https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ Horror Short Story PART 1 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9/1/2026 starting posting on 4/2/2026 COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 PART 1 “Sakina! ke tashi a wannan baccin na tabbata baki yi sallar Asuba ba! Shegen baccin nan asara ne 'karfe takwas na safe fa! kuma kin san yau graduation ɗin Afra ne, dole ki je!” Muryar Momma ta fado min kamar tsawa. A hankali na mirza ido, na yi hamma mai nauyi, zuciyata na jin kasala kamar an ɗaura min dutse na ɗaga murya cikin kasala ina cewa: “A’uzubillahi… wai da gaske ƙarfe takwas yayi? bare na tashi nayi ramukan sallah nan… amma wallahi Momma, banason zuwa wannan graduation ɗin kawai dole ne, ba yadda na iya.” Ta tsaya tana kallo na na ƴan dakiku, sannan ta girgiza kai cike da ɓacin rai “Sakina wai bazaki fito ba ko?” Na tashi zaune a kan gado, zuciyata na nauyi fiye da jiki. A daidai lokacin nan Momma ta juya ta cire hijab ɗinta, alamun ta gama shirin fita. “Momma gani fa, na gama sallah. Zuwa ƙarfe goma sha ɗaya zan shirya na je graduation ɗin,” ta faɗa da murya mai laushi amma mai ƙarfi. “To na ji,” Momma ta ce. “Amma kafin nan zo ki sayo min nama can Gadar Lado.” “To Momma,” na amsa, duk da cewa zuciyata bata so. Sakina yarinya ce cikakkiya, mai shekaru ashirin da huɗu a rayuwarta su uku aka haifa a gidan su — maza biyu da ita ce ta uku. Ta yi primary da secondary har ta kammala Diploma, daga nan ta fara Degree wanda za ta yi graduation ɗinta a shekara mai zuwa. Afra ƙanwarta ce, suka haɗa uba ɗaya. Ita kaɗai ce ƙanwarta ta jini. Afra tana zaune a gidan su tun bayan mutuwar mahaifiyarta. Yanzu haka ta kammala secondary school, kuma yau, 9/1/2026, ita ce ranar graduation ɗinta — ranar Juma’a. Ranar da ya kamata ta kasance ranar farin ciki amma zuciyar Sakina tana mata wani irin nauyi da ba ta iya fassarawa ba. Tun daga farkawa, akwai wani abu a ranta da ke mata ƙaiƙayi wani irin tsoro mara suna. kamar zuciyarta na mata gargaɗi — amma ba ta san me ba. Ta tsaya a bakin ƙofa, ta kalli sararin sama, iska mai sanyi ta buge ta, ta ja numfashi a hankali ta ce a ranta: “Me yasa zuciyata ke bugawa haka yau…?” Ba ta san cewa wannan graduation ɗin ba zai zama kamar sauran graduation ba, ba ta san cewa wani abu mai duhu yana jiran su ba … ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION TA FARA… 💀☠️ LIKE FOR MORE TYPING ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 2 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9/1/2026 starting posting on 4/2/2026 COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 TITLE: BEYOND THE RED CEREMONY Na fito daga gida sanye da doguwar riga, jikinta ya yi dai-dai da ni, ba matse ba kuma ba sake ba. Na rufe da mayafi orange, na saka flat shoe kasancewar bana iya sa high heel Tsayina matsakaici ne, jikina ma haka ba zan ce ni kyakkyawa sosai ba, amma Allah ya bani hallita da kwarjini — irin wadda ba ta hayaniya, amma tana ja hankalin mai kallo. A takaice, ni middle ce a kyawun mata, da na isa wajen taron, sai na tsaya cak. Dandazon mutane! Abin mamaki, wajen ya kasu gida biyu. A ɓangare ɗaya, an cika da poster na Ali Nuhu, babban jarumin Kannywood, suna masa kirari da King. A ɗayan ɓangaren, kuma Adam Zango ne a jiki kowa yasan sa da farar jini, kwalliya, magoya baya suna ta ihu. Kowanne rumfa na da nasa hayaniya. Ana ta muhawara mai zafi: “Ali Nuhu ne Sarki!” “A’a! Adam Zango ne jarumi na gaskiya shine sarki!” Na yi murmushi kaɗan ni dai ina sanye da facemask, saboda matsalar numfashi ta — asthma na tsaya a rumfar Adam Zango, ba wai don komai ba, sai don naga nan yafi cunkoso da nama me kyau . Hayaniya na ƙara ƙarfi, maganganu na kaɗawa. Cikin haka, na ji an dafa kafad’ata daga baya. “Ke baiwar Allah! ba mu yarda dake ba fa. Kin rufe fuska, ga leader a hannunki, kina team na Ali Nuhu Amman kinzo rumfar Adam Zango !” Na juya a hankali, na yi murmushi a bayan facemask ɗina, na ce cikin murya mai ɗan sarƙewa saboda numfashi: “Wallahi bana iya buɗe fuska yanzu, safiya ce kuma iska tana da haɗari a gare ni. Kuma a ganina, Adam Zango da Ali Nuhu duk ɗaya ne. ku dai kuke wannan haukar. Idan za ku binciki tarihinsu, zaku gane cewa suna haɗe — jiya da yau. Zango ya taba ɗaukar Ali a labarinsa, haka ma Sarki Ali yana ɗaukar Zango. Don haka ban san me zai faru a feature ba… amma na san haɗin gwiwa ne.” Wasu matasa suka fara ihu daga waje. Hayaniya ta tsaya cak. Sai muka ga napep yana chusa kansa cikin wani gida — ba birki! Gidan ya girgiza! Nan take aka watse, ana ta ihu da firgici. Ni kuwa ban tsaya ba nabi ta lungu-lungu na dawo gidanmu. Gida ne mai matsakaicin hali — ba mu talakawa ba, ba mu masu kuɗi sosai ba muna ci, muna sha, muna sutura, muna makaranta. Alhamdulillah. “Yaya Nabil ina kwana,” na faɗa ina wucewa. Sai ya kira ni da murya mai ƙarfi: “Sakina! ki shirya da wuri fa gaba ɗaya zamu fita, ke kaɗai kike bata mana lokaci!” Na wuce ina murmushi a raina. Graduation kamar dole ne sai an je kai na na ɗan ciwo saboda bana samun kitson ya kamata nayi stretching kafin shiri. Na shirya cikin red lace, ɗinkin pencil da tattara a ƙasa na yi adon pinch, na rataya mayafi launin pinch, na saka flat shoe. Wallahi na yi kyau — tubarakallah na fesa turare, amma har yanzu Yaya Nabil yana jirana da masifa. Da misalin 11:30, napep ya sauke mu a makarantar. Yau ne rana ta biyu da na taka kafata a HAYBIL PRIMARY AND SECONDARY SCHOOL, KANO — babbar makaranta ce, day and boarding. Class suna da yawa, bishiyoyi sun cika ko’ina, musamman bayan makarantar da aka ƙawata da salo na musamman. Sai zuciyata ta buga. Komai ja da baƙi ne — red and black an 'kawata wajen graduation cikin salo mai burgewa. Amma… ban san dalilin da yasa zuciyata ta tsinke ba. wani irin sanyi ya ratsa ni, na ji kamar wannan ba graduation na al’ada ba ne. ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION NA KARA KUSA… 💀☠️ https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 3 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9/1/2026 starting posting on 4/2/2026 COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 TITLE: BEYOND THE RED CEREMONY “Ga ƙanin Baban mu can… ki je ki gaida su ni kuma zan wuce ɓangaren maza.” Yaya Nabil ya faɗa cikin gaggawa, bai jira jin amsata ba ya juya ya ɓace cikin taron mutane. Na tsaya na kalli inda ya nufa. Hayaniya ce ko’ina. Ihu, dariya, magana suna gauraye kamar amo a cikin rami ban son cunkoso, ban son hayaniya — zuciyata ba ta da daɗi tun safe. A hankali na sulale, na fake ta gefe wasu sun gan ni, wasu ba su gan ni ba. Ban damu ba. Gaisuwa ce kawai bana buƙata, amma yau ma baki na yana min nauyi. Na shiga wani class na zauna. A nan na hango Habiba da Ummul ƙawayena tun secondary school suna zaune suna hira a hankali. “Assalamu alaikum,” na faɗa cikin murya mai rauni suka amsa, amma idonsu ya tsaya a kaina kamar suna nazari. “Ke kuwa yau ba kya kamar da,” Habiba ta faɗa tana lanƙwashe fuska. “Tun shigowar ki nake kallo, kamar wacce aka bi da abu.” Na tabe baki. “Ehh… kaina ne kawai,” na ce, duk da na san ba kai ba ne kaɗai. Ban gama rufe baki ba, sai aka ambaci sunan ƙanwata a speaker “AFRAH ABDULRAHMAN…” Amo ya ɗauke dakin. Na miƙe da sauri, zuciyata na bugawa da ƙarfi. Na fito waje na ɗaga wayata — Tecno Spark 8 na fara ɗaukar video da hoto guda ɗaya kacal. Da na kalli screen… hannuna ya sanyi Afrah ce amma ba Afrah da na sani ba Idonta sun fito waje. Jini yana zuba daga gefen idanunta kamar hawaye yana tsiyaya da guda gudan sa suna sauka akan leɓɓenbta bakin ta a buɗe yake faɗi kamar bakin mayya na saki numfashi da ƙarfi. “Ba gaskiya ba ne…” Na goge ido na, na sake kallo komai ya koma normal. Afrah na murmushi, tana daga takardar graduation na sauke ajiyar zuciya. “Wannan tsoron nawa zai kashe ni,” na furta a raina. “Ya Allah, kada ka bar na fara ganin abin da ba ya wanzuwa.” Na koma class amma jikina ya fara rawar sanyi Fitsari ya takura min na miƙe cikin gaggawa na nufi toilet. Da na shiga, na rufe ƙofa lace na ya dame ni, sai naja zip kafin na zauna akan toilet na gama fitsari. Na juya na buɗe bidet, ruwa ya fesa sai na ga ja, ba ruwa ba Jini ne. mai kauri ɗumi a kan hannuna. Na yi ihu — ihu mai tsage kunne. Hasken toilet ɗin ya fara rawa ya yi rauni… sai ya kashe cak naji wani Irrin kururuwa dariya daga nesa ba dariyar mutum ba. Dariya ce mai raɗaɗi, mai kaɗa zuciya toilet ya fara girgiza kamar ana girgiza kabari. Naja zip ɗina da sauri ina rawar jiki. Na miƙe cikin firgici — wayata ta zame ta faɗi ƙasa. Screen ɗin ta haske. Amma ba home screen ba abin da ya bayyana daga cikin wayar ya sa idona ya juya. HOTONA NE. Sakina Ina tsaye sanye da rigar graduation ja Idona na zubar da jini bakin na buɗe kamar na Afrah a rubuce da ja a ƙasa “KIN SHIGA. BA ZA KI FITA BA.” Na ji ƙasa ta ɗauke ta lafta ne da ƙasa kai na ya bugu a take na sake wani Irrin ihu mai giggittacen ƙara da wani fitsarin da bashi da linzamin na faɗi a sume. Abu na ƙarshe da na ji shi ne ƙarar gashi yana ja a ƙasa kamar ana jan gawar mutum. https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 4 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9/1/2026 starting posting on 4/2/2026 COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ، فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ، وَلَا تَجَسَّسُوا، وَلَا تَحَسَّسُوا.👌🏿 Ku nisanci zato domin zato shi ne mafi ƙaryar magana🤐 kuma kada ku yi leƙen asiri ko binciken abin da wasu suke aikatawa✍🏾 PART 4 THE SCREAM BEHIND THE MIRROR Na buɗe ido a hankali kamar wanda aka dawo da ita daga kabari kai na yana sara, zuciya ta na bugawa kamar zata faso kirji na , naji ƙanshin jini da wani wari irin na tsohon ɗaki da aka rufe shekaru masu tarin yawa dasuka gabata , na fara mirza ido nan nan hasken toilet ɗin ya dawo normal, komai ya yi shiru… amma shiru mai ban tsoro. Na taɓa gashin kaina, ɗan ƙwalin da ya faɗi yana nan manne da jini. Hannuna na rawa. A hankali na miƙe na ɗauki wayata daga ƙasa. Screen ɗin ya fashe, amma abin da ya fi tsorata ni shi ne hoton da ya tsaya a jiki. Afrah ce… amma ba Afrah da na sani ba Idon ta baki-baki, bakinta cike da jini, an rubuta da ja a ƙasan hoton “KE CE TA GABA.” Na saki ihu mai ƙarfi. “Waiyooo Mama na ” Na jefa wayar, ta bugi bango ta sake dawowa. ta tsaya chakk tana shillo a sama tana wani zubar da wani abu baƙi tamkar ruwan batir A madubi na ga wani inuwar mace a bayana. Doguwar gashi, sanye da rigar graduation ja… rigar tana diga jini ƙasa-ƙasa a hankali ta ɗaga kanta. Fuskar ta… tawa ce. “Ba ni bane!” na faɗa ina ja da baya har na bugi ƙofar toilet tayi murmushi, murmushin da bai da rai, ta fara zare idon ta masu kama da walwawalin rana babu ɗigon baƙi bare na kira shi da cikakkun ' ido “Kin fara gani Sakina…” ta ce da murya mai sanyi kamar iska daga sanyayyar hontoro mai ratsa sassan jikin ya daskare “Wannan graduation ba ta rayayyu kaɗai bace.” ta ɓacce ɓattt haske ya kashe cak. Na ji ƙarar takalmi yana matsowa kusa da ni… tak… tak… tak… sai wata murya ta buga ƙofar toilet da ƙarfi. “Sakina! Lafiyar ki kuwa?” muryar Habiba ce komai ya ɓace haske ya dawo na buɗe ƙofa da sauri na faɗa jikin Habiba ina kuka kamar mahaukaciya. “Ke lafiya kuwa?” ta tambaya cike da tsoro. na kalli madubi karo na ƙarshe rubutu ja ya bayyana a jiki **PARTY YA FARA. A take rungumar ta ta yi sanyi… sanyi irin na dutse na buɗe ido a hankali abin da na gani ya kulle min numfashi Habiba ba Habiba ba ce. Haƙoranta sun zalzallo, wasu suna rataye, wasu sun faɗi harshe ya fito tsawo, baki-baki kamar an ƙone shi Idonta guda ɗaya ya ɓace—ɗaya tilo yana tsaye a tsakiyar goshinta, yana kallo kai tsaye cikin raina. Jini na malala daga hancinta, yana digo kan rigata. Ta buɗe baki , ta ɓabaki da dariya. Dariyar ba ta kama da ta mutum ba—ta yi zurfi, ta yi sanyi, ta yi kama da amo daga ƙasa a hankali ta ɗaga yatsa ta nuna ni “Keee…” muryar ta ta fito kamar an goga ƙashi da ƙasa. Na saki ihu. A take, bench ɗin class suka fara rawa. Allunan tebur suna karkarwa kamar suna numfashi. Fanka ya yi ihu ya ɓalle daga sama—ya faɗo ƙasa da ƙarfi, yana juyawa yana watsar da iska mai sanyin ƙanƙara sai dariya ta cika class ɗin. Ba dariyar ɗalibai ba dariyar da ba ta da jiki. Ƙofofi suka rufe da kansu—bam! tagogi suka yi ƙara suna girgiza. Haske ya yi walƙiya—ya kashe—ya dawo. A duk inda na juya, fuska ɗaya nake gani: fuskar graduation ja… fuskar mutuwa. Habiba—ko abin da ya mallake ta—ta matsa kusa da kunnuwana ta raɗa: “An fara wanda ya ga jini, ba ya tsira.” Class ɗin ya giggice. Ihu, kuka, gudu—amma babu hanyar fita. Ni kuma na tsaya a tsakiyar wannan hauka… hannuna na rawa… zuciyata na bugawa da kalmar guda ɗaya: MOMMY NARNAH KANWAR SOJA ✍️🤌 https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 5 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9/1/2026 starting posting on 4/2/2026 COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 إِيَّاكُمْ وَالظَّنَّ، فَإِنَّ الظَّنَّ أَكْذَبُ الْحَدِيثِ، وَلَا تَجَسَّسُوا، وَلَا تَحَسَّسُوا.👌🏿 Ku nisanci zato domin zato shi ne mafi ƙaryar magana🤐 kuma kada ku yi leƙen asiri ko binciken abin da wasu suke aikatawa✍🏾 BA UPDATE RANAR LAHADI PART 5 THE SCREAM BEHIND THE MIRROR ZAN CHIGABA DA SALON BAYAR DA LABARIN SABODA YANZU SAKINA BAZATA IYA CHIGABA DA BAKU LABARIN ABINDA YA FARU...... Ta ji ciwo mai tsanani a hannunta. Ta kalli—jini yana zuba, yana gangarowa ya jiƙa ƙasan class. Gashinta ya faɗi kan kafafunta, yana manne da jini. Duk jikinta na rawa. Wani ƙarar gargadi ya daki kunnenta—kamar karar ƙararrawar da ke fitowa daga zurfin ƙasa. Ba ta san daga ina ba, amma zuciyarta ta tabbatar mata: lokaci na ƙarewa. Ta miƙe da ƙyar, tana ja da ƙafa, tana nema hanyar tsira cikin firgice. Class ɗin ya zama duhu ƙirin—babu haske, babu amo—sai bugun zuciyarta da numfashi mai yankewa. Sai wayarta ta yi walƙiya. Haske ya cika class ɗin na ɗan lokaci. Ta leƙo ta haska bango, ƙofa, kujeru—duk sun yi kama da fuskoki masu kallonta. Ta juya hasken a hankali, tana neman ƙofa Sai ta ga rubutu yana fitowa a iska, ja kamar jini, yana zubowa kamar yana digo: ONE HOUR LEFT TILL THE GRADUATION END… FOREVER Zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci. “FOREVER?” ta raɗa, muryarta ta karye. Hasken wayar ya soma rawar jiki. Allon ya yi sanyi kamar kankara. A bayan rubutun, inuwa ta motsa—ta kusanto. Ta ji wani abu ya shafi kafarta. Ba ta kalli ƙasa ba. Ta san idan ta kalla—ba za ta ƙara tashi ba. Ta ja numfashi da ƙarfi, ta tattara ƙarfin da ya rage mata, ta yi niyyar gudu—ko da zai kashe ta. A bayan ta, wata murya ta busa kamar iska daga kabari “Sa’a ɗaya ko ki fita ko ki zama ɓangare na bikin.” …Hasken wayar ya yi walƙiya sau biyu, sannan ya fara dusashewa kamar fitilar da ake kashewa a kabari. Ta fara gudu. Matakanta suna buga ƙasa da amo mai kaifi—tak… tak… tak…—amma duk lokacin da ta matsa, class ɗin yana tsawaita. Ƙofar da ta gani a nesa tana ƙara ja da baya kamar tana tserewa daga gare ta. Numfashinta ya rikice. Kirjinta na ƙonewa. Jini yana zuba daga hannunta yana barin layi ja a bayan ta. Sai kujeru suka fara motsi. Ba ta tsaya ba. Ba ta duba baya ba. Kujeru suka ja da ƙasa suna toshe hanya, tebura suka karkata suna fadowa kamar ana shirya fage. Wata dariya ta tashi daga ko’ina—ba murya ɗaya ba, dariyoyi da yawa, masu sanyi, masu ƙwanƙwasa ƙashi. “Ku zauna…” “Bikin bai ƙare ba…” “Jini bai isa ba…” Ta buga jiki da bango. Ta juya hasken wayarta madubi ne a bangon. Ta hango kanta a ciki… amma ba ita kaɗai ba. A bayanta—su ne. Dalibai cikin rigunan graduation ja da baƙi, idanuwansu sun ɓace, baki cike da jini, suna tsaye cikin tsari kamar hoton da aka ɗora. Wata ta matsa gaba—fuska irin Afrah—amma idonta ba a inda ya dace ba, idon ta ɗaya a saman ƙoshin ta kuma ba hanci a fuskar ta sai ƙaton baki mai girman gaske “Ke ce ta ƙarshe,” ta ce cikin murya mai taɓa kunne. “Bayan ki… bikin zai cika.” Sakina ta saki ihu, ta juya ta gudu—ƙofar ta bayyana a ƙarshe. Ta tura—ta buɗe da ƙarfi. Ta faɗo waje. Haske hayaniya kiɗa dariya Graduation na gudana kamar babu abin da ya faru. Ta kalli hannunta—jini ya ɓace. Ta kalli kafarta—gashi babu. Ta kalli mutane—suna murmushi, suna daukar hoto. Sai wayarta ta sake walƙiya a hannunta. Saƙo ɗaya ya bayyana 30 MINUTES LEFT. DON’T TURN AROUND. Ta tsaya cak. A bayan ta— dariyar da ta sani ta buga kunnenta. Ta san idan ta juya— babu dawowa. Sakina ta hango su huɗu—samari uku da mace ɗaya—sun ratsa bayan makaranta. Ba su tsaya, ba sa magana, kamar suna tafiya a cikin duniya ta daban, duniya da ba kowa zai iya gani ba. Ko wanne mataki su ke ɗauka, ƙasa tana girgiza kamar suna jan ƙasa da kafafunsu. Ta tsaya cak. Ko da take ganin sauran mutane suna harkar su—iyaye suna ɗaukar hoto, yara suna wasa, malamai suna dariya—ba su lura da su ba. Amma zuciyarta ta gane wani abu ba daidai ba ne. Da sauri ta juya hanyar gate, zuciyarta na bugawa, numfashi ya yi sauri. Burinta ɗaya: fita daga wannan makarantar kafin ya yi ƙyama. Amma kafin ta kai ƙafa uku—wani ƙarar ƙarfi ya shiga kunnenta, kamar ƙaƙƙarfar murya daga ƙasa mai zurfi. Ta tsaya, zuciyarta na bugawa har zata fashe. Ta juya a hankali—abinda ta gani ya sa jini ya tsaya a jiki. Su huɗun nan sun tsaya—amma ba kamar jikin mutum ba. Matar ɗaya ta fara narke kamar dutse mai narkewa, fuskarta ta zame, idonta ya rataya, bakinta ya buɗe fiye da kima. Samarin ukun kuma—sun canza siffa: ɗaya ya juya kansa digiri 180 na biyu hannuwansa sun tsawaita har suka taɓa ƙasa na uku ya ɗaga kai ya kalli Sakina kai tsaye da ido ɗaya a goshinsa A lokaci guda, duk suna da murya guda ɗaya mai sanyi “Ba za ki fita ba… sai an cika adadi.” Sakina ta ja da baya cikin firgice. Ta juya da gudu—amma gate na gaba yana fara rufe kanta a hankali, kamar wani abu yana jan ta. Ta danna gudu, zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Kafin ta kai ƙofar—hannun wani ya fito daga ƙasa ya cafke ƙafarta. Ta faɗi da ƙarfi, ta saki ihu—amma babu sauti da ya fita wayarta ta faɗo, ta yi walƙiya: allon ya nuna sabon rubutu mai ja, mai ɗauke da jini kamar yana digo: 15 MINUTES LEFT. ONE WILL REPLACE YOU. Ta ɗaga kai a hankali—su huɗun nan sun ɓace. Amma ƙasan bishiyar nan, takalmin graduation ja yana nan—sabon, amma daidai nata. Zuciyarta ta tsaya cak tsoro ya mamaye ta .. Makarantar ta zama fanko ƙirin babu ihu babu dariya babu motsin numfashi sai iska da gigginniyar kaɗawar bishiyoyi. Kamar an tsotse dukkan rayuwa daga cikin harabar, an bar bango da inuwa kawai. Sakina tana gudu ba tare da sanin inda za ta dosa ba ƙafafunta na rawar tsoro, numfashinta yana yankewa kamar ana tsinka shi da wuƙa. Duk bugun zuciyarta yana ƙara mata rauni, kamar zuciyar za ta tsinke daga kirjinta. Tana waiwaya baya—amma babu wanda take gani Sai dai… tana jin ana binta tamkar rundunar sojojin yaƙi , sautin sahun su na mata dukkan bugu a dodon kunnen ta sai wani sauti yake bayarwa wanda zai iya tauna ta jinta da motsin ta.. Nan take ta hango wani office a gefe ƙofar a buɗe take kaɗan, tana karkarwa a hankali kamar tana numfashi. “Nan zan tsira…” ta faɗa a ranta. Ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta shiga, ta rufe ta da sauri, ta jingina bayanta da ita. Ta zube ƙasa a hankali, tana sauke numfashi da ƙyar. Hannuwanta na rawa, idanuwanta cike da hawaye shiru. Sai wani motsi daga cikin ɗakin. Ta ɗaga kai a hankali—jikinta yana sanyi kamar an watsa mata ruwa daga kabari a can, kusa da tebur wata mata ce tsaye. Sanye da tsohuwar riga ja. Rigarta ta yi duhu, kamar an jiƙa ta da jini da lokaci ya ƙi busarwa a hannunta—jariri Jaririn bai motsi ba bai yi kuka ba. Bai numfasa ba. Matar tana kallon Sakina—amma ba da idanu biyu ba. Ido ɗaya ne kawai ke kallonta, ɗayan ya ɓoye cikin duhu kamar bai taɓa wanzuwa ba. Sakina ta ji sanyi mai kaifi ya ratsa jikinta, ya tsaya a ƙashin bayanta ya daskare. Ba zato ba tsammani, matar ta ɗaga kanta… ta yi murmushi Murmushi mara rai. Sai ta fara yin wani abu da jaririn… wani abu da zuciya ta ƙi karɓa, baki kuma ya ƙi furtawa saboda tsananin firgita , Sakina ta saki ihu mai tsaga kunne, da wani fitsarin da bashi da linzami takai idon ta ƙasa a maimakon taga fitsari sai taga jini ne kifita na bin ƙafafunta Ta juya da gudu zuwa ƙofa—ta buge ta, ta rufe, ta jingina jikinta da ita, tana kuka, numfashi na fita da wahala. “Ba ni gani ba… ba ni gani ba…” tana faɗa wa kanta ,tana numfashi mai ɗaukewa da wani nauyin jiki. Da ƙarfi ake buga ƙofar Amman ta daskare ta kasa ko motsi , nan take matar ta bayyana a gabanta Ba ta buɗe ƙofa ba. Ba ta shigo ba ta tsaya kusa da Sakina. Sakina ta ji ana shakar numfashinta. Da murya mai sanyi kamar ƙasa bayan rami, matar ta ce: “Sakina…” Jikinta ya daskare. Matar ta matsa kusa, ta miƙa jaririn gaba—fuskar jaririn a ɓoye, amma shiru ya fi ihu tsoro Ta raɗa mata: “Za ki ciyar da shi.” “Ke ce za ki ba shi madara.” Sakina ta girgiza kai, hawaye na zuba. “A’a… don Allah… ba ni…” Matar ta yi dariya—dariya mara amo, amma ta girgiza zuciya. “Lokaci yana ƙarewa.” “Ɗaya daga cikinmu dole ya cika gurbi.” ta ɓacce ɓatt hasken wayar hannun ta ya dawo sai wayar Sakina ta yi walƙiya a duhu. Rubutu ja ya bayyana a screen: 10 MINUTES LEFT. MOTHER OR SACRIFICE Sakina ta rufe idanu. Ta san wannan ba mafarki ba ne. Ta san—idan ta tsaya nan, ba za ta fita da sunan Sakina ba. Ta fara gudu Kafafunta na rawa, numfashinta yana yankewa Sai ihu ya tashi. Ihun jarirai—ba a gani a fili ba, amma muryoyinsu suna zagaye ta, suna shiga kunnenta, suna caka mata zuciya hannunta ya yi sanyi. Wani abu mara rai ya kama ƙafarta, kasusuwa ta kiji a ƙafar tana duba ƙasa taga ƙwarangwal na jariri ya buɗe baki yana cewa " zaki ban madarar ke nasha yunwa nakiji" nan tasa hannu a saman ƙirjin ta ta dungule gunɗaya tana girgiza bakin ta ya bushe ba ruwa ga ɗan banzan ƙishi nan da nan aka dafa. ta tabaya aka miƙa mita gorar ruwa bataga kowa ba yana leloo a sama bataye tunanin komai ba saboda bala'en kishi da ta tsinci kanta a ciki , tana budewa ta sa bakin ta nan taji kauri da wari a take furzar sai jini ta kama amai kamar zata amayo da kayan cikin ta tana ihu tana kururuwa ,, dariya mai amo aka ƙifta dashi wanda yasa ta zabura ya cigaba da gudu tana neman hanyar fitta Duk inda ta ja ƙafa—suna binta. “ALLAH NA!… INAI!” ta saki ihu ta juyo—babu kowa babu mutum Sai dai ihun jariran… suna ƙara kusantowa. Sakina ta ci gaba da tserewa, amma duk gudun da take yi— kamar tana gudu ne zuwa cikin su, ba daga gare su ba. Tsayawa yaye chakk ta so chigaba da gudu aman ko yatsa ta sun kasa motsawa domin an makireta ta kasa sarrafa komai nata “WELCOME BACK TO THE GRADUATION HALL.” Sakina ta tsaya cak ta ɗaga kai , abin ta hango yasa ta zube a sume ...... COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 7 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9 /2 /2026 starting posting on 4/2/2026 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 ✨ Ramadan na kusata! ✨🌙 Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka. 🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara. 🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu. Ramadan Kareem! 🌙💫 ₦ Harabar makarantar da take ciki ta canz bango ya tsufa cikin daƙiƙu, haske ya dusashe, ƙasa ta fara bayyana da layukan graduation stage da ta taɓa gani a hotuna… amma a wancan lokaci an cika su da farin ciki yanzu ba farin ciki. Gaba ɗaya ɗakin ya zama hall ɗin kammala karatu kujeru suna nan, amma babu mutane. A kan stage—jarirai uku suna kwance, shiru, idanuwansu a buɗe. Sai murya ta fito daga speaker, murya ɗaya da ta san ta taɓa ji a baya murya da aka ambata a GUGUWAR GRADUATION: “Ba a kammala kowa ba… sai an biya farashi.” Sakina ta ja da baya a jikin bangon baya, wani rubutu ya fara bayyana da jini: “CLASS OF THE DAMNED.” Nan take, matar riga ja ta bayyana a kan stage—amma yanzu ba ita kaɗai ba ce. A bayanta, inuwa-inuwa suna tashi, kowacce tana ɗauke da jariri. Matar ta yi murmushi, ta ce: “Kin tsira daga jarrabawa.” “Amma graduation… ba kowa ke wucewa ba.” Ihun jarirai ya koma kamar sautin applause—clap… clap… clap… amma da kuka a ciki. Wayar ta sake walƙiya: MAKE YOUR CHOICE. BECOME A MOTHER. OR BECOME A MEMORY. Sakina ta kalli hannuwanta—sun fara dusashewa kamar hoto da ake gogewa. Sunanta ya bayyana a screen, sai haruffa suka fara gogewa ɗaya bayan ɗaya: S A K I N A Ta saki ihu: “BAN YARDA BA!” Muryar ta amsa daga ko’ina: “Kowa ya ce haka.” Matar riga ja ta miƙa jariri ɗaya—yanzu jaririn yana motsi. Ya buɗe baki, amma abin da ya fito ba kuka ba ne… “WELCOME TO GUGUWAR GRADUATION.” Haske ya kashe. Sai sautin ƙarshe—sautin hula ta graduation tana faɗowa ƙasa. Sakina ta ci gaba da gudu, zuciyarta na bugawa kamar zata tsage. Kowa da kowa a makarantar ya ɓace, dukkan wuri ya zama duhu mai ɗanɗano na tsoro. Sai ga wani abu ya fado daga sama—ta yi tsammani ruwan sama ne, amma ya ɗauki siffar ruwa mai ja ja kamar jini, ya fara zuba a kanta. Jikin ta ya yi sanyi, kamar kankara na yawo a cikin ƙashi. Ruwan jini ya manne da fuskarta, ya shiga gashinta, ya manne da tufafinta, har numfashinta ya ɗan tsawaita, zuciyarta na bugawa cikin tsananin firgice. Ta tsaya cak, idonta ya buɗe sosai, sai ta ga cewa duk da gudu da ta yi, duhun class da office da ta tsere sun koma a gabanta. Kowane kusurwa, kowane bango, duk yana motsawa kamar yana kallonta, kamar suna jiran ta kammala minti ɗaya kawai. Sakina ta miƙe hannayenta da ƙarfi, tana neman hanyar fita, amma ƙafafunta sun kasa tafiya kamar suna manne da ƙasa. Wani ƙararrawa mai sanyi ya busa cikin kunne: “Ba za ki tsira ba… har sai kin tsaya… har sai kin zama ɓangare na abin da ke nan.” Ta saki ihu mai tsanani, amma kowa da kowa ya ɓace—duhu da ruwan jini kawai suka tsaya a kanta. Ta fara juyawa cikin tsoro mai tsanani, ido nata ya haɗu da inuwa mai lankwasawa daga sama. Ruwan jini ya ci gaba da sauka, amma yanzu yana murmurewa kamar yana rera murya, yana busa kamar numfashin wani mutum da aka rufe a cikin kabari. Zuciyarta ta tsaya cak—ta fara fahimtar cewa wannan ba mafarki bane, wannan gaskiya ne, kuma tsoron da take ji yanzu yana ci gaba da matsowa a cikin ƙashin kanta. Sakina ta hango ruwan jini yana zuba kamar sama ta buɗe, ta yi ƙoƙarin tserewa amma ƙafafunta sun tsaya, kamar wani ƙarfin da ba ta iya kawarwa. Ta yi ihu, sai zuciyarta ta daina bugawa na ɗan lokaci—ta suma a cikin firgice. . Ta farka a cikin sanyin firgice, zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Ko’ina duhu ne, amma idanunta sun fara gane wasu inuwa masu motsi a zagaye da ita. Murya babu, sai wani kukan cikin zuciya, da jijjiga mai sanyi a ƙashi. wani wuri mai duhu da tsoro fiye da tunani. Halittu marasa rai da baƙaƙen inuwa suna zagaye da ita. Fuskar su babu rai, idanunsu suna kallonta kai tsaye, muryoyinsu suna ƙara ihu cikin zurfin zuciya—kamar karar jini da kukan mutanen da aka manta da su shekaru. Ta yi ƙoƙarin motsi, sai ta gane hannuwanta da ƙafafunta an ɗaure da wani abu mai sanyi da mai kaifi, yana manne da fata da nama. Ta fara leloo, ta ɗaga kai, zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Duk wuri na zagaye da inuwa masu murmushi mara rai, suna kallonta da dariya mai sanyi kamar suna jin daɗin tsoronta Hannunta da ƙafafunta an ɗaure da igiyoyi masu tauri, kamar sun fito daga cikin kabari. Ta leko sama, wasu halittu ne—dogaye, fuskarsu ba ta ɗanɗana, idanu sun yi ja kamar harshen wuta, gashin su mai tsabta, amma duk da haka jikinsu yana kama da kayan sanyi da jini. “Me suke so da ni?” ta yi ƙoƙarin cewa, amma muryarta ta fashe, ta koma hawayen tsoro kawai. Duk lokacin da ta motsa ƙafarta, ɗan jijjiga ya shiga igiyar da ke ɗaure ta, yana sa ta jin ciwo mai tsanani. Halittun sun tsaya a zagaye, suna kallonta, ba sa motsi, amma zuciyarta ta gane: kowanne daga cikinsu na jiran wani abu. Sai ta lura wani ruwan sanyi ya fara zuba a kanta. Ta ɗan girgiza kai, zata ce ruwa ne, amma daga ƙasa ya fito… ruwan ja, kamar jini mai tauri, yana wanke jikinta, yana shiga cikin igiyar hannunta, yana sanya ta jin kamar tana nutsewa a cikin wani kabari mai rai. Ta yi ƙoƙarin ihu, amma babu muryarta. Sai zuciyarta ta tsaya, ta ji kankanin jijjiga a ƙashi, gashin kanta ya tsaya, hannunta na rawa, ƙafafunta ba za su iya ɗaukar nauyi ba. Ta leƙo sama, inuwa sunyi wani motsi mai tsanani—suka ɗan juyo kamar suna murmushi… ba murmushi na rai ba, murmushi na kabari. Daga gefen ta, ɗaya daga cikin halittun ya matso kusa da ita, hannunsa ya taɓa fuskar ta, sanyi kamar kankara, zuciyarta ta tsaya cik. Wannan shi ne lokacin da ta fahimci: ba zata tsira daga nan ba idan ba ta yi wani abu ba amma me za ta iya yi? Lokacin na ƙarewa… kuma kowace numfashi na iya zama na ƙarshe. COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 8 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9 /2 /2026 starting posting on 4/2/2026 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 ✨ Ramadan na kusata! ✨🌙 Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka. 🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara. 🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu. Ramadan Kareem! 🌙💫 Wani gajeriyar ƙato ya matso kusa da Sakina, jikinsa ya yi ƙarfi kamar ƙarfe mai dumi a cikin duhu. Hannunsa ya manna akan kafadar ta, yana matsa da ƙarfi, kuma murya mai ƙarfi ta fita daga bakinsa: “Dole ki zaɓa… lokacin na ƙurewa ya kusa.” Sakina ta ƙoƙarin motsa bakin ta, ta yi niyyar magana ko ihu, amma babu komai da ya fita—ba ta iya furta kalma ɗaya ba. Ta ji kamar harshenta ya matse, kamar wani abu ya ɗaure muryarta da igiya maras gani. Ta tsaya a hankali, idonta na fadawa, zuciyarta ta tsaya cak. Duk motsi ko numfashi yana cike da jin tsoro mai ƙarfi—kamar kowanne abu a cikin class ɗin nan yana kallonta, yana jira ta yi kuskure. Kurma ta zama, Sakina ta ji kanta a tsaye kamar wata mayya a cikin duhu. Amma duk da haka, zuciyarta na bugawa, tana neman mafita. Ta gane cewa kowanne ɗan tsokaci daga ƙato nan na iya zama ƙarshe—lokaci ya kurewa, kuma wannan ba ɗabi’a ce kawai ba, wannan gaskiya ne mai tsananin firgici. Duhu ya matso mata, inuwa sun yi yawa, suna zagaye da ita kamar wani zobe na kabari. Kowanne daga cikin halittun nan suna kallonta da ido mai wuta, ba su yi murmushi ba, amma kowane kallo na sa jikinta ya ji sanyi da ƙarfi. > Duk duniya ta tsaya cak a firgice, kuma Sakina ta fahimci: idan ba ta zaɓi ba… za ta zama ɗaya daga cikin su—har abada. Sakina ta tsaya tsaye, jikinta na rawa kamar ganyen da iska ke girgiza. Halittun nan da ke zagaye da ita sun matso kusa, kowanne kallo na ɗauke da sanyi mai kaifi da tsananin fushi da rashin rai. Duk motsi na ta yi kamar ƙanƙanta a hannunsu—kamar babu wanda zai iya tsira. Wani ɗayan ƙaton ya matso gaba ɗaya, fuskarsa ta rufe da inuwa, hannunsa ya ja Sakina kusa da shi. Murya mai ƙarfi ta fita: “Zaɓi, Sakina… ko ki tsaya… har abada!” Idanunta sun cika da tsoro, amma ta san cewa idan ta tsaya, ba za ta sake tashi ba. Ta tattara ƙarfin zuciya ɗaya kaɗai da ta rage, ta fara ja da ƙafa cikin ƙoƙari. Kowanne ƙoƙarin ta yana jawo su ƙato nan da nan, suna motsi da sauri kamar iska mai ƙarfi. Sai wani ƙato ya shiga tsakanin ta da hanyar fita, gashin kansa ya rufe haske na karshe daga wajen kofar. Sakina ta ji zuciyarta na bugawa kamar zata fashe. Ta yi ihu… amma wannan karon, muryarta ta canza—kurma ce kawai ta rage, babu wani amo. A nan ta fara fahimtar gaskiyar wannan wuri: ba makaranta ce, ba duniya ba… wannan wani labari ne mai rai, inda lokaci ya tsaya, kuma kowanne lokaci na batawa rai yana nufin ƙarshe. Jinin da ya dinga ruwa a cikin class ɗin nan ya fara motsi kamar yana neman ta. Yana zuba a ƙafafunta, ya manne da kafafunta, yana sa ta ji kamar tana nutsewa cikin ruwan ja mai sanyi. Kowanne mataki na ta ja su ƙato nan, suna ƙara matsa mata, murmushi a fuskarsu babu rai. Ta yi ƙoƙarin kallon ƙasa… sai ta ga rubutu a bango yana haskakawa da ja 5 MINT LEFT… FOREVER… Idanunta sun ɗaure a rubutun. Ta ji jikinta ya tsaya, zuciyarta ta bugi ƙasa da ƙarfi, kuma numfashinta ya tsaya cak. Duk motsi ko ihu yanzu babu abin da zai iya fitar da ita daga wannan wuri—komai natsuwa ko ƙarfin zuciya. Sakina ta fahimci: ko da ta yi ƙoƙarin tsira, wannan graduation ba zata taɓa ƙarewa ba. Lokaci da wuri sun haɗu don ɗaure ta cikin wannan duhu… har abada. INA MAFITA ??? COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 8 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9 /2 /2026 starting posting on 4/2/2026 SECOND TO THE LAST PAGE 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 ✨ Ramadan na kusata! ✨🌙 Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka. 🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara. 🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu. Ramadan Kareem! 🌙💫 ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 PART 9 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA Sakina ta tsaya a tsakiyar duhu, idanunta na bugawa kamar za su fita. Ta ji muryoyin nan suna zagaye da ita, suna magana amma ba ta gane su ba. Sun ce: “Zaɓi… zaɓi yanzu…” Ta rasa fahimta. Menene zaɓi? Me suke nufi? Ta dinga ja da ƙafa cikin firgice. Halittun nan sun kwance a gabanta, duk motsi da su ke yi yana ƙara sa ta ji tsoro da fargaba. Ta fara gudu. Duk inda ta ratsa, ganye da bishiyoyi sun yi kama da bakin ruwa mai sanyi, suna murɗe kafafunta. Ana jin sautin tsaye da faɗa, amma ba ta iya gane ko daga ina suke fitowa. Kowanne mataki yana ƙara raba ta da duniyar da ta sani. Azaba ta fara tashi a zuciyarta. Ta ji kamar tana nutsewa cikin duhu mai nauyi, wani nauyi mai ƙarfi da ba za a iya tsayawa ba. Hasken ja da fari yana motsawa, yana sa class ɗin, toilet ɗin, bishiyoyin… komai ya zama kama da mafarki mai ban tsoro da gaskiya. Ta yi ƙoƙarin tunawa: wannan ba graduation bane da ta sani… wannan GUGUWAR GRADUATION ce. Duk abin da ya kawo ta nan… bai da kyau. Fargaba ta mamaye zuciyarta, tana jin numfashi yana yankewa. Ta ji ƙamshi irin na jini, tsotsa na halittu, da murmushi mara rai suna zagaye da ita. Ta ratsa cikin bishiyoyi, kowanne reshe yana kama da hannu mai neman ta ɗaure. Kowanne ciyawa da ƙasa suna sauti kamar ana kira da ita zuwa wurin da ba za ta iya tsira ba. Duk ƙoƙarin ta na gudu yana ƙara sa halittun nan su matsa kusa da ita, suna kallonta kamar abun wasa da rai. Sakina ta rike kanta, zuciyarta na bugawa, idanunta na kallon duhu… ta fara gane: idan ta rasa ƙarfin zuciya yanzu, wannan GUGUWAR GRADUATION za ta ɗaure ta har abada. Sakina ta fara jin tsoron da bai taɓa ji ba. Lokaci ya yi ƙanƙanta: 5 minutes left… Ta yi ƙoƙarin gudu, amma duk mataki na sa halittun nan su yi ƙarin matsa kusa da ita. Kowane reshe, kowanne ciyawa, kowanne ƙasa… suna kamar hannu ne masu neman ta ɗaure. Sai kawai, daga cikin duhu mai tsanani, wata muryar sanyi ta busa kai tsaye: “Zo… kar ki ɓuya… lokaci yayi…” Sakina ta tsorata sosai, zuciyarta ta tsaya na ɗan lokaci, sannan wani ƙarin ƙarfi ya ja ta ƙasa. Ta ji ƙafafunta na rasa ƙasa, kamar an ja ta cikin wani rami mai zurfi. Ramin yana sanyi, yana ɗaukar ta cikin duhu mai zurfi da wari na jini da ƙamshi mai ƙunci. Ta yi ihu, ta yi ƙoƙarin ɗaga kai… amma babu komai. Ramin ya zama azabtarwa, bango da ƙasa suna motsi kamar suna rufe ta daga kowanne gefe. Kowanne numfashi da ta ɗauka yana cike da muryoyin ban tsoro, wasu suna kiran ta, wasu suna dariya da ƙarfi. Zuciyarta ta ƙara bugawa da tsanani. Idonta ya tsaya, yana ganin babu hanyar tsira, babu hanya ta fitowa. Kowanne sauti yana matsawa, yana cika zuciyarta da firgice da tashin hankali “ 2 MINNT LEFT… FOREVER…” Ramin ya yi kama da sabon duniya… duniya ce da ba ta san ta wanzu ba, kuma Sakina ta fara fahimtar cewa wannan GUGUWAR GRADUATION ba ta da dawowa. COMMENTS SECTION GROUP https://chat.whatsapp.com/ErBzFgfrIhE9QWSOhld1g1 https://chat.whatsapp.com/LDm6JQR1M3L5dOPu5dB0TM ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ 🩸 Storm of Graduation 🩸 Horror Short Story PART 10 / 10 BY NARNAH KANWAR SOJA ✍️ Writer of Dr Sadeeq This story is dedicated to all Dr Sadeeq fans Love you all ❤️ 9 /2 /2026 starting posting on 4/2/2026 THE LAST PAGE 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRON ✊🦚) Typing...📲 بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين اللهم صلي وسلم على نبينا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين 💕 ✨ Ramadan na kusata! ✨🌙 Alhamdulillah, muna gab da shiga wannan wata mai cike da rahma da albarka. 🕌 Mu shirya zukatanmu da ibada, mu ƙara kyautata halayenmu, mu kuma yi addu’a ga samun dacewa da gafara. 🤲 Allah ya sa mu kai ga Ramadan lafiya, ya karɓi azuminmu da ibadunmu. Ramadan Kareem! 🌙💫 ☠️💀 GUGUWAR GRADUATION 💀☠️ FINAL PAGE Kamar yadda nagayyamu ku labarin bashi da tsawo nayisa ne a bisa wani dalili kuma ina fatan ya ƙayyatar daki sako ne me muhimmanci wanda ya faru ne da gaske wacce ta bani domin in mayar dashi a labari sai dai na gyara inda ya kamata wasu abubuwan kuma bazai faɗu a zahiri ba Muna fatan Allah yasa mu shiga wanan wata mai albarka lafiya da kwanciyar hankali, Allah yasa mu fara lafiya mu gama lafiya , Allah ya sadamu da alkaire cikin ta , Allah ya karɓi ibbadunmu Ameen ya rabbil izzati. A duk lokacin da Ramadan ya shigo idan muna da time a koyaushe muna program na wasa ƙwaƙwalwa a addini in Sha Allah kamar ko yaushe zamu gabatar idan Allah ya bamu daman hawa online..... Afuwan Afuwan Afuwan, ga wanda nayi Wa laifi cikin sani ko rashin sani a sanadin rubbutu ina neman gafarar ku Saduwar Alkaire sai mun haɗu bayan sallah in Sha Allah da littafin AFNAN ....... &&&&&& Sakina ta faɗa cikin ramin, zuciyarta na bugawa da tsanani. Ko da ta yi ƙoƙarin miƙewa, duhu ya lullube ta gaba ɗaya. Sai haske ya fito daga wani gefen rami… Ta ɗan haska ido, zuciyarta ta tsaya cak. Gaba ɗaya, a cikin wannan rami mai girma, ta hango mutane da yawa a rataye. Jikin su yana zamewa, fuskar su cike da tsoro da azaba. Wasu suna motsi kaɗan, wasu kuwa babu rai… amma duk sun kasance a cikin wani hali mai ban tsoro. Sai kuma ta ji raƙumin ihu mai tsananin firgice, mai sa ƙashi su rawa, mai girgiza ramin daga ciki zuwa waje. Ihu ne da zai sa mai karatu ya ji tsoro mai ƙarfi, zuciya ta tsaya, ido ya ƙasa, numfashi ya yanke. “AAAAHHHHHHHH!!!” Ihu ne da ya karye zuciya, ya haɗu da muryoyin waɗanda aka rataye. Wani murya mai sanyi ta busa a kunne: “Zaɓi… ko zama kamar su…” Sakina ta girgiza, ta rufe idonta, amma duk da haka hotunan mutanen da aka rataye sun ci gaba da bayyana a cikin duhu. Kowanne murmushi da ihu yana cika zuciyarta da firgice da tashin hankali. Zuciyarta ta ce: “Ba… ba zan zauna kamar su ba… dole in tsira… dole in fita…” Amma ramin ya yi kama da gidan mafarki, kowane gefe na tattare da duhu, jini yana zubowa daga bango, kuma muryoyin ban tsoro suna zagaye da ita daga kowanne bangare. Sakina ta ɗan ja numfashi, ta fara neman hanya, amma duhu ya hana ta ganin komai, sai kawai mutanen da aka rataye da ihu mai ban tsoro… Ihun ya balle mata makogwaro. Ihu ɗaya tak. Amma komai ya girgiza — ƙasa ta motsa, bango ya yi rawa, inuwa ta tsawaita. Kan mutanen da aka rataye suka fara juyowa a lokaci guda, idanuwansu a buɗe, bakinsu a buɗe kamar suna son magana amma babu murya. Sai haske ya fado daga sama. Ja… mai kauri. A iska ta ga rubutu yana walƙiya kamar bugun zuciya: 5 SECONDS REMAIN Da kafin ta yi tunanin tserewa— aka ɗaga ta sama.Ba hannaye ta ji ba. Ba igiya ba. Kamar iska ce ta ɗaga ta. Kafafunta sun bar ƙasa. Hannuwanta sun daskare. Numfashinta ya yanke. Sai ta ji sanyi a wuyanta wani kakkakaifan zarton wuƙa mai sheƙi da walkiya Ba ta ga wanda ya riƙe ta ba. Amma ta ji ƙarfin hannun a bayanta. Murya mai amo ta sauko daga sama, ba kusa ba, ba nesa ba: “Lokaci ya ƙare.” Zuciyarta ta daki ƙarfi. Hawaye suka taru amma ba su zubo ba. Ta so ta yi motsi— ta kasa. Ta so ta yi ihu— ba murya A ranta kawai take ihu: “Don Allah… kar ku kashe ni.” Bakinta ya motsa. Kalmomin sun fito ba tare da sauti ba. Lips ɗinta na rawa, jikinta na karkarwa. Sai rubutun ya sake walƙiya: 3… Wuƙar ta matso kusa da fata. Ta ji sanyi ya ratsa jiki. 2… Dukkan hotunan ranar graduation suka shigo mata lokaci ɗaya— dariya, tufafi ja, fanka, hayaniya. Ta gane a wannan sakan: “Wannan ba graduation ba ne… hukunci ne.” 1… Bakinta ya motsa karo na ƙarshe: “Ya Allah ka taimake ne na tuba ASTA'GFURRULLAH INNALLILAHI WAI'NA ILLAIHIN RAJIOU'N ALLAHUMA AJIRNI FI MUSSIBATI ” Sai komai ya tsaya .. ana marin ta a kan fuskar ta ana cewa Sakina ! ke tashi kiye sallah ''''''' Sakina ta farke, tana gumi, zuciyarta na bugawa, tana ihu, tana cewa "Mommyyy! Mommyyy! Na ji tsoron… na ji tsoron sosai!" ta a zare idano tana bin ɗakin ta da kallo dayan bayan ɗaya ta daga kanta da hannun ta tana duba ko taji rauni ashe duk mafarki ne... Ta tashi daga bacci, dakin Bachi ya shiru, babu ƙwarin wuƙa, babu halittu, babu jini. Amma tsoron ya zauna a zuciyarta — har sai da ta ga ƙananan zubin gumi a goshi da hannunta da ke tunatar da mafarkin. Ita kawai ta yi murmushi, ta ce: "Alhamdulillah… mafarki ne kawai… Amma… ya kasance da kamar da gaske sosai!" Mommy tace, “Sai ke tashi, ki shirya, kiye sallah asuba mu tafi graduation na Afrah kina nan kina bachin asarar sai mun makara .” Sai ta diro Sakina a kan gado, tana cewa, “Wallahi Mommy, bazan je ba, zanyi sallah kuma wallahi daga yau na daina makara zan tashi da asuba "… Sakina ta juya ta tsaya kan gado, zuciyarta na bugawa cikin tsoro da ƙarfi. Ta ɗan ja numfashi, ta miƙe fuska da darewarta, tana cewa, “Wallahi Mommy… bazan je ba , !” tafe ta ta barta Domin chigaba da shirin ta Amma kafin ta yi wani motsi, wani inuwa mai tsawo ya bayyana a gefe na ɗakin. Fuskar sa bata bayyana ba, amma muryar sa ta busa cikin sanyi: “Wallahi… wannan graduation ba ta gama ba…” Sakina ta tsaya cak, zuciyarta na tsorata sosai, hannunta na rawa. Idanunta sun buɗe sosai, tana ganin duhu yana zagaye ta, kuma wani abu a hankali yana matso kusa da ita. Sai kuma ta ji wani abu ya busa cikin kunnenta, kamar iska mai ɗaci: “FOREVER…” A wannan lokaci, ta gane cewa ba mafarki ba ne. Wannan graduation… wannan GUGUWAR GRADUATION tunda ya fara mata gizo saboda tsananin firgita da tsoro da taki ciki tana faruwa a gaskiya FINAL ...... NARNAH ƘANWAR SOJA 08101235739 MU HAƊU A LITTAFI NA GABA BAYAN SALLAH IN SHA ALLAH AFNAN KAR KU MANTA AKWAI HIJJAB'S NA MANYA DA NA YARA FOR UR EID .....