[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _.............DA RABO_ *01* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM *Dedicated to my Trio*♥ Cikeda risinawa matashi mai kimanin shekaru 30 a duniya ya d’ago yana duban Dattijon mutumin mai kimanin shekaru 58 zuwa da tara kana yace “But Daddy.....” Katsesa yayi da fad’in “No SAMEER I don’t want to hear anything, what’s gotten into you Son.... Haba Sameer ni nasan ba haka na tayar dakai ba... Abinda nakeso da kai ka tashi ka tafi gidan Uncle d’inka ka basa hak’uri sannan ka d’auki matarka ku tafi magana ya k’are....” Jinjina kai yayi kana yace “Ok Daddy I’ll do as you say....” Murmushi Dattijon yayi kana yace “That’s my boy Allah ya maka albarka....” “Ameen Daddy...” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa had’ida fidda wayar salulansa daga aljihu.... Satan kallon sashen da Mummynsa ke zaune yayi aiko banda uwar harara babu abinda take aika masa.... K’arasawa ya d’anyi had’ida risinawa kana yace “I’m sorry Mummy... I promise this will never happen again in shaa Allah.....” Jinjina kai tayi kana tace “I hope so, Ace aure ko wata biyar mai kyau bakuyi ba an soma samun sab’ani irin haka ai babu dad’i... Dama naji batu mai dad’i kaji koh...” A hankali ya jinjina kai kafin ya fice daga parlorn.... Motarsa ya nufa ba tareda ya kula da Malam Sallau dake gaidashi ba... Ya jima k’ofar gidansu Siyama yana tunanin ta yanda zai soma bada hak’uri don sam hakan ba d’abi’arsa bace idandai ba ma iyayensa bane, a hankali ya rintse idanunsa had’ida furta “Goodness! Where do I start....” K’aran da wayarsa tayi ne ya sanyasa zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa daga d’aya b’angaren Sultan yace “Doc we’ve an emergency here at the hospital, Sameer we need you right away....” Shafe goshinsa ya d’anyi kana yace “Is my presence really necessary, just do what you can, I’m dealing with another problem here...Please...” ya k’arashe yana lumshe dogayen idanunsa masu yalwan suma.... Fuzar da iska Sultan yayi kana yace “Sameer it’s a boy.... He suffered a multiple deep burns... I’m afraid he’s dying...” Ta cikin wayar yake jiyo sautin kukan yaron wanda k’unan wuta ya masa babu dad’i, cikin sauri Sameer ya juya kan motarsa yana fad’in “I’ll be on my way....” Cikin sauri ya karya kan motar had’ida ficewa daga gidan mai gadi na faman d’aga masa hannu alamun a sauk’a lafiya.... **** *Kano* Cikin sanyin jiki suka shigo parlorn ko wacce tayi jigum jigum, budurwa mai kimanin shekaru 23 a duniya ne ta soma yab’e baki tace “Wllhi Allah Abbah shi yake biye Mamani take abinda taga dama, haka kurum mata ta tayar da bori wai zata tafi tabi MA’ARUF ni so nake wata rana a barta ta gwada fita nemansa ace yau shekaru 26 babu mutum babu labarinsa toh ta ina zaka soma nemansa, sai anyi magana ace tsufa ke d’awainiya da ita, mtsww...” Ta k’arashe tana jan tsaki.... D’ayar mai kimanin shekaru 19 tace “Wllhi Adda Nabila ni bana ganin laifin Baffah Wali idan ya fice mata a giya, kiga dai duk jikokin gidan nan rankatataf d’inmu ban cire kowa ba harda ke mai sunanta bata damu da kowa ba kullum damuwarta Ma’aruf yaron da tun yana shekara 4 ya b’ace sai anyi magana itada Mamy suce INDA RAI DA RABO, Allah na tuba da ace yana raye tsawon shekarun nan ai da ya bayyana mana....” K’aramar cikinsu mai kimanin shekaru 16 tace “Ahtoh sai anyi magana tace Babban Jika... Mu da yake Yayanmu uwa d’aya uba d’aya ma bamu kaita damuwa b.....” Had’iye kalaman nata tayi cikeda k’unk’uni tana duban wacce ke faman narka mata mugun kallo da alama bata jima da shigowa parlorn ba “Aunty Zulfah ina yini....” Gaba d’aya sauran biyun suka juyo suna duban sashen da k’anwarsu ke gaisuwa.... Ganin yanayin Addar tasu wacce ke sanye cikin kayan Bautar K’asa ya sanyasu shan jinin jikkunansu.... Ba tareda ta amsa gaisuwar tasu ba fuska a tsume tace “Mamy fah...?” Nabila mai bi mata a haife ne tace “Suna can sashen Mamani suna bitan karatunsu na aikin lallashi...” Girgiza kai kurum Zulfah tayi kana ta nufi k’ofa zata fice Mas’udah mai bin Nabila a haife tayi saurin katseta da fad’in “Allah Aunty Zulfah Mamani abinda take yayi yawa naga dai idan da akwai wanda b’acewar Yaya Ma’aruf zai damesa bayan Mamy da Abbah toh ya kamata ace sai kece tinda ranar da aka haifeki ranar Yaya ya b’ata....” Nabila ta k’arada “Shiyasa Mamani tafi tsanar Addah sama da kowa a jikokinta a nata tunanin sanadiyar haihuwar Addah Yaya ya b’ata...” “Ya isheku haka...!” Zulfa’u ta katsesu kafin taci gaba da fad’in “Ku bazakuyi hankali ba, ana cewa yaran Abbah sunfi kaf yaran gidan nan tarbiya amma kuna nema ku shafawa iyayenku bak’in fenti... Sai mai idan Mamani ta nuna damuwarta kan missing grandchild d’inta, badai jikanta bane toh ina ruwanku, idanku baku damu dashi ba sabida baku sanshi ba sai ku k’yaleta ita ta nuna damuwarta, wllhi kunji na rantse kar na sake zuwa gidan nan naji kuna k’anan maganganu kan wannan al’amari kunajina koh...” Ciki ciki suka amsa kafin Marliya k’aramar cikinsu ta k’arada “Aunty Zulfah yau ina kika baro Kausar naga baki kawota nan gida ba yau....” Harara kurum Zulfah ta watsa mata kafin ta fice ta nufi sashen Mamani.... **** *Kaduna* Fitowarsa kenan daga surgery wayarsa dake bisa teburinsa ta d’au ruri.... Dafe kansa yayi ganin mai kiran ba kowa bace illa Mummynsa sannan ta kirasa yafi sau a k’irga, shaf ya mance bai kashe wayar salulansa ba sanda zai shiga aikin domin kuwa akasarin lokuta idan zai shiga aiki kashe wayarsa yake donma kar a nemesa.... A hankali ya d’aga wayar had’ida zama cikin kujeransa.... Kafin ya sami zarafin magana Mummy ta soma balbalesa.... “Sameer ya maka kyau, nace ya maka kyau... Da ka fice zaka gidan Hajiya Faridan gidan uwar wa ka tafi....? Shine sabida tsabagen wulak’anci zaka barsu suna jiranka, ko kasan cewa harta Alhaji Madi bai fice ba ya tsaya jiran zuwanka amma ka kama ka watsa mana k’asa a idanu.... Ya maka kyau Sameer nasan haka zakayi wllhi da ban bari an baka auren Siyama ba....” Tinda ta soma magana bai katseta ba har saida takai aya, a hankali ya soma fad’in “Mummy calm down please, this isn’t good for your blood pressure.....” A hasale ta kuma cewa “Don’t ask me to calm down, jininan ma ya hau mana duk ba kaine sila ba....” A hankali ya shafi goshinsa can k’asan mak’oshinsa ya furta “Goodness..!” A fili kuwa cewa yayi “But Mummy cikinku babu wanda ya damu yaji daga gareni, babu wanda ya damu if I’m also suffering, Mummy this isn’t easy for me either.... Kin sani Mummy kinsan ina son Siyama kuma auren soyayya mukayi.... Kwana biyun nan bansan meke damunta ba... Amma koma meye na miki alk’awari I’ll save our marriage cos I still love my wife, l love her so much...” Ya k’arashe cikin sanyin murya.... Jinjina kai Mummy tayi cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa D’an Albarka haka nakeson ji maza ka wuce gidan Uncle Madi d’in daga asibitin zanyi waya wa Hajiya Faridan na sanar da ita aiki ne ya rik’eka a asibiti amma gaka nan zuwa....” Bai iya amsa Mummy ba har suka ida wayar, mik’ewa yayi had’ida d’aukar wayarsa da key ya nufi duba patient d’insa kafin ya fice... Sam baisan Siyama nada kishi haka ba, ya kamata ta fahimci yanayin aikinsa da kuma za’a iya kiransa emergency ko wani lokaci..... A farfajiyan gidan ya iske Alhaji Madi zaune saman kujeru na shak’awata jarida rik’e a hannunsa, don haka kai tsaye cikeda risinawa ya nufi sirkin nasa kuma amini ga Daddynsa... Daga can d’an gefe ya durk’usa kana ya soma gaida sirkin nasa.... Fuska babu walwala ba kaman yanda ya saba masa d’inba ya amsa... Sameer ya d’anyi gyaran murya kana yace “Uncle dan Allah ayi hak’uri bana gida Siyama ta fice kuma koda na kira layinta bata d’aga ba amma In sha Allah hakan bazai k’ara faruwa ba...” Cikeda k’osawa Alhaji Madi ya amsa da “Allah sa kada hakan ya kuma faruwa, a dinga kulawa Sameer, kasan cewa muna tsananin k’aunar Siyama kuma bamu k’aunar ganin kukanta, sanin kanka ne Sameer my children are my life, I can do anything for them ko menene, Siyama da Khalid sune farin cikin rayuwata ka fahimta...” A hankali Sameer ya jinjina kai kana yace “Ayi hak’uri Uncle za’a kiyaye In sha Allah....” Alhaji Maina ya kuma jinjina kai had’i da bud’e shafi na gaba a jaridar tasa kana yace “Ka k’arasa ciki ka samu matar taka....” Cikeda risinawa ya kuma mik’ewa had’ida godiyawa Alhaji Maina kafin ya nufi sashen Ammi mahaifiyar Siyama.... “You know what sis... I think you’re been too impulsive....” Matashin Saurayi mai kimanin shekaru 26 ya fad’i yana mai duban Addar tasa wacce ratansu shekara guda ne tak.... Pillow dake gefenta ta d’auka ta jefi dashi kana tace “You stay out of this Khalid... Ni ba sa’arka bace...” Fitoda manyan idanunsa masu rikita ‘yanmata yayi kana yace “Oh really Sis.... Alright, fine, ni shawari kawai nake badawa, stop being so paranoid, your husband would never cheat on you, I know Sameer so well, kuma da kika aureshi kin mance wanene shi, kin mance wa kike aure...? Well, Incase you forgotten Sister, he’s a Doctor, a surgeon for that matter... Emergency zai iya faruwa ko wane lokaci kuma za’a kirashi, so sister dear you’ve to get this through your head.... Ok...” Ya k’arashe yana janyo bakin gelan kitson kalaba manya dake zube kanta... Duka ta kai masa yayi saurin kaucewa a daidai sanda sukaji sallaman Sameer.... Daskarewa Siyama tayi had’ida lumshe idanu sakamakon jiyo k’amshin mijinta da tayi wanda tayi kewarsa a kwana guda tak... K’arasawa Khalid yayi yana fad’in “Yauwa gwara da Allah ya kawoka, you better take your wife with you before she breaks all my bones da wannan hannun nata....” Murmushi kurum Sameer yayi kafin ya mik’awa Khalid hannu sukai masabaha... Bayan sun gaisa Khalid ficewa yayi ya bar ma’auratan guda biyu... Kaman munafuki ya k’arasa cikin parlorn yana mai sand’a idanunsa kan matarsa tsan tsan k’aunarta na d’awainiya dashi.... Saida ya k’araso har gabanta kafin ya zauna shima dirshan saman babban carpet na alfarma da aka k’awata parlorn dashi.. Sameer baiyi wani aune ba ya rungume matarsa da hawaye ke gangaro mata, murya can k’asa cikin sigan lallashi yake furta “Hey it’s ok Partner I’m here now...” Aiko kaman jira take tayi bursting cikin kuka... Lallashinta yaci gaba da yi yana bata hak’uri.... “Honey I’m sorry... I didn’t mean to hurt you, but Partner ya kamata ki fahimci yanayin aikina, ko wani lokaci za’a iya nemana cikin gaggawa, Honey I thought you were the one encouraging me before, have you forgotten already, kin mance ke kike cewa taimakon mutane nake naci gaba da aikina a lokacin da iyayenmu suka buk’aci nayi aiki a company d’insu.... Partner I thought kin shirya ma faruwan irin hakan... Babu dare d’aya da zan fice surgery na barki ba tareda naji pain d’in barinki da nayi ba.... I love you so much Siyaam, I love you with every fiber of my being....” Ya k’arashe fararen dogayen idanunsa cikin nata hannayensu rik’e cikin na juna... A hankali tasa hannu ta goge hawayenta kafin tace “But Partner we just got married amma ace bakada time d’ina, yaya kake tunani zanji... Shin ka mance a daren aurenmu saida aka kiraka on emergency, watanmu biyar da aure amma ban tab’a samunka complete na sati guda ba, Partner I love you and I hate sharing you with anything or anyone else....” Dunk’ule hannunsu ya kumayi waje guda kana ya simbaci hannayenta idanunsa naga kyakkyawan fuskarta yake fad’in “I love you more Honey, and this time around I’ll make it up to you, zan d’auki hutun aiki.... Let’s go for a vocation, anywhere... Wherever you like, maybe sai muyi honeymoon d’in da bamuyi ba...” “Are you serious Partner...?” Jinjina mata kai yayi murmushi bai gushe saman kyalkyawan fuskarsa ba ... Rungumesa tayi tana fad’in “I love you so much Partner...” Khalid da Ammi ce suka sauk’o parlorn tare yanda suka tadda ma’auratan a haka... Tuni annuri ya cika fuskar Hajiya Farida yayinda Khalid dake faman danna wayarsa ya maida dubansa ga Siyama yana mai furta “Wow look who’s smiling now... Ammi I think the couple have already resolved their problems....” Banda harara babu abinda Siyama ke aika masa, cikin turo baki take furta “Ammi ki shiga tsakanina da yaron nan ni ba sa’arsa bace.... Besides no one ask you to interfere....” Ta k’arashe tana kuma watsa ma Khalid mugun kallo... “If you really think so, then you should’ve resolved this at your house ba sai kinzo nan gidan kina bud’e mana sirrin aurenki ba big sis....” “How dare you..!!” Ta fad’i sanda ta nufesa a guje... Gwalo shima ya mata kafin ya fice daga parlorn a guje yana fad’in “Catch me if you can.....” Ammi dake faman rabasu dole ta k’yalesu had’ida maidoda hankalinta ga Sirkinta dake durk’ushe wajen..... *** *Kano* *SameenaAleeyou📚* [25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _..............DA RABO_ *02* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *Dedicated to my Trio♥* Cikin sautin kuka dattijuwar matar mai kimanin shekaru 74 a duniya taci gaba da fad’in “Duk kece sila Halima, kece sila.... Sakaci da gangancinki yasa kika d’auki yaro k’arami mai shekaru 3 rak a duniya kika tafi dashi kasuwa bayan kinsan kina d’aukeda juna biyu kuma haihuwa na iya samunki ko wane lokaci.... Dama so kike ki b’atar min da jika kuma burinki ya cika kin salwantar da Ma’aruf bazan kuma ganinshi ba ni Hanne....!” Ta k’arashe tana mai ci gaba da kuka wiwiwi had’ida warware bakin zani tana rufe fuskarta.... Lami abokiyar zaman Mamy ce ta k’arasa ta kamo Mamani had’ida zaunarta saman sofa tana aikin ci gaba da lallashi, Karima da Dilje kuwa matan Baffah Wali da Matar Baffah Sirajo gaba d’aya yab’e baki sukayi had’ida ficewa sim sim don sun gama kallon show dama abinda yakaisu kenan yayinda Zulfa’u ta k’arasa ta rungume mahaifiyarta dake tsaye kaman ruwa ya shanye hawaye na kwaranya mata... Aiko kaman ance Mamani ta d’ago sunayin idanu hud’u da Zulfah ta mik’e tana ci gaba da tururi take nuna Zulfah da d’an yatsa tana fad’in “Me wannan annobar take a nan... Fice mun daga d’aki tun kafin kisa wani iftila’in ya kuma auka min, wannan yarinya haihuwarki musiba ne... Da ace ba’a haifeki ba jikana Ma’aruf da yana nan ina taredashi... Fita annoba mai farar k’afa shiyasa mijinki ma ya kasa juran zama dake aure kullum na tangal tangal, haka kurum an cuci jikana an lanjama mashi annoba da sunan mata....” Ba Zulfah kawai ba harta Mamy saida taji kalaman Mamani har cikin k’ahon zuciyarta, duk hak’uri irin na Mamy batasan sanda ta bud’i baki ta soma fad’in “A gaskiya Mamani kar ki sake jifan d’iyata da munan kalamai irin haka, Zulfa’u mutum ce kuma d’iyace kaman ko wata d’iya cikin gidan nan, sannan ko kad’an babu laifinta cikin abinda ya faru hasalima abun a tausaya ma rayuwarta ne tinda duk randa akace shekarar haihuwarta ta zagayo sai ta tuna ranace data kasance bak’in rana ma wannan zuri’a, idan bazaki lissafa Zulfa’u cikin jikokinki ba inaga bai kamata ki cireta daga cikin ahalin gidan nan ba.... Kiyi hak’uri idan kalamaina ya maki zafi......” Banda sallallami da tafe hannaye Mamani bata komai fad’i take “Aaa Halima kin rik’a kawai ki sha d’amara ki dokeni sai nasan kin cika matar Alk’ali....” “Mamani ni ba nufina kenan ba, Zulfa’u nake dubawa....” Ai bata kai aya ba Mamani ta fashe da kuka sosai tana fad’in Lami tayi maza ta kira mata Alk’ali a wayar Salula..... Zulfa’u kuwa rik’o mahaifiyarta tayi suka fice daga sashen... Zulfa’u ta dubi mahaifiyarta dake faman zuban hawaye a karo na biyu, kusanta sosai ta matsa kana ta kamo hannayenta “Mamy dan Allah ki daina kukan nan haka, na sani kina hak’uri da Mamani amma kici gaba don na tabbata akwai ranarda hak’urinki zai zame miki alkhairi don shi bai tab’a zama sharri ba....” Ta k’arashe cikeda kwantar da hankaliwa mahaifiyar tata.... Sauk’e ajiyan zuciya Mamy tayi kana tace “Zulfah shin sunsan ciwon da nake d’auke dashi cikin zuciyata samada shekru ashirin da shida, Ma’aruf d’ana ne, ni na d’auki abuna tsawon watanni tara a cikina sannan na haifeshi na kuma raineshi.....” Kukanta ya tsananta sanda taci gaba da fad’in “Shin bama wannan ba, meye naki a ciki da za’a tsangwameki a kafa maki k’ahon zuk’a, baga uwar mijinki ba baga Kakarki ba.... Zulfa’u ki yafeni dan Allah duk ni na jefaki cikin wannan rayuwa na k’unci da kika tsinci kanki ciki....” Cikin sauri Zulfah ta rungume mahaifiyarta tana mai k’ok’arin maida hawayenta take fad’in “Mamy ki daina fad’in haka dan Allah, haka fah Allah ya k’addara kuma kada ki mance bawa bai isa yayi ma kansa abinda Allah bai masa ba, Mamy idan kina fad’in haka ni kuma yaya zanji...? Dan Allah ki dinga kwantar da hankalinki mu ci gaba da Addu’a INDA RAI DA RABON Yaya ya bayyana zai bayyana kinji koh Mamy.....” D’agowa tayi tana kallon d’iyar tata wacce tun tasowarta ta zame mata garkuwa abin dogaro hak’ik’a duk wannan k’unci da take fuskanta tunda Zulfah ta mallaki hankalinta ta zame mata majingina abokiyar shawari, fatanta Allah ya yayewa Zulfa’u duk wasu damuwan da take ciki kama daga danginta zuwa mijinta, hak’ik’a Zulfa’u yarinyace mai tsananin hak’uri da jin k’ai, A hankali Mamy ta furta “Ubangiji ya miki Albarka Zulfa’u yasa Khausar ya kasance mai jin k’anki kaman yanda kikejin k’aina....” A hankali Zulfah ta amsa da “Ameen Mamy...” cikin zuciyarta kuwa ma iya cewa zuban hawaye yake don har wannan lokaci kalaman Mamani basu daina yawo a kwanyarta ba... Suna a haka sukaji sallaman Aunty Lami..... Fuska cikeda damuwa Aunty Lami ta zauna daga gefen abokiyar zamanta Mamy tana dnnarta da bata hak’uri gameda abinda Mamani ke mata cikin gidan... Su Nabila dake zaune parlor suna ganin Aunty Lami ta shigo suka kasa kunne donsu sam sunk’i jinin Aunty Lami, ansha basu labarin irin zaman rashin jituwa da sukayi da Mamy a baya amma yanzu wani jan Mamy a jiki take saikace ba kishiyoyi ba, harta yaran Mamy jansu take a jiki Nabila uwar ‘yan bala’i ita ke tinzira sauran k’anne nata suk’i sakin jiki da Aunty, Mamy kuwa sosai take masu fad’a tace su daina d’aukan maganganun su Aunty Dilje abinda ya riga ya wuce ya wuce, Allah yana shirya bayinsa a duk sanda yaso, Zulfa’u ce kurum takan saki jiki da Aunty Lami amma su Nabila Mas’udah da Marliya kam inaa sai Mamy tayi da gaske ma sukan shiga Sashen Aunty Lami, haka Mamy zatayita masu fad’a da nasiha tana nuna masu ko don rashin haihuwa da Allah bai baiwa Aunty Lami ba su dinga zuwa wajenta suna d’ebe mata kewa sabida sud’in sune ‘ya’yanta tinda sune ‘ya’yan mijinta..... Daga gida kai tsaye gidan Baffah Ado dake bayansu kad’an ta biya d’aukan Khausar, Hajiya na hankince a tsakar gida ita dasu Naja’atu k’annen Hafiz mijin Zulfah, sallamanta ne ya katse masu hiran tasu, daga can bakin tabarman ta d’an durk’usa tana gaida Hajiya, kaman koda yaushe ciki ciki ta amsa mata, Naja’atu da Sahariyya kuwa kallon arziki bata ishesu ba, sanin koda zata kwana a wajen bata gaishesu ba sud’in bazasu gaisheta ba, cikin sanyin muryarta tace “ Naja’atu ina yininku...?” Da k’yar Najah ta amsa Sahariyya kanma earpiece d’inta ta saka taci gaba da bin wak’ar dake faman tashi cikin wayar.... Zulfah bata kuma bi takansu ba ta dubi Hajiya tace “Hajiya dama nazo d’aukan Khausar ne....” Wani uban kallon wulak’anci ta watsa mata kana tace “Lallai Zulfa’u kin rik’a.... Kin wani kwaso k’afa wani wai kinzo d’aukan Khausar, naga idan kin kaita ma Halima sai lokacin da sukaga dama su maidata, auho wato ga mayu zamusha jininta, toh bazaki tafi da ita ba, idan kin mance na tuna miki nan gidan Uban Khausar ne kuma muke da iko da gadara da ita ba Halima da danginta ba, ki tashi ki ficemin Khausar bata nan sun fita dasu Ummi.....” Tinda ta soma magana kan Zulfah ke k’asa, cikin kwantar da murya tace “Hajiya kiyi hak’uri Babanta ne yace idan zan koma gida na taho da ita....” “Toh nace bazaki tafi da ita ba Zulfa’u, harni zakiyiwa gada kan d’iyar d’anah, aikin banza aikin wofi ke wato ga ‘yar boko mai bautan k’asa koh... Shiyasa na k’yamaci aurenki da d’anah wayasani gantalin mi kike tafiya da sunan bautan k’asa, wllhi wllhi Zulfa’u kinji na rantse idan ina raye bazan tab’a barinki kiyi tarbiyan Khausar ba, kuma koba dad’e koba jimawa auren da Ubanninku suka k’ulla tsakaninki da d’anah sai an warware... Annoba dangin tsiya.....Tashi ki fice mun....” Ta k’arashe tana mai janye b’angaren tabarma da Zulfah ke zaune bisa wanda saida ta dungura k’asa, su Naja’atu abin nema ya samu suka kuwa kwashe da shewa.... Hawayen da Zulfah ke rik’ewa suka shiga gangaro mata, a hankali ta mik’e ta fice daga gidan farin hijabinta duk ya b’aci da hawaye..... *SameenaAleeyou📚* [25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _...............DA RABO_ *03* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *Dedicated to my Trio♥* A hankali ta zame hannayenta dake cikin ruwan wanke wanke kana ta saci kallon gefen da Hajiya ke zaune hankalinta yayi nisa wajen tsinewa Zulfah da zuri’arta itada yaranta su Sahariyya.... A can bakin layi ta hangeta tana neman a daidaita, cikin sauri ta k’arasa idanunta na zuban hawaye sabida tsananin tausayin Aunty Zulfah, batasan sanda ta rungumeta sabon kuka na zuwa mata ba, mamaki ya ishi Zulfah jin yanda ta rik’eta tana kuka wanda ko ba’a fad’a maka ba itama nata tarin k’uncin take fitarwa.... K’ok’arin daidaita kanta Zulfah tayi don idan k’arami nayi kai a matsayinka na babba sai kayi k’ok’arin samun k’warin gwiwa... Rik’eta tayi kana tace “RAIHANAH ki daina irin wannan kukan kanki zaiyi ciwo.... Mai suka miki yau kuma...?” Budurwa mai kimanin shekaru 17 da ta kira da Raihanah share hawayenta ta shigayi kana tace “Aunty Zulfah abinda suka maki naji zafi, kiyi hak’uri dan Allah, wllhi banji dad’i ba gashi nima sun hanani gaisheki wai ni munafuka ce, kiyi hak’uri Dan Allah...” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Murmushi Zulfah tayi kana ta shiga share hawayen dake kwaranya idanun Raihana kana tace “Raihanah ki daina saka damuwa ma ranki kinji koh, nidake irin tamu k’addarar kenan da Allah yaso jarabtanmu da ita, Allah ya bamu ikon ci... INDA RAI wataran duk wad’annan abubuwan zasu gushe mana su zamto labari kinji koh, kar ki mance duk tsanani yana tareda sauk’i kinji koh... Maza koma gida kafin Hajiya ta fahimci kin fito waje....” Cikin sauri Raihanah ta jinjina kanta kana sukayi sallama da ‘yar uwarta Zulfah ta koma cikin gida a sace taci gaba da aikinta... Raihanah marainiyace wacce tun tasowarta take shan azaba da uk’uba wajen kishiyar mahaifiyarta wato Hajiya Asabe, duk wani aikatau na cikin gida Raihanah ta iyashi tun kafin takai yanda take a yanzu, sam Hajiya Asabe bata d’aga mata k’afa dukda cewa mahaifinsu nada rufin asiri dai dai gwargwado yanda zai d’auka masu ma’aikata na cikin gida son ransu, da k’arfin gaske Hajiya kan koresu musamman yanzu da Raihanah ta kuma zama ‘yan mata, ko wadataccen lokacin karatu bata samu kaman yanda sauran ‘yan uwanta ke samu, idan ta dawo daga boko aiki na jiranta haka idan ta dawo daga islamiyya aiki na jiranta, badon mahaifinta na raye ba tabbas da ko makarntar Hajiya bazata bari tayi ba. Duk matan da Baffah Ado kan aura basa jimawa a gidan Hajiya kanyi sanadin tafiyarsu, mahaifiyar Raihanah ce ma ta d’anyi k’argo a gidan ba’a koreta ba dashike Allah yasa akwai rabon Raihanah a tsakani saidai haihuwarta da kad’an mahaifiyarta tace ga garinku, da yawan mutane sunfi danganta mutuwar mahaifiyar Raihanah da saka hannun Hajiya Asabe domin kuwa k’iri k’iri Hajiya ke nuna nata nata ne na wani kuwa ba nata bane haka nan mutanen unguwa ke mata lak’abi da Ramin Kura ‘ya’yanta kawai take so, gaba d’aya gidan tarbiya bai wadacesu ba duk goyon Hajiya garesu, Raiha ita ta fita zakka don harta mijin Zulfah ma shaye shaye yake wai anyi masa auren ne ko zai daina ga hangen ‘yanmata duk budurwar da ya k’yalla idanu kanta sai yace yana so, da anyi magana Hajiya tace sharri akewa d’anta anga shine babban jika na miji a gidan. Mahaifiyar Zulfah da danginta sam basuso auren Zulfah da Hafiz ba amma babu yanda suka iya tuni Baffah Alk’ali mahaifinta ya bada aurentawa Hafiz d’an d’anuwansa, koda mahaifin Zulfah yazo mata da batun batayi musu ba sannan take ta amincewa mahaifinta dukda cewa ga irin halin da Hafiz ke dashi uwa uba ga yarinta da yake fama dashi a lokacin da sukayi auren don dudu bai wuce ratan shekaru uku zuwa hud’u ne tsakaninsu ba., Haka nan Zulfah tayita fama da rashin hankalin Hafiz da sunan biyayyawa mahaifi, tabbas ta sakama zuciyarta Allah bazai tozartata ba tinda yaga niyyanta ta kumayi alk’awarin taka muhimmiyar rawa wajen saita rayuwar Hafiz ya inganta don shine abokin rayuwarta a halin yanzu uwa uba sun soma aje zuri’a..... Tana tsaye bakin kwalta tana neman abin hawa idanunta sunyi luhu luhu, kalaman Mamani dana Hajiya basu daina zarya a zuciyarta da kwanyarta ba, wad’annan mata guda biyu su sukayiwa rayuwarta karar tsaye mahaifiyar mahaifinta da kuma mahaifiyar mijinta, tabbas ta had’u da k’alubale babba a rayuwarta.... Sam bataji k’aran horn d’in mota daketa faman tashi a bayanta ba, tamkar wacce aka zabura haka ta dawo daga duniyar tunani tana mai k’ok’arin juyawa taga mai wannan horn d’in yawa zai d’agata... Lokaci guda ta saki murmushi kana ta k’arasa ta bud’e marfin motar b’angaren mai zaman banza.... “Aunty B ina yini...? Allah sa dai gida kika nufa ki ragen hanya....” Duk maganganun da take bata bari sun had’a idanu da matar data kira da Aunty B ba, sai faman sunkuyar da kai take bataso Aunty B taga idanunta da suka kumbura ta fahimci kuka tayi.... “Zulfah....!” Aunty B ta ambaci sunanta cikeda kulawa kana tace “D’ago ki kalleni...” Kasa d’agowa tayi saima k’ok’arin dad’a kauda fuskar da tayi... Aunty B bata kuma tsayawa bin takanta ba ta shiga janyo fuskar nata tana ganin yanda idanunta sukayi jazir sukayi luhu luhu abinka da farar mace... Baki sake Aunty B tace “Gidan Hajiya Asabe kika fito koh, ta maki rashin mutuncin data saba koh...?” Aunty B ta k’arashe tana faman huci... K’ok’arin girgiza kai tayi had’ida k’ak’aro murmushi kana tace “A’a Aunty, sauri nake zan k’arasa gida na samu na d’aura dinner....” Aunty B ta tsareta da idanun tausayin d’iyar ‘yar uwar nata na kuma cika zuciyarta lokaci guda tanaji ta shiga gidan Alhaji Ado tayiwa Asabe d’add’aya don gwara su sani Zulfah nada dangin mahaifiya masu k’aunarta.... Lokaci guda Aunty B ta kashe motar kana ta fice tana mai furta “Jirani ina zuwa.....” Ganin yanayin da Aunty B ta fice a motar gashi ta nufi kwanar gidan Baffah Ado yasa gaban Zulfah yankewa ya fad’i, a d’ari ta sauk’a ta takewa Aunty B baya tana rok’onta tayi hak’uri tazo su tafi, ai idan gyalen Aunty B ya amsa itama zata amsa sai faman watsa sauri take yawa wacce ake tinzirata.... Hajiya dasu Sahariyya sun saka Raihanah a gaba suna tambayarta gidan uwar wa ta fita gulma, Hajiya ta dubi Naja’atu dake tsaye bakin famfo ta rik’e kunkumi tana jira mahaifiyarsu ta basu izini su lakkad’i Raihanah kana tace “Najah jeki d’auko min dorinar nan don ubanta tinda bazata fad’a ba....” Cikin muryar kuka Raihanah ke fad’in “Hajiya wllhi Allah babu yanda naje dan Allah kiyi hak’uri....” “Bazanyi ba munafuka, badai kin rainani bane har zan sakaki aiki ki tsallake ki fice, yi sauri Najah.....” Ta k’arashe tana janyo wuyar Raihanah a dai dai sanda Aunty B ta banko k’ofar tsakar gidan ta shigo.... Jifa da Raihanah Hajiya tayi kana ta maido da dubanta ga Aunty... Huci kurum Aunty B keyi kana tace “Hajiya Asabe kiji tsoron Allah ki tuna abinda kayiwa d’an wani za’ayiwa naka, kuma ‘ya’ya mata gareki gidan aure zasu tafi kuma bakisan wasu irin sirkai zasuyi arba dasu a gidan aurensu ba, bama wannan ba gameda Zulfa’u ki sani Zulfah ‘yar dangice bazamu zuba ido kicigaba da muzantata kina wulak’antata ba, aike abin ki gode mata ne don idan ba itaba babu mai auren wannan d’an naki... Kodashike ba laifinki bane Uwar mijinki ta bud’e maki k’ofa kiyiwa Zulfah haka amma ki sani idan a baya mun zuba maku ido yanzu bazamu zuba miki ido ki ci gaba da cin zarafinta ba, d’anki yayi kema kiyi wad’annan marassa ta idon yaran naki suyi....” Tinda ta soma magana Hajiya ke k’yarma tana dubanta, yaran suka hayyayok’o Najah ta janyo bokatin wanke wanke Sahariyya ta finciki bulalar hannun Hajiya da sunan zasu daki Aunty B... Murmushi kurum ta sakar masu tana mai gyara tsayuwarta tace “I dare you to try it, k’anan marassa kunya,... Na rantse da Allah maras kunyar data fasa cikinku, daga yau kun gama rashin kunya...” Sahariyya tayi saurin sauk’e hannunta sanin mijin Aunty B Soja ne, Najah ce tayi kanta gadan gadan Hajiya tayi saurin raba tsakaninsu tana fad’in “K’yaleta k’yaleta Auta...” Ta maida dubanta ga Aunty B kana tace “Bara’atu kinyi kad’an ki shigo har cikin gidana kimin rashin mutunci, amma tinda haka kika zab’a mu zuba nidake....” Tsaki Aunty tayi kana tace “Abinda kuka iya kenan, nidai na fad’a miki ki sakar ma Zulfah mara a mutunce, da da yanzu ba d’aya bane....” Daga haka sa kai tayi ta fice daga gidan had’ida buga masu k’ofa..... Najah sai faman fincika take tana fad’in “Haba Hajiya haba meyasa baki barni na cirewa matar nan rashin kunyarta ba, sai me don mijinta Soja wllhi Allah Hajiya da baki barni na gurji hak’waranta ba baki birgeni ba....” Ta k’arashe tana mai jifa da bulalar hannunta had’ida wucewa d’aki fuuu.... Hajiya ta kama farar kujera dake ijiye tsakar gidan ta zauna da k’yar zuciyarta naci gaba da tafarfasa... Sahariyya ta zauna gefenta tana tausarta, ita kuwa Raihanah ma iya cewa Allah ne ya ceceta, cikin sand’a ta wuce d’aki.... *** Har suka iso layin unguwarta bata daina tunani da fargaban abinda Aunty B ta aikata a gidan Hajiya ba, dubanta Aunty B tayi bayan ta ida parking kana ta dafata “Zulfa’u...!” D’ago idanu Zulfah tayi tana dubanta, Aunty B taci gaba da fad’in “ki kwantar da hankalinki komai zai wuce ya zamto labari kinji koh, zuciyarki mai kyaune nayi imani bazaki dawwama cikin k’unci ba da yardar Allah....” Jinjina kai Zulfah tayi a hankali kana tace “Na gode Aunty....” Aunty B ta kuma murmusawa kana tace “Always remember that we’re here for you kinji koh....” A hankali ta jinjina kai had’ida k’ak’aro murmushi kana suka kuma yin sallama sannan Zulfah ta wuce gida.... *** *Kaduna* Yauma kaman kullum shiryawa sukayi cikin pajamas d’insu mai launi guda, saman gadon ta hauro yanda yake zaune yana aiki bisa computer d’insa... Kiss ta manna masa a chick kana ta mak’ale cikin jikinsa bowl d’in crackers rungume a hannunta tana ci, ganin ya bada hankalinsa sosai ga aikin da yake ya sanyata sakin murmushi kafin ta d’au cracker guda ta shiga tura masa a baki tana fad’in “C’mon Partner open up, have som.... eat....” Kaucewa yake yana fad’in “Oh no no Partner I don’t wan to, stop... I said stop...!” Ina kaman cewa yake ta k’ara sai tsalle take akansa tana tura masa bakinsa.... Mirgino da ita yayi ya shiga mata cakulkuli ta ko ina su duka biyu suna dariya cikeda so da k’aunar juna.... Saida sukayi laushi gaba d’aya kafin ya janyota jikinsa suka kishingid’a, yatsunsu cikin na juna Sameer ke fad’in “You know Partner, I think Khalid was right.... Bai kamata idan mun samu matsala kad’an ki tafi gida ba, if we have problems kamata yayi mu solving matsololinmu just the 2 of us ba sai an samu third party ba ballantana yajega iyayenmu kinji koh, I want this to be first and last... Can you promise me Partner...” Cikin sanyin jiki ta jinjina kai kana tace “I promise Partner, insha Allah hakan bazai sake faruwa ba... I’m sorry...” Murmushi yayi kana ya manna mata light kiss a labb’anta kafin ya janyo laptop d’insa yana mai ci gaba da aikinsa... Hannunsa ta kuma janyowa kana ta kishingid’a a jikinsa, idanu a lumshe take furta “Hey Partner, guess how much I love you...?” Murmushi yayi had’ida kuma kwantar da kanta cikin k’irjinsa yana mai shafa kwantattun sumarta had’ida lumshe idanu... “Must I guess...?” Ya tambaya still idanunsa a rufe... Murmushi take tana duban kyakkyawar fuskarsa kana ta shiga janyo hannunsa tana fad’in “No no no don’t guess, come I wanna show you something...” Sauk’owa sukayi daga saman gadon Siyama tayi d’igyalgyal ta rufe masa idanunsa da tafukan hannayenta, saida suka iso bakin window kana ta bud’e tapka tapkan labulaye da aka k’awata manyan windows d’in dasu, sliding glass d’in tayi fresh air ya bugi fuskokinsu duk da cewa akwai sanyin Air-conditioner a d’akin.... Kallon taurari dake baje iya ganinka a sararin samaniya tayi kana ta saki murmushi ta cire hannayenta daga fuskarsa, tsayuwa tayi gefensa suna fuskantar window su duka biyu kana ta sakalo hannunsa cikin nata... Saitin kunnensa cikin sigan rad’a take fad’in “Open your eyes Partner...” Ta fad’i murmushi bai gushe saman kyakkyawar fuskarta ba... A hankali ya bud’e idanunsa had’ida sauk’esu ga sararin samaniya yana mai shak’an dadd’an iska, Muryar Siyama ya katse masa wasu tunani da sukazo zuciyarsa lokaci guda... Ta bayansa ta zagayo had’ida rungumarsa bata daina duban taurarin ba take fad’in “Ina sonka Partner iyaka yawan taurarin dake sararin samaniya....” Murmushi Sameer yayi kana ya kaikaito suna fuskantar juna, yatsa yasa yana gyara mata kitsonta guda da ya sauk’o fuskarta, lokaci guda yake furta “And I love you without a limit Partner, much more than all those stars shining in the Sky.... I love you more than love itself, I love you more than my own life Siyaam...” Tinda ya soma magana Siyama ta kasa daina kallonsa, batasan wani irin so Sameer ke mata ba, take taji k’walla na neman ciko idanunta, lokaci guda ta rungumesa tsam cikin jikinta tamkar mai tsoron kada wani ya k’wace mata shi... Murya na rawa take furta “Partner I don’t know what I do without you... I love you....” Rungumeta shima yayi cikeda sonta da k’aunarta.... A haka har bacci yayi gaba dasu.... *** Wajajen k’arfe 11pm ya shigo gidan yana faman huci, cikin bacci ta sinkayo muryarsa na faman doka mata kira... A firgice Zulfah ta mik’e zaune zuciyarta na faman yankewa.... “Zulfa’u..!!!” Ya fad’i a karo na hud’u, tsaki ya buga kafin ya nufi uwar d’akin.... K’iris ya rage bai bangajeta ba yanda ya turo k’ofar, matsawa gefe tayi fuska a tamke... “Wani rashin kunyar kikaje kikayi a gidan Hajiya, sannan abin naki har yakai ki dinga d’ebo k’annen mahaifiyarki suna zuwa suciwa Hajiyata mutunci... How dare you Zulfah...?” Tak’aitaccen murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo kana tayi saurin gimtsewa, dubansa da kyau tayi kafin taci gaba da fad’in “First of all, kar ka saka k’annen mahaifiyata ciki, sannan meyasa baka tambayi Hajiya da k’annenka mai yakai Aunty B gidan ba... Kai kanka sanin kanka ne hak’uri nake da mahaifiyarka da k’annenka don haka kada ka kaini bango....” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige... Shaye da tsananin mamaki Hafiz ke kallonta, shine Zulfa’u ke gaya masa magana haka, bai bari ta shigeba ya fincikota ta dawo da baya..... *SameenaAleeyou📚* [25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _................DA RABO_ *04* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *Dedicated to my Trio ♥* Cikin karaji Hafiz ke ci gaba da fad’in “Ni kike cema kina hak’uri da mahaifiyata.... Ni nake aurenki ko ke kike aurena... Idan kin mance bari na tuna miki Zulfah... Duk duniyar nan idan akwai mai k’arshen hak’uri toh kuwa shakka babu nine tinda kowa gudunki yake yana k’inki amma ni nayi hak’uri na amince da aurenki, na maki sutura, na baki matsuguni sannan nake ciyar dake.... Idan baki baki mance ba you’re nothing but a Curse to our family..... Shin bayan gata da na miki har kinada bakin magana...?!” Tunda ya soma magana take zuban hawaye zuciyarta naci gaba da k’una da tafarfasa.... Muryan Hafiz ya kuma dakan dodon kunnuwanta sanda yaci gaba da fad’in “Daga ranar da aka haifoki a zuri’armu farin ciki suka gushe, mahaifanmu suka rasa wani sashe na kasuwancinsu, al’umman gari kowa ya yarda kece silan komai, tsiyane ke bibiyarki duk yanda kika saka k’afa, gashi nan babban misali akaina tunda kika aureni na kasa mallakar kasuwancin kaina da kaina, har yanzu mahaifina ke d’awainiya dani dake...” Baikai aya ba cikin zuban hawaye ta katsesa da fad’in “Hafiz idan ka gaji da zama dani ka sallameni gaba d’aya, ka daina k’untata min kana cemin jeki gida kawai, ka bani shaidar tafiya gida mai tushe wanda idan na tafi babu mai dawo dani.... Ka bud’e baki kace na sakeki Zulfa’u.....” Ta k’arashe muryarta har na sark’ewa sabida tsananin kuka..... Banda kallon banza baya watsa mata komai, saida ya d’auki wasu dak’ik’ai yana watsa mata kallon banza kafin ya buga tsaki ya shige yana fad’in “Aikin banza abinda kika iya kenan.....” Har yakai k’ofa ya dawo da baya yana mai nunata da ‘yar yatsa yake fad’in “And let me warn you for the last time... Wllhi wllhi kinji na rantse duk randa kika sake tattaran wata dangin mahaifiyarki kukaje kukaci mutuncin Hajiyata ranar ne zakiga kalana da baki tab’a gani ba....!” Daga haka wucewa yayi ya shige uwar d’aki had’ida banko k’ofar da k’arfin gaske.... Zamewa tayi had’ida zama cikin kujera k’irjinta na mata zafin gaske.....” Ita kuma kalan tata k’addarar kenan, wannan shine rayuwarta... A hankali ta zame cikin kujeran hawaye basu daina gangaro mata ba, a nan yanda take kwance bacci yayi gaba da ita.... Cikin dare take jiyo muryarsa a tsakar kanta yana doka mata kira, babu wani lank’wasa murya balle kalaman soyayya yake sanar da ita buk’atarsa, sannan da zai biya buk’atar nasa haka nan zai tsallaketa tamkar kuyanga aka ijiye masa... Wannan shine rayuwar gidan auren Zulfa’u, sam batasan akwai wata soyayya tsakanin miji da mata ba saidaima wani abu da yafi kama da k’iyayya.... *** Safiyar Washe gari... Babu walwala a fuskarsa ya shigo parlorn, Marliya da Nabila zaune parlor Marliya na kallo yayinda Nabila ke karatu sabida jarabawarsu na k’arshen zangon karatu da suke fuskanta,... A tare suka gaida mahaifin nasu saidai babu wani walwala ya amsa masu... Da mamaki Abbah ke dubansu kana yace “Mai ya hanaku tafiya karatu....?” Nabila tace “Abbah lecture free week muke sabida satin sama zamu fara exams....” Jinjina kai yayi kana ya maido da dubansa ga Marliya yana jiran nata amsan... “Abbah midterm break muke....” Nan ma ya jinjina kai kafin ya k’arada “Ina Mamyn taku....?” A tak’aice.... A tare suka basa amsa da “Tana ciki Abbah....” Gyad’a kai kurum yayi kafin yasa kai ya nufi uwar d’akin Mamy..... Nabila da Marliya suka kalli juna don koda basu sani ba Mamani ce ta tinziro Abbah don ta had’asu fad’a da Mamy.... Nabila ta yab’e baki tace “Nifa wai sai naji mutane suna son Grannies d’insu suna wani jidasu ni kuwa wllhi Allah ya gani addu’a nake nawa ta mutu ko zamu samu peace cikin gidan nan....” “Umm Mamani case....” Marliya tace sanda take kishingid’a cikin kujera had’ida rungume throw pillow.... Aiko daga yanda suke zaune suka soma jiyo muryar Abbah ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba duk akan maganganun da Mamani ta kitsa masa gameda Mamy da Zulfah.... Nabila tayi jifa da handouts d’inta ta k’arasa jikin k’ofar sosai tana sauraren maganganun Abbah.... Marliya dai girgiza kai kurum tayi had’ida ficewa daga parlorn don batama fatan taji wani abinda zai d’aga mata hankali.... A bakin farandar Mamy Marliya suka kusan yin karo da Aunty Lami, ganin yanayin Marliyan ya tabbatar mata wani abin na faruwa... “Lafiya Marliya ina zaki haka cikin fushi....?” Aunty ta tambaya.... “Abbah ke fad’awa Mamy nah kuma shirin gari ya waye nake kalla amma bazan iya ci gaba da kallo ina jiyo sautin fad’arsawa Mamy ba....” Ta fad’i kaman zatayi kuka... Aunty ta janyota cikeda tausayawa kana tace “Kiyi hak’uri kinji Marliya kar kiyi kuka maza jeki parlor na kiyi kallonki, ki kalli tashan da kike so....” Marliya ta jinjina kai kafin ta nufi parlorn Aunty.... Murmushi Aunty tayi kafin tayi saurin kimtsa kanta ta nufi parlorn Mamy.... Mamakine ya cikata ganin Nabila mak’ale jikin k’ofa ta manna kunnenta... Girgiza kai Aunty tayi kafin ta k’arasa tana ambaton sunan Nabila cikin kakkausar murya... Nabila ta d’ago a zabure tana subanta, lokaci guda ta tab’e fuska ba tareda tace da ita komai ba, Aunty taci gaba da fad’in “Ki wuce a wajen banson sakarci da rashin kunya, mai zaiki jin tattaunawar iyayenki, rashin hankali ko mai....?” K’unk’uni Nabila keyi fuska a turb’une ta wuce Aunty tana mai ci gaba da k’unk’uninta cewa ita dai ba maras kunya bace.... Aunty ta bita da kallo yawa ta kikkifeta da mari sam tasu batazo d’aya da Nabila ba a cewarta yarinyar ita kad’ai ta fita zakka a gidan, sam Nabila batada ta ido, girman yarinyar akwai aiki inji Aunty.... Waje ta nema ta zauna a parlorn had’ida rapka uban tagumi tana jiran fitowar Abbah.... A b’angaren Nabila kuwa tana ficewa sashen Mamani ta nufa.... Sakina d’iyar Baffah Wali ta tarar parlorn tana kallo don babu a sashensu sai sunzo sashen Mamani suke kalla koda zata masu wulak’anci da masifa amma haka suke shanyewa sabida tsabagen son abin duniya... Kallon arziki basuyima juna ba Nabila ta shige uwar d’akin.... Bata sameta a d’akin ba amma taji k’aran zuban ruwa daga bayi hakan ya tabbatar mata tana band’akin.... Bakin gado ta samu ta hakince harda d’ora k’afa d’aya bisa d’aya tana jiran fitowar Mamani daga bayi..... *** “Sahariyya ki tashi ki dafawa yarinyar indomie tintine kin zaune sai aikin danna wayar banza kike....” Hajiya da Khausar ke zaune bisa cnyarta ta fad’i Tsuka Sahariyya tayi a hankali kana tace “Haba Hajiya nifah wllhi bacci ma nakeji wannan fitinanniyar yarinyar sam bata barmu munyi wani baccin kirki ba sai kuka take tana ambaton mamanta, ni wllhi Hajiya ki maidata gidan iyayenta don bazan masu bautar ‘yarsu ba nidai....” Tana k’arashe fad’in haka ta janyo earpiece d’inta ta manna a kunnenta.... Hajiya ta gyad’a kai had’ida furta yayi daidai, Najah dake faman mulka powder a fuskarta dukda cewa kayan makaranta ne jikinta kai kace biki zata yanda ta zauna tana zuba kwalliya a fuska, idanunta naga madubi take fad’in “Nidai kin gani shirin makaranta nake....” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye cikin matsattsun kayan makarantar nata.... Da mamaki Hajiya ke dubanta kana tace “Ke Najah ba Raiha tace an baku hutun kwana biyu ba, wani makarantar kuma zaki....” Tsuka naja tayi had’ida turo baki kana tace “Wllhi Hajiya k’aryan Raiha da Marliya ne, hala dai ‘yan ajinsune aka basu mudai ba’a bamu ba...” Ta k’arashe tana zira jakkan makarantar ta..... Hajiya ta maido da dubanta ga Sahariyya kana taci gaba da fad’in “Ke k’atuwar banza da ba makarantar kike zuwa ba ke ya kamata ki dafa mata, ace sau biyar kina zana jarabawar aji shida amma kin kasa ci gaba, dubi Zulfa’u dai da kad’an ta girmeki gashi har tana bautan k’asa, ga yarinyar can Nabilah tayi nisa ke kuwa haka nan baga karatun ba baga aurenba.....” A hasale Sahariyya ta katseta da fad’in “Nidai karma ki had’ani da wad’ancan matsiyatan Hajiya ehe, kuma da kike maganarki ince Yaya Hafiz ma tunda aka koresa yayi satan amsa bai koma ba aidai gwarani farawa ne banyi ba, gaskiya ni Hajiya babu ruwanki da maganar makarantata balle aurena....” Tana ida fad’in haka ta buge skirt d’inta ta shige parlor tana maimaita wak’ar dake tashi cikin earpiece d’inta... Najah ce ta dubi mahaifiyar tasu kana ta murmusa tace “Hajiya toh me amfanin Raiha tinda tace suna hutu ai sai ta dafa mata ta kula da ita kokuwa....” “Raiha wanke wanke take kuma tana gamawa zata gyara kayan miyan abincin rana yau za’a kaiwa Alhaji can Kasuwa.....” Najah ta jinjina kai tana mai darawa kana tace “Toh ai Hajiya sai ki mik’e ki shiga kitchen, ni na tafi sai na dawo....” “Toh a dawo lafiya....” Hajiya ta fad’i sanda take mik’ewa tsaye, parlor ta nufa ta dangwalawa Sahariyya Khausar tana fad’in “Saiki rik’eta naje kitchen d’in.....” Aiko ana ajiye Yarinyar ta fashe da kukan gaske sabida har ta gane Sahariyya irin tsawa da masifa data dinga mata a daren jiya don kawai tana kukan mahaifiyarta, yarinyar da duka bata wuce shekaru biyu da watanni bakwai zuwa takwas ba... Aiko Sahariyya ta bud’e murya ta daka mata tsawa wanda ya kuma birkitata harda d’auko wayar earpiece d’inta tana nuna mata zata zaneta.... Daga yanda Raihanah ke wanke wanke tana jiyo sautin kukan Khausar tausayin yarinyar ya cikata, cikin sauri ta tsame hannayenta ta nufi parlorn yanda Sahariyya da Khausar ke zaune... Cikin sauri ta k’arasa ta d’auketa ganin yarinyar ta dungura tana kuka..... Sahariyya ta daka mata tsawa, “Ke uban wa ya baki izinin d’aukarta....” Cikin sanyin murya tace “Addah Sahariyya kuka fah take...” “Toh anji kuka take saiki wuce ki ficemin da ita daga nan kafin na had’eku na daka.... Uwar kilibibi kawai....” Cikin sauri Raihanah ta fice tana jijjiga yarinyar da tuni tayi lamo cikin jikinta, d’akinta ta nufa ta d’auko zanin goyo ta goyata a baya kana ta koma bakin aikinta, tanayi tana jijjiga Khausar har bacci yayi gaba da ita..... *** Shaye da mamaki Mamani ta tsaya tana duban Nabilah dake zaune saman gadonta tana jijjiga k’afafu.... K’arasowa tayi cikin tafiyarta mai yanayi da d’ingishi sabida girma kana tace “Ke Halimatu lafiyarki kika shigo min har uwar d’aki ba tareda izinina ba kina faman kad’a k’afa... Hanshak’iya Mandiya...!” Ta k’arashe tana d’aura hannayenta bisa kunkuminta... Mik’ewa Nabila tayi kana tace “Mamani ina kwana.....” “Da ban kwanaba kya ganni maras kunya kawai....” Nabilah ta kad’a kai kana tace “Allah ya gani na gaisheki na fita.... Dama zuwa nayi na fad’a maki na jaddada maki wllhi duk randa mahaifiyarmu ta gaji da zaman gidan nan tace zata tafi toh ki sani tare zamu tafi don wllhi Allah kinji na rantse Mamy tana sa k’afa da sunan barin gidan nan muma saidai a nememu a rasa, daga ke har Abban sai ku zauna a gidanku cikin kwanciyar hankali kiji da sauran jikokin naki amma dai kam ba ‘ya’yan Abbah ba don wllhi tafiya zamuyi....” Tana gama fad’in haka ta fice abinta ba tareda ta kuma bin takan Mamani dake daskare wajen ba... Haba nan fah Mamani ta soma sbabi tana fad’in “Eh lallai yarinyar nan kin rik’a, laifin uban naku da ya k’yaleki kina boko yak’i aurar dake, dolema ki fand’are mana, ohni Halima bansan miyasa aka sakawa wannan maras kunyar yarinyar sunana ba, bakiyi halina ba wllhi, fitsararriya kawai mai halin uwarta...” Daga parlor yanda Sakina ke zaune banda dariya bata komai bud’e murya tayi kana tace “Ai sunanki da aka saka mata yasata biyo halinki Mamani...” “Kai waye a wajen nan maras kunya masu halin iyayensu mata...” Kafin ta fito Sakina ta mik’e ta fice tana ci gaba da dariya, sauri sauri ta nufi sashensu kai rahoto wa mahaifiyarta Karima matan Baffah Wali.... *** *Kaduna* A gajjiye ta shigo gidan jaka a hannu mayafi a hannu dogon takalminta a hannu, cikin kasaltacciyar murya take kwad’a masa kira don taga motarsa a parking lot hakan ya tabbatar mata yana gida... “Partner..! Partner...!! I’m home, where are you....” “Yes honey I’m here...” Ya amsata daga yanda yake... B’angaren da tajiyo muryar nasa ta nufa bayan ta zuba tarkacan hannunta a parlor.... Tsaye ta gansa bakin gass cooker yana juya sausage cikin pan ga bread da fresh lettuce a gefe alamun sandwich zai had’a.... Rungumesa ta baya tayi tana fad’in “Umm it smell delicious Partner, ayi sauri a bani naci I’m starving already...” Ta k’arashe tana d’ora hab’arta bisa kafad’arsa.... Murmushi yake yana ci gaba da zuba sausage d’in cikin plate kana yace “Partner kinsan wannan aikinki ne kawai karambani nake maki, don haka zo ki k’arasa ki samu ladanki...” Turo baki tayi had’ida dad’a matseshi kana tace “But you know I’m not a good cook Partner...” Juyowa yayi yana dubanta kafin ya d’anja hancinta yace “My wife can’t cook but she can run a company.... Am I right...?” Jinjina masa kai tayi kana tace “Exactly Partner.... Muje muci before it get cold....” Bata jira cewansa ba ta soma d’aukan abincin zuwa dining table... Misalin k’arfe goma da rabi sun gama duk wasu d’abi’unsu da suke kafin suyi bacci tuni ta haye saman gado ba tareda jiran Partner d’in nata ba, dubanta kurum yayi had’ida murmusawa kafin ya jawo computer d’insa ya shiga mail d’insa yana duba abinda yake tsammani... Aiko nan yaga sak’on ya shigo... A hankali ya rintse idanu had’ida sauk’e ajiyan zuciya... Rufe computer d’in yayi kafin ya k’arasa saman gadon yanda Siyama ke kwance tana duba sak’wannin da suka shigo mata a wastapp sai faman hamma take alamun bacci da gajjiya... Ta bayanta yasa hannayensa ya rungumota kafin ya zame wayar nata a hankali yana fad’in “Partner this is my time a ajiye wannan saida safe kuma....” Cikin kasaltacciyar murya take fad’in “Partner what are you doing, I’m exhausted please...” Matseta yayi kana yace “Okay maybe some little massage may help... wouldn’t they....? Or may be some kisses may help too....” Kukan shagwab’a ta soma masa tana turesa jin abinda yake mata tana fad’in “Partner no.... let go please, not now.. I know exactly what you’re up to....” Rufe bakinta yayi da sumba kafin ya kashe masu side lamp... *SameenaAleeyou📚* [25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _.................DA RABO_ *05* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Tafe suke cikin farfajiyan asibitin ko wannensu cikin shiga irinta k’wararrun likitoci, hannayensu rik’eda wasu ‘yan kofi da sukafi kamada disposable saman wasu ‘yan k’anan plates, shakka babu coffee ne ciki kasancewar safiya ce lokacin.... Wajene mai kunshe da mutane wanda yafi kamada a kirasa Cafeteria, can wani table suka nufa suka zauna yayinda wasu nurses ke mik’a masu gaisuwa, Sultan ne kawai mai iya amsawa shi kuwa Sameer saidai ya jinjina kai alamun amsawa... Hannu Sultan ya nad’e yana duban abokin nasa wanda gaba d’aya yau d’in bai gane masa ba, a hankali ya d’au coffee d’insa yana kurb’a ba tareda ya d’aga idanunsa daga duban Sameer d’in ba, ko ba’a fad’a maka ba yana cikin damuwa da tashin hankali... Sultan ya d’anyi gyaran murya kana yace “Are you sure you’re alright Sameer, it’s obvious you’re not yourself.... Wai meke faruwa ne.....?” Sauk’e ajiyan zuciya Sameer yayi kana yace “Sultan I don’t know how to break the news to her, sanin kanka ne I only have a week left here, to be honest with you banason transfer d’in nan domin hakan na nufin rayuwata tana shirin canzawa completely....” Murmushi Sultan yayi had’ida girgiza kai kana yace “Nasan haka zai faru abokina, bazaka iya tafiya kabar Partner ba koh...?” Murmushi Sameer yayi da gefen bakinsa kana yace “Ka sani kuma kake tambaya.... Sultan wannan transfer d’in is a disaster to me....” Ya k’arashe yana kurb’an coffee d’insa.... Sultan ya kuma murmusawa kana yace “So tari nakanyi tunanin wane irin so kakewa Siyama... Anya kuwa Sameer wannan nuna soyayya da kulawa taka batai yawa....?” D’ago idanu Sameer yayi yana duban Sultan kana yace “I love her with all my heart... Bazaka fahimci mai nake fad’i ba sai ka had’u da wacce kake so irin haka....” Sultan yayi tak’aitaccen murmushi kana yace “Banji akwai wacce zan mata irin wannan soyayyan Sameer, nifah a ra’ayina soyayya duk k’aryace kuma ina maka tsoron watarana da zaka yarda da maganata cewa babu komai cikinta face k’arya da yaudara....” K’uri Sameer ya masa kafin ya girgiza kai yace “Nida Partner hakan bazai tab’a faruwa damu ba cos we’re Magnets shiyasa nake tunanin transfer d’in nan ka iya kawo tashin hankali ma rayuwata...” Sauk’e ajiyan zuciya Sultan yayi kana yace “Dr kenan, kai bama tunanin iyayenka da basuda wani d’a kake ba sai Siyama... Besides Kano da Kaduna ai bakida hanci ne idan kaga dama duk bayan kwana biyu kana hanya...” Girgiza kai Sameer yayi kana yace “Ba kaman idan ina nan ko yaushe ba, nidai gaskiyar magana bud’e sabon asibitin k’una da gwamnatin tarayya tayi a jihar Kano baimin ba...” Dariya ya kufcewa Sultan kana yace “Haba Sameer nasanka da son taimakon al’umma wannan asibiti da aka bud’e ai sabida al’umma aka bud’eta kuma wayasan d’imbin burn victims da zaka taimaka a jihar Kano, tun had’uwata dakai nasanka mutum ne mai k’aunar aikinsa ba don komai ba sai don ganin ka taimaki al’umma so please kar ka bari wannan k’udirin naka ya gushe akan soyayyar da kakewa matarka don na tabbata itama bazataso hakan ba....” A hankali Sameer ya sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da iska kafin wata speaker ta soma announcing ana neman Dr Sultan da Dr Sameer sakamakon kawo wata budurwa da akayi k’unan wuta ya mata babu dad’i.... Cikin sauri suka mik’e suka nufi bakin aikinsu don ceton ran wannan budurwa.... **** *Kano* Shi kad’ai sai wani cika yake yana batsewa, tun bayan gaisuwarta da ya amsa bai kuma bi takanta balle karin kummalon data had’a masa, kallon arziki bata ishesa ba ya k’arashe saka cuff links d’insa, sanin ba magana zai mata ba ko zasu kwana a haka ya sanyata bud’e baki tace “Fita zakayi baka karya ba...?” Da wutsiyar idanu ya dubi sashen da take kana ya kuma kauda kansa, wani k’atutun bak’in ciki ya tokari k’ahon zuciyar Zulfa’u, wato shiru ma amsa ne..... K’ok’arin shanye wannan bak’in cikin tayi kana ta kuma yin k’asa da murya tace “Abban Khausar magana fah nake maka...” A hasale ya maidoda dubansa gareta yana mai darara mata tsawa “Wai meyasa bakida hankaline Zulfah, idan zanci sai nace miki zanci ne, idan nayi ra’ayin ci basai kinmin tuni ba, ko kinfi son cikina ne...? Abincinki ne yau banyi ra’ayin cinsa ba, sai ki ajiye kiyita cinsa har dare don bazan lamunci ayita min almubazzaranci da abincin gida ba....” Hawaye suka ciko idanunta, tayi k’ok’arin maidasu kana ta bisa da “A dawo lafiya....” Nan ma bai amsata ba yasa kai ya shige, har ya fice ya dawo da baya yace “Ki tabbata kinje kin baiwa Hajiya hak’uri kafin na dawo....” Cikin hawaye ta jinjina masa kai yana ficewa kuwa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya domin kuwa tanajin sanda wayarsa tayi k’ara ya d’aga yana sanar da budurwarsa gashi nan tafe a ajiye masa favorite d’insa... Da shike budurwar tasa d’iyar Hajiya Magajiya ce wata mai restaurant a can bayan layinsu, babu yanda Zulfah batayi ba ya rabu da Sawwama d’iyar Magajiya tinda kowa yasan halinta shashasha ce ballagaza maras kamun kai amma yak’i saurarenta, k’arshema mugun kashedi ya kafa mata akan alak’arsa da Sawwama, takai ta kawo Sawwama har nunata suke suna dariya idan tazo zata wuce bakin shagon mahaifiyarta... Babu yanda Nabilah bataida Zulfah ba kan ta bartada Sawwama zatai maganinta amma fir Zulfah ta hanata shiga maganar, hakan bashike hana Nabilah yab’a masu magana ba muddin tazo wuce k’ofar restaurant d’in.... *** Hajiya na zaune saman tabarma a faranda Khausar na kwance gefenta tana bacci don tunda Raihanah ta goyata take bacci, zab’en safe da ake a gidan radio k’arfe goma shad’aya take sauraro Zulfa’u tayi sallama.... Da gangan Hajiya ta k’ure sautin radio d’inta, jin ba’a amsata ba ya sata k’ara d’an bud’e murya tana kuma sallaman haba nan fah Hajiya ta hayyayak’ota da ruwan masifa don dama ta d’ago muryar nata... “Shegen iyayi da munfurcin banza, an amsa miki bawai ba’a masa ba amma sai nanatawa kike yawa biya karatu... Munafuncin banza kawai...” Hayaniyar Hajiya ya d’aga Khausar.... Tinda ta soma bala’i kan Zulfah na k’asa, da k’yar ta iya furta “Kiyi hak’uri Hajiya....” Aiko Khausar najin muryar mahaifiyarta ta nufeta a guje tana mai ci gaba da kuka saidai kafin ta isa Zulfah dake duban d’iyar tata cikin shauk’i da bege tuni Sahariyya da fitowarta kenan daga d’aki don ayi da ita dashike taji zuwan Zulfah, tuni tayi tsalle ta sure Khausar dake kuka tana fad’in “Bazakije ba anan ake koyamiki munafunci.....” Zulfa’u batasan sanda ta mik’e ta nufi Sahariyya ba sabida tsananin k’una da rad’ad’i da zuciyarta ke mata.... Fincike d’iyarta tayi tana mai furta “Sahariyya kinyi kad’an ki rabani da d’iyata.... Zan lamunci duk wani cin zarafi da zaku min amma banda d’iyata....” Khausar kuwa tuni ta kwanta cikin jikin Mamanta tana shan zuciya a hankali.... Hajiya da tuni ta saki baki tana kallon ikon Allah mik’ewa tayi had’ida rangad’a gud’a “Eh lallai Zulfa’u kin rik’a kin cika cikakkiya, bari kiji na fad’a miki idan kin mance, Sahariyya tafiki iko da yarinyar nan tunda k’anwar Ubantace, yo aurenki ko mutuwa yayi ba baki Khausar za’ayi ba Sahariyya kuwa za’a mallaka mata Khausar domin kuwa Ubanta ma ita yasha nono ya sake.... Ke Sahariyya karb’i yarinyar nan idan ta cika ta kuma fizgeta.....” Hajiya ta k’arashe tana dukan k’irji alamun fad’a... Zulfah tanaji tana gani Sahariyya ta fincike Khausar daga hannunta, yarinyar sai kuka take sabida tsananin tsoron Sahariyya da take tamkar zata shid’e lokaci guda kuwa Sahariyyan ke darara mata tsawa wai tayi shiru gaban mahaifiyarta.... Wasu irin hawaye masu d’umi su suka shiga gangarowa Zulfah, batasan sanda ta cukwikuye fuskarta gaba d’aya da hijabinta ba ta fice tana mai jiyo sautin kukan Khausar har cikin k’ahon zuciyarta da yanda Sahariyya ke darara mata tsawa tana fad’in kalaman b’atacin akan Zulfah.... Raiha dake kitchen tana girki ta window take duban Aunty Zulfah har ta fice ga kukan Khausar na tashi, tuni Raiha taji hawaye na gangaro mata, kaman wanda aka turo Hajiya kitchen d’in nan ta hangi Raiha na kuka ga abinci bisa murhu da alama tayi nisa cikin kukan ta bar abinci har ya soma k’auri.... Bata ankara ba batasan da shigowar Hajiya ba sai sauk’an Dundu masu ji da lafiya har guda uku dataji a bayanta.... Raiha ya mik’e a d’ari tana kurma ihu.... Hajiya ta rarumo muciya tana fad’in “Dan ubanki sai na dakeki kiyi kukan da dalili, shegiya munafuka wato salon akai abincin nawa Kasuwa ma Alhaji aji babu dad’i koh... Munafuka algunguma... Wuce ki duba min girki kafin nayi k’asa k’asa dake a nan.....” Raiha ya shige tana hawaye, Sahariyya dake tsaye bakin kitchen fad’i take “Ai Hajiya da buga mata muciyar kikayi sai ta fad’i uwar da aka mata take kuka...” Hajiya tace “An b’ata ran uwarta Zulfa’u ta fice tana kuka mana, basu ragema juna komai ba tsinannu munafukai...” Sahariyya ta k’arada “Wllhi kuwa Hajiya ni dama har kama suke min....” Jifa Hajiya tayi da muciyar tana mai ci gaba da sababi, Sahariyya ta take mata baya..... *** Kaman daga sama Sawwama da k’awayenta suka hango Zulfah na tafe fuskarta duk ta dauje alamun taci kuka, idanunta a kod’e... Sawwama tayi shewa tana jiran k’arasowarta duk a tunaninta akan Hafiz take kukan da shike bai jima da barin Kantinsu ba... Sawwama ta tab’a k’awayenta suka nufi Zulfah SameenaAleeyou📚 [25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _................DA RABO_ *06* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallo guda Zulfah ta masu ta watsar, lokaci guda taji wani k’arfin zuciya yazo mata, tabbas batada lokacin Sawwama balle na k’awayenta, kai tsaye tasa kai zata rab’a ta gefensu ta shige dashike tuni sun tare gabanta... A tare Sawwama da k’awayenta Sailuba da Zabba’u suka kuma shan gaban Zulfah, sai faman cika Sawwama take tana wani batsewa.... K’ak’aro murmushin k’arfin hali Zulfah tayi kana tace “Bansan kuna biyo mutane har titi ku sanyasu sayen abincinku na dole ba tunda dai naga wannan hanyar wucewace ba kantinku na nufa ba....” A tare su Sawwama suka kwashe da wata irin shewa had’ida tafe hannaye kana Sailuba tace “Ai munfi k’arfin mu taro mutane saidai su kawo kansu tinda mijin wata ya kawo kansa.....” Zabba’u tace “Fad’a mata dai k’awata....” Itako uwar gayyar sai faman jijjiga take tana famkan fankam.... Har cikin ranta taji zafin kalaman Sailuba amma sai ta daure ta murmusa don bataso su gano lagonta... A fili kuwa cewa tayi “Alama ta nuna haka, ko shakka babu mijin wata ku kuka rok’eshi yaci abinci a kantinku amma ba ra’ayinsa bane, sannan ko kad’an banga laifinku ba don kun ara kun yafa domin kuwa abinci kuke nema ku saka a bakin salati wanda baku samu gidan iyaye ba....” Haba nan fah Sailuba ta harzuk’a, ta yunk’ura zatayo kan Zulfah Sawwama tayi saurin tareta kana tace “Kan me zaki b’ata hannunki, ita tasan wanda zai mata lilis kan wannan magana data furta.... Karki mance a gabanki ya labarta min irin wulak’anci da ya mata itada abincin data girka kafin ya fito kuma kisha kuruminki don yanzu zan kirasa na zayyane masa komai idan ta koma gida sa wanye....” Ta kuma maido da dubanta ga Zulfah kana taci gaba da fad’in “Sunan matarsa kawai kike amma sanin kanki ne Hafiz nawa ne ni kad’ai sai yanda nayi dashi, idan nice ke zan sallamasa na daina fad’a da kishi akansa domin kuwa darajar iyayenku kawai kikaci kike zaune gidansa....” Izuwa lokacin zuciyar Zulfah ta soma rauni amma ta daure ta murmusa kana tace “Ashe dai inada sunan matar tasa, kuma ko sau goma zan girka abinci baici ba inada lada wajen ubangijina domin kuwa bautarsa nake ba kaman wacce take bautan gardi da babu d’igon lada cikinta ba.... Sannan Alhamdulillah da har nakeda mahaifa na k’warai da zanci darajarsu suka killaceni gidan aure ba kaman wanda aka awatsarsu bakin kwalta suna bautan k’artin banza ba....” Haba izuwa wannan lokaci Sawwama takai bango banda huci bata komai, tuni ta yaye d’ankwalinta bakin kwalta tana bugan k’irji da zubo nau’i nau’in ashariya tana fad’in a barta ta daki Zulfah... Tuni Zulfah ta wuce don batada lokacin Sawwama ga jama’a da suka soma taruwa ba mutuncinta bane a ganta bakin layi tana dambe.... Su Sailuba sai rik’o Sawwama suke suna bata hak’uri inaa sai ashariya da hauka take bakin layi, kan kace mai ta koma restaurant d’insu a guje ta d’au waya tana neman layin Hafiz.... *** A farfajiyan gidan ta hango Nabila na karatun jarabawa, Sadiya d’iyar Baffah Wali na gefe tana shanya, sam Nabila bataji tab’a gate ba tayi nisa wajen solving equation saida taji muryan Sadiya na gaida Zulfah.... Da mamaki Nabila ke kallon Zulfah yanda fuskarta ta kod’e, ko ba’a fad’a mata ba watsettsen mijin nan nata ko shegun danginsa ne suka mata wulak’ancin da suka saba.... Tattara handouts d’inta da kayan karatunta tayi ta nufi ‘yar uwarta wacce tana k’arasowa ta rungume Nabilan sai kuma ta fashe da wani irin kuka... Su Sadiya an samu nakai rahoto tuni tabar shanyar da take ta kafesu data mujiya.... Ganin haka ya sanya Nabila saurin janye ‘yar uwarta suka nufi cikin gida don tasan halin ‘yan gidan nasu... Tuni Sadiya ta nufi sashensu kai rahoto.... Aunty Lami da fitowarta kenan daga sashen Abbah ta hangi Zulfah da Nabilah rungume da juna sun shige.... Cikin sauri ta sad’ad’a ta soma binsu a baya, d’akinsu Nabilah suka shige ba tareda sun nufi d’akin Mamy ba... Aunty Lami tanaji tana gani aka gark’ame k’ofa alamun bazataji komai ba.... Badon taso ba ta wuce sashenta tana neman layin aminiyarta ta sirri.... Cikin hawaye Zulfah ke duban Nabilah kana taci gaba da fad’in “Nabilah na gaji na gaji, I’m giving up.... Bazan iya ba wllhi na gaji da rayuwar k’unci da nake a garin nan, na gaji da auren Hafiz danginsa budurwarsa ga kuma tsangwaman Mamani, gwara na koma Rano wajen kawunaina... Nabilah wllhi I’m tired.....” Ta k’arashe cikin tsananin kuka da rawar murya... Nabilah da zuciyarta ke faman tafarfasa hannayen ‘yar uwarta ta rik’e kana tace “Addah wllhi ni shaidace kinyi iyaka hak’urin da zakiyi da wad’annan azzaluman mutane, Addah duk hukuncin da kika yanke bazanga laifinki ba, amma Addah Kausar nake jiyewa idan kika tafi rayuwartace zata shiga garari wajen azzaluman nan mussaman idan Ya Hafiz ya auro wannan shegiyar Sawwamar mai zubin zabuwa... Addah kece mai ragar masu nasha fad’a miki duk shegen da ya miki karkiji shayin mayar masa koda Hajiyan Yaya Hafiz ne tinda bata rik’e girmanta ba, ke wllhi baki ragewa Mamy komai ba sai kuyi shiru ayita cutanku ana danne maku hakki, wllhi wanke idanunki zakiyi kici uban duk wanda ya shiga rayuwarki hakan ne kawai zaki samu peace kuma wllhi ko Mamani bance ki ragar mata....” Duk maganganun da Nabila keyi Mamy na tsaye bakin k’ofa tana saurarensu.... Bata ankara ba sai sauk’an rank’washi dataji a tsakar kanta... Gaba d’aya suka d’ago suna duban Mamy da babu walwala saman fuskrta, Nabilah na faman sosa kanta dake mata zogi take fad’in “Haba Mamy daga fad’in gaskiya...” Dak’uwa Mamy ta mata kana tace “Kinci gidanku da fad’in gaskiyar, wawiyar banza, a hakan ne zakici ribar duniya... Tashi ki bani waje baki ragarwa Bara’atu komai ba wannan, wajenta kika gado mugun hali.....” Nabila ta mik’e tana ture turen baki ta nufi k’ofa tana ci gaba da fad’in “Shikenan Mamy sai muyita zuba masu ido wllhi Allah Mamy ni gaskiya ki daina irin haka...” “Zakimin shiru ki fice ko sai nazo wajen na k’ara miki, sakarya kawai... Allah dai ya shiryaki.... Ki fice ki rufe mana k’ofa dama...” Jawo k’ofar Nabilah tayi had’ida yin k’wafa ji take kaman ta shige gidan Baffah Alhaji ta surfa masu rashin mutunci ko taji sanyi.... *** Zama Khalid yayi a kujera mai kallon nata kana yace “Siyaam please magana fah nake....” Harara ta kuma galla masa had’ida ture files d’in gabanta gefe kana tace “First of all stop calling me Siyaam don mutum d’ayane ke kirana da wannan sunan... Secondly, I’m not signing anything cos I’m pretty sure wasu kud’ad’e kake nema kaje ka had’a party na shashanci kaman yanda ka saba da ‘yanmatan ka... Tun muna saida juna kindly leave my office kafin na kira Daddy na sanar dashi exactly what you’re up to...” “There you go Sis, you’re hallucinating again.... Ke ko yaushe tunaninki negative, for crying out loud Siyama I don’t even have a girlfriend, please please sister I need you to sign this....” Ya k’arashe yana kashe mata murya D’aukan takardar tayi tana dubawa kaman zatayi signing d’in Khalid har ya soma murna yana gwad’ata saiji yayi ta watsa masa kayansa a tsakarka tana fad’in “You know what little bro, get out of my office right now... Kun saba kaida Daddy I won’t allow you to drag me into this, oya tashi ka fita bada sa hannuna ba....” Harara ya watsa mata kana yace “You know.... That’s why I hate you, kuma idan baki sani ba ki sani anyiwa Sameer transfer zuwa wani state d’in, kuma In sha Allah sanadin k’uncinki kenan....” Ya k’arashe yana mata muguwar murmushi... Sakare ta tsaya kalaman na mata yawo a kwanya, Partner d’inta kai badai Partner ba.... Kai no never babu abinda zai nisantasu... Toh ya akai bai ma fad’a mata ba.... Bata ida tunanin ba wayarta ta soma ringing.... Sunan Partner shine ya bayyana saman screen d’in... Ta jima tana duban screen d’in kafin ta zauna saman kujerarta da k’yar... Jiki babu laka tai sliding had’ida amsa kiran... Daga d’aya b’angaren Sameer yace “Hello Partner... Ya kike ya aiki, I can imagine you’re tired already... Can we have lunch together..? .... I’ve something important to tell you... Allah sa bakida aiki sosai....” Jiki a sanyaye tace “No no banida aiki....” Jinjina kai yayi kana yace “Good, I’ll pick you up then.... I love you..” Bai jira cewarta ba ya kashe... Siyama tayi k’urima wayar tana tunanin da gaske Partner zai iya tafiya wata gari ya barta...... *** Misalin k’arfe biyu da wasu dak’ik’ai Sameer ya iso company d’in, kai tsaye office d’in matarsa ya nufa yayinda sakatariyar tata ta shiga gaishesa ba tareda ta masa sha mak’i da shiga ofishin ba sanin matsayinsa wajen Siyama... Tsaye take jikin drawers na takardu tana duba wasu documents d’in sanda ya turo k’ofa a hankali ya shigo, riga da skirt ne a jikinta ya zauna d’amas wanda hakan ya kuma bayyana kykkyawar surarta... A hankali Sameer ya lumshe idanu yana mai shak’an k’amshin matarsa da ya kama ofishin, cikin taku da yafi kamada sand’a ya isa ya rungumeta ta baya... A tare su duka biyun suka lumshe idanu cikeda begen juna.... A hankali Siyama ta furta “Part-ner.......” v SameenaAleeyou 📚 [25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _...............DA RABO_ *07* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Har bakin gate Mamy ta rakota bata daina bata baki ba da nusar da ita ribar hak’uri a rayuwar zaman duniya.... Har cikin ranta Zulfah taji dad’in yanda mahaifiyar nata ta kwantar mata da hankali sai taji gaba d’aya damuwar da take ciki Allah ya yaye mata shi, Mamy ta umarceta ta koma gidanta kuma ta kwantar da hankalinta, da wannan tattaunawa tsakaninsu da Mamy Zulfah ta nufi gida.... Fitowarta daga layin kad’an taga sai manne unguwar ake da sabbin posters na Mutallab, batasan sanda ta saki murmushi ba tana addu’an Allah ya baiwa Mutallab sa’a a zab’en da za’ayi na Gwamnoni mai zuwa domin kuwa Mutallab mutumin mutane ne, mutum ne tuntuni mai taimakon Al’umma, yanada foundations da dama na taimaka ma gajiyayyu marayu musakai da sauransu, tun bayaso ya bayyana kansa har saida al’umma suka fito dashi Allah kuma ya bayyanashi.... Da yawan mutane sabida wannan taimakon nasa ke tsananin k’aunarsa da fatan ya k’arbi ragamar mulki a zab’e mai zuwa da za’ayi, wasu kuwa sabida tsananin kyaun halitta da Allah ya masa suke k’aunarsa bugu da k’ari matashi ne mai jini a jika domin kuwa a shekarunsa ta 40 yake, cikin ‘yan takara masu neman muk’amin kujeran governor kaf babu mai k’arancin shekarunsa... Wannan dalili yasa MUTALLAB yayi k’aurin suna duk yanda ka wuce hotunansa ke shawagi, Zulfah tana d’aya daga cikin magoya bayan Mutallab domin kuwa tanaji a cikin zuciyarta irinsu Mutallab suke kawo sauyi da ci gaban k’asa dama al’umma gaba d’aya... Murmushi tayi ganin yanda matasan keta aikin lik’a sabbin hotunansa kana ta tare adaidaita ta shige.... *** Hannayenta ya kamo bayan sun gama cin abincin, shinema ya d’an tab’a abincin Siyama kam cakalawa kawai tayi ta bari, ta k’agu taji maganar da Partner ke son sanar da ita shid’inma ya lura da hakan.... “Partner, gameda maganar da nakeso na sanar dake....” Ido ta d’ago tana dubansa kana tace “About your transfer....” Da mamaki yake dubanta yaya akayi ta sani.... Murmushi tayi kana tace “Kana mamaki na sani koh....?” Gira ya d’aga mata cikeda mamaki.... Siyama ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “I just found about it, Khalid ke sanar dani d’azu a office... Partner I thought ni ce ya kamata na soma sani...” Ta k’arashe tamkar zatayi kuka.... Shafe goshinsa ya d’anyi kana yace “I’m sorry Partner, and believe me I was about to tell you bansan ya akai Khalid ya sani ba har ya sanar dake, or maybe Daddy na tareda Uncle nake sanar dashi d’azu, so probably Khalid was there too... Honey I’m so sorry ba haka naso ta kasance ba kinji....” Ya k’arashe cikin sigan lallashi.... Murmushi ta d’anyi kana tace “Shikenan Partner na yarda dakai but ban sani ba idan zan iya rayuwa ba tareda kai ba...” Girgiza kai yayi kana yace “No Partner ba rabuwa zamuyi ta har abada ba, besides Kaduna da Kano bakida hancine, please karma ki saka wata damuwa ma ranki cos duk yanda zanje soyayyarki bazai tab’a canzawa ba koda zamuyi shekaru bamu tare I’ll still be the same Sameer that fell in love with you kinji koh....” Murmusawa ta kumayi kana tace “So I shouldn’t worry...?” Ya kuma kamo hannayenta cikin nasa kana yace “Sameer is all yours, you and only you...” Kasa daina duban kyakkyawan fuskarsa tayi kana tace “Ancemin matan kano sun iya k’wacen miji so kaga dole na damu....” Murmushi mai bayyana hak’wara yayi wanda yafi kama da dariya kana ya ciro wata k’aramar magnet cikin aljihun gaban rigarsa kafin ya janyo kujeran gefensa ya manna magnet din jiki kana ya d’ago ya dubeta itad’inma shi take duba... Sameer yace “Kinga wani space between magnet d’in nan da k’arfen nan...?” Girgiza masa kai tayi alamun a’a... Ya d’an murmusa kafin yace “Well, yanda kikaga babu space sun manne da juna toh haka muke Partner, babu space d’in wata so ki kwantar da hankalinki kece Partner d’ina ta har abada har na koma ga ubangijina kinji koh....” Hawayen da take mak’alewa suka soma zubowa, cikin sauri ta tashi ta isa kujeransa ta rungumesa.. Bata damu da sauran jama’an dake cikin restaurant d’in ba, Sameer d’inta shine mafarkin kowata d’iya mace... Cikin muryar kuka take furta “I love you Partner.... I love you so much....” Hannayensa ya had’e ya rungumeta kana yace “I love you more.....” Ya jima yana tsaye yana dubansu zuciyarsa bata daina masa zogi da k’una ba, jijiyoyin jikinsa sun tashi hakan nan idanunsa sunyi jazir alamun k’unan rai... Cikin sauri ya fice daga restaurant d’in ya koma motarsa.... Wasu irin hawaye masu tsananin zafi suna gangaro masa k’irjinsa na kuma masa zafi idan ya tuna kalan soyayyarsu da ya gaza samun irinta a rayuwarsa.... Cikin sauri tamkar zai tashi sama ya finciki motar yana ayyana ta yanda zai tarwatsa wannan soyayya ta ko wata hanyace..... *** Har ta iso unguwarsu bata daina ganin ana mammane garin da sababbin posters na Mutallab ba da alama rally d’insa za’ayi, har cikin ranta tanaso taga wannan rally d’in don ko babu komai itama tana d’aya daga cikin magoya bayan Mutallab, tabbas mutuwace kawai zata hanata fita ranar zab’e ta kad’a masa k’uri’a... Toh ya akayi bataji sanarwan wannan rally da magoya bayan Mutallab zasu gudanar ba domin kuwa sam shirye shiryen magoya bayansa a gidan Radio ta Magamar ‘yanci basa wuceta... Aiko bata ida tunaninba motoci suka soma shawagi suna wucewa sautin wak’ar MUTALLB na tashi cikinsu, abunka da mutum mai matasa yawa anyi tururuwarsu haka suke wucewa, wasu a babura wasu a motoci wasu kuwa a keke napep sai sannan ta lura keke napep d’in data shigama manne yake da hoton Mutallab, aiko wannan mutumi yabi ayarin mutane, tsaban farin ciki da Zulfah ke ciki batamayi la’akari da cewa ayarin masu rally suke biba domin kuwa har an shige k’ofar gidanta bata ankaraba.... Daga can kuwa wata hamshak’iyar Jeep ta doso wanda ko shakka babu contestant d’in ne cikinta, haba nan fah matasa suka kuma haukacewa... K’arshe me napep kasheta yayi ya fice a guje rik’eda poster yana fad’iwa Zulfah “Baiwar Allah kiyi hak’uri wllhi ga MUTALLAB....” Ai Zulfah ma sai ta tsinci kanta da fitowa daga cikin adaidaita tana raba idanu ta ina Mutallab d’in yake... Jama’a kaman anyi kasuwansu, maza da mata daga cikin gidajensu sai tururwan fitowa suke yara da manya..... Bata iya hangoshi ba dukda ya fito da kansa ta saman motar saidai fararen hannayensa da tayita hangowa yana d’agawa mutane hannu... Babban abinda yafi burgeta ya kusan sakata kuka shine yanda taga mutane kaman yashi sun fito domin nuna goyon bayansu ga shugaban da ake masa tsammanin adalci... Fitowarsa kenan daga kasuwa takaicin ‘yan rally d’in duk ya ishesa sabida sam ya tsani mutumin da ake rally d’in dominsa, sai tsaki yake yana kutsawa yana addu’an kada a k’ok’e masa sabuwar kimko d’insa da Alhaji ya basa.... Kaman ance ya kalli b’arin hagu ya hangota tsaye cikin ‘yan kallo..... SameenaAleeyou 📚 [25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _................DA RABO_ *08* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Idan ran Hafiz yayi dubu ya b’aci, wane iskanci Zulfah keyi cikin dandatson ‘yan siyasa..? Sabida tsabagen rashin mutunci har nan ta fito kallon taron ‘yan siyasa.... Ya kad’a kansa ba tareda ya bari ta hangosa ba sannan yasa kai yayi shigewarsa... Bayan wasu mintoci ta tsinci kanta tana mai fad’uwar gaba, innalillahi sai sannan tayi noticing layin da mai adaidaita ya ajeta bayan dandatson mutane sun d’an ragu... Hankali tashe ta koma jikin adaidaitan tana neman maishi ta bashi kud’insa koda da k’afane ta gangara tinda ba wani rata sosai bane tsakanin layin da nasu layin.... Mai adaidaita yana fad’in ta tsaya ya maidata inaa ko kulasa batayi tasa a fujajan ta shige ga lokaci da ya d’anja ba tareda tayi la’akari ba... Har ta isa gida k’irjinta bai daina bugawa ba, hango abin hawansa da tayi ya kuma tsinkar mata da gaba, k’ila tuntuni ya dawo gidan bata nan bacin minti shabiyar kacal ya d’ibar mata taje ta baiwa Hajiyarsa hak’uri ta dawo gida tayi abincin rana.... A hankali Zulfah ta lumshe idanunta tana ambato sunan Allah cikin zuciyarta, tsaye tayi a farandar ta kasa dosa k’ofan parlornta, saida ta kwashi tsawon wasu mintoci a wajen tana zullumi kafin tayi k’arfin halin yin sallama a k’ofar don tasan tabbas jimawarta tsaye a wajen k’arin laifi ne.... Shiru ba’a masa mata sallamarta ba, tayi tsammanin hakan musamman data hango shi zaune a doguwar kujera fuskarsa a murtuke sai faman kad’a k’afa yake wanda d’abi’arsace idan ransa ya matuk’ar b’aci... Zulfah tasha jinin jikinta, ta rasa da wanne zata fara, gaisheshi zatayi ko kuwa hak’uri zata basa ko kitchen zata fad’a ta soma girki, gaba d’aya sai ta nemi fushin da takedashi gameda abinda Sawwama da k’awayenta suka mata.... Cikin ‘yan kame kame ta soma fad’in “Ashe ka... dawo gida.... Sannu da dawowa barin.... Barin k’arasa kitchen.....” Idan kujeran da yake bisa ya amsa toh kuwa shakka babu shima zai amsa.... Sosai ta kuma shan jinin jikinta kafin tasa kai zata shige d’aki ta rage kayan jikinta... Muryarsa ne ya daki dodon kunnuwanta a daidai sanda ta murd’a handle d’in k’ofar.... “Daga gidan uban wa kika fito....?!” Tambayar da ya jefo mata... Cak ta tsaya had’ida rintse idanu k’irjinta naci gaba da bugu...... “Bakiji abinda nace bane.... Gidan uban wa kika fito...?” Ya kuma fad’i yana watsa mata mugun kallo..... A hankali ta dawo da baya sanda tayi k’ok’arin saita kanta kana tace “Ban gane daga gidan uban wa na fito ba.... Daga gidan Hajiya nake....” A fusace ya mik’e yana huci yake fad’in “Oh really... Bayan ganinki da nayi tsakiyan cink’oson maza har kinada bakin da zaki dubi tsaban idanuna kimin k’arya... How dare you Zulfah.....!” Ya k’arashe tamkar mai shirin kwasa mata mari.... Sauk’e ajiyan zuciya tayi kana tace “Kayi hak’uri Ya Hafiz wllhi hanyace tabi dani mai adaidaita yabi dani ta wajen amma wllhi gidan Hajiya na fito....” Wata murmushin rainin hankali yayi kana yace “Hanyar gidan Hajiya ya koma bayan layin nan koh...?” Shiru bata iya amsashi ba..... Ya kad’a kansa kafin yaci gaba da fad’in “Bansan kin koma ‘yar siyasa ba ai sannan banji iyayenki ma sun sani kije gida zanzo na samu Abban....” Ya fad’i yana saka hularsa alamun ficewa zai kumayi.... Gabanta ya bada dumm! Innalillahi had’a da iyayenta zai kumayi.... Cikin sauri kafin ya ida ficewa ta janyo rigarsa tana fad’in “Ya Hafiz Dan Allah ka saurareni.... Wllhi ba abinda kake tunani bane, iyakacin gaskiyata na fad’a maka hanya tabi dani wajen....” Fuzge rigarsa yayi yana fad’in “Nayi imani da Allah kika kuma kama min riga zanyi wargazaki a gidan nan.... Idan munje gaban Abbah da Alhaji sai ki fad’a masu gidan uban da kika fito....”. Daga haka yasa kai ya fice yana dialing layin Sawwama da ya tadda d’inbin missed calls d’inta.... Durk’usawa tayi a wajen takaicin kanta na damunta zuciyarta na mata zogi, lokaci guda hawaye suka shiga kwaranya mata..... Da k’yar ta iya mik’ewa ta kuma d’aukan mayafinta da jakanta ta ko zama bata kuma iyayi a gidanba ta fice sab’e da jakkarta tana hawaye.... Suna zaune parlorn Mamy suna lunch ta shigo tamkar wacce aka jefota.... A tare Nabilah da Marliya suka mik’e suna dubanta ganin yanayin da ta shigo.... Gijif ta zauna cikin kujera dafe da goshinta dake tsananin sarawa, Nabilah da Marliya suka kalli juna kafin Nabilah ta mata ido ta d’auki abincin ta wuce d’akinsu taci gaba daci.... Marliya tayi yanda tace d’in.... Kusan Zulfah Nabilah ta zauna tana mai k’are mata kallo... “Addah lafiya....? Wani abin ne ya faru...? Naga dai d’azu kika mana sallama, lafiya Addah...?” Ta kuma tambaya cikeda kulawa.... Har lokacin idanunta a lumshe sannan hannunta dafeda goshinta, a haka ta furta “Mamy fah.....?” “Tana sashen Abbah....” Nabilah ta bata amsa.... Lokaci guda Zulfah taji sabon kuka na shirin taso mata, cikin sauri ta mik’e ta nufi uwar d’akin Mamy had’ida kullo k’ofar tana mai fashewa da wani irin kuka.... Nabilah ta bita da kallo had’ida rapka uban tagumi.... Mik’ewa tayi ta fice ta nufi Parlorn Abbah..... Daga Mamy har Abbah dama Aunty Lami dake d’aya b’angaren sunsha mamakin ganin yanayin Nabilar wacce kaman an jefota...... “Ke lafiya...?” Mamy ta tambaya... Nabilah da ta masu tsaye aka tace “Mamy dama Addace tazo and she seems not well....” Abbah baice komai ba dama sunsan bazaice d’inba, gaba d’aya tinda d’ansa Ma’aruf ya b’ace ya dawo hakan, sai ya zamana tamkar bai damuwa da damuwar sauran yaransa sam basa gabansa, hakan sosai yakewa Mamy zafi, takanyi tunanin ko don su d’in ‘ya’ya matane kaman yanda Mamani ke yab’a masu maganganu ita sauran matan ‘ya’yan nata su Karima dasu Hajiya a cewarta duk sunzo sai aifan ‘ya’ya mata suke bacin ita kuwa uwar ‘yan maza ne domin kuwa duka ‘ya’yanta biyar maza ne... Hakan nan Mamani k’iriri take nuna masu tafison jikokinta maza wanda basu wuce uku ba, daga Hafiz wanda shine babba bayan b’acewan Ma’aruf(Alk’ali) haka nan take kiransa kafin ya b’ace saiko sauran biyun wanda duka ‘ya’yan Baffah Wada ne autansu Abbah..... Zubawa Abbah abinci Mamy take ta kasa k’arasawa, Aunty Lami da zuciyarta tuni tayi haske, murmusawa tayi tana duban Abbah da tuni d’an sauran walwalar fuskar ta d’auke dukda kasancewarsa mutum maras yalwan fari’a... K’arasowa Aunty Lami tayi ta amshi serving spoon d’in cikeda k’issa tana fad’in “A’a Mamy tashi kije kiji da ita zanjida Abbah....”. Ta k’arashe tana duban Abban da wutsiyar idanunta.... Aiko tamau ta hango fuskar nasa, ta saki murmushi a hankali.... Jiki babu k’wari Mamy ta mik’e ta kamo Nabilah suka fice.... Aunty ta gyara zama tana ci gaba da serving Abbah wanda yabi bada hankalinsa ga kallon tv... D’an gyaran murya tayi kana tace “Na zuba romon kifin.....?” Kafin yakaiga bata amsa sukaji sallaman Mamani Hafiz na biyeda ita... Tindaga k’ofa take surfa ruwan bala’i.... “Inyi haka kawai, a d’auki alak’ak’ai a lanjab’awa jikana toh wllhi bazai sab’u ba, yo bacin zaman hak’uri da yakeda ita mai zaiyi da ita.... Idan baza’a hukunta ta ba toh wllhi ni da kaina zan guntule wannan aure jikana ya huta... Kan me yaro sai wahala da jarababbiyar yarinya yake wacce sam babu alkhairi tattareda ita....!” Aunty ta mik’e cikeda nuna damuwa tana fad’in “Yi hak’uri Mamani kada jininki ya hau..... Allah baya son mutuwar aure ki daina fad’in haka, Zauna....” Ta k’arashe tana zaunar da ita bisa sofa tana mai ci gaba da tausarta... Shiko Hafiz hula gaban goshi sai wani hure huren hanci yake yanajin ya isa..... Abbah ya dubi Hafiz kana yace “Mai ta maka wannan karon.....?” Babu kunya balle tsoron Allah Hafiz ya soma fad’in...... “Abbah jiya Zulfah har gida taje taci mutuncin Hajiyana itada k’anwar Mhaifiyarta Bara’atu, sosai ran Hajiya ya b’aci sanda take sanar dani amma ban d’auki wani hukunci kan abinba, yau nace taje ta baiwa Hajiya hak’uri toh shine ta d’ibi k’afa ta tafi taron ‘yan siyasa ashe dama wai itama har siyasan ta shiga tana tara min matan unguwa a gida idan bana nan.... Gaskiya Abbah ni na gaji da zama da Zulfa’u dama dai darajarka takeci....” Ya k’arashe yana mai d’aga kai sama... Mamani ta kuma gyara zama daga saman sofa tana fad’in “Kaji koh ka daiji da kunnuwanka kuma idan har Hafizu ya saketa ina mai tabbatar maka babu mai kwasanta tinda shima jininta ya kasa da ita....” Abbah da zuciyarsa ke masa matuk’ar k’una sauk’e ajiyan zuciya yayi kana ya dubi Mamani yace kiyi hak’uri Mamani amma abin baikai ayi saki ba ai.... Lami tashi ki kiramin Zulfa’u....” Ya k’arashe yana duban Aunty Lami... Jiki na rawa ta mik’e ta nufi sashen Mamy, kafin ta isa sashen Mamy ta keb’e ta shiga neman layin aminyarta... Wata uwar shewa suka sake daga cikin wayar kafin Aunty Lami taci gaba da fad’in “Na gaya miki Kakar ta tasosa gaba sun taho neman saki, amma fah kinsan banaso ayi sakin nan yanzu gwara tayita yawo a tsakani ita baga zawarci ba ita baga aure ba, bata a gidan uban bata a gidan mijin, kullum tana bisa layi....” Suka kuma k’ek’yata dariya kafin Aunty tace “Zan kiraki anjima barin k’arasa kada suji shiru.....” SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _..............DA RAO_ *09* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Da sallama ta shigo parlorn kanta a k’asa Aunty Lami na biyeda ita.... Hafiz da Mamani suka rakatada mummunar kallo.... Abbah kuwa bayan abubuwan da Hafiz ya zayyano tayi ji yayi tamkar ya mik’e ya tufetada duka... Cikinsu babu wanda ya amsa sallamarta dukda sanin darajan sallamar, daga can gefen carpet ta risina had’ida furta “Abbah gani nan.....” Saida ya kwashe mintoci kusan uku kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Mai ya had’aki da mijinki...?” Tasan maganan bazai wuce wannan ba dama, a hankali ta d’ago ta dubi sashen da Hafiz yake, hularsa gaban goshi saima shafa wayarsa da yake alamun babu abinda ya shalleshi, tausayin kanta ya kuma rufeta... Muryar Abbah ta kuma tsinkayowa cikin fad’a wannan karon “Tambayarki nake, Mai ya had’aki da mijinki...?” Kafin ta samu zarafin bada amsa Mamani ta cafe “Yo ina zata amsaka tunda tasan batada gaskiya, nidai kawai a sakarwa jikana mara a rabasa da annoba ehe....” Bud’e baki tayi zatayi magana amma sai taji kuka yazo bakin nata, k’ok’arin saita kanta tayi dukda rawa da muryarta keyi kana tace “Abbah babu komai....” Mamani ta daka shewa daga zaune kana tace “Kaji ja’ira yo dole kice babu komai tunda kinsan bakida gaskiya..... Munafuka kawai...” Abbah ya kuma duban Hafiz kana yace “Maimaita abinda ka fad’i... Take Hafiz ya maimaita ko gizau babu a tattaredashi saima cewa “Abbah gaskiya aja mata kunne sosai don gaskiya banso ace na b’ata zumunta sabida taurin kunne irin nata....” “Yo zumuntan ma ya b’aci mana sai mai me akeda annoba wacce tun haihuwarta babu alkhairi....” Mamani ta fad’i Kasa daina dubansa tayi hawaye basu daina gangaro mata ba... Cikin rawar murya ta furta “Ya Hafiz kaji tsoron Allah....” “Da tsoronki zaiji.... Ja’irar banza...!” Mamani ta kuma fad’i yawa zata dunguro daga saman kujera.... “Zulfa’u da gaske mijinki ya hangoki cikin taron siyasa kuma bashi ya baki izinin hakan ba...?” Abbah ya kuma jefo mata tambaya... Zulfah na hawaye take jinjina kai lokaci guda take fad’in “Eh Abbah da gaskene amma Abbah....” Cikin daka tsawa ya dakarta da ita kafin yaci gaba da fad’in “Wllhi wllhi kinji na rantse miki kika kashe aurenki bazaki zauna min a gida ba don bakida muhalli cikin gidan nan, muhallinki shine can d’akin mijinki, duk randa kika kaisa bango ya sakoki ki nemi wani gidan uban ba dai gidana ba kinji na fad’a miki.....”. Daga haka mik’ewa yayi ya wuce d’aki ba tareda ya kuma bi takan kowa ba.... Mamani da Hafiz suka mik’e a tare Hafiz na fad’in “Kin gani koh Mamani na fad’a miki wannan annobar bazan tab’a rabuwa da ita cikin dad’in rai ba, ni na sani Abbah hak’uri kurum zai bani.... Nidai kawai an cuceni wllhi....” Ya k’arashe yana ficewa had’ida bubbud’e hanci.... Mamani ta mik’e tana d’angwala k’afa ta isaga Zulfah dake nan durk’ushe a wajen ta shiga surfa mata bala’i kai kace rufeta da bugu zatayi, Aunty Lami sai faman dannar Mamani take cikin zuciyarta kuwa banda rawa da murna bata komai, burinta ya cika tunda bata tab’a haifa ba ita wacce ta haifa d’in dangin babu ne tunda babu mai k’aunar yaran, ta jima tana tsara hakan a rayuwarta bazata bari Mamy ta rik’e gida ba ta haifi yara sannan ta sami soyayya da kulawan kowa, ta d’au alwashi INDA RAI saita tarwatsa farin cikin da tadda Mamy da Abbah a cikinta, sai ta haifar masu da tashin hankali wacce batada ranar k’arewa, saita haifar da gaba tsakanin Mamani da ‘ya’yan Abbah tunda ita bata samu daman haifa mata koda jika guda ba, sannan sai ta zama tauraruwa a gidan dukda cewa itace batada tilon d’ah a gidan... Saita dasa soyayyarta a zuciyar kowa baga Abbah ba baga Mamani ba kai harma Mamy da yaranta sai ta sayi soyayyar kowa ta yanda zata zamto tamkar hasken rana a gidan wanda ke gusar da hasken lantarki, ya zamana ba’a ganin kowa sai ita.... K’iris ya rage Hafiz baiyi karo da Nabila ba wacce tayi k’ebebe a bakin k’ofar... Banda uwar harara bata aika masa komai, yasan bazata gaishesa ba bazata kuma basa hak’uri ba koda zasu bagaji juna ne hakan yasashi rab’an ta gefenta zai wuce don sarai yasan wacece Nabila... Har yakai bakin farandar ya tsinkayo muryar Nabila tana fad’in “Duk wanda bai daraja mace ba babban alamace cewa baya daraja uwarsa....” Hafiz ya dawo da baya shaye da mamaki yake dubansa, shi Nabila ke fad’iwa magana a haka yana a matsayin yayansu gaba d’aya gidan koda ace baya auren Zulfah.... Dawowa yayi da baya yanda take nan a tsaye d’ankwalinta gaban goshi.... “Ke ni kike fad’awa magana...?” Ya tambaya yana faman huci... Dad’a turo d’ankwalin gaba tayi had’ida basa k’eya kana taci gaba da fad’in “Idan mutum ya tsargu yasan halinsa ne toh shakka babu dashi ake...” Hafiz ya tunzura ya d’aga hannu zai kwad’a mata mari tayi saurin duk’awa k’asa ya mari iska wanda saida k’arfin marin ta kusan aikasa k’asa badon k’ofa da ya dafe ba da ya tafi ya zube a k’asa... Ya d’ago yana huci yake kuma k’ok’arin k’arasowa gabanta yana fad’in “Ni sa’anki ne Dan ubanki... Ni zakima rashin kunya...?” Dariyan rainin hankali tayi kafin lokaci guda ta had’e fuska tace “Wllhi wllhi na girmi duka yanzu a gidan nan, kuma uba baifi uba ba Allah ka sake zagina sai na rama....” A daidai lokacin da Zulfah ta k’araso wajen bata jira komai ba ta wanke Nabilah da mari tana faman huci, bata daina mamakin kalaman da taji k’anwar tata na fad’iwa mijinta ba wanda yake a matsayin Yayansu gaba d’aya... “Addah kika mareni kan wannan ungrateful mijin naki....” Bata kai aya ba Zulfah ta fuzgo hannunta suka wuce tana fad’in idan batayi shiru ba zata k’ara mata.... Shi kuwa Hafiz har suka b’acema ganinsa mamakin Nabila yake, bai tab’a tsammanin rashin kunyar Nabilah ya kawo nan ba, lallai dole ya d’au mataki kan yarinyar nan don ko yayarta bata isa ta masa haka ba balle ita... K’ararramar yarinya da ita... INDA RAI sai ya cirewa Nabilah rashin kunyarta... K’wafa yayi kana yasa kai ya fice daga gidan zuciyarsa na masa k’una, dama ko yazo gidan iyakacinsa parlorn Abbah Mamy kuwa ba zuwa gaisheta mussamman yake ba dukda a matsayinta na sirkarsa saidai idan sun had’u a hanya ko a parlorn Abbah ya gaisheta amma bai tab’a taka parlornta da sunan gaisuwa ba... Nabila ta dafe k’uncinta tana duban Mamy da Zulfah dake faman surfa mata fad’a kan rashin kunyar data kuma b’ullo dashi a ‘yan kwanakin... Kuka Nabilah keyi tana fad’in “Wllhi Mamy Allah baku kyautawa, ita fah Addah tsoron Yaya Hafiz take sai ta tsaya yana mata cin kashi da cin mutunci, Mamy bakiji abinda ya gama fad’iwa Abbah ai na lab’e bakin k’ofa naji komai, wllhi Mamy wulak’ancin da yayiwa Addah kare bazaici ba, ko shine autan maza sai taci gaba da zama dashi.. Idan Abbah yace zata bar masa gida babu gidansu Aunty B ne babu gidajen danginki ne Mamy, ina aka tab’a aure da cin zarafi.....”. Zulfah ta katseta cikin daka tsawa “Babu ruwanki da rayuwar auren da nake sannan Ya Hafiz ba sa’anki bane da zaki masa rashin kunya da rashin mutunci, idan kullum muzguna mun yake babu ruwanki ban buk’atan damuwarki cikin rayuwar aurena kinjini koh....” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Su duka biyun hawaye suke daga ita har Nabilan da bata daina hawayen takaici ba.... Zulfah taci gaba da fad’in “Allah na gani bai mance dani ba, sannan shi ya k’addara min wannan aure, kuma bana fata na zamto sanadiyan tashin hankalin Abbah... Inda rai da rabon wata rana Allah zai ya sarremun lamurana nayi imani zai sauk’ak’a min ta yanda banyi zato ba banyi tsammani ba kinji koh Sister... So please na rok’eki stop meddling, ki daina shiga kinji, wata matsalar kurum zaki kuma haifar mun.....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Rungumeta Nabila tayi su duka suna hawaye mai ban tausayi, Mamy tasa bayan hannu ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta shiga tsakaninsu ta janyosu suka nufi d’aki Mamy na rungume da kafad’ar ko waccensu.... Nasiha ta kuma yimasu gameda rayuwar duniya da matsayi da kuma ribar hak’uri, gaba d’aya yaran nata ta had’e ta masu nasiha harmada Marliya wacce take autarsu... Bayan magrib Mamy da Aunty Lami suka kuma tausar Zulfah suka umarceta da ta koma d’akinta kafin Abbah ya dawo gida ya taddata... Aunty Lami ita tayimata rakiya har d’akinta ta kuma bata baki da nasihan hak’urin zama da miji musamman irin nata mijin... Sosai Zulfah taji dad’in shawarwarin Aunty Lami harda tayata daura abinci kafin ta wuce gida da shike ba itace da girki ba Mamy ce.... *** Bai tashi dawowa gidan ba sai wajajen 11:30pm lokacin har ta soma gyangyad’i a parlor wai donma tana kallon shirin fina finanfinan India da ake nunawa a tashan mbc bollywood.... Baiji mamakin ganinta ba don yasan zata dawo... Ya jima yana tsaye yana k’are mata kallon wulak’anci kafin ya daka mata wani uban tsawan datajisa uwa a mafarki... “Ke!!! Ba cewa nayi kije gida ba sai na nemeki, mai kuma ya dawo dake....?” Baccin da takeji ya watse itakam halin nasa ya daina bata mamaki saima tsoro... Gyara kwanciyarta tayi kana tace “Wanda ka kai masa k’ara ne yace na dawo sanin kanka darajarsa kake ci nake zaune gidanka...” Daga haka juyawa tayi ta basa baya Yayi k’wafa had’ida jinjina kai kafin ya fad’a d’aki, tana jinyo sanda yayiwa k’ofar sakata... Tayi k’ok’arin danne k’uncinta tana duban sashen da abincinsa ke ajiye, a hankali ta gyara kwanciyarta had’ida lumshe idanu dukda baccin ya k’aurace mata... A haka rayuwa taci gaba da wakana, a b’angaren su Sameer kuwa ana gobe zai taho Kano kusan kwana Siyama tayi tana zuba masa shagwab’a, gaba d’aya saiji tafiyar ta fice a ransa, ji yayi tamkar ya rubuta resignation letter ya zauna da Partner d’insa amma taimakon al’umma na d’aya daga cikin manyan burikansa na rayuwa.... Washe gari ma da k’yar suka rabu da juna yanda kasan wata uwa duniya zai tafi.... K’uri Sultan ya masu sanda Sameer ya kuma kirawo sunanta “Partner..!” Juyowa tayi tana dubansa kana tace “Ka mance wani abu...?” Saida ya d’ibi wasu dak’ik’ai yana dubanta kana ya kashe mata idanu guda kafin yace “I love you....” Murmusawa tayi sannan tace “I know Partner... Drive safe....!” Ta k’arashe tana cuno masa baki gaba alamun kiss.... Kaman kar ya daina dubanta haka yakeji, shi kuwa Sultan dake zaune gaban motan idan ransa yayi dubu ya b’aci kai kace akansu aka soma soyayya, saikace wanda zasu shafe watanni ba tareda sunga juna ba sannan ya tabbata daren jiya kwana sukayi suna abu guda.... Cikeda takaici ya ciro wayarsa a aljihu yana shafawa.... Jiki a sanyaye Siyama ta dawo cikin gidan sai tanaji gaba d’aya ya mata girma, tsayuwa tayi gefen madubin console tana duban hotonsu dake cikin k’aramar frame a hankali tayi murmushi tana shafawa kana tace “Allah ya kaimun kai lafiya Partner.....” Da dare tayima gaba d’aya sai taji babu dad’i, ta bud’e closet d’insu tana tunanin kayan baccin da zata saka, da ace yana nan k’ila da wannan zai zab’a mata, ko kuma wancan... Haka tayita tunani ko wanne ta d’auko sai ta mayar tana tunanin bashine Partner zai zab’a mata ta saka ba, gaba d’aya sai taji sabon tashin hankalin rashinsa na taso mata... haka nan a kitchen ma ta gama galantoyinta tana tunanin mai zataci, da ace Partenr na nan da ya dafa masu abinci mai sauk’i idan basuyi order ba.... K’walla suka ciko idanun Siyama sanda ta kwanta bisa gadonsu taji gadon ya mata fad’i.... Can k’arshen gado ta tak’ure had’ida rungume pillow hawaye na gangaro mata tsananin kewar mijinta na addabarta, ta mastu gari ya waye ta fice office ko zataji sanyi koda kuwa zata had’u da Khalid ne suyi fad’a... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *10* Washe gari daga office koda ta dawo gida wasu ‘yan kayayyakinta ta had’a cikin k’aramar akwati kafin ta d’auki hanyar gidansu...,Kallo guda zaka mata ka fahimci tsan tsan damuwar dake tattareda ita.. Babu kowa a parlorn sai k’aran alarm ta dafuwar oxtail dake tashi daga kitchen, mik’ewa tayi saman sofa ta d’an kishingid’a had’ida lumshe idanunta, tanajin sanda Malam Sallau ya shigo da suitcase d’inta ya ajiye daga bayan parlorn yana mai fad’in “Hajiya ga jakar a nan...” Ko zarafin amsashi Siyama bata samu ba har lokacin idanunta a lumshe suke, wasu irin tunani marassa kangado masu tada hankali su suka addabeta, yanzu idan Partner ya kasa jure rashinta kusanshi fah? Idan ya fad’a wata rayuwar fah..? Ko kuma idan yace zai k’ara aure fah... Shin waima da wasu irin mutane zaike huld’a....?” Ire iren tunanin dake zuwa zuciyarta kenan har Kubura mai aikin Ammi ta shigo parlorn Siyama bataji shigowarta ba... Turus Kuburan tayi tana duban Siyama dake kwance saman sofa idanu a lumshe ko takalmin k’afarta bata samu zarafin cirewa ba dashike d’aure yake da belt... Kubura ta kuma juyawa ta kalli akwati a gefe... D’an k’arasowa ta shigayi cikeda risinawa tana kiran Siyama... “Aunty..! Aunty..!!!..” Shiru Siyama bata amsa ba... Saida Kubura ta d’an buga kujeran kad’an tana k’ara fad’in “Aunty....” Sai sannan Siyama ta bud’e idanunta had’ida d’an yamutsa fuska... “Aunty lafiya kuwa...?” Kubura ta tambaya... A kaikaice Siyama ta dubeta fuska babu walwala kana tace “Banson gulmarku ta masu aiki d’auki jakata ki haura min da ita sama d’akina...” Kubura ta jinjina kai tana fad’in “A’a wai Aunty gani nayi kaman bakida lafiya shiyasa na tambaya....” Gajeren tsaki Siyama tayi don ta tsani shiga sharo babu shanu irinta ma’aikatan gidan Ammi musamman Kubura, kallon data watsa mata yasa bata kuma cewa komai ba ta ciccib’i jakan tana washe hak’wara don ko babu komai zatake samun na kashewa don Siyama akwai sake hannu shiyasa duk ma’aikatan gidan ke bata girma kama daga masu gadi har ma’aikatan cikin gidan itadai barta da basarwa wanda usulin d’abi’artace miskilace ta gaske ba kasafai take shiga hark’an mutane ba shiyasa ko k’awaye basufi a k’irga ba wanda takedasu, tanada zafin rai abu k’ank’ani ke b’ata mata rai hakan yasa duk wanda yasanta yake shan maganin zama da ita... Da yawan mutane sukan d’auketa mace mai gadara da isa da ji da kai wasu kuwa kan d’auki hakan da cewa goyon data samu ne na sangarci daga gidansu... Idan kaji hayaniyar Siyama toh fah ka tabbata Khalid ne ya tab’ata shiyasa mahaifinta ya d’auki muk’ami mai girma a kampaninsa ya damk’a mata.... Ammy dake zarya cikin makeken d’akinta tana waya nan ta hangi Kubura da jaka nik’inik’i tana haurowa zata shige d’akin Siyama... A’a mamaki ya kama Ammy cikin sauri ta katse wayar da take kana ta tsare Kubura da fad’in “Ke ke yaya wannan fah...? Daga ina....?” Kubura na haki take fad’in “Ammy Aunty Siyama ce tazo tana parlorn k’asa tana kwance, Ammy inaji dai babu lafiya ne don baki ganta ba gaskiya.....” “Ke ya isheni bani hanya na wuce....” Ammy ta katseta sanda take sauk’owa daga bene cikin tsananin tashin hankali.... Kwance ta hangi Siyama har lokacin.... Cikin sauri Ammy ta k’arasa gareta..... **** Kallon juna sukayi a karo na biyu kafin suka kuma tafe hannaye suna shewa irinta aminan asali, Hajiya taci gaba da juya super wax d’in dake hannunta kana tace “Ke Lami bakida kyau kin rantse sai kin mallaki tsohuwar nan...” Aunty Lami ta kuma juya idanu kana tace “Ai idan sunsan wata basu san wata ba, nid’in nan dai da a baya aka ambata da juya mujiya merere wanere sai an dawo ana bina tako ina... Sai na zamto almiski duk yanda na shiga na bar k’amshina....” Hajiya rik’e da hab’a take duban Aunty Lami kana suka kuma saka shewa, Hajiyar Hafiz tace ya labarin aminyar sirri....?” A tare suka kwashe da dariya kana Aunty Lami tace “Zancen kike nema bara kiga na tashi na tafi kafin Abbah ya dawo daga kasuwa don yau zai komo d’akina gwara naje na masa shiri tinda ita wancan bataga kwanciyar hankalin ba ma ballanta ta tsaya kulada miji....” Ta k’arashe maganar tana tura zanin cikin bak’ar leda.... Hajiya ta mik’e tana gyara d’aurin zani take fad’in “Ai ni babban abinda kemin dad’i shine yanda Mamani ke matuk’ar k’aunar Hafiz sam bata ganin laifinsa idan kuwa baki mance ba a baya itace dai tak’i jinin d’ana ta d’auki son duniya ta d’aura kan Ma’aruf yaronda sam ashe ba mai zama bane k’ashinsa ya jima da daddagewa cikin k’asa....” Aunty Lami tace “Hafiz kam ai d’an albarka ne tinda ya zage yake cimin uban yarinyar nan da kyau yanzu babu wacce ta tsayamin a wuya kaman wancan yarinya figeggiya marar ta idon nan...” “Nabilah koh...?” Inji Hajiya dake yamutsa fuska... “Keda kika sani, shegiyar yarinya gaba d’aya ta tsayamin a wuya tamin k’ebebe na rasa ta yanda zan b’ullo ma lamarinta.....” Hajiya tayi k’wafa kana tace “Kar ki damu k’awata itama haka zamu samo hanyar da zamu sabautar da rayuwarta, idan Mariya taga yaranta gaba d’aya suna wahala a gidan aure itama hankalinta sam bazai kwanta ba tinda dai dama itama ba dad’in takeji ba...” Aunty Lami ta jinjina kai kana tace “Shikenan ni zan wuce sai kinji wayata yanda muka kaya da sirkarki...” Suka kuma tafe hannaye had’ida shewa kafin Lami ta fice.... *** Ammi na k’arasowa yanda take wayar Siyamar ta d’au ruri, tamkar wacce aka zabura haka ta mik’e ta d’au wayar tana dubawa, hannayenta har rawa suke, hotonsa da ya bayyana da sunan Partner ya sanyatayin k’urima wayar, tun jiya take neman layinsa baya shiga tun bayan da ta kira taji isarsa, ta kira Sultan ma don taji ko lafiya saidai Sultan d’in ya sanar da ita sun rabu tun da rana don shi Abuja ya wuce... A hankali ta saita kanta kafin ta d’aga wayar.... “Partner....” Ya fad’i daga d’aya b’angaren cikin sassanyar muryarsa... Maimakon tayi magana sai kukan da ta sake masa.... Sameer yasan hakan ka iya faruwa, cikin kwantar da hankali ya soma fad’in “Siyama what’s wrong, meke faruwa...?” Cikin kuka take fad’in “Really Partner..? Are you seriously asking me that question...? Kasan sau nawa nayi trying layinka baya shiga, I was so worried about you, amma kai da alama baka damu kasan halin da ka barni ciki ba....” Ta k’arashe cikin tsananin b’acin rai... A hankali ya shafi sumarsa had’ida fuzar da iska kana yace “I’m sorry... Ki daina kuka kinji, I’m at work right now, we talk later kinji... I love you....” Daga haka bai jira cewarta ba ya katse wayar... Da tsananin mamaki take duban wayar.... Bata daina duban wayar ba take fad’in “He hangup on me....” Tayi saurin juyowa ta dubi Ammi dake zaune gefenta ta mata k’uri kana tace “Ammi Sameer ya bar sona, kin gani fah kashe wayar yayi, aikinsa yafi mahimmanci a wajensa fiyedani....” Rungumota Ammi tayi kana tace “Siyama don Allah ki kwantar da hankalinki ni irin wannan soyayya da kikewa Sameer har tsoro yake bani, shifa namiji ba’a nuna masa soyayya irin haka sabida b’acin rana, nasha fad’a miki ki koyi son abu baya baya irin wannan ne randa ya bijiro miki da halinsu na maza sai ki shiga damuwa koma ki jawa kanki wani cutan...” Shiru tayi tana duban Ammi zuciyarta na gaya mata wani abu, kardai maganganun Ammi su tabbata watarana Sameer ya rabu da ita.... Take taji gabanta yayi mugun fad’uwa lallai kuwa zata iya rasa rayuwarta idan irin wannan ranar tazo.... Duban Ammi ta kumayi kana tace “Ammi kina ganin Sameer zai iya rabuwa dani...?” Ammi ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Bance zai rabu dake ba Siyama amma ki sani ita rayuwar nan komai ka iya faruwa, ba lallaine rayuwarmu ta tafi yanda muka tsara muke kuma so ba, wasu lokutan dole a samu sauyin lamari, kuma dole musa a ranmu komai ka iya faruwa ballanta namiji da sam baida tabbas, kina ganin abinda Babanku ya min yaje yayi aurensa a can wata k’asar ba tareda sanina ba, ba don zuwan social media ba k’ilada har yanzu bamusan nada wata matar ba... Kuma yanzu da haihuwa ta shiga tsakaninsu haka zaku tashi bakusan kunada wasu ‘yan uwa ba... Ke ya kamata kifi kowa d’aukan darasi tinda kece mutum ta farko da kika gano Daddynku has another wife....” Tsoro da fargaba suka kuma kama Siyama, wannan dalili dama shiyasa ta zamto very paranoid, duk yanda mijinta yake tsoro da damuwar abunda ka iya zuwa yazo shike damunta, damuwarta kar Mijinta ya mata irin abinda mahaifinta yayiwa mahaifiyarta, so tari takan yarda Sameer na tsananin k’aunarta amma idan ta tuna yanda suka taso suka tadda iyayensu cikeda k’aunar juna sam bazakayi tunanin Daddy zai iya k’ara aure ba tareda sanin Ammi ba, wannan dalili yasa wani sa’ain take samun shakku dukda irin kula da soyayya da Sameer ke nuna mata, don bazata mance ba lokacin data gano Daddy nada wata matar ta hanyar facebook har saida tafi mahaifiyarta shiga tashin hankali, da k’yar ta yafewa magaifin nata don da ta d’au alwashin barin gidansa ne na har abada, shi kuwa a duniya yaransa sune rayuwarsa.... Da wannan tunani da maganganun Ammi yasa jikin Siyama yin matuk’ar sanyi, k’ok’arin danne zuciyarta tayi had’ida kashe wayar gaba d’aya don karma ta kasa jurewa ta kuma neman layin Sameer.... **** Tun daga waje yayi sallamada muk’arabban nasa don ba k’aramin gajjiya yayi ba burinsa ya shiga gida ya huta, yinin yau ranar sunyisa ne suna yawon campaign k’auyuka k’auyuka.... Baiyi mamakin ganinsu zube a parlor ba ko wacce ta rungume teddy bear d’inta tana bacci, k’aramar mai kimanin shekaru uku kwance cinyar ‘yar matashiyar mai kimanin shekaru shida su duka suna bacci, shi kuwa babban mai kimanin shekaru goma yana can gefe da alama shima gajjiya da buga game d’in yayi har bacci yayi awon gaba dashi.... A hankali yasoma takowa cikin parlorn had’ida k’urawa yaran nasa idanu cikeda tsananin tausayi da b’acin rai, har abada baijin Muhibbah zata samu lokacinsa dana yaransu, a baya yakan sakama ransa cewa INDA RAI da rabon ta daina a gaba amma ya lura hakan abune mai matuk’ar wahala, wannan shine rayuwar da Muhibbah ta girma akai ta kuma saba, so tari a baya sukan shirya tafiya k’asashe da ‘yan uwanta da iyayenta ba tareda saninsa ba wasu lokutan ma saidai yaga ana processing visa da sunan zasuyi tafiya Dad ya shirya tafiya zuwa k’asa kaza da yaransa gaba d’aya, bai isa kuma ya nuna k’in amincewarsa ba ko rashin yardarsa sai nasa mahaifin yayi fushi dashi, dashike Muhimma d’iyace ga aminin mahaifinsa, tun a lokutan baya kenan kafin mahaifinsa ya rasu, sannan lokacin da mahaifinsa ya kusa rasuwa saida ya kuma masa kashedi akan ya rik’e Muhibba ko mai zata masa idan har yana son gamawa da duniya lafiya wannan dalili yasa duk wani abunda Muhibbah zatayi yake k’ok’arin kawarda kai, yakai ya kawo yanzu bada ‘yan uwanta take yawon k’asashen dataga dama ba da k’awayenta gogaggun ‘yan bariki take, dama sam zaman gidan kam batayi rayuwar yaran da komai Nannies ke masu, a baya kafin commitments su masa yawa shi da kansa yake kulada yaransa idan ta tafi gantalinta.... K’aramar ya soma d’agawa da niyyar kaisu makwancinsu nan ko ya hangi busassun hawaye kwance a fuskarta, ta kuwa yi saurin k’ank’ameshi tana ambaton Daddy alamun da kukan tayi bacci, tsam ya rungumeta had’ida kwantar da ita saman kafad’unsa yana jijjjigata yana lallashi alamun yanaso ta koma baccin kaman daga sama yaji k’aran takalminta mai tsini waya manne a kunne tana aikin waya da k’awaye kaman yanda ta saba, suna kuma zuzutata da haukatata da sunan First Lady..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *11* Yana jin yanda ta nufi upstairs tana rangad’a kirawa ma’aikatan gidan, sam batayi tsammanin samunshi a sashenta ba dukda cewa taga motocinsa waje ga securities da suka k’aru hakan ya tabbatar mata yana gida.... Ta cikin k’ofar glass da ya raba staircase da cikin parlorn ta hango bayansa rungume da k’aramar ‘yarta mai suna Najma, saida ta juya idanunta kafin ta soma takowa ta shigo cikin parlorn tana fad’in “Ya akayi Murja ta barsu sukayi bacci a parlor, Gosh! I really don’t know what’s wrong with her, saida na fad’a mata ta tabbata ta kaisu d’akunansu don mai zata barsu zube a nan...?” Tunda ta soma magana k’ala bai ce mata ba har Murja ta k’araso a guje cikeda d’imauta ganin irin muguwar kallo da uwar gijiyar tata ke aika mata.... Aiko kafin ta samu zarafin magana tun daga nesa Muhibbah ta tsareta da fad’in “Murja what’s meaning of all this, me nace miki kafin na fita... Ta yaya zaki bar min yara zube a nan kaman sun rasa gatansu, kinacan kin sake bakida hanci kina shegen kallon nan naki koh...?” Cikin sark’ewar murya take fad’in “Haj... Hajiya kiyi hak’uri dama Irfaan ne yace zaiyi game bazai kwanta ba shine k’annen ke kuka saidai su zauna dashi shiyasa.....” Bata kai aya ba Muhibbah ta kuma darara mata tsawa... “Ni dallah rufe min baki before I lose my patience completely...” Cikin kid’ima ta kuma nufo mahaifin yaran zata karb’i k’aramar jiki na rawa.... Girgiza mata kai yayi kana yace “Jeki abunki...” Ya fad’i a tak’aice Cikin risinawa ta kuma basu hak’uri da alk’awarin hakan bazai kuma faruwa ba kana ta fice.... Kafesa da idanu Muhibbah tayi ganin kota kanta baibi ba ya nufi upstairs da d’iyarsa.... Cak ya tsaya da tafiyar nasa sanda ya sinkayo muryarta tana fad’in “Meye ma’anar abunda kayi kenan... Yaya zan baiwa mai aikina umarni kace ta barshi...? Kuma dai kasan ba iya d’aukan yaran nan zanyi ba, don babu wanda zan iya d’agawa cikinsu...”! Ta k’arashe tana jifa da jakkanta saman kujera..... Baice komai ba haka nan bai juyo ya dubeta ba yaci gaba da tafiyarsa... Haka ya dinga sintirin kai yaran d’akunan baccinsu had’ida tofa masu azkar na bacci kana ya sauk’o don tafiya sashensa, har lokacin Muhibbah na make saman kujera tana faman ci gaba da waya... Baice mata ci kanki ba ya sunkuya ya d’auki agogonsa da links dinsa saman center table.... Tab’e baki tayi sanda ya fice kana ta mik’e ta nufi d’akinta don shirin bacci.... Kaman ko yaushe saida tayi wanka ta shafa mayukan k’amshinta masu tafiya da hankalin mijinta duk kalan fushin da yake ciki, tayi wasu ‘yan kimtse kimtsen da take kafin bacci kana ta nufi sashen mijin nata.... Bata sameshi cikin d’akin ba hakan ya tabbatar mata cewa band’aki yake don tana iya jiyo zuban ruwa daga yanda take kwance saman gadonsa.... Sam bai kula da ita ba don hankalinsa naga warware hannun jallabiyar dake jikinsa da alama alwala ya d’auro... Kallo d’aya ya mata yaji zuciyarsa na masa tsananin k’una, wato Muhibbah tasan lagonsa tasan shi wane iri mutum ne, tunda ba wata matar yakedashi ba babu yanda za’ayi ya iya k’aurace mata shiyasa take abunda taga dama don tasan duk fushin da zaiyi zai dawo gareta... Bata ankaraba taji dakakkiyar muryarsa na fad’in “Tashi ki ficemin a d’aki, kuma kar na kuma ganinki cikin d’akin nan kinajina koh....” Da tsananin mamaki take dubansa kana tace “Ban gane ba, ni kake kora....?” “Do I need to repeat myself... Ki tashi ki fice nace..!!” Wannan karon cikin tsananin daka tsawa yayi maganar wanda saida ya figita Muhibbah ta mik’e babu shiri.... “MA’ARUF ni kake kora daga d’akinka, ka mance abinda Baba yace maka akaina...?” A zuciye yayo kanta yana k’ok’arin kai maita mari sabida tuno tarin kuncin rayuwar data jefasa ciki dukda kyakkyawan alak’arsa da jama’a, bai marenta ba sai sauk’e hannunsa da yayi tamkar ya tuna wani abun kana yace “Get out....” Kallo ta bisa dashi don bata tab’a ganinsa cikin tsananin b’acin rai irinta yau ba... Sa kai tayi zata shige tana fad’in “Fine zan fice maka a d’aki amma ka sani nima duk randa ka kwaso buk’atarka ka kawo gareni zan rama, kuma idan akan yara ne ai sunada Nanny mai kuladasu sannan yawan fita da nake ai gani nayi campaign nake maka....” Bata kai aya ba taji ya damk’ota ya dawo da ita cikin d’akin yana mai ci gaba da huci.... Idanuwansa sun kad’a sunyi jazir yake fad’in “Idan kina tunanin ni Ma’aruf zan nemi wani abu you’re very much mistaken, albarkacin Abbah kike zaune a gidan nan, sannan daga rana mai kaman ta yau ki sani bani buk’atar komai daga gareki, idan kinga dama yawonki ya kaiki har birnin sin babu matsalata ballantana damuwata, gameda campaign kuma I did not ask for your help nor your support, in fact I don’t need any of these from you.... Now, get out.... Get out I said....!” Ya k’arashe yana nuna mata tangamemen k’ofar d’akin dake bud’e... Da tsananin mamaki take dubansa kafin tasa kai ta fice zuciyarta na tsananin mata zogi, tana tafe tana mamakin itace yau Ma’aruf Mutallab zai wulak’anta, harda cewa baya buk’atar komai daga gareta...? Tabbas badon tsananin soyayyar da take masa ba da tuni tayi tafiyarta ta bar masa gidansa taji dad’in yawonta da kyau ba tareda fargaba ko tunanin miji ba, tana jin yanda Ma’aruf ya rufe k’ofar d’akin da k’arfin gaske... Tana isa sashenta ta fad’a d’aki ta d’au waya had’ida kiran aminiyarta Shamzy tana sanar da ita yanda sukayi da Ma’aruf.... *** Har wajajen k’arfe shad’ayan dare baiyi bacci ba, yana nan zaune a parlor yana ci gaba da dialing layinta amma baya shiga... Shamsu dake tasye jikin k’aramar fridge dake gefen parlorn kallo yabisa dashi jin yanata faman nanata abu guda.... “Com’n Partner.... Pick up your phone....” K’arasowa Shamsu yayi had’ida zama gefensa ya d’auki remote ya canza daga tashan labaru zuwa na movie kana ya maido da dubansa ga abokin nasa yace “Doc are you sure you’re alright...?” Fuzar da iska Sameer yayi kana yace “Bazaka ganeba abokina, Siyama has that nasty temper you know, abu k’ank’ani zai b’ata mata rai sannan sam bazatayiwa mutum uzuri ba.... Na tabbata fushi tayi, She is not answering any of my calls... And I miss her... so terribly....” Murmushi Shamsu yayi kana yace “Then give her space, ka barta ta huce idan Allah ya kaimu gobe you call her again..” Jinjina kai Sameer yayi kana yace “Wai yaushe zakayi aure ne...?” Tak’aitaccen murmushi Shamsu yayi kana ya kurb’i ruwa yace “Lokaci muke jira Sameer, May be k’arshen shekara....” Sameer ya jinjina kai kana yace “Toh Allah sa gaskiyar kenan wannan karon...” Shamsu ya kuma darawa had’ida mik’ewa yana fad’in “Zancen kakeso Doctor....” Sameer ya jefa masa pillow yana fad’in “A daina yaudaran yaran mutane haka nan ayi k’ok’ari a nutsu waje guda, first thing tomorrow morning kafin na fice Surgery zan samu Mama da batun, zaka sani ne mayaudarin banza kawai...” Banda dariya Shamsu baya komai har ya shige d’aki, jimawa kad’an Sameer ya mik’e shima ya kashe kayan kallon ya nufi d’akin da aka masa masauk’i gefe da na abokinsa Shamsuddeen..... Misalin k’arfe 8:am suka fito a tare daga sashen Mama zasu wuce aiki, Sameer sai dariyar sille Shamsu da Mama tayi yake, dole ne itama taso taga tilon d’anta ya ajiye Iyali amma sam aure baya gaban Shamsu... A haka har suka shige motocinsu Shamsu na shak’e da Sameer ganin yanda ya biyewa Mama suka masa tas... Kallo ya dinga bin ginin unguwar dashi yanajin wani sanyi cikin zuciyarsa, baisan dalilin jin hakan ba amma can k’asan zuciyarsa ji yake tamkar ya tab’a zuwa wajen, ko wucewa ko wani abu mai kama da haka, gashi dai unguwar mai yawan jama’a ne da hayaniya ba kaman unguwannin da ya taso cikinsu ba tsawon rayuwarsa, dukda hayaniya da yawan jama’a dake cikeda wannan unguwa sai yaji dad’in unguwar da kwanciyar hankali fiyeda tunaninsa, da k’yar ya karb’i tayin Shamsu ya sauk’a gidansu da niyyan yin kwana biyu kafin ya samu nasa apartment d’in don da hotel ya nufa amma Shamsu fir ya hanasa a dole yazo gidansu ya sauk’a... Shamsu abokin Sameer ne wanda sukayi makaranta tare a can k’asar India, a lokacin baida amini sai Shamsu harta gidan da suka kama GIDA GUDA ne, iyayen Shamsu sunsan Sameer haka iyayen Sameer sunsan Shamsu, hasalima Shamsu idan ya tafi Kaduna gidansu Sameer yake sauk’a shiyasa wannan karon Shamsun ma ya dage sai Sameer d’in ya sauk’a nasu gidan.... Haka Sameer yayita bin unguwar da kallo murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarsa yanajin natsuwa sosai cikin zuciyarsa..... *** Tana zaune gefensa yana karyawa cikin shirinsa na tafiya kasuwa sai faman zuba santi yake tana jin dad’i da sanyi har cikin zuciyarta, gradually burinta suna kan cika.... Sai faman murmusawa take tana kwarkwasa... Abbah ya kuma tand’e hannunsa kana yace “Zuba min kunun rabin kofi, Aunty Lami tayi yanda yace Abbah ya shiga kurb’an kununsa yana lumshe idanu... Kaman daga sama suka jiyo sallaman Mamani rungume da turmin zanin da Aunty Lami ta kawo mata daren jiya, sai faman wage baki take tana ci gaba da k’waza sallama dukda cewa sun amsa mata sallaman nata.... Tuni Aunty Lami ta shiga murmusawa tana kuma sadda kai k’asa had’ida gaida Mamani... Cikin sakewar fuska Mamani ke amsata tana fad’in “Lafiya lou sirkar arziki, nazo nuna ma d’ana abin arzikin da akewa uwarsa ya shaida...” Aunty Lami ta kuma murmusawa tana fad’in “Haba Mamani wannan ai ba komai bane ni uwa na d’aukeki.....” Mamani tana amsa gaisuwar Abbah take fad’in “Kaji koh, kaji d’iyar albarka abinda take fad’i, uwa ta d’aukeni....” Abbah da tun bayan b’acewar d’ansa Ma’aruf da k’yar ake ganin murmushinsa sai gashi nan yana murmusawa a hankali kana yace “Lami kawo mata abincin...” Kafin Aunty Lami ta basa amsa Mamani ta katse sa da fad’in “Wa ai nikam ‘yar gata ce don ina tunanin kafin naka ya iso gareka nawa ya riga isa gareni...” Aunty Lami ta kuma sakin murmushi tana fad’in “Dole mu kula dake sosai Mamani ko don mu samu albarka rayuwarmu tayi kyau....” Haba nan fah Mamani ta kuma washe baki cikeda jin dad’i.... Mamy dake tsaye jikin k’ofar kasa shigowa tayi sabida tsananin sanyi da gwiwoyinta suka mata, take taji hawaye na neman ciko idanunta, a hankali tasa kai ta juya had’ida komawa d’akinta don ji tayi sam bazata iya shiga ba, tausayin kanta ne ya kamata sanda ta zauna saman gado had’ida rapka uban tagumi da duka hannayenta biyu hawaye na gangarowa saman k’uncinta..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *12* Tsaye take tana linke kayan wanki da bata jimada shigowa dasu ba, sam duba wayar mijinta ba d’abi’arta bace, hasalima sai wayar ta k’araci ringing d’inta koda baya kusa bazata d’aga ba sannan bazata duba ba har sai yazo da kansa ya d’aga ko kuma ya samu missed calls, wannan d’abi’ace da mahaifiyarta ta horasda ita domin samun zaman lafiya mai d’aurewa a gidan aurenta.... Sau biyu kenan ana kira batakai dubanta ga wayar ba har ta k’araci ringing d’inta dukda cewa wayar a gefen kayan da take linkewa yake, jin ana sake kira yasata kai dubanta ga k’ofar band’akin ko zai fito amma shiru saima k’aran zuban shower da take iya jiyowa ga uban sauti da ya k’ure a d’aya wayar tasa domin d’abi’arsa ce tun yana matashi idan zai shiga band’aki sai ya k’ure sautin wak’a har yayi aure bai daina, tayi tayi ta hanasa wannan d’abi’a amma abu yaci tura k’arashe ta yanke shawarin tayasa da addu’a... Tunaninta guda kodai Hajiya ce mai kira, k’ilama zatace azo a d’auki Kausar ce, take taji farin ciki ya mamaye zuciyarta annashuwa da annuri sun cika fuskarta sakamakon tuno d’iyarta da tayi.... Cikin sauri tayi jifa da rigar da take linkewa ta suri wayar tana duban screen d’in, dukda lamba ce kawai babu suna hakan bai hanata tunanin k’ila d’iyarta bace, jiki har na rawa Zulfah ta d’aga wayar ta k’ara a kunnenta ba tareda tace komai ba ga k’irjinta dake faman lugude... Daga d’aya b’angaren cikin tsananin fad’a Sawwama ke fad’in “Dole kaki d’aga wayata munafukin Allah ta’ala, shine zakace min babu komai tsakaninka da Zabba’u toh yau k’wai ya fashe har hoton d’akin da kuke watsewa a hotel an nuna min, wllhi wllhi Hafiz idan kana tunanin zaka iya fooling wannan shashashar matar taka toh ni baka isa ba wllhi sai na danna maku rashin mutunci daga kai har Zabba’un zaka zo ne ka sameni....” Daga haka katse wayar tayi cikin tsananin b’acin rai da huci... Zulfah dake rik’eda wayar tamkar gunki ko motsawa ta kasayi, maganganun Sawwama ke ci gaba da yawo cikin kwanyarta, ta kasa motsawa haka nan ta kasa ijiye wayar har lokacin wayar na mak’ale a kunnenta... A haka Hafiz ya fito daga bayi ya hangeta rik’eda wayarsa tamkar wacce aka dasa, take zuciyarsa ta shiga masa zafi domin idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine a d’aga masa wayarsa.... Tsawa ya daka mata daga yanda take tsaye amma ko gizau batayi ba saima dubansa da takeyi da idanunta da suka kad’a sukayi jazir har lokacin tana nan tsaye, da k’arfin gaske ya fuzge wayarsa a dai dai lokacinda hawaye mai d’umi ya sauk’a saman k’uncinta.... Bai daina huci ba ya shiga duba kiranda ta amsa, d’ago murtuk’ekk’en fuskar da babu alamun annuri cikinta yayi kana yace “Ubanwa yace ki amsa min waya....?!” Bata amsa shi ba haka nan bata d’ago idanu ta dubeshi ba.,,, Ya kuma daka mata tsawa “Nace da izinin ubanwa kika d’aga min waya...? Yaushema kika soma tab’a min wayata a gidan nan...?” Shiru bata bashi amsa ba... “Ba magana nake miki ba..!!” Ya kuma daka mata tsawa... Saida tasa tafukan hannayenta ta share hawaye suka sauk’o fuskarta kana tayi k’ok’arin saita kanta tace “Kayi hak’uri....” A tak’aice.... Huci kawai yake yana dubanta kana yayi k’wafa yaci gaba da fad’in “Sai kinyi abu kicewa mutum yayi hak’uri bayan ni hak’urin zama dake nake, an lik’amin ke ana tausana ana bani hak’urin ci gaba da zama dake matar da babu wani alkhairi a tattaredake face sharri.. Wllhi kinji na rantse zan maki kashedi na k’arshe duk ranar da aka kuma kirata kika d’aga sai na karyaki kafin na maidake gidan iyayenki su baki tarbiya da kyau, duk kuma abinda kikaji daga wayata ke kika jiyowa kanki don babu ubanda ya aikeki d’agawa... Jaka mai farar k’afa....” Yana gama yab’a mata munan kalamai yayi shirinsa abinsa ya fice yana neman layin Sawwama da tak’i d’aga kiransa.... Can k’uryar d’aki Zulfah ta rakub’e idnunta na mata wani irin barkono don kukan ma nemansa tayi ta rasa, wannan shine mijin da mahaifinta ya zab’ar mata zama dashi har yake ikirarin idan tayi abunda aka sakota babu ita babu shi sannan kada ta dawo masa gida ta nemi wani uban ba shi ba, ita kuma kalan tata k’addarar kenan, haka Allah yaso ya jarabceta, inama ace Hafiz ya tsaya a zagi da wulak’anci kawai, inama ace aure ya k’ara ba bin matan titi ba, shin wannan shine wanda iyayenta suka zab’ar mata tayi rayuwar sunnah dashi..? Wannan shine uban ‘ya’yanta da zasu tashi suyi alfahari dashi su nunashi suce ga mahaifinsu...? Shin idan iyayenta sun zab’ar mata wannan mutumin ita tayi adalci wa ‘ya’yan da zata haifa kenan....? Take wasu hawaye masu tsananin rad’ad’i taji suna gangaro mata... Ta jima tak’ure a wajen tanayin mai isarta kafin ta mik’e ta nufi band’aki ta d’auro alwala ta shiga mik’a kukanta ga Ubangiji wanda batada gatan da yafi Shi..... *** Tun bayan shigowarta office d’in tayi amai ak’alla sau uku kenan, harta coffee d’in da sakatariyarta ta kawo mata hamamin kawai saida ya sata k’waza amai, gaba d’aya ta zama pale and weak, batajin kuzari sam a tattareda ita ga tashin zuciya da ya addabeta, a halin yanzu bata buk’atan komai face hutu saidai zamanta a office d’in ya fiye mata don bataso Ammy ta fahimci halin da take ciki idan har abinda take zargi ya tabbata.... Wani aman ne yazo mata ta mik’e a guje ta kuma fad’awa bathroom tana kumayi... Tamkar zata amayar harda ‘yan hanjinta haka take nishi.... Da k’yar da dafe bango ta fito daga bathroom d’in yanda ta tadda aminiyarta k’wara d’aya tak a duniya zaune saman kujera mai kallon nata damuwa kwance saman fuskarta alamun taji yanda take k’waza aman.... Kallo guda Siyama tayiwa Laila ta d’auke kai kafin ta isa k’aramar fridge d’in dake a cikin office d’in ta d’auko chocolate tana afawa a bakinta ko zata sami sauk’in tashin zuciyar da ya addabeta.... Zama tayi saman kujerarta ta d’an kishingid’a had’ida lumshe idanu tana mai maida numfashi a hankali.... Kaman daga sama ta tsinkayo muryar Laila tana fad’in “Siyama wai bazakije asibiti ba kina zaune da ciwo, ki duba ki gani yau d’aya yanda kika lalace.... Gyara zamanta ta d’anyi kana tace “Laila bazaki gane ba, ni na rigada nasan abinda ke damuna amma saidai idan shid’in ne I’m not ready yet, Wllhi ban shirya zama uwa ba, ban shirya d’aukan responsibilities ba Laila not now....” K’uri Laila ta mata kana tace “Tirk’ashi, toh amma kema kinyi kuskure da kika bari kika d’auki ciki baki shirya ba...” Siyama ta jinjina kai tace “I know Laila, wllhi na sani shiyasa ma na kiraki don bansan yaya zanyi ba sauk’ina d’aya Sameer baya nan balle ya fahimci wani abu...” Laila ta tab’e baki kad’an kana tace “Toh yanzu da kika riga kika d’auki cikin me kike so ayi, nidai a nawa ganin kawai ki hak’uri ki haife abinki tinda dai dama bamu isa muce komai sai mun shirya ma zuwansa ba, just take the risks ki haifa kawai....” Banda harara Siyama bata aika mata komai, gajeren tsaki tayi kana tace “You’re not helping... Idan na haihu yanzu komai na rayuwata canzawa zatayi, harta d’anda na haifah can come between us nida Partner, maybe ma yafi son d’an sama dani sannan zan iya rasa attention d’in mijina gaba d’aya... Bama wannan ba kawai I’m not ready to become a mother......” Laila ta jinjina kai kana tace “Tun farko you shouldn’t be so careless, da ace kina taking precautions da ba’azo nan ba... Amma yanzu shawari d’aya ce idan har bakison haife cikin nan muje ayi flushing d’insa and start taking precautions kin fahimta...” Siyama ta jinjina kai a hankali kana tace “Then it has to be today, like right now don banso na koma gida a halinda nake ciki....” Laila ta jinina kai kafin Siyama ta mik’e ta rufe office d’in sukayi ficewarsu... Suna tafe a mota take ganin sak’on shi na shigowa, a hankali ta saki murmushi kana ta furta “I’m sorry Partner.... I love you too...” Da gefen ido Laila ke dubanta had’da tab’e baki, a haka suka karyi kwanan asibitin..... Siyama na hawaye ga k’irjinta dake bugawa haka ta shiga d’akin operation d’in nan fuskar Sameer na mata gizo cikin zuciyarta da k’wayan idanunta... *** Nabilah da Aunty B sukayi jigum jigum suna duban Zulfah da tun zuwansu a haka take ta kuma kasa sanar dasu meke damunta... Nabila ta yab’e baki tace “Aunty wllhi karma ki tambaya wannan mijin nata da danginsa sun k’unsa mata wani abin ne....” Zulfah ta aikawa Nabila harara kana ta dubi Aunty B dake dubanta a yagalgale kana tace “Aunty karki biye na wannan yarinyar ni wllhi babu komai kewar Kausar ne kawai ya addabeni...” Aunty B ta jinjina kai tace “Ehhh naga alama ai, kewar d’iyarki shiyasa fuskarki duk ta kumbura, idan kewar d’iyarkice karki damu don yau zata dawo gareki... Nabilah tashi muje...” Aunty B ta k’arashe tana sab’a mayafi... Nabila kaman akan k’aya take tuni ta mik’e tanaji tamkar sallah... Zulfah tayi saurin shan gabansu tana fad’in “Aunty don Allah ku barta kawai ai idan ta gama hutun za’a dawo da ita...” Idan gyalen Aunty B ya amsa itama zata amsa ko kula Zulfa’u batayi ba ta fizgo hannun Nabila suka fice Nabilar na kuma ingizata.... Dafe kai kurum Zulfah tayi tana ambaton Allah don tasan yau sai yanda ta kaya tsakanin su Nabilah da Hajiya da yaranta... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *13* Cikin sauri Zulfah ta koma d’aki ta zura hijab ta fice bakin layi sauri sauri tana neman adaidaita..... *** Raihana suka tadda tsakar gidan goyeda Kausar tana dakar d’anyar kub’iyar miyan dare ga k’amshi daddawa dake faman tashi alamun ta d’aura sanwa tuni.... Baki har kunne ta k’araso ta rungume Nabilah tana masu sannu da zuwa don ba barinta ake taje gidajen Baffahnin nata ba balle taga ‘yan uwan nata.... Nabilah sai faman binta da kallo take yanda duk ta zagwanye ta wani lalace ba kaman yanda ta ganta kwanan baya ba kafin a masu hutun makaranta don makaranta d’aya Raihana da Marliya autar Mamy suke hasalima ajinsu guda ga islamiya ma anyi hutu duk kad’aici ya isheta, Kausar ce mai d’ibe mata kewa don d’an zaman da yarinyar tayi a gidan har sun saba.... “Addah Nabilah Ina Marliya wato tinda akayi hutu ko lek’owa ta dainayi....” Nabilah dai dubanta kawai take cikeda mamakin wai dama Raihana ke abincin gidan Baba Alhaji lallai Hajiya ta cika azzaluma... “Raiha kece mai abincin...?” Nabilah ta tambaya tana dafe da Raihanar... Murmushin yak’e Raihana tayi kana ta jinjina kai lokaci guda tana mai jijjiga Kausar dake bayanta... “Toh ina sauran gardayen gidan kike girki ke kad’ai...?” Raihanah ta d’an juya a tsorace ta hangi k’ofar parlorn Hajiya kana tace “Aunty Sahariyya tana d’aki tana bacci Najah kuma sun fita ina tsammanin ta raka Hajiya unguwa ne.... Amma ai na saba Addah Nabilah kullum ni nakeyi...” Tayi maganar tana mai murmushi mai cikeda ban tausayi... Dafata Aunty B tayi kana tace “Karki damu yarinya idan sunyi tunanin cutarki suke k’wararki suke sunyi kuskure domin kuwa kece dai kikaci ribar zama dasu duk yanda kikaje a rayuwa babu yanda bazaki iya zama ba don haka kece kikaci ribar zamada Hajiya kinji koh...” A hankali Raihanah ke jinjina kai tana shafa hannayenta da tuni sunyi kanta sabida tsananin tuk’a tuwo mai tarin yawa da ake aikawa kasuwa da sauran aikace aikace da suka girmi shekarunta.... Nabilah ta dubi Aunty suna jinjina mugunta irinta Hajiyar Hafiz kana tace “Aunty sauk’i abin Raiha na nan kuma na tabbata tana kulada Kausar amma da wa yasan yanda zasu ballagazantar da yarinyar nan don bawai imani ne dasu ba...” Aunty tace “Sauk’ota mu ganta...” Babu musu Raihana ta soma kiciniyar sauk’e Kausar take ta soma rusa kuka alamun baccin tsoro tayi.... Sahariyya da ta sinkayo kukan nata tamkar a mafarki uban tsuka ta buga kana ta yaye labulen window tana fad’in “Ke Raiha kukan uban mai kuma yarinyar nan keyi....?” Cak ta tsaya da kalaman nata tana kuma k’anne idanunta masu cikeda bacci tana hango fuskokin Nabila da Aunty B dake faman danna mata mummunar kallo.... “Ke Raiha su waye wad’annan tsaye sunama mutane kallon raini...?” Kafin Raihana ta bata amsa ta sinkayo muryar Aunty B mai cikeda charisma tana fad’in “Uwarki ne... Tambad’edd’iya marar kunya...” Kambala’in chan.... Sahariyya ta ambata cikin zuciyarta, lallai zata shayar da matar nan mamaki don ta lura kan matar hayak’i.... A fujajan ta gyara d’aurin k’irjinta ta nufo waje don dama d’abi’arta kenan zama da d’aurin k’irji musamman lokacin zafi.... “Wllhi wllhi babu matar da ta isa ta shigo har cikin gidan ubana ta zagi uwata... Wllhi kinyi kad’an fitsararrun yaranki ma sunyi kad’an...!!” Kafin Sahariyya takai aya Nabilah ta katsetsada fad’in “Fitsara har ya wuce wacce aka baku ita a matsayin tarbiya ai ya b’aci.... Wllhi kikayi gigin zagin Aunty gabana zan shayar dake mamakin da baki tab’a shansa ba rayuwarki gaba d’aya....!” Sahariyya ta daka tsalle tana tafe hannaye had’ida kururuwa tana mai gyara d’aurin k’irjinta, lokaci guda take furta “Lallai Nabilah kin rik’a ni kike zagi kanki tsaye don ubanki tamkar wata sa’arki ce ni...” “Badai ubana ba wllhi yafi k’arfin ki zagesa dukda kuskuren da ta tafka ya d’auki d’iya mai daraja sukutum ya baiwa wannan lusarin Yayan naku....” Haba nan fah Sahariyya tayo kan Nabilah tana huci tuni Aunty B ta tsare tsakaninsu suna gogan k’irji itada Sahariyya take fad’in “Kika kuskura kika tab’a d’iyata zakiyi kwanan guardroom billahillazi.... Bari kiji na fad’a miki ba wajenki nazo ba don ke ba sa’ar yita bace wajen uwarki nazo idan kuma ban sameta ba zan baki sak’o ki bata kuma ki tabbata sak’ona ya isa gareta k’aramar marar kunya....” Ta k’arashe tana mai hankad’e Sahariyya da tuni ta zube k’asa.... Tsoro da firgici suka cika Raihana tuni ta rungume Kausar suka rakub’e gefe guda.... Yunk’urin da Sahariyya tayo zata tashi sallama da karauniyar su Hajiya ya gauraye gidan, shigowarsu da kad’an Zulfah ma ta shigo a birkice.... Haba nan fah Sahariyya ta shiga runtuma kururuwa tana fad’in “Wayyo Hajiya wayyo Hajiyata taron dangi sukamin, wayyo k’ashin bayana wayyo k’afata....” Haba ai kankace mai Hajiya tayi jifa da k’ullin k’auri data samo a unguwa tayo kan Aunty B gadan gadan Najah kuwa tayi kan ‘yar uwarta Sahariyya tana taimaka mata, tuni Zulfah da Nabilah suka tare Auntyn su dukan da Hajiya ta kawo ya sauk’a kan Zulfah... Kausar da taga an kaiwa mahaifiyarta jibga da saida ya kusan aikata k’asa wani irin kuka ta cilla mai tsananin k’aran gaske... A tamanin Raihanah ta fice da ita daga gidan a guje sam batasan sun iso bakin kwalta ba... Gaba d’aya hankalinsa naga wayarsa ko zata kira, driving yake yana duban wayar alamun yana jiran kiranta amma shiru, k’iris ya rage baibi kan budurwar dake rungume da k’aramar yarinya ba... Wani irin birki Sameer ya danna lokaci guda had’ida kifa kansa yana mai ambato Allah.... Cikeda fargaban abinda ka iya faruwa ya d’ago fuskansa yana duban gaban motar nasa, ganin bai gansu ba yasa shi saurin bud’e marfin motar ya fito yana lek’en ina suka shige wani lungun suka shige.... Komai ya faru in a flash, tabbas yasan ya kusan buge mutane guda biyu amma ga tsananin mamakinsa bai gansu ba kuma baiga wani gidan suka shige ba bai kumaga wani lungun suka shige ba.... Tsananin horn da ake masa daga bayansa ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi.... Cikin tsananin huci Hafiz ke d’ago hannu yana fad’in “Dallah Malam ka wani zo ka tare hanya mutane zasu wuce... Sai kuzo da manyan motocinku na k’arya kuna k’ababawa mutane a kwalta....” Tunda ya soma magan Sameer ke dubansa yanajin wani abin na tsargar masa, bai iya amsa shi ba sai bud’e mota da yayi ya shige had’ida tada motar ya kaucewa Hafiz ya shige bai daina bambami yana fad’in titi bana uban kowa bane.... Kwanan da Hafiz ya shige Sameer ya dinga kallo yanajin kwanyarsa da zuciyarsa suna yunk’urin tuno masa wani abin.... A hankali ya dafe goshinsa yana ambaton Allah kafin yaja motar ya wuce gida.... *** Duk k’ok’arin Zulfah taga tayi k’ok’arin raba wannan fad’a abu yaci tura a haka Hafiz ya shigo ya taddasu, aiko Hajiya na ganinsa ta zube k’asa tana kururuwa tana fad’in zasu kasheta Zulfa’u da danginta zasu karta.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *14* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Abu kaman had’in baki nan fah yaran Hajiya gaba d’aya suka cafe suna rantse rantse da kururuwan cewa kashe masu uwa za’ayi.... Tsananin mamaki ya hana Aunty B da Nabilah furta komai sun zubawa sarautar Allah idanu suna ganin makirci irin wacce basu tab’a gani ba wajen Hajiya da d’iyoyinta... Hajiya taci gaba da fad’in “Wllhi tallahi saika saketa, wllhi ka gama zama aure da wannan matsiyaciyar....” Hafiz da k’irjinsa ya bada wani irin sauti ba tareda sanin dalili ba saurin k’arasawa ga Hajiya yayi kana yace “Amma dai Hajiya kinsan Alhaji ba bari zaiyi na saketa ba koh, kuma ai biyayya nake masa...” Bai kai aya ba Hajiya ta katsesa da fad’in “Biyayya..? Toh biyayyar taci uwarta, wllhi saika saketa wannan wataran ba saidai azo a samu gawata ba donma dai Allah ya kiyaye su Sahariyya na nan da wayasan abinda zasumin, kana gani dai ga ‘yar uwarka Shariyya tsaban bugu saida suka kwab’e mata riga suka kuma targad’ata a hannu... Wllhi Hafiz saika saketa idanma ubanta bazai karb’eta tabi bola ko tabi titi don na tabbata wannan tsiyar babu mai kuma kwasanta.....” Aunty B ce ta kece da dariya had’ida rangad’a gud’a kana tace “Ai idan baki mance ba ba bola ko titi kika d’aukota ba, a mutunce aka dank’a mata ku don babu tsiya a tattareda ita, sannan da wannan watsettsen auren shika sai yafi komai dad’i wajenmu barikiji na fad’a miki, idan har d’anki ya cika d’an halak yau Zulfa’u ta gama zaman aurensa, idan har ya haifu ya bata takardan sakinta kaman yanda kike ikirari....” Hajiya banda tsuma bata komai sai faman bin Bara’atu da kallo kurum take, takai dubantaga Hafiz da yayi tsuru gefe yana duban Aunty B ta yanda take shiga bata nan take fita ba kana tace “Ka daiji da kunnuwarka koh, toh ka sakar masu tsiyarsu idanba so kake nai maka baki ba, wllhi saika saki Zulfa’u....” Zulfah kuwa cikin kuka ta rik’e hannun Aunty B tana fad’in “Aunty don Allah kiyi hak’uri kada ki bari ya sakeni, Hajiya kuyi hak’uri don Allah wllhi hakan bazata sake faruwa ba In sha Allah....” “Ke dalla can rufe min baki, shegen rashin zuciya yawa kare ya tand’e.. Toh ya sakekin mana sai mai, kin wani b’are bakiwa mutane kina kuka wllhi sai ya sakeki ya gani idan bakida gata....” Hajiya zatai magana Hafiz yayi saurin katseta da fad’in “Inace matatace kuma nike zaman hak’urin nan da ita, kuma ai iyayenmu suka had’a wannan aure don haka gaskiya ni bazan saketa yanzu ba, ba yanzu nayi niyyan rabuwa da ita ba......” Baikai aya ba Hajiya ta fashe da kuka had’ida kamo bakin zani tana fad’in Zulfa’u da danginta sun shanye mata d’a, tuni yasa kai zai fice Sahariyya da Nabilah sukayi saurin shan gabansa a guje, Sahariyya na fad’in “Haba Yaya haba kan wannan abar zaka bari tsinuwar Hajiya ya kamaka ga mata bila adadi a gari wllhi ka sakar masu d’iyarsu ka huta....” Nabilah ta cafe da fad’in “Ahtoh nima dai hakan na gani Ya Hafiz duda dai ba shiri muke ba amma banso tsinuwar Hajiya ta kamaka ai dai gwara ka saki Addah Zulfah kowama ya huta....” Batakai aya ba ya soma kwab’e takalman k’afafunsa alamun zai kai masu bugu gaba d’aya, a d’ari suka arce kowa tayi bayan ‘yan uwanta..... Kasa fita yayi daga gidan don tuni Hajiya ta rufe k’ofa tana fad’in “Babu yanda zaije bai saki Zulfah ba, k’wafa kurum Hafiz yayi ya koma parlorn Hajiya yayi zamansa sai faman tsuma yake.... Hajiya zata bisa parlorn Zulfah tayi saurin fincikan hannunta daga rik’onda Aunty B ta mata ta tafi ta sha gaban Hajiya had’ida durk’usawa ya hawaye dake bin k’uncinta take fad’in “Hajiya don Allah kiyi hak’uri, wllhi idan Ya Hafiz ya sakeni Abbah tsinemin zaiyi, Hajiya kiyi hak’uri ki yafeni don Allah, idan dai Kausar ce na bar miki ita duniya da lahira amma dan Allah kada ki rabani da mijina, na rok’i arzikinki....” Tsananin takaicin Zulfah da ya rufe Aunty B da Nabila tamkar film haka suke duban lamarin suna mamakin wane irin rashin zuciyane wannan.... Itako Hajiya shewa ta buga tana k’arema Zulfah duba daga yanda take duk’e tana hawaye kana tace “Wllhi idan ni na haifi Hafiz Zulfa’u, idan ni na shayar dashi na tsawon watanni ashirin wllhi sai ya baki takardan saki yanzu basai anjima ba idan yaso Abban naki ya tsine miki kibi ‘ya’yan kaji dama yaya balle kin sami tsinuwar mahaifi ai saidai ki soma bin bola, cikani dalla dangin tsiya mai farin sawu....” Ta k’arashe tana fizgan bakin zaninta daga rik’onda Zulfah ta mata.... Juyowa Zulfah tayi cikin hawaye tana duban Aunty B dake tsaye tamkar gunki tana dubanta tama rasa takaici ko tausayin Zulfah takeji.... Jiki a sanyaye Aunty B ta isa ta kamo Zulfah ta mik’ar da ita tsaye had’ida rungumarta take kuwa wani sabon kukan ya kufcewa Zulfah, Rihanah dake tsaye gefe can rungumeda Kausar sai hawayene ke gangaro mata.... Nabilah kuwa tab’e baki tai tana duban kowa da idanu... Basukaiga barin gidan ba saiga Hajiya da mik’akk’iyar takarda hannunta tana faman washe baki had’ida tafiya irinta tak’ama... Dungurin Zulfah tai da takardan kana tace “Alhamdulillahi d’ana ya rabu da alk’ak’ai yanzu kasuwancinsa zai bunk’asa yanzu zaiga cigaba a rayuwarsa yanzu al’amra zasu soma tafiya masa yanda yake so... Maza a k’ara gaba akai farin sawu wani wajen...” Ta k’arashe tana dank’a mata takardan... Take Zulfah taji hawayenta sun k’ame, ta kuma juya takardan hannunta na tsananin rawa, takai dubantaga Hajiya da yaranta dake faman shewa Sahariyya da Naja’atu kana ta maido da dubanta ga Aunty B da Nabila.... “Aunty Ya Hafiz bai sakeni ba ki bari na shiga na tambayeshi naji daga bakinshi Dan Allah....” Girgiza mata kai Aunty B tayi kana ta amshi takardan ta rik’ota tace “Muje, muje Zulfa’u....” Zulfah na hawaye take fad’in “Aunty Kausar.....” Juyawa Aunty B tai ta hangi Kausar dake rungume hannun Raihana kana ta tafi zata amsota... Ai kan ta isa Hajiya ta isa ta fizge yarinyar tana fad’in “Wa aje da ita ina bayan ga ubanta mahaifinta nan a raye, yo ai ko mutuwa yayi ba k’arewan aure ba babu yanda zataje nan shine gidansu.... Ku dai ku tattara tsamin k’afafunku ku fice tinda anyi maku abinda kukeso....” Duk bala’i irin na Aunty B saida taji jikinta ya mata sanyi tausayin Zulfah da Kausar ya kuma kamata, sai tanaji sam bata kyauta ba donji take tamkar ita ta kashe ma Zulfa’u aure don koda Nabilah zatai magana Auntyn ita ta kwab’eta suka rungume ‘yar uwarsu suka fice.... *** Dubansa Shamsu ya kuma a karo na biyu yanda ko tab’a abincin dake bisa dinning table d’in baiyi ba har ya sauk’o daga sama wajen Mama, tasowa yayi daga parlorn ya dawo dining area d’in had’ida jan kujeran gefen Sameer ya zauna.... Dafasa Shamsu yayi kana yace “Still thinking about her, kodai zamuje Kaduna gobe ne, karka damu I’ll drive...” Girgiza kai Sameer yayi had’ida fuzar da iska kana yace “I don’t know I don’t know Shamsu,so many things on my mind.... can k’asan zuciyana inaji Partner is not ok, inajin kaman wani abin ya sameta, sannan a nan kuma Ina ganin abubuwa wanda suke min tamkar na sansu wani wajen, I don’t know bansan meke faruwa ba Shamsu....” Zuru Shamsu ya masa kana ya d’an sauk’e ajiyan zuciya yace “Toh ko dai bakason zaman unguwar ne...?” Cikin sauri ya girgiza kai had’ida fad’in “No no no, in fact this is the best.... Har ina tunanin randa Mama zata gaji da zamana a nan....” Shamsu ya d’an dara kana yace “Kasan Mama bazata tab’a damuwa ba In fact hakan sai yafi mata dad’i.... Kasan mai za’ayi tashi mu d’an fita...” Babu musu Sameer ya mik’e suka fice ko zai refreshing.... *** Ko k’afafunta ta kasa motsawa sai faman tamke idanu take ga tsananin jiwa dake shirin kada ita... Dole Laila ce tai driving d’insu zuwa gida.... Siyama ta kasa fitowa daga mota nan ma saida Laila ta taimaka mata, a bakin k’ofar parlor suka lab’e kana Siyama ta umarci Laila ta lek’a mata idan Ammi da magulmatan ma’aikatanta basa downstairs sai su wuce cikin sauri gudun kada Ammi ta d’ago komai..... Hakan kuwa akayi, Laila na na rik’eda ita har suka haura sama d’akin Siyama... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Siyama tai kana ta fad’a toilet don kuma kimtsa kanta.... Tsayuwa tai gaban madubi dake barhroom d’in tana duban kanta, b’angare na zuiyarta ta tambayarta _Siyama kin tabbata abinda kikai kinyi dadidai...?_ Take d’aya b’angaren ya shiga raya mata hakan shine daidai Siyama domin kuwa haihuwa yana nufin canza rayuwarki ne gaba d’aya, komai naki zai canza kama daga suffar jikinki zuwa hidiman kulada yara, ke kuwa baki shiryama wannan ba hasalima shi kanshi mijin naki haihuwa bata damesa ba domin kuwa ko a d’an irin tad’i da kuke na soyayya bai tab’a sako miki batun haihuwa ciki ba baima tab’a hasashoki da juna biyu ba balle yara, kin yanke hukunci mai kyau.... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai sanda ta jiyo Laila na k’wank’wansa mata k’ofar bayin tana fad’in me takene haka a bathroom tai sauri ta fito ta sha maganinta kafin lokaci ya wuce... Cikin wahalcecciyar murya tace “I’m coming,...” B’alle magingunan Laila taci gaba dayi tana aje matasu su zama ready... Tamkar wacce aka jefota saiga Ammi a d’akin ta shigo.... Gaban Laila ya yanke ya fad’i don bata mance gamuwarsu da Ammi ba sanda tai k’ok’arin raba k’awancensu da Siyama, don a cewar Ammi sam hankalinta bai kwanta da Laila ba gashi ita kuwa Siyama duniya batada k’awa sai Laila.... Gaisar da Ammi tai ta amsa a tak’aice kana tace “Ina Siyamar....?” Laila tace “Tana bayi...” Ammi ta jinjina kai kana ba tareda ta amsa ba.... Duban d’akin taci gaba da yi tanason gano wani abin.... Duban Laila ta kumayi a kaikaice kana tace “Idan ta fito kice Ina nemanta....” Babu musu Laila ta jinjina mata kai tana ficewa ta kwaikwayi maganarta had’ida buga tsuka.... *** Koda suka tafi can gidan Zulfan suka d’ebo ‘yan wasu kayayyakin sakawanta ba gida suka wuce ba kai tsaye gidan Aunty B suka wuce don Aunty B d’in tafiso da safe ta kaita wajen mahaifan nata tayi bayanin komai..... Koda Nabilah zata tafi na saida Aunty B ta kwab’eta cewa kada tacema Mamy komai tukuna... Haka Zulfa’u tai kusan kwana tana hawaye, abubuwa da dama sun cika mata kwanyarta da zuciyarta, uwa uba mutuwan aurenta, ga musiban da zataje can gida ta tarar wajen Abbah, wajen Mamy ma tasan bazata samu da sauk’i ba, ga d’iyarta can hannun Hajiya da d’iyoyinta wanda tasan sai abinda sukaga dama zasu mata tunda dai tasan tsanar da suka mata ya shafi d’iyarta..... A hankali ta rintse idanunta hawaye masu d’umi suka gangaro mata, cikin tsananin sanyi jiki ta mik’e ta nufi bathroom d’auro alwala..... *** Tinda ya isa gidan yaji gidan ya masa sarari da yawa, yakai dubansa ga kujeran da kullum idan ya dawo a wajen yake hangota kodai tana bacci ko kallo ko kuwa karatu... Ya jima sosai yana duban wajen kafin ya d’an tab’e baki ya k’araso ya zauna cikin kujera had’ida dafe kansa kad’an, kana ganin sa zaka fahimci yana cikin damuwa, ga Sawwama na tsananin fushi dashi sabida amanartarda sukaci shida aminiyarta ga matarsa bata nan..... Ya jima a parlorn har baisan sanda bacci yayi gaba dashi ba yana nan rik’eda waya yana jiran ko kiran Sawwama zai shigo.... Bashi ya farka ba saida gari yayi haske sallah yayi kana ya shirya cikin sauri ya nufi gidan Abbah kafin Abbah ya tafi Kasuwa.... Ya kuwa taki sa’a Abban bai fice ba, Mamy ya tadda da Nabilah na tayata shirya kayan karin kumallo saman darduman Abban wanda yake cin abinci bisa.... Nabila tana ganinshi haka yaci uban wanka harda hula gabanta ya yanke ya fad’i domin kuwa sam bataso Ya Hafiz ya fara zuwa ba, bataso a soma jin zancen ta bakinsa don tasan yanzu sai ya iya canza zancen... SameenaAleeyou 📚 [10/01, 19:22] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _...............DA RABO_ *16* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Abbah bai daina bambamiba yana fad’in rashin kunya irinta yaran zamani da sam basu ganin girman dattijai.... Maganganun mutumin ya sanya Sameer saurin fitowa daga motar da niyyar basa hak’uri domin kuwa sam ba d’abi’arsa bace cin zarafin d’anadam ballantana har dattijo kaman wannan, sosai yake ganin girman nasa iyayen da bazaiso wani ya wulak’antasu ba don haka shima bazai wulak’anta tsohon wani ba... “Baba dan Allah kayi hak’uri bada nufi nake maka horn ba kayi hak’uri don Allah......” Wani irin bugu k’irjin Sameer yayi a sakwanni sanda sukayi eye contact da mutumin nan, a b’angaren Abbah ma babu sauk’i take yaji bugun zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, wannan k’wayan idanu tabbas yasan irinsu, wannan fuska tabbas yasan makamancinsa, tamkar an tsunduma a fridge haka jikin Abbah yayi sanyi, Sameer bai daina duban mutumin ba yanajin wani irin yanayi maras fasaltuwa a tattaredashi.... Ganin mutumin ma bai daina dubansa ba ya sanyashi matsawa baya a hankali ko zai samu sauk’in bugun zuciyarsa kayi... K’aran wayan salulan Sameer ne ya dawo dasu duniyar da tunaninsu ya barota.... Cikin sanyin jiki Sameer ya d’aga wayar yana satan kallon mutumin da ya kasa daina dubansa... “Yes, yes gani nan zuwa In sha Allah....” Daga gani daga asibiti aka kirasa... A hankali yasa kai zai koma ya shige motarsa Abbah yayi saurin k’arasawa ya damk’o kafad’ar Sameer guda..... Shock d’in da Sameer ya tsinci kansa ciki har yafi na ganin Abbah da yayi.... A hankali yake kaikaito da kansa har ya sauk’e k’wayan idanunsa kan hannun Abbah yanda ya masa wani irin damk’a.... “Saurayi nan gaba ka dinga kula idan kana tuk’i....”. Cewar Abbah cikin dakewan murya... A hankali Sameer ya jinjina kai kana yace “Na gode Baba...” Daga haka cikin sauri yasa kai ya nufi motarsa Abbah bai daina duban yanayin tafiyarsa ba.... Har ya tada mota sai kuma ya juyo ya hangi mutumin nan dai na nan na kallonsa suka kuma had’a idanu.... Kashe motar Sameer yayi ya kuma fitowa ya nufi mutumin, ganin haka yasa Abbah saurin juyawa ya nufi motarsa data kasa tashi don dubata.... Yana tsaye jikin bonnet d’in motar Sameer ya k’araso ya tsaya dab gefensa, Abbah saiji yayi hannun saurayin nan saman nasa yana k’ok’arin amsar abin gyaran.... Abbah ya d’ago idanu ya dubi kafad’unsu yanda ya tsaya dai dai tsawonsu dai dai babu wanda ya d’ara wani, gabansa ya kuma yankewa ya fad’i babu wanda yazo zuciyarsa face d’ansa Ma’aruf, da ace yana raye da yana around shekarun wannan matashin ne, ya tuna Ma’aruf na yaro wani rana sun fita tun a lokacin Abbah yana caring and loving father kafin ya zamto abinda yake a yanzu, Ma’aruf na tsalle a wuyan Abbah yana furta “Abbah watarana zan kamoka tsayi idan na girma...?” Abbah yaja hancinsa had’ida manna masa sunba a kumatu kana yace “K’warai kuwa masoyina, zaka kamoni tsayi harma ka k’etarani.... Amma bazaka k’etarani ba sai na tsufa sosai na koma tafiya a durk’ushe idan Allah ya ara mana kwana...” Ma’aruf ya rungume mahaifinsa yana fad’in “Abbah na bazai tab’a tsufa ba...” Abbah ya rungumeshi cikeda so da k’auna yanai masa shillo..... K’aran tashin motarsa ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, Sameer ya sakar masa murmushi yana fad’in “Ta tashi Baba zaka iya tafiya yanzu....” Abbah da tun b’acewar d’ansa ba kasafai yake murmushi ba sai gashi ya murmusa a hankali yana duban Sameer, k’arasowa yai zai shige motar kana yace “Na gode saurayi...” Sameer ya jinjina kai yana furta babu komai Baba kana ya nufi nasa motar cikin sauri don yasan shi kad’ai ake jira a asibiti... Har saida motarsa ta rab’a ta gefen na Abbah kafin ta shige ya kuma yin horn had’ida d’aga hannuwa Abbah shima Abban ya d’aga masa hannu yana mai bin motar tasa da kallo sai sannan Abbah ya tuna bai tambayeshi sunanshi ba.... Abbah ya kwanta jikin car seat had’ida lumshe idanu yana mai gargad’iwa zuciyarsa cewa wannan bazai tab’a zama Ma’aruf ba domin kuwa d’ansa Ma’aruf ya jima da mutuwa shi ya sani ya kumaji hakan a jikinsa, zuciyarsa ce dai mai neman kawo masa rud’ani yanda yake gab da shekarun girma..... Kasuwar da bai iya zuwa ba kenan a dole ya koma gida ya kwanta a d’akinsa... Aunty Lami da fitowarta kenan daga kitchen nan ta hangi tamkar wucewar mutum sashen Abbah bacin tasan tuni Abbah ya fice kasuwa.... Cikin sauri Aunty Lami ta nufi sashen Abbah.... Ga tsananin mamakinta kishingid’e ta taddasa saman kujera a parlorn nasa, waje ta samu ta zauna daga gefensa tana tunanin anya lafiya.... *** Ammi ta kuma d’aga kwalin maganin dake gefen gadon Siyama, mummunar fad’uwan gaba ya sauk’ar mata, d’ago idanu tai ta kuma duban Siyama dake duk’unk’une cikin bargo tana bacci... Ammi ta shiga girgiza kai tana furta “Oh no no no what have you done to yourself Siyama....” Ta kuma bud’e drawer d’in tana d’add’aya da magungunan.... B’uruntun binciken da Ammi keyi ya d’aga Siyama daga bacci.... Cikin sauri ta shiga fuzge magungunanta hannun Ammi tana fad’in “Haba Ammi you know I hate it when people spy on me...” Ammi ta girgiza kai tana dubanta kana tace “Siyama ki fad’a min gaskiya meye wannan, wato zancen da Kubura kemin tayi daidai... Siyama ciki kika cire...? Talk to me..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya... A hasale Siyama tace da ita “Yes Yes Ammi I had an abortion....Ammi I’m not ready to take responsibilities for God’s sake... And please do not pressure me...” Ta k’arashe tana kuma nitsewa cikin lallausan blanket d’inta.... Girgiza kai kurum Ammi tai kana tace “Siyama mai kika zama kenan, ki kashe d’anki da kanki... Anya kinada lafiya kuwa....?” Mik’ewa Siyama ta kumayi tana dubanta kana tace “Ammi please enough..... Abinda ya riga ya faru ya faru a ra’ayina babu haihuwa nan kusa maybe a gaba in the future.....” Ammi ta jinjina kai cikeda tsananin takaici kana tace “Kinyi adalciwa mijinki...?” Dubanta Siyama ta kumayi kana ta d’an tab’e fuska tace “Mijina always supports me, so na tabbata shima yaji haka babu abunda zai damesa... Ammi please understand ba kowa bane keda ra’ayin haihuwa, koda d’an nan yazo duniya bazaiji dad’in rayuwa da iyayensa ba domin kuwa zai kasance ne like a mistake so please ki daina damuwa Ammi, idan grandchildren kikeso Khalid zai haifa miki kinji koh...” Girgiza kai kurum Ammi take tana duban Siyama da tuni tayi tunanin ba cikin hankalinta take ba kana tace “Don’t say I did not warn you, wataran d’an da kika ciren nan zaki nema da kud’inki, too bad lokacin bazaki samu ba...” “And I don’t care Ammi...” Ta fad’i tana duban mahaifiyar tata.... Shigowar Khalid ya katse tartaunawar sun.... K’arasowa yayi ya d’an rungume Ammi kad’an kana yace “Goodmorning beautiful...” Ammi ta murmusa had’ida jan sumarsa kad’an tace “Morning Son... An fito...?” Jinjina mata kai yai yana kurb’an shayinsa a hankali kana yace “Yes Mamy, Abbah yace yana son sak’on ya isa Kano a yau...” Jin ya ambaci Kano yasa Siyama dubansa... Ammi ta jinjina kai kana tace “Toh Allah tsare hanya, ka kula da kanka kaji koh....” “Insha Allah Ammi...” Khalid ya fad’i yana duban Siyama da tamkar batta a wajen.... Saida ya matso dab da ita kana ya d’an rank’wafo yace “Karki damu I’ll drove by and say hi to your husband... Sai kuma na sanar dashi rashinsa ya saki ciwo....” Pillow d’in dake gefenta ta d’auka ta jefawa Khalid yai saurin kaucewa yana dariya nan suka soma kasa hali Ammi na rabon fad’a.... *** “Alhaji lafiya dai ko...?” Aunty Lami ta tambaya tana duban Abban.... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yai kana yace “Lami shin idan mutum ya mutu yana dawowa...?” Wani irin k’ugi da murd’a cikin Aunty Lami ya bada lokaci guda, gabanta yai mummunar fad’uwa... Cikin inda inda take furta “Haba dai Alhaji ya kake irin wannan tunanin... Ina ka tab’a jin wanda ya mutu ya dawo...?” Abbah ya jinjina kai kana yace “Haka ne...” Daga haka bai kuma ceda ita komai ba sai mik’ewa da yayi ya fad’a uwar d’akinsa k’afafunsa na masa nauyi.... Wani irin kallo mai cikeda firgici da fargaba Aunty Lami ta rakasa dashi, dukda d’an sanyi dake kad’awa a garin bata daina jin gumi na tsartsafo mata ba... Tambayar kanta ta dingayi maiyasa Abbah zai mata irin wannan tambayar.... *** Zulfah ta kuma duban Nabila a karo na biyu tsananin mamaki kwance saman fuskarta... Anya Hafiz ne har zai mata wani halacci a rayuwarta... Kai kodai wani tuggun yake k’ulla mata...? Muryar Nabila ya kuma katse mata tunaninta.... “Addah bansan maiyasa ya b’oyewasu Abbah ba amma dai ni a ganina ki sanar dasu kar yazo a gaba ya k’ulla miki wani sharrin...” Duban Nabila tai sanda take maganar kana ta girgiza kai a hankali tace “Nabila idan har shi bai sanar dasu ba nima bazan sanar dasu ba sabida bashi Abbah zai la’anta ba ni zai tsinema ya kuma cireni cikin ‘ya’yansa, na tabbata bazakiso kiga rana makamancin wannan ba a matsayina na ‘yar uwarki...” A hankali Nabila ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Toh baki tunanin Aunty ta fad’awa Mamy...?” Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Mun riga mun gama magana da Aunty B, zan zauna a nan tareda ita har lokacin da naji na sanar da mahaifana hasalima ni yin shirun da Ya Hafiz yayi yafimin... Idan na ida bautar k’asana har aiki Aunty tai alk’awarin samar min, sanin lafiyar Kausar ne kawai damuwata...” Ta k’arashe damuwa kwance saman fuskarta.... Hannayenta Nabila ta kamo kana tace “Kar ki damu Addah idan don wannan ne ni zanke dubo miki ita In sha Allah koda Hajiya dasu Sahariyya zasu hanani...” Zulfah ta jinjina kai tana mai k’ak’aro murmushi had’ida rungume ‘yar uwar tata tace “Na gode Nabila...” “Babu godiya tsakaninmu nidake abu guda ne..” Nabilah ta fad’i tana maida mata martanin murmushin nata... A haka Aunty B ta shigo ta taddasu tausayinsu ya rufeta nan ta umarcesu su fito suje kitchen baki d’aya tasan hakan ka iya d’ebe masu kewa... Yini zubur Nabila tai saida ta tuna Mamy ta haneta da yin dare kafin ta soma shirin tafiya... *** Misalin k’arfe biyar na yamma bayan ya gama huta gajjiyan hanyarsa a hotel d’in Tahir guest in da ya sauk’a nan ya kira Sameer ya sanar dashi location d’in da zai samesa.... Tsaf Khalid ya shirya cikin k’anan kaya royal blue shirt ta amani da kuma bak’ar jeans sai watsa k’amshi yake as usual ya nufi motarsa ya d’auki hanyar da Sameer ya sanar dashi map na directing nasa daga cikin wayarsa... Daga can mai adaidaita ya ijiyeta sai buga sauri take don tasan by this time Abbah ya dawo daga Kasuwa... Bata ankaraba saiji tai ruwan tab’o ya wanketa har fuskarta.... SameenaAleeyou 📚 [10/01, 19:22] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _..............DA RABO_ *15* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Tsananin mamaki ya kama Nabilah da Mamy ganin Hafiz harda duk’awa yana gaida Mamyn abinda bai tab’a koda kwatantawa ba gaba d’aya rayuwarsa.... Yawa mutunin arziki haka ya sadda kai yana tambayan Mamy ko Abbah ya fice Kasuwa ne... Mamy kaw cikeda jin dad’i tace dashi “A’a bai fice ba Yana nan tukuna....” Hafiz ya jinjina kai yana d’an murusawa kana ya dubi b’angaren Nabilah da tayi sakare tana dubansa yace “Nabilah ya hutu ko har kun koma ne...?” Badon Mamy na wajenba kuma bataso ta fahimci komai ba tareda ta gane nufin Ya Hafiz ba da ta k’wand’ara masa zagi ta ruga a guje.... Da k’yar ta furta “Umm bamu koma ba...” Mamy tace “Ya Hajiyar taka...?” Nan ma fuska a sake yace “Hajiya na nan lafiya, amma ban shiga ba ma dama sai na fice a nan ne...” Mamy ta jinjina kai cikeda jin dad’i kafin Hafiz ya kuma duban Nabilah yace “Ya kamata kizo ma Addar taki d’an hutu ai kafin ki koma sch.....” Da tsananin mamaki Nabilah ke was dubansa tama rasa abin fad’i, batakaiga bada amsa ba Abbah ya fito cikin shiri.... Gaba d’aya suka soma gaidashi, shi kanshi Abban ganin Hafiz da farar safiya ya sanyasa yin tunanin ko akwai matsala ne... Koda suka gaisa da Abbah tambayar Hafiz d’in Abbah yayi ko lafiya ko akwai wata matsala ce... Hafiz yace “A’a Abbah lafiya lau babu wata matsala....” Abbah ya jinjina kana ya kuma fad’in “Yaya iyalin naka, da fatan dai lafiya kuke zaune...?” Nan ma Hafiz jinjina kai yai yace “Lafiya lou muke zaune Abbah babu wata matsala...” Ya k’arashe suna mai had’a idanu da Nabilah... Shi kanshi ya fahimci tsananin mamakin dake kwance saman fuskar Nabilah kuma ya fahimci Zulfah ba gida ta taho ba hasalima bata sanar da iyayenta komai ba, wannan shine kawai gatan da zaiwa Zulfah bayan zaman hak’urin data kwashe a gidanshi bazai tab’a bari iyayensu susan cewa aurensu ya k’are ba..... Mamy ce ta umarci Nabilah da ta d’auko wa Hafiz plate da cup ya karya kumallo... Nabilah ta fice jiki a sanyaye tana tunanin wannan kuma wane kalan tuggu Ya Hafiz ya k’ulla.... A daidai hanyar ficewa daga sashen Abbah Hafiz d’in ya cimmata, kiran sunanta da yayine ya sanyata tsayawa cak tana masa duba irinta bak’in munafuki.... “Ina Zulfah...?” Tambayar da ya mata kenan.... “Ai kai zan tambaya mai kake shirin k’ullawa Ya Hafiz, maiyasa baka sanar dasu Abbah gaskiya ba....?” Murmushi yayi kana yace “Nabilah kenan, ki tsammanin sanar dasu bazai raba tsakaninsu da Zulfa’u bane musamman Abbah....?” Cikin huci Nabila tace “Toh meye manufar b’oyewarka, shin wannan bashine abinda kullum kake fata da burin ya sami ‘yar uwata ba yanzu da burinka ya cika mai zai hanaka jin dad’i kardai kacemin son Addah Zulfah kake...?” Ta k’arashe tana murmusawa.... Gajeren murmushi yayi kana yace “Idan kina tunanin zan tab’a son Zulfah kinyi kuskure... Iyakacin abinda zan mata kenan bayan hak’urin zama a gidana da tai shine na rufa mata asiri kada Abbah ya tsine mata bayan cutar farin k’afa da take fama dashi.... Amma kuma idan kuka bari akaji there’s nothing I can do, ki sanar da ‘yar uwarki ko a ina take, she decides for her life....” Daga haka tab’e baki ya d’anyi had’ida d’aga kafad’a kad’an kafin ya koma parlorn Abbah hula a karkace.... Shiru tai tana dubansa ba wai don zuciyarta ya kwanta da abinda yake fad’i ba, itakam sam bata yarda da Ya Hafiz ba ta tabbata he’s up to something, mai zatai yanzu, tai shiru ne ko ta sanarda Mamy ne.... Toh ko dai ta soma kiran Addah Zulfah ne ta sanar da ita....?” Jiki a sanyaye ta wuce kitchen... Ita kanta Mamy canzawan Hafiz ya dameta Abbah dai dashike ba mutum bane mai yawan magana ko saka hankalinsa ya abu sam bai d’ago hakan ba, tun bayan b’acewar babban d’ansa Ma’aruf ya koma hakan, gaba d’aya sai ya zama wani irin murd’edd’en mutum and hard to deal with.... *** Fuskarta da idanunta sunyi luhu luhu alamun dare jiyan bata samu ta rintsa ba, a haka Aunty B ta shigo ta taddata gaba d’aya sai tausayin Zulfan ya rufeta, ta kasa daina tunanin laifin duk nata ne ita ta kashe mata aure.... Daga can gefen gado ta zauna tana mai k’arewa ‘yar ‘yar uwar nata kallo.... Zulfah ta d’ago kod’add’un idanunta had’ida k’ak’aro murmushi ta soma gaida Aunty B.... Aunty B ta amsa fuska d’aukeda murmushi zuciyarta kuwa k’unshe da tausayin Zulfa’un.... “Nasan daren jiya baki samu kin rintsa ba sannan shi aure ko yaya yake idan akace ya mutu dole rai ya sosu, Zulfa’u kiyi hak’uri, kiyi hak’uri don Allah wllhi ba ke kad’ai ba ni kaina banyi bacci yanda ya kamata ba, ki gafarceni don ji nake tamkar ni na kashe miki aure dukda ba son zamanki a gidan Hafiz nake ba.....” Zulfah ta k’ak’aro murmushi had’ida share hawayen da suka zubo mata kana ta matso ta kamo hannayen Aunty B ta rik’esu cikin nata kana tace “A’a Aunty ko kad’an babu laifinki ciki hasalima haka Allah ya k’addara iyakacin wa’adin zamana kenan da Ya Hafiz.... Aunty damuwata Abbah... Aunty mai zance mishi... Shikenan tsinuwarshi zai bini... Aunty idan yace na tafi na nemi wani uban ina zanje....?” Ta k’arashe hawaye masu d’umi na kuma gangaro mata.... Rungumeta Aunty B tai tana shafa bayanta take fad’in “Let it out, kiyi kukanki Zulfah, sannan Abbah kuma kar ki damu I’ll take responsibilities of everything..” Girgiza kai Zulfah tai cikin hawaye kana tace “No Aunty.... Bazan iya zuwa gidan ba don Allah ki barni na zauna taredake a nan please Aunty...” Shiru tai tana duban Zulfan cikeda tausayawa kana tace “Idan hakan kikeso shikenan bazan tak’uraki ba sannan nima bazanso mahaifinki ya miki baki ba, amma baki tunanin idan shi mijin naki yaje ya fad’i komai, sannan al’amari irin haka ba’a shiru Zulfa’u.....” Girgiza kai tai a karo na biyu kana tace “Nidai don Allah Aunty ki barni a nan koda zai sanar dasu...” Jinjina kai Aunty B tai had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya, cikin kwantar da murya taceda Zulfah “Naji Zulfa’u In sha Allah zaki zauna a nan gidan iya lokacin da kikeso kika kumaji ki tunk’ari mahaifanki da batun nima na samu ‘yar tayin zama tinda Major yakan tafi can kudu ya shafe watanni, maza tashi muje kiyi breakfast....” Zulfah ta k’ak’aro murmushi kafin ta mik’e tabi bayan Aunty B.... *** Shamsu na zaune parlor yana kallon tashan wasan k’wallon k’afa daga yanda yake zaune yana hango abokin nasa sai faman kai komo yake yana kuma shafa waya yana mannawa a kunnensa, ko ba’a fad’i maka ba kasan waye yake nema cikin wayar... Shi kad’ai sai faman fuzar da iska yake yana fad’in “C’mon Partner pick up your phone.... What’s wrong what’s wrong what’s so wrong Siyaam...?” Kaman daga sama saiji yai ta d’aga wayar.... Cikin sauri ya fice ya bar Shamsu na ihun team d’insu taci ball... Murya cikeda damuwa yake furta “Siyama what’s all this, meyasa kika kashe wayanki... I’ve been trying to reach you for good two days Siyama... What have I done to deserve such punishment Partner...? My goodness I was so worried about you, and ban kira Ammi ba cos banso hankalinta ya tashi... Are you sure you’re alright Partner...?” Ciza lab’e ta kumayi sabida mararta da har yanzu yake mata zogi kana tace “Oh really Sameer, did you really miss me...? Ko kuma kana can kanajin dad’inka acan ka k’yaleni a nan ba...” Fuzar da iska yayi had’ida girgiza kai mai hali dai baya fasawa, shin yaushene Siyama zata daina samun doubts gameda shi.... Shin kalan nata soyayyar kenan... A hankali ya furta “There you go again, Siyama yaushe zaki daina doubting d’ina, shin kinsan matsayin aure mai k’unshe da zargi....? Why Siyama.... Shin soyayyar da nake nuna miki ne na gaza ko meye laifina...?” D’an lumshe idanu tai kana tace “I miss you Partner, yaushe zakazo...?” A hankali ya lumshe idanu don ya fahimci topic d’in taso canzawa kana yace “Soon weekend in sha Allah.....” K’irjinta ne ya bada wani irin sauti don bataso yazo ya fahimci wani abin tafiso ta zama fully recovered kafin yazo... Cikin d’an In ina tace “No karka tak’ura kanka, karka stressing kanka da yawa ka bari next weekend sai kazo nasan yanayin aikinka babu dare babu rana sannan har weekends ba wani hutawa kake ba, kadai bari next weekend sai kazo banso kayita jele saman kwalta ga yanayin hanyoyin namu a yanzu....” Da k’yar ta k’arashe maganar sai faman tamke idanu take tana rik’e mararta... Sauk’e ajiyan zuciya yai kana yace “Shikenan idan kince haka....” Seconds suka d’an gifta kana yace “Partner...” Ta amsa da fad’in “Yes Partner...” A hankali ya furta “Always remember that I love you... Ko a ina zan kasance inasonki....” Jikinta ya d’anyi sanyi ba tareda tasan dalili ba, a hankali ta furta “Nima ina sonka Partner... Ka kula da kanka please...” “You do the same...” Ya fad’i kyakkyawan murmushi kwance saman fuskarsa... Suna ida waya da Siyama ya kira Mummynsa suka gaisa don through out yinin ranar bai samu ya kirata ba, sosai Sameer ke k’aunar iyayensa.... *** A b’angaren Siyama kuwa jigum tai tana duban pills d’in dake hannunta ta kasa afawa baki, gaba d’aya ta rasa sukuni cikin zuciyarta tun bayan faruwan wannan al’amari, da k’yar ta samu ta afa magungunan kafin ya kurb’i ruwa ta mik’e saman gadonta had’ida lumshe idanu ko baccin dole zai gaba da ita domin sam babu bacci cikin idanun nata.... **** Washe gari da sassafe Nabila ta soma shirin tafiya gidan Aunty Bara’atu, Mamy dai na hankalce da ita domin ta kula tun jiyan Nabila ta canza sosai tamkar wani abin na damunta, saida ta ida shirinta tsaf Mamy ta zauna gefenta had’ida ambato sunanta tareda jefo mata tambaya “Nabilah kin tabbata lafiya ce zata kaiki gidan Auntyn ku da farar safiyar nan... Ki sanar dani idan akwai wani abinda ya kamata na sani...” K’ok’arin saita kanta Nabilah tai dukda tsoro dake kwance k’asar zuciyarta gani take tamkar Mamy na iya reading mind d’inta... Saida ta d’an dara had’ida saka wasa wanda dama d’abi’artace kana tace “Kai Mamy yanzu bazanje gidan Aunty B ba sai babu lafiya.. Kawai nafison fitan safe ne sabida babu ‘yan sa ido sosai kinsan yanayin unguwar nan anjima kad’an zaki soma ganin suna fitowa da bencinansu....” Mamy ta jinjina kai tace “Shikenan Allah ya tsare, ki d’aga posata akwai naira d’ari biyu ki d’auka kiyi kud’in abin hawa...” Nabilah ta jinjina kai had’ida furta “Toh Mamyna na gode....” “Ki gaida Bara’atun....” Nanma amsawa tai da zataji kafin tasa kai ta fice cikin sauri... Fitarta da kad’an Abbah ya fito da niyyan fita kasuwa...Bai bar katangar gidansa ba motarsa ta tsaya ta kasa tafiya abinka da sharrin k’arfe.... K’iris ya rage motar bayansa bata bugi bayan nasa motar ba.... Sameer da yaso makara sakamakon damunsa da waya da akai daga asibiti tuni ya danna hannunsa saman horn.... Iyakacin harzuk’a Abbah yayi, baisan sanda ya sab’a babbar rigarsa ba yasa kai zai fito daga motar yana faman huci yake “Wai maiyasa mutane sam basuda hak’uri ne, kazo kabi ta sama idan ka matsu.....” SameenaAleeyou 📚 [12/01, 15:25] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _...............DA RABO_ *18* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallo mai d’aukeda alaman tambaya Mamy ta jefa mata wanda ya sanyata saurin cire hannu a abincin ga k’irjinta dake faman lugude.... Murya a shak’e taceda yaron “Kai jekace masa bata nan....” Mamy ta wurga mata mummunar kallo kana tace “Kinsan wanene...?” Baki a ture Nabila tace “Mamy yo zai wuce munafukan unguwar nan ne ‘yan saka ido, Mamy Allah nidai yaje yace bana nan koma kawai yace bazanzo ba....” Mamy ta jinjina kai had’ida yin k’wafa, mik’ewa tai ta nufin k’ofar parlorn ta d’aga labulen k’ofar yanda ta hangi Almajirin rakub’e daga bakin veranda... Har k’asa yaron ya duk’a ya gaida Mamy ta amsa kana ta k’arada “Yau an baku sadakan abincin dare...?” Girgiza kai yaron yayi kana yace “A’a Hajiya....” Mamy ta nufi kitchen d’inta dubo sauran abincin rana ta basu don dama duk ran girkinta sai ta basu sadakan abincin sun wadata shiyasa suka maida k’ofar gidan wajen zamansu, ranar girkin Hajiya Aunty Lami ne da sauk’i wani sa’in sai sun karad’a unguwar neman sadaka.... Mamy ta fito da sauran abincin rana cikin flask ta juye masa kana tace “Kaje ka tambayo wanene shi mai sallaman...” Almajirin ya jinjina kai cikeda murna yace “Toh Hajiya...” Jim kad’an yaron ya dawo had’ida kuma kwad’a sallama, Mamy da Marliya ce kawai suka amsa Nabila kam tayi kicin kicin da fuska tana satan kallon Mamy jira kawai take taji wani mai asaran lokacin ne yazo wajenta... Wani irin yankewa gabanta yayi ya fad’i sanda taji abinda yaron ke fad’i... “Wai mutumin da ya b’ata mata jiki d’azu ne, wai zuwa yayi ya bata hak’uri...” Mamy ta kalli Nabilah itama Mamyn take duba zuciyarta na harbawa.... Ba tareda Mamy ta d’auke dubanta daga Nabila ba take fad’in “Jekace babu komai ya wuce ba sai ya bata hak’uri ba koh....” Yaron tamkar mai tsoron juyawa yace “Hajiya Allah bazai tafi ba don tun d’azun yake jiranta...” Duban Nabila Mamy tai kana tace “Banson dogon magana tashi kije ki sallameshi kafin Abbanku ya fito sallahn isha ya taddasa....” D’an k’ara murya Mamy tai sanda take fad’iwa yaron “Jekace tana zuwa...” Yaron ya juya cikeda jin dad’i yana mai amsawa... Fuska a turb’une ta mik’e ta suri hijabin dake gefen Marliya ta nufi k’ofa.... Kana ganinta kasan a shirye take ta juye ruwan bala’i.... Wutan babban kwalta na streetlights sun haske wajen tamkar rana, kana iya ganin mutane masu kai komo, Almajiran nan dake faman warwason abinci kallo guda Nabila ta masu suka shiga taitayinsu, tayi k’wafa ta shigesu tana waigen ta yanda zata gansa.... Tsaye ta hangi k’eyarsa jingine jikin mota ya bada baya waya manne kunnensa da alama waya yake amsawa.... Saida ta gama jifansa da harara kafin ta nufesa a fusace..... Jikin mirror d’in motarsa ya hangeta tana zuwa hasken wutan lantarki ya haske fuskarta wanda bai faye haske sosai ba, tafiyarta kawai zaka gani ka fahimci tayi shirin juye ruwan masifa... Cikin sauri Khalid ya katse wayar da yake da ‘yar uwarsa Siyama kafin ya juyo domin fuskantar masifatunsa.... “Malam lafiya meye kuma ya kawoka k’ofar gidanmu...? Yama akai kasan cewa nan ne gidanmu...?” Ta k’arashe tana mai d’ora hannaye a kunkumi tamkar mai shirin rufesa da duka.... Tamkar bazaice komai ba haka ya tsareta da idanunsa har saida Nabilah ta soma taarguwa da irin duban da yake mata gashi ita ta kasa jure kallonsa cikin idanu.... Kallo guda zaka mata ka fahimci she’s not comfortable.... Harara ta jefo masa suka kuwa had’a idanu, lokaci guda ta d’auke kanta had’ida doka uban tsaki tace “Banda lokacin tsayuwa a nan, kuma wllhi idan Abbah na ya fito ya taddaka a nan kace wajena kazo zan sa almajiran nan su rakaka da duwatsu....” Daga haka sa kai tai zata shige saiji tayi ya finciko hijab d’inta ta dawo da baya..... Tsoro da mamaki ya wanzu saman fuskarta, ta lura wannan baida niyan ficewa daga rayuwarta cikin gagggawa, a hasale take fad’in “Wai don Allah mai kake nema daga wajena, what exactly do want from me....?” “You wannan know...?” Ya tambaya yana kashe mata rikitattun idanunsa had’ida murmusawa da gefen baki, lokaci guda kuma ya gimtse kana yace “First of all tambayarki nakeso nayi... Shin a gidanku ba’a koya miki furta sallamawa mutane ba... Ko kuma ba’a koya miki gaida manya ba....?” Murmushin rainin hankali Nabilah tayi kana ta fad’i cikeda tsiwa “Wannan kuma kanka ya kamata ka tambaya, k’ilan ba’a koya maka daraja mace ba a duk yanda ka ganta... Kuma wllhi ka kuma janyomin hijabi zan maka ihu a unguwar nan....” Khalid ya kafeta da idanu yana mamakin hali irin na Nabilah... Sakai tai zata kuma tafiya taji ya ambato sunanta karo na farko sannan batasan ya akai yasan sunan nata ba, take k’irjinta yayi wani irin bugawa... “Nabeelah....!” Cak ta tsaya ba tareda ta juyo ba, saida wasu dak’ik’ai suka d’an gifta kafin yaci gaba da fad’in “Idan kinfiso na baiwa Abbanki sak’on ya shiga miki dashi fine zan jirashi ya fito na bashi don na tabbata shi zai tsaya ya saurareni...” Saurin juyowa tai tana dubansa hannunsa rik’eda envelop fuskarsa babu alamun wasa.... Mamaki ya kamata, wani sak’o ne wannan ita mai ma ya had’ata da wannan mutumin... Cikin sauri ta dawo da baya tamkar zata kifa da k’asa... Khalid ya saki murmushi wanda idan bashi d’inba babu mai fahimtar yayi.... Wannan karon cikin kwantar da murya take maganar “Malam don Allah mai kake nema wajena, I don’t know you, bansanka ba bansan mai kake nema a wajena ba, ka kuskureni da mota kamin wanka da ruwan tab’o kaje na yafe maka, amma Dan Allah ka fice a rayuwata, I beg of you please....” Ta k’arashe tana had’e tafukan hannayenta waje guda... Gyara tsayuwarsa yayi kana yace “Karkiyi tunanin bibiyarki nake... You see this bruise...” ya k’arashe yana nuna mata ciwon goshinsa da Sameer bai jima da masa dressing ba kana yace “Don’t you think I’m too handsome to have it on my face....?” Dubansa Nabilah tayi baki a sake don batai zaton abinda zaice ba kenan, lokaci guda yaci gaba da fad’in “And my car... Ke tinda kike a wannan lungun naku kin tab’a ganin new brand irin wannan....?” Izuwa lokacin Nabilah ta gama isa wuya, ta lura wannan d’an rainin hankalin wulak’anci kawai yazo ya mata... Zatai magana ya mik’o mata envelope d’in yace “I want you to take look at this....” Yayi maganar yana bud’e envelop d’in.... Lokaci guda yaci gaba da fad’in “This is a list of all the expenses on the car that you’ll need to cover... Take... Karb’a mana....”. Ya k’arashe yana d’aura takardan saman hannunta.... Huci kawai Nabilah keyi sanda tabi takardan da kallo, Khalid ya kuma murmusawa kafin ya nufi motarsa yana fad’in “Make sure kud’in sun zama ready kafin na bar garin nan only then zan fice a rayuwarki kaman yanda kika buk’ata....” Kallo ta bisa dashi da gaske motarsa ya nufa ya barta da zungureriyar takarda cikeda zeros, cikin sauri ta take masa baya, zamansa cikin motar da wuya yajiyo k’aran keta takarda, da tsananin mamaki ya juyo yana dubanta... Tas ta keta takardan kafin ta watsa masa cikin motar nasa tana fad’in “Bazan biya ba, ai bani nace kayi tuk’in ganganci, kuma wllhi ka sake zuwa k’ofar gidan nan duk abinda ka gani kai ka jiyo....” Tana ida fad’in haka tasa kai tayi shigewarta cikin gida... Su Sadiya da Mamanta Karima suna lab’e suna gulma Nabilah tazo shigewa nan kaw suka sha jinin jikinsu don sarai tasan sun jima wajen suna kwasan gulma.... Tsuka ta buga had’ida furta aikin kenan, tasan tinda Sadiya da mamanta suka ganta Mamani taji wannan batu an gama amma ita yanzu bata Mamani take ba damuwarta wannan d’an rainin hankalin ya fice mata daga rayuwa..... *** Yau bayan an ida sallan asuba Sameer ma zama yayi kaman yanda yaga dattijan unguwan suna zama d’aukan karatu wanda ya danganci wasu littafan na addini... Sosai abin ya birge Sameer, yanaso yaga mutum na neman lahirarsa ba duniya kurum ba kaman yanda nasa iyayen suka d’ora rayuwarsa bisa neman duniya zalla, ya lura da mutumin da ya gyara masa mota kwanaki biyu da suka shige, dukda cewa mutumin ba mutum bane mai yawan magana hankalin Sameer ya kwanta dashi... Bayan an ida karatu, Sameer ya k’arasa ya gaida liman kana yabi sauran dattawan d’aya bayan d’aya suna gaisawa da yazo kan Abbah fari’arsa ta k’aru, shima Abban sai yaji wani shauk’i na d’ibansa na ganin saurayin.... Shi kanshi Sameer d’in ya lura da yanda Abbah yaji dad’in gaisar dashi da yayi tareda alamun bai mance shi ba, tare suka fito daga masallacin Sameer ya gyarawa Abbah takalmansa ya saka... Suna tafe Abbah ya dubesa fuska d’aukeda murmushi kana yace “A nan unguwar kake ne...?” Sameer ya d’an girgiza kai kana yace “A’a zuwa dai nayi Baba, asalina mutumin Kaduna ne iyayena da dangina duk suna can, aiki ya kawoni garin nan nake zaune gidansu Abokina, gidan Marigayi Alhaji Sa’adu Sharubutu... Munyi karatu tareda d’ansa Shamsudden...” Abbah ya jinjina kai jiki a sanyaye tabbas babu yanda za’ai wannan saurayi ya zama nasa d’an hasashensa ne kurum ya basa hakan, baisan dalili ba amma har cikin ransa yakejin wannan saurayi da ya sanar dashi sunansa Sameer... Har k’ofar gida Sameer ya rako Abbah kana ya masa sallama, ya lura da yanda yanayin Abban ya canza tinda ya basa tak’aitaccen labarinsa... Sameer yasa kai zai shige Abbah ya kirawo sunansa.... Dawowa da baya yayi cikeda risinawa, Abbah yace “Idan bazaka damu ba kazo muci abincin dare a gidana...” Sameer ya fad’ad’a murmushinsa kana yace “Kai Baba na gode matuk’a da wannan karammawa In sha Allahu zanzo...” “Amma Baba wani hanzari ba gudu ba shin zan iya zuwa da abokina Shamsu..?” Abbah ya jinjina kai yace “Kazo da duk mutanen da kayi niyya Malam Sameer ni na gayyaceku...” Sameer ya jinjina kai cikeda jin dad’i kana yace “Godiya muke Baba In sha Allah zamuzo...” Abbah yace “Ka kirani Abbah haka yarana ke kirana...” Sameer ya kuma jinjina kai had’ida furta “Abbah...!” Ba Sameer d’in kawai da ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi harta Abbah saida yaji wani shauk’i na sauk’ar masa... Fuskar Abbah kurum zaka kalla ka fahimci na cikin farin ciki, Mamy ta lura da hakan saidai bata tambayesa ba, yinin ranan zubur Abbah cikin farin ciki yake, Mamy na hankalce dashi ba abin ta tambayeshi ba ta janyo wani abin don ba kasafai yakeson yawan tambaya ba tun bayan b’acewar Ma’aruf, don haka taja bakinta ta d’inke.. Da yamma da zai fita yace da ita sunada bak’i a shirya masu sauk’a.. Babu musu Mamy ta amsa mishi had’ida mishi a dawo lafiya, as usual a ciki ya amsa mata... Shamsu sai mita yakewa Sameer cewa shi babu ruwansa da kowa a unguwar ba abinda zai kaisa wani gida dinner, da k’yar Sameer ya shawo kan Shamsu ya yarda zai rakasa, Khalid da yazo masu sallama ma aka had’a dashi sam yak’i shikam a cewarsa yanada wajen zuwa, Khalid d’in ne ya basu ride sanda zai koma... Ganin gidan da suka nufa ya sanyasa canza ra’ayi ya bisu suka d’unguma zuwa gidan gaba d’aya.... SameenaAleeyou 📚 [12/01, 22:08] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _...............DA RABO_ *17* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Cak Nabila ta tsaya tana kuma jin sauk’ar ruwan tab’on nan a jikinta wanda ya wanketa har fuskarta... Tayi k’ok’arin bud’e idanunta da harta suma tab’on ya tab’a... Babban abinda yafi bata takaici shine da alama shashashan matuk’in motar da ya mata wannan aika aika baisan yayi ba.... Kallo tabi motar tasa dashi wanda yake ruwan shud’i k’irar Mercedes, duk duniya babu wanda ya tab’a mata wannan wulak’ancin, lallai wannan mutumin da gani babban d’an rainin hankali ne wanda baisan mutunci tinda baisan ya tsaya ya bada hak’uri.... Zuciyar Nabila taci gaba da tafarfasa, kasancewar hanyar unguwar cike yakeda kwarai da k’wazazzafo yasa sam motar bai b’ace ma ganinta ba, tamkar mai neman wani abin haka ta shiga waige-waige..., Can ta hangi wata dutse, tuni ta k’arasa ta d’auki dutsen tana mai ci gaba da huci da tafarfasa... Cikin sassarfa ta kusan isa ga wannan had’edd’iyar mota data mata mummunar wulak’anci da babu wanda ya tab’a mata irin hakan.., Daidai gate din gidan da yake tunanin nan ne gidan da Sameer ya turo masa address yayi parking motar naci gaba da diri still idanunsa kan wayarsa da alama layin Sameer yake nema... Khalid bai ankara ba saijin sauk’an ringimemen dutse yayi daidai glass din k’ofar glass din dake saitinsa na matuk’in mota... Tuni wayarsa ta zame yai saurin kare fuskarsa da hannayensa yana karanto innalillahi... Saidai tuni glass din ta sameshi a goshinsa yanda ta tarwatse lokaci guda.... Cikin tsananin tashin hankali had’ida firgici ya finciki marfin motar nasa ya fito yana rarraba idanu don ganin maike faruwa dashi., tsawa ya sauk’a masa ko kuwa bomb ne ya kuskuri tashi dashi... Dashike glass din motar tasa mai duhu ne sam bazata iya gano matuk’in motar ba, ba tareda tsoro ko gudun waye zata gani ya fito daga motar ba taja ta kafe gefe tana jiran fitowar koma wanene don bata tsoron ta kife sannan bata barin saita kwana balle tai tsami.... Had’edd’en saurayi ne maiji da gayu da kyau ya fito daga cikin motar.... Cikin sakanni da basu wuce uku ba ta k’are masa kallo, nan ta kuma tinzira don ta lura irin yaran masu hannu da shuninnan ne marassa tarbiya balle sanin darajan d’an adam wanda tasan akasarinsu sai sun buga shaye shayensu suke d’aukan mota suyita tuk’in ganganci wasuma su dinga kad’e mutane.... Waige waige ya somayi sanda ya fito daga motar amma baiga kowa ba sannan baiga komai ba dashike duhun mangariba ta soma shigowa.... Wata murya mai zak’i cikeda fad’a ne yaji dirarta cikin dodon kunnuwarsa... “Gani nan behind you....!” Tayi maganar tamkar d’an wasan kokawa dake neman d’an uwansa... Karkatowa Khalid ya somayi har saida ya waigo zuwa gareta.... Take gabansa yayi mummunar bugawa ganin wata halitta gabansa domin kuwa sam baka gane kalan fuskarta yanda tab’o ya mata dama dama, gashi ta murtuk’e fuska ta d’ora hannu bisa kunkuminta... Nan ya soma tunanin idanba gamo yayi ba toh kuwa shakka babu wannan mahaukaciyace data k’wace daga turu... Cikin masifa muryar nata ya kuma katse masa tunanin nasa... “Don kana cikin mota wani na tafiyar k’afa wa ya baka damar ka wulak’antashi.... Ko kuwa dai shaye shayen naka bai fad’i maka gaskiya ne... Kodai baka gani ne aka d’auki mota aka baka a gidanku...?” D tsananin mamaki Khalid ke dubanta zuciyarsa na k’una, jin k’aramar yarinya na yab’a masa maganganu, nan kuma yayi tunanin ai wannan zai wuya idan tanada lafiyar kwanya ma.... Murmushi ya sakar mata kana yace “Zaki iya gane asibitinku..? Seems guduwa kikai daga asibitin mahaukata koh... Fad’a min sunan asibitin naku I can take you back...” Nabila ta kuma zuwa wuya jin ya kirata mahaukaciya bayan wanka da tab’o da ya mata... Maimakon ta rama bak’ar maganar da ya fad’i mata sai kallo data bishi dashi zuciyarta na harbawa da sauri wanda ta danganta hakan da tsananin b’acin rai..., Khalid ya shafi goshinsa yaji jini..... Duban yatsun hannunsa yayi yanda ya lakato jinin kana ya kuma duban Nabila dake ci gaba da huci..... Kiraye kirayen sallan magrib ne yasa Nabilah jan tsuka had’ida furta “Nan gaba ka dinga kula idan kana tuk’i...” Tasa kai zata shige Khalid yayi saurin tare gabanta fuskarsa a murtuke.... “Ina kike tunanin zaki tafi da wannan ciwon da kikaji min sannan a tunaninki waye zai gyara min motata...?” Dab da fuskarta yake maganar wanda hakan ya sauk’ar mata da matsanancin fad’uwar gaba, domin kuwa sam batada tsoro amma wannan mutumin ya firgitata don babu wanda ya tab’a mata irin hakan.... Kasa furta komai tai sai k’ok’arin jada baya da take sannan bata daina aika masa harara ba.... Ganin mutane sun soma fitowa masallaci yasa hankalin Nabila ya kuma tashi kada Abbah ya fito ya taddata a nan, take kuwa wayarta ta hau ruri Mamy na kira.... Murya a tamke tace “Malam ka bani hanya na wuce ai bani nace kake tuk’in ganganci ba...” Khalid ya kuma yunk’urin matsowa kusanta, jikin Nabila ya d’auki rawa tana k’ok’arin jada baya, fitowarsu Sameer da Shamsu ne ya ceceta hankalin Khalid ya koma garesu.... Tamkar wulk’awar walk’iya haka ta b’ace a wajen.... Mamaki duk ya cikasu ganin Khalid da ciwo a goshi ga kuma motarsa a fashe... “Subhanallahi wai hakan ta faru ne...? Na kiraka naji baka d’aga ba I thought ma rasa gidan kayi kuma sai naji baka d’aga ba...” cewar Sameer cikeda kulawa Gajeren murmushi Khalid yayi kana yace “Na d’an sami accident ne...” Shamsu ya cab’e zancen da fad’in “Ai idan ka shigo unguwar nan kawai ka d’aura hannunka saman horn idanba haka ba kayita kuskuren bige yaran kenan don iyayensu sakesu suke tamkar shanu....” Sameer yace “Ai sai muje asibiti a dubaka....” Khalid yayi saurin girgiza kai yace “No no basai munje asibiti ba ko a gida zaka min dressing doc...” “Are you sure basai munje ba...?” Sameer ya kuma bid’a “Yeah I’m sure Dr...” Khalid ya fad’i yana murmushi had’ida waigan ta inda yarinyar can tabi wacce ko k’yallinta bai kuma gani ba, cikin sa’a ya hangi wulk’awan hijab d’inta ta shige gate d’in wani gida... Harda sauk’e ajiyan zuciya Khalid yayi don da ace ta b’ace masa baisan ta yanda zai samota ba a wannan unguwa mai tarin gidaje... Masallacin ya bisu shima domin gudanar da sallan magrib... Daga sahun da Abbah yake ya hangi bayan Sameer, take yaji zuciyarsa na masa wani irin sanyi ya k’udirin niyyan da zaran an ida sallah zai cimma saurayin nan ya tambayeshi sunan shi saidai hakan bata samu domin kuwa ana ida sallah ya nemi saurayin cikin masallacin ya rasa nan ma jikin Abbah a mace ya komo gida.... *** Ta yanda Mamy ke shiga bata nan take fita ba, haka taiwa Nabila tas akan daren da tayo a unguwa, Nabilah sai ture turen baki take tana fad’in “Amma dai Mamy kiga fah yanda na dawo gidan nan jagab da tab’o koma tausayina bakiji ba kuma baki tunanin ko lafiya nake ba... Mamy fah motar k’iris ya rage bata bigeni ba shine mai motar ya wankeni da ruwan tab’o...” “Rufe min baki sakarcin banza, rashin hankalin da kika tsaya yaja hakan ya sameki ai, banda sakarci tun yaushe ya kamata ki dawo gida sai yanzu, itama Bara’atun ai hankali bai isheta ba dama... C’mon ni wuce ki cire wannan kaya kafin ki b’ata min waje.... Sa’arki d’aya Abbanku bai tambayi ina kike ba...” Fuuu Nabilah ta shige d’aki yanda ta tadda Marliya na aikin gyaran wardrobe d’insu wanda sanda zata fita tai d’ai d’ai dashi wajen neman hijab.... Marliya na mata welcome Sisi ko takanta batabi ba ta fad’a toilet, Nabila ta fita zakka cikin yaran Mamy gata batajin magana gata batason aikin gida idan kaga ana aiki toh Marliya ce wai donma Mamy na tak’ura mata, ita dai barta da masifarta.... Babu yanda Sameer da Shamsu basuyi ba Khalid ya tsaya yaci dinner koma ya bar motar tasa gobe da safe bakanike yazo ya duba amma fir yak’i ya tak’ura tafiya zaiyi yanda ya sanardasu da safen zai mik’a motar wajen gyara... Gidan da yaga ta shige nan ya nufa yanda ya tadda wasu Almajirai zaune daga can gefen gate d’in gidan alamun wajen tamkar wajen zamansu ne..... Daga can gefe yayi parking kafin ya fito yana zira hannaye cikin aljihun wando sai wani faman yatsina fuska yake... Yaro guda ya kira cikin almajiran kana ya tambayesa ko yaga shigan wata yarinya cikin gidan d’azu bada jimawa ba... Yaron ya d’an tsaya tamkar mai nazari.... Tuni sauran almajiran sun k’araso wajen sabida sun zata sadaka mutumin zai bayar kar a bawa guda cikinsu su rasa... Daga yanda suke tsaitsaye rungume da kwanukan baransu d’aya yace “Ba Nabilah bace uwar masifa ta shige har muna k’ok’arin mata dariya tayi wanka da tab’o...” Sauran sukace “Tab wa ka tab’a gani yazo wajen wannan masifaffiyar inaga dai cikin sauran yaran gidan ne..” D’ayan ya kuma cewa “A’a Garzali itace kawai ta shige da mangariban nan...” Zasuci gaba da musu Khalid yace “Ku dakata, sunanta Nabila...?” A tare suka jinjina kai had’ida furta “Eh sunanta kenan uwar masifa...” Khalid ya jinjina kai kana yace “D’ayanku ya shiga ya min sallama da ita..” A tare yaran suka kalli juna fuskokinsu cikeda tsoro... Khalid ya kuma dubansu cikeda mamaki kana yace “Tsoro kukeji..?” D’aya wanda yafisu k’ank’anta yayi saurin jinjina kai had’ida furta “Zata iya hanamu zaman wajen nan idan muka shiga hark’arta, babu mai iya koda gaisheta ne cikinmu sabida masifarta...” Khalid ya Kuma jinjina kai kana yace “Karku damu bazata maku komai ba tasan da zuwana....” Ya k’arashe yana mai saka hannu cikin aljihu... Sadakan kud’i ya basu wanda tsaban mamakin yawan kud’in basusan sanda suka soma had’e baki wajen cewa bari suyi masa iso da ita ba... Sai zuba masa godiya suke tsananin tausayin yaran na d’awainiya dashi, yaran da basu wuce ace suna makaranta ba, wasu ba takalma wasu kayan duk a b’arke... Sosai suka baiwa Khalid tausayi sanda yaji suna fad’in abubuwan da zasuyi da kud’in da yanda zasu b’oye kada matar Malam ta gani ta k’wace.. Wasu na fad’in zasu sai takalmi wasu na fad’in sun samu kud’in karin kumallo na sati guda koma fiyeda haka... Kasancewar jikinta ya b’aci yasa tai wankan darenta mai iyanin ta sauya shiga cikin kayan bacci, suna zube parlorn Mamy suna kallon tashan wasan kwaikwayo lokaci guda suna cin tuwo itada Marliya Mamy na gefe tana ci gabada yiwa Nbilah fad’an rashin natsuwarta... Cin tuwon kawai Nabila take tasan yau sai gari ya waye Mamy ta daina d’ago maganar gashi ba itace a d’akin Abbah ba, babban abinda yafi bak’anta mata rai shine yanda ake cewa tai koyi da k’anwarta Marliya... Sallaman yaro almajirine ya katse Mamy yanda ya sanar dasu ana sallama da Nabilah a waje... Tuwon da Nabilah kenan bata had’iyeba ya tsaya mata a mak’oshi.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _..............DA RABO_ *19* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Mamaki bai saki Khalid ba ganin gidansu Nabieela suka nufa, har k’asan ransa yake jin dad’i don dama nan yayi niyyan zuwa ya danna mata wani wulak’ancin kafin ya tafi tinda itace silan kwanansa har biyu a garin..... Marliya ce ta masu iso har parlorn Abbah, Khalid sai dubanta yake yana hango tsananin kamanninsu da Nabila gashi dai ita wannan ga dukkan alamu saliha ce kuma mai hankali ba kaman wancan uwar bala’in ba.... Haka kurum Sameer yaji yarinyar ta kwanta masa sai murmushi yake yana dubanta yanda take kaikomo da kayan ciye ciye da shaye shaye gabansu.... Tambayarta sunanta yayi ta d’ago a hankali tana dubansa kana tace “Marliya...” Sameer yace “Sannu koh Marliya mun gode.....” Kanta a k’asa tana murmushi ta fice.... Jim kad’an Abbah ya shigo ya taddasu, nan suka soma gaidashi gaba d’ayansu, Khalid sai yafi kowa zak’ewa da son suyi sabo sosai da Abbah saidai ya lura shi Abban wani irin mutum ne wanda yakeda tsananin tsarewa, harta uban gayyan wato Sameer ba wani hira suke ba da alama kawai Allah ne ya had’a jininsu... Tray mai d’aukeda ruwan sanyi Mamy ta hanga gefen fridge da alama Marliya ta mance bata kai masu ba, Nabilah ce gefenta tana had’a tray d’in abincin Mamani nan Mamy ta umarceta ta bar abinda take takaiwasu Abbah da bak’insa ruwa... Sam Nabila batason shiga kan mutane don tasan wani cikin bak’in ya fad’i mata ba daidai ba tana iya danna masa mummunar kallo wanda har sai sun had’a idanu bak’on ya fahimci haka idan kuwa babu Abbah wajen ta jifa masa magana tai gaba abinta.... Badon taso ba ta d’auki tray d’in ta nufi sashen Abbah, sam bata kawo zatai artabo da mutum mai irin kamanninsa ba cikin gidansu, wani wawan birki ta danna tana mai kuma k’yafta idanu alamun badai gizo yake mata ba, tabbas shi d’in ne, Innalillahi toh mai yakeyi a gidansu, mai ya kawosa gidansu harma parlorn Abbanta, wannan wane irin mutum ne tai gamo dashi, kardai yasan Abbanta ne...? Haka tayita jerowa kanta tambayoyi babu mai amsa mata su, Khalid kuwa tamkar ance ya juya sukayi idanu hud’u da Nabilah dake tsaye wajen tamkar an dasata, murmushi ya sakar mata had’ida kashe idanu guda irin taji mamakin nan koh.... Lokaci guda tai saurin saita kanta kana ta nufi parlorn kanta a k’asa, gaisuwan jam’u ta masu don bata fatan dogon gaisuwa ya shiga tsakaninta da d’aya daga cikinsu.... Sauri sauri ta fice daga parlorn k’irjinta naci gaba da bugu.... Saida ta sami bango ta tokare take iya sauk’e numfashi mai nauyin gaske, murmushinsa kurum take hangowa wanda ya kasa b’acewa daga k’wayan idanunta, da ace bata ganshi sau biyu kafin yau ba k’ila tace kamanni sukayi don ta tabbata babu abinda ya had’a Abbanta da wannan mutumin, toh amma shid’in ne dai, toh wai waye shi ne kam.... A hankali ta lumshe idanunta domin kuwa izuwa wannan lokaci lamuran mutumin ya soma bata tsoro... Aunty Lami ce tazo zata shige ta kafe Nabilah da idanun ganinta cikin yanayi wanda bata tab’a ganinta cikin irinta ba... K’arasowa tayi had’ida dafata kana tace “Nabila lafiya kike....?” Sai sannan Nabilah ta bud’e idanu tana duban Aunty Lami.... Saurin turb’une fuska tayi kana tace “Lafiya mana Aunty... Barin shige...” Bata jira cewan Aunty Lami d’inba tai shigewarta.... Kallo Aunty Lami ta rakata dashi tana mai nazarinta, gyara mayafinta tai kana tasa kai ta nufi parlorn Abbah.... Ganin da bak’i a parlorn ya sanyata sakin fuska sosai yawa mutuniyar k’warai tana wani aza mayafi ta k’arasa tana fad’in “Bak’i ne mukayi... Sannunku da zuwa....” A tare Shamsu da Khalid suka soma gaidata kafin Sameer ya had’iye abincin dake bakinsa shima ya d’ora da gaisuwan a lokacin da ya d’ago fuskarsa.... Wani irin mummunar fad’uwan gaba ne ya dirarwa Aunty Lami sanda tayi tozali da idanun Sameer, ta kasa amsa gaisuwan da ya mata ta kuma kasa daina kallonsa, badon a zaune take ba tabbas da jiri ya iya kayarda ita.... Abubuwan da suka faru shekaru 30 baya suka shiga dawowa kwanyarta, har saida Abbah ya furta “Lami ana gaisheki ko bakiji bane...” Sannan Aunty Lami ta iya kimtsa kanta.... Murya a d’an sark’afe ta amsa murmushin yak’e bai bar saman fuskarta ba.... Sauri sauri ta fice daga parlorn ta nufi nata sashen ta d’auki wayarta babu shiri.... Hajiya na faman rabon fad’an Hafiz da Sahariyya kan tak’urawa d’iyarsa Kausar da Sahariyya keyi taji wayarta na faman ruri cikin d’aka... Fad’i take “Ku kuka sani ku cinye kanku idan bazakuji maganata ba, wannan yarinya taka mai jinin tsiya a tareda ita gwarama kayi auren ka kaita can wajen matarka ta kular maka da ita...” Tana ida fad’in haka ta nufi d’aki tana lalumar wayarta yanda ta tadda wayar ta katse, ganin wacce tai mata kiran ya sanyata saurin sake dialing layin.... Hafiz dake mak’ure da wuyan Sahariyya fad’i yake “Wllhi kinji na rantse babu yanda zankai Kausar nan gidan zata girma tinda ku kuka tilastama uwarta barinta don haka dole ku kula da ita, kin sanni kinsan banida kyau kukan yarinyar nan na sakeji wllhi sai nayi ajalin idanunki k’wara... Shashashar banza...” Yana ida fad’in haka yayi jifa da ita kana yayi ficewarsa sai faman fito yake hula a karkace ya nufi wajen sahibarsa Sawwama..... Tinda Aunty Lami ta d’auki wayar Hajiya ta fahimci babu lafiya..... “Wai meke faruwa ne ni dan Allah ki sanar dani.....” Hajiya tace hankali tashe... Aunty Lami ta samu jikin gado ta jingina kana tace “Haule anya kin tabbata Ma’aruf ya mutu...? Haule anya Ma’aruf ya zama tarihi kaman yanda muke tunani, anya Ma’aruf bazai dawo garemu ba....?” Dukda bugu da k’irjin Hajiya keyi bai hanata dariyar yak’e ba kana tace “Haba Lami meye kuma kike neman maida mutane baya ana ci gaba a rayuwa, wane irin Ma’aruf...? Idan dai Ma’aruf d’an gidan Usman Mailafiya ne ya jima da mutuwa saidai mai kamanninsa, kinga kima daina sak’awa zuciyarki wannan mummunar zato don Allah....” Ta k’arashe tana zama bakin gado.... Girgiza kai kurum Aunty Lami take tamkar Hajiyan na dubanta kana tace “Inaga dai baki fahimci abinda nake nufi bane Haule amma idan da hali yau d’in nan mu had’u gidan Aminiyar sirri ta fad’i mana gaskiyar abinda tayida Ma’aruf Mailafiya don wllhi yau nikam nayi tozali dashi a raye....” Jikin Hajiya ya d’anyi sanyi, gyara zamanta tai kana tace “Shikenan Lami mu had’u gobe gidan Aminiya tinda dai yaukam kinga dare yayi, ke nake jiyewa kinsan wannan baud’edd’en mijin naki ba bari zaiyi ki fice ba ni kuwa nawa mijin dama a tafin hannuna yake... Ma had’u goben....” Aunty Lami ta amsada “Toh shikenan Alhaji na fita Kasuwa zan fito...” Daga haka sallama sukayi ko waccensu tana sak’e sak’e cikin zuciyarta..... *** Washe gari haka Nabila ta tasa Mamy gaba da tambaya ko tasan bak’in Abbah... Mamy ta umarci Marliya data kwashe dankali cikin mai kana ta dubi Nabilah dake shirya wanke wanken plates cikin drawer tace “Kici gaba da tambayata abinda bai shalleki ba kar kiyi aikin dake gabanki....” Nabilah ta turo baki gaba tace “Kai Mamy tambaya shikenan ya zama laifi ai da Marliya ce ko Addah suka tambayeki amsasu zakiyi, Mamy Dan Allah su wayesu...?” Girgiza kai kurum Mamy tayi kana tace “Nabilah ban sansu ba hasalima ban shiga parlorn ba har dai suka tafi kina gani ai... Toh yaya za’ayi na sansu kin kuma san Abbanki kinsan wane irin mutum ne ba kasafai yakeso ana haurawa kansa ba musamman idan yana tareda bak’i, ballanata ma kinsan ba shigan zanyi ba idan ba shine ya buk’aci hakan ba... Wai me bak’in suka miki ne...?” Ta k’arashe maganar tana mai jefo mata tambayar had’ida tsareta da idanu... Girgiza kai Nabila tai cikin sauri don bataso Mamy ta fahimci wani abin kana tace “A’a basumin komai ba kawai dai na tambaya ne.....” Kan Mamy ta kuma jefo mata wata tambayar ya mik’e ta d’au markad’en kayan miya ta zuba cikin blender.... Girgiza kai kurum Mamy tai kana tace “Allah sa dai ba wani tsaurin idon kika masu ba don nasan halinki....” Bata jira cewan Nabilar ba tai ficewarta... Nabilah da Marliya suka kalli juna suna k’unshe dariya,Marliya tace “Mamyna case... Addah Naby kema dai Dan Allah ki daina tinzira Mamy sai kuyi zaman lafiya...” Harara Nabila ta galla mata kana tace “Ke idan aka biyeta Mamy toh fah a gidan nan ma sai aci kashi akanmu, k’yaleta kawai haka zanci gaba da lallab’a kayana wataran zatai missing masifar nawa da taro mata magana...” Da mamaki Marliya ke dubanta kana tace “Addah did I hear you right...? Kikace wataran Mamy zatai kewar fad’anki, uhm kodai kodai Mamy ta kusa yin sirki ne....” Ludayin gefenta ta janyo zata kwad’awa Marliya, Marliya ta sukunya tana dariya kana tace “Kinga gaban mangyad’a nike kiyi hak’uri don Allah, nifah kawai tambaya nai.....” K’wafa Nabilah tai kana tace “Dama baki sunkuya ba, wllhi Allah sawak’e na tsaya kula wani namiji bayan duk halinsu guda ne, ga Addah can tayi auren wahala bataji dad’i ba ga Mamy ma ba wani dad’in auren takeji ba Aunty Bara’atu mijinta kullum baya nan wayasan uwar mai yake tsinanawa a can barikin, zamana a gida gaban iyayena yafin zaman gidan wani gardi da idan yamin badaidai ba garin nan sai ya mana kad’an don wllhi da ace ni ce Ya Hafiz ke aure da tuni ya gama shiga taitayinsa...” Sallaman Aunty Lami ne ya katsesu... Marliya ta amsa da sakin fuska yayinda Nabila ta tab’e baki taci gaba da abinda take... Lek’owa kitchen d’in Aunty Lami tayi tana fad’in “A’a ‘yanmatan gidan ne a kitchen, iyye kaga yaran Mamy....” Idan kayan miyan da take juyewa cikin tukunya sunyi magana itama zatai magana, Marliya ce dai gaisheta fuska fal fari’a kana tace mata Mamy na ciki... Har saida Aunty Lami ta ambaci sunan Nabila kafin Nabilar ta juyo a tak’aice tace da ita ina kwana... Shikenan gaisuwar bata kuma cewa komai ba... Jin muryar Aunty Lami yasa Mamy fitowa suka soma gaisawa, nan Aunty Lami d’in ke sanar da Mamy zata gidan Yayarta Rabi bataji dad’i ba.... Mamy tace “Ayya Allah ya bata lafiya, kinsan shigowar daminan nan sai a hankali yanayi ya canza sai ayiya cututtuka...” Aunty Lami tace “Wllhi fah Mamy abin saidai addu’a...” Mamy tace “Haka ne ki gaidata da jiki....” Aunty Lami ta amsa da “zataji sai na dawo...” Mamy ta amsa mata da “A dawo lafiya...” Nabilah na kitchen tana kwaikwayon maganan Aunty Lami kana tai k’wafa tace “Salon munafunci...” Juyowa tai ta dubi Marliya dake dubanta da mamaki kana tace “Ke kuma idan ina waje kika kuma biyewa wannan munafukar matar tana wani jan mutane da wasa wllhi kema sai na daina miki magana tam...” Dariya kawai Marliya tai kana tace “Um naga dai matar babanki ne don haka itada Mamy matsayinsu d’aya, besides Aunty Lami battada matsala tun tasowarmu haka muka gansu zaune lafiya da Mamy....” Tsuka Nabila tai kana tace “Aikin banza wannan da gani ruwan munafukai ne da ita shiyasa sam tamu batazo d’aya ba... Nidai na fad’a miki idan ina waje kema kiyi banza da ita kafin na tunb’uke miki hak’orin gaba....” Girgiza kai kurum Marliya tai tana dariya kana ta fice a kitchen d’in ta bar Nabilah da masifarta... *** Wajajen biyar na yamma Khalid ya sauk’a a Kaduna dashikema bai fito da wuri ba saida ya tsaya ya kammala wasu abubuwan.... A parlor ya tadda Siyama da Yesmin first cousin d’insa d’iyar Yayan Ammi dake karatu a Cyprus, rabonsa da ita zaikai shekara biyu ko fiyeda haka idan bai mance ba... Siyama na hangosa murmusinta ya k’aru kana tace “Speaking of the devil... Kinga gashi nan sauk’arsa kenan....” Baice mata komai ba sai uwar harara da ya danna mata Cikeda zumud’i Yesmin ta ajiye glass of lemonade dake hannunta ta juyo tana dubansa fuska fal fari’a..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *20* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* “Ya Khalid sannu da zuwa, ya hanya...?” Yesmin ta fad’i cikin kashe murya.... Kallon kirki bata ishi Khalid ba yace da ita “Kina lafia...?” A tak’aice... Nanma saida ta kuma murmusawa had’ida juya idanu kana tace “Lafia lou, it’s been a while...” Bai bari takai ayaba yace “As you can see I just got home, I’m pretty tired... would you please keep your greetings maybe for later....” Ya k’arashe yana d’aga mata giransa sama alamun Yes a gajjiye yake... Nan fah jikin Yesmin yayi sanyi ta juyo suka had’a idanu da Siyama, sosai Siyama taji kunyar abinda Khalid yayiwa yarinyar nan Yesmin tasan za’a rina hakan kallon su Ammi kurum take idan taji suna mafarkin had’a Yesmin da Khalid, basusan Khalid wane irin baud’edd’en mutum bane shiyasa... Har ya isa staircase Siyama ta d’an bud’e murya tace “Eyya shalelen Daddy sannu da hanya ko nazo na baka massage ne...?” Rolling idanunsa yayi yana mai dubanta a kaikaice kana yace “Spare me your false sympathy Siyaam...” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai yayi haurawansa sama... Duban Yesmin Siyama tai fuska d’aukeda murushin yak’e kana tace “Ehen mai ma nake ce miki....?” Girgiza kai Yesmin tai kana tace “Cousin anya Khalid zai soni kuwa...? Kiga fah abinda yayi...” Murmushin Siyama ta kumayi kana tace “Kar ki damu cousin idan dai Khalid ne ya wuce haka, but I believe you can change him....” Sauk’e deep breath Yesmin tai kana tace “But are you sure he doesn’t have a girlfriend...?” Murmusawa Siyama ta kumayi kana tace “Wa... Wannan...?” Ta kuma d’an murmusawa kana tace “Dukda fad’a da muke yawan yi Khalid bai tab’a b’oyemin komai ba na rayuwarsa... Idan da ace yanada I’ll be the first person to know.. My brother is single... Shifah wannan baida lokacin ‘yanmatan ma pride d’insa bazai bari ya nemi budurwa ba shiyasa nace miki idan kinyi hak’uri you can win him over...” Kurb’an lemonade Yesmin tai tana jinjina kalaman Siyama... A b’angaren Khalid kuwa Haurawa sama da yayi yaji dama bai shigo sashen Ammi ba gaba da’aya, Aunty Hidaya ya hango mahaifiyar Yesmin Yaya ga mahaifiyarsa.... Cikin sauri yasa kai zai juya saidai tuni Aunty Hidaya ta hangoshi, bud’e murya tai cikeda far’a kana tace “A’a Son suk’ar yaushe....?” K’ak’aro murmushi yayi yace “I just arrived Aunt.... Mun sameku lafia....?” Aunty Hidaya ta kuma murmusawa kana tace “Lafiya lau Saifullahi... Ya aiki...?” Murmushi Khalid yayi don ita kad’ai ke ce masa Saifullahi kana yace “Lafiya Aunt... Aunt Ammi fah...?” Aunty Hidaya tace “Ta shige d’aki but tana fitowa... inaga bathroom ta shiga....” Jinjina kai yayi kana ya mik’e a d’an gajjiye yace “Ok Aunt idan ta fito a ce mata na dawo... zan wuce d’aki na d’an kwanta before magrib...” Dakatar dashi Aunty Hidaya tai da fad’in “Kaga k’anwar taka a k’asa koh... Jiya ta dawo daga sch ta gama gaba d’aya sauran karb’an result, she was so excited sanda taji zanzo don ko hutawa batai ba tace zata biyoni Kaduna....” Ta k’arashe cikeda gwad’a d’iyarta Yesmin.... Tak’aitaccen murmushi yayi kana yace “Aunt I’m exhausted, see you later....” Yana ida fad’in haka ya fice cikin sauri ba tareda ya bari ta kuma janyo wani zancen ba.... Kallo tabi bayansa dashi k’asar zuciyarta tana furta lallai akwai aiki da wannan baud’edd’en yaron.... **** Yana zuwa d’aki wanka yayi ya rage kayan jikinsa zuwa masu sauk’i kana ya mik’e kan gadonsa... Wayarsa ya janyo ya shiga duban lambar da ya d’aukesa lokaci a garin Kano kafin ya samu don neman lambar ne ma ya dad’a zaunar dashi.... Kallon lambar yake yana murmushi lokaci guda ya shiga tura sak’o yana mai ambatawa cikin zuciyarsa _Karkiyi tunanin Khalid ya mance... No never, you must pay for what you did..._ **** Nabila ta kuma duban Addarta Zulfah a karo na biyu kana tace “Addah donma bakiga how Mamy scolded me bane ranan da nazo na jima, is like Mamy gani take Aunty Bara’atu is nothing but a bad influence to her children, gani take wajenta nake koyo duk wani rashinji... Yanzu ma bance mata ga yanda zaje ba kawai tasan dai zan shiga sch registration ne dashike an koma....” Zulfah ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana ta kamo hannayen Nabilah tace “Kiyi hak’uri Sis ni na janyo miki....” Girgiza kai kurum Nabilah tai kana tace “A’a you don’t have to apologize, I’m your sister, when ever you need me.... I got your back....” Rungumeta Zulfah tai cikeda farin ciki suka ci gaba da firansu.... Daga yanda Aunty B ke tsaye jinjina kai tai k’wayan idanunta suna kuma kad’awa, ‘yar uwarta Mariya bazata tab’a daina kallonta a matsayin mutuniyar banza ba, tun suna k’ana haka ta d’auketa har sukayi aure, har izuwa lokacinda iyayensu suka rasu suka barsu..... Hannu tasa ta goge hawaye guda da ya gangaro mata bata iya shiga d’akin ba sai juyawa da tayi da baya.... “Ya Kausar..? Kinje kin dubota...?” Zulfah ta tambaya damuwa kwance saman fuskarta.... Girgiza kai Nabilah tai kana tace “Banje ba tukuna amma In sha Allah daga nan zan biya...” “Yaya Hafiz fah.... Yana zuwa gida...?” Saida Nabilah ta aika mata wata kallo kana tace “Toh ni ina ruwana dashi da har zan fahimci yana zuwa ko bai zuwa....” Zulfah bata kuma cewa komai ba tinda ta fahimci tambayar Hafiz ya sanya ran ‘yar uwar tata b’aci.... Mik’ewa Zulfah tai ta bud’e drawer ta zaro wasu ‘yan kud’ade kana ta mik’awa Nabilah tace “Gashi ki sai mata tsara idan zakije and please hug her for me... Kema ga wannan ki sai maku wani abin keda Marliya....” Kallonta Nabilah tai ta kalli kud’ad’en kana tace “Addah save your money, now that you’ve to face another life zai maki amfani, nida Marliya bamu buk’atan komai, zandai karb’i na Kausar na sai maita...” Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Karki damu na karb’i alawee na ne na wannan watan, I’m still saving some, sannan babu abinda Aunty B bata min kinji koh so ki kwantar da hankalinki.... Inaso na kira Mamy but banso ta fahimci komai cikin muryata... Can you please hug her for me...” Ta k’arashe idanunta na rau rau.... Hannayenta Nabila ta rik’e cikeda tausayawa kana tace “Komai zai wuce Addah... Kar ki mance masu iya magana sunce INDA RAI DA RABO... Watarana zaki bud’e idanu ki tarar komai ya wuce, rayuwa ta zamto sabuwa mai dad’i, all your nightmares zasu gushe kinji koh... Never lose faith...” Jinjina kai Zulfah tai kana tace “Allah yasa k’anwata...” Nabila ta sakar mata sassanyar murmushi.... Sun jima suna tattaunawa kafin Nabilah ta d’auki jakarta da ‘yar folder d’inta ta makaranta tai masu sallama.... Tana tsaye tana neman adaidaita sak’o makamancin na jiya ya shigo mata daga lambar da bata sani ba... Karancewa tai had’ida jan tsuka ta danna delete, bata kuma bi takai ba ta tari adaidaitan ta ta nufi gidan Hajiya..... Saida ta tsaya bakin babban kwalta tai sayayyan kayan mak’ulashe na yara wa Kausar kafin ta nufi gidan... Akayi sa’a bata tadda Hajiya ba, da alama harta yaran Hajiyan ma basa nan, Raihanah kawai ta tadda zaune bakin barandar Hajiya suna wasa itada Kausar... Sosai Nabila taji dad’in ganinsu haka, tayi tsaye tana dubansu fuska fal fari’a.... Kausar ince ta fara hangota ta shiga d’aga hannaye sama tana dariya alamun ta ganeta.... A guje Nabila ta tafi ta d’aga yarinyar sama tana cillawa Raiha na dariyarsu... D’an gefe dasu Nabilah ta zauna Raihana na mata sannu da zuwa... Fuska a sake Nabila ta amsa kana tace “Yau ku kad’ai ne a gidan...?” Jinjina kai Raiha tai kana tace “Sun fita gaba d’aya d’iyar k’awar Hajiya ta haihu yau ake suna....” Nabila ta jinjina kai don taji dad’in hakan zata samu ta tambayi Raihana kalan goyon da ake baiwa d’iyar ‘yar uwarta..... “Raiha ki fad’imin gaskiya please Ya rayuwar Kausar yake hannun Hajiya da iyalanta....?” Take idanun Raihana sukai rau rau, lokaci guda tasa bayan hannunta ta goge hawayen kana tace “Addah Nabila ko ban fad’a miki ba kinsan irin rayuwar tsanar Addah Zulfah da sukai yayi tasiri ga rayuwar innocent Kausar... Addah Nabila banso Kausar tayi irin girman da nayi.... Inso taji dad’i ta rayu da mahaifiya tasan soyayya da shak’uwa irinta mahaifiya wanda ni na rasa tsawon rayuwata....” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Nabilar ma k’walla ne suka ciko idanunta, tai k’ok’arin dannewa don k’arfafa gwiwan Raihana kana ta kamo hannayen Raihana ta rik’e cikin nata lokaci guda take furta “Komai zai wuce Raiha, komai zai zama labari.... Hak’urinki bazai tab’a tafiya kawai ba, zaki cimma wani mataki na rayuwa da yardar Allah.... Believe me INDA RAI DA RABO.....” Ta k’arashe tana k’ak’aro murmushin k’arfafa gwiwa.... Jinjina kai Raihana tayi had’ida sakin murmushi kana tace “Haka ne Addah Nabilah wataran komai zai zama labari...” Nabila ta sakar mata murmushi kana ta mik’a mata ledar hannunta tace “Ga wannan sai ki adana mata please...” Cikedajin dad’i Raihana ta amsa tana mai godiyawa Nabilar domin ita duk wanda zai k’aunaci Kausar ya gama mata komai, har cikin ranta takejin yarinyar... Koda Hajiya da iyalanta suka dawo basusan anyi hakan ba, toh mai ma ya shallesu dasu, Hajiya ce ma mai d’an k’ok’arin kulada Kausar sabida jinin d’anta dake jikinta Najah kuwa ‘yar ko oho ce abinda Sahariyya ta d’aurata akai take bi, ita kuwa Sahariyyar tinda Hafiz ya mata kaca kaca akan Kausar ta kuma d’aukan karan tsana ta d’orawa yarinyar, batak’i ta wayi gari ta tadda yarinyar ta mace gaba d’aya ba, k’ila da har party saita had’a sabida farin ciki.... *** Shigowarta gidan kenan, dawowarta daga office ta hangi mota pake gefen flowers tamkar nasa, gabanta ya fad’i... For the first time da tab’a jin shakku cikin zuciyarta shin tana farin ciki ne da ganin Partner ko kuwa akasin hakan...... *SameenaAleeyou📚* *INDA RAI* _...............DA RABO_ *21* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Tijjani mai bayiwa flowers ta kirawo tana tambaya...... “Tijjani motar waye wannan....?” Da tsananin mamaki Tijjani ke dubanta don a tunaninsa idan kowa zai mance kamannin motar Sameer ai ita bai kamata ace ta mance ba..... Sosa kai Tijjani yayi kana yace “Hajiya ai motar Datta ne.... Bai jima da isowa ba .....” Jinjina kai tai had’id lumshe idanu, da gaske Sameer na cikin gidansu, abinda ya faru last week ya shiga mata yawo a kwanya, tunanin ta yanda zata soma fuskantarsa ya addabeta, gani take tamkar Sameer zai fahimci wani abin.... Saida ta sauk’e deep breath kafin ta iya samun strength ta bud’e motar ta fice.... Kallo guda zaka mata ka fahimci tsananin sanyi da jikinta yayi, a hankali tasa hannu ta tura k’ofar parlorn, ba kowa sai Yesmin dake aikin kallo.... “Hi cousin...” Yesmin tace tana sakar mata murmushi... Murmushin itama tai k’ok’arin maida mata kana tace “Are you alone....?” Yesmin ta jinjina kai tana mai gyara zama saman sofa take fad’in “Eh Mummy da Ammi sun fita, Ya Khalid kuma yana tareda bak’o a sashensa.....” Jinjina kai Siyama tai kana ta nufi upstairs don yin wanka, shiga tayi cikin sauk’ak’an kaya, doguwar riga mai laushin gaske as usual kai a bud’e.... Tsintar kanta tai da kasa fitowa daga d’akin sai faman sak’e sak’e take, bata tab’a tunanin cire cikin nan zai dameta irin haka ba, har cikin ranta take jin bazata iya fuskantar Sameer ba, what if ya ganeta..? What if ya tambayeta.... Mai zata soma ce masa....? A hankali ta lumshe idanunta tana mai ayyanawa this is the best for the both of them..... Parlorn ta nufo tana mai shafa samar wayarta a daidai lokacinda Khalid da Sameer suka shigo parlorn... Daga can ya hangeta saman bene tai looking very pale kaman tai ciwo, gaban Sameer ya yanke ya fad’i cikin sauri ya nufi yanda take tsaye ta kasa motsa koda ‘yar yatsanta ne.... Khalid kam cikama rigarsa iska yayi musamman da ya hangi wannan yarinya mai uwar rawar kan a parlor, gaba d’aya ya fice daga gidan don dama Sameer ne ya zaunar dashi..... Kallon juna suka shigayi tamkar wanda suka jima basuga juna ba, murya can k’asan mak’oshi Sameer yace “Partner...!” K’wallan da Siyama ke mak’alewa ya gangaro mata... Sameer bai wata wata ba ya rungume matarsa tsam cikin jikinsa... Fad’i yake “I’m here Partner... I’m here...” Sosai Siyama ta kwanta cikin k’irjinsa tana sakin kuka a hankali, abinda ta rasa na ‘yan kwanaki... Batai zaton tayi kewar mijinta har haka ba... Ita kuwa Yesmin yanda kasan ta sami tv haka take kallonsu, batai zaton ana irin wannan soyayyar a nigeria ba Nigeria d’in ma arewacinta.... Sun bala’in birgeta, Ita da Khalid kawai take hangowa cikin fuskokinsu, lallai cousin d’inta nada babban sa’a dama wannan shine mijin nata, he’s every woman’s dream... Gaskiya Siyama ta cab’a don babu macen da bazata so wannan had’edd’en gayen yake mutuwa akanta ba, gaba d’aya sun tafi da ita uwa wani duniya musamman data kuma jiyo muryar Sameer cikin damuwa yana furta “Partner are you sure you’re fine... look, kalli fah.... kalli yanda kika koma... My goodness Siyaam have you been eating...? Talk to me...” Ya k’arashe yana rik’e arms d’inta had’ida d’an jijjigata kad’an... Harara ta d’an jefa masa kana tace “What do you expect Partner bayan ka tafi ka barni... So abinci ma bazanci da kyau ba....” Murmushi ya sakar mata wanda ta jima bata gani ba kana yace “I’m sorry honey, zamu tafi tare wannan karon....” D’an zaro idanu tai tana dubansa bata kai ga magana ba su Ammi sukayi sallama.... Sameer ya d’anyi k’ok’arin zare jikinsa daga na Siyama cikeda kunya yana d’an sosa k’eya ya nufo parlorn gaisar dasu Ammi... Ammi fad’i take “A’a Dr sauk’an yaushe..? Sannu da zuwa lale...” K’arasowa yayi ya zauna saman carpet yana mai gaidata... “Mun sameku lafiya Ammi...” Ammi tace “Alhamdulillah Sameer, ya aiki...” Amsa mata yayi da angode Allah kafin Aunty Hidaya tace “Wannan ne sirkin namu..?” Ammi tace “Gashi nan fah sirkin naki...” Sameer ya duk’a ya gaidata itama cikeda karramawa, Ammi tai introducing Aunty Hidaya da d’iyarta Yesmin.... Yesmin ta mik’e a guje tabi bayan Siyama zuwa kitchen yanda ta tadda Siyamar ta saka Kubura ta markad’e masa lemun abarba... Rungumeta Yesmin tai tana fad’in “Cousin kin gama dacewa kekam babu abinda ya miki saura,this kind love ku bar mana saura nida Khalid....” Ta k’arashe tana d’an daka tsalle... Kubura da ta kafeta da idanu dariya ta kwashe dashi kana tace “Iska na wahalda mai kayan kara....” Yesmin ta juyo a kufule tana dannawa Kubura muguwar kallo don dama tun zuwanta gidan jininsu baizo d’aya ba ta lura son gulma ne da ma’aikatan... “Mai kikace...?” Yesmin ta tambaya... Kubura ta d’ago idanu kana tace “Au wai ni... Bance komai ba...” Siyama ta danno mata mugun kallo kana tace “I know you Kubura mai kikace...?” Kubura tace “Haba Aunty kinsan dai bana miki k’arya wannan yarinyar kawai k’aunata ce batai... Kuma ni naga ba son Khalid nake ba koh Aunty...” Ta k’arashe tana duban Siyama... Siyama ta murmusa don ta lura har yanzu Kubura bazata daina haukan da take da wauta akan Khalid ba a baya ta zaci tsaban yarinta ne amma yanzu ta lura hauka kurum Kubura keyi, gashi ko hanyar da Khalid d’in ya taka idan ance tabi bazata bi ba tsaban tsoronsa da take... Girgiza Siyama tai kana taceda Yesmin “Rabu da ita cousin haka take...” Yesmin ta kuma galla mata harara kana tace “I heard her loud and clear fah wllhi tace wani abin k’ilanma zagina tayi...” Kubura ta kuma watso wata maganar a hankali kafin Yesmin tai magana taceda Siyama “Aunty ga lemun yau dai zamuyi kewarki a gidan nan tinda Likita ya dawo gashi baki bani na kati ba yau.....” Tak’aitaccen murmushi Siyama tai kana tace “Wai ke Kubura kullum sai an baki na kati waima waye kike kira....?” Kubura ta zaro idanu kana tace “Aunty donma bakiga yanda a facebook samari ke bina ina masu wulak’anci ba sabida ni inada mijina gangariya ko kulasu banayi...” Saida Siyama ta dara kana tace “Ko kuma kece iskan ke wahalwa... Kinga ki shirya yanzu ki tafi gidana kije ki kintsa gidan kafin mu k’araso.... Ki haura sama ki d’auko min handbag d’ina...” Cikeda jin dad’i Kubura tace “An gama Hajjaju tamu Allah dai ya kare mana ke hasken zuciyar Dapta...” Janyo hannun Yesmin Siyama tai suka fice tana fad’iwa Kubura “Ni ki wuce kafin daren ya idayi....” Kubura sai murna take tasan yau tim Siyama zata cika mata aljihu.. Ta raka Yesmin da harara tana fad’i bayan sun fice... “Kuji wannan abin meyema Khalid d’ina zaiyi dake..? Wllhi yafi k’arfin ajinki, nan gani nan bari akwatin maye... Duk barikancinki bazai k’yalla idanu kanki ba ehe... Banza kawai, ni yanzu daga Facebook ma makaranta zan koma sabida na lura Khalid d’ina asalin d’an boko da gayu ne ...” Ta k’arashe tana jan dogon tsaki had’ida sauya taku..... Hhhhhh Wayaga su Kubura mata a gidan Khalid... *** *Kano* Banda taunar chewing gum bata komai sai wani d’add’aga idanu sama take tana tafiya tana bankad’a k’irji gaba, a yatsine ta k’araso teburin da yake kana tace “Ina saurarenka....” Kallo ya bita dashi yanda tai masa tsaye aka kana yace “Ki zauna mana....” Saida ta d’auki lokaci tamkar bazata zauna ba sai kuma ta finciko kurar ta zauna had’ida bashi baya tana mai ci gaba da taunar chewing gum... “A haka ne zamuyi maganar...?” Ya fad’i yana yana mai d’an rank’ofowa.... Hannu ta d’aga masa cikeda tsiwa take fad’in “Kaga Hafiz nifa ba k’aramar yarinya bace da zaka nemi rainan wayo, idan magana kakeso muyi kayi maganar gaskiya ka turo gidanmu idan kuma ba haka ni kada ka sake zuwa wajena don wllhi bazan baka kaina ka watse dani a waje ba kaman yanda kayi da wancan ‘yar agwagwan ehe...” Ta k’arashe tana mai danna masa aya..... K’uri kawai Hafiza ya mata yama rasa mai zaice mata sai sunkuyar da kansa da yayi yana sosa goshi a hankali..... Alhaji Tanimu mai kula da ginin da ake a gefen Kantin ne ya shigo yana faman washe mata baki, da gayya Sawwama ta mik’e ta nufesa cikin yanayin tafiyarta anayi ana rawa da k’irji ta isa gareshi tana fad’in “Alhajin kowa mai za’a kawo maka...?” Bai daina yak’e baki ba yake fad’in “A kawo min tuwo ‘yar kyakkyawa...” Ya k’arashe idanunsa k’yam a k’irjinta... A fusace Hafiz ya mik’e ya nufi Alhaji Tanimu zai kai masa naushi nan fah yaran Alhaji Tanimu sukayo kansa... Magajiya mahaifiyar Sawwama ta nufosu gadan gadan tana k’ok’arin rabon fad’a.. Sai fincika Hafiz yake yana fad’in Uban mai Alhaji Tanimu ke kallo jikin matarsa... Sawwama bata tab’a sanin Hafiz na sonta haka ba sai yau, dad’i ya mamaye zuciyarta ganin irin kishin da Hafiz ke nunawa akanta... Da k’yar aka raba fad’an Hafiz Alhaji Tanimu saida aka fidda Alhaji Tanimu daga restaurant d’in.. Shiko Hafiz a zuciye ya k’araso gaban Sawwama yana fad’in “Kin gama aiki a restaurant d’in nan, ince damuwarki a d’aura auren ne...?” Cikin fad’a Sawwama ma tace “Wllhi babu igiyanka akaina baka isa hanani zuwa nan ba...” A hasale yace “Haka kikace...?” “Kwarai kuwa haka nace...!” Ta k’arashe tana galla masa harara hannaye a kunkumi... K’wafa yayi kana ya d’auki mabud’in abin hawansa yayi ficewarsa daga Kantin... Yana fita Sawwama da Mamanta suka dubi juna suka shek’e da dariya, Magajiya tace “Kinmin daidai yanzu ne zaki fahimci matsayinki a wajensa idan har da gaske sonki yake....” Sawwama ta murmusa tana mai jijjiga ita kad’ai kana tace “Allah Magajiya ki tsaya ki gani tas saina mallakesa ni kad’ai a tafin hannu na.....” Shewa suka kuma sakawa Magajiya tana mai rangad’a gud’a.... **** *Kaduna* Tsaye take tana hangensa sai faman shirya masu dining table yake bayan ya gama dafa masu abinci mai sauk’i dai dai ci da dare, a hankali Siyama ta lumshe idanunta domin kuwa ko shakka babu tayi missing komai nasa... Juyowa yayi ya ganta tsaye a wajen tana dubansa, kashe mata idanu guda yayi kana ya k’araso ya sureta cak suka nufi teburin cin abincin sai faman cakulkuli yake mata tana zillewa... Zaunar da ita yayi saman kujera kana ya d’an rank’wafo yace “I’m the waiter here... Mai Queen d’in take son ci...” D’agowa tai tana dubansa kafin ta saki murmushi tace “Kai Partner... I missed your delicious dishes..” “I know that’s why I cooked for you honey....” Murmushi ta kumayi kana ta mik’e tace “I’ll serve....” Ba musu ya koma ya zauna yana dubanta yanda take serving abincin a hankali, nazarinta yake yana tunanin something is wrong with her, don gaba d’aya ya lura da canzawa da tayi ita kanta ta tsargu da irin duban da yake mata gaba d’aya gani take kaman ya hango abinda tai, mummunar fad’uwan gaba ne ya dirar mata sanda ta jiyo muryarsa na fad’in “Partner... You know you look like a pregnant woman....Are you sure babu ajiyana a tattaredake....?” Zaro idanu waje tai tana dubansa ba tareda ta iya ci gaba da serving abincin ba.... Murmushi saman fuskarsa ya mik’e ya k’araso gareta had’ida rungumeta ta baya hannayensa duka biyu d’aure saman shafeffen tummy d’inta... Kansa saman kafad’anta idanunsa a lumshe yake ci gaba da fad’in “Partner don’t you think is about time mu fara tunanin building namu family d’in....?” Saurin rintse idanu tai k’irjinta naci gaba da bugu, k’ok’arin saita kanta tayi kana tace “Let’s eat Partner, the food is getting cold already....” Ta k’arashe tana mai cire jikinta daga nashi jin ya soma sumbatar wuyanta.... Zata zauna kujeran gefe ya kuma janyota ta fad’o saman cinyarsa, murya can k’asan mak’oshi yake furta “Honey I missed you... I missed you so much....” Gaba d’aya sunyi nisa a wata uwa duniya har saida suka jiyo k’aurin k’onewan abincin kafin Siyama tai azamar k’wace kanta ta nufi kitchen d’in ta kashe gasscooker d’in da Sameer ya mance a kunne... Tsayuwa tai kitchen d’in tana mai maida numfashi, bata isa ta mik’awa Sameer kanta a daren yau ba domin kaw ta mance pills d’inta da a kullum take shan k’waya d’aya a gida.... Bata koma parlorn ba sabida tunanin mai zatai ya kub’utar da ita hannun Sameer yau, ruwan zafi ta hanga cikin electric kettle take ta janyoshi ta d’an bige kad’an ya zube mata a k’afa... K’ara ta k’walla wanda ya sanya Sameer nufo kitchen d’in babu shiri..... A hanzarce ya k’arasa ya d’age kettle d’in yayi saurin d’agota yana mata sannu had’ida tambayarta ya hakan ta kasance, kasa ce masa komai tai sai narkewa da tayi cikin jikinsa tanai masa kukan shagwab’a... Abinka da likitan k’una first aid d’insa ya d’auko bayan ya ciccib’eta ya kaita parlor ya kwantar saman kujera ya shiga mata dressing wajen, fad’i yake “Sannu Partner, does it hurt..? Sannu koh.. Zai daina yanzu In sha Allah... Barin baki abincin a nan.....?” Girgiza masa kai tai cikeda shagwab’a kana tace “Bazan iyaci ba na k’oshi please ka kaini d’aki...” “Alright but ko fruits zaki sha....” Bai jira cewanta ba ya kuma sungumarta ya nufi bedroom da ita kana ya dawo ya d’ibi fruits a bowl ya koma d’akin yana bata a baki a hankali... Kallonsa kurum take tana ayyanawa cikin zuciyarta da ace yanzu akwai d’iya ko d’a a gidan wannan gata da tarairaya duk bazata gansu ba saidai yayiwa gudan jininsa haka, dole k’aunar da yake mata da tarairayan da yake bata ya ragu a nata tunanin... Haka Sameer yayita riritata yana mata sannu har bacci yayi gaba da ita tana mak’ale cikin jikinsa.... **** Banda safa da marwa Aunty Lami bata komai cikin tsululun dare ita kad’ai a cikin d’aki, sanin matsayin aminiyar sirri a wajen Ma’aruf ya haifar mata da shakku cewa bata kashe Ma’aruf ba kaman yanda sukayi zaton tayi...... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *22* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *Gaisuwa fatan Alheri gareku Ahalin SAN Aminiyar Sirri na gaisuwa ta gode da nuna k’auna🤪🥰* Da k’yar bacci b’arawo yai gaba da Lami amma fah duk juyi sai fuskan matashin nan mai zubi da Ma’aruf ya fad’o mata, bata fata Mamy tai idanu hud’u da wannan saurayi kaman yanda tai, yanzu babban burinta bai wuce ta samu wata hanya da zata iya nesanta wannan saurayi daga gidan ba, don idanma ba shine Ma’aruf ba shakka babu jikinta na bata shi zai alank’antasu da Ma’aruf.... Washe gari da hantsi Mamy na zaune saman carpet a parlornta tana rage k’umbar hannayenta da k’afafunta, sai sautin karatun sheik Ahmad Sulaiman ke tashi ga wani had’edd’en k’amshin turaren wuta na ratsa sashen nata gaba d’aya, yaran nata duk sun tafi makaranta Aunty Lami tai sallama ta shigo rik’eda ‘yar k’aramar bokati na kindirmo had’ida fura k’ulle a bak’ar keda... Mamy ta fad’ad’a murmushinta suna gaisawa sanda Aunty Lami d’in ta k’araso ta zauna saman sofa ta sha lullub’i alamun fita zatai.... “Su Marliya duk an tafi makaranta koh...?” Ta tambaya murmushi kwance saman fuskarta, Mamy ta rage sautin karatun kana tace “Duk sun fice Nabila ma sun koma satin nan....” Aunty Lami ta kuma murmusawa tana furta “Allah sarki b’angaren namu duk sai yayi shiru, koda shike gidanma gaba d’aya tinda duk sauran yaran ma sun koma...” Mamy ta jinjina kai tace “Haka ne... Fitane zakiyi...?” Aunty Lami ta kuma murmusawa kana tace “Eh zanje gidan k’awata Hajiya Tani kinsan an saka bikin d’anta....” Mamy ta d’an murmusa kana tace “Kai Masha Allahu, Ubangiji Ya sanya alkhairi, ki gaidata idan kinje, lokacin bikin idan Allah ya kaimu ma lek’a...” Aunty Lami tace “Haka ne.....” Lokaci guda ta mik’awa Mamy ‘yar bokatin kindirmon da fura tace “Jiya aka kawomin daga gari mai kyau dashi...” Mamy ta amsa fuska d’auke da murmushi saida tinda taji k’amshin fura fuskanta ya d’an canza, ta shigo tuno d’anta Ma’aruf abinda yafiso kenan a rayuwarsa, kullum idan Abbah ya fice kasuwa sai ya dawo dashi, tinda Ma’aruf ya b’ace kindirmo da fura sukai k’aura ma gidan, shi kanshi Abbah sai ya zamto ko k’anshinsa baiso balle yayi ido dashi.... Aunty Lami tana hankalce da yanayi Mamy dama abinda take son gani kenan.... D’an muskutawa tai kana ta kwantar da murya yawa mutuniyar arziki tace “Mamy rashin Ma’aruf bai kamata yasa rayuwarki ya canza gaba d’aya ba, karki mance shifa Allah na son mai hak’uri da tawakkali, kar ki biye na mijinmu sabida ke kin fisa zuciya mai taushi dukda rauni da zuciyar taki kedashi... Mamy shifa duniya tinda muka zota toh fah duk daren dad’ewa wataran zamu barta, yau shekaru ak’alla talatin ya kamata ki mance komai kici gaba da gudanar da rayuwarki kaman da dukda cewa nasan hakan nada matuk’ar wahala amma daurewa zakiyi....” Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Haka ne Lami, kuma na gode da shawarinki masu kyau, tabbas Allah na tareda masu hak’uri da kuma tawakkali... Amma cireshi a zuciya gaba d’aya abune mai matuk’ar wahala, yau da ace naga gawan Ma’aruf da idanuna da abin bazai dameni har haka ba tinda na sani duk mai rai mamaci ne babu babba babu yaro babu tsoho lokaci tanayi dole a tafi.... Amma banga gawanshi ba, shin yana raye ko ya mace, idan yana raye a ina yake rayuwa...? Wane irin addini da tarbiya ya samu, shin a ina yake samun abincinda yakeci har ya rayu ya girma, inane makwancinsa.... Shin idan ya girma yanada iyalai ko baida shi....?” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’in “Lami wad’annan tambayoyi sune suka tsaya min a zuciya, sannan duk yanda nakaiga amintar da zuciyata cewa Ma’aruf ya mutu abin yaci tura, zuciyata tak’i amsa tak’i yarda cewa Ma’aruf baya raye a duniyar nan... Zuciyata tafi k’arfafa min cewa akwai ranar da zai dawo gareni ranar da zan kuma tozali dashi, ranar da bak’in cikina zai yaye zuwa akasinsa... Sannan inaji wannan rana gab take da zuwa....” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka wanke mata fuska....” Kaman daga sama sai jiyo muryar Mamani sukai tana fad’in “Daga baya kenan wai sadaka da bazaura, duk kinsan da wannan kika jajib’esa kikaje kika jefar dashi... Yo waye ma ya sani ko saidashi kikayi tinda babu irin abinda ba’ayi a wannan duniyar tamu, uwa takan haifi d’a ta toni rami ta bisne sabida bata sonsa, uwa takan haifi d’a ta saidashi ma k’ungiyar asiri ta shan jini don ta sami kud’i, munafuncin banza kizo kina damun mutane da bak’in iyayi, bazan daina miki Allah ya isa ba Mariya b’atarmin da jika da kikayi... Algunguma kawai....” Wiwiwiw nan ta shiga rera kuka kaman an kunna injin markad’e...Aunty Lami ta mik’e da sauri ta rik’eta tana bata baki ta fitar da ita zuwa sashenta... Tinda Mamy ta kifa kanta hawayene kurum ke zubo mata, jiki a sanyaye ta mik’e ta nufi uwar d’aki don yin alwala dama bata gabatar da sallan walha ba kaman yanda yake d’abi’a nata, tuni ta shiga mik’awa ubangijinta kukanta..... *** *Kaduna* Yana kishingid’e saman sofa a parlor yana kallon shirin The Dr’s da ake gudanarwa da hantsi ta sauk’o daga saman bene taci uwar gayu kaman ba itace jiya da dare take kwance nasha nasha ba.... Da mamaki Sameer ya d’ago ya dubeta kana yace “Ina zaki da k’afar taki, ko ta daina zafin ne....?” K’arasowa tai had’ida aje handbag d’inta saman kujera kana ta manna masa sumba a gefen fuskarsa tace “Partner nayi latti, presentation ake jirana zanyi a office....” Girgiza kai Sameer yayi yana dubanta kana yace “But Siyama k’afarki bata gama warkewa ba kin rufeta cikin takalmi, sannan duka duka fah jiya nazo kuma bazan wuce kwana biyu ba, yau zaki fice office ki barni... C’mon Siyama....” D’an juya idanunta tai kana ta zauna jikinsa ta kamo hannayensa ta langab’e kai gefe tace “But Partner you know I’m a successful career woman, tun kafin ka aureni kasan da wannan, Sameer so kake na neglecting aikina, please mana... Ko ka mance kai kake supporting d’ina before....” D’ago face d’inta ya d’anyi kana yace “Siyama ba cewa nake ki ajiye aikinki ba but at least tinda jiya na dawo ai na cancanci a bani kulawa na d’an kwana biyun nan da zanyi... Honey musamman fah sabidake na baro ayyukana na taso nazo, wannan shine tarban da za’a bani....?” Ya k’arashe yana mai kasheta da kallo... Hannayensa ya kuma rik’owa cikin nata still tana zaune saman cinyarsa kana tace “Partner kasan idan banyi presentation d’in nan yau ba Daddy bazaiji dad’i ba dama yace yanzu Khalid ya fini k’wazo a aiki a company d’in please mana Partner... I don’t want to let Daddy down...” Ta k’arashe kaman zatai kuka... Jinjina kai yayi kana yace “Fine, it’s alright... Kije, zanje na duba Mummy nima anjima... Take care of yourself ok....” Ya k’arashe yana sakar mata murmushi had’ida gyara mata mayafinta da ya zame ya rufe mata jikinta gaba d’aya... Dubansa take tsananin k’aunarsa na d’awainiya da ita, lokaci guda ta rungumesa tana furta “I love you Partner...” “I love you too...” Ya fad’i fuskarsa babu yabo babu fallasa.... Ko takan breakfast batabi ba ta fice cikin sauri tana amsa waya tana fad’in gata nan k’arasowa.... Kallo yabi bayanta dashi har ta fice kafin ya sauk’e ajiyan zuciya ya mik’e ya nufi dining table d’in shi kad’ai kad’aici na d’awainiya dashi, har sai yaji yayi missing Shamsu da Mama dashike idan bazai fice office da wuri ba tare suke karya kumallo gaba d’aya saman dining table.. A hankali ya saki murmushi abincin da bai iya ci ba ya mik’e ya haura upstairs ya shirya tsaf ya nufi nasu gidan.... A kitchen ya tadda Mummy tana directing ma’aikatanta abinda zasu dafa lunch don dama ita d’abi’arta kenan sam bata sakewa ma’aikata girkinta dole sai tana supervising nasu wasu abubuwan ma da kanta take don a wajenta Sameer ya soma koyon girki rabin yinin Mummy a kitchen ne shiyasa shima yasan abubuwa da dama gameda kitchen.... Innani ce ta soma hangosa zatai magana ya mata alamu da ido kan tayi shiru, Mummy naci gaba da fad’in “Ina Zilai tazo ta yanka veggies d’in nan banso a barsu haka nan....” Batakai aya ba saiji tai an rungumeta ta baya.... Ta saki murmushi don tasan mutum guda da zai mata haka, ba tareda ta juyo ba ta d’ago hannu ta d’an dunguri kanshi tana fad’in “Yaushe zaka girma ne wai Sameer, ko sai ka haifo min jikokin nawa ne sannan ka girma ka bar masu jikin nawa su ci gaba da tsalle akai....” Murmushi kwance saman fuskarsa yace “A wajen Mummy na bazan tab’a girma ba ko yara nawa zan haifa, suje jikin nasu Mummy d’in suyi nima su barmin nawa....” Murmushi tai cikeda jin dad’i kafin suka soma gaisawa, nan Sameer d’in suka gaisa da ma’aikatan kowa na fad’in yayi kewarsa musamman Innani data jima sosai a gidan tun Sameer d’in na yaro... Nan kuma aka soma haba haba dashi ana tambayarshi mai za’a kawo masa.. Mummy tace “Innani kina mancewa ne wannan ai saidai ya shiga ya dafa da kansa koda yake k’ila yanzu ya daina tinda yayi aure yanada mai mishi...” Murmushi kawai ya d’anyi baisan dalili ba amma sai yaji maganar Mummy ya masa wani iri, ko don Siyama bata mishi ne.... Duban Innani yayi kana yace a kawo mishi breakfast... Mummy ta kalleshi da mamaki kana tace “Ba tun jiya kacemin kazo gari ba, ko yanzu ne sauk’ar naka...?” Girgiza mata kai yayi kana yace “Tun jiya ne, daga gida nake Mummy....” Bata kuma cewa komai ba sai d’an sanyi da jikinta yayi, anya wannan aure na Sameer na jin dad’inta kuwa, ace miji yazo gari takannas a kasa dafa masa karin kumallo sai yazo gida...? Ita kad’ai take tambayar kanta cikin zuciyarta, tasan hak’uri irin na Sameer shiyasa kwanaki da suka sami sab’ani da Siyama tabi bayan d’iyar k’awarta Siyama daga baya saida taji bata kyauta wa d’anta ba tinda ita ta tayar dashi ta kuma san sarai Sameer mutum ne mai tsananin hak’uri da kai zuciya nesa toh amma katsalanda a rayuwar ma’aurata ma duk baida wani amfani.... Da kanta ta shiga kitchen ta had’o masa delicious ta dawo parlor ta tayasa zama yana ci suna hira, yana mata hiran abokinsa Shamsu da shima ya tab’a zama gidansu, ya k’arada suna gaishesu gaba d’aya... Yini zubur yayi a gidan har saida Daddy ya dawo suka gaisa suka b’ige da fira suma... Ba shi ya bar gidan sai bayan isha bayan Mummy ta gama cika mishi ciki da abinci... A b’angaren Siyama kuwa tuntuni ta dawo donma saida ta biya gida ta d’auko pills d’inta da ta mance sannan ta biya eatery ta sai masu abinci Incase Sameer baiyi ba... Koda ya dawo ta masa tayin abinci ce mata yayi yaci gidan Mummy, bata damu ba taci nata takai sauran kitchen... Yau dai kafin ya nemeta tayi k’ok’ari takai kanta dashike tasha maganinta na hana d’aukan ciki... *** Kwanan Sameer biyu ya tattara ya koma Kano ya bar Partner d’insa da kewarsa... A b’angaren Khalid kuwa baida buri da ya wuce Daddy ya kuma aikensa Kano, shi ko Daddy bai aikesa ba ma shi zaijeshi da zaran aiki ya ragu mishi, Yesmin tana nan zatai kwana biyu a Kaduna kafin ta koma Abuja don tuni Mummynta ta koma ta barta da hud’uban kar ta kuskura ta dawo Abuja ba tareda ta saye zuciyar Khalid ba... *** Aunty Lami da Hajiyar Hafiz zaune gaban Malam mai bugun k’asa ana masu duba idan Ma’aruf na raye... Malam ya buga k’asa yayi wasu zane da yatsun hannunsa guda biyu kana ya d’ago ya dubesu.. Har suna had’e baki wajen cewa “Malam yaya shin yana raye ko ya mutu.....??” SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *23* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Malam ya d’ago ya dubesu ba tareda ya furta komai ba, Hajiya tai saurin furta “Malam yaya... Shin kaga Ma’aruf na numfashi a doron k’asa....?” Kallonta Malam yayi ba tareda ya kuma furta koda kalma ba kana ya iza babbar rigarsa mai tsananin daud’a ya kuma zana layi guda da yatsarsa... Aunty Lami sai faman yakushin Hajiya take tana k’yafta mata idanu tana fad’in “Ke Haule mu dakata muji ta bakin Malam....” Gyaran murya Malam yayi kana yace “Abu ne a duhu....” Suka kalli juna cikeda k’osawa... Lami ta gyara zama sosai kana tace “Allah gafarta Malam bamu gane ba, kaman yaya abune a duhu...?” Malam ya kuma sab’a babban garensa kana yace “Kasa bai nuna min komai ba, ban hago tak’aimemen abinda ke wakana ba, zan baku hak’uri ku dawo wani lokaci....” Cikeda jin haushi Hajiya tace “Yo mai kake nufi kenan Malam, so kake kace muna biyanka a iska, kaga idan bazaka iya duba mana bane sai ka fad’i mana mu tafi wani wajen bawai kace mana bakaga komai ba....” Duk yanda Aunty Lami ke muskutin Hajiya ta kasa rufe baki sai faman b’araka take... Malam ya jinjina kai kana yace “Kuna iya zuwa wani wajen a duba maku amma ina mai tabbatar maku K’asa bazata min k’arya ba, duk yanda kukaje iyakacin abinda za’a gaya maku kenan, K’asa da Taurari bazasu min k’arya ba.. Amma tinda kun zab’i zuwa wani wajen sai anjimanku Allah bamu alkhairi...” Ya k’arashe yana k’ok’arin nad’e buzunsa... Aunty Lami tai saurin katseshi da fad’in “A’a baza’ai haka ba Allah gafarta, yarda da aikinka yasa mukazo nan, tinda kace haka ai sai mu tafi mu dawo wani lokacin....” Malam ya jinjina kai kana yace “Zan baku rana ku dawo rana itiyau kafin nan na k’irga taurari naga abinda zan iya gani....” Suka jinjina kai a tare kafin suka mik’e suka masa sallama suka d’au hanyar gida... Tinda suka fito Hajiya ke sababin cewa wannan bokan neman raina masu hankali yake dama sun nemi wani ne su k’yale tashan wannan gidahumin Malamin... Aunty Lami tace “Um um Laure mubi a sannu, tinda yace mu dawo ran sati ai sai mu dawo ba wani abu bane....” Hajiya ta jinjina kai kana tace “Yanzu abinda za’ai kisan yanda zakiyi kisha mana cikin mijinki muji alak’arsa da wannan saurayi da ya firgitaki kin fahimta idan yaso sai musan yanda zamu b’ullowa lamarin....” Shiru Aunty Lami tai tamkar mai nazari kana tace “Kinfa sanshi kinsan mijina wane irin rikitaccen mutum ne, haka nan yake a tank’ware yawa arnen da, fuskarsa ma kurum bazai bari na iya tambayarsa ba...” Hajiyar Hafiz ta buga tsaki kana tace “Ai kinji matsalarki shegen tsoron miji, ance ki kai sunansa gaban Malam kin kasa da yanzu kina zuba mulkinki son ranki, ni yanzu kinga duk taurin Alhaji saidai ya ganni ya barni don billahillazi sai nace ayi ayi idan kaw bance ba babu uban da ya isa yi...” Aunty Lami ta murmusa kana tace “Haule kenan ni fah baso nayi mulki nake ba babban buri na shine na zama tauraruwa a cikin gidana ya kasance kowa ni yake kallo kowa ni yake so wanda da zallan makirci zan iyayin hakan babu taimakon boka balle Malam bawai na mallake mijina na maidashi mijin tace ba, a nan ra’ayinmu yasha banban gaskiya....” Hajiya ta watsa mata kallo had’ida tab’e baki tace “Ai kinji, wake yayin auren haula bayan kanada masu share maka kuka,ke kikaga zaki iya... Nidai kinsan yanda zakiyi ki binciko mana wannan saurayi musan matakin d’auka akansa.... Ita kuma Aminiyar sirri ba zuba mata idanu zamuyi ba, zuwan takannas zamu mata ta sanar damu abinda tayida Ma’aruf kar mu zama wawaye...” Da wannan tattaunawa suka rabu, adaidaita guda daman suka d’ale, Hajiya Haule aka soma sauk’ewa kafin aka wuce da Lami.... *** A ‘yan kwanaki biyun da Sameer baya nan saida abin ya dami Abbah, ya lura baya ganinsa a masallaci haka nan ko k’yallin motarsa bai ganin goftawanta a unguwar, ranan dai bayan an ida sallan lisha ya tare Shamsu yana tambayarsa Sameer, abin har saida ya baiwa Shamsu labari, mutumin da a baya babu ruwansa da kowa a unguwar tamkar shi kad’ai yake rayuwarsa dukda Shamsun ma dangin hakan ne amma yana hankalta da dattawan unguwar yanda suke sabo da juna amma banda Alhaji Usman Mailafiya sai gashi lokaci guda sun shak’u matuk’a da Sameer har yana tambayarsa lallai Sameer akwai shi da saurin shiga ran jama’a... Shamsu ya d’an murmusa ya sanar dashi Sameer yaje dubo gida ne... Jikin Abbah yayi sanyi da ya fahimci ganin iyayensa Sameer ya tafi, da gaske dai wannan saurayi babu abinda ya alank’anta shi da Ma’aruf d’insa... Ranan jiki a sanyaye Abbah ya koma gida, harta su Mamy saida suka fahimci d’an canzawan nasa na kwana biyu, lokacin da Sameer ya dawo kuwa saida farin ciki ya nuna a tattareda Abbah, lallai bahaushe yayi gaskiya da yace sabo turken wawa.... A satin Hafiz ya d’aga masu hankali da maganan k’arin aurensa, abu kaman wasa wuta wuta aka tambaya sadaki da lefe gidansu Sawwama, wai zo kaga farin ciki wajen Sawwama da Magajiya, duk wani b’uli da suka san cewa ka iya jawo masu matsala musamman mutanen unguwarsu saida suka tosheta don Magajiya ta d’au alwashin wannan shekaran sai d’iyarta Sawwama ta tare d’akin miji ba d’akin saurayi ba kaman yanda tasha yin hakan a baya... Gidansu Sawwama basu yanke lokaci mai tsawo ba wata guda jal suka yanke dashike dama alla alla suke su mik’ata su huta, shi kanshi Hafiz ba wai d’aukin auren yake ba saidai baisan dalilin da yake matuk’ar so ayi auren wuta wuta ba, baisan ko rashin matarsa Zulfa’u bane yasa yake so ayi bikinshi da Sawwama nan kusa ko zai rage kewar matarsa da yake... Duk wannan bidiri da ake sam Zulfah bata sani ba, hasalima farin cikin kammala bautan k’asanta take, gashi Aunty B tace da zaran ta gama Iddarta zata samar mata gurbin aiki ya rage mata kewa, yanzu babban burinta bai wuce ta sanya mahaifiyarta da d’iyarta a k’wayan idanunta ba.... *** Kaduna.... “Mummy ya fah wuce duk yanda kike tunani, kawai Mummy kisa a fara maganar auren mu inaga ta haka ne kawai zan samu attention d’insa.... Please Mum talk to your sister...” Ta k’arashe kaman zata runtuma ihu ta cikin wayar... Daga d’aya b’angaren mahaifiyarta tace “Yesmin are you sure kinyi duk abinda nace kiyi...?” Cikeda shagwab’a Yesmin tace “Mummy I did everything you asked me to do, amma wllhi Mummy kallo fah ban isheshi ba, I’ve exhausted all my efforts already....” Cikin kwantar da hankali mahaifiyar tata ke fad’i mata “Ki kwantar da hankalinki ni zanyi maganawa Faridar kinji koh, kedai kawai just focus don’t lose hope kinji koh...” Yesmin ta jinjina kai a hankali kaman mahaifiyar tata na kallonta kana tace “Alright Mum, take care... Say hello to Daddy for me...” Daga haka katse wayar tai tana tunanin yanda zata karkato hankalin Khalid gareta... Kubura dake lab’e bakin k’ofa rungumeda bedsheets zata kai d’akin Mamy nan ta lab’e tana sauraren wayan Yesmin... Kusan cin karo sukai da Yesmin d’in da batasan Kubura na lab’e jikin k’ofarta ba... Wani mugun kallo Yesmin ta watsa mata kana tace “Ke wai meye kike bibiyata, lafiya...?” Kubura ta tab’e baki tace “Yo naga dai hanya ta biyo dani nan, d’akin Mamy zan shige Sirkar kirki...” Ta k’arashe tana d’aga gira samawa Yesmin... Yesmin ta bitada kallo tana maimaita kalmar sirkar kirki cikin zuciyarta... Gajeren tsaki kurum tai kana ta nufo downstairs... Hango Khalid da tai zaune tareda Ammi suna fira ya sanyata saurin komawa sama a d’ari ta d’auro makeup saman fuskarta... Daga yanda take k’arasowa tana iya jiyo muryar Ammi tana tambayarsa.. “Mai kuma zakajeyi Kano....?” A tak’aice yace da ita “Ammi I’ve unfinished business there...” Ammi ta kuma dubansa da kyau kana tace “Unfinished business...?” Jinjina mata kai yayi yana mai ci gaba da canza tasha had’ida furta “Yes Ammi but ba jimawa zanyi ba kwana biyu zuwa uku kawai zanyi...” Ammi ta jinjina kai kana tace “Ina maganar mu ta kwana...?” Ya d’an d’ago ya dubeta kana yace “Wanne kenan...?” “Ka sani sarai maganar k’anwarka Yesmin nake maka, naga alama yi kake kaman ma bakasan tana gidan nan ba... What’s wrong with you Son...?” Girgiza kai Khalid yayi had’ida kishingida cikin kujera kana yace “But Ammi I thought we’ve already talked about that... Ammi I’m not interested, I don’t love her for heaven’s sake..” “Kai kai rufe min baki meye haka...? Wani you don’t love her ka samu banson sakarcin banza, a ina zaka samu mace kaman ita donma ka samu anason baka ita ai dai kasan Yesmin ba class d’inka bace, Khalid ka natsu kaji abinda nake fad’a maka tun wuri ka aje wannan masifar girman kan naka ku daidaita da ‘yar uwarka nasan ba sonta bane bakayi kawai tsaban jidakan tsiyarka ne kake cewa haka, Yesmin tana nan a gidan nan har tsawon sati biyu don haka kafin ta tafi naji batu mai dad’i....” Kallon Ammi kurum yake ba tareda ya iya furta komai ba, rai b’ace ya mik’e yana fad’in “Da safe zan wuce Kano In sha Allah zan sami Daddy a office na mishi sallama....” Yana tafe Ammi na fad’in “Ka tabbata kayiwa Yesmin ma sallama...” Bai tsaya amsa Ammin nasa ba ya fice takaicin Yesmin na d’awainiya dashi... Jiki a sanyaye Yesmin ta koma sama ba tareda ta iya sauk’owa ba.. Washe gari Khalid ya sauk’a a birnin Kano.... Niko nace Nabilah kinada bak’o...LoL SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _..............DA RABO_ *24* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Suna barbaje a parlorn Hajiya suna tattauna batun auren Yayansu Hafiz Sahariyya ta kuma kwashewa da dariya had’ida rangad’a gud’a tace “Hajiya wllhi zanso ace Zulfah na gidan Ya Hafiz za’ai auren nan nasan bak’in ciki sai kusan aikata lahira...” Hajiya ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yanzu ne Hafiz ya nuna min cewa ni na haifsa, kuma banda abinki Sahariyya ai yanzu ma labarin ya risketa sai taji kaman tai hauka don kishi tinda sakinta akai aka auro wata, kuma a d’akin Zulfa’u za’ai jeren Sawwama, duk wata tsiyar Zulfa’u tattare mata zaiyi idan yaga dama ya zuba a shara tinda yak’i aminta a sanar da iyayenta babu aurensa akanta...” Suka kuma washe baki suna k’ek’eta dariya cikeda farin ciki... Naja takai dubanta ga Kausar dake wasanta hankali kwance kana tace “Yarinya kin kusa komawa gidan ubanki kiyi tashin hannun kishiyar uwa....” Sahariyya ta b’allawa yarinyar harara kana tace “Aikuwa kaman kin sani ana gama cin amarci zan kwashi wannan tsiyar na kaita gidan ubanta, badai gani yake muna musgunama gudan jininsa ba, tau kaw yanaji yana gani matarsa zata lallasa mata bugu bai isa cewa komai ba, aini naji dad’i ko banza jinin Zulfah zatai girman hannun kishiya...” Suka kuma b’allewa da dariya idan ka d’auke Hajiya dake zullumin abubuwan da suke fad’i, ko tak’i ko taso Kausar jininta ne, wannan abu idan ta tuna sai taji kaman idan ana musguna mata na d’anta Hafiz ake musugunawa, a d’an hasale tace dasu “Toh toh ya isa haka... Najah d’auko Kausar ki mata wanka...” Wani kallo Naja ta aikawa Hajiya kana tace “Tab wllhi ban iya rainon d’anda ban haifa ba Hajiya, Uwarta na biyu Raihana ta mata...” Ta k’arashe tana k’ishingid’a cikin kujera had’ida danna earpiece a kunnuwanta... K’wafa Hajiya tai kana ta mik’e ta d’auko Kausar da kanta ta shiga kwab’e mata kaya don Raihana na kitchen na aikin abincin rana da babu wanda yayi har saida ta dawo daga makaranta.... *** Fitowarsu kenan daga class suna tattauna lecture d’in da suka fito, sai dariya suke suna jinjina rashin mutuncin malamin nasu da yanda Nabilah bata tsoronsa har saida ya zamto idan bata aji sai ya gane, da yawan malamai sabida tsaurin idanunta da rashin tsoronta suka santa, gashi ba halin ka kayar da ita don babu laifi tana karatun ta daidai gwargwado.. Habib d’aya daga cikin course mates d’in nasu yace “Dr Manzo yau ya had’uda gamonsa... Ni tun last semester da akace zai d’aukemu kuma he’s very strict nace toh akwai aiki randa sukai arangama da Nabila....” Yusrah k’awarta k’waya d’aya tak saiko Habib da Safwan da suke taimaka masu da tutorials tace “Wllhi ni damuwata ma kardai taje ta janyo mutumin nan ya tsanemu mu shiga uku ga course d’in nasa ita kanta ba wai fahimta ake ba...” Safwan yace “Kuma kuna magana tayi k’us kaman bata wajen....” Harara ta watso masu gaba d’aya kana tace “Iyakaci yace na daina shigar masa aji ba shikenan ba tinda kuna nan zaku koyan.... Ke Yussy dan Allah kizo mu tafi wllhi na gaji sallah ma a gida zanyi...” Ta k’arashe tana rataye side bag d’inta.... Gaba d’aya suka shiga darawa suna fad’in tai a hankali Dr Manzo ba kaman sauran lecturers d’in bane yanda course d’insa take a baud’e haka shima yake a baud’e.... Zata kuma magana wayarta dake cikin jaka ta d’auki ruri.... Lalumar wayar ta shigayi tana fad’in “Sai kuyi ai daga ku har shi Dr Manzon banida lokacinku....” Aya ta sakawa kalaman nata ganin bak’uwar lambar da ake kiranta dashi, kaman bazata d’aga ba sai kuma ta d’aga a dak’ile don ba kasafai take d’aga lambar da bata sani ba don idan an fad’i mata abinda bai mata ba ko wanene mai kiran zaiji maras dad’i ne shiyasama wani sa’in bata d’agawa... Gabanta ne yayi mummunar fad’uwa jin muryar dake mata magana cikin wayar, ta kasa furta koda kalma sai lugude da k’irjinta ke ci gaba dayi, dukda cewa bai wuce a k’irga ba ta tab’a jin muryar tasa amma ko kusa bazata iya mance sautin muryar ba wanda shi kad’aine mai irinta a iyaka saninta.... Murmushi yayi a hankali kana yace “Are you surprise... Kin d’auka na mance koh...?” K’ok’arin saita kanta tai kana tace “Malam inaga wrong number ka kira please do not call this line again.....” Bai bari takai aya ba yace “Don’t think of hanging up on me.... Ina kallonki daga yanda nake, ki sallami samarukan naki kizo mu k’arashe deal d’inmu...” Waige waige ta soma tana neman ta yanda zata hangoshi amma ko k’yallin mai kamanninsa bata gani ba, murmushin yak’e tai lokaci guda ta kuma had’e fuska kaman tasan yana kallontan kana tace “Malam ba wani deal tsakanina dakai idan kuma ka matsa sai na biyaka kud’in gyaran motarka nima sai ka biyani kayana da ka b’ata...” Murmushi maras sauti ya kumayi kana yace “Ki daina wahalan juye juye just turn to your left....” Waigowa ta kumayi ta direction d’in da ya fad’i nan ta hangi motarsa pake k’asar bishiya.... Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Kaga Malam ka k’yaleni ka daina bibiyata....” Katseta Khalid yayi da fad’in “You haven’t asked about my wound... Ko kinsan cewa har yanzu bai warke ba, har yanzu ina ganin likita a sabida ciwon da kikajimin... To add it to your expenses zaki biya....” Saurin kasteta tai da fad’in “Malam kodai kai d’an 419 ne... Toh idanma kai d’an damfara ne babu abinda zaka samu daga gareni just stop stalking me...” Wannan karon sosai ta basa dariya amma ya gimtse yace “But you know I can press charges, ciwon dake fuskata is enough evidence kin yarda.....?” Fuzar da iska tai kafin ta kashe wayar ta nufi yanda motar tasa ke pake kaman zata tashi sama sabida tsananin huci da take.... Su Yusrah kam saidai hango k’allin mayafinta da sukai ta nufi wani wajen, Yusrah na kiran sunanta inaa ko tsayawa batai ba balle ta tankata... Gaba d’aya suka murmusa suna fad’in “Nabila case ko ya tab’owa kansa kuma sai Allah....” Yusra ta girgiza kai had’ida tab’e baki tace “K’awata ta kaina, ku k’yaleta zata dawo idan taje ta saita duk abinda ta taro, kaga Safwan ci gaba da ciremu daga ruwa kafin ta dawo tinda ance mutumin nan unannounced test yakeyi...” Basu kuma bi takanta ba sukaci gaba da abinda suke.... Koda ta iso babban abinda yafi bata takaici shine ta kusan minti uku masu kyau tsaye a wajen Khalid baisan tama iso ba yana kwance cikin motarsa yana shan AC, sarai tasan salon wulak’ancinsa ne yana kallonta itace dai bata ganin sa tinda glass d’in motar mai duhu ne... Kaman ta shige tai tafiyarta sai kuma ta shiga bubbuga masa glass d’in motar da iyaka k’arfinta.... A hankali ya shiga zuge glass d’in motar.... Lokaci guda ta d’ago idanu tana dubansa fuskarta kaman zata kurma ihu... Wani ni’imtaccen k’amshi ne had’ida tururin AC suka fara mata sallama kafin ta iya d’ago idanu tana dubansa Kwanceccen murmushi ta hango saman kyakkyawan fuskarsa, idanunta na duban wajen ciwon nasa da yace bai warke ba, bata hango ciwon ba sai d’an sauran alamun tabo alamun ya gama healing, batasan dalili ba amma sai taji zuciyarta ta nastu da ganin ciwon nasa ya warke, tai saurin d’auke idanu daga duban nasa, fuska a tamke tace “Malam wai mai na maka da tsanani kake bibiyata...?” D’an kauda kansa gefe kad’an yayi kana ya juyo yana kuma dubanta “First one has to say salam before anything else....” A kaikaice ta kuma dubansa kana tace “Kaga Malam let’s settle this once and for all, Im pretty tired gida nakeson tafiya... You want money... Is that the only thing that matters....?” Tayi maganar cikin tsananin fad’a Tinda ta soma magana yake dubanta ba tareda ko k’yafta idanu ba, sosai yakeso yaga mace na masifa irin haka, murmushi yayi da gefen bakinsa ba tareda ya katseta ba har ta ida masifan nata kana yace “Of course not... I just want you to learn how not to go through life hurting beautiful innocent people....” Baki sake take dubansa yanda yayi maganar babu ko alamun wasa tattareda shi... Murmushin yak’e tai kana tace “I think that’s what you’ve to learn.... I came because you scared me... I’ve to see your wound...” Ta k’arashe murya can k’asan mak’oshi.... Da mamaki yake subanta kana ya fito da kanshi sosai yana kuma dubanta, murya a hankali ya furta “Just my wound...?” Yayi tambayar idanunsa a kanne sihirtaccen murmushi kwance saman fuskarsa... Ganin irin duban da yake mata ya sanyata d’an daburcewa, a hasle ta kuma cewa dashi “Eh.. eh mana sabida na tabbatar ba 419 kazo kamin ba... If you don’t have more to say ni zan tafi friends d’ina na jirana....” Tasa kai zata wuce tajiyo sautin muryarsa na ambaton sunanta a karo na biyu bayan kiran sunanta da yayi randa suka soma had’uwa.... “Nabeelah.....!” Cak ta tsaya na wasu ‘yan dak’ik’ai kafin ta juyo a hasale tace “What again...!!!” “We haven’t finished talking yet, idan da gaske kin gaji kuma gida kike son tafiya toh ki shigo na kaiki...” Galala take dubansa kafin ta dawo da baya ta point kanta tana mai furta “Ni.. Na shiga wannan motar taka... Allah ya sawwak’e mun... Wait what do you think of me...?” Ta k’arashe tana mai d’aura hannu saman kunkumi... Khalid ya kauda kai gefe had’ida rausayar da idanu bai tab’a zaton akwai macen da zatai ta gaya masa maganganu baijin zafinsu ba sai wannan yarinya mai d’an uban masifan.... Dawo da dubansa gareta yayi kana yace “Idan kinaso naje na sami Abbah ne fine kinsan har parlornsa na sani...” Ya k’arashe murya babu alamun wasa... Cuno baki gaba tai tanaji kaman ta rufesa da duka don har yau batasan meye alak’ansa da mahaifinta ba gashi kuma har parlorn Abbah ta ganshi yana cin abinci... Wannan karon murya k’asa k’asa tai maganar “Kaga an hanani shiga motar strangers idan kanaso mu k’arasa maganar nan kowama ya huta ka fito daga motarka mu k’arasa... Yanda tai maganar cikin kwantar da murya sai ya masa banbarak’wai, da gefen bakinsa ya kuma murmusawa kana yace “No... Really, I’m scared of people ban saba da irin universities d’inku na nan ba...” Baki sake take dubansa, lallai wannan babban d’an rainin hankali ne... A fili ta furta “You’re unbelievable....” Tasa kai abinta tayi wucewarta cikin sauri... Tuni shima ya tada motar ya shiga bin bayanta, A hanya suka had’uda Yusra ta gaji da jiranta don harsu Safwan sun wuce hostel... Yusrah taga hamshak’iyar motar sai bin k’awarta take, kafin Yusrah tai magana Nabilah ta finciko hannunta tana fad’in “Kar kice komai wuce mu tafi...” Yusrah na waige take fad’in “Ke dilla ki tsaya muga waye, why is he following you... Dan Allah Naby ki tsaya mu....” Bata kai aya ba Khalid ya kuma shan gabansu da motar, Nabilah tazo wuya sabida tsananin k’uluwa ji take kaman ta d’au dutse ta kuma fasa masa gilashin mota.... Yusrah bata kuma sumewan tsaye ba saida ya shiga zuge gilashin motar ta hango matuk’un motar wanda har yafi motar had’uwa... Fuska babu alamun wasa yace “Shige muje.....” Harara kurum take galla masa kana tace “Too bad ban shiga...” Yusra ta kalli wannan ta kalli wannan, nan ta shiga mintsilin Nabila tana fad’in “Kiyiwa Allah ki cecemu mu shiga motar nan...” Nabila ta aika mata mugun kallo kana tace “Idan kin matsu kya shiga yakaiki daga nan yayi kud’i da kanki...” Ta kuma sa kai zata shige yace “Idan kinaso mu gama deal d’in once and for all kowa ya kama gabansa kina iya shiga motar, idan kuma yankan kai kike tsoro kaman yanda kikace har cikin gidan naku zan iya shiga...” Kaman zata kurma ihu haka take dubansa, rai b’ace ta finciki marfin motar tayi shigewarta baya “You better keep your word..” , Yusrah ma sim sim ta shige d’aya side d’in tana mamakin ina Nabilah ta samo wannan had’edd’en guy d’in babu ko labari... Kashe motar mai gaba d’aya yayi alamun idan ta dawo fronts eat zasu tafi.... A hasale ta kuma fincikar marfin motar ta koma gaba tasan idan bata dawo gaban ba haka zasuci gaba da tsayuwa gashi tuni la’asar ta shige.... Yusrah ta d’an kanne murya tana gaisheshi, tinda ya amsa a tak’ice bai kuma cewa komai ba, saima wayarsa data d’auki ruri, Siyama ce mai kiransa... Kaman bazai d’aga ba sai kuma ya d’aga, hannunsa guda na rik’eda waya guda kuma naga steering wheel... Kaman baison maganar yace “Yes Siyaam....” Daga d’aya b’angaren Siyama tace “Khalid we need to talk, is about Yesmin...” Saida ya d’an fuzar da iska yana jiran traffic ya basu hannu kana yace “I’m busy right now.... We talk later...” Yusrah kam tana daga baya tana k’arewa wannan miskili kallo da gani za’asha fama dashi, itakaw Nabila tinda taji ya ambaci sunan mace tabada k’eya tana duban window ko ba’a fad’i mata ba ta sani da budurwarsa yake waya, tayi k’wafa cikin zuciyarta tana mamakin duk wanda ta kasance budurwan wannan d’an rainin hankalin, don dagajin yanda yake maganawa budurwar ma ba dad’insa takeji ba, ta kuma tab’e baki ita kad’ai tana ayyanawa cikin zuciyarta ko maza sun k’are bazata tsaya da wannan d’an rainin sense d’in ba.... Tafiya kawai suke a motar babu mai cewa komai sai sassanyar music dake tashi cikin radio d’in motar, Yusrah dai tuni ta shiga shafa wayarta ana zuwa layin gidansu ta sanar dashi ga yanda zata sauk’a, ga mamakinta kaw harda sallama Khalid ya mata ya saci kallon Nabila dake sallama da k’awarta tana sanar da ita ta turo mata assignment question d’in Dr Man.... Bayan Yusrah ta fice Khalid yace “Mai ya hanaki kwafa a class sai ta waya za’a turo miki...?” Yayi maganar idanunsa naga kwalta Da gefen idanu ta dubesa kafin ta kuma kawda kai tace “Ra’ayina ne...” “Ba tareda ya dubeta ba shima yace “Ra’ayinki kokuma kina jira ayi solving a turo miki ba...” A kufule take dubansa kafin ta kauda kai ba tareda ta kuma cewa komai ba don ta lura shi wannan zaman lafiya ne sam baiso a rayuwarsa tanson tambayarsa yanda ya sami lambarta da yanda akai yasan sch d’insu amma tasan bazataji mai dad’i ba kuma bazatai hak’uri bata rama ba kawai ta fasa tambayan nashi, ana isowa layinsu ta hangi ‘yan islamiya nakan faman tafiya bata k’aunan suyi artabo da magulmatan ‘yan gidansu don tasan idan suka ganta motar wani shikenan zance ya karad’a gidan har ya isa ga Abbanta... Aiko suna tana fitowa daga motar ta hangi su Basma zasu tafi islamiya kuma sarai tasan sun ganta sai juyo suke ta danna masu harara suka wuce sim sim... Kotakan Khalid bata kuma bi ba tasa kai ta shige... Ya kai dubansa ga kujeran data zauna nan ya hangi note book d’inta ta mance kuma da alama littafi ne mai d’aukeda courses daban daban... Murmushi ya sake a hankali kafin yaja motarsa ya wuce yasan dole ta nemeshi ko don littafinta data mance.... Daga nan waya yayiwa Sameer yaji ko yana gida su gaisa, Sameer sai mamaki yake mai yake kawo Khalid Kano akai akai, nan dai Sameer d’in ke sanar dashi bai gida yana hospital... **** Mamy na hankalce da yanayin Nabilar, duk yanda akai wani abun na damunta... Suna zaune gaba d’aya a parlor da magrib Mamy ke tambayarta meke damunta... “Mamy ba komai....” Ta fad’i tana mai shan jinin jikinta... Jinjina kai Mamy tai kana tace “Idan ya dame ki kya fad’i...” Nabilah da Marliya suka kalli juna Marliya na k’ok’arin had’iye dariyarta.... Misalin k’arfe 10pm ta gama shirin baccinta ta d’auko wayarta da niyyan yin assignment d’inta ta nemi littafinta ta rasa... Cikin sauri ta shiga neman layin Yusrah tana tambayarta idan littafinta na tareda ita... “Yusrah tace “Gaskiya baya wajena ban tsammanin na wajensu Safwan ma....” Nabilah ta dafe kanta tana fad’in “Ya Salam, toh ina na jefar...” Yusrah tace “Hey wait... Could it be a mortar mutumin nan kika bari ba...?” Gaban Nabila ya yanke ya fad’i, saurin rintse idanunta tai tana tunanin tabbas ta yiwu a motar tasa ta mance...Ya Salam yanzu ya zatai ta ina zata soma nemansa... Lambar da ya kirata dashi takai kai ta tsura masa idanu na lokaci... Kaman zatai dialing sai kuma ta fasa tai jifa da wayar saman gado tana mai jin haushin kanta dama ta yarda ta shiga motar tasa... Cikeda masifa ita kad’ai take fad’in “No wllhi bazan kiraka ba... Oh I hate you..!” Ta k’arashe sakin k’ara... Marliya dake bacci gadonta daga can gefe bud’e idanu tai a hankali tana tambayar Nabila meke faruwa.... A dak’ile Nabila ta kalleta ba tareda tace komai ba.... Kwanciya kawai tai don bazata iya yin assignment d’inba tinda duk working d’in na cikin littafinta... Sanin cewa Mr Edward bai bari a zauna masa a aji ba tareda ganin littafinka ba kuma kana rubutu ya sata yanke shawarin kiran d’an rainin hankalin nan... Yana ganin wayarta murmushi ya kufce masa, shi kad’ai yana kallon screen d’in wayar a zuciyarsa yana furta “I know you’ll call...” Saida taji kaman ta katse kiran don takaici kafin ya d’aga.. Kishingid’a ya kumayi kana yace “So why is miss Grumpy calling me now..? Did you call to give me a goodnight scold or to ask me about my wound again......?” Fuzar da iska tai kana tace “Don’t get wrong ideas, I call because I think I left my book in your car....” Murmushi yayi don d’an rabuwan da sukayi na wasu mintoci har yaji kewar masifarta... Saida ya d’an d’auki lokaci kaman bazaice komai ba yana iya jiyo hucinta kana yace “Oh really... Sabida tsaban bakiso deal d’inmu ya k’are shine saida kikayi kikasan yanda kika bar book d’inki a mota ta... Alright since you insist on seeing me zan kawo miki littafinki but as you can see is pretty late now, ko babu matsala...” Murya na rawa kaman mai shirin kuka take fad’in “Think whatever you want to think nidai ka kawo min littafina...” Mik’ewa sosai yayi ya zauna yana mamakin canzawan muryarta kana yace “Alright fine ki karb’i littafinki gobe a makaranta..” Ta sauk’e ajiyan zuciya ba tareda tace komai ba,shiru ya gifta tsakaninsu na d’an lokaci kowa da abinda yake tunani kana yace “May I know where to keep the notebook...?” Wannan karon cikin kashe murya yayi maganar... A sanyaye tace dashi “I’ve class by 8, just come straight to auditorium....” Daga nan bata kuma cewa komai ba sai katse wayar da tai... Kallo yabi wayar dashi murmushi saman fuskarsa kafin ya shiga tura mata sak’o _Too bad I’m not used to waking up early..._ Girgiza kai kurum tai had’ida jifa da wayan tasan wannan baza’a tab’a abin arziki dashi ba... Washe gari sai raba idanu take tana neman ta yanda zata hangosa gashi har Malamin ya shiga aji... Yusra na hankalce da ita don tasan kwanan zancen.... Mr Edward ya soma going round ya hangi mutum tsaye bakin k’ofa yana taking excuse Nabila sai raba idanu take don tasan Allah ne ya taimaketa Mr Edward bai k’araso ta wajensu ba don bawai fad’ansa take tsoro ba attendance ne kawai bataso ta rasa... Mr Edward ya baiwa mutumin izinin shigowa, daga mazan har matan fad’in had’uwarsa suke... Nabila kam kanta na k’asa batasan wainar da ake toyawa ba saida Yusra ta shiga jjjigata tana fad’in “Ke tashi tashi kiga waye a nan...” Nabila na d’ago kai sukai idanu hud’uda Khalid yana maganawa Mr Edward a hankali alamun ita yake tambaya... “Oh there she’s mr...” Ya k’arashe yana pointing d’inta da littafin... Jinjina kai Mr Edward yayi kana ya kirawo Nabila tazo ta amshi littafinta, gaba d’aya idanu akanta ta mik’e ta nufi gaban hall, kallon kallo sukewa juna har ta amshi littafin kafin ta koma ta zauna... Suka kuma yin sallama da Mr Edward Khalid ya fice, sai mamaki take don batayi zaton ganinshi da uwar safiyan nan ba... Tana zama Yusrah ta shiga mintsilinta tana fad’in “I told you if you matters to him zai kawo miki... see gashi yazo, dukda dai nada jin kai amma kun dace...” Harara kawai Nabila ta aika mata kana ta shiga bud’e littafinta da tuni ya kama k’amshin turaren Khalid... *** A daren Daddy yayi wayawa Khalid ya sanar dashi maza ya dawo Kaduna something came up at the company ana buk’atarsa... Wasa wasa sabo na neman shiga tsakanin Nabila da Khalid dukda cewa ko ya kirata fad’a kawai suke, duk randa bai kira ba sai taji wani iri sai taji kaman ta kirashi koda zasuyi fad’an, har yanzu cikinsu babu wanda ya yarda yanajin wani abu gameda d’an uwansa.. Bikin Hafiz ne ya taso gadan gadan don tuni an shiga satin bikin, saidai har wannan lokaci Zulfah batada labari, Aunty B ce ta kirawo Mamy tana bata baki cewa kar ta d’aga hankalinta gameda Zulfah ma zatai mata magana yanda zata fahimta... Mamy tai mata godiya sannan ta d’an sami sauk’i cikin zuciyarta... Hakan kuwa akayi Aunty B tai maganawa Zulfa’u cikin natsuwa da kwantar da hankali had’ida nusar da ita duk abinda Allah ya k’addarawa bawa jarabawa ne, hak’uri shine riban rayuwar zaman duniya... Dukda tawakkali da Zulfah tai labarin auren Hafiz sosai ya d’aga mata hankali, taci kuka har ta gode Allah k’arshe ta fawwala wa Allah lamuranta... Ranar da ake jira tazo ranar auren Sawwama da Hafiz, tun safe marok’a ke busa algaita a gidan Magajiya, banda kad’e kad’e da raye raye ba’a komai... A b’angaren Hajiya ma babu sauk’i d’anta zaiyi auren gata auren jin dad’i ba auren wahala ba irin wanda yayi a baya, basu samu sun koma wajen Malam nakan buzu ba sabida hidiman auren Hafiz da yasha kansu... Da yammaci Magajiya ta rufo d’iyarta ta kawo don ko jiran ‘yan d’aukan amarya bata tsayayi ba kafin ‘yan d’auka suzo munafukan unguwarsu su zayyane masu wacece Sawwama a fasa aure... Su Hajiya suna tsaka da hidima sai sautin gud’e gud’e suka soma jiyowa Sa’adu Gurmi na gefe yana kad’ada gurmi Magajiya na gaba tana taka rawa d’aurin kallabi a gefe ga mayafi a kafad’a, tana tafe tana rawa har k’asa k’awayenta na biyeda ita rik’eda Sawwama cikin lullub’i.. Kowa ya daina abinda yake yana kallon ikon Allah... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *25* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Fatan Alheri gareku🤝 Haleematu Maikeke Sadiya Auwal Z BabyMahe Farida S Maina Maman Najwa Deejoh Omar Fatee Beni Maryam Mu’azu Alherin Allah yakai maku🥰 Hajiya da kanta zaune dirshan tai tsakar gidan tana kallon ikon Allah, ita ko a fina finai bata tab’a gani ko jin yanda akace uwar amarya ta rufo d’iyarta ta kawo ba tareda anje an amshi amarya ba... Aunty Lami ta d’an tab’a Hajiya kana tace “Haule yau ina ganin bariki tsirarta, yo ni duk zaman danayi a bariki ai ban tab’a cin karo da irin haka ba, anya kaw Haule ba ruwan dafa kanki kika d’ebo ba...?” Hajiya ta yatsina fuska kana tace “Haba Lami ya kike magana haka kaman baki sanni ba, yo ni ai walki ce daidai da uban kowa, ke nifah duk wanda sukazo dashi toh billahillazi shi zamuyi, kinga kafin su raina mana tashi mu tayasu tik’ar rawar, don wllhi nafi kowa jin dad’in auren nan...” Ta k’arashe tana mai shan d’amara da mayafinta... Haba nan fah fili ya kuma kacamewa uwar ango da amarya sai tik’ar rawa suke kowacce tanaso ta burge, idan Magajiya tayi k’asa Hajiya tai sama haka zalika idan Hajiya tai k’asa Magajiya tai sama nan fah k’awayen ko wacce ta shiga burge abokiyarta da lik’i... Mai Gurmi kaw mai zaiyi banda yaci gaba da kad’a masu gurmi yana washe su had’ida tattaran kud’ad’ensa.... Saida suka tik’i rawa sukai lis kafin aka shige da Sawwama parlorn Hajiya aka soma bada amana....Su Sahariyya suna daga waje ana faman cashewa Yayansu yayi auren gata auren masuyi ba aure irin na Zulfah ba da aka lik’a masa jaraba.... A can gidan Aunty B kuwa Zulfah na zaune tayi jigum tana tunanin rayuwa, a kullum tunaninta da mafarkinta shine INDA RAI DA RABON aurensu ya d’ore itada Ya Hafiz, tabbas ba auren soyayya sukai ba aurene na had’i tsakanin iyaye amma har k’asan zuciyarta tanajin zafin ace ta rabu da mijinta kuma uban ‘yarta, taso ace sun rayu tare sun raini d’iyarsu tare sai dai Allah bai k’addara hakan ba, ta kuma yi imani zab’in Allah shine zab’i na k’warai... Bata tab’a kawowa Ya Hafiz bazai maidata d’akinta ba bata tunanin saidai taji labarin aurensa daga sama ba sai gashi duk hakan ne ta kasance, tabbas mutuwar aure jarabawane mai tsananin wuya koda ace baka k’aunar mijin, fatanta Ubangiji ya bata ikon cin wannan jarabawa bazata kuma ta daina addu’a wa d’iyarta ba Allah ya inganta mata rayuwarta a duk yanda zata tsinci kanta.... Tana cikin wannan tunani ne taga kiran Mamy na shigo mata, jikinta ya kuma yin sanyi, a hankali ta d’aga wayar saidai kafin ta iya furta koda kalma kuka ya kufce mata, lallashi da shawarwari na gari Mamy ta dinga bata har saida Zulfan taji tausayin kanta dana mahaifiyarta sanin cewa mahaifiyarta batasan da mutuwar Aurenta ba har rana mai kaman ta yau, yinin ranar haka Zulfa’u tayishi jiki a mace... A can gidan biki kaw Hafiz da kansa yazo ya d’auki matarsa suka tafi gidansu bai bari ko wata mata ta kai mishi ita ba.. Suna isa Sawwama ta yaye lullub’in dake kanta don dama tuntuni ya isheta da nauyi k’awayen Magajiya ne suka hanata cire lullub’in tuntuni... Mik’ewa tai ta shiga bin gidan kallo ta fito da sauri tana hangen ta yanda zata hango uwar gidanta, wayam bataga kowa ba.... Dawowa parlor tai ta samesa yana kwance k’ullin kaza da ya shigo dashi kana tace “Ina matarka...?” Ba tareda ya dubeta ba yace “Tayi tafiya....” Sawwama ta kuma dubansa kana tace “Tafiya.... Tafiya fah kace.... Kasa jure amsar amaryar tata tai shi ya sanyata yin tafiya koko dai salon nata kishin kenan....?” Bai tankata ba yaci gaba da abinda yake.... Sawwama ta gyara tsayuwa tace “Magana fah nake maka...” “Toh ai maganar taki ne batada amsa...” Ya fad’i nan ma ba tareda ya dubeta ba... K’wafa tai tana watsa masa mugun kallo kana ta nemi waje ta zauna tana sakin hamma.... Ya ida warware ledar kan yayi wani aune Sawwama takai hannu ta cafko tsoka guda ta wuga a baki sai sautin taunarta ne kawai ke tashi.... Hafiz ya d’ago idanu yana dubanta tsaban takaici saida yaji dama bai warware ledar ba... Tsame hannunsa yayi kana yace “Kije ki d’auko plate a kitchen a haka ai bazai maki dad’in ci ba....” Ba tareda ta kallesa ba sai aikin tauna take tana gwaguyan k’ashi tace “Wayace maka kazar amarci a plate akeci, idan baka sani ba na k’ara maka ilimi a ledarta akeci...” Ta k’arashe tana kuma karyo cinyar kazar ta shiga dannawa a bakinta... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka yayi zaune dirshan a wajen yana kallon ikon Allah, ya tuna aurensu da Zulfah k’in siya mata kazar yayi har saida abokansa suka sai mata kuma ko da ya kawo batamaci ba hasalima da safe ya tadda ta d’uma masa kazar ta saka masa a flask idan bai mance ba da kazar marcin Zulfah yayi breakfast maiji da lafiya... Guntun tsaki yayi kana ya mik’e ya nufi kitchen d’auko plate, babban abinda ya bashi mamaki shine daga fitarsa zuwa kitchen veranda kawai ake tsallakewa amma koda ya dawo ya tadda Sawwama ta gama da kazar nan tas sai curin k’asusuwa da ya hango.... Tamkar maraya haka ya shigo da plate a hannu yana dubanta... “Ina kazar....?” Ya tambaya sanda yai mata tsaye aka... Wani kallo tai masa a dak’ile kana tace “Ban gane ina kaza ba, dama kazar na waye...? Ince tawace toh na cinye kayana...” Ta k’arashe tana sakin gyatsa mai k’arfin gaske.... Tsabagen takaici bai kumabi takanta ba ya shiga d’aki yayi shirin baccinsa... Haka nan ta shigo ta taddasa kwance da alama bacci ya soma yin gaba dashi... Dariyar rainin hankali ta saki kana tace “Eh lallai dole kazo ka bajemin a gado kana bacci, idan kasan wata bakasan wata ba....” Hannu tasa ta shiga bubbugashi tana fad’in “Hafiz... Tashi fah zakayi don yau ba ranar bacci bane....” Ta k’arashe tana juyi gabanshi had’ida zuge zip d’in rigarta.... Dirshan ya tashi ya zauna ga d’an banzan yunwar dake azalzalarsa, ko d’an sallahn nuna godiya ga mahalaccinsu da ni’imar da ya azirtasu dashi Sawwama ba bari sunyi ba ko dashike shima gogan aurenshi na fari Zulfa’u ta tarsasa masu yin sallah, dashike shima ba gwanin son sallar bane tuni ya shiga biyewa amaryarsa suka lula duniyar ma’aurata... Tun ango na zak’ewa had’ida nuna k’warewarsa har dai ya fahimci shi jariri gaban amaryar tasa, tun yana fahimtar mai ake ciki har dai ya rasa gane da wacce yake tare amarya tasa budurwa ce ko kuwa akasin haka, a dole Hafiz ya sakarwa amarya ragamar komai ya koma sai direction d’in da tabi dashi... Daren aurensa da Zulfah ya tuna dukda cewa a shaye ya dawo mata dare ne da bazai tab’a shafewa ba a tarihin rayuwarsa, sam babu had’i tsakanin Zulfah da Sawwama, jikin dake tsole masa idanu a waje ashe duk hotone ta gama sakwarkwacewa ko Zulfah data haihu ta shayar da d’iya jikinta yafi na amaryasa zama zamzam.... Gaba d’aya zuciyar Hafiz a cushe yake gashi bawai enjoying kasancewarsu yake ba ga uwar yunwa da gajjiya da suka kuma sauk’ar masa lokaci guda ga amarya batasan gajjiya.... Da k’yar Hafiz ya samu ya k’waci kansa kiran sallan farko ya tsarkake jikinsa ya d’auro alwala ya nufi masallaci abinda bai saba ba fita sallar asuba sai gashi a sahun farko yana jiran liman ya k’araso... Wasu daga cikin mutanen unguwar saida abin ya d’aure masu kai, idan yaga suna dubansa saidai kawai ya kawda kai gefe don bazasu gane bala’in da ya baro a gida..... Koda aka idar da sallar asuba kasa komawa gida yayi ala dole ya tsaya sauraren karatun bayan sallan asuba, bashi ya dawo gida ba saida gari ta soma haske, gaba d’aya jikinsa ciwo yake masa yawa an masa duka.... Cikin sand’a yake takowa tamkar mai tsoron kada wani ya jishi, a haka ya tura k’ofar parlorn ya shige sad’af-sad’af ya d’an yaye labulen k’ofar d’akin yana hangenta yanda ya hangota sai sakin minshari take ta barbaje tana bacci ko shakka babu bata gabatar da sallan asuba ba... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yayi kafin ya dawo parlor da k’yar yake d’aga k’afafunsa da kwankwasonsa da suka masa mugun tsami ya zube saman doguwar kujera tuni bacci yayi awon gaba dashi... Sawwama kaw tana tashi rana tsege-tsege ta shige band’aki ta jajjab’a wankanta ta fito tayi sallah a gaggauce kaman yanda ta saba, zuciyarta fari tas ta tsala wankanta ta cancad’a kwalliya ta fito parlor ta tadda Hafiz tamkar gawa sabida yanda ya sake jiki saman kujera yana baccin huce gajjiya, murmushi tai a zuciyarta tace duk yanda akai matar taka raguwace... Batabi takanshi ba ta kunna radio sautin wak’ar marigayiya Barmani mai coge ya shiga tashi, sai tik’a rawa take tana bin wak’ar dake tashi duk iya sallaman da ake bataji ba Sahariyya ta kalli Najah kana tace “Ke bazasujimu ba mu shige kawai...” Kai tsaye suka kutsa kai cikin parlorn sallama saman bakunansu.... Kallon arziki basu ishi Sawwama ba don ci gaba ma tai da tik’ar rawarta ta barsu nan tsaye da flask d’in abinci suna kallon ikon Allah.... Hango Yayansu kwance magashiyan saman kujera ya sanyasu kuma duban juna... Sahariyya tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ta isa gareta tana gaidata had’ida sanar da ita karin kumallo suka kawo.... Sai sannan Sawwama ta rage sautin kafin ta juyo ta dubesu a dak’ile “Toh da kuka kawo karin sai akace sai kun sanar dani, nan ba fili bane da bazaku ajiye ba, koko dai salon ku katsewa mutun jin dad’insa inyi...,?” Sahariyya ta kasa daina mata kallon mamaki, Najah tai k’arfin halin sakin murmushi kana tace “Wai dama Hajiya ce tace mu gaidaku mu dubo mata yaya kuka tashi....” Batakai aya ba Sawwama tace “Toh kun gani ai garau muka tashi, yanda kukazo kuka tadda matar gidan ya tabbatar maku da hakan idan kuma ba salon gulma ce irin taku ba...” Sahariyya ta had’iyi k’atutun bak’in ciki, a dak’ile tace da ita “K’warai munga kin tashi garau Yayan namu kuma fah munaso muji yaya ya tashi don muje mu sanar da Hajiya, sannan kud’in zuwa kawai ta bamu ba dawowa tace mu amsa wajen Yaya...” Ta k’arashe tana juya mata idanu itama.... Murmushi mai shewa Sawwama ta saki kana tace “Ke banson rashin kunya babu ubanda ya isa ya tayar min da miji lokacin tashinsa baiyi ba don haka ku wuce ku fice min a gida tunda sauran raha a fuskata, wacce ta aikoku d’in idan bata baku kud’in adaidaita ba kwa koma da k’afafunku...” Sahariyya zatai magana Najah ta janyo hannunta tana mai girgiza mata kai alamun tai shiru kana tace “Kinga Addah mu tafi kawai...” Sahariyya tai k’wafa kana ta janyo hannun k’anwarta suka sa kai zasu fice a dai dai lokacinda Sawwama ta janyo foodflask d’in da k’afafunta ta bud’e tai tozali da soyayyiyar k’osai nasha-nasha amaimakon wainar k’wai da kaji ko kifi kaman yanda tai tsammani hakan ya tabbatar mata flask d’in ruwan zafin da tai tsammanin ruwan shayi ne kenan ruwan kunu ne, tabd’i aiko bazata sab’u ba har sun isa veranda ta k’walla masu kira “Kai Kai ku dawo nan....!” A tare suka juyo suna dubanta... Sawwama ta gyara d’aurin kallabi kana tace “Meye wannan...? Waye kuke zaton zaici maku wannan abin, ku tattara ku maida ku kawo abincin da ake baiwa amare...” Ta k’arashe tana shura masu foodflask d’in da k’afarta.... Sahariyya da tuni hak’urinta ya gaza banda huci bata komai a zuciye tayo kanta sai kuma Najah tai saurin rik’ota.... Sawwama tai tsaye tana murmushi mai kamada ki kwatanta, Najah tace “Addah Sahariyya d’auka don Allah mu tafi aka gane muna fad’a da ita dariya za’ai mana tinda ansan yanda mukeda Zulfah....” Banda harara babu abinda Sahariyya keyi, itako Sawwama tuni ta tura k’ofar parlornta ta shige ta barsu nan tsaye da abincinsu suna iya juyo yanda ta k’ara sautin wak’arta tana ci gaba da tik’ar rawarta... Haka suka tattari kulolin suna mamakin wane irin bacci Yaya Hafiz yake duk wannan bidiri da ake baiko motsa ba balle ya tashi... Haka suka komo gidawa Hajiya nik’i-nik’i da sanyin gwiwa... Hajiya tana hangosu ta fito tana washe baki tana tambyarsu yaya ankai, yaya suka sami surkarta da d’anta.... Najah ta kalli Sahariyya da tuni ta saki tsuka ta dangwal kwanon hannunta tai shigewarta d’aki... Hajiya ta bitada kallo cikeda mamaki kana ta maido da dubantaga Najah tace “Wai juye abincin sukai suka baku kwanukan ku dawo dashi... Allah sarki kaji d’iyar albarka har wanke kwanon tai...” Batakai aya ba Najah ta katse ta da fad’in “Hajiya.. Abincinki akace mu dawo miki dashi amarya bataci snnan d’anki kuma kwance magashiyan muka taddasa don har muka shiga muka fito ban tsamman yasan munje ba, sirkarki kuwa ras take donma rawa mukaje muka taddata tana tik’a...” Daga haka sakai Najah tai zata wuce ta bar Hajiya rungume da kwanon k’osai tana k’are masa kallo... Har Najah ta isa bakin k’ofar parlor ta juyo taceda Hajiya “Aw na mance Amarya tace wainar k’wai da kifi ko kaza zataci had’ida shayi maiji da lafiya...” Tana ida fad’in haka ta saki labulen parlorn ta shige... Hajiya da zuciyarta ke faman bugu daurewa tai ta shiga masu sababi da fad’in “Yo ko ta fad’i haka ai batai k’arya ba, idan abinda takeso kenan ai sai a mata ba wani abu bane... Kudai shegen rashin hak’uri ne irin naku... Ince d’azun da rawar kanku kuka banne ni zaku kai mata kari don ku saba.. Kunje kuna masifa da rawar kai irin taku da kuka saba yo ba dole ku gundireta ba...” Ta k’arashe tana jefa k’osai guda a baki nan ta hangi Raihanah dake bakin famfo tana wanke wanke a gabanta akai komai, suna had’a idanu Hajiya ta sakar mata dak’uwa tana fad’in “Kin kalli uwarki mayya kawai.. Taso ki wuce ki tafi bakin babban kwalta ki sayo kifi yanzu ki d’aura idanma masu kifin bakin hanya basu fito ba ki wuce kasuwa ko tasha... Taso mana ina miki magana kahura kawai...” A d’ari Raihan ta k’arashe kashe famfon wanda da k’yar ake d’aure bakin hasalima ita kad’ai ta iya rufewa idan bata rufe da kyau ba ta bari ruwa yayita zuba haka zata fice mak’ota d’ebo ruwa a rijiyan mak’ota... Jiki na rawa ta k’araso wajen Hajiya ta amshi kud’in ta d’auko hijab d’inta ta fice sai zuba sauri take tsoron kada tayi latti Hajiya ta jibgeta... Daga yanda take tafiyar tana zuba sauri zaka fahimci sam ba’a nitse take ba tsoro da fargaba su suka cika mata zuciya, alla alla take ta samu masu kifin babban kwalta sun fito, aka kuwa yi sa’a mai teburi d’aya ya fito.. Sauri sauri Raiha ta sayi gammo guda na kifin kaman yanda Hajiya ta aiketa ta shiga zuba sauri don ta samu ta isa gida da wuri ga goyon Kausar a bayanta don dama haka take kusan yini da yarinyar a bayanta tana rainonta koda aikin gida zai kasheta tinda yaran Hajiya bayi zasuyi ba.. Kaman daga sama haka yaga giftawarsu ta gabansa, yayi saurin danna birki yana karanto innalillahi... Cikin sauri Sameer ya fito yana duba mutanen da ya kusa kad’ewa idan zai iya tunawa irin haka ne kwanaki ya kusan faruwa dashi sanda ya kuskuri wata budurwa d’aukeda k’aramar yarinya... Kausar na kuka Rainaha na kuka, ita Kausar kukan razana take yayinda Raihana ke kukan gammon kifin Hajiya da ya watse cikin culvert mai d’aukeda gurb’ataccen ruwa.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *26* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Sameer ya k’araso tamkar mai sand’a yana k’ok’arin duk’awa had’ida duban fuskar budurwar nan dake shesshek’ar kuka a hankali tana jijjiga yarinyar dake bayanta, duk sai yaji babu dad’i musamman da yaga gaba d’aya suke kukan babu babbar babu k’aramar, dama shi tuntuni mutum ne wanda kuka ke tsananin d’aga masa hankali musamman yaga mace ko k’aramin yaro na kuka duk yaji hankalinshi ya tashi... Murya a hankali ya furta “Sannu koh.... Bakuji ciwo ba...?” Sai sannan Raihanah ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa, maimakon ta masa magana sai kuma ta k’ara tintsirewa da kuka had’ida kifa kanta bata daina jijjiga Kausar da tuni ta bar kuka ba sai sakin ajiyab zuciya da takeyi..... Sameer ya d’an shafi sumarsa cikeda damuwa kana ya kuma kai dubansa ga budurwar mai tsnanin k’arancin shekaru a iyaka duban da ya mata.... Duk’awa ya kumayi gabanta wannan karon kana yace “Akwai yanda ke maki ciwo ne....?” Nanma shiru bata bashi amsa ba saima dad’a had’e hannayenta biyu datai waje guda tana matsan hawaye... Har ya cire rai bazatace komai ba sai kuma ta shiga girgiza masa kai alamun a’a.... Samun k’warin gwiwar dad’a tanbayarta yayi... “Inane gidanku...?” Wannan karon d’ago watery eyes d’inta tai tana duban mutumin sai kuma ta dad’a kai dubanta ga kifin da tuni watse cikin ruwan dotti kana tace “Ni bazanje gida ba Hajiya duka zatamin....” Yanda tai maganar yasa Sameer kuma dubanta sosai kana yace “Maiyasa zata bigeki.....?” Sabon kuka ne ya kuma zuwa mata bata iya bashi amsa ba sai nuna masa culvert da ta shigayi tana mai ci gaba da shesshek’an kuka, Sameer yakai dubansa sosai ga culvert d’in yana kallon abinda take k’ok’arin nuna masa, maido da dubansa gareta yayi kana yace “Idan na fahimceki aiken Hajiya ne ya zube a nan koh...?” Tai saurin jinjina masa kai tana mai share hwayenta... “A ina ake saida kifin...?” Ya tambaya yana dubanta... Alama kurum ta masa da hannu tsallaken titi ba tareda tace komai ba.... Sameer ya jinjina kai kana yace “Just wait for me here kinji koh, I’ll be right back...” Batace masa komai ba sai sadda kanta k’asa da tai tana matsan sauran hawayenta had’ida tausayin kanta da takeji don tasan yau dole ta daku hannun su Hajiya donma Sahariyya yau tanaji da nata k’unci da ta nad’i na jaki wajenta... Jim kad’an ya dawo da gammon kifi kusan guda biyar cikin leda kana yace “Shiga mota na kaiku gidan naku...” Dubansa ta d’anyi kana tace “A’a ni bazan shiga ba an hanamu....” Sameer ya d’anyi shiru tamkar mai tunani kana yace “Idan na tare maki adaidaita zaki shiga...” D’ago manyan idanunta masu tsananin haske tai tana dubansa sai kuma ta kauda kai gefe tace “Ai gidanmu babu nisa k’asan layin can ne....” Ta k’arashe tana mai nuni da hannunta... Sameer yakai dubansa ga yanda tai masa nuni ya d’ago left hand d’insa yana duba time sabida surgery da yakedashi a asibiti, bai kuma ce mata komai ba sai komawa motarsa da yayi ya zaro key d’in had’ida sakata a security lock sannan ya dawo yanda Raihanah ke tsaye tamkar wacce ruwa ya shanye... Duba guda Sameer ya mata kana yace “Muje ni zanyi maganawa Hajiyar bazata dakeki ba kinji koh...” Raihanah da k’irjinta ya bada sauti saurin girgiza masa kai tai kana tace “A’a ka barshi kawai zan koma dakaina...” Kallon da ya mata ya sanyata yin shiru, Sameer ya kuma fad’in “Muje..” Wannan karon babu musu ta shige gaba yana biye da ita har suka iso layin nasu... Koda suka iso k’ofar gidan kasa shiga Raihanah tai sai kallon ledae dake hannunsa take alamun tanajin tsoron shiga babu aiken kifin Hajiya... Sameer na hankalce da ita, mik’a mata ledar hannun nasa yayi yana mai dubanta... Hannu ta d’an mik’a zata karb’a sai kuma ta fasa.. Sameer ya gyara tsayuwarsa yace “Amsa ki kai mata sai ki sanar da ita ana sallama da ita a waje...” Girgiza kai Raihana tai kana tace “Kifin gammo gudane ai kawai...” Sameer ya jinjina kai yace “Babu damuwa ki kai mata ki fad’a mata sak’ona...” Jiki a sanyaye ta amsa had’ida masa godiya kafin tasa kai zata shige gidan cikeda fargaba da tsoro nan ta jiyo muryarsa yana tambayarta sunanta... A hankali ta juyo kaman mai tsoron magana tace dashi “Raihanah...” A zuciyarsa ya maimaita sunan kana yabi bayanta da kallo cikeda tausayawa, sau tari yakansha mamaki idan yaga iyaye na dukan yaransu kaman basusan cewa yara babban kyautace daga Allah wanda ba kowa yake badawa, yanaji a ransa duk randa ya haifi nasa yaran bazai dasa masu tsoronsa cikin zuciyarsu ba saidai tsoron mahaliccinsu, yaransa zasu zama abokansa ta yanda bazasu b’oye masa komai ba zasu sharing komai dashi, rayuwa mai cikeda jin dad’i yake hango masu shida Partner da kuma yaranda zasu haifa in feature... A hankali ya saki murmushi had’ida daidaita tsayuwarsa yana jiran fitowar Hajiya... Duk daga nesa Hajiya ke aika mata dak’uwa da ashariya tana fad’in uwar mai ta tsayayi sai yanzu zata dawo, tuni ta janyota ta shiga rank’washi Raihanah na bata hak’uri, tuni su Sahariyya da Najah suka fito kallo suna dariya don dama idan Raihana tayi laifi idan Hajiya na bugunta tsallen da take tamkar ‘yar kenwace ke basu dariya Cak Hajiya ta tsaya da bugun nata tana kallon damin kifin da tasan bata bata kud’in sayo kifi mai yawa haka ba... D’ago fuskarta Hajiya tai tana kallo kana tace “Ke tsaya badai karuwanci kike da masu saida kifin ba suke arha maki haka....” Ta shiga doka salati tana tafe hannaye had’ida kuma mak’uro Raiha tana fad’in “Raiha... D’ago ki kalleni don ubanki ki fad’amin mai kike basu suke maki arha... No wonder shiyasa kika dad’e mana kin shige shagon mai kifi ya gama matseki dole ki dawomin da damin kifi toh kuwa a kunnen ubanki don nidai bazaki janyo min zagi a gari ba...” Su Najah da Sahariyya an tab’o yanda ke masu k’aik’ayi tuni suka fito suma suka mata caa suna binta da kallon k’yama.. Cikin kuka Raihana ke fad’in “Hajiya ki tsaya kiji Hajiya wllhi ba haka bane babu abinda nayi Kausar itace shaidata...” Haba nan fah su Sahariyya suka kwashe dariyar rainin hankali kana Sahariyya tace “Kunji shegiya wai Kausar shaida a gidan uban wa kika tab’ajin yarinya k’arama ta bada shaida ke annabiya ce kokuwa salon iskancinki ne haka, ma uban wa zaki raina hankali... Hajiya ki kwab’e mata fatari ki gani idan ba’a gama bud’ata waje ba... Shegiya k’aramar karuwa...” Ta k’arashe tana kai mata rank’washi mai tsananin zafi wanda ya sanyata sakin k’ara.. Hajiya na huci take fad’in “Naja mik’o min muciya naci uwarta da kyau sai ta fad’imin uban da take shagon masu saida kifi...” Raihana ta bud’e baki zatai magana Hajiya ta gwab’e bakin da hannunta Sahariyya ta finciko Kausar daga bayan Raihanah ta ijiyeta k’asa, Kausar ta saki kuka mai k’arfi a daidai sanda Najah ta taho da muciyar tuk’a tuwo ta dank’awa Hajiya, Hajiya ta shiga shima mata tamkar an aikota.. Allah sarki Raihanah da ba’a bata dama tayi bayani ba sai ihun azaba take tana rok’on Hajiya da tai hak’uri zata fad’a... Abin tausayin shine dagaji kasan tsananin azaba ne kurum ya sanyata cewa zata fad’a ita kanta batasan mai take fad’i ba.. Daga yanda yake tsaye yaji shiru shiru bata dawo ba ga kunnuwarsa dake jiyo masa sauti kaman na kuka da hayaniya, gabansa ya fad’i ya yanke kardai dukan yarinyar nan ake... Bai wata wata ba ya yanke shawarin kutsa kai cikin gidan ceton yarinyar nan.... Hango Mace da yayi sai jibganta take tana ihu ga wasu gefe suna shewa ya sanyashi saurin k’arasawa ya amshe muciyar daga hannun Hajiya yana fad’in “Idan kika kasheta koda ace ‘yarkice sai na maka ki a kotu...!” Yanda yayi maganar gaba d’aya hankulansu ya dawo gareshi.. Ido cikin ido Sameer ke duban Hajiya, wani irin fad’uwan gaba had’ida firgici suka dirar mata lokaci guda... Ta tuna sanda ta toshe bakin Ma’aruf dake tsananin kuka yana kiran Mamynsa da tsumma ta jefashi bayan bus suka bar gari, ta tuna yanda ta damk’ashiwa Aminiyar sirri bayan ta gama azabtar da yaron... K’wayan idanun bazasu iya b’ace mata sabida k’wayan idanu ne masu tsananin wahala ace mutum ya mance, Hajiya ta kasa koda motsawa sannan ta kasa bud’e baki ta furta koda kalma guda ta kuma kasa janye idanunta daga duban wannan mutumi da gani take tamkar d’an marayan azikine Allah ya tayar da abinsa.. A b’angaren Sameer ma kallon fuskar matar yake kaman yanaso ya tuna yanda yasan mai irin fuskar saidai sam ya kasa tunawa, tamkar ya tab’a cin karo da muguwar mata mai tsananin kamanni da wannan matar a can wasu shekarun baya su kuwa su Sahariyya da Najah mutuwar tsaye sukayi suna santin wannan had’edd’en saurayi d’an gayun had’ida mamakin mai ya shigo dashi cikin gidansu.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _..............DA RABO_ *27* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Haule da gaba d’aya gumi ke tsartsafo mata k’ok’arin daidaita kanta tai kana tace “Toooh kaikuma asuwa... Wane uban ne ya baka izinin shigowa kan matan aure...? Bakai zubin masu saida kifi ba da sai nace kaine daduron nata, aikin banza aikin wofi...” Tinda ta soma magana Sameer ke dubanta, bai tankata ba sai duk’awa k’asa da yayi yana duban Raihana cikeda tausayawa yanda jikinta yayi luhu luhu ya tara jini... Sahariyya ma batasan sanda ta duk’a ba had’ida rafka uban tagumi tanai masa mayen kallo kaman zata lasheshi.... Kasa furta koda kalma yayi saima tsananin tausayin yarinyar da ya kuma rufeshi, d’agowa yayi yana ma Hajiya wani irin kallo mai tsananin firgitata kana ya mik’e tsaye yace “Duk yanda akai ba kece kika haifeta ba.. amma ki sani yatsa guda idan kika sake d’aurawa akanta....” Hajiya ta katsesa da fad’in “Mai zakayi... Nace mai zakayi... Hukuma zaka kiramin toh kira gwangwani uwar d’amara...” Bai furta komai ba sai duban da yake mata, ruri da wayarsa ta d’auka ya sanyashi tuna ashe jiranshi ake a asibiti... Wani kallo ya kuma baiwa Hajiya wanda ya k’irjinta bugu kaman an sauk’e guduma kana yasa kai ya fice daga gidan zuciyarsa bai daina masa wasu irin tunani sarara ba.... *** Hafiz bashi ya tashi sai wajajen k’arfe goma na hantsi, ya yunk’ura zai motsa yaji k’ashin bayansa na amsawa, banda sarawa babu abinda kansa keyi... Tsaye ya hangi Sawwama da kwaskwon turaren wuta sai zagaya gidan dashi take tana ‘yar wak’enta, hammar yunwa ya kuma saki ga k’amshin turaren sam bai masa ba, yayi k’arfin halin mik’ewa ya nufi band’aki, jim kad’an ya fito ya taddata a parlor tana kunna kayan kallo k’afa guda akan guda sai taunar chewing gum k’araras.... Zaune yayi gefenta yanata faman jira ta gaisheshi amma shiru baiji alamun zata gaishe shi d’inba.... Shafe goshinsa ya kumayi kana yace “Ba’a kawo breakfast bane...?” Idanunta naga kayan kallonta tace dashi “Sun kawo amma nace su maida...” Hafiz ya bita da kallon mamaki kana yace “Ban gane kince a maida ba, toh mai zanci... kokuwa kin dafa ne...” Galala take dubansa kana ta murmusa a hankali had’ida kuma tauna chewing gum d’inta tace “Aidai kai shaidane ko kantin abincin Mamata kaje kayan dad’i ake cika maka tumbi dashi don haka babu abinda zaisa a nannagomin k’osai da uwar safiya safiyarma na amarcina naci nayita tusa, bazai saku ba...” Ta k’arashe tana watsa masa mugun kallo had’ida maida idanunta ga kallon da take.... Jinjina kai yayi yana dubanta kana ya furta “Yayi kyau...” Jiki babu k’wari ya mik’e ya shige d’aki ya d’auko makullin abin hannunsa yasa kai zai fice.. Tsaye Sawwama tai a gabansa tanai masa kallon tambaya “Ina zakaje...” Ya bata wani mugun kallo kana yace “Ki matsa min a hanya...” Murmushi ta sakar masa kafin ta marairaice fuska tanai masa salo take fad’in “Haba Habibi duka duka fah jiya aka kawoni yau kuma zaka fita so kake ‘yan bak’in ciki su mana dariya...?” Ta k’arashe tana wasa da ‘yan yaysunta saman fuskarsa.. Samun kansa yayi da kasa mata musu saima d’an dubanta da yayi ta kuma kashe masa idanu... Wannan karon saida ya d’an fuzar da iska kafin yace “Sawwama yunwa nakeji...” Hannu ta d’ora saman k’irjinsa tanayi kaman tana d’an gyara masa kwalar rigar kana tace “Kar ka damu idan dai abinci ne yanzu za’a kawo maiji da lafiya kaji koh, haba karfa ka mance kantin abinci garemu...” Ya d’anyi k’arfin halin sakin murmushi kana yace “Toh Amarya a barni naje na gaida Hajiya...” Wasu salon take kuma masa had’ida langab’e kai tace “Hajiya ta ganka a wannan lokaci ai zatace ba lafiya muke zaune ba, kaga yau gaba d’aya bai kamata ka fice ba a gida ya kamata ka zauna muci soyayyarmu... Muje na wankeka...” Ta k’arashe tana k’ok’arin b’alle masa boturan riga.. Hafiz ya zaro idanu waje ga k’irjinsa da yayi mugun bugawa yanajin yanda har yanzu tin daga gadon bayansa yayi kwankwasonsa zuwa cinyoyinsa gaba d’aya ciwo suke masa a firgice yace “Ki wanki wa...? A’a Sawwama wanka kuma ai saidai na gobe...” Sawwama ta d’an murmusa kana tace “Nafa sani bakai wankan sabulu ba Habibi muje na cud’eka ta shiga turasa cikin d’akin yana turjewa... “Sanyi nakeji nida tab’a ruwa bacin alwala sai gobe ke alwalan ma rik’eta zanyi ya k’arashe yana k’watan kwalan rigarsa daga hannunta... Sawwama bata daina abinda tayi niyya ba take fad’in “A’a a yau a k’alla kayi wanka sau biyar... Kaga muje dan Allah....” Ya kuma zaro idanu waje ganin abinta da gaske take musamman data dannashi cikin d’aki... Banda innalillahi da salati baya iya komai, dafe kansa yayi gumi na keto masa, zata hauro saman gadon ya shiga matsawa baya yana fad’in “Kiyiwa Allah ki bani abinci first Sawwama tun jiya da rana babu abinda naci wllhi banida k’arfi....” Sallaman da sukajiyo daga bakin baranda ya ceci Hafiz, jin abokansa ne ya sanya Sawwama jan tsuka ba tareda ta amsa ba, masu sallama suka soma fad’in kodai babu kowa gidan ne.. D’aya yace kokuma basu tashi ba dai, k’ila mun masu sammako... A d’ari Hafiz ya mik’e dukda ciwo da jikinsa ke masa yana lek’e ta window yake fad’in “Wa’alaikumussalam... Magaji ku dawo karku tafi... Mun tashi...” Yana fad’i Sawwama na k’ok’arin janyosa amma tuni ya mak’ale jikin window tamkar wani d’an biri yana fad’iwa abokan su dawo, yanda kasan mai kiran azo a ceci rayuwarsa.. Suna dawowa da baya Hafiz yaji wata relief cikin sauri ya shiga kintsa kansa yana fad’in “Bani waje bani waje inada bak’i....” Sauri sauri yake komai Sawwama ta bisa da kallo sanda ya fice kana tai k’wafa tace “Bakai kace ka iya kai mace hotel ba har nice zaka rainama hankali ka nemi k’awata, kad’an ka soma gani wllhi wllhi sai na cire maka kwad’ayin duk wata mace... Sawwama nake...” Ta k’arashe tanayin k’wafa a hankali kafin ta fito parlor ta tadda abokan mijin nata sai gwad’ata suke amarya baki laifi A gefe guda kuwa sam basu gane kan abokin nasu ba kaman ba ango ba, suna ango kasha mai saidai ya kauda kai gefe yana sauk’e haki a hankali.. *** Tinda wannan mutumi ya fice daga gidan Hajiya Najah da Sahariyya ke ci gaba da santinsa suna addu’an Allah dawo dashi, Najah ta dubi Sahariyya kana tace “Addah wannan guy d’in dai kinsan dani ya dace..” Banzan kallo Sahariyya ta mata kana tace “Ke Najah ko a gidan giya akwai babba don haka wannan mutumin nawa ne...” Najah ta tab’e baki tace “Sai mu jira dai muga wace zai zab’a...” Ta k’arashe tana juya idanu had’ida watsa mugun kallo wa Addar tata.. Sahariyya tai k’wafa tana fad’in “Eh lallai yarinyar nan wuyarki ta rik’a da har zanke fad’i kina fad’i...” Najah ta shiga taku tana juya jiki take fad’in “A duba ko ajiki ansan wacce za’a zab’a ballanta sabbin jini irinmu ake yayi wllhi...” Sahariyya takai mata jifa da takalmi Najah ta kauce tanaci gaba da taku had’idayuwa Addar tata gwalo... Duk tattaunawar da suke Raihanah na d’aki na kwance tana saurarensu tana hawaye, gaba d’aya jikinta ciwo yake mata sabida bugun da taci, cikin zuciyarta take addu’ar Allah kawo mata d’auki ya shiryar da Hajiya da ‘yan uwanta idan kuma ba masu shirirya bane Allah ya fitar da ita daga wannan wahala da take ciki... A b’angaren Hajiya kaw tana can d’aki tana faman safa da marwa tabbas yau taga abinda Lami ta gani.... Ta shiga yarfe gumin dake tsartsafo mata, meke shirin faruwa dasu, sirrin da ya jima a b’oye sama da shekaru 30 yana neman bayyana kanshi.. Ta kuma janyo wayarta hannu na rawa ta shiga neman layin Lami Bugu biyu a na uku Lami ta d’aga... Daga yanda Aunty Lami taji muryan Hajiya Laure tasan babu lafiya, aje wuk’ar da take yanka albasa tai kana ta mik’e tsaye tana fad’in “Laure lafiya..?” Hajiya ta kuma yarfe gumi kana tace “Lami na ganshi wllhi na ganshi yau nayi idanu hud’u da Ma’aruf...” Aunty Lami ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Laure ki natsu kimin bayani yanda zan fahimta...” Cikin sark’ewar murya Hajiya take fad’in “Bayanin kenan Lami Ma’aruf na gani, wannan k’wayan idanu nashi bazan tab’a mancewa ba, shin Lami ya akai yanzu yake neman dawowa rayuwarmu, shin Aminiyar Sirri bata tabbatar mana da mutuwarsa ba, ko kuwa dai mutum na mutuwa ya dawo ne, Lami randa duk Mariya tai idanu hud’u da gudan jininta ina mai tabbatar maki cewa zata ganeshi...” Aunty Lami tai saurin tura k’ofar kitchen kana tace “Abinda nake sanar dake kenan, dolece ta kama mu wanke k’afafunmu muje mu samu aminiyar sirri don wllhi ko Malam zai tabbata yana fad’i mana abu a duhu baiga komai ba bazan yarda saurayin da na gani ba Ma’aruf bane.....” Haule ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kinga maza maza ki fito mu tafi, ni da kika ganni ko wanka bazanyi ba zan fito sai mun had’u a mahad’a...” Daga haka katse wayar tayi tana k’ok’arin shiryawa Aunty Lami ta kashe girkin da take tana tunani, tabbas idan asirinsu ya tonu sai tafi Haule fad’awa uku sabida ta tabbata koda Mamy zata yafe mata Alhaji Usman Mailafiya bazai tab’a yafe mata ba uwa uba jarabebbiyar tsohuwar nan Mamani tabbas sai taga bayanta tsawon shekarun data jefata cikin k’unci.... Marliya data kawo mata aike daga wajen Mamy tsaye kawai tayi tana maimaita sunan da taji Aunty Lami na ambata “Ma’aruf” shi kad’aine abinda ta iya jiyowa sai kuma taji muryar tata tai k’asa... Tsaye kurum tai tana tunani tabbas idan bata mance ba wannan sunan Yayansu ne da ya b’ace shekaru masu yawa hasalima saidai a hoto suka sanshi yana k’arami d’an shekaru uku....A haka Aunty Lami ta bud’e k’ofar kitchen ta tadda Marliya tayi tsaye tamkar gunki tana aikin tunani, k’iris ya rage Aunty Lami bata dungura k’asa ba sabida tsananin tsoro da taji, ganin Marliya ce ya sanyata sakin murmushin yak’e tana fad’i cikin sark’ewar murya “A’a Marlili kin..kin jima ne a nan..?” Murmushin Marliya ma tai mata kana ta girgiza kai tace “A’a Aunty isowata kenan... Ga wannan inji Mamy...” Ta k’arashe tana mik’a mata flask d’in hannunta Aunty Lami tai k’ok’arin saita kanta ta amsa dukda rawa da hannunta keyi, zata bud’e Marliya tace “Kunun nono ne bata jima dayi ba...” Nanma murmushin yak’e Aunty Lami tai kana tace “Ayya Mamy bata gajjiya tasan abinda nake so kice da ita na gode...” Marliya ta jinjina kai kana ta fice cikin sanyin jiki... Nabilah na kwance tana kallon shirin _Crush of the week_ Marliya ta shigo jiki a sanyaye ta zauna.. Nabilah nata mata labarin yanda ake gudanar da shirin tana kora kununta nan ta lura hankalin Marliya baya tareda ita.. Mik’ewa tai sosai ta zauna tana duban ‘yar uwar tata don da wuya kaganta cikin yanayi irin haka kana ta d’au throw pillow ta jifa mata tace “Ke meye haka, tunanin mai kike...?” Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Addah Nabilah shin Ma’aruf bashine sunan Yaya da ya b’ace ba years back....” Nabilah ta jinjina kai kana tace “Toh sai akayi yaya, ko kin samo wa Mamy shine..?” Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kinga yanzu da na kaiwa Aunty Lami kunun nan.... I overheard her talking on the phone kaman sunan take ambata kuma wayar nata kaman na sirri kaman bataso wani yaji...” Nabilah ta gyara zamanta sosai “Ma’aruf kawai kikaji ta ambata bakiji komai ba..” Nabilah ta tambaya Marliya ta jinjina kai kana tace “Addah Nabilah I don’t want to believe this, ban sani ba meyasa zuciyata tak’i aminta da wayar da Aunty keyi... Is like she’s hiding something... Oho I don’t know...” Jinjina kai Nabila tai tana hura hanci kana tace “Shiyasa na tsani matar nan tuntuni, something about her is fishy, tayita nunawa Mamy soyayya kuma bayan da ba haka take ba, who knows wayasani maybe she has something to do with our brother’s disappearance....” Girgiza kai Marliya tai kana tace “A’a kada kice haka, Allah shine masanin gaskiyar lamarin tinda banji komai ba bayan suna da naji ta ambata ta yuwu wani Ma’aruf d’in ne.. And please kar kicewa Mamy komai kada mu d’ago mata gyambon dake zuciyarta mu maidasa sabo...” Jinjina kai Nabilah tai kana tace “Idanma tana b’oye wani abin I’ll find out, kuma wllhi idan na fahimci cewa itace silar k’uncin Mamy sai yanda k’arfina ya k’are...” Ta k’arashe tana mai tsananin huci.... A b’angaren Sameer kuwa tinda ya isa asibitin yake jinsa wani iri, abubuwan da suke faruwa dashi a Kano sun d’aure mai kai, ji yake tamkar wasu memories ne da suka faru lokaci mai tsawo, shin kodai iyayenshi sun zauna a garin ne particularly wannan unguwar da a yanzu yake zaune cikinta, shin kafin suyi zaman Amurka k’ila nan ne garin da suka fara zama idan ba haka ba meyasa yakejin wani abu gameda environment d’in da mutanen cikinta... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya can wata b’angare na zuciyarsa na tuna masa yarinyar nan Raihan da halin da ya barta ciki... Agogon hannunsa ya kuma dubawa ko lokacin sallah tayi sabida yanada wani surgery da rana, wani tunani ne ya fad’o masa kana ya suri makullensa ya fice... Dai-dai k’ofar gate d’in yayi parking yana neman yaron da zai aika cikin gidan... Can saiga wani yaro yazo shigewa Sameer ya tare shi da niyyar aikanshi... Wata leda ya ciro cikin motarsa ya mik’awa yaron yace “Kaga nan gidan...” Ya masa nunida gidan Alhaji Sani mahaifinsu Raihanah... Yaron ya jinjina kai yace “Eh.. nasan gidan a unguwar nan nake..” Sameer yace “Good, ka shiga ka bada wannan sak’on wa Raihan...” Yaron ya d’an subeshi sai kuma yace “Raihan kuma nasan dai akwai Raihanah a gidan, ba ‘yar Hajiya bace shiyasa kullum Hajiya ke bugunta Mamarta ta jima da rasuwa tun tana yarinya shiyasa ta girma hannun Hajiya... Amma tafi kowa kirki a gidan..” Tinda yaron ya soma zuba Sameer ke dubansa yana jinjina lamarin, tabbas biri yayi kama da mutum, no wonder matar nan take jibgan yarinyar tamkar ba biladama ba ashe ba d’iyarta bace, wani tausayi ya kuma taso masa.. Duban yaron yayi yace “Maigidan na raye...?” Yaron ya jinjina kai yace “Yana nan saidai baya iyayin komai a gidanshi...” Shiru yayi na d’an lokaci yana tunanin abubuwan da yaji daga bakin wannan yaro mai yawan magana, tabbas zaiso ya had’uda maigidan nan dukda cewa ba huruminsa bane amma zuciyarsa sosai ta aminta da ya sadu da maigidan nan.. Yaron yana shigewa Sameer ya shiga motarsa ya wuce.. Sahariyya ya tadda tsakar gidan kwance saman tabarma da pillow tana karanta littafi yayinda Raihanah ke kwance har lokacin a d’aki... Sallama yaron yayi Sahariyya ta amsa mashi a dak’ile ta k’arada “Wajen waye kazo...?” tana maganar tana duban ledar hannunsa... Yaron yace “Wani mutumi ne yace a bada wannan ma Raihanah...” Jin an ambato sunanta ya sanya gabanta mugun fad’uwa tana tunanin kardai mutumin can ne ya dawo... Sahariyya ta aje littafin hannunta had’ida mik’ewa zaune tana mai gyara d’aurin k’irjinta taceda yaron “Kawo nan..” Yaron ya d’an doje yace “Nifah ma Raihanah akace na bada...” Sahariyya ta mik’e sosai tana fad’in “Kai banson iskanci kada ka bari na tashi... Waye ma ya aikoka...?” Yaron ya k’araso ya dangwala mata ledar kana yace “Wani mutumi ne mai kyau had’ida mota mai kyau...” Ai Sahariyya batasan sanda ta mik’e tsaye ba tana fad’in “Ina yake... Gudu jeka ka taremin shi...” Yaron ya mata wani kallo kana yace “Ai ya tafi.... Saidai kiyi hak’uri...” Harara ta watsawa yaron kana tace “Toh uwar mai kake jira kaikuma da bazaka fice daga gidan ba.....” Yaron na k’unk’unin shima Raihanah akace ya bada aiken ya fice, Sahariyya sai danna masa ashariya take.. Tai saurin bud’e ledar tana zazzagewa abubuwan ciki suna fitowa... Magunguna ne da na sha da na shafawa danginsu pain reliever... Take ta kuma yin kicin kicin da fuska kana ta shiga k’wallawa Raiha kira.. Jiki a sanyaye Raihanah ta fito ta tadda Sahariyya Wani kallo Sahariyya ke watsa mata kana tace “Munafuka duk salon yaudarar namiji kin iyashi k’arama dake, toh kaw kinaji kina gani maganin nan hanyar ruwa zan watsasu bazaki amfana dashi ba, b’ace min da gani anammimiya...” Hawayen da suka zubo mata ta kuma gogewa kafin ta koma d’aki cikin tafiya da yafi kama da d’ingishi... Sahariyya ta rakata da mugun kallo... *** Gaba d’aya sunyi zaune a mahad’a suna jiran k’arasowar aminiyar sirri, Hajiya tace “Lami anya Aminiya zatazo...?” Lami tace “Dole ma tazo domin kuwa idan asiri ya tonu ba mu kad’aine a rana ba saima ta fimu shiga...” Hajiya ta jinjina kai tana buga hannayenta a hankali tana waige waigen ta yanda zata hango Aminiyar sirri... Daga can suka hango mai tasi ya ajiyeta tana k’arasowa yanda suke sai waige waige take tamkar mai tsoron kada wani ya hangota... A tare Lami da Haule suka kalli juna kafin suka mik’e gaba d’aya sanda ta k’araso.... “Aminiyar sirri ganin ki yayi wahala...” Hajiya tace sanda take dubanta Murmushi matar ta saki wacce batakaisu a shekare ba kana tace “Haule, Lami shekaru talatin baya babu abinda ya canza a rayuwarku......” Lami ta nuna mata kujera kana tace “Sirrin dake b’oye shekaru talatin baya yana neman ya bayyana kanshi...” Murmushi Aminiyar Sirri ta saki kana tace “Mai kuke tunanin zai bayyanashi idan ba d’aya daga cikinku bane ta bud’i baki ta fad’i...” Haule tai saurin katseta “Tabbas mukeda babban dalili domin kaw Ma’aruf muke gani yana neman dawowa cikin rayuwarmu...” Ta kuma murmusawa kana tace “Bazaku tab’a canzawa ba.... Amma..” Ta k’arashe tana bud’e zip d’in jakanta... Kayan k’aramin yaro ta ciro d’aukeda bushesshen jini ta shiga warware masu... Lami da Haule suka dubi juna tabbas wannan shine kayan dake jikin Ma’aruf sanda suka sabautar dashi... Aminiyar sirri ta murmusa tace “Meyasa kuke tunanin zanbar Ma’aruf a raye bayan duk duniya babu aninda na tsana irin farin cikin mahaifiyarsa kuma nasan dani daku akan haka mukayi tarayya...” Haule da Lami suka kuma duban juna kana sukace “Aminiya idan kikaga abinda muka gani kema zaki yarda cewa tabbas Ma’aruf na raye....” K’uri ta masu kana tace “Laifukanku suke bibiyarku suka hanaku sukuni amma ina mai tabbatar maku ba Ma’aruf kuka gani ba, Ma’aruf ya jima da zama tarihi don haka idan bakune kuke son tonowa kanku ba kada ku bud’e sirrinku da kanku, randa duk aka fahimci akwai aminci na sirri tsakaninmu sanin kanku ne zargi zai mana yawa don haka shawarina a nan shine muci gaba da nisanta kanmu da juna domin tsira da mutuncinmu...” Haule da Lami suka dubi juna bawai don sun gamsu da ita ba... Har suka bar wajen hankulansu ba’a nitse yake ba, yauma kaman kullum Lami aka soma sauk’ewa kafin aka wuce da Hajiya.. Nabila da dawowarta kenan daga makaranta taga Aunty Lami ta sauk’a adaidaita guda da Hajiyar Yaya Hafiz, maganar da sukai da safe itada Marliya ya kuma dawo mata Sabo, wannan matar tabbas akwai abinda take b’oyewa ba abin kayi sharing da Mamy ba ba yarda zatai ba saidaima tace rashin kunyarka ne, amma what so ever she’s hiding saita tono shi da yardar Allah.. As they say no secret remains hidden forever... Cikin sauri ta k’araso murmushi saman fuskarta ganin Aunty Lami d’in zata shige cikin gida.. “Aunty sannu da dawowa...” Tayi maganar fuska fal fari’a abinda bata saba yi mata ba... Aunty Lami ta dubeta da mamaki don koda wasa Nabila bata tab’a mata hakan ba... Murmushin yak’e Aunty Lami tai kana tace “Yauwa Nabila ‘yan makaranta an dawo...” Nabilah ta jinjina kai had’ida amsar jakan hannun Aunty Lami ta rik’e mata suka jera tare suka nufi cikin gida Nabilah na fad’in “Lecture d’aya nayi shiyasa ban fita da wuri ba na kuma dawo da wuri..” Aunty Lami ta jinjina kai tana mamakin yanda Nabilah ta sake tana mata fira, har sashenta Nabilah tai mata rakiya rik’eda jakan Aunty Lami d’in, tai mata tayin abinci tace ta k’oshi, tai mata sallama fuska fal fari’a kana ta fice.. Aunty Lami sai mamakin canzawan Nabilah take lokaci guda.... *** Hankalin Sameer ya gaza kwanciya, sosai yake son tafiya gida sabida d’inbin tambayoyi da yakeson yima iyayenshi, washe gari ya shirya tafiya Kaduna ba tareda ya sanar da kowa ba don koh Siyama bai sanar da ita ba.... Kai tsaye gidansa ya shige don hutawa kafin ya nufi can gidan iyayenshi.. Kai tsaye ya nufi bedroom d’insu ya shiga rage kayan jikinsa donyin wanka, ya k’arasa bedside ya aje agogonsa da ya cire nan yaji k’afarsa ya taka wani abu kaman gidan magani.. Kai dubansa k’asa aiko gidan maganin ya taka... Ya shiga duk’awa a hankali k’irjinsa na tsananin bugu abinka da likita yana fata cikin zuciyarsa Allah yasa ba maganin da yake tunani bane... Wani irin bugu k’irjin Sameer yayi sanda ya d’auki maganin ya shiga juyawa.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *28* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Jiri ne yaji na niman d’ibanshi daga yanda yake durk’ushe, take idanunsa suka kad’a sukai jazir... Cikin wani irin yanayi yake furta “How could you... How could you do this to me Siyama...” Kasa ci gaba da magana yayi sai k’ok’arin mik’ewa da yake cikin sanyin jiki... Ya d’aga idanu yana duban picture d’insu dake ajiye gefen bedside d’in cikin k’aramar frame su duka biyun suna cikin tsananin farin ciki, take yasa hannu ya d’auko hoton had’ida k’ura mata idanun da suka koma jajazir, inama ace abinda yake gani ba gaskiya bane, Siyama itace mace guda da ya tab’a so tsawon rayuwarsa, shin da gaske ita bata sonshi to the point that bata k’aunar had’a jini dashi... Shin mai ya mata da tsanani shin menene laifinsa, shin tsananin soyayyar da yake mata ne laifinsa.... Siririyar hawaye mai tsananin zafi ya gangaro mashi... A hankali ya maida hoton ya ajiye, wankan da bai iya yayi ba kenan yasa kai ya fito daga d’akin, tamkar wanda ruwa ya shanye haka Sameer ke d’aga k’afafunsa,da k’yar ya iya sauk’owa daga staircase yaji jiri na neman kifa shi, zama yayi cikin kujera had’ida k’urama waje guda idanu, fatar jikinsa ta koma jazir haka nan idanunsa, abubuwa da dama ke ziyartar zuciyarsa.... *** Yesmin ba’a sama ba’a k’asa yau dai so ake a birge oga Khalid da alama, gaba d’aya abincin gidan ta d’auki ragama ta hana ma’aikatan saka hannu, Kubura ta cika tayi fam duk wani juyi da Yesmin zatai a kitchen harara kurum take aika mata had’ida tab’e baki musamman idan ta tuna wai duk don a janyo hankalin Khalid d’inta ake wannan abun.. Sai ‘yan wak’e wak’enta take na habaici tana giftawa... Yesmin kaw ko a jikinta sai rawar kai ake ana kiran Mummy tana kuma turo wasu recipes d’in, dama tun safe driver ya kaita tayo shopping d’inta da kanta abubuwan da tasan bazata samu a store ba... Ammi ce ta shigo kitchen d’in ta tadda Yesmin kace kace sai aiki take... Ammi na murmushi take fad’in “A’a lallai yau munada cin delicious babbar chef ce a kitchen d’in namu...” Yesmin ta murmusa cikeda kunya kana tace “I love cooking Ammi...” Ammi ta murmusa kana tace “Toh what’s the occasion, what are we celebrating...?” Nan ma cikeda kunya ta kuma murmusawa kana tace “Ammi I hope Khalid will like it....” Ammi ta d’an matso kusanta had’ida dafata kad’an kana tace “I’m sure he’s going to love it sweetheart... Mamanki ta fad’a min your passion about cooking tun kina k’arama unlike your own cousin Siyama wacce saidai a dafa a bata, I’m sure d’ana yayi dace..” Yesmin ta kuma murmusawa cikeda jin dad’i kana tace “Thank you Ammi..” Suka rungume juna cikeda jin dad’i kafin Ammi ta fice ta bar Yesmin a kitchen tana ci gaba da hidimanta had’ida dad’a zak’ewa... Bayan komai ya kammala Yesmin ta umarci su Kubura su jera komai bisa dining ita kuma ta wuce sama ta tsala wanka had’ida cancad’a kwalliya... Siyama data dawo a gajjiye nan taga ma’aikatan sai kai komo suke suna jeren had’add’un dishes da warmers... K’arasawa tayi ta shige bud’ewa ko wanne tana tab’awa tana lumshe idanu had’ida kad’a kunne don santi.. Yesmin ta fito ta taddata a haka, k’arasowa tai ta d’an tab’a Siyama kana tace “How do I look...?” Tai maganar tana juyi gaban Siyama.. Siyama ta jinjina kai tana had’iye abinda ke bakinta kana tace “Um gorgeous, you look just good... So, is my brother here...?” Yesmin ta d’an murmusa kana tace “Not yet, but I’m sure he’s on his way...” Siyama ta jinjina kai tace “You cook all this...?” Yesmin ta jinjina kai tana juya idanu Siyama ta d’an tab’e baki tana jinjina kai tace “Lallai Khalid is lucky, niko kinga babu abinda na iya when it comes to kitchen, Sameer shikeyin komai... Kinga let me go take shower sai nazo muyima abincin nan cin gaske cos I’m really really starving...” Jinjina kai Yesmin tai kafin taci gaba da kallon kanta cikin k’aton madubi da aka k’awata dining area d’in dashi... Kubura na lab’e tana dubanta ta cika tayi fam, jira kawai take Yesmin ta kauce ta cika aikinta... Suna zazzaune bisa dining d’in saidai basu fara cin abincin ba fira suke kanyi Khalid yayi sallama ya shigo, kallo guda zaka masa ka fahimci a stananin gajjiye yake, kusan komai yanzu sakar masa Daddy yake a company d’in a cewarsa he wants him to grow up, ballanta yanzu da Daddy yake on a business trip komai sakarwa Khalid d’in yake... Ammi ta sakar masa murmushi kana tace “You arrived just on time son.... k’araso” Murmushi ya sakar mata kana ya gaidata bata saki hannunsa ba saida ta zaunar dashi saman kujera tana fad’in “Lets eat son,...” Ammi ta shiga serving d’insa da kanta, Yesmin kaw sai faman sinne kai take musamman da taji Khalid na cewa yunwa dama yakeji amma yaso ya fara yin wanka, Ammi tace a’a shi kawai suke jira sai sunci abinci tukuna... Khalid na kallon yanda Ammi ke serving d’insa yana murmushi yana tuna a lokutan baya idan yana fushi haka Amminsa ke masa abinci kala kala tana lallashin shi, a nashi zaton sabida maganar da sukayi jiya akan Yesmin ne takeson lallashin shi... Siyama tace “Ammi da kin bari wacce ta dafa abincin tai serving d’inshi ai...” Ta k’arashe tana kai spoon baki... Cak Siyama ta tsayada zancen nata sakamakon sugar had’ida yaji da taji sun mata sallama saman harshe a dai dai lokacin da Khalid yakai spoon d’in abinci baki ba tareda ya kula Siyama ba Ammi na ci gaba da fad’in “Your Sister cooked specially for.....”Aya Ammi taiwa kalaman nata jin Khalid ya mik’e a zabure yana tsananin tari had’ida watsar da abincin dake bakinsa... Yesmin ta mik’e a razane tana dubanshi.. Ammi ta mik’e tana masa sannu had’ida rik’e shi...” Yesmin tai saurin tsiyaya drink a cup ta mik’awa Ammi jikinta har rawa yake... Ammi ta mik’a masa bakinsa tana fad’in “Sannu son sha ruwa....” Aiko yana kafa kai yaji barkwanon ya k’aru, ya fuzar yana ci gaba da tari had’ida duk’awa... Ammi ta dubi Yesmin tace “Yesmin mai kika saka a abincin..?” Yesmin da gaba d’aya ta daburce tace “Ammi wllhi ban saka komai ba, Siyama even tasted...” Aya tai wa kalaman nata ganin Siyama ma na tari had’ida fito da harcenta waje tana hurawa... Saurin d’aukan spoon Yesmin tai ta d’ibi abincin takai bakinta, bata iya had’iyewa ba itama ta wuce kitchen a guje ta zubda abincin bakinta tana neman abin shashe baki sabida tsananin barkwano had’ida tsami da zak’i... Kubura dake lab’e sai buga tsalle take tana cin dariya a b’angare guda kuma tausayin Khalid d’inta ya kama ta amma ko babu komai Yesmin tasha disgi kwalliya ta biya kud’in sabulu... Khalid ya d’ago a galabaice yana duban Ammi kana yace “Ammi yaushe Siyama ta iya girkin da za’a bar mata girkin gidan nan tayi...?” Siyama ta d’ago tana dubanshi magana k’unshe a bakinta saidai itama har yanzu barkwanon bai saketa ba, kafin ta samu zarafin magana Kubura tai karaf ta nuna Yesmin da fitowarta kenan daga kitchen taje ta watsar da abincin bakinta kana taci gaba da fad’in “Gata nan... Ga wacce tai girkin gidan yau gaba d’aya kuma musamman sabida kai tayi...” Wani irin kallo kurum Khalid ke aika mata, bai kuma cewa komai ba sai tattara car keys d’insa da folder had’ida wayar salulansa ya fice ya nufi b’angarensa.. Yesmin dake tsaye tamkar ruwa ya shanye take ta fashe da wani irin kuka tana fad’in wllhi wani ne ya b’ata mata abincinta kuma bata zargin kowa sai Kubura... Haba nan fah Kubura ma ta dinga rantse rantse ita ba itabace sharri Yesmin take mata don ta tsaneta... Ammi ta daka masu tsawa sukai shiru kana tace “Yesmin wuce sama, ke kuma Kubura ki wuce ki tattara dining d’in nan idan kin gama ki sameni d’aki...” Daga haka Ammi ficewa tai ta nufi b’angaren Khalid... Yana ganinta ya d’an rausayar da idanunsa had’ida fuzar da iska yasan bazai wuce maganan Yesmin tazo mashi dashi ba... “Ammi not now please...” Ya fad’i cikin kasaltecciyar murya Harara ta wurga mashi tana mai fad’in “Khalid kana jina ka saurareni da kyau, abinda ya faru ba laifin Yesmin bane sannan idanma laifinta ne ya kamata kai appreciating effort d’inta, all she’s doing tanayi ne sabida tana sonka Khalid, babban abin takaicin kai baka ma fahimtar hakan... Khalid wai mai ya shige kanka ne... Haka kakeso mu zuba maka idanu babu aure, mai amfanin zaman naka tinda ka kammala karatu ga aiki da yanzu ka kama ba dama what else bayan aure...Inyi...?” Sauk’e deep breath yayi had’ida zama cikin sofa kana yace “Ammi kin sani fah I don’t like being pressured... Please mana Ammi, how many time do we have to talk about this.... Ammi sau nawa zance banason yarinyar nan... Idanma auren kuke so nayi then ku barni na zab’i wacce nakeso kaman yanda kuka bar Siyama ta zab’a... But please Ammi don’t force me into an arranged marriage.... I don’t like that girl period...” Zama tayi gefenshi kana ta kamo hannayensa tana dubanshi, cikin kwantar da murya tace “Khalid... I only want what is best for you, meye laifin Yesmin, she’s beautiful, intelligent... family d’inta sanannu a garin Abuja gata ‘yar uwarka ce kuma tanada hankali and above all she’s deeply in love with you, Khalid mai kake nema sama da wannan...” Tinda ta fara magana take dubanta kana ya girgiza kai yace “Ammi duk abinda kika lissafo doesn’t matters idan dai har bana sonta... Do not pressure me please Ammi....” Ya k’arashe yana mai lumshe idanu had’ida kishingida cikin kujeran... A kufule ta mik’e tana fad’in “Rayuwarka ce ai sai kayi yanda kaso da ita, amma ka sani bazaka d’aukomin ko wacce irin shirgi kace zaka kawo min ita matsayin sirkaba kaji na fad’a maka....” Daga haka ficewa tayi fuu kaman zata tashi sama... A hankali yake ambaton sunan Allah wani haushin Yesmin da tsanarta na kuma taso masa.... Siyama kam bata kuma bi takan kowa ba saima tattara kayanta da ta shigayi ta had’esu waje guda don tanaso ta maidasu gida ta canzo wasu sets d’in.. Kubura ta ganta na tattara kaya tace “Aunty badai tafiya zakiyi ba...?” Harara Siyama ta galla mata kana tace “Kubura nafah sanki sarai akan Khalid, nasan babu abinda bazakiyi ba, nasan kece kika b’awatawa Yesmin abinci, wllhi ki shiga hankalinki idan ba so kike na sami Khalid na sanar dashi sonshi kike ba...” Kubura tai saurin k’arasowa cikin d’akin had’ida tura k’ofar kana ta risina gaban Siyama tace “Aunty Siyama kimin rai ki barni a haka nake kallon shi inajin dad’i yanzu kika fad’i masa ai saidai ya koreni gidan nan na daina ganinshi gaba d’aya, kofah magana bai tab’a min ba ni har tsoron gaisheshi nake... Ita wancan dai bata dace ba billahillazi Aunty...” Ta k’arashe tana wani gyara rigar jikinta irin itace daidan shi.. Girgiza kai kurum Siyama tai had’ida jan gajeren tsuka tace”Au bata dace dashi ba... Toh wace ta dace dashi ke...?” Kubura ta murmusa had’ida sinne kai tace “Wllhi kuwa Aunty” Dariya Siyama tai don abin dariya ya bata kana tace “Ni dalla banson sakarci zoki fitar min da jakkan nan....” Kubura ta d’auko jakan tana rok’on Siyama kada ta koma gidanta suyi zamansu a nan tinda Dr bai dawo ba... Siyama bata tsaya biye shiriritan Kubura ba ta tada mota ta wuce abinta... Tin daga gate d’in compound d’in nasu taji kaman k’irjinta na bugu bata gama aminta da bugun da k’irjinta keyiba saida ta hangi motarsa a parking space d’insu... Mamaki ya kamata shin yaushe Sameer yazo kuma ko waya bai mata ba, wata zuciya tace k’ilan yayi niyyan surprising d’inki ne.. Murmushi ta d’an saki kana ta janyo trolley d’in ta shige cikin gidan... Hangoshi da tai zaune saman kujera yasa gabanta kuma fad’uwa, gashi dai zaune kurum sannan TV na kashe kuma bawai aiki yake bisa computer ba ko danna wayarsa, a’a zaune kawai yake shi kad’ai, cikin zuciyarta tace this is not like him, koma surprise zai bata da ba’a parlor zata ganshi ba sannan da ace ma yana parlor d’in da yanzu ya taso ya bata hugs, tamkar mai sand’a haka take tafiyar har ta isa ta taddashi yanda ta hangi fatar fuskarsa tayi jajazir haka nan idanunsa da ya k’urasu ma waje guda... This isn’t the Sameer she used to know, yanayi ne da tinda take a rayuwarta bata tab’a ganinsa cikin makamancinta ba... Tai k’arfin halin k’ak’aro murmushi kana ta rungumeshi tana fad’in “Partner wane irin surprise ne wannan, oh I missed you....” Ta k’arashe tana kuma k’ank’ameshi saidai abinda ya bata mamaki shine bai maida mata martanin rungumarta ba saima b’anb’are hannayenta da ya soma daga cikin jikinsa cikin wane irin zafin nama.... Da tsananin mamaki Siyama ta d’ago tana dubansa ga wani irin huci da yakeyi... Murya na rawa tace “Partner what’s all this about... Wai meke faruwa ne...?” Da wasu irin idanu yake dubanta kana yace “Don’t touch me again...!” Kallonsa ta kumayi cikin rashin yarda da abinda take gani hawaye na neman ciko idanunta don duk wani sab’ani da zasu samu bai tab’a mata irin hakan ba, cikin muryar kuka take furta “Sameer wai meke faruwa don Allah...?” Cikin dakakkiyar murya ya kuma ceda ita “How long have you been lying to me...?” Duban idanunsa tai tana iya hango tsananin b’acin rai cikinsu had’ida tashin hankali, take jikinta ya d’auki rawa ta shiga girgiza masa kai tana hawaye, cikin murya irinta mai kuka take furta “I don’t get you Sameer, please what’s happening...?” Cikin karaji ya matso kusa da ita, fuskarsu dab na juna tana iya jiyo tsananin hucin da yake... Da iyaka k’arfinsa ya finciko hannunta ya d’aura mata gidan magani saman tafin hannun nata kana yaci gaba da fad’in “I know you’ve been taking contraceptions Siyama....And you know, I don’t need your damn explanation... The only thing I need to know shine meyasa kika min k’arya, why did you make me believe that you love me.... Why Siyama...?” Kuka take tana girgiza masa kai had’ida furta “Sameer please let me explain...” Cikin tsananin d’aga murya jijiyoyin jikinsa suna tashi yake furta “I told you I don’t need your explanations... Just tell me your reason for making a fool out of me... Tell me Siyama....!!” Ya k’arashe hawaye na gangarowa daga idanunsa guda wanda da gani na tsananin b’acin rai ne... A hankali ta furta “Partner...” Katseta yayi da fad’in “Don’t you dare call me Partner again, just answer the damn question...!!” Kasa furta komai tayi sai kuka da take harda shesshek’a bata tab’a zaton haka abin zai kasance ba.... Jin ta kasa furta komai sai aikin kuka yasa Sameer dake watsa mata mummunar kallo ci gaba da fad’in “I’ve shown you nothing but love.... Wannan shine abinda zaki sakamin dashi, ki hanani ganin gudan jinina, claiming you love me... Idan haka ake soyayya Siyama bana k’aunar irin soyayyar da kike mun, bansan reasons d’inki ba kuma banaso na sani...Amma ki sani ko ba dad’e ko ba jima zanga gudan jinina da yardar Allah...” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai mik’ewa da yayi ya fice daga gidan gaba d’aya... Siyama kaw kwanciya tayi a wajen tana kuka sosai, ganin kuka bazai ficceta ba ya sanyata mik’ewa ta nufi gida a fujajan.. Ammi saida ta razana da ganinta haka.. Cikin tsananin kuka da tashin hankali ta rungume Ammi tana fad’in “Ammi I cant lose him, I love him so much.... Please do something Ammi...” Ammi ta rungumeta sosai cikeda tashin hankali take fad’in “Mai ya sami Sameer d’in... Talk to me Siyama, ina Sameer d’in...” Siyama ta kasa furta komai sai shesshek’an kuka da take, da k’yar ta iya fad’iwa Ammi duk abinda ya faru kana ta k’arada “Ammi ban tab’a ganinshi cikin yanayin fushi irin wannan ba, Ammi ki ceceni kada ya rabu dani...” Ta k’arashe tana jijjiga Ammin... Rungumeta Ammi ta kumayi tana lallashi “Siyama irin abinda nake jiye maki kenan amma shegen taurin kunne irin naki kikak’i ki saurareni, kin gani koh maganin hana d’aukan ciki kawai ya gani yayi fushi dake irin haka, inaga yasan cewa kin cire mashi cikinshi.. Mai kike tunanin zaiyi...?” Cikin kuka Siyama ke fad’in “I don’t wanna think about that Ammi, nidai kawai save my marriage please...” Jinjina kai Ammi tai kana tace “Ki kwantar da hankalinki ki daina kukan haka, karma ki bari Daddynki yaji wannan batu, ni nasan mai zanyi...” Da wad’annan kalamai Ammi ta kwantar da hankalin Siyama har ta d’an samu tayi shiru amma kam ta k’ule a d’aki can k’asar zuciyarta bata daina fargaba da zullumin hukuncin da Sameer ka iya yankewa akanta ba dukda tasan cewa duk tsananin fushi dole ya yafe mata tinda yana sonta... Bayan sallan Magrib Ammi tayi gidansu Sameer da k’orafin cewa Sameer na wulak’anta mata d’iya ko Hajiya Fatahiyyah ta d’au mataki ko ta fasa k’wai ta sanar da Sameer komai... Hajiya Fatahiyya Momyn Sameer ta d’ago idanu a firgice tana duban mahaifiyar Siyama kana tace “Farida kar kimin haka bamuyi haka dake ba......” SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *29* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Ammi ta murmusa kana tace “Idan kaw haka ne ki kirawo d’anki kija masa kunne akan Siyama, bai isa ya wulak’anta min d’iya ba...” Momy ta murmusa kana ta zauna saman kujera tace “Shin ke maiyasa bazakiyi fad’awa d’iyarki ba wacce ko girki batasan tayiwa mijinta, shin Farida bazaki tambayi naki d’iyar ba mai takeyiwa mijinta.... Sanin kanki ne Siyama is a spoilt brat bacin soyayya babu abinda Sameer zaiyi da ita...” Murmushi Ammi tayi kana ta mik’e tsaye tana gyara mayafi tace “Hajiya Fatahiyya this conversation won’t take us anywhere, inaga lokaci yayi da Sameer ya kamata yasan komai, koshi wanene... Sirrin da ya kamata ya sani 30 years back...” Momy ta mik’e a fusace tana fad’in “Ke Farida ki iya bakinki, kijida taki d’iyar amma karki kuskura ki gusarwa d’ana farin cikin dana gina rayuwarsa bisa...” Hajiya Frida ta kuma murmusawa kana tace “Let’s see mai Sameer zaice idan ya fahimci matar da ya d’auketa da tsananin daraja da mahimmacin has been lying to him his whole life.....” Momy na tsananin huci take fad’in “Don’t even try that Farida, wllhi karki kuskura... Sameer is my son...” Daidai lokacin da sukaji an bud’e k’ofa an shigo.... Gaba d’aya suka juya a tare suna dubanshi, idanunsa suna kuma zuban wasu irin ruwa mai tsananin zafi.... Momy da tuni hawaye sun soma k’ok’arin ciko idanunta saurin kauda fuskarta tai daga barin dubansa.... A hankali Sameer yaci gaba da takowa cikin parlorn tamkar wanda ruwa ya shanye haka yake tafiyar.... “Mummy...” Ya kirawo sunanta a hankali cikin wani irin raunanniyar murya... Kasa juyowa ta dubesa tai saima dad’a rintse idanunta da tayi tana mai k’ok’arin saita kanta... Sameer yasa hannu ya share hawayen da suka zubo masa kana ya kuma cewa “Mummy is that true, Mummy please talk to me.... Da gaske ne baku kuka haifeni ba....?” K’ok’arin saita kanta tayi kana ta k’araso ta rik’o hannayensa guda biyu, a hankali take furta “Sameer kada ka yarda da abinda take cewa, we are your real parents, I’m your mother... Bansan meyasa take fad’in haka ba... Shin sab’ani kuka samu da Siyama...?” K’uri ya mata idanunsa babu alamun wasa ya kuma furta “Momy tell me the truth... Ki fad’a mun gaskiya, who my real parents are....” Kamo hannayensa tai suka zauna bisa sofa don already lokacin Ammin Siyama ta fice... “Son look into my eyes, I’m telling you the truth....Sameer kai d’ana ne... Please believe me Son...” Ta k’arashe tana shafa fuskarsa hawaye na k’ok’arin ciko idanunta... A hankali ya rungumeta badon ya yarda da abinda take fad’i masa ba sai don bazai juri ganinta cikin hawaye ba sannan baiso zuciyarsa ta k’aryata masa ita macen da yake tsananin k’auna sama da kowa a duniya, wacce ya girma ya santa a matsayin mahaifiya a gareshi... Jin hawayenta saman kafad’unsa ya kuma karyar masa da zuciya... A hankali yake furta “I believe you Momy please ki daina hawayen nan....” Momy ta d’ago tana dubansa kana tace “Bansan maiyasa Farida tace haka ba Son, kodai sab’ani ka samu da Siyama...?” Shiru yayi tamkar mai tunani kana ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata yace “Momy idan wani baison had’a jini dakai maybe kanada wani bak’in tabo ne... Ki kwanta ki huta you this isn’t good for your blood pressure...” Daga haka mik’ewa yayi jikinsa a sanyaye ya fice yayinda Momy ta bishi da kallo har ya fice daga parlorn tana tunanin mai Sameer yake son fad’i.... Yana ficewa sashensa dake cikin gidan ya nufa yai zaune a parlor yana tunanin rayuwa, a hankali ya lumshe idanunshi had’ida d’aura hab’ar shi saman hannayenshi guda biyu.... Zancen zuci ya shigayi shi kad’ai yana nazari.... What if da gaske su Momy basune iyayenshi ba, what if Ammin Siyama ta sanar da Siyama cewa shid’in maras asaline kar ta bari rabo ya ratsa tsakaninsu sabida bak’in fenti da rayuwarsa ke shafe da ita....? Wasu irin hawaye masu d’umi yaji suna gangaro mashi, shi kad’ai sai tauyin kanshi ne ke taso mashi, ya rasa tunanin meye zaiyi, shin abubuwa da suke kan faruwa dashi a garin Kano zaiyi tunanin warwarewa ko kuwa na nan gida Kaduna...? Baisan da wanne zai fara ba sabida kwanyarsa gaba d’aya ji yayi ta cushe, wani tunani ne ya fad’o masa ya mik’e jiki babu laka ya fad’a bathroom ya d’an watsa ruwa ko zai d’an wartsake, yana fitowa sashen Momy ya nufa yanda ya tadda bata a parlorn da alama ta haura sama hakan sai yafi masa sauk’i, cikin sauri ya k’arasa ma’ajiyan keys na gidan ya zari key d’in sashen Daddy ya fice.... Sauri sauri yake gudanar da al’maran nasa tamkar mai tsoron kada wani ya tadda shi, kai tsaye master bedroom d’in Daddy ya nufa kana ya shige bathroom, ma’ajiyan kayan wanke baki na Daddy ya nufa ya d’auki toothbrush d’in Daddy... Ya jima yana juya toothbrush d’in kafin ya bud’e ‘yar k’aramar jaka ta leda transparent mai d’an zip ya saka toothbrush d’in ciki, sauri sauri ya fito ya kulle sashen ya maida mabud’in ma’ajiyansa... Ko sashen nasa bai koma ba ya nufi motarsa da ‘yar jakar da toothbrush d’in ke ciki ya fice.... Bai zarce ko ina ba sai asibitinsu da a baya yake aiki.... Sameer ya jima zaune cikin mota yana tunanin abinda yake niyyan yi, tuhumar kansa ya shigayi anya yayi dai dai, shin idan yaga abinda zai karyar masa da zuciya fah....? Ya kuma lumshe idanu yana tuna abinda Siyama ta mishi, his heart’s already broken gwara kawai ya k’arasa abinda ya fara, da alama ya jima cikin duhu lokaci yayi da haske zai bayyana cikin rayuwarsa..... Ajiyan zuciya ya sauk’e kana yasa hannu ya tsinko sumar kansa guda ya nad’eta cikin leda kafin ya nufi cikin asibitin.... Kasancewar biyar na yamma ta gauta shiyasa ya tadda ma’aikatan wanda suka gama morning duty nakan tafiya, gaba d’aya sai murnar ganinsa suke, wani matashi ma’aikacin laboratory ne ya tsaya suna gaisawa da Sameer don tuntuni sosai suka saba ya d’auki Dr Sameer tamkar Yaya.... Auwal yace “Dr banjin lab d’in na bud’e wani abu ne kake so...?” Sameer ya mik’o masa ‘yar jakan hannunsa kana yace “Auwal I need a DNA result of this ASAP....” Auwal ya d’anyi shiru kana ya jinjina kai yace “Ok Dr first thing tomorrow morning, the result will be ready in sha Allah....” Sameer ya jinjina kai kana yace “Good... Idan ya zama ready kawai ka kirani zanzo na karb’a...” Auwal ya d’an shafi sumarsa yace “Haba Dr ai location kawai zaka fad’i min na kawo maka...” Sameer ya d’an murmusa kad’an kana yace “Kar ka damu kawai ka kirani zanzo na karb’a... Na gode koh...” Ya k’arashe yana d’an bubbbuga kafad’unsa... Auwal ya jinjina kai kana yace “Alright Dr yanda kace, sai kaji daga gareni....” Daga haka sallama sukai Sameer ya nufi motarsa kira na shigo mashi, ganin Siyama ce mai kiran ya sanyashi saka wayan a silent....Har Auwal ya soma tafiya ya kuma kiran sunansa yace “This is confidential, ko Sultan banso ya sani....” Auwal ya jinjina kai yace “In sha Allah Dr...” Sameer ya kuma jinjina kai kana yayi key wa motarsa.... Bai zarce ko ina ba sai gidansu Sultan don Auwal ya sanar dashi Dr Sultan yau trough out bai shiga asibitin ba.... Wayan Sultan d’in ya shiga kira sanda yayi zaune saman bayan motarsa.... *** “Ammi ya kukai, ina Sameer....?” Siyama ta tambaya tana duban Ammin da gaba d’aya ta zamto wata iri.... “Ammi talk to me dan Allah...” Ta d’an k’ara fad’i tana kamo hannayen Ammin cikeda damuwa... Kallo Ammi ta bita dashi kana tace “Siyama na goyi bayanki d’ari bisa d’ari kada ki tab’a yarda ki d’auki cikin Sameer, ki ci gaba da shan magani kada ki fasa....” Siyama ta bita da kallon mamaki kana tace “But Ammi.... Ba kece mai min fad’an shan magungunan hana d’aukan ciki ba, idan ban mance ba akan na zubda ciki saida kika kwana biyu bakimin magana.... Why the sudden change of mind...?” Hannayenta Ammi ta rik’o kana tace “I’ve my reasons Siyama, sannan ki sani duk wani dalilina don na kareki ne....” Wannan karon da tsananin mamaki Siyama ke duban mahaifiyarta.... “Ammi you making me nervous.... Is there anything I need to know...?” K’uri Ammi ta mata kana ta girgiza kai a hankali tace “No, babu komai.... I just feel like supporting your idea ne as my daughter.... Ki tashi ki tafi gidanki and make sure kinci gaba da shan magani....” Jiki a sanyaye Siyama ta mik’e tana mamakin mahaifiyar tata, toh meyasa ta canza ra’ayinta, mai Momyn Sameer ta fad’i mata....? Still tai tana murza mabud’an motarta a hankali kafin tasa kai ta fice daga gidan bata zarce ko ina ba sai gidansu Aminiyarta Laila.... *** Sultan ya dube shi a karo na biyu kana ya girgiza kai yace “Sameer ko zaka kwana kana fad’a min babu abinda ke damunka... Just tell me please maybe I can help...” Shafe fuskarsa yayi da duka tafukan hannayensa kana yace “Sultan how does it feel ace mutanen da kafi so a rayuwarka sun maka k’arya...?” Sultan ya gyara zama had’ida murmusawa an tab’o yanda ke masa k’aik’ayi... Kafad’ar Sameer ya dafa kana yace “Sameer this life has never been fair, and it will never be... Ka yarda.....?” D’ago rinannun idanunsa yai yana duban Sultan d’in kana ya jinjina kai yace “Yeah na yarda....” “Mai Siyama ta maka...?” Sultan ya jefo masa tambayar kai tsaye, shiru ne na d’an lokaci ya gifta kana ya girgiza kai yace “It’ll be better if we don’t talk about it...” Sultan ya masa k’uri yana nazarinsa, jin jina kai yai kana yace “Is ok if you don’t wanna talk about it... But whenever you feel like, don’t forget that I’m here bro....” Jinjina kai Sameer yai yana mai furta “Na gode abokina...” Sun d’an d’ibi lokaci Sultan ke jansa da fira dukda ba wani amsawa Sameer d’in keyi ba, yamma lis Sameer yayiwa Sultan sallama ya wuce... Tafiyar Sameer da kad’an wayar Sultan ta d’auki ruri, ganin mai kiran ya sanyashi sakin murmushi kana ya d’aga yana mai furta “Kaman nasan update d’in da zaki bani...” Shiru ya d’an biyo baya alamu magana ake daga d’aya b’angaren.... Sultan ya kuma murmusawa kana yace “Saura k’iris burina ya cika, idan kuwa ya cika kada ki manta kinada babban kyauta domin kaw kin taka muhimmiyar rawa...” Ya kuma murmusawa yana mai mik’ewa tsaye had’ida sakala hannu guda cikin aljihu alamun yana sauraren mai magana daga d’aya b’angaren... A hankali yake shafan sajensa kana yace “INDA RAI burina gab yakeda cika...” Ya saki dariya mai ‘yar sauti kafin sukai sallama ya katse wayar.... *** Kano Nabila ta d’aga appointment letter d’in tana kuma duba cikeda murna, baki har kunne take fad’in “Addah Zulfah gaskiya nai miki murna ubangiji yasanya alkhairi ya kuma sa a fara a sa’a...” Zulfah ta murmusa tana duban ‘yar uwar tata cikeda k’auna tace “Ameen Nabyn Mamy, amma ai ba yanzu zan soma zuwa ba sai na gama iddah...” Nabilah ta d’an tab’e fuska tace “Oho dai at least kema zaki tsara rayuwarki yanzu babu tak’urin Yaya Hafiz balle na Hajiya da watsattsun k’annensa...” Murmushin k’arfin hali Zulfah tai ba tareda ta furta komai ba... Nabila ta dubeta a kaikaice tace “Kar kicemin har yanzu tunaninsa da mafarkin komawa gidansa kike..?” Murmushin Zulfah ta sakeyi wanda da gani mai ciwo ne kana tace “Nabilah kenan, Yaya Hafiz bazan tab’a goge shi cikin tarihin rayuwata ba amma ki sani kaman yanda na ambaci tarihi tabbas ya zama tarihin, he’s already in the past, sannan koda ace babu dangantaka na zumuntan jini tsakaninmu aure ya had’a sannan kar ki mance akwai rabo tsakaninmu, Kausar ta kuma had’amu Nabilah... Hafiz Uban d’iyata ce Nabilah, we cannot change that...” D’an rausayar da idanu Nabila tai kana tace “Haka ne amma nidai bazan daina k’irgen sauran kwanakin da suka rage aurensa ya sauk’a gaba d’aya akanki ba, Kausar kuma muddin Raiha na nan banida haufin zata kula da ita fatana dai kar yace zai d’auki d’iyarsa ya damk’a hannun wancan ‘yar tashan matar tasa ba...” Zulfah tai shiru tana sauraren Nabila domin kaw ta tab’o mata yanda ke tsananin ciwo a gareta, duk randa ta tuna Hafiz na iya damk’ar rik’on d’iyarta hannun wata matar... Kaman Nabilah tasan abinda take tunani ta d’an dafata ta shiga calming d’inta, a haka Aunty B ta shigo ta taddasu tana fad’in “Ga k’osai ‘yar la’asar da zafinshi yanzu Tatu ta sauk’e...” Ta k’arashe tana dire masu k’aramar parantin... Aiko nan Nabilah ta dirk’o k’asa ta shiga cin k’osan tana dandalan barkono, Aunty B tace “Kidaici barkonon nan a hankali don zafi ne dashi...”Takai dubanta ga Zulfah tace “D’iyata zakisha kunun ne ta dama kafin ta tafi...” Zulfah ta girgiza kai tace “A’a Aunty zan sha kunun ayan d’azu dai inaga dakwai saura a fridge..” Ai bata gama rufe baki ba Nabilah ta mik’e ta nufi fridge tana fad’in “Su Aunty an iya waraya d’iyarki kawai kika sani, dama akwai kunun aya a gidan shine ko amin tayi toh wllhi rabona ne nasha nayi guzirin sauran..” Aunty B tace “Eh dai so so ne amma son kai yafi, kiji na fad’a miki nafison Zulfah tah..” Zulfah sai dariyansu take itako Nabila sai kwankwad’an kunun ayarta take tana lumshe idanu ko kulasu batai ba... Wayarta dake ringing ne ya d’auki hankalinta, ta nufo handbag d’inta a guje tana lalumen wayar take fad’in “Toh Mamyna na nemana nima, taga yamma tayi....” Aya ta sakawa kalaman nata ganin mai kiranta, tasan ba kowa bane illa bugun zuciyarta, domin kaw ganin bak’uwar lamba d’aukeda had’add’un lambobi yasa taji k’irjinta na bugawa, tasan shi kad’aine zataga kiransa taji hakan dukda bata d’aga wayar ta tabbatar da ko wanene ba.. Balcony ta shige sanda ta k’ara wayar a kunnenta su Aunty B da Zulfah suka bita da kallo ganin yanda kiran ya sanyata canzawa lokaci guda, da alama bataso suji wayan nata... Basu kuma bi takanta ba sukaci gaba da firansu suna cin k’osan... Koda ta d’aga wayar bata iya cewa komai ba, sannan tunda taji shiru daga d’aya b’angaren tasan shine... Tsuka tai zata katse kiran tana mai furta “Sai a kira mutum ayi shiru don rashin abinyi, toh ni inada abinyi...” Khalid ya katseta da fad’in “Don’t think of doing that, no one hangs up on me, wama yace miki ke ake nema, bansan ya akai na kiraki ba amma nasan dama addu’a kike na kiraki d’in, so don’t pretend...” Tamkar yana kallonta haka ta juya idanu kana tace “Allah kiyaye nayi fatan ka kirani ko na jira kiranka, kada ka mance da bakinka kace bakasan yaya akai ka kirani ba so kaine mai d’okin kaji daga gareni...” Tinda ta soma magana yake murmushi yana wasada hannun had’edd’iyar shopping bag d’in dake gefensa yana imagining yanda take murgud’a baki da juya idanu... A hankali cikin kashe murya yace “You haven’t asked about my wound..” A hasale tace “Toh ni ina ruwana da ciwonka, wai dan Allah baka da abinyi ne sai damuna...” “You know what your problem is....?” Shiru tai kurum tana saurarensa sanda yaci gaba da fad’in “You don’t know much about psychological trauma, that’s a serious problem... Ko tun kafin na kuskuri bigeki da mota haka kike...?” Kasa furta komai tai sabida tsaban takaici gashi ta kasa katse wayar mai yake nufi mahaukaciya ya d’auketa ko mai, for the first time da tai masa magana cikin tsananin raunanniyar murya “Idan ka kira ne just to insult me Dan Allah na rok’eka kada ka sake kirana...” Khalid yayi shiru yana saurarenta ba tareda ya furta komai ba... Su duka biyun sunyi shiru, yanajin sanda tai yunk’urin katse wayar... Yai yunk’urin dakatar da ita amma baisan mai zaice ba, hak’uri zai bata ko kuwa, ya ake bada hak’urin shine bai sani ba, tabbas ta d’auki maganarsa da tsananin zafi yana iya gano hakan a muryarta....A hankali ya lumshe idanunsa had’ida fuzar da iska yana kuma bin shopping bag d’in da kallo wanda yasan gobe akwai aiki gabansa muddin ya tunk’areta, kaman ya fasa tafiyar yaji amma b’angare na zuciyarsa tana kwad’aitar masa tafiyar more than ever, a hankali ya shiga d’an buga kansa da hannu yana tunanin maike damunshi gameda al’amarin yarinyar..... Mik’ewa yayi yana nad’e hannayen longs sleeve d’in dake jikinsa kana ya fad’a bathroom don gwara ya fice ball ko zuciyarsa zata samu sauk’i da tunaninta.... Yesmin kaw da shigowarta kenan ta ajiye masa k’aramar plate anyi wrapping da climfilm wani dad’i ne taji ya mamaye zuciyarta hango shopping bag da tai hadd’add’e kalan mata ajiye saman gadonsa, zuciyarta ta shiga raya mata ma ita zai bada, a hankali ta sad’ad’a tana lek’a cikin ‘yar jakan, bata gama sumewa ba saida taga abinda ke ciki, ita kad’ai ta fad’a duniyar imagination tana murna harda ‘yar tsallenta, jin yana yunk’urin fitowa ya sanyata saurin barin d’akin cikeda jin dad’i... Shiko Khalid yana fitowa ya hangi abu aje gefen bedside, ko bai tambaya ba yasan aikinta ne, yarinyar nan ta rainashi har d’akinsa take kawo mishi abinci yayi magana Ammi ta tasa shi gaba da fad’a, amma zai maganinta ta yanda ko hanyar d’akinsa aka kuma nuna mata bazatabi ba... Ya k’arashe yana mai yin k’wafa kafin ya d’auki plate d’in ya fice dashi bai dire ko ina ba sai kitchen a cikin sink, Kubura na lab’e tana ganinshi dad’i kaman ya kasheta.... *** A b’angaren Nabilah kuwa tinda tai wayan nan suka kula da canzawanta, gaba d’aya walwalarta ta d’auke k’arshema ce masu tai tafiya zatai.. Aunty B ta tab’e baki tace “K’ila dai sirkin namu ne ya tab’oki...,” Nabilah ta kuma turo baki gaba tace “Sirki, Sirki fah kikace Aunty... Nidai bani kula kowa kuma banida lokacinsu...” Aunty B tace “Aiko bazamu zuba miki idanu haka nan ba dole ki kawo mana Sirki...” Nabilah ta mik’e ta rataya handbag d’inta tana masu sallama, Zulfah ta mik’e da niyyan yimata rakiya koda bakin gate ne don ta lura akwai abindake damun ‘yar uwar tata tana son tambayarta.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *30* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Agogo Siyama ta kuma dubawa ya nuna k’arfe 10:00pm daidai, ba d’abi’arsa bace kaiwa irin wannan lokaci a waje, ko a baya idan yanada surgery da dare yakan sanar da ita ko ya sanar da sakatariyarsa ta kirata ta fad’a mata... Ko a mafarkinta bata tab’a zaton akwai abinda zatai Sameer yayi irin wannan fushin ba, tinda take dashi duk sab’anin da zasu samu bai tab’a k’in d’aga wayarta ba amma sai gashi yau ta kirashi yafi sau abinda yafi bai d’agawa k’arshema kashe wayar yayi gaba d’aya... Tana nan zaune wajen har gyangyad’i ya soma d’aukarta taji k’aran tab’a k’ofa... Ta mik’e zunbur tana mitsike idanu.... Kallon kirki bata isheshi ba yasa kai ya nufi upstairs.... Siyama tabi bayanshi a guje kana tasha gabanshi sanda yake shirin shiga d’aki... “Partner let’s talk please...” Tai maganar cikin raunanniyar murya... Baice mata komai ba saima k’ura mata idanu da yayi... Gaban Siyama ya fad’i sakamakon hango wani sabon tashin hankali da tai cikin k’wayan idnunsa, muryarsa ta jiyo yana fad’in “Ammi ta sanar dake wani abu gameda rayuwata ne...?” Tambayar ta kuma haifar mata da fad’uwar gaba, kasa furta komai tai sabida tsananin tausayinsa da ya sauk’o mata, tabbas ta lura akwai abinda ake b’oye masa ba’aso ya sani... “Tell me Siyama, Wannan shine dalilin..? Shine dalilin da yasa kika k’yamaci had’a zuri’a dani.... Was that the reason....?” K’walla suka ciko idanun Siyama, cikin rawar murya take furta “Partner believe me wllhi bansan komai ba nima.... Ban sani ba...” Jinjina kai yayi yana murmushi wacce tafi kuka ciwo kana yace “Don’t lie to me again, an jima ana min k’arya ana fooling d’ina... Amma ki sani wannan shine karon k’arshe, Sameer d’in da kike gani tsaye a gabanki ba d’aya yake da wancan Sameer d’in ba who fell in love with you and your lies.... No one, no one would ever fool me again... Sannan ko mai ake rufewa akaina I’d find out...” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige d’akinsa ya bar Siyama tsaye a wajen tana hawaye, ita kanta gaba d’aya ta rasa wasu irin abubuwa ne ke faruwa, duk abinda Sameer ya fad’i gaskiya ne akwai sirrin da ake b’oye masa amma ita kanta bata sani ba gashi yak’i bata chance ta masa bayanin cewa ita kanta batasan mai iyayensu ke rufewa ba.... Jiki a sanyaye ta shige nata d’akin tana tunanin kwana gida guda da Partner ba tareda tayi matashi da k’irjinshi ba.... *** Washe gari sassafe ya fice harta Siyama batasan lokacin da ya fice ba sai tashi tai taga babu motarsa, ta sauk’o k’asa ta hangi dining table d’insu babu komai bisa wanda da a baya ne da yanzu ta tadda breakfast maiji da lafiya, shiryawa tai ta nufi gida don ko office bazata iya zuwa ba... Tana isa gidan ta tadda Kubura da Yesmin na fad’a don Yesmin taga cookies d’in dataiwa Khalid a hannun Kubura tanaci tana lumshe idanu sannan koda ta tambayeta sai cewa tayi Khalid ne ya bata musamman... Ta yanda Yesmin ke shiga bata nan take fita ba Kubura ma tak’i yin shiru sai yafa mata maganganu take... Siyama ta dafe kanta tana fad’in “Waiku dan Allah bazaku tab’a jituwa ba, baku da wani abinyi ne....?” Yesmin tace “Cousin wllhi sai Ammi ta kori yarinyar nan I can’t stand her anymore...” Kubura tai shewa kana tace “Wllhi nida Ammi mutu ka raba, haka kikazo kika taddani a gidan nan kuma haka zaki tafi ki barmu ehe...” A kufule Yesmin tai kanta zata kai mata duka Siyama ta shiga tsakani daidai lokacin da Khalid d’in ya shigo cikin shiri wanda ko ba’ace maka ba fita zaiyi.... Gaba d’aya daga Yesmin d’in har Kuburan suka natsu, sai mugun kallo da suke aikawa junansu... Ko wacce daga cikinsu hangen d’an paper bag d’in dake hannunsa suke... Siyama ta dubesu duka biyu tai dariya kana ta maido da hankalinta ga Khalid dake tambayarta Ammi... Murmusawa tai tana duban ‘yan matan nasa kana tace “Kaga nima zuwana gidan kenan, why not ka tambayi ‘yan gidan...?” Ta k’arashe tana nuna masa su Yesmin da Kubura wacce tuni ta shiga goge table tana satan kallon kyawawan yatsun k’afafunsa dake jere cikin takalmi... Baice komai ba yasa kai ya nufi cikin parlorn Yesmin na gaisheshi kai a sanne... Idan jakan hannunshi ya amsa shima zai amsa, batasan yazo wuya da ita ba, baison shishigi sam a rayuwarsa.... Kubura ta kauda kai gefe tana dariyar mugunta, yayinda Yesmin ta had’iyi bak’in cikinta... Bai k’arasa staircase ba Ammi ta sauk’o tana fad’an tun daga bathroom take jiyo hayaniyan Yesmin da Kubura... Turus tai ganin Khalid yasha ado jampa da hula wanda ba kasafai yake hakan ba... Gaisar da ita yayi, ta amsa kana ta k’arada “Babana sai ina kuma...?” “Kano, inada pending activities acan...” Ya fad’i yana zira wayarsa cikin aljihu... Mamaki ya kama Ammi, wannan yawan zuwa Kano da Khalid keyi anya na lafiya... Shiru ta d’anyi kana tace “Khalid ka fad’amin gaskiya mai kake zuwa yi Kano...?” D’an dubanta yayi kana yace “Ammi yanzu da girmana za’amin wannan tambayar, Ammi aiki ke kaini...” Siyama kuwa tunda taji yace Kano ta soma tunani koma dai Sameer ya koma ne, idan kuwa haka ne tabbas gwara tabi Khalid taje ta samu mijinta don bazata tab’a bari ko wane irin al’amari ne ya rusa masu rayuwar farin ciki da suka taso cikinta ba.... Jinjina kai Ammi tai kana tace “Toh shikenan Allah taimaka, da fatan dai kayi breakfast...?” Yace “Nasha tea dai banson cin solid abu idan zan hau hanya...” Nan ma jinjina kai tai had’ida masa Allah ya kiyaye ya tsare hanya.. Siyama tai saurin cewa zata bishi... Daga Khalid d’in har Ammi kallon mamaki suka bita dashi... Khalid yace “Lafiya dai ko...?” Wani kallo ta aika mashi kana tace “Lafiyar kenan wajen mijina zanje ko laifi ne...” Ammi ta bita da kallo ba tareda tace komai ba don tasan kwanan zancen... Siyama taci gaba da fad’in “Kaga zamu tsaya gida na d’anyi parking...” A d’an kaikaice ya dubeta kana yace “Zaki b’atamin lokaci dai, wllhi 5 minutes zan baki ki shirya duk abinda zaki shirya....” Sosai take son tafiyar shiyasa bata tsaya tanka Khalid ba... Yesmin kaw tanata jira taga ma waye Khalid zai mik’a jakar nan sai gani tai ya fice dashi a hannunsa take zuciyarta ta soma zargin Khalid ba aiki yake zuwa Kano ba tabbas watace ke neman k’wace mata shi a can, idan kuwa hakane wllhi bazata tab’a bari hakan ta kasance ba Khalid nata ne ita kad’ai.... *** Momy zaune saman darduma ta ida sallan walha kenan sai ganin Sameer tai tsaye kanta idanunsa sunyi jazir.... Gabanta ya yanke ya fad’i, aje cazbahan dake hannunta tai kana tace “Sameer lafia...?” Baice komai ba sai dubanta da yake zuciyarsa naci gaba da mashi zafi.... A hankali yake furta “Momy can you please tell me the truth once and for all....” Girgiza kai Momy tai tana dubansa kana tace “Sameer why are you doubting your own mother... Why Sameer...?” Cikin zuban hawaye ya d’ago mata takardan dake hannunsa kana yace “I’ve a DNA result that clearly shows Daddy is not my biological father.....” Wani irin bugu k’irjinta yayi bata tsammanin Sameer zai tsananta binkice irin haka ba, hawaye ne taji suna kwararo mata bata tab’a tsammanin zuwan irin wannan ranar ba ranar da za’ace Sameer d’inta zai fahimci ba ita ta haifeshi ba... Muryarsa ya kuma katseta cikin tsananin rawa sanda yaci gaba da fad’in “Momy why...? Why Momy... Why did you decide to keep it from me..” Cikin kuka take furta “Because the truth will hurt you Son, Sameer bamu tab’a muzguna maka ba ko wani abu makamancin haka, a ko yaushe burinmu shine ka kasance cikin farin ciki, ka shigo rayuwarmu ka haskaka mana a lokacin da duniya ta mana k’unci....” Cikin rawar murya ya furta “But don’t you think I deserve to know who my real parents are... Suna raye ko suna mace, idan suna raye ina suke... Idan sun mutu inaso nasan matsayinku a wajensu...?” Momy ta share hawayen da suka kwararo mata jiki a snyaye ta k’arasa bakin gado ta zauna, tabbas batasan ta yanda zata soma ba, batasan ta yanda zata soma sanar da Sameer ga yanda akayi ya k’are a hannunsu ba, ta tabbata idan ta sanar dashi cewa suma basu san iyayenshi ba hakan sai yafi komai masa ciwo wanda k’uncinshi shine abinda batason gani a rayuwarta... A hankali idanunta naga wani b’angaren ta furta “Sameer ka fita don Allah and kar ka sake zuwa min da zancen nan....” Duban tsananin mamaki yake mata kana ya jinjina kai yace “Alright Momy, zan fita kaman yanda kika ce sabida har abada zaki tabbata uwa a gareni koda ace akwai sirrin da kike b’oyemin, but Momy zanci gaba da bincike har sai na gano su waye sukai sanadiyan zuwata wannan duniyar... I’m sorry idan kalamaina sun maki tsanani... I’m sorry Momy...” Daga haka sa kai yayi ya fice zuciyarsa na kuma raunana.. Gida ya koma kana ya soma shirin komawa Kano, abubuwa da dama su suka cunkushe a zuciyar Sameer, yana buk’atar a masa bayani a warware masa komai dalla dalla, da k’yar ya iya driving da taimakon Allah har ya isa garin Kano, daga Mama har Shamsu sam babu wanda ya gane kansa tinda ya dawo, k’arashe ma kulle kansa yayi a d’aki ya kwanta ko baccin dole wanda baiyiba tun daren shekaran jiya zai d’auke sa... *** Ga tsananin mamakin Siyama suna shigowa garin Kano a toy store taga Khalid ya tsaya, ta juyo tana masa duban mai kuma zasuyi a nan.... Ko takanta baibi ba ya fice ya shiga store d’in, Jim kad’an ya fito da ‘yar jaka a hannunshi.... Back seat ya bud’e ya aje shopping bag d’in kana ya bud’e mazaunansa ya shige... Ta dubesa a kufule tace “Khalid before ka shige sabganka take me to my husband first...” “Kinga you can’t be giving me orders cos I’m not driver...” Ta hararesa had’ida yin k’wafa kana ta juyar da fuskarta ga window dole ta shanye wulak’ancin Khalid tinda motarsa ce kuma shike driving, tasan dama kad’an yake jira akanta yayita rama duk abubuwan da take masa da kafin Daddy ya basa matsayi sosai a company.... Bata kuma tankashi ba duk hira da ya soma k’ok’arin janta dashi, idan ya kalli yanda ta had’e rai saidai ya kauda kai gefe yana murmushin mugunta.... Ganinsu a k’ofar gate d’in babbar jami’ar garin ya kuma sanyata dubansa shek’ek’e kana tace “Khalid wai yawon mai kakeyi dani ne, nace maka ka kaini wajen mijina kafin ka shiga sangan ka haba na gaji da zaman mota...” Idan kujeran da yake bisa ya amsa shima zai amsa... A hasale ta mik’a hannu ta danna horn tana fad’in “Khalid magana fah nake maka...” Ya d’an dubeta a kaikaice yace “Idan kin matsu ki kira mijin naki yazo ya d’aukeki mana...” Ta galla masa harara had’ida yin k’wafa... Su Nabilah suna tafe zasu wuce class da wani lecturer ya masu fixing sai ganin kiranshi tai na shigo mata, fuzar da iska tai kana ta saka wayar a silent... Wata kiran ta kuma shigowa, Yusrah da wata coursemate d’insu Faty da suke tace tare suka dubeta jin sai kiranta ake tak’i d’agawa.. Yusrah tace “Wai bazaki d’aga bane...?” A d’an dak’ile ta dubeta kana tace “Toh kinsan wanene...?” Yusrah ta murmusa tace”Khalid ne...” Nabilah ta d’an rausayar da idanu tace “D’an rainin hankali zakice...” Yusra da Faty suka dara kafin Faty ta tsaya business center karb’an handouts... “Dan Allah ki d’aga...” Yusra ta fad’i tana dubanta... “Na d’aga naji bak’a, kashe wayata ma zanyi...” Murmushi Yusrah tayi kana tace “Kalan taku salon kenan, amma dai da kin d’aga bakisan mai zaice maki ba...” Gajeren tsuka Nabilah tai kana tace “Banson nacinki na tsiya Yussy naji zan d’aga....” A dak’ile ta d’aga wayar ba tareda tace komai ba... Daga d’aya b’angaren yace “Bana kiran waya ya wuce d’aya ki kiyaye next time...” Murmushin takaici tai kana tace “And who cares...” Khalid ya shanye kana yace “Ki k’araso k’asan bishiyar dake gabanku kad’an...” A hasale tace “And who are you to give me orders....?” Murya a dake yace “Zan iya binki har cikin class d’in naku har gaban malamin naku ba wani abu ne idan hakan kika zab’a....” Bai jira cewarta ba ya katse kiran... Sauk’e ajiyan zuciya tai tana duban Yusrah ba tareda tace komai ba, takai dubanta ga location d’in da ya sanar da ita, yana tsaye ya bada baya kansa na k’asa da alama wayarsa yake dannawa.... Huci kurum take tana dubansa ga wani irin yanayi data tsinta kanta ciki bayan hangosa tsaye da tayi... Hannun Yusrah ta fincika suka nufi yanda yake... Yusrah na tambayarta ko tsayuwa bata amsa bataiba taci gaba da fizgan hannunta.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *31* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Yana nan tsaye yanda ta hangesa yana ci gaba da shafa wayarsa, sarai yaji k’arasowarsu amma yayi biris yaci gaba da abinda yake, tsaban haushi Nabila taji kaman ta kwab’e takalmin k’afarta ta jefi k’eyarsa dashi, ita kuwa Yusrah shan jinin jikinta tai had’ida matsawa gefe ta basu waje.... Bud’e bakinta kenan da niyyan magana ya juyo yana dubanta, idanunsu suka had’e waje guda, Nabilah ce ta soma kauda nata fuskar kafin Khalid yai murmushi da gefen bakinsa... “Baki iya sallama bane..?” Ya fad’i yana takowa kad’an zuwa kusanta... A kaikaice ta watsa wani kallo da gefen idanu kana “Meyasa bazaka fice a rayuwata completely ba....?” K’uri ya mata ganin yanzu ta daina masa magana da tsiwa ba kaman farkon had’uwarsu ba.... Gyara tsayuwarsa ya d’anyi gamida hard’e hannayensa ta baya waje guda kana yace “Is that really what you want... You want me out of your life... Kin tabbata daga zuciyarki kike fad’in haka...?” Saurin d’agowa tai tana dubansa jin tambayoyin da ya jero mata lokaci guda.... Ta kasa furta komai saima k’irjinta dake ci gaba da lugude... Khalid ya d’an murmusa ganin yanayinta yanda ya canza lokaci guda, gyaran murya ya d’anyi kana yace “Ina saurarenki....” Murya a raunane tace “Yes abinda nake so kenan, just stay away from me na tsani ganinka....” Ta k’arashe muryarta na sark’ewa... Khalid ya mata k’uri yana maimaita kalmar na tsani ganinka.... Lokaci guda ya jinjina kai kana yace “Alright, if that’s what you want...” Shopping bag d’in dake gefe ya d’auko ya mik’a mata ba tareda yace komai ba... Tabi jakan da kallo cikeda mamaki kana ta d’ago tana dubansa, wannan karon yanayin da bata tab’a ganin k’wayar idanunsa ciki ba ta gani... Jikinta yai wani irin mugun sanyi, a hankali ta shiga girgiza masa kai kana tace banaso bazan karb’a kayi hak’uri....” “I insist please... be nice for once....” Ya k’arashe yanai mata wani irin duba mai cikeda ma’anoni wanda yasa ta kasa daina dubansa, ganin tunaninta na neman gushewa ya sanyata saurin saita kanta ta koma Nabilarta, cikin hayaniya tace dashi “Nace maka banaso ko ana dole ne....!” Dariya ya kusa kufcewa Khalid mai hali da hali bazai canza ba Nabila kenan... Ya d’an gimtse yace “I’m pretty sure zaki so kyautana sabida abinda mata sukafi so ne ciki... Just take it....” Ya k’arashe yana kuma mik’o mata... Murmushi tai wanda za’a kirasa yak’e kai tsaye, kana ta kuma gimtse fuska tace “And who told you ni kuma inason duk abinda mata ke so.... Nace banaso bazan karb’a, if you may excuse me zan koma class...” Ta k’arashe tana d’aura hannu a kunkumi... D’an d’aga gira sama yayi kana yace “Oh really.... I’m also surprised that you don’t wear makeup...” Yai maganar yana tab’e baki... A hasale tace “Are you a fashion credit now....?!!” Surrender yai da hannayensa kana yace “Easy... you don’t need to yell... Besides I’m not saying you’re ugly, all I’m saying is that ya kamata ki amshi kyutana....” Banda mugun kallo bata aika masa komai, da fari ya soma acting kaman wani nice guy lokaci guda ya koma Khalid d’insa dama tasan bazai iya minti guda bai nuna halinsa ba.... A hasale tace dashi “You know, why not take that to your girlfriend... I don’t need it....” Murmushi yai mai bayyan hak’wara for the first time kana yace “I don’t have one...” Yanda yai maganar ya sanyata d’agowa tanai masa duban mamaki, lokaci guda Khalid yaci gaba da fad’in “Although a lot of girls are after me....” Nan ma murmushin yak’e tai kana ta kuma gimtsewa tace “Why not go date one of them and leave me alone... Ka tak’ura ma rayuwata...” “You not sure about that....?” Yayi maganar yana kashe mata idanu had’ida k’ura matasu wanda ya sanyata shiga wani yanayi... Su duka biyu sunyi nisa cikin duban juna dai dai lokacinda Yusra ta k’araso tana fad’iwa Nabilah malaminsu ya shiga aji tuntuni zai iya rufe k’ofa kuma don yanzu Safwan ya kirata... Nabilah tai saurin saita kanta kana tace “Muje Yusrah...” Yusrah dake k’ok’arin gaida Khalid Nabilah na janyeta Khalid ya mik’a mata bag d’in yace na Nabila ne.... Nabilah tai k’ok’arin wafcewa zata aje masa abinshi Yusrah tak’i sake mata, a daidai lokacin Siyama da ta gaji da jiranshi ta k’araso wajen tana mitan ta gaji da jiranshi, hango ‘yanmata guda biyu da tai ya sanyata sakin baki tana kallon ikon Allah, ashe kam ga abinda ke kawo Khalid Kano, ita bama wannan ba duk had’uwar Khalid daji da kansa bata zaci a irin wad’annan yaran zai tsaya ba, chabd’i lallai dole Ammi taji wannan batu, sauri ta k’ara don ta samu ta cimmasu saidai tun ‘yammatan sun wuce don da alama su basuma ganta ba, shiko Khalid baibar wajenba har saida yaga shigewarsu zauren karatu... Siyama ta k’araso wajen da sauri tana raka bayansu da kallon k’ask’anci ta maido da dubanta ga Khalid tana masa duban mamaki kana tace “Wannan shine aikin....?” Mugun kallo ya aika mata kana yace “So, meye naki a ciki...?” Siyama ta murmusa kana tace “The whole Khalid Masanawa ashe a nan zai k’are.... Dama akan wannan ne kake wulak’anta Yesmin...?” Ya kuma danna mata harara had’ida jan garejen tsaki kana ya nufi mota... Siyama tabisa tanaci gaba da maganganu, saidai sam Khalid bai amsata ba saima bada himma am driving da yayi... A haka suka iso unguwar da Sameer yake, ta d’ago tana duban Khalid d’in kaman zatai magana sai kuma ta fasa don tasan kad’an da aikinsa ne ya mata banza, Khalid yaja yai parking a k’ofar gate d’in had’ida yin relax cikin kujera alamun yana jira ta fita.. Ta d’ago da dubeshi a dak’ile kana tace “Miye haka, kaja kayi parking... What does this mean...?” “It means kina iya fita, gidan dake gabanki shine gidan, and kiyi sauri ki fice zan k’arasa masauk’i na huta....” Siyama tai k’wafa had’ida jinjina kai tace “Wllhi Daddy da Ammi sunji batun nan an gama kuma zigasu zanyi a saka bikinka cikin kwanaki....” Ya watso mata mugun kallo a kaikaice kana yace “Kiyi fin haka, ni dan Allah ki fice min a mota...” K’wafa ta kumayi tana watsa mashi mugun kallo kafin ta finciki marfin motar ta fice tana fad’in ya bud’e trunk ta d’auki kayanta..... Mama na parlor tana kallon tashan Discovery family taji bak’uwar sallama daga bakin k’ofa, ta rage muryar tv d’in a hankali kana ta amsa sallamar had’ida bada izinin shigowa..... Tabi matashiyar matar da kallo domin kaw bata shaidata ba, da fari’arta tai mata iso... Siyama ta k’araso ciki murmushi kwance saman fuskarta.... Daga can bakin carpet tai yunk’urin zama Mama tai saurin cewa “A’a dan Allah tashi ki zauna sama, sannu da zuwa...” Siyama tai godiya murmushi saman fuskarta kana ta zauna saman kujeran... Gaisar da Mama tayi cikeda d’a’a, Mama ta amsa mata da sakin fuska ta k’arada “Saidai ban gane daga inane ba...” Nanma murmushi Siyama tai had’ida gyara zaman mayafinta tace “Sunana Siyama, ni ce matar Sameer...” Nan fara’an Mama ya k’aru aka shiga sabon gaisuwa, Mama ta shiga haba haba da ita, da kanta ta tashi ta shiga kawo mata abin tab’awa musamman da taji sauk’anta garin kenan.... Siyama sai jinjina karamcin matar take, Mama ta zauna daga can gefe suna ci gaba da fira yanda a firan ta fahimci Sameer d’in baisan da zuwar Siyamar ba, a nan ne Mama ta d’an sha jinin jikinta... Siyama ta kuma tambayanta Sameer d’in... Mama ta d’an muskuta tace “Eh toh gaskiya inaga tinda ya fita sallar la’asar bai dawo ba, amma bazai wuce yana masallacin ba, anjima kad’an zai dawo...” Siyama ta d’an kauda kai gefe ta yatsina fuska kafin ta juyo tana sakin murmushi, Mama tai mata iso zuwa d’aki don ta huce gajjiya da kyau, itadai Siyama sai yatsine yatsine take tana duban gidan tana ayyanawa a ranta babu laifi dukda dai bai kai nasu kyau da had’uwa ba k’ila zata d’an iya jurewa ta zauna har ta samu ta shawo kan Partner su shirya.... *** A b’angaren su Nabilah kuwa tunda suka shiga aji Yusrah ta k’agu a bud’e jakan suga menene a ciki, Nabilah ta danna mata harara kana tace “Keda kika amso sai kisan yanda zakiyi da jakkar don nikam bazan d’auka ba.. Gwarama kisan yanda zaki samo shi ki bashi abunshi...”Ta k’arashe tana k’ok’arin tattare books d’inta.. Yusrah ta d’an harereta tace “Wllhi sai na bud’e...” Ta k’arashe tana bud’e jakkar... Da tsananin mamaki ta tsaya tana duban abindake ciki, tai saurin tab’a Nabilah tana fad’in “Ke kalli abinda ke ciki...” Nabilah tai pause tana duban Teddy Bear fara k’al mai kyau harda ‘yar crown akanta, dariya ya kusa kufce mata, lallai wannan yama gama rainata, itace zai kawowa abin wasa... Tai k’wafa kana ta finciki Teddy bear d’in hannu Yusrah kafin ta sami zarafin magana taci murya na tashi cikin teddy d’in _I’m sorry_... Suka dubi juna itada Yusrah cikeda mamaki suna kuma duban Teddy d’in... Nabilah ta sake motsa Teddy d’in domin tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyo mata nan kuma sukaji Teddy d’in ya sake fad’in _I love You_ Ai a d’ari ta saki Teddy d’in ya fad’i k’asa ta saki k’ara cikin firgita... ‘Yan aji suka juyo suna dubansu, Yusrah tai saurin d’auko Teddy d’in tana dariya had’ida furta “Lallai nashi salon daban ne wayyo Allah na... Wato dai bazai bud’i baki ya sanar dake ba saidai ya turo d’an aike da sak’o...Gaskiya k’awata na miki murna...” Ta k’arashe tana rungume teddy d’in cikeda nuna farin ciki... Nabilah da gaba d’aya jikinta ya mutu kasa furta komai tayi sai k’urama teddy d’in idanu da tai, can k’asar zuciyarta wani irin annashuwa takeji wanda batasan dalili ba, gaba d’aya sai ta koma wata sukuku da ita haka nan... Koda sukazo tafiya gida Yusrah ta damk’a mata jakan teddy d’inta tana fad’in “Matar Bear ki adanashi da kyau kuma don Allah ki amince ki zama baby bear d’inshi don wllhi kun bala’in dacewa...” Harara Nabilah ta galla mata kana tace “Allah ya sawak’e min, ina zuwa gida zan kirashi yazo ya amshi abunshi ko na jefar...” Yusrah ta dara tana fad’in “Ahab na yaushe k’wayar idanunki sun nuna kin kamu da son bear babe....” Nabilah ta kai mata duka Yusrah ta zille ta shige adaidaita tana dariya tana fad’in idan bear ya kira a gaisheshi... Nabilah ta rakata da harara tana fad’in zasu had’u gobe ne... Tinda ta shiga adaidaita itama kalaman take kan nanatawa cikin zuciyarta _I’m Sorry.... I Love you_ A hankali ta saki murmushin da batasan daga ina ya taso mata ba, har ta isa gida tinani take cikin adaidaitan.... *** Ya jima sosai a masallacin yana lazimi da kai kukansa ga mahaliccinsa situation d’in da yake ciki Allah ya kawo masa mafita... Ya mik’e ya maida Alkur’an ma’ajiyanshi... D’ago idanun da zai ya hangi Abbah daga can gefe wanda shima nashi kukan ya kawo wajen mahallicin shi, Abbah yana d’ago idanu sukai ido hud’u da Sameer wanda ya hangi rama da ya d’anyi... Su duka biyun suka k’urama juna idanu tamkar masu tunanin wani abun.... Sameer yai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ya sakarwa Abbah kana ya nufo yanda yake a zaune.... Saidai yana k’arasowane ya hangi damshin hawaye a idanun Dattijo Abbah.. Jikin Sameer ya kuma yin sanyi sakamakon hango hawaye da yayi cikin idanun Dattijon.... A hankali ya duk’a yayi zama irinta rak’umi a gaban Abbah... SameenaAleeyou📚 [08/02, 13:34] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _...............DA RABO_ *33* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Shamsu bai ida rufe baki ba Siyama ta shigo kanta a k’asa tana satan kallon Sameer wanda ya koma tamkar bai tab’a murmushi ba tsawon rayuwarsa... Shamsu ya mik’e ya basu waje ya fice gaba d’aya ko d’an zolayar data zamar masa d’abi’a bai tsaya yinta ba don ya fahimci abokin nasa da matarsa suna buk’atar ganawa mai mahimmanci... Daga can kujerar gefenshi ta zauna tana mai kuma shan jinin jikinta, a hankali ta furta “Partner...!” Wani duban da yai mata ya sanyata had’iye maganar nata... “What brings you here...? Wait da izininwa ma kika taho har garin nan...? Kodayake bai kamata na tsaya tambayarki batun neman izini ba tinda kinyi abinda yafi wannan.... Ki tashi ki koma yanda kika fito bana buk’atarki a nan...” Tai saurin d’agowa tana dubansa k’irjinta na bugawa da sauri, anya wannan Sameer d’inta ne kokuwa dai canza shi akai.... Ya kuma darara mata tsawa “Nace ki tashi ki koma yanda kika fito...!” Tai saurin zabura k’walla na k’ok’arin ciko idanunta, cikin muryar kuka take furta “Partner wllhi babu yanda zan koma sai ka saurareni, haba Sameer does it has to be like this... Can’t you see I’m suffering.... Sameer just pills ka gani fah... Kuma at least sai ka bani dama nai bayani, meyasa kake punishing soyayyarmu haka... Sameer we both know that we love each other so much, Please mana Partner...” Da tsananin mamaki da takaici ya d’ago yana dubanta kana ya girgiza kai yace “Did you just say love...? Siyama kinsan abinda ake kira so kuwa....?” Yayi maganar yana mata wani irin duba da rinannun idanunsa... A hankali ta sauk’ar da nata idanun k’asa... Sameer ya girgiza kai a hankali kana yaci gaba da fad’in “Da ace kinsan matsayin abinda kike fad’i da baki aikata abinda kika aikata ba.... Mutumin da yake sonka bazai tab’a k’yamatar abinda zai fito daga jikinka ba.... Shiyasa nakeson jin dalilin amincewa aurena da kikayi idan har bakison had’a zuri’a dani....” Tai saurin d’ago idanunta mai zuban hawaye tana dubansa, lokaci guda ta shiga girgiza kai tana furta “Ba haka bane Partner...” “Toh yaya ne..!!?” Ya tambaya cikin d’aga murya da ware idanu wanda daga gani zuciyarsa zafi take masa... Cikin muryar kuka taci gaba da fad’in “Partner I don’t want to share your love with anyone else, I want you to love me, just me and only me... Even your parents don babu yanda na iya ne shiyasa nake tsoron idan ka haifi yara zaka daina sona...” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka wanke mata fuska.... A yayinda Sameer ya mata k’uri yana dubanta.... Siyama ta gangaro daga kujeran da take zaune hawaye naci gaba da kwaranya mata ta durk’usa gabanshi, cikin muryar kuka taci gaba da fad’in “Partner I’m sorry... I really I am... I I I’m only human, and I thought I was doing what’s best for the both of us.... please forgive me.... I didn’t mean to hurt you...” Tuni zuciyarsa ta karaya, sam bai k’aunar yaga mutum na kuka balle ace mace macenma matarshi ta sunnah... A hankali yasa hannuwansa duka biyu ya tallafo Siyama dukda cewa abinda ta masa abu ne mai wuyan yafewa.... Tuni ta shige cikin jikinsa tana sakin wani sabon kuka... Murya can k’asa yake furta “Is ok... Ya isa haka ki daina kuka, abinda ban gane ba shine meyasa zaki aikata such a horrible thing like that... Bakiso ki haihu dani ne... Kina gudun abin kunya ne sabida kar ace uban ‘ya’yanki baida asali... Wannan shine dalilinki...?” D’agowa tai tana dubansa da watery eyes d’inta, lokaci guda ta shiga girgiza kai tana mai furta “What... Asali....? I don’t get you....” Gyara mata zama yayi kana yace “Don’t play a dumb here Siyama, wannan shine dalilinki ba wancan silly excuse d’in da kika bani ba.... C’mon sweetheart, idan har da gaske kina sona don’t lie to me anymore... Please... So tell is there anything you’re not telling me....” Ya k’arashe yana rik’e da ‘yan yatsunta... Saida ta had’iyi wani miyau sanda ta tuna kalaman Ammi cewa taci da shan maganin hana d’aukan ciki kana ta girgiza kai tace “I don’t anything please believe me Partner... Wai meke faruwa ne...?” K’uri ya mata da rinannun idanunsa domin kuwa har k’asan zuciyarsa yakeji akwai abubuwa da Siyama ke b’oye masa tin bayan abinda ya faru tsakaninsu...Cikin wane irin yanayi ya furta “It turns out mutanen da tun tasowata na sansu a matsayin mahaifa na basune suka haifeni ba...” A firgice Siyama ta mik’e zaune daga jikinshi tana dubanshi... Girgiza kai ta shigayi tana furta “But... how... How comes...?” Jinjina mata kai ya kumayi kana yace “Yes, Momy and Dad aren’t my real parents....” Cikeda shock Siyama tace “If they aren’t your parents, then where are your real parents...?” “I don’t know... Ban sani ba nima, bansan ya akai na k’are a hannunsu ba, dukda cewa basu tab’a nunamin wani abu ba basu tab’a muzguna min ba tsawon rayuwata dasu I think I deserve to know who my real parents are... Sannan na cancanci nasan dalilin da yasa na koma hannunsu, shin iyayena mutuwa sukayi kokuwa suna raye, idan har suna raye inaso na gansu na masu tambayoyi da dama idan kuwa sun mutu mai matsayin mutanen da na girma a hannunsu... I’ve a lot of questions....” Hannayensa Siyama ta rik’e fuskarta d’aukeda tsananin damuwa kana tace “I’m sorry Partner, this must be hard for you... Wannan lokaci ne da ya kamata na zamto ina gefenka, kayi hak’uri Partner...” K’ak’aro murmushi yai ya sakar mata kana yace “Now that you know... Shin kinaso kici gaba da zama dani a haka....Zaki iya ci gaba da k’aunata after learning all this...?” Ya mata k’uri yana dubanta... Murmushi ta sakar masa kana ta matso cikin jikinshi ta kwanta.... “I’ll always love and accept you for you are... remember, kaid’in nakeso just you...” A hankali ya jinjina kai gajeren murmushi saman fuskarsa kana yace “Are you sure..?” D’agowa tai tana dubansa kana tace “Wait.. Are you doubting me again...?” K’uri ya mata yana nazarinta kafin ya sakar mata murmushi ya janyota jikinsa ya rungume... Lokaci guda yayima waje guda k’uri yana nazarin abubuwa..... *** Nabila taima wayarta k’uri tana kuma juya Teddy d’in da Khalid ya bata, ita kad’ai take sakin murmushi tana mamakin salonshi, ko ba’a fad’a ba da alama kiranshi take jira.... Marliya ce ta shigo ta taddata a haka... Kallo ta bita dashi tana mamakin mai ya had’ata da teddy... Marliya tai saurin k’arasawa saman gadon had’ida fincikan teddy d’in tana fad’in “Addah Naby ina kika samo wannan...? Dan Allah ki bani....” Nabilah data d’an firgita fauce teddy din tai tana fad’in “Ke da Allah bani nan god’e god’e dake mai zakiyi dashi...” Marliya ta d’an b’ata fuska tace “Toh ke mai yakeyi wajenki...?” Nabilah ta d’an daburce lokaci guda ta shiga inda inda tana furta “Ni.. ni wa yace miki nawa ne na Kausar ne gobe zan kai mata...” Ta k’arashe tana tura Teddy d’in cikin drawer... Marliya dai k’uri ta mata ganin yanda ‘yar uwar tata ta zama nervous all of a sudden, gaba d’aya Nabilah canzawa take a ‘yan kwanakin... D’an gyaran murya tai kana tai mata seda safe ta wuce wajen kwanciyarta.... Nabilah dai kwanciya kawai tai amma zuciyarta fal tunani Khalid ne ciki, ta janyo drawer d’in data jefa teddy din ciki tana duba murmushi kwance saman fuskarta, Marliya dake k’yallare da idanu guda tamkar mai bacci sai karantar ta take... Vibration d’in da wayarta tai ne ta d’an razaneta... Tai saurin zabura k’irjinta na bugawa da sauri, shid’in ne mai kira... Ta lumshe idanunta a hankali had’ida sakin deep breath, saida wayar tai ringing kaman zata yanke sannan Nabilah tai k’arfin halin d’agawa.... Shiru kaman ba mai niyyan magana cikinsu.... Kaman daga sama don har ta cire rai bazai magana ba sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Are you still there....?” Ta rasa mai zatace kaman tai hanging up sai kuma tai k’ok’arin saita kanta don bataso ya fahimci halin da take ciki, da d’an fad’a take furta “Kaga Malam kazo ka amshi kyautarka babu abinda zanyi dashi ko nai maka kama da mai wasan yara ne...?” Ya murmusa a hankali daga yanda yake kishingid’e kana yace “Like right now... Can I come over...?” Juya idanu tai kana tace “Kaga Malam karma kai tunanin zuwa gidanmu don Abbah baya tolerating kowa ya tsaya masa a k’ofar gida...” “Idan ban mance ba gani na biyu da kikamin a gidanku a parlorn Abbah ne, so idan zanzo wajenki ba waje zan tsaya ba saidai a parlor... And I didn’t call to receive goodnight scolds.... And don’t sleep late because you’ve class tomorrow....Take care....” Daga haka katse kiran yai yana sakin murmushi ba tareda ya jira cewarta ba... Tabi wayar da kallo tana mamakin hali irin na Khalid.... Murmushi ta saki ita kad’ai had’ida girgiza kai kana ta aje wayar ta kwanta tana sakin murmushi tana maimaita kalmarsa ta k’arashe cikin zuciyarta.... Marliya dake mak’ale da idanu tana dubanta dad’i ya rufe ta ganin Addar tata is finally giving herself a chance to be in a relationship, ba kaman yanda idan an mata maganan saurayi a baya ba tayita fad’a da masifa kenan tana fad’in ita bazata tab’a yin aure ba don bazata d’auki wani disappointment ba ganin yanda Addarta Zulfa’u tasha wahala gidan aure... Lallai dole Mamy taji wannan batu.... *** Washe gari da rana su biyu suke zaune gaban Malaminsu suna kora masa bayani.... Wata laya ya aje saman k’asa da aka zana da yatsu cikin babban tray, ya aje cazbaha saman layar kana ya dubi Lami da Haule.... Haule da ta gama zak’uwa tace “Malam mai ka gani....?” Jinjina kai Malam yayi kana yace “Tabbas Ma’aruf na raye hasalima yana tsakankaninku kuma yana gab da dawowa cikin danginsa....” Aunty Lami ta shiga sallallami tana furta sun shiga uku sun lalace Aminiyar Sirri ta cucesu datasa suka amince ta kashe Ma’aruf.. Haule ta shiga mintsilinta tana fad’in tai shiru sunzo wajen mai share masu kukansu... Malam yace “Mai kukeso ayi...?” Cikin sauri Haule tace “Malam kafin ya bayyana cikin dangi munaso a gama dashi ma’ana a kasheshi...” Lami ta kalleta a firgice tana girgiza kai kana tace “A’a Malam a kuma badd’ashi a nisantashi da danginshi na har abada....” Malam yace “Naji ra’ayoyinku..... Yanzu abinda za’ai ko wacce a cikinku zata d’au ‘ya’yan calbin guda d’ai d’ai...” *** Hafiz na zube a parlor ya d’an sami baccin rana musamman da ya samu jarabebbiyar matarsa bata nan har wani hamdala saida yayi ya zube saman kujera bacci yai gaba dashi, nan cikin baccin nasa ya soma jiyo kururwa ana ihun b’arawo.... Ya mik’e zunbur ya fice a guje tamkar zararre ya nufi k’ofar gidan.... Cincirindon mutane ya taddata ana jajanta satar Babur da akai, sai lokacin ya tuna ashe a waje ya aje babur d’insa koda ya dawo daga kasuwa.... SameenaAleeyou📚 [09/02, 10:19] +234 703 745 3539: *INDA RAI* _................DA RABO_ *32* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Sam Abbah baiso Sameer ya fahimci halin da yake ciki don haka bai kuma d’ago kai sun had’a idanu ba, idanun nasa naga cazbaha da yake ja a hankali, Sameer ya d’an bud’e murya kad’an ya gaidashi... Abbah ya amsa cikin raunanniyar murya yana mai k’ok’arin had’iye damuwarshi.... Shiru na wasu ‘yan lokuta suka gifta.... Sameer yana son tambayar Dattijon wanda bai nuna komai a gareshi ba sai karamci tun had’uwarsu amma saidai baisan ta yanda zai soma tambayarsa damuwarshi ba, baisan mai zaice ba amma kam har cikin zuciyarsa yakejin zogin ganin bawan Allahn haka cikin damuwa.... Muryar Abban ne ya katse masa tunaninsa sanda yake fad’in “Rayuwa takanzo ma bawa da abubuwa da dama wanda bai tab’a zato ba balle tsammani, rayuwar duniya gaba d’ayanta jarabawace.... Ta fannuka daban daban Allah yakan jarabci bayinsa, idan bawa ya yarda da k’addara kyakkyawa da akasinta tabbas shi yaci ribar rayuwar duniya... Da yawan mutane sukan halaka sakamakon fad’uwa jarabawar da Allah yaso jarabtarsu da ita....” Tunda ya soma magana Sameer ke dubansa yanaji tamkar nasiha yake mashi tamkar ya shiga zuciyarshi yaga halin da yake ciki, Abbah yaci gaba da fad’in “Maiyasa tsawon rayuwata na danganta jarabawar da Ubangijina ya min da cewa laifin matata ne...? Mai yasa na biyewa mahaifiyata muka taru muka d’aurawa baiwar Allah laifi tsawon shekaru talatin....? Maiyasa rayuwata ta sauya tun daga wannan lokacin....?” Hawaye suka soma kwararo mashi sanda yaci gaba da fad’in “Shin da gaske banyi tawakkali da rashin Ma’aruf ba.... Mai yasa na kasa amincewa zuciyata Ma’aruf ya tafi tafiya ta har abada kuma bazai dawo gareni ba....” Babban mutum kaman Abbah ya kifa kanshi yana kuka sosai wanda ya karya zuciyar Sameer matuk’a, tsananin tausayin dattijon ya rufe shi... Kodaji zaka fahimci abubuwan da Abbah ke fad’i sun jima suna damunsa cikin zuciyarsa saidai bai samu wanda zai sharing dashi ba.... A hankali Sameer ya kai hannu ya dafa kafad’an Abbah guda... Abbah ya d’ago k’wayar idanunsu ta had’e waje guda su duka biyu zuban hawaye suke mai tsananin ban tausayi da tab’a zuciya... A hankali Sameer yake furta “Rayuwa haka takanzo mana da abubuwa masu tsananin ban mamaki... amma babu yanda muka iya dole mu amshi wad’annan k’addarori a bisa yanda sukazo mana....” Abbah ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Wad’annan sune k’addarorin da na kasa bud’e ido na gani tuntuni.... Idanuna sun rufe wajen d’aura laifin ga mahaifiyarshi wacce itama na tabbata rayuwarta ya kasance cikin tsananin na tsawon shekarun talatin, maimakon na zamto mai bata k’arfin gwiwa sai na kasance mai cuzguna mata da k’ara mata bak’in ciki, matata wacce nafiso wacce idanuna suka rufe na rasa farin cikina a tattareda ita, farin cikin da muka gina tun farkon had’uwarmu.....” Sameer ya masa k’uri cikeda son jin asalin labarin wad’annan bayin Allah..... D’an gyara zamansa yayi kana yace “Baba don Allah ka sanar dani labarinka.....” Abbah ya d’ago idanu yana duban Sameer wani irin duba mai cikeda shauk’i kana ya shiga girgiza kai lokaci guda yake furta “Labarina ya canza ne shekaru talatin baya...” Lokaci guda kuma yaci gaba da girgiza kai yana furta “A’a Sameer, banso na saka ma raina cewa Ma’aruf na raye, sabida na jirashi tsawon shekaru talatin ko zai dawo amma bai dawo ba....” Sameer da k’irjinsa ke tsananin bugu a hankali ya furta “Baba... Wanene Ma’aruf...?” Abbah yai shiru na wasu dak’ik’ai kana yace “Ma’aruf d’anah ne wanda na rasashi tun yana shekaru uku a duniya....” Gyara zama Sameer ya kumayi kana yace “Mutuwa yayi ko kuwa b’acewa yayi...?” Abbah ya d’ago ya kuma dubansa kana yace “Duka.... Ya b’ace sannan ya mutu....” “Ya akai kasan ya mutu....?” Sameer ya jefo mishi tambayar Murmushin k’arfin hali Abbah yai kana yace “Da ace yana raye da ya dawo garemu... Mun nemeshi a duk yanda ya dace mu sameshi amma bamu sameshi ba... Ma’aruf ya jima da mutuwa....” Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa tsaye saidai jiri ya kusan dawo dashi k’asa... Sameer yai saurin tallafo shi yana fad’in “Sannu Baba, are you alright...? Muje barin kaika gida...” Abbah ya girgiza kai yace “A’a kar ka damu zan iya tafiya....” Girgiza masa kai Sameer ma yayi kana yace “A’a muje na kaika....” Ya k’arashe yana rik’edashi... Murmushi Abbah yayi kana yace “Na gode...” Cikin zuciyarsa yana ayyana farin ciki da iyayen Sameer suke kasancewa ciki samun nagartaccen d’ah tamkar Sameer.... A haka suka fito har haraban masallacin, Sameer ya gyarawa Abbah takalmansa ya saka suna tafe yana tambayar Abbah ko yana shan maganin hawan jininshi da kyau abinka da likita..... A haka suka k’araso gida hannun Sameer rungume da kafad’un Abbah yana taimaka mashi, Aunty Lami dake tacan baya wajen famfo tana tattare wasu kaya a igiyan shanya ta hangi Abbah da wannan matashi wanda ta masa suna da Ma’aruf suna tafe rungumeda juna tamkar asalin d’ah da mahaifi.... K’irjinta yayi wani irin bugawa tamkar an ijiye mata guduma akai, jikinta ya d’auki karkarwa batasan sanda tai watsi da kayan dake hannunta ba, tabisu da kallo har suka b’acewa ganinta.... A fujajan ta koma d’aki ta shiga zagayawa gumi na karyo mata, shikenan ta faru ta k’are, kar dai wad’annan bayin Allah sun fahimci junansu ne....? Kardai hasashensu ya zamto gaskiya ne....? A kullum k’ara kusanci suke da juna, tabbas idan basuyi wani hobb’asa ba sunaji suna gani da gaske Ma’aruf zai dawo cikin rayuwarsu... Lami ta had’i wata miyau mai d’ankaren azaba kana ta shiga neman layin Haule jikinta har wani k’yarma yake sabida tsananin tsoro.... A kusan k’ofan sashen Abbah suka had’u da Marliya zata shige, nan ta tsaya tana gaidasu had’ida shiga damuwa ganin mahaifinta an tallafo shi... A d’an daburce tace “Abbah lafiya... Maike damunka...?” Sameer ne yace “Karki damu ba wani abu bane, da zaran ya kwanta ya sami hutu zai warware...” Abbah ya k’arada “Kiramin mahaifiyarki...” Cikin sauri fuska d’aukeda damuwa Marliya tace “Toh Abbah...” Nan take ta nufi sashen Mamy.. A yanda Mamy ta ganta ta tabbata babu lafiya.... Mamy tai saurin aje ludayin damun fura dake hannunta don tinda Aunty Lami ta bata shawrin ta sassautawa kanta da tunanin cewa Ma’aruf ka iya dawowa take k’ok’arin d’aukar shawarin dukda cewa can k’asar zuciyarta tanajin bazata iya ba domin kaw abune mai matuk’ar wahala... Matsar da langar tai kana tace “Marliya lafiya na ganki haka...?” Marliya ta d’an share k’wallan da suka ciko idanunta tace “Mamy Abbah ne...” Mamy ta mik’e zumbur cikeda tashin hankali take furta “Mai ya sami Abbanki...?” “Mamy Abbah baida lafiya, yana sashen shi... Yace kije...” Marliya bata ida fad’i ba Mamy ta fice a fujajan ta nufi sashen mijinta.... Sameer na k’ok’arin zaunar da Abbah had’ida jingina mashi bayanshi jikin cushion Mamy ta sako kai parlorn..... Take k’irjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri... Ta kasa ci gaba da tafiya ta tsaya cak tana kallon ikon Allah... K’wayan idanunta suka sauya lokaci guda sanda ta tsinci kanta tana mai ci gaba da takawa a hankali har ta isa garesu.... A dai-dai lokacinda Sameer ya d’ago k’wayar idanunsu suka sark’e waje guda.... Wani irin yanayi maras fasaltuwa suka tsinci kawunansu ciki.... Su duka biyu sunaima juna wani irin duba mai cikeda shauk’e, abubuwa da dama suke iya hangowa cikin idanun junansu... Abbah dake daga kishingid’e ya kafesu da idanu yana kallon duban da sukema juna zuciyarsa na harbawa.... Abbah ne ya katse shirun da fad’in “Na gode likita....” Sameer yai saurin dawowa cikin hankalinsa yai k’ok’arin k’ak’aro murmushi yace “Babu komai Baba...” Lokaci guda ya shiga gaisheda matar da bayyanarta gabanshi yai tsananin jefasa cikin wani yanayi maras fasaltuwa.... A b’angaren Mamy ma k’arfin hali tai kana tai k’ok’arin saita kanta ta amsa masa da sakin fuska bata daina mashi wani irin duba mai nuni da wani babban al’amari ba... Abbah ya fahimci halin da Mamy ta tsinci kanta ciki, domin kuwa yanayi ne wanda ya tsinci kanshi ciki a lokacinda ya soma had’uwada Sameer, baiso taci gaba da wahala tana sakama ranta Ma’aruf zai dawo garesu tunda Sameer ya tabbatar mashi yanada nashi iyayen hasalima aiki ya kawo shi nan sannan babu ta yanda za’ai Sameer ya kasance d’ansu Ma’aruf wanda ya jima da b’acewa, watak’ila dai yanayi da kamanni ne yakedashi irinta Ma’aruf d’insu, a halin yanzu bai k’aunar matarshi uwar ‘ya’ayanshi ta kuma kasancewa cikin k’unci, zai k’ok’arin kawar mata da duk wasu k’unci data kasance ciki a baya wannan shine kawai hanyar da zaibi ya mayewa matarsa gurbin tarin bak’in cikin da ya jefata ciki a baya.... Mamy ce ta katse shirun da fad’in “Abbah meke faruwa, Marliya tace min bakada lafiya....” Ta k’arashe tana matsowa kusanshi... Abbah ya sakar mata murmushi mai taushin gaske kana yace “Kar ki d’aga hankalinki Mariya, is a good thing wannan yaro Sameer yana wajen, bugu da k’ari k’wararren likita ne....” Mamy ta jinjina kai fuska fal fari’a tana mai furta “Allah sarki... Sannu bawan Allah...” Sameer ya d’ago ya dubeta fuskarsa d’aukeda murmushi yace “Babu komai Hajiya.... Ammm ni zan wuce, sai a kula da shan maganin BP d’inshi sannan ya rage yawan tunani...” Ya d’an juyo ya dubi Abbah kana yace “Baba a kula...” Abbah ya jinjina kai yace “In sha Allah Sameer... Na gode k’warai...” “A’a Baba ka daina godiya a gareni dan Allah an riga an zama d’aya....” Abbah ya jinjina kai cikeda jin dad’i daga shi har Mamy duban Sameer suke tamkar yaci gaba da zama haka a gabansu suna dubansa suna murmushi.... Ganin da gaske tafiya yakeda niyyanyi yasa Mamy saurin mik’ewa tana fad’in “A’a ka tsaya a kawo maka abinci...” Sameer yace “A’a Mama na gode...” Mamy tabisa da kallo jin ya kiratada Mama... Ta d’an murmusa tace “A’a zakaci wani abu dan Allah... Koda fura ne ka tsaya ka sha yanzu na damata ban jima da had’ata ba...” Take murmushin Sameer ya fad’ad’a ya koma ya zauna yana mai furta “Aiko inason damun fura sosai tun tasowata...” Gaban Mamy ya kuma fad’uwa, jikinta ya kuma yin sanyi tana mai duban Sameer d’in... A hankali ta mik’e ta nufi sashenta jiki a sanyaye ta had’o masa damun fura da kindirmo... Sameer kaw gyara zama sosai saman darduma yana sha yana santi don dama rabonsa da abinci mai k’wari tun daren shekaran jiya.... Abbah da Mamy sukai masa k’uri suna dubansa zukatansu nai masu wani irin dad’i, su duka biyun Ma’aruf suke hanga zaune wajen... Aunty Lami dake lab’e jikin k’ofa zuciyarta sai faman harbawa take musamman da taga yanda wannan matashi ke shan kindirmon, jikinta ya kuma tabbatar mata cewa lallai wannan Ma’aruf ne, dole su b’adda wannan mutumi a doron k’asa kafin ya dawo cikin rayuwarsu dumu dumu... Farin cikin da Mariya ta rasa shekaru talatin baya bazai kuma dawo mata ba... Tai k’wafa a hankali kafin tasa kai ta juya sashenta, sauri sauri ta soma shirin fita.... Nabila da shigowarta kenan ta tadda Aunty Lami a kid’ime na shirin fita... “Aunty fita ne zakiyi...?” Nabila ta tambaya sanda take zama bisa sofa... Aunty Lami da gaba d’aya ba’a hayyacinta take ba tace “Eh..eh a’a dama gidan k’anwata Zubaidah zanje yanzu akamin waya akemin bataji dad’i ba...” Nabila ta tsareta da idanu kana tace “Laa toh Aunty bara naje na fad’iwa Mamy zan maki rakiya...” Aunty Lami tai saurin d’agowa tana dubanta kana tace “A’a Nabilah kiyi zamanki kawai aima ba jimawa zanyi ba...” Nabilah ta murmusa tace “Allah babu komai Aunty bara na d’auko hijab d’ina....” Tasa kai zata fice Aunty Lami da k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi saurin dakatar da Nabilah tai da fad’in “A’a... um aima inaga bazan samu fita yanzu ba don ban sanar da Alhaji ba, ko zuwa gobe idan na sanar mashi sai muje kinji koh....” Ta k’arashe tana kwab’e mayafinta... Nabilah tai mata k’uri tana karantar ta kana ta murmusa tace “Shikenan Aunty yanda kikace....” Lami ta sakar mata murmushi wacce iyakanta fatar baki cikin zuciyarta banda tsinewa Nabilah bata komai domin kaw ta b’ata mata plan d’inta... *** A parlorn sashensu ya tadda Shamsu na kallon tashan ball as usual, shi kad’ai sai sakin murmushi yake zuciyarsa na masa wani irin sanyi.... Shamsu ya bishi da kallo cikeda mamaki sanin cewa k’unsheda tarin damuwa da bak’in ciki ya dawo garin, amma gashi daga d’an fitarshi ya dawo yalwace da fari’a.... Shamsu ya gyara zama had’ida ‘yar gyaran murya yace “Abokina wannan murmushin fah...?” Sameer ya kuma murmusawa yana mai zama cikin kujera ya dubi Shamsu kana yace “You know Friend.... I feel we’re connected somehow... Like something very strong connects us... I don’t know, but deep down inaji wani babban al’amari ya had’amu....” Shamsu gyara zama sosai yana dubansa kana yace “Wa kenan...?” Sameer yace “Alhaji Usman Mailafiya da iyalinsa....” K’uri Shamsu ya mashi kana yace “Wane irin connection kake tunanin zai iya kasancewa tsakaninku besides babu abinda ya had’aka da garin Kano....” Sameer ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana yace “I don’t know how... But I can feel it....” Jinjina kai Shamsu yai yana nazarin abin kana yace “By the way... You’ve a guest... A very special one...” Sameer ya d’an kaikaito yana masa duba mai nuna alamun tambaya “Guest... Wa kenan...?” “Your wife of course...” Take annurin fuskarsa ya d’auke... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *34* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Hafiz ya shiga mutsuka idanunsa da duka hannayensa biyu yana mai kai duba wajen da ya tabbata nan ya aje babur d’insa, lokaci guda yake ci gaba da sauraren muryan mutanen suna fad’in “Wllhi d’an banza ya arce da babur d’in babu irin binshi da gudu da bamuyi ba amma yayi nasaran arcewa da ita... Waima babur d’in waye...?” Hafiz bai iya amsawa ba sai silalewa da yayi a wajen had’ida dafe hannuwa biyu aka yana furta innalillahi, hankalin mutane ya dawo gareshi sukayo kanshi sunai jajanta mashi abinda ya faru... *** Ko wacce ta rik’e ‘ya’yan calbi d’aid’ai a hannunta suna jiran cewar Malam dake faman zanen k’asa yana motsa baki a hankali... Bayan wasu ‘yan lokuta Malam ya amshi cazbahan dake hannayensu dai dai yanda suka rik’e.... Duba ya shiga binsu dashi d’aya bayan d’aya kana yai gyaran murya yace “Abune da kamar wuya....” Suka kalli juna su duka biyun kana suka maida dubansu ga Malam... Hajiya Haule ta gyara zama sosai kana tace “Malam ban fahimceka ba, kaman yaya abune mai kamar wuya, b’atar da Ma’aruf a karo na biyu kake nufi ko kuwa salwantar da rayuwarsa....? Kai mana bayani yanda zamu fahimta...” Ta k’arashe k’irjinta na tsananin bugu... Dubansu yaci gaba dayi kana ya kuma gyaran murya yace “Abinda nake nufi duka biyu abune mai matuk’ar wahala, kasancewar kun riga da kunci galaba shekaru talatin baya zai wuya ku kuma cin galaba akan Ma’aruf, da ace kunyi amfani da damar da kuka samu tuntuni da yanzu kun wuce babin Ma’aruf amma baku kashe shi ba tun wancen lokacin hakan na nunida mai yuwa Allah ya k’addara masa rayuwa mai tsawo nan gaba.... Watak’ila ku kuma tonan asirinku ne yazo shiyasa Ma’aruf ke bibiyan tsakaninku...” Baikai aya ba Haule ta dakatar dashi da fad’in “Kai dalla can rufe man baki, yo har akwai wanda ya isa yaja damu wllhi k’aryarsa tasha k’arya, kai wannan dama da ganinka baza’ai abin arziki dakai ba, ke Lami tashi mu tafi kinji gidan Malamai da bokaye fad’i garesu har yaushe zamu tsaya wannan shashashan yana d’ura mana ruwa a ciki, yanda mukaci galaba kan Mariya shekaru talatin baya haka zamu sakeci....” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye had’ida mak’ale posa d’inta a hammata, bata daina sababi tana zagin bokan nasu ba cewa baisan komai ba... Malamin nasu ya murmusa kana yace “Kuje duk yanda zakuje a fad’in duniya saidai a fad’a maku abu guda domin kaw wannan dalili yasa na sanya ko wacce cikinku d’aukan k’waran cazbaha kuma kun d’auka kun d’auki k’addararku da yatsunku don haka ku k’ara gaba kar bala’inku ta shafeni...” Haba nan fah Haule taci gaba da sababi tana fad’in “K’arya kake mak’aryacin banza da wofi bala’i saidai ta k’are maka kuma k’addararmu ba hannunka take ba hannun Allah take ehe don haka nasara na garemu da izinin Allah...” Malam ya katseta da fad’in “Da ace kinsan k’addarar taku da gaske hannun Allah take da baki b’ata k’afarki tun fari kinzo nan ba, idan baki daina kumfan baki kin fice min a gida ba wllhi saidai ki bar gidan nan da shenyenyyun k’afafu...” Jin haka yasa Aunty Lami saurin janyo Haule dakeci gaba da kumfan baki suka fice a d’ari Lami naci gaba da kwab’arta.... Suna tsaye bakin layin suna neman adaidaita Lami ke ci gaba da fad’in “Kinga Hajiya Haule karma ki d’aurawa Malamin nan laifi, idan akwai wacce zamu d’aurwa laifi bai wuce tsinanniyar matar can ba....” “AMINIYAR SIRRI...!” Haule tace tana sakin huci, lokaci guda taci gaba da fad’in “Yo Makirar Sirri dai... Amma matar nan ta cucemu da har ta bari muka amince da ita....” Aunty Lami tace “Ba abin mu tona mata asiri ba mu tono asirin kanmu...” “Babu batun tone tonen asiri amma sai mun gunsura mata rashin mutunci inkaw ba hakaba ba sunana Haulatu ba....” Ta k’arashe tana mai sakin k’wafa sanda suka sakawa Adaidaita hannu... *** Sawwama dake make gaban motar saurayinta Alhaji Liti sai aikin taunar chewing gum take tana juya idanu mayafi a kafad’a... A d’an yatsine tace dashi Alhajin Shagali a nan bakin layi zaka ajeni zan k’arasa....” Alhaji Liti ya washe baki yana wani kanne idanu da hularsa dake karkace gefen goshi ya kai hannu ya d’an shafi cinyarta yace “Haba sahiba bazaki bari a k’arasa dake ba yanda yau kika farantan rai ya kamata na kaiki har makwancinki da mota basai kin taka k’asa ba....” Ta wani murmusa had’ida juya idanu tana mai gyara zaman rigarta take fad’in “Karka damu aljihuna daka cikamin yafimin komai, kaga idan ka k’arasa dani cikin layin za’a sami matsala....” Ya washe baki cikeda jin dad’i kana yace “Yanzu sai yaushe kinsan dai bazan jure rashinki na tsawon kwanaki ba...” Sawwama ta kuma taune chewing gum tace “Alhaji kenan, kar ka damu idan don wannan ne aljihuna nayin k’asa zakajini...” Alhaji na matsowa kusanta yake furta “Anya kuwa zan iya..?” Ta murmusa tace “Zaka iya Alhaji.. Sai ka jini...” Ta k’arashe tana bud’e marfin motar had’ida d’aukar ledar kaji da ya sai mata... Harda hura masa iska a fuska kafin ta fice, Alhaji ya saki murmushi yana mai washe dargajejjiyar bakinsa cikeda fatan su kuma had’uwa bada jimawa ba... Tana tafe tana kad’a jiki kaman yanda ta saba tana taunar chewing gum, nan ta hangi dandatson mutane sai faman jajantawa mijinta suke, tai saurin k’arasowa tana son jin abindake faruwa, durk’ushe ta tadda Hafiz ya rapka uban tagumi tsananin damuwa kwance saman fuskarsa.... Tana tambayar sababi Hafiz bai iya amsata ba sai duban da ya bita dashi yana mamakin ina ta fito haka, mutanen dake wajen ne suka koro mata bayani had’ida jajanta mata... Halin ko inkula ta nuna kana ta tallafo Hafiz tana fad’in “Yo sai mai zaka sami fin haka Habibi tashi mu shige ga kaji na kawo mana...” Tamkar rak’umi da akala haka Hafiz ya mik’e yabi Sawwama dake rik’eda hannunsa, yana son tambayarta yanda ta fito amma wani mugun shakkanta yake, suka isa parlor tana basa baki sanda take kwab’e mayafinta, k’amshin turaren maza da ya daki hancinsa shi ya sanyashi kuma d’agowa yanai mata wani irin duba, saida turarruka sana’arce don haka yasan k’amshin turare da dama kuma zai iya banbance maka turaren mace da na namiji... Zama gefensa tai ta bud’e k’ullin kajinta ba tareda ta masa tayi ba ta sanayasa gaba tana yagan kaji tana fad’in “Tsautsayi ne Habibi, kawai kaje ka sami Alhaji da batun ya sai maka wata tinda dai kaga kayan wancan shashashar matar taka sun k’are da an d’aga ko gado ne an saida ni na cika maka ka sai sabo...” Ta k’arashe tana gwigwiyan k’ashi da bakinta... Tinda ta soma magana banda binta da kallo baya komai, shi tinda yake bai tab’a ganin d’an Adam mai cin abinci irin Sawwama ba, idan ta aje kwanon abinci a gabanta saita mak’erin kwanon uwa uba ta samu kaza, kaza ko nawa ne zata iya b’addawa, shi da yake namiji quarter d’in abincin da Sawwama ke ci bazai iya ci ba, tinda ya aurota komai na gidan baya yakeyi, gashi yanzu ba wadataccen ciniki yake samu ba, nan da nan kayan abinci ya k’are yanda kasan a rumbu ake zubawa kuma shi gashi ba bashi abincin ake yaci ya k’oshi ba wani jik’on sai ya dangana da gidan Hajiya, kasancewar cinikinsa yaja baya a dole ya shiga saida wasu kayayyakin Zulfah dake rufe d’aki yana wasu hidiman da kud’ad’en ballantana yanda Sawwama ke son kaji ba’a kwana biyu sai an sai kaji kuma ba’a sayan d’aya don d’aya ya kasa mata... Kan ya ankara Sawwama ta d’age ledar kajin dake gabanta ta shiga saki masa gyatsa tana tanne hannaye... Ya d’an kauda kai gefe had’ida yin k’wafa kana yace “Wai ke bakisan abu ya sami mijinki ki kwantar masa da hankali ba saidai ki baje ledar kaji kinaci, haba Sawwama wace irin mata ce ke..?” Ya k’arashe cikin taushesahiyar murya... Tsegege take dubansa kana ta yatsina fuska tace “Toh kuka kakeso na sanyaka gaba inayi ko kuwa don kana cikin damuwa sai akace kar naci abinci... Kaga Hafiz karma mu soma wannan wasar dakai, kai da anzo kusanka sai ka soma jada baya kanajin tsoro kaman wanda za’a yanki naman jikinka toh ya kake so nayi dakai... A’a wllhi kar ka tak’urama rayuwata...” Ta k’arashe tana kad’a masa mazaunai had’ida ficewa ta nufi kitchen don neman abinsha wanda zai kwantar da kajin da ta nad’a... Yai k’wafa had’ida sauk’e ajiyan zuciya kafin ya nufi yanda ta aje mayafinta yana faman shinshinawa don tabbatarwa hancinsa abinda yake jiyowa... Yanajin motsinta alamun tana k’ok’arin shigowa yai saurin aje mayafin ya koma wajen zamansa... Tabisa da kallo a kaikaice kana ta d’auki mayafinta da handbag d’inta ta shige d’aki... Hafiz ya dafe kansa abubuwa da dama k’unshe cikin zuciyarsa.... *** Basmah jikarta d’iyar Baffah Ado ne ke rik’eda hannunta guda zasu tsallake kwalta sun fito gidan bikin jikar k’awarta, sai faman sababi take tana fad’i Basmah ta kula da hanya kar taja a bigesu... Basmah ta d’an b’ata fuska tace “Allah Mamani shiyasa duk yanda zakije babu mai maki rakiya, fisabilillahi wani irin kula ne banayi...?” Mamani ta katseta da fad’in “Ke rufe min baki banason salon rashin kunya da kuka sha a nonon iyayenku mata, iyayenku basuda aiki sai aifo mana mata a zuri’a wanda ba tallafa mana zasuyi ba saidai su cinye mana gara, yo da ace inada jikoki maza ai da ba haka ba nima ‘yar Hajjin nan da duk shekara sai na koma duk azumi kuwa na tafi umarah amma tinda naje sau d’aya ban koma ba, yanzu duba jikan Yayale yanda yayi bajinta a bikin nan ko uban yarinyar baiyi ba... Ke d’iyar Ado ce koh...?” Ta k’arashe tana duban Basmar wacce tazo wuya don takaici, tsaban jikokin basa gabanta bama ta tantance d’iyar waye cikin yarantan ba.. Jin Basmah tai mata banza ya sanyata d’ago ‘yar sandarta zata kwad’a mata tana fad’in “Ke koh ubanki bai isa na masa magana yamin banza ba... Nace ke d’in d’iyar waye...” Cikeda k’unk’uni Basmah tace “Baffah Ado mana autanki Mamani...” Mamani ta yab’e baki tace “Ai kaji gashi shi Adamu gaba d’ayama kaman baizo duniyar a sa’a ba, shi ba k’wakk’waran sana’a ba shi ba haihuwan yara maza wanda zasu taimaka masa a gaba yake ba ga matan nasa yawa agwagi kullum gasar haihuwar nan suke ga ba abinda akeso suke haifowa ba... Oh ni Halimatu...” Basmah data gaza hak’uri tace “Amma ai Mamani ‘ya’ya mata rahama ne baki zuwa islamiyya da kinji falala da yara mata ke k’unshe dashi ba, wllhi kekam inaga ko aji guda bakije ba a islamiyya yanda kasan zamanin jahiliya aka d’aukoki...” Batakai aya ba Mamani ta sauk’e mata sanda a baya tana fad’in “Toh islamiyya babu kalan wanda banyi ba ja’irar yarinya mai halin tsiya na uwarta... Yo wani alfanu zakuyiwa Adamu bayan cinye masa d’an abincin da yake fafutika da kuke...” Batakai aya ba ta hangi Basmah ta tsallake abinta ta barta nan tsaye tana sababin da babu gaira balle dalili... Mamani ta shiga doka salallami tana aikawa Basmah zagi daga tsallake had’ida nunata da sanda, lokaci guda tasa kai zata tsallake k’iris ya rage mai motar dake tafe saman kwalta d’in bai d’agata ba, Allah yaso ba wani tsananin gudu yake ba... Mamani ta d’ago masa hannu biyu sanda yaci birki tana fad’in “Toh bawan Allah naga dai kwalta d’in nan ta gwamnati ce don haka a dakata a barni na shige....” Tana tsallakewa tanai masa gwalo had’ida furta “Oho dai baka kad’eni ba dai jeka dai...” Maimaikon tsohuwar ta basa takaici saima dariya data basa, yaja gefe yai parking ya fito yana gaida Mamani had’ida furta “Sannu Baaba bakidaiji ciwo ba....?” Basmah tabishi da kallo tana tunanin inda ta sanshi nan ta tuna k’ofar gidansu ta tab’a ganinshi tareda Addah Nabilan Baffah Usman..... Mamani tace “Yanda ka gani yaro am babu abinda ya sameni, kyan k’irane dani...” Khalid ya d’an dara kana yace “Gaskiya Baaba na yarda kinada kyaun k’ira, ayi hak’uri dai ba tuk’in ganganci nake ba...” Mamani data fahimci ya mata zubin masu kud’i tace “Ahtoh idan kunga talaka saman kwalta yanda kasan gwamnatin nakune ku kad’ai, yaro yanzu dubi maton da kake tuk’awa saikace ta gwamna da shugaban k’asa... Oh wasu iyayen dai Allah ya amshi addu’arsu sun haifi masu mulki da masu arziki...” Jin zata saki layi yasa Basmah janyota tana fad’in “Mamani muje kar dare ya mana...” “Ke da Allah cikani dacan ba guduna kike ba, saidai ki k’arasa tafiyarki amma nikam saina d’ana wannan maton mai kama data gwamna, yaro zoka bud’emin...” Khalid na murmushi ya bud’e mata ya rik’e mata sandarta ya gyara mata yanda zataji dad’in zama, Basmah dai sai kallon ikon Allah take wato da ace bata gane Mutumin ba ahikenan idanma d’an yanke kai ne Mamani sabida tsabagen kwad’ayi da son abin duniyarta ta shige abinta, girgiza kai Basmah tai had’ida yin k’wafa ta shige ta rik’e Mamani kafin tai masa wani b’aranb’araman a motar, lokaci guda take tunanin yanda Nabilah zata d’au abin... Khalid na tafe Dattijuwar na jansa da hira wanda akasarin hiran nata marassa kangado ne ko ba’ace maka ba kasan tsufa ke d’awainiya da ita.. Bai ida shan mamaki ba saida Basmah ta nuna masa gidan nasu... Ya dubesu yana mamaki zuciyarsa na masa fari k’al don idan har wannan Kakar Nabilah ce tabbas yasan zai samu wajen zama sosai ta wajenta... Mamani sai yaba hankalinsa take yayinda Khalid yaji dad’in ci gaba da janta da fira... K’arahe dai har Basmah ta shige gida takaiwa iyayenta rahoton abindake faruwa, sukakaw yo gangami don ganema idanunsu dama tun kwanakin baya suke kad’a gurmi tsakaninsu cewa wani had’edd’en saurayi ke zuwa wajen Nabilah saidai babu wanda ya isa ya fito fili ya fasa gurmin sanin cewa wacece Nabilah... Nan suka hangesu tafe sun nufi sahen Mamanin da Khalid d’in... Nabilah kaw da dawowarta kenan daga makaranta ta sauk’a a adaidaita ta hangi motar Khalid k’ofar gidansu, mamaki ya isheta musamman data iso wajen taga alamun babu kowa cikin motar.. Gabanta na dukan tara tara ta nufi cikin gida.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *35* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Tinda ta shigo gida ta kasa zaune ta kasa tsaye, yanda take tunanin zataga Khalid bata ganshi ba, toh kodai ba motarsa bace... No she can’t be mistaken tabbas motarsa ce, toh ina yake...? Kodai aje motar kawai yai k’ofar gidansu...? Amma mai zai kawo motar tasa k’ofar gidan nasu...? Ita kad’ai sai sak’e sak’e take, ta sak’a wannan ta warware wancan, Marliya dake zaune gaban socket tana gugan kaya hankalce take da ‘yar uwar tata, a ‘yan kwanakin sosai ta fahimci canzawa da Nabilah tai, wasu lokutan ko magana kake mata bata amsawa sai ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, balle daren jiya yanda taji tana waya ta tabbata da wani take wayar... Nabilah ta kuma mik’ewa zata fice a karo na kusan hud’u... Marliya ta katseta da fad’in “Wai ina kike zuwa ne... Lafiya kuwa...?” D’an dubanta Nabilah tai a yatsine kana tace “Toh uwar sa ido kitchen zani wajen Mamy, koda magana ne... Uwata...?” K’unshe dariyarta Marliya tai kana tace “A’a Allah baki hak’uri...” Nabilah tai gajeren tsuka kana ta fice... Saida ta kuma sad’ad’awa ta lek’a sashen Abbah kaman wata munafuka kafin ta dawo kitchen ta tadda Mamy tuni ta ida abincin dare ta zuzzuba... Gaisar da Mamy ta somayi tana tayata jere abincin.... Mamy da tun ganin Sameer take fama da tinane tinane sama sama ta amsa Nabilar kana ta umarceta ta d’au abincin Mamani takai, Nabilah a duniyarta ta tsani a aiketa sashen Mamani, gaisuwa ma don dole ke kaita tasan saura sarai idan ta tsallake kwana guda bataje ta gaidata ba d’aid’aya Mamy zata mata... Babu halin ta doje taje ga Marliya a parlor na zaune bataga fuskan hakan ba balle ma ko a mafarki bata isa ta fad’iwa mahaifiyar tata haka ba... D’aukan abincin tai ta fice yanda taci karo da Marliya a hanya ta ida gugan zata nufo kitchen wajen Mamy kafin Mamy tai mata tatas daga ita har gugan nata tace wasanta ta zaunayi tana ganinta a kitchen donma itace ba Nabilah ba datasaba shan mitan Mamy wanda gwara ai maka duka a cewar Nabilah... Tareta Nabilah tai da fad’in “Ke Leeya wai bakiga bak’o ya shigo gidan nan ba....?” Marliya ta dubeta da mamaki kana ta girgiza kai tace bak’o kuma...?” Nabilah ta jinjina kai tace “Eh mana Abbah baiyi bak’o ba...?” Marliya ta d’anyi shiru tamkar mai tunani kana ta girgiza kai tace “Gaskiya ni banga wani bak’o ba hasalima Abbah bai dawo ba ko kinga motarsa a gareji ne...?” Nabilah ta d’an tab’e baki tace “Yo ina na lura, kinga zo kishige kafin Mamy ta lek’o...” Aiko bata kai aya ba Mamyn ta lek’o tana fad’in “Wai ba aikanki akai ba Nabilah... Ke kuma kin tsaya biyeta naki aikan na jiranki.... Tsayuwar mai kuke ne..?” Ko wacce tai hanyarta suna baiwa Mamy hak’uri, Marliya ta rab’a ta gefenta ta shige tana tunanin yau d’ain kaman wani abin na damun Mamy... Tana tafe tana tunanin mai ya kawo motarsa k’ofar gidansu, kaman daga sama ta hangesa da Mamani biyedashi da alama ya fito tafiya ne... K’iris ya rage Nabilah bata kifar da abincin ba, wannan wane irin mutum ne... Yau Abbanta gobe Kakarta... Shin miye tsakanin Khalid da mutanen gidan.... K’irjinta yaci gaba da wani irin bugu.... Tai saurin sa kai zata juya saidai tuni Khalid ya hangota... Bud’e murya yai kafin ta fice a k’ofar Mamanin yace “Aah k’araso mana aima tafiya zanyi....” Maganar da yayi ya sanya Mamani dake faman masa zuba kai dubanta ga k’ofar... Nabilah ta tsaya cak ta kasa ci gaba da tafiya, tamkar ta zunduma a guje haka taji gashi ta kasa juyowa... Mamani kaw ganin yarinyar da ake magana da ita tak’i juyowa ya sanyata yab’e baki tace “Ke wacece tsaye wajen nan ko bakijin magana ne...?” Nan ma Nabilah bata juyo ba sai rintse idanunta da tai da k’arfin gaske... Mamani ta nufeta cikin dogara sandarta tana fad’in “Ai wato ina fad’a maka Haladu sam yaran gidan nan basajin magana, gado sukai wajen iyayensu mata...” Jin zata saki layi ya sanya Nabilah saurin juyowa tana aika mata mugun kallo baki a cune, fuska babu alamun walwala tace “Aini aika na kawo kuma bansan kinada bak’o ba...” Tasa kai abinta zata shige d’akin dukda cewa Khalid tsaye yake wajen, da k’yar ta wuce gabansa musamman data tuna ko mayafi babu jikinta... Mamani ta dawo da baya tana fad’in “Kaga rashin kunyar tasu koh... Toh wannan ina fad’i maka itace babbarsu a rashin ta ido, batada kunya ina fad’a maka babban abin takaicinma wai sunana gareta...” Khalid kaw banda murmushi yana satan kallon Nabilah data had’e gabas da yamma baya komai, Mamani tace dashi shigo ai kaci abinci, baka bar gidan nan ba sai kaci abinci Yaron arziki Haladu....” Wato har cikin ransa yakejin banbarak’wai d’in nan idan ta kirasa Haladu shi bai tab’a sanin mai suna Khalid ake fad’iwa hakan ba sai a baki Mamani... Ya d’an shafi kansa kad’an yace “Baaba ba Haladu ba Khalid sunan...” Mamani ta dubesa tsegege kana tace “Kajimin dai, wayace maka ba sunan kenan ba, ai asalin sunan kenan Haladu mu haka muka sani, kuma ka kirani Mamani don haka kowa ke kirana kaji koh shige muje...” Ta k’arashe tana turo shi ciki ta dawo dashi parlorn, sosai sukaso baiwa Nabilah dariya ganin draman Khalid kesha shida Mamani... Batabi takansu ba ta mik’e zata fice Khalid ya bita da kallo yanda tai tamkar bata tab’a saninsa ba ko gaisuwar fatar baki bata masa ba... Mamani ta tsareta da fad’in “Ke ke dakata shige ki kawo masa faranti da cokali yaci abinci... Kuma ki kawo na ‘yan gayu don kin gansa sarai d’an gaye ne...” Nabilah ta dubeta a kufule kana takai dubanta ga Khalid wanda fuskarsa kega wayar salulansa, tana jira taji yace bazaici ba ta sami excuse d’in tafiya amma da yake d’an duniya ne shiru yai alamun zaicin kenan... Mamani ta katseta da fad’in “Zaki wuce ne kokuwa....?” K’wafa tai a hankali kana tasa kai ta shige kitchen d’in Mamanin da ba girki ake ciki ba kawai dai kayan amfani ne ciki... Plate da spoon ta d’auko ta d’auraye had’ida serving spoon ta ijiye saman tray ta dawo fuska a d’aure ta dangwala kusada k’afafunsa.... “Kaga rashin hankalin nata koh, toh k’one masa k’afafu su zama bak’ak’e tinda naki bak’i ne....” Nabilah datazo wuya hak’urinta ya gaza tace “Aidai wajenki na samo bak’in k’afar tinda na Mamy na fari ne tass....” Tai maganar tana murgud’a baki.... “Kaji koh.. Kaji rashin kunyar tata, ai Manu ya rasa d’ah tinda ya Ma’aruf sauran kam duk gayyan yuyuyu ne... Zuba mashi abincin...” Ta k’arashe tana gwagwiyan goro lokaci guda ta mik’e ta nufi d’aki kaman mai neman wani abin... Nabilah tai k’wafa kana ta bud’e flask d’in, tuwon shinkafa ce fara sol d’auri d’auri a leda, leda guda ta d’auka ta kwance ta saka cikin plate d’in zata kuma d’auko wata ledar yace da ita “Ya isa haka idan kuma ba tayani ci zakiyi ba...” Takai masa mugun kallo had’ida d’auke idanu tana mai gyara zaman rigarta duk gaba d’aya a tsarge take ga Mamani ta gama yarfata... Gaba d’aya a tak’ure take, ta soma k’ok’arin mik’a hannu zata janyo d’aya flask d’in yai saurin mik’a hannunsa ya tura mata kusanta, ba tareda dubeshi ba ta shiga kiciniyar bud’ewa... Khalid ya mik’o hannu zai bud’e tai saurin janye hannunta... K’uri ya mata yanda tai tsananin b’ata fuska, ya tab’e baki alamun ko inkula kana yace da ita “Na fasa taimakon ki bud’e da kanki kafin na kira Mamani nace mata rowa kike min...” Ta kalle shi a kufule kana ta janye idanunta tana tab’a marfin taji ya bud’u alamun ya bud’e kenan.... Lafiyayyar miyar taushe ne wanda yaji bushesshen kifi da naman Sa... K’amshin ya daki hancin Khalid sanda taci gaba da serving d’insa bawai don ranta naso ba... Tana gama serving d’insa ta soma k’ok’arin mik’ewa amma saiji tai ta kasa tashi sabida kallon da yake binta dashi, tai k’wafa cikin zuciyarta don ko magana ta kasa masa... Khalid ya janyo plate d’in kaman zai soma cin abincin, itakoh sai satan kallonsa take ganin kaman hankalinsa ya koma kan plate ya sanyata mik’ewa a hankali, daidai sanda Mamani ta fito hannunta rik’eda takardan foster Clark... “Ungo jeki had’o masa abin sha, kya bashi abinci haka babu ruwan zak’i ce maki akai shi ya saba cin abinci haka ne babu ruwan zak’i...?” “Mamani fah baice maki zaisha ba don Allah ki k’yaleni na tafi aiki fah nake...” Tai maganar kaman zata runtuma kuka... Shiko Khalid yana cin tuwon yana satan kallonsu ko tofawa baiyi ba... “Aiki a’a kecema agogo, nace kece ma agogo... Shige ki had’o masa aikin naki ya jiraki...” Nabilah ta gallawa Khalid da ya maida hankalinsa kan abincin da yakeci harara tai k’wafa a hankali... “Mamani da gaske baisha ki tambayeshi kiji....” “Ke banson rashin kunyar banza a ina yace miki bayasha... Kai Haladu wai bakasha abin zak’in d’akin tsohuwa ba...?” Khalid da bawai yama fahimci meye abinda ake shirin bashin ba amma duk dai salon kada Nabilah ta tafi yace “Idan an bani zansha Mamani....” “Toh kaji d’an gari.... Maza shige ki had’a masa d’auki k’ank’ara a firiji (Fridge)...” Mamani ta fad’i tana zama kujeran data tashi... Kaman zatai kuka haka ta shige kitchen, Hajiya Mamani taci gaba dajan Khalid da hira, idan tace Haladu shiko sai ya gyara mata yace Khalid ne, k’arashe ya fahimci Mamani ba daina ce masa Haladu zatai ba, sosai yaci abinci saida yaji mamakin kansa shida ba gwanin son tuwo ba amma tass ya cinye wanda Nabilah ta zuba masa... Nabilah ta shigo d’aukeda k’aramar tray da jug had’ida cup bisa, wannan karon ta warware d’ankwalin kanta ta d’an rufe jikinta dashike yanada d’an girma... Ta dire tray d’in gabansa, zata tashi Mamani ta kuma umartanta cewa ta zuba masa... Badon taso ba ta d’au cup d’in ta shiga tsiyaya lemun, citta ta samu a kitchen d’in ta d’an markad’a ta tace ta had’e da lemon tsami kad’an sai d’an fosterclarck d’in data zuba kad’an sai sugar nan koh ya bada flavor mai dad’i tamkar lemonade... Salon kar Mamani ta barta ta tafi yace ya gama cin abincin da an tattare wajen... Nanma Mamani ta umarci Nabilah data tattare wajen.... Nabilah data cika fam k’iris ya rage bata fashe ba ta d’ago tana watsa masa mugun kallo kaman zatai kuka... Murmushi ya sakar mata a hankali had’ida kashe mata idanu guda yana mai ci gaba da sipping drink d’insa... Fuuu ta wuce da kwanukan kaman zata tashi sama... Mamani tace “Maza ki fasa kwanukan na uwarkice babu asarana ciki ehe...” Ko amsata Nabilah batai ba ta shige abinta, ai komawa sashen Mamani da bata iyayiba kenan, ko kitchen wajen Mamy bata biya ba ta fad’a d’aki tana maida numfashi... Kaman wacce aka zabura tai saurin k’arasawa drawer d’in data aje teddy bear d’in da bata ta ciro tana duba... “Who are you... Maiyasa kake bibiyan kowa a family na... Mai kake nema....?” Tamkar mai magana da mutum haka take maganar... Ta jima tana duban Teddy d’in tamkar mai jiran amsa daga gareshi saiji tai wayarta na faman ruri... Ta d’an firgita kana ta aje teddy d’in zata nufi wayar nan teddy d’in wanda idan yai babban motsi ke fad’in wasu kalmomi ya kuma fad’i mata kalaman _I love you_ Kallo tabi teddy d’in dashi kana ta nufi wayarta dake k’aran alamun shigowar sak’o... Ta rausayar da idanu had’ida fuzar da iska kana ta d’aga wayar tana k’ok’arin karance sak’on... _I’m waiting for you outside.._ Saida ta karance kusan sau uku kafin ta zauna saman gado tana tunanin martanin da zata maida masa bayan haushin da suka k’unsa mata shida Mamani... _Mantuwa kai ko abincin ne bai isheka ba_ Ta rubuta ta tura masa.. Murmushi Khalid yai kana ya shiga tura mata reply kaman haka _Idan baki fito ba zan shigo har yanda kike na sameki kinsan zan iya... So you’ve 2minutes to decide, is either ki fito ko na shigo na sameki... Just 2 minutes.._ Rausayar da idanu tai kana takaima teddy d’in harara tace “Bazan fita ba saidai kai duk abinda kaga dama...” Marliya dake tsaye bakin k’ofa tsoro da mamaki suka kamata ganin Nabilah ta saka teddy gaba tana tsigalesa... “Addah Naby lafia..?” Marliya ta tambaya tana dubanta... Nabila ta d’an shafi goshinta tace “Lafiya mana mai kika gani...” Marliya ta k’arashe shigowa d’akin kana tace “Yo niko naga komai, kin saka gunki gaba kina masa masifa, waima ba cewa kikai ma Kausar zaki kai ba.. Addah Naby anya lafiya kike...? Marliya ta k’arashe tsoro kwance saman fuskarta.. Janyo hannunta Nabilah tai sanda wayarta ta d’auki ruri kana tace “I’ll explain to you later, bani hijab d’inki kiga na fita yanzu zan dawo, karma Mamy ta sani dan Allah...” Ta k’arashe tana kwab’e hijab d’in daka kan Marliya ta zira ta fice cikin sauri... Marliya ta bita da kallon mamaki tafito parlor a sanyaye.... A b’angaren Mamani kuwa sai k’irga kud’ad’en da Khalid ya bata take tana zirawa k’ark’ashin kwalla tana shimai albarka yanda kasan bata tab’a ganin tsaban kud’i ba ko sallama taji anayi zata tura k’ofa da sandarta sannan ta zaune akai kafin ta amsa sallamar... *** Jingine jikin motarsa ta taddashi ya bada baya waya manne kunnensa na hagu abinka da lefty..... Tai tsaye tana k’arema kwantattun sumarsa da a kullum cikin shek’i suke kallo, yanda ya bada bayan nan tamkar ta suri dutse ta runtuma ma k’eyarsa haka taji, tayi tsaye tana tunanin Khalid ya juyo yana dubanta, kaman wanda akacemasa juyo... Kallo guda ya mata ya d’auke kansa yana ci gaba da amsa wayarsa, wani takaicin ya kuma lullub’e Nabilah, tasa kai zata juya cikin gida sabida tsananin takaici saijiyo muryarsa tai yana fad’in “Ina zaki...?” Ta tsaya cak ba tareda ta juyo ba.. Badon Teddy d’insa dake duk’unk’une cikin hijab d’inta ba da tuni ta juya cikin gida hasalima da ko fitowa bazatai ba kawai dai don tana son maida mashi kayanshi ne... A hankali ta juyo ta taddashi yanda yake tsaye.... Khalid ya murmusa a hankali had’ida zira hannaye cikin aljihu ganin yanda Nabilah tasha mur... “Thanks for the food... it was delicious...” Ya fad’i idnunsa akanta.... Tinda ya soma magana idanunta ke k’asa tana duban k’fafunsa da Mamani ta zage mata nata k’afafun akansu, ta kuma duban nata k’afafun sai taji kaman yanzu Mamani ke zage mata nata k’afafun tai saurin maida yatsun k’afafunta cikin takalami, hankalin Khalid ya karkata kan abinda take duba yatsun k’afafunsa... Murmushi ya kusa kufce masa, lokaci guda yake furta “Sun maki kyau ne..?” Tai Saurin d’agowa a d’an razane tamkar wacce aka mintsila, lokaci guda ta had’e fuska tace “Allah ya sawak’e...” Khalid ya murmusa a hankali kana ya tab’e baki yana mai furta “You know there’re some certain things that we can’t simply hide...” D’agowa tai had’ida d’an masa wani duba “And there’re some certain people that we can’t simply stand them...” “Are you sure about that...?” Ya tambaya cikin kashe murya.... Bata kuma tsayuwa basa amsa ba ta mik’a masa teddy d’insa tana fad’in “Ga abinka nan banso, just stop stalking me please..” Khalid ya shiga kad’a d’an makulin hannunsa yana dubanta murmushi kwance saman fuskarsa.... Tai tsaye tana jiran taji ya amsa abinsa dashike kauda kanta gefe tai... Bata ankara ba sai k’aran tashin motarsa ta jiyo kafin tai wani aune ya bad’eta da k’ura ya bar wajen.... Tai saurin matsawa baya don kar ya had’eda ita baki sake tabi bayan motar tasa da kallo zuciyarta na k’una, amma wannan shi a sahun rainin hankalinma ajin k’arshe yake, kaman ta fashe da kuka haka ta shak’e wuyan teddy d’in ta nufi cikin gida ga ‘yansa idon unguwar zaune benci benci bakin kantina... Hango Aunty Lami da tai ta sauk’a a adaidaita kuma wannan karon ma Hajiyar Ya Hafiz na cikin keken ya sanyata d’an lab’ewa cikin sauri ta lalumi wayarta ta shiga neman layin Aunty B da shike ta sanar da Aunty B d’in komai gameda zarginda takewa Aunty Lami kuma Aunty B tace she should keep her updated gameda komai don tasha alwashin tayata zak’ulo gaskiyar al’amari, idan har da gaske su Lami su suka sanadiyan gushewar farin cikin ‘yar uwarta sai yanda k’arfinta ya k’are wajen d’aukan fansa ga ‘yar uwarta.... *** Sameer ya kuma dubanta da mamaki kana yace “Are you serious zaki baro aikinki a Kaduna ki dawo ki zauna dani a nan...?” Siyama ta kuma janyo hannunsa guda ta shige ciki tana mai furta “Of course Partner, na amince zan biyo aurena na kula da kai...” Sameer ya tura yatsun hannunshi guda cikin nata yayinda ya mata matashi da b’angaren kafad’arsa guda kana yace “Baki tunanin Uncle bazaiso hakan ba...?” D’an dubansa tai kana tace “Kaman ka mance Daddy duk abinda nakeso shi yake so, that won’t be an issue besides nayi serving company d’inshi na tsawon shekaru ya kamata yanzu kuma nabi mijina duk yanda zaije, I can’t afford to lose you Partner...” Ta k’arashe murya cikeda shagwab’a... Har cikin zuciyarsa yake mamakin canzawa da Siyama tai lokaci guda, wata b’angare na zuciyarshi kuwa najin dad’in canzawan da tai dukda cewa har yanzu yanaji kwance k’asar zuciyarsa kaman akwai abinda take b’oye masa, amma sam baiso tunanin nasa yaci galaba a zuciyarsa abinda ya bayyana dashi ake amfani yafi aminta da ya yardarwa kansa cewa da gaske she’s changed tinda gashi har kitchen yau d’in ta shiga tana tambayar Mama ta nuna mata yanda ake wasu abubuwan.... Washe gari Siyamar tai shirin tafiya don Khalid ya sanar da ita da wuri zasu koma Kaduna sabida aiki da ya taso masa, saida ya biya yayiwa Mamani sallama ya kuma cikata da goma na arziki kafin ya wuce d’aukar Siyama, duk wannan bidiri Nabilah batasan Khalid yayi ba don tana makaranta saidai ta labartawa Yusrah yanda taga Khalid jiya gidansu wajen Mamani da yanda suka wanye... Yusrah dai dariya ta dingayi tana fad’in lallai Khalid ya iya kamun k’afa ta k’arada “K’awata wllhi da gaske yake tinda ya soma biyo gida da kamun k’afa, kekam addu’arki ta amsu ki nemi lahira kawai wannan zankad’ed’en saurayi, ga kyau ga kud’i ga aji ga gayu mai kuma kike nema...” Banda harara Nabilah bata aika mata komai, takai mata duka da handouts d’in dake hannunta tana fad’in “Ke nake nema, toh ni ina ruwana da duk futures d’in da kika k’irgo maza duk halinsu d’aya ina nan kan bakata bazanyi aure ba..” Yusrah tace “Daina wannan fatan k’arshen shekara In Allah ya yarda zamukai teddy bear gidan oga bear...!” Nabilah ta kuma kai mata duka su duka suna dariya Nabilah na fad’in “Aifa saidai ku kai masa teddy bear amma bani ba...!” A haka suka rankaya zauren karatu... *** “Shamsu duk yanda za’ai a unguwar nan nakeso na samu gida tinda kaga Siyama ta dage zata dawo...” Sameer yace yana duban Shamsun... Jinjina kai Shamsu yai kana yace “Amma gidajen hayan unguwar nan ba taste d’inka bane Dr why not ka nema a wani wajen ga gidaje masu kyau daidai tsarinka da yanayinka, kai idanma kai gidajen hayan unguwar nan sun maka na tabbata Siyama bazata so ba, so kawai mu nema ta wani wajen.... Lokaci guda Sameer d’in ke girgiza kai alamun rashin amincewa kana yace “Kai ina, nifah unguwar nan nakeso duk yanda za’ai kawai ka sama min gida, batun Siyama kuma ai zama ne na temporary bawai permanent ba, nidai kasan yanda za’ai na sami gida a unguwar nan...” Shamsu dai k’uri kurum ya masa yana mamakin yanda sam Sameer baiso ya bar unguwar, a hankali ya d’an jinjina kai kana yace “Alright I’ll see what I can do...” “You must...” Sameer ya fad’i yana duba irinta abokan usul... Shamsu ya murmusa yace “Ok I must...” Murmushi Sameer d’inma yai yace “Now you’re talking bro....” Kafad’arsa ya rik’o suka shige cikin gidan.... *** *Kaduna* Kallon mamaki Ammi tabi Siyama dashi tana sallalami “No wonder yaron nan ya mak’ale baida aiki sai zuwa Kano ya maida Kaduna to Kano tamkar zuwa unguwa, ke kuma baki nemi gidansu yarinyar kinga waye ubanta ba...? Domin sanin kanki ne bazan bari ya kawo min ko wacce shirgi ba matsayin sirka...” Siyama ta tab’e baki had’ida yatsina fuska “Tab ai wllhi Ammi saima kinga yarinyar low class da ita wacce idan akace min Khalid zai kalli irinta matsayin mace zanyi musu, kwatakwata she isn’t his type, wllhi Ammi sai kinga yarinyar Yesmin ta d’arata a komai, bak’a k’irin da ita balle nace kyaune ya tsole idanunsa toh babu ko d’aya... Wannan ma kunya zakiji azo bikin one and only son d’inki aga wannan kucakar ya d’auko... Wllhi Daddy ma bazai bari ayi wannan shiriritan dashi ba...” Ta k’arashe tana cakalan grapes d’in dake hannunta cikin bowl ta tsinken toothpick.... Jinjina kai kurum Ammi take tana tsuma ita kad’ai, Khalid na nema ya tozartasu ya jajab’o masu d’iyar matsiyata, banda sakin huci bata komai, ta kuma kai dubanta ga Siyama wacce ke cin grapes d’inta hankali kwance kana tace “Shikenan duk kun watse kunyi garin Kano kun k’yaleni, shi yana can yana neman auren da ba yuwa zaiyi ba kekuma zaki tattare kibi mijinki toh ni kuma ku barni da wane tinda shi uban naku nacan wajen matarsa wata k’asar daban...” Dariya ta kufcewa Siyama ta aje bowl d’in hannunta tana fad’in “Wai Ammi ba kece mai bani shawarin nabi mijina a baya ba, toh yanzu na yanke shawarin binshi kaman yanda kikaso a baya zan aje aikina...” Ammi ta rakata da mugun kallo had’ida tab’e baki “Ke ni dama aurenki da Sameer bawai ya kwantamin bane tun farko don dai kawai keda mahaifinki kunfi k’arfina ne, mai za’ai da maras asali...” Siyama ta d’an tab’e baki tace “Ammi nifa I don’t care koma baida asali all I know is that I love him, besides baida wani mummunan hali...” “Ke dalla can rufemin baki, sanda kika haifu aka d’aga idanu aka kalli yaranki akace ina dangin mahaifinsu mai zakice..? Ko kuma yaran su girma su tambayeki su waye iyayen Babansu wane explanation zaki basu...?” Siyama tai shiru tamkar mai nazari tana duban wani b’angaren... Ammi ta kuma jinjina kai tace “Ina horonki da haihuwa da mutumin nan dukda nasan haihuwa ba ra’ayinki bane amma kada ki bari soyayya ta kaiki ta baroki, ya kalallameki da dad’in baki ki haifa masa yaran da a baya zakizo kina danasani, tun ba’aje ko ina ba ya rinjayeki kin aje aikinki zaki bishi, shin waima wane irin apartment ya kama maku...?” Siyama da gaba d’aya jikinta yai sanyi a hankali ta sauk’e ajiyan zuciya “Oho Ammi don’t know gaskiya but koma wane iri ne I’m pretty sure to my taste zai kama, saima kinga unguwar da yake zama Ammi asubahin fari Almajirai ke tashinku a bacci... Gosh! So annoying, waima don gidan da yake d’in nada d’an fasali...” Ammi ta jinjina kai tace “Toh kinga abinda nake fad’i maki koh... Amma idan kinason binshi a haka fine kijeki...” D’an tsuke baki Siyama tai ba tareda ta kuma cewa komai ba, nan ta b’atar da zancen da tambayar Ammi yaushe Daddy zai dawo... *** A satin Sameer ya sama masu gida a nan cikin unguwar, gidane madaidaici mai k’unshe da madaidaitan d’akuna guda biyu wanda basu faye girma ba sai parlor da kitchen a cikin parlorn saiko d’an wajen wanki da shanya dake a wajen kitchen d’in.... Banda yatsina fuska Siyama bata komai, ita da yace mata ya sama masu gida a zatonta gidan gaske ne ashe wannan abin ne wanda ko BQ bazata amsa ba.... Sameer ya k’araso ya rungumeta ta baya yana fad’in “Partner ya kikaga gidan ya miki...?” Yatsina fuska ta kumayi kana tace “You call this a house..? Wait waima dan Allah Partner waye ya baka shawarin kama wannan gidan, of all gidajen hayan dake garin nan ka rasa apartment d’in da zaka kama mana sai wannan, nibama wannan ba gaskiya unguwar baimin ba...” Tinda ta soma magana ya hard’e hannaye had’ida lank’washe k’afa dake jingine jikin k’ofa yake yanai mata wani irin duba fuska babu walwala... “Zaki iya zaman gidan ko bazaki iya ba...?” Taji tambayar tai mata wani banbarak’wai gaba d’aya tamkar an canza mata Sameer d’inta, da a bayane ta tabbata da saidai abi nata zab’in amma yanzu gaba d’aya duk ya canza kaman bashi ba... Tai kicin kicin da fuska ba tareda ta amsa shi ba, bai kumabi takanta ba yayi ficewarsa... Siyama data cika tayi fam zama tai cikin kujera tana tunanin abinyi ita datasan hakanema da bata soma cewa zata dawo garin ba, bak’in ciki bai gama gauraye mata zuciya ba saida ta jiyo muryar Almajirai sahu sahu suna rangad’a mata bara tamkar ta d’aura hannu aka ta kurma ihu haka taji... A hankali ta zamo saman carpet tana furta “Na shiga uku ni Siyama what have I got myself into...” K’aranda wayarta tai ya dawo da hankalinta, a hankali tasa hannu ta d’aga wayar Laila ce mai kiran nata.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *36* *©Sameena Aleeyou....✍🏽* “K’awata ya najiki haka.... hope all is well with you....?” Laila tace daga d’aya b’angaren.... Siyama na zaune dirshan saman carpet take fad’in “Laila na kawo kaina halak’a...” “Ban gane ba... Wani abin Sameer d’in ya miki ne...?” “Komai ma yamin, ke kinga gidan da ya ijeni ne, anya ba ramuwar gayyar abinda nai masa yakesonyi ba, if not na tabbata babu abinda zai zaunar da Sameer a wannan gida.... Wllhi bazan iya zaman wannan environment d’inba....” Laila ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai furta “Ya gane kin zubda ciki ne ko kuwa kin bud’e baki kin fad’a masa da zai maki wannan horon...?” Siyama ta shiga girgiza kai tamkar Lailar na kallonta kana tace “Babu abinda ya gane, kuma kinsan bazan tab’a bud’e baki na fad’i masa ba, duk wannan rigimar dai kan pills ne da ya gani.... Gaba d’aya kaman an canza masa rayuwarsa da tunaninsa..” Laila ta jinjina kai tace “Toh ke kuma yanzu wanne shawarin kika yanke, zaki daina shan maganin ko kuwa....?” Fuzar da iska Siyama ta d’anyi kana tace “Wllhi I’m lost Laila, gaba d’aya ma yanzu bansan wanne zanyi ba, kinsan dai inason Sameer so na gaskiya....” Laila ta jinjina kai tace “Na sani amma dai ki duba maganar Ammi da kyau k’arshe kece za’a bari da kayan kunya, nidai a nawa shawarin kici gaba da shan pills d’inki har lokacin da asalin Sameer zai bayyana miki, idan kinji kina iya haihuwa dashi fine sai ki saki jiki kiyita zubo masa ‘ya’yaye har yanda kike so tinda ra’ayinsa na haihuwa ya rinjayeki, idan kuwa kikaji asalinsa abin k’yamatane shawari ki nemi tsira ma kanki kisan yanda zakiyi ki guntile aurenshi dake, shawari ne...” Siyama ta zaro idanu waje tana fad’in “Laila na raba aurena da Partner fah kike nufi...?” “Toh saime don auren naku ya rabu, shi yak’i biyema ra’ayinki na rayuwa babu stress d’in haihuwa da yara sai kece zakici gaba da zama da wanda baisan asalinsa ba balle tushensa sabida kece uwar soyayya koh... Toh ki zauna kinaji kina gani duk wannan sadaukarwar da kike masa a rayuwa abu mai sauk’i ne wataran yayi replacing d’inki da wata lokacin kin zama chus uwar ‘ya’ya kinaji kina gani saidai ki zama ‘yar kallo a gidanki idan dai mazan zamani ne, ga babban misali nan a gidanku... Ni dai shawari nake baki idan kin d’auka don kanki idan kuma baki d’auka ba rayuwarkice kiyi yanda kika so da ita zaki fad’a min watarana....” Siyama tai shiru tamkar wacce ruwa ya shanye tana sauraren Laila tana kuma auna shawarin Laila dana Amminta, a hankali ta furta “Shikenan k’awata I’ll think about it....” “You don’t need to think about it, amintaka da soyayyar dake tsakaninmu bazai tab’a sa na cutar dake ko na baki shawari maras kyau ba Siyama, don’t ruin your own life da kanki, ked’in ‘yar asalice ‘yar dangi, mai ilimi kyau da gata kar ki tab’a bari rayuwarki ta gurb’ace kan wani namijin da a gaba bazaiga hakan ba k’awata....” Siyama da zauciyarta ta gama kwanciya da shawarin Laila a hankali ta shiga jinjina kai tana mai kuma nazarin kan batun, shawarwari Laila taci gaba bata tana d’orata bisa, Laila bata bari sun ida wayar ba har saida ta fahimci Siyama ta zama fully convinced da shawarwarinta kan nan sukai sallama..... **** A can Kaduna kuwa Ammi gaba d’aya ta d’aukewa Khalid wuta, shi kanshi saida ya fahimci hakan don gaisheta ya shigoyi ciki ciki take amsa masa, bai kawo komai a ransa ba face rashin kula Yesmin da yakene ya saka Ammi fushi dashi haka, dukda abin ya damesa sosai bai d’ago mata zancen ba don yasan Amminsa bata juran fushi dashi zata sauk’one da kanta su sasanta.... Yauma a d’aki ya taddata Yesmin na tayata sorting drawers na jewelries d’inta, kallo d’aya yayiwa Yesmin ya d’auke idanunsa daga b’angaren da take, itakoh nan ta shiga gaisar dashi tana faman kwainane, ya amsa mata a tak’aice fuskarsa babu yabo babu fallasa kaman bashine wanda idan ta gaisar dashi baiko amsawa ba, mamaki da wani irin dad’i suka kama Yesmin, yau ita Khalid ke amsa gaisuwarta har k’wayar idanunsu na hard’ewa, kaman ta buga tsallen murna haka taji, shikaw ba don komai yayi hakan ba saidon Ammi ta amsa nasa gaisuwar ta daina fushi dashi..... Saman stool ya zauna yana satan kallon Ammin wacce ta had’e gabas da yamma, yau d’inma ciki ciki ta amsa masa gaisuwar tasa... Ya had’iyi miyau yana mai kai duba gefen bedside yanda takan ije kayan motsa baki wanda ba sai ta buk’ata daga downstairs ba, robar dambun naman kaza ya hango amma saidai kad’an ne ya rage a ciki, ya d’an mik’a hannu ya janyo k’aramar bokatin ya bud’e ya somaci ba wai don son ci d’in yake ba... Cikeda rawar jiki Yesmin ta mik’e ta nufi k’ofa tana fad’in “Ya Khalid bara na k’aro maka downstairs...” Kafin ya sami zarafin magana ta fice cikeda rawar jiki ta sauk’a k’asa... Ammi da kaman jira take Yesmin d’in ta fice ta aje awarwaron hannun had’ida gyara zama tana kuma jefowa Khalid muguwar kallo wanda yai kaman baisan Ammin na jefa masa kallon ba, sai tura dambun naman yake bakinsa... Jin yanda Ammi ta ambaci sunansa yasa k’iris dmbun baibi masa wata hanyar ba... “Khalid..!!” Ala dole ya kasa had’iyar abindake bakinsa yai shiru yana saurarenta... “Kana jina wllhi bazaka maidani mutuniyar banza ka janyo min abin fad’i a duniya ba, tun wuri tun dare bai maka ba gwara ka sake tunanin kaji na fad’a maka...” Ya had’iyi dambun dake bakinsa ya janyo bottle water dake gefe ya bud’e ya d’an kurb’a kana yace “Ammi mai nayi kuma fisabilillahi, tinda na dawo daga Kano kike fushi dani, what have I done kuma...?” Ta kafesa da idanu tanai masa duban eh lallai ka cika... Jinjina kai tai a hankali kana tace “Kadaka nemi rainamin hankali, uban mai ke kaika Kano...?” Ya d’an dubeta cikeda mamakin tambayar da ta masa kana ya d’an kauda kai gefe yace “Ammi how many times do I have to answer this question... Ammi for goodness sakes aiki ke kaini....” Baikai aya ba ta katse shi da fad’in “Uban aiki... nace uban aiki, wato kama maidani shashasha bansan mai nake ba, toh Siyama ta sanar dani komai, dama wannan uban rawar k’afar dakake hanyar Kano bazai wuce akan mace ba, toh wllhi ka saurareni da kyau, ni bazan bari kaci mutuncina ka kawo min ko wacce irin shirgi ba, idan da gaske auren zakai ga matarka nan gida tana jiranka....” Khalid ya murmusa a hankali kana yace “Ammi I thought alhakin zab’ar macen da nake son ta kasance lifetime Partner d’ina a hannuna yake, dan Allah kar mu sake maganar nan Ammi...” Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa a daidai sanda Yesmin tai tsaye bakin k’ofa da tray d’inta k’arama ta dambu a hannunta hawaye na neman gangarowa daga idanunta... Cikin saurin Ammi ta katsesa da fad’in “Khalid karka fice a d’akin nan, ban gama magana da kai ba...” Cak ya tsaya yana saurarenta ba tareda ya juyo ba hannayensa skale cikin aljihun wandonsa... “Tell me who she’s, su waye iyayenta, meye sana’arsu idan ma’aikatan gwabnati ne wani mataki suka taka, idan masu mulki ne wace sarauta garesu.... ina saurarenka.....” Ta k’arashe tana mai takowa yanda yake... Sai lokacin ya d’ago yanaiwa mahaifiyar tasa wani irin duba cikin rashin yarda da kalaman dake fitowa daga bakinta... “Kai nake saurare Khalid....” Ammi ta kuma katse shi... Idnuwanshi sunyi jazir cikin wane irin yanayi yake furta “Is that what really matters Ammi... Is that what matters to you...?” “K’warai kuwa, a matsayinka na tilon d’anah namiji dole na bukaci sanin duk abinda na jero gameda macen da kake son kasancewa da ita....” Khalid ya kuma dubanta cikeda mamaki kana yace “I thought zaki tambayeni if I really love her, if I’ll be happy with her....?” Cikeda karaji tace “Farin cikinka kenan nake nema maka Khalid, farin cikinka shine namu kuma ba kowa bace farin cikinka illa Yesmin, yarinyar dake sonka tsakaninta da Allah....” “Well! I don’t love her Ammi....!” Ya kasteta cikin d’an d’aga murya idanunsa na firfitowa waje... Ammi bata daina huci ba take fad’in “Then learn, learn how to love her... Sabida itace matar dana zab’a maka and no one else...!” Duban Ammi kurum yake idanunsa na kuma kad’awa... Zuciyarsa cikeda k’una yake girgiza kai bai iya furta komai ba sai ficewa da yayi cikin sauri, k’iris ya rage basuci karo ba shida Yesmin dake tsaye bakin k’ofar kaman an dasata hawaye na gangaro mata alamun taji komai gaba d’aya tattaunawarsa da mahaifiyar sa, tsaye yayi yana k’are mata kallo ga tray a hannunta, itakoh Yesmin tuni ta sadda nata idanun k’asa hawaye naci gaba da kwaranyo mata.... For the first time da yarinyar ta bashi tausayi, baisan mai zai furta mata ba don haka d’an girgiza kai kurum yai yasa kai ya sauk’a k’asar benen cikin sassarfa.... Yesmin tabi bayanshi da kallo hawayenta na k’aruwa, itakoh Kubura dake lab’e k’asan staircase dad’i kaman ya karta ganin yanda Khalid ya gwale Yesmin dake rawar k’afar kai masa dambu... Sosai dad’i ya kama Kubura ta gama amintawa zuciyarta cewa Khalid ba abinda zaiyi da Yesmin, ko shakka babu shid’in rabonta ne... A hanakali tana mai sakin murmushi take furta “KubsyKhal....” Tai Wani murmushi domin kaw had’in sunayen nasu ya mata, ta lumshe idanu a hankali ta lula duniyar tunani tana hango kalan soyayyar da zasuyi a gidansu, k’aurin k’unan abinci da hancinta ya jiyo mata daga kitchen ya sanyata zabura ta nufi kitchen d’in a guje... A haka sati ya shud’e Yesmin na tunanin mafita, taji komai taji akwai yarinyar dake neman mata katanga da Khalid, saidai ba garin take ba balle ta tink’areta, menene abinyi...? Take tunanin Siyama ya fad’o mata, gidan Siyama kawai zata tafi tayi zamanta bazata dawo ba har sai ta saita ko wacce shegiya ce ke neman rabata da Khalid d’inta, ta kuwa sami Ammi da batun, Ammi tace tayi dai dai hakan shine mafita, tuni ta saka driver yakai Yesmin har garin Kano, ita kanta Yesmin tasha mamakin gidan da Siyama ke zaune cikinsa, idan ance mata Siyama zata iya zaman irin wannan gidan sai tayi musu... Jiki a sanyaye ganin yanayin Siyamar Yesmin ta zauna had’ida kamo hannayenta tana kuma k’arema gidan kallo... “Cousin ya haka.... Wannan ne gidan naku...?” Siyama ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida tab’e baki kana tace “Wai fah... Nidai dan Allah kada ki fad’awa Ammi don wllhi nasan kina fad’a mata aurena da Sameer ya k’are... Ni ban san uwar mai unguwar ke tsinana masa ba, kin gannin tinda nazo unguwar nan ko k’ofa ban tab’a lek’awa ba balle nasan kalan mutanen cikinta, bama zan iya adopting halayyansu da d’abi’unsu ba, daga kallo sai wayata idan ya fice asibiti...” Yesmin ta jinjina kai a hankali kana tace “Aiko nima bazanso aurenki da Ya Sameer ya k’are ba banci uwar yarinyar da Khalid ke b’ata lokaci kanta ba, saidai fah Cousin zaman gida yanzu bai kamaki ba domin kaw dole ki taimaka min mu samo gidansu yarinyar nan mu saka mata layi...” Siyama tai dariya a hankali kana tace “Bansanki da tashin hankali ba Yesmin, kodai Ammi ce ta ingizoki...” Yesmin ta fuzar da iska a hankali tace “Akan My Khalid babu abinda bazanyi ba cousin aidai kinsan yanda nake k’aunarsa, promise kawai you’ll help me...” Siyama ta kuma murmusawa kana tace “Kar ki damu I got your back ....” Yesmin ta murmusa cikeda jin dad’i kana suka mik’e Siyama na tayata d’aukan kaya zasu kai d’aya d’akin da ba kwana suke ciki ba.... *** A b’angaren Zulfah kuwa yau ne zata soma ziyartan wajen aikinta sannan a jiya laraba ne take fita daga iddarta, d’an zaman da tayi waje guda babu fita har wani haske ta k’ara, sannan yanzu hankalinta ya kwanta babu tsangwaman Hafiz dana danginsa, tinanin iyayenta da d’iyarta ke d’awainiya da ita, tanaji a zuciyarta sunyi kusan kasancewa ita da d’iyarta tare, tai murmushi tana kuma daidaita zaman mayafin abaya dake bisa kanta, Aunty B ta shigo tana sakar mata murmushi ganin yanda tayi kyau tayi kumari kaman ba Zulfa’u wacce Hafiz ya lahanta mata rayuwa ba... “D’iyata kinyi kyau...” Aunty B tace tana mai kamo hannayen Zulfah... Murmushi Zulfah ta saki a hankali kana tace “Na gode Auntynah...” “Muje na soma ijiyeki sai na wuce nawa wajen aikin...” Ta fad’i tana gyara zaman mayafinta tana mai kallon kanta a mirror d’in, car keys d’inta na hannunta... Jiki a sanyaye Zulfah ta d’au handbag d’inta mai launin shud’i wanda duka Aunty B ta sai mata sabida zata fara zuwa aiki, wadatattun kaya na gayu da kwalliya ta sai mata dukda Zulfa’un ba gwanar pente pente bace a fuska, iyakaci powder ne saiko man leb’e... Aunty B ta dubeta yanda take tafiya a sanyaye kana tace “D’iyata lafiya kuwa...?” Murmushi Zulfah ta kuma saki kana tace “Aunty I’m a little nervous, zan had’u da mutane da dama wajen aikina.... Sannan Aunty wai ni Zulfa’u za’ake hasko muryata gidan radio...?” Aunty B ta murmusa tace “Kowa da haka ya saba Zulfa’u, ki saki jikinki kiyi aikinki da kyau na tabbata sanda mutane suka soma sauraren dadd’an muryarki zasu k’aunaci shirye shiryenki domin kaw ba dad’in sauti da iya kalamai kawai ba harta d’abi’unki gwanin sha’awa ne abin birgewa....” Zulfah tai murmushi cikeda k’warin gwiwa kana tace “Har kullum bazan gajiya da maki godiya ba Aunty, Ubangiji kema ya faranta miki yanda kike faranta min...” Aunty na murmushi ta kamo hannayenta suka k’arasa mota tana mai kwab’anta da yawan gidiyan da take mata.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _.................DA RABO_ *37* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* Tsaye take kansa tanaci gaba da aika masa mummunar kallo, d’aurin kallabi a gefen kai as usual, ga taunar chewing gum da ya zamto d’abi’arta anayi ana hurashi had’ida yin k’as k’as.... Hannaye rik’eda k’ugu bata daina jijjiga ba take fad’in “Kanajina ba damuwata bace idan baka ciniki yanzu koma mai Kantin ne ya amshe kayanshi, wllhi duk yanda kaza ta shiga ta fita sai ka kawo min, ba shinkafa da tuwo aka aura maka ni kake bani ba ehe.... Yau kusan kwanaki uku kenan banci kaza ba jibi duk yanda na rame na d’aid’aice nayi bak’i, kaman ba jazir aka kawoni gidan nan ba....” Ta k’arashe tana juya idanu had’ida danna masa harara tana mai kuma hura chewing gum d’in bakinta..... Fuzar da iska yayi hannaye bibbiyu ya rafka uban tagumi yana dubanta, ga wata uwar rama da yayi gaba d’aya kayayyakinsa wuyan sun masa yawa, idanuwansa duk sunyi kwarmi sun firfito waje, kaman ba Hafiz duk ya canza... “Sau nawa zance maki kiyi hak’uri banida kud’in yanzu, kina gani kud’in da zan hau abin hawa zuwa kasuwa banida ita, jiya da na tari Alhaji da zancen ko amsani baiyi ba ya shige gida, wanne kikeso naji dashi Sawwama, shin ke ko tausayamin bakiyi ne....?” Ya k’arashe cikin k’asa da murya... Wani wawan harara ta kuma aika masa tana mai ci gaba da taunar chewing gum tace “Toh ni ina ruwana don Alhaji bai amsaka ba, Alhaji nake aure ko kai, kai nifa bara kaji na fad’a maka billahillazi babu abinda ya shalleni kaji ne dole ka nemo ka kawomin naci, kuma kasan banacin guda d’aya tak, biyu zuwa uku dole ka kawomin, idanma sata zakai kai ka sani... Malam da Allah ka tashi ka fice min na gaji da ganinka zaune cikin gida....” Iya wuya Sawwama ta kawo Hafiz.... Ya girgiza kai yana mai tuno Zulfah wacce duk abinda ya kawo gidan da sunan abinci sai tayita masa godiya tanai masa addu’o’in da duk k’iyayyar da yake mata sai yaji natsuwa da kwanciyar hankali cikin zuciyarsa, hakan bashi zai hana ya daddana mata wulak’anci ba, ya zageta ya muzantata ya tozarta iyayenta, daidai da rana guda bata tab’a ramawa ba, wasu lokutan haka yakan barta babu abinci dukda lokacin da take gidan samunsa yafi bunk’asa haka saidai yaje waje ya kashesuwa matan banza ko shaye shayen iska wanda ko d’aya yanzu bai isa ya kwatanta ba, duk wani kayan holewa sun fice masa a rai, toh ma ko yace zaiyi ina kud’in yi d’in, gaba d’aya duniyar tana neman tai masa d’aurin goro... A hankali ya mik’e ba tareda ya kuma tankata ba ya nufi k’ofa... Tuni Sawwama ta tare gabansa tana mai ci gaba da fad’in “Wllhi wllhi kaji na rantse maka idan baka dawo gidan nan da k’ullin kaji ba saidai kayi kwanan waje....” Ya dubeta idanu a raunane gashi sam bai iya mata gardama baisan dalili ba, sukuf sukuf ya fice tamkar wani gajiyayye... Da k’yar ya samu babur d’in da ya d’aukesa zuwa gidan Abbah da sunan idan ya isa zai bawa mai babur d’in kud’insa, shima mai babur d’in saida sukayita da wajewa yana masa gargad’in kada ya gudu masa da kud’i... Koda ya shiga gidan ya jima yana hango sashensu Mamy kaman mai tunanin wani abin, jiki a sanyaye ya shige ya nufi sashen Mamani... Mamani na zaune saman darduma tana gyara cazbahanta da ya hargitse taji sallama kamanta jikanta Hafiz... Ya shiga wage baki tanai masa lale.... Kallo guda tai masa ai batasan sanda ta saki ‘ya’yan cazabahan dake hannunta ba suka watse k’asa... “Kalu innalillahi wa inna’ilaihi raji’una... Laa ilaha illahu Mahammadar Rasulillahi.... Hafizu lafiya...? Meye haka..? Ciwo ne kayi.....?” Tayi maganar hannayenta dafe a k’irji... Banda shafa k’eya Hafiz baya komai... “Mamani naira d’ari zaki bani na sallami mai babur.....” Ya fad’i yana tsaye kanta... “Yo ni fah baka amsa min tambayata ba, ita shashashar matarka taka Zulfa’u bata kula dakaine kokuwa...?” Ambato Zulfah da tai yasa ya kuma kai mata duba had’ida lumshe idanunshi... “Mamani ki bani na sallami mai babur kar ya tara min jama’a...” Da dafe dafe ta mik’e tanaci gaba da salallami tana tambayarsa ko jinya yayi, can wajen ajiyarta a uwar d’aki ta lalumosa ‘yan hamsin guda biyu ta bashi “Ungo nan jeka biyashi ka dawo ka sanar dani uwar mai Zulfa’u keyi da ta bari ka lalace irin haka, kahurar yarinya mai halin uwarta, wato bari ta kasheka ta huta, kai wannan yarinya sam babu alheri tattareda ita, tsaban ta shahara ma ni ko a gidan nan na daina ganinta... Toh wllhi har yanda take zanje na sameta naci mata mutunci, haihuwarta yayi sanadiyar salwantar min da Ma’aruf d’ina gashi yanzu tana neman kaima ta aika lahira, toh ahir d’inta saidai ita ta mutu bakai ba, kai wannan yarinya gubarta yafi k’arfin annoba... Ni tin tana k’arama nacewa Manu babu alheri tattareda ita ya kaita bakin kogi aljanai su d’auka yak’i toh yanzu ga irinta waye ya sanima koda maita aka haifota ta lashe Ma’aruf gashi yanzu zata lashe Hafizu... Ohni Halimatu Manu ya haifo mana annoba a dangi....” Har Hafiz ya sallami mai adaidaita ya dawo Mamani bata daina d’ibewa Zulfa’u albarka ba... K’uri kurum ya mata don ko k’arfin magana baida ita, kwanuka dake gefe ya janyo ya shiga bud’ewa sauran karin kumallon safiya tuni ya shiga tura soyayyar doyar bakinsa yana had’iya yana muzurai... Mamani ta rafka uban tagumi ta sanyashi gaba tana kallo, tsabagen tsanan Zulfah ya tsaya mata a rai tama mance kwanakin baya ance mata Hafiz d’in ya kuma aure.... Ta mik’e da k’yar ta kawo masa ruwa tana tambayarsa ko shayine za’a had’a masa, ko amsata bai iya yi ba sai girgiza mata kai kurum da yake alamun a’a... Bayan ya ida tura sank’ararriyar doyar ne ya kora da ruwa nan yake fad’iwa Mamani wasu ‘yan kud’ad’e yazo ta bashi... Babu musu ta d’ebo masa cikin bandir d’in ‘yan d’ari bibbiyu da kwanaki Haladu yaron Kirki ya bata... Ta tasashi gaba tana tambayarshi meke faruwa.... Bai iya amsata ba ya mik’e yana fad’in zai kuma dawowa dama kud’in yazo ta d’an bashi sabida wasu ‘yan matsaloli da suka kunno masa.... Gaba d’aya kaman ba Hafizu mai son gayu da tirare ba, kaman wanda aka canza shi haka ya koma, ko d’an irin hira da yake zama suyi da Mamani yanzu ta lura baima zuwa ita idanba ta fara mantuwa irinta tsofi ba sai tace rabonta da ta skashi a idanunta ya doshi watanni, sam bai zuwa yanzu kaman da, gashi ita ta k’udiri niyyan bazata taka yanda Zulfa’u annoba take ba, amma yanzu kam ya zama dole taje gidan Hafizu tacima Zulfa’u mutunci taji dalilin da yasa ta bar mata jika ya d’aid’aice haka ba, haka tanaji tana gani Hafiz ya fice cikin sauri kaman zai kifa k’asa don d’an doyar da ya samu yaci yasa ya sami kuzari.... *** A gidan Radio Kafar ‘Yanci 96.8 kuwa sosai Zulfah ta sami karb’uwa daga wajen ma’aikatan gidan radion a karonta na farko taredasu, wata budurwa wacce Zulfah zata d’ara mata a shekaru da kad’an mai suna Atika ita taita nunawa Zulfah yanda shirye shiryen nasu ke wakana, ta kuma sanar da ita cewa itace take shirin nan na MU ZAB’I CANCANTA shirin da ake tattaunawa da kuma fashin bak’i gameda jagorancin da ‘yan siyasa suke a k’asar... Zulfa’u ta zaro idanu waje cikeda jin dad’i tana fad’in “Dama kece Atika Shu’aib dake gudanar da shirin Mu zab’i Cancanta, kai don dai bakisan yanda nake matuk’ar son sauraren shirin nan bane, sam bai wuceni musamman da yanzu zab’e ya kunno kai sosai..” Atika ta murmusa tace “Gashi yau kin had’u dani kuma nima naji dad’in had’uwa dake gashi Allah ya had’amu wajen aiki guda, ina fata Allah ya dafa mana cikin sana’armu...” Zulfah ta amsa da amin cikeda nuna jin dad’inta itama, kafin Atika tace “Muje ai inaga Manager ya iso yanzu za’a sake mana lokutan shirye shirye musamman sabida an d’ibi sabbin ma’aikata.....” Zulfah ta jinjina kai murmushi kwance saman fuskarta tana biye da Atika suka nufi babban d’akin gudanar da shirye shiryensu yanda a nan zasu gana da manager gaba d’aya ma’aikatan gidan Radio d’in.... *** Siyama tace “Gaskiya bansan wace unguwa yarinyar take ba amma a nan BUK take karatu, inaga can ya kamata muje mu fara nemanta kafin mu sami gidan nasu....” Yesmin dake zaune gefen mai zaman banza ta kad’a kai tace “Hakan yayi, namafi so mu soma samunta a makaranta muci mutuncinta da kyau a bainar nasi kafin mu biyota gidan ubanta mu mata...” Siyama ta d’an dara kad’an tace “Kallo d’aya nayiwa yarinyar naji bata kwanta min ba, Allah sa ma dai ba asiri ta masa ba don a yanayin danasan Khalid ko maganar fatar baki bazai yarda ya had’asa da irin wannan yarinyar ba balle har ajega batun soyayya...” Yesmin ta kuma cika tana fad’in “Toh wllhi bokanta yayi kad’an ya mata k’arya, zata gane shayi ruwa ne, zata gane ta d’auko size d’in takalmin da yama yawa.... Muje cousin mu soma nemanta....” Siyama ta d’an dara had’ida buga kan steering wheel tana fad’in “Dole nayiwa Ammi video don ya kamata taga komai...” Suka saka shewa a tare kafin Siyama taja motar suka wuce... *** Tuni Mamani tayi shirinta na fita, bata gayyaci kowa ba da sunan rakiya, ta kuwa yi sa’a tana fita ta hangi Mai adaidaita bakin layi nan ta tare had’ida sanar dashi unguwar da zai kaita, ita kad’ai cikin napep sai sababi take gaba d’aya ta cikawa Mai napep d’in kunne.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *38* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED! Sun d’au lokaci suna zaga cikin makarantar don ba sanin tak’amaimen yanda zasu sameta sukai ba, gashi ba sanin sunanta sukai ba balle department d’in da take ko kuma course d’in da take karantawa... Siyama taja tai parking don ita kanta ta gaji da zagaye da kai komo da suke, Yesmin ta d’an dubeta tace “Wai har kin gaji...?” “A d’an kaikaice Siyamar ta dubeta kana tace “Ba dole ba, kinga we can’t find her that easily, nidai inaga what we should do mu koma gida mu sake tunani...” Girgiza kai Yesmin tai alamun k’in amincewa kana tace “Haba cousin just think, kiyi tunani a yanda kika ganta da Khalid, baki iya tuna d’an wani sign ba like bishiya haka ko garden ko kuwa dai wani business center da zaki iya tunawa.... Don’t forget as they say a bari ya huce shike kawo rabon wani, na k’agu na ganta ido da ido na kafa mata concrete warning akan My Khalid... Please Cousin kar kice kin gaji please....” Ta k’arashe tana kamo hannayen Siyamar... Jinjina kai Siyama tai kana tace “Alright fine, let’s see... Idan ban mance ba yanda Khalid yai parking motarsa akwai wata bishiya wajen, sannan akwai wani signboard da ya d’auke hankalina kad’an kaman an rubuta welcome to department of Mathematics and Statistics, something like that...” Yesmin ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa toh yanzu kinga abinda zamuyi let’s ask where we can find the department, na tabbata from there zamu iya samunta, definitely a department d’in take idanma ba haka ba akwai dai abinda take zuwa yi department d’in kuma zai iya linking d’inmu da ita....” Siyama ta jinjina kai a hankali kafin tai starting engine suka soma tafiya.... Wasu samari suka tarar zaune saman wasu kujeru a garden d’in SUG nan suka tambayesu yanda zasu sami department of Maths and Stat, nan take samarukan sukai directing nasu har yanda department d’in take, sukai masu godiya kana suka kuma d’aukan hanya... *** Har suka iso unguwar bakin Mamani baiyi shiru ba... “Inyi yarinya saikace jikanyar ifiritu, duk wani kayan arziki babu shi a tattareda ita, jibi duk yanda yaron nan ya lalace ya koma tamkar bashi ba, inaji dai shima jininsa ta fara zuk’a toh wllhi ta gama cinye zuri’ata tun kan Ma’aruf, saidai taci kanta yanzu kam ehe....” Duk maganar da Mai adaidaita keyi mata cewa an iso bata saurareshi ba sai balbala masifa take, k’arshe dole ya nemi waje yayi parking ya had’e tagumi yana jiran ta sakawa maganganun nata aya... Sai bayan wani lokaci ta kula keken ta daina tafiya... Ta saka sandar hannunta ta dunguri k’eyar mai adaidaitan tana fad’in “Yaya haka... Kai dama mashin d’in taka a gajjiye take ne... Ya ka tsaya dani a nan ko ce maka akayi bazan biya kud’inka bane inyi....” “Baaba tintini naketa ce maki mun iso daidai ina zaki sauk’a amma baki saurareni ba shiyasa naja na tsaya ki gama maganar taki....” “Aw dama ba saurareta kake ba, wato ka k’yaleni inata magana ni kad’ai ga mahaukaciya koh... Toh ai sai kace min ka kawoni yanda na umarceka ba ka zauna ka had’e tagumi ba kaman wanda anka ka kawowa mummunar sak’o...” Ta shiga k’ok’arin lek’o kai tana ganin unguwar, tsaf ta hangi babbar durumin da take gane gidan dashi dashike a lokacin da Alhaji zai gina mar gidan da Mamani ake zuwa tsaban fitina irin nata da dai akace Zulfa’u za’a aura masa shine ta yanke k’afafunta daga gidan, gata dai duk tsufa da ya sauk’o mata da wuya take mance abu shiyasa gidan sam bai b’ace mata ba... “Yauwa kaga an iso ajeni nan...” Ta k’arashe tana laluma kud’in adaidaitan a lalitanta... Tana sllaman mai adaidaita ta shiga dogara sandarta sanda ta nufi gidan.... Da sandar hannunta ta dinga bugun k’yauren don ko sallama Zulfah bazata samu daga gareta ba.... Sawwama da tuni bacci ya d’auketa nan cikin baccin nata taji ana bugun k’ofa tamkar za’a b’alla... Ta buga uban tsuka tana mai kuma juyi cikin gado, abu kaman wasa bugun k’yaure yak’i k’arewa... Ta mik’e zunbur ta zauna tana tunanin wani shafeffe da man ne ke mata wannan d’iban albarka a k’ofar gida, yo ko bashi ta ciwo a mata bugun a nitse ballanta babu ko d’aya... Duk uban dake mata wannan d’iban albarkan sai yasan ya tada ita daga baccinta ko wanene kuwa kai koda Magajiyace mahaifiyar ta... A fusace ta fice babu ko kallabi balle mayafi ta nufi k’ofar.... **** Sun kusan shafe awa guda a wajen mutane sahu sahu sai wucewa suke, can suka hangi wasu ‘yanmata guda uku sun fito daga wani babban gini mai d’auke da rubutun ETF nan suka baza idanu kodai zasu iya gano yarinyar ciki, dashike Siyamace ta tab’a ganin fuskar tata nan ta shaidawa Yesmin d’in babu alamunta cikin ‘yan matan, har dai sun cire rai bazasu ganta ba saiko gata ta fito daga ginin itama tafe tareda k’awarta wacce Siyama ta gansu tare... Cikin sauri Siyama ta shiga nunawa Yesmin ‘yanmatan tana fad’in “Alhamdulillah kinganta gatan can mai red hijab.... Zo muje...” A tare suka finciki marfin motar suka fice Yesmin sai faman huci take yawa zata tashi sama... Nabila da Yusrah wad’anda sam basusan da isowar bak’in nasu ba hankali kwance suke tafiya suna firan class d’in da suka fito.... Kaman daga sama sai ganin ‘yanmata guda biyu sukai sun tare gabansu suna binsu da kallon k’ask’anci... Daga Nabilah har Yusrah tsayuwa sukai suna kallon ikon Allah.... Yesmin ta kuma yamutsa fuska tana dubansu kana tace “Cousin who is she among ‘em...?” Siyama dake toshe da hanci alamun suna wari da yatsa tai nuniwa Yesmin zuwaga Nabilah.... Wani dariyan rainin hankali Yesmin tai tana nunida Nabilah da yatsarta manuniya daga sama zuwa k’asa... “This thing... Wannan abar, kina nufin kan wannan abar Khalid ke rawar k’afa, toh ai ni banga mace a nan ba....” Yusrah da zuciyarta ke tafarfasa ta zuciya zatai kan Yesmin Nabilah dake faman murmushi tai saurin kamota ta dawo da ita baya tana fad’in “A’a don’t mind them baki lura ba... She and I aren’t the same scarecrow... So just let them be....” Ta k’arashe tana sakar masu murmushi had’ida janyo hannun Yusrah zasu rab’a su wuce... Yesmin da tuni ta saki baki cikeda mamakin maganan da Nabilah ta yab’a mata saurin finciko hijab d’in Nabilah tai tana fad’in “Ke you dare call me a scarecrow...Me? A scarecrow.... How dare you...?” Ta k’arashe tana k’ok’arin kai mata mari... Nabilah da har lokacin murmushi take gyara tsayuwarta ta kumayi tana duban hannun Yesmin da ya daskare tamkar an rik’e... “Try it... Do it.... Aw bazakiyi ba....?” Yesmin ta kasa amsata sai huci... Kafin tai wani aune taji sauk’an mari masuji da lafiya har guda biyu a fuskarta... Siyama da abin ya bata tsoro fiyeda zatonta sakin baki tai tana kallon Nabilah shaye da mamaki.. Yesmin ma rik’eda k’uncinta take duban Nabilah, da gaske marinta tai.... “What..? You want more...?” Nabilah ta kuma fad’i tana duban Yesmin d’in wacce ta soma fincika daga rik’onda Siyama ke mata tana fad’in “Cousin ki sakeni na nunawa yarinyar nan k’aramar maras kunyace ita don Allah ki cikni...” Siyama taci gaba da janye Yesmin tana fad’in “Ke wannan da gani ba mai cikakken hankali bane tinda ta sake ta mareki ba tareda sanin ko wacece ke ba, muje muyi shirin tink’aranta da kyau...” Ta turata suka nufi mota, Yesmin bata daina juyowa tana fad’in “Wllhi Khalid yafi k’arfinki kuma saikinsan kin mareni wllhi kaf danginku sunyi kad’an su k’waceki...” Huci kurum Nabila keyi sunaci gaba da tafiya, babu mai cewa komai daga ita har Yusran... Yusrah ta d’an dubeta tace “Nabilah su waye wad’annan...?” D’an dubanta Nabilah tai still fuskarta a b’ace kana tace “Oho ban sani ba amma dai ga dukkan alamu ‘yanmatan Khalid ne....” Yusrah tai shiru tamkar mai nazari, tana murna k’awarta ta sami miji ga wani fitinar na neman kunnowa... Sauk’e ajiyan zuciya tai tana duban k’awar tata wacce itama sak’e sak’en take cikin zuciyarta, idanma Khalid shi ya turosu zaiji daga gareta ne... Ita kad’ai sai faman k’wafa take... A haka har suka fito gate suna neman abin hawa gaba d’aya ran Nabilah a jagule ita bama wad’annan kucakan ne suka tsaya mata a rai ba, Khalid take nanatawa cikin zuciyarta tana k’wafa... Suna shigewa adaidaitan su Siyama dake lab’e daga angle suka soma bin bayan adaidaitan nasu don binciko yanda Nabilah ke zama dukda da fari sunyi tunanin ko hostel take zama amma hakan bai hanasu jira ba don tabbatarwa... *** Da k’arfin gaske Sawwama ta tura k’ofar wanda yasa k’iris Mamani bata zube k’asa ba, sandarta ta fad’i gefe k’ofar ta bige mata gwiwa kad’an abinka da jikin girma dama ba wai lafiyan k’afafune ya isheta ba... Rik’eda gwiwarta take fad’in “Wayyo wayyo k’afata....!” Tana duk’e ta kasa d’agowa sai tamke idanu da take... Sawwama dake tsaye rik’eda k’ugu tana faman yatsine yatsine wani uban tsuka ta buga kana tace “Sabida tsaban jaraba baran taku ta wuce kuyi a bakin hanya sai kun biyo mutane gidajensu kuna tak’ura masu kuna hanasu bacci ko cewa akai sadakar dole ne iyi... Shegen jaraba da fitina irin taku na tsofin mabarata... Zaki b’ace min da gani ko sai na kuma hankad’aki....!” Ta k’arashe cikin daka tsawa.... Da k’yar Mamani ta d’ago idanu tana duban matar dake mata d’iban albarka wanda tsawon rayuwarta babu wanda ya tab’a kwatanta hakan a gareta... Tirk’ashi! Ta fad’i cikin zuciyarta sanda tai tozali da matar....Tai k’ok’arin janyo sandarta ta mik’e sosai tana duban Sawwama dake faman yatsine yatsinen fuska tana jefa mata mugun kallo.... “Bakiji abinda nace bane ki fice ki bani waje..!” Sawwama tace tana mai kuma yamutsa fuska... Banda kallonta da Mamani take bata iya komai, toh ita kuma wannan d’in wacece....? Da k’yar Mamani ta tsaya bisa k’afafunta tana kanne idanu take duban Sawwama... “Daga duniyarmu kike kokuwa akasinta...?” Ta k’arashe tana zagaye Sawwama datasha matsu cikin ‘yar fingilan riga da wando wanda za’a iya kiransa da 3quater.... Mamani taci gaba da zagayeta tana kallo take fad’in “Ikon Allah gashi dai hausa ce bakinki ba yaren arna ba balle nace babbar kahurace ked’in.... Toh kodai b’atan hanya ne nayi ba nan bane gidan Hafizun....? Ga katarorin naki dai kaman curin sakwara, shi kaw sharab’an gashi dai kaman na masu wasan dambe tsala tsala haka nan, iko sai Allah.... Ke kaw baiwar Allah sanyi bai damunki...?” Tinda ta soma magana Sawwama ke dubanta baki sake, lallai tsohuwar ta iya cin fuska, tazo har gidanta tana yab’a mata maganganu wanda babu wanda ya tab’a yab’a matasu.... “Ke tsohuwar ashana ki saurareni nan, nafiki iya bariki barin fad’a miki, tun kafin banyi k’asa k’asa dake ba ki fice ki barmin gida bana cikeda k’anan....” Turo k’ofa da akaine ya sanyasu gaba d’aya maida hankalinsu ga k’ofar... Hafiz ne ya shigo rik’eda ledar kaza hannunsa sai buga sauri yake... Mamani ta saki baki tana kallon ikon Allah tabbas ba b’atan hanya tayi ba, nan ne dai gidan jikanta Hafiz... Toh ina Zulfa’u..? Sannan wannan mai k’iran arnan kan dutsen mai take cikin gidan... Tana kallo Sawwama ta k’arasa ta rungume Hafiz had’ida d’alewa jikinsa tanai masa oyoyo cikin salo.... K’iris ya rage Mamani bata saki sandarta ta dogarawa ba tana buga sallallami... “Laaa ha’ila ha illahu Muhammadarrasulillahi.... Na shiga uku ni Halimah mai zan gani.....?” Ta k’arashe tana neman wajen jinginuwa da zai mata waiji domin kaw tuni Sawwama dai ta tallabo bakin Hafiz ya shiga sumbata... Mamani ta rintse idanunta da k’arfin gaske tana karanto duk lazimin da yazo bakinta.... Shiko Hafiz da dabara ya k’waci kansa hannun Sawwama ya k’araso wajen Mamani cikin sauri yana fad’in “Mamani mai kikeyi a nan... Yaushe kikazo...?” Har lokacin ta kasa bud’e idanunta balle ta basa amsa sai salati take dokawa tana fad’in abinda da ake fad’I zai faru k’arshen zamani gashi Allah ya kawosu.... Jin zata fara kuka da kururuwa yasa Hafiz kamo hannayenta ya nufi tsakar gidan da ita har wannan lokaci idanun Mamani a rintse suke tana fad’in “Hafizu wacece wannan ince dai ba matan kwararo ka soma kawowa cikin gidan ba... Ohni Jikar mutum hud’u ita Zulfa’un na ina....?” Sawwama da takaicin tsohuwar ya kuma kamata tare Hafiz tai da fad’in “Ina kuma zaka shigar min ita.... Wllhi karma kayi tunanin kaita parlor na... Wace itama tukuna....?” Wani irin duba ya aika mata kana ya janyo kujera a nan tsakar gidan ya zaunar da Mamani... Cikin k’asa da murya yake fad’iwa Mamani... “Matatace Mamani ba karuwa bace, dan Allah kada ki sake dangantata da wannan kalma kinji koh...” Mamani ta kasa amsashi sai kallon dataci gaba da binshi dashi gaba d’aya kaman ba Hafizunta ba...Tanaji tana gani ya kuma mik’ewa ya nufi Sawwama dake faman cika tana batsewa... “Kakata ce....” Ya fad’i yana k’asa k’asa da idanu ganin irin muguwar kallon da take aika masa.... Tsuka ta buga kana ta mik’a hannu tana fad’in “Bani nan....” Don tuni hancinta ya jiyo k’amshin kaza.... Kai a k’asa ya mik’a mata ledar ta kuwa wafce kaman jira take... Mamani ta zuba masu idanu kaman ta samu Tv.... Sawwama ta galla mata harara tana mai ci gaba da fad’in “Kai nake jira kazo ka d’auko min paranti....” Ta k’arashe tana mai zama daga can bakin k’ofar d’akinta ta baje saman tabarma tayi d’ai d’ai ta kuwa bud’e ledar kajin k’anshi sai dakan hancin Mamani yake.... Mamani naji na gani Hafiz ya mik’e babu musu ya nufi kitchen ya d’aukowa Sawwama paranti... Zai mik’e tace “Zauna...” Ya koma ya zauna... “Bani a baki.....” Nan ma babu musu ya shiga d’auka yana kaiwa bakinta... Mamani da abin ya koma mata tamkar a shirin wasan kwaikwayo tagumi ta rapka tana kallon ikon Allah, duk wani umarni da Sawwama zata baiwa Hafiz cikin rawar jiki yakeyi... Tinda take a rayuwarta bata tab’a cin karo da abinda ya sanyar mata da jiki ba irin lamarin Hafizu da sabuwar matarsa, abin mamaki saiga k’walla na neman cikowa idanun Mamani tsananin tausayin jikanta da ya dirar mata, take ta soma tunanin toh ina Zulfa’u ake wannan bidirin a gidan... “Hafizu...” Ta ambaci sunanshi daga yanda take zaune.... Ya juyo yana dubanta, take yaji jikinsa yayo sanyi sosai ganin irin yanayin da Mamani ta shiga ciki... “Ina Zulfa’u...?” Ta tambaya tana dubanshi... Kafin ya sami zarafin bata amsa Sawwama dake taunar nama ta kwashe da dariya tace “Zulfa’u kike nema....? Toh jikarki bata gidan nan don tuni an jima da sakinta, kinga d’akinta can ya zama kango.....” Ta k’arashe tana kuma sakin shewa.. Mamani dataji abin kaman diran aradu kallo tabi Hafiz dashi wanda kansa ke k’asa tsawon wani lokaci... “Hafizu da gaske ka saki Zulfa’u...?” Ta tambaya tana dubansa... Saurin girgiza kai ya shigayi yana fad’in “A’a.... Ta tafiya tayi Mamani amma zata dawo...” Sawwama ta kuma sakin shewa kana tace”Ashe dai bakuda labari, tun wuri ku bazama duniya neman d’iyarku don rabonta da gidan nan watanni hud’u kenan tun kafin a auroni....” “Hafizu...!” Mamani ta fad’i tana dafe k’irji.... Lokaci guda taci gaba da jero salati tana tana tafe hannaye....Kaman wacce aka sakata mata batir nan ta soma kuka wiwiwi tana fad’in ahalil kitabi ta shanye mata jika... Haba nan fah Sawwama ta kuma tinzira tana balbala masifawa Hafiz cewa saidai ya fice mata da wannan tsohuwar a gida don idan bata daina zaginta ba tsaf ramawa zatai... Hafiz yasan Sawwama zata aika abinda tace tuni ya kamo Mamani suka fice daga gidan ko cinyar kazar nan ba’a gutsura mata ba dukda ranta ya biya... Da kanshi ya tarar mata adaidaita ya sakata ya sanarwa mai adaidaitan yanda zai kaita.. Haka Mamani ta tallabo bakin mayafi tanaci gaba da kuka tana fad’in shikenan Zulfa’u bata lashe Hafizu ba ga Ahalil kitabi ta shanyesa.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *39* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* A daidai k’ofar gidan Baba Alhaji Mamani ta umarci mai keken da ya ijeta... Ta lalumo kud’i a lalitanta ta biya mai adaidaitan, kai tsaye ta nufi gidan bata daina koke koke tana fad’in shikenan an shanye mata jika ba... A farfajiyan gidan ta hangi Hajiya Haule sai jibgan Rihanah take tana fad’in sai ta fito mata da kud’inta data d’auke, Kausar na zaune gefe tana kuka fuskarta dama dama da kunu yayinda Sahariyya da Najah ke murnan tsalle suna fad’iwa Hajuyarsu ta daki kud’inta da kyau, sam ko sauraro Mamani basuyi ba... Ganin za’a kashe mata jika ya sanyata k’ara sauri sai gani sukai Mamani ta tare dukan tana fad’iwa Hajiya ta had’e da ita ta daka... Gaba d’aya sukabi Mamani da kallon mamaki abinda bata tab’ayi ba shine ta nuna kulawa ko damuwarta kan jikokinta mata sai gashi yau ta tarewa Raiha duka har tana cewa a had’e da ita... Hajiya dake faman huci tana muzurai sai aikawa Mamani muguwar kallo a kwance take itako Sahariyya datafi kowa shara cewa tayi “Mamani ki kauce ki bada filiwa Hajiya tarbiyawa d’iyarta take, yo da kike cewa a had’e dake mai za’a daka a nan salon a k’arasaki ki janyowa mutane jangwamgwam....!” Batakai aya ba taji sauk’ar sandar Mamani a kafad’arta ta kaw rik’e wajen tana ihu... Mamani taci gaba da fad’in “Ke ki kiyayeni kinsha rashin kunya a nono koh... Toh billahillazi ki bar ganina haka nan ina dogara sanda tsaf zan murk’usheki wajen nan... Ja’ira maras ta ido...” Hajiya ta cafi zancen da fad’in “A’a nidai Mamani gaskiya ki daina aibanta min d’iya, idanma tayi rashin ta idon ai kinsan yanda ta samo....” Ta k’arashe tana danna mata harara... Tsananin mamakin rashin tarbiyan Hajiya da yaranta ya sanya Raihanah girgiza kai tana sosa wajen da aka jibgeta hawaye na kwaranyo mata... Jinjina kai Mamani tai kana tace “Yayi... Yayi Haule, ai bansan rashin ta idon naki ya kawo nan ba, amma ki jira kiga yanda duniya zatai dake, na tabbata ke kika tilastawa Hafizu sakin Zulfa’u, kin sabautar min da jika ta shige duniya yanzu kin kama wannan ‘yar marainiyar kina neman illatata.... Kiji tsoron gamuwarki da Allah....” Hajiya ta saki shewa tana tafe hannaye had’ida rangad’a gud’a kana tace “Yau akeyinta... Yanzu ke Mamani bakiji kunya ba, har da kike cewa an sabautar miki da jika, har yaushe kika soma son Zulfa’u a matsayin jikarki, wani irin tsana da muzantawa ne baki mata ba yanzu don Hafizu ya saketa ba abin kimin godiya bane, Toh barikiji na fad’a miki banson kinibibi da bak’in iyayi maza ki kwashi k’afafunki ki ficemin a gida....!” Ta k’arashe cikin d’aga murya tana mai mata nuni da k’ofa... Mamani da zuciyarta ke mata k’una a hasale ta shiga nuna Hajiya Haule da sandarta tana fad’in “Ke Haule ki kiyayeni idan kin shanye Sarki (Hakan Mamani ke kiran Baba Alhaji a matsayinsa na babban d’anta) baya ganin laifinki toh kul kada ki kuskura ki gwada rashin kunyarki akaina...” Hajiya bata bari takai aya ba tace “Shanye Sarki saidai kar a kuma, kinga nan....” Tai nuni da tafin hannunta kana tace “D’anki na nan sai yanda na juyasa, ko kasheki zanyi bazai tab’a ganin laifina ba saidai ma ya min godiya....” Suka saki shewa itada yaranta... Mamani da tuni hawaye sun soma zubo mata murmushi tai a hankali kana tace “Dama ita duniya abinda ka shuka shi zaka girba, ko kad’an banji zafin shanye naki d’an da Alahalil kitabi tayi ba... Hakan shine daidai, na kumaji dad’i da Zulfa’u ta rabu da auren wahala in sha Allahu alkhairi na gaba da ita....” Ta juya ta dubi Raihanah da Kausar dake rakub’e gefe guda tace “Ku taso mu tafi kun gama zaman gidan wannan azzalumar....” Raihanah ta mik’e a tsorace tana rungume da Kausar... Ai tuni Hajiya ta finciki Kausar tana watsa masu harara take fad’in “Koda wasa idan zaki d’auki jikar naki bisimillah amma wannan jikata ce yanda kikeji Raiha d’iyar d’anki ne haka nakeji Kausar d’iyar Danah ne don haka babu yanda Kausar zata tafi a nan gidan zata zauna...” Ta maida dubanta ga Raihanah kana taci gaba da fad’in “Ke kuma ki bita idan kinga dama amma ki sani ubanki na dawowa zansa ya d’aukoki, munafukar banza munafukar wofi....” Ta k’arashe tana janyo mata jakan kayanta had’ida jifanta dashi... Taci gaba da fad’in “Idan dai wannan tsohuwar kakar takuce sai kinyi d’andakinsani komawa gabanta domin kaw ba k’aunarku take ba...” Mamani bata amsata ba don gaba d’aya jikinta a sanyaye yake Sawwama ta gama kashe mata jiki ta nemi fad’a da masifan nata ma ta rasa, kamo hannun Raiha tai suka fice daga gidan, dukda cewa Raihanah bata saba da Mamani ba sannan ta sani Mamani bata son jikokinta ‘yanmata amma har cikin ranta takeji ya fiye mata zaman gidan mahaifinta gaban Hajiya... A haka suka isa gida Raihana na gane masu hanya.... *** Bayan ficewarsu Sahariyya ta koma gefe ta zauna ta had’e rai sosai donma kar Hajiya tayi tunanin sakata wani aiki tinda Raiha ta tafi, ga wanke wanken da bata ida ba... Tab aiko billahillazi bata isa ta sakata aikin wanke wanke ba saidai tayi da kanta, k’arashe ma mik’ewa tayi ta kad’e bujenta ta shige d’aki.... *** Yesmin tsaye gaban dressing mirror tana kuma shafa yanda Nabilah ta shata mari masu kyau har guda biyu... K’wafa ta kumayi a karo na babu adadi kana tace “Wllhi sai na shayar da ita mamaki, badai a unguwar nan take ba, yazo gidan sauk’i sai tasan ta tari fad’an da yafi k’arfinta... Shegiya d’iyar matsiyata...” Siyama dake zaune bakin gado tana duban Yesmin d’in sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “yanzu ta ina zamu b’ullo mata....” Yesmin ta juyo da dubanta gareta kana tace “Ni nasan ta yanda zamu b’ullo mata, badai tace ita maras kunya ba, zamu nuna mata munfita iya bariki da rashin kunya, k’aramace ita a wannan makarantar....” Siyama ta murmusa kana tace “Ni da police nake tunanin mu kawo mata...” Girgiza kai Yesmin tai kana tace “A’a ai bata nan zamu b’ullo mata, ta yuyu wannan ta saba kwanan station tinda kikaga haka, tuggu da makirci shine kawai zai rabamu da tsinanniya...” Siyama ta dara a hankali kana tace “Kinga zo muje kitchen ki sama mana abinda zamuci tinda kinzo na huta order...” A tare suka fice suka nufi kitchen d’in.... *** Mamani ta lura da yanda Raiha ke d’ari d’ari da ita, tausayin yarinyar ya cika mata zuciya... “Raihanatu sunanki koh....?” Raihanah ta jinjina kai a hankali alamun eh.... “Kodai kece Halimatu takwaran tawa..?” Nanma a hankali ta jinjina kai alamun eh kana ta k’arada ni ce... A fili Mamani ta furta “Alhamdulillah da ya kasance ba’a cikin wad’ancan watsattsun d’iyoyin Haulen aka sanyamin takwara ba... Ki saki jikinki kinji koh, nan gidanku ne... Da Manu da Sarki duka ‘ya’yana ne don haka nan ma gidan Babanki ne kinji koh...” Raihana ta k’ak’aro murmushi a hankali tace “Toh Mamani....” “Yauwa Raihantu... Kinci abinci kuwa...?” Shiru bata amsata ba, Mamani ta fahimci bataci abincin bane, flask d’in dake gefe wanda aka kawo daga wajen Baffah Wada ta janyo ta mik’a mata tace maza taci mai isanta, shinkafa da wake ne da mai da yaji.... Mamani ta mik’e ta nufi d’aki abubuwan data aikata a baya sai dawo mata suke, yanzu idan ba’a sami Zulfa’u ba itama tamada kamisho tunda tana d’aya daga cikin masu aibantata da muzantata da k’untatawa rayuwarta... Allah dai ya bayyanar masu da Zulfa’u ta nemi yafiyar yarinyar nan don bazataso ta mutu da hakkin Zulfa’u akanta ba.... Da wannan tunani ta zauna jiran dawowan d’anta Abbah... A haka bacci yayi gaba da ita... Raihanah kuwa tuni ta shiga tattarewa Mamani d’aki, ta gyare mata ko ina yayi tas tas gwanin ban sha’awa, tai wanke wanke ta goge ko ina, harta dangin kayan kallo su tv stand saida Raiha ta goge ko ina ta saka roomfresh waje ya d’auki k’amshi kaman ba d’akin tsohuwa ba, kiraye kirayen Sallahn azahar ya tada Mamani, mamaki ya cikata ganin ko ina a gyare bacin tasan yaran Baffah Wada da k’yar akeyi dasu suzo su gyara dama Marliya ce mai shigowa tai mata idan batada karatu.... Nan fah Mamani taga aikin Raiha ya zarce duk wanda ake mata, ita kad’ai sai murmushi take tana fad’in “A’a ikon Allah.. kaji yarinya d’iyar albarka... Oh ashe dai d’iyoyi mata rana ne dasu...” Tai maganar a hankali kana ta lek’a d’aya d’akin ta hangi Raiha na sallah cikinta nan ma tas tas kaman bashi ba... Ta kuma sakin murmushi cikeda jin dad’i kana ta nufo waje don gabatar da alwalan azahar sai shan mamaki take don harta taakar gidan tas ta share ta gyare... Mamani ta hangi kujeran zamanta nayin alwala a goge tsaf harda buta a gabanta, ta isa ga kujeran ta dafa ta zauna tana mamakin ina aka samo mata sabon buta... Saida ta d’aga tace “Au ikon Allah ashe dai butarce dai tawa...” K’al Raihanah ta wanke butar ta cika mata ruwa mai d’an d’umi bamai sanyi k’au ba... Mamani sai mamaki take tana ayyana hankalin yarinyar cikin zuciyarta.... *** Wajajen k’arfe biyar ya fito daga office, tafe akan hanyarsa ta komawa gida ya hangi motar Abbah na k’ok’arin shiga gida, bazai iya shigewa ba tareda ya tsaya sun gaisa da Abbah ba, daga can yayi parking ya sauk’o ya nufi motar Abbah wanda shima tuni yayi parking d’in sakamakon hango Sameer d’in da yayi.... Cikeda risinawa yake gaida Abbahn, Abbah ya amsa masa kaman ko yaushe, fuska fal fari’a... “Malam Sameer an taso aiki kenan...?” Abbah ya tambaya murmushi kwance saman fuskarsa... Sameer da shima murmushin ne kwance saman fuskarsa yace “Eh Abbah an taso, ya kasuwa...?” “Alhamdulillah... Mun gode Allah, ya wajen aikin naka... Anata fama da jama’a koh...?” Sameer ya d’an shafa kai yace “Alhamdulillah... Toh Abbah zan wuce a huta gajjiya...” Abbah da duk had’uwansu da Sameer bai fatan abinda zai rabasu cikin sauri ya tari Sameer d’in da tuni ya nufi motarsa da fad’in “Amm Dr nace ba ko zamu shiga kaci abinci.... Akwai fura mai kyau ma sai a dama maka...” Sameer baison ce masa a’a sabida tsananin nauyin mutumin da yakeji d’an k’ak’aro murmushi yai yace “Ai Abbah ban jima da cin abinci a wajen aikina ba...” Annurin fuskan Abbah ya d’an ragu, kaman zaice shikenan ka huta gajjiya sai kuma yace “Ko furan kasha Dr, tanada kyau sosai musamman nasa a dinga kawo mani...” Sameer ya d’an kuma shafar k’eyarsa babu yanda ya iya bazai iya jada Abbah ba sabida tsananin ganin girmansa da yake.... Cikeda risinawa ya amsada “Toh..To Abbah...” Cikin jin dad’i Abbah yace “Yauwa ko kaifah maza shigo da motar taka cikin gareji...” Babu musu Sameer yayi yanda Abban yace, suka nufo cikin gidan tare... Aunty Lami da fitowarta kenan daga sashen Abban don ita keda girki ta gama jere abinci kenan, nan ta hangosu sun jero suna tahowa Sameer rik’eda ‘yar jakkan Abbah.... Gabanta ya yanke ya fad’i, shikenan kullum kusancinsu k’aruwa yake, cikinta ya murd’a lokaci guda.... A daburce ta nufi sashenta tana tunanin abinyi, Aminiyar Sirri zata kira ko kuwa Haule... Gadai Ma’aruf har cikin gida yauma, ga kuma dama ta samesu domin kaw itace da girki... Hannunta rik’eda wayar salula ta rasa wace zata kira cikinsu, shawarin wa zata d’auka cikinsu... Lokaci guda ta yanke shawarin kiran ko wacce cikinsu don jin yanda zasuyi da Ma’aruf... Hajiya ta soma kira ta sanar da ita abindake wakana... Ai babu wata wata Hajiya tace tasan yanda za’ai tai amfani da wannan dama ta zuba masa guba yaci su huta, itakaw Aminiyar Sirri cewa tayi “Yanzu ke banda abinki Lami kika saka masa guba yaci kindai san babu wacce za’a kama saike, ita Haule da take tinziraki kiyi hakan ai tasan ba kamata za’ai ba tinda ba ita ta bashi abincin ba... Nidai shawari ki bari abi komai a sannu...” Lami ta amsada “Kumafah hakane gaskiyarce Aminiyar Sirri... Zanyi yanda kikace d’ain...” Daga haka sallama sukai tana mai ci gaba da kaikomo cikin d’aki... Nabilah dake lab’e bakin k’ofa bata jiyo komai ba sai AMINIYAR SIRRI... Nanata ta dingayi cikin zuciyarta, Aminiyar Sirri.... Cikin sauri ta fice daga sashen ta koma can k’uryar d’aki ta shiga neman layin Aunty B... Bugu biyu a na uku Aunty B ta d’aga... Cikeda damuwa Nabilah ke sanar da ita sabon sunan da ta jiyo daga bakin Aunty Lami Aminiyar Sirri... Shiru Aunty B tai kaman mai nazari kana tace “Aminiyar Sirri...? Toh mai hakan yake nufi...?” Nabilah tace “Abinda naji kenan Aunty, and ga dukkan alamu matar da take waya da ita itace Aminiyar Sirrin... Aunty could it be possible Aminiyar Sirri itace ta taimakawa Aunty Lami wajen ganin bayan d’an uwana Ma’aruf...?” Nanma shiru Aunty B batace komai ba, saida ta d’an d’ibi wasu dak’ik’ai kana tace “Watak’ila hakan ne Nabilah...” “Toh wacece wannan aminiyar sirrin...? I need to find out who she’s...” Ta fad’i tana mai jaddada kalamanta... Aunty B tace “Kodai itace wacce kike ganinsu tare ma’ana Hajiyar Hafiz....” Girgiza kai Nabilah tai tamkar Aunty B d’in na ganinta kana tace “A’a Aunty banjin itace domin kaw ita da Hajiya takan kirata nafi kyautata zaton watace daban sannan duk yanda akai su ukun sunyi tarayya wajen ganin bayan Yayana Ma’aruf.... Amma whoever she is sai na bincikota....” Aunty ta fuzar da iska tana mai ci gaba da fad’in “Don’t forget you’ve my support, You can always count on my support... Zan taimaka maki wajen binciko Aminiyar Sirri...” Nabilah tai mata godiya kana sukai sallama Aunty B tana mai gargad’inta kada tayi mahaifiyarta taji wannan batu domin ko shakka babu d’aga mata hankali zaiyi ya d’ago mata tsohon mik’in dake cikin zuciyarta... *SameenaAleeyou(Mrs💖)📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *©Sameena Aleeyou...✍🏽* *40* Abbah da Sameer zaune a parlorn suna cin abinci saman darduma, sosai Abbah yake kula da d’abi’unsa wanda suke matuk’ar kama da nashi musamman a lokacin da yake matashi kaman Sameer d’in, yana son tambayar Sameer wasu abubuwan amma saidai baisan ta yanda zai soma ba, baisan ta yaya zai soma jefo masa tambayoyinsa masu wuyan fasaltuwa ba, a b’angaren Sameer ma sosai yake jin abubuwa da dama gameda mutumin saidai shima baisan ta ina zai soma ba, Mummy ita kad’ai zata warware masa sark’ak’iyar da ya tsinci kansa ciki... Idan suka had’a idanu da Abbah saidai kaga ya sakar masa murmushi mai sanyin gaske a yayinda shi Sameer d’in sai ya sami kansa yana mai sadda idanu k’asa... Sallaman da akai ne ya sanyasu maida hankulansu zuwaga k’ofar bakunansu na mai amsa sallaman ba kowa bane illa Baba Alhaji Yayan Abbah... Abbah ya fad’ad’a murmushinsa yana mai fad’in “A’ah Yaya kaine tafe, shigo k’araso mana, bisimillah...” Ya k’arashe yana mai nuna masa wajen zama.... Yanayin fuskar Yayan nasa ya tabbatar masa akwai wani abin a k’asa don gaba d’aya babu walwala tattareda Baba Alhaji... Sameer ya risina ya gaidashi ya amsa sama sama, Abbah na mik’a masa hannu alamun suyi masabaha Baba Alhaji yace “Usman ina Raihanah....?” Shiru Abbah yayi yana tunanin wacece ma Raihanah tinda ba wai Hajiya na barinta ta fita bane... Shiko Sameer sunan sounds familiar to him, yanata tunanin ina yasan sunan... “Tambayarka nake ina d’iyata Raihanah..? Na dawo gida Haule ta sanar dani Mamani ta d’aukota ta taho da ita nan... Ce maka akai na gaza rik’onta ne ko mai..? Mahaifiyar tamu ma da kakeji kaike rik’eda ita sabida dai tafi nuna maka soyayya ne shiyasa take zaune gidanka, ka yankawa k’annenmu filaye cikin gidanka ka kashe masu zukata duk don ace kaiga gwani a dangi koh... Toh bada d’iyata ba ni zan iya rik’on kayana sam bazan yarda kaga gazawata ba...” Tinda ya soma magana kan Abbah ke k’asa shiko Sameer jiki a sanyaye ya mik’e yana neman had’o kalmomin da zai masu sallama dasu tinda ya lura sauraren conversations d’insu sam ba huruminsa bane.... Kaman wani munafuki haka ya fice yana k’ok’arin saita takalmansa, saidai fitowarsa kenan sukai caraf Mamani rik’eda hannu Raiha sai balbala masifa take sun nufo sashen Abbah... Gaban Raihanah ya yanke ya fad’i ganin fuskar mutumin da bazata tab’a mance taimakonsa a gareta ba nan gabanta, shima d’in cak ya tsaya yana dubanta domin kuwa tsaf ya ganeta, dama tanada relation da Abbah, toh kodai wancan mutumin shine mahaifinta, idan bai mance ba har k’ok’arin neman mahaifinta yayi don ya sanar dashi kalan wahala da d’iyarsa ke sha hannun matarsa, idan kaw Raihanah ta dawo nan gidan k’anin mahaifinta ne hakan sai yafi masa dad’i... Ya saki murmushi shi kad’ai kafin ta sami zarafin gaishesa fit ya b’ace a wajen... Tai wani sororo da ita don Mamani kam ma ko kulada mutum batai ba, abinka da idanun girma ga uwar masifa da take faman juyewa... “Ke shige muje nace ayita a rubuce cewa bazaki koma gaban Haule ba...” Ta k’arashe tana zungurin Raihanah da sandar hannunta, Rihanah data dawo daga duniyar tunani tai wuf ta shiga bin bayan Mamani... Sameer na fitowa suka had’uda Mamy wacce ta fito kitchen, a karo na biyu da ya kuma had’uwa da matar wacce yakejin wani babban al’amari gameda ita, kasa d’auke idanunta daga barin dubansa tai murmushi bai gushe saman fuskarta ba, Sameer ne yai k’ok’arin saita kansa ya soma gaidata... Mamy tai saurin katseshi da fad’in “A’a daga waje kuma k’araso ciki mana....” Ba abin yace mata a’a ba don sosai yake tsintar kansa da jin nauyin matar... Yana d’an sosa k’eya yake fad’in “Toh Hajiya na gode....” Dad’i kaman yakar Mamy ta shiga doka kirawa Nabilah da Marliya... Duk wannan abu a idanun Aunty Lami dake lab’e akayisu, cikinta ya bada wani irin k’ara kaman mai shirin sakin zawo... Ta dafe hannaye biyu a k’irji tana fad’in “Oh na shige na shiga uku ni Lami kullum k’ara kusanci suke.....” Jiki har na rawa ta koma sashenta ta rarumi mayafi ta fice fuuu... Nabilah dake lab’e tana duban Aunty Lami yanda take lek’en Mamy da wannan mutumi sosai abin ya bata mamaki, toh wannan d’in wayene sannan meyasa Aunty Lami ke lek’ensa.... Kiranda Mamy ke mata ya sanya batabi Aunty Lami d’in ba don ganin k’anda ta nufa daga ganin wannan mutumi da kwanaki ta ganshi parlorn Abbah, tanason sanin alak’arsa da gidansu.... *** Baba Alhaji na hango Raiha ya mik’e yana sab’a babbar riga yake fad’in “Ke shige mu tafi gida....” Bai kai aya ba Mamani da ta k’arashe dogorowa da sandarta tace “Bazata tafi ba, nace bazata bika ba.... Ai bansan ka zama shanyayye har haka ba, bansan Haule har haka ta shanyeka ba, auho ta bika ku tafi ku sabautar da ita kaman yanda kuka sabautar da Zulfa’u koh....?” Gaban Abbah ya yanke ya fad’i jin an ambato d’iyarsa Zulfa’u... Saurin d’ago kai yai yana duban Mamani da Baba Alhaji kana yace “Mamani mai kike nufi... Ina Zulfa’u... Shin ba auren Hafiz take ba....?” Lokaci guda Mamani ta saki kuka tana tattaro bakin zani take fad’in “Manu ka yafeni, ka yafeni tsanar Zulfa’u da nai a baya... Haule da d’anta sun sabautar da Zulfa’u ta shiga duniya babu wanda yasan k’anda take, Hafizu ya saki Zulfa’u ya auro Ahalil kitabi... Wayyo ni Halimatu kaicona... Tinda ta soma magana k’afafun Abbah suka gaza d’aukarsa, tabbas idan akwai babban mai laifi toh fah shine, shine ya tilastawa Zulfa’u auren Hafiz dukda cewa ba sonshi take ba sannan ya mata baki cewa idan ta kashe aurenta saidai ta nemi wani uban bashi ba kuma kadata kuskura ta dawo masa gida daidai da rana guda bai tab’a tuntub’ar yaji wani irin zaman aure d’iyarsa keyi ba, bai tab’a bata dama ta kawo kokenta wajen mahaifinta ba, a koda yaushe Hafiz ne yayi daidai a idanunsa... Shin wane irin mahaifi ne shi, anya hakkin Zulfa’u zai barsa a rayuwa, abu mai kaman wuya kaga hawaye idanun Abbah sai gashi k’walla sun ciko idanun nasa.... Gijif ya zame cikin kujera yana mai furta “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un....” Kalma bayan kalma a hankali can k’asar mak’oshinsa.... “ Kanajina Sarki wllhi Raihanah bazata koma gidanka ba kuma d’anka sai ya nemomin jikata yanda ta shiga ta fita idan kuma ba haka ba kotu ta rabamu....” Marliya da shigowarta parlorn kenan taji ana zancen Addarta Zulfah ta b’ace don tunda taji Raiha na gidan ta nufi sashen Mamani ta tarar basu a sashen shine ta nufo parlorn Abbah don taji muryar Mamani a nan.... Take idanun Marliya suka kawo ruwa, gabanta yaci gaba da bugawa cikin wane irin kuka ta fice a parlorn ta nufi sashen Mamy tana kuka tana k’wala mata kira... Daga Mamy har Nabilah da Sameer gaba d’aya mik’ewa sukai suna tambayar Marliya lafiya... Cikin tsananin kuka Marliya ta fad’a jikin Mamy tana shessheka take fad’in “Mamy Addah Zulfah....!” Mamy da gabanta ya yanke ya fad’i saurin d’ago Marliya tai tana tambayarta “Addah Zulfah...? Mai ya sami Zulfa’un... Marliya ki sanar dani mai ya sami d’iyata.... Ai Marliya bata kai ga bata amsa ba Raihanah ta shigo a guje tana kuka sosai take fad’in “Abbah ne... Abbah ya fad’i bai numfashi...” Mamy tama rasa wanne zatai, ai a d’ari Sameer ya fice ya koma sashen Abbah suka d’unguma gaba d’aya kowa bai cikin hayyacinsa sai koke koke da salati kakeji.. Kankace mai Sameer ya shiga k’ok’arin ceto rayuwar Abbah da yai wata irin sumewa dafe da k’irjinsa... Mamani hannu aka take kuka tana fad’in Baba Alhaji ya fice mata bata koh k’aunar ganinsa, tuni ya cikawa babbar rigarsa iska ya fice yana mai kuma jaddada masu sai ya dawo ya d’auki d’iyarsa.... Dole Sameer ya saka Abbah a mota Mamy na rik’edashi suka fice, suma su Nabilah tuni suka tari adaidaita sukabi bayansu cikin kuka shab’e shab’e.... SameenAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *41* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Nan da nan babu b’ata lokaci aka soma duba Abbah, daidai da dak’ik’a Sameer bai bar kan Abbah ba taredashi ake komai sanin cewa shima likitan ne.... Su Mamani dasu Nabilah an rasa mai dannan wani cikinsu sai kuka suke shab’e shab’e, dama dama ma Mamy itace mai d’an k’arfin halin juriya da karanto addu’o’i dukda cewa abubuwa da dama ne sukai mata caa cikin zuciyarta, ga Abbah kwance rai a hannun Allah ga kuma maganar b’acewar d’iyarta Zulfa’u, duk juriya da jarumtaka irinta Mamy saida k’walla suka shiga gangaro mata cikin zuciyarta take furta “Ya Allah ka dubemu ya Allah kar ka d’auki mijina yanzu, Allah ka d’aga kafad’unshi ya Allah... Allah kar ka bari bak’in tarihin da ya auku shekaru talatin baya ya maimaita kansa, duk yanda Zulfa’u take ka bayyana mana ita.... Bazan iya jure rashin wata d’iya ba....” Ta k’arashe cikin tsananin kuka wanda yasa Marliya da Nabilah k’arasowa suka rungume mahaifiyarsu suna kukan tare... Kan kace mai asibiti ya cika da dangi idan ka d’auke zuri’an Baba Alhaji wanda su kad’aine basu a wajen, bayan shud’ewan wasu dak’ik’ai Sameer ya fito daga d’akin da Abbah yake, gaba d’aya suka mik’e suna tambayarsa “Dr wane hali yake ciki...?” Sameer ya soma calming nasu a hankali “Ku kwantar da hankulanku, his condition is stable now, daga yanzu zuwa ko wane lokaci zai iya farkawa.....” Gaba d’aya suka shiga jero hamdala suna godiyawa Sameer... Mamani ta kafesa da idanu tamkar mai tunanin wani abin, hannayen Sameer d’in ta rik’e tana mai furta “Ubangiji ya saka maka da mafificin alheri likita ceton rayuwar d’anah da kayi...” Sameer ya murmusa a hankali yana mai duban tsohuwar wacce kallo guda ya mata yaji zuciyarsa ya natsu da ita, a hankali yake furta “Babu komai Baaba ai Abbah tamkar mahaifi na d’aukeshi, ku daina min godiya dan Allah...” Mamani ta jinjina kai tace “Iyayenka sunyi sa’an samun d’ah d’an albarka irinka, kaga ba irin jikana Hafizu ba wanda ya zama shanyayye watsattse shida mahaifinsa....” Jin zata saki layi yasa Baffah Wada saurin kamota ya zaunarta yana fad’i a hankali “Mamani asibiti muke bai kamata kina maganganu haka ba...” “Yo sai mai k’arya na fad’i....” Ta fad’i tana watsawa Baffah Wada muguwar kallo ta wafce hannunta ta k’arasa saman benci ta zauna tana mai ci gaba da surutanta... Shiko Sameer ba tareda ya fahimci maganganun nata ba ya d’an saki murmushi kana ya koma d’akin da Abbah yake.... Kwance ya sameshi idanunshi a rufe na’uran bature naci gaba da aiki.... Zama yayi daga gefenshi had’ida k’ura masa idanu, shi kad’ai yake ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarsa, a hankali Sameer ya tsinci kanshi yana mai kai hannayensa saman na Abbah ya dafa a hankali... Hannayen nasa sun jima saman na Abbah kafin daga bisani ya soma k’ok’arin janye su..... Kaman daga sama yaji Abban ya rik’e hannayensa gam yana mai furta “Ma’aruf kar ka tafi ka barni, nasan zaka dawo garemu... Na jima da ayyanwa cikin zuciyata cewa INDA RAI, DA RABON watarana ka dawo... Kar ka kuma tafiya D’ah nah....” K’wallan da Sameer ke rik’ewa suka shiga gangarowa, inama ace da gaske shine Ma’aruf d’in da suke nema, inama ace da gaske sud’in ne iyayensa, baiso yasama ransa hope d’in da ba haka bane... A hankali shima ya damk’e hannayen Abbah lokaci guda hawayen Sameer suka d’iga saman hannun Abbah wanda ya sanya Abbah bud’e idanunshi... K’uri yayiwa Sameer shima Sameer d’in Abbah ke kallo... Abbah yai k’ok’arin mik’ewa Sameer ya saurin taimaka masa yana mai goge hawayen fuskarsa don baiso Abbah ya fahimci hawayen nasa... Abbah bai daina nazarin Sameer ba yana mai dubansa... Sameer ya kula da hakan duk sai yaji ya kasa sakewa a hankali ya soma k’ok’arin mik’ewa yana fad’in “Family d’inka gaba d’aya suna nan barin sanar dasu ka farka....” Mik’ewan da zai yaji Abbah ya rik’o hannunsa guda, ya tsaya cak k’irjinsa naci gaba da bugawa... Abbah na daga kwance yace “Sameer kaima zuri’ata ne, daga sanda Allah ya kawoka cikin rayuwarmu ka zama family kaima, na gode da taimakon ka gareni, da ace baka nan kusa da bamusan abinda zai faru ba....” Sameer ya juyo a hankali yana duban Abbah kana ya sakar masa murmushi, bai iya furta koda kalma ba sabida wasu abubuwa da yakeji suna fizgar masa lokaci guda... Abbah yaci gaba da fad’in “Kai hak’uri abubuwan daka tadda suna faruwa damu nida zuri’ata... Nasan akwai abubuwa da dama da bai kamata kaga suna faruwa ba amma ka sani Allah shike gudanar da al’amaran bayinsa yanda yaso, shike jarabtan bayinsa da jarabawa irin wacce basuyi tsammani ba... Kayi hak’uri Sameer....” Girgiza kai Sameer yai yana mai kuma dafa hannayen Abbah yake fad’in “Abbah kowa a rayuwar nan nada kalan nasa damuwan sannan kaman yanda kace Allah shike jarabtan bayinsa ba tareda shawarin kowa ba, ka daina bani hak’uri kaji Abbah...” Shiru na wasu ‘yan dak’ik’ai suka gifta kan Abbah a k’asa kafin Sameer d’in ya d’an kuma gyaran murya yace “Abbah likita ya tabbatarmin kana buk’atan rage yawan tunani sabida zuciyarka datayi weak, idan har bakai k’ok’arin rage damuwa da tarin tunani ba kana iya samun bugawar zuciya wanda sam bama fata, so try as much as possible kaga ka rage yawan tunani....” Ya k’arashe cikin kwantar da murya mai nitsa zuciya... Abbah ya d’ago yana duban Sameer d’in kana yace “Anya Malam Sameer zan iya cire tunanin Zulfa’u cikin zuciyata bayan a lokacin da ya kamata na kasance mahaifi na k’warai a gareta ban kasance ba... Na muzguna mata da yawa, na bada gudummawa mai girma wajen ganin rayuwarta ta salwanta... Nabi sharrin shaid’an da son zuciyata, shin kana tunanin Zulfa’u zata yafe min.... Sam ban kasance mahaifin da zatai alfahari dashi ba.... Ni ne jigo na fad’awarta rayuwar k’unci data tsinci kanta ciki a yau... Kaicona...” Muryarsa ta shiga rawa sosai hawaye na gangaro mashi... Jikin Sameer ya kumayin sanyi da al’amarin Abbah.... Ya zauna gefe dashi kad’an yana bashi baki... “Abbah ka daina fad’in haka, dukda zamata dakai na d’an lokaci ne k’ank’ani, na fahimci kaid’in mutumin k’warai ne wanda ko wane d’ah zai alfaharin samunka matsayin mahaifi....” Abbah ya tsareshi da idanu yana mai girgiza kai kana yace “Sameer zan sanar dakai komai, kama daga b’acewan d’anah Ma’aruf har izuwa irin rik’on da na baiwa sauran d’iyoyina da Allah ya damk’amin su matsayin amana na kumayi watsi da wannan nauyi mai girma da Allah ya d’auramin duk a rashin d’ahnah Ma’aruf....” Shiru Sameer yai yana duban Abbah zuciyarsa bata daina raunana ba, hawaye basu daina zubo masa ba a lokacin da Abbah ke sanar dashi yanda ya watsar da d’iyoyinshi mata duk akan rashin Ma’aruf, sosai ya tausayawa Abbah da rayuwar da ahalin gidansa suka tsinci kawunansu ciki.... Jiki a sanyaye Sameer yace “Shin idan Ma’aruf ya dawo gareku kuna tunanin zai yafe maku k’ask’anta rayuwar k’annensa da kukayi duk a sabida rashinsa...? Shin da wasu idanu zaku duba Ma’aruf da ‘yan uwansa...? Shin meye laifin ‘yan uwan Ma’aruf....?” Tambayoyin da suka kuma sanya Abbah zuban hawaye sosai yayinda shima Sameer d’in ke zuban hawaye.... Aljihun gaban rigarsa Abbah ya zira hannu ciki ya zaro wata hoto ya mik’awa Sameer kana yace “Tsawon rayuwata a koda yaushe Ma’aruf na ajiye gefen zuciyata ban tab’a canzawa hoton nan ma’ajiyi ba daidai da rana guda tun bayan b’acewarsa... Inada yak’ini d’ahnah zai saurareni zai kuma yafemin...” Duk maganganun da Abbah keyi idanun Sameer naga hoton k’aramin yaro da bazai wuce shekaru biyu zuwa uku ba dake rik’e hannunsa... Hawayensa suka k’aru, k’afafuwansa suna barazanar kasa d’aukarsa... A hankali cikin rawar murya yaceda Abbah “Shin wannan shine d’anka Ma’aruf...?” Abbah ya jinjina kai a hankali kana yace “Shine Ma’aruf d’ina....” “Da ace yana nan zaikai kimanin shekaru nawa a yanzu...?” Sameer ya kuma jefo masa wata tambayar..... Abbah ya d’anyi shiru kaman mai nazari kana yace “Zaikai kimanin shekaru talatin da uku....” Sameer ya kuma jin zuciyarsa tai masa rauni tana mai kuma jadadda masa waswasinsa.... A hankali ya mik’e yana k’ok’arin saita kansa kana ya dafa Abbah kaman zai magana sai kuma ya kasa a hankali ya janye hannunsa ya fice cikin sauri sabon k’walla na k’ok’arin ciko idanunsa, abu guda zaiyi ya cire zuciyarsa daga d’inbin waswasin dake k’unshe cikinta, irin yanda yayi da iyayensa na can gida, bazai tunk’ari Abbah da batun ba sai ya tabbatar ma zuciyarsa ya kuma samu hujja mai k’arfi da zai tabbatar da hakan... Kai tsaye laboratory ya wuce yanda sukayi ganawa ta sirri shida d’aya daga cikin ma’aikatan lab d’in, tuni ya bada sample d’in jininshi ya kuma buk’aci a d’au na Abbah a b’oye a duba idan sun had’a dangantaka ta jini... Sameer na fitowa ya hangi family d’in Abbah zazzaune suna jiran tsammani, jikinsa ya kumayin sanyi sosai sanin cewa wad’annan zuri’a na iya zama zuri’arsa, idanunsa ya sauk’a kan Mamy tsananin tausayinta ya rufesa, ji yayi kaman yaje ya rungumeta yace mata shine long lost son d’inta, take kuma zuciyarsa ta shiga raya masa yanada buk’atan sanin ya akai ya b’ace ya rabu da danginsa tsawon shekaru shin jefar dashi sukai kokuwa b’acewa yayi...Sannan ya akai ya k’are hannunsu Mummy...? Wad’annan tambayoyi ne da ya kamata yasan amsoshinsu kafin ya yanke wani hukunci... Cikin sauri yasa kai ya shige ba tareda ya bari sun gansa ba... Kai tsaye bai zarce ko ina ba sai gidansu Shamsu... A b’angarensu Mamy kuwa haka suka d’unguma suka shiga duba Abbah kowa nason sanin halinda Abban ke ciki har saida Likitoci suka d’an dakatar dasu, ganin jikin nasa da sauk’i sosai yasa su Nabilah Marliya da Raihanah suka nufi gida don shirya abincin da za’a kawo masu asibitin da kuma wasu abubuwan buk’ata... Adaidaitansu na tsayuwa sai karo da gungun yara sukai cikin layin nasu tamkar wanda suke jiran isowarsu suka ci gaba da wak’e wak’e suna kiran sunan Nabilah cikin aibantawa da tsananin tozarci... Nabila Raiha da Marliya cirko cirko sukai suna kallon wannan ikon Allah, kan kace mai sunyo kansu suna ci gaba da tafi da wak’e wak’e cewa Nabilah karuwace, ‘yan sa idon unguwan tuni sunyi chaa ga d’oyoyin su Baffah Wadah suma duk sun fito suna kallon wannan bak’on al’amari mai ban mamaki... Kankace mai yaran nan sun shiga dunbuzan k’asa suna jifan Nabilah dashi..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *42* *©Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Cikin tsnanin tashin hankali Marliya da Raihanah suka shiga janye Nabilah wacce ta koma tamkar mutum mutumi suka nufi cikin gida da ita, da k’yar Nabilah ke iya d’aga k’afafunta ga mutane sunyi chaa kuma babu wanda yayi yunk’urin hana yaran abinda suke... Abu mai kaman wuya kaga kukan Nabilah saigashi k’walla sun ciko idanun nata, ta d’ago idanunta da k’yar tana duban mutane a daidai lokacinda ta hangi Siyama da Yesmin zaune cikin motar Siyamar suna faman sakin murmushin cin nasara lokacin guda suna d’aukar tozarcin da akewa Nabilah cikin wayoyinsu, hakan yayi daidai da zubowan k’wallan da suka mak’ale cikin idanun Nabilah, tinda take ba’a tab’a mata cin zarafi irinta yau ba, kalmar karuwa da aka kirata dashi yafi komai d’aga mata hankali, ji tayi duk duniya babu wanda ta tsana irin Khalid, domin kuwa shi ya janyo mata wannan wulak’ancin, da ace bai shigo rayuwarta ba su Yesmin bazasu san da zamanta ba balle su aibatata su mata sharri da b’atanci ga sunanta wanda yafi komai d’aga mata hankali.... Koda suka shiga gida ma d’aki ta fad’a ta kulle kanta ta kifa kanta ta shiga rusa kukanta son ranta, Raiha da Marliya duk jikkunansu yayi sanyi, yau d’in abubuwa ne da dama kekan faruwa cikin ahalin gidansu, haka sukai jigum jigum sunma mance aike suka dawo gidan, tsnanin tausayin Nabilah na d’awainiya dasu.... **** Shamsu ya dubi Sameer a karo na biyu kana yace “Sameer are you sure of what you’re doing....?” A kaikaice Sameer d’in ya d’an dubesa hannayensa duka biyu rungume da fuskarsa kana ya jinjina masa kai ba tareda ya furta koda kalma guda ba... Lokaci guda ya mik’e ya suri car keys d’insa, yakai dubansaga Shamsu da raunannun idanunsa kana yace “Da zaran result ya fito, idan har ya tabbata mutanen nan iyayenane zanje can gida Kaduna na tambayi su Mummy gaskiyar al’amari.... I’m confused Shamsu... Abubuwa da dama sun shige min duhu, ina buk’atar haske cikin rayuwata....” Ya k’arashe siririyar hawaye na gangaro masa.... Jiki a sanyaye Shamsu ya k’araso ya d’an dafa Sameer cikeda tausayawa, cikin tausashesshiyar murya yake fad’in “Sameer kar ka damu everything will be alright in sha Allah, komai zai bayyana maka da yardar Allah, na sani is not easy but ka k’ara hak’uri da sannu komai zai wuce....” Sameer ya d’an dubeshi kana ya jinjina kai yace “Na gode brother....” Daga haka k’ok’arin sa kai ya soma zai shige Shamsu ya take masa baya.... **** KADUNA Yana kishingid’e saman kujera gefen Ammi tanaci gaba da masa sannu don baijin dad’i kwana biyun, zazzab’i yake fama dashi... Kubura ta shigo d’auke da bowl na fruit salad ta ije saman stool d’in dake gefensa tana satan kallon yanda ya fad’a ya kuma yin haske a d’an rashin lafiyan kwana biyu da yayi, gaba d’aya tausayinsa ya rufe Kubura, cikin zuciyarta take ayyana inama sunyi aurene da ita ke jinyar kayanta ba Ammi ba, sai faman zuba shagwab’awa Ammi yake ana tambayarsa mai yake sonci yana basarwa, inama ma ita yake wannan shagwab’ar itakaw taita riritatasa kaman jinjirin goye... Duk wannan tunani da Kubura keyi tsaye take kansa k’ik’am shiko sai faman shafa wayarsa yake baimasan tana tsaye wajen ba... Ammi ta saki baki tana kallon ikon Allah, har saida ta dakawa Kubura tsawa kafin ta dawo hayyacinta... “Ke! Lafiyarki kikayiwa mutane tsaye aka....? Badai kin aje abinda ya kawoki ba... Toh tsayuwar kuma ta minene...?” Kubura ta d’an zabura kad’an tana k’ak’aro murmushi take fad’in “A’a Ammi wai dama nace ko akwai abinda yake buk’ata kuma...” Girgiza kai kurum Ammi tayi domin ita kanta ta soma fahimtar take taken Kubura kana tace “Jeki idan ya nemi wani abin na kiraki...” Kai a k’asa Kubura ta amsa tana mai satan kallon Khalid da kacaukam hankalinsa kega wayarsa, da alama sam baima saurari tattaunawarsu da Ammi ba... Ficewa tayi cikin zuciyarta tanai masa fatan samun lafiya... Shiko Khalid dialing layinta yaketa k’ok’arin yi amma bai shiga, ya d’an saki garen tsuka a hankali had’ida lumshe dogayen idanunsa... Ammi tace “Saif ka tashi ka sha fruits d’in ko kad’an ne, jibi duk yanda ka rame ina magani zai maka amfani baka cin komai, ko nima so kake ciwon damuwa ya kamani ne...?” Ta k’arashe cikin raunin murya... D’an duban Ammi yai daga kishingid’en da yake, tausayinta yaji ganin duk yanda itama ta shiga damuwa, a hankali ya mik’e zaune, Ammi tai saurin nufosa zata taimaka masa yana murmushi yace “Haba Ammi zan iya zama fah....” Ta d’an hararesa kana tace “Don dai bakaga yanda ka rame bane...” Tai maganan tana zuba masa fruits d’in cikin k’aramar bowl ta d’auko d’an spoon d’in tana k’ok’arin bashi a baki... Nan ma murmushin ya kumayi yana mai girgiza kai had’ida jinjina irin k’aunar da mahaifiyarsa ke masa... Amsa yai yana fad’in “Haba Ammi stop treating me like a kid again, I’m all grown fah....” Nanma hararan ta d’an jefa masa kana tace “Toh maza ci na gani....” Haka ta tasa Khalid a gaba yana tura fruits d’in, saida ta tabbata yaci sosai kafin ta k’yalesa, ya d’anji k’arfin jikin nasa kam ya kuma sami d’an appetite... Remote d’in dstv ya janyo yana k’ok’arin kamo tashan ball yaji k’aran shigowar sak’onni cikin wayarsa... A hankali ya mik’a hannu ya janyo wayar yana k’ok’arin dubawa, Whatsapp d’insa ya shiga bud’ewa don ta nan ne aka aiko masa sak’on... Ganin bak’uwar lamba yasa yaji kaman bazai bud’e ba sai kuma ya bud’e yana k’ok’arin dubawa.. Video ce da alama tuni ta bud’e da shike auto download ne wayar tasa... Sosai ya mik’e ya gyara zama yana kuma kallon video d’in, bai gama tabbatarda abinda yaran ke fad’i ba saida ya hangota tsaye tamkar mutum mutumi ana jifanta ana watsa mata k’asa, sannan duk wajen an rasa mai hana yaran... Yana ganin sanda hawaye suka gangaro mata ‘yanmata guda biyu wanda shakka babu ‘yan uwanta ne suna k’ok’arin janyeta..... Wani irin mummunar fad’uwan gaba ne ya sauk’arwa Khalid, take ya nemi zazzab’in da yake ya rasa, gaba d’aya ji yayi duniyar na neman juye masa, What’s all this... Ya fad’i a zuciyarsa, ya kuma duban wayar tasa yana jujjuyawa cikin rashin yarda da abinda ya gani... Teddy bear ake kira karuwa...? Karuwa fah....? Khalid ya dafe kansa da ya kuma masa nauyi a hankali, yama rasa tunanin mai zaiyi.... Lambar da aka turo masa video d’in yai k’ok’arin kira saidai bata zuwa... Ya kuma kaiwa kan lambar Nabilah kaman zai dialing sai kuma yaji bazai iya ba, ji yai Kano kawai yake son tafiya... Kaman wanda aka zabura dukda cewa yamma ce lis hakan bai hanasa tunanin hawa kwalta a daidai lokacin ba.... Sashensa ya nufa ya hau shiryawa gadan gadan... Ammi da ta fito tana tambayar ko za’a kawo masa fish pepper soup na ta tarar babu Khalid a parlorn... Tai mamakin daga d’an tashinta har ya sami k’arfin ficewa a parlorn.... K’ila sashensa ya koma ta fad’i hakan cikin zuciyarta had’ida zama cikin sofa tana canza tashan k’wallo da Khalid yakai, ga magungunansa da wayarsa duka a wajen ya bari.... Jim kad’an ana kiraye kirayen sallan magrib Khalid ya fito cikin shiri sai zuba k’amshi yake, Ammi ta saki baki tana kallon majinyaci ya ware lokaci guda... “Saif masallaci aka nufa ne...?” Ta tambaya tana mai sakar masa murmushi.... Ba tareda ya dubeta ba yana mai ci gaba da d’aura agogon hannunsa yace “Kano zanje Ammi....” Ya k’arashe yana mai d’aukar wayar salulansa dake bisa center table... Tamkar wacce aka zabura haka ta d’ago tana dubansa... “Kano...?” Ta maimaita... Ba tareda ya dubeta ba yana mai ci gaba da abinda yake ya jinjina mata kai alamun eh... Tuni yasa kai yana fad’in “Sai munyi waya Ammi....” Ai a d’ari ta mik’e ta sha gabansa tana huci take aika masa mugun kallo... Khalid ya tsaya cak yana duban mahaifiyar tasa... “Wllhi kaji na rantse bazakaje ba....” Khalid ya d’ago a hankali ya kuma dubanta.... “Amm.....” Bata bari ya k’arasa ba tace “Na riga na rantse, kan wancan matsiyaciyar yarinyar zaka d’ibi k’afafu ka d’ale kwalta ba isasshen lafiya ne dakai ba ni kuma kawai sabida gani shashasha sai na k’yaleka koh...? Toh bazakaje ba.... Wayasan uwar mai ta sanya maka kaci ka koma haka, tinda ka dawo ma kake rashin lafiya, wayasan kalan asirin data maka.... Toh wllhi wllhi bazakaje ba, sabida tsaban jarbar asirinta a daren nan zata kiraka ka tafi, idan asirinta yayi tasiri akanka ni bazaiyi akaina ba... Ban yarda ka fita a gidan nan da sunan barin gari ba kaji na fad’a maka....” Tana k’arashe fad’in haka tasa kai ta nufi staircase.... A hankali ya lumshe idanunsa ga zuciuarsa dake tsnanin masa zogi da rad’ad’i, a halin yanzu babu abinda yake sonji kaman yaji gaskiyar lamarin nan daga bakin Teddy Bear wanda, maganar tafi k’arfin waya a’a face to face baki da baki yakeson jin komai.... Da k’yar ya iya jan k’afafunsa ya nufi masallaci... Kubura dake lab’e ta gama jiyo komai duk abinda Ammi ke fad’i dafe k’irji tai tana fad’in “Na shiga uku ni Kubura, wato ashedai ba Yesmin bace kawai ke neman hana burina cika ashe akwai wata can... Harma asirce shi tayi... Tab! Aiko wllhi da sakel, ina nan ina tunanin wannan k’aramar alhakin Yesmin ashe akwai wata gogeggiya mai bin bokaye da malamai.... Toh wllhi bazata saku ba, Khalid nawa ne ni kad’ai sai na nuna mata malumanta sunyi kad’an, abinda banyi a baya ba yanzu zanyi.... Wllhi sai na mallaki Khalid...!” Ta k’arashe tana d’aga yatsa guda sama had’ida juya yatsar cikin salo na juya idanu.... *** KANO Hajiya ta cika tayi fam tana kuma hararan mijin nata.... “Toh yanzu sai ka baro masu Raihanan....? Kaga Alhaji gidan nan dai babu mai girki idan ba Raiha ba babu mai iyawa da d’awainiyar gidan nan, kawai makasu a kotu zakai dole a baka d’iyarka tinda babu uban da ya haifa maka ita ehe....!” Ta k’arashe tana sakin huci.... Cire hulansa Baba Alhaji yayi yana shafa kansa kana yace “Haule Mamani fah kike nufi nayi k’aranta a kotu....” “Toh sai mai idan kayi k’ararta ita ta haifa maka d’iyar da zata k’waceta haka kurum, shikenan yanzu tasa d’iyarka bata ganin darajarka, yanzu sam Raiha bazata d’aukeka matsayin mahaifi ba biyayya kuwa saidai tayiwa Manu tinda gidanshi ta koma da zama...” Ta k’arashe tana aika masa harara.... Sauk’e ajiyan zuciya Baba Alhaji yayi yana mai girgiza kai alamun a’a yake fad’in “A’a Haule banda maganar kotu idan an kwana biyu dai lokacin Mamani ta huce zanje na d’auko d’iyata...” Tsuka Hajiya ta buga had’ida kad’e masa buje ta mik’e tana fad’in “Aikin banza aikin wofi, k’ato da kai ka bari k’aninka da mahaifiyarka suna maka k’ak’a gida, toh wllhi nidai bazan kashe kaina da aikin gidan nan ba, kuma sanin kanka ne ma’aikata basu jure zaman gidan nan don haka duk abinda kaji ka gani kai ka sayo da kud’inka ehe...” Ta wuce fuu kaman zata tashi sama.... Tana isa d’aki ta tadda Kausar tayi kashi jikinta sai tangaririya ake da ita tsakanin Sahariyya da Najah an rasa mai wanke mata kowa cewa take wllhi bazatayi ba... K’atutun bak’in ciki ya tokari Hajiya don sam basusan d’awainiyar yarinyar ba tinda ubanta ya ajeta gidan sai Raihanah... Hajiya tai k’wafa tace “Kunsan Allah bazan lamunta wannan sangarci naku ba, kuna gani dai ubanku ya kasa dawo da Raiha gidan nan kun barni a kitchen ina fama da hayak’i da sunan ina maku girki, toh d’awainiyar Kausar d’inma ni ce kukeso na d’auka ko kuwa...?” Kafin takai aya Sahariyya dake mak’ale da earpiece a kunne tace “Wllhi Hajiya nidai bazan wanke kashin d’iyarda ban haifa ba, ai ubanta na raye maiyasa baza’a maidata gidan ubanta ba matar tasa taje can tai d’awainiyarta amma wllhi badai ni ba kinji na rantse bazanyi ba...” Hajiya ta kafeta da idanu had’ida yin k’wafa, ta dawoda dubantaga Najah wanda a nan take tunanin samun sauk’i... Tab’e baki Naja’atu ma tai tace “Wllhi nima banzayi ba saidai tayi tsutsa....” Tana ida fad’in haka ta fice abinta... Sahariyya kuwa gyara kwanciyarta tai ta ci gaba da chatting d’inta... A dole Hajiya ta d’auki Kausar ta nufi bayi da ita tayo mata wanka ta shiryata gashi Raiha ta sabarwa yarinyar da goyo haka Hajiya ta sab’ata ta nufi kitchen k’arasa dafa abinci don bazata iya barin yaranta su Sahariyya da yunwa ba..... *** Washe gari suna breakfast suna shek’ewa da dariya, Yesmin tace “Ai na fad’a miki cousin after everything I planned for bazai kuma duban yanda take ba, ita kanta bazata kuma fatan sake ganinshi ba, na tabbata by now ta tsaneshi ta tsani saninshi da tayi shiyasa nace miki ni nasan hanya mafi sauk’i da zamubi...” Siyama ta kuma darawa kana tace “Kai cousin ai bansan kin iya makirci har haka ba na tabbata Ammi taji batun nan har kyauta sai tai miki...” Dariya suka kumayi a tare had’ida tafe hannaye daidai lokacinda Sameer ya fito cikin shirin fita aiki... Yesmin ta gaidashi ya amsa babu yabo babu fallasa... Siyama ta bishi da kallo don tun daren jiya ta lura tamkar wani abin na damunsa saidai sam bai sanar da ita ga abindake damunshi ba itama bataja maganan ba don yanzu gaba d’aya ya canza mata kaman ba Partner d’inta da suke sharing komai a baya ba, tun bayan sab’anin da suka samu Sameer ya canza mata sosai... Ganin zai fice ya d’an sanyata bud’e murya tace “Partner breakfast fah...?” A d’an kaikaice ya dubeta kana yace “No zanci a office I’m late already....” D’an jim tai kana tace “Alright a dawo lafiya....” Kai kurum ya jinjina mata had’ida k’ak’aro murmushi ya sakar mata kana ya fice... Tinda ya doshi lab d’in gabansa ke matuk’ar fad’uwa yana tunanin abinda zai gani... Koda ma’aikacin lab d’in ya mik’a masa zungureriyar takardan da k’yar ya iya sa hannu ya amsa... Ya juyata yafi sau uku kafin ya soma k’ok’arin bud’ewa yana tunanin wannan takardar ka iya canza rayuwarsa ta har abada... Da basmala saman bakinsa ya bud’e takardan ya ciro paper d’in dake linke ciki ya shiga warwarewa.... A hankali Sameer ya soma bin takardan yana karantawa daki daki... Jiri ne yaji na neman kadashi sanda yayi araba da cewa yana d’aukeda jinin wannan bawan Allah kashi casa’in da tara cikin d’ari ma’ana da gaske Abbah shine mahaifinsa na asali.... Wasu irin zafafan hawaye suka shiga gangarowa Sameer wanda baisan na murna bane ko akasin haka.... Lokaci guda ya silale saman benci dake gefe a wajen hawaye naci gaba da gangaro masa..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *43* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Jiki a matuk’ar sanyaye Sameer ya mik’e ya nufi d’akin da aka kwantar da Abbah, Mamy na gefe saman abin sallah da alama sallar walha take shiko Abbah bacci yake domin kaw idnunsa a rufe suke.... Rakub’ewa Sameer yayi jikin k’ofar yana kallonsu sabbin hawaye na gangaro masa, ganin Abbah na k’ok’arin motsawa alamun zai farka ya sanyashi saurin komawa da baya yana mai rintse idanunsa masu zuban ruwa, wad’annan bayin Allah sune iyayensa, su sukai sanadiyan zuwansa duniya, sai yanzu yake fahimtar dlilan da sukasa yake jinsu matuk’a cikin zuciyarsa, sai yanzu yake fahimtar abubuwa da dama da yaji gameda wad’annan bayin Allah, a hankali ya linke takardan ya jefa cikin aljihunsa, Yana fitowa ne ya kusa cin karo da wata matashiyar mace tana tafe tana kuka da alama d’akin da Abbah yake ta nufa... Su duka biyu sukai tsaye suna duban juna sannan ko wannensu hawayene kwance saman kyakkyawar fuskokinsu, ko ba’ace maka ba kaga ‘yan uwan juna, kowa ya kasa baiwa d’an uwansa hanya sai kallon juna da suke su duka biyun, k’arasowar wata madaidaiciyar mace data d’an data ne ya sanya Sameer kaucewa yana k’ok’arin basu hanya, for the first time da Aunty B ta kuma yin tozali da fuskar nephew d’inta da ya b’ace shekaru talatin baya, k’irjinta yai wani irin yankewa ya fad’i, wannan fuskar Ma’aruf ce tsantsan take hangowa, har ya gifta ta gefensu ya wuce Aunty B bata daina binsa da kallo ba Zulfa’u kaw tuni ta shige cikin d’akin hankali tashe ta fad’a kan Mamy tana kuka... Aunty B ta take mata baya jiki a sanyaye tana son tambayar Zulfa’u wanene mutumin data gansu tare... Sosai Mamy ta rungume Zulfah tana hawaye itama a daidai lokacinda Abbah ya fito daga band’aki, tausayin d’iyarsa da matarsa ya rufesa... Zulfah taci gaba da fad’in “Mamy ina Abbah na, Mamy ku yafeni dan Allah, wllhi banyi nufin tada hankulanku ba sai don k’ok’arin gujema faruwar hakan, Mamy dan Allah ku yafe mun..” Ta k’arashe cikin shesshek’ar kuka... Daga bayanta take jiyo muryar Abbah yanda yake fad’in “Zulfa’u baki mana komai ba face biyayya idan akwai wanda zai rok’i gafararki toh kuwa babu shakka mune musamman ni mahaikinki, ni nayi sanadiyar jefa rayuwarki cikin k’unci, na tauye maki hakkinki da addinin musulunci ya baki, na tilasta maki kasancewa da mutumin da baki k’aunarsa mutumin da yaso salwantar da rayuwarki, ki yafeni Zulfa’u ku yafeni daga ke har mahaifiyarki....” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka... Jiki a sanyaye Zulfa’u ta taso ta k’araso gaban mahaifinta ta duk’a k’asa, cikin hawaye take furta “Abbah ka daina neman gafarata domin kuwa ni baka min komai ba, aurena da Yaya Hafiz k’addarane hakan Allah ya hukunta sai ya faru a shafin rayuwata, Abbah na tabbata burinka ka sama min abokin rayuwa na k’warai ne shiyasa ka zab’ar min Ya Hafiz... Dan Allah Abbah ka daina bani hak’uri kaji Abbah nah...” Abbah ya kifa kansa yana fidda hawaye masu tsananin ban tausayi... Itama Mamyn hawaye ke ci gaba da kwararo mata, d’aya daga cikin ranakun da take mafarkin kasancewarsu a rayuwarta, yau ga mijinta ya gane kuskurensa a rayuwa, Allahu Akbar... Wannan shine INDA RAI DA RABO, Sam mai rai kada ya yanke tsammanin yankewar rahamar Ubangijinsa domin shi d’in mai canza al’amra ne a duk sanda yazo, Allahu kasa mu dace, Ameen thumma Ameen... Hawayen da Aunty B ke mak’alewa ya shiga d’igo mata, sosai suka bata tausayi sanda Zulfa’u taci gaba da sanar da iyayenta irin taimakon da Aunty Bara’atu tai mata, tsawon lokacin nan da Hafiz ya saketa tana zaune hannun Aunty Bara’atu.... Hakan sosai ya faranta ran Abbah da Mamy sukaita jerowa Aunty B godiya tana nuna masu ai Zulfa’u d’iyartace don tai mata wannan ba komai bane hasalima ma kanta tayi.... Aunty Lami tai tsaye daga bakin k’ofa tana kallonsu, zuciyarta kaman zata fito ta fashe sabida tsananin takaici da k’unci, ala dole ta saita kanta ta shiga da sallama hannunta d’aukeda kwandon abinci.... A b’angaren Sameer kuwa kai tsaye office d’insu Shamsu ya wuce.... Daga yanda Shamsu ya gansa yasan babu lafiya, kamosa yai ya zaunar saman kujera mai kallon nasa yana tambayarsa ya akai..... Sameer bai iya ce masa komai ba sai hawaye dake ci gaba da gangaro masa... Shamsu ya d’an fuzar da iska kana ya mik’e ya dawo kusan Sameer d’in ya janyo wata kujerar ya zauna, dafa Sameer yai yana mai ci gaba da nazarinsa, murya a kwance yace “Sameer please talk to me.... Meke faruwa....?” Har lokacin Sameer d’in bai iya ce masa komai ba sai zaro takardan gwajin DNA da yai ya damk’a hannun Shamsu hawaye masu d’umi suna ci gaba da gangaro masa... Shamsu ya bisa da kallon mamaki kana ya shiga k’ok’arin warware takardan.... Tsananin Shock Shamsu ya tsinci kansa ciki, ya d’ago ya kuma duban Sameer wanda har lokacin kansa ke kife k’asa yana d’igan hawaye.... Da gaske dai wad’annan bayin Allah sune biological parents d’in Sameer, wannan shine ikon Allah, toh ya akai hakan ta kasance....? Ya akai tsawon shekarun nan basu sani ba, mai ya raba Sameer da iyayensa na asali..? Tambayoyin dake yawo a kwanyar Shamsu... Yana cikin tunanin ne ya jiyo muryar Sameer mai cikeda tsnanin rauni yana fad’in “Sune iyayena Shamsu, Alhaji Usman shine mahaifina.... Shamsu bansan mai nakeji ba a halin yanzu, shin jefar dani sukai ko kuwa kyautar dani sukai...? Shin meye asalin labarina... Mecece gaskiyarta....? Shamsu I need to find out...” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Shamsu ya dafasa cikeda tausayawa, saida ya sauk’e ajiyan zuciya kana yace “Toh yanzu ta ina zaka fara abokina... Shin ka sanar da Abbah cewa shine mahaifinka, kaine d’ansu da ya b’ace...?” D’ago rinannun idanunsa yai yana duban Shamsu kana ya girgiza kai yace “Not yet, ban sanar da kowa ba face kai, sannan bazan tunk’ari Alhaji Usman da batunba sai naje Kaduna na dawo, inada d’umbin tambayoyi da nakeson yima Mummy da Daddy...” Daga haka mik’ewa yayi yana mai furta “Zan wuce Kaduna yanzu In sha Allah...” Shamsu ya mik’e cikin sauri ya take masa baya yana fad’in “Sameer are you sure you can drive...?” Yayi maganar cikeda kulawa... K’ak’aro murmushi Sameer yai ya sakar masa kana ya jinjina kai a hankali yace “Kar ka damu abokina Insha Allah zan iya...” Cikeda nuna damuwa Shamsu yace “Toh ko dai nai driving naka ne...?” Nanma girgiza kai yai yana mai sakin murmushi yace “I’ll be fine Shamsu ka daina damuwa...” Nannauyan ajiyan zuciya Shamsu ya sauk’e kana yace “Shikenan if you insist, drive safe abokina.....” Sameer ya jinjina kai kafin suka soma sauk’owa daga benen.. Har wajen da ya aje motarsa Shamsu ya masa rakiya yana mai masa fatan sauk’a lafiya da samun nasara... *** Idan kaga Hajiya a kwanaki biyun nan da babu Raihanah duk ta fice hayyacinta tayi wajaga wajaga, ‘ya’yanta Sahariyya da Naja’atu sam babu mai taimaka mata da aikin gida cikinsu, ga hidimar Kausar dake gabanta... Tana zaune ta ida sanwar abincin rana ga Kausar da tun daren jiya ke kuka sabida tsananin zafin jikin da take fama dashi, da alama yarinyar batada lafiya, gaba d’aya Hajiya bata samu wadataccen barci ba ta tsaya jinyar Kausar, abin ya mata yawa kanta na neman zaucewa... Kaman wacce aka sinkaya haka ta mik’e ta sab’a Kausar a baya ta fice... Bata zarce ko ina ba sai gidan Hafiz.... Tun bayan bikin sai yau Hajiya ta taka gidan Hafiz dukda cewa ita Sawwamar bata tab’a d’aukan k’afafu taje gaida sirakanta ba iyayen mijinta... Hajiya bugun duniya tayi ba’a bud’e k’ofa ba ga Kausar dake sab’e a bayanta tana ci gaba da aikin kuka, sai faman jijjiga yarinyar take.... Bayan shud’ewar wasu mintoci taji ana k’ok’arin bud’e k’ofar don har ta cire rai baza’a bud’e ba ta soma neman mai adaidaita... A yatsine Sawwama ke dubanta tana wani kanne idanu alamun tashinta kenan daga bacci.... Hajiya baki sake take duban Sawwama domin kaw babu sitirar kirki jikinta don sanye take cikin kayanta na bacci.. Ta kasa furta koda kalma guda sai duban Sawwama da take babu ko k’yafta idanu... Banda watsa mata kallon wulak’anci Sawwama bata komai, ta lura da mamakin da ya kama Hajiya don haka ta kuma juya jikinta alamun ta kalleta da kyau kana tace “Lafiya...? Bashi ko Tara...?!” Yanda tai maganar cikeda isa da izza yasa Hajiya saurin saita kanta kana ta shiga wage baki tana yak’e tace “Baki shaidani bane...? Nice Hajiya mahaifiyar mijinki....” Saida Sawwama ta kuma binta da wani wulak’antaccen kallon kana ta d’anyi gajeren dariya tace “Na ganeki mana, shiyasa nake tambayarki, bashi ko tara...? Idan kaw babu d’aya daga ciki uwar mai kikazo mana gida da asubahin fari.....?” Gwiwoyin Hajiya suka sake tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi tace “Kodai baki lura bane ai gari ya waye tuntuni azahar muke hari...” Nanma tsuka Sawwama tai tana wani juya idanu had’ida jijjiga ita kad’ai kana tace “Toh naji gari ya waye, yanzu dai ki sanar dani mai ya kawoki....” Hajiya da k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi harara ta wurgawa Sawwama sanda ta saci kallonta taga wani gefen take duba, tana maido da dubanta ga Hajiya tai saurin saita kanta tanaci gaba da murmushin yak’e wanda bahaushe ke cewa tafi kuka ciwo... “Aidai da kin bari mun shiga daga ciki, bai kamata matar aure ta lek’o har waje haka ba....” Dakatar da ita Sawwama tai ta hanyar d’aga hannu kana tace “A’a a’a idan wa’azi kikeso maza ki tafi bakin kasuwa ko tasha ba’a nan ba, don na tabbata wa’azinki bazai karb’u a masallaci ba balle nace kije can ki haye mumbari.... Idan kuma sa ido ne ya kawoki toh ki wanke idanunki da kyau don kinada kallo bakiga komai ba tukun.....!” Ta k’arashe cikin salo na juya idanu... Baki sake Hajiya ke kallon ikon Allah, kalan rashin mutuncin da bata tab’a gani ba tsawon rayuwarta... K’arasowar Hafiz wajen ne yasa Hajiya saurin sadda kanta tana mai k’ok’arin saita kanta don bataso ya gano tsantsan tashin hankalin data fad’a, gwara tai k’ok’arin shanye wulak’ancin Sawwama da dai ace ta zama loser.... Yana shafa kai yake duban Hajiyar kana ya saci kallon Sawwama... Tsuka Sawwama tai ta shige ciki abinta tana binsa da wawan kallo... Hafiz tamkar wanda dodonsa ya gifta Sawwama na shigewa yai saurin k’arasowa ga Hajiya yana fad’in “Hajiya sannu da zuwa, ya kika tsaya daga waje, shigo daga ciki mana....” Ya k’arashe yana bata hanya... Kallonsa kurum Hajiya keyi tana hango kalan rama da bak’i da yayi, da ace bataima d’an nata farin sani ba tabbas da tace canzashi akai... Hankalin Hajiya idan yayi dubu ya tashi... Tai saurin tare Hafiz da tambaya... “Hafiz mai ya sameka ciwo ne kayi....?” Tai maganar cikeda tsoro da fargaba... D’an shafa kansa yai had’ida k’ak’aro murmushi kana yace “A’a Hajiya lafiyata lau mu k’arasa ciki.....” Yai maganar yana mai k’ara sauri don kar Hajiya ta kuma jefo masa wata tambayar.... Da k’yar Hajiya Haule ke iya jan k’afafunta da suka mata mugun sanyi har Hafiz ya yaye labulen parlorn suka shige.... Sawwama na hakimce saman doguwar kujera mai d’aukan mutum uku, k’afafu d’aya bisa d’aya sai faman shafa wayarta take... Cikeda d’ari Hajiya ta soma lalumar kujera zata zauna Hafiz na fad’in “Bismillah Hajiya zauna mana...” Kaman mai tsoron kujeran haka take k’ok’arin zama.... Aiko Sawwama kaman jira take ta tari Hajiya da fad’in “A’a a’a ina zaki zauna.... Kinga sauk’a k’asan tile ba kowani shirgi ke d’ale min kujera ba....!” Hajiya ta saki baki tana jira taga hukuncin da Hafiz zai d’auka saima kauda kai gefe dataga yayi yana sosa k’eya... Shikenan an shanye mata d’ah... Duban Sawwama da kyau tai wannan karon domin kaw tazo wuya... Da ‘yar yatsa Hajiya ke nunata kana tace “Amma ke dai bakida mutunci bakida kunya... Ni zaki duba ki wulak’anta in tsuguna in haifi mijinki ki wulak’antani... Kai kuma kana tsaye kana kallo ana min cin kashi baka kikkifawa ‘yar jakar uba mari ba... Toh wllhi kunyi kad’an daga kai har ita... Bokan naki ma yayi kad’an...” Sawwama ta katseta da fad’in “Ki sake kirata maras kunya zan nuna miki rashin kunya tsirarta don na lura har yau baki tab’a ganin rashin kunya zindir d’inta ba mai sutura kike gani...” Hajiya ta shiga zaro idanu waje hannaye dafe da k’irji har lokacin bakinta sake yake wai donma Kausar tayi bacci a bayanta... “Allah....! Eh lallai ikon Allah.... Kai Hafiz saketa ka rubuta saki nace banso ta k’ara ko sakan guda a gidan nan....” Hafiz ya dubi Sawwama dake faman aika masa harara kana ya maidoda dubansaga Hajiya yace “Hajiya gaskiya kiyi hak’uri bazan iya sakin matata ba gaskiya....” Hajiya ta dafe k’irji tana fad’in “Na shiga uku ni Haule.... Hafizu ni nake baka umarni kana cewa bazakayi ba...?” Saiga hawaye na gangarowa daga idanun Hajiya.. Jinjina mata kai Hafiz yayi yace “K’warai kuwa Hajiya idan nabi naki bazan zauna da ko wata mace a duniya ba tinda bakida aiki sai datse min igiyoyin aurena gaskiya bazan saki matata ba...” Ya k’arashe yana hura hanci... Hajiya batasan sanda ta shiga kwance goyon Kausar ba ta dangwala masu yarinyar gabansu tana fad’in “Ga d’iyarka sai kasan gidan uwar da zaka kaita amma bani ba... Shanyayyen banza da wofi... Ke kuma mu zuba nidake, har gaban bokan naki sai kin tafi kina kuka... Haule kikeji baki santa ba...!” Daga haka saita mayafinta tai ta fice tana huci yayinda Sawwama ta saki baki tana kallon Kausar dake kuka Hafiz d’inma Hajiya yabi da kallo har ta fice ga kukan Kausar da ya gauraye gidan gaba d’aya... “Kaga ka tsayar da ita ka bata yarinyar nan don wllhi bazan iya raino ba kaima ka sani, ba a gidan nan ba wllhi....!” Daga haka sa kai tai ta shige d’aki kaman zata tashi sama... Jiki a sanyaye Hafiz ya duk’a ya d’auki d’iyarsa ya aza a kafad’a yana jijjigata a hankali wasu irin tunani da wani abu mai kamada tausayi na yawo a kwanyarsa amma shi kansa bazai iya cewa ga abinda yakeji ba.... Har Hajiya ta shigo gida bata daina ashariya tana dannawa Sawwama da uwarta Magajiya tsinuwa ba... Sahariyya da Najah suka kalli juna lokaci guda suka shek’e da dariya don dama sunsan hakan zata faru idan dai Sawwama ce... Hajiya ta wurga masu harara tana jifa da mayafinta take fad’in “Ku kuma fah uban mai ya baku dariya....?” Suka kuma tintsirewa da dariya.. Hajiya tai k’wafa tace “Aikin banza aikin wofi kuma kuji na fad’a maku wllhi dole ku shiga kitchen ku girka abinci na gaji da bautan ‘ya’yan da ba gani suke ba... Duk fad’i tashin nan kanku nake amma yau wai Hafiz na gani aka d’ibemin albarka wanda tinda uwata ta haifeni ba’a tab’a min irinta ba ya kasa tab’uka komai.. Ohni Haule na shiga uku....!” Ta k’arashe tana mai kamo bakin zaninta tana share hawayen dake zubo mata... Sahariyya ta tab’e baki ta shige d’aki tana fad’in “Wllhi idan za’a mutu a gidan nan bazanyi girki ba...” Najah ma tab’e bakin tai tace “Nidai Allah ya gani karatu nake bazan iya aikatau d’in gidan nan ba...” Ta k’arashe tana mai ficewa waje... Hajiya tabi d’iyoyin nata da kallo had’ida kurma sabon kuka tana furta ta shiga uku.... *** Suna zaune a lambun dake bayan d’akin Abbah a asibitin suna tartaunawa irinta uwa da d’iya wanda suka jima basuyi ba... Mamy ta kuma kamo hannayen Zulfa’u tace “Kar ki damu In sha Allahu zamu ceto rayuwar Kausar daga hannun wad’annan azzalumai, duk yanda zamuyi In sha Allah rik’on Kausar zai dawo hannunmu kinji koh, ki kwantar da hankalinki...” Zulfah ta k’ak’aro murmushi tana mai jinjina kai tace “Toh Mamyna... Allah ya k’addara faruwan hakan...” Mamy ta amsa da Ameen a daidai lokacinda Aunty Lami ta k’araso wajen tana sakin murmushin da iyakacinta fatar baki.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *44* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* KADUNA Sosai Mummy tasha jinin jikinta ganin yanayin Sameer d’in, gaba d’aya ta kasa sakin jiki dashi kaman ba Sameer d’inta ba... Ita gani tayima gaba d’aya ya canza, Sameer matashi mai yalwan fari’a da son jama’a duk ya koma wani iri, da wuya kaga murmushinsa a yanzu, haka nan magana idan ba ta zame masa dole ba bai yinta, da ace batai ma d’an nata farin sani ba sai tace canzasa akai, gaba d’aya tinda yazo zata iya k’irga maganan da ya shiga tsakaninsu.... Misalin k’arfe takwas na dare bayan an ida sallahn lisha ya shigo sashen Mummy, tuni ta fad’ad’a murmushinta dukda a b’angaren Sameer d’in ba haka bane.... “Son an shigo...” Tai maganar tana mai daidaita zamanta saman kujera... Daga can kujeran gefe ya zauna ba tareda ya iya amsata ba sai jinjina mata kai da yai alamun eh... Kafin Mummy ta kuma samun zarafin magana Sameer yace “Daddy fah...? I thought ya dawo gari....?” Yai maganar a tak’aice... Mummy ta d’an dubeshi cikeda kulawa kana tace “Ya d’aga dawowarsa sai next week... Sameer wai dan Allah meke damunka... Talk to me Son...” Ta k’arashe murya cikeda damuwa... D’ago rinannun idanunsa yai yana dubanta lokaci guda yanajin wani irin zafi da k’una cikin k’irjinsa, yana son Mummy sosai, soyayya irin wacce d’ah keyiwa mahaifiyarsa amma ace ba itace mahaifiyarsa ba bayan tsawon rayuwarsa kan hakan ya taso, ta tabbata Mummy ba itace mahaifiyarsa ba, shekaru talatin da d’oriya ita ya tashi ya gani matsayin mahaifiya a gareshi, sannan tai masa rik’o irin wanda bazai tab’a kawowa cewa ba itace ta haifeshi ba, gwanda Daddy ma wasu lokutan bai d’aukan al’amaransa da mahimmacin kaman yanda Mummy keyi.... K’uri ta masa tana jiran mai zaice ga k’irjinta dake tsananin bugawa ganin sam babu wasa a tattareda fuskarsa... Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Mummy I’m going to ask you for the last time.... Mummy tell me, how am I related to you....?” K’uri Hajiya Fatahiyya ta masa idanunta na k’ok’arin kawo ruwa kaman yanda na Sameer d’in suka ciko da ruwa.... A hankali Mummy ta taso ta dawo kujeran da Sameer ke zaune, kanta a k’asa tana goge hawayen da suka gangaro mata, a hankali ta kuma d’agowa tana dubanshi shid’inma ita yake duba.... “Sameer my Son..... Na sani duk daren dad’ewa rana irin wannan zata riskeni, ranan da zan bud’e baki na fad’a maka cewa banice na haifeka ba...!” Suk’e ajiyan zuciya Hajiya Fatahiyya tai kana taci gaba da fad’in “Amma ka sani badason raina zan sanar dakai labarinka ba saidon dole, sirrin dake rufe shekaru da dama ya tono kansa, zan sanar dakai komai amma sai kamin alk’awari zakacigaba da kasancewa d’ah a gareni....!” Ta k’arashe cikin murya irinta mai kuka wanda yasa Sameer sanda kansa k’asa zuciyarsa na tsananin masa rauni... Ya jima a haka yana jiyo sautin jan numfashin Mummy irinta mai kuka wanda hakan ke tsananin sosa masa zuciya kana yaci gaba da sauraro muryarta tana ci gaba da fad’in “Shekaru talatin baya ka zamto d’ah a garemu nida Daddynka.... A wancan lokacin ahekarunmu kusan biyar da aure nida Daddynka amma Allah bai bamu haihuwa ba, asalina mutuniyar Dutsimma ce ta jihar Katsina kaman yanda ka sani Dad d’inka mutumin asalin garin Gombe ne.... A wancan lokacin dangin mijina sunyita kwad’aitar masa cewa ya sake aure ko zai samu haihuwa amma baiyi hakan ba ko nace Allah bai k’addara ba, kullum ina cikin kuka da damuwa na rashin haihuwa alhali shi Dad d’inka sam bai nuna damuwansa akan rashin haihuwata saidaima yaita k’arfafa min gwiwa yana sanar dani idan da rabo zamu samu gaba, sannan duk abinda kaga Allah ya hana bawansa yasan dalilinsa nayin hakan, da kalaman Dad d’inka masu tausasa zuciya nakan samu natsuwa, dukda cewa sam ban tsira hannun danginsa ba wajen gori habaici da maganganun marassa dad’inji... Ana haka kwatsam watarana mahaifinka ya samu aiki garin Dutse ta jihar Jigawa, wannan shine dalilin da yasa na sami sauk’i daga tsangwaman dangin miji, muka tattara muka dawo garin Dutse da zama ba tareda mijina yayiwa danginsa sallama ba domin kuwa tinda yak’i bin shawarinsu cewa ya sake aure duk sai suka juya masa baya, babu mai shiga hidimarmu sannan babu mai gayyatarmu hidimarsa, sosai abin yayiwa Dad d’inka zafi, mahaifansa duk sun rasu balle ya masu sallama saiko dangi wad’anda suke ‘yan uba......” Hajiya Fatahiyya ta d’anja fasali kafin taci gaba da fad’in “A shekararmu ta biyu a garin Dutse kazo cikin rayuwarmu, wanda ka kasance fitilar da ya haskaka mana rayuwa, mafarin farin cikinmu snnan mabud’in alkhairanmu....” K’walla suka ci gaba da gangarowa Hajiya Fatahiyya sanda taci gaba da fad’in “Dumba....!” Sai ta kuma jan fasali tana duban Sameer d’in wanda shima ita yake duba.... Mummy ta sadda kanta k’asa a hankali tana goge hawayenta kana taci gaba da fad’in “Wata rana Dumba tazo dakai rik’e a hannunta... Kanata kuka kana ambaton Mamynka, lallashin duniya Dumba tai maka kak’iyin shiru, niko ina daga window ina hango dramarku da Dumba, tausayin k’aramin yaron ya kamani sosai, na shiga d’aki yanda nake ajiyan biscuit da alawa na sadaka ma yara don d’abi’atace tuntuni tausayin yara k’anana da kyautata masu, na d’auko maka biscuit guda na bud’e na baka, tuni ka amsa kana ci ka saki hannun Dumba ka kamo hannuna ka kwanta cikin jikina kana cin biscuit d’inka har bacci yayi gaba dakai kana kwance cikin jikina, Dumba ta sami daman tashi ta gudanar da ayyukanta domin fir kukanka ya hanata sakat....” Cikin rawar murya Sameer ya katse Mummy da fad’in “Wacece Dumba...? Meye alak’ata da ita...?” Yai maganar hawaye na gangaro masa... Sauk’e ajiyan zuciya Mummy tai kana taci gaba da fad’in “Zakaji komai In sha Allah Sameer...” Lokaci guda taci gaba da fad’in “Na d’aukeka na kaika bisa gado na bayan kayi baccin, na zauna daga gefe ina kallon kyakkyawar fuskarka data cika da tsoro alamun wani babban al’amari ya matuk’ar firgitaka dukda k’aranci na shekarunka... Sanda Dumba ta ida ayyukanta nan take ce min zata d’aukeka ku tafi... Gaba d’aya Dumba ban gane mata ba a wannan ranan don da alama cikin tashin hankali take itama... Na tsareta da idanu kana na jeho mata tambaya... Dumba shin ina kika samo yaro...? Dumba ta shiga rarraba idanu kana tace “Hajiya rainonsa aka kawo min...” Na dubeta sosai kana nace anya Dumba ki sanar dani gaskiya ina mahaifiyar yaron nan yake kuka irin haka... Idan bakiso na kira miki ‘yansanda tun wuri gwara ki sanar dani gaskiyar lamarin.... Dumba ta shiga rarraba idanu ganin da gaske nike saita sanar dani yanda ta samo yaro ta duk’a har k’asa tana bani hak’uri tana fad’in zan sanar dake gaskiya Hajiya... Yaron nan rayuwarsa cikin had’ari take, yanzu haka aminai uku sun zaci ya jima a barzahu Hajiya ni kuma bazan iya kashe rai ba.... Naci gaba da dubanta da tsananin mamaki kana nace Dumba ban gane ba... So kike kicemin ked’in kwangilar kisa aka baki...? Kan Dumba na k’asa hawaye na d’igo mata tace k’warai kuwa Hajiya amma wllhi bazan iya ba don ban tab’a kashe koda k’aramar dabba ba ballanta d’an mutum k’aramin yaro kaman wannan wanda bashida hakkin kowa, na zab’i na barshi a raye ba kaman yanda sukai zato ba... Saidai bansan yaya zanyi dashi ba bansan ina zan b’oyeshi ba nayi tunanin idan ya k’ara girma kad’an na turashi almajiranci ta chan k’asashen Chadi yanda zai b’ace daga duniyarsu har abada.... Tinda Dumba ta soma magana hawaye ke zubo min had’ida tsananin tausayinka....” Mummy ta sauk’e ajiyan zuciya kana taci gaba da fad’in “Sameer ni na buk’aci Dumba ta barmin rik’onka a hannuna, aka kuwayi sa’a da maigidana ya dawo ya taddaka taredani gwanin ban sha’awa yanda ka sake dani kana amsan abincin daga hannuna, yayita mamakin ina na samo yaro nan na zayyane masa komai, shid’inma tausayinka ne tsantsan ya kamashi amma sai yace bazamu bi maganar Dumba haka kurum ba gwara mubi diddigi muji ina ta samo yaron nan don kardai ma sato shi tayi mutum a yau abin tsoro ne, watak’ila dangin yaron nan iyayensa nata nemansa wata k’ila ‘yansanda ke neman Dumba ta shirya wannan labari, nabi shawarin mijina washe gari muka tafi gidan wacce ta samo mana Dumba matsayin ‘yar aiki saidai bamu sami labari mai dad’i ba domin kuwa ita kanta dillanci masu aiki take sannan ta sanar damu ita kanta batasan ina zata samu Dumba ba, nan na soma yarda da maganganun mijina, wata k’ila Dumba mugun nufi ne tattare da ita, neman duniya munyi bamu sami Dumba ba gashi batako sanar damu sunanka ba, nida mijina muka yanke shawarin kiranka da suna Sameer, da fari Dad d’inka yaso a damk’a ka hannun hukuma ko cibiyar kulada marayu amma fir nak’i hakan nace nidai Allah ne ya bani d’ah daga sama, a dole ya amince da buk’atata muka rik’eka matsayin d’anmu, a wannan lokacin Dad d’inka ya sami aiki a jami’ar Amurka muka d’unguma muka nufi gida Gombe donyi masu sallama sunyita mamakin ganin mu da yaro kasancewar mun d’au shekaru ba tareda sunsan yanda muke ba hakan yasa sukai zaton ko haihuwa nayi wasu sukai ta cewa k’ila da ciki na tafi kenan, masu mana murna suka mana masu nuna bak’in cikinsu sukai, nan dai muka sanar masu sallama mukazo yi masu zamu koma k’asar Amurka da zama na wasu lokuta, duk duniyar nan bayan Dumba da bamusan yanda zamu sameta ba saiko aminiyata Farida su kad’aine sukasan cewa bamu ne muka haifeka ba.....!” Mummy ta k’arashe tana matse k’walla da bakin zaninta... Yayinda Sameer kansa ke k’asa hawaye naci gaba da gangaro masa tambayoyi da dama suna neman tarwatsa masa kwanya... A hankali ya d’ago ya dubi Mummy dake d’igan hawaye wani irin tausayinta da k’aunarta ya lullub’esa.... Jiki a sanyaye ya mik’e ya isa ga Mummy ya durk’usa had’ida d’ora kansa saman cinyarta yana kuka sosai, itama d’in kukan take sosai... Cikin muryar kuka yake fad’in “I’m sorry Mummy, Mummy I’m sorry... Dan Allah ki yafemin, hak’ika banida gatan data wuceki a fad’in duniyar nan, da ace baki amsheni ba k’ila da yanzu an kasheni kokuma an turani wani k’asar almajiranci kaman yanda wancar matar tace... Mummy banida abinda zan biyaku keda Daddy.... Allah shi kad’ai zai iya maku sakayya.....” Rik’o fuskar Sameer mai zuban hawaye tai itama tana hawayen take fad’in “Sameer ka daina mana godiya, har gobe kai d’ah ne a garemu koda ka sami asalin iyayenka ka sani har abada zakaci gaba da kasancewa d’ah a gareni... Sameer ka kawo haske da farin ciki ma rayuwata wanda na rasa a baya... Har abada kai d’anah ne koda ace ban haifeka ba amma a zuciyata you’re my only son.....!” Gaba d’aya suka kuma fashewa da kuka had’ida rungume juna... Idan ka gansu sai sun baka tausayi, cikin zuciyarsa yake maimaita AMINAI UKU, Ya sha alwashin INDA RAI sai ya binciko su waye Aminai uku su waye suka rabashi da iyayensa da danginsa, su waye sukai farautar rayuwarsa shekaru talatin baya........!” *** K’arfe biyu daidai ya sauk’a a garin Kano ko sallama baiyiwa Ammi ba ya fice abinsa, bai zarce ko ina ba sai gidan Mamani, aiko taji dad’in ziyarar tasa sai haba haba dashi take tana fad’in “Lale Haladu d’an gayu....” Tuni ta umarci Raihana data kawo masa abinci da abin sha... Tana ida kawo masa taceda Mamani zata sashen su Marliya lokacin kai abinci asibiti yayi zasu kai abincin Abbah... Mamani ta jinjina mata kai kana tace su kula da hanya itama tana nan tafe idan rana yayi sanyi..... Raiha ta amsa mata cikeda ladabi kana ta fice... Duban Mamani yai kana yace “Mamani waye babu lafiya...?” Mamani tace “Abbansu ne ke asibiti yau kwana biyu kenan...” Khalid ya d’anyi shiru kaman mai nazari har Raiha ta kusan k’ofar fita daga sashen Mamani yaceda Mamani su tsaya zai kaisu asibitin... Mamani tace “Kai Haladu da d’awainiya haka...” Khalid ya kurb’i ruwan gabanshi yace “A’a haba dai ai babu komai Mamani....” “Ayya Haladu yaron arziki....” Ta d’an bud’e murya ta kira Raiha tace “Maza kicewa ‘yan uwan naki za’a kaiku koh, ku jirashi yana nan fitowa...” Raiha ta amsa had’ida jinjina kai kana ta nufi sashensu Nabila... Mamani ta dubi Khalid dake k’ok’arin mik’ewa nan ta hangi rama da ya d’anyi shima.. Turus tai tana dubansa kana tace “Haladu lafiya kake kuwa... Jibi yanda ka rame ba kaman wancan lokacin da na ganka ba sannan d’an walwalan da kake yanzu du babu lafiya dai koh...?” K’ak’aro murmushi yai yana ciro car keys d’insa daga aljihu yace “Babu komai Mamani kawai dai gajjiyan hanyace, barinje mu duba Abban...” Mamani ta jinjina kai ba wai don ta yarda dashi ba tace “Toh abincin fah....?” Nan ma cewa yayi sai sun dawo yaci, Mamani dai dubansa take gaba d’aya kaman wani abin na damunsa, fatan alheri da adawo lafiya tai masu kana ya fice... Nabila ta dubi Raiha kana tace “Bak’on Mamanin ne yace zai kaimu....?” Raiha ta jinjina kai tace “Eh Addah Naby inagama ya fice tuntuni mu yake jira....” Daidai nan Marliya ta fito da basket na abinci tace “Mujenku koh...” Itadai Nabilah dubansu kurum take kafin ta zira takalmanta ta biyo bayansu don tuni Marliya da Raiha sun fice... Suka gaidashi ya amsa masu da sakin fuska kana ya bud’e masu backseat suka shige... Yaja ya tsaya yana jiran fitowarta... Tana tafe tana gyara zaman wuyan hijab d’inta kaman wacce akace ta d’ago idanu nan sukai ido hud’u yana tsaye ya hard’e hannaye fuskar nan tamau babu alamun walwala yana jifanta da firgitaccen kallo... Take ta d’aure fuska itama sai sakin huci tana tuna cin zarafin dasu Yesmin suka mata akanshi..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *45* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kaman zata sa kai ta juya sai ta jiyo muryar Marliya tana fad’i mata ta k’araso su tafi.... Ta d’an d’auki wasu dak’ik’ai tana tsaye kaman bazata motsa ba sai kuma ta dawo da baya, Khalid yana ganin haka ya bud’e mota ya shige... Itako Nabila tana k’arasowa ta nufi back seat saidai taji marfin motar a kulle, da shike glass d’an a zuge yake hakan ya bata daman danna masa harara daga cikin mirror shid’inma ita yake duba fuska babu walwala, bai tankata ba sai bud’e mata front seat da yai.... Marliya na dubansu tana karantarsu tabbas ko ba’ace ba wannan shine saurayin da Nabila ke ambatonsa, ikon Allah ashe ba Abbah kawai ba harta Mamani ya sani, Marliya tace cikin zuciyarta... Idanunsa a kanne yake dubanta, bataso ‘yan uwan nata su fahimci wani abu, hakan yasa ta nufi frontseat tana tab’awa kuwa ta jita a bud’e, fuska a tamke babu walwala ta shige.... Kaman wanda yake jira tana shigewa yaja motar ya soma tafiya... Bakajin komai sai sautin music dake tashi a hankali cikin motar.... Marliya ce kurum da Raihana ke magana jifa jifa a b’angaren Khalid da Nabilah kuwa kowa da abinda yake sak’awa cikin zuciyarsa... Tafiyar da bata wuce ta mintoci ashirin zuwa ashirin da ashirin da biyar ba ta kaisu asibitin.... Marliya da Raiha suka masa godiya suka sauk’a suka nufi cikin asibitin da kwandon abincin... Kafin Nabilah tai wani katab’us da niyyan fita saiji tai ya saka motar lock... Ta kuma jan handle d’in taji tabbas a kulle ne.... Tsananin takaici ya kuma cikata... Fuska a tamke ta juyo tanai masa wani irin duba.... Cikin tsantsan kufula take dubansa... Ba tareda ya dubeta ba yace “Tell me is it true....?” Da tsananin mamaki ta kuma dubansa zuciyarta na kuma tafasa... Cikin tsananin fushi take fad’in “Kaga malam ka bud’e mun k’ofa na fi....” Batakai aya ba ya katseta cikin tsananin fushi da d’aga murya lokaci guda ya juyo da fuskarsa yana dubanta... “I’m asking you to tell me the meaning of this...!!” Ya k’arashe yana nuna mata hoton video d’in dasu Siyama suka mata yara na mata wak’an karuwace.... Zuciyarta taci gaba da sosuwa tamkar zata fito waje, take taji k’walla na neman ciko idanunta... Banda watsa mata muguwar kallo Khalid baya komai, jin tayi shiru ya sanyashi jinjina kai had’i da sakin gajeren murmushi kana yace “So it is true.... Da gaske ne kenan... Why Teddy Bear....? Meyasa... Meyasa...? Why did you choose to break my heart.... Tell me why..!!!?” Ya k’arashe tamkar wanda zai shak’o wuyanta... Cikin tsananin tafasan zuciya idanunta na zubar da k’walla take fad’in “This is all your fault, da ace baka shigo cikin rayuwata ba da babu wanda zaimin wannan cin zarafin, meyasa baka tambayai wad’anda suka tura maka ba idan gaskiyace ko akasinta... Why do you even care...? Meye had’ina dakai meyasa bazaka k’yaleni ba ka fice a rayuwata ba... Ni Nabilah ban tab’a giving up ma fad’a ba sai akanka.... Why just can’t you stay away, why is it so hard for you...!?” Batakai aya ba ya katseta da fad’in “Because I Love you.... I love you so much, abinda kike tambaya ba mai yuwa bane... Ina Sonki Nabeelah....” Ya k’arashe cikin tsananin huci yana mai kallon k’wayan idanunta mai zuban hawaye.... A hankali tasa bayan hannunta tana goge hawayen kana tace “Please ka bud’e min na fice...” Tai maganar cikin tsananin sanyin murya... Ya d’auki wasu dak’ikai yana duban yanda jikinta yai sanyi sosai kafin yasa hannunsa akan security lock d’in ya bud’e... Har ta shige cikin asibitin tana matsan k’walla kalaman ina sonki da Khalid ya fad’i mata basu daina yawo a kwanyarta ba.... Da k’yar ta iya saita kanta kana ta nufi ward d’in da Abbah yake don sam bataso iyayen nata su gano wani abu.... Da sallama saman bakinta ta shigo d’akin, saidai tsananin sanyi jikinta yai ganin gaba d’ayansu idanunsu akanta ne... Nabilah tasha jinin jikinta domin kuwa tasan dole Mamy ta tambayi ina ta tsaya ga ‘yan uwanta tuni sun shigo, duba d’aya zakaiwa Mamy ka fahimci magana ne sosai a bakinta, su Marliya ma duk sunsha jinin jikinsu don har tunanin shigowar Nabilar suke.... Fitowar Abbah daga bayi ne ya ceceta Mamy ta had’iye tambayar da tai niyyan jefo mata ta k’arasa domin taimakawa mijinta.... Gaba d’aya suka rusuna suna gaida Abban sai amsa masu yake da sakin fuska yana fad’in su k’araso kusansa sosai su gaisa don ya shirya gina wata shak’uwa ta musamman da yaransa.... Abbah yace Mamy ta huta yaransa suyi serving nasa, jiki har rawa yake Nabilah ta mik’e tana k’ok’arin serving Abbah cikedajin dad’in yanda Babansu ya canza, tanayi tana satan kallon Mamy da har lokacin muguwar kallo kurum take aika mata.... Abbah sai jan yaran nasa da fira yake yana tambayansu abubuwa sosai gameda rayuwarsu musamman gameda karatunsu, gwanin ban sha’awa.... Knocking da akai a k’ofa ya d’an katse masu firan nasu, Mamy ta bada izinin shigowa, ya shigo sallama saman bakinsa wasu samari guda biyu suka biyo bayanshi da carton d’in ruwa da nau’in lemu har kashi uku.... Suka gaidasu suka fice... Khalid ya k’arasa shigowa Mamy tanai masa nuni da farar kujeran dake gefe, k’irjin Nabila sai faman lugude yake, Abbah yaso ganesa bayan sun gaisa nan Khalid d’in ke sanar dashi abokin Sameer ne da suka tab’a kai masa ziyara tare a gida... Nan fah aka soma sabon gaisuwa musamma da Abbah yaji cewa abokin Sameer ne.... Marliya ta k’arada fad’in shinema ya kawosu... Nabilah ta jefa mata kallo aiko itama kallon tuhumar Mamy ke mata.... Gaba d’aya ta kasa sakewa alla alla take ya tashi ya tafi, batasan uwar gulmar daya shigo dashi gaida Abbah ba da alama saida ya tsallaka kanti tsallake yayo sayayyan sannan ya shigo, wani irin muguwar haushinsa ke d’awainya da ita..... Mamy dai bata wani sake da Khalid d’in ba kaman yanda Abbah ya sake dashi, bai wani jima sosai ba ya masu sallama had’ida fatan samun sauk’iwa Abbah... Har suka k’araci zamansu Mamy bata sakewa Nabilah ba ita kanta tasan had’uwarsu da Mamy bazasu wanye lafiya ba she had a lot to explain to her... Daga nan ne suka tambayi Mamyn cewa zasu biya gidan Baba Alhaji su duba Kausar hakan yayi mata don dama suna k’ok’arin shirya randa zasu d’auko yarinyar itada Zulfa’u saidai sabida ciwon Abbah suka dakata sai ya sami sauk’i kar a kuma k’ara masa damuwa kan wata damuwa tinda tasan zai wuya Hajiyar Hafiz ta basu yarinyar cikin sauk’i.... *** Sun k’ule itada Lami a uwar d’aki suna tattauna lamarin, su k’ulla wannan su sak’a wancan kaman daga sama suka jiyo hayaniyar Sahariyya tana faman bambami, Hajiya da Aunty Lami suka dubi juna a tare, a tamanin Hajiya ta mik’e tana gyara d’aurin zani ta nufo waje Aunty Lami na take mata baya... Sahariyya ta kasa ta tsare tana d’aga k’irji sama tana ci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Billahillazi baki isa ba ba’a haifeki ba Kausar ta fiki gadara da gidan Ubanta, tinda ko yaushe yaga dama zai iya sallamarki kaman yanda ya sallami uwar yarinyar....!” Sawwama tai tak’aitaccen murmushi kana takai dubantaga yanda su Hajiya ke tsaye, lokaci guda ta gyara tsayuwarta had’ida tallabo Kausar dake rik’e a hannunta, cikin yatsina fuska had’ida kuma turo kallabinta gaban goshi tai nuniga Hajiya da ‘yar yatsa kana ta kuma duban Sahariyya tace “Kinga ko wancan ma haka tai ta bari, ki tambayeta kiji idan ta isa ta saka Hafiz ya sakeni.... Balle ke k’aramar ‘yar iska k’aramar marar kunya wacce ko ajin farko baki ida ba...!” Ba Sahariyya data saki baki tana duban ikon Allah ba harta Aunty Lami da Hajiyar Hafiz d’in tsaye sukai tamkar gumaka suna duban Sawwama wacce ta zame masu tamkar dodanniya.... Cikin taku na k’asaita ta k’araso gaban Hajiya kana ta dangwala mata Kausar tana mai fad’in “Gata nan.... Ai dama na fad’i maki kada kiyi gigin barinta gidana domin batada muhalli cikinsa sannan ba raino aka auroni nayi ba rainon d’anki da nake idan baki gode min bazaki k’aromin ba... Gata idan kunga dama ku jefarta waje amma wllhi wllhi kunji na rantse ba cikin gidana ba....!” Tasa kai tana k’ok’arin juyawa, banda huci da tafasa Sahariyya bata komai, duban Hajiya kawai take tana jira taga matakin da zata d’auka bataga alamun Hajiya zata motsa ba... A d’ari Sahariyya ta sunkumo Kausar tana fad’in “Wllhi billahillazi kinyi kad’an ki shigo har cikin gidan mahaifina kiciwa mahaifiyata kashi aka k’aramar karuwa, wllhi k’aryar iskanci kike Kausar bata gida sai gidan mahaifinta....!” Dariyar rainin hankali Sawwama ta d’anyi a tak’aice tana mai watsawa Sahariyya muguwar harara lokaci guda ta d’aga hannu ta d’auke Sahariyya da wata shu’umar mari wanda saida yasa tai kusan sakin Kausar a k’asa... A daidai lokacinda su Nabila su Raiha suka shigo gidan da sallama.... Tukunyar tafasheshen ruwan d’anwake dake gefe sai faman tafasa yake Sahariyya tai kan Sawwama tana k’ok’arin cakumota had’ida jifa da Kausar da batamasan ina take k’ok’arin jefata ba... Cikin wani irin zabura Raihanah ta saki k’ara ta nufi Kausar da tuni tayi ambaliya cikin ruwan d’anwaken nan, tukunyar ta hantsilo ta zubewa Raihanah a b’angaren jikinta a yayinda take k’ok’arin ceto rayuwar Kausar... Wani irin k’ara Raihanah ta saki sanda ta rungume Kausar da tuni kukanta ya d’auke cak.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Nabila da Marliya daskarewa sukai cikin tsananin tashin hankali yayindasu Hajiya suka d’imauce lokaci guda, harta Sahariyya da Sawwama saida suka tsaya cak da fad’an da suke suna duban Raihana da Kausar da tuni sunyi wanka da tafashesshen ruwan d’anwake.... Zulfah dake k’ok’arin saka k’afafunta cikin ward d’in Abbah wani irin bugawa k’irjinta yai jiri ya kusan aikata k’asa ba tareda sanin dalili ba, da dafe ta ida shigowa cikin ward d’in..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *46* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Aunty Lami ce tai kazar kazar aka kwashesu zuwa asibitin masu fama da matsalar k’unan wuta.... Gaba d’aya su Nabilah Hajiya da Marliya harmada Sahariyya suka d’unguma suka take masu baya... Suna isa asibiti aka wuce dasu emergency.... Dr Awwab abokin aikin Sameer a nan asibitin Kanon shi ya amshi case d’in nasu, saidai gaba d’aya shi kansa lamarin ya shige masa duhu musmman Kausar wacce ta k’one sosai domin kuwa idan ba sa’a ba k’unan ka iya tab’a zuciyarta kuma idan har hakan ne ta kasance yasan abu ne mai matuk’ar wahala ta tashi saidai wani ikon Allah musamman duba da k’aranci na shekarunta da tsananin taushi da fatarta kedashi, a sani hakan yasa dole ya nemi taimakon Sameer domin kaw babu kaman shi a asibitin wajen sanin fata da gyaranta.... Sameer yana gab da shigowa garin Kano akai masa waya daga asibiti cewa akwai emergency.... Bai wata wata ba ya wuce asibitin domin ceton rayukan bayin Allah da suka sami had’arin wuta.... A b’angarensu Nabilah kuwa suna reception kowa da addu’an dake bakinsa dukda cewa babu wanda ya iya tsagaita hawayensa, Aunty Lami ce mai k’arfin hali tana dnnanrsu don harta Hajiya dirshan tai a reception d’in tana matsan k’walla da bakin mayafi tana fad’in ta shiga uku ta lalace sun kashewa Hafiz d’iya.... Kukan nata banda k’ona ran Nabila baya komai ji take tamkar taje ta rufe Hajiya da duka don takaici... Aunty Lami ce tai k’arfin halin kiran Mamy ta sanar da ita halin da ake ciki da kuma asibitin da suke... Banda salati da ambaton Allah Mamy bata komai, sauk’in abin Abbah yana bacci baisan abindake faruwa ba, Mamy na cikin yanayin ne Zulfah ta turo k’ofa ta shigo da alama daga wajen aiki take, kallo guda taiwa Mamy ta kuma jin gabanta ya mugun fad’uwa.... A b’angaren Mamy ma duban Zulfa’un da tai si taji zuciyarta ta kuma yankewa, ta kasa jurewa domin kaw idanunta sun gaza b’oye hakan.... Cikin tsananin sanyin jiki Zulfah tace “Mamy lafiya ya na ganki haka kodai jikin Abbah ne....?” Mamy ta kasa jurewa sai k’walla da suka ciko idanunta, cikin sauri ta janyo hannun Zulfah suka fice daga d’akin gudun kada Abbah ya tashi.... Saida tai k’ok’arin kwantarwa Zulfa’u hankali kafin ta sanar da ita halin da ake ciki.... Tuni k’walla sun ciko idanunta, ta kuma duban Mamy tana mai k’ok’arin goge hawayen dake zubo mata take fad’in “Mamy duk laifina ne meyasa na bar masu d’iyata, meyasa na barta babu kula....!” Kuka yaci k’arfinta... Rik’eta Mamy tai ta zaunarta saman kujera dake gefe, cikin sigan lallashi da lallama take fad’in “Kar kice haka Zulfa’u, komai muk’addari ne daga Allah... Tuni Allah ya hukunta hakan, yau koda Kausar na taredake bazata wuce abinda Allah ya k’addara mata ba, kiyi hak’uri muyi masu addu’a Allah Ubangiji ya basu lafiya, yanzu ki tashi na kira Bara’atu zata taho ku tafi ku duba jikin nasu kinga ni bazai yuwu na tafi na bar Abbanku ba... Zulfa’u ki kwantar da hankalinki kinji koh don Allah kada ki d’aga hankalinki...” Banda jinjina kai Zulfah bata komai sai matsan hawaye da take... Jim kad’an Aunty B ta iso a fujajan suka wuce asibiti.... *** Kasancewar Kausar tafi jin jiki domin kaw gaba d’ayanta ta fad’a cikin tafashesshen ruwan danwaken sannan dashike k’aramar yarinyace sosai fatarta akwai taushi sosai hakan yasa k’unar yafi mata illa, Sameer na isowa ita suka soma attending, take aka preparing surgery aka shige da ita.... Sosai k’unar ya shiga jikin yarinyar domin kuwa ya riga da ya tab’a heart d’inta, sanda Sameer ya fuskanci k’unar ya shiga sosai take jikinsa yai sanyi domin yasan zai wuya yarinyar takai labari, Allahu Akbar ai kuwa basu jima da soma aikin ba zuciyar Kausar ta daina bugawa... Baisan dalili ba amma har ransa yaji mutuwar yarinyar, jikinsa yai matuk’ar yin sanyi, ya saba da irin hakan tinda ba yau bane ya soma aikin likitanci amma mutuwar wannan yarinyar a hannunsa yayi bala’ain d’aga masa hankali.... A hankali ya zame hannayensa yana mai k’urama na’urar dake nuna tsayuwan bugun zuciyar idanu... Dr Awwab ya girgiza masa kai alamun babu ta riga ta rasu.... Sameer ya lumshe idanunsa a hankali kana suka nufo waje shida Awwab sauran nurses na k’ok’arin shirya Kausar... A bakin theatre room d’in suka tsaya bayan sun kwab’e mask d’in dake bisa hancinsu da bakinsu suna tattauna lamarin yanda Awwab ke sanar dashi family d’in suna reception... Sameer ya jinjina kai yace “Kace su biyu ne masu case d’in...?” Awwab ya jinjina kai yace “Yes su biyu ne babbar tana ward nata bai shiga deep kaman na ita wannan k’aramar ba....” Sameer ya d’an jinjina kai a hankali kana yace “Ok ka sanar da nurses d’in they should get the second patient ready zan k’arasa nai magana da family d’insu....” Awwab ya jinjina kai yace “Ok sai ka iso....” Jinjina masa kai kurum Sameer yai kafin ya nufi reception... Zulfa’u da Aunty B suna isowa Su Marliya da Nabilah suka k’arasa a guje suka rungume Addarsu suna kuka... Aunty B kuwa banda jifa da kallo tskaninta dasu Hajiya bata komai, jira kawai take taji silan k’unan taji su waye sukai sanadi.. Zulfah ta kuma karaya ganin ‘yan uwanta sun rungumeta suna kuka, cikin tsananin rawar murya take furta “Nabilah ku fad’a min ina Kausar da Raiha...? Dan Allah ku fad’a min d’akin da suke naje na gansu....” Wani irin bugu Sameer yaji k’irjinsa nayi sanda ya danno reception yai tozali da mutanen da bai jima da sanin cewa ‘yan uwansa bane... Zulfa’u Nabilah da Marliya yake duba da raunannun idanunsa yanda suka rungume juna suna kuka.... Yana jiyo sanda Zulfah ke fad’in ina d’iyarta...? Zuciyarsa ta kuma karyewa... Kenan yarinyar ‘yar uwarshi ce ta rasu a hannunsa... Ta yaya zai soma sanar da ita cewa d’iyarta ta rasu... Shin wannan shine farkon abinda zai soma had’asa da ‘yan uwansa... Mummunar labari irin wannan, ta yaya zai iya jurewa ya tink’ari ‘yan uwansa da wannan batu...? Tsananin tausayinsu gaba d’aya shida ‘yan uwan nasa ya rufe masa zuciya.... A hankali ya soma takawa har ya isa garesu yai tsaye ba tareda sunsan cewa wani na tsaye kansu ba.... Aunty B kuwa nata aikin lallashinsu tana fad’in addu’a zasuyi ba kuka ba In sha Allah Kausar da Raihanah zasu sami lafiya.... Su Hajiya suna hango shi yayi tsaye suka nufi kansa suna tambayarsa Hajiya na fad’in “Likita ina jikata...? Ka fad’a mini ina tak...?” Muryar Hajiya ya sark’e sanda tai idanu hud’u da mutumin da ya bayyana gabanta matsayin likita, zuciyarta ta shiga harbawa da sauri, tsoro da firgici suka bayyana mata.... Ta soma tunanin kodai Ma’aruf gizo yake mata... Tsananin tashin hankali ya wanzu a tattareda Hajiya... Idanu hud’u sukai itada Aunty Lami wacce itama hakance ta kasance da ita, ko shakka babu su biyun suna buk’atar keb’ewa su tattauna lamarin Ma’aruf wanda ke barazanar tarwatsa masu rayuwa... Maganganun Hajiya ya dawo da hankulansu, gaba d’aya kallon sani suke masa... Sahariyya kaw tuni jikinta ya d’au rawa har ta mance mai ya kawosu asibitin ta shiga bin Sameer da mayen kallo tana yank’are baki had’ida komad’a ita kad’ai... Tabbas ba gizo yake mata ba wannan na nuni da alamun cewa shid’in nata ne da sannu zai zama rabonta tinda gashi Allah ya kuma had’asu, ita kad’ai sai sakin murmushi take tamkar tab’ebb’iya... Zulfa’u tai k’arfin halin maimaita tambayarta “Dr how’s my daughter.... How’s she doing.... Ina take dan Allah.. Shin zamu iya ganinsu...?” D’an jim Sameer yayi ba tareda ya iya furta koda kalma ba sai kallo da yake bin Zulfa’u dashi yana hango wasu abubuwa nasu dake yanayi... Cikin hawaye tana mai goge fuskarta take fad’in “Dr kamin magana dan Allah... Kace wani abu.... kace zamu iya shiga mu gansu na rok’ek’a dan Allah....” Kasa furta komai Aunty B tai sai k’ura masa idanu da tayi idanunta na k’ok’arin kawo ruwa.... Cikin sauri ta k’unshe bakinta jin kuka na k’okarin b’alle mata ta fice daga wajen tana mai sakin kukanta, tabbas wannan d’an ‘yar uwartace da ya b’ace shekaru talatin... Allah ya dawo dashi, tabbas ba gizo yake mata ba shid’in ne Ma’aruf ne... Zataso ta zamto mutum ta farko da zata tabbatar da hakan ko don takai wannan labari mai dad’i ga ‘yar uwarta wacce ta rasa farin cikinta da walwalarta shekaru talatin baya.... A tare Hajiya da Aunty Lami suka zame jiki suka fice daga reception din cikin tsananin d’imauta da damuwa... Yanda suke sauk’a daga dakalin k’ofar reception d’in zai tabbatar maka cikin tsananin tashin hankali suke... Aunty Lami hannu biyu dafe da k’irji take fad’in “Haule Haule mun shiga uku abinda muka shuka shekaru talatin shike farautarmu, Haule ba gizo yake mana ba wllhi shine....!” Cak ta tsaya da kalamanta sanda tai idanu hud’u da Aunty B itama sud’in take duba idanunta d’auke da hawaye...... SameenaAleeyou...📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *47* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin tsananin fuci Aunty B ta tunk’arosu, tana mai gyara fuskarta, murmushin takaici saman fuskarta... Kai tsaye ta fuskanci Hajiyar Hafiz tana mai fad’in “Hankalinki ya kwanta burinki ya cika kin kashe Kausar, nasan da ace kin samu dama tin daga fari da kin kashe Zulfa’u ma amma saidai Allah k’addara mutuwar Zulfa’u hannunki ba.... Shin Haule wace irin ‘yar Adam ce ke...? Shin ashe har zaki iya halak’a jikarki jininki da hannayenki.... Ko zaki musnta min k’unar dasu Kausar sukai ba yinki bane iye....? Kiyi magana mana ya kikai shiru.....???” Ta k’arashe tamkar zata damk’o wuyar Hajiya.... Hajiya ta saki murmushi wanda yafi kama da yak’e kana tace “Bara’atu kenan, k’arfin halinki na mugun birgeni... Yo idan na kashe Kausar sai mai uwar mai zaki iya yi... Ke wacece mai kika isa kiyi.... Banza irinki karan kad’a miya....” Aunty B da tuni ta gama isowa wuya ta nufo Hajiya gadan gadan zata shak’eta... Tuni Aunty Lami ta shiga tsakaninsu tana fad’in “Haba haba kukuwa... Ya kuke abu tamkar k’anan yara.... Shin da abinda kuke kuna taimaka ma Zulfa’u kenan...? Ya isa haka Bara’atu ki shige ciki Zulfa’u needs you....” Ta k’arashe tana janye Aunty B... K’uramasu idanu su biyun Aunty B tai kana tace “A juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe....” Hajiya ta sakar mata murmushi a tak’aice kana tace “Zaifi kyau idan kika daina saka hancinki a abinda bai shafeki ba....” Aunty B ta kuma murmusawa tana mai dubansu su biyun kana tace “Ko mai kuke b’oyewa ku biyun nan zai fito fili.... Mu zuba mu gani....” Daga haka sa kai tai ta shige.... Aunty Lami da Hajiya suka dubi juna ba tareda sun furta kalma guda ba.... Kasa sanar dasu Sameer yayi dole sai Awwab ne yazo ya masu bayani, Sameer na daga yanda yake yana jiyo sautin kukan ‘yan uwansa.... A hankali ya rintse idanunshi tausayinsu na d’awainiya dashi har saida wata nurse ta iskeshi ta sanar dashi an shirya second patient d’in kafin ya nufi theatre room d’in jiki a sanyaye... Tin daga k’ofa yake jiyo sautin kukanta cikin tsananin sanyin muryarta tana ambaton ina Kausar take..... Muryar sounds familiar to him, a hankali ya k’arashe shigowa cikin room d’in sauran nurses d’in na gaidashi.... Cak ya tsaya yana dubanta itace dai domin kaw k’unan wutan bai tab’a fuskarta ba, lokacin da ya soma kuskuransu itada k’aramar yarinya da motarsa ya soma tunowa, ya tuna kuskuransu na biyu da yayi lokacin data watsar da kifin da wancan azzalumar matar Baban nata ta aiketa... Ya tuna last ganinsa da ita a gidan Abbah a parlorn Abbah.... A b’angaren Raihana ma shid’in take duba domin kaw sam bata tab’a mance kamaninsa ba mutumin da ya tab’a defending d’inta so d’aya tak a rayuwarta daga muzgunawa da cin zarafi da Hajiya ke mata... Toh mai yakeyi a nan d’in...? Ta tambayi kanta.... Kafin ta nemo amsar tambayarta taji nurse guda na fad’in “Dr everything’s ready....” A hankali ya jinjina mata kai still idanunsa naga Raihanah... A hankali ya soma takowa har ya k’araso gabanta.... Jikin Raihanah yai sanyi da irin duban da yake mata dukda zogi da tsananin rad’ad’i da fatarta ke mata.... Duban nurses d’in yai kana yace “Get me the injection...” Jin an ambaci injection ya sata kuma dubanshi saidai gani tai ya sauya gaba d’aya tamkar bai santa ba haka yayi.... Hannu yasa yana k’ok’arin yaye farin k’yallen da aka rufa mata.... Ta kuma zabura tana dubansa saidai sam shid’in ba fuskarta yake duba ba da alama aikinsa yake k’ok’arin yi.... Tana jin sanda ya rik’o hannunta guda b’angaren da babu k’unan.... Daidai sanda idanunsu ya had’e waje guda, tsananin tsoro da firgici ne zalla cikin idanun Raihanah.... D’auke kai Sameer yai daga barin dubanta ya dawo da idnunsa ga yanda yake k’ok’arin zira allurar... Tana jin sanda yake zira mata allurar cikin tsanaki, hakan bai hanata rintse idanu ba dukda cewa zafin allurar baikai zafin k’unan da takeji a cikin jikinta ba... Sosai doguwar rigar material d’in ta kame jikinta, dole sai an saka almak’ashi ya iya tsaga rigar a rabata da fatarta.... Ya kuma umarni ma nurses d’in su mik’a masa almak’ashi.... Tsoro da firgici ya cika Raihanah dukda duru duru data soma gani alamun allurar da ya mata ya soma kamata.... Sameer ya kurama fuskarta idanu sanda take fad’i cikin magagi... “Mai mai zaka min... Mai zakuyimin...? Ina Kausar... Ku fad’a min yanda take.... Ku fad’a min tana lafiya....” A hankali ya janye idanunsa daga duban fuskarta ya shiga k’ok’arin b’arka rigar jikinta.... Yanajin sanda ta rik’e hannunsa da sauri dukda cewa idanunta a lumshe suke tana fad’in “Nidai ka... ka k’yaleni.... Ni please don’t....!” Duban bakinta yake yanda take maganar da k’yar... A hankali ya d’ago yana duban nurses d’in guda biyu mata... Sai kallon kallo suke ganin yanayin likitan nasu yau yasha banban da ko yaushe.... “Dr are you alright...?” D’aya daga cikin nurses d’in ta tambaya... Itama d’in dubanta yai kana ya jinjina kai a hankali alamun yana lafiya kana ya mik’a mata almak’ashin ya masu umarni su farke rigar.... *** Tinda ya shigo gidan yake raba idanu ta ina zaiga d’iyarsa, sosai yarinyar ta shiga ransa har cikin ransa yakejin yarinyar cikin d’an lokaci k’ank’ani da suka kasance tare don tinda Hajiya ta kawota shike rainonta shike d’awainiyarta saidai idan zai fita ne sai ya bartama Sawwama nan ma bada son ransa ba sai don babu yanda ya iya.... Wani shak’uwa mai tsanani ne ya k’ullu tsakanin Hafiz da d’iyarsa Kausar, bai tsamman yana son yarinyar har haka ba kodashike Kausar yarinyace mai tsananin shiga rai ga duk wanda ya lak’anceta balle shi mahaifinta akwai bond mai k’arfi tsakani.... Saman kujera ya aje ledar kayan wasan da ya siyo mata musamman, ya d’aga labulen uwar d’aki ko zai gansu... Nan ma shiru babu Sawwama balle Kausar, toh ina suka shiga...? Ya tamabaya yana mai sauk’e labulen... Saman kujera ya zauna ya shiga fidda toys d’in murmushi kwance saman fuskarsa, danginsu doll baby da sauransu ya tabbata zataso kayan wasan shi kad’ai yake raya hakan cikin zuciyarsa.... Yana a haka ne yaji shigowar Sawwama tana tafe tana amsa waya, sanda ta gansa zaune a parlor turus tai tana dubansa lokaci guda ta canza maganar da take da Alhajinta tana mai fad’in “Karki damu Magajiya ai nace maki zanzo, zanzoni In sha Allah... Yauwa a huta gajiya sai munyi magana...” Ta k’arashe tana mai katse kiran... Dubanta kurum yake domin kaw ba wai ya yarda da Magajiya ta gama waya ba, tun kwanakin baya jikinsa ke basa wani abu saidai baiso ya jefo zargi cikin zaman aurensu.... Cikin salo ta k’araso ta zauna hannun kujera tana mai fad’awa jikinsa had’ida masa salo take fad’in “Hafizy yaushe ka shigo....?” Birki tai ma kalaman nata ganin kayayyakin dake rik’e hannunsa.... Ta wani yatsina fuska kana tace “Wannan fah... Na zaci kaji ne a ledar ma....?” Girgiza mata kai yai kana yace “Ba kaji bane.... Ina Kausar...?” Nan ma yatsina ta kumayi had’ida gyara zama tana wani karkad’e wuyar riga had’ida taunar chewing gum kana tace “Aw baka had’u dasu a waje ba....?” Duban mamaki ya mata kana yace “Su wane....?” Tana mai rausaya had’ida jijjiga cikin taunar chewing gum d’inta irinta rik’akk’un ‘yan tasha kana tace “Su Sahariyya mana, ai sun biyo sawu sun d’auki Kausar, tana can ‘Yan turame....” Ta k’arashe kai ka rantse iyakacin gaskiyar ta fad’i.... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya shiga tattaran kayan yana fad’in “Barin tafi ‘yan turamen na sameta....” Sawwama tai saurin tare gabansa cikin salo kana tace “Haba Hafizy ina zaka daga shigowa, Kausar dai bazata b’ace ba k’arewa gidanku take ba wani wajen ba, aidai ka tsaya kaci abinci ko Hafizy musamman na maka girki abinda kafi so...” Ta k’arashe tana shafar fuskarta cikin salo... D’ago kai yai da niyyar magana Sawwama tai saurin d’aura d’an yatsarta saman labb’arsa tana mai furta “Shiiii karkace komai... Zo muje....” Ta k’arashe tana janyoshi har suka komo cikin parlorn... Lokaci guda ta zaunar dashi ta nufi kitchen ta had’o masa abincin da aka gama tsibbace shi da kayan tsibbace tsibbacenta na toshiyar baki... Zaman dirshan tai tana basa abincin tana shafa kansa tamkar wani d’anta, cikin salo da mad’e taita cika ma Hafiz ciki da abincin da aka kawo mata daga can kantin Magajiya.... Aiko yana ida ci yaji kansa na juyawa kaman mai jin bacci bai wata wata ba dama ta samu tuni ta janyosa d’aki don dama a hannu take don da ace bai dawo ba da tuni ta tafi wajen Alhajinta wa’iyyazu billah.... Ya Allah kai mana tsari daga aikin danasani.... Da yawan matan aure sun halak’a sun fad’aga halak’a da tsananin fushi da tsinuwa ta Ubangiji, zinace zinacen matan aure ba zallan ‘yanmata ba ta yawaita a duniyarmu, mu sani irin wad’annan bala’u suna d’aya daga cikin abinda ke kawo annoba cikin Al’umma... Manzon tsira SAW ya fad’i mana zinace zinace bazatai yawa a doron k’asa ba har ya zamana ana bayyanata face Allah ya jarabci wannan al’umma da cutar da babu wanda ya tab’a sanin irinta... Muji tsoron Allah mu komaga Allah mu gyara tsakaninmu da Ubangijinmu sai Allah yaji k’anmu ya kawo mana d’auki, Allah Ka gafarta mana kaji k’anmu ka shiryamu da zuri’armu ta farkin addininka... Ameen ya Rabbi..! *** Kan kace mai labarin mutuwar Kausar ya riski kowa idan ka d’auke mahaifinta, duk irin waya da Baba Alhaji mahaifinsa ke masa bai d’aga ba domin kaw tuni Hafiz ya b’ige da bacci, Sawwama na ganin wayar na shigowa saidaima tai tsuka ta katse kiran, k’arshe ma kashe ma kashe wayar tai gaba d’aya ta cilla gefe ta gyarawa Hafiz kwanciyarsa.... Iyakacin b’acin rai Baba Alhaji yakai, har shine Hafiz ke katse masa kira k’arshema ya kashe wayar gaba d’aya, lallai Hafiz ya cika d’ah maras tarbiya... K’wafa Baba Alhaji yai kana ya umarta liman da sauran jama’a dasu k’arasa da Kausar makwancinta domin kaw bazasu tsaya jiran tsammanin Hafiz ba.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *48* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tareda Sameer akai komai, daga nan bai wuce gida ba don ko Siyama batasan da dawowarsa ba, kai tsaye asibiti ya nufa wajen Abbah.... Ya jima yana tsaye k’ofar d’akin yana duban Abbah daga yanda yake kwance k’walla na neman ciko idanunsa.... Sam Abbah baisan da zuwan Sameer d’in ba domin kaw idanunsa a lumshe yake, Sameer ya rintse idanunsa da k’arfin gaske hawaye suka kwaranyo masa domin kaw baisan ta yanda zai soma ba saidai d’ago idanun da zaiyi sukai ido hud’u da Abbah wanda ya masa k’uri babu k’yafta idanu.... Cikin sauri Sameer ya shiga k’ok’arin saita kansa yana goge hawayen da suka wanke masa fuska.... Cikin sauri had’ida d’an sassarfa ya soma shigowa d’akin lokaci guda yake k’ok’arin d’aura murmushin k’arfin hali saman fuskarsa.... K’ok’arin bud’e baki yake da niyyan gaida Abbah saidai kuma Muryarsace yaji ta sark’afe lokaci guda... Daga shi har Abbah kasa daina kallon juna sukai saima sabon hawaye dake k’okarin ciko idanun Sameer.... Lokaci guda bakin Sameer ya shiga rawa... Bai iya furta ko kalma guda ba sai rungume Abbah da yayi cikin wani irin shauk’i yana mai fitar da kukansa gaba d’aya.... Tsananin sanyi jikin Abbah yayi dukda cewa ba k’oshin lafiya bane dashi ga wani irin damk’a da Sameer ya masa yana mai jin kukan Sameer d’in har cikin zuciyarsa da ruhinsa... Gaba d’aya Sameer ya mance da condition d’in Abban, lokaci guda cikin muryar kuka yake furta “Abbah why...? Why Abbah... Meyasa kuka rabu dani, meyasa baku nemeni ba...? Meyasa kuka barni na rayu ba taredaku ba... Why Abbah....?” Hannayen Abbah suka shiga rawa sosai sanda yake k’ok’arin dafa bayan Sameer cikin tsananin bugun zuciya.... Dukda rawan da hannun Abbah keyi bai hanasa k’ok’arin kamo kafad’un Sameer dake tsanin kuka ya d’agosa ba... Shima Abban kwantattun hawayene saman fuskarsa.... Cikin rawar murya Abbah ke furta “Ma’aruf...! Ma’aruf...!! Ma’aruf d’ahnah....!!!!” Lokaci guda ya kuma rungume Sameer da k’arfin gaske sai bursting cikin kuka da yayi... Suka k’ank’ame juna su duka biyun ko wannensu kuka yake sosai da kuka zuciyarsa.... Cikin kuka Abbah ke furta “Ma’aruf ka dawo...! Ashe zaka dawo garemu... Ashe zan sake ganinka..? Ashe kana nan raye d’ahnah... Mahaifiyarka tayi gaskiya datak’i aminta cewa ka mutu tunda jimawa... Ma’aruf ashe zaka dawo gareni.... Alhamdulillahi Alhmadulillah..! Allah na gode maka daka nunamin rana irin wannan kafin ka karb’i rayuwata... Allah na gode maka na gode...” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai kuma k’ank’ame Sameer cikin jikinsa.... Mamy dake daskare bakin k’ofa tai masu k’uri hawaye naci gaba da gangaro mata, tamkar mutum mutumi take takowa cikin d’akin idanunta basu daina duban Sameer ba tana hango Ma’aruf d’inta tun yana yaro har izuwa lokacin da ya b’ace mata.... Tsananin rawa hannayenta keyi sanda ta shiga shafa bayansa a hankali tana mai ci gaba da dubansa tana tuno rayuwarta da d’anta Ma’aruf, cikin rawar murya take furta “Zuciyata ruhina da gangan jikina bazasumin k’arya ba.... Tin daga randa na soma saka a k’wayan idanuna suka fad’amin cewa kaine.... Kaine Ma’aruf.... D’ah nah.....!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka da rawar jiki tamkar zata zube k’asa.... Cikin sauri Sameer ya tallafota lokaci guda ya rungume mahaifiyarsa su duka biyun suna kuka sosai, babu mai iya cewa komai cikinsu sai kuka da suke sharkaf da hawaye, sun jima a hakan kafin Sameer ya k’arasada mahaifiyarsa saman kujera ya zaunarta had’ida duk’awa gabanta... Ya rik’o hannayenta duka biyu yana dubanta cikeda ai da k’auna murmushi had’ida hawaye saman fuskarsa, lokaci guda ya kifa kansa saman cinyoyinta hawaye suna ci gaba da d’igo masa, itama Mamyn dafa kansa tai da duka hannayenta biyu hawaye naci gaba da d’igo mata.... Cikin sanyin murya yake furta “Mamy nah..! Mamy maiyasa kika bari suka rabani dake...? Why Mamy.... Maiyasa baki nemo d’anki ba, maiyasa kika bari muka kwashe shekaru sama da talatin bama tare Mamy why...?” Ya k’arashe yana mai kuma aje kansa saman cinyarta.... Cikin muryar kuka tana mai girgiza kai alamun a’a take fad’in “Ko kad’an d’ahnah... Ko kad’an bamuso rabuwarmu dakai ba saidai babu yanda muka iya da hukuncin mahaliccinmu, Ma’aruf d’ahnah ban tab’a cire ran cewa bazan sake ganinka ba daidai da rana guda.... A koda yaushe dakai nake rayuwa cikin zuciyata tsawon shekarun nan, d’ah nah ka yafeni ka yafemin....” Kuka yaci k’arfinta... Sameer ya d’ago yana dubanta hawaye naci gaba da gangaro masa yake share mata hawayenta tsananin tausayi da k’aunar mahaifiyarsa naci gaba da mamaye illahirin zuciyarsa.... Abbah ne ya taso daga saman gadon da yake ya k’araso har gabansu yanai masu duba cikeda shauk’i, tinda yazo asibitin saidai a d’agasa amma sai gashi yau ya mik’e har ya tako da kansa... Haka nan yai tsaye had’ida masu k’uri yanajin yanayin da ya jima baiji irinsa ba a rayuwarsa, gaba d’aya ya had’esu ya rungume su duka ukun suna rungume da juna fuskokinsu d’aukeda hawayen annuri zukatansu cikeda tsan tsan farin ciki da annashuwa had’ida godiyawa Ubangijinsu maras misaltuwa da ya nuna masu rana irinta yau..... *** “Daddy please zan bika...!” Tai maganar tana mai turo baki gaba had’ida rik’e hannun mutumin data ambato da Daddy.... K’uri ya mata fuskarsa cikeda taananin tausayi don yarinyar sosai ta saba dashi irin sabon da ya kamata tayida mahaifiyarta wacce sam bata samu hakan ba.... A hankali ya duk’a ya kamo hannayenta guda biyu yana mai share mata hawayen da suka kwaranyo mata... Cikin muryarsa mai cikeda taushi yace “Baby kiyi hak’uri kinji wajenda zanje yara basa zuwa, kiyi hak’uri ki zauna da ‘yan uwanki da kuma Nanny kinji koh...” Mak’e kafad’u tai sabbin hawaye suna zubo mata lokaci guda take furta “No Daddy I don’t wanna stay.... Please take me with you, I promise I’ll behave kaji please....” D’an fuzar da iska yayi ba tareda ya kuma cewa komai ba a daidai sanda wani matashi mai kimanin shekaru 35 ya k’araso cikeda risinawa yana fad’in “Sir lokaci na gab da k’ure mana kasan sun maka shaidan mutum mai tsananin mutunta lokaci da cika alk’awari....” A hankali ya jinjina kansa kana ya k’arada “Alright Akram... Zamu isa akan lokaci In sha Allah....” Mutumin da ya ambata da Akram jinjina kai yayi kana ya fice, jim kad’an ya fito ya nufi taron motocinsa da ko wanne yana d’aukeda sunan MUTALLAB wajen da ake rubuta lambar mota.... Mutanen sai gaidashi suke kowa na k’ok’arin shigewa mota cikin sauri domin su d’au hanya, kai tsaye ya nufi mota guda wanda nake taammanin tasace, har ya iso jikin motar Akram bai sani ba, idanunsa a lumshe yana sauraren radio.... K’uri yayiwa Akram daga yanda yake tsaye yana duban yanda Akram ke sakin murmushi idanunsa a lumshe... Ya saki murmushi a hankali had’ida girgiza kai kana ya d’an k’wank’wasa gilashin motar da yatsun hannunsa guda biyu.... Cikin sauri Akram ya bud’e idanunsa had’ida d’an zabura kana ya bud’e lock d’in yana mai daidaita kujeran zaman nasa yake fad’in “Sorry Sir... Na d’an sha’afa ne....” Ya k’arashe yana mai sosa k’eya.... Murmushi ya saki a hankali kana yace “Akram kenan.... Mai kake sauraro haka....?” Lokaci guda Akram ya bud’e sautin radio d’in da a baya ya rage kana yace “Shirin muryar ‘yanci nake saurare... Gaskiya gidan radio d’in suna k’ok’ari wajen sharhi da fashin bak’i kan abindake faruwa a gwabnatancen a k’asar nan.... Sir ya kamata ka fara sauraron shirye shiryen....” Tak’aitaccen murmushi kurum yai kana yace “Toh banda abinka Akram idan ka saurara ai tamkar ni na saurara, besides kasan ban saba sauraren radio ba...” Akram yace “Sir ya kamata ka fara sauraren irin wad’annan shirye shiryen domin ta haka ne zaka fahimci yanda siyasarka ta dosa tsakaninka da al’umma....” Yai shiru tamkar mai nazari kafin ya jinjina kai a hankali ba tareda yace komai ba.... Tafiyar minti talatin sukai kafin suka iso farfajiyan taron siyasan yanda ko ina d’auke yake da manyan hotunansa da sunansa MA’ARUF MUTALLAB..... **** Suna tafe cikin mota dawowarsu kenan daga gidan cin abinci sannan sun sayowa oga Sameer nasa tinda ya sanar da Siyamar cewa yau zai dawo, ba wai iya girkin tai ba balle ta dafa masa sayowan yafi mata sauk’i da zaran ya iso saidai ta saka a microwave ta d’umama.. Kaman daga sama Yesmin ta hangi motar tamkar ta Khalid na barin k’ofar gidansu Nabila domin goma idan za’a wuce idanunta naga k’ofar gidan ko zata hangi Nabilah... Gabanta yai mugun yankewa ya fad’i badai duk abinda suka turawa Khalid gameda yarinyar nan bai hak’ura da ita bane...? Ta tambayi kanta... Siyama ta lura da canzawan Yesmin lokaci guda domin taga ta daina amsa mata firanta.. D’an juyowa tai sanda suke k’ok’arin shiga layinsu kana tace “Lafiya cousin.... Ya naga kin canza lokaci guda...?” Yesmin tai saurin furta “Cousin Khalid na gani..” “Khalid kuma..?” Siyama tace Jinjina kai Yesmin ta kumayi cikin sauri kana tace “Wllhi motarsa na gani yanzun nan ya bar k’ofar gidansu tsinanniyan can.... Dan Allah juya motar nan mu koma....” Kallon mamaki Siyama ta bita dashi kana tace “Mu koma ina...? Badai kince ya tafi ba....” “Mu koma mu shiga har cikin gidan mui mata wankin babban bargo daga ita har iyayen nata inaga hakan ne kawai zaisa ta fita hanyar Khalid tunda bataji wancan warning d’in ba....” Siyama ta dara a tak’aice kana tace “Cousin bakida kyau, haka kishinki keda yawa koda yake gaskiyarki domin ko ni ce zAnyi fin haka akan Sameer....” Ta k’arashe tana mai danna reverse..... SameenaALeeyou📚 *INDA RAI* _.................DA RABO_ *49* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sai faman yatsine fuska suke sanda suka shigo gidan, ga k’ofofi kusan guda uku sun rasa wani k’ofar zasu dosa... Daga can suka hango yarinya tafe ta fito daga wata k’ofar ta nufi wani sashen.... Siyama tai saurin katseta da “Ke d’anzo mana...” Basma ta dubesu cikeda tsoro don haka kurum suka bata tsoro kana tace “Ni..?” Muguwar tsuka Yesmin taja kana tace “Eh ke, ko kinga wani a nan ne bayan ke...?” Basma ta k’araso tana duban cikin idanunsu.... Siyama tace “Dubi yanda take kallon mutane har cikin idanu yanda zaki gane gaba d’aya yaran gidan ba kunya ne dasu ba na rasa uwar da Khalid ya hanga jikin wannan mummunar yarinyar, banda tsiya babu komai a wannan gida...” Yesmin dake faman toshe toshen hanci tace “Ke ni wllhi banda warin talauci ban iya shak’ar komai tinda muka shigo gidan...” Basma dai banda binsu data muji bata komai, ta kalli wannan ta kalli wancan... Siyama ta tsaida dubanta ga Basma kana tace “Ina yayarki...?” “Wacce cikin yayyena...?” Basma ta tambaya... Kan Siyama ta sami zarafin magana Yesmin tace “Karuwan can da aka jefeta bakin titi....” Basma ta fahimci Nabila suke nema, hakan yayi mata don ko babu komai tasan wacece Nabila kuma tasan itace daidai da wad’annan matan....” Saida itama ta yatsina irin yanda taga sunayi da fuskokinsu kana tace “A iya sanina dai babu karuwa gidan nan, domin kuwa gaba d’aya gidan nan babu mai saka irin suturar dake jikinku... Koma dai wacece kuke nema ku k’arasa wancan k’ofar yanda ake karb’an gaisuwa zaku sameta....” Bata jira cewarsu ba tasa kai ta shige... Siyama ta bita da kallo kana ta dubi Yesmin tace “Cousin yarinyar nan ‘yar rainin sense ce, wato in directly fad’i mana take mune masu zubin karuwai... Ki dubeta bata wuce cikin cokali ba har tasan ta gaya wa mutane magana....” “Da kin barni na wawwatsa wa shegiya mari...” cewa Yesmin “A’a k’yaleta mu sauk’e gaba d’aya kan yayarta... Zo muje...”!Ta k’arashe tana mai janyo hannun Yesmin d’in.... Basma kaw ko saurarensu bata tsaya yi ba ta shige b’angarensu sashen Baffah Ado taje kaiwa ‘yan uwanta rahoto... Babu ko sallama haka suka banko k’ofar suka shigo, sai faman yatsina fuska suke suna bin mutanen dake zaune verandar da mummunar kallo.... Goggo Laraba k’anwar Baban Mamy ce ta sami zarafin masu magana “Bayin Allah lafiya, daga ina, wa kuke nema...?” Dattijuwar ta jero masu tambayoyin tana mai dubansu.... “Lafiyar kenan ku jawa Karuwar ‘yarku kunne ta fita daga rayuwar d’an uwanmu wllhi Khalid ko ya rasa mata babu abinda zaiyi da irin wannan gidan...” Cewar Siyama tamkar zata mari tsohuwar... Gaba d’aya jama’an dake wajen tsananin mamakin rashin ta idon Siyama ya kamasu... Wata daga gefe tace “Baiwar Allah ki tauna kalamanki ko babu komai zaki daraja furfuran wani ko don a daraja naki...” “Ke rufe mana baki...!” Yesmin ta katseta... “Matsiyata anga danshi jikin d’an uwanmu ana nema a rab’eshi a dangwali arziki, toh wllhi ko a ‘yar aiki Khalid bazai d’auki wannan kucakar ba....” Daidai nan Aunty B ta fito daga d’akin yanda suke zaune dasu Nabilah su Zulfa’u tana faman basu baki.... Nabilah taji wasu sabbin k’walla na zubo mata, tabbas tayi gamo da jarababbu wanda sukai karan tsaye wa rayuwarta.... Ace ana karb’an gaisuwar d’iyar ‘yar uwarta ake wannan d’iban albarka duk a ta dalilinta, gaba d’aya sai taji ta kasa daina zuban hawaye zuciyarta na mata zafi sosai... A fusace ta mik’e ta yunk’ura zata mik’e Marliya tai saurin rik’o hannunta.... Girgiza mata kai tai kana tace “Kada ki fuskancesu Addah Nabila...” Da raunannun idanunta masu zuban hawaye take duban ‘yar uwar tata kana tace “Shikenan sai na k’yalesu suci mana mutunci Marliya...? Idan rashin mutuncinsu zai tsaya kaina fine, amma bazai yuwu na zuba idanu sucima dangina mutunci ba, what if Addah ta fito daga bayi taji ana wannan zagin d’iban albarkan... Mai kike tunanin zataji bayan rasa d’iyarta da tayi a yau d’in...?” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka zubo mata.... Sosai Marliya ta rik’e hannunta kana tace “Insha Allah bazataji ba ma I believe Aunty B can handle them kafin ta fito ta sallamesu.... Please ki zauna karki fito ina zuwa...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye ta nufi tsakar gidan yanda Aunty Bara’atu taimasu Yesmin d’add’aya cikin salama... Ko kad’an basu fasa rashin mutuncin da sukayo dakonsa suka shigo dashi gidan ba, haka dai da k’yar aka samu suka fice a gidan bayan sun gama zuba rashin mutuncinsu, gaba d’aya illahirin mutanen gidan babu wanda ya biyesu har suka k’araci tsiyarsu suka fice bayan Aunty B ta tilasta masu cewa ko su fice ko ta kirawo masu ‘yansanda.... Itakaw Marliya tas tayi video d’in su Siyama sanda suke zuba rashin mutuncinsu, suna ficewa ta koma d’aki wajen ‘yar uwarta.... A daidai lokacin da bak’i ‘yan office d’in su Zulfah suka zo mata ta’aziya... *** Mamy ta kasa daina duban Sameer dake jikin window yana amsa waya, dukda cewa yau d’in tayi rashin jikarta d’aya daga cikin ahalinta sai gashi Allah ya maido mata d’aya daga cikin ahalinta, tabbas dole tai godiyawa Ubangijinta domin Shi d’in mai yalwata rahamarsa ce ga bayinsa, idan ya karb’e maka wani abin sai ya canza maka da wani abin domin ya zamto rahama a gareka.... Har Sameer ya ida amsa wayar Mamy bata daina dubansa ba wani irin murmushi ne wanda sam batasan tanayi ba shine saman labb’anta.... Sameer ya d’an kaikaito yana dubanta, wani sanyi da ya jima baiji ba cikin zuciyarsa yaji yana sauk’a masa a hankali..... Lumshe kyawawan idanunsa yai had’ida sakin sassanyar murmushi kana ya jefa wayarsa a aljihu ya k’araso gareta... Daga can gefe da ita ya d’an zauna cikeda kunya da rashin sabo, itama Mamy din hakan ne ya faru da ita... Murya a d’an k’asa Sameer yace “Ammm zan wuce zan koma asibiti...” Mamy tace “Ita Raihan fah...? Jikin nata da sauki sosai...?” Sameer ya d’anyi jim kana yace “Wayar da muka ida da colleague d’ina kenan, kar ku damu.... Please kar ki da’ga hankalinki In sha Allah zata sami sauk’i....” Mamy ta jinjina kai a hankali kana tace Allah shi yarda, anjima Lami zata taho sai na biya na duba Raihanar kafin na shige gida sabida ‘yan gaisuwa sunata min waya a nan kuma Abbanku baisan da labarin ba har yanzu...” Sameer ya jinjina kai kana yace “Hakane... Ya kamata a bar Abbah da batun sabida heart d’insa har yanzu weak ne sannan ga shock d’in da ya samesa na bayyanata... Zan wuce yanzu anjima sai nazo na d’aukeki....” Mamy ta jinjina kai kana ta k’arada “Toh shikenan Allah shi taimaka ya kuma tsare su kuma ya basu lafia...” Sameer ya amsada Ameen cikeda risinawa, daidai nan wayarsa ta d’auki ruri... Lambar Mummy ya gani tana kiransa, ya d’an kai dubansaga Mamy kana ya d’aga wayar yana mai sadda kansa k’asa... “Hello Mummy...” Kalaman da Mamy ta iyaji kenan kana Sameer yasa kai ya fice, ta bishi da kallo cikin tsananin sanyin jiki jin ya ambaci wata da Mummy wacce ko shakka batayi tasan Mahaifiyarsa ce data rainesa, d’ansu ya zamto mai iyayi hud’u... Ta k’arashe tinanin tana mai komawa zuwaga d’akin Abbah tamkar wacce k’wai ya fashema a ciki... Daga d’aya b’angaren Mummy taci gaba da fad’in “Son, I was so worried, you haven’t been answering any of my calls... Kaga dole hankalina ya tashi...” D’an jim yai yana mai karya steering mota kana yace “I’m sorry Mummy, I should’ve called to at least let you know na isa lafia, but mummy ever since I arrived here things haven’t been easy... I’m sorry for making you worried Mummy...” D’an sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Alhamdulillah tinda kana lafia, but please next time kar ka sake irin hakan...” In sha Allah hakan bazai sake faruwa ba... I’m driving right now, I’ll call you back kinji Mummy na...” Nanma ta jnjina kai kaman na gannta... Har zai katse kiran ya kuma jiyo muryarta “Sameer.... I know by now iyayenka na asali sun fahimci wanene kai sun fahimci cewa you’re their long lost Son...” Sameer ya d’anyi jim kana yace “Yes...Mummy.....” Ta murmusa a hankali kana tace “I’m so happy for you Son, na maka murnar kasancewa da iyayenka na asali...” Sameer yai murmushi a hankali kana yace “Na gode Mummy nah...” Hajiya Fatahiyya murmushi saman fuskarta tace “Drive safe...!” Har zata katse kiran Sameer ya katse ta da fad’in “Mummy.... I love you.... Always remember that...” Cikeda jin dad’i k’walla na gangarowa Hajiya Fatahiyya tace “I know Son, and I love you more... Allah shi maka albarka...” Sameer ya amsa da Ameen fuskarsa d’aukeda murmushi kana sukai sallama... Duk sai yaji jikinsa yayi sanyi tsananin tausayin Mummynsa ya tufesa a haka ya isa asibitin.... *** Fitowarsa kenan daga sashen Mamani, ya tsaya yana duban sashensu Nabila, gani yake tamkar zai hangota, dashike ‘yan gaisuwa sun d’an d’auke k’afa sabida almuru data sako kai... Kaman daga saiga Marliya ta shigo daga gate dawowarta kenan daga rakiyan ‘yan ajinsu da suka shigo mata ta’aziya... Tsaye tai tana duban Khalid da kacaukam hankalinsa kega kallon k’ofan sashensu... K’arasowa tai yanda yake bakinta d’aukeda sallama.... Khalid ya saita kansa had’ida amsawa Marliya sallamanta... Ta gaisar dashi ya amsa da sakin fuska don sarai ya ganeta k’anwar Nabilah ce... “Addah Nabilah kake jira...?” Marliya ta tambaya... Baikaiga bata amsa ba Marliya tace “Bazan b’oye maka ba wllhi idan zaka kwana a nan Addah Nabilah bazata kuma saurarenka ba bayan abinda sisters d’inka suka shigo gidan nan sukayi....” Khalid ya kuma dubanta da tsananin mamaki kana yace “Sisters d’ina...?” Marliya ta jinjina kai tace “K’warai Sisters d’inka... Ko basu ne wad’annan ba...?” Ta k’arashe tanai masa nuni da video d’in data masu sanda suke zage zage da zuba rashin mutunci... Tsananin mamaki ya kama Khalid sanda yake furta “Siyama... Yesmin....!” Marliya ta katse video d’in kana taci gaba da fad’in “Now I believe you understand why I don’t want you for my sister, babu wacce zataso taga ‘yar uwarta ta shiga irin wannan family d’in, dan Allah kayi hak’uri kar ka saka ‘yar uwata cikin matsala, this family is going through a lot already, kafin labarin abubuwan dake faruwa su isaga iyayenmu dan Allah k’yale ‘yar uwata ko zata fice daga matsin naka ‘yan uwan... Babanmu wani irin mutum ne wanda ba kowa ke fahimtarsa ba kuma kaga ba lafiya ne dashi ba.. Sannan mahaifiyarmu sama da shekaru talatin kenan tana cikin alhini da damuwa na b’acewar Babban Yayanmu sannan Sister d’inmu babba tayi fama gidan miji ga kuma rashi d’iyarta da mukayi a yanzu uwa uba ga ‘yar uwarmu kwance gadon asibiti... Baka tunanin muna ciki matsaloli already... Dan Allah kar ka k’ara kan wanda muke fama dasu, na sani nayi shishigi wannan ba hurimina bane... I only care about my family ne kawai that’s all...” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Jikin Khalid yai sanyi sosai tamkar wanda aka tsoma a freezer.... Ya stinkayo muryar Marliya tana ci gaba da fad’in “I know I shouldn’t be telling you any of this...Maybe idan kaji ka rabu da ‘yar uwata....” Da idanunsa da suka matuk’ar rinewa lokaci guda yake dubanta, zaka iya jiyo hucin dake fitowa tin daga k’irjinsa.... Dabda fuskar Marliya ya matso da nasa fuskar wanda ya sanyata tsanin tsoro da fad’uwar gaba, kaman zai magana sai kuma taji baice komai ba saima sa kai da yayi ya fice daga gidan cikin sauri tamkar zai kifa k’asa... Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana ta jiyo ta nufi cikin gida yanda sukai idanu hud’u da Aunty B.... *** Tafe suke shida Dr Awwab abokin aikinsa yanda Awwab d’in yaci gaba da fad’in “Already munyi moving d’inta to ward, tana room 3....” Jinjina kai Sameer yai kana yace “Alright I’ll... check on her.... Thank you Awwab...” Ya k’arashe yana mai sa kai zai shige.... Saurin katseshi Awwab yai da fad’in “Dr are you sure you’re alright...?” Kallonsa kurum Sameer yai kana yace “I’m fine... Why?” “So why are you thanking me anyway... Aikina nake bai kamata kamin godiya ba....” Sameer ya k’ak’aro murmushi da gefen bakinsa kana yace “Dukda aikinka kakeyi dole nai maka godiya cos I just found out she’s... She’s...” Awwab yai shiru yana jiran yaji mai Sameer zaice, baikaiga bud’e baki ba Sameer ya k’arashe maganar nasa da fad’in “She’s my sister...” Murmushi Awwab yai kana yace “Oh really... da munsan cewa k’anwarka ce tun a fari da bamu bari kayi mata aiki ba...” Ya k’arashe yana murmushi irinta wasa.. Murmushin shima Sameer yai kana yace “I’ll go ahead...” Awwab yace “Alright Doc nima zan wuce gida tinda kazo...” Sukai sallama Awwab ya wuce Sameer ya nufi room d’in da aka kwantar da Raihanah.... Lullub’e take cikin farin bandage kusan illahirin jikinta idan ka d’auke fuskarta.... Ya jima sosai yana duban fuskarta da tun shigowar sa idanunta ke lumshe tamkar mai bacci.... Yakai dubansa ga hannayenta wanda suma ba rufe suke cikin bandage ba alamun suma basu k’one ba.... Nan ya hangi yatsun hannun nata suna motsawa a hankali... Sameer ya k’araso jikin gadon nata sosai yana dubanta yana mai tuna sanda suka soma had’uwa, yana cikin tunanin ne ya soma jiyo muryarta tamkar mai kuka tana furta “”Kausar... Kausar ina Kausar... Aunty Sahariyya kar ku k’onata please ku k’onani instead...!” Ta k’arashe tana fincika tamkar zata tashi daga gadon... Sameer yai saurin rik’e hannunta guda ya hanata tashi.... Lokaci guda ta koma tayi lamo cikin gadon tamkar taci gaba da baccin, har lokacin idanunta a lumshe suke.... Sameer yai mata k’uri tsananin tausayinta na d’awainiya dashi... He was right all along... Da ganganci da son zuciya aka k’onasu tinda ya tab’a ganin irin azabtarwa da ukuba da ake masu a wannan gidan, tsanar Hajiya da ‘ya’yayenta ya kuma tasiri a zuciyar Sameer, idan kuwa har da gaske da ganganci aka kashe masa niece aka k’ona Raihanah he’ll press charges, sai yanda k’arfinsa ya k’are wajen karb’a masu ‘yancinsu... Ya k’arashe zancen zucin nasa shi kad’ai yana mai sakin huci... **** Ta k’ure sautin tv tana cashewa tana celebrating nasaran da suka samu na raba Nabilah da Khalid kaman daga sama taji an banko k’ofar... Tamkar sauk’an aradu haka Yesmin taga Khalid tsaye cikin parlorn, fuskarsa da idanunsa sun koma jazir tamkar bashi ba... Yesmin ta sandare sanda jikinta ya d’auki rawa, sosai ta razana da ganin yanayin Khalid, ta soma jada baya zata gudu, kafin tai wani aune saiji tai ya fincikota ya d’auketa da wata irin gigitacciyar mari, ta saki ihun azaba, bata gama susan b’angaren fuskarta da marin ya sauk’a ba ta kuma jin wata lafiyayya ta d’aya b’angaren... Yesmin ta kuma daburcewa tana sakin ihu... A gigice tasa kai zata fice a guje daga parlorn Khalid yai saurin sharb’e k’afafunta ta zube a k’asa, fincikar wayoyin kayan kallon yayi ya shiga labtawa Yesmin tamkar an aikoshi... Yesmin sai ihu take tana kiran cousin tazo ta taimaketa.... Siyama da fitowarta kenan daga wanka ta nufo parlor babu shiri jin ihun Yesmin yak’i k’arewa tamkar wacce ake zarema rai... Baki kurum Siyama ta saki tana kallon ikon Allah yanda Khalid ke jibgan Yesmin, ta gyara d’aurin towel d’inta ta isa da sauri ta fincike wayar ganin Khalid zaiyi kisa... A tsananin fusata Yesmin ke furta “Khalid meye haka, what do you think you’re doing... What’s gotten into you... Kasheta kakeso kayi....?” Ta k’arashe cikin tsananin huci... Banda mugun kallo baya watsawa Siyama komai, cikin wata irin dakakkiyar murya yana mai nunata da d’an yatsa yake furta “Don’t let me lose the little respect I have left for you.... You better respect yourself Siyama...!” Ya maido da dubansaga Yesmin dake zube magashiyan a k’asa tana nishi yace “Ke kuma ni ba sa’anki bane ban fara irin wannan wasan dake ba, this should be your first and last warning, don’t you dare meddle with my affairs.....!” Yana k’arashewa yai jifada igiyar wayan hannunsa ya fice tamkar kububuwar maciji..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *50* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tabbas tafiya Kaduna babu shiri ya kamasu, domin kaw dole Ammi taji wannan labari, ko shakka babu yarinyar nan asiri taiwa Khalid, Ammi has to know about this idanma ta kama a nemawa Khalid taimako ne sai a masa... Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye ta nufi wardrobe ta shirya.... Nan ta fito parlor ta tadda Yesmin har lokacin kuka take.... Siyama ta d’an rausayar da idanu had’ida fuzar da iska kana ta nufi Yesmin d’in... “Cousin ki daina kukan nan haka you’ll fall sick, dan Allah kiyi shiru haka nan...” Ta k’arashe tana dafe Yesmin d’in cikin sigar lallashi... Idanu a kod’e Yesmin ta d’ago tana dubanta kana tace “Cousin ni Khalid ya buga haka, tinda nake my entire life babu wanda ya tab’a duka na haka, kai ko Mum bata tab’a zungirina ba sai gashi yau namiji wanda ko aurensa banyi ba ya tara min na jaki.... Haba haba cousin meye laifina don kawai nace ina sonshi...” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... K’wafa Siyama tai kana tace “Ki kwantar da hankalinki Cousin da gani ko ba’ace ba Khalid an juya masa kwanya ba haka kurum aka barshi da zaizo ya mana wannan cin kashin kan wata banza kucakar yarinya, kar ki damu Yesmina wllhi idan dai ina numfashi Khalid bazai auri yarinyar nan ba, gobe gobe zamu wuce Kaduna Ammi tace mun ma Daddy ma yana hanya goben gwara susan halinda d’ansu yake ciki...” Da wannan Yesmin ta sami sauk’i cikin zuciyarta, tuni ta nufi d’aki had’a kayanta domin gobe asubahin fari zasu dira garin Kaduna.... *** Misalin k’arfe 9:30pm Sameer ya shigo gidan, babu kowa parlorn sai TV dake faman aiki shi kad’ai, ya d’auki remote control ya kashe kayan kallon, kai tsaye d’aki ya nufa yanda ya tadda Siyama na had’e kaya cikin suitcase.... Da tsananin mamaki yake dubanta dukda’ bai iya furta koda kalma guda ba sai dubanta yake faman yi, jin shigowarsa ya sanyata aje rigar hannunta cikin jakar kana ta iso gareshi fuska d’aukeda murmushi tana fad’in “Partner sannu da zuwa... Kasha hanya, naji mamaki da baka iso ba tuntuni, kodashike I guess asibiti ka wuce aiki ya rik’eka acan, are you hungry..? Muje nayi serving d’inka...” Ta k’arashe tana k’ok’arin janyo shi... Har lokacin dubanta yake fuska d’aukeda alaman tambaya... Dakatar da ita yai da fad’in “No its ok, I’m alright.... Can you explain to me what this is for...?” Ya k’arashe yana nuni da suitcase d’inta.... Murmushi ta saki kana tace “Oh d’azu Ammi tai waya Dad yana hanya gobe, kasan ya jima baya k’asa so ya kamata naje mu tarbeshi, we are leaving to Kaduna first thing tomorrow morning nida Yesmin....” “With whose permission...?” Yai maganar fuska babu alamun wasa yana mai zura mata idanu... Kallo ta bisa dashi kana tace “Sameer ce maka nayi fah Ammi ce ta kirani so kake nace mata bazanzo ba, kar ka mance she’s my mother....” K’uri kurum ya mata kana yasa kai ya shige yana mai rage agogon hannunsa yake fad’in “You’re not going anywhere....” Bai jira cewarta ba yasa kai ya shige bathroom... Tirk’ashi! Kallo tabisa dashi har ya shige tana mai tsananin mamakin yanda gaba d’aya Sameer ya canza mata, da a bayane basai ta tambaya ba duk abinda tayi daidai ne amma yanzu wai har order da doka yake kafa mata, toh ko dai ya daina sonta ne...? Ta tambayi kanta, babu amsa, cikin sauri ta lalumi wayarta ta fice kiran Laila domin neman shawari.... *** Aunty Lami sai faman safa da Marwa take, takai mari takai gawro ita kad’ai, yau d’in ita zata kwana wajen Abbah, Mamy nacan zata duba Raihanah kafin ta wuce gida sabida masu zuwa mata gaisuwa, ita kaw Raiha Mamani ce a wajenta ita zatake kwana da ita dukda cewa ba wani abin zata iyayiwa mai jinya ba da naka a kusa yafi, ma’aikatan lafiyar suke komai a asibitin... Zufa ya kuma ketowa Aunty Lami gani take tamkar Ma’aruf ya ganeta ya gane fuskarta tsaf itace matar data d’aukesa a kasuwa ta b’anb’are hannunsa daga na mahaifiyarsa a lokacin da Mahaifiyar tasa ta fice hayyacinta tana mai neman d’auki na jama’a sabida haihuwa data zo mata bagatatan... Ta kuma share gumin tana mai sakin numfashi da k’yar... Abbah ya bita da kallo cikeda mamaki don batasan idanunsa biyu ba, kaman daga sama taji muryarsa ya ambato sunanta “Lami...” Ta juyo a firgice alamun tsoro da firgici a tattareda ita.... Bata iya amsa Abbah ba sai zuba masa ta mujiya da tayi.... Abbah ya d’an gyara daga kwance zuwa kishingid’e kana yace “Lafiya kike tsaye wajen, mai ya hanaki bacci...?” Tambayar da Abbah ya mata sai taji tamkar Abbah ya riga yasan komai, ta rasa mai zatace sabida lokaci guda taji tamkar harshenta ta zarge, da k’yar ta iya furta “La... lafiya kawai banjin baccin ne akwai wani abinda kake so ne....?” Murmushi d’auke fuskar Abbah domin gaba d’aya yinin ranar annuri ta gaza d’aukewa a fuskarsa sabida d’imbin farin cikin da ya tsinta kansa ciki yace “A’a bani buk’atar komai, hasalima ni ji nake na warke banida wata buk’ata da ya wuce su sallameni a wajen nan haka na koma gida cikin ahalina mu kasance gaba d’aya tare....” Zuciyar Lami ta kuma tsinkewa don ita kanta ta jima bataga Abbah cikin irin wannan yanayi na farin ciki ba.... Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi kana ta k’araso gefen gadonsa ta zauna... Tana mai sakin murmushi take fad’in “Alhaji ga dukkan alamu kana cikin farin ciki...?” Abbah ya jinjina mata kai cikeda aminta kana yace “K’warai Lami ina cikin farin ciki wanda na rasashi a baya, Ibangijina ya dawo min da wannan farin cikin...” K’irjinta ya kuma bada Dam! Kardai sunsan cewa wannan likitan d’ansu ne Ma’aruf.... Idan kaw haka ne dole tasha cikin Abbah taji komai... Ta kuma gyara zama murmushin bai bar saman fuskarta ba tana mai k’ok’arin gyarawa Abbah pillow da yake bisa tace “Alhaji halan wani abin ne ya faru...?” Abbah ya kuma dubanta da fuskarsa mai k’unshe da tsantsan annuri kana yace “Babban al’amari ya faru Lami da sannu zaku fahimci hakan gaba d’aya...” Tinda taji hakan tasan Abbah baiyi niyyan ya sanar da ita komai yanzu ba, tasan halin mijin nata domin kaw wani irin baud’edd’en mutum ne haka nan kalamansa wasu lokutan a baud’e suke zaiyi magana amma sai ka rasa gane inda ya dosa,idan kaw bazai fad’i mata ba ita zata sanar dashi mutuwar jikarsa idan yaso hankalinsa yayi gida komai ya fanjama fanjan kawai, ta gaji ta gaji da zullumi gwara ta sani idan Ma’aruf ya bayyawa iyayensa ne.... Ita a halin yanzu batama k’i Abbah ya mutu ba akan asirinta ya tonu.... Bata kuma cewa komai ba ganin Abban ya lumshe idanunsa tamkar mai bacci, bayan giftawan wasu dak’ik’ai data tabbatar yayi baccin ta fice kiran Haule domin susan madafa.... *** A b’angaren Siyama kuwa tas ta d’auki shawarin Laila cewa kada ta bari wani k’ato ya mata mulkin fir’aunanci a gidanta da sunan yana aurenta, idan ta riga ta sabar masa da sai abinda yaga dama za’ai shikenan ta zama wofi a cikin gidanta don shi namiji tankar yaro ne duk abinda ka d’aurashi bisa shi yakeyi don haka koda wasa kar ta bari wannan raini ya shiga tsakaninsu, tuni taci gaba da shirinta washe gari sassafe ko sallama Sameer baici arziki a masa ba don shi tuni yayi asubanci ya nufi asibiti duba yaya patient d’insa ta kwana, fitarsa da kad’an suma suka d’aga zuwa Kaduna.... *** A gidan Hafiz kuwa tinda garin Allah ya waye yake jinsa wani iri haka nan, wani ikon Allah safiyar ranar da tunani da begen d’iyarsa Kausar ya tashi domin kawa daren jiyan yayi mafarki da ita, yarinyar ta k’ara masa girma tayi kyau daga can nesa taketa k’ek’eta masa dariya saidai da ya nufota zai d’auketa sai ta b’ace ma ganinsa... Tinda ya farka daga wannan baccin kewar d’iyarsa ya damesa, baikobi takan Sawwama ba ya fice cikin sauri da niyyan ya soma zuwa Kasuwa ya duba shago daga nan ya d’an sai mata tsaraba yakai mata... Yana isa Kasuwa dashike yanzu a kantin mahaifinsa yake zama don shi yanzu baida kantin baida jari baida komai a d’an zaman da yake a kantin Alhaji mahaifinsa yake d’an samun na kashewa.... A bakin kantin ya tarar da Tasi’u yaron shagon yanzu yakeda niyyan bud’ewa, suka gaisa da Tasi’u, nan Hafiz ke tambayarsa Alhaji bai iso ba....? Tasi’u yace “A’a ai kaman rashi naji ana cewa anyi, nima dai banje ba domin jiya ma ni na kulle kantin a hannuna mabud’an suka kwana, daga nan nima dama can zan wuce....” Hafiz ya dubesa da mamaki kana yace “Rashi...? Toh waye ya rasu....?” Badai Abban su Zulfa’u ba don yasan shine a asibiti... Tasi’u yace “Wllhi nima dai ban sani ba amma ina tsamman ba babban mutum bane...” Hafiz ya jinjina kai kana yace “Shikenan Tasi’u bari na wuce can gidan...” Tasi’u yace “Toh Maigida a sauk’a lafiya, Allah jik’an musulmi....” Hafiz ya amsa da Ameen kana ya shige yana tunanin toh kodai a mak’ota akayi rashin tinda da ace a gida ne da ko ba’a kira wayar salulansa ba za’a kira na matarsa... Da wannan tunanin ya hangi teburin mai kayan wasan yara, ya saki murmushi a hankali kana ya k’arasa ya sai doll baby da kuma dangin kacau kacau.... Sai buga sauri Hafiz yake ya isa gida yaji abindake faruwa ya kuma dank’awa Kausar tsarabarta, tuni ya tari babur ya d’ale yana mai sanar da mai babur d’in yanda zaya kaisa... Babban tashin hankalin da riski Hafiz shine ganin taron mutanen a k’ofar gidan mahaifinsa suke.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *51* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Da k’yar k’afafunsa suke iya d’aukansa, ji yake gaba d’aya k’afafun nasa suna masa nauyi, waye ya mutu a gidansu, makokin waye ake...? Meke faruwa ne...? Cikin sakanni zuciyarsa ta dinga jefo masa tambayoyi, daga can ya hangi Baba Alhaji mahaifinsa na masabaha da mutane suna kuma masa ta’aziya, zuciyar Hafiz ta kuma tsinkewa.... Yaci gaba da d’aga k’afafunsa da k’yar sanda ya nufo kusan mutanen sosai yaji ana cewa Allah shisa mai ceto ce.... K’afafun Hafiz suka d’auki rawa ba tareda yasan dalili ba... A daidai lokacin da sukai idanu hud’u da mahaifinsa sanda wani mutumi ke furta “Ga mahaifin yarinyar ma, sannu sannu kaji koh Hafizu Ubangiji ya baka masu zama yasa ita kuma mai ceto ce...” Sam Hafiz bai iya amsa shi ba, hasalima bai fahimci mai yake nufi ba gaba d’aya ya zama lost and confused.... Duru duru yake ganin mutane yanda sukai chaa sunai masa gaisuwa, yana jiyo muryoyinsu tamkar daga nesa.... Yana ganin sanda mahaifinsa ya mik’e ya nufi cikin gida bayan ya rakasa da muguwar kallo.... A gigice Hafiz ya tsallake mutanen ya nufi cikin gida yana mai kiran mahaifin nasa.... Cak yaja yayi birki sanda yaga mata sun cike farandar mahaifiyarsa... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka ya nufi dandatson matan yanaji kaman zai kifa da k’asa... Naja’atu ce ta nufosa a guje ta rungume tana kuka sosai.... “Najah lafiya , meke faruwa... What is happening... Talk to me Najah... Ina Kausar.... Where’s my daughter...? Look I bought her a lot of toys, nasan zatai murna... Kin gani....” Ya shiga k’ok’arin bud’e ledar yana ciro kayan wasan..... Ba Naja’atu dake rungume dashi tana kuka ba harta mutanen dake zaune farandar saida sukaji k’walla na zubo masu... Cikin tsananin kuka Najah ke girgiza masa kai sanda yake kuma tambayarta d’iyarsa.... Cikin muryar kuka take furta “Ya Hafiz Kausar babu....” Cak ya tsaya yana binta da wani irin duba cikin rashin yarda da kalaman da suke fitowa daga bakin k’anwar tasa yake furta “What do you mean Kausar babu... Mai kike nufi Naja’atu.....?” Cikin Kuka Najah ke fad’in “Yaya Kausar ta rasu, mun rasa Kausar , Allah ya karb’i abinsa....” Fuzgewa yayi daga rik’on data masa yana mai binta da wani irin duba yake girgiza kai kana ya shiga furta “No no no, my daughter is alive.... D’iyata tana raye..... I know she’s alive... Ni na sani... Ina Hajiya... Ina Hajiya nasan tana wajen Hajiya... Yanzu zan bata toys d’inta.....” Tamkar zararre haka shiga surutai, lokaci guda ya nufi d’akin Hajiya gadan gadan bai damu da matan da yake haye kansu ba shidai kawai yaga Kausar d’insa... Wata Innar Hajiya ce ta rik’esa tana basa baki tana fad’in yayita karanto innalillahi.... Inaaa Hafiz sai fuzgewa yake yana tambayan ina aka b’oye masa d’iya... Fad’i yake “Hajiya nasan baki son zamanta a nan fine na maki alk’awari daga rana mai kaman ta yau kin gama rik’onta zan d’auketa na tafi da ita.... Ni zan rik’eta zan rik’e kayana... Please ki fito min da ita I know she’s in there ku bani d’iyata please....” Ya k’arashe yana nuni da uwar d’akin Hajiya.... Innar Hajiya ta kuma jaddada masa cewa d’iyarsa ta rasu ta rasu babu dawowa...., Hajiya ta cafe da masifa tana mai furta “Da kin k’yaleshi ya shigo d’akin ya duba tinda ya tab’a ganin yanda akai k’aryar mutuwa...” Ta k’arashe tana muzurai... Hafiz durk’ushe k’asa rungume da kayan wasan yarinyarsa yake hawaye, lokaci guda yake furta “I only want to be with my daughter....” Wajen yayi shiru banda sautin fitar kukan Hafiz da kake iya jiyowa.... Ya d’ago idanunsa masu zuban hawaye yana duban mahaifiyarsa kana yace “Hajiya maiyasa akai mata sutura ba tareda an sanar dani ba.. Mai yasa aka kaita makwancinta ba tareda na mata addu’a ba... Mai yasa ba’a bari nayi bankwana da d’iyata ba...?” Ya k’arashe hawaye na kuma gangaro masa.... Fuska a tab’e Hajiya tace “Cikin abinda ka lissafa babu wanda ba’ayi ba, wayarka an kira yafi sau babu adadi kai har d’an aike an tura gidanka akaji gidan a rufe toh so kake a barta haka nan ayita jiranka sai sanda kaga dama ko mai...?” Bai kuma furta komai ba sai rintse idanunsa da yayi da k’arfin gaske... Sahariyya dake lab’e jikin labule tana lek’ensa sai faman yatsina baki take d’igon tausayi ko nadama babu a tattareda ita Fuskarsa jazir ya kuma d’agowa ya dubi mahaifiyarsa yana mai sakin huci a hankali, cikin dakakkiyar murya yace “Hajiya mai ya sameta... Mai yayi sanadin rayuwarta...?” Sahariyya da Hajiya suka had’a ido Sahariyyan na aikawa Hajiya wani irin duba... Take Hajiya ta shiga inda inda tana fad’in “Yo mai kuwa ya kasheta banda ajali ko kashe maka d’iyarka zamuyi... inyi, ko rashin yardar naka takai haka ne...?” Bai kuma cewa komai ba sai mik’ewa da yayi tamkar wanda ruwa ya shanye ya fice ba tareda ya kuma furta koda kalma ba... Naja’atu tabi bayansa cikeda tausayawa har ya fice kana ta maido da dubanta ga Hajiya da Sahariyya tanai masu muguwar kallo cikin sauri ta fice tana mai girgiza kai... Sahariyya ta rakata da muguwar kallo kana ta tab’e baki ta koma cikin d’aki tana mai danna earpiece a kunnenta ta saki sauti cikin kunnuwanta.... *** Zaune suke saman dakali k’ofar gida sai zuba zance suke irinta matasa, akasarin firan ya danganci siyasa ne da kuma wasanni k’wallon k’afa.... Daidai sanda mai amalanken rake yazo shigewa d’aya daga cikin matasan mai suna Auwalu ya tsaida mai amalanken, tuni mai rake ya gangaro yanda matasan ke zaune... Auwalu ya dubi Akram da hankakinsa kega wayar salulansa yace “Yauwa ga mai raken na kira a saya mana muji dadin yin zance ko ya kukace...?” Gaba d’aya sauran matasan sukace haka ne... Akram ya d’an dube abokan nasa a kaikaice kana yace “Amma dai bani na tsaida mai rake ba...?” “Koma bakai bane dole ka saya mana tinda mai gidanka na nema muk’ami idan ba haka ba mu hanaku k’uriunmu ko ya kuka ce..?” Nan ma suka amsa da wannan haka take, basu jira cewar Akram ba suka shiga zab’en rake mai rake na fere masu radio na kunnensa yana faman saurare... Akram fad’i yake “Kaga Malam ko wanne cikinsu sai ya biyaka kud’inka....” Mai rake na murmushi yake fad’in “Ai idan zasu zab’i MUTALLAB zab’in talakwa ko amalanken raken sukeso gaba d’aya sai na basu....” Suka kekate da dariya gaba d’aya harda shi Akram d’in, tabbas ya sani Mai gidansa yanada magoya baya da dama wanda idan za’ayi zab’en gaskiya tsakani da Allah zai iyaci... Akaci gaba da firan siyasa harda mai rake radio na bisa aiki, nan kuwa aka soma program d’in Muryar ‘yanci, Akram ya bud’e kunnuwa sosai yana jira yaji muryarta, baiji muryar tata ba sai na abokan aikinta daga bisani yaji d’aukacin ma’aikatan gidan radio d’in na mik’a mata sak’on ta’aziya na rashin d’iyarta da tayi... Tsananin mamaki ya cika Akram... Wai dama tanada aure harda yara...? Shi kad’ai yake tambayar kansa cikin zuciyarsa.... Bai kuma bi takan firan tasu ba har ya sallami mai rake ya basa kud’insa ya kuma ce ya rik’e canjin domin gudan dubu ne a aljihunsa... Matasan suka kuma ihu suna wasa shi suna fad’in sai Uban gidansa ko garin bakowa... Akram dai gaba d’aya zuciyarsa ta tafi wata duniyar... Abokinsa da suka taso tare a unguwar mai suna Yusuf shi ya fahimci nisan zango da Akram d’in yayi.... D’an dafasa kad’an yayi kana yace “Abokina akwai matsala ne...?” Akram ya d’ago ya dubi Yusuf kana yace “Muje daga gefe...” Babu musu Yusuf ya mik’e yabi bayan abokin nasa.... Daga can tsallake suka tsaya k’ofan gidansu Yusuf.... Yusuf yace “Akram lafiya dai ko...?” Akram yace “Yusuf dama tanada aure...?” Cikin rashin gane inda ya dosa yace “Aure... wace kenan...?” Akram ya d’an shafi goshinsa yace “Zulfa’u Mailafiya ta gidan radion Muryar ‘yanci....” Yusuf ya d’an murmusa a hankali kana yace “Aw dama baka sani ba...? Eh toh tanada aure batada aure...” Akram ya dubesa da alaman tambaya kana yace “Ban gane ba what do you mean tanada aure batada aure...?” Yusuf yace “From what I know sun rabu da mijin nata kwanakin baya can, kasan Atika abokiyar aikinta k’awar Saliha k’anwatace....” Akram ya jinjina kai kana yace “I want to know more about her,...” Yusuf ya d’an murmusa kana yace “Kar ka damu abokina zanyi k’ok’arina, zansa Saliha ta sanar da k’awarta zamu kaiwa Zulfa’u ta’aziya da sunan jamk’iyarku ko ya ka gani...?” Akram ya d’anyi shiru kana yace “Amma kanaga bazatayi tunani siyasa ya kawo mu ba....?” Yusuf yace “Haba Akram kasan MUTALLAB yanada magoya baya da dama yau ko siyasarce takaimu na tabbata bazamuji kunya ba duk yanda mukaje da sunansa....” Akram ya d’anyi shiru na wasu dak’ik’ai kana yace “Shikenan Allah shi wuce mana gaba..” Yusuf ya amsa da Ameen kana suka nufi cikin gidan gaba d’aya.... *** Tinda suka iso Kaduna suka had’a k’arya da gaskiya suka fad’iwa Ammi, Siyama harda cewa Khalid harda ita ya had’e ya daka... Ammi ta dafe k’irji tana salallami... “Khalid ne ya d’aga hannu ya dakeki...?” Ta kuma tambayar Siyamar... Cikeda makirci Siyama tace “Aw mamaki kike sha Ammi, Toh wllhi Khalid ya shige duk yanda kike tunani, baiga darajan girme masa da nayi a haife ba yasa hannu ya dakeni nima don kawai nace ya rabu da wancan dangin mayun....” Yesmin dake gefe da kumburarren bakinta tace “Wllhi Ammi ko shakka babu an juye masa kwanya bakiga yanda ya fice a hayyacinsa ba gaba d’aya....” Ammi tai k’wafa tace “Dad na hanya ai shine kawai maganinsa don wllhi bazai janyo mana kayan kunya ba....” Ta k’arashe tana mai kuma dialing layin Khalid d’in Kubura dake lab’e jikin staircase sai faman k’unshe dariyarta take tana kwaikwayan maganan Yesmin da yanda bakinta ya kumbura ya koma gefe guda, sai murna take tana tsallen Allah shi k’ara.... A daren Khalid ya dawo garin Kaduna saidai ko sashen Amminsa bai shiga ba, washe gari ma bai fito ba har saida ya tabbata mahaifinsa ya dawo don yana ganin sanda driver ya tafi airport d’aukosa, baiji mamakin ganin Khalid d’in baizo d’aukansa ba don tun a waya Ammi ta zayyane masa komai duk halinda ake ciki, shi kad’ai yake sakin huci har sai yafi Ammi fushi da lamarin musamman da shike an tab’o sanyin idaniyarsa Siyama wacce a duniya yak’i jinin yaga fushinta sabida tsananin sonta da yake.... Suna zaune gaba d’aya a parlorn ya sako kai, ko ba’ace ba yasan fitowarsa ake jira.... Kallo d’aya ya watsawa Siyama ya d’auke kai daga barin duban nata.... Can k’asa gefen k’afafun mahaifinsa ya k’arasa ya zauna... A hankali ya furta “Daddy sannu da zuwa... Ammi ina kwana...?” Baikai aya ba Ammi ta katsesa da fad’in “Da ban kwana ba zaka ganni...? Nace da ban kwana ba zaka ganni...? Ince kai ka zama sallamemme.... Ace tun jiya ka dawo gidan nan ka kasa lek’owa mu gaisa sabida ta zuba maka a ruwa kasha koh.... Harda wulak’anta ‘yan uwanka don kawai sun fad’i gaskiya...? Idan ka zab’eta sama da ‘yan uwanka ne sai ka tattara ka koma can ka zama cikakken sallamemme...” Siyama ta k’arada “Ahtoh fad’a masa dai Ammi..” Daddy ya cafi zancen da ambato sunan Khalid... “Khalid...!” Khalid ya d’ago a hankali yana dubansa kana yace “Na’am Daddy...” “Dad yaci gaba da fad’in “Khalid meke faruwa da rayuwar ka....?” A hankali ya furta “I’ll explain everything Dad....” Dakatar dashi yayi ta hanyar d’aga masa hannu kana yace “Ba sai ka min bayanin komai ba, mahaifiyarka ta sanar dani, ba kuma zan bari ka kawo mana abin fad’i a dangi ba, bazaka kawo mana yarinya maras cikakken asali ba da sunan mata, ga mata da yawa a duniya, kaje duk yanda kakeso ka kawo mace idan har family background d’inta nada kyau ni zan aura maka amma banda yarinyar da aka tabbatar batada cikakken asali balle tarbiya...” Khalid ya dubi Ammi da Siyama da tsananin mamakin jin yanda suka had’awa Dad zance ya hau kai ya zauna... Ammi ta katse hanzarin nasa da fad’in “Ga k’awarsa Yesmin babu abinda ya rasa mai zai kaisa wani duniya neman mace...” Daddy yace “Kaji koh... Inaso kamin rantsuwa babu kai babu wancan yarinyar sannan zaka auri ‘yar uwarka Yesmin....” Khalid ya d’ago da mamaki yana duban mahaifinsa kana yace “Daddy rantsuwa fah kace....? Daddy it doesn’t have to reach this point...” Ammi tace “K’warai kuwa it does ta hakane kawai zamu amince ka rabu da wancan tsinanniyar yarinyar.... Zaka rantse ne kokuwa...” Khalid ya dubi mahaifiyarsa kurum ba tareda ya iya furta koda kalma ba... Dad yace “K’yalesa tinda bazaiyi abinda mu muke so ba a matsayinmu na iyayensa muma bazamuyi abinda yakeso ba...” Yakai dubansaga Khalid da kansa ke duk’e k’asa kana yace “Khalid inaso ka maido min da duk wani abinda na mallaka maka na jin dad’in rayuwa sannan ka tashi ka fice min daga gida kar ka dawo har sai ranar daka amince da buk’atarmu...” Khalid ya d’ago a firgice yana duban mahaifinsa cikin rashin yarda da abinda kunnuwansa ke jiyo masa... Baki na rawa yace “Daddy.....” Dad ya kuma dakatar dashi da fad’in “Ka tashi ka fice mun a gida ka aje mabud’an section d’inka da na office d’inka.... I believe you can provide for yourself... Now..!!” Ya k’arashe cikin d’aga murya.... A hankali jiki babu laka ya mik’e ya nufi k’ofa.... Kubura dake lab’e bayan k’ofa hawaye suka shiga gangaro mata ji take kaman ta isa a guje ta rungumesa , ita kanta Yesmin d’in dake lab’e mab’oyarta sai taji babu dad’i ita ba haka taso ba bata zaci Daddy zai iya koran Khalid daga gidansa ba, ji tayi kaman ta ruga cikin parlorn tacewa Daddy duk abinda suka fad’i akan Nabila k’aryace.... Ta rintse idanunta tana hawaye... Tana ganin sanda Khalid ya dawo parlorn rik’esa keys a hannunsa da kuma suitcases d’insa biyedashi.... A hankali ya isa ya aje keys d’in gaban Daddy.... Siyama da Ammi mamaki ya cikasu ganin Khalid ya zab’i ya tafi akan yayi rantsuwa ya rabu da wancan yarinyar lallai da alama da gaske shanyesa tayi, jikin Ammi ya soma yin sanyin ganin Daddy da Khalid babu mai fasa k’udirinsa.... Har yasa kai zai juya Dad yace “Your car keys ajiyesu tinda suma ta dalilina ka samu....” Khalid ya kuma duban mahaifinsa cikeda mamaki, lokaci guda ya sadda kai k’asa ya cirosu a aljihu ya aje saman center table... Dad ya kuma fad’in “Your master cards ajesu suma....” A hankali Khalid ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya ciro wallet d’insa ya cire ATM cards d’insa ya ajesu saman table d’in.... Dad yace “Kar na sake ganinka k’ofar gidana balle k’ofar kampanina... Get out....!” Ya k’arashe yana mai nuna masa k’ofa.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *52* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* D’ago kai Khalid yai yana duban mahaifan nasa kaman zai magana sai kuma yai shiru baice komai ba, a hankali ya juya ya janye da suitcases d’insa, cikin wani irin yanayi yake d’aga k’afafunsa... Zuciyar Ammi ta shiga tsinkewa ganin da gaske Khalid fita zai a gidan, tasan d’an nata da mugun zuciya amma batai zaton zai iya tsallake conditions d’in da mahaifinsa ya kafa masa ba ya fice.... Cikin inina takeceda mijin nata.... “Daddyn Siyaam don’t you think you’re going too far, kaga fah ficewa zaiyi, ina zaije shi, mai zaici..? Dan Allah kai hak’uri ka rangwanta masa....” Wani mugun kallo Daddy ya watsa mata kana yace “Khalid baida muhalli a gidana until he’s learned his lessons...” Ammi ta kuma kai dubantaga Khalid da har ya kusan ficewa daga parlorn, cikin sauri ta kuma duban mijin nata kana tace “Idan bazaka masa afuwa ba ko credit cards d’insa ka taimaka ka bashi mai zaici ina zaije....?” A hasale Daddy ya kuma cewa “Nace maki har sai ya gane kuskurensa, babu abu guda a nan da zan basa sabida komai a nan ta dalilina ya samu, so idan har bazaiyi abinda ni nake so ba ya fice ya nema nasa da kansa yaji yanda ake nema da gumi....” Duk maganganun da suke cak Khalid yai tsaye yana saurarensu zuciyarsa na kuma masa zafi... Cikin sauri yasa kai ya fice tamkar zai kifa k’asa.... Kubura tabi bayansa da kallo had’ida d’aura hannu bibbiyu aka tana kuka tana fad’in ta shiga uku... Daddy bai kuma bin takan su Ammi da Siyama ba yai ficewarsa.... Harta Siyama saida ta sha jinin jikinta, ita kanta batai zaton abin zai kai nan ba, Daddy ya kori Khalid kuma Khalid baida niyyan janye ra’ayinsa, lallai abin ya girma.... Yesmin ne ta fito daga mab’oyarta a guje tana hawaye take fad’iwa Ammi “Aunt please talk to Daddy, he can’t send him away... Toh ina zaije shi.... Dan Allah ki masa magana” Harara Ammi ta watsa mata ba tareda tace komai ba ta haye sama zuciyarta na mata zafi sosai.... Yesmin jiki a sanyaye ta maido da dubantaga Siyama murya har na rawa take fad’in “Cousin this can’t be, we must do something....” D’an dubanta Siyama tai kana tace “Nima kaina abin ya dameni, amma karki damu don na tabbata Khalid bazai iya ba he would definitely give up, zai dawo ne sannan wannan shine kad’ai chance d’inki da zaku kasance tare, we should just keep an eye on Khalid, na tabbata Khalid baida abokin da ya wuce Baffah so definitely wajen Baffah zaje shi....” Yesmin ta goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Shikenan hakan yayi, but I don’t want him to hate me even more...” Siyama tace “Kedai nace miki ki bar komai hannu na a k’arashe Khalid baida zab’in da ya wuce ya yarda da duk wani condition da Dad ya kafa masa ciki kaw harda aurenki, so just chill kinji koh...” Ta k’arashe tana buga kafad’unta had’ida hayewa sama wajen mahaifiyarta.... Kubura ta fito daga mab’oyarta fuska duk hawaye yayinda ta hangi Yesmin itama fuskar tata jik’e yake da hawaye, nan sukai cirko cirko kowa tana aikawa juna muguwar kallo, tsuka Yesmin tai zata haye sama nan ta sinkayo muryar Kubura tana fad’in “Aikin banza wai harara a duhu, tusa kai babu k’warjini kuwa yawa ne, wllhi iska dai na wahal da mai kayan kara, mutum yace baya so baya so ko an tab’a soyayya dole ne... Billahillazi duk abinda ya samu Saifulllah mutum zaiji ne daga gareni....” Cak Yesmin ta tsaya ta daina taka matakalan ta kaikaito shaye da mamaki tana duban Kubura, batasan sanda dariya ya kufce mata ba tace “I don’t have your time, you filthy made....!” Lokaci guda ta haye sama kaman zata tashi sama.... Kubura ta kuma yin k’wafa ta goge hawayenta ta fita ta nufi gate a guje ko zata hango Khalid..... **** Ba shi ya koma gidan ba sai ana kiraye kirayen sallan isha.... Sawwama na zaune saman kujera tana kallon gidan talabijin na bollywood taji motsin shigowarsa, tana ganin sanda ya zube a veranda had’ida kifa kansa saman gwiwoyinsa, batace uffan ba bata tankasa ba saima tab’e baki da tai taci gaba da girgiza k’afafu d’aya bisa d’aya tana kallonta... Tana jin sanda Hafiz ya busting cikin tsananin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare amma ko gizau Sawwama batai ba, saida aka kwashe kusan mintoci kaman biyar a haka kafin ta juya idanunta had’ida sakin gajeran tsuka ta mik’e ta isa gareshi tana faman tauna chewing gum tana wani jujjya idanu had’ida aika masa harara, ta kwashi dak’ik’ai a hakan kana ta d’an rank’wafo had’ida sassauta murya tace “Hafizi lafiya...? Meke faruwa na ganka haka cikin irin wannan tashin hankali...?” A wahalce Hafiz ya d’ago yana dubanta, bai iya cewa komai ba sai rungumeta da yayi very tied yana kuma sakin kuka sosai tamkar wani k’aramin yaro, Sawwama ta rausayar idanu tana mai jin takaicin kukan nasa har cikin zuciyarta.... Cikin muryar kuka yake furta “Kausar Kausar babu Sawwama.... Kausar ta tafi ta barni.... Na rasa tilon d’iyata Sawwama....!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya mai ban tausayi.... Cikin zuciyarta banda tsuka bata komai, a fili kuwa tsan tsan damuwa ta nuna ta shiga salallami da kururuwa wanda kai kace gaskiyane har cikin zuciyarta ne... “Allah sarki Kausar yarinyar nan ashe ba mai zama bace, badon Allah ya k’addara hakan ba da tana nan abinta a nan, ai banci ta zamaba Hafizina bara na shirya na tafi makoki...” Ta ida maganar tana maici gaba kuruwa.... Bai iya furta koda kalma ba sai zubewa k’asa gijif da yayi yana mai kuma dafe kansa.... A haka ta d’auko mayafi ta taddashi nan zaune wajen yanda ta barsa, ta tab’e baki tana kuma aika masa harara, lokaci guda ta saki murmushin mugunta kana tace “Hafizina ai hak’uri ai mata addu’a ni na wuce don bai kamata ana can ana makoki ba ni ina nan.....” Nan ma Hafiz bai iya tankata ba har tayi ficewarta, shi kad’ai yasan abinda yakeji cikin zuciyarsa saiko mahaliccinsa.... Sawwama tana ficewa ta tari mai adaidaita tana kiran Alhajinta a waya.... *** A can asibiti wajen Raihana kuwa Mamani tayi zaune ta rapka uban tagumi tana kallon yarinyar, tsananin tausayinta na kuma ratsa zuciyarta, k’aunar yarinyar take har cikin zuciyarta, Bata tab’a zaton zata k’aunaci d’aya daga cikin jikokinta mata irin hakan ba, sai gashi Allah ya jefa mata k’aunan Raihanah cikin zuciyarta.... Tana a haka Dr Awwab yai sallama ya shigo nurses biyu biyeda bayanshi... Mamani tana ganinshi ta soma sakin murmushi tana fad’in “Datta an shigo...” Awwab murmushi kwance saman fuskarsa yace “Eh Baaba ya jikin jikar taki...?” Mamani fuska sake tace “Toh Alhamdulillahi zamuce an auna arziki tinda da ranta...” Awwab yace “Hakane Baaba... Emm nace ko zaki d’an jiramu waje munaso za’ai dressing...” Mamani tace “Na’am d’an nan za ai mai kace...” Nurse guda dake kwance drip tace “Baaba ciwon jikar taki za’a wanke...” Mamani ta yab’e baki tace “Yo na ganki a nan ai amma na tambayeshi....” Nurse tace “Allah baki hak’uri Baaba...” Mamani ta tareta da fad’in “Amin hak’urin ta kawomu yanda muke yanzu... Kajimin kilibibi irinta yaran zamani....” Dr Awwab ya k’unshe dariyarsa ya shiga baiwa Mamani baki lokaci guda ya shiga janta da barkwanci da shike gwani ne wajen barkwancin.... “Hajiya Baaba mu k’arasa daga waje mu barsu suyi aikinsu, banida round muje nai miki hira...” Mamani ta d’an dara cikeda jin dad’i don tuni ta sake da Awwab ko don barkwanci irin tasa.... Suna tafe take tambayarsa “Niko nace ina abokin aikin naka shi wancan likitan...” Awwab yace “Aw Sameer, ai shi aikin nasa da safe ne shiyasa ya tafi....” Mamani ta d’anyi shiru tana mai son tambayan Awwab abubuwa da dama gameda wancan likitan, haka kurum takejin babban al’amari a tattereda shi tun sanda ta soma arba dashi... Awwab zai kuma fad’in Baaba tace kirani Mamani kaji d’an nan... Yai murmushi yace toh Mamaninmu *** KADUNA D’an savings d’in dake jikinsa yai amfani dasu ya kama madaidaicin d’aki a hotel mai sauk’in kud’i.... Gaba d’aya ya kasa sakin jiki a hotel d’in abinka da wanda bai saba da kwanan irin local hotels haka ba, sai faman d’aga kai sama yake yana bin d’akin da kallo wai shi Khalid yau shine dai zaiyi kwanan wannan hotel d’in... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da iska, kishingid’a yai saman gadon had’ida zaro wayar salulansa a aljihu ya shiga shafawa... Daidai kan lambar wayarta ya tsaya had’ida kafe wayar da idanu... Teddy Bear sunan da ya saving lambarta dashi ya furta a hankali.... Yatsunsa yakai kan lambar kaman zai dialing sai kuma ya tsaya yana kuma kallon wayar... Gajeren tsaki yai had’ida cilla wayar gefensa.... Ya janyo pillow had’ida danna kansa ciki ko baccin dole zatai gaba dashi.... Washe gari sassafe wayar Baffah ne ta tadashi tun kwanciyar bayan sallan asuba da yayi... Ya janyo wayar da k’yar yana kallon screen d’in wayar.... Ganin mai kiran nasa ya sanyashi sakin tsaki a hankali, k’arfe bakwai da rabi na safiya kaman yanda ya bayyana mashi a fuskar wayan... Bai d’aga kiran ba har ta stinke ya kuma maida kansa ya kwanta nan sautin wayar ta kuma tadashi, har ila yau Baffah amininsa ke kiransa... Da tsaki ya d’aga wayar kana jin muryarsa kaji wanda bai sami wani wadataccen bacci a daren da ya gabata ba.... “Ka fad’a min idan bashi kake bina da zaka kirani this early...” Abinda ya soma fad’i kenan... Daga d’aya b’angaren Baffah yace “Khalid kana ina ne...?” “You haven’t answered my question... Why on earth zaka tasheni da sassafen nan... what for...?” Baffah yai gajeren tsaki kana yace “Drop that ego for once in your life Khalid ba’a fad’a da iyaye... Idan har kana son albarka cikin rayuwanka kabi bayin Allahn nan sauda k’afa... Ta yaya zaka zab’i mace akan iyayenka... Akan mai Khalid....?” Dafe kansa da ya masa nauyi yai kana yace “It’s too early for this.... I’ve headache already...” Girgiza kai kurum Baffah yai kana yace “Tell me your location...” Badon yaso ba sai don Baffah ya nace ya sanar dashi otel d’in da yake..... Mintuna kad’an Baffah ya iso hotel d’in shaye da tsananin mamakin wai Khalid ke kwanan irin wannan hotel d’in... Fuska a tab’e Baffah kebin ‘yar d’akin da kallo don shi ko wajen zama bai gani ba a cewarsa... Khalid ya dubesa a kaikaice kana ya watsar.... Sanin cewa idan zai kwana wajen a tsaye Khalid bazaice masa ga wajen zama ba yasashi zama bakin ‘yar gadon.... K’uri Baffah ya masa kana ya girgiza kai a hankali yace “I never thought ban tab’a tunanin...kai not even in my dreams, the whole Khalid Mainasara the one that I know zai iya falling for wata mace ba waima har ya bar luxury life d’insa his family and everything yazo yana living miserable life irin haka ba... Khalid for crying out loud...!” Bai kai aya ba Khalid ya katse sa da fad’in “Cut it out please... Will you? Haba kazo ka sakani a gaba kana min lecture, wanda kayi a waya bai isheka ba... Look Baffah this is my life and I hate it when people try to intrude...” Katsesa Baffah yayi da fad’in “You can call me intruder or whatever amma bazanga kana abu maras kyau na k’yaleka ba Khalid... Quit this nonsense ka tattara ka koma gida and apologize to your parents...” Cikin tsananin b’acin rai yayi maganan wanda tinda ya soma Khalid bai kallesa ba saima wani gefen da yake duba... A kaikaice ya dibeshi gira a sama yace “Are you done... Ka gama...?” Baffah yayi shiru yana duban sa kurum sanda ya isa k’ofa ya bud’e masa yana mai masa alama da hannu yake fad’in “Get out please....” Baffah yasan hakan ka iya faruwa yasan kafiya irinta Khalid mutum ne da sam bai tank’waruwa don haka bai Kuma cewa uffan ba sai mik’ewa da yayi jiki babu laka ya nufi k’ofa... Har ya isa k’ofar yaja ya tsaya, hannu yasa cikin aljihu ya ciro wallet d’insa ya zaro katin atm ya mik’a masa yana fad’in “One of your Bank cards Ammi ta bayar a kawo maka Incase you may need...” Murmushi yai kana yace “Ka mayar mata bana buk’ata....” Girgiza kai Baffah ya kumayi bai tsaya jan inja da Khalid ba yayi ficewarsa rai b’ace.... *** KANO Zulfa’u na kwance uwar d’akin Mamy k’aramar alk’ur’ani rik’e hannunta tana karantawa Marliya ta shigo da sallama A hankali ta goge hawayen da suka zubo mata kana ta dasa aya ma karatun nata ta amsa sallaman Marliya... “Addah wai wasu bak’i ke sallama a parlorn Abbah zasu gaisheki....” Da shike tunda akayi rasuwar parlorn Abbah ta waje na bud’e maza sukan shiga parlorn suyi gaisuwarsu musamman dangin Mamy dashike dangin Abbah wasu nacan gidan Baba Alhaji mahaifin Hafiz... Zulfah ta dubeta da mamaki kana tace “ Bak’i kuma.... Baki sansu ba..?” Marliya ta girgiza kai a hankali tace “Ban shiga ba Addah, Aunty B ce tace nai kiranki....” D’an jim Zulfa’u tai kana ta mik’e ta zura hijab d’inta, hannun Marliya ta janyo da nufin tai mata rakiya... A daidai k’ofar parlorn ta hangi Hafiz ya turo k’aramar k’ofan gate ya shigo cikin gidan... K’irjinta ya bada wani irin sauti, ganin Ya Hafiz ya sanyata shiga sabon tashin hankali domin kaw kamanninsa d’aya da d’iyarsa Kausar ne babu abinda yarinyar ta rage masa, take taji k’walla na neman ciko idanunta, tai tsaye ta kasa ci gaba da tafiya... Shima Hafiz d’in tinda ya hangeta sai ji yayi k’afafunsa sun kasa d’aukansa sai sabbin k’walla da yaji suna neman ciko idanunsa... Marliya takai dubantaga yanda Zulfa’u ke duba ganin ta kasa ci gaba da tafiya... Ganin Ya Hafiz ne ya sata k’ok’arin juyawa da zummar komawa cikin gida amma saidai tuni Zulfa’u ta janyo hannunta sun shige cikin parlorn yanda suka bar Hafiz nan tsaye tamkar wanda ruwa ya shanye.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *53* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Marliya ce ta fara yin sallama Zulfa’u na biyeda ita, muryar da ta daki dodon kunnuwan Akram sai yaji tamkar wacce yake saurare a gidan radio, d’ago idanu yai yana duban k’ofan wanda ya sanyasa yin idanu hud’u da mai sallaman domin kaw itama Marliyan su take duba idan ka d’auke Zulfa’u da kanta ke k’asa... Cikin sauri Hafiz ya take masu baya, bai shiga parlorn ba sai tsayawa da yayi daga bakin k’ofa yana jiyo abindake wakana, haka kurum yaji zuciyarsa sam bai kwanta masa dasu Akram ba musamman da yaga irin wankan shadda da hula da suka zuba.... Bayan sun gaisane Zulfa’u ke fad’in “Saidai ban gane daga ina bane...” Yusuf ya d’anyi gyaran murya bayan Akram ya d’an dubeshi a kaikaice.... Nan Yusuf yaci gaba da fad’in “Mu wakilan ALHERI Party ne, mun kasance muna matuk’ar k’aunan shirye shiryenki a tasharku ta gidan radio RY, muna kuma jin dad’i sosai yanda kuke k’ok’arin gayyato manyan manazarta masu fayyace gaskiyar abindake faruwa a siyasar k’asan nan da kuma wayarwa jama’a kai a b’angaren abinda ya shafi sanin mahimmancin k’uru’unsu... Wannan dalili yasa Party d’inmu ta wakilcemu a madadin d’aukacin sauran ‘ya’ayanta kama daga shi Eng Ma’aruf MUTALLAB mai neman takaran kujeran gwabna har izuwa sauran ‘ya’yan jamk’iya suka wakiltamu domin mu mik’a gaisuwar ta’aziyanmu na rashin da aka miki... Ubangiji yajik’anta yasa kuma mai ceto ce...” Gaba d’aya suka amsa da ameen ida ka d’auke Hafiz da k’irjinsa ke tsananin bugu da sauri da sauri, abinda yafi d’aga masa hankali ba komai bane illa ji da yayi Wai Zulfa’unsa ce ta soma aiki a gidan radio ba tareda yasan hakan ba harma wad’annan ‘yan iskan ‘yan siyasan suna saurarenta, watoma gaurayuwa kenan takeyi da maza tana masu interview... Bai ida tunanin nasa ba ya tsinkayo muryarta tana fad’in “Allah sarki mun gode k’warai da gaisuwarku, Allah Ubangiji kuma yasa a mizani amma saidai ina fata ba sabida siyasarku kukayi haka ba domin ni aikina kwai nakeyi yadda aka umarceni...” Yusuf ya murmusa yace “A’a Rankishi dad’e ko d’aya bamuyi hakan domin k’arawa jamk’iyarmu martaba sai don kyautata alak’armu da d’aukacin jama’an wannan jiha ina fata hakan bazai kawo wata mishkila ba...” Kafin Zulfa’u ta sami zarafin basa amsa sukaji an banko labule an shigo.... D’aga kan da zatai tai tozali da Hafiz sai faman huci yake lokaci guda yake nuna Yusuf da Akram da ‘yar yatsa yana fad’in “Idan baku tashi kun fice ba ina mai tabbatar maku zakuga babban mishkila, don mace na aiki a gidan radio hakan bai baku dama ku dinga bibiyan matan mutane ba kuna fakewa da siyasa!” Yanda yake maganan har wani irin zabura yake sabida tsananin b’acin rai... Zulfa’u ta mik’e a zabure tana fad’in “Ya Hafiz dan Allah ya isa haka... Not now please...” Tsawa ya daka mata da fad’in “Kimin shiru kekuma, shine sabida tsaban iskanci har aiki kika soma gidan radio kina watsa ra’ayinki na siyasa salon maza su biyoki har gida koh... Toh wllhi kinji na rantse kin gama wannan shegen aikin gidan radio din...” Tinda ya soma magana kuka ya kufce mata yayinda Marliya ta fice a guje ta nufi cikin gida neman d’auki ganin Hafiz ya fice a giya.... Gadan gadan yayi kansu tamkar wanda zai kai masu duka yana fad’in idan basu fita ba zaiyi ajalinsu... Ganin haka yasa Zulfa’u yin kansa a guje tana k’ok’arin janyoshi amma inaa tuni ya bangajeta ta fad’i k’asa... Sai lokacin Akram ya zabura ya mik’e yayi tsaye gaban Hafiz tamkar k’irajensu zasu gogi juna, In a husky voice Akram ke nunasa da yatsa yake fad’in “Don’t hurt her or else....” Hafiz na d’aga jijiyan wuya yake fad’in “Or else what...? Mai zakumin, zaku sa a kasheni ne irin yanda ‘yan siyasa irinku sukeyi zakusa ‘yan dabanku suyi ajalina ne ko mai... Ka fad’a mana...!” Ya k’arashe yana kuma d’aga k’irji saman yana sakin huci daidai lokacin dasu Mamy suka shigo babu shiri suna sallalami... Aunty B ce tai k’ok’arin janye Hafiz tana mai baiwasu Akram hak’uri yayinda Mamy ta nufi d’iyarta dake durk’ushe wajen a k’asa tana kuka mai tsuma zuciya.... Har bayan ficewarsu Akram Hafiz bai daina cewa Zulfa’u sabida maza ta soma aikin gidan radio ba, yana fincika daga hannun Aunty B yana fad’in idan k’arya yake ba sabida maza take aikin ba ta tashi ta musa... Tsananin zafi da zuciyar Zulfa’u keyi batasan sanda ta mik’e tana huci take fad’in “Idan sabida maza nakeyi meye naka a ciki, meye ruwanka a ciki, shin ka mance ni yanzu ba matarka bace... Ka mance hakan Ya Hafiz...? Ka mance inada dama da zan tsaya da duk namijin danaga dama, ka mance inada dama da zan baiwa duk wani namiji mai son aurena k’ofa... Ka mance babu iddarka akaina..? Ka mance babu kome a sakinmu...? Idan har ka mance duka wad’annan, well let me remind you...” Kuka sosai ya kufce mata sanda taci gaba da fad’in cikin rawar murya “Badon kar nace babu sauran alak’a da ya had’amu ba tinda gudan jinin dake tsakaninmu Allah ya karb’i abinsa... Amma saidai kai d’in d’anuwana ne na jini duk yanda naje nazo... Kuma har abada bazan daina baka girmanka na Yaya a gareni ba... Ka tsaya a madakacinka don’t cross your limits...” Tana ida fad’in haka tasa hannu ta goge hawayen da suka jik’a mata fuska kana ta shige cikin gida.... Mamy ta take mata baya cikin sauri yayinda Aunty B ta saki murmushin jin dad’i ganin yanda Zulfa’unta ta takewa Hafiz burki, kallon yayi daidai ta raka Hafiz dashi kana ta shige ta barsa nan tsaye tamkar wanda ruwa ya shanye... Jiki babu laka ya fice daga gidan abubuwan da Zulfa’u ta fad’i sunai masa yawo a kwanya.... *** Driving yake suna tattauna lamarin Hafiz shida Yusuf, Yusuf yace “A gaskiya da gani tasha wahalan zama da wannan mahaukacin.... Kai kaga yanda yayi jifa da ita kuwa...?” Akram da zuciyarsa ke masa zogi ya fuzar da iska a karo na babu adadi kana yace “Badon ina tunanin she’s still grieving na rashin ‘yarta da tayi ba wllhi kaji na rantse da na koyawa mutumin nan hankali yanda nan gaba duk macen da ya kasance da ita zai girmamata ya darajata....” Yusuf ya dara kana yace “Mutumina nasan halinka ai don naga irin duban da kake masa, toh ya kadai ganta hankalinka ya kwanta...” Sai lokacin Akram ya saki murmushi a hankali sanda traffic light ya nuna masu koren wuta alamun an basu hannu kana yace “Kajika da wata magana... Kaga muje na ajeka na wuce I’m sure oga na can na jirana...” Yusuf yai dariya yace “His excellency zakace.... Kodashike kaje ganin her excellency na birnin zuciyarka ne don haka bazaka amsa query ba...” Nan ma murmushin kawai Akram ya kumayi kana ya d’auki hanyar unguwarsu domin sauk’e Yusuf... *** MUTALLAB’S Tsaye yake gaban full length mirror yana d’aura agogo a tsintsiyar hannunsa sanda ta turo k’ofan d’akin ta shigo fuska a turb’une.... Kallo take kan faman binsa dashi yanda yayi banza da ita tamkar baisan wata halitta na tsaye wajen ba, yayi kyau sosai cikin jampan nasa mai ruwan toka da ya bita da bak’ar hula zubin damanga.... Sai sassayanyar k’amshinsa dake dakan hancinta tinda ta shigo d’akin wanda babu wai tayi kewarsa sosai.... Ganin zai d’auki wayarsa dake gefen bedside ya sata yin sauri tasha gabansa tana rik’e da kunkumi tana watsa masa mugun kallo take fad’in “Ma’aruf let’s end this game now, wane irin rayuwa kakeyi... Ka sanar dani gaskiya azumi kakeyi kokuwa bin mata ka fara da yasa ka kasa nemata....?” Idan hulan dake bisa kanshi ya amsa toh shakka babu shima zai amsa.... Duba d’aya ya mata ya d’auke kansa yana k’ok’arin rab’an gefenta d’iyarsa k’arama ta shigo tana fad’in “Daddy nima zan bika... Please don’t say no, kaga Uncle Akram yace gobe dani za’aje....” Ta k’arashe baki a ture.... Rage tsawonsa yayi ya kamo yarinyar ya zauna bakin gado had’ida d’aurata bisa cinyarsa guda kana yace “Yara basa zuwa Kiddy ki zauna a gida kinji koh...” Mak’e kafad’anta guda tai kana tace “But I don’t want to Daddy, ni banson zama da Mummy bana sonta....” Zuciyar Muhibba ta kuma yin zafi takaiwa yarinyar dake kwance jikin Babanta harara kana tace “Wannan wane irin wulak’anci ne ina maka magana kayi banza dani kana biyewa yarinya salon a koyawa yara k’in uwarsu tun suna yara...” Baice mata komai ba sai d’aga Najma da yayi ya mata ‘yan dabaru ta hak’ura ta fice wajen ‘yan uwanta... Dawowa d’akin yayi ya tadda Muhibba tsaye tana faman huci, dukda zafi da zuciyarsa ke masa hakan baisa yace mata komai ba sai d’aukan d’aya wayar salulansa da yayi ya nufo downstairs.... Cikin tsananin fushi da takaicin yayi banza da ita ta biyo bayanshi tana fad’in “Ni Wllhi sai ka fad’a min wacece shegiyar da kake cin amanata da ita... Wllhi sai ka fad’a min....” Ta k’arashe cikin muryar kuka.... Tsaye yayi yana dubanta don yanzu abubuwan Muhibba sam basa bashi mamaki, “Ki d’auka a duk yanda ya miki, banida matsala da wannan, duk abinda shed’anin zuciyarki ya raya miki toh ki d’auka a haka, wannan ke ta shafa bani ba... Zan miki kashedi guda d’aya koda wasa kada ki kuskura ki sako yaranmu cikin wannan matsalan, this is between us do not involve them.... Na fad’a miki tun ba yau ba I can take care of them with or without you.... So kada ma ki fara dasawa yara cewa an koya masu tsanarki, ke da kanki kika zab’i hakan.... So na fad’a miki kada ki kuskura idan ba haka zakiga other side d’ina da har yau baki tab’a gani ba.....” Yana ida fad’in hakan yasa kai ya fice cikin sauri zuciyarsa na tsananin masa zafi.... Kallo tabisa dashi had’ida fashewa da wani irin kuka.... *** A can asibiti wajen Abbah kuwa da mamaki yake kuma duban Aunty Lami kana yace “Lami Kausar jikata kike nufi...?” Aunty Lami ta jinjina kai tace “K’warai kuwa bansan dalilinsu na b’oye maka ba....” Ta k’arashe tana juya idanu... Abbah ya rik’e bangaren k’irjinsa dake masa zafi sosai, ya sauk’o daga saman gado yana tambayarta ina takalmansa... Har lokacin hannunsa na dafe da k’irjinsa.... Aunty Lami fad’i take “A’ah Alhaji ina zakaje... Ina zakaje a haka... Ka tsaya likita yazo ya sallameka...” Abbah fad’i yake “A’a Lami ahalina suna buk’atana dole naje na gansu bazan tsaya jiran likita ba....” Ya k’arashe maganan jiri na k’ok’arin aikasa k’asa... Aunty Lami ta bud’e murya tace “Alhaji..!!” A daidai lokacin da Sameer ya shigo ya furta “Abbah..!!” Da k’arfin gaske baisan sanda ya isa ya rik’esa ba.... Zaro idanu waje tai k’afafunta na tsananin rawa, yawun bakinta cak ya kafe lokaci guda ganin hasashenta na neman tabbata bata ida karaya ba saida ta sinkayo muryar Abbah na fad’iwa Sameer “Ma’aruf gida zanje...!” K’iris ya rage Aunty Lami bata saki fitsari a jikinta ba, da za’a tsaga jikinta tabbas da zai wuya a sami jini sabida yanda ta daskare lokaci guda.... A hankali ta furta “Ma’aruuf ne..!!!” SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *54* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Abbah fad’i yake “Ma’aruf meyasa kuka b’oyemin mutuwar jikata, kan wane dalili.... Na riga na warke maza ka kaini gida... Muje banson na sake yini a wajen nan balle kwana....” Sameer ya rik’e shi sosai yana fad’in “Calm down Abbah please... Mu jura likita yazo ya duba idan za’a iya sallaman naka... Please Abbah...” Girgiza masa kai Abbah yaci gaba dayi yana fad’in “A’a Ma’aruf na warke, ka d’aukeni kawai mubar wajen nan...” Har wannan lokacin Aunty Lami bata dawo cikin hayyacinta ba, abubuwan da suka faru baya suke faman yawo a kanyarta... Ma’aruf ya dawo, yaron da suka salwantar da rayuwarsa da k’arfin gaske gashi Allah ya dawo dashi, tabbas dawowarsa barazana ne ga rayukansu.... Cikin mintoci k’ank’ani tai wad’annan tunanin.... “Lami kirawo likitan ya bani takardan shaidar sallamar, jeki kirashi ya sallameni...” Sai sannan Aunty Lami ta dawo daga duniyar data tafi... Cikin rawar murya take furta “To...Na’am... To Toh Alhaji ....” Cikin sauri ta fice daga d’akin ba tareda ta dubi b’angaren da Sameer ke tsaye ba, tamkar wacce k’aya ke sokinta haka ta fice daga d’akin... Sameer ya bita da kallo zuciyarsa na raya masa wani abin musamman da ya fahimci itace ta sanarwa Abbah mutuwar tilon jikarsa.... Sam Aunty Lami batasan yanda take jefa k’afafunta ba, ko kirawo likitan bata iya tayi ba, tsintar kanta tai a bakin kwalta ba tareda sanin ta fito waje ba tsananin rud’ani da tashin hankali had’ida zullumi da fargaba data tsinci kanta ciki.... A daidaita ta tare ta hau cikin sauri ko ciniki bata tsayayi ba tamkar wacce ake biyeda ita a guje haka ta shige adaidaitan.... Da k’yar ta iya lalumo kalamai saman harshenta taceda mai adaidaita ka yanda zaya kaita.... A bakin layin su Hajiya ta sauk’a sai faman zuba haki da gumi take sanda ta fad’a cikin gidan tagajan magajan tamkar wacce aka jehota.... Hajiya na zaune bakin murhu da shike ‘yan gaisuwa sun d’auke k’afa... Firgit ta mik’e had’ida dafe k’irji tana fad’in “Lami lafiya na ganki haka...? Meke faruwa Lami...?” Naja’atu dake zaune daga can gefe tana wanke wanke kallon mamaki take bin Aunty Lami dashi ganin hawaye kwance saman fuskarta gashi gaba d’aya a birkice take tamkar wacce aka biyota a guje.... Lami naci gaba da waige waige ta kamo hannayen Hajiya cikin daburcewa take fad’in “Haule shikenan... Shikenan mukam Haule tamu tazo k’arshe....” Hajiya ta waiga taga babu mai kallonsu don ko kulada Najah dake wajen wanke wanke ma batai ba, tai saurin janyo hannun Lami suka shige madafi cikin sauri..... Naja’atu tai saurin d’auraye hannayenta ta take masu baya had’ida lab’ewa jikin k’ofar kitchen d’in.... Hajiya Haule na muzurai take tambayar Aunty Lami... “Lami wai meke faruwane ya na ganki haka....?” Aunty Lami na goge gumin da ya wanke mata fuska take fad’in “Ma’aruf ya dawo Haule... Shikenan kashinmu ta bushe... Haule idan muddin asirinmu ya tonu Alhaji Usman Mailafiya tsireni zaiyi shikenan na rabu da masoyina Haule... Wayyo Allah na wllhi ban tab’a danasani irinta yau ba Haule...” Ta k’arashe murya cikeda tsananin tsoro... Hajiya ta zaro idanu waje had’ida dafe k’irji tace “Lami kina nufin kicemin hasashenmu ya tabbata wannan likitan shine Ma’aruf...?” Jinjina kai Lami tai cikeda tsoro kana tace “Haule shine shine dai Ma’aruf ya dawo garemu... Wayyo Allah na Haule, idan Usman ya koreni ina zanje ni ba d’a ba balle jika ba iyaye a raye ba, ina zan dafa Haule...?” Muzurai Hajiya keyi tana faman sak’e sak’e cikin zuciyarta.... Cikin sauri ta kuma kamo hannayen Aunty Lami kana tace cikin k’asa k’asa da murya “Ki kwantar da hankalinki Lami asirinmu bazai tab’a tonuwa ba... Ni nasan abinda zanyi amma a halin yanzu ki koma kuma kiyi k’ok’ari ki daina bari wannan tsoron naki yana rinjayarki, ki watsar da komai ki nuna tamkar bakisan komai ba....” Aunty Lami da har lokacin a firgice take ta dubi Hajiya Haule tace “Haule ina zan iya rayuwa gida guda da Ma’aruf..? Gani nake kaman zai tuno fuskokinmu....” Hajiya tai wata shed’aniyar murmushi tace “Lami bazaki canza ba wannan tsoron naki har yanzu yana nan... Shekarun da yawa Lami na tabbata Ma’aruf bazai fahimci komai ba sannan da ace zai gane wani abu da ya fahimta tinda ya had’u damu tin ba yanzu ba don haka ki kwantar da hankalinki kici gaba da al’amranki kaman da kar ki janyo wani abinda zaisa asirinmu ya tonu... Jeki jeki kawai sai mun had’u mu duka UKUN na tabbata Aminiyar Sirri zatafi kowa gudun tonuwar wannan dadd’en sirrin.... Jeki Lami mijinki zai iya zargin wani abu....” Tana ida fad’in haka ta janyo hannun Aunty Lami suka nufo waje yayinda Naja’atu ta b’ace daga wajen cikin sauri tana mamakin tattaunawan dataji Hajiya da Aunty Lami keyi... Shin waye Ma’aruf shin kodai Yaya Ma’aruf d’an gidan Abbah suke nufi da ya b’ace shekaru da jimawa... Shin kodai akwai sa hannun Hajiyarta a b’acewarsa ne...?” Tambayoyin da suka cika zuciyar Naja’atu.. Dole tabi a sannu don gano wannan sirri da Hajiya ke k’ok’arin bisnewa bayan yana neman tona kansa, ta d’au alwashin bazata kuma bari Hajiya ta cuci wani ba koda kuwa Mahaifinta ne da Hajiyar ta riga ta shanyesa... Da wannan tunani Naja’atu ta koma mawanki jiki a sanyaye..... *** Koda Aunty Lami ta koma asibitin bata tadda Abbah ba, tayi tunanin hakan ka iya kasancewa don haka kai tsaye gida ta wuce yanda ta tadda gaba d’aya illahirin ahalin gidan suna hallare a parlor, Alhaji Usman Mailafiya na daga center yayinda sauran ahalin ke kewaye dashi, can ta hangi Sameer na zaune k’asa shima kusada k’afafun Abbah... Gaban Aunty Lami ya kuma tsinkewa musamman data hango kwantacciyar murmushi dake a fuskar Mamy... Abbah yayi gyaran murya kana yace gaba da fad’in “Kaman yanda kuka sani a gidan nan ko nace a ahalin nan mun kwashe sama da shekaru talatin muna neman d’an uwanku wanda ya b’ace mana a ranar da kikazo duniya Zulfa’u.....” Zulfah ta d’ago idanunta mai zuban hawaye cikin sauri tana duban Abbah yayinda muryar Abbah ta soma rawa sosai..... Sameer ya d’ago yana duban wacce aka kirada Zulfa’u... Tsananin tausayinta ya rufesa sanda take fad’in “Abbah Ka samu Yayana ne... Abbah ka sami Yaya Ma’aruf ne....?” Abbah na murmushi hawaye na gangaro mashi yace “Zulfa’u Allah ya bayyana mana Yayanku ya yaye mana bak’in ciki da muka jima a cikinta....” Idanun Abbah suka sauk’a kan Sameer dake faman bin ‘yan uwansa da kallo d’aya bayan d’aya... Gaba d’aya suka maida dubansuga likitan wanda azatonsu yana wajen ne kurum a matsayinsa na likitan Abbah... Murya na rawa Marliya tace “Abbah wannan shine Ya Ma’aruf... Shine Yaya na da ban sanshi ba sai labarinshi....” Sameer da siririyar hawaye ta gangaro masa a hankali yake furta “Nine Yayanki Ni ne Yayanki da baki sani ba little Sis....” A guje ta tafi gareshi sai kuma taja ta tsaya hawaye sun wanke mata fuska... Murmushi saman fuskokinsu tace “Can I please hug you...?” Ya jinjina mata kai a hankali murmushi saman fuskarsa yake furta “Of course.... Come here...” Ya bud’e mata hannaye ta tafi a guje ta rungumesa.... Su Nabila da Zulfa’u hawayene kurum suma ke kwaranyowa daga idanunsu... Sameer ya d’ago ya dubesu kana yace su taho suma... Gaba d’aya su duka hud’un suka rungume juna suna hawaye Cikin muryar kuka Sameer ke furta “I have beautiful sisters in the world....” Yana fad’i murmushi mai bayyana hak’wara na fita daga fuskarsa... Yanda suka rungume juna su duka hud’u suna hawaye yasa Mamy da Abbah zuban hawaye A hankali Mamy ta isa ta rungume yaranta gaba d’aya tana hawaye take hamdala ga Ubangijinta da ya nuna mata rana irin wannan, ga yaranta gaba d’aya a tareda ita... Harta Aunty Lami dake tsaye jikin k’ofa saida taji k’walla na neman ciko idanunta, ji tai bazata iya shiga parlorn ba cikin sauri ta juyoda baya tana mai goge hawayen da ya mak’ale mata a idanu... Ido hud’u sukai da Aunty Bara’atu... Sukai tsaye suna duban juna.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ 55 *©️Sameena Aleeyou ...✍🏽* NOT EDITED Cikin sauri Aunty Lami tasa kai zata shige Aunty Bara’atu ta janyota.... Kallon kallo suke aikawa juna lokaci guda Aunty Bara’atu ta saki murmushi kana tace “Kina mamaki ya dawo ne...?” Aunty Lami ta waiga gefe da gefe kana tace “Mai kike nufi.....?” Janyota Aunty B ta kumayi kana tace “Muje, ban yarda dake ba, you must be hiding something....” Lokaci guda ta tura k’eyarta suka b’ace daga wajen Aunty Lami na faman muzurai...... Parlorn yai shiru sanda Sameer ke labarta masu rayuwarsa da mutanen da ya tashi ya gansu a matsayin iyayensa, Mamy da Abbah saida suka zubda k’walla jin yanda iyayen goyon Sameer suka rik’eshi bisa gaskiya da amana ba tareda sunsan cewa ko su waye iyayenshi ba, sun d’au alwashin kaima iyayen rik’on Sameer ziyara ta musamman da kuma mik’a godiyarsu a garesu baki d’aya.... Yanda Mummy ta bashi labarin k’anda akai ya fad’a hannunsu haka ya sanar dasu Mamy, sosai abin ya d’aure masu kai, al’ajabi ya cikasu baki d’aya... Abbah yace “Wannan yana nuni da cewa tabbas Ma’aruf ba b’acewa kayi haka kurum ba, tabbas akwai mugu a tsakani wanda yaso rabaka damu koma yaso rabaka da rayuwarka baki d’aya....” Sameer ya jinjina kai kana yace “K’warai Abbah wannan shine abinda nake tunani bayan mahaifiyata ta bani labarin yanda akayi na b’ace daga gareta....” Zulfa’u datai jigum tana saurarensu sai cewa tayi “Toh Abbah shin wanene zai nemi ganin bayan k’aramin yaro irin haka a wancan lokacin....? Lallai wannan mutumi yakai k’ololuwa wajen rashin imani....” Abbah ya sauk’e ajiyan zuciya kana yace “Zulfa’u Duniyarmu cike take da mutane iri daban daban, kana tare da mutum wasu lokutan amma bakasan wanene mugu ba, masu iya magana sunce mugu baida kama...” Nabilah dake zaune gefensa so take ta tambayesa mecece alak’arsa da Khalid amma bata san ta yanda zata soma tambayar nasa ba... “Ya Ma’aruf ....” Ta kirawo sunansa a hankali.... D’agowa yayi yana dubanta jin sabon sunan da aka ambace sa dashi... Itama d’in taji wani iri don ba sabawa sukai ba... A hankali ta d’an sadda kai kana tace “Sorry... Can we please call you Ya Ma’aruf....?” Murmushi Sameer yai kana yace “You can call me Ya Ma’aruf or Ya Sameer duka sunana ne zan amsa kinji koh....” A hankali ta saki murmushi ita da sauran ‘yan uwan nata... Shigowar Aunty Lami ya hana Nabilah ci gaba da magana.. Murmushi har kunne Aunty Lami ta shigo tana fad’in “Masha Allah.. Masha Allah .... Finally Ma’aruf d’inmu ya dawo.... Alhamdulillahi Allah shine abin godiya....” Ta k’arashe tana mai zama gaban Sameer da yai mutuwar zaune yana duban matar, wacce duba guda ya mata yaji k’irjinsa ya buga dum kaman an aje guduma lokaci guda.... Aunty Lami ta kuma fad’ad’a murmushinta tana fad’in “Ma’aruf...! Ma’aruf ashe zamu sake sakaka a idanuwan mu....!!!?” Lokaci guda kuma ta shiga tattaro bakin zani tana goge hawayen dake zubo mata wanda zakai zaton tsan tsan farin ciki ne.... Sameer duk sau yaji wani iri ganin matar tana sharan kuka gabansa... Nabilah tab’e baki kurum tai tana kallon salon makircin matar Baban nata Abbah na murmushi yake fad’in “Lami d’anki Ma’aruf ya dawo garemu... Allah ya dawo mana dashi....” Ya dubi Sameer yace “Ma’aruf wannan itace mamarka Lami abokiyar zama ce ga mahaifiyarka....” Sameer ya sakar mata murmushi zai bud’a baki tai saurin cewa “Call me Aunty Lami..... Haka k’annenka suke kirana....” Ya kuma sakin murmushi kana yace “Aunty Lami......” Ta jinjina kai tana kuma sakin murmushi.... Murmushin yak’e kurum Sameer yake amma har ransa baijin ya sake da matar, sannan yana tuna kaman wani muhimmin abu ya tab’a had’asa da ita a wasu lokuta can masu tsawo.... Sameer bai sami zarafin sanar dasu cewa nada iyali ba har akai masa waya ana neman sa acan asibiti, shi kansa ya mance da sabgan wata Siyama, Farin cikin had’uwa da dangin sa da iyayensa ya sakashi mancewa da duk wani k’unci da Siyama ta jefa sa ciki..... Yana isa asibiti ward d’in Raihanah ya nufa duk da cewa director na asibitin ne da kansa yake nemansa... A hankali Sameer ya murd’a handle d’in k’ofar.... Kwance ya hangeta idanunta a rufe alamun bacci take... Ya jima yana dubanta kafin yaji motsin tab’a k’ofan toilet Cikin sauri ya janyo k’ofar a hankali ya shige don dama kiran nasa director na asibitin ne mai nemansa.. *** Duk saurin da yake gudun kada ya makara ya bar ogan nashi zaman jira saida ya makara sabida holdup mai tsawo data kuma tsareshi, cikin ransa yake ayyana tabbas yasan Boss ya gama shiryawa shi kawai ake jira tinda yasan African time ba tsarinsa bane.... Yana tsaka da tunanin ne wayar d’aya daga cikin tawagan nasu ya shigo masa.... Bai d’aga ba sai k’ara malejin motar da yai, Don ko ya d’aga yasan maganar guda ce His excellency ya shirya shi ake jira.... Aiko yana sako hancin motar cikin gidan yayi arban da taron mutanen nasu, wasu sun shige mota wasu suna tsartsaye cirko cirko a farfajiyan hamshak’in gidan, da yawan mutanen suna mamakin yanda idan za’ai fita ko taron siyasa koma abinda bai shafi siyasa ba yanda duk kaga Engr Mutallab toh fah sai kaga Akram, koda baya nan kuwa sai an jirashi, bai yarda da tuk’in kowa face na Akram, Akram ya zamto tamkar k’ani a gareshi, harta zumunta mai k’arfi saida iyayen Akram suka k’ulla da Mutallab.... Da yawan mutane sunso shiga tsakaninsu saidai Allah bai k’addara hakan ba.... A daidai k’ofar babban parlornsa suka had’u... Akram na sadda kai k’asa yake fad’in “A min afuwa your excellency....” Engr ya d’an girgiza kai kurum kana yace “Amma sanin kanka ne African time bashi a tsarina, sannan idan nayi alk’awariwa mutane cewa lokaci kaza zanzo toh ko dak’ik’a guda banson k’arawa.... I suppose kasan duka wad’annan by now.....” Kai a k’asa Akram yace “I’m very sorry your excellency uziri ne ya rik’eni amma In sha Allah hakan bazata kuma faruwa ba...” D’an girgiza kai kurum yai kana yace ”A dinga kiyayewa....” Cikin sauri Akram ya take masa baya yana fad’in “In sha Allah...” A haka suka nufi mota sauran jama’an na hangosu kowa ya mik’e suka nufi nasu motocin.... Suna tafe Engr Ma’aruf na hankalce da Akram, agogon jikin motar ya kalla ya kuma duba wanda ke d’aure tsintsiyar hannunsa, tabbas lokacin gudanar da shirin ne... Ya kai duban sa ga radio din jikin motar da alama yau dai Akram mancewa yayi qilan, samun kansa yayi da kai hannun sa jikin radio d’in motar ya murd’ata.... Akram ya d’an dubeshi cikeda mamaki sanin cewa maigidan nashi ba ma’abocin sauraren radio bane hasalima a baya ko kunna radio din motar baiyi saiko kira’a.... Jin bai kamo channel d’in ba yasa shi d’an duban Akram.... Cikin sauri Akram ya rage speed kana ya d’an dubi maigidan nasa, ya gane tashar Radio ‘Yanci yake nema, baiyi zaci Ubangidan nasa har ya zama attached to shirin ba, ya saki murmushi a hankali kana ya d’anyi gyaran murya yace “Ai kwana biyu ba’a gudanar da shirin sabida wacce ke gudanarwa anyi mata rasuwa, hasalima uzurin da ya rik’eni ta’aziya mukaje mukai mata....” Engr Mutallab ya dubesa da mamaki kana yace “Anyi mata rashi....?” Akram ya jinjina kai a hankali yace “Eh ranka shi dad’e d’iyarta ta rasu yau kwana uku kenan....” _D’iyarta_ Kalmar da Engr ya nanata cikin zuciyarsa, bai tab’a kawowa tana da aure ba, a hankali ya maida duban sa ga window ba tareda ya kuma cewa komai ba... Akram ya d’an dube sa ba tareda yace komai ba, lokaci guda ya kunna masu k’ira’an Alk’ur’ani mai girma cikin muryar marigayi Sheik Jabir.... *** KADUNA Yau kwanan sa uku a hotel d’in duk wasu savings d’insa ya k’aryar dole ya nemi kudi ya biya kudin d’aki sannan yaci abinci.... Drawer dake gefen gadon ya janyo ya ciro wallet d’insa ya zari credit card dinsa guda da bai baiwa Daddy ba a cewarsa wannan account d’in tsohuwar account d’insa ne babu kwabon Companyn mahaifinsa a ciki.... K’asa ya sauk’o domin yin payment saidai to his greatest surprise Card d’in was declined.... Mamaki ya cika Khalid bai tsamman Mahaifin sa nada access to wannan account d’in ba... Girgiza kai yayi don yasan wannan bazai wuce aikin Siyama ba....Wato dai shi har yanzu a gidan kallon yaro ake masa.... Fuzar da iska ya d’anyi had’i da shafa sumar sa kafin ya amshi card d’insa, idan bai biya ba k’arshe dai dole ya bar hotel d’in don ba barinsa zasuyi ya zauna a bati ba.... Ba don yaso ba ya shiga neman layin Baffah.... Baffah na parlorn Ammi tare da su Siyama suna tattauna lamarin wayar Khalid ya shigo masa..... D’agowa Baffah yai yana dubansu bayan ya dubi screen d’in kana yai murmushi yace “Kun ganshi nan na kira....” Ammi tai saurin cewa “D’aga d’aga muji mai zaice....” Baffah ya jinjina kai kana ya d’aga wayar Daga d’aya b’angaren Khalid yace “Kana ina ne...?” “Gida.... Why..?” Baffah ya fad’i a tak’aice “Can you come over to the hotel please....?” Khalid ya fad’i tamkar wanda baison maganar... Baffah ya dubesu su d’inma shi suke duba da shike a speaker ya saka wayar... Siyama ta masa ido kan yaci gaba da magana... Baffah yace “Mai kuma zan maka...?” Gajeren tsaki Khalid yai kana yace “Idan ba zaka zo ba just tell me na nemi hanyar fita before they kick me out... I can’t believe Daddy can go this far... He canceled all of my cards, I can’t even have access to account d’in da nake da tabbacin baida masaniya da ita....” Mik’ewa Baffah yayi yana fad’in “Alright alright gani nan zuwa....” Yana katse kiran Ammi tace maza yaje sa ya duba halin da Khalid d’in ke ciki idan akwai debts sai ya clearing ..... Siyama ta saka shewa tana fad’in “Ammi kin gani ko plan d’in yayi aiki yanzu dole Khalid ya dawo gida tinda baida zab’i....” Ammi ta murmusa kana tace “Ai gwara da aka saka masa pressure na tabbata yanzu zai nemi hanyar gida..... Yesmin harda mik’ewa tsaye tana tik’a tsallen murna... Ammi ta yab’e baki tace “Ke kuma meye haka god’e god’e....” Yesmin ta cuno baki tace “Kai Ammi, ai dai murna nake at last my Kay zai dawo....” Ammi batace komai ba sai tab’e baki da tayi kana ta mik’e ta nufi upstairs ... Siyama na dariya tace da Yesmin... “Kinga zama bata kamamu ba, get me my car keys upstairs...” Da mamaki Yesmin tace “Ina kuma zamu....?” Siyama ta murmusa tace “of course we’re gonna follow Baffah.... Kinga yi sauri kafin ya fice....” Yesmin ta dara cike da jin dad’in kana ya nufi upstairs kaman zata kifa.... Sauri sauri motarsu tabi bayan ta Baffah.... Baffah ne ya gama settling bills d’in Khalid d’in gaba d’aya a counter, ba tare da ya dubi Khalid d’in da tun fitowar su ke duban wani gefen ba ya nufi room d’in Khalid d’in, tattare suitcases d’insa da duk wani belonging d’insa ya dingayi without any hesitation.... Nan ya hangi cellphone d’insa saman gado... Ya d’auka da sauri ya shiga trying nan ya samu tana bud’e, kai tsaye contacts ya shiga yana duba weird suna don yasan yanda abokin nasa yake weirdo haka zai saving lambar Nabila.... Teddy bear ya gani harda hoton bear... Baffah ya girgiza kai had’ida murmusawa a fili ya furta “If not Khalid Mainasara who...?” Cikin sauri yayi copying lambar Nabilah kana ya fito janye da suitcases d’in.. Kai tsaye ya shige yana mai mik’awa receptionist d’an mabud’in.... Khalid ya tsaresa da kallon mamaki “Ina kake tunanin zanje....?” Ya tambaya yana duban Baffan.... Janyo sa Baffah ya shigayi da d’aya hannun yana fad’in “You need to end this nonsense right now...” Ya bud’e mota yana k’ok’arin danna kansa ciki Khalid yace “Ba abinda na kira ka kamin ba kenan, thanks for helping out, but I’m not going back to house.....” Yanda yayi maganar kana iya hango tsantsan kafiyar sa... Su Siyama da motarsu ke lab’e gefe suka dubi juna... Suna gani Khalid yasa kai zai shige ya bar Baffah nan tsaye... Cikin sauri Siyama taiwa Baffan idanu cewa yabi bayanshi... Aiko tuni ya soma binsa yana bashi hak’uri yana rok’on sa ya shiga mota su tafi.. Da sharad’in bazai kaisa gidan mahaifinsa ba ya shige motar Baffah, basu zarce ko ina ba sai gidansu Baffan, nan ma bai yarda ya bari mahaifiyar Baffan tasan da zuwan sa don kai tsaye sashen Baffan ya wuce kuma yace baiso kowa yasan da zuwansa.. Hankalin Siyama ya d’an kwanta ganin gidans u Baffah ya koma, Yesmin kam ba haka taso ba taso ya koma gida don tayi kewar sa sosai dukda ba shiga hark’arta yake ba... *** Kano Sanye yake cikin pajamas d’insa autarsa Najma na kwance gefe saman makeken gadon nasa na alfarma, shiru yayi had’da k’urama waje guda idanu, zancensu da Akram na kuma dawowa kwanyarsa, akwai tambayoyi da dama da yakeso yayiwa Akram gameda ita.... But what if she’s really a married woman...? Ya lumshe idanu a hankali had’ida furta istigfari a fili... Baisan dalili ba, sau d’aya tak ya saurari program d’inta amma muryarta ya kasa b’acewa daga kwanyar sa, shi ba ma’abocin sauraren radio ba amma rana guda tak da ya saurari shirinta yaji yana son sake saurara, maybe sabida itama tana supporting d’insa ne, maybe program d’in yake son sake saurare ba muryar ta ba, da wannan tunanin yaji ya d’an sami natsuwa cikin zuciyarsa... Ya karanto addu’a ya tofawa d’iyarsa yana k’ok’arin kwanciya kenan ta turo k’ofa ta shigo... Ko kallon arziki bata ishesa ba ya juya yayi kwanciyarsa.... Tsegege ta tsaya masa aka tana faman huci... “Engr....” Shiru bai amsata ba “Ma’aruf...” Nanma shiru bai amsata ba idanunsa a lumshe... Tasan weakness d’in mijin nata idan akwai abinda ke saurin raunanasa shine yaji mace na kuka, kai shi kuka entirely d’aga masa hankali yake... Take Muhibba ta fashe da kuka had’ida silalewa k’asa... Ya bud’e idanu a hankali ya sauk’esu kanta, fuskar sa ya d’aura saman hannayen sa guda biyu ba tareda yace da ita komai ba.... Muhibba ta kannare idanu taga ya tashi ya zauna nan ta kuma narkewa tana shak’an kuka... Kukan nata ya shiga d’aga masa hankali... Shafe kansa ya shigayi yana furta “That’s enough Muhibba... Ya isa haka nan....” Haba nan fah ta kuma narkewa... Engr ya fuzar da iska a hankali kana yakai hannu a hankali ya dafata yana k’ok’arin lallashinta don ya gaji da sauraren kukan nata... Tamkar wacce take jira ta rungumesa gaba d’aya had’ida kwantawa cikin jikinsa zuciyarta na mata fari don tabi shawarin k’wayenta gwara ta lallab’a mijinta su shirya kar azo a kafa gwamnati yayi aure ya watsar da ita wata tazo ta zama First Lady tana nan ita kuma ta koma ‘yar kallo a cikin gidanta, wata tazo ta rabata dashi da kuma yaranta da tayi imani sune rayuwarsa.... *** A tare Abbah da Sameer suka shigo d’akin da sallama saman bakunan su, Raiha na kwance tana shan fruits da Mamani ta yanka mata an ida mata dressing kenan Sister Salma nurse dake mata dressing ko yaushe... Mamani baki har kunne take amsa sallaman nasu musamman da taga Abbah ya sami lafia sosai har ya iya fito..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ 56 *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Hawaye suka cigaba da gangarowa Mamani dake rik’eda hannayen Abbah.... Cikin muryar kuka take fad’in “Alk’ali da gaske kake da gaske Ma’aruf ya dawo garemu.....” Abbah ya zaunarta saman kujera a hankali murmushi saman fuskarsa yake fad’in “K’warai Mamani, jikanki Ma’aruf ya dawo.... Ya dawo garemu.....” Kukan Mamani ya k’aru, k’ok’arin mik’ewa take tana fad’in “ Alk’ali muje maza kaini na ganshi... Kaini naga jikana.... Shin ya girma koh...? Yayi kamanni dakai koh... Alk’ali ka kaini na gansa kafin wani abin ya kuma gifta tsakaninmu.... Sameer dake tsaye gefe kansa a k’asa hawaye suka zubo masa.... Cikin dabara Abbah ya kuma zaunar da Mamani kana yace “Kwantar da hankalinki Mamani, babu abinda zai kuma gifta tsakaninki da jikanki da yardar Allah...” Ya k’arashe yana mai duban Sameer fuska fal fari’a... Shima Sameer d’in su yake duba.... A hankali ya soma takowa.... Ba Mamani kurum da tai zaune tana duban ikon Allah ba harta Raihanah saida ta tsinci kanta cikin wane irin Shock ganin wannan likitan na k’ok’arin zamtowa Yayanta Ma’aruf da ya b’ace shekaru da dama tun kafin a haifesu.... Har gaban Mamani dake zuban hawaye Sameer ya k’arasa ya duk’a... Ya d’ago idanu suna duban juna, hawaye na zarya a fuskokinsu.... Murmushi saman fuskarsa ya sanya tafin hannunsa yana share fuskar tsohuwar da ta zamto Kakarshi a yanzu.... Mamani ta kasa furta komai sai hawaye dake kwaranyo mata, abubuwa da dama suka dinga dawo mata, ta jima tanajin babban al’amari gameda likitan nan ashe dai shid’in jikantane da yafi soyuwa a gareta, shid’in jininta ne, Ma’aruf d’inta ne.... Lokaci guda hannayenta na rawa ta d’agosu gaba d’aya tana shafa fuskar Sameer hawayen farin ciki na kuma wanke mata fuska.... Cikin rawar murya take furta “Ma’aruf.... Ma’aruf d’ina..,, Da gaske ka dawo garemu masoyina..., Shin da gaske kaine...” Sameer na jinjina kai yana hawaye ya rik’e hannayenta duk biyu murmushi bai bar saman fuskarsa ba yake furta “Ni ne, ni ne Ma’aruf d’inki Kaka.... Na dawo na dawo cikin ahalina.....” Bai kai aya ba Mamani ta rungumeshi sosai sabon kuka na taso mata, tamkar wacce take tsoron kada a raba tsakaninsu haka ta rungumesa tana kuka take fad’in “Alhamdulillahi Allah mun gode maka, kaine abin godiya.... Allah mun gode maka da wannan babban baiwa daka mana... Ma’aruf...” Ta Kuma fad’i tana mai rungumarsa... Sameer ya maida mata martanin rungumar a hankali yana mai jin k’aunar tsohuwar da tsananin tausayinta cikin zuciyarsa... Abbah da Raihanah dake dubansu cikeda tausayawa suka goge k’wallan da ya zubo masu... Ashe dai mutumin nan d’an uwantane, mutuminda kwatsam lokacin da duk ta fad’a cikin damuwa yake zuwa rescuing d’inta, Allah sarki Allah mai yanda yaso ashe dai sunada babban alak’a ta ‘yanuwantaka.... Ta sauk’e ajiyan zuciya sanda ta sinkayo muryar Mamani tana fad’in “Alk’ali ka fad’imin ya hakan ta kasance, ya akai tuntuni bansan jikana na kusa dani ba....?” Abbah ya d’an dubi Sameer shima Sameer d’in Abbah ke duba... D’an gyaran murya yayi ya kuma kamo hannayen Mamani kana yace “Mamani you need to rest, ya kamata ki huta sabida a shekaru irin naki ba’aso zuciyarki na d’aukan abubuwa da dama, mubi komai a hankali kinji Kakata, ina nan yanzu babu wani abinda zai kuma rabamu da yardar Allah....” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa hannayensa rik’e cikin na Mamani... Murmushin itama take tana kuma shafan fuskarsa kana tace “Nidai ina son sanin komai gameda b’acewarka sannan a ina ka girma, su waye suka saceka... Kawo girmanka da karatunka... Su waye suka rabani dakai.... Shin kanada iyalai... Idan kanadasu ina suke.... Inaso naga d’iyoyinka na rungumesu cikin hannayena.....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Sameer ya mik’e daga tsugune ya zauna gefen Mamani ya kuma rik’o hannayenta cikin nasa kana yace “Da sannu zaki san komai Mamani, abinda nakeso yanzu shine ki huta anjima zan sanar dake komai da kaina...” Mamani ta girgiza kai tace “A’a nidai ka sanar dani yanzu... Ina d’iyoyinka....?” Sameer ya mata k’uri zuciyarsa na harbawa a hankali don sai yanzu ya tuna baiko sanar da iyayensa nada mata ba, ita kanta Siyamar sai yanzu ta fad’o cikin zuciyarsa.... Saida ya d’anyi gyaran murya ya d’ago ya dubi Abbah kana yace “Abbah I’m sorry I haven’t told you this part of the story....” Ya maido da dubansaga Mamani kana yace “Inada iyali wacce aurenmu shekara guda kenan.... Amma tukuna Allah bai bamu haihuwa ba....” Abbah ya dubeshi da kayu kana yace “Kanada mata Ma’aruf....?” Sameer ya jinjina kai yace “Eh Abbah, inada mata Siyama amma a hanlin yanzu tana can Kaduna shiyasa ban kawo maku ita ba.... Kai hak’uri Abbah ban samu na sanar daku da wuri ba... Abubuwa da dama sun faru ko nace suna kan faruwa...” Dafasa Abbah yayi kana yace “Babu damuwa Ma’aruf... A hankali zamusan iyalinka, itama a halin yanzu saika natsu ka sanar da ita abubuwan da suka faru... Kar ka damu kaji koh mubi komai a sannu....” Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “Na gode Abbah....” Mamani ta yab’e baki tace “Ya kamata dai a kawo mana ita, sashen dake gefena nan za’a gyare maka ka saka iyalin taka ciki...” Sameer ya murmusa yace “Yanda kikeso Mamani hakan za’ayi....” Cikin zuciyarsa kuwa zullimin yanda Siyama zata amshi nasa family d’in yake balle ace zata zauna a family house d’insu... A haka Awwab ya shigo daidai lokacin da Abbah ya isa jikin gadon Raihana suna gaisawa... Awwab ya taddasu gaba d’aya suka gaisa nan yake sanar dasu cewa yau za’a sallami Raihanar ma....Mamani da Abbah sukai hamdala suna godiyawa Allah da fatan ci gaba da samun sauk’iga Raihanah.... Sai sannan Sameer ya d’ago ya dubeta, sukai idanu hud’u... Ta sadda nata idanun k’asa a hankali.... Hannun Awwab ya kama kafin suka fice domin tattaunawa..... *** Zaune suke saman kujerun SUG da aka k’awata gefen azuzuwan nasu dashi, su Safwan dasu Yusrah na duba test questions d’in da suka fito sai jajanta applied questions d’in da Malamin ya masu suke masu tsananin rikitarwa... Yusrah tace “Toh Safwan idan kunyi kuka mu kuma muyi mai, ku masu jan ajinma kenan... Gaskiya mutumin nan zaici ubanmu a exams...” Safwan yace “Karku damu In sha Allah haka zai barmu mu wuce duk iyawarsa... Ni barin k’arasa na amshi folder na a cafe d’in Mouses naga yau k’awar taki ko iya magana batayi Dr KB ya bata tsaraba...” Ya k’arashe teasingly yana mai kallon Nabilah da har lokacin shiru take tamkar wacce ruwa ya shanye.... Yusrah ta maido da dubantaga Nabilah tace “Ke wai lafiyarki...? Na kula kwana biyun nan kaman wani abu na damunki, ko har yanzu jimamin rashin Kausar kike ne....?” D’an jifanta da gajeren harara tai kana tace “Muje da Allah....” Rik’e hannunta Yusrah tai kana tace “Nabilah we are not leaving this place har sai kin fad’a min abinda ke damunki... Nasan akwai wani abindake damunki, I know you so well... Na sani idan kina b’oyemin wani abin.... So just tell me please... Kinji k’awata...” Harara Nabilah ta kuma jifarta dashi kana tace “Stop being silly already... Muje da Allah, nace maki babu komai... Ba komai....” Yusrah ta kuma rik’o hannunta suna duban juna.... Gajeren tsaki Nabilah tai kana tace “Its pointless, banga amfanin fad’a miki ba, mu tafi dan Allah....” Yusrah ta kuma rik’e hannunta wannan karon with a serious face tace “Is it about Khalid....?” Kafin Nabilah ta sami zarafin bata amsa wayarta ta d’auki ruri.... Saurin lalub’ar wayar ta shigayi daga cikin jakarta, ta k’urama wayar idanu ganin bak’uwar lamba ce mai kira.... Kaman bazata d’auka ba har saida ta kusan katsewa kafin ta d’aga cikin sanyin jiki..... Daga d’aya b’angaren Baffah yai mata sallama kana ya k’arada “Allah sa ina maganane da Nabilah Mailafiya....?” Kaman wacce batason amsawa tace “Wake magana.....?” Baffah yace “Sunana Baffah abokin Khalid...” Gaban Nabilah ya yanke ya fad’i don rabonta da Khalid kusan sati guda kenan... She can’t deny the fact she really wants to hear from him, at least to know about his well being.... Muryar Baffah ya katseta sanda yaci gaba da fad’in “Idan bazaki damu ba magana akan Khalid...” Cikin tsananin tashin hankali take fad’in “What what happened to him... Mai ya sameshi....” Yanda tai maganar zai tabbatar maka da tsananin damuwa da tashin hankali da take ciki.... Baffah ya sami k’warin gwiwar mata magana... Bai b’oye mata komai ba gameda halinda Khalid ke ciki... Hankalin Nabila idan yayi dubu ya tashi... She couldn’t help but to feel guilty, gani take laifinta ne Khalid ya shiga halinda yake ciki a yanzu... Bazataso fushin iyaye yayi tasiri akan Khalid ba don tasan tabbas fushin iyaye na tareda na Ubangiji... Idanu rau rau take duban Yusrah kana tace “Yusrah I need to talk to his parents, bai kama suyi fushi dashi har haka ba... I need to convince them cewa bamu tareda Khalid....” Dafata Yusrah tai kana tace “Ban gane baku tare ba...” Nabilah ta jinjina kai a hankali tace “Is the truth Yusrah.... Dama tun can ba soyayya muke ba, so I see no reason da zaisa su sallami d’ansu a sabida ni...” Yusrah tai shiru na d’an lokaci kana tace “Toh what’s your plan now?..” Nabilah ta fuzar da iska kana tace “Of course I’ll confront his parents and apologize on his behalf tinda shi baisan abinda yake daidai a rayuwarsa ba, ni bazan tab’a rabuwa da nawa family d’in a sabida shi ba don haka shima bazanso ya rabu da nasa a sabida ni ba... Na sani fushin iyaye ka iya tasiri a rayuwarsa....” Yusrah ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “But this is none of your fault, it’s his decision... Ba ke kikace ya bar gida ba so banga dalilin zuwanki gidansu ba....” K’uri taiwa Yusrah kana tace “Idan har zuwana zai canza zuciyar iyayen then zanjeni.... I don’t want him to go astray....” “Toh waye zai kaiki gidansu sannan ta ya zaki fara fad’i a gida....?” Shiru tai na wasu lokuta kana ta d’ago tamkar wacce aka zabura tace “Aunty Bara’atu..... Aunty Bara’atu will help me... Har muje mu dawo su Mamy bazasu sani ba, zan sanar da Mamy gobe daga sch gidan Aunty B zan wuce idan yaso nida ita sai muje don dai day trip tinda ba wani nisa bane...” Yusrah tai shiru kana tace “Kenan bazakiyi classes gobe ba...?” Nabilah ta jinjina kai a hankali tace “Bazan shigo sch ba gidan Aunty B zan wuce, daga nan ma gidanta zamu wuce naje mata da batun don ta kwana dashi although bansan yanda zata d’auka ba....” Yusrah ta jinjina kai tace “Shikenan Allah ya zab’a miki abinda yafi alkhairi k’awata....” Nabilah ta amsada Ameen jiki a sanyaye kana suka shige... Koda suka sami Aunty B da batun da k’yar ta yarda a cewarta bataga dalilin baiwa iyayen Khalid hak’uri da zataje yi ba tinda ba ita tasa ya bijirema buk’atarsu ba... Hasalima zuwan nata ka iya worsen abubuwa... Da k’yar dai Nabila ta shawo kan Aunty B ta amince da buk’atarta... Har bakin gate Aunty B tai masu rakiya ta kuma basu kud’in abin hawa.... Har sunyi sallama Aunty B ta kirawo sunanta.... “Nabilah...” “Na’am Aunty...” Nabila ta amsa had’ida juyowa Takowa Aunty B tai kusanta a hankali kana tace “Yaya Zulfa’u....?” Dashike tun bayan rasuwar Kausar Zulfah bata dawo gidan Auhty B ba tanacan gidansu... “Tana nan lafiya, bakuyi waya bane yau....” Aunty B ta jinjina kai a hankali kana tace “Ki gaidamin ita idan kinje... Yayanku Ma’aruf fah...?” Nabilah tace “Bai yini a gidan kinsan likita ne....” Nanma jinjina kai Aunty B kana tace “Allah ya tsare... Yusrah ki gaida Mama kinji koh...” Yusrah ta amsada “Zataji Aunty mun gode....” Kana suka fice Jiki a sanyaye Aunty B ta komo cikin gida lokaci guda ta lalumi wayarta dake kan kujera, k’uri taima wani lamba hawaye tab idanunta... ‘Yan uwanta ne batada wanda yafi mata su a rayuwa... Ta sani Yaya Abidah bata ga maciji da Mamy.... Alwashi ta d’au ma kanta In sha Allahu kafin d’aya daga cikin su ukun su bar duniya sai ta daidaita tsakaninsu da taimakon Allah..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ 57 *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED A motar Sameer suka dawo gida gaba d’aya dashike anyi sallamar, Hajiya Mamani an kasa sakin Sameer gaba d’aya gani take kaman zai kuma tafiya ya barsu... Nan ta shiga ‘yan dube dube a d’akin nata cikin shirginta na tsofi da ba’a rasa ba tana neman abin baiwa Sameer... Shiko Sameer sai aikin murmushi yake zuciyarsa nai masa dad’i bai tab’a kawowa nada babban family irin haka ba, matan su Baffah Ado da d’iyoyinsu sukaita shigowa suna gaida Raiha had’ida barkawa Mamani na dawowar Ma’aruf.... Sameer ya yarda shid’in d’an dangine ganin yanda aketa shigowa ganinsa daga k’ofa k’ofa... Da k’yar ya samu ya silale daga sashen Mamani ya nufi parlorn Abbah yanda ya tadda iyayen nasa gaba d’aya, sai sannan Mamy ke tambayarsa gameda matarsa Siyama.... *** A can gidan Baba Alhaji kuwa Hajiya Haule tayi kicin kicin da fuska tana tunanin yanda akai har Ma’aruf ya rayu ya kuma dawo gida wajen danginsa, ko shakka babu Aminiyar sirri ta yaudaresu, amma idan tasan wata batasan wata ba, lokaci yayi da zata fasa k’wan kowa ya sani tinda dai abin ya zama haka.... Baba Alhaji dake cin abincinsa hankali kwance ta kuma watsawa mugun kallo kana ta karkata tai gyaran murya.... “Alhaji wai ni nace ka kaw san abindake faruwa...?” D’agowa yayi yana dubanta kana yace “Meke faruwa kuma....?” Gyara zama ta kumayi kana tace “Bakada labarin dawowan d’an d’an uwanka...?” Gyara zama ya kumayi had’ida aje cokalin hannunsa kana yace “Ban fahimceki ba Haule....” Hajiya Haule ta kuma tab’e baki tace “Yo ai bakada amfani a wajensu shiyasa ba’a sanar dakai ba, basu d’aukeka bakin komai ba, sam Usman baya darajaka baya baka girman da ka riga ka fishi, bacin haka ace an doshi sati guda da bayyanar Ma’aruf amma babu wanda ya sanar dakai.....?” Sauran abincin dake bakinsa ne ya kusa k’waransa... Ya kuma duban Hajiya Haule yace “Haule kinaso kice min Ma’aruf ya dawo gida bayan duk shekarun nan da aka d’iba baya nan....?” Hajiya Haule ta jinjina kai tace “K’warai kuwa.... Ma’aruf ya dawo...” Baba Alhaji yai shiru na d’an lokaci kana yace “Shine babu wanda ya sanar dani.... Usman bai fad’a min ba....” Hajiya ta kuma yab’e baki tace “Toh yaushe kuwa zai fad’a maka tinda ba amfani kakedashi a wajensa ba, ita kanta mahaifiyar taku k’ark’ashin kulawarsa take yo ba dole ba, gaba d’aya ya amshe girman naka, ‘yan uwanku girmansa suke gani ba naka ba tinda ya yanka masu matsuguni a gidansa, yanzu gashi ance Ma’aruf babban likita ne kuma iyayen rik’onsa da alama masu kud’i ne sosai, na tabbata Mamani babu abinda zatai dakai yanzu balle ‘ya’ayanka zaka kuma zama maras amfani a wajenta....” Ta k’arashe tana mai k’ura masa idanu..... Shiru yayi na wasu lokuta kalaman Haule na kuma tasiri a zuciyarsa... Lokaci guda ya mik’e ya hau zira takalma... Haule ta mik’e tana k’ok’arin rik’esa take fad’in “Ina kuma zaka....?” Ba tareda ya dubeta ba yace “Zanje naga d’an d’anuwana....” Bai kuma saurarenta ba ya fice cikin sauri tamkar zai kifa k’asa, wani abu na yawo cikin zuciyarsa... Hajiya Haule ta rakasada mugun kallo har ya fice kana ta buga tsuka tayi shigewarta d’aki... Najah dake zaune can gefe a idonta akayi komai sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tayi kana ta furta a hankali “Hajiya ina fatan babu saka hannunki a b’acewar Ya Ma’aruf....” Ta k’arashe tana mai lumshe idanu a hankali kafin ta mik’e don gabatar da sallar la’asar, tana idarwa tayi shirin islamiya abinta, tanajin Sahariyya da Hajiya na d’ibe mata albarka wai ta zama munafuka ta koyo salon munafunci ko kulasu batai ba ta fice abinta tanai masu addu’ar shiriya... A can islamiyar ta had’uda Marliya yanda Marliya ke sanar da ita cewa an sallami Raihanah ta dawo gida, Najah tace zasu tafi tare idan an tashi ta duba jikin ‘yar uwar tata.., Sosai abin kewa Marliya dad’i ganin yanda lokaci guda Allah ya shiryi Naja’atu ta dawo daga rakiyansu Hajiya.... *** Abbah da Mamy na zaune parlor suna firansu na mata da miji gwanin ban sha’awa Baba Alhaji yayi sallama, Mamy ta mik’a hannu ta janyo mayafinta ta rufa kafin Abbah ya basa izinin shigowa dukda ba jiran izinin nasa yake ba, da gadara ya shigo yana watsa masu kallo... Mamy ta gaidashi ya amsa a ciki... Abbah yace “Yaya kaine a tafe, sannu da shigowa....” Baikai aya ba Baba Alhaji ya dakatar dashi da fad’in “Dakata Usman kada ka sake cemin Yaya... Ai baka d’aukeni matsayin Yayan ba.... Na tabbata har cikin ranka bakak’i ace kaine d’ah na fari a gidan nan ba, duk wasu d’awainiya da suka kamata ace ni ne nan na d’aukesu ka d’auka ka yafa ma kanka ba don komai ba sai don ka zamto abin tink’aho da alfahari a dangi koh, kana neman ka k’wace girman da Allah ya riga ya bani... Toh duk yinka Usman na rigaka zuwa wannan duniya kuma nine d’ah na fari a wajen iyayenmu kuma kai baka isa kayi komai akan hakan ba....” Ya k’arashe yana mai dukan k’irjinsa cikeda zafin rai.... Abbah bai tankasa ba har ya gama kana yace “Yaya ka zauna mu gaisa tukuna...” “Aw mahaukaci wanda baima san abinda yake ba ka d’aukeni kenan, kasa su Ado sun rainani duk basu ganin girmana sai Naka shine yanzu bari ka nunawa d’anka Ma’aruf bani da daraja a gidan nan koh, ban tashi sanin cewa ya dawo ba sai yau... Sabida kafi k’arfi ka nuna masa cewa kanada Yaya koh, sabida ka sami d’aurin gindi daga wajen mahaifiyarmu koh...?” Abbah na girgiza kai yake fad’in “Ba haka bane Yaya... Dama naso na d’aukeka na kai maka shi har gida n......” Dakatar dashi Baba Alhaji yayi da fad’in “Bana buk’atar bayananka... Ina Ma’aruf d’in yake.....?” Sai sannan Mamy da kanta ke k’asa tace “Ya fice amma inaji ba nisa yayi ba....” Baba Alhaji ya kad’a kai kana yace “Dama idan ya dawo maza yaje gida ya sameni....” Mamy ta jinjina kai tace “In sha Allahu za’a sanar dashi...” Ko amsa bai basu ba ya fice ya nufi sashen Mamani kaman wani zai kifa.... Aunty Lami dake lab’e ta murmusa cikin zuciyarta tace “Aikin k’awata Haule yayi kyau kenan... Yanzu zan kirata na labarta mata don nasan wannan ba komai bane illa makircinta....” Ta k’arashe tana kuma sakin murmushi... Mamani ta had’e fuska tayi kicin kicin tana aika masa mugun kallo.... Baba Alhaji yaci gaba da fad’in “Mamani kin kasa gane duk wannan sharrin d’an uwanane, ya rabani dake, ya rabani da ‘yan uwana su Ado yanzu yanaso ya d’auke d’iyata ya rabani da Raihanatu... Tinda an sallameta ta shige mu tafi gida Ta k’arashe jinyar acan.....” Tsegege Mamani ke dubansa kana tace “Gafara kamin shiru shanyayye wanda Haule da bokayenta suka gama dashi... Toh bazata koma ba, nace bazata koma ba, ince sanda tana asibitin Haule ta hanaka kaje ka dubata sai yanzu ne zakazo kace ta koma gida... Salon Haule da asararrun ‘ya’yanka su k’arasata koh... Toh wllhi kaji na rantse ko bayan rainane ka d’auki rik’on Raihanatu ka maida hannun Haule Allah ya isa ban yafe maka ba....” Baba Alhaji ya d’ago yana dubanta cikeda mamaki.... Mamani tace “K’wari kaji baninda nace ai... Tashi ka ficemin ka koma wajen Haule ka k’are can....” Haka Baba Alhaji ya mik’e ya fice yana mai aikawa Raihanah da idanunta ke k’asa mugun kallo Hawayene ke zuba a idanunta, kalaman Mamani akan mahaifinta yana mata zafi sosai, ko babu komai ko yaya yake tasan mahaifinta ne kuma bazata canza hakan ba....Kuma tabbas kalaman Mamani kayi tasiri a rayuwarsa... Mamani ta dafata tace “Yaya dai Raihanatu jikin ne.....?” Raiha ta girgiza kai a hankali tace “A’a Mamani....” Mamani ta kuma dafata cikeda tausayawa tace “Karki damu kinji bazan tab’a bari Alhaji ya maidaki gaban Haule ba kinji koh....” Raiha bata iya cewa komai ba sai sadda kai k’asa data kumayi... Mamani ta mik’e tana fad’in “Ohni Halimatu toh yanzu waye zaike wanke ciwon naki gashi mun riga mun dawo gida, naga lokacin wankin ciwo naki yayi....” Batakai aya ba suka jiyo sallamar bak’uwar murya, ba kowa bace illa Salma nurse daga asibitin da aka sallami Raihanah.... Mamani ta washe baki tana fad’in “A’a lale lale... Ma’aikaciyar jinyace a gidan namu....” Salma na murmushi ta ida k’arasowa ciki tana mai gaida Mamani... Mamani tace “Yanzu kuwa nake jajen waye zai wanke ciwon jikata tinda mun komo gida saiga Allah ya kawoki....” Salma ta kuma murmusawa tace “Ai Mamani tuni Dr Sameer ya d’aukeni hayar yin hakan....” Raiha dake zullumin wankin ciwo sabida zafi tayi saurin d’ago kai tana duban Salma... Salma taci gaba da fad’in “Mamani Dr ko bai biyani ba zanyi duk abinda ya sakani sabida tsananin kirkinsa da ganin ya taimaki duk wanda ke cikin matsala... Balle ace har ya zab’eni na kula da k’anwarsa ai ni abin alfaharine a gareni...” Tanayi tana sassane kai alamun kunya... Mamani tace “Allah sarki Ma’aruf jikana, ta ko ina yabonsa ake... Allah dai yaci gaba da karemin shi....” Salma ta amsa da “Ameen Mamani....” Kana takai dubantaga Raiha tace “Raihanah ya jikin... Nazo mu fara koh...” Murmushi mai kamada yak’e Raihanah ta mata kana tace “Da sauk’i sosai....” Salma ta murmusa kana ta kwab’e mayafinta ta shiga had’e kayan dressing... *** Shi kad’ai yake huci yana tururi bayan yaji labarin da Hajiya ta zayyane masa gameda mutuwar d’iyarsa Kausar cewa Zulfa’u da k’anwarta Nabilah su sukazo suka tari fad’a da tashin hankali garin fad’a suka jefa masa d’iya a tukunya... Kada ya zargi kowa da laifin kisan d’iyarsa face Zulfah da danginta.... Ko sallama bai sami zarafin yi ba ya fad’a sashen Mamy yana mai dokawa Zulfa’u kira cikin tsananin karaji da b’acin rai... Babu shiri Nabilah ta fito jin muryar Ya Hafiz kaman zai d’age gidan.... “Ya Hafiz lafiya kake kiran Addah Zulfah haka....?” Nabila tace tana mai dubansa cikeda mamaki ganin yanda k’wayan idanunsa suka kad’a sukayi jazir.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ 58 *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ko zarafin amsa Nabilah bai samu ba yaci gaba da dokawa Zulfa’u kira cikin tsananin karaji... “Ki fito nan ki fuskanceni Zulfa’u...!!” A tare Aunty Lami da Zulfah suka k’araso haraban sashen, ganin yanayin Hafiz ya mugun d’agawa Zulfah hankali... Aiko kaman wanda yake jira yayo kanta gadan gadan Aunty Lami tai saurin shiga tsakani.... Fad’i take “Hafiz lafiyarka.... Wai meke faruwa ne l....?” Yana nuna Zulfah da d’an yatsa cikin tsananin huci yake furta “Bazan tab’a yafe miki ba Zulfa’u, bazan tab’a yafe miki ba... Kin cuceni kin rabani da gudan jinina Kausar.... Why...? Meyasa Zulfah... Sabida na sakeki, sabida baki k’aunata shine bari ki d’au fansa akan d’iyata... Kin cuceni... Ban tab’a danasanin had’a iri dake irinta yau ba.... Kuma wllhi kinj na rantse sai na d’au fansar mutuwar Kausar...!!” Zulfah dake tsaye hawaye na gangaro mata cikeda tsananin mamaki take fad’in “Ya Hafiz mai kake nufi... Shin kana tunanin zan iya kashe rai balle gudan jinina... Ya Hafiz Kausar rayuwatace, ta yaya zakai irin wannan tunanin....?” “Shut up...! Rufewa mutane baki munafukar banza....!!” Ya k’arashe yana mai zabura zai finciko Zulfah dake b’oyewa bayan Aunty Lami... A daidai lokacin da Sameer ya shigo... A d’ari yayi jifa da jakar hannunsa ya finciko Hafiz ya watsa shi gefe guda.... Hafiz da baisan ko wanene Sameer ba ya d’ago yana mai ci gaba da huci yayi kan Sameer ya dunk’ule hannu yana k’ok’arin kaiwa Sameer naushi Sameer ya rik’e hannun da k’arfin gaske shima hucin yake su duka biyu suna aikama juna muguwar kallo Hafiz yake furta “And who do you think you’re..? Kai waye da zaka shiga tsakanin miji da mata... Auho d’aya daga cikin ‘yan iskan samarukan nata masu bin matan mutane ne koh... Toh baka isa ba bari kaji na fad’i maka....” Ya k’arashe yana kokawan k’wace hannunsa daga rik’on da Sameer ya masa amma ya kasa ko guzau... Sameer bai daina huci ba yana kallon cikin k’wayan idanun Hafiz yake fad’in “The moment you intend to hurt my sister again sannan ne zaka san the real meaning of the word pain... I’lol forget we are cousins....!!!!” Ya k’arashe yana mai jifa da hannun Hafiz d’in wanda saida ya kusan fad’uwa k’asa Gaba d’aya duban Sameer d’in suke da tsananin mamaki don basu tab’a ganinsa cikin irin wannan yanayi ba, babu ya Aunty Lami wacce tuni taji ‘yan hanjinta suna juyawa, yanda taga kalan zuciyar Sameer tabbas duk randa yasan sune sukai sanadiyar rabuwarsa da iyayensa kashinsu ya bushe don sosai ta razana da ganin fushinsa.... Nabilah kaw tamkar ta zuba ruwa a k’asa tasha haka taji... Kame hannaye kurum tai tana kallon yanda yau Yayansu ke karb’awa ‘yar uwarta ‘yanci irin yanda babu wanda ya tab’a tsaya mata... Hafiz da yanzu ya fahimci ko wanene Sameer mik’ewa yayi yana sakin murmushi mai kamada warning, kana yace “Aw ashe ka dawo kenan... Ka gama yawon barikin naka ka dawo... Sai yanzu ne zaka karb’a mata ‘yanci... Ka makara ai....” Bai kai aya ba Sameer dake tsananin huci ya tako gabansa a hankali kana yace “Do not try me....!” Hafiz ya kuma murmusawa kana yace “Your Sister is a monster Ma’aruf... She’s nothing but a curse...!” Wata wawiyar naushi da Sameer ya aikawa Hafiz a baki da hanci ya hanasa ci gaba da magana... Hankali tashe Zulfah ta shiga janye Yayanta tana kuka sosai take fad’in yayi hak’uri... Aunty Lami ta fice a guje kiransu Mamy a can sashen Abbah don tuni Hafiz ya fad’i k’asa jini na fitowa daga bakinsa da hancinsa... Mik’ewa yayi a zabure yana fad’in “Your Sister is a killer... She killed my daughter... Ta kashe min d’iyata ta kashe Kausar...!!!” Sameer na huci Zulfah na kuma janyesa yake fad’in “You take back what you said you imbecile....!” Daidai lokacin su Najah da Marliya da shigowarsu kenan daga Islamiya .... Najah da tuni ta soma hawaye ta k’arasa a guje ta rik’e Yayanta Hafiz... Lokaci guda take fad’in “Yaya Hafiz Zulfah batada laifi... Ka daina cewa ita ta kashe Kausar.. Kausar lokacin mutuwarta ne yayi....” “Shut up Naja’atu you don’t know anything... That monster killed my daughter... Hajiya ta fad’a min komai how my daughter die because of her selfishness...” Ya k’arashe yana nuni da Zulfah dake tsananin kuka.... Cikin kuka Najah ke fad’in “Addah Zulfah batada laifi, idan ma masu laifin kake son sani ba kowa bane illa Matarka Sawwama da k’anwarka Sahariyya, those two are the cause... Su suka jefa Kausar da Raihanah cikin ruwan zafi... Su zaka tuhuma not Addah Zulfah...” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya... Jikin Hafiz yayi sanyi sosai, hawaye suka ci gaba da zuba masa.... Ya d’ago idanu yana duban Najah wacce itama hawayen take .... Naja’atu ta jinjina kai a hankali kana ta sassauta murya tace “Yaya Addah Zulfah mahaifiyar Kausar ce bazata tab’a kasheta ba... Tana k’aunarta fiye dakai... Rabatada d’iyarta da akai lokacin da take raye ba’a barsu sun kasance tare ba ya isa jefata cikin damuwa.... This is not you Ya Hafiz, na tabbata deep inside kanada zuciya mai kayu....” Ba Hafiz dake tsaye yana zuban hawaye ba harta Sameer saida yaji gaba d’aya gabb’ansa sun masa sanyi, suna gani Naja’atu ta janyo d’an uwanta suka fice tamkar rak’umi da akala... Sameer ya dube ‘yan uwan nasa da gaba d’aya sukai tsaye suna dubansa in a strange way.... Dafa Zulfah da har lokacin zuban hawaye take yayi, a hankali ya furta “Everything will be alright kinji koh... I’m here now, bazan kuma barin wani yaci zarafin d’aya daga cikinku ba... Never...” Zulfah ta rintse idanunta a hankali yayinda Marliya ta k’araso ta janye hannunta suka shige d’aki.. Nabilah ta saki murmushi tana mai kallon Sameer har ya b’ace ma ganinta kana tabi bayansu Zulfah da Marliya... Aunty Lami data ruga a guje kiransu Mamy ashe ba Mamy ta tafi kira ba lab’ewa tai tana kallon yanda ta kaya tsakanin Sameer da Hafiz... Ta shafe zufan da ya keto mata had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya.... Tana ganin sanda Sameer ya nufi sashen Mamani kana ta sad’ad’o ta wuce d’aki ta lalumi waya tana neman layin Hajiya Haule.... *** A tare Hafiz da Najah suka shigo cikin gidan, Najah na gaba Hafiz na biyeda ita... Hajiya dake zaune tsakar gida tana faman sak’e sak’e tana ganin shigowarsu ta mik’e don dama shigowar nasu take jira tunda tuni Lami ta kirata ta zayyane mata komai... Naja’atu batai aune ba Hajiya ta janyota ta shiga lapta tana fad’in “Shegiya mai halin annamimanci.. Ki rasa ma wanda zaki k’ulla sharri sai ‘yar uwarki ta jini... Wato Zulfa’u da danginta sun fiye maki naki ‘yar uwar munafuka annamimiya...” Ta rarumo muciya zata jibga mata Hafiz ya rik’e muciyar da iya k’arfinsa... Hajiya ta d’ago tana duban Hafiz shaye da mamaki cikin yanayin da Bata tab’a ganinsa a irinta ba.. Idanunsa sun sauya launi sunyi jajazir gaba d’aya haka nan fatar jikinsa tayi ja, jijiyoyin jkinsa sun mimmik’e banda wani irin muguwar kallo da yake watsawa mahaifiyar tasa... Hajiya ta soma fad’in “Hafiz kada ka yarda da wannan yarinyar munafukace... Ta guje ‘yan uwanta na jini ta zab’i ‘yan uba... Ka yarda dani d’ahna nice mai fad’i maka gaskiya....” Bai bari takai aya ba cikin dakewar murya yake furta “Ina take...!!!?” Hajiya tace wafah.... “Ina Sahariyya Hajiya..!!!?” Wannan karon cikin tsananin daka murya yayi maganar.... Hajiya ta rasata cewa sai inda inda da take... Fincike muciyar yayi ya soma tafiya yana huci tamkar zai kifa k’asa.... Sahariyya dake kwance saman gado earpiece manne a kunne tana sana’arta ta jin kid’a sai sauk’ar muciya taji a gadon bayanta tamkar sauk’an aradu babu zato balle tsammani... Sahariyya ta mik’e a gigice sabida wani irin azaban zafi dataji, ta saki ihun azaba had’ida jifa da wayar hannunta... Hajiya da Najah suka nufo d’akin a guje jin irin k’aran da Sahariyya ta saki.... Kururuwa taci gaba da yi tana fad’in “Yaya Dan Allah kayi hak’uri, Wayyo gadon bayana wayyo k’afata... Hajiya kizo ki ceceni....” Duk k’ok’arin Hajiya ganin ta janye Hafiz daga bugun da yake wa Sahariyya tamkar wanda ya sami busasshen hatsi amma ta kasa janyesa.... Duk yanda ya samu bugu yake tamkar wanda aka aiko, kai da gani kasan dukan huce takaici yake.... Najah da taga za’a kashe ‘yar uwarta cikin sauri ta tari dukan ta kare Sahariyya tana kuka sosai ta durk’usa a wajen tana fad’in “Yaya Dan Allah kayi hak’uri... Ya isa haka nan please Yaya Hafiz....” Badon yaso daina dukan ba sai don ganin Naja’atu na kuka durk’ushe gabansa yasa shi jifa da muciyar, ba tareda ya kuma furta koda kalma ba ya fice daga gidan.... Naja’atu tayo kan Sahariyya dake kwance tamkar bata numfashi ta shiga jjjigata tana kirawo sunanta, a guje ta tafi d’ibo ruwa don ta yayyafa mata domin da alama Hafiz ya sumar da ita... Hajiya ta d’aura hannu aka tana kururuwa tana fad’in wayyo ita Haule ta shiga uku.... *** Sameer na shiga sashen Mamani ya samu Salma zata tafi ta gama dressing ma Raihanah... Ta gaishesa ya amsa sama sama, bata tsaya jan dogon zance ba tai masu sallama ta wuce don ta lura da mood d’in Sameer d’in... A d’aya daga cikin kujerun parlorn ya zauna yana mai duban sashen da Raihanar take, ita ta soma gaisar dashi ya amsa a tak’aice kana ya mata yaya jiki tace da sauk’i... Shiru na wasu ‘yan dak’ik’ai ya biyo baya dashike Mamani na k’uryar d’aki bataji shigowar Sameer d’in ba... Gaba d’aya Raihanah a tsarge take da kasancewarsa a wajen... Ko d’ago idanu ta kasa don wani irin naiuyinsa takeji sosai... Idanunta suka sauk’a kan hannunta da yaketa dunk’ulesu nan ta hangi jini na d’iga a hannun nasa gabanta ya yanke ya fad’i... Kar dai ciwo yaji.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ 59 *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED “A’a Babban Mai gidan an shigo...” Mamani tace sanda take d’age labulen d’akin, Raiha dake k’ok’arin janyo bandage ta saki a hankali ganin Mamani ta fito... Sameer yai k’ok’arin saita kansa kana ya saki murmushi a hankali yana mai gaida Mamani... Birki tai ganin jini a hannunsa, ta shiga salati tana sallalami tana tambayarsa mai ya sami hannunsa.... Duk sai yaji wani iri ganin ba wani babban ciwo bane d’an karjewa ne wanda baida shakku dakan bakin Hafiz da yayi ne hak’waransa sukaji masa ciwon... Ganin hankalin Mamani ya tashi sosai ya sanyashi kwantar mata da hankali da nuna mata ba wani ciwo bane... Mamani tace “Yo dole in damu mana Maigidan, bakasan ko k’uda banaso ya tab’aka ba balle ciwo.... Bani nan na gani...” Ta k’arashe tana janyo hannun.. Ba wai don Sameer d’in yaso ba, abin na Mamani ya soma damunsa gaba d’aya maidashi take saikace wani jinjiri, kodai don bai girma dasu bane take masa hakan k’ilan... Raihanah takai dubantaga hannun nasa sanda Mamani ke jujjuyawa... Ta juyo ta dubi Raiha tace “Dubu bani abin wanke ciwon naki na wanke masa...” Raiha ta amsada “Toh Mamani tamkar wacce take jira... Sameer yaga bilhakk’i da gaskiya Mamani take.... Cikin sauri yace “A’a Mamani ai ba sai an wanke ba ciwon ba sosai bane, bendejin ma ya isa....” Mamani tace “Ka tabbata dai ko...?” Sameer ya jinjina mata kai, ta amshi bandage d’in hannun Raiha tana k’ok’arin warwarewa amma bata iya ba... Ta yab’e baki tace “Ohni Halimatu ai kaga tsiyar abin nasaran naku, ni ya ake kwancewa....” Sameer ya saki murmushi da gefen bakinsa ganin yanda take juya bandage d’in... “Ke Dubu zoki taimaka min, zaki iya tashi aiko...?” Raihanah ta amsada “Eh Mamani...” Shiko Sameer kallo ya bita dashi ganin ba k’oshin lafiya bane da ita, idanunsu suka had’e waje guda, Raiha tai saurin sadda nata idanun.... Sameer ya maido da dubansaga Mamani kana yace “Karki damu Mamani zan iyayi....” Mamani tace “A’a ta yaya zaka iya bayan hannunka guda da ciwo, Dubu maza warware ki d’aure masa barin nemo masa maganin zogi, ina tsamman akwai cikin d’aki...” Ta k’arashe tana mai shigewa d’aki... Sameer ya tsaya kurum yana kallon ikon Allah wai shi za’a nemowa maganin zogi, k’ila Mamani ta mance shi likitane... Ya maido da dubansaga Raiha dake durk’ushe gabansa tana warware bandage d’in a hankali tamkar mai tausayin bandage d’in... K’uri Sameer ya mata yana kallon yanda take gudanar da al’amranta cikin natsuwa da tsananin sanyi... Ya d’anyi gyaran murya a hankali kana yace “Barshi haka nan... Give me that... Jeki ki huta I can do it...” Ta girgiza kai a hankali kana tace “A’a zan iya Yaya....” Ya kafeta da idanu kana ya furta “Are you sure...?” Ta jinjina kai a hankali tana mai k’ak’aro murmushi bacin kaw banda bugu babu abinda k’irjinta keyi... Mik’ar mata da hannun yayi yana mai ci gaba da duban yanda take zagaye hannun nasa da bandage... Baisan mai yazo cikin zuciyarsa ba amma ba kowa ya tuna ba illa matarsa Siyama, shin ko yaya zata amshi ‘yan uwansa...? Wannan tambaya ya jima yana yawo a kwanyarsa, sanin hali da yanayin matar tasa.... Har Raihanah ta kusan ida zagaye yatsun hannun nasa da bandage d’in kana ta sinkayo muryarsa yana jefo mata tambaya.... “Ya jikin naki...? How are you feeling now...?” Idanunta naga abinda take tace “Da sauk’i sosai....” Sameer ya jinjina kai yace “Zogin yana raguwa....?” Nan ma jinjina masa kai tayi still idanunta naga aikin da take kana tace “Eh ya ragu, bai ciwo sosai saiko da dare....” Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “You’re lucky skin d’inki nada kyau....” Wannan karon d’agowa tai suka had’a idanu... Kawar dakai gefe yayi tamkarma bashi yai maganar ba, daidai sanda ta ida rufe masa ciwon... Ba tareda ya dubebtan ba yace “Kwanan nan zai warke gaba d’aya In sha Allah kinji koh....” Ta jinjina kai a hankali... Duban hannun nasa yayi yanda ta rufe masa tsaf kana yace “Thank you...” Bata iya cewa komai ba sai k’ok’arin mik’ewa da tayi a daidai lokacin da Mamani ta fito tana fad’in ta nemi maganin nata sama da k’asa ta rasashi taci gaba da fad’in “Yanzu haka Sakina ce ta shigo ta d’auka kai wannan yarinya tayo halin ubanta Ado, haka nan nayi fama dashi sanda yake k’arami, ba dai na aje abin amfanina ba sai na rasashi ga b’arna kaman b’era....” Sameer ya shafi sumarsa a hankali da d’aya hannun jin Mamani na maganganu da bai kamata suji ba, da gani wannan tsohuwa ansha fama da ita.... Mik’ewa tsaye yayi yana fad’in “Babu damuwa Mamani kar ki damu zan sha inadasu a gida... Yanzu zan zaga ko wane k’ofa ne na gaishesu kafin na wuce gidan Baba Alhaji na masa gaisuwa shima...” Mamani ta wage baki tace “A’a lallai kaga d’an Albarka... Yawwa nace ba....” Sameer ya d’ago yana dubanta... Mamani taci gaba da fad’in “Ya kamata ka dawo cikin gida nan da zama, ga sashen dake gefena nan babu kowa ciki dama Alk’ali ne zai gyare min na koma ciki amma yanzu tinda Allah yayi ka dawo sai ka dawo ciki ka zauna, kaga sai mu samu musan iyalin taka sosai koh....” Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “Babu damuwa Mamani zan sami Abbah da maganar...” Mamani ta fad’ad’a murmushinta tana fad’in “Allah sarki ashe dai bazaka k’i gida ba, ai yanda kake d’an gayun nan na zaci bazakazo cikinmu ka zauna ba, Allah Ubangiji dai shi maka albarka yaci gaba da kare mana kai daga duk mai nemanka da sharri...” Sameer yana mai amsa mata da Ameen yake ficewa amma har ya fice Mamani batai shiru ba tana mai ci gaba da masa addu’an kariya da tsari daga mugu... *** Shagon Magaji abokinsa ya shige daga gidan Hajiya, yanda Magaji ya gansa yasan wani babban abu na damunsa ga fuskarsa a kumbure... Magaji ya janyo benchi ya zauna kusan Hafiz kana yace “Duk wanda ya ganka Hafiz yasan kana cikin matsanancin matsala, abokina Dan Allah ka sanar dani meke damunka, naji kace fuskarka had’ari kayi, amma fah Hafiz ba fuskarka kurum ba ga dukkan alamu kai d’in cikin damuwa kake, ni tun bayan rabuwarka da Zulfa’u ban kuma gane kanka ba, ga wannan matar taka da maganganu keta fitowa akanta... Hafiz Wai Dan Allah meke faruwa dakai..... Ko kanaso kacemin har yanzu bakai tawakkali da mutuwar d’iyarka bane...?” Kafin Magaji yayi shiru kuka mai k’arfi ya kufce wa Hafiz... Jikin Magaji yayi sanyi sosai ganin yanda Hafiz ke kuka da iyaka iyawarsa.... Bai hanashi ba bai kuma furta komai ba sai shiru da yayi yana dubansa cikeda tausayawa... Saida Hafiz yayi mai isarsa kana ya tsagaita.... Magaji ya shiga shago ya kawo masa ruwa mai sanyi kana yace “Sha wannan...” Babu musu Hafiz ya amsa ya kifa kansa bai d’aga ba saida ya shanye tass... Magaji ya komo gefe da Hafiz ya zauna kana yace “Kayi hak’uri Hafiz ita rayuwar nan gaba d’ayanta daka gani jarabawace, duk wanda kaga yana taka doron k’asa toh fah cikin jarabwar mahaliccinsa yake walau na jin dad’i koko akasinta, Hafiz duk yanayi da kaga bawa na ciki toh ba komai bace face jarabawa, ta ko ina za’a jarabcemu, ta kasuwancimu ne a’a ta iyalanmu ne koko ta lafiyarmu da dukiyarmu, kai komai da kake gani za’a iya jarabtarmu akai, wasu lokutanma har kayi tunanin ko kai kad’ai ake turoma irin wannan jarabawa... Toh fah ba kai kad’ai bane, hasalima idan kaji halin da wani yake ciki zakace naka ba komai bane... Toh shi haka Allah yake gudanar da al’amaransa tsakanin bayinsa, kai k’ok’ari kaci jarabawarka a duk halinda ka tsinci kanka ciki, ba ina cewa lallai sai ka sanar dani abindake damunka bane, amma ka sani a duk lokacin da kake son yin maganar zaka iya samuna, zan saurareka In sha Allah kuma na baka shawari daidai gawardo... Allah shi mana maganin matsalolinmu...” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye don attending customer... Hafiz ya lumshe idanunshi hawaye suka kuma zubowa zuciyarsa nai masa wani irin d’aci, tinda yake a rayuwarsa bai tab’a dayasanin auren Sawwama ba irinta yau, baijin zai iya komawa gida ya fiskanceta a yau sabida tsananin zogi da rad’ad’i da zuciyarsa ke masa, yasan idan ya fuskanci Sawwama a halinda yake ciki yanzu komai ka iya faruwa tabbas zai iya kasheta har lahira, toh amma bazaiso yayi hakan ba sabida wa’azin da Magaji ya masa tabbas ya shiga jikinsa, bazaiso ya kuma wani aikin danasanin ba irin wanda ya taptapka a baya ba... A hankali ya mik’e ya isa cikin shagon ya tadda Magaji kana yace “Magaji kamin alfarma d’aya ka barni na kwana a shagon nan naka don bazan iya komawa gida ba....” Magaji yace “Ka wuce haka a wajena abokina, gidanmu gidanku ne, ka shigo cikin gidanmu ka kwana har iya lokacin da kake so...” Hafiz ya dafasa kad’an kana yace “Na gode abokina...” Magaji ya sakar masa murmushi kafin ya janyo masa kujera ya zauna a cikin shagon.... *** Sallamanta na uku kenan a k’ofar parlorn shiru babu wanda ya amsa, kaman zata juya sai kuma wata zuciya tace ta dai tsaya na wasu dak’ik’ai ko za’a amsa sanin halin matar gidan da yanayinta... Can jimawa kad’an saiga wata matashiyar budurwa wacce da gani kasan ‘yar aikice ta k’araso ta bud’e had’ida amsa mata sallaman tai mata izinin shigowa... Aunty Bara’atu ta ida shigowa kana ta tambayi yarinyar ko matar gidan na nan.. Yarinyar ta amsa mata eh tana sama kana ta nufi bene kiran matar... Kaida ganin gidan kasan anyi wasa da naira sabida tsananin tsaruwa da gidan yayi... Bara’atu ta d’aga idanu tana kuma k’arewa gidan kallo, cikin zuciyarta take ayyana duk wannan girman gida da had’uwarsa babu magaji cikinta lokaci guda ta rintse idanunta tamkar wacce ta tuna wani abin... Sauk’owar matar daga bene wacce nake tsammanin matar gidan ne ya sanya Aunty B saurin saita kanta had’ida mik’ewa tsaye... Cikin taku irinta mata masu ji da kansu da isarsu matar ke takowa cikin parlorn, saida ta iso tsakiyar parlorn tana mai ci gaba da k’arewa Aunty B kallo kana tace “Bara’atu mai ya kawoki gidana... Na zaci ta maki iyaka da nan ne kaman yanda na mata iyaka da yanda nake...” Aunty da kanta ke k’asa ta share k’wallan dake k’ok’arin kawowa idanunta kana tace “Yaya mun yini lafiya...?” “Baki amsa min tambayata ba Bara’atu...” Matar ta kuma fad’i Sai sannan Aunty B ta d’ago tana dubanta kana tace “Zuwa nayi na fad’a miki Ma’aruf ya dawo...!!!” SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ 60 *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Cikin wani irin yanayi matar da Aunty B ta kirada Yaya ta d’ago tana dubanta, ta d’auki lokaci mai d’an tsawo tana duban nata kana tace “Ma’aruf...?!!” Aunty B ta jinjina kai a hankali.... Tak’aitaccen murmushi matar tayi kana tace “Toh mai nawa ciki... Mai ya shafeni da zakizo musamman don ki sanar dani....?” Tasan hakan ne zai iya faruwa amma batai k’asa a gwiwa ba tace “Yaya karki mance kusanki da mahaifiyarsa, ki dubi girman Allah ki mance komai ki shirya da ‘yaruwarki, ita rayuwar nan babu tabbas, yau kaine gobe ba kai ba.... Kuma nayi imani badon kin mata iyaka da gidanki ba itada zuri’arta da zaki ganta, ko baki ganta ba nayi imani zata turo ‘ya’yanta.... Yaya girma muke ba k’ank’ancewa ba don Allah mu aje komai duk wasu abubuwa da suka faru a baya mu rik’i junanmu don bamu da wanda yafi mana junanmu....” “Kin gama.....?” Yaya Abida tace.. Aunty B ta d’ago tana dubanta.... “Toh idan kin gama ki tashi ki fice min a gida....” Cewar Yaya Abida dake hakince saman kujera.... A hankali Aunty B ta duk’a ta d’au handbag d’inta kana ta dubi ‘yar uwar tata tace “Yayah zan wuce... Bazan gushe ba ina rok’onki kimin wannan alfarma guda d’aya....” Yaya Abidah ta d’ago tana dubanta, Aunty B taci gaba da fad’in “Ki sassauta zuciyarki ki rungume ‘yan uwanki ki tuna bakida wanda suka fisu....” Daga haka Aunty B bata kuma cewa komai ba ta fice ta bar Yaya Abidah nan tsaye tana mai rakatada kallo har ta b’acewa ganinta.... Washe gari sassafe Nabilah ta dira gidan Aunty B, Aunty Bara’atu batai mamakin ganin Nabilar da safe ba don tasan Nabila da kafiya akan duk abinda tai niyya.... Jigum tai a d’aki tana ida shiryawa zuciyarta naci gaba da sak’e sak’en anya tayi dai dai kuwa...? Anya hakan ya dace ta biyewa Nabilah suyi tafiya bada ilimin mahaifanta ba....? Ta lumshe idanunta a hankali tana kuma tunanin lamarin, a hankali ta sauk’e ajiyan zuciya taci gaba da shirinta domin kaw alk’awari ta d’aukarwa kanta da yardar Allah Mamy da ahalinta bazsu kuma shiga k’unci ba matuk’a tana raye wannan shine dalilinta na ajiye Zulfa’u a gidanta a lokacin da suka rabu da Hafiz sannan zatai iyaka k’ok’arinta wajen ganin Mamy da Ya Abida sun shirya koda ace wannan shine abu na k’arshe da zata aiwatar a rayuwarta... Muryar Nabilah ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi... Tai saurin yafa mayafinta had’ida d’aukan jaka da mabud’an motarta kana ta fito ta iske Nabilah a parlor.... “Kinyi breakfast ne....?” Aunty B ta tambaya sanda take gyara zaman mayafinta tana mai duban kanta jikin madubin consul... Jinjina mata kai Nabilah tai a hankali kana tace “Nayi Aunty... Ke kawai nake jira....” Aunty B ta jinjina kai a hankali tana mai k’arewa Nabilar kallo kana tace “Nabilah are you sure of this....?” Sauk’e ajiyan zuciya Nabila tai hawaye na k’ok’arin ciko idanunta take fad’in “Aunty this is the only way....” Aunty B ta jinjina kai kana tace “Kinaso muje...?” Nabila ta jinjina mata kai a hankali alamun eh... Nan ma kad’a kai Aunty B tai kana ta kamo hannayenta tace “I’m here for you kinji koh.... Ko meye zai faru.... You have your Aunt kinji koh....” Nabilah ta jinjina kai a hankali kana tace “Na gode Aunty....” Aunty B ta sakar mata murmushi kana suka sa kai..... *** Da idanu guda take k’are masa kallo yanda yake shiryawarsa cikin tsanaki, babu abinda ya canzu cikin d’abi’unsa saima k’warjini da kyau da ya k’ara mata, ita kanta ta sani tana son Ma’aruf tana tsananin k’aunar mijinta, wasu lokutan takan rasa maiyasa take masa abubuwan da take masa, kodashike abune a fili, mijinta mai son kula da tarairayane ita kuma sam bazata juri wannan ba, mijinta maison nitsartsiyar macece mai kula da duk wani nauyi da hakki na rayuwar aure da Allah ya shar’anta ga duk wata mace mai aure sauk’esu amma ita sam bazata iya sauk’e wad’annan hakkin ba ciki harda kulada yaransa da tarbiyarsu wanda yaran nan yaranta ne amma ta sani sam basu gabanta kuma bazata iya sauk’e masu hakkinsu dake kanta ba a matsayinta na mahaifiyarsu, fita yawonta da gantalinta ma bazasu barta... Mijinta mai son mace mai killace kanta a gidane kaman yanda Alk’ur’ani mai girma yace _Kuma Ku zauna cikin gidajenku kada kuke fita irin yanda jahilan farko suke fita_..... Duk wad’annan abubuwa da mijin Muhibbah keso matarshi ta kasance cikinsu sam Muhibbah ba haka take ba hasalima d’an kwanaki biyu da tayi a gidan ba tareda ta fita ba duk sai taji babu dad’i... Mik’ewa tai zaune tana faman mutsuke idanu alamun bacci, ganin yaci gaba da sabgan dake gabansa ba tareda ya kulata ba ya sanyata mik’ewa ta tako a hankali ta tsaya bayansa, a hankali ta rungumesa ta baya had’ida d’aura hab’arta saman kafad’arsa guda tana mai kallon fuskokinsu cikin madubi.... Fuska babu walwala yake k’ok’arin kaucewa yana mai ci gaba da abinda yake, lokaci guda yake furta “I’m running late, people are waiting for me....” Ya k’arashe yana mai d’aura agogo a hannunsa.... Fuzar da iska Muhibbah tai tana mai binsa da kallo kana ta k’ak’aro murmushi, lokaci guda ta kuma takowa ta bayansa kad’an tana mai gyara masa zaman suit d’insa had’ida daidaita masa necktie d’insa.... Fuska a shagwab’e take fad’in “Bazakaje dani ba...?” “Ba taron mata bane....” Ya fad’i a tak’aice yana mai matsar da ita gefe had’ida d’aukan turare.... Cikin sauri ta rik’e hannun nasa ta amshi turaren tana k’ok’arin fesa masa cikin salo.... Duk abinda take kallon arziki bata ishesa ba, sauri sauri ya ida abinda yake ya fice ya barta nan tsaye.... A parlor ya tadda yaransa sunyi shirin tafiya makaranta, Najma tana hangosa ta taso a guje ta rungume tana fad’in “Daddy good morning...” Engr ya rungumeta had’ida manna mata peck a goshi “Morning my princess....” Ya kamo hannunta suka nufi dining table din yanda sauran ‘yan uwan nata suke... Gaba d’aya yaran gaidasa sukai fuskokinsu fal fari’a... Hakan take kasancewa da mahaifinsu sab’anin mahaifiyarsu da sam babu sabo tsakaninsu da ita.... “Daddy yau kai zaka kaimu sch....?” Hanan mai shekaru shida ta tambaya.... Shafa kanta yayi murmushi bai gushe saman fuskansa ba daidai sanda Murja ta k’araso da lunchboxes din yaran... “Kunaso na kaiku ne...?” Gaba d’aya yaran suka had’a baki wajen cewa eh... Fuskarsa d’aukeda murmushi yake fad’in “Alright kowa ya gama cin abincinsa and Daddy will take you to school today...” Yaran suka shiga murna suna tsalle musamman k’anana guda biyun, shi babban mai shekaru goma dama magana bawai ya faye yinta bane, haka nan yake tamkar wani miskili.... Harta Murja saida taji dad’i cikin ranta don sosai yaran suke bata tausayi musamman idan ta tuna cewa yaran basu nemi komai sun rasa ba face soyayyar mahaifiya... Muhibbah kaw daga yanda take tsaye tana dubansu ta cika tayi fam, wato sabida tsaban rainin hankali itace zaice mata sauri yake kada yayi latti amma ga yaransa nan ya sakasu gaba yana biyesu k’arewarta ma cewa yayi da kansa zai kaisu makaranta, dad’i da k’arin takaicinta shine yanda daga Ma’aruf har yaransa ita d’in bata gabansu, yaran ko sallama basu mata ba suka fice wanda ta tabbata da ace ubansu ne bazasu fita basu masa sallama ba, wato ma babu wanda ya d’auketa da wani kima da daraja cikin gidan... K’wafa tai kana ta haye sama tana neman layin Suby aminiyarta “Hello Suby.... Nifa na gaji Wllhi na gaji da zama waje guda, kinga masu gidanma ba noticing d’ina suke ba, gaskiya ni na gaji da wannan zaman don wllhi ji nake kaman banida lafiya.....” Daga d’aya b’angaren wacce ta kirada Suby dariya ta tintsire dashi kana tace “Toh Wai ki fito kiyi mai bayan babu business a k’asa.... Kedai kawai kiyi hak’uri na d’an lokaci ki kuma winning mutumin nan over ta haka ne kurum idan yaci zab’en nan zamu samu kasonmu, kuma kinga business d’inmu ma zata kuma bunk’asa tinda ba lallai yasan tak’amaimen kasuwancin da muke ba...” Muhibba ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana tace “Suby bazaki gane bane akwai matsala....” Suby ta kuma shek’ewa da dariya kana tace “K’awata nasan matsalarki bazai wuce abin ba, zan turo Jenny ta kawo maki anjima...” Muhibbah ta murmusa kana sukai sallama... Ta jima tana tsaye wajen kafin ta nufi bedroom d’inta... Kai tsaye closet d’inta ta nufa ta janyo wata ‘yar drawer.... Wata ‘yar farar leda mai d’auke da k’waya ta ciro lokaci guda ta saki murmushi.... Hancinta ta toshe da yatsunta guda biyu kafin ta afa k’wayan tana mai rintse idanunta.... *** Basu sha wahalan neman gidansu Khalid ba dashike ba gida ne b’oyayye ba, tinda Nabilah ta d’aga idanu ta kalli gidan gabanta yayi mugun fad’uwa, lallai dole ma su Siyama su nemi datse tsakaninta da Khalid.... Aunty B ta dafata kad’an kana tace “Kina buk’atar na rakaki cikin gidan...?” Murmushi ta sakarwa Aunty B tana mai girgiza kai kana tace “A’a Aunty, da kika kawoni ma kin gama min komai, this is my war ya kamata na fuskanceta ni kad’ai...” Aunty B ta jinjina kai a hankali kana tace “Shikenan ina jiranki a nan cikin mota, I know you’re strong enough to do this alone...” Nabilah ta fuzar da iska tana mai k’arfafawa kanta gwiwa, cikin ranta take furta “I can do this..I know I can...” *** Fitowarsu daga masallaci Hafiz ya d’auki hanyar gida tamkar wanda ake sinkaransa don ko sallama da Magaji bai sami zarafin yi ba.... Tinda mai babur ya ijesa k’ofar gidan yaji kansa na sara masa, babu abindake azalzalarsa face tsan tsan tsanar matarsa Sawwama, komai ya shiga dawo masa, ya d’aga kai ya kuma duban k’ofar gidan, idanunsa suka sauk’a kan mota k’irar Corolla dake pake k’asar bishiyar delbejiya dake a k’ofar gidan.... *** Kubura ta dubi Nabilah daga sama har k’asa kana tace “Baiwar Allah kikace fah wajen Mai gidan kikazo...?” Cikin dakewa Nabilah tace “Ko na sake maimaita maki ne...?” Kubura ta murmusa kana tace “Yo abinne da mamaki wai an baima d’an kura ajiyan nama... Bama kice wajen Hajiya kikazo neman taimako ba sai kice Alhajin d’ungurungum....” Ammi dake k’ok’arin sauk’owa daga staircase waya manne kunnenta ta katse Kubura da fad’in “ke Kubura Wai keda wayene wajen nan.....?” Kubura ta bud’e murya tace “Ammi salon bariki nake gani, wannan mai baran Wai wajen Alhaji tazo bama wajenki ba.... Shine abin ya d’aure min kai....” Ammi taci gaba da sauk’owa daga bene still waya manne kunnenta tana duban yarinyar dake tsaye da Kubura... Kan Nabilah a k’asa banda bugu babu abinda k’irjinta keyi, batasan idan zata iya d’agowa ta dubi mahaifiyar Khalid ba, batasan idan zata iya ci gaba da abinda ya soma ba....... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ 61 *©️Sameena Aleeyou...✍🏻* NOT EDITED Tin daga sama har k’asa Ammi ke k’are mata kallo, still waya na manne b’angaren kunnenta na dama... Daga d’aya b’angaren shiru Baffah yai yana sauraren sautin maganganun Kubura dake tashi a wajen..... Ammi ta k’araso har gaban Nabilah a daidai lokacinda Nabilah ta d’ago suna duban juna..... Gaban Nabilah ya yanke ya fad’i a karo na farko.... Sosai Ammi take dubanta tana k’ok’arin tuno yanda tasan wannan fuska.... “Baiwar Allah lafiya...? Daga ina kike....? Sannan maiyasa kike neman mijina....?” Lokaci guda Ammi ta jero mata wad’annan tambayoyi.... “Wajen Daddy nazo....” Nabilah tace tana mai d’auke idanu daga duban Ammi.... Kubura taci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Oh yau ni naga jaraba, Ammi na fad’i maki Yanzu haka irin masu neman taimakon nan ne da Daddy ke taimaka masu shine suka soma biyo shi har gida... Bani umarnin fitar da ita yanzu kiga aiki da cikawa....” Ta k’arashe tana nannad’e hannun riga tamkar wacce zata sunkuce Nabilar.... Sauk’owan Yesmin kenan daga sama cikin shirin fita da alama da Siyama take wayar cak ta tsaya tana duban yanda su Ammi ke tsaye carko carko, mamakin bai ida kama Yesmin ba saida ta hangi fuskar yarinyar dake tsaye bakin k’ofa Kubura ta mata k’ababa.... Da k’arfi Yesmin ta furta “Nabilah..!!” Daga Ammi har Kubura harma ita kanta Nabilar d’agowa tai tana duban Yesmin dake sauk’owa daga bene... Daga d’aya b’angaren Siyama tace “Mai kikace cousin... wata Nabilah kenan....?” Yesmin tana mai k’arasowa garesu idanunta kan Nabilah take ci gaba da fad’i cikin wayar “K’warai kuwa Cousin Nabilah’s here she’s right here in front of me.... Da alama duk wulakancin da muka mata bai isheta ba ta kawo kanta....” Duk maganganun nan a kunnuwan Baffah... A hankali ya furta “Nabilar Khalid....!” Yai saurin bud’e murya yace “Ammi ba damuwa naji kaman kinada bak’i ki gama abinda kike sai muyi magana...” Ammi tace “Alright Baffah I’ll get back to you...” Ta kashe wayar tana mai duban Yesmin da kyau kana tace “Explain... Wacece ita... A ina kika santa...?” Yesmin na murmushi mai k’unshe da Allah sarki idanunta kan Nabilah take furta “Ammi wannan itace yarinyar da Khalid ya d’imauce kanta har ya sab’a umarninku for the first time in his life.... “ Ammi tace “Kina nufin kicemin wannan itace yarinyar... Kan wannan abar Khalid ya bijire mana, ya zab’i ganin k’uncinmu sama da farin cikinmu.... No wonder naga kaman nasan fuskar nata ashe a wancan video d’in na santa, yarinyar da ‘yan unguwa suka had’u suna mata wak’an Karuwa...” Ta kuma maido da dubantaga Nabilah wacce ta kasa d’ago idanunta sabida tsananin k’una da k’irjinta ke mata... Murmushi Ammi ta saki kana taci gaba da fad’in “Aw shine kika biyoshi har gida, kika taso tin daga uwa duniya kika biyo namiji har gidansu... Eh lallai kin cika cikakkiyar kilaki...” “Ni ba kilaki bace, kuma ni ba wajen Khalid nazo ba, na sani Khalid doesn’t live here anymore...” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya.... Kubura ta rangad’a guda tana mai tafe hannaye da salallami take furta “Yau naga salo... Ni nan ina tunanin mijin Ammi aka zo k’wacewa har gida ashe nawa mijin aka biyo.... Toh wllhi kinyi kad’an Karuwan cikin gidan ma sunyi sun k’yalesa ballanta ke da na tabbata a naira goma bazai amsheki ba....!” Ammi ta saki baki tana duban Kubura shaye da mamaki, lallai ta yarda haukan Kubura ya fara yawa dole a nema mata taimako.... Ganin Ammi na mata wani irin duba yasata saurin yin shiru tana mai furta “Yo Ammi ai gaskiya na fad’i su karuwan cikin gidan sun san kansu....” Yesmin da tuni ta kufula ta yo kan Kubura tana fad’in “Wa kike kira karuwa....” “A wacce ta tsargu....” Kubura tace tana watsa mata harara.... Ammi ce ta raba tsakaninsu tana fad’in “Banison shashanci da hauka kuna jina koh....” “Ammi shiyasa nace Kimin iyaka da wannan lunatic maid d’in....” Yesmin ta fad’i fuska a shagwab’e..... Gajeren tsaki Ammi tayi had’ida girgiza kai kad’an don ta fara gajjiya da fad’an Kubura da Yesmin kan namijin da sam basa gabansa....Ta dubi Kubura tace “B’ace min daga nan, idan bakida aiki kije ki taya Tabawa....” Ta maidoda dubantaga Nabilah tace “Ke! Kinajina banason salon iskanci da bariki, tun muna shaida juna ki tattari k’afafuwanki Ki bari gidan nan, sannan ki fita daga rayuwan d’ahnah for good don shi ba mijinki bane kin jini koh, kinsan hausawa suna cewa idan kunne yaji toh fah jiki ya tsira, Don haka ki rufa ma kanki asiri kibi ta k’ofan da kika shigo ki fice tun kafin a fiddaki ta wata k’ofar....” D’agowa Nabilah tai ta dubeta kana ta kuma sadda kanta tace “Kiyi hak’uri Ammi bazan tafi ba har sai nayi magana da Daddy....” Yesmin ta dubeta shaye da mamaki kana tace “Eh lallai... Kinji koh Ammi, kinga irin salon nata koh.... Kawai ki bani dama na fidda maki ita right this minute....” Murmushi Ammi tai tana mai duban k’arfin hali irinta Nabilah kana tace “Baza’ai haka ba Yesmin... K’yaleta badai tace Daddy take son gani ba.... Let her come inside and wait...” Yesmin ta dubi Ammi zatai magana... Ammi ta kashe mata idanu guda.... Lokaci guda Ammi ta sakarwa Nabilah murmushi kana tace “Ki shigo parlor ki jira Daddyn anjima kad’an zai fito daga sashensa, shigo ki zauna, Yesmin tell Kubura to serve her drink...” Yesmin tai tsaye tana duban mamaki wa Ammi yanda ta janyo Nabilah ta zaunarta saman kujera.... Harda kunna mata tv kana tace ta saki jikinta anjima kad’an mijinta zai sauk’o.... Cikin sauri Yesmin tabi bayan Ammi, a staircase ta tari Ammi tana fad’in “Haba Haba Ammi ya zakiyi haka, ya zaki bar wannan ‘yar iskar yarinyar ta shigo cikin parlornki har ta zauna, maiyasa baki bani go ahead na fiddata ba, ita har ta isa tace Daddy tazo gani...? Ammi kuma fah kinsan I can’t stand the sight of her....” Banda harara Ammi bata b’alla mata komai, janyo hannunta tayi suka shige d’aki kana tace “Ashe ke banza ce shashasha, banda abinki ce maki akai bansan mai nake bane, wannan shine damarmu da zamuyi amfani da ita mu rabata da Khalid har abada, na tabbata idan har muka nunawa Khalid cewa wannan yarinyar har gida take bin manyan alhazawa tunda gashi ta biyo mahaifinshi tsaf zai yarda cikakkiyar k’aruwa ce, kinga shikenan Khalid ya rabu da ita har abada, zai dawo ya bamu hak’uri ya kuma amince da zab’inmu....” Yesmin ta zaro idanu tana duban Ammi cikeda mamaki kana ta tintsire da dariya tace “Amma Ammi ban tab’a yarda da hausar nan cewa abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi bazai hanga ba irinta yau, shikenan kuwa Ammi, Wllhi kin kawo shawari, Bara na kirawo Cousin ta baro duk abinda take tazo ayi a gabanta.... ** Tsaye Baffah yai yana dubanshi yanda ya kishingid’a saman kujera idanunsa a lumshe, tausayin abokin nasa ya cikasa, tunani yake ya sanar dashi ne koko kada ya sanar dashi, da alama Nabilar batason yasan taje gidansu, toh idan wani abin yaje ya faru fah tinda yasan ‘yan uwan Khalid da iyayensa sam basa son Nabilah hasalima she’s the reason Khalid yake cikin condition d’in da ya tsinci kansa ciki.... Toh ko dai ya fad’iwa Khalid d’in ne, maybe everything will come to an end.... Da wannan tunanin ya k’araso cikin parlorn, daga can kujeran gefen Khalid d’in ya zauna had’ida k’ura masa idanu.... Khalid ya k’yallara idanu guda yana duban Baffah, gajeren tsaki yayi kana ya gyara kwanciyarsa ya kwanta sosai cikin kujera yana mai furta “Don’t give me that look...” Baffah ya fuzar da iska yace “Khalid you need to end this for crying out loud... Jibi fah ka duba kaga duk yanda ka wani rame, kaman ba Khalid Mainasara da na sani ba... Haba Dude just put an to this already...” D’ago Khalid yayi yanai masa wani irin duba kana yace “Wait... Ka gaji da gani na a nan ne... Idan ka gaji da ganina ne just go straight and tell to my face, ba wai ka tsaya kana karanto min lectures d’inka da already na sani ba ka gane.... I’m fed up with you already...” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye zai nufi d’aki... Baffah ya bud’e murya yace “Do you really want to ruin your life just because of a girl...?” Cak Khalid ya tsaya kana ya karkato yana duban Baffah... Gajeren murmushin takaici yayi kana yace “Did you just say ruin my life..? Idan baka sani ba... It’s official, my life is actually a complete mess... So ka daina cewa zan ruining rayuwana...” Yasa kai yana mai ci gaba da tafiya.. Baffah ya kuma bud’e murya yace “Kasan cewa tazo Kaduna... Probably tana gidanku....” Wannan karon sosai Khalid ya juyo yana dubansa, saida ya d’auki dak’ik’a guda kana yace “What do you mean...?” Baffah ya mik’e tsaye kana yace “I mean Nabilah....” Kallonsa Khalid yake sosai kana yace “Nabilah kuma... Mai zai kawota gidanmu for what...?” Baffah ya d’an ciza leb’ensa yace “Khalid I’m sorry... But I told her everything... The situation you’re in right now... Inaga shiyasa tazo maybe to confront your parents....” Girgiza kai kurum Khalid yake idanunsa suka kad’a sukai jazir ji yake tamkar ya dunk’ula hannu yayita kaiwa Baffah duka... Cikin tsananin b’acin rai ya tako gaban Baffah, yana huci yake furta “How many times do I have to tell you, I hate people intruding into my life.... Why Baffah... Maiyasa zaka sanar da ita... Akan mai...? What if they did something to her...? You know perfectly well basa sonta, they’re capable of anything...” Baffah na b’alla masa harara yake furta “Because I cant stand seeing you like this.... I don’t want you to go astray, I don’t want you to ruin your life..” “Just shut up..!!” Khalid ya katsesa kafin yaci gaba da furta “I don’t need your concern.... Kuma na gama zama a nan...” Yana ida fad’in haka ya nufi d’aki kaman zai tashi sama Baffah na biye dashi na kiran sunansa inaa ko sauraronsa Khalid bai tsayayi ba, tuni ya soma parking stuff d’insa.... *** Laila ta dubi Siyama a karo na biyu kana tace “Look princess I’m not saying you should leave him for good, kawai zaki rabu dashi ne na d’an wani lokaci to teach him a lesson and to let him see your worth.... Sometimes dole mu bar abinda mukeso don mu karb’awa kanmu’yanci, kan mai zakije ki zauna cikin talakawa da talauci don kawai Sameer na son zama cikin talakawa, babu dangin iya balle na uba, ya bar gidansu gidan arziki ya koma zama cikin tsiya, idan ba mugunta ba mai hakan ke nufi... Look princess men are so selfish wasu lokutan, ki baro gidanku da aikinki da gatanki da komai ki koma zaman k’unci Wai duk kan soyayya, soyayyar da rana tsaka zaki iya ganinsa da wata macen tinda shi k’ofa uku ya rage masa bayan ke, yes he has the right ya auro Uku bayan ke... while ke kuma on the other hand bakida wannan damar, ya kashe maki kariya ya hanaki aiki... Nan gaba ya auro mai zuwa office da zuba kwalliya ki dawo ‘yar kallo cikin gidanki.... Toh wllhi kiyi ma kanki fad’a tun wuri kafin lokaci ya k’ure maki....” Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Siyama tai kana tace “Yes princess you’re absolutely right.... Ya kamata na karb’i’yancina daga wajen Sameer I can’t let him control me.... Bazan bar soyayyan da nake masa yaci galaba akaina ba.... I’ve to fight my battles....” Ta k’arashe tana mai hura hanci had’ida duban wani gefe guda.... Laila ta saki murmushi a hankali kana ta kurb’i drink... Tuni Siyama ta suri handbag d’inta sukai sallama da Laila... **** Tsananin mamakin abinda kunnuwarsa ke sauraro masa daga cikin gidan ne ya hanasa shigewa cikin gidan, banda ele da kacaniyan mutane had’ida wak’okin ‘yan bori baka jiyo komai... Hafiz yai tsaye yana sauraron ikon Allah yanda kasan bayan gari haka gidan ya koma..... Yana nan tsaye mutanen unguwa da fitowarsu kenan daga masallaci suka k’araso sukai masa sallama, da k’yar ya iya amsa sallaman nasu... D’aya daga cikin mutanen ya bud’e murya yace “Alhamdulillahi Allah ya kawoka, wato a gaskiya mun damu matuk’a da abindake wakana cikin gidanka, tun jiya abu yak’i ci yak’i cinyewa... Don munso kiran jam’ian hizba tun a jiyan amma wasu daga cikin committee na unguwa sukace mai gidan baya nan a bari nan da zuwa kwanaki uku idan har bai dawo ba sai a zattar da hukunci don bai kamata a apka masa gida kai tsaye ba dukda irin abubuwan dake faruwa cikin gidan....” Hafiz da har lokacin yawun bakinsa a k’afe yake, da k’yar ya lalumo kalamai saman harshensa yace “Malam Sambo wani abu ne ke faruwa cikin gidan nawa....?” Mutuminda ya kirada Malam Sambo bai kaiga basa amsa ba d’aya mutumin gajeren cikinsu yace “Kai kurma ne... Shin baka jiyo sautin kalangu da ‘yandaudu dake tashi cikin gidan... Kaga sam bazamu lamunci wannan abu ba, tarbiyan yaranmu muke jiyewa don haka dole ka tashi ka bar unguwar nan matuk’ar iyalinka zata maida gidanka gidan baje kolin shaid’anu... Haba ace an yini an kwana zubur ana abu guda tun jiya, babu dare babu rana babu sararawa balle sanin lokacin sallah, toh sam bazai yuwu ba mu bamu saba ganin irin wannan d’abi’a a unguwar nan ba, bazai yuwu a kawo mana gidan bori a unguwa ‘yan daudu da lalatattu suke mana safara ba, ya zama dole mu d’au mataki....” D’ayan ya jinjina kai yace “Wannan hakane, unguwar nan an mana shaida mai kyau bazamuso rana tsaka wani ko wata ya kawo mana mishkila ba... Kuma tinda ka jima a unguwar hakan bata tab’a faruwa ba sai yanzu...” Hafiz ya lumshe idanunsa a hankali hawaye masu d’umi suka zubo masa.... K’unci sun taru sun masa yawa a zuciyarsa.... Suna nan tsaye shida mutan unguwa wasu mazan suka fito daga cikin gidansa rungumeda ‘yanmata... D’aya Dattijon ya furta “Subhanallahi... Ka gani koh, kaga irin musiban dake faruwa tun jiya a gidanka.... Toh ya zama wajibi ka d’auki mataki kokuma mu mu d’auka....” Daga haka tafiya sukai suka barsa nan tsaye yana mai bin’yandaudun da zasu shige cikin gidansa da kallo... Da k’yar yake d’aga k’afafunsa ya nufi cikin gidan.... Hankalin Hafiz bai ida tashi ba saida yayi arba da masu kalangu da gurmi tsakiyar gidansa suna bugawa hayak’in kayan maye na tashi wasu watsattsu suna rawa maras kyaun gani.... Tuni wasu ‘yandaudun suka nufosa suna kai masa runguma, wannan ya jasa ta nan wancan ya janyoshi tacan.... Ganin bai kulasu ba da alama ma hankalinsa bai taredasu yasa d’aya d’andaudun gyara d’aurin k’irjinsa yana wani kareraye hannaye had’ida taunar chewinggum yake fad’in “Ohni ‘yar mamata shiko wannan kodai ‘yan matan basa gabansa ne... Kin gansa fah zalzal dashi...” Baibi takansu ba ya shiga raba idanu ta yanda zai hango Sawwama, yana danna kai a parlornsa k’auri da hayak’in kayan maye suka kusa kifar dashi, nan ma wani kayan tashin hankalin ya tadda, banda watsewa babu abinda ake... Wa’iyazubillah...Bai ida ganin babban tashin hankali ba saida ya danna kansa a bedroom d’insa yanda ya hangi matarsa da mazaje kusan uku akan gadonsa.... Zuciyarsa ta buga da k’arfin gaske.... Yayi saurin kauda kansa yana mai rintse idanunsa, jiri mai k’arfin gaske yaji na yunk’urin kifasa... Innalillahi wa innalillahi raji’un... Shi tinda yake bai tab’a ganin musiba k’arara irin haka ba, duk abubuwan da yayi marassa kyau a baya bai tab’a cin karo da shed’anu irinta yau ba... Shi bai tab’a zaton Sawwama takai har haka ba.... K’afafuwansa ne suka silale sai jinsa kurum yayi ya zaune a k’asa a nan wajen, hannunsa dafe da k’irjinsa dake tsananin masa zafi.... *** Wurgi Siyama tai handbag d’inta saman kujera tana mai bin Nabilah da kallon k’yama.... Lokaci guda ta saki murmushi kana tace “You again.... Wato baki daddara ba koh.... Shine kika biyoshi har gida... Shin wai ana soyayya dole ne.... My brother doesn’t love, why is it so hard for to understand....” Murmushi Nabilah ta saki kana ta mik’e tsaye ta tako gaban Siyama... Murmushin bai bar saman fuskarta ba take furta “Oh really?... The last time I checked ya zab’i ya rabu da family d’insa duk a sabidani.... So think kinyi kuskure a nan... Sannan ni kad’aice zan iya convincing Khalid ya dawoga iyayensa don nasan martaba da matsayin iyaye, idan ya zab’i wannan hanyar toh kuwa tabbas zaiyi nadama da danasani a gaba, bazanso ya kasance cikin masu hasara ba, domin kaw duk mai fad’a da iyaye yayi hasara....” Siyama tana mai ci gaba da aika mata harara ta nufi sama tamkar zata tashi sama tana mai k’walla kirawa Ammi.... A daidai lokacin Alhaji Yusuf Mainasara yayi sallama cikin parlorn... Nabilah tai saurin mik’ewa tsaye tana duban mai sallaman, Dattijon mutum cikin shiga ta kamala manyan kaya, tsananin kamanninsu da Khalid ta hango wanda ko ba’ace ba wannan shine mahaifin Khalid.... Tai saurin sadda kanta k’asa sanda Daddy ke k’arasa shigowa cikin parlorn yana mamakin baiga komai ba sai wata matashiyar budurwa duk yanda matarsa Hajiya Farida ta d’aga masa hankali cewa maza maza yazo parlornta, a zatonsa wani abinne ya faru ko kuma wani ne babu lafiya... Ammi da Yesmin dake lab’e jikin staircase tsgege Siyama tai tana dubansu, “What’s all this Wai meke faruwane...? Me wancan yarinyar takeyi a parlor... and naji kaman sallaman Daddy....?”Ta tambaya tana mai ci gaba da dubansu.... Cikin sauri Ammi ta toshe mata baki tanai mata alamu da yatsa cewa tai shiru.... Lokaci guda ta kwantar da murya a hankali tace “Tarkonmu ya d’anu, Yanzu abinda za’ai Siyama maza maza ki kira d’an uwanki ki fashe da kuka ki sanar dashi ga ‘yar iskan yarinyar nan ta biyo Daddy har gida har parlorn Ammi, make him believe yarinyar ‘yar hannu ce.... Oya Oya wuce mana.....” Ta k’arashe tana hankad’a Siyama d’aki... Siyama na fad’in “Haba Ammi ya zamuyi ma Daddy haka... You’ve gone too far gaskiya... Nidai bazan iya ba gaskiya....” “Aw kinfi so ya aureta koh... Toh ai shikenan, kina dai gani wannan shine damarmu...” Yesmin ta marairaice fuska tace “Haba cousin do this for me please... Ta haka ne kurum zan mallaki Khalid... Please...” Ta k’arashe kaman zatai kuka.... Juya idanu Siyama tai had’ida fuzar da iska kana tace “Alright fine naji...” Yesmin ta buga tsalle harda rungumeta don murna... A can parlor kuwa tuni Nabilah ta durk’usa gaban Daddy tana gaishesa cikin murya mai taushi idanunta a k’asa.... Tinda yake tsakaninsa da ‘ya’yensa babu wanda ya tab’a masa irin wannan gaisuwar... Daddy ya mata k’uri kana yace “Yarinya daga Ina... wajen Farida kikazo..? Ko wajen Siyama....?” Nabila ta girgiza kai a hankali still idanunta na k’asa kana tace “A’a Daddy wajenka nazo....” Gyara tsayuwarsa yayi da kyau kana yace “Wajena kuma....?” Ta jinjina kai a hankali kana taci gaba da fad’in “Eh Daddy wajenka....” Wannan karon zama yayi bisa kujera kana yace “Toooh... Daga ina kenan... Sannan maike tafedake...?” Har lokacin Nabilah na durk’ushe gabansa kana tace “Daddy is about your son Khalid...” Wannan karon annurin fuskarsace ta d’auke cak kana yace “Tooh... What about my son... Turoki yayi kokuwa dai kece yarinyar da ya bijire ma umarnina akanki....?” Ta girgiza kai cikin sauri hawaye na k’ok’arin ciko idanunta take furta “A’a Daddy, Khalid baisan nazo nan ba, hasalima banason ya sani... Daddy Khalid mutumin kirki ne don Allah kada kayi fushi dashi, na sani wasu lokutan yanada nasa matsalolin but believe me he’s a good man... He’s only human, Please Daddy don Allah ka yafe masa ka dawo dashi gida, ka tuna girman fushin iyaye, ka tuna yardar iyaye na tareda yardar Allah... Daddy idan baka yafe mishi ba rayuwarsa tana cikin garari....” SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ 62 *©️Sameena Aleeyou...✍🏻* NOT EDITED Daddy yai k’uri yana dubanta ba tareda ya furta koda kalma ba.... Tamkar wanda aka zabura ya mik’e ya shiga nuna mata k’ofa yana furta “Get out... Fice min a gida nace... Awho wato kinje ya tsaro maki abinda zakizo kice koh... Idan har da gaskene yana son yafiyata yazo da k’afafunsa ba Wai ya turo wani ba.... Zoki fice nace and don’t think of coming back.....” Su Ammi dasu Siyama dake lab’e jikin bene a idanunsu komai ke faruwa... Idanun Nabilah sukai rau rau... “Daddy Dan Allah hear me out....!” Ta fad’i tana mai kuma duk’awa k’asa.... Ammi ta dubi su Siyama ta k’yafta masu idanu, lokaci guda suka fito Ammi na fad’in “Tashi ki fice bamu son salon munafunci....” Ta k’arashe tana mai janyo Nabilah da hawaye ke zubo mata... Lokaci guda Ammi ta shiga hankad’ata bakin k’ofa yayinda Daddy ya haye sama yana nazarin yarinyar da maganganunta.... Har haraban gidan Ammi ke hankad’o Nabilah tana fad’in “Bak’ar munafuka baki tsaya kan d’ahanah ba harda mijin nawa shima tallata masa kanki zakiyi... Toh wllhi k’aryarki tasha k’arya, ke ni nan nafiki bariki wllhi... K’aryar rashin kunya kike...” Ta kuma hankad’ota ta fad’i har k’asa wannan karon.... K’afafun mutum ta gani tsaye gabanta, tai k’ok’arin d’ago idanu don gani ko wanene.... Ba kowa bane illa Khalid.... Fuskarsa ta sauya launi haka idanunsa... Ammi bata daina huci tana jifan Nabilah da munanan kalamai ba yayinda Siyama ke tayata, itako Yesmin k’ok’arin b’oyewa bayan Ammi take sakamakon hango tsagwaron tashin hankali da tai cikin idanun Khalid.... “That’s Enough Ammi!!!” Ya fad’i yana mai duban mahaifiyar tasa... Harara taci gaba da watsa masa kana tace “Awho kazo kabi bayanta ne bayan duk abubuwan da ‘yar uwarka ta sanar dakai a waya... Khalid shin kai wane irin shashasha ne... Maiyasa bazaka bud’e idanunka kaga kalan yarinyar nan na asali ba, ina ka tab’a jin budurwar arziki ta biyo saurayinta har wajen iyayensa, for once open your eyes and see what’s right....” Girgiza kai Nabilah take tana duban Ammi, wannan karon da muryar tsiwa take magana dukda hawaye dake fitowa daga idanunta “Ni bashi na biyo ba, ni wajen Daddy nazo...” Ammi da yaranta su Siyama da Yesmin baki sake suke dubanta kafin Ammi tace “Awho kaji koh... Kaji da kunnuwanka koh, mahaifinka ta biyo...” Nabilah ta kuma rintse idanunta jin irin fassaran da Ammi take mata, Yesmin da Siyama suka shiga tafe hannaye suna salati suna taya Ammi... Khalid da tuni ya gama zuwa wuya rasa abin fad’i yayi sabida wani irin zafi da zuciyarsa ke masa ganin yanda mahaifiyarsa take abunda sam babu girma cikinsa, ita dasu Siyama sam basuda maraba.... Lokaci guda Nabilah ta bud’e idanunta dake jik’e da hawaye jin munanan kalaman dasu Siyama suke jifarta da ita sunyi yawa ciki harda Daddynsu yafi k’arfinta saidai taje can ta nemi wasu love life d’in irinta ba Daddynsu ba ba kuma brother d’insu ba... Fuskokinsu take duba kana ta goge hawayenta, cikin huci take furta “You know what... You should go ahead and believe whatever you want to believe... I don’t give a damn.... Ya rage naku..” Ta maido da dubantaga Khalid kana taci gaba da fad’in “And you... Ya rage naka to fix your relationship with your parents..... Forget I ever exists...” Daga haka goge hawayenta tai kana tasa kai cikin huci zata shige.... Cikin sauri Khalid yasha gabanta shima hucin yake, su duka biyun suna aikama juna muggan kallo.... Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “So tell me, mai ya kawoki gidanmu....? Huh talk to me...? What if wani abin ya sameki, just what were you thinking...??” Ya k’arashe Yana mai zaro idanunsa waje... Murmushin takaici tai kana tace “Isn’t it obvious... Tinda kai baka san girman iyayenka ba, ni bazan bari ka zab’i hanyar da sam bazaikaika ga dacewa ba... Do you think I can leave my family for you...? Well no, bazan tab’a barinsu ba, idanda ace zasu zab’a min miji, ko wane iri ne zan amsheshi hannu bibbiyu matuk’ar zai faranta masu sabida na sani bazasu tab’a zab’a mun abinda zai cutar dani ba...” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’i cikin taushi “So please just end this right now, ka basu hak’uri sannan ka karb’i zab’insu....” Da tsananin mamaki yake dubanta wannan karon, he just couldn’t believe it, Teddy Bear ce take cewa su rabu for good... “What did you say...?” Ya furta a hankali.... Jinjina kai tai kana tace “Yes you heard me loud and clear.... Don’t ever think of me again...!” Ta kuma sa kai ta shige cikin sauri hawayen da take dannewa na zubo mata... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka Khalid yai tsaye a wajen... Ba Ammi kawai ba harta su Siyama tsaye sukai suna duban Khalid wanda ya koma tamkar ruwa ya shanye.... Ammi ta janyo hannayen yaranta su Siyama da Yesmin tana mai masu alamu da bakinta cewa suyi shiru su shige cikin gida kurum su k’yale Khalid da alama burinsu ya cika Khalid da Nabilah sun rabu rabuwa ta har abada.... Cikin sauri ya shiga bin bayanta yana furta “Hey hey!!...” lokaci guda ya finciko hannunta ta dawo da baya tana mai furta “Don’t touch me...!” Tsaye kurum Khalid yai yana kallon yanda hawaye ke zuba daga idanunta.... Gaba d’aya sai yaji babu dad’i ya tuna a halinda ya risketa da mahaifiyarsa da kuma ‘yanuwansa, kalan wulak’anci da cin zarafin da ya tadda suna mata.... A hankali yake furta “Did they hurt you... Let me see are you hurt...?” Cikin kuka take furta “Kar ka matso yanda nake, kaje kaji da iyayenka they’re all that matters....” Hango hannayenta yayi yanda suka kukkuje... A hankali ya dafe kansa yana mai fuzar da iska lokaci guda yake furta “See, kin gani koh... Shiyasa bansan mai ya kawoki nan ba... Gashi nan sunji maki ciwo, do you think I can bear seeing you hurt...You know you’re so naughty....” Da zafi zafi yayi maganar... Daddy dake tsaye balcony d’insa yana hangosu daga yanda yake, k’arasowa kusa sosai yayi yana mai sauraronsu... Nabilah taci gaba da fad’in “Among the two of us who’s been naughty... huh? So kake Ina gani ka d’auko hanyar halak’a na k’yaleka... Do you even think zan barka ka zab’i hanya maras d’aurewa, hanyar da zai kaikaga halak’a... Well, no.... Ko mai zasumin I don’t care as far as hakan zaisa ka sami amincewa da yardar mahaifanka domin yardarsu na tareda yardar Allah ne...” Ta d’an sassauta murya kad’an kana tace “Please enough of this already.... Let’s go our separate ways...” Murmushin k’arfin hali Khalid keyi kana ya matso da fuskarsa dab nata, lokaci guda yake fad’in “And who told you sabida ke na tafi na bar gida..? Oh c’mon give me break princess.... Kawai bazan tsaya amin auren dole bane, don har abada bazan tab’a son yarinyar da suke so na aura ba, I’ll rather die than na auri wannan yarinyar kin fahimta....?" Nabilah tai shiru tana dubansa yanda yake huci, tabbas har cikin ranta taji babu dad’i da yace ba sabida ita ya bar gida ba.... Lokaci guda tai kicin kicin da fuska kana tace “Well, yayi kyau... Thank goodness cos I don’t want to be in the image.... Rayuwarkace kayi yanda Kaso da ita Allah ya gani na fad’i gaskiya na fita... And ka sanar da wannan abokin naka kada ya sake kirana....” Cikin tsiwa tai maganar wanda yasa Khalid murmusawa don ta juye masa Nabilar da ya soma sani had’uwarsu ta farko... Ya bud’e murya yace “Fine naji... Zan amshi zab’insu...” Cak Nabilah ta tsaya tana saurarensa lokaci guda yaci gaba da furta “And zan fice daga rayuwarki na har abada, badon komai ba sai don banaso wani cikinsu ya kuma hurting d’inki....” Ta rintse idanunta hawaye masu d’umi suka zubo mata... Khalid yayi k’arfin halin furta “Alright Miss Grumpy nayi binda kikeso ki tsaya muyi proper goodbye please....” Bata tsaya ba saima sauri data k’ara tamkar zata kifeda k’asa.... Khalid yayi saurin bin bayanta amma ko kad’an bata bari ya cimmata ba.... A hankali ya furta “I love you... And I’ll always does....” Ya lumshe idanunsa siririyar hawaye ta sauk’o masa... Daddy da komai ya faru akan idanunsa a hankali ya koma da baya ya zauna yana mai nazarin abinda ya faru tsakanin Khalid da yarinyar nan, idan ya fahimci wani abu shine yaran suna tsananin son junansu kuma dukansu sun sadaukar da farin cikinsu ne domin kare junansu, amma idan har abinda Farida take fad’i kan yarinyar gaskiya ne mai yasa baiji ajikinsa yarinyar tanada wani aibu ba....? Toh amma bijire masa da Khalid yayi fah...? Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ya dauk’i ruwa dake saman k’aramar table ya kurb’a... Nabilah tana isa mota ta rungume Aunty B tana kuka sosai.... Aunty B jiki a sanyaye ta maida mata martananin rungumar kana tace “Let it out daughter... Yi kukanki....” Saida tayi mai isarta kafin ta iya furta “Aunty na rabuda Khalid rabuwa ta har abada....” Aunty B ta kuma rungumeta tana share mata hawayenta take furta “This is for the best Nabilah, hakan yafi tinda danginsu sam basa k’aunarki.... Kuma tabbas kinyi k’ok’ari da har kika taso kika nunawa Khalid rashin dacewan abinda yayi, k’arshen soyayya da zaki masa kenan ki nusar dashi kuskure babba da yayi a baya domin al’amarin iyaye nada girman gaske, Allah ya zab’ar maku abinda yafi zama alkhairi a gareku baki d’aya kedashi....” Jinjina kai kurum tai ba tareda ta iya furta koda kalma ba kana suka d’auki hanyar gidan wata k’awar Aunty B domin su d’an yada gajjiya su kuma yi sallah kafin su d’auko hanya don basuso dare ya masu.... *** Tamkar maras numfashi haka Hafiz ke zube a wajen, koda motsa ‘yar yatsansa ne ya kasa, ya kwashe kusan sa’a guda zube a wajen gashi babu abinda aka fasa a cikin gidan saima wasu sabbin ‘yandaudu dake shigowa cikin gidan.... Ashe Wai hakance take faruwa idan d’aya daga cikinsu yayi aure toh fah sai sunzo sun had’a masa kalan tasu bukin shine sallamarsu tsakaninsu dakai, toh ita Sawwama ba’ai mata nata ba sai yanzu.... D’andaudu guda ne ya kusa tuntub’e da Hafiz ya doka salati yana dafe k’irji ganin mutum zube a wajen... Lokaci guda yake furta “Na shiga uku ni Lanti waye haka nan zai kadani k’asa ya tonan asiri ya ragen farashi.....” Ya shiga haske fuskar Hafiz sosai da d’an tocilan jikin wayarsa, lokaci guda ya saki shewa yana fad’in “Kai kai kai kuzo Yo ai ni na taki sa’a nai babban kamu, wannan zankad’ed’en saurayi haka...” Ya shiga shafa fuskar Hafiz yana kareraya... Maganganunsa ya janyo hankulan sauran ‘yan uwansa ‘yandaudun suka d’ungumo sukayo kan Hafiz kowa na masa nasa salon karya jikin.... D’ayan yana fad’in ku bari a bisa a sannu inaaa gaba d’aya sunyi chaa akan Hafiz har saida hankalin Sawwama yazo garesu, tayo kansu tana fad’in “Toh Lanti wa kuka samu haka, kwayi hak’uri ku barma guda d’aya ai.....” Batakai aya ba sukai idanu hud’u da Hafiz dake zube wajen yana numfashi da k’yar.... Sawwama ta dafe k’irji tana fad’in “Na shiga uku mijin nawa....” Lanti yace “Aaaaah kice abin du namu ne... Ayyiriri gaskiya kin iya zab’e k’awata Yo dole kike b’oye mana shi ashe... Yau dai sai a barmu mu d’anah....” Ya k’arashe yana tafe hannaye.... Sawwama ta shiga turesu tana fad’in “Banson iskanci kunajina koh, kowa ya fice min a d’aki ku jira daga waje.....” Ta k’arashe tana k’ok’arin d’aga Hafiz.... Da k’arfin gaske ya fincike daga rik’on da ta masa yana mai tsananin huci dukda zogi da k’irjinsa ke masa.... Lokaci guda ya capko wuyanta ya shak’e da duka k’arfinsa, wasu irin ruwa suna fitowa daga idanunsa da suka koma tamkar jan gauta har saida ya danganata da jikin garu... Cikin wata irin dashesshiyar murya mai cikeda firgici yake furta “Wllhi yau sai na kasheki.... Matsiyaciya muguwa azzaluma.... Kin rabani da matata Kamilan mace natsestiya wacce batada kusanci da irin halayyanki, kin kashe Kausar, kin halak’amin rayuwa... Kaman yanda kika kashe mun aurena da d’iyata Wllhi sai na kasheki nima....” Ya kuma danne wuyanta sai zaro ido take tana yunk’urin yin nishi har saida’yan daduronta sukayo kan Hafiz suna yunk’urin janyesa... Wasu kuwa suka fice a guje don kar ayi kisa suna wajen, mai kalangu da garayama ya cika ma rigarsa iska a guje.... Da k’yar suka iya janye Hafiz daga shak’anda yayima Sawwama.... Yaci gaba da huci hawaye masu tsananin zafi suna ci gaba da zubo masa.... Fincika yake daga rik’on da suka masa yana fad’in duk wanda ya kuma zuwa kusansa sai ya kasheshi... Sawwama ta mik’e da k’yar tana mai watsa masa harara take fad’in “Koda wasa kada ka saka ka kuma cewa ni na kashe maka aurenka da d’iyarka, ka fara zargin kanka kafin ka tuhumi wani don duk abinda yake faruwa yanzu are consequences of your actions, kuma da kake cewa na kashe d’iyarka da aurenka uwarka da ‘yanuwanka zaka soma tuhuma baniba don ni tayasu kawai nayi.... Sannan da kake cewa nida tsohuwar matarka mun banbanta naga nidakai duk kanwar jace, nasan baka fasa komai ba a halayyanka don haka koda wasa kada na kumaji ka zageni... Sannan bari kaji na fad’a maka babban kuskuren da zaka tapka shine kayi tunanin rubutamin saki don wllhi sai ka fice min cikin gida, Don idan baka sani ba ka sani a lokacin da baka a hayyacinka lokacin da asiri ke tasiri akanka tsaf na sakaka ka sauya takardun gidan nan zuwa sunana, kuma babur d’inka da aka sace ba sacewa akai ba nice nan na sa aka d’aukemin, harta kantinka da ya kama da wuta ba Wai tsautsayi bane, a’a nice nan na saka aka kwashemin kayan ciki na kuma bada umarnin a bankama kangon gini wuta sabida gudun rana irinta yau ranan da zakace zaka rabu dani... Domin ni nan daka ganni duk abinda kaga nayi toh fa sai idan zan sami riba a cikinta... Don haka ka tattara k’afafunka ka fice min a gida tun kafin nasa su lallasa maka bugu ko ka sakeni ko baka sakeni ba na saku don bakada sauran amfani wajena.... Kai kira saminu gurmi ya sake mana sabon kid’a.....” Ta k’arashe tana juyi yayinda sauran ‘yantashan nata suka tayata da ele da gud’a.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un........ Abinda zuciyar Hafiz ke iya nanatawa kenan.... Wani hadiri hadiri da taurari yake hangowa cikin idanunshi, mai ya jefa kanshi ciki....? Shin anya Sawwama ‘yar adam ce...? Kenan gaba d’aya rayuwarsa ita ta kassara masa... Mai ya mata da tsananin haka....? Ya rintse idanunsa yana mai ci gaba da jefa k’afafunsa ba tareda yasan yanda ya dosa ba.... Suna tafe cikin motar driving kurum yake amma mind d’insa was somewhere else, Shamsu ya kula da hakan don ‘yan kwanakin sam baya gane abokin nasa, yasan definitely akwai abindake damunsa kuma koda bai fad’i mashi yasan it has to do with his wife, tinda yanzu Sameer ya samu iyayensa baida sauran damuwa da ya wuce matarsa, d’an dubansa Shamsu ya kuma ganin yanda yake driving d’in tamkar mai shirin barin gari, a hankali ya furta “Doc please drive slowly kasan banyi aure na ije iyali ba so banyi shirin mutuwa ba ka gane....” Sameer ya jefa masa harara kana yace “Toh ai ita ba’a mata shiri, shiyasa idan kayi niyya maza kafin k’arshen shekara ka cikawa Mama burinta ka kawo mata sirka...” Shamsu ya murmusa yace “Na fad’a maka ai na gaji da wannan gorin tsaf zan baku mamaki daga kai har Maman...” Sameer ya tab’e baki yace “Ba fad’a a baki ba a dai aiwatar sai mu yarda....” Nan ma murmushin Shamsu yayi kana yace “Yauwa speaking of aje iyali, Wai har yau Siyama bata dawo ba....? Sameer are you ba wata matsala....?” Kallonda Sameer d’in ya jefa masa ne ya sanyashi d’an yin shiru kana yace “Look I’m sorry, I didn’t mean to intrude kawai na damu dakai ne shiyasa na tambaya....” Sameer baice komai ba sai d’an duban gefen kwalta da yayi yana mai kuma k’ara speed....Sam bai kulada mutumin dake tafe tsakiyar kwalta d’in ba... Shamsu ne ya soma hangosa ya shiga salati yana fad’iwa Sameer mutum gabansu.... Sameer ma salati ya soma yana k’ok’arin danna birki had’ida danna hannunsa gaba’a d’aya kan horn amma inaaa ya riga ya hauro saman kwaltan sosai ji kake k’iiiiii k’aran birki ga kuma mutumin da suka bige kwance gefen kwalta...... Cikin sauri suka firfito waje suka nufi mutumin da suka bige wanda ke zube saman kwalta bakunansu d’aukeda ambaton Allah “Hafiz...!” Sameer ya furta a hankali... Shamsu ya dubesa yace “Ka sanshi ne...?” Jinjina kai yai kana yace “Cousin d’inane.... Taimaka min muyi sauri mukaishi asibiti...” ya fad’i yana mai nannad’e hannun rigarsa had’ida sunguman Hafiz Shamsu na taimaka masa, suka sakashi cikin mota kafin suka nufi asibiti mafi kusa..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *63* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Mamy ta kuma jan gajeren tsaki a karo na biyu sanda ta kuma dialing wayar Nabilah tajita a kashe, ga magariba ta sako kai, bata saba kaiwa haka a makaranta ba ko dama da take kaiwa magariba computer practical take tsayawa, sannan idan tanada aji 4-6 takan fad’iwa Mamyn sabida karta damu.... Takai dubantaga Marliya da shigowarta parlorn kenan kana tace “Kin sami wayan Yusran...,?” Marliya ta girgiza kai a hankali kana tace “Na kirata sau biyu bata d’aga ba.... Itama Nabilar na kuma kiranta bai shiga....” Mamy tai k’wafa kana tace “Wannan ai rashin hankali ne, idan ba rashin hankali ba Yo ko wayar k’awarta ba sai ta ara ba tace mana bazata dawo da wuri ba idanma nata babu chaji ne.... Zata dawo gidan nan ta sameni ne...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye... A k’ofa ta had’uda Zulfa’u wacce da alama daga sashen Mamani ta fito, ganin fuskar Mamyn kawai ya tabbatar mata hankalinta a tashe yake... “Mamy Nabilar bata dawo ba har yanzu...?” Zulfah ta tambaya cikeda nuna kulawa... “Inafah ta dawo... So take Abbanku ya kuma tambayana ko ta dawo gida... Wane irin karatu ne har yanzu bazata dawo gida ba, tayi ma kanta yace ta gama karatun...” Cikin fad’a Mamy ke maganar... Zulfah ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kiyi hak’uri Mamy in sha Allah lafiya lou take, kinsan wasu lecturers d’in sam basu san yakamata ba babu ruwansu da lokacin sallah wasu kuma ba musulmai bane so a mata uzuri Mamy...” K’wafa Mamy ta kumayi kana tace “Ai bazasu hanata yin waya ba... Idan kuma Abbanku ya kuma tambayan ko ta komo gida sai kije ki masa wannan bayanin tinda ita batada hankalin ta d’aga waya ta kira mutane...” Ta k’arashe tana mai nufan kitchen bata daina sababi ba.... Marliya da Zulfah suka dubi juna suna masu jinjina lamarin.... “Bani layin Yusran na kuma kira....” Zulfa’u tace tana mai duban‘yar uwar tata... Cikin sauri Marliya ta mik’a mata wayar dake hannun nata... Zulfah ta d’auki number d’in kafin ta soma dialing... Wayar sai faman ringing take ba’a d’aga ba... Har ta kusa tsinkewa kafin aka d’aga, muryar k’aramar yarinyace take fad’in “Hello bata kusane ta saka wayar a chaji ne....” Zulfa’u tace “Wannan ba wayar Yusrah bane....?” Daga d’aya b’angaren yarinyar tace “Eh wayartace amma bata kusa ne...” Zulfah ta jinjina kai tace “Ta dawo daga makaranta kenan...?” Yarinyar tace “Eh tinda rana ta dawo...” Duban Marliya da tai mata k’uri Zulfa’u tai kana tace “Toh shikenan sai anjima koh, idan Yusrah tazo kice mata Zulfa’u Addar Nabilah ce ta kira...” Yarinyar ta amsa mata kana ta kashe wayar... Jigum jigum sukai suna tunanin ta yanda zasu soma sanar da Mamy cewa k’awar Nabilah ta jima da komawa gida... Marliya tace “Addah kodai mu sanar da Mamy halinda ake ciki, kinga fah dare ya riga yayi, bamusan wane hali ‘yar uwarmu ke ciki ba....” Ta k’arashe fuska d’aukeda damuwa... Shiru Zulfah tai tamkar mai tunani kana tace “Marliya na rasa ta yanda zamu fara b’ullowa lamarin ne, gashi anjima kad’an nasan Abbah zai kuma tambaya muddin bai ganta ba... Toh idan dai bata makaranta ina take... Toh ko kinada layin sauran abokan nata ne...?” Marliya ta girgiza kai tace “Ai batada shirgin k’awaye kinsan halinta not everybody can stand her... Ita Yusrah dai itace d’aya k’awarta da na sani kuma coursemate d’inta ce komai tare sukeyi... Toh idan dai sun jima da tashi ita ina taje....?” Batakai aya ba muryar Mamy ya katseta da fad’in “Ban gane ba.... Ta baro makaranta tuntuni...? Toh ina ta tsaya....?” Zulfah ta d’an gyara murya tace “Mamy ki kwantarda hank.....” Bata ida maganar ba wayarta ya d’auki ruri... Lambar Yusrah da yanzu ta kira ake kuma kiranta.... Zulfah tai saurin d’agawa cikeda damuwa... Daga d’aya b’angaren Yusrah tace cikin ‘yan kame kame bayan sallama “Em em ina yini Addah Zulfah...” “Lafiya lou, Yusrah ce....?” “Eh itace dama bana kusa ne d’azun...” “Eh haka k’anwarki tace... Yusrah nace ko kuna tareda Nabilah ne... Munata kiran wayarta baya zuwa gashi dare ya sako kai already....” Yusrah ta soma fad’in “Eh ai amma mun tashi ita sai ta wuce gidan Aunty Bara’atu.... Akan haka muka rabu, amma ku kira wayan Aunty B d’in suna tare....” Nannauyan ajiyan zuciya Zulfah ta sauk’e kana taceda Yusrah “Toh shikenan mun gode Yusrah zan kira Auntyn yanzu....” Ta ida maganar tana mai duban Mamy da Marliya..... Duk yanda sukaida Yusrah ta fad’i masu, ran Mamy idan yayi dubu ya b’aci, wace irin rashin hankaline wannan... Kan wane dalili Nabilah zata kama hanya ta tafi gidan Bara’atu ba tareda sanin kowa ba...? K’wafa ta kuma yi a karo na babu adadi kana taceda Zulfah tai mata kiran wayan Aunty B... Zulfah ta danna nan ma bai shiga... “Bai zuwa Mamy....” Jinjina kai Mamy tai kana ta nufi d’aki sauk’inta ansan yanda take yanzu... Ita kaw Aunty Lami sai safa da marwa take tsakanin sashenta da sashen Mamy badon komai ba sai don ace ta nuna damuwarta itama.... Zulfah da Marliya dubanta kurum suke sam basuso Mamy tana fayyace mata cikinta gaba d’aya, don suma haka kurum bawai sun gama aminta da matar bane, tamkar tana b’oye wani abin haka suke gani.... Basu suka shigo garin Kano ba sai wajajen k’arfe takwas na dare, masallatai duk sun fito daga sallan lisha.... Kana ganin Nabilah zaka fahimci hankalinta a tsananin tashe yake, tasan a daidai wannan lokaci, lokaci ne da Abbanta ke zaune parlornsa kewaye da ‘ya’ayensa, idan baiga guda ba sai ya tambaya... Shikenan zata saka Mamynta a magana, donma yanzu Abbah ya sassauta da wasu halayyan nasa... Aunty B takai dubantaga Nabilah wacce gaba d’ai take dame kana tace “Relax daughter, ki kwantar da hankalinki zan shiga naiwa Abbanku bayani ta yanda zai fahimta kinji koh....” Nabila tai saurin dubanta kana tace “Aunty ce masa zakiyi ga yanda naje...?” Aunty B ta girgiza kai tace “Ya za’ai nace masa haka, wannan between us ne, our little secret.... Ni dai kawai nasan mai zan fad’i masu daga shi har Mamyn taku.... Kinji koh... So ki kwantar da hankalinki idan Ina nan in sha Allah bazakuyi kuka ba...” Nabilah ta murmusa tace “Na gode Auntynmu....” *** A can asibiti kuwa har wannan lokaci Hafiz bai farka ba.... Gaba d’aya Sameer a dame yake, hankalinsa gaba d’aya na tashe... Duk wasu abubuwa da Hafiz yayima k’anwarsa bai hanasa jin tausayin Hafiz d’in ba musamman da shike shine ya bigesa.... Likitoci suna kansa yayinda shida Shamsu suke reception sai faman safa da marwa yake.... Shamsu ya mik’o masa ruwan gora yana k’ok’arin calming nasa.... “Doc try to calm down....” Saurin katsesa Sameer yai da fad’in “How could you ask me to calm down.... Shamsu mutumin nan fah d’an uwana ne kuma ba fata ba yanzu idan hakan ta zamto silan ajalinsa zan jima inajin zafin hakan, domin gani zankeyi tamkar ni na kashesa.... Shamsu Hafiz can’t die.... He just can’t....” Ya k’arashe yana mai zama bisa benchi had’ida rufe bakinsa da duka hannayensa biyu cikin tsananin mutuwar jiki.... Shamsu ya zauna gefensa yana buga kafad’ansa guda a hankali yake furta “Bazai mutu ba in sha Allah.... Ka kwantar da hankalinka friend and pray for him kaji koh....” Sameer ya lumshe idanunsa a hankali ba tareda ya iya furta koda kalma ba... *** KADUNA Daddy na zaune parlornsa Ammi na gefe faranti dambun kaza gabansa yanaci suna fira Khalid yayi sallama... Ammi ce ta amsa masa sallaman nasa kana ya shigo jiki babu laka... Daga can gefe ya zauna kana iya hango d’an rama da duhu da yayi a ‘yan kwanakin... Kansa a k’asa ya soma gaida iyayen nasa..... Ammi ce ta amsa masa Daddy kam ko kallon kirki bai ishesa ba.... Ya dubi Ammi tai masa alamu da idanu kan ya baiwa mahaifin nasa hak’uri... Khalid ya d’an muskuta kana ya soma fad’in “Daddy kayi hak’uri....” D’aga masa hannu yai alamun dakatarwa kana yace “Mai ya dawo dakai gidan nan....?” Khalid ya had’iyi miyau da k’yar kana yace “Daddy hak’uri na dawo na baku, na sani abinda nayi ban kyauta ba... Bazan iya fad’a daku ba cos you’re my parents... I’m sorry Daddy and na yarda na amince zan karb’i zab’inku ma’ana na amince da auren Yesmin....” Cikeda tsananin mamaki Ammi ta d’ago tana dubansa, shi kansa Daddyn duban mamaki yake masa... Daddy ya gyara zama sosai kana yace “Ka tabbata da abinda kake fad’i...?” Khalid yai k’arfin halin jinjina kai kana yace “Eh Daddy na tabbata...” Alhaji Mainasara yace “Good...” Caraf Ammi ta cab’i zancen da fad’in “Ni dama nasan yarona mai biyayya ne kawai dai wancan watsetsiyar yarinyarce taso brainwashing d’insa...” Wani duba Khalid ya mata kana yace “Ammi please ki cire Nabilah a batun nan, ku k’yaleta haka tinda nayi abinda kuke so, nima kuyi abinda nakeso ku barta haka kedasu Siyama please...” Harara ta watsa masa kana ta mik’e cikeda murna tana fad’in dole taje taiwasu Yesmin da Siyama wannan albishir... Daddy ya bita da kallo har ta fice kafin ya maido da dubansaga Khalid... Gyara zamansa ya kumayi had’ida d’an gyaran murya kana yace “Saifullah ka tabbata zakabi umarninmu...?” Ya jinjina kai a hankali kana yace “In sha Allah Daddy.... fatana shine ku yafemin d’aga muku murya da bijire maku da nayi a baya....” Nan ma jinjina kai kana yace “Babu damuwa ni dama nasan kanada biyayya da sannu rana irinta yau zatazo... Na yafe maka tuntuni, Allah ya maka albarka....” A hankali ya amsada Ameen Daddy, suka d’an tab’a hiran company kad’an Daddy nata k’ok’arin shan cikinsa yaji ko don tak’ura da talauci ne yasa shi ya dawo yayi nadama amma shiru baiji hakan ba... Har saida Khalid d’in ya mik’e zai fice kana ya dakatar dashi da fad’in “You can now have access to your bank accounts... Ga sauran credit cards d’inka a drawer a can ka d’auka.... Sannan zaka iya komawa company office d’inka right away...” Khalid ya jinjina kai yace “Na gode Daddy....” Ya d’anja fasali kad’an kafin ya dawo da baya ya kuma risinawa yace “Daddy banso ka dubi wannan da wata manufa... But to be honest with you.... I’ll like to resign from the company.... Zan applying neman aiki a wani wajen... Bawai don wani abin ba sai don Kawai inaso na zama independent ne.... I hope you’ll understand me Daddy...” Shiru Daddy yayi na wasu ‘yan dak’ikai kana ya sauk’e ajiyan zuciya yace “Khalid ban fitar dakai waje karatu don ka dawo kayi aiki ma wasu ba sai don watarana ka zamto ka rik’e abinda zan bar maku koda bani a raye, domin kaw kai zaka gajeni a company d’in... Amma idan haka ka zab’a babu matsala ni zan sama maka aikin in sha Allah....” Khalid ya d’anyi jim kana yace “Daddy dama dai da so samune na nemi aikin da kaina ba tareda taimakonka ba please.... I hope that’s ok with you...” Shiru na d’an lokaci kana ya jinjina kai yace “Alright if that’s what you want... Bakada matsala dani, Ubangiji ya taimaka... Amma ka sani ko yaushe kaji kana son dawowa company d’in mahaifinka the door’s always open kaji koh....” Ya jinjina kai a hankali kafin yayi sallama wa mahaifin nasa ya fice.... *** Abbah ya gama jin bayanan Aunty B tsaf kana yace “Bara’atu ba nak’i maki bane amma abinda Nabilah ta aikata sam ba daidai bane kuma ba tarbiyan gidan nan bane.... Mai amfanin wayar hannunta da ko mahaifiyarta bazata kira ta sanar da ita taje gidanki ba... Maima zaisa daga makaranta ta shige can gidan naki... Shin makaranta tace zataje kokuwa gidanki...?” Cikin kakkausar harshe yake maganan... Aunty B ta kuma cewa ai hak’uri Abbah hakan bazata sake faruwa ba in sha Allahu..... Kan Nabilah na k’asa ta kasa furta komai sai faman rakub’e rakub’e take.... Ita koh Aunty Lami idanunta k’yam kansu don bata yarda iyakacin gaskiyar ba kenan... Daga parlorn Abbah acan sashen Mamy ma fad’a taitayi, daga Nabilar har Aunty B d’in bata k’yale kowa cikinsu ba.... Ita kaw Aunty Lami sad’ad’awa tai tabi bayansu don jin yanda zasu kaya da Mamy.... Aunty B da taga fad’an tai yawa da alama sosai ran Mamy ya b’aci don har tafi Abban nasu d’aukan zafi... Gyara murya tai tace “Gidan Yaya Abida na kaita...” Gaban Mamy ya yanke ya fad’i don rabonta da taji an ambaci wannan suna ta mance..... Ta d’ago tana duban Aunty B d’in..... Aunty B ta jinjina kai alamun tabbatarwa.... Zulfa’u ma duban Aunty B d’in take lokaci guda k’irjinta na bugawa yayinda Marliya da Nabilah suka rasa gane wacece Yaya Abida..... Ita kaw Aunty Lami dake lab’e jikin k’yaure dafe k’irjinta tai da duka hannayenta biyu.... Lokaci guda k’afafunta suka d’auki rawa.... Cikin sauri ta shiga jada baya da baya zuciyarta bai daina yankewa ba... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *64* *©️Sameena Aleeyou...✍🏼* Mamy tai shiru ba tareda ta kuma cewa komai ba, Zulfa’u ce ta janyo hannayen k’annenta suka shige suka barwa Mamy da Aunty Bara’atu parlorn domin su tattauna.... Mamy ta kuma duban Aunty B kana tace “Gidan Yaya Abidah... Maiyasa kika kai Nabilah....?” Aunty Bara’atu tai shiru na wasu dak’ik’ai kana tace “Na fad’a maki dama INDA RAI sai nayi silan k’ulla zumuncin da ya riga ya wargaje a baya, koda hakan zai zama k’arshen abinda zan k’ulla kenan a duniya....” Nan ma shiru Mamyn tai batace komai ba sai duban Bara’atun da tayi, lokaci guda ta koma ta zauna cikin kujera jikinta a mace.... Ganin haka yasa Aunty B zama daga can kujeran gefenta.... A can d’aki kuwa Nabilah da Marliya ne suka tsare Addarsu Zulfa’u da tambayan wacece Yaya Abidah.... Marliya tace “Dama Mamy tanada wata ‘yaruwa shine bamu santa ba, koda wasa ko a labari bamu tab’a jinta ba....” Dafata Zulfa’u tai kana tace “Marliya har abada babu sirrin da zai tabbata a rufe, a iya sanina shekarun baya can lokacin nima banida wayo sosai mukanje gidanta da Mamy, rana tsaka muka daina zuwa kuma koda na tambayi Mamy sai cemin tai Yaya Abida ta mutu bata raye, idan nai mata batunta sai tacemin ko sunanta kada na kuma ambata, ni kaina na mance da ita sai yanzu da naji Aunty Bara’atu na cewa gidanta sukaje da Nabilah.... Tabbas ni kaina nawa kan ya d’aure akwai wani sark’akk’iyar al’amari dake faruwa wanda iyayenmu basu fayyace mana ba....” Marliya ta jinjina kai a hankali kana tace “Toh ko maiyasa Mamy tace ta mutu...? Maiyasa suka datse zumuncinsu...? Maiyasa bamusan da ita ba...?” A tare ta jero duka wad’annan Tambayoyin..... Sauk’e ajiyan zuciya Zulfa’u tai kana tace “Mamy ce kawai zata iya bamu wad’annan amsoshin......” Tai maganar tana mai lulawa duniyar tunani... Itakaw Nabilah gaba d’aya ba saurarensu take ba, hankalinta yafi karkata kan halin data baro Khalid ciki... Shikenan sun rabu rabuwa ta har abada....Anya tayi adalci ma kanta..? Anya hukuncin data yanke tai daidai ma zuciyarta da ruhinta...? Toh amma hakan shine daidaima Khalid, hanyar daya d’auka a baya bamai b’ullewa bane, ta gwammaci ta sadaukar da farin cikinta kan taga rayuwar mutum guda tak data tab’a so ya tagayyara.... Ta lumshe idanunta a hankali had’ida jingine kanta da ya mata nauyi jikin gado.... *** Mamy taci gaba da fad’in “Maiyasa kika d’auki Nabilah kika kaita wajen matar da kinsan cewa ta jima da mutuwa a babin rayuwata da iyalaina.... Maiyasa kike son tono abinda ya jima a rufe... Bara’atu maiyasa kike son dawowa da jiya yau....” Cikin tsananin rawar murya tai maganar... Aunty B na hawaye ta taso ta durk’usa gaban Mamy had’ida rik’e hannayenta lokaci guda take furta “Wasu sirrikan suke bud’e kansu... Wasu sirrikan basu yarda su dawwama a rufe.... Ki sani’yar uwata ina sonki, ina k’aunarki ko mai zaije yazo, and I’ll forever be here for you.....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Lokaci guda suka rungume juna suna hawaye... Suna a haka wayar Mamy ya d’auki ruri, Sameer ne mai kirant, gaisawa sukai yanda Mamyn ta jisa a d’an birkice, tana tambayarsa ko zai shigo gidan ne kafin ya shige can gidansa sai ce mata yayi “A’a Mamy, ina asibiti dai tukuna...” Mamy tasa yatsa tana goge hawayen da suka mak’ale mata had’ida gyara zama sosai kana tace “Toh... Lafiya amma...?” Sameer ya d’an shafi sumarsa yace “Mamy Hafiz muka kawo asibiti ya d’an sami had’arin mota... But he’s out of danger now.. Amma dai bai farfad’o ba...” Mamy ta mik’e tana furta “Subhanallahi, wani asibitin kuke Sameer.... Ka kira su can gidansu Hajiyar tasa...?” Sameer ya sanar da ita asibitin da suke kana ya k’arada “A’a ban kirasu ba kece kawai na kira...” “Toh shikenan, gamu nan zuwa zan sanar da Abban naka yanzu, zai kira Alhajin ya sanar dashi...” Sameer ya amsada “Ok Mamy sai kunzo....” Sukai sallama kana ya katse kiran yana mai duban Shamsu da ya tallafi fuska da hannaye bibbiyu yana dubansa... Jin Mamy tana fad’i ma Aunty B yanda sukaida Sameer d’in cewa Hafiz ne babu lafiya ya sami had’arin mota yana can asibiti yasa gaban Zulfa’u mugun fad’uwa... Cikin sauri ta d’aga labulen d’akin ta fito, fuska d’aukeda tashin hankali take ceda Mamy zata asibitin itama... Aunty B ta galla mata harara kana tace “Kije ina...? Kije ki masa mai... Iyakaci addu’ace ince...? Toh ki masa ita daga nan....” Idanun Zulfa’u sukai raurau... Ta kasa furta komai sai sadda idanun nata k’asa da tai.... Tuni Mamy ta fice sashen Abbah Aunty B ta mara mata baya... Aka bar Zulfah tsaye wajen tana kokonton halinda Hafiz ka iya kasancewa ciki... Marliya ta dafata kad’an kana ta kamo hannunta ta zaunar saman kujera, har lokacin Zulfah bata dawo daidai ba, mutuwar Kausar ya dawo mata sabo... Gani take kaman shima Hafiz d’in mutuwa zaiyi... Shikenan duk sun tafi sun barta... Bazatace ga abinda takeji gameda Hafiz ba amma can k’asan zuciyarta tanajin wani irin rauni had’ida tausayin kanta... Ta lumshe idanunta a hankali sanda ta tsinci zuciyarta na addu’an samun sauk’iga Hafiz... Mutumin da ya d’aid’aita mata rayuwa ya tagayyara.... *** Sanda labarin ya riski Hajiyar Hafiz bayan Lami ta gama labarta mata tashin hankalin dake gabansu ne.... Tabbas idan kan mata ukun nan Mamy da ‘yanuwanta ya had’e shikenan kashinsu ya bushe su kad’ai za’a bari a rana.... Tagajan magajan ta nufi asibitin tana kuka yanda ta riski su Mamy tuni sun isa can, cikeda tausayawa Mamy ta k’araso yanda take tana bata baki had’ida k’arfafa mata gwiwa.... Hajiya bata daina kuka tana furta Hafiz d’inta bazai mutu ba... Shikenan mata d’ah namiji.... Ta kuma d’aura hannaye aka tana kuka kaman wacce batai imani da k’addara ba... A b’angaren Lami da Aunty B kuwa kowacce kallon kallo kawai suke aikama junansu.... Daga can Abbah da Sameer harma da Shasmu suna tafe tareda wasu likitoci guda biyu suna tattauna lamarin Baba Alhaji ya k’araso tagajan magajan sai sab’a babban riga yake... Abbah yaceda Likitocin ga mahaifin nasa ya iso.... Tuni Baba Alhaji ya nufesu yana tambayan ina Hafiz...? Ina d’ansa....?” Dr guda d’aya ya dafasa yana k’ok’arin calming d’insa yake sanar dashi Hafiz zai sami lafiya da izinin Allah.... Baba Alhaji yakai dubansaga Abbah da Sameer kana yace “Ya akai ku kuka fara sani...? Meke faruwa...?” Gaban Sameer ya fad’i don bai sanar dasu cewa shi ya buge Hafiz ba.... Baba Alhaji ya kuma fad’i cikin hasala... “Usman ka sanar dani meke faruwa... Ya akai kaida d’anka ku labarin had’arin ya soma riska...?” Dukda jama’a dake faman kai komo bai hana Baba Alhaji d’aga murya yana surfa bala’i ba.... Abbah ganin Yayan nasa zai tara masu jama’a ya d’an bud’e murya yace “Yaya baka fahimta ba... Sameer shine ya kiramu yake sanar damu kasan cewa shi ma’aikacin lafiya ne....” Baba Alhaji yace “Wanene kuma Sameer...?” Sameer ya d’ago idanu yana dubansa sanda Abbah yake furta “Dahnah Ma’aruf...” K’are masa kallo Baba Alhaji yayi ba tareda ya furta komai ba kana ya kuma sab’a babbar rigarsa yabi bayan likitocin don jin bayanin hoton k’irjin da sukaima Hafiz.... A cewar likitocin ya sami rauni sosai ta cikin k’irjinsa dad’ida k’ari alamu sun nuna cewa yana cikin matsanancin tashin hankali da damuwa had’arin ya samesa wanda ya janyo zuciyarsa tai rauni sosai.... Sameer ya dafe kansa a hankali sanda Shamsu ya janyo hannunsa suka keb’e da abokin nasa.... *** Washe gari Nabilah na had’uwa da Yusrah a makaranta sai rungumeta tai tana kuka sosai, lokaci guda take furta “Yusrah ina sonshi... Wllhi ina sonshi, na kasa yakishe tunaninshi cikin zuciyata....” Tausayinta ya cika Yusrah, rik’o hannunta tai da sauri suka fice daga ajin dashike babu malamin da ya shigo, nan suka keb’e yanda Nabilar ta labarta mata komai, duk yanda abin ya kasance.... Yusrah ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “K’awata ki kwantar da hankalinki ni wllhi inaji ajikina keda Khalid had’in Allah ne kuma d’an adam bai isa ya rabaku ba... Da sannu al’amara zasu daidaita bayan sunyi zafi... Kar ki mance duk tsanani na tareda sauk’i, kawai kici gaba da addu’a Allah ya kawo maku mafita....” Jinjina kai Nabilah tai ba tareda furta komai ba... Yusrah ta d’an murmusa tana dubanta kana tace “Ikon Allah da idan akacemin k’awa zata fad’a kogin love haka zance wllhi k’aryane... Where’s the tough Nabila that I used to know... Nabilar da maza basa gabanta... Mafad’aciya wacce baka gano lagonta da wuri... Lallai Khalid ya cire tuta cikin maza tinda har soyayyarsa ke neman canza wannan Nabilar daga mafad’aciya zuwa mai sanyi....” Dukan da Nabila ta kai mata ya sanyata shanyewa tana mai ci gaba da dariya... Nabila ta galla mata harara tana mai tattare books d’inta take fad’in “Sai ki tashi muje ai gashi can ya shigo...” Yusrah bata daina zolayarta ba har suka shige aji..... A b’angaren Zulfa’u kuwa tana zaune ne kurum a office amma zuciyarta na wani wajen daban.... Atika ce ta shigo ta risketa a haka, janyo kujera tai daga can gefe ta zauna tana mai bud’e folder d’in dake gabanta had’ida ciro takardan da zasu gudanar da shirin yau..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *65* Duk maganganun da Atika keyi sam Zulfah ba sauraronta take ba, ta ije takardun hannunta tana mai duban Zulfa’un.... D’an zungurinta da biron hannunta tai kana tace “Wai lafiya kike...?” Nannuyan ajiyan Zuciya Zulfa’u ta sauk’e kana ta d’an shafi fuskarta tace “Lau nake.... Mu fara gudanar da shirin koh....” Atika ta jinjina kai bawai don ta gamsu da amsar Zulfa’un ba kana tai alamu ga mai saka sauti da hannunta, suka rufe kunnuwansu da headphones su duka biyun ko wacce da takarda hannunta kafin suka soma gudanar da shirin...... **** Misalin k’arfe goma na hantsi Sameer ya shigo sashen Mamani, a parlor ya risketa ta ida shiri don dama ita yazo d’auka su tafi asibiti can wajen Hafiz.... Raihanah da Naja’atu na zaune daga gefe gaba d’aya suka gaidashi... Ya amsa cikeda kulawa sanda Mamani tai kiran Najah tazo ta duba mata takalminta maras nauyi parlorn ya rage saura Sameer da Raihanah, idanunsa naga ciwon Raihanan yana ganin yanda yake healing slowly... Gaba d’aya bata sakewa idan yana dubanta duk sai tajita ba’a sake ba haka nan, muryarsa ta kuma sinkayowa yanai mata yaya jiki, ta amsa a tak’aice... Ya jinjina kai kana ya k’arada “Salma tazo jiya....?” Nan ma jinjina kai ta kumayi kana tace “Eh tazo...” Ya jinjina kai a hankali ba tareda ya kuma furta komai ba.... Fitowan Mamani da Naja’atu ne ya katse firan nasu... Mamani ta dubi Sameer tace “Ai sai muje koh... Ke Naja’atu ince kinzo mu tafi tarene...?” Naja’atu tai saurin jinjina kai kana tace “Eh Mamani...” Sameer yace “Bara naje na kunna motar sai kun fito...” Mamani ta jinjina kai tana mai fad’in “Yauwa gamu nan fitowa....” Sallama Raihanah tai masu kana ta basu sak’on gaisuwa su isar zuwaga Yayanta Hafiz da addu’an sauk’i a garesa.... Suna fitowa ne suka had’u da Marliya itama ta take masu baya suka d’unguma gaba d’aya... Dashike Shamsu ne zaune gaban motar hakan ya sanyasu duka zama a bayan motar, a hanya Marliya ke tambayan Naja’atu jikin Sahariyya don tin dukan da Hafiz ya mata har yanzu bata sami ishesshen lafiya ba, hannunta guda ya karye haka nan ta sami rauni a k’afarta... Gaba d’aya Hajiya Haule ba a hayyacinta take ba, abubuwa suna kan faruwa ba yanda taso ba ga babban abinda yafi bata mamaki shine tun jiya da aka kawo Hafiz asibiti matarsa Sawwama bata tako k’afarta ba, wannan abu sosai ya dami Hajiya, tai k’udirin da zaran wasu awannni sun shura bata ganta tazo ba toh zata garzaya can gidan Hafiz d’in ta duba ko lafiya ko mai ya hana matarsa kasancewa dashi a daidai irin wannan lokaci.... Isowarsu da kad’an suke samun labarin farkawan Hafiz d’in... Kalman Zulfa’u itace a bakinsa sanda ya farka... Hajiya Haule dake zaune gefensa wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi... Ta mik’e zunbur tana karanto hamdala had’ida tambayarsa mai yakeso.... Maimakon ya bata amsa sai sunan Zulfa’u da ya kuma kira.... Daidai lokacindasu Abbah da Sameer suka shigo d’akin... Hafiz yaci gaba da fad’in “Hajiya ki taimakeni ki ceceni ki kirawo min Zulfa’u... Inaso na rok’eta gafara kafin na bar duniya.... Hajiya bazanso na mutu da hakkinta ba....” Ya k’arashe maganar da k’yar yana mai k’ok’arin kai hannu don dafe k’irjinsa.... Cikin sauri Sameer ya k’arasa yana fad’in “Take things easy, a halinda kake ciki yanzu hutu ya kamata ka samu....” Hafiz ya k’ura masa idanu yana mai tunanin tabbas yaga fuskar nan before he lost consciousness... Tabbas ya ga Sameer akansa na k’ok’arin taimaka masa.... Yai shiru suna duban juna shida Sameer d’in... Baba Alhaji ya k’araso cikin sauri yana dafe hannayen Hafiz d’in yake tambayarsa ya sanar dashi mai ya faru...? Ya akai ya sami accident...? Hafiz ya dubi mahaifin nasa, ya kuma duban Sameer dake tsaye gefe, ya maido da dubansaga mahaifinsa alamun zai soma magana, caraf ya sinkayo muryar Sameer na fad’in “It was me... Ni ne na bigesa da mota....” Ai bai kai aya ba Baba Alhaji yayi tsalle ya cakumosa yana fad’in “Kashesa kayi niyya, kashesa zakai akan ya saki k’anwarka... Shin kai mai ka sani Ma’aruf...? Fansa ka dawo d’auka....? Ka sanar dani fansa ka dawo d’auka....? Idan fansa ka dawo d’auka ka sani ba akan Hafiz zaka d’auka ba don ba shi yayi sanadiyan b’acewarka ba... Wad’anda zaka d’auki fansa akansu....” Baikai aya ba Hajiya tai wuf ta shiga k’ok’arin janye Baba Alhaji ganin zai saki layi.... Mamani dasu Najah suka shigo a birkice jiyo muryar Baba Alhaji da sukai yana tashi cikin karaji.... Marliya jiki na rawa ta isa tana k’ok’arin janye d’an uwanta ganin yanda Baba Alhaji ya shak’e masa wuya tamkar zai aikasa lahira... Mamani kam kuka ta saki tana fad’iwa Baba Alhaji ya sakar mata jika ko ta masa baki... Jin haka ne ya sanya Baba Alhaji janye hannayensa daga wuyan Sameer, Hajiya ba haka taso ba, taso ya aikasa lahira kowa ya huta, asirinsu ya rufu ruf rufuwa ta har abada.... Shamsu da shigowarsa kenan ya k’arasa a guje yana mai tallafo abokinsa yake tambayarsa ko yana lafiya.... Hafiz dake tari a hankali yana yunk’urin magana amma ya kasa.... Da k’yar ya iya furta “Baba dan Allah ka k’yale Sameer, babu laifinsa... Laifinane da nake tafiya ba tareda sanin yanda nake zuwa ba... Hasalima ni ya kamaci na rok’eshi gafara halinda na jefashi ciki.... Ya mik’o hannayensa yana k’ok’arin kamo hannayen Sameer lokaci guda yake furta “Ma’aruf ka yafe min please..... Ka yafe min duk wasu abubuwan da na maka.....” Sameer na sosa wuyarsa yake girgiza kai lokaci guda ya rik’e hannun Hafiz yace “Ka daina fad’in haka Hafiz, bakamin laifin komai ba.... Fatana Allah ya baka lafiya....” Hafiz da siririyar hawaye ke zubo masa yaci gaba da fad’in “Na gode.... Na gode Sameer, kanada zuciya mai kyau, dan Allah ka tayani rok’on Zulfa’u ta yafemin.....” Shiru Sameer ya d’anyi kana yace “Wannan tsakaninku ne Hafiz, ba hurumina bane.... Allah ya baka lafiya...” Hafiz ya jinjina kai a hankali yana mai rintse idanunsa wasu irin hawaye masu d’umi suka kuma zubo masa.... Jikkunansu sukai sanyi gaba d’aya, Baba Alhaji ya fice cikeda borin kunya yayinda Hajiya ta samu ta silale itama ta nufi can gidan Hafiz d’in dubo Sawwama don taji har wani tunanin Zulfah Hafiz ya soma, abinda bata fata ko bayan ranta ace Hafiz ya maidoda Zulfah d’akinta.... *** Akram ya dubi Yusuf a karo na biyu kana yace “Kanaga banyi mata hanzari ba....?” Yusuf ya kuma karyan raken dake rik’e hannunsa na dama kana yace “Kasanfa hausawa na cewa A bari ya huce shike kawo rabon wani.... Mutumina this is the right time, na tabbata tuni manema sun soma kawo mata hari so gwara kawai ka making move.... Mu k’arasa Atika tai mana iso....” Akram ya zuba duka hannayensa biyu saman steering wheel kana ya sauk’e ajiyan zuciya kad’an yace “Amma bazataga mun biyota wajen aikinta mun tak’urata ba....?” Gajeren tsaki Yusuf yai kana yace “Wataran fah kayan haushi ne dakai, idan bazakai amfani da damar daka samu ba kada ka kuma zuwa kanamin zancen wata Zulfa’u ka gane koh... Na fad’a maka ni nan na sanar da Atika ta shirya mana yanda za’ai muga Zulfah lokacin break d’insu, idan kuma baka shirya ganinta bane toh sai naji...”Ya k’arashe yana mai karyan rakensa.... Harara Akram ya watsa masa kana ya kunna motar, Yusuf yaja marfin mota ya rufe kana suka d’auki hanyar station d’in su Zulfah.... Suna tafe ne wayar salulansa dake aje gefe ta d’auki ruri, ya d’an rage speed kana yakai dubansaga screen d’in wayar, ba kowa bane illa boss d’insa Engr Mutallab.... Yai saurin d’agawa cikeda girmamawa, take Engr d’in ke sanar dashi ya bar duk abinda yake yazo Office ya sameshi... Akram yace “Alright your excellency gani nan zuwa....” Ya k’arashe yana mai karya steering motar, lokaci guda yake furta “Change of plans... Babu gani Zulfa’u yau...” Yusuf ya tab’e baki kad’an kana yace “Aidai da ka sanar dashi ka tafi neman aurene bazai katse ka ba....” Akram ya jefo masa harara gajeriya kana yace “Sallah ne kawai bazan katse ba idan his excellency yanada buk’atan ganina... Komai a bayansa yake...” Yusuf ya kuma tab’e baki yace “Naga alama ai... Kaga barin kira Atika na sanar da ita bazamu samu zuwa yau ba....” Atika dake faman rarraba idanu a a cafeteria d’in, tana hango ta yanda zataga su Yusuf shiru bata gansu ba, sai faman waige waige take gashi dai sun ida cin lunch d’insu.... Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Wai wanine kike jira...? Idan ba jiran wani kike ba kiwa Allah ki tashi mu koma office...” Hannunta Atika ta rik’e ta kuma zaunarta tana fad’in “D’an k’aramin lokaci kedai....” Zulfah ta girgiza kai kurum tana mai juya idanu had’ida jan gajeren tsaki... Daidai nan wayar Atika ta d’auki ruri, Yusuf ne mai kiran nata.... Tai saurin matsawa gefe tana tambayarsa mai ya hanasu zuwa har yanzu.... Nan Yusuf ke sanar da ita something came up dole suka canza plan.... Atika da tuni ta shak’i haushi cewa tai “Ni na fad’a maka wannan abokin naka is not serious, da alama Zulfah ba class d’insa bane don harta ogoginmu na nan station suna nuna kulawa akanta, idan baiyi da gaske ba zaiji a salansa....” Yusuf yace “Ya zakice haka, ogansa ne ya kirasa kedai kici gaba da mana sharan fada kawai please kinji... Yauwa na gode k’anwata...” Gajeren tsaki tai kana ta dawo taceda Zulfah su koma Office... Zulfah dai dubanta kawai tai kana ta tattari belongings d’inta suka nufi office... Suna tafe Zulfah ke tambayar Atikan ko lafiya take.... Atika tace lafiya lou wani saurayinta ne yace zaizo toh kuma sai yace mata uziri ya rik’esa... Zulfah batace komai ba sai jinjina kai da tai... Atika ta d’an dubeta kana tace “Waini Zulfa’u meye shirinki...?” Zulfah ta d’an dubeta kana tace “Ban gane ba... Shirina kaman yaya...?” Atika ta murmusa tace “Ina nufin kinada burin aure nan kusa..? don naga da yawan staff d’inmu idanunsu na kanki ne....” D’an dubanta Zulfah tai kana ta dubi wani gefen, lokaci guda take furta “After what I went through banajin nayi shirin kasancewa da wani namiji kuma...” Atika tai shiru na tsawon shud’ewan wasu dak’ik’ai kana tace “Does that mean you haven’t moved on from your ex husband... Kina sonshi ne har yanzu....?” Wani irin duba ta mata kana ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Wasu lokuta mukan tsinci kawunanmu cikin al’amra masu wuyan fasaltuwa, so tari Allah yakan jarabci bawansa da abinda yafi rainawa a rayuwa.... Ko a baya ba auren soyayya nayida Ya Hafiz ba... Idan kika tambayeni ban san wata soyayyan d’ah namiji ba face na iyayena da ‘yan uwana saiko d’iyata da na rasa... Hasalima ni Zulfa’u na taso cikin tsanane a tsakanin danginmu, harta mahaifina da Kakata basa k’aunata kan laifin da sam ban aikata, kan laifin b’acewan d’an uwana Ma’aruf.....To them I was nothing but a curse... Bayan mahaifiyata da k’annena guda biyu no one believes in me, sun yarda cewa mai farar k’afa aka haifoni har saida Allah ya wankeni ya kuma dasa k’aunata cikin zukatansu.... Toh kinga ni bansan wata soyayya ba bansan ya ake jinta ba... Idan nace maki ina son Ya Hafiz na maki k’arya don bansanma ya take ba, the only thing I know shine zaiyi wuya kayi rayuwar aure da mutum sannan a cikin rayuwar har Allah ya baku rabo cikinta kace bazakaji komai gameda mutum ba koda kuwa ace b’angare na tausayawa ne.... A halin yanzu babu wani shiri na aure ko soyayya a gabana, burina shine naci gaba da aikina da kuma samun nasara had’ida kwanciyan hankali.... Kin fahimta....” Shiru Atika tai tana dubanta har takai aya, tausayin rayuwar da Zulfah tai a baya ya cika mata zuciya, ta saki murmushi a hankali kana tace “Toh kisa a ranki cikin masoyanki harda k’awarki Atika... Sannan na yarda dake na yarda cewa ke ba mai farar k’afa bace kuma in sha Allah a tattareda ke akwai babban al’amari wanda kowa harta masu cewa kinada farin k’afa zasu amfana ta dalilinki....” Zulfah ta murmusa kana tace “Na gode k’awata nima ina k’aunarki tsakaniga Allah...” Sukai murmushi su duka biyun kana suka nufi cikin studio.... ** Tin daga k’ofar gidan gaban Hajiya ke bugun tara tara.... Jikinta bai ida sanyi ba saida ta shiga cikin gidan taga bad’alan da ake aikatawa ga hayak’in kayan maye had’ida warinsa ya gauraye gidan gaba d’aya, ta shiga toshe hanci tana tari da k’yar.... Can ta hangi Sawwama sai rawan ‘yan bori take tanayi tana kora barasa ga ‘yan daudu na tayata mai gurmi naci gaba da aikinsa... Hajiya ta d’aura hannaye duka biyu aka tana nishi da k’yar take furta “Na shiga uku... Na shiga uku ni Haule mai zan gani.....?!!” *** Kana ganin Muhibbah kasan a d’auke take, Najma ta shigo tana mata kukan yunwa, wani uban tsawa data dararawa yarinyar saida ya sanyata sakin fitsari a wando... Yarinyar ta shiga jada baya jikinta na rawa... Yamutsa fuska Muhibbah take ganin fitsarin da yarinyar ta saki tana mai furta “Oh no no this isn’t happening...” Gashi Engr yasa ta rage ma’aikatan gidan a cewarsa idan tayi niyyan shiryuwa da gaske sai ta fara da kulada iyalanta... Kira ta shiga dokawa Suwaiba wacce ita kad’ai aka bari harta Cooks d’in gidan Engr ya sallamesu... Suwaiba ta k’araso a guje tana mai risinawa.... Muhibbah na mata nunida Najma take fad’in “Take care of her... Ta isheni da kuka.... Uban mai kike da har yanzu baki ida lunch d’in ba....?” Suwaiba tace “Aunty aikin ne sunmin yawa... Kuma ai kaman naji Alhaji yace kece zakike abinci...” Wani uwar harara data watsawa Suwaiba kana ta isa ta janyo kunnenta guda tace “Na maki kama da mai dafa abinci...? Answer me..!! Na maki kama da mai girki....??” Suwaiba dake faman tamke fuska alamun taji zafin rik’on cikin sauri take girgiza kai alamun a’a.... Muhibbah ta jinjina kai tace “If you don’t want to get yourself fired toh kiyi duk wasu ayyukan da kikasan ma’aikata keyi gidan nan... Kuma Wllhi saura Engr ya dawo kice masa kece kikai abinci sai nayi d’add’aya dake... Tashi ki bani waje...” Ta tashi da sauri tana goge hawayen da suka zubo mata... Muhibbah ta kuma kiranta tana mata nuni da Najam tace “Ki gyara wajen nan kafin na dawo....” Tana ida fad’in haka ta haye sama... Najma tai saurin rungumar Suwaiba tana kuka.... Suwaiba ta rungume yarinyar cikeda tausayawa, badon tausayin yaran ba da ganin girman Engr tabbas da tuni ta bar aikin gidan... Matace tamkar ba ‘yar Adam ba ko ma d’iyoyin wasu bazakayi irin wannan rik’on ba balle yaran da ka tsuguna ka haifesu.... Suwaiba ta d’auki yarinyar suka nufi kitchen tare tana mai lallashi had’ida jantada wasa... Ita kaw Muhibbah tana zuwa d’aki, drawer mai d’aukeda kayan mayenta ta janyo... Ta ciro k’waya guda d’aya ta murmusheshi lokaci guda ta toshe hancinta guda ta shiga shak’a tana mai bubbuga kanta.... Saida taji kanta acan sararin samaniya kafin ta koma gefe tana hango duniyar na juye mata... Tana a haka ta jiyo k’aran shigowar motarsa... Cikin sauri ta mik’e tana k’ok’arin kimtsa kanta dukda cewa k’wayar bai saketa ba, hasalima datasan da wuri zai komo gida da bata sha ba.... Saida ta saita kanta kafin ta sauk’o k’asa.... Akram ne ya soma fitowa rik’eda jakan Engr d’in ya mik’a mata... Tai masa wani duba a yatsine kana tace ya aje a parlor ta k’arada in Engr d’in .... Akram ya bata amsada yana cikin mota... Tsaye tai tana mamakin mai yakeyi cikin mota, nan dai ta nufi motar... K’arar radio ta soma jiyowa cikin muryar wata mace mai dad’in sauraro yanda take furta “Toh jama’a masu saurarenmu yauma a nan zamu dasa aya... A shiri na gaba zaku jimu cikin wani sabon shirin... Kuci gaba da kasancewa damu a tasharku kuma zab’inku... A madadin mai kulada shirin da kuma abokiyar aikina tareda ni kaina Zulfa’u Usman Mailafiya muke cewa ku huta lafiya.....” Muhibbah takai dubantaga mijinta yanda yake kishingid’e jikin car seat idanunsa a lumshe sihirtacciyar murmushi kwance saman fuskarsa.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *66* Chaaa sukaima Hajiya Haule akai suna tambayarta daga ina take... Haule ta kasa amsasu sai nishi da take saki da k’yar sabida k’ahon zuciyarta dake mata tsananin zogi... D’aya yace “K’ila ‘yar lek’en asirice ma ‘yan hizba tinda makircin ‘yan unguwa ya gagara shine aka turo wannan matar...” Gaba d’aya suka amsada tabbas maiyuwa hakan ne... “Mai muke jira, mu lakad’a mata na jaki ta yanda gobe zata kuma zuwa wani wajen lek’en asiri ba....” Kan Hajiya ta sami zarafin magana suka shiga sauk’e mata duka ta ko ina, basaji basa gani bugu kurum suke mata har saida hankulansu Sawwama yaje wajen... Ga mamakin Sawwama mahaifiyar Hafiz ake bugu, suka tambayeta ko tasan matar ne, Sawwama tace atafau itama bata santa ba da gaske ‘yar lek’en asirice... Sawwama ta basu go ahead suci gaba da bugun Hajiya... Hajiya na magagi da mak’yark’yata take furta “Sawwama nice fah... Nice uwar mijinki fah...” Sawwama ta tinstire da dariya tace “Kuji makira Wai itace uwar mijina... Toh idanma uwar mijina ne sai mai... Ko shi mijin ne ba tsira zaiyi a nan ba balle ke... Wani mijin ma da tuni na basa rasidi... Idan baki sani ba toh ki sani ni Sawwama na gama auren wannan matsiyacin d’an naki mai farin k’afa maza a k’ara gaba....!” Hajiya ta d’aura hannaye bibbiyu aka tana furta “Wayyo! Wayyo!! Na shiga uku ni Haule... Na d’ibo ruwan dafa kaina... Amma wannan yarinya ke ba ‘yar halas bace... Nayi danasanin aurenki da Hafiz yayi... Matsiyaciya dangin fir’auna a nono kika sh....” Batakai was aya ba taji sauk’ar lafiyayyar mari a k’uncinta... Ta zaro idanu waje tana duban wacce tai marin ba kowa bace illa sirkarta Sawwama... Sawwama na huci taci gaba da fad’in “Ke har kin isa ki zagi mahaifiyata... Kinyi kad’an, kinada sauran azuzuwa kafin ki k’araso yanda nake a bariki...” Ta dubi sauran ‘yantashan nata tace “Kuci gaba da bugunta muddin bata tashi ta nemi hanyar tsira ma kanta ba...” Haba nan kakeji didim dim dim, sautin bugun dake sauk’a jikin Hajiya Haule... Gashi ihunka banza ne don sautin kid’a dake tashi bazai bari mutan unguwa su jiyo su ceceta ba... Haka Hajiya ta dinga birgima wajen d’ankwali gefe zani gefe sai bugunta suke tamkar an aikosu, itako sai birgima take wajen tana ihu tana neman agaji... Da k’yar Hajiya Haule ta samu ta arce a guje zani a hannu d’ankwali a hannu ga fuskarta da sumarta duk k’asa ya b’ata yanda tasha bugu... Yara kuwa suna hangota sai su arce a guje suna mata wak’an mahaukaciya, masu adaidaita ma idan ta tare basa tsayuwa don cewa suke mai tab’in hankaline.... Wani adaidaita ne ya nufo yanda take, tai maza ta haye saman kwalta d’in tana saka masa hannaye bibbiyu alamun ya tsaya... Daga mai adaidaitan har passengers d’in dake ciki wasu mata guda biyu, salati suka shigayi suna ambaton Allah, su kansu basu yarda cewa wannan matar ba mahaukaciya bace... Atika ta zaro idanu waje tana buga siddin mai adaidaitan tana fad’in “Malam kayiwa Allah ka kaucewa mahaukaciyar nan mu bar wajen nan kafin ta mana duka don wannan daga gani tsohuwar kamu ce...” Zulfah kuwa zaune kurum tai cikin adaidaitan tamkar gunki tana kallon ikon Allah... Hajiya tasa k’arfinta gaba d’aya ta rik’o adaidaitan ganin yana neman zille mata shima, lokaci guda take furta “Kayi wa Allah bawan Allah... Ka ceceni ka fitar dani a unguwar nan kafin su kasheni... Wllhi ni ba mahaukaciya bace... Kaga can gidan mahaukatan na ciki....” Zulfa’u da hawaye ke kwaranyo mata a hankali ta furta “Hajiya..!!” Haule tai saurin d’ago idanu tana duban fasinjar data ambato sunanta, ba kowa bace illa Zulfa’u tsohuwar matar d’anta Hafiz wacce ta making rayuwarta impossible a baya ta kuma sanya d’anta ya mata sakin wulak’anci... Mai adaidaita da Atika har suna had’e baki wajen cewa “Kin santa ne...?” Zulfa’u na hawaye take jinjina kai... Kan suyi wani aune Hajiya Haule ta fad’i k’asa sumammiya.... Suka shiga karanto innalillahi Zulfa’u na fad’iwa Atika ta taimaka mata su sanya Hajiya cikin napep d’in... Haka suka kwasheta zuwa asibiti.... **** Hankali kwance yake cin abincinsa yaransa na kewaye dashi suna hira cikin jin dad’i da raha idan ka d’auke matarsa da takega yaran tamkar dodanniya... Muhibbah tai tsaye daga can bayan dining table d’in tana duban yanda maigidan nata da yaranta, duk wannan walwala dake tattaredasu tasan tana zuwa wajen shikenan ya k’are, sannan ta lura da yawan jin radio da mijinta keyi wanda a baya ba d’abi’arsa bane, kuma ga dukkan alamu yawan sauraron radio d’in da yakeyi shi ya dad’a bada gudummawa wajen canzasa don dai tasan ba wai zamanta a gidan bane kurum yake jefa Engr cikin wannan farin ciki da annashuwa, shin meye gaminsa da radio..? Shin wane shiri yake yawan sauraro da har ya canzasa haka...? Lallai kuwa dole tai yanda zatai ta nemo wad’annan amsoshi nata... Lokaci guda tasa kai ta isa dining area d’in... Tana k’arasowa yaran suka mik’e suna shirin barin wajen.... Cikeda masifa tace “Kai kai ku dawo nan... Ina zaku..? Oh Wato kunga dodo koh... Shine daga zuwata kun wani mik’e zaku shige koh.... Salon munafunci ace ina maku wani abin koh...” Irfaan babban cikin nasu mai shekaru goma yace “Karatu zanje nayi, monday zamu fara exams...” Bai jira cewarta ba yaron ya shige... Ita kaw ta biyun cewa tai itama karatu zataje Yayanta ya koya mata... K’aramar ta uku tace wajen ‘yan uwanta zata itama..... Muhibbah ta rakasu da mugun kallo har suka shige kafin ta maidoda dubantaga mijinta wanda yabi bayan yaran da kallo har suka haye sama... Sai faman kumburi take ta janyo kujera zata zauna.. Lokaci guda shima ya ije spoon d’in dake hannunsa ya d’auki tissues paper ya share bakinsa kana ya mik’e daga kujerar... Muhibbah ta saki baki tana dubansa... Cikin sauri ta mik’e tasha gabansa fuska a narke tace “Kaima tashi zakai ka barni....?” Bai sami zarafin bata amsa ba wayarsa ta d’auki ruri... Ya d’aga kiran yana mai barin wajen... Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya shige... Lokaci guda taji zuciyarta na mata wani irin zafi, taji babu abinda take bid’a tamkar ta shak’i garin hodar ibilis don shine kawai zai mantar da ita bak’in cikin da take ciki a nata tunanin... Allah ka mamu maganin musiban shan kayan maye data addabi al’umma, baga yara ba baga manya ba, baga matan aure ba baga ‘yammata ba... Allah ka kawo mana sauk’i ka kare al’umman musulmi ameen.... *** Farkawan da Hajiya zatai a gadon asibiti ta tsinci kanta, take abubuwan da suka faru suka shiga dawowa kwanyarta, ta tuna cewa tabbas Zulfah ta gani, Zulfa’u dai data tsana tak’i jininta itace ta taimaka mata, don ko shakka babu Zulfah ce ta kawota asibitin nan... Wani irin kuka mai cikeda nadama da kaicon rayuwa ya kufcewa Hajiya... Tinda take a rayuwarta bata tab’a jin nadamar abubuwa da kurakuran data tafka a rayuarta irinta yau ba... Nurse guda ce ta lek’o jin sautin kuka na tashi daga d’akinda Hajiya take... Tai saurin k’arasawa tana tambayarta ko lafiya ko akwai wani ciwo da takeji ta cikin jikinta kuma... Inaa Hajiya bata amsata ba sai ma k’aran sautin kukanta da tayi, nurse ta fice kiran likita da sauri.... Haka likitan ma ba sanar dashi Hajiya tai ba sai faman zabga uban kuka take, da k’yar ta iya saita kanta ta shiga tambayar likita ina yarinyar data kawota nan... Dr yace “A Gaskiya Inaga ‘yanmatan sun tafi, amma guda d’ayar tace tana dawowa don ina tsammani ta tafi sanarda iyalanki halinda kike ciki ne, bata bar nan wajen ba har saida muka tabbatar mata cewa babu wani rauni mai tsanani jikinki kuma nan bada jimawa ba zaki farfad’o...” Nan ma rintse idanu Hajiya tayi sabbin hawayen takaici da kaico suna zubo mata, duk irin cin mutunci da wulak’anci da cin zarafin da tayiwa Zulfa’u batai tsammanin ko gawarta Zulfah ta gani saman kwalta a tagayyare zata taimaka mata ba, sai gashi ta taimaketa daga hannun matar da take tunanin itace daidai ga d’anta... Hak’ik’a ba Zulfa’u kurum ta zalunta ba harda d’anta Hafiz dake kwance gadon asibiti rai kwaikwai mutu kwaikwai... Ga kuma d’iyarta Sahariyya dake kwance gida tana jinyar karaya... Hajiya Haule ta kuma rintse idanunta tana furta “Wata irin rayuwa na jefa ahalina ciki ni Haule...” Tana a haka ne Baba Alhaji yayi sallama.... Shi kansa saida ya razana da ganin yanda halittar Haule ya sauya Wai donma ya tadda anyi treating ciwukan nata an kuma d’an kintsa jikin nata ba kaman yanda su Zulfah suka kawota ba... Zama yai daga gefe yana k’are mata kallo kana yace “Haule ki sanar dani gaskiya, mai kuma kikayi wannan karon...?” Da gefen idanu ta dubesa kana tace “Ban gane mai kuma nayi ba... Shin ko tambayata jikina bakai ba kawai sai ka hau tambayata mai kuma nayi... Oho wato gani sarkin aikata sharri koh....?” Huci Baba Alhaji keyi kana yace “Sanin haline da yafi sanin kama....” K’uri Haule ta masa kana tace “Mai kake nufi....?” Matsowa kusanta ya kumayi kana ya matso da fuskarsa dab nata, lokaci guda yake furta “Ma’aruf nake nufi... Kinfi kowa sanin nasan komai...” Kauda kanta gefe tai kana ta kuma maidoda dubanta garesa tace “Haba ai biri yayi kama da mutum, na jima ina kokonton cewa kasan bak’in sirri na, amma ka kasan yin komai akai sabida kaima akwai b’oyeyyen sirrinka, bacin haka da tuni ka koreni daga gidanka da kuma rayuwar ‘ya’yanka.... Fad’a min mai ya faru shekarun can....?” Shiru Baba Alhaji yayi yana muzurai ba tareda ya furta komai ba... Lokaci guda Haule ta soma murmusawa kana tace “Aminiyar Sirri.....” Ya d’ago da sauri yana dubanta... Haule ta kuma jinjina kai tace “Tabbas d’aurin gindi ta samu daga gareka ta fantsamo cikin rayuwarmu da taimakonka... Idan ban b’ata a lissafi ba itace wakiliyarka a wannan bak’in aikin da muka aikata....” Katseta yayi cikin daka tsawa “Haule..!!!!” Ko gizau Hajiya Haule batai ba saima murmusawa data kumayi kana tace “Bakaso ka bak’anta kanka a idanun danginka shine kai amfani da aminiyar sirri domin ta d’auki alhakin laifinka.... Ka sani munyi tarayya ne a wannan bak’in laifi kuma dawowar Ma’aruf ba rayuwarmu kurum yake barazanar tarwatsawa ba harda naka rayuwar... Kayi tunani idan d’an uwanka yasan abinda ka aikata ma d’ansa... Shin mai zai d’aukeka....? Kayi tunani idan mahaifiyarka tasan abinda ka aikata ma d’an d’anuwanka shin a wani sahu zata ijiyeka....? Idan ‘ya’yanka suka san wannan bak’in sirri naka shin da wasu idanu zasu kuma dubanka....? Duk wannan abin dubawa ne Alhaji.... Ni dama na riga nasan yanzu Hafiz ya gama tsanata domin kaw a nasa tunanin niceda alhakin gurb’ata masa rayuwa.... Yanzu idan wannan batu ya bayyana ya fito fili shikenan Hafiz zai tsana duka iyayensa, don haka musan abinyi... ‘Ya’yanmu bazasu tab’a sanin gaskiya ba....” Baba Alhaji yayi shiru yana nazarin kalaman Haule.... Hannayensa hard’e ta baya kansa a k’asa, lokaci guda ya d’ago yana dubanta kana yace “Haule ki sani zuciyata ta cika da kishi da hassada a baya, karki mance yanda mahaifiyarmu keson Usman da d’ansa Ma’aruf, nayi tunanin idan na b’atar da d’ansa hakalinta zai dawo gareni da iyalaina amma koda yaushe mahaifiyarmu tafi fifita d’anuwana sama dani, a idanun danginmu gaba d’aya shi yakeda girman da ya kamata ace nikeda ita....” Shiru yayi na d’an lokaci kana ya kuma d’agowa ya dubi Haule yace “Ban tsammaci cewa Ma’aruf na raye ba harma zai dawo garemu.... Nayi tunanin kun gama dashi tun a wancan lokacin....” Haule ta murmusa had’ida gyara zama tace “Aminiyar Sirri ita ta yaudaremu gaba d’aya.... Duk munyi tunanin Ma’aruf ya halak’a tuntuni, bata halaka shi ba saima tsiratar dashi da tai... Yanzu abu guda zamuyi mu wanke kanmu mu zame kanmu daga cikin laifin....” Baba Alhaji ya dubeta yace kaman yaya “Kaman yaya...?” Haule ta nurmusa ta gyara zamanta da kyau kana ta soma fad’in “Lami da aminiyar sirri su zamu d’aurawa alhakin laifin... Ita dama Lami batada wayo batada ra’ayin kanta sai abinda na fad’i mata, ita kuma Aminiyar sirri Hajiya Hannatu mahaifiyar Ma’aruf tanada dalilai masu k’arfi da zata yarda tabbas ita ta rabata da d’anta tsawon shekarun nan.... Abu mafi sauk’i a nan ni yanzu zan nuna cewa nayi nadama ne bisa abubuwan da nayima Zulfa’u a baya, kaima zaka nuna kaji dad’in nadaman da nayi sannan ka gyara alak’arka da d’an uwanka, abu na gaba ka nemi Ma’aruf ya auri d’aya daga cikin ‘ya’anmu Sahariyya ko Naja’atu.... Kaga shikenan mun rufe bakin kowa ruf don babu yanda za’ai koda asirinmu tonuwa zaiyi Ma’aruf yace zai maka sirakansa a kotu....” Baba Alhaji yayi shiru yana nazarin Hajiya kafin ya d ‘ago yana dubanta yace “Anya Haule.....? Anya Usman zai kuma yarda ayi wannan had’in bayan ga yanda ta kasance da Zulfa’u da Hafiz....?” Haule ta d’an hareresa kana tace “Wannan karon ba irin auren Zulfa’u da Hafiz za’ai ba, wannan karon zamu nuna duka munason abun ne sannan shima Hafiz d’in zamu sa ya kuma neman auren Zulfa’u don a daidaita komai, kada ka mance idan auratayya ta shiga tsakanin ‘ya’yanmu shikenan mufa mun tsira... Kuma nunawa zamuyi hakan shi zai k’ara dank’on zumunci, ga Sahariyya ga Naja’atu ka bashi auren d’aya daga cikinsu....” Baba Alhaji ya kuma dubanta yace “Toh idan shi Ma’aruf d’in baiso fah...?” Hajiya Haule ta yatsina fuska tace “Auren biyayya zaiyi domin ga dukkan alamu yaron yanada nutsuwa, kuma na tabbata idan ka sami d’an uwanka da wannan batu bazai maka jayayya ba domin sanin kanka ne Usman na ganin girma da kimanka bacin duk abubuwan da kake masa....” Baba Alhaji ya jinjina kai had’ida murmusawa yace “Shiyasa nake sonki Haule kin iya kawo solution ma komai... Yanzu daga nan wajen d’anuwana zan wuce na fara neman gafaransa bisa abinda ya wakana tsakanin Hafiz da Zulfa’u kafin daga bisani na bijiro masa da batun auren d’ansa Ma’aruf da d’aya daga cikin ‘ya’yana domin k’ara dank’on zumunci....” Haule ta fashe da dariya tace “An gama, nima daga yanzu nayi hankali na zama saliha Haule...” Suka fashe da dariya a tare.... Naja’atu dake rakub’e jikin k’ofa a kunnenta komai ya faru, wasu irin hawayene ke kwararowa daga idanunta, ta kasa yarda da abinda taji iyayenta sun aikata..... Ta rintse idanunta wasu hawayen suka kuma kwaranyo mata, fasa shiga d’akin tai sai komawa da baya da tayi idanunta basu daina zuban hawaye ba..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *67* Sallaman Mamy harmada Aunty Lami ne ya katse hiran Baba Alhaji da Hajiya Haule.... Tuni Haule ta koma ta narke kan gado yayinda Baba Alhaji ya mik’e yana mai amsa sallamarsu had’ida masu iso..... Kan kace mai Haule ta shiga tattaro bakin zani tana mai sake kuka tamkar an kunna engine, Baba Alhaji da idanunsa ke kannare yana duban yanayin Mamyn cikin sauri ya soma fad’iwa Hajiya Haule... “Haba Haulatu kukan nan ya isa haka, tin shigowata kike abu guda, shi ciwo ba’a masa kuka addu’a ake..... Cikeda makirci ta soma fad’in “Inyi dole nayi kuka Alhaji... Kuka ya zamemin dole, ace duk abubuwan da nayima Zulfa’u itace ta taimaka min, bata barni bakin kwalta na halak’a ba koma wajen wancan tsinanniyar matar Hafizun....” Katseta yayi cikin zaro idanuwa kana yace “Kina nufin matar Hafiz ne ta maki wannan wulak’anci sannan Zulfa’u ce ta taimakeki....?” Haule bakin zani a hannu ana goge hawaye take jinjina kai, cikin muryar kuka take furta “Saima kaga d’iban Albarkan da wannan tantiriyar yarinyar tamin, ashe annoba Hafiz ya auro ya kawo cikin gidansa bamu sani ba... Ohni Haule nayi uwa nayi mad’auki saida ya saki baiwar Allah Zulfa’u.... Matar arziki ‘yar uwarsa ta jini....” Ta k’arashe tana mai kamo hannayen Mamy... Banda bugu babu abinda k’irjin Aunty Lami keyi... Mai Haule take nufi...? Shin abinda idanunta ke nuna mata gaskiya ne...? Haule na neman yafiyar Mamy gabanta....? Lokaci guda k’irjinta ya kuma bugawa tamkar an sauk’e mata k’aton guduma..... Tinaninta ya katse sanda taci gaba da sauraro muryar Hajiya Haule dake rik’eda hannayen Mamy tana hawaye... “Wllhi sharrin shaid’an ne, ni dama tin can bana k’in auren Hafiz da Zulfa’u... Hanne ki yafeni ki rok’ar min Zulfa’u ta yafeni...” Girgiza kai Mamy tai had’ida rik’o hannayen Hajiya Haule kana tace “Ni ban k’ullaceki ba Hajiya, sannan Zulfa’u ma bata k’ullaceki ba, ai duk d’an adam ajizine, gaba d’ayanmu muna kure... Mukayi laifuka ma Ubangijinmu ma ya yafe mana ballanta mu ‘yan adam da muke ajizai... Ban tab’a rik’eki ba haka d’iyata ma bata tab’a rik’e kowa cikinku ba ko a baya da ta fuskanci k’yama da tsangwama daga dangi... Don haka ki kwantar da hankalinki fatanmu duka shine ki sami lafiya... Allah ya yafemu gaba d’aya...” Haule na share hawaye take amsawa da ameen yayinda taci gaba da fad’in “Ina Zulfa’un take... Ina d’iyata, na rok’eta gafara da bakina tinda Allah ya bani damar ci gaba da rayuwa bayan na zaci rayuwata ta k’are hannun mahaukaciyar matar Hafiz...Ohni Haule zan jima ina jin zafin abinda nayima yaran nan... Suna son juna da k’arfi na rabasu na sanya Hafiz ya rubuta mata takardar saki....” Batakai aya ba Baba Alhaji ya tari zancen da fad’in “Kinga irin mugun halin naki koh Haulatu... Ni dama nasan haka kurum Hafiz bazai saki matarsa ba idan ba umartansa kikai ba.... Zanje na sami d’an uwana na kuma basa hak’uri na fad’i masa wannan duk sharrinki ne Haule...” Hajiya ta kuma kamo bakin zani tana furta “Alhaji Wllhi na tuba.... Bada son raina bane sharrin shaid’an ne...” Ita kaw Aunty Lami kallon kallo kurum sukema juna itada k’awarta Haule, tabbas Haule nada tarin bayanai da zatayi mata.... *** KADUNA Kishingid’e yake saman sofa dake a cikin d’akinsa, idanunsa duka biyu a lumshe, tin daga ranar da suka soma had’uwa yake kan tunowa, ya tuna duba na farko da ya mata yaji wani abu ya tsargar masa tin daga tsakar kansa har zuwa ‘yar yatsarsa dukda cewa tab’o ya rufe mata Fuska, a lokacin ya zaci razana ne ya haifar masa da wannan yanayin, sai yanzu yake tabbatar ma kansa abinda ake kira love at first sight shine yanayin da ya tsinci kansa... Gaba d’aya rayuwarsa bai tab’a jin irin hakan ga wata mace ba, ta ya zai cireta a zuciyarsa rana tsaka, just how...?! A hankali ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida furta “I love you... I love you Teddy Bear.... So much....” Kaman daga sama yaji ana murd’a handle d’in k’ofar... Ya d’an bud’e idanunsa da suke a lumshe ba tareda ya mik’e ba yana mamakin waye zai shigo masa d’aki babu neman izini.... To his greatest surprise ba kowa bace illa Yesmin, an cab’a uban kwalliya sai kwarkwasa ake... Ya ma rasa mai zaice tsaban tsananin takaicin yarinyar da yakeji.... Ganin bai tankata ba bai koreta ba ya sanyata samun k’warin gwiwan zama gefen k’afafunsa... Tamkar wanda aka zabura haka ya mik’e yana wani irin huci yake dubanta.... Maimakon ta mik’e saima sakin murmushi da tai had’ida gyara zaman gashin kantin dake kanta da tai... “My Kay.... Dama kan batun wedding preparations d’in nan ne, kaga I want something big... A very grand....” Bata kai aya ba ya katseta da fad’in “Uban wa ya baki izinin shigo min d’aki....?” Dubansa tai had’ida shagwab’e fuska kana tace “Haba my Kay gani fah nayi yanzu nida kai mun zama d’aya... Aurenmu fah duka duka watanni ya rage, and I’m here to plan our wedding together kafin na wuce Abuja, already Momy nata cewa na koma don a fara gyara maka ni....” Ta k’arashe tana juya idanu... Murmushin takaici yai kana ya d’ago ya dubeta daga sama har k’asa... Fuskarsa dab nata yake furta “Oh really! A gyaraki..? For who....? Me...?” Ya saki murmushi a hankali had’ida shafar hab’arsa kana yace “Well I’m not interested... Kicewa Aunty Kar tayi asaran kud’inta, cos to me ke ba mace bace, bana miki kallon mace balle har ajega gyaraki....Now get out of my room, and don’t you dare.... Kada ki kuskura ki sake shigo min d’aki haka balle har kiyi tunanin zama kusa dani... Tashi ki fice nace kafin na watsar maki da hak’wara....!!” Ya k’arashe cikin daka tsawa.... K’walla tab idanunta take dubansa.... “Leave I said...!!!” Cikin sauri ta mik’e ta fice a guje tana mai fashewa da kuka bata zarce ko ina ba sai wajen Ammi, Ammi na zaune saman rug tayi d’ai d’ai ga laces zube gabanta sai d’add’agawa take waya manne kunnenta da alama da mai kayan take wayar, yayinda Kubura ke faman gyare gadon Ammin.... A guje Yesmin ta shigo ta fad’a kan Ammi tana kuka harda shesshek’a.... Cikin sauri Ammi ta katse kiran tana mai sanarda matar da suke wayar zata sake kiranta.... “Lafiya.... Ke Yesmin ki tashi kimin bayani.....” Cikin kuka Yesmin ke fad’in “Ammi Khalid ne....” Cikin d’an daburcewa Ammi tace “Khalid..? Mai ya sami Khalid d’in...?” “Cewa yayi babu abinda zaiyi dani Ammi... Ammi I did everything I could for him to love me back amma yak’i cewa yayi baya min kallon mace banida abinda yake so jikin mace....” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.... Kubura tamkar ta daka tsalle haka taji, ta shiga k’arewa kanta kallo tana mai ayyanawa cikin ranta mace irinta Khalid ke buk’ata... Ammi kaw gajeren tsuka tai kana tace “Kedai bakida wayo sam Wllhi Yesmina, saikace bakisan halin Khalid ba, Yo da baison naki zai amince da aurenki ne...? Banda abinki shi namiji ai d’an lallami ne, Kar kiyi k’asa a gwiwa kici gaba da binsa a sannu sai kiga ki samu kansa, share hawayenki ki bar kuka yanzu zanje na samesa muyi maganar lefe, sadaki da sauran hidima dama Daddynsa yace duk zaiji dasu... meye abin kuka bayan ya kusa zama naki gaba d’aya... D’akin da ya koreki d’inma ya kusa zama naki, da sannu zaki koya masa yanda zai soki....Share hawayenki banson ganinsu kinji koh...” Yesmin ta jinjina kai cikeda jin dad’i tana mai furta “Thank you Ammi na you the best...” Kubura ta rakasu da harara daga Ammin har Yesmin, cikin ranta take furta Khalid d’ina bazai tab’a sonki ba bak’ar mayya.... *** “Magana fah nake maka Khalid amma kayi banza dani...? Ko nima karata zakai daga d’akin naka...Inyi...?” Ammi ta k’arashe tana watsa masa kallo... Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “Ammi nifa bani da choice ita Yesmin d’in ba tana nan ba, ta zab’i duk kayan da take so zanyi transferring kud’in to account d’in Siyama idan yaso sai suje da Yesmin d’in ta zab’i kayayyakin da duk take so to her own choice...” Ammi ta kad’a kai kana tace “Kenan bazaka d’auketa kuje tare ba, ai kai ya kamata ka tayata sayayya ka tayata zab’a tinda kaine mijin nata kuma kwalliyar ai ma kai za’ai bama Siyama ba...” Shafa sumar kansa ya d’anyi ga wani irin nauyi da kan nasa ya masa sakamakon kwana da yini da yai yana aikin abu guda tunanin Nabilah.... A hankali ya furta “Ammi Ammi please ki k’yaleni haka nan, don’t push me to do something that later I’ll regret....” Baki sake take dubansa kana tace “Inye... Eh lallai Khalid ni kake kallon tsaban ido kake cewa na daina pushing d’inka... Toh yayi, naji bazan bazaka je sayayyan lefe ba amma ka sani dole ka shirya ka maidata Abuja....” A zabure ya d’ago kai yana dubanta... Jinjina masa kai tai alamun jadaddawa kana tace “Sarai kaji abinda nace, idan Yesmin ta tashi tafiya gida kai zaka kaita, iyanin ka gaishe da iyayen nata had’ida godiyar baka d’iya da sukai tinda kai bakasan abinda ya kamata ba....” Tana ida fad’in haka bata jira cewarsa ba ta fice... Kame kansa yai had’ida zama cikin kujera gijif yana mai furta “God! This is getting too stressful.... what have I gotten myself into, anya banyi gangancin amincewa da auren Yesmin ba....?” Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai ambaton Allah.... *** Kano A tare Mamani da Sameer suka shigo d’akin, Hafiz na ganinsu ya saki murmushi... Harda d’an gyara zamansa yana masu sannu da zuwa... Sameer ne ya amsa gaisuwar nasa yana mai k’arasawa jikin drawer had’ida aje manyan ledojin dake hannunsa, lokaci guda ya isa jikin gadon yana ma Hafiz d’in sannu da jiki... Hafiz ya amsa da sakin fuska yana mai masa godiya da fad’in maiyasa zai d’aura ma kansa wahala haka yayo sayayya... Sameer na murmushi yace “Kai haba babu komai, ya jikin naka dai... Dr din bai shigo bane...?” Hafiz yace “Da sauk’i sosai, ya shigo round d’azu yace X-ray d’in sai an sakeyi...” Sameer ya jinjina kai yana mai furta “Karfa ka damu babu wani abu kaji koh...” Mamani ta katsesu da fad’in “Wato ka sami d’an uwanka ka mance da cewa nima gaisheka nazo ko...? Toh idan ban fasa jinyar nayi tafiyata ba, d’an uwan naka ya tsaya yayi jinyarka.....” Ta k’arashe tana k’arasowa d’ingis d’ingis Sameer na taimakata lokaci guda murmushi saman fuskarsa.... Hafiz d’inma murmushi yake kana yace “Haba ‘yar tsohuwata kinsan nayi kewarki da yawa...” Mamani ta k’araso tana masa sannu da jiki kana ta yab’e baki tace “Lallai wannan mata taka ta cika hatsabibiya Hafizu, koda shike hakkine hakkin Zulfa’u ne ke bibiyarku daga kai har uwar taka, ince itama yanzu nikeji an sallameta a asibiti sabida Sawwama da hatsabibanta sun kusan rabata da rayuwarta...” Hafiz ya d’an mik’e da sauri yana duban Mamani kana yace “Hajiya suka daka....?” Mamani tace “Bakaji da kyau ba kenan...?” Daidai sanda wayar Sameer ya d’auki ruri ya d’an fice daga d’akin... Hafiz ya shak’i iska da k’yar had’ida fuzarwa lokaci guda ya lumshe idanunsa, ya waresu yana duban Mamani tamkar wani maraya kana yace “Gaskiyarki ne Mamani hakkin Zulfa’u ne.... Shi yake bibiyarmu....” Mamani ta jinjina kai tace “Naji dad’i daka fahimci haka..... Na bud’e maka lemun ne....?” Tai maganar tana k’ok’arin d’auko lemon kwali da suka shigo dashi.... Bata iya bud’ewar ba sai mik’a masa da tai tana fad’in “Abubuwanku na zamani ungo nan ni ban iya bud’ewa....” Hafiz ya amsa yana murmushin kasancewar tsohuwar taredashi lokaci guda Mamani ta gyara masa pillow dake kishingid’e bisa, Hafiz ya d’an kurb’i drink d’in kana ya sace duban Mamani dake faman zuba yace “Mamani nace ina Zulfa’un take...? Batasan banida lafiya bane batazo ba...?” Shek’ek’e Mamani ke dubansa kana tace “Tazo tai maka wata uwar....? Ince ka sallameta a rayuwarka gaba d’aya....?” Kusan k’warewa yayi da drink d’in kana yace “Mamani sallamarta fah kikace....?” “Aw na maimaita maka ne....?” Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “Mamani nifa ina son matata kuma ai sakin da na mata ba cikin hayyacina nai ba.... Kuma ma ai duk laifin Hajiya ne....” Yai saurin kamo hannayen Mamani yana mai rau rau da idanu yake fad’in “Mamanitah please don Allah ki taimaka min kisa baki matata ta dawo, idan Zulfa’u bata dawo rayuwata ba mutuwa zanyi Mamani kinga likita yace zuciyata dab take da kamuwa da cuta.... Don Allah Mamani kisa baki Zulfa’u ta dawo gareni....” Shek’ek’e take dubansa kana tace “K’wak’walwarka ta sami matsala koh....? Toh ka jini da kyau koda ace Zulfa’u ta zab’i komawa gidanka bazan bari ba.... Bazan kuma zama na zuba idanu kaida Haule ku kuma kassara mata rayuwa ba, kaidai Allah baka lafiya kurum ka nemi wata ka aura...” Fuska babu walwala yace “Ni matata nake so, ita kad’ai.... Kawai idan kin daina sona ne bazaki taimaka min ba sai ki fad’a min.....” Mamani ta tab’e baki tace “Eh lallai ka kuwa d’auko Dala ba gamo..... Toh bazan taimaka ba Ubana, wani yace kai wasa da damarka sanda ka sameta, saima kaji ana sanarwar aurenta ka kuma yin danasani....” Ta k’arashe tana gyara mayafinta... Banda mugun kallo babu abinda Hafiz ke aika mata, shigowar Sameer da Dr ya katsesu.... *** Zaune yake a parlorn ganin bak’in nasa, shi kad’ai sai faman sak’e sak’e yake..... He couldn’t get over it, duk yanda yayi ya yakice tunanin cikin zuciyarsa abin yaci tura... Kaman wanda aka sinkaya ya janyo wayar salulansa dake bisa centre table.... Layin Akram ya kira ya sanar dashi yana son ganinsa... Akram ya amsa cikeda risinawa sannan ya sanar dashi yana zuwa right away... Jim kad’an Akram ya k’araso, Muhibbah dake tsaye saman balcony d’inta idanunta k’yam sashen ganin bak’in na mijinta domin kaw gaba d’aya a ‘yan kwanakin ta fahimci yana acting very strange, ta k’udiri niyyan gano abindake damun mijin nata, kuma tasan through Akram kawai zata iya sanin komai.... Cikin sauri ta sauk’o k’asa ta nufi section d’in ganin Akram ya shige.... Cikeda risinawa Akram ya gaida maigidan nasa, Engr ya masa nuni da kujera kana yace “Bismillah shigo ka zauna....” Akram ya k’araso ya zauna yana mai tunanin ko tafiya ce ta taso masu... Engr yace “Akram wani aiki nake so kamin a matsayinka na wanda na yarda dakai....” Akram ya d’an dubesa jin maganar nasa sounds serious dukda cewa shi d’in ba mai magana maras amfani bane amma yau d’in yaji wani irin jadaddawa cikin muryar Uban gidan nasa.... Engr yaci gaba da fad’in “Inaso kamin wani bincike....” Akram ya jinjina kai a hankali yana mai amsawa da alright... Engr Ma’aruf yaci gaba da fad’in “Akan matar nan that work with the radio station....” Gaban Akram yayi wani irin yankewa ya fad’i, zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri, sinkayo muryar uban gidan nasa yai sanda yaci gaba da fad’in “I mean everything about her, her family background and all....Nasan ka tab’a fad’a min batada aure a yanzu, I need to know more... I mean more about her, ka fahimta...” Akram ya jinjina kai a hankali kana yace cikin sark’ewar murya “Oh...Ok your excellency.... Right away.... Zan binciko maka komai in two days time in sha Allah....” Engr ya jinjina kansa kana yace “Shikenan kana iya tafiya....” Kasa mik’ewa Akram yayi da fari domin kaw duru duru ya soma gani, da k’yar ya iya mik’ewa... Engr ya dubesa da kyau kana yace “Are you alright...?” Akram ya jinjina kai cikin sauri kana yace “La....Lau nake your Excellency.... Zan tafi yanzu...” Engr ya jinjina kai kana yace “Good...” Kana yace “Ka kira Kabir ka fad’a masa I need him to reschedule all my activities na gobe.....” Akram ya jinjina kai yana mai furta “Ok... Ok Sir...” Lokaci guda ya fice gabansa bai daina tsinkewa ba... Yana fitowa Muhibbah tai saurin bin bayansa.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *68* “Akram....” Ta kirawo sunansa tana mai d’an waige waige.... Tsayawa cak yai yana dubanta cikeda mamaki don tinda yake tareda mijinta yau kusan shekaru goma bai tab’aji ta ambaci sunansa ba koda wasa sai yau, tsakaninsa da ita saidai ta watsa masa kallon k’ask’anci ko gaisheta yai a gadarance take amsasa yau sai gashi ta ambaci sunansa dole abin ya basa mamaki.... D’an gyara tsayuwarsa yai kana yace “Da ni kike magana Hajiya...?” Muhibbah ta k’araso kusansa tana mai jinjina kai kana tace “Can I have a word with you...?” Kuma daidaita tsayuwarsa yai kana yace “Yes... Sure....” Muhibbah ta kuma waigawa gefe da gefe kana tace “I want you to be completely honest with me....” Akram ya d’an jinjina kai yace “Ina saurarenki Hajiya...” Muhibbah ta jinjina kai tace “Inaso ka fad’a min what exactly my husband is up to... And don’t lie to me....” Mamaki maganar nata yaso basa, ya d’an gyara tsayuwarsa kana yace “Hajiya... Ban fahimci abinda kike nufi ba...” Wannan karon d’an nurmusawa tai kana tace “Nasan ka fahimci abinda nake nufi sarai, domin kuwa sanin kanka ne akwai abubuwa da dama da mijina ke b’oye min wanda kai baya b’oye maka... So tell me mai yake shiryawa....?” D’an kauda kai gefe Akram yai kana yace “A gaskiya kiyi hak’uri domin kuwa wannan ba hurumina bane, tsakaninki da mijinki ne wannan...” Banda uwar harara babu abinda take aika masa, bata zaci wannan wawan zata sami matsala dashi ba.... K’ak’aro murmushi tai kana tace “Kar ka damu da tsakanina da mijina ai ni ce na tambayeka, so just tell me...” Nan ma shiru Akram yai kana yace “A gaskiya kiyi hak’uri Hajiya.... Ni zan wuce.....” Yasa kai daga haka.. Shayeda mamaki Muhibbah take dubansa, a ranta take ayyana lallai wannan banzan ya cika d’an rainin hankali... Har ya soma tafiya ya sinkayo muryarta tana furta “Kai Akram kake ko wa... Umarni nake baka a matsayina na matar uban gidanka idan kuma baso kake ka rasa aikinka ba....” D’an waiwayowa kad’an yai kana yace “I’m sorry.... I’m also following orders here... Hajiya kiyi hak’uri.... It’s really confidential....” Murmushin yak’e ta saki kana ta matso kusansa sosai tana wani kannare idanu had’ida d’aura hannu a kunkumi kana tace “You seems very tough....Kaga a fuska kafi kama da salihai marassa son hayaniya da tashin hankali just like your Boss....” Ganin tana kuma k’ok’arin kawo fuskarta kusan nasa ya sanyashi saurin matsawa da baya cikeda tsoro had’ida firgici.... Maimakon ta bada tazara tsakaninsu saima murmusawa da tai tana mai kuma ci gaba da kannare masa idanu kana tace “Ya dai.... don’t you like women.... Oh c’on pretty boy Don’t tell me tsoro kake....?” Tai maganar cikin sigan rad’a... Izuwa lokacin k’afafun Akram sun soma rawa... Fitowar wata Cook daga can gefen shuke shuke ya ceci Akram daga tarkon Muhibbah tai saurin saita kanta kana tace “Kana iya tafiya Akram... Ina saurarenka idan komai ya zama ready....” Bai iya bata amsa ba sai sa kai da yai cikin sauri yana k’ok’arin ficewa daga gidan.... Muhibbah ta kalli sabuwar Cook d’in da ta kawo ba tareda sanin mijinta ba don shi cewa yai a rage ma’aikatan gidan musamman masu girki ita kaw ba iyawa tai ba hasalima ko ta iya bazatayi ba... Kiranta tai ta k’araso da sauri kana tace “Vanessa ba na hanaki yawo cikin gidan nan ba...? Ko so kike ki rasa aikin ki...?” Matar tai saurin girgiza kai tana mai bata hak’uri.... Harara Muhibbah ta dalla mata kana tace ta shige ta bata waje kafin ta canza zuciyarta ta sallameta.... Har saida Vanessa ta shige kafin Muhibbah taja wani dogon tsaki ta nufi sashen bak’i yanda mijin nata yake... *** Shiru Abbah yai yana sauraren d’an uwan nasa da batun da yazo masa.... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kana yace “Yayah wani hanzari ba gudu ba... Bawai nak’i batun a maida auren yaran nan bane, zanfiso a tambayi ita Zulfa’un aji daga bakinta idan ta amince ta yarda zata kuma auren Hafiz a karo na biyu... Sannan Zulfa’u yanzu bazawarace hakkin zab’an miji a hannunta yake a shari’ance, ni a halin yanzu ma Yaya gaskiya alk’awari nayi babu d’ahnah guda da zan kuma ma auren dole, idan suna so falillahil hamdu ai hannunka bazai rub’e ka yanke ka yar ba, idan kuma basa so toh a gaskiya Yaya ina ganin hak’uran shi yafi alkhairi... Batun shi Ma’aruf kuma zanji ta bakinsa, idan ya amince yana son d’aya daga cikin Sahariyyar ko Naja’atun ba matsala bane, kamar yadda kace k’ara dank’on zumunci ne kuma Ma’aruf zai yarda cewa lallai ‘yan uwansa na k’aunarsa dukda cewa yayi shekaru ba taredasu ba... Amma Yaya saifa idan yace yana so.....” Baba Alhaji ya maida hularsa baya don ba haka yaso ba, yaso da zaran yazowa Abbah da batun yayi na’am ba tareda wani shamak’i ba... D’an jinjina kai yai kaman mutunin kirki kana ya sauk’ar da ajiyar zuciya yace “A zatona Usman bazan baka umarni kace zakayi shawari ko zaka nemi zab’in ‘ya’ya ba... Yaran da mu muka haifesu basu suka haifemu ba... Haba Usman shin har Yaushe ka zamto haka...?” Abbah ya d’anyi shiru kad’an kana ya gyara zamansa had’ida soma fad’in “Wato Yaya duk bank’i abinda kazo dashi ba... Amma baka duba munyi hakan da farko baiyi kyau ba... Ko ka mance da fari ikonmu muka nuna kan Zulfa’u da Hafiz amma k’arshe mai ya haifar...? Ina ganin iyaye suna tapka babban kure wajen tilasta wa yaransu auren wad’anda basaso sannan musulnci cewa yayi budurwa a shawarceta kar a bata mijin da ita bata so, tanada hakki a bata zab’i itama, ita kuwa wacce ta tab’a aure ragamar zab’an mijinta a hannunta yake... Shi kuwa Ma’aruf baka ganin idan mun tilasta masa auren wacce baya so bazaisa ya kallemu da wata manufa ba tinda yaron nan ba hannunmu ya tashi ba, cinsa shansa karatunsa fad’i tashinsa duk bamu sani ba, hasalima haihuwarsa kawai mukayi... Shi baka tunanin bazaiga munyi karan tsayewa rayuwarsa ba...? Sannan iyayensa na can da suka rainesa watak’ila sunada mu’amala kyakkyawa da fahimtar juna tsakaninsu... Baka tunanin ya kamata muyi koyi dasu... Sannan Yaya Ma’aruf yanada iyali, bamuda tabbacin idan yanada ra’ayin zama da mace sama da guda.... Wad’annan dalilai kad’ai Yaya ya isa mu d’agawa yaran nan k’afafu mu barsu su zab’i wad’anda suke so kar muyi karan tsayewa rayuwarsu tinda bamu zamuje mu zauna masu ba.... Kai hak’uri Yaya ban...” Dakatar dashi Baba Alhaji yai ta hanyar d’aga masa hannu kana ya mik’e yana sab’a babbar riga lokaci guda yake fad’in “Dakata Usman banaso na kuma jin komai... Har nine zaka watsan k’asa a idanu kawai don nazo neman alfarma wajenka.... Na jima da sanin cewa baka d’aukeni da wata daraja ba..... Kaje jik’a ‘ya’yanka ka shanyesu.... Amma ka sani muna gab da raba zumunta ta har abada dani dakai....” Daga haka ficewa yayi fuuu kaman zai tashi sama... Mamy dake k’ok’arin shigowa rik’eda flask d’in ruwan zafi ta kawo masu shayi, tana gaishesa ko amsata bai sami zarafin yi ba ya fice kaman zai kifa da k’asa ba daina furta Aikin aikin wofi ba.... A hankali ta ije flask d’in tana duban mijin nata da alamun tambaya.... Abbah ya fuzar da iska a hankali had’ida lumshe idanunsa.... Mamy ta sami waje daga gefensa ta zauna.... “Abbah lafiya dai koh....?” Ta fad’i fuskarta d’aukeda damuwa.... “Inafah lafiya Hannatu.... Kina jin zancen da Yaya ya kuma zuwa min da ita.....?” Abbah yace yana mai duban Mamy..... Jinjina kai Mamy tai don tasan hakan zata faru bayan bayanan Baba Alhajin dataji a asibiti can wajen duba Hajiya Haule da sukaje.... Matsowa tai sosai kusan mijin nata had’ida dafa hannunsa dake aje saman cinyarsa kana tace “Ka kwantar da hankalinka mijina, kuma kada kasa damuwa a ranka... Munayima ‘ya’yanmu addu’a kuma nayi imani bazasu tab’e ba sannan da sannu zasu sami abokan zama na k’warai..... Wannan ba abin d’aga hankali bane kaji koh....” Tai maganar sihirtaccen murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarta... K’uri Abbah ya mata yanajin sanyi da wani irin kwanciyar hankali cikin zuciyarsa, a hankali yakai hannu ya shafi fuskarta kana yace “Allah ya maki albarka Hanne na.... Hak’ik’a kin tuna min shekarun aurenmu na fari... Kafin b’acewar Ma’aruf...” Mamy ta kuma murmusawa tana mai dubansa itama... Aunty Lami dake lab’e jikin window wacce tin shigowar Baba Alhaji tazo jikin window d’in ta mak’ale don taji komai, zuciyarta banda k’una da tafarfasa babu abinda yake sanda taga farin ciki da kalan soyayya da Abbah ke nunawa Mamy.... Ta kuma d’ingile k’afa tana aikin lek’ensu yanda ta hango Mamy ta tsiyayawa Abbah ruwan shayi yana sha yana kuma jifanta da kalamai masu dad’in sauraro ga duk wanda ake fad’iwa.... K’walla da takaici sukaima Aunty Lami diran mik’iya, har saida tai datasanin lek’ensu.... Ji take kaman ta isa ta shak’e Mamy ko zata sami sanyi cikin zuciyarta... Duk abubuwan da tai ganin ta dasawa Abbah tsanar Mamy ciki harda salwantar da Ma’aruf sam basuyi aiki ba tsawon wannan shekarun, soyayyar Hannatu sam bazai gushe zuciyar Abbah ba... Hawaye masu zafi suka shiga keto mata sanda ta hangi Abbah na baiwa Mamy shayi ta yanda bakinsa ya goga jikin kofin... Mamy na nok’ewa tana darawa yayinda shi kuma Abbah ke kuma janyota yana mai magana k’asa k’asa wanda bata iya ji.... Shikenan Hannatu Farin cikinta ya dawo,gata da yaranta gaba d’aya a tattareda ita, ga soyayyar miji dana yaranta kai harma da duk wani wanda ke tarayya da ita, itako batada tsuntsu batada tarko, hasalima idan asiri ya bayyana cewa tana d’aya daga cikin wanda sukaso ganin bayan Ma’aruf kashi da shara sai sunfita daraja... Take taji batak’i taga gawan Mamy ba kowama ya huta.... Wani irin jiri ne ya kusa kifawa da ita ganin Abbah tsofai tsofai na nunawa Mamy soyayya da kulawa a shekarunsu na tsufa wanda ita koda wasa ko a baya da takeda k’uruciya sam bai tab’a nuna mata ba.... Ji kake Dimmm ta fad’o daga saman dakalin dake jikin window d’in da take lek’ensu... Babu halin tai ihu don kada su jiyota, ga uban azaba da takeji don da k’yar idan bata cire k’ugunta ba.... Tanajin sanda Abbah ya taso yana lek’en ko wani abin ne ya fad’i... Haka ta matse bakinta da hannayenta da iyaka k’arfinta tana mai tamke idanu had’ida mak’alewa jikin garu don kar ya ganta... Har saida taji juyawan Abban kafin ta lallab’a da jada ciki ta nufi sashenta, Allah ya rufa mata asiri bata ci karo da kowa cikin yaran gidan a hanya ba.... *** Sahariyya da Hajiya su duka biyun tare suke jinya, Hajiy fuska a kumbure ga jiki duk tabo, ita kaw Sahariyya k’afafu a d’aure sabida tun bugun da Hafiz ya mata bata warke daga kariyan data samu a k’afa ba, shi kaw Hafiz yana can asibiti yana nasa jinyar.... Naja’atu ita ce a tsakani tana taimaka masu.... Hajiya taci gaba da fad’in “Wacce duk ta dace Ma’aruf ya zab’eta ta more miji cikinku, gashi gangariya gashi likita....” Sahariyya dake faman washe baki tai saurin taran zancen Hajiya da fad’in “Ai Hajiya ni zai zab’a ma don nafi dacewa dashi kuma ma ai nice babba ni ya kamata a bashi matsayin mata...” “K’ya dai tsaya ya zab’a da kanshi cikinku....” Hajiya tace sanda take kuma fifita fuskarta da mahuci.... Sahariyya ta b’ata fuska tace “Hajiya Wllhi gwarama kiyi fatan ya zab’eni don Wllhi duk wacce ya zab’a ba bari mata zanyi ba babu ruwana da cewa ita k’anwatace....” Tinda suka soma zancensu, Naja’atu dake zaune gefe da lantern tana karatu kasancewar babu wutar nepa batace dasu komai ba sai sannan ta rufe littafinta tace “Addah Sahariyya da ma kin kwantar da hankalinki don indai nice Wllhi bana fatan a lik’ani ga wani namijin da baisona, saikace wacce ake neman kai da....” Ta k’arashe tana mai kuma bud’e littafinta..... Sahariyya ta harzuk’ota da fad’in “Dilla rufewa mutane baki yarinya, wa zaiga gaye kaman Ya Ma’aruf yace baiso, dama mai zaiyi dake k’arama dake wacce baki jima da soma k’irgen dangi ba, ko a k’afa aka aura masa ke wllhi kwanceki zai ya gudu..... Ni ce nan na dace dashi....” Ta k’arashe tana juya idanu daga yanda take zaune.... Girgiza kai Naja’atu tai kana tace “Allah shi kyauta ya baki sa’a yasa kada Ya Ma’aruf yace baki masa ba... Dear sister...” Ta k’arashe tana mai kuma duba littafinta... Haba nan fah Sahariyya ta hau sababiga ‘yar uwarta har saida Hajiya tasa baki..... “Banaso kuna samu banbancin ra’ayi, gaba d’aya Naja’atu kin zama munafuka.... Kina nema ki juyawa ‘yan uwanki baya, Wai har tarewa kike ki tafi wajen mayyan can Raihanah.... Toh kici gaba kar ki fasa..... Shashashar banza wacce batasan yanda ke mata ciwo ba....” Da tsananin mamaki Raihanah ke duban Hajiya, har itace Hajiya ke kira munafuka bayan taji bak’in k’ullin da suka shirya itada Alhaji wanda badon tana tsoron rasa iyayenta ba da tuni ta fallasasu kowa ya sani.... A hankali ta girgiza kai cikin zuciyarta tana addu’an shiriya ma iyayen nata... Ana a haka Baba Alhaji ya shigo tagan magajan sai bambamin bala’i yake.... Hajiya ta tareshi da fad’in “Yaya yaya meke faruwa.... Ya na ganka haka nan.....” Cikin huci yake furta “Ai komai ma ya faru.... Wai har nine Usman zai dubi tsaban idona yace baiyi na’am da shawarina ba.... Wai shi bazai kuma tilasta yaransa cikin aurenda basa so ba... wata tsiya wata tsiya, ke kijimin yaron nan.....” Hajiya dake dubansa ido a kanne cewa tai, “Yo ai kaine baka iya ba, cewa zakayi ka bada tinda daga yaran nasa har naka kanada iko dasu, nifa ko ba’a sulhunta auren Zulfa’u da Hafiz ba to fah ya zama dole a had’a auren Sahariyya da Ma’aruf....” Hajiya bata rufe baki ba Sahariyya tace “Yauwa eh wllhi Hajiya....” Baba Alhaji ya watsa mata harara yayinda Najah ta mik’e ta bar tsakar gidan sabida tsaban takaici, ta gwammace tasha zafinta a d’aki data zauna sauraren kayan bak’in cikin ahalinta..... **** A can asibiti wajen Hafiz kuwa bacci yake yana mafarkin abin k’aunarsa Zulfa’u,fuskarsa ta cika da annuri cikin baccin nasa, farkawar da zaiyi sukayi idanu hud’u da abokinsa Magaji.... Magaji ya sakar masa murmushi had’ida masa sannu da jiki.... Hafiz ya amsa yana mai bud’e idanunsa gaba d’aya.... Lokaci guda kuma ya d’an lumshesu kana yace “Batazo ba...?” Magaji yace “Wa fah....?” “Zulfa’u...” Hafiz ya fad’i idanunsa na kallon sama.... Girgiza kai Magaji yai kana yace “Wai har yanzu bazaka sarara da tunanin Zulfa’u har ka sami lafiya ba....? Haba Hafiz kodai bakaji abinda likitoci sukace bane.....” Lumshe idanunsa yai a hankali kana yace “Magaji idan kaga na cire tunanin Zulfa’u toh ka shaida shakka babu na daina numfashi ne... Numfashina yana ficewane tareda tunaninta... Magaji ban tab’a zaton ina k’aunarta har haka ba... Zulfa’u itace rayuwata domin kaw tin daga lokacin data bar cikin rayuwata ban kuma samun natsuwa da kwanciyar hankali da na kasance cikinsu a baya ba... Kai shaida ne...” Magaji ya jinjina kai a hankali kana yace “Duk naji wannan amma ka d’ibar mata lokaci kaima ka sami sauk’i tukuna....” Wata duba Hafiz ya watsa masa kana yace “Inaga dai baka fahimci abinda nake nufi bane... Na k’agu su sallameni a wajen nan na tafi na maidoda matata... Nifah idan basu sallameni cikin satin nan ba Toh fah gaskiya zan sallami kaina....” Magaji ya d’an murmusa kana yace “Lallai ka sami sauk’i abokina tinda har kake fad’in haka...” Shigowan Likita ya katse masu zancen.... *** Koda Aunty Lami ta isa d’aki da k’yar da jin jiki, nan ta nemi man zafi ta shafe kwankwasonta yanda ta buga, ga k’afarta guda da tuni tayi fushi ta kumbura abu kaman wasa.... Bayan kwanaki biyu aka sallami Hafiz ya koma gida, a b’angaren Baba Alhaji da Abbah kuwa sam babu sararawa a batun da Baba Alhajin yazo dashi, gaba d’aya ya d’aure Abbah da jijiyoyin jikinsa, Allah ya sani bai kasance mai tirjiya da tsaurin idanu ga na gaba dashi ba, Abbah irin mutanen nan ne da idan na gaba dasu yace ga yanda za’ai toh fah bai iya tsallakewa sannan bai iya cewa a’a, har yanzu dai bai fayyace ya wacce ya baiwa Sameer cikin yaransa ba sannan shima Sameer d’in sam baida wannan labarin, a b’angaren Zulfa’u kuwa Aunty Bara’atu dole ta kuma d’auketa daga gidan ta maidata nata gidan ganin idan ta barta gaban Abbah da Mamy Baba Alhaji na kuma sake aura mata Hafiz wanda a yanzu kusan baida buri da ya wuce yaga ya kuma mallakar matarsa Zulfa’u.... Yau tana zaune tsakar gida tana duba wasu takardun, shirin da zata gudanar safiyar washe gari idan Allah yakai rai sai jin ana knocking tai.... Tasan kuma dai ba Aunty bace ta dawo don da itace da horn d’in motarta zataji.... Kira ta shiga rangad’awa Safinatu mai aikin Aunty B, Jim kad’an Safinatu ta iso tana fad’in “Gani Aunty Zulfa’u....” Zulfah tace “Ki duba gate kaman knocking ake...” Safinatu ta amsa kana ta shige duba gate.... Zulfah ta maida hankalinta kan aikin dake gabanta..... Tana cikin duba wani k’aramar takarda ne a hannunta tana rehearsals kawai sai hango k’afafun mutum tai yana shigowa.... Tai saurin d’agowa don tabbatarwa don tasan shi kad’aine mai irin wad’annan k’afafun....Tai saurin rintse idanunta cikeda takaici don ko jiya ma saida ya bita har wajen aikinta... Safinatu ta k’araso tana fad’in “Aunty Zulfa’u nace dashi Aunty Babba bata nan amma yace shi wajenki yazo....” Zulfah ta jinjina kai kana taceda Safinatu “Jeki kawai....” Safinatu ta shige abinta.... Take ta had’e rai tamkar ba Zulfa’un da ya sani ma’abociya sakin fuska da son mutane ba.... “Ya Hafiz mai kuma ya kawoka gidan nan fisabilillahi... Sanin kanka ne idan Aunty ta dawo ta taddaka gidan nan bazai maka kyau ba ko nace bazai mana kyau ba....” Ta k’arashe maganar tana mai warware gyalen abaya dake d’aure kanta ta yafe shi zuwa kafad’unta... Farar kujera dake gefe ya zauna bisa kana yace “Wannan itace irin tarban da zakiwa mijinki...?” Girgiza kai Zulfah tai kana tace “Kana mancewa nifa ba matarka bace... Don girman Allah ka daina bibiyata kayi zamarka da matarka Sawwama don gaskiya ni dai kam bazan koma gidanka ba....” Hafiz ya mata tsuri yana dubanta kaman ba Zulfa’un da ya sani ba kana yace “Kar ki sake kiran wancan ballagazar da sunan matata... Matata d’aya ce nan gidan duniya, kuma kece Zulfa’u.... Karmu wahalar da kanmu na sani munason juna.... Wllhi a shirye nake na sake aurenki Zulfa’u, I’m ever ready....” Kauda kanta gefe ta d’anyi kana tace “Kayi hak’uri Ya Hafiz ina maka fatan alkhairi a rayuwarka, Allah kuma ya datar dakai da mace ta k’warai amma badai ni Zulfa’u ba....” Zuciyar Hafiz ta soma sosuwa, har shine Zulfah ke turning d’insa down, matar da a fari dangin sadaka aka basa, amma Wai yau har shi ke kwantar da kai yana rok’on ta koma gidansa tana sha masa k’amshi bayan yasan deep down tana mutuwar sonsa itama.... Mik’ewa yayi had’ida zira hannaye cikin aljihun wando ya d’an soma takowa gabanta kad’an.... Ta d’ago idanu tana mamakin yanda yai mata tsaye aka ya wani lank’washe wuya harda karkace hula ga hannaye cikin aljihu.... Bud’e baki yai kana yace “Tell it to my face that you don’t love me, you don’t feel anything for me.....” Yayi maganar cikeda gadara... Itakam ma dariya abin yaso bata yanda har yanzu Ya Hafiz bai daina jin kansa ba kana ta ijiye takardan hannunta tace “Dama can akwai wata soyayya ce tsakaninmu....? Ko ka mance dagani har kai dole aka mana, kuma gudan jinin dake tsakaninmu Allah ya amshi abinsa.... Don haka kamar yanda nace maka kaje Allah ya had’aka da madadina saliha, wacce zata so ka tsakani da Allah....” Fuzar da iska yai kana yace “Baki amsa min tambayata ba....Ki fito fili ki fad’a min baki sona idan har da gaske babu d’and’anin soyayyata cikin zuciyarki.....” Shiru ya d’an biyo baya, bata furta komai ba sai k’urama waje guda idanu da tai..... D’ago kai tai da niyyar magana K’aran horn d’in motar Aunty B ya katseta... Gabanta yai mugun fad’uwa, idanunta sukai rau rau tana mai dubansa, lokaci guda ya mik’e tana fad’in “Ka gani koh... Dan Allah ka fice kafin ta shigo ta taddaka....” Ko gizau baiyi ba banda kallon k’urilla da yake mata..... “Ya Hafiz magana nake maka... Dan Allah ka fice before she sees you here....” Bai kuma cewa komai ba sai juyawa da yai ya soma tafiya, lokaci guda ya juyo yana dubanta itama d’in shi take duba Hafiz ya furta “I won’t give up on you....” Daga haka sa kai yai ya fice kaman mai shirin tashi sama... Zulfah ta lumshe idanunta a hankali tana ambaton Allah.... Shiko Hafiz a k’ofar da zai sadaka da cikin gidan suka had’uda Aunty B.... Ta bisa da kallon mai ya kawosa gidanta.... Gaisar da ita ya soma ta dakatar dashi da fad’in “Lafiya mai ya kawoka gidana.......?” Hafiz ya d’ago idanu yana dubanta... Ta kuma jinjina kai kana tace “Ina saurarenka, mai kazo min gida...?” “Matata nazo gani....” Ya bata amsa kai tsaye... ‘Yar bazawarar murmushi Aunty Bara’atu tai kana tace “Matarka...? Matarka fah kace....? Ikon Allah.... Ita Sawwamar ce tazo nan gidan...?” Hafiz ya had’iye wani abu mai zafi kana yace “Matata Zulfa’u....” Nan ma murmusawa ta kumayi kana tace “Ai bari kaji na fad’a maka Hafiz, Zulfa’u tai maka nisa, nisan da bazaka tab’a samu ba.... A iya sanina Zulfa’u ba matarka bace a halin yanzu domin kaw babu aurenka akanta... Saidai ka shiga jerin masu neman aurenta, amma abin takaicin shine bazaka sameta ba domin kaw wutsiyar rak’umi ya riga yayi nesa da k’asa... Saidai a k’ara gaba amma ba nan ba.... Kaje can Allah had’aka da rabonka.... And to make it clear to you, banso na dake ganin k’afafunka cikin gidana... Ina kuma fatan hakan ya zamto kashedi na k’arshe....” Tana ida fad’in haka ta danna lock wa motarta ta nufi cikin gida.... Hafiz ya bita da kallo tamkar wanda ruwa ya shanye, da k’yar ya iya d’aga k’afafunsa ya fice daga gidan.... Wani mugun kallo Aunty B ta watsawa Zulfah dake mata sannu da zuwa, kana ta shige d’aki ba tareda ta amsata ba... Zulfah ta dafe kanta a hankali tana ambaton Allah, ko shakka babu tasan Aunty ta had’uda Hafiz ne a hanyarsa na ficewa daga gidan.... *** Bayan sun fito daga taron jama’an ne suka d’an samu keb’ewa, abinka da mutumin da jama’a ke matuk’ar so, da k’yar Engr ya samu ya silale daga dandatson jama’an dake fatan samun kujerar muk’ami ta gwamna da yake nema.... Ya cire hularsa ya shiga fifita da ita, kana iya hango kwantacciyar sumarsa da suka jik’e da zufa, dukda AC dake hurawa dashike lokacine na tsananin zafin rana.....Akram ya k’araso rik’eda wata ‘yar takarda hannunsa kana ya mik’ama ubangidan nasa cikeda risinawa... Ya amsa yana mai murmusawa lokaci guda yana mai duba takardan... Baiso ya fahimci halinda yake ciki don haka k’ok’arin saita kansa yayi kana ya soma koro masa bayani.... “Rankashi dad’e duk wani bayanai gameda ita da zan iya samu suna k’unshe cikin takardan nan.... Sannan k’asa kad’an lambar wayartace.....” Engr ya jinjina kai a hankali, murmushin bata gushe saman fuskarsa ba... Lokaci guda ya soma furta “Na gode k’warai Akram....” Akram ya girgiza kai yana mai furta “Ka wuce haka a wajena your Excellency, bacin duk abubuwan daka min a rayuwa, ina fata watarana nima nayi abinda zan saka maka....” K’uri Engr ya masa yana mai son karantar yanayinsa.... D’an aje takardan yai saman table dake gabansa kana yace “Akram... Akwai matsala ne... Akwai abindake damunka ne wanda baka sanar dani ba...?” Akram ya d’an k’ak’aro murmushi had’ida girgiza kai yace “Babu... Babu komai your Excellency.... Zan iya tafiya... Zanje na duba idan jama’anmu kowa ya sami motar shiga....” Ya k’arashe maganar yana mai mik’ewa ya nufi k’ofa..... Engr ya kirawosa ya dawo da baya.... Kansa a k’asa,don ko duban idanunsa baisonyi bacin abinda Muhibbah ta bijiro masa dashi.... “Zauna....!” Engr yace yana mai dubansa.... Babu musu Akram ya zauna.... Gyara zama Engr yai kana yace “Banso kana d’aukan duk wasu abubuwan da nake maka a matsayin watarana zaka biyani, cos to me you’re my younger brother.... You’re not only an employee Akram... You’re family.....” Akram yai saurin d’agowa yana duban Ubangidan nasa... Engr ya jinjina masa kai a hankali kana yace “So babu ramuwa tsakaninmu kaji koh....” Akram ya jinjina kai a hankali... Engr yaci gaba da fad’in “Inaso ka wakilceni a wajenta, ma’ana inaso ka soma gabatar dani kafin na gabatar da kaina.... Amma banso ka sanar da ita ko ni wanene har sai nan da wani lokaci... For now zan dinga kiranta a waya amma kai zaka dinga zuwa a madadina.....” Banda bugu babu abinda k’irjin Akram keyi.... Mai yasa yana k’ok’arin manceta da yunk’urin cireta cikin zuciyarsa Engr zai masa haka... This will be hard for him... Gashi babu hali yace masa a’a... Shin kodai ya sanar dashi gaskiya ne cewa sunyi tarayya wajen son mace guda ne....? SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *69* Akram na ficewa Engr yaci gaba da juya takardan hannunsa, har lokacin murmushi ne kwance saman fuskarsa... Idanunsa ya sauk’a kan lambar wayar da aka kawo masa a matsayin nata, ya d’auki lokaci mai d’an tsawo yana duban lambar wayar tamkar wani mai niyyar haddace lambar.... Ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an had’ida fuzar da iska... Wayarsa dake aje gefensa yakai dubansa ga fuskar wayar, nan ma saida ya jima yana duban wayar tasa kafin yasa hannu ya d’auki wayar, ya shafi screen d’in wayar ya kawo haske... A hankali ya soma loda lambar wayar cikin tsanaki a wayar tasa.... Koda ya gama jera lambobin saida ya tsaya ya d’auki lokaci yana tunanin abinda yake shirin yi... This is not like him, bai tab’a zata rana irinta yau zata riskesa a rayuwarsa ba bayan duk zaman hak’uri da yayi da Muhibbah ko ince yake kanyi.... Anya kuwa ba damuwa yake shirin k’aro ma kansa ba kan wanda yake ciki da matarsa Muhibba...? What if itama ta kasance kaman Muhibbah ko ma worse than Muhibbah....? Yayi saurin shafar sumarsa a hankali kana yace toh amma according to Akram yarinyar ‘yar gidan tarbiyace kuma rashin dacen miji tai a fari wanda yayi sanadiyar mutuwar aurenta.... Ya d’an mik’e tsaye a hankali yana zagaye tangamemen parlorn mai d’aukeda kujeru kusan set uku.... Idanunsa suka sauk’a ga tangamemen k’ofan glass da aka k’awata parlorn da ita, yana hango mutane yanda suke faman kai komo wanda da dama fitowarsa suke jira..... Ya kuma tsurawa lambar idanu, samun yatsarsa yai yana mai dialing lambar da ya gama lodawa a wayarsa da sunan lambar yarinyar kenan.... Zulfah na faman baiwa Aunty B hak’uri gameda riskan Hafiz da tai a gidan wayarta ta d’auki ruri.... Ko takan wayar batabi ba ita dai damuwarta Auntynta ta bar fushi da ita... Aunty B ta d’an aika mata harara kana tace “Ki amsa kiran nan da ya ishemu ya cika mana kunnuwa...” Zulfah ta d’an turo baki gaba tace “Nidai bani amsawa Aunty sai kince kinyi hak’uri....” Dariya taso bata kana tace “Naji nayi... Maza tashi ki amsa kiranki....” Zulfa’u ta rungumeta da sauri cikeda farin ciki tana mai furta “Ko kefa Aunty na...” Har wayar ta tsinke kafin aka sake kira.... Aunty B tace “Ni d’agani kada ki k’arasani... Gwara dai na sanar dake don wllhi idan giyan soyayya ya d’ibeki Hafiz ya hure maki kunne kika kuma aurensa saidai ki nemi mai tsaya maki badai ni Bara’atu ba kuma ba ‘yar uwata ba.... Ki amsa kiran nan haka...” Zulfah na murmushi take fad’in “Ba dolenki ki tsaya min ba Auntyna... Kinga wata lamba ce bansan mai ita ba, banson d’agawa kardai Ya Hafiz ne....” Aunty B tace “Ki dai d’aga kiji koma waye, it might be something urgent....” Zulfa’u ta d’aga wayar da sallama tana mai k’arawa a kunnenta.... Wani abu yaji yana tsargar masa cikin zuciyarsa sanda muryar nata ya daki dodon kunnensa, tabbas itace Muryar da ya saba saurare ne a radio.... Daga can b’agaren kuwa Zulfa’u taci gaba da fad’in “Hello... Assalamu’alaikum... Wake magana...? Hello....” Shiru ba’a amsata ba.... Muryar matarsa Muhibba da ya sauraro tana shigowa ya katse masa hanzarinsa... D’if ya katse kiran ba tareda yace komai ba.... Muhibbah ta k’araso yayinda Suwaiba maid d’inta ke biyeda ita rik’eda basket d’in abinci nik’i nik’i.... Batai wata wata ba ta k’arasa ta rungume mijin nata tana fad’in “Excellency na nayi kewarka, mutanen nan basa barinka ka huta... Jibi duk yanda ka rame kai bak’i....”Ta dubi Suwaiba tace ta ije abincin a wajen ta fice, Suwaiba tai yanda tace.... Cireta yai daga jikinsa yana mai bintada kallon mamaki ganin abinda bai saba gani ba, Wai shine yau Muhibbah ke biyosa da abinci office.... A hankali ya k’arasa ya zauna saman kujera bai daina binta da duban mamaki ba... Muhibbah ta ije ‘yar mayafinta saman hannun kujeran kana ta isa ta janyo basket d’in ta bud’e zip d’in dake sama ta d’auki plate da serving spoon ta shiga k’ok’arin serving d’insa.... Lokaci guda take furta “I know you must be hungry Excellency na...... It’s your favorite, look... Nasan zakaci s....” Dakatar da ita yai da fad’in “Wait... I just don’t get it.... Wani kika kawo abinci....? Since when kika soma kawo min abinci wajen aiki....?” D’an murmusawa tai kana tace “Tun sanda na maka alk’awarin canzawa... Kaga fah nice da kaina na girka maka..... And I’m here to feed you myself....” Ta k’arashe tana mai ci gaba da zuba abincin cikin bowl..... Girgiza kai yai cikeda takaici kana yace “Drop the act Muhibbah... Kar muyi wannan wasan dake, na sani sarai kinyi hiring cook da take abinci ba ke kikeyi ba, har restaurant d’in da kikaje kikai hiring cook d’in inada labari, kawai na zuba maki ido ne naga gudun ruwanki.... I’m pretty sure canzawa overnight zai maki wahala so na d’ibar maki lokaci na tabbatar shin da gaske kinyi shirin canzawan ko kuwa dai zaki koma ruwa....” Ta d’an muskuta kana tace “Haba Excellency na Haka ake encouraging mutum, kamata yai kake ganin good side d’ina ba kullum kaita kusheni ba... Wllhi I’m changing for the better, I promise you...” D’an tab’e baki yai a hankali kana yace “Idan kin canza don kanki Muhibbah don ba mani kikai ba, ki sani ko mai bawa yake aikatawa shi zai accounting kayansa babu wanda zai masa... Kin fahimta....” A hankali ta jinjina kai kana tace “Haka ne Excellency na.... Dad’ina dakai akwai matsowa mutane Allah kusa shiyasa nake dad’a sonka kuma wannan kyakkyawar d’abi’a taka kad’ai ta isa ta saye zukatan mutane wajen zab’inka matsayin mutumin da zai shugabancesu ya kuma jagorancesu... Allah ya shige maka gaba a duk abinda kasa gabanka Excellency na... Amma kuma banda neman aure idan har yana cikin agenda d’inka....” Ta k’arashe tana dubanshi wanda shid’inma ita yake duba, hab’arsa bisa hannayesa guda biyu ya mata tsuri yana dubanta... A hankali ya furta “Ita addu’ar taki ta k’arshe bazaki min fatan Allah yamin zab’i ba...” Saurin mik’ewa tai ta k’araso ta zauna gefensa ta kamo hannunsa guda kana ta shige cikin jikinsa, idanunta a lumshe take furta “I can share you with my children but not with any woman.... Ni Muhibbah ni kad’aice Matar Ma’aruf, haka take a rubuce a zukatan iyayenmu da danginmu.....” Engr da tuni yayi nisa cikin wata duniyar ta tunani sam bai ida sairaren maganganun da Muhibbah keyi ba... Duk wannan sabon salon kalallama da take masa ba komai take sonji ba face abinda take zargin mijin nata na b’oye mata, gashi babu yanda batai da wancan mai d’an banzan taurin kan ba yaqi sanar da ita komai, batai zaton zata sami matsala dashi har haka ba, lallai akwai yarda da amana mai tsanani tsakanin Akram da mijinta, amma idan yasan wata baisan wata ba muddin bata sami biyan buk’ata daga wajen mijinta ba tasan ta yanda zata b’ullo masa.... *** KADUNA Tun sassafe ta tashi tanata faman kintsawa da shike yau take komawa Abuja, gashi da masoyinta Khalid zatai tafiyar gaba d’aya bata sama bata k’asa... Taso su tafi da motarsa amma shi yace sam saidai subi train.... Ba hakan taso ba tafiso shi yayi driving ya kaita har gida amma babu yanda ta iya don tasan tana provoking d’insa abu mai sauk’i ne yace bazai tafiyar ba kuma, don haka dole take lallab’ashi... Wata had’edd’iyar leshi d’inkin doguwar riga da yasha tsaga har kusan cinya ta saka, saiko d’an mayafi data rufe gashinta babu d’ankwali akan nata kana iya hango kitson gashin kanti dake kan nata..... Rigar ta matseta sosai tamkar tai numfashi ya b’arke, badon tsago mai tsawo da aka masa ba ma zai iya b’ekewa, sannan rabin k’irjinta a waje yake.....Ta shigo d’akin Ammi da k’yar tana mai doka kirawa Ammin.... Khalid dake zaune gefe saman sofa dake a cikin d’akin wulak’antaccen kallo ya bita dashi baki a tab’e.... Ta sakar masa murmushi tana mai fad’in “Ina kwana My Kay...” Bai amsata ba sai cewa da yayi “Yanzu ke a haka kinyi shigar mutunci kenan har kuke kiran wata Karuwa.... Tsakaninki da Allah dake da ita wayafi kama da sunan da kuka dangantata dashi....?” Yesmin tai kicin kicin da fuska... “Tambayarki nake....?” Ya kuma fad’i yana dubanta... Baki a ture ta shiga duba jikinta kana tace “Haba my Kay what’s wrong with my clothes... 21st century fah muke.....” Jinjina kai yai kana yace “I see... Kinsan Allah, kinji na rantse maki bazan had’a hanya dake da wad’annan ‘yan iskan kayan jikin naki ba.... Don ni ba d’an iska bane...” Mamaki ya cika Yesmin ganin dai Khalid a waye yake, maiyasa zai mata haka ko don bai sonta ne.... Duban kanta ta kumayi kana tace “Nidai gaskiya su nake son sakawa...” Ta d’an murmusa tace “Kodai kishina kake MyKay....” Ya watsa mata muguwar kallo kana yace “God forbid..! Ai idan kinji ana kishin mutum ana sonsa ne....Kiyi yawo tsirara ma idan kinso, ko a kwalata... Nidai what I know shine bazan had’a hanya dake da wannan shigar taki ba, Don nima sai ai tunanin d’an hanu ne... Idan kinga dama kin canza don kanki idan baki canza ba don kanki....” Ya k’arashe yana mai mik’ewa ya nufi sashen mahaifinsa don yimasa sallama.... K’atutun bak’in ciki ya tokari mak’oshin Yesmin, tai sakare a wajen har Ammi ta fito daga bayi ta taddata... Ammi ta tambayeta maike faruwa bata sanar da Ammin ba saidai kafin su tafi saida ta koma ta canza shiga wanda ya d’anfi wancan shigar tata... Daddy ya sakawa Khalid albarka da fatan sauk’a lafiya, ya k’arada “Sama’ila zai ajeku a train station d’in....” D’an jim Khalid yai kana yace “Dama Daddy motata tana wajen Baffah zai k’araso ya ajemu, akwai yanda zamu biya tareda Baffan ne....” Jinjina kai Daddy yai ya kuma saka masa albarka kana sukai sallama... Wajen Amminsa yaje ya mata sallama itama taita masa kashedin saura yaje ya nuna halinsa ma iyayen Yesmin ya nuna masu dole aka masa baison d’iyarsu.... Jin mahaifiyar tasa kurum yayi amma shi kansa bai tunanin abinda yake shirin yi daidai ne.... Ammi tai masu sallama gaba d’aya had’ida shi masu albarka kana Baffah yazo ya kwashesu.... Saida suka isa har tashan jirgin, ya tabbata Yesmin ta shiga ta zauna a kujerarta kana ya fito ya kirawo layin Baffah...... Baffah na tafe yaga kiran Khalid, ya d’aga yana tambayarsa ko mantuwa yayi.... Khalid yace “Kana ina...?” Baffah yace “Gani na shige Sterling bank kad’an....” Khalid yace “Dawo da baya...” “Ban gane in dawo da baya ba... Mai ka mance Khalid... Shinma Wai ba yaznu zaku tashi ba...” “Idan bazaka dawo bane ka fad’a min....” Girgiza kai kurum Baffah yai kana ya karya kan motar ya koma da baya... Yesmin tanaji ana announcing tashin jirgi abin ya dameta ganin Khalid bai dawoba bayan ga wajen zamansa a gefenta, ta mik’e tana lek’elek’en cikin jirgin... Gabanta ya shiga bugun tara tara ganin bata hango ko k’yallin Khalid ba.... Gashi babu halin ta fice don tuni jirgi ta soma tafiya... Tamkar ta tsuguna wajen ta runtuma ihu haka taji sabida tsaban bak’in ciki.. Batasan sanda hawaye suka soma sauk’a mata ba... Lallai yau ta yarda Khalid ya cika babban d’an rainin hankali da wayo... Haka tanaji tana gani jirgi ya tashi da ita babu Khalid babu dalilinsa.... *** Baffah na isowa ya masa k’uri shaye da mamaki kana yace “Ina Yesmin d’in....?” Dafa marfin motar yai kad’an kana yace “Ka gane ka hau taxi ka koma gida please....” Mamaki ya cika Baffah... Fitowa yai daga cikin motar kana yace “Ban gane ba... Toh Wai ba tare zaku tafi ba....” Khalid bai amsa shi ba sai shigewa cikin motar da yayi mazaunin driver ya aje hularsa gefe d’aya Seat d’in... Ya d’ago ya dubi abokinsa Baffah kana yace “Allah sadamu da Alkhairi, sai munyi waya....” Khalid na k’ok’arin rufe motar Magaji yai saurin rik’e marfin motar kana yace “Khalid Wai meye haka... What exactly do you mean... Ina Yesmin...? Ina ka nufa...?” Dubansa yai kai tsaye kana yace “Kano.... Shikenan kaji... Zaka iya barina na shige....” Girgiza kai kurum Baffah yai kana yace “You’re unbelievable Khalid... Shine ka bar Yesmin d’in ta tafi ita kad’ai... Haba Khalid, I thought zakabi umarnin iyayenka da gaske....” Kallo ya watsa masa kana yace “Da nace zan aureta ai biyayya na masu, ko ita k’aramar yarinyace da sai na d’auketa na maidata gida...? Tinda ba cewa nayi na fasa auren ba kaga ban bijirewa umarnin nasu ba, ai.... Kana iya barina na tafi....? Banso rana yamin... Idan kuma zakajene bisimillah...” Girgiza kai kurum Baffah yai kana yace “A sauk’a lafiya... Allah ya tsare hanya...” Khalid ya amsada Ameen had’ida janyo marfin motarsa ya rufe... Baffah na kallon yanda ya kwashi motar da k’arfin gaske ya bar wajen.... Addu’a kurum Baffah ya rakasa dashi kafin ya soma saka hannu yana taran taxi.... *** Abbah yai shiru yana sauraren d’an uwan nasa da ya gama harzuk’a sabida rashin samun goyon baya da yayi daga Abban.... Baba Alhaji ya mik’e yana mai ci gaba da fad’in “Shikenan Usman.. Kaje ka rik’e ‘ya’yanka... Ai iyakacina kake son nuna min... Yayi... nace yayi daidai Usman.....” Dai dai lokacinda Sameer yai sallama, sam baiji dad’in yanayin da ya tadda mahaifin nasa da kuma yayan mahaifin nasa ba... Ko gaisuwar Sameer Baba Alhaji bai sami zarafin amsawa ba sai duba da bisa dashi kana yai ficewarsa tamkar zai tashi sama... Sameer ya k’arasa kusan mahaifinsa had’ida duk’awa ya gaidashi... A hankali ya amsa masa yana mai k’ok’arin k’ak’aro murmushi had’ida d’aurawa bisa fuskarsa.... Sameer ya d’an dubi yanayin mahaifin nasa kana yace “Abbah lafiya....? Meke faruwa...?” Abbah ya murmusa a hankali kana yace “Babu komai Ma’aruf... An shigo... Za’a wuce aiki kenan...?” D’an jim Sameer yai yana mai karantar mahaifin nasa kana ya d’an muskuta yace “Abbah ka tabbata babu komai... Abbah naga yanayinda Baba Alhaji ya fice... And I heard him shouting at you....” Abbah ya d’an murmusa cikeda jin dad’in yau gashi da d’ansa wanda damuwarsa ya damesa.... Gyara zamansa ya d’anyi had’ida gyaran murya kana yace “Ma’aruf, banaso ka d’aga hankalinka... Wannan tsakaninane da d’an uwana kaji koh... So tari hakan takan faru tsakanin ‘yan uwa daga k’arshe zasu kasance a turba guda sabida su ‘yan uwan junane... Kaji koh....” Ba don ya gamsu ba ya d’an jinjina kai yace “Amma Abbah I worried so much about your health... Shiga damuwa ko tashin hankali ba naka bane sam, shiyasa nake so naji idan zan iya taimakawa....” Abbah yai shiru tamkar mai nazari na wasu ‘yan dak’ik’ai kana ya ambato sunan Sameer... “Ma’aruf...!” “Na’am Abbah...” Sameer ya amsa had’ida d’agowa ya dubi mahaifin nasa... Abbah yaci gaba da fad’in “Wato Ma’aruf Baffanka ya bijiromin da wani al’amari ne mai wuyan sha’ani....” Sameer ya jinjina kai a hankali cikeda son jin abinda Abban nasa ke sanar dashi... Yayinda Abbah yaci gaba da fad’in “Ya bijiro min da batun yanaso ya baka d’aya cikin yaransa ka aura...” Jin maganar yai tamkar sauk’an aradu, yai saurin d’agowa yana duban mahaifinsa had’ida had’iyar miyau d’in da ya daskare masa lokaci guda a mak’oshi.... Shi kuma aure... Aure yanzu... Aure dai.... Waima su waye ma yaran Baba Alhajin... Shi yama mance bazai iya cewa gasu nan ba, toh Wai ma yaushe ya gama da rigimar Siyama balle har yajega wani k’arin aure... Hasalima shi baida tsarin aje mace sama da guda a gidanshi, yasan Siyama tanada wuyar sha’ani amma yayi imani soyayyar da sukedashi ma junansu is very strong wanda baya haufi duk yanda sukakaiga samun sab’ani daga k’arshe zasu kasance tare sabida wannan k’auna mai tsanani dake tsakaninsu.... Muryar Abbah ya dawo dashi daga duniyar tunaninda ya tafi... “Kar ka damu Ma’aruf, alwashi na d’auka bazan kuma tilastawa d’aya daga cikin ‘ya’yana auren wad’anda basa so ba bayan abinda ya faruga ‘yar uwarka Zulfa’u.... Na riga na sanar dashi bazan iya tilasta maka ba shine dalilin da yasa kaji yanata fad’a har yake ikirarin cewa zumuncinmu na gabda tsinkewa muddin nak’i amince masa kan maganar had’a yaranmu....” Zufa ya shiga tsartsafowa Sameer, wannan shine tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, tabbas ko kad’an bazaiso ya zamto sanadiyar yankewar zumuncin iyayensu ba....Toh amma shin Wai ya zai ne...? Bai kaiga lalumo amsa ba wayarsa ta d’auki ruri daga asibiti ake kiransa ana nemansa urgently... Bai samu zarafin k’arasa maganar da sukeda Abbah ba ya fice babu shiri, Abban ya masa fatan sauk’a lafiya.... Har ya isa asibiti har ya shige surgery d’in da aka kirawosa akai maganganun Abbah basu daina masa Yawo a kwanyarsa da kuma dodon kunnuwarsa ba.... *** Kasancewar basuda aji k’arfe goma shabiyu har sai k’arfe biyun rana yasa suka nufi masallaci kafin ai sallah suyi su kuma nemi abinda zasuci before su koma class... Suna tafe suna labarin ajin da suka fito dashike gaba d’aya suke tafiyar hardasu Safwan da Al’amin coursemates d’insu.... Nan suka ratse wani cafe don sayan handouts na ajin da zasu shige later sabida malamin ba mutunci bane dashi yanzu sai ya kori mutum muddin bakada material d’insa... Su Safwan suna gefe suna aikin musu kan wani equation data kasa balancing masu yayinda Nabilah da Yusrah suka shige shagon.... Nabilah cewa tai “Wllhi jiri nikeji bazan iya tsayuwan shop d’in nan ba don nasan basu dashi a k’asa zasuce sai sunyi photocopy, kya karb’a ki taho mana dashi... Ki sameni a masallacin...” Yusrah ta jinjina kai tana mai furta “Love fever ke damunki yarinya amma kink’i yarda....” Harara ta watsa mata kana tace “Kyaji dashi, wannan ke ta shafa...” Bata jira cewar Yusrah ba ta fice ta k’yaleta shagon yanda taketa faman kyakyata dariya... A waje ta taddasu Safwan suka tambayeta Yusrah fah, tace dasu zata sameta masallaci.. Nan suma suka had’a hanya donsu Hostel suka nufa tinda ba aji har sai k’arfe biyu... Tin daga can ya hangeta tana tafe tareda wasu samaruka har biyu, sanye take cikin d’inkin atampa riga doguwa had’ida madaidaicin hijab d’inta da ya tsaya a daidai gwiwarta mai kalan ruwan k’asa.... Wani sanyi ne yaji ya ziyarci zuciyarsa bayan da ya shige babban ajin da suka saba gudanar da lectures ciki baiga kowa ba sai gashi ya taddata a hanya bata bar haraban wajen gaba d’aya ba, yasan tabbas ba k’aramin sa’a ya taka ba, saidai hangota da wad’annan samari da yayi ba k’aramin sosa masa rai yayi ba musamman da yaga yanda fuskokinsu ke cikeda annuri alamun sunajin dadin firan da suke.... Wayarsa ya d’aga ya shiga dialing layinta.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *70* K’aran horn kawai sukaji a bayansu, dab dasu kaman mai motar na shirin bin kansu.... Ko gizau batai ba saima ci gaba da tafiya da tayi, su Safwan kaw Cikin sauri suka waiga baya suna mamakin wannan mai motar da duk fad’in hanyar dake makarntar ya zab’i yabi bayansu.... Al’amin yaja muguwar tsaki, a fusace ya kauce yana mai duban motar yake fad’in “Dalla Malam lafiya...? Ko ta kanmu zakabine...?” Yai maganar yana duban motar don ba ganin mai motar yake ba dashike glass d’in motar mai duhu ne.... Nabilah da ta gama cika tazo wuya cewa tai, “Ku k’yalesa yabi takanmu kawai ya wuce....” Safwan ya murmusa kana yace “za’a ba za’ai haka ba, mu matsa mu basa wajen ya shige...” Nabilah tace “Aiko wllhi bazan matsa ba saidai yabi takaina tinda dai hanyar bata gidansu bane...” Kaman wanda akace ya k’ara danna horn d’in... Zuciyarta sai faman tafarfasa yake, ita kad’ai sai hura hanci take tana huci tana tunanin kalan rashin mutuncin da zataiwa mai motar nan muddin ta juyo.... Cikeda tsiwa da masifa ta waigo tana mai furta “Mai zai hana kabi takaina ka wuce idan dai har nan ne kawai hanya a fad’in makarantar....” Cak tai burki ma kalaman nata sakamakon bud’e marfin motar da yai ya sako k’afafunsa ya fito, yana sanye da lallausar yadi mai ruwan toka d’inkin half jampa ta masa kyau sosai, kansa babu hula sai b’akin sumarsa da yaiwa kan nasa k’awanya.... Tai k’ok’arin d’auke kanta daga barin duban nasa kana ta d’an dubi Al’amin tace “Kuje kawai Al’amin sai mun had’u anjima a class...” Safwan yace “Are you sure...?” Jinjina masa kai tai ba tareda tace komai ba.... Ganin abokan tafiyar nata sunsa kai yasa Khalid soma takowa hannayensa mak’ale cikin aljihun wandonsa.... Fuska a tamke take duban wani gefen sanda ya k’araso.... Kallo ya bita dashi kafin ya d’anyi gyaran murya had’ida maida hannayensa duka biyu baya ya d’an rank’wafo yace “Kin kyautama kanki da kika sallami samarukan naki....” Maganan da yayi ya sanyata d’ago idanu tanai masa mugun kallo, ganin shid’inma ita yake duba babu ko k’yafta idanu ya sanyata kuma kauda kai gefe kana tace “What brought you here...?” “Isn’t it obvious... Bazan jure rashinki ba teddy bear.... Tell me who are those guys...?” Ya k’arashe yana bin bayansu Safwan da kallo.... Girgiza kai tai a hankali kana tace “Wannan ba matsalarka bace.....” Khalid ya tsareta da idanu kana yace “Kar na sake ganinki taredasu.....” Galala ta d’an dubesa had’ida yin ‘yar bazaurar murmushi kana tace “Did you hear yourself now....? And since when ka fara gindaya min doka...?” Tai maganar tana hura hanci hannunta guda rik’eda kunkumi... Khalid ya saki murmushi don abinda yakeso kenan yaga wannan tsiwar tata da yai kewa kwana biyu... A hankali ya soma takowa dab kusanta, Nabilah taci gaba da huci tana aika masa mugun kallo dukda tsananin bugu da k’irjinta keyi...Saitin kunneta yake rad’a mata “You know teddy dear... I’ve missed this... So much... Amma nafi kewarki, nasan kema kinyi kewata... Lets end this now don nasan we both can’t do without each other.... I know you love me teddy bear koda ace baki fad’a ba but I know you does... So much cos I see it into your eyes....” Ya k’arashe cikin tsananin kashe murya tamkar mai rad’a... K’irjin Nabilah yaci gaba da bugu da sauri da sauri... Cikeda huci ta d’ago kanta da hannunta tana mai furta “Kaga Khalid listen....” Aya tai ma kalaman nata sakamon k’aran da ya saki had’ida rik’e hancinsa alamun ta bige masa hanci.... Ta waigo a zabure tana dubansa cikeda kulawa yanda ya dafe hancinsa yana furta “Auuchh what’s with you...” Cikeda kulawa take furta “Sorry sorry yi hak’uri please... Does it hurt...?” Ganin yanda duk ta daburce yasa Khalid jin wani sanyi cikin zuciyarsa a hankali ya saki hancin nasa da har ya d’an canza launi zuwa ja.... K’uri ya mata da kyawawan idanunsa ba tareda ya iya d’aukesu ba, sosai yanayin storo yake mata kyau dashike bata cika shiga yanayin ba, idanunta sosai suke masa kyau ita ta shiga yanayin... Ganin ya mata k’uri ya sanyata k’ok’arin saita kanta kana tace cikin k’asa k’asa da murya “I guess you’re alright... Please ka tafi, class zan koma anjima kad’an...” Khalid ya murmusa da gefen bakinsa a hankali kana yace “Are you sure you want me to leave....” Ta juyo a hankali tana dubansa kana ta jinjina kai tace “Yes ka koma wajen matarka da zaka aura.....” Murmushi Khalid ya kumayi had’ida fitar da iska a hankali kana yace “Bazan iya sadaukar da soyayyarki ba teddy bear... You’re the one I love, no one else... I tried amma na fahimci bazan iya ba... I love only you... And I’m ready to fight for you, for our love, for us to be together...” Wane irin sanyi jikin Nabilah yai tama rasa mai zatace sai k’walla dake k’ok’arin ciko idanunta yayinda Yusrah ke tsaye gefe murmushi kwance saman fuskarta sabida Khalid da soyayyarsa ga k’awarta sun bala’in burgeta..... Kaman wacce akace ta waiga nan ta hangi Yusrah rungumeda handouts d’insu... Tai saurin k’arasawa kaman zata kifa tana k’ok’arin janyo hannun Yusrah take fad’in “Muje kinji... Zo mu tafi.....” Dogewa Yusrah take tana fad’in “Mu tafi ina bayan yanzun nan class rep yace malamin bazai shigo ba yace saturday zai fixing class, kowa ya watse ma....” Khalid ya tari zancen nata da fad’in “Well, in that case inaga muma sai mu wuce gida ai koh.....” Nabilah ta kasa cewa komai saiko Yusrah da murmushi ya kasa gushewa saman fuskarta ta bud’e baki tana gaida Khalid... Ya amsa mata da sakin fuska fiyeda lokacinda suka soma had’uwa.... Khalid ya k’arashe amsa gaisuwar nata yana mai danna security lock d’in motar sa nan ya bud’e kana yace “Muje koh....” Bai jira amsarta ba ya nufi motar.... Nabilah ta rakasada harara yayinda Yusrah ta shiga janyota tana fad’i k’asa k’asa “Wllhi baki isa kice bazamu shiga ba....” Hararan Yusran ma tai badon taso ba ta nufi motar Khalid d’in sanin cewa ko tace bazata shiga ba Khalid sai yasan yanda yai ya sanyata shiga.... *** Hajiya Magajiya ta narkawa ‘yarta Sawwama muguwar kallo kana tace “Ashe ke babbar mahaukaciyace ban sani ba, bayan duk uwar rashin mutuncin da kikayiwa Hafiz da ‘yan uwansa kina tunanin zai amsheki a karo na biyu ne... Ai shikenan ya kubce maki domin ita dama guda d’ayace tak...” Sawwama ta kuma tura baki gaba kana tace “Magajiya wllhi bazan bari Hafiz ya auri wata ba muddin ina numfashi baida wata mata gidan duniyar nan bayan ni.... Ni idanma bazaki kuma tsayamin ba zan wanke k’afata na koma wajen Malamin can da ya mana aikin farko ya shawo min hankali mijina ya karkata zuwa gareni....” Shewa Magajiya ta saki had’ida rangad’a gud’a da tafe hannaye kana tace “Yanzu ne na tabbata kin cika d’iyata, dama gwadaki nake don mu ba’a jadamu a zauna lafiya bamu kuma sadaukar da fad’a cikin sauri, don haka yanzu na tabbata kin dawo cikin hankalinki.... Tashi mu tafi... Babu boka babu Malam da bala’i wannan karon sai Hafiz ya dawo gareki....”Ta k’arashe tana janyo mayafinta dake shanye saman igiyan shanya.... Fuuuu suka fice itada d’iyarta Sawwama... Hajiya na baje tsakar gida tana fifita ma ciwonta wajenda bai ida warkewa ba ta sauraro dishesshiyar muryar Magajiya wanda sigari ya gama k’onasa tana banka sallama... Gaban Hajiya Haule ya yanke ya fad’i, cikin zuciyarta take tambayar kanta uwar mai Magajiya tazo yi mata gida...? Bata ida tunanin ba ta hangosu suna tafe uwar na gaba d’iyar na bayanta.... Dafe hannaye a k’irji Magajiya tai ta shiga jero sallalami tana fad’in “Ni haihuwar maguzawa haka jikin naki yayi Haule.... Sannu sannu kinji da jiki.... Ke Sawwama baki sanar dani haka jikin sirkar taki yayi ba... Yo ina nasan jikin naki yayi tsanani haka....” Sahariyya dake zaune parlor ne ta d’ago labule don ba iya fitowa zatai ba har yanzu kariyarta bata ida warkewa ba, daga yanda take zaune ta bud’e murya tana fad’in “Ke tsohuwar ‘yar bariki koda wasa, karkizo nan ki mana salo, ince d’iyar taki itace sanadiyar ciwon Hajiya.... Yanzu kun d’ibo k’afafu babu kunya ta tasoki gaba zaku kawo wa mutane fitsara....” “Keee kul ahir d’inki....!” Sawwama ta dakatar da ita kafin taci gaba da fad’in “Koda wasa ba’a zagi mahaifiyata a kwana lafiya... Tambayi tsohuwarki kiji dalilinda ya kwantar da ita jinya.... Yanzun nan zan karye miki d’aya k’afar taki ki zama gurguwa da kyau.....” Zuciyar Sahariyya banda tafarfasa bata komai, batasan sanda k’walla masu zogi suka ciko idanunta ba jin kalan maganganun da Sawwama ke yab’a mata gashi babu halin ta tashi ta rama... Ta rarumo takalmin gefenta ta jifa masu tana ci gaba da zaginsu.... Sawwama tayo kanta gadan gadan Magajiya ta rik’eta tana fad’in “K’yaleta ‘yar albarka, da daidainka kake fad’a wa zai fad’a da nakasasshe, ai tsakaninmu da mai nakasa saidai sadaka... Kinga Hajiya Haule gaisuwa mukazo da ban hak’uri had’ida ban gajiya a matsayinki na uwar mijin d’iyata.....” Batakai aya ba Haule dake tururi ta katseta da fad’in “Wllhi ko a hanya Hafiz ya kuma nuna yasan d’iyarki baki zan masa.... Ku fice man a gida kafin rayukanku su b’aci.....” Ta k’arashe tana huci kaman wata zakanya.... Shewa Magajiya tai had’ida juyi tsakar gidan kana tace “Ai baki Sani ba Haule, Hafiz da Sawwama ai auren zobe sukai idan kinga sun rabu toh ki rubuta d’anki ne ya mutu....” Haule da k’irjintake tsananin suya cikin kufula ta soma rarrafowa zatayo kan Magajiya daidai nan Baba Alhaji yai sallama.... Tuni Magajiya ta saita kanta ta shiga janyo mayafi tana sinne kai ciki, murmushi kwance saman fuskarta ta duk’a tana k’ok’arin gaidashi, tai idanuma d’iyarta ma ta duk’a gaida Baba Alhaji itama.... Nan kuwa ya saki fuska sosai yana amsa masu ganin an duk’a ana gaidashi a cikin gidansa, don tun bayanda Raihanah ta bar gidan rabonsa da yaga an masa irin wannan gaisuwar a cikin gidansa saiko yanzu da Najah ta koma saliha.... Hajiya Haule ta saki bakida hanci tana kallon salon makirci.... Nan Magajiya taci gaba da jajanta ma Baba Alhaji abinda ya faruda Hajiya Haule ta kuma bada hak’uri kan abinda Sawwama tai da tabbacin haka bazai kuma faruwa ba.... Tai ma Sawwama idanu nan Sawwama ma ta shiga bada hak’uri harda kuka tana fad’in sharrin shaid’an ne ba halinta bane... Baba Alhaji da gaba d’aya jikinsa yai sanyi nan ya shiga amsan hak’urinsu yana fad’in ai babu komai duk d’an adam ajizi ne..... Haba nan fah Hajiya ta fashe da kuka tana fad’in “Alhaji yanzu yarda kayi da makircin wad’an nan... Wllhi munafunci ne ba har zuciya bane..... Na shiga uku ni Haule....” Baba Alhaji ya dakarta da ita da fad’in “Haba Haule, tinda sunzo sun tako har yanda kike sun nemi yafiya da afuwa mai zaisa bazaki yafe masu ba, kowa ya cancanci dama ta biyu.....” Magajiya ta murmusa jin nasaran da suka samu kana ta isa kusan Hajiya ta kuma duk’awa ta kwanto da kai kusanta sosai, cikin sigan rad’a take furta “A makarantar makirci ajin farko kike har yanzu Haule... Babu boka babu Malam mu zuba kowa tasa ta ficcesa....” Ta d’ago tana duban Haule da hawaye suka wanke mata fuska ta shiga gogema Haule hawayen tana furta “Ki daina kukan nan haka nima duk sai kisa naji kukan.... Muyi hak’uri da juna don mahaillicinmu ma muna masa kure ya yafe mana... Ko ba haka ba Alhaji....” Ta k’arashe tana duban Baba Alhaji had’ida kashe masa murya... Cikin sauri ya jinjina kai yace “K’warai kuwa.... Kar kiji komai Hafiz zai maida matarsa d’akinta in sha Allahu....” “Laaaaa! Shikenan shikenan sun asirce min miji..... Wllhi wllhi kinci uwar k’arya Magajiya.... Wllhi....” Batakai aya ba Baba Alhaji ya katseta da fad’in “Haba Haule... Wane irin taurin zuciya ne haka... Duk wanda ya kwantar da kansa ya baka hak’uri sai ka amshi hak’urin nasa... Ku tashi kuje komai ya shige da izinin Allah....” Magajiya ta kuma murmusawa tana duban Haule kana ta mik’e tana kuma sinne kai cikin mayafi, sai faman murmusawa take da bakinta gefen hak’orin makkanta, k’asa k’asa yake duban Baba Alhaji kana tace “Toh mun barku lafiya Alhaji... A dai k’ara hak’uri, yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba.....” Baba Alhaji sai Washe baki yake yana satan duban Magajiya da kalan murmushin da take masa har suka fice yana mai tabbatar masu Hafiz ya maida matarsa an gama..... Har lokacin idonsa naga k’ofa Hajiya kaw bata daina dubansa baki sake ba.... “Alhaji! Alhaji!! Har saida ta ambato sunansa a karo na uku kafin ya maidoda dubansa gareta yana fad’in “Barin k’arasa ciki... Ina Naja’atu ya kawo min abinci na.... Ke Naja’atu....” Ya k’arashe yana bud’e murya alamun yana neman Najah..... Sahariyya da akai komai a gabanta tsorone ya fara cika mata zuciya tana tunanin kardai abinda Hajiya ta shuka ne suka soma girba.... Da rarrafe Haule ta nufi d’akin mijinta tana fad’in “Amma Alhaji ka bani mamaki....” Yana mai kwab’e babbar rigarsa ya katseta da fad’in “Da nayi mai....?” Haule ta kuma sakin baki tana duban ikon Allah kana tace “Au bama kasan mai kayi ba Alhaji... Yanzu kai bazaka iya tantance makirci da akasinsa ba... K’iri k’iri kasan wancan shed’aniyar da d’iyarta makirici ne zalla ya kawosu ba komai ba.... Ko ka mance haka mukayi ma K’aninka da matarsa, ka mance irin wannan hak’urin muka basu.....” Murmushin ko inkula Baba Alhaji yai mata kana yace “Banda abinki Haule shikenan kowa sai ya zama irinki... Sabida d’abi’arkice makirci shiyasa kike ganin kowa makiri ne.... Tinda sun gane kukurensu ni inaga ai shikenan Hafiz ya maida matarsa itama Zulfa’un sai ya had’esu duka biyu....” Baikai aya ba Hajiya ta katsesa da fad’in “Wllhi k’arya kenan, wannan watsesstiyar d’ahna ya gama zaman aure da ita.... Wannan tsaf zata kar mutum... Wllhi badai Hafiz d’ina ba....” Da wutsiyar ido ya dubeta kana yace “Akwai wani Hafiz d’in ne.....? Na gama magana Hafiz zai maida iyalansa don sakin baida wani alfanu cikinsa......” Daga haka band’aki ya shige ya bar Haule tana sallalami tana mamakin Yaushe Baba Alhaji ya soma mata musu... Lallai Magajiya bata zauna kurum ba da shiri ta shigo mata gida... Dik yanda za’ai ya zama dole ta tashi tsaye ta sami lafiya ta koma wajen bokanta kafin komai data mallaka su kufce mata..... *** Gyara tsayuwarsa yai jikin mota k’afarsa a hard’e yana ci gaba da wasa da d’an makullin motar kana yace “Idan bazaki introducing d’ina wa Mamy ba, zan shiga nayi da kaina don dama kinsan wajen Mamani kam banida matsala.....” Nabilah dai sai waige waige take duk a tsarge take jinta don bata saba tsayuwa da maza a waje ba kana tace “Kaga ni zan shige yanzu za’a fito masallaci sallan azahar, and banso mutane suyita kallona a nan suna wucewa....” Ya d’an gimtse kana yace “teddy bear I’m serous, inaso family d’inki susan dani sabida bada wasa nazo ba.....” Yayi maganar babu alamun wasa a tattaredashi wanda saida ya haifarwa Nabilah da bugun zuciya.... Batasan mai zatace masa ba sai duban k’asa da tai..... Daidai lokacin Sameer ya fito daga gidan da niyyan tafiya masallaci.... Khalid yana hango Sameer ya saki murmushi don bai manta ba dama sun tab’a had’uwa a gidan saidai a wancan lokacin Sameer ya sanar masa cewa alak’asar da mutanen gidan sabo ne kawai sabida zaman unguwa guda, a halin yanzu baisan asalin alak’ar Sameer d’in da ahalin gidan ba.... K’arasowa Sameer d’in ma yai yana mamakin hango Khalid da k’anwarsa Nabilah a tare..... “Aaa Dr ashe zan sameka a nan....” Khalid ya fad’i sanda ya shige Nabilah ya k’arasa ya baiwa Sameer hannu sukai masbaha.... Gaban Nabilah ya fad’i jin muryar Yayanta Ma’aruf suna gaisawa da Khalid.... Cikin sauri ta k’araso zata shige cikin gida, kai a k’asa taceda Sameer “Ina yini Yaya...” Ya amsa mata a tak’aice bata kuma cewa komai ba ta shige cikin gida..... Daga Sameer d’in har Khalid d’in kallo suka bita dashi har ta shige cikin sauri.... Sameer ya dubi Khalid yace “So you two know each other....?” D’an shafa sumarsa yai kana tin kafin na had’uda kai a gidan nan nasan miss grumpy.....” Yai maganar yana murmushi.... Shiru Sameer ya d’anyi kana yace “Amma kasan alak’ar dake tsakanina da ita.....?” Sai sannan Khalid ya d’ago yana dubansa with a serious face kana ya furta “Ban fahimceka ba....” Dafasa Sameer yai yana murmushi kana yace mu k’arasa masallaci za’a shiga sallah.... Idan mun fito you’ve a lot to explain to me kasan bazan bari a yaudari k’anwata ba....” Ya k’arashe yana mai ci gaba da warware hannun rigarsa da yai folding wajen alwala Khalid ya bisa da kallo yana mai nanata kalman k’anwata da Sameer yace har suka shige haraban masallacin *** Yasmeen tai d’add’aya a parlorn tana ci gaba da aikin kuka wanda tin isowarta garin takeyi..... Mahaifiyarta kaw sai faman cika take tana huci, ita kad’ai takai mari takai bango tana mai jinjina rashin mutuncin da Khalid ya masu.... Cikin kuka Yesmeen taci gaba da fad’in “Momy Wllhi nayi imani Kano ya tafi wajen tsinanniyar can ya tafi tinda gashi Ammi tayi waya tana tambayar mun sauk’a lafiya... Momy nidai Wllhi bazan tab’a bari Khalid ya auri wata bani ba... Kigafah kalan wulak’ancin da yamin ya barni a train station yayi tafiyarsa.....” Ta k’arashe tana mai kuma jejjefa k’afafu tana kururuwa.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *71* Mamakine ya cika Khalid jin cewa Iyayen Nabilah sune Iayayen Sameer na asali, wannan shine ikon Allah, who would’ve thought mutanen da Siyama ta tsana zasu juya su zama dangin mijinta....? Yai k’asaitaccen murmushi a hankali yana mai jinjina kai Don ko babu komai sosai abin ya masa zak’i.... Yana ganin kiran Ammi na shigo masa yayi biris yak’i d’agawa don yasan k’arshen zancen, k’arshe ma saka wayar yai a flight mode sanin cewa bazasu daina kiran nasa ba... Yana can sashen Mamani suna firan Yaushe rabo yayinda Sameer ke zaune parlorn Mamy suna tattaunawa kan batun Khalid d’in da Nabilah..... Mamy ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Amma Ma’aruf kana ganin wannan al’amari mai d’orewa ne..? Banso azo ana samun sab’ani musamman da ya kasance d’anuwan matarka ne....” Turowa kad’an yai daga cikin kujera kana yace “Mamy munyi magana sosai da Khalid kuma ya tabbatar min cewa da aure yake son Nabilah, sannan na yarda da halayya da d’abi’un Khalid Mamy... Yana dai da hali irin nasa na rashinji wasu lokutan but I assure you he’s a good person... Bawai don ya kasance dan uwa ga Siyama ba no, na sanshi tun yaranta yaron kirki ne Mamy... Amma saidai wani hanzari ba gudu ba...” Mamy ta d’ago tana dubansa kana tace “Umhum ina saurarenka....” Sameer ya d’an fuzar da iska kana yace “Mamy iyayen Khalid suna yunk’urin had’a aurensa da wata ‘yar uwarsa ce wanda sam shi bai k’aunarta... Kinji a yanda matsalar take, ni kuma sam bazan zauna a cutar da ‘yar uwata ko a k’untata mata ba, bazanso tai auren da zatazo tana shan wahala ba koma azo anacewa da an sani da ba’ayi ba....” Jinjina kai Mamy tai kana tace “Wannan gaskiya ne Sameer, abinda yafi dacewa tun kafin maganan nan ya isa gaban Abbanku ka sami shi Khalid d’in kuyi magana, yaje yabi umarnin iyayensa yayi masu biyayya daga shi har Nabilar suyi hak’uri da juna, ni zan sami Nabilah nai mata magana, ka fahimta....” Shiru ya d’anyi kaman mai nazari kana yace “A’a Mamy baza ai haka ba, idandai suna son junansu inaga bamuda hurumin datse masu farin cikinsu, komai d’an gwaji ne a rayuwa, inaga mu baiwa Khalid dama ya gwada nasa k’ok’arin wajen shawo kan iyayensa da nuna masu kuskuren dake cikin k’ok’arin da suke wajen auren da sam babu soyayya cikinta tinda kinga a nan gidan Auren Zulfa’u da Hafiz aya ce, ta zama izna ga masu yunk’urin irin wannan had’in da akeyi ba tareda baiwa yara daman zab’an abokan zamansu na rayuwa ba.. Aure is a lifetime commitment Mamy, one has to be very careful wajen deciding....” Mamy ta jinjina kai cikeda gamsuwa da bayanan d’an nata kana tace “Haka ne Ma’aruf, kayi gaskiya Ubangiji ya maka Albarka....” Sameer ya amsada Ameen Mamy kafin ya mik’e yana fad’in “Barin shiga na duba Mamani....” Mamy tace “Toh a fito lafiya....” Nabilah dake mak’ale jikin k’ofar d’akin Mamy taji komai, tsanin mamakine ya cikata, Wato wannan Siyamar itace matar Ya Ma’aruf... Kam bala’in can.... Matar datazo har cikin gidan nan ta gama rashin daraja ashe gidan sirakanta ne....? Aiko wllhi bataci bulus ba bashi taci Dan Wllhi wannan rashin darajan da tayi cikin gidan nan tsaf saita kwashesu ta maida cikin aljihunta saidai ba sunanta Nabilah ba... Ta saki murmushi a hankali tana hasasho ramuwar gayyar da zataiwa Siyama matar Ya Ma’aruf... Ita a halin yanzu ma bata ta tata da Khalid kawai burinta ta k’untatawasu Siyama ta huce takaicinta... Da wannan tunanin ta koma cikin d’aki ta haye kan gado ta lumshe idanunta tamkar mai bacci jin Mamy ta nufo cikin d’akin.... Sameer yana tafe sashen Mamani ya tsaya yana hangen k’ofar sashen Aunty Lami tamkar mai son tuna wani abin... Haka kurum kaman wanda aka umarcesa ya nufi sashen nata sallama saman bakinsa.... Aunty Lami dake k’uryar d’aki tana waya da Haule, Haule na labarta mata kalan rashin darajan da Magajiya tazo har cikin gidanta tai mata nan ta sinkayo muryarsa mai cikeda k’warjini yana sallama... Gaban Lami ya yanke ya fad’i tamkar wacce aka aje mata guduma... Gaba d’aya saima ta daburce ta shiga amsa masa sallamar nasa cikin in ina.... Daga d’aya b’angaren Haule da itama ta sauraro sallamar tasa wanda ko shakka babu itama fad’uwar gaban ya haifar mata, cikin sauri taceda Lami “Dama ta sameki ki gama mana shi duk mu huta da fargaba da fad’uwar gaba...” Bata jira cewar Lami d’in ba ta datse kiran....Da k’yar tai k’ok’arin saita kanta kana tai masa izinin shigowa..... Aunty Lami harda karkad’e masa kujera tana fad’in “Lale lale Uban masu gida, shigo abinka....” Murmushi saman fuskar Sameer ya shigo kana ya soma gaidata bayan ya daidaita bisa kujera mai d’aukan mutum biyu wato two seater... Gaba d’aya Lami ya kasa zaune ta kasa tsaye dikda d’ingishi da take sakamon fad’owa da tai jikin window sanda take lek’ensu Abbah da Mamy.... Kankace mai ta cika gaban Sameer da kayan ciye ciye da shaye shaye tana fad’in “D’an gidana kaci abinci please... Ko kana son wani abinne yanzun na had’a maka....” A hankali ya d’an murmusa kana yace “Karki damu Aunty aima a k’oshe nake, dama cewa nayi bara na shigo na dubaki don jiya Mamy ke cemin bakiji dad’i ba kin samu buguwa a k’afarki....” Aunty Lami ta kuma mik’ar da k’afar tana mai tamke idanu alamun zogi kana tace “Wllhi am Uban masu gida... Kaga waccan k’yauran kitchen d’in shine fah na buga dashi, ka ganshin nan ya jima a haka nan, toh Abbanku bai samun zama balle a gyara ga gidan sai ‘yanmata saima ka rasa waye zaka aika....” Sameer ya d’an karanceta a hankali kana yace “Karki damu Aunty zan turo mai gyara anjima kad’an a duba in sha Allah... Allah ya baki lafiya....” Ta amsada “Haba Uban masu gida, ayi haka... Kai na kuwa gode fah... Allah dai shi saka da Alkhairi.... Ohni Lami yau ga Ma’aruf d’in ya dawo garemu har mun soma ganin alfanunsa... Allah mun gode maka da ka bayyana mana shi....” Ta k’arashe tana mai kamo bakin zani tana share hawaye tamkar gaskiya.... Sameer shiru yai tamkar mai nazari don baiga abin godiya da kuka a nan ba, kana ya d’anyi gyaran murya yace “Babu komai Aunty, ki kwantar da hankalinki na dawo gareku in sha Allah kuma bazan sake b’acewa ba...” Yayi maganar yana mai dubanta with a straight face.... Aunty Lami da bugun k’irjinta ya k’aru a hankali ta saki zanin da take share hawaye dashi tana duban cikin idanun Sameer da baya fad’i mata komai sai tsan tsan tsoro da fargaba ga k’warjininsa da ya hanata sukuni tin shigowarsa.... Kakkaurar miyau ta had’iya da k’yar kana ta saki murmushin yak’e tace “Haka ne Uban masu gida... Toh ko ruwan kasha mana...” Mik’ewa yayi hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa kana ya d’aura sassanyar murmushi saman kyakkywar fuskarsa yace “Na gode Aunty ban jima da shan ruwa ba next time in sha Allah...” Aunty Lami ta bisa da kallo har ya fice tanaji cikin ranta tamkar yayi tuntub’e wajen ya fad’i gawa kowa ya huta, ta maidoda dubantaga ga contaminated drink d’in data kawo masa wanda ko kallo bai ishesa ba, tai k’wafa ta d’auka ta nufi kitchen dashi ta juye cikin sink, cikin ranta take ayyana cewa next time bazai tsallake ba idan ya tsallake wannan, tai murmushi sakamakon tuno abinda yafiso tun yana yaro wanda dashi zasuyi amfani su gama dashi kana tai k’wafa a fili ta furta “Muje zuwa Ma’aruf da sannu zaka fad’a tarkonmu...” *** Jinge kansa yake jikin car seat d’in idanunsa a lumshe yana mai ci gaba da kad’a ‘yan yatsun hannunsa jikin steering wheel d’in motar.... Yusuf da duk tsawon lokacin karantarsa yake gyara zamansa ya d’anyi kana yace “We’ve been waiting here fo edges idan kanawa Allah muyi abu guda d’aya don wllhi na gaji....” Da wutsiyar idanu Akram ya dubesa kana yace “Toh idan naje mai zance mata, kaina na kawo kokuwa Ogana nakema sharan fage...?” Yusuf ya fuzar da iska a hankali had’ida tab’e baki kana yace “Rashin bin shawarinka ya janyo maka, saida na fad’a maka tun farko be frank with him, ka sanar dashi komai....” Baikai aya ba Akram ya katsesa da fad’in “In sanar dashi mi... Cewa munyi tarayya wajen son mace guda kokuwa mai kakeso na sanar dashi...? Ni kama san abinda yafi damuna.... Wllhi ban sani ba if I can do this.... I’m not sure...” Ya k’arashe yana mai taunar lip d’insa na k’asa a hankali... Yusuf yaci gaba da karantarsa a nitse kana yace “Alright here’s what you should do, amma shawarice....” Akram ya dubesa da gefen ido kana yace “Ina saurarenka.....” K’asaitacciyar murmushi Akram yayi bayan Yusuf ya gama basa shawarin hukuncin da zai yanke, wanda kuma sosai yayi na’am da shawarin abokin nasa da wannan matsaya suka nufi gidan Aunty Bara’atu kaman yanda Atika ta kwatanta masu..... Kallon Atika da Aunty Bara’atu kurum take tana mamakin yanda suka tasata gaba sai tayi ado don zata fita zance... D’an turo baki gaba tai kana tace “Wllhi Aunty da dai kin daina biye Atika matsala ce bai ganta ba, ni ko zamanin da nake budurwa ma ai ban fita zance ba balle yanzu da nake bazawara....Kuma harda wani ado Aunty aima sai yace sonsa nake....” Hararan da Aunty B ta narka mata ya sanyata yin shiru.... Atika ta k’unshe dariyarta sanda take ajiye had’edd’iyar doguwar riga ‘yar dubai mai launin ruwan hoda Wato peach saman gado, harara Zulfah ta rakata dashi had’idayin k’wafa na zan kamaki ne... Atika ta kuma darawa kana tace “Aunty wannan ‘yar gidan naki saifa kinyi da gaske don wllhi ko a office haka nake fama da ita, duk wanda yace yana sonta sun b’ata kenan, harta Manager yanzu bata masa murmushin da take masa da, shi wannan abokin Yusuf d’in ma na tabbata don dai kin saka baki ne bansan ko gidan Hafiz takeso mu koma ba....” Nan ma harara Zulfah ta narka mata kana Aunty B ta tari zancen da fad’in “Ai Hafiz saidai yaga Katin gayyata da izinin Allah.. Mai ake da jinin Haule jinin tsiya....” Zulfah ta marairaice fuska tace “Kai Aunty Hajiya fah tayi nadama...” Muguwar kallo Aunty B ta kuma watsa mata kana tace “Idan Hajiya Haule zata shekara tana cewa ta tuba tayi nadama bazan tab’a yarda ba... Ke idanma ta tuban ba komawa gidan d’anta zakiyi ba kin gama zaman aure dashi....” Atika ta mik’e tana amsa wayarta da ake bugawa... Ko ba’ace ba kasan bak’on nasu ne ya iso, nan Yusuf ke sanar da ita gasu sun iso... Aunty B tasa Zulai ta bud’e masu parlor k’ofan gaba... Zulfa’u kaw gaba d’aya sai jinta take wani iri haka nan ga bugu da k’irjinta keyi, yau ita Zulfa’u ce zata fita wajen wani da sunan yazo neman aurenta, da gaske dai Ya Hafiz ba mijinta bane... Toh mai zatace, ya ma ake firan.. Abu ne da bata sanshi ba tun tasowarta tinda Hafiz ma rana tsaka akace an bata shi.... Tana tsaka da tunanin muryar Aunty Bara’atu ya katseta “Ki k’arasa shirinki a hankali Zulai ta kai masu abin tab’awa....” Gabanta ya kuma bada sautin rasss... A hankali ta jinjina kai kana tace “Toh Aunty....” D’aukar doguwar rigar tai tana k’are mata kallo kana ta zirata, ta d’ago tana duban kanta jikin mirror sosai ya mata kyau ya zauna a jikinta, zallan powder ta shafa shima don Atika ta tak’ura mata saiko d’an man baki data shafa, ta d’au mayafin rigar ta rufa akan sumarta wanda yake a tsefe ta tufkeshi a tsakiya mai yalwan cika dukda bai faye tsawo ba... Atika tai tsaye tana dubanta kana tace “K’awata kin fito, babu wanda zai tunanin kin tab’a aure balle haihuwa... Masha Allah son kowa k’in wanda bai samu ba....” ‘Y’ar gajeriyar murmushi tai kana “Kedai kyaji dashi... Ni wllhi don dai kun tak’ura min ne amma harga Allah banyi shirin soma wani relationship yanzu ba....Not now gaskiya....” Ta k’arashe tana mai zama saman gado gijif.. Atika ta dara kana tace “Ni wllhi badani kike, Akram fah had’edd’en gaye ne na gaban goshin Governor to be d’inmu... Ni dama tinda Yusuf yace min program d’inki na kashesa nace za’a iso wajen.... Nidai Wllhi karki badamu ehe ki bari kawai musha biki, amma fah ina tausayin manager don Wllhi shima da gaske yake sonki....” Hararanta Zulfah ta kumayi kana tace “Kedai kyaji dashi....” Suna a haka Aunty Bara’atu ta turo k’ofan d’akin ta shigo ta dubi Atika tace “Haka akeyi kun k’yale bayin Allah sunata zaune... Ki lek’a ku gaisa kafin na taso k’eyar k’awar taki...” Atika ta mik’e ta d’au mayafi tana mai darawa kana tace “An gama Auntynmu...” *** A parlor Sameer ya bar Shamsu da Khalid suna firan ball ya shiga amsa kiran Mummynsa.... Koda suka gaisa Hajiya Fatahiyya sai cewa tai “Sameer, Son are you sure you’re alright... Daga muryarka inaji kaman wani abu na damunka... What’s wrong son.... please tell me...” Fuzar da iska yai a hankali don yasan Mummy ta masa farin sanin da bazai iya b’oye mata damuwarsa ba.... Katse shirun nasa tai da fad’in “Is everything alright with your family...?” Sameer ya d’an gyara zamansa sosai sakamakon tuno buk’atan Baba Alhaji da yayi kana ya soma fad’in “Mummy lafiya kenan zan iya cewa... Amma yanzu duk ba wannan ba Mummy... It’s Siyama.. Siyama itace damuwata a halin yanzu... Mummy I don’t understand her anymore... She’s something else, tinda ta tafi gida bata dawo ba and ko kiranta nayi wasu lokutan ta d’aga wasu lokutan bazata d’aga ba... Maganan da muke dake har yanzu batada labarin na sami biological parents d’ina talk less of introducing her to them... Mummy na fara doubting if Siyama really loves me...” A hankali ta saki ajiyan zuciya kana tace “Sameer na sanka da hak’uri da barin abu ma zuciya, amma har idan zaka cutu bana goyon bayan kaci gaba da mata uzuri.... Amma mu bar zancen nan har mu dawo k’asar in sha Allah da kaina zanje na samu Faridar ayi mai yuwa idan Siyama zatai zaman aure fine, idan kuma bata shirya zaman auren bane sai mu sani... Ka k’ara hak’uri Sameer, in sha Allahu komai ya kusa daidaita kaji koh...” Kaman tana dubansa ya jinjina kai kana yace “Mummy kar a mance ai mana addu’a jikin d’aki mai tsarki... Na gode k’warai Mummy na a gaida Daddy ace ina mishi add’uan samun lafiya... Allah yasa a dace ya kuma dawo daku lafiya...” Ameen Son ta amsa masa dashi kafin ta k’arada “Ka gaishar mun da Mamy da Abbah and your siblings of course, Allah bai yi zamu had’u yanzu ba, amma da zaran mun sauk’a a Nigeria zamu had’u da yardar Allah tinda ta Kano zamu sauk’a... I love you so much Son, never forget that... Nida Daddynka muna sonka.... Allah ya maka albarka ya shige maka lamuranka...” Cikeda jin dad’i had’ida peace of mind yace “Ameen Mummy nah....” Sukai sallama har zai katse kiran ta kuma ambato sunansa “Sameer!” Ya amsa a hankali yana mai jin zuciyarsa tai masa rauni ba tareda sanin dalili ba... Mummy taci gaba da fad’in “Thank you for coming into our lives... Thnak you for making us happy... Thank you for completing our family... Thank you for giving me that chance to be a mother to you.... Thank you for being that son I always wanted to have.....” Izuwa lokacin hawayene ke zubowa daga idanun Sameer ji yake tamkar ban kwana Mummy ke masa, a hankali yake furta “Mummy pls stop... Ki daina mun godiya, iyayena haifana sukayi but keda Daddy are my life... Most especially you Mummy, bazan tab’a iya biyanku d’awainiyar da kukayi dani ba Allah ne kawai zai biyaku.... I love you so much Mummy... So much....”. Ya k’arashe hawaye na gangaro masa... A hankali itama ta goge hawayen da ya zubo mata kana tace “I love you too son.... Allah ya sadamu da Alkhairi...” Sameer ya amsada Ameen Mummy nah... Jikinsa a matuk’ar sanyaye sukayi sallama... Kwanciya yayi rigingine bisa gado yana tuno rayuwarsa da Mummynsa tun tasowarsa kyakkyawan murmushi kwance saman fuskarsa.... *** Kanshi na bisa cup ya d’aura lips d’insa kenan da niyyan kurb’an ruwan ya sinkayo sallamanta cikin muryar nan nata mai dad’in sauraro, ruwan da bai iya kurb’a ba kenan ya d’go yana dubanta, ta masa kyau sosai har fiyeda lokacinda sukaje mata gaisuwar ta’aziyar rasuwar d’iyarta can gidan mahaifinta.... Shigowarta parlorn yayi daidai da bugun gate da ake, daga yanda suke suka soma sauraro muryan Hafiz.... Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i... A hankali ta furta “Ya Hafiz.....” SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _.................DA RABO_ *72* Tinda ya hangi mota k’irar Mercedes a k’ofar gidan yaji hankalinsa sam bai kwanta aiko kaman jira yake Zulai tana bud’e masa ya soma tambayar ina Zulfa’u.... Zulai ta soma inda inda tama rasa mai zatace masa, tsawa ya darara mata tuni ta shiga ‘yan kame kame, saidi juyawan da zaiyi ya hangi takalman maza k’ofar parlorn, wani abu yaji ya sauk’a masa a k’irji tamkar an ije gingimemen dutse.... Ya watsawa Zulai harara kana ya shige fuuuu kaman zai tashi sama ya nufi parlorn... Kafin ya shige sai ganin Aunty Bara’atu yai gabansa tamkar wacce aka jefota “Karma ka soma wannan tunanin, shige mu tafi” ta nuna masa hanyar waje.... Banda huci da harararta Hafiz baya komai, Ita kuwa Zulfah a can cikin parlor gaba d’aya ta rasa sukuni, hankalinta yafi karkata wajen Aunty B da Ya Hafiz, dikda fira da Yusuf ke k’ok’arin janta dashi bawai fahimtarsa take ba, gaba d’aya ta kasa kunnuwarta ga sauraren tattaunawar Aunty Bara’atu da Ya Hafiz dikda cewa k’asa k’asa Aunty Bara’atu ke maganar... A kufule Hafiz yace “Amma Aunty Zulfa’u fah da aurenta maiyasa zatake kula wasu mazan....” Muguwar kallo ta aika masa kana tace “Kaine ka d’aura mata auren... Nace kai ka d’aura mata auren...?” Hafiz yaci gaba da huci da kumbure kumbure.... Aunty B tai k’wafa kana tace “Shige nace kafin na sunkuceka aka na fiddaka.... Tsaya waima ban maka iyaka da gidan nan ba...?” Wannan karon gajeriyar murmushi yai kana yace “Haba Aunty ashema Zulfah ta bar gidan nan kenan....” Aunty B ta gyara tsayuwarta kana tace “Kaga Hafiz shige ka fice tin kafin raina ya b’aci...” Ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Aunty B, ji yake tamkar ya shak’e matar nan data zamto masa shamak’i da farin cikinsa da kuma cikar burinsa... Yana sauraro muryoyinsu yanda suke fira cikin nishad’i da kwanciyar hankali, zuciyarsa taci gaba da masa zogi sanin cewa Zulfarsa ce cikin parlorn nan... Miyau mai d’ankaran zafi ya had’iya kafin ya furta cikin zuciyarsa “This is far from over..” Cikin huci yana mai aiakawa Aunty B duban k’iyayya ya juya kaman zai kifa k’asa.... Aunty B ta murmusa kana tace a hankali “Dama d’aya ce Malam Hafiz kuma kayi wasa da ita, mu zuba nidakai....” Bata bar wajen ba har saida ta tabbata Hafiz ya bar gidan.... Wani lungu ya samu ya mak’ale yana jiran fitowarsu, Aiko mintoci kad’an ya hango munafukar sabuwar k’awar nan tata Atika kaman yanda yake kiranta Munafuka, sun fito sunyoma samarukan nasu rakiya zuwa wajen motar tasu, daga yanda yake yana hango d’aya mai maroon d’in boyal d’in ya kafe Zulfa’u da idanu, zuciyar Hafiz taci gaba da tafrfasa, gashi sosai Zulfah ta masa kyau, tsantsan soyayyarta na kuma azalzalansa, idan za’a mutu bazai daina bikon matarsa ta dawo garesa ba, kuma wllhi da ko wanene ya shirya yak’in neman auren Zulfa’u a karo na biyu.... A hankali ya fito daga mab’oyar tasa ya nufosu, Atika da ba wani saninsa tai ba amma hangosa da tai saida gabanta ya fad’i don ba komai ta hango saman fuskarsa ba face tashin hankali tsagwaranta.... Cikin sauri Atika ta soma fad’in “Ka kar ka damu Oga Akram ka samu k’awata an gama in sha Allahu...” Yusuf yai karaf yace “Yauwa k’anwata nasanki da k’ok’ari aci gaba da k’ok’arin shawo mana kan gimbiyar....” Baikai aya ba suka sinkayo muryar Hafiz yana fad’in “Baza’a shawo kan nata ba bak’in munafuki....” Gaba d’aya suka juyo suna duban Hafiz wanda keta faman hure huren hanci yana cika.... Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i yayinda Yusuf yace “Kaikuma waye....?” Hafiz yai wata k’asaitacciyar murmushi kana ya dubi Zulfah da gaba d’aya tashin hankaline ya nuna a fuskarta kana yace “Au dama baki fad’a masu kinada miji ba, basusan cewa ke d’in matar aure bace....?” Yusuf ya d’an murmusa don ya gane Hafiz tsaf tsohon mijin Zulfah ne kuma sun had’u kwanaki a gidansu Zulfa’un sanda sukaje mata gaisuwar rasuwa.... Takowa Yusuf yayi kusansa kad’an yana k’are masa duba daga sama zuwa k’asa, dab fuskar Hafiz ya matso da tasa fuskar kafin ya rage murya yace “Tsohon miji zakace, a halin yanzu Zulfa’u ta mai rabo ce....” Ai baikai aya ba Hafiz dake tururi yakai masa shak’a a wuya yana mai furta “K’arya kake wllhi tawace har abada...!” Zulfah da Atika suka zaro idanu waje cikeda tashin hankali ta k’arasa tana fad’in “Ya Hafiz dan Allah ka sake shi, kar kaji masa ciwo....” “Rufemun baki munafukar banza munafukar wofi wacce batasan komai ba sai cin amana, kin had’e kai da wannan Kawaliyar k’anwar uwar taki kuna cin amanata....” Tinda Zulfa’u take Hafiz bai tab’a k’ona mata rai irinta yau ba, Aunty Bara’atu yake kira Kawaliya.... Batasan sanda hawaye suka soma gangaro mata ba, ta kasa katab’us yayinda Atika tai saurin rik’ota.... Akram ya d’ankai dubansa gareta yaga hawaye na zubo mata, duban Atika yai kana yace “Ki shiga da ita ciki...” Babu musu Atika ta jinjina masa kai kana ta janyo Zulfah tamkar rak’umi da akala suka shige cikin gida.... Maidoda dubansa ga Hafiz Akram yai kafin ya tako har gabansa yasa hannu ya cire hannayensa daga wuyar abokinsa kana yaceda Yusuf “Ba girmanka bane fad’a da mahaukaci, lets go....” Hafiz ya saki Yusuf yana k’ok’arin rik’o Akram saidai hannu guda Akram yai amfani dashi wajen damk’e hannun Hafiz d’in da ko motsata ya kasa.... Murya a dake yake furta “Komai nada iyaka... Yanada kyau kasan madakatarka a rayuwa.....!” Daga haka jifa da hannun Hafiz d’in yai suka shige mota... Akabar Hafiz da sosa hannunsa yanda Akram ya murd’e masa... Yana ganin yanda suka kwashi mota suke shige suka bar masa k’ura.... Suna tafe Akram na sak’e sak’e cikin zuciyarsa, hukuncinda ya yanke yayi daidai, yafi kyau shid’in ya nemi auren Zulfa’u don baijin zai bari His Excellency yayi takara da wannan lunatic d’in.... A b’angaren Hafiz kuwa wajajen k’arfe taran dare ya shigo gidan mahaifinsa, wata sabuwa Baba Alhaji ya bijiro masa da zancen maida matarsa Sawwama d’akinta... Hafiz yana kumbure kumbure yake duban Hajiya kana yace “Amma dai Baba ka mance nima na kusan mutuwa kan munafukar yarinyar nan, Baba wllhi ba sona take ba, nayi imani kasheni kawai takeson yi... Haba haba saikace neman kai dani kuke... Kuda zakuyi yak’in dawo mun da farin cikina Zulfa’u kunje kuna yunk’urin dawo min da ajalina... Nidai wllhi gaskiya Baba...” Dakatar dashi Baba Alhaji yai da fad’in “Kai rufemin baki... Shikenan kai duk wacce ka aura saika rabu da ita, so kake da k’anan shekarunka a soma k’irga maka aure... Ni nace zan dawo maka da Zulfa’u ince....?” Hafiz ya d’ago da sauri yana washe baki yace “Allah da gaske Baba....?” Baba Alhaji ya jinjina kai kana yace “K’warai kuwa nai maka alk’awarin dawo maka da matarka Zulfa’u gareka amma da sharad’i....” Cikin zumud’i da k’osawa yace “Mecece sharad’in Baba...?” Baba Alhaji ya murmusa kana yace “Alhamdulillah abinda nakeson ji kenan.... Sharad’in itace zaka maida matarka Sawwama d’akinta, ka mance komai ka maidata....” Saida ya zabura da jin batun mahaifin nasa... D’an girgiza kai ya soma yana fad’in “Haba Baba Dan Allah... Wllhi ni yanzu ko a k’afa aka d’auramin Sawwama zan kwance na gudu...” Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Idan kanason Zulfa’u zaka maido Sawwama gobe gobe d’akinta... Na gama magana...” Daga haka mik’ewa yayi ya shige d’aki yabar Hafiz zaune wajen yana sak’e sak’e da zullumi... Hajiya kaw salallami kawai tana salati tana furta zama bai ganta ba *** Washe gari Khalid yai shirinsa ya nufi Kaduna dukda sanin cewa zasu kwashi ‘yan kallo musamman da mahaifiyarsa, gashi sam sun kasa samunsa a waya, fitowarsa kenan dashike gidan Sameer ya sauk’a a nan unguwar ya hangeta tafe ta nufi babban kwalta da alama makaranta ta nufa..... Saida ya sak’i sassanyar murmushi don dama yana tunani idan ta riga ta tafi makaranta ba lallai su samu suyi sallama ba.... Ya gefenta ya rab’o had’ida rage glass d’in motar yana sakar mata sassanyar murmushinsa yake furta sallama... Murmushin itama ta sakar masa wannan karon had’ida amsa masa... Khalid yaji dad’in murmushin da ya gani saman fuskarta kana yace “Is a good thing I found you here, da ban fito da wuri ba maybe da ko sallama bazamu samu muyi ba....” Ta d’an dubesa da alaman tambaya... Jinjina mata kai yai kana yace “Kan hayata nake zan koma Kaduna yanzu....” Nabilah ta d’an sadda kanta k’asa kana tace “Toh Allah shi kiyaye hanya ya kaika lafiya....” Khalid ya amsada Ameen kana ya k’arada “Shiga muje na ajiyeki a school d’in....” Yayi maganar yana bud’e security lock.... D’an dubansa tai kana tace “Karka damu yanzu zan sami adaidaita, kaje kawai kar kayi rana kasan yanayin yanda hanya suka koma yanzu....” Yana murmushi yake furta “Tsoro kike kar a sace miki ni....?” Ta d’an fito da idanunta waje had’ida murmusawa kana tace “Nidai bance ba...” “Toh idanba tsoro kike ba ki shigo nai dropping d’inki....” Zata kuma magana yace “No more excuse shige muje....”Ya k’arashe yana mai bud’e mata frontseat Saida ta d’an juya idnunta kafin ta k’arasa ta shige.... Wani sassanyar k’amshine da ya gaurayu da sanyin AC sukai mata sallama cikin motar tasa, wani ikon Allah tin jiya dataji Yayanta Ma’aruf da Mamy suna tattaunawa kan batunsu da Khalid d’in sai ta tsinci kanta tana mai tsananin jin nauyinsa, gaba d’aya saiji tai ta kasa sakewa cikin motar ma.... Shi kansa Khalid d’in ya kula da canjin nata, wannan kallon rainin da take masa sam yau batai masa ba saima avoiding k’wayar idanunsa da takeyi.... tsakiyar motar ta hangi had’edd’en cappuccino cikin disposable cup da blueberry cookies da alama breakfast d’insa kenan.... Bai bari ta d’aga idanunta ba yace “Bismillah...” D’an tab’e baki tai kana tace “Aaa wannan ai saiku, ni ina wannan zai k’osheni, nasan iyakacin karin kumallon naka kenan...” Khalid ya murmusa yana karyan kwana yake furta “Seems like kin fara sanin mijinki tun yanzu....” Ai baikai aya ba ta kuwa watso masa muguwar kallon mai firgitasa... Ya kuma sakin murmushi yana mai ayynawa cikin ransa ai saidai ba Nabila ba... Khalid yaci gaba da fad’in “Bakida labarin Sameer da Mamy harmada Mamani sun bani...?” Wannan karon kauda kai tai daga barin duban nasa had’ida tab’e baki kana tace “Ai basukeda alhakin badani ba, Abbah na ne kawai zai haka, kuma a iyakacin sanina aurenka da Yesmin ya kusa....” Bai kuma cewa komai ba jin ta ambato Yesmin har saida ta d’an kaikaito da fuska ta dubesa, sai yau ta k’are masa kallo, ashe kullum kallon tsoro take masa.... Khalid yakai mak’ura wajen had’uwa, ba laifin Yesmin bane data nace masa, irin mutanen nan ne da duba d’aya zaka masu kaji sun shige ranka.... Kaman yasan dubansa take aiko yana juyowa suka had’a idanu, tai saurin d’auke idanunta daga barin dubansa, babu wanda ya kuma cewa komai cikinsu har suka iso cikin babban jami’ar.... Yusrah da dandatson ‘yan ajinsu ana cike k’ofar lecture hall ko ba’ace ba isowar malami ake jira hamshak’iyar BMW d’in nasa tai parking, kowa sai santin motar yake ga kalan ja dama da d’aukan idanu.... Ta kama handle zata fice kenan tajiyo muryarsa yana fad’in “teddy bear zan tafi yak’in neman aurenmu kimin addu’a.....” Juyowa tai tana dubansa sai kuma ta sadda idanunta k’asa sakamakon yanayin data hangi fuskar nasa ciki.... Kasa cewa komai tai har saida Khalid yace “Bakida abinda zakicemin ne...?” A hankali ta furta “Toh ni mai zance....?” K’uri ya mata gaba d’aya ta daburce kana yace “You pray for me, for us....” Ta d’an dubesa harda wani jinjina mata kai alamun tabbatarwa.... Duban dandatson ‘yan ajinsu tai kana ta hango k’awarta Yusra daga can gefe tana duban motar tana murmushi kana tace “Em... Allah kaika lafiya, drive safe....” Ta kama marfin motar zata bud’e taji tak’i bud’uwa..... Juyowa tai tanai masa duban tuhuma... Ya d’an d’aga giransa kana yace “What..?” Shaye da mamaki take dubansa kana tace “Ka bud’e min na fice kafin malaminmu ya k’araso....” Sai sannan ya saki murmushi kana yace “Oh Aw sorry na mance k’ofar nan ta sami matsala bata bud’ewa ta ciki saita waje... Wait barin bud’e miki....” Nabilah ta bisa da kallo sanda ya fice ya zagayo bud’e mata marfin motar itada sam bataso ya fito ba balle a ganshi yana bud’e mata k’ofar mota.... Aiko mai motar har sai yafi kashe dandatson mutanen fiyeda motar kanta.... Kunya ya cika Nabilah sanda Khalid ya bud’e mata marfin mota, a d’arare ta fito don ko ba’a ce tasan illahirin mutanen dake wajen su suke kallo, Khalid ya rank’wafo saitin kunnenta kana yace “You take care, and kar na sake ganinki da wad’ancan yara mazan....” Harara ta galla masa kana ta d’an saita kanta tace a hankali itama “Thanks for the ride, and safe trip...” Daga haka tasa kai ta shige kaman zata kifa don ji taima kaman k’afafunta hard’ewa suke.... Khalid ya bita da kallo har ta shige kafin ya koma motarsa ya wuce shima... Aiko Nabila na k’arasowa Yussy ta janyo hannunta suka shige tana fad’in kalan burgewar da sukai itada Khalid.... *** Wajajen shabiyun rana ya masa a Kaduna, yana isowa gidan kai tsaye sashensa ya wuce kafin wanima yasan ya dawo gidan, Aiko Kubura ta hango giftawansa, ta saki bokatin da take shanya kana ta nufi sashen Ammi a guje tana rangad’a mata kira.... Siyama da tashinta kenan daga bacci ta sauk’o k’asa tana neman abin kari taci karoda Kubura tamkar wacce aka jefota.... “Ke ke meye haka.. Lafiya?” Siyama ta dakatar da Kubura.... Kubura na haki take nunida waje.... Siyama da takaici ya cikata tsaki tai kana tace “Mutanen nakine suka motsa kokuwa....?” Kubura taci gaba da haki tamkar wacce abin gudu ya biyota kana tace “Aunty Siyama ya dawo....” Siyama ta yatsina fuska kana tace “Shi wane....?” Kubura tace “Saifu mana Aunty Siyama... amma fah shi kad’ai babu abokiyar tafiyarsa babyn dank’on da aka lik’a masa....” Harara Siyama ta galla mata kana tace “Ke banson sakarcin banza....” Kubura tace “Wllhi gaskiya nake fad‘I maki Aunty gayacan ya shige sashensa.....” Siyama ta jinjina kai kana tace “Maza haura sama ki fad’iwa Ammi....” Daga haka ta fice sashen Khalid kaman zata tashi sama... Khalid yana k’ok’arin kwab’e riga da niyyan shiga watsa ruwa Siyama ta banko k’ofar d’akin ta shigo.... Fasa cire rigar yayi sai tsaki dayaja a hankali lokaci guda yake furta “The next time you coming into my room, would you bother to knock... Dear Sis...” Ya k’arashe yana mai k’arasowa gabanta.... Siyama na huci furta “Kai yanzu abinda kayi ya maka daidai Khalid.... Rashin mutuncin da kayi ka kyauta kenan...?” D’aga mata hannu yayi kana yace “Wait wait, hold your lectures Siyama, as you can see I just got home... Fice min a d’aki.....” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa... Muryar Ammi ne daki dodon kunnuwarsa “Bazata fice ba, ka mareta kawai sai nasan ka cika....”Hannayensa dafe da kunkumi ya d’an kauda kai gefe yana k’ok’arin calming kansa.... Juyowa ya d’anyi kana yace “Ammi ina yini....” Dakatarshi tai ta hanyar d’aga masa hannu kana tace “Bazan amsa ba... Cikakke, aidai kaji dad’i ka aikata abinda kakeso ka watsaman k’asa a idanu... Sai ka sanar dani da baka kai Yesmin d’in Abujan ba gidan uwar wa ka tafi....” Karaf Siyama tace “Har sai kin tambaya Ammi, wajen watsetsiyar can ya tafi ya gama watsewa...” Izuwa lokacin zuciyar Khalid ta gama tafarfasa, shi kad’ai sai murza hannunsa dake k’ok’arin kaima Siyama mari yake... Badon Allah ya kiyaye ba tabbas data kwashi tsaraban maruka.... “You watch your mouth....” Ya fad’i idanunsa akan Siyama wanda suka gama komawa jazir.... Ammi ta shiga tafe hannaye tana fad’in “Lallai na yarda basu barka haka ba.... Shin uwar mai suka jik’a suka baka Khalid.... Ka fad’a min... !!!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya Baisan sanda shima a harzuk’e jijyoyinsa sunyi sama yake furta “Abinda suka jik’a suka baiwa Siyama ta kasa rabuwa da Sameer nima shi suka jik’a suka bani.... Cos yarinyar da kuka tsana kuke jifarta da sharri turned out to be Siyama’s sister in-law... Nabilah ba kowa bace face k’anwar Sameer wanda suke uwa d’aya uba d’aya..!!!” Yayi maganan yana mai takowa dab gaban Siyama Ba Siyama datayi mutuwar tsaye ba harta Ammi neman yawun bakinta tai ta rasa balle tai tunanin kalamai ka iya zuwa kan harshen ta.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *73* Girgiza kai Siyama take cikin rashin yarda da abinda kunnuwanta ke jiyo mata, lokaci guda ta kamo hannayen Khalid tana mai furta “Khalid tell me this isn’t true.... Wasa kakemin koh, babu abinda ya had’a Sameer da wad’annan mutanen.... Tell me you’re just joking...” Fincikar hannayensa yai kana yace “Since when muka soma wannan wasar dake abinda kikaji gaskiya ne Nabilah k’anwar mijinki ne....!” “What was that...?” Muryar Daddy ya katsesu..... Lokaci guda Ammi dake faman girgiza kai itama cikin rashin yarda ta shiga furta “Karka sauraresa, shak’iyancin Khalid ne kawai ya motsa don an hanasa auran yarinyar shine bari ya dangantata da Sameer, yo ina Sameer ina zuri’ar yarinyar can dangin mayu.... Kai ko a halitta Sameer yayi kama da wad’ancan mutanen ne.... Wllhi k’arya yake tsantsan Daddyn Siyaaam kar ka yarda dashi.....” Siyama dake tsananin kuka kuma janyo hannayen Khalid tai tana jijjigawa da iyakan k’arfinta take fad’in “Khalid tell me is isn’t true... Ka fad’a min k’arya kake...!!!!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya.... Daddy ne ya k’araso ya janye hannayen Siyama daga na Khalid yana mai k’ok’arin kwantarwa Siyamar hankali.... Cikin kuka Siyama ke furta “Daddy Wllhi k’arya ne, of all people those people can’t be my husband’s family.... Daddy not my Sameer....” Ta k’arashe cikin shesshek’ar kuka.... Duban Khalid dake faman watsama Siyama muguwar kallo Daddy yai kana yace “Khalid..!” D’ago kai Khalid yai ya dube mahaifin nasa had’ida furta “Na’am Daddy..” lokaci guda yaci gaba da furta “Ka sameni a parlor na...” Babu musu Khalid ya jinjina kai kana yabi bayan Daddyn yana mai watsawa Siyama da Ammi ke tausanta harara.... Daga can gefen k’afan mahaifin nasa ya zauna had’ida risinawa kana yace “Daddy barkada gida, ina yini....” Amsa masa mahaifin nasa yai kana yai gyaran murya ya soma fad’in “Khalid maike faruwa...? Shin abinda naji kana fad’i gaskiya ne cewa yarinyar can k’anwar mijin Siyama ne....?” Jinjina masa kai Khalid yai had’ida gyara zamansa kana yace “Daddy abinda kaji gaskiya ne, Nabila k’anwar Sameer ne, recently Sameer ya sami biological parents d’insa, and it happens to be Nabilah k’anwarsa ce Daddy... Wato Daddy akwai abubuwa da dama da suke faruwa a gidan nan wanda sam basa dacewa tin daga kan yanda ake gudanar da al’amran gidan nan... Daddy ba wai ina fad’in gazawarku bane a matsayinku na wad’anda hakkin kula da tarbiyan gidan nan ya rataya a wuyarsu bane most especially you Daddy... Amma maganar gaskiya fah Daddy kuskuren tin daga sama ne, ya samo asali ne daga wajenka, ka baiwa Ammi wani irin power a gidan nan wanda sai abinda taga dama akeyi, Daddy I’m not saying baiwa matarka dama da freedom kuskure bane, but Daddy everything has a limit, ina ganin a matsayinka na shugaba a gida ya kamata ka zama kaikeda final say matuk’ar bai kaucewa Shari’a ba, Daddy karfa ka mance Allah da kansa ya gargade masu imani cewa su tsare kawunansu da iyalansu daga shiga wuta, shin Daddy mecece makomar gidan nan...? Yanzu ga Siyama a gida itama bata d’auki auren da daraja ba balle mijinta sabida abinda ta taso taga akeyi kenan a gidansu, turbar da mahaifiyarta ta d’aurata bisa kenan... Sam Ammi da Siyama basu d’auki d’an adam da wata daraja ba idanba wanda suke so bane... After what she’s done a gidansu Sameer bansan da wasu idanu zata dubesu matsayin sirakanta ba, Daddy mai ya haifar da haka...? Rashin samun wadataccen tarbiya ne tin daga fari shi ya haifar da haka.... Opinion d’in kowa a gidan nan baida daraja idandai ba daga Siyama ya fito ba, Ammi bata d’aukan maganan kowa ko shawarin kowa saina Siyama, and Daddy kaikuma duk abinda Ammi ta fad’i a gidan nan shikenan daidaine kayi na’am dashi without overlooking it... Daddy please ya kamata a daina irin wannan rayuwar a gidan nan, a duba lamarin Daddy.....” Ya k’arashe cikin tsananin k’ank’an da kai da kuma murya.... Shiru ya gifta tsakaninsu tamkar mahaifin nasa bazaice komai ba, saima d’aura hab’arsa da yayi saman hannayensa guda biyu da ya dunk’ule waje guda.... Muryar Ammi ce ya katse shirun da ya ratsa cikin parlorn... “Toh wllhi ba k’anwar Sameer ba, yau idan uwar Sameer ce wannan yarinyar babu abinda ya shalleni, wllhi bazaka aureta ba muddin ina numfashi, yo sai mai... Allah ya kiyayeni na had’a jini da matsiyata, kuma shima Sameer d’in sai ya sakar min d’iyata, wllhi bazata zauna dashi ba, naji dad’i da rabo bai tsaga tsakaninsu ba, rabuwa ya zama dole, gwara da Allah ya bayyana mana....” Bata ida maganar nata ba Siyama ta shigo tana kuka tana fad’in “Ammi wllhi bazan rabu da mijina ba.... Gaskiya ni bazan iya rabuwa da Sameer ba don wllhi ina sonshi ina k’aunarshi har kwanan gobe, Sameer is nothing like his family, tsautsayi ne da k’addara yasa suka zama danginsa, kuma ma ai su Mummy ne iyayensa shida wad’ancan mayun jini ne kawai ya had’su, but his real family are here.... So Ammi don’t think of separating us... Nida Sameer are magnets babu wanda ya isa ya rabamu not even his so called new family, yanzu zan tafi ba sai anjima ba, yanzu zan koma to win my husband back don ya zama dole na rabasa da wad’ancan annoban....!” Tana ida fad’in haka ta fice fuuuu Ammi na k’walla mata kira ko saurarenta bata tsayayi ba... Ammi ta maidoda dubantaga Daddy tana fad’in “Daddyn Siyaam kaga fah tafiya zatayi, kayiwa Allah ka dakatar da ita kartaje su lashe min ita kaman yanda suka lashe Khalid...” Ganin bai amsata ba ya sanyata janyo Khalid tana fad’in “Tashi tashi wuce maza ka k’wato min car keys d’inta...” Khalid na tirjewa Ammi na turasa, fad’i yake “Ammi kinsan Siyama idan tayi niyyan abu no one can stop her....” “Ka shige nace kafin na maka baki...” Duban mahaifiyar tasa kurum yai had’ida girgiza kai kana ya fice yabi bayan Siyama... Ya maido da dubantaga mijinta wanda ta koma masa tamkar TV kana tace “One of these days d’aya daga cikin yaranka zasu sakamin hawan jini, wani irin musifa ne wannan ace yara duk sun haukace kan dangin mayu, da ina tunanin Khalid ne kawai iftila’in ya auka masa ashe harda Siyamar kanta, yo na Siyama ma ai shine babban tashin hankali tinda an riga anyi aure, Toh wllhi ko ina mutuwa ina tashuwa ne bazan bari Khalid ya auri yarinyar can ba, kuma Siyamar ma ko kotun k’oli zamu tafi wllhi sai Sameer ya sakar min d’iyata don bazan tab’a had’a iri da dangin tsiya ba ehe....” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice fuuuu tana k’walla kiran yaran nata.... Birki tai a d’ari sakamakon hango Siyama da tai cikin mota Khalid na tsaye gaban motar tana fad’in ko ya kauce mata a hanya ko tabi takansa..... Ammi ta isa jikin motar a guje tana fad’in “Nafa fad’a maki babu ke babu tsinannen yaron nan ki fito a motar nan Siyama....” Siyama fad’i take “Ammi idan sama da k’asa zasu had’e Wllhi baki isa ki rabani da Partner ba, kuma wllhi yanzu ba sai anjima ba zan tafi na soma yak’in raba mijina da wad’ancan jarababbun.....” Khalid fad’i yake “Siyama calm down, ki bari abi komai a sannu, ki sauk’o ayi magana ta nutsuwa babu wanda zai rabaki da mijinki amma hanyar da kika d’auko ba mai b’ullewa bace just calm down first....” Bai rufe baki ba Siyama ta kuma baiwa mota wuta alamun batada niyan fasa abinda tai niyya... Gani zatabi kan Ammi yasa Khalid saurin janyo mahaifiyarsu gefe dake kururwa Siyama kaw taja mota ta fice a guje k’iris ya rage bata had’ada security mai bud’e mata gate d’inba Ammi hannu aka take furta “Na shiga uku na lalace ni Farida mi nayima yaran nan suka zab’i wasu tsinannu kwashesu sama da mahaifiyarsu.....” Ta shiga rera kuka bataji bata gani, da k’yar Khalid ya iya janyota ya shigar da ita cikin gida.... *** Akram na risine gabansa ya ida amsa wayar da yake, saida ya d’an b’ata lokaci yana duba abu cikin wayar kana yace “Ina saurarenka...” D’an gyara zamansa Akram yai kana yace “Mun gana da ita yarinyar jiya, kuma na sanar da ita abinda ke tafe damu, and daga dukkan alamun mun samu goyon bayan K’anwar mahaifiyar tata wacce take zaune gabanta, amma your Excellency wani hanzari ba gudu ba....” Engr ya gyara zamansa kana yace “Umhum go ahead ina saurarenka...” Akram ya kuma d’an turowa daga cikin kujeran kansa a k’asa kana yaci gaba da fad’in “Sir, ina ganin zaifi kyau idan baka bayyana mata kanka a halin yanzu ba, ma’ana naci gaba da isar mata sak’onka zuwa nan da d’an wani lokaci sabida tsohon mijinta yanada matsalan tab’in k’wak’walwa kuma Sir a matsayin da kake idan kowa yasan cewa kai kake nemanta wannan tsohon mijin nata can cause a biggest scandal for us, ni kuma hakkinane na kare reputation d’inka and your career in politics kasan abokan hamayya k’iris suke jira Rankashi dad’e...” Shiru yai yana nazarin maganganun Akram d’in kana yace “Haka ne Akram.... Kayi daidai, hakan yayi... Bansan da mai zan biyaka ba bayan duk abubuwan da kake min.... Hak’ika ka cika d’anuwa na k’warai....” Murmushi kwance saman fuskar Akram yace “Ka wuce haka a wajena your Excellency, ban biyaka rabin abubuwan da kake min ba dama family na gaba d’aya, you made me who I am... Bama ni kad’ai ba d’imbin mutanen da suka zama abinda suka zama yau ta dalilinka bazasu k’irgu ba, Allah ne kawai zai biyaka, muna kuma fatan Allah ya k’ara mana irinku cikin al’umma....” Daidai nan Muhibbah ta shigo d’aukeda farantin fruits ta zuba gayu cikin riga da skirt English wears wanda suka zauna a jikinta sosai ga k’amshin turaren humra dake tashi a jikin nata wanda duk d’ah namijin data giftasa dole tsikar jikinsa ya tsargar masa.... Akram yai saurin mik’ewa kana ya risina yaceda ubagidan nasa “Sir ni zan wuce...” Engr ya jinjina kai yace “Alright Akram, ka samu Sufi ya baka list d’in k’ungiyoyin masu neman taimakon nan sai asan abinda za’a fara taimaka masu dashi koh....” Ya jinjina kai yana mai furta “Alright your Excellency right away...” Ko kallon yanda Muhibbah take baiyi ba ya fice cikin sauri duka irin shu’umin kallon da take aika masa.... Akram na ficewa ta kuma matsowa jikin mijin nata tana mai fad’in “Excellency na ga fruits na kawo maka, nasan idan na biye naka bazakaci komai ba har sai ka jira yaran nan sun dawo daga islamiya....” Ta k’arashe tana mai d’auko yankakkiyar kankana da cokalin fork..... Girgiza kai ya d’anyi had’ida kauda kai gefe kana yace “Shin wai wane irin kunnen k’ashi ne dake Muhibbah, sau nawa zance maki idan ina tare da bak’i a parlorn nan kar ki shigo, kin fito babu ko mayafi cikin wannan shiga kin wuce duk tarin ma’aikatan dake cikin gidan nan a haka kin nufo har parlorn nan... Kanki d’aya Muhibbah....” Murmusawa tai jin Wai yau Engr ke damuwa da ita har haka, ashe dai har yanzu yana k’aunarta tinda gashi yana kishinta.... Aje plate d’in ta d’anyi kana tace “Toh Banda abinka Excellency na gani nai daga kai sai Akram ne ai...” “Akram d’in muharammin ki ne shi...?” Ya jefo mata tambayar... Gyara zama ta kumayi kana tace “Toh ai gani nai Akram ya riga ya zama d’an gida a gidan nan kuma ai.....” Dakatar da ita yai ta hanyar d’aga mata hannu kana yace “That doesn’t justify your actions, kinyi kuskure karki sake nan gaba...” A hankali cikin yanayi na shagwab’a da turo baki gaba tace “Bazan sake ba in sha Allah... kuma ai gani nayi yanzu baka wani kulawa dani a gidan nan dukda k’ok’arin da nake wajen ganin ka janye k’udirinka akaina, Ma’aruf dan Allah ka yafemin haka nan mu koma tamkar yanda muke da, I promise to be a good housewife kaji please.... Ko dai neman aure kake ban sani ba...?” Statement d’inta na k’arshe ya sanyashi d’agowa yana d’an dubanta, sai kuma ta basa tausayi sakamakon hango k’walla tab idanunta da yayi, ya sani Muhibbah ta canza sosai akan yanda take da idan zai mata adalci ya kamata ya zamto mai yafiya a gareta tinda duk d’an Adam ajizine, daidai da yaransu yanzu takan d’an basu kula fiyeda yanda take balagazantar dasu a baya don har wani sabo ne da SHAK’UWA ya soma shiga tsakaninta da yaran wanda ko shakka babu yaji dad’in hakan..... A hankali yasa hannu ya tallafota ya fad’o jikinsa, kaman jira take Aiko nan ta saki kuka mai tsuma zuciyar mai saurare... Ya shiga lallashinta yanda salon nasu ya soma canzawa, aiko nan ta sami damar janyo hankalin mijin nata har saida ta sami kulawa da soyayyarsa wanda ta jima bata sami irinsa ba..... *** Mamani taci gaba da salallami tana duban Sameer “Ikon Allah yanzu shi yaron nan Haladu ashe d’anuwan iyalinka ne...?” Sameer ya jinjina kai yace “Su biyu ne wajen iyayensu Mamani...” Mamani ta jinjina kai tace “Allah sarki Aiko Haladu yaron kirki ne, ni ai tuni munyi sabo dashi, lallai kaje gidan mutunci kayi aure Ubana, na tabbata matar taka ma mutuniyar arziki zata zama, yakamata yanzu kam ka kawo mana ita nan mu ganta mu saba, dama nayi magana da mahaifinka sashen gefena nan za’a gyara maka ku d’an zauna ko na k’ank’anin lokaci ne musan matar taka mu saba, Kaga ai yafi ta shigo cikin dangi a santa a saba da ita tinda Allah yayika D’an zuri’a....” Murmushi Sameer ya sakar mata kana yace “Babu damuwa Mamani yanda duk kikace hakan za’ai....” Mamani ta Washe baki cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa Ubana Allah dai shi maka Albarka, kai naji dad’in yin na’am da hukuncina da kayi.... Allah ya shiga lamuranka....” Sameer ya amsada Ameen Mamaninah ... Yai maganar yana d’an waige waige ganin baiji d’uriyar Raihanah ba... Kaman wacce ta kula yana neman wani abin tace “Akwai wani abin ne Ubana...?” D’an girgiza kai yayi kana yace “Em nace ina Raihaan take ne ban ganta ba...?” Mamani ta yab’e baki tace “Aw Raihanatu ai kuwa d’azu Marliya da Naja’atu suka shigo suka jajib’eta Wai sun tafi islamiya, babu yanda banyi ba ta bari jikin nata ya ida warkewa amma sai cemin tayi zata iya zuwa Wai hadda ya taru mata gwara taje ta rage....” D’an girgiza kai yai yana mai mik’ewa tsaye yake fad’in “Ciwon nata da saura bai gama warkewa ba she might catch infection out there... Ina ne islamiya nasu....?” Yanda yai maganar sosai damuwa ya nuna a fuskarsa har saida Mamani ta fahimci damuwar da fuskar nasa ya nuna.... “Nan layin baya ne, masu jajayen kaya zaka gansu....” Jinjina kai kurum Sameer yai kana ya nufi k’ofa yana fad’in “Sai na dawo Mamani.....” “A dawo lafiya...” Ta fad’i tana mai bin bayansa da kallo yanda ya fice cikin sauri..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *74* Layin bayansu ya nufa kaman yanda Mamani ta sanar dashi islamiyansu Raihanah nan yake, Aiko nan ya hangi wani dogon gini yanda sautin karatu ke fitowa ko shakka nan ne makarantar sannan ga baburan malaman a pappake a waje... Lokaci guda Sameer ya nufi ginin, a gefe ya paka motarsa kana ya sauk’a ya nufi cikin makarantar, wasu malamai ya samu kusan su hud’u a k’ofar wani aji tamkar tattaunawa suke, Sameer ya k’arasa ya masu sallama, gaba d’aya suka amsa mashi suna mai basa hannu alamun masabaha.... Nan Sameer d’in ya sanar dasu abindake tafe dashi... Malam Isyaku d’aya daga cikin malaman yace “Amma kuwa Raihana yarinyace mai k’wazo idan dai har zata iya zama inaga babu laifi a barta taci gaba da zuwa makarantar sabida ko d’azu da zan shige ajinsu naji tana bada haddarta tiryan tiryan harma tafi wad’anda suke zuwa makarantar, irinsu datse masu karatun babu dad’i....” D’an murmushi da gefen bakinsa Sameer yai kana yace “Wato Malam ba nak’i ta zauna bane, shi ciwo musamman k’una idan bai gama warkewa ba sam ba’a so ana shiga wajen da k’wayoyin cuta zasu iya shafan ciwon, ayi hak’uri a barta ta k’ara samun sauk’i sosai kafin ta dawo makarantar mai gaba d’aya...” Su Malam Ayuba suka shiga jinjina kai suna fad’in “Wannan gaskiya ne, ai komai saida lafiya....” Malam Isyaku da yaji hujjojin Sameer yafi nasa yana murmushi yake fad’in “Amma dai rankashidad’e kai d’in likitane... Don idan ba likita ba babu wanda zai tsaro wannan bayanai...” Gaba d’aya d’an darawa sukai kafin Malam Ayuba ya mik’e yana fad’in bari a kirawota.... Sameer yai masa godiya yanda sauran Malaman sukaci gaba da tattaunawarsu.... Mamakine ya cika Raihanah jin cewa Yayanta ne yazo d’aukanta, hartasu Marliya da Najah suma mamakin ne ya kamasu, gaba d’aya ma sai suka rasa wane yayan nasu ne yazo d’aukan Raihanah tinda abu ne mai kaman wuya kaji wani nasu yazo makarantar a baya, ko PTA meeting ne saidai suga ana zuwama wasu amma banda su shiyasa sosai abin ya basu mamaki.. Suna tafe tana d’an jan k’afar tata da bai ida warkewa ba tana sak’e sak’e da zullumin waye yazo d’aukanta har islamiya.... Bata ida tunanin ba ta hangosa gefen malamansu kansa kife bisa wayar salulansa, yana sanye cikin k’anan kaya, navy blue check wato riga mai zanen gidan dara long sleeve, haka jeans d’in jikinsa ma blue d’in ne, da matuk’ar wuya kaga Sameer da t-shirt idan dai ba check bane, akasarin kayan nasa check ne masu dogayen hannu da masu gajerun hannu, ta yanda da yawa wasu a asibitin nasu ma suke banbancesa kenan, wasu har lak’abi suke masa da Dr-check, duk ranan juma’a kuwa shigar dogayen kaya yake harda hula, saiko wani zubin yakan saka suit musamman idan zai halarci wani taron.... Wani irin muguwar fad’uwar gaba Raihanah taji, ko mai yasa Ya Ma’aruf zaizo d’aukarta...? Sai kuma ta soma tunanin Salma nurse mai mata dressing tasha sanar da ita irin k’aida da kaffa-kaffa da Dr Sameer ke dashi dashike akasarin hiran da Salma zata mata akan Sameer d’in ne, Salma batada zance saina Dr Sameer dukda cewa shid’in baisan tanayi ba... Kanta a k’asa ta k’araso tana gaida sauran malaman, suka amsa mata da sakin fuska had’ida mata sannu da jiki, ta d’an maidoda dubantaga Sameer wanda har lokacin idanunsa nakan waya.... A hankali ta furta “Ya Sameer ina yini....” Ya amsa mata a tak’aice kana yace “Ki k’arasa mota ina zuwa...” Jinjina masa kai kurum tai kana tace “Toh..” A tak’aice.... Saida ta d’anyi nisa da tafiya kafin ya ida abinda yake cikin wayar kana ya k’araso yaiwa malaman sallama... Tana nan tsaye jikin mota taji k’aran security lock alamun an bud’e motar, Aiko shid’inne ya k’araso fuskarsa sam babu walwala, bata tab’a ganinshi cikin yanayi irinta yau ba... K’asa k’asa take dubansa, tana jin sanda yace “Shige muje....” Babu musu ta bud’e marfin motar ta shige a d’arare,sai faman cije leb’e take a hankali bata son ya fahimci halinda take ciki don gaba d’aya wandon islamiyan nata data saka ya sosa ciwon ya fama kad’an.... Yana kunna motar sautin karatun Alk’ur’ani mai girma yaci gaba da tashi cikin muryar Sheik Sa’oud Shureim, da alama karatun yake saurare dama, ga wani k’amshi na musamman dake tashi cikin motar tasa, haka kurum taji wani irin nutsuwa ya sauk’ar mata cikin zuciyarta, da gefen idanu take satan kallonsa har wannan lokacin babu walwala saman kyakkyawan fuskarsa... Ta janye idanunta a hankali zuciyarta nabin k’ira’ar cikin suratu Yaseen yayinda ta maida dubanta gaba d’aya zuwaga window.... K’arar ringing d’in wayar salulansa k’irar Samsung shi ya sanya Sameer rage sautin karatun Alk’ur’anin.... Ya d’aga wayar wanda daji kasan daga can asibitin nasu ake nemansa..... Cikin muryarsa mai cikeda charisma da dad’in saurare yake fad’in “Ni kuma gashi bana kusa, ina Awwab yake... Contact him mana....” Magana akai daga d’aya b’angaren sai jinjina kai da yai yana furta “Ok ok gani nan zuwa, prepare the patients....” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai canza hanya da yai..... Raihanah ta dubesa da tsananin mamaki ganin ya canza hanyar gida, kaman yasan duban nasa take nan ta sinkayi muryarsa yana fad’in “Meyasa kika fita ba tareda sanina ba...?” Batakaiga basa amsa ba ya kuma jefo mata wata tambayar “Salma bata sanar dake k’a’idojina bane wanda duk patients d’ina dole subi wad’annan k’aidojin....?” Sai sannan ya d’an cire idanunsa daga kwalta ya kaikaito kad’an yana dubanta, gani yai idanunta a k’asa tana wasa da ‘yan yatsuna hannunta, a hankali ta furta “Kai hak’uri Yaya bazan sake ba....” Maida idanunsaga tuk’in dayeke yai ba tareda ya kuma cewa komai ba saima d’an k’ara volume d’in karatun da yai sakamakon ragewa da yayi sanda zai amsa waya... Raihanah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida lumshe idanu, ita duk damuwarta ma hanyar asibiti taga sun nufa ne, kenan ba yanzu zasu koma gida ba... Haka nan dai idanunta na lumshe taketa bin sautin karatun cikin zuciyarta da sam batasan bakinta na furtawa ba.... Sameer yakai dubansa gareta yaga yanda bakin nata ke furta karatun a hankali idanunta masu yalwan girma a lumshe, bai tab’a samun daman k’arema fuskarta kallo ba sai yau, Raihaan kaman yanda shi yake kiranta, bata a layin mata masu haske sannan kai tsaye bazaka kirata b’ak’a ba, hancinta ba mai tsawo bane hasalima ya d’an baje kad’an daga k’asa, full lips gareta dikda cewa bakin nata madaidaici ne kana iya hango d’an tudu kad’an da bakin nata kedashi haka nan tanada yalwan idanu da dogayen gashin ido wanda ya k’ara ma idanun nata kyau sannan tanada lostawar kumatu wanda ko magana take zakaga suna lotsawa karatun da take bi yanzu ma sai faman lotsawa suke, daga nesa ma bazakai mata kallon kyakkyawa ba harsai ka matso kusanta, haka nan suke ita da Nabilah sam basu d’auko haske irin na sauran family members d’in nasu ba, ita Raihanah kam ma bata ragewa mahaifiyarta komai ba sam bata kama da dangin Baba Alhaji wannan yasa kamanninta ya fita daban da sauran ‘yan gidan..... Shiyasa ma Haule ke mata lak’abi da dangi mayu... Tana jin alamun tsayawa ta bud’e idanunta, nan ta gansu a farfajiyan asibitin..... Sameer ya bud’e central lock kana ya mik’a hannunsa bayan motar ya d’auki wasu files da farar labcot d’insa... “Muje...” Kalmar da ya fad’i mata kenan.... Babu musu ta kama marfin motar ta fice tabi bayansa cikin sauri ga yanayin tafiyar tasa sassarfa ne ita gashi gaba d’aya tafiyar nata d’ingisawa ne... Yana tafe ma’aikatan asibitin na jefo masa gaisuwa duk yanda ya shige... Saida zai d’auki wata hanya ya tunada Raihanah... Juyowa yai yana dubanta yaga tana jan k’afarta da k’yar da k’yar.... Tsayuwa yai yana observing d’inta kana ya girgiza kansa a hankali, yasan hakan ka iya faruwa... Saida ta k’araso kusansa kanta a k’asa, duk a tsarge take ganin yanda ya k’urawa k’afarta idanu, hannu yasa ya amshi jakar islamiyar nata yana mai furta “Give me that....” Ita dai sakar mishi kawai tai tana mai tambayar kanta ko maiyasa ma ta fito da jakar oho dama barinta tai a mota... Wani office taga ya bud’e masu wanda ga dukkan alamu mallakarsa ne.... Ya shige ciki tabi bayansa, Office ne maiji da lafiya gashi ya had’uda gayu don mai office d’in ya k’ure wajen tsafta da gayu... Tai tsaye sororo yayinda Sameer ke jikin table yana duba laptop d’in dake bisa table d’in... Saida har ya gama abinda zaiyi ya juyo ya ganta nan tsaye sai rarraba idanu take kaman taci kud’in aika.... Sofa dake gefe ya mata nuni dashi kana yace “Ki zauna acan...” Babu musu tai yanda yace.... Tana gani ya tattari wasu takardun da labcot d’insa ya nufi k’ofa, har yakai k’ofa ya juyo ya d’an dubeta kana yace “Idan zakiyi sallah ga bathroom and akwai abin sallah a gefen wancan drawer d’in... I won’t take long kinji... Ki jirani a nan...” Cikin sauri ta shiga mana masa kai sai faman muzurai take... Har ya kuma juyawa zai fice ya d’anyi birki ya kuma juyowa, kai tsaye jikin k’aramar fridge dake a cikin Office d’in ya nufa ya bud’e ya ciro goran fresh yogurt ya ije gefenta, daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice cikin sauri had’ida jan k’ofar office d’in.... A daidai k’ofa ya had’uda Awwab yana fad’in “Dama zuwa nai na fito da kai don ance min ka iso ka nufi Office....” Suna tafe cikin sassarfa Sameer yake fad’in “Wai dama kana nan shine sai an nemoni...?” Suna nufa wata k’ofar Awwab ke fad’in “Ai tinda kaga an dage a nemoka is serious kuma ba mutum d’aya ba kusan three patients ke jiranmu, na shiga na gansu gasu yara abun babu dad’in gani, Allah ka tsaremu daga sharrin wuta duniya da lahira..” Ameen Sameer ya amsa dashi daidai sanda suke isowa d’akin theatre d’in.... Raihanah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta sami daman k’are ma ofishin kallo, takai dubantaga lallausar carpet d’in da k’afafunta ke bisa tana mai ayyanawa cikin ranta _Wannan ma ai ya isheni sallah basai na d’auko abin sallah ba_ don already lokacin magrib ya kusa.... K’ofar da ya nuna mata matsayin bathroom nan cikin office d’in ta nufa, saidai hoton da ta hanga saman table d’insa cikin k’aramar frame ya mugun jan hankalinta, ta k’arasa jikin table d’in tana mai k’arema hoton kallo, murmushi saman fuskarta ta d’auki hoton tana duba, ko ba’ace ba wannan ce matarsa, sunyi kyau har sun gaji sannan sun bala’in dacewa da juna, duk yanda gayu yakai wannan mata tasa takai sannan ko ba’ace ba kasan suna matuk’ar k’aunar junansu.... Sun mata kyau har sun gaji... Ta jima tana duban hoton kafin ta maida ta aje saman table d’in.... Can gefe kuma jikin gini an k’awata wajen ne da tarin Awards and Medals na shaidan d’inbin nasarori da ya samu, nan ta k’arasa tana bi tana karantawa d’aya bayan d’aya, duk wanda ta karanta sai ta saki murmushi hardai ta jiyo ana kiran sallah daga masallacin cikin asibitin, nan ta nufi bathroom d’in tayo alwala kaman yanda ya nuna mata.... Har ta ida sallan magrib babu Sameer babu dalilinsa.... Haka nan tai zaune ta rabka uban tagumi tana zaman jiran tsammani.... *** K’arfe bakwai da rabi na dare ta shigo garin Kano, Allah ne kawai ya kiyaye mata hanya amma kam ita kanta tasan tayi rough driving yau d’in, wai donma tayi gamo da checkpoints da dama yau d’in a hanya amma da tuni ta tsufa garin Kano.... Kai tsaye unguwar nasu ta nufa, tana ganin gidan da Sameer ya kama masu da sunan nasu gidan ta tab’e baki ta nufi gidan da takeda tabbacin na sabbin iyayensa ne.... Koda ta ida parking saida ta tsaya tana k’arema gidan kallo fuska a yatsine, Wai yanzu nan shine mahaifar Partner d’inta, Wai yanzu wad’annan sune tushen partner... Kai haba Haba inaa da sakel, Wllhi alwashi ta d’auka duk yanda zatai saita raba Sameer da wad’annan mutanen... Lokaci guda ta fito daga cikin motar kana ta d’auki handbag d’inta dake bisa d’aya seat d’in, ga mayafin dama da ba wani na kirki bane an sab’asa bisa kafad’a.... Sai faman kad’a d’an makullin mota take, Aiko nan almajiran dake zama k’ofar gidan suka mata chaaa suna fad’in “Hajiya Allah ya kiyaye... Hajiya Allah ya kare.....” Sunayi suna kallonta tamkar a zuba masu ita a kwanon baran nasu sun cinyeta, wasu na faman shafa motar tata..... Siyama kaman ta had’iyi rai don takaici... Sai faman toshe hanci take tana k’yank’yan da jikinta... Wani uban tsawa ta dararawa Almajiran nan tana fad’in “Kai ku matsa min a hanya kafin ku shafa min wani cutan....!!” Tai maganar tana mai ci gaba da toshe hanci had’ida jan skirt d’inta sama ga takalaminta mai uban tsini da take taku dashi cikin k’warewa... D’ayan Almajirin yace “Basaida na fad’a maku ba karkuje arniya ce gashi kun gani ai....” Suka kwashe da dariya suna duban yanda Siyama ke taku sauran har suna kwaikwayon yanayin tafiyar tata.... D’aya da bai ida cin tuwo miyar kukan dake cikin kwanon baransa ba jikin farar benz d’in Siyama ya isa Aiko nan ya mata fenti da tuwo miyar kukan nan.... Yaran suka kuma tintsirewa da dariya kana suka bar wajen gudun kada a gansu..: Ko darajan sallama basu samu daga Siyama ba, tana tsaye tsakiyar verandar Mamy sai faman yatsina fuska take tana kuma k’arema gidan kallo don wancan zuwan nata ana makokin Kausar sannan zuwan na Nabila ne shiyasa sam bata samu ta k’arema gidan kallo ba, hannu a kunkumi take kuma juya kai tana jinjina kai baki a tab’e take bin lungu da sak’o na gidan da kallo “Tabb! I can’t believe this... Wai wannan gidan tantabarun shine gidansu Partner, wllhi sam bazata saku ba, dole na raba mijina da wad’annan matsiyatan...” Ta k’arashe tana mai kuma yamutsa fuska.... Fitowar Mamy kenan daga kitchen ta hangi mata tsaye k’ofar parlornta sai faman kalle kalle take.... Mamaki ya kama Mamy tana tunanin toh ko wace wannan..... Lokaci guda Mamy ta nufota tana mai furta “Sannu baiwar Allah.... Lafiya....? Daga ina....?” A tare Mamy ta jefowa Siyama wad’annan tambayoyi... Maimakon ta bata amsa ko ta sami darajan gaisuwa saima kaikaitowa da tai tana mai k’arema wacceke mata tambayoyin kallo daga sama har k’asa.... Hasken wutan lantarkin da ya gauraye cikin gidan shi ya baiwa Siyama daman ganin cikin k’wayar idanun Mamy wanda hakan ya bata tabbacin wannan matar tanada alak’a mai k’arfi da Sameer d’inta don ga tabbaci daga k’wayan idanunta wanda yake baisa maraba dana Sameer, cikin bak’in nasu bai cika bak’i sosai ba ya d’anyi kalan ruwan k’asa kad’an maimakon bak’i.... A hankali Siyama ta saki murmushi bayan ta ida duban Mamy daga sama zuwa k’asa kana tace “Mijina nazo nema....” Karaf a kunnuwar Nabilah da fitowarta kenan daga parlor hannunta rik’eda plate d’in data ida cin abinci.... Aiko Nabilah ta saki murmushi sakamakon hango Siyama da tai, daga yanda take kafin Mamy ta sami zarafin baiwa Siyama amsa ta bud’e murya tace “Finally our unbearable sister in-law has arrived...” Tai maganar tana dariya lokaci guda ta iso gaban Siyama wacce k’irjinta ya soma bugu tinda ta sinkayo muryar Nabilah.... Mamy duban Nabilah dake murmusawa tana k’arewa Siyama kallo tai kana tace “Kin santa ne...?” Nabilah ta kuma murmusawa kana ta dubi Siyama tace “A gidan nan mun girma da mutuntawa da daraja na sama dakai, but unfortunately Mamy Sirkarki ba haka take ba...!” Ta k’arashe maganar tana mai watsawa Siyama muguwar kallo... Mamy da kanta gaba d’aya ya d’aure d’an bud’e murya tai taceda Nabilah “Wai meke faruwa ne... wacece wannan Nabilah...?” Gyara tsayuwa Nabilah tai still idanunta naga Siyama da suke faman aikawa juna muguwar kallo tamkar su shak’e juna kana ta saki murmushi a hankali tana mai k’arewa Siyama kallo daga sama zuwa k’asa kana tace “Wannan ba kowa bace Mamy face sirkarki matar Yaya Ma’aruf d’anki...” Allah sarki Mamy nan da nan murmushi ya cika fuskarta ta shiga d’aga labulen parlor tana fad’in “A a lale lale bismillah, Aiko Ma’aruf bai sanar damu zuwan naki ba, yi hak’uri da rashin fahimtar da na maki, ke Nabilah maza ki kirawo Auntyn ku.... Ta k’arashe tana gyarawa Siyama yanda zata zauna.... Nabilah kuwa dad’a matsowa kusan Siyama da tai tsaye tana hura hanci tai, murmushi saman fuskarta take kaiwa Siyama runguma lokaci guda take furta “Welcome to the Family Sister in-law...” Cikin sigan rad’a saitin kunnen Siyama take rad’a mata “I’ve got a lot of surprises for you Aunty Siyama... Get ready to receive them...” Tana ida fad’in haka ta saki plate d’in hannunta aiko sai jikin mayafin Siyama sauran miyan dake jikin plate d’in ya b’ata mayafin nata gaba d’aya.... Siyama ta d’ago idanunta da suka kad’a sukai jazir tana duban Nabilah dake ci gaba da murmushi, sai kuma ta zaro idanuwa waje tana fad’in “Aw sorry sorry, wayyo I’m too clumsy.... Gashi kuma bakicin miyar kuka na b’ata miki jiki dashi... I’m sorry... K’arasa ciki sirkarki na jiranki... Bara naje na kirawo sauran sirakan naki don ku gana da juna....” Tana ida fad’in haka ta tintsire da dariya kana tasa kai ta wuce tana wani kad’a jiki irin yanda takeyi idan ‘yan shak’iyancinta suna kusa.... Siyama data koma tamkar mutum mutumi shaye da tsananin mamaki take duban gyalenta da ya koma koriya koriya ga k’amshin kuka da daddawa dake tashi jikinta..... Sai faman yatsine yastine take har saida Mamy ta kuma mata iso kafin ta shigo parlorn shima ba don taso ba sai don wani irin k’warjini da matar tai mata kuma wani ikon Allah ta nemi duk wani courage na watsawa matar rashin mutunci ta rasa musamman da taji Nabilah na cewa sirkartace.... Kan kace mai tuni Mamy ta cika gaban Siyama da kayan motsa baki wanda ko kallo basu ishi Siyamar ba....K’afafu d’aya bisa d’aya take ci gaba da yatsine yatsine tana faman k’yank’yan da jikinta tamkar wacce ke zaune cikin bola.... *** Tin tana karanta calendar dake manne jikin bangon Office d’in har dai ta soma gyangyad’awa, babu Sameer babu dalilinsa, har aka kirawo isha ta tashi tayi, nan yanda tai sallar ta d’an kishingid’a gyangyad’i na sand’arta.... *** A can gida kuwa sai tururwar zuwa ganin matar Ma’aruf ake, su matan Baffah Ado da yaransu, su Sakinah Basma Sadiya da sauransu, su Sakina iyalan gulma abin nema ya samu dama ana son ganin matar Ya Ma’aruf duk wannan gayu da ajin nasa, harda d’aukar takalminta sukai bakin k’ofa suna k’arema takalmin kallo harta lambar size d’in takalmin saida suka duba, Basma kaw har saka takalmin saida tai, Siyama dake hangosu daga cikin labulen parlorn tamkar ta d’aura hannu aka ta zunduma ihu haka taji, ina zata iya standing wad’Annan halittun da sunan dangin mijinta, ko a mafarki bata tab’a hasasho tsayuwa inuwa guda da irin wad’annan mutanen ba.... Muryar Aunty Lami da tun shigowarta ta kasa motsawa daga kusan Siyama ya dawoda Siyamar daga duniyar tunaninda ta tafi.... Saida ta murmusa ta kuma gyara zama had’ida waigawa gefe da gefe ta tabbata babu kowa a parlorn sai su biyu kana tace “Sirkarmu kenan... Ai na fad’a miki indai mutanen gidan nan ne saidai fah kiyi hak’uri don gaba d’aya haka suke, wasu irin mutane ne nima nan da kike gani da k’yar nai adopting zama dasu... Amma karki damu with time zaki saba zaibi jikinki and if you really loves Ma’aruf, then you’ve to put up with his family....” Batakai aya ba Siyama dake faman watsa mata kallon k’ask’anci ta tari zancen da fad’in “I love him more than love itself, kuma mun riga mun tsara rayuwarmu babu ku cikin rayuwarmu and I assure you I’ll do everything in my power naga na rabashi da wannan rayuwar da ya jefa kansa ciki sabida he doesn’t belong here...” Ta k’arashe tana mai juya idanu cikin salo na harara.... Wani irin dad’i ne ya mamaye zuciyar Lami, suna neman hanyar kauda Ma’aruf a karo na biyu toh ga dama cikin sauk’i ya samesu, indai har shida wannan shed’aniyar matar tasa soyayyarsu mai k’arfi ne tsaf tayi imani zata rabashi da kowa nashi suyi nesa dasu....Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai duban Siyama da hankalinta yafi tafiya zuwa ga kiran da taketa dannawa a waya ba’a d’agawa, sai faman huci take tana hura hanci, ta kirasa yafi sau babu adadi bai d’agawa, kuma ita haka take idan tana son abu toh fa sai ta samu, dan haka ci gaba tai da kiran nasa... Raihanah da tuni bacci b’arawo ya saceta cikin baccin nata takejin ringing d’in waya yak’i k’arewa, ta bud’e idanunta a hankali yanda taji wayar naci gaba da ruri kuma ba’ada niyyan daina kira... A hankali ta mik’e ta isa jikin table d’in nasa yanda ya mance wayar nashi gashi bai kashe ba... K’urama screen d’in wayar idanu tai yanda taga sunan wandake kiran ya bayyanada Partner, “Partner..” Ta nanata a hankali, nan ta shiga tunanin kalmar tana sosa idanunta da bai ida wartsakewa daga d’an baccin da tai ba, sam tunaninta bai kawo mata tace matarsa bace Partner, saima tinanin nata ya tafi wani wajen daban ta soma tunanin toh kodai work partner d’insa ne...? Toh ko dai yayi zaton a wani wajen ya mance wayar ya amshi na abokin nasa dan ya kira yaji ina ya barta bacin haka wannan kira tai yawa, bata ida tunanin ba kiran ya kuma shigowa... Still tai tana kallo wata zuciyar na cewa toh ki d’aga kiji wannan kira k’ila ba lafiya ba... A hankali tasa hannu ta d’aga wayar sallama saman bakinta ga muryar tata da sauran bacci a ciki.... Zumbur Siyama ta mik’e daga d’aya b’angaren jin mace ta amsa wayar mijinta zuciyarta na wani irin tsinkewa.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *75* “Wacece ke...?” Kalmar da Raihana taji an fad’i kenan daga d’aya b’angaren... Tamkar wacce aka zabura haka tai zumbur ta ware idanunta, ragowar baccin taji ya watse, lokaci guda ta nemi baccin da takeji ta rasa... Kasa furta komai tayi sai raba idanu da take tamkar mage a tukunya.... Siyama da tuni jikinta ya d’auki rawa sabida tsananin tashin hankali da kishi da suka sauk’ar mata lokaci guda, cikin wani irin murya mai cikeda kaushi take kuma furta “Nace wacece ke...? Sannan mai ya had’aki da wayar mijina..?!!!” Jin Siyama ta ambaci wayar mijinta ya kuma sa gaban Raihana fad’uwa, k’irjinta tamkar wacce aka ije mata k’aton dutse... Cikin sauri ta cire wayar daga kunnenta tana duban screen d’in, k’ara karanta sunan tai Partner... Da sauri ta rintse idanunta tana mai dafe kanta da jinjna wauta irin tata, sam bata kawo sunanta Partner matarsa ya sakawa ba... Tana jiyowa daga can b’angaren Siyama naci gaba da fad’in hello hello... Bata iya amsata ba sai katse kiran da tayi cikin sauri, ta koma mazauninta da sauri tana mai ci gaba da rarraba idanu don haka kurum muryar matar tasa ya mugun firgitata.... A can kuwa Siyama tsaye ta mik’e tana kuma neman layin Sameer but still ba’a d’agawa, k’oluluwan tashin hankali takai, a iya rayuwarta abinda take tsoro ace Sameer ya soma biye biyen mata, a yanda take da muguwar kishin mijinta tabbas tasan zata iya yin komai to keep him all alone for herself.... Aunty Lami ta kafeta da idanu kana ta d’an gyara zama had’ida matsowa kusan Siyama da gaba d’aya bata a hayyacinta kana tace “Ya mijin naki....?” Wani irin duba Siyama ta watsa mata ba tareda tace komai ba.... Aunty Lami ta murmusa, tsaye ta mik’e ta matsoda bakinta saitin kunnen Siyama, cikin sigan rad’a take furta “Kiyi hattara da ahalin gidan nan suna gab da rabaki da Sameer, amma shawarice idan kin d’auka....” Tana ida fad’in haka ta saki murmushi kana ta fice salin alin.... Kallo Siyama tabita dashi har ta b’ace ma ganinta kafin ta fuzar da iska mai zafi... Muryar wata Dattijuwa ce ya katseta daga duniyar tunanin neman mafitawa rayuwarsu ita da Partner da tai..... Nabilah na rik’eda Mamani yayinda Mamani taci gaba da dogarawa tana fad’in “Wai ina kishiyar tawa takene...? Tinda kishi ya hana ta shigo ta gaidani gani nan ni zan shigo na gaidata da kaina.... Ke Mariya ina kika b’oye min kishiyar tawa ce...?” Nabilah dake rik’eda ita tana murmusawa take furta “Kedai mu shiga daga ciki Mamani kinsan kishiyar taki taci uwar gayu tafiya ma wahala ke mata....” Ta k’arashe maganar sanda take taimakawa Mamani ta zauna saman kujerar gefen Siyama... Banda huci da tururi Siyama bata komai, sai aikawa Nabilah kallon tsana da take, Nabilah kaw ko ajikinta murmushi ne fal fuskarta.... Gyara zama sosai Mamani tai had’ida kaikaitowa tana fuskantar Siyama, ta kuwa washe baki takai duka hannayenta biyu ta kamo hannayen Siyama, cikeda jin dad’i take furta “Allahu Akbar... Oh ni Halimatu ashe dai rana irinta yau zatazo... Ashe zanga matar Ma’aruf kafin na bar duniya... Saura kuma naga d’iyoyinsa.... Sannu kinji ‘yar nan...” Ta d’anja fasali jin Siyama ta mata dinkim bata amsata ba saima ta mujiya data zuba mata tamkar taga wani halitta daga wani planet.... Juyowa tai ta dubi Nabilah dake k’ok’arin k’unshe dariyarta Marliya na girgiza kai wa Nabilar kana Mamani tace “Ke Nabilatu Wai bata magana ne...? Kodai kishiyar tawa bihim ce... Ya ina mata magana ta zuba min wannan pici picin idanun nata kaman ni na sammata, wannan badon tsufa danai ba ma nawa idanun sunfi nata girma...” Ta k’arashe tana mai gwalalo idanunta a fuskar Siyama wacce lamarin Mamani ya soma bata tsoro... Daga Marliya har Nabilah kasa rik’e dariyarsu sukai... Mamani ta juyo garesu tana fad’in “Kai bani son k’aniya... Ku fad’a min meke faruwa a nan... wacece wannan...? Idan kuma yaren da nake ne bataji kuzo ku mata wanda zataji kafin na tashi na sassab’a maku...!!” Nabilah tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Mamani kinsan kishiyar taki girman turai ce yawo cikin gajimare k’ila dai bata fahimtar abinda kike fad’i ne... Ki canza mata harshe...” Mamani ta maida dubantaga Siyama wacce ta kasa d’auke idanu daga barin duban Dattijuwar kana tace “Auho kice min dangin nasara Ma’aruf ya auro... Ke kaw kinsha bamabam da Haladu yaron arziki... Da kika tashi zuwa cikin danginsa sai ki koyo yaren da suke fahimta... Fi’ilin banza da wofi, yo har ni za’a nunawa yaren jajayen kunne... Ke barikiji na fad’i miki sanda Mammadu na ke raye babu kalan hazon da bai k’etara dani ba... Yo maima kuka samu ‘yan k’arshen zamani....” Ganin Mamani ta saki layi ta fara zuba masifa yasa Marliya duban ‘yar uwarta Nabilah da duniyar tai mata dad’i gamon da takeso Mamani da Siyama, girgiza kai kurum Marliya tai kana tace “Mamani Aunty Siyama tana saurarenki kawai dai baki bata dama tayi magana bane tintinin ke kiketa magana tin shigowarki babu ko hutawa..... Kuma zataje gaidaki kenan sai gaki nan kin shigo...” “Ke dalla chan rufe min baki, uwar kinibibi, yo gani zabiya ko mai...? Inyi...?” Tai maganar tana mai tsare Marliya da idanu.... Cikin sauri Nabilah ta kamo Mamani tana fad’in “Mamani muje kinji zata shigo har sashenki ta gaisheki idan bata gaisheki a nan ba, wanda zai sata na dole na zuwa....” Ta k’arashe tana mai watsawa Siyama muguwar kallo.... Mamani ta mik’e tana ci gaba da sababi da yab’awa Siyama mugayen maganganu... Suna tafe sashenta take ci gaba da fad’in “Inyi kajimin ja’irar yarinya, yo wannan badon Yayanku yace min ‘yaruwar Haladu bace sai nace babu abinda ya had’asa da wannan mai k’irar zabon, Banda Farin fata da dogon hanci banga mai Yayanku ya gani tattareda wannan mai k’irar itacen ba, ko ni nan a haka nafita kyaun gani....” Nabilah ta gyara mata cushion tanaji Mamanin naci gaba da sababi har ta zauna kana ta umarceta ta nemo wayar salulanta ta kirawo mata Yayansu Ma’aruf gashi su Najah sunce shine yaje makaranta ya d’auki Raihanah kuma har yanzu basu dawo ba, ga wannan matar tasa mai suffan karan rake data kuma b’ata mata zuciya.... Sake kira Nabilah tai tace da ita wayar bata shiga.... Mamani ta jinjina kai tace “Ko wata duniyar yakaimin jika oho.... Kodashike jika na yaron arziki ne bazaiyi wani abu maras kyau ba, Allah sa dai lafiya suke yanda yanzu duniyar tamu ta koma....” Nabilah ta amsada Ameen dai Mamani, k’ila kiran gaggawa akai masa daga can asibitin nasu sai ya wuce da ita....ta k’arada kinason wani abu ne...?” D’an dubanta Mamanin tai kana tace “Kunna min talabijin na rage takaicin wancan zabuwar matar Yayan taku....” Dariya ya kusan kufcewa Nabilah, kunna mata TV d’in tai ta silale ta fice don tanaji har lokacin sababi take.... A can parlorn Abbah ma jajen rashin dawowar Sameer d’in da Raihanan suke ga kuma wayarsa da bata shiga, sannan ga matarsa data bayyana wanda sam Sameer d’in bai sanar dasu zuwan nata ba..... Mamy ta kuma dialing wayar amma bata shiga... Jigum tai tana mai furta “Allah sa dai lafiya suke...” Abbah dake faman zagaye parlorn hannayensa hard’e a baya iska ya fuzar kana yace “Amma ai koda emergency ne ya taso masa sai ya kira ya sanar damu don kar mu damu, ba ya d’auki yarinya ya tafi da ita...” Mamy tace “Alhaji Raihanah fah patient d’insa ce ta yuwu zuwa asibitin da ita ne ya kama shisa ya tafi da ita...” Abbah yace “Wannan duk ba hujja bace....” Bata kuma cewa komai ba sai sadda kanta k’asa da tai.... Abin magana da bai kasawa a gidan, tuni an soma yayatawa tsakanin sashensu Basma su Sakina, Ya Ma’aruf ya d’auki Raihanah daga islamiya ba’asan yanda sukaje ba ga matarsa ma nan gidan tana jiransa.... Lami ma tuni tayi waya ta shafawa k’awarta Haule halinda ake ciki..... Haule kaw tace bataga ta zama ba, dama ya samesu, dole suyi amfani da wannan damar.... Sahariyya da Hajiya ta ida wayar a gabanta bore ta dingayi tana fad’in wllhi sai taci uwar Raihanah muddin bata janye idanunta kan Ya Ma’aruf, shegiya k’onanniyar banza.... Najah dai batace uffan ba saima mik’ewa da take k’ok’arinyi.... Sahariyya ta janyota daga nan yanda take zaune tace “Munafuka hardake kuke had’e kai da wancan k’onanniyar... Shine dan munafunci ko ki fad’a min shi yaje islamiyar taku ya d’auketa.... Toh wllhi idan za’a mutu ni ce nan zan aureshi kuma sai na mata iyaka da mijina....” Najah kallonta’yaruwar tata take kana ta tintsire da dariya tace “Addah Sahariyya kina bani dariya Wllhi, shin duk fah wannan kunfan baki da hura hanci da d’aga jijiyan wuya da kike shifa Ya Ma’aruf d’in baima San kinayi ba, kuma ai inaga ba akan Raiha zaki d’aga hankali ba, kan matarsa data iso zaki d’aga hankali, indai Raihanah ce na rantse miki bai d’auketa matsayin komai ba face ‘yar k’aramar k’anwa kuma patient d’insa da yai treating d’inta....Ki tada hankali kan Aunty Siyama wacce taji gayu tasha gayu ta k’oshi, ki soma tunanin yanda zakiyi gogawa da ita wajen kishi amma ba Raihanah ba...” Ta k’arashe tana mai janye hannunta had’ida kuma tintsirewa da dariya.... Jikina sanyaye Sahariyya ta sakar mata hannu, tana mai k’arewa kanta kallo maganganun Najah na mata yawo a kwanyarta cewa tai tunanin idan zata gogawa da matarsa wacce take ‘yar gayu wajen kishi.... Kai dole koda d’ingishi ne sai taje taga matar Ya Ma’aruf taga kalanta.... Ta d’aga kai tana duban Hajiya dake faman cangwala k’afafu da k’yar tana kuma aza mayafi lokaci guda ta dubi Sahariyyar tace “Idan Alhaji ya dawo kice na tafi can gidan....” Ai bata kai aya ba Sahariyya ta katseta da fad’in “Nima zanje Hajiya...” Haule ta dubeta shek’ek’e kana tace “Da wannan k’afar taki da bata ida warkewa ba, idan abin gudu ya biyomu a hanya nayi yaya dake...?” Sahariyya batako kulata ba ta rarrafa ta d’auko wata sandar gora da Hajiya ke jinginewa bayan k’ofa ta dafa tace “Wllhi sai naje naga matar tasa naga mai zata nuna min....” Tsaki kurum Hajiya tai don ta yadda Sahariyya ta gama haukacewa kan Ma’aruf, ita batama san a halin yanzu so take ta janye yunk’urin had’in yaranta da Ma’aruf d’in dataso ayi muddin ta sami hanyar salwantar dashi cikin sauk’i.... Ko sauraren Hajiya bata kumayi ba ta soma dogarawa tai gaba abinta... Hajiya ta take mata baya cikin cangwala k’afafu itama don dukansu biyu basu warke daga jinyar da suke ba.... Kallo Najah tabisu dashi had’ida girgiza kai tanai masu addu’an shiriya... Tana zaune Sahariyya ta shigo tana faman kumbure kumbure tana mitan Baba Alhaji ne ya korota yabi Hajiya suka tafi gidan Abbah Najah dai batace komai ba sai k’unshe dariyarta da tai, Sahariya ta galla mata harara tana fad’in “Dariyar mai kike...?” Najah tace “Allah baki hak’uri ta Ya Ma’aruf...” Wannan suna da Najah ta kira Sahariyya dashi sai taji gaba d’aya bak’in cikinta ya yaye... *** A can asibiti kuwa tinda ta amsa kiran matarsa mistakenly bata kuma bi takan wayarsa ba, ta matsu baizo sun tafi ba, babu kalan tagumin da batayi ba, alla alla take yazo yakaita gida... Tana nan zaune tana tunanin taji an turo k’ofa, muryoyinsu takeji wanda ko ba’ace ba shida abokin aikinsa ne, tanajin abokin nai masa sallama had’ida masa tinin wani conference na likitoci musamman surgeons da zasu halarta gobe.... shab shikam yama mance da wata Raihanah, har saida ya danno kai cikin Office d’in kafin ya tuna ashe tare sukazo, yai saurin kusto kai cikin Office d’in yana tunanin halinda ‘yar mutane da ya barta a ciki take.... Aiko tana ganinsa ta mik’e zumbur tamkar wacce aka zabura... Idanu suka k’urama juna kafin Raihanah tai saurin sadda nata idanun k’asa.... Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “Sorry na barki jiran office, bansan zan jima haka ba... Aikin ne yazo da complications...” Cikin sauri ta soma girgiza kai kana tace “A’a babu komai Yaya.... Idanma ka jima ai ceton rai ka tsaya yi, nasan ciwo da rad’ad’in k’unan wuta wanda bana fata ko mak’iyina ne yayi experiencing abinda naji... Da fatan aikin naku ya tafi yanda kuke so....?” Idanunsa akanta tamkar mai nazari kana ya jinjina kai a hankali yace “It was successful....” Yana kallon bakinta yanda take furta “Alhamdulillah” a hankali.... Kaman babu mai cewa komai cikinsu sai kuma yace “Muje nakaiki gida nasan suma sun damu....” Tamkar wacce take kan k’aya tai wuf ta nufi k’ofa tana mai jinjina kai.... Sameer ya kuma binta da kallo kana ya knarasa table d’insa ya d’auki wayar salulansa da ya mance nan.... Baiji mamakin ganin tarin kira ba don hakan ne wasu lokuta kan kasancewa dashi idan ya shiga aiki ya mance wayar a kunne... Jefata a ljihu kurum yai kafin ya takewa Raihanah baya ya rufo office d’in.... Suna tafe yana observing d’inta yanda take taka k’afar nata... Sunanta taji ya ambata for the first time wanda ya haifar mata da fad’uwan gaba ta kasa ci gaba da tafiya.... Sameer ya k’araso bai janye idanunsa daga k’afar nata ba.... “Sau nawa Salma ta miki dressing yau..?” Ya tambaya still idanunsa akan k’afar nata wanda ke rufe cikin uniform d’in islamiyarta.... Ba tareda ta d’ago ta dubesa ba tace “Yau batazo ba dama taje akwai yanda zataje yau d’in bazata samu zuwa ba....” Jinjina kai yai a hankali kana yace “Kenan yau ba’ai dressing ba...?” Nanma jinjina masa kai kurum tai still idanunta na k’asa.... Still yai tamkar mai nazari sai kuma yace “Biyoni....” Yai maganar yanabin wata k’ofa.... Babu musu ta take masa baya dikda bugu da k’irjinta keyi, tana mai zullumin ina kuma suka nufa... Dressing room taga an rubuta a k’ofar yanda suka nufa, kasancewar dare ne shiyasa babu jama’a sosai a asibitin, nurses d’inma wanda suke duty basu da yawa kaman na rana, da alama ma babu kowa cikin d’akin.... Offices d’in da suke wajen ya d’an lellek’a ko zai sami wacce zata mata dressing amma shiru bai samu ba... Ita dai kallon ikon Allah kurum take, tana gani ya isa jikin wasu drawers ya soma d’ibo kayan aiki, innalillahi ai nan bugun zuciyar Raihanah ya k’aru, mai Ya Sameer ke k’ok’arin yi... Kaman wanda yasan tinanin da take... Idanunsa naga bandage d’in da yake had’awa yace “Tsorona kike...? I can hear your heartbeat.... Don’t worry I promise to be gentle....” Ita dai batace komai ba saima kallon hannunsa da take yanda yake shirya kayan dressing d’in... Sameer ya murmusa da gefen bakinsa still idanunsa naga abinda yake yace “Next time idan Salma ta sanar dake bazata sami zuwa ba ki sanar dani right away kinji koh, ya riga ya fara healing idan an bari aiki zai koma baya...” Jinjina masa kai kurum take amma sosai k’irjinta ke bugawa.... Ya d’ago idanunsa yana dubanta, sosai tsoro ya wanzu saman fuskarta, idanunta suka kuma firfitowa waje... Tinani take ta yanda zata fara bud’e k’afarta gashi kuma wando ne jikinta... Innalillahi itakam bala’in kunyarsa takeji, tsaye yayi yana nazarinta kaman wanda yasan tinanin da take.... Suna a haka muryar Awwab da wata nurse Christian wanda suka fito daga theatre tare ya katsesu... Mamaki ya cika Awwab ganin Sameer a d’akin dressing “A a Doc you still here, baka tafi ba wai....I thought ka tafi tuntunin.... Wait what are you doing here....?” Sam bai lura da Raihanah dake zaune gefe ba yaketa jerowa Sameer wad’annan tambayoyi... “Kaman muryar Margret naji, ko ba tare kuke ba...? Sameer ya bid’a ba tareda ya amsa d’aya daga cikin tambayoyin Awwab d’in ba.... “Eh tare muke she’s on duty....” Awwab yace yana mai duban Sameer d’in “Akwai wani abu ne...?” Ya tambaya yana kuma suban Sameer d’in.... D’an turo baki gaba kad’an yai had’ida duban cikin d’akin yanda Raihanah ke zaune... Le k’asa Awwab yai ya hango Raihanar.... “Who’s she...?” Awwab ya tambaya yana mai duban Sameer d’in..... Turasa Sameer yai suka fice gaba d’aya yana fad’in “Zaka kiramin Margret d’in ne tai mata dressing... I’ve to take this call...” Ya k’arashe yana k’ara wayar Abbah a kunnensa Da fad’a Abbah ya soma masa cewa ina ya d’auki Raihanah ya kaita, ga dare kuma bai sanarda kowa ba.... Sameer ya d’an sosa k’eyarsa kad’an kanshi a k’asa kaman Abban na kallonsa “Em Abbah ai hak’uri, kiran gaggawa na samu daga asibiti, amma gamu a hanya in sha Allah....” Abbah yace “Naji wannan, matarka kuma fah...? Kasan da zuwanta baka sanar damu ba....?” Sameer ya ware idanunsa a hankali “Abbah matata kuma...? Kana nufin Siyama tazo gida....?” Daga d’aya b’angaren Abbah yace “Baka san da zuwan nata ba kenan....?” Sam baiso iyayensa su fahimci wane irin zama suke da Siyama, k’ok’arin saita kansa yai kana yace “Oh...Har ta iso kenan... Kuyi hak’uri Abbah ban kawo maku ita da kaina ba amma gani a hanya in sha Allah....” Daga haka sallama sukai da Abban yana mai duban Mamy da tai jigum tana jiran ya ida wayar.... Mamy tace “Asibiti yake koh....?” Jinjina mata kai kurum Abbah yai kana yace “Mariya akwai abinda na fahimta a rayuwar auren yaron nan.... Kaman auren nasa cike yake da tarin matsaloli....” Ajiyan zuciya Mamy ta sauk’e a hankali “Nima nayi tunanin hakan tin sanda nai ido biyu da iyalin nasa, kuma bai kawo mana ita duk tsawon lokacin nan ba... Nayi tunanin na tambayesa sai kuma naga ba hurumina bane...” Jinjina kai Abbah yai a hankali kana yace “Wannan hakan matsalarsu tasu ne, ina fata su zamto masu warware matsalolinsu da kawunansu basai wani yaji ba...” Ta jinjina kai ba tareda ta furta komai ba sai nazarin abin da take.... *** Tsare Akram tai sosai da manyan idanunta tanai masa kallon tuhuma,lokaci guda kuma ta saki murmushi ta mik’e ta nufo yanda yake.... Gefe dashi ta zauna tana wani karkad’a jiki murmushi bai bar saman fuskarta ba.... “Akram I’m a business woman, sanin kanka ne ban dogara da dukiyar da mijina keda ita ba, inada tawa dukiyar.... Kuma ina mai tabbatar maka I can make you what your boss fails to make you.... Idanma baka son wannan I can offer you something more than that.....” Ta k’arashe tana kashe murya had’ida kashe masa idanu guda.... Mik’ewa tsaye yai yana mai murmusawa da gefen bakinsa kana yace “Duk ba sai kinyi wad’annan ba Hajiya, never bazan tab’a cin amanan Excellency irin haka ba, but rest assure auren da mijinki yake nema bazai tab’a yuwa ba.... Here is my plan....” Ziryan ziryan ya zayyano mata yanda abin zai kasance..... Ta saki murmushin jin dad’i kana tace “Who’s she... who’s the girl, sanar dani...” Nanma murmushin yai da gefen bakinsa kana yace “Sanin ko wacece ita to you is not necessary, just trust me, auren bazai tabbata ba....” Mik’e k’afa guda tai tana mai ci gaba da kad’a k’afar tata take furta “And I’m ever ready to support you financially, duk wani abinda ake buk’ata daga lefe zuwa sadaki zan baka kai har gidan da zaka ajeta ni nan zan baka....” Nanma dai murmushin yai kana yace “Karki damu Hajiya I’ve everything under control, idan bazaki damu ba ni zan wuce....” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye.... Muhibbah ta kuma sakin shu’umar murmushi kana tace “Naji dad’i da muka kasance on the same page.... And let me remind you this, ka tabbata ka cika alk’awarinka idan ba haka ba, you’ll both lose her daga kai har boss d’in naka... Coz when it comes to my husband I can be very dangerous.....” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta... Shid’inma murmushin yake kafin ya d’an tako gabanta kad’an, murmushin bai gushe saman fuskarsa ba hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa na jampa yake furta “You don’t want to have me as an enemy, coz I can expose your little secret... I know exactly the kind of business you run.... So idan baki so mijinki yasan musabbabin yawon k’asashen da matarsa keyi da sunan business trips, kada ki kuskura ki shiga hurumin Zulfa’u...” Zaro idanu waje tai tana dubansa da tsananin mamaki, ta had’iyi miyau da k’yar don batai tsammanin Akram zai iya sanin wannan sirri nata da ko danginta basu sani ba... Bai daina murmushin ba ya furta “Just a piece of advice, do not double cross me...” Daga haka sa kai yai ya fice daga parlorn cikin sauri..... Muhibbah ta sauk’e huci mai zafi ga kanta da ya d’auki chaji lokaci guda... Cikin sauri ta haura sama ta nufi drawer d’inta ta d’auko k’wayar had’ida tsura masa idanu... Lokaci guda ta shiga b’allewa tamkar zararriya haka ta shiga afawa a baki, saida ta afawa kusan hud’u lokaci guda kafin ta zube saman gado had’ida lumshe idanunta.... *** Daga bakin k’ofa yaja ya tsaya ganin har Sawwama ta dawo gidan, hularsa a karkace ya hard’e hannaye k’irji had’ida jinginuwa jikin k’ofar yana k’are mata kallo, kana ganinshi kasan yau a Hafiz d’insa ya fito.... Sawwama dake faman goge kayan kallo sam bataji motsin shigowarsa ba har saida ta mik’e zata nufi d’aki nan ta ganshi k’ik’am tsaye akanta ya kafeta da idanunsa masu sumar da ita.... Sosai ya mata kyau don tayi kewarsa sosai, tai saurin mik’ewa ta nufesa tana mai furta “Hafizina bansan kana tafe ba da na girka maka wani abin.... Muje ka kwanta ka huta yanzu zan shiga kitchen na dafo maka abinci mai sauk’i, kar ka damu Magajiya ta had’oni da duk wani abin buk’ata....” Kasa k’arashe maganan nata tai jin ko motsasa daga yanda yake ta kasa... Ta d’ago tana dubansa da mamaki, ta d’an saki murmushi kad’an.... “Lafiya dai Hafizina...?” “Uwarki ne ba lafiya...” Kalmar data sinkaya kenan daga bakin Hafiz, gabanta ya yanke ya fad’i... Sai yanzu ta tuna babu wani shirin asiri data dawo dashi gidan..... Ta saki murmushin yak’e “Haba Hafizina na riga na baka hak’uri, nasan muna son junanmu.... Mu baiwa maras d’a kunya muci gaba da zaman aurenmu, nai maka alk’awarin duk wasu abubuwa marassa kyau da nake a baya na dainasu daga yanzu, zan kula dakai yanda baka tsammani Hafizina....” Ta k’arashe tana marairaicewa..... Tamkar wanda ya tina wani abin ya murmusa da gefen bakinsa, ta gefenta ya rab’a ya shige cikin d’ajin yana wani faman k’obarewa..... Sawwama ta bisa da kallo dikda cewa tasha jinin jikinta da ganin yanayin Hafiz d’in....... *** A can gidan Abbah kuwa a parlorn Abban Mamani ta ritsa Sameer da iyayensa, ta yanda take shiga bata nan take fita ba, fad’i take “Inyi toh Wllhi sam bazata saku ba, wannan ai gubace ba macen zaman aure ba, ni nasan irin wannan matan barikin sam ba kunya bace dasu.....” Baba Alhaji ya tari zancen da fad’in “Hajiya ni dama na gama magana ga k’anwarsa Sahariyya zaune gida babu miji kawai sai a had’a aurensu don bazamu zuba idanu wannan yarinya da ya auro matsayin mata ta rainamu ba kuma Mamani ina mai tabbatar miki wannan yarinya da kike gani zata iya rabaki da jikanki a karo na biyu, tun kafin abin yakai nan mu aura masa ta gida kinga mun d’auresa....” Abbah duban Baba Alhaji kurum yai had’ida girgiza kai, yayinda Mamy ta kasa furta koda kalma guda, har lokacin kanta na k’asa... Sameer d’ago kansa yai yana duban wan mahaifin nasa da tsananin mamaki.... A hankali ya furta “Baba ku bani dama nayi magana da Siyama please...” Mamani ta katsesa da fad’in “Yo wani dama, wannan batu naka yayi daidai Alk’ali, yanzu basai anjima ba a soma shirye shiryen biki....” Abbah ya d’anyi gyaran murya kana yace “Amma Yaya, Mamani bawai nak’i maku bane wannan had’I, kaman yanda Ma’aruf ya buk’ata a basa dama yayi magana da iyalin nasa... Sannan Yaya baku tunanin abinda ya faru damu baya gameda had’in Hafiz da Zulfa’u ya maimaita kansa... Ni dai a ganina da an janye wannan batu...” Haba nan fah Baba Alhaji ya soma kumfan baki yana fad’in “Toh kinji koh, Mamani... Kinji abinda d’anki yake fad’i koh, a kullum anaso mutum ya kasance mai kyakkyawan zato amma banda Usman... Minene aibun yara na... Maiyasa zai dinga dawo da abinda ya riga ya wuce....Idan har haka ne wannan ya kuma tabbatar min bai d’aukeni matsayin d’anuwa ba kuma wanda yake gaba dashi... Na tabbata da ace d’aya daga cikin yaran Ado ko Wada ne tsaf zai amince amma dashike d’iyata ce shiyasa zai nuna k’yamarsa... Tinda haka ne ni na cire kaina da ahalina daga wannan zuri’a... Usman daga rana mai kaman ta yau ka mance kanada D’anuwa mai irin sunana...!” Daga haka yasa kai zai fice... Mamani dake hawaye tai saurin tare gabanshi tana fad’in “Shin sai na mutu ne ku sami jituwa tsakaninku...? Shin bazaku mance komai ku rik’e ‘yanuwantakarku ba.... Shin kuna tunanin mahaifinku dake kwance a k’asa zaiji dad’i da ace za’a tayar dashi a nuna masa yaransa sun kasa rik’e zumuntarsu balle su d’aura yaransu bisa... Shin wannan wace irin rayuwa ce mai cikeda rashin yafiya....!” Tai maganar tana mai dafe k’irjinta... A d’ari Abbah ya tashi ya tallafota yana mai bata baki da sanyaya mata zuciya, shima Baba Alhajin kasa fita yai sukai chaa kan mahaifiyar tasu ganin tana numfashi da k’yar... Sameer da tashin hankali ya nuna sosai saman fuskarsa, tuni ya umarcesu su kwantarta saman kujera a matsayinsa na likita.... Ruwa Mamy ta kawo ta mik’awa Sameer ya shiga baiwa Mamani yana fad’in ta d’auki a hankali.... Mamani ta bud’e idanunta da k’yar ta d’aura kan ahalinta... Baba Alhaji Abbah Mamy da kuma Sameer wanda gaba d’aya sannu suke mata... Bud’e baki tai da niyyar magana, Sameer yai saurin damk’e hannunta had’ida girgiza kai alamun kar tace komai, cikin nutsuwa da kwantar da hankali ya soma fad’in “Mamani bazamuso wani abu ya sameki ba, ban jima da sake had’uwa dake ba, ina fata Allah ya ara mana kwanaki masu tsawo wanda zanyi taredake Kakata... Duk dai ni ne matsalar a nan....” Ya d’ago yana duban Abbah kana ya dubi Mamy ma... Dawo da dubansaga Baba Alhaji yai kana yace “Baba na amince da zab’inka.... Zan auri d’iyarka kuma k’anwata idan hakan zai kawo peace a wannan family d’in....” Ya maido da dubansaga Mamani murmushi kwance saman fuskarta, a hankali ya kuma damk’e hannunta cikin nasa kana yace “Zan auri jikarki Mamaninah... Muna sonki muna son ki kasance cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali....” Hawayen Farin ciki ya sauka fuskar Mamani yayinda Baba Alhaji ya shiga Washe baki yana ayyanawa a ransa burinsa ya kusa cika... Abbah da Mamy kallon juna sukai kana suka dubi d’an nasu cikeda tausayawa... Tabbas sun sani d’an nasu sadaukar da farin cikinsa yai ga family d’insu... A hankali Mamy dake danne hawayenta tasa kai ta fice daga parlorn sim sim... Abbah duk’awa yai kad’an ya dafa kafad’an Sameer kana ya furta “Allah ya maka Albarka....” Mamani da Baba Alhaji a tare suka amsada Ameen Baba Alhaji naci gaba da fad’in ai sai a soma shirye shiryen biki a tsai da rana..... Daga yanda suke lab’e jikin window wani irin dad’i ne ya dabaibaye zukatansu... Haule tamkar tayi jifa da sandar hannunta ta buga tsalle haka taji, shikenan yanzu basuda wata matsala, Ma’aruf ya amince zai auri Sahariyya wacce a wajensu daidai take da ajalinsa... Ko wannan shu’umar matar bata basu had’in kai ba ga d’iyarsu zatai masu komai... Lami ta janyota suka koma gefe... Shewa suka saka had’ida tafe hannaye.... Haule ta gyara sandarta tace “Ke ni dama wannan shegiyar matar tasa da ganin yanda take kallon mutane nasan bazamu samu wani qofa ta wajenta ba... Yanzu komai zai zo mana cikin sauk’i....” Lami ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Anya kuwa Haule... Toh mai zai faru idan d’iyarki ta juya mana baya... Kuma nayi imani babu macen da zata sami wannan had’edd’en saurayi ta salwantar da rayuwarshi... Anya kinaga Sahariyya bazata fara son Sameer ba...?” Tsuka Hajiya taja kana tace “Uwar soyayya ce, yo sai mai, ai ita kanta bazata san tuggun da muk’e had’awa ba, ke nida mijina mun riga mun gama tsara komai, kinga idan Sahariyya ta auri Ma’aruf zamu sami k’ofa mai sauk’ine wajen tsunduma cikin rayuwarsa, idan bamu cimma burin hallak’asa ta wannan ba, ma’ana idan ya haye tuggunmu ko asirinmu yazo ya tonu daga baya kinga abin zaizo mana da sauk’i tinda mun zama sirakansa....” Lami ta d’anyi shiru tamkar mai nazari kana tace “Toh ni kuma fah... Da wane ido Alhaji Usman zai kalleni....?” Haule ta murmusa kana tace “Toh Banda abinko ai naki tonan sililin mai sauk’i ne akan Aminiyar sirri... Idan har za’a yafewa Aminiyar Sirri kinga kenan ya zama dole a yafe miki tinda duk kusanci da Ma’aruf tafimu..... Kinga idan wannan aure ma ya tabbata zamu had’asu fad’ane yasu yasu mu had’e mata baki mu d’aura duka laifi akanta... Kinga shikenan mun had’asu fad’a mun fita da fitarmu...” Lami ta shiga juya maganganun Haule tana jinjina basira irinta Haule kana tace “Kai amma kin birgeni Haule, Wato idan baka iya kama b’arawo ba shi b’arawo sai ya kama ka... Wannan shawari tayi daidai Hajiya Haule....” Haule ta dara kana tace “Babu wani shegen bokan da zai sake ci mana kud’i tinda duk Malamin da muka kai masa koke ce mana yake abu a duhu, da makirci kawai zamu kauda Ma’aruf a karo na biyu mu kuma b’adda Aminiyar Sirri tinda amfaninta ya k’are mana....” Shewa suka kuma sawa had’ida tafe hannaye, duniya tai masu dad’i... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RAO_ *76* Marliya da Nabilah ya tadda a parlor sunyi jigum sakamakon hawaye da suka gani fuskar Mahaifiyarsu dawowarta daga parlorn Abbah, duk a tunaninsu hakan ya faru ne dalilin zuwan Siyama matar Ya Ma’aruf.... Sameer ya dubesu yanda sukai jigum jigum kana yace “Ina Mamy...?” Sai sannan sukaji shigowar tashi, suka had’a baki wajen cewa “Sannu da shigowa Yaya..” Kana Nabilah ta amsa tambayar tasa da cewa “Mamy tana d’aki tun d’azu tak’i sanar damu meke damunta....” Marliya ta k’arada “Kuma tace mu fita mu bata waje she wants to be alone...” Shiru yai tamkar mai nazari kana ya jinjina kai yace “I’ll check on her...” Bai jira cewarsu ba ya nufi corridor da zai sadaka da d’akin.... Saida yai knocking da sallama saman bakinsa kana ya nemi izinin shiga... Saita kanta ta d’anyi had’ida goge hawayen fuskarta kana ta masa izinin shiga.... Tai k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta tana nuna masa wajen zama... Idanunsa akanta ya k’araso ya zauna kana ya sadda kansa k’asa... Zuciyarsa sai faman tafarfasa take sanda ya tuna kalan rashin mutunci da Mamani tace Siyama tayi a gidan, kansa na kife k’asa jijiyoyin goshinsa sunyi rud’u rud’u, shi kad’ai sai dunk’ule hannunsa yake yana murzasu, kaji tsoron mutumin da bai faye saurin fushi ba, idan yayi fushin nasa babu kyau.... Mamy ce ta katse shirun nasa da fad’in “Baban Abbah an shigo...” Sameer ya d’ago jajayen idanunsa wanda siririyar hawaye ke sauk’a ya sauk’esu kan mahaifiyarsa.... Ganin hawaye idanun d’an nata sai ya kuma d’aga hankalin Mamy, tai saurin tasowa daga wajen zamanta ta dawo yanda yake, hannayensa ya kamo ta rik’e kana tace “Na sani ka yanke hukunci mai tsauri ma kanka,... Ma’aruf idan baka son wannan aure da suke shirin maka dan Allah ka barni na tsaya maka d’ana for the first time, bana buk’atan komai face Farin cikinka.... Kaji d’ahna....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Rungume Mamy yayi lokaci guda kuka mai k’arfi ya kufce masa... Wanda har saida yasa jikin Mamy yin sanyi.... Cikin muryar kuka yake “I’m sorry Mamy... Dan Allah ku yafe min.... Ban tab’a danasanin auren Siyama irinta yau ba... Amma Mamy na muku alk’awari Siyama bazata sake tozartaku ba, ku yafe min....!!!” Ya k’arashe cikin shesshek’ar Kuka.... Jikin Mamy a sanyaye ta d’ago fuskarsa tana fad’in “No Ma’aruf, matarka bata tozartamu ba, kasan Kakarka akwai tsufa a tattareda ita shiyasa, rashin fahimtace kawai, kuma wannan shine zuwarta na fari... Amma idan mukace ta tozartamu mun mata k’age... Tasa hannu tana share hawayen da suka wanke masa fuska wanda ya koma jazir kana tace “Don’t take any drastic measure kaji koh, ka zauna kayi magana da matarka na tabbata zakuyi sorting komai, ai bata san damu ba, itama abun yazo mata ba zata ne... So ka bata dama da lokaci ta san family d’inka kaji d’ahna....” K’uri kawai yaiwa Mamy cikeda jinjina dattako da hak’uri irin nata... A hankali ya furta “Mamy are you covering up for her...?” Girgiza masa kai tai murmushi kwance saman fuskarta kana tace “A’a D’anah, haka abin yake, Siyama bata mana komai ba, ka tashe kaje gida ka sameta , dan d’azu da na shigo ina nemanta Nabilah tace min ka shigo ka janyota waje bata kuma dawowa ba....” D’an kauda fuskarsa yai yana duban wani gefen kana yace “Ki kwanta ki huta Mamy, and karki sa damuwa a ranki, ni nace zan auri d’iyar Baba Alhaji idan har hakan zai kawo tsakanin iyayena....” Mamy ta dubeshi cikeda tausayawa kana tace “Ka tabbata Ma’aruf...?” Jinjina mata kai yai a hankali kana yace “Na tabbata Mamy... Ki daina sa damuwa ma ranki, hakan bazai kyau ma lafiyarki ba...” Murmusawa ta kumayi kana tace “Ubangiji ya shiga lamuranka ya kuma maka Albarka...” A hankali ya amsada Ameen Mamy na... Dan ta kawar masa da zancen na ta kawo zancen iyayen goyonsa su Mummy, Sameer ya kirawosu a waya ya had’asu suka gaisa dukda cewa sun tab’a gaisawa amma yanzu an riga an zama d’aya... Mamy ta tambayi jikin Daddy yanda Mummy ta tabbatar mata na samun sauk’i sosai cikin yardar Allah, da zaran an sallamesu a asibitin ma zasuyi umrah su godewa Ubangiji kafin su dawo Nigeria.... Sosai Sameer da Mamy sukaji dad’in samun lafiya da Daddy keyi... Mummy ta tambayi ‘yan uwansa nan Sameer ya kirawo Nabilah da Marliya suka gaisa da Mummy, mata mai dattako da son mutane injisu da fad’i.. Sameer d’an gata mai iyaye biyu... Daga wajen Mamy kai tsaye gida ya wuce lokacin dare ya d’anja, a parlor ya tadda Siyama sai faman cika take tana batsewa tana hura hanci.... Ko takanta baibi yasa kai zai shige.... Saurin tare gabansa tai bata daina cika tana hura hanci ba lokaci guda take furta “Partner yanzu bayan dik abinda kamin kana nufin bazaka bani hak’uri ba, kuma na zaci daka sami family d’inka a ni zaka soma sanarma... I was so wrong...” Aya ta dasama kalaman nata sakamakon hango yanayin da taga fuskar mijin nata ke ciki.... Wani irin duba mai cikeda gsrgad’i yake aika mata, ga idanunsa da suka koma ja.... Hannunsa dake b’ari ya d’ago yana tsananin huci yake nunata da yatsa guda “If you’re still my wife today is because of Mamy... Bazan sakeki ba Siyama sabida umarnin Mamy amma first thing tomorrow morning ki koma yanda kika fito, ki koyo tarbiya da sanin darajan iyaye, duk randa kika koyi wad’annan nida zamu ci gaba da zama matsayin ma’arauta...!!!” Daga haka bai tsaya saurarenta ba yasa kai ya nufi d’aki kaman zai kifa.... Siyama tabisa da kallo cikeda mamaki.... Innalillahi tayi zaton soyayyarsu tayi k’arfin da zata raba Sameer da iyayensa.... A hankali ta silale ta zauna wajen saman sofa k’irjinta na tsananin bugu... No no this can’t be happening, bazai yuwu ba, she can’t lose Sameer.... Wasu irin hawayene taji suna neman ciko idanunta, Laila k’awartace kawai ta fad’o ranta.... Washe gari ko takan Siyama baibi ba ya fice daga gidan, a b’angaren Siyama wannan karon batabi shawarin Laila ba dan batayi shirin rabuwa da Partner ba jin Lailar na bata shawarin ta rabu dashi for good kawai kowa ya huta tinda gashi she cant stand his family kuma Ammi ma batai na’am da sabon familyn Sameer d’in ba... Khalid ne ya fad’owa Siyama, tasan shine kawai zai iya baiwa Sameer hak’uri su sasanta, da dabara sai ta rabasa da wad’annan mutanen.... Hakan yasa sassafe itama tai shiri ta d’auki hanyar Kaduna..... *** KADUNA Khalid ya dubi Daddy da mamaki kana yace “Daddy business trip kuma, ka mance I’m not longer working for the company...” Dafasa kad’an Daddy yai kana yace “Zamuyi tafiya ne not because you’re not longer working with the company but because you’re my son...” A hankali Khalid ya jinjina kai yana mai ganin kuskurensa a matsayinsa na d’ah mai biyayya... “Kayi hak’uri Daddy ba nufi na ba kenan to make you feel this way... I’m sorry, kanada duk wata dama da zaka umarceni nai koma menene matuk’ar bai kauce hanya ba....” Daddy ya jinjina kai cikeda jin dad’i kana yace “Naji dad’i daka fahimci haka Son, Allah shi maka Albarka....” Khalid ya amsada Ameen Daddy.... “Kwana biyu zamuyi, so get your things ready before 12:pm zamu wuce in sha Allah....” Jinjina kai Khalid yai kana yace “Alright Daddy right away...” Murmushi Daddy yai kana ya fice ya nufi sashen Ammi.... Suna zaune itada Laila k’awar Siyama Lailar na mayar mata yanda sukai jiya da Siyama a waya, sai dad’i Ammi takeji cikin sauk’i Siyama zata rabu da Sameer tinda gashi bayan family d’insa yabi... Sunaci gaba da k’ulla yanda zasu kuma karkato hankalin Siyama sallaman Daddy ya daki dodon kunnuwarsu.... Laila ta risina ta gaida Daddy kana ta fice cikin sauri tana fad’in “Ammi zan wuce anjima yanda mukayi zan kiraki na sanar dake...” Ammi tace “Yauwa Laila, yanda kukayi d’in duk saiki sanar dani tinda ni bazata d’aga wayata ba...” Laila ya jinjina kai tace “In sha Allah Ammi...” Ammi tace ta gaida gida kafin ta maidoda dubantaga mijinta sai faman hura hanci take... Daga yanda yake tsaye ya d’anyi gyaran murya yace “Ina kwana Farida.... Tinda ni ban kai ki gaidani ba....” Stegege Ammi ta dubesa kana tace “Idan yau na wayi gari gidan nan ban gaida kai ba sabida ina k’ok’arin kashe wutacen da yaranka suka kunno mana ne tinda kai bazaka nema masu mafita ba....” Ta k’arashe tana huci... Tab’e baki yai kad’an kana yace “Duk yanda kika d’auka, zuwa nayi na sanar dake zamuyi tafiya nida Khalid, kuma tafiyar ba kan komai bace face kan maganar aurensa....” Haba nan fah Ammi ta mik’e sosai ta shiga washe baki tana duban Daddy... “Da gaske kake Daddyn Siyaam...?” Murmushi yai a hankali kana yace “Yanda kikaji haka ne, zanje maganar auren Khalid once and for all....” Tasowa tai tsaye ta rungume mijin nata tana fad’in “Kai amma naji dad’i Daddyn Siyaam, at last labari mai dad’i ya riskeni.... Tareda Khalid d’in zaku tafi...?” Jinjina mata kai yai kana yace “Yes tare zamu tafi da Khalid and zamuyi like 2days in sha Allah....” Ammi ta kuma Washe baki tace “Hukuncinka yayi daidai, Kaga yanzu mahaifin Yesmin zai tabbatar da gaske muke kuma mu ba mutanen banza bane....” Khalid dake tsaye bakin k’ofa mamaki ne ya cikasa jin Daddy ya canza zance wajen Ammi, abinda ya sanar dashi yasha bambam da wanda yake sanarda Ammi... What’s going on here, maiyasa Daddy zai masa haka...? Wata zuciyar tace he’s still your father, he has his own reason na aikata abinda ya aikata, maybe sabida yasan baka son auren da suke niyyan maka ne.. Maybe sabida sun umarceka ka kai Yesmin gida kak’i shiyasa ya fito maka ta wannan hanyar... Koda ya shigo sallama wa Ammi take kuma ja masa kunne gameda Yesmin d’in bai nuna mata sunyi wata magana ta daban da Daddy ba, hasalima ya bita akan tafiyar neman aurensa zasuyi kaman yanda yabar Mahaifin nasa kan tafiyar Kasuwanci zasuyi bai nunawa d’aya daga cikin iyayen nasa akwai wani b’oyayyen lamari gameda tafiyar tasu ba... A haka suka d’auki hanyar Abuja, Khalid da kansa ke driving Daddy bai d’auki koda driver ba a cewarsa tafiyar tasu ne su biyu... Koda Siyama ta iso gida ta iske Khalid baya nan bataso hakan ba, Ammi ta sanar da ita Abuja suka tafi kan maganar auren Khalid d’in, matsalolinsu suna kan warwaruwa a hankali dikda Siyamar tace mata batai shirin rabuwa da Sameer ba hasalima ita yanzu bata auren Yesmin da Khalid take ba, neman hanyar gyara nata auren take don ta haka ne kawai zata samu Partner ya dawo gareta ya rabu da wad’ancan mayun.... *** Yamma lis suka isa garin Abuja, kai tsaye wani gida mai d’ankaren kyau dake Jabi suka nufa, a iya sanin Khalid Daddy baida gida a Jabi, yasan gidajen Daddy guda biyu na Abuja babu wannan a ciki, kuma ba gidansu Yesmin bane, toh gidan waye nan..? Baikaga samo amsar tambayarsa ba wani security man mai sanye da blue uniform ya k’araso ya bud’e masu yana mai risinawa had’ida gaida Daddy... Shi dai Khalid shigewa gidan kawai yai bayan maigadin ya bud’e masa k’ofa, wani b’angare cikin parking lot d’in Daddy ya nuna masa yace yai parking a nan.... Babu musu Khalid yai kaman yanda Daddyn yace sai k’arema gidan kallo yake yanajin kaman wani abu na shirin faruwa a wannan gida.... Muryar Daddy ne ya katse masa tunanin nasa “Muje Khalid...” Babu musu Khalid yasa k’afa ya fito daga cikin motar yayinda security d’in ya k’araso yana fito da luggages d’insu daga bayan booth... D’aga kai Khalid yai yana duban gidan wanda yake bai faye girma ba d’an cute haka dashi, idanunsa suka sauk’a kan kayan wasan yara dangisu motoci da kekuna daga chan gefe... A hankali ya saki murmushi don Allah yayisa mai son yara gashi kuma shi shine k’aramin a gidansu, yanada burin idan Allah ya k’addari yayi aure ya cika masa gidansa da yara shi kuma zai cika gidan da kayan more rayuwa wa yaran... Hannayensa na sakale cikin aljihun jeans d’insa ya kuma sauraro muryar Daddy yana fad’in “Bisimillah shigo Khalid...” Gaban Khalid yaci gaba da fad’uwa sand’a ya sa k’afarsa a bakin k’ofar da zai sadaka da main parlor na gidan.... Gabansa bai gama fad’uwa ba saida ya hango dank’areren hoton mahaifinsa manne cikin parlorn gefe dashi wata matace wacce bazata wuce shekaru 39 a duniya ba, wacce sam ratan dake tsakanin shekarunta da Siyama bazai wuce shida zuwa bakwai ba shi kansa bata basa yakai shekara goma ba... Da k’yar yake iya d’aga k’afafunsa yana kutsa kai cikin parlorn.... Wani sabon tashin hankali daga d’aya angle na parlorn ya hango wani hoton da ya kuma d’aga masa hankali... Daddynsa da wancan matar a tsakiyan hoton, yara ‘yanmata guda biyu sun sakasu a tsakiya d’aya bazata wuce shekaru goma ba k’aramar bazata wuce shekaru bakwai ba, fuskokinsu sun cika da annuri.... K’afafun Khalid suka kasa d’aukansa, ji yayi kansa na juya masa cikin sauri ya maidoda dubansa ga Mahaifinsa dake tsaye yana kallonsa... Cikin rud’ani Khalid ke fad’in “Daddy what is this.... What is all this.... Meke faruwa Daddy.....?” A hankali Daddy ya dafasa kana yace “Sit down first and try to calm down....” Girgiza kai Khalid yake cikin rashin yarda da abinda yake gani kana yace “No Daddy... Are you really asking me to calm down after what I’m seeing... Daddy who are these people... Who’s this woman... Tell me Daddy do you really have another family...?” Yayi maganar yana mai k’arasowa gaban mahaifin nasa cikin rashin yarda da abindake faruwa..... Kasa furta komai Daddy yai sai duban Khalid d’in da yakeyi.... Lokaci guda Khalid ya shiga girgiza kai kana ya soma furta “So is that why you told Ammi neman aurena zakaje...? So bayan Aunt Helen da take America, you have another wife here... Tell me Daddy, be honest with me for once in your life... How many wives do you really have.... Bayan Ammi, Aunt Helen and now ga wata kuma.... Mata nawane kaci amanar mahaifiyata dasu...?!!” Baikai aya ba yaji sauk’an mari da saida ta kaisa k’asa a kumatunsa..... Khalid ya d’ago dafe da k’uncinsa yana duban mahaifinsa dake tsaye yana sakin huci cikin tsananin b’acin rai..... Nuna Khalid yake da yatsa cikin tsananin fushi da fad’a yake fad’in “Ban tab’a cin amanar mahaifiyarka ba, kuma idan na auri mace samada guda Ubangijina ya halatta min na auri daga d’aya har zuwa hud’u... If I keep it from your Mum is because I know exactly the type of woman she really is....” D’an sassauta muryarsa yai kana yaci gaba da fad’in “Khalid for the past few weeks na kula kaid’in ba kamar mahaifiyarka da ‘yar uwarka kake ba, zuciyarka tafi nasu taushi da kyau, Khalid wannan shine dalilina na fayyace maka gaskiya sabida akwai rayuwa akwai mutuwa, yau idan bana raye kasan kunada wasu ‘yanuwa...” Ya k’arashe maganar idanunsa na kallon makeken hoton nasu.... Daddy yaci gaba da fad’in “And about Helen banida mata a k’asar Amurka nayi haka ne sabida kar mahaifiyarka ta zargi inada mata cikin k’asar nan, na sani muddin ta sani zatayi komai don ta rabamu shiyasa na karkata hankalinta zuwa nisan duniya can America.... lokaci guda Khalid ya d’ago idanunsa mai zuban hawaye yana duban mahaifin nasa lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “But still that doesn’t justify your actions Daddy, we have the right to know our siblings, Siyama ta cancanci tasan tanada wasu k’annen... Why Daddy...?” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa... Dafasa kad’an Daddy yai kana yace “I wish I can do that son....” Juyawan da Khalid zaiyi yayi ido hud’u da matar jikin hoton nan, tana takowa tamkar mai tsoron yanda take aje k’afafunta.... Cikin sand’a ta k’araso kusan mijinta, cikeda yanayi na tsoro take duban Khalid d’in kana tace da Daddy cikin sigan rad’a “Why did you bring him here....?” A hankali shima ya furta “Na cika miki burinki ne zan bari Humaira da Ijlal susan ‘yanuwansu....” Ta saki murmushi a hankali dukda cewa har lokacin d’ari d’ari take da Khalid d’in “Sannu da zuwa... Please K’araso ka zauna....” Ta furta a hankali kaman mai tsoron magana fuskarta d’aukeda kyakkyawan murmushi, tana maganar tana k’arasawa cikin parlorn had’ida nuna masa kujera... Kaman mai tunanin wani abu, fuskar matar a zahiri ya masa kaman ya tab’a saninta wani waje... Samun kansa yai da k’arasawa ya zauna a nan yanda ta umarcesan... Ganin bai gwaleta ba ya sanyata samun k’warin gwiwa, ta dubi Daddy fuska fal fari’a kana tace “I’ll set the table...” Ta k’arashe tana nunida dining area... Jinjina mata kai Daddy yai kana ta wuce kitchen cikeda jin dad’i... Har lokacin shock d’in bai rabu da Khalid ba..... Tana cikin had’a plates taji wayarta na k’ara ta k’arasa da sauri ta d’aga still bata daina shirya plates d’in saman dining table ba... “Da gaske Ya Ma’aruf...? Gaskiya naji dad’i su Humaira zasuji dad’in ganinsu Irfaan sosai, na zaci siyasa ya b’oyeku gaba d’aya...?” Shiru ne ya biyo baya alamun ana magana daga d’aya b’angaren.... A hankali kuma ta nufi balcony tana mai ci gaba da amsa kiran.... Sauk’e ajiyan zuciya ta d’anyi kana tace “Toh Yaya ka sanar da Muhibbar ce....?” Daga d’aya b’angaren sauk’e ajiyan zuciya ya d’anyi kana yace “Not yet, shiyasa idan yaran sunzo wajenki sai mu samu dama muyi magana....” Jinjina kai tai a hankali kana tace “Haka ne Yaya, yafi idan ka sanar da ita don aure a sirrancen baida wani amfani tinda gashi nan ni yanda nake fama da nawa auren har yau ya kasa had’amu yayi introducing d’inmu... Ko dashike yau ya kawo min d’ansa kuma ga dukkan alamu bazan samu matsala dashi ba....” Gyara zama sosai Engr yai kana yace “Daula are you sure you’re happy...? You know you’re my only sister kuma hakkina ne na kula dake koda kina gidan aurenki don nayi rantsuwa ma iyayenmu zan kula dake bayan ransu....” Hawayene suka ciko idanunta, tasa bayan hannunta ta goge kana ta saki murmushi tace “I’m happy Yaya, I’m very happy musamman yanzu da mijina yake shirin gudanar da al’amra yanda suka kamata....” Murmushi ya d’anyi kana yace “Gobe in sha Allah yaran suna hanya....” Daula ta amsa masa da fatan Allah kawosu lafiya kana sukai sallama.... Parlor ta dawo yanda ta tadda Khalid tsaye jikin hotunan yana shafa fuskokin yaran da akace sisters d’insa ne, Daula tai tsaye tana dubansa, lokaci guda taga ya saki murmushi yana mai furta “Who’s Humaira among you and who’s Ijlaal......?” *Toh fah! Masu iya magana sukace sannu sannu bata hana zuwa... Mai karatu da sannu da sannu tafiya tana kan yin nisa, b’oyeyyun al’amra suna dad’a bayyana, idan mukaci gaba da tafiya a sannun nan zamu kuma gano wasu abubuwan da izin Allah ciki harda tambayar da ya jima yana maku Yawo WACECE AMINIYAR SIRRI...? Da sannu zamuji ko wacece ita da kuma gudunawar da ta bada wajen salwantar da Ma’aruf had’ida sanin dalilinta na aikata hakan... Na gode da yanda kuke hak’uri Kuke bibiyata dukda rashin samun post akai akai....Alkhairan Allah ya kaimaku duk yanda kuke..!* SameenaAlleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *77* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Bayan ya gama shirinsa a nan yanda aka sauk’esa guest room kasa fitowa yai parlorn domin cin abincin, tsaye yai a window yana mai nazarin rayuwa, sallaman Mahaifinsa ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi.... “Khalid, kai muke jira, fito muci abinci...” Cikin taku a hankali ya k’araso had’ida zama saman gado...”Daddy you go ahead and eat ni inaga ba yanzu ba....” Bai amsa shi ba saima zama da yai gefensa, shiru ya ratsa tsakani kaman babu mai cewa komai... Gyaran murya mahaifin nasa yai kafin ya soma fad’in “Akwai abinda kake buk’atan sake sani ne...?” Fuzar da iska ya d’anyi had’ida kauda kai gefe yana mai murza tafukan hannayensa tamkar mai murza mai kana yace “No Daddy, I’m in no position to question any of your decisions.... Kuma kan abinda ya faru d’azu a parlor kai hak’uri....” Dafasa kad’an Daddy yai zuciyarsa na masa sanyi, tin tasowar Khalid yake ganin Khalid yaro maras jin magana har yake fifita Siyama sama dashi, ya kasance yafi yarda da Siyama sama dashi, ashe dai k’iriniyace kawai irinta yarinta amma a zahirin gaskiya d’an nasa mutumin kirki ne wanda kuma yasan yakamata dikda k’arancin shekarunsa.... Hannun Khalid guda Daddy ya kamo kana yace “Do you want us to go out... Any place you’ve in mind....” Wannan murmushi mai bayyana hak’wara Khalid yai kana yace “A’a Daddy babu yanda zamuje, muna nan a nan tareda family d’inmu... I want to meet my sisters....” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa.... Daddy yaji dad’i harda d’an bubbuga kafad’ar Khalid kana yace “K’annen ka sun dawo daga islamiya, nayi mamaki da bakaji k’iriniyarsu ba, koda yake you really are preoccupied shiyasa bazakaji hayanaiyarsu ba...” Ya d’an murmusa kad’an shima ba tareda yace komai ba... A tare suka nufo parlorn shida mahaifinsa... Yaran gaba d’aya suna saman dining table don already lokacin dinner ne... Mahaifiyarsu sai fama dasu take da gani yaran akwai k’iriniya babu laifi.... Hango wani mutumi da sukai tareda mahaifinsu ya sanyasu zuba masa ido ga kuma kamanni da yakeyi da Daddynsu... Ijlaal tace “Mummy who’s he...?” Mahaifiyar tasu ta d’an rank’wafo kad’an saitin fuskan yaran, cikin murya k’asa k’asa take furta “Girls go and say hello to your brother...” Gaba d’aya kallon mamaki suka bita dashi kafin Humy ta ije fork d’in hannunta kafin tai magana mahaifiyar tasu ta kuma masu alamu da idanu kan suje su gaida Khalid... A tare suka fito daga cikin kujeran suka nufo Khalid da ya kasa janye idanunsa daga barin dubansu... Saida suka k’araso gabansa Humy ta d’an ja baya kad’an tace “Wait how comes bamu sanka ba...? Da gaske kai Yayanmu ne... And ina kake all these while... Mummy ce mamarka kaima...?” Khalid yai tsaye yana duban yarinyar da jinjina wayonta... Daddy ne ya d’anyi gyaran murya ganin Khalid yai tsaye sakare kana yace “Kids ku k’yale Yayanku ya huta yai tafiya ya gaji... Muje koh....” Ya k’arashe yana mai kamo hannayensu, Ijaal ta saki hannun Daddy ‘yar k’aramar ta k’arasa da gudu ta rungume Khalid tana mai furta “Welcome Yaya... Kar ka sake tafiya ka barmu kaji, dama a sch su Nazira suna cewa sunada brother... Nima nace masu yanzu inada brother..?” Tai maganar tana mai langab’e kai... Samun kansa yai da sakin murmushi kana ya durk’usa ya rage tsawon sa gabanta, hannayenta ya kamo kana yace “Of course you can...” Annuri ya cika fuskokin illahirin mutanen parlorn... Khalid ya dafa fuskarta kad’an kana yace “And you are...?” Humaira tai saurin cewa “She’s Ijlaal and I’m Humaira but you can call me Humy...” Khalid ya murmusa yana jin son yaran na shiga cikin ransa a hankali Ijlaal tace “Zance masu my brother is handsome and he has muscles duk wanda ya bullying d’ina a sch zai rama min....” Wannan karon dariya suka d’anyi gaba d’aya kana Khalid yace “Of course I won’t allow them to bully such a beautiful princess like you....” Ijaal na Washe hak’wara tace “Da gaske Yaya nafi Addah Humy kyau...?” Juyawa yai ya kalli Humaira da mood d’inta ya d’an canza kana ya saki murmushi ya mik’a mata d’aya hannun yana mai furta “Come here...” Da sauri ta k’arasa Daddy dai table ya shige wajen matarsa suna kallon draman yaran nasu cikeda jin dad’i.... Khalid ya dafa kansu su duka biyu kana yace “I know you must’ve watched that cartoon... What’s its name again...?” Ya d’anyi shiru kaman mai tinani kana yace “Frozen..” Harda tsallensu sukace “Yes Elsa and Ana....” Khalid ya jinajina kai murmushi bai bar saman fuskarsa ba kana yace “Good, just like Elsa and Ana you both are beautiful princesses...” Yaran suka rungumesa gaba d’aya suna fad’in “We love you brother..” Rungumarsu yai wani irin sanyi na ziyartar zuciyarsa.... A b’angaren Daddy ma dad’i ne ya mamaye zuciyarsa, hukuncin da ya yanke na zuwa da Khalid baiyi kuskure ba, kafin washe gari yaran sun sake sun saba sosai da Khalid gwanin nan sha’awa... A d’aki Daddy yake labartawa Daula halinda ake ciki na maganan auren Khalid d’in da draman da ake da mahaifiyarsa... Tausayin Khalid ya cika zuciyarta, Khalid yanada zuciya mai kyau he deserves to be happy, zataso ya auri macen da yake so... Ta d’an muskuta kana tace “Toh yanzu shikenan kuma sai ka zuba ido a aura masa macen da bai so, haba Abu Humaira ta ya zakai ma d’anka haka...?” Sauk’e ajiyan zuciya Daddy yai kana yace “For secondo ban tab’a goyon bayan Khalid ya auri Yesmin ba cikin zuciyata, nadai nunawa mahaifiyarsa hakan ne don mu rabu lafiya, kinsan banason hayaniya...” Mood d’inta ya d’an canza, shin har yaushene mijinta zai daina tsoron matarsa ya soma gudanar da al’amransa tamkar maigida a gidansa... Ganin tayi shiru tamkar wacce tai nisa a tunani yasa Daddy rik’o hannunta kad’an kana yace “Nasan mai kike tunani, Daula wllhi duk yanda naso na takawa Farida birki bana iyawa... Inada zafi a waje wa mutane amma when it comes to Farida nafi k’ank’ara sanyi, duk decision d’in data yanke ji nake yayi... Kimin addu’a please....” Ya k’arashe kaman wani k’aramin yaro... Tausayin mijin nata ya cika zuciyarta, da ciwo Kaga babban mutum haka ya koma tamkar wani lusari.... Rungumo kansa cikin k’irjinta tai kana tace “Kar ka damu Abu Humaira, jarabawace Allah ya baka ikon ci, wataran komai zai zama labari da izinin Allah, bazan gushe ba ina mai maka addu’a da samun sauk’i cikin lamuranka....Amma ga shawari gameda auren Khalid...” Wannan karon d’agowa Daddy yai yana dubanta sosai.... *** KANO Ya Abida ta kuma duban k’anwar tata a karo na biyu kana ta girgiza kai tace “Wai shin har yanzu baki daina zuwa min da wannan zancen ba...? Sanin kanki ne abinda kike nema bazai tab’a yuwa ba... A sanadiyarta Iyayenmu suka mutu da bak’in cikina... A sanadiyarta na rasa d’ah na mafi soyuwa a gareni, a sanadiyarta na rasa mijina... A sanadiyarta na rasa duk wani farin ciki da na kasance cikinsa a baya.. Duba duba kiga girman gidan nan babu kowa cikinta, dagani sai tarin dukiya... Babu Magaji... Babu kowa sai halittun tsuntsaye... Tin daga ranan da na rasa Ma’aruf na saka ma raina nima na zama macecciya.... Nake zama cikin gidan nan bana fita ko ina bana sauraren tv ko radio bana rayuwa tareda kowa.... Jira nake nima tawa ta sameni... Na rasa komai, na rasa komai Bara’atu sai tarin dukiyar da Abbas ya mutu ya barmin wanda shima nayi imani da bak’in cikina ya mutu koda bai fad’a min ba... Wacece sila...? Duk wannan abubuwan da suka faru k’anwatace sila..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..... Da sauri Aunty B ta rungumeta tana mai furta “Shiyasa nace miki lokaci yayi da zaki ci gaba da rayuwa kaman kowa Yaya, lokaci yayi da zaki mance komai, ki rungumi k’addara wala’alla Ma’aruf d’inki na raye kaman yanda Ma’aruf d’in Ya Mariya yake raye, kar ki mance bayan tulin shekarun nan Ya Mariya ta cire Rai daga samun Ma’aruf d’inta sai gashi ta sameshi, Yaya wala’alla naki Ma’aruf d’in ma yana raye... Daga shi har Fatima bamu sake jin d’uriyarsu ba bayan wad’annan shekarun.... Jikina yana bani basu mutu ba, zamu samesu zamu sake had’uwa dasu kaman yanda muka had’uda Ma’aruf k’arami... Lokaci yayi da zaki fita daga wannan rami da kika binne kanki ciki.... You’ve to live again dan Allah Yaya....” Ta k’arashe cikin tsananin raunin murya mai cikeda kuka.... Ya Abida ta kifa kanta tana tunin d’anta mutanen data rasa a rayuwarta a shekarun baya..... Har Aunty B ta koma gida bata daina kuka ba, tashin hankalin da ita kanta batada cikakken wayo sanda abubuwan suka faru ya dawo mata Sabo, wani al’amari ne da k’addara ta riga fata aukuwa.... Su kuma kalan tasu k’addaran kenan... Shin shi musulmi ba’a sanshi da hak’uri da d’aukar k’addara bane a duk yanda tazo masa...? Shin maiyasa tasu k’addaran tazo a haka...? Shin maiyasa ‘yaruwarta bazata zama mai yafiya da d’aukan k’addara ba....? Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suna masu gangaro mata... Wannan itace k’addararsu..... A haka Zulfa’u ta shigo ta taddata.... Zama tai gefenta zuciyarta nai mata rauni, da matuk’ar wuya kaga hawaye a fuskar Aunt din nata sai abu yakai mak’ura, hannu ta mik’a kana ta rik’o na Aunty B tace “Aunty meke damunki dan Allah... Ki sanar dani....” Murmushin k’arfin hali Aunty B tai kana tace “Zulfa’u wata rana zuri’armu zata cika, mutanen da muka rasa a baya zasu dawo garemu... Shin Zulfa’u ana mutuwa a dawo...?” Mamaki ya cika Zulfa jin irin maganganun da Aunty take marassa kan gado.... Dafe hannayen nata tai kana tace “Aunty bansan meke damunki ba, amma ki sani you can always count on me, sabida kema ko Yaushe kina tsaya mana dagani har ‘yan uwana cikin jin dad’i ko akasinsa, Aunty kema bazan barki ba a lokacin da kike buk’atan wani....” Rungumeta Aunty B tai sosai Hawaye naci gaba da kwaranyo mata..... Cikin zuciyarta take addu’an Allah ya kawo masu wata rana da ahalinsu zasu zama k’ark’ashin inuwa guda kuma su yafi juna.... *** A ‘yan kwanaki biyun da Khalid yai dasu Aunty Daula kaman yanda yake kiran matar Baban nashi sosai suka saba, daga ita har yaran nata sosai Khalid yaji dad’in zama dasu suma kuma sunji dad’in zama dashi har saida Aunty Daula da yaranta suka buk’aci Khalid ya k’ara masu kwanaki, abu kaman wasa sai gashi har sun doshi sati, wani irin rayuwa mai dad’i da babu hayaniya ko tashin hankali cikinta yake experiencing, rayuwar da sam bai samu da mahaifiyarsa da ‘yaruwarsa ba wanda su a kullum son kansu suke ba kaman Aunty Daula da yaranta ba wanda soyayyan ‘yan uwa ya cika zukatansu.... Ji yayi ya sake sosai dasu har bayaso ya baro su, inama zasu had’u gaba d’aya harda Siyama da Ammi suyi irin wannan rayuwa mai ban sha’awa da tarin memories masu d’ad’in tunawa.... Da k’yar su Humaira da Ijlaal sukai sallama da Khalid saida Aunty Daula da Daddy sukaita fama dasu Khalid d’inma ya masu alk’awarin sake visiting d’insu soon sauk’in abin ma su Irfaan cousins d’insu sunzo sai suka d’ebe masu kewan Yayan nasu.... Wasa wasa satityikw sun shud’e, a ko wane b’angare shirye shirye suke gudanarwa, can Kano gidan Abbah shirye shiryen Bikin Sahariyya da Sameer suke dikda cewa a b’angaren ango ba haka take ba, gaba d’aya shi ya yama mance da wani shirin biki da ake yafi bada muhimmanci ga aikinsa Wanda yake ceton rayukan al’umma ne, har yau ko saka amaryar tasa a ido baiyi ba, kaman yanda ba hakan ta kasance ga b’angaren amaryar ba, dikda cewa bata ida warkewa sosai ba hakan bai hanata gudanar da shirye shiryenta ba, daga ita har Haule basu sama basu k’asa, dik wannan buduri da suke Najah dai kallonsu kawai take da matuk’ar sanyin jiki... Anya idan ta bari burin iyayenta na aurawa Ya Ma’aruf Addarta Sahariyya tayi daidai, Ta tina binda taji iyayen nata suna tattaunawa kwanaki a asibiti lokacin kwanciyar Hajiya, tagumi ta rafka tana neman mafita, fad’in gaskiya na daidai da tonuwar asirin iyayenta ne, Toh amma idan tai shiru kuma abin sai yafi muni, ta basu dama suci gaba da b’arna a doron k’asa ne... A hankali ta rintse idanunta tana rok’on Allah ya kawo mata mafita.... A b’angaren Akram ma yanzu kam sun sansanta sosai da Zulfa’u har yana maganan turo magabata dikda cewa itace mai d’an taka masa birki, ga Hafiz ma da har yanzu ya kasa ya tsare sai matarsa ta koma garesa yayinda a can b’angaren Daddy kuma a nan Kaduna ya k’udiri niyyan farantawa d’ansa Khalid koda hakan zai haifar da tashin hankali tsakaninsa da matarsa, duk yanda Siyama taso ta shawo kan Sameer su shirya abu ya gagara, Ammi da Laila kaw sosai suka sa azamar raba Sameer da Siyama rabuwa ta har abada, wannan ya baiwa Laila da Sultan daman cika burinsu (Idan baku mance ba Sultan abokin Sameer ne wanda suka taso a nan Kaduna tare kuma yake cin dunduniyarsa sabida wata manufa tasa)... Wasa wasa har takai Laila ta soma k’ulla wata dangantaka tsakanin Siyama da Sultan dikda cewa sun kwana da sanin tsakanin Sultan d’in da Sameer.... Yauma suna zaune a wani waje na shak’atawa su ukun, sai k’ok’arin cheering Siyama suke wacce gaba d’aya da ganinta kasan hankalinta bai jikinta, mik’ewa Sultan yai kana yace yana zuwa... Laila ta masa wani duba Kafin ya shige.... Dafa hannayenta dake zube saman table Laila tai kana tace “K’awata Wai meye ne haka, dan Allah ki saki ranki baki ganin we’re here to make you feel better, Sultan zaiji babu dad’i idan yaga duk efforts d’insa kina basarwa...” Da mamaki Siyama ke duban Laila kana tace “Laila kin San abinda kike fad’i kuwa...? Nifa ban gane wannan kyautatawa da Sultan ke min ba bayan duk abinda nayima abokinsa... Ni bansan wayace ki gayyato mana shi ba ma....” Murmushi Laila tai kana tace “Aw ke yanzu baki gane nufin Sultan akanki ba...? Toh idan baki gane ba ki bud’e idanunki sosai ki fahimcesa... Sultan is trying to give you what Sameer refuses to give you... Sultan zai iya maye gurbin Sameer a wajenki idan kin basa dama kuma ya baki duk wata kulawa da soyayya da Sameer ya kasa baki....” Wannan karon tsaye Siyama ta mik’e cikin tsananin b’acin Rai take duban Lailar... Lokaci guda take furta “Kin faran shan k’waya ne Laila ban sani ba, da auren Sameer akaina kike cewa na baiwa wani chance waninma of all people abokinsa... you must be insane Laila...” Kamo hannunta Laila tai ta zaunarta, saida ta gyara zama kafin taci gaba da fad’in “Haba Siyama ya kike neman ki badani, saikace wata ba wayeyyiba, ki dubeki son kowa kin wanda ya rasa, gaki kyakkyawa gaki da karatunki gaki d’iyar masu kud’i... Duk wad’annan qualities d’in kin had’a sannan ki bari wani namiji yake baki wahala, haba Siyama karfa ki mance ke kin juyawa mahaifiyarki baya a sabida shi sannan shi ya kasa defending d’inki gaban family d’insa, think about it Sameer ba sonki yake ba, da ace yana sonki da bai miki haka ba... Da duk wad’annan features d’in da kikeda ki tsaya namiji k’wara yana baki wahala, tell me meye Sameer yafi Sultan dashi, profession d’insu guda idanma kasancewarsa likita ne ya rufe miki idanu kika kasa gameda shi.. Saidai kuma idan kyaun hakittarsa ne ke rud’inki...” Wani duba Siyama ta watsawa Laila kana tace “Laila sanin kanki ne ban tab’a son wani d’a namiji ba sai Sameer kinsan hakan tin muna high school, banjima kuma akwai wani d’ah namiji da zan mallaka masa gurbin da Sameer ya mallaka cikin zuciyata... I cannot...” Tab’e baki Laila tai tana dubanta kafin ta mik’e a fusace tana fad’in “Toh gaskiya ni idan bazaki bud’e idanunki kiga abindake faruwa a gabanki ba zan barki da iyawarki, kiyita wulak’anta kanki kan wanda bai d’aukeki da wata daraja ba, Kinga tafiyata.!””” Daga haka Laila tasa hannu ta d’auki jakarta ta wuce fuuu tamkar mai shirin tashi sama... Siyama ta bita da kallo tana kiran sunanta inaa Laila ko juyowa batai ba... Daidai nan Sultan ya k’araso hannunsa rik’eda cup d’in ice cream guda biyu.... Murmushi ya sakar mata kana yace “Ina k’awar taki..?” Murmushin yak’e Siyamar tai kana tace “Ta ta wuce I guess....” Sultan ya zauna yana mai aje mata kofin ice cream guda yake fad’in “Too bad gashi na kawo maku ice cream din nan da nake baku labari duk garin nan babu mai dad’insa kuyi tasting da kanku kuji...” Yayi maganar da siga ta barkwanci... Tak’aitaccen dariya Siyamar ma tai... Daga yanda Laila ke tsaye shu’umin murmushi tai kana ta ciro wayarta cikin jaka ta shiga kashe masu hotuna lokaci guda take furta “Saini Laila amaryar Sameer... Bani sa abu a gaba naga kasawa, na sami shaidu k’warara da zanyi amfani dasu wajen datse aurenki da Sameer, na farko shaidar zubar masa da ciki da kikayi na biyu cin amanansa da abokinsa...” Ta kuma tintsirewa da dariya had’ida jefa wayarta cikin jaka kana ta bar wajen.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *78* Gaba d’aya Hajiya Haule da Baba Alhaji sun hura wuta sosai kan maganar auren Sameer da Sahariyya, babu yanda Abbah baiyi ba su d’an k’ara lokaci amma inaa sun azalzala ayi ayi auren, ko Sahariyyar dake matuk’ar d’aukin auren bata rawar k’afar da iyayenta keyi gashi har rana mai kaman ta yau basuga idon ango ba, Hajiya Haule ta tasa Baba Alhaji gaba da cewa yaje ya sami k’aninsa da batun, don gaba d’aya basu san wanne Sameer ke ciki ba.... Hafiz dake gefe ya cika yayi fam sai hura hanci yake yana aikama iyayen nasa kallon wulak’anci.... Hajiya takai dubansa garesa yanda ya cika yai fam kana tace “Kai kuma fah....?” K’wafa yai a hankali “Amma Hajiya gaskiya ni baku kyauta min, nayi abinda Baba Alhaji keso na maida tsinanniyar can d’akinta maiyasa ni baza’a cika min nawa burinba, maiyasa za’a min alk’awarin dawo min da matata kuma ak’i cikawa... Idan duniya da gaskiya idan ba wani al’amarin kuke b’oyewa gameda aurawa Sameer Sahariyya ba ai nima sai ku hura wuta a had’a auren da nawa...” Hajiya ta tab’e baki kad’an tana duban Baba Alhaji kana tace “A’ah toh, ai ga Baban naka... Babu yanda banyi ba yayi maganar dawoda Zulfa’u amma yayi k’ememe yayi banza dani, bansan wata kalar muguwar asiri Magajiya da d’iyarta suka hura masa ba... Gashi nan tambayesa kaji daga bakinsa....” Baba Alhaji dake muzurai cikeda fad’a ya soma fad’in “Ni ba wai nak’i Zulfa’u ta koma gidan Hafiz bane, ince shika uku ya mata, a ina kuka tab’a jin anyi shika uku an gyara aure... Kuma banda abinka me ita wannan yarinya Sawwama ta rageka dashi...” Baikai aya ba Hafiz ya mik’e cikin hura hanci da d’aga kafad’u sama yake fad’in “Nifah Baba Alhaji saki d’aya tak naiwa matata don haka babu wanda ya isa yace bazan iya maidata ba, kuma idan bazaka sa baki ba a had’a aurenmu da Sahariyya wllhi wllhi kaji na maka rantsuwa zan tono ko mene shirinku kuma zan fallasaku a bainar jama’a, sannan bayan haka zan rabuda Sawwama ta hanyar da bakai zato ba...” Ya k’arashe tamkar zaikaiwa mahaifin nasa bugu, sai faman hura hanci da d’aga kafad’a da wuya yake.... Hajiya da ‘yan hanjinta suka kad’a don tasan tsaf Hafiz zai aika abinda yace, idan yaso tsaf zai binciko sirrinsu, murmusawa tai kana tace “Sha kuruminka d’ah na idan dai Zulfa’u ce ta koma gidanka an gama babu shegen da ya isa ya datse aurenku, ince nice nan sanadin rabuwarku, toh ka kwantar da hankalinka aurenku ya koma an gama... Ka kwantar da hankalinka kaji d’ah na Zulfa’u ta dawo gareka an gama...” Murmushi da gefen baki Hafiz yai yana wani jijjiga shi kad’ai kana yace “Ku tabbata zaku cika alk’awarinku, don idan ba haka ba....” Ya kuma yin wata murmushi kana yace “Wllhi tallahi billahi zan mance ku iyayena ne, zan kuma iya zama barazanaga rayuwarku....” Daga haka sa kai yai ya fice daga gidan gaba d’aya.... Hajiya Haule da tashin hankali ya nuna k’arara ta fuskarta ta dubi mijinta “Kanaji abinda yake fad’i koh.... Toh wllhi tun wuri kasan yanda zakaida yaron nan don ko shakka banayi Hafiz zai aika dik abinda yace... Uban da yace kasashi maido da wancan hatsabibiyar yarinyar, sanin kanka ne idan yaso sai ya bankad’o duk wasu sirrika da muka jima muna aza masa k’asa...” Daga haka ficewa tai fuuu bata tsaya sauraren mijin nata ba... Tashin hankali ne sosai ya wanzu saman fuskar Baba Alhaji... Tirk’ashi, aiko bazaiso Hafiz yasan cewa nada wani bak’in k’ulli a zuciyarshi ba, kama daga ‘ya’yansa har zuwa ‘yanuwansa kai harta jama’an gari sai sun k’yamacesa shida baida burin ya zamto mutumin da al’umma zatai alfahari dashi dukda hakan ya kasa samuwa a gareshi, wannan d’aukaka ta d’anuwansa da yake burin ya zamto shikeda ita sam bai samu ba, yanzu asirinsa ya tonu kuma ai shikenan babu mai kuma masa kallon yanada wani kima.... Yarfe zufan daya tsartsafo goshinsa yai kana ya mik’e ya shiga aza babbar rigarsa bai zarce ko ina ba sai gidan Abbah... Abbah ya jinjina kai a hankali “Ban tari numfashinka ba Yaya, amma gameda Zulfa’u bazan canza zancena ba, zan kirawota muji daga bakinta, karka mance Shari’a ta bata damar zab’awa kanta miji, zab’an mijinta ba a hannunmu yake ba, iyakaci namu mu gudanar da bincike mu kuma bata shawari, amma banda maganar tilastawa...” Kad’a ‘yar yatsarsa kurum yake yana duban d’anuwan nasa, baisan wace irin shegiyar taurin zuciya Usman kedashi ba, tin suna yara haka nan yakeda kafiya akan kalamansa, idan yayi magana toh ita kenan guda d’aya, sanin kansa ne wasu abin d’aga masa k’afa yake matsayinsa na wandake gaba dashi... Baba Alhaji ya kuma gyara zamansa had’ida fitowa kad’an daga cikin kujeran ba tareda ya janye idanunsa daga duban Abban yake fad’in “Ina ita Zulfa’un take....?” “Tana can Gwammaja gidan k’anwar mahaifiyarta Bara’atu...” Cewan Abbah dake k’ok’arin danna remote d’in tv sakamakon wutan nepa da aka kawo... Shiru Baba Alhaji yai tamkar mai nazari kana yace “Lallai lallai ta tattara ta dawo gida, idan yaso gobe idan Allah ya kaimu sai mu zauna gaba d’aya mu tuntub’eta muji idan akwai wanda take so ne, idan kuma babu bazamu zuba mata ido ta tare gidan Bara’atu da ita kanta tarbiya bawai ya isheta bane, ni sam ban yarda da tarbiyarta ba balle har a bata rik’on yarinya.... Sannan shi kuma Sameer d’in idan ya shigo sai ka sanar dashi lallai lallai ina nemanshi...” Daga ida fad’in haka mik’ewa yai yana sab’a babbar riga ya nufi k’ofa... Jinjina kai kurum Abbah yake yana mai fad’in “A sauk’a lafiya Yaya....” Ko amsashi bai sami zarafin yi ba ya fice cikin sauri tamkar wanda ake ingizasa... Daga nan bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Magajiya, yau zuwansa na uku kenan saidai tarban da ya samu yau yasha bambam da zuwan da yai sai biyu a baya.... Ta fito parlorn cikin kwalliya na kece raini kaman kullum, sai watsa k’amshi take dikda k’aurin hayak’in wuwi da sigari da hancinka ka iya shak’o maka, don k’amshin tiraren daban yake tashi haka ma warin k’ayan mayen, koda Baba Alhaji ya tambayeta sai ce masa tai yaran mak’otanta ne marassa jin magana saitin windows d’inta suke zuwa su hura hayak’insu.... Ta marairaice fuska sosai kana tace “Alhajina shin wai baka yarda dani bane...?” Baba Alhaji ya murmusa “Na yarda dake mana Magajiya, ni abinda ban gane ba yau d’in naga sai b’ata fuska kike ko wani ne ya tab’a min ke....?” Rausayar da idanu tai cikeda kisisina da salo na kashe murya take fad’in “Toh ba d’anka Hafiz bane yake gurza ma tilon d’iyata wulak’anci ba, har yau zaman doya da manja suke sam yak’i aminta da ita bacin duk magiya da kwantar da kai da take masa.... Ni tsoro nake kar yace zai kuma rabuwa da ita a karo na biyu...” Ta k’arashe tana wani rau rau da idanu tamkar budurwa mai tashen k’uruciya.... Baba Alhaji ya murmusa ya kurb’i lemu mai sanyi da aka kawo masa kana yace “Idan don wannan ne karma ki d’aga hankalinki, na riga na gama magana da Hafiz, kafin nazo nan ma maganar da mukai kenan, aurensa da Sawwama mutuwace kawai zata raba muddin ina numfashi... Ki kwantar da hankalinki kuma ki sanar da ita Sawwamar ta kwantar da hankalinta babu uban da ya isa ya raba aurenda na maida koda kuwa Haule ce....” Wani shu’umin murmushi Magajiya tai kana tace “Da gaske Alhajina...?” Jinjina mata kai yai yana mai janyo parantin cake da aka ije gabansa.... Dad’i kaman ya kashe Magajiya cikin sauri ta mik’e ta d’uki tray d’in tana wani kareraya take k’arasowa gabansa had’ida fad’in “A’a yi zamanka Alhajina bara na mik’a maka wannan ai aikina ne....” Baba Alhaji ya kuma Washe baki yana kad’a kai cikeda jin dad’i yake fad’in “Allah ko Magajiyata... Anya kuwa bazaki sa na soma jina kaman saurayi d’an ashirinda ba....” Ta kuma rausayar da idanu tace “Ai kafi haka a wajena, Allah dai ya nuna mana ranan da zan shiga gidanka Kaga soyayyar da baka tab’a cin karo da irinta ba....” Haba nan fah Baba Alhaji yaci gaba da washe baki yana k’yak’yata dariya cikeda nishad’i yana mai ci gaba da kod’a Magajiya.... *** Wayar na manne kunnenta na hagu tayi shiru alamun tana sauraren magana daga d’aya b’angaren, cikin sanyin murya irin tata tace “Mamy Abbah kuma..? Mamy cewa yai na dawo...?” Daga d’aya b’angaren Mamy tace “Zulfa’u kinsan halin Baban naku waima yanzu abin yayi sauk’i tun bayan bayyanar Yayanku, kinfi kowa sanin halinsa ai....” Zulfa’u da hawaye ke k’ok’arin cikowa idanunta tace “Mamy wllhi Allah nasan bayin Abbah bane, nasan haka kurum bazaice na tattara na dawo gida ba, Mamy nan fah da can duk d’aya ne, kuma ma nan d’in yafimin sauk’in tafiya Office...” Sauk’e ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Zulfa’u nima na fad’a mishi hakan, amma yace lallai lallai gobe ki dawo gida, tinda naga Baba Alhaji ya fice daga parlornsa nasan wani zance ka iya biyo baya tinda gashi ya hura wuta sosai kan maganar auren Yayanku da ‘yar wajensa Sahariyya...” Shiru Zulfah tai tana nazarin maganganun Mamyn kana tace “Baba Alhaji yazo Mamy...?” Mamy tace “Yanda kikaji... Banason dogon bayani Zulfa’u ki tattara gobe kizo gida zan nemi Antin taku a waya nai mata bayanin komai....” A hankali Zulfah ta jinjina kai tamkar Mamyn na dubanta kana tace “Shikenan Mamy zanyi yanda kukace in sha Allah....” “Yauwa sai kinzo, Allah shi miki Albarka...” “Ameen Mamy...” Sukai sallama kana Zulfah tai jigum tana tunanin, yanda Baba Alhaji ya hura wuta kan batun auren Ya Ma’aruf da Sahariyya ko shakka babu akwai abinda yake shirin yi tsakaninta da Ya Hafiz, idan kuwa nufinsa ne maida aurensu da Ya Hafiz gaskiya ba’a kyauta mata ba... Tana tsaka da tinanin Aunty B ta shigo ta taddata... Tsaye tai tana duban Zulfa’un da tai nisa duniyar tunani.... Aunty B ta k’arasa ta ije kayan gugan data shigo dashi saman gado, gefen Zulfa’u ta zauna had’ida d’an dafata kad’an “Daughter lafiya... meke faruwa naga kinyi nisa cikin tunani haka...?” Sauk’e ajiyan zuciya Zulfah tai “Aunty, Mamy ce muka gama waya da ita...” Aunty B ta jinjina kai “Umhum ina jinki....” Gyara zama Zulfa’u ta kumayi kana tace “Cewa tayi Abbah yace lallai lallai gobe na koma gida, and daga bayananta kaman maganar bazai wuce akan aurena da Ya Hafiz ba... Aunty idan hakan ta kasance bansan ya zanyi ba, tsoro nake kar suce zasu kuma had’a aurenmu a karo na biyu tinda gashi Baba Alhaji ya hura wuta kan batun auren Ya Ma’aruf da Sahariyya...” Shiru Aunty B tai tamkar mai nazari kana tace “Bazai yuwu ki koma gidan Hafiz ba, bazan bari ba....” Dubanta Zulfa’u tai da idanunta da sukai raurau “Aunty idan sukace na koma fah... Bazan iya bijire masu ba...” Girgiza kai Aunty B tai had’ida gyara zama sosai “Toh ke Zulfa’u mai zai hana ki baiwa yaron nan Akram dama iyaye su shiga maganar tinda gashi naji Atika na cewa tin satin da ya shige yaketa damunki da batun turo magabatansa amma kink’i basa k’ofa, na tabbata idan sukaga kin tsaida manemi bazasu miki dole ba, saidai idan kuma har yanzu kina son Hafiz d’in ne....” Fuzar da iska maras k’arfi Zulfah tai had’ida muskutawa “Aunty bazan b’oye maki ba, da fari bansan mai nakeji ba, I was so confused about Ya Hafiz amma yanzu ina mai tabbatar maki bana son Ya Hafiz, shi ma Akram banjin ina sonsa Aunty... Bansan menene na hanzarin ba, dadai sun barni zuwa wani d’an lokacin to get my head cleared...” Sauk’e ajiyan zuciya Aunty B tai kana tace “Akram yaron kirki ne Zulfa’u kuma ni nan nasa anmin bincike akanshi and his background, baida wani aibu, mai zai hana ki bashi dama Zulfa’u, idan dai iyayenki sun matsa nidai a nawa shawarin da ki bari su maida aurenki da Hafiz gwara miki wannan yaro Akram... Amma fah shawarice... Ki natsu kiyi tunani kuma ki fad’iwa Ubangijinki ki fawwala masa lamranki domin zab’insa shine maki alkhairi...” A hankali Zulfah ta jinjina kai kana tace “Toh Aunty zanyi yanda kikace zanyi tunanin... kuma zanyi addu’a dikda cewa cikin yinta nake ko yaushe....Na gode da shawarwarinki Aunty... thank you for always being there..” D’an rungumeta Aunty B tai kana tace “Anything for you daughter... Allah Ubangiji ya miki zab’i mafi alkhairi...” Zulfa’u ta amsada “Ameen Aunty na...” *** Koda Sameer ya sami sak’on Wan mahaifin nasa bai k’asa a gwiwa ba ya amsa kiran nasa, saidai bai sami Baba Alhajin gida ba saiko Haule da yaranta, musamman Haule tasa Najah ta bud’e masa parlorn Baba Alhaji, sai wani nan nan dashi ake, Sameer bai mance farkon zuwansa gidan ba sanda ya buge Raihanah ya tadda Haule da wannan maras kunyar ‘yar nata da ake yunk’urin aura masa matsayin mata sun tasa Raihanah a gaba suna aibantata... Tinda ya shigo gidan gaba d’aya a tsare yake sosai, ganinsu ya kuma tuno masa abinda ya tadda suna ma Raihanah a wancan lokacin, kansa na bisa wayarsa Haule ta shigo tamkar zata zube ta masa sijjada, sai rawa jikinta keyi tana kuma tura k’eyar Najah tana fad’in tai sauri ta ije masa kayan motsa baki dake hannunta... Najah dai girgiza kai kurum tai kana ta k’arasa ta aje masa tray d’in tana gaidashi... A tak’aice ya amsa sannan har lokacin fuskarsa babu walwala.... Ga mamakin Haule jira take yaji yace ina amaryarsa take, shiru kakeji saima sinkayo muryarsa tai yana tambayar Najah Baba Alhaji... Najah tace “Ai ba dawo ba Yaya...” Jinjina kai kurum yai kana ya dubi agogon hannunsa.... Haule ta watsawa Najah harara sanda take ficewa kana ta kutso kai ta shigo parlorn, baki har kunne take sakin murmushi da sallama... A tak’aice Sameer ya gaidata don tuntuni baisan maiyasa tasu batazo d’aya da matar ba ko bayan da ya fahimci matar yayan babansa ne, ko hakan nada alak’a da saninda ya mata a fari ne sai Allah.... Dik yanda Haule taso tajasa da hira ta kasa samun fuska, harta firan kawo kayan lefe da shirinsa na biki dataita k’ok’arin bijiro dashi babu ko kamun kai Sameer bai amsa mata ba, k’arshe dai data gama kid’inta da rawarta mik’ewa tai tana fad’in “Ka saki jikinka fah kaci komai nan gidanku bara na kira maka Sahariyyar tana can tana shiryawa...” D’an dakatar da ita yai da fad’in “A’a da kin barta don zuwan ba nata bane...” Haule bata bari ya dasa aya ba tace “A’a karka damu tindadai kazo dole ta fito ku gaisa...” Kallo kurum yabi Haule dashi yanda take rawar k’afa har ta fice... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa “What have you gotten yourself into Sameer... Baka gama da problem d’in Siyama ba ga wani na kunno maka kai....” a hankali ya fuzar da iska mai zafin gaske yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa he’s doing this for the sake of the family, he cannot allow his family to fall apart bayan k’unci da suka fuskanta a lokacin da ya b’ace, he has to sacrifice and do what they ask him to do, for the sake of everybody’s happiness.... Yana tsaka da tunanin wayarsa ta d’auki ruri... Sanda Sahariyya ta shigo parlorn waya yake dan haka bai amsa sallamarta ba, sai wani sanne sanne kai take ita a dole an fito zance wajen saurayi.... Duba guda ya mata ya d’auke kansa, har lokacin waya yake.... Sahariyya ta k’arasa ta zauna a kujera mai kallon nasa.... Sai faman sakin murmushi take tana k’irga ‘yan yatsunta yawa mutumiyar arzikin gaske... Lokaci guda taga ya mik’e yana fad’i cikin wayar “I’ll be on my way...” Zunbur Sahariyya ta mik’e tana binsa da kallon mamaki.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................ DA DABO_ *79* “Yaya ina zakaje kuma bacin ko gaisawa bamuyi ba...” Tai maganar tamkar mai shirin kuka... Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ya dubeta ba, ganin yaja ya tsaya yasa Sahariyya ci gaba da fad’in “Kaga fah ko ruwan da aka kawo maka baka sha ba, dan Allah ka tsaya ko ruwan ka d’an sha...” Tai saurin k’arasawa ta shiga k’ok’arin bud’e drinks d’in tana zubawa a cup... Yanda tai maganar cikeda girmamawa ya hana Sameer gwaleta, karkatowa yai kad’an yana duban yanda take serving drink d’in har rawa jikinta keyi.... Ta d’ago kai sukai ido hud’u nan taga dai har lokacin fuskarsa tamau, ta maida kanta k’asa tana mai furta “Ina yini...” Saida ya kwashe wasu sakanni kaman mai nazarin wani abin sai kuma yace “Lafiya..” A tak’aice... “Yaya ka zauna dan Allah...” Ta fad’i cikin kashe murya, wani duban ya mata ya sanyata had’iye sauran kalaman nata, duk duniya Sahariyya bata tab’a cin karo da wanda takejin bala’in shakkarsa kaman Sameer ba, ikon Allah wai ita Sahariyya kejin shakku da tsoro had’ida fargaban wani bil’adam kaman haka, a iyakacin saninta tsabagen k’aurin suna da tai na rashin kunya da rashin mutunci yasa duk saurayin da yazo wajenta idan halinta bai koresa ba toh kuwa jama’an unguwa sai sun koresa, amma yau ita ke jin azabebben fad’uwan gaba da tsananin shakkun wani mutum haka... Ta had’i miyau da k’yar, har lokacin tana nan duk’a gabansa dikda cewa k’afar tata bai ida warkewa ba amma ko zafin tsugunon da tai bataji.... Sameer ya d’an gyara tsayuwarsa kad’an yana karantarta kana yace “Yaya jikin naki...?” Nan fah Sahariyya taji maganar tasa tamkar wacce aka jefota, dad’i ya cika zuciyarta ashe har ya damu da ita haka.... Cikeda jin dad’i ta amsa masa da cewa “Da sauk’i Yaya aima saura kad’an ne, gobe muke komawa wajen mai d’aurin dama...” Jinjina kansa yai har lokacin tsaye gabanta yake hannayensa dafe da kunkumimnsa, saida ya d’an gyara tsayuwarsa kana yace “Menene asalin abinda ya sameki, me ya janyo faruwar ciwon...?” D’agowa tai tana dubansa wani irin dad’i na mamaye illahirin zuciyarta, a hankali ta furta “K’addara ce Yaya...” Sameer ya jinjina kai kana ya maimaita “K’addara... Kin yarda da k’addara...?” Wannan karon a d’an zabure ta d’ago tana dubansa, lokaci guda ta saki murmushi wanda yafi kamada yak’e kana tace “Na yarda da k’addara Yaya...” “Good..” Ya furta a hankali yana mai jinjina kai yayinda Sahariyya ta shagala sosai da annashuwa, sinkayo muryarsa tai yana fad’in “Idan kin yarda da k’addara kaman yanda kika fad’i maiyasa kika biyewa mahaifiyarki kuke aibanta k’anwarki Raihaan don kawai bata kasance d’iyaga mahaifiyarki ba..?” Wannan karon azabebben fad’uwan gaba taji ya sauk’a mata, ta tuna farin zuwansa gidan tun Kafin susan cewa shine Ma’aruf, nan fah Sahariyya ta shiga muzurai tana neman abin fad’i lokaci guda ta soma kame kame da inda inda... Sameer ya girgiza kai a hankali yana mai aika mata wani kallo lokaci guda ya sakale hannayensa cikin aljihun wandonsa kana yaci gaba da fad’in “Wacce kika k’ona da ganganci itace ta yarda da k’addara amma bake ba, nasan kinsan wa nake nufi.... Anyways Allah ya baki lafiya, ni zan wuce suna kirana a asibiti.... Idan Baba Alhaji yazo sai ki fad’a mishi nazo ban sameshi ba....” Daga haka bai jira cewarta ba yasa kai ya fice... Sahariyya dake dab’e wajen tamkar wacce aka dasa kasa motsa koda d’an yatsarta tai, dik a tunaninta Sameer damuwarsa akanta yake nuna mata ashe ba haka bane, magana yaso yab’a mata kuma ba akan kowa ba sai kan shegiyar k’anwar nan nata... Wani irin zogi da rad’ad’i taji zuciyarta na mata, idanunta suka kad’a sukai jazir hawayen da basu shirya fitowa ba suka shiga zarya a kumatunta, wani irin tsanar Raihanah takeji kaman ta shak’eta ta mutu, fuskar Raihanah take hangowa tana mai furtawa a fili “Na tsaneki na tsaneki shegiya stinanniya munafuka algunguma mayya..!” Idanunta na zuban hawaye masu rad’ad’i take maganar cikin tsananin karaji... A haka Haule ta shigo ta taddata, ganinta a duk’e tana hawaye ya sanya Haule k’arasawa da sauri ta shiga jijjigata tana fad’in “Ke Sahariyya... Lafiya... Meke faruwa.. Ina Ma’aruf d’in....?” Sahariyya na hawaye take fad’in “Hajiya dik laifin munafukar Raihanar nan ne, annamimiya mai halin munafukan farko, nunawa take itace mutumiyar arziki keda ‘ya’yanki faragurbi... Munafuka wayasan kalan salon munafuncin da take masa can gidan Mamanin... Ni wllhi Hajiya kisa Baba Alhaji ya dawo da ita gida, Allah kad’ai yasan mai take masa acan mai shegen son mazan bala’i....” Ta k’arashe tana goge hawayen da suka wanke mata fuska... Murmusawa kad’an Haule tai kana tace “Banda abinki mai Ma’aruf zai da wannan banzar yarinyar tausayice kawai take basa, kinsan shi ya mata aiki lokacinda ta k’one kuma Allah yayisa mai tausayi da tausasawa bacin haka ke ko a hanya yayi kama da wanda zai tarayya da Raihanah ne ai Ma’aruf saike naki ne, domin kaw an gama magana ki kwantar da hankalinki yanzu zan kira mahaifiyarsa mujin batun lefe a ina anka tsaya... Karma wannan ya tada miki hankali, ci gaba da shirye shiryenki, ki kirawo Fa’iza yau kuje ku cire ankonku muma ku ciro mana ankon gida iyanin....” Kalaman Hajiya ya d’an tausasa zuciyar Sahariyya, ta saki murmushi tana mai furta “Shisa nake sonki Hajiyata...” Hajiya ta rungumeta tana fad’in “Aikinfi min wancan shashashar k’anwar taki wacce bata k’aunar uwarta....” Ta k’arashe tana aikama Naja’atu dake tattara wajen hrara... Giriza kai kurum Najah tai ba tareda cewa komai ba ta fice da parantin dake hannunta.... *** Kasancewar washe gari baida zuwa asibiti da wuri ya sanyashi yada zango gidansu abokinsa Shamsu don sun kwana biyu basu had’u ba, Shamsun ma wata k’aramar kwangila ya samu nan cikin gari da wata company shisa shima d’in bai zauna ba kwana biyun.... A parlor Sameer ya samu Mama suka gaisa tana masa tsiyan shida abokinsa aiki duk ya b’oyesu gwarama shi nada iyali amma abokin nasa bai ije kowa ba sai bautan neman kud’i.... Sameer ya d’an sosa k’eyarsa yana mai furta “Zai aje ne Mama....” Yai maganar yana duban k’ofa yanda Shamsu ke k’arasowa cikin parlorn hannunsa rik’eda mug alamun bai jima da tashi ba... Mama ta dubi Shamsun baki a tab’e kana tace “Allah yasa yaji gori ya aje d’in, mutum gansameme kullum saidai ya tashi ya ishi mutane da tsifface tsiffacen baison cin wannan da safe baison cin wancan, idan kaji gori kai aure muma ma huta da wannan tsirin naka... K’aton kawai...” Ta k’arashe tana yab’a masa muguwar kallo... Sameer kaw sai sakin murmushi yake yana duban yanda abonkin nasa ya had’e gira sosai.... “Mama fah safiyar da saura dan Allah a k’yaleni haka nan, kofa karin kumallo banyi ba...” “Tafi can ka rufewa mutane baki, Kaga Sameer ka d’auki hotonsa ka raba a masallatai ko Allah zaisa a dace...” “Mama neman kai kike dani...?” Shamsu yace yana mai mik’awa Sameer hannu domin yin masabaha... Mama tace “Ahtoh naga abin naka bana k’are bane ai....” Sameer dake danne dariyarsa yace “Yanda kikace hakan za’ai Mama...” “Toh ai ba masallaci ya kamata kukai ba makarantar ‘yanmata ya kamata kukai tallan nawa...” Shamsu yace yana mai zama gefen Sameer... D’an darawa sukai gaba d’aya kana Mama ta mik’e tana tambayan Sameer mai za’a kawo masa... Cikeda ladabi yace “A’a Mama nikam a k’oshe nake na gode....” Mama tace “Aiko dai kaji mai Iyali, wanine dai sai anyita fama dashi....” Shamsu ya tari zancen nata da fad’in “Nima ruwan tea d’in nan kawai ya isheni Mamana...” “Kadaiji dashi..” Mama tace sanda take bari masu parlorn... D’an shaking hannu suka kumayi suna dariyar draman Mama kana Shamsu yace “Doc,ya akai ne... Kwana biyu ko k’yallinka ba’a gani, ko zumud’in angoncin ne ya soma b’oyeka....” Yai maganar cikeda zolaya... Gajeren tsaki Sameer yai had’ida b’alla masa harara kana yace “Aure ko damuwa....” Shamsu ya d’an dara kad’an “Yaushe aure ya koma damuwa, ince gashi kaida Mama kun hanani sakat.... Ni gwarama da kazo coz dama inatason mu had’u naji what are your plans...” Fuzar da iska Sameer yai a hankali had’ida fitowa daga cikin kujeran kad’an, saida ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa kana yace “Wannan kuma saidai ka tambayisu Abbah don ni kaina ban sani ba....” Dariya mai bayyana hak’wara Shamsu keyi yana mai furta “Sameer kenan, gaba d’aya sai ka juye min Sameer d’in dana sani sanda muke sch kafin ka auri Partner....” Nanma dai d’an duban nasa kawai Sameer yai wannan karon harda tab’e baki kad’an “Kaidai baka tab’a d’aukan abu serious, na kawo maka matsalata kana dariya...” “Toh kuka kakeso nayi.., Kai ba d’an gata bane, su Mummy Sun aura maka Siyama yanzu gashi su Abbah zasu aura maka Sahariyya... Ni amin Auren mana idan inada gatan....” Har yanzu dai dariyar bata bar saman fuskar Shamsu ba.... Mik’ewa tsaye Sameer yai yana zira hannaye cikin aljihu... Shamsu dake sipping tea ya d’ago yana dubansa kana yace “Ina kuma zakaje naga dai shigowarka kenan...” Agogon hannunsa yake dubawa lokaci guda yake furta “Is pointless talking to you, bazaka tab’a canzawa ba Shamsu kai komai a rayuwa shiririta ka d’aukesa...” Ganin da gaske Sameer tafiya zai yasa Shamsu kamo hannunsa ya maidasa ya zaunar yana fad’in “Haba surgeon abin bai kai nan ba, kasan dai dole na tab’a haline zauna, lets talk...” Kallon ko inkula Sameer ya aika masa sanda yake zama bisa sofar..... Zamansa yai daidai da soma kiran wayarsa, hannu yasa ya ciro wayar dake aljihun wandonsa, mamakine ya cikasa ganin mai kiran nasa... Shamsu ya da yaga yayiwa screen d’in waya k’uri yace “Ya dai lafia....?” Sameer yace “Kana maganar Siyama kaga ga Daddynta na kira...” Ya k’arashe maganar yana mai receiving call d’in, dikda cewa yanajin bai kyauta ba don tin bayan da Siyama ta tafi bai sanar da Daddyn komai ba.... Bayan sun gaisa cikeda mutuntawa Daddy yace “Sameer inason ganinka....” Duban Shamsu Sameer ya d’anyi Shamsun ma Shi yake duba, jin Sameer yai shiru daga d’aya b’angaren ya sa Daddy ci gaba da fad’in “Ina Kano karka damu basai kaje Kaduna ba, ina nan Tahir kazo ka sameni...” Harce har na had’ewa yake furta “O... Ok Daddy, zanzo yanzu in sha Allah...” Daddy yace “Good, saikazo.....” Datse kiran yai yana mai duban Shamsu... Shamsu ya d’aga masa gira alamun tambaya... Fuzar da iska kad’an yai kana yace “I’ve to go, Daddy keson ganina yana nan Kano.... Allah sa ba maganan Siyama zaimin ba don gaskiya zanji kunya tinda ni banje na sameshi ba shi ya taho ya sameni...” “Kaima kasan bazai wuce hakan ba, bacin haka mai zaisa ya nemeka har Kano...” Shamsu yace yana mai mik’ewa tsaye shima.... Girgiza kai Sameer yake a hankali tamkar wanda yai nisa cikin tunani kana yace “I don’t know... Kaga bara naje na sameshi naji ko menene..” Ya mik’a masa hannu suka d’anyi handshake kana Shamsu yace “Shikenan Abokina sai munyi magana... Zamu had’u later idan kana hospital ne ma sai ka fad’a mun...” “Ok until later..” Sameer yace kafin ya fice.... *** Daddy ya gyara zama sosai yana mai ci gaba da furta “Sameer, sam ban kiraka nan akan maganar matarka Siyama ba don nasan iyaka hak’uri kayi da Siyama, ni kaina shaida ne don a baya komai tayi bayanta nakebi bana considering d’inka.... Sameer kayi hak’uri ka yafeni bisa duk abubuwan da na maka baya because of my selfishness...” Cikin sauri Sameer ya d’ago yana duban Daddyn Siyama, lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “No Daddy, dan Allah ka daina rok’ona gafara, baka tab’a mun komai ba ni, har kwanan gobe Uba kake min koda bani auren Siyama sabida kaid’in Abokin Daddy na ne....” Daddy yai murmushi cikeda jin dad’i kana yace “Allah ya maka albarka Sameer...” Sameer ya amsada Ameen a hankali, Daddy yaci gaba da fad’in “Wato Sameer abinda yasa na kiraka ba komai bane face kan maganar Khalid da k’anwarka Nabilah... Nasan kasanda batun....” Wannan karon mamaki ne sosai ya nuna a fuskan Sameer don sam bai kawo hakan a zuciyarsa ba, baiyi zaton mak’asudin zuwan Daddyn ba kenan....Jinjina kai yayi yana mai d’aura murmushi kad’an saman fuskarsa... Daddy ya jinjina kai yace “Alhamdulillah..” Saida ya kuma gyara zamansa kana yaci gaba da fad’in “Inaso kamin jagora wajen mahaifinka na nemawa d’ah na Khalid aurenta....” Shiru ne ya d’an ratsa tsakani har saida Daddy yace “Akwai matsala ne....?” Girgiza kai Sameer yai kana yace “A’a babu matsala Daddy ni zan maka jagora har wajen Abbah na, bakada matsala idan don wannan ne... A koda yaushe fatanmu shine zab’in Alkhairi...” Daddy ya murmusa kana yace “Toh Alhamdulillah, yanzu na baka wuk’a da nama inaso kafin na bar garin nan na sami mahaifinka muyi magana ta manya, sai ka soma tuntub’arsa muji yaushe yake free, sai ya bamu rana...” Sameer ya jinjina kai a hakali yace “Shikenan Daddy zan tuntub’esa kaman yana kace...” Daddy yai masa godiya kafin sukai sallama Sameer ya fice..... *** A can gidan Abban kuwa Zulfa’u durk’ushe take gaban Iyayen nata Bana Alhaji da Abbah, Baba Alhaji ya kuma gyara zama kana yace “Ke muke saurare Zulfa’u kinyi shiru, shirunki na nufin kin amince da komawa gidan mijinki na fari kenan....” Abbah yai saurin katsesa da fad’in “A’a Yaya shirun bazaura baya nufin Eh ne, idan baka mance ba ko shari’a cewa tayi Budurwa ce shirunta ke nuni da Eh amma banda bazawara, Yaya karmu mata dole, akwai lokaci, munada nan da wattani biyu gaba idan har tayi shawari ta tantance sai ta sanar damu amma babu batun tilastawa, koda bata tab’a aure ba ma nayi alk’awari bazan kuma tilasta ma d’aya daga cikin yarana ba, ina kuma fata iyaye masu wannan d’abi’a su farga su daina...” Banda uwar harara babu abinda Baba Alhaji ke aika masa... Ala dole ya jinjina kai kana ya dubi Zulfah da kanta ke k’asa tin shigowarta yace “Maza tashi ki shige gida, amma ki sani bazamu zuba miki ido ba kaman yanda Babanki keso mu sakaki gaba muna kallo, kafin wa’adin nan ya cika kizo mana da zance mai dad’i....” Jinjina kai kurum tai ba tareda cewa komai ba don idan ta bud’e baki tabbas kuka ne zai fito.... Cikeda tausayawa Abbah ke dubanta, cikin muryar mai taushi yaceda ita “Tashi kije mamata.... Allah Ubangiji ya miki albarka ya miki zab’i mafi alkhairi...” Baba Alhaji ya saki baki yana kallon d’an uwan nasa, k’wafa kurum yai ba tareda cewa komai ba saima karkad’a kai da yake tamkar wani k’adangare.... Zulfah tana shiga gida ta fad’a jikin Mamy sai kuka, haka Mamy taita lallashinta tana nuna mata ko wani bawa da kalan tasa k’addaran a rayuwa ita kuma kalan tata k’addaran kenan.... Koda Sameer yazo ya sami Abbah da batun shikam Abbah mamaki ma abin ya bashi ganin lokaci guda maganan auren yaran nasa ne yaketa kunno kai kaman wad’anda ake ingizawa, da farko Ma’aruf ne da Zulfa’u yanzu kuma ga Nabilah....Shiru yai tamkar mai nazari har lokacin baice komai ba.... Sameer ne ya d’an gyara zamansa had’ida gyaran murya kad’an kana yace “Abbah idan baka shirya tarbansu ba babu matsala ni sai na sanar da Daddyn sai zuwa wani lokacin....” Girgiza kai kad’an Abbah yai kana yace “Ba nufina ba kenan Ma’aruf, shin tambayan izini zasuzo ko kuwa neman aure zasuzo, idan neman aure zasuzo toh fah dole sai nayi magana da d’iyata, na sani d’anuwan matarka ne kuma babu wani dogon bincike tinda kai ka sansu tare kuka taso amma d’iyata fah? Dole sai anji daga gareta...” Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “You’re right Abbah...” Abbah yace “Yauwa yayi kyau daka fahimci hakan, zan sami mahaifiyarta ta tuntub’eta muji nata b’angaren... Idan ta amince tana son D’ansu shikenan sai suzo muyi magana, don burin ko wane uba kenan yaga d’iyarsa data isa munzanin aure a d’akin mijinta... Duk yanda mukayi da mahaifiyarku zan sanar dakai kai kuma saika sanar dashi....” Sameer ya amsada “Toh Abbah hakan yayi....” Abbah ya jinjina kai kana yace “Toh kai ya batun naka auren....?” Gaban Sameer ya yanke ya fad’i, shi harga Allah mancewa yakeyi da wani aure dake gabansa... Ganin yayi shiru yasa Abbah cewa “Anya Ma’aruf kana farin ciki da hukuncin da ka yanke...?” Gaba d’aya sai yaji jikinsa ya masa mugun sanyi da tambayar mahaifin nasa, ta yaya zai sanarda Abbah yana Farin ciki da wannan hukunci da ya yanke ma kansa bayan yasan ba hakan bane, toh amma wannan hukunci ne da ya riga ya yanke ma kansa dukda sanin cewa shi kansa baisan ko zai iya ba...Baikaiga bashi amsa ba sukaji sallama daga k’ofa, Aunty Lami ce ta shigo sai washe baki take tana kod’a Sameer da fad’in “A’ah Kaga ashe ma ga angon a nan... Ango mai tagwayen mata dama nemanka nake....” Murmushin yak’e kawai Sameer keyi yayinda Abbah ya tsare yana dubanta... “Sameer yace wani abu ne Aunty...?” Aunty Lami dake k’ok’arin zama saman kujeran gefen Abbah tace “Dama kan maganan lefe ne, kasan Mamy dai ‘yar kunyace ta d’an fari tsakaninku shine ta wakiltani mu tattauna komai, kama daga kayan lefe zuwa duk wani abu na Al’ada da za’a buk’ata kaga sam bamuda wani sauran lokaci wata biyu ne jal ya rage mana baima cika ba...” Sameer ya d’an shafa kansa kana yace “Wannan duk babu matsala Aunty, duk abinda ake buk’ata a fad’a mun, kayan lefen kuma zan maki transfer din kud’in zuwa account d’inki idan akwai abinda yayi short sai a sanar dani...” Aunty Lami ta shiga Washe baki tanaci gaba da kod’asa yayinda Abbah yabi d’an nasa da duban tausai, harga Allah tausayin Sameer yake don yasan wannan aure tilasta ma kansa kurum yayi..... Wayar da ake bugowa Sameer d’in ya sanyashi mik’ewa ya fice don amsa kiran yayinda Aunty Lami taci gaba da kid’inta tana rawarta don sam Abbah bai kulata ba tinda shi ba farin ciki yake da wannan aure ba.... *** Koda Mamy ta tuntub’i Nabilah da batun Khalid bata bata k’wakk’waran amsa kai tsaye ba, ita Nabilar gani take kaman anyi gaggawa, wai ita ake maganar aurenta bayan ga Addah Zulfah yanzu a gida ita kam da dai an bari ba yanzu ba har ta tafi IT, miyema na gaggawan.... Mik’ewa Mamy tai ta dubi Nabilah da har lokacin kanta ke duk’e k’asa kana tace “Idan nima kunyata kikeji ga Addarki nan sai ki sanar da ita, idan baki sonsa kar a b’ata masu lokaci na sanar da mahaifinku....” Sai sannan ta d’ago tana duban Mamy da idanunta da sukai raurau, ita fah Wai son Khalid bane batayi hasalima bata tab’a soyayya da wani d’ah namiji ba bayan Khalid d’in, amma abinne yazo mata a bazata, sannan sai tana ganin kaman anyi hanzari, bata ce komai ba har Mamy ta fice... Zulfa’u ta kamo hannayen ‘yar uwarta murmushi kwance saman fuskarta take fad’in “Nabilah karki dubi wai dan gani nan a gida, shi aure ba haka yake ba, koda ace ban tab’a aure ba kowa da lokacinsa, sau nawa k’arama a gida takanyi aure ta bar yayyenta, hakan ba yana nufin laifinsu bane ko gazawarsu ce, a’a lokacinsu ne baiyi ba don shi aure hab’o ne da zaran lokaci yayi toh fah sai anyi, haka nan wasu nasu lokacin a kusane ballantana ke da har kike jami’a da girmanki da hankalinki, nidai a nawa ganin idan har kina sonsa ki basu dama....” D’ago idanu tai tana duban Zulfa’un kana tace “Nifah Addah Zulfah bawai son Khalid bane banayi, hasalima kinsanni banida wani saurayi tun tasowata idan bashi ba sabida no one stands me, fad’ata kawai ta ishesu shid’in dai shine nake tunanin fad’an nawa ne yafi komai birgesa, kuma Addah danginsa fah basa k’aunata especially wannan matar Ya Ma’aruf d’in meyasa all of a sudden zasu amince ya aureni, something doesn’t add up gaskiya....” Girgiza kai Zulfah tai kana tace “A lokacin da basu k’aunarki basu san wacece ke ba, kumama banda abinki Siyama ai matar Yayanki ne so na tabbata abubuwan data miki da bazata miki yanzu ba indai har tana k’aunar d’an uwanki toh ko shakka babu kema zata k’aunceki, duk bama wannan ba, shi uban gayyan tinda yana sonki ai an gama komai tinda dashi zaki zauna badasu ba...” Dubanta kurum Nabilah keyi kana tace “Amma Addah ke kinsan illar ace dangin miji basa k’aunarka tinda ya faru dake dasu Hajiyar Ya Hafiz da yaranta...” Zulfah ta d’an murmusa kad’an had’ida girgiza kai “Wannan yasha bambam da nawa Nabilah, shi Khalid mutumin k’warai ne kuma shi ya nuna yana k’aunarki ni kuma Ya Hafiz dole aka mana kuma bai k’aunata shiyasa ya kasa karb’a mun mutuncina wajen ‘yanuwansa, na tabbata Khalid bazai bari wani nasa ya muzguna miki ba ko ya tozartaki, kuma kema shaidace akan hakan... Amma zab’i na gareki k’anwata, abinda kikeso muma shi muke so... Allah ya miki zab’i na alkhairi kinji koh....” Nabilah na murmushi ta rungume ‘yar uwar nata tana fad’in “Allah ya shiga al’amranmu gaba d’aya Addah ta....” Zulfa’u da ce ta sanarda Mamy yanda sukai da Nabilah, tabbas Khalid baida wani aibu idan ka cire mahaifiyarsa da ‘yaruwarsa Siyama, kuma ko wane aure dole yazo da kalan nasa tangard’an tinda abu ne wanda shaid’an bai k’aunar yaga anyishi, babban abinda ake buk’ata shine ma’arautan su kasance masoyan juna ne duk soyayyar wani daban akan iya samu daga baya, tabbas Abbah ya cika alk’awarinsa na baiwa yaransa dama wajen zab’en abokan zamansu... Bayan kwana biyu ya sami Sameer da batun don bai kamata abar babban mutum irin Daddy yaita jiran tsammani ba, Abbah ya tabbatarwa Sameer sirkinsa Daddy ka iya zuwa neman auren d’iyarsa Nabilah ga d’ansa Khalid, dikda cewa har yanzu Sameer d’in bai shiryada Siyama ba sosai yaji dad’in wannan had’ida za’a kumayi Don ko babu komai Khalid d’an uwane a wajensa koda bai auren Siyama, tare suka taso k’aramin k’ani ne a wajenshi they’re practically brothers... Baiyi k’asa a gwiwa ba ya sami Daddy da batun.... Sosai Daddy yaji dad’in martanin da ya samu daga iyayen Sameer d’in tuni ya shirya ranan tunk’aran mahaifin Sameer da batun, mutum biyu ya wakilta tare dashi shine cikon na ukun, mutane biyun kuwa duka sirakansa ne, Mijin d’iyarsa Siyama Wato Sameer saiko Yayan matarsa Wato Engr Ma’aruf.... *** K’uri Muhibbah ta masa sanda yake ci gaba da feshe jikinsa da tiraren, kaman wacce ta tina wani abu ta mik’e ta amshi turaren tana mai ci gaba da fesa masa, hannu ya mik’a ya d’auki hukarsa dake saman drawer a nan closet d’in, tai saurin amsa tana k’ok’arin saka masa, tsaf ya sauk’e kyawawan idanunsa saman fuskarta, kana iya hango tsananin damuwa da tashin hankali cikin fuskar tata.... Hannunta ya kamo duka biyu har lokacin idanunsa na tsareda ita, ta d’ago idanunta da sukai rau rau, tai saurin sadda idanun nata k’asa yawa mutumiyar arziki... Hannu yasa ya tallafi hab’arta, ya d’ago, A hankali ya furta “Kuka...?” Kaman wacce akace nan hawaye suka soma zarya a fuskarta....Cikin murya irinta mai kuka take furta “What do you expect...? Aure fah zaka tafi nema.. Ba dole nayi kuka ba...” Ta k’arashe cikin salo na ban tausai.... Murmushi ya sakar mata kana yasa tafukan hannayensa duka biyu ya tallafi fuskarta “Ki kwantar da hankalinki neman aure zan tafi amma ba nawa bane wannan karon, rakiya zanyi wannan karon....” D’an turo baki tai kana tace “But still naka na zuwa...” Da gefen bakinsa ya d’an murmusa kana yace “I thought we’ve already talked about that...” Jinjina masa kai tai kana tace “Haka ne Excellency na, and you’ve no idea how happy I’m daka zama pure and transparent baka b’oye mun komai ba, farin cikinka shine nawa mijina... You’ve my unconditional support ba’a siyasarka kawai ba harta a neman aurenka muddin zaka kasance cikin farin ciki.... Burina na faranta maka mijina...” Ta k’arashe cikin salo na kashe murya had’ida shafar fuskarsa... K’uri kurum ya mata kaman mai son fahimtar wani abu.... Gajeren murmushi ya sakar mata kana ya shafi fuskarta kad’an yana mai duba agogon da bai jimada d’aurawa a tsintsiyar hannunsa ba.... “Suna jirana... Sai na dawo koh....” Ya k’arashe yana mai gyara zaman hularsa da tasha tangaran sai k’yalli take.... Karkace kai Muhibbah tai tana dubansa, shu’umin murmushi saman fuskarta take furta “A dawo lafiya Excellency na, you take care....” Yana ficewa dariya ta tintsire dashi had’ida fad’awa kan gado da baya, a fili take furta “Ma’aruf kenan, lallai iska na wahal da mai kayan kara, kayi kuskure da ka amince nid’in zan zuba maka ta mujiya ka kawomin wata ‘yariska gidan nan da sunan amarya....” Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da dariya.... Wayarta dake gefen gado ta janyo ta shiga neman layin Akram.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *80* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Shiru Akram yai yana saurarenta daga d’aya b’angaren, shi kansa baisan ina suka dosa ba shida Boss d’in nasa balle yace mata ga yanda suka nufa.. Fitowar Engr yasa Akram katse kiran yana mai sanar da ita zasuyi magana... Cikin saurin ya fito da niyyan bud’e masa front seat, kaman ko yaushe jama’ansa suka nufosa, masu kawo koke da matsaloli nayi masu gaisuwa nayi... Gaba d’aya hak’uri ya basu kasancewar baiso ya makara dan yanda zaijesa nada matuk’ar mahimmanci, ya dubi Akram yace dashi ya tsaya yaji matsalar kowa ya kuma rubuta ya aje masa.... Akram ya d’an sosa kai kana yace “Your Excellency fitar namu fah....? Sannan waye zai tuk’aka, ko na kira Jalo ne...?” Gyara zaman babban garensa yai kana yace “Karka damu zan driving da kaina, just stay here ka saurari matsololinsu....” Ya k’arashe yana mai nad’e babban rigar tasa sanda yake shiga mazaunin matuk’i..... Jinjina kai Akram yai ba tareda zuciyarsa ta sami natsuwa ba, shi kansa baisan dalilin hakan ba... Har Engr ya fice daga gidan Akram bai koma daidai ba, zamewa yai daga cikin mutanen ya nufi sashen Muhibbah yana mai dialing wayarta.... *** “Ma’aruf d’an siyasa....” Daddy ya fad’i bayan sun gaisa.... Murmushi saman fuskar Engr Ma’aruf yake fad’in “Ya zamuyi Ya Engr mutane sun zab’omu sunce mu tsaya masu, kuma tinda ku manyanmu kunk’i ku tsaya...”Yai maganar yana mai d’an murmusawa kad’an... Jinjina kai Daddy yai shima k’aramar dariyarce saman fuskarsa, lokaci guda yake furta “Da mahaifinka nada rai tabbas da yayi matuk’ar alfahari dakai....” Wannan karon k’aramar murmushi ya d’an saki yana mai tuna Babanshi, mutuminda ya maidasu ‘ya’ya a lokacinda suka rasa iyaye, mutuminda ya maidasu masu galiho a lokacinda suka rasa gata, mutuminda ya masu sutura a lokacinda suturarsu ta yaye... Tabbas dole yaji hud’ubar Baba ya rik’e Muhibbah kaman yanda yai masa alk’awarin rik’eta amana da kuma yin hak’uri da ita.... Babanshi shine musabbabbin aurensa da Muhibbah kuma alk’awari ya masa wanda ya zama dole a gareshi ya cika muddin yana son gamawada duniya lafiya.... Jikin Daddy ya d’anyi sanyi ganin yanayin Engr d’in ya d’an canza.... Gyara zamansa ya d’anyi had’ida yin gyaran murya kad’an “Babanka mutumin kirkine Ma’aruf, har gobe shi d’in babban Yaya ne kuma uba ne a gareni, duk wani matsayi da na taka a yau ta dalilinsa ne, cikin k’udurar Ubangiji, banida abinda zan biyasa dashi bacin na rik’e masa amanar tilon d’iyarsa Daula, bazan tab’a bari wani ya muzgunawa Daula ba muddin ina numfashi a doron k’asa domin ita d’in amanace a gareni.. (Wannan na d’aya daga cikin abinda yasa Daddy ya kasa sanar da Matarsa Farida labarin aurensa na biyu..) Abubuwanda Babanka yaima mutane na alkhairi basa k’irguwa Ma’aruf, ko shakka banayi footsteps d’insa kake bi.... Ubangiji ya dafa maka ya kuma baka nasaran abinda ka sa gaba....” Engr ya amsada “Ameen Yaya Engr,....” (Haka nan Ma’aruf ke kiran Daddy Ya Engr kasancewar shima Daddy d’in civil engineer ne) Sallaman Sameer ne ya katse hiran tasu, Daddy ya mik’e yana fad’in “A’a Sameer ka iso...?” K’arasowa cikin parlorn yai yana mai risinawa had’ida mik’awa Daddy hannu dan musabaha yake furta “Eh Daddy na iso, aiki ne ya d’an rik’eni a asibiti...” “A’a babu komai, his Excellency d’inma gashi nan ya iso, ai sai mu d’au mik’ati koh...” Ya k’arashe yana mai d’aukan agogonsa saman center table had’ida d’aurawa a hannunsa na hagu... Sameer ya k’arasa ga mutuminda tin shigowarsa suka kasa janye idanunsu daga barin duban junansu.... Hannu ya mik’awa Engr alamun musabaha... Shid’inma hannun ya mik’o masa har lokacin duban juna suke ido cikin ido, wani yanayine da su kansu bazasu iya cewa abinda sukeji ba.... Sanda hannunsu ya had’e waje guda haka nan ta mik’e tsaye tamkar wacce aka sinkaya, Hajja mai kulada gidanta na amana da tin bayan mutuwar mijinta take gidan take kuma kula da ita dubanta tai ganin yau d’in ta fito har yanda bata iya fitowa cikin gidan tin bayan mutuwar maigidan.... Cikin sauri ta k’arasa gareta kana tace “Hajiya akwai abinda kike buk’ata ne...?” Dubanta tai da idanunta da kullum suke a kod’e kaman ta maras lafiya kana tace “Ma’aruf..!” Tana fad’in haka kuma sai ta juya ta koma cikin gida tamkar kazar da k’wai ya fashe mata a ciki.... Idan da sabo Hajjah ta saba da hakan, d’an fuzar da iska tai had’ida girgiza kai kana taci gaba da abinda take... Introducing junansu Daddy yai kana suka d’auki hanyar gidan Abbah... Tinda suka iso unguwar yakejin wani abu na tsargar masa, yakanzo unguwar sau tari yakan shige unguwar sau tari a matsayinsa na cikakken d’an siyasa mai neman takaran kujeran gwamna, amma wannan zuwan yanaji wani al’amari ne da baisan ya zai fasalta shi ba, tin bayan had’uwarsa da wannan matashi Sameer d’in yakejin wannan yanayi a tattaredashi, ji yake tamkar dik shekarun da yai a garin kaman akwai wani abu mai girma na rayuwarsa da ya rasa, sunan yayi rakiya ne amma sam hankalinsa bai jikinsa... Ji yake tamkar wani babban al’amari ne ke shirin faruwa dashi, wasu irin tunani yake tamkar wanda yake yunk’urin tina wani abu a shekaru masu tsawo.... Take kansa ya shiga mugun sara masa, bazaice ga maganganun da akai wajen neman auren ba, iyakacin abinda ya sani shine yayi rakiya amma duk wasu tattaunawa da akai da sunayen mutanen da aka ambata a wajen bazaice gasu nan ba, baisan kalan yanayin da yakeji ba, wasu irin tunani yake wad’anda kaman yana ganinsu a mafarkansa lokacinda yake k’uruciya, fuskar matar da ya hanga gittawarta a cikin gidan bai b’ace daga kwanyarsa da k’wayan idanunsa ba, kaman ya tab’a sanin mata mai irin fuskar a can baya wasu shekaru masu tsayi, saidai fuskar da ya sani tafi wannan yarinta da k’uruciya... Meke shirin faruwa dashi...? A ina yasan mai irin fuskar matar can...? Dafe kansa dake tsananin sarawa yai yana mai rintse idanunsa, lokaci guda ya mik’e ya shiga zagaye tapkeken parlorn nasa thoughts d’in bai k’yalesa ba har wannan lokaci, ji yake wasu abubuwa da suka faru dashi in his past suna yunk’urin dawo masa, ji yake bayansa na kiransa... Ji yake akwai wani babban gurbi na rayuwarsa da tsawon shekarun nan yake a bud’e yana yunk’urin cika kansa.... Yanda yaga rana haka yaga dare, wad’annan tunani sun kasa barinsa, kama daga had’uwarsa da Sameer izuwa zuwansa wancan gidan nemawa Khalid aure... Haka kurum yaji k’aunar Sameer ya shigesa har cikin ransa, zaiso su k’ulla alak’a da Sameer d’in don ko babu komai yanaji through Sameer zai sami amsoshin tambayoyin da suka k’ulle masa kai a halinda yake ciki... Harta Muhibbah bata gane kansa ba, dan koda ta tambayesa ya al’amarin ya kasance mai ya faru... Sam Engr bai iya bata amsa ba, ko bindiga za’a saka masa bazaice ga yanda al’amarin neman auren ta kaya ba, wad’annan tunani sunfi komai yawo a kwanyarsa, ya k’udiri niyyan binciko musabbabin abinda ya faru dashi da kuma k’anwarsa shekarun baya koda ace mutumin da ya kasance ya d’aukesu matsayin ‘ya’ya bai raye..... Shiru yai had’ida d’aura hab’arsa saman tafukan hannayensa ya shiga tunanin abinda Baba ya sanar dashi gameda karan kansa da k’anwarsa Daula a lokacinda Baban ke jinyarsa ta ajali..... _Ma’aruf! Ma’aruf!! Shine kalama guda tak da kake fad’i a lokacinda na tsinceku.... Ko an tambayeka sunanka iyakacin abinda kake fad’i kenan, hakan ya bamu tabbacin tashin hankali ne daka tsinci kanka ciki ya shafe maka tinaninka wanda ka mance komai saiko kalmar sunanka da bai fice a kwanyarka ba da kuma saman harshenka... K’asar duwatsu da muk’e tonon zinari a nan na tsinceku kaida yarinya jaririya k’udundune cikin zanin goyo, a lokacin bazaka wuce shekaru shida a duniya ba, ga kuma jaririyar daka rungumeta cikin hannunka... Na tambayeku ya akai kuka kasance a wannan k’ungurumin daji mai cikeda had’ari baka iya cemin komai ba sai kalmar sunanka Ma’aruf da kaketa nanatawa, a lokacin da muka tsinceku nida abokan tafiyata sai naso dank’aku hannun d’aya daga cikin yarana Kafin mu mik’a cigiyarku ga hukuma, amma koda mukazo tafiya sai kayi gudu ka kama k’afata kana fad’in kalmar Baba kuma kak’i kowa ya amshe jaririyar dake hannunka, ganin haka yasa na d’aukoku na kawoku gida wajen iyalina dashike ni a lokacin banida d’a ko k’wara dukda kasancewar nid’in sabon aure ne ban jima da yin aure ba, wani abin mamaki shine sanda na kawokuga Iyalina sai Allah ya jefa k’aunarku a zuciyarta, na sanar da ita yanda na sameku can Mining side k’asar duwatsu na tsinceku, tausayinku ya cika zuciyarta musamman wannan jaririya da aka raba da mahaifiyarta, na sanar da iyalina cewa zaku d’an zauna na kwana biyu likita ya dubaku a maku magani kafin na mik’akuga hukuma, mukai matsaya akan haka nida ita, bayan kwana biyu da shak’uwa ya kuma shiga tsakaninku sai cemin tai itakam bazata iya rabuwa daku ba, ba kaman Daula wacce ita da kanta ta rad’a mata wannan suna, dikda cewa dangina da nata basuso haka ba musamman da sukaga bamuda ‘ya’ya sai ku d’in kawai ga kuma tarin dukiya da mahaifina kedashi wanda ni kad’ai zan gajesa bayan bashi duniya ni kuma kune magadana don tuni nayi hakan a rubuce tinda banida mahaifiya banida yayye ko k’anne saiko dangin nesa dagaku sai iyalina Hafsatu wacce ta rigayemu gidan gaskiya kaman yanda ka sani, ciwon dajin mama shi yai ajalinta...._ Wannan karon Engr goge hawayen da suka siraro masa yai sanda ya tuna Mamarsa mai tsananin k’aunarsu wacce haihuwarsu ne kawai batayi ba amma duk wani kulawa da k’auna da uwa ke baiwa ‘ya’ya tabbas Mama Hafsatu ta basu wannan, Ubangiji yakai rahama makwancinki Mama, da ace mutanen duniya zasu zama irinki da Duniyarmu ta cika da albarka... Ya saki kalla uwar murmushi kafin yaci gaba da tuna jawabin Baba a gareshi... _Kaman yanda ka sani mahaifina Alhaji Mutallab maiDala shine mammallakin MUTALLAB’S Mining Company... Kamfanin hak’an ma’adanai na k’asa kama daga zinari zuwa duk wasu duwatsu masu daraja, Babana Mutallab Maidala ni kad’ai Allah ya bashi baida kowa sai tarin dukiya, dukiyarda nan gaba zaku gada kaida ‘yaruwarka Daula... Ma’aruf ka rik’e Daula amana ka kula da ita dikda cewa nasan na mik’ata hannun da za’a kula da ita, amma kasa ido akanta dikda haka, Daula itace sanyin idaniyana... Ka kular min da ita.. Sannan Muhibbah..._ Wannan karon nannauyan ajiyan zuciya ya sauk’e kafin yaci gaba da tinanin wasiyayyar Baba gameda Muhibbah a gareshi... _Muhibbah amanace a gareka kaman yanda ka sani mahaifinta amini ne a gareni, duk cikin d’iyoyinsa ya kasance yafi son Muhibbah, wannan dalili yai mata lak’abi da Muhibbah ya kuma rok’i alfarmata kan nai mata duk abinda takeso bayan bashi a raye ko menene matuk’a baifi k’arfina ba, wannan dalili yasa sanda tace duniyar nan bata son kowa sai kai banyi k’asa a gwiwa ba na aura maka ita, nasan baka sonta biyayya kawai kamin a matsayina na Uba a gareka... Ubangiji ya maka albarka yasa watarana kayi arba da danginka na asali dikda cewa kasha sanar dani cewa kaida Daula baku da iyayen da suka wuce nida Hafsatu, amma ina fata wataran INDA RAI Allah ya sake had’aku da asalin iyayenku... Ma’aruf ka rik’e amanan mutum Biyu Matarka Muhibbah ko mai zata maka da kuma K’anwarka Daula dikda cewa tana gidan aurenta..._ Wad’annan sune wasiyyan Babanshi a gareshi.... Yasa duka tafukan hanbayensa ya share fuskarsa had’ida fuzar da iska mai d’umin gaske, dubansa yakaiga Muhibbah wacce ke baccinta hankali kwance kana ya k’ura mata idanu tamkar mai tinanin wani abin, ya d’au lokaci yana duban nata kaman mai nazarin wani abu har saida ya soma jiyo kiraye kirayen farko na assalatu kana ya muk’e ya nufi bathroom da zummar d’auro alwala... Raka’atanil fajri ya soma gudanarwa a gida wanda dama d’abi’arsa ce duk ranar duniya kafin ya fice masallaci sallan asubahi.... Gaba d’aya yau d’in wane iri yake jinsa.... *** KADUNA Babu abinda Ammi ta fasa na shirye shiryen Bikin Khalid da Yesmin, ko Daddy bai tsaida Rana ba a cewarta ita zata tsayar saidai dik abinda zai faru ya faru, yauma sun ida waya kenan da Aunty Mahaifiyar Yesmin Don Yesmin d’in ta matsa mata ita zata dawo taga Khalid d’inta ta gaji da zamar Abuja, Ammi tace ta dawo kayanta ai duka gida ne da Abujan da Kadunan tinda mahaifiya takema Yesmin... Khalid na kishingid’e d’akinsa yana duban hotunan Nabilah da ya sata a dp d’inta shi kad’ai sai sakin murmushi yake yana tina farkon had’uwarsu da kalan tsiwar da tai masa gashi tin jiya yake neman wayarta ya kasa samu, ji yake kaman yai tsuntsuwa ya gansa a Kano, kaman daga sama sai ganin hamshak’an Gezna yai farare da kaloli Ammi ta watsa saman rug tana fad’in “Gasu nan tinda kai bakasan kai shiri ma kanka ba....” Da tsananin mamaki ya tashi ya zauna sosai... “Ammi wad’annan fah... Na menene... Kinsan dai banson saka kayan da daga nesa za’ai noticing d’ina, banson saka kaya masu haske da d’aukan ido ni ba wani basarake ba...” Baikai aya ba ta katsesa da fad’in “Kai tafi can ka rufewa mutane baki, wane ango ne ka tab’a ganinsa babu kwalliya ranan bikinsa...” Sai yanzu ya fahimci kayan na menene.... Ammi taci gaba da fad’in “Sai ka zab’i color d’in da zaku saka ranan dinnner shisa na had’o maka da Golden brown da kuma Royal blue tinda nasan ranan d’aurin aure White zaku saka... Amma inaga dai ka zab’i golden brown d’in tinda naji Yesmin d’in ma Momynta na cewa tafi son golden d’in akan blue d’in, tinda dukanku farare ne sosai zai haskaku... Gameda huluna kuma munyi magana da Maman Falmata ita take sak’ama akasarin gwamnoni da manyan ‘yan siyasa zata turo kalolin designs sai ka zab’a, hula ne masu kyau sak’ar Maiduguri, ai dai zanna kake sakawa inji...”Tinda ta soma magana ya rafka uban tagumi yana dubanta.... “Inata magana ka zuba mun ta mujiya, kaga bazan zauna na zuba maku idanu kaida Babanka ba, na biye nashi sam bazai maganar auren nan yanzu ba...” “Toh wai Ammi saurin mi akene....? Kuma ma banda abinki Ammi Daddy ai shine mai karb’a min auren koh... Mu jira muga gudun ruwansa tinda shine wakilina....” Tinda ya soma magana take aika masa muguwar kallo, k’wafa tai kana tace “Ai bakinku d’aya dakai dashi, idanma wani abin kuke b’oye mun Allah zai kamaku, dik abinda kuke k’ullawa Allah zai tonosa..” Tasa kai zata fice Khalid dake k’unshe murmushinsa don yanzu abin Ammin dariya ya soma basa ya bud’e murya yace “Kayan fah Ammi, na biyoki dasune....?” Harara ta galla masa kana tace “Ka tattara ka kaisu d’inki ban janye k’udirina ba...” Yai murmushi yana mai bin mahaifiyar nasa da kallo, dukda hali irin nata haka nan yake k’aunarta baida ya ita, tausayinta ya kamasa sanda ya tuna tabbas akwai gagarumin tashin hankalin dik randa tasan Daddy nada wata matar harda Yara... Khalid ya dafe fuskarsa da tafukan hannayensa biyu yana tunanin ko ba dad’e ko ba jima wannan ranan tana nan zuwa, ranan da Ammi zatasan wannan batu... Baisan mecece makomar family d’insu ba dik randa wannan labari ya fito fili... A hankali ya sauk’e siririyar ajiyan zuciya, murmushi kwance saman fuskarsa sanda ya tuna ‘yan k’annensa haka kurum yaji yana son magana dasu, lokaci guda ya shiga neman layin Aunty Daula.... *** ABUJA Suna tsaka da batun auren Khalid d’in wayarsa ta shigo mata, nuna masa screen d’in tai murmushi saman fuskarta take furta “Kaga ango na kira ana batun shi....” Daddy ya murmusa kad’an kana yace “Ai naga alama yanzu Khalid yafi ji dake sama dani, d’auka amma karki sanar dashi shirina, ba yanzu ba....” Jinjina kai tai kana ta d’au wayar da sallama... Gaisawa sukai cikeda barkwanci kana ya tambayi k’annensa, Aunty Daula tace dama tasan kiran nasu ne, tuni ta mik’e ta nufi playground tana k’walla kiransu tana fad’in ga yayansu on the phone, ai har suna rige rigen amsar wayar suna zuba masa shagwab’an yaushe zaizo shi... Daddy dai murmushi kurum yake zuciyarsa na masa wani irin sanyi... Aunty Daula ta dubi Daddy tace “Toh ya maganan su lefe da sauransu fah...?” Daddy ya jinjina kai yace “Wannan wuk’a da nama na hannunki uwar ango... Ke zaki shiga kasuwa kiyi komai...” Aunty Daula ta jinjina kai tace “An gama rankashi dad’e... Amma nidai gani nake da an sanar da Khalid don shima yai nasa wasu ‘yan shirye shiryen k’asan aure fah ba wasa bane, maganan lifetime commitment ake...” Jinjina kai yai a hankali kana yace “Nasan da wannan, abinda yasa banso maganar ya isa kunnen Khalid yanzu, nasan zai iya sanar da Farida tinda mahaifiyarsa ce, zaiji sam bai kyauta ba dole ya sanar da ita, itakuma zatai amfani da k’arfin ikon da take dashi akansa a matsayinta na mahaifiyarsa ta b’ata komai ta hanashi Farin cikinsa, I’m doing this for my son, b’oye masa da nayi ba komai bane face sabida cikan burinsa... Daula INDA RAI zan cika burin d’ahna Khalid da izinin Allah....” Murmushi ta saki mai taushin gaske ta saki had’ida d’aura kanta bisa kafad’ar mijin nata tana mai lumshe kyawawan idanunta.... D’an dafa fuskarta kad’an yai suna shak’ar numfashin juna kana yace “Ji nake kaman kar na tafi na barki Daula...” Yai maganar yana mai rik’o hannayenta su duka biyun suna fuskantar juna....Murmushi ta sakar masa kana tace “INDA RAI wata rana zamu kasance tare gaba d’aya babu b’oye b’oye like a one big happy family, In sha Allah...” Murmushi bai bar saman fuskar Daddy ba ya kuma kai tafin hannunsa ya shafi gefen fuskarta na dama kana yace “I can’t wait for this moment to come... Ina rok’on Allah yasa Yana nan kusa...” Su duka biyu sukai k’uri suna duban junansu na d’an wani lokaci kana Daddy yace “Ni zan wuce Kaduna, duk yanda abun ya kasance zan kiraki na sanar dake komai, for now inaso ki gama sayyayan duk wasu abubuwa da ake buk’ata,akwai number k’anwar mahaifiyar ita Nabilar da Sameer ya tura min sai ki kirata ku tsara komai ki kuma tambayeta wasu abubuwan...” Aunty Daula ta jinjina kai tace “Shikenan, zan kirata in sha Allah sai mu tsara komai...” Hannayensa Daddy ya bud’e mata kana yace “Come here...” Cikeda kunya ta k’arasa ta shige cikin jikinsa... Suka k’ank’ame juna tamkar su dawwama a haka ba tareda wani abin ya gitta tsakaninsu ba, haka Aunty Daula ta rabu da mijin nata cikeda bege da alhini... *** Gaba d’aya yau d’in Yusrah bata gane kanta ba, ta kuma zama wata sukuku da ita haka nan, har suka fito daga second class d’in tana nan haka sukuku, babu wani abinda ta fahimta, ganin abin take tamkar a mafarki Wai ita ake batun aurensu da Khalid kuma har an saka rana lokaci guda dana Yayanta Ma’aruf, abinda yafi bata mamaki shine tinda akai maganar auren Khalid bai nemeta ba, bai kuma sanar da ita komai ba.. Mai hakan yake nufi...? Ta lumshe idanunta a hankali tana mai zama bisa carpet d’in masallacin.. Yusrah da tuni ta d’auro alwala zama tai gefenta tana zira safarta dara cire sanda zatai alwala lokaci guda take maganawa Nabilar... Ganin hankalin Nabilah bai tareda ita ya sanyata d’an dungurinta kana tace “Ke Wai meyene haka, tin safe kike haka nan... Wai meke faruwa ne, kinga d’azu a class k’iris ya rage wannan d’an rashin mutuncin bai koreki daga ajinsa ba, wai dan Allah meke damunki....?” Idanu Nabilah ta zuba mata kana ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an tace “Wai aurena ake shirye shirye... Could you imagine...” “No.... Are you serious...!” Yusrah tace sanda take mik’ewa tsaye cikeda murna harda sakin k’aran murna gaba d’aya ta mance masallaci suke har saida Nabilar ta janyota had’ida d’aka mata duka tace “Ke bafah a class kike ba....” Yusrah ta zauna tana mai ci gaba da fad’in “Ke Wai da gaske kike....? Aure with who....?” Lokaci guda kuma taci gaba da murmushi tana nunata da d’an yatsa take fad’in “Wllhi da shine... I’m certain dashi ne.... Haladu na Mamani... Wayyo angon teddy bear... Allah yayi, wllhi dama kunyi masifar dacewa...” D’an tsuka Nabila tai kana tace “Bansan misa Abbah ke hanzarin ya aurar dani ba saikace na tare masa wani abin...Kuma shi d’an rainin hankalin ko wayarsa ban sake ji ba ko ma waye zai jida kai oho....” Tai maganar cikin fad’a... Yusrah na murmushi ta dafata kana tace “Kan ango yayi zafi toh ki kirasa kiji lafiyarsa mana....” Wani uwar hararanda Nabila ta b’alla mata ya sanyata had’iye sauran zancen... “Kar Allah sa yayi lafia idan sai na kirasa, kema kinsan idan za’a shekara a haka bazan kirasa ba, kuma bazan nuna masa nasan komai gameda batun auren ba... Ke ni haushi ma yake ban wllhi...” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye da zummar d’auro alwala... Yusrah ta murmusa tace “Ah lallai na yarda abin yazo... Allah huci ran Amarya...” Harara Nabilah ta galla mata ba tareda ta kuma cewa komai ba don harga Allah wani irin mugun haushin Khalid d’in takeji... Koda ta koma gida ma Mamy da Aunty B ta tadda nan suna zancen, fuska a tamke ta gaidasu don gaba d’aya har mutanen gidan nasu haushi suke bata, ji take kaman ta nufi parlorn Abbah ta sanar dashi cewa itafah bata amsa auren Khalid ba toh amma rashin kunyar nata baikai nan ba, Koda ta iska Marliya a d’aki tsiya ta dinga mata musamman data fahimci ko labarin Bikin bata k’aunar ayi... A can parlor kuwa Aunty Daula ce ta kirawo layin Aunty B Dan su samu su tattauna maganar kawo lefe da sauransu... Da sallama Aunty Daula ta soma cikin siriryar muryarta mai dad’in saurare... Wani irin fad’uwan gaba Aunty Bara’atu ta tsinci kanta ciki ba tareda sanin dalili ba...... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *81* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sun ida wayar sun samu matsaya kan cewa ranan biki ma’ana ranan d’aurin aure sai su taho da lefen gaba d’aya, wani ikon Allah harta Mamy ma wani irin yanayi ne mai wuyan fasaltuwa ta tsinci kanta ciki sanda tai maganada abokiyar zaman mamar Khalid, muryarta baida maraba data marigayiya mahaifiyarsu, tamkar marigayiyace ke magana haka nan sukaji sautin muryar... Aunty B ta numfasa ta dubi Mamy tace “Muryar matar nan sai ya min kaman nasan mai irinta amma na kasa gane ina san mai irin muryar...” Sauk’e nannuyan ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “Muryar Hajja Mama naji a tattareda matar can... Babu abinda ya raba muryarta data mahaifiyarmu....” Numfasawa Aunty Bara’atu tai kana tace “Allah mai iko, shisa na kasa gane ina nasan mai irin muryar ashe dai irin muryar Mama Hajja gareta, kinsan ni ban wani san Mama Hajja sosai ba ina k’arama Allah yai mata rasuwa....” Take fuskar Mamy ya soma sauyawa, abubuwan da suka faru a wancan shekarun suka shiga dawo mata, k’walla masu zafin gaske suka ciko idanunta, dafa hannayenta Aunty B tai kaman zatace wani abu sai kuma ta kasa don ko shakka babu dukda juriya irin tata itama d’in sai ta kasa magana, zuciyarta tai rauni sosai, a hankali ta mik’e ta nufi waje ba tareda ta iya furta koda kalma ba.... Aunty Lami dake lab’e tana dubansu, murmushi ta saki a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta “Muddin Aminiyar Sirri tana tsakani bazaku tab’a kasancewa cikin farin ciki ba koda kuwa zaku nunawa duniya cewa cikin Farin ciki kuke, can a k’asar zuciyarku bazai kasance haka ba domin kaw wata gyambo ce da batada magani can k’asar zukatanku...” Ta kuma murmusawa kafin ta juya sad’af sad’af ta koma sashenta... *** Washe gari ta kama juma’a, tafe suke itada Atika a farfajiyan ofishin nasu, fitowarsu kenan daga d’akin gudanar da shirye shirye, ga tsananin rana da ake kwand’arawa... A gajjiye suka iso d’akin hutun nasu had’ida zubewa saman kujeru a gajjiye.... Atika ta rage mayafinta tana mai gaida Aunty Zilai colleague d’insu dake shirin fita daga d’akin sai zolayarsu take musamman Zulfa’u dashike Aunty Zilai mace ce mai barkwanci da son mutane... Sauk’e ajiyan zuciya Zulfah tai sanda d’akin ya rage saura su biyu tana mai fifita da takardan dake hannunta a hankali... Gyara zama Atika tai had’ida tsare k’awar tata da idanu.... D’an dubanta Zulfa’u tai kana tace “Ke kuma fah, wannan kallon na menene... Meke faruwa?” Atika ta d’an murmusa kad’an kana tace “Ai ke zan tambaya meke faruwa..? Irin wannan ajiyan zuciya da kiketa faman sauk’ewa akai akai tin muna hanya, kodai kiran manager d’in ne bakiso zuwa ba... Ni bakima sanar dani mi ya faru ba... Don’t tell me kin sauya ra’ayi dashi za’ai...?” Gajeren tsuka Zulfa’u tai kana tace “Ke ai kinga matsalarki kenan, you talk too much, har mutum ya rasa wanne zai amsa miki....” Atika ta d’an dara kad’an “Zulfa’u mai farin jini mai masoya... Nidai banga aibun Akram ba kuma shima Manager baida wani aibu wllhi, matarsa ma mutuniyar arziki ce takanzo gidan radio d’in nan kwanakin baya, very simple and friendly wllhi...” Harara Zulfah ta galla mata kana tace “Bazakiyi shaidan mace akan kishi ba, kinsan ance kumallon mata, kibar mace akan mijinta, duk kyaun halinta da kirkinta dole tai kishin abinda take so, ke ni wai ce miki nayi ina sonsa ne ma... Wllhi Atika ni dik kin isheni bari Oga Ameer ya shigo na kaiki sammaci kotunsa....” Atika ta dara kad’an kana tace “Aunty Zulai ma tayi ta barni, randa dik bana station d’in nan sai kunyi kewata... Kinga tashi mu samu muyi sallah mu koma kafin d’an nacin nan Ameer ya soma kirana, sam banson a had’ani program dashi Wllhi, fidda ficce ne dashi kaman mace...” Zulfah ta d’an dara tana mai fad’in “Ai Wllhi babu maganin surutun nan naki irin Ameer, jekiyo alwalwa ni na mik’a nawa tintini...” Ta k’arashe tana mai kurb’an bottle water dake rik’e hannunta... “Aw shine na biyeki naketa zuba, ashe kin riga liman tintini, ai sai kimin bayani...” Tai maganar tana mai d’an jan skirt d’inta sama kad’an, kana ta nufi d’auro alwala... Tab’e baki kad’an Zulfah tai murmushi saman fuskarta take furta “Ke dai kika sani kuma, uwar ‘yan zuba...” Wani ajiyan zuciyar ta kuma sauk’ewa tana tunanin encounter da jiya ta samu da Hafiz, ta tina abinda ya fad’i mata cewa bazata tsere masa ba dik rintsi sai ta dawo gareshi, he would make sure of that, ita d’in tasa ce shi kad’ai and no one else... Fuzar da iska mai d’umi tai a hankali, daidai nan wayarta ta soma ringing.... Takai dubantaga wayar dake aje saman table, lamba ce babu suna, ta d’an d’auki lokaci tana duban lambar har saida ta kusan tsinkewa kana ta d’aga da sallama... Shiru ba’a ce mata komai daga d’aya b’angaren ba, ta kuma yin sallama a karo na biyu nan ma shiru ba’ace komai ba, toh waye wannan mai kiranta yai shiru, tin kwanaki hakan ke faruwa da ita tin tana gidan Aunty Bara’atu, sai a kirata ai shiru kuma kaman da different lines ake mata hakan, da ace da layi guda ne tabbas da tai noticing layin ta daina d’agawa... D’an tab’e baki tai kana ta katse kiran tana mai addu’an neman tsari daga duk mai nemanta da sharri cikin zuciyarta.... Katse kiran keda wuya taji sautin shigowar message a inbox d’inta, saurin bud’ewa tai da niyyan karance sak’on, saidai abinda ta gani cikin sak’on ya bala’in d’aure mata kai had’ida bata mamaki... _Sallamarki kad’ai ta wadatarda zuciyar dake k’ishin ruwan sauraren muryarki_ Ta karance sak’on yafi sau abinda yafi, ta lura dik ranar da ba itace on duty na gudanar da shirin da take yi ba sai mai kiran nata ya kirata a ranan, dik randa itace da duty ta gudanarda program toh ko shakka babu mai kiran nata bazai kira ba... Toh waye wannan...? Tambayar daya tsaya mata a Rai, a haka Atika ta k’araso ta sameta, bata b’oyewa Atika komai ba harta sak’on saida ta nuna mata... Atika ma sosai abin ya bata mamaki, Toh ko waye shi kuma wannan sai Allah.... Dafa Zulfa’u Atika tai kana tace “Karkisa komai ma ranki k’awata, ci gaba da fawwalla wa Allah lamuranki da sannu zai rik’i ragamar al’amranki... Ki kwantar da hankalinki kinji koh... Dikda bamusan wanene wannan Mr Unknown d’in ba shima ki sakashi cikin jerin masu neman aurenki wa ya sani ko da Mr Unknown za’ai...” Ta k’arashe cikeda shak’iyanci.... Zulfah ta galla mata harara kana tace “Ai ke matsalarki kenan komai sai kin sako wasa ciki, wllhi dikdai wanda ya zamto mijinki nada aiki, ni ki tashi muje kafin su soma damun mu da waya...” Ta k’arashe tana gyara zaman mayafinta had’ida mik’ewa tsaye... Dariya Atika keyi suna tafe tana kuma zolayarta da *Mr Unknown* A haka dai har ranar ta k’are masu tinanin sak’o da wayar Mr Unknown kaman yanda suka saka mashi itada Atika bai k’yaleta ba... A hanya suna tafe suna neman adaidaita Manager ya k’araso, babu yanda baiyi ba ya rage masu hanya atafau Zulfa’u tak’i ala dole Manager ya k’yalesu badon yaso ba, haka Atika ta dinga mata mita a hanya.... Zulfah dai cewa tai taji amma wllhi bazasu shiga motar Manager ba... Kaman daga sama sai ganin Hafiz sukai gabansu tamkar wanda aka jefo... Take wutan fuskar Zulfa’u ya d’auke gaba d’aya, Atikar ma had’e rai tai tana watsa masa muguwar kallo.... Gaban Zulfa’u yaja ya tsaya yana wani huci shi kad’ai “Baba Alhaji ya sanar dani yanda sukaida Abbah... Zulfah kar mu bawa iyayenmu wahala, lokaci yayi da zaki daina wannan game d’in naki ki dawo gidan mijinki....” Kaman jira Atika take nan ya katsesa da fad’in “Wane mijin...? Ko tayi aure ne ban sani ba... Ko haka shi Baba Alhajin yace maka...?” Da tsananin mamaki ya kaikaito yana duban Atika, lokaci guda ya d’aura hannayensa saman kunkuminsa yana k’are mata duba ta wulak’anci “Ke kuma wacece da ina magana da matata zaki tsoma baki... How dare you..?!” Atika kaw dikda k’irjinta dake bugawa bata fasa aika masa harara ba tana fad’in “Ni ce bakinta idan ita bazata bud’e baki ta saka ka a yanda ya dace dakai ba... Ka fitar hark’arta ka daina wahalar da iyayenka don Zulfa’u ta maka wuya wllhi, ta riga tai maka nisa, nisarda har abada bazaka kuma hangota ba...” “Ke...!!” Ya fad’i cikeda mamaki yana mai matsowa kusanta, daidai lokacin Zulfa’u ta shiga tsakaninsu, har lokacin fuskarta a tamke yake... “Ya Hafiz banson sauran mutuncin da nake ganinka dashi ya k’are, kaiwa Allah ka fita hark’ata ko ba don komai ba ko dan darajan Khausar dake kwance k’asa...!” Mamaki ya cika Hafiz, bai daina huci yana duban Zulfah ba, fad’i yake “Ni kike cewa na fita hark’arki Zulfah... Kinajin abinda kike fad’i kuwa... Ni Hafiz kike cema na fita hark’arki... Toh waye kike so ki aura.. Wancan d’an iska karen farautar ‘yan siyasan ko kuwa wannan manemin matan banzan manager d’in naku kike so... Tell me waye kike so cikinsu...” “Kan hanya muke Ya Hafiz, zaka iya adana rashin hankalin naka har mu bar bakin kwalta?...”. Bata kai aya ba ya d’aga hannu da niyyan kai mata mari yake fad’in “Ke ni kike fad’iwa magana haka saikace wani sa’arki....!” Bai ankara ba sai ji yai an damk’e hannunsa ya gagara koda motsata.... Gaba d’aya suka kai dubansu gareshi don suma kansu basuji zuwan nasa ba.... Cikin dakekkiyar murya Akram Ke fad’in “If you dare lay a finger on her, zan nuna maka akwai banbanci tsakanin namijin K’warai da kuma namijin da ya rako mata duniya....” Magaji dake gefe sai sannan ya k’araso yana janye Hafiz yake baiwa su Zulfa’u da Akram hak’uri.. Yana jan Hafiz d’in yake ci gaba da fad’in “Da ace nasan rashin daraja zakazo yi wllhi ban kawoka ba, Dan Allah kuyi hak’uri... Zulfa’u Kiyi hak’uri, laifina ne dana kawosa, bansan abinda zaizo miki ba kenan... A kullum nuna mana yake ya canza bansan har yanzu yana nan da halinsa ba... Kuyi hak’uri Dan Allah..” Fincika Hafiz yai yana fad’in “Sai wani basu hak’uri kake saikace an masu wani abin... Baka ganine I’m the real victim here, wannan d’an iskan d’an siyasan shi yake hure mata kunne, kuma Zulfa’u k’anwata ce zan iya hukuntata a ko ina a kuma koda yaushe...” Ya kuma fincika ya tako gaban Akram yana ci gaba da huci yake fad’in “Bari kaji na fad’a maka, ka rubuta ka ajiye kai Karen farautan ‘yan siyasa... Zaka iya hure mata kunne ta saurareka amma na sani kud’inka bazai tab’a sayan soyayyar Zulfa’u ba don abin duniya bai rufe mata ido ba ni zan baka shaida akan haka... Amma ka sani abinda har ka mutu bazaka tab’a samu daga gareta ba...” Yai wata murmushi har lokacin fuskarsa dab dana Akram kana yaci gaba da fad’in “I’m her first husband her first love... Na saka gudan jinina cikin jikinta tai wata tara ta fito duniya ta kuma raineta... Kar ka mance sunce da tsohuwar zuma ake magani...” Murmushi da gefen baki kurum Akram keyi kana yace “Duk abinda ka fad’i are now in the past, and I promise you gabanta zaifi bayanta kyau, ka rubuta ka ajiye....!”Ya k’arashe maganar yana mai murmusawa cikeda k’asaita, k’asa k’asa suke maganar don tuni Yusuf ya bud’ewa su Zulfah da Atika mota sun shige... Hafiz da zuciyarsa ke tsananin masa d’aci ya yunk’ura zai kai damk’awa Akram... Akram ya kuma gyara tsayuwarsa kana yace “And one more thing, kar ka kuskura ko labari na sake jin kana harassing d’inta,... Idan ba haka ba...?” Ya kuma yin wata murmushi kana yasa hannu ya d’an bubbuga kafad’an Hafiz yace “I’ll forget kaida ita kun had’a jini...” Daga haka sa kai yayi ya nufi mota... Hafiz naci gaba da huci ya shiga bibbige yanda Akram ya dafasa... Magaji na janyoshi yana wani doguwa yake fad’in “Toh mai zaka min, ‘yan dabanku na siyasa zaka turo min ko mene... Kai naci uwarka a bariki barikaji mu mai license mukai...” Dafasa Magaji yai yana mai ci gaba da sababi kana Magaji yace “Yanzu kuma da waye kake wai, baka ganin yayi gaba ne ya Barka da k’ura.... Abokina magana ta gaskiya lokaci yayi da zaka daina wannan haukar taka kaje gida ka rungumi Sawwamarka ku sasanta kuyi zaman lafiya, ka k’yale Zulfa’u ta auri wanda take so...” Ya k’arashe maganar yana k’unshe dariyarsa Harara Hafiz ya galla masa kana yace “Ai na jima da sanin kaima hassadar dawowar matata kake min, kuma wllhi duk sai na baku mamaki sai na dawo da matata gareni... Wannan d’an siyasan da ‘yan daba yake tak’ama toh baisan da wa yake takara ba, zan nuna masa neman aure ba takaran kujeran mulki bane da ake saya da tsabar kud’i...” Magaji na murmushi yake fad’in “Shima soyayyar akwai wanda ake saye da kud’i sai kai hattara...” Hafiz na ci gaba da watsa masa harara yake fad’in “Wllhi banda Zulfa’u banida haufi akanta...” Yai murmushi yana mai shafa hab’arsa kad’an kana yace “Zan b’ullo masa ta yanda bai tsammani ba, badai gadaransa ‘yaniskan gari bane... Toh mu zuba nida shi... Sawwama...!” Yayi wata murmushi yana mai duban Magaji da bai fahimci nufinsa ba... Dafa Magani yai kad’an kana yace “Zata min amfani abokina... Tada babur muje kaji...” Shi kad’ai sai sakin murmushi yake yana ayyana yanda plan d’insa zatai aiki.... Magaji dai girgiza kai kawai yai kana ya tada mashin d’insa yana fad’in “Allah ya kyauta...” *** “Bazan barta ta koma hannun wannan Animal d’in ba Yusuf... I must do something, ai kaji abinda yace, mahaifinsa Ke nuna iko akanta, I know Zulfa’u, nasan akwai abinda Ke holding d’inta back shisa ta kasa barina na turo... Amma wannan karon zan yi iyaka k’ok’arina naga ta bari iyaye Sun shiga maganan once and for all... She’s not safe da wannan lunatic d’inba tareda ita, d’an uwanta ne zai iya kasancewa da ita a koda yaushe... I really need to protect her... Bazan barta da wannan mahaukacin around ba...” Ya k’arashe cikin tsanin nuna damuwa yana mai zagaye parlorn... Yusuf ya nusa kad’an kana yace “Toh miye abinyi...?” Wani duba kurum Akram yai masa ba tareda cewa komai ba kana zira hannayensa cikin aljihu... *** A can gidan su Zulfan ma itada Atika k’ulewa sukai k’uryar d’aki... Atika ta rapka uban tagumi tana dubanta “Toh ko Aunty B zamu sanarwa, magana ta gaskiya Zulfah Hafiz baida hankali, kar watarana ya miki wani abin kinga yau k’iris ya rage bai mareki bakin kwalta ba, badon Allah ya kawosu Akram ba da bansan ya abin zai kasance ba... Wllhi nidai a nawa shawarin tun wuri gwara ki tsaida miji kafin wannan Baba Alhajin ya kuma zancen maidaki gidan Hafiz...” Ta k’arashe tana mai tab’e baki... Siririyar iska Zulfah ta fuzar had’ida sauk’e gajeriyar ajiyan zuciya kana tace “Karkiceda Aunty Bara’atu komai, kinsan halinta da d’aukan abu da zafi yanzu sai taje har gidan Hajiya ta taka ma iyayen Ya Hafiz birki, shi kuma Baba Alhaji ba bari zai ba har gida zaizo ya sami Abbah ya d’aga mar hankali a banza... Kawai ki k’yaleni I can handle him...” Atika dai dubanta kurum take baki a tab’e kaman daga sama suka jiyo ringing d’in wayar Zulfa’u ba kowa ke kira ba illa Akram... *** KADUNA Nik’i nik’i take shigowa da akwatin kayan nata sai faman haki take dan tin daga harabar gidan driver ya ije mata, Kubura dake gefen Ostriches tana jefa masu abinci sai cazgan dariyar Yesmin take tana ayyanawa cikin zuciyarta “Madalla Allah shi k’ara...” Ta kuma tintsirewa da dariya tana kuma jefa ma dababbobin abinci, sai Yesmin ta d’ago kai tana harararta sai Kubura tai kaman batasan da isowar nata ba... Yesmin tai k’wafa tana mai ci gaba da jan luggage d’inta.... Cikan murya kaman ta mai wak’a Kubura ke jifarta da habaici sanda ta iso daidai yanda take “Mutum yace bai yinka bai sonka, sai ka gane ka kama kanka... Shidai cusa kai babu k’warjini babban yawa ne... Anyiriri K angon K Khalid angon Kubura kana yafasu muna jin dad’i....” Yesmin tai birki tana bintada kallon mamaki “Ke da waye kike...?” Kubura ta shiga waige waige tamkar mai duba wani abin, Yesmin data dad’a k’uluwa tace “Dake nake k’aramar maras kunya, tsaban kin rainani kina ganina da kaya bakisan kizo ki amsa ba sabida kin sami d’aurin gindi daga wajen Ammi koh...?” Dariyar rainin hankali wannan karon Kubura tai kana tace “Toh wama yasan da zuwan naki, ai ce nake dagani sai dababbobin nan ne a wajen nan...” Yesmin ta kuma harzuk’owa tana fad’in “Ke ni kike kira dabba...?” Kubura ta Kuma murmusawa tana wani jijjiga kana tace “Wlhi ba’a bakina kikaji ba...” Tayo kanta gadan gadan a daidai sanda motar Siyama ta sako hanci.... Tana ida parking suka fito itada Laila, dan yanzu kullum Lailar na lik’eda ita... A guje Kubura ta tafi tana fad’ida Siyama “Oyoyo Aunty na sannu da dawowa..” Ta k’arashe tana amsar handbag d’in Siyamar... Harara Siyama ta galla mata kana tace “Saikac banga rashin kunyar da kike tsulawa Yesmin ba, kin wani kwaso gudu kin taho nan...” Yesmin tace “Wllhi cousin yarinyar nan d’aurin gindi ta samu daga wajen Ammi shisa take fetsararta san ranta, wai harda kirana dabba kiji fah...” Kubura baki a ture tace “Wllhi Aunty Siyama ni bance mata dabba ba, aidai a bakinta kikaji...” Ta k’arashe tana juya idanu... Girgiza kai kurum Siyama tai kana tace “Bani jakata ki d’auki jakan kayanta ki shigar mata...” Kubura ta kuma b’ara fuska tace “Kut Aunty gani fah wannan tilin kayan ina zan iya...” Kallon da Siyama ta watsa mata ya sanyata d’aukan ta nufi cikin gida tana mai watsawa Yesmin muguwar kallo... Siyama ya maido da dubantaga Yesmin kana tace “Wai dawowa kikai ne...? I thought Aunty tace sai bayan biki keda gidan nan...” Yesmin tai kicin kicin da fuska tace “Wllhi bazan iya va cousin, I’m dying to see my Kay, bazan iya kwanakin nan ban ganshi ba...” Daidai sanda idanunta suka sauk’a kansa ya fito daga sashensa waya manne kunnensa, yana sanye cikin shiga ta k’anan kaya Red shirt da yayi tsananin fito da kyan fatarsa, gaban rigar an rubuta _Mango_ da ruwan zinari sai faded jeans, k’afafunsa sanye suke cikin takalmi k’irar sandals kalan bak’i.. Ya mata kyau matuk’a wanda har su Siyama da Laila suka shige cikin gida bata fahimci hakan ba.... Kaman wanda akace ya juya ya hangota ta kafa masa idanu tamkar tsohuwar mayya.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *82* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin ranshi yake furta wannan yarinyar idan mayyace ta kama mutum toh harta b’argon dake cikin k’ashinsa sai ta lashe.... Kaman daga sama ya jiyo muryarta tana fad’in “My Kay badai fita zakai ba...?” Mamaki ya hanasa furta komai, Yesmin ta d’an murmusa a hankali tana juya idanu kana tace “Yi hak’uri ko gaisawa bamuyi ba na tsareka da tambaya....” Batakai aya ba ya katseta “Ke wai ke wata irin mayyace... Wai tsaya ma what’s your class of degree....?” Ta dubesa da mamaki sai kuma ta murmusa ta mance tambayar da ya mata ta farko saita biyun take yunk’urin amsa masa “I graduated with second class upper...Ashe fah bakaje grad d’ina ba su Ammi ne sukaje....”Tai maganar tana kuma yauk’i had’ida juya idanu.... Gajeren murmushi yai wacce tafi kama data takaici kana yace “Aka sai maki result dai, don a ajin dak’ik’ai ban tab’a cin karo da babbar dak’ik’iya irinki ba, da kina gane karatu kaman yanda kikace da baki tsaya b’ata lokacinki wajen mutumin da sam baisan kinayi ba... And let me remind you this... Wllhi wllhi... Kinji na miki rantsuwar musulmi, kika kuskura kika sake ki yarda aka aura miki ni Khalid Mainasara a matsayin miji, sai kinyi nadamar da baki tab’a irinta ba tinda kika fad’o duniya.... So advisably ki sami Ammi tinda gaki nan Allah ya kawoki ko nace nacinki ya dawo dake, ki rok’eta ta taimake ki ta rufa miki asiri ta janye wannan auren shiriritan da take yunk’urin had’awa... Dan wllhi kika sake kika yarda kika biye mata akai wannan auren, na miki alk’awarin ganin dark side d’ina da duk duniyar nan babu wanda ya tab’a ganin sa.... It’s a promise...!” Yana ida fad’in haka bai jira cewarta ba yasa kai yai ficewarsa yana kuma making call.... Yesmin tabisa da kallo hawaye tab idanunta, wannan wulak’anci na Khalid ya isheta, inama zata iya ciresa cikin zuciyarta da tayi hakan ko dan samun farin cikinsa ne, amma hakan bamai yuwa bane, zataci gaba da juran duk wani wulak’ancinsa tasan wuyarta suyi aure ne tuni zata koya masa yanda zai k’aunaceta... Ta saki murmushi a hankali had’ida goge hawaye mai d’umin da ya ziraro mata.... Fitowar Siyama da Laila kenan zatai rakiyawa Lailar ta hangi Yesmin tsaye tana faman goge hawaye ta k’urawa motar Khalid dake ficewa daga gidan idanu.... Sallama Siyama tai da Laila, dan mai d’aukar Lailar waje yai parking, kana Siyama ta k’araso wajen Yesmin... K’uri tai mata tana duban yanda take matsan k’walla.... Siyama ta dafata a hankali kana tace “Wa ya sakaki kuka cousin...? Tell me was it Khalid...?” Cikin sigan lallashi Siyama tai maganar Yesmin ya kuma goge hawayenta tana mai jinjina kai ga tsananin rawa da muryarta keyi “Who else cousin...? Sauk’ata kenan, amma irin tarbar da zaimin kenan.... Tell me please cousin, Am I really a bad person... Why is it so hard for him to understand how much I love and care about him... Wllhi ina son Khalid fiyeda yanda nake son kaina cousin...” Ta k’arashe sabbin hawaye na ziraro mata... Numfasawa Siyama tai kana ta d’an dafata kad’an “Yesmin ba laifinki bane dan Allah ya jarabceki da sonsa, amma kema bak’in nacin tsiya ne dake dole ki hau masa kai, karfa ki mance a train station yai tafiyarsa ya k’yaleki last rabuwarku amma har kin kuma kwasan k’afafu kin dawo masa, Ke ko ‘yar ajin nan ta mata baki d’an ja ne, kiga dai nida Sameer dikda na sani muna matuk’ar son juna nakan d’an basa space dan in nuna masa matsayina da darajata a wajensa amma ke ko yaushe sai ki bari Khalid yaita cin kashinsa akanki, toh wllhi ki farga dan in ba haka ba, hardai kina nan da wannan halin nacin tsiyar naki kika auresa a haka sai ya gasa miki gyad’a a tafin hannu, I know Khalid so well, girma ne ma ya d’an canzasa, sanda muke k’uruciya babu wanda ya ragarma toh wllhi kiyi hattara ki d’an koyi jan aji koda d’an kad’an ne....” Baki a ture Yesmin Ke dubanta kana tace “Banja ajin ba ya cazga min wulak’anci balle naja masa, ni wllhi idan dai akan my Kay ne saidai na yarda banida ajin...” Ta k’arashe tana mai nufan cikin gida.... Siyama ta murmusa a hankali kana tace “Allah ya baki sa’a...” A b’angaren Laila kuwa tana ficewa ya tadda Sultan na jiranta, front seat ya bud’e mata ta shige ta zauna... “Toh ya..? Any improvement...?” Ya tambaya sanda take daidaita zamanta cikin motar... Murmushi ta saki idanunta naga kwalta kana ta ware masa tafin hannunta tace “Siyama tana nan, tana nan tsakiyar tafin hannuna sai yanda na juyata a halin yanzu.... Ina mai tabbatar maka Sameer bai gabanta a yanzu...” Murmushi mai sauti Sultan yai kana yace “Kinci sunanki Poison, kice kin gama poisoning zuciyarta....” Ta kuma murmusawa tana jijjiga kana tace “I told you to trust me on that, yanzu abu na gaba zamu taking next step...” Sultan ya kuma jinjina kai a hankali kana yace “Mai kenan....?” Juyowa tai tana dubansa wannan karon kana tace “Zan zigata tasa Sameer ya rubuta mata takardan saki, idan tak’i zanyi amfani da nawa strategies d’in na sakashi ya saketa, Kaga you will finally have your chance, sannan nima zan mallaki Sameer ni kad’ai...” Sauk’e ajiyan zuciya yai yana mai murmusawa kana yace “Da Bansan da mai zan saka miki ba idan hakan ta kasance....” Laila ta kuma rausayar da idanu tana mai dubansa “K’iris ya rage burinmu ya cika.... “ *** A b’angaren Khalid kaw koda ya fice gidansu Baffah amininsa ya nufa.... Zaune suke su duka biyun a farfajiyan gidan saman fararen kujeru dake k’asar tapkeken bishiyar mangoro da yayiwa harabar k’awanya.... Ya d’auki lokaci yana shafa wayar salulansa ba tareda ya amsa tambayar da abokin nasa ya jefo masa ba... Baffah ya kuma d’ora k’afarsa d’aya bisa d’aya yana duban Khalid d’in da har lokacin natsuwarsa naga wayarsace.. “Khalid magana nake maka fah...?” Baffah ya kuma fad’i cikeda k’osawa... Ba tareda ya dubesa ba yace “Ina saurarenka ai, ko ka mance kunne Ke sauraro ba ido ba, just go ahead and keep on talking, I’m listening to you... Mai ma kake tambaya...?” Murmushi mai bayyan hak’wara wannan karon Baffah yai had’ida girgiza kansa kad’an “Idan bakai haka ba baka cika Khalid Mainasara ba.... Tambayarka nake miye shirye shiryenka na Bikin tinda Ammi ta rik’e wuta...?” Wannan karon d’ago kai Khalid yai yana dubansa na wani lokaci kaman zaice wani abu sai kuma ya murmusa da gefen baki ya kuma maida kansaga wayarsa, saida ya kuma d’iban wasu dak’ik’ai, har Baffah ya cire rai bazai amsa shi ba sai kuma ya sinkayo muryarsa na fad’in “Tin jiya nake neman layinta but I couldn’t reached her...” Yai maganar damuwa na nunawa saman fuskarsa.... “Ita wa...?” Baffah ya tambaya. D’agowa yai yanai masa wani duba kana yace “My teddy bear....” Baffah ya murmusa a hankali kana yace “Toh ba sai kaje Kano ka dubata ba tinda zuwa Kano bai maka wuya....” Kallon ya kuma watsa masa kana yace “Da inada halin yin hakan da nayi kaima ka sani.... Ammi tace idan na kuma tafiya Kano ba tareda saninta ba bazata tab’a yafemin ba.... Baffah do me a favor....” D’agowa sosai Baffah yai yana dubansa had’ida ware idanu alamun yana sauraren abinda zaice..... “Kaje Kano ka dubo min lafiyarta since I can’t call Sameer and ask him about her....” Dariyar da tafi kama data almara Baffah yai kana yace “You can’t be serious.... Ni in d’auki k’afa in tafi har Kano sabida yarinyar da bakada tabbacin aurenta, Allah ya sawak’e bazanje ba....” Tinda ya soma magana Khalid Ke danna masa harara “Kar ka sake cewa banida tabbacin aurenta tinda baka had’a sanida Allah ba....” Yai maganar yana mai mik’ewa tsaye.... Shima Baffah d’in tsaye ya mike yana dubansa “Ina kuma zaka....?” “Babu ruwanka da yanda zanje Malam...” Yai maganar yana mai zira wayarsa cikin aljihun wandon jeans d’insa had’ida zaro car keys d’insa... Bai kuma ceda Baffah komai ba yasa kai yai shigowarsa.... Baffah dake tsaye kameda kunkumi yana duban ikon Allah d’an bud’e murya yai yana ambato sunan Khalid d’in, amma ko tsayawa baiyi ba balle yai tunanin juyowa.... Gajeren murmushi Baffah yai had’ida girgiza kai, harga Allah bai tab’a tsammanin irin wannan ranar na zuwa ba, gaba d’aya wannan yarinyar ya canza Khalid... Lallai ya yarda soyayya ka iya canza mutum... Sauk’e gajerar ajiyan zuciya yai yana mai girgiza kai kad’an kana ya nifi cikin gida.... *** KANO Suna zaune parlorn Mamy su duka ukun, kallon program d’in Ultimate Cake Off suke a tashar Real-time... Tayi tsuka kusan na uku kenan sanda ta hangi wayarta dake jikin socket ta kuma kawo farin haske ta d’auke, ya isa jikin socket d’in tana mai kuma jan tsuka a hankali... Tin shekaran jiya wayar tata take wannan haukar shisa mutane da dama basa iya samunta, gashi yau ta d’auke gaba d’aya.... Zulfah da hankalinta rabi kega tv rabi naga k’ofar shigowa dan tinda akace iyayen Akram mai neman aurenta sunzo gidan bata sami sukuni ba, sai duban k’ofa take tamkar mai jiran shigowar wani..... Duban ‘yaruwar tata dake jijjiga wayar salular nata tai kana tace “Wai mi ya sami wayar taki ne...?” “Wllhi Addah k’ila battery taci k’ila kuma ta buga mai gaba d’aya ne...” Mik’a hannu tai tana fad’in mu gani.... Babu musu Nabilah ta mik’a mata.... Sallamar Aunty Bara’atu ya mantar dasu batun duba wayar... Marliya ta mik’e a guje ta tafi ta rungumeta tana fad’in “Oyoyo Aunty....” Gaba d’aya sannu da zuwa suka shiga mata had’ida gaidata.... Ta tambayesu Mamy sukace da ita tana kitchen...Jinjina kai tai kana tace “Shine ku na ganku a nan ba kitchen d’inba..” Nabilah tai karaf tace “Yanzu shigowarmu mu mun isa Hajiya Mamy na kitchen muna kallo, ai da daga yau babu mai kuma kunna tv cikinmu...” Tai maganar tana kame baki... Aunty B ta murmusa tace “Ai kekam maganinki sai Mamyn mijinki nada fama....” Nabilah ta turo baki tace “Kai Aunty.. Toh ba sai ya shiga ya girka mana ba...” “Tafi can ki rufe min baki” Aunty B tace tace kana ta dubi Zulfah “‘Yar gidan akwai maganar da zamuyi bara naga Mamy a kitchen ina zuwa....” Jinjina mata kai kurum Zulfah tai ba tareda cewa komai ba... Ta kuma kai dubantaga Nabilah wacce Ke k’ok’arin yin filla filla da wayar salulanta k’irar samsung kana tace “Beels bani size d’in takalminki....” Nabilah na Washe baki tace “Aunty takalmi zaki sai min....?” Bata tsaya amsa shiriritar Nabilah ba ta nufi k’ofa tana duba size d’in takalmin da take tinanin nata ne... Nabilah ta bud’e murya tace “Aunty 38/39 ne kar a sayo min kasasshe size d’in Marliya... Sai ni ‘yar gatan Aunty...” Gaba d’aya darawa suka d’anyi kana Aunty B ta kuma jefo mata tambaya “Dogayen riguna fah, bani length d’insu, size d’in inners d’inki kam zan iya k’iyascewa....” Wannan karon da tsananin mamaki Nabilah Ke dubanta yayinda Zulfa’u da Marliya suka dubi juna murmushi saman fuskokinsu.... Take annurin fuskar Nabilah ya d’auke cak.... “Aunty harda ke a wannan auren had’in bakin da suke k’ok’arin yi....?” Tai maganar baki a ture Galala Aunty B Ke dubanta kana tace “Da waye yace ki kawosa da kika san baki sansa..? saikace ba kece kwanaki kikai kuka akan danginsa sun tasamma rabaku ba, yanzu dan iyayi zaki wani ishi mutane....” Har lokacin bakin Nabila a ture ne... “Ni wllhi Aunty bani na kawosa ba shi ya kawo kanshi, kuma fah Aunty mamarsa ba k’aunata take ba, aike shaida ce....” Jinjina kai Aunty Bara’atu tai don tuni Aunty Daula ta sanar da ita shirin Daddy kana tace “Idan Mamarsa bata k’aunarki Babanshi na k’aunarki kuma shima Khalid d’in na k’aunarki sannan Auntynsa tana k’aunarki...Sannan kinada ilimin zama da mutane...” Bata kuma tsayuwa sauraren Nabilar ba ta shige kitchen wajen Mamy... Auntynsa da Aunty B tace yasa Nabilah kuma dubanta, batace komai ba sai d’an tab’e baki da tai kad’an, Zulfa’u ta d’an dunguri k’eyarta tace “Inye Kaga amaryar Haladun Mamani, shikenan yarinya sai Kaduna....” Marliya kaw sai dariya take yayinda Nabilar tai raurau tana duban Zulfah... Saurin rungumeta Zulfah tai tana fad’in “You’ve us all baby sis, zaki tadda alkhairi In sha Allahu....” Nabilah bata iya cewa komai ba sai lumshe idanunta da tai tana tunanin Wai Khalid ya kusa zama mijinta in less than 2mnths.... Abin kaman wani almara.. Marliya kaw fad’i take azo a ciro masu ankon gida ko ‘yar kamun nan a masu a k’irawo masu DJ dan basa son biki lami ehe... Banda uwar harara Nabilah bata danna mata komai.... Zulfah dai mik’ewa tai ta nufi d’aki yanda wayarta Ke faman ruri zuciyarta cikeda k’aunar ‘yan uwan nata.... Gabanta ne ya mugun fad’uwa ganin lambar Mr Unknown ne dan jiya tayi saving layinsa d’aya..... Kasa d’aukar wayar tai sai ma k’ura mata idanu da tai.... Saida har tsinke tana nan tsaye a haka... Nan take aka kuma sake kira, sunan sai nunawa yake Mr Unknown... A hankali ta d’an fuzar da iska kana tai bismillah ta d’aga wayar sallama saman bakinta.... Yau kam batai gaggawan katse kiran ba kaman yanda takeyi a kullum... Cikin wani irin sanyin jiki take furta “Bawan Allah shin maiyasa kake kirana kayi shiru...? Mutum ne kai kokuwa Aljan...? Shin wani abu kake nema wajena... Kokuwa na tab’a maka wani laifi ne....? Idan babu ko d’aya, Dan Allah ka dena kiran wayata na rok’i arzikinka... Banajin ajikina kai d’in mai cutarwa ne... Dan Allah ka dena kirata haka nan... Allah shi bamu alkhairi....” D’if ta kashe wayar zuciyarta na bugawa da sauri da sauri... Kashe kiran keda wuya taji k’aran shigowar sak’o _Zuciya mai muradin k’auna bata cutarwa..._ A hankali ta furta “Anonymous..” Fuzar da iska kad’an tai had’ida zama bisa gado tana mai kuma karance sak’on nasa, wani irin sanyi da yanayi maras fasaltuwa jikinta keyi a dik sanda ta amsa kiransa ko ta karance sak’onsa.... *** Dariya suka kwashe dashi had’ida tafe hannaye, Haule ta mik’a mata hannu suka tafe.... Lami tace “Wato Haule bakida kyau, shikenan yanzu zaki had’asu fad’a ki jefa gaba mafi muni a tsakaninsu....” Haule na jijjiga tana wani duban Lami take fad’in “A ranar d’aurin auren Sameer Aminiyar Sirri zata bayyana masu... Sannan duniyarsu zata sauya, ‘Ya’yan Mariya gaba d’aya bama Sameer kawai ba sai sun tsaneta, Mariya zatai ido hud’u da Butulci da kuma cin amana mafi muni.... Zamu zamto mu kad’ai muke shanawa... Zaki zamto tauraruwa a idanun ‘ya’yanta da kuma mijinta.... Na fad’a miki Lami idan kika rik’i Haule toh fah har abada bazakiyi kuka ba.... Wata d’aya jal ya rage muga rugujewarsu har k’asa, mu bayyana Aminiyar Sirri a tsakaninsu... Muga yanda fuskokinsu zasu sauya idan suka fahimci ko wacece ita da duk kalan k’uncin data jefasu ciki.... Tabbas zamu koma gefe muna dariya muna shagalin bikinmu....” Lami ta kwashe da dariya suka kuma tafe hannaye kana tace “Ranar da gidan Biki zai koma tamkar gidan mutuwa a b’angaren wasu... Yayinda a namu b’angaren abin zai kasance mafarin Farin ciki mai dawamma....” Suka kuma bushewa da dariya suna ci gaba da tafe hannaye.... Naja’atu dake lab’e bakin k’ofa hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata, ta dubi Hajiya da Aunty Lami yanda suke dariya suna fad’in muguntarsu suna tafe hannaye... Shin ta aikata ne ko ta k’yalesu su cimma burinsu.... Yaya zatai ne...? Ta wane hanya zata b’ullo ganin burin Mahaifanta bai cika ba.....? Ta kuma saka bayan hannunta ta goge hawayenta sanda zuciyarta ke ayyana mata _Do the right thing_ A hankali ta janye jikinta ta shige daga wajen Tsakar gida ta koma ta rapka uban tagumi had’ida k’urama waje guda idanu, a haka Sahariyya da aminiyar ya Fa’iza suka shigo nik’i nik’i da kayan anko na K’awayen su da suka riga suka bada kud’i... A gajjiye suka zube saman tabarman da Najah Ke zaune bisa, Sahariyya ta ije crutches d’in da take dogarawa dashi tana watsawa ‘yar uwar tata muguwar duba, a yatsine take tambayarta Hajiya.... “Tana d’aki tareda Aunty Lami...” Ta fad’i sanda take k’ok’arin bari masu wajen, Fa’iza ta bita da dak’ilellen kallo ganin tana nuna mata kalan ankonsu tana tambayar ra’ayinta Naja’atun bata kulata ba.... Fa’iza tace “Tooooh ke kuma fah... Kishi ko hassada...?” Sahariyya ta amsata da fad’in “K’yale munafuka duka biyu take....” Daidai lokacinda Hajiya Haule da Aunty Lami suka fito, da alama tafiya Lami d’in zatai... Lami ta dubi Sahariyya tana Washe baki take fad’in “A’a Kaga amaryar mu...” Sahariyya harda d’an sanne kanta ita a dole kunyar Aunty Lami ta soma ji.... Suka had’a baki itada Fa’iza suna gaidasu.... Hajiya ta isa ta d’auki yadin material d’in tana fad’in “Kai gaskiya yaran nan kun iya zab’e... “Sai juyawa take tana mannawa jikinta.... Fa’iza kaw cikeda zagwad’i ta d’ago leshin da suka sayowa Hajiyar tana fad’in “Hajiya ya kikaga wanda muka zab’o maki, ai yau tsaf saida muka zagaya Kwari gaba d’ai dan zab’o maki leshin da zaki kece raini uwar Amarya....” Haule ta kame d’an guntun hancinta ta shiga rangad’a gud’a tana wasa kanta matsayinta na uware Amarya Lami na zigata.... Sahariyya ta shagwab’e fuska tana fad’iwa Aunty Lami ta taimaka ta rok’ar masu Sameer ayi dinner dan yanda ta samo mijin kece raini cikin k’waye ya kamata ayi dinner ta nuna masu tafisu sa’a.... Aunty Lami ta dafa kafad’arta tace “Kwantar da hankalinki Sahariyya, uban dinner ma sai anyi, don babban buduri zamuyi a Bikin nan.... Babban biki za’ai a Zuri’ar Mahmood Mailafiya, Bikin da ba’a tab’a irinsa ba, Biki Uku kuma za’a had’a.. Ga naki da Ma’aruf, ga na Nabilah da Zulfa’u....” Batakai aya ba Hafiz da shigowarsa kenan ya tari zancen da fad’in “Wata Zulfa’un....?” Sahariyya da k’awarta Fa’iza kaw tini suka tattari kayansu suka shige parlorn Hajiya suna kiran k’awayensu suzo su amshi ankonsu... Aunty Lami ta murmusa da dubi Hafiz kana tace “Afff bakada labari, ai itama an tsaida ranar aurenta rana guda dana k’anwarka Sahariyya, bada jimawa aka kawo tambyar aurenta ba kuma ina mai tabbatar maka an basu ranar buki...” Tinda ta soma magana yake dunk’ule hannayensa waje guda, Haule na mata ido tai shiru inaa Lami sai zuba take yawa an bud’e famfo.... Take idanun Hafiz da fatarsa suka sauya launi zuwa ja.... Shi kad’ai sai sakin tururi yake.... Baiceda kowa komai ba sai gani sukai ya fice daga gidan.... Haule na kiransa ko saurarenta bai ba yayi ficewarsa... Ta maidoda dubantaga Lami tana mata duban tuhuma.... Lami ta kame baki tace “Yo ni na mance tsohuwar matarsa ce ashe....” Hajiya Haule tace “Yau kin b’allo mana ruwan teku bamuda jirgin ruwa... Mai tsaida wannan ruwan da kika b’allo sai Allah Lami....” Aunty Lami tace “Ahap zaiyi ya daina dan ko mutuwa zai wannan yarinya Zulfa’u bazata yarda ta koma gidansa ba... Kece bakiso maida masa matarsa ba Haule...” Haule ta dubeta da mamaki... “Ni kuma...? Kaman yaya ni....?” Murmusawa Lami tai kana tace “Ba ko wani makirci kikeda bakin zarenta ba Haule... Keda kikeda Aminiyar Sirri a hannunki...?” Ta k’arashe tana kannare idanu... Numfasawa Haule tai kana tace “Kuma fah haka... Amma sanin kanki ne mijinki nada kafiya Lami, babu yanda bamuyi ba nida Alhaji ganin ya maidawa Hafiz matarsa amma k’ememe yak’i... Bana tinanin akwai mai iya tank’warasa... K’yale Hafiz nasa mai sauk’i ne... Nidai tinda zamu gwara kawunansu ranan biki hakan yafi min komai dad’i a duniyata....” Suka kuma tafe hannaye kana Haule tace “Muje na taka miki zuwa waje...” Haka nan sukaci gaba da tattaunawarsu da tsara yanda zasuga k’uncin Mariya ranan Bikin ‘ya’yansu.... **** Tamkar wani zararre haka ya shiga har cikin ofishin nasu, ana tare shi ana janyoshi hakan bai hanasa kutsa kai cikin gidan radio d’in ba, tsakiyar gidan radio d’in ya tsaya yana k’walla mata kira da iyaka numfasawar shi.... Tana d’akin gudanar da shirye shirye ta sinkayo muryarsa na ambato sunanta cikin wane irin sautin... Juyawa tai ta dubi Atika wacce itama ita d’in take duba... Babu shiri ta cire headphones d’in dake mak’ale kunnenta ta nufo waje Atika na biyeda ita... Su Ameer da securities suna ta k’ok’arin fiddashi amma ya doge yace bazai fita ba har sai Zulfa’u tazo.... “Ku k’yaleshi Ameer....” Ta fad’i daga can nesa yanda take tsaye... Hafiz ya juyo yana mata wani irin duba... Lokaci guda yake takowa gabanta... Hawaye ta hango kwance saman fuskarsa yana mai k’arasowa gareta... “Da gaske ne.... Aure zakiyi... Ki fad’a min da bakinki... Da gaske ne abinda nakeji....?” Ya k’arashe idanunsa suna kuma yin jazir... A hankali ta jinjina masa kai “K’warai da gaskene abinda kaji Ya Hafiz, wata guda ya rage aurena....” Murmushin data tafi kama data rainin hankali Hafiz yai kana yace “You must be kidding Zulfa’u.... Gidan duniyar nan bakida mini sai ni Hafiz... Na miki imani a wannan ranar saidai a maida aurenmu amma wllhi tallahi muddin ina numfashi bazaki auri wani bayan ni ba....” “Ya Hafiz, please don’t make a sin here... Ka tafi dan Allah...” Tai maganar tana mai nuna masa hanya.... Jinjina kansa yai yana mai tab’e fuska, lokaci guda yake ci gaba da fad’in “You don’t know what I’m capable of, idan har da gaske kina sonshi kuma kin damu dashi, toh kiyi gaggawan bashi shawari ya fasa aurenki da yake yunk’urin yi, dan idan ba haka ba....” Murmushi yai ga hawaye dake gangarowa daga idanunsa lokaci guda yaci gaba da furta “Rayuka da dukiya zasu iya salwanta ta dalilin hakan, Babu Wanda ya isa ya mallakeki matuk’a ni Hafiz ina numfashi a doron k’asa.......” Daga haka sa hannu yai ya share hawayen da suka wanke masa Fuska kana yasa kai ya fice cikin sauri... Hawayen da take k’ok’arin maidawa suka shiga ambaliya a fuskarta.... Atika ta k’araso da sauri ta rungumeta... Sosai Zulfa’u Ke kuka tana fad’in “Atika what if yaje yayiwa Akram wani abin....?” Atika na lallashinta take fad’in “Bai isa ya masa komai ba Zulfah, Hafiz bai isa yiwa Akram abinda Allah bai masa ba, kurari ne kawai da cika baki dan kice kin janye auren Akram... Karma ki bari zuciyarki ta raya miki wani abin... Ci gaba da fawwala wa Allah lamuranki...” A hankali ta lumshe idanunta wasu hawayen masu d’umi suka kuma gangaro mata.... Atika ta janyo hannunta suka shige studio Saidai gaba d’aya kasa gudanar da shirin tai, dole Ameer ya canjeta... D’akin hutu ta shige dan gaba d’aya batajin kanta daidai... Tana isa d’akin ta tadda wayarta dake chaji jikin socket tana faman ruri... Mutumin nata ne mai kira.... Ta k’urama wayar idanu tamkar bazata d’aga ba... Sai kuma ta tsinci kanta da son d’aga kiran... Ta d’aga cikin rawar murya irinta mai kuka.... Yau d’in daga sallama bata iya cewa komai ba sai busting cikin kuka da tai had’ida saurin katse kiran.... Kaman kullum sak’on ya shigo mata... _Kuka bata kamaci kyakkyawar muryarki mai dad’in sauraro ba...Ita murya mai kaman sarewa tafi dad’in a saurareta a matsayin abin nishad’antarwa da d’ebe kewa ga mai saurarenta, Ina fata kalamaina su sanyaki murmushi su kuma gusarda damuwarki koda na k’ank’anin lokaci ne..._ Ta samu kanta tana mai sakin murmushi bayan ta ida karance sak’on, haka kurum taji wani irin sanyi na ratsa cikin zuciyarta, tana fatan Allah ya nuna mata wannan bawan Allah koda sau d’aya ne tak a rayuwarta... Shin waye shi...? Sauk’e ajiyan zuciya tai tana mai kuma karance sak’on... **** Murmushi Sawwama tai mai cikeda ma’anoni tana mai duban mijin nata da tin dawowarta gidan maganar arziki bai shiga tsakaninsu ba.... Saida ta kuma mik’ewa tsaye kana tace “Sharad’in shine zaka dawo gareni bazaka kuma juya min baya ba...” Hafiz dake huci ya jinjina kai yace “Na maki alk’awari muddin kika cika mun burina ni Hafiz bazan kuma k’yaleki ba...” Nan ma dai murmushin tai tana mai shafa fuskarsa da duka tafukan hannayenta, lokaci guda ta mik’e had’ida basa baya... Cikin dakekkiyar murya take fad’in “Zan taimaka maka kuma Zulfa’u zata dawo gareka...” Mik’ewa tsaye Hafiz yai ya tako kad’an har zuwa gabanta.... Lokaci guda yake sakar mata murmushi, itama d’in murmushin take sakar masa... Hannu yasa ya kamo k’ugunta ya matsota kusansa.... Fuskarsu dab da juna yake furta “Ni d’in naki ne sai yanda kikai dani.....” Tamkar zakin da ya kwana babu abinci haka ta janyo Hafiz ta shiga sarrafasa.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *83* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A haka sati guda ta shud’e, ta ko wanne b’angare shirye shiryen bikin suke... Tabbas dik abinda aka masa lokaci INDA RAI zaizosa, zaune Aunty Daula tai bayan ta ida waya da Nabilah da kuma Aunty B... Ita kad’ai sai sakin murmushi take tana jinjina hankali irin na Nabilah, babu yanda batai ba ta sanar da ita abubuwan da take so a zuba mata a kayan lefe amma fir Nabilah tak’i sanar da ita... Tabbas Khalid yayi dace, gaba d’aya lokaci guda k’aunar Nabilah da danginta ya ratsa zuciyarta, ta k’agu ranan biki yazo su had’u suga juna... Tana nan a haka wayar Daddy ya shigo mata, tambayarta shiryen shiryen yai shima kana suka d’an tattauna batun dan lokaci bai jira... Abu kaman wasa gashi yanzu satittika ake k’irgawa.... Yana ida wayar Baffah yai sallama a k’ofa, Daddy ya amsa had’ida masa izinin shigowa... Cikeda risinawa Baffah ya k’arasa saman tampatsetsen carpet d’in turkey dake malale a wargajejen parlorn ya zauna daga can gefen Daddyn, Daddy ya mik’a masa hannu sukai masabaha kana Baffah ya gaida Daddyn cikeda girmamawa.... Daidaita zamansa Daddy yai saman d’aya daga cikin kujerun alfarma da sukaiwa parlorn nasa k’awanya.... “Baffah..” Daddy yace had’ida yin gyaran murya.. Baffah ya amsa cikeda fargaban wannan kira na gaggawa da Daddyn yai masa.... “Nasan zakaji mamakin nemanka cikin sauri da nai lokaci guda....” Jinjina kai Baffah yai a hankali kana yace “Haka ne Daddy...” Daddy ma ya jinjina nasa kan “Abinda yasa na nemeka cikin gaggawa ba komai bane illa sanin cewa da nayi Khalid baida aminin da ya wuceka....” Baffah ya kuma jinjina kai yana tinanin mai kuma Khalid d’in yai wannan karon... Daddy ya d’an murmusa ganin gaba d’aya kaman Baffan a tsure yake kana yace “Ka kwantar da hankalinka abokinka baiyi komai ba, hasalima ma baisan abindake gudana ba....” Fasali ya d’anja kafin ya zaro checkbook dake aje saman k’aramar table d’in dake gefen kujeransa.... B’allan guda yai kana yayi rubutu jiki ya mik’awa Baffah.... Baffah yabi check d’in da duban mamaki “Daddy na menene...?” Ya tambaya yana kuma juya takardan... Gyara zama Daddy yai kana yace “Inaso kaje Kano ka sami Nabila a madadin Khalid, nasan ango yakan baiwa amaryarsa wasu ‘yan kud’ad’e kodai na events ko wasu hidiman gabanta dan ba’a raba mata da hidima....” Gaba d’aya Daddy sai ya kuma d’aure kan Baffah... Shi gaba d’aya ma sai ya rasa wacece ma Nabilah... Daddy ya d’an murmusa kad’an kana yace “Na sakaka a duhu koh... Toh karka damu bari na fayyace maka komai da kuma dik wani shirina... Ina kuma fatan na sami goyon bayanka d’ari bisa d’ari a matsayinka na aminin d’ah na....” Dikda Baffah baisan shirin Daddyn ba amma sai ya sami kansa da jinjina mar kai yana mai furta “Zaka sameni mai yi maka biyayya da bin umarninka in sha Allah Daddy....” Daddy yaji dad’i sosai ya jinjina kai yana furta “Shiyasa ban tab’a danasanin kasancewarka abokin d’ah na ba dan nasan kaid’in yaron arziki ne..” Mugun sanyi jikin Baffah yai ko da Daddy ya karanto masa shirinsa na auren Khalid d’in taryan taryan, ya tina kwanakin baya yanda ya baiwa Ammi da Siyama full support d’insa wajen ganin an raba tsakanin Khalid da Nabilah, ya tina dik fad’i tashin da akai wajen datse tsakaninsu ya bada nasa gudummawar, tabbas sai yaji bai kyauta wa amininsa ba, bai kyautawa abokantakarsu ba, sanin kansa ne tin tasowarsu Khalid bai tab’a soyayya da wata mace ba sai Nabilah, instead ya basa goyon baya yai supporting d’insa like a brother sai ya biyewasu Ammi da son zuciyarsu ganin sun datse k’aunar dake tsakankanin zukata biyu da Allah ya had’a, tabbas maganan da jiya Khalid yai masa yayi gaskiya cewa shid’in bai tara sani da Allah ba, Allah ka iya canza al’amaransa a duk lokacin da yaso, domin kaw shid’in Buwayi ne gagara misali... Ko a mafarki bai tab’a zaton auren Khalid da Nabilah mai yuwu bane sai gashi lokaci guda Allah ya sauya zuciyar mahaifinsa, tabbas ya yarda shi aure nufi ne na Allah kuma wani bai auren matar wani... Yayi alk’awarin baiwa Daddy his unconditional support har burinsa ya cika na ganin auren ya tabbata cikin yardar Allah, ta hakan ne kawai zai sakawa abokinsa butulcin da yai masa a baya.... Bayan sun ida tattaunarwasu da Daddy ya mik’e yanaiwa Daddyn sallama daidai sanda Khalid yai sallama ya shigo parlorn... Mamaki ya cika Khalid d’in ganin Baffah tareda Daddy har suna sallama da juna, since when suka zama close haka..? Ga wata ‘yar takarda hannun Baffan da sam baiso Khalid d’in ya gani... Kallon kallo sukabi juna dashi sanda Baffan zai fice, Baffah sai sakar masa murmushi yake... Sosai Khalid ya karkata yana duban Baffah dake k’ok’arin ficewa yana mamakin wannan al’amari... Take masa baya yai niyyan yi sai kuma ya sinkayo muryar Daddy na kiransa, dole ya fasa bin bayan Baffah ya komaga kiran mahaifinsa... Daga can gefen k’afar Daddyn ya d’an zauna yanai masa sannu da gida.... Daddy ya amsa masa da yalwar fari’a kana yace “Dama ina nemanka....?” Gaban Khalid ya fad’i ganin amininsa bai jima da ficewa daga parlorn ba... Badai wani abin yayi ba, tinda shine sarkin laifi a gidan Siyama ce ‘yar lele... Murya har na sark’ewa yace “Daddy nayi wani abin ne...?” Girgiza masa kai Daddy yai alamun a’a kana ya d’orada “Bakayi komai ba Son... Wani aiki nake so kamin a can Abuja, toh bansan ko kanada lokaci ba....” Cikin sauri Khalid ya shiga girgiza kansa yana fad’in “Haba Daddy, ka wuce tambayan lokaci a wajena, umarni kawai kai d’in zaka bani....” Daddy ya jinjina kai cikeda jin dad’i “Allah shi maka albarka... Akwai gidana na can estate d’in dake Gwarimpa, za’ai renovating... So inaso kai supervision aikin... Idan akwai wasu fittings da kake sona canzasu to your taste sai a canza.... Ka fahimta....” Khalid ya jinjina kai a hankali kana yace “Daddy su Aunty Daula zaka maida can.. Ko zaka maida Ammi Abuja ne....?” D’an murmusawa Daddy yai kana yace “Kawai inaso a gyara gidan ne Son Incase of tomorrow... Kasan ance gida biyu maganin gobara....” Ya jinjina kansa a hankali “Haka ne Daddy... Yaushe kakeso a fara....?” “Kar ya wuce cikin week d’in nan if possible....” “Alright Daddy... In sha Allah za’ai yanda kace....” Daddy ya murmusa cikeda jin dad’i kana yace “Allah shi maka Albarka Son...” Khalid ya amsada Ameen Daddy kana ya mik’e... A hanyarsa ta ficewa ya had’uda Ammi ta cika tayi fam sai faman danna masa muguwar kallo take... Kafin yai aune ta janyo hannunsa tana fad’in “Shige muje dama shigowarka nake jira...” Khalid na tambayar “Mi nayi kuma Ammi....? D’an sakar min hannun...” Bata saki hannun nasa ba bata fasa janyosa zuwa cikin parlorn Daddyn ba take fad’in “Bazan sakeka ba, na gaji da wannan wasan yaran da ake dani a gidan nan ehe....” Ta k’arashe sanda suka iso cikin parlorn gaban Daddy... Daddy ya d’ago yanai mata duban mamaki... Har lokacin huci take, ta shiga nuna Khalid da yatsa tana duban mijin nata “Toh gashi nan... Inaga idan yaji daga bakinka zai fi aminta cewa baida mata sai Yesmin.... Na gaji na gaji da yin k’anan muryawa Mahaifiyar Yesmin... Kullum cikin bata baki nake ina sanar da ita za’a tsaida magana k’wakk’wara... Daddyn Siyaam wannan harda naka laifin, gaba d’aya ka zubawa Khalid idanu yana nema ya maida mutane tamkar wasu mutanen banza... Toh wllhi bazan zuba maku idanu ba, maganar aurene dole a tsaida magana d’aya yanzu kam... Na gaji da wannan come gaba come baya da ake....” Ta k’arashe tana bud’e hannayenta alamun fad’a... Tagumi Daddy ya rapka yana duban yanda Ammi ke falfala masa ruwan fad’a tsaye akansa saikace wata uwarsa... “Kin gama...?” Ya tambaya yana dubanta... Wani kallon wulak’anci ta watsa masa daga nan yanda take tsaye kana tace “So kake na maimaita maka...?” Girgiza kansa yai a hankali kana ya dubi Khalid yace “Jeka abinka kaji....” “Toh Daddy...” Khalid yace sanda yake k’ok’arin ficewa... Ammi ta bisa da kallo baki sake tana furta “Aww yanzu cewa zakai yaje, a maimakon ka tirsasa ya sakama ransa ya auri Yesmin an gama... Haba Daddyn Siyaam Wllhi kai kake d’aurewa yaron nan gindi yake raina mutane... Khalid! Khalid!!..” Tabi bayansa tana kira saidai bata cimmasa ba dan ya jima da ficewa... Dawowa tai ta kuma yin tsaye akan mijin nata kana tace “Toh yanzu da ka k’yalesa ya tafi sai inji meye shirin naka ai....” Ta k’arashe tana mai zama gefensa... Murmusawa Daddy yai kana yace “Ko Ke fah Farida.. Shi miji idan anaso yayi abu ba’a nuna masa isa da gadara, indai ta wannan hanyar akeso yayi abu toh fah bazai yi ba, amma idan aka biyo ta hanyar kwantar da kai sai ya kwanta miki ma ki taka gadon bayansa ki shige abinki...” Ammi tasha jinin jikinta tana duban sabon sauyin data samu daga mijin nata, tinda suke dashi yau sama da shekaru talatin bai tab’a yi mata magana mai kamada wannan ba, kullum dik abinda take so abinda tai niyya shi ake, da alama yanzun hannunka mai sanda yake mata... “Ban fahimceka ba Daddyn Siyaam...” Ta fad’i tana mai karkatowa zuga dubansa sosai... Murmushin Daddy ya kuma sakar mata kana yace “Soon zaki fahimceni Farida tah...Kuma na miki alk’awari nan bada jimawa ba Khalid d’inki zai aure.... Ki kwantar da hankalinki kinji koh....” Ya k’arashe yana mai kamo ‘yan yatsun hannunta had’ida murzasu kad’an... Take annuri ya cika fuskar Ammi, tasan mijin nata bazai tab’a bata kunya ba tanada hundred percent guarantee akansa, dik abinda takeso shi yakeyi, bai tab’a keta dokarta ba a tsawon shekarun da sukai tare, mai ma zaisa taji wannan karon bazai abinda take so ba...? Lokaci guda ta kuma sakin murmushi tana duban Daddyn kana tace “Shisa nake matuk’ar k’aunarka mijina, kana min duk abinda nake so a koda yaushe...” Ta k’arashe tana mai kwantar da kai cikin k’irjinsa.... Lumshe idanunsa kurum Daddy yai, daga shi saiko Mahaliccinsa ne yakeda tabbacin suka san abinda yake ji cikin zuciyarsa... *** A b’angaren Khalid kuwa abubuwan da suke faruwa a ‘yan kwanakin gaba d’aya sun d’aure masa kai, sun dagula masa lissafi... First canzawar Daddy, had’uwarsa dasu Aunty Daula, kusancin Daddy da Baffah yanzu kuma ga aikin gyaran gidansa na Gwarimpa da ya d’aurasa bisa... Dafe kansa yai a hankali yana furta “What are you up to Daddy...?” Ya fuzar da iska a hankali had’ida girgiza kansa kad’an lokaci guda yaci gaba da shirya kayansa... Aunty Daula ya kira ya sanar da ita yana hanyarsa ta zuwa Abuja gobe da izinin Allah... Wai zo Kaga murna wajen Aunty Daula da yaranta... Tin a ranan suka soma shirye shiryen tarban Khalid... *** KANO Sawwama dake zaune gefen mahaifiyarta ta turo kallabi gaba sai taunar chewing gum take irin na matan da suka makara a bariki... D’aga k’afa tai ta d’aura d’aya bisa d’aya tana wani jijjiga take furta “Magajiya kenan... Ai na riga na samo lagon Hafiz... Zanyi dik abinda yake so daga k’arshe na k’yale shegiyar Zulfa’un ta auka ramina.... Haba ya kike kokonto na saika ba rainonki ba... Kinga nan...” Ta d’aga tafin hannunta tana nuna mata kana taci gaba da fad’in “Na kamasa a nan tinda ya bari nasan lagnosa...” Dariya sukai itada mahaifiyarta kana Magajiya tace “Kinyi min dadai... Kici gaba karki fasa komai...” Suka kuma saka shewa suna tafe hannaye... Daidai nan Dillaliya tai sallama yara na biyeda ita d’auke da saitin akwatina nik’i nik’i.... “Gafara dai! Gafara dai !!! Inji masu gidan suna nan....?” Dilla iya tace sanda take kwab’e mayafinta tai d’amara dashi... A tare Sawwama da Magajiya suka fito... Dilalliya na nunima yaran cewa su ije akwatinan a nan tsakar gidan.... Magajiya tabi akwatunan da kallo kana ta isa ta mik’awa Dillaliya tafukan hannayenta biyu suka tafe tana fad’in “Anyiririri Billahillazi na soma jiyo k’amshin amarci.... Kai ta wajena akwatunan nan sunci kud’insu...” Ta k’arashe tana jujjuya ‘yar k’aramar akwatin mai suffan jaka wacce ake zuba ‘yankunne da sark’a ciki..... Dillaliliya na Washe baki take fad’in “Yo ai na fad’a miki bana kawo kayan banza... Nan da kike gani akwatinan wata yarinya ce sakin wawa, juyasu da kyau ki gani sabbi ne dal ko lamba ba’a cire masu ba....” Magajiya tace “Wllhi na gani kaw....” Daidai nan wasu ‘yandaudu suka fito daga wani d’aki suka nufo akwatunan suna shewa da gud’a suna fad’in Uwarsu zata amarce, suna gud’a suna d’aga jakkunan.... “Kai ku ije akwatunan nan ban gama biyan kud’inba...” Cewar Magajiya tana fuzgewa hannun ‘yandaudun... D’ayan ya wani kame zani yana gyara d’aurin k’irji da kallabi yake fad’in “Yo ai Babanmu ne zai biya... Wayyo wa yaga ni Laminde gidan Ubana na bariki....” Suka kuma kwashewa da dariya gaba d’aya kana Sawwama tace “Wai ku dakata, wai auren waye ake batu, Nifa ban gane ba...?” ‘Yandaudun suka had’e hannayensu waje guda suka tafe had’ida yin salo yanda dai sukeyi kana d’ayan ya kame baki yace “Au Tab! Wai Ke bakida labari... Toh uwa guda nawa mukeda a bariki.... Uwarmu dai itace zata amarce mu kuma mu tafi mata zaman d’aki...” Suka k’arashe suna kuma tafe hannaye..... Sawwama ta dubi mahaifiyarta da mamaki.... D’aga mata gira tai kana tace “K’warai kuwa Sawwama aure zanyi na raya sunnar ma’aiki nima....” Sawwama da mamaki ya cikata tace “Magajiya aure... Aure kuma da waye...?” Magajiya na juya idanu take fad’in “Sati Uku ya rage na amarce Sawwama, ranar Bikin zaki San waye angon.... Kunga ku tattari akwatunan nan ku shigar min ciki...” Taceda ‘yan daudun.... Nan suka shiga kwasan kayan suna wani yauk’i su a dole ga mata.... D’ayan har cewa yake “Ni banma San a waye zan bada d’inkin nawa anko d’in ba....” Sawwama dai kallo ta bisu dashi har suka shige yayinda Dillaliya da Magajiya suka ci gaba da tattauna cinikinsu don harta sauran su kayan d’aki yau take so su kammala cinikin komai tinda biki ya gabato.... *** Aunty B ta numfasa tana duban ‘yar uwar tata kana tace “Sati uku kacal ya rage a d’aura auren....” Yaya Abida ta d’ago kod’add’un idanunta tana dubanta kana tace “Kije kisan yanda zakiyi ki hana wannan auren aukuwa Bara’atu.... Sanin kanki ne wannan auren daidai yake da maimaita bak’in tarihi.... Ki hana wannan auren aukuwa....!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji tana mai baiwa Aunty Bara’atu baya.... Mik’ewa tsaye Aunty B tai kanta a k’asa kana tace “Yaya banida ikon hana aukuwar wannan auren.... Da ace inada iko hanawa wllhi da kafin nazo gareki da na hana... Ki yarda dani.....” Juyowa tai sosai tana duban Aunty B kana ta tako gabanta kad’an.... “Bara’atu karki bari ayi wannan aure...!!!” Daga haka bata kuma cewa komai ba sai shigewa k’uryar d’aki da tai ta bar Aunty B nan tsaye cikin tsananin kad’uwar zuciya da mutuwar jiki..... Wasu hawaye masu d’umin gaske suka gangaro mata.... Fuzar da iska tai kad’an kana ta isa jikin k’ofar d’akin ta dafa, kanta na kife bisa k’ofar take fad’in “Na barki lafiya Yaya... Ubangiji yaci gaba da kareki....!”” Daga haka sa kai tai ta fice daga cikin gidan tana matsan hawaye... A can cikin d’aki kaw wani hoto dake sanye cikin k’aramar frame ta tsurama idanu, mutum uku ne jikin hoton, Wani dattijon mutumi sai wata matashiyar mace da k’aramin yaro da bazai haura shekaru uku ba... Ta shiga shafa saman hoton tana hango rayuwar da sukai a baya, rayuwa mai dad’i mai cikeda ni’imomi.... Ta rintse idanunta a hankali wasu hawayen suka kuma zubo mata... A hankali ta mik’e ta isa malank’ayin hoton ta kuma ratayesa... Lokaci guda take furta “Ma’aruf bazai biya diyan Ma’aruf ba...!” Tai maganar tana mai k’urama hoton idanu..... *** Raihanah na zaune k’asa kusan k’afafun Mamani tana warwarewa Mamanin k’unshi a k’afafunta lokaci guda suna kallon maimaicin shirin draman Dad’in kowa da ake nunawa a tashar Arewa24 Sameer yai sallama... Mamani ta shiga Washe baki tana fad’in “Shigo abinki angon gobe..” Raihanah kaw gaba d’aya sai ta tsinci kanta da daburcewa musamman dashike kanta a bud’e ne ko d’ankwali babu, jan top ne a jikinta saiko zanin tampa, ida tsifanta kenan Mamani tace ta cire mata k’unshi, gashi hannayenta gaba d’aya b’ace suke da k’unshi, gaba d’aya sai jinta take a tsarge... Tana jin suna gaisawa da Mamani ta kasa koda d’ago idanu ne balle ta gaidashi..... Shiko Sameer tinda ya shigo duba d’aya yaima bayanta ya d’auke idanunsa gabansa na wani irin yankewa, sam bai kawo Raihanah bace zaune wajen dan shi zai iya rantsuwa baisan yaya suffar jikinta yake ba dikda cewa shi yai treating ciwonta, dashike ba abinda yake dubawa ba kenan, aikinsa kenan yai treating ciwo nothing more.... Mamani sai jansa da firan biki take bai iya amsawa saidai murmushi da jinjina kai kurum da yake mata, ita kaw Rainah banda addu’an samun mafitar yanda zata mik’e ta bar wajen bata komai.. Kaman wacce addu’arta ya amsu taji ya mik’e yana amsa waya... Harda ‘yar ajiyan zuciya ta sauk’e wanda ta tabbata badon tv dake kunne ba da Mamani ta jiyo sautin ajiyan zuciyarta... Muryar Mamanin ne ya katseta da fad’in “Yauwa sannu ‘yar albarka, maza tashi ki wanke hannun naki ki dama masa furan nan da d’azu Babanku ya aiko.... Ta mik’e tana mai gyara d’aurin zaninta “Toh Mamani...” D’aki ta nufa daidai sanda ya ida wayar yana k’ok’arin komowa parlorn, ai a d’ari ta fad’a d’akin tana mai kuma sauk’e ajiyan zuciya, bathroom ta fad’a ta wanke hannunta kana ta bud’e wardrobe ta ciro hijabin da ya kusan kaiwa gwiwarta ta zira, kana iya tudun sumarta yanda ta tupke shi tsakiya dashike sumar nata mai yalwan cika ne kuma bata saka mar relaxer... Idonsa k’yam a k’ofar d’akin da yaga ta shige tamkar mai jiran fitowar nata, dik bayanan da Mamani ke masa ba wani fahimtar ta yake ba, yafi maida hankaliga duban k’ofar... Aiko tana fitowa sukai ido hud’u, tai saurin maida nata idanun k’asa tana gaidashi... Ya amsa yana mai duban k’afarta mai ciwo da yanayin tafiyar nata.... Ita dai Raihanah kitchen ta shige abinta dan kawo masa damin fura kaman yanda Mamani ta buk’ata.... Tana cikin had’a kindirmon ta cirota kenan daga cikin fridge Marliya ta shigo ta isketa.... “Patient d’in Yaya mi kike a kitchen... Salon Ya Ma’aruf yace an sakaki aiki tinda islamiya ma hanaki zuwa yai...”tace sanda take k’arasowa cikin kitchen d’in... Gajeriyar murmushi Raihanah tai kana tace “Tinda mashi zanyi aikin bazai hana ba... Kinga shigo ma ki tayani...” Ta k’arashe tana mik’a mata bowl.. Marliya ta kame baki tace “A’a kedai cika ladarki hajiya patient..” Raihanah ta d’an langab’e kai tace “Kai Marliya yanzu bazaki tayani ba....” “Cikata ladanki kawai patient d’in Yaya dama Mamy ke nemanki bara naje nace kina zuwa...” Bata jira cewan Raihanar ba tai ficewarta da d’an gudu gudu.... A can parlor kaw Sameer mik’ewa yai da niyyar tafiya Mamani ta tsaidashi da fad’in “Aff ai kuwa Raiha na kitchen tana dama maka fura bazaka tsaya kasha ba....” D’an sosa k’eyarsa yai da makullin mota “A’a Mamani a barshi har na dawo, ana nemana ne a can asibiti....” Mamani ta jinjina kai tace “Oh ni yaron nan sam baka hutu saikace agogo... Toh Allah shi tsare amma ka lek’a kitchen d’in ka amsa ko a mota sai ka sha....” Da toh ya amsa mata dan baiso ya kuma jan zancen yasan tinda ta soma fad’in sai ya amsa toh bazata k’yalesa ba har sai ya amsa d’in.... Yana jiyo muryarsa tanai masa addu’an Allah ya tsare... Lokaci guda tabi bayansa da kallo tausayinsa na d’awainiya da ita... Anya batai katsalandan ma rayuwarsa ba, ta rasa da wa zata had’asa aure sai d’iyar Haule...? Toh amma ai ‘yar uwarsa ce ta daifi masa wancan ballagazar matar tasa ko babu komai Sahariyya bazata rabasu dashi ba kaman wancan mai zubin awakan, idan ya tuna yanada iyalina gida dole ya waiwayesu....kuma yanzu Haule tayi hankali ta tuba ta gyara halayyanta... Dik d’an adam kuma ajizi ne tinda itama a baya ba haka take ba saida ta nemi yafiyan ahalinta, da wannan tinani ta d’an samu zuciyarta yai sanyi... Tsaye yai a k’ofar kitchen d’in yana duban yanda take kokawa da ice block saikace wata mai fasa gini duk ta wani daddage k’arfinta.... Abin yaso basa dariya, gyaran muryar da ya d’anyi ne ya sanyata saurin juyowa... Ta daidaita zaman hijabinta tana mai maida idanunta k’asa, sihirtaccen murmushi saman fuskarta “Laa Yaya ka gaji da jira koh... Dama yanzu zan kawo maka...” Sameer ya ida shigowa cikin kitchen d’in yana duban yanda take gudanar da al’amranta wanda zai tabbatar maka ita d’in ma’abociya hidima da kitchen ne “Is okay, kiyi min packaging kawai zan tafi dashi ne...” Jinjina masa kai tai kana tace “Ok bara na d’uko jug cikin drawer...” Gaba d’aya a daburce take gashi ya tsaya ya tsareta da idanunsa... Drawers dake k’asa ta soma dubawa bata sami jug ciki ba, dole tasan suna drawers d’in sama kenan... Sanin cewa tsawonta bazai kai ba dole ta shiga neman abinda zata taka ta ciro jug d’in... Shiko Sameer harda kame hannaye yana kallon ikon Allah... Toh mai take nema haka...? Bai ida tinanin ba yaga ta d’auko k’aramar kujera irin ta zaman kitchen ta d’ale tana k’ok’arin mik’a tsawonta alamun dai har yanzu tsawon nata bai k’arasa ba... Girgiza kai kurum yai yana mai d’an murmusawa kad’an, sai ganinsa kurum Raihanah tai gefenta ya bud’e drawer d’in... “Wanne zan ciro miki...?” Ya tambaya yana duban jugs d’in dake jere cikin drwer d’in, kusan guda uku... Murmushi saman fuskarta tace “Ko wanne ma Yaya...” Dubanta yai yaga wanda idanunta Ke bisa kana yasa hannu ya ciro shi... Daidai saitin kunnenta ya rage sautin muryarsa yana fad’in “Be careful kinsan har yanzu ked’in patient ce...” Bai jira cewarta ba ya ije mata jug d’in saman sink Wane irin kunyarsa ya rufeta, ta k’araso kai a sanne ta isa ta d’auraye jug d’in kana ta juye damin furan ciki... idanunsa naga wayarsa sanda ta k’araso ta mik’a masa jug d’in cikeda risinawa... Ya amsa yana fad’in “Da fatan dai baki zuba sugar ba..?” Girgiza masa kai tai alamun a’a kana tace “Ban saka ba Yaya....” “Good..” Ya furta yana amsar jug d’in lokaci guda ya shiga magana a wayarsa... Ta bisa da kallo tana mamakin wannan bawan Allah kullum cikin amsa waya yake... Daga nan ta shige amsa kiran Mamy.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *84* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sayayya iri guda Mamy taiwa Raihanah da Marliya, jin yarinyar take har cikin zuciyarta... Haka nan Allah ya jefa mata k’aunar yarinyar had’ida tausayinta musamman idan tuna cewa ita d’in marainiyace batada mahaifiya a raye...A hankali ta kuma sauk’e ajiyan zuciya sanda ta jiyo sallama daga parlor tamkar ta ‘Yaruwarta Bara’atu...Mik’ewa tai had’ida amsa sallamar kana ta nufi parlorn.... Aunty Bara’atu ta gani zaune dirshan saman kujera... Gabanta ya tsinke ya fad’i, ta k’arasa a hankali tana mai dafa kafad’ar Aunty Bara’atun... “Bara’atu...” Mamy ta ambata cikin tsananin sanyin murya... D’ago kai Aunty Bara’atu tai tana duban Mamy da idanunta da sukai matuk’ar raunana.... A hankali Mamy ta zauna gefenta jikinta na kuma yin sanyi... “Ke d’in baki kasance mai rauni ba cikinmu... Dik yanda akai akwai abindake damunki... Ki sanar dani ‘yar uwata, shin kinje kinga Yaya Abida ce...?” Wannan karon d’agowa sosai Aunty B tai tana duban Mamy sai kuma ta kauda fuska gefe, lokaci guda take furta “Mamy haka munaji muna gani zamu bari a aurawa Ma’aruf yarinyar da bai k’auna, kuma munsan yanda mahaifiyarta da ita kanta Sahariyyar suka baida gudummawa wajen tarwatsa rayuwar Zulfa’u... Anya bamu yi kuskuren aminta da wannan auren ba.... Shin bamuda wata hanya da zamu dakatar da wannan aure...?” Sauk’e ajiyan zuciya Mamy tai kana tace “A koda yaushe mu kasance masu kyautata zato Bara’atu... Kuma babu yanda banyi da Ma’aruf ba cewa karya tilastawa kansa wannan aure amma sai cemin yai yaji ya gani zai iya.. Toh kinga kuwa banida ikon hanawa haka nan mahaifinsa ma... Addu’a ita kurum zamu ci gaba da yi, dik abinda yake alkhairi ne Ubangiji ya tabbatar dashi... Sharri kuma ya kawar mana... Na sani Bara’atu kin damu dani kin damu da ahalina... Hasalima kinfi fifita damuwarmu sama da taki damuwar, gidan duniyar nan babu abinda zan iya biyanki dashi saidai na miki fatan dacewa na kumaci gaba da addu’an Ubangiji ya karkato miki da hankalin mijinki gareki...” Fasali Mamy ta d’anja kana taci gaba da fad’in “Dik yanda ‘yaruwa ta k’warai takai Bara’atu kin kai... Kina tare dani a dik sanda nake tsananin buk’atarki, yayinda ni bani kasancewa taredake lokutan naki buk’atun... Daidai da rana guda baki tab’a juyama d’aya daga cikin ‘yanuwanki baya ba... Kin rik’i amanar Yaya Abida dika cewa tasha tureki daga gareta dik a sabida baki yanke alak’a dani ba, kina nan a tsakaninmu kina nuna mana zallan k’auna.... Ki amshi girman daga garemu, kece kike kula damu a maimakon mune zamu kula dake... Bara’atu bansan ya rayuwata data iyalaina zaya kasance ba da ace na rasaki...” Ta k’arashe cikin tsananin Murya irinta mai kuka... Saurin rik’o hannayenta Aunty B tai idanunta suna yunk’urin kawo ruwa itama, lokaci guda take girgiza kai tana duban Mamy “Ki daina fad’in haka Mamy... Abinda ya dace shi nakeyi.... Hakan ce ya kamata ya kasancega ‘yanuwa.... Mamy ina k’aunarki ina kuma k’aunar zuri’arki... Ina kuma fatan Allah yaci gaba da tsareki da kuma ahalinki...Sannan bazan gushe ba ina addu’an Allah ya had’e kan ahalinmu....” Lokaci guda tasa ‘yar yatsanta ta goge hawayen da ya d’igo mata, take suka rungume juna hawaye na zarya daga idanunsu... A haka Zulfa’u da dawowarta kenan daga wajen aiki ta taddasu... Jiki a sanyaye tai sallama ta shigo parlorn.... “Mamy.. Aunty..!” Ta furta cikin tsananin sanyin murya... Take ko waccensu ta soma k’ok’arin saita kanta.... Aunty B ce tai k’arfin halin d’aura murmushi saman fuskarta, tana mai duban Zulfa’un take fad’in “Wannan zuwa wajen aikin ya kamata a dainashi haka nan... Kamata yai ace yanzu kuna gida a killace daga ke har Nabilar, dama zuwa nai na tattareku ku koma can a soma maku gyara dan mun gama magana da mai gyaran amaren zatazo cikin satin nan....” Zulfa’u dai murmushin da tafi kama da yak’e tai idanunta naga mahaifiyarta dake matsan sauran k’walla... A hankali ta isa aje handbag d’inta saman kujera kana ta k’araso tana mai tsaresu da idanu... “Aunty Wai meke faruwa ne...? Kuka fah na tadda kukeyi...” Tace sanda take zama gefen Mamy da har lokacin bata d’ago sunyi ido hud’u da d’iyar tata ba... Murmusawa Aunty B ta kumayi kana tace “Yo ba dole muyi kuka ba Zulfa’u... Irin wannan ni’ima da Ubangiji ya lullub’emu dasu, ace zaka aurar da d’oyoyi har biyu lokaci guda kinga kaw ai kuka ya zamto mana dole, kukan farin ciki muke d’iyata....Allah ya cika min buri ya amshi addu’ata bazaki koma gidan wancan shashashan tsohon mijin naki ba, kinga kuwa ai dole na zubda hawayen Farin ciki...” Murmushi tai tana mai duban mahaifiyarta da itama murmushin ne saman kod’edd’en fuskarta... Allah sarki Bara’atu, ita dai komai sai ta nemo masa mafita, bazata tab’a ganin damuwa a tattareda Mamy da ahalinta ba har sai tasan hanyar da zata biyo dan taga ta taimaka wajen kawar masu da wannan damuwar... Idan da ace duka ‘yanuwa haka suke tabbas da an sami k’aranci gaba da muguwar k’iyayya tsakanin Al’umma.... Tuni su Marliya da Raihanah sun soma shirye shiryensu, wani d’auki suke kaman ba’a tab’a buki a zuri’ar tasu ba, kodashike dole ma suyi d’auki domin kaw dangin ba’a tab’a Bikin bane tinda auren Hafiz da Zulfa’u da akai a baya shida babu duk d’aya ne, domin kaw biki ne akayi shi ba cikin farin ciki ba, dikda d’auki da suke basa d’aukin Bikin Aunty Sahariyya da Ya Ma’aruf sanin cewa su d’in two different people ne, hasalima tausayinsa suke kamilin mutum irinshi bai cancanci mata irin Sahariyya ba... Dik wannan d’auki da suke sam Naja’atu batayi, babu wanda yasan maike damunta harta Hajiya babu yanda batayi taji meke damun Najah na amma Najah tak’i fad’i mata komai, Sahariyya da k’awarta Fa’iza kaw cewa sukai hassada ce kawai irinta Naja’atu taso ace itace zata auri Ya Ma’aruf ba Addarta Sahariyya ba... Ita kaw Najah bata cewa komai saidai ta tab’e baki, daidai da d’inkin anko d’inta ma bata bada ba, ita kad’ai tasan mai take sakawa cikin zuciyarta.. *** Washe gari tin sassafe Baffah ya tasa k’aninsa mai bi masa a haife wanda ratan shekara d’aya ne zuwa biyu tsakanin su cewa sai ya masa rakiya zuwa Kano... Baba Ali badon yaso ba yai shirin rakiwa d’an uwan nasa... Suna tafe saman kwalta Baba Ali Ke fad’in “Wllhi badon ka tak’urani ba BillahillAzim bazanje ko ina ba... Kai nifa tin sanda aka soma yima mutane d’iban awakai saman kwalta na daina zirga zirga dik k’aunan yawo irin nawa... Yo Allah na tuba idan mutanen nan sukai wuf dani uban waye zai biya kud’in fansata... Kai ni bama wannan ba, yanda nake fata zalla sai k’ashi suka min bugun zazzab’en dawa ai harta k’asusuwana baza’a samu ba....” Baffah na dariya yana buga kan steering yake furta “Kai mutumina... Haba Alaji Aliko, Ali zaki mazajen fama...Wai ina kurin da cika bakin ne....” Baba Ali yace “Kai inaa da ne wllhi....Maza suna daji yanzu...” Baffah ya kuma tintsirewa da dariya... Wannan na d’aya daga cikin abinda yasa yace Baba Ali ya masa rakiya, don tafiya saida irin su Baba Ali ko babu komai zakaci dariya, Baba Ali irin mutanen nan ne masu k’anan jiki da tsananin barkwanci... A haka suka isa garin ta Dabo, kai tsaye gidan Engr Ma’aruf Mutallab suka nufa kaman yanda Daddy ya sanarma Engr d’in da zuwan nasu, tuni dama anyi shirin tarabansu... Tarba ta karramawa akai masu a gidan Engr, Muhibbah bata sama bata k’asa sam bazakace itace bace yanda ta kwantar da hankalinta take gudanar da al’amranta... Abin har baiwa Engr mamaki yake tamkar ba Muhibbar da ya sani ba, batun k’arin aurensa sam bai d’aga mata hankali.. Ko dan bataga auren ya tashi gadan gadan bane, maybe shiyasa sam bai dameta ba... Sosai yake jin dad’in canzawar da Muhibbah tai, har k’asan zuciyarsa yake jin dad’in hakan, fatansa Allah sa hakan mai d’orewa ne... Abinka da wanda sam bai faye zama ba bacin gaisuwa da sukaidasu Baffah bai kuma saka su idanunsa ba, hidimominsa da sabgogin gabansa sunada yawa... Dik kyau da tsari da gidansu Khalid kedashi sai sukafi santin wannan gida da aka sauk’esu, kai da gani kasan Nira ta tsufa hannun masu wannan gida, sashe guda na bak’i aka masu masauk’i babu abin buk’atar da babu... Baba Ali ya fito yana k’arema tangamemen sashen da aka masu masauk’i kallo, “dank’ari mak’ari Wato dai gida ne saikace otel d’in k’asashen turawa” Yai maganar yana kewaye k’ayattacen swimming pool dake a b’angare guda cikin sashen.... Harda buga tsalle yana ihu yake fad’in “Kai Baffah ai sai kace min tafiyar k’asan waje zamuyi tikitin jirgi ne kurum ya rage mana.... Kaga gida tamkar a turai.... Wai ma tsaya meye alak’an mutumin nan dasu Khalid ko d’iyarsa yake nema... Nima na samu amin connection tinda naga auren yanzun dik connections ne....” Darawa Baffah yai kana yace “Wllhi idan zaka sakamin bindiga bansa alak’an Daddy da wannan mutumin ba, kasan manyan mutanen nan k’ila ko kasuwanci ko siyasa ta had’asu tinda Engr Ma’aruf cikakken d’an siyasa ne mai neman takaran kujerar Governor...” Jinjina kai Baba Ali yai kana yace “Hakk’un... Ai cewa nake nan ne gidansu yarinyar da sai nace ashe da Ammi batasan waye d’anta Ke nema ba tinda nasan halin matar sam tak’i jinin talaka...” Dubansa Baffah yai kana yace “Har yanzu ma batasan da batun auren ba kuma nasanka da zuba da b’arankan baki Ali, dan girman Allah na rok’i arzikin ka ko Khalid kada yasan wannan batu balle ya isa ga mahaifiyarsa...” Baba Ali ya zaro idanu waje “Toooh babban magana... Wannan wane irin aurene haka b’oyewa tamkar wani abin k’i... Naga dai aure shelansa ake ba b’oyesa ba....” Baffah yace “Babu ruwanka kaidai kawai kayi abinda na sakaka....” Hannu yasa yaja fatun bakinsa alamun ya ja masu zip ya saka masu sakata kana yace “Bakada matsala my lips are sealed...” Baffah ya jinjina kai yace “Good...!” Zuwa dare suka kira Sameer suka sanar dashi suna Kano, Sameer yace babu matsala gobe idan Allah yakai rai zai masu jagora zuwa gidansu don dama shi suka kira suka sanar dashi zasuzo gaisuwa a madadin Khalid tinda Daddy ya aike Khalid d’in wani waje bazai sami zuwa ba sannan ga lokacin biki na kuma k’aratowa.... Washegari kaw wajajen k’arfe goma na safiya suka fito cikin shiri, tuni suka tadda abinci kala kala tamkar wanda sukai order da sunan breakfast... Su Baba Alin an dad’e ba’a gamu ba tuni aka gyara zama akaja girki, ko wanne sashe na gidan tafiya mai d’an nisa zakai kafin ya sadaka da wani sashe don haka sam basu jiyo hayaniyar cincirindon ‘yan siyasa daketa kai komo a harabar gidan ba... Banda kukan tsintsaye ma dake saman bishiyoyin da yai k’awanya wa sashen nasu basa iya jiyo komai... Suna tafe Baba Ali na zuba zancen in yai kud’i zaiyi kaza zaiyi kaza yayinda Baffah ke neman Sameer a waya dan sanar dashi cewa sun ida shiri shi suke jira... Akram da isowarsa gidan kenan ya hangi mutane na fitowa daga gate d’in da zai sadaka da b’angaren bak’i na cikin gidan.... Baisan dalili ba amma ganin wad’annan matasan ya d’aga masa hankali... Toh bak’i ne akai a gidan....? His Excellency nada bak’i amma ace bai sani ba...? Su waye wad’annan...? Kasa samo amsar tambayarsa yai ga k’irjinsa dake tsananin bugu, yana gani suka taho ta gefensa zasu rab’a su shige yai saurin kifa kansa ga wayarsa yana shafawa lokaci guda yana satan kallonsu k’asa k’asa Baba Ali sai bin d’inbin jama’an dake cike mak’il a gidan sahu sahu da kallo yake, Baffah na muskutinsa yana fad’in “Kai haba wannan irin kallo saikace ba daga garin gwamna ka fito ba...” Dik yanda suka gifta sai sunyi sallama ma mutanen da suka tadda.. Nan suma suka samu wasu empty kujeru dake barbarje haraban gidan angle angle suka zauna suma... Firansu sukaci gaba da yi hankali kwance yayinda a b’angaren Akram hankalinsa ya gaza kwanciya... Su waye wad’annan da yaga sun fito daga sashen bak’i masu mahimmanci...? Zamansu da kad’an motar Sameer ta kutso kai cikin gidan dan tuni sun sanar dashi gidan da suke ya kuma ce ya sani dan Gidan Engr Ma’aruf MUTALLAB ba b’oyeyye bane a garin.... Take bugun k’irjin Akram ya k’aru, bai gama daskarewa ba har saida Sameer ya bud’e marfin mota ya fito... Koda ace sau d’aya suka tab’a had’uwa bazai mance fuskarsa ba domin kaw ko sati ba’ai ba Zulfa’u tai introducing d’insu ma juna, ya tina yanda Sameer d’in ya tsattsaresa da tambayoyi a matsayinsa na mai neman auren k’anwarsa... Toh mai ya had’asa da wad’annan mutanen...? Mai kuma ya had’asu da Engr..? Badai Engr ya fahimci su d’in sunyi tarayya wajen soyayyar mace guda bane... Idan ba haka ba what’s all this...? Yai saurin kauda kansa gefe ganin sun mik’e da alama ficewa zasuyi.... Yana nan a haka ya hangi Engr ya fito daga sashen cikin gida.... Akram ya rasa wanne zaiyi baya fata shida Sameer su had’u gaban His Excellency, hakan can ruin his plans... Da sauri ya zaga bayan motar da yake tsaye jikinta ya lab’e yana hangesu daga nesa yanda suke gaisawa, bai iya jiyo mai suke cewa amma yana iya hango yanda fuskokinsu suka cika da annuri... Yana nan a haka a lab’e wayarsa data soma ruri ta razanesa.. A d’an firgice ya cirota cikin aljihun wandonsa yana duba mai kiran nasa... Yusuf abokinsa ne dake main gate cikin motar Akram d’in yana jiran fitowar Akram su shige... Kaman munafuki haka ya d’aga wayar cikin yin k’asa k’asa da murya.. Daga d’aya b’angaren Yusuf ya soma fad’in “Ya na jiku shiru ko yau oga ya makara ne...?” Cikin k’asa k’asa da murya Akram Ke fad’in “Yusuf kamin wani aiki... Akwai wata mota k’irar BMW da yanzu zata fito mai launin bak’i dan Allah kabi bayansu kaga yanda suka nufa dan na tabbatar da hasashe na...” Yusuf yace “Ban gane ba.. Toh tafiya campaign d’in namu fah....?” Cikin daburcewa Akram yace “Shisa nace kabi bayansu kasan su waye su d’in tinda ni banida halin yin hakan, wannan fita dole ce akaina, k’auyuka biyu zamu zaga yau da his Excellency, ai kaga I can’t come up with any excuse... Kawai kabimin bayansu and find out who they are..” Bai jira cewan Yusuf d’in ba ya katse kiran yana mai kuma lek’ensu yanda suka shige motarsu ta Sameer na jagorantarsu... Yana ganin sun shige ya fito daga mab’oyarsa yana hangan Engr dake gaisawa da jama’a... Shiru yai na wani d’an lokaci, yai nisa cikin tunani.. Toh kodai Muhibbah nada wata masaniya ne kan wannan al’amari...? Toh ko dai ba abinda yake tunani bane... Da ace hakan ne yasan by now da Engr ya tsaresa da batun.. Toh kodai ya zuba masa idanu yaga gudun ruwansa ne...? Lokaci guda ya shiga girgiza kai yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa Engr can never find out about his plans...Yayi alk’awarin bazai sanar dashi komai ba har sai bayan ya mallaki Zulfa’u... Da wannan tinani ya k’arasoga Engr d’in yana wani k’asa k’asa dakai yana gaidashi, tuni Engr ya mik’a masa hannu sukai masabaha dan shi baison wannan tsananin girma da Akram ke basa kasancewarsa mutum mai sauk’in kai da k’aunar Al’umma... Babu jimawa convoy d’in motocinsu suka soma ficewa sahu sahu, akasarin motocin lambar Mutallab19 suke da, ma’anar 19 d’in kuwa shine shekarar gudanar da zab’en nasu wato shekara ta dubu biyu da shatara miladiya.... Abinka da mai farin jini da yalwar alkahiri zo Kaga yanda gari ya kacame da nuna k’aunaga matashin d’an siyasan.... Zulfa’u da sauk’arta kenan daga adaidaita zata shige ofishinsu motocin su MUTALLAB sukazo zasu wuce k’ofar ofishin nasu, mutane ta ko ina hannu ake d’aga masa ana gaidashi... Tsaye tai bakin wajen itama tana dubansu dikda cewa ta makara yau d’in amma dole ta tsaya kallon d’an siyasan da bata tab’a k’auna irinsa ba, watak’ila idan a rabon yau d’in ta ganshi ido da ido sai ta ganshi... Atika nata damunta da waya inaa ko kula wayar tata batai ba... Sautin wak’ok’insa da mawak’an gawurtattun ‘yansiyasa suka wak’esa shine kawai Ke tashi... Dik dandatson muatenen da suka shige sai ya masu alamun gaisuwa da hannayensa.... A haka har suka k’araso kusan gidan radio d’in sosai yayinda Zulfa’u ta shaga da kallonsa... Yau Allah ya nufa taga Mutallab da idanunta, ta kasa tab’uka komai sai duban da take binsa dashi yanda yaketa amsar gaisuwan mutane... Kaman daga sama Akram dake cikin motar yana tuk’awa ya hango wata tamkar Zulfa’u... Dama tinda suka iso kusan gidan radio d’in nasu yake jin gabansa na fad’uwa ga kuma wad’ancan mutanen da yasa Yusuf ya bisu ya bincika masa su waye su... Abinda yafi basa mamaki shine yanda ta kafe idanunta ga samar motar tana kallon Engr dake d’aga ma d’inbin masoyansa hannu... Ji yai kaman ya kwali motar da bala’in gudu saidai kuma baida ikon yin hakan.... Sannu a hankali idanun Engr suka sauk’a kan wannan baiwar Allah data kasa janye idanu daga Barin dubansa, wani irin abu ne yaji yana tsargar masa sanda idanunsu suka sark’e waje guda, yayinda a b’angaren Zulfa’u bugun zuciyarta ya k’aru, k’warjininsa ya cika mata idanu... K’ok’arin janye idanunta tai amma sai ta kasa ga k’irjinta dake bugu da sauri dasuri... Kasa janye idanu yai daga barin duban nata, wani abu wanda bazai iya kwatantawa ba na kuma tsargar masa.... Akram ya d’aga kai sama yana duban Engr lokaci guda ya kuma kai dubansa ga Zulfah dake tsaye har lokacin duban Engr take wane irin sihirtaccen murmushi da bai tab’a gani daga gareta ba kwance saman kyakkyawar fuskarta... Cikin sauri ya janyo wayarsa ya shiga k’ok’arin dialing layinta.... Hakan yasa tai k’ok’arin lalumar wayarta dake cikin jaka, daidai nan Atika ta k’araso tana fad’in “Amma kinsan Aunty Zulai tana d’akin gudanar da shirye shirye ke take jira... Kuma yau d’in kece bak’uwarmu ta mako...” Zaro idanu waje tai kana tace “Ke dan Allah wai interview za’ai dani...?” Atika tace “Sake tambayata... Kinga dan Allah muje amarsusu....” D’an murmusawa tai tana mai bin bayan motocin da kallo.... Atika ta kuma kai dubanta gareta tana d’an murmusawa take fad’in “Ashe tawagar oganku ne dole ki tsaya a nan kiyi ta raba idanu ko zaki hango ango...” Harara Zulfah ta galla mata kana tace “Abinda kika iya kenan ai jin baki....” Tasa kai ta shige cikin radio station d’in zuciyarta nai mata wani irin sanyi haka kurum, ita kad’ai sai sakin murmushi take, yau tayi ido hud’u da Engr Mutallab, governor d’insu mai jiran gado da yardar Allah... A haka ta isa d’akin gudanar da shirye shiryen, annashuwa fal zuciyarta, hakan sai ya bata daman amsa duk tambayoyin da aka mata cikin sauk’i da shauk’i... A b’angaren Engr ma hoton fuskar budurwar can ya kasa b’acewa daga k’wayan idanunsa... Mai yasa yakejin kaman ya tab’a ganin fuskar wani waje... Kaman ya san mai irin fuskar... Maiyasa kuma ya kasa cire hoton fuskar daga k’wayan idanunsa..? Maiyasa zuciyarsa ta kasa daina tuno wannan fuskar... Could it be ya tab’a sanin mai irinta wani wajen ne...? Toh a ina zai sani...? Wata zuciya tace kaid’in mai huld’a da jama’a da dama ne... Watak’ila ka tab’a ganin mai irin fuskar ne... Toh amma tambayar mai yasa kake jin yanayin da kake ji....? Wannan amsarce ya kasa samowa har suka isa yanda zasuje.... *** Baffah da Baba Ali sun zaga ko ina sun kuma gaisa da dangi, hartada Mamani saida suka shiga suka gaisheta, Baba Ali ya sami Mamani sukaita zabga zance har sai yaji kaman kar su tafi, dan ko babu komai Mamani ta skashi nishad’i hali yazo d’aya... Hartadasu sashen Baffah Wada da sauransu duk sun shiga sunyi gaisuwa...Daidai da gidan Baba Alhaji saida sukaje... Saidai Sameer bai masu rakiya ba don tinda ya masu jagora zuwa cikin gidansu yai ficewarsa shima, Aamiru d’an gidan Baffah Ado shi ya zazzaga dasu sauran wajajen... Kasancewar Nabilah na makaranta shiyasa ma basu had’uda ita ba, gidan Aunty Bara’atu sukaje daga k’arshe yanda suka sanar da ita mak’asudin zuwan nasu gashi basu sami Nabilah ba kuma ance yini zatai a makaranta... Aunty Bara’atu tasan yanda Nabilah ta d’auki zancen auren nan, kuma Daula ta sanar da ita duk shirin mahaifin Khalid, bata tantama turo abokan Khalid d’in da Daddy yai nada nasaba da shirye shiryensa... Dan haka bata b’oyema Baffa komai ba sanin cewa ta riga tasan shirin Daddy, kuma yanzu idan sukace zasuga Nabilah wani rikicin zasu kuma b’allowa domin kaw sosai Nabilar Ke fushi da Khalid... Duk wasu shirye shirye daga bakin Aunty Bara’atu suka samu suka kuma dank’a mata sak’on Daddy, da fari k’in amsa tai a cewarta basai Daddy yayi haka ba... Baffah yace wannan ai na amaryace kuma dama ko wacce amarya anai mata hakan... Zaiso su gana da Nabilah amma saidai goben fitar sassafe zasuyi, Aunty B tace kar ya damu zata tura masa layin k’awar Nabilar Yusra idan duk da abinda zasu tattauna sai ya dinga communicating da Yusran... Sosai hakan yaiwa Baffah, Har ransa yake jin karamci irin na Aunty Bara’atu, kuma ya yarda Khalid gidan Dattako yazo.. *** A b’angaren Akram kaw tinda suka komo daga campaign hankalinsa ya gaza kwanciya, ya k’agu ya had’uda Yusuf yaji yanda ya kaya masa da bak’in gidan Engr... Ga mahaifiyarsa data tsaresa da wasu tambayoyi had’ida tuhuma... “Akram ni tinda ka k’irgo kawunanka a masu zuwa nema maka aure babu Gwamna mai jiran gado ciki zuciyata Ke fad’amin wani abin... Akram anya kuwa...? Wane irin aure ne wannan zakace ko gayya da yawa bakaso ayi, shifa aure d’an shela ne ba b’oye b’oye... Ka fad’a min mai kake b’oyewa Akram ni mahaifiyarka ce....” Shafa sumarsa yai a hankali kana yace “Umma ni babu abinda nake b’oyewa, kuma abinda yasa ban saka his Excellency a masu zuwa tambayamin aure ba sabida shine zaije ya amsa min auren, kinga bai kamata na d’aura masa d’awainiya da yawa ba, kuma Umma wane gayya za’ai tinda ita Zulfa’un ita tace batason babban buki...Babu yanda banyi da ita ba amma sai ce min tai wannan ba aurenta na fari ba kenan dan haka ita batason a kambaba Bikin, ni babu wani abinda nake b’oye miki Umma ki yarda dani....” Numfasawa tai kana tace “Shikenan tinda kace haka, biki naka ne kaida ita sai yanda kuka tsara abinku... Amma ka tabbata Gwamna shine Wakilinka...Dan sanin kanka ne shid’in tamkar uba ne a wajenka... Tin bayan rasa mahaifinka babu wanda yai d’awainiya dakai da danginka sama dashi, toh kada kayi wasa da amana... Har kullum wasiyyata a gareka kenan...” Jinjina kai yai dikda k’irjinsa dake tsananin bugu kana yace “In sha Allahu Umma, na miki alk’awari Excellency shi zai karb’a min aure...” “Shikenan tashi kaje, Allah shi maka albarka ya kuma dafa maka...” Ameen Umma ya amsa dashi kana ya mik’e ya fice yana neman layin Yusuf... Koda suka had’uda Yusuf yasha mamakin jin cewa masu neman auren k’anwar Zulfa’u ne wad’ancan d’in... Toh ko mai ya had’asu da Engr..??? Wannan tambayarce shi kansa Yusuf d’in bai sani ba shima... *** A can Abuja kuwa Khalid da ‘yan uwansa lullub’e suke cikeda Farin ciki, sosai sukai murnan zuwansa, baga Aunty Daula ba baga yaranta ba... Shi kanshi Khalid d’in bazai k’arya ta cewa dik sanda yake taredasu yakan tsinci kanshi cikin Farin ciki, yana samun farin ciki a tattaredasu wanda ya rasa daga nashi ‘yanuwan da sukafi kusanci dashi... Wani rayuwa yake experiencing wanda baiyi ba a baya, rayuwace da ‘yanuwa Ke k’aunar juna suka kuma damu da damuwar juna, where everybody’s opinion matters... Ba irin rayuwar gidansu ba da ba’ayin abu sai idan abinda wanda sukeda k’arfin iko ne suka fad’i, ba kuma a d’aukan shawarin kowa da mahimmanci sai nasu... Ya kuma sakin murmushi yana duban yanda yaran keta tsalle kowacce tana fad’in saidai yaci abinda suka tarbesa dashi, dangin chocolates ne da kayan mak’ulashe, abinka da yaro... Aunty Daula ta shige tsakiyan yaran tana fad’in “Toh a k’yale Yaya ya huta, kunga bai jima da isowa ba...” Khalid na murmushi yace “No it’s ok Aunty... Nayi kewarsu nima ...” Ya kamo hannayensu yana amsar kyautukansu d’aya bayan d’aya yana nuna Farin cikinsa... Lokaci guda shima yake dank’a masu nasa tsaraban da yayo masu... Haba nan fah suka kuma shagala da murna da farin ciki, wata irin k’aunace tsakanin Khalid da yaran... Aunty Daula dai k’yalesu tai ta tafi kitchen dan ci gaba da shirya masu dinner d’in tareda taimakon mai aikinta Karima.... Da dare bayan sun ida cin abinci take tanbayarsa mutan gidan su Ammi da Siyama, Khalid yace duk lafiya suke... Yanda yai maganar tamkar mai d’aukeda damuwa, dan ta kula tinda yaran suka bar parlorn suka nufi b’angaren karatu dan yin homework d’insu yanayin Khalid d’in ya canza sosai tamkar wanda yai nisa cikin tunani... D’an gyara zamanta tai tana mai karantarsa kana tace “Problem..?” Murmusawa yai a hankali ba tareda yace komai ba... Muskutawa ta kumayi kana tace “Kaman kayi nisa cikin tunani tunda yaran suka tashi... Akwai matsala ne..? Ko akwai abinda kake so ne...?” Murmusawa ya kumayi had’ida d’an fuzar da siririyar iska kana yace “It’s about my Dad, he’s been acting strange lately.... Inaji kaman akwai abinda yake b’oyemin... Like he’s up to something.. Na kasa gane mai yake shiryawa... Da fari yamin introducing d’inku abinda ya kasa yi tsawon shekarun nan, kwatsam yanzu yaji ya had’ani daku... Na biyu wani sabo da kirki na musamman na shiga tsakaninsa da abokaina, and now kwatsam ya sakani kular masa da gyaran gidansa na nan Gwarimpa har yana tambayar ra’ayina.... Wad’Annan abubuwan sun d’aure min kai.... Like, what is he planning..? Could it be aurena da Yesmin suke shiryawa ba tareda sanina ba shida Ammi... I know my Dad nasan yanda yakejin maganar Ammi, kuma na sani yanda Ammi tai niyyan had’a aurena da d’iyar sister d’inta toh fah sai tayi... And shi kuma Daddy abinda tace shi zaiyi.... Idan hakan ta kasance da gaske I don’t know... Ban sani ba ko inada k’arfin hak’urin da zan iya jurewa nai masu biyayya...” Ya k’arashe cikin tsananin nuna damuwa... Numfasawa Aunty Daula tai cikeda tausayinsa kana tace “Toh kai baka son zab’insu ne...?” D’agowa yai ya d’an dubeta kad’an kana yace “I’ll be honest with you Aunty... Yesmin ‘yar uwatace, toh zaifi kyau idan ta tsaya a matsayinta na ‘yar uwata... Amma any other relationship aside from wannan bazai tab’a yuwa ba tsakaninmu....” Numfasawa kad’an Aunty Daula ta kumayi kana ya ambato sunansa... Wannan karon ma d’an duban nata yai “Ka yarda da mahaifinka....?” Ya jinjina mata kai a hankali... “Ka yarda bazai maka abinda zai cutar dakai ba....?” Shiru yai wannan karon tamkar mai nazari kana yace “Na yarda...” Yai maganar cikin murya mai rauni.... Jinjina kai Aunty Daula tai kana tace “Wasu lokutan iyaye sukan hanga mana abinda yafi kyau da dacewa a garemu... Ko yaya ne believe me babu iyayenda zasuso suga ‘ya’yansu ba cikin Farin ciki ba, shiyasa wasu lokutan idan sun mana zab’i sai muga kaman sunyi katsalandan ma rayuwarmu ne ko suna nuna k’arfin ikonsu akanmu ne, Toh ba haka bane tsaban soyayyace da suke mana wanda su a nasu Ganin akwai abinda suka hango wanda mu ba lallai mu hango ba... Khalid Iyayenka suna sonka suna kuma k’aunarka, saidai su irin nasu hanyar da zasu nuna maka nasu k’aunar kenan... Never kada ka tab’a doubting wannan... Sannan a koda yaushe dik yanda kakai da son abu toh ka nemi zab’in Allah ciki sai Kaga nasara, farin ciki da kwanciyar hankali wanda bakai tsammanin samu ciki ba...” Khalid da zuciyarsa tai matuk’ar masa sanyi da jawaban Aunty Daula, samun kansa yai yana mai jinjina mata kai kana yace “Hak’ik’a naji dad’in shawarwarinki gareni Aunty... Kuma kaman yanda kikace zab’in Allah is always the best... Na gode k’warai for listening to me, and also for your kind advice...” Aunty Daula ta murmusa kana tace “Babu komai, this is what family are for after all... Yanzu yaushe zakaje duba gidan...?” D’an numfasawa ya d’anyi kad’an kana yace “Gobe nake son lek’awa in sha Allah, dan already tin ina kaduna nayi magana da wani company.. So idan naje naga yanayin aikin sai a soma right away...” Jinjina masa kai ta d’anyi kana tace “Shikenan idan ka dawo goben sai ka kaimu shopping together with the kids, I’m sure that will be fun....” Khalid ya murmusa yace “An gama Aunty na...” Itama murmushin tai daidai sanda yaran suka shigo parlorn rik’eda littafansu da suka ida homework ciki... Washe gari sosai sukaji dad’in fita shopping gaba d’ayansu, malls da dama suka dinga zagyawa Aunty Daula na jidan kaya abin har ya soma baiwa Khalid mamaki tamkar wata mai had’a lefe irin kayan da take jida, sannan akasarin kayan sai ta tambayi ra’ayinsa take d’auka ko kuma idan ta kula ya k’urama wasu kayan idanu Toh su take zab’a.... Shi dai bai kawo komai ba, dik cikin kirkinta ne da girmama opinion d’in duk wanda take taredasu ya d’auki Hakan.... Basu dawo gida ba saida ta tabbata rabin kayan da zasu zuba a lefe choice d’in Khalid ne.... Wani Sabo na musamman na kuma shiga tsakaninsu gaba d’aya, sosai yak’e ganin girman Matar Baban nashi dikda a zahiri baifi ta k’ere masa da wasu shekaru k’alilan ba... K’annensa kaw jinsu yake tamkar ciki d’aya suka fito, basuda maraba da Siyama a wajensa... A b’angaren Ammi kaw bata damu dan Khalid d’in na Kaduna ba don ita dik tinaninta hakan na cikin shirin Daddy ne na aurawa Khalid Yesmin... *** A yayinda biki ya rage saura sati guda Sawwama da Hafiz suka isa territory d’in gungun ‘yan iskan...Tafiyar kusan awanni uku ya kwashe su daga gari zuwa cikin dajin ... Sawwama ta juyo ta dubesa kana tace “Ka tabbatar da abinda kake shirin yi...? Ka shirya mu shiga...?” Jinjina mata kai yai “I was born ready...” Sawwama ta murmusa kana tace “Wannan itace Fadar Babba Duna... Shugaban duk wani wanda yai k’auri a fannin garkuwa da Bil’adama a k’asar nan, rashin imanin Babbba Duna ya wuce dik yanda kake tunani, cire kan d’an adam a wajensa ba komai bane... Biyoni muje....” Hafiz dai sai waige waige yake yana duban k’ungurumin dajin da suka shigo had’ida mamakin ina Sawwama tasan irin wad’annan mutane... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *85* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Wane irin sunk’urumin daji ne da baka jin sautin komai sai kukan tsintsaye, kallo guda zakaiwa Hafiz ka fahimci tsananin tsoro dake tattareda shi, dole ne yai hakan bashida wani zab’i muddin yin hakan zaisa matarsa Zulfa’u ta dawo garesa... Ganin dai bazasu daina kutsa cikin dajin nan ba ya sanyashi janyo hannun Sawwama dake gaba dashi da saurin gaske, cikin k’asa k’asa da murya tamkar mai tsoron kada wani yaji abinda zai fad’i yace “Ke dakata... Wai har yanzu nufinki bamu iso wajen Babba Duna ba, ko kina nufin kice sai munga k’arshen dajin nan ne....? I thought you said mun iso fadarsa... Toh ina Fadar take...” Murmusawa tai da gefen baki kana tace “Dad’ina dakai saurin karaya saikace ba namiji ba.... Toh banda abinka da nace maka mun iso Fadar Babba Duna ai gabaki d’aya katafarin Dajin nan shi yake mulka... Wai tsaya ka canza zuciyarka ne...? Idan ka canza zuciyarka ne shikenan sai Mu koma....” Numfasawa Hafiz yai yana mai kame kunkuminsa, shayeda tsananin mamaki yake dubanta “Mamaki nake ina kika san irin wad’annan gaggan ‘yantaddan...?” K’asaitaccen murmushi Sawwama tai tana mai aika masa duban kama rainani kana tace “Wai da da nace maka inada makullin cin nasararka a hannuna ka zaci wasa nake...?” Girgiza kai Hafiz yai kaman d’alibi gaban malaminsa kana yace “Ni duk a tunanina ‘Yaniskan cikin gari kike magana ba manyan ‘yan fashi da makami ba....” Ta kuma murmusawa had’ida gyara tsayuwarta “Bana huld’a da k’anan ‘yan iska.... Biyoni muje...” Fuzar da iska yai yana mai kuma bin dajin da kallo lokaci guda yake biyeda ita, wasu mutane guda biyu suka soma hangowa jikin wata bishiyar gamji mai tsananin duhuwa ko wannen su rungume da manya manyan bindigogi, murtuk’a murtuk’an mutane bak’ak’e k’irin dasu, haka nan k’wayan idanunsu jajazir babu alamun annuri ko rahama a tattaredasu.... Daga can gefe gefe tsinta tsinta suna hango mutane jifa jifa suma duka rik’e suke da makaman yak’i... Hafiz ya had’iyi miyau da k’yar dan shi zai iya rantsuwa bai tab’a ganin bindiga ido da ido tsirarta ba sai yau da Sawwama ta kawosa wannan waje.... Abinda yake gani a finafinai gashi na faruwa a karan kansa... Koda suka iso saida mutum guda ya cajesu tsaf kafin ya nuna masu saman wata Dutse yace su jira acan... Babu musu suka k’arasa suka zauna, hankalin Hafiz dai dik ba’a kwance ba yayinda Sawwama ko ajikinta saima taunar chewing gum d’inta take... Hafiz banda Uwar harara bai aika mata komai, yana ayyanawa cikin zuciyarsa lallai babban kilaki ya aura a matsayin mata... D’an dubansa tai taga yana faman watsa mata muguwar kallo.... Tab’e baki tai kad’an kana tace “Ya dai lafiya ko wani abin ka gani...?” Girgiza kai Hafiz yai yana mai kuma dubanta kana yace “Ke yanzu tashancin naki bai tsaya a Alhazan gari ba harda ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane kike bi... Tell me Sawwama maza nawa kikai huld’a dasu kafin ni..!!!” Yai maganar yana faman bubbud’e k’irji da hanci saikace bashine ya gama rakub’e rakub’e ba.... Tintsirewa da Dariya Sawwama tai tana dubansa... Ya kuma harzuk’a “Au dariya ma na baki... Ke ko kunya bakiji ba...” Dakatar dashi tai da fad’in “A’a Kaga Malam daina min ihu aka, ni nan taimaka maka nake ka samu ka kuma mallakar Matarka Zulfa’u a karo na biyu... Idan kuma kace zaka kawo min rainin hankali wllhi kaji na rantse saidai a maidama Hajiya k’ok’on Kan d’anta dan idan naso sai ai gunduwa gunduwa dakai yanzu a wajen nan...!!” Cikin karaji tai maganar tana kallon yanda alamun tsoro da tashin hankali suka kasa b’oye kansu a fuskar Hafiz dikda k’ok’arin b’oyesu da yake... Lokaci guda ya kuma tintsirewa da dariya ta shiga shafa fuskarsa tana fad’in “Relax mijina... Karka damu ni d’in har yanzu mai k’aunarka ce so ka kwantar da hankalinka... Kuma da kake cewa har mazan daji Ina bi toh kai kuskure domin kaw babu mata a tsarin Babba Duna... Dama idan kace akasin mata Wato Ina nufin maza...” Tana maganar tana yawo da ‘yar yatsarta a sassan jikin Hafiz had’ida kashe murya irinta gogaggun kilaki.... A firgice Hafiz yajada baya yana mai girgiza kai had’ida duban Sawwama da tsananin mamaki wanda bai tab’a irinta ba.... “Sawwama so kike kice abinda kika kawo ni ayi dani kenan... Sawwama wata irin biladama ce ke.... Ki d’auko mijinki na sunnah ki damk’asa ma ‘yanluwad’i....!” Bai kai aya ba ta katsesa da fad’in “Kaga Hafiz nifa ka isheni... Idan bakaso burinka ya cika ka dawo da Zulfa’u sai ka tashi ka tafi is not a big deal...” A zuciye ya mik’e yana aika mata muguwar kallo yake fad’in “I was so stupid da na yarda dake... Na yarda notin kaina sun kwance da har na yarda Ke d’in zaki taimaka min na dawo da matata.... Kafurci na baikai nan ba, bazan aikata wannan laifin ba Sawwama kinga tafiyata....” Juyawan da zaiyi sai cin karo da bakin bindiga yai an saita k’irjinsa... K’iris ya rage Hafiz bai saki fitsari ba sabida tsananin firgita, abinda yake gani a fina finai na neman aukuwa dashi.... Mik’ewa Sawwama tai tana mai murmusawa kana tace “Hafizi na kenan... Hafizi na Sawamma haka kuma angon Zulfa’u... Ka kwantar da hankalinka Ina mai tabbatar maka babu abinda zai faru dakai.... Ai ni na maka alk’awari kuma ya zama dole na cika maka.... Babba Duna owes me big time, akwai bashina akansa sabida haka aikin da zai mana baida buk’atan biyan reward ka fahimta....” Ta k’arashe tana sakin murmushi, lokaci guda tai alama ma d’aya daga cikin yaran Babba Duna da yai pointing bindiga a k’irjin Hafiz da ya janye bindigar.... Basu jima ba wasu k’artai biyu da wani d’an tsakurkurin mutumi tsakiyarsu suka nufo yanda suke daga can k’asa da wajensa suke.... Sawwama ta mik’e tana sakarma d’an tsakurkurin mutumin da murtuk’a murtuk’an mutanen nan Ke tsaronsa murmushi.... Daga can tsakurkurin mutumin nan da bai wuce a hure ba ya shiga maida mata maetanin murmushinta yana bud’e hannaye alamun sannu da zuwa yake furta “Barkada zuwa Fadan Babba Duniya... Kyakkyawa mai kyawawan ‘yandaudu..... Fad’i dik abinda kike babu b’ata lokaci za’ai miki... Ki fad’i duk Uban da kikeso a saco miki shi a fad’in k’asar nan.... Idan barikin Soji ne yake yawo dashi matsayin masu tsaronsa Ina mai tabbatar miki sai mun sace miki shi.... Babba Duna bai tab’a saka abu a gabanshi yaga gazawa ba....” Ya k’arashe yana k’ek’yata dariya.... Hafiz da tinda wannan tsakurkuri mai wani irin siffa kaman ba d’an adam ba ya soma magana ya b’oye Bayan Sawwama sai rarraba idanu yake, shi dik a zatonsa zaiga Babba Duna murjeje ne sai yaga wannan k’aramin alhakin.... Amma yayi kama da tsagerun shed’nu matuk’a sannan kallo guda zaka masa ka fahimci shekaru sun fara kamashi ma’ana tsufa ya sauk’o masa, da gani kasan wannan ya jima yana kafurci a duniya.... “Na gode Babba da wannan karramawa taka gareni.... Mijina na kawo, ai masa aiki....” Ta k’arashe tana janyo Hafiz daketa k’ok’arin b’oyewa bayanta... Babba ya kafe Hafiz da idanu kana yace “Mai ake so ai maka Pretty boy....?” Hafiz ya kuma hard’e rai jin Babba yana admiring d’insa.... Sawwama ta d’an mintsileshi alamun yai magana... Babba ya bud’e murya yace “Kar ka damu pretty boy ka fad’i duk abinda za’a maka idan dai a k’ark’ashin alfarman Sawwama ne, bakada matsala... Fad’i ko mai kake so...” Hafiz ya gyara tsayuwarsa yana hango tsakiyar kan Babba kana ya zaro wayarsa a aljihu ya shafa... Lokaci guda yai taku kad’an zuwa gaban Babba ya nuna masa hoton dake bisa screen d’in.... Babba ya amshi wayar ya k’urama hoton idanu kana wayar ta shiga zaga hannun yaransa, wannan ya kalla ya mik’ama wannan har ta dawo hannun Babba.... “Mai kake so ai masa... Wasu sassa na jikinsa akeso a ciro maka...?” Saurin girgiza kai Hafiz yai kana yace “Ajiyanshi kawai nakeso na baku na wani d’an lokaci...” Babba ya murmusa irinta basawa kana yace “Na maka alk’awarin ko tandu nan ya barni wajen iya ajiya.... Amma ina mai tabbatar maka idan ajiyan ya kuskuri kufcewa komai ka iya faruwa....” Hafiz ya dubi Sawwama, itama d’in shi ta duba kana ta murmusa tace “Wuk’a da nama na hannunka Babba....” Babba Duna ya jinjina kai kana yace “Yaushe ajiyar taku zata soma aiki...?” Hafiz yai karaf yace “Nan da kwanaki biyar....” Babba Duna ya d’aga ‘yan yatsun hannunsa tamkar mai lissafi kana yace “An gama pretty boy angon mai ‘yandaudu....” Hafiz ya kuma dubansa kana yace “Banaso ya escape...Bana so kuma a samu failure...” Babba Duna ya tako gabansa kad’an yana mai k’arewa Hafiz duba lokaci guda yake furta “A wannan daji babu wanda ya isa ya fice bada izinin Babba Duna ba muddin ya riga ya shigo fadar Babba toh fah saida amincewarsa ya fice, zaman daji saida shiri pretty boy...” Tin bayan shigowarsu dajin sai sannan Hafiz ya saki murmushi, tabbas yanaji har cikin ransa Zulfah ta dawo gareshi an gama babu wanda zai kuma shan gabansa.... Koda sukazo ficewa rasa hanya sukai kaman yanda Babba Duna yace, har saida akai masu jagora suka sami hanya,... Wannan dalili yasa suke lak’abi wa Dajin da Fadar Babba Duna,domin kaw dajin kewaye take da shirinsa, hakan yasa ba’a iya kamashi tsawon shekarun da yai yana ta’addanci... Sannan hakan yasa yai k’aurin suna ya shahara a fannin garkuwa da d’anadam.... (Ya Allah ka kawo mana k’arshen wannan ta’addanci ya addabi k’asarmu ya zamto ruwan dare, Allah karka barmu da wayonmu Allah ka kawo mana d’auki Albarkan Annabi d’an gatanka ya Allah) Ameen thumma Ameen..! *** Muhibbah dake zaune tsakiyar parlor sai faman murmushi take tana ayyanawa cikin zuciyarta yanda Engr zaiji idan yaji labarin auren masoyiyarsa da Babban yaronsa Akram.... Dole ma itace zatai masa breaking wannan news d’in taga kalan reaction d’insa... Babu boka babu Malam babu tashin hankali auren mijinta bazai yuwu ba... Ta kuma murmusawa tana juya glass cup d’in dake hannunta wanda a ido juice ne amma a zahirin gaskiya k’wayoyin maye ne a ciki.... Lokaci guda ya mik’e tana jin kanta a sararin samaniya duniyar na mata dad’i... Takawa ta dingayi har ta isa jikin tapkeken hoton Engr, a hankali ta shiga shafwa tana mai murmusawa “I can’t wait to see your face idan labarin cin amanarda amintaccenka yai maka ya riskeka..... Wannan kyakkyawan murmushi dake bisa fuskarka nasan zai gushe... Sannan babu mai kuma dawo maka da wannan murmushi sai ni Muhibbah... Your one and only wife... You must accept the fact that your home is right here with me...!!!” Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da dariya tamkar mai tab’in hankali... Cikin tafiya datafi kama da tangad’i take takowa har ta zube saman kujera.. Nan bacci yai gaba da ita... A haka yaran nata suka shigo dawowarsu kenan daga islamiyya suka tadda Mahaifiyarsu nan kwance, idan da sabo hakan yabi jikinsu kasancewar dama tin can basa samun kulawa daga wajenta sunma fi sabo da Murja wacce duk wani d’awainiya da mahaifiya kema d’anta ita take masu... Murja ta k’urama yaran idanu cikeda tausayawa yanda sukai tsaye suna duban mahaifiyarsu, waima gwamma yanzu suna iya ganin nata, a baya sai su shafe kwanaki basu sakata idanunsu ba, Murja ta k’arasa ta rik’o yaran tana mai saka murmushi saman fuskarta take fad’in “Muje ku canza kayan makaranta kunga Mummy na bacci...” Yaran basu ce komai ba Irfaan ya soma shigewa yayinda Samha ta take masa baya, tabbas murja k’ok’arinta kawai take amma ta sani izuwa wannan lokaci yaran sun soma gane abu tinda sun soma girma... Haka sanda sukaje Abuja gidan Aunty Daula kwanakin baya kaman kar su dawo yanda Aunty Daula Ke nuna masu zallan k’auna irin wanda basu samu daga mahaifiyarsu ba, dan ma Allah yasa mahaifinsu na matuk’ar nuna masu k’auna da kulawa... *** A can gidan Aunty Bara’atu ake gyaran amaren, sanda Bikin ya rage saura sati biyu dama ta tafi dasu can gidan nata, tuni Zulfa’u ta d’auki hutun wajen aiki yayinda Nabila ce kawai ke ficewa makaranta itama sabida exam ne da suke rubutawa wanda daga shi sai tafiya Industrial training da muke saka ran zatai a garin mijinta da yardar Allah... Sam Aunty Bara’atu bata barinta ta fice ba tareda makarin rufe fuska ba nik’ab, idan Kaga amaren dole Kaso sake kallonsu yanda sukai kyau fatarsu ta kuma murjewa tai santsi alamun suna samun gyara da kulawa na musamman, yaran Aunty Bara’atu kenan, aima dole susha gyara ciki da waje, gyara mai tsafta da babu cutarwa cikinta babu kuma algus... Yauma dai wani dahuwar kazar Aunty Bara’atu ta shigowa Zulfa’u dashi sanda aka ida mata halawa, sai faman ture turen baki take tana fad’in ita ta gaji da wannan tsirface tsirfacen abubuwan da ko a auren fari ba’ai mata su ba.... Aunty dai jinjina kai tai tace “Na dai ji amma sai kin cinye tas kin shanye roman nan, kinsan ance idan kanada kyau k’ara da wanka...” Atika na gefe sai k’ek’yata dariyarsu take tana fad’in “Allah dai ya bar mana ke Auntynmu....” Zulfah kaw saidai ta gallawa Atika harara dan ita ke ziga Aunty Bara’atu a cewarta.... Aunty ta dubi Atika dake gefe tana darawa kana tace “Ki tabbata ta cinye bara naje Ina zuwa...” Batakai aya ba Atika ta bata amsada “An gama Auntynmu...” Zulfah ta galla mata harara had’ida yin k’wafa... Matsowa kusanta Atika tai tana kuma k’ek’yata dariya take fad’in “Aaa gaskiya dole Yaya na Akram ya k’aro sadaki Anty ta gama masa komai....” Duka Zulfah ta d’aka mata a cinya tana fad’in “Kedai Allah ya shiryaki... Mutum abinda ya iya kenan jin baki...” Atika ta kuma darawa tace “Allah huci ran amaryar yayana Akrami....” Murmusawa kurum Zulfah tai amma ita kanta batasan meke damunta ba dan gaba d’aya ji take maraban auren da aurenta na fari k’alilan ne, dan idan tace tana k’aunar Akram tayi k’arya, tsakani da Allah bata tab’a jin sonsa a ranta ba saidai batasan dalilin da yasa ta amsa ma auren nasa ba, k’ila sabida azalzalawa da Baba Alhaji da d’ansa Hafiz sukai mata ne... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai tana bin sangalalin k’afafunta da kallo yanda suketa faman shek’i da d’aukan idanu alamun sunsha dilka da halawa... A hanakli ta furta “Allah kaine masanin maiyasa abubuwa suke faruwa yanda suke faruwa, Ya Allah lamurana suna hannunka... Ya ka zamto majib’incinsu...” lokaci guda taji ta samu natsuwa da wannan addu’a.... Gama addu’anta keda wuya wayarta dake jikin socket yai alamun k’aran shigowar sak’o... Hakan ya haifar mata da fad’uwan gaba ba kowa ya fad’o ranta ba illa Mr Unknown.... *** A can makaranta kaw su Nabilah suna fitowa daga exams aka dami Yusrah da kira, gashi dai da alama bata son amsa kiran ne gaban Nabilar... Nabila ta fahimci hakan dan tin fitowarsu a first paper kafin su shiga second paper Yusra Ke k’usk’us a waya... Har suka isa masallaci kira ake Yusrah na sakata a silent.... Nabila kaw yi tai tamkar bata a wajen saima duba question paper d’in jarabawar da suka fito take... Sanda Yusrah ta tafi alwala ta bar wayar saman jakanta gefen Nabilar kasancewar ita Nabilar ba sallar zatai ba shisa ta zauna daga gefen masallacin tana kuma duba takardanta, kaman daga sama wayar Yusrah ya kuma ruri... Kai dubantaga jakan tai lokaci guda ta janyo jakan zata d’au wayar... A d’ari Yusrah ta k’araso ta fuzge jakanta tana fad’in “Nifa banson sa ido...” Harara kurum Nabilah Ke galla mata kana tai k’wafa tace “Kici gaba, ce miki akai bana lura dake ne a ‘yan kwanakin nan... Sarai nasan akwai abinda kike b’oyemin, kema hardake a shirye shiryen wannan auren munafuncin da ake shiryawa koh... Toh kici gaba Allah ya baki sa’a, dan Allah karki fasa...” Yusrah na darawa kad’an take fad’in “Haba tawan kema kinsan bazan miki haka ba, dik abinda zai faranta miki shi nakeyi... Haba amaryar oga Bear..” “Mtsww.. Ke kika sani kuma...” Ta fad’i tana mai aika mata muguwar kallo... Yusrah ya dara had’ida mik’ewa tana mai ci gaba da fad’in “A daina cika mana baki dai munsan anaso ana kaiwa kasuwa....” Ko tankata Nabilah bata sami zarafin yi ba, har yanzu ta kasa daina tinanin Wai Khalid baiko kirata ba har wayarta ta lalace ta kuma gyara duk bai nemeta ba... Anya wannan aure mai yuwa ne kuwa... Anya ba ramuwar wulak’anci data masa Farin had’uwarsu yai niyyan mata ba, idan ba haka ba ita ko a wasan kwaikwayo bata tab’ajin labarin ango irin Khalid ba... Takaicin kanta dana Khalid d’in ya kuma cika mata zuciya... Batai wani gayya ba itakam, harta coursemates d’insu ma ba ita ta basu katin gayyata ba Yusrah ce duk tai wannan, suma ba duka ta bari Yusran ta gayyata ba, daga su Safwan da Al’amin saiko tsiraru cikin matan wad’anda suke mutunci.... *** Yusuf ya mik’e tsaye yana duban mamakiwa abokin nasa.... “Ban gane ba Akram... Toh Wai kana nufin har yanzu invitation card bai isa hannun his Excellency ba...?” Jiki a matuk’ar sanyaye Akram Ke duban Yusuf kana ya d’an tab’e baki kad’an yace “Yusuf I can’t look him in the eyes.... Wllhi bazan iya mik’a masa katin nan ba.... Bansan da wasu kalmomi zan kare kaina a gabanshi ba... Mutumin da ya kasance Gata a gareni da ahalina.... Shin Yusuf wane irin yaudara da cin amanane wannan...? Ya yarda dani ya aminta dani ni kuma na saka mishi da butulci... Tell me Yusuf am I really doing the right thing....?” Ya k’arashe yana mai ci gaba da juya cards d’in hannunsa.... Fuzar da iska Yusuf yai kana ya d’an duk’a gaban Akram d’in..... “Akram jibi za’a d’aura maka aure da Zulfa’u... Duk wani tunani da zakai yanzu toh fah ihu ne bayan hari.... Ka sani shi aure muk’addari ne... Allah ya nufa Zulfa’u ba matar his Excellency bace taka ce, so stop blaming yourself for what is happening.... Kar ka mance shi so dangin mutuwa ne bai duba rarrashi, nikam na fahimceka d’ari bisa d’ari ina kuma tabbatar maka His Excellency would understand you even more.... So stop all these ridiculous thoughts, and get yourself together...” A hankali ya jinjina masa kai kana ya kuma d’agowa yana dubansa, mik’a masa wata takarda yai linke cikin takarda kana ya had’a masa da invitation card d’in yace “Kaine zaka kai masa wannan a madadina....” Yusuf ya kuma binsa da kallon mamaki... “Ban gane ba Akram.... “ Mik’ewa tsaye Akram yai yana fuskantar Yusuf d’in yake ci gaba da furta “Kaman yanda na fad’a maka bazan iya kallon cikin idonshi ba.... Nasan zaiji tsananin mamaki idan katin bikina ya riskesa... Hakan yasa nakeso kada ka bashi katin har sai ana gobe d’aurin aure.... Zai tambayeka Ina nake... ko kuma ya kira wayata.... Toh zan kashe wayata, sannan idan ya tambayeka ka sanar dashi nayi tafiya na tafi k’auyen su Umma kuma k’auyen k’auyene tukuf da ko service na waya babu.... Kawai abinda nake so ka sanar dashi shine.... Shi d’in shine Alwalin aure na... Ma’ana shi na wakilta shi zai karb’a min aure.... Promise me zaka isar da sak’ona gareshi abokina....” Ya k’arashe cikin tsananin raunin murya.... Saida Yusuf ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana ya dafa Akram kad’an yace “I promise you, zan isarda sak’onka da yardar Allah....” Akram ya murmusa a hankali kana ya kuma zaro wata takarda ya mik’awa Yusuf d’in yace “Wannan wa amaryata zaka bada, nasan kwana biyu zataji wayata a kashe kuma zataga ban nemeta ba... Toh idan ta karance wannan takardan Zata fahimceni...” Wannan karon murmushi kwance saman fuskarsa ya k’arashe... Yusuf d’inma murmushin yai kana suka rungume juna... Akram yana furta “Na gode d’an uwa.... Kai d’in ka wuce aboki a wajena... Kar ka tab’a mance wannan...” Wannan karon darawa kad’an Yusuf yai kana yace “Kai ango dan zakai aure basai ka bar min wasiyya ba da Allah... Kaga bara naje na amso d’inkuna na d’azu Matazu ya kirani yace ya gama... Ina fata ka amso hulunan fitan angoncin naka...?” Jinjina masa kai Akram yai yana mai furta “Naka wasa ne... Komai nawa intact yake.... Kaga da Allah ka ajiye takardun nan da mahimmanci and make sure ya isa ga wad’anda aka rubuta dominsu...” Yusuf yace “Baka da haufi ango... Sai munyi telephone...” “Alright shikenan sai na jika...” Sukai sallama Yusuf ya fice.... *** Tin ana sauran kwana biyu biki ake bidiri a gidan Hajiya Haule, daga ita har d’iyarta Sahariyya shige da fice kurum suke, ba k’aramin shiri sukaima wannan biki ba da alama.... Dikda cewa Sahariyya da sandar crutches take dogarawa hakan sam bai hanata gudanar da shagulgulan bikinta ba, bata damu da cewa auren bai gaban angon ba ita dai tinda shid’in zata aura an gama mata komai, jiya ta gudanar da bridal shower gashi yau ma sai shirye shiryen kamu suke, Sahariyya jin kanta take mai babban sa’a cikin k’awaye... Selecting k’awayen ma suke itada Fa’iza sai kin kai a gayyaceki.. Kankace mai k’anan maganganu ya shiga yawo tsakanin k’awaye... Hakan bai dameta ba dama hakan ne takeso ta zama ita d’in dai ake zance.... A b’angaren Sameer bai gari ma ya tafi taron bita (Seminar) na kwana biyu a birnin Ikko, bazai dawo ba sai ana gobe d’aurin aure, Hakan yafi masa sauk’i don dama wannan aure shida babu a wajensa tamkar d’aya ne....Shi gaba d’aya yama mance da ana shirye shiryen biki da wata amarya har saida Shamsu ya kirasa yana zolayan yak’i dawowa ya mak’ale a Lagos ko sai sun biyosa da amaryarsa ce.... Sameer ya d’an mik’e d’aga yanda yake kishingid’e yana murmusawa kana yace “Tinda kana nan zaka wakilceni dan yanzu haka ma wasu team daga Korea kuma zamu tarba cikin satin nan... And my presence is very important, bazan iya katse abinda nake na dawo ba...” Da mamaki Shamsu ke fad’in “Yanzu mahimmancin abin har ya wuce aurenka....?” Sameer ya d’an fuzar da siriryar iska kana yace “Auren da na d’aika da mahimmanci a fari ka daiga yanda abu ya sauya mana da Siyama balle wanda sam dama ba har zuciyata bane, kawai na amsa ne dan ganin cewa zuri’armu bata tarwatse ba... So yafi ma da na basu space suyi bukinsu lafiya su gama, naci gaba da taron bitana a nan...” Murmusawa Shamsu yai “Dr Sameer Faruq Yarima ko na ce Dr Ma’aruf Usman Mailafiya....” “Duk wanda ka fad’i yayi Architect...” Yai maganan shima yana d’an darawa... Hira ta abokai sukaci gaba dayi Shamsu bai daina zolayarsa ba kana daga bisani sukai sallama.... *** Tafiya yake cikin motar ba tareda sanin tak’amaimen yanda ya nufa ba, shidai kurum yasan ya d’auki hanyar ficewa daga cikin gari, gaba d’aya ji yake zuciyarsa tanai masa d’aci, sam baijin ya kyautawa his Excellency... Zuciyarsa gaba d’aya a jagule take, sai faman fuzar da iska yake yana buga kan steering wheel, ga wani irin gudu da yake falfalwa saman kwalta tamkar mai barin Duniyar.... Yana shige wani check point na sojoji da kad’an wata mota tai masa overtaking.... Bai damu ba yai k’ok’arin canza hanyarsa saidai tuni motar ta kuma yunk’urin shan gabansa... Nan ne fah hankalin Akram ya soma karkata ga tinanin maiyasa wannan motar Ke bibiyarsa.... A hankali yake rage speed dan ganin gudun ruwan masu bibiyan nasa... Rage speed d’insa keda wuya wasu maza guda biyu suka fito suka finciki marfin motar nasa... Suna shiga d’aya da ya zauna daga backseat ya saka masa bindiga a k’eya yana mai furta “Keep moving...” Hankali tashe Akram Ke karanto innalillahi mai kuke nema wajena..? Su waye ki....?” Na gefensa ya buga masa k’arshen bindiga a k’eya yana mai furta “You talk too much... Kai abinda muka umarceka idan kanason ci gaba da numfashi....!!” Tuk’i Akram yaci gaba dayi yana bin duk wani umarninsu dikda dishi dishi da yake gani sakamakon buga masa k’otar bindiga da d’anta’addan yayai.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _.................DA RABO_ *86* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Saida suka saka kan Akram cikin wani bak’in jaka mai kaman buhu kafin suka kutsa dashi cikin dajin, a k’alla sunyi tafiya mai nisan kilomita ashirin da k’afafu a k’iyasin Akram dan shi dai ba ganin komai yake ba hannayensa d’aure suke sannan kanshi rufe yake... Bayan sun share tafiya mai tsawon gaske yaji sunja sun tsaya, guda d’aya yasa hannu ya zame jakan da aka rufe masa kai dashi.... A hankali Akram ya soma bud’e idanunsa yana gani dishi dishi... Fincika yaci gaba da yi yana fad’in “Su waye ku, mai kuke nema a wajena...?” D’ayan yakai masa naushi a ciki yana fad’in “You never learned your lesson... Ance maka kai shiru ka faye surutu da yawa...” Daga can Akram ya soma sauraro wani familia voice yana fad’in “Shisa ka iya siyayasa sosai sabida surutu irin naka...!” Da tsananin mamaki Akram ke dubansa, Hafiz ya K’araso har gabansa yana murmushi kana yace “Kaji mamaki koh.... Ka zaci ka mallaketa an gama ko... Well, you’re very much mistaken... I told you countless time babu mai raba tsakanina da Zulfa’u, amma taurin kunnenka ya hanakaji... Dama na fad’a maka dan kana a matsayin d’ansiyasa ba kai kad’ai kasan ‘yan iskan gari ba... Mu da masu daji muke huld’a ba k’ananan ‘yaniskan da k’waya ya haukata ba...” Yana murmushi yakai hannu saman kafad’an Akram yana d’an bubbugawa yake fad’in “Ango ango... kar ka damu zan d’auko mata hotunan amarya nazo har nan na nuna maka....” Fincike kafad’arsa Akram yai yana tsananin huci yake furta “You coward... Why would I even be surprised, abinda ka iya kenan... Bazaka iya fuskantar matsalarka head on ba, bazaka iya sayan soyayyarta da zuciyarka ba saidai kayi amfani da hanyar ta’addanci abinda kafi wayo akai... Babban matsalar a nan shine kai dak’ik’i ne na k’arshe ka kasa fahimtar ita soyayya ba’a mata dole...!” A zuciye Hafiz yakai mai naushi a hanci, yana mai ci gaba da huci yake furta “K’arya kake... Zulfa’u tana k’aunata if only baka hure mata kunnen ba da k’arerayinku na ‘yansiyasa... And let me remind you this Zulfa’u was mine, she is my mine and she shall remain mine....!” Dariya Akram yai yana mai tsartar da jinin dake bakinsa yanda Hafiz ya naushesa “I promise you, even if you’re going to end my life right this moment bazata kuma dawowa gareka ba... Kaman yanda hannun agogo yake tafiya clockwise Toh haka rayuwar Zulfa’u dakai yake, babu komawa baya....Tai maka nisanda har abada baza kuma mallakanta ba....!” Naushi Hafiz ya kuma kai masa yana mai furta “Shut up... Shut the hell up... Baka San mai kake fad’a ba, Karen farautar ‘yansiyasa.... You’re now under my custody sai yanda nai dakai... And I promise you sanda zaka fice a dajin nan Zulfa’u ta koma gareni, sai kaje kaci gaba da k’arerayinku na ‘yansiyasa ma wata.... Have I made myself clear..?” Ya k’arashe yana kamo hab’ar Akram had’ida d’ago kansa.... Murmushi kurum Akram Ke masa ba tareda ya furta komai ba.... Lokaci guda Hafiz ya d’anjada baya ya dubi yaran Babba Duna yace “Keep an eye on him...” Gaba d’ai jinjina masa kai sukai kana yasa kai ya kutsa ya fice daga dajin.... *** Tsananin mamaki ne ya cika Engr, toh ina Akram zai tafi ba tareda ya sanar dashi ba....? Ya kuma juya envelope d’in sak’on Akram d’in yana mai duban Yusuf da kansa ke k’asa... “Ina yace maka ya tafi...?” Yusuf ya had’iyi miyau da k’yar “Dama cewa yai k’auyen mahaifiyarsa zai tafi kuma ko ka kira bazaka samesa ba dan babu network na waya a wajen....” Cikeda rud’ani Engr ya jinjina kansa a hankali kana yace “Amma bai sanar dakai komai ba...?” Gyara zama Yusuf yai kana yace “Iyakacin abinda ya sanar dani kenan sai kuma sak’on nan da ya bada a baka....” Engr ya numfasa a hankali yana mai k’urama envelope d’in idanu.... “Shikenan na gode k’warai, kana iya tafiya...” Yusuf ya mik’e cikeda risinawa yai sallama wa Engr.... A hankali ya soma ware envelope d’in, katin gayyatar aure da ya soma cin karo da ita shi yafi komai d’aure masa kai, k’irjinsa na bugu da sauri da sauri, sam baima kula da wasik’ar dake bayan katin auren ba... A hankali ya soma zaro katin Bikin yana warwareta... Wane irin bugu yaji k’irjinsa na masa, badon yaga sunan Akram b’aro b’aro jiki ba da sai yace k’ila ba Akram d’in da ya sani bane... But what is all this...? Ta ya za’ace right hand man d’insa zai aure a basa short notice irin haka..? Ya za’ace auren Akram baida labari sai ana gobe d’aurin aure.... Wane irin al’amari ne wannan....? Gabaki d’aya kansa ya k’ulle, ko kulada sunan amaryar bai ba har saida Muhibbah ta shigo cikin parlorn dan dama tinda taga shigowar Yusuf abokin Akram ta lab’e daga bakin k’ofa, dik kuma taji abinda suka tattauna.... “Excellency na, meke faruwa ya na ganka haka...?” Tai maganar cikeda kulawa.... Kai kurum ya d’ago yana dubeta da idanunsa da tuni sun canza launi zuwa ja... Har saida gaban Muhibbah ya d’an fad’i dan tasan kalan b’acin ran mijin nata... K’arasowa tai a hankali idanunta kan invitation card d’in dake rik’e hannunsa guda... Hannu ta amshi card d’in tana mai karantawa, zuciyarta na mata wani irin dad’i, ji take tamkar tai shewa ta nuna tsantsan Farin cikinta amma babu halin yin hakan.... Zama tai gefensa mamaki kwance saman fuskarta lokaci guda take furta “Akram ne zai aure....? Shine baka sanar dani my Excellency na... Haba ai da na baida nawa gudummawan... Akram ai d’an gida ne ya wuce normal employee....” Dik wannan maganganu da take Engr bai tankata ba hasalima yai nisa duniyar tinani, kaman daga sama ya kuma sinkayo muryarta tana karanto sunan amaryar... Da tsananin mamaki ya d’ago yana kuma dubanta, cikin sauri ya fuzgi katin hannunta, ga k’irjinsa dake tsananin bugawa tamkar zai fice... Sunanta kenan... Tabbas he cannot be mistaken, sunanta kenan... Toh kodai ba ita bace... What is all this...? D’agowa yai yana duban Muhibbah da tai sakare itama tana dubansa, kan kace mai yasa kai yabi bayan Yusuf yana mai doka kira ma securities na gidan kan cewa su dakatar da Yusuf... Ai a take Muhibbah ma ta take masa baya tana tambayarsa lafiya.... Masu gadin main gate ne sukai waya first gate suka sanar da securities d’in first gate d’in cewa su dakatar da mutumin da ya fice yanzu.... “Em Sir, muje ana nemanka a ciki...” security guda d’aya ya fad’i yana mai nunawa Yusuf d’in hanya alamun su koma cikin gidan... Yusuf ya d’anyi jim kana yace “Toh mai kuma ya faru...?” Security man d’in yace “I don’t know sir, I’m only following orders....” Jinjina kai Yusuf yai kana yasa kai yabi umarnin security d’in... Engr da k’arasowar sa kenan cikin wani irin huci yake furta “Where is Akram...!!!? Tell me where the hell is he..? I need to speak to him right this moment... So tell me where the hell is your friend..??!!” Cikin tsananin karaji yai maganar wanda gabaki d’aya mutanen dake wajen saida suka razana... Muhibbah ma dake gefe sai k’yafta idanu take kaman taci kud’in aika, kai kace bata San komai gameda al’amarin ba.. Yusuf ya shiga kai cikin razani “Rankashi dad’e... Wllhi bansan yanda Akram yake ba... Iyakacin gaskiyata na fad’i maka... Bansan ko kuma wajen Ummansa zamuji takaimu garin nasu ba... But I swear na rantse iyakacin gaskiyata na fad’a maka..” Jinjina kai Engr yai kana yace “Kaje gidan nasu ka sami mahaifiyarsa ka tambayeta gameda batun... Idan itama batasan komai ba ta sanar dakai inane k’auyen nasu... Ka fahimta...?” Jinjina kai Yusuf yai kana yace “Zanyi yanda kace your Excellency...” Jinjina kai Engr ya kumayi kana ya tako gaban Yusuf kad’an cikin murya mai cikeda gargad’i yake furta “Ina son amsoshi kafin rana ta fad’i... And one more thing... Don’t you dare think of betraying me kaman yanda abokinka yamin....” Yusuf ya d’an dubesa ganin yanda yake turiri alamun ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci kana yace “Sir believe me... Akram bazai tab’a cin amanarka ba... Whatever he’s done, I’m sure he has his own reason for doing that...” A zuciye Engr yace “I did not ask for your opinion... Kawai kai abinda na saka ka...” Jinjina masa kai yai kana yace “Yanda kace, Sir...” Daga haka sa kai Yusuf yai ya fice daga gidan cikin sauri... Yayinda Engr Ke tsaye kameda kunkuminsa cikin tsananin mamakin d’an adam... Securities kaw gabaki d’aya kowa ya sanne kai ya kama gabansa ganin Ogan nasu cikin wane irin yanayi da zasu iya cewa basu tab’a ganinsa ciki ba.... Muhibbah dake murmusawa cikin zuciyarta a fili kaw k’arasowa ga mijin nata tai had’ida d’an dafasa kad’an tace “Excellency na... Wai meke faruwa ne...? What’s going on... What’s all this, dan Allah ka sanar dani...” Baice da ita komai ba saima sa kai da yai ya nufi cikin gida, yanayin tafiyarsa kad’ai zaisa ka fahimci tsananin b’acin ran da yake ciki.... Muhibbah tabi bayansa da kallo kana ta tintsire da dariya tana mai furta “Akram kaid’in na daban ne... Ka cancanci duk wani kyauta daga gareni... Lallai ka iya buga game... Wasan tana buguwa yanda nake so...” Ta kuma tintsirewa da dariya kana tabi bayan mijinta tana fad’in “Excellency na please wait... Talk to me please....” A parlorn k’asa ta taddashi ya had’e hannayensa biyu ya d’aura hab’arsa bisa hannayen alamun yai nisa cikin tunani... A hankali ta isa ta zauna gefensa, dafasa kad’an tai tana mai tattaro natsuwarta waje guda “Excellency na... Dan Allah ka sanar dani mai Akram yai maka haka da taanani... Ban tab’a ganinka cikin irin wannan yanayi ba...” Fuzar da iska yai a hankali kana yace “It’s so painful ace mutumin da ka aminta dashi ya yaudareka...” Ta sauk’e gajeriyar ajiyan zuciya had’ida kamo yatsun hannunsa “This world is full of fake people Excellency na.... Mutane suna taking advantage d’inka kasancewarka mai tausayi da tausasawa, idan ka janyo mutum inuwa shi sai ya turaka rana... But I’m here for you Excellency na... Ko menene ke damunka nai maka alk’awari together we’d overcome it.... I promise you...” D’ago rinannun idanunsa yai yana dubanta kana yace “Ya sanar dani zai nema min aurenta, ya sanar dani zaimin yak’in... Only to get this in return.... I trusted him my whole life... He’s practically brother to me, daidai da dak’ik’a guda ban tab’a tsammanin haka daga gareshi ba....” Sauk’e ajiyan zuciya Muhibbah ya kumayi tana mai kuma janyo hannayensa alamun rarrashi “Excellency na... Kar kaga laifin Akram... What if ku biyu d’in Kun aukawa soyayyarta lokaci guda ne...?” Cikin sauri ya dubeta kana yace “Then he should’ve at least told me, ba wai ya k’yaleni kaman wani soko ba... A yanda nakejin Akram ni mai sadaukar masa da soyayyatace... But I was wrong about him...!” Cikin karaji yake maganar.... Muhibbah ta kuma gyara zama kana tace “What If Akram was been loyal to you... What if ita yarinyar ita ta tsara haka.. Maybe in the process na yana nemawa Uban gidansa aure kwatsam ita matar ta kamu da sonsa... Kasan mata akan abinda suke so, kawai ce masa zatai suyi aurensu don ita shi take so bakai ba...Maybe Akram yaso ya sanar da ita yin haka like cin amanane amma tak’i yarda ta yaudareshi da kalamai na soyayya har hakan ta kasance... Baka tunanin duk wannan na iya faruwa Excellency na...? Bawai kishi nake ba, no I’m telling you this because ni d’in kai nakeso kuma na damu dakai, bana kuma so na ganka cikin damuwa...” D’agowa yai yana dubanta lokaci guda kalamanta na Yawo a kwanyarsa... Ganin tarkonta kaman ya d’anu ya sanyata mik’ewa tana mai furta “Kai tinanin dik abinda na fad’a maka... Kaida Akram kun had’u da sharrin mace ne... Amma na tabbata Akram bazai tab’a aikata hakan a gareka ba, domin kaw da ace zai aikata hakan da tuntuni tsawon shekarun nan da yayi, amma koda wasa baka tab’a samunsa da shaidar cin amanarka ba... Wannan ba sharrin kowa bane illa ita matar....Bara naje na kawo maka something to calm you down....” Bai iya cewa komai ba har Muhibbah ya fice daga parlorn... Maiyasa yake ji a k’asan zuciyarsa Zulfa’u bazata tab’a yin abu makamancin abinda Muhibbah Ke fad’i ba... Maiyasa yake jin ya yarda da ita koda ace bai tab’a kasancewa da ita ba....? A hankali ya mik’e tsaye yana mai zarya a parlorn had’ida tinanin yanda zai shawo kan lamarin... Koda Yusuf ya dawo babu wani haske, da alama Umman Akram ita kanta batasan da tafiyar Akram ba, sannan a cewarta basuda wani k’auyen tik’is bayan garinsu Rano, kuma anyi waya Rano baije can ba....Ita kanta Umma abin ya soma damunta gashi gobe ake shirin auren Akram d’in... Engr yace ta kwantar da hankalinta In sha Allah zasu samu Akram za kuma suji dalilinsa na yin abinda yayi.... *** RANAR D’AURIN AURE, RANAR DA ZATA KASANCE MAFARIN FARIN CIKIN WASU HAKAN A B’ANGAREN WASU TA ZAMTO AKASIN FARIN CIKI,RANAR DA WASU SIRRIKA ZASU BUD’E KAWUNANSU DA KANSU... ABUJA. Sam Khalid baisan Daddy ya iso garin a daren jiya ba, sai a masallaci sallan asubahi suka had’u... Gaisawa sukai suka nufo gida tare, sam Khalid bai mamakin ganin Daddyn ba tinda gidansa ne zai iya zuwa ko k’arfe nawa ne....Suna tafe Daddy yace “Fitar sassafe zamuyi Khalid, nasan Auntyn taka bata sanar dakai ba koh...?” Mamaki ya kama Khalid “Daddy wani waje zamuje... Ko kaduna zamu koma...?” Murmusawa kad’an Daddy yai kana yace “Ina zuwa...” Jim kad’an ya shigo rik’eda wata jaka ya mik’a masa.... “Akwai kaya a ciki inaso idan kai wanka sai ka saka su...” Mamaki ya cika Khalid, ya kasa yarda da abinda yake gani na faruwa... Daddy bai kuma bi takansa yai ficewarsa, murmushi kwance saman fuskarsa.... Da tsananin mamaki Khalid Ke bud’e jakan... K’irjinsa ne yai wani irin yankewa ganin kayan dake cikin jakan, saida ya kwashe sakanni yana mai k’urama kayan idanu kafin ya soma cirosu... Shadda ce ‘yar Ubansu, babbar Getznar sai yauk’i da shek’i take, fara k’al mai d’aukan idanu... Saida ya ida cirowa kana ya shiga warwarewa, Babbar riga ce sai ‘yar ciki da wando.. Kallo guda zakaiwa kayan kasan duk mad’inkin da ya d’inka kayan ya k’ware wajen iya d’inka kayan hausawa ta zamani.... Khalid ya fuzar da iska kad’an yana mai kuma juya kayan... Tabbas hasashena ya tabbata Daddy aure zai masa da Yesmin... Toh mai yasa zasu b’oye masa irin haka, shin suna tinanin bazai masu biyayya bane... Abubuwan da suka faru a ‘yan kwanakin suka shiga dawo masa daki daki... Wannan shine manufan Daddy na canza masa lokaci guda... Why Maiyasa Daddy zai masa haka...? Wata zuciya tace ka bishi a haka don tabbatar da abinda zuciyarka Ke raya maka... Zato kawai kake har yanzu tinda bai bud’i baki ya sanar dakai komai ba... Koda yayi wanka umarnin mahaifinsa yai ya shirya cikin wannan manyan kaya na alfarma... Tsaye yai yana kallon kansa cikin full-length mirror, shi kansa wani girma yaga yayi ma kansa had’ida wani k’warjini na musamman, dan har saida ya tsinci kansa da matsananciyar fad’uwan gaba, yanaji ajikinsa yau d’in ranace ta musamman a garesa dikda zuciyarsa dake ayyana masa cewa idan har aurensa da Yesmin ake shirinyi, toh yau d’in zata iya kasancewa rana mafi tashin hankali a rayuwarsa... Ya lumshe dogayen idanunsa a hankali daidai sanda Aunty Daula ta soma knocking k’ofar d’akinsa... Bata izinin shigowa yai yana mai d’an takowa daga cikin closet d’in... Aunty Daula ta shigo sallama saman bakinta tana fad’in ya fito su karya su d’au hanya... Daskarewa tai tana dubansa yanda ya fito sak ango... Aunty Daula ta gaza b’oye Farin cikinta tana fad’in “Masha Allah Yayansu... Ka fito ras dakai...” Murmusawa yai kad’an kana yace “Aunty wai meke faruwa ne... Dan Allah ki sanar dani...” Ta kuma murmusawa a hankali kana tace “Ba’aji mutuwar sarki a bakina ba... Amma before anything, we’re all waiting for you downstairs, Daddy yace baiso mu makara... Muna jiranka...” Bata jira cewansa ba ta fice cikin sauri tana kuma murmusawa... A hankali ya fuzar da iska mai d’umi kana yasa kai ya nufo k’asa....Su Humy har suna had’e baki wajen cewa “Woow kayi kyau Yaya...” Ijlal tace “Kaima yau ka zama Daddy ne, ka saka irin kayanshi...” Gaba d’aya suka d’an dara.. Humaira ta kuma cewa “I’ve never seen wanda babban kaya ya mishi kayu irinka ba Yaya.. Pls ka dinga sakawa kaji...” Murmushi kurum yai had’ida shafa kanta, idanunsa naga mahaifinsa da ya kasa janye nashi idanun daga Barin duban Khalid d’in, ga wani musulmin murmushin Farin ciki saman fuskarsa... Shi kanshi d’an nashi ya masa kyau har ya gaji, ga wani girma da k’warjini na musamman da suka sauk’ar masa... Aunty Daula tana satan kallon d’ah da mahaifin yanda suka zubawa juna idanu gwanin ban sha’awa da tausai... Cikin sauri ta shiga serving Khalid d’in tana tambayar shi idan akwai wani abinda yake so... Shidai Khalid gaba d’aya bai wani iya cin abincin ba, ya k’agu baiji shirin Daddy akansa ba... Aunty Daula ta dubi su Ijlaal da suka ida cin abinci tace maza suje Karima ta ida shiryasu, idan zasuyi fitsari ma duk suyi kafin su d’auki hanya.. Itama dai mik’ewa tai dan ta lura d’ah da mahaifin suna buk’atan kad’aicewa suyi magana... Dining area ya rage saura su biyu, Khalid sai juya spoon yake cikin mug, da ganinsa kasan hankalinsa bai jikinsa... Kaman daga sama saijin hannun Daddy yai saman nashi... Ya d’ago a hankali yana duban mahaifin nasa A hankali Daddy yasa duka hannayensa ya kamo kafad’un Khalid ya mik’ar dashi tsaye suna fuskantar juna.... Murmushi saman fuskar Daddy, kana iya hango kwantattun k’walla cikin idanunsa lokaci guda yake furta “You look very handsome my son.... Kai d’in a yau zaka kuma cika babban mutum, idan ban tab’a fad’a maka ba Khalid toh yau zan fad’a maka... I am very proud of you Son, kai d’in ka cika d’a mai biyayya... Na gwadaka ta hanyoyi daban daban kuma duk kaci jarabawarka.... Ko yanzu na bar duniya nayi imani kaidin zaka iya kulamin da ahalina... Allah Ubangiji ya maka Albarka, ya albarkaceka da zuri’a d’ayyiba masujin k’an iyayensu da yi masu biyayya kaman yanda kai mana....Ina kuma fata zakai Farin ciki da zab’in da nai maka da kuma hukuncin da na yanke a gareka...” Izuwa lokacin zuciyar Khalid tai rauni sosai.... Cikin sauri ya kamo hannayen Daddy, cikin k’ok’arin dakewar murya dukda rauni da yakeji daga can k’asar zuciyarsa ya soma fad’in “Daddy dik abinda ka yanke akaina kayi daidai... Kuma bazan tab’a questioning d’inka ba... And zaka sameni ina mai yi maka biyayya.. I know you love me and bazaka zab’a min abinda zai cutar dani ba....Na sani our family isn’t perfect, we have our differences, if there’s one thing da mutum bazai zab’a ba shine family d’inshi... We don’t choose our family... Haka Allah yake gudanar da al’amarinsa... Saidai mu wayi gari mu ganmu tareda mutanen da yaso ya ganmu dasu ya kuma zab’a mana a matsayin family d’inmu... Daddy inaji a cikin zuciyata cewa nid’in mai sa’a ne da Allah yasa na kasance d’anka.... Thank you for everything Daddy....” Hawayen da Daddy Ke mak’alewa suka ziraro, lokaci guda ya rungume d’ansa sosai cikin jikinsa yana jin k’aunarsa na ratsa zuciyarsa... Aunty Daula dake hangosu daga kitchen share hawayen da suka gangaro mata, tausayin d’ah da mahaifin ya cika zuciyarta.... Murmushi Daddy ya sakar mashi yana mai gyara masa zaman hularsa kana ya warware agogon dake d’aure hannunsa ya shiga d’aurawa Khalid d’in da kanshi... Murmushi kwance saman fuskarsa, shima Khalid d’in murmushi yake... Daddy yaci gaba da fad’in “There... Now you look even more handsome...” Khalid ya kuma sakin murmushi kana yace “Na gode Daddy...” Shafa fuskarsa Daddy yai kana yace “Khalid a yau zamu tafi amsar aurenka da macen da Allah ya zab’a maka a matsayin abokiyar zama... Are you happy...?” K’ak’aro murmushi yai dikda tsananin bugu da k’irjinsa keyi kana yace “Yes... Yes Daddy... I’m very much happy...” Kana ganin yanda yai maganar zaka fahimci k’arfin hali ce kawai... “Well, sai mu d’au hanya kar mu makara...” Ya k’arashe yana mai kiran matarsa Daula... *** Kai da Kaga Hafiz Kaga ango, sai watsa k’amshi yake yasha wanka cikin dakakkiyar shaddarsa, bakinsa kaw ya gaza rufuwa tamkar gonar auduga, Sawwama dai bata tankasa ba har ya ida shirinsa, koda yace mata babu fatan Alheri sai ce masa tai fatan alherin kenan ta gama masa da ta had’asa dasu Babba Duna.... Ya isa yai kissing goshinta yana murmusawa kana yace “Tabbas kin bani gudumawar da tafi ta kowa....Bazan tab’a mantawa ba, nai miki alk’awari...” Murmusawa tai kana ta mik’e ta d’au mayafinta dake lank’aye saman k’ofa... “Rakiya zakimin...?” Ya tambaya yana dubanta... Murmusawa tai kad’an kana tace “A’a kaje bikinka...” Hafiz ya d’anyi rau rau da idanu cikeda shagwab’a kana yace “Bazaki raka mijin naki tarbo k’anwarki ba... Kinsan fah kece Yayar....” Nanma murmusawa tai kana tace “Zanso nai maka rakiya amma nima wani auren zan tafi... Mahaifiyata da mijina zasuyi aure rana guda...” Da mamaki Hafiz ke dubanta kana yace “Kina nufin Magajiya yau take aure...?” Jinjina masa kai tai kana tace “K’warai kuwa, Kaga dole na tafi can na k’yaleka da amaryar ka kusha shagali nima na taya nawa mahaifiyar nata shagalin....” Ya murmusa ya shafi fuskarta kana yace “Kice ina mata fatan alheri, kuma nayi murna sosai... Daga baya zanzo har gida nai mata murna...” Sawwama ta jinjina kai tace “Zan isarda sak’onka in sha Allah...” Daga haka sakai tai abinta ta fice, tabar Hafiz shi kad’ai sai shafan hab’a yake yana sakin murmushi..... *** Cikin dabara ya samu ya tsinka igiyar da tin jiya yake k’ok’arin b’allata da akai amfani da ita wajen d’aure masa hannu...Hannayensa gaba d’aya sunkuwa b’aci da jini alamun yaji jiki wajen kwancen hannun... Ya waiga yaga har yanzu dai masu tsaron nasa bacci suke basu farka ba dan jiyan tatil sukai da barasa, tinani ya somayi, mai zaiyi yanzu, idan yace zai gudu a wannan daji da baisan yaya aka shigo dashi ba baisan ta ina zai soma bi ba, baisan wata hanya zai soma bi ba tinda kanshi cikin buhu aka shigo dashi... Ya dafe kansa kad’an yana tinanin abinyi, kuma dole yai acting very fast kafin su tashi, aljuhun d’aya daga cikinsu data d’an zame ya hango wayar salula... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ya lab’ab’a ya d’auki wayar da k’yar da sand’a.... Dubawa yai yaga chaji ya kusa k’arewa one percent ne... Dole yai dik yanda zai yayi making call d’in cikin sauri.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *87* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kasancewar k’aramar wayace yasa Akram baisha wahala wajen bud’eta ba, sauri yake ya shigar da lambobin dan sai warning battery d’in yake masa yana nuna alamun low battery.... Wani ikon Allah lambar da ko nashi lambar waya bai haddace kamanshi ba sai yaji yana k’ok’arin kufce masa tsaban tashin hankali da ya tsinci kansa ciki... Ga wayar gab take da d’aukewa gaba d’ai danma Allah yasa Nokia akwai amanan rik’e chaji ne.... A hankali ya soma k’ok’arin saita kansa yana jera lambobin a natse.... **** Tsaf ya ida shirinsa cikin manyan kaya dan tuni Daddy ya sanar dashi cewa yau ake d’aurin auren Khalid, sam bai kawo gidan da Khalid Ke neman aure gidansu Zulfa’u bane, all he knows shine Akram ya yaudaresa zai kumayi k’ok’ari ya mance da komai, dan haka ya yanke tafiya auren Khalid maimakon amsawa Akram aure kaman yanda Akram d’in ya buk’ata ta bakin abokinsa Yusuf.... Muhibbah dake zaune gefe tana dubansa tamkar ta zuba ruwa a k’asa tasha dan Farin ciki, a hankali ta taso daga yanda take zaune ta iso garesa, links d’in da yake mak’alawa hannun rigarsa ta amsa taci gaba da saka masa, har lokacin tana iya karanto tashin hankali kwance cikin fuskarsa tasan kawai daurewa yake matsayinsa na jajirtacce mai shirin zama shugaba ga d’unbin al’umma... “Excellency na yanzu auren Khalid dai zaka tafi kenan....?” Tamkar bazai amsata ba haka yai, saida ya kwashe wasu sakanni kana yace ta mik’a masa turare... Babu musu ta isa gaban dressing mirror ta d’auko turaren, zai amsa ta girgiza masa kai alamun a’a kana ta shiga fesa masa... K’uri kurum yai mata ba tareda ya tankata ba har ta ida abinda take.... Murmushi saman fuskarta tace “Wow yau d’in kayi kyau na musamman mijina karfa kaje kafi ango yin kyau... Ka ganka kuwa...?” Yanda tai maganar sai taso basa dariya, yasan k’ok’ari kawai take to cheer him up... Gefen fuskarta ya d’an shafa kana yace “Toh ni na wuce... Jalo will drive me....” Muhibbah ta kuma murmusawa kana tace “Toh a dawo lafiya Excellency na... I love you...” Bai tsaya amsata ba yasa kai ya fice... Aiko yana ficewa tai tsallan murna ta fad’a kan gado tana juyi, Allah mai iko wato dai cikin sauk’i labarin auren mijinta ya shirirnce, lallai ita d’in mace ce mai sa’a... Wayarta dake gefe ta janyo ta shiga neman layin k’awayenta su Shamzy dan yau dole suyi party na murnan nasarar wargaza al’amarin auren mijinta, yau dole ta had’iyi strong k’wayoyi da zasu kaita can sararin samaniya.... Koda Akram ya gama jera lambobin sai akai rashin sa’a babu network a wajen, gashi yana hango d’ayan ya soma motsawa alamun ya kusan tashi, k’irjin Akram ya kuma bugawa, a hankali ya soma lab’ab’awa ya isa jikin wani dutse da yake hangowa.... Cikin sand’a ya samu ya haura saman dutsen,ya shiga k’ok’arin neman service, sai faman jefa wayar sama yake , da k’yar ya samu ya kamo service..... Bugu d’aya a na biyu wayar ta soma ruri.... Engr dake zaune owners corner cikin hamshak’iyar Ford d’insa nan yaga kira na shigo masa da bak’uwar lamba, wayar da yasan mutane k’alilan ke da lambar... Mamaki ya cikasa, ya k’urama wayar idanu har ta kusan tsinkewa kana ya d’aga.... Daga d’aya b’angaren cikin tsananin tashin hankali Akram yake fad’in “Sir... Sir it’s me Akram...You need to hear me out...” Gaban Engr ya yanke ya fad’i, cikeda karaji ya dakatar dashi da fad’in “You’ve got some nerve... How dare you Akram.... Bayan dik abinda na gani you still have something to say... After making me look like a complete imbecile, after making the fool out of me... After betraying my trust har kanada guts d’in da zaka kirani... Har kana....” Katse sa Akram dake waige waige yai da sauri yana furta “Sir you have to believe me... Duka wannan makai nakeyi... Sir you need to read that letter nasan baka karanta ba, amma idan ka karanta you’ll understand me... I wrote everything there... Every single thing... Sir please read that note we’re running out of time...” Girgiza kai Engr yake cikeda rud’ani yana fad’in “What letter Akram.... Wani letter kake magana....?” Suna maganan network na seizing... Akram yaci gaba da fad’in “Sir kar ka tab’a mance wannan... Ni d’in zan iya baka rayuwata....Never doubt that.....”D’if wayar ta katse... Engr yaci gaba da fad’in “Hello..! Hello Akram... Can you hear me... Hello Akram are you there...?” Shiru ba’a babu amsa... Cikin sauri Engr ya kuma dialing layin... Saidai ji yai bata shiga.... Kalaman Akram sun d’aure masa kai, wane letter kenan Akram ke magana... Take ya tina katin Bikin Akram cikin envelope Yusuf ya kawo masa, he need to go back and check that envelope.... D’an duban Jalo yai kana yace “Jalo juya kan motar... Mu koma gida....” Cikeda risinawa Jalo yace “Ok Sir....” lokaci guda yabi umarnin ubangidan nasa... A can daji kuwa sauk’ar k’asar bindiga Akram yaji a k’eyarsa saida wayar ta fad’i ta tarwatse... D’an ta’addan yasa hannunsa duka biyu ya d’ago Akram ya shiga kilansa kaman an aikosa lokaci guda ya shiga janyosa a k’asa yana doka kirama sauran ‘yanuwan nasa yana sanar dasu Akram tried to escape...Aiko gaba d’aya suka tashi a firgice suka nufosu nan suka had’u suka shiga dukan Akram ta ko ina jini na bin jikinsa gwanin ban tausayi.... *** Kan kace mai ‘yan d’aurin aure sun soma hallara, gidan Abbah ya soma cika da bak’i ‘yan d’aurin aure... Abbah sai sab’a babbar riga yake yana tarban mutane, gaba d’aya k’ofofin babban parlornsa aka hangame... Dik wannan d’awainiya na amsan bak’i da yake bai saka d’an uwansa Baba Alhaji a idanunsa ba saiko sauran k’annensa su Baffah Wada da Baffah Ado saiko Hafiz da bai sama bai k’asa bakinsa ya gaza rufuwa, jinsa yake ko aurensa na fari baiyi Farin cikin da yake ciki a yau ba... Sai wannan nan nan da Abbah yake, su Baffah Wada har mamaki suke irin kwalliyar da Hafiz ya chab’a Magaji abokinsa ma abin mamaki yaketa basa, gashi karaf abokansa ya gayyata, koda Mukhtari ya tanbayesa baya kishi Zulfah wani zata aura sai ce masu yai su tsaya suyi kallon show yanda auren Zulfah zai tashi daga kan munafukin d’an siyasan nan ya dawo kansa... Su Mukhtari dasu Magaji dai kallon ikon Allah kurum suke suna mamakin anya abokinsu bai sami tab’in hankali ba, ta ya za’ace ranar aure an sauya shek’a an dawo kansa... Hafiz yace sudai suyi kallo kawai.... Huzaifah yace “Munaji muna gani muna kuma saurare angon Zulfa’u....” Gaba d’aya abokan suka sa dariya idan ka d’auke Magaji da zuciyarsa ta kasa natsuwa... Anya ba wani mugun abin Hafiz ya k’ulla ba dan yasan yanda ya d’auki Akram da muguwar gaba....Fatansa dai Allah sa ba abinda yake tinani bane.... *** A can gidan Baba Alhaji kaw tuni Hajiya tasa an k’ure mata kid’a dan cewa tai a banbance gidan biki da gidan makoki, harta kwalliyar nan irinta zamani saida Hajiya tasa aka tsara mata itama, ga wata uwar gwaggwaro da aka d’aura mata dan cewa tai yau d’in na musamman ne, gidan shak’e yake da k’awayenta ana tayata murna yanda kasan itace amaryar.... K’awayen Sahariyya kaw su Fa’iza sai dad’a d’aura Hajiya suke keken aljanu suna haukatata suna fad’in irin kyaun da tai.... Najah ta kuma kai dubantaga mahaifiyarta yanda take tik’an rawa tsakar gidan, a hankali ta lumshe idanunta had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya... Saida takai k’ofar gidan kafin ta kuma huyowa ta dubi Hajiya, cikin zuciyarta take furta “I’m sorry Hajiya... Ki yafeni....” Daga haka sa kai tai ta fice a gidan.... Sanda ta isa sashen Mamani ta tadda ‘yanmatan gidan sai gugan ankonsu suke tare a parlorn Mamani, su Raihanah su Marliya dasu Sadiya... Sai kacaniya ake baka ma d’aukan zancen kowa sabida yanda hayaniyarsu ya cika wajen.... Najah ta k’arasa tana tambayar Raihanah Mamani... Raihanah tace “Inaga suna can wajen kitchen itadasu Umman Kazaure kije dai ki duba....” Ta kuma duban Sadiya tace “Sadiya dan Allah ga rigata a goge min...” Sadiya ta d’an jefa mata hararan wasa tace “A nawa....?” Karaf Marliya tace “Chab aiko Ya Ma’aruf ne zai biyaki kinsan patient d’insa ce ya hanata aiki....” Gaba d’aya suka sa dariya Karima na fad’in “Chapd’i aiko ku rufa mata asiri kafin Addah Sahariyya uwar kishi tajiku... Marliya ta tab’e baki tace “Yo ba sai taji d’in ba wake tsoronta ince dukanmu nan Yayanmu ne, sai mai dan ya nuna kukawarsa akan Raihanah...” Ita dai Raihanah batace komai ba sai girgiza kai da tai ta janyo hannun Najah tana fad’in “Muje na tayaki neman Mamani....” A can hanyar k’ofar da zai sadaka da sashen Abbah suka hango Abban tareda Mamani da alama muhimmiyar magana suke tattaunawa... Daga yanda suke k’arasowa suka soma jiyo muryar Abban na fad’in “Wllhi Mamani bansan yanda Yaya ya tsaya ba, abin nima ya bani mamaki ace auren yaranmu nawa har uku ga nashi guda amma ko k’yallinsa babu... Toh ina yaje a irin wannan rana mai matuk’ar mahimmanci....?” Mamani tace “Alk’ali kasan halin d’an uwan naka, yanzu haka wani sabgan ya shiga amma ina mai tabbatar maka zuwa jimawa zaka gansa....” Abbah yace “Toh Allah yasa...” Juyowar da zai ya tarar Naja’atu da Raihanah na gaidashi cikeda risinawa... Abbah ya amsa masu da sakin fuska, suka gaida Mamani ma.... Ganin dai suna tsaye kaman da magana a bakinsu yasa Abbah cewa “Ya dai yarana akwai wani abin ne...?” D’an duban Raihanah Naja’atu tai ga k’irjinta dake bugu kana tace “Abbah dama Mamani nake nema...” Abbah yace “Toh toh kuce Kakar taku kukazo gaidawa ashe ba Abbah ba...” Gaba d’aya suka d’an saka dariya kana Raihanah tace da Najah bara taje taji halinda gugan kayanta Ke ciki.... Mamani ta dubi Naja’atu tace “Yaya dai ke ‘yar gidan Haule... Inji lafiya...?” “Lafiya Mamani magana dama nake so na maku...” Abbah da tuni ya sab’a babbar riga zai shige Naja’atu tai karaf tace “Abbah maganar harda kai...” Abbah ya juyo cikeda mamaki, itama kanta Mamani mamakin ne ya cikata... Abbah yace “Toooh, amma lafiya kuwa Naja’atu koh...?” Naja’atu tace “Abbah akan b’acewar Ya Ma’aruf ne... Abbah nasan su waye suka b’atar dashi, kuma har yanzu ma sunada wata shiri...”” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Kalaman da Mamani da Abbah suke iya nanatawa kenan kurum..... Mamani ta had’iyi wani miyau da ya tokare mata mak’oshi da k’yar.... Ganin Mamani na k’ok’arin zubewa yasa Abbah saurin rik’ota Naja’atu na taimaka masa... Duban Naja’atu yai kana yace “Taimaka min mu k’arasa da ita can yanda babu mutane sai ki sanar dani komai...” Naja’atu ta jinjina masa kai sukai yanda Abban yace, can gefe bayan sashen Mamani yanda babu kowa sai tabarmai yanda ‘yanmatan gidan sukai zaman yin k’unshi, nan suka samu suka kwantar da Mamani a wajen Naja’atu nai mata fifita suna binta da sannu itada Abbah... Duban Mamani Abbah yanda take numfasawa da k’yar kana yace “Mamani zaifi kyau idan bakiji wannan labari ba, ki bari ni naji komai, hakan bazai kyau ma lafiyarki ba...” Girgiza kai Mamani tai kana tace “Alk’ali zanji komai... Inaso naji komai, inaso naji wasu azzalumai ne suka jefamu cikin wannan uk’uba da k’unci tsawon rayuwarmu... Inaso naji komai Alk’ali...” A hankali Abbah ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya jinjina kai... Duban Naja’atu dake duk’e wajen tana kallon Mmani cikeda tausayawa Abbah yai kana yace “D’iyata muna saurarenki... Sanar damu mai kika sani... Daga ina kikaji kuma waye ya sanar dake....?” Naja’atu tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka siraro mata, lokaci guda ta gyara zamanta kana ta shiga karanto iyaka abinda taji d’aga Hajiya Haule da mahaifinta Baba Alhaji da kuma Aunty Lami, ta kuma sanar dasu shirya aurama Sameer Sahariyya dasu Hajiya da Baba Alhaji sukai don su cimma burinsu na kawar da Ma’aruf a karo na biyu... Tinda ta soma magana hawaye ke zarya a fuskokinsu gaba d’aya... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Wannan wane irin al’amari ne, idan ance Haule da Lami zasuyi haka bazaiji mamaki ba sabida kishi...Amma Baba Alhaji fah... Ta yaya d’an uwansa zai masa haka...? D’an uwansa na jini... Yana ganin yanda suka rayu shekara da shekaru cikin k’unci da alhini na rashin d’ansu.... Shin wace irin rayuwa duniyar yau ta tsinci kanta ciki... Ace d’an uwanka na jini zai aikata maka mugun aiki irin wannan... Kaicon rayuwa mai cikeda mugunta da k’iyayya had’ida muguwar hassada da k’yashi.... Mamani dafe k’irjinta dake tsananin mata zafi kurum tai tana mai girgiza kai idanu a lumshe ga hawaye dake gangaro mata, lokaci guda take furta “Sun cutar damu... Sun zalunci baiwar Allah Mariya...Sun rabata da gudan jininta tsawon shekaru... Sunsa mun d’auki laifi gaba d’aya mun aza mata tsawon shekarun nan... Mariya ki yafeni... Ki yafe min baiwar Allah.....!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Naja’atu ma kuka take tana furta “Mamani Abbah ku yafeni... Tin kwanki naso sanar daku amma na kasa, banida k’arfin Zuciyar yin hakan har sai lokacinda nake tinanin lokaci ya k’ure... Ku yafeni su d’in iyayena ne...” Saurin rungumota Mamani tai kana tace “Baki makara ba Naja’atu... Wannan sadaukarwa da kikai Kika zab’i ki sanar damu gaskiya dikda sanin cewa sud’in iyayenki ne, Ubangiji Allah ya saka miki da gidan Aljannah, ya baki rayuwa mai inganci a gidan duniya... Kuma yanzu da mukaji gaskiya jikana bazai had’a iri da Haule ba... Tashi kije abinki Allah ya miki albarka... Kinyi abinda ya dace...” Jiki a sanyaye Naja’atu ta mik’e ta fice... Mamani ta dubi Abbah tace “Ma’aruf bazai auri d’iyar Haule ba kaji na fad’i maka....” Abbah ya jinjina kai ba tareda ya iya koda duban mahaifiyar tasa ba... lokaci guda ya soma k’ok’arin Mik’ewa yana fad’in”Zanje na bada auren Nabilah da Zulfa’u, shi kuma Ma’aruf an fasa nasa auren....” Dakatar dashi Mamani tai da fad’in “Babu aure guda da za’a fasa...” Abbah ya dubeta da tsananin mamaki... Jinjina masa kai tai tace “Ince dama sabida ni ya amince da auren d’iyar wajen Haule...? Toh na tabbata dik wanda zan canza masa da ita baza’a sami matsala daga garesa ba... Kuma ina fatan hakan ya zame masa Alheri ya kuma izna da ishara gasu Haule....” Jinjina mata kai Abbah yai kana yace “Dik yanda kikace Mamani...” *** A yayinda ya rage saura mintoci a soma d’aurin aure su Khalid suka samu isowa, har yanzu ya kasa daina jinjina lamarin cikin zuciyarsa yana ganin abin tamkar mafarki... Ta ina layinsu Teddy Bear zai b’ace masa dikda cincirindon mutanen da yake hangowa tin daga bakin layin nasu... Ya dubi Daddy dake zauna gefensa Jafaru driver d’insa na jansu yayinda motar su Aunty Daula da yara Ke biyedasu... So yake ya tambayin Daddyn amma ya kasa saima sakin wani irin ajiyan zuciya da yakeyi... Like shin mafarki yake ko gaskiya, idan har mafarki ne baya fata a katse masa wannan mafarki nasa har sai yaga abinda ya kwancewa buzu nad’i... Shin dama aurensa da Nabilah Daddy Ke shiryawa all this while... Waidai da gaske ne abinda yake ganin na shirin faruwa...? Bai gama shan mamaki ba saida yaga su Baffah da wasu tsiraru cikin abokansu sun k’araso sunaima Daddy sannu da isowa... Khalid kaw aikama Baffah wata muguwar kallo yai wanda yake nufida ka jira had’uwarmu.... Baffah dai k’unshe dariyarsa yake yana kuma yima Daddy sannu da sauk’a, Khalid sai b’alla masa harara kurum yake yayinda sauran friends d’insu su Misbahu D’anisa suka k’araso suna zolayan ango... Ga wani annuri na musamman dake haska fuskar Khalid d’in.... A b’angaren Aunty Daula kaw tinda suka iso wannan gari gabanta ya tsananta fad’uwa, gaba d’aya wani iri takejin kanta ta rasa maike mata dad’i, a yayinda su Daddy suka shige babban parlorn Abbah Aamiru d’an wajen Baffah Wada yaimasu Aunty Daula jagoranci zuwa sashen Mamy, k’irjin Aunty Daula ya tsananta fad’uwa... Haka sukaita gaida mutane ‘yan biki hardai suka k’arasa cikin parlorn, yanda wasu Gwaggwanyen su Zulfa’u na can Kazaure suka tarbi su Aunty Daulan da Mamy basuma ganta ba abinka da hidiman biki... *** A can parlorn Abbah kaw auren Nabilah da Khalid aka soma d’aurawa, sanda kunnuwan Khalid ya jiyo masa ana d’aura aurensa da Nabilah a hankali ya lumshe idanunsa, can k’asan zuciyarsa na samun wani natsuwa da bai tab’a samun irinta ba, siririyar hawaye ta gangaro daga idanunsa guda... Daddy dake dubansa taisayin Khalid d’in ya kamasa tabbas d’an nasa yasha gwagwarmayar soyayya... Allahu Akbar wannan shine INDA RAI tabbas DA RABO... Yau d’in Allah ya cika ma d’ansa wani babban buri cikin burikansa... Fatansa Allah ya albarkaci sabuwar rayuwar da d’an nasa ya tsinci kansa ciki a yau d’in.... Wani ikon Allah shine har wannan lokaci babu labarin zuwan masu auren Zulfa’u, abin har ya soma damun Abbah, ya waiga nan ya waiga can, ya dubi Baffah Wada su d’anyi magana k’asa sannan ya dubi Baffah Ado ma, su kansu duk abin ya damesu... Hafiz ya k’araso had’ida ciro sadakinsa cikin aljihun babbar riga yana fad’in “Abbah na fad’a maka dama wannan d’an siyasan wllhi babban mak’aryaci ne yaudarar Zulfa’u kurum yai Abbah... Abbah ni ne mijin Zulfa’u, ni d’an uwanta ne Abbah... Abbah wllhi muna k’aunar junanmu ka taimaka ka maida aurenmu... Abbah kar mu bari mahassada su mana dariya...” Mamaki ya cika illahirin mutanen dake wajen... Kallo ya koma kan Hafiz da Abbah, wani irin al’amari ne tamkar film suke gani na faruwa.... Tamkar gunki haka Abbah ya zubawa Hafiz idanu... Hafiz yaci gaba da sab’a babbar riga yanayin kalan tausayi dan jama’an wajen su tausaya masa... “Abbah Zulfa’u matata ce... K’addara ta rabamu kuma yanzu ma k’addara zata maida aurenmu... Abbah please ka duba lamarin nan ko dan ‘yanuwantakanmu kar ka bari bare suji kanmu.... Abbah ka dubi girman Allah kaji tausayinmu ka maida aurenmu... Wad’annnan mutane ba zuwa zasuyi ba...” Baffah Wada da takaici ya ishesa nan ya katse Hafiz da fad’in “Kai Hafiz bamu son shashanci kanaji koh... Ya ranar auren yarinya zakazo da wani batu wanda hankali bazai kama ba... Mu k’ara masu lokaci Suna nan tafe na tabbata...” Hafiz ya kuma sab’a babbar riga tamkar zararre ya isa gaban Baffah Wada yana fad’in “Baffah wllhi manemin auren Zulfa’u gawurtaccen mak’aryaci ne nai maka imani idan zamu kwana a nan bazai bayana ba, domin kaw aikinsa kenan Yaudara....” Baffah Wada ya girgiza kai yace “Bama san hauka Hafiz ka tashi ka daina wannan rashin hankalin Naka...!” Cikin tsananin huci Hafiz Ke duban Baffan nasa yana fad’in “Baffah dana kune ‘yan bak’in ciki kar matata ta dawo gareni...Toh Allah ya nuna min kuma kana gani za’a maida aurenmu... Idan ba mayaudari bane toh ina yake maiyasa bai bayyana ba, maiyasa bamuga masu amsar masa auren ba...Ina suke idan da gaske ne...?!!!” Kaman daga sama suka jiyo wata murya mai cikeda k’warjini tana fad’in “Gamunan mun iso....!!” Ba Hafiz da tuni ya daskare ba harta su Abbah da tsananin mamaki suka juyo suna duban bakin k’ofa.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _.................DA RABO_ *88* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Mamaki ya cika Daddy ganin Engr na kutso kai cikin parlorn, mutane kaw sai faman bud’a masa suke, Jalo na biye dashi har suka isa mazaunin su Abbah suka zauna suna masu yi masu masabaha.... Mutane kaw sai k’asa k’asa da murya suke suna ambato sunan Engr suna fad’in shid’in ne dai da gaske, abinka da sanannen d’an siyasa....Marok’a kaw tuni suka soma wasa shi suna fad’in Alkhairansa.... Mamaki ya cika Abbah dikda cewa shi d’in ba ma’aboci siyasa bane yasan Engr Ma’aruf Mutallab matsayinsa na d’an takaran gwamanan jiha da yai fice, kuma ko shakka baiyi sanda Mahaifin Khalid yazo nemawa Khalid d’in auren Nabilah tare sukazo da shi Engr d’in... Toh amma abinda bai gane ba... Shin dama Engr Mutallab yanada alak’a da mai neman auren Zulfa’u ne...? Wannan tambaya shi yaketa yawo a kwanyar Abbah, gaba d’ai ya gaza fahimtar meke faruwa har saida ya sinkayo muryar Baffah Wada yana tambayar Engr “Rankashi dad’e shin kune masu amsar auren Zulfa’u....?” Murya a dake Engr yace “K’warai mune....” Baffah Ado yace “Toh ai sai aci gaba da gudanar da d’aurin aure....” Hafiz da jikinsa Ke tsananin karkarwa had’ida tsuma cikin sauri ya katsesu da fad’in “Ta ya za’a aura mata mutumin da ya b’oye kanshi ya kasa bayyana kanshi... Baffah kar azo ai auren da za’azo ana danasani a baya....” A zuciye Baffah Ado ya mik’e yana nuna Hafiz da d’an yatsa yake fad’in “Kai Hafizu wllhi billahilAzim idan baka shiga taitayinka a wajen nan ba zan maka rungumar buhun dawa na fiddaka da k’arfin gaske, ka shiga hankalinka tin wuri ka daina maida mutane k’anan mutanen... Cikinmu babu sa’anka....” Hafiz yaci gaba da huci yana rarraba idanu ga gumi dake keto masa..... Baffah Wada ya dubi Engr yace “Kuyi hak’uri d’an yau ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba, Malam Imam muci gaba da abinda ya taramu.... Imam ya jinjina kai, yana mai kuma tambayar Baffah Wada wanda shine Alwalin Zulfa’u... Yana k’ok’arin tambayar Engr kenan sukaji wata murya tana fad’in “Ku dakata...!” Gabaki d’aya juyowa sukai suna dubanta, mahaifiyar Akram ce sai Yusuf da Kawunan Akram guda biyu da sukazo suka tambaya masa auren Zulfah.... Mamaki ya kuma cika mutanen parlorn, wannan wane irin al’amari ne.... Aka bada hanya ma Umma da tawagarta suka shige.... Baffah Wada yace kece wace...?” Umma tace “Ni ce Mahaifiyar Akram... Wad’annan da kake gani k’annena ne kuma su sukazo suka tambayawa Akram auren Zulfa’u...” Kawu Jafaru yace “Tabbas mu mukazo muka tambaya mashi auren Zulfa’u... Amma kwana biyu da suka shige yazo ya sameni ya sanardani yana so ranar aurensa sadakin da ya bayar da sunan aurensa da Zulfa’u ya juya ya zama sadakin Ubangidansa yana so auren ya tashi daga kanshi ya koma kan Ubangidansa Engr Ma’aruf Mutallab... Koda na tmbayeshi dalili sai cemin yai na mishi wannan alfarmar mai yuwa zai iya tafiya wani waje mai nisa a wannan ranar dan bazai iya fuskantar Ubangidan nashi ba....” Umma ta k’arada “A kwanakin nan d’ah na Akram ya sauya k’warai, babu yanda banyi ba ya sanar dani abinda ke faruwa musamman tsakaninsa da Gwamnan gobe.... Sai bayan da muka nemeshi muka rasa Yusuf abokinsa ya sanar damu komai, ya sanar damu cewa Gwamnan mai jiran gado shine asalin manemin wannan yarinya Zulfa’u, kuma tabbas ya wakilta d’ah na Akram yai masa jagoranci ne... Ina mai rok’onku da ku baiwa wannan bawan Allah auren d’iyarku shid’in mutumin kirki ne....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye suna gangro mata.... Girgiza kai Engr yai kana yace “Ummah ki barni na karb’awa Akram aurenta ni mai iya sadaukar masa da komai ne....” Girgiza kai Ummah take ta kuma had’e hannayenta waje guda tana fad’in “Kai d’in kai kafi kowa cancanta ka zama mijinta... Gwamana dan Allah kabi wasiyyar Akram ka amsawa kanka auren Zulfa’u a yanzu... Na rok’eka....” Ta k’arashe tana hawaye... Daddy yai saurin dafa hannayen Engr yana mai sakar masa murmushi yake fad’in “Kai d’in mutumin kirki ne, mutumin arziki ne da kowa yai maka shaida ta k’warai...Wanda kowa zaiso had’a zuri’a dakai....”Daddy ya kuma kai hannunsa kan na Abbah da ya koma tamkar gunki yana kallon wannan ikon Allah lokaci guda Daddy yaci gaba da fad’in “Alhaji Usman ka bani dama na tambaya kuma na karb’awa K’anina Ma’aruf auren d’iyarka.... Shi d’in mutumin kirki ne... Kar ka mance fad’in ma’aiki ne... Idan na gari yazo neman auren d’iyarku toh ku bada, rashin bayarwan ka iya haifar da fitina... Alhj Usman ni Engr. Ahmad Madi Mailafiya Ina tambayawa K’anina Engr. Ma’aruf Mutallab Maidala auren d’iyarka Zulfa’u... Shin ka bashi a d’aura auren yanzu...?” D’agowa Abbah yai yana dubansa yayinda Hafiz Ke faman girgiza kai yana adu’an yaji kalmar a’a daga bakin Abbah... Su Baffah Wada Baffah Ado da sauran jama’an wajen dake fatan amasar Abbah ta zamto eh gaba d’aya tsit parlorn tai ana jiran amsar Abbah.... Maida dubansaga Engr Abbah yai, dikda cewa Engr ya kasance sanannen d’ansiyasa amma baisan dalili ba sosai mutumin ya kwanta masa a rai tintini dukda cewa shi d’in bai kasance mai hidima da ‘yan siyasa ba.... Fuska a murtuk’e Abbah ke duban Engr kana ya soma fad’in “You take care of my daughter... Ka kular min da d’iyata... Itad’in ta kasance d’iya mai biyayya, kuma taga iftila’i da yawa na rayuwa... Ta cancanci Farin ciki....” Jin abin yake tamkar a mafarki... Allah ya isa buwayi kuma gagari misali... Tabbas shid’in shine mai sauya al’amara a lokacinda yaso ya kuma ga dama... Yazo nan wajen da niyyan amsawa Akram auren Zulfa’u ne sai gashi aure ya tashi daga kan Akram ya koma kansa... Shin waye ya isa ya juya wannan idan ba mai mulkin sama da k’asa ba... Lokaci guda Engr yake fad’iwa Abbah “Nayi maka alk’awarin d’iyarka bazatai kuka ba in sha Allah... Zan knaunaceta da duka zuciyata dan dama tuntuni zuciyar mai k’aunarta ne, mai k’aunar sauraren muryarta ne.... Ni Engr Ma’aruf Mutallab Maidala nayi maka alk’awarin kular maka da d’iyarka har k’arshen numfashi na....” Haba nan fah parlor ya kacame da farin ciki, wane ikon Allah harta mutanen da basu San kan labarin ba irinsu Khalid sai abin yai matuk’ar burgesu... Farin ciki da annuri ya cika fuskokin mutanen... Take Engr ya wakilta Daddy ya amsa masa auren Zulfa’u... Ikon Allah kenan, Daddy ya taho Kano da niyyar amsawa d’ansa Khalid aure sai gashi ya amshi aure biyu, wannan abin farin ciki da yawa yake... Nan fah Hafiz yaji duniyar tana juya masa... Babbar rigarma baisan sanda ya cire yayi wurgi da ita ba, ji yake tamkar ya k’arasa ya shak’o wuyan Engr saidai bodyguards d’insa guda biyu kawai sun isa suyi watandan Hafiz...Al’ajabi ya cika illahirin jama’an dake wajen, nan fah hargowa da kacaniya ya kacame tsakanin Al’umma tuni labari ya famtsama cikin gida, ga kuma wani k’ishin k’ishin da sukeji cewa auren Sameer bada Sahariyya aka d’aura ba, da k’anwarta aka d’aura dan haka kowa sai cewa yake da Naja’atu aka d’aura auren Yaya Ma’aruf.... Tinda Hafiz yasa kai ya fice babu wanda yaga koda wulk’awarsa, Magaji sai sauri yake ya samu ya cimmasa kafin yai wani abinda zai janyo masa kwanan police station tinda yasan idan yayi haukarsawa Akram yasha bazai wa Babban mutum kaman Engr yasha ba... Shiko Khalid tinda suka fito daga taron d’aurin auren ya tsare Baffah da tambayoyi... Baffah na k’ek’yata dariya yake fad’in “Haba ango dika wad’annan tambayoyin ta ina zan soma amsa su... Kaga muje chines restaurant ka shirya mana gajeriyar liyafa, Ko ya kukace guys....?” Ya k’arashe yana duban su Misbahu..... Baba Ali yace “Nidai dik ba wannan ba, tinda yak’in neman auren nan dani akai, ya kamata a kaini naga amaryar nan kafin na bar garin nan...” Baffah ya dangwari k’eyar Baba Ali yana fad’in “Toh Sarkin ‘yan magana, fad’a masa dakai akai yak’in neman aurensa...” Baba Ali yace “Yo ba gaskiya nake fad’i ba... Kaga da Allah muje nasan shi kanshi angon ya matsu baiga amaryar sa ba... Dole na bata labarin gwagwarmayar neman aurenta da aka sha taredamu....” Murmusawa kurum Khalid yake dan shi kanshi sosai yake son ya sakata a idanunsa... Yusrah Baffah ya kirawo ta sanar dashi suna can gwammaja gidan Aunty Bara’atu, dashike Baffah yasan gidan sabida lokacinda sukazo sunje har gidan wajen Aunty Bara’atu babu wani b’ata lokaci yai jagoranciwa abokan nasu... Khalid gaba d’aya ganin abubuwan da suke kan faruwa yake tamkar a mafarki.... Tuni Aunty B tasa an kuma gyare masu parlorn waje, ga tarban abinci na musamman da aka jere masu, saida suka biya masallacin gefen gidan suka gabatar da sallar azahar kana suka k’araso gidan... Ita kaw Nabilah tinda aka sanar da ita an d’aura aurenta take kuka tamkar ranta zai fice, gaba d’aya haka ta duk’unk’une cikin farar laffayan da aka d’aura mata tana zabga kuka wanda ita kanta batasan na menene bane. Shin na farin ciki ne ko kuwa akasin Farin ciki.... Shin anya mijin da aka aura mata mai k’aunarta ne... Idan yana k’aunarta maiyasa har rana ta yau ranar d’aurin aurensu bata saka shi a idanunta ba bataji daga gareshi ba... Shin menene makomar aurenta....?” Kaman daga sama ta soma jiyo k’awayenta su Hameeda dasu Barakah coursemates d’insu k’alilan da suka gayyata suna lek’en window suna fad’in “Ga ango ga ango...” Dumm!!! Sautin da k’irjinta ya bada, tana jiyo muryan maza da dama daga window yanda suke gaisawa da mutane... Tuni Aunty B tasa akai masauk’i a parlor... Babu yanda ba’ai da Nabilah taje su gaisa ba fir tak’i saima sabon kukan da ta fashe dashi... Khalid kaw jin ance tak’i zuwa tanata kuka ya sanyasa mik’ewa tsam ya nufi d’akin yana mai neman izini wajen Aunty Bara’atu... Aunty tace yaje shi ai daga ita amaryar ce saiko k’awayenta... Khalid kaman zai kifa haka ya nufi d’akin... Tanajin su Hameeda na gaidashi bugun zuciyarta ya k’aru, ga k’amshin nan nasa na cikin motarsa da sam ya kasa b’acewa daga hancinta yana tashi cikin d’akin... Sai faman shan zuciya take sanda ya isa saman gadon ya zauna a gefenta... Bugun zuciyarta ya ninku.... K’uri yai mata yana kallon yanda ta tak’ure waje guda ta kasa koda d’ago kanta ne... A hankali ya d’an kwanto da kansa saitin fuskarta dake kife “Teddy bear.... Look up... D’ago ki kalleni....Kinada labarin ke d’in matata ce yanzu.... Teddy bear yau anyi aurenmu... Mu d’in ma’aurata ne yanzu...” Yanda yake maganar ya kuma sanyata sakin kukan... Kukan da sam baijin dad’in sautinsu cikin kunnuwarsa da zuciyarsa... D’an gimtsewa yai kad’an kana yace “Nasan maiyasa kikak’i d’ago kai ki dubeni, kika kuma k’i ki daina kuka... You’re still mad at me... Oya tashi ki scolding d’ina yanda kike so kinji koh...” Yai maganar yana k’ok’arin yaye mayafin data kifa kanta ciki... Janye jikinta tai tana fad’in “Ni ka k’yaleni... Ba kai ne... Ba kai ne ba....” Ta kasa ci gaba da maganan sai Sabon kuka... Wannan karon rungumota yai cikin k’irjinsa yana fad’in “I know teddy bear, ni d’in mai laifi ne... I’m sorry please forgive your Bear... Daga yanzu bazan sake barinki ba, zamu kasance tare har k’arshen rayuwar mu... Your bear is here with you... Hash now...!” Cikin sigan lallashi mai cikeda kulawa yake maganar yayinda Nabilah ta kasa turesa daga jikinta saima cukwikuye fuskarta da tai cikin babbar rigarsa ga sautin ajiyan zuciyarta dake tashi, zukatansu suna bugawa lokaci guda... Haba su Hameeda sun shagala da kallon irin wannan soyayya, wannan ta tab’a wannan wancan ta tab’a wancan... Barakah harda saita wayarta a sace tana masu video a cewarta wannan soyayya bata gani ita kad’ai ba dole takai gaba.... Khalid dai da k’yar ya lallab’o amaryarsa ta fito parlor da rakiyarsu Yusrah suka gaisa dasu Baffah... Sai zolayan Ango suke suna dariyar yanda gaban rigarsa ya b’aci da kwalliyan Amarya danginsu janbaki da gazal... Ko ba’ace ba kasan Amarya taci kuka a gaban babban garen ango.. Shiko Khalid d’in sai wani tsimewa yake yana b’allawasu Baffah harara... *** A can gidan Abbah kuwa gama d’aurin auren da kad’an Sameer ya iso, Shamsu ne ya d’aukosa daga can airport, fitowar safe yai dan ya riga ya gama abinda zai a Lagos d’in, baisan daliliba amma sosai yaji zuciyarsa ta karkata zuwa Gida.... Sanda ya isa ya tadda mutane ‘yan d’aurin aure Sun watse saiko d’aid’aiku dake parlorn Abbah suma d’in su Daddy ne saiko Engr da suka tsaya tattaunawa lamarin... Gaisawa dasu kawai yai kana ya nufi can gidansa dan kintsawa, har wannan lokaci baida labarin wainar da ake tuk’awa, saidai Abbah ya sanar dashi yayi farin ciki da dawowarsa dan akwai muhimmin abinda ya kamata ya sani... A can cikin gida kaw tinda Mamy tai tozali da Daula hankalinta ya gaza kwanciya, bugun zuciyarta ya ninku babu shiri ta d’aga waya ta sanar da ‘yar uwarta Bara’atu cewa maza tazo taga wannan abin al’ajabi da take gani na faruwa a idanunta... Aiko babu shiri Aunty Bara’atu ta fito ta nufi gidan Mamy afujajan... A can gidan Baba Alhaji kaw Haule na tsaka da tik’an rawa Lami ta kira wayarta cikin d’imauta da tashin hankali.... Da k’yar ta iya d’aga wayar dan bata fatan abinda zai katse mata wannan farin ciki da annashuwa da take ciki.... Jin muryar Lami d’in a birkice yasa Haule saita kanta kad’an kana tace “Lami ki natsu ki sanar dani meke faruwa.... Mufa yau ranar farin cikinmu ne an d’aura auren Ma’aruf....” Lami tace “K’warai an d’aura auren Ma’aruf amma fah abu ne a duhu...!” Gaban Haule ya bada Dumm! Domin kaw ta tsani wannan kalmar *Abu a duhu* kaman yanda bokansu yaita fad’a masu gameda b’acewar Ma’aruf d’in... “Ban gane abu a duhu ba Lami...? Wane irin abu a duhu..? Shin ba’a d’aura auren Ma’aruf d’in bane....?” Aunty Lami ya katse zufan da take ya tsartsafo a goshinta kana tace “Haule k’warai abu a duhu domin kaw babu tak’amaimen wanda zaki tambaya yace miki ga matar da aka d’aura mata aure da Ma’aruf saidai kowa yanada tabbacin ba Sahariyya bace matar...” Tashin hankali gobarar gemu...!!! Take Haule ta soma gani bibbiyu... Mai kid’a yana kuma k’ure speaker Haule ta malmalo ashariya ta watsa masa... Tamkar wata zararriya take fad’in “K’arya kenan... Wllhi k’arya kenan... Babu ubanda ya isa yaga bayana ni Haule.... Lami bakiji da kyau ba... Wayyo wayyo Wayyo na shiga Uku..!!!” Duniya ta shiga juya ma Haule upside down, Haule ta warware d’aurin kanta tai d’amara tana kururuwa... Haba nan fah mata aka soma kame baki ana ‘yar k’us k’us abin nema ya samu... Sahariyya kaw ihu take bataji bata gani, ... A haka Baba Alhaji ya shigo yana washe baki tamkar Sabon Ango saidai tashin hankalin da ya tadda gidan nashi ne ya bala’in tada masa hankali domin kaw zani a hannu yaga Haule sai ihu take tsakar gida tana tsalle had’ida kururuwa.... Suna a haka Sahariyya ta fito daga d’aki tamkar zararriya tana kilan Basmah data kawo mata rahoton anyi auren Yaya Ma’aruf amma ba ita bace Amarya.... Bugunta kurum Sahariyya take da sandar crutches d’inta tana fad’in “Dan uwarki sai na halak’aki... Mai mugun alkaba’iri.... Yau sai na cire miki son gulma da munafunci.....Ku barni na karta shegiya mai mummunan fata...!!!” Haba nan fah jama’a akai kan Sahariyya ana k’ok’arin rik’ota had’ida ceton Basmah da take shan duka da sandar k’arfe hannun Sahariyyar... Naja’atu ce ta k’araso ta fincike sandar hannun Sahariyya... Lokaci guda tana huci take fad’in “K’warai Addah Sahariyya Ya Ma’aruf bai cancanceki ba, kuma idan da wacce zaki daka nice nan ba Basmah...!!” Gabaki d’aya kallo ya dawo kan Naja’atu.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *89* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Haule da bataji batun da kyau ba, matsawa kusan Naja’atu tai tana k’are mata kallo shaye da tsananin mamaki “Ke mai kikace....? Maimaita naji dan uwarki....” Naja’atu dake rungumeda Basmah wacce har lokacin matsan hawaye take tace “Hajiya nasan kinji mai nace, kuma kinfi kowa sanin cewa Ya Ma’aruf bai cancanci zama mijin Addah Sahariyya ba....” Batakai aya ba Hajiya ta shiga salallami tana tafe hannaye “Kice bak’in ciki kike da ‘yaruwarki ta jini Naja’atu... Na shiga uku ni Haule, yanzu Najah sabida tsaban hassada da k’eta kawai dan shi Ma’aruf d’in bai zab’eki ba shine sabida kutungwila irin taki saida kika shiga kika fita kika hana auren ‘yaruwarki yuwa... Haba ai biri yayi kama da mutum kenan dake aka d’aura auren... Toh kaw baki isa ba, idan mutuwa kike sai an kwance an d’aura da Addarki dan mu ba Ke muka bashi ba ehe....!” Tinda ta soma magana Naja’atu Ke girgiza kai tama rasa abin fad’i ta yarda mahaifiyarta ta gama yin nisa bazataji kira ba... Sahariyya dake tsaye tana huci tamkar zakanya a d’ari tai kan Naja’atu ta shiga fincikarta tana kai mata bugu ta ko ina tana fad’in “Wllhi yau koni ko ke a gidan nan... Munafuka mahassadiya makira annamimiya....!!” Tuni su Fa’iza sukai kan Sahariyya suna k’ok’arin janyeta, ihu kawai Sahariyya take tana bugun dik yanda hannunta ya sauk’a koma wanene, bataji bata gani tamkar sabuwar kamun hauka.... Baba Alhaji kaw tuni ya janyo hannun Haule suka keb’e dan ko takan d’iyarsa Sahariyya baibi ba... Kwab’e babbar rigarsa yai had’ida maida hular kansa baya, ya dubi Haule data kame kunkumi tana girgiza tana huci... “Ke Haule Wai meke faruwa ne...? Meye na tadda na faruwa a gidan nan... wane batu nakeji cewa an canza auren Sahariyya...?” Sororo Haule Ke dubansa kana tace “Shin nada kai waye yafi cancanta ya amsa wad’annan tambayoyin...? Kaida kake wajen bukin d’aurin auren ina ka makara har aka maka wasan kura da yaranka... Idan har kana wajen d’aurin auren ta yaya duk haka ya faru....?” Gaban Baba Alhaji ya bada Dumm! Tabbas baya wajen aka d’aura auren... Haule datai sakare tana dubansa jikinta na kuma yin sanyi, gyara tsayuwarta ta kumayi kana tace “Alhaji ina saurarenka, a gidan uwar wa ka makara hakan takasance... Shin ba cemin kai ka fice d’aurin aure ba... Toh idan ba auren ‘ya’yanka ka tafi ba auren uwar waye ka tafi....? Ko kana shirya wani abin ne ba tareda sanina ba...?” Ta k’arashe tana tsattsaresa da idanunta da tuni kwalliyan da akai mata ya soma zazzgowa ya b’ata mata fuska kaman ‘yar wasan tashe... Tinda ta soma magana yake aika mata muguwar kallo... Cikeda borin kunya yake fad’in “Yanzu ba lokacin nuna yatsaga juna bane, kamata yai mu tafi gidan Usman muji uban waye ya bashi daman yai mana wasan k’wallon kondo da yara...!” Ya k’arashe yana kuma rarumar babbar rigarsa.... Haule tace “Yauwa yanzu naji batu....” Har sun kai k’ofa Baba Alhaji yaja yai birki yace “Toh amma ai Naja’atu da Sahariyya dik abu gudane... Inaga mubar zancen a haka...” Muguwar kallo Haule ta watsa masa kana tace “Eh lallai na yarda Kai Hafiz ya gada a rashin lissafi.... Dik yanda akai sunada nasu dalilin na canza auren nan, dole mubi kadin lamarin sannan a tinaninka zamu iya tank’wara Naja’atu mu cika burinmu ne.... Ai Sahariyya itace mabud’in cikan burinmu....” Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Kuma kince wani abu.....” Take suka fice afujajan suka nufi gidan Abbah, kotakan su Sahariyya basu bi ba, gidan biki ya koma gidan rabon dambe... Ana a haka Su Amara suka shigo gidan da baya da baya suna tik’an rawa sun k’ure kid’an wak’ar nan da ake yayi na AURE MARTABA... Dama ba’a gayyaci Amara da tawaganta ba suna shak’e da haushin Sahariyya dan Bikin ko wata budurwa ya tashi a unguwar dole a aikama Amara anko da katinta itada mutanenta toh Bikin Sahariyya su Fa’iza selecting sukai dan haka ba’a gayyacesu Amara ba, koda sukaji an fasa biki suka shigo d’aukan fansa... Tashin hankalin Sahariyya ya ninku gashi su Amara hidimansu babu mutunci sun sakata tsakiya sai tik’an rawa suke suna mata lik’ida k’osan rogo da suka shigo dashi ciki kwano..... *** Dikda cewa batasan mahaifiyarsu sosai ba sabida tanada k’anan shekaru Allah yai mata rasuwa tabbas wannan mata tanada fuska irinta mahaifiyarsu.... A hankali taci gaba da takowa tana duban matar wacce keta faman sakin murmushi tana gaisawa da jama’a, d’abi’unta da murmushinta irinta mahaifiyarsu ce... Aunty Bara’atu tasa hannu a hankali tana goge hawayen da suka gangaro mata, Mamy tana hangota ta k’arasa gareta suka rik’e hannayen juna suna ci gaba da kallon Aunty Daula wacce sam bata kula da irin duban da matan Ke mata ba... Mamy ta janyo hannun Aunty B a hankali suka k’eb’e... Lokaci guda suka had’a goshinsu waje guda suna hawaye.... Aunty B cikin rawar murya take fad’in “Fuskar Mama Hajja... Mamy fuskar Mama Hajjah na gani... Tell me Ya Mariya wacece wancar matar...? Shin munada alak’a da ita ne...? Dikda k’ananan shekaru na bazan mance fuskar mahaifiyar mu ba... Ya Mariya wacece matar nan...?” Mamy tai k’ok’arin saita kanta kana ta shiga share ma Aunty B hawayenta, lokaci guda take k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta “Wannan matar da kuke waya mai murya irinta Hajja Mama itace wannan Bara’atu... Daula ba murya kawai takedashi irinta mahaifiyarmu ba, harta fuskarta irin tata ce.... Tambayar a nan shin munada alak’a da ita ne... Ko kuwa dai zallan kamanni ce...?” Aunty B ta dube ‘yaruwar tata kana ta nunfasa tace “Daula ita kad’ai zata amsa mana wad’annan tambayoyi, a hankali zamu santa zamu San asalinta, ta nan zamu fahimci idan ita d’in tanada alak’a da Mahaifiyarmu....” Jinjina mata kai Mamy tai kana tace “Haka ne...” Muryarta ne ya sark’e sakamakon sauraro hayaniyar Haule da tai daga tsakar gida tana fad’in a fitina sanar da ita uban da yace ai mata wasan k’wallon kwando da yaranta... Baba Alhaji na biyeda ita... Babu shiri Aunty Bara’atu da Mamy suka dubi juna... Aunty B tace “Mamy meke faruwa...?” Girgiza kai Mamy tai kana tace “Wllhi ban sani ba, amma kaman muryar Hajiya Haule nakeji... Muje muji ko menene...” A d’ari suka nufo tsakar gidan saidai yanayin da sukaga Hajiya Haule ciki saida ya firgitasu, fuskarta gaba d’ai kwalliyar ta cab’e, janbaki ya koma kumayi gazal dasu mascara sun zagwanyo zuwa kumatu, tamkar wata dodanniya haka Haule ta juya, ga uwar d’amara data sha uwa zata tashe, uwa Uba ga d’aurin zaninta daidai k’wanjinta ya tsaya saikace mai haye wuta, ga sumarta da sunan anyi retouching dik na shirin biki sun mimmik’e wasu na kallon gabas wasu na kallon yamma saikace wani k’aho....Sai tsima take tana tsalle, Lami kanta da taga Haule a haka saida taja birki ta koma da baya tana dafe k’irji, dan da ace a hanya taci karo da Haule a haka shakka babu zatace gamo tai... Shiko Baba Alhaji sai wani muzurai yake yana sab’a babbar riga.... Mamy da tsananin mamaki take duban Hajiya Haule kana tace “Hajiya lafiya na ganki haka... Meke faruwa ne....?” Hajiya na jijjiga take fad’in “Inafah lafiya Mariya... Mijinki ya mana wasan k’wallon kwando da yara wacce aka baiwa d’ansa daban wacce ya aura masa daban....” Mamy da Aunty Bara’atu suka dubi juna.... Girgiza kai Mamy tai “Ban gane ba Hajiya Haule... Mai kike nufi....?” Duban mijinta dake tsaye bayanta gaho tai kana tace “Kai mata bayani yanda zata fahimta kai mata bayanin yanda k’aninka ya raina mana hankali, mun baiwa d’ansa auren Sahariyya ya aura masa Naja’atu... Toh bazata saku ba dole a warware wannan aure a maida kan Sahariyya....” Sai sannan Aunty Bara’atu ta murmusa kana ya matso kusan Haule.... Murmushi bai bar saman fuskarta ba take fad’in “Da gaske Hajiya Haule... Toh amma meye abin tashin hankali, naga dai Sahariyya da Naja’atu duk abu guda ne... Maiyasa kuka dage sai Sahariyya ce zata auri Ma’aruf... Shin kunada wata b’oyeyyiyar al’amari ne da bamu sani ba Haule....? Ko kuwa dai akwai wani abinda kuke shiryawa ne...?” Huci Haule taci gaba da yi tana rarraba idanu lokaci guda take fad’in “Ke Bara’atu ki shiga taitayinki, babu ruwanki a wannan magana, ‘ya’ya dai ‘ya’yana ne kuma kuma mu ba Naja’atu muka baiwa Ma’aruf ba, Sahariyya muka bada kuma dole, ya zama wajibi a warware wannan auren yanzu ba sai ‘yan d’aurin aure Sun gama watsewa ba a d’aura aure da Sahariyya kowa ya shaida....” Kaman daga sama suka jiyo muryar Mamani tana fad’in “Auren da Allah ya riga ya k’ulla babu d’an adam d’in da ya isa ya warware... Kuma dama su munafukai ranan jin kunya na nan na zuwa masu....!!” Gaba d’ai juyawa sukai suna duban Mamani dake k’arasowa Abbah na tafe gefenta, idanunsa k’yam kan d’an uwansa Baba Alhaji yanai masa wani irin duba da idanunsa da suka kad’a sukai jazir... Haba nan fah Haule ta soma shan jinin jikinta... K’ak’aro murmushin yak’e tai kana tace “Au Mamani baki fahimta bane...” “Sakani na fahimta Haulatu...” Mamani tace tana mai kuma k’arasowa... Haule taci gaba da fad’in “Wato abinda faruwa jikarki Sahariyya an yaudareta an maida sadakinta na k’anwarta Naja’atu...” Murmusawa Mamani tai kana tace “Kinyi kuskure Haule, sadaki dai tabbas na k’anwar Sahariyya ya juya amma kuma ba jininki ba....” Tashin hankali da ba’a saka masa rana.... Da tsananin mamaki Haule ke duban Mamani, murmushin da yafi kama da yak’e ta soma yi... “Kin mance ai Naja’atu jinina ne... Kuma itace k’anwaga Sahariyya....” Baba Alhaji da hantar cikinsa ke tsananin kad’awa duban mahaifiyar tasa yai kana yace “Mamani Wai meke faruwa ne... Meke faruwa ne a nan... Kai Manu mai ka aikata da ‘ya’yana..? Waye ya baka izinin canza auren yarana...?” Ya k’arashe yana mai isa gaban Abbah cikeda tsananin huci... Shima Abban huci yake yana duban cikin idon d’anuwan nasa, he can’t believe d’anuwansa na jini zai aika masa irin wannan mummunan aiki.... Cikin karaji Abbah yake fad’in “Ka bani mamaki... Ka bani mamaki Yaya.... Shin har kanada k’arfin halin kallon cikin idona....?” Jikin Baba Alhaji ya soma sanyi yayinda Haule da Lami suka soma duban juna, hawaye masu tsananin d’umi suka shiga gangarowa daga idanun Abbah sanda yaci gaba da fad’in “For years.... Shekara da shekaru kana kallon yanda nida matata muke shan wahala, kana ganin yanda mahaifiyar tasha wahala amma sabida son zuciya irin naka ka zab’i Kaga mun rayu cikin k’unci da d’aurawa junanmu laifi... Yaya ka fad’a min shin mai na tab’a yi maka da tsanani...? Shin k’oyayyar da kake min har yakai ka rabani da gudan jinina....? Shin wane irin zalunci ne wannan....?” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Kalaman da illahirin mutanen wajen suke nanatawa kenan a zuciyarsu, sauk’in abu mutanen dake wajen duk na gida ne Gwaggwanyen Kazaure ne saiko Aunty Daula dake d’aki da alama bata ma San wainar da ake toyawa ba, tana dai jiyo kaman hatsaniya daga waje amma da shike ta kasance mace maras shiga hurumin da bai shafeta ba shiyasa ma bata fito ba..... Su Haule da Lami kaw da za’a tsaga jikinsu tabbas da zai wuya a sami jini sabida yanda suka daskare sakamakon jiyo irin kalaman dake fitowa daga bakin Abbah... Kenan hakan na nufin asirinsu ne ya tonu ko kuwa....? A daburce Baba Alhaji ya soma fad’in “Kai Usmanu yanzu rashin kunyar naka har ya kai ka dubi tsaban idanuna ka dinga jifata da sharruka irin wannan had’ida wasu kalamai marassa kan gado bayan cin amanan da ka min na canza auren yarana da kai.... Ni ban ma san mai kake nufi da wad’annan kalaman naka ba...!!” Kan ya kai aya Mamani dake zuban hawaye ta katsesa da fad’in “K’arya kake ka sani.... Kasan komai Alhaji Alk’ali bazai maka sharri ba... Kaida wad’annan azzalumai biyu ku kukai sanadiyar rabuwarmu da Ma’aruf...” Tai maganar tana nuna Hajiya Haule da Aunty Lami dake faman rakub’e rakub’e tana raba idanu kaman mage a ruwan zafi, ga wane irin gumi dake faman keto mata.... Mamy data tari zancen kaman wani sauk’an guduma kasa fahimtar komai tai sai bin mutanen dake wajen da idanu da take, take kanta ya shiga huya mata, ita bama ta fahimci abindake wakana ba... Mamani taci gaba da fad’in “Ku sani Allah baya bacci kuma wasu sirrika dik tilin k’asan da aka aza masu toh fah ran dik Allah yaso bayyanasu toh da kansu zasu tono kansu... Alk’ali ka bani kunya kaci amanan ‘yanuwantaka... Ka biyewa sharrin wad’annan shed’anun matan ka cutarda ahalinka shin har kanada k’warin gwiwar ci gaba da rayuwa cikin ahalinka... Shin har kana iya bud’e idanu ka dubi d’an uwanka da iyalinsa tsawon shekarun nan.... Shin wane irin mugun zuciya ne da muguwar gaba had’ida mummunar k’eta zaisa ka aikata irin wannan bak’in laifi mai tarin zunubi... Shin ta yaya zaku raba k’aramin yaro d’an shekaru uku wanda baida hakkin kowa da iyayensa.... Shin da wasu idanu ka soma duban Ma’aruf a lokacinda Allah ya dawo mana dashi.... Shin dukanku da kuka salwantar dashi da wasu idanu kuka soma dubansa....? Ku fad’a min da wasu idanu kuka soma duban jikana Ma’aruf..!!!??” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana k’ok’arin duk’awa daidai nan Sameer da shigowarsa kenan tareda Engr yayo rakiyawa Engr dan ya gaisar dasu Mamy suka tarar da wannan iftila’i... Cikin sauri Sameer ya taro Mamani Engr na taimaka masa... Cikin sauri Abbah ya mik’a masu kujeran tsuguno na zaman mata a kitchen dake a tsakar gidan suka zaunar da Dattijuwar wacce basai ance maka ba zuciyarta ta matuk’ar raunana.... Sameer da ya tuni ya tsinci abubuwa da dama da Mamani Ke fad’i take idanunsa suka kad’a sukai jazir, dan sai yanzu yake fahimtar wasu abubuwan.... Sai yanzu ne wasu abubuwan suke dawowa kwanyarsa.....Sai yanzu yake samu amsoshin wasu tambayoyi da suka jima suna Yawo a kwanyarsa.... Take idanunsa suka kuma kad’awa suka rine, fatar jikinsa ta juye ta koma jajazir haka nan duk wata k’ofa da gashi ya ratsa cikin jikinsa saida suka mimmik’e ya d’ago yana dubansu d’aya bayan d’aya, gaban Baba Alhaji ya k’arasa sanda hawaye mai tsananin zafi ta ganagro masa, lokaci guda yake duban Baba Alhaji dake faman huci irinta mai borin kunya, cikin wata irin murya mai cikeda tsoro da kad’a zuciyar azzalumai yake furta “Duk abubuwan da naji da gaske ne.... Ku kuka rabani da iyayena da dangi na...? Kuka jefa rayuwar mahaifiyata cikin garari.... Is it true...?!!!” Ya k’arashe yana mai duban cikin idanun Baba Alhaji hawayen k’unan rai har suna rige rigen zubowa daga idanunsa da suka kad’a sukai jazir.... Daidai lokacin Mamy dake takowa gaban Haule da Lami cikin yanayi mai ban tausayi, ta dubi Lami ta dubi Haule tana tina yanda ta rik’i Lami tamkar k’anwa a gareta ba kishiya ba... Lokaci guda take furta “‘Yan uwa na d’aukeku... Ban tab’a d’aukanku da wata muguwar nufi ba... Allah Shi ne shaidata.... Lami... Haule shin kuka rabani da Ma’aruf....? Ku bud’e baki ku fad’a min.... Ku bud’e bakunanku ku sanar dani dalilinku na aikata haka a gareni....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Mamani ce ta kuma mik’ewa da k’yar cikeda tausayin Mamy ta isa gareta ta kamo hannayenta tana mai furta “K’warai Mariya wad’annan azzalumai su suka rabaki da gudan jininki... Su suka nisantamu da Ma’aruf, suka jefa gaba tsakaninmu suka sa muka d’aura miki laifin da bakiji ba baki gani ba bayan mun mance kece mahaifiyarsa da ganganci bazaki tab’a salwantar da gudan jininki ba sabida duk k’aunar da zamu nuna masa a bayanki ne... Mariya ki yafeni, ki yafe min duk wasu abubuwan da na miki keda ‘ya’yanki.... Ku yafeni Mariya.. Hak’ik’a yau d’in bazan iya duban cikin idanunki ba... Ked’in kin cika matar kirki, uwa ta gari kuma abokiyar zama ta kwarai sannan sirika wacce ko wace uwar miji zatai mafarkin samu, Mariya ki yafeni....!!”Ta k’arashe cikin tsananin kuka.... Lokaci guda Mamy dake hawaye sosai ta d’agota, bata iya cewa komai ba sai rungume Mamani da tai su duka biyun kuka suke sosai.... Haule dake faman yatsine yatsinen fuska tana kallon wannan drama a cewarta, shewarta ne had’ida rangad’a gud’a ya dawo da hankalin katafarin jama’an dake wajen.... Gaba d’aya duban Haule suke tamkar sabuwar kamun hauka lokaci guda Haule ta soma fad’in “Munji mu d’in maciya amana ne... Munji mud’in azzalumai ne.... Amma dik muguntarmu da makircinmu a bayan AMINIYAR SIRRI muke.....!!!!” Da tsananin mamaki suke kuma dubanta... Lokaci guda Haule Ke takowa ta k’araso gaban Mamy... Tana wani murmushi had’ida jijjiga take fad’in “Mariya kenan.... Kin zaci mu muka rabaki da d’anki tsawon shekarun nan koh....? Toh a tinaninki zamu cika wad’annan burika namu babu taimakon AMINIYAR SIRRI NE....?” Wane irin bugu k’irjin Aunty Bara’atu yai lokaci guda.... DUMBA sunan da yazo zuciyarta kenan Cikin tsananin rud’ani Mamy tace “Wacece AMINIYAR SIRRI...?” Haule ta kuma murmusawa kana tace “Kin fimu kusanci da ita....!!!” Da tsananin mamaki Mamy ke duban Haule, lokaci guda hawayen dake idanunta taji sun k’afe... Tsananin hucinta ya k’aru “Haule kina nufin kice DUMBA itace ta taimaka maku kuka salwantar da Ma’aruf.... Shin dama Dumba tana k’asar nan tsawon shekarun nan...?” Take wannan suna DUMBA tai ranking a k’wak’walwan Sameer, tabbas ya tab’ajin wannan suna, idan bai mance ba DUMBA itace matar da Mummynsa tace ta basu shi.... Toh wacece DUMBA.... How’s she connected to all this...?!!” (Idan mai karatu bai mance ba dai DUMBA itace matar data bada rik’on Ma’aruf (Sameer) hannun Hajiya Fatahiyya). SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *90* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali Sameer Ke takawa har ya isa gaban Mamy... “Mamy wacece Dumba...? Mecece alak’arku....? Ya akai Dumba ta mik’a rik’ona hannun Hajiya Fatahiyya Mummy na....? Idan ban mance ba according to Mummy ta bani labarin cewa ita wannan Dumbar itace matarsa ta bata rik’ona, sannan aikatau takewa Mummy na... Koda Mummy na ta tambayeta cewa daga ina ta samoni sai ta sanar da ita cewa Aminai uku suna yunk’urin hallak’ani shisa ta yanke shawarin turani wani waje mai nisan zango na tafi almajiranci har Allah ya nufa ta mik’a rik’ona hannun Mummy Fatahiyya.... Shin Mamy ita wannan Dumban wacece ita dan koda na tambayi Mummy ina zan sami Dumba a lokacinda nake neman iyayensa na asali Mummy ta sanar dani cewa ita kanta batasan yanda Dumba take rayuwa ba a halin yanzu.... Yanzu na samu wasu k’arin haske na sanadiyar b’acewata na kumaji wad’anda sukeda alhakin hakan... Tambaya guda da zan maki Mamy shin ita wannan Dumbar wacece... And how are you related...??” Waje yai tsit da jin zancen Sameer da tambayoyinsa ga mahaifiyarsa, kowa so yake yaji wad’annan amsoshi... Mamy ta d’ago kai tana dubansa kana tace “Ma’aruf... Hak’ik’a Dumba ‘yar uwata ce da muka taso tare... Dumba d’iyace ga Yayar mahaifiyarmu, sanda ta rasa iyayenta rik’onta ya koma hannun mahaifiyarmu... Kaman yanda na baka labari cewa mud’in ‘yan asalin garin Jada ne ta jihar Adamawa, mahaifinmu haifeffen garin Jada ne, mahaifiyarmu kuwa asalinta ‘yar k’asar Mali ce, bafulatanar K’asar Mali ce, yak’i ya tarwatsa iyayensu a wancan shekarun, shi kuma mahaifinmu a lokacin Soja ne, lokacinda aka turasu yak’i da ‘yanta’adda acan k’asar Mali lokacin ya had’u da mahaifiyarmu har ya aureta kasancewar zasu jima sosai a k’asar Mali suna yak’i da ‘yan ta’adda hakan yasa yai aurensa a can... Sun kwashe shekaru da dama suna zaune a Mali suna yak’an ta’addanci har Allah ya albarkacesu da yara ‘yanmata guda biyu, ni da kuma babbar Yayarmu Abidah.... Toh a wannan shekarun ne lokacin Ina k’arama mahaifinmu ya yanke shawarin dawowa damu k’asarsa ta haihuwa Nigeria sabida gaba d’aya yak’i ya cinye yankinsu mahaifiyata a k’asar Mali, kusan danginta gaba d’aya saiko d’aid’aiku yak’i ya had’edasu ciki harda mahaifan Dumba.. Sanadiyar da yasa rik’on Dumba ya koma hannun mahaifiyarmu kenan.... “ Numfasawa tai kana tace “Barin dakata a nan kar labarin ya shiga cikin wani labari a tak’aice dai kaji alak’ar dake tsakanina da Dumba....” Sameer ya numfasa kad’an kana yace “Toh ya akai Dumba ta zama wacce alhakin b’acewana Ke hannunta....?” Wannan karon su Lami da Haule ta kalla kana tace “Wannan ne nima ban sani ba Ma’aruf, Inaga su ya kamata su sanar damu yanda suka had’e kai da Dumba wajen yunk’urin salwantar da rayuwarka... Domin kaw a iyaka sanina rana tsaka Dumba ta matsa min da cewa zata tafi ta nemi danginta a Mali idan mu mahaifinmu d’an Nigeria ne ita bazata tab’a mance cewa asalinta Mali bane.... Dama tin da jimawa Dumba tanada wannan buri shiyasa ko aure tak’i tayi a Nigeria tace har sai ta koma k’asarta ta haihuwa.... Tambayar a nan bansan ya akai ta zamto aminiya gasu Haule ba har suka had’e kai wajen salwantar dakai....” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Haule tana fad’in “Ko a wancan lokacin bama jituwa da Dumba, kuma tabbas Dumba tayi gaskiya da tace Aminai uku suna yunk’urin halak’a rayuwar Ma’aruf.... AMINIYAR SIRRI ba Dumba bace kaman yanda kika d’auka, Aminiyar Sirri tafi Dumba kusanci dake...” Ta k’arashe maganar tana duban Bara’atu da kanta Ke kife tana hawaye... Dum! Dum!!Dum!!! Sautin bugun k’irjin Mamy.... Gaba d’aya kallo ya komaga Aunty Bara’atu.... Girgiza kai Mamy ta shiga yi cikin rashin yarda da abinda take gani, lokaci guda bakinta na tsanani rawa take furta “A’a... A’a Haule, hakan ba mai yuwa bane.... Haule hakan bazai tab’a kasancewa gaskiya ba....!!!” Haule ta shek’e da wani irin dariya kana tace “Gata nan gabanki ta musa idan ba itace AMINIYAR SIRRI BA, ta musa idan ba itace ta jagoranci ragamar salwantar da d’anki ba... Gata nan gabanki....” Innnalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Allahumma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha.... Kalaman da zuciyar Mamy Ke iya nanatawa kenan, k’ololuwar tashin hankain data tsinci kanta ciki bazai misaltu ba, ta ya za’ace ‘yaruwarta ta jini zata mata haka... Ta ya za’ace ‘yaruwarta da ta aminta da ita zata mata wannan babban butulci... Kai gaba d’aya jama’an dake wajen kansu ya k’ulle... Harta su Abbah dasu Mamani saida tashin hankali ya nuna sosai a tattaredasu, tashin hankalin da zasu iya cewa tun bayan b’acewar Ma’aruf basu sake fuskantar irinta ba.... Wato Aminai uku da sukai yunk’urin Salwantar da Ma’aruf kaman yanda Dumba ta fad’i Haule ce da Lami had’ida Bara’atu... Kai wannan irin butulci da mai yai kama, Ke duniya mecece cikin ki bacin tarin maciya amana da azzalumai.... Dik yanda Engr yaso ya fice a wajen ya basu privacy tinda yaga rikici ne na family amma ya kasa, ji yake bazai iya tafiya ba har sai yaga k’arshen al’amarin nan, ji yake can k’asar zuciyarsa tamkar ya tab’a rayuwa a wata duniya irin tasu....Tausayin mahaifiyar Sameer ya cika zuciyarsa, ga wani shauk’i da yakeji tinda yaji an ambaci Sameer da suna Ma’aruf, wani ikon Allah ashe sunansu d’aya gashi labarinsu yaso yayi shige tinda shima Sameer ba a gaban iyayensa ya girma ba shima rabasa da nasa iyayen akai... Tabbas labarin rayuwarsu yaso yai shige.... Kasa furta komai Mamy tai, ta kasa tab’uka komai, saiko tsayuwa sororo da tai gaban Aunty Bara’atu... Sameer yasa duka hannayensa biyu ya tallafi mahaifiyarsa ganin tayi rauni sosai, shin waye ma bazai rauni ba da jin irin wannan labari mai tsananin tashin hankli.... Girgiza kai Mamy taci gaba da yi tana duban Aunty B sa kanta ke kife k’asa, tabbas da ace k’asa zai gsaga ta shige ciki da hakan ya fiye mata sauk’i... Ta ya zata iya d’ago idanu ta dubi ‘yar uwarta...? Ta yaya, bayan wannan babban al’amari dake faruwa dasu.... Murya a matuk’ar sanyaye Mamy Ke fad’in “Bara’atu d’ago fuskarki ki k’aryatasu... Nasan hakan sam ba mai yuwu bane... D’ago kice min K’arya suke ‘yar uwata... Kinji, Dan Allah d’ago ki k’aryata wannan mummunar sharri da suke jifanki da ita... Bara’atu kice min k’arya suke ba kece Aminiyar Sirri ba... Kinji ‘yar uwata...!!” Ta k’arashe tana mai jijjiga Aunty Bara’atu da har lokacin fuskarta Ke kife k’asa....Haule da Lami suka dubi juna suna masu aikama juna makiran murmushi.... A haka Mamy taci gaba da jijjiga Aunty B da iayaka k’arfinta, wannan karon zaka iya hango tsananin tafasa da zuciyarta keyi sabida yanda fuskarta ta rine zuwa jajazir haka nan k’wayan idanunta... Fad’i take “Bara’atu ki k’aruatasu nace... Ki k’aryatasu ‘yaruwata, bazaki tab’a min haka ba ni na sani... A lokacinda na rasa Ma’aruf kina taredani.... Baki tab’a k’yaleni ba daidai da dak’ik’a guda... Dik kalan tashin hankalinda na shiga, taredake nai overcoming d’insu, a lokacinda kowa ya juya min baya ked’in kina taredani ‘yaruwata... Abinda suke fad’i bazai tab’a yuwa ba.... Ki cemin k’arya suke Bara’atu..!!!” Aunty B da itama kanta ahesshek’ar kuka take, a zuciye ta fincika ta d’ago tana duban Mamy lokaci guda take furta “Eh... Eh Ya Mariya ni ce Aminiyarsu ta Sirri.... Taredani suka shirya komai... Na taimaka masu sun cika burinsu na kawarda Ma’aruf gaban iyayensa.... Kuma ni ce nan na mik’a shi hannun Dumba...” Innalillahi wa Inn’ilaihi Raji’un.... Kalman da zuciyoyi sukaci gaba da nanatawa kenan.... Aunty B na kuka sosai take duban Mamy da tai mutuwar tsaye a wajen tana dubanta cikin rashin yarda da abubuwan dake faruwa.... Lokaci guda Aunty Bara’atu taci gaba da fad’in “Mamy inaso ki tuna mai ya faru a ranar da Ma’aruf zai b’ace....” Mamy da hawayen dake idanunta suka k’afe a hankali ta soma furta “Babu abinda ya b’ace a kaina gameda wannan rana da abu biyu suka auku dani... Muhimman abubuwa guda biyu, RASHI da kuma SAMU.... Ranar da na rasa d’ahna Ma’aruf, kuma ranan da na haifi d’iyata Zulfa’u..... Wata ranace ta Alhamis mai cikeda tsananin zafin rana... _WAIWAYE_ Shekaru ashirin da Shida da suka Shud’e...... Zaune suke saman tabarma itada d’an nata da bazai haura shekaru uku ba, wata matashiyar budurwa tai sallama ta shigo... Da alama budurwar a gajjiye ta shigo hakan yasa ko gaisarda matar data tadda zaune saman tabarmar batai ba saima fad’i da take “Auchh! Gaskiya ana rana Mamy... Kinji waje kuwa... Wllhi badon jarabawa da muke ba da gobe bazanje poly ba ni wllhi na gaji...” Ta k’arashe tana matashi da jakkanta had’ida d’an kishingid’a gefe... Matar data kirada Mamy murmusawa tai had’ida d’an muskutawa kad’an sabida bayanta da yai mata tsami sakamon zungureren cikin dake jikinta, haihuwa ko yanzu ko anjima “Banda abinki Bara’atu mai kukai a karatu, yanzu fah kuka fara...Shekararki ta farko fah kenan, kuma ki godewa Allah cikinmu uku kin sami damar tafiya gaba da sakandare kagi da k’anan shekarunki tinda har yanzu baki kai ashirin ba, dan haka koda wasa kada kiyi sake da damarki kinji koh....” Murmusawa Bara’atu tai kana ta mik’e ta rungume Mamy tana fad’in “Yah Mariya mai zanyi a rayuwar nan idan babu ke... Ina k’aunarki sosai ‘yaruwata shisa sam bazan iya zaman gidan Ya Abidah ba na zab’i na zauna dake....” Murmusawa Mamy tai had’ida d’an dungurinta kana tace “Amma ai Yaya Abidar ita ta fara rik’onki kafin nima nai auren koh... Ita d’in uwace a garemu dukanmu dikda abinda ya faru....” Cikin sauri Bara’atu ta janyo hannayen Mamy tana fad’in “Dan Allah kada ki soma tuno abinda ya faru baya kinsan likita ya hanaki shiga damuwa ko dan lafiyar abinda Ke cikinki sannan idan Abbah yazo ya taddaki cikin damuwa fad’a zaiyi shima...” Mamy ta murmusa a hankali kana tace “Tabbas Usman shi ya dawo min da Farin cikin da na rasa a baya... Amma Bara’atu har yau na kasa cire alhakin mutuwar Fatima da Ma’aruf a wuyana.... Shin ta yaya zan bar yaro d’an shekaru shida da jaririya sabuwar baihuwa cikin tsumman goyo....?” Aunty Bara’atu ta kuma kamo hannayenta tace “Babu laifinki Mamy, hakan Allah ya k’addara kuma kema kinyi iyaka naki k’ok’arin ganin kin kub’utar dasu amma Allah bai nufa sud’in masu rayuwa bane... Ina fata Yaya zata fahimci haka watarana, ta daina d’aura alhakin b’acewar d’anta Ma’aruf da kuma ‘yar autarmu Fatima a wuyarki....” Numfasawa Mamy tai had’ida da kai dubantaga Ma’aruf daketa wasan sa hankali kwance... Bara’atu ma kai dubantaga Ma’aruf d’in tai kana tace “Da Ma’aruf Babba yana raye k’ila da yakai shekaru goma sha da ya soma zama saurayi.... Nasan yanda kike k’aunar Ma’aruf Babba Mamy, kuma wannan suna Mamy shi ya saka miki har yabi bakinmu gaba d’aya....” Mamy ta kuma murmusawa had’ida goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Ma’aruf d’ah na... Haihuwarsa kawai Yaya tayi amma inajin har k’asan zuciyata tamkar na fita k’aunarsa... Kuma ban cire rai ba INDA RAI DA RABON wata rana Allah ya kuma had’amu....” D’an murmusawa Bara’atu tai kana tace “Mamy Ma’aruf ya tafi kuma Allah ya bamu wani Ma’aruf d’in... Dik irin k’aunar da kikewa Ma’aruf Babba ki had’asu kan Ma’aruf k’arami tinda dama shi d’an Gata ne wajen Kakarsa da iyayensa....” Mamy ta kuma murmusawa tana mai duban d’an nata yanda yaketa wasan sa hankali kwance... Muryar Bara’atu ne ya dawo da ita daga duniyar tinanin da ta tafi tana mai furta “Ma’aruf... Zo yaro na...!” Dubanta yai sai ya mak’e kafad’a ... “Aw bazakazo ba sarkin ‘yan k’iwa...” Nanma mak’e kafad’a yai kana ya fad’a jikin mahaifiyarsa yana mai furta “O’o nidai Mammy.....” Cikin muryarsa da yake gwari gwari irinta yara.... Aunty Bara’atu tace “Toh ai shikenan dama na sayo maka motar wasa kuma bazan baka ba....” Ambato mota da tai yasa yaron zuwa gareta a guje yana fad’in sai ta basa mota, “Laaa Kaga yaro zai tara min jama’a Nifa wasa nake maka....” Mamy tace “Ah toh aiko sai ki bashi tinda kin iya zolaya....” Abu kaman wasa yaro ya dinga kuka sai an sai mai jiyin jiyin.... Baiji bai gani kuka yake.... Mamy ta dubeta tace “Kinsan mahaifinsa baya nan balle ya fita ya sai masa, kuma Kakarsa data k’wallafa rai akansa tanajin kukansa zaki ganta a nan tana sababi, ni kuma ga halinda nake ciki wllhi sam bansan tashin hankali, da kukan Ma’aruf zanji ko kuwa da fad’an Mamani zanji, ki tashi tun wuri tin dare bai maki ba kije ki nemo mota....” Bara’atu ta mik’e tace “Aiko bara na tafi bakin kasuwa na sayo mai....” A haka ta zira mayafinta ta nufi k’of, yayinda Mamy taci gaba da rarrashin Ma’aruf da kaman an saka masa batir sai kuka yake.... Jim kad’an Bara’atu da dawo a firgice... Mamy tace “A’a lafiya Bara’atu...? Har kin dawo....” A d’an daburce tace “Mamy Dumba ce tazo daga gidan Yaya tace tana nemana kuma ba lafiya take ba...” Mamy da damuwa ya nuna itama a fuskarta tace “Wai DUMBA bata wuce ba...? Inji tin shekaran jiya tace zata bar garin nan...?” Bara’atu tace “Inaga sabida jikin Yayan ne yasa Ya Dumba bata tafi tin shekaran jiyan ba... Amma tace min yanzu haka akan hanyarta take shisa tazo kirana naje na zauna da Yaya Abida....” Mamy ta numfasa tace “Toh Bara’atu ko zamuje tare ne....?” Girgiza kai Bara’atu tai kana tace “Mamy sanin kanki ne Yaya ta miki iyaka da gidanta... Ga kuma halinda kike ciki... Dan Allah kada kije Yaya ta miki wani abinda zai d’aga miki hankali yai affecting d’an cikinki... Ki barni ni zanje kinji koh... Zan kula da ita....” Jinjina kai Mamy tai jiki a sanyaye dikda cewa har lokacin Ma’aruf kuka yake “Toh shikenan Bara’atu, kije Allah ya tsare kinji koh... Allah kuma shi miki albarka....” A hankali Bara’atu ta jinjina kai kana ta fice cikin sauri.... Juyowa Mamy tai tana duban Ma’aruf da har lokacin yak’i yin shiru sai kukan a sai masa mota yake.... A hankali ta dafasa tace “Ma’aruf... Mota kake so...?” Ya jinjina mata kai cikin sauri.... D’an fuzar da iska tai a hankali dikda bayanta da takeji kaman abu na mintsilinta, bata fatan Mamani ta shigo ta taddasu hakan tasan abun bazai kyau ba, dan idan Mamani tai mata tatas Bara’atu ba shiru zatai ba sabida fad’a irin nata itama, ita kuma bata fatan abinda zai d’aga hankalinta dana mijinta tinda mahaifiyarsa ce, idan kaji Mamy ta samu sab’ani da mijinta toh fah ka tabbata akan mahaifiyarsa ce kuma kan an tab’a tilon jikanta Ma’aruf ne... Hakan yasa Mamy ya zaro mayafi tace “Muje bakin kasuwan na sai maka....” Tiryan tiryan suka d’au hanyar kasuwa tana rik’eda hannun d’anta ga zungureren ciki da ya sauk’a k’asa sosai... Sun isa kasuwa ana cikin mota abu kaman wasa ta soma jin ciwo na k’aruwa, sam bata kawo haihuwa zatai ba, aiko ashe dai haihuwarce tazo, azaba yasa ta saki hannun Ma’aruf tana kame mararta da cikinta... Kan kace me matan da suke kasuwar sun rufu akanta ana k’ok’arin bata d’auki na gaggawa... Tana iya jiyo sautin kukan Ma’aruf yana ambato sunanta “Mamy! Mamy!! Mamy!!!....” Itama d’in ambato sunansa take “D’ah na, ku agazamin akwai d’ahna a wajen nan... Ma’aruf!!!” Inaaa tuni sarkin kasuwa ya iso da mota matan nan sun saka Mamy ciki an nufi asibitin general da iya dan babu wanda ya saurari cewa da take d’anta d’anta duk a zatonsu d’an cikinta take nufi.... Mamy ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Daga wannan lokaci ban sake jin d’uriyan d’ah na Ma’aruf ba.... Farkawa nai na ganni kwance a gadon asibiti ga kuma jinjira a gabana nad’e cikin showel, abinda na fara fad’iwa nurses d’in shine “Ina D’ah nah... Ina Ma’aruf...? !!” Nurse ta kusa dani ta d’auko jinjirar da na haifa ta mik’a min tana mai fad’in “Ba yaro kika haifa ba yarinya ce Gata nan....” Cikin wane irin k’ara nake furta tare nake da d’ah na su bani d’ah na... Nurses sukace su basuga wani yaro ba ni kad’ai aka kawo ni.... Haka na dinga kuka ina fad’in su bani d’ah na, har saida suka min alluran bacci sannan dan ko jinjirar da na haifa na kasa d’auka.... Ko bayan dana dawo hayyacina na tadda labarin haihuwata ya isa ga ‘yanuwan mijina, Haka Mamani tamin chaaa a asibiti tace bataji ba bata gani ba sai na nemo mata jikanta Ma’aruf da ganganci na d’aukesa na tafi dashi kasuwa na salwantar dashi, wannan dalili yasa k’iyayyata data d’iyata Zulfa’u yai tasiri a zuciyar Mamani a cewarta ganganci na ne yasa na tafi dashi dikda ansan tsautsayi sannan ita kuma Zulfa’u itace mai farar k’afa yasa ranan da zatazo duniya d’an uwanta ya b’ace... A b’angaren mijina ma ban sami wani sauk’i ba domin kaw shima da hukuncin mahaifiyarsa yake aiki.... Bara’atu......” Birki ta d’anja sanda ta ambaci sunan Bara’atu kana ta d’ago kod’add’un idanunta a hankali tana dubanta.... Mamy ta sa hannayenta biyu ta share fuskarta kana taci gaba da fad’in “Bara’atu ‘yar uwata ita kad’ai ce bata gujeni ba... Kuma bata juya min baya ba... Tana nan taredani tsawon shakarun nan... Dan harta aure data tashi yi saida naita bata baki nace bazai yuwu ta k’are rayuwarta a kula dani da kuma yarana ba... Bara’atu ta sadaukarda lokutanta dukiyarta soyayyarta da duk wani abinda ta mallaka a gareni da ahalina... Dikda cewa mijinta ba mazauni bane, bata zab’i ta bishi ba, ta zab’i ta zauna dani a nan ta kula dani da kuma ahalina.... Bara’atu itace komai nawa tsawon shekarun nan wacce nake gani naji sanyi, wacce take d’ebe min kewa da soyayyarta mai tsafta, wacce take nuna min hanya a lokacinda na tassama b’acewa, K’anwa data zamto tamkar uwa a gareni... Shin ta yaya matar da muka aminta da ita nida ahalina zata mana haka..? Shin ta yaya zuciyata zata aminta da hakan ....’”” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata... Aunty B da kukanta ya tsananta durk’usawa tai gaban Mamy hannayenta biyu had’e waje guda lokaci guda take furta “Ki yafeni Mamy... Ki yafeni ‘yar uwata....!!” Ta kasa ci gaba da magana sai kuka.... Wajen yai tsit sai sautin kuka kawai da kakeji... Haule ta tako tazo tsakiyarsu tana mai sakin shewa kana tace “Toh Mariya kin daiji wacece Aminiyar Sirri kuma tsawon shekarun nan har bayan bayyanar d’anki Ma’aruf bamu daina Aminci da AMINIYAR SIRRI ba..... Ba mijina bane kawai maci amanan d’an uwansa k’anwarki itace gasunk’umar maciyiya amana... Hasalima mu taimakon Ma’aruf muka tasamma yi wannan munafukar k’anwar taki itace tazo da shawarin a salwantar dashi... Itace AMINIYAR SIRRI...” Wata Murya sukaji daga bayansu tana fad’in “Idan kunyi tunanin Bara’atu itace AMINIYAR SIRRI kunyi babban kuskure... AMINIYAR SIRRI ta rayu ne a tsakaninku cikin jikin Bara’atu..... A yau d’in zaku bud’e bakunan ku da kanku ku fad’i duk irin bak’in aikin da kuka aikata......” Gabaki d’aya suka juya suna duban k’ofa.. Matar da babu wanda ya tsammaci ganinta a waje irin wannan..... “Ni ce nan AMINIYAR SIRRI... Sirrikan zasu ci gaba da hak’o kansu... Wasu sirrika ne da wasu mutane suka jima da binnewa... Wasu sirrika ne da aka jima da aza masu k’asa... Kyawawan ayyuka sukan tafiyar da munana... Saidai wasu sirrikan basu yarda su b’oye kansu... Sukan bayyana kansu domin hakan ya zamto izna ga al’umman da zasuzo a baya....!” Ta k’arashe tana isa gaban Mamani da tai mutuwar zaune tana jin kalaman nata.... Yayinda gwaggwanayen Kazaure suka mik’e zumbur, Mamy da Aunty Bara’atu sukai mutuwar zaune suna kallonta.... Wani irin bugu k’irjin Engr yai saida ya dafe garundake gefensa sakamakon ganin fuskar wannan mata da yai.... Take k’wak’walwarsa ta shiga tina wasu abubuwa da suka faru shekaru masu tsawo... Haka ya dinga hango hotunan abin cikin k’wayar idanunsa tin sanda Mamy ta soma kwararo bayananta bugu da k’ari bayyanar wannan matar cikin k’wayan idanunsa... Dikda girma da ya kamata fuska ne da ya jima yana masa gizo a kwanyarsa da k’wayan idanunsa...... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *91* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wancan, hakance ta kasance... Wata sabuwa ana wata ga wata... Sameer da kansa gabaki d’aya ya k’ulle bud’e baki yai yace “Wai meke faruwa ne a nan... Wacece ke kuma...?!” Matar ta maida dubantaga Sameer kana tace “Ni ce Aminiyar Sirri.. Nima kuma nayi tarayya ne da wata Aminiyar ta Sirri a yayinda na tura wata Aminiyar ta Sirri ta wakilceni tsakaninsu.....!!” Haule da Lami harma da Baba Alhaji da mugun mamaki suke kallon matar nan... Wato ita Lami bama tasan mijin Haule nada babban kaso cikin zunubin da sukai tarayya ba sai yanzu.... Ita dik a nata zaton su uku suka k’ulla wannan sharri... Daga ita sai Haule saiko Aminiyarsu ta Sirri... Toh yanzu ga wasu batu suna fitowa daga baya... Lami kanta abin ya soma bata tsoro... Take ta tina jawabin Malaminsu na taubbu da ya tab’a sanar dasu muddin basuyi aikin da kyau ba Toh fah bazasu tab’a fahimtar komai ba, Abu a duhu ne zaita bayyana masu... Eh lallai ta yarda da batun Malam na cewa Abu a duhu... Ta yarda aikin had’aka akai wajen kawar da Ma’aruf tinda ga wasu fuskoki da batasan dasu ba cikin aikin suna kan bayyana... Yanzu kam kan kowa ya kwance.... Wane irin al’amari ne wannan...?? Take Sameer ya shiga girgiza kai yana huci lokaci guda yake furta “Aminiyar Sirri Aminiyar Sirri..! Aminiyar Sirri....!!Shin Wai menene wannan Kalmar...? Maiyasa har yanzu magana k’wakk’wara ya kasa bayyana...? Maiyasa har yanzu gaskiya guda d’aya ta kasa fitowa... What’s all this..??” Abbah ne ya nufi Sameer yana furta “Mu fice a nan d’ahnah, muje ka huta...” Girgiza kai Sameer yake cikeda rud’ani yana furta “No Abbah I need to know everything, every single thing....I need to get to the bottom of this...!” Baikai aya ba Ya Abida ta katsesa da fad’in “Babu wanda zai bar wajen nan sai an gama warware komai...!” Usman akwai abinda ya kamata kaima ka sani....!!” Abbah da k’irjinsa ya buga kuma dubanta yai kana ya d’an girgiza kai yace “Ya Abidah kin jima kina shan magani na cutar damuwa (depression) inaga har yanzu baki ida warkewa ba... Ya kamata duk mu watse, duk wanda ya zalinci wani mu fawwala ma Allah komai, a b’angarena nida iyalina na tabbata bamuda matsalar yafiya....” Matar da ya kirada Ya Abidah ta katsesa da fad’in “Usman ni d’in na jimada warkewa... Sannan akwai wasu sirrika da basu tab’a yardane su binne kansu... Ko Mamani...??” Mamani da tuni idanunta sun kad’a girgiza kai ta soma tana k’ok’arin mik’ewa take fad’in “Kinga Abidah.... Maza ki fice mana a gida, magana ya riga ya k’are... Yanzu dai ga Ma’aruf Allah ya bayyana mana shi kuma in sha Allah dik muguntar mugu da k’ullin mai k’ulli bazai sake kama jikana ba... Jeki ki tafi can da k’uncin rayuwarki ki....” Batakai aya ba Ya Abidah ta katseta da fad’in “Dama muguntarsu bai tab’a tasiri akan Ma’aruf ba ko sau d’aya ne kaman yanda sukai tunanin yayi... Kaman yanda sukai tunanin ya tafi tafiya ta har abada da bazai kuma dawowa ba.... Sannan sirrin da kikeso ki ci gaba da b’oyewa d’anki Usman bazai tab’a b’oyuwa ba muddin za’a warware wannan al’amari....” Mamaki ya cika illahirin jama’an dake wajen idan ka d’auke Engr da har yanzu bai dawo daga duniyar tinanin da yai nisa ciki ba, memory d’insa ne kawai take flashing back... Hotunan abubuwa sunata dawowa kwanyarsa... Mamani ta dubi Abbah tace “Alk’ali kada ka saurari matar nan... Na rok’i arzikinka kaji d’ahna....!” Ta k’arashe tana k’ok’arin kamo hannayensa.... Girgiza kai Abbah yake cikeda d’imauta lokaci guda yake furta “A’a Mamani.... Inaso naji abinda matar nan zatace....” Juyowa yai yana duban Ya Abidah lokaci guda yake furta muna saurarenki....” Ya Abidah ta jinjina kai kana taci gaba da fad’in “Banso kukaji wannan daga bakina ba, amma ku sani dole ce tasa zan amoda wannan Sirri da ya jima a rufe...” K’irajai sukaci gaba da bugu.... A yayinda Ya Abidah taci gaba da fad’in “Kaman yanda kuka sani nida ‘yar uwata Mariya bama ga maciji, na mata iyaka da kaina, na kumayi iyaka ma kaina da ita da yanda take rayuwa dama duk wani wanda ya jib’inceta.... Saidai hakan baisa na kasa cika alk’awarinda na d’aukawa mahaifiyarmu ba cewa nid’in zan kula da ahalinmu bayan babu ita a raye.... A lokacinda Mariya tai aure taci kuka sosai na rashin ‘yaruwarta wacce take magajiyar mahaifiyarta a tareda ita... Kun sani Babbar Ya itace tamkar mahaifiya a lokacinda babu mahaifiya.. Ban halarci aurenta ba, haka ban taka yanda take ba... Kuma ita batada ikon takowa yanda nake.... Harta Bara’atu da Dumba duk saida nai masu iyaka da Mariya matuk’a sun zab’i zama dani... Basu d’auki hud’uba ta ba dikda cewa Sun nuna min sunyi na’am da hukuncin da na gindaya masu.... Hakan sosai yake ci masu tuwo a k’warya musamman Dumba wacce suka taso tareda Mariya tamkar k’awaye, a b’oye sukan fita su tafi gidan Mariya bada sani na ba, hakan yasa basu yanke alak’a kwata kwata da ita ba kaman yanda na umarcesu... D’an fasalai taja kad’an kana taci gaba da fad’in “Wata rana kwanta bacci nai mafarki da mahaifiyarmu tana kuka tana cewa na kasa rik’e mata amanan zuri’arta... A mafarkin nima Ina kuka Ina sanar da ita cewa Mariya itace taci amanata ta salwantar da Zuri’armu... Mama Hajja bata daina kuka tana fad’in bazata tab’a yafe min ba.... Wannan mafarki ya d’aga min hankali sosai, yasa k’iyayyar ‘yaruwata ya kuma tasiri cikin zuciyata, Mama Hajjah ta rasu batasan cewa Mariya ta tsiratar da kanta ta k’yale Fatima da Ma’aruf ta kasa kula dasu kaman yanda ta d’auka min alk’awari.... Koda na sake bacci mafarki na sakeyi Mama Hajja na cemin kece Babba ki kula dasu.... Ranan nayi zurfi cikin tinani na kuma d’au alwashin kula da sauran ahalinmu da suka rage koda ace bazan iya duban idanun Mariya nace na yafeta ba... Koda ace bazan iya kasancewa da ita inuwa guda ba, domin kaw ganin fuskar Mariya ba komai yake haifar min ba face tina iftila’in dana fuskanta had’ida mutanen da na rasa dik ta dalilinta.... Wani rana na tsinci tataunawar Bara’atu da Dumba suna cewa zasu tafi su duba Mariya dan a kwanakin bata gane jikinta... Hankalina ya tashi sosai hakan yasa nabi bayansu a sace har naji dalilin rashin lafiyarta juna biyu gareta, a lokacin tana d’auke da jaririn cikin d’anta na fari.... Koda naji wannan batu gida na koma ba tareda sunsan cewa na fita naji tattaunawar su da Mariya ba... Koda na dawo gida bayan kwana biyu sai naji inason na san halinda ‘yaruwata Ke ciki.... Na d’auki mayafi nayi nad’i irinta buzaye ta yanda babu mai gane kamanni na, na fice na nufi gidan Mariya.... Nan ma lab’ewa nai ina hangota daga tsakar gida tana gudanar da aikace aikacenta.... Shigarta d’aki da wuya kishiyarta Lami ta fito tana ‘yan waige waige tamkar maras gaskiya, ni kuma koda naga haka jikina sai ya bani akwai abinda wannan matar take k’ullawa, bansan mijin Mariya ya k’ara aure ba dik a tinanina Mariya ita kad’aice ashe mahaifiyarka ta tilasta maka auren Lami bayan Mariya ta shafe shekara guda tak a gidanka babu koda b’atan wata...” Abbah ya jinjina kai cikeda al’ajabi domin kaw anyi haka, Mamani ita ta tilasta masa yima Mariya kishiya dan kawai ta shekara gidan miji babu juna...... Ya Abida taci gaba da fad’in “Hakan yasa mafarkin da nai da Mama Hajjah ya shiga dawowa kwanyata cewa na kula da ahalinmu.... Ana a haka naga Haule matar Alhaji d’an uwanka ta fito daga d’akin Lami suna k’usk’us suna cewa ta shige d’aki mu cika aiki.. Shegiya mai shegen munafunci da iyayi ita a dole ga matar so.... Malam yace wannan biso idan muka bisne a k’ofar d’akinta hardai yana cikin k’asa bai fito ba toh kuwa tabbas bazata haife abinda Ke cikinta ba saidai ya mutu a cikin cikinta amma bazai tab’a fitowa duniya ba kaman yanda wannan laya yake bisne a k’ofar d’akinta... Suka kuma sakin shewa had’ida tafe hannaye a hankali.... Lami taceda Haule maza ta fito tai mata rakiya kafin wani ya gansu... Jin haka yasa na kuma b’oyewa har suka fice... Naga wajen da sukai bison jikin d’akin Mariya, daga nan fitowa nai ina k’ok’arin ficewa a sad’ad’e na b’ata hanya... Toh fah a nan ne na kuma karo da wani tashin hankalin wanda ya tabbatar min cewa tabbas Rayuwar Mariya na cikin had’ari babba bama ita kad’ai ba harda kai Usman da jairinku dake cikin Mariya... Alhaji d’an uwanka da matarda ka girma ka santa a matsayin mahaifiyarka su na hango suna tattaunawa wata muhimmiyar magana da alama basuso kowa yaji kuma shakka babu naji sun ambaci Mariya da mijinta...Jikin yai sanyi sosai da ganin irin rayuwar da ‘yaruwata Ke ciki... A haka na koma gida Ina tinanin al’amarin... Washe gari na kuma b’adda kama ba tareda sanin kowa naje na toni wannan laya na canza da wata layar....” Jikin Aunty Lami yaci gaba da tsuma maganar Malam ya fito cewa ABU A DUHU, dama ya sanar dasu muddin aka samu tangard’a wajen bisne wannan layar toh fah za’a haifo cikin kuma itama Mariya bazata mutu ba, sannan dik wani shirin da zasuyi bayan wannan haske bazai tab’a bayyana masu ba, sunyita cin karo da Abu a duhu, Wato ashe dai wannan mata ita ta toni wancan layar tasu... Muryar Ya Abidah ta sinkayo yanda taci gaba da fad’in “Koda nazo fitowa a sace na kuma cin karo da Mamani da kuma Baba Alhaji suna tattaunawa wannan karon tamkar shi yake tsoratar da ita, da alama D’an nata yasan wani Sirri nata da bataso kowa ya sani... Lab’ab’awa nai na saurari abinda suke fad’i wanda yai matuk’ar bani al’ajabi Mamani rok’on Alhaji take tana fad’in “Alhaji ka bar zancen nan a nan Usman bazai tab’a sanin ba nice na haifesa ba domin kaw mahaifiyarsa ta jima da rasuwa kuma shid’in d’ah na ne....” Alhaji ya kuma b’allawa Mamani harara kana yace “Kin jima kina ci mun fuska akan Usman, ni ne d’anki na asali amma kin d’auki soyayyar duniya kin basa, gabaki d’aya dukanmu ‘ya’yanki babu wanda kike masa soyayyar da kikewa Usman... Yanzu tinda matarsa ta sami juna biyu hankalinki ya kuma karkata kan Usman da iyalinsa...” A hasale Mamani tace dashi “Toh naga kai dik matar daka aura sai wannan jarabebbiyar matar taka ta koreta... Ni ba matar Usman nake so ba jikana dake cikinta nake so zan kuma bata dik wani kulawa da take buk’ata muddin jikana na cikin jikinta...” Baba Alhaji ya jinjina kai yace “Ni kuma na miki alk’awarin koda an haife wannan ciki sai na salwantar dashi, kuma baki isa kiceda Usman komai ba, dan wllhi kinji na rantse idan har kikai yanda yasan inada alhakin b’acewar d’ansa toh sai na tona miki asiri sai na sanar dashi cewa mahaifiyarsa ta jima da mutuwa kuma kece silan mutuwar ta... Bazai yuwu Usman yafini nasara a rayuwa ba....” Ya Abidah ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Ga tsananin mamakina kuka naga Mamani tanayi tana rok’on d’an nata kada ya tab’a sanar da Usman cewa ba ita ta haifesa ba domin kaw mutuwa zatayi tabbas idan ta rasa soyayyan d’anta Usman.... Tabbas basuyi zaman dad’i da mahaifiyarsa ba amma tana jin k’aunar d’an data rasu ta bari tamkar ita ta haifesa.... Sannan k’annensu gaba d’aya sunfi k’aunan Usman samada Babban Yayansu Alhaji, Usman ya zamto tamkar uba a gidan tamkar shine magajin Alhaji Mahmood Mailafiya, girma soyayya da komai mashi ake badawa....” Goggo Mairo ta Kazaure dake tsananin kuka ita ta katse Ya Abida da fad’in “Mamani dama D’an Yaya Hurera ya rayu bai mutu ba kaman yanda aka sanar damu dashi da ita duk sun mace... Shin dama naki d’an shine ya mutu... Innalillahi wa innalillahi raji’un...!!!” Sabbin kuka ya ya kaure yayinda Mamani ta kasa d’ago fuskarta sai hawaye masu tsananin d’umi dake gangaro mata.... Ya Abidah taci gaba da fad’in “Wannan ne dalilin da yasa Alhaji ya tsani d’an uwansa Usman da zuri’arsa, Usman d’an uba ne a wajensu da ya d’auke soyayyar mahaifiyarsa da kuma ‘yanuwansa da suke uwa d’aya uba d’aya daga gareshi, hakan yasa yaji duk duniya baida mak’iyi kaman Usman kuma baida buri da ya wuce yaga Usman ya rayu cikin k’unci.... Mamani na hawaye a wancan lokacin taceda Alhaji taji ta gani tabbas bazata ce komai ba amma kada ya tab’a sanar da Usman wannan sirri nata domin rasa Usman na nufin rasa rayuwarta ne.... Wannan rana hankalina ya tashi sosai da jin wannan batu... Tin daga wannan rana Babu wanda yasan cewa ina bibiyan al’amran Mariya, duk wani shirin asiri da su Haule suke ina lalaltawa hakan yasa asirinsu bai tasiri akan Mariya saidai bokansu yace dasu *Abu a duhu* ba kowa yake b’atawa ba illa ni Abida .... A lokacinda aka haifi Ma’aruf nasan wad’annan azzalumai bazasu k’yale Mariya da d’anta ba tinda sun lashi takobin ganin bayansu nima sai na d’aura d’amaran wargaza dik wani shirinsu... Hakan ya hana Bokayensu ganin haske Saudi abu a duhu, wannan dalili yasa su Haule suka razana matuk’a da hidiman Mariya sukai tinanin tanada wani shirin da yafi nasu k’arfi.... Ganin bazasu daina jifarta da asiri ba yasa na yanke shawarin Bara’atu ta koma wajen Mariya da zama tinda ita Allah yayita mafad’aciya maras sanyi da tsoro ba kaman yanda Mariya ta kasance mafi sanyin hali a cikinmu ba.... Na kuma gargad’i Bara’atu cewa ta saka ido kan zaman da Mariya take a gidan mijinta da mutanen da Allah ya k’addara mata zama tare dasu.... A haka Bara’atu ta karanci Lami ta karanci duk wani wanda ke tareda Mariya... Su Lami da Haule basu daina jifar Mariya da d’anta Ma’aruf da asiri ba, dik asirin da sukai Bara’atu zata sanar dani zan kuma San hanyar da zamubi mu warware..... Kwatsam Mariya ta kuma samun ciki sannan har wannan lokaci basu daina jifarta da d’anta da muggan asirai ba, hakan yasa Bara’atu cewa anya bazamu d’auke Mariya daga wannan gida mai tarin had’ari a gareta ba dashike lokacin suna zama ne duka gida guda gidan marigayi Mahmood Mailafiya... Duban Bara’atu nai kana Nace “Bara’atu bazamu raba Mariya da mijinta da d’anta ba ga kuma wani rabo ya kuma knno kai, mai yuwa farin cikin Mariya yana a cikin wannan ahalin ne.... Abunda zamuyi zamu b’ullo musu ta hanyar da basu tsammani bane bazamu bari suci gaba da cutar da ‘yaruwarmu da ahalinta ba.... Bara’atu tace min toh ya zamuyi Yaya ga tsohon ciki a jikin Ya Mariya kuma ko sati bamu jima da kwance k’ullin da suka bisne k’ark’ashin bola ba wanda aka linke takarda da harufan sunan Ma’aruf har sau uku dashi... Tabbas wad’annan mutane bazasu k’yaleta da d’anta ba, ga kuma wani rabon na zuwa... Ina tsoro kada a haifosa a wannan duniya mai kewaye da tarin miyagun mugaye... Duban Bara’atu nai nace ta bani kwana biyu zansan yanda zan b’ullowa al’amarin.... Toh fah daga nan ne na tashi na tafi na samu Mamani... Sosai Mamani taji tsoro da mamakin cewa nasan sirrinta da bataso ya isa kunnen Usman har d’anta yake razaninta dashi.... Zama nai nace ta sanar dani gaskiya idan ba tanaso na tona wannan sirriga Usman ba... A haka Mamani ta sanar dani cewa Usman d’an mijinta ne marigayi, mahaifiyarsa auren zumunci akai mata da Mahmood Mailafiya, tabbas sun zuba kishi sosai a lokacinda suke tare matsayin kishiyoyo, koda aka auro mahaifiyar Usman sai Allah ya basu RABO a tare dikda cewa Mamani akwai d’anta Babba mai shekaru uku shine Alhaji.... Haka nan sukai goyon cikinsu tare tare kaman masu haifan tagwaye, wani ikon Allah wata haihuwarsu d’aya sannan Allah ya nufa suka haihu rana d’aya, toh abinka da zamanin wancan lokaci da ba damuwa da zuwa asibiti akai ba ungozoma guda ta karb’i haihuwarsu su duka biyu a gida, Allah mai yanda yaso sai ita mahaifiyar Usman Allah yai mata cikawa ya raya d’anta ita kuma Mamani Allah ya karb’i nata d’an ya kuma rayata... Allah kenan mai yin yanda yaso babu kuma wanda ya isa ya tambayesa dalili domin kaw shid’In buwayi ne gagara misali.....Ya raya wanda yaso ya kuma kashe wanda yaso... Toh nan ne Mamani ta amshi d’an Hurera data rasu ya maye gurbin nata d’an da shima ya rasu, ta shayar da Usman matsayin d’anta... Yayinda kowa yai zaton cewa Harira da d’anta gaba d’aya suka rasu... Bayan ita Ungozoma d’in data san wannan Sirri babu wanda ya sani harta Alhaji Mahmood bai sani ba, bayan wasu shekaru Ungozoma d’in taso su sanar da Alhaji Mahmood wannan batu amma fur Mamani tak’i tace Usman D’anta ne kuma babu wanda zaisan wannan Sirri akai rashin sa’a d’anta Alhaji ya lab’e yaji tattaunawarsu, Toh nan ne tsanarshiga Usman yai k’amari tinda yaji cewa ashe shid’in bama d’an mahaifiyarsu bane amma tafi fifitashi sama da sauran ‘ya’yanta sannan soyayyar da take masa har ya shafi d’ansa Ma’aruf gashi shi koda Haule ta samu cikin d’anta na fari Hafiz batai d’aukinsa ba sannan bata masa soyayyar da take wa Ma’aruf... Hakan yasa Baba Alhaji da matarsa Haule suka dad’a tsananta k’iyayyarsu kan wannan yaro Ma’aruf... Na dubi Mamani nace nasan bakiso wannan Sirri naki ya isa ga Usman, kuma nasan kina k’aunar jikanki Ma’aruf baki k’aunar abinda zai samesa... Mamani ta jinjina min kai tace hakane... Na numfasa kad’an kana nace idan haka ne inaso mu k’ulla wani aminci na sirri.... Tace dani kaman yaya kenan...? Nace da ita inaso ki sanar da d’anki cewa lokaci yayi da zai kawar da Ma’aruf.. Kin yarda ya kawar da Ma’aruf amma da sharad’i... Sharad’in shine zai k’yale Usman da sauran zuri’arsa da zai haifa nan gaba shida iyalinsa su rayu cikin aminci... Da mamaki Mamani ta dubeni kana tace bazata iya bari tanaji tana gani a halak’a Ma’aruf ba, zata iya basa rayuwarta... Nace da ita kaman yanda zaki iya basa rayuwarki toh haka nima zan iya basa tawa rayuwar.. Ki bar min ragamar komai nai miki alk’awari ni kuma bazan bari su salwantar da Ma’aruf ba... Zan sa yai nesa da wannan duniyar da aka jima ana farautar rayuwarsa.... INDA RAI wata rana zai kuma dawowa cikin rayuwarki bayan ya kub’uta daga sharrin wad’anann azzalumai.... Abu guda zaki min shine kisa d’anki ya yarda da sharad’in da zaki gindaya masa cewa zai k’yale Usman da sauran iyalansa su rayu cikin aminci... Kinga daga nan bamuda sauran damuwa... Ma’aruf yayi nesa dasu sannan zasu k’yale ‘yar uwata da ahalinta su rayu cikin aminci babu zullumi da d’ar d’ar d’in cutarwa...” Sosai Mamani taci kuka jin bazata rayu tareda Ma’aruf ba amma hakan yafi mata idan har zai tsira daga sharrin Baba Alhaji wanda batada ikon magana akai sakamakon babbar makamin da yake dashi na sanin sirrinta... Na fad’a mata tin a wancan lokacin zan rufe sirrinta amma tabbas INDA RAI wataran wannan sirrin zai hak’o kanshi ya bayyana kanshi... Muka samu matsaya da Mamani akan haka, daga nan ni kuma na sami ‘yaruwata Bara’atu nace tasan yanda zatai ta sami yardarsu Haule ta nuna masu itad’in tana taredasu d’ari bisa d’ari za kuma ta taimaka masu su kawarda Ma’aruf.... Hakan kuwa akai Bara’atu ta sami su Haule ta sanar dasu tasan basu k’aunar Mariya kuma suna iayaka k’ok’arinsu ganin sun sabautar da ita da ahalinta, toh asiri dai baya tasiri akan Mariya dan Mahaifinsu yanada wani lak’ani kuma ma ita d’aya ya bayar shiyasa asiri baya kamata, shiyasa dik asirin da suke mata bokayensu Ke sanar dasu basa ganin komai saidai ABU A DUHU... Da shike Allah yaso b’atar masu da tinani sai suka yarda cewa Mariya tanada wani shiri na musamman shiyasa asirinsu bai tasiri akanta da d’anta abinda zasuyi su jefata cikin k’unci shine su kawar da Ma’aruf a doron k’asa... Hakan shine kawai zai k’untatawa Mariya... Koda su Haule suka tamabayeni maiyasa ina ‘yaruwarta zasu yarda su had’e kai da Bara’atu ta zamto Aminiyar su ta sirri sai ce masu tai sabida Mariya itace sanadiyar rugujewar ahalinsu fansa zata d’auka ma ahalinta da suka rasa ta sanadiyar Mariya... Da wannan batu su Haule suka yarda da Bara’atu... Mijin Haule ya sami Haule da batun ya bata wuk’a da nama ta kassara rayuwar Ma’aruf... Haule ta kuma jin dad’i dan ita da mijinta shafi guda suke... Bara’atu tazo ta sameni da batun su Haule suna yunk’urin kassara Ma’aruf daga nan ni kuma muka shirya yanda zamu fitar dashi cikin duniyar da ake k’aunar ganin bayansa.... Da fari mun yanke shawarin Dumba ta tafi dashi can k’asar Mali yai nesa da gida har Allah ya kawo sanda zai dawo don munyi imani INDA RAI DA RABON watarana zai kuma dawo mana... Daidai nan Bara’atu ta cab’i zancen da fad’in “Mun shirya had’uwa dasu a kasuwa yanda na tabbatar masu matar da zan bata Ma’aruf ‘yar k’ungiyar shan jini ce.... Kuma Ma’aruf zai fice a rayuwarsu har abada... Sun yarda dani Sun yarda duk zan aika abinda nace.... A kasuwa na janye hannun Ma’aruf da sauri sanda ake k’ok’arin kawo d’aukiwa Mamy sakamakon haihuwa da yazo mata... A tasha na had’uda Dumba na damk’a mata Ma’aruf sai kuka yake... Nima zuciyata ta karaya... Tsugunawa nai na rungumesa kana nace INDA RAI DA RABON mu sake had’uwa Ma’aruf d’ahna... Na rok’i Dumba kan cewa ta kula dashi da kyau.... Dumba tace dani itama Ma’aruf d’anta ne kuma zatai duk yanda zatai taga ya samu rayuwa mai kyau da inganci... In sha Allahu Allah zai raya Ma’aruf. kuma INDA RAI wata ran zai dawo ya fuskanci kurayen da sukai farautar rayuwarsa a lokacinda basuda k’arfin halak’a shi.... Haka muka rabu da Dumba tana rungume da Ma’aruf da har lokacin kuka yake yana ambaton Mamynsa...” Ta juyo tana duban Mamy da hawaye suka wanke mata fuska lokaci guda taci gaba da fad’in “Wannan shine dalilin da yasa na d’aukake ahalinki na kuma sadaukar da rayuwata ga ahalinki Mamy... Na sani da zuciya d’aya muka tseratar da Ma’aruf amma daga baya zuciyata ta kasa aminta da cewa hakan ba babban laifi bane... Na kasa saka ma zuciyata hakan ba zalunci bane mai girma .... Shiyasa nai komai dan naga kin kasance cikin Farin ciki... Shiyasa ban tab’a rabuwa dake ba... Sabida girman laifin da na aikata a gareki ‘yaruwata....” Ta k’arashe tana mai duk’awa saman gwiyoyinta gaban Mamy wacce ta kasa tab’uka komai sai hawaye... Wajen yayi tsit duk wanda yace bai zibda hawaye ba yayi k’arya.... Abbah ma kasa tab’uka komai yai sai jin abubuwan yake tamkar a shirin film, ta ya Mamani zata b’oye wannan babban al’amari a gareshi... Ai girman mahaifiya ta wuce wasa... Ya cancanci yasan wacece mahaifiyarsa ta asali.... Ya Abida ta isa ta d’ago Aunty Bara’atu, hawaye na gangaro mata take girgiza kai tana furta “Idan da mai laifi ba Ke bace Bara’atu... Tabbas nice mai laifi... Shin na aikata haka ne domin ‘yar uwata ta d’and’ani abinda naji na rashin d’ah ko kuwa na aikata hakane dan ina tsoron kada na kuma rasa wani d’a a karo na biyu... Ina tsoron kada watarana makircinsu yai tasiri akan Ma’aruf k’arami... Mariya a yau na rok’eki gafara ki yafe min.... Ki gafarta min ‘yaruwata....!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Sameer dake gefe ne ya share hawayen da suka jik’a masa fuska kana ya k’araso ya d’ago Aunty B ya kuma kamo hannun Yaya Abida ya had’e dana Mamy ya rungumesu gaba d’aya, lokaci guda yake furta “A naku fahimtar kunyi Hakane ne ba don komai ba sai don ku cire Ma’aruf cikin k’ingurumin daji mai cikeda duhuwa da tarin had’ari... Na gode maku gaba d’aya, Allah ya k’addari bazan girma taredaku ba amma cikin rahamar Sa da buwayarsa sai ya kuma dawo dani kama yanda kukace INDA RAI Da RABON watarana na dawo gareku zan dawo... Abinda nakeson ji yanzu shine shin ina Ma’aruf Babba wanda naci sunanshi shin ya akai ya salwanta... Sannan maiyasa aka d’aura alhakin b’acewarsa kan mahaifiyata....?” Wannan karon Mamy ce ta dubesa kana tace “Ni ce zan baka wannan labarin Ma’aruf domin kaw a hannuna Ma’aruf ya b’ace ko nace ‘yan ta’addan suka kashesu shida Fatima....” “Wacece Fatima..?” Sameer ya tambaya Mamy ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Fatima itace d’iyar mahaifiyarmu k’arama, kaman yanda na sanar dakai a baya cewa mahaifinsu Soja ne zuwansa Mali ya auro mahaifiyarmu, nida Yaya Abidah acan k’asar Mali aka haifemu bayan mun dawo Nigeria aka haifi Bara’atu da Kuma fatima... Sanda mahaifiyarmu ta haifi Fatima girma ya soma kamata dan lokacin har Yaya Abida tai aure a nan Kano ya auri wani Alhaji Abbas Maidubabe kuma har Allah ya albarkaceta da d’anta k’wara d’aya mai suna Ma’aruf sannan Ma’aruf har ya soma girma dan yakai kusan shekaru shida zuwa bakwai a k’alla... Mahaifin Ma’aruf Alhaji Abbas Maidubabe attajiri ne sannan yana yawan tafiye tafiye na kasuwanci zuwa mak’wabtan k’asashe a wancan lokacin.... Mukan taho nan Kano hutu wa Ya Abida daga can Jada garin mahaifinmu.. Wata rana munzo mata hutu ta daga zata bimu Jada taga gida sannan takai Ma’aruf ma yaga garin mahaifiyarsa, dad’ida k’ari ga mahaifiyarmu data kusa haihuwa ko yau ko gobe... Da k’yar Alhaji Abbas ya amince kan cewa ta tafi taredamu musamman da shike harda d’ansa Ma’aruf a tafiyar, yaron da ya k’wallafa ransa akanshi sabida shi kad’ai Allah ya bashi ga girma da ya soma kamashi... Ma’aruf shine magajin shi shine sanyin ianiyarshi shine yake d’aga ido ya kalla yaji sanyin cewa ya haye gorin ‘yanuwansa da suka addabeshi a baya cewa shid’in shine bai haihuwa dan dik matar data aureshi k’arshe tafiya take ta k’yalesa muddin tana son haihuwa. Ashe RABON shi na tareda Ya Abida... Wani zuwan shi Jada sunkai kaya ya ganta ya aureta har Allah ya azirtasu da Ma’aruf, kuma tin daga kan Ma’aruf shikenan ko b’atan wata bata sake ba.... Kaman yanda na fad’a maku cewa mahaifinmu Soja ne, yayi yak’i yasha fama sosai da miyagun ‘yan ta’adda, ashe suna yunk’urin kafawa mahaifin mu tarko ganin shid’in jajirtacce ne akan aikinsa.. Ya kafa masu k’ahon zuk’a ya hanasu sakat... A ranar da muka iso gida Washe gari suka shigo har cikin gidanmu suka kashe mahaifinmu, ga mahaifiyarmu da tsohon ciki... Haka muka fita a fujajan Muna neman hanyar tsira ganin muma sun nufomu suna yunk’urin kashemu... Da k’yar muka samu muka b’uya basu ganmu ba, dan dama koda sukazo kashe mahaifinmu saida ya tabbata yayi yanda zamu samu tsira tinda yasan shi suke farauta.... Tashin hankali maras misaltuwa muka shiga, da k’yar muka samu muka isa asibiti sabida mahaifiyarmu da har ta soma zuban jini... Kan kace mai akace saidai ai mata aiki a cire abindake cikinta... Hakan kuwa akai... Koda mahaifiyarmu ta farka sunan mahaifinmu kawai take kira tana fad’in sun kasheshi, ganin mahaifiyarmu haka ya kuma karyar mana da zuciya.... tashin hankali dai da ba’a saka mata rana., A haka mahaifiyarmu ta barwa Yayarmu Abidah Wasiya cewa ta kula damu ko bayan babu ita dan tanaji bazata tashi ba... Haka Ya Abidah taita kuka tana sanar da ita cewa in sha Allahu zata tashi kuma zamu tsira gaba d’aya... Ita dai mahaifiyarmu bata daina cewa ta kula damu ba.... Ta tabbata mun tsira daga hannun wad’ancan azzaluman... Kud’in asibiti ya k’are mana ga mahaifiyarmu kwance babu lafiya ga shi k’anin mahaifinmu da ya rage mana shima ba wani k’arfine dashi ba, uwa uba a wancan lokacin babu hanyoyin sadarwa masu sauk’i na zamani balle Ya Abidah ta sanar da maigidanta halnda ake ciki... Gashi k’wakk’waran motsi bamu isayi ba dan idon ‘yanta’addan akanmu yake... A haka Allah yaima mahaifiyarmu cikawa..!!” Wannan karon kowa ya tsane hawayen da ya gangaro masa, Mamy taci gaba da fad’in “Toh daga wannan lokaci Baffah Kawure yace mu tafi muyi nesa da ahalinsa kada laifin d’anuwansa ya shafesa... Dan da k’yar ya yarda ya amince suka tsaya shida Ya Abida dan ganin anyiwa mahaifiyarmu sitira an kaita makwancinta na gaskiya... Sanin cewa nemanmu ake ruwa a jallo yasa nace Yaya ta bari mud’in mu fara gaba nida Dumba da kuma yaran gaba d’ai Bara’atu, Ma’aruf saiko ‘yar jaririyar k’anwarmu, sosai Yaya Abida tamin kashedin cewa na kulada Ma’aruf da Fatima... Nai mata alk’awarin cewa zan kula dasu da yardar Allah kuma bazan bari wani abin ya samesu ba... Muka fito a fujajan muka nufi tashan mota jaririyar tana goye bayana yayinda hannuna ke rik’eda Ma’aruf... Ashe basu bar unguwar ba akan idonsu muka fito zamu gudu, ganin haka yasa naceda Dumba mu raba hanya dan mu b’atar da tinaninsu, Dumba ta rik’e Bara’atu suka soma gudu yayinda nima na rik’i Ma’aruf muka d’au wata hanyar ga jaririya Fatima a bayana... Da k’yar muka samu muka isa tashar mota... Bayan motoci sun tashi ashe suna biyedamu saida mukai nisa da tafiya kana suka tsaida motar da muke ciki, nan na hangesu sai lek’en motoci suke suna neman mace mai goyo da yaro.... Ganin haka yasa na razana sosai, na kwance Fatima na mik’ata hannun Ma’aruf nace su b’oye k’asan kujera kunsan manyan motoci irin na da har sai mutum ya zauna k’asan seat ma... Yayinda suka umarce duk wani wanda Ke cikin motar ya fito.......suka turamu daji da alama basu gane ina d’aya daga cikin mutanen da suke nema ba kuma basuga yaro da goyo a tare dani ba... Babban tashin hankalin da na tadda bayan sun sakomu daga dajin shine babu Ma’aruf babu Fatima a mab’oyar dana b’oyesu....Ta k’arashe cikin wane irin sauti mai ban tausayi... “Jama’an dake wajen suka tabbatar min ‘yanta’addan sunyi awon gaba da wasu tsirarun mutane dake cikin motar kuma ga dikkan alamu sun kashesu.... Hakan na nufin iftila’in ya ritsa da Ma’aruf da kuma Fatima...” Ji yayi bakinsa ya bud’e ya soma kwararo bayanai tin daga lokacinda ta b’oyesu k’asan kujerar motar hannunsa rungume da jaririyar... Cikin tsananin mamaki da al’ajabi had’ida rud’ani illahrin jama’an dake wajen suka maida dubansu gareshi.... Idaniyansa sunaci gaba da zuban ruwa yaci gaba da fad’in “A lokacin da kika tabbatar Ma’aruf da Fatima sun samu mab’oya mai kyau tsoro da firgici had’ida tashin hankali ya sanya Ma’aruf ya fice a guje rungume da Fatima, babu wanda yaga wulk’awarsa sai gudu da yake falflawa cikin k’ungurumin daji rungume da jaririyar... Ma’aruf bai tsaya ko ina ba sai tsakankanin wasu duwatsu da yake tinanin Sun tsira kenan daga azzaluman mutanen.... A wannan tsakankanin duwatsu wani bawan Allah ya tsincesu har suka zama ‘ya’ya a gareshi...!” Yana ida fad’in haka ya d’ago fuskarsa da ya jik’e sharkaf da zufa ya kuma gauraye da hawaye yana mai bin illahirin mutanen dake wajen da kallo d’aya bayan d’aya har saida idanunsa suka sauk’a kan matar da ta kasa daina takowa izuwa gabansa cikin wane irin yanayi mai ban tausayi.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *92* *©️Sameena Aleeyou....✍🏽* *Beautiful Comments everywhere.... Masha Allah😍🥰 Sameena na maku fatan alkhairi a dik yanda kuke....🤝* Kasa furta komai tai sai takowa izuwa gabansa da take, fusakar k’aramin yaron shi yake gizo a idanunta... Rayuwarsu yana k’arami shi take hangowa... Shin ta yaya zata mance wannan fuska, fuskar da kullum take kwana ta tashi da ita cikin idon zuci... Ma’aruf, Ma’aruf take gani gabanta... Tabbas shi d’in ne... Gashi nan da gaske a gabanta, tanaso ta tab’a fuskarsa ta tabbatar hakan ba d’aya bane daga cikin mafarkan da take... Allahu Akbar, Mai Rai baya cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa... A haka ta k’araso har gabanshi su duka biyun duban juna suke cikin wane irin shauk’i mai ban tausai, hannayenta suna matuk’ar rawa take k’ok’arin d’agowa kana ta shiga shafa fuskarsa har lokacin bata iya furta koda kalma ba sai kallonsa da take da idaniyanta da suka matuk’ar raunana.... Shid’inma dubanta yake idaniyansa basu daina zuban ruwa ba... Da gaske dai itace a k’wayar idanunsa... Tabbas what he went through as a child wasn’t easy... The traumatic experience da yai going through yana k’arami shi ya tafiyar da tinaninsa yasa ya mance komai, amma wannan fuska jigo na rayuwarsa da kaman yanda sunansa bai b’ace masa ba bai tinanin wannan fuskar ta b’ace masa na har abada... Mamy da Aunty Bara’atu na hawaye suka dubi juna cikin wane irin shauk’i suna mai kuma duban wannan buwayar Ubangiji da suke kallo na aukuwa a gabansu, Allah sarki tabbas INDA RAI toh fah akwai RABO, bayan duka wad’annan shekarun yau ga Ma’aruf ya dawo garesu, ga Ma’aruf Babba ga kuma Ma’aruf k’arami, kai lallai Allah mai lullub’e bawansa da tulin Rahamoninsa ne, bayan cire tsammani sama da wad’annan tulin shekaru yau saiga Ma’aruf Allah ya dawo masu dashi garesu, family d’insu sun kuma had’ewa waje guda, bayan tilin iftila’in da suka fuskanta, bayan sab’ani da rashin fahimta da yai tasiri cikin rayuwarsu yau gashi komai ya bayyana masu, komai ya fito sarari....Which of the favors of your Lord will you deny...! Cikin rawar murya take k’ok’arin ambato sunansa har lokaci bata daina shafa fuskarsa zuwa k’irjinsa da hannayensa ba, dik yanda hannunta ya sauk’a ajikinsa bin hannun nata kurum take da kallo tana mai tabbatarda cewa Eh shid’in ne dai gashi nan gabanta, ba gizo bane yake mata... A haka hannayenta suka iso izuwa yatsun hannunsa lokaci guda ta d’ago yatsun hannayen nasa tana dubawa, idanunta suka sauk’a kan d’an wani mark k’arami dake a cikin hannunsa wanda yake exactly irin na mahaifinsa ne, kuma tin yana k’arami shima yanada wannan tabo...Take taji wani irin kuka yazo mata mai k’arfin gaske, zuciyarta ta gama raunana, k’arfin jikinta yai rauni, k’afafunta suka gaza d’aukanta lokaci guda ta fad’a jikinsa tana wani irin kuka mai ban tausai.... Take Engr ya rungumeta sosai shima yana cazgan kukan da tinda yazo duniya bai tab’a irinsa ba... Allahu Akbar gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen sai suka zamto masu tamkar tv, kowa hawaye ne kurum Ke gangaro masa mai gauraye da murmushin Farin ciki had’ida tarin al’ajabi... Harta su Haule saida jikkunansu ya sanyaya... Tabbas yau d’in sun yarda da K’udurar Ubabgiji ta wuce gaban wasa, buwayarsa ya wuce gaban tinanin d’an Adam... Akwai darussa mai tarin yawa a rayuwar wad’annan bayin Allah... Abida tayi sadaukarwa ga ‘yar uwarta Mariya, ta kuma fidda d’anta daga cikin ramin da azzalumai suka hak’a dashike da zuya d’aya tai hakan sai gashi Allah yaji k’anta ya dawo mata da nata d’an gareta.... Tabbas wannan ya isa ya zamto izna da ishara ga masu hali irin tasu, mu kasance masu yad’a soyayya sama da k’iyayya, mu kasance masu sadaukarwa a duk lokacinda mukeda ikon yin hakan, Allhairanmu Sufi sharrinmu yawa, tabbas idan muka rik’e wad’anann bazamu tab’e ba da izinin Ubangiji.... Ya Abidah kuka take sosai tana k’ank’ame da Engr yayinda shima Engr d’in ya kasa sakinta, sosai shima ya k’ank’ameta yana kuka tamkar ba shi d’inba... Allahu Akbar yau ina Babansa yaga wannan rana mai tarin alkhairi a garesa.... Cikin murya irinta mai kuka take furta “Ma’aruf d’ah na.... Ma’aruf ka dawo.. Ka dawo gareni.... Da gaske kaine ba mafarki nake ba.... Da gaske kaine nake rik’e dakai yau.... Da gaske bazan farka daga wannan mafarki ba.....!!” Kuka ya kuma cin k’arfinta... Cikin kuka shima Engr yake jinjina kai yana mai furta “Ammmah nah.... Ni ne da gaske ni ne.... Ni ne Ma’aruf d’inki.... Ba mafarki kike ba ni ne right in front of you... Ubangijinmu ya cika Rahamarsa a garemu, Ya sake had’amu bayan wasu shekaru... Bayan na mance rayuwar da mukai a baya, bayan na mance komai gameda ahalina.... Amma Ke d’in jigoce da zuciyata da ruhi bazasu tab’a mancewa ba, randa dik sukai arba da kyakkyawar fuskarki dole su tina hakan.... Ammah na tino komai... Kallon fuskarki ya maidoda tinanin yaron da ya b’ace sama da shekaru talatin da bakwai baya...!” Zuciyoyi suka kuma raunana... Allah Akbar abin godiya, baka jin komai wajen sai sautin fitar kuka daga can k’asan zukata.... Lallai wannan ahali yau rana ce mai matuk’ar mahimmanci a garesu... Daula data fito dan tambayar ta ina zatai alwala dan already magrib ya sako kai, tin bayan sallan la’asar ake gudanar da wannan warware warware basu suka ida warwaran ba sai goshin sallan magrib, abubuwa da dama ne suka auku tsakanin sallan la’asar da kuma sallan Magrib.... Ganin mutane cirko cirko yasa Daula shan jinin jikinta har sai take tinanin dama bata fito ba ashe, sam batai tsammanin ganin mutane haka a tsakar gidan ba dikda cewa gida ne na biki amma batai zaton ganin manyan mutane haka ba harda maza, kuma ya dukkan alamu mihimmin abu suke tattaunawa, ga wani irin yanayi da d’aukacin fuskokinsu Ke ciki..... Har tasa kai zata juya ta hango wani tamkar Yayanta rungume da wata mata yana share mata hawaye., Yanayin data gansa ciki bata tab’a ganinsa cikin irin yanayin ba tsawon shekarun da sukai tare.... Jiki a matuk’ar sanyaye Daula ta soma takowa tana mai bin jama’an dake wajen da duba a matuk’ar d’arare... Toh lafiya... Badai wani abin bane ya sami Khalid ko Daddy tinda tasan hakan ne kawai zai kawo Yayanta gidan sirakan Khalid... Toh amma tambayar anan shine wacece Matar da Engr Ke rungumeda ita ya kasa sakinta.... “Yaya...!” Ta furta tana mai dubansa jiki a sanyaye sanda ta k’araso garesu... Sai sannan Ya Abida ta karkato tana duban wacce tai magana sakamakon sinkayo murya irinta mahaifiyarsu da tai, su Mamy da Bara’atu bugun zuciyarsu ya kuma k’aruwa sanda suke kuma dubanta, tabbas sunji da kyau Yaya ta kira Ma’aruf da bai jima da bayyana masu ba.... Kodai hasashensu ne ya zamto gaskiya...? Basukaiga bashi amsa ba sukaga Engr Ma’aruf ya nufeta yana kuma janyo hannunta lokaci guda yake furta “Daula finally... Yau mun had’udasu... Come zo, zo kigani da idanunki.....!” Gaba d’aya kallo guda zaka masa ka fahimci har yanzu Shock d’insa bai sakesa ba dikda juriya da k’arfin hali da yake k’ok’arin nunawa.... Daula da jikinta ya gama sanyi duban Engr take tana duban mutanen da ya kawota gabansu mata guda uku Mahaifiyar Nabilah saiko wasu guda biyu wad’anda kallo guda zaka masu ka fahimci ‘yanuwan juna ne dan ga wani sihirtaccen kamanni da sukedashi.... Ganinsu su uku haka a gabanta take ya haifar mata da wani irin fad’uwan gaba, taji k’irjinta tamkar an sauk’e mata guduma... Kai tsaye bazatace ta tab’a sanin masu irin fuskokinsu ba amma sai tanaji can k’asan zuciyarta kaman sunsan juna tinda jimawa, like they’re connected somehow.... Cikin rud’ani take duban Engr da ya kasa sakin hannunta kana tace “Yaya what is going on here...? Is something wrong...? Wani abu ne ya samu Daddy da Khalid...? Please talk to me...!” Ta k’arashe cikin tsananin nuna damuwa, yayinda Yaya Abida, Mamy da kuma Aunty Bara’atu suka kasa d’auke idanunsu daga barin dubanta.... Wannan tabbas ‘yaruwarsu ce Fatima, domin kaw mahaifiyarsu ziryan suke kallo a gabansu.... Engr kansa kasa furta komai yai sai kallonsu su hud’u d’in da yake yau Allah ya kuma had’asu gaba d’aya... Sameer da sassanyar murmushi ta kasa barin fuskarsa takowa yai kad’an ya tsaya daga gefen Engr wani ikon Allah sai kamanninsu da Engr ya fito k’arara... K’wayan idanunsu yai shige da juna dan irin k’wayan idanun su Mamy suka d’auko... Sai yanzu suke fahimtar abubuwan da sukaji gameda juna had’uwarsu ta fari ashe sud’in tushe ne guda... Abbah dake gefe matsan k’walla ya kumayi farin cikin da yake ciki ya gaza b’oyuwa, dole ne ma ya taya Mariya Farin ciki bayan irin gwagwarmayar rayuwa data fuskanta, a hankali ya silale ya fice sanda zuciyarsa ta shiga tino masa abubuwan da yaji gameda Mamaninsa, babban abinda yafi d’aga masa hankali tana sane da duka wannan ta d’auki karan tsana da tsangwama ta d’aura kan Mariyarsa bama ita kad’ai ba harda Zulfa’u da take jinjira ce a lokacin kuma ba ita ta haifo kanta a wannan rana ba, Mamani bata tsaya a nan ba tasa shima kansa ya dinga ganin laifin Mariya duk da sunan yana biyayyawa mahaifiyarsa...Shin ta ina zai soma d’aukan girman hakkin Mariya da Zulfa’u....Dole ne ya nemi waje ya keb’e shikad’ai, Mariya yau d’in cikin Farin ciki take bai kamata ya aza mata nasa damuwar ba, bayan tilin iftila’in data fuskanta a rayuwa yau d’in ta cancanci farin ciki... A daidai hanyar fita idanunsa suka sauk’a kan Lami dake sanne sannen kai tamkar tsohuwar munafuka... Idanunsu kaw suka sark’e waje guda... Duba guda Abbah yai mata ya d’auke kansa kana yai shigewarsa.... Wani irin k’ugi da cikin Lami yai da ace akwai wani gefenta tabbas da sai yaji wannan sauti... Suna murnan yau zai kansancega Mariya da ‘yaruwarta ranan tozarta ranan bak’in ciki sai gashi ya faru akansu, sai gashi ya juye ya koma kansu, ashe farin ciki mai d’orewa da aukaci burin samu a yau d’in ashe ba nasu bane, wacce suka kafa mata tarkon bak’in cikin ashe itace dai mai samun farin ciki.... Lami taji duniyar gaba d’aya tai mata d’aci...Ji tai inama ana iya maida hannun agogo baya tabbas da ta maida ta gyara kuramuren da tai, tabbas da bata biyema Haule sukai son zuciya ba... Yau wa gari ya waya...? Ita batada tsuntsu batada tarko, ko Abbah bai koreta ba bata tinanin zata iya ci gaba da zama tana fuskantar Mariya da Ma’aruf harma dashi kanshi Abban... Ita ba zuri’a ne da ita a gidan ba balle su kasance tareda ita... She’s all alone now, Tai imani Haule ta jima tana munafunatarta kenan dikda cewa tana nuna mata tare suke aikata komai, ashe tana b’oye mata wasu abubuwan... Sai yanzu ta fahimci nufin Haule na aurawa Ma’aruf d’iyarta Sahariyya Wato ita da mijinta idan Ma’aruf ya auri d’iyarsu su sun tsira ita kad’ai za’a bari a rana.... Lallai Haule ta cika makira butulu....! Tamkar kazar da aka tsamo cikin ruwan zafi haka Lami ta janye k’afufunta ta nufi nata sashen zuciyarta na mata d’aci.... Ga goggonayen Kazaure sai b’alla mata harara had’ida Allah wadar suke har Lami ta bar wajen.... Su Baffah Wada da Baffah Ado kuwa sun kasa aminta da wannan al’amari da ya bayyana kansa yau, koda ace mahaifiyarsu tsananin soyayyar Usman yasa ta rufe sirrin cewa shid’in ba d’anta bane sunaga Ya Usman ya cancanci yasan gaskiyar Al’amari yasan wacece mahaifiyarsa ko dan ya dinga isar da addu’arsa gareta, girman mahaifiya ya wuce wasa koda ace haihuwarsa kawai tai rainonsa da shayarwansa dik na wuyan Mamani amma dikda haka ya cancanci yasan asalin labarin, hakan baikai ya baiwa Mamani dama ta rufe wannan babban Sirri a gareshi ba... Ya Usman mutumin k’warai ne d’an uwa da kowa zai alfahari dashi, shid’in shine katangan family d’insu shine kuma Uba a garesu... Tsananin tausayin d’an uwan nasu ya kamasu, suna gani Baba Alhaji ya rab’a ta gefensu ya fice sim sim cikeda borin kunya... Suma d’in waje suka nufa dan gabatar da sallahn magrib suna fatan su tadda Abbah a masallaci su kuma supporting d’insa a irin wannan lokaci mai matuk’ar wahala a gareshi... Sameer da Engr ma a tare suka fice suka nufi masallaci jama’a ‘yan unguwa sai kawo masa gaisuwarsu suke suna fad’in yau ga his Excellency har unguwarsu kaikace already yaci zab’en ne sabida yanda jama’a Ke tururuwar zuwa gaidashi, har wad’nda basa zuwa wannan masallacin yau saida sukaje... Sameer kaw na taredashi sai sakin murmushi yake yanajin dad’i har k’asan zuciyarsa na kasancewarsa tareda d’an uwansa... A cikin gida kaw banda tafasa babu abinda k’irjin Haule keyi, tabbas da za’a tsaga k’irjin Haule watak’ila aji yanda zuciyarta ke tafarfasa sabida tsananin k’unan zuciya... Ji take tamkar ta k’arasa ta shak’e Mariya da ahalinta gaba d’aya su mutu ta huta da wannan bak’in rana da take gani.... Idanunta suka sauk’a kan Yaya Abida yanda ta had’e ‘Yanuwanta gaba d’ai ta rungumesu gaba d’ai suna hawayen Farin ciki ga annashuwa da annuri da ya kasa barin fuskokinsu.... Haule tamkar zakanya haka take huci tana dubansu yanda kasan zatai tsalle ta wantsalo ta capkosu ta cinye d’aya bayan d’aya haka nan take dubansu, tamkar d’an wasan Dambe a filin kokawa haka Haule Ke bud’e hannaye tana haki tana duban bayin Allahn nan da duniyarsu ta yalwatu da Albarka... Wato Bara’atu da Abida sun cuceta sun jima suna tarwatsa duk wani shirin da take... Idanunta suka sauk’a kan Bara’atu da itace ta munafuncesu ta k’ulla aminci k’arya dasu... Tabbas sai yanzu take ganin wautansu.. (Niko nace Haule ai shi mugunta fitsarin fako ne... Kuma kece dai baki sani ba amma dik kalan asirinki da imani da ‘yan tsubbu da kikai bawa baya tab’a yiwa d’anuwasa bawa abinda Allah bai k’addara masa ba.... Asiri da sihiri gaskiya ne tinda har yai tasiri akan fiyayyen halitta babu wanda yafi k’arfin sammu ko sihiri ya kamasa saidai duk wannan zai faru ne da izinin Ubangiji... Mariya batada wani makari sai Allah data rik’a Wanda yafi k’arfin bokayanku da malaman tsubbunku... Su Haule sai a koma islamiyya a yak’i jahilci idan kinada sauran RABO)... Tasa kai cikeda takaici zata fice dan wani irin haushin mijinta ne ma ya taso mata, wato shima ya munafunceta ne ashe yasan wani sirri da ita bata sani ba, yasan Usman ba d’an Mamani bane amma bai tab’a koda gigin gaya mata ba tsawon shekarun nan da suka jima suna k’ulla makirci tare... Lallai ta yarda namiji ba d’an goyo bane... K’wafa tai tasa kai zata fice dan yau ji take dik wanda ya tink’areta kansa zata huce duk wani takaicinta.... Kaman daga sama Aunty Bara’atu ta hangota zata fice cikin sauri ta k’arasa gaban Haule had’ida shan gabanta, dakakkiyar murmushi saman fuskarta “Haba Haule har zaki fice babu sallama... Akwai sauran buduri fah dan nasan har yanzu bakisan wacece matar Ma’aruf ba... Kuma sai ki tafi babu ko sallama duk irin wannan kwalliya da kika cab’a... Haba Haule ni ce fah AMINIYARKI ta sirri...!” Ta k’arashe tana kuma sakin murmushi kana tace “Ko yanzu Kasuwa ta watse Haule d’ankoli yaci riba... Mariya dai gata nan daram dak’am saidai gani daga nesa ga ‘yanuwanta kewaye da ita, ga d’anta Ma’aruf tareda ita... Bugu da k’ari ga ‘ya’yanta sun samu zaratan Maza na k’warai wad’anda Al’umma Ke alfahari dasu.... Wa gari ya waya yanzu Haule....?....” Ta kuma murmusawa kana tace “Barka da shiga duniyar k’unci Haule, aci gaba da girban shuka na tabbata duk abubuwan da kikaji kika gani yanzu na gaba sai sunfi d’imautaki.... Sai a tanadi ruwan barekata a gefe na rage k’unci....” Ta k’arashe tana mai kuma murmusawa had’ida juya idanu lokaci guda ta d’agawa Haule yatsa guda tace “Chau.... Aminiyar Sirri..!” Haba Haule kaman ta yanki Jiki ta fad’i ta mutu ta huta haka nan taji tsaban bak’in ciki dake cazganta... Tanaji tana gani yanda Mamy da ‘yanuwanta suka cika da farin ciki..... Tamkar wacce ake hankad’ata haka ta fice fuuu tanaci gaba da huci tagajan magajan... Yara Almajirai sai gudu suke a hanya suna kauce mata a tinaninsu mahaukaciya ce sabuwar kamu..... Wani kayan tashin hankalin had’ida mamaki Haule ta tadda gidanta,gungun ‘yan daudu ta gane shak’e a k’ofar gidan ga mai gurmi da garaya na kad’a masu sun nufi cikin gidan ga wata mata tsakiyarsu lullub’eda mayafi, sai tik’an rawa suke suna kad’a kafad’a da kwankwaso suna tururwan shiga gidanta... Mamaki ya cika Haule tai birki tana kallon ikon Allah Mai gurmi kaw bai fasa kad’awa ba... Su Amara da ayarinta dake tsakar gidan suna wak’e Sahariyya da ta fice a hayyacinta tana kuka tamkar ranta zai fice ai birki sukai da nasu shagalin ganin iyayensu Sun faso taro..... *** A can gidan Aunty Bara’atu kaw dik wainar nan da ake toyawa amaren basuda labari, Zulfah ce ma gabanta ya tsananta fad’uwa musamman dataga ango Akram bai kirata ba kuma bataji daga garesa ba gashi Atika ta kira wayan Yusuf taji ko lafiya yafi abinda yafi amma wayar Yusuf bai shiga, itama Atikar dik abin ya soma damunta musamman da sukaga angon Nabilah ya kasa barin gidan, dan koda suka fice da rana rakiya yaima friends d’insa zuwa masauk’i amma gashi yanzu haka ma ya dawo yana jiran Nabilah a parlor.. Haka dai Atika taita bata baki tana cewa lafiya Akram yake in sha Allah.. K’ila dai kan ango ne yai zafi tinda aure ba wasa bane... Da k’yar Nabilah ta kuma ficewa wajen Khalid sai faman ture turen baki take tana fad’in itafah an tak’ura mata... Yusrah tana mata rakiya zuwa k’ofa ta juya tana fad’i k’asa k’asa “A sha love lafiya amaryar Bear...” Harara Nabilah ta galla mata kana tace “Wai bazaki shigo ba kina nufin ni kad’ai zan shiga...?” Yusrah ta kuma k’unshe dariyrta tace “Wa ki rufamin asiri kada oga Bear yai jifa dani ta taga... Kedai Ina wajen su Addah Zulfah idan kun gama...”Bata jira cewan Nabilah ba ya juya a guje.... Nabilah na kiranta inaa Yusrah ko waigowa batai ba ta shige cikin gida abinta.... K’irjin Nabilah yaci gaba da bugawa... Amma Yusrah tasan kan tsiya datace zatai mata rakiya ta koma... Zatai maganinta ne.... Ta d’aga kai ta dubi k’ofa tasan yana ciki yana jiranta, wani ikon Allah Wai Khalid ne take matuk’ar jin nauyin Keb’ewa taredashi a yau d’in saikace ba Khalid d’in data saba tsefesa da masifa ba... Da k’yar ta iya saita kanta ta gyara mayafinta ta nufi parlorn sallama saman bakinta cikin muryrta da bai fitowa sosai.... Khalid dake zaune yana shafa wayarsa saurin janye idanunsa yai daga wayar had’ida k’urama k’ofar idanu... Teddy bear d’insa ya hango shirye cikin shiga irinta matan aure, yalwataccen mayafi wanda yakai har gwiwarta, tana sanye cikin leshi golden yellow da yai matuk’ar mata kyau dikda fuskanta kife yake a k’asa... K’uri yai ma k’afafunta yanda take takowa a hankali yana kallon zanen flower na lalle da aka rangad’a mata wanda ya dace da kyakyawar fatarta da ya amshi gyara sosai.... Har yanzu ganin abin yake tamkar mafarki Wai Nabilarsa ta zama matarsa... Haka ya dinga tino tun farkon had’uwarsu da irin gwagwarmayar da suka sha kafin su mallaki juna... Tsan tsan k’aunarta na kuma ratsa duk wani k’ofa na zuciyarsa.... A hankali ya mik’e tsaye sanda ta iso cikin parlorn... Har lokacin kan Nabilah na k’asa ya kasa d’agowa ta dubesa sai bugu da k’irjinta keyi... Khalid ya tako a hankali har zuwa gabanta.. Ganin ya taso ya nufota ya sanyata d’an saurin d’ago fuska sai kuma ta maida kanta k’asa... Ta lura ya sauya shiga shima, half Jampa ce dark ash jikinsa kansa babu hula sai sumarsa da yasha gyara ga k’amshin nan nasa ya cika parlorn gaba d’aya... Shiko Khalid cikin zuciyarsa cewa yake yanzu haka had’o masifar da za’a masa ake tinda gashi ko gaisuwa har yanzu bai samu ba... Kaman wacce taji zancen zucin nasa nan ta soma gaishesa cikin tsananin sanyin murya wanda har saida ya sanya Khalid jin wani abu na tsagar masa, gaisuwa mai cikeda wani irin ladabi ta masa ba irin wanda ta saba masa a baya ba, tabbas ya kuma yarda sud’in ma’aurata ne... Take yaji kimanta na k’aruwa cikin idanunsa a hankali.... A b’angaren Nabilah kaw har ta cire ran Khalid bazai amsa mata gaisuwarta ba ta sinkayo muryarsa na fad’in “Mu zauna mana first... Ko sauri kike ne....?” Satan kallonsa ta d’anyi tanaso ta danna masa harara amma ta kasa ga k’irjinta dake matuk’ar bugu.... Bata ankaraba saijin tattausan hannunsa tai saman nata, bugun k’irjinta ya k’aru, tamkar rak’umi da akala haka ta shiga bin bayansa har saida ya zaunarta saman kujera... Shima yai masauk’i ma kansa a gefenta... Ta d’an matsa gefe kad’an tana mai gyara zamanta... Yai kaman bai kula da abinda take ba saima k’ok’arin ciro wayarsa da aka soma kira cikin aljihu da yake.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *93* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Magaji da fitowrsa kenan daga masallaci an ida sallan lisha, yana k’ok’arin bud’e shago ‘yar wak’ensa a bakinsa sai cin karo da mutum yai zaune gefen shagon ga duhun dare da ya soma shiga...Baiji mamakin ganin Hafiz mak’ale wajen ba saidai yanayin da yaga Hafiz d’in ciki ya d’aga mar hankali.... Tak’ure yake gefen dakalin shagon Magaji very miserable, duba guda zaka masa ka fahimci Hafiz ya fice hayyacinsa gaba d’aya, a idanunsa Engr Mutallab yaita alkhairima jama’an unguwarsu, ya tabbata salon munafunci ne kawai irinta ‘yansiyasa... Magaji ya d’an dubeshi kana yace “Wai dama nan kazo...?” Bai amsashi ba saima kauda kai gefe da ya kumayi sakamon hasken wutan lantar da nepa suka dawo dashi ya haske fuskan Hafiz.... Zama gefensa Magaji yai yana mai furta “Abokina, hak’uri da saka ma zuciya dangana da amsar k’addaran cewa Zulfa’u yanzu ba taka bace shine kawai zai ficceka.. Amma duk wannan shiga damuwa da tada hankali babu abinda zai haifar maka illa....” Baikai aya ba Hafiz ya katsesa da fad’in “Kaga dalla Malam ya isheka... Idan wa’azi kake so ka tafi bakin masallaci mana ka d’au speaker, ka wani Zo nan zaka cika min kunne, da wanne zanji da k’watan matata na fin k’arfi da akamin ko da wannan surutur naka... Kuma da kake cewa na amshi k’addarar na rasa Zulfa’u kai waye yace maka na rasata kenan... Wllhi sai yanda k’arfina ya k’are, ba yana gadara shi mai neman takaran kujerar governor ba idan shugaban k’asa ya tsaya takara Zulfa’u sai ta dawo gareni... Babu mutumin da ya isa babu wani d’a namijin da ya isa ya mallaki Zulfa’u bayan ni Hafiz not even wannan D’an siyasan, Ka fahimta...?!!!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye yana wani zazzaro idanu tamkar wani k’waro....Magaji ya murmusa a hankali kana yace “Abokina kenan, bakaci yak’i da yaron gida ba kana tinanin zakaci yak’i da uban Gida...? Hafiz lokaci yayi da zaka daina wannan damuwar, yanzu fah Zulfa’u ba sa’ar aurenka bace....!” Hafiz dake faman danna masa harara jinjina kai yake kana yace “Na jima da sanin cewa baka k’aunar Farin cikina, bari kaji na fad’a maka tsaban kud’insa baya tsoratani, kyautar da yake ma ta riyace nayi imani dan ba har zuciya bane, wa ya sani ma ko d’an k’ungiyar shan jini ne ace a shekarunsa arba’in da ‘yan d’oriya ya mallaki irin wad’annan k’azaman dukiya aima dole ya tafiyarta ta hanyar siyasa tinda bata tsaftacecciyar hanya aka sameta ba dama... Ni dama ban tab’a sonshi ba tuntuni bak’in munafuki...!” Magaji ya d’an murmusa kad’an “Hafiz kenan ya kamata kasan cewa ba duka ‘yan siyasa bane suka taru suka zama d’aya, komai da kake gani akwai na gari akwai na banza, ko wace irin hark’ace kuwa ba zallan siyasa ba harta cikin malamai akwai na kirki akwai na banza ‘yan kasuwanni ma’aikatan gwamnati da sauransu ka sani na gari basa k’arewa haka na banzan ma, toh ka dainayin kud’in goro kana zagin jama’a domin kaw Allah zai tsayar daku yai maku hisabi, kuma da kake cewa babu wanda yasan source d’in dukiyarsa ka mance shid’in gada yai daga mahaifinsa, ka mance sune masu Mutallab’s Mining company, kamfanin da gaba d’aya west Africa tayi zarra tayi fice bayan wasu manyan kafanonin da suke dashi, idan har zakai masa k’azafin d’an k’ungiyar asiri bakai masa adalci ba..” A fusace Hafiz ya mik’e yana huci yake nuna Magaji da d’an yatsa “Zan maka kashedi na k’arshe daga yau kada ka sake cemin ga abinda zanyi tinda kai ba Ubana bane..!!!” Daga haka yasa kai ya shige fuuu tamkar zai kifa.... Jinjina kai Magaji yai cikeda mamaki had’ida tausayawa abokin nasa kana ya numfasa yace a fili “Eh lallai na yara kwanyarka ya tab’a Hafiz...” Magaji ya tina a da Hafiz ya sami Zulfa’u a b’agas dan dangin kyauta ya sameta yaita wulak’antata yana muzguna mata sai gashi yanzu da dik wani abinda ya mallaka bazai sameta ba, ta riga ta kufce masa, rayuwa kenan... D’an hakin da ka raina watarana shike tsole maka ido... Tabbas haka ne gashi ya faru kan abokinsa ya gani.... *** Har lokacin bai d’aga wayar ba saima k’ura ma wayar idanu da yai, shi harga Allah yanzu har tinanin d’aukan wayar Ammi yake, yasan maganar bazai wuce kan wannan mayyar yarinyar ba... Nabilah ta d’an dubesa taga yai k’urima waya, kaman ta tambayeshi ko lafiya sai kuma tai shiru had’ida maida idanunta kan yatsuna hannunta da taketa faman juya zoben dake yatsarta guda.... Tana a haka ta sinkayo muryarsa yana gaisuwa had’ida ambato Ammi.... Wani irin bugu k’irjinta yai tamkar an ije guduma, ta tuna karonsu da mahaifiyar Khalid gashi har yanzu basuyi wani tak’amaimen magana da Khalid d’inba balle taji ya matsayin aurensu wajen family d’insa.... Tana ganin yanda tin bayan gaisuwa ya k’urama waje guda idanu alamun daga d’aya b’angaren akwai abindake faruwa, dan shiru yai kurum yana saurarenta... Ammi kaw taci gaba da bambamin masifa “Kan me zakai tafiya bazakai sallama da Yesmin ba, kuma tsaban wulak’anci da raini irin naka Khalid ka tafi har Abuja dik kwanakin nan ka kasa zuwa gidansu Yesmin ka gaida Aunt d’inka... Ya maka daidai, Allah ya baka sa’a kaci gaba da dik abinda kake....” Khalid shaye da mamakin irin rainin dake tsakaninsa da Yesmin Wato ma k’ararsa takai wajen Ammi lallai yarinyar nan bata sansa ba har yanzu, amma ta nemi sanin ko shi wanene yanzu... Kasancewar ga Nabilah wajen kuma baiso ta fahimci akwai wata matsala ya sanyashi cewa “Ammi ban zauna bane, kiyi hak’uri zan kiraki back sai muyi maganar...” A fusace tace “Khalid don’t you dare hang up on me, ban gama maka magana ba kana jina koh... Ba aiki ba idan uwar aiki ne ya tareka ka kirata ka bata hak’uri ku sasanta...” Dunk’ule hannayensa kurum yake sabida tsananin tafasa da zuciyarsa keyi, wllhi sai ya cire rainin dake tsakaninsa da Yesmin hardai bata daina had’asa da mahaifiyarsa ba.... K’ok’arin saita kansa yai kana yace “Shikenan Ammi zanyi yanda kikace....” Ammi tace “Yauwa yanzu dai naji batu... Allah shi maka Albarka.... Ga sets d’in akwatina da nai order sun iso, anjima Siyama zata d’auki pictures ta tura maka...” Bata jira amanarsa ba sukai sallama.... Shiru yai yana shafa wayarsa na d’an wani lokaci har saida Nabila ta d’an saci kallonsa, ko ba’ace ba kasan yanada damuwa dan duk k’ok’arinsa ya b’oye hakan zuciyarda ta damu dashi dole ta iya karanto hakan.... D’ago idanu tai tana k’ok’arin karatarsa Wannan karon idanunsu suka sark’e waje guda domin kaw shima d’in ita yake duba... Murmushi ya saki ganin tayi saurin maida idanunta k’asa, ya d’anyi gyaran murya kad’an yace “Wai ni teddy bear wannan sanne sannen da ake min na minene...? You know nafi sabo da masifarki, wannan sanne kai da shiru d’in duk ban saba dasu ba, ko sai mun tafi Kaduna ne a tsfeni ya k’arashe yana kwanto da fuskarsa dab nata.... Aiko kaman jira take ta jefa masa muguwar harara kana ta kuma kauda kai gefe... Khalid ya murmusa kad’an yace “Yauwa better kinga da kika min wannan kallon yanzu na yarda teddy bear d’itace ba’a canza min ita ba...” Wannan karon murmushi ta d’anyi ba tareda ta dubesa ba.... Shima murmushin saman fuskarsa yake dubanta kana yace “So Amarya ya taro...?” A hankali ta amsa masada “Alhamdulillah..!” A tak’aice... D’an gyara murya yai had’ida daidaita zamansa kana yace “Masha Allah...!” Gaba d’aya tattaro natsuwarsa ya kumayi kana yaci gaba da fad’in “Teddy bear... I know you’ve a lot of questions to ask, an saka bikinmu and you didn’t hear from me, banzo ba banyi waya ba, stuff like that... And you’ve every right to be mad at me... I’m sorry kinji koh... And I promise randa dik aka kaiki gidana I’ll explain everything to you kinji koh...” Ita dai bata iya d’agowa ta dubesa ba har lokacin idanunta nakan zobenta da take juyawa... Idanun Khalid suka sauk’a kan abinda take, sosai lallen hannunta ya masa kyau special red one d’in da akai a fingers sosai suka masa kyau... Bata ankara ba saijin hannayensa tai saman nata... Tai saurin d’agowa tana dubansa shid’inma ita yake duba.... “kinji abinda nace...?” Ya tambaya yana tsareta da idanu ga k’irjinta dake matuk’ar bugu gashi yak’i sakin hannayenta saima murza yatsun da yake a hankali....A hankali ta jinjina masa kai alamun Eh dik wani iri take jinta, cikin dabara take k’ok’arin janye yatsun hannunta shiko Khalid yak’i saki saima dad’a d’an matsesu da yai ya nuna mata k’arfi kad’an... Ta d’ago idanunta masu cikeda tsoro wannan karon tana dubansa, Wato dai dik masifarta dai zai nuna mata k’arfinsu ba d’aya bane... Ya saki murmushi yana duban yanda dik ta wani daburce, kauda shirun yai da fad’in “K’unshin nan yayi kyau teddy bear... Yana gogewa a sake min wani dan inaso sosai...” Harara ta d’an jefa masa wannan karon... “Ni ka sakemin hannu naje kafin a soma nemata....” Tai maganar tana turo baki.... Kallon d’an bakin nata da ya k’ware wajen iya tsiwa da masifa yake bai daina murza ‘yan yatsun hannun nata ba yake fad’in “Babu wanda zai nemeki sunsan da waye kike tare... Besides ko d’aukanki nai daga nan muka wuce babu mai tuhumata saidaima ace nayi daidai... Ko bazaki yarda ki bini bane...?” Ya k’arashe maganar sanda yake zame zoben da taketa wasa dashi a yatsarta... Gajeran harara ta kuma galla masa kana tace “Tab, aiko kaini sukai yanzu bazan zauna ba dan sai na dawo na ida exams d’ina...” Khalid ya murmusa yace “Meye a ciki kullum sai na kawoki kiyi ai... Saura nawa ne ki gama...?” “Monday in sha Allah nake gamawa, saura last paper ne...!” Khalid ya jinjina kai a hankali kana yace “Kinga zaman kano ya kamani.. Dan k’afarki k’afata bani barin garin nan without you teddy bear... So gwarama ki sakama ranki...” Ya k’arashe yana mai janyo wata k’aramar shopping bag dake gefen k’afarsa k’asa... Ita dai kauda kanta gefe kurum tai, sinkayo muryarsa tai yana fad’in “Ni zan wuce, zan fara biyawa wajen Daddy first before na shige masauk’i tinda kink’i yarda ki bini.... Tashi muje Kimin rakiya...!” Mik’ewa tai tana gyara mayafinta ta shiga bin bayansa a nitse... Saida suka kai k’ofa kana ya juyo yana dubanta yanda take takowa a natse da alama bata saba da d’aura zani ba, ya tako kusanta kad’an kana ya d’an rage murya yace “Being matar aure suites you teddy bear... Kinyi kyau sosai...” Nan ma bata amsa shi sai sakin murmushi da tai a hankali, Khalid ya kuma matsowa a hankali kana ya d’an rank’wafo saitin fuskarta, k’irjin Nabilah yaci gaba da bugawa jin d’umin numfashinsu kusan na juna, murya can k’asan mak’oshi yake furta “Anything for your Bear..?” Yanda yai maganar cikin salo na kashe murya saida ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba ga numfashinsa dab saman fuskarta, saurin janye fuskarta tai a d’an daburce tace dashi “Saida safe...!” Khalid ya girgiza kai yace “Ba wannan ba...” Bugun zuciyarta ya k’aru ganin yana kuma matso da fuskarsa kusan nata, ji tai tamkar ta hankad’asa amma batada wannan k’arfin, can k’asar zuciyarta kurum take addu’an abinda zai karkata hankalinsa... Aiko kaman daga sama wayarsa ta soma ruri, ya gyara tsayuwarsa yana mai zaro wayar... Wannan karon dagaji da abokinsa Baffah suke maganan dan taji yana cewa su had’u GRA yanzu zai tafi wajen Daddy..... Daga nan paper bag d’in hannunsa ya mik’a mata, tai kicin kicin da fuska alamun bata son amsa saidai yanda taga ya matuk’ar tsarewa ya sanyata amsa tana mai masa godiya dikda batasan minene ciki ba... “Inda na isa masauk’i zan kira, and monday kar kowa ya kaiki sch zanzo na kaiki da kaina kinji koh...” Jinjina masa kai kurum tai tana satan kallon yanda ya mak’ala ring d’inta a ‘yar yatsan hannunsa k’arama dikda haka bai isa k’asa ba tasan neman maganane kawai ya sanyashi yin hakan, can k’asan zuciyarta murmushi take ita kanta tasan itada Khalid hali yazo d’aya they’re both very stubborns ita kaw yanzu ko musu bata iya masa balle tsiwar data saba yi masa... Sukai sallama Khalid ya tafi da kewar matarsa... Ita kaw har ta shige gidan k’irjihta bai daina bugu ba, Yusrah dake jiranta parlor nan ta sakata gaba da zolaya Nabilar na aika mata harara, batabi takan Yusrah ba dan cike take da haushinta, ta isa ta bud’e paper bag d’in kwalin wayace d’an ubansu k’irar Samsung hardasu sim da komai, ta saki murmushi had’ida lumshe idanu tana shak’an k’amshinsa da ya kama ‘yar jakar... A haka Yusrah ta shigo ta taddata.. *** A can gidan Haule fah? Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana... Mamaki ya cikata sanda ta kutsa cikin gidan ‘yandaudun nan sukai chaaa suna ele suna fad’in ga babbar Yaya ta iso a bata fili.... Suka janyo hannayen Haule dake binsu da kallon mamaki, tuni suka jefa Haule tsakiyar filin rawa suna gewayeta gurmi da garaya naci gaba da tashi... Can Haule ta hango Sawwama da d’aurin nan nata gaba na kallon yamma bayan na kallon gabasa sai karkad’a k’afa take tana jijjiga alamun rawa daga zaune.... Haule ta murmusa dan dik a zatonta Sawwama tayi haka ne ta kwaso ‘yan daudu da mai gurmi dan ta cazagawa Sahariyya bak’in ciki tinda an fasa bikinta.... Haule ta k’arasa gaban Sawwama tana huci tana nunata da ‘yar yatsa “Ke k’aramar kilaki, k’aramar shed’aniya ni nafi k’arfin kizo har cikin gidana kice zaki cazga min bak’in ciki... Naci uwarki a bariki barikiji na fad’a miki... Tin wuri ki tattari wad’annan ‘yaniskan ku fice min gida tinda ba bayan gari bane...!” Ta k’arashe tana kuma fincika.... ‘Yan daudun nan suka shiga kame baki cikin salo suna fad’in “Aaaa Haba yayarmu tarban da zaki mana kenan... Kuma ma ai nan gidan Ubanmu ne zama daram babu fashe Billahillazi...!” Suka k’arashe suna tafe hannaye... Kan Haule ya d’aure ta dubesu tace “Waye Uban naku....?!” Salo sukai suna masu kame baki da tafe hannaye suke furta “Chaasss! Ayyye Lantana shafa mata...!” D’ayan yace Wanda aka kirada Lantana gyara d’aurin k’irji yai had’ida rik’e hab’a kana yace “Waa ki rufa min asiri in mutu a d’aki maza su kaini... Ba’a ji mutuwar sarki a bakina ba wllhi....!” Haule fah ta soma firgita da lamarin dan har yanzu bama ta lura da matar dake daga gefen mai garaya fuskarta lullub’e cikin mayafi ba.... Harta Sahariyya dake cikin nata damuwar gyara zama tai bayan ta ida birgimanta a k’asa tana kallon wannan show dake gudana a gidansu, kai kowa a wajen tsayuwa baima idanunsa abinci yai da ganin wannan ikon Allah... Haule ta k’arasa a fusace ta finciko Sawwama tana fad’in “Ke dan uwarki me kike shirya ma d’ahna bak’ar mayya zuri’an jarababbu...” Batakai aya ba Magajiya ta mik’e had’ida yaye rufin kanta tai d’amara da gyalenta ta finciki d’iyarta Sawamma ta koma baya kana tai tsaye gaban Haule tana mai furta “Ke kada ki kuskura ki kuma tab’a min lafiyar d’iya dan wllhi kinji na rantse miki wad’annan mata mazan da kike gani su sauya miki kamanni....!” Al’ajabi had’ida mamaki ya kuma kama Haule... Dariyar datafi kama data takaici Haule tai kana tace “Yo ai sai kuce min tafe kuke gaba d’aya, kuce bayan gari ne yau gaba d’aya a gidan namu, au ta kasa ne shine bari ta d’auko uwarta ta tayata... Yo ai kun bani kunya tinda kukayo zugan wad’annan asararrun... Ashe dai na cika aji shakkun tunk’arata...!” Wannan karon murmushi Magajiya tai tana mai k’arema Haule duba daga sama har k’asa kana tace “Sauk’inki d’aya baki kai na zuba kishi dake ba, dan haka gwara ki saduda kiyi biyayya mu zauna lafiya...” Haule fah bataji batun da kyau ba, mai wannan kilakin take fad’i ne....? Bata ankara ba tajiyo muryar Magajiya tana fad’in Mai gurmi yaci gaba da aikinsa, tana fad’i tana tik’an rawa daga tsakiya ashararrunta na tayata.... Su Amara k’irjin biki mai zasuyi itada k’awayenta banda dariya, harta Sahariyya saida taji dariya ya kufce mata ganin wannan drama dake faruwa a gidansu wanda yafi kama da wasan kwaikwayo tama mance itama cikin nata damuwar take, harta su Fa’iza k’awayen Sahariyya dariya Kawai suke suna fad’in saidai fah Sahariyya tai hak’uri amma wannan al’amari dole su dara su kuma kai gaba... Haule da duniyar ta kuma juya mata a matuk’ar sanyaye ta isa gaban Magajiya tana fad’in “Mai kikace...?” Wannan karon cikin sanyin gwiwa sosai tai maganar... Magajiya ta murmusa tace “Yafi miki da kika saduda da wuri... Ki jira mijinki shi zaizo yai maki sauran jawabi, kina iya shigowa fili mu taka a halin yanzu...” Ta k’arshe tana mai janyo hannun Haule tana sakata tai rawa tana bin sautin garayar tana furta “Rawa Haule rawa Haule....!” Bibbiyu Haule ta soma gani... Itace Alhaji zai mata wannan cin kashin... Aure! Aure yai ba tareda saninta ba, aurenma ya rasa waye zai auro mata sai Magajiya... Take taji wani irin kuka na zuwa mata dan dik yanda takai da ganin ya d’aure bata isa ba bazata iya ba, tana jin yanda zuciyarta Ke fincika daga k’irjinta kaman zai fice... Itakam ta gwammci mutuwa da ganin irin wannan rana.... Zame hannayenta tai daga rik’onda Magajiya tai mata had’ida zama dirshan a k’asa ta jinginu jikin garu ta dafe kai tana furta “Na shiga uku ni Haule... Na shiga uku... Hafiz ya kawo mana annoba cikin zuri’a da ya auro d’iyar matar nan... Yanzu jarabawar bai tsaya akanshi kawai ba harda mijina... Na mutu, Haule k’arshenki yazo...!” Ta k’arashe tana mai sakin wani irin kuka da batasan ya kufce mata ba, suko su Magajiya da ayarinta basu fasa shagalinsu ba su Amara na tayasu.... A haka Hafiz ya shigo gidan ya tadda wannan kwamacala dake faruwa a gidan mahaifin nasa... *** A can gidan Abbah kaw yanke shawarin had’uwa Washe gari sukai gaba d’aya a can gidan Babbar Yayarsu Abidah bayan kowa ya d’an sami natsuwa zuwa goben... Haka yayi masu gaba d’aya, saidai yau d’in sun kasa rabuwa da juna suka yanke shawarin kwana su duka hud’un a gidan ‘yar uwarsu Mariya, dan yau d’in ji suke tamkar kada su kuma rabuwa da juna, ga yaran Daula tuni sun sake suma sunata murna yau Mominsu ta had’uda family d’inta, tuni dama Daula tayi waya ma Daddy ta sanar dashi halinda ake ciki Farin ciki da al’ajabi ya cika Daddy, yace tai zamanta cikin ‘yan uwanta don da har zai turo driver ya d’aukosu zuwa masauk’i itada yara... Abin fah sai son barka ta ko wanne b’angare Farin ciki ne maras misaltuwa, daga bisani Engr da Sameer sukaima iyayen nasu sallama suka fice kaman kada su rabu da juna, nan Sameer yai rakiyawa Engr zuwa waje suna tafe suna kuma tattaunawa, bayan Engr ya wuce shima Sameer d’in sashen Mahaifinsa ya nufa yana mai zullumin halinda zai tadda mahifin nasa ciki bayan tulin abubuwan da suka faru a yau d’in.... Da sallama saman bakinsa ya nufo cikin parlorn sanda Abbah yai masa izinin shigowa... Ga mamakin Sameer murmushi ya gani kwance saman fuskan Abbah sam bazakace yanada damuwa ba sai ka karancesa sosai ka iya gano hakan.... “Shigo abinka, k’araso Ma’aruf... Dama ina nemanka akwai maganar da zamu tattauna....” Sameer ya zauna daga gefen k’afan Abbah yana mai gaida Abban... Abbah ya amsa masa har lokacin murmushi ne saman fuskarsa wanda ko ba’ace ba kasan k’arfin hali kawai yake... Bayan Sameer ya zauna Abbah yaci gaba da fad’in “Akan batun aurenka da d’iyar wajen Yaya...!” Gaban Sameer ya yanke ya fad’i, dan shi har ya mance da batun wata Sahariyya.... Ya sinkayo Abbah naci gaba da fad’in “ Nasan mai yuwa kanada labarin an sauya aurenka da k’anwar Sahariyya...” Wannan karon d’agowa ya d’anyi cikeda mamaki kana Abba ya jinjina kai yace “Da alama bakada labari... Ma’aruf..!” Ya kuma kiran sunansa cikeda kulawa... Wannan karon jiki a sanyaye ya d’ago yana duban Abban... Abba yaci gaba da fad’in “An maida aurenka kan ‘yaruwarka RAIHANAH... Bayan dik abinda suka faru nasan bakada wani tambayar da zakai gameda wannan al’amari... Kasan Raihanah itace matar da Allah ya zab’ar maka kuma inaso ka rik’eta amana, kada ka dubi abinda mahaifinta yai mana nida mahaifiyarka harma da kai... Ita d’in yarinyar kirkice, Allah Ubangiji yai maku albarka, ya azirtaku da ziri’a d’ayyiba... Ina labarin d’aya matar taka...?” Sameer da ya tsinci zancen tamkar sauk’ar aradu dikda cewa yaji wani irin sanyi na sauk’ar masa cikin zuciyarsa sanda akace bai aure d’iyar Haule ba, saidai baima San mai yakeji gameda auren Raihanar ba, wani feeling ne da bai isa ya fasalta ba a halin yanzu... Muryar Abbah ya sinkayo yana fad’in “Kai nake tambaya Ma’aruf.... Ina labarin matarka...?” Sameer ya d’an sosa kansa kad’an kana yace “Em Abbah dama... Dama sai naje Kaduna na dubata...” Abba ya jinjina kai yace “Toh dama lallai lallai kaje ka duba iyalinka, ka had’e kan iyalanka ku zauna lafiya kaji koh..” Sameer ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Zanyi yanda kace in sha Allah Abbah...” Abbah ya murmusa kana yace “Allah shi maka albarka...” Kai a k’asa ya amsada Ameen Abbah a daidai sanda Mamy ta shigo da sallama... Kallo guda zakai mata ka fahimci ta damu da damuwan mijin nata, Sameer yai mata sannu da shigowa kana ya mik’e ya basu waje, can k’asar zuciyar tinanin al’amran da suka saka shi a tsaka yake, ala dole ya amsama Abbah gameda maganan aurensa da Siyama dan bazai iya musama Abbah ba sannan a halinda Abbah yake ciki yanzu bai buk’atan k’arin tashin hankali, ya saki murmushi a hankali sanda ya tuna aurensa da d’iyar Haule Wai ya juye kan Raihanah... Al’amarin Allah kenan, haka yake gudanar da al’amaransa ba tareda shawartan kowa ba.... Ya lumshe idanunsa a hankali yana tuno tin sanda ya soma had’uwa da ita farkon dawowarsa Kano sanda ya kusan bigeta da mota tun kan yasan sud’in ‘yanuwan juna ne.... Ya kuma sakin murmushi a hankali kana yasa kai ya fice... Mamy ta dubi Abba da yai shiru tin bayan shigowarta saima k’ok’arin kamo tashan labarai da yake... Saurin kai hannunta tai ta amshi remote d’in ta kai masa tashar NTA d’in dan lokacin labarun tara ne... Har lokacin nan Abbah bai dubeta ba saima maida hankalinsaga tv da yai dikda cewa da gani bama fahimtar labarun yake ba.... Mamy ta d’an sauk’e ajiyan zuciya sanda takai idanu kan tray d’in abincinsa dake gefe da alama ko tab’awa baiba tinda ita tana hidiman biki Lami ce ke kula dashi ta bata girkin ranakun... K’arasawa Mamy tai ta janyo tray d’in tana k’ok’arin serving d’insa Abbah ya katseta da fad’in “Karki zuba abincin nan Mariya a k’oshe nake...” Mamy ta d’anyi raurau kana tace “Toh mai kaci ya isheka, gani fah baka ko tab’a abincin ba tintini...” Jinjina mata kai yai kana yace “Ina sane, kawai na k’oshi ne...” Mamy tai shiru dan tama rasa abin cewa gaba d’ai, sai sauk’e ajiyan zuciya da tai, a hankali ta d’an kuma muskutawa zuciyarta cikeda tausayin mijin nata lokaci guda take furta “Nasan kana cikin lokaci mai matuk’ar wahala a rayuwarka... Nasan hakan ba abu ne mai sauk’i amma ina rok’onka dan Allah kai hak’uri ka d’auki duk abubuwan da suka faru a matsayin k’addara kaji mijina...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya wanda ya sanya Abbah juyowa yana dubanta cikeda tsananin tausaya mata, shin wane irin kyakkyawar zuciya Mariya kedashi.... Bayan dik abubuwan dataji ta zab’i ta yafewa wad’annan azzalumai, lallai ita d’in tana zuciya mai kyau... Sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an yana mai k’ura mata idanu... A hankali yakai hannayensa saman nata... Mamy ta d’ago tana dubansa cikeda tausayinsu su duka biyun.... K’wallan da Abbah keta k’ok’arin mak’alewa suka gangaro... “Ki yafeni Mariya...!” Kalman data soma fita daga bakin Abba kenan... Mamy ta girgiza kai tace “Dan Allah ka daina bani hak’urin nan haka dukanmu nan abin nan ya shafemu ba ni kad’ai ba, kuma mu godewaAllah da har ya warware mana komai...” Girgiza kai kad’an Abbah yai “Ke d’in kece kikafi kowa a cikinmu, Mariya wala’alla hakkinki shine ya kamani har mutanen dana aminta dasu sukaimin cin amana mafi muni... A lokacin da Ma’aruf ya b’ace na biyewa son zuciyata naita zarginki da laifi nima, banyi la’akari da halinda kika tsinci kanki a natsayinki na mahaifiya ba, ban kasance taredake nai supporting d’inki ba saima biyema masu laifin da nai muka had’u muka cuzgunama rayuwarki... Zan jima inajin zafin wannan abun a raina...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Mamy da kanta Ke kife tana matsan hawaye itama, lokaci guda take furta “Wannan duk muk’addari ne daga Allah, mu d’auki hakan a matsayin k’addarar rayuwarmu... Sannan mu godewa Allah da ni’iman da yai mana a yanzu mu daina kuma duba baya...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Abbah yai mata k’uri yana godiya wa Allah can k’asan zuciyarsa da wannan baiwa da yai masa na samun mace irin Mariya...! A hankali ya matsa kusanta ya rungumota cikin jikinsa su duka biyun hawaye suke...! *** A b’angaren Engr kaw tinda ya isa gida yake nazarin takardan da Akram ya bar masa, ya kasa aminta Muhibba can go this far, ta yaya zata masa haka... Kenan watak’ila tanada masaniya kan yanda Akram d’in ya tafi tinda she’s his accomplice.... Baisan kishin Muhibba yakai wannan peak d’in ba, a had’a baki da ita a yaudare mijinta, mijin da ya d’auki gaskiyarsa da yardarsa ya bata... Ya fuzar da iska a hankali yana mai had’e tafukan hannayensa waje guda... Kaman wacce aka wuntsilota haka ta shigo babu ko sallama bayan ta gama baccin asaranta, dan har ya dawo gidan bata sani ba saida ta tashi ta hangi motar da ya fita da ita a parking lot alamun ya dawo, dik yini zubur d’in nan da Engr yai a waje Muhibbah bata kira taji lafiyarsa ba dikda kasancewarsa mutum mai hada hada da yawa... Kallo d’aya yai mata ya watsar... Ta k’araso tana mik’a had’ida hamma alamun har yanzu akwai bacci a idanunta... Gefe dashi ta zauna had’ida kwantar da kanta cikin jikinsa, cikin murya irinta wanda bacci bai ida sakesa ba Muhibbah Ke fad’in “Excellency na ashe ka dawo, inacan inata bacci I didn’t expect you to be home this early, na zaci meeting d’inku da party chairman yau ne...!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin hamma... Jin ko gizau bai kulata ba ya sanyata saurin d’agowa tana dubansa, kasancewar kansa a kife yake yasa bata fahimci halinda fuskar nasa Ke ciki ba saidai ta hangi takardan dake hannunsa wanda ya kifa masa idanu, bata kawo komai ba don a zatonta batada alak’a da takardan.... Murmusawa ta d’anyi tasan dik gajiya Ke damunsa tinda mijin nata bai samun wane isasshen hutu da lokacin kansa sai na mutane... A hankali ta kuma kai hannayenta saman kafad’arsa tamkar mai massage... Cikin salo na kashe murya take fad’in “Excellency na baka son hutu... Waima tsaya, have you eaten..? Should I bring you something to eat...?” Cikin wane irin razananniyar murya yace da ita “Get your hands off me...!” Muhibbah data nemi baccin idanunta ta rasa a zabure ta mik’e tana dubansa cikeda tsoro.... Tai far da idanu “Excellency na mai kuma ya faru.... Ko wani ne waje ya b’ata maka rai...?” Ta k’arashe tana zaro manyan idanunta.... Bata ida razana ba saida ya d’ago fuska, nan ta hango tsananin b’acin Rai dake kwance cikin idanunsa... K’irjinta ya shiga bugawa ta soma tinanin kardai dubunta ne ya cika Engr ya san tana shan drugs... Toh amma she’s been very careful bata basa wani k’ofa da zai fahimci hakan ba tinda shi bama mazauni bane, Toh kodai yasan itada k’awayenta safaran miyagun k’wayoyi shine sana’arsu... Wata zuciya tace kai da zai sani da tuni ya Sani k’ila dai wani abin ne daban.... Muryarsa ne ya kuma dawowa da ita daga duniyar tinaninda ta tafi... “Why did you do that...? How dare you lie to my face...?!” Ya k’arashe cikin wata irin murya mai razanarwa yayinda Muhibbah ta shiga willi willi da idanu k’irjinta naci gaba da bugu..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO *94* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Take ta soma rau-rau da idanu tamkar mai shirin kuka, lokaci guda take furta “Haba Excellency na wani abin nayi ne... Kodai wani ne ya b’ata maka rai wajen taro....?” Tsaye ya mik’e yana dubanta sosai kana ya mik’a mata takardan dake hannunsa... Gaban Muhibbah yai wani irin yankewa ya fad’i, toh wannan kuma takardan minene...? Ta tambayi kanta, ta kuma d’agowa tana dubansa, gani tai ya tsume sosai babu alamun wasa a tattare dashi, ga idanunsa da suka kad’a sosai alamun b’acin rai... Ta k’ak’aro murmushin da tafi kama da yak’e “Excellency na wannan kuma na menene...?” “Ki karb’a ki karanta sai kimin bayanin dalilin da ya sakaki sikata abinda kika aikata, and don’t you dare lie to me....!” ‘Yan hanjinta suka kuma kad’awa gashi ya tsareta da idanunsan nan masu firgita marassa gaskiya... “Ki karb’a nace..!!!” Ya kuma fad’i cikin daka tsawa Wannan karon... Jiki har na rawa Muhibbah ta amshi takardan ta soma karantawa, k’irjinta na bugun tara-tara... Wato Akram tona masu asiri yai wajen Engr, lallai tayi wauta data yarda Akram can betray Engr... Jujjyya takardan ta shigayi tana fad’in “Excellencyna ban fahimci komai ba fah ni... What’s all this...?” Ta k’arashe cikin murya mai kalan tausai... Girgiza kai yai kad’an yana dubanta kana yace a hankali“The nerve...! Har kinada k’arfin gwiwar k’aryata abinda kika karanta yanzu... So tell me where’s Akram... Since you’re his ally na tabbata kinada masaniyar yanda ya tafi fad’a min ina yake....!” Muhibbah ta kuma turo baki kana tace “Ni dai wllhi bansan yanda yake ba... I have no idea....” Engr ya kuma jinjina kai kana yaci gaba da fad’in “So, are you happy now...? Kina farin ciki tinda kin lalata auren mijinki....? Fad’a min kina farin ciki da hakan...?” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu... Yatsina fuska tai kana tace “Toh mai kake tinani Excellency na... Na zauna na zuba idanu ka kawo min wata mata cikin gidan nan, kaima kasan da nace maka na amince dan banida option ne, kuma da na fahimci kunyi tarayya da Akram wajen sonta sai nai amfani da wannan damar, haba Excellency na, wannan yarinyar ba class d’inka bace... How in the world ma zaka soma neman aure kana takara da yaronka... Ai ni taimakon ka ma nai na rabaku cikin salama, Kaga ‘yan adawanka na siyasa bazasu sami abin tsegumi ba...” Tsawan da ya daka mata ya sanyata had’iye sauran maganganun nata... Ya kuma takowa gabanta kad’an kana yace “Don’t you dare talk about her like that ever again, wannan ya zama gargad’i na k’arshe... Don’t push me to the wall Muhibbah....!” Ya k’arashe yana mai rab’awa ta gefenta ya nufi bathroom da niyyan d’auro alwala.... Muhibbah ta juya idanu had’ida yin jifa da takardan, a fili taja wani uban dogon tsaki kana ta tintsire da dariya tace “Ko a yanzu dai ni ce da riba tinda baka aureta ba batun auren yabi ta shanun sarki... Ma’aruf kenan, ai gidan duniyar nan baka da mata sai ni Muhibbah...!” Ta kuma tintsirewa da dariya kana ta kad’a k’afarta ta fice tana wani juya jiki take fad’i a hankali... “Idan ka matsu dani ka biyoni har b’angarena...” *** Washe gari kaman yanda suka shirya had’uwa gaba d’aya gidan babbar yayarsu Abidah hakan ce ta kasance, koda Aunty Bara’atu takaimasu Zulfah labarin abubuwan da suka faru a jiya d’aurin auren nasu ba k’aramin mamaki abin ya basu ba, Aunty Bara’atu ta sanar dasu komai dik abubuwan dasu Haule suka jima suna k’ullawa da yanda sukaita warwarewa da sirrikan da suka bayyana a jiyan, saidai bata sanar da Zulfa’u cewa aurenta ya tashi daga kan Akram ya koma kan uban gidansa kuma d’an uwanta ba, mamaki da al’ajabi yaita kamasu, Nabilah ta kad’a kai yafi abinda yafi kana tace “Wllhi Aunty ni dama na jima da karantar matan nan mugayen munafukai ne, Ke kiga Aunty Lami d’in nan yanda take kaffa kaffa da Mamy dama nasan naci na ciki mugayen banza azzalumai...” Zulfah ta d’an harereta tace “Ke kuma ya isa haka kafin ki fara...” Aunty B tace “Batta ta fad’i cikinta ai ba k’azafi aka masu ba... Kunga ku tashi mu shirya yanzu his Excellency zai turo motoci a kwashemu mu tafi can gidan Ammah (Ya Abidah)...” Nabilah tai far da idanu tace “Kai ashe dai munada RABON shiga gidan gwamnati... Ayyye mun zama k’annen his Excellency....!” Atika ta mik’a mata hannu suka tafe tace “Fad’i dai ki saka fad’i...” Gaba d’aya darawa sukai kana Aunty B ta kuma duban Atika tace su had’e kayan Zulfa’u waje d’aya dan daga can bazata dawo nan ba gidanta za’a wuce da ita... Atika tace “An gama Aunty...” Zulfah dai har yanzu abin mamaki yaketa bata, ashe dai bawan Allahn nan jini suka had’a dashi shisa tinda ya fito siyasa taji bata tab’a cin karo da d’an siyasan dake matuk’ar bugeta ba kaman shi dikda cewa alkhairansa ga Al’umma ne yasa ya zamto gwaninta a fagen siyasa ashe dai harda jini suka had’a, Allah sarki wannan shine ikon Allah, Kullum tana burin ganinshi ido da ido sai gashi yanzu zata ganshi a arha tinda ya zamto d’an uwanta, in sha Allahu kaw sai ta bashi labarin ita babbar fan d’insa ce d’aya daga cikin magoya bayansa... Tana jin Aunty Bara’atu da Atika na magana k’us k’us batabi takansu ba ta mik’e ta nufi bathroom da niyyan d’auro alwala kafin su shige dan ita mace ce mai yawan zama cikin alwala muddin tana cikin tsarki... A b’angaren Nabilah ma har yanzu abin al’ajabi yake bata jin cewa Aunt d’in Khalid matar Babansa k’anwar mahaifiyarsu ce, lallai wannnan shine ikon Allah mai gudanar da Al’amransa yanda yaso, bata tab’a zaton hakan mai yuwuwa bane saidai tabbas ba’a mamaki da ikon Allah domin kaw shid’in ne mai cikakken iko akan komai.... Kasancewar jarabawa suke shisa nata k’awayen babu ko k’wara harta Yusrah ma ta tafi da safe sunyi dasu Safwan zasu shiga tutorial da safen, sauk’in abin ma ita nan gidan Aunty Bara’atun zata dawo tinda ba yanzu zasu tafi can Abujan ba sai ta gama jarabawarta, ga wannan al’amari kuma da ya b’ullo kai, tana ganin Khalid na kiranta tak’i d’agawa tasan zancen bazai wuce yace zaizo su tafi gidan Ammah tare bane dan haka tama k’i d’aga wayar nasa, tsaf tasan halinsa yanzu sai yaje yaita bata kunya gaban iyaye, maganin bari karma a fara bazata d’aga ba saidai su had’u can gidan Ammahn.... Bayan shud’ewan wasu mintoci kaw hamshak’iyar Jeep d’in ta faka k’ofan gidan Aunty Bara’atu driver na jiran fitowarsu, ita dai Zulfah ta kasa aminta kasa yarda cewa Atika bata b’oye mata wani abu, dan ta kula falli da murnan Atika yama ninka lokacin da akace an saka aurenta, gashi har yanzu basuji daga Akram ba amma ko a jikin Atika... Saima wani Farin ciki da annashuwa data lura ya k’aru mata, wata zuciyar tace tinda kikaga haka toh ko shakka babu Akram na cikin k’oshin lafiya, k’ila wasu sabgogin nasa suka sha gabansa, amma fah ace kayi Amarya abin da kamar wuya da mamaki ka kasa koda d’aga waya ka kirata ne... Ta k’arashe tinanin tana mai sauk’e ajiyan zuciya a daidai sanda motar ya paka... Atika itace a front seat yayinda Aunty B Zulfa’u da kuma Nabilah Ke zaune daga bayan motar... Zulfah ta d’aga idanu tana duban ginin gidan tana iya tinowa a shekarun baya tun tana k’arama sun tab’a zuwa da Mamy taga Mamy ta fito tana kuka shikenan kuma bata sake jin d’uriyar matar daga Mamy ba, Allah sarki ashe dai rana irin wannan na zuwa masu ranan da zasu dunk’ule waje guda... Tinaninta ya katse sanda taji Aunty Bara’atu tana fad’in su k’araso Hajja mai aikin Ammah na amana ta nufosu tanai masu lale lale baki har kunne ganin gidansu da ya mutu shekara da shekaru yau ya dawo cikin rayuwa, rayuwa mai cikeda tarin albarka... Atika ta janyo trolly d’in Zulfa’u ta nufi bayan Hajja dake fad’in suje ta nuna mata d’akin da zata ije jakar... Atika dai sai zanzali da falli take tana kuma jinjina lamarin Wai yau Zulfa’u ce ta zamto matar Engr Mutallab daga gidan Hafiz, lallai Allah ya isa mai jujjuya al’amara yanda yaso ya kuma ga daman su gudana... Tabbas mahuk’urci mawadaci, ita tana mata Farin cikin ta rabu da Hafiz ta samu Akram ashe fin Akram tama samu, wannan shine INDA RAI tofah akwai RABO..... Ji take tafi kowa farin ciki ma Zulfa’u k’awarta...Tuni ta soma hango Zulfah a Office d’in First Lady dan tasan Zulfah ta kusa bankwana da station d’insu... Can suka taddasu Mamy su Aunty Daula, Aunty Daula tana ganin Nabilah ta tafi ta rungumeta tana fad’in ko ba’a ce mata ba ga ‘yar gidanta amaryar d’an gidanta Khalid... Tuni su Ijlaal ma suka nufosu suna rungumarsu one by one, kan kace mai Zulfa’u Sarkin kuka idanunta sun shiga k’ok’arin kawo ruwa, yau gasu da zuri’arsu gaba d’aya a tare... Nan fah d’aukacin mutanen dake wajen ma idaniyansu suka shiga zuban hawaye.... Yaya Abidah ta isa tsakiyan Nabilah da Zulfah, tana hawaye ta rungumesu gaba d’aya suma hawayen suke... Mamy, Aunty B da kuma Aunty D suka isa suka rungumesu gaba d’aya suma... Aunty B ta mik’e tana amsa wayan Sameer da alama sanar da ita yake zai biya ya d’auko Raihanah da Marliya dan su biyu ne basu a wajen saiko Engr Ma’aruf da nasa family d’in su Muhibbah da yaransa da har yanzu suma basu samu isowa ba... Aunty Bara’atu tace “Sameer Sarkin aiki, kai har weekends d’inma bazaka huta ba....?” Daga d’aya b’angaren Sameer yace “Aunty dole ce ta kama emergency aka samu kuma ni ake buk’ata a wajen...” Aunty B tace “Allah dai ya dafa maku gaba d’aya, aikin naka is not easy... Kodashike taimakon Al’umma ne, Allah ya baka ladanka...” Sameer ya amsada Ameen Aunty na... Ku bamu mintina kad’an gamu nan isowa in sha Allah...” Aunty Bara’atu tace “Take your time shima babban Yayan naku har yanzu bai iso ba, k’ila wani uzurin ya rik’esa....” Sameer yace “Alright zan kirashi naji...Kinsan Excellency mai hidima da jama’a ne sosai....” Aunty B tace “Toh shikenan sai Kun iso, Allah ya tsare...” Sameer ya asmada Ameen Aunty kana sukai sallama.... *** A can gida kaw har yanzu gaban Raihanah bai daina fad’uwa ba, gashi Mamani tin safe babu wanda ya sakata a idanu, itakam sosai ta damu da Mamani dikda abubuwan da suka faru, dan d’an zaman da tai gabanta ta kula Mamani mutuniyar kirkice in her own ways dikda cewa tanada nata hayyan mabanbanta, ko kusa bazata had’a zaman gaban Mamani da zaman da tai gaban Haule ba... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya tana duban rantsetsiyar doguwar rigar da Mamy ta bata tace ta saka, tasan dai can gidan Yayar Mamy zasu tinda yanzu maganan is all over babu wanda baisan Mamy sun had’eda zuri’ararsu gaba d’aya ba, amma koda wasa batasan cewa ita d’in matar aure bace har yanzu, auren ma yayansu Ma’aruf mijin da Yayarta Sahariyya was about to marry him.... Sosai rigar tai mata kyau ta zauna a jikinta d’as, Marliya ta tak’urata sai ta d’anyi kwalliya a fuskarta... Murmushi kawai Raihanah tai kana tace “Toh Wai a waye zanyi kwalliyan ne...?” Marliya tace “Gidan biki fah zamu tafi, kika sani ko ki had’uda naki Prince Charming d’in mu kuma shan nik’i soon...” Ta k’arashe tana kashe mata idanu... Harara Raihanah ta d’an aika mata kana ta girgiza kai tace “Ke koh... Zaki sani ne...” Marliya ta kuma darawa tace “Eh dai naji....” Gyara d’aurin kwalinta take gaban mirror lokaci guda take ci gaba da fad’in “Na kasa daina tinanin abubuwan da suke kan faruwa, Wai yau Mamy da family d’inta gaba d’aya a had’e waje guda.... Allah mai iko...” Raihanah dake nad’e mayafin rigar akanta tace “Ikon Allah kenan Marliya, ya wuce gaban tinanin d’an adam... Mamy ta cancanci Farin ciki Bayan dik tulin k’alubalen data fuskanta a rayuwa, ita d’in tanada zuciya mai kyau , dole duk wani masoyinta yai mata Farin ciki....” Marliya tace “Haka ne kam, Kinga tsaya na d’an shafa miki koda powder ce kawai kafin Ya Ma’aruf ya iso....” Juya idanu kawai Raihanah tai had’ida girgiza kai kana tace “Wllhi Marliya kin faye fitina, Nabilah ce maganinki, Ana ganin itace mafad’aciya fad’arta batayi saida dalili, kece mai damunta da fitina, kija gefe ki nok’e kaman ba ke ba....” Marliya ta tintsire da dariya tace “Allah sarki Addah Beels d’ina wllhi zanyi kewarta sosai...” Raihanah ta murmusa a daidai lokacinda sukaji sallaman Yayansu Ma’aruf a k’ofa... Wani irin fad’uwan gaba Raihanah taji ya sauk’ar mata lokaci guda... *** A can gidan Engr kaw bai sanar da Muhibbah yanda zasuje ba saidai ya umarceta data shirya yaran gaba d’aya dan duk tare zasu fita, ga wani kwalliya na musamman da mijin nata ya buga, saikace wani sabon ango, ta lura yanayin da yake ciki a yau d’in zata iya cewa bata tab’a ganinsa ciki ba tsawon rayuwarsu saiko lokutan data haifo masa yaransu, Toh what’s he up...? Ta tambayi kanta sanda ta hangosa na sauk’owa daga bene waya manne kunnensa... Zumbur ta mik’e gabanta na wani irin yankewa dan wani irin azabebben kyau ya mata ga k’warjininsa da ya kuma fitowa sosai, haka kurum taji hankalinta bai kwanta ba..... Ya k’araso yana mai saka wayar a aljihu daidai sanda su Najma Irfaan da kuma Samha suka k’araso suna rungumesa suna fad’in “Daddy you look handsome..!” Ya d’auki Najma ya azata a kafad’a yayinda ya shafa kan Irfaan da Samha yace maza su shige Patrick ya bud’e masu mota.... Muhibbah ta raka yaran nata da muguwar kallo a cewarta munafunci ke sa suke nuna sunfi son ubansu sama da ita, bacin haka dik gayu da tasha basuce ta masu kyau ba sai Ubansu, munafukan banza kawai... Duban Engr ta d’an kumayi kana tace “Wai ina ne kam zamuje my Engr....?” Ba tareda ya dubeta ba yace “It’s Sunday, after all... Idan munje zaki gani...” Daga haka sa kai yai ya shige Najma tana fad’in zata sha ice cream d’in cold stone... Muhibbah dai tab’e baki tai kana tace a zuciyarta k’ila sabida weekend ne shiyasa zasu fita gaba d’aya da yaran tinda sun jima basu d’an fita haka ba kullum hidiman siyasa bai bari ya zauna, wata zuciyar kuma tace K’ila sabida misunderstanding d’in da kuka samu jiya ne kikai banza dashi shiyasa yau ya shirya maku fita to make it up to you... Ta wani murmusa ita kad’ai tana jin kanta, a hankali ta shiga buga kafad’anta tana fad’in “Ke d’in amanarsa ce dole dik yanda yakaiga fushi ya sauk’o ya baki hak’uri..!” Ta kuma murmusawa kafin ta d’au handbag da mayafinta saman sofa ta take masu baya... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *95* *©️Sameena Aleeyou✍🏽* Suna tafe cikin motar yake sanar da ita yanda zasuje da kuma dalilin zuwan nasu, mamaki da al’ajabi ya cika Muhibbah... Gyara zama ta d’anyi tana dubansa sosai, lokaci guda take furta “Anya kuwa Excellency na... ‘Yan uwanka fah kace...? Mai yasa tintini basu nemeka ba, sai yanzu da sukaga ka zama mai fad’i aji, Nidai inaga kud’inka suke kwad’ayi babu wani ‘yanuwankan nan....” Wane irin duba da yake aika mata ya sanyata had’iye sauran maganganun nata.... Ta d’an muskuta tana yatsina fuska lokaci guda taci gaba da fad’in “Ni dai shawari nake baka ka bincika da kyau, Frauds sunyi yawa...!” Ba don shid’in bai kasance daga cikin maza masu dukan mata ba tabbas da ya shasshafeta da mari masu kyau, sannan yaransu dake bayan motar baiso su d’ago wani abu, shisa ma yai mata shiru, amma kam duba guda zaka masa ka fahimci tsananin b’acin rai da maganganun Muhibbah ya jefasa ciki, ta yaya zai kawo mata wannan labari mai dad’in gaske da yaso surprising d’inta dashi ta karb’i zancen a haka... A matsayinta na matarsa abokiyar rayuwarsa, tsawon shekarun nan ya zaci zatafi kowa nuna Farin cikinta, ya zaci zata tayasa Farin ciki bayan tulin shekarun nan da yayi cikin duhun rashin sanin ina asalinsa... Tareda ita akaita gwagwarmaya lokacin da ‘yan adawa sukaso b’ata masa suna cewa baida asali wanda badon Allah ya kiyaye ba da maganan yai tasiri, amma dik Muhibbah ta mance wannan, ya yana sanar da ita mahaifiyarsa na raye kuma ya sameta amma tana cewa Allah sa ba ‘yan wanki bane... Bai iya furta mata komai ba sai murza tafin hannunsa a hankali da yake sabida tsananin b’acin rai.... Ta d’an saci kallonsa had’ida tab’e baki kad’an, ita dai dikda cewa ya sanar da ita tinaninsa da ya b’ace sanda yake k’arami ya dawo amma bata yarda wad’annan mutanen ba dukiyar mijinta suke bibiya ba dan haka kawai taji sam bata yarda dasu ba, tin kafin tayi ido hud’u dasu taji ta tsanesu sosai... ***** A tare Marliya da Raihanah suka gaidashi, ya amsa idanunsa kan Raihanar, ta masa kyau sosai, rigar ta amsheta... Har saida yaji ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta, dikda cewa itad’in nata idanun a k’asa suke... Bud’e murya ya d’anyi kana yace “Kun shirya...?” Suka jinjina kai a tare Marliya na fad’in “Eh mun shirya Yaya....” Jinjina kai shima d’in yai kana yace “Alright kuje mota ku jiran barin duba Abbah Ina zuwa....” Amsa mar sukai da toh kana yasa kai ya juya, sai sannan Raihanah ta d’ago ta dubesa sanda yake ficewa... Yau d’in shadda ce dakakkiyar wagambari mai ruwan sararin samaniya da akai mata d’inkin jampa jikinsa saiko hula zanna bukar mai kalan shud’i wato dark blue wanda ya dace da zarenda akai ado ma kayan dashi, yayi kyau matuk’a kaman wani sabon ango... Koda Sameer ya isa sashen Abbah bai tadda Abbah ba, dan rufe ya tadda sashen nasa, Toh Ina Abban ya tafi kuma ai yau d’in weekend ne....? Kasa samo amsar yai hakan ya sanyashi juyowa yana tinanin yanda Abbah ya tafi, daga nan sashen Mamani ya lek’a nan ma sammakal bata nan kaman yanda bak’in Kazaure ma dik sun tafi da alama wasu kuma suna b’angaren su Baffah Ado.... Ajiyan zuciya ya sauk’e a hankali kana ya nufo waje ya taddasu Raihanah, alamun bud’e mota da sukaji ya sanya Marliya saurin kaman marfin backseat ta shige abinta... Raihanah tai rau rau tana duban Marliya dake mata alama da ta shiga gaba.. Girgiza kai kurum tai dan ita yanzu ta gama gane Marliya neman magana ne da ita had’ida jin baki, haka nan ta kama marfin front seat d’in ta shige dik tana jinta wane iri... Itakam maiyasa dik sanda suka kasance tare take jin wannan yanayi...? Tambayar da ta tabbata bata da amsar sa, hakan sai ya tuna mata d’aukota daga islamiya da yai kwanakin baya, tana jin sanda ya daidaita saman driver’s seat bugun zuciyarta ya k’aru gaba d’aya a tak’ure take, Allah ya sani mugun nauyinsa takeji... Zata iya cewa har suka isa yanda zasuje a d’arare take... Tanajin sanda ya ida parking ya bud’e central lock, Marliya ta kama marfin motar ta fice yayinda itakam Raihanah ta shiga kiciniya da seatbelt dan sanda zasu wuce road safety ya umarceta ta d’aura seatbelt, gaba d’aya sai kokawan zame jikinta take daga cikin seatbelt d’in... Sameer yai mata k’uri yana duban yanda take kokawa da seatbelt... A hankali ya d’an rank’wafo had’ida kai hannu yana k’ok’arin cire mata, yanda fuskokinsu sukai dap da juna ya haifar masu da fad’uwan gaba mai tsanani, dan gaba d’ayansu bugun zuciyarsu saida ya k’aru.... Tai saurin janye fuskarta k’irjinta bai daina bugu ba, gashi ya kasa janye jikinsa saima k’ura mata idanu da yai abin har sai ya soma bata tsoro, maiyasa zai mata haka...? A iyaka saninta shid’in ba mutumin banza bane... Tana tsaka da tinanin taji ya mik’e ya daidaita zamansa saman nasa kujeran tamkar wanda ya tuno wani abin... Murya a hankali taji yana furta “Kina iya fita, be careful next time kar Ki had’a seatbelt da rigarki...” Ita dai kai kurum ta jinjina masa dan har yanzu jikinta a mace yake, da k’yar ta iya ficewa daga cikin motar k’afafunta sai rawa suke tamkar wanda zasu gaza d’aukarta.... Shiko Sameer jingina cikin motar yai had’ida lumshe idanu... God! Wai yau shi Sameer ke jin wani abu gameda wata mace ba Siyama ba..? Ya d’an ware idanunsa kad’an yana mai murmusawa a hankali, shi kad’ai yasan zancen da yakeda zuciyarsa saiko mak’aginsa...A haka su Engr suka k’araso, Sameer yai saurin daidaita kansa kana shima ya fito daga motar tasa, kai tsaye wajensu ya nufa suna gaisawa, take Engr ya soma introducing family d’insa ma Sameer... Muhibbah dai da alama hankalinta dik bai wajen dan tin a mota Shamzy ta isheta da waya bata d’agawa saidai ta danna a silent... K’arshe Shamzy text ta turo mata cewa dik yanda za’ai su had’u anjima dan Oga Bash yace kaya masu yawa zasu fitar a satin da za’a shiga, so itama dole ana buk’atarta.... Rausayar da idanu kurum tai sanda ta ida karance sak’on, yanzu dik basa samun attention d’inta sosai tinda ta soma prioritizing zaman aurenta sama da business d’insu... She can’t afford to lose this millions dole dik yanda za’ai tasan wata hanyar da zasuke had’uwa dasu Shamzy su Bash a store d’in Bash na saida garin siminti a zahiri amma a bad’ini waje ne na hada hadan miyagun k’wayoyi... Shi kansa Engr ya kula gaba d’aya mind d’in Muhibba was somewhere else amma baice mata komai ba saima jerawa da sukai shida Sameer suka nufi cikin gidan suna fira, Sameer d’aukeda d’iyar Engr k’arama... Basu kaiga main k’ofar shiga gidan ba Daddy da Khalid suka iso, hakan yasa Engr da Sameer dakatawa dan gaisawa dasu Daddyn.... Muhibbah dake tsaye daga can b’angaren da suka parking motarsu tana amsa waya lokaci ta ida wayar nata tana sanarda Shamzy cewa gidan biological parents d’in Engr sukazo dan ya sanar da ita dik abindake faruwa cikin mota saidai bai bata labarin auren nasa ba dan shima magana ne mai zaman kansa... Muhibbah ta janyo hannun yaranta guda biyu suka nufi gidan sai wani yatsina fuska take tana mak’ale da hannayen yaranta, ko takan su Engr batabi ba.... Tana shiga cikin gidan Daula ta mik’e ta tarota tanai mata sannu da zuwa dashike sunsan juna, babu b’ata lokaci Daula ta shiga introducing Muhibbah masu Mamy su Ammah, su Zulfah dai suna daga can d’akin da aka sauk’i Zulfa’un, sun barbaje abinsu Atika nata faman basu dariya Nabilah na tayata saikace ba Amarya ba abinka da gwana wajen surutu... Ita dai Raihanah har yanzu bata dawo daidai ba tinanin abinda ya faru tsakaninta da Ya Ma’aruf a mota bai saketa ba, zata iya cewa har yanzu tana jin kaman sauk’an d’umin numfashinsa saman fuskanta sanda yazo zare mata seatbelt d’in... Allah ya gani dik yanda za’ai a komawa bazata yarda ta shiga gaban motarsa ba... Tana jin su Atika da Nabilah na kuma kwashewa Haule da Lami albarka Zulfa’u na kwab’arsu amma kaman ingizasu take.... Marliya silent crook ta shiga labarta masu yanda aka fasa auren Sahariyya da Ya Ma’aruf da irin kuka da ihun da Sahariyya ta dingayi da yanda su Amara suka tisata gaba da habaici da rashin daraja, dan Basma ta kawo mata labarin komai... Haba nan fah suka kuma samun abin yi sai dariya suke harda kwanciya saman gado, Nabilah tace inama tana wajen akai wannan drama a gidan Hajiya, Wayaga losers... Babun bad’inu, Sahariyya bata auri Ya Ma’aruf ba ga kuma Ya Hafiz bai Auri Zulfah ba.... Atika tace “Ai saidai ya hangomu cikin annakiyan BMW k’irar Jeep muna daga sama muna masa waving tsakaninmu dashi kenan...” Suka kuma tintsirewa da dariya yayinda Zulfah ta katsesu da fad’in “Ku dai haka babu kyau wllhi, never return evil with evil, kuyi masu fatan samun sauk’i cikin iftila’in da suka tsinci kansu ciki, duk fah yanda kukaje kukazo ‘yanuwanku ne kuma dik d’an adam ajizine... Babu fah wanda yafi k’arfin kuskure...” Nabilah tace “Chapp! Ai duk kuskuren da za’a maimaitasa ba sau d’aya ba ba sau biyu ba sunansa ganganci da son zuciya... Wllhi abinda suka shuka ne suke girban kayansu... Yanzu ke har kin mance abinda wad’annan azzalumai suka maki keda Khausar... Wllhi ko tausayi basu bani ba, Aima basuga komai ba wllhi, sai Ya Hafiz da Addah Sahariyya sun koma ‘yan jagoran barawa Hajiya.....” Atika tace “Gayamata Beels nawa shiyasa nake sonki...” Zulfah ta tab’e baki tace “Da shike hali yazo d’aya ba ai dole ki sota...” Atika ta kuma mik’ama Nabilah hannu suka tafe suna dariya...Zulfah dai girgiza kai kurum tai kana tace “Allah ya yaye maku..” Atika na dariya tace “Ameen dai Akaramakiya matar Akr...” Tamakar wacce ta tuna wani abu haka ta kame bakinta da duka hanayenta biyu bata k’arasa ambato sunan Akram d’in ba....Zulfah ta aika mata harara kurum had’ida girgiza kai, idan kabi na Nabila da Atika sai su zautarka....A haka Aunty Bara’atu ta shigo ta taddasu ta sanar dasu maza su fito parlor suyi gaisuwa.... Kowaccensu ta mik’e tana neman mayafi, gaban Zulfah sai fad’uwa take yau zata gaisa da Mutallab.... Ganin ta fad’ad’a murmushinta yasa Atika janyota baya tai k’asa k’asa da murya tace “Nidai karkije kiyita Washe baki, kuma karkice Ke supporter d’insa ce ehe...” Harara kurum Zulfah ta galla mata had’ida murmusawa.... Gaba d’aya suka nufo parlorn suka dudduk’a suna gaidasu d’aya bayan d’aya.... Sanda Nabilah take gaida Daddy ta saci kallon Khalid dake faman aika mata duban zamu gamu... Sai wani fuskewa yake shi a dole fushi yake da ita.... Daddy kaw da fari’a yaketa amsa masu gaisuwar nasu yana saka masu albarka.... Shiko Engr tinda ta fito idanunsa akanta suke... Ya kasa janyesu daga barin duban nata, dik yanda yake kissima kamanninta daga muryarta da yake saurare harta zarce masa nan, ita d’ince da gaske gabansa, shid’in ma’abocin sauraren muryarta ne, yau gata nan gabanshi cikin idanunshi masu muradin ganinta.... Tina cewa da yai ita d’in kuma matarsa ce sai ya saki wani sassanyar murmushi a hankali....K’uri yai mata yanda take sakin murmushin nan nata mai sanyaya zuciya ga duk wanda takema, he couldn’t believe this is happening.... Muhibbah tai masa k’uri tana karantarsa, ta kuma juyowa tana duban Zulfa’u dake magana da Aunty Daula kyakkyawan murmushi saman fuskarta, ita kanta saida ta raina kanta da ganin wannan mata, tayi kyau sosai cikin d’inki atampa ruwan shud’i had’ida mayafi ruwan shud’i shima, kana ganinta Kaga Amarya sabida wani annuri da fuskarta keyi... Muhibbah ta kuma duban Engr sai taga kaman kaya iri guda suka sa... Tana tsaka da tinanin wayarta ya d’auki ruri Shamzy ce mai kira, lokaci guda ta saci idanun jama’an dake wajen ta d’an fice tana amsa wayan.... Sai bayan ficewarta Zulfa’u ta waigo sashen da Engr yake, wani irin fad’uwan gaba ta tsinci kanta dashi... Gabanta yai wane irin bugawa ba tareda sanin dalili ba... Shid’inma ita yake duba, tai k’ok’arin saita kanta kana ta soma gaidashi... Saida ya saita kansa kafin ya iya amsa mata gaisuwan... Gani tai ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta, gaba d’aya sai tajita a tsarge musamman sanin cewa da tai itafah matar aure ce yanzun.... K’arasowan yaransa ne ya ceci Zulfa’u daga irin duban da Engr Ma’aruf ke mata, gabanta sai faman bugawa yake da sauri da sauri harsaida ta tuhumi kanta meke faruwa da ita... Kiraye kirayen sallan zuhur da aka soma yasa mazan ficewa masallaci dan gabatar da nasu sallan, Irfaan na tsakaninsu rik’eda hannun Daddynsa suka nufi masallacin gaba d’ai... A cikin gida kaw bayan wad’anda zasuyi sallah sun ida Mamy cewa tai dik su shige kitchen su taya Hajja shirya abinci... Aunty Daula tace “A’a Mamy akwai amare cikinsu da dai an bari nida sister ma taya Hajjah ta k’arashe tana duban Aunty B... Mamy tace “A’a, idan amaren ne fah...? Ince gidajen mazajensu zasu tafi... Maza maza kowa ta shige, division of labour Daula Ki d’ebe maki group d’in Zulfa’u Raihanah da Marliya kema Bara’atu Ki tasa naki team d’in gaba, Atika da Nabilah....” Zulfah ta zaro ido tace “Mamy ai dai da baki had’e wad’annan fitinannun waje guda ba wllhi babu aikin da zasuyi...” Mamy tace “Shisa na had’e su biyun k’ark’ashin Bara’atu daidansu....” Gaba d’aya dan darawa sukai kafin Aunty B tace “An gama Hajiya Mamy....” A parlor suka tadda matar Engr k’afafu d’aya bisa d’aya sai chatting d’inta take.... Aunty Daula tace “A’a Mummy Irfaan sorry mun barki Ke kad’ai mu k’arasa kitchen mana....” D’an yatsina fuska tai kana tace “Um um Daula kinsan kitchen ba wajen zuwana da garaje bane, ni tafiya ma zanyi K’awata Shamzy na Emergency yanzu aka kirani, idan Excellency na yazo pls sai ki sanar dashi....” Ta k’arashe tana yafa mayafinta had’ida d’aukan handbag d’inta.... Nabilah da Atika yawa sun samu Tv haka suka bi matar nan da kallo, ko darajan sallama su Mamy basu samu ba balle Ya Abidah uwar mijin nata...Aunty B ta dubi Daula tace “Haka d’an uwan naki yake fama....” Daula dai murmusawa kawai ta d’anyi kana tace “Ai a haka ta rage wasu abubuwan....” Aunty B tace “Ni yaran ne ma abin tausayi....” Daula tace “Hm muje kedai na baki labari...” Aiko babu musu Aunty B ta take mata baya.... Zulfah da k’arasowarta kenan ta taddasu Atika da Nabilah suna zancen matar Ya Ma’aruf Babba.... Girgiza kai kurum Zulfah tai kana tace “Ku dai ba’a rabaku da abin magana, yanzu itama wannan d’in daga had’uwarku rana guda har kun nemo makusarta, matarda ko saninta bakuyi ba... Ni dai ina fad’a maku ku dai yi a hankali kuma mata ne... Barin Ke Nabilah gidan sirakai zaki tafi, wllhi ku bi duniya a sannu....” Nabilah ta b’ata fuska had’ida turo baki “Ni wllhi Addah Ke komai sai kince ba haka ba ba’ai dadai ba... Kuma bayan gaskiya kawai muke fad’i tinda ba shaidan zir mukai ba da idanunmu muka gani...” Zulfah ta girgiza kai tace “Nidai bazan fasa fad’a maku gaskiya ba....” Atika tace “Allah huci ran matar gwamna...!” Sai kuma tai saurin k’unshe bakinta sanda Zulfah ta kuma tambayarta “Matar wa kikace...?” Atika na Washe baki tace “Matar aure nace....” Zulfah tace “Ce miki akai banji abinda kika fad’i ba.. Wane gwamnan kike nufi...?” Batakaiga bata amsa ba Mamy ta katsesu da fad’in “Mai kuma kuka tsayayi wajen kunaji an fito daga nasallaci....” Ai bata kai aya ba suka shige gaba d’aya... Sameer Mamy ta hanga ya shigo rik’eda hannun Irfaan d’an gidan Engr... Mamy ta tsaresa da tambayar ko ya lek’a Abbansa Kafin ya taho nan... Sameer ya d’an numfasa yace “Mamy dama inaso muyi maganan...” Mamy ta jinjina kai kana tace “Mu k’arasa daga can...” Babu musu yabi bayan mahaifiyar tasa ya saki hannun Irfaan da tuni ya nufi wajen k’annensa da Kakarsu da suka santa a yau... Yaran sun baibayeta harda yaran Daula gaba d’aya sai zuba mata shirirta suke tana biyesu... Allah sarki rayuwa, wata irin rayuwa ce mai cikeda nishad’i Yaya Abidar Ke experiencing a halin yanzu wanda bata fatan abinda zai datse wannan Farin ciki da annashuwa da take ciki.... Hak’ik’a ba tarin dukiya bane jin dad’in rayuwa, Farin ciki da annashuwa wasu aba ne da dukiya bata iya sayensu... Sosai Engr yasha mamaki sanda ya dawo ya tadda Wai Muhibbah ta tafi... Zancen cewa k’awarta na emergency sam bai shiga kansa ba tinda tin suna mota ga ya fahimci take takenta... A b’a gareni yaran kaw tafiyar mahaifiyar tasu baiko damesu ba saima cewa da sukai a barsu gidan Ammah su kwana koda d’aya ne, kakar tasu ma ta goyi bayan hakan dan tanason taji d’umin jikokinta wanda bata samu taji ba tsawon shekarun nan.... Wajajen la’asar Daddy yai masu sallama da niyyan washe gari idan Allah ya kai rai zai tafi Abuja akwai aikin da zai gudanar can kafin ya wuce Kaduna... Sukai sallama da matarsa Daula da yaransa dan cewa yai su bari kawai sa taho tareda Khalid da Nabilah tinda gobe take gama exams d’inta suma sai su samu time sosai da ‘yanuwansu.... Hakan sosai yaima Daula dad’i.... Bayan sun ida sallama da mijin nata Khalid ne ya mik’e yai masa rakiya zuwa mota.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *96* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tsaye suke jikin motar Daddy sanda Daddyn yaci gaba da fad’in “You’re a gentleman now Khalid... Soon enough zaka soma aje Iyalai, har kullum wasiyyata a gareka ka kula da family d’inka Khalid... Take care of our family, my family.... Kai hak’uri da mahaifiyarka da kuma ‘yaruwarka Siyama, na sani idan labarin aurenka ya riskesu komai ka iya faruwa, amma a matsayinka na namiji kuma magidanci a halin yanzu... Inaso kabi komai a sannu sannan kai hak’uri da kowa kaji koh....” Khalid ya jinjina kai a hankali kana yace a sanyaye “Amma Daddy maiyasa shayibun bazai kaika ba, idan yaso ni sai na taho dasu gaba d’aya...” Daddy ya d’an murmusa kad’an “Banda abinka Khalid idan na tafi da Shayibu ita matar taka ai baza’a rasa wad’anda zasu mata rakiya ba koh... Toh gani ai motar tai maku kad’an, shi Shayibun dai ya zauna ni zan tuk’a kaina kada ka damu kaji koh...” D’an jim Khalid yai kana yace “Amma Daddy....!” Katsesa Daddy yai da fad’in “Ya isa Khalid kayi abinda nace kawai... Allah shi maku albarka gaba d’aya....” Khalid ya amsada “Ameen Daddy, Allah ya tsare ya kiyaye hanya...” Dik jiki a mace yake maganar... Daddy ma ya amsa mar da Ameen.... Har yasa kai zai shige mota sai ya kuma juyowa ya dubi Khalid.... Lokaci guda ya rubgumesa sosai, saitin kunnensa yake rad’a masa “Take care of my family...!” Wani irin bugu Khalid yaji k’irjinsa na mai haka kurum... Yanaji yana gani har Daddy ya shige mota yai mata key, kaman wanda aka dasa haka yai tsaye a wajen har saida Daddy ya fice daga gate d’in gidan.... Jiki babu laka Khalid ya furta “Be safe Daddy...!” Jiki a natuk’ar sanyaye ya juya ya komo cikin gida, harta Nabilah saida ta kula da canzawan Khalid d’in... Dikda fushi yake da ita amma sai taji tana son sanin matsalarsa saidai Khalid d’in sam bai bata k’ofar jin damuwar tasa ba, k’arshe ma sallama yai masu ya koma masauk’insa.... Suma dai daga nan gida suka tattafi yayinda Aunty B ta tsare Zulfa’u a d’aki tai mata nasiha sosai mai ratsa zuciya sannan ta k’arada “Idan mijin naki ya iso kafin ku wuce gidanku zai biya dake wajen Abbah kinji koh....” Tana danne hawayenta take jinjina kai alamun taji, saidai tuni hawayen sun soma zubowa.... Gaba d’aya sai jikin Aunty B d’inma yai sanyi.... Matsowa kusanta tai sosai kana ta kamo hannayenta tace “Zulfa’u d’ago ki dubeni....” kasa d’agowan tai har saida Aunty Bara’atu ta maimaita... Nan ya ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubanta... Lokaci guda Aunty B d’in ta rungumeta cikeda tausaya mata, take kukan Zulfah ya k’aru sosai.... Har saida Aunty B ta matse nata k’wallan kana tace “Haba Zulfa’u kukan nan ya isa haka, aure fah bafa mutuwa bace, idan kina haka ita kuma Nabilah tai yaya....? Kukan nan ya isa haka kinji koh....” Zulfah naci gaba da goge fuska cikin muryar kuka take fad’in “Aunty shin meye makomar aurena a karo na biyu... Shin iftila’in dana fuskanta a gidan aurena na fari shi zan kuma fuskanta... Aunty ina mijina...? Baisan an d’aura mana aure bane... Maiyasa ya kasa koda kirana a waya balle na sakashi a idanuna.... Aunty tsoro nake kada na kuma tarar da rayuwa irin wacce nayi a gidan tsohon mijina... Ni kuma kalan nawa jarabawar kenan Aunty...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Ga tsananin mamakinta murmushi taga Aunty Bara’atu tai wannan karon kana ta kuma kamo hannayenta kad’an tace “In sha Allah kin baro wancan rayuwar kenan, rabuwa ta har abada... In sha Allahu zaki tadda Farin ciki da haske mai wanzuwa a sabuwar rayuwar da kika tsinci kanki ciki.... Ki kwantar da hankalinki kuma ki karb’i zab’inda Allah yai maki dan a koda Yaushe zab’insa shine mafi alkhairi a garemu kinji koh...!” Jikinta ya kuma yin sanyi sosai kana ta shiga jinjina mata kai a hankali... Sallama suka kumayi Aunty Bara’atu ta nufi wajen ‘yar uwarta Ya Abida suka kuma yin sallama.... Atika ma dai mik’ewa tai tana fad’in “Toh amarsu ta ango, yanzu kam sai munyi talaho kuma....” Shaye da mamaki Zulfa’u Ke dubanta kana tace “Wai tsaya kina nufin kema tafiyar zakiyi ne....?” Atika dake sab’a mayafi tace “Sake tambayata, mai kuma zan zauna na miki bayan ango yanzu zai shigo....” Zulfah ta girgiza kai cikin rashin yarda kana tace “Kina nufin bazakimin rakiya ba kenan....?” D’an darawa kad’an Atika tai kana tace “Yo rakiya na nawa kuma bayan wanda nai maki, ko so kike ango ya fatattakeni kam, ai sai na hau masa kai... Kinga kedai zamuyi waya kawai, daga baya kuma mazo ganin d’aki taredasu Aunty Zilai....” Zulfah tai k’wafa ganin dai da gaske Atika ma tafiyarta zatai, gashi sai shak’iyanci take mata tana fad’in ta wanke idanunta da kyau dan ango shigowar bazata zai mata... Dik wannan hannunka mai sanda da Atika Ke tai mata itafah bata fahimci komai ba, hasalima bata kawo komai a ranta ba, suna a haka yaran Engr suka shigo a guje har suna rige rigen mik’awa Zulfah sabuwar hijabi da cazabaha Ammah ta basu su kawo mata... Ta amsa fuska fal fari’a had’ida yi masu godiya, ta ije saman abin sallah dake linke gefe...K’aramar ta d’auka ta d’aurata bisa cinya tana kuma tambayarsu sunayensu... Nan da na yaran suka saki jiki suna zuba mata zance musamman Najma da take jinta Tamkar d’iyarta Khausar... Suna a haka suka jiyo sallaman babansu, gabanta ya yanke ya fad’i... Tai saurin gyara zaman mayafinta had’ida amsa sallaman.... A guje yaran suka tafi suka rungume Babansu idan ka d’auke Najma da tak’i matsawa daga jikin Zulfah.... Yaran suka shiga zuba masa shagwab’a yana biyesu, Samha fad’i take “Daddy ni dai nafi son gidan Ammah please Daddy banso na koma gida... Shima Irfaan hakan yace baiso ya koma gida wajen Mummy....” Shafa kansu yai kana yace “Alright za’a kawo maku uniforms d’inku sai kuyi kwana biyu ma granny ko...” Gaba d’aya tsalle suke suna murna harda rungumesa suna fad’in we love you Daddy.... Shima ya rungumesu yana kissing kansu... Abin sosai ya baiwa Zulfah sha’awa ganin yanda Engr Ma’aruf keda kyakkyawan alak’a da yaransa yanda ake so ko wane uba ya kasance da yaransa.... Ficewa yaran sukai suka nufi sashen Ammah dan sanar da ita Daddynsu yace zasu zauna a gidanta... Ya d’ago yana duban Najma yanda tai kwance lif jikin Zulfa’u.... Murmushi ya saki a hankali kana yace “Princess ba oyoyo wa Daddy ne...?” Sai sannan ta tashi ta nufoshi da gudu ta rungumeshi... Zulfah ta saki murmushi tana mai gaidashi.... Fuska a sake shima ya amsa mata, a zatonta fita zai dan harga Allah tinaninta ya biyo sahun yaransa ne... Amma ga tsananin mamakinta sai gani tai ya zauna daga saman kujera mai kallon gadon da take zaune bisa had’ida d’aura d’iyarsa saman cinyar sa dake ta faman zuba masa shagwab’a yana kan biyeta... Itakaw Zulfah k’uri ta masu dan harga Allah sosai suka birgeta... Sosai ta shagala da kallonsu har saida ta jiyo muryarsa yana fad’in taje taiwa Aunty goodnight kiss itama... A guje ta taho taima Zulfah peck a kumatu tana fad’in “Goodnight Aunty...!” Zulfah ta Shafa kanta tace “Goodnight Princess...!” Daga haka ficewa yarinya tai cikin d’an tsalle da gudu irin na yara... Gaba d’aya suka bita da kallo murmushi saman fuskokinsu Engr na fad’in “Watch your steps baby...Be careful... I love you...!” Maido da dubansaga Zulfah yai wacce har yanzu bata daina bin k’ofar da kallo tana murmushi ba, ya zuba mata kyawawan idanunsa yana dubanta, har saida taji bugun zuciyarta na k’aruwa... Tai saurin waigowa aiko nan idanunsu suka sark’e waje guda.... Tai saurin sadda nata k’asa dan bazata iya juran duban cikin idanunsa ba.... Engr ya d’an gyara zamansa kad’an yace “Amarya har kukan ya k’are ne.... Ko don bakiga an tafi dake gidan naki bane tinda har yanzu gidan Mamanki kike....” Yanda yai maganar dole ya baka dariya, dan dagaji had’o kalaman kawai yake amma bawai ya saba da surutun bane.... D’an murmusawa tai kad’an ba tareda tace komai ba, shiru ne na ‘yan wasu dak’ik’ai ya raba tsakani.... Kowa da abinda yake sak’awa cikin zuciyarsa... A b’angaren Zulfah ma iya cewa tambayar kanta take ta faman yi shin mai ya zaunar da bawan Allahn nan a d’akin... Idan sawun yaransa ya biyo ai sun tafi... Toh mai kuma yakeyi...? Batakaiga samo amsar ba ta sinkayo muryarsa mai cikeda charisma yana fad’in “Emmm... Munyi magana da Ammah zaki zauna a nan for the meantime before a ida gyaran naki sashen.... Idan akwai dik wani abinda kike buk’ata Ammah ba sirkarki bace mamarki ce... Ko mai kike so don’t hesitate to tell her kinji koh...” A’a gaba d’aya kan Zulfah fah ya k’ulle Wai meke faruwa ne....? Batakaiga samo amsar ba ta kuma sinkayo muryarsa naci gaba da fad’in “Nasan you might be a little confused, but karki damu... Ga wannan Ki karanta, idan kin gama karantawa anjima kad’an zan shigo nai maki bayanin komai... But for now read this first...” Ya k’arashe yana mai aje mata takardan da Akram ya bariwa Yusuf ya bata saman gado.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... What’s all this... Wai meke faruwa ne...? Meye wannan yake faruwa yanzu da ita...? Gaba d’aya jikinta ya koma sanyi k’alau... Itafah bata fahimci komai ba... Wai me hakan yake nufi ne...? Ta k’arashe tinanin tana mai bin bayan Engr da ya fice yana amsa waya da kallo.... Tamkar wacce aka zabura tai wuf ta d’au takardan tana juyawa k’irjinta bai daina bugu ba.... Sosai hannayentake rawa sanda ta soma warware takardan.... Taji jiri na neman d’ibanta.... Ta mik’e zumbur zuciyarta naci gaba da wani irin tsinkewa... Shin abinda take gani gaskiya ne koko akasinsa... Shin dama Engr Mutallab shine mutumin da ya soma furta yana sonta, ashe Akram da fari ba kanshi ya kawo ba Ubangidansa ya kawo.... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa sanda take ci gaba da karanta wasik’ar... Wasu irin hawaye taji suna gangaro mata d’aya bai jiran d’aya.... A hankali ta lumshe idanunta da suka jik’e shakaf da hawaye sanda takai k’arshen rubutun... Ta zauna gijif saman gado har lokacin takardan na rik’e hannunta.... Ita harga Allah tama rasa mai takeji... Wane irin al’amari ne wannan, abu saikace a film... Ji tai kukanta na k’aruwa sosai lokaci guda.... Bata ankara ba sai jinta tai cikin k’irjinsa ya mata runfa had’ida rungumeta.... Wani sabon fad’uwan gaba ta tsinci kanta ciki... Cak ta nemi kukan da take ta rasa sai bugu da k’irjinta yaci gaba dayi... Ita tsoro ma abin ya soma bata, sai yanzu abubuwan da suka faru sukaita dawo mata, hannunka mai sanda da Atika ta dinga mata, Aunty Bara’atu da tace mijin da Allah ya zab’ar mata shi ta aura... Ashe wannan shine nufinsu... Engr Mutallab mai neman takaran kujeran governor kuma Yayanta Ma’aruf shi ne mijinta.... Ya Salaam taji zuciyarta tamkar zillo yake cikin k’irjinta... Lokaci guda ta rintse idanunta dan gaba d’aya ta kasa katab’us cikin k’irjinsa... Jin tai tsit tamkar an d’auke ruwa ya sanyashi d’an sakinta kad’an yana mai dubanta.. Zulfah kaw jin ya saketa ya sanyata janye jikinta a hankali zuciyarta bai daina bugu ba... Yanada tabbacin koda bai bud’e baki ya sanar da ita cewa shid’in ne mijinta yanzu ta fahimci hakan... Ganin tana k’ok’arin ci gaba da janye jiki daga kusansa ya sanyashi d’aura hannunsa guda saman nata ya d’an rik’eta kad’an hakan ya hanata ci gaba da janye jikinta.... Jikinta yaci gaba da rawa sosai dan har yanzu bata dawo daidai ba... Ganin yanayin nata ya sanyashi d’an sakar mata hannun kana yai gayran murya kad’an yace “Ki huta idan Allah ya kaimu da safe zamuyi magana koh... Goodnight...!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye had’ida ficewa daga d’akin... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Ai yana ficewa Zulfah data koma tamkar mutum mutumi a d’ari ta mik’e ta nufi dressing mirror tana duban kanta... Itace matar shi Wai.... Wai shid’in shine mijin da aka aura mata... Shisa babu wanda ya damu dikda cewa babu wanda yaga idanun Akram...Ta lumshe idanunta a hankali wani irin abu na fizgar mata a zuciya... Motsi kad’an tai kaw sai taji har yanzu tamkar cikin k’irjinsa take... Tai saurin ware idanunta ta shiga lalumen wayanta... Atika dake zaune parlorn mahaifiyarta tana labarta mata yanda Al’amarin Allah ya juye sai ganin kiran Zulfa’u tai, ta d’aga tana darawa dan tasan by now k’awar tata tasan dawan garin.... Jin yanda Atika ke k’ek’yata dariya ya sanya Zulfan kuma kufula... “Kin kyauta ma kanki... Ya miki kyau...!” Ta fad’i a hasale.... Daga d’aya b’angaren Atika na dariya tace “Da nayi mai....? Ango shi zai breaking news d’in wa amaryarsa kinga laifina da ban fad’a miki ba...” K’wafa Zulfa’u tai kana tace “Allah zan kamaki ne zaki sani....” Atika ta kuma darawa kana tace “Haba ta His Excellency ni Ki rufamin asiri kafin kisa Excellency yaji na b’atawa amaryarsa rai a hanani shiga gidan gwamnati..” Tsuka tai a hankali kana tace “Ke kika san wannan kuma maras m kawai...” Atika ta kuma darawa kana tace “Ta Excellency kinga kashe wayar nan kafin ango ya shigo yace wannan k’awar taki ta faye gulma... Saida safe asha love lafiya....” Ko jiran amsar Zulfah batai ba ta katse kiran tana mai ci gaba da darawa.... Zulfah tai k’wafa kurum kana ta silale jiki ta kwanta kan gado, ko zarafin mik’ewa tai alwalwan shafa’i da wuturi ta kasa, tana jin Najma ta turo k’ofan ta shigo tana fad’in ita wajenta zata kwana, hakan sai yaima Zulfa’u dad’i sosai dan da batasan yanda zata kaya da tinanin nan da ya tsaya mata a rai ba, ko banza Najma zata d’ibe mata kewa.... Tuni ta rungumo yarinyar suka haye gado tanajinta tamkar d’iyarta... *** Gaba d’aya hankalinsa gaza kwanciya yai, ga wasu irin mafarkai da yake gameda mahaifinsa... Ya kuma kiran wayan Daddy ya jita a kashe har yanzu... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum zuciyar Khalid Ke nanata masa, haka kawai yake jin tamkar wani abu ya sami mahaifin nasa.... Time ya duba jikin wayarsa yaga lokacin sallan asuba ya kusa... Bathroom kurum ya fad’a ya d’auro alwala ga kansa dake matsanancin masa ciwo sakamon samun rashin wadataccen bacci da baiba daren jiyan..... Raka’atanil fajir ya soma gabatarwa kafin ya fice masallaci kwatsam yaji wayarsa na ruri.... Gabansa ya yanke ya kuma fad’uwa.... Cikin sauri ya janyo wayar yana dubawa, bak’uwar lamba ce mai kiran nasa... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida tattaro duk wani k’arfin halinsa ya d’aga kira..... Daga d’aya b’angaren aka soma tambayarsa “Am I speaking to Architect Khalid Mainasara...?” Khalid ya jinjina kai yace “Yes speaking... How may I help you...?” Mutumin yaci gaba da fad’in “I am calling from the National hospital here in Abuja... Your father Engr Mainasara had a terrible car accident a yammacin jiya.... And he was rushed.....” Baikai aya ba Khalid ya mik’e a birkice yana fad’in “How’s my father doing... Tell me, ina mahaifina.... Talk to me....!” Ya k’arashe cikin tsananin d’imauta... Mutumin yace “Try to calm down Sir, a yanzu haka Babanka yana ICU namu yana samun kulawa na gaggawa... Muna fatan cikin yardar Allah ya tashi kafad’unsa...” Daga haka katse kiran mutumin yai yana mai kuma baiwa Khalid baki had’ida kalaman k’arfafa gwiwa dikda cewa Khalid baima yarda mahaifinsa na raye ba sabida wane irin crack da yakeji zuciyarsa nayi tin daga can k’asa.... Take yaji k’afafunsa sun gaza d’aukansa... Ya zame ya zauna gijif saman kujera yana mai d’aura hannayensa saman bakinsa... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, abinda yaji zuciyarsa na nanata masa kenan... Lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “A’a Daddy na yana raye... Zai tashi yaga burinsa ya cika... Family d’insa sun had’e waje guda.... My Dad is alive.... Yana nan da rai.... I’m sure of it... Na sani...” Ire iren sumbatu da Khalid keyi kenan... Lokaci guda yaji wani irin kukan da yaketa dannewa na k’ok’arin faso k’irjinsa.... Allah sarki haka Khalid ya kifa kansa ya dinga kuka yana fad’in mahaifinsa na nan da rai, ida ka gansa dole ne ma ya baka tausai... A b’angaren Nabilah haka kurum taji tamkar wani abu na faruwa da Khalid d’in musamman da taga ta kira wayarsa har sau uku bai d’aga ba, tasan dik fushin da zai da ita bazai k’i d’aga kiranta haka kawai har sau uku ba... Take taji zuciyarta ya karaya sosai, tana son sanin halinda mijinta Ke ciki... Baccin data kasa komawa kenan itama taita jero sallolinta.... Washe gari Engr Khalid ya samu da batun don baisan ta yanda zai soma tink’aran Aunty Daula da wannan labari ba, Engr yaita basa baki had’ida k’arfafa masa gwiwa ya kuma sanar dashi shi zai sami Ammah da batun... Koda labarin accident d’in ya isa masu Abbah sai cewa Abbah yai maza su shirya su tafi, Aunty Bara’atu, Aunty Daula da yaranta ,Khalid da kuma Nabila suka d’auki hanyar Abuja bayan Abbah da Mamy sun kumayima Nabilah nasiha mai shiga zuciya, gashi tinda ya dawo makaranta taji wannan batu hankalinta ya tashi sosai, tausayin Khalid d’in ya cika mata zuciya ashe shisa bai sami zarafin d’aga wayarta ba, lallai yana cikin matuk’ar tashin hankali... Taga yanda a kwanakin ya shak’u sosai da mahaifinsa... Dole ma hankulansu ya tashi dan basuga yanayin halinda jikin Daddyn ke ciki ba, fatanta Allah ya tashi kafad’un Daddy ya basa lafiya...Dikda tana cikin yanayi na rabuwa da gida amma halinda mijinta Ke ciki sai yafi d’aga mata hankali, ga Aunty Daula ma wacce batasan soyayyan kowa ba tsawon shekarun nan bayan d’an uwanta Ma’aruf saiko na mijinta, itama dik ta koma abin tausai... Wannan shine ana wata ga wata dan acan gidan Abban ma yanzu kam hankalinsu ya soma tashi na rashin sanin tak’aimemmen yanda Mamani ta tafi ga girma a tattare da ita, dole hankulansu ya tashi, in Kaga Abbah duk a birkice yake shima... Can gidan gidan Baba Alhaji ma abin babu sauk’i tin sanda Magajiya ta iso gidan a matsayin kishiyar Hajiya Haule abubuwa suka dad’a kwab’ewa... Ga Hafiz ya tada hauka wa mahaifin nasa cewa sai ya saki Magajiya dan bazai dinga shigowa gidan mahaifinsa yana karo da ‘yan daudu ba... Toh a can gidan Engr ma bayan zab’e da ya k’arato sosai maganan b’acewar Akram ya soma d’aga mai hankali a halin yanzu, dan harta Umman Akram d’inma yau sawunta na biyu kenan a gidan tana kuka tana fad’in ya taimaka ya nemo mata d’anta baida kowa sai Engr d’in kuma maraya ne... Kar ya dubi girman laifin da Akram d’in yai masa ya taimaka ya bincika yanda za’a sami Akram... Engr ya sanarda ita ta kwantar da hankalinta idan ta kama za’ai tracking har layin da Akram yai amfani ya kirasa dashi last... Da wannan batu mahaifiyar Akram ta d’an sami sauk’i... Dole Engr ya had’a binciken da jami’an tsaro.... A b’angaren Sameer kaw yaso ya tafi ya duba jikin Daddy saidai Mummynsa da Daddynsa yau suke dawowa daga k’asar Saudiya yanda aka sallamo Daddyn nasa daga can Saudi German bayan kwashe sama da watanni hud’u yana jinya a can..... Dama tuni sun sanar dashi ta Kano zasu sauk’a... Tarba na girma suka samu daga iyayen Sameer dikda halin tashin hankalin da suke ciki hakan bai hanasu karrama iyayen rik’on Ma’aruf ba mutanenda bayansu Sameer baida wanda suka fisu, Alhamdulillah jikin Daddy yayi kyau sosai dan Sameer d’in yaji dad’in yanda yaga jikin Daddyn nasa yayi kyaun gani... Allah sarki Sameer da Mummy tamkar su had’iyi juna dan Farin ciki... Mamy da Abbah har rasa kalaman da zasuyi amfani wajen mik’a godiyarsu ga wad’Annan bayin Allah da suka rik’e masu d’a tamkar nasu sukai.... Sai Hawaye kurum da Mamy keyi... Mummy Fatahiyya ta rungumeta tana fad’in “Hajiya Mariya ai d’ah na kowa ne... Dik wanda kikaga ya rik’i d’an da ba nasa ba a wulak’ance dan kawai bashi ya haifesa ba Toh ki tabbata wannan mutumin baida zuciya a k’irjinsa idan kuma yanadashi Toh fah itada babu dik d’aya ne... Shi d’ah basai ka haifa ba ya zamto naka... So tari zaka haifi d’an baka mora ba wani daban ya moreshi.... Shi wanda baka haifan ba sai kafi moranshi sama da naka.... Haka Allah yake gudanar da Al’amaranshi.... Kin gama min komai da kika haifo min d’ah kaman Sameer cikin Duniyar nan....” Ta k’arashe tana kuma kamo hannayen Mamy da itama hawayen take.... Kirkin mutanen har ya zarta misali, haka kalaman Hajiya Fatahiyya sukaita yawo a kwanyar Abbah, tabbas dik abubuwan data fad’i gaskiya ne... Ko menene Mamani tai a baya ya rik’eshi da duka soyayyarta kuma bata masa rik’on sakainan kashi ba... Idan har ya cika d’a mai biyayya dole ya nemota yanda ta shiga ta fita ya kuma saurara daga b’angarenta.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *97* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Babu b’ata lokaci Sameer ya soma shirye shiryen bin iyayen nasa zuwa Kaduna a Washe gari, dan hakan ne ya kamata sannan daga can zai biya ya duba jikin Daddy... Nan Abbah ya umarcesa da ya d’auki matarsa ya tafi da ita, babu musu ya amsawa nahaifin nasa, sai sannan su Daddy suke samun labarin k’arin auren da Sameer yai, sukaita mamaki Mummy har tana dungurinshi tana fad’in wato ya tsere ma Babansa, su dai su Mamy sai mamakin yanda Sameer ke matuk’ar wasa da Mummynsa suke, da gani ba k’aramin Sabo da shak’uwa bace tsakaninsu... Sai sannan ake breaking wannan labari wa Raihanah kasancewar zatabi mijinta su tafi... Ita harga Allah abin mamaki yaita bata, Wai itace matar Ya Ma’aruf... Ita Raihanatu itace akai mata aure da Ya Ma’aruf ba Addarta Sahariyya ba... Take taji wane irin rauni kuma can k’asar zuciyarta...Ta sani Ya Ma’aruf mutumin kirki ne da ko wacce mace zatai alfaharin samu a matsayin miji... Amma harga Allah ji take auren yai mata diran sauri, ko da wasa bata tab’a kawowa aurenta na nan kusa ba... Abbah da Mamy sukaita bata baki suna nuna mata in sha Allah Ma’aruf zai zamto alkhairi a gareta kuma bazata kuka da zab’insu ba da izinin Allah... Ita dai kanta kife kurum yake sai Hawaye dake gangaro mata cikin sabon mayafin da Mamy ta rufa mata da kanta, tana jin sallamansa bugun zuciyarta ya k’aru... Zama yai daga gefe kad’an kusan k’afan Abbah... Abbah ya kuma masu nasiha mai shiga jiki sosai musamman Sameer da yanzu mata biyu Ke gareshi... Mummy kaw tuni itama ta shiga nan nan da Raihanah, abin sosai yai mata dad’i, ita d’in shaidace yanda D’an nata ya sha wahala da aure, sam zamansu da Siyama rabi a gidansu Siyama tayisa, tabbas taji dad’in wannan aure na Sameer tana kuma fatan nutsuwar da bai samu a baya ba ya samu yanzu... A d’aki Mamy taci gaba da lallashin Raihanah tana sanar da ita, nan Kano zata zauna... Yanzu rakiya kawai zasuyima iyayen goyonsa amma da zaran al’amara sun daidaita yace nan Kano zai ajeta kusa da gida... Da wannan batu na Mamy Raihanah ta d’an sami sauk’i a zuciyarta... Da dare suna zaune d’aki itada Marliya tana tayata shiryawa lokaci guda tana ci gaba da zolayarta “A’a ashe dai ashe dai patient ce matar... No wonder dik abinda ya shafi patient Yaya Ke baiwa abin kulawa na musamman ashe dai....” Raihanah ta galla mata harara tana ci gaba da share hawayenta.... Marliya ta d’an marairaice fuska tace “Allah sarki ki hak’uri mutuniyar gobe war haka ina nan ina kewarki...” Raihanah dai batace komai ba sai goge hawayenta data ci gaba dayi.... Marliya ta ije rigar da take linkewa kana tace “Toh Wai ma wasu kaya zaki tafi dasu bayan inaji d’azu Ya Ma’aruf na fad’iwa Mamy da zaran kun tafi Kaduna zai maki sayayya... Inye yarinya kin mori miji d’an gayu mai taste...” Jifa mata rigar dake hannunta tai kana tace “Idan bazaki tayan ba Ki tashi Ki fita.. Na mori miji ta ina bayan wannan matar tasa tsoro take bani harga Allah. kuma yanzu Addah Sahariyya mai zata kirani tinda kinsan yanda ta d’aukaki auren nan... Nidai Allah dan bazan iya musu masu Abbah bane da.....” Kasa ci gaba da magana tai sakamakon sallamansa da suka jiyo daga k’ofa... Marliya tai zumbur ta mik’e tana mai k’ok’arin gaidashi lokaci guda ta fice ta basu waje... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa... Banda sautin dum dum! K’irjinta bai komai, gaba d’aya ma sai ta daburce ta mance mai take, da k’yar ta iya lalumo kalmomi saman harshenta ta soma gaidashi... Saida wasu dak’ik’ai suka d’an gauta kana ya amsa mata yana mai karantar yanayinta, ita dai dik tsarge take, ko bata d’ago ta dubesa ba jikinta na bata tsareta yai da idanunsa... Har ta ciren ran bazai kuma cewa komai ba ta sinkayo muryarsa na fad’in “Gobe idan Allah ya kaimu before mu wuce akwai yanda zamuje... So ki shirya da wuri ko...” Jinjina masa kai kurum tai ba tareda ta iya amsawa ba, gaba d’aya sai yaji jikinsa ya masa sanyi... A ‘yan shekaruntan nan ta tari labarin aurenta haka dole abin ya dameta, sosai tausayinta ya cika zuciyarsa... Koda bata d’ago idanunta ba zai iya ta tabbatarwa hawaye take... Gaba d’aya sai yaji babu dad’i, alk’awari ya d’aukarwa kansa koda ace bai sonta zai koya ma kansa yanda ake sonta... Koda ace bai tab’a son wata d’iya mace sama da Siyama ba bazai tab’a bari Raihanah ta fahimci hakan ba sabida ta cancanci fiyeda hakan.... Tana jin ficewarsa yana amsa kira ya sanyata saurin mik’ewa ta nufi bathroom tana mai kuma tintsirewa da sabon kuka... Sameer yana iya sauraro yanda take shesshek’ar kuka daga toilet, ya lumshe idanunsa a hankali yana mai ije ‘yar jakan kayan da ya shigo mata dashi saman gado... Cikin sauri yasa kai ya fice daga d’akin dan kukan nata sosai yake breaking d’insa.... *** A can Abuja kaw tinda suka isa sukaga condition d’in Daddy hankulansu suka kuma tashi, tabbas Daddy yana matuk’ar jin jiki dan ko d’akin da yake ba’a bari a shiga, da k’yar suka k’yale Auhty Daula da Khalid suka shiga bayan sun saka kayan sukuf irinta ma’aikatan lafiya... Haka hawaye ya dinga d’iga masu ganin Daddy kwance unconscious... Addu’o’i sukai masa kana suka fito dan babu halin Kwana ma’aikatan lafiyan basuda buk’atan kowa ya kwana wajensa musamman dashike har yanzu baisan yanda yake ba, na’urar bature ne kawai da buwayar Ubangiji ke aiki akansa.... Haka suka d’unguma suka nufi gida jiki dik a mace, Nabilah da Aunty Bara’atu suke k’ok’arin d’ebewasu Ijlaal kewa musamman Humaira data fara wayo ta fahimci abindake faruwa.... Haka nan sukai dinner babu dad’i gaba d’aya abincin ba wani ci sukai ba, baranma Khalid da sam ko fitowa parlorn baiba tinda suka dawo daga asibiti... Daga Aunty B har Aunty Daula sun kula da yanda gaba d’aya hankalin Nabilah bai taredasu, mosti ba motsi ba sai ta lek’a k’ofa... Tinda tai wanka ta shirya cikin kayan baccinta mai taushi yalwatacce ta haye gado taredasu Ijlaal amma ga dikkan alamu ba baccin take ba... Aunty B ta numfasa ta d’an tab’a Daula kad’an tace “Ban tsamman mijinta ya saka wani abu a cikinsa ya kamata ko d’an tea ne takai masa, she cant let him go to bed with an empty stomach, ga kuma halinda yake ciki...” Cikin sigan rad’a tai maganar... Aunty Daula ta jinjina kai tace “Nima tinanin da nai kenan...” A tare suka had’e murya suka kirawo sunanta, gabanta ya yanke ya fad’i.... Aunty B taci gaba da fad’in “Nabilah ya kamata Ki lek’a kiga halinda mijinki ke ciki... This is a serious situation for him, Kinga ko abinci baici ba,and you can’t let him go to bed like that....” Aunty Daula ta jinjina kai tace “Haka ne... Khalid is going through difficult situation, he needs you... Ki tashi kije kitchen and prepare something for him koda tea ne..” Jinjina kai kurum take a hankali tana mai sauraren Aunties d’in nata, lokaci guda ta mik’e ta sauk’o daga saman gadon a hankali kana ta isa ta bud’e suitcase d’inta ta ciro hijab ruwan madara ta d’aura saman yalwataccen riga da wandon baccin nata... Aunty Daula tace ta sami Karima tai guiding nata yanda stuff d’in kitchen d’in suke aje... Babu musu ta jinjina mata kai kana ta fice... Da taimakon Karima ta ida dafa masa ruwan shayin ta had’e saman tray kana ta nufi d’akin nasa dake nan down floor... Sallama saman bakinta take knocking... Khalid da ida sallansa kenan ya taso yana k’ok’arin bud’ewa dan tuni ya d’ago muryar teddy bear d’insa dikda sanyi da muryar tata tai.... Ya sakar mata sassanyar murmushi na k’arfin hali.... Hanya ya bata kana yace “Come on in...” Ta rab’a a hankali ta shige k’irjinta sai bugu yake... Haka nan ta zauna cikin d’akin a d’arare sai rarraba idanu take ga sanyin AC da yaima d’akin k’awanya had’ida dadd’an k’amshinsan nan... Jim kad’an ya fito daga closet sanye cikin white inner shirt da ash sweatpants, da alama ya canza jallabiyan data shigo ta tadda jikinsa ne wanda ko ba’ace ba sallah ya ida... Daga gefenta ya d’an zauna yana mai karantarta... Lokaci guda ya sinkayo muryarta tana gaidashi.. Bai amsata ba sai kamo yatsun hannayenta da yai ya rik’e cikin nasa, lokaci guda ta d’ago tana dubansa.... Sai snn ya d’an amsata a tak’aice kana yai mata alama da ido kan tai serving d’insa tea d’in.... Sarai ta gane mai yake nufi da yai mata alama da idon kan tai serving d’insa amma saidai yak’i sakin hannunta.... Ganin ya kuma mata alama da ido yana duban tray d’in ya sanyata masa alama itama da idanun kan ya sakar mata hannunta, lokaci guda take furtawa a hankali “Can I have my hands back...?” Murmushi ya sakar mata kad’an kana ya saki hannun nata.... Ta duk’a a hankali tana had’a masa, dik abinda zata zuba sai ta tambayesa, shiko dik wani motsinta ya kasa janye idanunsa daga gareta... Bayan ta ida had’awa ta mik’a masa cikeda risinawa.... Ya amsa yana mai furta “Thank you teddy bear....!” K’ak’aro murmushi ta d’anyi ba tareda cewa komai ba, yana sha yana tsareta da idanu... Ya kuwa sha sosai dan baima San sanda tea d’in Ke shige masa ba sakamakon duban fuskarta da yake... Bayan ya gama ne ta shiga had’a tray d’in tana fad’in bara Takai kitchen... Kaman mai tsoron idan ta fice bazata dawo ba sai ji tai ya rungumota ta baya yana fad’in “Please stay... Please stay here with me kinji teddy bear....!” Ya k’arashe idanunsa a lumshe.... K’irjjnta yaci gaba da bugu, ta kasa tab’uka komai, tana jin sanda ya dawo dasu baya yai masu masauk’i saman kujeran... Gaba d’aya sai jinta wane iri take... Khalid yaci gaba da furta “I don’t know if I can do this Nabila... I don’t know... Ta ina zan soma sanar da Ammi abubuwan da suka faru... Da Wanne zan soma mata...? Accident d’in Daddy...? Introducing Aunty Daula da yaranta ko kuwa da batun aurena zan soma mata... Nabilah I’m lost..... I don’t where to start... I’m completely lost....!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Tausayinsa ya cika mata zuciya take taji kuka na neman zuwa mata amma sai ta daure dan tasan shid’in na buk’atan juriyarta a halin yanzu..... Cikin murya irinta lallashi take furta “We are all here for you... You are not alone... Together we can do this kaji... And Daddy zai sami lafiya in sha Allah... Mu ci gaba da masa addu’a kaji, abinda ya kamata muyi focusing yanzu akai kenan kaji.... I’m here... For you....!” Ta k’arashe cikin rawar murya dikda juriya da take k’ok’arin nunawa... Khalid ya kuma kamo hannayenta yana mai furta “Thnak you teddy bear...!” Ya k’arashe yana mai kuma janyota cikin jikinsa, saitin kunnenta yake maganar tamkar mai rad’a “Teddy bear... please sleep here beside me....!” Yai maganar yana mai k’ok’arin zame hijabin jikinta... Nabila da gaba d’aya ya gama daburcewa saurin d’agowa tai a d’an razane tana dubansa... Sai kuma ta sadda kanta.... Ya kuma sakale yatsun hannunta cikin nasa kana ya furta “Don’t you want... to sleep beside your bear.... “ Janye hannayenta ta soma a hankali, cikin d’an daburcewa take furta “Zan... zanje karsu fara nemata...” Murmusawa yai a hankali kana yace “Babu wanda zai nemeki... Alright idan bazaki kwana a nan ba, do me a favor...” Ya d’an dubesa a hankali.... Still yatsunta cikin nasa yake ci gaba da furta “Stay with me har nayi bacci, idan nai bacci sai ki tafi... I just want you beside me teddy bear that’s all... Please don’ say no... Kinji....” Ya k’arashe kaman wani mai shirin kuka... Jinjina masa kai tai a hankali kana tace “Alright deal.... Idan kayi bacci zan tafi... You better go to sleep now..!” Ta k’arashe da sigan fad’a... Khalid ya murmusa cikeda jin dad’i had’ida jinjina kai yace “Deal....! Come here ya k’arashe yana mai janyota jikinsa, yai masu masauk’i saman gadon, Zame jikinta tai had’ida jera pillows tsakaninsu tana mai satan dubansa take furta “Ina kallonka daga nan oya go to sleep...!” Shidai dariya ta basa sosai hakan yasa yai mata k’uri daga yanda yake kwance, murmushi saman fuskarsa... Idan ta juyo taga yana dubanta saiko ta kuma duk’unk’unuwa cikin hijabinta tana fad’in idan bai juya ba ita zata tafi... Khalid ya juya yana mai gimtse dsriyarsa had’ida furta “Allah huci ran Princess..” Yana gani ta soma gyangyand’i ita a dole jiransa take yai bacci... Jim kad’an kaw bacci yai gaba da ita.... Khalid ya janye pillows d’in a hankali kana ya janyota kusanshi ya ja bargo ya rufa masu...Sosai ya lumshe idanunsa yana shak’an dadd’an k’amshinta, a haka shima bacci yai gaba dashi... *** KANO Washe gari kaman yanda ya umarceta ta shirya hakan ce ta kasance, daga nan cikin d’aki yanda take tana iya sauraro muryarsa yana gaida Mamy had’ida sanar da ita cewa yanzu zai biya ya d’auko su Mummy suyi sallama dasu....Zuciyarta taci gaba da tsinkewa, addu’an samun strength kawai take cikin zuciyarta tana mai neman agaji da taimakon ubangijinta da ya bata ikon jurewa... Ga tinanin Mamani ya kasa barin zuciyarta, haka zata tafi basuyi sallama ba, sosai wanna abu ya tsaya mata a zuciya, fatanta Allah sa tana cikin k’oshin lafiya a dik yanda take.... Tana ji Mamy tana cewa bara ta shiga ta dubo Raihanar, bugun zuciyarta ya k’aru... Wato dai da gaske shid’in mijinta ne... Ta lumshe idanunta a hankali siriryar hawaye ta gangaro mata, saurin saita kanta tai sakamakon jiyo shigowar Mamy da tai, bazataso Mamy ta danganta cikin yanayin damuwa da tashin hankali ba dan jiyan kusa raba dare tai a d’akin tana bata baki da kuma nasiha... Sai take ga kaman bata kyautawa Mamy ba kar ta d’ago bata son auren D’anta ne.... Mamy ta sakar mata murmushi kana tace “Daughter kin shirya...?” Ta jinjina mata kai a hankali kana tace “Eh Mamy...” Jinjina kai Mamy tai kana tace “Toh maza gashi nan yana jiranki a parlor zaku wani wajen before kuzo ku wuce koh...” Nan ma jinjina kai tai kana tace “Toh Mamy...” Mamy tace “Allah miki albarka kinji....Idan kun dawo sai ku shiga wajen Abban naku tare kuyi masa sallama ko...” Nan ma jinjina Mata kai tai had’ida amsawa kana ta nufi parlor k’irjinta na matuk’ar bugu idanunta a k’asa... A tinaninsa bazata saka kayan da ya kawo mata jiya ba sai gani yai ta saka sun kaw mata kyau... Kyakkyawan murmushi ya saki ba tareda ya sani ba, sosai yaji dad’in saka kayan da tai.... Idanunta a k’asa ta k’araso gareshi had’ida risinawa ta gaidashi.. Ya amsa yana mai shagala da duban yanda tai masa kyau sosai.... Shiru ne ya d’an biyo baya har tana dak’ida kana ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Muje koh...” Babu musu ta risina had’ida bin bayansa... Yanda suka jera dole su birgeka... Yana sanye cikin jampa fara k’al da tai matuk’ar amsar fatarsa saiko bak’ar dara wanda ta k’ara fito da hasken fatarsa, kai da ganshi kaga sabon ango sai watsa k’amshin nan nasa yake... A haka suka nufi motarsa,yau d’in da kansa ya bud’e mata front seat ta shige kana ya zagaya ya zauna a mazaunin driver.... Gidansu Shamsu suka soma zuwa yanda ya kaitawa Maman Shamsu suka gaisa ya kuma sanar da ita yau suke tafiya Kaduna daga nan Abuja zasu shige dan duba jiki Daddyn Siyama... Mama tai masu fatan sauk’a lafiya had’ida saka masu albarka... Daga nan gidan Ammah suka wuce sukai mata sallama itama, har Zulfa’u ma ta fito suka gaisa, gaba d’aya fatan alkhairi sukai masu da sauk’a lafiya had’ida sak’on gaisuwa ga jikin Daddy.... Daga gidan Ammah basu zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Haule, gidan Mahaifin Raihanah.... Bugun zuciyar Raihana ya k’aru, tsoro da firgici suka wanzu sosai saman fuskarta, harga Allah batasan ya yanda zata soma jerawa dashi su shiga cikin gidan da sunan mata da miji ba.... Shi kanshi ya kula da yanda gaba d’aya ta daburce, ya fahimci tsananin tsoron da ya wanzu saman fuskarta... Sai faman rakub’e rakub’e take bayansa ta kasa cimmasa, gashi tin daga waje suke jiyo hayaniyar ‘yan daudu sai faman shewa suke cikin gidan.... Sameer ya d’an dakata kad’an har ta cimmasa, a hankali suke takowa har suka shigo cikin gidan sallama saman bakunansu dikda cewa muryar Sameer ne kawai mai iya fita, itakam Raihanah saima k’ok’arin mak’alewa bayansa da take.... Haba nan fah kallo ya koma kansu, gaba d’aya illahirin jama’an dake tsakar gidan suka bar abinda suke suka zuba masu ta mujiya... Haule dake kokawan k’watan tukunya hannun ‘yan daudu dan idan ta dafa abinci ta bari a nan kitchen saidai tazo ta samu an lashe mata tukunya gardawa sun cinye shisa sam da zaran ta d’aura abinci saidai tai zamanta ta jira ya dafu ta d’auke ta gudu dashi d’aki suci da ‘ya’yanta dan idan ba haka ba to kaw tabbas ma gardawa ta girka, ga Sahariyya ta k’aro wualk’anci tinda aka fasa aurenta da Sameer sai Naja’atu ne ma ke k’ok’arin taimakawa mabaifiyar tata, ga Baba Alhaji tinda yayi Amarya yanaji Haule na drama da ‘yan daudu a waje amma ko lek’owa baiyi, saidaima Magajiya ta fito tana mik’a ta mik’awa ‘yandaudunta sauran takardan tsiren da suka cinye ita da angonta a d’aki... Haule saidai taji hawayen da basu shirya zuba ba suna gangaro mata... A ‘yan kwanaki ukun dik Haule ta fice hayyacinta, kaman ba ita ba.... Tanaji ‘yandaudun nan suna fad’in “Wai Wai Wai bakin ‘yan gayu yau akai a gidan namu... Lale lale barkanku da zuwa... Namu ne ku ko nasu...?” Suka k’arashe cikin salo.... Ita dai Raihanah saima dad’a b’oyewa da tai bayan Sameer abin na kuma basu tsoro had’ida al’ajabi ganin irin wad’annan mutane cikin gidan Baba Alhaji.... Wani mugun kallon da Sameer ya aikama ‘yandaudun suka shiga ja da baya suna kame baki had’ida furta “Wai bari mu matsa kar maza suyi faccakali damu...” Haule baki sake take dubansu yanda sukai mata bala’in kyau tamkar wasu taurarin cikin film, har malmalar tuwon dake cikin tukunyar hannun Haule ya fad’o Haule bata ankara ba.. Wai Raihanah ce take gani haka kaman wata sarauniya.... Sahariyya dake daga d’aki tana fad’in “Ya kuka daina fad’an kuci gaba man....” Birki tai ma kalaman nata sakamakon hangosu da tai hasken hantsi ya haske masu fuska har wani kashe idanu suke.... Ai take taji wani irin jiwa na d’ibanta... Raihanah da k’irjinta ke bugu ganin irin duban da Addah Sahariyya Ke masu tuni jikinta ya d’auki rawa zata kuma mak’alewa bayan Sameer amma sai jiyo sauk’an hannunsa tai saman nata ya rik’eta gam.... Idanun Sahariya suka sauk’a kan hannayensu yanda suke mak’ale cikin na juna... Zuciyarta yai wani irin tsinkewa k’afafunta taji sun gaza d’aukanta... Kasa tab’uka komai tai itama sai dubansu da take baki sake daga ita har mahaifiyarta Haule... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *98* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED! Haule ta saki tukunya tana gyara d’aurin zani had’ida murje idanunta alamun tabbatarwa... Eh da gaske dai Raihanah take gani tarda Ma’aruf ba mafarki bane... Sameer ya d’anyi gyaran murya kad’an kana yace “Kina mamaki ne...?” Haule ta kuma matsowa kad’an tana nunasu da yatsa dan tama kasa furta koda kalma.... Lokaci guda labb’anta dake tsananin b’ari taji suna furta “Al... Alhaji... Alhaji fito kaga kayan al’ajabi... Ashe ga makirar da k’aninka ya aurawa d’ansa....!” Ta k’arashe tana kuma kururwa had’ida dannawa Baba Alhaji kira... A fusace ya fito Magajiya na biyedashi tana sanye cikin kayan bacci ‘yar kanti mai tsantsi ta d’aura zani sama sai wane yamutse fuska take alamun bata jima da tashuwa ba, Sai narkewa cikin jikinsa ake tana fad’in “Dalin Dalin dan Allah kaiwa matarka magana wllhi fitinarta Ke tadamu a gidan nan, sai taita biyewa yaran nan suna kokawa da farar safiya, kuma fad’ar bai wuce kan abinci, gaskiya Nidai Dalin Dalin ka taka mata birki kasan banson hayaniya..” Ta k’arashe tana narkewa cikin jikinsa ... Shiko Baba Alhaji tuni ya soma hura hanci yana fad’in “Wai ke Haule shikenan garin Allah na wayewa kinyi da kowa ken....!” Aya ya sakawa kalaman nasa sakamakon hangosu da yai tsaye tsakar gidan.... Haule kaw k’ek’ashe da idanu take duban Magajiya sai faman huci take, alla alla take dare tai Baba Alhaji ya bar d’akin Magajiya kaman yanda Shari’a ya tanada, ko banza wani k’uncin zai ragu mata... Lokaci guda Haule Ke fad’in “Ka nad’e a d’aki ana d’irka maka tsiddabaru kai a dole ga mai Amarya.... Toh sai ka fito ka ganema idanunka, an nad’e d’iyarka ma da sunan Amarya... Ka ganta nan... Ko kunya tana mak’ale jikinsa ta nuna mana ita cikakkiya ce.....!” Ta k’arashe tana hura hanci.... Raihanah da tuni k’walla sun ciko idanunta cikin sauri ta fuzge hannunta cikin na Sameer ta duk’a da saurin gaske tana k’ok’arin gaidasu saidai gaba d’aya ma kasa furta komai tai sabida kuka da yazo bakinta gadan gadan.... Sameer kaw da tsananin mamaki yake duban Haule, ko kunyar idanunsa bayan dik abubuwan da tai masu shida mahaifansa da ‘yar uwarsa Zulfa’u bataji ba.... Bai ida mamaki ba saida ya sinkayo muryan Baba Alhaji yana huci yake fad’in “K’yale ja’ira munafuka... Kina jina sai ya sakeki dan wannan aure bai d’auru ba dan dama Usman mutunci na yai niyyan ci....” Ya maido da dubansaga Sameer dake faman binsa da kallon mamaki kana yace “Kai kuma sai ka sakar min d’iya dan ba ita nayi niyyan baka ba, idan baka sakar min d’iya yanzu cikin salama a cikin gidan nan ba zaka amsa sammaci a kotu... Daga kai har Manu Billahillazi k’ararku zanyi....” Sahariyya ta shiga doka tsalle tana murna Sameer zai saki Raihanah dan ko bata sameshi ba ta gwammaci dukansu su rasa da dai ace harma Wai Raihanah ce matar tasa.... Haule ta jinjjna kai tace “Ahtoh sai muji Uban da ya basu dama su aurar da yarinyar da ba tasu ba... Munafuka jibi yanda take mannewa cikin jikinsa kaman wata mage tana san san da kai na minafinci....” A kufule Baba Alhaji yayo kanta yana furta “Zaki tashi Ki wuce ciki ne ko sai na jibgeki... Ja’irar banza.....!” A d’imauce ta yunk’ura ta tashi tana k’ok’arin nufa d’akinsu saiji tai gam Sameer ya rik’o hannunta cikin nasa, idanunta masu zuban hawaye ta d’ago tana dubansa, ga tsananin mamakinta wane irin yanayi taga fuskan nasa ciki wanda zatai rantsuwa bata tab’a ganinsa cikin irin yanayin ba.... Haule ta wani zabura ita kad’ai tana duban yanda Sameer ya hana Raihana shigewa zuwa garesu... Shi kanshi Baba Alhaji da tsananin mamaki yake duban Sameer d’in... Lokaci guda yake furta “Eh lallai na yarda bakada mutunci baka gada ba... Sakar min d’iya dan ba kai ka haifa min ita ba, ba kuma ubanda ya aura maka bane ya haifa min ita... Sakarta nace....!” Ga tsananin mamakinsa muryar Sameer ya sinkayo cikin wane irin dakewa yana furta “Babu yanda zata shige..!!!!” Yai maganar cikin tsananin tsimewa, had’ida rik’o hannunta... Gaba d’aya suka zuba masa ta mujiya... Saida ya tabbata dik shi suke duba fuskokinsu cikeda tsoro kana Sameer yaci gaba da magana cikin tsimewa “Dama sallama mukazo muyi maku.... And to make sure bamu tafi da hakkokinmu akanku ba, amma ga dikkan alamu bakuda buk’atan hakan... Mun barku lafiya... Shige muje...!” Ya k’arashe yana mai janyo hannun Raihanah da har lokacin jikinta bai daina rawa ba... Haule ta soma sallalami tana fad’in “Eh lallai kin cika Raihanah da har zaki zab’i namiji samada mahaifinki... Kin rik’a kin cika tabbataciya.....” Maganganun Haule ya kuma sanya Raihanah fashewa da sabon kuka ta shiga k’ok’arin k’watan hannunta daga cikin nasa, amma saidai sam Sameer d’in yak’i sakinta saima damk’e hannun da yai sosai yana aikama Haule wani irin mugun kallon tsana da k’yama ya tina dik kalan abubuwa da Haule dasu Baba Alhaji suka masa shida Mamynsa harmada Abbah... Sai faman tururi kurum yake yana duban Haule da idanuniyansa da suka kad’a sukai jazir, ko sauraron Raihanah dake matuk’ar kuka tana fad’in “Ya Ma’aruf kai hak’uri ka barni naima Abbah biyayya na rok’i arzikinka... Shid’in magaifina ne...!!” Sam bai iya sauraronta saima ci gaba da duban Haule da yake cikin matuk’ar b’acin rai, kai kace sai taking out dik wani b’acin ran da ya shiga da k’unci a baya akan Haule.... Su Sahariyya sai murna ake Haule ma sai jijjiga take tana ayyanawa cikin zuciyarta cewa ko babu komai bazata tashi a 2 zero ba idan bataci wani yak’in ba taci wani, ko Babu komai idan ta murk’ushe auren Raihanah da Sameer yanzu a nan wani buri nata ya cika... Bata ankara ba sai ganin Magajiya tai ta tako gaban Baba Alhaji, lokaci guda Magajiya Ke dubansa, murmushi ta saki had’ida langab’e kai kad’an “Haba Alhajina... ‘Ya’ya dai duka naka ne, kuma ko shakka babu abun kunya ne dai kun riga kun tapkashi, mai sunan duk wannan borin da kake na cewa sai ya sakar maka d’iya...? Kokuwa rik’on saikainan kashin da kayiwa d’iyarka kakewa borin kunya kake cewa a saketa....?” Baba Alhaji ya kasa furta komai sai muzurai... Haule tai karaf tace “Toh ke kuma uban wa ya kasa dake da zaki d’auka...?” Murmusawa Magajiya tai kad’an kana ta dubi Baba Alhaji tace “Da kai nake Alhaji na...?” Cikeda borin kunya ya soma fad’in “Toh ai toh ai fin k’arfi aka nuna min kan d’iyata.....” Daidai nan Sameer ya k’araso gaban Baba Alhaji murya a shak’e wanda dagaji kasan maganar fita masa kurum yake, lokaci guda yake furta “Bayan dik abubuwan saka min, bayan duk abubuwan da kaima iyayena... And especially my father... Na yafe maka, kuma ina rok’on Allah ya yafe maka.... Amma kar kace na saki matata dan bani na zab’awa kaina ita ba sannan itama ba ita ta zab’eni ba, Allah shi yai hukuncinsa akanmu... Ina kuma fata hakan ya zama wa’azi a gareku akida matarka Hajiya Haule...!”Ya k’arashe siririyar hawaye wanda da gani na tafasan zuciya ne tana gangaro masa.... Gaba d’aya k’uri suka masa jikkuna a sanyaye... Raihanah ta duk’a tana hawaye, lokaci guda take furta “Baba...! Baba..!!” Kuka yaci k’arfinta... Wajen yai shiru bakajin komai sai sautin kukan Raihanah, ga tsananin mamakin Haule sai gani tai Baba Alhaji ya dafa kan Raihanah, cikin murya mai tsananin rawa yake furta “Ki tafi tareda mijinki.... Ki tafi tareda mijinki.... Tashi kije..!!” Abubuwan da yake iya furtawa kenan... Raihanah ta d’ago tanai masa duban mamaki... Baba Alhaji yaci gaba da jinjina kai yana furta “Ki tafi tareda mijinki...!!!” Yana ida fad’in haka ya juya ya nufi d’aki cikin sauri tamkar mai shirin kuka... Tuni Sameer yasa hannayensa duka biyu ya d’agota... Cikin b’angaren jikinsa yai mata masauk’i yana mai share mata hawayen fuskarta... Sahariyya ta d’aura Duka hannayenta biyu aka tana furta “Na shiga uku Hajiya kina gani kuwa....? Shegiya k’onenniyar nan ce fah Wai matar tasa... Hajiya karki barta tabisa... Mutuwa zanyi...!!” Ta k’arashe tana kururwa... Ko takansu Sameer bai kuma bi ba ya janyo hannun matarsa suka nufi k’ofa... ‘Yandaudu suka saki tafi suna yaba dacewa dasu Raihanah da Sameer sukaida juna... Yayinda Magajiya ta saki gud’a tana taya ‘yandaudunta kod’a Raihanah da Sameer.... Haule kam mutuwar tsaye tai a wajen tamkar wata gunki ta kasa yarda Baba Alhaji ya gwaleta irin haka... Ta bud’e murya yana fad’in “Alhaji barin Raihan kai ta tafi... Shikenan ka yarda ka sallamarta ma abokan gabanka.....? Na shiga uku ni Haule....!!!” Sahariyya kaw tukunyar dake faman tafasa da ruwan zafi ta nufa ta d’auko a guje tabi bayan su Raihanah tana furta “Wllhi yau sai na k’arasa k’onaki mai gaba d’aya kowa ya huta... Saidai a daidai hanyar fita suka kusan yin karo da Hafiz da baisan tana zuwa ba aiko nan ruwan ya dawo kanta ya kware mata... Ta shiga talewa tana ihu tana tsalle had’ida birgima a wajen... Hafiz kaw ko d’auki bai k’ok’arin kawo mata ba sai matsawa gefe da yai yana kallon yanda take birgima a k’asa tana ihu sabida zafin k’unan dake ratsata... Murmushi ya saki kana yace “Alhamdulillah yau kinji azaban irin abinda kikawa d’iyata Khausar.... Allah shi k’ara...!” Daga haka yasa kai ya kutsa cikin gidan yanda ya tadda ‘yandaudu sunyi chaa wa mahaifiyarsa sun d’aura mata tukunyar tuwo aka suna rawa suna zagayeta Haule kaw sai cazgan kuka take har abin tausai.... Hafiz yai kansu a haukace tamkar sabon kamu.... Nan suke sanar dashi uwarsu Magajiya taima rashin arziki shisa suke ladabta ta dan dama Magajiya bata koda sa’insa da Haule saidai ta saka sojojinta ‘yandaudu su handling mata Haule... A d’ari Hafiz ya nufi d’akin Mahaifinsa yana fad’in ko ya saki Magajiya ko shi yaje ya saki Sawwama... Magajiya ta mik’e tana wuraga masa harara... “K’aramin maras kunya, ai bari kaji na fad’a maka zuri’armu sun zama d’aya billahillazi mutuwa ce zata rabamu... Uwarka kuma idan tana son zama lafiya toh tabi umarni na....” Hafiz yakai dubansa ga mahaifinsa da ya kasa furta komai sai duba daga gefe.... Girgiza kai kurum Hafiz yai cikeda takaici kana ya fice a gidan tamkar zai kifa k’asa.... A hanya Najah ta had’udasu Sameer, Raihanah ta rok’esa yai parking suyi sallama da Najah, hakan kaw akai... Suka rungume juna suna hawaye... Najah tace “Kin cancanci Farin ciki Raihanah... Ki yafe mana dik abubuwan da muka maki a baya ‘yaruwata....” Raihanah ta kuma rungumeta tana hawaye lokaci guda take furta “Allah ya yafemu gaba d’aya Naja’atu... Wllhi ban tab’a rik’eku ba tuntuni....” Najah ta jinjina kai tana matsan k’walla kana taci gaba da fad’in “Hajiya ta zama ‘yar kallo a gidanmu... Mahaifinmu ya koma baida ta cewa... Gidanmu ya koma matattaran ‘yandaudu da duk wasu mutanen banza... Amma, abinda suka shuka ne... Ko da hakkinki kawai Allah ya bar Hajiya bazataga da kyau ba, balle d’inbin mutanen da suka sha wahala dik a sabida son zuciya irin nata... Raiha ki yafewa mahaifiyata kuma kice Addah Zulfah ma ta yafe mata ko ta sami sassauci cikin lamuranta...” Raihanah ta kuma sa yatsunta tana share ma Najah hawaye kana taci gaba da fad’in “Allah zai kawo sauk’i cikin lamuran iyayenmu in sha Allah... Ko Babu komai Hajiya uwa ce a gareni domin kaw dik irin rik’onda tamin ta zab’i ta rik’eni bata salwantar dani ba, kinga kaw ita d’in uwace a gareni.... I love you so much Sis...!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Naja ta kuma rungumeta tana fad’in I love you too ‘yaruwata....” Cikin murya irinta mai kuka.... A haka suka rabu cikeda kewa da alhinin juna... Isansu gida da kad’an Sameer ya fice ya d’aukosu Mummy yanda sukai sallama gaba d’aya suka d’auki hanya bayan su Abbah dasu Mamy sun kuma masu nasiha... Haka Raiha ta rabu dasu tana kuka musamman Marliya da yanzu sukai sabo sosai, gashi har suka tafi babu labarin Mamani.... **** ABUJA Suna zaune Office d’in Dr d’in bayan ya ida sanar dasu condition d’in Daddy... Mik’ewa tsaye Khalid yai yana mai shafe fuskarsa da duk tafukan hannayensa cikin tsananin tashin hankali da dik k’ok’arin mai k’ok’ari bazai b’oyu ba.... Aunty Daula kaw kifa kanta kurum tai wasu irin hawaye na gangaro mata.... Khalid ya isa gaban Dr d’in lokaci guda cikin tsananin tashin hankali yake furta “No Dr.... There must be another way.... Can’t we take him abroad...?” Dr ya girgiza kai a hankali kana yaci gaba da fad’in “I’m afraid you can’t... I’ll only advise you to continue praying for him... Chances d’in rayuwarsa.... Kad’an ne... I’m sorry I had to tell this...” Ya k’arashe yana mai girgiza kai a hankali had’ida zare glasses d’in dake mak’ale idanunsa.... Lokaci guda Khalid yake girgiza kai yayinda Aunty Daula ta k’unshe kukan da yazo bakinta gadan gadan jin kukan na zuwa mata da k’arfin gaske.... Khalid dake duban likitan da rikitattun idanunsa tamkar zai shak’osa haka ya rank’wafo daf fuskansa yana tsananin huci yake furta “How dare you say that... My father isn’t going die, you hear me...? So do everything, every possible thing you can to save my father...!” Girgiza kai kad’an Dr yai kana yace “I’m sorry Khalid, but you’ve to accept the truth...!” Khalid ya shak’o wuyarsa yana jijjigasa da iya k’arfinsa yake furta “Just do your damn job and save my father’s live, you incompetent...!!!” Cikin sauri Aunty Daula ta shiga janye Khalid tana hawaye take fad’in “Khalid ka nitsu ka ambato Allah cikin zuciyarka, kar ka bijirema rahamar Ubangijinka.... Allah shine mai warkarwa ba likita ba... Lets continue praying for him kaji....!” Jiki a sanyaye Khalid Ke furta “Aunty Daddy can’t die... He just can’t..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya mai raunin gaske... Lokaci guda yasa kai ya fice daga office d’in cikin sauri... Nabila da Aunty B dake zaune reception nan sukaga fitowar Khalid ya gifta ya nufi waje cikin tsananin tashin hankali... A tare suka mik’e gabansu na tsnananta fad’uwa... Nan suka hango Daula ma ta fito tana matsan hawaye... Gaba d’aya suka nufeta... Aunty Daula ta rungume ‘yar uwarta Bara’atu tana fad’in “I don’t want to lose him... I love him with all my heart... I don’t want to lose my husband..!!” Ta k’arashe tana mai kifa kanta cikin jikin Aunty B... Ai a d’ari Nabilah tabi hanyar dataga Khalid yabi.... Wani Dr ne yazo ya shigesu ya nufi ofishin Dr Hameed babban likitan dake jagorantar team d’in likitocin da case d’in Daddy Ke hannunsa... Nan Dr Hameed yake sanar dashi halinda matarsa da d’ansa Khalid Ke ciki... Likitan ya jinjina kai yana mamakin Wai dama Engr Mainasara yanada wata mata bayan mamar Siyama matar Sameer da sukai makaranta tare...? Abin ya tsaya masa a Rai... Da wannan tinanin ya ije report d’in dake hannunsa saman table d’in Dr Hameed kana yai ficewarsa.... Fitarsa da kad’an yaga wayan Sultan na shigo masa... Gaisawa sukai Dr Nazir na tambayarsa yau ya tina dashi ne... Sultan yace daga d’aya b’angaren “Ai ni na fika mutunci Nazir tinda ni ina nemanka ko Abuja naje... What about you... Kana neman mutum ne...? If I haven’t forgotten the last time da muka had’u a auren Sameer ne...” Nazir ya katsesa da fad’in “Hold on.. Speaking of Sameer.... Naga Father in-law d’insa a nan Abuja, yayi accident jiya, anyi rushing d’inshi wajenmu... Amma abin mamakin shine babu matar Sameer wajensa sannan babu mahaifiyarta saiko d’anta Khaleed da amaryar Baban nasu... Nasha mamaki sosai, dan ko idon Sameer ma ban gani ba....” Sultan ya mik’e sosai yana furta “Wait, hold on..! Wai Ahmad Mainasara da nasani kake ce min yayi accident...? Ko dai wani daban kake nufi...?” Nazir yace “How can I be mistaken bayan ina d’aya d’aga cikin Dr’s team da case d’insa Ke hannunsu.... Shisa nace maka nasha mamaki da naga babu Sameer babu matarsa babu kuma mahaifiyar matarsa dan to be honest with you jikin Engr Mainasara is getting worse.. I’m afraid he’s dying...” Sultan da mamaki ya cikasa yace “And kace sai bak’in fuskoki kake gani wajensa...?” Nazir yace “Of course yanda kaji....” Sultan ya murmusa a hankali kana yace “Kaga kiranka da nai yayi amfani... Well, na gode da wannan information da ka bani.... Sai anjima Doc...!” Ya katse wayar yana shafa hab’arsa a hankali... Ko banza ya samu abinda zai amfani dashi ya sami yardar Siyama dana mahaifiyarta... Babu shiri ya shiga neman layin Laila yace tasan yanda za’ai ta kaisa wajen mahaifiyar Siyama yanada muhimmin abu da zai sanar da ita.... *** A can asibiti kaw jigum jigum sukai dan izuwa lokacin Aunty B tace ya zama dole a sanar da mahaifiyar Khalid halinda ake ciki, domin yin shirun ba komai zai haifar ba illa ya k’ara complicating abubuwa... Mai faruwa ya riga da ya faru, kuma ko mai za’ai hakan bazai canza baya ba, dan haka gwara kawai a sanar da ita.... Khalid ya numfasa a hankali kana yace “But Aunty how....? Ta yaya... I know my mother, idan taji batun nan komai ka iya faruwa regardless of my father’s condition... How am I going to do all of this Aunty... Just how...?!” Ya k’arashe yana fuzar da iska mai d’umin gaske.... Aunty B ta nunfasa kad’an kana tace “Maybe a samu wani wanda takejin maganan shi... Sisters, brothers... Or maybe friends...But we can’t wait any longer.... Magana ta gaskiya kenan...” Mik’ewa tsaye yai yana mai fuzar da huci, lokaci guda yake zaga parlorn a hankali, shi kansa bai hasasho k’uran guguwa da tashin hankali dake tink’aroshi.... Toh waye ma zaije ya samu da wannan zance, waye Ammi ke sauraronsa... The only person da Ammi ke d’aukar magananta Aunt d’insa ce mahaifiyar Yesmin saiko dama dama Hajiya Fatahiyya momyn Sameer toh itama tinda ta soma yak’in raba Auren Sameer da Siyama suka daina shiri sosai, kuma ma ai Hajiya Fatahiyya bata nan... Last option d’in saidai fah yaje ya sami Mummyn Yesmin ne... Toh amma zuwa wajen Aunty Hanne Maman Yesmin yana nufin tada wani babban yak’in ne muddin taji cewa ya auri wata daban ba Yesmin d’inta dataci masa buri, kawai zai sake worsen situation d’in ne.....Dafe kansa yai kad’an yana ambaton Allah... Itadai Aunty Bara’atu da ta tatane da ita da kanta ta tari mahaifiyar Khalid da batun amma saidai wannan family issue ne bai kamata tai masu katsalandan ba, kuma idan har ta shiga batun toh fah saidai ta k’ara dagula abin ta kuma janyowa ‘yaruwarta Daula wani tashin hankalin wanda bata fatan hakan.... Gaba d’aya dai yinin ranan rasa abin yi sukai sai faman sak’e sak’e da warware ware Khalid yake.... *** A can Kano kaw neman Akram ake ruwa a jallo, lambar da yai amfani da itama da alama an gaza tracking layin, gaba d’aya hankalin Engr da na mahaifiyar Akram ya kai k’ololuwa wajen tashi, gashi a yammacin yau d’in ‘yansanda suka sami motar Akram d’in can wani gidan mai da aka jima da daina amfani dashi can hanyar fita gari.... Sanda suka kira Engr suka sanar dashi babu b’ata lokaci ya isa wajen, yai conforming cewa motar Akram ce, nan jami’an tsaro sukaci gaba da gudanar da bincikensu gameda abinda ya shafi motar had’ida baiwa Engr assurance d’in cewa bazasu huta ba har sai sun zak’ulo komai gameda b’acewar Akram, domin kaw tsintar motarsa da akai hakan na nufin Akram ba tafiya yai kaman yanda yace ba, dik yanda akai akwai wani abu a k’asa... Mai yuwa sacesa akai tinda ga motarsa an tsinta.... *** A can gidan Abbah kaw dik yanda suke tinanin zasu sami Mamani sunje amma babu Mamani babu labarinta, harta mutanen Kazaure sunce bataje can ba dan tin a biki da suka rabu da ita cikeda fushinta basu kuma jin d’uriyarta ba, hankalin Abbah dasu Baffah Wada yakai k’ololuwa wajen tashi, k’arshe dai Abbah cewa yai dole a bada cigiyan Mamani, ta ko ina abubuwa babu sauk’i, lokaci ne da ya zamto tamkar na farin ciki amma ta wasu fuskokin akasin Farin ciki ne... Wasu irin tashin tashin na hankula suka tsinci kansu ciki... A b’angaren Lami ma tashin hankali maras misaltuwa take ciki, itada shara a gidan basuda maraba, babu maibi takanta dan damuwan dake gabansu kad’ai ma ya ishesu... Haka takanyi jigum a d’aki tana tinanin abinyi, dik zaman gidan ya isheta ta gundura, ta tabbata har abada zaman gidan bazai kuma mata dad’i ba saidai ta mutu ita kad’ai a d’aki dikda cewa tayi imani dan hankalin Mamy bai tattareda ita ne a halin yanzu sabida b’acewar Mamani amma ta tabbata da yanzu Mamy tayita tausarta tana bata baki dikda ma ita akaima laifi, tasan halin hak’uri da kirki irin na Mariya... Amma wannan cin amana da tai mata da yawa take, harga Allah tana kunyar fuskantarta... Uwa uba Abbah da takeji kaman ta tattari i nata i nata ta tafi ta bar gidan Kafin ya saketa, Toh Wai idanma an saketa ita ina zataje tace an saketa a halin yanzu.. God’e god’e da ita sai ta hau tattaran k’afa taje tace an saketa... Ta share hawayen da suka kuma zubo mata... Tabbas yau d’in tana nadama da bata tab’a yin irinta ba tsawon rayuwarta... *** A guje tabi bayan Hafiz tana kuma fuzgo rigarsa tana fad’in “Wllhi baka isa ba, mai kake tinanin zakai... So make a kamamu mu k’arashi rayuwarmu gidan Yari ko mi....?” Hafiz ya fincike rigarsa bai daina huci ba yake furta “I’ll be very glad idan hakan ta kasance... Na tabbata idan aka kamaki da laifin garkuwa da d’an Adam mahaifiyarki zata had’iyi zuciya tinda Ke kad’aice d’iyarta, Kinga banida sauran damuwar ganinta cikin gidan mahaifina....” Ya k’arashe yana huci.... Girgiza kai Sawwama take lokaci guda take furta “Lallai na yarda baka cikin hankalinka Hafiz.... Idan kai wani abu foolish both nidakai will end up in jail... Haka kake so...?” Hafiz ya murmusa kad’an kana yace “ Toh ni kuma wata rayuwa ce mai dad’i ta ragemin a halin yanzu... I’ve lost everything, every single thing... Na rasa d’iyata Khausar sannan na rasa Zulfa’u... What else... Ki fad’amin mai kuma nake tsoron rasawa...?!!” Ya k’arashe cikin daka tsawa hawaye na tsartowa daga idanunsa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “I have nothing to lose.... So Idan bazakije ki tilastawa mahaifiyarki ta tafi ta k’yalemin iyaye na ba... I’m gonna show you what I’m really capable of..!” Ya k’arashe yana mai ficewa cikin sauri... Sawwama tabi bayansa tana doka masa kira amma inaa ko tsayawa baiba.... Sawwama ta koma cikin gida a guje tana lalumen wayan salulanta... *** Hab’arsa d’aure saman hannayensa biyu da ya dunk’ule waje guda... Da alama yayi nisa cikin tunani... Lokaci guda ta aje masa ruwan tea d’in gabansa had’ida zama gefenta kad’an.... Ya sakar mata sassanyar murmushi had’ida furta “Na gode Matar....!” Ta d’an saki murmushi a hankali tana mai sadda kanta, zata juya kenan taji ya ambto sunanta... Gabanta ya yanke ya fad’i, yauce rana ta farko data tab’a ji ya ambaci sunan nata... Ta juyo hankali tana mai amsawa... Gefensa yai mata nuni dashi yace tazo ta zauna.... Gabanta ya kuma tsinkewa but she can’t say no to him... A hankali ta tako har kusan nasa... Before tai aune taji ya kamo hannunta ya zaunarta kusansa sosai... K’irjin Zulfa’u yaci gaba da bugu.... Shiko Engr k’uri yai mata yana babu ko k’yafta idanu, dik sai tajita ba’a sake ba, ya d’an kurb’i tea d’in kad’an da gaba d’aya ya mance da zafin tea d’in sabida yanda ya shagala da kallon amaryar tasa... Zafin da yaji saman harshensa ya sanyashi d’an sakin k’ara kad’an had’ida cire cup d’in daga bakinsa yai saurin ajewa k’asa, hakan yasa Zulfah tai saurin waigowa tana tambayarsa mai ya faru, daidai ya d’ago kenan bayan ya ije cup d’in fuskokinsu suka had’e waje guda... Tsinin hancinsu suka had’e su duka biyun suna jiyo hucin numfashin juna...... Wane irin yanayi ne maras fasaltuwa suka tsinci kawunansu ciki.... Zuciyoyinsu suka ci gaba da bugawa, so take ta janye fuskarta amma ta kasa, k’arar da wayarsa tai ya sanyata saurin janye nata fuskar zuciyarta bata daina bugawa ba... Engr yai k’ok’arin saita kansa had’ida janyo wayar saman table... Jin ya soma amsa waya ya sanyata tattaro duk wani strength d’inta tana k’ok’arin tashi amma sai ji tai hannunsa saman nata ya rik’ota, hakan ya hanata ci gaba da tafiya... Tai saurin rintse idanunta k’irjinta naci gaba da bugu, batada wani zab’i dole ta dawo da baya ta zauna a d’arare... Da alama da jami’an tsaro masu binciken Akram yake wayan... Ta k’ura ma yatsun hannunsa idanu yanda ya sakalesu cikin nata, ko motsi mai kyau ta kasa sabida tsananin nauyinsa da takeji.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *99* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tinda ya ida wayar taji yai shiru baice komai ba saima k’urama fuskar wayarsa idanu da yai, tanaso ta tambayesa meke damunsa amma bazata iya ba, ta d’an saci dubansa a hankali har lokacin fuskar wayarsa yake duba, toh kodai ta tambayesa ne...? Tai tambayar ma zuciyarta... Kaman wanda yaji zancen zucin nata ya soma fad’in “Seriously, I’m exhausted... I’m tired of all this...” Ya d’an karkato sosai yana dubanta had’ida d’aura d’aya hannun nasa saman nata, yai crossing hannayen nasu cikin na juna kana yaci gaba da fad’in “Iyakacin abinda nake buk’ata a halin yanzu shine na kasance taredake, na k’yale dik wannan damuwa behind, and to be with you... In somewhere far away from here... Yanda babu stress d’in komai... Just....the two of us” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa had’ida k’ura mata idanunsa masu rikitar da ita.... Gaba d’aya sai jinta take wane iri haka nan, tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ta d’ago had’ida d’an dubansa kad’an... Saida ta d’an muskuta kana tace “Har yanzu babu wani labari gameda Akram...?” Ya d’an fuzar da iska kana ya girgiza kai kad’an “Wayar da na gamayi kenan... Har yanzu babu wani tak’aimemmen bayani gameda case d’in nasa... Amma dai jam’an tsaro zasu tsananta bincike...” Shiru ne ya d’an ratsa tsakani kana yaci gaba da fad’in “Idan wani mugun abu ya sami Akram bazan tab’a yafewa kaina ba.... Na sani Akram bai kyauta ba ta wani fuskar... But dikda haka ya zab’i ya sanar damu gaskiya a ranar d’aurin auren koda ace bai fuskancemu ba, ya zab’i ya sanar damu ta wata hanyar, nida Akram are practically brothers, ina sonshi tamkar yanda nake son k’anina.... Idan wani mugun abu ya sameshi zanji a raina na kasa tsareshi ne... Shin kina ganin zan iya jagorancin Al’umma if I couldn’t protect my own family....? Why am I having this feeling now.... I feel like stepping down... Inaji kaman bazan iya...!” Ya k’arashe cikin murya mai cikeda nuna damuwa da kulawa.... Zulfa’u tai masa k’uri tana dubansa cikeda tausayawa... Lokaci guda ta d’an gyara zamanta kana ta soma fad’in “K’warai zaka iya, domin kaw kaid’in zab’in al’umma ne... Kai d’in su suka tsaida kai ba kai ka fito da kanka ba, hannunta ta d’aura saman nasa wanda ya sanyashi d’ago idanu yana dubanta, murmushi saman fuskarta taci gaba da fad’in “You are our choice... Kai ne zab’inmu a matsayina na number one fan d’inka...” Murmushi saman fuskarsa yace “Did you say you are my number one fan...?” Jinjina masa kai tai a hankali murmushi bai bar saman fuskarta ba.... Lokaci guda taci gaba da furta “Idan ka janye zaka breaking zuciyoyin d’inbin magoya bayanka ciki harda ni....” Wannan karon murmushi mai bayyana hak’wara yai kana yace “Ban tab’a samun k’arfi gwiwa kan abinda nake nema ba irinta yau.... Thank you so much.. My number one...” Ya k’arashe yana mai k’ura mata idanu.... Murmushi kurum tai had’ida sadda kanta k’asa, nan ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Sanda Akram yake zuwa wajenki, did you notice something about him...? Or maybe akwai wani wanda ya sanar dake suna samun sab’ani...? Na sani inada d’inbin masoya haka nan ina d’inbin ‘yan adawa masu son ganin bayana, so bazanyi mamaki dan sun tsare babban yaro na ba... Abinda ban gane ba a nan shine, idan har kidnappers ne suka sace Akram... Maiyasa har yanzu basu fara batun ransom ba... Wannan dalili yasa nake tinanin idan ba ‘yan adawanmu na siyasa bane suka sace Akram toh waye zai sacesa haka...? Ko kina tinanin tsohon mijinki zai iya aiwatar da hakan...?” Ya k’arashe in a serious tune.... Wannan karon saida k’irjin Zulfah yai wani irin bugawa... A fili ta furta “Ya Hafiz...!” Ta d’ago tana duban Engr da shima ita yake duba..... Lokaci guda ta shiga tino threats d’in da Hafiz ya dinga jifanta dasu hardai bata janye batun Auren Akram ba, cewa da ya dingayi idan har tana sonsa Toh fah saidai ta rabu dashi dan idan ba haka ba dik abinda ya masa ita ta janyo... Take taji zuciyarta na wane irin tsinkewa... Bata tab’a tsammanin Ya Hafiz zai iya cutar da mutum har haka ba dikda cewa tasan zuciya irin nasa amma baza tai tinanin he can go this far ba... Lokaci guda take girgiza kai tana mai furta “No... No Ya Hafiz bazai iya aikata haka ba.... Bazai iya sace mutum ba...!” Ta k’arashe fuska fal damuwa.... Kamo hannayenta Engr yai kana yace “Zulfa’u... D’ago ki kalleni....” Zulfah ta d’ago idanunta masu rauni tana dubansa, lokaci guda yaci gaba da furta “If you know something zaifi kyau idan kika sanar dani ni kuma zan sanarda jami’an tsaro, yin hakan zai taimaka... Rayuwar Akram yana cikin had’ari.... Kuma idan har Hafiz zai iya aikata haka, now I understand maiyasa Akram zai nemawa kansa aurenki ba ni ba... Hakan yana nufin Akram ya min yak’in ne ba tareda sani na ba.... Now I understand... Shisa ya biyewa Muhibbah dan ya kaucar da hankalinta... Ya tari battle d’in shi kad’anshi.... Wannan shine irin soyayyar da Akram kemin....” Ya k’arashe yana duban Zulfah da tuni hawaye sun soma ciko idanunta... Engr ya kuma jinjina kai yana mai ci gaba da furta “Akram yanada reasons d’inshi da yasa yai abinda yayi... Yanzu na fahimta... Akram ba butulu bane kaman yanda kowa ya d’auka... Now more than ever bazan huta ba har sai na samo shi....” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye... Itama d’in tsaye ta mik’e hawaye na gangaro mata cikeda tsoro take furta “Ban tab’a zaton Ya Hafiz zai aikata mugun abu irin haka ba.... Ashe da d’an ta’adda nai rayuwan aure a baya... Ko da wasa ban zaci zai aikata mugun abu irin haka ba....” Ta k’arashe cikin tsananin kuka.... Kamota yayi had’ida mata masauk’i cikin jikinsa, lokaci guda yake shafa bayanta a hankali alamun lallashi yana mai kwantar mata da hankali... Saida ya tabbata tayi shiru kafin yai mata sallama ya nufi wajen Ammah da yaransa ma yai masu sallama kana ya fice yana kiran jami’an tsaro a waya..... Yau d’in ya shirya sanar da Muhibbah cewa ita d’in tanada abokiyar zama a halin yanzu dikda baisan da wata fuska zata d’auka ba... *** KADUNA Tin jiya take mafarkai marassa kyau gameda Daddy da kuma Khalid, gashi cikin su duka biyun ta gaza samun layukansu, baccin rana da ta tashi yanzu ma mafarkin ne ya d’agata... Yanzu kam hankalinta yakai k’ololuwa wajen tashi, Daddy bai tab’a kwanaki haka bai kira yaji daga gareta ba, kai ko fad’a sukai zai sauk’o da kansa ya kirata, amma kam wannan abu da mamaki da kuma tashin hankali yake, shima Khalid da bai yini ya kwana ba tareda sunyi waya ba yau d’in dik bata jisa ba, ko jiya ma da sukai waya sama sama ya amsata ya katse kiran yana mai ce mata yana zuwa aiki ya taresa... Sai faman kumbura take tana sauk’e huci... A haka Siyama da Laila suka shigo da ganin Siyamar hankalinta a matuk’ar tashe yake.... Ammi na ganinsu a haka ta mik’e itama babu shiri.... “Ke ke lafiya....? Meke faruwa...? Ya na ganku haka....?” Basu kaiga bata amsa ba Siyama ta bud’e murya taceda Sultan ya shigo..... Mamaki ya kuma cika Ammi, duban Sultan tai dan kaw tsaf ta ganesa abokin Sameer ne.... “Yaya dai.... Lafiya dai koh....?” Ammi ta kuma fad’i tana dubansu su duka ukun..... Sultan ya d’an duk’a yana gaidata.... Bata amsashi ba sai cewa da take “Wai lafiya na ganku haka nan....? Kaikuma uban wa ya baka izinin shigomin parlor...? Ke Siyama banson sakarcin banza tambayarki fah nake, uban me wannan abokin shashashan mijin naki ya shigo min har parlor.....?” Siyama daketa k’ok’arin k’unshe kukan dake bakinta kama hannun Ammi tai ta zaunarta saman kujera lokaci guda take furta “Ammi kin sami Khalid d’in....?” Ammi kanta ya kwance gaba d’ai.... Sororo take duban Siyama kana tace “Mai ya sami Khalid talk to me Siyama.... Wai meke faruwa ne...??” Caraf ta sinkayo muryar Sultan yana fad’in “Hajiya babu abinda ya sami Khalid amma ya sami mijinki....!” Da tsananin mamaki Ammi ke dubansa, kaucar da hannun Siyama dake rik’e da ita wacce hawaye ke bin k’uncinta tai kana ta mik’e sosai tana kuma dubansu musamman Siyama wacce hawaye ke kwaranyo mata.... Ammi ta isa gaban Sultan tamkar wacce zata shak’osa dan har saida tsoro ya d’an nuna a fuskar Sultan d’in.... Ammi tace “Maimaita abinda kace....” Sultan da tuni ya d’an soma daburcewa yace “Mijinki ya sami had’arin mota a hanyarsa ta komawa Abuja daga Kano... Yana can babban asibitin birnin tarayya.....” Bai kai aya ba Ammi ta shiga girgiza kai tana furta “A’a badai mijina ba.... Ina Khalid....? Khalid ya sani.....? Nasan bai sani ba shima, bai sani ba koh....?” Gaba d’aya ta daburce masu lokaci guda.... Siyama ta kuma rik’ota tana k’ok’arin calming d’inta saidai inaa Ammi fad’i take “Siyaaam Daddynki.... Daddynki Siyaaam kice min na cikin k’oshin Lafiya... Call Khalid right now... Just call him.... Bai sani ba shisa bai sanar damu ba koh....?” Ta k’arashe cikin murya mai matuk’ar nauyi... Lokaci guda kuma kaman wacce aka sinkara ta maidoda dubantaga Sultan tana kuma hura hanci take fad’in “Ta yaya zaka rigamu sani muna a matsayin family d’insa...? Ta yaya kaine zaka kawo mana wannan labarin...? Ta yaya zamu yarda ba k’arya ka guntula mana ba...??!” Wannan karon Laila ce ta tari maganar.... “Ammi, ba accident d’in Daddy bane zai baku mamaki da tsoro daga ke har Siyama... Abinda zakuji yanzu shi zaifi komai baku mamaki da tsananin tsoro.....” Daga Siyamar har Ammin juyowa sukai sosai suna duban Laila shaye da mamaki.... Siyama ta bud’e murya tace “Laila so kuke kuce mana Daddy bashi a raye...?” Laila ta girgiza kai kad’an tace “K’warai Daddy yana nan a raye amma fah rai kwaikwai mutu kwaikwai sannan ba wannan ne nufi na ba da nace abinda zakuji gaba zai matuk’ar baku mamaki da tsoro....” A harzik’e Ammi tai kanta tana fad’in “Ke banson salon iskanci da rashin kunya Ki bud’e baki Ki sanar damu abinda kika sani.... Meke faruwa...?” Laila ta dubi Sultan... Siyama ta subesu cikeda mamaki dan batai zaton akwai wani abinba kuma iyakaci accident d’in Daddy suka sanar da ita, suka kuma ce zasu rakata wajen Ammi su taimaka mata wajen sanar da Ammin.... Sinkayo muryar Sultan Siyama tai yana ci gaba da fad’in “Already family d’insa sun sani, dan dik suna tare a asibitin ciki harda d’anki Khalid...!!” Gaban Ammi yai wani irin tsinkewa ya fad’i, ta d’an girgiza kai tana fad’in “Kana nufin kace min Anty Hanne sister ta da Khalid sun sani basu sanar dani ba....?” Wannan karon mik’ewa tsaye Sultan yai kana yace “Ban tsamman sister d’inki ta sani....” Daga Ammi har Siyama duban mamaki suke bin Sultan dashi yayinda Laila ta tari zancen da fad’in “Ammi shin kinsan mijinki nada wata mata...?” Gaban Ammi ya bada Dumm! Dan ta tsani a d’ago labarin mijinta nada wata mata cen k’asar turai dikda ba wani zuwa wajenta sosai yake ba.... Ammi ta tab’e baki kad’an kana tace “Nasan yanada mata Helen, so kuke kuce ita da take daga can America ta rigani sani ko kuwa...?” Sultan ya girgiza kai a hankali kana yace “Ban tsamman matar mijinki baturiya ce... Dan wannan bahaushiya ce ‘yar k’asar nan kuma musulma sannan harda yara tanada...” Baikai aya ba Ammi ta katsesa da fad’in “Kai rufe min baki bana son iskanci da rashin kunya... Ku wuce ku fice min a gida idan abinda ya kawoku kenan....!” Hayaniyar Ammi ya sanya Yesmin dake bacci fitowa babu shiri, Kubura dake kitchen itama ta fito a guje Mama Kaltume mai dafa abinci itama ta nufo parlorn babu shiri jin muryar Uwar gijiyar tasu cikin tsananin tashin hankali.... Siyama data tari zancen kaman wani almara, takowa gaban Sultan tai tana binsa da kallon mamaki lokaci guda take furta “Sultan... Mai keke nufi...? Are you sure of what you’re saying...? Ka ko san mai kake fad’a....? You’re talking about my Dad here Sultan....!” Jinjina kai Sultan yai alamun tabbatarwa kana yace “I’m quite certain Siyama... Your Dad has another family here in Nigeria... Daga source mai kyau na sami wad’annan information d’in, Nazir aidai kinsan Nazir abokinmu nida Sameer toh shi ya sanar dani komai dan yana d’aya daga cikin likitocin dake rik’eda case d’in Daddy.... Siyama I’m sorry you had to find out like this ... Bansan maiyasa Sameer zai b’oye miki ba, dan idan har na sani toh definitely shima ya sani.... Ace Dad d’inki yana cikin hali irin wannan na rayuwa ko mutuwa bai sanar dake ba... Ko shakka babu maybe akwai abinda yake b’oye miki...!” Siyama da tuni ta yankin jiki ta zauna gijif cikin kujera girgiza kai take tana fad’in “No Partner bai sani ba, da ace ya sani da ya sanar dani... The only person dake da laifi a nan Khalid ne....” Yesmin da bata jima da sauk’owa ba tai karaf tace “Cousin karfa kiga laifin My K laifi na Daddy ne da dik babu wanda yasan da labarin yanada wata mata har saida Allah yasa da asirinsa zai tonu yayi accident koh Ammi...?” Ta k’arashe tana duban Ammi wacce ta koma tamkar bata a wajen sabida yanda duniyar Ke juya mata... Ahmadinta bazai tab’a munafuntarta haka ba... No hakan ba mai yuwu bane... Itafa bata yarda da koda kalma guda bane data gama sauraro daga bakin Sultan da Laila... She needs to go and see it herself... Dole taje ta tabbatarwa idanunta.... Lokaci guda tamkar wacce aka sinkara ta nufi upstairs a d’imauce tamkar zata kifa.... Siyama tabi bayanta a d’ari tana tanbayarta ina zata... Ba tareda ta dubeta ba sai haurawa sama kurum tai ta isa closet ta shiga firfito da kaya tamkar hankalinta bai jikinta.... Siyama tai saurin rik’eta tana tattara kayayyakin da Ammi ke firfito dasu tana watsasu saman gado.... “Ammi please, you need to calm down first.... Ina zaki haka...? Dan Allah Ammi please...!” Katseta tai da fad’in “Tambayata kike ina zani Siyaam... Are you really asking me that...? After what you’ve just heard..... Har kina tambayata ina zani....? Of course Abuja zan tafi... Right this moment domin na tabbatar ma idanuna gaskiyar abindake faruwa.... First accident sannan kuma ga wata mata da bamu sani ba... Who knows what we’re going to find out next.... Dan haka yanzu babu b’ata lokaci zan tafi Abuja... And don’t you dare think of stopping me....!” Ta k’arashe tana mai kuma jefa kayan fuskar Siyama.... Cikin sauri Siyama ta fice tana mai dokawa Kubura kira, nan take ta umarci Kubura ta hau sama ta shiryama Ammi kayanta zasuyi tafiya yanzu yanzu.... Yesmin tai karaf tace aiko itama zataje tinda ance Khalid na can.... Cikin mintuna k’alilan sukai shirin tafiya Abuja.... Ammi, Siyama, Yesmin saiko Kubura... Su Laila da Sultan suna ficewa suka kwashe da dariya, Laila tace “Kai amma naji dad’in wannan al’amari... Kai wannan aboki naka yaci kyauta.....” Sultan yai wata k’asaitacciyar murmushi kana yace “Kinga yanzu Siyama zata kuma zama furious da Sameer, zatace yasan Daddynta yayi accident bai sanar da ita ba, haushinsa zai ninku cikin zuciyarta.... Daga nan mu kuma sai mu executing all of our plans.... Sameer zai rabu da Siyama once and for all, zan mallaketa Ke kuma zaki mallaki Sameer, dan Sameer ba komai ya rasa daga Siyama sai kula, kece zaki bashi wannan kulan Ta yanda zai mance ya tab’a soyayya da wata mai irin sunan Siyama... Kinga daga nan shikenan....” Laila tai k’asataccen murmushi kana tace “Ka biyani Sultan, gaskiya kwanyarka naja amma baikai na My Sameer ba....!” Suka kwashe da dariya a tare kana Sultan yaja mota suka wuce yana mai fad’in su jira suji wayan Siyama idan suka isa Abuja suka tarar da abinda suka fad’i masu gaskiya ne... *** A can Kano kaw koda Jami’an tsaro suka isa gidan Hafiz domin interrogating nasa basu taddashi ba saiko matarsa Sawwama, dikda cewa Sawwama ta razana da ganin jami’an tsaro bata bada wata k’ofa da jami’an zasu fahimci tanada saka hannu a b’acewar Akram d’in ba hasalima sai k’ok’arin implicating Hafiz d’in da ta kumayi tana nuna masu cewa itama zaman hak’uri take dashi dan gaba d’aya ya makance da soyayyar Zulfa’u ko hakkinta na auratayya baya bata a matsayinta na matarsa... Ta kuma yin raurau da idanu tana ci gaba da fad’in “Officer ku taimaka ku zak’ulo yanda yake wllhi ni kaina tsoro yake bani a halin yanzu... Idan dai akan Zulfa’u ce na yarda mijina zai iya aikata komai....!” Ta k’arashe tana matsan k’wallan k’arya... D’ansanda guda d’aya yai wasu ‘yan rubuce rubuce jikin wata k’aramar takarda kana ya dubi Sawwama yace “Madam zamu tafi for now, amma muna iya dawowa ko yaushe sannan idan kinji wani abu gameda mijinki, inform us right away kinji koh....” Jinjina masa kai tai da saurin gaske yawa mutuniyar arziki kana tace “An gama yallab’ai... Na gode fah...!” D’an sandan dake sanye cikin bak’ar suit instead of kaki ya jinjina kai shima kana yai mata godiya suka fice sauran biyun na biye dashi... Suna ficewa ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana ta isa ta d’auki wayarta da sauri... Bugu biyu a na uku Babba Duna ya d’aga.... Sawwama taci gaba da fad’in “Babba karkaji komai na riga nayi implicating Hafiz, babu wanda zai zargeni balle kayi tinanin za’a zak’uloka....” Babba ya kwashe da wata jahilar dariya kana yace “Ke dama kina tinanin ina tsoron wani k’aramin maras kunya mai saka uniform a k’asar nan ne.... Ki k’yalesu su nemi idan zasu iya... Kin kyauta ma kanki da kika zame kanki amma ki sani mijinki ya shigo hannun Babba kenan ya zama namu....” Sawwama ta fuzar da iska kad’an kana tace “A halin yanzu Hafiz bazaimin wani amfani ba, amma inada sharad’i Babba....” Babba yace “Ina jinki mecece sharad’in Ki.....?” Sawwama ta mik’e tsaye sosai kana tace “Kasan a shekarun baya nida mahaifiyata mun baka ‘yandaudu d’ai d’ai d’ai har guda uku kai waqfin daji dasu kai asiri da al’auransu wanda har rana mai kaman ta yau babu su babu dalilinsu, banaso kaima Hafiz wannan mummunar abu... Idan komai ya lafa ka sakeshi ya dawo cikin ‘yanuwansa kafin nan ni kuma nayi tafiyata zuwa waje mai nisa....” Babba ya kuma fashewa da dariya kana yace “Bakida matsala amma bazan miki alk’awari ba.... Dik abinda ya faru da mijinki shi ya janyo dan ba’a bijire ma Babba.....!” Daga haka bai jira cewarta ba ya katse kiran Juyowa yai yana duban Hafiz da jini ya b’ata masa fuska sai haki yake, an d’add’aure masa hannaye da k’afafu ga Akram daga gefensa shima a d’aure.... Babba ya shafi fuskar Hafiz yana mai furta “Pretty boy Kaga yanda dik kasa yaran Babba sukaji rauni ma wannan kyakkyawar fuskar taka.... Banso abubuwa suka kasance haka a tsakaninmu ba.... Maiyasa zakace ka juya ma Babba baya kai waye da zaka shigo dajin nan kace zaka bada order alhalin Babba ke mulkinta....?” Ya kuma murmusawa a hankali kana yace “Wato ka fahimci kaima ka zama loser bari ka taimaki d’an uwanka loser ka fitar dashi daga dajin nan koh...? Toh ka b’ata....” Hafiz na tananin haki yake furta “Inace ni ne nan na kawoshi, toh nace ku fitar dashi, ku rik’eni instead... Shi hakan bai maku ba....?” Dariya Babba ya kumayi kana yace “Idan kyawawan maza irinku har guda biyu suka shigo hannun Babba kuna tinanin zaiyi sake su kufce masa ne....? Kashhh! Hakan bamai yuwuwa bane dan dikanku biyu Babba ya yaba daku... Kuma da sannu zaku zama mallakin Babba, hakan yasa ba’a had’aku waje guda da sauran mutanen da muke garkuwa dasu ba..... Ku huta tagwayen amare na...!!!” Ya k’arashe yana mai kuma bankewa da wata irin dariya maras dad’in saurare... Hafiz ya juyo a hankali yana duban Akram dake tsananin huci yana bin bayan Babba Duna da mugun kallo wanda yaransa suka sanyashi tsakiya suka nufi wajen mutanen da suke garkuwa dasu dan amsar kud’in fansa.... Hafiz yai tsaki a hankali yana mai kuma fincika cikin d’aurin da aka masa.... Akram ya tsaresa da jajayen idanunsa ga tsananin huci da yake.... A zuciye Hafiz yace dashi “What...!? Meye ka wani k’uramin idanu....!!” Fincika Akram yai yana fad’in “The nerve...! Har kanada bakin daka min tsawa bayan kai ka jefani a wannan bala’ain....!” Fincika Hafiz ma yai kana yace “Da ace baka soma d’aura idanunka kan matata Zulfa’u ba dik da hakan bata faru ba, da yanzu ina tareda matata... Nayi warning d’inkacountless time amma bakaji ba yanzu ga halinda muka tsinci kawunanmu ciki... You’re at fault here...!” Da tsananin mamaki Akram ke duban Hafiz kana ya kuma zabura yana fad’in “Kai har ka isa.....! Don’t you dare throw the blame on me, dak’ik’ancinka da jahilcinka shi ya kawomu nan... Ka kasa fahimta wa’adin zaman k’addarar Zulfa’u da kai ya k’are... Kuma dama na fad’a maka ita d’in ba tsararka bace, kuma nima ba tsarata bace.... Amma yanzu na tabbata ka fahimci hakan.... Bari kaji na fad’a maka, koda ace na kamun da son Zulfah a baya... The moment da na fahimci Boss d’ina is into her as well na janye zuciyata amma ban janye k’afafuwata da makamai na ba domin kaw mashi nake yak’in.... To keep his reputation clean nai haka dan nasan yanda kake mahaukacin nan muddin akace His Excellency ne mai nemanta zaka ruining komai from the very start, na tabbata zaka had’a kai da ‘yan adawa da wannan doluwar matar tasa ku taru ku b’ata sunan his Excellency shisa nayi playing game d’in.... Ka fahimta....!” Ya k’arashe yana mai ware idanunsa gaba d’aya.... Hafiz yai shiru tamkar wanda ruwa ya shanye... A hankali ya shiga jinjina kai tamkar wani k’adangare, lokaci guda ya tsartar da miyau wanda Ke gayraye da jini daga bakinsa kana yace “Yanzu na fahimci komai....” Akram da bai daina aika masa harara ba yace “Tinda ka fahimci komai yanzu sai musan yanda zamuyi mu fidda kanmu daga wajen nan Kafin mutanen nan su cimma burinsu akanmu....” Hafiz ya buga uban tsaki kana yace “Ta ya zamu iya fita daga dajin da Duna ya gama kewayeta da sihirinsa.....?” Akram dake aika masa harara yace “Allah shi zai fiddamu....!!!” Daga haka babu wanda ya kuma cewa komai cikinsu sai sak’e sak’e da suke cikin zukatansu.... *** Saida ‘yansandan suka tabbata sun binciki dik wani wanda keda alak’a ta kusanci da Hafiz saida suka masa tambayoyi, hankalin Haule ko ba’ace ba yai matuk’ar tashi, babu Hafiz babu dalilinsa ga ‘yansanda na binciken yanda yake, ga Sahariyya kwance babu lafiya danma Allah ya rufa asiri k’unan bai shiga sosai ba... Haule dafe kanta tai da duka hannayenta biyu tana duban officers kana tace “Rankashidad’e wllhi wannan sharri ne d’ah na ba d’an ta’adda bane... Wllhi sharri ne kumin rai kar ku kulle min d’ah a gidan yari wllhi shi ba d’an ta’adda bane....!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka had’ida zube gwiwoyinta k’asa hannayenta duka biyu dafe da kanta.... Magajiya dake gefe tana jijjiga fad’I take “Ranaka shidad’e kowa ya kwana da sanin cewa Hafiz ya lashi takobin hana auren Zulfa’u yuwuwa dan haka zai ko menene dan ganin Akram bai auri Zulfah ba, kuma kowa shaida ne dik abinda Hafiz ke k’ullawa tare yake k’ullawa da wannan makirar uwar tasa....Rankashi dad’e a halin yanzu rayuwar d’iyata kanta na cikin had’ari a matsayinta na matar wannan d’an ta’adda ku taimaka ku zak’ulo Hafiz dik yanda ya shiga ya fita kafin ya hallak’a nawa d’iyar.....” Ta k’arashe cikeda nuna damuwa.... Haule da hawayen idanunta suka kafe gaba d’aya dan jin irin sharrin da ake k’ullawa d’anta gaban idanunta... Cikin sauri ta zabura zatai kan Magajiya take fad’in “Amma ke wannan ‘yar wuta ce.... Ko a labarin munafukai masharrantar farko ban tab’a cin karo da irinki ba....” Magajiya ta mak’ale bayan Officer tana fad’in “Yallab’ai ka gani koh.... Ka yarda itada d’anta duk ‘yan ta’adda ne tinda gashi nima tana yunk’urin hallak’ani...” ‘Yansandan suka janye Haule daga kan Magajiya suka watsarta gefe suna mai fad’in zasu tafi yanzu amma zasu dawo kuma dole su saka idanu kan Haule sabida ita kad’aice zatai kinking d’insu to Hafiz..... Haule zubewa tai a wajen tana kukan nadama da bata tab’a yin irinsa ba a rayuwarta.... Koda wasa bata tab’a hasasho irin wannan musiba da yake ciki a halin yanzu ya tunk’arota ba.... Kaicon rayuwa mai cikeda tarin son zuciya... Lallai yau ta kuma yarda makirci makaranta ne mai k’unshe da azuzuwa iri daban daban... Ta kuma yarda da wannan hausar da akace duniya tafi gabaruwa iya jima.... Naja’atu dake rakub’e gefe tana kuka sosai, k’arasowa tai ga mahaifiyarta tana fad’i cikin kuka “Hajiya lokaci yayi da zaki yada makaman yak’inki Ki tuba kibi Allah Ki yarda shikeda cikakken iko akan komai....!” Haule na tsananin kuka wanda bata tab’a yin irinsa ba ta rungumo Najah tana ci gaba da fad’in “Naja’atu Yayanku Yayanku Najah... Najah sun k’ullawa Hafiz d’ina sharri.....!” Ta zabura da sauri tana janyo rigar Baba Alhaji take fad’in “Alhaji karka bari wannan azzalumar da d’iyarta su k’ullawa d’anmu sharri... Kai kanka kasan Hafiz ba d’an ta’adda bane koda ace yanada muguwar zuciya... Alhaji ka taimaka kaje kaima jami’an tsaro magana... Laifin garkuwa a k’asar nan ya zama babban laifi karka bari a kama d’anmu da ita....!” Fincikewa Baba Alhaji yai yana watsa mata muguwar kallo daga yanda take duk’e k’asa “Uban da ya aikesa ya aikata laifin... Dama tinda naga ya nace sai ya maida Zulfa’u nasan cewa bak’ar zuciyarsa da yayi gado a wajenki bazai barsa ba, dan haka tsuntsun da ya janyo ruwa shi ruwa ke bugu, babu hannuna ciki... Wayasani ma ko tare kuka k’ulla kedashi tinda dama kowa ya sani bak’ar makirace ke....!” Magajiya na murmushi ta shiga janyo Baba Alhaji tana fad’in “Muje Dalin Dalin... Muje karma ranka ya b’aci kaji koh....!” Ta waigo tana duban Haule dake duk’e tana duban mijinta cikeda al’ajabi kaman ba tare suka jima suna k’ulle k’ullen makircinsu ba..... Magajiya tai mata gwalo had’ida kashe mata idanu guda ta janyo hannun Baba Alhaji yabi bayanta kaman wani soko.... Haule dake duk’e wajen wane irin kuka ne mai ban tausayi taji na fito mata, Sahariyya da akai komai gaban idanunta itama, kuka ta fashe dashi daga yanda take kwance mai ban tausayi..... **** Tsaye Engr yai cikin parlorn yana amsa kiran jami’an tsaron, bayan sun ida wayar ne yaji shigowarta tana tafiya tana karo da k’ofa ita kad’ai.... Mamaki ya cikasa ganin irin yanayin da Muhibbah ke ciki na tsananin maye.... Engr yayo kanta da sauri ganin zata kifa a k’asa garin tangad’i.... Saurin tallafota yai yana binta da kallon mamaki.... Murya can k’asan mak’oshi yake furta “Maye.... Muhibbah...!!” D’agowa tai a galabaice cikin tsananin maye tana dubansa, lokaci guda ta tintsire da dariya tana mai nunasa da ‘yar yatsa take fad’in “Wai da gaske ka auri wannan kucakar yarinyar....? Ma’aruf da bakinka kake fad’a min kayi aure....??” Ta kuma fashewa da dariya tana mai ci gaba da layi, har lokacin Engr na rik’eda ita yana duban ikon Allah, abinda yakeji wai Wai akwai mata mashaya sai gashi nan har cikin gidansa..... K’ok’arin janyota zuwa cikin parlorn ya soma amma tak’i shigewa sai faman nunasa da yatsa take tana fad’in “How... dare you... Ma’aruf.... How could you.....?” Tana maganan tana nunasa da yatsa tana tangad’i.... Lokaci guda hawaye suka soma gangaro mata sanda taci gaba da fad’in “You’ll never be Happy Ma’aruf... Nai maka.... Alk’awarin bazan tab’a barinku ku kasance cikin farin ciki ba.....is a promise.... Kuma bari kaji na fad’a maka, bazan bar maka ‘ya’yana ba... I’m leaving with them, kaima ka sani ni ba matsiyaciya bace... Inada dukiya... Kuma dik k’asar da nakeso mu rayu da yarana zan tafi dasu.... Horon da zan maka kenan shine bazaka sake sakasu a idanunka ba..... Wannan alk’awarine....!!!” Ta k’arashe tana mai zubewa cikin jikinsa alamun bacci yayi gaba da ita.... Azata yai a kafad’arsa ya haura da ita sama d’akinta... Saman gado ya shimfid’ata had’ida gyara mata kwanciyar.... Yai zaune gefenta had’ida k’ura mata idanu tausayinta na d’awainiya dashi... Ya sanya ma ranshi zafin kishi ne ya sanyata aikata abinda ta aikata, baiji har cikin zuciyarsa ta jima tana ta’ammudi da miyagun k’wayoyi.... Sauk’e ajiyan zuciya yai had’ida k’urama drawer dake gefe idanu.... Kaman wanda aka sinkaya ya k’arasa ya janyo drawer d’in.... Gabansa ne yai mummunar fad’uwa sakamakon ganin tulin gidajen kayan maye da akai amfani dasu suna zubowa.... Mamaki ya cika zuciyarsa ya shiga d’aukan ledoji da kwalayen yana gani mamaki da fargaba fal zuciyarsa..... Cikin sauri ya kaikato yana duban Muhibbah dake bacci wasted zuciyarsa na kuma tsinkewa, lokaci guda yaci gaba da juya kwalayen yana ambaton Allah a hankali... Hakan na nufin Muhibbah ba wai yau bane ta saba ta’amuddi da miyagun k’wayoyi kenan... Ya dafe kansa a hankali yana mai karanto innalillahi.... Zuciyarsa naci gaba da harbawa... K’aran shigowar sak’o cikin wayarta da ya jiyo daga cikin jakkanta ya sanyashi saurin janyo jakkan kana ya ciro wayar... K’ura ma sak’on idanu yai zuciyarsa na kuma tsinkewa... Bash ne ya turo mata sak’on yana sanar da ita rana iti yau zasu fitar da huge amount of chocolates ta shagonta so ta zama ready..... Ya karanta yafi sau abinda yafi yana nanata chocolates cikin zuciyarsa... Haka kurum yaji kalmar chocolates bai kwanta masa ba tinda yasan Muhibbah Manyan shagunan kayan k’arau na mata takedasu har guda biyu babu wani shagonta da ya danganci abin ci.... Ya kuma juya wayar yana mai kuma karance sak’on.... Take wani tinani ya fad’o masa, yai saurin k’arasawa ya d’auki yatsarta ya shaga jikin wayar nan wayar ta bud’e..... Engr yaci gaba da duba sak’onni da tarin kira dake cikin wayar wanda akasarinsu daga Bash ne saiko k’awarta Shamzy.... Sosai sak’onnin suka basa tsoro da mamaki... Kenan Muhibbah bawai shan miyagun k’wayoyi take ba har safaransu zuwa k’asashen k’etare take... Wannan shine sana’arta, shine sana’ar data b’uya bayansa.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... This is a serious crime... This is terrible, abinda yake gani is just horrible...!!! Matarsa uwar ‘ya’yansa itace mai safaran k’wayoyi.... Take yaji wane irin gumi na karyo masa... Ya maido da dubansaga Muhibbah da har lokaci ko motsawa batai saima minshari da take sakewa d’aya na bin d’aya.... Take yaji zuciyarsa nai masa wane irin k’una.... Safaran miyagun k’wayoyi... Matarsa criminal ce kenan.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Mai take nema haka a duniya da tsanani da har zata jefa kanta cikin irin wannan musiba... Ya mik’e a hankali hannayensa hard’e a bayan ya k’arasa har gabanta yana duban kyakkyawan fuskarta.... Ya duk’a a hankali had’ida kamo hannayenta... Har lokacin bai janye idanunsa daga barin duban nata ba... Cikin wata irin dashesshiyar murya yake furta “Why...? Why Muhibbah...? Mai yasa kika zab’i wannan rayuwar... Maiyasa kika zab’i jefa kanki a halak’a... Menene bana miki da har sai kinyi sana’ar saida miyagun k’wayoyi... Ta ina na rageki Muhibbah...? Tell me na rageki da wani abu ne...? Meyasa Muhibbah...? Meyasa bakiso na cika ma Baba alk’awarin da na d’aukar masa....Why are you so stubborn...?!” Ya k’arashe cikin d’an d’aga murya tamkar tana saurarensa.... Ya jima a haka yana tinani kala kala had’ida sak’e sak’e da warware warware... Shid’in jagorancin Al’umma yake yunk’urin yi... Gyara daga kansa ya kamta a soma gani... Zai dik yanda zai ya tabbatar ya kawo k’arshen wannan ta’addanci da matarsa ta tsinci kanta ciki... Fatansa Allah yasa Muhibbah batada hannu cikin fitar da k’wayoyin watak’ila hukuncinta yayi sauk’i... Fatansa Allah yasa amfani kawai k’awayenta masu fitar da k’wayoyin suke da shagonta... Muddin aka kama Muhibbah da laifin fitar da muggan k’wayoyi baisan ya zaiyi ba zaiji tamkar yayi failing Babansa ne.... Ya dafe kansa a hankali yana ambato Allah... Lokaci guda ya tsinci kansa yana mai d’aurawa karan kansa laifin halinda Muhibbah ta tsinci kanta ciki... Ji yake tamkar gazawarsa ne watak’ila ya jefata cikin wannan mummunar k’addara.... Da wannan tinani ya mik’e ya fice daga d’akin.... *** ABUJA Daga yanda Daddy ke kwance cikin d’akin saman gado suna iya hangosa idanunsa a lumshe suke har yau, kana iya hango na’urorin da sukai k’awanya wa Daddyn....baka sauraren komai sai k’aran sautinsu dake tashi a hankali.... Nabila takai dubanta ga Khalid dake tsaye gefenta yayi k’uriwa mahaifin nasa... A hankali takai hannunta had’ida d’aurawa saman nasa, ya d’an juyo yana dubanta, lokaci guda yakai d’aya hannun nasa ya d’aura saman nata... Nabilah ta k’ak’aro murmushi ta sakar masa lokaci guda take furta “I know you can make it through... I know my bear is very strong...” Ta d’an kuma matsowa kusansa kad’an kana tace “I’m here for you.... Kaji....!” Saurin rungumeta yai tsam cikin jikinsa kana ya soma fad’in “I don’t know what I do without you teddy bear... Thank you for being here... I love you....!” A hankali taji bakinta na furta “I love you too my bear....” Ammi, Siyama da kuma Yesmin da k’arasowarsu cikin ICU d’in kenan tareda jagoranci wata nurse mutuwar tsaye sukai suna kallon Khalid da Nabilah dake rungume cikin jikin juna..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *100* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* K’aranda Yesmeen ta saki ya sanyasu waigowa babu shiri a tsananin firgice, daga Nabilah har Khalid dubansu suke da tsananin mamaki dan basu tsammaci ganinsu kwatsam haka ba.... Nabilah tai saurin matsawa daga jikin Khalid tana k’ok’arin sadda kanta k’asa.... Yesmin taci gaba da nunasu da yatsa tana fad’in “Ammi kin gani koh... Mayyar nan har taji labari ta biyosa mu bamuji ba.... Wllhi Ammi yau karki yarda ki bari ta fice a asibitin nan ba tareda kin masu iyaka na k’arshe ba...” Ta had’iyi sauran zancen nata akamakon wane irin muguwar kallo da ya jefa mata, a hankali yake takowa har ya k’araso gaban Ammi yana k’ok’arin had’o kalaman da zai soma mata dasu.... Sukam Ammi da Siyama har yanzu dai mutuwar tsaye sukai suna dubansa shayeda tsananin al’ajabi.... Khalid ya d’an fuzar da huci a hankali kana yace “Amm...Ammi barka... Da zuwa... I didn’t know you were coming... Jikin Daddy da sauk’i... Come muje ki ganshi....!” Ya k’arashe dik a d’an daburce yana k’ok’arin janyo hannunta saidai ko gizau bata motsa ba..... Cak shima ya tsaya yana duban Nabilah da yake facing d’inta daga yanda take tsaye ga hannunsa rik’eda na Ammi amma ko motsawa tak’iyi.... Saida ya had’iyi wata miyau kafin ya iya kaikaitowa a hankali yana dubanta ga tsananin bugu da k’irjinsa keyi, shi kanshi yasan kawai yau ko mai ta fanjama fanjam ne... Siyama ce ta sami zarafin cewa “Ba sai kace mana jikin Daddy da sauk’i ba, wanda suka fika damuwa su sanar damu jikin nasa da sauk’i sun sanar damu... Khalid what’s all this.... Meke faruwa a nan ne wai...?” A kaikaice ya dubeta fuska babu walwala yace “Wait Siyaam... Are you seriously asking me that..? Baki ganin Daddy a kwance... ... Well, let me remind you idan kin mance mai ya kawo Ki nan.... Our father got into an accident Siyama, look kalli cen, gashi cen a kwance...!” Ya k’arashe yana nuna mata d’akin da Daddy Ke kwance wanda suna iya hangosa ta cikin glass...Cikin fad’a fad’a yai maganar... Siyama dake faman aika masa mugun kallo tace “Don’t you dare take it out on me, ba wannan nake tambayarka ba... Mai wance tantiriyar maras kunyar k’anwar Sameer d’in takeyi a nan... And why are you two together...?” Yesmin dake k’ok’arin lab’ewa bayan Ammi tace “And they’re even hugging each other...!” Ta k’arashe murya can k’asan mak’oshi tana kuma b’oyewa bayan Ammi da har wannan lokaci bata tanka ba.... Dafe da kunkuminsa kurum yake dubansu, yama rasa mai zai masu banda dannawa Siyama da Yesmin muguwar kallo da yake... Siyama ta kuma ambato sunansa, saidai kafin takaiga cewa wani abu Dr Hameed ya shigo cikin ICU d’in Aunty Daula na biyedashi yana ci gaba da fad’in “Zamu iya cewa mijinki is out of danger a halin yanzu, sabida munga jikin nasa na amsar treatments..... “ Dr Hameed yai birki ganin mutane tsartsaye carko carko a lobby d’in.... Ita kanta Aunty Daula tsaye tai tana kallonsu gaba d’aya wanda ko ba’a ce mata ba tasan su Ammin Khalid ne dan tasansu a hoto... Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i.... Siyama da ta kuma kaikaitowa sosai tana k’are mata kallo daga sama har k’asa a hankali ta soma takowa har ta K’araso gabanta... Ta juyo ta kuma duban Khalid dake faman aika mata mugun kallo, murmushi Siyama ta saki a hankali tana kuma duban Aunty Daula... Lokaci guda take furta “So, is she the one...?” Tai maganar tana nuna Aunty Daula da yatsarta manuniya a wulak’ance.... Saurin takowa gabanta Khalid yai yana k’ok’arin janye Siyama yake fad’i a hankali “That’s enough Siyama, don’t make a sin here...!” Fincika Siyama tai tana huci take furta “Don’t you dare Khalid... Let me go... Ka sakar min hannu nace... Tell me is she the one... Itace matar Daddy da yaci amanar Ammi da ita... Yarinya k’arama haka, yarinyar da bata shige ta zama d’iyar cikinsa ba... Tell me Khalid is she our father’s wife...?!!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji tana huci... A zuciye Khalid yace “Yes... Yes!! She’s our father’s wife Siyama, and don’t you dare disrespect her..!!!” Girgiza kai kurum Siyama take tana duban Khalid da kuma Aunty Daula, lokaci guda take furta “Unbelievable..! This is crazy... This isn’t happening...!!!” Khalid dake tsananin huci har lokacin hannun Siyama na cikin nasa janyota ya somayi yana fad’in “Lets get out of this place.... We need to talk...!” Ganin haka yasa Nabilah saurin k’arasawa kusan Aunty Daula dan tana iya hango tashin hankali k’arara saman fuskar Aunty Daular.... Siyama kaw wani irin fincika tai ta fuzge hannunta daga rik’onda Khalid yai mata tana binsa da wani irin duba, lokaci guda ta maida dubantaga mahaifiyarta da har lokacin ganin abin take tamkar a film... Siyama ta k’arasa kusan Ammi da sauri tana fad’in “Ammi kina ganin abinda ke faruwa... Ammi kina ganin irin cin kashin da Daddy yai mana... How dare he zai auri k’aramar yarinya irin wannan... Yarinyar da he’s old enough to be her father..!” “SIYAMAAA!!!” Khalid ya daka mata tsawanda har saida ya tuna asibiti suke kuma asibitin ma ICU.... Dr Hameed ya d’anyi gyaran murya kad’an kana yace “Ammm inaga zaifi kyau idan kuka fita kuka tattauna a waje, coz this is an ICU please....” Siyama ta watsa masa muguwar kallo kana tace “Kai dalla yiman shiru... Sai mai idan ICU ne... So what..!!” Ta k’arashe tana mai kuma takowa gaban Aunty Daula saidai tuni Nabilah tasha gaban Aunty Daula tana fuskantar Siyama dake tsananin huci kai kace kwand’arawa Aunty Daular mari zatai... Siyama bata daina huci ba take aika masu muguwar kallo lokaci guda take furta “Ke kuma asuwa da zakizo kisha gabanta.. Ko so kike na had’a dake...?!” Nabilah ta murmusa kad’an kana tace “Kiyi hak’uri akwai majinyata cikin wajen nan, ciki harda Daddy... Kiyi saving dik wani hayaniyarki har mu fice daga nan please...!” Da tsananin mamaki Siyama ke duban Nabilah baki sake, bama ita kawai ba, harta Yesmin kallon mamaki take bin Nabilah dashi... Bud’an bakin Siyama sai cewa tai “Ke k’aramar karuwa mai bin maza har gida... Ke bakiji kunya ba, mu kamaki kina manne jikin namiji.. Har kinada bakin fad’i ma wani gaskiya...!” Khalid da zuciyarsa Ke tsananin tafasa ya tari zancen da fad’in “Siyama idan baki respecting Aunty Daula a matsayinta na matar babanki ba zaki bata girma a matsayinta na Aunt d’in mijinki Sameer... And don’t you dare... Kar ki kuskura ki sake kiran matata karuwa... Wannan ya zama na k’arshe...!” Yanzu kam gaba d’aya sun kuma shiga duhu... Daga haka janyo hannun Nabilah yai yana mai fad’i mata a hankali ta fice da Aunty Daula sai handle situation d’in.... Nabilah ta jinjina kai kana ta isa ta kamo Aunty Daula da har lokacin bata iya tab’uka komai ba sai duban abin take tamkar a film... A d’ari Siyama ta tare hanya tana fad’in “Suje ina... Suje ina... Khalid what’s all this please... Please tell me ba gaskiya bane... Khalid kana so kacemin wannan matar k’anwar mahaifiyar Sameer ce... Sannan kaikuma kayi aure... Ka auri k’anwar Sameer... Khaleed please... Juts what are you trying to tell us...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..... Jinina kai Khalid yai a hankali kana yaceda Nabilah su fice... Nabilah rik’eda hannun Aunty Daula da ko shakka babu hawayene Ke d’iga a idanunta suka rab’a ta gefen Siyama suka shige.... Khalid ya dubi Siyama dake tsaye tana bin bayansu Nabilah da Aunty Daula da kallo da har saida suka b’ace mata “Haka ne Siyama... Dik abinda kikaji gaskiya ne....” Ya tako gaban Ammi dake tsaye wajen tamkar ruwa ya shanye kana ya d’an risina ya kamo hannayenta “Ammi...! Ammi d’ago ki kalleni please...!” D’agowa tai tana duban Khalid tamkar wanda aka canza sa, duban rashin sani take masa da idanunta da suke tab da tarin k’walla.... Jikin Khalid yai matuk’ar yin sanyi, hannayenta cikin nasa yake furta “Ammi... I’m sorry, you had to find out like this.... I’m sorry I couldn’t tell you earlier, and I take full responsibilities of everything that’s happening, let’s talk somewhere kinji Ammi na...!” Ya k’arashe cikin murya mai rauni... Ga tsananin mamakinsa shafa fuskarsa Ammi ta shigayi tana binsa da kallo tamkar wanda ya b’ata ya dawo, lokaci guda take girgiza kai tana furta “Khalid kace min ba gaskiya bane... Son kace min k’arya suke Daddynka baida mata bayan ni... Kuma kaima bakai aure ba koh... Kamin magana Khalid..!!” Ta k’arashe tana jijjigasa hawaye na gangaro mata... Khalid da jikinsa yai matuk’ar yin sanyi jinjina mata kai ya shigayi a hankali yana mai furta “Ammi da gaske ne... Dik abinda kikaji da gaske ne... Ammi Daddy yanada wata mata bayan ke, and not only that... Daddy yanada wasu yaran bayan nida Siyama... And...” Ya d’anyi birki kana yaci gaba da fad’in “And Nabilah is my wife Ammi... Matata ce yanzu..!” Girgiza kai kurum Ammi take tana dubansa cikin rashin yarda, ga wane irin huci da take sakiwa... Lokaci guda ta finciki hannayenta cikin nasa kana ta nufi d’akin da Daddy ke kwance, dafe glass d’in dake jikin ginin d’akin tai tana hangosa ta cikin glass d’in daga yanda take tsaye... lokaci guda wane irin kukan da babu zato b’alle tsammani na fito mata, cikin karaji take furta “How dare you... How could you.... Ta ya zaka min haka... Ta ya zaka min haka Ahmad.... Ka tashi,,,,Nace ka tashi ka sanar dani duk wad’annan abubuwan dake faruwa ba komai bane face k’arerayi....!” Ta shiga bugun glass d’in da iyaka k’arfinta tana ci gaba da fad’in “Ka tashi Ahmad... Ka tashi ka sanar dani k’arya ne... Wllhi bazaka mutu ba sai ka tashi ka sanar dani da bakinka kalan cin amanar da kamin... Ka tashi nace..!!!!” Ba Khalid dake k’ok’arin janyeta tana tarjewa ba harta Siyama yanda Ammi ta fice gaba d’aya a giya ya firgitata... Babu shiri ta taho tana taya Khalid suna k’ok’arin janye mahaifiyarsu..... Yesmin kam har yanzu ganin abin take tamkar almara Wai her Kay ne ya auri yarinyar nan...? Ai tuni ta fice tabi bayansu Nabilah.... Nabilah da Aunty Aunty Daula cirko cirko sukai reception Nabilah na maida yanda abubuwa suka faru ma Aunty Bara’atu da bata jimada k’arasowa ba.... Aunty B ta kama Daula ta zaunarta saman kujerar dake jere a wajen kana ta d’an dafata kad’an tace “Daula are you alright...?” Hawayen da take mak’alewa ta d’an saka yatsun hannunta tana gogesu lokaci guda take k’ok’arin k’ak’aro murmushi tana jinjina kai take furta “Yes... I’m fine Aunty B... Kar ku damu dani...” Ta k’arashe tana kuma goge fuskarta.... Nabilah da Aunty Bara’atu suka d’an dubi juna kana Nabilah tace “Aunty you’re not ok... Inaga zaifi kyau idan muka tafi gida kawai....” Aunty B ta jinina kai tace “Gaskiya mu tafi kawai tinda dama dare yayi....” Basu kai aya ba Yesmin da k’arsowart wajen kenan ta taresuda fad’in “Ku tafi Ina..... Ai Wllhi babu yanda zakuje sai My Kay yazo ya baki takardan sakinki... Mayya jarabebbiya kin lik’e mishi kinga jan fata zaki lashe shi... Toh Wllhi sprit d’insa mai k’arfi ne barikiji na fad’i miki....!!” Ta k’arashe tana shan gaban Nabilah sai wani jijjiga take tana huci.... Aunty B ta dubi Nabilah ta dubi Yesmin... Lokaci guda taceda Yesmin “And you are....?” Yesmin na faman yamutsa fuska tana aika masu muguwar kallo take furta “Ni ce matar Khalid... Kuma Wllhi Wllhi sai ya saki wannan mayyar dan baida mata bayan ni....” Mahaukaciya suka d’auki Yesmin, Nabilah tace “Aunty don’t mind this lunatic, muje kunji.....!!” Batakai aya ba saiji tai Yesmin ta janyota ta dawo da ita baya tana fad’in sai ta nuna mata ita mahaukaciya ce.... Waigowan da Nabilah zatai ta had’a mata da mari mai shegen kyau wanda yasa Yesmin sakinta babu shiri, ta kame fuskarta tana ihu tana tsalle ta kuma yowa kan Nabilah saidai tuni hankalin receptionists da wasu nurses yayo kansu suka shiga kokawan rik’e Yesmin dake bore tana tsalle tana fad’in su bari ta nunama wannan k’aramar ‘yariskar tsan tsan hauka.... Nabilah kaw ta shiga b’oyewa bayan Aunty B tana fad’iwa malaman jinyan su taimaka su kame Yesmin su wuce da ita psychiatric ward dan da gaske haukarta ne ya tashi.... Yesmin na fincika tana fad’in su cikata, inaaa kaman cewa take su kuma kameta.... Sai tsalle take tana furta “Wllhi k’Arya take ni ba mahaukaciya bace... You’ve to believe me....!” Ta k’arashe tana mai yankawa nurse guda data rik’eta cizo a hannunta... Nabilah kaw fad’i take “Kun gani koh she’s dangerous please take her out of here... she might harm someone...!” Yesmin taci gaba da tsalle tana k’ok’arin zillewa tamkar wata ‘yar biri tana fad’in ita ba mahaukaciya bace.... Saidai tuni wata nurse ta k’araso da Allura... Yesmin taci gaba da ihu tana fad’in kada sui mata allura ita da hankalinta... Takai dubantaga Khalid da k’arasowarsa wajen kenan... Ta shiga k’walla k’ara tana fad’in “My K tell them ni ba mahaukaciya bace... Please tell them su sakeni da hankalina....” Basu saketan ba saima k’arasowa wajensa da Nabilah tai cikin sauri ta mak’ale jikinsa tana fad’in kalan tsoron da Yesmin ta bata... Shiko tuni ya mak’alata cikin jikinsa yana fad’in “I’m here now teddy bear... Bazan bari ta cutar dake ba....” Yanda Nabilah tai rau rau da idanu tai kalan tausai sai ka rantse har cikin ranta tsoron Yesmin take.... Yesmin kaw kaman Ta had’iyi zuciya ta mutu yanda ta gansu mak’ale da juna ga Khalid na kuma ririta munafukar yarinyar nan haba nan fah ta kuma doka wani ihun tana fad’in sai ta kashe Nabilah.... Tuni nurses d’in nan suka cazgwad’a mata allura had’ida fitarta daga wajen.... Nabilah ta saki rigar Khalid a hankali dan ita sai yanzu abinda tai ya soma bata kunya... Shiko d’an d’ago fuskarta yai kana yace “Are you alright...?” Jinjina masa kai tai cikeda kunya kana tace “I’m fine... Ina Ammi...?” D’an sauk’e ajiyan zuciya yai kana yace “She... passed out...!” Nabila tai saurin d’agowa a zabure tana dubansa... Dafata yai kad’an kana yaci gaba da fad’in “But she’s going to be alright... Dr yace Shock ne yasata sumewa, ga kuma stress... So sun kwantarta ta huta... Tana ma bacci yanzu haka, Siyama na tareda ita....!” Nabilah ta dubesa cikeda tausayawa, zatai magana ya k’ak’aro murmushi ya sakar mata kana yace “Don’t worry I’m fine... Muje mu sami su Aunty Shayibu ya kaiku gida it’s late already...!” A hankali ta jinjina masa kai tausayinsa bai saketa ba, kaman rak’umi da akala ta shiga bin bayansa har suka iso suka tadda Bara’atu naci gaba da baiwa ‘yaruwarta baki.... Khalid ya d’anyi gyaran murya kana yaceda Aunty B... “Aunty inaga kuje Shayibu ya maidaku gida... I’ll be staying here...” Aunty B ta jinjina kai kana tace “Khalid kai hak’uri kaji... Na sani this isn’t easy for you, tsaka mai wuya kake amma kai hak’uri in sha Allah komai zai wuce...” Cikeda tausayin Khalid d’in tai maganar.... Cikeda k’arfin hali irinta maza ya jinjina mata kai had’ida k’ak’aro murmushi yace “Don’t worry Aunty, I’ll be fine... Just take care of Aunty Daula please...” Jinjina masa kai tai kana tace “In sha Allah...!” Aunty B ta kamo hannun ‘yaruwarta suka fice... Nabila ta d’ago a hankali tana duban fuskan mijin nata cikeda tausayinsa, murya mai cikeda rauni tace “Do you want me to stay...?” Khalid ya kamo yatsun hannunta yana kallon lallen biki da sun d’an fara fading, takai dubantaga yatsun hannun nata yanda ya rik’esu yana duba... Sosai ta kula shi mutum ne mai son k’unshi dan so tare muddin suna tare toh yayita juya yatsun hannunta kenan yana kallon k’unshin.... Sinkayo muryarsa tai yana fad’in “No kije gida teddy bear... You need to rest as well...” Murya a hankali tace “Are you sure...?” Ya d’aga mata gira kana ya d’an sauk’o da bakinsa saitin kunnenta yace “Unless kuma za’a bani wani abu da zai keeping d’ina company while I’m here missing you....” Ya k’arashe maganar yana matso da fuskarsa nasa kusan nata sosai har saida tsinin hancinsu ya had’e....Kunya dik ya cikata dikda cewa babu mutane sosai wajen sannan kowa sabgansa yake babu mai kula dasu... Harara ta galla masa had’ida saurin janye fuskarta tana mai d’an turesa daga jikinta lokaci guda take furta “What are you doing, goodness it’s embarrassing.....” Tai maganar tana ‘yan waige waige Kubura da dosowarta kenan ta hangesu a wannan yanayi ai a d’ari tai birki tamkar zata dungura k’asa ta kame k’irjinta tana karanto “inna kalu lillahi mi zan gani ni Kubura...?” Ta kasa gaba ta kasa baya sai kallon wannan kayan al’ajabi take wanda su bama su san tana wajen ba... Lallai yau tayi mugun gani Khalid d’inta mak’ale da wata... Murmushi yai da gefen bakinsa dan ko babu komai yaga abinda yake son gani tsiwar nan tata... Janyota ya kumayi kana yace “Muje na rakaki...” Daga haka suka nufi k’ofa, saida ya rakata har k’ofan mota yana fad’in ta kular masa da kanta kafin ya dawo cikin asibitin... D’akin da aka kwantar da Ammi ya nufa yanda ya tadda Siyama na zaune gefen gadon da take bisa har lokacin matsan k’walla take..... Daga cen d’an gefe yaja ya tsaya yana duban mahaifiyar tasu cikeda tausayawa... Ya d’an K’araso kusan Siyama hannayensa sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa, idanunsa kan Ammi dake bacci yaceda Siyama “How’s she doing...?” Siyama ta d’ago pale eyes d’inta tana duban Khalid d’in shaye da mamaki, saida ta muskuta kad’an kana tace “Seriously Khalid... Tambayata jikin Ammi kake..? Kana can kai a dole ga mai mata... Look, kalli mahaifiyarmu Khalid.. She’s broken amma ko ajikinka instead ta sami kukawarka kana can kana siding da mak’iyanta...” Katseta yai da fad’in “Enough please Siyaam..!” Ta katsesa da fad’in “Don’t call me Siyaam.... This is serious Khalid... Ta ya zakaiwa mahaifiyarka haka....? What kind of a son does that to his very own mother..?” Khalid ya fuza da huci a hankali kana ya d’an bud’e murya kad’an yace “Will you please stop complicating things Siyama... For crying out loud this isn’t easy for me either... Instead Ki tausasi Ammi sai kuma aza wutan rigima kike... Haba Siyama kina gani Daddy fah har yau unconscious yake... Haba, ya kamata Ki fahimci what’s done has already been done... You can’t change the fact that Aunty Daula is our father’s wife... Kuma...!” Katsesa tai da fad’in “Don’t play the victim Khalid... So, Tell me... Does Sameer knows.... Shima ya sani bai sanar dani ba....?” Khalid ya d’an kame naman goshinsa kana yace “Siyama please....” Ta katsesa da fad’in “ Just tell me idan shima ya sani, no more secrets please Khalid...” A hankali ya jinjina mata kai kana yace “But ya kamata Ki gane ba hurumin Sameer bane sanar dake about this, kuma shima all of a recent ya sani.....” A zuciye tace dashi “Don’t you dare cover up for him....” Tab’e baki yai wannan karon had’ida janyo kujeran dake gefenta ya zauna kusan kan mahaifiyarsu... Lokaci guda ya zaro wayarsa yana shafawa yayinda Siyama taci gaba da b’alla masa harara tana sauk’e k’wafa a jere... Idanunsa naga wayarsa yace da ita “Kunyi waya da Aunty Hanne ne...?” A harzuk’e tace dashi “Ban sani ba...!” Ya kuma tab’e baki alamun ko inkula kana yaci gaba da abinda yake cikin waya..... Bayan shud’ewan kaman awanni biyu acan d’akin hutu na nurses yanda aka kwantar da Yesmin ta mik’e tana dafe kanta da yai mata nauyi... Lokaci guda ta shiga tuno abubuwan da suka faru... Ta zabura zata sauk’o daga saman gadon nurse guda ta k’araso tanai mata sannu had’ida tambayarta yanda takeji.... Harara ta b’alla masu tana fad’in su bata hanya ta shige uban wa yace masu ita mahaukaciya ce.... Suka kaw bata hanya ta shige tana tangad’i had’ida kame b’angaren kanta guda... Sarai sunsan da hankalinta iskanci ne tsantsan hakan yasa sukai maganinta suka danna mata allurar bacci maras k’arfi... Tana ficewa suka kwashe da dariya had’ida tafe hannu d’ayar tana fad’in “Maganin mai haukar rashin kunya kenan...” suka kuma tafe hannaye.... Yesmin na tafe taci karo da Mahaifiyarta Aunty Hanne Kubura na gaba zatai mata rakiya zuwa d’akin da Ammi Ke kwance.... Aiko Yesmin na gani mahaifiyarta Ta fad’a jikinta tana kuka sosai... “Mummy shikenan na rasashi, na rasa my Kay Mummy....” Mummy Ta shiga jijjigata tana fad’in “Ke Yesmin lafiyarki... Tashi kimin bayani....” Itakaw Kubura dama tana shak’e da haushin Nabilah dan ta hango k’iris ya rage Khalid bai sumbaceta ba, yanzu kuma ga wannan shashasha mahaikaciyar na kukan Ta rasashi... Ji tai tamkar takai mata naushi ko ta huce haushinta.... Yesmin na kuka jikin mahaifiyarta take fad’in “Mummy my Kay fah auran kucakar nan yayi... Kuma Mummy d’azu harda marina tai ta kuma k’ala min sharrin hauka aka cazgwad’a min injection na mahaukata amma ko a jikinsa... Mummy Wllhi tsafesa tai I’m sure of it..!!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka... Dariyar Kubura kawai suka sinkaya dan dikda haushin da take ciki saida taji dariya tazo mata amma Wllhi malaman asibitin nan sun bala’ain birgeta da suka tabbatarma wannan shashashar cewa ita mahaukaciya ce mai son wanda bai k’aunanta.... Mummy da Yesmin suka watsa mata harara a tare kana Mummy tace “Kikace Khalid yayi aure...? Kuma shashashar inane Ke da zaki tsaya k’aramar yarinya Ta tsinka maki mari baki tattaleta da maruka masu kayu ba....?” Yesmin Ta jinjina kai tana kuma matsan k’walla.... Ai tuni Aunty Hanne Ta shiga janyo hannun Yesmin tana fad’in “Muje naji uban da ya tsaya masa ya auri wata ba Ke ba.....” Yesmin Ta shiga share hawaye tana fad’in “Yauwa Mummy na shisa nake son Ki.......” Suka d’unguma suka nufi d’akin Ammi..... Khalid yana ganin sun shigo ya d’auke kansa tamkar bashi a wajen, yanaji Siyama na gaisawa da Aunty Hanne tana maida mata ba’asi... Mik’ewa ma yai yana dialing layin matarsa lokaci guda yake k’ok’arin gaida Aunty Hanne.... Ta amsa da k’yar had’ida rakasa da mugun kallo.... “Kai Saifullahi ina zaka kuma...?” Ta tambaya tana dubansa... Waya mak’ale kunnensa yake furta “Aunty ina zuwa.... Kuyi a hankali please Dr yace a bar Ammi ya d’an sami baccin....” Daga haka bai tsaya sauraren kowa ba yai ficewarsa yana waya da habibiyarsa.... Daga Yesmin har Kubura mayen kallo suka bisa dashi har ya b’ace masu..... Aunty Hanne kaw ta dubi Siyama tace “Wai haka Saifullahin ya zama ne....?” Siyama tace “Anty ya wuce haka ma... Zauna ga waje...” Ta k’arashe tana tura mata kujera... Tattauna lamarin suka dinga yi har dai Ammi ta farka ta taddasu suna zancen nan Siyama ta fice ta nufi kiran likita.... *** KANO Washe gari sassafe ta tashi ta soma had’e kayanta waje guda... Tanayi tana kuka, ita a ganinta cin mutuncinta kawai mijinta yai niyyan yi... Kuma tasan harda munafuncin wannan uwar tasa amma bacin haka tayi imani Excellency d’inta yafi k’arfin ajin wannan yarinyar, dama ita tinda taji Wai ya sami danginsa tasan sai an d’ago wani kutungwilar, dan munafunci za’ace ‘yaruwarsa ce.... Ta goge hawayen da suka zubo mata, tana huci ta nufi d’akin yaranta yanda tasa Murja Ta had’a mata kayan yaranta a cewarta zata biya gidan munafukar uwar Engr Ta kwashi yaranta.... Murja hankali tashe take fad’in “Hajiya dan Allah Ki hak’uri..” Wani uban tsawa Muhibbah ta darara mata... “Ke kiyi abinda na sakaki banson shegen felek’e....!!” Jiki har ba rawa Murja taci gaba da had’a kayan.... Yana daga parlorn k’asa dake cikin sashen nata yana sinkayo masifar da takewa Murja.... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yayinda hankalinsa ya karkata kan labarun da ake has kowa wasu yara ‘yan mata ‘yan makarantar sakandare aji biyar sunyi drugs over dose sun mutu har guda uku... Cikin tsananin tashin hankali Engr ke kallon labarun.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *101* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Kota kansa bataiba tasa kai zata fice ya bud’e murya had’ida doka mata kira.... Muhibbah taja ta tsaya tana sauk’e huci a hankali...... Lokaci guda ta juyo tana yamutsa fuska.... Engr ya tako gabanta kad’an “Ina zakije...?” Yanda yai mata tambayar ya sanyata dubansa tsegege kana tace “Mai ya dameka da yanda zanje... Inada sauran amfani a gidan nan ne... Mai kuma zan zauna nai maka...?” Jinjina kai yai a hankali kana yace “Kinsan yanayin da jiya kika dawo gidan nan cikinta....?” Ta kuma dubansa dan harga Allah bata iya tina tayi wani b’aran b’arama ba, tabbas tasan Shamzy ce ta dawo da ita gida dan bazata iya driving a halinda take ciki ba... Shan mur tai sosai kana tace “Koma a wane irin hali na dawo laifinka ne... Kuma Wllhi bara na kuma jaddada maka, bazan bar yarana ma wancan kucakar ba... I’m leaving with them.....” Jinjina kai yai a hankali kana ya shiga nuna mata tv da remote d’in dake rik’e hannunsa... “Look... Ki kalla da idanunki Muhibbah, ki kalli yara k’anana yanda miyagun k’wayoyi yai masu illa... Shin ya zakiji yau idan akace Samha na d’aya daga cikin yaran nan....? Tell me how would you feel idan kikaga d’iyarki cikin irin wannan yanayi...? Ba a shan k’wayoyi kawai kika tsaya ba Muhibbah har safaransu kike...? Shin kinsan rayuwaka nawa suka salwanta a dalilin haramtacciyar business d’inki...? Shin kinsan yara nawa suka haukace wasu suka mutu dik a dalilin wannan mummunar kasuwanci kuma haramtacciya...? Hibbah do you really know how many lives are ruined dik a dalilin san zuciya irin naki....?Why mai na rageki dashi.... Menene bana miki...? Maiyasa kika zab’i wannan hanya.... Drug trafficking Muhibbah....??” Ya k’arashe cikin tsananin tashin hankali wanda ya sauya launin idanunsa.... Tinda ya soma magana idanunta Ke k’asa k’irjinta na bugawa... Ya akai yasan hakan... Lallai ko shakka babu she messed up big time yesterday.... Muryarsa cikin tsawa ya kuma katseta “Answer me..!! Why mai yasa kika jefa kanki kika jefamu da yaranmu cikin halak’a... Answer me Muhibbah....??!!” A harzik’e wannan karon ta d’ago tana hawaye “Eh... Yes sana’ata kenan, dan kar kowa ya zargeni nakeda manyan stores na kayan k’arau.... Kuma sabida rana irinta yau na fad’a business d’in da zai kawo min kud’i nan take... Nafi k’arfin nai relying akan dukiyar miji... Kuma na wuce miji yamin gori inada nawa arzikin wanda zai isheni da ‘ya’yana harma da jikokina... And let me remind you this, wllhi wllhi babu kai babu yarana... Yanzu ba sai anjima ba zan kwashesu mu tafi....!!” Ta k’arashe tana mai goge hawayen idanunta kana tasa kai ta wuce fuuu yanda Murja ta fidda mata suitcases d’inta.... Cikin rashin yarda da abinda yakeji yake dubanta... Da gaske dai sana’ar muggan k’wayoyi matarsa keyi... Cikin sauri ya take mata baya yana doka mata kira amma inaaa tuni ta shige mota.... Engr yana fad’in kada securities su bud’e mata gate amma Muhibbah tai kansu tamkar zata d’agasu sama dole suka hangame mata gate had’ida kaucewa kada ta had’e dasu.... Babu shiri ya nufi car park yana dokawa Patrick kira... Patrick na tambayarsa ina zasu ko tsayawa saurarensa Engr baiba ya amshe car keys d’in dake hannun Patrick ya nufi mota guda ya shige ya tada... Take shima ya fice daga gidan da d’an karan gudu yabi bayan motarta.... Su Murja dasu Patrick da sauran Securities sukai tsaye suna kallon ikon Allah hankulansu dik a tashe ganin yanda masu gidan suka fice..... Muhibbah tana isowa tai parking ta kutsa cikin gidan tagajan magajan tamkar mahaukaciya sabuwar kamu... Gudu gudu ta fad’a cikin gidan tana fad’in a fito mata da yaranta, sauk’in abin yaran duk basu nan sun tafi makaranta.... Zulfah da ida sallan walharta kenan ta soma jiyo wannan hayaniya, ai babu shiri ta mik’e ta shiga linke sallayar kana ta nufo parlor..... Kicib’is sukaida Muhibba dake faman huci tamkar wata zakanya.....Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i dan sosai ta razana da ganin yanayin matar Engr.... Muhibbah tai birki tana k’are mata kallo daga sama har k’asa... Lokaci guda ta tintsire da dariya tana mai ci gaba da nuna Zulfa’u take fad’in “Ki jibeki... Ke har kin isa Ki jera dani....” Ta kuma yin k’asaitaccen murmushi tana jijjiga lokaci guda take furta “Allah wadan mijina ya rasa macen da zai d’aura idanu a kanta saike...? What a low taste of him...! Bari kiji na fad’a miki bana saudakar da fad’a cikin sauk’i, wllhi sai kinyi da kinsanin auremin miji da kikai... Gayyan matsiyata, ina yarana...!!” Ta k’arashe tana daka tsawa wanda ya sanya Zulfa’u d’an zabura kad’an dan ko iya amsata batai ba tama kasa.... Harga Allah ita bata k’aunan wani tashin hankali a halin yanzu.... Muhibbah ta kuma darara mata tsawa “Nace ina yarana ko bakiji bane... Munafuka algunguma kin wani tsaya kina k’are min kallo.....!” Muryar Ammah ce ya katsesu da fad’in “Zulfa’u Zo Ki wuce ciki abinki, k’yaleni da ita....” Zulfah ta d’ago idanunta da sukai raurau tana duban Ammah... Muhibbah kaw gyara tsayuwarta ta kumayi tana mai aikawa Ammah walak’antacciyar kallo.... Ammah ta k’araso gareta tana mai dubanta babu alamun wasa a tattare da ita.... “Ga dikkan alamun baki sami wadatacciyar tarbiya ba.... Allah kad’ai yasan kalan hak’urin da Ma’aruf yai dake...” Muhibbah dake faman yatsina tana aika mata muguwar kallo tace “Baiwar Allah bakisanni ba so zaifi kyau idan baki katsalandan cikin rayuwata ba... Bar gani kin zama mahaifiyar Ma’aruf rana tsaka ni nan da kike gani nice Ma’aruf, na bashi kulawar da baki ba , dan haka har abada bazaki tab’a zama mahaifiyarsa a idanuna ba.... Dan ko shakka babu k’aryar banza ce wan....!” Batakai aya ba taji sauk’an wata jahilar mari a kumatunta wanda ya haifar mata da d’aukewar ganinta lokaci guda.... Wayoyin kanta gaba d’aya taji suna spark... Ta saki ihu tana mai kame k’uncinta, lokaci guda ta d’ago tana lalumen waye ya wanketa da irin wannan mari da tsawon rayuwarta babu wanda ya tab’a mata... Ido hud’u sukai da Engr da bai jima da shigowa ba.... “Excellency na kan wannan matar da baka jima da sani ba ka mareni...” Nan ma bata kai aya ba ya kuma wanketa da wata marin maiji da lafiya wanda ya kusa kurmatata... Muhibbah dake dubansa da tsananin mamaki dafe da k’uncinta take fad’in “Excellency na... Yanzu marina ka kuma yi kan wan.....” Marin ya kuma watso mata Ammah tai saurin rik’e hannunsa banda sakin wani irin huci mai tiriri baya komai.... Ammah taci gaba da fad’in “K’yaleta haka Ma’aruf... Ba halinka bane dukan mace.... Lusarin namiji shike dukan mace....” Engr dake tsananin turiri ga idanunsa da suka kad’a sukai jazir fad’i yake “Ammah Ki k’yaleni na bata abinda na kasa bata tsawon shekarun nan.....” Ya kuma maida dubansaga Muhibbah dake tsaye sororo dafe da k’uncinta cikin rashin yarda da abinda take gani Wai yau ita Ma’aruf ke mari haka mutumin da tsawa mai tsanani ma bai mata idan ba ta b’aci ba, iyakaci ta b’ata masa rai saidai ya bata space na kwana biyu amma yau shike wanketa da wasu irin bahagwayen tagwayen maruka... Maidoda dubansaga Muhibbah ya kumayi kana yaci gaba da fad’in “For years ina tolerating d’inki, knowing cewa Ke d’in amanace a hannuna... Muhibbah gaba d’aya shekarun nan nayisu ne ina hak’uri dake ba don komai ba sai dan na cika ma Baba burinsa da kuma alk’awarin da na d’aukar masa... Allah shine shaidana... I’ve never loved you, but na zab’i na zauna dake nai hak’uri da duk wasu halayyanki marassa kyau... Only to get this in return....? How dare you zaki bud’e baki kice zaki aibanta mahaifiyata .... Ke har kin isa...? Dik rashin kunyarki akaina naji nayi tolerating.... But to my own mother... kinyi k’arya.... No Muhibbah baki isa ba.... Kije dik yanda zaki je I’ll not stop you.... Amma abu guda da nakeso ki sani bazaki d’auki d’aya daga cikin yarana ba.... Ki tafi dik yanda zaki tafi... If you like go to hell... Amma bazaki tafi da one of my children ba... Since when ma kika fara k’aunarsu... Stupid Kawai.... Now get out... Get... the... hell out of here!!!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa yana mai nuna mata k’ofa hawayen zafin rai na tsartowa daga idanunsa.... Kallon mamaki take binsa dashi kana tace “Ma’aruf ni kake kora daga rayuwarka kamar wata bola... Ma’aruf ni Muhibbah amanar Baba kake kora... Ma’aruf Rana d’aya ka watsar da dik shekarun da mukai tare ka zab’e mutanen da ka sansu rana tsaka..” A zuciye ya kuma cewa “Ki fita nace before I lost control..!!!!” Tsawan da saida ya sanya Muhibbah jada baya cikeda firgici... Ita kanta Zulfa’u dake rakub’e daga baya saida ta firgita da ganin wannan yanayi nasa, cikin ranta take ayyana lallai b’acin ransa baida kyau.... Muhibbah na hawaye tasa kai Ta fice cikin sauri tamkar zata kife k’asa, lokaci guda ta juyo tana dubansu gaba d’aya kana ta murmusa tace “This isn’t over Ma’aruf... This is far from over... Wllhi wllhi I’ll ruin you.... I’ll take you down to the ground... Mark my words...!!” Daga haka sa kai tai ta fice a guje tana kuma cazgan kuka mai tsuma zuciya.... Engr kaw tsuka ya buga cikeda b’acin rai yake furta “Pesky Idiot...!!” Lokaci guda ya zaro wayarsa ya d’an fice ya shiga neman layin makarantar yaransa dan ya sanar dasu koda wasa kar su bada yaransa ma wannan mahaukaciyar ko taje d’aukansu.... Zulfah Ta K’araso da sauri ta kama Ammah had’ida zaunarta saman kujera, tai saurin nufan dispense ta taro mata ruwa ta kawo mata... Ammah ta amsa tana mai saka mata albarka.... Jim kad’an Engr ya shigo dik ransa a Jagule yake, Zulfah ta d’an saci kallonsa kana ta mik’e ta basu waje shida mahaifiyarsa... Kallo ya bita dashi har ta shige kafin ya maidoda hankalinsa ga mahaifiyarsa.... Murya can k’asa ya soma fad’in “Ammah kiyi hak’uri dan Allah... Wllhi da ace nasan Muhibbah zatazo har cikin gidan nan ta aibataki da na jima da rabuwa da ita tin kafin zuwan wannan rana....” Girgiza kai kad’an tai kana tace “Kada ka bata takarda Ma’aruf... Kai hak’uri zafin kishi ne kawai ya sanyata yin hakan amma zata sauk’o zata shiryu in sha Allahu... Ko dan albarkacin yaranta kai mata afuwa...” Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyar tasa kana yace “Ammah ta ya zan iya ci gaba da zama da matarda batasan darajan iyayena ba... Ta ya zanci gaba da zama da matarda bata baiwa mahaifiyata kimanta da darajanta ba... Ammah darajarki da kimarki ya wuce haka a gareni....” Ammah ya kuma jinjina kai kana tace “Sanin inada wannan daraja da kima a wajenka yasa nace kai hak’uri karka bata takarda, da sauk’o da kanta dik yanda zataje kaji koh... Kai hak’uri Ma’aruf... Ka k’ara akan wanda kake... Idan zuciya ya b’aci ba’a yanke hukunci cikin b’acin rai kaji koh..” A hankali yake jinjina kai yana amsa mahaifiyar tasa dikda zuciyarsa dake matuk’ar masa zafi... Ammah tace “Allah shi maka Albarka ya shiga lamuranka...!” Ya amsa da Ameen Ammah... A hankali... Shiru ne ya d’an ratsa tsakani kana Engr ya d’anyi gyaran murya yace “Ni kaw Ammah ina son tambayarki dangin Abbah na... Naga babu wanda ya tab’a koda lek’owa....” Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Tin lokacin da mahaifinka ya rasu suka kwashe dukiyarsa sukai tafiyarsu ban kuma ganinsu ba, a cewarsu ni nai ajalinsa na kuma salwantar dakai dan naci dukiyarsa.... Basu kuma waiwayata ba har rana mai kaman ta yau...!” Ta k’arashe tana mai goge hawayen da suka d’igo mata... Engr ya d’an matso kusanta kad’an had’ida kamo hannayenta, cikeda tausayin qalubalen rayuwa da mahaifiyar tasa ta fuskanta yake furta “You’ve went through a lot Ammah na.....!” Ta saki murmushin k’arfin hali tana mai dafe fuskarsa take furta “Dik ya zama labari yanzun... Allah ya maido min dakai abinda yafi duk wata dukiya da zasu d’iba.... Kuma da ya tashi dawo min dakai sai ya dawo min harda dik wasu ahalina da na rasa a baya kuma kaima har ka hayyafa kayi Naka ahalin....Na gode ma Ubangiji na da wannan rahama a gareni...!” Ya saki murmushi a hankali zuciyarsa nai masa sanyi kana yace “Haka ne Ammah na... Ahali shine gaba da komai... Ubangiji ya kuma had’e kawunanmu da alkhairi...!” Ammah ta amsada Ameen sassanyar murmushi saman fuskarta.... Daga wajen Ammah mik’ewa yai ya nufi d’akin Zulfa’u dan itama Amman kitchen ta shige duba Hajjah wacce take tamkar K’awa a gareta.... **** A can Abuja asibiti kaw dik yanda Khalid yai ya daidaita tsakanin ahalinsa dakeda b’angare biyu a halin yanzu abu yaci tura, shin wanne zai zab’a wanne zai bari... Ga matarsa da matar Babansa b’angarensu guda sannan a d’aya b’angaren ga mahaifiyarsa da ‘yaruwarsa Siyama da kuma nasu tawagan... Ma iya cewa a halin yanzu rashin lafiyan Daddy yafi damun Khalid dasu Aunty Daula, ita kaw Ammi da nata ayarin basuda buri da ya wuce Daddy ya tashi ya warware wannan badak’ala da ya had’a, dan ita Ammi cewa tai ita bata yarda ma Daula matar Daddy bace har sai Daddyn ya tashi ya sanar da ita hakan da bakinsa sannan bata yarda Nabilah matar Khalid bace itama har sai Daddyn da yaje ya d’aura auren ya farka ya k’aryata auren munafuncin da yaje ya k’ullawa d’anta.... Haka ake zamana asibitin kaman zakuna a fagen daga ana hangen juna daga nesa nesa, Aunty Hanne na gefe na ziga Ammi cewa koda wasa kada ta yarda ta amince Daula matar mijinta ne sannan Nabilah matar d’anta ne... Khalid na daga tsakiya tsakankanin mata shi kad’ai har abin tausayi... Idan ka gansa dole ne ma ka tausaya masa, babu hali ya nufi yanda matarsa da Aunty Daula suke Ammi zata doka masa kira tana fad’in idan ya k’arasa wajen tsinannun can saita d’aga masa nono... Haka badon yaso ba zaka ga ya juya har abin taisai... Shida Nabilah saidai kallo daga nesa har su baka tausai... Gashi ga matarsa amma bai isa ya tink’areta ba itama bata isa ta tink’aresa ba... Yesmin da Kubura kaw hakan ba k’aramin dad’i yai masu ba tamkar su zibda ruwa k’asa su sha..... Shi kansa Dr Hameed har yana tinanin tink’aro wad’annan family da suke nema su maida masu asibiti filin cecekuce dan ma Allah yasa su Aunty Daula basa biyesu... Dik zafin zuciya irin na Aunty Bara’atu tana k’ok’arin danne kanta dan tasan a halinda ‘yar uwarta ke ciki bata buk’atan tashin hankali.... Dr Hameed ya nufosu da result d’in hoton chest d’in Daddy dan tabbatar da cewa bai sami matsala a heart ba ko wani internal bleading.... Gaba d’aya suka taso ta ko wane b’angaren suka nufosa.... Aunty Daula na hawaye take tambayar Dr Hameed sakamakon result d’in... Kafin yakaiga bada amsa Ammi ta fuzge result d’in tana fad’in “Bak’ar munafuka kin wani taso kina hawaye na munafunci, ni danai shekaru sama da talatin taredashi banyi kuka ba saike... Dan ki nunawa duniya ke kin cika munafuka koh...!” Aunty Hanne ta tari zancen da fad’in “K’yale munafuka ta nuna ta fiki k’aunar mijinki....!” Dr Hameed ya d’anyi gyaran murya kana ya soma fad’in “Wato....!” Dakatar dashi Ammi tai da fad’in “Ya isa basai taji halinda mijina ke ciki ba, it doesn’t matter ta sani ko kar ta sani....Dan a idanuna ita ba matar Ahamadi Mainasara bane....Kaga likita shige kaje abinka....!” Ta k’arashe tana mai danna result d’in cikin handbag d’inta.... Khalid da zuciyarsa ke tsananin tafarfasa muguwar kallo kurum yake aikama Aunty Hanne da Ammi.... Lokaci guda yake girgiza kai cikeda takaici.... Jiki a sanyaye Aunty Daula ta juya ta koma yanda ta baro Aunty Bara’atu da Nabilah su Yesmin da Siyama sai faman aika masu wulak’antaccen kallo suke daga nesa.... Daga Aunty Bara’atu har Nabilah k’arfin hali kurum suke amma kam su Siyama sukaisu k’ololuwa... Shiko Khalid cikin sauri yai k’ok’arin takewa Dr Hameed baya, sai sinkayo muryar Ammi yai tana fad’in “Khalid koda wasa wllhi karma kai tinanin zaka bisa Office ya sanar dakai ka zago ka fad’a ma wannan shu’umar yarinyar da a haife na haifeta.... Idan kuma ka sanar da ita condition d’in Daddyn Siyaam ban yafe maka ba...!” Aunty Hanne dake gefe ta shiga jinjina kai tana fad’in “Kinyi daidai Farida...!” Khalid ya juyo yana duban mahaifiyar tasa cikeda takaici... Takowa yai zuwa gabanta kana yace cikin tsananin k’unan rai “Really Ammi....? Wai dan Allah mai kike so ne.... Mai kike so ai yanzu dan Allah ki daina dik wad’annan abubuwan... Do you want me to beg on my knees..!” Yai maganar yana mai kai gwiwoyinsa k’asa... Lokaci guda ya had’e hannayensa duka biyu waje guda yana mai ci gaba da furta “Ammi please... Stop all this, please put an end to this ko dan halinda Daddy yake ciki... Dan ki k’yale Aunty Daula haka nan... Ta cancanci tasan halinda mijinta Ke ciki itama... Ammi na rok’i arzikinki ki sauk’e dik wani fushin da kike da Daddy akaina... Amma Ki k’yale Aunty Daula haka nan... Tanada zuciya mai kyau...” “Kai dalla cen rufe min baki...! Sun baka a ruwa kasha... Toh kaima ka sani bawai na gama dakai bane da wannan kwashesshen auren naka... Jira nake shi wanda ya had’a wannan Auren shiriritar ya tashi ya kwanceta dan wllhi kaji nai maka rantsuwa ina numfashi baka isa kai zaman aure da yarinyar nan ba...!” Aunty Hanne Ta k’arashe da fad’in “Yauwa fad’a masa dai yaji da kyau.. Matarsa guda d’aya ce nan gidan Duniyar k’anwarsa Yesmin...!” Wani irin muguwar kallo Khalid ya watsa mata kana ya mik’e yana bug’e gwiwar wandon jeans d’insa yanda ya duk’a lokaci guda yake furta “Amma dai Aunty ya kamata a d’an ringa dubawa ana kama girma....” Aunty Hanne ta shiga sallalami tana kame baki “Saifullahi ni kake maida ma martani... Eh lallai na yarda ba haka kawai suka Barka ba....!” Ammi tai k’wafa kana tace “Nan gaba bama maida martani ba had’emu zai gaba d’aya yace zai zane sabida an tab’a danginsa na asali, matarsa da uwarta... Yayi Khalid... Ya maka kyau... Toh ka dakemu mana kawai sai nasan ka cika...!” Shidai bai kuma tofawa ga tsananin zafi da k’irjinsa ke masa, tsakaniga Allah he’s tired of all this... Bai kuma cewa komai sai sa kai da yai ya fice gaba d’ai daga cikin asibitin dan hakan ne kawai yafi masa sauk’i a halin yanzu... *** KANO Tagumi Haule ta rapka tana duban ‘yandaudu dake baje tsakiyar gidan nasu suna buga lido da karta ga k’aurin hayak’i da ya kaure gidan gaba d’ai.... Dr Awwab ya ida duba jikin Sahariyya ya bata dik wasu magunguna da take buk’ata kana ya dubi Haule yace “Jikin nata da sauk’i sosai k’unan is not that deep so basai an kaita asibiti ba, with the help of these prescriptions zata sami sauk’i cikin yardar Allah....” Haule ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Likita mun gode sosai...” Awwab yace “Kuyi godiya ma Allah dan shi ya kiyaye sannan kuyi godiya ma Sameer dan shi ya turoni na dubata....” Yai maganar yana had’e kit d’insa... Haule da Sahariyya suka dubi juna cikeda al’ajabi... Haule tace kana nufin kace Sameer d’in shine ya turoka ka duba Shariyyar...?” Awwab ya jinjina kai kana yace “Eh Hajiya Dr Sameer shi ya turoni...” Wasu sabbin hawaye suka ciko idanun Haule babu shiri....Tasa bakin zaninta tana gogewa.. Lokaci guda take ceda Awwab “Mun gode Ubangiji ya saka da alkhairi... Zamu nemi kud’in aikinka mu biyaka daga baya...!” Awwab yace “Sameer ya wuce haka a wajena... Magunguna da treatment dik kyauta ne kuma in sha Allah zanke lek’owa ina duba yanayin jikin nata.. Allah shi k’ara afuwa....!” Ya k’arashe yana mai masu sallama kana yai ficewarsa ‘yandaudu na d’aga masa yatsa ko takansu baibi ba.... Sahariyya da Haule suka dubi juna suna mamakin ya akai Sameer ya sani har ya turo abokinsa duba Sahariyya... Najah da shigowarta kenan tace “Ni ce nan na kira Raiha na sanar da ita halinda Addah Sahariyya ke ciki gashi ko tasin kaita asibiti a duba lafiyarta babu ga Baba Alhaji dai yanzu bama gabansa dan ‘yandaudu ma sunfimu ‘yanci yanzu a gidan nan shisa na yanke shawarin sanar da Raiha ita kuma ta sanar da Ya Ma’aruf... Ku gode ma Raihana ku godema Ya Ma’aruf dan bayan dik tilin abubuwan da kukai masu sunada zuciya mai kyau zuciyar yafiya.... Basu k’ullaceku a zukatansu ba....” Haule da jikinta ya kuma matuk’ar yin sanyi share hawayen idanunta ta kumayi kana tace “Hak’ik’a duniya makaranta ce... Mugunta hassada da k’iyayya ba komai zasu kaika ba sai tarin danasani da d’inbin madama.... Yau ga Ma’aruf yaron da naso salwantarwa tin yana k’arami ya taimaki d’iyata bai k’yaleta ta rub’e a kwance ba, bai k’yaleta ta salwanta kaman yanda naso salwantar dashi ba... Sannan Raihanah yarinyar da tin tasowarta batasan komai daga gareni ba face gallazawa da azabtarwa daga gareni da kuma ita kanta Sahariyya... Sahariyya ita ta k’ona Raihana ta kuma so sake k’onata a karo na biyu Allah ya maida mata mugun nufinta kanta... Gashi yau Raihana Ta taimaketa... Kaicon wannan rayuwa mai cikeda tarin danasani....!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka... Sahariyya ma kuka take tana furta “Tabbas wannan hakki ne... Hakkin Kausar da kuma Raiha shine ya bini.... Inama Kausar tana raye na rok’eta gafara... Inama na kasance mutuniyar arziki... Kaicon wannan rayuwa...” Ta k’arashe tana kuka mai tsuma zuciya itama.... Naja’atu dake faman share nata k’wallan itama cikeda tausayin mahaifiyarta da ‘yar uwarta Ta shige tsakankaninsu ta had’esu ta rungume suna kuka mai tsuma zuciya... A haka Lami ta shigo ta taddasu d’aukeda jakkan kayanta... Haule ta shiga goge hawayenta tana fad’in “Lami lafiya na ganki haka... Ina zaki da jakkan kaya...?” Aunty Lami ta kuma goge ragowar hawayen idanunta dan itama daga gani taci kuka harta gode Allah... Maimakon ta baiwa Haule amsa sai cewa tai “Haule haka gidanki ya koma matattaran ashararru....? Haule haka rayuwa ta juya mana...?” Haule ta kuma share hawayenta kana tace “Lami abinda muka shuka ne... Yau ga sakamako muna girba.... Ina zakije da kaya...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Lami ta kuma sab’a jaka kana tace “Zuwa nai na miki sallama zan koma can garin mahaifina, zaman garin nan ya gagareni Haule... Kunyar idanun Mariya da Alhaji Usman bazai barni naci gaba da zama k’ark’ashin alfarmarsu ba... Haule zan tafi can garin mahaifina na zauna a k’auyen tukuf dan ya fiyemin wala’alla na sami sauk’in azaban zogin da zuciyata kemin.... Ko jiya da naje gidan Kawu Liti a nan Unguwar rijiyar zaki Zo kiga yanda matarsa da yaransa sukai min cin kashi cewa bazasu amsheni gidansu ba dan labarin abinda mukai ya karad’e ko ina cikin gari... Koran k’are sukai min cewa na tattari makirci na na k’ara gaba ba a gidansu ba.. Kuma banga laifinsu ba Haule tabbas sunyi gaskiya...!” Haule ta jinjina kai tana mai kuma matsan k’walla tace “Shikenan Lami Allah yaso saduwarmu... Ni kaina banida k’arfin halin fuskantar Mariya da mijinta....Dan bamu cancanci yafiya ba saidai rahamar Ubangiji....!” Lokaci guda suka rungume juna suna kukan nadama wanda basu tab’a irinsa ba... **** KADUNA Mamaki ya kuma cikasa, shida yazo shan cikin Sameer yaji ko yanda labarin accident d’in Daddyn Siyama sai ga wani babban surprise da ya tadda daga abokin nasa.... Lallai shi d’in mai sa’a ne... Yanzu kam ya gama samun makamin da zai datse auren Siyama da Sameer rabuwa ta har abada.... Sultan ya kuma gyara zama had’ida aje glass cup d’in dake hannunsa kana yace cikeda mamaki “A’a Wai Sameer haka abotan namu ya koma ne...? Yanzu da ace ban kiraka ba da bazan san Kana nan Kaduna ba kuma da bazan san Daddy ya dawo daga jinya ba, sannan ga babban abin mamaki Wai kaine da mata biyu Sameer... Come on Sameer mai zumunci ya zama ne dan Allah....?” Sameer ya d’an murmusa kad’an yana mai aje cup d’in hannunsa saman center table shima kana yace “Sultan, everything happened so fast... Wllhi nima daka ganni ban zauna ba, kuma dan dai Mummy ta turo Raihanah ta kawo mana drinks ne.....” “Da bazan san kayi aure ba ma...!” Sultan ya tari numfashin Sameer d’in da fad’in haka.... Sameer ya d’an murmusa kad’an kana yace “Abokina kenan... Dik yanda zan maka bayanin yanda abubuwa suka kasance bazaka fahimta ba... Amma tashi muje daga waje sai mu tattauna...!” Sultan ya mik’e cikeda k’osawa yana fad’in “Then you make me understand... Dan ni gaba d’aya ka canza min Sameer, saikace ba abokina aminina da na sani ba... Koda shike kaje Kano kayi sabbin Family sabbin friends da kuma sabon wajen aiki dole ma ka mance ni...” Gajeren murmushi Sameer ya kumayi, suna tafe yake ci gaba da fad’in “Kaima kasan ba haka bane Abokina... So stop being ridiculous...” Sultan ya d’an murmusa had’ida sakale hannaye cikin aljihun wandonsa lokaci guda yake ci gaba da jefo tambayoyi na siyayasa ga abokin nasa wanda ya d’auki dukkan yardarsa ya basa... Cikin amsoshin Sameer d’in ya fahimci tabbas Siyama bata da wannan labari na k’arin auren Sameer, don koda yace masa Amarya ce tasa ya mance dashi sai ce masa yai batama tareba tukunna gaban Mummy take yanaso ya soma sanar da Siyama kafin su tare... Hakan yasa Sultan ayyanawa cewa Dama ta sameshi... Shi kad’ai sai sakin murmushin cin nasara yake... *** Ita kaw Raihana gaba d’aya haka kurum taji ta tsani wannan abokin Ya Ma’aruf d’in dan taga sanda Mummy ya aikota kawo masu ruwa yanda ya kafeta da idanu, gaba d’aya sai taji ta tsanesa bai mata ba.... Suna kitchen ita da Mummy tana taya Mummy aikace aikace da shike Mummy dama chef ce mai zaman kanta dan a wajenta Sameer ya koyi mu’amala sosai da kitchen... Dan tinda suka taho Kaduna Mummy tai mata register a makarantar ta kama daga aikace aikacen kula da tsaftan gida da jiki gayu da girki dik Mummy koya matasu take tamkar wata d’iyarta gashi sosai Allah ya had’a jinin Raihanar da Mummy... Mummy ta k’udura a ranta cewa in sha Allahu sai ta gyarama Sameer d’inta matarsa tsaf ta yanda dik wasu abubuwa da ya rasa a aurensa na baya zai samesu yanzu... Hakan yasa taja Raihanar sosai jikinta dan ta sake da ita.... *** A can Abuja fah....? Wani Sabon tashin hankali yanda Ammi ta dake ta rufe idanu saidai su tafi gidan Aunty Daula su zauna gaba d’aya, Aunty Hanne naci gaba da zigata cewa gwara suje can duk su tare waje d’aya ta gane ma idanunta yanda kud’ad’en mijinta Ke tafiya... Ammi kaw ta hau kan shawarin Aunty Hanne tace ata fau saidai su d’unguma gaba d’aya su tafi gidan Daula tinda mijinta dai shi ya sayi Gida dan haka babu Uban da ya isa ya hanata zama cikin gidan... Siyama tace tayi daidai hakan za’ai, Yesmin kaw ba k’aramin dad’i hakan yai mata ba dan ko babu komai Yesmin zata samu Ta saka idanu kan Nabilah da Khalid.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *102* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Da tsananin mamaki Khalid Ke duban mahaifiyar tasa, da gaske take gidan Aunty Daula zata tafi... Shin wannan wane irin musiba ne da yak’i ci yak’i cinyewa... A hankali ya soma girgiza kai hannayesa dafe da kunkuminsa yake duban Ammi da Siyama yanda sukai masa k’ebebe aka.... Lokaci guda Khalid ke furta “No Ammi... I won’t allow you to go there, idan san zama cikin mutane kuke ga gidan Aunty Hanne why not bazakuje....” Katsa tai da fad’in “Naga gidan Hanne na zab’i gidan nawa mijin ai.... Kai Khalid bari kaji na fad’a maka... Idan mutuwa kake kana tashi baka isa ka hani zuwa wannan gidan ba... Siyama shige muje....!” Saurin tare gabanta yai yana fad’in “Ammi please don’t do this... Na rok’i arzikinki kar kije Ki d’aga masu hankali... Idan kinaso ni zan biku dik yanda zakuje but please Ki k’yalesu haka nan....” Siyama dake faman danna masa mugun kallo tace “Wai Khalid wa Ammi kake dika wad’annan abubuwan... I can’t believe you are doing this to your very own mother... Khalid Wai anya kanaso kai albarka kuwa....?” Da tsananin mamaki yake kaikaitowa yana mai duban Siyama... Ya karkato sosai yana dubanta kana yace “Really Siyama... What do you even know about albarka... Tell me Siyama, kin baiwa aurenki daraja..? Kin baiwa mijinki daraja...? Kin baiwa mahaifinki dake kwance daraja by disrespecting his own wife... Siyama is that what you call albarka.... Answer me wannan shine neman albarka a wajenki..!!!” Ya k’arashe cikin tsananin b’acin rai jijiyoyinsa na mimmik’ewa.... A zuciye Ammi tace “Khaliiiddd!!!!” Bai daina kallon Siyama ba yana mai ci gaba da huci yake furta “No Ammi Ki k’yaleni na fad’a mata gaskiya for once in her life idan har ta rasa mai fad’i mata gaskiya ne....!” Bai kai aya ba sai sauk’an mari yaji a k’uncinsa.... Ya d’ago dafe da k’uncinsa yana duban Ammi datai marin tana sakin huci... Lokaci guda taci gaba da furta “Bani address d’in gidan kafin nai maka abinda yafi mari....!” Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyar tasa yanda tana ganin gaskiya tana rufe idanunta... Tsawa ta kuma daka masa “Zaka bani ko sai na maka baki kabi daji....!!!” Jiki a mace ya zaro wayarsa cikin aljihu ya rubuta mata address d’in had’ida mik’a mata... Ammi tace da Siyama “Maza amsa ki gani...” Siyama na watsa masa harara ta finciki wayar had’ida forwarding address d’in zuwa nata wayar.... Ko tsayawa basa wayar hannu da hannu batai ba saima danna masa da tai cikin aljihunsa tana mai aika masa muguwar kallo... Ammi ta buga tsaki kana taceda Siyama “Shige muje Hanne suna jiranmu....” Babu musu Siyama tabi bayan mahaifiyarta tana mai watsawa d’anuwanta Khalid mugun kallo... Haka yanaji yana gani har suka b’ace masa bai saki k’uncinsa yana mamakin hali irin na Ammi ba, gaskiya sai yanzu ya kuma tabbatar da k’ok’arin Daddy tsawon shekarun nan da yai da ita a matsayin matarsa... Cikin wane irin yanayi ya nufi Intensive care unit... Ya shiga d’akin da Daddy ke kwance... K’uri ya masa daga nesa yana hangosa idanunsa a lumshe.. A hankali ya isa jikin gadon kana ya kai hannunsa saman na Daddy ya dafa... Saida ya cire nose mask d’in dake mak’ale fuskarsa kana ya soma fad’in “Daddy I’m sorry... But I don’t know if I can take this anymore.... I thought I was strong enough to face all this...But then na fahimci bazan iya ba... You need to get better Daddy... You need to get out of this place please Daddy... I can’t.... I’m sorry...!” Ya k’arashe yana mai kifa kansa saman hannun Daddy guda hawaye suna bin k’uncinsa... Sosai Khalid yake kuka mai ban tausai, saida yai mai isarsa kafin ya kumayi ma mahaifin nasa addu’a ya fice... **** A can gidan Aunty Daula kaw, kasancewar basu jima da dawowa Daga asibitin ba yasa dik suna parlor bama su haura sama ba tukuna.... Jin k’aran doorbell yasa Nabilah saurin mik’ewa tana fad’in “I’ll get that...!” Dik a zatonta Khalid ne ya dawo.... Da tsananin mamakinta tsaye ta gansu carko carko sai faman cika suke suna yatsina fuska... Yesmin ta bud’e murya tace “A bamu hanya mu wuce, masu gida sun k’araso....!” Tai maganar tana mai bangaje Nabilah da har lokacin kallon mamaki take binsu dashi... Suka kuwa kutsa kai suka shigo cikin gidan daidai sanda AuntyB taji shirun Nabilah yai yawa ta k’araso k’ofan itama... Da mamaki take dubansu... Aunty Hanne tace “What..! Ko korarmu za’ai.....?” Ga tsananin mamakinsu murmushi sukaga AuntyB ta sakar masu kana ta soma fad’in “Aa Haba dai, ai nan gidanku ne... Nan ya kamata ku sauk’a dama... Ku shigo, ku shigo bismillah....” Ta k’arashe tana kuma basu hanya.... Tuni Aunty Bara’atu ta umarci Karimatu mai aikin Aunty Daula ta taya Kubura haurawa da suitcases d’insu Upstairs... Nabilah ma dai bata kuma zaman parlorn ba ta haye parlorn sama abinta... Aunty Daula kaw Allah kurum take ambato cikin zuciyarta, ba’a asibiti bane kawai k’addarar had’uwa dasu ya kamasu ashe har gida zasu biyosu... A hankali take furta “Ya Rabb! You know best why you put people through the things they go through.. Give me all the strength to win my battles and to overcome the challenges... Ya Allah..!” Bud’e idanunda zatai ta sauk’esu kan Ammi dake tsaye gaban k’atoton family picture d’insu tana k’are ma hoton kallo... Ta kuma juyawa tana duban na Daddy da Aunty Daula wanda sukai su biyu.... Take Ammi taji wani irin kukan da babu shiri na kubce mata.... Siyama ta k’araso jiki a sanyaye da dafa mahaifiyar tata, cikin muryar kuka Ammi ta d’ago tana fad’in “Siyaam da gaske Daddynki aure yai ba tareda sanina ba... Siyaam mai nai masa da tsanani... What have I ever done to him to make him hates me like this....Mai nai masa da tsanani... Shin laifi ne dan ina k’aunarsa... Shin ta hakane zai saka min irin k’aunar da nake masa....?” Kuka yaci k’arfin Ammi.. Aunty Hanne Kaw sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Amma dai wllhi Farida mijinki anyi mai budurwar zuciya jibesa a hoton nan geme geme ko kunya Babu rungume da d’iyar cikinsa Wai matarsa....!” Ta k’arashe tana kuma tab’e baki... Lokaci guda Ammi ta waigo tana dannama Aunty Daula dake tsaye kanta kife wanda ko ba’ace ba hawayene ke zubo mata... A fusace ta isa gabanta tana fad’in “Bakiyi kuka bama munafukar Allah... Ke ko kunya bakiji ba, ki dubi mutum tsofe tsofe Ki auresa, hankalinki kwance sabida tsaban san abin duniya da ya rufe miki idanu.... Ki d’ago kanki ki daina nok’e nok’e ki dubeni tinda har kin iya haifan yara tareda mijina....!” Wannan karon Aunty Bara’atu ce ta matso ganin cin kashin tai yawa... Lokaci guda take duban Ammi kana tace “Baiwar Allah dik fah wannan bambami da kumfar baki da kike na gaba ya riga da yayi gaba... Mai aukuwa ya riga ya auku... Babu abinda zaki iya canzawa, kuma da ta kama ki amoda bak’in cikin abinda mijinki yai maki bama Daula zakiyi ba... Sai ki jira har randa mijinki ya farka sai ki tarbesa da rashin mutuncin naki dan shi yasan dalilin da yasa bai sanar dake ba... Kije ki binciki halinki da yanayin zamantakewarki da mijinki amma ko da wasa bazan zuba ido kici kashi akan ‘yaruwata ba....!” Batakai aya ba Hanne ta katseta da fad’in “Ke kul ahir d’inki.... Kada ki kuskura dan da alama bakisan da su wa kike ba....!!” Jin haka yasa Aunty Daula haurawa sama a guje tana kuka sosai... AuntyB kaw watsa masu kallo sama da k’asa tai kana tace “A koma islamiya a koyi kishi mai class....!!!” Haba nan fah Aunty Hanne taci gaba da hura hanci tana bambami... Ita kaw Ammi fincikar hotunan tai had’ida sauk’osu k’asa dan indai tana gidan ba’a isa lank’aya hotunan wad’annan maciya amanan ba... *** Aunty B tana haurawa Ta tadda Daula zaune a d’aki ta had’e kanta da gwiwoyinta tana hawaye... Dafata tai kad’an saidai Kafin AuntyB takaiga cewa komai Daula ta d’ago cikin hawaye tana fad’in “Gaskiya take fad’i.. Maiyasa zan aure mata miji.... Dik abinda zasumin nayi deserving... She’s the real victim here...” Ta k’arashe tana mai kuma share hawayen idanunta... Aunty B ta dafata kad’an kana tace “Fatima ko d’aya babu laifinki a nan, kuma Allah yasan dalilin da yasa ya barki ki fuskanci abokiyar zamanki ba tareda taimakon mijinki ba.. Daula ko wane aure na zuwa da obstacles d’insa... Babu ta yanda za’ace rayuwarki a gidan aurenki ya tafi smoothly ba tareda wani tangard’a ba... Kowa da kike gani in one way or the other yanada nasa problem d’in, yanada nasa battle d’in da yake fighting.... Rayuwa gaba d’ayanta jarabawace... Yanzu idan kikaji kalan jarabawar da wata ke fuskanta gidan aurenta sai Kinga naki tamkar a aljannah kike... So karma wannan abin ya dameki.... Mijinki na k’aunarki, sannan ga Khalid yaron kirki, you’re not alone... Dan hakan kici gaba da masa addu’a har Allah ya bashi lafiya kinji koh... This too shall pass...!” A hankali Aunty Daula ta saki murmushi kana ta rungume Aunty B tana furta “Sai yanzu na kuma fahimtar kyawawan halayyarki da ya sayi zukatansu su Mamy suke matuk’ar k’aunarki.... Ke d’in ‘yaruwace da ko wace ‘yaruwa zatai mafarkin samun irinki... Thank you for being here....!” Suka rungume juna AuntyB naci gaba da dannarta.... *** A can parlor kaw Aunty Hanne ce ta mik’e zata tafi bayan ta gama ziga Ammi, tace da Yesmin ko zasu tafi gida Yesmin tace wa ai tana nan sai taga abinda ya kwance wa buzu nad’i babu yanda zata... Aunty Hanne tai tafiyarta ta k’yale Yesmin nan gidan Aunty Daula... Suna zazzaune parlor kowa da abinda yake sak’awa su Ijlaal suka turo k’ofa suka shigo driver ya d’aukosu daga islamiya.... Carko carko yaran suka tsaya suna ganin sabbin bak’in fuskoki a gidansu.... Idanun Ijlaal ya sauk’a kan Siyama da har lokacin bata daina kukan cin kashin da Daddynta yaima mahaifiyarta ba a cewarta, dan auren wannan yarinya da yayi tamkar tozarci ne a garesu.... Da gudu Ijlaal ta tafi ta rungume Siyama tana fad’in “You must be Aunty Siyama Our big sister....I’ve seen your photo before, Ya Khalid ya nuna mana....” D’agowa tai tana duban Siyama da sauran hawaye suka mak’ale idanunta, lokaci guda tace “Are you crying.... kema kina kuka sabida Daddy yana hospital... Ki daina kuka kinji, Malam yace a islamiya we should pray for him... Yace idan Daddy yaga muna kuka he won’t be happy... Daddy zai sami lafia kinji Big sis....!” Ta k’arashe tana mai gogewa Siyama hawayenta da hijab din islamiyarta... Lokaci guda ta kuma rungumar Siyamar ita a dole lallashin Siyama take... Dik yanda Siyama ke so ta janye yarinyar daga jikinta amma ta kasa.... Wane irin sanyi taji jikin nata yai mata lokaci guda.... Ita kaw Humaira dake tanada d’an wayo tsaye tai tana duban fuskokin Ammi da Yesmin da babu alamun annuri tattaredasu saima b’allawa Ijlaal dake rungume da Siyama muguwar kallo da suke, sannan ga hotunansu yasha k’asa gefen k’afafun Ammi, tuni yarinyar tasha jinin jikinta sosai.... Ta isa tana janyo hannun Ijlaal tana fad’i a hankali “That’s enough Ijlaal let’s go upstairs....!” Da k’yar Ijlaal d’in ta saki Siyama tabi ‘yaruwarta Humaira... Siyama tabi yaran da kallo har suka b’ace ma ganinta... Ammi ce ta doka uban tsaki kana ta mik’e tana fad’in ita zata haura sama... Siyama ta d’an bud’e murya tace “Ammi wane d’akin zaki sauk’a...?” Wani kallo Ammi ta watsa mata kana tace “Wani d’aki ko ya wuce na mijina.... Ai banida d’akin sauk’a a gidan nan sai nashi....!” Daga haka tasa kai tai hayewarta sama.... Siyama ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai sauk’e idanunta kan hoton dake yashe k’asa... Ijlaal ta k’ura ma idanu tamkar mai tinanin wani abu... Murmushin da batai zato ba balle tsammani taji ya kufce mata a hankali.... Yesmin kaw k’uri taima Siyama cikeda mamaki.... *** A can sama kaw su Ijlaal suna haurawa suka tadda Nabilah zaune tai k’urima window kaman mai jiran isowar wani... Suka isa da gudu sunai mata oyoyo... Nabilah ta rungumesu tana masu sannu da dawowa... Humaira ta dubeta kana tace “Aunty Beels who are those people downstairs...? They seemed scary, I don’t want them here....!” Ta k’arashe tana tura baki.... Karaf Ijlaal tace “No I want our big sis here.... We’re family, after all... Right Aunt Beels....?” Jinjina mata kai Nabilah tai kana tace “Of course we’re family Princess... And family suppose to love each other... Always remember that kunji koh....” A hankali yaran suka jinjina mata kai.. Nabilah ta murmusa kana tace “That’s my girls... Oya get changed and wash your hands... I’ll serve us dinner here...” Ijlaal ta katseta da fad’in “No I want to eat downstairs with Aunt Siyama....” Gaban Nabilah ya yanke ya fad’i... K’ak’aro murmushi tai dan bataso yarinyar ta fahimci komai kana tace “Alright Princess.... We eat downstairs ok... Oya get changed and wash your hands sai muje koh...” Yaran suka nufi closet sukai yanda tace..... Suna tafe Nabilah na tsakiyarsu Humaira ke tambayarta “Aunt Beels ina Yaya... Why isn’t home yet....?” Daidai sanda Yesmin ta k’ara so yanda suke tana jiran taji amsar Nabilah... Nabilah ta Shafa kan Humaira kana tace “Zai dawo ne Princess... Muje koh....” Suka jinjina mata kai kana suka wuce tamkar babu Yesmin a wajen... Ta saki murmushi tana duban Nabilah kana tace a fili... “Mai waje ne yazo dan haka mai tabarma dole ya nad’e... Matar Khalid ta iso wacce akai fake aure da ita dole ta tattare ya nata ya nata tai gaba....!” Ko tsayawa saurarenta Nabilah batai ba sabida yaran, dan haka ne ma ta janye hannayensu suka nufo k’asa.... Har lokacin Siyama na zaune parlorn tana shafa wayarta.... Ijlaal ta saki hannun Nabilah ta nufi Siyama a guje ta kuma d’alewa jikinta tana zuba mata surutu, labarin sch islamiya friends d’inta da sauransu... Dik k’in yara irin na Siyama saida ta tsinci kanta da sauraren shiriritar yarinyar nan.... Ita dai Nabilah sai satan kallonsu take daga dining area, tai serving Humy kana tai serving plate d’in Ijlaal ma tana kiranta tazo taci dinner.... Ijlaal kaw ta tafi ta d’auko plate d’in ta dawo parlor wajen Siyama harda d’aukowa Siyama spoon ta aje masu abincin Wai saidai suci tare... Tin Siyama batason amsa yarinyar har dai ta soma amsata da k’yar... Gyara mata plate d’in tai gabanta kana tace “Oya go ahead and eat.... I had dinner already...!” Ijlaal ta d’an jinjina kai tace “Is that so... Why didn’t you wait for me...? Toh ki bani a baki..’Please please please!!” Yarinyar ta soma isan Siyama... Kasa korinta tai sai amsar spoon d’in da tai ta soma bata a bakin kaman yanda ta buk’ata... Su dai su Nabilah da Humaira daga yanda suke zaune suna kallon drama Ijlaal da Siyama... Sai bata a baki take tamkar ba Siyama ba.... Idan tai wani shiriritar har darawa kad’an Siyama keyi... Bata San dalili ba amma haka kurum taji yarinyar ta tsaya mata a rai.... Har saida tace mata ta k’oshi kafin ta daina bata... Yarinyar ta mik’e ta d’auki picture d’insu tana k’ok’arin d’agawa alamun tanaso Ta maidasu wajen zamansu.... Siyama ta dubeta kana tace “Wait, what are you doing... Put that down zaiji maki ciwo....” Yarinyar ta turo baki tace “So nake na maida...” Siyama ta k’araso ta amshi picture d’in kana ta lank’aya... Ta dubi yarinyar tace “Happy....?” Jinjina mata kai tai tana murmushi kana tace “Inaso ai mana dake da Ya Khalid da Humy da Aunty Beels... Wait, kema kinada miji ne... Ina yake...? Do you have children...?” Wannan karon wani irin bugu k’irjin Siyama yai... Tai k’urima yarinyar kana ta waigo tana duban dining area yanda sukai idanu hud’u da Nabilah.... Siyama ta rasa mai zatace da yarinyar dan ba kowa ya fad’o ranta ba face Sameer... A hankali ta mik’e kana ta Shafa kan Ijlaal tace “Good night beautiful...!” Daga haka bata kuma bi takan kowa ba ta haye upstairs yanda ta tadda Ammi ta tasa Aunty Daula gaba da fad’in ta nuna mata d’akin mijinta dan nan ne masauk’inta.... Siyama tace “Ammi please that’s enough... Zamu iya kwana nidake da Yesmin a guest room ba sai kinje d’akin Daddy ba please....” Wani irin wawan kallo Ammi ta watsa mata kana tace “Toh sannu uwata... Nace bazan kwana a guest room d’inba... D’akin da suke cin amanata ciki, nan zan kwana....” Ita kanta Siyama saida kalaman Ammi suka d’an mata nauyi.. Ta girgiza kai kad’an tace “Haba Ammi that’s enough please...!” Ammi ta kuma hayayyak’ota yayinda Aunty Daula ta girgiza ma Siyama kai alamun ta k’yaleta kawai... Kaman yanda Ammin ta buk’ata haka Aunty Daula ta bud’e mata d’akin Daddy harda kawo mata sabon bedsheet... Ammi tace waye take jira ya shimfid’a... Babu musu Aunty Daula ta shimfid’a mata... Ta haye kan gadon tana mai rakata da bak’ar harara.... A b’angaren Siyama tana isa d’aki wayarta ta d’auki ruri Sultan ne mai kiranta.... Dik yanda taso danne zuciyarta abin yaci tura, cikin ‘yar daburcewa tace “Sultan.... You are kidding me right...? Kaga nifa yanzu har tsoro kiranka Ke bani....” Sultan yai k’asaitaccen murmushi Daga d’aya b’angaren kana yace “Idan kinaso Ki tabbatar ma idanunki, Ki bar dik abinda kike Ki taho Kaduna gobe... Ni kuma zan maki jagorancin zuwa ganin abinda baki tab’a zato ba balle tsammani.... The surprise of your life....!” Siyama ta mik’e zunbur daga zaune kana tace “Sultan Wai dan Allah meke faruwa ne...? Ka sanar dani please... I can’t wait till tomorrow, I don’t have that kind of patience....!” Murmusawa Sultan ya kumayi kana yace “Na fad’a miki Siyama, is a surprise... Idan har kinaso Ki sani ki baro dik abinda kike kizo Ki gani da idanunki dan banso a baki labari zaifi kyau idan kika gani with your own eyes... Kin daisan bana k’arya....!” Ya k’arashe yana shu’umin murmushi lokaci guda ya katse kiran.... Hankalin Siyama idan yayi dubu ya tashi, gaba d’aya ta kasa zaune ta kasa tsaye... Toh menene Sultan zai nuna mata.... Menene haka da tsanani....? Taci gaba da bubbuga wayarta saman tafin hannunta tana mai zagaye d’akin.... A haka Ijlaal ta turo k’ofar ta ganta.... Siyama tai tsaye tana duban Yarinyar.... Ijlaal tace “Aunty, you couldn’t sleep...? Do you want me to hug you...?” Siyama da batasan dalilin zuban hawayenta ba cikin sauri ta bud’ewa Ijlaal hannayenta tana fad’in “Please hug me....!” Cikeda tausayawa Ijlaal ta tafi ta rungume Siyama dake hawaye... Sosai Siyama ta k’ank’ame yarinyar tana jin wane irin rauni cikin zuciyarta.... A haka suka kwanta cikin jikin juna har bacci yai gaba dasu, Yesmin data shigo ta gansu haka k’ebebe ta tsaya tana kallon ikon Allah... Cikin zuciyarta take ayyana cewa anya wannan yarinyar ba mayya bace, jibi dik k’in yara irin na Siyama amma lokaci guda ta manne ma Siyama, har tana k’ok’arin jefa mata rauni cikin zuciyarta.... Lallai dole tasan abinyi kafin soyayyar yarinyar yai tasiri zuciyar Siyama.... *** Nabila dake zaune ta kasa bacci dan har yanzu babu Khalid babu dalilinsa... Sai juyi take gefen Humaira dake baccinta hankali kwance... Jin kaman motsi daga downstairs ya sanyata mik’ewa zunbur ta zira hijab kana ta nufo k’asa.... A Daidai k’ofan d’akinsa ta hangesa zai shige... Yaja ya tsaya had’ida sakar mata murmushi wanda ko ba’a ba tasan na k’arfin hali ne... Gaba d’aya itama sai taji zuciyarta ya kuma mata rauni, tsananin tausayinsu gaba d’aya na ratsa ta..... Ga k’walla da suka ciko idanunta... Ganin haka ya sanyashi saurin k’arasowa gareta had’ida rungumeta... Kaman jira take nan ta saki mashi kuka a hankali.... Khalid ya rik’eta sosai yana fad’in “Is okay teddy bear I’m here now....!” Gaba d’aya shima da k’yar yake maganan, dan saida hawayen da yake k’ok’arin maidawa ya d’igo masa.... Cikin murya mai tsananin rauni Nabilah ke fad’in “Where have you been...?And meyasa kaki d’aga any of my calls... You’ve got me worried you know....!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata.... A hankali yai mata masauk’i a gefen jikinsa yana mai furta kana suka nufi cikin d’akin nasa yana mai furta “I’m sorry teddy bazan sake ba kinji love...!” Yesmin da Kubura da suke lek’en wad’annan masoya kusan gware sukai garin lek’e ba tareda sun ankare ba, dan Kubura bata tsammaci ganin Yesmin ba haka Yesmin d’inma bata tsammaci ganin Kubura ba.... Yesmin ta saki k’ara tana kame goshinta yanda sukai gware da Kubura.... Cikin sauri Kubura tajada baya had’ida danna switch d’in wuta tana mai furta Wayyo nayi gamo... Dan Yesmin ta shafe fuskarta da mayukan gyaran fata na bacci.... Ganin Yesmin ce ya sanyata jan uban tsuka itama Yesmin d’in tsukan taja Kubura na dariya tana fad’in “Ya kikaga Kajal da Sharupkan sun birgeki koh... Ai kawai ki d’au ta Annabawa oga Khalid sai gani daga nesa k’walelenki.....” Ta k’arashe tana gwalowa Yesmin had’ida tintsirewa da dariya.... Yesmin dake faman huci a d’ari tai upstairs ta shiga bugun k’ofar Ammi tana fad’in ta fito ta gani.... Babu shiri Ammi ta fito tana mustuke idanu... Su AuntB da Aunty Daula ma fitowa sukai jin bugun k’ofan da Yesmin keyiwa Ammi... Yesmin bata jira komai ba ta shiga janyo hannun Ammi tana fad’in “Ammi gayacan mayyan nan a d’akin Khalid zata lashesa....” Ammi ta dafe k’irji tana fad’in “Na shiga uku ni Farida kauce bani hanya....!” Ta ture Yesmin ta nufi downstairs tamkar zata kifa.... Aunty B da Aunty Daula suka dubi juna cikeda al’ajabin hali irin na Ammi, dik sahun da suke ajeta ta zarta tinaninsu.... Dafe da fuskarta yake furta “A lokacin da aka d’aura aurenmu na zaci shikenan yak’in ya k’are mana... Ashe akwai saura a gaba... Nabilah I can’t wait for all of this to end and to finally be with you... Mu biyu nidake a wata duniya mai dad’i da babu hatsaniya cikinta.... Na k’agu na nuna miki irin k’aunarda nake miki teddy bear...!” Ya k’arashe yana mai kuma tallafo fuskarta da duka hannayensa biyu, su duka biyun suna duban cikin idanun juna cikeda shauk’i.... Kaman daga sama suka soma jiyo ana bugun k’ofar da k’arfin gaske... Mamaki ya cika fuskokinsu... A zabure Khalid ya mik’e yana mamakin k’arfin hali irinta mai bugun k’ofar nan.... A zuciya yaja k’ofar saidai kafin yakai ga magana sukai idanu hud’u da mahaifiyarsa sai faman jijjiga take... Lokaci guda take k’are masa kallo... Yana sanye cikin inner black v neck saiko three quarter mai ruwan shud’i... Ammi tace “Ina take....?!” Jin muryar Ammi ya sanya k’irjin Nabilah saurin bugawa... Tai k’ok’arin janyo hijabinta ta zira, sai faman muzurai take.... D’an sosa kunnensa kad’an yai kana yace “Wace kenan Ammi...?” “Ka fini sani... Ina take nace...?!” “Ammi wayace miki tana nan...?!” “Zaka matsa ne ko kuwa...?!” Ta kuma fad’I cikin daka tsawa.. Girgiza kai kurum yake murya a shak’e yak’e furta “You’ve went too far...!!” Turesa gefe tai tana fad’in “Kaucemin kafin na had’a dakai...” Tuni ta fad’a cikin d’akin tana fad’in “Ina kike munafuka...?!” Khalid yai saurin take bayanta yana fad’in “Ammi you can’t do this...!” Harara ta watsa masa tana kuma watsa wa Nabilah dake tsaye kanta a k’asa muguwar kallo.... “Zo ki fita munafuka...Fita nace...!” Ta k’arashe tana k’ok’arin janyota... Khalid da mamaki ya kasa sakinsa saurin rik’o hannun Nabilah yai, cikin tsnanin k’unan rai yake furta “Ammi We’re not doing anything wrong here... After all, She’s my wife, and you can’t just barge in......” Baikai aya ba Ta katsesa da fad’in “Kamin shiru nace... Minafiki...!” Ta kuma duban Nabilah dake tsaye hawaye na d’igo mata kana tace “Kin kasa hak’uri har ku tare ne shine bari ki biyosa... Dangin marassa kunya, gadon k’anwar uwarki mai aure mazan mutane kikai ba laifinki bane...Wuce ki fita kafin na fitar dake....!” Sosai Nabilah ke kuka ta shiga k’ok’arin b’anb’are hannunta Daga rik’onda Khalid yai mata... Yak’i sakinta saima damk’e hannun nata da yai sosai har kaman zai ji mata ciwo sabida yanda ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci.. Duban Ammi kurum yake da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja... Nabilah kaw na kuka sosai taci gaba da k’watan hannunta Daga rik’onda Khalid yai mata... Ammi dake ci gaba da huci bud’e murya tai kana tace “Khalid idan baka sakar mata hannu ta fice ba wllhi kaji na rantse maka zaka nemi wata uwar amma ba ni ba...!” A hankali ya saki hannun Nabilah jin kalaman Ammi na k’arshe... Nabilah da kanta ke kife cikin hijabi ta fice da sauri tana ci gaba da kuka.... Yesmin dake lab’e saman staircase harda tsallen murna take... Saidai kaman daga sama taji ta tinstiro tamkar za’a wurgota k’asa.. Ta saki wane irin ihu mai cikeda razani... Sai kuma taji an rik’e k’afafunta tana reto a tsakani.... AuntyB ta gani rik’eda k’afarta guda Ta daddage k’arfinta lokaci guda Yesmin Ke furta “Aunty Kimin rai dan Allah kada ki jefoni k’Asa... Wayyo... Wayyo na shiga uku... Aunty kimin rai mutuwa zanyi idan kika jefoni... Wayyo Allah na...!” AuntyB da babu alamun raha tattareda ita tace “Daga yau kin daina munafunci na miki alk’awari...!” Ta kuma yunk’ura kaman zata saki k’afar Yesmin... Yesmin ta kuma sakin ihu tana doka kirawa jama’an gidan suzo su ceceta... A d’ari Ammi ta fito tana hangen kan Yesmin dake reto daga can saman staircase... Shiko Khalid tsaki ya danna kana ya zari wayarsa yai ficewarsa ko takan Yesmin dake ihun taimako baiyi ba. Ammi ma tana doka masa kira yazo ya ceci ‘yaruwarsa hannun dangin mayu amma inaa ko saurarenta baiba ya fice abinsa... Yesmin na ihu Ammi na ihu, Kubura kaw mai zatai banda dariya... Fad’i take Aunty wurgota zan capke....” Su Aunty Daula da Siyama suke ta faman baiwa AuntyB baki kan tai hak’uri kada ta jefa Yesmin..... Aunty B kaman zigata suke sai tayi kaman zata saki Yesmin sai kaji Ammi da Yesmin na sakin sabon ihu... AuntyB tace “Zaki sake..? Zaki sake shiga sharo babu shanu... Zaki sake shiga tsakankanin ma’aurata..!” Yesmin na ihu kaman ranta zai fita take fad’in “Wllhi na tuba... Bazan sake ba... Wayyo dan Allah kada ki jefani kimin rai...!” Da k’yar da sid’in goshi AuntyB ta janyo Yesmin ta fasa jefota daga saman bene... Yesmin ta zube a wajen tana maida numfashin azaba... Aunty Bara’atu tace “Dan Allah gobe ma Ki sake kinji... Kada ki fasa...!” Daga haka ta shige d’aki abinta Ammi kaw sai Sanna tayo sama a guje tai kan Yesmin dake numfashi da k’yar tana dubata, Siyama kaw gajeren tsuka kawai taja abinta had’ida komawa d’aki... Kubura kaw bata daina dariya ba dan har video saida tai recording a wayarta yanda Yesmin ke reto daga sama tana ihu gashi dama fuskarta mulke yake da mayukan bleaching inji Kubura... Ko banza ta sami na kallo tana darawa... Haka takai masu d’aki itada Karimatu mai aikin Aunty Daula suna kallo suna k’ek’yata dariya... **** KANO SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *103* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Ga dukkan alamu dai ta tabbata akwai saka hannun Hafiz a b’acewar Akram tinda gashi shima Hafiz ya b’ace b’at babu shi babu dalilinsa, Jami’an tsaro basu fasa binciken yanda zasu sami Akram ko Hafiz ba... Magajiya ta gyara zama sosai tana duban Sawwama kana tace “Hafiz bazai tab’a fitowa a raye ba kema kinsan waye Duna... Dan haka abu mai sauk’i amsar kud’in sassan jikin Hafiz zamuyi kinga riba ya zama namu....” Sawwama ta nusa kad’an kana tace “Amma Magajiya baki tinanin abin nan ya dawo kanmu, kinga fah Akram yanada matsayi sosai wajen mijin Zulfa’u, kuma Engr Mutallab ba k’aramin mutum bane a gari... Anya kinaga baza’a zak’ulo mu ba.... Hafiz da Akram ba kaman sauran ‘Yandaudun da muka saba kassarawa bane.... Anya kuwa kinaga zamusha...?” Tsuka Magajiya ta buga kana tace “Ta yaya za’a zak’ulo mu... Ke tin kafin a haifi uwarki Duna ke satan mutane yana garkuwa dasu yana amsar kud’in fansa... Kuma kaman yanda ya sanar dake babu wani maras kunya mai k’aryar uniform da ya isa ya kawo k’arshen ta’addancinsa a fad’in k’asar nan... Dan haka bazamuyi biyu babu ba, dole ya bamu diyan Hafiz dana Akram....!” Daidai nan Baba Alhaji ya d’ago labule yana bin Magajiya da wani irin duba.... Jikinsa har k’yarma take... Sawwama da tsoro ya d’an nuna a fuskarta duban mahaifiyarta tai taga babu ko alamun gizau a tattareda ita sannan ta dubi Baba Alhaji taga naci gaba da huci.... Sawwama ta duk’a ta d’au mayafinta tana fad’in “Ni zan wuce Magajiya sai munyi waya....” Ta d’ago tana duban Baba Alhaji da yai k’ebebe a hanya yana binta da muguwar kallo... Lokaci guda yake furta “Kije ina bak’ar munafuka azzaluma... Ashe saida min d’an nawa kukai... Kuka bisa da sharrin shi ya sace Akram... Toh dubunku ya cika asirinku ya tonu... Yanzu ba sai anjima ba zan kirawo ‘yansanda suyi gaba daku... Kuma Wllhi billahi sai kun fito min da d’ah na...!” Sawwama data d’an razana saurin rik’o babban rigar Baba Alhaji tai tana fad’in “Haba Baba kaima kasan bazamu tab’a yin haka ma Hafiz ba... Ba sai ka kaiga kiran ‘yansanda ba....!” Ta k’arashe tana mai kashewa Magajiya idanu alamun ta tayata shawo kan Baba Alhaji.... Baba Alhaji kaw bige hannun Sawwama yai daga jikin rigarsa yana fad’in “Kyaci uwaki bak’ar munafuka azzaluma... Sakar min riga...!” Sawwama bata cikasa ba saima dad’a marairaice masa da take tana kuma duban Magajiya dake ci gaba da taunar chewing gum d’inta alamun koma a k’asar gyalenta, lokaci guda take ci gaba a kashe ma Magajiya idanu alamun ta shawo kan Baba Alhaji kar ya fice kiran Jami’an tsaro... Ga tsananin mamakinsu muryar Magajiya suka sinkayo tana fad’in “Barsa yaje... Dan Allah kaje Kaga waye zamu jefa rana....!” Tai maganar tana mai takowa zuwa gaban Baba Alhaji kana taci gaba da fad’in “Kanada shaida....?” Baba Alhaji yai shiru sai muzurai, sai kuma yace “Allah shine shaidata....!” Dariya Magajiya Ta kece dashi kana tace “Allah baya zama gatan azzalumai bara kaji na fad’a maka... Ai shi ba azzalumin kowa bane kuma ya sanya zalunci ta zamto haramun tsakanin Al’umma... Ko ka mance kalan zaluncin da kai kaiwa d’an uwanka... Ka mance cewa kaso kassara rayuwar d’an uwanka da gudan jininsa... Toh mai zaisa kai mamaki dan wasu sun tasamma kassara rayuwar Naka d’an... Ai bari kaji na fad’a maka dik abinda mutum keyi a duniyar nan ko ba dad’e ko ba jima kansa yake komawa... Abinda kai shi za’a maka... Ashe k’aryar zalunci kake... Dan Allah ga fili ga doki... K’ofa a bud’e take ka tafi wajen jami’an tsaro Kaga yanda zan jefa maka laifin alhakin mutuwar d’anka a wuyanka kuma duniya kaf su yarda kaman yanda muka jefa ma d’anka Hafiz alhakin b’acewar Akram... Kadai san wannan shine a dakeka kuma a hanaka kuka koh...? Toh bismillah shege ka fasa... Jeka ga hanya...!” Ta k’arashe tana jijjiga gabansa had’ida kuma turo d’aurin kwali gaban goshi... Ga mamakin Sawwama hawaye ta gani na kwaranyowa daga idanun Baba Alhaji... Lokaci guda yasa gwiwoyinsa duka biyu yana rok’on Magajiya yana fad’in “Kiyi min rai dan Allah kada ki bari a kashe Hafiz... Wllhi Ina son d’ah nah... Dan Allah ki ceceni ki dawo min da Hafiz gareni, na tuba wllhi....” Ya k’arashe yana had’e hannayensa biyu waje guda... Magajiya na jijjiga take murmusawa cikeda k’asaita ganin Baba Alhaji duk’e gabanta yana rok’onta... Saida Ta kuma takowa har gabansa kana ta d’an shafi kansa tace “Dalin Dalin... Wllhi har ka bani tausayi... Zanso Hafiz ya dawo gareka amma saidai kashhhh..!!! Qaddara ya riga fata... Duna baya ganin abu yayi masa ya k’yale sannan dik abinda Duna yayi amfani dashi toh fah wani bil’adama baya kuma amfana da wannan abin... Duna salwantar da wannan abin yake.... Shawari d’aya tak ya rage gareka idan har kanaso ka amfana da d’anka Toh fah saidai kabi sahu mu amshi kud’in diyan shi... Kaga shike nan baka haifosa ya koma a hotiho ba, ko banza ka amfana da kud’in sassan jikinsa....!” Ta k’arashe tana mai zaro idanunta da suka sha Farin tozali a fuskar Baba Alhaji da har yanzu k’yarma yake.... Girgiza kai yake yana duban Magajiya shaye da mamaki kana yace “So kike kice na saida d’an nawa...?” Murmusawa ta kumayi kana tace “Ni taimakonka nake kar ka tashi a tutan babu don ina mai tabbatar maka cewa kaida Hafiz saidai ku had’u a lahira kuna la’antar juna dan bakuyi aiki mai kyau ba a duniya balle nace had’uwarku zai maku dad’i... So shawari ya rage maka....!” Ta k’arashe tana wani taku tsakiyar d’akin... Gumi ta ko ina ke tsartsafowa Baba Alhaji... Yana duk’e a wajen sai kece gumi yake... Wannan wace irin bak’ar ranace a rayuwarsa... Da kansa ya amince ya amshi kud’in sassan jikin d’ansa Hafiz.... D’an da yaci buri akansa har yaso salwantar da d’an d’anuwansa dik a sabida dashi... Yau gashi da kanshi zai bari yanaji yana gani ‘yan ta’adda su salwantar dashi bashida kuma halin hanawa.... Tuni ya kwabe hularsa da babban rigarsa ya zauna dirshan a tsakar d’akin yana kuka sosai... Sawwama ko duban mahaifiyarta tai had’ida jinjina mata kana tai ficewarta abinta... *** Da k’yar ta iya mik’ewa tana duban Shamzy dake gefenta tana shiryawa, Shamzy ta bud’e murya tace “Wai ni Muhibbah har yanzu k’wak’walwarki bata iya d’aukan strong drugs... Jibi fah tin jiya kike yashe a nan sai yanzu...” Tsuka Muhibbah tai had’ida kame b’angaren kanta dake tsananin mata ciwo kana tace “Ina Bash... Bai iso bane....?” Shamzy ta tab’e baki tace “Bash fah tin asuba yake jiranki a gidan nan, yana parlor... Kece kin kasa tashi a bacci daga testing new products d’inmu....” Tsuka Muhibbah ta kumayi kana ta mik’e da k’yar ta k’ara saman k’aramar table dake d’akin ta d’au maganin ciwon kai ta afa had’ida korawa da ruwa kana ta nufo downstairs yanda Bash ke zaune yana jiranta... Daga k’ofa ta hango bodyguards d’insa sun k’akk’ame.... Bash na hangota ya k’araso gareta yana fad’in “Finally the Queen is awake.... Kema kinsan na tsani jira Muhibbah.. Sabgogin gaba na sunada yawa... Badon nasan business zamu tattauna ba da bazan tsaya jiranki kina b’ata min lokaci ba... So did you get my message last night...?” Gajeren tsuka tai kana tace “Bash ba wannan ba, wata alfarma nake so kamin....” Bash ya gyara tsayuwarsa kana yace “Kaman mai kenan...?” Muhibbah ta kuma takowa gabansa kana tace “I want you to sabotage my husband’s campaign... Inaso jami’an tsaro su kama muggan miyagun k’wayoyi a wajen campaign d’insa ta yanda duniya zata fahimci shid’in ba mutumin kirki bane kaman yanda suka d’auka... Ina so abin ya kasance tamkar shid’in raba miyagun k’wayoyi yakewa matasa.... I want to see him on the ground...!” Ta k’arashe tana tsananin huci... Murmushi Bash yai had’ida gyara tsayuwarsa kana yace “Why do you want ruin your husband... I thought duk munaso yaci zab’e ta yanda sana’armu Zata bunk’asa ba tareda kowa ya saka mana idanu ko ya zargemu ba tinda mukeda gwabnati... Why the sudden change of mind...?” Muhibbah na huci take furta “Engr ya koreni... So ni kuma ka sanni.. The word losing is not even in my vocabulary.... Shisa nake so Kafin ya wulak’antani ni zan d’aid’aitasa...!” Bash ya murmusa a hankali yana shafar hab’arsa kana yace “Idan har hakan bazai shafi business d’inmu ba ai ba matsala bane... You have my unconditional support....Zan saka yarana su shiga ayarin campaign d’in mijinki... Za kuma mu kira jami’an tsaro mu sanar dasu akwai miyagun k’wayoyi a wajen... Daga nan kinga shikenan....” Muhibbah ta murmusa kana tace “Jibi zai fita campaign a yanda na sani... Ka sanar da yaranka su zama ready...!” Murmushi Bash yai kana yace “And what do I get in return....?” Murmusawa Muhibbah tai kana tace “A big reward idan har hakan ta kasance....” Ya kuma murmusawa yana shafa hab’a kaman wani tsohon maye kana yace “Consider your husband ruined...!” Daga haka dariya Muhibba ta kece dashi cikeda jin dad’i.... *** ABUJA Babu wanda Siyama ta masa sallama sun waye gari suna shirye shiryen tafiya Asibiti amma babu Siyama, haka Ijlaal data farka babu Siyama kuka taita masu dan daren jiyan tare suka kwana cikin jikin juna, Aunty Hanne kaw tana zuwa sassafe suka k’ule a d’aki itada Ammi a cewarsu sune k’arshen tafiya asibiti... Duk an watse dake da safe suke tafiya asibtin, su Ijlaal ma sun tafi makaranta.. Haka kurum AuntyB taji zaman su Ammi su biyu daga ita sai Hanne a gidan bai mata ba....Hakan yasa taceda Daula su fara gaba daga baya Shayibu zaizo ya kaita... Aunty Daula kam bata kawo komai ba sukai gaba abinsu... Har saida su Ammi sukai tinanin k’afa ya d’auke gaba d’aya kana suka lab’ab’o suka fito... Aunty Hanne ta d’aga Bakin zaninta ta zaro k’unshin magani a leda ta mik’awa Ammi... Ammi tai zuru tana dubanta tana juya ledar... Loakci guda take furta “Ya Hanne nifah kinsan abubuwan tsubbun nan naki tsoro suke bani, shi kuma wannan na menene...?” Tsuka Anty Hanne tai kana tace “Ba don abubuwan tsubbun da nake baki ba zaki samu kan mijinki ne ki dinga abinda kikaga dama a gidansa... Ba don magungunan nan ba ce miki akai Mijinki zai aure a b’oye gudun kar ki sani ne...? Toh yanda yai auren nan a b’oye wannan magunguna su zasu datse auren mijinki da wannan shu’umar yarinyar... Ita kuma yarinyar da suka lik’ama Saifullahin daga baya maji da ita... Dan ita ban d’auketa wata aba ba ma...!” Ammi tai jigum tana juya maganin kana tace “Amma dai Babu na kisa a ciki ko Hanne kinsan dik bak’in kishina bazan kashe rai ba....” Nan ma tsuka Anty Hanne tai kana tace “Ke da anyi magana sai kice babu na kisa... Tsaya kiji idan zaki sha giya kisha Ta dubu Farida ki daina wani tsoro tsoro...” Ammi tace “Naji dai... Babu na kisa, babu mugun cutarwa su rabu kawai abinda nake so kenan...” Anty Hanne tace “Babu na kisa, saidai da zaran kin barbad’e wad’annan a kusurwowin gidan nan, da zaran mijinki ya fito daga jinya ya shigo gidan zaiji ya tsanesu daga ita har yaran nata ina mai tabbatar maki saidai subi ‘yanuwansu su koma yanda suka fito....” Ammi tace “Hakan yamin dan bazan juri kallon wannan kayan k’ask’ancin ba....!” Haka suka nufi ko Wanne kusurwa na gidan suna barbad’awa har suka shige store d’in kitchen.. Aunty B dake biyedasu cikin sand’a suna shigewa store d’in ta janyo k’ofar da sauri ta rufe kif k’ofar tai jamming dasu Ammi ciki.... Hankali tashe suka shiga bugun k’ofa cikeda firgicin waye ya rufesu gashi basuga kowa ba dai... Ga duhun store gashi babu wani wadataccen vent.... Ammi ta dubi Anty Hanne tace “Hanne kodai aljanu ne suka rufemu.. Kinga bugun duniya bamuji d’uriyar kowa ba...!” Anty Hanne tace “Anya kuwa Farida... Kodai yaranta basu tafi makaranta bane...?” Kaman daga sama suka soma jiyo wata irin dariya mai ban tsoro tana furta “Ku sani Ramin mugunta k’urerre ne... Yau kun hak’i kabururukanku da kawunanku...Hajahjjahhhhhaaahhh..!!!!” Aka kuma tuntsurewa da wata irin dariya.... Ammi da tuni jikinta ya d’auki rawa, a matuk’ar tsorace take fad’in “Bawan Allah dan Allah waye ka..kai... Kai mana rai... Kada ka kashemu a wajen nan....!” Dariyar aka kuma fashewa dashi kana muryar taci gaba da fad’in “Ni ne wanda yasan sirrikanku da kuka bisne....” Tiryan Tiryan muryar ya karanto laifunkansu da abubuwan da suke kuma k’ullawa,... Yanzu kam ba Ammi kawai ba harta Anty Hanne ‘yan hanjin cikinta sun kad’a jin wannan mutumi mai wargajejen murya yasan komai nasu... Ammi ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Bawan Allah kai mana rai wllhi mun tuba....!” Muryan ya kuma fashewa da wata irin bahaguwar dariya kana yace “Maiyasa Zanyi rangwame wa matar data kasa rangwantama d’anta da mijinta... Maiyasa zanyi rangwamewa azzalumai masu cutar da bayin Allah a doron k’asa.....Hahhhhhahahahahahahahhha!!!!” Muryar ya kuma sakin wani irin dariya.... Ammi da tuni ta soma sakin fitsari ta shiga d’aga kai sama ko zataga mai wannan magana.... Ta ramin k’ofa Aunty B ke lek’enta kana ta kuma saita voice changer na wasan su Ijlaal taci gaba da bud’e murya da taimakon abin tana ci gaba da fad’in “Ina kallonki Farida saidai Ke baki kallo na.... Kuma ‘yar uwarki da kika aminta da ita bata k’aunarki....Cin dunduniyarki take... Ki tambayeta Gata gabanki....” Ammi ta kuma razana ta juyo tana duban Anty Hanne dake faman girgiza kai tana fad’in “Ni... ni... No Farida bazan tab’a cin amanarki ba....!!” Muryar yaci gaba da fad’in “Hahhhajahahaha mugu shi yasan makwancin mugu.... Faridah...!!!!” Ammi jiki na rawa tace “Na...na’am....!!!” Muryar yaci gaba da fad’in “Shin Hanne Ta baki garin magani ki zuba a ko wacce kusurwa ta gidan nan ko bata baki ba....?” Jiki na kyarma ga uban gumi dake keto mata Ammi tace “Anyi haka... Wllhi ta bani...!” Muryar yace “Kuma kinbi ko wata kusurwa kin barbad’a.... Anyi haka ko ba’ayi haka ba...?!!!” Ammi na matuk’ar kyarma tace “Anyi wllhi ta bani kuma na barbad’a....” Muryar yaci gaba da fad’in “Koda ta baki ta sanar dake maganin da zai kori kishiyarki da yaranta ne... Haka ne ko ba haka ba....?!” Cikin sauri Ammi ta jinjina kai tana furta “Haka ne yallab’ai...!” Dan yanzu bata mamakin wannan murya da tafi dangatata da ta mutanen b’oye yasan duk abubuwan da suke shiryawa.... Muryar yaci gaba da fad’in “Toh wannan magani bana korar kishiyarki da yaranta bane kaman yanda ta fad’a miki....!” Gaban Ammi ya bada Dumm!!! Ta waigo sosai tana duban Anty Hanne dake muzurai tana mamakin sharrin da ake k’ulla mata gaban idanunta... Muryar yaci gaba da fad’in “Kinaso kisan amfanin wannan magani...?!!” Murya har na rawa Ammi tace “Eh... Eh Yallab’ai inaso na sani....!!” Muryar ta kuma kecewa da dariya kana tace “Wannan magani da kika barbad’a da hannayenki a ko wacce kusurwa ta gidan nan bata komai bace face ta mutuwar d’anki Khalid...!!!” Ammi ta saki k’ara tana yarfe gumin dake kuma keto mata, lokaci guda Ta duk’a saman gwiwoyinta tana kururwa take fad’in “Kamin rai kada ka kashe min tilon d’ah na na rok’i arzikinka....!!” Muryar ya kece dariya kana yaci gaba da fad’in “Bani zan kashesa ba dan mutuwa da rayuwa bata hannuna kuma kema bata hannunki... Saidai kece zaki zama sanadiyar mutuwar d’anki da kanki... Dan wannan magani da kika barbad’a da zaran d’anki Khalid ya shigo gidan nan zai mutu... Hanne tayi haka ne dan Khalid d’in bai aure d’iyarta Yesmin ba, ta zab’i a kashe Khalid kowa ya rasa tinda ‘yarta bata samu ba... Kinga alhakin mutuwan d’anki na wuyanki....!!!” Muryar ya k’arashe yana mai kuma bankewa da dariya... Hannu bibbiyu Ammi ta dafe kai tana furta “Wayyo na tuba... Wayyo Allah Khalid d’ina... Dan Allah ka taimaka min na fice na cire magungunan nan.... Wayyo ni Farida...!!” Muryar ya kuma kecewa da dariya kana yace “Kema bazaki fita ba balle ki hanasa shigowa...!!” Ya kuma kece dariya... Ammi ta d’aura hannaye aka tana furta “Na shiga uku na lalace ni Farida... Khalid kamin rai kada ka shigo gidan nan....!!!” Ta juya ta kalli Aunty Hanne da mamaki ya kasa sakinta... Ammi tayo kanta tana furta “Kin cuceni Hanne... Kin cuceni... Ki rasa abinda zaki saka min dashi sai hallak’a d’anah dan kawai baison wannan mayyar d’iyar taki.... Wayyo ni Farida wllhi Khalid ya mutu mutuwa zanyi nima.... Hanne kin cuceni kin d’aurani a turban halak’a....!!!” Anty Hanne na kuka take fad’in “Wllhi sharri ne ta ya zan miki hakaFarida, ta ya zan kashe Khalid... Khalid fah d’ah na ne... Wllhi ba maganin kashe Khalid bane....!!!” Inaaa fincika Ammi take tana fad’in “Kar ki matso kusana Hanne... Kin cuceni kin ci amanan zumunci... Wayyo Khalid dan Alla kada ka shigo...!!” Ta zabura ta nufi k’ofa tana jijjigawa da iyaka k’arfinta amma ta kasa koda motsawa abinka da gini mai aminci.... Ammi fah gaba d’aya ta fice hayyacinta... Ita yanzu bata kanta take ba... Ta Khalid d’inta take kada ya shigo wannan gida tinda idan ya shigo toh fah saidai a fidda gawansa.... Ga unguwanni ihunka banza yanayin ginin ma kawai bazai bari aji meke faruwa ba, gashi kowa sabgan gabansa yake.... Aunty B Ta koma gefe ta zauna tana k’ek’ata dariya a hankali, harda hawaye... Daga yanda take zaune tana jiyo Ihun Ammi tana jan Allah ya isa ma ‘yar uwarta Hanne a bisa wannan turba data d’aurata bisa... Sad’af sad’af Aunty Bara’atu ta fice daga gidan ta kulle ta nufi kwalta ta d’auki cab ta tafi asibiti... Sai dariya take cikin mota idan ta tuna yanda Ammi ke rok’on gafara da neman tsira... Tai k’wafa a hankali kana tace “Daga yau kun shiga taitayinku munga su Haule ma...!!” Ta kuma tinstirewa da dariya.... **** Akram ya dubi Hafiz a karo na biyu kana yace “No Hafiz we are leaving this place together, bazan tafi ba tareda kai ba....!” Hafiz ya kuma girgiza kai kana ya mik’awa Akram layar d’aya daga cikin yaron Babba guda d’aya wanda suke amfani da ita su b’ace Wanda suka sata da k’yar cikin aljihun yaran Babban kafin su fice operation.... Hafiz yace “Akram one of us must leave this place... Alive.... And it has to be you....Just go Akram...!!” Akram ya kuma girgiza kai had’ida mik’awa Hafiz layar yace “Hafiz bazan tafi ba tareda kai ba.... Bazan tab’a tafiya na Barka ba....!!!” Ya k’arashe idanunsa na k’ok’arin kawo ruwa had’ida jifar da layar yana mai furta “You know.. I’m not leaving either..! Girgiza kai Hafiz yake yana k’ok’arin maida k’wallan da suka ciko masa idanu kana yace “Akram will you please stop being so stubborn...! karfah ka manta tafiyarka na nufin ceton d’inbin Al’umma ne tinda mun riga munji plan d’insu... Kuma Sawwama da mahaifiyarta zasu linking d’inmu to hideout d’insu na cikin gari... Mai amfanin idan muka zauna dukan biyu muka bari azzaluman mutanen nan suka hallak’a mu.... Kuma hakan na nufin mun barsu suci gaba da fasadi a doron k’asa kenan....Akram you need to get out of this place right now..!!!” Hafiz ya k’arashe cikin murya mai kaushin gaske.... Akram da hawaye ke zubo masa a zuciye yace “Hafiiizzzz!!!!” Hafiz ya jinjina masa kai yana share hawayen da ya gangaro masa kana ya k’araso da sauri suka rungume juna, lokaci guda kuka mai k’arfi ya k’wace masu.... Cikin muryar kuka Hafiz Ke furta “Im sorry Akram I got you into this.... Ka yafe min... Kuma dan Allah idan kaje kacewa Zulfa’u ta yafe min... Ka rok’a min gafara a wajen kowa kaji....!!!” Kuka yaci k’arfin Hafiz.... Akram na hawaye yake furta “I’ll come back for you Hafiz.... Zan dawo na fiddakai in sha Allah kaji....!!” Suka kuma rungume juna kaman kar su rabuda juna... Lokaci guda Hafiz Ke b’anb’are Akram d’in daga jikinsa yana fad’in “Just go... Go now Akram..!!!” Lokaci guda Hafiz ya dank’a layar hannun Akram kana ya juyar da fuskarsa yana hawaye sosai... Shima Akram d’in na hawaye ya juya a guje ya soma gudu.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *104* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Da tsananin mamaki Laila Ke duban Sultan kana tace “Sultan ba wannan ya kawoni ba, sanin kanka ne bama ‘yar wannan wasa nida kai.... So kake kace min da gaske aure Sameer d’in yai....?!” Da gefen idanu Sultan ke dubanta yana bisa kujerarsa mai juyawa ta ganin majinyanta... Ya dad’a k’obarewa yana kuma juyi bisa kujerar kana yace “K’warai kuwa... Aure maiji da lafiya... Yarinya shakaf for your information... Kinga Laila zamanki a nan bazai yuwu ba... Siyama zata iya zuwa asibitin nan any moment tinda bamuyi ga yanda zamu had’u ba, na dai sanar da ita da zaran ta shigo garin ta kirani... So kawai Ki tafi you can’t be seen here...!” Ya k’arashe yana mai had’e tafukan hannayensa biyu waje guda ya saita fingers d’insa saitin bakinsa still yana kuma juyi akan kujerar tamkar wani basarake... Da tsananin mamaki Laila Ke dubansa kana tace “And what about our plans...? Mai kake nufi Sultan...?!” Da tsananin mamaki yake dubanta kana yace “Come on Laila don’t be stupid, ai babu wani pending business da ya rage tsakaninmu... With or without you Siyama bazata tab’a komawa Sameer ba, especially now da yai aure... So Kinga I don’t need you anymore....!” Ya k’arashe yana mai tab’e baki had’ida bud’e hannayensa alamun ko in kula... Tsaye kurum Laila tai tana binsa da kallon mamaki, lokaci guda ta buga kan table d’insa kana tace “K’arya kake Sultan baka isa ba...!!! Kanaso kace dik video d’inku da Siyama da na d’auka a park da kuma cikin da Ta zuban bazai maka amfani bane...? Kai har ka isa kace zaka yadani...? How dare you Sultan....!!!” D’an kuma tab’e baki yai kana yace “Bance fah bazai min amfani ba, yeah for sure zaimin amfani, it will make Sameer even more furious... But what I want to you to understand here is that... Sameer ya riga ya sami madadin Siyama, Ke babu abinda zai dake... Dama a haukarki bayan yasan tare kuke komai da Siyamar maybe ma kece kika zigata ta zubar masa da ciki and all those contraceptions da taita d’irka, Toh mai zai dake... Ke ni fah bari kiji na fad’a miki wllhi ko auren Siyama nai naga k’afarki a gidana ‘yansanda ne zasu rabani dake... So gwarama Ki sani tin yanzu da zaran na auri Siyama toh kun gama k’awance....!” Ya k’arashe with his full confidence yana mai kuma jaddada mata... Laila da hawaye ke k’ok’arin ciko idanunta girgiza kai kurum take tana furta “You’re unbelievable Sultan... I can’t believe you’re doing this to me... How dare you used me...!!!” Ta k’arashe cikin daka tsawa hawaye na gangaro mata.... K’asaitaccen murmushi Sultan yai kana yace “You know Laila... Just get out of my office...!” Ya k’arashe yana mai nuna mata k’ofa daga yanda yake zaune... Laila da tuni hawaye sun wanke mata idanu nunasa da d’an yatsa take lokaci guda take furta “Wllhi k’aryarka tasha k’arya Sultan... Idan har bazan sami Sameer ba Toh kaima bazaka sami Siyama ba... Wllhi sai na sanar da Siyama komai from the very start... Dik kalan abubuwan da muka k’ulla tare wajen ganin mun raba aurensu da Sameer... Wllhi kayi kad’an Kaga downfall d’ina Sultan... Just watch me..!!” Ta k’arashe tana mai kad’a yatsarta saman fuskarsa cikin tsananin huci... Lokaci guda tasa kai zata fice daga office Sultan yai saurin janyota baya, lokaci guda yake dubanta fuska a matuk’ar murtuk’e ya damk’eta sosai ya had’eta jikin gini... Lokaci guda yake furta “Is that a threat...??!” Ya kuma murmusawa a hankali kaman bashine ya murtuk’e fuska ba lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Well sweetheart, If you think you know me...you are quite mistaken... You don’t want to have me as an enemy... So zaifi miki kyau idan kikai abinda nace... Just stay.. away from Siyama... Babu Ke babu ita... End your fake friendship with her... Idan kuma ba haka ba...!” Ya kuma murmusawa kana yace “Then I’ve no choice than to show you my true color...!!” Ya k’arashe yana mai jifa da ita gefe.... Laila ta mik’e da k’yar tana watsa masa mugun kallo... Lokaci guda ta finciki k’ofar ta fice tana mai furta “This is far from over Sultan....!” “Fita munafuka... Get out, I don’t want to see your face ever again...!!” Ya k’arashe yana mai tura k’ofar da k’arfin gaske... Siyama da tuni ta lab’e daga bayan wata k’ofar taugune tai a wajen tana danne kuka mai k’arfi da yazo bakinta.... Banda Innalillahi zuciyarta bata iya ambato komai.... Hannu guda Siyama ta d’aura akanta had’ida toshe bakinta da d’aya hannun dan kar kukan da take ya fito.. Kukan da bata tab’a irinsa ba tsawon rayuwarta... Shin haka duniya ta koma... Cin amana daga mutanen da ka aminta dasu... Laila babbar k’awarta ce haka nan Sultan babban abokin mijinta Sameer ne... Shin ta ya zasu masu wannan cin amana mai girma, ashe duk tsawon shekarun nan basuda burin da ya wuce suga sun rabasu itada Sameer... Dik mugayen shawarwari da Laila ke bata gameda Sameer d’in ashe dan ta rabasu ne ta mallakesa... Ashe Sultan cin dunduniyar Sameer yake ba abokin k’warai bane matarsa yake so.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Shin Maiyasa cin amana ya wanzu tsakankanin al’aumma.... Shin Ta ya zakai haka wa mutanen da suka aminta dakai suka d’auki dukkanin yardarsu suka baka... Shin wannan wace irin zalunci ne mafi muni....!!! Kuka ya kuma zuwa wa Siyama.... Cikin sauri ta mik’e ta sid’ad’e ta fice daga Office d’in gudun kada Sultan ya ganta..... Haka Siyama ta nufi motarta tana kuka sosai kaman ranta zai fita... Bata tab’a data sanin irin abubuwan da taiwa mijinta Sameer irin yau a rayuwarta ba.... Haka ta kifa kanta saman steering wheel tana kuka sosai, kukan da ko ba’ace ba daga cen k’asar zuciyarta yake fitowa... Wane irin kuka ne da zata iya rantsuwa bata tab’a yin irinsa a rayuwarta ba.... Ta rasa kukan mai take guda d’aya, shin kukan cin amanan da Laila tai mata ne...? Ko kuwa kukan rasa Sameer gaba d’aya da take gab da yi ne...? Ko kuwa dai kukan Partner d’inta yayi aure ne...? Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Sameer d’inta fah... No no way munafuncin Sultan ne... Partner bazai tab’a auren wata mace bayanta ba... Sameer nata ne ita kad’ai... Su d’in Partners ne babu yanda za’ai wani mutum na Uku ya shigo between them, idan ma hakan zai kasance toh fah saidai d’ansu... Kuma tinda basuda d’ah su d’in dai Sune partners.... Cikin sauri ta Tashi motar ta fice daga asibitin a guje, dole taje ta gani ma idanunta... Inaaa not her Sameer....!! Wata zuciya tace ‘Toh idan shima auren yai irin yanda Daddynki yaima Ammi fah..? Shin zaki iya yafe masa...?’ Zuciyarta ta kuma tsinkewa... Lokaci guda taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri... Ta shiga girgiza kai ita kad’ai tana mai furta “No... No .... no Sameer bazai min haka ba... We made a promise to each other.... Mu biyu zamu rayu har abada... Sameer is mine alone... He’s mine... He’s mine..!!!” Ta k’arashe sabon kuka na kuma kufce mata had’ida danna wata wawiyar birki sakamakon shigewa da tai bama ta lura da traffic light da ya tsaidata ba... Tai saurin kame kanta da duka hannayenta biyu tana mai rintse idanunta.... Allah ya rufa asiri basui karo da motar dake gabanta ba amma kam tasha surutu wajen mutane... Ita dai bama tabi takansu ba dan tashin hankalin da take ciki yafi k’arfin tinaninsu.... *** A kitchen ya iske Mummy da Raihana suna shirin kwab’a dough na yin chicken bread... hannayensa sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa ya d’an karkace yana dubansu yanda suke gudanar da al’amaransu tamkar d’iya da uwa, gwanin ban sha’awa... Mummy ta mik’o apron ta d’aurawa Raihanah da kanta kana tace “Yauwa d’iyata, toh yanzu kin shigo kitchen... Let’s get started....” Juyowar da Mummy zatai sukai idanu hud’u dashi ya kame daga jikin k’ofa yanata kallonsu.... Mummy ta sakar masa murmushi kana tace “Son shigo mana... Come and join us...!” Ta k’arashe tana mai bud’e drawer had’ida ciro sauran kayan had’in... Raihanah kaw tinda taji Mummy ta ambaci Sameer ta nemi natsuwar da take ciki ta rasa, gaba d’aya sai ta daburce, ga k’irjinta daka bugu da sauri da sauri... K’arasowa yai cikin kitchen d’in har lokacin hannayensa sakale cikin aljihu kana ya nufi Mummynsa yana lek’en abinda take k’ok’arin kwab’awa lokaci guda yake satan kallon Raihanah daketa k’ok’arin zira hannayenta cikin gloves na aikin kitchen.... Mummy ta saci kallonsa taga yanda idanunsa suke... Murmushi ta saki kana ta juyo sosai tana dubansa... Saida ta d’anyi gyaran murya kafin ta soma fad’in “You know Son, I think zaifi kyau idan ka zama malamin yau...!” Tai maganar tana mai zame apron d’in dake d’aure jikinta ta shiga k’ok’arin d’aurawa Sameer d’in... Yayinda Raihanah ta daskare wajen, zuciyarta naci gaba da bugawa... Innalillahi Wai Mummy itada Ya Ma’aruf zata barta... Wai shi zai mata cooking class d’in yau.... Innalillahi Wayyo Allahnta itakam tasan tabbas babu wani abinda zata fahimta yau d’in.... Mummy ta gama d’aura masa har lokacin bai daina satan kallon Raihana da gaba d’aya ta koma sukuku da ita ba... Mummy ta d’an ja chicks d’insa da duka hannayenta biyu kana tace “You behave... I leave you in charge.... Kuma a kular min da d’alibata dan yau d’in ta zama d’alibarka...” Murmushi Sameer yai yana duban Mummy cikeda so da k’aunarta kana yace “But Mummy I hope kin fad’awa d’alibar taki I’ve my own kitchen rules, and one must abide those rules...!” Ya k’arashe yana mai duban Raihanah with a straight face wanda har saida ya d’an sanyata zabura... Ta lab’e a bayan mummy tana lek’ensa a hankali.... Murmushi Mummy tai had’ida jan hancinsa kad’an tace “Na maka alk’awari d’alibata tafi Ta kowa kula....Kuma koda wasa kada ka razana min ita.... Amana na baka...” Wannan karon murmusawa yai kad’an had’ida jinjina mata kai... Mummy ma Ta murmusa kana ta dafa Raihanah kad’an tace “Daughter idan yai miki wani abin Ki kwand’ara min kira kinji zanzo na samesa ne....” Ita dai Raihanah batace komai ba saima sanne kai da take... Mummy ta fice tana kiran mai aikinta Larai.... Kitchen ya rage saura su biyu... Gaba d’aya motsi k’wakk’wara ta kasa, sai k’ok’arin gyara gloves d’in hannunta take... Sameer ya kafeta da idanu murmushi na k’ok’arin kufce masa... Lokaci guda ya d’an sha mur kana yace “Rule number 1: No wearing of gloves in my kitchen....” Ta d’ago da sauri tana dubansa... Gani tai babu alamun wasa a tattare dashi ya had’e fuska sosai... Ta had’iyi miyau da k’yar kana tace cikin sanyin murya “But Mummy tace yana daga cikin tsafta na kitc...” Katseta yai da fad’in “Rule number 2:Dik tsarin da na bayar shi kawai ake amfani da a kitchen d’ina and no but....!” Raihanah ta had’iyi sauran maganan nata had’ida kifa kanta k’asa... Murmusawa yai a hankali kana ya tako kusanta a hankali... K’irjinta sai bugawa yake ganin na kwantowa kusanta sosai... Ta ware idanunta sosai ganin da gaske kusanta yake matsowa... Lokaci guda ta rintse idanunta tana mai karanto dik addu’an da yazo bakinta... Bata ankara ba saijin zuban ruwa tai Daga famfon sink... Nan taga ashe hannayensa yake wankewa kuma daf jikin sink d’in take tsaye dama... Saida har ya gama wankewa kana ya janyo towel ya goge hannayen nasa dashi.... Sauk’e ajiyan zuciya tai had’ida d’an kaucewa kad’an kana ta shiga k’ok’arin d’auko bowl d’in da flour d’in Ke ciki... Amma mai..? Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Rule number3...” Raihanah tai saurin tsayawa cak tana jiran taji rule number 3... K’arasowa yai cikin taku irin nasa kana ya dubi bowl d’in ya dubeta... Hannunsa ya mik’a kaman zai amsa bowl d’in ya d’aura hannayensa saman nata, yana iya jiyo yanda hannayen nata ke rawa sosai... A hankali ya matso da bakinsa saitin kunnenta kana yace “Rule number 3 a cire wannan tsorona d’in a ajiye gefe dan ba asibiti muke ba, kuma ba allura a hannuna....!” Wane irin ajiyan zuciya ta sauk’e still idanunta suna lumshe... Tana jin sanda ya amshi bowl d’in yace ta mik’a masa flour kaman bashine ya gama rad’a mata magana a kunne ba... Cikin ‘yar dabuwrcewa ta mik’a masa flour d’in.... Ya d’ago ya d’an dubeta kad’an sanda zai soma kwab’awa... Ai kafin yai magana Raihana tai saurin cewa “Rule number 4...!” Dariya taso basa ya d’an gimtse kad’an kana yace “Yes rule number 4: student must pay attention and.... she must participate in everything... Oya coma...” Ya k’arashe yana jada baya kad’an had’ida mata alama da idanunsa kan tazo ta tsaya a gabansa... Wani irin bugu k’irjin Raihanah yai.. Innalillahi itakam anya bata yafe classes d’in yau ba... Wayyo Allah ta ina zata tsaya gabansa....Batakaiga samo amsa ba ta sinkayo muryarsa wannan karon a dake yana fad’in “Rule number 5, I don’t repeat myself...!” Cikin sauri ta matso had’ida yin yanda yace, jikinta sai karkarwa yake... Ganin haka yasa Sameer d’an kwanto da kansa daga yanda yake tsaye a bayanta, saitin kunnenta yake rad’a mata “I said rule number 5, I don’t repeat myself... Ko kin mance mai na fad’i maki a rule number 3 ne....?” Cikin ‘yar daburcewa ta shiga jinjina kai tana fad’in “Kace baka son tsoro...!” Murmusawa yai kana yace “Good kin tuna.... Lokaci guda taji hannayensa saman nata bata ankara ba saiji tai ya saka hannayen nasu waje guda suna kwab’in dough d’in... Tana iya jiyo yanda yake murza ‘yan yatsun hannunta a hankali cikin flour d’in... Tai saurin rintse idanunta dan yanayi ne da zatace bata tab’a tsintar kanta ciki ba... Gashi gaba d’aya runfa yai mata daga yanda yake tsaye bayanta... Tamkar ta kurma ihu ko zai k’yaleta haka nan taji... Sarai ta gane wannan dalilin nasa ne yasa ya hanata saka gloves... Gaba d’aya Raihanah ji take tamkar k’afafuwarta zasu gaza d’aukarta badon Allah yasa na tsaye bayanta ba tabbas tasan da k’asa zata zube... A haka aka ida kwab’a fulawar.... Ta saki wani irin ajiyan zuciya a hankali sanda taji ya zame hannayensa... Addu’a take Allah kawo Mummy kitchen d’in tace ta fasa class d’in yau... Kaman daga sama sukaji wayarsa ta soma ringing... Dan wanke hannayensa yai ya goge yana k’ok’arin amsa kiran lokaci guda ya nufi back door daka kitchen d’in.. Nan dabara Ta fad’o mata, kawai gwara ta sad’ad’a ta fice daga kitchen d’in kafin ya ida wayar da yake... Cikin sand’a tamkar wata munafuka ta soma tiptoeing tana d’an lek’en k’ofar da yake tsaye.... Har ta kusan kaiwa k’ofar fita Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Rule number 6: Ba’a fita daga kitchen until we’re done...!” Rintse idanunta kurum tai had’ida tsayawa cak yanda take... Bai kuma bi takanta ba ya koma ga abinda suka baro.... Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Looks like kin mance rule number 4..!” Kaman zata kurma ihu haka ta dawo jiki a sanyaye tamkar wata mai shirin yin kuka... Ya saci kallonta da gefen idanu... Kauda fuskarsa yai had’ida sakin murmushi a hankali... Ta tsaya gefensa sai kuma taga ya matsa baya alamun tazo ta tsaya a wajenta na d’azu... Zatai magana Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Rule number 7: No asking questions..!!” Babu musu ta shige ta tsaya gabansa tana fad’i cikin zuciyarta wane irin karatu ne wannan da za’ace ko tambaya ma bazakai ba... Lallai da haka ake koyan karatu da babu mai iyawa... Bata ida tinanin nata ba ta kuma jin hannayensa saman nata ya janyo ya zubasu saman rolling pin wannan karon... Gently ya shiga murza hannayen nasu dake had’e waje guda saman rolling-pin d’in... Tana jin wasu salo da yake mata wanda gaba d’aya sai ya juya mata tamkar ba Ya Ma’aruf d’in data sani ba... Sosai jikinta Ke rawa jin d’umin numfashinsa saman wuyarta... Ta rintse idanunta sosai kaman wacce zata k’walla ihu... Bata komai cikin zuciyarta face addu’an abinda zai distracting d’insa... Wai fah da gaske Ya Ma’aruf matso da fuskarsa saman nata yake... Innalillahi, ai a d’ari ta janyo bowl mai d’auke da garin flour cikin zuciyarta tana ayyana ai wllhi saidai tai breaking rules d’in nasa... Daidai ta janyo bowl d’in kenan shi kuma ya bud’e idanunsa da suke lumshe, kace zaburanta akai yanda tsoro ya nuna sosai a fuskarta, ta saki bowl d’in had’ida losing step.. Sameer yai saurin tarota Ta dawo jikinsa gaba d’aya flour d’in ya wanke masu jikkunansu.... Daidai sanda Siyama ta nufo kitchen d’in Mummy na biyeda ita tana k’ok’arin dakatar da ita... Turus Siyama ta tsaya tana kallon wannan ikon Allah... Partner d’inta, Sameer d’inta rungume da wata haka, ga wani irin kallon k’auna da yake jifa mata, kai da gani kasan they must be having a good time... Wani irin kuka mai k’arfin gaske Siyama ta saki tana mai k’unshe bakinta da dika hannayenta biyu had’ida girgiza kanta alamun bama ta yarda da abinda take gani ba....Ta juya da sauri tana mai rintse idanunta yayinda Mummy tabi bayanta tana ambato sunanta...Cikin sauri Raihanah ke k’ok’arin cire jikinta daga na Sameer... Bai saketa ba har saida ya mik’ar dasu tsaye sosai kana ya dubeta cikeda kulawa yace “Are you hurt...?” Saurin girgiza masa kai tai alamun a’a kana tace “Lafiya nake Yaya... Just go after Aunty Siyama please kaji...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya tana mai bige flour da ya b’ata mata jiki... Cikin sauri Sameer ya kwab’e apron d’in dake d’aure jikinsa ya nufo parlor yana doka kiran Siyama... Siyama dake kuka sosai rungume Mummy tai tana fad’in “Mummy tell me please abinda na gani ba gaskiya bane... Mummy Sameer bazai tab’a min haka ba... Pls Mummy kice min ba gaskiya bane...!!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Mummy Ke k’ok’arin lallashinta tana fad’in “Siyama just calm down please... Ki saurareni Siyama...” Inaa kuka kawai Siyama keyi kaman ranta zai fita.....Daidai sanda Sameer ya k’araso wajen, a hankali yaceda Mummy taje ta k’yalesa da Siyama... Mummy ta jinjina kai kana ta saki Siyama ta nufi kitchen wajen Raihanah da tsoro da tashin hankali sun gama dabaibayeta dan tuni hawaye sun soma sintiri saman fuskarta... Mummy ta isa ta rungumeta cikeda tausayawa tana lallashinta.... Sameer ya jima yana tsaye wajen yana duban yanda Siyama Ke cazgan kuka mai ban taisayi wanda har saida yaji can k’asar zuciyarsa cewa kaman bai kyauta mata ba, gaba d’aya tausayinta ya dabaibayesa... A hankali ya soma takowa yanda take had’ida rungumarta ta baya... Saidai cikin tsananin kuka ta k’waci jikinta tana fad’in “Don’t come near me... Just don’t touch me....!!How could you Sameer...!! Ta ya zaka min haka...? You are just like my father... You are even worse than him.... All men are the same, all of you are the same...” “Siyamaaaa!!!!” Sameer ya daka mata tsawa da fad’in haka yana mai rik’e duka hannayenta biyu... Bata fasa dukan k’irjinsa tana fad’in ya saketa ba... Sameer kaw fad’i yake “Just listen to me Siyama... Ki saurareni nace...!!!” Fincika tai Daga rik’on da yai mata da k’arfin gaske tana dubansa da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda take furta “Mai zan saurara Sameer... Bayan dik abinda na gani da idanuna.... Partner... Partner... Please tell me, am I that easy to forget about.... Wannan shine alk’awarin da mukai ma juna...?” Ta k’araso gabansa da sauri tana mai tallafo fuskarsa da dika hannayenta biyu take fad’in “Partner, I know I’ve wronged you...I know I’m not perfect... But I love you Sameer... I love you with all my heart and soul... Sameer I’m only human....sab’anin da muka samu baikai ka mance dani ko ka kawo wata cikin rayuwarmu ba... Sameer please look into my eyes and tell me dik abinda na gani ba gaskiya bane... Please kaji... Kaji Partner... Tell me ba gaskiya bane..” Ta shiga jinjina kai tana kuma goge hawayen lokaci guda ta shiga janyo hannunsa tana fad’in “Lets go to house... Nai maka alk’awarin bazan sake barinka ba, and zanyi dik abinda kake so... I’m ready to mend my ways... Pls Partner lets go back like before kaji...!!” Ta k’arashe tana kuma rik’o fuskarsa lokaci guda ta shiga janyo hannunsa tanaci gaba da fad’in su tafi gidansu... Saidai cak taji Sameer d’in ya k’ame ko motsawa baiyi... Ta juyo tana dubansa da watery eyes d’inta... Lokaci guda Sameer d’in ke fad’in “Siyama just listen to me first... Rayuwar da mukai a baya bazamu sake maimaita irinta ba... A lot of things have changed Siyama..” Cikin sauri ta katsesa da fad’in “No no Sameer please kace min ni kad’aice matarka please kaji partner...!!” Ta k’arashe tana kuma tallafo fuskarsa da duka hannayenta biyu... Girgiza mata kai yake lokaci guda yake furta “Ba haka naso sanar dake ba... But yes Siyama a halin yanzu mata biyu Ke gareni ba ke kad’aice matata ba.... This is the truth Siyaam...!” Ya k’arashe yana mai kamo hannayenta... Ji tai duniyar na juya mata... Sameer da bakinsa yake cewa ba ita kad’aice matarsa ba... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Cikin sauri ta shiga jinjina kai dan tama nemi hawayen ta rasa... Lokaci guda ta d’ago tana dubansa cikin tsananin fuci take furta “You know.... I won’t allow this to happen... That girl... Is leaving this house right this moment, she has no place in our lives...!!!” Ta k’arashe tana mai komawa cikin gidan a gigice.... A d’ari Sameer ya take mata baya yana doka mata kira amma inaaa tayi gaba.... Raihanah dake zaune gefen Mummy tayi jigum ganin Siyama ta shigo tamkar wacce jefota ya sanyata mik’ewa zumbur a tsananin tsorace, lokaci guda tai bayan mummy jikinta sai rawa yake.... Mummy ta mik’e babu shiri tana k’ok’arin tare Siyama da tai kan Raihanah gadan gadan tana fad’in “Mummy sai yarinyar nan ta bar gidan nan... Mummy no one can come between us nida Partner... Mummy ki k’yaleni na fiddata...! Ta kuma fincika tana kuma k’ok’arin janyo Raihanah dake tsananin kuka cikeda tsoro.... Dik iya k’ok’arin Sameer wajen ganin ya janye Siyama abu yaci tura... Sai fincika take tana kuma k’ok’arin janyo Raihanah tana fad’in wllhi sai ta bar gidan.... Baiyi niyan marinta ba amma hakan ne kawai zai maidota hayyacinta ganin yanda gab’a d’aya ta fice a giya... Siyama dafe da k’uncinta ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa, cikin rashin yarda da abindake faruwa da ita take furta “Partner... Yau ni ka mara... Sabida kayi aure... Sameer ni ka d’aga hannu ka mara kan wannan kucakar yarinyar da ko a hanya bata isa ta biyo length d’in da nake ba.... Sameer ni ce Siyama fah...?!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Mummy hankali tashe ta shiga tsakankaninsu, rai b’ace take furta “Ya isa haka... Siyama kiyi shiru haka nan... Idan kun dawo hayyacinku sai ku zauna ai magana ta hankali..!” Mummy bata kai aya ba Siyama taci gaba da fad’i cikin muryar kuka... “Mummy Partner ya daina sona... Wllhi yanzu Sameer bai k’aunata... Sultan was right... Babu abinda Sameer zai dani yanzu...Partner kar ka bari burinsu ya cika... Pls Sameer kar ka bari burinsu Sultan ya cika...!” Da tsananin mamaki Sameer ke dubanta kana yace “Sultan...? What are you trying to say Siyama....?!” Ya k’arashe sounding curious.... Lokaci guda Siyama ta kuma d’agowa tana duban Sameer kana tasa hannu ta goge hawayen fuskarta... Lokaci guda Laila da Sultan da dik shirinsu akansu ya shiga dawo mata... A hankali take furta “Partner... I’m sorry... Sameer please forgive me.... Please don’t leave me...!” Mamaki ya kuma cika Sameer ganin yanzu kuma mashi Siyama ke bada hak’uri.... Mummy dai janye hannun Raihanah dake matsan hawaye tai suka nufi upstairs... Sameer ya kuma gyara tsayuwarsa yana duban Siyama kana yace “Ina jinki.... What does Sultan has to do with all of this... What is going on..?!” Ya k’arashe cikin d’an d’aga murya.... Goge fuskarta ta kuma yi tana k’ok’arin saita kanta, lokaci guda take ci gaba da da fad’in “I have something to confess Sameer... But please karkaga laifina... Dik abinda nayi ban tab’a daina sonka ba daidai da rana guda... Kuma sharrin Laila ce da Sultan....” Yanzu kam sosai ya zama confused.... Cikin tsananin nuna b’acin rai yake fad’in “Siyama...Stop beating around the bush, and tell me what exactly is going on..!!!” A hankali tiryan tiryan Ta dinga bashi labarin abubuwan da suka faru har dai yau da asirinsu Sultan da Laila ya tonu taji dik shirinsu akanta... Cikin kuka Ta had’e hannayenta biyu waje guda tana ci gaba da fad’in “Shisa nace kafin Laila ta fad’a maka ni zan sanar dakai... Sameer I’m sorry... I... I was so stupid and naive... I’m sorry for killing your child... Please forgive me...!!!” Ta k’arashe tana k’ok’arin janyo k’afarsa... kauda fuskarsa gefe kurum yai hawaye na gangaro masa... Cikin wata irin murya yake furta “How could you.... How could you Siyama....!!” Lokaci guda ya kaikaito sosai yana dubanta da idanunsa masu zuban hawaye masu matuk’ar zafi.... “After taking all those contraceptions bai maki ba, so har cikina kinje kin cire... Gudan jinina Siyama... Allah kad’ai yasan adadin ‘ya’yan da kika halak’a min Siyama...” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai girgiza kai... Cikin kuka Siyama ke fad’in “Wllhi d’aya ne kawai Partner... Sameer please forgive na tuba bazan sake ba... !” Gani tai ya mik’e daga kujerar da yake zaune bisa lokaci guda yake furta “You know what... Just get out of here Siyama... Get out of my sight... Tashi ki fita I don’t want to see your face, you disgust me....!!” Siyama ta kuma kamo k’afarsa tana fad’in “Partner wllhi na tuba please don’t leave me... Partner wllhi bazan iya rayuwa ba tareda kai ba... Sameer please forgive me na rok’eka... I love you please Partner...!!” Fincikar k’afarsa yai, cikin tsananin huci yake furta “Did you just say you love me...? Kin kaw san mai ake kira so Siyama... After killing my own flesh and blood har kinada bakinda zaki bud’e kice kina sona... Come on, give me break Siyama... You love no one but yourself... Abinda ranki yake so shi kike aiwatarwa komin muninsa...You never loved me Siyama... Idan da ace kinasona da bazaki k’yamaci wani b’angare na jikina da Allah ya ajiye cikin jikinki ba... Just get out Siyama... Get out kafin na miki abinda zamuzo muna regretting daga ni har ke...!!!” Ta kuma yunk’ura zata kamo k’afarsa ya darara mata tsawa da fad’in “I said get the hell out of my sight Siyama..!!!!” Tsawanda saida ya zaburata a gigice tai sama tana doka kiran Mummy danma Allah yasa yau Daddy baya gidan ya d’an samu ya fita sannan washe gari suke shirin zuwa duba jikin Daddyn Siyamar gaba d’aya tinda shi Daddyn Sameer d’in ya d’an sami k’arfi.... Babu shiri Mummy ta nufo downstairs jin irin kukan da Siyama keyi... Tai saurin kamo Mummy tana fad’in “Mummy please Ki bashi hak’uri... Mummy kice kar ya rabu da ni dan Allah... Wllhi ina sonshi dan Allah Mummy...!” Gaba d’aya ta ma birki ta Hajja Fatahiyya... Mummy fad’I take “Sameer mai kuma ya faru....?” Ko zarafin amsa Mummy bai samu ba saima k’arasawa da yai ya shiga janyo hannun Siyama da iyaka k’arfinsa yana fad’in “Just get out... Zo ki fita nace, I don’t want to see your face...!!” Haka ya dinga janyo Siyama tana dogewa tana rok’on Mummy Ta mar magana... Dik kiran duniya da Mummy ke masa ya taya yai mata bayanin meke faruwa inaa har saida ya fitar da Siyama zuwa harabar gidan... Lokaci guda ya juya ya komo cikin gidan ya barta nan yashe tana kuka tana ambato sunansa.... A k’ofa suka had’uda Mummy hankalinta dik a tashe... “Ina Siyamar...?” Ta tambaya tana dubansa.... Hawayenda yake k’ok’arin dannewa yaji suna zuwa idanuna lokaci guda yake furta “Mummy what if wannan d’an shi kad’ai Allah ya hukunta zan samu... Mummy why..? Maiyasa Siyama zata cireshi... Maiyasa zata hanani ganin gudan jinina... Mummy all I did was to love her.... Abinda zata sakamin dashi kenan....!! Mummy ke shaidace irin soyayyar da naiwa Siyama only to get this in return... Mummy I thought she loved me... I was wrong... Siyama kanta kawai take so.. She doesn’t care about other people’s feelings...She’s so selfish..!” Raihanah dake mak’ale jikin staircase hawaye suka kuma gangaro mata, lokaci guda Ta juya Ta koma d’aki had’ida kifa kanta tana kuka mai tsuma zuciya... Cikin sauri Mummy ta k’arasa ta shiga janyo hannunsa har ta zaunarsa saman kujera... A hankali Mummy Ke fad’in “Sameer kai hak’uri... Haka Allah ya hukunta wannan cikin baza’a haifosa ba... Siyama dai ta zama sanadin fitarsa ne amma ko bata cire ba bazai wuce k’addararsa ba kaji Son... Kai hak’uri ka yafewa Siyama, naji dik abinda kuka tattauna kuma a yanda na kula Siyama zigan muguwar k’awa tabi wacce bata nufinta da komai face sharri... Akwai irin wad’Annan mugayen abokai wanda su a kullum suga ka taggayara d’an rufin asirin da Allah yai maka da ni’imar da yai maka suga ka rasa just like your friend Sultan....” Wannan karon d’agowa yai yana duban Mummyn, kafin ta jinjina kai tana mai ci gaba da fad’in “Naji komai Sameer... Kuma na yarda Sultan minafikinka ne dan haka kawai Siyama bazata k’ago labari ta fad’i ba, kai kanka shaida ne Siyama nada wasu hali nata na sangarta amma bazata tab’a maka k’arya ba... Kuma tana k’aunarka Sameer, kawai dai rashin sa’a akai ta girma babu kwab’a amma Siyama yarinyar kirkice kai kanka ka sani tinda tare kuka taso...” Shidai Sameer shiru kurum yai ba tareda ya furtawa Mummy komai ba, ta kuma numfasawa kana tace “Girman kenan Sameer dole sai ana kai zuciya nesa especially now da ka zama family man... Nasan Siyama Ta maka abubuwa da dama but na yarda yanzu ta gane kurenta kuma she’s ready to mend her ways... Sameer my son please kar kayi hukunci cikin fushi.. Ka natsu kai tinani kaji... Ubangiji ya maka Albarka ya shiga lamuranka... Bara naje na Duba kitchen d’in... “ Har mummy ta tashi bai iya cewa komai ba sai k’ura ma waje guda idanu da yai dan har wannan lokaci zuciyarsa bai daina suya ba... *** Siyama kaw tana ficewa gidansu da Sameer ta nufa... Ko ina yayi k’ura tsaban an jima babu kowa ciki.... Tai tsaye a parlor jikin madubin console, lokaci guda tasa hannu Ta d’auki hoton nasu dake cikin k’aramar frame.... K’uri taima hoton tana tina rayuwarsu na baya... Wasu hawayen suka kuma gangaro mata... Cikin parlorn ta k’araso ta zauna tana tina wasu moments masu dad’i da suka kasance cikinsu a gidan nasu.... Shin ta ya ma zata iya ci gaba da rayuwa ba tareda Sameer ba.... Haka ta tak’ure saman kujera rungume da hoton nasu dikda yunwa dake azalzalan cikinta, tana kallo Sultan na kiran wayarta wani sabon kuka ya kuma kufce mata.... *** Iyaka Laushi da galabaita su Ammi Sun gama yi, ga yunwa ga zafin store ga tsananin tashin hankalinda Ammi ke ciki... Sai wajajen la’asar su Khalid da Nabilah suka soma dawowa gidan dan rashin ganin Ammi a asibiti ya d’a damesa gashi bata d’aga wayarta, dikda cewa yayi tinanin ko har yanzu fushin ne take dashi amma dai yanaji can k’asar zuciyarsa kaman babu lafia..... Wani abinda ya kuma saka su Ammi a uku shine yau ranan chanjin securities masu tsaron gate ne, wanda ya kwana ya riga ya tafi kuma wanda zai chanji aikin yau bai iso ba wannan dalili yasa babu kowa a gate balle aji kururuwarsu.... Ammi dake zaune gefen buhun shinkafa tana jin k’arar tsayuwar mota ta tashi da k’yar ta nufi window tana ihu... Ganin motar Khalid ya kuma sanyata sakin wani sabon k’ara tana fad’in kada ya shigo... Khalid da Nabila da tuni sun soma jiyo tamkar kururuwa duban juna sukai kana suka fito daga motar babu shiri.... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _...............DA RABO_ *105* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Babu shiri suka nufi yanda suke sauraro muryan... Ta window store d’in kitchen suke hangen Ammi da tai sharkaf da zufa, dan tashin hankali ko d’ankwali babu akanta... Da iyaka k’arfinta take fad’in “Khalid kamin rai kada ka shigo cikin gidan nan, na rok’i arzikinka ka fice kada ka shigo..!!!” Khalid da mamaki ya cikasa, duban juna sukai shida Nabilah kana ya d’an soma takowa kad’an cikeda tashin hankali... Kafin ma ya sami zarafin maganan Ammi ta kuma doka wani uban ihun tana fad’in “Nace kar ka shigo.. Kada ka shigo Khalid... Ka koma nace.... Kamin rai ka fice daga gidan nan... Nabilah Ki ceceni ki fitar dashi daga gidan nan... Kada ki barshi ya shigo na rok’i arzikinki..!!!” Yanzu kam ba mamaki kawai abin Ke basu ba harda tsoro.... Nabilah tai saurin rik’o hannun Khalid dake k’ok’arin kuma kutsa kai cikin gidan yana fad’in “Ammi Wai meke faruwa ne... Meke faruwa cikin gidan... Ki barni na shigo na fiddaki Ammi na...!” Cikin tsananin tashin hankali yake maganan... Ammi na kuka take fad’in “Khalid my son ka yafeni... Kamin rai kada ka shigo cikin gidan nan....!!!” Girgiza kai kurum yake, cikin tsananin tashin hankali yake fad’in “Ammi I’m sorry... Bazan iya tsayuwa a nan ina gani kina cikin tashin hankali na k’yaleki ba... Zan shigo na fiddaki... Koma menene cikin gidan saidai ya sameni amma dole na shigo na fiddake....!!!” Ya kuma nufan k’ofa cikin sassarfa... Hannu biyu Ammi ta d’ora aka tana ihu tana fad’in “Nabilah..!!! Nabila kada Ki barshi ya shigo... Idan kinama Allah ki hanasa... Idan kina k’aunarsa Ki hanasa.. Wayyo ni Farida... Nabilah Ki ceceni kada ki barsa ya shiga..!!!” A d’ari Nabilah da jikinta Ke tsananin rawa ganin irin wannan tashin hankali ta k’arasa tasha gaban Khalid tana kuka sosai take fad’in “Please just don’t enter tinda tace haka... Kabi umarninta please..!” Tai maganan tana had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o... Cikin tsananin huci yake fad’in “Kin ko san mai kike fad’a Nabeela... Mahaifiyatace fah a ciki... Kuma ga dikkan alamu taimako take nema, tsananin soyayyar da take min yasa take cewa kada na shiga dan kar abindake cutar da ita cikin gidan ya cutar dani... Who knows meke faruwa cikin gidan..! I’m sorry Nabilah but I can’t just sit back and do nothing... My Mother needs me..!!!” Ya k’arashe yana k’ok’arin kaucarda Nabilah gefe.... Ammi ta kuma d’aura hannunta aka tana sabon ihu... Cikin sauri Nabilah ta kuma shan gabansa tana kuka take fad’in “Ni zan shiga, you stay right here kaji... Ni zan shiga naga meke faruwa...!!” Cikin rashin yarda yake girgiza kansa kana yace “Are you kidding me teddy bear...? Ta ya zan barki ki shiga cikin had’ari... Kema kinsan ko mafarki kike hakan bamai yuwa bane... Just stay right here kinji koh...!!” Janyosa Nabila ta kuma yi tana kuka sosai take fad’in “Bakajin mai Ammi ke cewa ne... Dan Allah ka k’yaleni ni na shiga....!!!” Wani irin tsawa ya daka mata da fad’in “Nabeeeelaa!!!! Just get out of my way...” Bata matsa ba bata daina kuka ba... Ammi daga window tana hangosu tana kuka... Lokaci guda taceda Khalid... “Khalid kafin ka shigo gidan inaso kazo na fad’a maka wani abu... ka k’araso nan d’ah nah....!!” Juyawa yai yana duban Ammi daga yanda take ta ramin window... Girgiza kai kurum yai kana ya nufi kiran Ammi... Nabilah kaw yana shigewa ta arce a guje ta shige cikin gidan had’ida maida k’ofa ta rife kif... A kid’ime Khalid ya waigo ya nufo k’ofar yana doka mata kira inaaa ko saurarensa batai ba ta nufi kitchen wajen su Ammi.. Dik jijjiga k’ofa da kiran Nabilah da Khalid keyi bata sauraresa ba... Kai tsaye store d’in kitchen ta nufa ta bud’e su Ammi jikinta har lokacin rawa yake.... Ammi na hangota Ta k’araso a guje ta rungumeta tana kuka sosai take fad’in “Na gode... Na gode miki Nabila... Thank you for saving my son... Thank you Nabilah... Bazan tab’a iya biyanki ladan abinda kika min ba....!!!” Ta k’arashe cikin kuka sosai tana mai kuma kifa kai cikin jikin Nabilar... Nabila dai gaba d’aya wane irin sanyi jikinta yai da ganin irin wannan bak’on al’amari daga wajen Ammi... Cikin sauri kuma Ammin ta mik’e tana fad’in “Maganin... Maganin... Muje mu share kafin ya shigo... Muje muje...!” Ta shiga janyo hannun Nabila tana tambayar yanda tsintsiya da sandar mop yake... Babu shiri Nabilah ta isa ta d’auko tsintsinya da sandar mop... Dik wani lungu da sak’o da Ammi ta barbad’a maganin nan saida suka share tsaf suka goge, Ammi harda bulbula ruwan hypo sosai dan tabbatar da ko burbud’in maganin bazai zauna ba.... Aunty Hanne ce ta fito fuska sharkaf hawaye cikeda borin kunya tazo zata wuce, Ammi ta d’aga mata k’eya tana fad’in “Allah shiga tsakanin na gari da mugu... Nidai daga yau na tuba kema Allah sa ki gane ki tuba Hanne...!” Aunty Hanne dai mayafi a hannu ta fice jiki a matuk’ar sanyaye... Ita dai Nabilah sai kallon wannan ikon Allah take... Abu saikace wani a film... A k’ofar fita ta tadda Khalid wanda ke faman bugu Nabila ta bud’e masa... Tsaye yai yana duban Aunty Hanne cikeda mamaki saikace kazar da aka tsamo cikin ruwan zafi, tafiya ma da k’yar take ga zufa sharkaf jikinta... Cikin muryar kuka Aunty Hanne ke duban Khalid d’in kana tace “Saifullahi wallhi bazan iya kasheka ba kai kasan haka ai...!” Da tsananin mamaki Khalid ke subanta kana yace “Kisa kuma Aunty..?” Aunty Hanne na matsan hawaye ta shigesa ko zarafin amsa masa bata samu ba... Khalid ya d’an take mata baya yana kiranta amma inaa ko tsayawa Aunty Hanne batai ba saima Ammi data fito tagajan magajan tana fad’in “Kada ka bita... Ka dawo nan Khalid... K’yaleta Ta tafi kafin tai maka wani mugun abin... Aniyarki Ta biki Hanne... Wllhi idan Khalid ya rasa mata babu abinda zai da d’iyarki... A sauk’a lafiya...!” Ta k’arashe tana tafe hannaye... Da tsananin mamaki Khalid ya waigo yana duban mahaifiyarsa, lokaci guda Ammi ta k’araso gareshi a guje ta shiga Shafa jikinsa tana fad’in “Babu abinda ya sameka dai koh....!!” Khalid da mamaki ya kasa sakinsa girgiza kai kurum yake cikeda rashin yarda kana yace “Wai Ammi Wai meke faruwa ne... What’s all this....??” Kasa magana Ammi tai sai rungumesa da tai hawaye na gangaro mata... Lokaci guda take furta “Khalid ka yafe ni... Ka yafe min d’ah nah..” Ta k’arasa ta janyo Nabilah ta had’esu duka biyu ta rungume tana fad’in su yafeta... Gabaki d’aya taananin mamaki ne ya cikasu.... Ammi na tsakiyarsu rungume dasu suka nufi cikin gidan, Nabilah da Khalid basu daina duban juna ba suna duban Ammi cikeda mamaki... Shigarsu gidan da kad’an su Aunty Daula dasu Aunty Bara’atu suka dawo.... Har lokacin Ammi hawaye take tana neman gafaran su Khalid.... Su Khalid basu ida shan mamaki ba saida sukaga Ammi ta nufi gaban Aunty Daula da k’irjinta ke tsananin bugu, ga mamakin Aunty Daula hannayenta Ammi ta kamo tana hawaye sosai take fad’in “Ki yafeni... Ki yafeni Daula... Nayi niyyar maki mugunta sai reshe ya tashi juyawa da mujiya... Na gina miki ramin mugunta keda ‘ya’yanki sai na tashi afkawa ciki nida nawa d’an.... Da ace yau na rasa Khalid tabbas da nima halak’a zanyi... Daula ki yafeni, wllhi na yarda abinda shuka a duniya shi zaka girba...” Take Ammi ta labarta masu dik abinda ya faru babu abu guda k’wakk’wara data b’oye masu... Yesmin dake kallon wannan tashin hankali wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi... Aunty Daula ma kukan take had’ida kamo Ammi dake k’ok’arin duk’awa ta hanata k’arasawa...... Lokaci guda suka rungume juna suna hawaye sosai... Aunty Daula fad’i take “Ki daina bani hak’uri Ammi kema tabbas ba’a kyauta maki ba... Amma tuni Allah ya hukunta hakan... Ni baki min komai ba wllhi kuma nafi kowa jin dad’i da Allah ya k’addari kika fahimci hakan... Ubangiji ya yafe mu gaba d’aya ya kuma tashi kafad’un mijinmu..!” Allah sarki duk wanda zaice bai kuka ba a parlorn nan sai wanda baida zuciya cikin k’irjinsa... Gaba d’aya baka jin komai sai sautin fitan kuka a hankali, harta Aunty Bara’atu saida k’walla ya zubo mata had’ida tausayin Ammi... Kai harta Kubura da Karimatu dake lab’e Daga k’ofar kitchen saida sukai hawaye... Allah sarki babu abinda yafi zaman lafiya yafiya da yad’a soyayya sama da k’iyayya dad’i a duniya... Hak’ik’a wane irin sanyi da aminci ne ya sauk’a a wannan ahali had’ida sakeenaah.... Aunty B ta k’araso ta kamo hannun Ammi da na Aunty Daula tana hawaye itama kana tace “Alhamdulillah...! Mijinku zaifi kowa Farin ciki idan yau ya tashi ya wayi gari ya ganku haka... Yau Allah ya cika masa burinsa...!” Ta juyo tana duban Aunty Daula sosai kana tace “Daula banida haufi akan zakiyima abokiyar zamanki biyayya a matsayinta na wacce ke gaba dake a haife da kuma a zamantakewar aurenku...” Cikin sauri Aunty Daula ke jinjina kai tana hawaye alamun tabbas hakane... Aunty B Ta maida dubantaga Ammi kana taci gaba da fad’in “Toh nima dai zan rok’i yafiyarki Ammi... Amma kafin nan inaso na sanar dake zuciyata taji wasai sanin cewa abokiyar zaman ‘yaruwata ta fahimci gaskiya kuma ta gane cewa Allah shikeda cikakken iko akan komai ba boka ko Malami ba... Allah shike k’addarawa kuma shike badawa ya kuma hana ga wanda yaso... Boka ko Malami basu isa suyi maka abinda Allah bai maka ba.. Basu isa su hana faruwan abinda Allah ya riga ya hukunta ba...” Ammi na hawaye take jinjina kai tana fad’in “Wannan haka ne Bara’atu.. Wllhi na yarda kuma na tuba tuba na gaskiya..!” Aunty B tace “Alhamdulillahi... Tinda kin fahimci haka... Yanzu zan sanar daku dik yanda abin ya faru...!” Gaba d’aya sukai jigum suna duban Aunty B had’ida saurarenta.... Nan Aunty Bara’atu ta labarta masu dik yanda abin ya kasance... Sukaita al’ajabi wannan hikima irin na Aunty B da hangen nesanta... Lallai ita d’in ta cika jajirtacciya wacce takai a yaba mata... Cikin salama ta wargaza mugun nufin su Ammi kuma tayi k’ok’arin karkatoda hankalinsu da tinaninsu zuwaga fuskantar gaskiya da kuma k’auracewa sab’o... Kubura da shashashanci daga yanda take tsaye ta k’yak’yace da dariya tana fad’in Inama tana wajen.... Ganin kowa yaimata zuru yana dubanta ya sanyata had’iye sauran dariyarta had’ida kame bakinta da duka hannayenta biyu saidai ita kanta Ammin dariya sosai abin ya bata musamman data tina yanda take rok’on gafara... Shiko Khalid d’an darawa yai kad’an kana yace “Aiko da na shigo kin rasani gaba d’aya kin huta...” Ammi ta janyo hannun Nabilah tana fad’in “Toh ai ga savior d’inka kana tafe tareda ita, yanzu na yarda na tabbata banida matsala indai wannan heroin d’in tana tareda kai....!” Ta k’arashe tana mai rungumo Nabilah dake sanne kai had’ida k’unshe dariyarta cikin jikinta.... Gaba d’aya wannan karon d’an darawa sukai kana Ammi taci gaba da fad’in su Khalid da Nabila su yafeta kuma in sha Allahu bazata sake zama matsalaga rayuwar aurensu ba... Su Kubura babu kai nan ta had’e hannayenta biyu waje guda ta shiga tafawa ita dole nuna murnanta take Ammi zata k’yale Khalid yai rayuwarsa da matarsa cikin salama, dan ita ko bata samesa ba ta gwammaci ta gansa yana rayuwa cikin Farin ciki... Yesmin kaw jikin a sanyaye ta k’araso ta duk’a gabansu tana hawaye sosai, lokaci guda take rok’on Khalid da Nabilah gafara.... Hannayenta biyu had’e waje guda take ci gaba da fad’in “Ya Khalid dan Allah ku yafe min, ku yafe min dik abubuwan da nai maku... Especially you Nabila... Dan Allah ku yafe min, na yarda Allah shike jefa soyayya cikin zukatan mutane... Na yarda haka Allah yaso ya gina soyayyar junanku cikin zukatanku... Ku yafe min katsalandan da naitayi ma rayuwarku da tak’ura maku da k’ok’arin raba tsakaninku... Dan Allah ku yafe min...!” Nabilah ta janyo hannayen Yesmin tace “Ban tab’a rik’eki ba cikin zuciyata Yesmin... Allah ya yafemu gaba d’aya... Nima ki yafe min wasu abubuwan da nai maki...” lokaci guda Yesmin ta rungume Nabila tana hawaye sosai... Yesmin ta d’ago tana duban Khalid, kafin tai maganan Khalid ya girgiza mata kai kana yace “Is ok Yesmin... Ki sani ni ban tsaneki ba kuma inasonki a matsayinki na k’anwata, wannan soyayyarce a tsakaninmu bata aure ba kinji koh... Kuma inaso kisa ma ranki cewa kinfi k’arfin wulak’ancin ko wanne d’ah namiji... You’re beautiful, you’re strong and you’ve your love ones beside you... So never allow someone to look down on you kinji koh... Kar ki tab’a bada k’ofa ma wani namiji ya rainaki... Da sannu zaki samu wanda zai maki irin k’aunan da kika cancanci a nuna miki....” Yesmin na murmushi hawaye na kuma gangaro mata take furta “Na gode Ya Khalid... Thank you so much...!” Gaba d’aya annuri ne ya cika fuskokinsu, Yesmin ta isa ga Ammi suka rungume juna, lokaci guda take fad’in zataje ta duba Mummynta sannan ta tabbata itama ta tuba ta dena biye biyen malaman tsubbun da take, dan tana fata wannan abu da ya faru ya zama idan da wa’azi a gareta itama.... Farin ciki ya wanzu, rahamar umabgiji ya lullub’esu... Zukata sun cika da salama, saidai Allah son Barka da fatan Allah ya baiwa Daddy lafiya ya fuskanci wannan ahali nashi mai cikeda aminci.... Koda su Ijlaal suka dawo daga sch haka Aunty Daula taita introducing d’insu ma Ammi, Ammi na rungumarsu, Allah sarki mai za’ai da k’iyayya da gaba... Allah ka wadatamu da soyayya sadaukarwa da kuma yafiya.... Aunty Daula tsaye tai Daga k’ofa tana hangen su Humaira da Ijlaal yanda suke tsalle jikin Ammi suna zuba mata surutu a dole labari suke bata... Aunty Bara’atu tai k’uri ma ‘yar uwar tata murmushi kwance saman fuskarta... Lokaci guda Aunty Daula ta waigo tana duban Aunty B d’in... A hankali ta tako gareta had’ida rungumeta... Lokaci guda take furta “Shin mai zanyi ba taredake ba ‘yaruwata....? Ban san da kalaman da zanyi amfani dasu wajen nuna miki godiyata ba Aunty Bara’atu... Da ace ‘yanuwa zasu zama irinki tabbas da duniyarmu Ta cika da alkhairi....” Cikin tsananin rawar murya taci gaba da furta “Thank you so much... ‘Yaruwata.... Thank you for uniting my family...!!” Cikin sauri Aunty B ta rungumeta tana mai furta “Kukan nan ya isa haka Daula... Hakan shi ya kamata ‘yan uwa suyi... Family d’inki nawa ne... Idan ya falling apart tamkar nawa ne yai haka idan ya dunk’ule waje guda tamkar nawa ne ya dunk’ule waje guda... Allah ya had’e kan dik wani family da suke fuskantar barazanar tarwatsewa waje guda....!” Suka kuma rungumar juna... Khalid ne ya hauro upstairs da sauri yana fad’in ina suke...Gaba d’aya su Ammi su Aunty Daula suka nufosa suna tambayar lafiya ko wane abin ne ya sami Daddy... Murmushi ya kasa Barin fuskar Khalid lokaci guda yake sanar dasu “Ammi.. Aunty... Daddy regained consciousness, he’s out of coma, Alhamdulillah...!!” Ya k’arashe yana rungumar mahaifiyarsa cikeda Farin ciki... Haba nan fah aka shiga hamdala da gode ma Allah... Wani sabon Farin ciki ya riskesu... Ammi tace “Ai sai mu tattara mu d’unguma mu tafi asibitin gaba d’aya... Hakan kaw akai suka d’unguma k’wansu da k’wark’watansu dan hardasu Ijlaal yau suka nufi asibtin, Siyama ce dake Kaduna kawai bata a wajen.... Idan Kaga wannan ahali dole kaima kai masu farin ciki.... Yau d’in rana ce ta musamman a garesu.... Khalid shi ya soma shiga d’akin Daddy yanda ya hangi Daddyn kwance bisa gadon sa ta jinya, wannan karon an rage yawan na’uran da suke taimaka ma lafiyar nasa.... Cikin murya irinta majinyata Daddy ke furta “Khaleed... My son, come here...!” Ya k’arashe yana k’ok’arin d’ago hannun nasa yana mik’ama Khalid.... Khalid da hawaye suka wanke masa fuska da ganin Daddy yau ya bud’e idanu na magana har na ambato sunansa... Abu ne da yai zaton shikenan bazai sake gani ko ji daga Daddyn nasa ba... Lallai Ubangijinsa ya cika abin godiya.... Cikin sauri Khalid ya isa ya damk’e hannun Daddy, yana hawaye sosai yake furta “Daddy... Daddy ka tashi.... I thought I was going to lose you Daddy..!!” Ya k’arashe yana mai kifa kansa gefe kafad’a Daddy da babu bandage.... Daddy ya d’ago d’aya hannun nasa da k’yar maras cannula kana ya dafa kan Khalid kad’an yace “Khalid I’m sorry... Na Barka da abubuwan da bazaka iya warwarewa ba... Na barkada d’awainiyar da ba taka ba.... Khalid d’ah na ka yafe min kaji.... Na sani it wasn’t easy for you... Ni yafi cancanta na had’e kan iyalaina ba kaiba... Ka yafe min kaji d’ah na.. Kai d’in ka cika d’ah na gari kuma mai biyayya....” Cikin sauri Khalid ya d’ago kansa yana duban Daddy da idanunsa masu zuban hawaye, lokaci guda yake furta “No Daddy.... Babu abinda kayi... Wannan hukuncin Ubangiji ne shi ya k’addari hakan.... Fatanmu shine Allah ya k’ara maka lafiya...” lokaci guda Khalid Ke murmushi kana yaci gaba da fad’in “Daddy yau inada babban Albishir a gareka....” Lokaci guda Khalid ya mik’e ya isa ya bud’e k’ofar... Yayinda Daddy yai k’uri yana kallon masu shigowa.... Wani irin zabura yai kaman zai mik’e daga saman gadon ganin masu shigowar... Khalid yai saurin k’arasawa ya rik’esa yana fad’in ya kwantar da hankalinsa.... Ga tsananin mamakin Daddy murmushi ya gani saman fuskokin Matansa guda biyu Farida da Daula... Yai saurin d’ago kai yana duban Khalid kana yace “Shin abinda nake gani gaskiya ne Khalid..?” Khalid ya jinjina masa kai a hankali kana yace “Gaskiya ne Daddy... Abinda kake gani haka ne...!” A hankali Daddy ya lumshe idanunsa siriryar hawaye ta gangaro masa...A hankali ya ware idanun nasa yana mai furta hamdala ga Ubangijin rahama a bayyane.... Ya juya b’angaren dama yaga Ammi na sakar masa murmushi hannayenta saman nasa hannun dake wannan b’angaren siririyar hawaye bisa fuskarta itama, ya kuma juyowa b’angaren hagu nan ma Aunty Daula ce tayi yanda Ammi tai... Kafin yai magana Ammi tace “Daddyn Siyama kai shiru haka nan you’re still weak..!” Aunty Daula ta jinjina kai tace “Haka ne Dr yace banda yawan magana...” Ya kuma kallonsu duka biyu yana murmushi shi kad’ai yasan kalan farin cikin da yake ciki... Suna a haka Khalid ya kuma shigowa d’aukeda Ijlaal a kafad’arsa hannunsa guda kuma rik’eda Humaira nan suka shigo suka gaida mahaifin nasu suna fad’in irin kewarsa da sukai... Daga nan su Nabilah dasu Aunty Bara’atu ma dik suka shigo suka gaida Daddy... Wayar Siyama ne dai Khalid bai samu ba gashi ya d’anja sosai balle ya kira Sameer ya sanar dashi dan dikda baida tabbacin Siyamar Kadunan Ta tafi yasan babu yanda zatace face wajen Sameer d’in a irin wannan yanayi na tashin hankali da suke fuskanta... Ammi ce ta sanar dashi sunyi waya da Hajiya Fatahiyya ta sanar da ita Siyamar na Kaduna... Hakan yasa hankulansu kwanciya.... *** KADUNA Washe gari da k’yar Siyama ta farka dan daren jiya ba wani baccin kirki Ta samu ba bayan ta ida sallan asuba ne ma bacci b’arawo yai gaba da ita, K’uri tai ma gefen gadon wajen kwanciyar Sameer tana ganin kaman zata ganshi kwance wajen... Ta lumshe idanunta a hankali wasu hawayen suka ziraro mata....K’ila ma yana can tareda ita, tinanin da yazo zuciyarta kenan... Kuka mai k’arfi ya kuma kufcewa Siyama, sosai Ta rungume pillow tana kuka mai tab’a zuciya... Ko takan wayarta batabi ba har wannan lokaci, dan gani take Tamkar Sultan ne mai kiran nata... Bathroom ta fad’a tai wanka nan d’akin Sameer d’in komai na buk’ata akwai, bathrobe d’insa tai amfani da, ta jima tana shak’an k’amshin shower jell d’insa da tai amfani da... Lokaci guda ta nufi closet d’insa ta shiga bin kayansa da kallo lokaci guda take shafasu d’aya bayan d’aya... Siyama ta kuma sa hannu tana goge hawayen dake kuma gangaro mata... Taita tina rayuwarsu na baya a cikin gidan... Da k’yar ta tafi nata d’akin ta shirya... Koda ta fito parlor duban dining area tai sai tana ganin kaman zata hangosa ya fito daga kitchen yana fad’in ‘Partner breakfast’s ready...’ Ta saki murmushi a hankali,Sameer ita ya kamata ta tabbata yaci abinci kafin ya fice wajen aiki amma a b’angarenta ba haka bane Shine yake tabbatarwa taci abinci kafin ta fice aiki... Sameer wane irin miji ne da tayi imani samun irinsa a wannan zamani yakeda matuk’ar wahala... Ta kuma share hawayen da suka gangaro mata... Jiki a sanyaye Ta nufi kitchen dan nema ma kanta abinda zata saka a cikinta... ** Yana cikin d’aura agogo Raihanah Ta shigo sallama saman bakinta, sanye yake cikin jampa ruwan k’asa da yai matuk’ar amsarsa...Ganin yanayinsa ya kuma sanyaya mata gwiwa... Kanta a k’asa ta gaidashi, ya amsa idanunsa naga abinda yake.... A hankali take furta “Mummy ce tace na dubaka ko lafia taga baka fito ba...” Shiru na d’an lokaci har kaman bazai amsa ba sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Daddy ya fito...?” Jinjina masa kai tai alamun eh... Sameer ya jinjina kansa ba tareda cewa komai ba yana mai brushing sumarsa gaban dressing mirror, ya mik’a hannunsa yana k’ok’arin d’aukan hularsa dake saman drawer a wajen, nan hular ta subce ta fad’i k’asa, baikaiga d’aukowa ba ya hangeta Ta duk’a ta d’auko masa, kanta a k’asa take mik’a masa, bai amsa ba saima k’ura mata idanu da yai yana karantarta... ya kula yau d’in mood d’inta a b’ace yake.... hannayensa biyu yasa ya tallafo fuskarta had’ida k’ura mata idanu... Cikin sassanyar murya yake furta “Hey...What’s wrong... Did something happen...?” Ya tambaya yana tallafe da fuskar nata.. Ganin Ta kasa magana saima hawaye dake k’ok’arin gangaro mata ya sanyashi saurin kamo hannunta suka zauna saman kujera... Hannayenta ya kamo cikin nasa had’ida k’ura mata idanu... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *106* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Kasa magana tai, ta kasa amsasa sai hawaye dake ziraro mata, batasan ta ya zata soma fad’in abindake damunta ba, shin ta ya ma zata soma ce masa ga dalilin kukanta...? Batasan soyayya ba dan bata tab’a yi ba amma ko shakka babu ta kasa cire damuwar abinda ya faru jiya tsakanin ya Ma’aruf da Aunty Siyama... Ta rasa mai take ji cikin zuciyarta, shin tausayin Ya Ma’aruf take ko kaw tausayin Aunty Siyama take..? Shin Kodai tausayin kanta take..? Ko tsoron fuskantar k’alubalen dake gabanta take...? Tambayoyi ne da dama cikin zuciyarta da batasan ta ya zata iya amsama kanta su ba, yanayi ne cikin zuciyarta da batasan ta ya zata fasalta yanda takeji ba... Hannayensa taji saman fuskarta ya tallafo fuskar nata... Bai kuma tambayarta ba wannan karon sai saka hannunsa guda da yai ya soma share mata hawayen... Jin hannunsa saman fuskarta ya kuma sanyata sakin kuka a hankali... Janyota cikin jikinsa yai wannan karon yana mai furta “Come here...! It’s ok.....!” Yaci gaba da lallashinta a hankali yana shafa bayanta har kukan nata ya tsagaita.... Yana iya jiyo sautin bugawan zuciyarta cikin k’irjinsa.... Yanayi mai hawahalan fasaltuwa ya tsinci kansa ciki... Yanayi ne da zai tabbatar yakan tsinci kansa ciki muddin yana tareda matarsa Siyama... Toh Maiyasa yake jin haka tareda Raihanah..? Shin son yarinyar ya fara ko kuwa dai tausayinta yake har yanzu...? Shi kansa baida wannan amsa... Yanajin sanda take mutsu mutsun cire jikinta Daga nasa, a hankali ya d’an d’agota sassanyar murmushi saman fuskarsa... “Feeling better..?” Ya tambaya yana dubanta... Ba tareda ta dubesa ba sabida tsananin kunyarsa da takeji, ta jinjina masa kai a hankali... mik’ar dasu tsaye yai a tare kana yace bari yaje yaga Daddy.... Ta jinjina masa kai a hankali har lokacin fuskarta a k’asa tana mai share ragowar hawayen idanunta... Har ya soma tafiya ya sinkayo Muryarta tana fad’in “Yaya...!” Juyowa yai yana dubanta... Lokaci guda taci gaba da fad’in “Dan Allah ka yafewa Aunty Siyama kaji....!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya.... Jim yai yana dubanta, lokaci guda annurin fuskarsa ya d’auke... A hankali ya tako zuwa gabanta kana ya kuma kamo hannunta suka zauna saman kujera... “Wannan dalilin da yasaki kuka...?” Shiru bata amsasa ba... Ya d’an kauda kai gefe kad’an had’ida fuzar da huci a hankali.... Karkatowa ya kumayi yana dubanta kana yace “Raihaan bana son ki sake min zancen Siyama kinji koh....!” Yanda Yai maganar ya sanyata d’agowa tana dubansa... Sadda idanunta tai kana tace cikin sanyin murya “Kai d’in zuciyarka mai yawan afuwa ne... Kuma idan har zaka yafewa Baba Alhaji da Hajiya dik abubuwan da sukai maka, mai yasa bazaka yafewa Aunty Siyama ba....? Aunty Siyama tana k’aunarka kuma ta gane kuskurenta dan Allah ka yafe mata... Dik d’an adam ajizi ne Yaya... Please ka yafe mata kaji... And... and everybody deserves a second chance..!” Yai k’uri yana dubanta kana ya kuma fuzar da fuci a hankali.... Hannunta guda ya kamo cikin nasa kana yace “I’ll think about it....!” Daga haka mik’ewa yai yana duba agogon hannunsa kana yace bara yaga Daddy.... Ta jinjina masa kai har ya fice.... A hankali ta mik’e had’ida sauk’e ajiyan zuciya kana ta shiga tattare masa d’akin... A can parlor Sameer ya iske Daddy da Mummy da alama isowarsa suke jira... Daga can saman carpet ya zauna had’ida gaida Iyayen nasa... Suka amsa cikeda sakin fuska dikda tausayin d’an nasu da ya cika zukatansu... Daddy ya d’an bud’e murya yace “Doc an fito...?” Sameer ya jinjina kai yana k’ok’arin k’ak’aro murmushi “Eh Daddy... Allah sa dai bamu makara ba...?” Daddy ya girgiza kai kad’an “No aima inaga tafiyar nan mu barta har zuwa gobe idan Allah ya nufa zamu kai... D’azu mukai magana da Uncle d’in naka, jikin nashi da sauk’i Alhamdulillah, so yace mu barshi ma fito gobe kawai idan Allah ya nufa...” Sameer ya jinjina kai yana hamdala da jin cewa jikin Daddyn Siyaam da sauk’i sosai... Daddy ya kuma katsesa da fad’in “Sameer dama akwai maganar da nakeso mu tattauna...” Jin haka yasa Mummy mik’ewa ta basu waje... Sameer ya gyara zamansa gaban Daddy yana mai furta “Alright Daddy..” Lokaci guda yaci gaba da fad’in “About your wife Siyama... Mummynka ta sanar dani komai, abu baiyi dad’i ba amma babu yanda muka iya da hukuncin ubangiji.... Nima dai hak’urin zan baka Sameer... Kai hak’uri, ka yafewa matarka ka kuma had’e kan iyalanka... Siyama tana cikin wane yanayi na tashin hankali duba da halinda mahaifinta ya tsinci kansa cikin, kai hak’uri ka tausasi zuciyarka kaji ko...Wannan shine girman..... Yanzu yau mun bar maganan tafiyar, kaje ka sami iyalinka ba sai kowa ya shiga maganar ba, ku sasanta kanku idan yaso in Allah ya kaimu goben sai mu tafi Abujan gaba d’aya...” Idanunsa a k’asa yake jinjina kai kana yace “In sha Allah Daddy... Zanyi yanda kace..” Daddy ya murmusa kana yace “Allah shi maka Albarka....Tashi kaje..” Ya kuma risnawa had’ida amsa Daddy, lokaci Dad d’in Ke cewa “Kace da Mummyn naka ta kawo min maganin...” Sameer ya amsa da toh Daddy kana ya shige... *** Tana duk’unk’une waje guda a parlorn sabida tsananin ciwo da kanta ke mata ta kuma sinkayan ringing d’in wayarta, wannan karon d’an uwanta Khalid ne mai kira... Take taji sabbin hawaye na zuwa mata... Ta d’aga da k’yar Murya a matuk’ar sanyaye....Jin yanayinta ya sanyaya masa jiki dikda albishir mai dad’i da yake shirin sanar mata.... Mik’ewa tsaye yai cikeda kulawa... Lokaci guda yake furta “Siyama what’s wrong...? Where are you...Siyama meke faruwa...?” Lokaci guda ta fashe mashi da kuka tana mai furta “Khalid... Partner... Khalid Sameer yayi aure... Partner yayi aure Khalid.... Sameer bai k’aunata... Yayi fushi dani Khalid, ya samu madadina....!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Shafe goshinsa kad’an Khalid yai cikeda tashin hankali dan dama yasan hakan ka iya faruwa muddin labarin auren Sameer ya isaga ‘iyar uwar tasa.... Cikin kwantarda hankali yake furta “Siyama listen to me, just calm down kinji....!” Cikin kuka take ceda Khalid “How could you expect me to calm down Khalid, ko bakaji mai nake ce maka bane.... Sameer yai aure... Aure fah yai Khalid... He doesn’t care about me anymore....!” Khalid yace “Siyama Sameer na sonki dan yayi aure doesn’t mean ya daina sonki, Ki kwantar da hankalinki kinji...” Girgiza kai kurum take tamkar Khalid d’in na ganinta tana mai ci gaba da goge hawayenta take fad’in “Khalid please tell me.... Am I really a bad person... Why is all this happening...? First it was Daddy and now Sameer... Khalid this isn’t fair... It is not fair..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka wanda ya kuma raunana zuciyar Khalid... Cikeda tausayin ‘iyar uwar tasa yake furta “Siyama... Sis, please listen to me... Ki daina kuka kinji....!” Shiru ya d’an biyo baya sai sautin ajiyan zuciyar Siyama... Khalid yaci gaba da fad’i cikin kwantar da hankali “Siyama... Some times in life, we just have to accept things the way they’re... Ba komai muke samu yanda muke so ba, bazai yuwu mu samu komai yanda muke so ba Siyama... Some times dole muyi hak’uri mu karb’i k’addara a yanda tazo mana...So we just learn to let go and move on.... Please stop stressing yourself out Siyama...!” Ya k’arashe cikeda kulawa yana mai furta “So tell me, where are you now...?” Ta kuma share hawayenta kana tace “Kaduna... But I’m leaving now...Its pointless staying here, after all....!” Ta d’an fuzar da iska kad’an tana gathering strength d’inta kana tace “How’s Daddy doing... Ya jikin nasa...?” Khalid yace “Daddy is doing better, in fact he’s out coma...” Hamdala taji bakinta na furta murmushi saman fuskarta dikda hawaye dake ci gaba da gangaro mata...Ta k’arada... “And Ammi... How’s she.. How are things there...?” D’an numfasawa yai kana yace. “Things turned out the way we least expected... But komai lafia...!” Jinjina kai take tana mai ci gaba da shiri take fad’in “Zan d’auki hanya yanzu in sha Allah...” Cikin sauri Khalid ya katseta “Wait... Wane hanya kike magana...?” Tana mai ci gaba da abinda take tace “Abuja of course...!” Girgiza kai Khalid yai kana yace “A’a Siyama, a halinda kike ciki you cannot drive.... Kiyi hak’uri har zuwa gobe sai ki biyo train... A halinda kike ciki you can’t even travel Siyama...!” Dafe kanta dake tsananin sarawa tai kana tace “Kar ka damu bro zan iya... Just pray for me kaji... I love you...!!” Daga haka bata kuma jiran cewarsa ba ta katse kiran Khalid na fad’in “Siyama.. Siyama please...!” D’if yaji ta katse kiran.... Nabilah ce ta k’araso nan garden d’in da yake tsaye cikin asibitin.... Ganin yanayinsa ya d’an tada mata hankali.... Tambayarsa tai meke faruwa...? Ya d’an fuzar da iska kad’an kana yace “Siyama ce.... Bazai yuwu na barta ta d’auki hanya a halinda take ciki yanzu ba.... I need to call Sameer, he’s the only person that can stop her right now...!”Ya k’arashe yana dialing layin Sameer, gaba d’aya kallo guda zaka masa ka fahimci a tsananin birkice yake... Allah sarki d’an uwa ya wuce wasa.... Nabilah tai zaune tana duban yanda ya manne waya a kunnensa sai safa da marwa yake yana jiran Sameer ya d’aga wayarsa.... “Come on Sameer, pick up your phone...!” Sai faman nanata hakan yake... Kira na biyu a na uku Sameer ya d’aga.... Ko gaisuwa Khalid bai tsaya ba ya shiga sanar dashi halinda ake ciki... Shima Sameer d’in bai wata wata ba ya katse kiran yace gidan ya nufa, zai dakatar da ita.... Hakan yasa Khalid samun relief sosai... Sameer kaw gudu ya dingayi bisa kwalta, yana isa gidan ya fad’a ciki yana doka mata kira “Siyama..! Siyama..! Partner..!! Where are you... Siyama...!!” Haka ya dingabi k’ofofin gidan yana dubata... Saida ya shiga d’akin baccinsu ya hangi hotonsu kife saman gado alamun tareda hoton tai bacci... Girgiza kai Sameer yai a hankali kana ya fice babu shiri dan ga dikkan alamu Ta riga ta fice daga gidan.... Wayarta ya soma k’ok’arin kira saidai sam bata d’agawa, k’arashe ma katse kiran take.... Hanyar da yasan zai iya samunta yabi yana mai falfala gudu bisa kwalta.... Commotion d’in da ya hanga ya sanyashi yin slow.... Take ya paka motarsa a gefe ya nufi dandatson mutanen cikin sassarfa... Aiko nan ya hangi motar Siyama an kwankwatsa ga mutane chaaa sai cecekuce ake a wajen.... Babu shiri ya nufi wajen yana neman ta yanda zai ganta... Nan ya hangota tsaye cikin mutanen sai jefa masu masifa take itama da shike ba tayar baya bace, d’ayan har yana cewa zai suing d’inta.... Sameer ya k’araso yana mai girgiza kai had’ida tambayar ba’asi... Take d’ayan ya basa bayanin yanda abin ya kasance, yaci gaba da fad’in “Tasan bata a hayyacinta Ta hau kwalta wllhi bazan yarda ba sai ta biya ni damages dan Bazan d’auki asara ba...” Siyama taci gaba da huci tana fad’in “Motar taka dika nawa ne... Kai kud’inta a biya... Kan wannan amalanken ne zaka bud’e baki kana min shouting aka... Who do you think you are...?!!” Mutumin ya kuma zabura.. Sameer yai saurin tare gaban Siyama yana mai baiwa mutumin hak’uri had’ida masa alk’awarin za’a biyasa dik wasu damages d’insa... Da taimakon Sameer aka samu mutumin nan ya k’yale Siyama... Ita bama ta lura da jinin dake bin goshinta ba yanda glass ya tsaga sai masifa take tana juye dik wani b’acin ranta da bak’in cikinta ga mutanen nan.... Janyo hannunta Sameer yai yana fad’in “Ya isa haka Siyama... Shige muje....!” Zata fincike hannunta yai mata wani ido babu musu ta shige fuuu kaman zata kifa k’asa... Haka suka zauna cikin motar babu mai cewa komai har dai taga Sun d’au hanyar gidansu Sameer d’in.... Lokaci guda Sameer idanunsa naga kwalta yake fad’in “What do you think you are doing Siyama...? Yanzu ba don Allah ya kiyaye ba who knows what could’ve happened to you...!” Cikin d’an fad’a fad’a yai maganar... Shaye da mamaki take dubansa kana tace “Oh! Really now Sameer...? Now you care about me... Toh na mutu ma mana tinda baka damu dani ba....!!” Idanunsa naga kwalta, cikin tsananin b’acin rai yake furta “Don’t... Don’t you dare change the subject... Baki ganin abinda kikai koh... Kuma kinyi laifi maimakon ki bada hak’uri kina dad’a ingizasu....!” Katsesa tai da fad’in “Please don’t add to my headache...!!!” Girgiza kai kurum yai yana mai danne zuciyarsa.... Ganin sun shigo close d’in gidan ya sanyata kuma karkatowa tana dubansa kana tace “Meye haka kuma...? Mai kake tinanin kanayi Sameer... Ni fah bazan shiga gidan nan yarinyar can tana ciki ba... Idan bazaka kaini can gidanmu ba Toh ka kaini gidan Daddy na... Amma bazan shiga gidan nan da yarinyar nan ciki ba...!!” Bai amsata ba sai ma horn da yai aka bud’e masa gate.... Siyama tai masa k’uri tana kallon ikon Allah yanda Partner d’inta ya mugun canzawa, tayi imani da da ne yanda tace haka za’ai amma Wai yanzu shike mata abubuwa a gadarance... Wata zuciya kuma tace toh keda kike neman yafiyarsa, ai bisa kawai kiyi hak’uri... Tina Raihanah da Tai ne ya kuma cuzguna mata zuciya... Yana ida parking ya fito ya zagayo mazauninta ya finciki marfin motar had’ida fuzgo hannunta, lokaci guda suka nufi cikin gidan Siyama na fincika tana fad’in ita bazata shiga cikin gidan ba muddin wannan kucakar yarinyar na ciki.... Ta balcony Raihanah ke lek’ensu gabanta na tsananta fad’uwa... Allah ya sani ko sunan Siyama taji sai gabanta ya fad’i balle ta ganta... Babu shiri ta juya ta koma d’aki a guje Ta fad’a kan gado tana maida numfashi... Take ta kuma d’aure hannu aka tana tino cewa d’azun fah da tai gyaran d’akin Ya Ma’aruf ta mance d’ankwalinta da zobenta a can... Ta rintse idanunta kurum tana karanto innalillahi..! Bai zarce da Siyama ko ina ba sai d’akinsa... Ya isa ya d’auko first aid na gidan ya soma treating ciwonta fuskarsa a murtuk’e... Ita kaw sai b’alla masa harara take, cikin zuciyarta tana ayyana cewa yanzu haka ya gama cin amanarta da wannan kucakar yarinyar, ga d’akin tas tas yasha gyara na musamman dan shi kansa Sameer d’in saida ya fad’i haka cikin zuciyarsa sanda suka shigo.... Siyama bata ida tinanin ba ta hangi d’ankwali linke saman gadon da k’aramar zobe bisa... Kuka ne kurum taji yana zuwa bakinta.... Da gaske dai Sameer d’inta yanada wata bayan ita... She’s not ready to share him... K’uri tai masa yanda yasha mur sosai yana k’ok’arin rufe ciwon nata da bandage... Zuciyar Siyama taci gaba da tafarfasa... Lokaci guda take ci gaba da fad’in “So she was here... Maybe ma you two spent the night together.... Kai ko kunya bakaji ba Sameer... Just look at yourself...!” Da tsananin fuci yake dubanta kana yace “I don’t have time for your stupid tantrums... And don’t think sabida naje na d’auki yana nufin mun dawo normal like before bane... Sabida mutum uku nai haka Mummy, Daddy and Raihana...!” Yai maganar yana mai jinjina kai alamun tabbatarwa kana taci gaba da fad’in “Yes Siyama ki gode masu, if you’re still my wife... It’s because of them... And one more thing Siyama... You’re not in any position to question my authority... Wannan ya zama gargad’inki na k’arshe....Treat your wounds yourself.. !!” Ya k’arashe yana mai jifa mata bandage d’in a fuskarta.... Siyama ta saki baki tana binsa da kallo, wane irin kuka na zuwa mata.... Jiki a sanyaye Ta kwanta bisa gadon tana cazgan kuka.... Juyin duniya Mummy tai Siyama ta fito taci abinci tak’i fitowa... K’arshe Raihanah ita ta d’auki abincin ta nufi d’akin Sameer dashi ba tareda Mummy Ta sani ba.... Raihanah tai knocking a k’ofa amma shiru ba’a kulata ba.... Ta sakeyi nan ma shiru.... Har kaman zata juya da abincin sai kuma taji an bata izinin shigowa.... A hankali ta tura k’ofan ta shigo sallama saman bakinta tikda lugude da k’irjinta keyi yawa zai tarwatse tsaban tsoro.... Kallo d’aya Raihanah taiwa Siyama taji gabanta ya wani irin tsinkewa... Siyama sanye take da d’aya daga cikin kayan mijinsu, Black long sleeve check da ya kuma fito da hasken fatarta, gashin kanta mai tsananin tsantsi da shek’i a jik’e yake dik ya kanarnard’e alamun yanzu Ta murjesa da towel, daidai da jeans d’in jikinta na Sameer ne dan jakan kayanta na cikin nata motar bata samu ta d’auko ba bayan accident d’in da ya auku... Folding hannun rigar taci gaba da yi tana mai k’arewa Raihanah kallo daga sama har k’asa.... Babu Wai tasha jinin jikinta da ganin yanayin halittar yarinyar dan sam bata k’are mata kallo ba sai yanzu... Babu shakka Allah yai mata kyaun diri da Babu d’a namijin a bazaiso mallakar mace irinta ba... Siyama taci gaba da watsa mata mugun kallo tana mai zagayeta, yayinda Raihanah ta kasa katab’us saima karkarwa da jikinta keyi tana tuhumar kanta anya batayi ganganci shigowa ba.... Wani tsawa Siyama ta darara mata wanda ya sanyata kusan kifa tray d’in dake hannunta.... Siyama taci gaba da fad’in “Munafuncin banza da wofi kin wani d’auko abinci nik’i nik’I kega mai hankali ko..? Idan kinaso Ki nuna min kin cika mai hankali sarkin kirki Toh Ki rabu da mijina shine zan tabbatarda generosity d’inki... D’ago ki kalleni....!” Kasa d’agowa tai sabida hawaye dake ziraro mata... Siyama ta murmusa a hankali kana tace “Badon cushe ba babu abinda Sameer zai dake... You’re not even his type... Ke ki dubi kanki ki k’are ma kanki kallo Sameer ba daidai ke bane.... Kinga yanda nake sanye da kayansa toh haka muke nidashi Magnets...!” Ta k’arashe tana mai alama da hannayenta lokaci guda taci gaba da furta “Now get out... Wuce ki fita kafin na kwab’a miki abincin nan a fuskarki..!!” Raihanah dake kuka sosai cikin sauri ta juyo ta fito daga d’akin d’aule da tray d’in... Saidai a daidai staircase Siyama ta kuma kiranta ta tsaida ita... Takowa yanda take Siyama tai. Kana tace “Wait... It was you... So kece kika d’auki wayarsa a asibiti kwanakin baya da na kirasa....?!” Ta kuma murmusawa kana tace “Wato kin jima kina bibiyan mijina har wajen aikinsa...” Raihanah da hawaye ke gangaro mata girgiza kai tai kana tace cikin rawar murya “Ba bibiyarsa nake ba shine likitan da yai treating ciwona sanda na k’one... Ki yarda dani Aunty Siyama wllhi ba bibiyarsa nake ba....” Siyama ta kuma murmusawa a hankali kana tace “So you’re even aware of my husband is a plastic surgeon... Barin dad’a k’onaki da abincin nan sai yai treating naki da kyau....!” Ta k’arashe tana mai fatali da tray d’in abincin dake hannun Raihanah... Allah ya rufa asiri abincin babu zafi... Hakan yai daidai da fitowar Mummy... Sosai taiwa Siyama fad’a hardai k’arshe fad’an ya juye ya koma nasiha mai ratsa zuciya.... Mummy taci gaba da fad’in “Siyama this is not you... This is not who you are.... Ina Siyamar da na sani mai taimakon marayu da mabuk’ata...? Don’t allow yourself to get carried away by your emotions... Raihanah batada laifin komai, hasalima k’ok’ari take taga ta kyautata miki... Siyama dik abinda kwanciyan hankali bai badashi ba toh ki sani tashin hankali bazai badashi ba...” Siyama ta d’ago idanunta masu zuban hawaye kana tace “Mummy maiyasa Sameer zai kawo wata cikin rayuwarmu idan ba daina sona yai ba...” Ta k’arashe cikin rawar murya... Kamo hannayenta Mummy ta kumayi kana tace “Sameer loves you Siyama... He never stopped loving you... He always does... Da ace bai sonki da bazaije ya d’auko ki ba.... So please kar Ki baiwa mak’iyanku dama su cimma burinsu na ganin sun rabaku kinji...!” A hankali Siyama ke jinjina kai had’ida kwanciya cikin jikin Mummy hawaye na ziraro mata... Tabbas idan tana k’aunar Sameer batada zab’in da ya wuce tai hak’uri Ta amshi k’addararta a yanda yazo mata dikda tasan hakan abune mai matuk’ar wahala.... *** KANO Suna ida waya da inspector Bala wata wayar ta shigo masa... Da tsananin mamaki yake bin wayar da kallo ganin ba kowa bane yakeda wannan layi nasa na musamman.... Dikda bugu da k’irjinsa keyi hakan bai hanasa d’aga wayar ba... Tamkar wanda aka zabura ya kuma mik’ewa tsaye yana furta “Akram.... Akram is that really you....?! Akram tell me mai ya faru dakai....?!” Da k’yar Akram dake tsananin haki yace “Sir abubuwa ne da dama.... They cannot be discussed over a phone call.... We need your help, I cannot go directly straight to the police... I need back up...!!” Engr yace ”Where are you now...? Just text me your location....!” Babu musu Akram yace “Alright Sir, right away...” Jim kad’an sak’o ya shigo wayar Engr.... Bai nemi kowa ba sai Jalo da ya kira ya sanar dashi ya kira party chairman ya sanar dashi campaign d’in da zasu fita ayi rescheduling d’insa zuwa satin sama... Something urgent came up.... Hakan kaw akayi Yayinda Bash da Muhibbah suke shirinsu na tarwatsa Engr Ma’aruf.... Sam basuda labarin wannan change of plans na Engr... shirinsu shine a goben su b’ata masa suna a bainal jam’a su kuma tarwatsa masa rayuwa... Tareda wasu Jam’ian tsaro guda biyu Engr suka riski Akram.... Ba tareda b’ata lokaci ba Engr ya kirawo family Dr d’insu ya duba Akram a safe house d’in da suka ajesa dan babu wanda yasan Akram d’in ya dawo kuma hakan ne zaisa su cimma burinsu cikin sauk’I wajen capko muggan ‘yan ta’addan nan Babba Duna da yaransa harmada Sawwama da Mahaifiyarta da babu wanda yasan sunada alak’a dasu Babba Duna bacin yanzu da Allah ya toni asirinsu... Dr ya fito ya tadda Engr zaune a parlor shida jami’an tsaron da alama fitowarsa suke jira.... Engr ya mik’e yana fad’in “Dr how’s he...? Kana ganin jami’an tsaro zasu iya interrogating d’insa a halin yanzu...?” Jinjina kai Dr yai kana yace “An gode Allah Babu wani deep wounds sosai, a hankali zai healing... He’s stable zai iya amsa dik wani tambayoyinsu Inaga a halin yanzu.....” Engr ya jinjina kai had’ida mik’awa Dr hannu sukai masabaha kana yace “Na gode Dr... Let me walk you out...” Dr ya jinjina kai yana mai furta “Aaa babu komai your excellency... Allah dai ya basa lafiya....” Lokaci guda suka jera a tare suka fito tareda Engr yayinda polisawan suka shiga d’aukan bayanai daga wajen Akram.... Musamman da shike Babba Duna tsohon d’an ta’adda ne da ya jima yana ta’addanci a doron k’asa sama da shekaru masu yawa..... SameenaAleeyou 📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *107* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sanda Engr ya shigo d’akin Akram d’in ‘Yan sandan sun ida tattare duk wasu bayanai da zasu d’auka.... Inspector Bala ya dubi Engr kana yace “Your Excellency mun d’auki dik wasu bayanai da zamu d’auka kuma wannan yak’i ne Babba muke tunk’ara sabida shi wannan d’an ta’adda Duna yanda kasan hawainiya haka yake canza kala, shekara da shekaru wanted ake nemansa, ko wacce gobnati haka take zuwa ta tafi ta bar Duna, sannan babu kalan jami’an tsaro masu tunk’aho da uniform da basuyi azaman kame Duna ba amma Sun gaza, Sabida Duna d’an ta’adda ne mai had’arin gaske, amma yanzu in sha Allah komai yazo k’arshe zamu kamo Duna mu gurfanar dashi gaban Kuliya domin a yanke masa hukuncin duk wasu laifuka na ta’addanci da ya aikata..... A halin yanzu muna buk’atar had’in kanku musamman shi Akram d’in da aka ijesa hostage a wancan dajin.... Sannan rankashi dad’e daga baya nan da Akram yai mun fahimci cewa Hajiya Magajiya sirkar Hafiz kuma matar Baban shi Hafiz d’in sunada saka hannu ita da d’iyarta a wannan ta’addanci.... Zarginka ya tabbata your Excellency...” Engr ya jinjina masa kai kana yace “Toh yanzu shi Hafiz yana can hannun Duna kenan...?” Inspector ya jinjina kai kana yace “Kuma rayuwarsa tana cikin had’ari Babba according to Akram’s statement....” Kakaitowa Engr yai yana duban Akram da hannunsa Ke d’aure cikin bandage, cikin sauri Akram ya sadda kansa k’asa sakamakon nauyin Uban gidan nasa da yake... Duban Inspector Engr ya kumayi kana yace “Inspector, kenan hakan na nufin babu wani case akan Hafiz a halin yanzu...?” Inspector ya girgiza kai alamun a’a kana yaci gaba da fad’in “Eh to bazance kai tsaye babu case akansa ba, abu ne da Alk’ali zai hukunci your Excellency... Amma case mafi girma dake kan Hafiz a halin yanzu shine case na kidnapping Akram... Idan Akram yayi filing case against him Toh fah dole ya gurfana gaban Alk’ali domin ya amsa laifinsa na garkuwa da Akram da yai....” Akram ne ya katsesu da fad’in “Never... Bazan tab’a filing case against Hafiz ba, Hafiz mutumin kirkine da rud’ani na soyayya ya rufe masa idanu bai gane gaba bai gane baya, Hafiz mutumin kirki ne da ya zab’i ceton d’unbin Al’umma sama da rayuwarsa.... Hafiz ya samu chance d’in tserewa daga hannun Duna amma ya zab’i ceton nawa rayuwar data sauran Al’umma.... Hafiz is a total opposite of what you all think of him.... Deep inside his chest there’s heart that’s capable of loving.... He’s not a monster that we all thought he was....Kawai dai ya sami gurb’ataccen tinani ne daga iyayensa, wanda suka haddasa masa gaba tai tasiri cikin zuciyarsa....!” Tinda Akram ya soma magana Engr Ke dubansa... Lokaci guda Akram d’in ya taso da k’yar sabida jikinsa dake tsananin masa ciwo, ya tako gaban Engr, kansa a k’asa yake furta “Sir, please we need to rescue Hafiz... We cannot allow Babba Duna to have him killed.... Babba Duna fasik’i ne wanda ya d’aura kwad’ayin fasik’ancinsa akan Hafiz, if we don’t act very fast and smart...I’m afraid everything might be possible....!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Dafasa kad’an Engr yai kana yace “Akram I promise you... In sha Allah, zamu karb’o Hafiz daga hannun Babba Duna alive da yardar Allah... Babu abinda zai sami Hafiz da izinin Allah.... Mutumin da ya sadaukarda rayuwarsa ga d’unbin Al’umma Allah zai tsaresa da tsarewarsa... Ka kwantar da hankalinka kaji koh.... Hafiz zai kub’uta..!” Ya k’arashe yana mai dafa kafad’an Akram d’in.... Lokaci guda Akram Ke jinjina kai kana yace “Thank you....Your Excellency....!” Jinjina masa kai Engr yai kana suka fice tareda Inspector suna kuka tattauna lamarin.... Tsaye Engr yai a waje bayan tafiyar su Inspector Bala yana tinanin rayuwa da abubuwan da suke kan faruwa.... Allah sarki ashe dik yanda suka d’auki Hafiz, mugun mutumi mai son zuciya ba haka bane... Ya zab’i shi ya bada nasa rayuwar dan a capke Babba Duna once and for all d’inbin Al’umma su tsira, tabbas idan har haka ne Hafiz ya cika jarumi wanda yai sadaukarwan da ba kowa zai iya irinta ba... Yana nan a tsaye wayar Detective Najib ya shigo masa... Detective Najib private investigator ne da Engr ya d’auka dan yai masa binciken shagunan ‘yankunnaye da sark’ar zinari na mata da matarsa Muhibbah ta mallaka wanda Engr d’in ke zargin ana tafiyar da hada hadan saida muggan miyagun k’wayoyi masu barazana ga rayuwar Al’umma musamman matasa wanda shan wad’annan miyagun k’wayoyi ya riga ya zama ruwan dare, babu mace babu namiji.... Tsaye yai yana nazari bayan sun ida waya da Detective Najib, the last abinda zaiso shine ace an kama matarsa uwar ‘ya’yansa da wannan mummunar laifi.... Detective Najib ya sanar dashi bai samu wani abu suspicious ba a halin yanzu hakan na nufin kai tsaye bai isa ya tunk’ari Muhibba ba, musamman yanzu da take tsananin fushi dashi, baiso abin yakai ga jami’an tsaro amma baida wani zab’i, muddin Muhibbah bata saduda ba toh fah baida wani zab’i da ya wuce ya sanar da jami’an tsaro dan tsaida wannan b’arna dake wanzuwa, bazaiso ace yau ga nashi d’iyoyin suna ta’ammudi da miyagun k’wayoyi ba, kuma idan har da gaske neman takaran kujerar Al’umma yake Toh ya kamata ya fara proving hakan ta hanyar mik’a natarsa ga hukuma domin a gurfanar da ita gaban Alk’ali ta amsa laifinta... Ya sani wannan abu ne mai matuk’ar wahala daka iya janyo cecekuce tsakanin Al’umma, sannan abu ne dake barazana ga kujerar da yake nema, even his reputation yana barazanar b’aci muddin akace yau an kama matarsa da wannan laifi....! A hankali ya lumshe gajjiyayyun idanunsa ya kuma bud’esu.... Idan har da gaske yana son kawo canji a wata b’angare na k’asarsa Toh ya kamata yai proving, baida wani zab’i da ya shige ya mik’a Muhibbah da muk’arrabanta ga jami’an tsaro koda hakan na nufin downfall d’insa ne... Da wannan tinani Engr ya komo ciki wajen Akram, yanda ya tadda Akram d’in kwance tamkar mai bacci idanunsa a lumshe... Daga gefensa Engr ya zauna had’ida masa k’uri kaman mai tinanin wani abin.... Shi kad’ai ya saki murmushi kana ya isa ya janyo bedcover ya rufawa Akram.... Ya jima yana zaune wajen kafin aka soma knocking.... Engr ya tashi ya nufi k’ofar... Umma ce mahaifiyar Akram.... Engr ya bata waje ta shigo tana hawaye, lokaci guda take tambayarsa Ina Akram d’inta.... Bai wata wata ba ya nuna mata d’akin da Akram d’in yake, nan da nan Umma ta fad’a kan d’anta tana kuka sosai tana tambayarsa mai sukai masa.... Akram ya rik’o hannayenta yana mai furta “Ummah na Ki kwantar da hankalinki gani nan gabanki I’m alive... Babu abinda ya sameni sai raunuka....!” Lokaci guda Umma Ta kuma rungumarsa su duka biyu suna hawaye.... Cikeda tausayawa Engr Ke dubansu kana ya d’an sakala hannayensa cikin aljihun wandonsa, lokaci guda yai gyaran murya kad’an yana mai furta “Umma tinda kinzo Inaga zaifi kyau idan kika tsaya kika kula da Akram...” Jinjina masa kai tai cikin sauri tana mai furta “Ubangiji dai ya biyaka da gidan Aljannah Gwabna... Yanda kake kula da Akram Allah ya shiga lamuranka kaima...” D’an murmusawa kad’an Engr yai kana yace “Ummah Akram d’an uwana ne, Ko mai zanyi masa ma kaina nayi.... Sannan a cikin mu biyun shine zan gorzo kuma jarumi mai sadaukar da Farin cikinsa ga d’an uwansa... Mai kula da d’an uwansa ta hanyoyin da D’an uwan nasa bai zato ba balle tsammani....” Ya k’arashe idanunsa kan Akram, shima Akram d’in Engr yake duba kuma tsaf ya fahimci kalamansa, tabbas har cikin zuciyarsa yaji dad’i da Engr ya fahimci shi d’in ba munafukinsa bane.... Ya saki murmushi a hankali k’walla na k’ok’arin ciko idanunsa... Murmushin Engr ma ya sakar masa kana yace “Get some rest... Akwai jami’an DSS guda biyu da aka sanyasu su bibiye Magajiya da d’iyarta Sawwama dan Sune zasu kai Jami’an tsaro ga wannan hideout d’in na Duna da yaransa...” Akram ya katsesa da fad’in “Sir, Hafiz na cikin had’ari mafi muni... Kuma na mishi alk’awarin zan koma gareshi... Pls ka k’yaleni na koma ma Hafiz....!” D’an jim Engr yai kana ya d’ago yana duban Hafiz.... Lokaci guda yake furta “Akram, wannan ba aikinka bane, ka barshi wa jami’an tsaro... Probably yaran Duna suna nan suna nemanka, fitarka had’ari ne mai matuk’ar gaske... Kai hak’uri abi shawarin Hafiz, yanda yace Sawwama da Mahaifiyarta su zasu linking Jami’an tsaro dasu Babba Duna... Ni ba jami’in tsaro bane amma nai maka alk’awarin bazan huta ba har sai Hafiz ya kub’uta da izinin Allah...!” A hankali Akram ya tako gaban Engr kana yace “I trust you... Sir,..” Lokaci guda Engr ya jinjina kai yana maiyiwa Akram d’in da Ummansa sallama.... Har yakai k’ofa Akram ya kirawo sunansa.... Juyowa Engr yai yana dubansa.... Lokaci guda Akram ya tako gabansa... Murya can k’asa dan baiso mahaifiyarsa taji yake furta “Sir, I have something very important to tell you... It’s about your wife...” Saurin d’agowa Engr yai yana dubansa, kana Akram ya sadda kansa k’asa a hankali... Matsowa kad’an ya kuma kana yaci gaba da fad’in “I’m sorry idan ban sanar dakai tinda wuri ba.... I don’t know how you’re going to take it Sir, but your wife... Is a drug dealer...!” K’uri Engr yai masa, shi kansa Akram d’in yasha mamaki ganin baiji wani gizau ba... Saima kafesa da idanuwa da yai kana yace “Since when...? Tin yaushe kasan dika wad’annan...?” Sadda kansa k’asa Akram ya kumayi kana yace “About 4 to 6 months ago... Sir kai hak’uri idan ban sanar dakai da wuri ba...!” Girgiza kai Engr yai kana yace “Na fahimceka... Kar ka damu Akram, a halin yanzu ni kaina nasan wacece Muhibbah.... Na kuma san sana’ar da take a bayan fage.... Smuggling miyagun k’wayoyi....Amma in sha Allah bazan rufe idanuna daga ganin gaskiya na k’yale ba, koda ace Muhibbah ta kasance mahaifiya ga yarana... Idan zanyi rantsuwa cewa zan kare Al’ummar k’asata, lafiyar su, rayukarsu da kuma dukiyoyinsu toh ya kamata chanji ya fara daga kaina... I know it is not easy amma zan kwatanta da yardar Allah...!” Murmushi Akram yai yana dubansa cikeda tausayawa kana yace “Sir, you deserve all the happiness in this world.... Ka cancanci Farin ciki... Kai d’in mutum ne wanda a kullum burinsa ya kyautata wa Al’ummansa, kai d’in mutum da a kullum kake fara kawo matsalolin Al’umma samada naka.... Allah Ubangiji ya yalwata rayuwarka da farin ciki....” Ameen Engr ya amsa dashi yana mai duban Akram d’in.... Lokaci guda ya janyosa ya rungumesa... Umma dake lek’ensu Ta k’ofa hawaye suka gangaro mata... Tabbas basai kun had’a alak’a ta jini ku zama ‘yan uwan juna ba, haka Allah ke jefa soyayya tsakankanin mutane.... Fatanta Allah yasa wannan zumunci na Akram da Engr yakaisu har Aljannah... *** A can daji wajensu Babba Duna kaw, wata jahilar mari ya kuma watsawa Hafiz wanda saida jini ya kece daga bakin Hafiz d’in da hancinsa.... Duna ya kuma kamo hab’ar Hafiz da iyaka k’arfinsa yana mai furta “Kai d’an iska... Kai har ka isa... Uban wa yace maka wani zai iya ganin k’arshen mulkin Duna....?!” Hafiz da bakinsa bai mutu ba yana ci gaba da huci yake furta “Allah shi zai kawo k’arshenka... Kuma ka rubuta ka ajjiye ko yanzu ka kasheni ni ne nan na zama sanadiyar kama ka... Inaso wannan ya zauna cikin tarihin rayuwarka...!!!” Duna ya kuma d’aukesa da mari kana yace da yaransa su bank’are masa Hafiz..... Nan da nan yaran Duna sukai yanda ogansu yace.... Kallo Duna ya dinga binsa dashi kana yai wata murmushi yace “Ai kasheka ma a nan yana nufin Duna ya maka rahama kenan... Ai na kasheka gaban matarka daka yarda da ita bayan na gama amfani dakai shine zaifi komai maka ciwo... Wannan mutuwar sai tafi a azaba a gareka kana kallon fuskar mutanen da ka aminta dasu kuma babu abinda zasuyi domin su ceceka.... Ta yanda ko ban kasheka ba zuciyarka zata kumbura Ta fashe sabida bak’in ciki.....!!” Ya dubi yaransa kana yace “Ku nad’o min shi, taredashi zamu shiga gari...!!” Babu musu yaran suka kuma yin yanda Babba Duna yace... Hafiz bai daina b’alla masa harara da idanunsa da kaman sun juya ba sabida tsananin bugu da yasha hannun wad’an nan azzalumai... Ko d’aga k’afarsa bai iyawa saima janyota da yake... D’aya daga cikin yaran Babba yace “Babba shi kuma wancan yaron da ya gudu fah.....?” Babba yai wata shegiyar murmushi yana shafa tsakiyar malu d’insa da fatar har ta soma yamutsewa sabida tsufa da barbad’anci ga wata siririyar farar fenti a tsakiyar kan an zana doguwar layi da ita daga goshi har k’eya kana yace “Dik yanda ya shige idan cikin tandu ya shige sai mun bincikosa shima mun kashesa....!” Yaron Babba ya jinjina kai kana yace “Baka saka abu gabanka Kaga kasawa....!” Babba yai wata k’asaitacciyar murmushi kana yace su fidda da makamai su d’au hanya..... *** A can gidan Baba Alhaji kaw Magajiya ta tasa shi gaba sun d’auki hanya, yana tambayarta Ina suka nufa ko zarafin amsa shi bata samu ba, Haule na zaune tsakar gida ta rapka uban tagumi suka fito suka shigeta.... Kallo kurum Haule Ta bisu dashi tana mai goge k’wallan da suka ciko idanunta, duniya kenan Wai yau ita Alhaji kema wannan d’anyen aiki... Lallai Ta yarda mulkin duniya mai k’arewa ne Allah shi kad’ai yakeda tabbatacciyar Mulki kuma Mafi adalaci.... Tabbas A DADE ANAYI SAI GASKIYA(Inji Biebee Isa) Itakam ta yarda da hakan dan taga ishara akan nata rayuwar... K’arya fure take bata ‘ya’ya....Ta kuma kamo Bakin zaninta ta goge hawayenta.... Ficewarsu da kad’an gungun ‘yan daudu suka shigo sai hayaniya da kacaniya suke daga mai barandami sai mai tab’arya sai mai adda da gatari, sunbi Sawwama a guje tasha da k’yar dan sin riga sunji sirrinsu Magajiya da Sawwama ashe dik ‘yandaudun da suke b’acewa a nemesu a rasa ashe saidasu ma ‘yan ta’adda suke ayi asiri da sassan jikinsu.... Haule ta mik’e a birkice tana tambayarsu lafiya....? Had’ida dafe k’irjinta... D’ayan wanda yake rungume da gatari yace “Ina take... Ina shegiyar kishiyar taki take... Wllhi muma yai sai mun cire mata sassan jiki yanda take saida mu ana cire mana namu sassan jikin...!!!” Ya k’arashe yana kuma wasa gatarin a k’asa.... Sahariyya da Najah babu shiri suka fito suka rungume mahaifiyarsu ganin wannan kayan tashin hankali dake aukuwa gidansu.... Haule cikin rawar murya take fad’in “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kunaso ku cemin gasunk’umar’yar ta’adda nake zaune da ita cikin gidan nan... Na shiga uku ni Haule wllhi ko tsuntsu ban tab’a kashewa ba, iyakacin asiri na ban tab’a kashe rai ba... Ma’aruf kawai naso aikatawa hakan shima Allah bai nufa ba dan ya nuna min shikeda cikakken iko akan komai.... Yanzu kunaso kuce matar nan saida mutum take ai tsafi dashi....!!” D’ayan yace “K’warai kuwa dan ta saida ‘yan uwanmu kuma munji daga bakin d’iyarta sirkarki sannan kema naki d’an abinda suke shirin aikatawa dashi kenan da kuma had’in bakin mijinki...!” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!! Tashin hankali da ba’a saka masa rana... Take Haule ta soma gani bibbiyu duniyar na juya mata.... Bama tasan sanda ta cire d’ankwalin kanta tana furta “Hafiz...! Hafiz d’ina kuke nufi...?!! A’a badai Hafiz d’ina ba...!” Lokaci guda Haule ta shiga janyo Sahariyya da Najah da tuni sunyi mutuwar tsaye tana fad’in “Kunji koh... Yayanku... Zasu kashe Yayanku.... Na shiga uku ni Haulatu... Ya Allah ka kawo min d’auki ka kare min d’ah na ka tsare min shi.... Ya Allah yanda ka kare Ma’aruf daga sharrin da muka nufesa dashi a baya ya Allah ka kare min nawa d’an daga sharrin wad’annan bayi Naka..... Ya Allah kada ka barnida iyawata, Ya Allah ka zamto majib’icin lamurana....!!” Ta k’arashe tana mai duk’a gwiwoyinta gaba d’aya k’asa cikin wani irin kuka mai ban tausayi.... Naja’atu ce ta k’araso ta d’ago Hajiya Haule... Najah na hawaye take fad’in “Allah zai kare Ya Hafiz Hajiya... Kici gaba da masa addu’a....!” Hajiya ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Najah lokaci guda take furta “Najah gidan Mariya zan tafi... Dole naje na rok’i yafiyar Mariya... Naji da kunnuwana ko ta yafeni wala’alla zan samu sassaucin wannan uk’uba na rayuwa da nake ciki...!” Lokaci guda Haule ta zari mayafi tana hawaye ta nufi gidan Abbah.... Naja’atu ta maidoda dubantaga ‘yan daudun kana tace “Ku kuma Allah yasa wannan ya zamto wa’azi a gareku ku gane cewa wannan hanya da kuka biyo ba turba mai kyau bace... Ita wacce kuka aminta da ita take d’oraku akan mummunar hanya na fasik’anci da sab’awa mahaliccinku gashi ta tabbata cewa azzalumarku ce.... Shin maiyasa zaku bijirewa rahamar ubangijinku...? Shin Maiyasa zaku maida kanku mata bayan Allah yayi ku maza...? Shin da Allah yaso da sai ya halitto duniyar nan Duka mata ko duka maza... Amma ba haka yaso ba, ya rabamu jinsu mabanbanta domin ya cika rahamarsa a garemu, sashenmu su samu natsuwa da sashe... Wannan rahamarsa ce a garemu... Ina fata daku da masu wannan mummunar d’abi’a irin taku zaku wa’azantu ku tuba ku karb’i halittar da Allah Yai maku a matsayin rahama a gareku...!!” Tinda Naja’atu ta soma magana jikkunan ‘yan daudun nan yai sanyi sosai.. Kan kace mai sun soma warware zannuwan da suke d’aure dasu had’ida d’ankwalayen kansu.... D’aya daga cikin su yana hawaye yake furta “Wllhi gaskiya kika fad’i... Mu d’in mun kasance masu bijirewa rahamar ubangijimu... Daga rana mai kaman ta yau na daina Daudu kuma zan koma gaban iyayena na rok’i yafiyarsu...!” Ya k’arashe yana mai jifa da zanin hannunsa had’ida goge gazal d’in dake girarsa.... D’ayanma yai jifa da takalmin k’afarsa ta mata yana mai furta “Nima daga yau na daina kamanceceniya da mata, iyayena sunmin iyaka da gidanmu dan haka zanje na mik’a kainaga hukumar hizba su zasu taimaka su dank’ani ga iyayena... Allahu Akbar su Shazali ashe Magajiya ce ta kashesu....!” Ya k’arashe yana mai kuma matse k’wallan da suka ciko idanunsa... Haka ‘yandaudun nan suka dinga tuba suna fad’in sun daina kamanceceniya da mata da dik wani aikin assha da suke... Daka masu cewa zasu koma garinsu gaban iyayensu sai masu cewa zasu mik’a kansu ga hukumar Hizba... Sahariyya ta k’araso ta rungume ‘yaruwarta Naja’atu hawaye na gangaro masu su duka biyun.... *** A can gidan Abbah kaw Haule duk’e take gabansu tana kuka na nadama wanda bata tab’a irinsa ba... Mamy dake hawaye a hankali ta kamo kafad’un Hajiya Haule ta d’agota, lokaci guda ta rungumeta ba tareda ta iya cewa komai ba sai hawaye dake gangaro mata.... Baba Alhaji ya d’an kamo gefen rigarsa ya share k’wallan da ya mak’ale masa a idanu shima.... Lokaci guda yai k’ok’arin saita kansa kana yace “Zama a nan bai ganni ba dole na tafi ga jami’an tsaro domin ceton rayuwar Hafiz....” Mamy dake share hawayen idanunta jinjina kai tai kana tace “Wannan haka ne Abban Ma’aruf...!” Haule dake rakub’e tai saurin cewa “Usman zanso naje dakai can wajen jami’an tsaron, zamana a nan hankalina bazai kwanta ba....!” Abbah ya d’an dubi Haule kana ya dubi Mamy lokaci guda yake furta “Inaga ku zauna a nan zaifi... Ni zanje na sami jami’an tsaron....” Haule na hawaye take fad’in “Dan Allah ka barni naje Abbah... Ina matuk’ar son sanin halinda d’ah na Ke ciki..!!” Abbah ya d’anyi Jim kana ya jinjina kai a hankali... Mamy tace itama zata tafi taredasu... Gaba d’aya su duka ukun suka d’unguma suka nufi ofishin ‘yansanda domin filing report... Har yanzu Abbah ya kasa gasgata Wai d’an uwansa Baba Alhaji zai iya aikata hakan wa Hafiz, d’ansa na cikinsa da ya haifa... Gaba d’aya jikin Abbah a matuk’ar sanyaye yake yana mamakin shin Baba Alhaji wane irin mutum ne mai matuk’ar son zuciya... Ashe dik abubuwan da suka faru basu ishesa ishara ba.... Can wani b’angare kaw na zuciyarsa yana fad’a masa rashin imanin Baba Alhaji bazai kai nan ba... Allah sa ba hakan bane da gaske... Dan dik abubuwan da yai masa bazai so ya tab’e har haka ba... *** A nan hideout d’in nasu kaw suka had’u gaba d’ayansu... Baba Alhaji sai muzurai yake cikeda firgici.. kana ganinsa basai ance maka hankalinsa a matuk’ar tashe yake ba... Magajiya ta kuma darara masa tsawa da fad’in “Ka shige nace... Kana wani tafiya kana lalumen hanya....!” Suna cikin tafiya saiga Babba Duna ya fito daga cikin kangon ginin tamkar wanda aka jefosa.... Kallo guda zaka masa ka fahimci wannan anyi shed’anin k’arshen zamani wanda ya tsufa yana b’arna da fasadi a doron k’asa.... Baba Alhaji saida ya firgita da ganin Babba Duna... Magajiya ta risina ta gaida Babba kana tace “Abokin huld’a kuna daji muna gari muna maku yak’i.... !” Babba ya kuma kecewa da dariya kana yace “An gaida mai ‘yandaudu... Wannan shine sabon member da kikai masa register...?” Magajiya ta jinjina kai tace “Shine wannan, mijina kuma mahaifiga Hafiz....” Gaban Baba Alhaji ya tsananta fad’uwa a daidai sanda aka fito da Hafiz... Wani irin tsoro da firgici had’ida rud’ani suka d’arsar masa a zuciya ganin yanda azzaluman mutanen nan suka sauyawa Hafiz d’insa kamanni sabida tsananin bugu.... *** Bayan Sawwama kaw tasha da k’yar Daga hannun ‘yan daudun nan kaw take jami’an DSS d’in suka take mata baya ba tareda saninta ba, d’ayan ya shafi ‘yar k’aramar na’uran magana dake mak’ale kunnensa yana mai furta “Positive Sir, we need backup ASAP...!” SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *108* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED A nan police station su Mamy sunyi jigum jigum suna jiran ba’asi daga jami’an tsaro, Hajiya Haule abin tausayi idan ka ganta dole ta baka tausayi, haka nan Mamy keta dannarta tana bata baki... Wasu ‘yansanda ne suka fito daga wata k’ofa Abbah na biye dasu... Nan su Mamy ma suka mik’e ganin zugan ‘yansandan sun fice, jagaban nasu wanda da gani basai ance maka shine jagora ba waya yake yana fad’in team d’insa sun zama ready.... Hilox da motocinsu Jami’an tsaron suka nufa yayinda Mamy da Haule suka nufi wajen Abbah yanda wani jami’in tsaron ke kuma jadadda masa kada suyi yunk’urin bin bayansu sabida had’ari dake tattareda yanda suka nufa d’in... Haule na hawaye take fad’ida Abbah “Ni dai Alhaji Usman ka taimaka ka barni na bisu... Inason sanin halinda d’ah na Ke ciki.... Ka taimaka ka k’yaleni na bisu Hafiz d’ina na can....!” Ta k’arashe tana mai had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o... Daga Abbah har Mamy tausayi Haule tai mugun basu, bazasu iya k’yaleta a wannan yanayi ba, Abbah ya nusa kad’an kana yace “Inaga mubi bayan nasu...” Mamy ta jinjina kai tana mai furta hakan yayi, nan suka nufi motar Abban kana suka take ma jami’an tsaron baya... **** Girgiza kai kurum Baba Alhaji yake yana duban wannan tashin hankali da tinda yazo duniya bai tab’a ganin irinta ba.... Jikinsa har wane irin tsuma yake, ya dubi Magajiya dake tsaye yawa ‘yar gunda tana faman k’yak’yata dariya ganin yanda Hafiz ya koma abin kwatance..... Cikin wane irin murya mai cikeda tashin hankali Baba Alhaj Ke fad’in “Amma Magajiya kedai babu zuciya cikin k’irjinki idan kuma akwai toh fah ta riga ta gama bushewa... Shin mai muka maki da tsanani...? Mai Hafiz ya maki da zaki jefasa cikin wannan mummunar tashin hankali irin haka....?!” Banda uwar harara bata aika masa komai, lokaci guda taci gaba da fad’in “Kai saurara Alhaji nifa taimakon ka nake idan bazaka amshi kud’in fansar sassan jikin Hafiz ba nifa gaba Ta kaini, kuma da kake cewa mai Hafiz yamin, idan baimin ba ai yayiwa d’iyata dan haka ko a k’asar gyalena idan Babba yaga dama yai gunduwa gunduwa dashi yanzu gabanmu babu abinda ya shalleni matuk’a zan caske kud’ad’ena....!” Ta k’arashe tana watsa masa mugun kallo lokaci guda Ta shige k’ofar da Babba da wani yaron sa suka bi... Cikin sauri Baba Alhaji jiki na wani irin kyarma ya k’araso zai kwance Hafiz.... A wane irin fusace Hafiz d’in yace dashi “Don’t ...! Kada ka kuskura kazo kusana... Kada ka yarda kai kuskuren tab’ani...!!!!” Yai maganar yana tsananin haki.. Baba Alhaji da hawaye ke gangaro masa kuma mik’a hannu yai kaman zai tab’a Hafiz d’in lokaci guda yake furta “Hafiz... Dah na ka yarda dani... Wllhi bazan tab’a aminta da shirinsu ba... Babu yanda na iya ne... Ka yarda dani Hafiz...!!!” Tinda ya soma magana Hafiz ke binsa da wane irin duba wanda shi kad’ai yasan irin zogin da yakeji cikin zuciyarsa, ya kasa aminta Wai Uba zai yarda a had’a kai dashi a aikata wannan zalunci mafi muni ga d’an cikinsa.... Hafiz na Hawaye yake fad’in “Ban tab’a dana sanin aikata duk wasu munanan abubuwan da na aikata a baya ba irin yau... Kuma ko ba’a kasheni ba naji dad’i sosai a zuciyata sanin cewa kaida Hajiya yanzu kunji zafin a raba d’ah da iyayensa kaman yanda kukayima Abbah... Wannan bai isheku ba Baba kukayi kukasan yanda kuka had’a aurena da Zulfa’u da zigan Hajiya naita muzgunawa Zulfa’u ina azabtar da ita dan kawai cikan burinku na ganin kun cuzguna ma dik wani jinin Abbah... Wllhi nayi danasanin yi maku biyayya tin fari... Nayi dana sanin auren Zulfa’u balle ku samu daman muzguna mata, wllhi da ace tun fari nasan manufarku kenan da ban aureta ba na k’yaleta tai auren soyayya da wanda take so, amma bawa baya tara sani da Ubangijinsa.... Aurena da ita na cikin k’addarar rayuwarmu... Kuma Alhamdulillahi ko yanzu na bar duniya naji dad’i Zulfa’u zata samu rayuwa mai inganci fiyeda wanda tai baya....Haka kurum sabida san zuciya irin taku kuka tarwatsa mana ahali kuka jefa gaba a tsakaninmu....!” Hawaye basu daina gangarowa a idanun Hafiz ba yake ci gaba da fad’in “Yau ga sakamakon dik munan abinda kuka aikata ko nace muka aikata muna gani... Dan haka kada ka kuskura kai yunk’urin cetona... Idan taimako daga gareka ne ka sani bana so...!!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci daidai sanda Sawwama ta shigo a birkice... Takalma a hannu d’ankwali a hannu tamkar mahaukaciya sabuwar kamu.... Birki tai ganin Baba Alhaji duk’e yana kuka ga Hafiz nan gabansa magashiyan wanda badon Farin sani da taiwa Hafiz d’inba da zata iya rantsuwa akan bashi bane canzasa akai.... Wani irin jahilar birki Sawwama taja tana d’ora hannu aka... Dik rashin imaninta da futsararta saida ta firgita ta razana da ganin Hafiz... Take jikinta ya d’auki karkarwa.... Ta nufi Hafiz d’in cikin tsananin tashin hankali, lokaci guda take furta “Hafizi na....!!! Hafizina kaine haka... Haka suka maka..??!” Banda jahilar duba da Hafiz Ke aika mata bai iya komai, hucin hakinsa kurum kake iya saurarowa sabida tsananin b’acin rai.... Tayo kansa gadan gadan... Daidai lokacin da ya ida tsinka igiyar da aka d’aure masa hannunsa da wata fashesshiyar kwalba da ya saci idanun yaran Babban Duna ya d’auka.... Yana nan likimo yana aika mata firgitacciyar kallo tamkar mayunwacin zakin dake kwanton b’auna ga dabban dake farauta..... Tana isowa Hafiz ya shak’o wuyarta da iyakacin k’arfin da Allah ya masa yana fad’in sai ya aikata lahira.... Yayinda Baba Alhaji ya mik’e yai kansa yana fad’in yazo su gudu kafin su Duna su k’araso... Fincika kurum Hafiz yake yana fad’in sai yayi ajalin Sawwama... Daidai sanda suka soma jiyo sautin jiniyan motar polisawa... D’aya daga cikin yaran Duna ne ya shigo a birkice yana fad’in polisawa sunyiwa ginin nasu zobe.... Duna da Magajiya dake tattaunawa na sirri a wani b’angare dake cikin kangon ginin shak’o wuyar Magajiya yai yana fad’in “Kin shirya hakan da polisawa ne... Saida kika bari bamuyi fitowar shiri ba.... K’aryarki tasha k’arya babu wanda ya isa yaga k’arshen Duna...!!” Magajiya na muzurai yake fad’in “Wllhi ban sani ba... Banida masaniya... Ta ya zan maka haka...? Dan Allah ka yarda dani Babba...!!” Fincikota Babba yaci gaba da yi bakin bindiga manne gefen kanta har suka k’araso yanda su Hafiz suke... Har wannan lokaci Hafiz bai saki Sawwama ba Baba Alhaji na janyesa.... Yaran Duna kaw tuni Sun fita suna fafatawa da jami’an tsaro, sai bata kashi suke tsakaninsu.... Yau dai rana ta b’aciwa su Babba dan layun da suke amfani dasu su ciza bindiga bata shigarsu harsashi bai kamasu idan jami’an tsaro sun tink’arosu basu fito dasu ba, Take Duna ya kuma lalumar aljihunsa... Nan fah yaji wayam, sai yanzu kalaman Hafiz ke dawo masa cewa sai yayi sanadin Capkesa, Wato wannan shine nufinsa, sace layarsa yai sanda yake k’ok’arin shafasa da burin biyan buk’atarsa dashi... Lallai ya yarda Hafiz shu’umi ne na k’arshe.... Babba Ya Muna laluma yaji da gaske fah babu... Wani irin k’ara ya saki had’ida sauk’ewa Magajiya k’otar bindiga a tsakar kanta wanda saida ya sanyata zubewa a k’asa... Da alama dai dubun Duna ne ya cika.... Sanda ‘yan sanda suka k’araso cikin kangon ginin take suka saitasu da bingoginsu suna fad’in “Freeze... Hands in the air.... No body moves..!!!” Gaba d’aya d’aga hannaye sukai alamun surrender banda Hafiz da ya zube wajen tamkar matacce... Baba Alhaji yai kansa yana ambato sunansa yana rungumarsa ba tareda yabi takan jami’an tsaro dake k’ok’arin hanasa yin hakan ba... Sawwama ma dai zube take wajen tana numfashi da k’yar sakamon shak’eta da Hafiz yai.... Su Magajiya dasu Duna dik haka suka d’aura hannayensu aka... Su Duna dai Babu layun da za’a ciza a gagari bindigar Jami’an tsaro sannan bata kashi da ‘yansanda sukai da yaransa sun kashe yaransa da dama... Yau saiga Duna masu uniform sun taso k’eyarsa gaba, gashi d’an tsakurkuri sai shed’ana da mugunta... Gasunk’umin d’an ta’addan da ya gagari jami’an tsaro... Wannan shine fa INDA RAI DA RABO.... Engr dasu Detective Najib ne suka k’araso wajen... Kallo guda Engr yaima Duna zuciyarsa ta tsinke... Tabbas dikda tsufa da shekaru da suka nuna a Fuskar Duna bai mancesa ba... Shine dai wancan d’an ta’addan da yai sanadiyar tarwatsewar ahalinsu... D’an ta’addan da ya tarwatsa ahalinsu Ammansa... Tabbas bazai mance fuskar Duna ba sanda suke nemansu mota bayan mota a lokacin da yake rungume da Daula, hanyarsu ta dawowa daga Jada zuwa Kano.... Lokacin da ya fantsama daji shida Daula yana mai k’ok’arin nema masu tsira daga wajen wad’annan azzalumai... Lokaci guda yaji k’walla na ciko idanunsa da tuni sun kad’a sunyi ja.... A daidai lokacin da Jami’an tsaro suka taso k’eyar babban d’an ta’adda wanda ya shahara ya kumayi k’aurin a fannin garkuwa da fashi da makami a fad’in k’asa baki d’aya Engr ya k’araso garesu had’ida masu umarnin su tsaya... Babu musu suka tsaya suna masu bin umarninsa domin kaw shid’in shi yai dik k’ok’arinsa wajen ganin an capke Duna an kuma ceto Hafiz kaman yanda yaiwa Akram alk’awari.... Duna ya d’ago jajayen idanunsa yana duban Engr dasu.... Engr dake tsananin huci d’an rank’wafo da kansa yai kad’an dan Duna sam baida tsawo, hannayen Engr hard’e a baya yake furta “Ka gane ni...??!!” Duna ya kauda kai gefe... D’aya d’ansandan ya buga masa bakin bindiga a k’eya yana fad’in “Yi magana mana..!!!” Duna yai wani salo da harshensa irin yanda yakeyi kana yace “Ba kaine d’an takaran mujerar gwabna a k’ark’ashin jamk’iyar Adalci party ba...!” Engr na tsnanin huci yake furta “Ba wannan nakeso ka tina ba...!” Duna ya kumayin salo da harshensa tamkar tsohon maye ba tareda yace komai ba.... D’ansanda ya kuma darara masa tsawa yana mai buga masa bakin bindiga... Dakatar da d’ansanda Engr yai Ta hanyar d’aga hannu kana ya kuma duban Duna cikin tsananin karaji yake furta “Nasan zaka iya tina Wani Soja a can garin Jada wasu shekarun baya da yaso ya kawo k’arshen ta’addancin ka... Ka kasheshi kabi iyalansa zaka hallak’a... Nasan zaka iya tina Sanda Iayalansa suke tsere maka a tashar mota... Akwai wani yaro cikinsu da kuma k’aramar yarinyar ta goye... Nasan ka tina... Nasan ka tina komai yanzu..!!!” Ya k’arashe hawaye na tsarto masa... Duna yabisa da kallo shaye da mamaki kana yace “So you’re that boy..!” Engr ya jinjina masa kai kana yace “And that boy is your downfall... Yanzu zaka girbi abindaka shuka..!!! Ku d’aukeshi daga nan..!!!” Ya k’arashe yana mai kauda kai gefe had’ida k’ok’arin saita kansa sakamakon hawaye dake k’ok’arin ciko idonsa... Juyowar da zai sukai ido hud’u da Mamy wacce basu jima da isowa ba,da alama taji tattaunawarsu da Duna... Kuma itama taso ta ganeshi cikin wad’ancan ‘yanta’ddan... Mamy na hawaye tana duban Engr, lokaci guda take furta “Ma’aruf... Shine wannan...Shine ya kashe Mahaifin mu... Bazan tab’a mance wannan bak’ar fuskar tasa ba... Shine..!!” Kuka yaci k’arfin Mamy yayinda Haule Ta matso ta rik’eta sosai jikinta a matuk’ar mace itama... Jinjina mata kai Engr yai yana k’ok’arin daidaita kansa kana yace “Yes Mamy... Shine wancan d’an ta’addan... D’an ta’addan da yai sanadiyar rugujewar ahalinmu...Yau Allah ya kawo k’arshensa shima... Zai kuma girbe abinda ya shuka..!” Ganin kukan Mamy na k’aruwa ya sanya Abba d’an janyo hannunta kad’an ya nufi mota da ita yana fad’in “Muje ki zauna Mariya... Kukan nan ya isa haka... Yau an kama wanda ya kashe Baba kuma za’a bi maku hakkinku.... Allah baya barin zalinci ya tabbata...!” Haka Abbah yaita bata baki har suka isa mota... Yayinda motoci jami’an tsaro sukaci gaba da zarya a wajen... Kasancewar jami’an tsaro sun gewaye wajen da igiyoyi na tsaro da gudanar da bincike yasa Haule bata samu daman tsallaka fence d’in ba.. Tana nan tsaye tana jimamin Ta yanda zata hango Hafiz d’inta.... Can ta hango wani kaman shi saman gado mai suffar keke irinta motar d’aukan majinyata Wato ambulance.... Haule ta rikice ta nufi wajen a d’ari tana ambato sunan Hafiz d’inta... Saidai sam kwance kawai Hafiz yake tamkar bai numfashi dan tuni ma jami’an lafiya dake taredashi cikin bayan ambulance d’in soma k’ok’arin d’aura masa na’urar oxygen dan ceton rayuwarsa... Haule hannaye bibbiyu aka take kuka... Yayinda Engr ke tsaye gefenta yana bata baki had’ida k’arfafa mata gwiwa cewa ta kwantar da hankalinta Hafiz zai sami lafiya da izinin Allah.... Haule dai kuka kurum take tana fad’in Hafiz kada ya tafi ya barta.. Can ta hangi Baba Alhaji dasu Sawwama dasu Magajiya an taso k’eyarsu hannayesnu rufe cikin handcuffs.... Tai kukan kura ta nufesu tana tsine masu albarka... Babu kaman Baba Alhaji da a cewarta dasa hannunsa aka tasamma hallak’a d’ansu... Taci gaba da kuka tana fad’in “Bazan tab’a yafe maka ba Alhaji.. Ka cuceni ka zalunceni... Wannan shine sakayyar da zaka min bayan shekarun da muka kwashe muna tare... Mu k’ulla tare mu warware tare, amma rana tsaka kabi wad’annan tsinannun Allahn ka amince a salwantar da rayuwar d’anka gudan jinjnka... Allah ya isa tsakanina da kai...!!” Baba Alhaji na kuka sosai yake fad’in “Haule wllhi ba laifina bane ki yarda dani... Wllhi tilasta min akai... Amma kinsan bazan tab’a yiwa Hafiz haka ba... Haule ina son d’ah na ina son d’anmu... Ki yafe ni Haule na...!!!” Haule na kuka take fad’in “Kada ka sake kiransa d’anka dan babu uban da zaima d’ansa na cikinsa haka kan wata shashashar mace.... Wllhi nayi dana sanin aurenka da duk wasu muggan abu da muka k’ulla tare a baya...!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka.... Engr dai sadda kansa k’asa kurum yai zuciyarsa na masa rauni... Wannan shine k’arshen dik wanda yace zai gina rayuwarsa kan zalunci... Akwai darussa masu yawa a rayuwar wad’annan ahali ta ko wanne b’angare.... Tabbas mahak’urci yana tareda riba, yau gashi su Mamy da sukai hak’uri har k’arshen mutumin da yai sanadiyar mutuwar mahaifinsu da tarwatsewar ahalinsu Allah ya nuna masu... Gashi yau an capke Duna dik ta’addancinsa, yau ga Baba Alhaji da matarsa mutanen da suka tasamma salwantar masu da d’ansu yaron da baiji ba bai gani ba sabida son zuciya irin nasu yau gashi su da kansu suna tuhuman juna da d’aura alhakin salwantar da nasu d’an a wuyan juna... Kaico irin wannan rayuwa... Ubangiji ka kiyashemu aikin dana sani da son zuciya...Ameen... Haka aka wuce dasu Magajiya aka jefasu bayan hilox yanda akewa criminals... Za’a haura da Baba Alhaji kenan ya hangi Abbah daga gefe idanunsa sunyi matuk’ar raunana... Baba Alhaji ya sadda kansa k’asa cikeda nauyin d’an uwan masa, lokaci guda ya rok’i d’an sandan cewa ya basa sakanni yai magana da d’an uwansa... Da k’yar d’ansandan ya k’yale Baba Alhaji yai magnar mintina da basufi biyu ba da Abbah... Kai a k’asa Baba Alhaji ke furta “Ka yafeni Usman... Ka yafe min dik abubuwan da nai maka.... Hak’ik’a naso tarwatsa ahalinka sabida son zuciya da k’yashi da hassada irin nawa, sai gashi Allah ya tsare maka ahalinka sabida shi baya mulki da zalinci... Yanda naso tarwatsaka sharrina ya koma kaina... Na tarwatsa nawa ahalin da kaina... Babu wanda zaiso ya sake d’aga idanu ya dubeni cikin iyalaina... Babu wanda zai yarda cikinsu cewa bazan tab’a yiwa Hafiz haka ba...! Usman ka yafeni... Wllhi wannan hakkinka ne Ke bibiyata... Naso na salwantar da Ma’aruf tun yana k’arami... Na tilastawa Mamani ta tarwatsa farin cikin dake tsakaninka da matarka Mariya ta hanyar d’aurawa Mariya laifin b’acewar Ma’aruf... Na kuma tilasta mata had’a auren Hafiz da Zulfa’u ba don komai ba sai dan na tabbata ahalinka babu kwanciyar hankali a tattaredasu.... Usman duk wad’annan abubuwan ni ne nan na tilastawa Mamani yinsu, tsangwamar Mariya da yaranta idan har tana so sirrinta na cewa ba ita ta haifeka ba ya rufu... Idan ba haka ba zan sanar dakai komai... Ba komai yasa nai haka ba sai dan sanin cewa kana matuk’ar k’aunar Matarka Mariya kuma ta haka ne kawai zan ganka cikin k’uncin rayuwa... Idan har ka rasa kwanciyar hankali da zaman lafiya cikin gidanka da iyalanka nasan tamkar rayuwar kawai kake amma Farin ciki ya k’aurace maka... Na kuma had’uda mata shed’aniya irin Haule sai na kuma samun wata dama...!” Baba Alhaji dake kuka sosai ya kuma had’e hannayensa waje guda yana rok’on yafiyar Abbah da ko d’agowa ya kalli Baba Alhajin ya kasa... Shin mai ya tsare masa da tsanani a rayuwa da har zai masa irin wannan k’iyayya... Ashe d’an uwa zaiso ya jefa rayuwar d’an uwansa cikin garari irin haka... Kai kaicon rayuwa mai cikeda tarin hassada k’yashi da mugunta... Ko duban Baba Alhaji Abbah bai iya yi ba sabida zuciyarsa dake tsananin suya da d’aci had’ida rauni... Yana jin sanda d’ansanda ya tasa k’eyar Baba Alhajin... Bai daina bud’e murya yana fad’in Abbah ya yafe masa ba had’ida cewa “Usman kamin rai ka d’aukar min lauya kada ka bari a yanke min hukuncin laifin da ban aikata ba na rok’eka Usman..!!!” Abbah dai rintse idanunsa kurum yai wasu irin hawaye masu d’umi suka gangaro masa.... Ganin yayi weak sosai yasa Engr K’arasowa ya tallafesa, gaba d’aya tausayin Abbah Mamy da Zulfa’u sun cika zuciyar Engr dan a gabansa Baba Alhaji yaita confessing muggan abubuwan da yaiwa d’an uwansa.... Ace d’an uwanka ne yai maka irin wad’annan abubuwan, baida buri face ya ganka ka tagayyara... Shin mai za’ai da k’iyayya hassada da gaba...Kaicon zuciya mai cikeda wad’annan cututtuka.... Engr bai bar wajen ba saida ya sanya one of his men ya maidasu Mamy gida... Itakaw Haule dama cikin ambulance d’in da aka d’auki Hafiz ta shige, sanin cewa magaifiyarsa ce ita shisa basu hanata ba... Tareda ita aka nufi asibitin... Daga bisani ne su Engr suka nufi police station d’in yanda zasu bada nasu statement d’in, Engr ya kuma filing wani case akan Duna... Toh Duna kanma dama nemansa ake ruwa a jallo dan haka cases d’in dake bisa wuyarsa ma bazasu lissafu ba, D’an ta’adda ne da hukuncin kisa ya hau kansa koda ma ba’aje kotu ba ballantana kuma aje.... Tsabaragen ta’addancin Duna bazai yuwu a Detaining nasa a nan police station kafin a shiga kotu ba dole aka tafi da Duna prison dan ajesa a police station na nufin an basa lasisin escape ne.... Tinda Engr ya sako k’afa a k’ofar ofishin Zo Kaga yanda manema labarai kesonji daga bakinsa duba da yanda ya jajirce a matsayinsa na d’an k’asa mai kishin k’asarsa ya kawo k’arshen wannan d’an ta’adda da ya gagari Al’umma... Sam Engr bai b’oye masu cewa ba shi kad’ai yai wannan yak’i ba harda su Hafiz su Akram Wanda suka sadaukar da rayukansu dan a kame wannan hatsababibin d’an ta’adda.... Kame Duna ba k’aramin Martaba da d’aukaka ya k’arawa Engr ba, dan tuni labari ya karad’e ko ina, hartaga jamk’iyarsu sunyi matuk’ar alfahari dashi tin ma bai d’ale karagar mulki ba yake sadaukarwa da jajircewa wajen ganin al’umman k’asarsa sun zauna lafia... Toh inaga ya hau kujerar mulki... Kai daidai da jamk’iyar adawa saida suka jinjina masa.... Jama’an gari kaw ya k’ara samun karb’uwa a wajensu dikda yace sam shi ba don haka yai ba.... Da jagorancin Akram aka tafi dajin Babba Duna aka kub’utar da d’inbin jama’an da ya sacesu ya ijesu dan amsar kud’in fansa Daga iyalansu.... Zo Kaga farin ciki wajen jama’a... Kan kace mai labari ya karad’e k’asa ko wane kafan yad’a labaru breaking news d’in da ake nunawa kenan.... Kame Duna ba k’aramin nasara bane dan zai bada dama ya zak’ulo duk wasu wanda suke mu’amala dasu na sace mutane da yin garkuwa dasu dan amsar kud’in fansa tinda bazai yarda ya tafi k’asa shi kad’ai ba ciki kaw harda gurb’atattun k’usoshin gwabnati da ake had’e bakin dasu akeyin wannan ta’asa.... Allah ka kawo mana k’arshen wannan ta’addanci a k’asarmu baki d’aya.. Ka yalwatamu da aminci da zaman lafiya had’ida shuwagabanni adilai masu jin k’an al’ummansu... Ameen Ya Rabbi..! Detective Najiba ne ya k’araso yanada Engr ke tsaye yana amsa waya wanda ko ba’a fad’i maka ba da sahibarsa ce sakamakon wane irin annuri da ya cika fuskar tasa... Saida Najeeb ya jira Engr ya ida wayar kafin ya k’araso gareshi ya risina yace “Sir, it’s confirmed... Muhibbah tana d’aya daga cikin manyan Drug dealers na k’asar nan... Shagunanta ana saye da cinikayyan kayan maye a b’oye.... Sannan tanada wasu shaguna a nan mak’wafciyar k’asarmu Wato Kamaru yanda suma aka smuggling miyagun k’wayoyi.... Sannan ta tabbata a gobe zasu fitar da kaya Ta wannan shagon nata na saida sark’ok’in mata.... Daga nan zamu executing plan d’inmu and capture them..!” Ya k’arashe yana mai nuna masa wata video na sirri da ya samu daga jikin CCTV footage na babban kantin Muhhibar.... Jikin Engr yai mugun sanyi ganin yanda ake tsaga soson gidan ‘yankunnaye ake jera muggan k’wayoyi sam bazaka zaci akwaisu ciki ba sai idan ka sani....Wato ta haka suke snuggling k’wayoyin ta yanda baza’a gane ba.... Take yaji wasu irin k’walla suna ciko idanunsa... Saurin mik’awa Najeeb wayar yai yana mai barin wajen cikin sassarfa.... Najeeb ya bisa da kallo cikeda tausayawa... *** A b’angaren Muhibbah kaw sai faman tsinuwa take tana ashar sabida plan d’insu bai working ba, Engr da tawagarsa basu fita taron campaign ba... Komai ya rushe mata ya ruguje, taso ganin downfall d’in Engr a yau... Taso a nuno fuskar Engr Ma’aruf MUTALLAB a yau a matsayin gurb’ataccen d’an siyasa mai b’ata matasa mai d’aurasu akan turban ta’amuddi da miyagun k’ wayoyi sai gashi Shamzy ta kunna mata TV yanda ake hasko fuskarsa a matsayin jan gwarzo mai k’aunar Al’ummarsa da k’ok’arin kawo sauyi a k’asarsa..... Wane irin k’ara Muhibbah ta saki had’ida jifan tv d’in tana mai furta “Wllhi k’arya kenan... Ma’aruf baka isa ba... Wllhi baka isa kai nasara ba muddin ina raye... Nayi azaman ganin downfall d’inka kuma sai na gani... Babu gudu babu jada baya... Kai kanka ka sani bana sadaukar da fad’a cikin sauk’i.... I’ll ruin your reputation is a promise..!!” Ta k’arashe tana tsananin huci wanda da gani kasan miyagun k’wayoyi sun fara zautar da kwanyarta.... Bash ne ya shigo yana shu’umin murmushi yake duban tv d’in lokaci guda yake furta “Seems your husband is now the hero of the country... Ya tashi Daga d’an siyasa ya koma mai kamen masu laifi.... Kar fah ya gangaro zuwa kanki...!” Ya k’arashe yana shu’umin murmushi.... Muguwar kallo ta b’allawa Bash kana tace “He wouldn’t dare to do that.... I’m the mother of his children... Bai isa yamin abu makamancin haka ba... Kuma kafin yaga downfall d’ina sai naga nasa....!” Bash dai murmusawa kurum yai kana yace “Muhibbah kar fad’anku da wannan mijin naki ya b’ata mana kasuwancinmu, Kinga manyanmu Daga sam ba zasuji dad’I ba....” Muhibbah ta b’alla masa harara kana tace “Na fad’a maka koda wasa bazai tab’ani ba... Babu abinda za’a fasa... Gobe za’a fitar da kaya, idan na caski wad’annan dalolin zan d’ibi yarana mu gudu mu bar k’asar... Engr bazai sake ganinmu ba....!” Jinjina kai Bash yai kana yace “I hope so domin I can’t afford to lose this millions....” Da wannan batu suka kwana a ransu na fitar da k’wayoyinsu zuwa k’asashen k’etare... Saidai kaman yanda suka shirya ba haka abin ya kasance masu ba... Ana tsaka da hada hada kaman kasuwanci gaske ake kwatsam jami’an tsaro suka bayyana.... Kan kace mai sun buk’aci kowa ya k’ame... Muhibbah da Bash da basu jima da isowa ba suka dubi juna.... Shamzy ma dubansu tai tana mamakin yau polisawa ne a kantinsu... Bash ya b’allawa Muhibbah kallon tuhuma... Lokaci guda ya d’anyi k’asa da kansa kad’an yana mai furta “What is this Muhibbah...? Mai jami’an tsaro suke a nan...? Setting d’inmu up kikai...?” Muhibbah na muzurai take furta “Ta ya za’ai nai haka Bash... I have no idea mai ya kawosu nan...!” Lokaci guda ta k’arasa ga Jami’an tsaron tana mai furta “Em officer Lafiya mai ya kawoku nan... Bazai yuwu ku shigo cikin Kantina kuna d’agawa customers d’ina hankali ba... We are not selling any illegal item here... As you can see wannan shago ne na kayan k’arau....!” Officer ya jinjina kai kana yace “In that case we are going to search the area..” Dik k’ok’arin Muhibbah na ganin ta cire tsoro tattareda ita saida ‘yanhanjinta suka murd’a... Ta daburce lokaci guda, ta shiga k’ok’arin hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu saidai batada ikon yin hakan.... Take sukaci gaba da search d’insu tareda jagorancin Detective Najeeb... Haka suke ciro gidan ‘yankunnaye da sark’a suna zazzagewa suna tsaga soson ciki da ake d’aura sark’ok’in bisa... A cikin search d’insu suka samu wasu... Take d’ansanda guda ya k’adadi yana sarawa ogan nasu had’ida furta “Positive Sir...!” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un...! Ai take Muhibbah ta soma masu bore tana fad’in sharri aka k’ulla mata... Ko saurarenta ‘yansanda basuyi ba suka shiga kamensu da masu cinikin nasu.... Muhibbah na fincika tana fad’in su sanar da ita munafukin da yai mata cune kwatsam sukai idanu hud’u da Engr..... Fincika ta shigayi tana tsananin huci take fad’in “It was you... How dare you Ma’aruf... Ta ya zakai haka ma uwar ‘ya’yanka.... Bazan tab’a yafe maka ba Ma’aruf....!!!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka.... Girgiza kai kurum Engr yake cikeda tausayinta, lokaci guda yake furta “I’m sorry Muhibbah... But I have no other choice... Bazan iya zama ina gani kina aikata b’arna da tarwatsa rayukan al’umma ba... Muhibbah I can’t turn a blind eye... Ba haka naso al’amra su kasance ba but you weren’t listening to me Muhibbah... Wannan shine sakamakon ayyukanki... Kiyi hak’uri kije ki amsa laifukanki ni kuma na miki alk’awari I’ll never leave your side Muhibbah... We would face this together har ki gama serving sentences d’inki... Idan har da gaske kinyi tuba na hak’ik’a...!” Ya k’arashe cikeda tausaya mata... Cikin kuka take furta “You did this on purpose Ma’aruf... So kake dama ka cireni daga cikin rayuwarka dan ka kasance da wancan bamagujiyar amaryar taka, shine bari kamin k’age... Sarai ka sani laifin smuggling k’wayoyi zai shafe mutum sama da shekaru goma sha biyar a gidan yari shine zaka wani ce tare zamu facing komai... Ka cuceni ka cuceni Ma’aruf... Wllhi bazan tab’a yafe maka ba, kuma bani buk’atan dik wani taimako daga wajenka... I’ve my own money da zan d’auki very good lawyer da zai kareni gaban Alk’ali dan wllhi bazan tafi prison ba, zan fito kuma zan k’wace yarana daga gareka... Mugu kawai azzalumi mai sak’a alkhairi da sharri... Bayan dik abinda Baba Mutallab yai maka ta haka zaka saka masa cin amanar da ya d’auka ya dank’a maka... Wllhi bazan tab’a yafe maka ba Ma’aruf..!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka yayinda ‘yar sanda macen ta kuma hankad’a k’eyar Muhibbah tana fad’in “Shige muje.. Criminal..!” Lumshe idanunsa yai a hankali sanda aka shige da Muhibba wasu irin hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro masa... **** ABUJA Jiki a matuk’ar sanyaye Siyama ta d’ago tana kuma duban Daddy da Ammi da suka ida mata nasiha kan tai hak’uri Ta amshi k’addarar rayuwarta yanda yazo mata, ta zauna da mijinta da abokiyar zamanta lafiya.... Share k’wallan da suka gangaro mata Siyama tai kana ta kuma k’arasawa jikin Daddy Ta rik’o hannayensa lokaci guda take furta “Daddy please forgive me... Kuma kace Aunty Daula ta yafe min... In sha Allahu I’m a changed person now...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Janyo kanta gefen k’irjinsa Daddy yai yana mai furta “Come here my little princess.... Baki min komai ba sannan Daula ma bata rik’eki ba.... Dukanmu ‘yan adam ne masu aikata kuskure kinji koh.... Ki sami Mijinki ki bashi hak’urin dik abubuwan da kika aikata masa marassa kyau... Ubangiji yai maki albarka Mamata...!” Ya k’arashe yana shafa kanta... Hawaye suka kuma gangarowa Siyama, lokaci guda ta rungume Daddy tana mai furta “I love you so much Daddy...!” Daddy yace “I love you too my Baby...!” Ammi dake gefe d’an yatsarta ta saka ta goge hawayen da suka gangaro mata daidai sanda Ijlaal ta shigo ta fad’a jikin Siyama a guje tanai mata oyoyo had’ida furta ta tafi batai mata sallama ba kuma tayi kewarta sosai... Siyama ta kuma matse yarinyar cikin jikinta tana mai fad’in “Oh I’ve missed you too my little angel.... I’m sorry I had to leave without saying goodbye the other time... Kiyi hak’uri bazan sake ba kinji...!” Turo baki yarinya tai tana mai kuma shigewa cikin jikin Siyamar take fad’in “Aunty please don’t leave us ever again.... Wait..! Aren’t family supposed to be living together..? Maiyasa zaki tafi Toh....?!” Ta k’arashe tana kuma turo baki gaba had’ida yin rau rau da idanu... Duban Ammi da Daddy Siyama Ta d’anyi taga dai zuba masu idanu suma sukai murmushi saman fuskokinsu... Hannayen Ijlaal Siyama ta d’an kamo kana tace “Princess do you remember the other time you asked me if I have a husband..?” Ijlaal ta jinjina kanta alamun eh.. D’an dafa kanta Siyama ta kumayi kana tace “Well, yes I do have a husband... And I have to go and live with him...” Ta k’arshe murmushi saman fuskarta bata daina shafa sumar Ijlaal ba... Ijlaal ta d’an tab’e baki kad’an kana tace “Is that so... Then I’ll follow you to your husband’s....Don’t you want me there...?” Ta k’arshe kaman mai shiri kuka... Siyama ta qare idanunta had’ida fad’ad’a murmushinta kana tace “That would’ve been very very beautiful my princess... Idan Daddy da mummy zasu barmu of course tare zamu tafi...! Ta k’arashe tana mai kuma janyo yarinyar cikeda farin ciki... Ijlaal ta juya tana duban mahaifin nasu cikin ‘yar tsallenta take fad’in “Please please Daddy say yes...!” Aunty Daula ce ta shigo parlorn rik’eda tray na fruits tana mai fad’in “Aiko da mun huta da fitina maza akaiwa Aunty Siyama tacan...” Gaba d’aya d’an darawa sukai Siyama na fad’in “My baby batada fitina... She’s the most calm girl in the entire Nigeria... Right princess...!” Tsalle Ijlaal ta kumayi ta haye jikin Siyama tana murna... Ammi ke tambayar Aunty Daula ko Nabilah ta ida shiri dan anjima da dare ake shirin kaita gidan mijinta Khalid dake nan Abujan.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *109* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Aunty Bara’atu da Siyama ke tayata shiryawa... Wai har Siyama ce ke nad’a mata lafaya, oh Allah mai iko shin waye zai tab’a zaton Nabilah da Siyama zasu zauna inuwa guda.. Lallai ikon Allah ya wuce gaban wasa, ita kanta Nabilar duban Siyama kurum take yanda take ta k’ok’arin shiryata Wai saikace ba Siyama ba... Siyama dai fah Matar Ya Ma’aruf kuma ‘yar uwar Khalid da ta d’auki karan tsangwama ta saka mata yau gasu nan kaman basu tab’a k’yamatan juna ba, kai gaskiya babu abinda za’ai da k’iyayya da gaba... Kubura ce ta turo k’ofar ta shigo sai wage baki take tana fad’in “Yau dai sai gidan angon biyoo (bear) sharupkan d’in Nigeria.... Aje can ayita zuba soyayya muna nan muna tagumi...” Siyama ta watsa mata harara sai kuma ta dara a hankali dan harta Nabilar ma dariya ta bata... Siyama tace “Yanzu kin aje makaman yak’inki kenan kin rungumi K’addara.....” Kubura ta wani murmusa a dole taji kunya kana tace “Ni kaza...kar kisa amaryar beyoo ta zauneni...wllhi Aunty Siyama dama wancan uwar iyayi d’in taki ce banso ya aura amma Ammi ta dage... Ai wllhi yafi k’arfin class d’inta... Amma yanzu tinda ga teddy ai hikenan, suje suci soyayyarsu muna nan muna zuba tagumi....” Darawa suka kumayi Siyama na fad’in “Zaki maimaita a gabanshi....” Tana maganan tana duban k’ofa yanda Khalid ke k’ame ya hard’e hannaye... Sam Kubura batasan yana tsaye wajen ba taketa zuba yawa an bud’e famfo... Kaikaitowan da zatai ta hangesa k’ame wajen yana sauraren abubuwan da take fad’i, fuskar nan nasa a murtuk’e kuwa... Tashin sense, ai Kubura batasan sanda ta had’iyi wani miyau da ya tokare mata mak’oshi ba... A daburce ta aje aikan data shigo dashi daga wajen Ammi tana mai furta “An Anty Siyama dama dama wannan na kawo... Inji Ammi ne, Wai na Anty Nabila ne...” Ta soma k’ok’arin risinawa tana gaida Khalid da ko kallo bata ishesa ba ya wane had’e rai sosai...Ai a d’ari ta fice k’afafunta har suna hard’ewa.... Siyama tabita da kallo tana dariya take fad’in “Ki dawo ki maimaita dik abinda kikace gabansa...” Ai inaa ko tsayawa Kubura batai ba suna iya jiyo yanda take sauk’a daga matakalan cikin gudu gudu tana mai fad’in ta shiga uku.... Gajeren tsaki Khalid yai kana ya ida shigowa cikin d’akin... Siyama ta dubesa tace “Haba Khalid yarinyar nan tanaji da kai amma kai ko ‘yar gaisuwan nan bata shiga tsakaninku..” Gajeriyar tsakin ya kumayi kana yace “Toh ni sa’anta ne... Ni bansan mai ya hana Ammi maida wannan mahaukaciyar yarinyar garinsu ba, ta jima a birni amma ta kasa wayewa...” Siyama ta d’an dara kad’an kana tace “Aiko Ammi da Kubura sai Allah.. Kubura ai ta zama d’iyar Ammi k’anwarka mai bi maka...!” Ta k’arashe teasingly... Gajeren tsakin ya kumayi yana mai sakala hannayensa cikin aljihu lokaci guda yake jifar Sahibar tasa da wani irin duba ganin tai banza dashi tamkar batasan ya shigo ba... Siyama ta d’an saci kallon Nabila ta kuma duban yanda Khalid ya kafeta da idanu kana ta bud’e murya tace “Wai wa yace maka ango yana ganin Amarya before akaita... Kaga ka fita kafin na kirawo maka Aunty B....” Baice komai ba saima tsimewa da ya kumayi, lokaci guda ya kuma duban agogon dake d’aure hannunsa kana yace “Nifa idan bazaku kaita ba ne zan d’auki matata mu tafi...” Wannan karon baki sake Siyama ke dubansa kana tace “Lallai abu ya girmama, Allah shi huci ran angon teddy bear nai maka na Kubura... Kaga Partner muke jira shi zai kaimu...” Khalid ya d’an dubeta kad’an kana yace “Sameer fah suna tareda Daddy tuntuni downstairs... Please Siyama ki azalzala masu ku fito ku tafi, ni badon ina jiran Baffah ba da tuni na d’auketa mun tafi, I can’t wait any longer...” Ya k’arashe maganar yana zaro wayarsa cikin aljihu... Har lokacin nan bakin Siyama a rik’e yake kana ta dubi Nabilah ta ida aika masa harara tace “Toh Nabilah kin dai ji angon naki, Kafin ya bamu kunya gaban sirikai bara naje nacewasu Aunty su fito mu tafi tinda Sameer d’in ya k’araso...” Ita dai Nabilah batace komai ba saima sadda idanunta k’asa da tai tana mai ci gaba da aika masa harara ta k’asa k’asa.... Aiko Siyama na ficewa ta kuma d’agowa tana mai ci gaba da b’alla masa harara, tana ji yana yiwa Baffah kwatancen gidan.... Saida ya ida wayar ya tsaya yana d’an ci gaba da shafa wayar na wasu dak’ik’ai kana ya kaikaito yana dubanta yanda tasha mur sosai... Murmushi ya saki a hankali kana ya tako kad’an ya k’araso gabanta... Tinda sama har k’asa yake k’are mata kallo yanda lafaya d’in ya zauna sosai jikinta, ya mata kyau sosai tamkar dominta dama aka k’era.... Hannayenta ya kamo yana mai furtawa a hankali “Teddy bear kinyi kyau...!” Ganin har lokacin kanta kife yake gashi tamau a murtuk’e ya sanyashi saka hannu ya d’an d’ago hab’arta kad’an, bata dubesa ba saima kauda kanta gefe da tai... K’uri yai mata yana dubanta, dan sosai ya hango k’walla tab idanun nata... Ya d’an gyara tsayuwarsa a hankali kana yace “Teddy bear aren’t you excited... Gidanmu fah zamu tafi... Finally Allah ya cika mana burinmu... Baki Farin ciki da hakan Nabeela... Ko na miki wani abu ne...?” Ya k’arashe murya a d’an raunane... Hannu tasa tana share hawayen da suka d’an gangaro mata kana tace “Mamy nake tinani da Abbah...!” Ya saki sassanyar murmushi a hankali cikeda tausayinta, kana ya kuma kamo hannayenta yai masu masauk’i saman sofa... Hannayensu ya sakala cikin na juna kana yaci gaba da fad’in “Yanzu ni ne Abbah kuma ni ne Mamy, I’ll take care of you kaman yanda sukeyi koma fiyeda yanda sukeyi...” Ta d’an dubesa kad’an... Jinjina mata kai yai alamun tabbatarwa kana yaci gaba da fad’in “Nasan Mamy bata goyonki toh ni har goyaki zanyi.. Yayi maki..?” Dariya ya bata wannan karon, ta d’an dara kad’an don tasan k’ok’ari yake ya cheering d’inta up... Shigowansu Aunty Bara’atu da Aunty Daula ne ya sanya shi mik’ewa yana d’an sosa kai, yayinda Nabilar ma tai saurin matsawa Daga kusansa.... Gaisar dasu Khalid Aunty Daula sai zolayarsa take ya biyo sahun matarsa tinda sunk’i kai masa... Murmushi kawai Khalid yake har ya fice Daga d’akin bata daina zolayarsa ba... Tuni Aunty B ta k’arasaga Nabilah da tuni ganin k’annen mahaifiyar tata ya kuma sanyata kuka... Tare suka zaunarta sukai mata nasiha mai tsuma zuciya musamman duba da iftila’ain da suka fuskanta a rayuwa gashi yau komai ya zama tarihi, Aunty B taci gaba da fad’in tabbas cikin rayuwarsu na baya akwai darasi sosai gameda alfanun hak’uri tinda taga ga yanda yau hak’urinsu ya kawosu... Mahak’urci dama ance mawadaci kuma Allah da kansa yace yana tareda masu hak’uri... Kuma shakka babu hak’uri ta kaisu ga cin nasaran rayuwa... Haka dai sukaita mata nasiha kana sukace zasu tafi su kaita gidan mijinta... Nabilah ta kuma fashewa da Sabon kuka tana rungumar Aunty Bara’atu tana fad’in “Aunty dan Allah kada ki tafi ni dai ki barni....” Gaba d’aya sai ta raunana masu zukata suma... Aunty B ta d’ago fuskarta tana share mata hawayen lokaci guda take furta “Haba Nabila, Kukan nan ya isa haka... Kuma ma banda abinki ga Auntynki Daula kuna nan tare gari guda, gobe da yardar Allah nima zan d’auki hanyar Kano... Kiyi hak’uri Ki zauna kiyi biyayyawa mijinki da sirakanki kinji. Balle ma ke kika mori dangin miji, suna matuk’ar k’aunarki kuma dik auratayya ya riga ya had’a dik an zama tushe guda... Kiga dai yana Siyama ke nan nan dake yanzu daga ita har mahaifiyarta, ki gode da wannan rahama da Ubangijinki yai maki kinji... Kema Ki k’aunacesu yanda suke k’aunarki Ubangiji ya baku zaman lafiya ya azurtaku da zuri’a d’ayyiba... Mamy zatafi kowa Farin ciki idan taji yanda Allah ya sauya zukatan sirakan d’iyarta Daga k’iyayya zuwa soyayya mai tsafta...!” Ta k’arashe murmushi kwance saman fuskarta... Murmushi Aunty Daula ma take kana ta k’araso ta rungumesu su duka uku... Aunty B tace “Oya muje Yayanki Ma’aruf na k’asa yana jiranmu...” Jiki a matuk’ar sanyaye Nabilah ta mik’e tabi bayan iyayen nata kanta a k’asa... A nan parlorn k’asan suka taddasu Daddy Ammi da Kuma Sameer d’in... Daddy ya kumayiwa Nabilah nasiha da wasilci da hak’uri sannan yace shi d’in kaman Abbanta ne babu wani surkunta, ita dasu Siyama su Ijlaal duk d’aya suke wajensa kaman yanda Sameer yake wajensa... Haka Daddy yai masu addu’a da fatan alheri Ammi ma Ta tofa nata albarkacin da fatan alheri, harda rungumar Nabilah tai mata rakiya har mota tana kuma jadadda mata dik Khalid yai mata wani abin waya kawai zata d’aga ta kirata ta sanar da ita... Su dai su Aunty Daula sai dariya suke ganin yanda Ammi ta hak’ik’ance cewa idan Khalid yaima Nabila wani abin ta kirata right away Ta sanar da ita zatai maganinsa ne... (Wayaga su Ammi mai sirka an tuba... Lol).... Siyama na gaba, Sameer Ke driving saiko su Aunty Daula da Aunty Bara’atu da suka saka Nabila a tsakiya... Koda suka isa gidan Aunty D da Siyama ne suka haura da suitcases d’inta sama, suka shirya mata kayan tsaf cikin sip, suka kuma gyara gidan dikda a gyaren yake.. Ko ina very need and beautiful.... Aunty B da Sameer kaw suna k’asa suna kuma yiwa Nabilah nasiha da bata hak’uri.... Sameer ya kamo hannayenta cikin nasa kana yaci gaba da fad’in “Khalid mutumin kirki ne, and he loves you very much... After all, you deserve all the happiness in this world...little sis, come here give me a hug....” Ya k’arashe yana bud’e hannayensa, cikin sauri ta k’arasa ta rungume d’an uwan nata tana hawaye... Siyama da sauk’owarta kenan tai tsaye tana dubansu, jikinta a matuk’ar sanyaye take taji hawaye na gangaro mata... Ta d’an saka bayan hannunta ta goge hawayen... Lokaci guda Aunty Daula ta k’araso, ta isa ta d’an rik’o hannun Siyama, murmushi Siyama ta sakar mata had’ida d’aura kanta bisa kafad’ar Aunty Daula... Idan kaga wannan ahali a halin yanzu dole su birgeka su kuma baka sha’awa... Haka suka tafi suka bar Nabilah da kewa... Ta mik’e tana bin tsarin d’akin da kallo dan kafin su tafi saida Siyama da Aunty Daula suka rakota har nata d’akin... Komai gwanin ban sha’awa... Taji wani irin sanyi mai cikeda ni’ima na ratsa dik wani k’ofa na zuciyarta... Tana nan tsaye tana faman k’arewa d’akin kallo taji alamun tsayuwar mota... Cikin sauri ta isa ta janye labulen window d’in tana lek’e... Khalid ta hango tareda Baffah.. Baffan ne yai dropping nasa dan tana ji Khalid d’in na cewa bazai shigo ba... Baffah yace a’a dare yayi gobe kafin ya wuce dai zai tsaya tinda dama mak’asudin zuwansa duba jikin Daddy ne kuma yayi abinda ya kawosa... Khalid yai k’wafa a hankali kana yace “Dama kanada mutunci ne... Idan kaga dama goben ma kai tafiyarka kada ka tsaya dan Allah...” Baffah ya dara yana kuma lek’o kansa ta glass d’in mota yake ci gaba da fad’in “Ban isa ba ai Gimbiya Yusrah ta bada sak’o a kawo wa k’awarta kaga dole na tsaya na bada sak’on Sarauniya kada a hukunta ni...” Darawa kad’an kurum Khalid yai kana sukai sallama, Nabilah kaw mamaki ne tsantsan ya cikat... D’an darawa tai a hankalk ita kad’ai tana mai kuma shan mamaki kana tace “Shegiya Yussy Wato ashe ashe dai soyayya suka k’ulla da Baffah Aiko asubahin fari zan kirawo ‘yar duniya nasha labari...” Jin kaman sautin steps d’insa alamun yana haurowa ya sanyata fad’uwan gaba, tai saurin k’arasawa tana janyo mayafinta... Tsulum ta zauna saman gado had’ida rufa mayafin, sai faman wasa da yastun hannunta take....Tana jin alamun ya shige nasa d’akin ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida yaye mayafin... Tinanin Yusrah ya kuma fad’o mata, ai bazata iya jira till tomorrow ba, cikin sauri ta janyo wayarta ta shiga dialing layin Yusra, bata d’aga ba, nan ta kuma bud’e shafin sada zumunta na whatsapp tana magana ma Yusran ta nan... Shiru shiru tana jiran reply d’inta har dai ta soma bin sauran wasu sak’onnin nata da suka shigo wayar yanda ta lek’a group d’insu na makaranta ta tadda tarin congratulations da fatan Alheri da akaita aiko mata.. Murmushi take tana bi d’aya bayan d’aya tana karantawa... Hardai ta soma kaman gyangyad’i... Sam bataji alamun shigowarsa ba sai fitannen k’amshin shower jell had’ida wasu arnan perfumes da sukaima k’ofofin hancinta sallama... Tai saurin ware idanunta sai ganinsa tai duk’e gabanta ya k’ura mata idanu, kyakkyawar murmushi saman fuskarsa da hasken k’wan wuta ya haske tarau... Ta d’an zabura ta tashi zaune tana kuma dubansa, sanye yake cikin silk jallabiya mai ruwan sararin samaniya... Ta shiga murtsuka idanunta da hannayenta biyu... Dariya taso basa kana yace “Wai haka kike bakida wahalan bacci... Oya taso kije kiyo alwala ina jiranki...” Ya k’arashe yana mai mik’ewa had’ida zama bisa gadon, lokaci guda ya kafe wayarsa da idanu kaman mai tura sak’o... Kaman mai tsoron sauk’owa daga saman gadon haka ta sakalo k’afafunta k’asa, harga Allah wani irin fad’uwan gaba da nauyinsa takeji... A hankali ta furta “Nifa nayi sallah...!” Ba tareda ya dubeta ba yace “Na sani zamu sake wani daban ne...” Idanunsa naga wayar salulansa yai maganar... A hankali ta mik’e daga saman gadon ta soma tafiya tamkar kazar da k’Wai ya fashema a ciki... Ya saci kallonta yana mai sakin murmushi da gefen bakinsa... Yana nan zaune wajen ta fito sai faman yarfe hannunta take, neman hijab ta somayi, aka kaw yi sa’a tana bud’e first drawer ta gansu a jere, ta d’auko guda d’aya tazira kana ta k’araso cikin d’akin kanta a k’asa... Khalid da tin fitowarta idanunsa ke kanta mik’ewa yai ya nufota yana mai karantar yanayinta... Saida ya d’anyi gyaran murya kana taga ya shiga janyo hannunta yana fad’in “Let’s go...!” Ita dai d’aga k’afafunta kawai take tana biye dashi har suka iso d’akin nasa wanda shima ya had’u iyaka had’uwa.... Nan ta tadda har darduma ya shimfid’a masu, gidan gaba da’aya sai k’amshi yake dan su Siyama saida suka tirara gidan da turarruka masu k’amshi kafin su tafi... Nan Khalid yajasu sallah raka’a biyu... Ya jima yana addu’o’i da mik’a godiyarsa ga Rabbil Izzah da ya nuna masa wannan rana mafi kyau cikin rayuwarsa... Tana jin sanda ya juyo ya d’aura hannunsa na dama saman goshinta ya karanto addu’o’in sabbin aure kaman yanda yazo a shari’a... Nan yai mata ‘yan tambayoyi gameda addini musamman abinda ya shafi fiqhu, ita har mamaki ma abin yaso bata ganin yanda yake zayyano mata tambayoyi gameda addini sam batai zaton yanda yake d’an gayun nan yasan addini har haka ba.... K’uri yai mata yana kallon yanda tai relaxing jikin bedcover da ya sauk’o ya rufe jikin gadon Daga k’asa... Ya d’an labgab’e kai kad’an kana yace “Ya naga kina lumshe idanu badai bacci kikeji ba...” Gajeren murmushi tai ba tareda cewa komai ba... “Wait, you can’t go to bed without eating anything... I’ll be right back...” Bai jira cewarta ba ya fice... Ta samu daman k’arema d’akin nasa kallo... A ranta take cewa Wato shi fah wannan andai yi d’an gayun gaske, ta kuma tab’e baki kad’an kana ta isa gefen tv dake a cikin d’akin tana bin cd plates na TV games dake zube wajen da kallo... A ranta tace oh shi kuma k’ato dashi Wai game yake bugawa... Nan ya taddata tsaye tana duba plates d’in... Ya isa saman rug ya aje gasasshiyar chicken da yoghurt d’in dake hannunsa, bata ankara ba sai jin jikinta tai cikin nasa ya mata rumfa Ta baya, hannayensa ya mik’o ya d’aurasu saman nata yanda tai rik’eda gidan cd plate d’in ya shiga juyawa tareda hannunta, tamkar mai rad’a saitin kunnenta yake furta “Do you want to play...?” Nabilah da gaba d’aya a daburce take d’an girgiza kai tai kana tace “Besides I don’t know how to play TV games...” Dagajin yanda take maganar kasan da k’yar take.... Idanunsa a lumshe still hab’arsa saman wuyarta yake furta “Don’t worry I can teach you... Besides indai muna tare dole ki iya playing... Come let’s eat first...!” Ya k’arashe yana mai janyo hannunta yai masu masauk’i saman rug d’in... Ya soma k’ok’arin bata a baki ta d’an mak’e kafad’a tana fad’in ita ta k’oshi... Wannan karon mur yasha sosai kana yace “No teddy bear you must eat something...Oya open your mouth..!” Ganin yanayinsa babu alamun wasa ciki ya sanyata bud’e baki babu shiri... Haka yaita bata idan tak’i bud’ewa ya d’aure fuska sosai har dai saida ta saka masa kuka tana fad’in ita ta k’oshi kana ya K’yaleta... Janyota jikinsa yai yana lallashinta kana yace suje su buga TV game... Haka Khalid yai mata matashi cikin jikinta dikda cewa har yanzu d’ard’ar take dashi... Suna nan a haka suna buga game d’in har Ta soma dariya ganin sai lallasa mata yake dan ita bawai ta iya bane, sai gashi kaman zai barta taci sai kuma yaci wasan... K’arshe jifa tai da control path d’in ta shiga kai masa duka tana fad’in that was cheating.... Sosai yake dariya yana kare dukan har dai ya janyota ta fad’o saman k’irjinsa....K’irjinta ya tsananta fad’uwa, Khalid yana iya jiyo yanda zuciyarta Ke bugawa da sauri da sauri, tsoro ya nuna sosai saman fuskarta, tai k’ok’arin yunk’ura zata tashi amma saiji tai ya kuma rik’ota sosai....Daga nan ne wasan nasu ya canza salo daga TV game, wasanda k’wak’walwrta da tinaninta suka gaza d’auka, gaba d’aya yau d’in bear d’in nata ya canza mata...(Nima dai k’wak’walwata ta gaza d’aika dan haka na janyo masu k’ofa na fito.. Lol)... *** A hankali ya bud’e idanunsa ya sauk’esu kan kyakkyawar fuskarta, da gani kasan baccin tsoro da azaba kawai take, ga ragowar hawaye yanda suka bushe saman fuskar nata... Abubuwan da suka faru daren jiyan sukaita dawo masa... Tausayinta da soyayyarta na kuma ratsa duk wasu k’ofofi na zuciyarsa... A hankali ya sumbaci saman lumsassun idanunta yana mai furta “Thank you for last night teddy bear... Thank you for making me the most happiest man on earth....I love you so much... So much..!” Ya k’arashe cikin sigan rad’a yana mai kuma sunbatan labb’anta a hankali.... Tana jin sanda ya bar saman gadon wasu hawayen suka kuma gangaro mata, ta bud’e lumsassun idanunta a hankali sanda ta tabbata ya shiga bathroom tana yunk’urin tashi da k’yar, amma mai? Ji tai kaman an dadd’ure gab’ob’in jikinta... Ta kuma lumshe idanunta a hankali ita kad’ai tasan mai takeji, da k’yar ta iya tattaro duk wani strength d’inta ta mik’e da bin bango ta bar d’akin dan bazata iya zama ya fito ya taddata ba... Koda ta shirya a nata d’akin lamo ta kumayi saman gado abubuwan da suka faru daren jiya suna kuma dawowa kwanyarta kaman wani a mafarki, wasu abin ta d’an saki murmushi dan ita da kanta sai yanzu take baiwa kanta dariya, wasu abin kaw saidai ta d’an rintse idanunta had’ida rufe fuskarta da tafukan hannu alamun taji kunya... Tana jin k’aran tab’a k’ofarsa alamun zai fito ya sanyata saurin lumshe idanunta tamkar wata mai bacci... K’amshinta ne ya soma masa sallama kana ya hangeta kwance saman gado, tana sanye cikin atampa mai laushin gaske d’inkin riga da skirt wanda ya zauna d’amas a jikinta, ya saki murmushi a hankali had’ida takowa cikin d’akin gefenta ya zauna yanda fuskanta yake kallo, bugun k’irjinta ya k’aru musamman da taji k’amshin nasa yana ratsa k’ofofin hancinta... K’uri yai mata yanda idanunta Ke rawa alamun ba bacci take ba, ya kuma murmusawa da gefen baki kana yakai hannu ya d’an shafi fuskarta yana fad’in “Teddy bear I know ba bacci kike ba, oya bud’e idanunki mu gaisa...” Shiru tak’i bud’ewa saima damk’e idanun da ta kumayi... Ya kuma murmusawa a hankali yana mai furta “Toh shikenan idan bazaki bud’e ba zamu kuma playing TV game yanzun n....” Ai Baikai aya ba ta bud’e tana mai shirin saka masa kuka.... Sosai ta basa dariya ganin yanda dik ta wani birkice, a ranshi yace ko ina tsiwan da masifan yau suka tafi....? Janyota yai cikin jikinsa yana mai k’unshe dariyarsa yake fad’in “Is ok teddy bear wasa nake miki...Tv game ya huta abinshi... Wai haka kikeda tsoro kaman farar kura teddy bear..!” Baikai aya ba suka soma jiyo horn daga gate... D’aga idanunsa yai yana duban agogon bango dake mak’ale jikin garun d’akin ya nuna k’arfe 10:15am... A hankali ya furta “who could that be..?” Ya mik’e a hankali yana mai furta Bara ya duba, ita dai jinjina masa kai kurum tai had’ida bin bayansa da kallo, sai yanzu ta samu ta k’are masa kallo, sanye yake cikin lallausar yadi navy blue anyi mata d’inkin half jampa mai gajeren hannu, yayi kyau sosai da ka gansa kaga sabon ango... Kafin ya k’araso k’asa har security ya bud’e masu gate, Siyama ce rik’eda hannun Ijlaal sanda Khalid d’in ya bud’e masu k’ofa.. Ijlaal ta fad’a jikinsa a guje abinka da d’anuwa.. Nan ta shiga zuba masa zance tana tambayarsa Aunt Beels... Ya d’auketa ya aza a kafad’a suka nufi cikin parlorn suna gaisawa da Siyama... Daga sama tana sauraro murya kamanta Siyama, dan Siyama muryarta mai d’an gwab’i ne sannan irin mutanen nan ne masu magana da sauri sauri.... Jim kad’an taji an bud’e k’ofa, Ijlaal ce ta fad’a jikinta cikeda murna, Nabila ta rungume yarinyar cikeda Farin ciki itama, nan take labarta mata tareda Aunty Siyama suke da Uncle Sameer zasu wuce Kaduna tare, ama Uncle Sameer na mota yana jiransu bai shigo ba... Nabilah ta d’anja hancinta tana tambayarta su Aunty Daula dasu Humaira.. Nan take sanar da ita Aunty B ma Ta wuce Kano yau... Su Daddy dasu Ammi da Aunty Daula kawai aka bari gida... Ijlaal sarkin surutu haka taita cika Nabila da zance dikda yau d’in Nabilar ba wani biyeta take ba dan itama fama da kanta take... A can parlor kaw zaman Siyama da kad’an saigasu Kubura da Karima Shayibu ya kawosu nik’i nik’i da food warmers, Kubura sai tura Karima gaba take dan bata mance b’aran b’araman da tai jiya ba... Allah ya rufa mata asiri suka tadda Siyama nan gidan dan wllhi da a k’ofa zasu saka su juya... Suka gaidashi Siyama na tambayar waye ya kawosu.. Karima ce ta iya bata amsa Kubura kam tuni ta nufi dining table da flask d’in dake hannunta... Khalid ya saki tsuka a hankali kana yace “Wai ita Ammi dole sai ta Aiko yarinyar nan ne.. Mai yasa ku baku taho da breakfast d’in ba...?” Siyama ta d’an dara kad’an kana tace “Kan hanya fah muke nace bara naima Nabilah Sallama, Partner na waje na jiranmu daga nan Daddy zamu biya mu d’auka...” Khalid yace “Wane Daddyn...?” “Uncle ba, Daddyn Sameer” Jinjina kai tai daidai sanda su Kubura suka taho zasu wuce suna yima Siyama Allah kiyaye.. Ta amsa tana zolayar Kubura da fad’in “Mutuniyar na zaci Ammi ta turoki gidan Yayan naki ki masu zaman d’aki ne...” Ai wuf Kubura ta fice kaman wacce ake turata.. Siyama kaw sai dariya take tana duban Khalid da ya sha mur, lokaci guda yake furta “Wllhi ku kesa yarinyar nan tana raina mutane...” Dariyar Siyama Ta kumayi kana tace “Haba Khalid yo Kubura har abin fushi ne, yarinyar dama batasan maike mata ciwo ba, dik abinda take shiririta ne kawai had’ida k’auyanci da ya kasa sakinta... Kaga bara nai sallama ma Nabilah mu wuce, na bar partner nata jira na...” Dining table d’in ya nufa yana duba breakfast d’in yayinda Siyama ta nufi upstairs.. Zaune ta tadda Nabilar Ijlaal na faman cikata da zance... Nabila ta d’anyi k’ok’arin gyara zamanta suna gaisawa da Siyamar cikeda mutunta juna,Siyamar nai mata sannu da jiki dan Khalid ya sanar da ita Nabilar bata jin dad’i tana upstairs.. Ita dai Nabilah sadda kanta k’asa kurum tai cikeda kunya... Siyama taci gaba da fad’in “Toh Nabilah ga amanar baby brother na, a kula min dashi please... Khalid yana sonki, despite dik abubuwan da muka mishi wajen ganin mun rabaku, he never gave up sabida yana sonki... My brother deserve all the happiness in this world... Ku d’in kun cancanci junanku... Ina maku fatan alkhairi da zama lafiya...” Ta k’arashe hannayensu cikin na juna... Murmushi Nabilar ma tai kana tace “Mun gode Addah Siyama, ke Allah ya cika gidanki da Farin ciki da kwanciyar hankali...” Suka kuma rungumar juna sallama... Nabilah ta d’an dafa tana k’ok’arin mik’ewa danyiwa Siyama rakiya... Saurin zaunarta Siyama tai a hankali tana mai furta “Ina zakije a haka, a’a a’a na yafeki rakiya wllhi... Abinci ma ya kawo miki nan dan bazaki iya sauk’a ba... Ijlaal come let’s go my baby...!” Ijlaal ta ije wayar Nabila da take game ciki taima Nabilar sallama suka fice Siyama na d’aukeda ita... Basu tadda Sameer parlor ba da alama yana can waje wajen Sameer... Can d’in kaw suka taddasa sukai sallama baki d’aya Khalid d’in na masu fatan sauk’a lafiya.... *** KADUNA SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *110* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED Mummy da Raihanah sukai masu tarba, yanzu kam Raihanah Ta k’aware sosai a fannuka daban daban da ya shafi tattalin gida da na iyali, dole ne ma Mummy ta zage dantse wajen koyawa matar Sameer tattalin iyali da kula dan bazataso a maimaita abinda akai da Siyama ba... Wajajen isha suke shirin tafiya gidansu yanda Sameer ya zaunar da Siyama yake sanar da ita cewa yanzu basu kad’ai bane... “Siyama a lot of things have to change, but I want you to always remember that I love you... Dan nayi aure ban daina sonki ba Partner... Har yanzu dai ked’in ce Siyamata.. My partner...!” Ya k’arashe yana kamo hannayenta cikin nasa... Murmushi Ta saki a hankali kana tace “Partner, na fahimci komai, kuma in sha Allah zaka sameni ina mai yi maka biyayya... Dik abubuwan da nayisu a baya bazanyi repeating d’insu ba yanzu in sha Allah, nai maka alk’awari... Iyakacin abinda nakeso shine ka yafe min... Please forgive me Sameer..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Yai mata k’uri yana dubanta k’aunarta na ratsa zuciyarsa, a hankali ya furta “Come here..!” Ta k’arasa cikin jikinsa tana mai lumshe idanu... Bayan Mummy ta ida shirya Raihanah da yi mata ‘yan nasihohi da tsananin mamakinsu Siyama suka gani ta k’araso ta kamo hannayen Raihanah lokaci guda take furta “Are you ready... Welcome to our home Raihanah...!” Raihanah ta d’an d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Siyama... K’ak’aro murmushi Siyama tai kana tace “Partner yana jiranmu, Mummy idan kin mana izini zamu tafi...!” Ta k’arashe cikin rawar murya dikda hawaye dake k’ok’arin gangaro mata... Lokaci guda Mummy ta isa ta rungume Siyama cikeda tausayin Siyamar take sanya mata albarka dan yau d’in harta gafaran Raihana saida Siyama ta nema.... Mummy ta had’esu su duka biyun ta rungume tana kuma saka masu albarka had’ida ‘yan nasihohi, shin wa zai kaita Farin ciki idan matan d’an nata suka had’e kawunansu haka suka zauna lafiya, tabbas zaman lafiyarsu shine cikan buri da kwanciyar hankalin d’anta Sameer.... Mummy na tsakiyarsu suka k’araso parlorn yanda suka tadda Sameer da Ijlaal suna zaune suna jiran fitowarsu, Ijlaal na zaune bisa laps d’insa, a hankali ya mik’e yana duban kyawawan matan nashi yanda Mummy ke tsakiyarsu rik’eda hannun ko wacce daga cikinsu.... Wasu irin k’walla ne yaji suna k’ok’arin ciko idanunsa, shin dama irin wannan rana na zuwa...? Which of the Favours of your Lord will you deny..! A hankali ya tako har gabansu rik’eda hannun Ijlaal, lokaci guda Mummy ta d’ago hannayen nasu ta dank’a saman na Sameer... Ita kanta Mummy hawaye ke gangaro mata, a hankali take furta “Sameer these two beautiful women amanace a wajenka, kar ka tab’a manta wannan kaji d’ah na... Ubangiji ya maku albarka ya yakwataku da zaman lafiya da kwanciyar hankali... Allah ya albarkaceku da zuri’a d’ayyiba....” Tinda Mummy ta soma magana kan Raihanah na k’asa hawaye na d’igo mata yayinda Siyama ta kafe Sameer d’in da idanu itama hawayen take... Sameer yai k’ok’arin saita kansa kana ya rungume Mummy yana mai furtawa a hankali “Thank you for everything Mummy.... I can’t ever repay you for everything you’ve done to me.... I’ll always hold you here...!” Ya k’arashe yana mai nuni da k’irjinsa... Kumatunsa ta d’an kama irin yanda take masa tin yana yaro kana tace “Silly... Oya kuje dare yanayi....” Gaba d’aya murmusawa sukai kana suka kuma yin sallama... Har mota Mummy tai masu rakiya yanda Siyama da Ijlaal suka shige baya yayinda Raihanah Ta shige gaba Doctor Sameer Ke driving... Hiran Ijlaal da Siyama shi yai keeping nasu company cikin motar dan Amarya Raihanah kam bata iya cewa komai, tinda ta shige motar kanta kife yake tana twisting ‘yan yatsunta.... Saida suka biya mall ya d’anyi masu window shopping had’ida d’an abubuwan tab’awa kana suka nufi gida... Wani ikon Allah Wai Siyama ce ta zage damtse tana ta kintsa gidan, dik yanda Raihanah taso tai aiki Siyama ta kasa ta tsare ta hanata, suka tsuke da riga da wando itada Ijlaal sai faman aikinsu suke, Ijlaal d’in ta dage ita taya Siyama take.... Rabin aikin nasu wasa ne,Ijlaal ta d’an yarfawa Siyama ruwan dake hannunta tana fad’in “Catch me if you can...!” Haba nan fah Siyama tai jifa da sandar mop ta shiga bin bayan Ijlaal a guje, yarinyar sai k’yak’yata dariya take suna zaga parlorn.... Ba Sameer da shigowarsa kenan yai tsaye yana dubansu cikeda jin dad’i harta Raihanah dake k’ok’arin taimaka masu da aikin sosai suka bata sha’awa tai tsaye tana dubansu saikace uwa da d’iya... Ganin Sameer da tai ne ya sanya gabanta wane irin fad’uwa, tai saurin mak’alewa jikin staircase tana lek’ensu daga nan... Aiko Siyama na hango Sameer tai wajensa a guje had’ida watsa masa ruwan hannunta itama... Taci gaba da bin Ijlaal a guje tana fad’i wa Sameer shima ya kamata idan zai iya.... Aje bags d’in hannunsa yai ya shiga folding hannun rigarsa yana mai furta “Let’s see Partner...!” Take ya shiga bin bayansu shima yanda suka ci gaba da zagaye parlorn gaba d’aya... Tsantsin moping ya kusa kada Ijlaal ta fad’o kan Siyama yayinda Sameer ya tarosu gaba d’aya suka fad’o kansa... Gaba d’ayansu suka ci gaba da k’yak’yata dariya Ijlaal na fad’in she won.... A kunne Siyama ke rad’a masa “Partner muje ka shirya...!” Duban idanunta ya d’anyi, tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi tana mai jinjina masa kai.... A tare suka mik’e ita dashi kana ta dubi Ijlaal tace “Princess wait for me here, abar aikin nan haka sai na dawo... Just watch your cartoon ok...!” Jinjina mata kai Ijlaal tai yayinda Sameer ya bud’e shopping bag guda ya ciro mata ice cream yana mai fad’in asha kad’an kar ai mura... Ta amsa tana tsalle had’ida masa godiya.... *** Suna haurawa sama wanka yai yayinda Siyama ta fito masa da jallabiya sabuwa k’ar ruwan silver, ita taketa k’ok’arin taimaka masa wajen shiryawa abin sai mamaki yake basa, kallo guda zakai mata kasan k’arfin hali ne kawai take... Ta kuma d’auko perfumes tana fesa masa harda d’auko su hairbrush tana taje masa sumar... Yanda take abu kazar kazar zaka fahimci tsananin dauriyace kawai... Shi kaw Sameer k’uri yai mata cikeda tausayinta... “Partner...!” Ya ambato sunanta a hankali bata amsa ba....Ya saka kira nan ma bata amsa ba bata kuma dubesa ba saima ci gaba da abinda take da tai.... “Partner..!!” Ya d’an k’ara fad’i da k’arfi had’ida rik’e hannunta da take amfanida wajen fesa masa turaren.... Cak ta tsaya ba tareda taci gaba da abinda take ba.... Sameer yaci gaba da fad’in “Partner look up.... Kalleni...!” Da k’yar Siyama ta d’ago idanunta siririyar hawaye na gangaro mata.... Bai tab’a jin zuciyarsa ta mugun karaya irinta yau a rayuwarsa ba, a hankali ya furta “Siyama... Are you sure about this..?” Ta k’ak’aro murmushi tana mai goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Dik abinda zai saka ka Farin ciki nima ina son wannan abin Partner....This is how much I love you...!” Tausayinta ya kuma kamasa... Lips d’inta ya sumbata a hankali yana mai furta “Ban tab’a gani ko jin labarin mace irinki ba Siyama... You’re one in a million... Kinada zuciya mai kyau...!” Mumusawa Ta kumayi kana tace “Don’t make me blush partner... oya shall we..!” Ta k’arashe tana mik’o masa hannu... Murmushi ya saki kana ya kamo hannun nata suka nufi k’ofa.... Har k’ofan d’akin Raihanah Siyama ta mar rakiya, Sameer ya tsaya cak bakin k’ofar yana dubanta cikeda tsananin tausayi... Siyama dake sakin murmushin k’arfin hali hannunsa ta kamo ganin yai sakare yana dubanta kana tace “Partner don’t worry I’ll be fine... Good night... you take care..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin juyawa wani irin kuka na zuwa mata.... Takowa yai kad’an yanda take kana ya rungumeta Ta baya “I love you Partner..!” Ya fad’i idanunsa a lumshe... Hawayen da take ta k’ok’arin dannewa suka zubo mata.... Tana jin sanda ya saketa ya nufi d’akin Raihanah.... Durk’ushewa Siyama tai a wajen had’ida k’unshe bakinta tana cazgan kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.... It is not easy at all... Saida ta koma d’aki tai kuka mai isanta kafin ta dawo k’asa ta d’auki Ijlaal yanda ta samu tuni har tai bacci tana kallo... Siyama ta k’arashi tattare wajen kana ta d’auki Ijlaal suka nufi d’aki... Sauk’inta ga Ijlaal tareda ita amma kam da batasan yanda daren zai kaya mata ba, dan haka taita juyi tana ganin time sam yak’i tafiya, zata iya cewa bata tab’a ganin dare mai tsawo irin wannan a rayuwarta ba... Washe gari kaw sassafe Ijlaal ce ta tada ita da k’iriniyarta, nan sukai wanka suka shirya had’ida d’an tattare waje kana suka nufo downstairs, ta jima tana kallon k’ofan d’akin Sameer kana ta sauk’e nannuyan ajiyan zuciya sanda ta jiyo muryar Ijlaal daga k’asa tana faman kwand’ara mata kira... Murmushi ta saki ita kanta tasan Ijlaal kyautace a gareta daga Allah... Tai saurin nufan k’asa tana fad’in “Coming Princess...!” Tare suka fad’a kitchen Siyama na k’ok’arin had’a masu breakfast dikda kitchen ba wajen warginta bane amma tana kan k’ok’arinta wajen ganin ta had’a abinda kowa zai iya ci.... Ijlaal na gefenta suna faman kwab’e kwab’ensu gwanin ban sha’awa, idan sunyi abu yai kyau sai Kaga Sun tafe hannaye cikeda murna... Sameer dake tsaye jikin k’ofan kitchen yana dubansu murmushi bai bar saman fuskarsa ba, kasancewa cikakkiyar matar gida da zama uwa ta gari sosai yaiwa Siyama kyau... Ijlaal ce ta soma hangosa yanda ya hard’e hannaye yana dubansu, ta isa gareshi da gudu tanai masa good morning... Bugun zuciyar Siyama ya k’aru, batasan da wasu idanu zata dubi Sameer ba, bayan kalan abubuwan da taji jiyan.... Dan haka ci gaba da soya pancakes taci gaba da yi ba tareda ta dubesu ba... Shiko Sameer idonsa na kanta dikda surutu da Ijlaal Ke zuba masa....Nan tace ya k’arasa yai tasting pancakes d’in da sukai itada Aunty Siyama.... Ya mik’e yana furta bara ya tab’a yaji.... Gefen Siyama ya tsaya yana duban yanda tai k’urima abinda take... Ya gutsiri pancake guda da fork d’in da Ijlaal ta mik’a masa kana ya saka a baki ya soma taunawa yana mai dubansu su duka biyu.... K’uri sukai masa suna jiran suji response d’insa, Ijlaal tai saurin cewa “So, how does it taste...?” Tai maganar tana mai alama da hannu... Kaman bazaice komai ba dan harta Siyama tsaye tai itama tana jira taji mai zaice.... Lokaci guda sukaga ya lumshe idanu yana mai furta “This is... Delicious... I love it...!” Tsalle Ijlaal tai had’ida mik’awa Siyama hannu suka tafe cikeda jin dad’in Sameer ya yabi abincinsu... Siyama ce ta d’an dafa Ijlaal kana tace “Princess take those to dining table, Can you..?” Jinjina mata kai yarinyar tai tana fad’in “Of course I can...” Ta k’arashe tana mai tattare set of plates zuwa dining table... Sameer dake tsaye gefenta hannayensa ya kuma sakalewa cikin aljihu kana ya d’anyi gyaran murya yana mai furta “Partner... Good morning...!” K’ok’arin saita kanta take cikin zuciyarta tana mai furta you can do this Siyama, lokaci guda ta kaikaito tana dubansa kana tace “Morning Partner... How was your night...?” Bai amsata ba sai k’ura mata idanu da yai murmushi saman fuskarsa... Lokaci guda ta d’an murmusa mai kamada yak’e kana tace “Great I guess..” Murmushi yai kad’an kana ya jinjina mata kai.... Ta d’an murmusa itama kana tace “Naji dad’i since you are happy... Ya Amarya...?” Murmusawa ya kumayi kad’an kana yace “Ya K’anwarki zaki ce...” Ta d’an murmusa kad’an itama kana tace “Toh Ya k’anwata...!” D’an murmusawa Sameer yai kana yace “Partner I never thought you can cook like this...” Murmusawa ta d’an kuma yi kana tace “Ai na fad’a maka na canza gaba d’aya... Em dama inaso nace maka zamuje gidan Mummy nida Ijlaal anjima kad’an daga nan zamu wuce shopping... So we don’t have to disturb you kaida Amarya, oh k’anwata...!” Ta k’arashe tana mai goge hannunta da kitchen towel... Girgiza kai yai kad’an kana yace “No Partner you don’t have to go anywhere... Besides I love to see my beautiful women beside me... Ba sai kinje ko ina ba...” Ta murmusa a hankali kana tace “Please Partner I insist... Besides I want to take Ijlaal out.... Please say yes kaji Partner...!” Ta k’arashe tamkar mai shirin kuka... Jinjina kansa yai kad’an kana yace “Alright fine... just because you insist...” Murmusawa tai kad’an kana tace “Thank you Partner... I’ll go check on Amarya...” Ta k’arashe tana nuni da hanya... Murmushi yai yana mai jinjina mata kai kana ya nufo dining area wajen Ijlaal... Yinin ranar dai su Siyama basa nan Sun baiwa Ango Sameer sarari yanda zai kula da amaryar sa sosai, soyayya mai tsafta yake nuna mata wanda ita bama tai zaton irin soyayyar na existing a gaske ba, dik a zatonta sai a littafan soyayya da finafinan India hakan ke faruwa ashe dai anayi da gaske, ko dan ta taso cikin kyara da tsangwama ne a gidan Haule shisa take ganin hakan...? Koda shike tana iya hango tsananin k’aunarta a k’wayan idanunsa dikda cewa har yanzu d’in bata wani dake dashi ba musamman idan ta tina abinda ya riga ya ratsa tsakaninsu, harga Allah wane irin nauyi da kunyarsa takeji... Bayan sun dawo ne Sameer ya fice ya nufi gidan Iyayen nasa su Mummy dan gaidasu, nan ne Siyama da Raihana suka d’an samu daman zama tare sabo mai tsafta na k’ok’arin shiga tsakaninsu, harta tsaraban shopping saida Siyama ta kawowa Raihanar nata...Siyama ta sanar da ita ta kwantar da hankalinta ta d’auketa tamkar yaya su taru su farantawa mijinsu, dama a b’angaren Raihanah kam babu wannan matsalar, harta su shiga ruwan zafi akai akai saida Siyama ta nusar da ita din ta kula abokiyar zaman nata yarinya ce sosai... Sam bazakace wannan Siyama bace, gaba d’aya lokaci guda Allah ya canzata... Suna nan a haka Laila ta kirata tana tambayarta ko ta dawo daga Abuja dan taji k’ishin k’ishin Sameer yayo mata kishiya k’aramar yarinya.... Siyama tace tana zuwa zata kirata later dan dole tai tinanin abinda zatacewa Laila bayan abubuwan da taji daga garesu itada Sultan... Raihanah ta d’an dubeta kana tace “Aunty Siyama wani abin ne Ke damunki....?” Dan gaba d’aya ta kula tinda Siyama ta ida wayar yanayinta ya canza.... D’an dubanta Siyama tai kana tace “Bansan ya zan sanar dake ba Raihanah.... Laila aminiyata ce da na d’auki dikkan yardana na bata amma taci amanata...” Take dai Siyama ta labarta mata dik yanda sukai dasu Laila... Raihanah ta numfasa cikeda tausayin Siyama kana tace “Aunty Siyama kin had’u da sharrin muguwar k’awa... Amma itace a rana, abinda zakiyi ki k’yaleta tazota sai ki nuna mata tamkar bakisan da zancen ba ko kuma kin sani kina neman shawarinta kiji mai zatace, daga nan ne Ke kuma sai exposing d’inta Ki nuna mata kin San komai kinsan ko ita wacece hakan sai yafi mata ciwo... If possible mu had’a plan d’in harda Ya Ma’aruf shima ya kirawo Sultan yace dashi yazo gidansa yana neman shawarinsa gameda yanda zai sanar dake batun k’arin aurensa... Kinga daga nan sai a exposing munafukai....” Siyama ta kuma dubanta cikeda mamakin hikima irinta Raihanah kana tace “Perfect... Wannan shawari naki yayi Raihanah... Zamuga yanda fuskokin munafukai zai sauya...” Ta k’arashe cikeda murna tana fad’in “Kinga bara na kira Partner yanzun nan and tell him about our plan...” Lokaci guda Siyama ta mik’e ta nufi upstairs a guje d’auko wayarta tana mai kuma godiya wa Raihana.... Murmushi kurum Raihanah keyi tana duban yanda Siyama ke farin ciki... *** Kaman yanda suka tsaran haka kaw akai, Sameer ya kirawo Sultan yayinda Siyama ta kirawo Laila tai inviting d’inta itama.... Laila ta kuma gyara zama tana fad’in “Ai wllhi k’awata kada kika yarda, wannan ai rainin wayo ne ma, ke kinfi k’arfin wani d’ah namiji ya had’aki da wata mace Siyama... Wllhi ajinki ya wuce nan... Na sha sanar daki girman class d’inki amma baki ganewa... Wllhi kada kika yarda ai mai yuwa ya zab’a ko ke ko kucakiyar yarinyar..” Ta k’arashe tana wani karkad’a k’afafu had’ida kurb’an drink dake bisa center table... Siyama ta numafasa kana tace “Allah ko k’awata...” Laila ta kuma jinjina kai tana mai fad’in “K’warai kuwa... Ai nasha mamaki dama har yanzu bakisan da matar ba, tana can gidan uwarsa ya b’oyeta...” Jinjina kai Siyama ta kumayi kana tace “Ina zuwa k’awata...!” Mik’ewar Siyama da kad’an Sultan ya shigo kaman yanda Sameer ya sanar dashi ya shige kawai parlorn na bud’e tinda Siyama dai bata nan baisan ta yanda zai soma sanar da ita zancen aurensa ba balle yai maganar dawo da ita.... Sultan ya turo k’ofa ya shigo sai faman muzurai yake.. Kaman daga sama ya hangi Laila zaune saman d’aya daga cikin kujerun da sukaima parlorn k’awanya... Wani irin wawan birki yaja yana watsawa Lailar muguwar kallo... Itama Laila a d’ari ta mik’e tana binsa da kallon mamaki.... Sultan na nunata da d’an yatsa yake fad’in “Ke Uban mai kike gidan nan, shu’uma Wato kin kasa hak’ura da abokina shine bari ki biyosa har Gida koh.....!” Ya k’arashe kaman zai shak’ota.... Dariya Laila tai tana nunasa da d’an yatsa itama kana tace “Ji wannan kwarton mai bin matan mutane ai kai zan tambaya uban mai kake gidan nan.... Kai ko kunya bakaji kana bibiyar matar abokinka... Kai wllhi tir da aboki irinka Sultan....!” Sultan ya kuma takowa cikin parlorn yana mai furta “Shut your trap you filthy witch... Ga babban abin kunya tattareda Ke kina k’ok’arin snatching mijin aminiyarki... Kuma ma har sau nawa zan miki iyaka da Siyama... Ke wata irin mayyace Laila...!” Murmusawa Laila tai kana tace “Siyama ta gayyatoni gidan nan dan na k’wata mata ‘yancinta wajen Sameer kasan she cant do without me....!” Ta k’arashe tana jijjiga... Sultan da mamaki ya cikasa saurin cewa yai “K’arya kike munafuka, Sameer kika biyo sabida kinsan Siyama bata nan shine bari kiyi amfani da wannan daman cos Sameer invited me here....!” A’a Laila fah ta soma shan jinin jikinta... A d’an daburce tace kana nufin Sameer ne ya gayyatoka...? Kafin Sultan ya bata amsa Sameer ya turo k’ofar parlorn yana mai fad’in k’warai ni na gayyatosa.... Laila da Sultan suka dubi juna cikeda firgici had’ida tsoro.... Inda inda suka soma suna nuni da juna daidai sanda Siyama ke sauk’owa daga stirs tana mai tafe hannayenta lokaci guda take furta “Well well well.... Wai akace K’ARAHEN MUNAFUKI JIN KUNYA... Tin daga nan duniya munafuki zai soma girban kayan kunya a idon duniya har a isa k’iyama yanda zai girbi babban abin kunya mafi muni sannan ai masa masauk’i a k’asar jahannama dan dama nan ne fadan munafukai.... Laila kinji jiki wllhi kin bani kunya... Muguwa azzaluma mai datse sinnan ma’aiki.... Wannan zaki tashi bomb a gari wllhi... Kinji kunya munafukar banza....!” Ta k’arashe tana mai dungurin Laila da tuni jikinta ya soma karkarwa.... Dikda sanyin AC dake tashi a parlorn bai hana Laila rawar d’ari tana fad’in “Wllhi wllhi Siyama bazan miki haka ba, wllhi sharrin Sultan ne... Ki yarda dani k’awata...!” “Yimin shiru munafukar banza da wofi....Babu wani k’arya da zaki kuma min dan naji komai dik abinda kuka tattauna a office d’in wannan babban munafuki kwarton banzan.... Dan haka babu ni babu Ke...Ke Billahillazim ko hanyar da nake bi na kuma ganinki sai na baki mamakin da baki tab’a shan irinsa ba tsawon rayuwarki.... Banza kucaka wllhi ko a layi babu abinda mijina zai dake...!” Ta juyoga Sultan dake muzurai cikeda kunya... Kafin tai magana Sameer ya katseta da fad’in “No k’yalesa Partner namu dashi ne... Babu mai fita a gidan nan kekam...!” Ya k’arashe yana mai jefa wayarsa cikin aljihu had’ida k’urama agogo idanu tamkar mai jiran sak’o.... Sultan sai faman yarfe zufan dake kuma keto masa yake, ko duban idanun Sameer ya kasa... Yayinda Sameer d’in ya kafe agogo da idanu yana k’irga dak’ik’ai... Laila tazo zata shige kai a k’Asa tana cazgan kuka, Siyama tai saurin tare gabanta tana fad’in “Kije ina... Ai Babu yanda zakije sai naga k’arshen munafuncinki.... Laila na hawaye ta durk’usa tana rok’on Siyama gafara, Siyama ta finciki skirt d’inta tana fad’in “Ni karki tab’ani bak’ar ashana... Karki tab’ani balle ki shafa min zunubin annamimanci...!” Sultan ya d’ago da k’yar kaman zai magana sai kuma suka jiyo ana danna bell.... Da tsananin mamaki Sultan ke duban Sameer da tuni ya nufi k’ofa fuska a murtuke kaman bai tab’a dariya ba ga wani irin duba da yake watsawa Sultan d’in wanda Ke kuma gigita Sa..... Sultan bai ida mamaki ba saida yaga ‘yansanda biyu sun shigo Sameer na nuni da Sultan d’in yana fad’in “Gashi nan officers ku tattare shi.... Kwarto ne mai bin matan mutane....!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da watsawa Sultan d’in k’azamin kallo.... Sultan da polisawa Ke k’ok’arin cuffing d’insa fad’i yake cikin daburcewa.... No no Sameer... No Sameer you can’t do this to me...!” Ya kuma duban officers yana fad’in “No no officers you can’t just arrest me.... Wai mai nai ne... Sameer what is this... Sameer let’s talk sensibly, you can’t do this to me... Haba abokina...!” Cikin tsananin fuci Sameer ya k’araso gabansa yana furta “Did you just call me your friend...? Lallai na yarda bakada kunya Sultan.... Amma tarbiyan da baka samu ba ina mai tabbatar maka zaka samu yanzu... Officers take him away...!” Ya k’arashe yana mai watsa masa knazamin kallo... Laila ta yunk’ura zata tashi ganin ba’a had’a da ita ba... Lokaci guda Siyama ta janyota ta shiga zuba mata dundu daga yanda take durk’ushe tana k’wallawa Raihana kira ta mik’o mata muciya a kitchen.... Laila sai ihu take tana neman agaji dan wani ikon Allah ta kasa katab’us.... Da k’yar Laila ta samu ta zille daga bugun da Siyama ke mata tako ina... D’an kwali a hannu Ta fice a guje haka takalma sai ihu take yayinda Raihanah da Ijlaal dake mak’ale jikin staircase sukaita k’yak’yata dariya.... Laila kaw tana ficewa wasu karnukan bakin layin suka kuma rakota sun ganta tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu..... ***** KANO Two weeks After Abubuwa da dama ne suka faru a d’an wannan tsakani, su Sameer da Raihanah sun taho Kano yayinda suka baro Siyama da Ijlaal can Kaduna, cikin abubuwan da suka faru tsakanin harda shiga kotu, ga shari’ar su Baba Alhaji ga kuma na Muhibbah daga b’angaren Engr, gaba d’aya Engr d’in bai samu ya zauna ba, ga kuma zab’ensu da tuni ya kunno kai dan har anyi na shugaban k’asa da ‘yan majalisun tarayya saiko sauran Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.. Uwa uba ga Ammah a ‘yan kwanakin bata gane jikinta hakan yasa Zulfa’u da yaran sukaci gaba da zama nan gidan Amman dan bama su sami natsuwar komawa can gidan Engr ba.. Tuni Engr ya yowa mahaifiyarsa da matarsa visa dan da zaran anyi election kawai ya yanke shawarin tattaransu gaba d’aya harda yaran nasa dan suje k’asa mai tsarki a duba jikin Ammah daga cen suma su samu suyi aikin umrah.... Saidai har yanzu ko labarin hakan Zulfa’u bata samu ba, toh inama ya zauna balle ta sakashi idanunta, tinda aka soma election d’in nan sai su kusan kwanaki biyu basu sakashi idanunsu ba kullum cikin meeting da sabgogi yake, ita har tausayi yake bata ga trial d’in Muhibbah da shima yai tsayin daka akai dan sam hidimar siyasarsa baisa yayi neglecting Muhibbah ba dik randa za’a shiga kotu sai yai squeezing ya halarci zaman dikda cewa Muhibbah nunawa take bata buk’atarsa, k’arshe dai har ta soma saduda dan satin sama satin zab’ensu Engr Kotu zatai deciding makomar su musamman data fahimci cewa basuda wani k’wakk’waran shaida da zai wankesu gaban Alk’ali daga ita har accomplices d’inta su Bash... A b’angaren su Hafiz kaw..... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *111* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A b’angaren Hafiz ya samu sauk’i sosai har an sallamesa ya komo gida yanda yake ci gaba da samun sauk’i a hankali, yau d’in babban bak’onsa ne ya kawo masa ziyara wato Akram.... Hafiz na kishingid’e Akram na daga gefe saman sofa suka kuma k’yak’yata dariya sanda Akram d’in ya d’ago masu zancen dajin Babba Duna.... Hafiz yace “Gashi yau kaman ba’ayi shi ba, toh haka Duniyar ma take gaba d’aya... Wataran sai a wayi gari babu kowa an shafe kowa an kuma shafe komai...!” Akram ya jinjina kai yana mai furta “Wannan haka ne, Ubangiji yasa mu dace...” Hafiz ya amsa da Ameen kana ya k’arada “Ya labarin election..? Kasan da har nayi fushi dakai sai kuma na tina yanzu zama bai ganku ba tinda aski ya taho gaban goshi...” Akram ya d’an murmusa kad’an kana yace “Wllhi kaikam dai, yanzu ma silalewa nai na fice suna can mak’il suna jirana... Gashi shima Excellency sam hidimar court case d’in matarsa ya kasa masa hankali, abin ba’a cewa komai...” Hafiz ya d’an jinjina kai kad’an kana yace “Wllhi Akram Bawan Allahn nan tausai yake bani, ya had’uda iftila’i da dama na rayuwa daga shi har Zulfa’u sun cancanci Farin ciki...!” Akram ya jinjina kai a hankali kana yace “Excellency Al’umma ne a ranshi mutum ne mai k’ok’arin kawo buk’atun al’umma farko kafin nashi....Kuma dikda yanda yakeda d’inbin magoya baya daidai da rana guda bai tab’a sakawa ransa cewa shi zai lashe zab’en nan ba, a kullum maganar sa Allah shi mamu zab’in Alkhairi...” Hafiz ya d’an jinjina kai yana mai furta “Allah sarki alamun adalan shuwagabanni kenan... Allah ya bashi ikon k’watanta adalci idan har ya nufesa da rik’on kujerar...” Akram ya amsada Ameen a daidai sanda Naja’atu tai sallama tana fad’in “Ya Hafiz time din shan maganinka yayi...” sam batasan yanada bak’o ba... D’an jada baya tai tana k’ok’arin gaida Akram da tuni yai mutuwar zaune yana dubanta... Bata kuma duban yanda Akram yake ba, kanta a k’asa ta k’arasa ta ijiyewa Hafiz maganin gabanshi ta b’abb’alla masa had’ida zuba masa ruwa, Hafiz yai mata godiya yana mai tambayarta ko Hajiya ta komo daga islamiya...? Najah ta amsa masa da a’a basu dawo ba tukuna, da shike Hajiya da Sahariyya sun shiga islamiyar matan aure dake bayan layinsu... Hafiz yace “Shikenan jeki abinki, na gode...!” Ta jinjina kai tana mai ficewa kanta a k’asa... Akram ya kuma binta da kallo har saida Hafiz ya d’anyi gyaran murya kafin ya janye idanunsa daga barin duban k’ofar... Cikeda da d’an jin nauyi Akram ke shafa kansa kana yaceda Hafiz “Toh Abokina Inaga nikam zan koma kafin su fara nema na...” Hafiz ya d’an mik’e zaune kad’an yana mai godiyawa Akram d’in, harda d’an tasowarsa yai masa rakiya zuwa k’ofa yana kuma masu add’uan nasara a forthcoming election d’in.... Haka Akram ya tafi fuskar Naj’atu bai daina masa gizo ba.... Tafiyar Akram da kad’an su Hajiya kaw suka dawo, nan Hafiz ke shaidawa Hajiyan Akram har yazo ya tafi, Hajiya Haule tace “Allah Sarki Aiko ba rabon mu gaisa ba...” Hafiz yace “Zaku gaisa ne wataran Hajiya tinda dik ana tare yanzu....” Haule tace “Haka ne... Ai wannan yaro Akram shida mijin Zulfa’u babu abinda zamu iya saka masu dashi saidai addu’ar Akhairi.... Musamman mijin Zulfa’u... Allah dai ya basa nasaran abinda ya saka gaba... Oh Duniya yanzu Zulfa’u ce muke cin albarkacinta a rayuwa... Kai Allah ka dad’a rufa mana asiri ka kuma tsaremu da aikin dana sani....” Hafiz ya amsada “Ameen Hajiya jiki a matuk’ar sanyaye, dan kokaci guda yaita tina rayuwar aurensu da Zulfah.... D’an muskutawa yai kad’an kana yace “Waini Hajiya ya labarin shiga kotun su Baba Alhaji ne...?” Nan da annurin fuskar Haule ya d’auke... Ta d’an muskuta kad’an kana tace “Yo ni ina zan sani.... Ai tsuntsun da ya janyo ruwa shi ruwa Ke bugu... Kuma babban abin kunya gayacan d’an uwan nasa da yaita k’ulla masa k’ulleliya shi yai tsaye kan case d’in nasa... Abban ku Usman shiketa d’awainiya dashi Nidai kam nayi rantsuwa ko zaman shari’ar bazan halarta ba...” Ta k’arashe cikeda k’unan zuciya... Hafiz yai jigum yana saurarenta kana yace “Hajiya hannunka baya rub’ewa ka yanke ka yar, karki mance dukkaninmu masu laifi ne amma aka yafe mana... Kuma Baba Alhaji sharrin Magajiya ya had’udashi...” Haule ta katsesa da fad’in “Kada ka sake ambato min sunan wannan tsinanniyar matar.... Taje can ta k’arata daga ita har d’iyarta dashi Alhajin da ya jefa kansa cikin uku....” Ta k’arashe tamkar mai shirin kuka.... Kaman daga sama sukaga Sahariyya, Naja’atu da kuma Raihanah da bata jima da shigowa ba sun shigo sun duk’a gaban Yayansu Hafiz.... Hajiya Haule dake k’ok’arin maida hawayenta, da gani kasan k’arfin hali kurum take amma tana kewar mijin nata itama, bud’e baki tai tana fad’in “Ku kuma meye haka kuka wani tasa shi a gaba haka... Lafiya...? Ke Raiha yaushe kika shigo...?” Raihanah tace “Ban jima da shigowa ba Hajiya, ina yini...” Haule ta amsa da sakin fuska harda tambayarta mai gidanta dikda cewa shekaran jiya tare suka shigo da Sameer d’in...Nan Raihanar Ke gaida Hafiz tana masa sannu da jiki... Daga Hafiz har Haule k’uri sukai masu ganin sunyi jigum jigum... Hajiya ta kuma fad’in “Kunyi jigum jigum ku muke sauraro.... Najah da Raihanah harmada Sahariyya duban juna suke suna zullumin ta yanda zasu soma sanar da Hafiz da kuma Hajiya buk’atarsu.... Haule tai tsuka a hankali kana tace “Raiha nasan kinfisu hankali fad’a min meye kuka tasamu gaba haka kaman masu karb’an bashi...” Raihanah ta d’an muskuta kana tace “Hajiya dama kan batun Baba ne.... Jiya Ya Ma’aruf ke sanar dani yanda Lauyan Baba sukai da Abbah... Muddin anaso Baba Alhaji ya kub’uta shaida k’wakk’awara za’a kawo cewa baida tarayya dasu Magajiya... Kuma sauran shaidar da akeda hope akai guda d’aya ne....” Haule ta d’an muskuta kana tace “Toh mu ina zamu samo shaidar tinda bai shawari damu ba....!” Duban Hafiz Raihanah tai yanda taga idanunsa sun kad’a sosai fuskarsa tai jazir, sai faman murza zanin gadon dake bisa yake, da gani kasan ransa k’una kurum take.... Sahariyya taci gaba da fad’in “Hajiya Ya Hafiz shine k’arshen shaidar Baba, shi kad’aine zai bada shaida gaban Alk’ali cewa Baba baida saka hannu a ta’addancin su Magajiya....” Murmushi da tafi kama da yak’e Haule tai kana tace “Aiko idan sai Hafiz yaje ya bada shaida saidai a yanke masa hukuncin koma menene, mutumin da aka had’a baki dashi wajen ganin bayan Hafiz d’in... Aiko ko ya amince zaije ni ban amince ba ehe...!” Ta k’arashe jikinta na tsananin tsuma... Naja’atu da Raihana suka dubi Hafiz da ya b’ace shiru tamkar bashi a wajen kana Raihana ta soma fad’in “Ya Hafiz please do this for our father... Dan Allah ka yafe mishi... Bamuda wanda yafishi Babanmu ne dik yanda akaje akazo.... Kuma kai shaida ne sharrin Magajiya ne tinda kaima ka auka wa sharrin Sawwama before... Dan Allah save our father, he can’t go to prison... Kaga yanzu hakanma ance inmates d’in da suke tare sun masa duka har hak’ori Sun cire masa... Shin haka zamu zuba idanu muga mahaifinmu... Muma fah duka ‘yan adam ne masu kure...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Sahariyya da Naja’atu suka had’a baki suma suna rok’on d’an uwan nasu yayinda hawaye suka ci gaba da gangaroma Haule... Gaba d’ayansu ma hawayen suke.... Siririyar hawaye ta gangarowa Hafiz.... Kauda kansa gefe yai kad’an yana mai share hawayen dake ci gaba da zubo masa... Lokaci guda ya juyo yana duban ‘yanuwan nasa masu zuban hawaye.... “Please ku tashi ku fita zanyi bacci....!” Yai maganar yana mai d’aura kansa bisa pillow... Hawaye basu daina zubo masa ba idanunsa a lumshe... Duban juna sukai Najah zata kuma magana Raihanah ta girgiza mata kai alamun ta k’yalesa.... Jikkuna a sanyaye suka mik’e suka fito Daga d’akin.... Raihana Ta dubi ‘yan uwanta Sahariyya da Naja’atu kana ta kamo hannayensu tace “Akwai sauran ranaku kafin shiga kotun, in sha Allahu da sannu zamu shawo kan Yaya yaje ya bada testimony d’insa a kotu... In sha Allah Baba will be set free.... Our family will be whole again..” A tare Sahariyya da Naja’atu suka rungume Raihana sunai mata godiya wajen jajicewarta ganin Babansu ya kub’uta... Haule dake rakub’e Daga k’ofa tana dubansu tausayinsu ya kamata, babu kaman Raihanah da idan ta tina abubuwan da tai mata a baya sai taji kaman a maida lokaci baya ta gyara amma saidai hakan ba mai yuwa bane... Tana ganin yanda suka rik’i hannayen juna suka nufi cikin parlorn... Sai yamma Raihanah ta koma gida yanda ta tadda Zulfa’u da yaran mijinta can gidan Mamyn... Abinka da an kwana biyu ba’a had’u ba nan suka b’ige da murna gwanin dad’i, Marliya kaw cewa tai dole ta kira Nabila suyi video call taga dik an hallara babu ita... Hakan kaw akai Marliya ta kirawo Nabila dik suka gaisa Nabila kaman tai kuka ganin Raihana a Kano ga Addah Zulfah ma dik an had’u a gida babu ita.. Khalid dake gefenta harda lek’owa suka gaisada Marliya yana mai sanar da ita soon Nabilar ma zatazo... Nabila ta d’an b’alla masa hararan wasa tana fad’in ya tafi ya k’yaleta su gaisa da ‘yanuwanta... Aiko bai tafin ba hardai Marliya dake d’an jin nauyinsa tai masu sallama... Nabila ta turo baki gaba tana harararsa, janyota jikinsa yai yana fad’in “Wai dik wannan fushin kan tafiya Kano ne...?” Turo bakin ta kumayi kana tace “Toh bakai bane ka k’yale mutum ya gaisa da ‘yanuwansa ka wani mana k’ebebe shisa Marliya ta katse kiran... Allah Ammi zan kira na fad’a ma...” Khalid ya murmusa kad’an kana yace “Da sauk’i tinda ba Kadunan zaki tafi Ki kai k’aran nawa wajen Ammi ba...”. Yai maganar yana wasa da yatsun hannunsa cikin sumarta da yasha gyara sai k’amshi yake.... Gyaran kwanciyarta tai cikin jikinsa tana fad’in “Ni dan Allah yaushe zanje Kano wllhi inason ganin Mamy, Kaga ko vid call d’in nan da mukai Mamy batabi takaina ba...” Ya murmusa kad’an yana mai fad’in “Ai Mamy ce maganinki, idan kika dameni da batun zuwa Kano ita zan kirawo na kai k’ararki... Keda Kano sai kin haihu shima tare zamuje...!” Zabura ta d’anyi tana dubansa da idanunta da sukai rau rau.... Khalid ya kuma kwanto da fuskarsa saitin nata had’ida d’aga mata gira guda... Lokaci guda yake kuma matseta jikinsa yana mai fad’i cikin sigan rad’a “Teddy bear don’t you think lokaci yayi da zamu samo Baby bears...!” Ya k’arashe yana rikirkitata da salonsa... K’ok’arin k’watan kanta take tana fad’in “What’s that smell kaji k’aurin abinci na k’onewa, please ka k’yaleni naje na duba....” Bai saketan ba yake fad’in “Then we cook another one teddy bear...” Haka ya kuma janyota tanata k’ok’arin k’watan kanta, da k’yar ta samu ta cire jikinta daga na Khalid ta nufi kitchen a guje tanai masa gwalo dan idan ta biye na Khalid tabbas abincin zai k’one... Zaune yai yana binta da kallo da rikitatattun idanunsa yana mai fad’in zai kamata ne.... Nabila dai kitchen ta shige tana dariya... *** Sai dare su Zulfah suka tafi suka barsu da kewa, Raihanah ce kawai kwance d’akin Mamy, Ta ida sallan isha ta d’an mik’e wajen... Marliya nacan k’ofan Baffah Ado sashen su Sakina yayinda Mamy ke sashen Abbah.... Kaman daga sama ta jiyo sallamarsa, da alama dawowarsa kenan daga asibiti... Ta mik’e zumbur tana k’ok’arin amsa masa sallamar, saidai kafin takaiga amsawa har ya shigo cikin d’akin yana mai tsareta da idanu... Sannu da zuwa tai masa tana k’ok’arin linke abin sallahn.. Ya amsa yana mai kuma tsareta da idanu tamkar mai jiran wani abin... Itafah harga Allah har yau nauyinsa takeji gashi ya iya tsareta da wannan idanun nasa... Muryarsa ta sinkaya yana fad’in “Haka akewa miji sannu da zuwa...?” Ta d’an d’ago tana dubansa, gani tai ya tsime sosai.... Ta d’an kauda fuska tana k’ok’arin shanye murmushinta dan idan da Sabo ta soma sabawa da wannan tsimewar tasa wanda ta lura d’abi’arsa ce yanzu zakaga yana murmushi yanzu zakaga ya tsime... A hankali ta furta “Toh ya akeyi Yaya...?” Tai maganar tamkar mai koyon magana... Hannayensa ya bud’e mata ba tareda cewa komai ba, ta gane mai yake nufi dan haka a hankali take takowa zuwa gareshi, saida ta k’araso dab kusansa kana ta d’an saci kallon k’ofa tamkar mai tsoron kada wani ya shigo... Ya gane nufinta gani take d’akin Mamy ne she can’t hug him in here... A hankali shi ya tako ya k’araso gareta had’ida rungumarta.... Ta kuwa yi lamo cikin k’irjinsa, saitin kunnenta yake rad’a mata “This is my sannu da zuwa...from now on... Kinji koh...!” A hankali ta jinjina masa kai tana mai k’ok’arin janye jikinta, ya kuma rik’eta kana yace “Are you ready....Kin shirya mu tafi...?” Da mamaki take dubansa kana ta d’an sadda kai tace “Yaya ina zamu...?” “Gidanmu zamu tafi, kwana a nan d’in ya isa haka, I want my wife beside me...!” Ya k’arashe yana mai shafar bayanta a hankali tamkar mai lallshi... Ta d’anyi still cikin k’irjin nasa sai kuma tace “Amma ai Mamy batace ba fah....!” Tai maganar tamkar mai shirin sakin kuka... “Mamy da kanta ta buk’aci hakan... Bakida labari....?” Ta kuma d’agowa tana dubansa... Jinjina mata kai yai alamun tabbatarwa kana yace “Should I help you park your things...?” D’an Jim ta d’anyi kana tace “Toh amma idan Mamy taga ina parking Kaya ni mai zance mata...?” Tai maganar tana turo baki gaba... Bata ankara ba sai ji tai ya sumbaci bakin a hankali yana mai furta “Kice mata zakibi mijinki zaku ci gaba da cooking classes d’inku...” K’walalo idanuwa waje tai tana dubansa cikin sauri, lokaci guda kuma ta sadda nata idanun k’asa tana fad’in “Ni dai wllhi kunya nakeji Yaya dan Allah kawai ma ka barni a nan kaji...!” Tamkar mai shirin kuka haka tai maganar... Sameer ya d’an sha mur kad’an kana yace “Bakiso ki ci gaba da classes d’inki ne... Ke ‘yar gata da miji ne ma ke koya miki... Or have you ever heard of matar da mijinta Ke koya mata girki.....?” Ta d’Anyi Jim tana dubansa sai kuma ta girgiza kai alamun a’a... Sameer ya jinjina kai yace “See....!Kinga Ke mai sa’ a ce...” D’an gyaran murya tai kana tace “Yaya Wai Maiyasa kake girki, wannan ai aikin mata ne su aka sani da shiga kitchen...” Yanda ta jefo masa tambayar ya sanyasa kafeta da idanu... Murmusawa yai kad’an kana yace “Lokacin da mukai zaman US nakan shiga kitchen na taya Mummy a nan na koya... Daga nan ya zama one of my hubby...” D’an jinjina kai tai kad’an kana tace “Toh mai kenan matarka zatai ta birgeka if you can cook better than her...?” Murmusawa ya kumayi kana yace “Naki sai yafi nawa, idan kinyi musamman domin ni sai yafi birgeni, and one more thing... Matarka is your companion, your friend and your partner... She’s not your maid nor your slave....So babu wani aibu dan once in a while ka girka mata abinci... One mistake da nai da Siyama shine na nuna mata nid’in zankeyi shiyasa batayi... Amma yanzu she changed her ways, kuma haka yafi komai min dad’i....” D’an murmusawa tai kad’an kana tace “You really love her..!” Ya jinjina mata kai yana mai furta “So much....” Lokaci guda ya kuma kamo yatsun hannunta kana yace “I love you both....!” Ta murmusa tana mai kwantar da kanta cikin k’irjinsa, sallaman Mamy ya sanyasu janye jikkunansu daga cikin na juna.... *** Masha Allahu, Allah shi ke bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso domin ya jarabci bayinsa... Anyi Election lafiya, sakamako ya fito a Washe gari, yanda aka bayyana Engr Ma’aruf Mutallab a matsayin wanda lashe zab’en ... Gari ya cikada rally da murna, dik yanda ka shiga shagalin murna kawai zakaga anayi, masu adaidaita da masu babura babu yasu... Toh saidai muce Allah shi tayasa rik’o ya basa ikon kwatanta adalci.... Harta gidan mahaifiyarsa saida jama’a suka cika mak’il sai zuwa masu san Barka ake... Su Marliya da Raihanah ma can suka yini sai dare Sameer ya biya ya d’aukesu dan shima yana tare da Engr d’in through out the day... Aunty Bara’atu ma nan gidan Ammahn ta yini suna tayasu amsar bak’i ‘yan murna... A gajjiye lik’is ya shigo gidan danma da k’yar ya samu ya janye jikinsa daga wajensu party chairman da sauran masu muk’amai a jamk’iyar tasu, ga kuma mutane da tuni Sun soma tururuwar kawo masu barka... Wajajen k’arfe goma ya shigo gidan yanda ya taddata da Ammah sunata kallon labaru ana hasko zab’en da kuma wanda yai nasaran... Kaman ta mik’e ta haye jikinsa haka taji dan murna amma bazata iya yin hakan ba kasancewar da mahaifiyarsa zaune wajen.... Samha da batai bacci ba tana nan zaune tareda ita ake kallon yana shigowa ta tafi da gudu ta haye jikinsa tana fad’in “Daddy congratulations... I saw it on the news, you won the election....!”Cab’eta yai yana mai furta “Na gode baby... Addu’a zaki min kinji Allah yamin jagoranci...” Ta jinjina masa kai su Ammah da Zulfah na amsawa da Ameen.. Daga nan ya k’arasoga mahaifiyarsa yana satan kallon Zulfah suke gaisawa da mahaifiyar tasa tana mai kuma masa Barka da fatan alheri had’ida ‘yan nasihu dangane da hidiman da ya shafi Al’umma.... Bayan ta d’an masa ‘yan nasihohi ne ta mik’e tana fad’in zata shiga ta kwanta dama isowar nasa take jira... Samha ma mik’ewan tai da niyyan tafiya sai kuma ta d’an juyo tana duban mahaifin nata.... Engr ya d’an bud’e murya yace “Princess akwai abinda kike so ne...?” K’arasowa kusansa tai kana tace “Dad we’re missing our mum... When are we going to see her... Why isn’t she here with us.... Ba kaci election ba..? She should be here celebrating with us... What happened to our mum....?!”Ta k’arashe cikeda nuna damuwa... Zuciyarsa Ta tsinke lokaci guda, anzo wajen yanda zai breaking wannan labari mai nauyi ga yaransa... Harta Zulfah dake gefe saida zuciyarta Ta yanke... Engr ya d’an kaikaito yana duban Zulfah dan baisan mai zaicewa yarinyar ba.... K’uri yaiwa yarinyar yana k’ok’arin nemo abinda zai fad’i mata sai ganin hannun Zulfa’u yai ta dafa Samha, lokaci guda take furta “Sweetheart your Dad has something very important to tell you....Amma ba yanzu ba Coz he’s a a little bit tired now... Kuma kema ya kamata kije kwanta sabida ki tashi da wuri ko kin manta we have plans for tomorrow...?” Ta k’arshe tana kashe mata idanu guda.... Saurin jinjina kai tai cikeda murna tana fad’in Ta tina, lokaci guda ta manna masu peck a kumatu tana mai masu saida safe.... Zulfah ta bitada kallo har ta shige murmushi saman fuskarta.... Engr kaw sauk’e ajiyan zuciya yai a hankali yana mai sauk’e gajiyayyun idanunsa kan Zulfa’u... Lokaci guda soyayyarta na kuma ratsa ko wace kafa ta zuciyarsa.... Juyowa tai taga ya tsareta da idanu... Ta d’an sadda kanta tana murmushi.... Hannunta ya janyo yana mai fad’in ta k’araso cikin jikinsa.... Ta matso cikeda d’an jin nauyinsa.... Nan yai mata masauk’i cikin jikin nasa yana mai lumshe idanu.... Lokaci guda yake furta “Everything is stressing out.... All I need right now, is to be with you....!” Ya k’arashe yana mai bud’e idanun nasa had’ida sauk’esu saman fuskarta.... Ta d’an murmusa kad’an ga k’irjinta dake tsananin bugu.... Tallafo fuskarta yai yana kuma dubanta cikin idanu kana yace “I don’t think I can take half of this without you...Thnk you for taking care of my family, my mum and my children....Thank you for being here... Thank you for everything, my number 1...” Murmushi saman fuskarta take furt “Dan Allah ka daina min godiya saika naji kaman wani abin nayi... Yaranka yarana ne... Sannan Ammah ko baka aurena she’s still my mum, itada Mamy basuda maraba wajena....!” Murmusawa ya kumayi k’aunarta na fizgarsa... Lokaci guda yake ci gaba da furta “You know, at first lokacinda na soma jin muryarki... I thought na fad’a soyayya da shirin da kike gudanawa ne... Daga bisani sai na zaci da muryarki na fad’a soyayya.... And now that I started to get to know you ... Sai na fahimci ba zallan muryarki bane ba kuma zallan kyaun fuskarki ko na jikinki ba... Zuciyarmu sun jima da had’uwa a wani waje na daban, basu samu damar kasancewa tare ba sai yanzu.... Zulfa’u I want you to know that I love you... So much... I’ve never felt like this for any woman before... A baya nayi zaton moment irin wannan bazai tab’a zuwa a rayuwata ba... Na karb’i k’addarata Muhibbah a matsayin matata... But as they say INDA RAI DA RABO.... Toh yau gashi ina gani, gani nan tareda matarda nakeso, nake kuma fatan na k’arashi rayuwata tareda ita... I’ll love you, take care of you and above all I’l respect you till my very last breath..!”Ya k’arashe cikin wane irin sanyin murya, Zulfa’u kam tuni hawaye sun shiga gangaro mata... She was like is this for real, shin Wai ita Zulfa’un ce yau namiji ke sanar da ita duka wad’annan, Zulfa’u da aka camfata mai Farin sawu... Zulfa’u data sha Uk’uba a rayuwar gidan aure har saida tai tinanin dik mazan duniya halinsu guda ne... Zulfa’un da tai tinanin babu sauran Farin ciki a rayuwarta nan gaba da zata tadda... Ashe irin wannan rana na zuwa da zata samu soyayya da girmamawan miji.... Tabbas ta yarda Allah shine mai canza al’amra a lokutan da yaso.... Ta kuma yarda da wannan kalma da akace INDA RAI to fah shakka babu akwai RABO... Mai rai kar ya zamto mai cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa.... Tana fata da addu’a ga sauran ‘yanuwanta mata da suke experiencing what she went through a gidan aurenta na baya suma kar su cire Rai daga rahamar Ubangiji... Allah ya shirya mana mazajenmu ya sanya masu soyayyarmu da tausayinmu cikin zukatansu... Ya Ubangiji Allah ka zaunar damu lafiya tareda abokan rayuwarmu daka hukunta mana zama taredasu.... Ameen ya Rabbi..! Ganin tana hawaye ya sanyashi kwantota cikin jikinsa yana lallashinta a hankali lokaci guda yana rikitata da salon k’aunarsa mai cikeda maturity....Yanayin da bazasu so wani abu ya datse masu ba, kaman daga sama wayarsa ta soma ruri... Cikeda jin nauyinsa ta kuma mak’ale kanta cikin k’irjinsa... Tana jin sanda yake amsa wayar da ko ba’a ce ba urgently ake nemansa... Jim ya d’anyi kana yace su tsammacesa nan bada jimawa ba... Engr ya tallafo fuskarta sanda ya ida wayar kana yace “See, bazasu bar mutum ya huta ba... Wannan kafin ai swearing in a shiga office kenan... Kiyi hak’uri Zulfa’u I’ve to go, wannan shine mijin da kika aura mai hidimar Al’umma... Nasan ya kamata na ware maki lokacin ki... Amma kiyi hak’uri nai miki alk’awarin before ai swearing in lokutana gaba d’aya zan mallaka miki... Kafin na shiga aikin Office gadan gadan....” Murmusawa ta d’anyi kana tace “I’ll always support you in everything, nasan rabin abubuwan da kake ba dan kanka kake ba... Dan jama’anka kake... Sabida haka, zaka sameni Ina mai k’arfafa maka gwiwa in sha Allah wajen ganin ka kimanta sauk’e nauyin da Allah ya d’aura maka...!” Wani irin dad’I da sanyi ne ya lullub’e masa zuciya, ya kuma shafar fuskarta yace “What do I do without you.... Allah ya miki albarka....!” Ta amsa da Ameen tana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye take fad’in suje Ta Mar rakiya... Suna tafe yake fad’in gobe in sha Allah zata taimaka masa su sanar da yaransa batun mahaifiyarsu a natse yanda bazai affecting d’insu ba.. Zulfa’u ta jaddada masa idan dai wanna ne baida matsala... Har k’ofa tai masa rakiya yanda Ta hangi Akram da ‘yansandan da tuni an basa matsayinsa na governor elect sun nufi motoci a hanzarce suna k’amewa... Akram na hangosu yai saurin sadda kansa dan harga Allah wane irin girman Zulfa’u yake ganina halin yanzu... Dole ne ma yaga girmanta a matsayinta na matar Uban gidansa... Kai a k’asa ya k’araso harda risinawa yana gaida Zulfa’u, sai saman taji ashe ma Excellency Ma ya ambaceta da... Itakam this too formal for her Meye wani Excellency Ma, Wai ita Zulfa’un ce yau ta zama her Excellency.. Abin sai yanata mata wani banbarak’wai... Sallama suka kumayi da Engr yanda suka nufi mota shida Akram yanda Akram d’in Ke masa bayanin wasu abubuwa... Zulfa’u kaw har yanzu wannan Excellency Ma da Akram ya ambaceta dashi bai daina mata banbarak’wai a kunne ba saima da Atika ta kirata tana ihu tana kiranta da her Excellency abin ya kuma mata bak’o Zulfah tace “Zaki sani ne tinda ke yanzu kin zama ‘yar rashin mutunci ko ganinki ba’ayi....” Atika tace “Allah huci ran her Excellency, zuwa ya zaman min dole ni da zanzo a bani komishina Ta mata...” Sukai dariya a tare Zulfah na fad’in mai hali bai fasawa... Nan dai suka ci gaba da hiransu Zulfah na tambayarta labarin station d’insu... Gaskiya tayi kewarsu gaba d’aya... Atika tace zasu hallaro suzo suyi masu murna.... Haka dai sukaci gaba da zance har dai daga bisani sukai sallama... *** Bayan kwanaki biyu akai zaman kotun su Muhibbah yanda aka yanke masu shekaru goma sha biyar a gidan yari... Allah sarki abin akwai tausayi kam amma wannan shine sakamakon ayyukansu... Sanda za’a wuce da ita prison Engr ya k’araso ya buk’aci a barsu su gana.... Muhibbah ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa lokaci guda take furta “Ma’aruf ka yafe min... Ka yafe min dik abubuwan da nai maka a baya... Gidan yari shi ya kamaceni bayan rayukan mutane da dama da nayi ruining... Hak’ik’a shan miyagun k’wayoyi bazaikai d’an Adam ga komai ba face tab’ewa... Ta’ammudi da miyagun k’wayoyi ya taka rawa wajen sauya min kwanya da tinani har takaiga na ballagazantar da aure na da kuma ‘ya’ya na.... Nayi watsi da rufin asirin da Ubangijina yai min... Yau ga halinda na tsinci kaina ciki... Ina rok’on Allah yasa hakan ya zama wa’azi ga masu hali irin nawa... Ma’aruf yau ina rok’onka gafara dan Allah ka yafe min...!” Ta k’arashe tana mai had’e hannayenta biyu dake d’aure cikin handcuff waje guda alamun rok’o.... Girgiza kai yake hawayen da yake mak’alewa suna kuma gangaro masa lokaci guda ya kamo hannayen nata yana furta “Muhibbah na yafeki duniya da lahira... And about our children zan kula dasu da dikkan iyawata... Fatana shine Allah yasa wannan ya zamto sanadin shiriryarki Muhibbah... Zan dinga kawo miki yaranmu lokaci zuwa lokaci suna kawo miki ziyara... This is a promise... Na fad’a miki bazan abandoning d’inki ba sabida dukanmu ‘yanadam ne masu kure... We will face this together..” Murmushi ta d’anyi kana tace “Na gode Excellency na....Na manta ban congratulating d’inka ba... Congratulations Allah ya tayaka rik’o dama kai d’in na Al’umma ne... May Allah guide you through...!” Engr ya amsada Ameen kana yace “You take care of yourself....!” Jinjina masa kai tai tana murmushi lokaci guda tana share hawayen da suka zubo mata daidai sanda ganduroba mace ta janyota suka shige.... Washe gari akai zaman nasu Baba Alhaji ma yanda Hafiz da ba’ai tsammani ba yaje shi ya bada shaida... Zo Kaga yanda Baba Alhaji yake kuka yana murna, haka ya rungumi Hafiz su duka biyu suna hawaye... Abbah na waje na jiransa, Baba Alhaji yana hango Abbah ya tafi ya rungumesa su duka biyun suna hawaye gwanin ban tausayi... Lokaci ne na yafewa juna... Komai yai tsanani yana tareda sauk’i.... Rahamar Ubangiji ya lullub’esu.... ‘Yan uwan da suka taso cikin sab’ani da juna yau gasu nan k’ark’ashin inuwa guda... Zumunci al’amari ne mai girman gaske... ‘Yan uwa kada muyi wasa da zumunci... Musaka sharri da Alkhairi, mu kuma zamto masu yad’a alkhairi da yafiya had’ida soyayyan junanmu a tsakani.... Haka suka d’unguma suka nufi gida cikeda Farin ciki, k’annensu su Baffah Ado da Baffah Wada suna hango ‘yan uwan nasu suka tafi suka rungumesu suna masu nuna Farin cikinsu, haka Baba Alhaji yaita godiya wa Abbah yana fad’in ya basa girman, kuma ya yarda Allah shike d’aukaka wanda yaso a cikin Al’umma... A gida guda sai Allah ya d’aga k’arami Daga cikinku ya bashi wani mulki ko arziki ba don komai ba sai dan hakan ne yaso ta kasance... Abbah kaw cewa yai har gobe Baba Alhaji shine dai gaba dashi babban yayansu... Suna nan a haka a k’ofar gidan Baffah Ado da ya ida waya ya k’araso masu da labari mai dad’i cewa an sami Mamani.... SameenaAleeyou📚 *INDA RAI* _............... DA RABO_ *112* *©️Sameena Aleeyou...* Daga Abbah har Baba Alhaji har suna had’e baki wajen tambayar Baffah Ado ina Mamanin take... Baffah Ado ya labarta masu yanda akai, ashe gidan d’iyar k’awarta Hajiya Marka ta tafi dashike Ita d’iyar k’awar tata k’awar Matar Baffah Ado ne, kuma Mamani ta rok’esu kan cewa kada su sanar da yaranta ga yanda take ita kaw d’iyar Hajiya Marka taga kullum wannan tsohuwa cikin damuwa da kuka take ga shekaru da suka ja, hakan ba daidai ne ga lafiyarta ba, wannan dalili yasa ta yanke shawarin sanar da yaranta... Babu b’ata lokaci suka nufi gidan Hajiya Rabi d’iyar Hajiya Marka marigayiya k’awar Mamani.... Mamani tana hango Abbah sabon kuka ya kece mata... Allah sarki shima Abban kukan yake sosai lokaci guda ya tafi ya rungumeta yana kuka sosai yake fad’in “Mamani mai yasa zaki tafi ki barmu... Munsha wahala sosai wajen nemanki... Mai yasa zaki gujemu Mamani na...!” Cikin muryar kuka Mamani ke fad’in “Usman bansan da wasu idanu zan dubeka ba... Abinda na b’oye maka tsawon rayuwarka abu ne mai girman gaske d’ah na.... Nayi kishi sosai irin na jahilcin zamin da nida mahaifiyarka amma Allah shine shaidata haihuwa itace tai sanadiyar mutuwar Harira... Usman ka yafeni idan na b’oye maka dika wad’annan d’ah na....” Ta k’arashe tana kuka sosai.... Abbah ya kuma kamo hannayenta yana hawaye lokaci guda yake furta “Na yarda dake Mamani, kuma tabbas da ace zaki kashe mahaifiyata da nima kin had’a dani amma kika d’aukeni kika bani duk wani kulawa da uwa ke baiwa d’anta... Shin ta yaya zan mance duka wad’annan... Mahaifiyata haihuwata kawai tayi amma kece duk wani d’awainiyata tin ina tsumman goyo har izuwa girmata, hakan bazai tab’a shafewa a idanuna ba... Zanci gaba da yiwa mahaifiyata addu’an samun rahama har tsawon rayuwata sannan kema zanci gaba da baki matsayin mahaifiya da nake baki tin tasowata... Babu abu guda da zai canza Mamani na....!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa hawaye naci gaba da gangaro masa.... Mamani ta tallafi fuskarsa tana hawaye sosai lokaci guda take furta “Tabbas ba sai ka haifi d’ah ya zamto Naka ba... Na yarda da wannan kalma da hausawa me cewa D’ah na kowa ne... Kada kaga yaro ka wulak’antasa ko Allah ya k’addari rik’onshi ya fad’o hannunka kai masa rik’on sakainan kashi, bakasan waye zaka mora a rayuwa ba, d’an wani sai yai maka abinda Naka d’an bai maka ba... !” Abbah na hawaye yake jinjina kai kana yace “Mamani tare muke da ‘yanuwana... Zamu d’aukeki mu koma gida gaba d’aya...!” Mamani ta d’an sarara da kukanta kana tace “Kana nufin harda Alhaji..?” A hankali Abbah ya jinjina mata kai yana mai duban k’ofa yanda su Baba Alhaji dasu Baffah wada suka sako kai cikin d’akin... Mamani tana ganinsu a haka sabbin hawaye suka shiga zarya a fuskarta... Haka Baba Alhaji ya duk’a yana kuma neman gafarar Mamani harmada Abbah... Allahu Akbar hawayen Mamani suka gaza tsayuwa yau ga ‘ya’yenta a had’e waje guda, gasu nan sun yafi juna, mai yafi wannan Farin ciki, ko yanzu Ubangijinta ya kirayeta ya cika mata burinta taga irin wannan rana.. Yanzu batada buri da ya wuce ta sami Mariya da Zulfa’u ta nemi nasu yafiyar... Haka su Abbah sukaita godiyawa Hajiya Rabi kana suka d’unguma suka koma gida gaba d’aya cikeda Farin ciki... Kan kace mai labari ya zaga family Mamani ta dawo... Kowa sai murna da San Barka yake... Mamani ta nemi yafiyar Mamy dama yaranta, rayuwa ta koma kaman da harma fiyeda da, Wai zo Kaga murna wajen Raihanah da Sameer, har sai aka rasa wa yafi murna... Su Nabilah ma sunyo waya daga Abuja Khalid yace bai isa ba dole su taho Kano su gaida Mamanin Haladu....Lol Mamani da kanta taje taiwa su Zulfah murna ta kuma nemi yafiyar Zulfah, Engr da baisan Mamani sosai ba yanata d’an mata surkunta nan ya fahimci Mamani kam babu ruwanta da wani surkunta... Ya cikata da goma na arziki harda kyautar sabuwar mota dal aka dawo da Mamani gida... Sai kuka Mamani take tana fad’in yau dik Ta dalilin Zulfa’u ta samu wannan d’aukaka... Rayuwa kenan, d’an hakin daka raina wataran shike tsone maka idanu... Dik yanda D’an adam yake kada ka rainasa Allahn da ya haliccesa shi Yasan mai ya aje wajen.... Bayan dawowar Mamani Mami Ta rok’i Abbah kan yaje ya maido da Aunty Lami, da fari yak’i yarda da hakan har saida Mamy taita masa magiya tana nuna masa yanda ya yafema kowa itama ta cancanci yafiya tinda ta gane kurenta, sannan dik Abinda ya faru muk’addari ne daga Allah, hakan tuntuni na rubuce... Da wad’annan batu na Mamy Abbah ya yarda suka tafi har k’auyen su Aunty Lami tareda Mamy... Aunty Lami ta rame tai bak’i ta fita hayyacinta kaman ba ita ba, zaman k’auye surfe da daka ma kawai sun isheta gashi gidansu mahaifinsu malamin zaure ne wanda bayan rasuwarsa Almajiran basu bar gidan ba sauran matan Babanta da wasu daga cikin yayyensu maza sun ci gaba da kulada almajiran dan haka wahala ce tsantsan ta tadda a wannan gida... Aiko tana ganin su Abbah haka ta duk’a ta dinga kuka tana rok’onsu yafiya musamman Mamy.... Mamy tace “Babu komai Lami Allah ya yafemu gaba d’aya, yasa wannan ya zamto wa’azi a gareki da masu hali irin naki...” Aunty Lami sai jinjina kai take tana hawaye had’ida da kuma neman gafararsu.... Wani irin kima da darajan Mamy ne suka k’aru a idanunta.... Daga bisani suka d’unguma suka komo gida, har lokacin Aunty Lami a d’arare take.... *** A b’angaren su Zulfa’u kuwa tuni an gama processing visa d’insu, cikin kwanakin suka d’aga zuwa k’asa mai tsarki, kafin su tafi saida Engr ya kaisu duba Muhibbah gaba d’ayansu harda Zulfa’u da yaran... Muhibbah taita masa godiya tana rungumar yaranta, Ta kuma dank’a amanansu hannun Zulfa’u dan batada haufi Zulfa’u zata rik’e mata su da aminci... Haka suka tafi Muhibbah na cikeda kewarsu danma Ta soma karatun Islama a nan prison d’in, idan ka ganta ma bakace ita bace, babu shan k’waya babu ta’ammudi da miyagun k’wayoyi daga ita har Shamzy yanzu sosai suka rungumi sanin addininsu.... Sauk’arsu a k’asa mai tsarki aka wuce da Ammah asibitin ta dan dama tin suna Nigeria an riga an ida dik wani abinda za’ai.... Nan Ammah ta buk’aci Engr ya d’auki matarsa su tafi wani wajen su keb’e tinda ita a nan Gata nan ga yaran ga kuma Hajjah sannan ga Akram ma... Tana ganin zai kyau idan sukai amfani da wannan dama suka d’an tafi wani wajen kafin su koma Nigeria ya soma hidiman office... Tamkar Mahaifiyar tasa Ta shiga ransa, burinsa kenan su d’anyi amfani da wannan tsakani shida matarsa su kasance tare.... Babu wani b’ata lokaci ya sai masu tikitin k’asar Maldives, Akram shi yai masu processing komai cikeda ladabi had’ida girmamawa.... Washe gari suka d’aga zuwa k’asar Maldives.. *** MALDIVES *Anantara Dhigu Maldives Resorts* Ita dai tinda suka iso wannan k’asa mai d’inbin Ni’ima take jinta tamkar wani duniyar ta daban suke, Wai dama akwai irin wad’annan wajaje a fad’in duniyar nan... Kai lallai ganin wannan waje ra’il aini ya kuma sanyata tsarkake Ubangijinta a zuciyarta wanda ya k’agi halittar wannan waje da yafi dacewa da a kirasa da Aljannar duniya... Ikon Allah Wai ita Zulfa’u yau dai gata a island nan tsakiyar tsibiri abinda take gani a talabijin da hotuna yau gata cikinsa, Daidai da d’akinda take ciki tsakiyar ruwa yake, ruwanda view d’insa ma kawai kwanciyar hankali yake haifar maka had’ida wane irin natsuwa cikin zuciya.... Ta kuma juyi saman gadon da aka k’erasa da zallan itace akai masa wane irin kwalliya da shell, komai dai a wannan waje abin birgewa ne, ga wani irin ni’imtaccen iska na kad’a dik wani kafa na jikinta.... Laushin bargo da bedsheets ya kuma sanyata lumshe idanu tana sakin wane irin murmushi a hankali... Tinda ya bata kayan da zata sanya idan tai wanka bata kuma ganin gittawansa ba, tadai daure Ta kuma mik’ewa tana duban kanta jikin full length mirror dake nan cikin d’akin wanda akai masa kwalliya da shell shima.... Rigace bak’a doguwa wanda tafi kama data turawa... Ta d’an murmusa kad’an Wato yau irin shigar da yake so ya gani jikinta kenan... Wata zuciya tace “Yanayin wajen bana saka atampa bane k’ila shisa ya kawo miki wannan ki saka.... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai gyara sumarta ta d’auresa cikin bakin mayafin rigar, ita kanta tasan babu Wai tayi kyau Masha Allah son kowa kin wanda ya rasa... Kyaun da ita kanta bata tsammaci tana da irinta ba.... Tana nan tsaye wayarta ta kuma yin k’ara... A hankali ta isa saman gadon tana duba wayar... Gabanta ne yai wani irin tsinkewa ya fad’i... ‘Mr Unknown..’ Sunan da ya soma zuwa zuciyarta kenan.... Tai saurin bud’e sak’on tana karantawa.... Gabanta ya kuma tsinkewa... _Nasan kina son sanin ko ni wanene..._ Wannan shine sak’o na biyu da ya shigo.... Zulfa’u har ta soma tsorata tana tinanin toh ko dai gamo Tai ne... Tayi zaton wannan bawan Allah ya daina turo mata anonymous messages d’insa tin ranar aure sai kuma ga wani yau... Ta had’iyi miyau da k’yar dan bata fatan abinda zai kawo mata cikas ga wannan sabon rayuwa mai cikeda Ni’ima data tsinci kanta ciki... Bata ida tinanin ba wani sak’on ya kuma shigo mata... _Idan har kina son sanin ko ni wanene ki biyo wannan k’ofa da kike hango beautiful ocean d’in nan daga wajen...._ Ta d’an kuma d’ago kai tana waige waige.. Text ya kuma shigo mata... Shin anya bazataje taga waye wannan bawan Allah da ya dameta ta sanar dashi Tanada aure ba, toh ya ma akai yasan tana nan... Wata zuciyar tace toh idan kuma da gaske ba mutum d’in bane fah...? Take dai taji zuciyarta tana k’arfafa mata gwiwa da tajeta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta nufo hanyar da akace tabi... Wani ikon Allah k’aytaccen waje ta tsinci kanta wanda har saida yafi yanda Ta fito k’ayatuwa.. Tsoro ya soma cikata anya ba birnin mutanen b’oye take ba... Wai meke faruwa ne da ita...? Ta tambayi kanta tana mai kuma waige waige... Sak’on ne ya kuma shigo mata yanda yace ta juyo bayanta kad’an zata hangosa... Gaban Zulfa’u ya tsananta fad’uwa... Da k’yar take kaikaitowa har dai ta ida jiyowa gaba d’aya yanda ta hangi wani teburi mai d’aukeda fulawowi wanda yasha tsari iyaka tsari harta su wine glass cups gasu nan a jere, saikace wacce ta fito date irin na turawa...Gabanta ya kuma tsinkewa ga wani view na rana da ya kusa fad’i daga can k’arshen teku tana hangowa... Gefe kad’an ta hangi bayansa, sanye yake cikin three quarter da fara k’al d’in shirt wanda gaban rigar an rubuta _I am urs_ sabida duhu bama ta ita hangosa gaba d’ai sai hasken rigar nasa take hangowa... Hannayensa sakale cikin aljihu ya bada baya yana hangen yanda iska ke kad’a ruwan teku had’ida kyawawan bishiyan kwakwa da sukaima wajen kawanya.... Gaban Zulfa’u ya kuma yankewa ya fad’i, ji tai k’afafunta sun soma takowa zuwa yanda yake... Tana soma takowa kaw wasu wuta suka fara haskawa Daga k’asa dik yanda Ta taka masu kaman candles cikin kwalba.... Dik yanda ta saka k’afarta daga gefe gefe wad’annan wutacan suna haskawa... Wani irin murmushi ne taji yana zuwa mata had’ida sanyi cikin zuciyarta wanda zata ce ita kanata batasan yanda zata misalta kalan abinda takeji ba, yanzu kam ko shakka babu ta fahimci shine... Wato dai Engr shine Mr Unknown d’inta... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai k’arasowa yanda yake.... Tana ida k’arasowa ya wani juyo cikin slow motion yana mai zare beach glasses d’in da ya rufe idanunsa dashi wanda suka kuma fito da yarintarsa bama kace yakai shekarun da yake ba.... Gabaki d’aya ta zama speechless sai ido da take binsa dashi, ganin tai sororo da ita ya sanya Engr d’an kwanto da kansa kusanta kana yace “You look beautiful, I love you...!” yai maganar yana mai d’aga mata gira guda.... Sadda kanta kurum tai bata daina murmushin ba, lokaci guda take furta “So you’re Mr Unknown....?” Engr ya kuma murmusawa yana mai kamo hannayenta duka biyu kana yace “And now I’m Mr well known...!” Wannan karon murmushi mai d’an bayyana hak’wara tai kana tace “Ka tsoraceni you know...!” Tai maganar cikeda shagwab’a.... Murmushi mai bayyana hak’wara yai wannan karon shima kana yace “Toh ke menene ba abin tsoro ba wajenki, ko kin mace abinda kika min cikin jirgi...” D’an darawa tai kad’an had’ida rufe fuskarta da tafukan hannaye... Ya d’an murmusa shima kana ya kamota ya sakata cikin jikinsa had’ida rungumarta daga baya, su duka biyun suna facing view d’in ranar nan data kusa fad’i ga iska na kad’a ruwan teku a hankali... Kansa ya d’an d’aura saman kafard’arta, lokaci guda ya lumshe idanunsa yana shak’an k’amshinta mai sanyaya zuciya.... Itama d’in lumshe idanunta Ta d’anyi a hankali kana ta furta “This place is beautiful...!” Ya kuma d’aura duka hannayensa saman cikinta had’ida d’an dad’a matsota kad’an kana yace “And ya k’ara kyau da ya amshi bak’uncin kyakkyawa irinki....!” Nan ma dai murmushin tai kana Engr ya d’an juyo da ita suna fuskantar juna, lokaci guda yake furta “‘Yanmata ji mana... Can I take you out for a date...?” Yai maganar yana wani d’aga gira da kashe idanu... Sosai ya bata dariya ganin wannan yanayi Daga wajensa, saikace bashi ba, ga wani yarinta da ya sauk’o masa.. Ta d’an juya idanunta kad’an had’ida sakalo hannunsa cikin nata kana tace “Well, no....!” Engr ya d’anyi rau rau da idanu kana ya marairaice fuska yace “But why...?” Juya idanu Ta kumayi cikin salo kana tace “Because I’m already taken...!” Ya d’anyi still yana duban yanda acting d’in yai bala’in amsarta kana ya gyara tsayuwarsa yace “By who if I may ask...?” Zulfah Ta kuma gyara tsayuwart kad’an itama had’ida sakalo hannayenta saman wuyarsa kana tace “By the most handsome, generous and honest man I’ve ever seen in my life...!” Engr dake murmushi yana duban fuskarta kunkuminta ya kuma matsowa cikin jikinsa kana yace “Who’s that man da ya siye zuciyar wannan kyakkyawar with all those qualities you’ve mentioned....?” Zulfah na murmushi suna d’an motsawa kad’an su duka biyun tamkar masu rawa kana tace “He’s right here I front me.... And I love him with all my heart.... I am yours.. !” Ta k’arashe tana mai karance haruffan gaban rigarsa kaman yanda yake a rubuce... Murmushi ya kasa barin fuskar Engr, ganin abin yake tamkar mafarki... A hankali ya sumbaci bakinta, murya can k’asar mak’oshi yake furta “I love you... My number one....So much..!” Lokaci guda ta shige cikin jikinsa suka kuma rungume juna suna masu lumshe idanu, zallan soyayyar junansu ne ke ratsa zukatansu... A haka suka isa table d’in suka d’an tab’a abincin daga bisani cak ya d’auketa tana zillewa bai ajeta ba har saida suka isa k’ayataccen d’akin nasu.... Wane irin soyayya mai tsafta had’ida maturity Engr Ke nuna mata.... Ta yarda tabbas shid’in masoyinta ne... Dik yanda Ta d’auki soyayya ashe ya zarce nan dan ita zatace bata tab’a yinta ba sai yanzu.... Kulawa da tattalin juna kam sunyisa a wannan tsibiri, wata irin rayuwa suka tsinci kawunansu ciki wanda zasuyi fatan su dawwama cikinta.... Saida suka shafe sati biyu masu kyau suna nunawa juna tsantsan k’auna mai tsafta a wannan ni’imataccen waje da zai dawwama cikin tarihin rayuwarsu kafin daga bisani suka dawo k’asa mai tsarki yanda suka gudanar da aikin umrarsu suma, kwanaki da bazasu kai goma ba suka k’ara a nan Saudia dan tini likitan a zai duba Ammah ya dubata kuma Alhamdulillah ta sami lafiya, a saidiyar ma sabon shafi soyayya suka bud’e kaman kullum su tabbata a haka, har wani haske da k’warjini Engr ya k’ara, kana ganinsa Kaga family man... Haka zai jidesu gaba d’aya suyita zaga malls suna sayayya, daga bisani suka d’aga zuwa k’asarsu ta gado Wato Nigeria.... Dawowarsu Nigeria Zulfa’u ta tare gidanta, su Atika dasu Aunty Zulai suka kawo mata ziyara, Atika sai tsiya take mata Wai Allah yasa an k’unso masu tsarabar D’an Maldives ko na Saudia... Atika taci gaba da fad’in “Mutuniyar Excellency Ma wllhi har wani haske da kyau kika k’ara, Wai me Excellency yaita baki a can Maldives d’in ne...?” Harara Zulfah ta galla mata kana tace “Kedai kyaji dashi... Allah ya shiryeki... Gayacan a parlornsa muje na rakaki Ki tambayesa da kanki....” Zaro idanu Atika tai tana k’unshe baki lokaci guda take furta “Rufa min asiri bankai nan ba wllhi.. Kar kisa sojojin his Excellency su bundugeni....” Darawa sukai a tare daidai sanda maids d’inta guda biyu masu sanye da uniform irinta ma’aikatan restaurants suka shigo kitchen d’in tana ci gaba da sanar dasu abinda zasuyi.... Atika dai sai dubanta take tana kuma jinjina lamarin... Al’amarin Allah kenan, yau Zulfa’u ce haka ta zamto babbar mace... Allah mai yanda yaso, mai baima wanda yaso d’aukaka a lokacinda yaso... Koda su Atika sukazo tafiya saida his Excellency da matarsa suka cikasu da goma na arziki, abin ba’a cewa komai, tinkan Engr ya shiga office yaci gaba da hidiman Al’umma, zukata sun samu natsuwa albarka ya yalwatu, da alama gwabnati ne da za’ai tafiya ta matasa harmada dattawa saidai Allah son barka... *** A can b’angaren Siyama kaw a ‘yan kwanakin bata gane jikinta, wane irin ciwon ciki mai tsananin gaske take yawan fama dashi wanda idan ya tashi mata bata iya tab’uka komai, tuni su Raihana da Sameer sun koma can Kaduna wajen Siyama yanda akai referring nata zuwa can Asibitin Koyarwa na Ahmadu Bello dake Zaria... Gwaje gwaje aka gudanar yanda aka gano Siyama na d’auke da cutar cancer ta mahaifa sakamakon magungunan hana d’aukan ciki da taita amfani dasu har sukaje suka toshe bakin mahaifar yanda suka taru suka haifar mata da wannan matsala...Allah sarki Zo Kaga tashin hankali wajen wad’annan bayin Allah, harta Raihanah saida ta shiga natsanancin tashin hankali maras misaltuwa, babu kaman Sameer da yafi kowa shiga tashin hankali ko ita Siyamar bata kaisa shiga tashin hankali ba, tabbas kowa ya tausayawa Siyama gabaki d’aya Zuri’a Sameer na zaune gefenta hannayenta cikin nasa, tana kwance saman gadon marassa lafiya.. A haka shima bacci ya soma satansa sabida daren jiya sam bai rintsa ba.... A haka su Ammi da Mummy harma dasu Raihanah da Ijlaal suka turo k’ofar suka shigo.... Sameer ya bud’e idanunsa a hankali yana dubansu, take yaji zuciyarsa ta kuma raunana sanda ya maido da dubansaga Siyama dake kwance har kokacin idanunta a lumshe da alama bama taji shigowar nasu ba, Ammi ta kauda kanta gefe kad’an tana matsan k’walla... Lokaci guda Mummy ta k’araso gareshi had’ida dafe hannunsa, k’ok’arin k’arfafa masa gwiwa take da fad’in “Stay strong Son.... Siyama zata sami lafiya kaji.... Kaci gaba da mata addu’a....” Jinjina kansa kurum yake amma shi kad’ai yasan mai yakeji cikin zuciyarsa.... Ijlaal ta K’araso jiki a sanyaye takai hannunta ta dafa Siyama dake kwance saman gadon... A hankali yarinyar take furta “Aunt Siyama, please you need to get better... I miss you so much, I want you back at home.... Mummy tace you’re now my Mummy, please Ki dawo wajenmu kinji Mummy na... I love you so much...!” Ta k’arashe tana mai kwantar da kanta saman k’afafun Siyama.... Allah sarki dik wanda zaice bai zubda k’walla cikin d’akin nan ba yayi k’arya, zukatansu suka kuma raunana.... Kamo Ijlaal Sameer yai yana k’ok’arin maida nasa hawayen yake sharewa yarinyar nata hawayen lokaci guda yake furta “Mummynki would get better kinji Ijlaal, kici gaba da mata addu’a kinji...!” A hankali yarinyar ta jinjina kanta tana mai kwanciya cikin jikin Sameer da tuni wasu hawayen sun gangaro masa... Raihanah ta kifa kanta hawaye na gangaro mata, shin ta yaya zata mance halaccin Siyama a gareta, matar data bud’e mata k’ofofin alkhairai na gianta, matar data zamto sanadin cikan burinta da farin cikinta.... Tabbas Siyama ta cika matar kirki da ba kowata mace zata iya jarumta da sadaukarwan da tai ba.... Da ace bawa zai iya fatan cuta ya k’aura daga jikin wani d’an uwansa Bawan ya dawo kansa tabbas da tayi addu’a ciwon Siyama ya tashi daga kan Siyama ya dawo kanta.... Siyama ta cika abokiyar zama da ko wata mace zatai fatan dacewa da abokiyar zama irinta, Ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen na kuma gangaro mata... Mummy ce ta umarce Raihanah data ja Ijlaal zuwa d’an waje Ta lallasheta... Raihanah ta masa cikeda kulawa kana ta janyo hannun Ijlaal tana fad’in “Muje Princess, Aunty Siyama would get better in sha Allah...!” Mummy Ta maidoda dubantaga a Sameer kana tace “Bazaka saka wani abu a cikinka ba Son... Ga fruits a nan ko shi bazaka tab’a ba...?” Sameer ya girgiza kai yana fad’in “Mummy na k’oshi, I’m not hungry, Dr nake jira yazo muji sakamakon gwajin ya sanar damu wani stage ciwon yake... Mummy I can’t lose partner...Mummy I can’t lose Siyama...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Mummy ta rungume kansa cikeda tausayinsu gaba d’aga hawaye na kuma gangaro mata... A haka Ammi ta k’arasa ta dafe hannun Siyama guda tamkar zatai mata addu’a sai kuma kuka ya b’alle mata... Allah sarki wannan kayan tausayi da yawa yake... Harta Mummy kasa lallashin Ammi tai dole ta k’yaleta tai kukanta... A haka su Daddy Aunty Daula Khalid da kuma Nabilah suka turo k’ofar d’akin suka shigo.... *Toh Mai Karatu mu had’u a shafin k’arshe na wannan dogon labari da ya d’aukemu dogon zango... Da izinin Allah a shafi na gaba kuma shafi na k’arshe zamuji yanda wannan labari zata kaya....* *Taku har kullum Sameena Aleeyou😍🤝* Sameena Aleeyou📚 *INDA RAI* _................DA RABO_ *_(2019)_* *113* K’ARSHE..... *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* D’aya bayan d’aya Dr d’in Ke dubansu kaman bazaice komai ba sai kuma ya buk’aci ganin Sameer da Daddy a can Office d’insa... Babu musu Sameer da Daddy suka take masa baya... Suna isa Office d’in Sameer ya mik’e daga zaunen da sukai saman kujera yana fad’in “Talk... Kai magana Dr, tell me wani stage yake...? Talk mana... Ka min magana mana..!!” Gaba d’aya ya kirice, kana ganinsa kasan a daburce yake dole ya baka tausayi..... D’an dafa kafad’arsa Daddy yai kana yace “Take it easy Sameer, ka kwantar da hankalinka kaji...” Duban Daddy kad’an Sameer yai ba tareda ya iya cewa komai ba, lokaci guda Dr AT(SHAK’UWA CE) ya sauk’e gajeriyar ajiyan zuciya yana mai mik’awa Sameer file d’in Siyama gabansa sanin cewa Sameer d’inma likita ne.... Cikin rawar hannu Sameer Ke tab’a file d’in kaman wanda aka sanya masa shokin, lokaci guda ya ture file d’in ya d’ago kansa kad’an yana duban Daddy kana yace “Daddy I can’t, bazan iya karantawa ba... I just can’t...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Duban Dr AT da ya dafe kumatunsa da yatsarsa guda yana duban Sameer cikeda tausayawa Daddy yai kana yace “Dr please, just go ahead and explain everything.... Sanar damu matakin da ciwon nata yake...!” AT ya jinjina kai a hankali kana yace “Alhaji, ciwon Siyama yana early stage ne, but a yanda takwarana likita Sameer ya susuce gaba d’aya hakan yasa na rasa ta yanda zan masa bayani.... Alhamdulillahi an gano da wuri, yanzu abinda ya kamata ai shine, zata undergoing therapy session kaman na zuwa watanni uku haka....” Daddy ya jinjina kai yana duban Dr AT dake ci gaba da zayyano masa bayani.... Kana yace “Toh Dr idan anyi wannan therapy sessions d’in shikenan hakan na nufin an k’one ciwon...?” Dr AT ya d’an girgiza kai yana mai kuma gyara zamansa saman kujerarsa kana yace “Hakan zai bamu dama ne to understand it’s behavior sannan kuma mu k’one k’arfin ciwon kafin yayi yad’o cikin jijiyoyin jini, and... Abu na gaba bamuda sauran zab’i da ya wuce mu cire mahaifar gaba d’aya....!” Daddy da jikinsa yai sanyi sosai a hankali ya furta “Does that mean bazata tab’a haihuwa ba kenan....?” AT ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an yana mai zare farar gilashi na k’arin k’arfin ganin daga idanunsa kana yaci gaba da fad’in “A halin yanzu ceton rayuwarta yafi komai mahimmanci... Chances na rayuwarta baida yawa dikda cewa musan rayuwa da mutuwa duka suna hannun Allah ne...” Dafa hannun Daddy Sameer yai kana yace “Daddy lafiyar Siyama shine gaba da komai a halin yanzu... Ban damu ko zata haihu ko bazata haihu ba... It is her that I love Daddy...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Dafasa Daddy yai cikeda jin dad’in yanda yake k’aunar d’iyarsa, tausayinsu gaba d’aya ya kuma kama Daddy... Lokaci guda Daddy ke goge hawayen da ya mak’ale masa a ido yana d’an bubbuga kafad’an Sameer... *** Bayan watanni uku akaima Siyama aiki kuma Alhamdulillahi anyi nasara.... Kwance take saman gadonta na marassa lafiya idanunta a lumshe sai sautin na’urorin bature dake tashi lokaci zuwa lokaci.... A hankalin ta soma Ware idanunta da sukai tsananin mata nauyi....Tar ta k’arashi bud’esu tana kallon pop dake bisa kanta... ta d’an kaikaito a hankali tana duban Sameer dako shakka babu a nan gefen nata ya kwana, hannunsa guda cikin nata, kansa kwance gefenta... Ta saki murmushi a hankali sanda siraran hawaye suka zubo mata.... “Partner...!” Ta fad’i da k’yar.... Bai tashi tashi ba, da alama baiji ba har saida ta d’an sake bud’e murya kad’an ta fad’i....”Partner..!!” Kaman a mafarki haka ya sinkayo muryar nata, yai saurin ware idanunsa yana mai mik’ewa zaune.... Lokaci guda yake kuma rik’o hannun nata yana dubanta yake fad’in “Partner... You’re awake... Thank Goodness... You’re finally awake Partner...!!” Ya k’arashe yana mai kwantar da kansa saman kafad’arta kad’an hawaye na gangaro masa.... Jinjina masa kai take itama tana hawaye... Lokaci guda Sameer ya d’ago yana kuma dubanta had’ida shafa fuskarta yake fad’in “I thought I was going to lose you Partner.... Please don’t leave me kinji....!” Ya k’arashe yana mai sunbatar hannunta.... Murmushi ta sakar masa ba tareda ta iya furta komai ba, saima hannunta guda da takai saman cikinta tana shafawa a hankali.... K’walla suka kuma ciko idanunta, sanda suka gangaro Sameer yaji d’umin sauk’arsu saman hannayensu da ya had’e waje guda yana mai dafe fuskar nata da hannayen nasu.... D’agowa yai yana duban yanda hawayen Ke gangaro mata..... Ya kuma matsowa cikeda kulawa yana fad’in “Partner.... Akwai yanda Ke maki ciwo ne... Tell me kinajin wani abu ne...?” Dik a d’an rikice yake maganar.... Girgiza masa kai tai a hankali kana tace “Partner this is the consequences of my actions, this is my punishment, I can’t bear a child....now I can never see my child... I can never give you a child partner...!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.... Kuma rik’o hannayenta Sameer yai yana fad’in “Don’t say that Partner... Godiya ma Allah ya kamata muyi da ya baki lafiya ya kuma tasheki... Ni Ke d’in nake so Siyama... Haihuwa kyautace Daga ubangiji ya baiwa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso ba dan komai ba sai dan ya jarabci bayinsa, wasu da lafiyar da komai bazasu haihu ba sabida Allah bai k’addari zasu haihun ba, wasu idan sun haihun ma yaran su zamto fitina a garesu ko wani abu mai kama da haka.... And one thing da ya zamto mana darasi a wannan rayuwar shine basai ka haifi d’a ya zamto Naka ba, just like me and my Mummy, mummy ba ita ta haifeni ba but I’m her son, sannan Mamani da Abbah... Mamani ba ita ta haifi Abbah ba but Abbah is her son.... So as you and Ijlaal, Ijlaaal is your daughter Siyama, she’s our first daughter...!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai kuma k’arfafa mata gwiwa.... Murmushin itama tai tana mai jinjina masa kai wasu hawayen na kuma gangaro mata kana ta d’an d’aura fuskarta saman hannunsa tana mai sakin murmushi a hankalin wasu hawayen na kuma gangaro mata... A haka Ijlaal da Raihanah suka turo k’ofar suka shigo rik’eda basket na abinci... Ganinsu a haka ya d’an saka Raihanah sadda kanta ita kaw Ijlaal a guje ta tafi ganin Siyama ta farka, nan suka shiga rungume juna suna fad’in irin kewar juna da sukai, Raihanah ta k’araso tana gaidasu Sameer na tsareta da idanu dan sai yanzu yake fahimtar wasu changes tattareda ita, ga wane irin cika data k’ara, baidai ce komai ba sai k’are mata kallo da yake wanda ita kanta saida ta tsargu da wannan irin kallo da yake binta dashi, gaisawa dai kawai take da Siyama amma ta sani idanunsa k’yam suke akanta dan harta ‘yan yatsun hannunta Ta kula dubansu yake daki daki.... Hakan bai hanata gudanar da abubuwanta kazar kazar ba dan bataso ya fahimci ta gane yana mata kallon k’urilla.... Lemon with hot water kaman yanda Dr Ahmad Tahir yace shi za’a soma bata idan ta farka hakan yasa Raihana mik’ewa tana k’ok’arin had’a mata dikda muguwar hajijiya dake yunk’rin kada ita ga mijin nasu ya tasata gaba da kallon k’urilla.... Ganin tana d’an dafe kanta sanda take k’ok’arin janyo flask na ruwan zafi ya sanya Sameer saurin mik’ewa yana fad’in ta bashi ya k’arasa had’awa, k’in sakar masa tai saima cewa da take ya barshi zata iya.... Ya tsareta da idanu sosai yana fad’in ta bashi flask d’in... A shagwab’e take mak’e masa kafad’a tana fad’in itafa zata iya.... Sameer yai mata k’uri yana duban cikin idanunta, Sai sannan hankalin Siyama dake ta biyewa Ijlaal yayo kansu, tai kwance tana duban yanda su duka biyun suke rige rigen kyautata mata, a hankali Ta saki murmushi mai sanyi.... Saidai nan ta hangi Raihanah tamkar tana layi jiri na shirin kada ita... A d’ari Sameer ya tarota ta fad’o hannunsa.... Ya shiga d’an jijjigata yana ambato sunanta... Daga Siyama har Ijlaal hankali tashe suke dubansu.... A hankali ta soma bud’e ido tana kuma dafe kanta... Daidai sanda Dr AT ya shigo ya taddasu haka... Nan ya kirawo nurses guda biyu suka taimakawa Raihanah zuwa next room.... Sameer da gaba d’aya a birkice yake ya mik’e yana duban AT dake rik’e da result d’in Siyama, kafin yai magana Siyama tace “Partner go... Just go to her, je kaga meke damunta....Nikam Alhamdulillah ai...besides ga Baby na tareda ni...” Ta k’arashe tana kuma janyo Ijlaal.. Ya d’an shafi fuskarta yace “Are you sure...?” Jinjina masa kai tai tana murmushi.... Murmushin shima ya sakar mata yana mai kuma shafar fuskarta... A tare suka fice da Dr AT yana fad’i masa sakamon result d’in Siyamar wanda yai kyau sosai... Daga AT har Sameer d’in test suka buk’aci nurses su gudanarwa Raihana, Sameer dake zaune gefenta idanunta a lumshe yatsun hannunta ya kamo yana kuma duban k’umban da kyau... Shi kad’ai ya saki murmushi yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa... Amma dai bara ya jira yaji daga bakin Dr AT.... Jim kad’an kaw saiga AT rik’eda result... Sameer ya mik’e yana tambayarsa meke faruwa.... Murmusawa AT ya d’anyi kana yace “Sameer mai tagwayen mata....” Sai kuma ya mik’a masa result d’in yana zolayarsa da fad’in “Ko shima na karanta maka ne tsoro kake...” A tare suka d’an murmusa kana Sameer yace “Tinda na rigada nazo nan kaine likitan a nan so just tell me...” Murmusawa AT ya kumayi kana ya mik’a masa hannu alamun musabaha yana mai furta “Congratulations Madam is carrying your baby.... You’ll soon be a father....” Jin abin yake kaman a mafarki da gaske dai shine zaiyi d’ah.... Kai Ubangijinsa ya cika abin godiya, Ya yayewa matarsa Siyama cutar da take fama dashi sannan at the same time ya albarkacesu da samun RABO.... Ashe da RABON yaga jininsa.... Take yaji hawaye na Farin ciki suna gangaro masa, tabbas tsanani na tareda sauk’i kuma ance mahak’urci mawadaci... Baisan sanda ya rungume Dr Ahmad Tahir ba yana mai cikeda Farin ciki had’ida godewa Ubangijinsa.... AT na ficewa Raihanah Ta bud’e idanu a hankali, nan taga Sameer zaune gefenta yana kallonta murmushi saman fuskarsa.... D’an dafe kanta kad’an tai kana tace “Mai ya sameni, Ina Aunty Siyama.... Tasha tea d’in...? Bara naje na bata....” Ta k’arashe tana k’ok’arin sauk’owa.... Bai bari ta sauk’a daga kan gadon ba sai rungumota da yai yana fad’in “Partner you stay right here...” Dubansa tai jin ya ambaceta da Partner.... Ta d’an dubesa kad’an kana tace “Nima Partner d’inka ce...?” Ya sakar mata murmushi yana mai shafan fuskarta kana yace “Of course you’re my Partner... We’re life partners...” D’an Jim tai kana tace “Does that means kana so na kaman yanda kake son Aunty Siyama...?” K’uri yai mata cikeda tausayinta dan lately yai neglecting d’inta gaba d’aya harma bai fahimci cewa tana d’aukeda juna biyunsa ba balle ya bata kulawan da ya dace... Koda shike halinda Siyama ta tsinci kanta ciki na cuta shi ya karkatar da tinaninsa dan bai tab’a kawowa bazai rasa Siyama ba... Shafa fuskarta ya kuma yi ganin hawaye na gangaro mata kana yace “Raihaan have I ever told you tin sanda na soma bigeki da mota sanda na soma d’ora idanuna kanki.... Tin lokacin na kamu da k’aunarki.... So never doubt, kar ki tab’a kokoton son da nake miki kinji koh...” Ta jinjina kai a hankali tana mai dubansa.... Janyota ya kumayi cikin jikinsa yana mai shafa bayanta a hankali.... Tana kwance cikin k’irjinsa take fad’in “Wai menene ya sameni..? Nifa na warke mu koma wajen Aunty Siyama....” Kanta na cikin jikinsa yake fad’in “No ki huta a nan... Babu abinda ya sameki Babynmu ne ya sanyaki fainting...” Ta d’an d’ago tana dubansa.... “Baby...?” Jinjina mata kai yai murmushi saman kyakkyawan fuskarsa.... Hannunta ya kuma kamowa yana mai ci gaba da fad’in “You’ll soon be a mother.... You’re pregnant My love...!” Jin abin tai wane iri Wai ita keda ciki.... Ta kuma dubansa tana kuma duban kanta.... Lokaci guda ta d’an kai hannunta saman cikinta tana mamaki... D’ago fuskarta yai kana yace “Do you love our child...?” Ta saki murmushi a hankali tana mai girgiza masa kai, a hankali take furta “So much.... But idan na haifeshi ko menene zan baiwa Aunty Siyama ne....Ita zata zamto mamanshi ko mamanta... Please ka amince min...” K’uri yai mata k’aunarta na kuma fizgarsa... Siyama da basu San da shigowarta ba tintini... Ta k’araso cikin d’an d’ingisawa ta dafa kafad’ar Raihanah.... D’agowa Raihanah tai tana dubanta nan taga hawaye saman fuskar Siyama... Lokaci guda Siyama ta d’an kwanto ta rungumeta wasu hawayen na kuma gangaro mata... Su duka biyun hawaye suke..... Sameer ne ya had’esu gaba d’aya ya rungume yanda ya hangi Ijlaal tsaye gefe, janyota yai itama ya rungumesu gaba d’aya zuciyarsa na masa wane irin sanyi yana mai mik’a godiyarsa ga Ubangijin Rahama.... Sati guda Siyama ta k’ara a asibiti aka sallameta, gashi dik wanda sukazo duba Siyama sai ta sanar dasu Raiha nada ciki, gaba d’aya ita ke d’aukin cikin saiko Sameer dan Raihanah kam fama da kanta kurum take, dikda Siyama bata ida warkewa ba batai k’asa a gwiwa wajen kulada Raihanah ba, ita da Sameer an rasa waye gwani wajen bata kulawa na musamman... Wani sa’in dukansu biyu suke d’aura kunnuwansu saman cikin Wai suna jin ko ya soma motsawa, haka Raihanah zatai ta dubansu tana dariya.... Oh shakka babu rayuwa tai dad’i sai san barka.... ** A can b’angaren su Engr kaw yau ake bukin shgul gulan swearing in, za’a rantsar da mai girma gwamna da muk’arabbansa su shiga Office yanda shima zai samu ya rarraba muk’amansa.... Zulfa’u na kwance saman gadon, dan tin kafin ya shige wanka take nan kwance ta kasa tashi, babu yanda bai ba ta taho suyi wankan tare amma tak’i saima dad’a lumewa cikin bargo da tai, Ta janyo k’aramar hotonsu da aka sanya cikin k’aramar frame Wanda Ke aje gefen bed side d’in Engr tana kallo, hotonsu ne da suka d’auka a Maldives Island, ta saki murmushi a hankali dan wannan waje memories ne da bazai tab’a gogewa cikin zuciyarta ba... Wayarta dake gefen bedside d’in ta janyo ta shiga gallery tana kuma kallon pictures d’in da suka d’auka, wasu a bakin beach wasu a wajaje na nan sha’awa... Wasu pictures d’in su duka biyu sunyi funny faces... Harda video da suka d’dd’auka.... Idan ta tina abubuwan da suka faru saidai kawai ta d’an saki murmushi.... Engr k’arshene wajen mantar da mace dik wani damuwar dake damunta, a bainar jama’a gashi nan zaka ganshi very calm and gentle amma idan suka keb’e ita kad’ai tasan mai Gwamnan nata yake juye mata... Ta kuma lumshe idanunta a hankali tsantsan k’aunarsa na azalzalanta.... Kaman daga sama sai jin d’igan ruwa mai d’an d’umi tai a bayanta.... Kan tai aune ya mirgino da ita suna fuskantar juna.... “Tashi muje na wankeki tinda na kula kasalanki da k’iwanki ya soma yawa, idan na biye naki zamu makara....!” Ya k’arashe yana k’ok’arin janyota jikinsa.... Baki a ture take fad’in “Haba my Governor... Is my presence that necessary, Nidai kawai bazan iya zuwa ba.... Wllhi bacci bai isheni ba....!” Ta k’arashe tana kuma sakin hamma had’ida mik’a tana mai k’ok’arin turasa daga jikinta.... Rausayar da idanunsa ya d’anyi kana yace “Alright idan bazakije ba saidai kada a rantsar dani.... Muyi swearing in d’inmu a nan... Dama nafi san hakan....!” Ya k’arashe yana mai kashe mata idanu had’ida wasu salo nasa na musamman.... Ai a d’ari ta shiga turasa tana fad’in zata tashi, tana k’ok’arin zillewa daga hannunsa.... Saidai mik’ewar da zatai jiri ya d’an taso mata.... Ya dubeta da kyau kana yace “My lady.... Are you sure you’re alright...?” Jinjina masa kai tai tana mai kuma sakin hamma tareda mik’a take fad’in “I’m fine don’t worry about me... Let me use your bathroom k’iwan zuwa nawa nake...” Ta k’arashe tana mai fad’awa bathroom d’in, shidai Engr kallo ya bita dashi had’ida d’an ware idanunsa kana ya mik’e yana k’ok’arin shiryawa, ya kula kwana biyun ta canza sosai... Yana nan tsaye closet ta fito tana rik’e baki da hanci take fad’in wannan shower jell d’in nasa baida dad’i da alama ya canza.... Dubanta ya d’anyi kana yace “Baby ban canza ba fah... Wannan dai da kike so ne....” Ta d’an yamutsa fuska kad’an kana tace “Really... Toh gaskiya flavor d’in ya daina min dad’i ka canza wani....” Jinjina mata kai yai yana mai takowa kusanta, lokaci guda ya d’an kamo k’ugunta yana mai furta “Right away, an gama your Excellency Ma, sai wanda kika zab’a.... But wait, are you sure babu abinda kike b’oye min...?” D’an zaro idanu tai tana dubansa kana tace “Ni kuma...!” Ya d’aga mata gira guda still yana rik’eda k’ugunta.... Lokaci guda yakai hannunsa guda saman flat tummy d’inta yana furtawa a hankali “Are you sure babu ajiyana a nan...?” Zabura ta kumayi tana dubansa, sai kuma maganarsa ya soma ringing a kwanyarta.... Ta d’an muskuta kad’an kana tace “No ni dai babu komai... Just get dressed up kafin ka makara..” Tai maganar tana mai zillewa Daga rik’on da yai mata kana ta nufi k’ofa a d’an guje tana mai shafe cikinta dan tuni taji wani strength yazo mata... Bud’e murya ya d’anyi yana mai fad’in “Be careful Love... Watch your steps kar kimin asara....!” Ita dai ko kulasa batai ba kayanta ta shige tana mai kuma murmusawa dafe da cikinta... Langab’e da kai Engr ke dubanta har ta b’acewa ganinsa tsantsan soyayarta na azalzalansa, rayuwarda yaita mafarkin samun irinta a gidansa, yau gashi nan yana experiencing... Ashe dai tabbas yanada RABON hakan.... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai k’ok’arin shiryawa da kayan da Ta fitar masa.... Haka suka d’unguma suka fita shida family d’insa gwanin ban sha’awa.... Da shike akan kunnawa ‘yan prison tv su kalli news a nan Muhibbah take kallon bukukunan rantsar da Engr matsayin gwamnan jiha ga Zulfa’u da yaransu a gefensa gwanin ban sha’awa sun bala’in dacewa da birgewa... Hawaye suka gangaro mata tana mai gogewa a hankali, Allah sarki da yanzu itace nan tsaye gefensa sanda ake rantsar dashi amma sai gashi tana gidan kaso ake rantsar da Excellency d’inta... Kai kaicon aikin danasani.... Shamzy ta dafata a hankali cikeda tausayawa dan dole ne ka tausayawa.. Murmushin k’arfin hali kurum Muhibbah tai tana mai tashi daga wajen dan harga Allah bazata iya jure ci gaba da kallon ba.... Abinda yaiwa Muhibbah dad’i shine ziyara da suka kawo mata har nan prison gaba d’ayansu, sukai nasu murnar tare da yaranta gwanin dad’i, batada abinda zata sakawa Engr dashi sai addu’a... A haka akaci bukunan rantsar da mai girma gwabna, dangi gaba d’aya an hallara su Mamani su Abbah su Daddyn Siyama Daddyn Sameer, su Mamy su Ammi Aunty B Aunty Daula da dai sauransu, su Nabilah ne dai basu zo ba dasu Siyama su Raihanah tinda wata mai kamawa ake bikinsu Naja’atu da Akram da kuma Shamsu abokin Sameer da Marliya, ga kuma na Dr Awwab da Sahariyya dan tinda yai treating d’inta Allah ya nufa ashe Sahariyya ce matar, Dr Awwab ya tab’a aure amma yanzu basa tareda matar, ya jima babu aure tin bayan rabuwarsu da wancan har saida Allah ya had’asa da Sahariyya a halin yanzu... Da RABON shine mijinta, wannan karon harta su Amarah saida Sahariyya ta gayyata, sukaita murna suna bata hak’urin abubuwan da sukai mata baya... Daga wajen shagulgulan rantsuwa aka shige da Zulfa’u asibiti dan ta kusa fainting a can yanda aka tabbatar masu tana d’aukeda juna biyu... Wai Zo Kaga murna wajen Engr sai kace ba’a tab’a masa haihuwa ba... Zuri’a tanata Albarka sai san Barka da alama ta ko wanne b’angarorin an sami RABO... Saidai muce Allah shi raba lafiya ya kuma bada masu jin k’an iyayensu wanda zasu amfani Al’umma baki d’aya..... Tuni Engr ya rarraba muk’amai ciki harda Hafiz, shima ya sami appointment a gwabnatin Engr yanda aka basa SSA to the security matters, Wato Senior Special Adviser to the Security matters dan tinda ya taka babban rawa wajen capke Oga Duna mai girma Gwabna Wato Engr yaga baza’a kyale Hafiz haka nan ba, dole ai tafiyar taredashi dan ya ringa taimakawa ana capko b’ata garin Al’umma.... Su Hafiz an zama babban mutum har wani kamala ya k’ara saidai ko batun aure baiyi, haka Mamani zata tasa sa gaba tana k’are masa tanadi saidai yace oho dai yaji, gani yake kaman garin neman aure zai kuma nemo irin Sawwama shed’aniya jarabebbiya da taso jefasa a halaka... *** ABUJA Agogon dake d’aure tsintsiyar hannunsa na hagu ya kuma dubawa yana mai fad’in “Wai ina Shayibun ya tsaya ne, banso muyi missing flight d’in nan, dan idan muka rasa wannan flight d’in saidai mu fasa tafiya Kano...” Baki a ture take harararsa kana tace “Tab! Aiko wllhi saidai kai ka fasa amma nikam sai naje, biki har uku... Lallai ma ai ko a mota ne sai na tafi...!” Tsareta da idanu yai fuska a tsare kana yace “Waye zai barki Ki hau titi kije Kimin asara, ai keda tafiya by road sai kin haihu... Ni da ta nine ma bazakije Bikin nan ba kawai dan dai kin dage ne...” Cuno baki ta kumayi cikeda shagwab’a tana fad’in “Wato baby ne damuwarka bani ba koh....?” Khalid dake k’ok’arin k’unshe dariyarsa janyota jikinsa yai yana fad’in “Wane ni teddy bear, ai ban isa nace haka ba... No one can ever replace you... Kawai banso kisha wahala ne kinsan ina matuk’ar k’aunarki da dik abinda zai faranta miki...” Murmusawa tai a hankali tana mai dubansa cikeda k’aunarsa daidai sanda suka soma jiyo alamun bud’e gate Shayibu ya iso d’aukansu zai kaisu Airport..... A hankali ta furta “I love you... My bear...!” Ya manna mata kice a hankali yana mai furtawa “I love you more...teddy bear...!” Lokaci guda ya sakalo hannunsa cikin nata yana fad’in “Shall we...” Jinjina masa kai tai tana mai shigewa cikin jikinsa suka nufi k’ofa.... *** KANO Taro yayi taro, zuri’a tai Albarka, an cika iyaka cika a wanann biki.... Kowa ya hallara, su Mamani ba’a sama ba’a k’asa... Ita bama ta ‘yan biki take ba wak’ar nan ta Engr na lashe zab’e da Rarara ya rera masa shi tasa aka k’ure mata sai tik’an rawa take kayanta Goggonayen Kazaure na tayata lokaci guda jama’an dake wajen na darawa cikeda nishad’i.... Su Sadiya sai d’aukarta suke suna fad’in yau sai status d’insu yai kuka.....Lol A can b’angaren Mamy kaw,su Ammah dasu Aunty Daula, Mummyn Sameer harma da Ammi sune acan suna nasu bidirin harda Aunty Hanne da Yesmin sunzo... Aunty B ce ta shigo tana sanar da Mamy yanda sukaida Major Kabir Kaita mijinta da a yanzu ya kuma samun matsayi ya dawo gareta yana mai bata hak’uri kan cewa ta bisa cen Lagos tinda yanzu tayi settling family d’in nata kaman yanda ta buk’ata daga garesa wanda hakan ne musabbabin samun sab’aninsu dan cewa tai bazata abandoning family d’inta a halin da suke ciki a baya ta bisa ba, hakan yasa sukaita samun sab’ani toh yanzu dai ga Allah ya karkato mata da hankalinsa.... Su Mamy dasu Daula su Ammah sukace k’warai tabi mijinta dan ta cacanci Farin ciki itama bayan d’inbin SADAUKARWAR da taiwa Ahalinta.... Major Kaita ya shigo ya gaisa dasu ya kuma basu hak’uri da jaddada masu cewa zai kula da ‘yar uwarsu ya kuma bata kulawan da bai bata a baya ba... Farin ciki ya lullub’e ahalin Aunty B bayan dik abubuwan da tai masu basusan da mai zasu saka mata ba tabbas addu’arsu ce zaita isa gareta har yanda take... Nan Aunty B tai baiwa mijinta hak’uri itama dan ko shakka babu tana k’aunarsa... Haka sukai sallama da sauran ‘yan uwa ba’a ida Bikin da ita ba tabi Mijinta Major Kaita suka tafi daga can Lagos d’in zasu wuce k’asar Russia yanda zai gudanar da wani course... Shagalin biki yaci gaba da gudana bayan an gama koke koken sallama da Aunty Bara’atu babu kaman Zulfa’u wacce take ‘yar gidanta.. Aunty B d’in ta jaddada mata da zaran ta haihu in sha Allahu dik yanda take zata baro tazota ganin grandson ko granddaughter d’inta.... Su Zulfa’u, Siyama, Raihanah harmada Yesmin suka d’unguma suka nufi gidan Baba Alhaji zasu taho da amaren gaba d’aya nan wajen Mamani yanda za’a gudanar da family eve, suka shiga gidan kace kace Haule na lale dasu... Ita kam Yesmin can k’ofa aka barta tana faman danna waya, nan taji taci karo da mutum... Ta d’ago dafe da goshinta tana watsa masa harara... Shima fuska a murtuk’e yake dubanta, kan Hafiz yai aune ta shiga silla masa masifa... Da tsananin mamaki yake dubanta kana yace “You watch where you’re going next time....” Ta kuma hararsa tana fad’i a hankali “he’s so mean...” Tana maganar tana sosa goshinta... Juyowa yai kad’an kana yace “Mai kikace....?” Hararsa itama tai kana tace “Kai mai kaji nace..?” Ga tsananin mamakinta murmushi taga yayi da gefen bakinsa kana yace “Naji kince he’s so handsome that I couldn’t take my eyes off him...!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice yana kuma sakin murmushi... Tsaye tai tana bin bayansa da kallo har ya b’ace mata murmushin da bata san daga ina bane ya kufce mata.... A haka suka fito da amaren yanda suka nufi hamshak’an motocinsu na alfarma dake jiransu waje tareda jagorancin Matar mai girman Gwamna kuma First Lady Zulfa’u.... Bayan sun isa gidan Mamani ne suka tadda draman Mamani da Khalid ya kasa ya tsare yace matarsa bazatci sha daka da Mamani ta bata ba a cewarsa kar yai affecting babynsa... Mamani ta dangwari k’eyarsa tana fad’in “Kai Haladu bana san iyayi d’in nan Naka... Wato kaima ka iya felek’e toh sai taci nace sai taci... Ungo d’auka kici, Wato kai ga mai mata da d’ah koh... Ungo Ci shadakanki kai waysan mai akaci da cikinka....” Ta k’arashe tana mai mik’awa Nabilah dake masa gwalo tana fad’in “Yauwa Mamani na yau dai bayana kikabi kin gwansa d’an gaban goshi...” Mamani tace “Ai kema ba sabida ke na bada ba dan tattab’a kunnena dake cikinki na so ne... Kinsan d’an Haladu dole ya zama na gaban goshi na... Gaba d’aya suka dara daidai sanda Su Mamy dasu Ammi harma dasu Haule dik suka shigo za’ai family pictures, Nan Khalid ya fice kiransu Abbah a cewarsa ya kamata ai gaba d’aya... Jim kad’an kaw suka shigo gaba d’ayansu mazajen harma dasu Engr dasu Sameer su Hafiz... Gaba d’aya sunsha manyan kaya da huluna masu d’aukan idanu gwanin ban sha’awa saikace sun fito daga sallan idi... Mamani na tsakiya zuri’arta na hallare gewaye da ita hawaye ya d’igo mata tana ayyanawa cikin zuciyarta yau Ina Mahmud Mailafiya yaga wannan kayan Farin ciki... Ko yanzu tabar duniya Alhamdulillah itakam babu abinda zatace sai godiyawa Ubangijinta...Allahu Akbar Zuri’a tai Albarka... Wai akace INDA RAI DA RABO.... Take camera man ya saita camera d’insa don d’aukan wannan kyakkyawan ahali yayinda nima na aje alk’alamina da nai amfani da ita wajen rubuto maku wannan labari mai cikeda abubuwa iri daban daban ciki nace kai nima dai bara na d’auko maku hoton wad’Annan ahali... Take na saita camera d’in wayata nima na d’aukar maku hoton... Nasan su Ahalin SAN suna nan suna jira suga hoton nan dan ga su Sadiya Auwal su Oum Imaan su Fatee Beni su Bintaa su Laweesa su Mrs Deen su Maman Sadiq su Baby Mahe su Nafisa Wala su Maamah su Halima Mekeke su Oum Noor su Zynab Maude su Maryam Mu’az, Maman Hanan, Yasmeen, Hauwa Muhammad, su Bilkeesu,Raheela, su Maryam Muhammad... Su su su kai kunada yawa duk kunsan kanku masu jiran ganin hoton nan... DA RABON kuga hoton yasa na d’auko maku... LOL ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! A nan na kawo k’arshen wannan labari mai taken INDA RAI DA RABO.....Dikkan yabo da godiya Sun tabbataga Allah da ya bani damar kammala wanann littafi cikin kwanciyar hankali bayan dogon zango da aka kwashe ana rubutunsa... Fad’akarwar dake ciki Ubangiji yasa mu amfana dashi, kurakuren dake ciki Allah ya yafemu gaba d’aya... Ameen! Jinjina gareku dan kun cancanta... Engr Sholyngaye Aunty Hasken Annuri Aisha Amaal Bappah Sameena Aleeyou Novels(SAN) Zauren Biebee Isa(ZBI) Ubangiji ya bar k’auna🤝 Ina kuke Trio😍 AKA Partners💯 littafin nan d’aukacinsa sadaukarwace gareku... Ko ban fad’i ba ku kunsan namijin k’ok’arin da kukai wajen ganin littafin nan ya kammala... Ubangiji ya bar k’auna... Raliya Garba(Rally), Maimuna Mansoor(Anmunah), Aishatu Dahiru Audi(Shawty)....Sonso fillah❤️ Sameena Ke maku fatan Alheri a dik inda kuke🤝 SameenaAleeyou📚