[10/26/2025, 6:26 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚 🌸 'YAR MAHAUKACIYYA 🌸📚* Mallaki: Husaina S. Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚 © 2025 – Duk haƙƙoƙin mallaka na musamman ga marubuci. Group din comment banda maza ko ka shiga sai ka fita👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/BXejgVglv85CWkdVCo2qUg?mode=wwt ⚠️ GARGADI ⚠️ Wannan labari ƙirƙire ne gaba ɗaya, daga tunanin marubuciya. Bashi da alaƙa da wani mutum, gida, ko wuri na gaske.Idan wani suna,ko muhali ko abin da ya faru a cikin labarin ya yi kama da na ainihi, to hakan dai haɗuwa ce ta bazata, ba da gangan ba.Manufar marubucin ita ce nishaɗantarwa, ilmantarwa, da faɗakarwa, ba batanci ko ɓata suna ba.Duk wani hali, tunani ko ra’ayi da aka bayyana, na cikin tunanin marubuciyya ne kawai.Kar a ɗauki labarin nan da tsanani fiye da yadda marubuci ya nufa. *SHIMFIƊA* *Akwai wasu haihuwoyi da ke zuwa duniya da albarka, akwai kuma wasu da suke fitowa da wulakanci a gaba. Ita ce Sumayyah, ‘yar shekara ashirin, wacce duniya ta fara yiwa hukunci tun kafin ta iya magana.* *An haifeta a A cikin wani ƙauye,cikin gidan Malam Sule Giɗaɗo, malamin soro mai mata uku. Hauwa’u, Rabi, da Zulaihat. Duk gidan nan cike yake da tsantsar kishi, nuna bambanci da ƙyamar juna. Amma mafi talaucin su ba na kudi ba ne-talaucin adalci ne.Rabi, mahaifiyar Sumayyah, ita ce suka kira “Mahaukaciya.” Tana yin magana da kanta, tana dariya a lokacin da babu wani abu mai ban dariya. Idan ta shiga kasuwa, yara sukan jefa mata duwatsu,wanda hakan jarabtace daga Allah subhanahu wata'ala.da zarar ta fita yara zasu fara kiranta da“Ga mahaukaciyar matar Malam! Ga uwar ‘yar wulaƙantacciya!”Wannan magana ce da ta yi katutu a zuciyar ‘yarta. Duk inda Sumayyah ta wuce, idanu ke binsa da raini. A makaranta, ko a wajen mata, babu wanda bai taɓa kiranta da “’Yar mahaukaciya” ba.Uban su, Malam Sule, bai taɓa tsayawa ya kare ta ba. A wurinsa, kalmar matansa biyu ne,gaskiya. Duk abin da Hauwa’u ko Zulaihat suka faɗa, shi zai amince da shi, koda kuwa zai karya ɗiyarsa .Sumayyah tana da ‘yan uwa guda biyar maza da mata, amma babu ɗaya da yake ganin ta kamar ‘yar uwa.Sadiya, ‘yar Hauwa’u-mai zafin rai, mai kishi.Lubna, ‘yar Zulaihat-mai gulma, mai mugunta.Khalid, ɗan Hauwa’u ɗan gata, mai tsanar Rabi.Yusuf, ɗan Zulaihat mai son nuna isa Baban ɗa aguri Baba Sule.Sai kuma Amina, ƙaramar yarinya mai bin umarnin uwar.Gidan Malam Sule kamar fili ne da aka shuka tsanar Sumayyah. Koda ta yi ƙoƙari ta gyara, Daga cikin ƙauyen su, babu wanda ya taɓa yi mata kallon mutum cikakke.Rayuwa ta zama masaƙiƙiyar hanya- ƙauye da ke yi mata dariya, gida da ke yi mata tsana, uba da ya zama shiru, da mahaifiya da ke cikin duniyar da ba kowa ke iya ganinta ba.Sai dai abin da duniya bata sani ba shi ne- cikin wannan yarinyar akwai asirin da zai girgiza gari, sirrin da zai bayyana gaskiyar mahaifiyarta da wautar waɗanda suka yi dariya.Wannan shi ne farkon labarin da ke tattare da hawaye, ƙiyayya, da ƙaddara.Labarin Sumayyah, ‘YAR MAHAUKACIYYA- wacce rayuwa ta ɗora wa nauyin da bai kamata ta ɗauka ba, amma ta ƙi rushewa.* ________________free book __Page -1 A cikin Jihar Kano, tsakanin ƙananan garuruwa da ke tsakanin Bunkure da Garko, akwai wani ƙaramin ƙauye da ake kira Gidan Giɗaɗo. Ƙauye ne da yake cikin zurfin karkara, inda hayakin girki ke tashi da safe, ana jin karar sare itace da kiran Sallah daga ƙaramin masallacin.Mutanen ƙauyen su ne irin waɗanda suka dogara da noma da kiwo,rayuwarsu cike da haɗin kai da ɗan ɗabi’ar al’ada. Kowa ya san kowa, labari ba ya ɓuya. Duk abin da ya faru a gidan mutum, kafin rana ta faɗi sai ya ratsa kowane gida.Gidan Malam Sule Giɗaɗo, malamin soro wanda ke koyar da yara karatun Alƙur’ani,da yawan Almajirai,shi ne ginshiƙin addini a ƙauyen. Ya yi suna har ma aciki birane.Gidansa ne aka haifi Sumayyah, yarinya mai kyakkyawar fuska, amma an ce tun haihuwar ta, ta fito da “baƙar sa’a” saboda wasu al’amura da suka faru a lokacin haihuwarta.Cikin Rayuwar.Wulakanci da Kaddara. Kukan jaririya ya tsinke shiru a gidan Malam Sule Giɗaɗo-gidan da kishi da adawa suka mamaye fiye da komai. A wannan daren, sama ta yi duhu, iska tana kadawa kamar tana shaidar cewa sabuwar rayuwa da zata sauko duniya zata gamu da kalubale.Rabi tana kwance kan tabarma wace duk ta ya galgale, jiki ta sai rawa yake saboda ciwon naƙuda da gajiya. Amma duk cikin wannan halin da take ciki babu wanda ya tsaya kusa da ita sai tsohuwar dattijuwar da ta shigo ta iske ta tana na ƙuda haka ta yaye mayafi ta ta shiga,taimaka mata kun dai san yadda haihuwar ƙauye take babu bati haihuwa a sibitia. Daga ɗaya gefen ɗakin, Zulai ne wanda malale yake da daɓe suminti gaban ƙofar yasha fante farar wuta.muryar Zulai ce ta karaɗe ɗaki tana cewa da Hauwa’u:“Nidai Fata na kada baƙar kadarar nan ta haifa mana iri jinsin su! Dan Walhi jikina na bani wannan haihuwar sai tabi jini!.”Shewa suka yi sanan suka juya suka fita.Rabi ce ta juya idanu cikin hawaye ciki yanayi na sanbatu naƙuda ta ce.“Ya Allah, kai ne ka fi kowa sani. ka kare min 'yata!”Da haka ta rungumi jaririyar, wacce daga wannan rana duniya ta fara yiwa hukunci tun kafin ta iya magana.Sunan da Malama Sule ya sanya mata shine SUMAYYAH-bayan ta fara wayo Zulai da Hauwa'u suka fara laƙaba mata shine 'Yar mahaukaciyya hakan ya bawa samar mutane ƙauye da kiranta da wanan sunan.“Yar Mahaukaciya.”Tun tana jaririya har ta fara girma, kalmar nan ta zame mata kamar inuwar da bata rabuwa da ita.A kowanne lokaci ina ta shiga mutane ko ta wuce kasuwa, yara sukan tsayar da ita suna cewa:“Ga ‘yar mahaukaciya! Ga ‘yar Rabi wadda take tsince-tsince abola!” Tun Sumayyah na yin kuka har ta koyi yin shiru. Sai-dai shiru nata ya fi kuka nauyi.Idan ta shiga makaranta, malamai sukan nuna ban-banci tsakani ta dasu Sadiya da lubna; idan ta dawo gida, Baba Hauwa’u da Baba Zulai sukan nuna ƙyama. Uban ta, Malam Sule wanda ake kira “Malam Giɗaɗo”saboda darajarsa a gari- bai taɓa tsaiwa ya kareta ba.A wurinsa, kalmar matansa biyu ce gaskiya. Idan suka ce Rabi ta yi kuskure, to, ko da,da gaskiya ce, sai ya hukunta ta.Sai dai duniya bata san sirrin da ke cikin wannan yarinya ba.Sirrin da zai girgiza gida Malam Giɗaɗo,da kuma ƙauye, har ma da mutanen da suka sha dariya a kanta. Rayuwar Sumayyah ce za ta zama littafi mai ɗauke da hawaye, ƙiyayya, da ƙaddara amma daga ƙarshe, gaskiya ce za ta yi nasara.Tunanin da yaro ke yi na farin ciki da nishaɗi idan aka ambaci makaranta, bai taɓa zama cikin zuciyar Sumayyah ba. A wurinta, makaranta ba wurin koyon karatu ba ne- wurin ƙuntatawa ne, wuri ne da ake tuna mata da laifin da bata aikata ba.Da safe, tana tashi kafin kowa. Sai ta wanke kayan Innar ta, ta share ɗaki, sannan ta kama hanyar makaranta da littafinta guda ɗaya wanda ya ci wahalar duniya. Duk lokacin da zo wucewa ta ƙofar ɗaki Baba Hauwa’u domin fita ta kofar baya Saboda zaman Almajirai, Sadiya sai tayi mata tsaki tana sukar ta da kalamai marasa daɗi ta ce.“Ke ‘yar mahaukaciya, kar ki yi amfani da kofar nan, ki bi ta babbar ƙofa. Ba nason ganin fuskarki tana gilmawa kamar hadari fuska sai muni tsiya baƙi kamar na zunubi.” haka Sumayyah zata yi shiru ta ratse ta wuce.ta san idan ta yi magana, Baba Hauwa za ta ce tana raina manya.ko ta tsine mata tass ƙarshe ta zuga Malam ya buge ta.Koda ta yi kuka,haka Baba Zulai za ta hauta da laba'i tace ta isheta da kuka.Saboda haka tayi mata shuru ko ta ƙara mata. Haka rayiwar ta ta ci gaba.A makaranta kuwa, labarin ba ya canjawa. Lokacin da malamai suka kira sunan ta cikin lissafin ɗalibai, wasu yara sukan fara dariya wasu yara da suke kusa da ita suka tun tsire da dariya ɗaya daga ciki tace:“Gaskiya Malam, wannan ai ba ta da hankali. ‘Yar mahaukaciya ce fa.” lokaci da kalmar ta fito daga baki dayar shaida Sumayyah ta rintse ido tare da zubar da hawaye masu zafi.malamai suna fita sauran ɗaliban suka hau waƙa suna dukan benci,suna cewa:“Summah mahaukaciya! Ki yi rawa mana!”koda ta kai kara karshe laifi kanta ya koma haka aka hukunta ta. Bayan da ta koma gida kamar kullum haka ta kaiwa mahaifinta ƙara,Sai dai Malam Sule bai taɓa zuwa makarantar ya tambayi halin ‘yarsa ba.ko ya kai ƙara akan korafi da take kai masa ba,Shi kawai yana ganin duk abin da ake faɗa a kanta gaskiya ne. Yau ta kama Jum'a karfe goma aka tashe shi daga makaranta tun a hanya Sadiya da Lubna suke mata waƙa har suka isa baban Zaure gidan inda suka samu Malam Sule yana gani ta ya daure fuska ya fara masifar"Tom daga an ganki an ga 'yar sarki marasa haƙuri yau kuma da me kika zo?” Ciki kuka mai cin rai tace"Baba Sadiya Da Lubna ce suke tsona ta wai ni...“Tsawa ya daka mata tare da nuna ta da hannu ciki muryar sa ta Malaman Soro ya ce“ Karya sukayi!Nace karya sukayi Sumayyah ba daga Rabi kika fito ba? Kenan baki da maraba da mahau...” bata jira ya karasa ba ta kwasa cikin gida a guje Sadiya da Lubna kuwa toshe baki sukayi suna dariya. Abayan Sallah Isha'i Sumayya ta rufe musu kofa wanda Doka ce da Malam ya kafa wa iya Sumayyah da mahaifiyar ta, bayan bacci ya fara ɗaukar tana kwance gefen mahaifiyarta, kallo Innar ta tayi tana kallon Yadda take yin magana da kanta cikin bacci, tare da kaiwa jikin ta yakushi da cizo.karshe ta fashe da kuka, tana cewa: “Sule, ka yi min adalci… Ka tuna da alkawarin aure!”da haka kuma tayi shuru kamar ba ita ba,Wannan kalmomi ne yasa Sumayyah tashi ta rafka ta gumi kalmomin suka fara yi mata yawo cikin kunnen ta har ta rufe idanuta a fili ta furta.“Wane ne mahaifina a gaske? Me ya sa yake shiru? Me ya faru da mahaifiyata?”Lumshe ido ta tayi cikin hawaye.tace “Duniya ta ƙi fahimtar ta..” *Zuciyarta ta cika da tambayoyi da za su zama asalin labarinta. Saboda a cikin shiru, akwai sirri.A cikin hawaye, akwai gaskiya. Kuma a cikin wannan yarinya da ake kira “’Yar Mahaukaciya”, akwai ƙarfin da zai girgiza duniya. *Comment lik da Shering shine zai karfafa min gwiwa dan Allah a Amin kara free Book ne amma nace ba kullum zan rika Update ba* [10/28/2025, 1:15 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚 🌸 ‘YAR MAHAUKACIYYA🌸📚* Mallaki: Husaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ________________free book __page-2 Sai da tayi 'yan Addu'o'in da tasani,kafin ta kwanta.Rana ta tashi kamar yadda take tasowa kullum, amma ga Sumayyah, kowace rana sabuwar jarabawa ce. Haske bai taɓa zama alamar farin ciki a gare ta ba, sai dai tunasar da ita cewa ta sake tsallake wata rana cikin wulakanci da rashin tausayi. Da safe ta tashi da kyar, jiki babu ƙarfi, idanu wanta sun kumbura saboda kuka. Ta ɗauki bokitin ruwa ta nufi rijiya da take nesa da gidan su,tafiya take da kyar da dama jiya bawani abinci kirki ta ci ba. Hanyar rijiya ba mai nisa ba ce, amma a gare ta kamar tafiya cikin duhun da babu haske take. Ji take tamakar anayi mata yasa acikin ta, tun da ta doshi guri yaran da suke wasa,wasu na wucewa, suka fara tsaiwa suna kallonta suna dariya.“Yar mahaukaciya, ki kawo mana ruwa mu sha, kar ki yi dariya ki haukace mana, Aguri nan!” Ta tsaya, ta ɗan kalli ƙasa, hawaye suka gangaro mata. Ta yi shiru, ta juya ta ci gaba da tafiya.lokaci da ta isa ta samu wasu matan ƙauye suna hira. Tana isowa, hirar ta tsaya. Kowa ya juyo yana kallonta da murmushin raini hankali. “O Allah ya rabamu da hauka koda bana tiburan bane?” wata ta faɗa cikin dariya.Wata mai ɗauri ƙirji ta bigawa Sumayyah harara tare da cilla guga cikin rijiya tace., “Eh ai ita ce ‘yar da bata da uba. Ai Malam Sule ma yana gudunta bare mu kuma mutane gari,yo hauka yake zai sake bari tsatson sa ya biyu ta guri mahaukaciya.”Da sauri Sumayyah ta jingina da rijiyar, zuciyarta kamar zata tarwatse. Amma ta yi haƙuri. Ta hanana zuciyar ta shiga damuwa, cikin ranta taji wata zuciyar na ce mata “Ki yi haƙuri Sumayyah, rayuwa ba ta tsaya kan baƙin rana ba sai dai tana koyar da juriya.” Bata iya ƙarasawa guri su ba har sai da suka gama nasu jan ruwan kafi ta janyo nata.Da ta koma gida, ta iske Baba Hauwa zaune tana ɗinki. Tana zuwa zata wuce ta ce. “Ke kuma, wane irin jinkiri ne haka? Ko kin tsaya kina tattaunawa da mahaukata irin mahaifiyarki? Yo in ba hauka ba ina dalilin zama haka!”Sumayyah ta sunkuyar da kai, ta mika mata bokitin ruwa.Baba Zulai da take aikatau ɗin awara ta ce “Allah ya ƙyauta, amma irin su wanan yaran ba su da albarka. Haka uwar, haka ‘ya.”babu wand ta tankawa bare su samu abin kai wa Malam ƙara.Da ta gaji ma ɗaki ta shiga abinta guri mahaifiyar ta. Da yamma bayan ta gama ɗora wa Baba Zulai sanwa tuwo dare, ɗakin mahaifiyarta.Inna ta shiga tana zaune tana kallon sama, tana murmushi kamar tana magana da wanda ba kowa ke gani sa ba.“Inna ta..!,”Sumayyah ta ce cikin rauni.Inn ta juyo, ta ƙyalkyale da dariya, sannan ta kama hannunta.“Sumayyah, su sun manta, amma Allah bai manta ba kizo nayi maki wanka na goyaki na kaiki baki rami.” Hawaye ta goge da bayan hannu takafi ta ce. “Inna ta! me suke nufi idan suna cewa ba ni da uba? Ina ce Malam Giɗaɗo shine mahaifina?”Inna Sai da ta ƙarewa Sumayyah kallo kafin ta Ƙyal ƙyale da dariya tace“Sule Saurayi nane ya sai min kajal da janbaki kina so Na ara miki?"Inna ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta lumshe idanu.ta ɗora da cewa“Ki girma, ki sani da kanki. Gaskiya ba ta ɓoye har abada. Amma ki sani, wanda yake da gaskiya, sai ya sha wuya kafin ta bayyana.” kuka Sumayyah ta fashe da shi tare da cewa."Inna ta, na kasa gane wa,yau zaki magana da kyau ajima akasi ta Allah ka kawo sauƙi cikin rayiwar mahaifiyya ta ko nasan suwaye dangi ta.” Tun daga wannan rana, tambayar “Wacece ita?” ta zama abin da ke damunta fiye da komai. Ta daina jin zafi daga kalmar “’Yar mahaukaciya.” Yanzu tana jin cewa wata rana, zata nuna musu cewa hauka bata gajiya bace, hauka na iya zama hikima da duniya ta kasa ganewa. Da dare, lokacin da kowa ya kwanta,kasa bacci tayi a hankula ta buɗe ƙofar su ta fito ta zauna ƙarƙashin tsohuwar wata bishiyar kuka dake bayan gida ɗakin su.ta zauna ta ɗaga kanta samma Tana kallon sama wani siriri hawaye ne suka shiga gangaro mata cikin kasan zuciyar ta tace. “Ya Allah, kai ka halicce ni, kai ka san dalilin da yasa ka saka ni cikin wannan gida. Idan akwai gaskiya, ka bayyana ta. Idan ni ba yar wulaƙanci bace, ka nuna min haske.”Sai da taji anna kiran Sallah ta maza ta faɗa ɗaki dan tasan yanzu Malam zai bi ɗaki-ɗaki yana tashi saboda sallah asuba. Bayan kwana biyu yau ta kama ranar Litinin, duk yadda taso ta tafi makaranta akan lokaci bata tafi ba Sadiya da Lubna kuwa tun tuni su jima acan sai da ta gama gyara gidan da kwashe karan da Almajirai suke karatu dare kafi ta isa makaranta. Suna zaune cikim aji Sabuwar malama ta shigo, sabuwar malamar da aka kawo daga birni,Malama Ruqayya, tun da ta shigo ta lura da yanayin Sumayyah. Tashi farko taji yariyar ta shiga ranta, kiran ta tayi bayan kowa ya fita break ta ce. “Sumayyah, me yasa nake ganin kina da zafin zuciya amma kina ɓoyewa?”Sumayyah ta yi shiru, hawaye suka cika idonta.Malama Ruqayya ta sake magana cikin tausayawa.“Na san kaddara tana iya zama nauyi, amma Allah baya rubuta ciwo sai da magani. Ki ƙarfafa zuciyarki.”kai ta girgiza tare da aminta da maganar ta.sannan ta sallameta.Tunda tabar guru.Kalmar nan ta zama abin da Sumayyah ke maimaitawa a ranta kullum. “Allah baya rubuta ciwo sai da magani.” Sai dai tana tambayar kanta-a ina maganin nata yake?”haka suka koma ciki aji, duk da a kaso tamani bisa ɗari babu abin da Sumayyah take fuskanta a ciki karatun da ake musu. Rana ta sake tashi a gidan da kalmar “adalci” ta dade da mutuwa. Gidan da dariya ta wasu, ke nufin hawaye ga wasu. A yau, an shirya babban liyafa a gidan Malam Sule.wanda bisa addu'a da Malam Sule ya yiwa wani Alhaji Musa mai da'awa kan wata kwangila da yake so ya samu buri sa ya cika shine ya haɗa musu Babbar liyafa.kowa ya shirya Sadiya da Lubna kamar sun shiga kanti ɗan kurma saboda tsabar ƙamshi, kwaliya kam har da su barbaɗa kumatu. Ana jiran Alhaji Musa mai da'awa ya ƙaraso har da iyalin sa. Baba Hauwa da Baba Zulai jikin su sai rawa yake burin sun bai wuce ko Sadiya da Lubna zasu dace ba guri yaran Alhaji musa mai da'awa.Ko tsinke ne ya faɗi sai su sa Sumayyah ta ɗauke, ko wanka sun hana tayi wai bazata yi wanka ba kar wani yace yana so. Itama bata damu ba dan bata jin za'a barta taje guri walima bare har ta ga wani yace yana sonta hasalima ita bata sha'awar aure wani me kuɗi. Inna kuwa, Malam ne ya kulle ta da kanshi aɗaki wai kar ta zo ta kashe musu guri da wari, Hankali ta kwance jikinta yayi busu-busu da ƙasa tana waƙar da babu wanda ke fahimta. Sumayyah tana ta hidima, tana ɗaukar abinci tana kaiwa Babbar falo Malam wanda sai ka ɗauka ba acikin gidan yake ba saboda tsabar haɗuwar da har da sol.Ba kowa yake shiga ɗaki ba sai Manyan mutane masu zuwa temako guri sa. Bayan ta kammala lokaci da take ƙoƙarin zama motar su ta ƙaraso babu wanda ya bi ta kanta guri tarbar Alhaji Musa mai da'awa da matar sa da samari yaran da guda uku, Baba Zulai da Baba Hauwa har da zubewa har ƙasa suna yiwa yaran ciki gaisuwa su kuma suna fusgewa waisu 'ya'yan manya. Ko da ta gaji da jira, babu wanda ya lura da ita hada-hadarsu kawai suke.shawara ta yanke ta tafi ɗaki guri Innar ta Baba Hauwa ta fito daga cikin ɗaki tana washe baki kamar gonar audiga, Muryar ta har,har ɗewa take saboda sauri magana. “Ke... tsohuwar..manya.. yanzu ..Allah kinan..? A nan naɗe kamar tsohuwar manya! Aikin banza in aka ce maka Mutum ba kanshi kallo ba. fa ka banu!” Sumayyah ta ɗago kai cikin hawaye, ta ce cikin murya mai rauni, “Baba Hauwa na yi kuskure ne? Ina tsaye ne ko zaku buƙaci wani abun kar ku kira kuji bana kusa”Baba Zulai da ta biyo bayanta tana dariya, “Eh ai kin yi kuskure, kin haihu daga Rabi! Haka kawai, asalin ku kuskure,haka kawai kusa a riƙa kiran dangimu da masu cutar hauka!” Da sauri Sumayyah ta rufe kunnenta da hannuwan ta, tana girgiza kai tace. “Ya Allah, kai kaɗai ka isa, kai kaɗai ne mai ganin ɓoyayye.” ta sake buɗe ido ta da lokaci daya suka juya zuwa jajaye, ta ce “Ya Allah maye laifina dan Na fito daga jikin mara lafiya?” tsaki suka buga Baba Zulai taja hannu baba Hauwa tace."Kin ga zo mu koma mar su san yana da wata 'yar baje ya lalace. Da haka suka sake fadawa daki Malam, tana juyo muryar Alhaji musa da'awa yana cewa"Hajiya gashi kowa turmi biyu babu yawa” Kamar Zasu kifa haka suka fara yiwa Alhaji musa godiya"Alhaji Allah ya saka ya kawo nasarori ya kaɗe hau da bala'i”Ciki isa Yake amsawa da haka suka miƙe zasu fita da sauri Baba Hauwa ta kaɗawa Yusuf ido tun da yaga ni ya gane me take nufi da sauri ya fita. A tsaye ya samu Sumayyah tana tsaye. Tsayawa ya yi daka mata tsawa “Ke tsohuwar muna fuka wato laɓe kika fara yi mana ko?” Jiki ta har rawa yake ta zube akan gwiwar ta ta fara magiya. "Wallahi Yaya Yusuf ba laɓe nayi muku ba, ina jira ne ko”Wata iri kwarfewa ya yi mata ji kake ta faɗi ƙasa dabassss sai da jiri ya ɗauke ta balet ɗin jikin wando sa ya cire tare da jan ƙafar ta aƙasa sai da ya kaita ɗaki Baba Zulai kafi ya sakawa ƙofar sakata, dukan ta ya fara. “Ni zaki karyata wato karya nake miki!Agaban baƙi zaki tsinka ni ko?”Kuka take tana neman agaji amma hakan bai hana Yusuf kilar taba kamar baiwa. Sai da yaga tayi lagab a ƙasa sanan ya buɗe kofar yana zuba uban gumi da kar ta miƙe ta fito atsaye ta samesu Baba Zulai ta lailayo Ashar ta maka mata"Kan bura'ubancan kayasa Mai zan gani 'Yar mahaukaciyya aciki ɗaki na Kai Yusu yanzu Dan tsiya ka rasa inda zaka kaita sai tura kar Malam?” Baki ya cono uwa na gafiya ya fara yiwa Baba Zulai masifa“Haba Babar mu so kike na kaita wacan jujin ɗaki nasu salon kwalara ta kama ni, Ke duk abin da za'a miki ba kya gani”Yana gama faɗa ya buga tsaki tare da cilli da bulala ya fice.tana kallon su Lubna da Safiya suna ta ɗaga kayan da aka kawo mu amma bata da damar zuwa ta gani har da lace ɗin da za'ayi yayi acikin ƙauye su wanan sallah, ɗaki Baba Hauwa suka ɗunguma tare da lissafi telan da zasu kaiwa ɗinki haka itama ta ja jikin ta da ƙar ta shiga nasu ɗaki. Kwanan Sumayyah biyu tana kwance, jiki ta na ciwo ga mugun zazzaɓi saboda tsabar dukan da tasha guri Yusuf hakan kuma bai hana ta daina ɗaukar ruwa da wasu aiki gida ba, babu wanda ya damu da ita bare ta sa ran samu magani Ko da magani zazaɓi ne. Inna ce zaune sai kukan yinwa take, tana rera surutu na kiran abinci cikin muryar da take cike da soki burotso. Gajiya Sumayya tayi ta fashe da wani kuka, tana jin kamar zuciyarta zata fashe. Da yamma Baba Hauwa ta shiga ɗakin inda Sumayyah ke kwance, gani har yanzu bata fito tayi sharar yamma ba,ta tsaya bakin ƙofa tana kallonta tare da doka mata uwar harara babu tausayawa a cikin idon ta. “Ke Sumayyah..!wane iri sakarci ne ya hana ki fitowa kiyi mana shara kina kallo duk gyanye ya zubo ko dalili a fita ana zagi matan Malam ana mana kudi goro ana kiran mu da mahaukata gaba ɗaya?banda tugu da iya muna furci wanan ɗan dukan shi zai sa ki sharɓe wai baki da lafiya.”Sumayyah ta yi shiru. kamar yadda ta saba, bata mayar da martani ba. Haka Baba Hauwa ta ƙari faɗan ta ta tusa ƙeyar ta, har tsakar gida ta share gidan har da waje guri zanam karatu Almajirai wanda Malam yace Almajirai su daina duk Sumayyah ce zata riƙa yi.Da dare, bayan kowa ya kwanta, ta fito da ƙyar ta tsaya bakin ƙofar ɗaki. Tana sauraron irin maganganun da Inna ke yi tana dariya ita kaɗai.Sai kuma taji muryar Innar ta na cewa. “Sumayyah, kar ki ji tsoro. Wata rana za ki san gaskiya. Wata rana haske zai shigo cikin duhu. Kuma ranar, zasu gane ke ba ‘yar hauka bace…”da sauri ta waiga ɗaki ta kallon Innar ta kafin ta sake motsi Inna ta sake buɗe baki ta cikin bacci ta ce. “Ki kula da duk wanda zai zo miki da taimako, kar ki yi gaggawa. Ba kowa ke da zuciya tsarkakakkiya ba. Amma akwai wanda Allah ya rubuta zai zo ya goge miki hawaye.”da Bango Sumayyah ta jingina kanta na mata wani iri sarawa hawaye na gangaro mata a hankali, tana jin kalaman Inna kamar ana shigar da su cikin ranta ne da wuta. Washe gari, tana zaune gefe guda a fili makaranta, Malama Ruqayya ta lura da tabon da ke gefen hannunta. Ta kira ta gefe. Guda inda Babu yara sosai tace. “Sumayyah, wannan ciwon fa? Me ya same ki?”Sumayyah tayi ƙasa da idon ta, ta girgiza kai. “Ban sani ba Malama. Nima kawai gani sa nayi.”Malama Ruqayya ta jinjina kai, tana kallonta cikin tausayawa.“Ki sani, ko da duniya ta yi miki hukunci, Allah ba zai taɓa mantawa da ke ba. Idan akwai gaskiya a rayuwarki, zata bayyana-ko da bayan shekaru.”Sumayyah ta amsa da “Amin Malama,”Cikin murya mai sanyi. Amma zuciyar ta tana ta bugawa. Ranar Asabar ta kama babu makaranta haka kuma lokaci tashi yayi daga makarantar allo fita tayi samo gwangwani madara saboda tana fafe su ta kai gidan masu Alala su bata kuɗi hakan ne ya faru da hanzari ta fita kofar gida, wata ƙatuwar mota ce ta tunkaro kofar gidan Malam Giɗaɗo baƙa kana gani kasan atajirai ne aciki. Wasu mutanene su uku aciki, suna neman gidan Malam Sule Giɗaɗo. Kallon farko da Sumayyah ta yi musu, ta ji zuciyarta ta rikice, hankali ta bai kwanta da na gaban ba, Gashi baƙi ga muni tsiya tunda ya kafe ta da kallo ya kasa ɗauke idon sa akan ta,sanye yake da farar shadda, kana gani sa zaka san bashi da imani sai kato ciki kamar an kifa ƙwarya. Gani Sumayya tana ƙoƙarin wuce su ya washe baki tare da ɗaga mata gira ya yafito ta da hannu.“ 'Yan mata ina kuma zaki zo mana muna da tambaya ne”Sai da gabanta ya fadi dan Muryar sa ko daɗi sauraro babu. Jikinta na rawa ta matsa baki motar turo kai ya yi kamar zasu haɗa Fusakar kana jin tashi turare sa kasan na 'yan Duniya ne, muryar sa ta sake ji"Da alama sauri kike? in baza ki damu ba Gidan Malam Sule Giɗaɗo muke tambaya” Sai da ta yatsina fuska kafi tace“Eh... Ga gidan kunzo”dogo hannu ta yabi da kallo wanda chocolate ne duk jirwaye ruwa ya kama hannu, gargasar hannu ta ita ta luluɓe datti hannuta. Ƙoƙarin buɗe motar Yake tare da cewa“Da dai zaki ƙarasa ladan ki ki mana Sallama da shi”Ji tayi kamar ta ɗora hannu ta fasa ƙara.“Subhanallah…” ta furta a hankali, tana ja da baya.Sai dai kafin ta sake magana, Yusuf ya fito da sauri, ya ƙaraso gare su yana zabbga mata harararta.“Ke wai wace iri shasahar yariya ce,anya ba baƙin ciki kikewa Babanmu ba?In ba haka ba tun ɗazu bayin Allah nan suke tsaye suna tambayar ki kina ya ƙuna su sai kace 'Yar wata cikakiyar mai hankali” Bakin Yusuf har wata kumfar masifa yake,Shikam Alhaji ɗan gambo wanda yake ji tamkar ya kamo Sumayya ya mana a ƙurjin sa ko ya samu sauƙi haka yake ji, wani abu ya raya acikin ransa sanan ya juyo cikin nutsuwa da ya aro wa kansa, ya kalli Yusuf. “Ka bari ta tafi, ɗan uwa maibi uzuri ta mai ƙarfi ne,” ya faɗa cikin murya mai taushi, kamar na Allah.dariya ya yi tare da tsara kalamomin da zai ɓata Sumayyah guri wanna hamshaki mai kuɗi. "Ranka yadade Uzuri ta na banza, ai kufi uzuri nata daraja jakar banza sai wari tsiya ka ganta nan sai ta kwashe mako huɗu ba tare da ruwa yaga jikin ta ba.... *Up up up azo Amin comments da Shering da like Yan amanna akwai abubuwan nishadi fadakarwa dakuma tausayi acikin rayiwar Yar mahaukaciyya* [10/29/2025, 7:19 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚 🌸 'YAR MAHAUKACIYYA 🌸📚* Mallaki: Husaina S. Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚 © 2025 – Duk haƙƙoƙin mallaka na musamman ga marubuci. _______________free book __Page -3 Alhaji Sa'idu (Alhaji Dubai) ya yi murmushi mai cike da kwarewa ta 'yan duniya, yana kallon Sumayyah da idanuwan da Na cikakken ɗan bariki San nan ya juya ga Yusuf cikin murya iri ta mutane ƙwaraiya ce. “Yaro, ka kira min Malam Sule, ka ce Alhaji Ɗan Dubai ne ne yazo. Ina son ganinsa.” tun da Yufus yaji sunan da yayi fice a Lagos ya haɗiye miyau.jikin sa ya hau ɓari “To Alhaji, yanzu nan,” ya amsa cikin rawar jiki.gudu da sauri ya haɗa kamar wanda yake ɗauke da saƙo daga sarki.Yana isa Baban zaure sallamar baki, ya tarar da Malam yana karanta wani hatimi,Yusuf ya tsaya daga ɗan baya yana huci saboda gudun da ya yi, ya ce,“Malam... Malam! Yau da kayi baban Kani Alhaji Ɗan Dubai ne yazo... yana waje!”Kafin Malam ya maida numfashi, hannunsa ya fara rawa. Hatimin dake hannunsa ya faɗi ƙasa, ya ɗago cikin tashin hankali. Da wata iri murna yace."Ka tabbata Yusufa ko dai idon kane Alhaji Ɗan Dubai da na lagos?”Baki Yusuf ya sake wage wa ya ce“ Allah Baba Alhaji Ɗan Dubai dai wanda kasani ɗin nan na Legas! Motar sa ma tana nan a waje, har da mutane biyu tare da shi.” Malam Sule ya miƙe da sauri, jikinsa na rawa kamar wanda aka tsikara da wuta. Ya fara tafa hannaye yana bulin-bulun da babbar riga tare da ambaton “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” cikin muryar farin cikin kamar ya cashe da rawa. Ko da Sumayyah ta tafi ta samu gwangwani madarar ba sai yara da suka kusa tura ta su maida ita mahaukaciya da gudu ta shiga gida ta kofar baya har da Masu jifan ta. Takalman sa Yasa hagu da dama tare da cewa. “Allah ya kawo wannan rana! Kai Yusuf, zo muje mu tarbe shi! Kai yi tsaf ka gyara rigar ka, kasan masu damar nan basa so ƙazanta. Wannan mutum ne da idan ya taɓa mutum, sai ka ce alheri ne yake zubowa daga sama!” Yusuf ya gyara rigarsa da wandon sa da sauri, yana kallon Malam da murmushi mai cike da yaudara. “Malam, Allah ya kawo lokacin ka kenan amma ya kamata amin baban Kasafi?. Wannan Alhaji Ɗan dubai ɗin fa mutum ne mai alheri sosai dan cewa akayi kyautar mota da gida aguri da ba abu ne mai Wahala ba,sanan naji ana cewa yana taimaka wa malamai. Sosai Bari ma in buƙatun sa suka biya” Dariya Malam Sule yiyi ya shafi fari gemu sa, ya gyara rawani kansa, ya ɗauki misbaharsa da ƙamshi mai ƙarfi ajiki.suka fita Kofar gida. Saboda ya nuna isa da cewa shiga malam ne na gaske sanan ya yi wa Su Alhaji Ɗan Dubai bazara yasa shi cokewa ya bawa Yusuf izini yaje ya taho dasu,yana zuwa Yusuf ya yi musu jagora, ya durƙusa gaban Alhaji Ɗan Dubai har ƙasa abin da ko malam baya yiwa ya ce.“Ga shi can Malam ɗin.”Alhaji Ɗan Dubai ya miƙe daga jikin motar da tulu ciki sa, ya ɗan gyara igar sa tare da cewa abokan cin mushe sa.“Alhaji Dollar, Alhaji Iri bisimillah”suna Isa gaban sa Alhaji Ɗan Dubai har da cire takalma kamar su haɗa baki suka ce“Assalamu alaikum Alaranma barka da warhaka!” ya tamkar mutumin ƙwarai.hannu Malam ya miƙa ciki Murya manya yace.“Wa alaikumus salam warahmatullah!”cike da nutsuwa, amma jikinsa har yanzu bai daina rawa ba“Wallahi Alhaji Ɗan Dubai nake gani tsaye a gaba na! Na dade ina addu’a Allah ya haɗa mu, yau kuma ga shi ya cika!”Sai da Alhaji Ɗan Dubai ya saba ƙato tubisa kamar me tsohon ciki kafi yace.“Alhamdulillah, Malam yau gashi Allah ya haɗa” Hannu Kalma ta sake bashi "A...Almajiri malam dai ai nasha gani ziyarar da kake kaiwa Manyan Malama iri su Malami buzu da sauran su wane mu” Dariya Alhaji Ɗan dubai ya yi ya kiftawa Alhaji Dollar ido sanna yace. "Allah gafarta Malam na zo ne da saƙo daga gwamati te makawa malamai wanda ake kaiwa gari gari dan inganta masallatai shine mukayi tambaya akace ai guri ka zamu zo.”wani iri Farin ciki ne ya kama Malam giɗaɗo yasan zai ci kuɗi afili kuma gemu sa ya shafa yana furta"Masha Allah, Allah ya yi albarka ai inda zamu riƙa samu mutane iri ku da duniya ta zauna lafiya 'yan Aljana iri ku basu da yawa.” kai suka jinji Alhaji Ɗan Dubai ya sake cewa. "Allah gafarta Malam Amma kuma, akwai wata magana ta daban da nake son muyi a sirri.” Malam giɗaɗo ya haɗiye miyau, ya ɗan sunkuyar da kai. “A’a, babu matsala, za mu iya shiga ciki.” a tunani sa wani mugun hasafi zai sake masa asiri saboda idon mutane ya bukaci su kebe guri guda. Yusuf ya sa a gaba yana nuna musu hanya, yana ta murmushi saboda yasan wannan ce damar da zai kashi rabon sa. Suna shiga, Alhaji Ɗan Dubai ya zauna a kan babbar kujera, yana dube-dube da ido irin na mashuran masu kuɗi.Ya ɗan ja numfashi, Malm yana zuwa kan wani kato buzu ya zauna tare da tankwashe kafafu sa.ya yi gyran murya da matsar da tawada da alkaliman da suke bahe akan buzu. Nutsuwa Alhaji Ɗan Dubai ya yi shida amini sa sannan ya ce cikin ladabi da sai ka rantse mutumin kirki ne. “Allah ya ja kwana, wannan yarinya da na gani a waje nan, wacce Yusuf ya ce ‘yar gidan ku ce…? Ta kace itama?” Malam ya ɗan karkata kai, tare da tafiya dan nazari Alhaji Ɗan Dubai ya katse masa tunani da cewa.“Naji kamar kamar ya ce Sumayya ko sakeena.!!”Ya fada yana satar kallo Malam. Hannu Malma ya tafa“O..O.. Sumaiyya kenan itama yariyar Guri nace sai dai mahaifiyar bata da hankali zargi da muke itama abin ya shafe ta har tayi suna ma dan Wani sa'ilu sai kace gidan su 'Yar mahaukaciyya zava kawo kanan.”farin ciki ne ya cika zuciyar Alhaji Ɗan Dubai fall da da alamu bazai sha wahala ba guri samu abu da yake so. ya lumshe ido, ya dan jinjina kai yana murmushi.“Toh… jinƙai kenan,” ya ce, yana duban Malam da wani murmushi mai ma’ana. “Allah sarki Allah gafarta,na lura akwai wani abu a cikin idonta… sai naga kamar tana ɗauke da wata hikima da ba kowace mace ke da ita ba.” ya tsaigata dan yaga yadda zasu ɗauki maganar tasa.Malam ya yi dariya kadan.“To ai duk hauka tana da nata hikimar, Alhaji. Amma dai ka bar wannan, meye saƙon da kake tafe da shi?”Alhaji Ɗan Dubai ya zaro wata envelope daga aljihun rigarsa. Ya ajiye a gaban Malam Sule, yana murmushi da ladabi. “Wannan kuɗi ne na godiya, saboda addu’o’inku da taimakon ku da kuke yiwa malamai da almajirai. Kuma akwai wata ƙaramar bukata… amma sai in ka amince kuma akawai tari alkairi aciki.” Malam Sule ya yi saurin ɗaga envelope ɗin da hannunsa yana dariya. “Subhanallah! Alhaji, kai fa mutum ne da Allah ya albarkace! Bana jin akawai abin da zaka roƙa baka damu ba..!” Yusuf da yake gefe ya kalli envelope ɗin da idanu ji yake kamar ya fusgo ta da ido, yana taɗe harshensa.Alhaji Ɗan Dubai ya lumshe ido ya dan ɗaga kai. “Akwai wata ƙaramar magana da nake son mu yi game da waccan yarinya da ke waje…” Ya ɗan ja numfashi ya ce cikin murya mai sanyi amma cike da mugunta: sai da gaban Malam da na Yusuf ya buga fatan su kar yace zai haɗa ta aure da iyali da gasu Lubna da Sadiya can a gida., kafi suyi dogo tunani sake jin muryar Alhaji Ɗan Dubai. “Malam, ina son ka bar ni in ɗauke ta na duba ta a Legas. Akwai wata dama da nake ganin zata taimaka mata... kuma kai ma za ka amfana.”Malam Sule ya tsaya cak. Kalmar “ina son ka bar ni in ɗauke ta” ta ɗan girgiza shi a farko. Ya ɗan gyara zamansa yana duban Alhaji Ɗan Dubai, sai kuma ya saki murmushi fari ciki da yaji ba batu aure bane. “Alhaji, ɗauka kuma? Kana nufin taimako kenan ko ya.....?” Alhaji Ɗan Dubai ya yi murmushi irin na mutumin da ya saba wasa da hankali mutane.“Eh, taimako mana, Malam. Kamar yadda na faɗa maka- yarinyar tana da wata alama ta hankali da hikima, amma a karkashin hauka da talauci. Ina da wata makaranta ce ta matan marasa gata a Legas. Ina so in ɗauke komi Ni zan ɗau nauyi ta a can, zata samu kulawa, ta koya ilimi, kuma ta taimaka ma kanta. Ba komai bane illa taimako sanan kaima zaka samu sauƙi ci da iyali.” Malam ya ɗan yi shiru. A ransa ya fara hasashen kuɗi, kuma idanunsa sun rufe da abin duniya. Ya kalli envelope ɗin da yake a gabansa.ko makaho yasan kuɗi ne ba nawasa ba acikin envelope dinnan. Alhaji Ɗan Dubai ya ɗora da cewa.“Ka kwantar da hankalinka, Malam. Ba tare da wani matsala ba, zan ajiye maka abin da zai taimaka wajen kula da sauran yaran ka da kuma makarantar ka ta, tsangaya sannan zan turo wasu kudade daban don kula da da mahaifiyar ta wace kace tana da matsalar kwakwalwa.” sai Yanzu Malama ya samu damar zaro ido gani Alhaji Ɗan Dubai ya sake zaro wata leda ɗauke da bandir ɗin kuɗi, ya ajiye a gefen kujera cikin nutsuwa. Yusuf ya ji kamar ya fasa ihu saboda farin ciki. Idonsa yana kallo tamkar ɗan akuya da aka nuna masa gyaɗa. Malam Sule ya haɗiye miyau, zuciyarsa tana rawa. “Alhaji Ɗan Dubai, wallahi kai mai taimako ne. Ba zan taɓa hanaka ba. Amma dai yarinyar fa, tana da mahaifiya, ko da kuwa tana da tabin hankali. Dole ne na faɗa mata ko?..” *Dan Allah shering saboda manzo Allah kar ku manta free ne aiki ku shine Comment like* [10/30/2025, 4:56 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-4 Alhaji Ɗan Dubai ya yi dariya mai sautin makamar ta tsofafi bokaye yace."Malam, irinawannan yaran mahaukatan ai abin a tausaya musu ne?Ni dai kawai ka bani amincewa, sai in zo in ɗauke ta gobe da safe. Kuma na bar kuɗin da zai wadatar da mahaifiyar ta da dawainiyar haukan ta.” Ya tura ledar kuɗin ɗari biyar x10- bundun miliyan biyar.Sai da Malam ya zabura kamar wanda aka haɗa masa shokin. Hannunsa ya fara rawa yana ƙoƙarin ɓoye farin cikin da ke ratsa zuciyarsa. “Subhanallah! Alhaji Ɗan Dubai, wannan alheri ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba.ainda ka barshi ma.”Yusuf da ke gefe ya ƙaraso da sauri yana cewa,“Alhaji, wallahi kai mutum ne mai hankali. Na dade ina addu’a Allah ya kawo mana kai cikin gidanmu sai gashi kazo.” Alhaji Musa ya yi murmushi yana shafa gemunsa.“Na gode. To kai kuma, Yusuf, zan baka aljihun ka na musamman. Kai ne zaka tabbatar ta shirya gobe da safe. Kar kowa ya sani. Kasan irin fitinar da mata suke yi sai kaji ƙananu magan ganu.” “Na gane, Alhaji,” Yusuf ya faɗa yana kwaɓe baki cikin murmushi.Da suka fita daga falon,Yusuf ya bi Alhajin da ido kamar mai kallo aljanna.“Wannan mutum, wallahi, ba kamar sauran mutane bane,” ya ce cikin zuciyarsa. Bayan su gama tsara yadda zasu gobe har baki mota Malam ya raka Alhaji Ɗan Dubai ya raka shi yana sheƙa godiya. Da daddare, Malam Sule ya shiga ɗakinsa hankali sa akwamce irin na wanda Aljihu sa ya cika da kuɗi. Ya ɗan gyara rawaninsa, ya ɗaga hannu sama ya ce, “Alhamdulillah! Allah kai mai azurta bawanka ne. Idan wannan yarinya ta tafi, to wani alheri a gare ni.” Inna ce kwance bacci ya ɗauke ta da wuri saboda abinci da ta samu taci yau Malam da kanshi ya zuba musu abinci ya basu wanda sai da Sumayyah tayi mamaki. Bacci ta ya yi nisa ta fara suru tai kamar me tabi aljanu tace."Sumayyah… za su ɗauke ki… za su ɗauke ki daga haske zuwa duhu…”Sumayya da take gefe tana cin tuwo tsari ta cire hannu ta ta fara tofa mata addu'a da haka ta daina surutai ta ci gaba da bacci ta.Washe gari da safe da wuri, Yusuf ya tashi da sassafe fada ɗaki su Sumayyah tin daga nesa yake ƙwallah mata kira a zabure ta miƙe jikin ta na rawa tunani ta tayi wani laifi ne, a ƙofar ɗaki suka haɗu, ya ɗaure fuska kamar wani boss yace.“Sumayyah, yau Malam ya ce ki shirya, akwai wani Alhaji da yake son zai taimaka miki.za ki tafi ki zauna a wajen shi lilimi zaki kyauta batare da ƙwandalar Malam ba. Ai dama Malam yana son taimaka miki ko dan hali da mahaifiyar ki take ciki damace da babu.” Sumayyah ta ɗago kai, idonta cike da tambaya. Muryar ta na rawa tace. “Ni kuma Yaya Yusuf? Amma Inna tafa?.”Baki ya washe. “Kar ki damu, an ce za a kula da ita sosai. Wannan dama ce babba, Sumayyah. Ki tafi, ki ga duniya duniya ta ganki.” Cikin ranta wani abu ya fara yi mata yayo“Ki kula da duk wanda zai zo miki da taimako, ba kowa ke da zuciya tsarkakakkiya ba…”kalmar Inna kenan da ta faɗa a daren da ya gabata.Zuciyarta ta fara bugawa da karfi. Ta ɗan dafa ƙirji, ta ce cikin murya mai rauni: “Amma Yaya Yusuf Sadiya da Lubna suma zasu… me yasa bana jin daɗin wannan tafiya?kuma...” wani iri lafiyaye mari ya kifa mata tare da nuna ta da yatsa."Zanci Ubanki yanzu ance miki zuwa nayi na lalaɓa ki tom kisani ko kiji kwanciyar hankali ki kar kiji tafiya babu fashi”kunci ta dafe hawaye na sauka a hankali kan kumci ta Baba Zulai da Baba Hauwa kam shewa suka yi kamar a gidan biki baba Zulai ta ce."Yo Allah na tuba dama ai sai dai temako dan iri wanna 'ya'yan mahaukatan ko mijin aure basa samu.Sadiya da Lubna suka ƙyal ƙyale da dariya. Bayan gari ya daɗa haske, ƙauyen ya yi shiru.sai kukan tsuntsaye suna tashi daga kan bishiyoyi, sai kuma iska mai sanyi tana kaɗawa tana ɗauke da ƙamshin ruwan sama. Sumayyah ta zauna a bakin ƙofa tana kallon hanya, cikin zuciyarta tana jin wani irin nauyi kamar an ɗaura dutse a kirji. Ta ɗaura hijabinta na tsoho tayabo da Inna ta daɗe tana amfani da shi, saboda babu wanda ya ba ta sabo. A gefe, Yusuf na ta faman cika da batsewa ya ce:"Ki gaggauta mana Sumayyah, Alhaji bai cika son jira ba. Kuma ki daina wannan yanayin kamar wacce aka tura ta dole. Ke fa za ki samu rayuwa mai kyau a Legas.”wata muguwar faɗiwar gaba taji duk da bata san nisan Lagos ba amma tana ji masu zuwa neman kudi na cewa kwana biyu ake a hanya batare da anje ba, share hawayen idon ta tayi da gefe hijab ɗinta. Ta Kasafi inda Yusuf yake tace. “Amma Yaya Yusuf… Inna bata san zan tafi ba. Kuma jiya nayi mafarki… ina ganin kamar ana ɗaukata da ƙarfi, Inna tana kuka tana cewa ‘kar ki tafi! Dan Allah Ni ku barni guri Inna ta” Yusuf haka wani dogon tsaki tare da buga mata harare.“Ke ki tsaya da mafarki ki, dama 'Yar mahaukaciyya ana rabata da mafarki hauka ne? Ke baki san wani lokaci Allah yana ɓoye alheri cikin abin da kike jin tsoro ba. Ki tashi mu tafi kafin Malam ya fito.” Tana miƙewa suka ji ƙarar mota daga nesa, ta ƙaraso cikin ƙofar gidan, Mota ce fara mai gilashin baki ba iri ta jiya ba. Tana tsayawa, Alhaji Sa'idu Dan Dubai ya fito cikin riga mai tsada da hula ja. Hannu ta ya kama har ƙofar gida Yusuf: na gani sa ya zube ya gaida Alhaji Ɗan Dubai, shikuma Alhaji Ɗan dubai ya bashi hannu tare da cewa.“Madalla! Itace yariyar”a zumat bai gane ta ba.Yusuf ya ce, “Eh Alhaji, ta shirya kamar yadda ka ce.” Alhaji Ɗan Dubai ya kalli Sumayyah daga ƙasa zuwa sama, sai ya ɗan ɗaga kai yana murmushi.“Kin fi yadda na zata. Kar ki damu, za ki ga rayuwa mai kyau. Ki shige mota mu tafi.” Sumayyah ta tsaya, ta kalli ƙofar shiga gida. Da sauri ta maida kallo ta kan yusuf tace “Inna ta… bari in ce mata sai na dawo.”tana ƙoƙarin juyawa Yusuf ya riƙe hannunta.“Ke karki damu, Innarki ba ta cikin hayyacinta yanzu. Alhaji na jiranki fa!”turjewa ta fara tana kuka.ciki zafi rai Yusuf ya kira ƙani da Khalid,Cikin ƙanƙanin lokaci, suka tura ta cikin motar. Alhaji Ɗan Dubai ya shiga mazaunin gaba, sai direba ya tayar da mota. Motar tana fara tafiya, suka ji muryar Inna daga cikin gida-da sautin da ya fi kowane tsoro ɗan Adam tana cewa. “Sumayyahhhh! Kar ki tafi!! Kar ki tafi da su! Ba alheri bane! Za su ɗauke ki daga haske zuwa duhu! Sumayyahhhh!!!” duk iri riƙo da Malam da Baba Zulai suka mata sai da ta girgizar dasu. Ta fito da gudu gashi kanta duk ya dik-dige saboda cigar sa da take da hannu, idanu ta suka yi jajaye, tana gudu kamar wacce wuta ke bint. turus tayi gani motar ta ɓace tana tada ƙura.Ta fāɗi ƙasa tana ihu tana bubbuga ƙirjinta tare da ɗiban gari kasa tana afawa a bakin ta. “Ina kuka kai ta? Ku dawo da ‘yata! Ku dawo da ita! Ku mauhakata ne.”Dariya Amina ƙaramar 'yar Malam ta ƙyal ƙyale da ita tace."Rabi ai kece mahaukaciyar ba wasu ba kaji aiki Hauka” Da ƙuwa Malam yayi mata tare da kaɗasu gida. Har Inna sai da ya kaɗa su cikin gid. Malam Sule ya tsaya daga nesa yana kallo hanya, zuciyarsa na karyewa da abin da ya ji, amma sha’awar kuɗi ta rufe komai. Ya shiga gida yana faɗin, “Allah ne yasan alheri.da ke tattarai da yariyar nan yar kusu ƙa.”Inna ta sake fitowa daga ɗaki da tashiga,ta ɗago kai cikin zufa da ƙura, ta kalli sama tana kuka: “kune kuka ɗauke ta daina kama ku na kaiku an kama ku” Kara Malam ya ɗako da gudu ta faɗa ɗaki tana ran taɓa ihu Baba Hauwa tace.“Au ashe haukata banza kike da ki tsaya mana” ***----*** A cikin mota kuwa, Sumayyah jikinta ya yi sanyi. Ta jingina a jikin gilashi tana kallo hanyar ƙauyensu da ke ƙara nisa. A cikin zuciyarta wani irin tsoro ne ya fara girma- tsoro wanda ba ta san dalilinsa ba.Ta ɗan kalli Alhaji Ɗan Dubai da ke gaba yana waya cikin dariya: “Eh, na ɗauke ta yanzu. Ta yi kyau fiye da yadda nake tsammani. Ku shirya wajen kamar yadda na faɗa.”Zuciyarta ta sake bugawa! Ta kalli Yusuf da ke gefe yana lumshe ido saboda zasu rage masa hanya zuwa ciki gari, ta ce cikin murya mai rauni: “Yaya Yusuf… wannan tafiya… me take nufi da ‘ku shirya wajen’?”Yusuf bai ce komai ba, kawai ya ƙara sunkuyar da kai yana wasa da wayarsa da Alhaji Ɗan Dubai ya kawo masa sabuwa fill a kwali.Zuciyarta ta fara bugu da ƙarfi, sai ta runtse ido tana ambaton “Hasbunallahu wa ni‘mal wakeel...” bayan su shigo cikin ƙwayar birni kano aka sauke Yusuf Sannan motar ta ɗauki hanyar da bata san inda take kaiwa ba. Kwanan su biyu ba tare da ta rintsa ba marar ta taga ɗaure wa da fitsari dan baza ta iya cewa zata yi ba, duk abin da aka bata bata iya ci dan gani take ƙarshe ta yazo. Cinkus daki tsuma, yanayi iska da ta sauya kaɗai ta isa kasan ka shiga Lagos bayan su dan huce gurare da baza ta iya cewa gasunan unguwar ba.Motar ta tsaya a gaban wata babbar ƙofa da aka rubuta da manyan haruffa:“Cibiyar Ilimi ta Mata-Alheri Foundation.” Sumayyah ta kalli rubutun, zuciyarta tana rawa. Amma ta lura da wani abu -duk da sunan da ke ƙofar, babu wata alama ta makaranta a wurin. Babu yara, babu murya, sai shiru mai nauyi da ƙamshin turaren da ya haɗu da wari-iri na bariki. Alhaji Ɗan Dubai ya fito daga mota, ya gyara rigarsa tare da ɗaga mata gira ya ce:"Gashi munzo! nan ne, ‘yar albarka. Nan za ki zauna. Karki damu, komai zai gyaru nan gaba.” wata mace da ke tsaye a ƙofa cikin kaya masu fidda tsirai. Ya kalla yana kashe mata ido yace “Saffy chic ga sabuwar yariya ce,Ki gyara ta sosai.”Saffy Chic ta kalli Sumayyah a gadarance tare da binta da up and down . Ta ɗauke kai cikin raini, ta ce:“Zo ki bi ni.” Sumayyah ta bi ta a hankali, zuciyarta na harbawa. Suna shiga tsoro ya daɗa kamata, ta ga matan da yawa, wasu suna zaune cikin kayan masu bayyana tsiraici, wasu suna dariya suna shan abin da ta kasa gane ko menene. Gashi ji take kamar ana kallonta da ido masu cike da ta’addanci da yaɗa alfasha. Saffy Chic ta ja hannunta ta shiga da ita ɗaki guda. A ciki akwai kaya masu kyau duk da kowane kasa sai tsun bayyana suran bawa- iri su riga da siket, da turare da takalma haka bangare ƙananu kaya kowane kala akawai. Saffy Chic ta jefe ta da wasu kayan, ta ce:“Alhaji ya ce ki sa wannan. Bayan kin gama, za ki ci abinci kiyi wanka. Ki sa su yanzu.” Sumayyah ta tsaya cak, hawaye suka taru a idonta.“Ina makarantar da Alhaji ya ce zai kawo ni?Wannan wane irin wuri ne?”Saffy Chic tayi dariya iri ta matan duniya ta yi ta ce:“Ke yarinya,makaranta ce… ta rayuwa.”tana faɗi haka ta juya ta fita ta rufe ƙofa.A nan Sumayyah ta zauna, jikinta na rawa. Ta tuna muryar Inna a ƙauye tana cewa “Kar ki tafi da su! Ba alheri bane!” Ta sa hannu ta rufe fuskarta, tana kuka cikin rauni.“Ya Allah…” ta ce cikin kuka, “Ka fitar dani daga kaddara… idan wannan wuri ba alheri bane, ka fitar da ni kafin zuciyata ta mutu.kafi Sheɗe ya yi galaba akaina.” Bayan wani duk da haka bata ɗago ba tana kan dumdumemiyar katifa ta kifa kanta tana kuka, aka buga ƙofar da ƙarfi muryar Saffy Chic ta sake fitowa"Ki fito yanzu! Alhaji na jiranki a ɗaki”A lokacin ne zuciyarta ta fara sanin cewa ta shiga ƙofar da ba a komawa daga cikinta.Rikon ta ta fara da ta barta ta huta zazzaɓi ne ajikin ta tsaki Saffy Chic tayi ta rufe mata kofa ta fice. [11/2/2025, 5:38 AM] OUMMU MUWADDAH: Follow the Husaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah) WhatsApp Channel. channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ________free book _page-5 Babu wanda ya sake shigowa inda Samayya take har dare, hakan ya yi mata daɗi.Saffy ce ta murɗa kofa ta dawo ciki wata iri shiga mara kyau gani, ciki fashashiyar muryar ta iri ta 'yan shaye-shaye mai cike da umarni a ciki ta ce.“Ki shirya. Alhaji na son ganinki yanzu. Kar ki sake min tambaya,ki sani in kika bi umarnin to rayuwarki za ta canza.”Sumayyah ta kalle ta cikin tsoro. “Amma… me zan je in yi wurin Alhaji da dare haka?”Saffy ta yi murmushi.“Zaki ga komai da idonki. Ki taho kada ki tsaya tambaya.” Cikin fargaba, Sumayyah ta bi ta har suka shiga babban wani ɗaki me cike da kayan alatu. An cika wurin da kayan alatu- kujeru masu sirdi, ƙamshin turare mai nauyi, da sautin dariyar maza da mata. A can tsakiyar ɗakin, ta hango Alhaji Ɗan Dubai zaune a kan kujera mai faɗi, yana dariya da wasu manyan mutane masu kuɗi-wasu da babban ciki, wasu da farin gemu.gefe su duk yaran 'Yan mata masu ƙananu, a tskiyar parlour wata yarinya ce mai kyawu gaske,tana ta rawar banza cikin night gown duk ta kama jikin ta. Sumayyah tana shiga, duk suka juya, Idanu suka zuba mata kamar yadda karnuka ke kallon nama mai ƙamshi. Wani daga cikin manyan ya ɗaga kofi lemo yana dariya:“Alhaji, wannan sabuwar ce? Kai, kai! Ka ce kaya sun sauka!” Wani kuma ya da gefe yace: “Wannan fa ba irin tamu bace Ga ga duk kan alama sabuwa ce, ba ta saba da irin wannan rayuwa ba.”Alhaji Ɗan Dubai ya yi Murmushi yana kallon Sumayyah. “Eh, sabuwa ce.. kuma tana da kyau. Ku bari in koya mata yadda ake zama ‘yar gari mai sanan sai ta fara kawo muku ziyara.”Yana rufe baki dariya ta cika ɗakin. Sumayyah ta tsaya cak, jikinta ya mutu gaba ɗaya. Hannu ta soma rawa, idanunta suka cika da hawaye.Ta tuna Innar ta, da maganarta ta ƙarshe, zuciyarta ta soma dukan uku-uku.Ta juya da ƙarfi za ta gudu,Saffy ta rufe ƙofar ta tsaya a bayanta tana murmushi.“Kin riga kin shigo,kaddarar ki ta fara daga yau.”A wannan lokacin ne Sumayyah ta gane cewa duk wanda ya shiga wannan gida- ko dai ya lalace.kifa kanta tayi tsakani tsinyar ta tana kuka, tana ambaton:“Ya Allah, ka bani ƙarfi. Kada in zama ɗaya daga cikin su…” ***** *Tuna baya* Rabi yarinya ce mai kawaici da kunya.A lokacin baya,Malam Sule Giɗaɗo yaro ne matashin ankawo shi almajiranta Bunkure, ya taso da ƙazo kuma shine Baban yaro aciki Almajirai Malam Idi hakan ya sa duk saure almajiran Malama idi suke shaka sa acikin wanan hali Ya hadu da Zulai ya aure ta haihuwar ta daya ya sake aure Hauwa, yana da haka ɗauka kaka ta tazo masa acikin ƙauye su,ya shahara, guri yiwa mutane kauye Giɗaɗo wa’azi, ya zama mai jama’a, wanda kowa yake girmamawa.lokaci Da ya sake zuwa gaida Malam Idi, ba don neman aure ya zo ba, sai don neman gaida Malami sa, wato mahaifin Rabi. Bayan su gauisa da nutsuwa Malam ya Kali Sule yace. “Sule ga yarinya ta Rabi,na baka ita a matsayin sadaka domin Allah.”Sai da gaban Sule ya buga dan Shi rabi bata taɓa burge shi ba Gasali na Matan sa biyu sun isheshe rayuwa.Rabi da tazo kawo masa ruwa ta tsaya cak. Kallon mahaifinta kawai take yi, idanunta suka cika da hawaye. Ta so ta ce a’a, amma kalmar “na baka ita sadaka” ta rufe mata baki. Haka Nauyi Malam idi da kuma kwarjinin da yasa shi amincew da zumar washe gari zaizo da shedu a daure masa aure. Haka kuwa akan yi washegari Malam Sule ya dawo da magabatan aka ɗaura musu aure wanda a take a lokaci ya tafi da Rabi. Bayan kwana biyar da faruwar haka, cikl dare gobara ta tashi babu gidan da bata shigaba wanda yasa iyaeye Rabi konewa musru, hakan ya jefa Rabi ciki tashin hakali da damu wanda hakan shi kuma Yayi wa Malam Sule daɗi ga samu hanyar ƙuntata ma har ta gaji ta bar masa gidan. Daga wannan rana, rayuwarta ta sauya gaba ɗaya.a gidan Malam Sule, Rabi ta tarar da matan sa biyu- Zulai da Hauwa.Su biyun sun haɗu gaba ɗaya wajen wulakantarta.A wurin cin abinci, haka zasu fara yaɓa mata magana ciki waka ko wasa tauna kamar kullum suna zama Zulai ta kalleta ta ce.“Ke fa matar sadaka ce, ba ‘yar gida ba. Me kike nema anan?” haka ta zame hannu ta ta barsu, shewa sukayi suka ci gaba da cin tuwo su. haka rayuwar ta taita guda na acikin gidan Malam Sule.Idan ta yi ƙoƙarin shiga cikin su, sai su zage ta, su kwace mata abin hannunta. Malam Sule kuwa, ko da ya ga hakan, bai ce komai ba.A idonsa, Rabi ba komai bace face kyautar da aka bashi-a matsayi matar sadaka.Kullum tana kuka cikin sirri, tana roƙon Allah: “Ya Allah, ka bani haƙuri, ko da kuwa zuciyata zata tarwatse.”Haka rayuwarta ta koma kamar ta bawa a cikin gida,ana ɗaukar ta ba mace ba, tamkar wacce aka kawo don yi wa sauran mata hidima.Wata rana, Zulai ta zubar da abinci a ƙasa.ta kwaɗawa Rabi kira da gudu ta fito daga nata ɗaki jikinta na rawa haka ta durƙusa agab Zulai tace"Yaya Zulai gani.”tsaki tayi ta tura ɗaukali gaban goshi tace."Rabi, ki tsabtace nan. Ai ke ce ‘yar sadaka, aikin banza ya fi dacewa da ke.Ubanki saboda tsabar kwaɗayi ya liƙawa Malam ne Sadaka.”Haka Rabi ta durƙusa tana share guri, hawaye na sauka daga idonta.Cikin zuciyarta tana jin kamar wani abu yana murɗawa,Ba wai saboda aikin bane, amma saboda yadda ake kallonta tamkar ba ta da ƙima. Da daddare, tana cikin kuka sai Malam Sule ya shigo, ba tare da jin tausayinta ba.“Kedai anyi mashiriciya Yariya ce ke da baza Afrika yi miki fada ba, in ba kaddara ba mai zai haɗa Ni dake ”Wannan magana ta sake d ɗanna mata ciwo a zuciya.Haka ta rayu cikin wulakanci, zargi, da kunci.Zuciyarta ta fara yin rauni-amma ba ta faɗa wa kowa ba. Bayan shekara guda da wannan halin, Rabi ta samu ciki.Sai dai maimakon farin ciki, ta fara fama da matsanancin damuwa. Zulai da Hauwa suna ƙin taimaka mata, suna cewa: “Ke ma matar sadaka ce, dan masifa sai da kika bin malam da Asiri har kika samu ciki kin? Wallahi sai mu hana ki kwanciya hankali a gidan Malam.”Suna yi mata duka da wulaƙanci, Malam Sule kuma ya yi duma kamar bai san abin da ke faruwa ba.Rana ɗaya cikin dare, Rabi ta tashi da ciwon ciki da zafin kai.Tana ihu tana cewa: “Kai na! Kai na! Ya Allah ka ceci Ni ka ceci ɗana!”Sai da mutane unguwa suka cika gidan masu tausayi ta basu da yawa domi duk mutaneZulai da Hauwa ne kuma gasu haifaffen cikin kauye.Tun tana kukan kanta kashe ta koma yin dariya lokaci ɗaya.tana kaiwa mutane duka tana surutu. “Ni matar sadaka ce… amma ɗana ba sadaka bane!”Daga wannan rana, hankalinta ya tafi.Babu wanda Wanda ya taɓa kaita asibiti Ciwon zuciya da ta jima tana ɗauka a asirce, ya fashe ya koma hauka babu kasuwar da bata zuwa sai tafi tafiya mai nisan gaske ta dawo duk nisan dare.Duk wanda ya gan ta sai ya ce, “matar Malam ta haukace. Bayan ta haifi ɗiyar ta, Sumayya, mutane suka fara kiran ta da “Mahaukaciya.”Sumayya ta taso cikin wannan hali, tana kallo mahaifiyarta tana kuka tana dariya, tana sai ta tafi yawo da Sumayyah a bayan ta tayi tafiyar kwana biyu uku batare da ta waiwayi gida ba haka kuma babu mai neman su.Duk abin da ta tsinta abola tare zasu ci da Sumayyah yariyar yar wata bakwai.Ruwa ko da na kwata ne bata fargabar sha ko ta bawa Sumayya tasha.Hakan yasa aka fara kiranta da *Yar Mahaukaciyya* Wannan shi ne asalin haukar Rabi-hauka da ta samo asali daga zalunci, wulakanci, da ciwon zuciya, ba daga aljani ko sihiri ba.wanan labari yana nuni da irin zafin rayuwar mace da aka tilasta mata aure saboda “sadaka”, wanda ya jawo bala’in da ya rikide zuwa hauka. *Gundari labari* Daren Da haka Alhaji Ɗan Dubai ya kama hannu Sumayyah zuwa wani hadaɗe ɗaki, tun da ta shiga hakali ta ya sake tashi dan Alhaji Ɗan Dubai baiji kunyar taba a gaban ta ya jire rigar da take jikisa ya tun karo ta, zubewa tayi kamar mai sahafar aljanu tana roƙon sa. “Dan Allah Alhaji kaji tausayi na kar ka lalata min rayuwa wallahi bani da kowa sai Inna”dariya ya bushe da ita"Hahhha Haba yariya duk iri dukiyar dana narkar akan ki kuma ta tashi abanza kamar ki fara dan Wallahi ba tausayi ne da niba, an gaya miki a banza muke neman kuɗi?” ya fada yana labe lebe kamar tsoho busuru.yana sake zuwa zai kama ta sai kuma taya lumshe ido ya kifa kan gado Shaɓar kamar matacce bacci ne mai nauyi ya dauke shi da alamu giyar da yasha ga tafiyar mota da yayi yasa shi bacci.Zubewa tayi ƙasan gadon, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Wani irin shiru ne ya mamaye ɗakin, ta bishi da kallo ko afuska Alhaji Ɗan Dubai bashi da kyau kallo bare wata mu'amula ta haɗa ka dashi.tana juyo hayaniyar mutane har da ƙarar kiɗa.ta goge hawayen da suka zubo mata.“Ya Allah,ka ɗauke ni daga nan,ina Inna ita ne take yanzu? Me yasa aka kawo ni nan? Wannan ba makaranta bace… guri yaɗa alfasha ne...” Tana fadi haka ta rufe fuskar ta da tafin hannuta, tana rawar kuka mara sauti. Da haka bacci ya ɗauke ta bata san Lokaci da Alhaji Ɗan Dubai ya fita ba sai jin kara buɗe ɗaki tayi. Da sauri ta gyara zaman ta a tunani ta Alhaji Ɗan Dubai ne ya dawo. Wata mata ta ce ta shigo Fusakar ta taci Bleaching har wani tantarewa fatar ta take saboda tsufa da kuma mai lalata mata fusakar da Bleaching shugowa tayi tana cin chew gam. idanunta duk sun jeme alamun wahala da shekaru sun bayyana. Tsohuwar ta kalli Sumayyah da yan zuma take kuka, ta zauna kusa da ita.“Ki daina kuka, yarinya. Idan kika yi kuka anan, Zaki mutu cikin ƙunci da hawaye. Kin riga shigo inda mutane ke haɗu da kaddara.” Sumayyah ta kalle ta cikin tsoro.“Wane wuri ne wannan? Me yasa suke kiran shi da makaranta?”Tsohuwar tayi murmushi cikin sanan ta tura kofar ɗaki ta ce.“Makaranta ce, amma ba ta alheri ba. Wuri ne da ake sayar da mutuncin ‘yan mata. Alhaji Sa'idu Ɗan Dubai da abokansa suna kawo sabbin mata kamar ki, suna amfani da su don kuɗi da nishaɗi. Sannan idan mace ta lalace ko ta ƙi amincewa… to sai su siyar da ita guri matsafa.” Sumayyah naji haka ta fashe da kuka.“Ya Allah… to me zan yi yanzu?taya zan kuɓuta.”Tsohuwar ta matsa kusa da ita, ta kama hannunta. “Ki saurare ni da kyau. Ki boye damuwa, ki nuna kamar kin amince da komai. Ki bar zuciyarki cikin addu’a.Akwai wata hanya guda ɗaya da zaki iya iya kubuta wanda ba kowa ne ya san da ita ba sai-ta hanyar Sabuwa mai girki. Ita ce ke da sirrin fita fita kuma aminiya tace.shawar da zan baki, ki jira lokaci ya yi. Kada ki yi gaggawa, kice zaki karanbani fita.” Sumayyah ta kalleta idon ta fall ƙwallah. “Yaya sunan ki Baba?” Tsohuwar ta yi murmushi."Sunana Hauwa’u… amma a nan suna kirana da Kaska.(Raɓi mai jini).” Tana faɗa mata ta miƙe tsaye, ta kalli Sumayyah a karo na ƙarshe kafin ta fita.“Ki tuna kalmomi na, 'Yan mata. A wannan wuri, kalmar ‘Allah’ tana da ƙarfi fiye da kuɗin Alhaji.”tana faɗa ta fice ta rufe mata ƙofar, Sumayyah ta kwanta a hankali, zuciyarta tana harbawa, ta lumshe ido tana maimaita addu’a, “Hasbunallahu wa ni‘mal wakeel…” [11/7/2025, 4:38 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-6. Bayan kwana uku bata sake saka Alhaji Ɗan Dubai a ido taba kana kuma yasa ta a ciki Nutsuwa, ko abinci bata sani wanda yake kawo mata daga an ƙwanƙwasa mata ƙofar tana buɗewa dai taga an ajiye an bar guri, ciki dare kam tamkar rana haka take ji motsi mutane banda kaɗe-kaɗe da wake-wake, yau tsayi sati ta canja babu karyar duk da baƙa ce amma fatar ta tayi kyau ta murje kyawun ta ya fito sosai, yamma ce yau kuma yau Alhaji Ɗan Dubai ya dawo daga tafiyar da ya yi, gidan gaba ɗaya ya kaure da sowa, cikin firgici Safy chinc ta faɗo ɗaki tunda Sumayyah ta ganta tasan ba lafiya ba, miƙewa tayi jikin ta narawa tace."Aunty Safy meyake faruwa naji magana kuna naga bakar bakya cikin kwanciyar...” Tare mata nufashi tayi tace.“Sumayya Yau Alhaji ya dawo kuma har da wasu baƙi wanda ba 'yan nan kasan ba a labari da naji wai safarar mata zai fara zuwa ƙasar waje ina tsoro kada Alhaji ya haɗa dake yanzu haka fitar da yaran gidan ake suna zaba... Knocking aka bafar wanda yasa Safy faɗawa bayan labule ta buya Alhaji Ɗan Dubai ne da Zee Cash wace taci uban Attached har gadan baya hannu da ɗauke da manyan farata, kana gani jiki ta kasan na matan bariki ne. Taku take tana tauna chew gam jikake tass kass. SA bulbula ƙamshi turare rake baki Alhaji Ɗan Dubai ya washe lokaci da suka yi ido huɗu da Sumayyah gefe gado ya zauna ya saki wani lalattace Murmushi sanan yace. “Zee Casha ina so ki gyra min ita, kisan turawan nan suna son bak'ar fata dan Allah kuyi da jiki kar ki jami asara” sai da sako murnushi mai jan hankali kafi tayi far da ido ta tace. "An gama Alaji na”Bata jira me zai sake cewa ba ta kama hannu Sumayyah suka shiga Kamar banɗaki da yake manne da ɗaki sai da ta karewa Sumayyah kallo kafin ta miƙa mata wasu kayan bacci Dream Luxe tare da daka mata Tsawa. "ƙiyi hanzari ki sa mu fita”Jikin ta na rawa ta amsa sai da ta juya mata baya kafin ta saka rigar, ko bra bata, bata tasa ba,hakan yasa dukiyar Fulanita suka bayyana, iya kar rigar gwiwa, tin daga ƙasa zuwa sama ta kalli jikin ta ido ta ya ciko Zee Cash tana ƙoƙarin fita Sumayya ta rike mata hannu da sauri ido ta na fitar da hawaye tace. “A haka zan fita Hijabi fa?”Dariya Zee Cash ta fara tana tafa hannu har sai da ido ta ya ciko da hawaye sanan tace."Ke Uban waye yace miki nan gidan gidan saka Hijab ne Malama ki fito daga yau zaki manta da hijab da wata kunya.In Allah ya temake ki ma ki tafi ƙasar waje.” Wata iri bugawa ƙirji Sumayyah ya yi kafin ta sake magana Zee ta ja hannu ta da karfi suna fita, yana zaune inda suka barshi, kallo Alhaji Ɗan Dubai ya ƙarewa Sumayyah ya kalli Zee Cash yace. “Zee yariyar nan fa ba Ƙaramin kuɗi zata kawo ba, har na tuna lokaci kika zo gidan nan”ƙugu Zee Cash ta fara kaɗawa kafi tace.“Ai ina ga har yanzu akwai wanan ƙuruciyar ko ta kauce ne?”ta faɗa tana wurgawa Sumayyah harara.Dariya Alhaji Ɗan Dubai ya yi.“Mata!Mata ba'a raba ku da kishi aike Zee Cash bainu ce bakya tsufa sai dai ki sake sabo toho” Duk da haka bata saki rai ba suka fita. Tunda suka fita, zuciyar Sumayyah ta fara bugawa da wani irin sauri, kamar zata fasa ƙirjin ta,ta fito. cak ta tsaya gani duk wasu yara masu ƙananu shekarun suna taye kowace da shiga mai bayyana tsiraici,mazan da suke zaune akan manyan kujeru ko ba asanar da kaiba kasan sun ci sun ta da kai.farar fata suna da yawa.Alhaji Ɗan Dubai ya zauna kusa da manyan mutane,hayaniyar mata da maza ta kaure kamar masu cin kasuwa, babu wanda in ya ɗora idon sa akan Sumayyah baya sake sha'awar kallo ta kowa da irin kallon da yake mata. Wani mutum dogo mai farin yadi da tabarau ya nufo ta, Zee Cash ta sakar masa wani lalattace murmushi ta ce.“She’s fresh... pure one. Straight from the house.” Mutumin ya ɗaga gira yana kallon Sumayyah kallo iri na mazan 'yan duniya sannan ya murmusa.“Good... I like her.”Alhaji Ɗan Dubai ya shafi tunbi sa ya kallon mutumin yace. “Alhaji Armani Nake gaya maka wanan yariyar garanti ce, duk wanda ya fanshe ya samu Babar kadara,Haka in ana maganar inganci rami kasamu bakar mace.” Dariya suka sa suka tafa. Zee Cash ta matsa kusa da Sumayyah ta murɗa mata hannu a hankali tana ɓoye azaba da take mata da murmushi.kafi ta fara mata magana kamar me raɗa. “Ki nutsu, kin nuna kema wayayi ce.”Sumayyah tayi sauri share hawayen da bayan hannu ta da sauri.wani bature ne da tun zuwa Sumayyah ya kwadaitu da ita. miƙewa ya yi da kwalabar giya, yana layi, har ya kai inda Sumayyah take tsaye jiki ta na rawa zagaya ta ya fara yana lika mata Dalla agoshi.. *KANO* Amir ɗan asalin ƙasar Lebanon ne, mahaifinsa Attajiri ne da kasuwanci ya kawo shi Najeriya tun shekaru baya da suka gabata. A nan Kano, musamman unguwar Nasara G.R.A, mahaifinsa ya gina gida mai faɗi da tsari irin na Larabawa, wanda yake cike da shukoki na zamani.Amir matashi ne dogo mai cikakken jiki. Fatar jikin sa fara ce mai haske, idanunsa manya ne masu ɗaukar hankali, suna da ɗaukar hankali idan ya kalle ka. Gashin kansa baƙi ne mai laushi da sheƙi saboda yawan gyran da yake sha, ƙasumbar sa da take zagaye da fuskarsa ta ƙara masa kyau da kwarjini. Hancinsa dogo ne madai-daici, girarsa tana da yalwa, mai ɗan lanƙwasa tamkar hannu aka sa guri lanƙwasa ta. Ammar mutum ne mai nutsuwa, bashi da yawan magana sai dai in ta kama ko ya zama dole sai yayi.Duk lokaci da ya yi magana, muryarsa tana fita a hankali cikin salo mai daɗi,cike da sanyi wacce ke jawo hankalin mai sauraro.Ammar iri mutunan ne masu ilimi. Yana gudanar da harkokin kasuwanci tsakanin Kano da Legas, yana shigo da kaya daga Dubai da Beirut. An san shi a cikin ‘yan kasuwa a matsayin “Amirul Nasara”, saboda irin tsarinsa, gayunsa, da yadda yake hulɗa da manyan mutane cikin salo na ladabi da mutunci.duk wani aiki mahaifinsa Alhaji Ibrahim Matawalle shi yake ɗorawa.turaresa ɗaya ne wanda duk wani wanda yake tare dashi ya sanshi da shi,turare ne na musamman daga Lebanon ake kawo masa.Motar sa wace yafi hawa Range Rover Sport ce, abawai dan bashi da wasu motoci ba. Riga ce “white kaftan” ta yi masa kyau kamar wadda akayi ta da silki, hannunsa na riƙe da wayarsa yana duba e-mail saboda wata sabuwar kwangila.Kamfanin Al-Labani Constructions Ltd. ya samu gayyata zuwa Lagos domin tattaunawa da wani babban kamfani na kasashen waje. Ba ya son tafiya, amma muryar mahaifiyar sa Hajiya Maryam, ta yi matukar tasiri agare shi. Nufashi ya sauke ya ɗauki ƙaramar Akwati ya fita bedroom ɗin Hajiyarsa ya shiga yana zuwa ya iske ta zaune da alamu lafila ta gabatar cikin nutsuwa ya zube a gaban ta har sai da tayi adu'a suka shafa atare, cikik kulawa ya dube ta. “Hajiya Insha Allah zan tafi ki samu cikin addu'a da fatan nasara”Kansa ta dafa ciki Nutsuwa tayi masa addu'a sosai da fatan nasara kafi ya miƙe ya fito. drive NE ya kaishi Airport din Malam Aminu kano. Bai jima ba girjin su ya tashi. ƙarshen watan Yuni. Rana ce mai ɗan zafi, iska tana kadawa a hankali, bai isa Gidan su da ke Lagos ba sai bayan Sallah magariba, wanka kawai ya yi ya gabatar da addu'a da ake binsa sanna ya kawanta dan A gajiye ya dawo, washe gari ma bai fita ba dan tautaunawar tasu sai yamma dan haka da yayi Break fast komawa yayi bacci bai tashi ba sai karfe biyu da rabi Bratheroom ya fara shiga ya yi wanka ya wanke bakisa wanan ɗauro Alwala, bayan ya idar da Sallah ya fita ya ci Abinci, ƙarfe uku dai-dai Motar Ammar ta tsaya a gaban ginin kamfanin Global BuildTech Ltd., kamfanin da suka gayyace shi don kwangila da Al-Labani Constructions.Sanye yake da,dakakiyar Shadda, tsintsiayar hannu sa ɗauke da agogo azurfa,fuskarsa cike da nutsuwa. Bayan sun gama,tattaunawa, Company Al-Labani Constructions.ya yi nasara,Farinci sosai Amir ya shiga, dan Rayiwar Lagos bata burge shi gashi zai koma Kano cikin kwana biyu da yarjejeniyar Hannu jari. Yana fita daga ofishin, ya ɗaga idonsa sama, yana murmushi, zuciyarsa farin ciki. yana nufar mota. Ihu suka fara dan babu wanda ya taɓa samu kwarji, wanda har Baturai zai rika masa liƙi da dalla tun bai biya buƙatar sa da yariya ba, ciki harshe nasara yace ya siye ta Dalla ɗari ihu aka sa ana tafi a take a guri ya ajiyewa Alhaji Ɗan Dubai kudisa Cash haka sauran mutane suka zaɓi yaran da zasu tafi dashi. Yana ajiye kwalabar giyar ya kama hannu Sumayyah suka shiga mota kuka Sumayyah ta fara tana bu-buga kofar mota Har suka fita daga gidan. Washe gari Ammar sauri yake sosai dan baya so ya yi shigar dare lokaci da ya isa Roundabout lokaci Sumayyah da baturai suka isa kallo wanda zai cece ta take, ido ta ya kai kan Ammar. Yawan Comment shi nai ƙarfi gwiwa ta [11/10/2025, 12:01 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Masu buƙatar magana dani WhatsApp:08169621656 Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-7 Lokacin da idon Sumayyah ya sauka kan Ammar,Jitayi wata iri nutsuwa ta shige ta.Wani irin daɗi da fatan ceto ya haɗe mata guri guda.Cike da kwari gwiwa ta fara buga gilashin motar tana ihu da karfin, ciki ƙaraji me haɗe da kuka.“Don Allah ku taimake ni! Ku cece ni! Don Allah!”matashi bature dake gefenta ya sa hannu ya buge mata hannu yana muryar sa ta turawa yace. “Keep quiet, girl!”bata San me yake nufi ba bare ta gane yare nasa, haka ta sake yinƙuri komawa jiki window motar. **** Tun da Sumayyah ta bat gidan Malam Sule Gidaɗo duniya ta dawo musu sabuwa kuɗi sun wadata harda jannareto malama ya siya da sabuwa tv, hakan yasa Sadiya da Lubna girman kai da ɗagawa, jinsu suke sunfi kowa kaf kauye Giɗaɗo kowa suka ga dama taka shi suke gashi yanzu gidan duk an malale shi da suminti, yasha shafe farar kasa kai ka ce gidan sabuwar amarya ne, Baba Hauwa ce zaune tana ta asuwaki da Ƙirjin kaza Baba Zulai kuwa ana turakar Malam daga waje kana jiyo 'yar dariyar su, surutun Inna ne yake tashi me ciki da kuka.tana zaune ƙarshe bango, jikin ta duk sawu duka, muni ɗaki ya kazanta,saboda rashi gyra ga yawan fitsari da take yasa ɗaki ya fara murtuka²tsutsi, da kudancin cizo kannan duk ya dugduge ta daɗa baƙi miƙewa tayi ta fito tsakar gida, hango Baba Hauwa yasa tafiya da sauri tana zuwa, Baba Hauwa bata ankara ba Inna ta suma hannu ciki ciyar kasa ta dauka ta koma gefe tana ci tana dariya, miƙews Baba Hauwa tayi ta kalle ta, wani mugun ashar Ta lailayo ta makawa Inna. “Malam Yaya Zulaihat Sadiya maza ki kira Yusuf yazo yaci Uban yariyar nan yanzu saboda Allah matar nan dan Ta raina ni! Ni zata zo ina cin abu tasamin Hannu”ruwan bala'i Baba Hauwa take ta surfa hakan yasa Malam da Baba Zulai fitowa Lubna na fito ta tafi ciki ɓaci rai batayi wasa ba ta ɗauke Inna da wani mahaukaci mari.Zaki na ɗiban Albarka takewa Inna babu gani ta haife ta bare ta samu darajar ta na matar mahaifi ta. Kuka Inna ta fara tana cili da kafar kazar zata shiga Ɗaki Baba Zulai ta fusgo ta. "Ina zaki tsohuwar munafuka wato kinyi tsiyar zaki koka ɗaki, Oni Zulai dama ance mahaukata tsawon rai gare su,gashi tamu har yanzu rai yaƙi halin.... Yusuf ne ya sugo da danƙo markaɗe Ai Inna na gani sa ta kwasa a guje tayi waje ta ƙofar baya binta yayi Baba Zulai ta ƙwalla masa kira. “Dawo karka bita bakin duniya ya kama,ai komai dare zata dawo ne damu take zance Malm muje.”Da haka taro ya watse kowa ya kama gabansa. 🌸🌸 Idon Ammar ne yakai kan motar kallo daya ya yiwa motar ya kauda kai tare da lumshe ido sa.lokaci da aka bada hannu ammar ya sake buɗe manyan ido sa, baza ka taɓa gane motar da Summayyah take ciki yake kallo ba,har zasu juya ya sa drive ya taka burki, Direbansa ya dubi Ammar cikin mamaki, tare da cewa “Oga, what happen?”Ammar baice da shi komai ba sai dai ido sa har yanzu suna kan motar da aka saka Sumayyah. Cikin 'Yan sakanan zuciyarsa ta buga da karfi kamar ana dukan ganga lokaci da ido sa ya kai kan su Sumayyah da kiss ɗin da Baturai yake ƙoƙarin yima Summayyah. A hankali ya ce.“Follow that car... now.” Direban bai yi wata-wata ba, ya shiga bin motar da sauri. Haka suka ci gaba da bin motar har zuwa wajen wani katafaren gida, gida ne na alfarma kai kace ba anan kasar yake ba, manyan masu Security a ƙofa. Ammar, sun dau mintes 5 kafi ya ce da direban,“Stop here.” fitowa ya yi daga motar yana kallon gidan cikin mamaki. Wannan ba irin wuraren da yake zuwa bane. Ginin ya yi girma, amma akwai duhu da shiru alamu rashi gaskiya ya bayyana agidan. A lokacin da suka shiga gidan tsoro ne ya sake kama Sumayya, da sauri ta dafe kirjin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.A hankula tace. “Shikenan, yau zan,mutu. Me yasa na bari na shiga wannan gida? Me yasa Baba zai min haka Shikenan an rabani da Inna ta bata da kowa?”ta sake tura kanta cikin cinyoyin ta.wata yar duma-dumar buduwa ce ta jawo ta da ƙarfi, duk da ba fara bace amma kana gani ta kasan babu ɗigo musulunci a tare da ita, janta take har ta shiga da ita cikin wani ɗaki mai duhu.bayan 'yan daƙiƙu haske ya gaureye ɗaki ɗakin ne na gaske, wanda aka ƙawata da kayan kwalliya da turaren wuta mai ƙamshi mayuka iri na waje har da kayan sawa. A tsakiyar ɗakin kuwa akwai gadon roba mai yalwa da farin zanen satin, Har da furani a sama.tana kaita ta fice ba tare da tace komi ba, Sulalewa ƙasa Sumayyah tayi, ta fara dukan Carpet ɗin tsakiyar ɗaki tana kuka. “Ya Allah ka cece ni daga wannan masifa. Ban san inda nake ba, ban san me ake son yi dani ba...” A gefe kuwa, Ammar yana tsaye jikin motar sa, wayar sa ya ciro daga aljihu wando sa,kira wani abokin sa da ya dake cikin hukumar tsaro.ASP Mubarak.duka biyu Ya yi picking call ɗinshi. Yana Ammasa sallma ya sake lumshe ido kamar wani mace kafi ya iya ɗaga laɓan sa a hankula yace. “Mubarak, please I just saw something strange, some men were taking young girls into a compound. I think it’s human trafficking.”Da sauri Mubarak ya ce. “Send me the location, Ammar. Don’t go inside yet. We’re coming immediately.”godiya Ammar ya yi takaice ya kalli agogon hannunsa, zuciyarsa cike da tashin hankali yace.“Ya Allah, ka ba ni ikon taimaka mata…” Cikin gida kuwa, Classic Don ne ya shigo ɗakin da ake shiryawa Sumayyah. Idanunsa cike da jaraba da da kwaɗayin zai more da yariya ƙarama,murmushi yayi kamar zaki da yaci ganima. Cikin wata hausar da mara daɗi ji yace.“Ka ga yanzu ka zama nama.zamu ji daɗi zan baka kuɗi dayawa da yawa,”ya ce yana matsowa kusa da ita.Da sauri Sumayyah ta ja baya, tana hawaye, tana girgiza masa kai. “Don Allah kar ka min haka, ka tausaya min, ka tuna Allah kasani bani da kowa sai Inna ta kuna bata da lafiya…” dariya yasa yana tunkaro ta dan bakomi yake ganewa a cikin hausar taba.yaja ƙoƙarun kai mata hannu,sai ankirari ya kaure layi gaba ɗaya. “Open up! Police!” Daya daga cikin, 'Yannmata da suka gyra Sumayyah ta firgita da gudu ta fita daga ɗakik ta nemi maɓuya, Classic Don ya kasa motsi saboda razana jikin sa ya hau rawa.ba tare da ya motsa ba aka fara dukan ƙofar parlour har suka ɓalla ta.Jami’an tsaro suka shigo da bindigogi a hannu. ASP Mubarak ya yi magana cikin tsawa. “Everyone freeze!” Ammar wanda ya tsaya daga baya ya shigo, idanunsa suka sauka kan Sumayyah wacce ke zaune a kasa tana kuka ita duk ruɗe da Classic ya yi atunanin ta haukan su ne na fafar fata yake. Sai da taji maganar mutane da yawa ta ɗago da sauri,Ammar ta gane dan bazata manta fusakar sa da iri ɗinban karan mahaukaciya da yamata lokaci da take roƙon ya temaka mata.a jiyar zuciya ta sauke. Wata irin nutsuwa ta shiga zuciyarta tabbas tasan yanzu zata fita daga hannu mugaye mutananan masu jan kunnuwa. Mubarak ya kalli jami’ai ya ce."Arrest all of them. Including that man”ihu Classic Don ya fara yana kiran sunan Alhaji Ɗan Dubai yana cewa siyan Summayyah yayi da kuɗi masu yawa.babu wanda ya kula sa.saima Umarni da ASP Mubarak ya bawa jami’an suyi aiki. Gaba yada kata tare yan nata uku da Classic Don aka watsa su cikin mota Aka rufe. Tun da aka fita dasu tana durƙushe a guru ko motsi kirki ta kasa, sai kallo da ta kafe Ammar dashi tana hawaye.gajiya tayi da shuru kamar me magana da zuciya yace."Ko mu barki anan?.” A hankula tace“Ka… ka ceci ni...nagode”ba tare da ya yi magana ba ya durƙusa kusa da ita,. “Ki godewa Allah bani ba.… everything will be fine.” (Nikuwa Ummu Muwadda nace Malam Ammar Sumayyah bata ji yare nasara)😃😃🫣. Cikin ranta ta ce.“Ya Allah, ina godiya da ka aiko da bawan ka dan ya fitar dani daga wanan jahannama.”wata Iska mai daɗi ta ratsa su da haka ya miƙe ya fara taku."Ki biyo ni kin ga dam”Da sauri ta bishi ko Mayafi bata nema ba, baya suka zauna ita dashi ya kalli drive yace"Ka kaimu Al-Noor hospital” Ba musu drive ya kai dau haya,sannu-a-hankali,suka isa katafare Hospital wanda yake cike da shukoki masu zubi da tsari,ganyen bishiyoyi da ke gefen wanda suka raba titi nan dake ciki asibitin Al-Noor Clinic da ke tsakiyar Lagos. Haske ta ko ina baza ka dauka ciki asibitin kake ba,Bayan su Isa wani Room aka shiga da Summayyah duk wani bincike ƙwarare Doctor ya gabatar, fuskokin mutane uku ne a bakin gado Ammar, ASP Mubarak, da likita. Likitan ya yi gyran murya. “Alhamdulillah, ba ta samu raunuka masu tsanani ba. Amma tana cikin tsananin firgici da rashin lafiya saboda yunwa da tsoro. Zata ɗan huta kafi ki tafi.” Jinjina kai Ammar ya yi.Ya tsaya yana kallon fuskarta wacce take lullube da farin asibiti, hawayen da ta kwanta da su sun bushe amma idanuwanta suna nuna alamar tsananin wahala da ta sha. A zuciyarsa ya ce, “Me yasa irin waɗannan mutane suke cin zarafin yara masu ƙananu shekarun? Allah ya tsine musu.in kuma masu shiryawa ne Allah ya ganar dasu.” Bayan likita da ASP Mubarak sun fita Ammar ya zauna a kujerar gefen gadon. Robar ruwa ya ɗauka zai sha. ta motsa, ta ɗan buɗe idon ta tana kallonsa, tana ƙoƙarin miƙewa. Ammar ya yi saurin da katar da ita cikin. “Don Allah, ki kwanta. Ba sai kin yi magana ba.” Cikin rauni ta ce. “Na… na gode. Ka ceci rayuwata.”murmushi ya yi mara sauti,muryarsa cike da sanyi ya ce. “Ki godewa bani ba,ki sani yanzu kina cikin aminci yanzu. Ki kwanta ki huta.”tsintar kanta tayi tana bin Umarni sa. Ta maida idanuwanta ta rufe, tana jin muryarsa na sake ƙara mata natsuwa da Kwari gwiwa. Washegari da safe, rana ce ta fito mai zafi ta ruwa.da addu'a ta tashi, ta ji jikinta ya dan samu sauƙi, amma zuciyarta cike da nauyi da tambayoyi. A bakin window ta hango Ammar yana tsaye yana waya yake bata gani fusakar sa sai faffaɗan bayan sa,sanye yake da farar riga sport.ciki daddaɗar Muryar sa mai cike da iko da kamala yace. “Eh… Mubarak, kawai ka bar su tafi tunda basu yiwa yariyar komi ba i dan yalin su ne zasu sake a gaba.”bayan sunyi Sallama,ya kashe wayar ya juyo, idanunsu ne sarƙe guri ɗaya. Lokaci ɗaya ta ji kunya ta lullube ta,da sauri ta juyar da kai.Baki ya taɓe. “Kin farka?” ya tambaye ta cikin natsuwa. “Eh.” “Yaya jikin ki?” “Alhamdulillah…, ina kwana” ta faɗa tana wasa da dogon yatsu hannu ta.gani taki saki jiki yace. “Ina so ki nutsu ki kwantar da hankali ki, sanan Duk abin da kike bukata, ki faɗa min.”kai ta girgiza.“Na gode, amma bana son zama anan zaka maida Ni guri Inna ta dan Allah bata da kowa sai ni.” Kansa ya dafe dan kan sa har ya fara masa ciwo wanan yar maganar da yayi. kallo ya bita dashi na ɗan lokaci, yana mamakin yariya ƙarama amma tana da izza da kunya irin ta mata masu tarbiyya.lokaci ɗaya ya ji wani iri yanayi a kanta gani hakan yake tamar tausayawa ne. “Zan kan akiki gurita amma sai kin daɗa samu sauƙi ki faɗan maye sunan me yasa ki da yan uwanki?” Idonta ne ya ciko da hawaye, cikin rauni ta ce. “Na rasa Soyayar Yan uwa, na rasa Soyayar mahaifin na rasa lafiyar Mahaifiyar da zata soni..Sunana Sumayyah Yar mahaukaciya” Da mammaki yace."Waht..!Ke wanne wani iri sunane?” Da Sauri ta kifa kanta tana kuka mai ban tausayi jikin sane ya yi sanyi tabbas yariyar nan tana bukatar temako taku ya yi har kan bed din yannu yasa ya kamo hannu ta. “Kin saurare mu daga yau bazaki sake kuka bazaki sake kuka ba, zan kaiki zauna a gidan Hajiyata Kano na ɗan lokaci.kafi na maida ki gida.”A razane ta ɗago muryar ta har rawa take"Kano..!kuma nan ne gari mu ina a kauye Bunkure da garko Dan Allah ka kaini naga Inna ta?” “A Kano?Amma ki sani.Ba na so ki koma inda za ki sake fuskantar haɗari. Ki zauna tare da Hajiyata za ta kula da ke kamar ‘ya.”kai ta girgiza masa “Inna tafa tana so gani na babu mai bata abinci”tana fadim haka ta lumshe ido hawaye ya zuraro mata, ta sake cewa "Ya Allah ka kula min da Inna ta kamar yadda ka turo wanda ya temake ni”Ammasawa ya yi da “Ameen...” miƙewa tayi da sauri ta kamma hannu sa."Dan Allah zaka launi Bunkure?”tsawa ya daka mata."Baki gajiya da surutu kinsa kaina sai ciwo yake, bazaki ba.”Yana faɗi haka ya rufe kofar ya fita.“Kuka tasa kamar ƙarama yariya tana kiran sunan Inna ta... *Shering dan Allah da comment DA like Yan Ammana* [11/13/2025, 6:28 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-8 Inna Na fita daga gidan ta kutsa ciki gonakin haka take gani kamar ta samu ceto, har zuwa bayan Sallah Isha'i bata dawo cikin Malam kuwa babu wanda ya damu da dawowar ta. Gani duhu ya yi yasa ta dawowa ciki gari wuyan da take hana ta riƙe kanta,ce ta adabeta haka yasa ta kutsa maciyar ciki kauye duk inda tayi yara suna tsonakar ta wasu na tula mata ƙasa da wakar da suka saba mata, bata damu ba ƙarshe guri daya ta lafe tana neman wuta inda zata gango abinci da ta ɗauka tana ciki wannan yanayi wani me tsire wanda yake yawo dashi a faranti tare da wutar aci bal-bal ya tsawa guri wasu matasa gudu uku dariya ta ƙyal kyale da ita tana taɗe baki bayan ya zuge wa samari guda biyu ya juya da zumar ya kaimusu ina ta faɗo guri kamar wace aka wurgo,bata tsaya wasa ba ta ɗaki tsike uku kan kace kabo ta hata mashi a ciki ta Garbu mai nama na juyo ya sake gani tsinke Uku a hannu ta wani Ashar ya lailayo ya maka mata Samarin suka fashe da dariya ɗaya daga ciki yace."Ai Garbu kayi sadaka domi tun da kajuyo ta Kwashi tsinke huɗu ta haɗiyar kamar tsohuwar manya yanzu kuma ga tsinke shiga ciki zafita na Mahaukaciya har taci uku.” Yana faɗa suka kwashe da dariya dariya yayi jamar faske yace.“Haba intaci ta zauna lafiya taci hanji cikin ta.” Yana faɗi haka ya dauki wata sabuyar bulala darbejiya (maina) ya bita wani kango ta faɗa ya bita ciki zafi nama, jiki hango ya sameta da sari ta miƙa masa ragowar tsinke daya da yayi ragowa ahannu ta.Dariya ya yi me sauti. "Hhhh bake.mahaukaciya Zaki gane?Zaki dawo hanyyaci ki lokaci da kika ci Ubaki da duka sai na daki kuɗina”Bata san me yake nufinsa hakan yasa ta fara dariya a tunani ta ko magana yake mata mai daɗi aikuwa tana miƙa hannu babu tausayi Garbu ya zuba mata saman yatsu hannu ta wata kara ta kwalla hakan yasa ya saki murmushi muguta haka ya sake jiki ya rika dukanta duk inda ya samu duk da yaga jikin ta ya yi ruɗuɗu haka baisa yaji tai sayinta ko da na second guda ba karshe ma bet din wandosa ya zame ya fara zuba mata ciki rashi sa'a ya sharɓa Mata kan ido wata iri ƙara Inna ta saki tare da sulalewa ƙasa, kamar wace ta mutum.jiki garbu ne ya ɗau ɓari dan gani yayi jini na fitar ta ciki indo nata gashi kamar ta mutu hakan yasa ya kwashe kayan naman sa ya gudu karshe bunkure ya wuce dan dama taulo ne yake kawo shi ciki kauye Gidaɗo Saurayi da suke tare da matasa da suka siyi nama ne hankali da ya kasa kwanciya da bin da Garbu ya yi Ina yashi tashi yabi bayan su da mamakin sai ya samu garbu baya ciki ga ido ta aruɗe na hagu na fitar da jiki tsoro ne ya kama da hudu kar ace shine ya fita da hudu yana fitar da haki yana zuwa Babar maciyar ya iske Yusufa yana taɗi da Laure me sai da kunu da sauri ya ƙarasa kallo juna su yai murya na rawa Yace. "Yusuf Matar mahifiki fa tana ciki Kwango Tsallake da alama wani ya doke ta kuma ido ta na fitar da jini dan Allah kaje tana bukatar temako ka”wani mugu tsaki yaja. "Ta jima bata mutu ba yar asara waya sani ko satar tata ta aikatawa shine wani ya make muguwa, kaga Tanimu ka matsa ka bani guri kana gani taɗi nake zaka zo ka kawo zance Uwar wasu wasu ma da duk mahaukata ne.” Jikin Tami ne ya yi sanyin yaga gwagwarmaya rashi imani a tatare da Tsufa tabbas Yusuf da Mahaifinsa ba kanana azalimai bane.tafiya yake kafar sa tana nema ta gagre shi dauka ya kasa samun mafita gida ya wuce ya sami Inna zuwaira mahaifiyar sa Zaune tana izza wutar karanta."Assalamu alaikum Inna kina zaune yaudai anyi mana dare tuwo.”Sai da ta Jiye Fitalar da take hannun kafi ta kalleshi."Wallahi tanimu Sarajo ne bai mana niƙan akan kari ba gashi karar damina jamar na fasa ihu."Sai da Tanimu yayi dariya kafi yace."Inna duk laifi ki ne Ya'ya Babandi yace ki daina wahalar da kansa matar sa zata kawo miki iya ciki ki dai nikuma wallahi In dan nine na yafe zan ke ci waje...” “Kar kace haka Tanimu matan yazu ba'a shefar su duk da Fa'iza tana da kirki amma kasan Matana yanzu gani suke in suka kyautatawa surukai kamar su faɗi da ƙar fina ban tsufa kuma sai na zauna sai an dafa an baki ka zauna In sha Allah Yanzu zan ƙarasa sai ka sami kaci irin miyar da kake so ma nayi.” Dariya ya yi ya zauna akan buhu da yake tamkar tabarma ya juma cikin dogo tunani duk zance da Inna zuwaira take bai san ma yanayi ba sai da sake kwaɗa masa kira. "Tanimu..!Tanimu dai..!!” A furgice ya waiga. "Na'am Inna ta.”sauke tukunyar miyar tayi tace."Tanimu me yayi zafi har kayi zurfu ciki tunani da baki maganata taso zo naji me ya sami autan maza."Da sauri ya tashi dan yana bukatar shawara. Yana zama ya kama hannu Inna. "Inna ta Yanzu Misali kina gani wani acikin wani hali, kuma kina da ƙarfi temaka masa zaki Bari ya mutu ko zaki te make shi?”Shuru Inna tayi na Wasu daƙiƙu kafi ta sauke ajiyar zuciya."Tanimu na idan har kan bazai jefani masifaba zanyi haka cike da gwari gwiwa da yaƙi Ni numa watarana Zan samu ceto a guri wani.“Manyan Haƙora sa ya buɗe ciki fari ciki yace. "Inna ta Matar Malama Sule Gidaɗo ce aka samu wani mugun ya daketa ƙarshe na ganta akwance kamar ido ta ya damu matsala..."Salati Inna Zuwaira ta fara raf kawa.Muryata na rawa. Tanimu kuma har kasami kwari gwiwa zama kana fito shin yanzu in Ni ka gani ciki wanan halin haka zaka tsallake Ni ka wuce..”Muryasa na rawa Yace. “Wallahi Inna har yaro Miji ta Yusuf nayi Wa magana Amma a ƙarshe cemin yayi tama mutu” Mikewa tayi ta janyo mayafi ta akan igiyar sanya ta kama hannu sa“tso muje ka temake Ni na ɗako ya.” Hannu ta ya kama"A'a inna yanzu ki zauna tunda kawai wuta ki ɗora ruwan zafi bara naje kafin na dawowa nasan ya yi zafi ko wanka ne sai ki mata.Yarda tayi da maganar sa ta koma ta zuba ruwa shi kuma ya fita. Yana fita bai tsaya ko ina ba sai A kango Tsallah, yadda ya barta haka ya sameta, fita yayi ya shiga Rago Rabi'u me kalanzi ya suyo,Pure water guda biyu me sanyi ya tafi da lokaci yaji tsoron gani lokaci daya ido ya kunbura har ya manne da jiki ya bushe jiki sa na rawa yana anbato Sunan Allah ya ƙarasa inda take sai da ya gurfana agabta kafi ya fara yaya fa mata ruwan ikin wata iri tsawa kamar mace zaki ta kurma wani Uban ihu btare da buge-buge tana surutai”Idona kar ka zo zai cire min ido wayo ido na ya faɗo ƙasa.”Kasa daurewa Tanimu ya yi fusgo ta tare da rungume ya fashe da kuka, sai A lokacin Inna ta saki ajiyar zuciya tare da yin shuru a kan ƙirji Tanimu tana maida ajiyar zuciya sai da ya yi kuka sosai sanan ya rabata a ƙirjin sa cikin wata iri murya yace.“Baba zaki je gidan mu.?”Kai ta girgiza masa da ido ɗaya take kallo sa dan yada ido ya kunbura sosai ko ɗaga shi baza ta iya ba. Ruwa ya miƙa mata ta amsa, ko ƙarar haɗiyar ruwa baka ji hakan ta shanye ta yar da ledar sanan ta kalle shi. "Zaka kaini guri Sumayyah, tana kuka na goyata zaka kaini nono zata sha.”Ido ya rintse wasu hawaye masu zafin suka gangaro masa,"Zan kaiki yashi muje zaki ci tuwo?”Baki ta washe ƙoranta,wanda suka jima da dafewa da dauɗa."Zanci zaka saimi 'Yar tsala akwai daɗi.”Kai ya ɗaga mata mikewa tayi da Sauri tana sosa kanta.shi ya fara fita ita kuma tabi bayansa tana tafe tana waige dan Garbu Gizo yake mata har suka isa gida. Suna Zuwa Inna zuwaira ta tare ta takawo hannun zata taɓa ta da Sauri ta janye. "Kar ki taɓa ni zan gayawa Sumayyah”Shuru tayi ta kalli Tanimu Yanzu abin na farko ka yi mata dabara mu gasa mata iri ya buɗe sai muga yadda yayi sai kaje guri Ade likita ka sanar da ita ko akwai magani da zata bata saboda kumburin ido.”Kai ya daga cikin Sarewa dan shirya farga yake ido ya buɗe tun da yaga idon yake fargaba. Da wayo da dara aka gasa mata ido sai da suka yi anfani da Dangwali yaɓa(Vasili) sanan ido ya buɗe wata ƙara Tanimu yasa tare da yin baya numfashi sa na ɗaukewa, Jikin Inna zuwaira na rawa tace.“Tanumi lafiya me ka gani a cikin ido kake ƙwallah ihu haka?”Kuka ya fashe dashi, da Sauri Inna zuwaira ta karaso. "Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun!”Sai da ta maimaita sau Uku kafi ta sana ido ta ya fara fitar da hawaye, ciki kuka Inna zuwaira tace. "amma ko waye ya yi wa wanna baiwar Allah haka Yaci Amma kuma Allah bazai taɓa bari sa yaji dadi ba Ya umurce ina ganin Baiwar Allah nan bala'in ta sake gani ba domin kwayar ido tashe kuma...”Cikin kuma Tanimu ya dakatar da Inna sa."Insha Allah ina zata sake gani Zata warke zata sake gani da ido ta bani da tabbaci Allah yana gani kuma zai yi iko sa akanta.”Jiki Asanyaye tace."Allah yas.” Duk yadda suka so ta yarda suyi mata wanka Inna kitayi hakan yasa suka barta dole taci tuwo sosai dan sai da taci kwasa uku. A guri ta kwanta ta kama bacci.Sai da tayi bacci Tanimu ya kallo Inna sa jiki babu Kwari. “Inna bara naje Guri Ade nayi mata bayani ko akwai wani taimako da zata biya mana.”Addu'a ta masa da fatan nasara sanan ya fita. YUSUF Tunda Tanimu ya tafi da Inna Yusuf ya gani murmushi mugunta ya yi ya koma dandali ya ci gaba da sanfgar gaban sa.tare da ƙiyasta Shari kala-kala acikin ransa. Lokaci da Tanimu ya isa kamis ɗin Ade lita ya samu mutane biyu dole yabi layi bayan sun fita ya faɗa mata komi saidai baice mata Matar Malam Sule Gidaɗo bace.A iya ɗan karatu da tayi yasa ta dube shin tace. “Gaskia Tanimu ba zan yake maka hukunci ba saboda ba nan bangare na karanta ba Salima Ni bangare Haihuwa karantar yanzu abu masu sauki san baka magani sabar da kunburi dana zazzaɓi ta fara anfani dashi kafi muga yadda halin zaiyi.”Godiya ya mata akayi lifai kudi magani 2k da haka ya koma gida. Washegari dai da suka kai ruwa rana tasha magani sanan ya nuna fushi Da ta yarda aka mata Inna Zuwaiara tayi mata wanka a cikin kayan ta ta bata wasu marasa nauyi riga da zani tasa. Tayi kyautar a guri bacci ya sake ɗauke ta ɗan Zazzaɓi ne sosai ajikin. *** *LAGOS* *** Tun da ya fita har Sallah magariba Ammar bai dawo Hospital ba Hakan kuma yasa taji babu daɗi cikin ranta tace."Sumayyah ki lalaɓa shi ya kaiki kano ko yaƙi maida ki sai ki hudu saidai kin fita daga Wanan baƙi gari da yadawo dake.wawa sawa har guri goma babu Ammar babu shi ƙarshe kwanciyya tayi da haka bacci ya ɗauke. Washegari da wari wata Nurses ta shigo da wata sabuwar abaya Black ce mai adon Pink colour,Da kallon Summayyah bita, Zuwa tayi ta dafata."Yayanki yace ki shirya Yanzu zai zo zaku tafi Kano.”Da sauri ta dira ta faɗa Bratheroom bata jima ba ta shirya tayi kyau kamar, kyawunta ya fito tamkar yariya yar shekara Ashirin da Biyar ido ta tamkar an zana mata kwali duk yadda ta wuƙilta su sai sun ɗau hankali mai kallo su,bata juma da fitowa ba Ammar ya shigo fusakar sa babu yabo babu falasa.sai da ta ɗan rusuna"Ina kwana?”"Kina lafiya?”Da haka bai sake kallo taba ya ya nufi Hanyar fita da Sauri tace.“Kayana fa a ina an zuba su?”Bai kalle taba sai agogo Diamond ɗin da ya kalle.“Ki jefar dasu bamu buƙata ki gito ina mota.”Zata sake magana ya fice, kayan tabi da kallon,sanan ta juya tafita, ko a mota agaba ta ya zauna ta zauna abaya drive ya kasi zuwa Airport. Tsoro tashi hankali babu iri wanda bata shiga taruɗe sosai da taji wai ita zata hau jirgi har ya fara taka ƙafar bene Summayyah na tsaye juyowa yayi cike da mamaki yana kallo ta gani bazata ta bashi ammsa ba yasahi boɗe baki ɗakar."Jirgin ba mota bace da zai tsaya jiran ki.”Madadi ta bashi amsa sai ta fashe da kuka abin kona masa rai yayi ya dawo azafafe ya damƙi hannu ta ido sa har ya canja kallah. “baki gaji da gari bane kike kuka ko so kike na maida ki inda na ɗauko ki?”kai ta fara girgiza masa muryat me cike da shagaɓa da yarinta ta buɗe."Ina ji tsorodan Allah me zai hana mu tafi a Kafa inaga zaifi.”Dariya da take da mugu tsada wace ko iyaye sa sukan sha wahala kafi suga yayi ta, Saboda yawan surutu da da dariyar sa baza ka taɓa gane damuwar sa ko farin cikin ba. Dariyar ya fara mata ita kanta kallo sa take gashi yana mata guzo sai ya yi mata kalla da yan ciki finafinai India iri masu Bala'in kyaunan tawani fanni kuma kana ganisa Kasan Balarabe ne, sai kuma ya fara bata tsoro ita sai yanzu ta fahimci fari sa ba iri namu bane yasha banban ga manyan ido wanda in ya tsare ka dasu dai ka kasa kama kwanta iya kasubar da kaɗai zata tabbatar maka da zaki ne a tsaye zaki da ya amsa sunan, tariga ta gama dulmiya da kallo sa taga ya juya izuwa mara fara'a yace. “Tom ke jiki ki gwada tafiya ƙasa sai mu haɗi a can”Gani da gaske shigewa zai ya barta yasa ta cire talman ƙafar ta ta kwasa aguje har taje inda yake tsaye rigar jikinsa ta kama gam kamar me shiri buga yaƙi da kuraye haka ta rintse ido suka shuga ciki ba ita ta sake shiba sai da yace."Ki cikani kar ki yagamin riga.”A hankula ta fara buɗe ido har ta sake akan zaratan mazaje Manyan ido sa sun juma a haka ƙarshe Ammar ya sake bashi tare da hura isa.babu juma aka kawo musu Kayan ciye-ciye. Sai da akyi sanarwa sanan Jirginsu ya tashi daga Lagos zuwa Kano. Hasken rana ya ratsa ta ta ciki gilashin jirgii kallo ƙasa ta fara tana jin sabuwar rayuwa a gareta. A gefe ta kuma Ammar ne yake duba wayar hannuesa,sai dai zuciyarsa da ido ta ya rasa me a ciki su da suke hanna shi ƙare mata kallo, wata zuciyar tace "Kasani ko idanuwata suna tattare da wani Sirrin da suka fi naka”A fili yace "Ni..!No Bazai iyuyu ba.”Da kallo Sumayya ta bushi bata da iko tambya. Shima A hankali ya juyo ya kalle ta, sai ta ɗauke kai tana murmushi tana ji ƙirjinta na wata iri bugawa.Tunda kan yadda take wasa da yatsu hannu ta zuwa rigar da ta rufe mata ilahirin jikinta tabi da kallon ya sauke ajiyar zuciya Aciki tanshi yace. “Wannan yarinyar ba kamar kowace ba ce. Ƙaddara ce ta haɗa mu, Allah ya bani iko nikaya guri iyaye ta lafiya ba tare da cutarwa ko zanba ba.” Karfe uku da rabi na rana jirgin su Ammar ya sauka a Filin jirgin Mallam Aminu Kano.Lokaci da sanyi iska ya sauya iska tana kaɗawa a hankali. Sumayyah ce ta fara fitowa cikin nutsuwa, sanye da doguwar riga ta abaya mai launin baƙa kanta lullube da scarf mai laushi wanda Ammar ya siya mata a Lagos. Tun daga nesa, Hajiya Maryam ta fito daga mota tana murmushi. Fuskarta cike da annuri da natsuwar mace mai hankali da kima fara ce sai dai farinta iri na fulani ne baka na Ammar ba. Ammar ne ya ƙarasa inda take ya rungume ta cikin girmamawa."Nayi kewar Hajiyata da Daɗan Girkinta mai sani nutsuwa.” Sumar kansata sosa ciki farin ciki “Nima haka Ammar ɗin Hajiyar ka tafika shiga damuwa da rashi shi na Sa'o'i.” Juyawa ya yi ya kalli Summayyah wace take jira ace At ta gudu"Hajiya ga wacce nake gaya miki,tana buƙatar hutu da kulawa nan Hajiya ta ba da ganan ba.” Yalwata far'ara ta tayi ta kalli Sumayyah cike da tausayi da fahimta tamkar ta juma da sani ta.“Assalamu alaikum, ‘yata ƙaraso kiji Dumin Mahifiyarki Karki biyew Ammaru.” kasa ƙarasawa Sumayyah tayi sai durƙusawa da tayi cikin ladabi, ta amsa. “Wa alaikumus salam Ina Wuni da fatan mun same ki lafiya?.”Hannu ta ta kama ta haɗa ta da jikin ta"Tashi dan Allah” gefe Fuskat Summary ta shafa.“Ki kwantar da hankalinki, kin samu gida. Ki ɗauke ni kamar uwarki, ba buƙatar jin tsoro ko kunya nice mahaifiyar Ammar ki sa Aranki kuma Mamanki ce” hawaye suka ciko idon Sumayyah, ta kasa magana, sai dai ta girgiza kai tana share hawayenta. Ammar ya juyo ya yi murmushi ciki ransa ya ji daɗin yadda Hajiya ta karɓe ta da buɗaɗɗiyar zuciya.“Hajiya Itafa kuka nayiwa yariyar nan wahala dam kin daina Wahalar da kanku ki Kani gida na kagu naci Girgiki nan naki mai sani ba manta da kowa da komi.”bata biyewa Ammar ba sai da ta samu Sumayyah tayi shu sanan suka shiga mota Ammar ne agaba kusa da drive Hajiya Da Sumayya kuma a back seat. Suna is gidan Sumayyah ta fara bin gidan da kallo,gida ne mai tsari da kwalliya irin ta Larabawa lambuna har ukune kowane cike yake da Bauchi kayan ciye-ciye iri na kasashe waje,da furanni masu kamshi kala-kala ruwa na gudana daga bututun fountain a tsakiyar su. In bada ban tasan Ammar bai taba cutar da ita ba da cewa zatayi sai da ita yazo yi ran Iya fallo in zaka iya cewa Allah ya gama salamar ka anan gidan duniya maganar Hajiya ce ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula,"Sumayya kije ga daki can na biyun da yake samma Nana ne ɗakin ki koyi wanka zan Sa Hameda mai aiki ta kawo miki kayan da zaki sauya, sannan ki fito mu ci abinci.” Godiya tayi sanan ta shiga ɗakin cikin mamaki.take bin ɗaki da kallo kaya na more rayiwa babu abin da babu manyan turaruka masu ƙamshi ga makeke Mirror da zaka iy gani kanka tundaga ƙafar ka har izuwa kanka, bed din tabi da kallo balcket gado green ne sai fulawoyin da akayi ado da su white haka ma labule launin su ɗaya da zani gado, da ƙamar window ce daga sama da ke fitar da iska mai sanyi.tsaya wa tayi a tsakiyar ɗakin tana kallon komai kamar mai mafarki. A hankali hawaye ya sulalo mata. “Ya Allah… har yau ina raye. Ina gidan da ba a mafarki ba, dama ace Inga inna ta cikin gidan nan dama ace zata zo muji daɗi nan ko da Na wuni ɗaya.”ta zauna a gefen gado, ta rufe fuska da tafin hannu tana kuka cikin ɗaciki zuciya”Fa tunani halin da innar ta take ci. Bayan tayi duk abin da Mahafiyar Ammar ta umarce ta, ta fito da doguwar riga ta Abaya dan babu kayan gargajiya kamar nata a gidan tunda ba wasu yara ne dasu ba, tun da ta hango ta baki hajiya yaƙi rufu wana ji wani farin ciki in taga Sumayyah tanaji wata ƙauna ta musamman a tare da ita. Kallo ɗaya Ammar ya mata ya ɗauke kai suka zauna a dining. Hajiya Maryam tana kallonta tana nutsuwa da tausayi yarinyar. A hankali tace. "Ammar baka faɗa min sunan kanwar taka ba” sai da yayi miƙa kamar wanda ya gaji kafi ce."Gajiya ki tambaye ta zata gaya miki”Tasan Zai riƙa,mai da kallo ta tayi kan Sumayyah “ 'Yata, mene sunanki?”saibda ta saci kallo Ammar taga loma kawai yake zuvawa kamar bai san da zaman taba sanan tace.“Sumayyah Yar mah.....” kallon. Da Ammar ya tsare ta dashi ne yasa haɗi ragowa abinci ba bi shiri, Murmurshi Hajiya tayi. “Da kyau. Sunan ki sunane na masu albarka. Kin san ma’ana sunan?”Ta girgiza kai tayi tana wasa da da COKALI hannu “Ma'nar Sumayyah, shine mace wacce take da tsarkin zuciya.”Idonta ne ya sake cikowa da hawaye taa ce.“Da gaske Hajiya? to Allah ya sa nima na cancanci hakan.” Ammar da yake ke gefe yana goge bakin sa da Tissues, bai ce komai ba sai dai zuciyarsa ta cika da tausayin ta bai san lokacin da ya fara ba kuma yanji zai iya temaka mata koda kuwa hakan zai zama yankewa nashi farin ciki. Kwana biyu da zuwan Sumayyah ta fara sabawa da gidan. Hajiya ta fara koya mata yadda ake kula da furanni,da yadda ake yin girke-girke na Lebanon da Hausa, tana koya mata karatu da adu’o’in safe da yamma. Ranar Asabar suna zaune a lambu, rana na. taho faɗuwa. Iskar yamma tana kaɗawa, furanni suna motsawa. Ammar ya fito daga Part ɗinsa da ke gidan, yana sanye da Three quarter wando na jeans sai t-shirt copy colour ta kama ƙirji sa ta fitar da ainihi surar sa, ƙamshi yake yana taku cikii izza hannunsa ɗauke da fulas. Idon sane yakai kan Sumayyah tsaiwa ya yi yana kallon yadda take bawa furanni ruwa, tana murmushi cikin natsuwa.daga gani yanayi ta na Farin ciki da haka.Hajiya ta lura da yadda yake kallonta, sai tayi gyran murya tayi murmushi cikin hikima. “Ammar…” ta kira shi cikin natsuwa, juyowa yi“Na’am Hajiya?” “Inaji Ajiki na Sumayyah.Allah ya kawo ta gare mu da hikima. Ka kula da ita, saboda wata rana, zaka gane dalilin hakan.Ina roƙan ka dan Allah karka bari tayi kuka” Ya ɗan yi shiru, yana tunani.“In Sha Allah Hajiya zan ƙoƙarin haka,”ya masa cikim ladabi guri ya nema ya zauna suka shiga wata hirar. Da dadare, Sumayyah tana kwance tana kallon POP.tayi nisa cikin tunaninta kan abin da ya faru,a gidan Alhaji Ɗan Dubai, safarar mata, da yadda Ammar ya cece ta.numfashi ta sauke “Ya Allah, idan wannan sabon farkon rayuwata ne, ka bani ƙarfin juriya, ka saka da alheri ga wanda ya ceci ni. Kasa na koma guri Inna ta cikin Amince kabawa inna ta kariyya” A gefe guda, Ammar ne, a zaune bisa makeken gado da sanyi A.c dana fanka yana ratsa kwanyar sa,yana duba wasu takardu,duk da ainki da ya sha masa kai zuciyarsa bata daina tunanin Sumayyah ba. Maganar sa lokaci da ya ceceta ta dawo masa cikin kunuwana sa.“Na gode, ka ceci rayuwata.” takardun ya rufe, ya lumshe ido, yana murmushi a hankali. “Sumayyah…” ya faɗa a hankali... Bacci ne ya fara daukar ta Cikin bacci tayi mafarki inna ta ciki wani iri hali mai ban tsoro tana ta kuka gashi kamar wawake take bata tagi abinda ke gabanta. Wani iri ihu ta kurma hakan yasa Ammar jin igiyar saboda dare ya fara yi. Bare ma uguwa iri tasu babu hayaniya bare kaka sa ji wani sauti ciki han zari ya miƙe. “Sumayyah..!me yake faruwa da ita....”Wani ihu nata ya sake ji ko takalman bai nemaba ya fita da gudu kafin ya karasa Hajiya taje. Lokaci da ya shiga Bedroom ɗin Hajiya tana zaune ta sata ajiki ta tana tofa mata Ayatulkursiyyu dasu li'ilafi Jamal yasa ta samu ƙaramar nusuwa maganar Ammar ce tasa ta waigawa. “Hajiya Me ya faru da ita?”cikim ruɗewa Hajiya tace."Wallahi nima Ammar ban sani ba Na fara bacci naji kukan ta yanzu nake son naji me yake faruwa ko wani abu ya tsorata tata.” Hannu sa ya harɗe kan ƙirjin sa ya kalle ta da kyau har yanzu kuka take."Sumayyah Me kika gani ya tsorata ki da bazaki iya Salati ba sai ihu?”tsare ta ya yi da ido tana ɗagowa sai ta sake fashewa da kuka. “Dan Allah ku mai dani guri Inna ta bata da Kowa saini ina tsoro ta batta wallahi ta shiga wani hali bazan yafewa kaina ba dan Allah Hajiya kisa ya maidani Giɗaɗo ko dan Inna ta”Tana faɗi haka ta sake fashewa da sabo kuka wanda ya ɗagawa Hajiya hankali... *Amin Afuwa dama na faɗa muku Update ba Kullum ba* *Albisiri kuma masu jira Agama littafin ITACE KADDARA TA tom kuzo ku mallaki naku daka kuɗi ƙalilan babu tsada ku karanta Complete ɗinsa ₦ ɗari uku tabiya buƙata kar ki bari Labari Sultana da Sultan Hajiya ya wuce ki, ko hawan jini gare ki Tom ga magani sa nan Ki nemi Littafin itace Kaddara ta ki kore damuwa da takaici Duniya.Ga account number da number da zaki tura shedar biya domi ki mallaki naki* *Account number 0341904756. USAINA SALISU GT Bank: SHEDAR biya 08168621656* [11/16/2025, 4:04 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-9 *Gidan Malam Gidaɗo* Yusuf ne ya shigo ko Sallam babu tsaki ya ke tare da ball da kwanika Babu wanda yace uffan har ya samu guri ya zauna da Kallo Baba Zulai ta bishi,kujera yar tsugono ya dasa ya zauna tare da ƙare mata kallo.“Babarmu Wai yanzu matar nan dan ta tsinka mana mutunci shine taje ta kwanta A kango Shikuma shege yaron can Tanimu har da ɗaukar ta ya tafi da ita gidan su dana ce ya kawota sai yace in ya kawota wai me zamu yi mata banda azabtar wa”Sallati tasa da tafa hannu"Shikenan ta daɗa ja mana zagi a kasuwa” ƙwafa ya yi zai yi magana malam ya shigo. *Lagos* Bayan ASP Mubarak ya saki Classic Don bai zarce ko ina ba sai Gidan Alhaji Ɗan Dubai tin da Alhaji Ɗan Dubai ya gansa yasan ba lau ba dan yana ta zagi da turanci yana sai an biya shi kuɗi sa da sauri ya tare cikin ladabi iri na riƙaƙu yan Duniya."What happened is Classic?”Sai da ya buga tsaki kafi yace.“ Follow me, my money, the girl ran away from the police.” Sai da ƙirjin Alhaji Ɗan Dubai ya buga lalashi ya fara yana nuna masa wasu yan mata, fur classic yace bai san wanan ba ƙarshe bindiga ya ciro a ciki Aljihu sa ya fara harbin ƙasa da gudu Alhaji Ɗan Dubai ya shiga wani ɗaki ya ɗauko masa kuɗi sa sai da ya irga yaga ko biyar bai taɓa ba sanan ya fita.asahar ya lailayo ya maka“Wallahi Yariyar nan bata ci banza ba, sai naje gurin Tsoho ubanta an biya ni duk abin da na kashe, ni za'ayiwa bura uba” *Nasarawa Kano* Tsakani Hajiya da Ammar juna suka kalla ya ɗauke kai, Hajiya ta fara shafa bayan ta."Sumayyah kuma shine sai kinyi kuka kar ki damu insha Allah Gobe zan sa ya mai dake Ai zaki gane ko?”Kai ta ɗaga mata.sai da Hajiya ta lallashe ta sosai sanan suka fita har Ammar ɗin. Suna fita ta sauke ajiyar zuciya,“Allah… badan niba, Allah ka bani kwanciyar hankali… ka raba ni da tsoron da ya cinye zuciyata.” hannunta ta sa ta sharce hawayen da suka gangaro mata.Sai da Tayi Addu'a sosai sanan ta kwanta. Tunda ya koma ɗaki bacci gagarar sa ya yi a fili ya furta"Wai ita me yake damu ta duk da hawalar da tasha buri take ta koma cikin su?” tsaki ya ja ya sake juyawa ya gyara kwanciyar sa. Tun Asuba Sumayyah ta shirya take juyi ciki ɗaki gajiya tayi ta zauna gefe gado ta sauke Nufashi a fili ta ce."Su fa masu kuɗi basa son tashi da wuri sai aita fama basu tashi ba, yanzu ma inaga tara tayi amma basu tashi daga bacci ba” Sai tara 'Yar aiki Hajiya ta kira ta, jikin sai rawa yake ta fita parlour ƙasa, Hajiya ce kawai kan Daining tunda ta hango Sumayya fara'ar taƙaru "Sunu da zuwa yar albarka ina fata kin tashi lafiya?”kasa jurewa tayi tana zuwa zata gaida ta ta fashe da kuka, Murmushi Hajiya tayi ta ɗagota ta rungume ta kamar yarinya ƙarama. “Allah ya mayar miki da farin cikin da aka kwace miki. Banso ki zama raguwa kizama mace me juriya da jajurcewa!,” Hajiya ta furta cikin tausayi, tana shafa bayanta.ajiyar zuciya kawai Sumayya take saukewa. cikin sigar lalashi ta ce.“Allah ya ba ki kwanciyar hankali fiye da wanda kika taba samu Abaya ina fata daga yau baƙin ciki ki ya ƙare, Zan cigaba da Addu'a Yariyata Sumayyah, farin cikin na har abada ya luluɓe wanan zinariyar zuciyar.” Ammar da ya fito yanzu ciki Shadda sa bazum blue block ta masa kyau kamar sabo ago yana tsaye a bakin ƙofa, yana binsu da kallo baisan me yasa ba, yake jin ƙaunar Yariyar duk lokaci da yaga Hajiyar sa tana janta ajiki.basu yi tunani ya zo ba. Idonsa ya sauka a kan Sumayyah, yadda take jijjiga kai da yadda take tsanan ta kukan ta, da hannunta da ke rike da Hajiya kamar bata so ta sake ta yaji ɓaci ran yanayin da hmya fara haduwa da ita.kasa shiga yayi ya kasa komawa.Zuciyarsa tashiga bugawa da sauri.“Wannan yarinyar… me suka mata haka?”Ya fada a ransa cikin zafin rai.“Me ya sa duniya tayi mata tsauri har haka? Kuma me yasa tun ranar farko da na ganta zuciyata ke jin kamar ina da hakkin kare ta?” lumshe idon sa ya yi dan danan wani irin ɓacin rai mai zafi ya taso masa.ya furzar da iska mai zafi, ƙoƙarin juyawa yake Hajiya ta kira shi. “Ammar.” tsayawa ya yi cak. “kazo ka rareshe ta zan haura sama kayi break fast din da ita kafi na fito”Kai ya daga a hankali, don shi in akwai abin da yake masa wuya bai wuce yawan magana ba.kujerar daining yaja wace take kallo tata ya zauna shuru ne ya ratsa su, na wasu daƙiƙu gani ba zata yi magana ba ya fara juya Spoon aciki Chips wanda yake haɗe da soyayaye waina kwai, ya na kallo ta.“Kina kuka Saboda kin fiso ki koma inda za'a maida ki baiwa ko?” Jajaye ido ta ta ɗago."A'a saboda Inna tane kawai ina tsoro abin da zai sameta” Shiru ne ya sake ratsa tsakani su sanan ya dago kamar me ciwo hamgum. “Ki sani daga yanzu zan tsare ki. Zan kare ki. Kuma babu wanda zai kara cutar da ke.”Ya faɗa yana kallo fuskar ta.Goge guntu hawaye fusakar ta tayi."Nagode Amma Ina so na koma Bunkure Inna ta tana can tana..…”tsawa ya daka Mata ido sa dan-danan ya yi ja jikin sa har rawa yake gani ta fashe da kuka yasa shi ɗaukar gogar ruwa mai sanyi yasha,yana ajiyewa ya tashi ya matsa kusa da ita, ba tare da ya taba ta ba.“Ki daina tsoro.ki sani zan maida ki gida yau shikenan tunda bakya son zama damu” Shuru tayi ba tare da tace komi ba har ya gama ci ya goge baki sa da tissues ya miƙe “kije ki shirya zan fito da mota”Har sai da hakonta suka fito saboda murna, kallo ya bita dashi har ta haura sama shikuma ya fita. Bayan kamar 20 mintes Hajiya ta fito sai da ta fara shiga Bedroom ɗim da Sumayyah take ta kira ta sanan suka sauka ƙasa suna zuwa Ammar ya shigo yana duba agogo wayar sa ya kalli Hajiya. "Hajiya zan kaita Daddy yana hanya nasan har na dawo bai iso ba”Kai Hajiya ta jinjina Hawaye ya cika ido ta,kwana biyu da tayi da Sumayya tashiga ranta sosai. Rungume ta tayi "Allah ya kare ki ya duba rayiwar ki, Zanzo na duba ki kafi azumi sanan Zaki zomi da Sallah kinji 'yata?” Kai ta ɗaga tana hawaye“Eh Hajiya zanzo Nagode Allah ya dubaki yadda kika kula dani”Babar Ket ta miƙa mata."Ammar zai baki kuɗi ɗinki kisa wasu,Wasu kuma ki bari sai Sallah”Har ƙasa ta zube ta sake mata godiya sanan suk fita Ya zauna A drive seat ita kuma for seat, tun da suka tafi, ya saka waƙar India mai sa tausayi kamar yaresa na gado haka yake bi waƙar cikin Sallo, satar kallo sa kawai take shikam idon sa yana kan hanya yana bin wakar yana jin daɗi yanayi hanyar ƙauye Saboda yanaso rayuwar ƙauye. Sai da suka yi nisa Sosai ya kalle ta."Ke Kar fa ki saida nifa.” Jiki ta ne ya hau rawa tana rantsuwa"Wallahi Ya Ammar bazan sai da kaiba Ni ban san ma yadda ake sata ba, nan ne hanyar garimu ko...ko wan can Zaka tambaya mun kusa shiga Gari giɗado” Burki ya taka yana kallo yadda duk ta ruɗe dariya ya fara mata, sai kuma tayi shuru,suman tsaye tayi bata taɓa gani wanda dariya take ma kyauba iri Ammar shi komi yayi kyau yake masa, maganar sa taji. "Ki rage tsoro ko Kya samu sallama aciki ranki ”shuru tayi ya sake kunna motar... **** Malam na shogowa ya bisu da kallo, wuyansa da kwato carbi mai dubu.gyran murya ya yi.“Tom lafiya aka tsaya cirko-cirko kuna kafe ni da kallo.?”Ajiyar Zuciya Baba Zulai ta sauke. "Malam inafa Lafiya ace Matar nan shikenan kullum ta riƙa ja mana zagi da sunan Mahaukaciya ce ita gaskiya ya kamata ka ɗauki mata ki...”Duk abin da ya faru ƙarya da gaskiya sai da ta haɗa, Nan kuwa ya hau kamar fulawa da aka zan baɗa Mata yis. Cikin fushi ya kalli Yusuf. "Kai Yusuf duk yadda za'ayi kaje ka dawo da ita ayau ba sai gobe... Sallamar Alhaji Ɗan Dubai ce ta hana kowa motsi Yusuf ya miƙe yana rawa."Yau kace akwai cin uwar sabada agidan nan tab Malam Mutumin kane yazo wata ƙila wasu kuɗi yazo ƙarawa.” Tafiya Malma ya yi da sauri har Malin-malin ɗinsa tana niyar kada shi.Baba Hauwa tace.“A'a Malam yi a hankali” Yana fita ya iske Alhaji Ɗan Dubai a tsaye cikin nan nasa agaba, kansa sai tsatsafar gumi yake na azaɓa,yana niyar Zubewa Alhaji Ɗan Dubai ya shaƙi kwalar Malam Sule Gidaɗo. "kar ka tsunguna min Tsoho Alla kwankwan nunafiki dama gadar zare ka shirya min na gama baka kuɗi shine kuka sa Police sukaje suka karɓa maka yar ka tom Wallahi baku isaba yadda kake ganina tsohon ɗan tasha ne goge ɗan bariki, Bani da dama guri neman na Abinci”Ba Malam ba hata Yusuf da Khalid sai da tsoro ya shigesu lallai yau su haɗu da ƙwallo dan Iska, yadda yake ruwan Ashar tsaf zai danfara malam A ƙasa. Duk layi da motar Ammar ta gilma sai Yara sun bita suna “laaaa ga balaraɓe tare da 'Yar Mahaukaciya kamar bai san da zaman yaran ba haka yake tunƙi cikin nutsuwa. Tunda suka tinkari ƙofar gidan su gaban ta ya fara faɗuwa. " Inaalillahi wa'inaalaihi rajun, Wa nake gani kamar Alhaji Ɗan Dubai.”Ta faɗa tana me sake kallo Ƙofar gidan nasu da mutane suka fara taruwa, Gani shine yasa ta sauri riƙe hannu Ammar. "Shine wallahi..!Kar muje shine Wallahi..! shine nasan zuwa ya yi ya maida ni dan Allah mu koma kar ka kaini gurinsu nasan Babana basu ni zaiyi kuma ga Yaya Yusuf aguri.” Kuka take kamar zuciyar ta zata fito, Ammar kam kamar be san akan mai take magana ba ya cigaba da tuƙi sa cikin kwanciyar hankali har suka ƙarasa inda Su Baba Malma suke...... Shering and like [11/17/2025, 1:01 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-10 Cikin fidda rai ta cire hannu ta daga jiki hannu sa ba tare da ya kalle taba yace.“Wan can ne Mahaifi naki?”Kai ta ɗaga masa hawaye masu zafi suka gangaro mata "Amma Kace zaka kula dani kuma Hajiya ta ce Amana ce ni A hannun ka.me yasa zaka mai dani in da na baro?” Sai da ya buɗe murfi motar sanan yace"fita muje”Jiki babu ƙwari ta beɗe 'Yan matan ko nace ƙwailaye kwaye su Sadiya ne ɗaya daga ciki ta waiga karaf ido ta ya kai kan Sumayya, Rashida da take gefe Lubna ta kwaɗa shewa.“La Shikenan ma Baban su Sadiya ga 'Yar mahaukaciyar nan ta dawo sai ya tafi da ita can su ƙarata” Ido Malam da yayo waje ya fara kar-katar da kai yana kallo In da aka ce Sumayya na guri da sauri Alhaji Ɗan Dubai ya saki Malam Sule Gidaɗo ya tako inda Sumayya take tsaye jikin sa na kyarma.Hannu Yasa zai riƙe ta Muryar Ammar ta karaɗe guri. “Kar kayi kuskure ɗora hannu ka a kanta,Otherwise, you will regret it in a way you have never experienced in your life.” DA fari ya ɗauka Wanine daga ciki Yaran Malam,Ciki matsanan cin ɓacin rai ya waigo."Ko Ubanka Malam gashi Bai isa...ya..” Kasa ƙarasa zagi da ya ɗako yayi saboda wanda ya gani agaban sa.Ɗan A tajiri mai kuɗi nan wanda Duniya take Alfahari dashi (Ammar Sheikh Kareem Al-Labban)Mashahurin attajiri.An san sa a ko’ina saboda yalwar arziki da sirrin kasuwanci.yana tsaye kamar bashi ba,ya harɗe hannu sa, murya na rawa ya fara magana ciki ƙinƙina. "Ammar ɗana kaine anan?Me ya kawo ka wanan kauye maye Alaƙa ka da wanan mutanan??” Ɗaure fusak yayi kamar bai taɓa dariya ba“Ni zan tambaye ka me ya haɗa ka da ƙanwata ka sani ko scend ɗaya ka sake tamakar ka sallami kanka daga guri aiki ne bana ji akawai wanda zai mai daka matsayi da kake kai.” Zubewa Alhaji Ɗan Dubai yayi gwiwa har ƙasa.“Ɗana Ammar ka teamka,kamin rai wallahi Alhaji shine gatana Aiki nan shine gatana ba..wai... "Shut up your mouth here. Kasan da haka kake aikata haramci kana safara yara ƙanana kai Guba ne a cikin al'uma, karka kuma min magana in kuwa ka sake kasani Wallahi..! wallahi..!! Wallahi..!!! Ka kori kanka” Da haka Ammar bai sake cewa komi ba sai motar sa da ya nuna masa.Takalman sa Alhaji Ɗan Dubai ya kwasa a hannu ya shige mota tare da bari layi da Gudu. Sai A lokaci Yusuf ya saɗaɗa kusa da Malam tare da yi masa magana cikin raɗa. "Malam yariyar nan fa ta sake zuwa da Alkairi kasan wanan yaro waye kuwa?”Kai Malam ya girgiza yana kafe Ammar da kallon kamar wanda zai gudu ya barsa. "Malam Maifinsa hata ƙasashe waje so suke su kulla kasunci dashi Ai nasan kana ji Sheikh Kareem Al-Labbani Mashahurin attajiri nan a rediyo ko?”Malam ya daga kai jiki sa yana rawa kamar mazari Yusuf ya sake cewa. "Tom wanan yaro da kake gani zubi Larabawa ɗansa ne wasu na cewa shi kaɗaine ɗansa aduniya wasu kuma sunce yana da ƙanwa” Tun kan Yusuf ya rufe baki Malm ya zube a gaban Ammar."Sannu da zuwa! Yanzu kake tafe? Ke Sumayya dan Ubanki tarbiyar da na baƙi kenan kina gani ɓaƙo ki barshi a waje?”Tunda Malam ya fara Zuba, Ammar yake binsa da ƙallo yaga Son Abin duniya a ido Malam yaga tsantsagaro son kai a tatare dashi. Sumayya ce ta ƙaraso inda Baba ya zube kamar kayan wanki ido nan yaci uban farin kwali kamar tsoho kwarto."Yace ka shiga.” Kamar bazai magana ba, bayan wasu mintes ya dubeta“Ina Innar taki take?”yana faɗa ya sake tsuke baki sa gulma Jama'a suka fara. "Kai kunji 'Yar mahaukaciyya ta yowa Balarabe asiri ya biyo ta har Ƙauye Giɗaɗo yana neman Mahaukaciyar Uwar ta”Duk iri surutu da suke yana jinsu amma bai ce musu uffan ba.Malam naji haka ya miƙe “tashi muje ciki dama tun yau kwana biyu muke nema ta Wallahi ko sama ko ƙasa Mun rasa ta, ai kasan Mahaukata da Ɗan banzan yawo tom ai kan nasu ne ba ɗaya ba duk nisan guri haukarsu gaya mus..... Bai kai ƙarshe ba Sumayyah ta tafi luuuuuu zata faɗi sumamiya. *** Kwanan Inna biyu a gidan su Tanimu ta samu kulawa Sosai kuma ido ta ya warke babu kumburin sai dai bata gani da ido ɗaya dan ƙwayar ido ta fashe, Abinka da cutar mara Lafiya hakan bai wani ɗaga mata hankali ba Inna Zuwaiara ce ta fita gidan Baban ɗanta Babandi Sai Tanimu kawai ta bari a gidan. Surutu kawai Inna take wanda baka gane mai take nufi shikuma yana duba takardu makarantar sa sai dai ƙirjin sa yana yawan bugawa ya rasa dalili haka. Kafi Baba malam ya taɓa ta tuni Ammar ya ɗauke ta, ya kalli Malam."Ka nuna min ɗaki Mahaifiyar ta zan kaita can” Dukan uku-uku ƙurji Malam ya shiga yi dan zai iya rantse wa da Allah tun da Sumayya tasa ƙafa ta fice babu wanda ya ƙara tura kansa ciki. Jikinsa na ɓari suka kutsa ciki gidan,Baba Hauwa ce ke wanki jikin tulu ruwa gani mutun ya shigo Salam daga kasan maƙoshi yasa ta miƙewa tare da dafe ƙirji. "Wa'innahu Sulaimanu Wa'innahu.. "Ke sakarai Shasahar mutun ne Ba Aljani ba, kina nufi Akwai wani sheɗani da zai iya tun karan Gidan Malma Sule batare da Ayar Allah ta kona shiba, Tom wanan da kike gani babban mutum ne,baƙo Sumayyah ne.”Malam ya faɗa tare da nunawa Ammar ɗaki,tsaki ta doka musu. "Matsee Yaya Zulai kizo kiga wani Iko Allah 'Yar Mahaukaciya ta jawo mai jan kunuwa”Da gudu Baba Zulai ta fito zani a hannu. Lokaci da ta fito Ammar ya juya musu baya ya shigar da Sumayya cikin ɗaƙi.Kasa jurewa tayi tabi bayan sa daga Window ta tsaya tana leƙa su. Ammar yana zuwa ya shinfiɗar da ita kan ya galgalaliyar tabarma ido sa har ya canja launi ya ɗago ya kalli Yusuf"Inaso Mahaifiyar ta ta dawo kafi ta farfaɗo ko nawa ne zan baka, Abani ruwa” Da gudu Yusuf ya fita har yana Turai Baba Zulai. Saboda tsabar kiɗima zaici kuɗi.tunda ya fita yake falfala gudu bashi ya tsaya ba sai atsakar gidan Su Tanimu yana zuwa ya fara kurma wa Inna kira.Inna da take gefe a zaune, ta miƙe ta koma bayan Tanimu tana kuka."A'a baza niba zai zaneni baza niba” Ran Tanimu ne ya ɓaci“Kar ki damu babu Uban da ya isa ya fitar dake daga gidan nan.”Yana fadi haka ya kama hannu ta suka fita taskar gida. Yusuf yana tsaye ya zuba uban doro.yana Gani Inna ya tafi,Hannunta ya kama"Zo mutafi gida Ga shegiyar yar kican mai jaye jaye maza ta.... Jin hanunta ko motsawa baiba yasa shi waiga wa Tanimu ya gani ya ruƙe mata hannu."Babu inda zata duk lokaci da tatashi gani ta tazo ta ganta anan gidan Amma baza ta sake shiga wacan baƙi gidan naku ba marasa mutunci azzalumai..... Mari Yusuf ya dauke tanimu dashi, ciki zafi nama Tanimu ya rama ko kawa ce ta kaure musu ciki Jim zafi Yusuf ya fara ihu. "Wayo jama kuzo ku taimaka min Tanimu zaiwa matar babana faɗe,babu mutane a gari ne dan Allah ku fito kar ku bari yaci mutunci aure” Ta ko ina mutane suka riƙa shigowa Abinka da kar-kara har da masu Sandina kamar 'yan farauta, batare da bincike ba suka rufe Tanimu da duka har suka far fasa masa jiki. Inna Zuwaiara da ta tunkari gidan taji hayani ta kaure yasa ta faɗa da gudu, Fuskar Tanimu ta gani duk an bubuge ta har da jini sallati tasa ta tura kai cikim mutane tare da bawa ɗanta kariya, cikin hikima da dabara tayi musu bayanin, zagi Yusuf suka fara gani reshe yana neman juyewa da mujiya yasa shi Sulalewa ya gudu. Lokacin da Ta koma Sumayyah ta farfaɗo kalo kalo Suka fara da Ammar da Yusuf Malam ya gane tambayar Yusuf yake so yi amma girman kai tsiya ya hana shi magana cewar Malam. "Kai yusuf Ina ita Rabi take?”Kalar tausayi ya koma"Wallahi Baban mu Tanumi ya hana kuma da duk kan Alamu ɗan Isakan yaro nan akwai manufar sa akan ta shiyasa duk iri dukan da aka masa ya hana na taho... "Muje ka kaini gidan”Ammar ya faɗa. zubar Sumayyah ta miƙe"Nima zani saboda ya san nice na dawo zaifi yarda” Su Huɗu suka nufi gidan Su Tanimu Malam,Yusuf, Ammar,sai Sumayya. Tun daga waje Malam Sule yake rafka Sallama har Inna Zuwaiara ta amsa tare da ratayo mayafi atamfa ta fito gani Malam yasa ta zubewa har ƙasa tana gaida su jikin ta har rawa yake,Saboda A ƙauye Giɗaɗo Malam tamakar Sahabi haka suka ɗauke shi duk abin da ya furta Umarni ne a guri mutane Ƙauye. da hannu ya nuna Inna Zuwaiara. "Tashi Anan tshuwar banza ni zaki ci Ammana Tom ki sani ina so Rabi kuma yau sai na kwana akan buzu, za kusan Ba'a taɓa Malami soro,a wanye lafiya sakarya mara rabo” Jikin inna Zuwaiara na ɓari ta fara bashi haƙuru."Ka temaka kayi haƙuri Wallahi babu komi a zuciyar Tanimu sai alkairi ka san.... "Inna babu an fani ki bashi haƙuri Don Allah ki tashi iri wanan malamai iri sune Ake janyo harshe su ayi.. Saukar Carbi Malam yaji a hannu sa."Allah wadaran da sami ɗa mara tarbiya iri ka Zuwaira kinyi Asara haihuwa.” Malam ya faɗa yana gyra zaman asuwaki bakina. Zai sake janyo masa riga Ammar ya ɗaga musu Hannu."Stop, you know that I'm not going to sleep tonight.Ku fito da ita Bazan jure shirme ku ba” Sai Yanzu Tanimu ya lura da Ammar da ke tsaye Wani iri kwarji ya masa lokaci da ya kalli cikin kwayar idon sa. murya na rawa yace. "Tana ciki ɗaki”Taku Ammar ya fara kamar yasan gidan. Bai san me yasa yake buri yaga matar ba, ƙaunar matar ta shiga ransa.bayan sa suka bi hata Sumayya bayan Ammar tabi. A fili tsakar gidan ya tsaya yana wara ido Tanimu ya tunkaro ɗaki da yake bangare gabas mukulli yasa ya buɗe ya shiga ya kamo hannu Inna, Sumayya na ɗaga ido ta hango Inna, taga ido ɗaya babu wani iri ihu tasa ta zura da gudu ta rungume Innarta tana wani iri kuka mai gigi ta zunciyya... *Ayi hakur Rashi Comments yasa gwiwa ta take sanyi da kuna comments zan iya Update sau biyu arana in kun gyara har Read more zanke yi da yawa* [11/18/2025, 6:25 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-11 Ina na gani ta ta tafar hawaye ta ido ɗaya tana shafa Fusakar ta cikin kuka take cewa"Sumayyah tace wanan ta dawo, Sumayyah zo na goya ki mu tafi gida?”Ƙara rungume ta tayi tana kuka.“Me ya sameki Inna ta?waye ya ji miki ciwo Wallahi bazan yafewa kaina ba nice naja miki da inanan da duk haka bata faru da keba”Babu wanda ya iya magana sai malam da ya kaɗe Malin-malin ɗinsa yana taku ciki taka iri ta malamai na gari yaje har inda suke. " 'Yata Sumayya tsautsayi ne tashi muje gida yanzu sai akaita asibiti dama mai yin jiyar ta aka rasa tunda gaki kinzo ba shike nan ba”Da wani iri kallo Mamaki ta bishi. Murya ta narawa. "Baba amma a ka kasa kaita Asibiti sai da na dawo wanan wace iri rayiwa ce me Inna ta tayi muku ne aduniya” ido ya shiga ƙifta mata yana mata alamu tayi shuru zai buɗe baki aƙamshi turare Ammar ya doki hannci sa.Bai kula suba sai ɗurkusawa yayi ya kama hannu Inna"Kizo mu koma gida baza ta sake tafiya ta barki ba”kallo Ammar tayi ta ƙyal ƙyale da dariya tare da kai hannu kunne sa ciki zafi nama Sumayyah ta tare."Inna baƙo ne mai zaki masa..”Hannu yasa ya kautar da Hannu Sumayya.“Ina ruwanki ita mamata ce.“Dariya Inna tayi tana sosa kanta da baka taɓa gane tsagar kitso ba tace."Kwarkata ce Sumayya ga ta an ciki gashi sa”Surune ya ratsa tsakani su dan Sun kafe juna da kallo gashi ko wanne ya kasa ɗauke ido sa daga kan ɗan uwansa. "Me kake yi ne Ammaru Kar ka mai da kanka yaro ƙarami a gaban Yariya ƙarama.”kamar wanda aka tsira da Allura haka ya miƙe yana cin-cin magani.“ki kamata mu tafi”Jiki a sanyaye ta kama Inna har suka ƙarasa inda Inna Zuwaiara da Tanimu suke tsaye kwace hannuta tayi ta koma guri tanimu“Ke Sumayya baza Ni ba Yusuf zai da keni Da Malam kizo mu zauna guri wanna yana daya min Nama”Gigicewa Yusuf ya yi ya fara Kame-kame. "Kai Babar Sumayyah yaushe na taɓa dukan ki kawai in komawa ne baza ki ba sai ki faɗa sai kin min....”Ƙutttt ya haɗiye ragowar maganar sa,saboda iri kallo da Ammar ya masa.kuɗi ya ciro ciki Aljihu Sadda sa Zasu kai 20k.“Kaje ka suyi Kayan ciki ammata farfasu.” Yadda kasan Yayiwa Yusuf Asiri haka, yake bin umarni sa, ko dan zuciyar sa ta riga ta mutum Oho.Kallo Malam yayi, da ido ya karanta masa yadda zai da kuɗi sanan ya fita, sanan ya koma kusa da Inna Murmushi ya sakar masa izza da kwarjinin da suka sake bayyana sai da gaban Malam dana Ranmu ya buga dan Basu taɓa gani Balarabe mai kau haka ba ko A ciki Film, hannu ta ya kama. “Inna Kunga na bada a siya miki Nana kuma naki ne ke kaɗai in kina so kici kizo mu koma gida in ab haka ba damu cinye bake”Da sauri ta saki Tanimu ta koma guri sa. "Zani zan bika zaka bani??”Kai ya ɗaga mata . Kusa da Tanimu ya koma, jikinsa kyarma yake,sai da ya kawashe 2 mintes sanan ya miƙawa Tanimu hannu shima haka ya bashi. “Muna godiya da temako da ka mata Allah ya bada lada yasa”Ameen nagod Sosai”Kusa da Inna Zuwaiara yaje ya rusana godiya ya mata ya curo 30k ya miƙa mata Taso taƙi karɓa sai ya miƙawa Tanimu,sanan suka fita fur Inna ƙinyar da tayi ta tsaya kusa da Malam. Lokaci da suka Isa gida Sadiya da Lubna duk an canja kaya Fusakar taci uwar hoda da barbaɗa kumatu, har da turare su ɗan haɗi, suna shigowa, har rige rige zubewa ƙasa suke suna gaida Ammar, ko kallo su baiba sai hannu da ya ɗaga musu suka shige ɗaki Inna. Da gudu Sadiya ta dawo jiki Inna ta."Inna ta wallahi Wanan yamin da zai Aure Ni da na huta Dan Allah Inna kiyi wani abu”Uwar Harara ta doka mata.“Keni barki Tsoro ma take bani kyausa Wallahi ya yi yawa sai kace na mijin Aljan” Tun da suka shiga babu wanda ya iya cewa ƙala sai gajiya yayi ya kalleta.“Kisa abu ki share komi dare za'a kawo kaya gobe zan dawo”kai ta ɗaga duk da bata san wane sako yake magana ba.Fita ya yi Inna ta tare shi“Kace zaka bani Nama kuma zaka gudu”Kai ya ɗan dafe tare da saki murmurshi.“Sorry Yanzu...”Kallo Sumayyah ya yi domin ta tuna masa sunan yaro da ya aika.“Yaya Yusuf ne Inna ki dawo zai kawo miki”Sakin sa tayi tana dariya.Bai sake kallo taba ya fice sai da kansa ya sara gani Ido su Baba Hauwa dasur Lubna har da Amina auta da Khalid duk sun zuba masa ido Amina ce ta miƙe duk da yariya ce Amma an hore ta da ladabi mage zubewa tayi akasa. "Ɗan Uwan su Yaya Sumayyah Allah ya kaika Lafiya mungode da kasa Baba Rabi ta dawo gida”Ragowar Chanji Jiki sa ya ciro duk da bansan nawa bane Amma daga gani zasu kai dubi Hamsi, Khalid ne ya sauri tare hannu ta. “Karka bata, bata da wayo yanzu cewa zata yi kashe su zata tayi”Bai ce dashi komi ba ya ajiye tare da fita. Yana fita ya iske Malam Sule zaune kan Duwatsu da Almajirai suke zaman karatu dare miƙewa yayi tare da dogon carbi sa, yana ja.“marhaba da yaro kiki har ka fito,Tom madala munfa gode da temako Allah yi Albarka madalla”Kai ya jinjina masa har zai tafi Malam ya riga shi ƙarasawa jikin motar da kansa ya buɗe masa motar. "Sai dai Banji sunan Baban yaro nawa ba”Ammar Kamar yadda Aminiya ya faɗa”Yana faɗa masa haka ya shige ciki kotar kansa ya tura cikin motar"Ammaru dan Allah ko zaka temaka yaude Hannu na dukan ciya Wallahi ko na gari babu agidan Allah kuma ya temaka kazo” Sai da ya kunna motar ya ɗago ya kalle shi.“Kaje ciki ragowar canji na kenan gobe akawai saƙo za'a kawo harda kayan abinci” Ƙasa ya zube kan Malam kawai Ammar yake hangowa."Allah ya ja dare, Lallai iyaye ka basu haihuwar banza ba, Anyi fara haiguwa anan Anna gani ka Anga ɗan Babban gida Malam Har ka tuna min da wani Hadisi da....” “Nagod Sai an jima”Ammar ya katse shi ɗan Surutu ya ishe shi ga Uban yawu da yake tsalle a baki Malam, yana bari guri Malam ya juya da sauri har da ɗan gudu sa. Ko Sallama baiba ya ja tunga a tsakiyar tsakar gida. "Tom kuɗi da me jan kunuwan nan ya kawo a hannu wa suke”Masifa Baba Hauwa ta fara“Waikai Malam dan Allah ina zaka kai don Abin duniyar ka Dazu da Alhaji Badamasi akace ya kawo maka Zakka amma madadi ka bari mu raba sai kazo ka zuba ido sai Ana raba da kai”Mugun tsaki ya buga tare da miƙa hannu yana karkatar da kai. "Abani ko ran kowa ya ɓaci agaidan nan”Amina ce ta mike.“Wallahi Baba Kuɗi suna guri Khalid har ya zari dubi biyu a ciki”Duka Malam ya kaiwa Khalid ya kauce tare da watsar da kuɗi yana magana kamar tsoho ɗan daba ya fice, Malam kuma ya gurfana yana bin kuɗi kamar tsoho gurgu yana tsince yana mikewa ya cusa cikin Aljihu yana zare ido. "Haka dai Malam Wallahi baka da girma sai naji kinka”Cewar Baba Zulai, da take nunke kaya.Yana ƙoƙari fita waje Yusuf ya shigo, da ƙatuwar leda, baki ya washe. “To!to Yusufa kaine tafe Ince dai guri Garbu mahauci kaje dan Kasan guri sa nake siyan ɗanye Nama yana gani ka yasan abinda ke nane.”Malma ya faɗa yana miƙawa Yusuf hannu ya amshi ledar hannu, shi kuma hankali sa yana kan Ɗaki Inna Rabi, a fusace ya waigo. “Baba Ina tawa Sallamar dan tunda naganku nasan Anyiwa gidan Sallma mai kyau”Tantaro masa yayi.“Kai rabu da mutsiyaci Hannu jarirai gare shi Saidai naji kamar yana cewa Yabawa Yariyar can Sumayya naka kaje yana gurinta”Ciki zafi ya tunkari ɗaki su Sumayyah wace tunda Ammar ya fita take kwale ma tana kashe iyaye ledoji da da suke ciki Kamar juji. Ba zato Yusuf ya faɗo atsorace ta kalleshi"Yaya Yusuf samu da zuwa...” "ke dakata Ina Ajiya ta da wance dogo ya bayar ki bani?”Ciki rashi fahimta ta sake kallo sa.“Yaya Yusuf wace ajiya kuma akanwa kake magana”Madadi ya mata bayani Mari ya ɗauke ta dashi. “Zanci Ubanki Sumayya wato kinje birni kin waye zaki fara karya In banda mugun Hali abaki kuɗi nawa dubu ɗari ki sauna kina kafeni da ido kamar na kyawa shegiya Mai bakar fata.” Kunci ta dafe ta fara hawaye."Wallahi Allah yaya Yusuf babu abin da ya bani kuma ko Inna ta zaka tambaya.....Rufe ta yayi dakua ta ko ina .... *Ayi hakur babu Editing, Shering da comment da Like shine aiki ku Free book ne har ƙarshe 'Yan Ammana* [11/20/2025, 2:42 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYA 📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- haƙin mallaka na musamman ga marubuciya. ____________free book _page-12 Babu wanda yace Yusuf kabari, Sadiya da Lubna kuwa murna harda tsale. gani ba zata faɗa masa Gaskiya ba ya ajiye abin dukan ya fita yana yarce gumi ido duka haɗa da Baba Zulai.“Yusuf bari na gaya maka gaskiya koda yaron nan ya ba da kuɗi kasan Malam bazai taɓa bari yariyar nan da kuɗin ba, kaje kana ta wahalar da kanka akan aiki banza.”Fusaka ya sake tamkewa.“Babar mu maganar gaskiya zan iya Allah ya isa kina kallo fa har bunkure ya sa ni naje, na suyo masa nama, har da ido yake min magana kar nasiyo na yadda akace na dubu biyar na siyo saboda na faranta masa amma shine za'a ci ammana ta”Hannu Baba Hauwa ta ɗora aka . " laa'ila ha'ilalahu Yanzu kai Yusufa mahaifin ka ka ke faɗawa haka Lallai ɗan Malam yaƙi halin malam”harara Inna Zulai ta wurgawa mata. “Sannu kanwa uwar gami Shegiyar ta motsa,Saboda ba Khalid Malam ya dora ba shiyasa komi kike nuna hasadar ki a fili.” Miƙewa tayi a fuskar."Haba Zulai nayiwa Yusuf hasada nayiwa wa? Ai ni bana fata Khalid ya kwashi zunubi Iri na Yusuf kudai kuje ku tayi”Malam da yake ɗakin shi yana Salamar wata mata da tazo gurim shi, yana daga ciki yana jiyo hayaniyar matan nasa, agurguje ya sallame ta ya koma ciki gida yana shiga kowa ya nutsu. dubi biyu² ya basu, kafi ya dire takar dar nama.“In kunga dama ku gyara a zuba a miya in kuma baku ga dama ba abarshi iska ta buleshi da ƙura” Yana faɗi haka ya juya.miƙewa Baba Zulai tayi kamar babu 'ya'yan su aguri.“Malam dama ina so zamu yi magana a kan Sadiya da wannan ya...,”Shuru tayi tabi Baba Hauwa da kallon banza. "A bazan Man kare wallahi An dai yi faɗuwar baƙar tasa”Baba Hauwa ta faɗi tana kaɗa kan 'Ya'yanta Lubna da Amina suka wuce ɗaki. ***** ****** Tafiya yake hankali kwance sai dai Yana cike da tausayi Inna Sumayya da son sani ya aka yi ido ta ya fashe. taya zai yiwa Hajiya bayani halin da yariyar nan take ciki, ciki ƙiyayar 'Yan uba.tsaki ya ja, ya shiga call ɗin number mahaifinsa sai dai bata shiga, Alamu ya nuna har yanzu bai sauka ba, sai da ya gama bucking ɗin duk wani abu da zai kaiwa Sumayyah da mahaifiyarta sannan ya nufi gida. Tun daga ƙofar parlour yake kwaɗa Sallama shuru babu kowa, sai dad-daɗan Ƙamshi wanda kullum haka Parlour mahaifiyar sa yake kasancewa, sai dai na yau ya ban-ba ta da ko yaushe dan Abin sa yau zai dira shiyasa gyran ya ban-banta dana ko yaushe. Kitchen ya nufa dan yasan yanzu Hajiya tana can.wani lace ne iya gani ka san sai sun Hajiyar, lemon green ne sai Flower's whit gyarare gashi nan har gado baya ta ko ina sheƙi yake yana zuwa ya rungume ta da saki mata lafiyaye peck a goshi. Juyowa tayi ciki yalwataciyar fara'a. “Sannu da zuwa na zata zaka dawo min da ita.”Annuri fuskar sane ya ɗauke tunawa da halin da ya barta, kallo ɗaya Hajiya ta masa ta fuskanci akwai Matsala.Kafaɗar sa ta dafa. "Ammar, ina fatan komi Lafiya in ce Babu matsala acan ɗin??”Iska ya furazar ya matsa kusa da Food flask cup ya ɗauka ya tsiyayi ruwan zafi,tea ya haɗa mara suga Sosai ya fara kurɓa. "Ni Hajiya wai yaushe Abi zai shigo na duba tim har yanzu banji alamu zuwa sa ba.”kawar da zance yayi, ta riga tasan halin Ammar ba kowa ce matsala yake sauri faɗa ba matukar yana da ya ƙini zai iya gyra ta. Ammasar tambayar da ya mata ta bashi.“Bana ji zai haura 30 mintes bai sauka a Airport ba ka shirya da sauri zamu je tare.” “Ok”yana faɗi haka ya fita zuwa nasa nasa part ɗin, Bathroom ya shiga ya faɗa bathtub ya juma yana wanka kamar bai yi wanka ba ɗazu, ya fito ƙugun da ɗaure da tawel sai da ya shafe jikin sa da Cram masu tsada da sa laushi fata duk da Allah ya wada tashi da laushi skin, amma yana amfani da mayukan gyran jiki.tsawa ya yi gaban waldrop yana tunani kayan da zai sa ya jima kafi ya zaɓi Trousers da T-shirt block tare da gyara sumarsa Sak asali Labanis ya bayyana a jikin sa diri da haiba ya sake bayyana nau'o'in turarika masu kashe zuciya yasa tare da ɗaura agogon diamond a tsintsiyar hannu sa cap yasa black da Sandal din ta takalmi baƙi. (Nuna OUMMU MUWADDAH sai da nace ma Tubarkallah masha Allah) Taku yake iri na jarumai har ya ƙaraso Baban Parlour, phone ɗin sa ya ciro cikin aljaihu wando sa, bana ji mai Aka ce a ɗaya ɓangare, Ammar Ya lumshe ido kamar mai jin bacci."Tom Hajiya Ammar ɗinki dai yana Parlour yana jira” Da haka ya gimtse kira ƙafar sa ya ɗauka ya ɗora saman Centar teble ya ƙaro Volume ɗin kiɗan wata waƙar Larabawa ce girgiɗa ƙafa yake tare da lumshe ido yana bin waƙar cikim ƙasan zuciyar sa ya shagala cikin wanan halin Hajiya ta fito har da siriri glass a fuskar ta duk da ta kai Shekaru 47 amma ɗauka zaka yi shekaru ta bai gaza 30 Year ba.tun da yaji ƙamshi turare ta ya buɗe ido. “Masha Allah Yajiya anya Kawai mace mai tsafta da kyau iri Ummu na banji hakan a kwana kusa”Sumar kansa ta sosa tare da ɗan ya mutsata.“Ammar kar ka zama mai son kai, Ka sani 'Ya'ya da yawa zasu ƙalubalance ka” Miƙewa ya yi ya kama hannu ta suka fara taku ciki isa“Hajiya gobe zan koma Giɗaɗo zan kai wa Sumayya saƙo”Dariya tayi tana fata Allah yasa abin da yake ranta ne yake shiri faruwa,a fili kuwa cewa tayi “Allah ya kaimu, nima kafin azumi yazo zan je na duba ta” Kai ya jinjina Suka fita Compound, Back seat suka zauna shida Hajiya driver ya zauna mazaunin sa. ****** ******* Ta jima cikin ɗaki Malam sanan ta fito tana tura ɗan kwali gaba goshi, waƙa take mai cike da shaguɓe.Baba zulai ta cilla mata harara"Hauwa ya naga kamar kina min wani gani-gani ko da magana.”Dariya tayi me cike da takaici. “Wa..! Nina isa nace banten sarki ya yi ɓurtu, ai ido ne wa, kuma duk nisan dare gari zai waye Allah na tuba mun jima munaji kar kyaran ka...” Fitowa Sumayya ce ta dakatar da Maganar da Baba Hauwa take ƙokarin furtawa. Da ƙyar sumayya ke tafiya shiru suka yi suna binta da kallo. Har ta gama shin fiɗa tabarmar a ƙofar ɗaki su,ciki ta koma ta kamo Inna ta zaunar da ita sannan ta fito da uwar bolar da take ɗaki, ta bayan gida ta fitar da ita ta watsar. Cak ta tsaya gani Akwatu kayan da Hajiya ta bata an gama badali su Sadiya turmi uku Lubna turmi atamfa biyu Amina kuma Aka hada ta da Baba Hauwa turmi biyun lass ɗin da Hajiya ta bawa Sumayya a rage mata girman su, ta gano hannu Baba Zulai kala uku. "Hauwa Amma yariyar nan ba ƙaramar makira bace, da wanan kayan gidan Ubanwa zata kaisu.”Harara Baba Hauawa ta wurgawa Sumayya."Hoho mata muguwa mai mugun hali, Dangi hauka da Aljanu” "Babar mu don Allah,ki barmi wanan Lace ɗin Gobe naje kasuwa dashi”Cewar Sadiya da take ta faman jinjiga Baba Zulai. tsaki tayi.“Kinga fa Allah bazan baki ba, da yau da gobe duk Malam a ɗaki na yake so nake na gwangawaje lass ɗin nan ajikina ko na samu ladan Aure”Tana faɗa ta kara lass ɗin a saman ƙirjin ta. Hawaye ne suka zubowa Sumayyah masu zafi, Zuciyar ta ta sake karaya, lokaci da ta hangi Inna ta na miƙa hannu ita ma abata, ƙoƙarin miƙewa Inna take da sauri ta Sumayya ta ƙara sa inda take ta goge Hawaye ta. "Inna ba na hana ki riƙa miƙa hannu in kika ga abu a hannu wani ba, Ko so kike nayi kuka, ki bari zanje neman gwangwani madara in nasiyar Zan siya miki Atamfar sallah”A fili Inna ta nuna murnar ta, tana nuna jikin ta tare da alamu zata shafa hoda tayi kwalli kai Sumayya take ɗaga mata hawaye da take ƙoƙarin hana zubar sa ya sake zubo mata.maganar baba Zulai taji. "Sadiya Dan Allah tashi ki azamin wutar nan ki zuba dadawa can Kin san Malam kamar kure yake guri nama yanzu in ya fara tsaya min aka kamar tsohon maye haka yake.”Dariya Sadiya tayi ta tashi tana waƙar Kawu ɗan sarki ta Ungollo na ciwo. Lokaci da ake kiran sallah magari ba lokaci Farfesy Kayan ciki ya kammala, babban tire ta samo ta kasa shi kashe-kashe tare da zubawa Malam nasa a ƙaramar Samira, kowa kaso ɗaya aka bashi sai da kowa ya gama ɗauka Baba Zulai ta kwaɗawa Sumayyah kira da suke zaune Kamar kurame ita da Innar ta, Inna ce ma me yawan suru ita kaɗai. "Sumayya..! Sumayyah..!!!”Shuru babu magana miƙewa tayi A zafafe ta tunkaro inda Sumayya take zaune tayi nisa ciki tunani rayuwa.Duka ta ɗana mata."Ke 'Yar mahaukaciya dan naga alama kinfi jin daɗi a kira da sunan ki kije ki ɗauka naki ne ke da uwar ki, naman bai yi afki ba shiyasa aka haɗa muku in kuma bakwa ci gaba takai mu” Taji shigar dukan Sosai, jikinta na ɓari ta nufi in da nasu yake dan har Isakar tsakar gida ta tule shi da ganye maina duk ya fara tule shi da ƙura, ƙoƙarin ɗaukan faranti tayi Baba Hauwa ta daka mata tsawa."A jiye min faranti salon a zubami guba, ki kwashe a hannu ki, ki matsa ki bani guri.” Ajiye tayi ta juya tana zuwa Inna ta fara miƙa mata hannu.“Sumayyah Zanci nama, zaki Bani Allah ina so zaki bani??”Hawaye ne ya cika Ido Sumayya tayi sauri gogewa da tafin hannuta, ta miƙa mata naman, kafin kace kwabo ta cinye shi. Jin-jiga kafaɗar Sumayyah tayi "Sumayyah ban ƙoshi ba, Allah zaki daɗa min Kinga fa yinwa nake ji kiyi Haƙuri Sumayya ki daɗami”Fashewa tayi da kuka ta faɗa jikin Inna.kuka take sai dai Babu ƙara ta juma ajikin ta Sanan ta ɗago kai. "Inna kin manta da akwai samu akwai rashi? kinsan yanayi da muke ciki a gidan nan me yasa baza ki haƙuri da abin da kika samu ba”Turɓine fusaka Inna tayi wai itama tasan faɗa gani za tayi fushi yasa ta cewa. "Gobe in na fita nayi aiki Sosai Nama zan fara sai miki kafi mu samu kuɗi ɗinki”kai ta hau kaɗawa tana murna da haka Malam ya shigo ya kora su ɗaki suna daga ciki suna jin hirar su har da su Sadiya da Iyaye su. Ciki farin ciki suke hira. *Alhaji Ɗan Dubai* Ko da ya tafi bai koma Lagos ba dan Business ɗunsa na safar mata ne yake kai shi Lagos ko aiki da da uban gidan sa ya tura sa. Safa da marwa yake ciki makeke Bedroom ɗinsa, Hajiya Fatiha matar sa ce da take kwance ta bisa da kallo."Alhaji lafiya naga tun da ka shigo banga walwalar kaba.?”Zama ya yi gefe Bed din kafin ya furzar da iska mai zafi“Kibari kawai Hajiya Fatiha Ban taɓa asara kamar na wanan Lokaci ba, Riba mai yawa ta tunkaro ni sai dai tsinane yaro nan Ammar ya lalata komai” Tashi tayi daga kwanciyar da tayi ta dawo jikin sa."Ammar wane fa?”Ammar mana yaro Alhaji nawa”kafe shi da kallo ta yi.“kamar ya ban gane ba kamin bayani”kwashe komi ya yi ya faɗa mata. Ajiyar Zuciya ta sauke."Kenan yana da Alaƙa da ita kome?” "Bana ce ba Amma wallahi sai na lalata rayuwar sa ba'a cin bashi na a zauna Lafiya sai na ɗai-ɗai ta shege Uban nan nata, dan shine kwallo shege, Sai dai naga A-lamar tana so Ammar zanyi anfani da son da take masa na ruguza farin ciki ta, ban taɓa samu naƙasu aciki Kasuwanci na ba sai akan yariyar nan, naci buri a akanta Amma yaro nan har da min baraza nar Sallama daga guri aiki.” Dariya Hajiya Fatiha tayi "Wanan me sauƙine, mu fara raba alaƙar Ammar ɗin da ita sanan musa duniya ta juya mata baya ta rasa madafa kaga dole ta neme mu. Kuma bariki da bata so tayi dole sai tayi shi”Dariya Alhaji Ɗan Dubai ya yi mai sauti"Bana bukatar ta,a yanzu bayanta kawai nake so gani”Yana faɗi haka ya fita. *Nasarawa* Tunda suka shiga mota babu mai magana dama haka tafiya da Ammar take da wuya kaji shi yana yawan surutu, sai ma in da Hajiyar sa ne ko kuma Abin sa suke tafiya.suna isa Airport ɗin Malam Aminu Kano driver ya nemi guri packing din mota yagyra packing ciki nutsuwa suka fita, Ammar ya kama hannu hajiya suka fara tafiya sai da su kayi nisa sanan ya kalle ta. "Hajiya Gobe aiki zai miki yawa nasa a kawo kan sa zaki gyra zan kaiwa Innar Sumayya” "Allah yasa zamu gani Ammar sai dai ina so naji halin da yariyar nan take ciki da Mahaifiyar ta.”peck ya mata a goshi sanan yace. “Ummu zan kai ki ma sai ki ganta, yanzu taya zan baki labari nida ba ɗan Jarida ba ko marubuci labarai ”kunnesa ta kama“Ba sai ka kai ni ba zansa drive ya kaini” Suna gurin a tsaye Abi ya fitowa har da Manager da P.A ɗinsa da suri Ammar Ya faɗa jiki Balarabe mutun wanda shekaru ne kawai ya ban-banta shi da Ammar. “Abi, ahla wa daula....kif kéinit l-tari’? Kteer mshta’lak.” “Abi,Sannu da zuwa..Ya hanya? Na yi matuƙar kewark.”Bayan sa ya shafa tare da peck ɗinsa a hannu ciki lafazi yaran Labanis. “Ya Ammar! hibib Albi..ana kaman mshta’lak. El-hamdellah ‘a Saléme.” “Ammar! Masoyin zuciyata...ni ma nayi kewara.”P.A da Manager da suke tare da Abi ne suka rusina suka gaida Hajiya. kallo Ammar suka yi shima suka gaida shi hannu ya ɗaga musu dan bai cika so yana magana da iyaye sa ana katse shi ba Abin ya dube shi. "Jeet men America deghri ‘a Nigeria...‘anjad eshta’telkon kelkon.” Peck ya masa ba tare da ya sake ce masa komi ba.Abi ya ƙaraso waje Hajiya. "kin kara kyau Kamar ba Ummu Ammaru ba gaskiya budurwa nan tana jin daɗi”Duka ta kai masa a ƙirji“Wallahi kasa naji kunya Ammar da P.A ɗinka suna guri baka ji nauyi sai?” Hannu ta ya kama yasan dama sai ta sako zance Ammar yana guri,kullum bata son Abin da zai sa ta jin kunya Agaban yaro ta. Mota suka shiga Ammar ya zauna a for seat driver ya ɗauki hanya. Yau yajima bai yi hira iri haka ba Bacci ne ya fara ɗaukar sa ajiki Abinsa kira ya shigo masa ƙaramin tsaki ya saki.sanan ya picking call ɗi. “Hello Fu'ad”Banji mai aka ce a ɗaya ɓangare ba sai tashi da yayi daga jikin abin."Ok ka shigo dashi ina Parlour Hajiya”Katse kiran ya yi babu jimawa Fu'ad ya shigo yaro ne matashin baza su wuce sa'anni ba,Sai dai daga gani yaro Ammar ne gaisawa yayi da Abi ya gaida Hajiya Sannan ya ajiya Leda biyu ta viva.“Ranka ya dade duk an gyra sai dai a ƙara wanke wa” “Oky Hajiya gashi ya kawo.Fu'ad kai shi cikin Freigd”Yana kaiwa Ammar Ya miƙe suka fita da Fu'ad. Washe gari Tin da Hajiya tayi Sallah bata koma Bacci ba, tana kitchen tana aiki, Aiki biyu ta haɗa dana Ammar dana Mahaifinsa Sosai aiki ya kacame mata Deluwa 'Yar aiki ta bata gari taje gani gida shikuma kuku tin da aka kamasa yana zuba musu guba aka kai shi virus bata sake naiman wani kuku ba, tace ta haƙura da mai girki duk wahalar aiki tace zata iya kayanta. Sai 11 Ammar ya fito cikim shiri sa yadi ne light Blue yasa, iri aikin hannu nan da hula zanna bukar ya yi kyau sosai, ƙamshi kawai yake zubawa.ɓurintu Hajiya ya ji a kitchen da sauri ya faɗa ta baya ya rungume ta. “Sorry Hajiya ta na saki aiki Sorry”Kan sa ta shafa aiki ya zame mana jiki karka damu ɗana kayi break fast aiki ka ya kammala”Godiya ya mata ya koma parlo Tea ya sha sai chips ya goge bakin sa da Tissues sanan ya koma kitchen. “Wow Hajiya wanan flask ɗinan ya yi min kyau” "kayi addu'a matar ka tazo ma da iri sa,Ammar zo ka tafi time na ƙurewa Ban so dare a yayi maka a hanya”Godiya ya yi ya kira Madu mai gadi ya dauka masa Flask ya saka a cikin but ya mata sallama tare da cewa ta gaida Abi in ya fito ba zai jira ya fitowar saba.Tun da ya ɗauki hanya yake jin wani iri farin ciki na ratsa zuciyar sa yanayi Fusakar Sumayya da tafiyar da suka yi jiya yake tunawa, sa'i² ya saki murmurshi. ****** ****** Tinda aka fito masallaci Sumaiyya ta fita daga ɗaki tsunma tasa ta ɗaure ƙofar gudu Inna kar ta fita bata ganta ba tayi wani guri.Bola bola take bi ko zata samu gwangwani madara sai dai yau kamar baki ta gaza samu har goma da rabi gwagwani uku ta samu bakin ta duk ya bushe har jiri take ji gashi takalmi ta da tazo dashi Sadiya ta ƙwace sai wani haɗu bauta tasa, shima saboda tsabar yawo da tayi ya tsinke leda tasa ta ɗaure dashi.Sha ɗaya da rabi ta taki sa'a ciki wata bola da take gefe rami gwagwanaye ne birjuk da Alamu ba'a juma da zubar da su ba kasa boye farin ciki ta tayi. "Allahmdllhi Allah na gode maka Allah yasa kaltu mai Alala ta siya kan naira ashirin na samu kuɗi siya wa Inna ta Nama” Ciki sauri ta fara zuba gwangwani ciki buhu ta wasu yara ne da aka musu break daga makarantar boko suna hango Sumayya, suka tsayar dariya ɗaya yayi dutse wuta ya ɗauka ya saita bayan Sumayya ba zato taji saukar dutse tasss a gadon bayan ta miƙewa tayi tare da gantsare wa hawaye masu zafi suka sulalo mata. Dariya yaran suka sa.“'Yar mahaukaciya Uwarki kema kin fara haukar ne naga kin fara bin bola kinaci leda”Ihu suka fara suna mata waƙa ga mahaukaciya 'Yar macukule, gani yaran sun fara ihu suna tula mata ƙasa, ya sata haƙura da kwashe ragowar gwangwani tabar guri duk da haka wasu sai da suka raka ta da gudu. Tafiya take ido ta A rufe ji take kamar zata yanke jiki ta faɗi har Allah yasa ya sa ta ƙaraso gida, Ammar da yake waje jikin motar sa, gefe ɗaya motar da ta kawo kayan ɗaki ne da kayan abinci da ta riga shi yo gaba a gefe.Tana ƙoƙarin tashi babu wanda ta kula dashi sai kiran sunann ta da taji, muraya da bata taɓa zato sunan ta na da daɗi furta wa ba. “Sumayyah....! ” Da ƙyar ta iya ɗaga Ido ta kalleshi, hannu sa da suke kan ƙirjin sa ya saki tsoro furgici ya cika shi iya jiya da ya Barta bata da maraba da mahaukaciya ciki ransa yace Anya Sumayyah da na bari jiya ce ko kuma wata da ban?”Jin bashi da amasa ya sake ɗagowa ya dube ta ido sune ya sarƙe da na juna wani iri yanayi ya shi ga,ya kasa tantace ainihi abu da yake ji akanta. Taku ya yi kusa da ita. “Wannan duk na maye, Maye wanna ajikin ki,I na kuma kika je yanzu da safiyar nan??”Hawaye ta fara Numfashi ta yana ƙoƙarin ɗaukewa kasa jurewa ya yi ya fusgo ta ta faɗo jikin sa kuka ta fashe dashi, ba tare da tsantsamin ƙazantar da take jikin taba ya sake yi mata masauki akan kirjin sa yana shafa bayan ta alamu rarrashi......... [11/23/2025, 4:27 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-13 Ga nin yadda kuka ta ke ƙara tsananta ne ya sa Ammar lumshe ido, zuciyarsa na kai komo tamkar ana murɗa ta. Wani irin tausayinta ya sake shigar sa, ya ji tamkar ya ɓoye ta a cikin kirjinsa har abada. Sai da ya jira kuka ya lafa kaɗan kafin ya matsar da ita gefe, ya kalli fuskarta a hankali. “Sumayyah… me ya faru? Waye ya miki haka?” Kallon da ta yi masa ba irin kallo bane na yau da Kullu ji take kamar ana daɗa Ƙawata mata fusakar sa Sai dai tasan Ya mata nisan da bata isa tasa a ran ta zai so ta ko ya ƙaunace taba. Da sauri ta kauda kai tana share hawayen da ya ƙi tsayawa. “Ba komai… kawai na gaji ne.” Ammar ya girgiza kai, idosa ya ƙanƙance suka sauya.launi izuwa ja. "Har tsawon yaushe zaki juri yi min karya? Sumayyah...! Ni ban zo nan don ki rikita ni ba ko Na zama silar shiga tsakani ki da dangi kiba. Ki sani duk abinda yake damunki, na san akwai wanda ya haddasa hakan kuma bazan iya shuru Na zuba miki ido ba ki duba jikin ki jiya ba haka Na barki ba.”yana Faɗi ya kafeta da Sihirtatu idanunsa. Shiru ta yi,ta kama kallon ƙasa. Sai bayan wasu sakanni tayi ƙoƙarin raba jikinta daga nashi. “Dan Allah ka barni… Zan je in duba Inna tun kafi Asuba Na fita nasan yanzu Yinwa take ji. Kuma In yaya Yusuf Ko Baba ya ganni da kai a haka Sai ya dake ni ya min faɗa…” Zai yi magana,malam ya yi Sallama daga cikin, idon sa ya ci Farin kwalli, sauya sallon magana ya yi kamar ta tsofaffin waliye."To...to Ammar Ke tafe kuma kaƙi shiga ciki Ke Mai yasa bakya rabo da sakarci”Magana zata yi Ammar ya dakatar da ita.“Ni ne ban shiga ba, kayan nan na Mamar Sumayya ne ina so a naimo wanda zasu saka Na biya su” Gaba ɗaya jikin Malam ya hau tsuma kamar tsoho ɗan tauri.“Haba Akwai tiƙa-tiƙan mata har biyu aciki bara naje sai suyi abiya su, Mudai babu abin da zamu ce dakai sai Godiya”Tamkar kurma haka Ammar ya masa da Sauri Malam ya afka cikin gida. suna tsakar gida anyi baje baje da kayan kari kumalo, ya faɗo tafa hannu ya fara"Tom..tom ki tashi arziƙi ya sake Sallama agidan ku wannan MAHAUKACIYYA aka kawo wa kayan Saiti in kuka saka za'a biya ku da kuɗi mai tsoka”Wanni banzo kallo Suka bishi dashi."Malam yaushe ka fara tausayi ta da sonta har zaka bari asa mata kayan ɗaki muku ma mana zaune ko ledar tsakar ɗaki bani da ita” “Matseeee ke dai Hauwaila har abada baza ki daina shiririta da sakarci ba,yo ko kare hauka ne ya cijeni zan yi asara kuɗi na sai wa wanna Mahaukaciyar kaya ne sai dai in baki iyaye ne ke ɗawainiya dani.”ya faɗa yana zaro ido kamar baƙin kure. Baba Zulai ce ta miƙe.“Ai kuwa ko wanne asarare ne ya siya Wallhi yana tafiya zan fido su, su dawo ɗaki na dan nice uwar gida a ɗaki na ya kamata a saka su.” “Jita da Allah figai-gai dake Zulai tom surukin kine kina yin sake dama zata kwace miki,na dai gaya miki sharɗi kar gi rawar kai wallahi dan babu wani taimako da zan sake miki ki kayi wasa da wanan damar”tin da Malam ya fara suba-ɗaɗar sa Baba Zulai taken kifta masa ido yayi shuru kada Baba Hauwa taji shirin su akan Ammar haka ya miƙe ya fice. Malam na shiga cikin gida ya juya ya dako Baban Vasket ya dawo ya tsaya agaban ta, ya kalla ta.“Ki shiga ki zaunar da Inna.Zan shigo yanzu?”Kai kawai ta ɗaga kamar yarinya ƙarama.Ta shiga gida a hankali.Ammar ya tsaya na tsayi sakanni biyu yana kallon ƙofar, zuciyarsa na bugawa a hankali ya furta. “Wallahi idan wani ya kuma taba min ke… Zan lalata masa rayuwa, zan nuna masa ke mai gata ce”ya furta cikin ɓacin rai. flask ya ɗauka da jaka, ya nufi ƙofar cikin nutsuwa. ACIKIN GIDA Inna Sumayya na zaune cikin ɗaki gefe guda ta takure jikin ta, tun tana kukan yinwa har ta haƙura, Sumayya ta taɓuɗe ƙofar da sauri ta kama hannu ta, ta zaunar da ita tana goge mata fuska da ruwan ɗumi.basu juma da zama ba Ammar ya shigo, ya durƙusa gaban Inna. “Inna, sannu. Na kawo muki abin da za ki ci.”Kallo sa tayi,ta dan saki murmushi. “Naman… kakawo min zaka sai min powder nayi kwalliya?” Ammar ya yi murmushi kaɗan,ya kama hannu ta Ya dubi Sumayya, a tare zuciyar su ta buga wani baƙo al'amari ya ziyarce su da kar ya iya kauda kai. “Ki samo plate ki zuba mata”Ya furta,Sumayya tana ƙoƙarin mikewa Inna ta riƙe mata hannu “Sumayya kar ki tafi Yusuf zai sake duka na” Ido suka haɗa da Ammar da sauri ta kauda kanta dan ta kasa jure kallo da yake mata.cire hannu Inna ya yi daga jikin Sumayya “Babu wanda ya isa ya ƙara cutar da ku.ko ya dake ki, kina da ɗa yanzu zan tsaya miji na kare martaɓar ku Insha Allah” Babu Hauwa da Baba Zulai da Malam da tsuke laɓe gabansu ya buga suka haɗa ido, Idon Baba Zulai ya yi jajir saboda takaici da ɓacin rai, wai za atemaki Rabi da 'yarta. Karo suka kusa yi da Baba da ya tunro kai cikin Ɗaki Baki ya washe.“Sumayya kece dama zuw nayi nace Ku fito za'a share ɗaki za su fara shogo da kayan ga shi fiɗa can kicewa baƙon naki ya fito da ita Innar taki ko” "Tom Baba bara na gaya masa sai na fito da Innar ta...”Ammar ta gano ya kama hannu Inna.ta kasa boye farin ciki da take ciki tabbas ba duka masu kuɗi suka zama masu girman kai ba, Tabbas Ammar ya fita daban.Idon ya zuba mata saboda ta tare Hanyar, Baba zulai kuwa tacika tayi fam kamar ta fashe.Muryar sa suka ji wace yaune jinsu na biyu, dan ko da yazo shiga bai kalli in da suke ba bare yace tatafasa a sauke. "Zaki iya bamu guri?” matsawa tayi tana bin Su da kallo yadda Inna ta saki jiki dashi suna zuwa kan Baban Buhu da aka shin fiɗa masu Baba Hauwa da Baba Zulai suka shiga ɗaki don sharewa duk da Sumayya ta gyara dakin bayan dawowar ta. Tun da suka Zauna Sadiya ta zauna gefe ta kafe su da kallo duk motsi da zai sai sun haɗa ido da Sadiya, gashi da ga ya kalle ta sai yaji kamar wanda ake masa shocking, ya kasa gane wani iri yanayi yake ji a kan yariyar, gashi ido ta ko ƙiftawa ba yayi akan sa. Ji yayi yana so ya mata magana.kamar daga sama suka ji Maganar Ammar."Kema kizo ki zauna kici”Mutuwar tsaye tayi natsayi daƙiƙu biyar cikin zaro ido."Wace wai ni Sadiya?”Kai ya ɗaga mata da sauri ta taso tana karya jiki.Gaban Sumayyah ya wata iri bugawa da karfi tsiya tun da ta zauna ya tura mata Flack ɗin farfesu gaban ta, shi kuma yana bawa Inna abaki.Ta ƙasa yake kallo Sadiya so yake ya gano me yasa shi kallo ta amma ya kasa wani ɓari yana jin haushi kansa a kan janyo ta kusa da su da yayi, amma ya kasa gano dalili da nayi haka. *After 4 hours* Sai da aka gama gyra ɗaki tass sanan Baba Hauwa da Baba Zulai suka fito suna fitowa suka ga Sadiya acikin su, Cak suka tsaya gani Sadiya a gaf da Ammar tana tsoma baki ciki hirar su Baba Zulai ta tsalala guɗa sai da kowa ya kalle ta sai dai banda Ammar da yake ji tsanar Matan Malam fiye da kowa na gidan. "Yaya Zulai lafiya naji kina murna har da tsalala guɗa?”Bari Hauwa baza ki gane ba,taya zan ki murna bayan Yau Rabi zata kawanta a katifa kamar mu Kullum da damuwar baiwar Allah nan nake kwana nake tashi Tom yanzu kuma buri na ya cika taya bazan farin ciki Afili ba.” Tsaki Baba Hauwa tayi“Wallahi Yaya A yanda na sanki bazaki taɓa murna....’?”Hararar da Malam ya doka ma Baba Hauwa ce tasa ta Rufe bakin tare da murnushi da ita kaɗai tasan Ma'anar shi acikin ranta... [11/27/2025, 8:52 AM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-14 Motsi kaɗan Sumayyah na gani Yadda Sadiya take kallo Ammar, zata masa magana Sadiya ta muskuta.“Yayan Sumayya wai wanan naman da mai aka dafa shi ban taɓa cin iri wannan naman mai daɗi haka ba?”Mama ta ce tayi zan sa ta ƙara yi muku....”Bai ƙara sa faɗa ba Sumayyah ta mike ta bar musu guri da kallo Ammar ya bita gaban sa ya faɗi, miƙewa yayi yana ƙoƙarin binta Sadiya ta murmusa ."Nabiyo ka yayan Sumayya?”Hannu ya ɗaga mata almu karta bishi. Jiki amace ya kutsa ta tsakiyar su Baba Zulai ya nufi ɗaki su Sumayyah.Yana gota su Baba Zulai ta taɓe baki."Ji muguwa baƙin hali ya motsa wato bata so kowa ya raɓe ta Aikuwa zata mutu da baƙin cikin mu wallahi”Ban da tagumi babu abinda Baba Hauwa take ita ta zuba ido ne taga iya gudun ruwan Baba Zulai. Tun da Sumayyah ta shiga bata tsaya ta duba iri gyran da aka yi wa ɗaki nasu ba kan gado ta faɗa ta saki kuka mara ƙara, zuciyar ta na zafi, Tabbas ta gama yarda zuciyar ta, ta kamu da son Ammar sai dai dole ta cire shi a rayuwarta dan tasan zare ba kalar yadin bane.ƙamshi turare sa shine ya fara mata sallama dan ita bama taji sallamar tasa ba gefe gado ya zauna."Ki taso zamu yi magana”Ƙin tashi tayi, sau Uku yana Mata magana amma ko gizau, cikim ɓaci rai ya daka mata tsawa.“Ba da ke nake ba,Or will you argue with me?”mikewa tayi ta zauna tana kauda kai,cikin kaukausar murya wace bata taɓa jin yayi ba ya ce."Na zama ɗan isa muna zaune kin barni acan ko, me hakan yake nufi??”Shuru bata ce masa ƙala ba kuma bata jin zata iya furta masa wani abu."Baza ki magana ba ko so kike na bar muku gidan ku?”Nanma bata yi magana ba hakan yasa kan sa ya fara sara masa,miƙewa ya yi. “Zan tafi bazan sake dawowa ba tunda baki son zuwa na...”Gani da gaske tafiyar zai yasa ta buɗe baki kamar wace ƙurji ya mata dashe a maƙoshi."Me yasa zaka daina magana dani kayi da Sadiya sanan ina kallo yadda take ƙare maka kallo kaima....”Kafeta da kallon da yayi ne yasa ta yi ƙasa da ido ta, ta rasa meye cikim ƙwayar ido sa da yake hana ta kallo sa akwai wani Sirri mai girma atattare da shi. Murnushi laɓa ya yi ya dawo ya zauna yadda zata kalle shi da kyau."Nima me..!me kuma nayi?”ɗagowa tayi ido ta fall da kwallah."Kaima kana kallon ta”“Bakya so na kalle ta”Kai ta girgiza masa“Tom me Hakan yake nufi ko kina kishi na?”Kanta ta ɗaga da sauri idon su ya sarke cikin na juna, babu wanda ya iya ɗauke ido sa akan na ɗan uwansa tsayi mintes 5 sanan ya iya janye nasa.“Baki bani Ammasa ba” Yatsun hannu ta,ta fara wasa dasu,ta kasa cewa komai. Hannu ta ya kamo ziciyar su ta buga wani iri Socking ya shige su atare sai da ya tataro nutsuwar sa sanan yace “Sumayyah Zaki aure ni,zan baki kulawa, zan baki farinci fiye da yanda kika samu Abaya,Innar ki zata samu farin ciki, zan ɗauke ta daga wanan gidan, zaki aure Ni?”ido tane ya tsaya na Lokaci guda hawaye ya fara zubowa, Hannu sa ya sa ya fara goge Mata yana jin wani abu na fusgar sa. a hankali yace.“Ki yarda dani Wallahi bazan cutar da ke ba,ki sani ban taɓa sani so ba sai akan ki bansan taya ake gane kana so wata 'ya mace ba, sai da na haɗu dake, ki yarda zan baki kulawar da wata ɗiya mace bata taɓa samu ba”shuru tayi ya saki murmurshi"Zan Sanar da Hajiya ta fadawa Abi azo anema min Aure ki Kema ki sanar da Baba,”Kai ta ɗaga masa ya miƙe har inda Akwati kayan da Yazo mata dashi jiya daniyar ya ɗauke ta da ƙarfi ya ɗauka sai dai yaji saƙal alamu babu komi aciki kallo ta yayi. “Ina kayan ciki?”“A..Uhum....dama su Baba Zulai ne suka ce suna so shine suka ....“ Shout Up Bana so Shirme dama Hajiya su ta bawa Maza jeki kawo Kayan nan yanzu ina jiran ki”Mikewa tayi sai kuma ta fashe da kuka sosai ta tada hankali ta.Shi abin ma dariya yaso ya bashi ɗaure fusaka ya yi kamar ba shiba ya sau-sauta murya.“Baki so a karɓo kayan”Kai ta ɗaga Iska ya fuszar “Muje na siya miki wasu”Daga haka bai sake cewa komi ba ya fice bai samu kowa ba A tsakar gidan sai Inna da bacci ya ɗauke ta. tafi mintes goma ba tare da ta motsa ba har yazu ta kasa gasgata Wai ita Ammar yace yana so ko dai mafarki take motsi tayi sanan ta ɗauki kodaɗe hijab dinta ta fice.Ɗaki Malma taje ta durƙusa abakin ƙofa tayi Sallma,duk da taga akwai mashin A waje yana tare da baƙin sai da tayi Sallama uku sanan Malam ya Amsa. “Baba dama Ammar ne yace muje zai siya min kaya shine nace sai na tambaye ka”daga ciki ya ce.“Amma kin san kina da 'Yan uwa bazai yu-yu yazo ya raba min kan iyali ba in har kin san ke kaɗai zai saiwa Tom gwama tun farko ki haƙura.”Murya na narawa tace."Baba in ma bai sai musu ba ni Sai Na bar musu nawa”dariya Malam ya yi mai sauti daga waje tana juyo sauti dariyar sa"Shikenan kada kiyi dare.“Insha Allah baba” A mota ta sameshi waya yake."Ok Ki shirya Ɗan uwanki ya kusa zama Ango”Daga ɗaya bari akayi magana ɗan Tsaki ya yi.“Oky Salma is better bey” Tana tsaye kallo ya bita dashi“ki shigo ko kina jira mijin ki ya ɗauko ki?”waige ta fara ta turɓune fusaka“Dan Allah kai shuru kar wani yaji mu, a ƙauye mu ba'a iri wanan maganar Saboda za ace mutun ɗan iska ne”fitowa ya yi daga motar ya zagaya inda take ya buɗe mata front seat.“Ammar ba ɗan iska bane amma He could be a little jealous of the woman he married.”ya juya har she ne gudu kar ta kuma cewa wani abu tana shiga ya rufe suka ɗau hanya. *Alhaji Ɗan Dubai* Tun da ya fice yake lisafa ta yanda zai burin sa zai cika ya yima kansa Alƙwari daga Malam har Sumayya da Ammar babu wanda zai tsira, bari ma Sumayyah da tafi ja masa a sarar miliyoyin kuɗi, tafiya yake Aciki motar sa Anaconda white tun da ya hau titi yake waya, yana zuwa zoo round, zai juya ya daki motar da ta shigo, tsaki ya buga ciki gadara iri ta mai arziki ya fito yana narka Sahar, motar da ta bugu tashi yake duka. “wanne ɗan bura.... shege ne wanye Ubanka a ƙasar nan? wallahi ka fito sai naga wanda ya tsaya maka”Tun da ya fara bugu yana zage-zage Hankali Sumayyah ya tashi hawaye ta fara, Atunanin ta ya gane ta so yake ya tafi da ita bata san tinted glass ne a motar ba, Ammar zai buɗe motar ta rike hannu sa."Dan Allah Kar ka buɗe ba kace zaka tsaya min ba ko ka manta wane wanan Alhaji Ɗan Dubai ne kuma nasan zai mai dani guri mutane sa ne”wata iri kasala ce ta kama sa tunda ta riƙe masa hannu, ji yake kamar ya fusgo ta, ya mannata da jikin sa sai dai bazai iya ba yana so ya kare mata mutumci ta. Lumshe ido ya yi ya sauke su akan kyakyawar Black beauty fusakar ta"Sai kin ce kina so na kuma ki min Peck a hannu sai na barki amota naje naji dashi” rutse ido tayi Saboda bala'in kunyar da take ji.“Ina son ka da gangar jiki na baki ɗaya bana fatan ranar da zata zo kaji baka sona na fara sonka tun aranar farko, na shirya farantawa maka zan hidimta maka tamkar baiwa da uban gidan ta”kasa jurewa yayi janyo ta jikinsa ya ƙan ƙameta.ya sakar mata Peck agoshi. Muryarsa ƙasa-ƙasa “Wallahi Sumayya, ban san ya zan fara gaya miki ba… Amma ina cikin wani hali na ƙaunar ki da ke cinye zuciya ta a hankali, Sometimes I feel like I can’t even breathe without you…”Ya ɗaga idanuwansa a hankali kamar me jin bacci,“Kin zama zuciyata, kin zama numfashina. Every day, every moment… kina cikin tunanina a koda yaushe. Wani lokaci sai in tsinci kaina ina murmushi ni kaɗai saboda ke. Na rasa ya akayi 'yar jariryar yariya ta sace zuciya”Ya ja numfashi tare da kama hannunta.“Ki dubeni ki ga ki kallo ƙwayar ido na… zaki ga babu wasa ba acikin su. I’m deeply in love with you.Ki sani ba soyayya ta yara nake miki ba, ba soyayyar wuce-gadi ba. Soyayya ce da ta ratsa jini da ɓargo na.”Ya ɗan kama hannunta, yana jin yadda jikin ta yayi sanyi. “Idan na rasa ki… wallahi I don’t know what will happen to me. Kin zama tamkar hasken da nake gani da shi. You’re my peace… my everything.”zai sake magana bugu motar ya tsanan ta."Wai ɗan gidan Uban wane acikin motar ne da bazai fito ba.” Alhaji Ɗan dubai ya sake faɗa.abinka da abin gulma dan-danan guri ya cika maƙali da ɗan Adam kowa jira yake yaga ishshe da ya hadasa gosulo ba tare da ya fito ya bada hakuri ba. *Ƙauye Giɗaɗo* Yusuf ne ya shigo, ido sa ya sauka kan Food flask har da iri ƙashushuwa da Inna ta zubar wani kwano shan ruwa Yusuf ya yi ball dashi gan goshi Inna ya sauka ciki bacci Inna taji saukar abu akan goshi ta, ihu tasa kafi ta gama miƙewa har ya ɗan fashe sai dai baya fitar da jini sosai. Baba Zulai da Baba Hauwa da kowace tana ɗaki suka fito da gudu Malam da Sallamar ɓaki sa kenan ya ƙarasa shigowa da sauri.Yusuf suka gani zaune kamar ba shi ya aikata ba ya sa flask ɗin agaba yana cin nama, Baba Zulai ta taho zani na neman kwacewa. "Haba Yusufa mai kayi haka Saboda Allah baka so Hankali na ya kwanta sarai na gaya maka ƙudirimu ni da Malam akan yaro nan so kake kaɓata komi da baƙi halin nan naka.”ta faɗi tana ƙarasawa guri da Inna take dafe goshin ta.“Wallahi Babarmu natsani naga matar nan ciki jin daɗi gaba ɗaya hankali na tashi yake, dan tsabar samu guri kalli fa harda kwanciya kan buhu mu” "Ungo nan Yusufa🖐️..Nace karɓi nan🖐️ Wai baka so ƙanwar ka ta shiga gidan daɗi? kasan shiri da mukayi akan Sadiya itama Ana gamawa da ita zamu koma kan Lubna dan haka talauci mun kusa fan-fan fan dashi agidan nan” Tsaki ya yi ya fice yana mita.Malam ya kalli Matan sa."Kukai Mahaukaciyar nan ɗaki karta tara mana maƙota ke kuma Hauwa ki kira Lubabatu taje shago can ta amso magani saɓar da kunburi” ƙwafa Baba Hauwa tayi."Allah ya kyauta Amma wallahi sam Malam baka A dalci agidan nan” [11/27/2025, 10:25 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-15 Dariya Baba Zulai tayi."O iko Allah kedai Hauwa Hasada ce zata kashe ki ke yanzu da arziƙi a gari wasu ba gwara Gari ku ba Kisan in dai Sadiya ta shiga daula Kamar kece kika shiga sanan ke kanki kinsan In dai Sumayya ce ta samu arziƙi nan Babu abin da zaki samu sai tari baƙin ciki da nadama dan tasan Yadda muka azabatar da ita uwarta kawai zata taimakawa bamu ba, gara ace Ya auri Sadiya da ita, wallahi ko tsirara zanyi yawo sai Sadiya ta auri Balarabe yaro nan”murmushi mai cike da takaici Hauwa tayi“Yanzu Allah Yaya Zulai kin dage sai anyi wannan cikumurɗi soyayar mutum ɗaya”taku ta fara. “Sai kiyi Hauwa. So baruwan sa da kyau Hauwa so ne yakan shiga zuciyar sarki ya kanai-kanai ya hana sarki sukuni akan baiwar sa,ki yi addu'a da fatan alkairi wanan shine”Da haka Baba Zulai taja hannu Inna da karfi suka shiga ɗaki. Lumshe ido Ammar ya yi yaja ƙaramin tsaki."Muje ya ganki bana so kimin musu kinji.”Kai ta ɗaga a tare suka fita ido Alhaji Ɗan Dubai ne ya kara yo waje, mutane da suke tsaye suka fara gulma"Kai ai Ammar ne yaro Sheikh Kareem Al-Labban mashuru atajirinan, tab ai dole ya yi jin kai, yaro da yake da dukiyar da ko tataɓa kune sa basu isa su ƙarar da dukiyar ba bare kuma 'ya'yansa”sai da ya gama ƙarewa al'umar guri kallo da iri maganganu da suke faɗa akan sa sanan ya kalli Alhaji Ɗan Dubai ya saki murmurshi da yasa gaban Alhaji Ɗan Dubai faɗuwa.“Kayi Haƙuri matata ce taja”Ya kali Sumayya ya kashe mata ido“Kibawa Alhaji haƙuri kinja muyin masa ɓarnar mota”Alhaji Ɗan Dubai ji yayi kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu saboda baƙi ciki ba zato yaji muryar Sumayya. “Kayi hakuri bai lura da kaiba dan Allah kayi haƙuri kar kayi...“Hannu ta Ammar ya kama"Ya isa ke da nace ki bashi haƙuri sai ki, tsaya yi masa bayani shiga mota zanji da komi” buɗe mata motar ya yi ya shiga ya rufe ya maida hankali sa kan Alhaji Ɗan dubai da sauran dattijai."Kaje Company zan sa Fu'ad ya kawo maka wata motar.”Yana fadi haka ya ciro bandir ɗin dubi dari biyu ya bawa Alhaji Ɗan Dubai."Ka bawa mutanan da suke tsaye.”Bai jira mai zai ce ba ya shige ya barsu a guri”Ƙwafa Alhaji Ɗan Dubai ya yi."Wallahi sai na illata rayiwar ka sai na lalata duk wani naimanka da na mahaifika tunda har ka shiga gona ta, ka kaunce zani a kasuwa”Wani ɗan Shaye-shaye ne ya dafa kafaɗan sa.“Yane zaka bamu hakin mu ko surutu zaka zauna yi?”A tsorace ya miƙa musu sanan ya shiga tasa motar ya nufi Sharaɗa. Basu tsaya ko ina ba sai Ado Bayaro mall, ɓagare dogaye riguna suka nufa siyaya yayi komi uku kowane da ledar sa da ban bata iya ce masa komi ba sai guri da take bi da kallo.wani shashe na zuciyar ta yace."Waisu masu kuɗi komi nasu da ban yake ne ji wani mota da na wuce abaya yara na wasa babu mai hana su...“Madan wanan kayan ya miki na sai miki?”Ammar ya tambayeta ciki wani iri kallo mai tsayar da zuciya."Ni ban taɓa saka riga da wando ba kuma...“Zaki fara daga yau zan siya miki zan kai ki gidan Hajiya sai ki wanka kisa acan kafi mu koma gida nafiso na fara gani ki dasu kafin kowa.”Bata iya ce masa komi ba haka ya jido kaya kamar bai san ciwo kuɗi ba sanan suka nufi Nasarawa. Mintes 30 mai kyau su isa katafare gidan da babu kamarsa a cikin G.R.A ɗin mai gadi ne ya buɗe musu Gate. Sai da ya yi ta fiya mai zurfi ya yi isa parking space, ya fito da iya kayan da zata sa. bata iya buɗe motar ba sai da yazo ya buɗe mata.yau ji tayi tana jin kunyar Hajiya.Sai da suka fara taku ya kalle ta."Yau ranar farko hajiya zata ga surukar ta nasan wanan ranar tafi mata rana dubu.”Tsayawa tayi ya kalle ta cikin mamaki.“What happened? Kika tsaya” Murza ƙaramin yatsan ta ta fara"Kabari maganar tayi ƙwari mana sai ka sanar da ita.”Taku biyu ya ƙara zuwa inda take ya kama hannu ta."Ki sa Aranki gobe ma ana iya ɗaura mana aure Hajiya buri ta kullum taga nayi aure atunaninki yanzu bazata amince ba ko bakya Sona?”Ya bita da wani fitinan nan kallo."Har abada bazan ƙi kaba”murmushi yayi ya manna mata peck a bayan hannu, suka ci gaba da tafiya da Sallama suka shiga ƙayatace parlour.babu kowa, guri zama ya nuna mata. Shi kuma ya taka zuwa ma dai-dai cin Fridge ya buɗe ya dauko bottle water ya ajiye kan Centar teble da ƙarami Cup Na sulba"Kisha bari na kira Hajiya”Kai ta ɗaga masa taku yake mai cike da izza da jarumta bayan sa take bi da kallo wani sanyi na ratsa duk wani san-sa na jikin ta, tana ji farin ciki da bata taɓa jiba atare dashi. Handles ya murɗa tare da sallma Umarnin shiga ta bashi tana kan prayer rug da alama lafila tayi, gefe bed ya zauna tayi addu'a suka shafa tare."Ammaru har ka dawo ko babu nisa unguwar tasu?”Kasa ya dawo kan Carpet."Hajiya Surukar ki na kawo muki ta gaida ki.”Murmushi tayi"Ammar banso zolaya Ni ba kakar ka bace dan kaga abin da nake so gani a rayuwata shine kake so ka shiga zolaya ta dashi ko.” “Ummu By God, I won't do it to you, I won't even tell you the woman I'm going to marry, otherwise I won't do it to you.”Murmushi tayi iri nasu na manya tashiga linke prayer rug ta maida saman Badeside drower, “Muje na gani ina wasa kake min Ammar sai na cire kunne ka”Dariya yayi yana sosa kune da Hajiya ta kama. hannu su rike da na juna suka fita parlour. Sumayyah na hanngo su ta zube kan Carpet bisu take da kallo aranta tace."Dama nima Inna ta tawarke muyi rayuwar farin ciki tare duk da nasan badamu samu daula iri tasu ba ko hira da ita ne zairage damuwa...” “Wa nake gani kamar 'Yata Sumayya?”Ƙasa tayi da kanta“Hajiya nice Ina Wuni?”Haba Sumayyah sauri kike ne haka?”Kafin Sumayya ta bawa Hajiya Amsa Ammar ya amshe zance."Hajiya Gulma ne iri nata wai dan nace zan gabatar da ita shine ga tun awaje takeso mu juya wai kunyar ki take ji”Dariya tayi.“Ai da kabar ta ni sai naje har gidakasan 'yata ba iri ka nace.”Ummu kenan har ki fara ware Ni tun yanzu?”Ya faɗa yana kafe Sumayyah da kallo itam dagowa tayi tana mamaki yadda baya jin kunyar mahaifiyar sa.ido su ya sarƙe da na juna kowane yana zubawa ido kowa wani siri.Hajiya ce ta lura da haka ta bugi ka faɗan Ammar."Zaka bata abincin ko sai ka gama ta kura ta.”Narkewa Yayi jikin Hajiya"Ummu me kika mana yau?”dambu shikafa sai Chips salad da kunu kankama?”Miƙewa yayi ya kama hannu Sumayyah Hajiya ta cilla masa kallo da yasan ma'anar sa, Da sauri ya saki nata hannu cikin borin kunya.“A....uhu.. Hajiya dafa taya ni zata Saboda Allah taya namiji zai iya aiki mata”harara tayi masa “lokaci da kake Shiga kitchen ka dafa abin da kake so na sani sai yanzu” Shuru ya yi ya shike kitchen, Warmer mai kayu ya samu ya zuba gasansu Naman kaji ya zuba ya rufe, yaje ƙato Fridge da yake shaƙe da kayan ciye-ciye dangi drink ya kwaso bottle water guda biyu sai dogo Cup wanda yake ɗauke da daɗe lomo Kwankana sai ƙamshi Citta yake ga wata muguwar raɓa ya fito, yana 'yar waƙa, gaban Sumayyah ya ajiye ya sake juyawa babu wanda ya tanka masa hakan ne yasa shi komowa yana ƙoƙari zama Hajiya ta dubeshi."Ammar me kake ne haka babu Dambu babu Chips sai nama da Lemo ka ajiye?” Tamakar yaro ƙarami me shiri kuka ya kalleta."Hajiya babu wanda yace sannu da aiki kuma kuna kallo na sha wuya”Kauna iri ta ɗa da mahaifi yasa ta mitso inda yake tsaye“Haka iyaye suke shan fama saboda ku da iyaye ku, nasan baza ka iya ba zauna naje na haɗa muku”Murmushi ya mata."Ummu kawai ke da ita kuce min sannu zan karasa lada na”Kafin Hajiya tayi magana Sumayyah tace."Sannu Yaya Ammar ka huta mana”dariya Hajiya tayi tana girgiza kai.Shikam Gogan naka da sauri ya miƙe “Yawa dama haka nake so ji.”Bai jima ba ya fito, tsakiya ya dire ya dauko Pillow guda uku na kujeru."Hajiya ga naki kema ga naki”Ya faɗa yana nuna musu inda zasu zauna, babu musu kowa ya zauna, Bayan su fara cin Abinci Ammar ya kalli Hajiya.“Hajiya Ki danar da Abi Yaro ki ya girma 2 Week nake so asa dan Allah Hajiya kisa suje gobe su neman aure kinji” "Wallahi Ammar baka da kunya mu ba haka muka yiwa namu Iyaye ba, wai ina rashi maganar ka ya tafi ne yau kan bai fara ciwo ba.”Shuru yayi ya fara sosa kansa, daga haka bai sake magana ba, Sumayya kam Tamkar ruwa ya cinye ta haka tayi shuru sai juya Shoop take da hannu.badan ta koshi ba ta cire hannu, bata taɓa jin dambu mai daɗi wanna ba su gidan su na gero ake babu zogale sai rama, babu mai arziƙi sai dai ka haɗa da ruwa a haka ma yana shaƙe ka. Bayan su kammala Sumayya ce ta wuce kitchen ta wanke kwanikan kafi ta fito Ammar baya parlour kuma baza ta iya tambayar Hajiya ba. “Sumayya Ammaru yace ga kayan naki kije ɗaki ki na sama ki sanka sai kisa zai fito ya maida ki gida”Godiya tayi sanna ta haura samma ɗaki yana nan kamar akwai mai kwana aciki a gyra komi, Bratheroom ta shiga ta wanke jiki ta tas taji daɗi wanka, rabonta da wanka tun anan gidan. Fatar ta ta sake kyau duk da ba fara bace amma baƙi ta yafi na wasu fafare mata ɗaukar hankali abinda da kyakyawan mace ga hanci ga ido ga tsayeye baki.Ta jima tana mulkawa jikin ta Cram masu tsada da sa laushi skin sanan ta gayar tuzaze gashita da yake da tsoho kitso sai a yau taji tana son gura Kanta kitso da yafi wata biyu babu gyara. Kayan tasa Pink colour n da ratsin white a jiki wando ne falazo da riga iya gwiwa sun mata kyau, Jaysey Veil shima white yane kanta tayi kamar tasan yadda ake yafa shi, da sabo plate din takalmin tayi kyau taku ta fara har ta sauka ƙasa, tana ƙoƙarin zama Ammar ya shigo Three quarter wando na jeans yasa sai t-shirt light Blue colour ta kama ƙirji sa ta fitar da ainihi surar sa Sandal din takalmin yasa kalar rigar yana ganita ya karaso da sauri. “Wait wace ke me kika zo yi gidan?”Kallo sa tayi taga babu alamu dariya ko alamu ya santa muryar ta na rawa tace."Yaya Ammar nice fa Sumayyah.”Tsaki ya saki ƙaramin.“Wace Kuma Sumayya Ni ban sanki ba wane ya baki izini zuwa gidan mu”dan danan hawaye ya fara kawowa fusakar ziyara badai ya kawo gidan sune dan ya wulakanta taba..... [12/2/2025, 12:18 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-16 Tana kokarin juya baya domin barin falon taji ya riko hannun ta gam.Dariya Ammar ya fashe da ita har da dafe ciki, yana kallon yadda jikinta ke rawa. "Haba My Sumayya, wasa nake miki fa. Yanzu ke har kin yarda zan iya manta kyakkyawar surar ki saboda kin canza kaya? Ai ko cikin duhu na ganki zan gane ki bare yanzu da kika zama tamkar Hurul-a'in.Tsayawa tayi Cak batare da ta juyo ta kalle shi ba, da sauri ya koma inda take ido sa ya sarke cikin nata,wanda suka rine saboda kukan da ya taso mata."Wasa?" ta furta a hankali muryar ta na rawa. "Wasa nake miki mana. Kin yi kyau dayawa Sumayya, wallahi har na kasa gaskata cewa kece a gabana. Kin ga yadda kayan nan suka karbe ki kuwa? Kamar a jikin ki aka dinka su." Ya faɗa yana mata wani irin kallo mai narkar da zuciya yana zagaye ta.Hajiya dake tsaye abakin kofa tana kallon ikon Allah ta saki murmushi. "Kyale shi Sumayya, halin Ammar sai shi. Banda Ni da Abi banga wace yakewa iri wanan wasan ba,ka sani in ka tsokano tsuliyar dodo tace ta fasa maga Yadda zakai.”Juyawa tayi ta kalli Sumayya “Masha Allah, tabarakallah, gaskiya kin yi kyau sosai 'yata. Allah ya yi muku albarka."Sunkuyar da kai ta cike da kunya,“Nagode Hajiya."Agogon hannun shi ya kallah."Hajiya bari mu tafi kar dare ya yi, kinsan gidan su akwai 'yan sa ido."Sai da ta ɗan sansauta fara fusakar ta ce.“Ammar Iyali tane kuma surukinsu zaka zama kar kayi ɓatanci a kan su.kuje Allah ya tsara ka tuƙa motar a hankali, Sumayya ki gaida min da mahaifiyar taki kin ji? Idan mun zo neman auren zan shigo har ciki mu gaisa." Wani iri sanyi taji a ranta. Ita da ake kira 'yar mahaukaciyya, yau gata a gidan da ko a mafarki bata taba tunanin shiga ba, ana girmama ta. "Zata ji Hajiya, nagode sosai."Sallama tayi mata ta fita ta basu guri peck ya yiwa Hajiya a goshi sanan yabi Sumayya. A jikin motar ya sameta, ya bude mata mota ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver. Motar ta danyi kara kadan sannan ta silale ta bar harabar gidan.Suna tafiya a mota, kamshin turaren da ya fesa mata da sanyin AC ya sa ta lumshe ido. Ammar ya kalle ta ta gefe ido. "Hope dai baki yi fushi da ni ba ko?" Girgiza kai tayi, "A'a Yaya Ammar, kawai na zata dagaske baka gane ni bane." Murmushi ya yi, ya sa hannu ya dauko wata leda mai kyau a gidan baya ya mika mata. "Karbi wannan, waya ce a ciki da ɗan kudin kashewa. Bana so kina wahala kafin na aure ki. Kuma maganar da na gaya wa Hajiya da gaske nake, nan da sati biyu nake so a daura mana aure, so ki shirya." Gabanta ne ya fadi, ba don tsoro ba sai don fargabar su Inna da Baba Zulai.Taya zata bar Innar ta a gaban su Baba Zulai ahaka ma bata tsira ba bare babu kowa nata.Muryata na rawa ta ce"Yaya Ammar, Inna fa?"Murmushi yayi wanda haƙorar da suka ɗan bayyana kaɗan"Ki bar komi a hannu na. Ni zan san yadda zan yi Inna. Ke dai kawai ki kula min da kanki."Suna shiga Giɗaɗo,Kallo ya koma kansu. Motar Ammar mai tsada da kyalli ta ja hankalin Almajirai Malam har da dattawa da suke taya Malam zama suna zaune akan karoni wasu kuma kan buzu wasu kuma kan ice ana hira.Bai tsaya Saitar inda suke ba, sai da ya je Ya tsaya dai-dai kofar gidan, ya fito ya zagaya ya bude mata kofa. Tana fitowa, guri ya ɗau shiru ido ne kawai yake binsu. Wasu na zaton wata bakuwa ce aka kawo, sai da ta juya ta kalli Ammar tana murmushi.Nagode Yaya Ammar. Allah ya kai kai gida lafiya." "Amin Gimbiya ta. gobe zan turo Driver ya kawo kayan lefe da sauran su abubuwa. I love you."ido ta zaro.“Kai yaya Ammar mune zamu aure da kanmu babu,magabata?”Dariya Yayi."No wasa nake, but kar ki sanar zamu zo naiman aure ki kawai Abi da wasu nashi zasu zo, wanan kayan ki bawa 'yan uwanki”Amsa tayi Kafin ta bashi amsa,Baba Zulai ta fito daga gida tana gyra ɗauri zani, tana masifa. "Wace shegiyar ce take mana horn a kofar gida haka kamar tsohuwar kila..." Maganar ta ta makale a makogwaro lokacin da idonta ya sauka kan Sumayya, da yadda taga canji ta lokaci guda. baba Zulai ta waro ido, ta kalli motar, ta kalli Ammar, sannan ta kalli Sumayya daga sama har kasa. "Sumayya? Kece ko kuwa idona ne yake min gizo?"Sumayya ta gyara tsayuwar ta, wani kwarin gwiwa ya zo mata wanda bata taba ji ba. "Nice Baba. Yaya Ammar ne Sila gashi wanan na Sadiya da Lubna."Baba Hauwa ce itama ta zuro kai tana leƙowa kofar gida, tana ganin Ammar ta saki baki. "Ikon Allah!Nidai naga ta yadda buri Yaya zulai zai cika? Lallai Yaya Zulai ta kade har ganyen ta." Ammar bai ko kalli inda suke ba, ya shige motar sa ya ja ya bar su da kura da kuma bin motar da kallo.Taski Baba Hauwa tayi"Yaya gaskiya surukin nan naki ba ƙaramin kallo bane.”harara take mata tana yafitar ta da hannu tayi shuru.Gajiya Sumayya tayi da tsaiwa ta ɗauki ledar ta, ta shige gida tana taku ɗai-ɗai, ta bar Baba Zulai da Baba Hauwa baki bude, zuciyoyin su na tafasa kamar zasu kone kurmus. Baba Zulai ta bi bayan ta da gudu, "Ke Sumayya! Zo nan! Daga ina kike? Wa ya baki wadannan kayan na alfarma? Kar dai kin fara bi..." Sumayya ta juyo, fuskarta dauke da murmushin da ya kara tunzura Baba. "Baba lokaci ya yi da zaku daina wahalar da ni. Yaya Ammar aure na zai yi, kuma ba mai hana wa da yardar Allah.In ma kuna tunani wani abu Tom wallahi tun wuri ku daina.”Ta shige dakin mahaifiyarta ta bar Baba tsaye tana salati tana tafa hannu. "Lallai yarinyar nan ta raina mu! Hauwa! Hauwa! Zo kiga tashin hankali ido buɗe zai afkawa gidanmu..."ke dai Yaya aini bani ba shiga tashi hankali daga Ni har yara na Wallahi leda malam sai ku sake sabo shiri” Tana faɗi haka ta juya nata ɗaki dan gani take in ta zauna ɓata lokaci zasu aguri.Sumayya na shiga ta iske Inna duk ta fita hayyacinta.har da fitsarinta da ta makaka akan sabuwar ledar tsakar ɗaki gashi goshinta a kumbura saboda jifan da Yusuf yamata. Gaba ɗaya farin cikin da ta shigo dashi ya mutu warwas, ya koma baƙin ciki da takaici marar misaltuwa. Hawaye ne masu zafi suka zubo mata, tana jin yadda zuciyarta ke mata zafi saboda cin zarafi da gallazawa. Ya zata bar Innar ta a hannun mutanen nan? Wannan zafin ne ya ƙara ƙarfafa mata gwiwa kan cewa shawarar Ammar ita ce mafita, kuma dole ne ta riƙe shi da hannu biyu.Da sauri ta shafe hawayenta, ta fara aiki. Ta ɗauki Inna a hankali ta zaunar da ita gefe, tana ta maimaita mata “Sannu Inna ta, sannu.” Daga nan ta yayafa ruwa, ta fara share ledar tsakar ɗaki. Ta wanke tabarmar da omo har sai da ta tabbatar ba wari. Bayan ta gama tsabtace ɗakin, ta dawo kan Inna. A hankali ta cire mata datti da fitsarin da ya ɓata mata jiki. Ta ɗaura mata sabon zani mai tsabta. Ta duba kumburin goshinta, ta shafa mata man shafawa mai sanyi don rage radadi.Bayan ta kammala komai, ta gyara Inna a kan sabun gado da Ammar yaKawo musu. ta zaunar da ita gefen ta rungume ta. Sai yanzu ta tuna da wayar da Ammar ya bata jiki a sanyaye ta bude ledar wayar, ta ciro wayar kirar iPhone mai kyau da kyalli. Tana riƙe da wayar, sai taji kamar tana wata duniyar daban."Sati biyu?" ta furta a zuci. "Aure nan da sati biyu? Ammar ya ce shi zai san yadda zai yi da su." Tunanin Hajiya da kalaman ta sun sake dawo mata, sun tabbatar mata da cewa wannan gida ne na mutunci, kuma Allah ya fitar da ita daga wahala. "Godiya ta tabbata ga Allah."Wata murya mai zafi ta katse tunaninta. Baba Zulai ce ta dawo har bakin ƙofa, fuskar ta kamar wanda aka daka mata barkono. "Ke! Tunda kika dawo dan iskanci kin ki zuwa ki faɗa mana inda kikaje da gardi ƙato?kizo ki mana bayani dan Malam bai shirya ammsar abin kunyaba.tin da yaro nan yanzo gare ki shikenan ki ɗorawa kanki girman kank tsiya? Wallahi Tallahi, wannan aure da kika ƙulafincimn kina tunani zai aure ki,Tom ki sani mudun Zulai Baba kandala na raye ba zai taɓa yiwuwa ba! Sai na rufuzashi kuma na faɗawa duniya Mahaukaciyar Uwar taki, zan gaya musu ke ƴar mahaukaciyya ce, dan kada su aurea a haifa musu mahaukata!" ta faɗa tana huci da nuna ta da yatsa.Sumayya ta miƙe tsaye, tsayin ta ya kusan kai na Baba. Ta kalle ta cikin idanuwa, ba tare da tsoro ko fargaba ba. A yanzu ba Sumayyar jiya bace. “Baba, ku daina. Kun riga kun cutar da ni fiye da yadda zan iya jurewa. Duk abin da kuke so ku faɗa, ku faɗa. Ammar ya san komai. Kuma insha Allahu zan bar wannan gida nan da sati biyu. Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya zalunce ni a nan! Ko mahaifiya ta”Ta fada cikin kwarin gwiwa wanda ya firgita Baba Zulai.Baba Zulai ta kifa hannu a baki, tana salati, haushi da kishi sun cika mata zuciya. Ta kasa magana, sai numfashi take sama-sama. “Yarinya ta raina ni! Wannan yarinya ta raina ni! Hauwa! Hauwa! Zo ki gani! Zo ki gani!” ta juya tana kiran Baba Hauwa da niyyar ta hada kai suyi wata shawarar ta wulakanta Sumayyah.Bata yi aune ba taji muryar Baba Hauwa ta dawo mata da martani. “Yaya aini bani ba shiga tashi hankali daga Ni har yara na Wallahi zunubi da muka kwasa na baya na ya ishe ni.”tana faɗi haka ta maida kanta cikin ɗaki ta ta gyara zaman labile ta,.Duk abin da suke cewa Sumayya bata ce Inda ba sai da taga Baba Zulai ta matsa zuge musu labule duk da ƙurjinta yana bugawa tasan yau sai ta sha duka guri Yaya Yusufa.Tana zama ta kalli mahaifiyar ta dake kwance cikin kwanciyar hankali. Ta rungume wayar hannunta sosai. Mafarkinta na cikawa. Nan take ta kunna wayar, hasken allon ya haskaka fuskarta. Bata san ya ake nemo lamba ba bare ma tasan da layi aciki ko ababu zubawa wayar ido tayi, tana dai gani waya a hannu su sadiya amma ki da wasa bata taɓa karanbani cewa su bata ta ɗana ba.Bata juma ba kira ya ya shigo ruɗewa ce tasa ta danne wayar gudu karwani yaji, bata san kashe wayar tayi ba baki ɗaya..... [12/6/2025, 2:13 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-17 Haki ta fara saukewa a hankali gani wayar ta daina ruri, ta runtse idonta, tana jin dadin kwanciya tayi a gefen Innar ta, yanzu tana da kariya. *Alhaji Ɗan Dubai* Duk wani shirin ya gama tana dinshi,akan Ammar da Kuma Gidan Malam Sule Gidaɗo.zaune yake kan doguwar kujera Matar da na Gefa dariya tayi mai Sauri."Wayo Alhaji in dai ana son gani fara'ar ka tom tambaya wani tungu zaka shuka babu abin da ya shige maka gaba a yanzu face Yariyar ƙauye can.”wayar da ya tatara hankali sa akai ya ajiye saman Senter table.“Kedai ki jira lokaci da bomm ɗinnan zai fashe”yana fada yana shafa tulun ciki sa. Shirye-Shiryen ya kama agidan su Ammar Tun bayan komawar sa gida. Tun bayan kwamciyar Sumayya ta shiga cikin wani yanayi na nutsuwa mai ban mamaki, duk da cewa kwanaki biyu kacal suka rage a zo neman auren ta. Sai dai bata san Yaya Baba da su Baba zasu karɓi al'amari ba, Baba Zulai ta zama kamar sabuwar magaukaciya tun da taji furcin Sumayya na karshe.“Baba lokacin yayi da zaku daina wahalar dani.Ammar aure na zaiyi, kuma ba mai hanawa da yatsar Allah”Hanalin tane ya sake tashi tuna wanan maganar ta Sumayyah kasa zama tayi ta shiga nanm ta fita nan gashi Hauwa Hassada da baƙi cikin sun rufe mata ido, hararar Haɗi Ba Hauwa take ta doka uwar ƙwafa, tana jin haushin yadda Baba Hauwa da ƴaƴanta suka daina shiga harkarta gaba ɗaya sunƙi haɗuwa su mara musu baya,A fili ta furta."Zaku gane baku da wayo duk ranar da Ammar ya shigar hannun mu”tsaki tayi ta faɗa daki ta tana kiran Sadiya da take ɗaki tana shege bacci nan nata mai nauyi tsiya. *Bayan kwana biyu* Ammar ya cika alƙawari. Ya tura Abi da manyan Aminai sa guda uku.Tun kafi su zo sai da ammar ya bada Odar ta lemo kuma da ruwa da gasasu nama kaji da da lafiyaye abici ya turo aka kaiwa Sumayya Su Baba Zulai da su Malam zuba ido kawai suke suna kallo iko Allah da yadda za'ayi da Kayan.Ita kanta Sumayya tana mamakin yadda Ammar ya tsara komai. Tana ta kula da Innar ta, tana shafa mata magani, har wanka ta mata ta canja mata kaya gudu kar su ce zasu shigo cikin gidan tunda su 'yan birni ne ba iri su ba. Yau da yammacin ranar Alhamis, wajen ƙarfe huɗu (4:00 PM) na rana, motar alfarma ta shigowa layin.Bata tsaya ko ina ba sai ƙofar gidan Malam Sule Gidaɗo,mota ce kirar Lexus LX 570, wadda Ammar ke Driving. Tun da suka fito yara suka cika guri cacum wai ga larabawa.Mata na zuro kai ta jiki katanga wasu ta jikin zanar kara,suna mamakin me ke faruwa. Da ciki kuwa suna jin Hayaniya mutane,Baba Zulai ce ta fara lekawa ta wata 'yar ƙofa Ganin Abi da tawagar sa cikin manyan shiga ko da bata tambaya ba tasan wancan mahaifi Suriki ta ne wato Ammar miji Sadiyar ta dan Malam ya riga ya mata rubutu jiki mudubi ya sanar da ita Mutuwa ce zata raba wanan aure.Malam ne da yake Zauren ya sauri fita ya zube gwiwa har ƙasa ya haifa Abi da sauran Mutane da yazo su ciki girmana abi ya muƙa masa hannu.“Haba dan Allah tashi don Allah ”tare suka rankaya zuwa ciki ɗaki Sallmar baƙi Malam,lafewa Baba Hauwa tayi jikin ƙofar dan ji mai zasu tautauna. A zuciyar ta tace “Wannan fa ba mutum ne kawai ba! Wannan babba ne! Wannan ne yazo neman auren ɗiya ta lalai Sadiya tana da Goshi.?Bayan sun gaisa, Abi ya fara magana da Malam, cikin harshe mai gaskiya da kwarjini, da dattako."Malam," Abi ya faɗa, "Mun zo ne don neman auren ƴar ku, Sumayya,Yaro na Ammar ya ganta yana so sanan san Allah in har kun amince wannan auren bama so a sashi dogon lokaci. Muna neman ayi auren nan da sati biyu kamar yadda muka tsara. Duk abin da ya kamata ku sani game da ɗana, zaku iya zuwa kuyi bincike akaina da kuma shi. Kuma duk wani sharaɗi da ya kamata ayi, mu a shirye muke mu cika shi." Duru-duru Malam yayi ga ƙoshi ga kwanan yinwa, ya kasa buɗe baki ya yi magana dan tun zamansu Ya ankare da tsaiwar Baba Zulai a guri,wadda take tsaye tana ta yi masa alamar 'Kada ka yarda!' da idanuwan ta.hakan yasa jikin sa ya fara fitar da zufa kamar Wanda ake sheƙawa ruwa. Jin Malam ya yi shuru Alhaji Shu'aibu mai Nasara Amini Abi ya taba Malam"Malam, ba mu zo nan don bata lokaci ba.I dan Har akwai wata matsala kwa iya sanar damu?Iam kuma kuna tunani wanda zai kula da mahaifiyar ta ne? bayan an daura aure, Ammar zai sa a maida ta zuwa wani gida mai zaman kansa (flat) da Ammar ya gyara mata, inda za a ba ta kulawa ta musamman da ma'aikatan lafiya.kuma babu nisa da inda Yariyar zata zauna zata riƙa duba ta a duk lokacin da take bukata." Gumi Malam ya sharce da baki malin-malin ɗinsa magana ta yi masa nauyi. Ba zai iya cewa A'a ga wannan babban mutumin ba.kuma bazai iya cewa ya Sadiya ayi musaya ba, kar yazo yayi biyu babu.Baki ya buɗe zai yi magana...Baba Zulai ta kasa jurewa. Ta danna kai cikin ɗaki fuskarta kamar babu Alamu wasa. "Amma Malam! Ya mukayi da kai ashe duk maganar ka ƙaryace kace min aure akan sadiya za'ayi yanzu kuma naji suna zance Sumayyah, Tom wallahi Wannan auren ba zai taɓa yiwuwa ba! Wannan yarinya ƴar mahaukaciyya ce! Mahaifiyar ta tana da ciwon hauka, a haka ku zaku kwasa kuna so ku samu iri na hauka!"ta zube gaban Abi, harda hawaye shaɓe-shaɓe."Alhaji Ɗan Allah kuyi mana rai nida Sadiya Wallahi mune muke sonku ku sani Sumayyah bata da wasu dangi duk sun ƙone ƙurmis, bata da wani asali.”tanayi rana face majina da bakin zani ta,Abi ya kalleta cike da mamaki da girmamawa yaga tsagwaro rashi ɗa'a a guri Baba Zulai. "Malama," Abi ya faɗa da kakkausar murya. "Mun san komai. Kuma mun yanke shawara tun da jimawa. A Musulunci, wannan ba wani abu bane da zai hana aure. Muna da ƙwararrun likitoci da za su kula da Mahaifiyar yariyar. kuma mun san yadda ake cutar da ita a cikin wannan gida. Yanzu, Malam, muna buƙatar amsar ka. Auren zai yiwu a cikin sati biyu ko a'a?"Malam ya buɗe baki,bakin sa na rawa. "A'a," Malam ya furta da rawar murya. "Na yarda. Auren zai yiwu. Allah ya ba da sa'a." ajiyar zuciya suka sauke Baba Zulai kuma ta ɗora hannu zata ƙwalla ihu yayi karfi halin ɗaga mata ya tsa. [12/16/2025, 7:18 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-18 “Zulai ke Zulai?kar ki kuskura ki mana hauka aguri nan maza ki ɓace daga guri karna taso”Mutuwar tsaye Baba Zulai tayi yau ita Malam ke ɗagawa murya agaban bare lalai yau akwaia tsalle a gidan sai ta hana kowa bacci matuƙaumr bazai cika mata buri taɓa.Ciki fushi ta kada zani ta tayi cikin gida batare da ta damu da manyan mutane da suka bita da kallo ba. Sai da suka yi goma ta arziki sanan suka fita da kayan da ammar ya siya aboye yace abasu in sun zo. Har waje malam da wasu makotan sa suka raka su, bai san har da Ammar ɗin ma aciki ba abinka da motar manya bazaka gane na ciki ba. Bayan tafiyar su Abi, Malam ya koma cikin gida bakin sa har kunne, da Baba Zulai ya fara karo ta riƙe ƙugu kamar me shiri shiga gasar dambe.kamar bai san abin da ya faru ba duk da ƙirji sa na dakan sakwara haka ya yi ta maza ta nemi kujera yar tsuguno ya dasa mazaune da,yana zama ta tsaya masa sanan kansa.“Ka yarda! Ka sayar da yarinyar nan! Ka kashe ni! Ina duban da kamin cewa Sadiya ce matar shi ba Sumayyah ba!She Malintar taka ta karya ce, Tom wallahi yadda ka muzan tani agaban Mutane sai na muzan taka agaban duban baƙi da suke zuwa guri ka sai na nuna musu cewa ƙarya malinta kake sai...." Sadiya da shigowar ta yanzu taji ke ake cewa ta ruga cikin ɗaki da gudu tana kuka kamar me aljanu, ba za ta iya jurewa ace Sumayya ce zata auri wanan ktakyawa kuma ɗan masu kuɗi ba tariga ta gama gayawa ƙawaye ta na ƙauye Giɗaɗo itace budurwa da yanzu kuma ace Sumayya ce zata zama matar ɗan wani attajiri wanan ma hauka ne.kuka take kamar zata shiɗe.Baba Hauwa da Lubna kuwa dariya suke cikin ransu dan gani suke reshe yana neman juyewa da mujiya,ga ƙoshi ga kwanan yinwa. Sumayyah wace tun shigowar Baba Zulai da iri ruwan ashar ɗin da take makawa yasa ta fitowa bai sa ta gane akan me Baba Zulai take ruwan bala'i ba sai da Malam ya shigo ta gane inda zance ya dosa,tana jin duk abin da ya faru.ƙokarin komawa take Baba Zulai ta zube ƙasa warwars Al'amurra sun gama tabbatarwa Suma tay, Malam ne ya fara tsaiwa kanta cikin ruɗewa yake kiran sunan ta.“Bango gidan Dan Allah ki tashi kada kice zaki min haka nayi Miki alkwari duk mai yuyuwa babu wanda Sadiya zata aura in ba Ammar ba”Cewar Malma su jikin sa ya jiƙe sharkaf da gumi cikin zaro manyan ido sa ya waigo.“Wai ku mahaukatan inane kuna kallo bango Gabas tana shinfiɗe amma baza ku kawo ruwa ba”Ciki. Fushi Baba Hauwa tace. "Allah yasa bango kudu da arewa ce baki ɗaya ai in dai ka hau motar kwaɗayi wallahi zaka kwana da takaici duniya banda kaddara da ɗorawa kai masifa ace ki liƙe kice sai yarki ta auri mutum bafa komai ne asiri keyi ba, in kuma tace zata tilasta tazo ayi bayan ranta”Ran Malam ne ya sake ɓaci ya wawuri takalmin ya jefa Mata ta kauce ta juya ɗaukwali.“A Banza wallahi.” Malam ya juya yana kiran Sunan Baba Zulai.“Dan Allah kar ki mutum kibar Ni Wallahi zan hana aure nan ko da kuwa nawa aiki yaƙi yi zan baza malaman buzu da na gudu ko uba har sai munga haƙan mu ya cinma ruwa."Tunda Baba Zulai taji haka ta saki murmushi a zuciyar ta,ba tare da sun san suman ƙarya tayi ba, Sumayya na miƙawa Malam ruwan ya fara yayafa mata miƙewa tayi kalau da ita, kamar ba ita ba Malam na ƙokari kama hannun ta ta fusge "Kar ka taɓa Ni matuƙar baka cika min burina ba." *Ayi hakuri kwana dayawa ba ajini ba Kusan yanayi rayiwa Allah yasa mu dace. Sanan babu Editing* [12/21/2025, 11:49 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-19 Haka Ta shige jiki babu kari ta fada daki Malam fita yayi dan akira sa ya yi baki.Zama Sumayya yayi ta zuba uban tagumi tarasa me yasa Matan Baban ta dama Mahaifinta basa kaunar su ita da Innar ta, bayan kamar Sa'a daya kira ya sake shigowa jikin ta na rawa ta danna rashi sa'a tayi ba guri ɗagawa ta danna ba kiran ne ya sake shigowa canjawa tayi sai kuw murayr Ammar ta kauraye guri duk da ba Has free yasa ba. “Madan kin barni cikin zulumi da tunaninta Ina kika shiga ne Ammar ya?”Muryarta na rawa ta amsa."Ah..Dama. basan guri da zan danna nayi magana ba yanzu ma da kar nagano guri ....”Dariya da ya Ƙyal ƙyale da ita ce ta katse mata maganar da take. "Haba Mana Colm down Tana na Zanzo anjima karki damu zan koya miki kinga ba sai kin sake cewa baki iya ba Yawa Hajiya zata zo gobe ta ganki”Allah ya kai mu kace ina gaida ta.”No bazan zama dan aike ba, zan tura miki number ta sai ki kirata kinji.” Ido ta zaro kamar taga kura daji "Kai Wallahi ban iya ba kawai kace ina gaida ta in kazo Sai ka kira ta mu gaisa zaifi.”baki ya tabe kamar a gabanta."Ok in shiga gida zan kira na hada ku karkayi nesa da wayar.”Kai ta ɗaga"Tom Allah ya kaika Lafiya.”Ameen nagode Yar aljana” Suna shiga ciki parlour Hajiya sa yashiga tana zauna da Yan uwa ta guda biyu sai bababr Aminiyar ta matar Gwamna, yana shiga aka fara tsokanar sa.“Ammar ango barka da shigowa Gajiya Yaro nan fa har yafara zama babban mutum baki lura da haƙa ba?”Cewar Hajiya Badawuyya Autar su Hajiya, Safiya Hajiya tayi."Badawuyya kufi kusa ke da ɗan naki samma baki girma kamar ba ɗanki ba” Bai tanka mata ba duk yadda taso taja shi sai guri hajiya Munubiya da yaje ya zube yayar Hajiyar sa bayan ya gaida su, ya kalli Hajiyar sa."Hajiya abu ya sanar dake abi ya sanar dake abin da suka tautana ni har muka zo bai ce dani komi ba fa..”Allah Ammar zanso naga yariyar nan da ta sace zuciyar ka har ta sa kake yawan magana mutum da magana take masa wahalar wai yau kaine gaban Gajiya Babba da Hajiya da Aunty kake neman yadda akayi”Shury ya mata tare da mikewa ya bar musu Parlour gaba daya.Sai da suka gama shirya yadda za akai lefe sanan suka watse kwana uku aka barshi kai laife. *ALHAJI ƊAN DUBAI* Kiran Abi be ya shigo yana zaune ciki wasu matan manya da yake hada su da manta.hannu yasa kamar yana cikin yara ya musu alamu suyi shuru tsitt kuwa sukayi kamar ruwa ya cinye su."Assalamu alaikum Ranka yadaɗe Allah ya kara lafiya danisan kwana.“Lafiya Kana ina ne Inaso gani ka Kasan Aure Yaroka Ammar ya taho 2 Week So Yanzu Lokaci na kuratowa kazo zamu lisafi kafi Lokaci za afitar da abin da za'a rabawa ma'aikata lokaci bikin.”Murmushi ya saki wanda shikadai yasan ma'anar sa, tsayi mintes 5 babu amsa ."Hello Alhaji Ahmed kana kan layi kuwa?” "Ahem..eh..Ranka ya dade afuwa insha zan zo zuwa magarib sai mutsara komi gida zanzo ko inda muka saba haɗuwa.”Ina gani kazo gida bayan sallaha magarib zafi.”Tom Alhaji Allah ya kara lafiya da nisan kwana sai nazo ɗin.”Suna Gama magana Wata ƙatuwar mace wace taci ta tada kai ka kashewa Alhaji Ɗan Dubai ido."Wai Ɗan Dubai dan Allah mai zauna ka hadani da uban gidanka Kai kasan ina da tari dukiya kawai burgeni yake inaso mu riƙa rage dare shine buri na.”dariya ya yi ya shafa tunbi sa.“Haiya Sailuba kenan har yanzu baki san waye Alhaji kareem Al-Labban ba kwata kwata mata Duniya basa burge sa matar sa ɗaya kamar ta tsafi ita kaidai ce take burge sa dan haka shawara kyauta ku ɗauke Hankali ki daga kans kar ki janyo wa kanki tono silili wallahi.”yana faɗi haka ya niƙe wata number ya turawa sako ya fuce ya barsu. After 5:00pm Sai da ya juma a kofar gidan sanan ya ɗauki waya ya kira Number Sumayya bugu biyo ta dauka tana tsakar gidan Hakan yasa kowa ya bita da kallo, Baba Zulai ta kwafa ta buga mata harara ta ci gaba da tsintar wake da take. "Hello Ina wuni..."Ina waje ki fito ina jiran ki.”Yana faɗi haka ya katse kiran.ajiyar zuciya ta sauke ta bi wayar da kallo..."Sumayyah Wata har kin iya dogo munafurci kifa boye abu aƙuginki saboda kar mu sani waike wane iri mugun hali kika ɗebo ne?” Taso ta share ta amma sai ta aro jarumta ta kalleta."La Baba Ai Ammar ne ya kawo kuma naga agidan nan kowa yana da ita dan nanuna tawa kamar bazata burge kuba shiyasa ma bayi karanbani ba”tana faɗi haka ta shige daki inar ta ta zura mayafi abayar ta da turare ta fito barsu da ƙamshi turare ta."In ba babar mu wataran sai naci kundun uban yariyar nan tsabar rashi mutun ci tun yazu ta fara mana kallo banza“Sadiya Ta faɗa tana hura hanci.dariya Baba Zulai tayi"Ki barta Sadiya gobe sammako zanyi zuwa Rafin Malam duk wani tsibu da ƙulu boto Malam mai yatsa ɗaya ya iya kuma zan bada ko nawa ne dan naga aure nan ya rushe kamar rushewar gini”Shewa suka sa kamar ana biki.da haka suka ci gaban da aiki su.tun da ta fita ta kafe motar da kallo so take taga inda Ammar yake tsaye amma babu almu a jikin motar.wayar tace ta sake ƙara, da sauri ta ɗauka, kamar me shiru kuka ta fara tambayar sa. "Na duba ko ina amma bangan kaba kuma kace kana waje wai ina ka shige ne.?”Kin shiga ciki motar kinga bana ciki zaki min raki?”Ido ta zaro."Yaya Ammar Allah 'yan gidan mu basa zance amota dan Allah ka fito waje bazan iya shiga mota...“Baza ki iya shiga mota ba amma ai kin bi gardi har Lagos ko?Nine baki yarda dani ba Shiyasa bazaki shiga mota guri na ba.”Idon tane ya ciko da ƙwallah."Wallahi Yaya Ammar in na shiga mata gurika surutu za'a min kuna Yaya Yusuf ya zane..” " Shouting Up Ni zan koma bazan zauna ai ta ƙare min kallo a layi nan naku ba ki koma gida kar ki bata ran yan ƙauye ku da wanan bagidaje yayan naki”Yana faɗi haka ya kunna motar, kamar ƙiftawar ido ta tsaya agan motar kamar bai gangata ba ya sake baya da motar zai bar guri ta fara dukan gilas ɗin, Murmushi ya yi ya sake ɗaure fusakar sa ya sauke gilas ɗin motar har ido ta yayi ja kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai."Zaki iya shigowa”murfi motar ta kama zata shiga Daga ƙofar gidan su Aka daka mata Tsawa."Ke Sumayya gidan Uban wa zaki zaki faɗa motar wani Allah ya tona mikio asiri dan Ubanki”Yusuf ne yana magana yana tun karo ta jiki ya fara bari yan zuwa zai ɗauke ta da mari ido sa yayi arba dana Ammar da sauri ta saki hannu ta."Kai ashe kaine ai ban sani ba ke kuna sakare bakya ce Baban mutum ne nazata kwashe² da kika saba ne yauma kika kwaso wani.”Iri kallo da Ammar ya a sake masa ne yasa Yusuf bari guri jikin sa na rawa. Sun ɗan juma a haka ya dubeta."Ko na tafi ne?”Jiki babu ƙwari ta shiga, Lumshe Ido sa yayi yana ji wata iri nutsuwa na ratsa shi tabbas Yariyar nan tana da baiwa, in har yana tare da ita takan kasa kama kansa.ita kum tun da ta zauna fargaba haɗuwar ta da Yaya Yusuf take in ta koma dan tasan wanan harara da ya masa akanta zai fanshe,Murya Ammar taji kamar daga samma"Aunty Sumayya ina Wuni tunda gaisuwar ma wahala take miki”Kunay ce tasa ta rufe fusakar ta.“Kai ai karami shine yake gaida babba ba wai yaro ba." Dariya ya yi ya ɗauki gorar ruwa ya kurɓa sanan ya kalle ta."Tom ai naga gaba ɗaya mutane gidan nan naku nema suke su furgita min ke Allah ya kawo lokaci bari gidan nan mu huta.... [12/23/2025, 10:38 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-20 Jin tayi shuru bata bashi amsa ba yasa shi juyawa ya kalleta, ganin yadda take faman wasa da yatsun hannunta cikin fargaba yasa ya kashe motar baki daya. "Sumayya, karki damu da su. Muddin ina raye, babu wanda ya isa ya cutar dake. Insha Allah nan da kwanaki kadan zan fitar dake daga wannan gidan."Wani sanyayyen murmushi tya bayyana a fuskar Sumayya, wanda ya ƙara mata kyau da kwarjini. "Nagode Yaya Ammar, amma tsorona daya; kar Baba Zulai ta shiga tsakaninmu. Kaga yadda suka biyo ni da kallo kuwa?gashi so suke...."kenan kema kin yarda da canfi mutane ki yarda da Allah shike yin komi ba mutum ba dan haka ki manta dasu.”Shuru tayi babu ammasa hakan yasa, ya yi dariya, ya mika mata wani ƙaramin kwali mai kyau. "Wannan turare ne da agogo, Hajiya ce tace na kawo miki. Sannan batun Baba Zulai, Allah yana tare da mu. Ke dai ki duƙufa da addu'a." Bayan sun dan taba hira,Ammar ya kalli agogo"Ranki yadade zan tafi akwai aiki agaba na zanje sai munyi waya” Kai ta girga “Tom ai baka koya min yadda ake anfani da wayar ba”Kai ya dafe sanan ya amsa sai da ya koya mata yadda zata gane sosai sanan ta fita daga motar zuciyarta fari fes. Bai bar anguwar ba sai da yaga tashiga cikin zaure gidan su sanan ya bar layi. tana shiga zaure gidan, gabanta ya fadi. Yaya Yusuf ne yana tsaye jikin bango, yana huci kamar tsohon zaki jiran shigowar ta kawai yake. "Wato Sumayya har kin isa ki raina ni ko? Dan kin samu dan birni mai mota shi yasa kike kallonmu kamar wasu tsumma? Tom yau zan kade miki ƙuran da take kanki dan kutumar ub...."Baba Hauwa ce ta katse shi"Haba Yusuf wai sai yaushe yarinyar nan zata san ƙaunar 'yan uba ne dan Allah ku tausaya mata,Sumayya ba marainiya bace muddin ina numfashi. Kaje ka nemi dai²tawa da kanka, amma ba kan yarinyar nan ba.daga yau bazan sake bari kucutar da ita ba"tsaki Yusuf ya ja ya fice daga gidan yana zage-zage. Hawaye ido ta ta goge ta rusuna“Baba Hauwa nagode Allah ya saka da alheri”Ameen Tace suka shig cikin gida. *ALHAJI ƊAN DUBAI* A gefe guda kuma, Alhaji Ɗan Dubai ya isa gidan Alhaji Kareem Al-Labban bayan sallar magarib kamar yadda suka yi alkawari. Suna zaune a wani katafare Parlour na alfarma, Alhaji Kareem ya kalle shi cikin nutsuwa. "Alhaji Ahmed (Ɗan Dubai), kasan amana dake tsakaninmu. Ina son wannan bikin na Ammar ya zama abin alfahari shikadai ne yaro na daga shi bani da wani magaji inaso akyakyautawa ma'aikata” Alhaji Ɗan Dubai ya gyara zaman sa, zufa ta fara keto masa duk da sanyin AC dake dakin. "Ranka ya dade, za ayi komi cikin tsari kamar yadda ka buƙata?sai dai ni ina gani kamar Yarinya ce ’yar talakawa,kamar bata dace da yaro mu ammar ba?" Alhaji Kareem ya kura masa ido dan bai tsamaci haka daga guri Alhaji Ahmed ba.nisawa ya yi ya daki Murmushi iri na manyan mutane. "Ina ga wanan ba abin daga hakali bane daga Ni har kai babu wanda zai zauna masa da ita so bamu da damuwa da haka”Ɗan Dubai ya gyada kai,badan ranshi yaso ba soyayi zugar da tayi tasiri tun anan, sai dai ko hakan bai damu ba Akwai tanadi da yayiwa ammar da shegiyar yariyar da ta jamasa asara. *GIDAN MALAM* Tun kafi ketowar alfijir Baba Zulai da Sadiya sun gama shiryawa tsaf. "Sadiya, shirya bana so mufita akan ido jama'a tun kafin asuba zamu kama hanyar Rafin Malam. Dole ne mu raba wannan zaren tun kafin a kai ga saka shi" Sadiya ta yi dariyar mugunta, "Ina tare dake Babarmu gara mu raba su yanzu kafin ta je can birni tana mana takama da feleƙe Dan Wallahi Babar mu in naje gidan sa Har Uwar tashi sai naci ubanta tunda ta nuna tana son Sumayya."dariya Baba Zulai tayi suka ci gaba da shiri su ciki sirri. Alhaji Ɗan Dubai ya fito daga gidan Alhaji Kareem yana goge gumin fuskarsa. Wani mugun murmushi ya subuce masa yayin da yake tada motarsa. "Alhaji Kareem, kana tunanin zanyi abin da zai faranta maka ko wanan shege ɗan naka? To zan tsara maka abin da zai raba danka da wannan yarinyar har abada.Dole ne na shirya tarkon da zai sa Alhaji Kareem ya tsani Sumayya, shi kuma Ammar ya ga laifinta. Zan hada su da babban laifi, wanda ko Ammar ba zai iya kare ta ba," ya fada a fili yana bankawa motar sa wuta. Washegari tun kafin assalatu, Baba Zulai da Sadiya suka sace hanya suka nufi dajin Rafin Malam. Tafiyar kusan sa'a biyu ce a kan a kafa kafin su isa bukar Malam Mai yatsa ɗaya. Wurin yana da kyan gani amma cike da kwaramniyar tsuntsaye daji da hayakin turaren da ke fita daga kogon dutse. Suna isa, suka tarar da Malam zaune, idanunsa sun yi jawur. "Zulaiha! Kun zo neman rugujawar katangar da kuka kasa hawa ko?" Ya fada cikin muryar mai cike da kuwa mara daɗi sauraro. Baba Zulai ta zube tana tana masa wani kirari"Haka ne Malam. Wannan yarinyar Sumayya tana neman fi karfinmu. Muna so a raba wannan auren, a sanya kiyayya tsakaninta da Ammar, sannan a sanya Ammar din ya koma son Sadiya. Har aure ya koma kanta" Malam Mai yatsa ɗaya ya buga kasa, wata irin tsawa ta daka a dajin.hoto ammar ya bayyana yana kwance sai da ya nuna musu hoto sa sanan ya hoto ya bace ya kalli Baba Zulai."Abin da kuka nema yana da tsada. Domin yarinyar nan da shi kanshi suna da tsari na addu'a. Amma zan baku wani magani da zaku binne a kofar dakin Innarta. Duk ranar da kafar Sumayya ta taka wurin, duk abin da Ammar zai gani a jikinta zai zama kaskanci da maita bazai taba gani farin ta ba sai baƙin ta. Amma ku sani, idan asirin ya karye, kanku zai dawo!" Sadiya ta gyaɗa kai cike da zumudi, "Malam ko mene ne mu shirya mude. Burinmu dai mu ga Sumayya tana kuka, muna dariya.na mallaki wanan atajiri dan birni"dariya ya bushe da ita ya hada musu laya da wani ruwa da zasu hada su binne tare, basu bar guri malam mai yatsa ɗaya ba sai da Baba Zulai ta tafe masa dubu talatin sanan suka masa sallama.A lokacin da suka dawo gida, Sumayya tana zaune tana hira da Innarta, zuciyarta cike da farin cikin tunanin kiran da Ammar ya yi mata dazu ya dabaibaye zuciyar ta da ƙaunar da mara misaltuwa. Ba ta sani ba cewa makirci yana kewaye da ita ta kowane bangare ga Alhaji Ɗan Dubai daga birni, ga kuma su Baba Zulai a gida. Sumayyah tana gani su ta miƙe tana masu sannu da zuwa ko kallo inda take basu ba suka shige ɗaki ransu fari ƙal.sunazama Sadiya ta ran gaɗa guɗa"Yanzu aka fara wasan, Sumayya. Ke da kike jin kun sani guri mutuwar ki ta kusa, kwanan nan zaki zama abar kyama a idon kowa.har shi wanda kika dogara dashi."baki Baba Zulai ta bige mata."Wanan shege baki naki sai ya tuna mana asiri gari azarɓaɓinki.”Dariya ta Ƙyal ƙyale da ita."Tom Babar mu na daina...” [1/6, 9:29 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-21 Da haka suka shiga abin da yake gaban su. Cikin dare misali biyu da rabi Baba Zulai ta mike Sadiya na kwance ta daka mata duba.murginawa ta sake zata koma bacci."Sadiya Dan Ubanki tashi waye yace miki ana bori da sanyi jiki,yanzu ne lokaci aiki mu dan haka tashi muyi abin da ya dace duk kafi lokaci ya ƙure mana”Miƙewa tayi azabure tana murje indo ciki sanɗa suka bude ƙofar , suka fita basu samu kowa ba, Baba ce ta kurkusa a baki kofar su Sumayyah, karamar wuka ta zamu ta fara haka kofar sai da tayi zurfi sanan ta karbi layu ta saka maida ta rufe ta yayafa ruwa sanan ta saka basasar ƙasa,da hanzarin suka koma ɗaki suna maida nufashi. Kiran Sallah Asuba shine yasa Sumayyah fitowa tana wuce ta dauro alwala ta koma daki ido Su Baba Zulai yana kai tana wuce suka kwashe da dariya tare da tafawa.sumayyah na idar da Sallah wani azababe ciwon kai ya kama ta dakar ta iya rashi ta nemi guri ta kwanta kusa da Inna ta. Har gari ya yi haske bata fito ba.baba Zulai ce ta yaye musu labule kofar ɗaki a kwance ta same ta. "Sumayya yau kuma wani sabo iskanci ne bazaki fito tsakar gida kiyi aiki ba sai kibi gado ki kwanta ai sai ki bari sai anyi aure naki ki fara nunawa mutane isa dallah ki tashi ko naje na sanar da Malam” Da ƙar ta iya miƙewa tana dafa bango ta kalli Baba Zulai."Ba Wallahi kaina ke ciwo dakar nake iya daga ido kiyi hakuri bawai kin fitowa nayi ba” "Matseeeee karyar banza ayi dai mu gani”Da haka baba zulai ta fice. Kwaci tashi yau tsayi sati guda Baba Ammar babu kiran sa haka kuma in ta kira sai dai taitaji wani iri turanci.Shirye-Shirye biki ya kankama saura kwana uku yau ne aka kawo laife set bakwai an zuba kaya sosai, duk yadda Sumayya taso taga kayan nan haka Baba Zulai ta kafe tace ta bari in taje gidan ta ta kare musu kallo hata ɗinkaku ciki bata bar sumayya ta dauka ba Ƙarshe ciki sirri ta bawa Sadiya takai aka mai dasu dai-dai sawar ta. *AMMAR* Tin da bikin ya motso ya rasa mai yake masa dadi ,gashi fusakar Sadiya yake gani duk yadda yaso ya tuna Sumayyah ya kasa ko kira ta ya tafi zaiyi sai ya nemi number ya rasa, ya kasa sanarwa da kowa, matsalar da take damu sa.har biki ya rage kwana uku aka kai lefe. *ALHAJI ƊAN DUBAI* ya riga ya gama tsara komi, dan har sabo gidan Ammar ya sani dashi ake shirya komi dan Sani lokaci abin da za Asama Alhaji Ɗan Dubai ya sani Ammar bai sani wai duk dan ayi masa bazata kayan daki kuwa tuni suka ce sunyafe Ummi ce zata yiwa Sumayya. Bayan su fito daga gidan Alhaji Ɗan Dubai ya kalli Mustapha yaro sa da suka fito daga gidan Ammar kai wasu kujeri ya tun tsireeda dariya yace.“ Mustapha Wallahi yaro nan har ya fara bani tausayi domi iri muguntar da na shirya masa bai isa ya tsallake ba”Wanan Haka yake Alhaji Allah yaro baisan wuta ba sai ya taka, baisan ba'a taɓaka azauna lafiya ba”Dariya suka yi suka tafa sanan Mustapha ya tuƙa suka bar layi. *3 Day* Kofar gidan Malam Sule Gidaɗo damƙar yake da Malam zaure da almajira ana ta yawo da tuwo mutane kowa yana zuba ido zuwan ango da iyaye sa domi kuwa labari ya iske su atajiri Sumayyah zata aura.Ciki gida kuwa Sadiya ce ta fito da wata arniyar shadda kana gani kasan ta manya ce dan Bazum ce tasha aiki ajiki da mayafi da takalmin duk aciki lefe ta dauka Sumayya kuwa da ƙar Baba Zulai ta dauko atamfa mai tsada ce sosai sai takalmin wanka da mayafi ta bata, kallo ta bita dashi ta wirga mata harara. "Kimga saboda baki duniya na dauka miki wanan inkuma so kike baki ya miki yawa sai na kwaso miki tsiyar ki kije can ki ƙarata duk abin da ake muku bakwa gani yaran yanzu” Shuru Sumayya tayi hawaye na zuba a kan fusakar ya, daki Inna ta tace ta zube kayan tasha layi kafi ta samu ta shiga wanka, ko da ta fito dangwali yaɓa ta shafa ko arzikin hoda bata samu ba tayi kuka kamar ranta zaifita babu mai rarashi ta taji lokaci da Sadiya ta fito wasu dangi Baba Zulai na zolayar ta. "Sadiya Yar Baba wallahi sai kace kece Amarya wanan ango da yasan dake da baikai kanshi guri hauka ba.”budar baki Sadiya tace."Ku kuke abin ku dama ai nice Amarya ba wata ba kuma zaku gani lokaci zai nuna kansa ”Shewa suka sa."Shegiya Sadiya kar kisa Sumayyah ta hadiyi zuciya ta Mutum saboda baƙi ciki” Har suka gama surutun su, tana ji haka kuma bata yi karan bani fitowa tsakar gida ba dan ko ta fito bamda kyara da hantara babu abin da zata sha, a guri dangi mahaifin nata dana matan baban ta.11 dai-dai ɓangare aungo sukazo sai dai Babu Alhaji Ɗan Dubai dan shi ance ya zauna ta kula dama su zuwa daga baya yana salmar su. Waliye Sumayyah dana Ammar su Halara a masallaci shedu ake gabatarwa wandda addini ya tana da.ammar suna gefe shi da wasu abokasa, zuciyar sa ta fara masa hudu da kuma tilas tashi akan abin da tun dare jiya yake jin haka shine daidai. Ciki sauri ya tunkari masallaci, da sauri Abdullah aboki da ya tare sa "Kai bana so shirme iyaye mune a ciki mai zaka yi kuma indai Sumayyah ce nan da 'yan daƙiƙu zata zama taka.”Da sauri ya dago ƙirjina wata iri bugawa. "Abdullah hakan ne bana so Sadiya nake so aure shiyasa nake sauri kar amin ba dai-dai ba wanda hakan zai iya zama barazana da rayiwata gaba ɗaya.” Sororo Abdullah ya yi dan gano yake zaki aure ne yake damusa ba tare da wata damuwa ya bashi hanya ya wuce.ciki ya kutsa kansa duk wanda ya gansa sai ya bashi hanya dan yasan ango ne, ko kaci da ake kokari daura aure ya sauri karasa wa. "Dan Allah ku da kata Ni Sadiya nake so ba Sumayyah dan Allah..... [1/7, 9:01 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-22 Babu wanda bai kalli Ammar ba, Abi ne ya mike da sauri ya kama Ammar kasa yayi da murya Ammar. "Ammar lafiya kake? Sumayyah ce fa yariyar da ka kawo mana ita,Me ya shigi kanka ne?” Lokaci ɗaya jijoyoyi kansa suka tashi Ya fashe da kuka kamar yaro ƙarami tare da fadawa kan Abi. "Abi wallahi nima ban sani ba amma haka kawai nake ji kamar in na aureta shine silar bari na duniya Abi dan Allah in dai kana sona kawai ka yarda na Auri Sadiya kaga itace muka san Asali....” Da sauri ya rufe masa baki"Amma Ammar ina jiye maka tsoro ranar ladama dan Allah yaro na kayi tunani me yasa zaka yiwa yariyar nan haka, ita fa tamkar marainiya....”Tafiya Ammar ya yi lu'ulu'u kamar zai fadi da sauri Abin ya kamo sa. "Ammar Lafiya baka da lafiya??” “Abi ko sunan ta naji an abanta kaina sara min yake jinake nufashi na yana so ɗaukewa, Abi a kan wata zaka so ƙarasa rayiwar naka yaro?”Kai ya girgiza zuciyar sa nayi masa ciwo, kama sa yayi ya zaunar dashi, sanan ya koma kusa da manyan mutane ya sanar dasu a sauya aure daga kan Sumayyah zuwa kan Sadiya fara'a Malam da Yusuf kasa boyuwa tayi ciki zumi ɗin aka daura auren akan sadaki naira dubu dari uku.shedu suka sheda,Yusuf har da gudu sa ya ƙarasa ciki gida ya sheda musu na aka hau tsalala guda. Maganar Sa'ade da taje jikin Window su Sumayyah ce ta doki dodo kunne Sumayyah. “Allah mai kyauta da ƙari Kaji kudirar Allah An taho da zumar Aure Sumayyah ya koma ka Sadiya dama Allah bai rubuta Sumayya itace matar tasa ba Yariya Allah yasa ki shigar A Sa'a dama kin fi kala da matar many... Sulalayewa Sumayyah tayi sumamiya babu wanda yasan ta suma dan a tsakar gida bidiri kawai ake Baba Hauwa ce ta nufo daki Da gudu tana zuwa ta samu Sumayyah a sanƙame hawaye ta fara. "Sumayyah..! Sumayyah ki tashi kada ki bari wanan abu ya ɗaga miki hankalin kin ga jarabawa da tafi wanan insha Allah Allah zai misanya miki da mafi alkairi Kisani kina zaune Gaskiya, zata yi halinta kuma ƙarya fure take bata 'Ya'ya wallahi”Duk surutu da Baba Hauwa take Sumayyah bata san tana yiba ruwa ta dauka ta yayafa mata da Sallati ta farka suna haɗa ido da Baba Hauwa komi ya dawowa mata sabo hawaye ido ta ta goge ciki karyewar zuciya tace. "Baba Hauwa da gaske Ammar bani ya aura ba Sadiya ce matar sa bani ba?”Hawaye itama Baba Hauwa ta fara gegewa. "Sumayyah ki daure nasan akwai ciwo amma dan Allah karki bari sheɗe ya yi galaba akanki Wallahi Allah dama ya riga ya rubuta can dama bake ce matar Ammar ba, ki Sani ko Ba Sadiya ba dole zai auri wata kiyi musu addu'a kiyiwa kanki addu'a Allah yasa hakan ya ame miki alkairi kina zaune zaki ga sakaiya domin Allah baya bacci ”Kai ta gigiza kukan Inna suka ji da take bacci tun dare jiya bata farka ba sai yanzu, da sauri Sumayya ta fada jikin ta kuka ta saki mai kara tana sake ƙankame Innar ta sai da suka shafe 30 minute sanan Ta tsaigata har Baba Hauwa ta fita ta dauko mata tuwo basu sani ba sai da suka lafa sanan Baba Hauwa ta matso ta mikawa Inna tuwo, duk yadda ta juya amma Inna taki ci sai kwauda kai da ta riƙa yi Kamar tasan me ya faru. A na cikin haka Suka ji maganar Baba Zulai tana faɗa. "Dan Allah ku kwashe kwanikan tuwo nan ga suruki nanan zai shigo,ke Suwaiba ɗauke yaro nan naki daga kan 4 shi kullum cikin kashi yake,yara sai shege cin tsiya ba dole su ta Kashi ba”. Hayaniyar maza daga ji su Ammar ne haka kuwa akayi daga wasu maza biyu sai AMMAR da Abdullah suna zuwa kofar ɗaki Inna Ammar ya zame babu zato Baba Hauwa da Sumayyah suka ganshi a tsaye a kansu suna haɗa ido da Sumayyah ya yi sauri ɗauke kansa gaban Inna yaje kamar bazai magana ba suka ji murya sa. "Inna kici abinci, ko kinaso na baki da kaina?.... [1/8, 10:56 AM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channehttps://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-23 Kauda kai Inna tayi ya sake maida kansa inda take zata sake kauda kai ya sauri kamo hannuta ciki saunyi murya yace. "Ki yafe min Inna nasan Uwa bazata taɓa fushi da Dan taba ko zakiyi fushi dani?”Kallo sa tayi hawaye na zubo mata babu magana hankici ya ciro daga aljihu sa ya fara goge mata hawaye, sai da ya goge mata ya saka hannu sa aciki robar tuwo da kansa ya riƙa bata. Sumayyah kam ta kafe shi da kallo amma ko kallo inda take ba yayi sai da yaga ta fara kauda kai sanan ya cire hannu sa ruwa ya miƙa mata na hannusa ta karɓa tasha, ya miƙe ba tare da yace musu komi ba ya fita. Kuka zata guza Baba hauwa ta yi sauri da katar da ita. "Haba Sumayyah sai kace ba yariyar da nasani ba Nasan akwai ciwo amma ki daure karki bawa maƙiyi damar ya miki dariya yanzu akwai takalmin da Lubna ta suyo a ciki zan ɗako miki ɗaya kisa, kinuna baki damu da aure nasu ba hakan zaisa suji kunya kiji” Kai kawai ta iya ɗaga mata ta fita. Bata juma ba ta dawo har da powder da jan baki da kwali kwaliya tayi sama-sama tayi kyau abinka da Black Beauty har madarar turarer ta saka mata sanan ta kama hannu ta suka fita suna fita lokaci an gama hoto da ango da amarya zunzo zasu fita suma Su Sumayyah suka fito, wan nan ne haɗa ido su na biyu a yau a wanan karo shine ya kasa ɗauke ido sa daga kanta ita kuwa kamar bata san da tsaiwar sa aguri ba Sai da Abdullah ya bugi kafaɗar sa sanan ya dawo hayyaci sa sai da suka fita sanan Sumayyah ta samu guri nesa da ƙawaye Sadiya ta zauna tun da suka lura da ita suka fara dasa baƙaƙe maganganun in tayi kamar ta bar guri Baba Hauwa tayi mata alamu da ido karta tashi haka ta daure har lokaci sallah Azahar tayi alwala ta shige daki su. 'Yan ɗauri aure na komawa kan fara hada-hada Ummi babu abin da ta sani haka kuma Abin ya gargadi kowa akan kada asanar da kowa halin da ake ciki iya wanda suke guri su haƙa su binne saboda gudu surutun mutane. Da yake magana ce ta wanda in ya faɗa ake ji kamar bayi wani abu aguri ɗauri aure ba. Kasa zaune abi yayi ya kasa tsaye ƙarshe wayar Ummi ya kira ya sanar da ita yana parlo. Da ƙar ta iya ya kice baƙi ta haura sama tun da ta ganshi gaban ta ya fara dukan uku² tasan ba lafiya ba. "Allah ya temake ka ina ango ne ko ka fara kewa ne tun yanzu” Hannu ta ya kama.“Ummu Ammar akwai matsala fa” Rass kirji ta ya shiga bugu ciki rawar murya tace."Abi wace iri matsala badai fasa bashi aure kayi ba ina shi Ammar ɗin ya tsaya??”Gaba ɗaya ta rikice hannu ta ya kama ya zaunar da ita gefe bed."Colm down An ɗaura aure dai² lokaci da aka sai Sai dai Ammar ya furje shi yar uwar ita yariyar yake so wai ba ita ba duk yadda naso na ganar dashi ilar yin haka amma ya kafe yana ta wani iri sambatu.... “ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakili.Abu Ammar ina Sumayyah ina Shi Ammar ɗin?” “Ki kwatar da hankali ki mun baro su shi da su Abdullah zasu shiga ya gaida surukansa amma... Mikewa Ummu tayi da sauri Abi zanje naga Sumayyah dole tana bukatar kulawa dan Allah kabarni naje”kai ya kada mata."Bana so mutane Su san hali da ake ciki fitar ki zai iya jan hankali al'umma ki bari zuwa gobe”Wallahi Abin bazan iya jira ba dan Allah ka temaka min yariyar nan bata da kowa sai Ammar amma yanzu ya yi mata haka shikenan ya raba alakar shi da ita me yake damu sa ne?” Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa"Shikenan ki tashi zan sa Aminu ya yi driving ɗinki”mikewa tayi handbag dinta ta ɗauka sai mayafi ta fita ta kofar kitchen tana isa Parking space motar su Ammar na tsaiwa, ciki taƙama ya fito yana baza Babar riga tun da ya hango Ummu kirji sa ke bugu tara-tara tun karar ta yayi da zumar suyi magana kafi ya ƙaraso ta shige cikin mota jikin sane yayi sanyi gaban sa ya tsanan ta faduwa yana kallo ta fice haka yaja kafa suka shiga parlo nan aka fara zolayar sa yaƙe kawai yake bawai dan hakali sa akwance ba. *Gidan Malam* Tun da Sumayyah ta shiga bata sha'awar sake fitowa tana ji ana ihu masu DJ sunzo za afara kida hakan yasa ta miƙe da zumar ta kare musu ƙofa dan wasu har keƙe su suke wai suna san gani Inna da Sumayyah kokari tura kofar take Kaf ido ya ya sarke da fusakr Ummu cike da fargaba da Mammaki ta fara hada magana. "Ummu...kece..yanzu Ina Yan.... "Ya Isa Sumayyah mushiga daga ciki”Karfin Hali faɗaɗa fara'a tayi tare da bata hanya Ummi ta wuce, tana shiga guri ta nema ta zauna tana bin Sumayyah da kallo wace ko motsin kirki ta kasa. "Sumayyah zo ki zauna”Jiki babu kwari ta zauna kasan kewar tsakar ɗaki."Ummu ina Wuni ya taro”Hawaye Ummu ta fara. “Sumayyah ki yafewa Ammar ki kuma yafemi Wallahi nasanr Ammar baya ciki hayyaci sa” "Ummu Ya Ammar bai taɓa min kimiyya ba Wallahi hasali mi Ni taimako na yayi daga muguwar rayiwar da naso na faɗa ko iya haka Ummu ya temake Aure kuma nufi ne na Allah bawa bai isa ya canja ƙaddara da tazo masa ba dama Wanan aure Rubuttace Al'amarin daga Allah waye ya isa ya canja zane ƙaddara mu”Sosai Ummu ta ji dadi furici Sumayyah mikewa tayi tsaye ta kafe Inna da kallo wace Bacci ya mata dadi saboda maganin bacci da Sumayyah ta ba sanan ta saki ajiyar zuciya. “Sumayyah Akaro na biyu nazo da ƙoƙon bara ta A gare ku Dan Allah ina fata zaki amma kuma baza ki bani kunya ba.”batare da Sumayyah ta ɗago ba tace. “Ummu bana fata ranar da zaki roƙi abu aguri na nakasa yi miki wallahi komaye na aminci matukar bai saɓa Addini da shari'ar Muslunci ba” Kusa da Sumayyah ta dawo. "Sumayyah Inaso ki Wuri Abi Mijina Wallahi nasan baza kiyi nadama duk da Nasan Mijina ya kwana biyu kuma yara basa don Aure me shekaru da yawa” Wata iri firgita Sumayyah tayi tare da miƙewa jikin ta na tsuma."Ummu wallahi kaina ya kulle ban gane abin da kike don ce...."Murmushi Ummu tayi ta dafa kafaɗar Sumayyah."Sumayyah nasan kin san me nake nufi amma bara na sake mai-maita miki Inaso in har kin Amince ki aure mijina Sheikh Kareem Al-Labbani Mahaifi Ammar Kuma mijina Wannan shine kadai roƙo da nake mi.... Sulalayewa Sumayyah tayi ƙasa Sumayyah.... [1/9, 3:40 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73 *Ayi hakuri Babu Editing dan Allah* *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-24 Ciki tashin hankali Ummu ta ƙasa inda take sunan ta ta fara kira."Sumayyah..! Sumayyah..!dan Allah ki tashi...“ Inaalillahi wa'inaalaihi rajun mai zan gani baiwar Allah wace ke me kikayiwa Sumayyah??”Baba Hauwa da ta shigo ta bawa Sumayyah kayam Lubna ta sauya saboda yini biki,kallo ta Ummu tayi murya a sanyaye."Wallhi baiwar Allah babu abin da na mata hasali ma nice mahaifiyar Ammar maso naga halin da take ciki ne.”Sake daure Fusakar Baba Hauwa tayi tare da zama kusa da Sumayyah ta ɗora ta kan ciyar ta."Allah sarki ai da yake Sumayyah tamu mai tawali'u ce Babu komi Allah yasa haka ya zame mata Alkairi kuma mungode da kulawar ki”Muushi Ummu tayi dan yasan Baba Hauwa a matuƙar hasale take, miƙewa tayi ta bude randar gwauro bayan kaure ta ɗauko ruwa mai sanyi ta mikawa Baba Hauwa."Ki sa mata suma tayi da Alamu maganar da na gaya mata itace ta firgita ta... "Haba Baiwar Allah ya tana ciki wani hali zaki sake jefata kubar ta da iya wanda kuka sata Cuta ce dai an riga acuci marainiya Allah sai dai Allah ya saka mata da gan-gawa.”Ajiyar zuciyar Ummi tayi."Ki kwantar da hankali ki Bazan taɓa cutar da Sumayya ba inaji ta Araina tamkar Ammar kuma maganar da nazo da ita a nawa tunani zai rage mata radaɗi abu da yake damu ta.”Baba Hauwa bata sake magana ba sai ruwa da ta fara yayafawa Sumayyah bayan tsayi mintes goma ta farfado ido biyu tayi da Baba Hauwa ciki sanyi halitta ta furta."Dama nasan mafarki ne Bazai taɓa zama gaske ba taya ma zan Auri Abi wanan ba gaskiya.... “Gaskiya ne Sumayyah babu mafarki aciki kuma zan tsaya kai da fata dan naga wanan al'amarin ya yu fata na ki amice kuma zaki ga alfano da abin da na gaya miki”Kalli Baba Hauwa take bisu,su dukka biyu ta kasa gane me maganar su take nufi karfi hali tayi ta sake kallo Ummu."Baiwar Allah kusa ni cikin duhu dan Allah ku warware Ni daga ciki wanan lamari” Murmushi Ummu tayi. “Hajiya kar ki fa wani damu Sumayyah ce kadai take so ta maida lamari babba, nazo nemawa mijina aure ta wato mahaifin Ammar tunda shi ammar ɗin yaƙi ba sai ayi tuwo na maina ba mu baza mu taɓa gujewa Sumayyah ba sukuma wanda suka raba wannan alaƙa a hankali Gaskiya zata yi halinta insha Allah” Sosai Baba Hauwa abin ya razana ta amma domi ta nuna su Baba Zulai Allah mai iko ne kuma suma da arziƙin ta take tafe, zata yi fatan Wanan al'amari ya tabba dan hakan sai ya fi girgiza su mai arziki kacokan Sumayyah zata aura.fara'ata ta faɗaɗa.“Kai wai da wanan abin ne Amma Sumayyah har da suma wallahi nafi kowa farin ciki idan har haka ta kasance sai dai wani hanzari ba gudu ba bana so kowa yasan maganar nan har sai ranar da aka tsara ta daura aure gudu sheɗanu mutane” Sabunta Sumayyah Tayi ta bar jiki Baba Hauwa.hawaye na bin fusakar ta."Baba Wallahi Bazan iya zama da Abi ba, shine fa Mahaifi Ammaru, kuma mijin Ummu wanan ai cin Ammana ne kuma Ammar bazai taɓa yafe min ba” "Haba Sumayyah meye abin cin Ammana aciki Sunnha maiki Sallallahu alaihi Wasallama cefa kuma In ma cin amana ne waye ya fara bashi ba ,Forget Ammar and what the world will say, be his wife and I agree with you.dan Allah karki kawaye baya”. Saidai take kuka ita tama rasa ya zatayi haɗuwa su kayi Ummu da Baba Hauwa suna ta kawo mata kauli da ba'adi har kunyar Ummu ta shige kai kwai ta iya ɗaga wa Hammadallah sukayi 100k Ummu ta ciro cikin Handbags ɗinta ta ɗora kan ciyar Baba Hauwa. “Dan Allah ayi hakuri da wanan kafu Abi yazo da kansa....“Kai Sumayya ta fara girgiza wa Ummu."Dan Allah Ummu kar yazo wallahi bazan iya haɗa ido dashi ba wanne roƙo mafi girma da zan iya miki dan Allah ” "Haba Sumayyah in baizo ba taya zaku saba zama ne fa na din-din.... “Hauwa wai me kike a ɗaki yariyar nan nafa kasa gane miki tun da al'amari....”Sauran maganar ne ya tsaya mata gani Ummu duk da ba sani ta tayi ba taga Ammar ajiki ta saki fuskar ta tayi. “Wa nake gani kamar Hajiya gajiyar Al'uma bata hana ki fitowa ba Hala makawa kikayi ai can ne ɗaki nawa??”Cewar Baba Zulai da take ta yaƙe baki kamar ganar audiga” Dakar Ummu ta ita tataro ragowar Murmushi fusakata tayiwa Baba Zulai.“Wallahi kam na fara zuwa naga ɗiyata kafin sai na ga ita surukar tawa”tana fadi haka ta miƙe Baba Hauwa ta rufa mata baya jiki Baba Zulai na rawa ta busu suna fita tsakar gida ta dubi Baba Zulai."Kinga kuma gashi an fara kira na shida inaga in tazo kawai na ganta a kula min da ita kafi tazo”Godoya Baba Zulai tayi tana ƙokarin fita Sadiya na turo kai da ƙaruwar 'yan fi a kanta sai kayan da ta cire, ruwan Ash'ari yake makawa yaran da suke bin bayanta. " Yara sai kace Tumakai 'ya'Yan jara Alkur'ani duk wanda yasake bi mu zanci gato...”Asha Auzubiallahi wanne wace iri Yariyar ce baiwar Allah Ai yara Rahama ce dasu ki daina iri haka ke uwa ce mai bada tarbiya in kina iri wanan zagi taya zaki bada tarbiyya?” Baki Sadiya ta taɓe.“Kujimu da mata ke kuma daga ina dan Ban sanki a dangi Malam ko na Babarmu ba”Murmushi Ummu tayi zata yi magana suka ji maganar Baba Zulai. "Ubanki Sadiya nace Ubanki, Surukar kice Babar Ammar Shasha mahaukaciyar banza”Wuri-wuri Sadiya tayi tana kifta ido.da sauri ta zube zata kama ƙafar Ummu, Ummu tayi sauri janyew."Karki samu Allah ya miki Albaka”bata jira me zasu ce ba ta fice tabar dadɗan turare ta.Ajiyar zuciya ta sauke.“Nashiga Uku wanan 'Yan bura...make mata Baki Baba Zulai tayi."Wato zagi dai baza ki fasa ba har abada” Tun da Ummu tabar gidan take tausawa Ammar iri matar da ya kwaso wa kansa dole ne ta tashi tsaye in ba haka ba Ammar zai faɗa mugun halin da bai taɓa tunani ba,haka ta koma gida jiki babu ƙwari. *After 6:00pm* Bayan an gama kidan DJ har su tashi motocin suka fara jerin gwano na daukar Amarya Habaici da ihu babu kalar wanda Sumayyah bata shaba karshe rufe musu ƙofar su tayi ta kwanta. Lifaya Sadiya tasa babu ƙarya tayi kyau dan Ance amarya ko ta buzuzu ce kyau take sabuwar Motar Ammar aka saka.Sai karfe takwas suka isa gidan Ummu duk wata tarɓa da akewa Amarya Ummu ta sa anyi mata kuma da kayan daukar Amarya surutu kam ansha da yiwa Sadiya murna ta samu daula. Sai bayan tara Ammar ya shigo shida tawagar abokan sa shi kaɗai ya haura sama a zaune ya same Ummu baki gado, da alamu tayi nisa ciki tunani Muryar Ammar ce ta doki dodo kunne sa."Ummu kina zauna”Da kallo ta bushi har ya yiwa kansa mazauni ƙasan Carpet ɗin da yake gaban gado.saki fuska tayi "Ammar kain?”Kasa ya yi da kansa ya gaida ta sanan yace "Ummu ki yafe nazo nayi...”Kasa karsawa ya yi ya fashe da matsanancin kuka ya juma yanayi sanan ta ɗauki ruwan miƙa masa ai da yasha ya samu Nutsuwa ta kama hannu ta kira sunan sa. “Ammar, yau ka zama miji. Ka bar yarinta a bayanka, ka rungumi nauyin da Allah Ya ɗora maka.”Ammarbya sake sun kunyar da kai yana goge hawaye da ya gangaro masa, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ta kara da cewa. “Matar da ka aura ba baƙuwa ba ce. Amana ce da Allah Ya ba ka. Idan ka ji tana yin kuskure, ka tuna kai ma ba cikakke ba ne. Ka rufa mata asiri, ka gyara ta da haƙuri, ba da tsawa ba.Ka kula da harshenka, domin kalma ɗaya na iya gina gida ko ta rusa shi. Ka rika yi mata magana da taushi, domin mace zuciya ce kafin ta zama jiki.Idan ka samu saɓani, ka zaɓi sulhu. Kada ka bar fushi ya zama shugabanka. Ka zama maigida da ake girmamawa saboda adalci, ba don tsoro ba”Ta sauke nufashi ta kama hannu sa. "Ammar Ka nemi halal ka ciyar da iyalinka, ka yawaita addu’a. Aure ba ya ɗorewa da ƙarfi, sai da tausayi da tsoron Allah.”kai kawai yake iya girgiza masa jiyake kamar ta hana shi tafiya sai tsinkawo muryata yayi tana cewa “Tashi kaje Allah ya maka Albarka ya baku zaman lafiya..” [1/12, 12:22 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-25 Mikewa yayi jiki babu ƙwari kamar an kwara masa ruwan sanyi ji yanke yau duniyar tayi masa zafi. Har ya sauka parlour ƙasa baya jin sa a dai-dai, tsaki Abdullah ya buga. “Mastwww Wallhi Ammar kana da matsala kai iri rawar kan nan ma na an gwaye banga kana yi ba kazo muyi mu kai ka, mu wuce gida kasan kusan muna da matan mu kuma mu suke jira” “Abdullah nace ku tsaya ne,Abdullah you know I don't like this kind of nonsense.in baza ka tsaya ba, zan iya tafiya ba tare da kowa ba” Yana fadi haka bai sake jiran me Abdullah zai ce ba ya fice, binsa suka yi Sunayi masa dariya har suka isa parking space. Tun kafin su ƙarasa, ya shiga sabuwar motar sa Abdullah ne ya zauna kusa dashi Fu'ad ya musu driving sunyi tafiya bawai mai nisa sosai ba suka isa bayan Asibitin Nasarawa.gidan Ya haɗu sosai dan har yafi na Abi girma, ƙamshi ya riga ya gama cika Parlour sallama sukai shuru babu kowa guri Suka nema suka zauna,cikin ɗaure fuska Ammar ya kalle su. "Bara na fito da ita, sai muyi abin da ya dace ku wuce ko?” “Dama Ammar ai bamu ce zama muka zoba” “Bazallah bar shege Kar ka bata mana rai sai muce anan zamu zauna har muga yadda zata...” “Matseeewww Abdullah Wallahi kai banza ne har abada baza ka girma ba” Yana faɗi haka ya shiga Bedroom yana sallama gaban sa ya faɗi wani iri jiri ya ɗauke shi da sauri ya dafa bango.Sadiya da Ido ta yake kan shi tun Sallamar sa tayi sauri dirowa daka kan gado nufosa tayi. "Subahallah lafiya baka da lafiya?” Ƙoƙarin kama sa take ya yi sauri ɗaga mata hannu.“Kar ki damu kizo zaku gaisa da abokaina, bana so ki yi magana bayan gaisuwa ko mai zasu ce miki” Kai ta ɗaga ji take kamar ta rungume shi ko ta samu nutsuwa yau itace tare da wanan kyakyawam mutumin hamshaƙi mai kuɗi wallahi nasan yanzu, wata ƙila ya mallaka mini katuwar mota mai... “Ko bakya son zuwa na tafi?” "Uhum...Ah.... A'a ai kai nake jira ka tafi sai na bi bayan ka” Bai sake ce mata komi ba ya wuce tana bin bayan sa har suka isa parlour, tun da suka zauna guri ya yi tsit. Wani iri kallo ya bita dashi da yi mata Alamun ta gaida su,amma ta kasa ganewa me yake nufi, sai ma bin Abokan ammar da ta sake yi da kallo, ranƙwafowa Ammar yayi ya mata rufa, ya sake kasa da Muryar sa. “Ke me kike yine? ki gaida” Wani iri Lumshe Ido Sadiya tayi ta saki wata iri a jiyar zuciya sanan ta kalle su, sauya salon Muryar tayi ciki yauƙi. "Ina yini ku ya ku kaji da jama'a Allah ya huta gajiya, insha Allah in gajiyar biki ta sake mu zamu zo har gida muyi..... “Be quiet, nobody asked yo?”cikin tsawa ya faɗa yana dalla mata harara, tsit tayi Fu'ad da dariya ta gama kama sa da sauri ya miƙe ya fice shima harara ya bishi dashi. “nonsense”Gyaran murya Bazallah ya yi“Ammar ya kamata muyi abin da ya kawo mu”Shiru sukayi Sallama Bazallah ya sake ya fara musu wa'azi ya tunasar dasu zaman Aure da kyautatawa juna, aka yi musu addu'a suka ajiye ledoji suye baki suka mike shi ya raka su sanan ya dawo ya rufe ƙofa yana murɗa kofar Bedroom ɗin nepa ta ɗauke cike da mamaki ya zaro Phone ɗinsa da zumar ya haska sai jin saukar ƙarfe yayi ta dai-dai wuyansa kara ya saki tare da zubewa ƙasa jini ne ya fara bin ta bayan kunnen sa sai kuma haske nepa ya dawo. Sadiya ce ta ƙaraso in da ya ke a kwance ta fara kuka.kafin ta motsa mutum da ya make shi ya fito ta bayan labule kamar wasa sai ga wasu daga ciki Bratheroom kusan mutane bakawai har na waje 8 a razane Ammar ya sake ƙoƙari tashi Saurayi da ya yane fusakar sa da baƙi hirami ya take masa hannu da iri takalmin boll dinan, yar ƙara ya saki. "Ashh” ɗaya daga ciki ya daka tsalle ya faɗa kan gado ciki zuciya da ɓaci rai Ammar ya dakawa Saurayi tsawa. “You are crazy, you don't respect marriage.” naushi ya kaiwa Ammar a fuska har sai da baki sa ya fashe. “Kai ɗin baza zaka zauna kana gaya min magana son ranka tom kasani baka ga komi ba aciki abin da muka zoyi dan kafi ka fara karɓar haki ka mune zamu karɓa, daga baya ka samu... Wani iri ihu Ammar ya kurma ya nufi inda Saurayi yake ciki zafi nama matasa biyu suka fusgo Ammar ya faɗo kasan Carpet har sai da ya saki yar ƙara. "Dama kawai muyi abin da ya kawo mu mu wuce gani mu a haka yake gani kamar zai iya damu” Dariya wanda aka kira da Dama yayi. "Hahaha Baushe bar shege ai na fasa sumar dashi kafi mu aikata abin da ya kawo mu dole yaga komi akan ido sa sai mu farɗe ta zamu tafi dan Ubansa” Ritse ido yayi hawaye masu zafi suka gangaro masa,Sadiya tana taji haka ta ɗora hannu aka. "Wayo Allah nashiga uku shike nan ni tawa ta ƙare dan Allah ku temaka kumin rai wallahi bana so kowa ya taɓa ni sai Balarabe miji..... "Jini da shegiya manya yariya tom ki sani ni Dama nine ango ki na yau kuma ko macewa kika yi, yau ɗin nan sai nayi abin da aka samu” "Nashiga Uku ni Sa...”wata muguwar Fusga Dama ya mata tare da jefa ta kan gado Batar re da kunyar saura maza bakwai da suke guri ba haka ya hau tuɓe kayan jikin sa ya faɗa kan Sadiya, Ihu Ammar ya kurma tare da zubewa ƙasa sumame. *Giɗaɗo* Cikin dare A firgice Sumayyah ta farka kirjin ta yana dukan uku-uku. “Inaalillahi wa'inaalaihi rajun Ya Allah duk A halin da Yaya Ammar da Sadiya suke Allah ka kubutar dasu Allah kaji kansu,” Numfashi ta sauke, ta dafe dai-dai saitin zuciyar ta lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka. “Me yasa nake ji kamar wani abu na faruwa da Yaya Ammar da Sadiya taya zan fita na sanar da Baba wanan mugun mafarki danayi??” Wata zuciyar ta tuna mata."Sumayyah ina rabaki kada kije ace ko ba haka bane kizo kiji kunya, ki sani ba ko wane mafarki ne yakan zama gaske ba.” Tajima tana jin bugu zuciya sanan ta miƙe ta nufi banɗaki Alwala ta ɗauro ta gabatar da Sallah raka biyu da yiwa Ammar da Sadiya zaman lafiya da Zuri'a na gari. Sai da maza bakwai suka afkawa Sadiya kafi na takwas ɗin ne Dama ya dakatar da Shi ya ɗauki ruwa ya watsawa Ammar a furgice ya farka a kwance Ya samu Sadiya da Alamun ko numfashi bata yi, kan bed ɗin tamkar anyi ado da jini farin blacked ne amma ya koma ja. Ido sa ya rufe lokaci da ɗaya saurayi ya kwanta kan Sadiya.ido sa na zubar da hawaye me zafi ya fi Sa'a biyu sanan ya miƙe yana miƙa sai da yaran suka fita, Dama yazo gaf dashi ya miƙa masa wani gwangwani. Kallo Ammar ya bisa dashi ɗaure fuska Dama yayi. “Malam karɓi kasha bana so na azabtar dakai ta hanyar duka shiysa na sama poisoning kasha Hankali kwamce zaka ji komi na jikin ka ya daina aiki” Ciki razana Ammar ya kalle shi.."Wa..wa..wa...ne yake son halakani da matata dan Allah ka sanar dani ni dai nasan bani da wata alaƙa daku?” “Hahaha Yaro man kaza Ka sani fansa ce kuma wanda yake tare da kune ya turo mu anyi mana biyan da baka isa mu karɓi naka kuɗi ba sanan ka sani Wallahi na sake baka, baka amsa ka shaba Tom tabbas zan kira ƙarti mazan can su taka ka yadda lakar ka zata daina aiki ga kuma azaba da zaka sha” Lumshe ido Ammar yayi tare da karɓa sai da ya shanye sanan ya yi cilli da da gwangwani, dariya Dama yayi ya ɗauke gwangwani ya fice.... [1/22, 6:16 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-26 Yana sha Ko 2 minte baiba ya zube a ƙasa jikin sa yayi sanyi, baki sa ya rufe, hawaye ne kawai yake fita daga ido sa, wani iri zafi da kishi Na Kama masa gashi bashi da damar tashi yaje inda Sadiya take kwance,yadda yaga rana haka yaga dare Sadiya kam har bayan Sallah Asuba bata farka ba haka Ammar idon da yana kan bed dinsa sadiya take kwance. Tun guri Karfe biyu Bacci ya kauracewa Ummu tashi tayi a tsorace. “ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakil”Abi da yake gefe ne ya tashi ciki damuwa ya kama hannu ta “Lafiya Ummu me yake faruwa ciki dare?” "Abi Amar Wallahi wani mugun mafarki nayi tabbas Ammar yana ciki wani hali dan Allah katashi muje” “Com dwon mana Me yasa kike haka ne rashi sabo ne kin manta yau ya shiga sabuwar rayuwa addu'a zaki masa a hankali zaki....” "Ab...Abi dan Allah ka tsaya ka fahimce Ni Wallahi wanan ba rashi sabone ko wani abu ba tabbas jiki na Yana bani Ammar yana ciki wani hali dan Allah me yasa baza ka tsaya ka duba magana taba” Sosai ya sassauta murya ya fara kwantar mata da hankali ciki nutsuwa har ta rage tsoro da fargabar da take, Bathroom ta faɗa Alwala ta dauro tayi sallah raka'a biyu ta jima tana addu'a da kai jikanta guri mai duka akan Ammar da matar sa. Sallah Asuba ita ta tashe ta bayan tayi Sallah Kitchen ta shiga dan haɗawa Ammar break fass shida Amarya sa. Sai 8 ta fito lokaci Fu'at yazo bayan tasa A cikin Vaskeet ta miƙa masa yana ammasa zai juya ta dakatar dashi. "Fu'at ka jira tare zamu” Cikin dariya ya fara zolayar ta. "Haba Ummi ki bari rana ta ɗaga sai kije Wai tun yau har kin fara kewar Ammar ɗin?” “Fu'at ba zance ne na kewa ba ko zumuɗi kawai inaso naga yadda... "Babu inda Zata Fu'at maza ka wuce kace wa AMMAR ya kira tsohuwar nan ta kasa samu salama saboda baya gidan” Abi na faɗi haka Fu'at ya fice yana dariya Da sauti Ummu ta shige Kitchen dan Ita da gaske gidan Ammar zata shiga. Tun asuba da Sumayyah ta tashi tayi Sallah bata koma ba jiki ta duk asanyaye yake Allah-Allah take gari ya waye taji kiran Sadiya ko hankalin ta ya kwanta. Tun da Fu'at yaje baki gate yake Aiki Horn amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa tsaki ya doka gani mai gadi yaki zuwa ya buɗe masa gate da kansa ya buɗe dan yaga da alamu a buɗe ƙofar take yana buɗewa ya koma cikin motar ya shiga yana isa parking space ya gara parking baya ya bude ya dauki Vaskeet din ya fita ciki isa ya tunkari ƙofar parlo da mamaki sa sai ya tarar da buɗe sallama ya fara jin shuru kuka gaba daya hankali sa ya kasa nutsuwa yasa ya danna kansa cikin parlo hankali sane ya sake tashi ganin kowace kofa abude kuma kamar ba dai-dai komi yake ba da sauri ya tunkari bedroom Ammar ya fara karo dashi kamar gawa ido sa ya kai kan Amayar Ammar da sari ya kwalla ihu tare da ja da baya ido sa ya kaɗa ya yi full. Parlour ya dawo yana jan Kafa da kar wayar sa ya janyo yana ƙoƙarin kiran Ummu kiran ta ya shigo hannu sa na rawa ya ɗauka. “Hallo Fu'at na jira Ammar Bai dauka ba ka karasa ka bashi waya.?” “Hallo Fu'at kana jina kuwa.?” Wani miyau ya haɗiye mai ɗaci Muryar sa na rawa. "Ummu... Ummu kina... Ummu dan Allah ki taho ke da Abi ki yanzu.” Yana faɗi haka ya katse kiran. A gigice Ummu ta hausa samma a hanyar fitowa suka haɗu da Abi jikin ta na rawa da sauri ya kama ta gani tana niyar faɗuwa. "Me kuma ya faru?” "Abi Dama sai da nagaya maka Akwai Matsala yanzu Fu'at ya kira ni yace mu taho akwai matsala” Duk da yashiga matsanancin tashi hankali amma baibari ta gane ba ciki dabara yace. "Tom bara na kira shi Fu'at din kije Parlour ina zuwa” Da sauri ta ɗauki mayafin ta da Handbag ta fice Wayar sa ya fido ya kira Fu'at 2 miss Call sanan ya ya picking. "Hello Fu'at me yake faruwa ne?” “Abi dan Allah kuyi sauri kuɗi Yanzu haka na kira police station suna kan hanyar zuwa ina tunani wasu ɓata gari sun shiga gidan Ammar Anyi repin dim matar sa” “ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakil”yana faɗin haka ko katse kiran baiba ya fito a firgice bai samu Ummu a Parlour kasa ba yana fita Compound ya same ta sai Safa da marwa take bai yarda ta gane halin da ya ke ciki ba guri Mansur drive yaje ya sanar dashi yaje gidan surukan Ammar ya ɗauko mahaifiyar ta da mahaifinta, suna fita Mansur ya fice. Gudu yake cikin 20 minute sai gasu a gidan ammar,Ummu bata jira Abi ya gama parking ba ta ficewa A tsakiyar Parlo Ummu ta iske Fu'at ƙoƙarin shigewa Tayi Fu'at ya sauri rike ta ido sa na fitar da hawaye. "No..! Ummu dan Allah kar ki shiga yanzu 'yan sanda zasu zo suyi aiki.... Tsawa ta daka masa “Me yasa Fu'at Ammar ne fa da matar sa sun kashe min shi ko Nasan ya mutu Inaalillahi wa Inna ilahi... "Dan Allah Ummu kiyu shuru bana tunani Sun mutun sai dai Halin da suke ciki ne ya yi.... Tura shi tayi da ƙarfin ta. "Matsa ka bani guri dole naje magana Ammar ko a wane iri hali yake” Bata sake tsawa saurare saba lokaci Abin ya shigo tare da D.P.O da sauran ta wagar sa tana shiga ɗaki kan Ammar ta fara kai ido ta tafi zata jiniga shi ta hango Sadiya ƙara ta ƙwalla zata zame ta faɗi Abi ya tare ta ta faɗa jikin sa, Nuna sadiya ta fada. “Abi Kalli ruwaye waɗan nan?wane mara tausayi ne Me yariyar nan tayi musu...?” *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-27 Bai kula taba sai kamo ta da ya yi suka fice daga ɗaki Mata ne 'yan sanda suka shiga bince kafi suka rufe Al'aura Sadiya Ammar kuma maza biyu ne suka saka shi amota gaba tare da Sadiya suna ƙoƙari fita Malam da Baba Zulai sai Yusuf suka iso ciki kaɗuwa ta fara tambaya ko sadiya ta mutum ne Tsakani Ummu da Abi Babu wanda ya iya bata Amma sai Mace 'Yan sada ta ce. "Baiwar Allah har yanzu tana raye sai dai zamu je Asibi domin likitoci suyi nasu bincike dan Allah ki kwantar da hankali ki kinji” Kai ta girgiza tana matse kwallah da baki zani ta A motar da Aka kawo su a motar suka nufi asibiti.Tun da suka isa aka fara dukufa kan bince Saka mako Safiya ne ya fara fito. Doctor ya kira iyaye Sadiya da Na Ammar sanan D.P.O Bayan su zauna ya gyaran murya ciki kwantar da Hankali yace. “Da farko ina mai baku haƙuri bisa wanan iftila'i da ya afku Labarin mara daɗi, a bincike da mukayi Ba iya mutun ɗaya ne ya keta hadin taɓa Mutane ɗai² har bakwai zuwa takwas wanda hakan zai iya je fata.... Kwaran Da Baba Zulai ta ƙwalla ce ta zube ƙasa tana wasu iri surutai yasa Doctor dakatar da bayani da yanke da Alamu Baba Zulai Aljanu take Yusuf ne Da Baba Malam suka fitar da ita aka bata ɗaki gudu. Ummu kuwa banda sunan Allah babu abin da take an bato, komi ya tsaya mata suwaye suke san Hallaka yaro ta da matar sa Adare su na farko waye yake son gani bayansu..?”tambayar da bata da Ammsa take Sallmar wata Nurses ce ta dawo da hankali kowa kanshi Sakamakon Ammar ne ya fito ammasa ya yi sai da ya maida Fari Glass ɗinsa ya duba takardar da take ɗauke da bayani sanan ya ajiye Ummu ya kallah yaga shi take kallo tausayi ta yasa ke kama ta ya sani tun Ammar yana yaro shine Doctor su zabbaɓi comment in AMMAR yana yi Hankali ta sai ya tashi na wani ma ya tashi, bare taji abin da ya samo yaro ta. Gyaran murya ya yi. “ehamm A Gajiya Dan Allah ko zaki bamu guri sabo... "Doctor Mutuwar Ammar ɗin ce baza ka iya sanarwa agaba na ba sai na fita?” yadda tayi furci ciki karaya yasa shi girgiza kai. "No Ajiya, Amma ina gani kika fita.. "Doctor kayi bayani ka Babu abin da Zai faru na riga falwalawa Allah al'amura na” “Masha Allah Alhaji Haƙikani Gaskiya ko suwaye sun su bawa Ammar Poisoning ma'ana (Guba) wace takan iya shafar gabobi da dama a jikin ɗan Adam,gwargwado irin gubar, da Adadin ta da hanyar da ta shiga jikin.” “ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun”Abi yake ta maimaitawa Ummu kam hawaye kawai take maganar ma ta kasa, maganar Doctor ce ta katse kowane daga iri tunani da yake. “Sai da Muce Allahmmdullilah saboda shi a bince da mukayi bai samu rikicewar ƙwaƙwalwa ma'ana(Brain) ko rikicewa tunani, Ana shi bincike da muka samu Ammar ba zai iya motsin ba sai an dage guri kula da lafiyar sa sanan ida nusa sun riga sun juya su tsaya guri ɗaya amma duk abin da za'a ce xauki damar magana ce kawai babh sanan zaku ci gaba da taya shi da addu'a dan A halin da ake ciki addu'ar kuce kaɗai mafita. “ Allahuma ajirni fil'musibati wakilni khairai minha” Cewat Ummu da take ta mase hawaye, Abi ne yayi ƙarfi halin cewa. “ Doctor zamu iya shiga mu ganshi shi da matar tashi” "Yariyar dai Yanzu ana kan yi mata ɗinki da ƙara mata ruwa zuwa ajima zaku shiga” Godiya suka masa suka fita lokaci da suka fita aka fito da Ammar daga room ɗin gashi da aka shigar dashi ɗaki hutu aka kai shi. Ɗakin hutu suka shiga gaba ɗaya, kowa zuciyarsa cike da raɗaɗi. Ammar yana kwance a kan gadon asibiti, na’urar numfashi na amsa aikinta, idanuwansa a akafe, fuskarsa ta rame fiye da yadda aka saba ganinsa. Ummu ta durƙusa gefen gadon, ta kama hannunsa duk biyu tana shafa shi tamkar. “Ya Allah… Ammar ɗana, ka bashi iko cin wanan jarabawa” ta faɗa cikin kuka mai karya zuciya. Abi kuwa yana tsaye gefe guda, idanuwansa sun cika da hawaye, gani Ammar kwace babu inda yake motsi aikin sa,amma da yake namiji ne dole ya riƙe kansa. Ya ɗora hannusa kan kafadar Ummu. “Ki yi haƙuri Ummu, komai daga Allah yake, kina daɗa ɗaga masa hankali.” A ɗakin daban kuma Sadiya tana kwance, ruwan drip na shiga jikinta a hankali. Baba Zulai zaune a gefenta tana karanta Ayatul Kursiyyu tare da face majina da baki hijab ɗinta, Yusuf kuwa yana yawo a ɗaki ya kai mari ya kai gwaro. “Wannan wane irin jarabawa ne Wallahi Babar mu nafi tunanu wanan Yar Mahaukaciyar da sa hannu ta aciki ture ne wanana baza mu yarda ba” Yusuf ya faɗa yana girgiza kai. Baki Malam na kufa saboda Azabar yinwar da yake ji ya fito tun farar sabiya bai karya ba tasar cewa. "Yusuf Fatana Kada Sadiya ta mutu duk wani buri na Ya dori akan yaro nan Allah yasa yaro nan ya riga ta tafiya ko masa mu gado” Da Sauri Yusuf yace. “Ameen dai Baban mu, Amma ban taɓa gani masifa iri wanan ba daren aurenta?” Bayan wasu mintuna Nurse ta shigo ɗakin da Ammar yake kwance. “Dan Allah lokaci ya yi, zamu kai shi ICU domin kulawa ta musamman.” Miƙewa Ummu tayi ta riƙe hannun Ammar da ƙarfi kamar za a ƙwace mata shi. “Allah Ya duba ka ya baka kafiya Don Allah ku kula min da shi, shi kaɗai nake da shi.” Kai Nurse ta girgiza cike da tausayi. “In sha Allahu, za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu.” Suka tura gadon Ammar zuwa ICU, Ummu da Abi suna binsu a baya, sai da suka isa ƙofar room aka dakatar dasu aka rufe ƙofar.A Respect ‘yan sanda ne suke tattaunawa da D.P.O, suna rubuta bayanai, suna tambayar masu gadi, kowa yana ba da nasa labari cikin ruɗani. Numfasawa D.P.O yayi Ya dubi S.P. “Wannan ba fashi na dare kawai ba,Wannan shiri ne tun da dadewa.” Abi da tsaiwar sa kenan ya kalleshi cike da tsoro. “Shiri? Kana nufin akwai wanda ya san Ammar? Ko yake ƙulla masa wani mugu abu Tom wane zaiyi wa ammar haka?” D.P.O ya ɗan ja numfashi. “Za mu bincika komai. Daga maganin da ya sha, zuwa mutanen da suka shiga gidan.” Ummu da ke tsaye gefe guda ta jikinta ya yi sanyi. Ta tuna mafarkin da ta yi a daren jiya. Hawaye suka sake gangaromata “Ya Allah… ka nuna mana gaskiya, ka tona asirin masu mugunta.” Dan-danan Labari ya yaɗu asibitin ya fara cika da jama’a. Kamar wutar daji, labarin abin da ya faru da Ammar da Sadiya ya watsu cikin dangi da abokai. Motoci manyan mutane suna jerin gwano ɗaya bayan ɗaya, zuciyoyi cike da fargaba. Alhaji Ɗan Dubai ne ya shigo har da matar sa fusakar da gaba ɗaya ta gama bayyana tashi hankali yana tsaiwa ya kalli Abi. “Abi, me ya faru ne, Allah yasa dai Ammar yana raye?” Alhaji Ɗan Dubai ya tambaya cikin rawar murya. Kamar wanda yake jira ya gunza ihu “No ka kwantar da hankali ka AMMAR insha Allah zai tashi yana raye, kuma Alhamdulillah, amma yana cikin wani hali mai tsanani, Ammar yana bukatar addu'a mu.” Suna ji haka, matar Alhaji Ahmed Ɗan Dubai ta saki kuka, tare da zauma kan kujerar tana bugun ƙirji. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji‘un! A daren aurensa kuma?wanne wace iri masifa ce Ita ina ita amrya ko tana wanne hali?” Babu wanda ya kula ta saboda Da ‘yan uwan Ammar su fara zuwa ‘yan uwa na jini da na ne da wanda suke mazauna Kano haka dangi Ummu suma duk sun kewa asibiti,Kowa tambaya yake yi, kowa kuka yake yi, amma babu wanda ke da cikakkiyar amsa. Ummu tana zaune a kujera, hannunta a ɗauke da tasbihi, bakinta na motsi da zikiri, idanuwanta sun kumbura da kuka. Ba da jimawa ba, daga ɓangaren Sadiya ma labari ya isa gasu Sumayyah da Baba Hauwa haka suka hauwo abin hawa suka zo Asibiti, Lubna da Sumayyah sunyi koka sosai dan sun shiga sunga Sadiya A halin da take cike ciki. Karshe Nurse hana shiga tayi guri Sadiya. “Dan Allah kuyi hakuri da fatan za a yi haƙuri, marar lafiyar tana bukatar hutawa.” Wata daga cikin Innar Sadiya ta yi magana da murya mai cike da zafi, da masifa. “Wane irin zalunci ne wannan?A dake mu kuma a hanamu kuka wallahi Allah ya tunawa Duk wanda yayiwa Sadiya Asiri?” Sauran dangi suka amsa da Amee. A gefe guda,manyan mutane ɓangare Ammar sun taru kusa da ICU. Wasu na addu’a, wasu na kuka, wasu kuma zuciyarsu ta cika da fushi. Wani ƙani Ummu mai Suna Masuwar yace. “Wallahi duk wanda ya aikata wannan, aiki sai ya fuskanci fushin Allah!” Abi ya ɗaga hannu ya ce. “Ku kwantar da hankalinku. Wannan ba lokaci ba ne na hayaniya, lokaci ne na addu’a. Da Addu'a Allah ya tona musu Asiri ko suwaye”Da Ameen suka Ammsa, sanan kowa ya koma ga Ubangijinsa. Alhaji Ɗan Dubai kam duk wanan haukar da yake bai kula da Sumayyah ba a tunani sa Sumayyah ce kwance buri sa Ya mutu shikenan buri sa ya gama cika ko yaji ta farfaɗo yaje ya faɗa mata shine sikar shigar ta wanan hali sanan ya karasa kashe ta... [2/5, 11:40 AM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-28 *Kauye Gidaɗo* Baba Hauwa ce da Lubna suka shirya don zuwa Asibitin Kofar ɗaki Su Sumayyah ta tsaya ta kira ta."Sumayyah ko zaki? ki fito muje kiga hali da take ciki?”kai ta ɗaga. "Eh Baba zani bara na wanke kafa ta sai mutafi ” Tom tace ta fita, Sumayyah tabi bayan ta wanke jikin ta tayi sanan ta saura kaya awaje ta samesu Sunjima sanan suka samu abu hawa. Malam ne da Baba Zulai sai Doctor suke gudu zuwa room ɗin da sadiya take kwance kuka Baba Zulai take tana kwaɗa ihu suna zuwa kofar aka dakatar dasu Doctor yashiga gudanar da aiki sa. Sai da ya shafe 1 hours ya fito yana yakice gumu Malam ya kira lokacin ya yi dai-dai da Fitowar Abi daga room din da Ammar yake tare suka shiga Officer din Doctor sai da yayi rubuce-rubuce sanan ya dago ya kalle su. “Da Farko ina me baku haƙuri domin yariyar nan ta gamu da Gang rape (ma'a fyaɗe na kungiya , ma'ana mazaje fiye da ɗaya sun haɗu sun tilasta wa mace yi abu ba tare da yardarta ba.) Wanda ya haifar mata STIs ma'ana matsalar ƙwaƙwalwa,da yawan tsoro da firgici,” Doctor na tsaigata zance sa Malam ya kurma ihu. " Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun Shikenan Sadiya yanzu duk buri ki bazai cika ba Wallahi da zanga wanan mutane da Kashe su shine mafita agare Ni tsinanu na Ala.... "Assalamu alaikum Abi wai Wanan mutum shi kaɗai aka ilata yake tamana surutu baya gani Ammar ko tashi yar yar Gwal ce da duk zai shi... "Dan Allah Alhaji Ahmed kayi shiri tariyar Abin a tausaya mata ne dama Haka Allah ya ƙaddara akanta wanan abu zai faru bakan marainiyar Allah wace Mahaifiyar ta Ta jingina da ita Sai gashi Sadiya ya Allah kabawa Sadiya Lafiya ka dub iri zalunci da akayi wa barwar ka Ka tona Asiri wanda suka aikata mata wanan mumunan aiki” Ras gaban Alhaji Ɗan Dubai ya buga Muryar sa na rawa ya fara tambayar Abi. "Alhaji..wai... Wai..me naji kana faɗa ne kana nufi dama Ammar ba Sumayyah ya aura ba wata ce daban?” Kai ya jinjina. "Tabbas Ammar ba ita ya aura a lokacin da Kuma je Ɗaura aure........Ni kuma na gargaɗi kowa kan kada a sanar da kowa barshi a haka” " Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar³” Sai da ya mai-maita sau uku sanan ya fita yana yarkata gumi yana zuwa respect suka hadu da Sumayyah da Baba Hauwa da Lubna da suke neman ida ɗaki Sadiya yake sai ga Gaban Alhaji Ɗan Dubai ya sake bugu gani Tabbas ba Sumayyah bace saboda kaɗuwa da tashi hankali baisan Lokaci da suka bar guri ba fita ya yi ya fara kiran number Dama duka uku ya ɗauka. "Hallo....!hello..!! Dama ban taba sani kai mahaukaci kauye bane sai yau da kasan ba yariyar bace shine baka sanar dani Dama Wallahi ka guji haɗuwa ta dakai Sai na kashe ka sai ɗai-ɗaita rayiwar duk wani dangika tsinanene ɗan Haram” Dariya Dama ya bushe da ita. “Hhhh karya kake Ɗan Dubai na daka na ba da ruwa uban waye yasan yariyar in ba kaiba.” "Dakata ƙarami ɗan iska duk abinda kaci nawa dai-dai da nera ɗaya ka dawo da abu na Nabaka nan da awa 2” Dariya Dama ya sake bushewa ya yi, cikin kaukausar furci ya ce. “Ahamed wallahi yadda aka n manaci ya mutum baya dawowa Tom naci kuɗi nan kasani duk yadda kakai da tauri rai guri kazo kuma duk wani shiri da zaka yi na riga ka yi shashashan banza da yofi” "Haka kace Dama zan nuna ma Ni kwallo shege ne zan nuna maka na fika zafi kai kasani Ni rayiwar Lagos nayi kai ka faɗan ina kaje abariki.” “Matseeeeee Shasha tsohon banza” Yana faɗi haka Dama ya katse wayar. Kafa yayi yana juwa suka yi ido huɗu da Abi rassss kirji sa ya buga kame-kame zai fara Abi ya dakatar dashi da zaiwa. "Alhaji Ahmed ko kaga Fu'at jiki Ammar ne ya motsa wai karkarwa yake zasu shiga dashi ICU Shine na fito ne mansa.” Idanuwan sa ya Lumshe tare da saki wata ajiyar zuciya.ya saki murmushi godiya da Allah. "A'A Alhaji ai tun da mukazo ban sake gani sa Amma Alhaji har yazu ina jinjina lamari nan yanzu Ammar ya auri wata ba Sumayyah ace nakasa samu labari. Batare Da Abi ya tanka masa ba ya koma cikin hospital yabar sa yana bige-bige waya. Bayan Sun Sumayyah sun fita daga gida babu jumawa Ɗaki Innar Sumayyah da ya tsage ya fara buɗewa,babu kowa a gidan sai Inna ciki hukunci Ubangiji gaban dagi ya shafece ya zube, ba tare da ya danne kowa ba ihu Inna take na kiran sunan sumayya da haka moƙota suka riƙa shigowa dan temaka mata wasu matasa ne guda biyu suka fitar da Inna gidin maina tare shifiɗa mata buhu ta zauna. Khalil ne ya shigo Baba Hauwa ya kira ya sanar da ita abin da ke faru Umarni ta bashi yakai Inna ɗaki ta, sanan su kwashe buliluka su kaisu gefe guda da haka suka yi sallama bata sanar da Sumayyah gudu karta ɗaga hankali ta. Tare da maƙota aka rika fitar da kasar da har suka kwashe tass shawar suka yanke su haƙa fandisho kafi Malam ya dawo zaiji daɗi haka. Haka kuwa sunayi dan danan da Almajiran Malam suka fara haka ana ciki haƙan Ililu Almajiri Malma ya haƙo wata leda mai rubutu har da turare a ciki babu wanda ya sanarwa ya zare ya zura cikin aljihu sa ya fita, a babban zo zaure ya tsaya ya fito da takar dar takarda ce ta farraƙu mai dauke da sunan Ammar da Sumayyah salati yake yana jingina rashi imani na Babba Zulai sai gashi Allah ya sakawa Sumayyah abin da suka aikata ya koma kansu. Gabaɗa yan gidan Malam ne a zaune a respect kowa zance zuci yake wani na Aiyana alkairi wasu akasin haka Nurses ce ta shigo. “Ina 'yan uwan Sadiya zaku iya shiga ta farfaɗo , Amma dan Allah banda yawan surutu.” Hamdallah sukayi suka tafi jiki babu ƙwari, tun da suka shiga Sadiya take zubar da hawaye, Malam da Baba Zulai ne jiki gado suna aiki yi mata saunu, ciki harɗewa murya ta fara kiran sunan Sumayya. "Sumayyah zonan.. Zonan dan Allah?”Jiki babu gwari Sumayyah ta ƙara sa baki gado hannu ta miƙa mata. “Sadiya Yajiki naki Allah ya baki lafiya Insha Allah zaki warke ki koma gidan ki ciki Aminci” Katse ta tayi da cewa. “Sumayya ba wanan nake bukata ba yafiyar ki nake nema da ta mahaifiyar ku na sani mun cutar daku ko iya hakin ku bazai bari na rayu ciki salama” Kuka Sumayyah ta fara. "A'a Sadiya ni bantaba ruƙe ki araina ba Wallahi na yafe miki har abada Allah ya baki lafiya kijin” Goge hawaye ta tayi tace. "Dan Allah in na mutum ki auri Ammar dama miji kine ba nawa ba,muka shiga muka fita Ni da Batun sai da muka raba gashi na aure shirye sai dai haka bai zame min alkairi ba” Da gudu Sumayyah ta fita tana kuka kallo ta Ya maida kan Baba Zulai. "Babarmu dan Allah ki tuba ki koma ga Allah wallahi wanan ishara ce Allah ya nuna mana tun anan duniya mun azabat da Innar Sumayyah da Sumayyah mun hana tayi rayiwar jin dadi yau gashi muda muke gani mun samu duniyar bata da Ana fani a dare Aurena agaban miji da na aura maza bakwai sunyi min faɗe sun yiwa zuciya ta baban ila wanda mune mukajawa kanku zunibi da muka aikata ne yake biyar mu, kisani ki da zan rayu sau dari zan mutum sauri saboda mijin da na aura zai riƙa kallo na da wanan abi duk da nasan bama rayuwa zan yiba. Kuka Babba Zulai take tana kifta mata ido, Murmushi takaici Sadiya tayi. “Babanmu kaine kashi bayan duk wani abu da muke aikatawa kaine ka daure mana gidan muci zarafi baiwar Allah nan tun da na taso ban taba gani kayi wa Inna kallo mace ba baka taɓa yiwa Sumayyah kallo 'yar da ka haifa ta a ciki kaba, kaine silar ciwo Inna, kaine ka wargaza gidan ka da kanka Shim wai wane iri uba muke dashi da yake ƙirƙiran malami kaci Ammar mahaifi Inna tabba Allah bazai barkuba.” Tana faɗi haka ta fara firgita tana fisge-fishe da haka doctor ya kora su waje. Bayan sati ɗaya Allahmmdullilah jiki Ammar kullu kara samu sauƙi yake dan Har likita aka kira daga waje har ya fara sarrafa jikin sa kuma yana iya furta ɗai-ɗai, Doctor ya kira Ummu da Fabi da Fu'at da zai riƙa kula dashi gida zaune suke suna jiran cewar likita. Bayan sun gaisa ya fara gargaɗi da cewa. "Da fargo sai mugodewa Allah subhanahu wata'ala domin Ammar ya auna arziki ba karami ba sai dai ina gargaɗi ku, ba kowane abinci zaku riƙa bashi ba sai wanda muka umarce ku dashi. Kamar.Shayi mara kauri,Pap/custard, sai shinkafa mai laushi hankali turawa, kayan lambu, ku guji mai maiyawa aciki, da Yaji, abinci mai nauyi har sai mu sake dubawa” Godiya suka yiwa doctor sanan ya dauko wata farar takarda zan rubta wanan magunguna sai a karni a pamis zaki riƙa bashi Vitamins (B-complex)saboda taimako jijoyoyi, da kuma kariya daga ciwo hanta da koda.zamu haɗa ku da kwarare likita wanda zai riƙa masa gwaji (monitoring& tests) da Blood test, Urine test,ECG, CT-EEG, wanda bama fata , insha Allah nan da Wani lokaci indai abin dokar likita after 1 month ma zai dawo dai-dai.” Hannu Abi ya bashi sanan ya nufasa yace. "Doctor ita fa yariyar naji kace ta haɗu da tsoron da firgici kuma har yanzu banji kuna faɗi mataki da Za'a ɗauka na gargawa ba.... [2/5, 1:09 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-29 Maganar ta domi Allah sai mun haɗa da rokon Allah cutar wace an riga an zutar da ita ba'yi reping ɗinta dan ta rayuwa ba ayin ne dan ta rasa rayuwar ta gaba ɗaya sai dai muna baki ƙokarin mu insha Allah zata warware baki ɗaya” Tashi sukayi jiki babu kwari, sai da suka shiga ɗaki Sadiya suka mata yaji sanan suka miƙe kamar daga Sama suka ji maganar Sadiya. "Maman Ammar...!!”Da Sauri Ummu ta dawo dan gaba ɗaya tausayi Sadiya take gani take kamar Aure Ammar ne ya ja mata.zama yayi ta kama hannu sadiya. "Ɗiya ta Sadiya me ya faru kina son wani abune?” Shirin hawaye da ya gangaro mata ta sa gefe hannu ta ta goge. “bana son komi sai neman gafara Ammar na mucutar da shi mun rabashi da wace yake so yake kauna mun rabashi da farin cikin dan Allah ko bana raye ina neman Alfarma ki roƙamin gafara guri sa,.”da sauri Ummu ta rungume ta wasu hawaye masu zafi ta goge ta sau saita murya. “kar ki damu insha Allah zaki tashi ki koma ɗaki ki, kuma ki Sani tun kafin zuwan mu Duniya Allah ya riga ya rubuta al'amari sa wanda babu wanda ya isa ya goge kisani da ke Da Ammar da Sumayyah wanan zane ƙaddara kune dole kuma sai ya faru, babu wanda ya isa ya goge ki ne mi. Gafara guri Allah maji roƙo bayi sa insah Allah zai yafe miki, Allah yayafe mana baki ɗaya” Kai ta jijina Ummu ta miƙe ta dubi Baba Zulai. "Yanzu Fu'at zai kawo muku abinci Zuwa Yamma dan dawo” Godiya tayi da Sa albaka sanan Ummu tabi Abi mota wance Har da AMMAR aciki. Tunda da suka shiga mota abubuwa suke dawo masa sabani Hoton Sumayyah yake dawo masa gaban sa na tsanan ta faɗuwa sai dai ya kasa manya lokaci da yake cewa Sadiya yake so ba Sumayyah ba wani waye ne ya zubo masa wanda Fu'at ne ya lura da hakan ƙasa yayi da Muryar yace. “yaya dai ko jikin ne?” Kauda kasa gefe yayi dan baya bumatar jin komo daga baki kowa buri sa suje gida. Su Abi na fita Sumayyah da Lubna suka shigo cikin Asibiti lokaci da suke shiga ɗaki da Sadiya take Lokacin Babba Zulai ta fara rafka Sallati. “ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakil ƙaluu Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun me zan gano Sadiya..! Sadiya dan Allah ki tashi kar ki mutu mi barni wallahi duk Ni najawo don Abun duniya na da gani cewa Sumayyah naza ta hutaba gashi na kashe 'yata da kaina” Da gudu Sumayyah da Lubna suka ƙarasa cikin ɗaki gani Sadiya a sankame ido ta akafe tana kalli saman ɗaki zaka san tafiya tayi nisa Lubna na ɗora hannu aka zata kallah ihu doctor da Nurses guda biyu ruka shigo kora su sukayi waje suka hau gwaje-gwaje babu bata suka tabbatar da rai yayi halinsa. (Allah sarki Sadiya ashe cuta bata tashi ba Allah ubanji ya yafe miki Allah yasa mutuwa tazama hutu agre ki dama musulmi baki ɗaya. Shi yasa akullum ake so ka riƙa aikata alkairi baka san Sa'id da zata zoba ko kana tafe ka da ciwo ko babu) Bayan sun gama tabbatar wa Doctor ya fito da gudu Baba Zulai ta tare shi. "Ta mutu ko Likita Ni dama nasan tun da tayi Salati Nasan ta mutum?” "Dan Allah Hajiya kiyi mata Addu'a duk wani musulmi in ya rigamu gidan gaskiyar addu'a yafi bukata ba koke ko.... Kafi doctor ya kai ƙarshe Baba Zulai ta sulale ƙasa asume Lubna kuwa tana guza ihu ta hau aljanu Sumayyah kuwa hawaye take da furta sunaye Allah. Sai da suka juma ahaka Yusufa ya shigo ciki kaɗuwa da tashi hankali tunda yaji abin da ya faru ya fara kiraye kiraye waya Fu'at ma da shigowar sa kenan Abi ya sanarwa da rasuwa tuni suka ɗungumo zuwa asibitin. Cikin ƙanƙane lokaci asibiti ya cika koke-koke da Aljanu babu kalar wanda dangi Baba Zulai da masoyan ta basu baya kwanar Baba Zulai Ramatu ce ta guza ihu ta taho da gudu ta shaƙi wuyan Sumayyah. Tana Magana iri ta masu iskokai. "Sai kinci Ubanki kece kika tira mutane su illata Sadiya da mijinta saboda kina baƙi ciki bai aure ki wallahi sai kin faɗi gaskiya ko mucilla ki uwa duniya, Yiiiiii Ayyyyyyy baizai yuyu ba” Da sauri Baba Hauwa ta je inda Ramatu ta shaƙe wuyan sumayya. “Haba Ramatu ya kike magana kamar ƙugurmar Jahila” "Ki daina kiran goɗiyar mu wanna Ba Ramatu bace Sarki fatake ne aguri nan” Ummu da shigowar kenan ta daure fusakar ta ko tsoro Babu ta tsaya gaban Ramatu. "Malama cikata in ba haka ba Wallahi sojajin da suke baki geta su fitar mana dake banda shirka da so sai Kum bata gawar mamaciya so kuke sai kun sake jamata wani abu mutuwa daya dan Allah in har kaunar ta kuke kumata addu'a kuma duk wanda yasan hayaniya ta kawo shi mun gode kowa ya tafi” Tafiya ramatu tayi zata fadi sai ta fara jera Ashitawa sau biyar. Abin ne suka shiga cikin da Malam da Yusuf da Alhaji Ahmed (dan Dubai) sai Khalid suka fito da gwara Safiya suna wucewa da ita mata aka kaurewa da kuka da Masu Salati har aka shigar da ita anbulas. Nan masu tara keke napep da masu mota kowa ya faraw hawa sai gidan Abi. Babu jumawa labari ya karaɗe duniya sharare atajiri nan surukansa ta rasa ranta wanda babu wanda yasan dalilin rasuwar nata dan ma'aikata basu bada kofar sani haka ba tunda Aka kai gawar Sadiya Ɗan Dubai yake shige da fito so yake Sumayyah ta fito koda Compound Ni yasamu damar da zai jata dan yayiwa kansa al'washi itama sai ya muzanta tata. 05:0pm akayiwa Sadiya Sallah jana'iza sai dai Babu wanda yayi karanbani sanar da Ammar haka abokan sa duk sun hallata ko da ya gansu yayi mamaki gani su Atare sai dai cewa sukayi sun masa baza tane dan zuwa duba shi. Bayan kwana biyu duk wasu hujoji Hukuma ta gama tantarawa akan gidan ammar da Aka shiga wanda babu wanda yasan da bincike da ma'aikata suke. Baban Parlour kasa Baba Zulai ce da tawagar ta kana gani ta zaka san tana ciki tashi hankalin mutuwar Sadiya kuma ta dake ta zance take da ƙasa Sumayyah da Lubna har dasu ake aiki in ma'aikata gidan Ummu zasu aiki abincin. Yau Laraba gidan Abi cike yake da Al'umma an gudanar da Sadakar Uku sadiya A masallaci da karfe 11 na safe wanda ya samu Halartar manyan Malamai da Kusosin gwamnati duk wanda ya yi gaisuwa sai ya duba Ammar kokadan ya ki buɗe baki yayi magana tun da suka dawo sai daga daki ya rage daga shi sai Fu'at danan ya buɗa laɓansa daƙar yace. "Ummu nake so gani Please Fu'at kira min ita” Duk da mamaki ya cika sa Amma umarni ubangi dan sani duk akwai abota miƙewa ya yi ya kuwa ta ciki al'umma ya je Parlour da Ummu take amsar gaisuwa ya kira ta. Da sallama suka shiga yana gani ta wasu hawaye masu zafi suka sulalo masa hannu sa ya ɗora kan nata. "Ummu na gasa gano me ake boye wanan manyan mutane duk namaye?ina Sumayyah duk da na kasa manta yadda naki aure wanda bansan Dalili ba ina ita wace na aura suwaye suka turo a kashe Ni Ummi ina yariyar da suka yiwa rayiwar ta baban illa Ummu kunsan kuwa Sumayyah aka turo ayi wa haka wanda ina zargi Alhaji.... Maganar Alhaji Ɗan Dubai ce ta dakatar da shi wani kallo tsana Ammar ya bishi dashi.dariya Ya saki. "A barka Ammar kace ka tashi ya kuma ƙarin hakuri na rashi matarka kai Allah ya la'anci wanan bakaƙe kafuran da suka yiwa Amaryar ka raga-raga wai Ammar kai... “Alhaji dan Allah ya isa me ya kawo ka” Ummu ta faɗa tana tsare shi da ido. "Abin ne yace na kira ki sarki labani ne yazo gaisuwa so an iske bakya Parlour baki sai akace kina daki ammar.” "Ok tom kaje ina fitowa sanan dan Allah a riƙa sani iri maganar da za'a faɗawa mai jiya” "Shikenan hajiya tuba nake ayi min afuwa Allah ya tashi kafada” Yana fita Ummu ta rage tsayi. “Ammar kayi Hakuri wanda yafi mu don Sadiya ya Amshi abarsa sai dai ka mata addu'a sanan insha Allah bama tunani zasu wuce yau ba'a kama su ba dan an kama huɗu daga cikin wanda suka aikata laifi” Kai ya jingina sanan Ummu ta fita, kallo Fu'at ya yi. "Fu'at Sumayyah fa tana nan ko tana gari su?” “Ranka ya dade tana nan”' Shuru ya yi bai sake cewa komi ba Sai 12 sanan sarki labani ya tafi da tawagar sa bayan jim kadan sai ga motar police data D.E.S kyatatace naman kaji da ruwan robar da Alhaji Ɗan Dubai yake sha ya kurɓa ya yagi cinyar kaza. "Alhaji kai dai Allah ya baka bawar Al'uma yau kuma har da Jami'an tsaro a gaisuwar”yake Abi ya yi tare da miƙe. Parking space suka ajiye motar sanan Ma'aikata biyu suka fito suka bude motar da ake zuba masu laifi Zan'zaro Dama aka kama aka nufe manyan rufunar da suke Compound wata iri zabura Alhaji Ɗan Dubai ya yi gani Dama a hannu su ƙoƙarin zurawa yake da gudu ya fita daga gidan Wani police yace. “ You are under arrest.” [2/9, 11:25 AM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸* Mallaki: Husaina S Abdullah (Oummu Muwaddah) 📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya. ____________free book _page-30 *END* Samma yayi da hannu sa ɗaya daga cikin police ɗin ya kamashi zai saka shi amota ya dakarat da shi kusa da Abi ya koma. “Alhaji Wallahi karda ka yarda da mutane na karya suke mi shari ne da makirnaci kai Dama a ina...... Sak ya yi tare da rintse ido jin ya furta sunan Dama, shi da yaso ya lakabawa wani gashi ya tonawa kanshi asiri guri kama sunan Dama kai tsaye. Ummu da fitowar kenan ciki ta kaici da karasa inda Alhaji Ahmed Ɗan Dubai ya ke zai fara mata rantse-rantse ta ɗauke da wulakantace mari guda biyu. "Me yasa Alhaji Ahmed Alhaji ya dauke ka tamkar ƙani sa, ya baka.matsayi babba,me yasa zaka yiwa yaro da haifa haka wanan wace iri kiyayya ce me Alhaji ya maka” Kansa yayi kasa dashi tare da tisa keyar sa batare da ya ce mata komi, suna shiga Abi yace. "ASP MUTAKA DUNBULUM kuje zan biyo ku daga baya Nagode da kokarin ku” Godiya shima ya musu sanan suka tafi, ciki Ummu ta koma shikuma Abi da Babban Aminisa Alhaji Umar sai Malam suka bisu bata tsaya ko ina ba sai bedroom Ammar yana zauna ya kafe dan karamin hoto Sumayyah wanda ya mata amota lokaci da yaje zance da kallo motsi shigowa ne yasa shi binta da kallo har ta nemi guri ta zauna. Gani yadda fuskar ta ta sauya da alamu har kuka tayi yasa shi cewa. “Ummu me ya faru” Murmushi karfi hali tayi. “Ammar Duk yadda ka dauki wani amatsayi masoyi Sai ya juye maka ya koma makiyi shiyasa aka ce ba'a guziri masoyi da makiyi Ko mafarki bana tunani Alhaji Ahmed zai ci Ammar Abi ko ta yaro da ya haifa ashe buri sa ya lalata rayiwar Abi da ta yaro sa me yasa me wasu muta ne suka dauki Duniya ne??” Huci ya furzar tare da magana jijiyoyin kansa duk sun tashi. “Ummu duk laifina nane, laifina ne da na boye muku halin,da mugun Ayunkan sa da yake aboye, ummu rashi imani Alhaji Ahmed ya kai har safarar ƙanani yara yake yana kaiwa manyan mutane Lagos Ummu yara ƙananu Ummu ko kin san Sumayyah ma daga hannu sa na karbo ta?” Sosai Ummu ta girgiza da iri mugun dabi'u da Yaro miji ta ya ke aikatawa.Sai dai yanzu tayi farin ciki da asiri sa ya tonu ko ba komai an ceci wasu 'ya'yan faɗa tarko sa. Abi ne sai Malam da Asp Muntaƙa, sanan Alhaji Ahmed Ɗan Dubai da tawagar sa Matasa shida wanda ake kan nemo maza uku duk abu da ake zargin su dashi sun ammasa agaban Abi da Malam Sule, Abin ya kalli Asp. “Asp duk wani hukunci da ya dace muna roko a zartar musu muna so abiwa yariyar haki ta da na miji ta” Yana miƙewa Alhaji Ɗan Dubai yace "Wani na rasa wane ɗan bur...ne ya tona min asiri Ni dai nasan daga Ni sai ku muke waya Dama wallahi kasani in ma kaine ka ɗana min tarko saboda nasa anemo ka akashe kasani kayi abanza dan Ni dan nada manyan mutane nasan duniya natara kaine zaka kwana aciki” Murmushi ta kaici Abi ya yi ya koma ya zauna ya kira sunan Alhaji Ahmed Ɗan Dubai. "Alhaji Ahmed ka sani Babu wanda ya tona maka Asiri kasani Allah baya bari zalunci tun faga lokaci da abin ya faru la fito kana waya da Mutane ka ka tuna lokaci da nazo ka nuna kamar na gano ka nace Fu'at nake nema tom kasani tun da ka fara magana nake tsaye amma saboda ido ka ya rufe da bakin zalunci baka san da zuwa naba tun daga sanan na sanar da hukuma suka fara bibiyar ka har na'ura naɗar magana da aka sanya maka ba sani ba wanda shine ya temaka muka kai ga kama sauran abokan ta addaci ka” Yana fadin haka ya fice. Bayan sun koma Yamma nayi Malam da iyalan sa suka ce zasu koma gida Roƙo ummu tayi da Abar Sumayyah anan sanan zata sa a ɗako Innar ta saboda zata fara gani likita Baba Zulai an koma ga Allah yanzu dan ko magana bata iya yi mutuwar Sadiya ta dake ta, har da kayan abinci suna tafiya bayan Sallah magariba Ummu ta bata abincin ta kaiwa Ammar sai da ƙirji ta ya buga bata nunawa Ummu ba baban tire ta ɗauka ta nufi daki da Sallama ta shiga Fu'at ne ya Ammas Ammar kam kamar me bacci lumshe ido sa ya yi dan kunyar haɗa ido yake da ita. “Yaya Fu'at ina wuni ya me jiki?” “Lafiya Lau Sumayyah jiki da Sauki ya kuma karin haƙuri Allah ya mata rahama?” "Ameen Mun gode Gashi Inji Ummu tace na kawo” “Oky babu matsala ki ajiye kan Centar teble mun gode” A jiyewa tayi tana fita Ammar ya bude da ido sa ido suka haɗa da Fu'at saki fuska yayi. "Kai ashe guny ɗin nan ba bacci yake ba Amma da ka bude ido ka ko Hauswa ai sai ta maka” Dogo tsaki yanar tare da kawar da kansa gefe. Tsayi sati guda haka suke Inna kuwa duk ta canja Ana kaita Asibiti duk bayan kwana ɗaya ta rage yawan surutu marasa ma'ana ga yawan bacci da take samu ga cima mai kyau ɗaki guda aka ware Musu. Bangaren Kauye Gidaɗo kama Abubuwa ne suke su tabarbare. Baba Zulai kullum ciki surutai Malam na ɗinka mata rubutu da tofi a gani su firgici mutuwar Inna ne lamari har ya fara basi tsoro suru take ita kaɗai gashi kullum furucita kan asiri da tsubiu ne baki ta baya taba faɗi al kairi Wani lokaci kuma sai tayi dariya kamar me hira da wata dan-danan zance ya karaɗe kauye kowa yana tofa albarkacin bakinsa. *Bayan wata biyar* Fu'at ne ya kamo hanu Ammar izuwa Parlour jiki ya yi kyau sai dai tafiyar ce bata gama kwari ba Jiki Inna kam Allhmdllh dan ta daina surutu kuma magana take ciki natsuwa in ka ganta baza ka taɓa cewa Innar Sumayyah ce ta canza, baza kace ta taɓa ciwo hauka ba dama damuwace ta jefata.Baza kaɓa cewa Innar Sumayyah ce a, Sumayyah tana kasan Carpet kusa da Ummu wasa take zobe hannu ta na Azurfa ƙamshi turare Ammar wanda jiya bata ya gushe shi ya fara ciki Parlour da Salam suka iso da kallo suka bisu Sumayyah ce kaɗai ta kasa ɗaga masa do ta kalleshi dan tafi karfi sati biyu bata shiga bedroom ɗinsa ba tun da ta fuskanci daga ta shiga yake rufe idon sa ta daina shiga. Bayan ya zauna sun zauna Ummu ta yi gyran murya tace. "Inna dama kece baki sani ba lokaci baki da lafiya bayan Allah ya rubuta Ammar Sadiya ce matara sa Sai muka yanke hukunci akan Sumayyah ta auri abi Tom Allah da iko sai Wannan iftila'i ya afku haka ya janyo tsaiko so yanzu kuma,Allahmmdullilah sai mu sanya ranar Aure sai aje asamu mahaifin ita Sumayyah mune mi amincewar sa” Wata iri mutuwar faduwar gaba ce ta riske Ammar da sauri ya kalli Sumayyah da kanta yake ƙasa, sai ka ɗauka aciki nutsuwa ta, ba zato yaji Inna nacewa. “Nikam Babu abin da zance daku sai Fatan Allah ya saka da Alkairi ya yauƙaƙa arziki da kwamciyar hankalin Wallahi Ni dai na amince ” Godiya Ummu tayi ta kalli Abi tare da Saki Murmushi. "Abu Bakace komi ba?” Miƙewa ya yi fuskar sa babu yabo babu fallasa yace. “Allah ya zaɓa abinda yafi Zama alkairi” Yana haurawa Samma Ammar ya zunguri Fu'at ido sa yayi jaji saboda tsanani ɓaci rai da firgici a ƙsanan makoshi ya masa magana. “Fu'at zaka fitar dani daga nan ko sai zuciya ta taga tarwatsewa” Tausayi sa Fu'at yaji tabbas daga kasan zuciyar sa yake furta maganganu nan cikin sanyi rai ya kama sa suka bar guri wanda babu wanda ya sani. Suna shiga ya saki kuka kamar karamin yaro. "Why Fu'at me Ummi take son dani taya yariyar da naso ace zata auri Abi na, kenan zata dama second mother's ɗina no....” “Com down Ammar zamu sa Su Ummu su janye baka lura da abin shima bai gamsu da maganar ba Ummu ce kawai take so haɗa wanan aure.” Cikin tswa yace. “No..!no..! Fu'at itama yariyar tana so tana so ta ɗauki fansar abin da na mata ne ta hanyar aure Abin,wanda Wallahi ban san lokaci da na furta hakan ba Why wallahi bancan-caci haka aguri ta” “Sorry Bro dan Allah ka samu nutsuwa Insha Allah komi zai dai-dai” "Fu'at baza ka gane ba, Wallhi har yanzu ina so Sumayyah but dan Allah duk yadda za'a yi kasa tashi bedroom ɗin yanzu Please ” Ya ƙarasa maganar ciki karyewa zuciya.Kai Fu'at ya ɗaga masa Phone dinsa ya ciro Call ɗin Ummu yayi babu jumawa Ummu ta dauka. "Hello Fu'at lafiya kake kira bayan kana cikin gidan?” "Am..Amm... dama..dama Ummi nace Ko Sumayyah tana kusa dan Allah drinks ɗin mu ya kare so ina taya Ammar alwala ne shine nac ta ko zata temaka mana dashi” Murmushi tayi a filin kuma sai tace. “Ayya sorry bara nasa Jamila ta kawo muku muna wani aiki a kitchen” Bata jira me zaice ba ta katse kiran.ido suka haɗa da Ammar ya ɗage masa gira. “wai tana taya Ummu aiki a kitchen rai dai Jamila” “Hmm baza ta barta ba Ummu tana son hukunta Ni da Abin da Ni kaina ban san taya na aikata ba, Please Fu'at dan Allah ka fita duk yadda za'a yi kasa ta shigo 10 minutes zan gane in har yanzu tana sona ko a'a ” Miƙewa yayi dole ya fitar yana fita suka haɗu da Jamila yar aiki hajiya da sauri ya tare ta. “Jamila..! Jamila dan Allah ɗan tsaya” Dakatawa tayi ta kafe Fu'at da kallo sai da ya waiga yaga babu Alamun kowa sanan ya yi kasa da Muryar sa. "Sumayyah da?” “Tana Kitchen zata dauki Abinci Innar ta.” “Ok ita da Ummu ne ko ita kaɗai” Sai da jamila ta waiga taga mai Fu'at yake waige taga babu sanan ta dawo da hankali ya kanshi. “A'a Ummu ta haura Samma zata huta” Hamdallah yayi."Please dan Allah ki mana wani temake ki kaimata wanan lemo da kika dauki kice ta kai ɗaki Ammar ky zaki haɗa Abi kunu” Sai da tayi dumm kamar bata gamsu ba Ya haɗe hannun alamu roƙo. “ Please Jamseee dan Allah” Tafiya tayi tana cewa. "Ni dai Wallahi Yaya Fu'at babu ruwan kaine kasani” Naji ɗin.yace sanan ya samu bayan labule ya maƙale sai da aka dauko wasu daƙiƙi sanan Sumayyah ta fito jiki babu kwari.handles ta murɗa tare da Sallama a tunanin ta Fu'at yana ciki ta shiga babau kowa Sai Ammar da Ya kafe ta Da Mayu ido sa ko kiftawa baya yi ɗauke kanta tayi a tunani ta bacci muzuru yake ido abude. Har ta gama jerewa zata miƙe yace. “Sumayyah ki amice ki auri Abina Saboda nayi miki laifi” A tsorace ta waigo dan tun da Ake cewa yana magana ita bata taɓa jiba tun da ya samu lafiya sai yau gani ta kafeshi da ido yasa shi miƙe wa da sandar sa sa yake dogarawa taku ya yi har daf da ita kamar zasu manne da juna yasa ta yin baya.wani muskil murmushi ya saki. “Na zama abin gudu ko sani na gama nakasa gashi girma ki ya wuce ki tsaya dani” Da sauri ta kalleshi ido ta da yake kokarin anbaliya ya fara fitar da ruwa. Kafin tayi magana ya sake magana. "Dan Allah Sumayyah ki yafe kuma ina son ki janye aure Abi ki sani shi ɗin da baba nane kuma ko ba komai ai..... “In ban Aure shiba wa kake so na aura, Shi yayarda zai zauna dani Kuma Ummu.... Jikin sa ne ya ɗau rawa idanuwan sa suka rune zuwa jajaye. Zai sa ake magana ta sake cewa. “Bazan iya bijirewa Ummu ba tayi min halakci dan Allah ina neman Afuwar ka.” “Sai dai in dama can ba sona kike ba, Taya Sumayyah zaki amince da Abin da bakya so nasani har yanzu nine zaɓi ki kuma kina kauna dan Allah ki faɗawa Ummu nine wanda kike so ba Abi ba” Dariya tayi mai tafe da Hawaye. “Kana so na zauna da Miji yar uwata haba dan Allah Ni baza iya ba Kaima Allah. Wata iri fusga ya mata ta faɗo jikin sa da yake na mini ne duk da rashi kwari kafa hakai baisa ya faɗi fa ciki kaukasar murya yake.magana. “Amma ai Aure bai Haramta ba Tinda ita yar uwar taki bata raye Meye yasa kike da tauri kai Samma da ba haka kike ba” Ture shi tayi daga jikinta. "Wallahi Ni bazan iya watsawa Ummu kasa a ido ba, kuma zan koyawa kaina son.... Nauyi Maganar taji sai kuma ta fashe da kuma mai cin rai ta juya zata fita taji murya sa. "Tabbas zaku iya rasa rayuwa ta matukar kika auri abi ina so kuma ɗan Allah ki yafe duk iri laifi da nayi miki zuciya ta tana min wani iri zafi da bana jin zan iya kaiwa... Da gudu ta faɗa jikin sa. "Ka daina faɗi haka haka ma Sadiya ta faɗa gashi ta rasu ta barmu na yarda zan faɗawa Ummu bana so Abi kaine duniya ta ya kai dan ƙare rayiwa ta Ina sonka,bazan taɓa bari kana, inda zanyi zaɓe so dubu kaine wanda dan zaɓa I Love so much Yaya Ammar. Kasa daurawa yayi sai da yayi hugging din ta ya mana mata pick a hannu sun juma a haka suna sauke nunfashi a hankali ta fara zare jikinta daga nasa ido suka haɗa ya akar mata murmushi da yasa jikim ta bada wani yarrrrr ƙoƙari gudu take ya dammake hannu. “Ina zaki bayan ban gaya miki yadda zaki ce da Ummu” Kare fiskar ta ta fara da ɗaya hannu. “Yaya Fu'at fa zai iya shigowa” Ƙaramin tsaki ya saki. “Tunda Fu'at ɗin mahaukata dole ya shigomi ɗaki babu izini” Shuru babu yace ƙala n sanan Yace. "Duk yadda Ummu taso kice Ni kike so Ni zaki aura kinji in tace mu haɗu kice tun farko dawowa na bamu haɗu ba” Ido ta zaro waje. "kai Yaya Ammar karya da kenan tasan fa ina zuwa kawo muku abinci.” "Haba Sumayyah karyar ceto Ammar ne fa dan Allah kice zaki yi” Kai ta ɗaga masa da sauri yace. “Yawa Oya Let's go” Fita tayi shi kuma yabi makeke gado ya kwanta yana lumshe ido akan ido Fu'at Sumayyah ta fita da sauri ya faɗa. "Wallahi Ammar ya kusa tona mana Asiri yanzu da Ummu ta fito ta same ku fa” “Sai kuma gashi bata fito” Tsaki Fu'at yayi ya zauna. Kitchen ta koma ta dauki Abinci Innar ta shiga nasu bedroom turus tayi gani Innar ta har ta gama cin nata ta idar da Sallah magarib jiki babu kwari ta zauna. "Inna ta wai har kinyi me?” “Ke gafara ki bani guri wai ina kika shiga ne Ummu ta turo kiran ki bakya nan” Dariya ta ƙwakwallo. “Wai Ummu har ta manta ta sani kwaso kaya baya shine da naji isakar guri tamin dadi na zauna” Shuru Inna ta mata bata sake cewa komi ba. Bayan Sallah Isha Ummu ce ta shigo ta same ta tana gyarawa Innar ta guri kwanciya tun da ta ganta Gaban ta Ya faɗi, “Sumayya aiki kike Oya kawo Abi na Compound ina jiranki zaku tattauna” Miƙewa Sumayyah tayi tazo gaban Ummu ta zube. “Ummu dan Allah kiyi hakuri akan abin da Zakiji daga baki na Wallahi bazan iya aure Abi ba Ina masa kallo uba ne, Ummu ya kamata aduba iri halin da Ammar zai... “dakata Sumayyah shi Ammar ɗin bai duba iri Halin da kika shiga ba ya auri yar uwarki dan Haka mun gama magana babu fashi gobe in Allah ya kamu za'a ɗaura aure duk wasu surutu ya ƙare.” Ƙara Sumayyah ta gunza. “Wayo Allah Shikenan zan mutum Dan Allah ummu an karki rabani da Ammar Ni wallahi shi nake so dan Allah ki tausaya mana” Cak ta tsaya tana kallo iko Allah yau Sumayyah ke magana iri haka tabbatar Akwai sanya hannu ammar dan ta lura kullum yana yana saka mata dance Sumayyah tana basarwa wato shine daga ji maganar aure shine shi kuma zai yi mata tasa huɗubar.da sauri ta ajiye blanket ta fice, Inna da take zaune kam kujera tana kallo iko Allah ta mike kiran Sumayyah tayi tana zuwa ta dauke ta da mari. Tana murɗa handles ta samesa a tsaye fitowar sa daga wanka kenan. Daure fuska tayi. “Ammar me kace da Sumayyah, shi ka manta Maihaifinka ne yake nemana aure ta” Sai da Ammar ya rintse ido tare da Haɗiye yawi mai ɗaci kamar bashi ya ce. “Ummu akan me kike magana me Sumayyah tace wanda na zama abin tuhuma?” "Wallahi Ammar zai mare ka kar kaga baka da cikakiyar lafiya Yariyar nan ta amince tun da jumawa yanzu kuma tace ba haka ba.” Kamar yaro goye ya kamo Hannu ta. "Haba Ummu Com down Wallahi I don't know ko Fu'at zaki tambaya ji da ita bamu magana” Zama tayi kan kujera ta daidaita Muraya. "Ammar dan Allah karkayi haka ne yasa kake so mai damu kannu mutane.” Zama ya yi yadda da gaske zata yarda dashi yace. "Ummu da kuna maganar ku dazu nasa muku baki?”kai ta girgiza."Tom me yasa baki yarda dani ba ki faɗan ita fasawa tayi?” "Ammar na shiga Ruɗani taya za'ace Mun gama magana yanzu dakar nasa abi ɗinka yayarda zai je Compound wai dan su fuskanci juna Amma ina zuwa ta furje wai ita akwai wanda take so bashi ita Uba ta ɗauke shi. “Tom ummu ku barta mana yanzu fa ko dan da ka haifane ba'a masa dole kuma shi kanshi Abi fa cewa kikayi daƙar kinga kenan baya murna da Haɗi kawai kubuta wanda take so.” miƙewa tayi a zafafe "Wallahi bazai yuyu ba Sai dai na sauya mata da Fu'at dan Wanda take so har yanzu bata rashi nikaum” "Wane ya faɗa Wallahi ummu ina sonta a kullum santa karuwa yake Please sai yanzu saki fuskanci damuwar Ɗanki Ummu” Sai da ya faɗa kuma yaga ta gafe shi da kallo kame-kame ya fara. “uhum..Ahhh.ummu kada fa kimin mummunar fahimta bawai yana nufi nine na zuga ta ba” Ficewa tayi bata re da tace komi ba. Dafe kumci ta tayi wasu waye masu zafi suka shiga gangaro mata. “Sumayya kin manta Halaccin Ummu a gare ki,ki tari tsabar ido ta kice kin fasa so kike duniya ta zage mu so mu zama masu don kanmu, me yasa baza kokari rama halaci ba.” Ciki kuka Sumayyah tace. “Inna ta In har Zan kamanta Adalci da kaunar, Ammar ya kamata na nunwa yayi ɗawainiy dani ya jefar rayiwar sa ciki haɗari duk raboda Ni kisani ciwo da ya affaka da Cin zarafi da akayiwa Sadiya duk nice Sila Dan Allah Inna ta ki bari ko yaya ne na zauna da Ammar na kamanta kaunar da sadaukarwa da ya min” Tana faɗi haka ta zube a guri ta saki kuka mai tsuma zuciya. *BANFAI* Alhaji Ɗan Dubai ne da shi da tawagarsa aka tsaryar dasu gefe guda kuma Asp Muntaƙa dunbulum ne aka kafa masa camara bayani ya fara. “ Assalamu alaikum kamar yadda kuka sani suna Asp Muntaƙa dunbulum mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jahara kano wa ɗan nan mutane da kuke gani ana zarginsu da aikata manyan laifika karkashi sashi na ɗari uku da goma shabi..gamar yadda kuke gani sun shiga gidan mata da miji ta sun aika fade tare da zubawa miji poisoning wanda sukayi kokari hallaka mijin a karshe matar tarasa ranta” Juyara da Canada akayi kan Dama. “Kai zaka iya fada mana yadda akayi kuka shiga gidan da dalili zuwanku kuma me yasa kuka aikata hakan?” “Ni Alhaji Ɗan Dubai ne ya bamu kuɗi shi ya kaimu gidan ma tare da kashe mana wutar gidan sanan muka shiga shi ya faɗa mana yadda zamu in mushiga mu bamu tunani shi Namiji zai rayu ba” Akayi daga kan Dama aka maida kan Alhaji Ahmed Ɗan Dubai nan ya bada labari duk abin da ya faru da dalili yi musu haka. Bayan sati biyu kotu ta yanke musu ɗauri rai da rai sanan kutu ta bada umarni ake gidan da ya ke aikata haramci sa arushe gidan a gina kato masallaci.Soaai Alhaji Ɗan Dubai ya shiga tashi hankali atunani sa bazai jima ba zai fito sai gashi babu wanda ya nemeshi gudu kar sunan su ya baci. Ta jima tana kuka hakan ya sa Inna ta jin babu dadi, a hankali ta jata jikin ta ta fara rarashi ta, cikin shasheƙar kuka tace. “Inna dan Allah karki rabani da Ya Ammar wallahi har yanzu son shi bai dishashe a cikin zuciya taba, Ban taba Kallo Abi a matsayi Wanda zan Aura ba sai Uba Agare ni taya zan iya rayuwa da mahaifina matsayin miji” “Shikenan naji Allah yasa hakan ya zama alkairi gobe In Allah ya kaimu zan koma Giɗaɗo zan nemi mahaifin ku da ya sauwaƙe min dan Bazan iya zama dashi ba in Allah ya kaimu zan nemi haya ko wanko ne na rika yi” Sai da Sumayyah ya buga lokaci da ta furta rabuwa duk da tasan babu zama a tsakani ta da mahaifi nata.nisawa tayi tace. “Inna dama...Fa..Uhum. Babanmu tun lokaci Bikin Sadiya Baba Zulai tasa ya sauwake miki yanzu babu sauran zama atsakani ku baki ga bai taɓa zuwa duba ki ba” Ta faɗa ido ta na cukowa fall da hawaye, Murmushi tayi ta shafa bayan ta. “Auta Karki damu Allah yasa hakan ya zame min alkairi Amma duk da Haka gobe zan koma can na nemi gidan na zauna kafi ta Allah ta kasan.... “Dan Allah Inna ta ki daina faɗi haka in kika barni dawa Zan Rayu? bani da kowa faɗi duniyar nan sai ke?” "Haba Sumayyah ki dan Mutuwa dole ce ko mu dade ko mujima dole wataran sai mu tafi” "Insha Allah Inna ta Bayanzu ba Sai na tara kudi na biya miki Aiki Hajji ki ga iri 'ya'yayana” Duk hirar da suke Ammar yana ji su lokaci ya fito ɗauka abu A parlour da yake manne da Ɗakinsu. Washegari Ummu ce da Ammar sai Fu'at zaune A parlour magana suke duk da babu wanda yasan me suke tautaunawa guri suka nema suka zaunar Sumayyah ta gaida Ummu Ammar da Fu'at suka gaida Inna.Duk yadda ya kafe Sumayyah da kallo amma taki kallo sa, bayan jim kadan Inna ta kalli Ummu tace. "Hajiya dama yanzu nake cewa zan koma ƙauye mu saboda zama na bazai yuyu anan ba ga shiri biki Sumayyah” Murmurshi Ummu tayi “Inna in kin koma wa kike dashi Acan sanan Nasan da Ku rabu da Malam ammar kuma ɗaki ya mallaka miki gida Anan Tarauni dan Haka yanzu Fu'at zai kaiku ku gano babu wani gyara da Za'a masa sai dai abu da ba'a rasa ba Yau kuma Abi ya tafi shi da Abokan wa dan neman Aure Sumayyah.” Inna taso ta nuna rashi Amincewa ta wai dakwai kyar tayi yawa Sai Da Ammar ya marairaice kamar zaiyi mata kuka sanan ta Amince. Gidan Ba wai Babba bane sosai sai dai Ya mutukar haduwa komi a kwai aciki ɗakuna Uku ne Sai Kitchen duk wani Kayan more rayuwa akwai aciki kayan sawa ne babu, Godiya ta rikawa Fu'at kamar shine Ammar ɗin Sumayyah kam fita tayi tayi kukan ta ta more ta goge ta dawo suka wuce gida. *ƘAUYE GIƊAƊO* Lamarin Baba Zulai ya dada ta'azara dan Har duka take kaiwa almau hauka ya bayyana sosai banda Kashi da fitsari da take a kwance gashi kanta kam duk ta tsige shi da Hannu Malam kam komi ya tsaya Sai ya kwana uku huɗu babu mutumin da yazo bare ya samu abin rufa wa kai asiri, komai na duniya ya jagule masa, Yusuf kam Yau ya faɗa wani gida ya garƙama Sata sai da suka masa lulus sanan suka yasar da shi abayan gari bayan wasu kwana lalura ta bayanna ciwo kafa ne ya kama shi duka kafa biyu (Bone cancer) wace take zaizaye masa kafa duk yadda yaso Malam ya kai shi asibiti amma furr yaƙi yace ba ciwo Asibiti bane. Bayan wata Uku malam yana zaune Almajirai sa duk sun gudu sun koma wasu garuruwa ya zubar tagumi masu zama ma duk sun daina yafa gani baƙi motoci har uku baisa ran guri sa aka zoba dan atunai sa Alhaji Namadi ne Makocirda yake tashe yanzu ya yi baki, gani motar ta tsaya kusa dashi da sauri ya mike gani Abi, Abi na fitowa ya karaso yana masa sannu da zuwa ciki baban Zaure aka musu shimfida suka zauna bayan sun tattauna Abi yazo da bukatar neman Aure Sumayyah akan Ammar bai isa yace A'a ba dan yanzu yayi nadama gashi baisan ida zai samu Sumayyah ba bare mahaifiyar ta yanemi yafiyarta duk ya iske labari Alhaji Namadi yace ya taba gani ta A yankaba su je siyan kayan miyya da Sumayya da wani yaro sai dai baiyi tunani a gidan su Ammar take zaune ba nunfasawa yayi yace. "Ranku yadade ban tari numfashi kuba Saidai A halin da Ake ciki Bansan Inda Sumayyah da mahaifiyar ta suke ba Tun da akazo aka dauke mahaifiyar ta Itakam Sumayyah tun da akayi Sadakar Sadiya banasn inda tayi ba.” Jinjina kai Abi yayi. "Tom Ahalin Yanzu Sumayyah da mahaifiyar ya duk suna cikin ƙoshi lafiya sai da yardar su ma muka samu zuwa nanan” Fashewa ya yi da kuka. “Allah sarki Sumayyah Allah sarki na cutar da ita da mahaifiyar dan Allah ka kaini na roƙi yafiyarta Wallahi nasan Haki ta ke wahalar dani Komi ya cakuɗe kumi ya lalace yanzu Gidan Malami kamar Ni Ace sai mufi sati Uku batare da An ɗora ko an sauke ba” Hakuri Abi ya bashi sosai kuma yaga nadama a fuskar sa a take a guri ya kira Fu'at ya sanar dashi ya kawo kayan abinci gidan su Sumayya, suna kokari an tsaida Ranar aure Sati mai zuwa saboda Abi yace ba sai ya yi komi ba shima Uba ne ga Sumayyah zaiyi komi, suna ƙoƙari tashi Kani Mahaifi Tanimu da na mahaifiyar sa suka zo dan neman Aure lubna soyaya su tayi karfi Kuma Tanimu yana da Nasibi a kasuwanci wanda Ammar ne aboye ya bashi Jari yace karya sanar wa da kowa hakan, albarka ta shiga cikin Neman sa a yanzu haka shago sa na kayan masarufi uku wadda yake makil da kaya, Hana su Abi yayi tafiya dama ya rasa wanda zasu zo su amshi kudi yar tasa wai mugun halin sa yasa kowa ya guje shi tare dasu Abi aka amshi kuɗi Lubna da sa rana wata shida abi ya yi magana. "Ban tari nufashi kuba Amma zanso Ace an haɗa aure ta dana yar uwarta dan Allah amin wanan alfarma” Kanin Mahaifin Tanimu ne yace. "Alhaji Kasan shi yaro maraya ne Allah nema ya duba shi wani Yaro Ammar suruki Shi Malam Sule saboda temako da yayiwa Mahaifiyar Sumayya ya dauki Makudan kudi ya bashi Allah yasa masa albarka shine yake gini abin da yasa muka nemi wata Shida lokacin yayi dai-dai da gama Gidan sa da Yake kasan Abinka da Maraya babu matallafi Sai Allah” Ya ƙare Maganar yana dariya. "Nuna ko dan Saboda Abin da zanyiwa Ita Lubna dole sai nayi ɗan bige-bige zan so Bar nata wata shidan” “Alhaji Bashir ne Ya tare zance. “Insha Allah na daina nayi kayan daki yariyar duk wani abu da zava bukata na dauki nauyi” Zubewa ya yi har kasa yana godiya,Abi yace. “Kar ka damu shi kuma Yaro zan Sa Yaro na Fu'at yazo yaji abin da ba akarasa ba sai ayi insha Allah duk bazai gagara ba” Godiya sukayi zasu tashi Yusufa ya fito yana jan gindi ihu yake tun ƙarfi sa Azabar ciwo na cin sa har ya dangana ga Baban Zaure. “Babanmu kamin rai wallahi gara a yanke kafar nan da wanan Azabar” Surutu yake yana kaiwa kafar yakushi duk da Ɗumamewar da guri yayi da wari amma Abi baiji tsantsamin saba haka ya kama sa ya sa Wasu mata sa da suka leko zaure kallo Yusufa su kama shi amota aka sashi zasu wuce dashi Asibiti Khalid aka kira daga guri leburanci da yake ya shiga ya riƙe Yusufa. Basu tsaya ko ina ba sai Cikin Hospital dan-danan dashi wani ɗaki bayan wani lokaci doctor ya fito Abi ya sanar sai dai fa Acire kafafu dan duk sun tashi daga aiki, Malam yasa Khalid ya kira dan neman Amincewar sa, batare da shawara ba ya Amince, Abi ne da Khalid suka sa Hannu aka shiga dashi Tiyata. Sai da Aka shafe awa biyu aka fito da Yusuf kafafuwan sa duk sun koma dungulmi ita guwar sa zuwa ciyarsa ne kawai bata taɓu ba, sosai Khalid ya dada mika lamurran sa ga Buwayi gagara misali, tare da Tasbihi. Har bayan Sallah magariba Sumayyah dasu Inna basu dawo ba, Abi kam ya dawo ya sanar da Ummu halin da Yusuf yake ciki ya sanar ayi musu abinci a kai musu,ita ma Ummu ta tausayawa Yusuf bayan Abi ya haura sama Ammar ya kira Fu'at. "Malam kana ina wai har yanzu baka dawo da Sumayyah ba” "Gani nan zan shigo Parlour sai na gaya maka yadda mukai” Zai sake magana sai ga Fu'at ya shigo da kallo tuhuma ya bishi ya gane me yake nufi amma sai ya share. "Ummu sannu da gida” Yawa Fu'at ya gajiyar ka Allah ya saka da Alkairi.” "Ameen Ummu” Zama ya yi yana kokari daukar romot ya dallah masa Harara. "Ina Sumayyah kazo kake wani basarwa” "Tana Gidan su mana kasan dai zamanta anan ai ya kare sai dai akawo ta Matsayi mata.” "Me sarai kasan fa ba cikakiyar lafiya gare niba kuma sai ka barta acan taya zan rika zuwa hira kafin Sati” Dariya fu'at yayi. “Wallahi guy ɗin nan kana lokaci 1 week baza ka jira ba, sai ka tashi ka koma can da zama kasan Ummu baza ta lamuci haka ba Yawa gobe zanje gidan su Sumayyah zan kai musu abu sanan zanje guri yaro da zai aure yar uwarta ya bani sako,So Bazallah zai zo ya zauna dakai.” Baki ya tabe ya ɗauki sandar sa ya haura sama,washe gari da wuri Fu'at ya shirya dai kai sako Abi dana Uncle Bashir murna guri Malam har da kuka, Tanimu ma da Innar da harda kuka basu san Wace iri godiya zasu yiwa wanan bayi Allah ba wanea ta silar Sumayyah da innar ta aka musu duk wannan alkairi. Bayan kwana uku Aka Sallmi Yusufa an haɗa shi da Keke guragu da mashi Wanda yake an fani da na'ura godiya da neman yafi babu iri wanda Yusuf baiba Ana i kwana Biyu biki Ammar yasa aka gyra ɗaki Inna na Giɗaɗo har sabo feti akayi Shida Fu'at suka kaisu suna zuwa kofar cida Malam da Khalid suka kwashi kayan Inna dana Sumayyah suka shiga dasu ciki dandano mutane suka cika ana kallo Innar Sumayyah farin ta ya fito tayi kyau ta zama babbar mace. Har Sumayyah zata fita Ammar ya yi sauri rufe kofar da sauri ta daugo ta kalle shi.Kafe ta yayi da kallo. "Ina zaki ke ko iri kewar nan tawa baki ba kuma kina sani ki gudu ko?” Ido ta fara kif-kiftawa zata magana cikin shagwaba ya dakatar da ita da cewa. "Gobe masu Henna zasu zo da masu Mek up Sai kuma me kike buƙata?” Lumshe ido tayi ta bude ciki shagwaba tace. "Sai kai kaine bana so ka sake kubuce” Hannu ya kawo zai kamata ta zame. "Maye haka” "Kome zaka faɗa ka faɗa amma banda taba ni” Laɓe ƙasa ya cije sanan ya sake lumshe ido. "Ammar naki ne har abada Insha Allah kamar yadda Sai mutuwa zata raba Abi da Ummu na nima ina fatan haka” Zai sake magana ta fice tare da tura masa peck ta hannu, Murmushi yayi ya sa hannu kamar ya amsa ya manna dai-dai saitin zuciyar sa tare da kwanciya kan kujeran. Tana sakar kafarta Baba Zulai ta fito ko zani kirki babu a jikin ta farce duk yayi zaƙo-zaƙo jikin ta kuwa duk sawu farata zube wa tayi tana kama Sumayyah. "Mune muka muki asiri Ni da Sadiya ta muka aurawa Sadiya mijiki kiyafe mana nice Mahaukaciya me kashi a kwace, Ita Sadiya da ka take cin Abinci, Hauwa tana dariya da kafarta” Gani Baba Zulai bata Hayacin ta yasa tayi mata dabar ta zame ta wuce Amina kuma ta kamata ta maida ɗaki Sumayyah kam har kuka tayi ta tausayawa Baba Zulai halin da take ciki. Bayan kwana biyu Sumayya a sake murjewa duk wani haɗi magunguna anyiwa Sumayya da Sadiya Ummu kam Yar Sudan ta dauko dan ta gyra Sumayyah har Lubna tasa akayisa tayi kyau baki ta na kyau, Ammar kam tiri-tiri kira baya bari ta ta huta bayan Sallah karfe biyu shedu suka sheda aure Sumayyah da Ammar, Tanimu da Lubna abinci waja-waja Gidan Lubna ma ba laifi yayi kyau gida ne na zamani har da dan Gate dinsu. Karfe huɗu aka zo ɗaukar Sumayyah kuka ta fashe dashi har da ƙanƙame Innar ta bazata tafiba, gajiya Abdullahi da Bazallah sukayi suka fita waje Ammar da ya maƙale amota yana gani su ya fito yana dogara Sandar sa. "Ya naganku haka ina Sumayyah da yan uwansa?” Bazallah da yazo har wuya dama shi abu kakilan ne yake tunzura shi yace. "Wallhi Ammar bazan sake shiga gidan nan ba Yariyar nan duk ta narke ita auta wai bazata tafi ba Sai anje gobe kamar ba ita ba Haba na gaji ga matan ciki duk inda mukayi suna bin mu da kallo sai kace wasu... Bai kai karshe ba Ammar ya bar guri cikin gidan ya shiga har ɗaki Inna ya shiga sai gani sa sukai [2/12, 10:38 AM] OUMMU MUWADDAH: *YAR MAHAUKACIYYA* 30 *END* DA sauri Inna ta mike saboda surukuta babu zato sai jie tayi an kama hannu ta kokari kaucewa tayi taji ya kara kamma ta,tare da kai bakin sa dai-dai kunne ta ciki raɗa ya ke mata magana. “ Please ki tashi mu tafi itama Innar mu gobe zata koma zuwa dare sai na kaiki ki ganta” Kai ta fara karkatawa alamu bazata ba ransa ne ya fara bacci karfi sa ya tattaro ya damoko ta ya yi samma da ita sauran matan da suke daki suka saka guda tare da dariya hannu ta ya kama suka fice daga gidan ko guri Baba bai nufa da ita.Mata biyu ne suka bishi Kanwar Baba sai makociyar su wace suke shiri da Innar Sumayyah. Tunda suka dau hanya take kuka bai hana taba saboda mutane da suke ciki, suna isa gidan Abi part ɗin Ummu ka wuce da ita Ummu tayi mata nasiha mai ratsa zuciya tayi musu faɗa ita da Ammar, har da ita aka raka su part ɗin su dan abin yace baza su zauna a waje ba sai agida daya. Bayan duk anyi abu da al'ada ta tanadar Ammar ya maida Sumayyah cikakiyar mace, sai dai tasha bakar wahala,ahaka ma dan Ƙafafuwan sa basu gama warkewa ba, Sumayyah ansha raki Ammar kam sai tarairaya yake, washegari Ummu ce tayi musu break fass A gidan Malam kam Inna ta gama shiri ta tana kokarin saka hijab ɗinta sai ga Malam kamar an jefo sa Da sauri ya zube kamar wani yaro da mamaki ta dube sa murya na rawa. “Babar Sumayyah yana ga kina ta shiri hahaha ai nazata kin dawo mana gaba ɗaya.?” Daure fuska tayi kamar ba ita ba."Ban gane ba Malam Tom wa na ajiye anan da zan zauna dama Sumayyah ce kuma bata nan kaga zama bai kama niba” "Dan girman Allah Rabi ki taimaka min wallahi ina sonki dama can shari sheɗan ne ki sani Sumayyah baza ta ji dadi ba duk ranar da tazo gidan bata da guri wanda zata faɗa ya kamata amanta sa komi” Murmushi tayi sanan ta zauna nesa dashi. “Hmm Malam yanzu Sumayyah ai ba Yariya bace kuma duk yanayi da ta shiga abaya bai zame mata damuwa ba sai yanzu, zata saba insha Allah” Rararafe ya fara kamar gurgu matsawa tayi ta kafe shi da kallo.“Haba Rabi mai yasa baki dauka shawara da hausa fa nake miki magana ina so ki dawo ɗakin ki shine magana” "Uhum Malam kenan da farko ina mai baka hakuri magana ta gaskiya munyi magana da Alhaji Bashir aboki Mahaifi AMMAR ai nasan ka sanshi Tom bana so na zama karamar mace dan Allah kayi hakuri ” Dan danan fuskar sa ta canja lokaci guda yaji kansa na juyawa yayi danasani gashi rabi ta dawo yariyar ta kamar lokaci da take budurwa farin ta ya dawo kyawu ta da yarintar ta duk ya dawo, cikin karfin hali yace. “Shikenan Rabi ai baxan ja da mai karfi fa dama taya kina gani.... "A'a Malam kar muyi haka da kai dan Allah ka sani bani na guje kaba kaine ka fara duk kayi ƙoƙari zama dani a lokaci bani da wani anfani a guri ka na gode Allah ya kara arzikin da wata Allah ya bawa Yaya Zulai lafiya kamar yadda na samu tawa” Kokari Magana take wani yaro ya kwaɗo sallama. "Salamu Alaikum Wai Ace Babar Sumayyah tafito Alhaji Bashir ne yazo” .ita kanta Inna sai da taji kunya saboda hakan kamar cin fuskane ga Malam ba zato taji yace. “To..to... Kaje fatan kaji Yara manyan gobe sufa babu ruwan su Allah yasa dai mu dace” Ameen ina tace tana mikewa Malam ya dauke mata Akwati bishi tayi jiki babu kwari a kofar gida suka ga Alhaji Bashi ya harɗe hannu sa Kan Ƙirji sa Mutun fari kyakyawa kana ganisa kasan Addini ya ratsa jiki sa, Bafilatani mai na gaske fusakarsa bata nuna yawan shekaru sa. Gaisuwa sukayi ta mutunci tare da yiwa Malam ishani godiya. Da ƙamshi ya bude mata sai da tayi masa godiya sanan ta shiga motar. Bayan Sati ɗaya yau bayan Juma'a aka daura Aure Innar Sumayyah da Alhaji Bashir wanda ya samu Halartar manyan mutane Abin ne wakili ta shikuma Kabir mahaifinsa. Ammar ne ya shogo cikin gida Sumayyah na zaune ɗaya daga ciki kujeru Parlo goro ya jiye mata masur kyau da sauri ta dauka tana murna cikin nishaɗi ta ce. "Beby na Kasan najima banci goro ba wallahi inaso goro” Harara wasa ya mata tare da kama yatsar hannu ta yana murzawa. "Beby na goro Aure Uncle Bashir ne fa.” Kai Amma nayi murna wallahi dama tausayi yake bani Allah yasa dai wanan aure ya kawo masa shima nashi dan dan wallahi tausayi yake bani mutum har ya fara tsufa bashi da yaro ko daya, bawan Allah Mai kirki dashi” Murmushi yayi tare da yi mata peck a bayan hannu sanan Yace. “kika san waye Amraya” Lumshe ido tayi tayi wa kanta masauki a jiki sa. “sai ka fadan Ni ma ban sani ba” Batare da wata damuwa ba yace."Innar Sarki haƙuri itace” Da sauri ta raba jiki ta da nashi hawaye ta fara ciki mamaki yake binta da kallo gira ya daga mata. "Lafiya me kuma aka mai ki, da ga fadi abin fari ciki sai ki kama kuka” “Haba.beb yanzu saboda Allah taya Inna zata yarda ta aure shi wanan sai ace son kan mu yayi yawa Wallahi Ni yanzu zanje na same ta” Daure fusaka Ammar yayi. "Tab ɗin jan Kaji mu da yariya Tom aure dai an daura kuma tun da kika ce haka ba zaki fita ba bare kije ki daga mata hankali ko kin fiso tai ta zama babu aure, kuma Inna ai baza a sata sahu wanda zasu hakura da aure ba banda ma Rabo ai bata isa haifar kamar kiba” Ya karasa fada yana kokari kamota da sauri ta jaye jiki sa tara hararar sa murya ya daga. “Nafita kinsan abu namu sai inda mai ya kare” Wuni ranar zuciyar ta babu dadi ita gani take kamar za ace kwadayi duk sun aure masu kuɗi ammar kam sai 11 ya dawo lokaci har ya fara bacci. *After 10 month* Parlour sai tashi hayani kasa kasa Parlo ya gaji da haduwa gana gani kasan an kashe kuɗi Ammar ne sai Ummu a gefe da Sanan Fu'at da Matar sa Jamila sai Inna Yara ne jarirai ne ɗaya Hannu Ummu ɗaya hannu Sumayyah kyawawa ne masha Allah Inna ce ta ke saukowa ita Da Alhaji Bashi daga samma ciki kauna suna zuwa Alhaji Bashi ciki wasa yace. “Ranki ya dade Amarya Alhaji Kareem Allah ya ja kwana da sutura daga ke babu kari” Dariya tayi. "Yaran ka dai na jinka kai baka gajiya da zolaya kuma waye ya hana ku kari aure aini na jima da yarjewa dan-dai aboki naka kamar tsoro mata yake” Ammar da Ya saba da jin iri wanan wasan nasu tsamma ya tashi ya koma kusa da Sumayyah peck ya manna mata ita da jariri sanan ya mannawa kato ciki ta. “Beby niƙan bazan yi iri ta Abi ba kina haihu zan sake aure so nake gidana ya cika da yara.” Naushi ta kai masa a ciki ya saki kara. “Ashhhh Ummu Yariyar nan zata kashe ni” Harara Ummu ta masa. “Ammar Akwai abin da kamata da bata maka ba” Baki ya bude zai fadi abin da suke da sauri fara rufe masa baki dariya yake yana cewa."Ummu wai dan nace Ni da wuri zanyi wani aure shine da zata illa ta miki Auta” Kunya ce ta kama Sumayyah tayi kasa da kanta Bayan Alhaji Bashir ya fita taho da kani sa wanda rabon sa da Nigeria Shekara goma sha uku yau yake dawowa saboda yayansa ya samu karuwa wanda tsayi rayuwa da shekara siti da biyar bai samu raboba har Allah ya amshi ran matar sa wanda tsayi shekara goma bai sake aure ba Sai yanzu da ya auri Inna ta haifa masa yara biyu duk maza. Bayan fitar da babu jimawa Ammar ya dawo kusa da Sumayyah. "Beby na tashi mu tafi gobe kya dawo” Narkewa tayi. "Beb inaso gani Uncle Sagir da Aunty Rahama yanzu fa zaka gansu dan Allah” Kusa da ita ya koma"No Beby na gaskiya yau nazo har wuya Wallahi bazan iya jira ba,in kuma zakiwa Inna magana sai ta bamu daki shi.... "Duka ta kai masa da sauri ya kauce matsowa ya sake zata murɗa masa hannu yakai ya dauke jariri Jamila ya mikawa ya koma zai dauki Sumayyah tana gani haka ta mike tana mita Fu'at da Jamila dariya suka rika musu Da haka suka yi musu Salama. Suna fita ko 30 minute basu da tafiya ba Sai ga Abba da Uncle Sagir sai Matar sa Maryam da yaranta, Sagir.na matsawa Fusakar, Maryam ta fito Da sauri Inna ta mike Itama Maryam jikin ta na rawa tace. "Ya...ya..Ra..bi” Inna kam kuka ta fashe dashi." Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun da gaske ne ba mafarki nake Ba Maryam ɗinta ce tabbas itace ashe zan sake gani iri dangi na A duniya” Da gudu Maryam ta faɗa jiki ta ta saki kuka mai tsuma zuciya kallo su suka fara da son sani inna tasan Maryam Ummu kam cewa take badai Inna ita yar gari su Maryam bace sai da suka juna sanan suka samu nutsuwa ciki dashashiyar Murya Inna tace. "Maryam ya akayi kika kubuta bayan kaf yan ƙauye mu babu wanda ya kubuta ke ya akayi kika kubuta bayan gobarar da akayi?” "Yaya Rabi kafin gobarar ta tashi kinsan yadda nake da ammaki bayan na fito naje nayi fitsari da haka na fita saboda babu ƙyaure a kofar shiga gidan mu hakan yasa nayi tafi naje gidan maina na kwanta babu jimawa gobara ta fara cin gidaje wanda han guri da nake kwance saboda karan da aka ajiye saman soro sai da ya kama ciki iko Allah na farka da na ina tari ina gudu har nabar ciki gari ban samu kaina ako ina sai a baban titi daga haka ban sake sani inda kaina yake ba sai aguri Uncle Bashir wanda ya kaini Asibiti bayan farfaɗo wa ta yake sanar dani babu wanda ya rage aciki kauye, nayi kuka kamar bazan sake samu wani farin ciki arayiwa taba amma silar da ya mai dani tamkar yar da ya sani makarantar masu kuɗi ya inganta rayiwa ta bayan na isa muzali aure ya aura wa kani sa saboda baya so wasu su tozar tani” Babu wanda bai tausayawa Maryam ba da dada jadada godiyar Alhaji bashir da karamci iri nasa, sun jima kowane yana bada labari yadda rayiwa ta zame masa, addu'a babu kalara wace basu yiwa Alhaji Bashir ba. Tun adare Inna ta bawa Sumayyah labari Maryam yar kani mahaifi tace uwa daya uba daya wanda suka taso gida ɗaya, murna sosai Sumayyah tayi tasamu abokiyat shawara tun Asuba Sumayyah bata koma bacci ba dan so take taje taga Aunty Maryam.aji Ammar ya rika ha mata wanda sai da yaga ranta ya fara bacci sanan ya shirya suka tafi. .bayan sati ɗaya anyi sunan yara sunci suna Baban Inna da Maihaifin Abba (Alhaji Bashir) ana kiransu da Waleed da Walidi. Bayan wata uku Sumayya ta haifi yariya mace wace taci sunan Sadiya An kashe kudi bayan wata Uku Baba Zulai Allah ya mata rasuwa, Yusuf kam abu ya gagara sai zaman daki yake, Lubna ta haihu ta haifi yaro namiji yaci sunn mahaifi Tanimu, Ammar ya hudewa Malam shago sai dai bayan wata shida shago ya kama da wuta komi ya kone. Bayan Shekara Uku Inna ta sake samu mace Taci runan Mahaifiyar ta, Sumayya kuma ta samu yaro na miji wanda aka sa sunan Abin, Rayuwa ta juya Sumayyah ta sahi daga Yar mahaukaciya ta zamar abar so da mutane kauye Gidaɗo har fata suke suga Sumayyah yar mahaukaciya saboda tari alkairi da takawo kaye Gidaɗo har Titi Abi yasa gwammna ya musu an kawo musu ruwan sha da wutar lantarki cigaba sosai suka Yar mahaukaciya ta a kawo musu. Bayan shekaru goma sha biyar Kasan da Husaini sun zama samari Sadiya ma ta zama budurwa kamar yar shekara Ashiri a nutse take Haka kani ta Fadil Ammar an zama uba zaune suke a Falo Fadil na rokon Ammar ya siya masa mashi, da haka Sumayyah ta shigo da tsoho cikin ta da sauri Fadil ya koma jikin ta. "Please Mom dan Allah kice Dady ya siya min Mashi Allah bazan yi gudu ba” "Wallahi Daddy karka siya so yake suyi riƙa hauka dasu Uncle Hussain” "Mom ki rabani da Yaya Sadiya ciwo hassada ta ya motsa” Ya tsina fusaka tayi saboda ciwo da yake tsinkina ta. "Abban Sadiya Dan Allah ka sai masa na huta da matsa jiki da yake” Mikewa Ammar ya yi ya zo inda take. “Mai kyau lafiya kike?” Kafi tayi magana marar ta ta riƙe da sauri ta riƙe shi Kuka Sadiya zata yi ya hanna ta Da sauri Fadil ya fita ya bude mota Ammar kuma ya yi samma da Sumayyah ta yana zuwa ya aka ta aciki Hospital suka wuce babu jumawa ta haifi yara biyu duk mata murna babu kalar wace Ammar baiba haka Inna da Ummu.Ranar suna sunci sunan Ummu da Inna. *Tammat bihammdulla Ina me nemann yafiya da Afuwar duk wani kuskure da kuka gani na ciki litattafi yar mahaukaciya domi dan Adam ajazi ne,Ina rokon Allah ya yafe kuskure da nayi abin da yake na dai-dai Allah ya bamu lada baki daya Ina mai bada hakuri na rashi Editing na wanan book gaba daya zaku ga littafin ba anutse na yi shiba* *Idan mai Albashi da Wanda suka biya kudi book ɗin gidan Baba Jibo in sha Allah biyu ga ramadan zaku samu dacomments din book ɗi* ~Nagode Nagode nice taku har kullum Husaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah)~