki yace kin yadda??         "Kamar jira yake ta bashi amsa ya sungume sai bedroom dinshi ya kaita, can tsakiyar gado ya kwantar da ita kan ya cire jallabiyar shi ya faɗa saman ruwan cikinta, "sai  data ɗanyi ƴar ƙara jinshi a saman ta, "babu wani ɓata lokaci yafara kissing dukan sassan jikinta, "sai nishi yake still yana kan romancing ɗinta, "ita kuma sai wani turje masa take daga bisani kuma taci gaba da mayar mashi da martani dan wasu irin saƙonni yake aika mata dasu wanda baki bazai iya faɗan su ba.   Ganin abun nasu na shirin makantar dani yasa nabaro musu ɗakin 🙈   ******      ''Yau ta kama weekend, kowa yana gida yana hutu amma banda su Amatu da suka fita ziyara saboda sun kwana biyu basuyi ba kuma babu lokacin zuwa saboda makaranta shiyasa yau da yake weekend suka fita duk tare da mazan su. Gidan su amatu suka fara zuwa da gidan aunty hajara kan sukazo gidan mummyn Abdulrahman, bayan sun gama hirar su ne sukazo gidan ammie.    Nan suka babbaje anata hira kai kace ba surukkai bane saboda ammie zama tayi cikinsu ana ta hira ciki kuwa harda samha data biyo su sai kuma su marasa kunyan mazajen nasu. kaddai kuso kuga Abdulrahman ba kunya ba tsoron Allah, rungume yake da Amatu tun shigowar su, sai da ammie tayi mashi magana kan ya saketa yana wani cin magani. Hira suke gwanin sha'awa ga ammie tayi musu tarba na musamman dan tasan da zuwan su, "zama sukayi a tsakiya palour anata hira ana dariya da kuma ƴan tsokane-tsokane, "ana cikin hakane Amatu ta fara kakarin amai, "da gudu ta shiga toilet ɗin ƙasa tafara kwaranyo amai, sai data kai kusan tsawon minti biyar kan aman ya tsaya, Abdulrahman sai sannu yake mata, suma gabaɗayan su suna bayanta suna jero mata sannu.   "Ammie ce ta shigo toilet ɗin taja hannunta suka haura sama, "Abdulrahman yabi bayan su aiko ammie na ganin shi aika mashi da hararan ya biyosu zai gane, "cike da jin haushi ya koma palour ya zauna kamar wani maraya, "Abdul kuwa sai dariya yake mashi, "ameerah kam duk hankalinta ya tashi gashi tana son tabi ammie kuma tana tsoron kar yadda ta hana mijinta ya bita itama ta hanata shiyasa kawai ta nemi wuri ta zauna tana jiran fitowar su.    Ɗakinta ammie takaita ta zaunar da ita saman gado, cikin kulawa tace ƴata yaushe kika fara wannan aman ne?? Amatu ta sunnar dakai ƙasa tace jiya na fara shi, ammie tace mijinki ya sani? Gyaɗa kai tayi alamar a'a, ammie tace to meyasa baki faɗa mashi ya kaiki asibiti ba?? Cikin rashin sanin amsar da zata bata tayi shuru.    Ƙura mata ido ammie tayi na ɗan wani lokaci tana nazari dan tun shigowar ta gidan ta lura da yanayinta, sai kuma yanzu dataga zahiri amma ɗuka da haka bata gasgata abunda take tunani ba. "sai kawai ta fita daga ɗakin, bada jimawa ba sai gata ta dawo da waya a kunnenta, sai dai banji abunda tace ba naga ta aje wayar ta koma wurin Amatu.    A palour kuma kowa jiran fitowar ammie yake, Abdulrahman kuwa yadda kukasan zaune yake saman ƙaya haka ya matsu baiga lafiyar babyn shi ba. Suna nan zaune a haka sai ga wata ƴar dattijuwan mata wadda zata kai sa'ar ammie, "sanye take da fararen kaya riga da wando, da alama dai nurse ce.    Gaishe su kawai tayi ta haura sama, gabaɗayan su suka zaba mata na mujiya👀 a yayinda take haurawa sama....... Ayi hƙr da wannan Comment     Share [3/10, 4:14 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''                    Page 89-90 """"Da sallamar ta ta shiga ɗakin ammie, daga ciki ammie ta amsa mata haɗe da tarbo ta ta ida shigowa ɗakin. Batare da sun tsaya wani dogin bayani ba dan ammie ta sanar da Its komai, "sai kawai ta umarci Amatu data kwanta saman gado, ba musu ta kwanta akan lafiyayyen gadon ammie da yasha gyara. Wasu ƴan gwaje-gwaje tayi mata da allura sannan ta bata wata ƴar kwalba tace taje tayi fitsari a ciki.    Bada jimawa ba sai gata ta dawo, ta miƙawa matar kwalbar, "murmushi matar tayi bayan ta gama karewa fitsarin kallo sedai bata ce komai ba. Ammie da duk ta matsu bataji sakamako ba tace Dr zaynab yadai ko ansamu ne? Dr zaynab tayi murmushi tace eh hajiya insha Allah shine amma sai natafi da wannan kwalbar asibiti na duba saboda mu ƙara tabbatar wa. Cike da murna ammie ta hau yi mata godiya sannan ta ɗauko wasu maƙudan kuɗi tasa mata a jaka. Dan tasan halin Dr zaynab indai hannu da hannu ta miƙa mata baza ta amsa ba.          ""Amatullahi kuwa sandarewa tayi kamar mota mai remote ta zura musu ido sai yadda akace tayi takeyi, "bayan ammie ta sallami Dr ne ta juyo kan amatu tace ƴata ina fatan yanzu ba abunda yake damunki? Eh yanxu daidai nake jina kawai bakina ne bayamun daɗi, ammie tace "owk tau ga wannan ki tsotsa ni zan sauka ƙasa in samar maki abunda zakici kinji ta ƙarasa faɗar maganar haɗe da miƙa mata vitamin c ɗin da Dr ta kawo.     Tana miƙa mata ta fice daga ɗakin, har takai bakin ƙofar fita ta juyo ta kalli amatu tace karki fita yanzu zan turo maki su Ameerah, Amatu da fara'a ta amsa da toh. Ammie na ta fita ta miƙe tsaye tana kai kawo, "ita dai ganin komai take kamar a mafarki, "ashe da dalili nakejin duk yanayi na ya sauya??hmmm ashe ƙaruwa na samu?? Taɓɓ waya ga Amatullahi da baby?😍ita kaɗai fa take maganar ta. "Tana cikin hakane taji motsin su Ameerah, da sauri ta koma bakin gado ta kwanta harda sa bargo ta rufe jikinta, Abdulrahman shine kan gaba, yana isowar wurinta ya zauna saman drowan dake jikin gadon gami da da yaye bargon cike da kulawa yana tattaɓa jikinta yace baby na ya jikinki, "kuma me waccen matar tazo ta maki?? Kamar wacce ta daɗe tana ciwo harda cewa washh sannan ta ɗago kanta ta jingina da gadon tana kallon shi tace lafiya ƙalau nake kawai jikina ne ba daɗi shine ammie ta kira Dr ta duba ni.    "Ɓata rai yayi yace toh ni miye amfani na a matsayina na likita kuma mijinki, hahaha kuji shi fah sai kace wani likitan gaske 😍. Abdulraheem dake tsaye shida Ameerah suna kallon ikon Allah saura kaɗan dariya ta suɓuce masa sai ya danne ta.     Ameerah ta ɗan matso kusa da Amatu tace besty tunda mijinki kawai kika sani ni nayi nan, ta juya da niyar fita, Amatu tayi saurin saukowa daga kan gadon tace "haba my meerah sorry dawo mu zauna, ta ƙarasa faɗar maganar haɗe da jan hannuntu suka zauna saman gado. Abdulraheem yace nikam na fita Allah ya baku lafiya. Batare daya saurari amsar su ba ya fice daga ɗakin, ameerah kuma cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace Amatu cikine dake ko? Itama amatu tayi ƙasa-ƙasa da murya tace hmmm waya faɗa maki?       Uhmmm babu wanda ya faɗamun nidai kawai naga alamu ne, ta ƙara da cewa da gaske cikin ne dake? dan naga harda likita aka kira ta dubaki ameerah ta faɗa. Amatu tace eh insha Allah shine amma karki faɗawa kowa kinji, ameerah ta amsa da toh sannan ta fice daga ɗakin. Maida duban ta tayi kan Abdulrahaman dake latsar wayan shi tace yaya yadai naji kayi shuru? Ɗago da kanshi yayi ya watsa idanunshi cikin nata yana kallonta ba ƙaƙƙautawa, ƙasa tayi da idonta dan bazata iya jurar irin wannan kallon da yake mata ba.     Cikin sanyin murya yace baby ciki ne dake ko? Shuru tayi masa dan tana tsoron karta ce shine likita tace ba shi bane kuma haka tana tsoron tace ba ciki bane likita tace cikin ne, shima shurun   yayi na ƴan sakanni kan yace "baby ki faɗamun mana nifah nasan kina ɗauke da juna biyu kawai nayi shuru ne saboda ina son saina tabbatar ne kafin na sanar dake dan naga alamar ke baki ko sani ba.     Murmushi tayi taja bargo ta rufe harda kanta tace nima bansani ba sakamakon Dr muke ji...........sai ga ammie ta shigo da murnar ta tace tau Alhamdulillah Allah mungode maka da kyautar daka bamu Allah ya saukar ki lafiya Amatullahi.    """Wayyo zo kuga murna wurin Abdulrahman, saboda tsabar farinciki bai san sadda ya ɗaga ammie ba, dan tayi mashi babban albishir ɗin da bazai taɓa mantawa dashi ba. Ture shi ammie tayi daga jikinta, "yana dariya ya nupi wurin amatu, ba kunya ya wani haye saman gado, "aiko ammie dataga haka ƙafarta kawai taja tana murmushi tana kuma mamakin yadda akayi abdulrahman ya fitsare haka ko kuma daman hake yake tun yana yaro idan abun farinciki ya sameshi oho?? Ita dai tasan cewar tun haɗuwar ta dashi ba haka yake ba.      Amatullahi cike da jin kunya ta ƙara shigewa cikin bargo dan gabaɗaya kunyar ammie ta rufe mata ido, musamman ma da Abdulrahman ya ɗagata, "jitayi kamar ta nutse cikin ƙasa, "amma wani ɓangare ɓa zuciyarta daɗi takeji. Fincike bargon yayi ya tura shi gefe sannan ya janyota jikinshi ya rungumeta kamar zai mayar da ita cikinsa. Ita dai mutsu-mutsu kawai take tana jin tsoron kar ammie ta dawo dan taga fitar ta, Abdulrahman ko a jikinsa wai mahaukaciya ta faɗa rigiya tace wanka ta shiga yi. Sumbatar ta kawai yake yana sa mata albarka haɗe dayi mata addu'a Allah ya sauketa lafiya.   "Kusan mintin su ashirin a haka dan harya fara fita hayyacinsa, "Amatu da taga yana shirin wuce gona da iri tace plsss yaya abdul ka bari muna gidan ammie ne fah, "ko ƙala baice mata ba yaci gaba da sarrafata dan  Abdulrahman akwai iya sarrafa mace duk yadda yakai ga romancing ɗinki ko bakiso ba dole ki biye masa dan in wurin kwanciya ne kam Abdulrahman saidai ya koya maka.😎    Wani ƙarfi ne yazo mata, tasa duka hannuwanta biyu ta tureshi sannan ta mike zaune ta gyara ɗankwalinta daya faɗi saboda jarabar shi kan ta sauka daga kan gado, "shi kuma jinginewa yayi da kan gado haɗe da lumshe ido na ɗan wani lokaci kafin ya sauko daga kan gadon ya iso wurinta. Gabanta ya tsaya yana gyara mata rigarta data juya gefe, "komi batace ba harya gyara mata sannan ta kalleshi tace kaga abunda kaja ko? Duba fa kaga yadda rigarka tayi squeeze yanxu idan ammie ta gani ko su ameerah me zakace??      "Ince naji ɗumin mata ta mana, "ko akwai laifi, ya faɗi maganar haɗe da ɗage girar sa sama, "tunkuɗe shi tayi ta fice daga ɗakin ta barshi nan tsaye, "murmushi kawai yayi ya gyarawa ammie gadonta kan ya isa wurin madubi ya gyara rigar shi sannan ya fito palour. Cikin haɗe rai ya fito palour dan bayason wani yaga alamun wasa a tattare dashi bale har akai ga tsokanar shi. "Zama yayi kan one seater yana latsar wayan shi, Abdulraheem yace toh ko baka faɗamana ba munji, abdulrahman ya ɗago kanshi ya kalleshi baice ƙala ba yaci gaba da latsar wayan shi dan yasan neman magana kawai yake Ammie da yanzu ta shigo palon tace ahh har kin fito keda nace kiyi xamanki ki huta? "Cike da shagwaɓa tace ammie naji sauƙi ne kuma babu daɗi ina zaune ni kaɗai shiyasa na fito. Ammie tace tau bari in kawo maki abincin dana dafa maki ko?    Amatu tace a'a ammie bana jin yunwa, ammie tace "toh bari insa maki a kula kije dashi gida, "toh kawai tace ammie ta shige kitchen, "Abdulraheem yace tau ku tashi mutafi idan kun shirya, Amatu da ameerah suka tattashi ko wacce ta ɗauki mayafinta da jakarta Abdulrahman kuma yana nan zaune yana jinsu amma bai tanka ba balle harya tashi sai da ammie ta fito daga kitchen gansu a tsatsaye tace ahhh badai tafiya zakuyi ba?    Abdulrahman yace eh ammie tafiya zamuyi. "Ammie da takejin kamar karsu wuce tace tau bari ina zuwa, ta haura sama, bada daɗewa ba sai gata ta sauko riƙe da wasu ledoji guda biyu, ta miƙawa Amatu da Ameerah, Abdulrahman ya ansa na Amatu wai baya son ta wahala, shima Abdulraheem ansar na ameerah yayi ya riƙe. Ammie tayi murmushi tace tau su sai su ɗauki wannan tayi musu nuni da wasu kuloli guda biyu.     Ba abun suyi godiya ba ammie tace sunyi laifi dan ammie ko kaɗan batason idan tayi kyauta ayi nata godiya sai kawai kowaccen su ta rungumeta haɗe dayi mata sallama. Nan suka fito farfajiyar gidan inda suka tarar da samha da hanan sun shigo gidan dan ammie ta aikesu sai yanzu suka dawo. "Da gudun su suka ƙaraso wurin su suna musu bankwana kan suka wuce.      Bayan sun isa gida kowa ɗakin shi ya shiga ya watso ruwa haɗe da ɗauro alawla dan lokacin magariba yayi, "jallabiya kawai Abdulrahman ya zura ya wuce masallaci, amatu kuma bayan ta idar da tata sallar ɗakinshi ta shiga bata ganshi ba sai kawai ta dawo palon ƙasa ta zauna tana jiran ya dawo suci abinci, shuru har aka kira sallar isha'i, tashi tayi taje tayi sallar sannan ta sake fitowa palour, ta zauna kenan sai gashi ya shigo.    Murmushi ya sakar mata haɗe da buɗe hannuwanshi alamar tazo, ba musu taje da gudu ta rungumeshi, ya ɗagata sama yana juyi da ita kafin ya direta ƙasa yace baby kinga na daɗe ko? Na tsaya sallar isha ne, murmushi tayi mashi tace "ai bakayi laifi ba, shima murmushin yayi mata haɗe da jan hancinta yaja hannunta suka zauna ƙasa wurinda yaga ta jera musu abinci, "tana zaune saman cinyarshi ya fara bata a baki itama tana bashi. ******* Zaune yake a bakin gado da waya a kunneshi, gabaɗaya ya mayar da hankalunshi kan wayar da yakeyi, "da alama dai wayar nada mahimmanci dan baiko san lokacin data shigo ɗakin ba, adaidai lokacin yake faɗin "toh abba dan Allah ka ƙara haƙuri kasan idan ka fito fili ka faɗamashi cewar kai kasa aka sace yarrrrrrr..... Sai kawai ya hangeta ta madubi, "da sauri ya katse wayara haɗe da miƙewa tsaye suna kallon kallo, cikin ruɗu ta fara ja da baya tana cewa......... Comment        Share [3/12, 10:02 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''        Page 91-92 """"Cikin ruɗu ta fara ja da baya tana cewa Abdul wa aka sace ne? Dawa kake waya?duk a lokaci ɗaya ta jero masa waƴannan tambayoyin wanda cikinsu babu wanda ya iya amsa ta saboda wata irin nannauyar ajiyar zuciyar daya sauke, dan ya ɗauka ko ta gane inda maganar ta dosa, shuru sukayi na yan mintuna ta juya zata fice daga ɗakin dan taga alamaun baida niyar amsata.    "Da sauri yasha gabanta, ya janyo hannunta suka zauna gefe gado, yace my ameerah ki kwantar da hankalin ki, am..dam..daman ƙanwar abokina ce aka sace amma yanzu an gano wanda ya saceta shine nake faɗawa abba yayi musu jaje sabida yasan mahaifin yaron. Ajiyar zuciya tayi tace wai Alhamdulillah har hankalina ya kwanta, daman nazo dubawa ne ko ka fito daga toilet in kawo maka lunch ɗinka? Duk da cewar yanajin yunwa amma baya jin zai iya cin abincin kuma ba abun yace ya ƙoshi bane ta tisa sa agaba kamar uwarshi tana jero mashi tambayoyin da a halin yanzu bai shirya amsa mata su ba, sai kawai yace taje ta kawo.   Tashi tayi ta shiga kitchen ta zubo mashi sauran farfesun kayan ciki da jollop ɗin taliyar da Amatu ta aiko mata dashi, dan taci nata shi kuma cewa yayi sai ya fito daga toilet, shine ma dalilin dayasa ta tarar dashi yana waya. Da sauri ta haɗa komai takai mashi, batare data zauna ba tace mashi yaci zataje ta watso ruwa, toh kawai yace mata ta fice daga ɗakin.      Tana shiga ɗakinta ta fara kaikawo haɗe da game tafukan hannuwanta wuri ɗaya tana bubbuga su, girgiza kai tayi tace inaaa ya za'ayi in yarda da maganar ka bayan naji kana cewa idan aka fito fili aka faɗamashi cewar kai kasa aka sace ta?? Toh me hakan yake nufi? Wa aka sace?? Waye ya sace ta?Abba? Da ƙarfi tace noooo ya za'ayi abban Abdul yayi sata? Wannan ba halinshi bane tayi maganar a lokacin data sassauta murya. "Dafe kanta tayi da sauri a lokacin da zuciyar ta ke raya mata cewar ko Abdul kidnapper neh? Girgiza kai tayi da ƙarfi kamar wadda zata cire kan dan bata yadda da abunda zuciyarta ta rayo mata ba dan ta yadda da Abdul mutumin kirki ne kuma ko a mafarki aka faɗamata cewar Abdul kidnapper ne bazata taɓa yadda ba. "Gaskiya ya zama dole insan abunda ke faruwa da mijina. "Zuciyar ta tace toh ina ruwanki da bibiyar lammuransa?shuru tayi tana wani ɗan nazari sai kuma ta yamutse fuska alamar tunanin datayi baiyi mata daɗi ba. Wata zuciyar tace ai mijinki ne kuma da ikon yin bincike akan shi, yess kawai ta faɗa ayayinda murmushi ya bayyana a fuskarta, sedai bansan kona menene ba.   Da sauri ta shige toilet, agurguje ta watso ruwa ta fito, ta shafa jikinta da mai, sannan ta saka daguwar rigan baccin ta tasaka hula kan ta fice daga ɗakin, ɗakinshi ta shiga ta tarar dashi kwance saman gado da alama ma harya gama cin abincin dan bataga kulolin abincin data kawo mashi ba. Saman gadon ta haura tana mai tambayar ina abincin data kawo mashi, yace ai tun ɗazu ya gama yakai su kitchen, "murmushi tayi tace owk my Abdul ka hutashsheni ta faɗa gami da cusa kanta cikin faɗeɗen kirjinsa. A hankali ya rungumo abar sa yaja blanket ya rufe su   Nima na rufe babin su 😎          Bayan kwana biyu    Abdulraheem ne zaune a palour shida daddyn Amatullahi, cikin girmamawa Abdul ya gaishe shi, haka ma daddy da fara'arshi ta amsa mashi yana mai tambayar shi iyalin nashi, Abdul yace lafiya ƙalau take. Daddy  yace masha Allah haka akeso, yanzu ya maganar mu?Abdul ya duƙar da kanshi ƙasa dan ji dayayi gabaɗaya daddy yai mishi wani irin kwarjini har yakejin ina ma ace baizo ba daya fasa faɗar maganar har zuwa wani lokaci, sedai kuma hausawa kance idan dama tazo maka kayi amfani da ita akan lokaci karta wuce kuma duk jinkirin da zasuyi watarana dole zasu faɗa toh miye amfanin jinkirtawa..... "Tsinkayo muryar daddy yai yana cewa Abdul yaya dai naji kayi shuru, kawai ka faɗi maganarka babu komai kasan dani dakai an zama ɗaya yanzu na ɗauke ka tamkar ɗan dana haifa a cikina, karkaji tsoron komai ina sauraronka.      "Abdul ya gyara zama haɗe saita kanshi ya saci kallon daddy yaga shima kallon nashi yake sai ya sadda kanshi ƙasa, a hankali ya fara magana kamar..... Amm daddy daman kan maganar sace Amatullahi da akayi ne shine nakeson in faɗamaka ko waye. Murmushi daddy yai irin nasu na manyan mutane yace Allah sarki aini harna manta dan koma wanene nabarshi da Allah, amma gaskiya zanso insan ko waye. "Abdul da yanayin sa ya sauya wanda na kasa gane daɗin maganar daddy yaji ko akasin haka?              Sai Abdul yace Eh toh daddy zan faɗamaka amma wani hanzari ba gudu ba, yanzu daddy idan wani ne na kusa dakai ya aikata maka hakan ya zakayi?? "Jin irin tambayar dayayi mishi yasa daddy ruɗewa yana saƙe-saƙe, dan yama rasa amsar da zai bashi sai yake tunanin kodai shine? "bazato kawai Abdul yaji yace toh ko kaine? Gaban Abdul ya shiga dukan uku uku, gashi ba halin yace "eh kuma su samu matsala dashi idan kuma yace "a'a yayi ƙarya. Duk ji yayi ya burkice, kwanyar shi taɗau zafi, ya shiga cikin "RUƊANI" sabida tsananin tunane-tunanen da yakeyi.   Daddy da gabaɗaya ya shiga cikin damuwa da kuma "RUƊANI" dan ya kasa gane ma Abdulraheem ɗin "yace wai Abdul lafiyan ka ƙalau kuwa, naga duk yanayinka ya sauya. "Abdul ya ɗago idonshi da suka koma kalar ja danya shiga cikin danasanin dalilin dayasa ya amince wa abba suka sato Amatu, "runtse idonshi yayi da ƙarfi ayayinda yake tunanin lallai ya zama wajibi ya sanar ma daddy komai tunkan lokaci ya ƙure musu. "Buɗesu yayi ya ɗora kanna daddy "yace daddy dan Allah ka dubi girman Allah ka yafe mana laifin da muka aikata maka nida abbana, "wallahi sharrin sheɗan ne da kuma rashin haƙuri irin namu, dan Allah ka yaf....... A razane daddy ya miƙe tsaye kalli Abdul da idonshi suka canza launi, cikin dakiya yake magana, "yace Abdul yanzu kanason kace mun harda abbanka aka haɗa baki wurin sace ƴata? To akan wani dalili?  Abdul ya katse shi ya fara bashi labarin abunda ya faru. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace lallai biri yayi kama da wando. A ɗan tsawace yace yanzu Alhaji ibrahim saboda kuɗi zai sace mun ƴata?? "Wallahi naji mamakin haka kuma kaima ka bani mamaki, "shi idan kuɗi sun rufe mashi ido ai kai bai kamata su rufe maka ido ba. "Girgiza kai daddy ya shiga yi haɗe da cewa babu komai kawai ka tashi ka wuce. "ko alamar tashi Abdul beyi ba illah kamo ƙafar daddy da yayi yana roƙon shi dayayi haƙuri, cike da jin takaicin Alhaji ibrahim wanda ya harya shafi Abdul tunda shine ma ya sato Amatu da kanshi ya fisge ƙafar shi daya riƙe yace Abdul ka tashi ka wuce nace ko? Ya faɗa da babbar murya. "Ƙwallah ce taf a idon Abdul wanda su basu zuba ba kuma basu koma ba balle ya rage jin haushin kansa dayake ji a yanzu, "ɗago kanshi yayi da niyar magana sai yaga wayam, daddy baya palon, "duƙewa yayi a wurin kusan tsawon minti talatin kafin ya tashi daƙyar dan yadda ƙafar shi tamai nauyi ya fice daga palon "A farfajiyar gidan ya tsaya yana kallon ko'ina sedai babu alamar motar daddy da alama dai yabar gidan, shima jan jikinsa yayi ya shige motarsa da tunanin halin da abba zai shiga idan yaji yadda sukayi da daddy gashi yayi mishi alƙawarin duk yadda za'ayi bazai taɓa bari abokantakar su ta samu matsala ba, amma ga yadda lamarin ya kasance. ******* ******* ********* """"Keeeee" dakata ya faɗA da sauri haɗe da ƙarasawa wurinta ya riƙeta yace haba baby ya kikeson kisani asara biyu? Gaskiya karki kuma hakan. "Tsuke bakinta tayi ta turo shi gaba wanda ba ƙaramin sha'awa suka ba Abdulrahman ba tace toh toh niba ɗaukowa zanyi ba? Abdulrahman yace to bagani ba tunda tsawonki baze kai ba basai kice in ɗauko maki ko?    "Ɓata rai tayi ta wani juya mashi baya da niyar sake hawa kan kujerar, Cike da jin haushi ya wani fusgota da ƙarfi ta faɗo jikinshi, cikin faɗa yace, wai meyasa bakya jin magana ne, sau nawa zan faɗamaki kibar wannan haye-hayen tunda ba abun dole bane, kuma kina ganin yanzu bake kaɗai kike ba ammai sai kiyi ta wani abu ƙaramar yarinya, yanzu idan wani abu ya sami babyn mu me zakice iyeee??   "Kuka tasa mashi ta fice da gudu daga kitchen ɗin, shi kuma kallonta kawai yayi harta wuce sannan yasa dogayen hannun shi saman drower ya buɗe ya ɗauko wata farar roba mekyau me ɗauke da zuma, kan ya fito daga kitchen ɗin da niyar haurawa sama dan ya ɗauka ko ɗaki ta wuce ashe tana palour hakimce saman kujera. Murmushi yayi ya isa wurinta ya duƙa agabanta yace sorry baby na nayi laifi ayi mun afuwa, ya faɗa cikin marairaicewa at d same tym kuma yana miƙa mata zumar. Murmushin itama tayi ta karɓi roban ta aje kusa da ita sannan taja hannunshi alamar ya miƙe, ba musu ya tashi ya zauna kusa da ita ya ɗauko robar zuman ya buɗe ya fara bata a baki, yace amma yau cokali ɗaya zakiyi ba uku ba, murguɗa mashi baki tayi shiko yayi saurin cafke bakin ya fara bata hot kiss, suna tsaka da haka sukaji ana knocking. Da sauri ya zare bakinshi daga nata yaje ya buɗe kofar, umar ya gani tare da samha, murmushi suka sakar wa juna kan yayi musu iso suka shigo ciki, samha ta ƙarasa wurin Amatu data miƙe tsaye ta fara zuwa wurin su danjin muryar su suka rungume juna, Abdulrahman ya wani bankawa samha harara wanda a take ta saki Amatu tana ɗan murmushin dole, danta gane abunda yake nupi da hararar. "Amatullahi kuma bata lura ba, jan hannuta tayi suka zauna suka fara hira dan samha akwai surutu ga kuma jininta ya haɗu dana amatu kullum idan tazo gidan haka zasuyi ta hira har cewa take bazata gida ba nan zata kwana, "Abdulrahman kuwa kallo ɗaya yake mata ta figi gyalenta ta wuce dan tasan halinshi. Suna tsaka ga hira samha ta fiddo wasu haɗaɗɗun invitation card daga jakarta ta miƙawa Amatu tana murmushi tace aunty ga wannan na auran aunty lubna ce, Umar dake gefe yace keeee bakijin magana ko, wayace kikawo? Ba saida mummy tace karki kawo ba? Abdulrahman ya wani ɓata rai danjin an anbaci lubna yace toh koma dai menene babu inda matata zataje ke kuma da kikawo shi sai ki ansa ki komar dashi, yana gama faɗar haka ya fice waje, umar ma ya take masa baya. ""Cike da jin kunya da kuma haushin karan banin datayi ta kalli Amatu, zatayi magana ta katseta tace karki wani damu kanki danya faɗi haka anjima zan lallashe shi kuma zai bari muje kinji ko?cike dajin daɗi samha ta amsa da toh, Amatu kuwa tadai faɗa ne dan ita bata ko taɓa ganin lubnan bama hasalima a bakin samha taji labarin lubna, sedai haryau samha bata faɗa mata cewar ai lubna tayi son Abdulrahman ba... Readers wai ina labarin lubna????uhhhhh ku biyoni dan jin labarinta Lashminzy cehhhh [3/15, 5:47 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا ۚ وَاذْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنْتُمْ أَعْدَاءً فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُمْ بِنِعْمَتِهِ إِخْوَانًا وَكُنْتُمْ عَلَىٰ شَفَا حُفْرَةٍ مِنَ النَّارِ فَأَنْقَذَكُمْ مِنْهَا ۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ And hold firmly to the rope of Allah all together and do not become divided. And remember the favor of Allah upon you - when you were enemies and He brought your hearts together and you became, by His favor, brothers. And you were on the edge of a pit of the Fire, and He saved you from it. Thus does Allah make clear to you His verses that you may be guided. Juma'at mubarak         Page 93-94 "Lubna tun lokacin dataso zubawa Abdulrahman magani su mummy suka kamata, tun daga ranar ta shiga damuwa da kuma danasanin abunda ta aikata, kwanan ta biyu a gidan su khadeejah inda ta bata shawarar taje ta nemi yafiyar mummy da kuma mahaifiyar ta dake fushi da ita, sedai me daƙyar taje ta nemi yafiyar mummy dan tsananin jin kunyarta data dabaibaye ta bisa ga abunda ta aikata. "ummanta dake ita kuma mai zafin kai ce ƙin haƙura tayi saida lubna ta sanarwa mummy halin da ake ciki, mummy ta kira umma tayi ta mata faɗa akan bai dace tana gaba da ƴarta ba, kuma tunda ta nuna nadamarta ai ya kamata ta yafe mata, sannan umma ta janye fushin da tayi ta ita sukaci gaba da zaman su kamar yadda suka saba.    "Bayan wani lokaci da faruwar haka can wani ɗan uwansu wanda ake kira da jafar yazo neman auran ta daman tunda daɗewa yake sonta sedai rashin ganin fuska yasa yaɗan janye bawai dan ya haƙura ba, tunda yaji labarin ta dawo kano ya fara bibiyar ta kamar yadda a da yake bibiyarta tun kafin ta koma Abuja. Wata rana ran juma'a yazo gidan su, sedai bai nuna wurinta yazo ba, cewa yayi wurin umma yazo ya gaisheta.   Bayan sun gaisa da umma yake tambayar ina lubna take, dake tun a da tana jin ɗan jita-jitar cewa wai yana son lubna, sedai ita bata yadda ba dan bataga wata alama ba a tattare dashi ba, amma a wannan karon ta gasgata dan cikin satin nan kusan kullum sai yazo kuma tambayar shi ɗaya ina lubna, "haka umma zataje ta kirawo mashi lubna wanda a ƙalla suna kwashe tsawon awa biyu suna hira duk da bawani surutu take ba, shi kaɗai yake ƙiɗinsa da rawarsa harya gaji ya wuce.   "Shi kuma shurun nata sam baya damunsa, burinsa kawai ta bashi dama, dan yasan idan harya kai ga mallakarta a matsayin mata toh pah an wuce wurin dan acewar shi sai ya saita ta kuma ya sanya mata sonshi a zuciyarta. Haka kullum yake jawo ƙafa kamar wani marasa aiki, yazo yayi ta mata surutu wanda a yanzu ta ɗan fara sabawa dan inyayi magana tana bashi amsa ba kamar da da in yayi magana take share sa ba.       """"Yau ta kama juma'a babbar rana, ranar da jafar bazai taɓa mantawa ba a rayuwar shi domin kuwa yau ne lubna ta furta cewar tana sonshi kuma ta amince zata aure shi, saboda ta lura yana tsanin sonta ga kuma shawarwarin da khadija ke bata akan ta amince dan mace lokacinta kaɗan ne da zarar wannan lokacin ya wuce ko mashinshini ɗaya bazata samu ba.   "Aiko data sanar ma jafar bakin shi sam yaƙi rufuwa saboda murna, bada daɗewa ba ya sanar ma ƴan gidansu, "dake abu na gida ne kuma duk danginsu sun san halinshi yaro ne mai nutsatse mai hankali da tarbiya domin kuwa yayi gado a wurin mahaifin shi da mahaifiyar sa domin mahaifin shi malami ne, "mahaifiyar sa ma haka, malama ce sabida tana koyarwa a wani makarantar islamiya dake anguwar su wanda tun tasowar shi yasan makarantar dan shima can yayi har zuwa lokacin daya sauke al qur'ani mai girma. Ba'a wani dauki lokaci me tsawo ba akasa ranar aure nan da wata ɗaya, "saboda a shirye suke daga su har zuwa su lubna ɗin. "Mummy taji daɗi sosai da taga invitation card ɗin lubna, haka ma samha harda ɗauka tayi zata kaiwa Amatu mummy ta hanata ashe ɗan yau da baƙin taurin kai sai da samha ta ɓoye guda ɗaya ta kaiwa Amatu.     Wannan kenan "A ɓangaren su Amatu kuwa hira sukaci gaba dayi har kusan la'asar sai ga Abdulrahman da umar sun dawo dan tunda suka fita basu dawo ba sai yanzu. "ko zama umar beyi ba yacewa samha su wuce wacce ke bayan Amatu sai wani noƙe-noƙe takeyi a ɓoye gudun kar Abdulrahman ya ganta dan kar tasan kar. "Amatu dake gabanta dan samha na bayanta tana leƙo umar tana mashi gwalo wai anan zata kwana cikin yin ƙasa-ƙasa da murya yadda babu wanda zai iya jiyota sai shi da hankalinshi ke kanta kuma yake kallon saitun bakinta yake gane abunda take faɗa. "Aikuwa yace mata zai faɗawa ya Abdulrahman idan batazo sun wuce ba, "sai gata ta fito daga bayan Amatu duk ranta ɓace, haka sukayi musu sallama suka wuce. "Umar sai dariya yake ta mata a hanya. Bayan sun tafi ne Amatu ke tambayar shi wacece lubna wai? Dan duk lokacin da samha tazo gidan sai tayi ta bata labarin lubna, "Abdulrahman yace lubna ƴar'uwar mummyn su ce kuma tayi zama a gidan su samha ne, so sun matuƙar shaƙu da juns sai kuma ta koma garinsu, kuma... Da kamar zaice mata ai tayi son Abdulrahman sai kuma ya fasa kawai dan nashi ra'ayin. Wata hirar ya ɗauko musu, sukaci gaba dayi, inda Amatu ke faɗa masa ai gobe tanason taje saloon ɗinta taga yadda abubuwa ke tafiya danta kwan biyu bataje ba, sai yace mata ta bari jibi zai kaita saboda gobe tun ƙarfe bakwai zaije asibiti (a zahiri school zashi saboda gobe yana da classes ɗinda zai ɗauka da yawa) kuma sai yamma zai dawo😃 kuji Abdulrahman da rainin wayo, hmmmm kashinka ya kusan bushewa wollah😏 Dukda bataso ba amma haka ta amince masa dan tasan dama da wuya yabarta ta tafi ita kaɗai, dan ko sau ɗaya bata taɓa fita ita kaɗai ba sai tare dashi ko dasu Ameerah, wanda ba kasafai haka ke faruwa ba. ********* Abdulraheem kuwa ikon Allah ne kawai ya dawo dashi gida lafiya dan yadda yake driving kamar wani mashayin giya, bayan ya iso gida motar ma daƙyar ya iya paka ta ya fito ya nupi part ɗinsu, da shigar shi direct ɗaki ya wuce dan baiko tsaya kalle-kalle ba bare harya san da mutum a wurin. "Yana shiga ɗakinshi ya yasa key ya rufe dan a halin da yake ciki sam bayason damuwa, "Ameerah dake palour tun jin ƙarar motar shi yasa ta fito palour da niyar ta bashi tsoro irin na wasan nan sedai kuma yanayin data ganshi yasa ta fasa.   "Tsayawa kawai tayi tana kallon shi harya haura sama zuwa ɗakin shi inda take biye dashi a baya sai kafin takai ga isa ɗakin harya rufe ta bam, dan haka kawai ta shige ɗakinta cike da damuwa dan kwana biyun nan ta rasa gane kan mijin nata, gashi bata da halin ta tambaye shi sai inya huce yahau yi mata ƙarya yana cewa aiki ne sukayi mashi yawa wanda sarai tasan ba haka bane akwai abunda yake ɓoye mata shiyasa ta ƙudurtawa ranta cewar sai tayi bincike ta gano abunda yake damunsa har yake ɓoye mata. Nace anya kuwa ameerah?? Karfa kije garin bincike ki ganowa eyes ɗinki abunda sukafi ƙarfinshi😎   Toilet ya faɗa ya watsa ruwa wanda yakai kusan minti talatin a cikin kafin ya fito, daidai da wayar shi na ringing, sedai damuwar da yake ciki ya hanashi ɗaukar wayar dan bayajin zai iya koda gaisawa da wani balle harya kai gayin hira, shiyasa da shigowar shi ya rufe ƙofar dan bayason Ameerah taga halin da yake ciki tayi ta tambayar shi ko lafiya dan bayason ya huce haushin akanta. Zama yayi saman gado bayan ya sanya jallabiyar sa yayi tagumi duk ya rasa abunda keyi masa daɗi, yanzu me zai faɗawa abba?? yana ta ƴan saƙe-saƙe, Sedai duk wannan tunanin da yake tayi wayar shi na nan na ringing, "tsuki yaja ya miƙa hannu ya ɗauki wayar da niyar kashewa sai kawai yaga............ Manage with dis, cus am not feeling fyn Pray for me plzzzz [3/15, 4:16 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy''' My fans plsss kuyi hƙr da rashin jina da kukayi na kwana biyu, wlh banda lfy ne amma yanzu nasamu sauƙi insha Allah zaku dinga jina akai-akai, plsss ku tayani da addu'a       One love ❤        Page 95-96    "Sai kawai yaga daddy ne ke kiranshi, aikuwa da sauri ya ɗauki wayar ya ƙara a kunnenshi, daga can ɓangaren daddy yace ɗana Abdul fushi kakeyi dani saboda na tafi na barka cikin wani yanayi ko?? Kayi haƙuri a lokacin  raina ne ya ɓaci saboda abunda abbanka yayi mun "dan a rayuwata ban taɓa tunanin cewar abbanka zai aikata mun irin wannan ɗanyan aiki ba, amma yanxu babu komai ka kwantar da hankalinka komai ya wuce, kuma insha Allah wannan ya zama sirri tsakanin nida kai da abbanka da kuma Amatullahi danko mahaifiyarta bazan faɗa mata ba. "Kamar irin an watsa wa mutum ruwa mai ƙanƙara haka Abdul yake jin wani irin sanyi na ratsa zuciyar shi, "rasa ma ta ina zai fara godewa daddy yayi dan ba ƙaramin halacci yayi musu  ba. Godiya ya shiga yi mashi marasa adadi. Daddy ya ƙara da cewa basai yaje wurin abban ba, shi dakanshi zaije ya sameshi suyi magana cikin lumana. Abdul yace toh. "Bayan sun gama wayar ya miƙe da sauri haɗe da naushin tafin hannunshi da ɗayan hannun nashi yace yeahhh Allah na gode maka da kasa mutumin na ya fahimce mu, Allah ya saka mashi da gidan aljannah. Cike da murna ya koma bakin gadon ya zauna yana cewa tau an gama da wannan babin saura next part. "Murmushi ya saki wanda bansan ma'anar shi ba kan ya tashi ya fita daga ɗakin ya shuga ɗakin Ameerah, lokacin tana sallar magariba, fita yayi ya ɗauro alawla ya wuce masallaci, wanda bashi ya dawo ba sai da akayi isha'i dan sai daya tsaya nafilfili sannan ya dawo gida.   A palour ya tarar da ita, tana zaune kan two seater tana kallo, da ganin shi tayi saurin tashi ta isa gareshi, dan yanzu taga yanayin shi ya sauya izuwa na farinciki. Murmushi tayi mashi tace sweet Abdul ɗina ya aikin yau? Murmushi yayi mata shima yace aiki zaki tambaya ba lafiyar jikina ba? Ɗan narkewa tayi haɗe da tsuke baki tace toh bana ganka ba kuma lafiyar ka ƙalau, kuma, kuma ɗazu ina ta maka magana ka shige ɗaki ka barni harda sa makulli ka rufeeeee...sai kawai ta fashe da kuka, da sauri ya ƙaraso kusa da ita ya ɗauketa sai bedroom ɗinshi ya direta, kan ya share mata hawaye yace sorry my meerah wallahi abubuwa ne sukayi mun yawa shiyasa amma yanzu an wuce wurin ki kwantar da hankalinki insha Allah hakan bazata taɓa faruwa ba kinji, ya faɗa gami da manna mata kiss a goshi. Murmushi tayi na jindaɗi sannan tace tana zuwa, bada jimawa ba sai gata ta dawo ɗauke da tray, ajiyewa tayi tazo kusa dashi taja hannun shi ya sauko ƙasa ya zauna, suna fuskantar juna, bismillah sukayi a tare sannan suka fara cin haɗaɗɗiyar jollop ɗin shinkafar da taji haɗi sosai, sai santi yake yana ɗauko hirarraki kala da kala yana bata. Bayan kwana biyu "Ya Abdul jiya nayi mafarkin wai na haihu kuma yaron dana haifa yana mugun kama dakai, Amatu ta faɗa tana murmushi, shima murmushin ya sakar mata wanda har seda haƙoransa suka bayyana yace tau Allah ya nuna mana wannan rana, "Amatu ta amsa da ameen, haɗe da tambayar shi yaushe zai kaita saloon ɗin, dan haryau bai kaita ba kuma yaƙi bari taje ita kaɗai. Cikin sigar lallashi dan yanzu idan ya faɗi wani abun tana iya kwaɓe masa yama rasa ta ina zai fara lallashinta, "yace baby karki damu insha Allah yau zamuje amma sai Abdul ya dawo mun tattauna akan maganar da nace miki zamuyi ta yau. "Cike da jin daɗi ta rungume shi haɗe da manna masa kiss a goshi tace kuma daga nan zamu biya gidan aunty hajaru ko? Ya bata amsa kai tsaye. "Suna cikin hakan ne sai ga Abdulraheem ya shigo tare da Ameerah, gaishe da junan su sukayi kan suka samu wuri suka zauna, Abdul da zolaya yace ango na amarya kullum kana maƙale da ita kamar cingum. "kafin Abdulrahman yace wani abu ameerah ta katse shi tace Allah kuwa kamar ka sani, ai ina ganin duk ranar da aka waye gari babu ita akwai babbar matsa.......Amatu tayi wuf ta karɓe zancen da cewa hmmmm ai shi da sauƙi nikam idan na wayi gari babu shi ai nima biyar shi zanyi, in yaso ma haɗe a can. "Murmushi ameerah tayi tace kedai bari muma rufe wannan babin dan ba babi bane najin daɗi Hmmm wallahi kam Amatu ta faɗa.    "Shuru dukan su sukayi na ƴan mintuna kowa da abunda yake saƙawa, Abdulrahman kam gabaɗata hankalin shi ya fara tashi dan tsoron abunda zai biyo baya yakeji, Abdul ma haka sedai zuciyar shi na raya mashi cewar kamar bazata damu ba zata ɗauki hakan a matsayin ƙaddara ne. "Ameerah kuma tunaninta ɗaya yadda Amatu zataga kamar cin amanarta tayi ta aure wanda takeso. Amatu kuwa sumul take jinta ta kasa kunne tana sauraro taji abunda zasu faɗi.    """A hankali cikin sanyin murya me kashe jiki ya fara magana yace Amatullahi, "yadda ya kira sunanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara yasa tayi saurin ɗagowa ta kalleshi sai kuma ta kawar da kanta dan yadda gabaɗaya taji kwarjininsa ya lulluɓeta. Shuru tayi bata amsa ba sai a karo na biyu ya ƙara kiranta kafin tasamu damar amsa shi, "ɗan jimmm kaɗan yayi cikin ƴan sakanni ya kalli Abdulrahman da har zuciyarshi ta fara karaya ga kuma Ameerah duk yanayinta ya sauya. Amatu ma haka duk ji tayi jikinta ya matu dan yadda taga suma cikin ƙanƙanin lokaci yanayin su ya sauya shiyasa ma ta mayar da hankalinta kan abunda zasu faɗa mata dan har zuciyarta ta fara raya mata cewar ko rasuwa akayi ne. "Kallonta Abdulraheem yayi yace Amatullahi... Sai kuma yayi shuru, sai Ameerah ta taɓa shi da ƙafarta alamar yaci gaba da magana sannan ya ɗora da cewa a rayuwa duk wani abu da mutum zai aikata a rubuce yake, "duk wani ƙaddara mekyau ko mara kyau dazata samu mutum toh daman a rubuce yake, kuma duniya kamar makaranta ce, idan ka kwantar da hankalinka ka karance ta ka zauna lafiya idan kuma kasa gardama kaga saɓanin haka. "A rayuwa ana son mutum ya kasance mai haƙuri. "Ko cutar ka akayi  ka haƙura ka nuna bakomai bane insha Allah wata rana zakaci ribar wannan haƙurin...    ""Ya ɗan taƙaita anan. Amatu kam gabaɗaya ta sale dajin irin kalaman da Abdul ke faɗi wanda ta kasa gane ainihin inda maganar tashi ta dosa. Abdulrahman kam shuru yayi ya duƙar da kanshi ƙasa dan ko kallon amatu baya iyayi saboda sabuwar kunyarta data lulluɓeshi lokaci guda. A karo na biyu, Abdul ya sake kiran amatu wanda a yanzu ta gaza amsa shi. Cigaba da maganar shi yai yace da ace mutum yana da ikon komawa baya ya gyara duk wani kuskure nashi da mun gyara. Murmushi ya saki wanda a iya leɓon shi kawai suka tsaya yace Allah sarki ammie sai datace kar muyi haka mu zauna mu fahimci juna kafin mu aikata amma muka bujire mata, yanzu ga sakamakon bujire matan da mukayi..    ""Cikn ƙarfi hali amatu tace wai dan Allah meya faru ne haka ku taimaka ku faɗa mun hankalina ya kwanta, kodai wani ne ya rasu?? Ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka. "Cikin tausaya mata Ameerah tace besty ba mutuwa akayi ba, mune nan ta faɗi tana nuna kanta dasu Abdul, Amatu duk ta rikice sun sata cikin RUƊANI tace kune me? Me kuka aikata?? dan Allah ameerah ki faɗa mun idan su bazasu faɗa mun ba plssss na roƙeki, ta ƙarasa maganar a yayinda hawaye ke ambaliya a fuskarta, wanda ba ƙaramin zafi Abdulrahman yakeji ba aduk lokacin da hawayen nata ya zuba.      "Cikin dakewa da dauriya  Abdulrahman yace Amatullahi dan Allah ki yafe mana abunda muka aikata miki, kinji dan Allah, wallahi duk abunda muka aikata bawai munyi ne da niyar cutar dake ba sai dan ceto rayuwata da ɗan uwana yayi. "Cikin zaro ido tace kamar ya nifa bangane ba kunsani a cikin duhu fah, plssss ku fito fili ku faɗamun yadda zan fahimta. Tsoro ne sosai ya shiga jikin Ameeerah dan gani take kamar idan amatu taji wannan lamarin shikenan zata cire ta daga matsayin ƙawarta zuwa maciya amana.  kuka ne ya kufce mata da danasanin amincewa datayi ta auri wanda ƙawarta keso. Abdul kuwa yama rasa ta ina zai fara gashi amatu sai faman roƙonsu take dasu faɗa mata, "yace da kinsan abunda zamu faɗa maki da bakiso zama a wurinnan ba ya faɗi can ƙasan zuciyar shi. Tashi tayi ta duƙa gaban Abdulrahman ta riƙe hannuwan shi duka biyu tace plsss mijina idan su bazasu iya faɗamun ba kai ka taimaka ka faɗamun kaji?? Shuru yayi mata ayayin da yakejin zuciyar shi na wani irin suya dan a gaskiya bazai iya kallon ƙwayar idonta yace mata ga abunda ya aikata mata ba. Cike da ɓacin rai dajin haushin su dukansu ta miƙe zata bar palon, abdul ya tsayar da ita, be tsaya wata-wata ba ""yace Amatullahi BANI ABDULRAHEEM KIKE AURE BA ABDULRAHMAN KIKE AUREEE... Hmmmmm rikici kenan, readers wai ya kuke tunanin Amatu zatayi? Shin zata ɗauki ƙaddara ko bazata ɗauka ba?? Wani matsayi zata aje ƙawarta Ameerah data auri wanda takeso??? Hmmmm duk ku biyoni dan jin yadda lamarin zai kasance [3/17, 8:56 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫            *RUDANI*        💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by     Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS         ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 '''vote me on wattpad @lashminzy'''         Page 97-98 "A firgice ta juyo cikin wani irin yanayi ta fara pointing ɗin Abdulraheem gami da sakin wani ɗan guntun murmushi tana girgiza kai tace plssss ya Abdulrahman (tana magana ne da Abdulraheem) ka daina banason irin wannan wasan plsss. "Ameera da duk hawaye ya cika mata fuska daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta datayi mata nauyi ta ƙaraso wurin Amatu ta dafata, tace besty wallahi ba wasa bane abunda Abdulraheem ya faɗa gaskiya ne, "cikin rikicewa tace Ameerah harda ke cikin wannan mafarkin? Dan Allah ki watsa mun in farka daga wannan mummunan mafarkin, ta ƙarasa maganar da ƙwalla taf a idonta.      "Cikin dauriya da jarumtaka, Abdulrahman ya ɗago idanunwanshi da suka canza launi zuwa ja kamar gwarwashi ya watsa su akan Amatu kan ya kira sunanta cikin murya mai ban tausayi yace Amatullahi ba mafarki kike ba dan Allah ki buɗe idonki ki kalle mu ki kuma fahimce mu da basirar da Allah ya baki kinji ma.......Girgiza kai ta farayi tana ja da baya, "Wai da gaske ba mafarki nakeyi ba? Na shiga uku ni Amatullahi wani irin RUƊANI ne ya shige ni wanda yasa na kasa banbance ku? Wallahi kun cuceni kunci amanata, ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya, da sauri Ameerah ta ƙaraso wurinta da niyar dafata, Amatu ta dakatar da ita ta kalleta ido cikin ido tace wallahi kin bani mamaki,  yanzu harda ke za'a haɗa baki a cuceni? Ameerah kinfi kowa sanin yadda nakeson Abdulraheem amma har kika yarda sheɗan yaci galaba akanki kika auri masoyina?? Ameerah wai kece kuwa wacce nasani mai son farincikina? Wacce ko abu tagani tanaso idan na nuna inaso take barmun?   "Amatullahi dan Allah kiyi haƙuri munsan bamu kyauta ba amma dan Allah ki sauraremu kiji abunda zamu faɗa maki, Abdulraheem ya faɗa cikin marairaicewa, "Cike da ɓacin rai da kuma jin haushin kalamanshi cikin faɗa da gunjin kuka tace ashe duk sonda kake mun na banza ne? Abdul me zaka faɗamun? Kana tunanin akwai wasu kalamai ne da zakayi amfani dasu wurin fahimtar dani ne?? Ɗan guntun murmushi ta saki wanda yafu kuka ciwo tace "kunyi amfani da damar ku na zama ƴan biyu kun cutar dani, wallahi Allah sai ya sakamun, ta ƙarasa faɗar maganar a yayinda hawaye ke zubo mata.   Sharewa tayi, ta juya wurin Abdulrahman dake zaune kamar wani gunki tace kai kuma maye natacce burinka ya cika ka aureni amma kasani daga rana irin ta yau niba matarka bace dan wallahi sai ka sakeni idan ba haka ba kotu ce zata rabani dakai kuma wannan ƙazantar tana magana tana pointing ɗin ɗan ƙaramin cikin dake jikinta, daka ƙunsamun wanda acikin rashin sani hakan ta faru toh ka ɗauka tamkar ba'ayi shi bane dan yau ba gobe ba zan zubar shi. "Tana faɗar haka bata ko jira amsar su ba ta haura sama da gudu. Gabaɗayan su daskarewa sukayi a wurin, Abdulrahman ya tashi da niyar yabi bayan ta Abdulraheem ya dakatar dashi, Ameerah naganin haka itama ta haura sama a guje dan batasan abunda Amatu zatayi ba dan yadda taga ta haura sama kamar wacce zata tashi sama, "daidai bakin ƙofar ɗakin sukaci karo, kafin Ameerah tace wani abu Amatu ta bangajeta ta sauka ƙasa. "Ko kallon inda su Abdul batayi ba ta fice daga palon. "A tsorace Abdulrahman ya tashi ya fito waje jin ƙarar tashin mota, sedai kafin ya iso harta wuce amatsiyacin gudu wanda indai ba ikon Allah ba daƙyar ta iya kai gida lafiya. Da sauri ya koma palon ya ɗauko makullin mota danya take mata baya, Abdulraheem ya dakatar shi yace karka bita, Abdulrahman ya banko mashi wata uwar hararara cike dajin takaici yace what are u saying? Matata na cikin wannan yanayin zan barta a haka?, idan na rasata fa?? Iyeee kodan ba matarka bace?? Tsuki yaja haɗe dayin kwafa ya nupi parking space, ba ɓata lokaci ya tayar da motar ya fice a guje. "Abdul ka sakeni wallahi bazan iya zama dakai Amatu na cikin wannan halin ba, plsss ka sauwwaƙe mun kaje ka auri Amat....bata ƙarasa ba sakamakon marin daya yayi mata cikin ƙunar rai  yace kina da hankali kuwa? Dame zanji ne wai? Ko Kin taɓa ganin yaya ya saki mata ƙani ya aura alhalin yayan na nan da ranshi? Gabaɗaya duk a rikice take danko maganar da take faɗi batasan tayi ba, kuka ta fashe dashi ta shige part ɗinsu ta ɗauko  gyalenta ta nupi hanyar fita, da sauri ya sha gabanta yace ina zaki? Cikin ko in kula tace gida zani, agadarance yace babu inda zaki. Kallon uku saura ta aika mashi sannan tace wallahi sai naje ƙafarka ko ƙafata? tana faɗar haka ta raɓa ta gefenshi ta wuce, aikuwa kamar leda haka ya fincikota yace Ameerah dani kike musayan yawu? nine fah mijinki Abdulraheem? Cike dajin zafin riƙon dayayi mata tace me kake nupi? Me kake tunani? Yanzu baka tuanin halin da Amatu zata shiga? Baka duba girman laifin da muka aikata mata ne? Kodan baka damu da halin da ɗan uwanka zai shiga bane shine ni zaka hanani zuwa ganin halin da ƴar uwata zata shiga? Abdul miye ke damun ƙwaƙwalwarka ne? Mu muka aikata mata laifi ba ita bafa?    "Shuru yayi duk jikinshi yayi sanyi, sai kawai ya juya batare dayace mata komai ba ya shige gida, ya ɗauko makullin mota ya fito, lokacin har ameerah ta wuce, da sauri ya tayar da motar ya fita waje, yana tafiya yana waige-waige ko zai ganta, cikin sa'a kuwa ya ganta zata shiga taxi, da sauri ya fito ya ƙaraso wurinta yace plss my Ameerah kiyi haƙuri muje in kaiki duk inda zaki wallahi da gaske nake, jin yayi rantsuwa ne yasa ta bawa mai taxin haƙuri sannan tabi bayan shi suka shiga mota suka wuce. """Tuƙi take harna fitar hankali, bata ji bata gani kawai da sunan tana tuƙin ne amma bata san inda take saita kan motar ba, duk inda ta gitta sai an bita da kallo, wasu ko sai zagi suke ɗura mata suna cewa wannan mahaukacin direba dan yadda take tsala gudu babu mai gani yace macece ke tuƙin. Gudu take sosai harta kawo daidai traffic light dake ba cikin hayyacinta take ba yasa bata lura ba tawuce da gudu sai ji kake ƙiiiii................ Share [3/27, 10:08 PM] ‪+234 816 787 6616‬: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 ```vote me on wattpad @lashminzy``` Page 99-100 """Sai ji kake ƙiiiiiiii taja wani irin wawan burgi wanda duk da irin burkin data ja saida motar ta bugi paul (pal waya) ɗin kafin ta tsaya, da sauri mutanen dake kan titin suka taso sukayi gaggawar zuwa inda take, kowa abun mamaki yake bashi ganin macece, "wasu ko marasa imanin tsuki kawai sukeyi su wuce abun su, "mashi imanin kuma tsayawa sukayi suna mata barka dan basu ɗauka abun zai tsaya a iya haka ba. Wasu ƴan matasa ne guda biyar, maza uku mata biyu, suka iso wurin, ɗaya daga cikinsu me suna fauziya, a ɗan rikice ta juyo tana kallon ƴan uwanta tace wannan ba Amatullahi bace matar Dr Abdulraheem? Ta faɗa tana pointing ɗin Amatu data daskare a wurin ta kasa ko magana. Babban yayansu yace ƙwarai kuwa itace amma meya faru da ita hakane? Fauziya tace yaya abunda ya faru da ita ba shine ya kamata mu sani ba, taimakonta ya kamata muyi dan naga kamar bata cikin hayyacinta, ummi yayar fauziya tace Eh wallahi yaya mu taimaketa kasan fah muma mijinta shine wanda ya ceto rayuwarmu dan haka muma mu taimaka mata. Daga nan suka kutsa cikin mutanen suka iso gabanta, fauziya ta kamata tace aunty sannu, kowa ya maida kallon shi zuwa garesu, cikin mutanen dake wurin wani yace ke malama lafiya? Ummi tace ƴar uwarmu ce gida zamu kaita. Cikin rashin yadda mutumin ya tambayi Amatu, duk da cewar bata ganesu ba amma taga kamar ta taɓa ganin su a wani wuri sai kawai ta girgiza kai alamun tasan su. "Daga nan kowa ya fara watsewa, daman kuma bataji ciwo ba illah gaban motar ta data lotsa da kuma ƙwayaƙwan motar duk sun dagargaje. Jan hannunta fauziya tayi takaita cikin motar su, sannan ummi da babban yayan su suka shiga, motar Amatu kuma sauran maza biyun ne suka shiga, basu zarce ko'ina ba sai gidan su Amatu, da shigar su Amatu ta fita daga motar a guje ta shige palon su inda ta tarar da mummy na cin abinci, da sauri mummy ta ajiye plate ɗin abincin tayo kan Amatu cikin rikicewa take tambayarta lafiya ta ganta a haka? Kuka ta fashe dashi ta faɗa jikin mummy tana cewa wallahi mummy sun cuceni. "'"""Mummy ta ɗago kanta tace Amatu su waye suka cuceki? Mummy daman ba Abdulraheem nake aure ba? Mummy tace kamar ya ban fahimceki ba? Kuka ta fashe dashi tace mummy ina nupin ba Abdulraheem ne mijina ba Abdulrahman ne mijina!!! "Tsaki mummy taja tace inji wani mahaukacin? Toh ƙarya ne kawai dai ana son a shiga tsakanin ku ne amma wannan ba gaskiya bane, "wasu hawaye masu zafi suƙa zubo mata tace mummy ba jinayi a waje ba su dakansu suka faɗa mun, nan ta kwashe komai ta faɗamata. kuma mummy wai harda Ameerah aka haɗa baki aka cuceni? Mummy yanzu kin taɓa tunanin Ameerah zata iya auran wanda nakeso? Innalillahi wa'inna ilaihirraj'iun kawai mummy ke maimaitawa sannan ta kalleta tace yanzu maganar nan da kike faɗamun gaskiya ne?Amatu ta girgiza kai alamar eh. "Hmmmm lallai biri yayi kama da wando,,, waton sunyi amfani da damar su ta kamanceceniyar su sukaci amanar mu ko?Toh kwantar da hankalinki wallahi dani suke zancen mummy ta faɗa ayayin da take shafa bayan Amatu. Tana cikin shafata ne idonta yakai ga su fauziya, sakin Amatu tayi ta kallesu tace sannun ku dan sai yanzu ta lura dasu duk kuwa irin gaishetan da suka dingayi amma ina hankalinta naga kan ƴarta. Gaisheta suka ƙarayi ta amsa haɗe da sakar musu fuska, su kuma ganin gidan ba lafiya ba yasa basu tsaya wani dogon zance ba suka wuce akan nan da kwana biyu zasu dawo, mummy ta amsa da toh sannan suka wuce, "wurin Amatu ta koma ta zauna tana facing ɗinta tace daughter wannan kukan da suka saki nayi maki alƙawarin suma sai sun zubar da fiye dashi. Su fauziya na fita sukaci karo da Abdulrahman a farfajiyar gidan, ya ƙurawa motar Amatu data lanƙwashe ido, fitowar su fauziya ya dawo dashi cikin hayyacin shi, cikin tsoro da wani irin murɗawan ciki yake binsu da kallo dan duk a tunanin shi ƴan gaisuwa ne 🙈😂 su kuma dake basu san cewar Abdulraheem ɗin ƴan biyu bane sai fauziya ta ƙarasa wurin shi tace Dr Abdul ina wuni, suma duk suka gaishe shi amma shuru bai amsa su ba sai ma wuce su dayayi ya shige cikin gida. "Da kallo suka bishi harya shige cikin palon, fauziya tace wannan gidan kam ba lafiya yake ba, ummi tace ina lafiya kuwa mudai mu wuce gida kar baba yace mun daɗe, ɗan autan su yace toh da dai yafi, amma nifa nan da kwana biyu sai na dawo inji takamaiman abunda ya faru, sai babban yayan su yace kai wallahi wurin jin ƙwaƙwafinka zaka malgaya lokacinka baiyi ba, dukan su suka sa dariya gami da shige wa mota. ""Abdulrahman na shiga palour ƙamshin turaren shi ya daki hancinta,,, ɗagowa tayi ta kalleshi tun daga kan ƴan yatsun ƙafar shi har zuwa kan fuskar shi, sai tayi saurin tashi tsaye tace karka kuskura ka shigo mana gida, "mummy dake fitowa daga ɗaki tayi saurin ƙarasowa wurin Amatu ta zaunar da ita sannan ta kalli Abdulrahman da jiyake kamar yayi kuka ko zasu saurareshi, tace waton kai mara kunya ko? Duk abunda kukayi kaida ɗan uwanka bai isheka ba sai kun biyota har gida kun ƙarasata ko, toh ta Allah ba taku ba, kuma bari kaji kamar yadda ta faɗa wannan cikin dake jikinta sai nasa an cire shi saboda nasan shiya baka ƙarfin gwiwar zuwa har cikin gidan nan... Ƙara takowa yayi zuwa cikin palon cikin ɗaga murya mummy tace auww sai ka shigo kenan? Toh ka shigo tunda gidan kune?tana faɗin haka ya dakata haɗe da duƙawa cikin marairaicewa yace mummy dan Allah ki taimakeni kiyi haƙuri Wallahi ba da gangan muka aikata ba dan Allah ki saurareni kiji. Cikin faɗa mummy ta katse shi" ka fita nace ko? Tashi yayi sum-sum ya wuce batare daya sake koda juyowa ba, "yana fita yaci karo dasu Ameerah, Ameerah kam ko kallon shi batayi ba ta shige cikin palour. ""Abdulraheem kam tunda yaga yanayin Abdulrahman yasan ba lafiya ba,,, ƙarasowa kusa dashi yayi yace ɗan uwa dan Allah kayi haƙuri insha Allah komai zai dawo normal, yana faɗar haka yasa kai zai shige cikin palon Abdulrahman ya riƙo hannun shi, cak ya tsaya haɗe da juyowa sai Abdulrahman ya juya mashi kai alamar karya shiga."Batare daya ce wani abu yaja hannun shi suka nupi wurin mota, take suka tayar da mota suka bar gidan......... "Ameerah na shiga palon sai kuma ta dakata saboda ji datayi ƙafafunta sunyi mata nauyi a ɗaya ɓangaren zuciyarta ko tunani take da wani ido zata kalli mummy? Hawaye ne sukaci gaba da zubo mata, mummy kuwa tana ganinta tayi saurin isa wurinta, ta rungumeta tana cewa yi shuru Ameerah, Ameerah kuwa sai ƙara kuka take tana cewa mummy Amatu, plsss kic...tabarrr.. fushid...dani kinji, tayi maganar ne cikin shasheƙa sabida kukan dayaci ƙarfinta. Cikin lallashi mummy ta zaunar da ita ta ɗauki wayarta ta kira number aunty hajara, tace mata tazo yanxu-yanzu, tana faɗar haka ta katse kiran taci gaba da lallashin Ameerah. Amatu kam tunda taji Ameerah na kuka sosai ta shige ɗaki dan bazata iya jurar ganinta tana kuka haka ba........ Share [3/27, 10:08 PM] ‪+234 816 787 6616‬: 💫🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 ```vote me on wattpad @lashminzy``` Masoyana dan Allah kuyi hkr da rashin jina da kukayi kwn biyu, wlh schl ne ya ɓoyeni. But never forget, one heart ❤ Page 101-102 "Ko minti biyar ba'ayi ba sai ga aunty hajara tazo, sallamar datayi a iya laɓɓanta kawai suka tsaya saboda halin da taga Ameerah ita tama ɗauka ko mijin nata ne ya rasu,,,, ƙarasa shigowa tayi ta samu wuri ta zauna saman kujerar dake facing ɗinsu, cikin son taji abunda ke faruwa tace mummy lafiya? Mummy tace ina kuwa lafiya, ta zayyana mata duk abunda ke faruwa, aikuwa a hasale aunty ta taso tayo kan Ameerah tana huci kamar wata zakanya, cikin canjin murya tace ""Ameerah kina da hankali kuwa? Me suka rageki dashi da zaki cucesu? Ko kin manta Amatullahi ƙawarki ce da zaki auri wanda takeso??? "Wallahi kin ban kunya,,,, Ameerah miye bayin Allahn nan basuyi mana ba,,, amma kirasa hanyar da zaki saka musu da ita sai wannan? "Toh wallahi umma zan kira in faɗamata abunda kikayi, ta ƙarasa maganar a yayinda take matsar wayarta. Da sauri Ameerah ta isa gabanta ta rusuna haɗe da riƙe mata ƙafafuwa tana bata haƙuri,,, mummy ta taso tazo wurinsu ta janye Ameerah dake duƙe a gaban aunty hajara tana bata haƙuri, cikin bada umarni mummy tace hajara kada ki kuskura ki kirata, kuma ko ba yanxu ba banason kowa yaji wannan maganar. Dake ta ɗauki mummy a matsayin ƴar uwarta, dan kam mummy tayi mata abubuwa da dama kuma koba komai tana gaba da ita shiyasa takejin nauyin ta musa mata, sai kawai ta ajiye wayar kamar tayi kuka haka takeji,,, sedai kota kansu batabi ba ta wuce ɗakin Amatu. Cikin ko'in kula da halin da aunty hajara ke ciki taja hannun Ameerah zuwa ɗakinta. """"""""Su Abdulraheem na fita direct gidansu mummy suka nupa, dan sun san halin ammie balle datayi musu kashedin akan idan daga baya komai ya kwaɓe musu karsu kuskura suzo wurinta, dan sai datace karsuyi haka amma sukaƙi ji. Bayan sun isa palon mummy suka shiga daidai tana fitowa daga kitchen, tana ganin su tayi saurin Zuwa wurinsu, cikin rikicewa tace Abdul meya sameku na ganku haka? shuru dukansu sukayi sai da suka kusan kwashe minti biyar babu wanda yayi magana cikinsu, harta juya zata wuce Abdulraheem yayi ƙarfin halin cewa mummy tamu ta ƙare. Duk da damuwar data tsinci kanta sai dataji kamar tayi dariya saboda maganar dariya ta bata, amma tana juyowa sai ta mayar da fuskarta fuskar tausayi tace ya akayi ne, Abdul yace mummy zauna, ba musu ta samu wuri ta zauna, Abulrahman kuwa jiyake kamar wurin bazai iya ɗaukar shi ba saboda tsananin damuwar datayi mashi yawa, fita kawai yayi batare dayace musu ƙala ba. Dukansu kallonshi sukayi harya fita, sedai fitar shi keda wuya suka jiyo tarin shi, a ruɗe suka fito waje Abdul ya riƙeshi haɗe da fesa mashi iskan bakinshi daga kanshi zuwa goshin shi wanda a hankali tarin ya fara tsayawa, cikin galabaita haɗe da dafe zuciyar shi yana nishi kaɗan kaɗan yace mummy, Abdul mutuwa zanyi dan Allah kuje ku bata haƙuri kuce karta zubar mun da ajiyata, yana faɗar haka ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sai kuma ya fara tari babu sassauci wanda harya fara fitar da baƙin jini. "Cikin hanzari Abdul da mummy suka kamashi suka sashi a mota, Abdul ya wuce dasu asibitin su, mummy sai hawaye takeyi tana sharewa wasu na zubowa har suka iso asibitin, suna isa Abdul yayi saurin fitowa yaje ya kira wasu likitoci guda biyu, ciki harda usman, ba ɓata lokaci aka kaishi emergency room, taimakon gaggawa suka bashi, daƙyar aka samu tarin ya tsaya, sannan sukayi mashi allurar bacci haɗe da ɗora mashi drip, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon agaba dashi. Abdulraheem na fitowa mummy ta tareshi, cikin tsantsar damuwa tace Abdul ya yake, saboda ya kwantar mata da hankali dan yaga duk a rikice take, yaja hannunta suka shiga ɗakin, ganin Abdulrahman a kwance yasata saki ajiyar zuciya da hamdala, zama tayi gefen gadon tana kallonshi, Abdulraheem kuma ya fita dan akwai wasu magungunan da yake son ya ɗorashi akai shine yakeson yaje ya siyo. "Bayan Abdul ya dawo ne mummy ta tashi zataje gida ta girko mashi abinci saboda samha na gidansu hanan dan ta mayar da gidan tamkar gidansu, da ita zatace ta dafo mashi abinci. Abdul yace toh sannan mummy ta fice. Da musalin ƙarfe shida na yamma mummy ta dawo, lokacin Abdulrahman harya farka sedai damuwar dake kwance a zuciyar shi yasa ya lumshe ido kamar mai yin bacci, yana sauraron hirar mummy da Abdul, wanda duk akan abunda ya faru ne. Mummy tace su kwantar da hankalin su insha Allah da kanta zataje tayi magana da mummyn Amatu ta bata haƙuri a wuce wurin. Abdulrahman ya ɗan buɗe idonshi kaɗan yace mummy Allah bazasu haƙura ba saboda harda korata fa sukayi kuma ni abunda ke damuna shine karsu zubar mun da ajiyata "wallahi mummy komai zai iya faruwa idan aka taɓa lafiyar matata da ajiyata.......Abdul dake gefen shi ya dafashi yace plssss calm down ɗan uwa komai zai wuce ka daina sa damuwa a ranka kaga abunda ya faru dakai yanzu ko? Shuru yayi ya jinginar da kanshi jikin gadon. Cike dajin tausayin shi mummy tace son tashi kaci abinci """""Shuru yayi mata wanda ko bai faɗamata ba tasan baida niyar ci dan hakanan halayyarshi take idan bayason abu kace yayi shuru yake maka,,, cikin lallashin shi ta samu yaci spoon biyar shima daƙyar danta bashi a baki ne yaci. "Bayan ya gamaci yasha magani sannan aka cire mashi drip danya ƙare. Bayan an cire ya shiga toilet ya ɗauro alawla sannan ya fara gabatar da sallar azahar da la'asar ɗin data wuce shi, yana idarwa aka kira magariba nan yayi harda ita ya zauna a wurin yana lazumi har akayi isha'i yayi ta, mummy tata sallar tayi daga gefe, Abdulraheem kuma masallacin dake cikin asibitin yaje yaje yabi jam'i. Da misalin ƙarfe tara suka karɓi takardan sallama, dan Abdulrahman cewa yayi bazai kwana ba yaji sauƙi, mummy ta aza ko wasa yakeyi sai dataga yana shirin fita tukunna tasa aka karɓar musu takardan sallama suka wuce. Bayan sun isa gida mummy ta wuce part ɗinta Abdulraheem kuma part ɗin Abdulrahman ya wuce dan nan zai kwana saboda bazai iya kwana shi kaɗai a gida ba kuma ba abun yaje gidan ammie ba ta tisasa agaba da tambayoyi. "Wanka Abdulraheem yayi yasa wata jallabiyar Abdulrahman ya kwanta haɗe da jawo wayar shi ya fara dialing number sedai wannan karon a kashe take saɓanin ɗazu da yayi ta kira ana rejecting, tsaki yaja ya tura wayar gefe yaja blanket, ya rufe jikinshi. Abdulrahman shima kwance take ya kasa bacci sai kiran Amatu yake amma ba'a picking daga ƙarshe ma rejecting akayi aka kashe wayar baki ɗaya... """Duk ji yayi babu daɗi kuma daya rufe idonshi ita kaɗai yake gani tana mashi yawo, tashi yayi ya shiga toilet ya ɗauro alawla ya fara nafilfili, wanda bashi ya gama ba sai kusan ƙarfe biyu na dare sannan Ya kwanta. Ɓangaren su Amatu kuwa damuwace fal ranta wanda hakan ya hanata samun cikakke bacci ga kuma ciwon kan daya isheta wanda kukan datayi ne ɗazu ya jaza mata ciwon,,,,, haka ma Ameerah kuka kawai takeyi ƙasa-ƙasa dan ɗakin mummy take kuma mummy taja mata kunne akan kadata kuskura taji kukan ta kuma kukan yaƙi tsayawa shine takeyinsa a hankali. A taƙaice dai wannan daren a daddafe suka ganshi harda aunty hajara da mummy, su ammie kuwa dasu samha kam basu kosan wainar da ake toyawa ba. Bayan kwana biyu.......... share 🌞💫🌞💫🌞💫 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Story & written by Lashminzy 💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥 ```vote me on wattpad @lashminzy``` Page 109-110 "Idonta dake kulle ta buɗesu a hankali jin ba'a ƙasa ta faɗi ba, kallonshi tayi ta wani yatsine fuska haɗe da cewa tnx ta zame jikinta daga nashi ta wuce palour,,,,hijabinta ta ɗauko batare data kalli inda yake ba ta haura sama. Shiko tsaye yayi kamar wani gunki yana kallonta harta ɓace wa ganinsa. "Fasa shiga kitchen ɗin yayi ya haura sama ya shiga ɗakin shi ya sauya kaya zuwa jallabiya ya wuce masallaci, bayan ya dawo ne ya shiga kitchen ya ɗauko plate da cup ya hauro dasu sama, a bakin ƙofarta ya tsaya ya yafara bugawa a hankali, sedai har kusan minti biyar beji alamar mutum ba balle kuma yasa ran za'a buɗe dan ƙofar gamƙe take da makulli, maƙe kafaɗa yayi irin ko a jikin shi ɗinnan, ya shiga ɗaki, bada jimawa ba sai gashi ya fito da wani makulli a hannun shi. "Soka ɗan makullin yayi ya buɗe yasa kai ya shige ɗakin sannan ya mayar ya rufe ya zare makullin yasa cikin aljihun jallabiyar shi, kayan dake hannun shi yakai saman ɗan center table ɗin dake tsakiyar ɗakin ya aje, sannan ya cire jallabiyar shi ya rage daga shi sai singlet da boxers, bakin ƙofar toilet ɗin ya isa yana jin yadda take wasa da ruwa wanda take yaji kamar ya shiga ya tayata, sedai beko gama tunanin da yake ba yaji motsin zata fito. "Da sauri ya ɓuya bayan labule" "Ita kuwa fitowa tayi da wani ɗan ƙaramin towel a jikinta wanda ko cinyarta bai gama rufewa ba, ƙarasawa tayi bakin madubi tana ɗan gwaggoge jikinta da wani ɗan karamin towel, sanin ita kaɗai ce a ɗakin yasa ta kwance towel ɗin ta gyara mashi zaman shi "Aikuwa karaf idanun shi suka sauka a nashanun Amatu da suka ƙara cika kamar an hura baloons, kallon su da yayi ba ƙaramin tayar mashi da hankali sukayi ba, hakan yasa ya kasa daurewa kawai batare da yayi fargabar wani abu ba yaje ta bayanta ya rugumeta. "Dake ta bashi baya tana kallon madubi dan shima ta cikin madubin ne ya kallesu. "A tsorace ta kurma ihu har towel ɗin dake jikin ya kwance ya faɗi ƙasa, Murmushi Abdulrahman yayi yace matsoraciya kawai toh nine mijinki, a ɗan zabure ta juyo suna facing juna cike da mamakin yadda akayi ya shigo mata ɗaki bayan tasan ta rufe harda makulli, ganin irin kallon da yake mata ne yasa tayi saurin kallon direction ɗinda yake kallo, aikuwa taga jikinta yake bi da kallo ko ƙyaftawa bayayi. Da sauri ta zame daga jikinta daga nashi taja towel ta ɗaura tana mai banka mashi hararar da beko san tanayi ba, dan zama yayi kamar wani gunki ya tsura mata ido har ta ɗaura towel ɗinta daya faɗi. Wurin wardrope taje ta buɗe ta ɗauko wata night gown me shara-shara ƴar guntuwa da pant ta saka, ko brazier bata saba saboda yawan takura mata da takeyi, haka harta gama shiryawa yana tsaye yana kallon. Niko nace kodai suma yayi mu yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo? 😂lolx "Sai bayan ta gama shiryawa tazo zata fita taji ƙofar a rufe, murmushi yayi ya ƙaraso wurin ta yayi hugging ɗinta ta baya yace haba baby wannan irin rikitarwa haka ai sai a kwashi gawata, murmushi yaso ya suɓuce mata sai kanne ta wani ɓata rai ta juyo suna fuskantar juna tace ya Abdul leave me alone! Duk da ya tsani amai tsawa amma saboda itace bai nuna komai ba sai ma Ƙara matseta dayayi ajikinshi har sai data saki ƴar ƙara yace saboda me zan ƙyaleki? Shuru tayi masa ta ƙwace kanta daga gareshi tace ka bani makulli na? Ya waro ido yace yaushe na ɗauki makullinki ni dana shigo ta sama! Kukan shagwaɓa tasa masa harda bubbuga ƙafa a ƙasa tana wani turjewa sai kace ƙaramin yaron da aka anshewa sweet😂 "Ni Allah ka bani makulli na? Tamke fuska yayi alamar babu wasa yace ina zaki je? Batayi wata gardama saboda irin yunwar da takeji tace am hungry zan shiga kitchen ne! "Dariyar zuci yayi yaja hannunta zuwa wurin center table ya zaunar da ita a ƙasa, ya saukar da kayan ƙasa shima ya zauna haɗe da nannaɗe ƙafafun shi sannan ya buɗe ledar, kaza ce gasashiya da friedrice cikin take away da kuma hollandia yoghurt, zuba musu yayi cikin plate ya ƙara matsowa gap da ita yadda zaiji daɗin bata a baki. "Ɗebowa yayi a spoon da niyar ya bata a baki ta kauce haɗe da rufe bakinta tana yatsine fuska cikin shagwaɓa tace ya Abdul plss ka matsar dashi a gaba na amai zanyi, ta ƙarasa faɗar maganar harda fiddo wasu ƙwallar ƙarya wanda daƙyar ta fakeshi ta matso su, cikin kulawa ya matsar da abincin a gabanta yace toh me kikeson kici, kinsan banason ki zauna da yunwa ko? Toh, ni indomie nakeson naci kuma asa yaji da yawa, toh yace yana miƙewa saboda bayason duk wani abu dazai samu lafiyar matar da kuma babyn shi, yace bari inje in ɗauko key ɗin mota insiyo maki ko? Da sauri ta tashi tsaye tasa mashi kukan shagwaɓa, ni fa banason na waje kai nakeson ka dafa mun da kanka, ta faɗa haɗe da cuno ɗan ƙaramin bakinta mai bala'in burgeshi a duk lokacin da take shagwaɓa. "Juyowa yayi wurinta suna fuskantar juna yace karki damu baby na farincikin ki o nawa dan haka duk abunda kike so shi za'ayi, just give me 15mins kawai, yana faɗa ya ciro makulli daga aljihun jallabiyar shi dake rataye jikin wardrope ya buɗe ya fita. Yana fita taja tsuki haɗe da marin kanta tace oowoooo dama abunda baza'a iya samun shi kusa nace ba, wallahi na kwafsa, kwafa tayi ta haye saman gado ta kwanta tana jiran shi ya dawo, daga nan bacci yayi awon gaba da ita, wanda ba ita ta tashi ba sai lokacin data jita a jikin mutum, a hankali ta fara buɗe idonta har ta watsa su a kanshi, cike da jin bacci tace ya Abdul na ƙoshi fah. Lallashinta ya farayi daƙyar kafin ya samu ta faraci, a hankali yake bata harta gama ci ya bata ruwa tasha sannan ya kwantar da ita saman gado, kwashe su plates ɗin yayi bayan ya cinye rogowar indomien data rage, su kaza kuwa yabar batun su saboda babyn shi bataci ba shima haka yaƙi ci yakai cikin fridge yasa dan karsu lalace. Ɗakin ya dawo bayan ya kimtsa ko'ina, ya kashe ƙwan wutar ɗaki ya rage sai disco light dake haska ɗakin, can gefenta yaje ya kwanta a takure dan jiyake kamar yaje ya rungumeta sedai ganin yadda take wani sha mashi ƙanshi tana iya sai hankalin shi yakai ƙololuwar tashi ta hanashi aiwatar da abunda yakeso dan haka kawai yaja blanket yayi musu addu'a ya kwanta. Washe gari........... Share [3/28, 6:52 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮 (Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς) 💫🌞💫🌞💫🌞 *RUDANI* 💫🌞💫🌞💫🌞 Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу Ꮮasིhིmིiིnིzིyི Page 111-112 "Washe gari" Koda Amatu ta tashi rungume ta ganta a jikinshi wanda shi kanshi besan lokacin da yayi hakan ba, Karewa kyakyawar fuskar shi kallo tayi yadda yake bacci hankali kwance, a hankali yake fitar da numfashi, Cikin baccin shi yakejin kamar ana son akwace mashi wani abu, kara matseta yayi ya cigaba da baccin shi, itakuwa zuba mashi ido tayi taga yadda ya kara matsota jinkin shi. Duba agogo dake makale a dakin tayi taga har lokacin sallar asuba ta wuce, da sauri ta zame jikinta daga nashi ta sauka saman gadon ta koma can gefen shi tasa lallausan hannunta ta fara bubbuga shi a hankali, Wata irin mika yayi hade da jawota jikin shi, a hankali ya bude eyes dinshi ya zuba mata, murmushi ya sakar mata yace baby har kin tashi? girgiza kai tayi alamar eh, Shi kuma wayan shi dake gefen shi ya duba yaga lokacin sallah ya wuce, da sauri ya dagata daga jikin shi ya sauka saman gadon gami da cewa baby shine baki tasheni naje masallaci ba? Cikin dan shagwaba tace toh nima ai yanzu na tashi, kallonta kawai yayi batare da yace wani abu ba ya shiga toilet ya dauro alawla ya fito ya zura jallabiya ya wuce masallaci, ita kuma bayan ya fito ne ta shiga tayo alawla ta fito ta daura zani da dogon hijab ta tayar da sallah, bayan ta idar ne ta zauna tana karatun Al Qur'ani, ko daya dawo tana nan zaune tana karatu, shima gefenta yaje ya zauna ya jawo Qur'ani ya fara karantawa, basu suka tsaya ba sai da gari ya washe sosai sannan suka rufe Qur'anin. "Tashi tayi zata nade daddumar yace ta barshi da zai nade, komi batace ba ta cire katon hijabin data saka ta kafin ta fita daga dakin. Shima fita yayi ya wuce nashi dakin saboda yayi wanka saboda yau akwai class din da zai ma lecture by 10am. "Toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin riga da wando na yadi wanda suka matukar karbar jikinshi, turare ya feshe jikinshi dashi sannan ya bude side drowan dake gefen gadonshi ya dauko wasu takaddu yasa cikin jakar shi, "Sannan ya rataya jakar ya fito, dakinta ya leka bai ganta ba, kasa ya sauko ya sameta a palour tana jera mashi breakfast, gabadaya palon ya cika da kanshin arish da ferfesun kayan ciki. "Ji tayi kamar mutum a kanta, da sauri ta dago kanta suka hada ta sakar mashi murmushi hade da rungumar shi, cikin sweet voice dinta tace ya Abdul har zaka fita ga breakfast dinka na gama? Tabe baki yayi yace no nayi latti idan na fita zanci a restaurant, ai jitayi kamar an buga mata guduma a kahon zuciya, cike da tsananin jin kishin shi na addabar ta tace" Plsss ya Abdul kayi hakuri da shareka danayi jiya nasan shiyasa bazaka ci abinci na ba, plsss am sorry wallahi bazan sake ba, ta karasa maganar hade da fiddo kwalla, cike dajin zafin hawayen nata dake zuba ya kara rungumota jikin shi yace nima wasa nake maki, ai idan ba matata Amatullahi ba bazan iya abincin wata ya mace ba sai ammie na da mummy, so ki kwantar da hankali yanzu zan zauna inci ko? Ya dage mata gira. Kawar da ita yayi daga jikinshi ya aje jakar shi sannan ya zauna hade da tankwashe kafafun shi, itama haka zama tayi suna fuskantar juna kafin tayi serving dinsu, "Cikin kwanciyar hankali suke cin abincin suna hira irin ta mata da miji masu matukar ji da junan su, haka har suka gama cin abincin, ya tayata kwashe komai suka kai kitchen, palour suka fito ta dauki jakar shi ta rataya a kafadarta, hannuwan su na sarke dana juna suka fita har farfajiyar gidan, can wurin parking space suka tsaya suna hira, suna jin kamar karsu rabu da juna, haka dai badan suna so ba sukayi ma juna sallama ya wuce a yayinda take daga mashi hannu harya fice daga gidan. "Ameera dake gyaran palour tazo wurin window tana kakkabewa idonta ya sauka akan su Amatu dake jikin Abdulrahman har suka isa wurin mota, ido ta zuba musu har suka gama zancen su ya wuce, da sauri ta fito ta tari Amatu, harara ta watsa mata tace sannunku? Waton kince inja aji ke kina nan kina zuba love ko? Murmushi Amatu tayi tace injiwa kawai dai naje rakashi ne. Dakuwa Ameerah ta kaiwa Amatu akai tace Allah bakida mutunci kuma sai na rama....Amatu tace kiyi hakuri wallahi naso injawa ya Abdul aji amma jiya yadda naga duk ya damu a kaina kuma koba haka ba bai dace ace ina wulakanta mijina ba shiyasa kawai yau da safen nan na nemi sulhu a wurin shi kuma daman ina da niyar in fadamaki mun janye wannan kudurin namu saboda ba hanya bace mai bullewa face hanyar rage mutunci da kima a idon miji. Numfasawa Ameerah tayi tace gaskiya hakane Besty, bari ma kigani dana gama gyaran palour na zanje in hadawa Abdul delicious kuma idan ya dawo zan bashi hakuri dan wallahi jiya da yau komi ban dafa ba, dazu dazai fita takadda ma ya aje mun a palour saboda yayi yayi in bude kofa naki, babu hakurin da bai bani ba daga jiya haryau da safe amma na share shi, dan haka yanzu zanje in roki gafarar mijina. Dariya Amatu tayi hade da zaro ido tace lallai ke kinfi iska barna, Ashe ni bankoyi komai ba? 🤔hmmm kedai wuce ki kirashi yanzu kafin yayi maki kishiya. Harara Ameerah ta banka mata, batare datace komai ba ta wuce, Amatu kuwa murmushi tayi hade da girgiza kai ta wuce part d'inta. **************** Abba ne tare da ammie yana bata labarin abunda su Abdulrahman sukayi kuma har ma an mayar dasu, ammie tace yaushe aka mayar dasu bansani ba? Abba yace tun shekaran jiya Alhaji Ibrahim ke fadamun. Bata rai ammie tayi Abba yace lafiya Aisha? Dan guntun murmushi tayi tace ai da nice uwar yaran nan bazan taba bari su koma ba sai na gama wahalar dasu, wai kasan ma shekarajiya da naje saloon sai dana biya gidan? Hmmm nan naci karo da mummyn yan biyu wai tazo bada hakuri nikuwa na cije nace wa Haj rukayyatu karta yadda ta bari yaranta su koma. murmushi Abba yayi yace ai daman ku mata haka kuke da karamin tunani, idan ba haka ba kuda ya kamata ku sulhunta su shine zaku raba kawunan su? """"Gaskiya ku daina hakan baida kyau kinji ko! Dukar da kanta kasa tayi tace toh Alhaji insha Allah bazan sake ba, wannan ma kuskure ne, toh Allah ya kyauta, ta amsa da ameen sukaci gaba wata hirar. ************ Bayan Abdul ya dawo da daddare, sosai yaga canji a tattare da Ameerah, kuma hakan ba karamin dadi yasa shi ba dan koda yaje asibiti a takure yake harya dawo sai yanzu da yaga irin tarbar da tayi mashi, hade ba bashi hakuri, daman ba fushi yake da ba hasalima burin shi bai wuce su dawo yadda suke ba, sai gashi cikin lokaci kadan sun dawo kamar basu ba. A tare sukaci abinci tana bashi yana bata har suka gama, da kanshi ya kwashe su plate yakai kitchen ya dawo, nan Palour suka zauna suna hira, har yake fadamata wai yana tunanin tana da juna biyu. Cike da jin kunyar shi tace ita kam bata yadda ba aiko yace toh gobe zai gwadata danya tabbatar mata. Murmushi tayi ta shige daki da gudu, aikuwa shima ya bita, kan gado ya sameta tayi ruf ada ciki, bayan ya haye yana mata cakulkuli sai dariya take tana cewa ya dagata karya karya ta, sauka yayi ya koma gefen ta yana tsokonar ta daga nan salon wasan nasu ya canza. Da gudu 🏃‍♀🏃‍♀na fitar musu a daki tun kafin Abdul ya koreni...😁 A bangaren su Amatu....... Ayi manage plss Share [3/29, 6:53 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮 (Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς) 💫🌞💫🌞💫🌞 RUDANI 💫🌞💫🌞💫🌞 Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу Ꮮasིhིmིiིnིzིyི : بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ" يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُون Alhamdulilah today is another beautiful day. Haza yaumul akbar; yaumul shukur, yaumul salama! Alhamdulillahi ala ni'matil Islam. May Allah shower His endless blessings upon U & Ur family and May He turn all your noble thoughts, feelings, wishes and heart desires into reality. Ameen JUMA'AT MUBARAK. Page 113-114 "Bangaren su Amatu ma hakan ce ta kasance dan itama tarba mekyau tayi mashi, sai nan take dashi kamar yadda shima hakan yake da ita. Kwana jindadi sukayi daga su Ameerah har su Amatu da kuma mazajen su dan su kwashi gara sosai. "Washe gari da yamma Abdul ya fito zai fita sai ga su fauziya da ummi da sauran yan uwanta sunzo, Abdul na ganin su ya fasa shiga mota ya koma wurin su suka gaisa sannan yayi musu jagora har cikin gidan shi. Da sukaga Ameerah sunyi mamaki sosai dan a tunanin su koya saki Amatu ne saboda sun taba zuwa bikin Amatu akace an daga sai suka koma gida toh dazai sake auren basu samu damar zuwa saboda sunyi tafiya shiyasa ma basu San cewar Ameerah ya aura ba. Bayan sun gaisa da ita me har suna dan hira yayan su yace wai ina Amatullahi ne? Dan murmushi Abdul yayi yace ai yayan shi ke auren ta bashi ba, cikin rudani da sonjin yadda akayi haka ta faru yace kamar ya kenan? Abdul ya fara basu labarin tun farkon haduwar shi da Amatu da kuma haduwar shi Abdulrahman wanda shine dalilin da yasa aka daga auren shi. Fauziya tana dariya tace no wonder🤔 Ashe ranar da muka hadu da Amatu saman hanya tazo a guje bayan mun kaita gida zamu fito muka ganka Ashe bakai bane shi ne? Hmmm lallai wallahi kuna bala'in kama sosai. Murmushi Abdul yayi yace bari ma yaje ya kirata su gaisa, fauziya tace a'a bari dai muje ko, duk suka amsa da toh suka dunguma zuwa part d'inta. "A palour suka tarar dasu ita da Abdulrahman tana kwance saman cinyar shi tana bata labari, sosai suke nishadi sedai zuwan su Abdul ya katse musu jindadin, gaisawa sukayi kafin Amatu ke cewa ai kamar ta taba ganin su, fauziya tace Eh mune Dr Abdul ya kawo lokacin bikin ki, Ayyah Allah sarki toh bari in kawo muku ruwa, ta mike tana yamtsu fuska saboda kasalar dataji dan yanzu cikinta ya fara nauyi idan ta dade a zaune dakyar take tashi, duk ji zatayi jikinta yayi tsami. Kitchen ta shiga ta dauko musu drinks Ameerah ta bita kitchen ta taimaka mata da dauko sauran donought da cin-cin dinda tayi dazu wanda duk kwadayinta ne yasa yinshi. "Can gaban su ta aje musu ta samu ta zauna, Abdulraheem yayi introducing dinsu a wurin Abdulrahman da Ameerah yace musu ai wata rana sun taba accident ne su dukan su shine aka kawo su asibitin su toh babanta su mutumin kirki ne kuma dan zaman da sukayi yasa suka saba da juna. Abdulrahman dan murmushi yayi yace Allah sarki Allah yabar zumunci, kuma dan Allah kuyi hakuri da shareku danayi rannan lokacin bana jindadi ne, a tare suka hada baki wurin cewa ai babu komai, ummi kuwa mamaki take wai danya gane su. Nana sukaci gaba da hirara su kamar irin sun San junan su sosai dinnan, har invitation card din auren su suka bayar daman wannan ranar da sukazo sunzo kawo wa ne toh kuma ganin kamar ba lafiya ba yasa suka bari sai yau su kawo. Aikuwa Abdul yaji dadi sosai yace zai zo har gida ya taya baba murna, sai kusan magariba suka wuce. ******************* So, kauna, tattali, da shagwaba babu wanda Amatu bata gani a wurin Abdulrahman, duk wani motsi nata akan idonshi yake, baya bari tayi duk wani aiki dazai sata wahala, ko makaranta shike kaita, idan an tashi ya dauko ta. "Yanzu ta kara girma da kyau fiye dana da komai nata ya cicciko, Abdulrahaman sai kaf-kaf da ita yake, ko a school duk wani motsi nata a sane yake dan yana sa mata ido sosai kada wani kato yayi ta kalle maahi ita. "Baya ga haka, duk wani abu da zata bukata Abdulrahman ya aje mata, ko aiki da bekai ya kawo ba baya bari tayi, da zarar yaji tace wash hankalin shi zai tashi ya fara cewa lafiya me kikeso, ita kuwa duk tabi ta firgita shi ko school yaje matsuwa yake bai dawo wurinta ba. Haka ma su Ameerah soyayyar karuwa kawai take, kullum cikin nunawa junan su gata suke, cikin Ameerah watan shi uku. Kulawa kam tana samun shi sosai wurin Abdul. Lokacin da Amatu tasan Ameerah ba karamin dadi taji ba dan tafison duk wani abun Alkhairi da zasu samu su sameshi a tare. Gidan nan nasu kam ya zama gidan kallo dan cikin su babu mai nuna ma wani iya kula da mata haka suma matayen. Kullum idan sun fita basu da aiki sai jido kayan babies dana maza dana mata, su man shafawa dasu pampers dasu kayan wasa babu irin wanda basu siya sun aje ba. A bangaren su Ammie da mummy da aunty da kuma mummyn Amatu suma tanadi sosai sukeyi wa cikin su, fatan su dai Allah ya sauke su lafiya. Bayan wata uku............ Amatullahi ce zaune saman kujera tayi rashe she da plate din awara mai zafi a gabanta, awarar taji yaji sosai dan yadda take hura baki tana wash amma bata fasa ci ba sai data cinye tas, tace Alhamdulillah hade da tashi dakyar dan yanzu cikin ta yayi nauyi tashi dakyar zama dakyar kai komai ba wuya yake bata. "Ko school ba kullum taje zuwa ba balle kuma saloon dinta kwata kwata tabar zuwa sedai duk wani abu da ake bukata su bola zasu kirata su fadamata, idan ma kaya ne suka kare datayi order za'a kawo mata har shago. Kitchen ta shiga ta wanke plate ta dawo ta zauna tana kallo danshi ke debe mata keqa idan Abdulrahman baya nan. "Ameerah ce ta shigo tana murmushi tace me ciki ya kadaici? Murmushi Amatu tayi tace dadin abun bani kadai bace 😏 sai suka dariya. Hira suka cigaba dayi daga bisani suka shiga kitchen wurin sana'ar su waton danwake. Kullum sai sunyi danwake, Abdulrahman kuwa bayason danwake, kullum cikin mita yake yana cewa Allah ya nuna mashi an haifi yaran nan dole yaga wacce zata kara daga mashi danwake a gida, su kuwa suyi ta mishi dariya suna cewa besan dadi ba. *********** Kwance take a saman gado tan juyi duk ta har gitsa gadon sai faman nishi take tana wash,,,wash ash........ Share [3/30, 6:18 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮 (Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς) 💫🌞💫🌞💫🌞 RUDANI 💫🌞💫🌞💫🌞 Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу Ꮮasིhིmིiིnིzིyི Page 115-116 hawaye ne ke kwaranya a idanunta, yayinda gabadaya jikinta ya Saki tana jin duk ilahirin jikinta na ciwo, juyi take tana dafe mararta dake tsananin jinshi kamar zai balle, wani abu takeji yana mata yawo a kasanta tana jin tamkar zata yunkura ya fito sedai saboda tsananin azabar da takeji yasa ta kasa nishi balle ta fiddo da abunda takejin ya tsaya mata a gaba. "Yunkurawa tayi cikin dauriya ta zamo kasa, duk da hakanan cikin nata sai wani irin murdawa yakeyi, hannunta tasa saman madubin dake kusa da gadonta tana laluben wayarta, daidai lokacin da hannunta yakai kan wayar taji wani irin ciwon Mara ya taso mata wanda jitake kamar za'a fitar mata da rai. Take ta ture wayar ta fadi a kasa cikin rudewa da zafin azabar ta kurma wani irin ihu, tana fidda munfashi sama-sama, sai kiran sunan Abdulrahman take da Ameerah da mummy tana suzo su taimake ta, haka taci gaba da kuka tana juye-juye tana kiran su Suzi su ceceta har takai ga ko magana bata iya yayi, daga karshe kuwa dauke wuta tayi. Abdulrahman na class yana lectures tare da wasu yan level 300 gaban shi ne keta faduwa tun farkon zuwan shi class din sedai be kawo komai a ranshi ba amma jin faduwar gaban ya tsananta yasa ya fita daga class din ya zaro wayar shi daga cikin aljihu ya kira number Amatu, sedai harta karaci ringing d'inta ba'a dauka ba haka yayi ta kiranta har kusan sau goma bata dauka ba. Beyi wata-wata ba ya shige motar shi ya bata wuta, cikin yan mintuna kalilan ya iso gidan, a bakin kofa ya tsaya yana knocking ba'a bude ba, wasa-wasa harya kai mintuna goma beji motsinta ba kuma ya duba part din Ameerah basu nan. Wayar shi ya dauko yasa sake dialing ba'a dauka ba. Amatu kuwa harta suma ta kuma farfado wa saboda jin wayar ta data fado kusa da ita tana ringing sedai azabar da take ciki ya hanata daukar wayan, kokari ma take ta jawo wayar ta dauka amma ra kasa, dakyar hannunta yakai ta jawo wayar a daidai lokacin an sake kira, batare data duba me kiran ba ta dauka hade da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Cikin firgici da tashin hankali Abdulrahman yace baby ki bude kofa gani nazo gidan, cikin galabaita da rawar murya tace inaa,,,daakin saamaaa......bazan iya fitowa baa....,mutuwa zanyiiiiiiii,,,,,,,Sai hannunta ya kashe wayar batare data sani ba. Cikin rikicewa Abdul ya fara kiranta yana maganganu marasa kai duk ya rikice, jin bata amsa shi ba yasa shi kallon screen din wayar yaga Ashe ma ta kashe. "Wata iriya kara ya saki hade dasa hannun shi ya banki kofar da karfi, amma ina kofar bata bude ba, haka yaci gaba da buga kofar yana wasu maganganu marasa kan gado, dakatawa yayi yaje can wurin me gadi a rikice yace Auwalu bani karfe, bani karfe, Auwalu megadi ya tsaya yana kallon shi yana cewa lafiya yallabai?? Ko kallonshi Abdulrahman beyi ba ya bugeshi ya shige dakin aikuwa yaci karo da wani katon karfe dan dogo dashi, daukowa yayi ya fito da sauri ya isa bakin kofar daidai wurin lock din ya saita ya buga karfen da karfi, take kofar ta bude, da sauri ya yar da karfen ya shige a guje, megadi na take masa baya. A kasa ya ganta tayi daddaya ko numfashi bata fitarwa ga wani ruwa dake fitowa daga jikinta, wata kara ta saki saida megadi yaji tsoro, da hanzarinsa yasa hannuwan shi ya kinkimeta ya fita da ita waje da sauri, can wurin motar shi yaje yasata a gidan baya, ya zagaya ta daya gefen ya shiga. Wani irin gudu yake na fitar hankali, cikin ikon Allah suka iso asibitin lafiya, ko parking bai gama ya fito ya zagaya ya fito da ita, a bakin kofar shiga ciki ya hadu dasu Abdul da Ameerah, dake asibitin su Abdul ya kawota. Wata uwar kara Ameerah ta saki a lokacin dataga Abdulrahman ya dauko Amatu bata numfashi, take taji wani irin jiri na dibarta, basuyi aune ba suka ganta tayo luuuu zata fadi kasa, Abdul ya tarota sedai ina harta suma, Amatu kuwa saman wani gado aka daurata akayi labour room da ita dan sun fahimci nakuda takeyi. "Wani daki aka kai Ameerah aka bata taimakon gaggawa, take ta farfado tana kiran Amatullahi, Abdulraheem dake kusa da ita yace meerah kiyi hakuri Amatu haihuwa zatayi yanzu haka tana labour room plsss ki tayata da addu'a Allah ya sauketa lafiya. Hawayene ya gangaro mata najin tausayin Amatu tace muje in ganta, ta fada tana saukowa daga kan gadon, beyi musu ba yace suje dan bayason wani abunda zai bata mata rai harya kai ga shafar abunda ke cikinta. Waje suka fito suka nupi labour room sedai anan bakin kofar suka tsaya dan ba'a bari a shiga, ko Abdulrahman yana nan waje sedai hankalin shi ba'a jikinshi yake ba, duk yabi ya firgice sai kai kawo yake, idanuwanshi sun canza launi zuwa jaa, addu'a kawai yake Allah ya sauki babyn shi lafiya. "Ciki room din kuwa sai kokarin taimakon ta suke wurin ganin ta haihu amma inaaa ta gaza duk wata dubara da zasuyi sunyi amma haryanzu bata haihu na kusan awa hudu suna kanta, wata likita ce tace anya kuwa haihuwar ce dan naga nakudar nata yadau lokaci kuma dai gashi abunda ke cikin yunkurin fitowa yake. Dayar tace toh kinsan wasu suna kwana biyu suna nakuda wasu kuwa kwana daya mudai Allah dai yasa basai anyi mata operation ba. Suka ce ameen a yayinda likitar ta fito waje. Da sauri suka tareta Abdulrahman yace Dr ya matata take ki fadamun? Cikin sigar lalllashi tace kayi hakuri ta kusan haihuwa insha Allah, tana fadar haka ta wuce, Abdulrahman kofar ya nufa da niyar shiga yajita a rufe, kiran sunanta ya farayi yana kuka mai ban tausayi, Ameerah ma haka kuka take tana cewa Abdulraheem su bari ta ganta. Shima Abdulraheem dauriya ce kawai yayi dan bayason su taru su ringa mata kuka ne bayan kuma addu'ar su kawai take bukata a hanlin yanzu. Suna nan tsaye sai ga likitar ta dawo dawani paranti a hannunta, tana bude kofar da makulli ta shiga, duk suna tsaye suna kallon ikon Allah kuma suna jin kukan Amatu da nishinta wanda duk ya kara tayar musu da hankali. "After 8 hours" Duk hankalin kowa ya gama tashi dajin haryanzu Amatu bata haihu ba, hatta su mummy dasu aunty hajara dasu ammie suna wurin dan tunda su Abdul sukaga haihuwar batazo ba suka sanar dasu sukazo asibitin. Kowa hankalin shi a tashe yake. Addu'a kawai suke mata, gashi an hanasu ganinta. Suna nan jigum-jigum sai ga Dr Halima tazo wacce daga baya tazo itama tayi iya kokarin ta amma abun yaci tura, da sauri likitar ta fito tana cewa ina mijinta yake? Dama kamar jira yaje a kirashi da sauri ya mike haryana sarkewa wurin cewa gani! Matar ka nason ganinka tana fada ta koma ciki, ya shikuma yabi bayanta kafa na rawa harya isa wurin Amatu da fuskarta harta canza kala saboda galabaita. A wahalce take magana tana cewa mutuwa zanyi Abdul dan Allah ka yafe mun kacewa su mummy su yafe mun, bakinta ya rufe da hannun shi yace a'a bazaki mutu ba, my baby ki daure kinji, toh kawai tace da dafe mararta tana cewa kaji yana yawo amma yaki fitowa ko? Cikin damuwa ya ya dawo saitin kanta yafara mata addu'a yana tofawa yana cewa ke kidingayi, a yayinda likitoci keta kasanta suna tura cikin ta a hankali. Itama nishi take tana kara yunkurawa, Abdulrahman kuwa sai addu'a yake mata yana cewa ki daure kinji, haka sukayi tayi har kusan minti talatin sai kawai sukaji ta saki wata kara, take santaleliyar yarinya ta fado, ko mintu biyu ba'ayi ba wata ta sake fadowa, sedai fadowarta keda wuya numfashin Amatu ya dauke. "Da hanzari likitoci suka yo kanta wasu kuma suka kwashi yaran dan su gyara su, Abdulrahman hankali ya tashi ya bubbuga Amatu yake amma inaaa ko alamun tashi batayi ba, har likitoci sunyi wa yara wanka sunsa musu kayan dasu ammie suka kawo. Waje suka fito da yaran suka kaisu wani daki, aikuwa farinciki fal ransu Amatu ylta haifi yan biyu kowa sai murna yake, sunma manta da halin da Amatu ke ciki dan duk a tunanin su ana can ana kintsata ne shiyasa ba'a basu damar ganinta ba. "Shigowar Abdulrahman ya katse musu rahan da suke ciki, kowa kallonshi yake ya koma kamar wani mahaukaci hawayene ke bin kuncin sa. Da sauri mummy ta taso tana son lafiya ina Amatu take?? Kuka ya fashe dashi mai sauti yana cewa bazan iya rayuwa batare da ita dan Allah kuje kuce ta tashi karta tafi ta barni, gaban mummy ya iso yace mummy kice ta tashi........ Tashin hankali ba'a sa mashi rana, mummy tace meya samu Amatu? Tana ina? Mummy Amatu ta wuce kice ta dawo.... Hankalin kowa ya tashi a wurin Ameerah kuwa da gudu ta fita suma suka mara mata baya,,,,,A bakin kofa sukaci karo da likita tace Dan Allah kuyi hakuri ba kuka zakuyi ba addu'a zakuyi mata, ammm kuma tana ciki sedai bazaku iya tafiya da ita ba sai kun cika wani file saboda duk wanda ya rasu a wannan asibitin haka ake masa so plsss ku bamu ten minut........... Wata irin danka Ameerah takaiwa likitar tana cewa wallahi bata mutu ba ki fito mana da yar uwar mu,,,,,kuka ta fashe dashi tana dukan likitar su mummy suka kwace ta dakyar, Abdulrahman kuwa ya dade da suma, duk hankalinsu ya gama tashi. Kowa kuka yake wiwi, Abdulrahman kuwa anyi wani daki dashi, mummy kam hawayenta sun kafe se addu'a kawai take acikin zuciyarta.......... Share [3/31, 8:31 AM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮 (Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς) 💫🌞💫🌞💫🌞 RUDANI 💫🌞💫🌞💫🌞 Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу Ꮮasིhིmིiིnིzིyི ~Second to the last page~ Page 117-118 "Suna nan zaune jigum jigum sai ga wata likita ta fito da fara'ar ta tace ina tayaku murna patient dinku dogon suma tayi...... Ai da sauri suka shige daki, suka kuwa ga Amatu zaune a bakin gado, tana hawaye tana kiran ya Abdul, da gudu Ameerah ta fita ta shiga dakin ta aka kwantar da Abdulrahman tana haki tace ya Abdul Amatu bata rasu ba ka taso muje tana kiranka. Kamar a mafarki yakejin ana mashi magana sedai da sauri ya bude idonshi yace ina take? Tana labour room, aikuwa harma ya rigata fita daga dakin ya isa dakin da take. " Duk mutanen dake dakin harda su likitoci dasu ammie hankalinshi beko kai garesu ba, shidai burinshi kawai yayi ido biyu da babyn shi. Da gudu ya isa wurinta ya rungumeta kamar zai mayar da ita cikinsa duk ya kanainayeta da hannunwan shi, gashi jikinta har yanzu akwai inda ke mata ciwo amma haka ta daure ta irin rungumar da yayi mata harda sumbatar ta a goshi. "Ammie da duk kunya ta isheta tace kai Malam bakaga mutanen dake wurin nan bane? Sai a sannan ya juyo yaga kowa ya zuba mashi ido yana kallon shi, da sauri ya saketa ya koma gefe yana sunnar da kai kasa. Abdul kuwa yana daga gefe yana murmushi, a ranshi yace wannan dan uwan nawa ni control ji yadda ya dawo kamar wani zararre a cikin yini daya kawai 🤔 Barka su mummy suka shiga yiwa Amatu kafin suka fita gabadayan su dan likita zata dubata, bayan minti talatin lokacin har kusan karfe goma na dare suka shigo har an kintsa Amatu kuma an kawo mata babies d'inta masu dasu kusa da ita. Murmushi take ita daya har Ameerah suka shigo, aunty hajara sai washe baki take tanacewa wai tayi wa danta Mubarak kamu duk suka fashe da dariya. Haka sukayi ta hira harda su daddy da Abba sai kusan sha biyun dare suka tashi zasu wuce, Abdulrahman kuwa ko kunya babu ya daddage wai shi wallahi anan zai kwana haka kuwa suka kyaleshi ta kwana tare da matar shi da twins dinshi, sai sa mata albarka yake tana ta mata sannu dan yasan ba karamin azaba Tasha wurin haifo twins din ba. Tunda safe Ameerah ta tisa Abdul a gaba sai ya kawota ko breakfast batayi ba suka fito, lokacin da suka iso asibitin har drip dinda akasawa Amatu ya kare, a daki suka tarar dasu Abdul yana rungume da baby daya haka itama Amatu tana rike da daya. Bakin gado suke suna hira suna kallon twins dinsu, hotuna Abdul yashiga yi musu yana posting a media, nan da nan kuwa friends dinshi suka fara mashi congratulations wasu na zolayar shi suna cewa ya zama daddy yanzu. Suna cikin hakane sai ga su Ameerah sun shigo, gaisar da juna sukayi kafin suka samu wuri suka zauna Ameerah ta amshi babyn dake hannun Amatu tana cewa kai wallahi se yanzu na lura yarinyar nan da babanta take kama sosai. Amatu ta wani bata rai tace babu wani dani take kama, Abdulrahman yayi dariya hade da janyota jikinshi yana shafa bayanta yace ai na fiki kyau ne shiyasa sukayi kama dani, ya fada harda yar guntun dariyar sa. "Dukan takai mashi hade da matsawa daga kusa dashi tana bata rai, Abdulraheem yace auntyn mu babu wani kin fushi kyau kuma ma yaran dake suke kama bada shi ba. Murmushi tayi tace yauwa kanina daman nasan karya suke dani suke kama saboda jinina yafi nashi karfi, Abdulrahman ya waro ido, yace jita kamar wata likita wai jinina yafi karfi? Injiwa? Ammie dake shigowa ita da mummy dasu samha da hanan da Umar tace injini duk suka fashe da dariya. "Ciki suka ida shigowa kowa na rige-rigen daukar twins, hanan ta anshi wacce ke hannun Ameerah samha kuwa taje zata anshi na hannun Abdulrahman ya watso mata harara yace kee dakata karki jagwalgwala mun baby da kazamin hannun ki. Aikuwa ta fashe da kuka taje jikin mummy tana kuka, ammie kuwa ta anshe babyn ta mika mata tace rabu dashi inma kinga dama ki rama duk dukanki da hantarar da yake maki akan yarshi yaji ko akwai dadi. Duk dakin suka sa dariya banda shi daya sha toka yana wani ciccije labba, sukuwa ko ajikinsu sukaci gaba da hirar su, Ammie tabawa Amatu breakfast dinda sukazo dashi nan ta zauna tanaci tare da Ameerah dan yunwa takeji sosai. "Da misalin sha daya na rana aka sallamesu, Direct gidansu Amatu suka wuce dan sun kira mummy sunce basai tazo ba an sallame su, nan cikin gidan suka bane kolinsu harda su Abdul ana ta hira daga bisani su Abdul suka fita su mummy da Ammie suka wuce gida samha da hanan kuwa cewa sukayi basu tashi ba Ammie tace sai sun wuce su bari gibe su dawo, dan dole suka wuce. '""Ya rage daga Ameerah sai aunty hajara da mummy sai kuka makwafta masu zuwa barka, Ameerah sai dare Abdulraheem ta wuce da ita gida dakyar dan cewa tayi ba inda zata sai da mummy ta lallasheta kafin ta wuce, Amatu sai dariya take mata tana cewa kizo mun da kayan da muka siyo a cikin wardrope din dakina na sama Ameerah ta tsuke baki tace bazan dauko din ba. Abdulrahman kuwa shima haka ya wuce gida jiki a mace yana tunanin yadda zai kwana har arba'in batare da Amatu ba, tsaki yaja yaci gaba da tukin shi. Washe gari da safe Ameerah ta shirya ta dauki breakfast ta kaiwa Abdulrahman, a palour ta tarar dashi, bayan sun gaisa ta mika mashi ta kuma ce zata shiga dakin Amatu akwai kayan da tace akai mata, toh kawai yace ta haura sama, yadda tace haka tayi, wardrobe ta bude ta dauko mata kayakkin da suka siyo da nata da kuma na babies. Kodata fito bataga Abdulrahman ba kawai sai ta wuce taje ta samu Abdulraheem dake waje wurin mota yana jiranta, a boot suka sa kayan sannan ta zagaya ta gefen mai zaman banza ta shiga ya tayar da motar suka wuce. "Bayan sun isa har cikin gida Abdulraheem ya shiga ya kara gaida Amatu da mummy sannan ya wuce asibiti. Nan dakin Amatu Ameerah da jide kayan ta hau jera mata su cikin wardrobe itama Amatu hannu tasa suna jerawa, Ameerah na cewa ta zauna ta huta ai ba'a san me jegi da wahala ba ama ina sam Amatu taki yadda, haka suka ta jera kayan tare. "Wata takarda ce ta fado cikin kayan da Ameerah ke jerawa, da sauri tasa hannu ta dauka, Amatu tayi saurin fisgewa tana dariya tace waton zaki kallanmun sirri ko? Ameerah tace sirrin me kuma? Amatu tace ina ruwanki, marairaicewa Ameerah ta farayi tana yasata mda Allah akan ta bari ra gani sannan Amatu ta yadda tace wannan takaddar Abdulrahman ne ya aiko mun da ita. *FLASH BACK* Wata rana ina zaune a palour lokacin da nayi wa Abdul yaji sai megadin gidan aunty hajara ya kawo mun wannan taddar wai inji wani, nidai bansan ya akayi yasan bana gida una gidan ba, dana bude taddar shine naga abu kamar haka......... """"Assalamu Alaikum matata farincikina, da fatan kina cikin koshin lafiya? Dan Allah kiyi hakuri bisa ga laifin da muka aikata maki ko ince na aikata maki dan nasan nine silar komai. " Nasan haryanzu kina sona sedai laifi daya dana aikata maki wanda ya shafi harda soyayyar mu nakeson in goge shi yau kuma ina fatan zaki fahimce ni? Amatullahi wallahi nasoki kamar hauka kuma haryanzu ina kan sonki!!! Dalilin da yasa gangar jikina ta gujeki dan zuciyata a kullum cikin begenki take, shine "wata rana daddare ina kwance daddy ya aiko kirana yake fadamun ai ya Samar mun wata makaranta a Cyprus kuma Insha Allah gobe zamu wuce tare dashi saboda akwai abubuwan da yakeson yayi a can dan haka in shirya tunda safe flight dinmu zai tashi. "Daddy na yayi mun surprise ne saboda ya burgeni in kuma jidadi dan na dade ina burin inje Cyprus karatu shiyasa daddy yayi mun surprise kuma babu halin ince a daga tafiyar gashi dare yayi sosai dan kusan karfe goma ne na dare babu halin inzo gidanku a wannan lokacin, haka na shirya da safe muka wuce badan raina yaso ba kuma abun haushin shine wayata ba bansan inda na jefar da ita ba balle in kiraki in fada maki. Kuma tun da naje ban sake dawowa naija ba dan daddy cewa yayi bazan dawo ba sai na kammala karatuna, kullum fatana da Addu'a ta itace kada Allah yasa ki manta dani kiyi wani sabon saurayi. "Amatullahi wallahi kodana tafi can da sonki natafi kuma da sonki na dawo a ranar dana dawo nazo gidanku akace bakya nan kullum nazo haka ake cemun har wata rana nazo akace aurenki akeyi ba'a Bari ki fita ba, wannan ma shine dalilin kamuwata da ciwon zuciya. Plsss kiji tausayi na kiyi hakuri ki dawo kinji matata! Nabar ki lafiya, ki kula da babyn mu. Dan munfasawa Ameerah tayi tace lallai kuwa yayi kokarin rashin ki da yayi amma kuma dai toh🤔 haka dai Allah ya kaddara shiyasa hakan ta faru, amma yanzu komai ta wuce sedai labari. Amatu tace wallahi kuwa nan sukaci gaba da aikinsu suna hira har suka gama. "Aunty hajara ce ta shigo dakin da wasu ledoji a hannunta toilet ta shiga bada dadewa ba sai gata ta fito kallon Amatu tayi tace daughter tashi kiyi wanka kar ruwanki su huce ta fada tana zama kan gado, dan tsuke baki tayi ta cire kayanta ta shige toilet tana mita wai duk za'a kona mata jiki, Aunty hajara kuwa shuru ta mata, dan yau batason rigimar ta. Bayan kwana biyar............ Yau ake sunan Amatu ko'ina na gidan ya cika da mutane, su Ameerah sekai kawo ake da dan cikinta a gaba. Amatu tasha kyau kamar amarya haka ma babies ansa musu kaya iri daya masu bala'in kyau, yara sunci sunan......... Share [4/1, 10:10 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮 (Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς) 💫🌞💫🌞💫🌞 RUDANI 💫🌞💫🌞💫🌞 Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу Ꮮasིhིmིiིnིzིyི Godiya ta musamman ga ɗaukacin masoyana da kuma masoyan RUƊANI..... RUƊANI FANS GRP 1,2&3 RUƘAYYATU FANS GRP ZUCIYAR ƊAN ADAM FANS TAƘWACEN MIJI FANS SO KO WAHALA FANS JANAF NOVELS FANS ƘADDARA KO SANADI FANS MUNAT & KAOJE FANS KUN CUCENI FANS JALAL KO JAMAL FANS na gaisheku WANNAN SHAFIN NAKU NE......... Bilkeesu adam meerah(takwara) Hawwer a hisham Babyn md Teemah baiwar Allah Aysha Ummu zar'in Ummu arfat Aunty maryam Aunty maymuner Na'ima Swt janaaf Swt Raheenart Mugirat Musa (ƴar garinmu) Waƴanda ban ambaci sunanku ba kusani cewa kuna cikin raina, ni lashminzy ina ƙaunar fiye da yadda kuke zato. One love ❤ ~LAST PAGE~ Page 119-120 """Yara sunci sunan mummy (hajara) Ana kiranta da Amrah mummyn Amatu(ruƙayya) ana kiranta da Afrah, biki yayi biki anci ansha an zubar dana zubarwa haka zalika an saci na sata domin kuwa ranar duk wani ɓarawo yayi kuɗi a gidan dan an kashe kuɗi kamar ba gobe. Komai anyi shi a wadace duk wanda yazo bikin nan yasan anyi ɓarin kuɗi hatta da gidan talabijin saida aka nuna, kayan rabuwa kuwa kama daga su jakunkuna, atampa, plates, memo, bokatai kala da kala dasu dusbin da fans kai abubuwa dai gasunan barkatai duk an bugasu domin kuwa kowa ya kawo nashi gudun mawar. "Abdulrahman na hango can bakin gate ɗin gidansu Amatu yasha wata dakakkiyar shadda kamar ranar auren shi, fuskarshi ko ban faɗa ba ansan cike take da annuri,,,, tare yake da abokanshi ko wanne hannunshi riƙe yake da wata haɗaɗɗiyar jaka an manna hoton Amrah da Afrah a jiki, wasu sun bar nasu cikin mota wasu kuwa nasu na hannun su, da alama dai daga wurin wani taro suke (walimah). "A gaba yake sauran abokan suna baya, cikin abokan ne na hango Abdulrahman shima sanye cikin shadda irinta Abdulrahaman sedai kowa da kalar tasa. "Tafiya suke suna hira da wasannin su irin nasu na wayayyu kowa fuskar shi cike take da annuri, can palon baƙi Abdulrahman yakai su dake ansan da zuwan su kuma an shirya musu abubuwa da yawa shiyasa batare da ɓata lokaci ba suka shiga palon, anan suka baje kolinsu, kowa abincin son ranshi yakeci dan abincin da aka dafa sunkai kala goma, kowa sai lodawa yake ana hira ana santi. "Bayan sun gama ci ne Abdulraheem yasa Ameerah ta kira Amatu da babies ɗinta daman dalilin dayasa kenan sukazo duk da wasu sun zo barka amma da yawansu sun dawo saboda yaran akwai shiga rai gasu da kyau kamar ka sace ka gudu dasu. Ba'a ɗauki wani lokaci mai tsawo ba Amatu ta shigo ita da babies ɗinta Ameerah na riƙe da Amrah, Amatu kuma na riƙe da Afrah, har suka shigo palon idon Abdulrahman nakan Amatu dan jiyake wani irin kishinta na taso mashi dan yadda tayi shigarta riga da skirt ne sun ɗan kamata sai ta yafa gyale har kanta saboda tasan Abdulrahman da baƙin kishi yana ma iya disgataa gaban mutane. """Dan haka yayi mata lokacin bikin su fauziya da sukaje dinner, liƙi kawai ta tashi tayi shine wasu ƴammata da ƙannan su maza sukazo suna liƙi dan kawai by mistake namijin ya taɓeta shikenan fa Ya haukace musu seda Abdulraheem yayi ta lallaɓi kafin ya samu ya haƙura ya figi Amatu suka wuce bikin da bata ƙara zuwa ba kenan har aka ɗaura aure aka kai amare bata ƙara zuwa ba. "Kabeer ne ya ansa Afrah dake hannun Amatu, usman kuma ya ansa Amrah, nan suka gaggaisa kowa nata yaba yaran da kuma sa musu albarka, sosai Amatu da Abdulrahamn sunji daɗin addua'rsu, Haka suka ɗanyi hira kaɗan kafin su Amatu suka fita, sedai ƙafarta ƙafar na Abdulrahman dan tana fita ya take mata baya, adaidai corridor ɗin ƙofar ya tsayar da ya anshi Afrah dake hannunta, kallonshi ta tsaya tanayi dan ba ƙaramin kyau yayi mata ba, haka shima gani yake gabaɗaya in za'a tars matan duniyar nan ita kaɗaice zai iya kallo amatsayin macce me kyau. "Shafo fuskarta yayi ta firgigit ta kalleshi haɗr da sakar mata murmushi, shima murmushin ya sakar mata yace baby kinyi kyau sosai, anya bada ke zan wuce ba kuwa? Hararan wasa ta aika mashi gami da cewa uhmmm babu wani kaje ka sake ɗaura mun wahala nikam hakama ya isheni,,,,,Uhmmm kawai yace yana tunanin lokacin da zata haihu yasan ba ƙaramin wahala tasha ba aikuwa dole taji shakkun ƙara haihuwa nan kusa,,,,A fili yace kaji ragguwa, kallon irin dan bakai bane tayi mishi ta miƙa hannunta ta anshi Afrah su wuce dan Ameerah ta daɗe da wucewa. "Ba musu ya miƙa mata yace sai nazo anjima dan kusan kull sai ya zo wai dan ma Ammie na mishi faɗa akan ya rage zuwa tunda ba'a kanshi aka fara mata ba. "Kafin tace wani abu ya rungumeta da tare da Afrah ya sunbace a baki sannan yabar wurin, kamar wawiya haka ta tsaya tana kallonshi harya shige palon kafin ta tattaro sauran hankalinta ta wuce cikin gida da tunanin irim ƙaryar da zatayi wa aunty hajara dan ko nam da can ba'a son tana fita wannan ma dan ya zama dole ne. "Da shigarta ko aunty hajara ra tareta tace mekika tsaya yine naga Ameerah ta rigaki dawowa?Cikin inda inda tace toh daman wasu ne suka tsaya ganin baby,,,,,,badan aunty hajara ta yadda ba tace naji ta anshi Afrah suka shige ɗaki dan za'a sake musu wanka ne duk da cewar yamma yayi amam haka kullum ake musu wanka biyu harda Amatu. Da misalin ƙarfe takwas na dare lokacin kowa ya watse se wasu yan dangi da ba'a rasa ba, zaune Amatu take tana ba Afrah nono sai wani cije leɓo take danjin zafin yadda afrah ta kama nonon sai zuƙa take, tana gama ba Afrah, Amrah tasa kuka itama haka ta bata sai wani yatsine fuska take Ameerah kuwa sai dariya take tana cewa ashe shayarwa da wuya mudai Allah yayi mana da sauƙi, Cikin wasa Amatu tace ba ameen ba. Ameerah kuwa murmushu tayi tace daɗin abun dai kowa dai nason sauƙin😏 Amatu batace komai ba taci gaba da shayar da ƴan biyunta. Bayan wata bakwai Zaune take a palour tana wasa da Afrah fitinanniya dan Allah ya ɗauro mata rigima da koke-koke in dare yayi, dan ma yanzu tayi sauƙi amma fa bata jin magana, da an kwantar da ita zata nemi ta tashi ko wasa kake mata tayi ta maka dariya, in aka kunna tv haka zata ƙura mashi ido kamar wacce tasan ma'anar shi. Amrah kuwa tamkar mahaifinta take dan babu ruwanta ko irin kukan nan na yara batayi kai ko wasa kake mata bata fiye dariya ba, sumi-sumi takae kamar wata mara lafiya, sau dayawa mutane kance ko bata da lafiya ne basu san haka yanayinta yake ba. Ameerah ta haihu lafiya ƙalau dan bata daɗe tana naƙuda ba ta haihu, ta haifi ɗa namiji ansa mashi sunan abba waton ibrahim khalil suna kiranshi da khalil, fari ne tas tamkar mahaifin shi, shima anci ansha a bikin shi, kowa ya nuna farincikin shi. "Wani ɗan abun wasa ta riƙe tana mata wasa dashi, sai tayi kamar zata bata sai kuma ta ɗaga sama, ita kuwa afrah sai washe baki take tana dariya, Abdulrahman ne ya shigo palon cikin sanɗa, ta bayan Amatu yaje daidai ta ɗaga abun wasan sama ya anshe, aikuwa cikin tsoro ta juyo. "Tana ganinshi tayi murmushi tace shine zaka ban tsoro ko? Sorry maman ƴan biyu ya ɗafa ayayinda yake ɗaukar Afrah da tun ganin shi take mashi dariya. Zama yayi saman kujera yana mata wasa Amatu kuma ta shiga kitchen kawo mashi abinci dan daga masallaci yake kuma shi take jira ya dawo suci tare kamar yadda suka saba. Bayan shekara goma Su Amatu an ƙara girma an ƙara sanin abubuwa da dama game da zaman aure, yanzu haka ta gama degree ita da Ameerah suna aiki a wani sabon company da Daddyn Amatu ya buɗe na teaching techniques and computers, kampanine na ƙera computoci da kuma sarrafasu da koyar da yadda ake amfani dasu da sauran su, kampani ne babba, duk wani abu daya shafi computer anayi a wurin, kuma ko wani aiki da ɓangaren da ake yinshi. Kullum sai sun fita saturday and sunday ne kawai ba'a zuwa, amma duk aikin da suke zuwa bai hanasu kuƙa da ƴaƴansu da mijin su ba, suna matuƙar ƙoƙari wurin basu kulawa haka ma mazajen. ************* Wasu kyawawan ƴammata na gani guda uku da wasu maza guda biyu suna wasa a wani haɗaɗɗen garden, ƙaramin namijin mai suna Affan shine ya daki Waleedah akai saboda ta ɓata mashi motocin roban shi daya jera su yana turawa, kuka tasa ƙafin tayi daka tsalle ta cijeshi a hannun ta arce a guje. Kuka ya farayi ya bita a baya yana wallahi sai na rama har suka shigo palon Amatu, da sauri Amatu ta tare Affan dake shirin dukan Waleedah tace yi haƙuri affan kaji ƙyaleta, yana huci yace Allah mummy sai na rama jipa inda ta cije ni harya fashe. "Afrah tace aikuwa, ta arce sai wurin Ameerah taje ta faɗa mata, tare sukazo Tace ina waleedan take? Bana hanaki cizo ba? Allaha saina sassaɓa maki da shegen kanta kamar na ƙwallo. Waleedah dake bayan Amatu ta laɓe ta fashe da kuka dan ance mata me kan ƙwallo😁 yarinyar Ameerah kenan wacce aka haifeta bayan shekara biyu da haihuwar khalil. Sam bata jin magana ga baƙin tsokana da tsoro shiyasa tasu tazo ɗaya ita da Afrah dan itama haka take. "Affan kuma ɗan Amatu ne shi kuma an haifeshi bayan shekara uku da haihuwar su Amrah, shima babu ruwanshi kamar Amrah sedai akwai son wasa dan aduk al'amuranshi sai ya haɗa da wasa. Abunda ke haɗashi da daddyn shi kenan waton Abdulrahman. Suna cikin hakane Abdulrahman ya shigo wow wai kunga yadda ya dawo kuwa? Ya ƙara kyau da girma harda ɗan gemu ya tara, fuskarshi ta ƙara faɗi da kyau, yana cewa toh sun fara ko? Su kullum cikin rigima suke, Affan ne ya ƙarasa wurinshi yana nuna mashi wurin da waleedah ta cije shi dan har wurin yayi jini, Sorry yace mashi ya ɗauko tissue ya goge mashi. "Bayan ya goge mashi Ameerah taja hannunshi suka fice daga palon, su Afrah suka take mata baya, Amatu kuma jan hannun waleedah tayi suka zauna tana lallashinta haɗe dayi mata nasiha cikin hikima akan ta daina cizo babu kyau mutum zai shiga wuta. Tana cikin mata nasihar ne taji motsin su Amrah tana wasa, da gudu ta tashi ta fita, murmushi kawai Amatu tayi tana girgiza kai tace yarinta kenan, matsowa kusa da ita Abdulrahman yayi yace aikema haryanzu yarinta na cinki tunda haryanzu baki barmun rigima da shagwaɓa ba, ya faɗa yana mata dariya. Hararar sa tayi tana tashi tace kai kuma da jaraba ba itama ta faɗa tana dariya,,,,, batyi aune ba taji ya biyota yasa hannu zai riƙota harya kamo ɗankwalinta ta cire ta ruga da gudu, ya fara binta suna ta zagaye palour, dake ta ɗanyi gwaɓi gwaɓi kuma ba'a haɗa gudun namiji da mace aikuwa ya kamota ta faɗo ƙirjinshi, rungumeta yayi yana faɗi wana kama?? "Murguɗa mashi baki tayi tace kai ɗin, yace ni ɗin?Tasa hannunta tayi pointing ɗinshi tace Eh kai ɗin, aikuwa ya sungumeta sai ɗakin shi can tsakiyar gado ya kwantar da ita kafin ya koma ya rufe ƙofar. Kan gado yaje ya sameta batare da ɓata lokaci ba ya fara aika mata da wasu manyan saƙonnin da faɗan su ɓata lokaci ne, itma biye masa tayi suna ta jiyar junan su daɗin da basa taɓa gajiya dashi. Da gudu na fito daga ɗakin ganin abun nasu na shirin makantar dani nace ALHAMDULILLAH!!! ALLAH YA BAMU MAZAJE NAGARI DA MATAYE NAGARI MASU ƘAUNAR MU TSAKANI DA ALLAH ALLAH abun godiya ALLAH nagode maka daka nunamun naga farkon littafin nan lafiya kuma naga ƙarshen shi lafiya, kurakuren dake ciki Allah ka yafe mun Abun amfanuwa kuma Allah kasa Ya amfanar damu. Taku ce lashminzy