TUDU A KAN KWARI    LABARIN SOYAYYA MAI DAUK’E DA RUƊANI, CAKWAKIYA,GANGANCI,BAN TAUSAYI. ..Daga Alƙalamin Sayyid writer (Legend) *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* 🌻🌻🌻 _"Ƙungiyar Marubuta masu tasawa, Rubutunmu shi ne tafiyar da ke wuce lokaci, mu ne masu ɗaukar harshen gobe a yau. Marubuci ba ya zana kalma kawai, sai dai ya zana mafarki a zuciya, ya maida shi haske ga al'umma. Wannan shi ne alwashinmu a matsayin mu na matasan marubuta. Taken mu shine ɗaga darajar Marubuta masu tasawa."_ 🌻🌻🌻 Sadaukarwa… Na sadaukar da wanan littafin ga Mahaifina da mahaifiya ta, Allah yak’ara muku lafiya da nisan kwana da kuma arzik’i. Wanan k’irk’irarren labari ne banyi dan cin zarafi wani ko wata ba. Sanarwa… Tudu akan kwari ba sabon labari bane, tsohon labari ne dayasamu ƴan gyare-gyare da sauye sauye. Godiya… Ina godiya ga Allah (S.W.T) da ya bani baiwa da damat rubutu mai amfani da ilmantar wa Ina godiya ga duk masu bibiyata domin sune ƙarfin gwiwa ta. Gaisuwa…    Ina gaisuwa ga marubutan littafin A Gidan Aure na baki ɗayansu. 1.  Ina miƙa saƙon gaisuwa ga Anty Hussaina s Abdullahi, wacce ta kasance babbar yaya a gareni (Allah ubangiji ya raya muwaddah da sauran ƴan-uwanta). 2.  Ina miƙa saƙon gaisuwa ga Ruƙayya Yusuf ibraim (A.Y. M. Palace Nova). 3. Ina miƙa saƙon gaisuwa ga Salamtu Hussaini (Queen bee) 4. Ina miƙa saƙon gaisuwa ga Hadizatu Mrs kd Marubutan littafin A gidan Aure nah,sanan ina gaisuwa ga dukannin marubuta mussaman. Ummulkhair s panisau Queen Waleedah Jamila umar janafty Maryam laminu gwarzo Muhammad lawan prp. Dama sauran marubuta baki ɗaya. SHIMFID’A…..                Pegi na farko… 01 Matashiyar buduruwa ce wacce a k’alla baza ta huce shekara 22 ba,tsaye take cikin madaidaicin office wanda  ya ƙawato da ado. Dik da office ɗin bai kasance mai girma ba amma yana da kyawun gani, bata cika shi da kayan kyalele ba amma ya tsaru. Kasancewar shigowar ta kenan cikin office d’in ba ta kai ga zama ba idon ta ya sauka kan flowers d’in dake zube kan table daga gefe, da mayalwacin mamaki ta nufi wajen. Kallon followers ɗin tayi sosai tabbas ba ita ta ajiye su ba, kuma jiya ita da kanta ta kulle office ɗinta. knocking d’in kofar office ɗin a kafara ba tare da ta juyo ba ta bada umarnin shigowa. Baba Masinja ne ya shigo yana faɗin. “Barka da ƙaraso wa ranki ya daɗe.”        “Barka dai Baba.” ta faɗa tana fara buɗe flowers d’in cike da mamaki, sai kuma ta juyo ta kalli Baba Masinja. “Am Baba waɗanan kayan kuma daga ina haka?.”     “Yawwa ranki yadade dazu da sassafe wani mutumi ya kawo yace naki ne,harda wata takarda ma kiduba cikin drower ɗinki.”         “NI.” ta faɗa tana nufar wajen da drower d’in take, bud’ewa tayi idanun ta suka sauka akan lafiyayyiyar takarda da tasha ado.  “M.A” d’in da ta gani jikin takardar ne  ya sata jan tsaki,a fili ta furta  “Wannan wace irin maita da masifa ce, wanan wane irin mmutum ne haka mai nacin jaraba?.” Baba Masinja jin ta fara faɗa yasan ta gane idan saƙon ya fito, hakan yasa yaja mata ƙofar ya fice ko ba komai shi kam yaci kyautar manyan kudaɗen da mutumin ya bashi. Guri ta zamu ta zauna hannun ta riƙe da takardar, ƙarar shigowar saƙo wayarta ne ya katse mata gajeren tunanin da ta fara. Hannu takai kan desk ɗin da wayar take ta ɗauka, wani dogon ja tsaki taja bayan ta kalli saƙon, fara karanta wa tayi har ta gama sanan ta ƙara jan wani tsakin. “Ni gaba ɗaya mutumin nan ya fitini rayuwata,shike nam turo da saƙo kala kala ƙarshe a kira wayar baza ta shiga ba Kullum a ɓoye kamar mara gaskiyya gashi yau har ta kai ga yafara tura mata saƙo cikin office”     Haka ta yini tana faman tunane tunane, ta kwashe wacan ta ƙara wancan, sauƙin ta ma office ɗin nasu ba mai hayaniyar ma’aika ta bane. Sai zuwa ƙarfe huɗu da kwata ta fara shirin tafiya domin tasan yanzu Asiya zata ƙaraso domin bata taɓa huce ƙarfe huɗu ba ta zo ba, gashi yau har ta gota. Ba ta ƙarashe tunanin ba taji anturu ƙofar, Asiyan ce ta shigo bayan ta kuma Nawfal (wanda yake shugaba wajen aikinsu, kuma yake nuna mata soyayya ta gaske, sai dai ita bata ko kula, tana kulashi ne a matsayinsa na shugaba a inda take) Murmushi ta saki mai cike da yaƙe ganinshi, domin yau bata ko samu damar zuwa sun gaisa ba.    “Wai dama Sir yau kashigo office d’inan,banga ka ba sai da mutuniyar ka tazo.” “Gashi kuwa kin ganni.”  ya bata amsa a daƙile wai shi adole fushe yake, Shiru tayi ta cigana da haɗa kayanta dan dama ita kara take masa  a matsayin sa na shugaban ta a wajen aiki, amma ko kad’an bata tab’a jin wani sonshi ba,balle dan yayi fushi zata ji babu dad’i      “Meenaarh haɗe kayan mutafi mana.” Asiya tafad’a da alamar k’osawa,dan ita tun daga office d’insu hankalin ta yayi gida gashi tana zuwa Nawfal ya tsayar da ita kusan minti talatin yana mata surutan wai Ummi bata sonshi.    “Muje.” Ummin tafad’a tana kama hanya zata fice, Nawfal ne yafara ficewa sanan Asiya ita kuma Ummi ta t’saya ta kulle office d’in tabi bayansu    “Kayi hak’uri Nawfal zamuyi magana da Meenarh insha Allahu komai zai dai daita.”    Asiya tafad’awa Nawfal ganin yanda Ummi ta watsar dashi kamar ba tasan yana fushi ba. “Badamuwa Asiya nagode sai najiki.” Nawfal ya faɗa dai dai lokacin da Ummi ta k’araso wajen. Ka ɗa kai yayi  yatafi hakan yasa su ka shige tasu motar  Asiya taja su. Sai da sukayi tafiya mai nisa Ummi ta buɗe baki tace  “Asiya kinsan kinsan mutumin nan har takai yafara turumun da saqo?.”   “Wane mutumi.kuma wane kalan saqo?.” Asiya ta tambaya hankalinta nakan driving ɗinta. “Wanan M.A.M ɗin mana.” Ummi tabata amsa idonta a rufe “To ai yadad’e yana turo miki saqo ko?.” Asiya ta ƙara faɗa ba tare da ta juyo ba. “Asiya zan zage ki wallahi,d’azu da nazo office kawai naga flowers harda rings ga kuma katuwar love letter,ko karantawa banyi ba naga message d’inshi.”  Ummi ta k’arashe Maganar tana mik’awa Asiya wayar, Karɓar wayar Asiya tayi tana cewa. “To ki tsaya kiyimun bayani amma kina mun magana a gajarce.” Harara Ummi ta maka ta sanan tace “Duba dai kigani.”  Shiru Asiya tayi ta karance saƙon baki ɗaya sanan ta miƙa mata wayarta ta.   “Meenarh a ɗan ƙaramin binciken da nayi akan mutumin nan duk da bani da wani assurance na cewa shine, Amma tabbas wanan logo d’in da sunan na wani babban company ne a legos,sanan akwai wasu branches a Abuja da nan kano,na duba sosai wajen samu hoton asalin hoton owner ɗin amma ya gagara, komai a ɓoye.” Kallon ta Ummi tayi sanan tace “lallai sannun ki Asiya da wanan dogo bincike,amma taya kike tunanin mai wanan dukiya zai b’ata lokacin sa har haka?, yana turumun da messages.”  “Abinda nima nake tunani kenan,Amma insha Allahu ko waye zai zamana Alheri ne…… Katse ta Ummi tayi ta da cewa  “Wane alheri kuma Asiya bayan da kud’in auren wani akaina,ko kema kin fara mantawa ne?.” “ Uhm ni kyale wanan batu.! Ummi ya kike ganin zamuyi da Nawfal?.” Asiya ta faɗa ganin har sun kusa isowa gida. Shiru Ummi tayi tabbas tana so su rabu lafiya da Nawfal,duba da kasancewar sa Mutumin kirki mai nagartatun halaye, amma kamar shi ɗin ba zai fahimci haka ba.”Kinyi shiru.”  Asiya tafad’a tana karya kan motar zuwa cikin layin su. “Kinga doctor anjima mayi maganar.” Ummi  ta faɗa ganin sun k’araso gida. Parking Asiya tayi bakin wani gida mai d’auke da k’aramin gate,inda Ummi tabude k’ofa ta fito kai tsaye gidan tashiga inda ita kuma Asiya ta k’ara jan motar zuwa wajen wani madaidaicin gida shima da ke d’auke da k’aramin gate ~~~~    Da sallama Ummi tashiga cikin gidan nasu, inda ta tarar da mahaifiyar ta Hajiya tsugun ne bakin bayi tana d’aura Alwala. sallamar ta k’ara maimaita wacce tayi ta farko ba’a amsa ba, Amsa sallamar Hajiya tayi tare da fad’in.“Sannu da dawowa.”    “Yawwa sannu da gida hajiya.” Ummi tafad’a tana a jiye jakarta ta nufi wajen d’aura alawan itama.   Bayan ta idar da sallah ne tafi to daga cikin kyakyawam d’akin ta wanda ya k’awato da kayan ado dai dai masu k’aramin k’arfi, kai tsaye d’akin hajiya ta nufa domin amsa kiran da tayi mata.      Da sallama ta shiga d’akin inda tasamu Hajiyan zaune bakin gado, itama zama tayi sanan tace “Hajiya gani.” Hajiya bata amsa mata ba sai nuna mata gefen gadon tayi da hannu, da sauri ta tashi ta nufi inda taga kayan a zube a ƙasa, maka mantan kayan da aka kaimata office ɗinta a fili ta furta. “Innullahi wa inna illahir rajiun, wanan wane mutum ne yake son jamun masifa haka ne.”        “Ummi ba sai na miki bayani ba tunda gashi kinsan daga inda suke,kuma baxan tambaye ki wanene yakawo miki ba, sai dai in tunamiki da kud’in auren wani akanki sanan kuma na k’ara tunamiki da irin halin da kika jefa kanki damu ciki a baya…         “Hajiya wallahi tallahi bansan way’anan kayan daga ina suke ba.” Ummi ta katse hajiyar da murya mai cike da kuka.      “Kinga tashi ki bani wuri, nafad’a miki abinda zanfad’a miki idan kinga dama ki d’auka idan baki gani ba karki d’auka.”  Tashi Ummi tayi ta fuce. “zo ki kwashe kayanki ki fice mun dasu daga d’akinan.    Dawowa tayi ta kwashe kayan fa fice.  A tsakar d’akin ta, ta watsar da kayan ta kifa kai a kan gado ta fashe da kuka “wanan wace irin rayuwa ce da uwar da ta haife ka ma bata fahimtar ka”.     Kuka tayi mai isarta sanan bacci b’arawo ya d’auke ta. Bata tashi ba sai da  kiran sallan magariba  yata da ita.    Bayan tayi sallah ne ta d’auki wayarta ta kira Asiya domin tasan tabbas Hajiya baza ta tab’a barin ta zuwa ko ina ba, sai da Asiya tayi sallan i’sha’i sanan tasamu shigowa lokacin Ummi da Hajiya na zaune a tsakar gidan kan tabarma kowa ce na sabgar gabanta  ciki ciki Hajiya ta amsa gaisuwar da  Asiya ke mata,tunda ga nan Asiya ta fuskanci Ummi ta k’ara jawo musu wani abun.    Tashi sukayi suka nufi cikin ɗakin ummi wanda Asiya bata bari sun kai ga zama ba ta fara magana. “Ummi me kuma kika yi.?”    “Me nayi ni uwar laifi ko.” Ummi ta bata amsa tana zama gefen gadon dake cikin ɗakin.  “To ai naga  yanda Hajiya take kallo na ne.” Hannu Ummi ta d’aga mata ta nuna mata tulin kayan da aka kawo mata.   “Daga ina kuma way’anan ni Asiyatu.?” “Daga wajen jarababben mutumin nan da yake neman ya dawo dani cikin tashin hankalin.” Ummi tafad’a alamar ta gama fusata.    “Ki daina fadin haka Meena tashin hankali da muka shiga a baya yatafi insha Allahu,kuma kowa ne wanan insha allahu bazai zamar mana tashin hankali ba.”    (nikam nace wanan wace irin masifa ce ina masoyi ya taba zama tashin hankali? lol) Legends pen. TUDU A KAN KWARI.      (Short stroy) Mallakar Sayyid writer (Legend) *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* 🌻🌻🌻 _"Ƙungiyar Marubuta masu tasawa, Rubutunmu shi ne tafiyar da ke wuce lokaci, mu ne masu ɗaukar harshen gobe a yau. Marubuci ba ya zana kalma kawai, sai dai ya zana mafarki a zuciya, ya maida shi haske ga al'umma. Wannan shi ne alwashinmu a matsayin mu na matasan marubuta. Taken mu shine ɗaga darajar Marubuta masu tasawa."_ 🌻🌻🌻          Pegi na biyu 02. Washe gari tun zuwan ta office take ai kin tunani yanda rayuwa ta fara tun daga tashin ta zuwa girmanta,  irin soyayyar da tasamu daga mahifinta, mahaifiyar ta, yayarta da kakannin ta har zuwa lokacin da komai ya canja na rayuwarta, Tudu akan kwari ya gifto ciki yayi gaba da farin ciki,nustuwa da kulawa daga rayuwar ta ya gayyato mata tashin hankali da damuwa Kuka ya zamema ta abun yi a ko yaushe. K’arar wayarta ne yadawo da ita daga tunanin da take yi, hannu takai ta d’akko wayar ta kara a kunne tare da fad’in    “Hello.”  daga can bangaren aka amsa da cewa       “MEENATAH.” Da sauri ta zare wayar daga kunne ta, ta duba sunan dake jiki saidai pravite number ce ma ashe. “Kinyi mamaki ne.?” aka k’ara fada daga cikin wayar. Ya za’ayi ta manta da wanan Muryar yaza’ai ta manta da wanan sunan, sunan da ba wanda yake kiranta dashi sai shi kad’ai cikin wanan muryar, da sauri ta katse kiran tare da fad’in  “Innanullahi wa,inna illahir rajiun, me Mukhtar yadawo yi cikin rayuwa ta.”  Firgit ta tashi ta nufi wajen da ta ajiye kayan da aka kawo mata jiya wayanda bata ma bude su ba,  d’akko su tayi zuwa kan table d’in ta sanan tafara bud’e su wata envelope ce ta fad’o da sauri ta kai hannu ta bud,e ta, hotuna ne suka zuba daga ciki, tsugunnawa tayi ta fara kwashe su tana kallon su. Hoton wani kyakyawan farin saurayi mai kama da larabawa ne ya bayyana a jikin hoton farko, yana sanye cikin ash colour na jacket wacce tazo masa har gwiwa da ga kasa kuma neavy blue din wando jeans ne a jikin shi. Ƙafar shi sanye ciki black boots na takalmi, da alamun hoton ma ba a nigeria bane duba da yanayin background d’in. Fuskar shi ta tsurawa ido tana so ta ga kama ko da guda d’aya ce da Master, haka taga ma amma bata ga wata kama ba hakan yasa ta juya zuwa hoton gaba. Still kyakkyawan matashin ne shima dai ba a nigeria din bane, cikin rashin k’warin gwiwa ta bude hoton gaba sai dai abinda ta gani yasa ta mike da sauri da fadin “wallahi shine! master ne!.” k’ara kurawa hoton ido tayi shine ɗin ne cikin shigar shi ta k,ana nan kaya golden yellow din riga da blue din wando,wuyan shi yasha sark’a, hannun sa cike da zobe, idanun sa sunsha kwalli.   Kai kana ganin wanan hoton ka ga rikak’en ɗan daba, wanda yake tashen rashin jin magana.  Ta dad’e tana kallon hoton wani irin yanayi take ji, wani abu take ji yana shiga zuciyar ta, da sauri ta huce hoton zuwa na gaba.        WACECE UMMI? Amina Kamal Alhassan Shine asalin sunan ta. Haifaffiyar garin Zaria cikim unguwar Gyallesu.  Mahaifinta  Sunan sa Alhaji Kamal—Alhaji kamal mutum ne mai wadatar zuci tun yana k’arami yake da neman nakai sosai,shekarar shi 22 yayi auren shi na farko inda ya aure Wata mai suna Amina,wacce sukayi rayuwa cikin soyayya mai dad’i, Kamal yaso Amina. Kamar yanda ita ma Amina taso Kamal ta masa biyayya a gidan Aure, har yakai ga Kamal yaji cewa Mace daya ce a duniya Amina.  Shekarar su Uku da aure Allah yayiwa Amina rasuwa wajen haihuwa– haihuwarta ta farko inda ta mutu tabar yarinyar ta wacce taci sunan Goggo mahaifiyar Kamal Nafisa, dai dai lokacin da arziki yafara samuwar wa Kamal.   Yaji mutuwar Amina har sai da ya kusa zaucewa bayan lokaci kadan Goggo ta nema mai Auren Saliha yar gidan k’awar ta, Kamal baiyi musu ko jayayya da mahaifiyar sa ba, ya karb’i auren Saliha, lokacin nafisa yar su ta na da shekara d’aya da rabi.   Saliha ba mace bace mai mugunta ta rike nafisa kamar ƴar da ta haifa,ta kasance mai biyayya ga Kamal har sai da takai ga itama ta  shiga zuciyar sa, shekarar su biyar da aure saliha ta samu ciki, lokacin kam soyayya ta kullo tsakanin ta da Kamal haka ma Nafisa ba zaka taba cewa ba yarta bace ta cikin ta. Lokacin da cikin Saliha yakai lokacin haihuwa, sosai Kamal ya tsora ta sabida tunanin kar ita ma ta mutu kaman Amina domin tabbas zuciya na son mai kyauta ta mata,a yanzu yana son Nafisa kaman yanda ya so Amina.    Cikin ikon Allah Saliha ta sauka lafiya, inda tasamu yar ta mace. Wacce akasa mata sunan Amina, amma suna kiranta da Ummi. Tun daga kan Ummi basu kara samun haihuwa ba.  Nafisa da Ummi baza kata ɓa bambance tsakanin su ba, Nafisa nason Ummi so na gaske na jini da jini,  haka Ummi nason Nafisa so na jini da jini.    Ummi ta taso cikin wani irin gata daga wajen mahaifinta wanda har yakai mahaifiyar ta na jin kishi da sunan da aka saka mata. Yanda Nafisa take iya sadaukar da abu Ummi ta samu kad’ai ma ya isa ya kagane irin soyayyar da take mata. Ummi ta kasan ce yarinya mai wani irin taurin kai da kafiya ta masifa bata tank’waruwa akan abinda tai niya haka ba ta sawuwa akan abinda ba tai niya ba Ummi kenan.    Bangaren halitta Ummi ta kasance mai baiyyanan nen kyau ne,irin mutanen da a kallo daya zaka ga kyawun ta,Ummi yarinya mai rawar kai,gayu kam har ba’a magana wajen Ummi, k’awar ta a duniya kwaya d’aya ce tak Asiya wacce suke jikin gidan su.  Asiya yarinya ce mai saukin kai da saukin hali wanda ta samu a wajen mahaifiyar ta SAHURA da suke kira mama, domin mama bak’aramin hakuri take da abokiyar zaman ta atine ba tun mijin su na raye har Allah yayi mai rasuwa. Mama ce ke da yara uku maza biyu mace d’aya wacce itace Asiya, Atine kam ba ta haihu da alhaji ba yar ta k’waya daya Halima a gidan tsohon mijin ta tahaife ta wanda ya rasu, duk irin mugun halin Atine Mama ba tace tabar mata gida ba lokacin da aka raba gadon alhaji. Haka ta cigaba da hakurin zama da ita, kullum tana mata rashin mutumci da rashin arziƙi yarta kam Halima rashin mutunci da rashin kunya sai wanda ta manta, babu irin rashjn mutuncin da ba tayi a unguwa kula maza kam ko Karya ta shafa mata lafiya. Mama da Hajiya kam abun ba’a magana zama suke kaman wasu yan uwa.    Tun tasowar Ummi a irin taurin kanta Hajiya da Goggo ne kad’ai ke tsawatar mata taji,haka yasa Ummi kwata kwata bata shiri da gidan Goggo dan saita shekara bataje ba, Ummi na da shekara 13 akayi bikin Anty Nafisa bayan ta kamalla diploma dinta.    Mijin anty nafisa mai suna Musaddiq wanda yake matsayin lawyer mai zaman kansa, mutumin kirki ne bashi da wata damuwa kwata kwata, soyayya sosai Ummi take samu daga mahaifin ta har zuwa lokacin da k’addarar ta canja har zuwa lokacin da ta d’ora TUDU AKAN KWARI. ~~~~~~~              k’arar wayar ta ne yadawo da ita daga d’an tunanin da ta tafi yi na rayuwarta, jawo wayar ta sai dai 5missed call ta gani yabata mamaki,ta na me akayi mata way’anan kiran haka?.   Bata kai ga samun amsa ba kiran yak’ara shigowa dauka tayi tare da sawa a kunne. “Ranki ya dad’e! ina matuk’ar godiya.” wani irin dum taji kirjin ta yayi,domin yanda sassanyar muryar ta shiga kunnen ta tare da saukar mata da wani mugun tsoro. Jin shirun da tayi ya bashi damar cigaba da magana.   “Barka da kasancewa cikin kyakyawan lokaci abar sona… “ENOUGH!.” Ta faɗa a d’an tsawace, bayan tayi karfin halin tattaro nutsuwar ta da k’arfin gwiwarta tace  “Mukhtar ya kamata kasan ka gama raina mun hankali a rayuwar duniya, yakamata ka ƙara cire Ummi daga rayuwar ka,kamar yadda kayi abaya,domin Ummi tatafi daga rayuwar ka har Abada.” “Ba har abada ba Ummi, a duniya ke ta wace haka ma a lahiri ke tawace, Ummi kar kiyi tunanin inada numfashi zan bari wani abu dai zai rabani da ke ya wanzu a rayuwa, karki yi tunanin baikon da akayi miki da Affan zai zama wani katanga tskanin na dake, sai dai ya zama wani bango a gareki da zai karemun ke dafa wasu mazan.” Kashe wayarta tayi gaba daya,domin tabbas maganga nun Mukhtar zasu iya haifar mata da wata muguwar damuwa, domin kuwa  yanzu tara ba kanta da soyayyar Mukhtar har abada. Knocking ɗin kofar aka farayi a zabure ta ɗago tana kallon ƙofar….. Legend's pen TUDU A KAN KWARI. Mallakar Sayyid writer (Legend)          Pegi na uku 03 Baba masinja ne ya shigo tare da cewa “Ranki ya daɗe kina da baƙi” Mai da kanta ƙasa tayi tana sauke a jiyar zuciya, kusan mintina uku tace “waɗanne kalan baƙi kuma Baba?.”  “wasu yan mata ne haka kaman ba musulmai ba.” Baba masinja faɗa “kace su shigo.” Kyawawan yan matane guda biyu suna sanye cikin riga da mini skirt kana ganin su kasan ma,aikata ne daga wani company. Hannayen su rike da kwalaye da akayi Warping nasu da fold peaper. Shigowa sukayi suka ajiye gaban table dinta. Ita kuma tana binsu da kallo.”Daga ina?.” Ta tambaye su. A Ɗaya daga cikin su ce tace “From The C.E.O M.A.M Nig limited.” Ba tare da Ummi ta kallesu ba tace “full name?.” “Sir Mukhtar A Master.” Shiru Ummi tayi tare da ƙasa da kanta, tsahon minti biyar sanan tace “ku kwashe kayan nan ku fita dasu daga nan.” jin shiru babu amsa ne yasa ta d’ago kai daga sai dai bata ga kowa cikin office d’in ba,wani mugun tsaki taja. “wai me Mukhtar yake so ya mayar mata da office ne?.” Gaba daya tunda Mukhatar ya shigo rayuwar ta take fama da k’aluba le kala kala, waƴanda ta kasa game musu. Tabbas taso Mukhtar tana kan son Mukhtar amma bata fatan ta sake komawa halin da ta tsinci kanta abaya tun daga ranar da tafara haduwa da master har zuwa yanzu babu wani abu da yake dai dai a rayuwarta . Shekaru shida da suka huce. Ranar da kaddarar ta ta sauya, ranar da tafara haɗuwa da master a rayuwarta, baya ga sanin sunansa da kowane mutum ke unguwar yayi, amma wasu basu san fuskarshi ba.     Ranar  ta kasance ranar juma’a da misalin karfe 08:03 na safe. Danda zon ɗaliibai ne ke kok,arin shiga makarantar secondary ta mata mai suna (Shikeh Ahmad community secondary school) cikin dandazo d’aliban na hango Ummi da Asiya way’anda a lokacin bazasu huce shekara sha biyar ba zuwa sha shida, suna sanye cikin uniform na junior student, tafiya suke kaman basu a cikin d’aliban da suka makara, babu wata damuwa a tattatare  dasu, sun gab da gate ɗin makarantar ne suka jiyo hayaniya daga gefen makarantar, kai tsaye Ummi ta nufi wajen domin ganewa idont. Asiya ce ta riko hannun ta tare da cewa “Meena wai bakya ganin uban lattin da mukayi amma zaki tafi kallon rigima.”  wani kallo Ummi tayi mata sanan tace “ke wallahi sai naje nagane wa idona bance ki biyoni ba.”. Cika ta Asiya tayi ta nufi cikin school itama Ummi ta nufi inda tajiyo hayaniyar, matasan samari ne irin marasa jin maganan sun gaye wani matashin saurayi wanda ake kira da Tsalha. “Da alama munfunci ka akaita.” cewar Ummi tana k’arasowa wajen domin kowa yasan halin Tsalha da munafunci. “kai kudaina b’ata mana lokaci kuyi mai abinda nasako.” cewar wani matashin saurayi wanda da alama shine ogan su, kallon sa Ummi tayi tsaf yana sanye cikin riga da wando na k’anan kaya wandon nan ya zazzago har ƙasa (ass down) suma ta taru akanshi ta kuma cukurkud’e waje daya, bata samu ganin fuskar shi ba ya juya mata baya, amma tana hango sarƙoƙin dake maƙale a wuyan shi. A hankali ta tako har inda yake sanan tace “Haba malam,kamar baka da imani zaku sa mutum haka a gaba,har kana cewa kar su b’ata maka lokaci.” Tun daga farkon fara maganar ta yake jin saukar Muryar ta acikin dodon kunnen sa, jin tayi shiru yasa shi waigo wa. idanun sa suka sauka akan k’aramar kyakyawar fuskar ta,cikim rashin sa’a idanun su suka had’e da na juna,wani irin abu yaji a zuciyar sa inda itakam Ummi bataji komai ba sai ma murgud’a masa baki da tayi tare da cewa.      “Malam mene kake kallona,ni hak’uri na baku’ nasan halin Tsalha da gulma da munafunci amma kuyi hak’uri idan zaku iya, idan bazaku iya ba kuyi duk abinda kuka ga dama halinshi yaja masa” Tana fad’in haka takama hanya ta huce, gaba d’aya a tarihin rayuwar shi babu macen da ta taɓa kallon idon shi ta gayamai magana haka sai wanan k’aramar yarinyar.   “Master mene abun yi?.” d’aya daga cikin yaran shi ya fad’a  “barshi ya huce.” ya bashi amsa agajar ce cikin muryar nan tashi ta rik’akk’un ƴan daba. Sosai Tsalha yaji dad’in taimakon da Ummi tayi mishi amma munafukat zuciyarshi sai ta raya mishi wai Ummi da Master na da alaƙa, cikin ranshi yana cewa. “Dole na sanar da mahaifin yarinyar nan,yasan rashin kumyarta har takai ta tari manyan ƴan daba haka ido-da-ido.” Ummi kai tsaye cikin makaranta ta nufa, kasancewar ba jaka a hannun ta yasa tahuce kai tsaye batare da ta tsaya wajen da ake tare masu makara ba.  Gaba daya Ummi ta manta da wanan lamari da yafaru kafin zuwan ta makaranta, k’arfe 12:30 aka tashe su kasancewar yau juma’a ce. _____MASTER_____ Tun da yarinyar nan tabar wajen yaji gaba d’aya kamar ta tafu da wani abu daga jikin shi, dakyar ya lallaba suka koma gida sai dai ko da suka koma kasa fahimtar komai yayi, gaba d’aya yarinyar yake son sake gani,so yake ya ganta yaja nata horning akan abinda tayi masa, wanda shi kan shi bazai ce ga abinda tayi masa ba. Ganin bazai iya jurewa ba yasa shi tashi ya nufi can makarantar tasu. Yafi awa d’aya zaune yana jiran su fito domin tabbas sai yaci mutuncin yarinyar nan sanan zai iya bacci, abinda yasawa zuciyar shi kenan. yana nan zaune d’aliban suka fara fituwa har sanda Ummi tafito wacce bata ma kula dashi ba ta kama hanyar gida.   A baya ya fara binta har su karaso idan babu hayaniyar mutane sosai. Cikin kaushin Murya ya fara mata magana. “Ke.” Tsayawa tayi ba tare da tuyo ba, domin ko ba da ita ake ba kiran ya shige ta, ƙara maimai tawa yayi “Ke.” Juyowa tayi idanun ta suka sauka akan fuskar sa. Wani irin abu taji ya dake zuciyar ta mai kama da tsoro, amma dake ita din jaruma ce dake wa tayi amma sai dai takasa kallan sa cikin ido, har ya karaso inda take. Asiya kam tun farko ta gane shine Master shugaban yan daba na unguwar su, mutumin da kowa yake tsoro babba da yaro, mata da maza, a ranta tace  “Me Ummi taja mana haka ne?.”  “Malam lafiya zaka dinga bina a baya kana ƙwala mun  kira kamar wacce kake bu bashi.” Ummi ta faɗa cikin wani k’aramin k’warin gwiwa bayan tagama yak’i da tsoro a cikin zuciyar ta “Nazo yi miki warning ne.” yafad’a shima cikin sauke murya daga k’arfi zuwa sanyi “warning!  waye kai?.” Ummi ta jero masa way’ayanan tambayoyin cikin salon rainin hankali irin nata.” “okay! shikenan kije.” yafad’a yana mamakin kansa na yanda ya kasa komai   “Ko baka ce ba ai zanje.” Ummi tafad’a tana hucewa,ita dai Asiya baki sake take kallon wanan lamari.    Tunda ga wanan rana Mukhtar Master yakamu da wani abu a cikin ranshi, rana bata tab’a fitowa tafad’i bai saka Ummi a cikin idanun sa ba, wanda shi kanshi bai san menene dalilin wanan ba, haka itama Ummi duk sanda yayi mata magana sai dai tayi mishi rainin hankali ta huce, baza tace tana jin ba dadi da tare ta dayake ba sanan ba zata ce tana jin dadi ba, Sai dai yau da gobe tafi ƙarfin wasa. Haka rayuwar tai ta juyawa yau fari gobe bak’i a kullum wata shak’uwa ce take ratsa Mukhatar da Ummi wanda babu wani da yasan wanan  alak’ar kasancewar Mukhtar Master cikaken mara jin magana ne a unguwa, shi bazakace masa yaron yan siyasa ba sabida idan yatashi rashin mutuncin sa har su ba kyalewa yake,basa sace sace shi da yaran sa ko haurawa mutane gida amma duk wani aikin ta’asa bazaka rasa su a ciki ba.    A zuwa yanzu sun d’auki shekara guda da rabi tare da Ummi,kullum shak’uwa sabuwa ke shiga zuciyoyin su. wacce ta zama soyayya mai k’arfi sai dai k’arancin shekaru na Ummi duk da a yanzu ta girma ta matsayin s.s2 amma bata fahimci hakan ba, rashin nutsuwa da mai da hankali irin na Master kuma shima baisa shi ya fahimci yafad’a son Ummi ba.    A kowacce rana sukan had’u sau uku ko sau hud’u lokacin tafiya makarantar boko, lokaci dawowa, lokacin tafiya islamiya wani lokacin su had’u lokacin dawowa.    Asiya na musu iya ka cin k’okari ba ruwan ta dafad’awa wani, sai dai a kwana biyu ta fara fahimtar Ummi takamu da sonsa Master, mussamam da yazama a yanzu tana yawan maganrashi fiye da yanda take yi da. Asiya tana k’okarin taga ra fahimatar da Ummi kan cewa ta dakata ta fahimci tafara son Master domin tasan abu ne mai kamar wuya, amma Ummi taƙi fahimta, amma tana son tasamu lokaci ta zaunar da ita tayi mata bita. Legend's pen TUDU A KAN KWARI.    (Short stroy) Mallakar Sayyid writer (Legend) Pagi na huɗu 04    Da sallama Ummi ta shigo gidan nasu, sanye take da doguwar riga da kuma hijabi light blue, uniform din su na islamiyya kenan.  Ba ta sami kowa t’sakar gidan ba yasa ta huce kai t’saye cikin d’akin ta. Bayan ta cire uniform ne tafito ta shiga d’akin Hajiya, zaune ta same ta, tana karatun Al,qur ani. hakan yasa tafito tanufi cikin kitchen ta zubu abinci.   Batayi nisa cikin cin abincin ba Asiya ta shigo cikin gidan, zama sukayi tsakar gidan sai da Ummi ta kammala sanan Asiya tace su tashi su shiga d’aki. Sai da suka zauna a ɗakim Asiya tace “Ummi inaso ki fahimci magana ta, babu wasa ko shirme a maganar da zanyi.” Ɗaga kai Ummi tayi alamun taji.    “Ummi kin fahimci wani canji kwana biyu a tsakanin alak’ar ki da Mukhtar?.”  Asiya tafad’a tana kallon Ummi wacce ta girgiza kai alamar “a’ah”.  “Ummi ki fahimce ni, tabbas kwana biyu alak’an ku ya canja, ko ta wajen sa ko ta wajenki.” “Wai wane irin canji kike magana a kai Asiya?.” Ummi tafad’a alamu k’osawa da maganar. “Ummi soyayya: soyayya tashiga zuciyar ki, ko da shi  bata shiga zuciyar sa ba.”  Tsaki Ummi taja kafin tace “To Asiya shikenan ni bazanyi soyayya ba ko kuma bazan so shi ba?.” “Meena ba haka bane.” Asiya tafad’a cikin kwantar da Murya sabida idan tana son Ummi ta fahimce tane,shiyasa take mata Amfani da wanan sunan (Meena).    “Meena ba haka bane, dole zakiyi soyayya amma kisani Mukhtar ba irin mutumin da zakice zakiyi soyayya dashi bane.”  “ko zaki iya fad’amun wani dalili.” Asiya bata kai ga bude baki ba suka jiyo Hajiya na rafka salati, da sauri suka tashi suka nufi cikin d’akin ta.     “kai wanan yaro Allah ya wadaran sa ya la’ance shi.”  Hajiya tafaɗa ta cikin Wayar da take. Su Ummi kam gaba ɗaya hankalinsu nakan wayar anan ne suka jiyo ana cewa.    “Wallajillhi sun sassarashi kuma sun hana a d’auke shi ma balle akai shi asibiti.”     “kai wanan yara Allah yayi mana katangar k’arfe dasu da sharin su.”  Hajiya tafad’a sanan takashe wayar ta. Ummi ce ta mat’so tare da cewa “Hajiya meyafaru haka?.”  “Hhm wanan la’anan yaron meyake da sunane.? ,su kaje su ka sassara yaron wajen Marka,sanan suka hana a d’auke shi a kai shi asibiti, kai wanan yaro Master yake kowa Allah ya la’ance shi.” wani mugun abu me nauyi kaman dutse ya dirga a kirjin Ummi ya tsaya cak, da kyar ta iya mikewa tafice Asiya ta rufa ma ta baya.  Zama sukayi jugum jugum ba ma iya magana kowa da abinda ke yawo a zuciyar sa, sai kusan minti goma sanan Asiya ta ce. “ yanzu kinga dalilin?.” Ummi bata iya cewa komai domin ita a yanzu babu abinda yake damun ta kaman zagi da la’antar da Hajiya tayi wa Master.     Washe gari a hanyar su ta tafiya Makaranta ne Ummin take tambayar sa.   “Wai yaya me yahad’aka da wani yaro jiya?.” “Wanne kenan.” ya tambaye ta shima “jiya yara nawa ka kula?.” “Akwai na safe akwai na yamma.” yabata amsa cikin halin ko in kula.  “To kuma nawa ne ka daina mutane fa suna zagin ka.” “To a zage ni mana Meena, mene abun haushi ko zai dame ki?.” “zai da meni mana.” Ta bashi amsa. Tsaya wa yayi cak sanan yajuyo dan bak’aramin dadi maganar tayi masa ba, domin yariga da ya gama tabbatarwa yakamu da son Ummi mai girma. “yanzu Meena dan anzage ni sai kidamu?.” yasake maimaita mata tambayar. Ba tare da  taji nauyi ko wani abu ba ta sake bashi amsa. “ Tun da nace zan damu zan damu mana,kai bakasan yanda nake son ka bane?.”  Runtse ido tayi bayan tadawo daga tunanin da ya d’auke ta, tabbas tasan taso master kamar ba gobe, sai dai a yanzu kam tacire shi da komai nashi a rayuwar ta,kuma ba ta fatan ta k’ara had,a hanya da abinda ya shafe shi.  Tashi tai tafara had’a kayanta dukda lokacin tashi baiyi ba amma gaba d’aya bata jin zata iya k’arayin komai a yau d’inan. kasancewar ita kad’ai zata tafi ba tare da Asiya ba dole sai dai tahau keke, hakan yasa kai tsaye ta nufi gate ta fara tafiya.  Tafiya kad’an ce zata kawo ka bakin titi,amma Ummi a yau sai taji tafiyar na k’ara ninka kanta. Idon ta na kallon k’asa take tafiya, sai ji tayi anriqe hannunta katamau, Har tana kok’arin faduwa. A  fusace ta jiyo sai dai idanun ta ne suka fad’a cikin nasa, wanda yasata had’iyar wani irin yawo jikake “muk’ut.”  Wani irin murmushi ya sakar mata wanda yasa zuciyar ta rawa, da sauri ta dauke kan ta tare da fusge hannun ta haɗi da ja baya duk a lokaci guda. Hakan ba ƙaramin dariya ya bawa kyakyaan farin matashin mai kama da larabawa. tabbas wanan zaki iya rantsewa cewar bazai iya furta ko da kalma d’aya bace da harshen hausa, domin tunda ga kyakywar kwantanciyar fatar shi, har zuwa kwantanciyar bak’ar sumar shi, duk na larabawa ne. Cikin wani irin salo ya bude baki tare da fad’in. “Hajiya meenahhh.” ya faɗa yana jan ƙashen sunan, sanan ya ɗora da cewa. “ Kin canja gaba d’aya.”.Wani  irin dogon tsaki Ummi ta ja sanan tafara k’ok’arin huce wa. Hannu ya ƙara sawa zai kamo ta, tayi saurin zamewa tare da cewa. “kar kar da ka kuskura hannun ka ya ƙara ta ɓani.”  “Okay Madam.” ya faɗa yana ɗaga hannu biyun sai kuma yace. “ But please…” Hannu ta d’aga mishi alaman dakatarwa.    “kai tunanin ka kanada wani abu da zaka k’ara fad’amin? kai tunanin ka akwai wata kalma taka da zata k’ara shiga k’wak’walwa ta?, wallahi mukhtar babu wani abu naka da zai k’ara shiga kunne ya zauna face ya fita ta inda ya shiga.”   Shiru yayi yana kallon ta, tabbas Meena ta canja, canji sosai wanda ba iya na jiki ba har na zuciya, domin tabbas Meena bata taba iya juriya akan lamarin sa, tabbas yana da babban aiki a gaban sa na dawo da soyayyar sa cikin zuciyar Ummi. Dukda ta ta soyayyar ko rawa ba tab’ayi ba duk tsawon fad’i tashi da yayi a rayuwa.    Cikin wani irin  yanayi ya k’ara bud’e baki “Meena bance ki yadda da kalamai na ba, Meena bance kalamai na su zauna a kanki ba, amma dan allah kiji ni ko da baza su kar’asa shiga kunnen ki ba. Na yarda ni mai babban laife ni Meena , idan kin kirani da butula ma bazan ce ba haka nake ba, Meena idan kin kirani da Marar imani a soyayya bazan yi musu ba, amma dan allah ki fahimce ni, kiji ni ko da bazaki yarda dani ba.”        “Mukhtar wanan ba Ummin da ka sani shekarun baya bace, ba shasha shar yarinyar da tazab’i soyayya akan iyayen ta bace, ba banzar yarinyar da tazab’i farin ciki wani bace akan na iyayen ta, Mukhtar nasan kaina.”   “Ki daina jifan kanki da way’anan kalamai Meena, ko a da d’inma kin san kanki.”   “Mitcheww.” ta ja wani dogon tsaki sanan ta huce domin tabbas hucewar ta shine alheri, domin matuƙar way’anan idanun nasa suna kallon ta, wanan muryar tashi nashiga kunne ta, to tabbas zata iya manta komai da duk wani alwashin ta domin tabbas a iya wanan tsayuwa ta tabbatar wa da kanta babu wani abu da yarago a son da tayi wa Mukhtar Master. ~~~Mukhtar kam yana cikin tashin hankali babba ba k’arami ba domin gaba d’aya ya gama ganin tsantsar k’i da tsanar shi a zuciyar Ummi. Kai tsaye mota ya shiga yaja bai t’saya ko ina ba sai USMAN SHIRAZ SPECIAL HOSPITAL babban asibitin kud’i daka jahar kano, asibitin da yatara manyan likitoci na k’asashen k’etare. Cikin v.i.p ya nufi wani d’aki kai tsaye ya bude k’ofan d’akin ga shiga.    Babban d’aki ne da ake ajiye patients,wata mata ce da baza ta huce shekara 37 ba zaune kan gado da alama itace mara lafiyan, duba da kanula dake d’aure a hannun ta, k’ara sawa yayi inda take tare da zama gefen gadon, cikin muryar rashin lafiya tace     “sannu da zuwa.” Da murmushi sosai a fuskar sa ya amsa da cewa. “sannu ya jikin naki.?”  “jiki alhamdulillah ya aikin?.”     “Aiki ai mun bari shi legos, bari na koma wajen likitan nan ko ya zo.” yafad’a tare da tashi. Kai tsaye wani makaken office ya nufa, inda yasamu wata nurse yayi magana da ita, bayan yan mitina tafito daga cikin office d’in sanan ta bashi dama ya shige. Gaisawa sukayi da likitan sanan yace  “Doctor nazo ne akan maganar gwajin da kuka yiwa mata ta!.”    ____UMMI____ kai tsaye tafiya ta fara ba tare da ta tsaya neman wani mai keke ba, sai da tayi tafiya mai nisa sanan ta tsaya, sakamakon zafin da taji kafarta ta fara,      ita kanta tayi mamakin irin tafiyar da tayi domin tafi rabin tafiyar, bata sha wahala ba ta samu keke ta k’arasa gida, yau ba ta ko lek’a d’akin hajiya ba tayi cikin d’akin ta, kan gado tafad’a ta kwanta tare da fashewa da wani irin kuka marar sauti, gaba d’aya rayuwar soyayyar ta da Master ce tafara dawo mata cin kwanyar kanta kamar wacce take kallo a majigi.    Tun daga ranar da kalmar so tafita daga bakin Master zuwa kunnu wanta, wani b’angare na farin ciki ya tsaya a rayuwar ta, har zuwa yau. ~~~~~~        “Meena dagaske kina sona.” maganar da fara yi mata amsakuwa a kunne kenan, lokacin da ta furta kalmar cewa “bakasa irin son da nake maka.” Wanan Murmushin da zata iya cewa ta zarar shi da wani Murmushi a rayuwar ta, tazara ce mai yawa, ta sakar mishi tare da d’aga masa kai.      (Allah ubangiji ya rufe sani gaibu ga bayinsa, yabarwa kanshi kad’ai sani domin shine Al’maliku al kalik,u.)  Tabbas da Ummi tasan saurin da takeyi a wanan lokaci zai zamana shine,sauri na k’arshe da zata k’arayi cikin farin ciki na tsawon lokaci mai yawa da tayi shi da kyau. Da ace tasan saurin da take zaizamana sillar bud’ewar damuwa da matsala mai tsawo a rayuwar ta da batayi shi ba.  “Ummi ki daina saurin nan dan Allah yayi yawa.” Asiya tafad’a ganin duk sun huce sauran d’aliban dasu ka taso tare. “Asiya bakisan yanda nakeji ba, kyautar da yaya mukhtar yace zaiban gaba d’aya ta rufe mun idanu.”    Tsalha da yazo hucewa ne yabi Ummi da idanu jin ta ambaci kyauta da kuma yaya Mukhtar, canja akalal tafiyar shi yayi zuwa bin bayan su Ummi da Asiya way’an da gaba d’aya rayuwar su basu kula da wani mutum da ke bin su ba.   Cikin filin makarantar gwamnati dake kan hanyar su ta dawo daga islamiyya inda nan ne wajen had’uwar su da Master, domin wajen yayi nisa da islamiyar tasu kuma yayi nisa da gida. Zaune suka tarar dashi yana sanye cikin kayan shi yan kullum wato k’ananan kaya, da sauri Ummi tak’arsa kusa da shi tare da fad’in.      “Yaya na nadawo.” kallon ta yayi cikin so da k’auna sanan yace. “Yawwa Meenatu an dawo lfy?.” “lafiya klau yaya, yanzu ina kyautar da kace zaka mun.” Tsalha dake gefe kam yana ta faman baza ido ko idanun sa zasu hango masa wane yake tare da Ummi. Sai dai idanun basu bashi damar gani ba sosai har zuwa lokacin da Mukhtar ya zaro zube ya zura Ummi hannu, da sauri Tsalha ya juya.     Ummi kam wanI irin farin ciki taji lokacin da Master ya saka mata wanan zoben a d’an yatsa sanan yak’ara da cewa.  “Meena ina so kiyi mun alk’wari guda d’aya.” cikin tsantsar soyayyar da itama batasan adadin girman ta ba tace. “Yaya wane irin alk’wari ne?.”   “Amina inason kiyimun alk’wari duk runtsi duk wuya duk t’sanani da zafi ba zaki  guje ni ba, Ummi zan so ki sama da raina, zan tsaya akan son ki iya kacin numfashi na, sonki zai zamar me ni jagora a cikin rayuwa ta, zai zame mini fitila mai haske a cikin duhun rayuwa ta. Ummi zan rayu da sonki zan mutu da sonki zan tashi da sonki.” Wani irin murmushi mai tsayawa a zuciya Ummi ta sakar mai sanan tace. “Yaya na so ka a sanda bansan mene ne so ba, na girma da son ka a cikin rayuwa ta , zan rayu da sonka a cikin rayuwa ta, sanan za rok’i na mutu da sonka a raina, yanda zan tashi dashi, sonka shine yazamar mini bangon da nake jingi na dashi, bango da yazama ma tokara a gare ni, akan ka nasan farin cikin rayuwa yaya, sanka ne zai zame mini hanyar farin ciki na har abada.” “Idan har ina ganin ki a kusa dani, ko ina ganin ki a cikin duniya ba ni da wata damuwa ko bacin rai Ummi, kinzame mini alkhairi mai girma a rayuwa ta, ke cd mace ta farko da ta nuna soyayya ko kulawa a gare ni Ummi. Na so ki da duk kan numfashi na, zan soki ko babu numfashi a tare dani.” “Yaya idan son ka  zunubi ne, to wallahi bazan tu ba bah.” Legend's pen TUDU A KAN KWARI.      (Short stroy). Mallakar Sayyid writer (Legend)          Pegi na biyar 05….  “Ummi ki kula da zoben nan kar Hajiya ta gani.” Asiya ta fad’awa Ummi dai dai lokacin da take shiga gida, Murmushi Ummi tayi sanan tace.  “karki damu Asy zan kula,amma dai kifara soyayya.” banxa Asiya tayi da ita ta shige gida. Dai dai bakin k’ofar gida Ummi taci karo da Tsalha na fito wa daga cikin gidan, wani irin dum taji a k’irjin ta yayi, bawai dan tsalha baya shiga gidan ba ha sali ma Tsalha d’andakin hajiya ne,amma yau kawai ta ji gaban ta yafad’i ta tsora ta da ganin shi. Jiki ba k’wari tashiga cikin gidan, tun daga kallon da ta ga hajiya na ma ta taji wani irin abu ya tsaya mata a ma ƙoshi, da kyar ta iya had’iye wani yawo mai mugun d’aci sanan tace. “Hajiya nadawo.”  “Daga ina?.” cikin rawar baki tace “Maka..rantahh.” Tasowa Hajiya tayi zuwa inda take sanan tace   “Wace makaranta?, na ce wace makarantar dan uban ki.” shiru Ummi tayi gaba d’aya ta gama tsorata, ba tai aune ba sai ji wani azababben mari tai a fuskarta, tu ni tayi tangal tangal zata fad’i domin tabbas marin ya shige ta.     “Wallahi Ummi sai kinci uban ki, mu zaki mayar yan iska?, a turaki makaranta ki tsaya yawon kula samari, wanan ne karo na uku da tsalha ya ganki, yayi miki magana na farko a matsayin shi na wanda ya isa dake amma baki gyara ba, ya ganki na biyu yayi miki magana shine zakice yayi ta fad’a to gashi yaganki na uku.”       Cikin rawar murya da rashin sanin abin fad’a tace. “Wallahi Hajiya k’arya yake.” “Karya ko?.” Hajiya yafad’a tana k’ara jawo ta, ta fara kimar ta kamar ba ita ta haife ta ba, sabida hajiyan gani take ta gama raina mata hankali domin ga zoben da Tsalhan yace anzura mata a yatsa, kuma tasan a rayuwar Ummi babu irin wanan zoben a hannun ta. Sai da tai mata mai isarta sanan ta kyale ta tashiga d’aki tare da fad’in. “Kuma ki jara ya dawo shima ya d’ora miki nashi, sanan ba sai nace na ra baki da kowanne d’an iska ba Ummi, ki cigaba karki daina.” Daga haka tashige d’aki abunta, da kyar Ummi ta iya jan jiki tayi d’akin ta, Kuka sosai tayi kafin bacci ya d’auke ta wanda bata tashi ba sai washe gari. Da t’samin jiki ta tashi domin baya ga duka da tasha a durku shen da take kuka bacci ya d’auke ta. Agogon d’akin ta kalla ganin k’arfe shida na safe yasa ta tashi, ta nufi cikin Kitchen ruwan zafin ta tagani akan tukunya ta d’iba ta shiga toilet, ta dad’e tana gasa jikin ta, tana hawaye kafin tasamu ta watsa ruwan ta fito.     Sai da tafara gabatar da sallar asuba sanan tadawo ta d’ora magriba da isha, bayan ta idar ne tahau shirin ta na makarantar boko    ____Master kam tun rabuwar shi da Ummi kai tsaye gidan dan majalisa Hamisu k’waro suka nufa shi da yaran sa, inda suka je yimasa warning akan aikin da yasasu kuma bai biya su cikon kud’in su ba.      Ba tare da sallama ba suka shiga cikin gidan har zuwa babban d’akin da yake zama da b’akin sa, kamar ko da yaushe yau ma d’in tare yake da bak’in nasa suka shigo, tsai tsaya wa suka yi carko carko ba tare da sunce ko k’ala ba, amma kana ganin yanayin su ka tabbatar da ba zaman lafiya suke da b’ukata ba, hannu na rawa Hamisu k’waro ya bud’e drower d’in dake kusa dashi ya zaro musu cikon kud’in su ya basu, duk da su ne suke sasu ai kata ta’asan amma suna mugun jin tsoran su.    Roget shine babban yaron Master shine yasa hannu ya karb’i kudin sanan suka juya suka fice, d’aya daga cikin mutanen dake zaune da Hamisu k’waro ne yace. “Honorable wai kuma tsoron way’anan yaran kuke?.” wani kallo Honorable Hamisu k’waro yayi mai sanan yace. “Murtala wasa kake, ai way’anan yan iskan yaran abin tsoro ne ga k’asa ma ga baki d’aya bamu ba, domin way’anan kwata kwata basu da wani amfani a rayuwa, amfanin su d’aya ne idan aikin ta’addanci ya tashi.” “To honorable kusa a kame su mana.” Murtalan yasake fad’a. “To kai Murtala banda abun ka, idan aka kame su su waye zasuyi mana aikin ta’adancin ko zamu sa ko yaran mu?.”  gyad’a kai Hamisu yayi yana mamaki  ( wanan wace irin rayuwa ce yan uwa,  mutumin da zakayi aikin ta’addanci akan sa ko domin ka burge shi, shine zaifara ai ba taka).    Daga gidan Honorable kam su Master kasuwa suka biya. Domin Master da yaran sa ba irin yan daban da abince ke ga garar su bane, ko way’anda suke cin abincin siye, ko gidan dasuke zama zakayi mamaki idan kashiga domin ko ina a kintse yake tsaf tsaf, domin kowa da akwai aikin da aka raba masa yanayi kullum da safe, sanan duk wanda yab’ata waje ko yaci wani abu to fa sai ga gyara a lokacin. Siyayyar kayan abinci sukayi sosai sanan suka dawo gida, inda Master ya raba ragowar canjin gida uku domin kowa yasan yanda akeyin rabo,kaso d’aya na saving ne wato ajiya sabida matsalal yau da gobe ko rashin lafiya, kaso d’aya na Master sanan kaso d’aya na sauran yaran ne Roget da Badoo. Sai dare sanan tunanin Ummi yadawo kanshi, ko tana wane hali? duk yanda yaso ya ayyanawa zuciyar sa Ummi na cikin farin ciki abu yaki yi yuwa, zuciyar shi ta ƙi yarda da hakan. Da k’yar bacci ya d’auke shi. Washe gari kam da huri ya shirya ya nufi hanyar da suke had’uwa da Ummi duk da yasan yanzu k’arfe 7 na safe ne kuma Ummi tana kaiwa 7:45 watarana ma har 8. B’abgaren Ummi kam bayan ta gama shiryawa cikin unifoam ne ta fito t’sakar gidan, inda ta tarar da Hajiya na shara Abba kuma yafito daga d’akin sa. “Abba ina kwana.” tafad’a tana durkusa wa.“kin kwana lafiya?.” “Lafiya klau Abba.” tafad’a tana juya wajen Hajiya wacce ta tare ta da cewa. “Wanan shirin kuma na menene?.” “A’ah Hajiya ya zaki tambaye ta shirin menene bayan kinsan na makaranta ne. Abba ya bawa Hajiyar Amsa. “kaga na riga na gama gane ka, bazaka iya t’sawatar wa da yarinya nan ba,sabida son da kake mata yayi maka yawa.” Cikin fushi Abba yace. “kinga Hajiya ba na son cin mutunci da rashin kunya, me kike so na yiwa yarinyar nan?, bayan kinga ma yi mata duk wani hukunci, kince kin dake ta bayan na dawo na shiga d’akin naga ta a kwance, naga yadda kika fasa mata jiki, so kike nima na k’ara mata wani yanda zamu kashe ta ko mu illata ta?.”   “Kaga ni ba wanan ba, yanzu dai wallahi yarinyar nan ba inda zata fita. makaranta dai ba ki isa ki koma a yanzu ba, ba kunzo k’arshen zango karatun ba?, to ke da zuwa sai temprint.”  Hajiya ta fad’a tare da shgewa d’aki, Abba ne ya kalli Ummi sanan yace.     “Maza kije ki cire kayan ki kinji, makarantar kiyi hak’uri zuwa ga ba.” “Toh Abba.”kawai tace tare da tashi ta shiga d’aki.Wani kukan ta k’ara fashe wa dashi wanda ba ta tsaya ba sai shigowar Asiya.  “wai bazaki makarantar bane na ganki a kwance?.” Asiya ta tambaya tana k’ara shigo wa cikin d’akin.  jin shirun Ummi ne yasata k’ara mat’sawa inda take, sai jin shashek’ar kuka tayi. “Ummi is everything okay?.” shiru Ummin ta k’ara yi. “please Ummi talk.” hijabin jikinta ta d’aga tare da nuna wa Asiya bayan ta, da sauri Asiya takai hannu wajen tare da Cewa.“Ummi me yafaru waya dake ki.” jiyowa Ummin tayi a karo na farko tun shigowar Asiyan sanan tace. “Hajiya.”  “Me kikayi?.” Asiya ta tambaya cikin k’asa da Murya.      “Allah ubangiji ya tsinewa Tsalha.” Ummi tafad’a sanan ta bata labarin duk abunda ya faru, tun daga dawowar ta har dukan da akayi mata, har abinda yafaru yau da safe.     “Ummi ya kamata muyi magana akan makomar rayuwar ki da Master,abinda nasha fad’a miki ko da yaushe kenan.” Tashi Ummi tayi ta d’akko jakar ta, peaper ta yago sanan ta d’auki biro ta hau rubutu. Bawanu long note ta rubuta ba, ta nad’e ta tare da mik’awa Asiya. “Nasan Mukhtar yana can yana jira na, dan Allah karki fad’a masa komai kawai ki bashi wanan kice mai banda lafiya. Kara Asiya tayi tare da mik’ewa ta fice.     _____MASTER Ganin har k’arfe 08 na neman hu cewa.  Ba Ummi ba d’oriyar ta, ya tayar mai da hankali sosai da sosai, yana cikin wanan tashin hankali ya hango Asiya ita kad’ai ba Ummi. Da sauri ya k’arasa tare da cewa.“Asiya ina Ummin?.” murmushi yak’e tayi sanan tace. “Ummi bata da lafiya,amma ga wanan takarda tace a baka.”  karb’a yayi ba tare da jikin shi ya yarda da abinda Asiya tafad’a,, kafin ya bud’e takardar ya karanta Asiya ta b’ace, Kalaman cikin takardar sun matuk’ar sanyayar mai da jiki.     “Yaya ina sonka, ina sonka ina sonka zan rayu da kai zan mutu da kai, duk tsanani da zafi zan kasamce da son ko, dan allah yaya duk abinda zai faru karka janyewa soyayya ta.”       Gaba d’aya kalamn Ummi sun tafi da duk wata nutsuwar sa. jikin shi yana bashi wani mummunan al’amari, tabbas baya tunanin yasa yarinyar nan tayi TUDU A KAN KWARI? tafa d’a soyayyar sa bayan bai kama ce ta ba. Haka yayi ta zama a wajen har san da Asiya tadawo. Ba k’aramin mamaki tayi ba ganin Master inda tabarshi, sai dai wanan karon da yaran sa bashi kad’ai bane, a hankali ya k’araso inda take sanan yace.      “Asiya zan tambaye ki, ki fadamun duk gaskiyyar da kika sani kada kiyimun k’arya, meya faru da Ummi?.” Zama Asiya ta zaiyyane wa Master duk abinda tasani. sanan ta jaddada masa sunan Tsalha domin ita fa duk sabon da sukayi tsoron Master take.     Daga nan kai tsaye gida Asiya ta nufa, tana Allah Allah ta shirya ta nufi gidan su Ummi domin tana son su gama duk wata shawara a yau, da sallama tashiga cikin gidan, sai dai rashin amsawar da akayi mata ya tabbatar mata da Mahaifiyar ta bata nan.      Anty ce tsakar gidan tana zaune kan turmi, bawani kaya bane a jikin ta d’aurin kirji ne, domin anty ba ma’abociyar saka ya bace, duk yawon da zatai cikin unguwa da wanan d’aurn kirjin sai hijabi, gata irin mai rushe shen jiki ce amma haka take yawo. da anmata magana sai tace ba aure gare taba, indai kaga anty da complete kaya to unguwa ta nesa zata, amma ko gidan iyayen ta ko shiga cikin kasuwa haka take yawo.     “Ke ubanki wakike wa wanan kallon? shegiya mai kama da d’inya.”    Anty tafad’a tana zabgawa Asiya uwar harara, Asiya bata ce da ita k’ala ba ta huce. domin daman Ummi ce ke tanka mata.    Halima ce tafito daga cikin d’akin su tana sanye cikin d’inki doguwar riga ta lace da ta kame jikin ta sosai da sosai, Ƙafar ta tana sanye cikin uban heels din takalmi, sai uban kamshi turare take yi.     “To kema Umma kya kula wanan shegiyar yarinyar, tana ji gidan ubanta ne kuma sun cinye shi a gado.”  Halima ta fad’a tana tunkaro inda Anty take.    “ke halima kyaleni inci ubanta, Uwar ta ma haka muka buga da ita ta kyaleni balle kuma yarta.”        “Dan Allah Anty kyale yarinyar nan, ki kalle ni.”  kallon ta anty tayi sanan tace “naganki.”  “Zan fita.” Ta faɗa tana kashe ido “zuwa ina?.” “Nema.” Taba ta amsa tana fara tafiya “to Allah ya tsare hanya.” fitowa Asiya tayi zuwa gidan su Ummi. “To gantalalliya. An fice kenan.” “Gantalalliya ba tahuce wacce tafita yawon ta zubar ba. A  gaban Uwarta har tana cewa a tawo mata da tsara ba.” Asiya tafaɗa  tare d ficewa.  “Wallahi sainaci uban ki, shegiyar yarinya mai kama da ɗinya.” ~~~~~ Zaune suke cikin ɗakin Ummi. kasancewar Hajiya batanan ya basu damar sakewa suyi magana. “Ummi ki yiwa kanki faɗa, ki nema wa kanki sauƙi, ki nema mana.  na tambaye ki wani abu mana?.” Ɗaga kai Ummi tayi alamun ina jinki. “Hajiya tasan da Master kika tsaya?.”Girgiza kai Ummi tayi. “Amma tayi miki wanan dukan? to kisani Ummi duk randa hajiya tasan da Master kike tsayawa, wallahi abunda zatai miki sai yafi wanan, karki ga Abba yana supporting nake wallahi ko shi yasan da Master kike tsayawa Ummi zaki ji jiki.” “Asiya kamar bikin sa soyayya ba?.” “Ta ina zan santa nida ban taɓa yi ba.” “To Asiya kifita daga lamarin soyayyata dan Allah.”  Shiru Asiya tayi domin taga ne gaba ɗaya Ummi taga ma tafiya akan lamarin Master.   ~~~~~ Washe gari ma Ummi bata samu damar zuwa makaranta ba. Hajiya ta hana ta haka sukai ta fama har tsawon sati guda.      Gaba ɗaya Mukhtar yafi ta haiyyacin sa,ya shiga damuwa, tunani yayi masa yawa, abinda bai tab’a ba a rayuwar sa kenan damuwa akan lamarin wani, tun tasowar sa har zuwa girma da rayuwar sa amma gashi ya shiga akan Ummi yashiga damuwar da bai tab’a ba, shiga irin ta ba, idanuwan sa kullum zafi suke masa. Ummi kawai suke son gani, Zuciyar shi kullum zafi take masa, Ummi take son gani. A yanzu ko yayi shaye shayen na sama na lokaci kad’an ne, tunanin yake dawo wa cikin zuciyar sa. Har takai da ya fara sambatun da kiran sunan Ummi da daddare.                Yau takama monday. Ummi ta sami damar zuwa makaranta, domin yin temprint. Sanyw take cikin bak’ar doguwar riga ta abaya, tayi rolling da jan mayafi, tana sak’ale da jakar rataye ta zuwa unguwa. Domin sunyi magana da Abba zata biya gidan Anty Nafisa, dan har yanzu Hajiya ba sakar mata fuska take suyi magana ba.       Asiya ce tafito daga naso gidan itama tana sanye cikin doguwar rigar lace tasa k’aramin veil mai kyau, yan mata da sukeji ta tashe da kyau ga ilimi, domin dukkan su ba banza ba suna da k’ok’ari sosai afanin boko da arabic, rankayawa sukai suka nufi makaranta, Ummi sauri kamar ta tashi sama domin tabbas tasan yau zata had’u da Master nata, Mutumin da ta tabbatar wa da kanta shine mahad’in farin cikin ta.         “ki rage wanan saurin karkije ki fad’i.”  “Asiya duk randa kika k’ara cewa na rage sauri akan lamarin Yaya Mukhtar,wallahi sai namiki rashin mutunchi.”       Ummi taba wa Asiya amsa tana cigaba da saurin ta , tab’e baku Asiya tayi sanan tace    “ki kamo gobe ma.”   page[11&12]       Tsyawa Ummi tayi ganin sun k’araso wajen da suka saba had’uwa da master, Asiya kam gaba tahuce domin bata da niyar tsaywa,ta cire hannun ta akan lamarin Master da Ummi tunda ta fuskanci kamar Ummi batason tana shiga lamarin        “Asiya ina zaki.” kallon ta Asiya tayi sanan tace       “Tafiya zanyi mana Ummi mai zan tsaya nayi.”       “wai ke Asiya mene haka,sai kitafi ki barni anan?.”        “kinga Ummi na fuskanci ba b’ukata ta kike akan lamarin ki ba nacire hannuna gaba d’aya sai dai nayi miki fatan nasara.”     daga haka Asiya takama hanya ta huce, tsayawa Ummi tayi tabbas bata kyauta wa Asiya da take hantarar ta akan lamarin nan,amma gani take kaman bata son soyayyar ta da Master dane gaba d’aya,itakam duk wanda zaiyi tunanin raba ta da Master sai inda k’arfin ta yak’are, (tana wanan tunanin ne roget yaron Master ya samu damar yi mata way’anan hotonan da master ya tura  mata a office)         bata fargaba sai mutum tagani a kusa da ita, wani lallausan murmushi ya sakar mata,irin wanda kwana biyi yake gani a mafarkin da takeyi.       a hankali ta mayar masa da martanin murmushi sanan tace        “Yaya.” “Meenah i missed you.”       “missed you more yaya, dan allah kar ka kara nisa da gani na.”     “insha allah, Ummi dan allah kiyi mun alkwari kasancewa tare dani har abada.”      hannunshi ta kama ta d’ota a saman nata sanan tace      “yaya a ko yaushe ka tuna da wanan alk’warin dani Ummi ka d’auka, duk tsanani duk wuya ina tare da kai,ina tare da sonka.”        murmushi yasake sanan yace  “nagode sosai Ummi naa, nima nayi miki alkwarin zaka sance bango a gareki, zan kasance t’sanin da zaki dinga takawa a ko yaushe, zankasance fitila mai haskaki a ko yaushe, Ummi ina sonki da dukkan rayuwa ta, Ummi kece macen da nafara so a rayuwa ta, banta b’awa wani tarihin rayuwa ta ba amma Ummi yau zan baki.”         tafiya suka farayi sanan Ummi tace ina sauraronka      “Da farko sunana Mukhtar Adam Mukhtar haifaffaen garin jigawa,mahaifina d’an asalin garin kano ne amma zama yakai shi jigawa inda anan yake aikin shi,mahifiya ta yar asalin dutse ce anan suka had’o da mahaifina sukayi aure,haihuwata da kwana d’aya allah yayi wa mahaifiya ta rasuwa, inda k’anwar mahaifiyata Anty Halima ta k’arbe ni, Anty halima itace macen da nafara so kamar Uwa ina sonta a  matsayin mahaifiya duk soyayyar  da d’a yakewa mahaifi Anty Halima na keyi wa.     na tasu cikin gata daga wajen Mahaifina,Anty Halima da kuma Abba mijin anty halima, ina da shekara Uku Allah yayiwa mahaifina rasuwa daman kuma baiyi wani auren ba bayan rasuwar mahaifiya ta, kasancewar a garin jigawa muke bansan wasu dangin mahaifina na nan kano ba haka itama mahaifiyata ita da Anty halima kawai iyayen su suka haifa,family din su ba irin mai yawan nan bane, suma su biyu ne a wajen iyayensu kuma sun rasu, ita kuma Allah baibata haihuwa ba.      Anty Halima da mijin ta suka cigaba da rik’eni yanda suke mun har zuwa lokacin da yan uwan mijin ta suka sashi a gaba sai yak’ara aure,Anty Halima ba tadamu ba nima kuma banda mu ba,ana haka Abba ya auro Jummai wata me siyarda awara anan farkon layin da muke, tun shigowar Jummai kasan da tashin hankali ta shigo domin Anty Halima bata kula ta ba,sai taita sababu da surutu dana fito waje zata k’wad’eni to anan Anty Halima zata kulata itakuma ta sami abinda take so, ana haka Jummai tasame ciki,nan fa Abba ya maida duk wata kulawa kan Jummai duk da bawai ya daina kula da Anty bane amma ya canja yamaida kaso 80 na kukawar shi ga Jummai anty kuma kasu 15,wata rana na shigo d’aki na tarar da Anty ta na kuka,ba dinga tambayar ta meyafaru tace bakomai.        Kukan dana ga Anty nayi yasani a damuwa har nakasa bacci gaba d’aya, cikin dare naji Anty tana addu’a akan Allah yabata haihuwa,tun daga lokacin nima nafara tayata addu’ar ana wanan zaman ne Jummai ta haifi yar ta mace wacce aka sakamata Lahira sunan Maman Jummai ne.      Abba yad’auke kaso 15 din kulawar dayake bawa Anty ya k’ara mai da ita kan Jummai ya zamana ni da Anty munzama yan kallo a wanan gidan,tun a wanan lokacin na taso da tsanar Jummai,Lahira har da Abba haka mukayi tazama nida anty har bayan shekara biyu fa haihuwar Lahira .      Nadawo daga wasa kawai naga Jummai tashiga wani shago Musa mai kayan miya wanda dama mak’wafcin ta ne sanda take siyar da awara,lokacin banfi shekara 7 dan haka banyi tunanin abunda suke ba kenan kawai dai a yanayin da tashiga yasa na gane ba abin gaskiyya zasu aika ta ba, ko da nasar da Anty sai tace k’arya nake dana dage da rantse rantse sai tace ba ruwana.     bayan sati biyu naje makarantar dare da mukeyi sau naji yan wasu ajina ana musu bayanin akan bai hallarta mace ta kwanta da namiji wanda ba mijin taba ko tashiga d’akin wanj namijin hakan yasa na d’auki alwashin sai na tonawa Jummai asiri ko Abba zai rabu da ita yadawo wa da Anty farin cikin ta (ban san cewa zanyi TUDU NE AKAN KWARI  wanda zai tarwatsa duk wani farin ciki a rayuwar da nake ciki ba,wanda zai juya sama ta ta koma k’asa)            Ranar talata da bazan manta da ita ba nadawo daga wanan wajen wasan da nake zuwa naga Jummai ta shiga wanan d’aki, kai tsaye na nupi wajen sana’ar Abba nace yazo ba lafiya a gida a kid’ime ya biyoni shida abokan sa guda biyu sunje nace ba lafiya yasa suka yo mai rakiya dai’dai shagon Musa na tsaya nace ya shiga ciki,tsayawa yayi yana cewa “ina ne nan, me zanyi a ciki.” gyad’a kai nayi sanan nace        “Abba ba lafiya kashiga ciki.” jin haka yasa d’aya daga cikin abokan nasa danna kai yashiga sai dai fitowad da yayi a guje yasa su abba tambayar shi ko lafiya,rike Abba yayi sanan yace    “bazaka shiga ba kai haladu shiga kagani.”      d’aya abokin nasu ne yashiga shima ya fito yana maimaita innullahi wa inna illahir rajiun       a kid’ema Abba ya fusge ya shiga sai dai shirun da sukaji yasasu ka bi bayan shi.    a kwance suka tarar dashi alamun ya suma, Jummai kam iyhu ta fashe dadhi da fad’in      “nashiga uku ni jummai na shiga uku.” sanan ta nuna ni da yatsa tace      “yanda kazama sanadin tonuwar Asiri na wallahi sai nazama sanadiyyar to nuwar naka asirin.”      da k’uruciya bangane me take nupi ba aka kama Abba aka fita dashi zuwa chemist,kai tsaye nayi gida domin sanar da Anty sai dai mutane na gani a k’ofar gidan sunyi carko carko wasu suna shiga wasu nafita, da gudo nayi cikim gidan sai dai ji nayi anrik’e ni.     wani b’akin mutum dogo da alaman d’an sanda ne domin nagane shi ana kiran shi da Judge da k’arfi na fusge hanuna sai dai ya rik’eni da karfi yanda bazan iya k’wace wa ba tun ina fushe fusge har na nutsu domin a yanda nake ganin ana fitowa da gidan cikin tashin hankali dole nasan wani abu ne yafaru.     Ana haka wata k’awar Anty tafito,kallo na tayi sanan tace Mukhtar zo nan,cikani yayi natafi tare da cewa      “Adda me yafaru a gidan mu.”   cikn rauni da sanye ta ce       “Mukhtari sai hak’uri Allah yayiwa Halima rasuwa.”     kamar anbuga min guduma haka naji maganar tata sai dai maganar da naji ana fad’a ta dawo dani daga fad’uwar da nake shirin yi      “aka kashe ta dai ko, kai Jummai ce takashe ma Uwa gata can yan sanda zasu tafi da ita.”      ban k’arajin komai ba natafi k’asa sumamme, sai dare na gane inda nake lokacin har abinne gawar anty ita kuma Jummai yan sanda sun tafi da ita, gida ya rage dagani sai Abba.      Bayan kwana uku da kashe Anty Abba yafara wata rashin lafiya sakamakon Musa yagama fad’an duk wata gaskiya domin tun kafin Abba ya aure Jummai suke tare har sukayi aure,yarinyar ma da akace yar Abba ce ashe yar wajen Musa d’in ce,wanan abu ya k’ara tashin ciwon nashi,kwanan sa biyu yana jiya Allah yad’auki ransa sai dai kafin ya mutu sai da ya damk’a amanata a wajen d’an sanda abokin sa wanda shine sanadiyar duk kasancewa ta a wanan hali,Ummi nasha wahalal rayuwa mai yawa a hannun wanan mutumin,nasan zafin maraici a hannun wanan mutumin,naga mummunar rayuwa a hannun wanan mutumin,Ummi k’arshe nina kashe wanan mutumin.      juyowa Ummi tai ta kalleshi inda shikuma ya d’aga mata kai alaman eyh     “to garin ya? kuma wace kalal azabar rayuwa kasha a wajen sa.”       “Ummi zan k’arasa miki amma ki gama da makarantar nan,inda zamu tafi sai na baki.”      toh kawai tace sanan takama hanya ta shige cikin makaranta,zuciyat ta fal da tunani kala kala a game da rayuwar Master,wanda ya k’arawa soyyayarsa girma da k’arfi a cikin zuciyar ta.      Ummi ba su gama da makaranta bs sai wajen k’arfe 04 hakan yasa bata samu biya gidan Anty nafisa ba,kai tsaye gida suka dawo tare da Asiya wacce tabata duk wani labari da Master ya bata, sosai tausayin Master ya shiga zuciyar Asiya itama a wanan karon, a haka suka k’araso gida inda ko wacce ta shiga nasu gidan.      kamar ko yaushe da sallama Ummi tashiga cikin gida, tayi mamakin kin amsa sallamar da Hajiya tai mata duk da tasan bawai sakar mata fuska take ba saidai tana d’an amsa sallamar ta da gaisuwar ta,d’aki tashiga jiki ba k’wari ya hau canja kaya, sai dai sallamar Goggo da tujiyo ya matuk’ar tsorata ta a fili tace.     “Me yakawo wajan jarababbiyar matar kuma.”  Goggo kam fad’i take      “Sahura ina yarinayar nan,.”   “Tana fa ciki Goggo itama yanzu ta shigo daga yawon zancen nata.”      Hajiya ta bawa Goggo amsa, Zama Goggo tayi sanan tace      “Bari shi yazo idan tsoron ta yake mu ba tsoron ta muke ba,ta turo shi yaron yazo ayi musu aure.”      “Zai dai fi Goggo,tunda yarinyar nan ba tsoron baccin ran mu take ba, duk kwanakin da na d’auka bana mata magana a banza, yau tana fita sai da ta tsaya a wajen sa.”        “innullahi wainna illaihi rajiun.” Ummi ta fad’a tare da d’ora hannu akanta,wanan wane irin mai sa ido ne yake mata wanan mummuna binciken?      “ba kyajin Goggo tazo ne, ko ita zata shigo ta gaisheki rik’ak’iyya?.”        Hajiya ta fad’a daga nan tsakar gidan “kaya nake cirewa.”  Ummi tafad’a a ranta tana cewa kamar Hajiya ce yar Goggo sabida yan da halin su yazo d’aya.      jiki ba k’wari ta gama cire kayan sanan ta canja zuwa riga da wando kasancewar yanayi zafi da ake fama dashi, haka ta fito tsakar gidan kamar mara laka a jiki,daga nesa ta tsugunna k’asa tare da cewa     “Goggo sannu da zuwa,ina wuni.” “ke za’ai wa sannu,uhm uwar masoya.” Googo tafad’a tana tab’e baki,kallon ta Ummi tayi a ranta tana cewa wanan tsohowa da kinibibi take, kitchen Ummi tashiga ta zuba abinci, tana cikin ci Abba yashigo gidan sakamakon kira da Goggo tasa Hajiya tayi masa, sai da suka gaisa da Hajiya sanan tace        “Kaga Kamalu a matsayina na mahaufiyar ina baka Umarni akan cewa maza maza yarinyar nan tafito da miji ayi mata aure,domin bazan zauna ka zuba mata ido ba tunda ta zab’i kule kule maza.”        “aure kuma Goggo duka duka yaushe Ummin ta ta girma.”     Abba yabata amsa cikin tausasawa  “to indai bazaka yi mata aure ba inaso a yanzu a gabana ka haramta mata kula kowanne namiji,fita indai ba muhimmiya bace.”     daman wanan shine plan d’in da suka shirya da Hajiya     gyada kai Abba yayi sanan yace   “toh Goggo.” Ummi ce ta tareshi da cewa   “a’ah Abba nazab’i ayi mun auren.” kallon ta sukayi gaba d’ayan su, Hajiya cikin t’sananin tashin hankali tace      “Ubanki Ummi nan zaki zo kiyi mana maganar banza.”       “Hajiya akan kuce zaku rabanj da Yaya Mukhtar gwanda kuyimun auren kawai.”      “Au har yazama yayanki? wace uwar ce ta haifa masa ke?.”      Abba ne ya katse Hajiya da cewa  “Saliha me kikeyi hakane?.” sanan ya juya ga Ummi yace       “kinsan abinda kike fad’a kuwa?,Aure ba abu bane na wasa Ummi, sanan ba a kowane mataki ake yiwa yarinyar aure ba,bikiga yayarki Nafisa ba, saidai ta kammala diploma a k’aramar jami’ah,sanan akayi mata aure,kuma bikiga wanda ta aura ba?, mutumin arziki duk sanadiyar tayi ilimi ne.”           “Abba nima a yanzu nayi ilimi fiya da mata da yawa,kuma idan cigaba da karatu ne ana cigaba ko a gidan aure ne.”       “Ubanki Ummi shegiyar yarinyar da rashin kunya.”     Goggo ta kat’se su     “to Goggo ina laifin yarinya anan da yahuce na Ubanta da bai tashi ya kwakwad’e ta ba.”     Hajiya ta fad’a ta na makawa Abba da Ummi harara         “Ummi ba yanzu za’ayi miki aure ba,ki maida hankali akan karatun ki, Allah yayi miki albarka.” cewar Abba yana niyar tashi     “A’ah Abba dan allah ni dai ayimun.” tabbas lamarin Ummi yafara bawa Abba mamaki,dagaske dai auren take so!     “Abba kayi shiru dan Allah.” kallon Ummin yayi sanan ya kalli Goggo da Hajiya      “Ummi kice masa yazo ya sameni.” daga haka ya fice,Ummi ma tashi tayi ta shiga d’aki abun ta,Hajiya kam kallon Goggo tayi sanan tace       “Goggo kinji shi kuwa?.” “najishi Saliha, yanuna yarinya yarsa ce ba ta wani ba.”      “chab da sake wallahi tallahi.”  Hajiya tafad’a tana mikewa tsaye      Ummi bata iya bacci ba sai da ta sanar da Asiya wanan labari,Asiya tayi farin ciki sosai da sosai sai dai tana ganin Har yanzu Ummi ba ta fuskanci TUDU AKAN KWARI da take k’ok’arin d’orawa ba,wanda tsallake shi abu ne mai mugun wahala .      Asiya na nan zaune tana tunanin mafita wa Ummi Halima ta shigo cikin gidan,hannayen ta rik’e da manyan ledoji guda biyu,Kallo d’aya Asiya tayi mata ta d’auke kai       “Ke yar matsiyata wa kikewa kallon banza.”        Halima tafad’a tana wata uwat jijjiga “Banza nake wa.”     Asiya tabata amsa ba tare da ga d’ago ta k’ara kallon ta ba,da gudo ta tawo tayi kan Asiya daniyar zane ta domin tsabar neman tashin hankali yasa ta manta da heels din takalmin dake k’afarta,jikake Tum tafad’i a k’asa, da sauri Anty tafito tana fad’in    “ nashiga Uku ni Atine,dawa Allah ya had’ani idan ba mat’siyata ba, banda bak’in ciki shine zaki kadata anan wajen.”     Mamace tafito da d’aki domin tasan bak’aramin aikin Anty bane tace zata daki Asiyan da ko motsim tashin ta ba’aji ba,fitowar ta yayi dai dai da k’ok’arin kai dukan da Anty ke shirin yiwa Asiya   “A’ah a’ah Atine karki fara,wallahi tallahi.” page[13&14]              “Atine nafara gajiya da mugayen halayen ku a cikin gidanan h’akurin da nake dake bafa na dole bane,sanda muke zaune dake k’ark’ashin inuwar miji d’aya ne yazama dole,shirun da nake miki na mutunta wane amma tunda kinga bakya son hakan,Atine kitarka ta naki ya naki ki barmun gida.”       Mama tafad’a cikin b’acin rai,ita kanta Anty tasan ta b’atawa Maman rai domin duk zaman da suke Mama bata tab’a cewa ta bar mata gida ba,ko yaran ma da suke cewa tabar musu gida Maman hanasu take to amma yau da kanta.      “kinga sahura zancen na barmiki gida bai taso ba domin munzama d’aya,kuma daman zaman duniya ai zo mu zauna zo mu sab’a ne.”     Murmushin takaici Mama tayi duk da daman ita ma d’in bawai dan tabar gidan take magana ba kawai dole zaita mata baraza nane “zo mu sab’a d’in to Atine ni nagaji da wanan sab’awar, dan haka kika kwashe naki kiyi gaba Allah yahad’a kowa da alheri.”         “Sahura zo kiji.” Anty tafad’a tana kama hannun Mama zuwa cikin d’aki     “Sahura idan nabar gidan ina na kama,kinsan bani da kowa sai Allah sai ke, kuma kinga ni amanar mai gidan muce a wajen ki tunda kece babba,kiyiwa Allah kiyiwa ma’aiki ki hak’uri.”          “shikenan yahuce amma gaskiyya ki fata harkar auta ta,domin nasan Umar dai dai ke ne.”       “tom nagode.”  Anty ta fad’a tare da tashi ta fice zuwa nata d’akin,Halima ta rufa mata baya.     Washe gari  Asiya da farin ciki tashiga gidan su Ummi nuna mata sabuwar keypaf da yaya Umar ya siya mata sakamakon rubuta jarabawar jamb da zasuyi,sai dai labarin da Ummi ta bata ya dakatar da wanan farin ciki daga  fuskar ta       “Ummi wai kina da hankali kuwa?.” “Kamarya ina da hankali.” Ummi taba wa Asiya amsar tambayar da ta mata      “Ummi banga alamun kina da hankali ba da har zaki fifita soyayyar wani akan ta mahaifiyar ki,Ummi kinsan mahaifiya kinsan girman mahaifiya.”           “Nasani Asiya amma wanan magana ake ta rayuwa ta gaba d’aya, ko zan zauna ne a gidan suyi ta kallo na.”      Girgiza kai Asiya tayi sanan tace  “A’ah Ummi baza su so suyita kallon ki ba kisani Ummi har yanzu yara ne mu, ba mukai cikakken lokacin da xa ace har munyi fito na fito da iyayen mu akan maganar aure ba.”        “Asiya ba fito na fito nayi da iyayena ba,alfarma na rok’a wajen mahaifina.”     murmushi Asiya tayi sanan tace  “Ummi kisani wanan TUDU AKAN KWARI daikike k’ok’arin d’orawa abune mai matuk’ar wahala wajen tsallakewa, wanda a k’arshe ma ba tsallakuwa zai ba,wahala zaki sha ki hak’ura.”        “Asiya wane irin mugun baki kike mun,Asiya kar dai ace bak’in ciki kikemun.”        “Kinsani bazan tab’a zama mai bak’in ciki a rayuwar ki ba Ummi,sai dai mai goyan baya da baki shawara akan rayuwa Ummi, Dan allah ki nutsu kiyi tunani mai kyau.”      murmushi Ummi tayi sanan tace “Asiya nayi duk wani tunani da yakama ta nayi,Aure baitaba zama haram ba,kuma bai tab’a zama rashin biyayya ba.”          tashi Asiya tayi ta matso kusa da Ummi tare da d’ora hannun ta a kafad’ar ta        “shikenan Ummi Allah ubangiji ya tabbatar da alheri,sanan inaso ko wane hukunci Abba ya yanke miki bayan ganin Master ki kasance mai biyayya tunda shima ya numa biyayya kuma hak’in mune biyayya ba su ba.”        rumgume Asiya Ummi tayi sanan tace “Insha allah Asiya nagode.”        “Ungo wayar kirashi Tunda kina da number din sa.”      karb’a Ummi tayi ta saka number da take haddace akan ta tatafi kira.    ______MASTER_______       zaune yake tare da yaran sa cikin mai t’sakaicin gidan dayake naso, ko wanne yana sabgar gabansa,wasu na bushe bushen hayak’in su wasu na nad’e nad’e.      Wayar shi tashiga ruri alamun kira nashigo wa,ganin bak’uwar number yasashi d’an jan lokaci kafin ya d’aga.       Sasanyar Muryar tace ta daki dodon kunen sa       “Assalamu alaikum.” “Amincin Allah ya tabbata a gareki yah Ummi.”       dariya tayi kafin tace  “Ya akai ka ganoni.”       “Haba Ummi na me zai sa nakase gane wanan zazzak’ar muryar taki.”       dariya tayi sanan tace “Toh baka amsa sallaman ba.”       “Amin wa’alaiki salam.” dariya tayi jin yanda yaraba amsa sallaman sanan tace     “Yaya barka da safiya fatan kayi bacci mai dad’i.”     “mai dad’i tare da mafarkin ki,sai dai rashin sake ganin ki jiya ya rage mishi dad’i.”      dariya Ummi tayi sanan tace “Yaya albishirin ka?.”     “Goro fari sol Ummi nah.” ya amsa cikin zak’uwa domin baitab’ayin waya ta soyayya ba sai yau,wani irin farin ciki yakeji,wani irin yawo zuciyar shi nayi a sararin samaniya      “Yaya ba yanzu zan fad’amaka ba sai mungama waya.”       dariya yayi sanan yace  “Ai girman kine ranki yadad’e, amma wanan wayar ta wace?.”       “Wayar Asiya ce,jiya yaya Usman ya siya mata kasan zamuyi jamb.”       “Nasani Ummi na saura kema ko?.” yak’areshi maganar da alaman tambaya     “Nasani Abba zai siyamum kafin lokacin,yaya baka k’arasamini labarin ka ba.”      “Ummi anjima idan mun had’u zan k’arasa miki.”     “Toh yaya amma kasan me?.” girgiza kai yayi kaman tana kallonshi sanan yace    “A’ah.” “Abba yace yana son ganin ka,za’ayi mana aure.”     Kaman saukar arado haka yaji maganar tata,sanan tafara masa amsakuwa a kunne, da k’yar ya iya cewa      “Ummi na banason wasa.” yaya ba wasa nake ba fa dagaske ne.”     “Toh Ummi mene yakawo maganar?.”  “Had’uwar da mukayi da kai jiya shine Tsalha yakaiwa Hajiya labari,kuma Goggo tazo shine tacewa Abba lallai ayimun aure.”       sosai Mukhtar yaji dad’in zancen nan na Ummi,duk da ya manta tarin abu dake gaban shi,Mummuna tabon daya shimfid’awa rayuwar shi.        “Shikenan Ummi yaushe yake so nazo.”      “Yau da daddare mana.”   “Shikenan Ummi na bari nafara shiri tun yanzu.”     dariya tayi sanan takashe wayar,Master kam zama ya gyara yafara tunanin ta inda zaifara,kama daga shirya kanshi,domin bashi da wani kayan arzik’i guda daya da zaisa yaje gaida siriki balle kuma hula da takalmin arzik’i duk kayan shi na gayu ne,hannu yasa ya tab’a sumar kanshi ita kanta tana b’ukatar a kwashe ta.     Sunan Tsalha ne yadawo masa kunne da sauri yakira yaran sa sanan yace     “Waye Tsalha a cikin gari?.” Shiru sukayi gaba d’ayan su kafin daga baya rooget yace     “ina wanan gayen da muka tare ranar da kafara had’uwa da Madam.”  d’aga kai Master yayi alamun ya gane,sanan rooget d’in ya d’ora da cewa  “Tabbas shi naji ana cewa Tsalha a cikin gari.”     “To inaso aje a zubar  masa da mummunan jini.”     Master yafad’a tare da tashi yabar wajen,fita suma su rooget d’in sukayi zuwa cikin gari,basu sha wata wahala ba suka gamu da Tsalha,wanda yadawo daga yawon d’akko rahoto, binshi sukayi abaya har yabar wajen da babu cikowa sanan suka k’addamar mai.    Jini iya Jini sun zubar mai kam,sai dai basuyi mai raunin da zakai shi lahira ba,sai dai doguwar jinya.  Master kam su rooget nafita shima yanufi wani shagon aski dake unguwar su,aka kwashe mai wanan cibiri-cibirin sumar dake kansa,lokaci d’aya duk wasu kamanin sa suka sauya,a hanyar shi ta dawowa ya had’o da mai yankan farce nan ma yatsaya aka yanke masa,sanan yadawo gida ya fara duba cikin kayan sa,sai da ya bincika sosai sanan yagano wata blue d’in shadda, wacce taci uban squeezing yana k’ok’arin buge ta su rooget suka shigo gidan, da farko basu ganeshi ba domin kamanin sun canja Badoo ne yace.     “Wai Master me ke faruwa haka?.” hararar su Master yayi domin yaji haushin kallon da suke masa ga dariyar da Rooget ke b’oye sanan yace     “Me ka gani.” “Bangane me nagani ba,gashinan ka aske sumar ka,kamar ma har farce kayanke,gashi kana neman buge manyan kaya kasa.”       “Gidan sirikai na zani.” Master yafad’a yana cigaba da tafiya,dariyar dasu ka saki ne su biyun yasashi juyowa,cikin muryar dariya Rooget yace      “Kaga Master a gidan sirikai.” Wata dariyar suka k’ara saki sanan Badoo yace      “Idan kaje me zaka ce musu?.” “Banason iskanci fa.”  yafad’a tare da cigaba da tafiya,suna ta faman dariya yaje yabuge kayan ya ajiye su,sanan yadawo inda suke,lokacin sun daina dariyar zama yayi sanan yace    “Abdullahi, Isah.” d’ago da idanun su sukayi suka kallesu domin su kansu sun manta rabon da akira su da asalin sunayen su.     “Ina tunanin lokaci yayi da zan ajiye wanan rayuwa sanan kuma zaku ajiye,muka ma gaskiyya, a yau zanje gaida mahaifan Ummi kuma a yau zan a jiye du wata mummunar d’abi’a da nakeyi,domin nasan a yanzu nakai matakim da zansan na girma kuma ina fatan kuma kusan hakan.”       Shiru sukayi gaba d’ayan su,domin basu san meza suce ba,domin ko a harkar ma shine gatan su,shine mai gidan su,idan kuwa ya ajiye dole suma su a jiye.      “Bazan yi muku dole ba,amma sai dai zan fita hak’k’in ku domin mun aika ta aikin b’arna a baya a tare hakan yasa a lokacin a zan ajiye zanso na ajiye tare da ku,kafin zuwa lokacin da zamuyi nadamar da bata da amfani.     Girgiza kai Badoo yayi sanan yace “haba Master! yanzu akan soyayya zaka ajiye mana cin abincin mu?.”       “ba ajiye muku cin abinci zanyi ba,akwai wasu hanyoyin cin abinci da dama.”     Master yafad’a yana kallon su domin ganin yanayin jikin su      “ka sake tunani dai Master.” cewar Badoo d’in,shikam Rogeet cewa yayi    “Bani da abinda zanfad’a domin hakan yayi, yana da kyau a kowanne lokaci d’an adam yadinga waiwayar baya yana tuba akan zunuban sa.”       “Masha allah! Allah ya karb’i tuban mu.” Master yafad’a tare da shigewa cikin d’akin da yake nasa      “Kai baka da hankali ne Rogeet?, baka da wanj ra’ayi sai na Master?, sai abunda yace shi zakayi?.”      Badoo yafad’a yana janyo Rogeet d’in kusa da shi      kai ya girgiza sanan yace “ Badoo kaine baka da ra’ayi amma ni daman inda ra’ayin ajiye wanan rayuwar da muke fama da ita, na duba bi TUDU AKAN KWARI da nayi sanan nasan ta idan zanfara gyarashi.”    da haka Rogeet yayi cikin d’akin su ya hau had’a kaya,dole ya koma ga iyayen sa, wanda yabarsu sabida rud’in abokai da na duniya.          Master na cikin d’aki yaji alamun fito da kaya,tashi yayi ya lek’o ganin Rogeet nafito wa da jakar ghanna most go ne yace dashi     “Mene haka?.” “Master zan koma gida! zan koma ga iyaye na.”      “Tabbas kayi tunani,nima da ace ina da iyayen da zankoma wajen su da kafin aure na da Ummi sai naje, Amma dan allah kafin katafi kaban labarin me yaraba ka dasu?.”    Master yafad’a yana samun waje tare da zama,shima Rogeet d’in zama yayi kan jakar ghanna most go d’in haka ma Badoo dandamali kan rijiya yasamu ya zauna.     “Dukkan ku nan kusan asalin suna na kawai,baku san asalin gari mu ba da komai, to ni d’an asalin garin kano ne amma cikin k’auyin kano KURA, mu 13 ne wajen mahaifin mu,ni kad’ai ne wajen mahaifiyata, wacce ta d’auki soyayyar duniya ta d’oramun, duk da irin rashin k’arfi ma mahaifin mu, kusan gidan yawa dai mussaman na k’auye,mun taso ne cikin rashin kula daga mahaifin mu, kasancewar muna dayawa a gidan,mahaifiya ta na k’okari sosai akaina, ni kad’ai nasamu damar yim karatun boko a cikin y’ay’a 13 na mahaifin mu sabida mahaifiya ta nason na zama wani a rayuwa. Page[15&16]  Da k’yar nasamu na kammala k’aramar secondary,lokacin na hadu da abokan da suka fara koyamun shaye shaye, Mahaifiyata bata son wanan d’abi’ar kullum addu’a take allah ya rabani da wanan abokan nawa amma kullum k’ara kusa nake dasu.     Tun farko mahaifina baiso nayi karatun boko ba,ba wai dan yana da dalili ba sai dan kar mutane su zageshi a kan yakasa sa yaran shi a makaranta sai mahaifiya tace tasa kani, wanan shaye shaye da nafara yazama kamar wani abu da mahaifina zai fake dashi yadinga musgunawa mahaifiya ta, amma hakan baisa nayi hankali na daina ba, tsangwama da habaicu babu wanda mahaifiya ta bata sha a wajen a bokam zaman ta, har zuwa lokacin da nasa k’afa nabar gari har zuwa yau ban koma wajen mahaifiya ta ba,ban k’ara jin wani labari daga garesu ba,tabbas na aikata babban laifi a rayuwa ta,nayi wa mahaifiya ta butulci, na sa ta taji kunya a idon duniya.”     Kuka sosai Rooget yakeyi, tabbas ya aikata babban kuskure a rayuwar sa, gashi anan d’in ma bai cin ma wani abun kirki guda d’aya da zaije yanuna acan ba.    “Tabbas rayuwar ka cikin kuskure ce,ka aika ta babban laifi,sai dai shawarar da zan iya baka bata huce ka zauna ka nutsu kanemi k’wak’warar sana’a,sanan kaje gida da zuwan gaida mahaifa, kadawo ka cigaba da sana’a har allah ya dafa ma kaika lokacin daza ka sa mahaifiyar ka alfahari.”             DARE        Bayan sallar magriba ya hau shirin sa cikin shaddar da yad’auko, tasha gugar da Rogeet yayi mata,kanshi da ya sha aske d’auke da hula,k’afar shi sanye da takalmi way’anda duk aikin Rogeet ne.     Kai tsaye k’ofar gidan su Ummi ya nufa, yafi minti goma tsaye da tunanin ta inda zaifara,sai daga baya yayi tunanin kiran wayar da Ummi ta kirashi d’azu.      Dai dai lokacin Ummi na zaune tsakar gida bayan tayi shimfid’ar tabarma,Hajiya na cikin d’aki tana ta aikin zubawa Ummi da Abba harara, ji take kaman ta shak’esu gaba d’aya kuma tayi alk’warin indai itace uwar Ummi sai ta gayawa yaron nan maganar da zata hanashi k’ara zuwa wajen Ummi,domin tabbas ta riga da taga ma yiwa Ummi mijin aure.      Asiya ce tashigo gidan, bayan tayi sallama ne ta matsa kusa da Ummi tare da rad’a mata cewat Mukhtar na waje, kallon Abba tayi sanan tace      “Abba yana waje wai.” “tashi kije kiyi masa iso.” Abban yafad’a dai dai lokacin da itama Hajiya ta mik’e da niyar fitowa.      Kallon shi Ummi take sosai yayi matuk’ar kyau,kamar ba Master da kowa ke tsoro ba,dodon mutanen gari, ganin Ummi na kallon shi baki a sake yasa shi cewa     “Ko banyi kyau bane?.” dariya tayi sanan tace      “Lallai Yaya! wane ya isa yace bakayi kyau ba a wanan kyakyawar shigar.”      “Dan allah da gaske kike Ummi.”  ya tambaya cikin sauri amma da yanayi wasa, ita ma cikin yanayin wasan tace     “da gaske mana yaya! Allah har kyalki kakeyi kaman wata.”      “naji dad’i Ummi yanzu me za’ayi?.” “shiga ciki mana.”   Tabashi amsa tana shigewa, kirjin Mukhtar wani irin bugu yake dum dum, zuciyar na wani mugun tsalle kamar zata fito, cikin secon guda zuciyar shi na bugawa sau biyu, kamar mai tausayin k’asa haka yake taka k’asa, ciki ciki yayi sallama domin wani irin nauyi yaji bakin shi yayi masa,     Amsa sallamar Abba yayi sanan yayi mik’amishi hannu alamar musbaha, kasa da kai Master yayi sanan ya girgiza kai ya nufi wajen da Ummi ta nuna mishi ya zauna.     Hajiya na daga tsaye tana kallon irin rawar k’afar da Ummi keyi har dasu kawo ruwa sanan ta shige d’aki     Abba ne yace “To bawan Allah ko zan iya sanin ka kafin komai?.”     wani irin dum kirjin Master ya bayar cikin rawar Murya yafara magana      “Sunana Mukh..tar.”  “to malam mukhtar ko ban sanka ba bazan kasa sanin mahaifin ka ko wani naka ba?.”      Abba yafad’a alamun dai yana son k’arin bayani a cikin sunan nashi     “Iyaye na ba y’an garin kano bane amma ni a kano nayi rayuwa ta cikin wanan unguwar.”       “Ko me ya rabaka da iyayen naka?.” Hajiya tafad’a tana k’arasowa wajen ta zauna, kallon ta Master yayi sanan yace     “Mutuwa.” Abba ne yace “Allah yajik’ansh da rahama, amma anan d’in da kake zaune kai da wane kuma wace sana’a kake ko aiki da aka sanka akai?.”       “Ina zaune tare da abokai na.”     “Sana’a fah!.”   Hajiya ta sake tambayar  “Bawata tsayayyiyar sana’a bace wacce za’au ta fad’anta”     “Au baka da tsayayyiyar sana’a kakw hurewa yarinya kunne?.”     “Saliha!.”  Abba yadakawa Hajiya tsawa sanan yace    “Maganar aure ba ta mace bace dan haka kitashi kibar wajenan idan bazaki iya shiru da bakin ki ba.”     Harar Abba tafarayi k’asa k’asa tace  “ba inda zani wallahi.”     Abba ne yayi gyaran Murya sanan yace  “To dawace sana’a kake so na baka auren yarinya ta?.”      “A yanzu bani da sana’ar da zan rik’e Ummi sai dai kafin zuwa k’ank’anin lokacin da Zamuyi Aure da Ummi zan mallaki sana’ar da zamu zauna.”     Murmushi Abba yayi sanan yace  “Ina son na k’ara sanin ka sosai.”     d’ago kai Master yay ya kalli Abba sanan yace     “Baba fuskata ba b’oyayyi bace ada,amma yanzu fuska ta abar b’oye wace?.”     “ Wane kai.”   Hajiya tafad’a azabure tare da tashi,domin a d’ago kan da yayi ta hango kamanin Master domin daman idonta a kanshi yake       “Wane Kai.”  Tasake maimaitawa, abba ne yace   “Wai saliha meke damunki ne dan Allah.” “Kaga alhaji kyaleni, kasan wane wanan.” tafad’a tana nunashi da yatsa,girgiza ma ta kai Abba yayi ganin kamar ta zabura ko firgita sanan yace    “Ki nutsu dan Allah.” “Na nutsu ba kasan wane a cikin gidan ba ko! to wan nan la’ananne dan iskan yaron nan Master shi ne a gaban ka.”     A furge ce Abba ya mik’e tare da fad’in innullahi wa inna illahir rajiun      Ummi da Asiya dake cikin d’aki ne suka fito da sauri jin Innullahin da Abba ya furta.    Mik’ewa Master yayi zuwa inda Abba yake sanan ya durkusa kan gwiwo yin sa,cikin murya mai bayyana rauni yake magana     “Abba tabbas nine Master mai mummunan hali,dan daban da kowa ke tsoro, na kamo da matsanan cin son Ummi yar ka, na durkusa akan gwiwo na ina neman kabani auren yar ka Ummi tun ranar da na fuskanci nafara son Ummi nayi nisa nafara ajiye munanan hali na, a sanda ummi ta sanar dani kana buk’atar ganina, nak’arasa a jiywa ragowar halin, na tuba a sanadin soyayyar Ummi, Abba ka tausayamun dan darajar da Allah yayi maka na d’an adam.”       Shiru Abba yayi dan gaba d’aya baya fuskantar komai akan maganganun da Master ke masa, da sauri Ummi ta k’araso wajen tare da durkusawa yanda shima Master d’in yayi sanan tace      “Abba dan girman Allah, dan girman annabin Allah, Abba karka rabamu, Abba ina sonshi.”    Hajiya ce takai hannu ta finciko ta k’asa da sauri Mukhtar yayi kanta da niyar rik’eta Abba ya dakatar dashi da fad’in      “Karka kuskura ka tab’ata.” Tsayawa Mukhtar yayi yana kallon Abba haka ma Ummi,Asiya tana tsaye daga dokin k’ofa tana faman zubar da hawaye,gab d’aya su ukun sun zama abun tausayi inda Abba da Hajiya suke cike da tsantsar tsoro da kuma mamakin k’arfin hali irin na Ummi, can Abba ya kalli Ummi sanan yace     “Ummi ke ce na isa dake,kece na haifa dan haka daga rana mai kamar ta yau na raba ki da wanan yaron.”    Da sauri Ummi ta rik’e k’afafun Abba tana kuka     “Abba dan Allah dan annabi,Abba dan son da kake wa mahaifin ka, ka taimakamun karka rabani da shi,Abba ina son shi Abba sabida shi nake rayuwa.”     jikake tass Hajiya ta zubawa Ummi wani gigitaccen mari wanda yaja Asiya saurin tawowa ta fad’a kan Ummi,Mukhtar kam ji yayi kaman ya shak’e Hajiya wani azababben kallon yake mata mai cike da jin haushi.     “Kallenk da kyau y’ata na daka ba kuma yadda zakayi dani kuma katashi kafice mana daga gida.”    Hajiya ta fad’a, tashi yayi ya k’ara zuwa kusa da k’afar Abba ya tsugunna da sauri Abba yajanye k’afarshi sanan yace     “Karka kuskura ka tab’amun k’afa yarinya dai y’ata ce kuma bazan bawa d’an daba irin ka ba dan haka kayi maza kafuce mun daga gida.”     Tashi Master yayi yana tangal tangal kamar wanda yasha wani abun da sauri Ummi ta fincike jikin ta daga na Asiya tayi inda yake tare da rik’o mai hannu,tsayawa yayi cak ba tare da yajuya ba ya fara magana     “Ummi kiyi hak’uri.” “Ni zan baka hak’uri Yaya,sanan ina so karik’e wanan a zuciyar ka ni Ummi idan bakai gawa ce.”      jiyowa yayi ya kalle ta sanan yace  “Ummi ke kad’ai ce Mutum a rayuwa ta,ki sani ina sonki,zan kuma cigaba da sonki har zuwa numfashi na na k’arshe.”     daga haka yafice itama a hankali ta taka batare da tayiwa kowa magana ba tayi cikin d’aki ta kwanta jin wani irin jiri na d’ibarta     (Rabuwar masoyaaa tana da k’unci          zamiyo ban kwana rai duk yayo k’unci       idano sun gaza barci           soyayya tai sark’e zanzo zanzo tawo zamu zauna😭😭🥹)      lol Ummi da Master sun rabu    page[17&18]        Kwanciya Ummi tayi tana rufe idon ta,    Sama Sama tafar jiyo murya kamar ta Goggo, cikin ranta tafara fad’in     “Me kuma ya kawo wanan jarabbiyar matar cikin daren nan?.”      k’ok’arin bude idon ta da yayi mata nauyi kamar ba wacce ta kwanta yan mitina ba tafara yi, a hankali take bude idon nata,ganin zara zara yasata saurin k’ara bude idon, tabbas zara zara take gani    “Ya Allah.” Ta furta a fili sanan takai idon ta zuwa gefe da gefen ta,abun mamaki kamar a kulle take, da sauri tafara ki ciniyar kwance kanta.     Mutanen dake zaune cikin d’akin ne, su ka fara ganin alamun motsi daga gawar dake d’akin.     Da sauri Anty Nafisa ta tashi tayi wajen gawar tana tab’ata tare da fad’in    “Ummi! Ummi!! Ummi!!!.”   D’aya daga cikin mutanen dake cikin d’akin ce tayi waje ta sanar da Hajiya wacce ke tsaye ita da Abba tana fad’a masa kan cewa yazo yayi sallama da Ummi tunda angama shirya gawar ta ta, maganar da matar ta fad’a ce taso saurin juyo su kalleta sanan Hajiya tace     “Lami me kikace?.” “Tabbas Saliha Ummi ba mutuwa tayi ba ga gawarta can na motsi.”     Asiya dake zaune daga gefe ce ta tashi da sauri tayi cikin d’akin da gawar Ummin kece wacce daman fitowar ta kenan shima fitowa akayi ds ita sabida irin kukan da tasa gawar Ummin a gaba tanayi, Hajiya da Abba rufa mata baya sukayi suma zuwa cikin d’akin, lokacin har angama kiciniyar kwance ta daga d’aurin da akayi mata.     Da sauri Asiya tayi inda take tare da rungume ta tana fad’in    “Daman na fad’a muku ba yanda za’ayi Ummi ta mutu amma kuka kasa yarda kukace wai na rud’ene.”     kallon ta Ummi tayi sanan tace  “Asiya me yafaru ne.”      Goggo ce tashigo d’akin tare da fad’in  “Yau naga abunda ya girme ni, ace yarinya kwanan ki har hud’u kwance ba ko numfashi,sai kuma ranan da za kaiki k’asa ki mik’e.”   ba k’aramin mamaki Ummi tayi ba duk da bawai ta yarda da maganar Goggo bane amma tabbas tasan wani abu yafaru, bud’e baki tayi da niyar tambaye Abba.      Sai dai tana kai ido kamshi wani abu da yafaru yadawo mata wanda a tunanin ta bai wuce daren jiya ba, shiru tayi tana k’ara tuna irin cin mutunci da su Abba sukayi wa Master a daren jiya.     Goggo ce ta kalli Abba sanan tace “Sai ka fita kaje ka sanar da mutanen da ka tara cewar gawar ta tashi.”     daga haka ta fice waje,shima fitar yayi yana godiya ga Allah, nan fa zance yafara zaga mutanen dake cikin gida da way’anda ke k’ofar gida cewar Ummi ta tashi      Fitowar Abba aka fara yi mishi murna saka makon da ake mishi ta’aziya daga cikin gida ma haka abun yake, Anty Nafisa ce ta tashi ta shiga had’a ruwan zafi domin Ummi ta wanke jikin ta.      ***      Gidan ya kasance ba kowa daga Abba sai Hajiya da Anty Nafisa sai kuma Asiya,Ummi da matso da son sani abunda yafaru a cikin gidan da kuma halin da Master ya shiga domin tasan tabbas yana cikin babar damuwa ta rashin ta.     “Asiya bazaki sanar dani abinda yafaru bane wai?.”      Murmushi Asiya tayi sanan tace  “Ummi kina da damuwa ki tsaya mana kiji abinda Abba zai yanke, sai dai Ummi karki manta da alk’warin da kikayimun.”      “Wane alk’awari uwata?.”  Ummi tafad’a tana mata kallon tara saura kwata, Numfashi Asiya taja sanan tace     “Ummi akwai alk’warin da kikayi zaki d’auki duk wani hukunci da Abba ya yanke,bayan yaga Master.”       “Asiya wanan hurumin nawane ki kyale ni.”    Shiru Asiya tayi batace komai ba ***     (kwana hud’u kafin yau) A hankali yake takawa har yak’arasa gida,ba tare da ya iya ko sallama ba yafad’a cikin gida, Rooget ne kad’ai cikin gidan yana faman tunanin rayuwa da na iyayen shi, kamaf anje fo mutum haka yaganshi da sauri ya mik’e tsaye tare da cewa     “Master lafiya?.” Shiru Master yayi masa yana k’ok’arin shigewa ciki amma sai dai yakasa,ji yake kaman baya ake dawo dashi,salub’ewa yayi jikake tum yafad’i k’asa da sauri Rogeet yayi kanshi yana k’ok’arin d’aga shi.      B’angaren gidan su Ummi kam, Asiya fucewa tayi gaba d’ayi jiki ba k’wari haka Abba ma yatashi ya shige d’ake rai a jugule Hajiya kam zuciyar ta fara tas,al k’warin da ta d’auka na had’a auren Ummi da Affan d’an gidan aminyar ta zai cika kuma ko ba haka ba yanzu Ummi ba takai shekarun da za’ayi mata aure ba ga kuma kalal mutumin da ta dakko musu, haka kowa ya shige cikin d’aki *** Asiya na shiga gida tafashe da kuka mai k’arfi wanda yajawo hankalin mutan gidan zuwa kanta,kan cinyar Mama da ke zaune tsakar gida ta fad’a,  da sauri Mama ta fara tambayar ta lafiya, Anty da munafuncin yafito da ita daga d’aki ma cewa take      “Ke Asiya lafiyan ki zaki shigo mana gida kamar Anyi mutuwa?.”         Asiya bata ko kula Anty ba ta cigaba da kukan, abunda ya fusata Mama ta daka mata t’sawa da cewa      “Ke ba magana ake yi miki ba ne, idan bazaki yi shiru kiyi magana ba kitashi daga jiki na.”    Tashi Asiya tayi ta shige d’aki  “Aou akan ki fad’i menene shine kika zab’i ki shige d’akin?.”  Anty ta fad’a tana tab’e baki a ranta tana addu’ar Allah yasa ba lafiya ba ma, jin Mama ba tace komai ba yasa ta shige d’aki.      Halima dake kwance ce ta kalli Anty sanan tace   “Shishigin ki, gashinan kinje sun miki banza.”   Zama Anty tayi sanan tace      “Ke ni naso ace wani mummunan labari ne ko za’ace yaronan Umar ya mutu ko wani abu ya sameshi.”    tab’e baki Halima tayi sanan tace  “to ke ina ruwan ki da zaki yimusu wanan mugun bakin? ki kyalesu da halin su.”     “A’ah gwanda dai wani abun ya samesu su Halima ban k’i a tashi da safe ace duk sun mutu ba.”     “Ba amin ba.” Halima tafad’a dan ita Anty bata gane ta bane amma mugun son Umar take kuma sai ta aure shi zata iya samun sauk’i a zuciyar ta ***     Washe gari bayan Abba yadawo daga salla ne yashiga d’akin Ummi ya tashe ta domin yana so yayi magana da ita, domin ta fuskanci a yanzu Ummi rarrashi da kulawa take buk’ata kuma yasan hakan bazai samu a wajen mahaifiyar ta ba, shiyasa ya yanke shawarar tura wajen Nafisa domin yasan ita zata iya rarrashim Ummi.     Jin yana ta Sallama ba’a amsa ba yasashi shiga cikin d’akin,ganin ta kwance yasashi cewa     “Ya salam Ummi mekike baki tashi sallah ba?.”     jin shiru yasashi k’arasawa inda take tare da kai hannu yafara dukan gadon da take kwance akai yana fad’in     “Ummi! Ummi!! Ummi!!!.” amma ina shiru ba alaman motsi, hannu yakai saman hancin ta, ga mamakin sa yaji bata fitar da numfashi     “Ya allah.” Yafad’a a zabure tare da d’aukan ta cancara kas sukayi waje     Hajiya dake kok’arin d’aura alwala ce ta tare da cewa     “Alhaji lafiya?.” “Ina lafiya yarinya bata mumfashi.”     “Numfashi kuma! ajiye ta anan asama ta ruwa.”     Kanajin yanda take magana kasan itama ta rud’e gaba d’aya, a jiye ta yayi kan daddumar da take shimfid’e a wajen, wacce baya raba d’ayan biyu tunta jiya ce da aka shimfid’a , ruwa ake zuba mata sosai amma kamar ba zuba mata ake ba, cikin muryar kuka Hajiya tace    “Alhaji kaga wanan yarinyar kamar ba zuba mata ruwan ake ba, ko zaka d’akko mota kawai muhuce asibiti kawai.”    Mik’ewa yayi kawai ya fice ba tare da ya iya magana ba, ko a waje ma kasa ta b’uka komai yayi kawai ya tsaya jikin bango kamar bishiya.     Malam Audu ne yafito daga massallaci yana k’ok’arin shiga gida    “A’ah Malam lafiya dai ko?.”     Kallon shi Abba yayi sanan yace “ Malam Audu ba lafiya ba, yarinya fa Ummi ce bata da lafiya mota nake nema zamu kaita asibiti.”     “Abba jira na nemo mai mota.”    Umar da yazo wucewa ya tsaya jin Abba nacewa ba lafiya ba, kallon shi Abba yayi sanan yace   “To Umar bari na fito da ita.” ***    Fito da ita yayi dai dai da tsayuwar da mai motar da Umar yakirayi yayi, kuma hakan yayi dai dai tsayuwar Badoo a wajen domin suma tun jiya sun kasa gane kan Master, hakan yasa suka yanke zasu Ummi suji ko mene.     Anshiga fito da Ummi,Umar ya shiga gida sanar da Mama, fitowar tasu suma yayi dai dai, da sauri Mama ta k’arasa tana taimaka wa Hajiya da Abba gamin kamar Ummin dake kwance tana neman kayar dasu.      Akan idon Badoo aka gama komai har shigar da Ummi mota da kuma tafiyar su zuwa asibiti, haka yadawo ya sanar da Rogeet lokacin and’an samu sauki domin bacci ya kwashe shi,Amma jiya duk su ukun ba wanda ya iya runtsawa.     Kasancewar safiya ce babu wasu manyan likito ci, sai k’ananu da nurses, ganin kamar zasu bata musu lokaci yasa hajiya ta d’au wayarta ta kira aminyar ta Hajiya Balki mahaifiyar Affan wanda suke son had’a auren su da Ummi.     Hajiya Balki na kwance kan makeken royal bed din ta cikin wani makeken bedrom,bacci take cikin kwanciyar hankali babu wata damuwa a tattare da ita, k’arar da wayar ta k’irar Samsung take ne yatashe daga baccin da take, a yat’sine ta yafito wayar tana kallon screen d’in, ganin sunan aminyar ta ne yasa ta d’auka tare da fad’in      “Saliha ina fatan komai lafiya?.” daga can bangaren Hajiya ce ta amsa da fad’in     “Ba lafiya ba aminiyata, Ummi ce ba lafiya ko numfashi batayi, yanzu munzo asibiti kuma babu wasu manyan likitoci, shine nace ko zakiyi wa Affan magana mu kaita asibitin shi?.”    Hajiya ta k’are maganar da alamar tambaya “Ya salam! me zai hana maza ku huce da ita bari na sameshi, kafin ku isa zai k’araso.”      “Toh shikenan ngde.”  Hajiya tafad’a tare da kashe wayar, ita kam Hajiya Saliha mik’ewa tayi ta nufi part d’in Affan.   Tafiya tai mai d’an tsaho kaman ba a cikin gida d’aya suke ba,har ta k’arasa ma daidaicin part d’in da shima ya k’ayatu da kayan alatu, kai tsaye bedroom d’in shi ta nufa tare da sa key ta murza k’ofar.     Kwance yake d’ai d’ai kan makeken gadon shi yana bacci shima cikin nashi kwanciyar hankalin    Affan! Affan!!.” tafad’a tare da dukan katifar dake kwance     “i’m awake!.” yafad’a yana d’aga hannu     “Tashi maza ka huce asibiti ankawo maka patient.”   A d’an zabure ya tashi tare da fad’in  “Ya salam! Mom waye ba lafiya?.”      “Ummi yarinyar da zaka aura.” d’an turbune fuska yayi sanan yace     “Kamar yarinyar da zan aura, wallahi zaki ja nafasa fita.”    “Fasa fita d’in tun da kaine ka haifi kanka, maza tashi kaje yarinya na b’ukatar emergency check up kana nan kana shirme.”   Tashi yayi yashiga toilet, a gaggauce ya shirya k’asa da minti 15 yafice ko breakfast bai tsaya ba domin ba ma’abocin cin abinci mai nauyi bane ko da huri      Zuwan shi asibitin yayi dai dai da zuwan su Hajiya,lokacin ana k’ok’arin saka Ummi a kan gadon da ake tura marasa lafiya, k’arasawa yayi tare da kama gadon akaja shi dashi, kai tsaye theater room aka nufa da ita inda Affan ya k’ure duk wani iya aikin shi wajen ganin ya ceto numfashin Ummi da yatafi gaba d’aya! amma shiru     page[19&20]   Sama da awa uku Affan da wasu k’arin likito ci suka d’auka akan Ummi, sunyi iya yin su Amma abun kamar baya yake, numfashin ta ko kad’an baya fita banda zuciyar ta dake bugawa in a slow motion da tabbas zasuce Ummi ba ta da rai          Hankalin kowa ya tashi mussaman da suka ga likitoci sun dad’e kan Ummi amma babu wani kyakyawan saka mako, lokacin Anty nafisa da su Goggo da sauran yan Uwa duk sun k’araso, Hajiya tafita hayyacin ta domin gani take kamar itace ma takashe Ummi ko saka ta a halin da take ciki,sauran mutane kam sunyi jigun jigun domin babu wanda yasan mak’asu din rashin lafiyar idan ka cire Asiya.    Asiya kam a yanzu bata iya bud’e baki, domin iya kukan da tayi anan wajen yasa mata mat’sanan cin ciwon kai wanda har yakai bata iya ko motsi da kan.     Umar kam bayan ya samu musu mai mota ya koma gida yayi wanka,shine yatawo da asiya a machine dinshi bayan ya biya ta gidan Anty Nafisa ya sanar da ita ***     Badoo bai b’oye komai ba yasanar daRogeet halin da yaje ya sami Ummi,sosai Rogeet yake mamaki duk da yasan bazai huce mahaifan Ummi sun hana Master bane, shine dalilin da yasa suka kasance cikim wanan halin gaba d’aya     “Yanzu Rooget menene abun yi?.” Badoo yafad’a domin yanda yake ganin Master kwance yasan dole sai ya buk’aci ganin likita     “Kaga Badoo tun d’azu nake ta trying lambar Dr Affan amma baya d’auka, inaso nasanar dashi ko shi zaizo gida ya duba shi ko nan asibitin zamu kawo shi.”     “To yanzu ka k’ara gwada lambar idan batayi ba kawai ku d’auke shi dan gani nake wanan kamar ba bacci yakeyi ba.”   k’ara gwada lambar yayi amma still bai d’auka ba     “Tashi mu tafi asbitin kawai.” Rogeet yafad’a yana mik’ewa isar su  asibitin yayi dai dai fitowar su Dr Affan, daga d’akin da Ummi take ciki      Dr Affan ne yace da Abba “Yanzu Alhamdulillah insha allahu zuwa anjima zamu k’ara komawa,kawai ku cigaba da Addu’a.”    Shiru Abba yayi da duk kansu ma gaba d’aya kowa jikin shi ya mutu     Wucewa Dr Affan yayi zuwa office d’in shi, sai dai bai k’arasa shiga cikin office d’in ba aka shigo da Mukhtar shima kwance kan gado ana faman turashi, Rogeet ne ya k’araso inda Dr Affan ya tare da fad’in      “Dr ina ta kiran ka baka samun damar d’agawa ba, Master ne gashinan kwance rai a hanun Allah.”     Kallon gadon Dr Affan yayi sanan yace “Meyasa meshi haka?.”    “Wallahi bamu da masaniya.” Bin gadon Dr Affan yayi zuwa d’akin dake kusa da na Ummi, basu sha wahala ba akan Mukhtar kamar Ummi ba,sabida shi ciwon shi mai sauk’ine. ***    Sai bayan Azahar Affan ya samu nutsuwa bayan ya koma gida yaci abinci ya sake wanka, Rogeet yakira zuwa office d’in shi    “Isa mene ya same Mukhtar?.” “Wallahi Dr bana ce ba amma dai nasan Master yatafi gaida sirikan shi ne.”    Kallon shi Dr Affan yayi sanan yace “Wane sirikai kuma?.”    Nan Rooget ya hau bashi labarin tun daga soyayyar Mukhtar da Ummi har zuwa kiran da tayi masa akan iyayen ta nason ganinshi gar zuwan da yayi da kuma daowar da yayi sanan ya gaya masa abinda Badoo ya gano da safe gidan su Ummi     “Ummi kace?.” Dr Affan ya tambaye shi d’aga kai yayi alamar Eyh     “Shikenan tashi kaje idan yatashe sai kusan yanda zaku kula dashi.”    Tashi Rogeet yayi yafice shikam Dr Affan tunani yafara tun daga haduwar su da su Master irin taimakon da Master yayi masa lokacin da wani abokin fad’an shi na makaranta yasa akashe shi,Allah yakawo masa su Master suka kwace shi, tunda ga wanan lokaci yake taimakon master ta ko ina har zuwa san da yafara aiki.          Zuwa yamma Master ya samu ya farfad’o, amma b’angaren Ummi kam abun ba’a magana, gaba d’aya mutane sun fara fitar da rai da Ummi har dasu likitocin ma, babban dalili bugun zuciyar ta ma k’asa yake k’arawa lokaci zuwa lokaci, wanda shine kad’ai abinda ya ke nuna cewa Ummi na da rai.      ***    Washe gari A yanzu kam za’ace jikin Master yayi sauk’i domin har abinci yana iya ci sai dai gaba d’aya tun da ya tashi babu zancen da yake sai na     “Ummi na tuba,Ummi zancanja hali.”  Dr Affan ne yasashi a gaba ya tambayeshi wace Ummi,wand tuba yayi.     Master bai b’oye masa komai ba yagaya masa tun daga soyayyar shi da Ummi har abinda yafaru last     Dr Affan tun a lokacin yagane Ummi itace patient dinsa domin sai da yak’ara tambayar Mahaifiyar shi bayanai akan Ummi.     Hajiya Balki kam ba shiri ta bud’e baki tafara zayyana mai domin ita a tunanin ta yafara tausayin yarinyar ne.       Domin alak’warin dasu kayiwa juna ita da Saliha na auren yaransu, amma gaba d’aya yaran suna neman karya musu alk’wari.       Dr Affan yaji dadin yadda Master yafara tunanin canja hali, sanan a ranshi yad’auki alk’warin indai Ummi ce Master sai ya aure ta        B’angaren Ummi kam haka za’ace gwanda jiya akan yau,domin gaba daya jikin nata k’ara saki yake.     ***     “Oh ni! kai cona kai con rayuwa ta, nasa jika ta a masifa sabida son duniya.”     Goggo dake zaune cikin taron mutanen dake cinjiyar Ummi take fad’a     Babu wanda ya kulata domin gaba d’aya a yanzu kowa yayi sanyi ba mai iya magana.     Jin shirun da sukayi yasa Goggo dagowa ta kallesu Hajiya ta had’a uban tagumi, Anty Nafisa na zaune ta had’e kai da gwiwa, Mama na zaune tana jan carbi, Asiya na zaune tasa kanta a jikin Mama.     Bud’e baki tayi da niyar yin magana,mai kawo abinci daga gidan Hajiya Balki yayi sallama tare da k’araso wa wajen.       “Sannu d’an nan da k’ok’ari baka gajiya da wanan hidima ta kawowa ita ma Hajiyar bata gajiya,kullum sai ankawo sau uku to allah yayi albarka.”    tafad’a a jere kamar mai wak’a     “Amin.”   yafad’a mata a dak’ile sanan ya kalli sauran yace    “ya mai jikin?.” “Da sauk’i Musa.” Mama tafad’a domin a zuw yanzu kowa yasan sunan shi sabida yawan kawowa da yake     “Allah yak’ara Afuwa.” yafad’a tare da hucewa bai ko kalli goggo ba       Page(21&22)    Da daddare Dr Affan ya salmi Master sanan ya bashi shawarwari akan yadda zai gyara rayuwar shi da yan kud’ad’e.    Haka suka koma gida, Master yakasa hakuri zaije ganin Ummi ko da gobe ne.   Daga d’akin su Master kai tsaye d’akin Ummi yahuce domin duba ta.     Sai dai yanda yaganta ya d’aga mai hankali domin gaba d’aya bugun zuciyar tata ya tsaya, babu wani abu dake nuni Ummi na da rai.   A gigice yake duba duk wani abu da ya kamata amma ina abu yaki gaba yaki baya,   “Tabbas Ummi ta mutu.”    yafad’a afili amma ta ina zaifara sanar da iyayenta, waya da dauka ya kira Mahaifiyar sa yasanar da ita sanan yakara da cewa    “Mom i’m scared, bansan ta inda zanfara fad’awa iyayen ta da yan uwan ta ba.”    cikin kulawa da tausayawa tace “My son claim down kaji, kasa nurse takira maka Maman Asiya ko Nafisa insha allah zasu san yadda zasuyi, nima i’m on my way.”    “okay mom.” yana tsaye wata nurse tazo hucewa yasata ta kira mai ko maman asiya ko anty nafisa.     Duka su biyun su ka zo cikin yan mintina Mama na gani Ummi jikin ta yabata ita kam Anty Nafisa cewa tayi.    “likita gamu ta warke ko?.” yanayin rud’ewar ta kawai yagani yasashi cewa.    “Ban dake fa Maman Asiya kawai akan rashin lafiyar Asiya ne.”    “To ai nima rashin lafiyar Asiyan ta tab’ani, baka ganin tare muke da mahaifiyar tata tun zuwan mu.”     Anty Nafisa tafad’a,kallon Mama yayi sanan yayi mata alamu da ido akan ta kori Anty Nafisa.    “Kinga Nafisa jeki, barni nayi magana dashi.”   tashi Anty nafisa tayi tafice, kallon Mama Dr Affan yayi sanan yace    “Mama ga Ummi nan babu rai.” A razane ta kalleshi     “Me hakan ke nupi?.” “Mama nasan ke zaki fi fahimta yasa na kiraki, Ummi sai dai ayi hakuri.”    “Innullahi wa inna illahir rajiun.” Mama tafad’a tare da samun waje ta zauna.     A hankali take takowa,kana ganin yanda take tafiya kasan tana cikin wani hali ko wata damuwa, a haka ta k’araso inda suke zaune.         Anty Nafisa da tadawo ta daga masu hankali ce tace       “Ku ga yanda take tafiya! kuga! Wallahi Hajiya wani abu yafaru.”          “Nafisa dan Allah ki nutsu ki bari ta k’araso mana.” Wata k’awar Hajiya tafad’a, kallon ta Goggo tayi sanan tace       “Ke Tsibatu banason shishigi! wace nutsuwa zatayi yar uwarta na kwance asibiti.”    Daman Goggo haushin natar take ji tunda tazo ta k’i tabarta ta d’ibi abuncin da takawo wanda yaji uban nama         “Sahura lafiya dai ko?.” Hajiya tafad’a domin tabbas yanda taga Maman ya matuk’ar tsorata, Mama ba takai ga bud’e baki ba suka jiyo muryar Hajiya Balki wacce Affan ganin kamar Mama ma tashiga tashin hankali yasa shi k’ara kiran Mahaifiyar tasa, inda tace masa tana dab da shigowa asibitin domin tabbas tasan halin da Sahura xata shiga idan tasamu labarin cewa Ummi ta mutu.      K’arasowa inda suke tayi tare da cewa “Sahura samu waje ki zauna, ko me za’a fad’amiki ai ba zai kamata a fad’a miki kina zaune.”             “Dan allah Balki mene ne? Sahura mene yafaru dan Allah?.”     Hajiya tafad’a tana kallon su duka, Hajiya Balki ce taje ta rik’e ta tana cewa    “Saliha dan allah ki zauna ki nutsu, ko ma menene ai zakiji ko.” ihun da Anty Nafisa ta saki tare da zubewa k’asa ne ya dawo da hankalin su kanta,dai dai lokacin da Asiya ma ta zube tare da fashewa da ihu.    Wai ashe aljanin su ne suka zo yi musu jaje “Innullahi innullahi, subhanallahi subhanallahi, auzubillahi auzubillahi.”     Goggo tafad’a tana mik’ewa tsaye  “Wallahi yarinyar nan mutuwa tayi tunda kika ga wanan yaran sun zube kamar rak’umai, bana manta sanda babban mutum ya mutu wanan yarinyar ita tafara wanan ihun.” tafad’a tana nuna Anty Nafisa       Nanfa asibiti ya rud’e da koke koke har wasu ma mak’waftan su su ka taya su zubewa kun san aljanu da kara😂🤭     Dai dai lokacin dasu abba suka samu k’arasowa cikin asibitin, zuwan su Abban ne yayi k’ok’ari wajen saita su har aka samu aka fara tafiya dasu gida kafin sukayi cike cike a tafi da gawar Ummi.      Bayan sallah magriba kafin isha’i wanan abu duk yafaru, kafin lokaci k’ank’ani labarin mutuwar Ummi ya karad’e unguwa gaba ki d’aya, sanan Anty tashiga gida gida tana bada ba’asi wai.     “yarinyar ce takeson wani gagurumin d’an daba shine Hajiya tayi mata duka har ta mutu.”    Kasancewar itama bata da tabbaci domin jita jita taji, amma mutum mai sharri, sai da tabi kowa tana fad’amasa.    A dai dai wanan lokacin labarin Mutuwar Ummi ya riske su Master,    Innullahi wainna illahir rajiun, wata mummunar faduwa daMaster   yayi zuwa k’asa, sai kayi tunanin kwakwalwar sa ta bugu,a sume ya k’arasa k’asa.      Hakan wanan dare ya kasance daren kuka ga kowanne b’angare gidan su Ummi da b’angaren su Master.    Washe gari akayi haka kowa ya tashi duk da basu samu bacci ba, sunyi kukan har sun gaji, ko magana basa iyawa har zuwa lokacin da akayiwa gawa wanka ka aka ajiye ta.    WANAN SHINE ABINDA YA FARU Page[23&24]    “To ai yanzu sabarni na aure wanda nakeso ko?.”   Ummi tafad’a tana kallom Asiya bayan ta gama bata wanan labarin.    “Ummi ba wai ba’ason ki auri Master bane dan ba’a sanki, idan ta soyayya ce za’a barki ki aure shi Amma Ummi ko tarbiyar yaranki a halinki.”   Anty Nafisa da tashigo yanzu ta fad’a,  Ummi bata ma kalli Anty Nafisa ba balle ta kula da Mutanen dake bayanta, ta bud’e baki tace    “Daga sanda na Aure shi ya zama a halina,     rayuwa ta, abunda ya shafe ni ba ku ba.” jikake taff! Hajiya ta k’wad’e Ummi da mari cikin fushi tace.    “Yanzu Ummi akan soyayya, akan saurayi kika zab’i kigayawa iyayen ki magana,  kigayawa yar uwar ki kwaya d’aya da allah yabaki Ummi kinja tunani.”    Hajiya tafad’a cikin kuka. Anty Nafisa kam tasowa tayi zuwa wajen Hajiya ta rungume ta tare da fad’in.       “Kiyi hakuri yajiya, yarinta ce ke damun ta.” “Ba wata yarinta da ke damuna, nasan abinda nake, ku ya kyaleni da rayuwa ta tunda ta wace, banason shishigi ban shiga rayuwar mutum ba kar yashiga tawa.”     “Wai Ummi mene ke damunki haka ne baki da hankali.”   Asoya tafad’a cikim fushi da fusata “Dalla malama fita daga sabgata kema banason shishigi rayuwar ku ce?.”    Ummi ta katse Asiya cikin nuna matuk’ar fushi da jin haushi.   “ Ba rayuwar mu bace amma Ummi muna da hakk’in fad’a miki gaskiya a kowanne lokaci.”   “Rik’e gaskiyyar ki Asiya, kifita daga rayuwa ta kibarni.”        Shiru Asiya tayi sanan daga baya ta mik’e zata fice.   “Tabbas ko bakiyi nadamar fad’amana bakak’en maganganu ba a matsayin mu na iyayenki, zakiyi nadamar fad’awa Asiya a matsayin ta na aminiyar da tazama yar uwa a gareki.”    Hajiya tafad’awa Ummi lokacin da Asiya ke ficewa, Duk irin b’acin rai da damuwa da Ummi ke ciki tabbas taji na dad’i kan abinda tayiwa Asiya.  Asiya kam nafita gidan su tayi kai tsaye tafad’a d’akin ta ta kwanta tare da fashewa da kuka.  Haka Hajiya ta fice Anty Nafisa ma ta fice, Abba dake tsaye jikin d’aki duk jikin shi ya mutu.  Goggo ce ta kalli Ummi ta tab’e baki sanan tace.   “Ke kam wanan yarinya kingama asara duniya da lahira.”      “Mitcheww.”Ummii taja dogo  tsaki “Tsaka ma tayi ta gama.” Goggo tafad’a tana ficewa. Haka wanan gida gaba d’aya suka kwana cikjn b’acin rai da damuwa , mai makon su kasance cikin farin ciki.   Washe gari tun safe Asiya ta gama had’e kayanta tsaff, zatahe kaduna gidan k’an war Mama kafin lokacin fara jarabawar su ta Waec.    “Wai yanzu Asiya bazaki je kiyi sallama da matar nan ba? itace tayi miki abu?.”   “Wallahi Mama banson k’ara shiga gidan a rayuwa ta.” Asiya tabawa Mama amsa bayan ta takura kam taje tayi sallama dasu Hajiya.  “Kinga Asiya tashi kije kiyi Sallama dasu kafin ranki ya b’aci.” “HHaha daman duk wanda ya hau motar k’wad’ayi, karshe a tashar hulankaci zai sauka.”  Anty dake cikin d’aki tafad’a “Yoo daman anty ai k’arahen alewa k’asa.” Halima tafad’a itama daga cikin d’akin “Karshen bariki kuma da nasani.” Asiya dake zaune tabasu amsa, ai kamar kububuwa Halima tafito daga d’akin tayo kan asiya tana fad’in. “Ke wallahi tallahi idan kina cin k’asa ki kiyayi ta shuri, ni ba sa’ar ki bace yanzu zan sa a b’ab’alla mun ke.” Mama bata ko kallesu ba, domin tasan a tanzu Halima ba fad’awa Asiya magana zatayi tai mata shiru ba dole sai ta dama, dukane kuma wanan ba ta isa ba tunda dai ita tashiga sabgar ta.   “Aou Ashe badad’i kenan?.” Asiya tafad’a cikin sigar rashin kunya,  “To k’arya akayi miki da zaki ce ashe ba dad’i.” Anty dake fitowa daga cikin d’aki tafad’a cikin hargowa.   “To nima k’arya nayi?! ba k’arshen bariki da nasani bane.” “Ya isa Asiya tashi kifice.” Mama ta dakatar da ita  Tashi Asiya tayi tafice tana gunguni a ranta tana sanye cikin doguwar rigar lace tayafa k’aramin blue d’in mayafi. “ Atine nasha fad’a miki kifita sabgar yarinyar nan kunk’i ko to zanyi maganin ku.” “Kiyi maganin namu gida ne ko, insha allahu mun kusa tashi mubarmuki tsiyar ki.” Anth tafad’a tana jan hanun Halima suka shige. “Halima ki takura wa wana mutumin yabaki gidan nam mu koma ko masa mu mu huta da gori.” Anty tafad’awa Asiya cikin k’asa kasa da murya. “Ai Anty yau ko gobe.”   A soro Asiya  ta cika karo da Yaya Umar, Kallonta yayi sanan yace.   “Yanzu Auta kin dage yau zaki tafi, baza kijira gobe muyi sallama ba?.”      “Yaya ai yanzu ma munyi sallama, sanan kai zaka kaini har tasha.”  “Asiya chaina fa zantafi, ba tafiyar kasuwanci ba tafiyar karatu, a k’alla sai nayi shekara hud’u zuwa biyar, lokacin fa duk kunyi aure da yaran ku.”   Dariya tayi sanan tace   “ Gaskiyya dai yaya, amma bari naje nayi sallama dasu Hajiya nadawo.”  Da haka tafice, tafi minti biyar a soron sanan tayi sallama a hankali, Ummi dake kwance cikin d’aki ce ta tashi zaune, tabbas ko a iya jiya tasan tayi kewar Asiya, jiran shigowar Asiyan take sai da tajiyo muryata suna magana da Hajiya.   “Hajiya ina kwana?.”    “Lafiya k’lau Asiya mun kwana lafiya?.” “Alhamdulillah Hajiya, daman sallama nazo yimuku zan tafi kaduna gidan, Anty Larai.” Durum Dum Dum! Ummi taji gaban ta yafad’i, Anty Nafisa da tafito daga d’akin ta ke zaune kasancewar har yanzu bata tafi gida ba ce tace.   “A’ah Asiya me yayi zafi haka?.” “Bakomai Anty kawai ina son samun canjin waje ne da wasu abubuwan.”   “Hakane Asiya amma ai da ko gida na kin bini amma Kaduna yayi nisa.” Dariya kawai Asiyan tayi sanan tace. “Baba faa?.”   Hajiya ce ta amsa mata da cewa. “Yana waje amma k’ila ku had’u.” Tashi tayi tsaye tare da cewa. “Tom Hajiya, Anty nahuce, sai nadawo.” “Allah yatsare hanya Asiya.” Anty nafisa tafad’a itakam Hajiya cewa tayi. “Allah yayi miki albarka Asiya.”  Da amim ta amsa tafice, A zaure ta ci karo da Abba nan ma suka gaisa tayi masa sallama. Hajiya ce tace da Anty Nafisa “Wallahi ko a haka Ummi tayi rashin Mutanen arzik’i.”     “Bari hajiya abun har ba’a magana wallahi.” Daga cikin d’aki kam Shiru Ummi tayi tabbas bata kyautawa Asiya ba, ko kuma bata kyautawa kanta ba.    Dai Dai sanda yaya Umar ya saka ta a motar da zata kaita kaduna, idanun ta suka sauka akan master dake zaune cikin mota, idonshi a rufe kaman mai bacci.   Tsaki taja ta kauda kanta gefe daga kallon, shi har zuwa sanda motar su ta tashi zuwa kd. A yammacin wanan ranar Anty Nafisa ta tarkace ko motsan ta, tare da yaranta suka koma gida, bayan sun gama damben tsiya da Ummi, domin yau Ummi kokawa ta kama ta da ita.   A yanzu gida ya watse daga Ummi sai Hajiya sai Baba, Goggo ma tace bazata zauna Ummi takashe ta da b’acin rai ba. Page[25&26] Haka rayuwa taita juya Ummi takasa farin ciki, iyayen ta kullim cikin fushi suke da ita, itama fushi take dasu.      Ta d’auki soyayya ta d’ora a ranta a kullum zancen Master na cewa.   “Tayi masa alk’warin bazata guje shi ba a ko wanne irin yanayi.”  Shine abunda ke yawo a ranta, sanna tayi imamin cewa Master na can na jiran ranar da zata samu musu yanchi shi da ita. Abin da yadamu Baba sosai, Shine yanda Ummi ta watsar da komai na rayuwar gidan, abinci ne idan an bata taci idan ba’a bata ba ta hakura.    Sabida Hajiya  wani lokacin idan takaici ya isheta, na yanda tazab’i soyayya akan iyayen ta sai ta hana ga abinchi, ita kuma haka zata zauna sai dai idan baban ya zo duba ya tambye ta taci bataci ba.   Gaba d’aya ya shiga damuwa mai girma akan Ummi, yau ya yanke shawarar zai nemi Nafisa suyi shawara. B’angaren gidan Mama kam, su Anty sun tashe, saurayin Halima ya basu makeken gida.   Sai dai a gidan b’angaren Anty daban na Halima daban shima Nashi daban.   Na Anty na daga gefe sai kuma nasu ajire, Rayuwa suke shida Halima kamar mata da miji, itakam Antu duniya sabuwa.   K’awaye sai zuwa suke tana ce musu ai Hlima ce tayi aure, basu da wata damuwa. Yaya Umar kam yatafi Chaina karatu, Zuciyarshi d’auke da sirrin da yayi alk’warin zai rik’e bazai tab’a bayyanashi ba domin yasan bashi da wani amfani. Mama kam duk irin ba dad’in da suke da Any sai da taji gidan ya mata bad dad’i mussaman da ba Asiya ba Umar hakan yasa tace lalle Asiya tadawo.   Wacce tana can kaduna tasamu nutsuwa amma kuma kullum tunanin ta na kan Ummi da Master. Ummi dai tayi b’aki ta rame tafi ta hayyacin ta, tadawo abun tausayi gaba d’aya, abinda yake k’ara tsorata Abba kar ta mutu tabarsu da hakk’i.    “Yanzu Abba wacce shawara kake so?.” Anty Nafisa dake zaune kusa da Abba a cikin falom gidan ta ta tambayeshi. “Nafisa ko Matata da Mahaifiya ta, banne mi shawarar nan a wajen su ba saiki.    Kina ganin yanda yarinyar nan tafita hayyacin ta gaba d’aya ta canja.” “Hakane Abba ni kaima da naje gida shekaran jiya sai da naji ba dad’i.” “To yanzu me kike ganin ya dace?.” “Abba ina ganin kasa ta ta k’arawo yaron kace mai zaka bashi ita amma da sharad’u ka wayanda nasan bazaka rasa su ba, nasan kuma zai amince tunda nima sai da na tambayi Asiya kan yanda yake sonta, kuma ta tabbatar mun zai iya canjawa akanta.”   “Shikemam Nafisa Allah yasa mudace.” “Amin Abba.” ****    Zaune suke gaba d’ayan su a tsakar gidan, Abba, Hajiya,Ummi, Anty Nafisa da kuma Goggo.   Abba ne yafara magana kamar haka. “A iya nazari da shawara da nayi, Ummi.”  yakira sunan ta, d’agowa tayi ta kalleshi, sanan ya d’ora da fad’in.   “Zanbaki dama a karo na biyu, ki k’ara kawomin shi yaron da kika kawo a wancan karon.”    “Abba!! da gaske.” Ummi tafad’a a zabure, da mamaki kowa yake kallon dariyar da suka dade basu gani ba a tare da ita.       “Dakata Ummi kiji, akwai sharad’in da zan sama sa idan har ya amince dasu to zan bashi Auren ki.”    “Abba wallahi zai amince! zai amince wallahi.”    “Amma kana ganin hakan yayi?.” Hajiya tafad’a tana kallom Abba, bai kai gaba ta amsa ba Goggo ta tare da cewa.   “Sahura baki da imani ne? kina tuna lokacin dakika ga dariya ta k’arshe a fuskar Ummi? shine kuma zakice hakan yayi?.”   Shiru Hajiya tayi duk da dai a ranta bataso Hakan ta faru ba kwata kwata.   Tashi Ummi tayi tai cikim d’aki tana fad’in “Ina masu cewa nayi TUDU AKAN KWARI? ina masu cewa TUDU AKAN KWARI wahala zansha bazai tsallaku ba zandawo?, to yau gashi ni Amina nayi TUDU AKAN KWARI kuma na tsallake kayana.”    Dariya Anty Nafisa tayi sanan tace Allah yasa ya tsallaku.    Haka kowa ya tashi babu komai a ranshi sai Hajiya da har yanzu batayi naam da wanan abu ba a ranta, domin ta tabbatar wa da ranta Ummi taso ta tozarta tane kuma mahaifin ta ya biye mata.    D’aki Ummi ta shiga ta marasa me zatayi a rayuwar ta kuka ko farin ciki, dogon jiran da tayi yau ya tabbata abba yace yar da zai bawa Master Auren ta ta ina zata fara?.    Tashi tayi tafi ta wajen Anty Nafisa ta karb’o aran wayar ta. ta loda number Master da ke kanta tashiga dialing…        “Dear customer the MTN number you try to call is kindly switched off, please try again later.din..din…dinn.”    Abinda Ummi taji kenan, tsaki taja sai ta juya kiran zuwa ga number Asiya.    Asiya dake kwance gaba d’aya tunanin gida ya sata a gaba mussaman da Mama tace lalle tadaow gida domin tagaji da gidan ita kad’ai.   k’arar wayarta ne yadawo da ita daga tunanin da take       Ganin sunan Anty Nafisa, ya sata d’auka da fad’in.   “Hello Aunty ina yini?.” “Lafiya klau.” Ummi ta amsa tana dariya, jin maganar Ummi yabawa Asiya mamaki, sai dai ba ta nuna ba.   “Lafiya dai ko?.” Asiya tafad’a a gajarce “Lafiyar ce takawo hakan ai.” “To ya akayi?.” Asiya ta k’ara fad’a “Dalla malama wai ni kikewa haka?.” “Nayi Ummi ke d’in uwata ce ko ubana? ko ya yata ko wane dayake da alak’a dani?.”      Shiru Ummi tayi tasan ko menene itace bata kyautawa Asiya ba, domin tabbas tasan asiya na da mugun hakuri akan rayuwa.   “Kiyi hak’uri Asiya dan allah, Wallahi duk abinda mafad’a ba’asan raina bane.”   Shiru Asiya tayi kafin daga baya tace.   “Shikenan Ummi ya huce yanzu ya akayi?.” “Asiya Abba ya amince na k’ara kawo Master a karo na biyu, sai dai yace akwai sharad’in da zai sa mai.”   “To Alhamdulillah nasan indai akanki ne Master ba sharad’in da bazai d’auka ba.”  Asiya tafad’a cikin tsantsar farin ciki sanan ta d’ora da cewa.   “Ummi nima fa nasamu miji a kaduna.” Dariya Ummi tayi mai sauti sanan tace “Aiyiriyiri Asee beb anyi kasuwa bani labari.”   “Gobe zan dawo ai mayi magana.”  “Toh shikenan Asiya amma kinsa mene matsalal?.”   “A’ah.” Asiya ta amsa. “Tun fa da abin nan yafaru bansamu kira ko saqo da ga master ba, hakan bai dameni ba dan nasan zata iya kasancewa dama ce bai samu ba, amma dana kirashi yanzu naji Switched off sai naji hankali na ya tashi.”       Shiru Asiya tayi tana son tuna wani abu da yashafi Master “ko kad’an baki samu sak’o daga wajen shi ba.”   Ummi tafad’a a ranta kama tana fad’in. “Innullahi wainna illahir rajiun.” domin kuwa sai yanzu ta tuna tabbas taga jaka a hannunshi lokacin da ta ganshi a tasha…..   Meyake faruwa ne?   Page[27&28]     “Ummi kijira ni gobe idan nadawo mafita muje, sabida kinga  a yanzu ba lallai Hajiya tabarki fita.”     Asiya tafad’a a fili amma zuciya tana tunanin anya Master bai hakura da Ummi ba.   Shiru Ummi tayi tanajin wani iri a zuciyar ta har Asiya ta kashe wayar,     “Yanzu ace Master baya lafiya ya zatayi da ranta?.”   Tambayar da Ummi ke nanatawa kanta kenan, gaba d’aya yinin ranar.     Nauyi sosai take jin zuciyarta tayi mata, sanan koma ko menene yasamu Master tabbas alhakin nakan Abba da Hajiya ne. Har dare Ummi na nan Zaune waje d’aya sallah kad’ai ke ta da ita sai cin abinci, shima sau d’aya taci.    Sallamar Hajiya Balki ta jiyo a gidan nasu, ai kuwa tuni Ummi ta had’e rai.   “Mitcheww.” sautin tsakin da yafiti daga bakin Ummi kenan.   Mik’ewa tayi tare da barin wajen.  Zama Hajiya Balki tayi tare da kallon Hajiya.  “K’awata ina fatan komai lafiya dai ko?.”  “Ina lafiya k’awata.”       Hajiya tabawa Hajiya Balki amsa. “To menene yafaru?.” “Yau naga k’arshena a gidan nan, naga iya kata Bilki.” “Wane irin karshe wai Saliha?.” Hajiya Balki ta tambaya domin takasa gane inda zancen Hajiya ya nufa. “Hhhmmm.”  Hajiya ta sauke ajiyar zuciya sanan ta d’ora da fad’in. “Yau Uban yarinyar nan da kakarta ke harda Nafisa suka had’e mun kai, su ka nuna Ummi ta zab’i wanda take so, a tak’aice yasake bawa wanan yaran dama a karo na biyu.” “chab lallai Saliha kuma kike zaune haka?.” Hajiya Balki tayi wanan tambayar “Uhm Balki idan ban zauna ba me zanyi, tashi zanyi nafita ina kuka ko me?.” “Saurareni k’awata! kuka ai banaki bane nuna isa zakiyi, ki nuna ke macece, ba kya had’e kayanki ki bad musu gidan?.” Da kallo Hajiya tabi k’awarta Balki, sanan tace     “YAJIIII?.” “Hhhm abinda banyi ba azamanin k’urciya sai yanzu zanyi a girma na?.” “Tsaya Hhhhm Saliha! tsaya Hhhm! a nuna miki rashin isa, bakya iya yimusu baraza na?.”    “Shikenan Balki zan san yanda zanyi nadau mataki., amma dai masan wnn yaron ko duniya zata tashi bazai aurar mun yarinya ba.” ***   Washe gari “Wai Ummi wanan kiran na lafiya ne?.” Asiya dake cikin mota ta fad’a  “Bansani ba Asiya wanan wace irin tafiya ce kukeyi kaman baya ku ke komawa?.” “Hahaha Lallai Ummi! kinsan wanan shine kira na 48 da kikayimun tundaga tasowar mu, kawai dan nazo muje mu nemi Master.” “Yaya Mukhtar dai ko?.” Ummi ta katseta da sigar tambaya “Kuma waye dai gamu mun tsaya, napep kawai nake nema ya.” “Allah sarki Yaya Umar.” cewar Ummi Asiya kuma ta k’ara da cewa “Wallahi fa da yanan duk tafiya da dawowa shine.”  Mai napep ne yatsaya gaban Asiya ya fara daukan kayanta yasa a mota, suka nufo gida.    Duk naci irin ma Ummi saida tajira la’asar sanan suka fita neman Master ita da Asiya.    Kai tsaye gidan su ka nufa duk da basu san gidan ba sai da tambaye tambaye.  Gark’ame k’ofar take da mukulli, Kallon Asiya Ummi tayi, wacce itama kallon ta takeyi.   “Asiya me hakan ke nufi?.” “Wallahi Ummi bana ce ba amma bari mu tambayi mak’waftan su.”  gaba sukayi inda suka same wani mai kanti, Asiya ce tafara masa magana.  “Dan Allah bawan Allah tambaya muke.”  Matshin mai cikar kamala ne yakalle sanan yace.   “To baiwar Allah, Allah yasa na sani.”  “Dan Allah malam wancan gidan ina mutanen ciki suke?.”   Tafad’a tana nuna masa gidan, k’ara kallon gjdan yayi sanan ya kalleta tsaf.  “Yarinya kinyi kalal mutunci da tarbiya mene ya had’aki da wancan gidan.”  Da sauri Ummi ta katse shi da cewa.    “Eyh Malam d’an uwan mune yab’ace shekara da shekaru muna neman shi, sai yanzu aka sanar damu yana nan.”  “To wanan gidan dai da, da mutane amma yanzu sun kwashe kayansu wajen sati biyu ba sa gidan, da magajiya mai k’arfi ma sun saida gidan sun shiga duniya.” “Innullahi wainna illahir rajiun.” Asiya da Ummi suka furta lokaci guda. *CIGABAN PART (1)* Page[29&30]  “Asiya yanzu mene abunyi dan Allah ina zanfara neman Master, nasan dole ba nisa yayi ba.”   Ummi tafad’a cikin kuka, da tausayawa Asiya tace. “Tabbas nasan Master bazai yi nisa ba, sabida yasan dole zaki tsaya tsayin daka akan soyayyarku.”   “Amma ina yaje haka? har da saida gida.” “Ummi k’ara dubawa fa zamuyi, tunda kince Abba kwana biyu ya baki, ki kawo Master.”  “Ni Wallahi Asiya ina cikin Mummunar damuwa, nayi TUDU AKAN KWARI sai lokacin da nake tunanin na tsallake shi, sulb’i zai dawo dani baya” “Ba haka bane Ummi insha Allahu zai tsallaku yanda kike tunani.” “Yawwa Yara wancan yana d’aya daga cikin mutanen dasuka Zauna a cikin gidan.”  Maitashin nan mai cikar kamala yafad’a yana nuna musu hanyar da mutumin yabi.  Da sauri Ummi da Asiya suka bi matashin suna fad’in bawan Allah. Tsayawa yayi tare da jiyowa, duk kansu sun ganeshi Badoo ne, shima ganin su yasa shi tsayawa har suka k’araso.  “A’ah Anty Ummi kece?.” “Eyh Wallahi nice dan Allah Master fa?.” Ummi tafad’a tana kallon shi dan ita bazama ta iya tuna sunan shi ba. Kallon hanyar gidan nasu yayi sanan yace. “Ni kaina a yanzu bana ce ga inda Master yake ba, balle kuka Rogeet, abinda dai nasani shine, bayan ansamu labarin cewa baki mutu ba Master yadawo gida cikin damuwa, daman kuma tun lokacin da Mahaifin ki ya hanshi ke, yayi nadama akan abinda yake, Asibit d’aya kuka kwanta k’ark’ashen kulawar likita Affan, yadawo gida da kwana d’aya yasamu labarin kin mutu, yayi kuka iyakacin kuka, har ya shirya tafiya zuwa wani waje can daban cikin garuruwan kudu, labarin baki mutu ba baisa ya canja ra’ayin shi ba, an sai da gida yatafi kudu, Rogeet ya koma gida sama da sati guda kenan ko biyu, a tak’aice dai bank’ara jin komai daga garesu ba, Amma tabbas idan kika samu Rogeet zaki san inda Master yake.”   “To inane garin su Rogeet d’in?.” Ummi tafad’a cike da k’arfin gwiwa, Da kallo Badoo da Asiya suka bita, kafin Asiya tace.   “Me zakiyi da garin su kuma Ummi.” “Asiya zanje can ne nasamu bayanin inda Master yake, ko yafad’a masa cewa Baba ya amince da auren mu yadawo.”  “Ummi karma kifara amma inane garin nasu.” “Rogeet d’an sokoto ne.” Badoo yafad’a, maimaita sunan “Sokoto.” sukayi dukkansu sabida sunan nisa bana gaske ba tsakanin sokoto da kano.   “Bani cikakken Address.” Ummi tak’ara fad’a, Badoo bai musu ba yabata duk wani bayani da yakamata, a ranshi yana mamakin irin soyayyar dake tsakanin Ummi da Master.  “Wai Ummi me kike nufi yanzu sokoto d’in zaki?.” Asiya ta tambayi Ummi ganin kamar shirin tafiya sokoto d’in take.   “Asiya idan banje ba ya zanyi?.” “Yanzu idan kikaje shima ya cemiki yana kudu ko kuma yabar k’asar nan ma sai kibishi?.” “Asiya ya zanyi dan Allah? yakike so nayi.” “Ummi ban hanaki zuwa ba amma kiyi tunani kafin yin komai.” Asiya tafad’a tare da tashi ta nufi gidan su.   Daga Ummi har Asiya kwana sukayi tunanin Mafita akan wanan lamarin.   ***Washe gari*** Hayaniyar da Asiya ta juyo a tsakar gidan su ce ta farkar da ita daga baccin da take, wanda bata dad’e da komawa ba.    “Wallahi tallahi baki isaba ko kibiyani kud’in gado na ko kuma nasa yan sanda sutafi dake, tinda dai yanzu Allah yayimun arzik’i.”   Asiya ta juyo murya nafad’in hakan, da sauri ta tashi ta nufi tsakar gidan, ga mamakin ta Anty ta gani da Halima.   “Atine ko baki zo kin mun tijara ba nasan kinyi arzik’i.”  Cewar Mama domin tasan kawai masifa ce ta shiga da Anty gidan, sabida ta nuna musu suttura da kuma canjin da jikin ta yayi,  domin ko mak’iyi yaga Anty yasan ta canja.    “Yawwa to tunda kinga arzik’i ai shikenan, kece mitsiyaciya dan haka kije ki rik’e kud’in gado marasa albarka.”   “Kud’i marasa Albarka ai basu huce na bariki ba.”   Cewar Asiya da tafito yanzu.  “Ke Asiya bana ciki da iskanci kuma ciki yanzu.”   Mama tafad’a tana nunawa Asiya hanyar d’aki.   “Ah! kace rasa kunyar na ciki, idan kika mara kunya nan zaki k’araso ki maimaita.”   Halima dake wani cika da batse wa tafad’a. “To idan ta maimaita dakuwa zatai ko me? ai ba k’arya tayi ba, babu kud’i marasa albarka kaman na bariki, kud’in da huta kake ci.” Ummi da tashigo yanzu tafad’a. Dariya Anty da Halima suka kwashe da ita lokaci d’aya.  “A’ah Rai ko gawa?.” Halima tafad’a a shak’iyance. “Karya yarinya tamun rashin kunya dauje bakin ta zanyi daga ita har Asarariyar Uwarta. Ummi tafad’a tana k’arasa shigowa cikin gidan. “Asiya Ummi ku shige cikin d’aki kafin ranku ya b’aci.” Mama tafad’a musu cikim fad’a, ba shiri suka shige cikin d’akin, Halima kam cikin kururuwa take fad’in.   “Wallahi yaran nan sai kunsa da wacce kuke, wallahi sai kunyi danasin fad’in wanan maganar.”    Ficewa tai Anty tabi bayanta. “Can da sugada.” Mama tafad’a sanan ta k’walawa Ummi da Asiya kira, fituwa sukayi sanan tace.    “Ku fita sabgar yarinyar nan Halima, yanzu tayi k’arfin da bawani abu bane dan ta illata ku.”   “Toh shikenan insha Allah Mama zamu kiyaye.”   Ummi tafad’a sabida tanaso Mama tabasu waje ne suyi magana da Asiya.    Mama nafita Asiya tace da Ummi. “Ina muka kwana?.”    “Asiya nasamu kud’i 15000 nasan zasu iya tafiya zuwa sokoto, Amma bansan ta inda zanfara tafiya ba.” Kallonta Asiya tayi sanan tace “Dafarko Ummi ina kika samu kudi?.” “Banki na nafasa.”  Ummi tabata amsa, bata k’ara jan zancen ba sabida tasan Ummi tadad’e tana asusu. “Ummi ni a gani na mai zai hana shi wancan mu bashi kud’in yaje sokoto d’in.” Kallon ta Ummi tayi sanan tace.  “Asiya kuma zaije?.”  “Zaije mana Ummi insha Allah.” “Allah yasa.”  Ummi tafad’a sanan suka tashi suka fice, bash sha wahala ba su kasamu Rogget sana suka fad’a musu buk’atar su “To amma dai kunsan zaku bada ishashen kud’in mota ko?.”  Rogget d’in yafad’a yana bin su da kallo. “Kaman nawa?.”   aaaiya tafad’a. “Ko dubu sha bakwai haka.” Ummi ce tafito da kud’in jikinta dubu sha biyar zata mik’a masa asiya ta masa ta k’ara dubu uku yazama sha takwas.  “Ga wanan dubu sha takwas ne, nasan zasu isa ko?.”  Asiya tafad’a tana mik’a masa kud’in, karb’a yayi sanan yace.   “Eyh zasu isa.” “To yanzu zuwa yaushe zaka tafi?.” Ummi ta tambayeshi. “Eyh ko zuwa jimawa ne.” “To Allah yatsare sai munjika.” Asiya tafad’a tana kama hanun Ummi suka huce.   Dariya sosai Rogget yayi sanan yace.  “Makakku, ni ko garin nasu ma ban rik’e sunan shi ba balle har naje, kunyi zakka.” *****   Bayan Sati guda. Abba har yagaji da jiran Ummi akan Master, kamar yadda itama tagaji da jiran Rogget da bashi ba labarin shi.    Yauce ranar k’arshe da Abba yabata, idan bata kawo Master ba, zaiyi mata baiko da wanda Hajiya ke so, sanan kuma zata koma makaranta.   Tun safe Ummi da Asiya ke yawon bulayi a gari, sun rasa ina zasu dosa, Kamar daga sama suka hango Rogget yana tawowa inda suke. Suma fara tafiya sukayi zuwa inda yake har suka had’u, da sauri Ummi tace.   “Ya ake ciki?.” Hannu Rogget yasa a alajihu ya ciro takarda ya mik’awa Ummi.  “Ta mece wannan?.” “K’arba mana.” Page [31&32] yafad’a yana mik’ama ta, hannu tasa ta amsa tafara bud’ewa.   Rubutun Master idon ta yasauka akai.   “Meena nasan duk lokacin da wanan takarda ta isa gareki nayi nisa da ganin ki, nayi nisa da zuciyar ki. ina mai baki hak’uri akan hakan Ummi.   Matsalolin da suke tun karar mu masu yawa ne Ummi kuma bazamu iya yak’i dasu ba.  Ummi yan uwanki, ahalinki bazasu so ni ba, kina da kyakyawan ahali Ummi, dakika taso cikin farim ciki da soyayya.  Bazan tab’a yafewa kaina ba idan nazama sanadiyar ruguza wanan farin ciki na ahalin. Muna da abubuwa guda biyu da muke yak’i akansa. A halinki Gobe ta Yakamata Ummi muyi duba akan wanan, abubuwa ne masu mahimmanci ga kowanne mu. Ina so Ummi kije kiji da Ahalinki nima zanje na gyara gobe ta. Idan muna da rabon sake had’uwa zamu had’u Ummi insha Allah    Daga naki har kullum  Mukhtar Master.”   Wani mugun ihu Ummi tasaku tare da zubewa k’asa da sauri Asiya tayi kanta, tana fad’in.    “Ummi! Ummi!! Ummi!!!.”   “Yanzu Asiya Mukhtar ya kyauta mun? , duk fad’i tashin da nake dan ganin soyayyar mu takai gaci, nayi fad’a da yar uwata, nayi da aminiya ta, Mahaifiyata ta fita sabgata duk akanshi, amma bazai iya jurewa ba shi, sai yanzu da komai yazo k’arshe.”  Kuka ne yaci k’arfin ta, takasa k’arasa maganar.  “Kiyi hak’uri Ummi, kowanne d’an Adam yana rayuwa ne akan doran k’addarar sa kuma baisa ya canja wanan ba.” “Amma yanzu Asiya wanan ita sakayya itace ribar TUDU AKAN KWARI.” kuka ne mai k’arfin gaske yaci k’arfin ta, wani irin dum dum take ji acikin k’irjin ta.  cikim kuka tak’ara magana. “Ya Allah kaine kasa ka mun soyayyar Mukhtar Allah ka ciremun ita, ko da hakan zaija na rasa raina.”   “Ummi wai mene haka dan Allah kiyi hak’uri.” Asiya tafad’a itama cikin nata kukan  “A yanzu wanan yazama izina gareku bake kad’ai ba Ummi.” Mama dake tsaye bakim d’akin nasu tafad’a tare da shigowa ciki.     Bata hanasu kukan da suke ba sai ma ta d’ora da cewa. “Duk abinda ku kaga iyaye sun hanaku tun a lokacin farko, to wanan abun ba alheri bane a gareku, iyaye basa tab’a bawa yaro abinda zai cuceshi, sann kusani duk wani wanda zai so ku a duniya a bayan uwar da ta d’auke ku a ciki ne.”    “Tabbas Mama yanzu nayi nadama nayi danasin bijirewa Mahaifiya ta tun a lokacin farko.”   Ummi tafad’a cikin matsanam cin kuka, Rungume ta Asiya tayi suka fara kuka mai tsuma zuciyar mai sauraru.  Dukkanin su zuciyoyin sa fal da rauni. “Ummi yanzu lokaci bai k’ure miki ba, kije kins mi yafiyar Mahaifiyar ki sanan ki nuna mata a shirye kike domin yi mata biyayya.” “Toh Mama.” Ummi tafad’a cikin kuka. Tashi tayi ta wanke fuskar ta, sanan ta nufi gidan su.   Kai tsaye d’akin Hajiya ta nufa, inda ta same ta zaune kan gado tana danna waya.   A hankali tashiga d’akin bakin ta d’auke da sallama.   Ciki ciki Hajiya ta amsa sallamar tare da cigaba da abinda take. Zama tayi daga k’asa cikin sanyi da rauni tafara magana.  “Hajiya nasan ni mai laifi ce a wajenki Amma dan Alah dan girman Annabi kiyi hak’uri kiyafemun, Wallahi Hajiya nayi nadamar zab’ar soyayya akan iyaye na, sanan nayi miki alk’warin daga rana irin ta yau zan kasance maiyi miki biyayya har k’arshen numfashi na.”   Sosa da Sosai Hajiya taji dad’in maganganun Ummi, amma sabida nuna mata girman laifin ta yasa tace.   “Shikenan Allah yasa da gaske kike.” “Amin dagaske nake Hajiya dan Allah kice kinya femun ko na samu sauk’i a zuciya ta, kuma namiki alk’warin dakaina zan sanar da Abba cewar na shirya Auren Affan.”  “Ummi idan nace banji haushi akan ki ba nayi miki k’arya, Amma kuma bantab’a rik’e ki a raina ba ko da na kwana d’aya, kije Allah yayi miki albarka nagode.” Tashi Ummi tayi tanifi cikim d’aki ta kwanta. Da dare da kamta ta sanar da Abba komai na cewa t hakura da Master. Sosaj Abba yaji dad’i.   Washe gari kafa da kafa taje gidan Goggo tabata hakuri da Gidan Anty Nafisa.  Haka Rayuwa ta juya Ummi zuwa farin ciki, duk da lokaci da dama tana tuna master kuma tanajin sonshi a cikin ranta, ta sawa ranta yau da gobe dole zata manta Master.   Ana haka su Ummi suka gama rubuta jarabawar su ta Waec, a lokacin ne kuma akayi musu baiko da Affan wanda ya shirya zuwa k’asar America k’aro karatu.    Haka rayuwa ta cigaba da juyawa yau fari gobe baki, har zuwa sanda su Ummi suk rubuta jamb sanan suka sami Addmission a jami’ar Bayaro University kano.   A yanzu Ummi tacanja daga ita har Asiya sun k’ara kyau, da gayu tsakanin su da iyayen su biyayya ce da soyayya sai kulawa.   A yanzu Hajiya ta komawa Ummi kamar da Yar gata yar lele haka Abba da Anty Nafisa.   Tana aji biyu a jami’a Dr Affan yadawo hutu tare da Matar shi yar asalin Nigeria dake karatu a america, ko da Hajiya Balki tayi masa maganar Ummi sai cewa Yayi yana jira tagama karatu.  Kwance tashi ba waya a wajen Allah a yanzu har su Ummi sun kammala jami’a sa sakamako mai.   A yanzu tabbas kaga Ummi da Asiya bazaka ce sune ba domin sun zama kyawawan yan mata masi ilimi da wayewa, sai dai fa Ummi ta rage dik wata rawar kai da hayani ta zama so cold abubuwa da yawa bata fiya magana akai ba.   Duk wasu burinka rayuwa Ummi tacire su. Ana haka akayi wa Asiya baiko inda akasa shekea d’aya ita kuma Ummi ana jiran dawowar Affan.   Suna wanan zaman ne Asiya tasamu aiki a asibiti na wanda yakawo kud’in ta, kasancewar ita fanin hak’ori ta karanta ita kuma Ummi Entrepreneurship hakan yasa tasamu aiki a company.    Tun zuwan ta company MD din companin yake nuna mat soyayya, duk yadda Ummi taso tasa ka soyayar shi arai takasa, duk da tasan babu soyayyar Affan ko kad’an aranta kuma tasan ba auren ta zaiyi ba.   Ta kud’ri Aniyar fara son Nawfal tunda taga itama Hajiyar a yanzu tadawo daga rakiyar Affan d’in, Sai dai har yanzu zuciyar ta takasa k’arb’ar Nawfal bata san kome ne dalili ba.    A yanzu bikim Asiya Saura watanni shida, Amma ita ba ko labari, idan Goggo tayiwa Hajiya maganar Affan sai tace ita ma batasna abinyi ba.   Baiko ne dai gashi Anyi wajen shekara Biyar amma har yanzu shiru babu wata maganar.   Hakan yasa A yanzu Asiya ke bata k’warin gwiwa kan ta koyi son Nawfal tunda dai yana son ta kuma mutumin arzik’i ne.   Bata tab’a tunanin sake ganin Master ko jin shi ba A rayuwar ta.   WANAN SHINE LABARIN TUDU AKAN KWARI NA UMMI. Page [33&34]   B’ud’e idanu wanta tayi ta gama ganin rayuwar ta gaba d’aya a majigi, duk irin Butulcin nan da Master yayi mata shine yake k’ara mata magana.    Tashi tayi tashiga bayi, wanka tayi sanan ta d’aura alwala tafito.   Dadduma ta shimfid’a bayan tasaka bakar doguwar riga da dogon hijabi, ta tada Sallah.  Addu’a tayi sosai bayan ta idar da Sallah akan Allah yakare ta daga k’ara fad’awa komar Master a karo na biyu, domin tabbas ta ga zuciyar ta na shirin jama ta wani aikin.   Saida Ummi tayi kwana uku ba tafi ko nan da can ba hatta wajen aiki ta daina zuwa sabida gudun sake had’uwa da Master.    B’angaren Master kam Rashin Lafiyar Matarshi tasa shi a gaba hakan yasa yabawa Ummi hutu.    Zaune yake cikin d’akim asibitin da aka kwantar da Zainab.    tana daga kwance kan gadon, shi kuma yana daga gefen gadon, cikin muryar mara lafiya take magana.   “Yallab’ai yakama ta ace ka k’ara dagewa akan lamarin Ummi domin gudum sake rasa ta a karo na biyu.”   Kallon Zainab yayi cike da su da kulawa sanan yace.    “Ranki ya dad’e idan har nasake rasa Ummi a karo na biyu ya tabbata ba rabo na bace, ke daice rabona kuma ina mai godewa Allah a hakan ma.”  Murmushi tayi a ranta kuma tana godewa Allah domin tasan duk sanda Master kewa Ummi bazai sa ya hulak’anta ta ba, bayan ya sameta.   “Yallab’ai a yanzu kace duk abinda take yi bata san ma kayi aure ba, to ya kake gani kuma idan tasani.” Girgiza kai yayi sanan yace.  “Ranki ya dad’e Wallahi bansaniba, rigimar Ummi karuwa tayi a yanzu data girma ma.”    “A gani na karka sanar da ita hakan yanzu, kabari ka fara samun kanta sanan kuma kaga lafiya ta, kasan ciwom da nake dashi ba lallai nayi tsohon rai ba, ba lallai nafita daga asibitin nan ba…   “kidaina fad’in haka Zainab da rayuwa da mutuwa duk na  Allah ne, insha Allahu yanda kika shigo asibitin nan da k’afarki haka zaki fita da ita.” Murmushi tayi sanan tace. “To Allah yasa, Amma ranka yadad’e ka d’auki shawarar tawa, kafara shawo kanta a yanzu sai kayi mata bayani daga baya, insha Allah zata fahimta.” “Zainab a ko dayaushe zaka sance mai yiwa Allah godiya da yabani ke, sanan zan k’ara gode miki da shigowa rayuwa ta da kikayi, kika tallafe ta dai dai lokacin da narasa madafa, kika tashk rayuwa ta lokacin da nake ganin ta mutu, Zainab a duniya banj da kalaman da zanyi amfani dasu wajen yi miki godiya, A matsayin a na mijinki indai har aljannar ki tana k’ark’ashin kafata Zainab na d’aga miki ki shige.”    *** Nawfal ne Zaune cikin office d’in Asiya, Kallonshi tayi sanan tace.   “Nawfal ina fatan dai lafiya ko?.” Girgiza kai kawai yayi batare da yace uffan ba.  “To yanzu kayi shiru bansan me zan iya ce maka ba?.”   “Asiya kinsan matsalal, kinsan damuwar tawa, da ina fama da iya neman soyayyar ta, yanzu gashi tsohon saurayin ta yadawo.”   “Ga kuma wanda akayi mata baiko dashi, zaidawo cikin wanan satin, kuma bamusan da me zai dawo ba.” Asiya ta fad’a, da mamaki yad’ago ya kalle ta sanan yace.   “Ba an warware baikon nasu ba.” “Eyh Abban ta yaje zancen awarware baikon har ma an mayar masu da kud’in su, sai dai basu amsa ba.”   “Wanan Ai shirme ne.” Nawafal yafad’a yana k’ok’arin tashi.  “Nawfal tsaya kaji dan Allah kad’inga sawa kanka sauk’i akan lamarin nan, idan Ummi matarka ce to dole sai ka aure ta, idan kuma ba rabon ka bace duk tashin hankalin ka bazaka aure ta ba.”   “Hakane Asiya nagode, insha Allah zan kula.” Daga haka yasa kai yafice, ita kuma ta tashi ta nufi office d’in sahibinta Dr Mansur.   Tana tafe tana ta lissafin k’alubale na rayuwa da Ummi tasamu. A dai dai bakin k’ofar office d’in ta tsaya, ganin office d’in a kulle yayi matuk’ar bata mamaki.    Daga inda take ta lek’a can parking space,ganin motar shi wajen ya k’ara bata mamaki.    Komawa office d’in ta tayi ta d’auko spare key na office d’in nashi ta dawo. A hankali tasa Key ta murza, sanan tashiga bakawo falon hakan yasa tafara kok’arin nufar d’aya room d’in.  Kasancewar office d’in mai Room and falo ne a hankali take tafiya gaba d’aya jikin ta ya mutu, zuciyar ta tayi nauyi, batasan mene zaifaru ba amma jikin ta ya bata abu mara dad’i.    Motsin da ta jiyo a cikin d’akin yasata k’arasa wa wajen, tare da sa hannu ta murd’a.   Da sauri ta gimtse idon ta, tare da sakin k’ofar.  Dr mansur kam a zabure ya mik’i yayi kanta yana fad’in.   “Asiya! Asiya!! Asiya!!!.” Bata tsaya ba tafice, domin tabbas abinda tagani ya matuk’ar bata mamaki.   Gani ta fice yana sashi dawowa cikin office d’in nashi, tare da kallon yaron dake kwance.   “Ahmad get out.”  Tashi yaron da aka kira da Ahmad yayi tare da fara sa kayan shi, yana abu kamar mace har ya shirya sanan yazo inda Dr mansur yake sanan yace.   “Yanzu sai yaushe?.” “Zanbiyo gidan naku da daddare.” Dr mansur yafad’a, domin shi tsoran shi ba ganin da Asiya tayi masa ba, yanda zata je ta yad’ashi.    Tashi yayi bayan yaron yafita ya nufi office d’in ta, dai dai lokacin da tagama had’a kayanta.   “Asiya dan Allah kitsaya kiji ni.” “Mansur me zanji daga gareka, so kake kacemun karya ne abinda nagani ba haka bane.”   “Asiya nasani abinda kika gani gaskiyya ne, Asiya ina neman maza amma wallahi a yau nayi nadama kuma natuba, dan Allah Asiya kiji k’aina kiji tausayina Asiya, natuba Wallahi.”   Shiru Asiya tayi tana kallon sa, sanan tace. “Allah ubangiji yasa tuban gaske kayi, kuma insha Allahu zan rufa ma asiri tare da tayaka da addu’a , amma sai dai nafasa auren ka mansur domin abinda na gani bazai taba gogewa daga rainaba cikin sauk’i.”   Duk da yaji ba dad’i na fasa auren shi da tayi amma cewar zata rufamai asiri yasa shi jindadi, domin daman ba auren yakeso ba, zaiyi ne kawai sabida bakin mutane.   “Nagode Asiya, bazan hanaki fasa aure na ba domin tabbas duk wacce taga namiji a irin wnn halin baza ta fara auren shi ba.” “Sanan zan ajiye aiki na.” Kallon tayayi sanan yace.    “Dan Allah a’ah karkiyi haka.” “Bazan iya zama ina kallon a haka ba domin bazan iya mantawa da abinda nagani ba, amma tabbas nayi nisa dakai zan mata da abinda nagani.”   Shiru yayi sanan yace. “To dan Allah zanema miki ai wajen abokin Dr Lamir, Wallahi shi mutumin kirki ne.”   “Shikenan zanyi tunani.” daga haka ta d’auki jakar ta tafice ***  “Wai ni Saliha ina aka kwana maganar wanan yaron da ya zubar mun da jika.”   Kallon Goggo Hajiya tayi sanan tace.  “Wallahi Hajiya nima abun ya dameni sabida ko jiya sai dai yak’ara yiwa mahaifin yaron magana amma sunki amsar kudin, haka ita ma mahaifiyar yaron sabida butulci wai haushi na takeji.” “D’an Adam kenan, tamanta tsanar da tasa kikayi wa yar ki, akan tak’i d’anta, amma yanzu yaro ya ajiye yarinya shekara hud’u shine zataji haushinki.” “Bari dai Goggo ni dai yanzu muntsya akan yanda shi Alhajin ya yanke, babu baiko tsakanin Ummi da Affan, duk sanda suka shirya su amshi kud’in su.” “Tabbas hakan yayi Saliha, kuma yanzu wanan lokaci ne da zamu bawa Ummi damar gabatar da wanda takeso.”  “Hakane Goggo Amma kamar kince ta gabatar miki da Nawfal ko?.” Gyad’a kai Goggo tayi sanan tace “Eyh ta gabatar da shi Amma banga wata soyayya a idon ta ba, kuma ni baiyimun ba, wani d’an tuturna dashi.”  Dariya Hajiya tayi sanan tace. “To Goggo idan kuma shine mijin jikokar taki fa?.”  “Haka Allah yaso kuma bayanda zanyi.” Goggo tafad’a da haka suka cigaba da hira,domin tabbas a yanzu ansamu fahimta mai k’arfi tsakanin Goggo da Hajiya, daman tunda akan lamarin Ummin d’in ne. ***   K’arar Wayar Ummi ne ya katse ta daga kallon da takeyi, wanda a zahiri ne take kallon tv d’in amma ba kallon take ba.   Hannu tasa tad’au wayar ganin sunan Lil sister wanda tayiwa Asiya saving dashi.  “Hello Asee.”  daga can b’angaren Amsa Asiya tayi tare da fad’in.   “Kina ina?.” “Lafiya kike kuka Asiya?.” “Ba lafiya ba da matsala tsakanina da Dr Mansur.”  “Subhanallahi, kibiyo ina gidan Anty Nafisa.” To tace sanan ta katse wayar Page[35836] Anty Nafisa dake zaune ce tace.  “Wai Ummi kinzo tun safe, gadamuwa fal ranki amma kinkasa magana.” Kallon Anty Nafisa tayi, ido cikin ido sanan tace.   “Anty bani da bakin magana domin bansan ne zance ba.” “Maganar Affan ce? ina ba Abba yagama magana ba? Girgiza kayi tayi sanan tace.  “A’ah Anty matsala Affan k’arama ce akan wanan.” “Innullahi Ummi wace irin matsal ce wanan?.” Shiru Ummi tayi na tsahon sakanni sanan tace.  “Anty Master yadawo.”    “Yadawo daga ina?.” Anty Nafisa ta tambaya cikin rashin ganewa.   “Yadawo daga inda yaje, sai dai ba’a wanan salon yadawo ba.” “A wane salo yadawo?”   “Anty A salon da inda akace miki Master ne bazaki yarda ba Anty.” Nan Ummi tashiga bata labarin duk wasu gifts da akatura mata har zuwa binciken da sukayi suka gano wanene shi da kuma kamfanin mAm.  “mAm kikace Ummi?.” D’aga kai Ummi tayi sanan tace. “Wallahi Anty.” “Gaskiyya Master yazo da wani salo,Amma Ummi idan har ya shiryu mene zai zama matasala ?, daman ai bashi ne ba’aso ba halin shine ba’aso.”   Kallon Anty Nafisa Ummi tayi sanan tace “Anty Abunda yayi mun fa?.” “Wane abu yayi miki Ummi?.” Anty Nafisa ta tambaye ta domin son sani.  “Anty kar kice mun kin manta mana.” Sallamar Asiya ce ta dakatar da maganar da Ummi keyi.  Da sauri Ummi ta tare da cewa.  “Me nake gani kamar hawaye a idonki.”   Zama Asiya tayi sanan tace.  “Ummi mai zanyi? idan ba kuka ba.” Anty Nafisa ce ta tare su da cewa. “Asiya lafiyan ki kuwa?.” Girgiza kan ta tayi sanan tace.  “Anty Mansur ba mutumin arzik’i bane kwata kwata.” Da mamaki Anty Nafisa tace.  “Subhanallahi shi Mansur din kuma?.” Ummi kam cewa tayi “ai daman nasa kuma nafadamiki tun lokacin farko.” Kuka Asiya tafara sanan tafara basu labarin duk wani abu da yafaru  “Amma Allah la’anci Mansur dan uban sa, shege.” Ummi tafad’a cikin Masifa sanan ta d’ora da cewa.   “Daman tun farko na tsani wanan shegen Mansur d’in da rayuwarsa, Allah ya taimake mu ya kuma rage mana wahala.” “Ke fa Ummi yaushe ne zakiyi hankali dan Allah?.”  Anty Nafisa ta tambaya, Kallon ta Ummi tayi sanan tace.  “To Anty wanan ai rage mana akayi da ace sai bayan Auren aka sani fa, azo ai ta fama da shi wajen saki, kuma mutane sufara magana, yanzu kam idan sukaje ance anfsa maganar da zasuyi kadan ce.” “Alllah ya kyauta, yanzu Asiya mai kika yanke?.” Anty Nafisa ta tambaya, sai da ta d’anyi Jim sanan tace.  “Na yanke shawarar fasa Aurensa sanan na ajiye masa aikin sa, Amma yace wai zai samo mun wajen abokin shi, duk da nace banaso.” “Me zakiyi da wani Aiki wajen Abokin shi ke kam?.” Ummi tafad’a tare da tashi ta dawo kusa da ita, hannu ta d’ora kam kafad’ar ta sanan tace.   “Ni ina ganin wanan abun ayiwa Allah godiya ne, da ya rage miki wahala, domin tabbas dai sai bayan auren ku kika gane wanan labarin kinga ai babban Abune mai wahala, kuma hukunci da kika yanke shine dai dai, Asiya muna zaune Allah zai kawo miki mijin Aure nagari, gaba d’ayan mu.” “Tabbas Asiya maganar da Ummi tafad’a miki gaskiyya ne.”  Anty Nafisa ta k’ara fad’a. “Nagode Anty Nagode Ummi.” Duka Ummi tad’akawa Asiya sanan tace. “Sannu da Godiya.” “Nikam Ummi ya maganar Nawfal da Master?.” Asiya ta tambaya. “Uhm Nawfal ba mu samu munyi magana ba shikuma Master ban sake fita ba balle muhad’u.”   “Yawwa wai nikam Asiya mai Master yayiwa Ummi ne?.” Anty Nafisa ta tambaya. “Bangane ba Anty?.” Asiya ta mayar mata da tambyar. “Laifin da zai sa har takasa Amsar soyayar shi a wanan karon.”  “Haha Lallai Anty, duk ba mu san uzirin shi ba, Amma tabbas Master bai kyauta ba, duk da zamu iya cewa hakan yafi Alheri domin da awanan lokacin ya tsaya to tabbas Ummi ko ta k’arfi ne sai ta bishi duk inda zai kaita, ya rabata da yan uwan ta da kowa na ta.”   “Hakane Asiya Amma ina ganin a yanzu ai yadawo a matsayin da kowa ce mace zata so samun shi a matsayin Miji.”   “Hakane Anty.” Asiya tafad’a daga haka hirar ta tsaya, sai da sukayi sallar magariba sanan suka fara shirin tafiya.   Tafe suke a hanya cikin motar Asiya, wacce Ummi ce ke driving motar, k’arar kiran da yashigo cikin wayar ne, ya katse wa Ummi maganar da take shirin yi.   Tabbas a yanzu ta gane number Master duk da ya kan canja lamba ya kirata. Nunawa Asiya Wayar tayi tare da cewa bana raba dayan biyu Mukhtar ke kira. Page [37&38] Daga wa tayi ba tare da tayi magana ba, sanan tasaka wayar a speaker.   “Naji dadi da kika daga wayar.” yafaf’a cike da sassanyar muryar shi, Shiru Ummi tayi ba tare da tace komai ba.  “Ranki yadade ko bacci kike?.”  “Mutuwa nake.”  Tabashi amsa a gajarce, Dariya yayi mai sauti sanan yace.  “Ay hakuri Ranki yadad’e sanan agaida mini da Asiya.”  Kallon Ummi Asiya tayi itama Asiyan ta kalleta.  “Wake magana ne?.” Dariya ya karayi sanan yace.  “Dan Allah ranki yadad’e alfarma Rana d’aya nakeso a bani ke da Asiya, Zan zaiyyane miki komai da yafaru, idan kinji zaki iya yafe mun idan kuma baxaki iya ba, duk wani hukunci sa kika yanke zan k’arb’a nabi.”   Shiru Ummi tayi na tsahon lokaci sanan tace.   “Ka tabbatar duk hukuncin dana yanke zaka karb’a.” “A Ranki yadad’e, sai dai ina rok’on ki da ki saura reni da kunne fahimta sanan kiyi adalci agareni.”  “Insha Allah.” “Yanzu yaushe aka bani?.” yafad’a da irin salon muryar shi ta da,domin yaga kamar hankalin ta baya tare dashi.   Dariya tayi mai d’an sauti kafi  tace.   “Duk sanda kake da lokaci.” “Gobe dan Allah.” “Allah yKaimu.”  tafad’a tare da kashe wayarta sanan ta juya ta kalli Asiya.   “Mene kuma kike kallona ?.” Asiya tafad’a dan taga yanda take kafe ta da idanu.   “Hakan yayi dai ko?.” “Yayi mana Ummi daman yana da kyau a zauna a fahimci inda matslaal take, idan da rbo sai kiga shi din ne dai.” “Tab da TUDU AKAN KWARI ya tabbata.” Ummi tafad’a taba dariya ita Asiyan dariyar tafara sanan tace.  “Yanzu dai Allah yasa su Hajiya su Amshe shi.”  “Amin dan Annabi.” Daga haka suka cigaba da hira har suka karasa gida.   Mutane ne tsaye daga k’ofar gidan su Asiya. “Innullahi me yake faruwa a k’ofar gidan Mu.” Asiya tafad’a hankali a tashe, itama Ummi cikin tashin hankalin tace.  “Gadai mutane tsyaw Allah yasa Lafiya.” “Wanan tsayuwar ba ta lafiya bace Ummi, ke dai yi parking.” Guri Ummi tasamu tayi parking sanan su kafito zuwa k’ofar gidan, ita dai Asiya tunda idon ya yakai kan Mama hankalin ta ya kwanta, dan koma mene daga bayane.  A haka suka karaso wajen, idanun sune suka sauka akan wata yagalgalliyar mata da kuma wata babbar mace sai yarinyar kimanin yar shekara uku. “Mama lafiya su waye way’anan haka?.” Asiya tafad’a bayan sun k’araso wajen. Hajiya ta bata amsa da cewa.  “Anty kice da Halima da kuma yar Halima.” Kallon Hajiya Asiya da Ummi sukayi sanan Ummi tace.  “To me ya kawo su, su kuma mutanen da suka zagaye nan fa.” “Hak’uri ake bawa Maman Asiya wai ta k’arbeta.” Asiya ce tayi caraf tace. “Wallahi never 👎 ba tayanda za’ayi bayan hulaknci da sharrin da tinga bin mu dashi, yaushe taje gidan su Suwaiba, bayan har kudin auren yaya Umar ankai tace wai isakanci yake yi acan chaina sukuma suka daowa da kudin suka cw amfasa bayan wanan sharri kala nawa.” “Kinga Asiya shege cikin da Hajiya ja Ummi ku shige naku gidan, duk mai tausayin su ya dauke su yakaisu nashi gidan, ai duk sun san halinta.”  Nan mutane su fara watsewa, itaku Anty ko magana bata iyawa sai mungun wari dake fitowa daga cikin ciwon k’afarta, ga yar shegen Halima sai taka ciwon take. Itaku halima cutar kanjamau din dake jikin tace tasa ta rame takoma kamar wata tsohuwa. Haka Asiya tashige da motar ta tabarsu a wajen domin kuwa ya watse.   “Gaskiyya Atine kim cucemu, da mutane sun sanki da hali mai kyau ai da sun taimake mu, amma dik sun miki muguwar shaida.”  Halima tafad’a domin tagaji da tsayuwar da suke, ga kuma ciwon dake jikinta duk yagama k’arar mata da karfi, dan a yanzu bama sajim warin dake tashi daga ciwon Aunty. Kuka Anty tafashe dashi tare da cewa.  “Ni Atine nayi Asara nayi nadama, yarinyae da naki zaman lafiya da kowa akan ta, ita ke zagina.” Haka suka k’araci zaman su,kafin suka tashi suka cigaba da tafiya. *********   “Wai Asiya maganar ki akan me take ne ni bangane ba?.”   Mama kenan take tambayar Asiya bayan tafaa mata cewar tafasa Auren Mansur. “Mama kamar yafda nafad’a miki wallahi nafasa Auren Mansur kuma shima ya yasani, kowane lokaci zai iya aiko k’arbar kudin shi da kayan shi” “To Asiya babu dalili ne da zaki iya fad’a ko bani bawa wa yan uwanki da yan uwan mahaifin ki, Asiya bakya ganin girman da kukayi ne?.” “Mama Aure lokaci ne, kuma girma ba akan wani muke ba, duk wanda zaiyi magana yaje yayi, nipa Mama har aikin shi na ajiye mishi.” “Allah magani makwoci maye ni Sahura,Asiya wallahi karki ga ina sake miki kidinga iskanci ai jibi yayan naki zai dawo kya mai bayani.”  Daga haka Mama ta tashi ta huce.   “Yaya zaidawo Amma ko yafad’amun lallai mutumin.” ************ A gidan Anty Nafisa suka shirya had’uwa da Master, haan yasa tun k’arfe biyu suka tafi gidan.   B’angaren Master kam yana zaune kusa da Zainab waccce ba’a dad’e da fitowa da ita daga d’akin treatment be.  “Katashi kaje haka, kar taita jiranka.” Murmushi yayi sanan ya kalli Zainab.  “Nikam bansan meyasa kike abu kamar ba kyajin kishi na ba?.” Dariya itama tayi, to akan me zatayi kishi ta wahalal da kanta, tun had’uwar su tafako ya gayamata wacece Ummi da irin son dayake mata.  Tsahon way’anan shekarun bai dai na son taba itakuma kuma haka, to akan wane dalili zata wahalal da kanta. “Kinyi shiru?.”   “Me kakeso nace? kasan dai ina sonka, ina son abinda kake so wanda zai baka farin ciki, to mene zaisa nasako kishi a ciki?.” ****************   K’arfe uku dai dai Master yayi parking Glk dinshi a k’ofar gidan Anty Nafisa, waya ya dauka ya kira lambar Ummi.   Sai da takusa katsewa sanan tasamu d’agawa.  “Ranki yadade na k’araso.” “Uhm kad’an jira.” tafad’a tare da kashe wayar  Bata wani jima ba akayi masa iso zuwa babban falon gidan, Ummi ce tafara zama sai bayan yan mintina Asiya ta sami isowa.   Tabbas taga sauyi a jikin Master dam daman tunda yadawo basu taba haduwa ba.   “Ah Asiya abinda yasa na nemi ganin ki, shine inaso kiyi adalci a cikiin duk abinda zanfad’a, sanan nasan ke zaki bawa Ummi shawara tagari akan duk abinda yakamata.”  “Insha Allah zanyi duk abinda ya dace.” “Masha Allah.” yafad’a cikin muryar shi mai zak’i da amo.  “Tun a lokacin da Abba yahana ni Auren Ummi a karo na farko naji nayi danasanin duk wani hali da nake dashi.” Page [39&40]   Tabbas nayi duk wani danasani da yakamata, har zuwa kwanciya ta a asibiti da sallama ta.  Ummi samum labarin mutuwar ki, ya tsayar mun da duk wani karf’i, da kwarin gwiwa da nake dashi a rayuwa, na gwammace  ace nima tawa rayuwar ta k’are.   kwatsam kuma naji labarin farfad’owar ki  Ummi wani abu yashige ni a wanan lokacin, nida nasaki a wanan halin bani da yadda zanyi na taimakeki sai yan uwanki da nasa kika bijirewa, sune suke taimakokin ki.  Menene amfani na cigaba da zama dake tunda nasan ba karb’a ta zasuyi ba, nasa ki cigaba da bijire musu kina musu abinda bai kamata ba kinayim TUDU AKAN KWARI wanda bazai taba tsallakuwa ba.   Hakan yasa na yanke shawarar yin nesa,wanda nasan dole zaki ji ba dad’i amma nasan hakan zai amfane ki gaba, na yanke shawarar yin can nesa ko rayuwata ta gyaru ko ta k’arasa b’aci duk d’aya.   Natafi ba tare da nasan inda nakama ba, natafi ba tare da nasan inda na nufa ba, natafi ba tare da nasan me zan samu can inda zani ba.    Anan k’addara ta mik’ani garin legos, na yanke shawarar zuwa garin ne domin nasan duk wata rashin kunya ta akwai wayanda suka fini.  Sauka ta garin legos yayi dai dai da cin karo da Zainab da nayi tare da wasu matasa su uku , suna neman yi mata fashi. Da farko nayi kamar na kyalesu natafi abinda ya shafe ni, sai kuma naji baxan iya ba. Nayi iya kacin yi na, sanan na kora way’anan matasan, tabbas Zainab taji dad’in hakan har yasa ta dage sai taji wani abu akaina. Ummi ban boye mata komai ba tinda ga sanda nasan rayuwa har zuwa haduwa dake da kuma rabuwar mu. Zainab ta kasance mace ta gari, domin ita ta d’auke ni a gidan ta har na koma na gyara diploma ta sanan tabani aiki a companin ta. Daga baya tazo mun da kud’irin tanaso ma aure ta, Zainab bata tab’a saremun gwiwa akan sonki ba har takai ga na Aure ta.” A zabure Ummi ta mik’e tare da fad’in  “What?.” “Mukhtar kayi Aure?.” “Zauna Ummi na k’arasa gayamiki mana dan Allah.” “Babu abinda zan k’arasa ji mukhtar.” Asiya ce ta rik’eta tare da cewa. “Ummi nutsu dan Allah.” “Asiya to me zan zauna nayi tunda yariga yayi Auren shi, Ai yasan ina sonshi yasan dani ya tafi ya barni, bai damu da halin da zan shiga ba, to kasani a bayan tafiyar ka Abba dakanshi yasa na nemo ka zai bak  Aure na.” Nan tashiga shaida mishi duk abinda yafaru. “Wanan takardar tun kafin wanan lokacin nabawa Baddo shine bai kawo ba sai da yaci kudin ki amma baimasan garin su Abdullahi ba.” “Ummi Allah bai kaddara Auren mu ni dake a wanan lokacin ba sai yanzu.” “Tabbas Ummi idan kika nutsu akwai abinda Allah yake so ya nuna muku shiyasa bai bada damar yin Auren ku a wancan lokacin ba.” Asiya tafad’a hannun ta na rik’e da Ummi, Shiru dai Ummi tayi tabbas tasan har yanzu tana son Master so kuma ba kad’an ba. Tashi yayi daga inda yake zuwa gabanta tare da durkusa wa da dukkam gwiwam shi a k’asa, a hanakali cikin kwantar da murya yafara magana. “Ummi nasan na kasance mai laifi a wajenki tun daga tafiya ta har zuwa auren zainab, amma inaso kisani komai yafaru ne bisa tsari na ubangiji dan Allah Ummi kiyi hak’uri ki k’ara karb’a ta akaro na biyu.”  Shiru Ummi zuciyarta na wani irin bugu dum dum. “Please🥺.” Yak’ara fad’a a hankali. “Shikenan Mukhtar i will think about it.”  “What think please🥹.”  Yafad’a murya kaman zaiyi kuka, A hankali Asiya ta zame jiki tabar wajen zuwa d’aki.  “Mukhtar kasan dole sai nayi magana da iyayena, banaso na k’ara jawo abinda zaka gudu kabarni.” “I will fight the battle with you Ummi.” Shiru tak’arayi daga baya kuma ta mik’amasa hannunta.  da sauri ya bud’e zoben ya zura mata a hannu tare da cewa. “Insha Allah Ummi i will stay with you forever no matter what.” Shirun tak’arayi tabbas inda ta zuciyar ta ne tanajin dama takasance a haka tare da Mukhtar domin tabbas zuciyar ta na mugun son Mukhtar. Zama tayi shima ya zauna a kujerar dake kusa da ita, yafara magana a hankali cikin kwantar da murya. ****************** Tun a airport yake zuba idon ganin Ummi amma shiru hakan yasa yakasa daurewa ya tambayi mahaifiyar shi Hajiya Balki. “Mom where is my Wife?.” Kallonshi tayi sanan tace. “Ai kai zamu tambaya tunda kai kad’ai muka gani.” “No Mom ba Angelina ba, wanan yarinyar ya ma sunan ta?.” Banza tayi masa dan ita bata gane wacce yake nufi ba. “Mom magana fa nake please.” Yafad’a murya cike da shagwab’a kaman zaiyi kuka. “Affan bana ciki da iskanci wace matace dakai da ta huce wacce mai sunan arna da har ka manta sunan ta.” “Mom yarinyar da kuka aura mun fa.” “Ni bansan yarinya da aka aura ma ba sai dai wacce akayi maka baiko kuma iyayen ta sun janye wanan baikon.” “What Mom baiko kuma i thought anyi mana Aure da ita.” “Oh kana tunanin anmaka aure da ita shine kabarta a hulak’ance kenan.” “No mom ba haka bane.” “To kuma yane kai kasani iyayenta sunyi duk mutuncin da zasuyi kuma sungaji Last week Mahaifinta yasamu naka da maganar dawowa  da kud’in domin sungaji kuma tasami wani da takeso.” “That’s impossible Sabida nema cikin nema haramun ne kuma sun riga sa sun ba da ita.” “Ehh daman abinda yasa Mahaifinka ya d’an tsaya kenan kadawo aji idan kana da interest akanta sai ayi muku auren idan kuma baka dashi sai a barmu su kud’in.” Da sauri ya tare da cewa. “Momi nidai inason ta.” “Ai shikenan sai kaje kasameshi kagayamai.” ************** Zaune yake gaban Dad d’in shi bayan yaga ma zayyana mai cewa shi yanason Ummi kuma yana son Auren ta. “it’s okay Son zan tura uncles dinka suje suyi magana a tsaida date na d’aurin auren.” “Okay Dad thanks you.” Affan yafad’a tare da tashi ya fice, Kai tsaye part dinshi ya nufa ya zuba wanka cikin lallausan farin yadi da ya matuk’ar amsar kyakywar fuskarshi. Sai kamshin turare yake zubawa, hannushi sak’ale da agogon rolex, yayi kyau matuk’ar kyau. Cikin Bak’ar GLK dinshi yashiga kai tsaye gidan su Ummi ya nufa. ****************** “Yanzu kai Nawfal kana ganin Auren yarinya da bata sonka ba TUDU AKAN KWARI bane, wanda zaiyi maka wahalal wajen tsallakewa, Nawfal k’iyyar wata macen tabbatacciya ce fa.” Anty Amina yayar Nawfal ke fad’a masa bayan yasami Mahaifin su da maganar kan a tura gidan su Ummi. “Yaya Abban yace zasu je shida su Uncle, idan Mahaifin ta ya amince yabada Shikenan idan kuma ya hana zan hak’ura Amma tabbas inason Ummi, Akan Ummi zan iyayin TUDU AKAN KWARI ko da kuwa bazan iya tsallakewa ba.”   “Idan da alkhairi a lamarin ka da yarinyar nan Allah ya tabbatar idan babu Allah ya watsar da lamarin.” Shiru Nawfal yayi batare da yace komai ba, shi dai kawai fatanshi ace Abban Ummi yabawa su Abban shi Auren Ummi komai zaizo mai da sauk’i daga baya. Wayarshi ya d’auka ya kira number Asiya wacce ke zaune d’aki suna shirin dawowar Yaya Umar gobe. Tana ganin wayar tafara ring takai hannu zara d’auka amma sunan Nawfal da tagani yasata tsayawa. Wani irin tausayin sa ne yakamata, tabbas zata gayamasa ya dakata da lamarin Ummi a yanzun. D’aga wa tayi tare da fad’in “Assalamu alaikum.” Daga can b’angaren nashi amsawa yayi da “Barka da Safiya fatan ban tashe ki ba.” Dariyar yak’e tayi sanan tace “Katashi lafiya ya mutan gidan?.” “Lafiya klau Asiya mutan gida na lafiya ya naku.” “Lafiya klau suke wallahi.” “Masha Allah.” sanan yad’ora da cewa. “Asiya nayi magana da Mahaifina d’azu da safe kam suzo su nema mun auren Ummi.” Daram haka kirjin Asiya ga buga, idan akace mata Nawfal yaji yanda kirjin ta yabuga bazatayi mamaki ba. “Naam Nawfal ke kace.” “Nace nayi magana da Abbana yau da dadare zasu zo tambayamum auren Ummi, ko da matsala ne?.” “Eyh A’ah.” “Mene Eyh A’ah kuma?.” “Nawfal da bakayi gaggawa ba.” “Haba Asiya wace Gaggawa kuma duk jiran da nayi shine zakice nayi gaggawa.” “Bahaka nake nufi ba Nawfal amma da kasani kasanar da ita.” Shiru yayi dan a maganar Asiya ya fuskanci akwai matsala. “Asiya zan iya samun a gida.” Shiru tayi na yan mintinan daga bisa ne tace. “Yes.” Bayan sun kammala wayar ne ta danna lambar Ummi sai dai taji alamun tana wyaa ne, tashi tayi tare da Hijab din ta ta nufi gidan nasu.  Hajiya na zaune a tsakar gida tagaisheta tare da fad’in. “Hajiya Ummi na ciki.” Kallon tara saura Hajiya tayi mata sanan tace. “Kajimun yarinya da kinibibi idan tana nan aikin sani idan batanan ai kinsani.” “A’ah Hajiya nakira wyaarta ne naji bata tafiya.” “To tana ciki.” Hajiya tafad’a tare da cigaba da Abinda take, tashi Asiya tayi tanufi d’akin, kwance ta sameta waya a kunne tana magana k’asa k’asa.  D’aka mata duka tayi tare da cewa bakiga nahsigo bane.  “Zan kiraka anjima Asiya bazata barni nayi wayar nan ba.” Ummin tafad’a murya can k’asa, Asiya bataji abinda kace ba sai Ummin da taji tace. “Bye love you.” “Ke da ubanwa kike waya haka Ummi?.” “To uwata da ubana nake waya.” “Ke banason iskanci bawanan ne yakawo ne ba.” Gyara zama Ummi tayi sanan tace. “To meya kawoki har zaki katsemun waya da masoyina.” “Ummi Nawfal ne yakirani tare da fad’an mu wai yayi magana da mahaifin sa kan zasu zo wajen Abb anjima.” A furge ce Ummi ta tashi tare da fad’in. “Me yake damun Nawfal haka ne?.” “Ummi zauna kiji.” Asiya tafad’a tare da kamo Ummi ta zauna. “Relax wanan abun fa muma da namu laifin sabida bamu sanar dashi komai ba kan dawowar master.” “Amma kuma Asiya yasan koda wasa bantaba cewa ina sonshi ba ko hirar soyayya bantaba dashi ba kuma yasan akwai baiko akaina.” “Hakane Ummi yanzu yace zai zo ya sameni kawai ina ga kifito ayi duk maganar da za’ayi ta k’are.”    “Kinga fa yanzu wayar da muke da Mukhtar kan gobe yau da daddare zaizo gaida Abba.” Sallamar da suka jiyo a tsakar gidan ce ta katse musu maganar da suke. Hajiya ce ke fad’in. “Wanake gani haka kamar Affan.” Har rige rige ake tsakanin zuciyar Ummi da Asiya wajen bugawa kafin suka maimaita sunan.  “Affan.” “Chab.”  Ummi tafad’a tare da ficewa wajen dai dai lokacin da zai zauna. Bai kai ga kallon ta ba Asiya taja ta cike tare da fad’in. “Ke Ummi me yashiga kanki, tijara zakije kiyi masa ko me?.” “Wallahi zagen sa zanje nayi nasa shi yafita daga gidan tunda bana ubansa bane?.” “Shikenan kina numai kinji haushin watsar dake da yayi.” “Bangane ba Asiya.” “Nitsu ki fahimce ni, ai tunda kika yazo bayan yadawo to da alamun akwai abinda yakeso, to da wanan zakiyi amfani kici uban shege sanan ki watsar dashi.” “Taya bangane ba?.” Ummi ta tambayi Asiya. “Kinyi wanka ko bakiyi ba?.” “Nayi.” Ummi tabata amsa baki asake kamar sha sha sha. “Tashi ki d’au wanka d’an ubansu nima aramun doguwar riga.” Tashi Ummi tayi ta d’akko musu kayan cikin yan mintuna suka shirya, sun tsala uban kyau ko wacce rik’e da jaka suka fito. Hajiya dake zaune ce takalli tare da cewa. “Ni Saliha ina kuma zaku haka?.” Affan da tunda suka fito idan sa ya sauka kan Ummi,  a hankali k’asa k’asa yake kallonta. Asiya ce tayi saurin cewa. “Zamuje Gidan anty nafisa ne zancen anko.” “Ankon wa kuma?.” Hajiya ta tambaya dan ita bata harbu jirgin su ba. Dariya sukayi mai cike da aji ba tare da sunce komai ba. “Ummi wai bakiga Affan ba.” Anzo wajen da Asiya ta fad’awa Ummi, kallonshi tayi sanan tace. “Waye shi?.” Kama baki Hajiya tayi sai yanzu ta d’ano jirgin nasu. Shikam Affan jin maganar yayi kamar saukar aradu wai tambaya take waye shi. “Dr Affan fa.” Hajiya ta k’ara fad’a, Asiya ce tai saurin cewa. “Oh wai Doctor Affan d’inan.” “Shi Asiya har kun mantashi kenan.” Dariya sukayi sanan Asiya tace. “like wanda kace anmasa Engagement da Ummi ko?.” “Like.” Affan yafad’a a ranshi yana k’ara mamakin irin girma da kyan da yan matanan sukayi sanan gashi ko ganeshi ba suyi ba ita gwanar tashi ma ko magana bata iyawa Dariyar Ummi ce ta dawo dashi daga tunanin da yake sanan tace. “Dr Affan how far me yakawo ka kuma?.” A hankali ya furta.  “Tafiya da Matata.” Page [41&42] Dariya suka tuntsire gaba d’aya dai dai lokacin kuma wayar Ummi tayi Ringing, d’agawa tayi tare da fad’in. “Hello Babe.” Da sauri Affan ya runtse idonsa domin ji yayi kamar ta buga mai abu akansa. “oh you’re outside already.” tak’ara fad’a sanan kuma tace “okay gamu nan.” wanan duk shirin Asiya ne wanda kuma suna da tabbacin komai yayi yanda yakamata. “Hajiya sai mundawo.” Ummi tafad’a batare da sun jira cewar ta ba suka fice. Da gudu suka shige gidan su Asiya sabida kar tsautsayi yasa ya biyo su yaga inda suka shiga. “Hajiya zan huce.” “Tun yanzu Affan?.” “Eyh Hajiya daman nazo na gaida ki ne.” “To shikenan Affan nagode Allah yayi albarka.” “Amin ya Allah ga wanan tsaraba ce.” yafad’a yana mik’amata tulin kayan da yazo da su. Ko a waje bai gansu ba hakan ya tabbatar mai da Saurayin nata yatafi dasu,ko da yakoma gida bai boyewa Hajiya Balki komai ba  da yafaru a gidan. “To yanzu Affan komene yafaru laifin kane, yarinyar nan bawani sonka take ba tunda akayi muku baiko kaita hulak’anta ta, to yanzu gashi har ta tsayar da wani kuma kasan ta da taurin kai tun tana k’arama ba abune mak sauk’i zaisa ta karb’i auren ka akaro na biyu ba.” “Amma Mom nima da bana sonta sai yanzu kuma ai already anyi mana engagement.” “Affan engagement fa ba aure bane, ana iya sokeshi ko wane lokaci.” Tashi yayi ya huce office d’in Abban shi.Sai da yasan yayi duk yanda zaiyi wajen tunzura daddyn shi akan maganar auren sanan yabar office d’in. ************ “Gaskiyya Asiya bansan brain d’inki yafi nawa jaa ba sai yanzu Wallahi Allah.” Dariya Asiya ta fashe da ita sanan tace.  “To Ummi ai da nabarki naga hauka kike shirin yi mana to ina dalili.” Kirani Nawfal ne ya shigo wayar Asiya, da sauri taja wayar tare da cewa “ ke ya zamuyi da Nawfal.” “Ni Wallahi Asiya bansaniba kawai mu fad’a mai gaskiyya.” “Gaskiyyar me Ummi wace k’arya mukai mai?.” “To ni bansaniba.” Ummi tafad’a tana cire kayan jikin ta, daukan wayar Asiya tayi tare da karawa a kunne. “Ranki ya dad’e na iso fa.” “To shiknan bari nazo.” tafad’a tare da kashe wayar sanan ta kalli Ummi. “Idan nakiraki sai ki fito.” “To kifara dubawa kiga wancan d’an rainin hankali yatafi dai ko.” “Ni kinga har na ma manta.” Asiya tafad’a tan ficewa bayan tasa Hijab domin a ganin ta wanan kwalliyar bata kamata taje masa da ita ba. Tsaye yake jikin motar shi tasame idon shi a rufe,  k’arasawa tayi tare da yin Sallama, amsa ma ta yayi tare da cewa. “Ban takura ki ba ko?.” Murmushi tayi sanan tace “Wace takura kuma?.” “Nasaki fitowa akan damuwa ta.” “Uhm ba wani nan.” Dogon numfashi yaja sanan yace. “Asiya dan Allah fad’amun gaskiyyar komai karki boyemun.” “Duk abunda zai fito daga bakina zallan gaskiyya ce sai dai ba lallai tayi maka yanda kakeso ba.” “Ina jinki Asiya.” “Nawfal tun a farko ka nuna kanason Ummi Amma bata amince ba, ganin yanda kake nuna soyayya yasa nake k’ok’arin nuna mata kyawawan halayenka ko Allah zaisa taso ka, to kasan so shiyake ganin guri bawani ke gane mai ba.” “Hakane Asiya go straight to your point.” “Nawfal har a yanzu Ummi bataji zata iya baka ragamar rayuwarta ba, bawai dan baka da kyawawan hali ba ko kuma baka kaiba, kawai har yanzu zuciyar ta bataji zatayi naam dakai ba.” Shiru yayi for atleast 10mins sanan yace. “Shikenan Asiya nagode sosai da sosai, Nasan kinyi duk abinda yakamata Nakuma gode Allah yayiwa Rayuwa albarka yabaraki kema da Mansur.” Dariyar yak’e tayi sanan tace. “Amin tho amma ba mansur d’in ba.” “Oh shima bakiji zaki iya bashi ragamar rayuwar ki ba?.” “Nawfal Ummi fa ba iya ta tace bazata iya baka ragamar rayuwar ta ba, nice naga haka, sanan shi Mansur ai akwai dalilin daya ja haka.” “Asiya ai bakice mun Ummi ta fad’a ba sanan shima mansur d’in zan iya jin dalilin.” Shiru tayi alamun bazata iya fad’a ba. “Tom shikenan Asiya nagode.” “Shikenan Nawfal Allah yasaka da Alheri.” Daga haka ya shige motar shi ya huce, itama ta koma gida, gaba d’aya takwashe duk abinda yafaru tasanar da Ummi sanan ta d’ora da cewa. “Wallahi Ummi bakiga yanayin sa ba abun tausayi.” “Nasani Asiya Amma meyasa baki fad’a mishi dalilin rabuwar ku da Mansur ba? kika sani ko sonki yake.” “Allah ya kyauta.” Kawai Asiya tafad’a domin batasan me zatace ba. ***************** Yau ne Ranar da za’ayi wa Zainab Babbar tiyata wacce take sirad’in ko rayuwa ko mutuwa.   Gaba d’aya Tun safe Master yakasa zaune yakasa tsaye,  yana zaune kusa da zainab akan gadonta. Zainab ce ta kalleshi ya sunkuyar dakai alamun yana wani tunanin sanan tace. “Mijinaaa.” A hankali yad’ago kai yakalle ta batare da yayi magana ba.  “Dan Allah ko bayan Raina na dinga kasancewa cikin ranka, kar kamanta dani da huri.” “Zainab ki daina fad’in haka ba mutuwa zakiyi ba Insha Allahu zaki tashi.” “Kasani idan namutu a yanzu ba laifi na bane Allah ne ya amshe ni dan Allah ka kula da Abinda ke ciki na domin nasan ba lallai bane shi yatafi sabida a yanzu yakai wata 7.” Azabure ya d’ago ya kalleta tare da rik’e hannunta. “Zainab daman na fad’amiki ciki ne dake daman amma kika ki yarda kikace dani ciwon ne.” “Nima sai a zuwan mu asibitinin Dr Shiraz yasanar dani kuma yace za’acire d’an cikin kafin ayi aikin.” “Zainab insha Allahu zaki tashi za’afito dake lafiya.” “Ya maganar tura iyaye wajen Mahaifin Ummi.” Damamaki yabita da Kallo sanan yace. “Zainab wai bakya ta lafiyar ki ta zancen Aure na kike, Zainab zan hakura da turawa har sai amfito dake daga theater munsake magana.” “A’ah yaballabai katura.” “Zainab bazan turaba nagama magana.” Shiru ne yabiyo baya na tsahon mintin kafinan yatashi yashiga toilet. Page[42&43] B’angaren Ummi kam tun safe take jiran kiran Master Amma shiru m, har suka zo tafiya airport tawowa da Yaya Umar. Gaba d’aya hankalin ta baya tare da ita yanaga Tunanin Master har suka k’arasa cikin airport d’in. Bawani jira sukayi ba jirgin su Yaya umar d’in ya sauka, dukkaninsu suka nufi wajen fitowar su kowa fuskar shi d’auke da fara’a. Kyakyawan matashin dake tawowa, ya d’auki hankali duk wata mace dake wajen, kallo ya koma kanshi hatta su Ummi da Asiya ido suka zuba mai.  A hankali yake taku cike da nutsuwa, gayu da kuma izza, taku yake na cikakkun maza, masu kwarjini.  Duk irin kyawun Master dasu Ummi ke fad’a bai kama ko k’afar wanan matashin Saurayin ba. “Nikam Ummi wanan kamar yaya fa.” Asiya tafad’a tana kallon yanda yake tunkarusu. “Ni banga kama ba amma dai gashinan yana yin inda muke.” Murmushin da Yasakar musu ne yasa Asiya daka uban tsalle tare da fad’in. “Yayahhhhh.” Tayi kanshi da gudu tare da rungumeshi, shima kuwa ya rungume ta tare da fad’in. “I missed you lil.” Cikin sasannayar murya dake fitar da kowanne harafi na turanci. “i Missed you more Yaya.” Cigaba da  tawowa yayi hankalin yan mata nakasan su Mussaman da sukabi Asiya tace Yaya, dawasu har sunfara jin haushin ta sunyi tunanin Saurayin tane ko mijin ta. A haka yak’araso har inda Ummi take, Kallon ta yayi sanan yace. “Masha Allah yara duk kungirma, ina mai gidan nake.” Dariyar yak’e Ummi tayi domin tun zuwan shi wani abu ya mak’e mata arai sanan cikin rawar baki tace. “Batare muke ba.” Dariya Asiya tayi sanan tace. “Ni baka tambayi nawa mijin ba?.” “Ke ai nasan bakiyi Aure ba.” Yafad’a suna cigaba da tafiya zuwa inda motar su take. “To ita wayace maka tayi Aure?.” “Ai da zantafi nasan tana relationship da Master yake kowa and nasan is hardly su rabu bayan wanan soyayyar.” “Basu rabu ba Yaya amma har yanzu basuyi Auren ba.” Asiya tafad’a dai dai lokacin da take bud’e masa boat domin su sa akwatin shi. Kallon Ummi yayi sanan yace. “Ummi gaskiyya tafad’a.” Ummi data kasa sakewa ce ta gyad’a kai alamun Eyh. Sai da suka shiga motar sanan yak’ara cewa. “To yanzu yaushe ne Auren.” “Yaya kacika tambya ko so kake a had’e da naka auren.” “Kawai ina mamaki ne, amma i know definitely something happened.” “Nothing happened yaya gashi ta koma ma kamar kurma da sai tabaka labarin.” Ummi dai batasan meke damun ta ba, hakan yasa ta zab’i yin shiru, har suka k’arasa gida. Mutane sun hallara A Gida anata murnar dawowar Yaya Umar, Ummi dai tarasa meke damunta, amma ta lak’ana hakan da rashin jin Mastet da tayi tun safe. A hankali ta salub’e ta koma nasu Gidan,sanan tasamu kiran Master dake zaune bayan shiga da Zainab d’akin theater. Yana ganin wayar amma yakasa d’auka gaba d’aya tausayin Zainab yacikashi, yana ganin kanshi mai butulci, wanda yayi watsi da rashin lafiyar ta ya shiga neman Ummi. Haka taita kira baisami d’auka ba ganin tayi masa kira sama da biyar, sanan ta hak’ura tare da kwantawa. *********************   “Affan nayi magana da Mahaifin yarinyar nan amma yanuna baisan da wanan magana ba, wai su sunjanye baikon su.” Hajiya Balki ce tayi saurin cewa. “Toh Amma Alhaji haka zaka tsaya, bazaka nuna mishi power ba?.” Murmushi yayi sanan yace. “Hajiya naso nayi haka amma Alhaji idi yahanani sakamakon ko da anje kotu basu da wani abu da za’a iya, tunda basuyi auren ba.” “But Daddu gaskiyya ni inason ta.” Affan yafad’a, kallon shi Abban yayi sanan yace. “Kana sonta ka tafi kabarta na tsahon shekara Hud’u?.” “Dad komene yafaru ya riga yafaru kawai ni kayi magana inason ta.” “Daman fa Alhaji zance a hak’ura bai taso ba ainaga bamu amshi kud’in auren ba ko?.” Hajiya Balki tafad’a domin ita duk abinda d’anta keso tofa tana sonshi. “Hajiya ni nagama magana, kuyi duk yadda zakuyi idan wani abu yataso sai ku nemi ni.” Abba yafad’a tare da tashi, Affan ne ya matso inda take tare da cewa. “Mom yanzu mene abun yi please?.” “Affan karka damu yau zanje nasamu mahaifiyar ta.” “Okay Mom please.” ******************************  Hinin ranar Ummi bata samu Master a waya ba, abinda ya matuk’ar tayar mata da hankali tare da sama damuwa, baya ga yanayin ta datake ji badai dai ba.   Asiya ce dake zaune gefe tace. “Wai yanzu Ummi mene abunyi ko tashi zakiyi muje mune meshi.” Dariyar yak’e Ummi tayi sanan tace. “Lallai Asiya sai kace yarinta zan koma neman master, ai sai dai yadawo da kashi.”  Dariya Asiya tayi sanan tace.  “Lallai yanzu nasan kinzama mutum.” “Au da ba mutum bace.” Ummi tafad’a tana nuna kanta, dariya Asiya tayi sanan tace.  “Eyh da muna mutum ce yanzu kam nasan ko da Master yak’ara tafiya ba abinda ake fata ba, bazaki damu ba, ko shiga wani hali.”  Dariyar tayi sanan tace. “Uhm ayi sha’ani kawai, amma banjin zank’ara zurmawa a soyayyar har na k’arasa Kuskuren yin TUDU AKAN KWARI wanda har yanzu yake bini shekaru Sama da biyar.” K’arar shigowar text a wayar Asiya ne yakatse musu hirar tasu, dauka Asiyan tayi bayan tagama karantawa sanan tace.  “Ummi bansan mai Nawfal yake nema ba fa, wai yanaso muhad’u muyi magana.” “Uhm koma mene zamuji amma nasan Nawfal sonki yake.”   Ummi tafad’a tana d’aukan wayar ta tare da kunna data ko zata sami messages daga Master. “Sona fa, shi yanzu har yayi healing daga rashin ki.” “Ummi bakisan ana iya canja so daga wanda kakeso zuwa wani dayake kusa dashi ba?.” “Bansani ba sai a bakin ki kuma banyarda ba.” Dariya suka fashe da ita sanan Ummi tace kice masa yazo yau, kinga ko ma mene sai kiji. Danna wayar tayu tamayar mai da reply. ************************  Anfito da Zainab daga theater kuma ana saran samun nasara.  Dr Shirza ne ya kalli Master dake zaune a cikin office d’in shi.  “Mr Mukhtar Inaso kafad’amun komai dake gaskiya.” “Game da me fa doctor?.” “Game da matarka.” “Okay inajin ka.” “Dafarko dai anyiwa Matarka aiki kuma muna fatan samu nasara, matar ka na buk’atar kulawa ta gaske a yanzu, irin kulawar da za’ace mutum yana tare da ita bbu motsi ko da na yan sakanni.”  “Banganeba Doctor?.” “What i mean is matarka na bukatar wank a kusa da ita wanda zai dinga kula da ita ko yaushe, kamar mutum biyu yanda ko d’aya bayanan d’aya na nan.” “To ni likita me nake da bazan iya kula da ita ba har haka?.”  “Bansani ba amma nasan dai ba kowanne namiji bane zai iya wanan.” “To ni zan iya insha Allah.” Master yafad’a cike da kwarin gwiwa. “Allah yasa.” Dr shirza yafad’a sanan yad’ora da cewa. “Abu na biyu shine akwai damuwar dake damun matarka a zuciya wand tak’e boyewa.” Shiru Master yayi yana tunanin daga baya kuma yace. “Dr i don’t think akwai abinda Ke damun Zainab har ta boyemun.” “Bakwa ko wata irin magana ko kai zakai wani abu bataso ko kana hanata wani.” “Magana daya dai nasan zan k’ara Aure amma kuma tanaso.”  Dariya Doctor Shiraz yayi sanan yace. “Dan tace maka tanason shine kake yin zancen, mata zasu iya nuna maka suna son abu kuma ba haka bane, bare ma zancen kishi, idan badamuwa kabar maganar zuwa nan da sati d’aya idan jikin ta yayi k’wari.”  Shiru yayi tabbas yanason magana da Ummi amma kuma lafiyar matarshi ce abu nafarko,yasan Ummi mai fahimtar shi ce.  Daga haka yatashi yakoma d’akin da aka mayarda Zainab sai kuka jaririn ta dake wata 7 ansa shi cikin kwalba. *****************  Da misalin karfe 4 na yamma Hajiya na zaune tsakar gida sai kuma Goggo daga gefe tana faman b’are wake.  Sallama hajiya Balki tayi tare da shigowa, da fara’a Hajiya ta amsa sallamar tare da fad’in.   “Balki yau ke ce a gidan maraba.” Daga tsaye Hajiya Balki ta amsa da. “Nice zuwa nai akan maganar Ummi da Affan.”  “A’ah to shigo ciki mana.” Hajiya tak’ara fad’a tana tafiya. “Bafa sai nashiga ba nazo sanar daku cewar za’akawo kayan lefe gobe.” Dariya Hajiya tayi sanan tace “Wane kalan kayan lefe kuma?.” “Kayan lefe na Aure sanan sati d’aya zamuzo dashi.”  “Da ke a garin jahilai kika taso ko me?.”    Goggo tafad’a tana mikewa. “Ke matar nan na fahimci ba hankali a tare da ke, ko a zamanin turawan mallaka ba’ayi haka ba balle yanzu a zamamin yancin kai da kai.”  Goggo tak’ara fad’a, Hajiya kam cewa tayi. “Balki Affan yariga da yayi wasa da damar shi, a yanzu Ummi tafi k’arfin na tan k’wara ta kamar baya, idan Affan ya nemi soyayya a wajen ta, tabashi madalla, idan kuma ta hana shikenan, ba zamuyi mata auren dole ba.”  Tsaki Hajiya Balki tayi sanan tace. “Wallahi Baki isa ba, kuma dani kike zancen.” Daga haka tafice suka suka shige d’aki kamar komai bai faru ba. Page [44&45] _________Bayan Sati guda_______ A yanzu sati guda kenan Ummi bataji daga Master ba, tayi fushi ta fusata har k’arshe ga Abba ya matsa mata kan ta samu tafitar da wani.   B’angare Asiya kam sun dai dai ta da Nawfal an saka musu rana wata biyu masu zuwa. Soyayya suke tare da mutunta juna, inda Ummi a wani b’angaren take ganin kamar tayi biyu babu.  B’angaren Hajiya Balki a sati d’ayan nan tayi duk yansa zatayi amma duk inda taje sai ace bata da wanan damar, Affan kam yadamu matuk’a akan lamarin Ummi.   B’angaren Umar kam hutun kwana biyu, yafara zuwa interview da manyan campanunawa damam tun yana chaina yafara applying hi  A yanzu ya zab’i wani babban campanu guda d’aya da suka bashi babban muk’ami  ***************   Umar ne cikin shigar k’anan kaya da k’ara fito da asalin kyawun shi, kai tsaye gidan Hajiya ya nufa, inda yasame ta zaune ita da Goggo data dawo gidan da zama.  Sallama yayi musu tare da gaidasu,Goggo cike da fara’a ta amsa haka ma Hajiya. “Daman Hajiya nazo ne muyi magana da ke,domin bansan ta inda zanfara da Mama ba shiyasa nazo nayi dake a matsayin ki na Uwata.”  Har cikin ran Hajiya take jindad’in yadda Umar ke girma mata, ita daban dan kar ace tayi son zuciya ba ma da Ummi zafa nemawa auren shi. “Shikenan Umar zamu iya yi anan ko sai munshiga ciki.” “A’ah Hajiya muyi anan d’in.” “To ina jinka.” “Hajiya maganar Gaskiyya guda d’aya itace inason Ummi, nanu nawa Mama alamu amma tace babu ruwanta wai naje nasami Ummin dakai na hatta itama Asiya abinda take cewa kenan, kuma ni a iya bincike na Ummi babu wanda ke zuwa wajen ta, bansani ba ko kune kukayi mata miji.” “maganar gaskiyya a yanzu bamuyiwa Ummi miji ba, kuma babu wani dake zuwa wajenta, sanan ni shawarar da zanbaka itace kasami mahaifin ta da maganar tunda dai shawara kazo ne ma.” Hajiya tafad’a ranta fari fat. “Idan kuma bazaka iya ba ni sai nayi mai maganar.”  Goggo tafad’a itama nata ran fari k’al. Abba da yashigo ne yace. “Ai ba ma sai an tambayamun ba.” Yafad’a yana shigewa d’akin Ummi wacce kijin su tinda ga farko, ita bata masan me take ji ba, domin bazata ce tana farin ciki ba sanan kuma bazata ce tana bak’in ciki ba, ita kanta tasan samun Yaya Umar sai dace. “Ummi kinji abinda dik suka tattauna, kuma banaso nayi miki dole, amma a shawrar da zanbaki karki karbar wanan zab’in.” “Abba na amince Allah yasa hakan alheri ne.”  “Amin Ummi Allah yayi miki albarka.”     Fitowa yayi sanan yace da Hajiya. “Kiramun Maman a waya kice ta shigo nan.” Kiran Mama Hajiya tayi bayan mintina sai gata tashigo tare da Asiya. Bayan kowa ya zauna ne Abba ya kalli Mama sanan yace.  “Umar yazo mun da magana wacce kuma babba ce akan yarinya Ummi .” “Tom muna jinka Alhaji.” Mama tafad’a duk da tasan mecece maganar. “Umar yazo akan yanasom Auren Ummi, kina da masaniya?.” “Eyh ina da masaniya Alhaji, amma Ummi y’atake a wajena, nasan komai akan rayuwar ta, har mutum da takeso nasani, sanan a baya angwada yimata dole amma ba a haifi d’a mai ido ba, shiyasa na hanashi sanar daku.” Abba baice komai ba sai kiran Ummi da yayi, wacce tafito jiki ba kwari. “Ummi kinji maganar da muke tattaunawa?.” d’aga kai tayi sanan tace. “Abba naji.” “Me kika yanke game da maganar.” “Abba na amince zan auri Yaya Umar.” Da matuk’ar mamaki kowa yad’ago yana kallonta harda kuwa Asiya. “To kowa yaji dai, Allah yasa albarka.” Amin kowa ya shiga fad’a kansa tsaye. *********** Bayan kwana uku. Abu kamar wasa Ummi ta daina shiga gidan Mama sai dai Asiya tashigo. Sunsami magana da Yaya Umar, tare da fahimta mai k’arfi, sanan kuma Ummi bazatace batason Yaya Umar ba, domin a kwana ukun nan yarage mata kaso mai nauyi nason master da damuwa. Mujuya bangaren Master. Zainab tatashi sanan kuma duk wata kulawa yana bata, duk da duk rabim tunanin shi naga Ummi da a yanzu baya samun ta a waya.  Tunda Zainab tatashi bai maganar Ummi ba, da farko idan tayi banza yake mata har ta daina, tabbas taji dadi hakan, ko da kuwa bai janye ba amma ya daina nunawa a gabanta. Soyayya tskanin Nawfal da Asiya kamar wasa sai karfi takeyi, an sanya lokacin Auren su da nasu Umar Sati hud’u. Kowanne b’angare soyayya suke zubawa mai tsafta domin shima Yaya Umar kwararreni a b’angaren soyayya. Lokaci d’aya Ummi tayi blocking numbers d’in Mastet daga bayama ta canja sim. Master yayi tryiing yafi a k’irga amma bata tafiya, sai dai Zainab tayi kwana goma a asibiti sanan yasamu fitowa, sakamakon zuwan rogeet wanda shima a yanzu yasamu nashi rufin asirin, sosai da sosai. “Baba inason zuwa wajen Ummi Wallahi.” Kallon Master Rooget yayi sanan yace. “To mai kake jira muje mana.” Motar Rogeet suka shiga kai tsaye suka nupi gidan su Ummi. Dai dai lokacin  da Ummi da Yaya Umar suka zasu fita zuwa kasuwa, fiowarsu daga gidan  Hajiya yayi dai dai da parking d’in motar su Master. Sai dai Ummi takalli motar amma bata gane ba sabida ba acikin mototicin Master domin shi number d’inshi sunfita daban. Master kam bugun zuciyarshi ne ya tsaya na lokaci guda domin ko makaho indai zai kalli Ummi da Yaya Umar yasan akwai soyayya a tsakanin su. Har su Ummi suka bud’e mota suka shiga Master bai iya cewa komai ba. “Master yaushe rabon ka da Ummi.” “Sama da kwana goma kuma babu kira babu text, kuma dai dai lokacin da take jiran iyayena su sami nata.” “Amma kasan wnn shneYayan Asiya K’awarta wanda yatafi k’asar waje?.” Girgiza kai Master yayi sanan yace. “Banganeshi ba gsky.” “A iya tunani rashin ka yasa Ummi ta bashi dama, tabbas a yanzu Ummi tayi give-up akanka Master.” “Nagani Wallahi, kuma nima a yanzu lokaci ne da zan duk’ufa akan Raywuar Zainab da abinda ta haifa.” Daga haka Su Master suka juya zuwa Asibiti Page [End] B’angaren Su Ummi kam cike da soyayyaa suka je kasuwa suka siyayyar dazasuyi har suka dawo. Akwana a tashi Gashi yau Allah yakawo mu ranar da ake daurin Auren Su Ummi da Asiya, Tunsafe Ummi ke faman kuka wanda babu wanda yasan na mene,anyi rarrashin har angaji. Itakuwa Ummi tana tunanu duk wata wahala da tasha a rayuwa sabida Master sai gashi k’arshe bashi ne mijin taba, lallai alamarin Allah da girma yake. Tana wanan tunanin Yan d’aurin Aue suka dawo tare da shaida an d’aura auren Ummi da Yaya Umar, Asiya d Nawfal. Shikenan komai yafaru ba kuma yadda aka iya da hukuncin ubangiji. Ummi ta d’auki aniyar yin biyayya ga mijinta iyaka cin yinta, domin tabbas a yanzu Master ba ma harramin ta bane, zata cirewa rayuwarta gaba d’aya tunanin shi. Wanan kenan Haka b’angaren Master ya d’auki alwashin cire Ummi da duk wani tunanin ta a rayuwar shi, ya kuma yardar wa kanshi komai nufine na ubangiji, duk wata tataburza da suka sha shida Ummi a karshe ita d’in ba rabon sa bace. Zainab na zaune yashigo cikin shiri, kallon ta yayi sanan yace.  “Zaki iya shiryawa mufita unguwa.” “Zan iya mana, jirani.” Tafad’a tana mik’ewa, yan mintina kad’an tafito cikin shirin ta, tayi kyau abinta. Sai da suka fara biyaea ta wani Babban shop da ake sai da kayan electrics, sukayo Ummi mahaukaciyar siyayya, da mamaki Zainab take kallonshi wanan kayan ko na waye oho?. fitowar su kenan bayan angama zuba kayan a yar k’urk’ura su kuma suna k’ok’arin shiga tasu motar suka ji ana cewa. “Dan Allah ku taimaka mana da Abinda zamuci.” Zainab ce ta tsaya tana k’ok’arin bud’e jakarta ta zaro kud’i, shikuma Master ya juyo, idanun sa ne suka sauka akan matashiyar buduruwa mai suffar tsofaffe sai kuma k’aramar yarinya. Kallon sani yakeyi wa matar haka itama, can kuma matar tace. “Maater.” Kallonta yak’arayo ko zai ganeta amma yakasa. “Halima ce.” “Wace Haliman?.” “Halima gidan su Asiya makwafciyar Ummi.” Sai a lokacin Master yaganeta. “Me kuma kikeyi anan?.” Nan Halima tafara bashi labarin irin halin da suke ciki ga kuma yarinyar ta sanan Anty na wani kango a ajiye sai sunyi bara suke kaimata. “Lallai duniya abun tsoro ce, Yaran da kuka gama bi da sharri gasu can yau ake auren su kuk gaku kunk’are a hulakance.” Da mamaki Halima tace,  “yau ake auren Ummi da Asiya, duk asirin Da anty tayi na karsu Auro gashi yagama k’arewa.” “Asiri kuma?.” Master ya tambayeta, cikin kuka halima tafara fad’in. “Ai Aunty ce tayi Asiri akan kar su Auro Asiya tak’i samun miji da huri sanan Ummi aka hana auren ku sanan aka cirewa Affan tunanin ta a tafiyar da yayi.” “Duk abinda yafaru yana rubuce a k’adaddarmu amma haka yafaru ta sanadiyar ku, kuje Allah yasa rayuwa ta sa kuyi hankali, dukda yanzu gashinan tajuya muku.” Kuka Halima tak’ara fashewa dashi, sukuma sh Mastet suka huce. A cikin mota kam Zainab ce ta kalli Master sanan tace. “Yanzu yau ake auren Ummi da kuma wani bakai ba?.” “Gashi kinji.” “To su wayanan d’insu Waye?.” Zainab tak’ara tambayar shi. “Zainab A labarin Asiya da nabaki nace miki akwai kishiyar Mamanta da yarinyar ta, to itace wanan.” “Amma basu yiwa kansu Adalci ba.” “To gashinan rayuwa tafad’a musu ai.” Maater yafad’a dai dai lokacin da suka shiga layin su Ummi. Da mamaki mutane suke kallon yar k’urk’ura maj cike da kaya ta tsaya dai dai gidan su Ummi. Master ne yace da Zainab. “Ki sauka kifara shiga.” Tom tace tare da fitowa, daga cikim gida Zainab ce tashiga da sallama, bayan ra kuma masu shigo da kayane. Anty Nafisa dake faman kawo abinci ce ta tare da cewa. “Maraba sannu da zuwa.” Cike da wayewa, halin Anty Nafisa tabbas ya burge zainab. “Yawwa Amaryar na cike ko.” “Ey wancan d’akin zaki shiga.” Anty Nafisa tafad’a tana nuna mata d’aki. Tom zainab tace sanan ta kalli masu shigo da kayan tace. “Ku ijiye kayan anan t’sakar gidan.” Sana tahuce, Ummi na zaune cikin d’akin da wasu kawayen ta yan uwan su, Da gefe kuma Asiya ce wacce take shiri domin ita yanzu za’azo tafiya da ita. Da sallama zainba tashiga sanan tasamu waje ta zauna bayan sun amsa mata tare da bata izini. A kallon farko Zainab ta gane Ummi hakan yasa ta kalleta tare da cewa. “Sunana Zainab, Matar Mukhtar.” Wani irin dum Ummi taji a k’irjinta amma cike da dakewa tace. “Sannu Zainab.” “Yawwa Amarya, Allah yasanya Alheri.” “Amin Amin.” Ummi tafad’a taba kallon wata a cikin k’awayenta sanan tace. “Kice ma Anty Nafisa akawo mata abinci.” “Ai tare muke dashi yana daga waje.” Zainab tafad’a tana kallon Ummi, wani irin abu Ummi taji da kyar ta iya cewa. “Allah sarki nakam gode sosai.” Asiyace tace. “Ai kya tashi kije ku gaisa dai ko.” Ummi batace komai ba ta tashi tasa mayafin ta tare da ficewa. Mutanen dake tsakar gida nata mamakin uban kayan da akw zubewa. Dan harsu Hajiya da Gaggo sunfito, da kallo suka bi Ummi da tafito, itama da mamaki take kallon kayan. “Ke wanan wace?.” Anty nafisa tafad’a cikin kasa kasa da murya. “Matar Master ce.” Ummi tafad’a hankalin ta na kan Uban kayan da aka zube. Komawa tayi tare da cewa Asiya  “ zo ke.” Tashi Asiya tayi tafito itama mamakin ne ya hanata magana dan tasan wnn aikin Master ne. “ chab aiki ga mai k’are ka, fita kika dame yazo.” Asiya tafad’a tana tura Ummi, fita tayi, ta hangeshi ya kafe k’ofar gidan nasu da ido, sai da taji wani abu yabi jikinta lokacin da suka had’a ido. A hankali tak’arasa inda yake tare da cewa. “Gani.” Murmushi yayi sanan yace. “Yanzu dai kin girma kinyi aure yakamata ace kidaina wanan abun dakike.” “Me nake?.” “Wanan abun mana.” “Kaga ni ya akayi sauri nake.” “Ai bance ba sauri kike ba amarya.” “Uhm.” tafad’a tana cuno baki. “Ummi kinga yanda kaddara ta tsara mana ko?.” Shiru tayi batace komai ba, shikam yad’ora da cewa. “Ummi nasan kin soni, nima kuma na soki, ina miki fatan Alheri a rayuwar ki ta gidan Aure, Allah yabaki zaman lafiya da mijinki, sanan nima zan rik’i matata tare da fatan zaman lafiya da ita.” “Allah Yabaku zaman lafiya nagode.” itama tafad’a a hankali “Ga kaya nan sai ki d’auki wanda zaki d’auka kibawa Asiya sauran itama kice ina mataa fatan alheri.” “Mungode Allah yak’ara arziki.” “Amin yah Allah, kice da Zainab tafito idan kinshiga.” Bata iya cewa komai ba ta shige gida jiki ba kwari. ko acikin gidan ma bata iya cewa komai ba, sai  sak’om Master da ta fad’awa Zainab. Sai bayan Zainab ta tafiti sanan tabasu labarin komai. Daga haka a cigaba da biki har aka kai amare Gidan Yaya Umar makeken gidane da ya tsaru ta kuma k’awata da ado. Su Ummi any bake bakw a cikin gida, ana jiran shigowar ango da abokansa. Bajima suka shigo shida abokansa, bayan sunyi yar Nasiha sanan suka tafi aka bar Amarya da kuma ango. Yaya Umar ne yace da Ummi. “Amarya ran gida.” Murmushi tayi daga cike batare da tayi magana ba. “Ummi da farko babu abunda zamuce da Allah sai godiya, da yanuna mana wanan rana, Ummi akwai abinda nakeso kisani, bawai nafara sonki bayan dawowa ta daga Chaina bane, nafara sonki tun randa nafara girma nafara sanin mene ne so, sai dai lokacin dakika girma kikai nafara nunamiki so, kika fad’a wata soyayya mai girma, Ummi na fuskanci yanda kike matuk’ar son gayen hakan yasa na hak’ura ba tare da na daina sonki ba,  a takaice Ummi na shafe duk shekarun da nayi a chaina tare da sonki. babbar damar da nasamu  shine dawowa na tarar dake babu aure, a lokacin nasawa raina insha Allahu zank’ara komawa soyayyarki sai dai kuma nasake samun ki tare da shi wanan mutumin, kuma nasan indai nafito miki da wanan maganar zaki dubu Mama da Asiya ki amince kamar yadda nasan Hajiya da Alhaji zasuyi, Ummi naciga ba bibiyar duk wani abu naki har nasamu labarin sab’ani dakuka samu wanda yazama hanyar da kusanto da buk’ata ta, bansaniba Ummi ko kina fushi d hakan ko kuma na tukureki Amma kisani ina sonki.” Jikin Ummi yayi sanyi sosai, a hankali ta furta “ nima ina sonka Yaya Umar.” “Da Gaske Ummi?, yaushe kika fara sona.” K’asa tayi da kanta sanan tace. “Tun ranan da mukaje taro ka a airport nafara sonka, sanna kuma a lokacin na yardarwa zuciya ta nadaina son Master.” “Naji dad’i nagode da soyayya Ummi.” “Uhm Uhm Uhm.” This is the End TSOKACi _*    Tundaga wanan rana soyayya mai tsafta tafara gudana tskanin Yaya Uma da Ummi, soyayya take nuna masa mai tsayawa a rai. _*    Asiya da Nawfa suna zauna lafiya kamar dama tunda sunason junan su, suma tasu soyayar suke yi mai tsafta _*    kamar yadda d’an adam yake 9 bai cika 10 ba haka Ko sau d’aya Master bai tab’a daina son Ummi ba sai dai so ba irin na aure ba ko rayuwa tare, so na har abada a cikin zuciya _*    Anty tadawo takuma yi nadama su Mama sun hak’ura sunyafe mata, bayan kwama biyu da hakan Allah yayi mata rasuwa. _*    Bayan shekara da Auren su Ummi Allah ya albarkace ta da samum k’aruwar yaya mata guda biyu wayanda suka ci sunan Mama da Hajiya haka Asiya ta haifi na ta d’an namiji da yaci sunan mahaifin ta _*    yaron wajen  Zainab ya girma cike da tarbiya da kuma kula _*   Anty nafisa ma ta zama babbar mace da yaranta da mai gidan suna zaune cikin farin ciki _*    Akwai mutunci  sosai tskanin Master da Yaya Umar haka tskanin Ummi da zainab _*   _*   Master yak’ara Aure inda ya Auri Halima bayan ta tuba tayi hankali a hanun Mama ya aure ta, biyayya sama da k’asa takewa kowa _*   Bayan wasu shekaru kamar 20 babban zumunci ya kullo tsakanin wanan ahali inda d’an wajen Ummi ya auri yarinyar wajen Master Allah kenan Wanan shine k’arshen labarin TUDU AKAN KWARI ina fatan ku ilimantu da wanan labarin   Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah   Allah ina k’ara gode maka da kabani damar sauke wanan littafin abubuwan da mukayi dai dai Allah kabamu lada, wayanda suke na akasin haka Allah ka yafe mana. Jinjina da godiya ga duk mambobin kungiyar Taurarin marubuta writer’s association  Allah yak’ara had’a kan mu baki d’aya Nagode