[12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________________ Page 4️⃣1️⃣ Na daɗe ina kukan har sai da na gaji don kaina na tashi na share hawayena, so nake yi na je na yi alwala na gabatar da salla amma ban san ta inda zan fara ba ga shi ina son shiga banɗaki na tsaftace jikina kafin na yi sallan. Ganin wankin hula yana neman ya kai ni dare ya sani tashi na fito waje, cike gidan yake da mutane jinsin maza da mata kowa yana harkan gabansa daga matan har mazan babu wani shigar arziki balle ta mutunci. Mafi yawan matan zani ne a jikinsu ɗaurin ƙirji mazan kuwa gajeren wando da ya tsaya daidai gwiwansu masu kunya daga ciki suka ƙara da singileti. Na fi mintuna biyar a tsaye a ƙofar ɗakin na kasa gaba na kasa baya illa bin kowa da nake yi da ido. "Madam lafiya kin yi tsaye sai ƙare mana kallo kike yi in ce dai lafiya ko?". Na yi an yi zancen a zafafe kamar za a rufe ni da duka, da sauri na waiga don ganin wanda ya yi furucin. Wata matashiyar budurwa ce tsaye ta riƙe ƙunta tana ƙare mi kallon tsaf kamar yadda ni ma nake bin ta da kallo. Kafin na ce wani abu ta daura mini mari na yi saurin dafe kuncina don ba ƙarya marin ya shige ni sosai har sai da na ji idanuna sun kawo ƙwalla. "Ke waye da har ina yi miki magana za ki tsaya kina kallona maimakon ki ba ni amsa? Yau sai kin faɗa min uban da ya tsaya miki a cikin gidan nan da har ya ba ki damar da za ki yi min wannan ɗiban albarkan". "Me na yi miki za ki mare ni?". Na yi zancen har izuwa lokacin ina dafe da kuncina, da alama tambayar ta fusata ta don sai da ta riƙe haɓa kafin ta furzo zancen. "Kan uban can! Lalle ba ki san da wacce kike magana da ita ba ne shi yasa kika tsaya a gabana ina faɗa ki na mayar mini da martani. To yau zan nuna miki ƙarshen barikinki da iya shegen da kike ji da shi". Ta kacumo wuyan hijabina ta riƙe tamau har sai na soma tari, duk cikin dandazon jama'ar tsakar gidan babu wanda ya taso balle ya kawo mini ɗauki. Kowa ya mayar da hankali kan abin da yake yi. "Me ye nake gani haka Baraka? Kashe ta za ki yi ko kuwa? Sakar ta na ce". Hajiya Babba ta yi zancen yayin da take fitowa daga ɗakinta ta fincike hannun Baraka daga jikina. "Baraka na sha gaya miki cewar ba na son rigima a cikin gidan nan. Babu wanda nake ajiye kara ya tsallake shi face ke don hakan ba za ka tara min ciwon kai ba. Yanzu ba sai an jima ba ki shiga ki haɗo duk abin da yake mallakinki ne ki fice ki bar min cikin gida, tun da ba kuɗi muka haɗa muka gina gidan tare da ke ba". Take jikin Baraka ya soma rawa ta zube a ƙasa ta na magiya. "Don girman Allah Hajiya ki rufa min asiri kar ki bari na tozarta na kunyata a idanun maƙiya. Kin san yanzu ƙiris ake jira ya faru a soma yamaɗiɗi da kai. Hajiya ki rufa min asiri wannan shi ne na farko kuma na ƙarshe". Cikin zafin rai Hajiya ta soma cewa"sanin kanki ne Baraka ni ba na yafiya kuma ba na sauƙa daga kan maganar da na riga na furta. Don haka ki shiga ki haɗo kayanki ki bar min cikin gidan, daman na sama wanda suke son ɗakin kuma har na dafe ƴan sulallana". Tana dasa aya a nan ta waigo kaina. "Ke kuma me ye kike buƙata?". Na yi ƙasa da kaina kafin na ce"banɗaki zan shiga, sai kuma ina so na yi alwala". Ta nuno ni da ƴar manuniyar ƴatsarta kafin ta furta"zan ɗaga miki ƙafa ne kawai saboda ke baƙuwa ce kuma Aminu ya kawo ki to za ki ci albarkacinsa. Zan ba ki ruwa da buta da bargon kwanciya wanda za ki yi amfani da shi, amma ina so ki sani kuma ki sa a cikin kanki cewa a gidan komai na sayarwa ne komai da kike ji da gani ke za ki nemawa kanki hatta ruwan wanke ido kin ji ni ko?". Jikina yana ɓari na ce"e na ji na gode sosai". Ba ta tanka mini ba ta shige ɗaki babu jimawa ta fito, ta ba ni bango, buta sabuwa sai kuma pure water guda uku. Na karɓa na durƙusa har ƙasa ina yi mata godiya, ba ta bi ta kaina ba ta yi shigewarta cikin ɗakinta bayan ta gama gindawaya Baraka gargaɗin kar ta kuma fitowa ta iske ta ba ta bar cikin gidan ba. Na shiga ciki na ajiye bangon na zuba ruwan guda biyu a butan na bar ɗaga na sha, na fito na rasa gane ina ne banɗakin don haka na isa wajen wasu mata na yi musu sallama. Maimakon su amsa sai na ga duk sun kafe ni da idanuna kamar wacce ta zo da wani sabon abu. "Don Allah ni baƙuwa ce a gidan nan yau na zo. Banɗaki nake nema ina so na shiga". Duk su ukun suka fashe da dariya har da tafa hannu suka mayar da ni kamar magiji da sun kalle ni sai su tuntsire da dariya. Haka na gaji da tsayiwa na bar wajen na koma can gefe na tsaya. "Ki na neman wani abun ne?". Na ji an furta a kusa da ni. Na ɗaga kaina ina ƙarewa wacce ta yi zancen kallo sanye take da hijabi fari irin wanda ake ƙira da sunan half sunna. Na ja dogon numfashi na fesar kafin na ce"ni baƙuwa ce banɗaki nake nema". Ta yalwata annurin fuskarta kafin ta ce"mu je mana to na nuna miki". Ta yi gaba ina bin ta a baya har muka isa bakin banɗakin ta yi mini ishara da hannunta alamar na shiga. Na sakeke na tsaya ganin mutane tsaye cirko-cirko a ƙofar banɗakin suna lamarin gabansa babu abin da ya sha musu kai. Fahimtar abin da nake nufi da abin da yake yi mini yawo cikin raina ya sa ta faɗin"kar ki damu ki shiga abin ki, zan tsaya miki a wajen babu wanda zai shigo kanki". Na waro idanuna waje cikin firgici na ce"a shigo kaina kuma?". "Kaɗan ne daga cikin abubuwan da mutanen cikin gidan nan za su iya aikata. Don haka ki shiga abin ki ina tsaye a nan babu wanda zai shigo". Na jinjina kaina ba don na gamsu da abin da ta ce da ni ba, na shiga banɗakin na yi abin da zan yi na fito sai dai duk a firgici nake. Na yi alwala muka dawo ciki na yi mata godiya sosai ta nuna mini babu komai na shige ɗakin da aka kai ni. A bisa tabarman na yi sallan magrib da isha'i ko da na shafa addu'ar da na yi na zauna, na zabga tagumi ina tunanin makomar rayuwata da yadda lamura suke sauyawa. Na daɗe a zaune har sau da dare ta yi nisa, kafin yunwa da ba kasancewa ƙanwar uwata ba ta dawo da ni cikin hayyacina. Na dafe cikina da hancina suke kukan yunwa na waigo da nufi ɗauko ledar da Aminu ya kawo mini na ga waje wayam babu shi babu alamarsa. Ta yi zumbur na miƙe ina ta waige-waige amma ban ga komai ba hatta pure water guda ɗayan da na ajiye ban gani ba. Na durƙushe akan gwiwoyina ina shararo kuka da dukan ƙarfina, ga wani yunwan da nake fama da shi kamar ƴaƴan hanjin cikina za su tsintsinke, tun ina durƙushe sai da na kwanta a ƙasa na dinga juyi riƙe da cikina da yake murɗawa. Na kasa yin bacci tsabar yunwan da yake nuƙurƙusata take wani zazzaɓi mai zafi da ratsa jiki ya rufe ni na koma sauƙe numfshi da ƙyar. Da wani irin kuzari Anty Sawwama ta wayi gari ranar ta fito waje ta soma kici-kicin haɗa wuta domin ɗaura abin kari, tana cikin aikin Umar a fito ya iske ta ya durƙusa har ƙasa ya gaishe ta ta amsa fuskarta ɗauke da walwala, tare Yaya Alhassan da Amir ma suka fito suka tsuguna suka gaishe ta ta amsa tare da sanya musu albakar da addu'ar Allah ya datar da su a cikin wunin wannan ranar. "Umma ke da kanki za ki yi girkin ba za ki ba ri Asma'un ta zo ta taya ki ba". "Har yaushe zan jira zuwan Asma'u ita ma da sai ta gamo aikin gidansu kafin ta zo. Ina so yau na yi girki na musamman ga Amatullah don tun gabannin faruwar wannan lamarin babu wani abin da take ci na kirki". Ta ja dogon gashin ta fesar kafin ta ci gaba"wallahi yanzu ba ni da wani burin da ya wuce ganin Amatullah cikin farin ciki. Ba ni da wani sauran buri da ya zarce na ga rayuwarta ta gyaru wanda ya aikata mata wannan aika-aikan kuma a hukunta shi daidai da abin da ya aikata". Cikin jimami Amir ya furta"ai wallahi da zan ga wannan mutumin sai na yi masa lakanin da ko uwar da yi naƙudarsa, idan ta gan shi ba za ta shaida sa ba". "Babu wannan maganar Amir amma tabbas doka za ta yi aiki akan sa. Ba ma shi kaɗai ba hatta matar da aka yi abun a cikin gidanta sai ta ɗanɗana kuɗanta". "Hakan shi ne daidai, Allah ya datar da mu". Anty Sawwama ta yi furucin da duk suka amsa da amin, tare suka yi aikin don daman ta sabar da su akan hakan, sai da suka gama haɗa komai aka tattare wajen Umar ya shimfiɗa tabarma aka jera kayan karin kumallo. "Bari na je na taso ta". Anty Sawwama ta yi zancen tana tashi ta nufi ɗaki wayam ta tarar da ɗakin babu kowa, take ta dafe ƙirjinta cikin tsananin tashin hankali ta dudduba ɗakin hatta katifa sai da ta ɗaga. A fito jikinta yana ta rawa su Yaya Alhassan duk suka taso suna tambayar lafiya. "Ba ta ciki ban ga Amatullah ba ta cikin ɗakin". "Ba ta ciki kuma Umma?". Yaya Alhassan ya yi zancen yana faɗawa cikin ɗakin, shi ma babu inda bai duba ba amma wayam babu ko alama haka ya fito jikinsa a sanyaye aka karaɗe ko'ina a cikin gidan. Banɗaki, kicin, ɗakin ajiya babu inda ba duba ba. Suka tsaya cirko-cirko kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa. "To Umma ko ta fita ne ba mu sani ba?". "Amir ina za taje? Wani gida ta sani a cikin unguwan nan? Wajen waye za ta fita ta je ta?". Cikin damuwa Yaya Alhassan ya ce"Umma ki kwantar da hankalinki in Sha Allah babu wani abun da zai faru, bari mu fita mu duba. Da yarda Allah Amatullah za ta dawo cikin aminci". Ya juya yana kallon Umar"ka zauna tare da ita bari mu je da Amir". Yana gama faɗin haka suka fita, haka suka karaɗe cikin gari duk inda suke tunanin za a dace sai da suka je amma ba yi dace ba. Bayan sallan asr lilis suka dawo gida. Anty Sawwama tana ganin shigowan su ta miƙe"ya na gan ku haka ina ita Amatullah ɗin?". Ba su amsa mata ba sai da suka ƙariso suka zauna suna. Duk su biyun suka kasa cewa komai illa kallon juna da suke yi. "Alhassan ka buɗe baki ka yi min magana mana. Ina Amatullah take?". "Umma babu inda ba mu duba ba amma ba mu same ta ba. Duk inda muke tunanin da a dace mun je, kaina gabaɗaya ya kulle ina Amatullah za ta je wanda ba za ta iya sanar da ɗaya daga cikinmu ba?". Da hanzari Amir ya ce"to ko wajen Ummanta ta je?". Anty Sawwama ta jijjiga kanta alamar a'a"ba ta je wajen mahaifiyarta ba don wannan ƙawar tatan da suke gida ɗaya Amira ta zo nan gidan wajen ta. Wanda hakan yake nuni da cewar ba ta je can ba, kuma na ƙira Zulaihatu ma ta ce ba ta je wajen ta". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! To ina Amatullah ta shiga?". Haka suka zauna jimgum-jimgum kamar masu karɓan gaisuwar mutuwa, babu abin da Yaya Alhassan yake yi face ƙiran wayan dangi yana tambayar su ko suna tare da Amatullah. Amma duk wanda ya ƙira ba a dacewa. Ya sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya yana zare wayan daga kunnensa tare da faɗin"Umma ba a dace ba, ba ta je wajen su ba". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Umar ɗauko min hijabina na fita neman yarinyar nan don zama bai kama kama ni ba". Da sauri Yaya Alhassan ya riƙo hannunta ya zaunar da ita"don Allah Umma ki kwantar da hankalinki kin san fa kina da hawan jini. Bai kamata ki fita ba a wannan halin da kike ciki, ki bari mu mu je mu nemo ta a duk inda ta shiga". Ta kafe shi da ido"Alhassan jiya cikinku akwai wanda ya yi magana da ita ne?". Ya sadda kansa ƙasa"ni ne na yi magana da ita ƙarshe". "Wani magana suka tattaunawa da ita?". "Umma maganar da muka yi da ke ne. Kuma ban mata dole ba na ba ta daman ta je ta yi tunani kafin ta yanke ko wani irin hukunci". Ta ɗan jim kafin ta ce"Allah ya sa ba abin da nake tunani ba ne ya faru". "Umma me ye kike tunani?". "Wataƙila ta gujewa aurenka ne Alhassan". Ya waro idanunsa waje"me ye zai sa Amatullah gujewa aurena? Umma shin ina da wani aibun ne?". Ta dafa kansa"ba ta da wani aibu Alhassan amma wannan hashashe ne kawai na zuciyata wanda ba na fatan hakan ya kasance". A sanyaye ya furta"to Umma bari mu je mu ƙara duba. Amma don Allah ki kwantar da hankalinki". Murmushi kawai ta sakar masa suka tashi suka fita ba su dawo ba sai bayan sallan isha'i suka shigo cikin gidan cikin mutuwar jiki. "Ba a gan ta ba ko?". Anty Sawwama ta furta yayin da suke shigowa cikin gidan. Sai da suka zauna kana Amir ya yi ƙarfin halin faɗin"Umma ba a dace ba". Ta sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kafin ta ce"Amatullah amana ce a gare ni ba zan so duk abin da zai cutar da ita. Yanzu ban san halin da take ciki ba". "Umma ni babu abin da nake tunani ma kamar tijarar da mahaifiyarta za ta yi mana idan ta ji wannan maganar". Amir ya yi zancen cikin tashin hankali. Haka suka kwana a zaune yadda suka ga rana haka suka ga dare. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 4️⃣2️⃣ Washe garin ranar da ƙyar nake iya buɗe idona na jigata na zama majinyaciya tuburan ko yatsan hannuna ba na iya ɗagawa, duk yadda na so na tashi na gabatar da sallan asubahi na kasa tashi haka na ci gaba da zama yashe a wajen numfashina yana fita da wani irin sauti mai ban tsoro da haifar da firgici. "Ya Subhanallahi! Lafiyarki kuwa?". Na yi an jefa mini tambayar lokaci guda ana ɗago n daga inda nake yashe, dishi-dishi idanuna suke gano mini wacce ta takaima mini daren jiya ta nuna mini banɗaki. "Lafiyar ki kuwa ki na ji na?". Ta ƙara watsa mini tambayar tana riƙo hannuna ta sanya cikin nata tana murzawa a hankali. Da ƙyar na iya raba tsakanin haƙwarana da suka manne da juna tamkar wanda aka sanya mayen ƙarfe a tsakaninsu na furta zancen can ƙasan maƙoshina. "Don Allah ki taimaka mini da ko ruwa ne na sha, kar yunwa da ƙishirwa su yi ajalina". Ba ta amsa mini ba ta tashi ta fita babu jimawa ta dawo ta miƙo mini buredi da shayi. Ban yi wata-wata ba na karɓa kofin na kafa bakina sai da na sha kusan rabi kana na dire kofin, na soma yagan buredin ina ci hannu baka hannu ƙwarya. Take na ji cikina ya murɗa na ji tamkar ana ɗauɗaure mini dukkan kayan cikina, babu shiri na fita waje da sauri na dinga warara amai kamar zan amar da dukkan kayan cikina. Sosai na galabaita jikina ya yi sanyi ƙalau ko tashi daga wajen na kasa yi. Ta fito daga ɗakin tana ta jeranta mini sannu ta kawo mini ruwa na kurkure bakina na kwance fuskana kana na yi alwala. Ta riƙe ni muka shiga cikin ɗakin ita ta gyara wajen da na yi aman, ta dawo ta zauna a gefe na har sai da na iddar da sallan asubahin da na yi a makare na shafa addu'an da na yi kana na waigo ina kallon ta. Kafin na yi magana ta riga ni. "Sannu ya ya jikin nakin?". Na ƙirƙiro murmushin da iya ka cinsa kan leɓena na dasa a fuskata kafin na ce"alhamdulillah da sauƙi na gode sosai da irin kulawarki gare ni, ga shi kuma ko sunanki ban sani ba". Tun da na soma maganar take ta kallo na har na kai aya, ta gyara zamanta kafin ta ce sunana"La'aniyatu". Na waro idanuna waje cikin da mamaki na maimaita sunan"La'aniyatu kuma?". Ta gyaɗa mini kanta"sunana kenan, ba ki taɓa cin karo da irin sunan ba ko?". "Gaskiya tun da nake ban taɓa jin makamamcin irin wannan sunan ba. Amma kuwa kin san ma'anar sunan?". "Ina kuwa zan san wani ma'anarsa ni dai sunan da mahaifiyata ta sa min kenan. A cewarta sunan ne ya yi mata daɗi kuma da shi kowa yake ƙira tun tasowa ta har yanzu da nake yi miki wannan maganar". "Tirƙashi! Ita ma mahaifiyarta kin a cikin gidan nan take?". "Ƙwarai kuwa, Hajiya Babba ita ce mahaifiyata". Muƙut na haɗiye wani miyau mai ɗaci daga maƙoƙarona ina sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya ban san lokacin da zuffa ya keto mini ba na fara fiffita da bakin hijabina. "Ke kuma me ye sunanki?". Kalamanta suka yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka, sai da na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na ce"sunana Amatullah". "Daga wani gari kike don na ga alamar ke ba ƴar cikin garin nan ba ne, tun daga yanayin Hausarki na ga ne haka. Sannan me ya rabo ki da gidan iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi jarumtar faɗin"sannu a hankali za ki san komai game da ni. Amma kafin zuwan wannan lokacin ina son ki yi mini wani alfarma guda ɗaga". Ta gyara zamanta alamar tana ji da saurarona hakan ya ba ni damar ci gaba da maganan cikin ƙwarin gwiwa. "Ina son na san wasu abubuwa dangane da tsarin gidan nan, wanda za su taimaka mini wajen gudanar da rayuwata a cikin gidan nan ba tare da wani matsala ta faru ba". Ta ɗan jim tana ta kallona kafin can ta furta"da farko dai kowa da kika gani a cikin gidan nan zaman kanta take yi, mafi akasarinsu iyayensu ne suka kore su ko kuma suka aikata wani mummunan abin kunyan da ya hana su zama a gaban iyayen ala dole suka haɗo kayansu suka baro iyaye da danginsu. Wasu kuma sun gagari iyayen ne shi ne suka sallama su suka shigo duniya, da yawan matan da za ki gani a cikin gidan akwai bakin uwa akan su wannan dalilin ya sanya ba sa kunya ko shakkan aikata komai. Abu na biyu shi ne komai na gidan nan na sayarwa hatta ruwan da za ki wanke idanunki da shi, in har ki na son zamanki cikin gidan nan ya yi tsawon rai dole sai kin zama fitsararriya ta buga wa a jarida wacce ba ta bari ko ta kwana, sai kin zama wacce ba ta raina ruwan shuka wacce duk wanda ya ɗaga mata ɗan ƴatsa sai ta karya shi komai tsufa ko kuma furfuransa". Babu shiri na dafe ƙirjina"na shiga uku! Wani irin zama ne wannan? Sannan wani irin sana'a matan gidan nan suke yi da suke iya ɗaukan nauyin kansu, tun da komai na sayarwa ne a cikin gidan?". Ta murmusa kafin ta furta"kowacce da kike gani tana da hanyar da yake kawo mata kuɗin shiga sai dai mafi akasarinsu jikinsu ne jarin su. Jikinsu suke bayarwa domin biyan buƙatan ransu. Suna hulɗa da manyan mutanen masu madarar kuɗi a hannunsu da masu riƙe da madafun iko. Ummata tana da ɗaurin gindi a garin nan don ta san manyan mutane da suke da ikon juya lamarin jahar nan shi ya sa take cin karenta babu babbaka babu wanda ya isa ya taɓa ta ya kwana lafiya". "Jikinsu fa kika ce suke bayarwa domin biyan buƙatansu. Zina kenan fa?". "Ƙwarai kuwa kuma ke ma ina mai tabbatar miki idan har ki na zaune a cikin gidan nan, a kwana a tashi wataran sai kin bi layin da suka bi. Don shi kaɗai ne hanyar rayuwa a cikin gidan nan shi kaɗai ne mafita ga duk wata macen da take zaune a cikin gidan nan". Na zabga tagumi da hannu bibbiyu ina sauƙe numfashi wani na bin wani tamkar wacce ta yi gudun ceton rai, ta dafa kafaɗuna"ba ki da wani mafita da ya wuce wannan, in kuma ba haka ba sai dai yunwa da ƙishirwa su yi ajalinki. Don ko mutuwa za ki yi babu mai kawo miki agaji a cikin gidan nan, kowa harkan gabanta take yi babu ruwan wani da wani. Kin ga rayuwar cikin gidan nan rayuwa ce da babu imani a cikin ta balle tausayi don haka tun wuri ma gwara ki yi ɗamara". Na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na ce"babu wani mafita sai wannan? Ni wallahi ko aikatau ne zan yi don na ciyar da kaina". Na yi ƙuri tana kallona tamkar ba da yaren Hausa na yi maganar ba. "Ba na ce babu ba amma dai na sanar da ke abin da yake a zahiri ne. Idan tun farko kin ga ba za ki iya ba ina mai ba ki shawarar tun kafin tafiyar ta yi nisa gwada ki koma gaban iyayenki don na ji ana cewa mutumcin kowacce mace a iske ta a gaban iyayenta komai talaucinsu. Ina takaicin ganin yadda kullum a cikin gidan nan sai an yi baƙin mata wasu sa'annina wasu ma na fi su a shekaru". Kafin na yi magana aka ɗago labulen ƙofar ɗakin babu neman izni Aminu ya faɗo cikin ɗakin ya bi mu da kallo kafin ya ƙariso ya zauna. "La'aniyatutu manyan gari wannan ɗin ma kin zo ki hure mata kunne ne kamar yadda kika saba? To ina so kin san wani abu guda ɗaya duk abin da kika ga ya sa ɓera fitowa daga raminsa ya faɗa wuta to haƙiƙa ya fi wutan zafi da ƙona a gare sa". Ta banka masa harara tana cuno baki ta ce"ni fa ka daina ɓata min suna, sannan ni ba wani hure mata kunne da na zo na yi na dai faɗa mata gaskiya ne kawai sannan ban mata dole ba in ta ga dama ta yi amfani da abin da na ce da ita in ta ga dama ta watsar da shi a nan da muka yi maganar". Tana gama faɗin haka ta tashi ta fita tana ƙananun magana. "Ina kwana an tashi lafiya". Na gaishe shi cikin girmamawa maimakon ya amsa sai ya jefo mini wata tambayar ta daban. "Ba wannan ba ne ya kawo ni na zo na ji hukuncin da kika yanke ne?". Na sadda kaina ƙasa ina sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na ce"zan zauna". "Za ki zauna?". Ya maimaita abin da na ce na gyaɗa masa kaina alamar e da hakan ya ba shi damar ci gaba da zancen daga inda ya tsaya. "Kin yi kyan kai kuma ina mai tabbatar miki da cewar ba za ki yi dana sanin zamanki a cikin gidan nan. Tun da na fara ganinki na hango wani a tattare da ke bariki za ta yi miki riga da wando". Na yi hanzarin katse shi"ni ba bariki na zo yi ba, zan nema sana'an da zan riƙe kaina da shi". Da mamakina sai na ga ya fashe da dariya har yana riƙe ciki sai da ya yi mai isars kafin ya ce"ba yau na saba jin irin wannan kalaman ba hasalima duk wacce kika gani a bariki da irin wannan kalaman take farawa, amma idan tafiya ta yi tafiya sai zancen ya sauya. Da ƙafarki za ki zo ki na neman wanda zai kwana da ke......". Na runtse idanuna tare da kai hannuna na toshe ƙofofin kunnuwana"ba zan taɓa aikata zina ba". "Lokaci ne zai tabbatar da hakan ƴan mata. Yanzu dai akwai wani abun da kike buƙata ne?". "Babu wani abun da nake buƙata, don wanda ka kawo jiya ma ban yi amfani da shi. Sama ko ƙasa na neme shi na rasa". "Ai mantawa na yi ban gaya miki ko filin tsakar gidan nan za ki fita ki ja ƙofar ɗakinki ki rufe shi da makulli. Don akwai ɓerane masu suffa mutane a cikin gidan nan da kuma masu dogon hannu, zan karɓo miki makulin ɗakin a wajen Hajiya Babba sannan zan taho miki da abin kari". Bai jira abin da zan ce ba ya tashi ya fice ya bar ni zaune a cikin ɗakin mamaki ya hana yin ƙwaƙwƙwaran motsi, so nake yi na yi karatun alƙur'ani amma ban ga alamar zan sama littafin alƙur'ani mai girma a cikin gidan ba, don haka na kifa kai da gwiwana ina karato abin da yake haddace a cikin kaina. "Da kin bar karatun nan tukunnan kin sa wani abu a cikin cikinki ƴan mata". Na tsinkayo muryar Aminu a tsakiyar kaina, na ɗago kaina ina duban sa yayin da yake ajiye wani baƙin leda a gabana kana ya miƙo mini wani ɗan makuli na kai hannu na amsa. "Wannan shi ne makullin ɗakin duk inda za ki motsa ki ja ƙofarki ki rufe ta, in ba haka ba kuwa an dinga yi miki sakiyan da babu ruwa, wataran hatta tabarman da kike kwance akanta sai an ɗaga ki an ajiye a gefen an ɗauke ta". "In sha Allah zan na rufewa". "Da kin yi kyan kai kuwa, ga abincin nan ki samu ki ci. Zan ciyar da ke na tsawon sati guda kafin ki waye da wasu abubuwan daga nan kuma zan bar ki da halinki ke za ki fita ki nemo ki ciyar da kanki har ni ma na raɓe a jikinki". Jikina ya yi sanyi ƙalau na kasa cewa komai har ya fita daga cikin ɗakin na ɗade zaune a inda ya bar ni ina ta saƙa da warwara a cikin raina. Ganin yunwa tana neman yi mini lakani ya tursasa mini jawo ledan na buɗe awara ne da buredi sai pure water guda biyu, na soma ci don maganin yunwa ba don ina jin daɗi ko ɗanɗanonsa a bisa harshena ba. Sai da na cinye tas na shanye ruwan guda ɗaya na bar ɗaya a waje na yi bacci ban san adadin awannin da na kwashe ina baccin ba sai hayaniyar da na ji kamar a cikin mafarki ne ya tashe ni. Na fito ƙofar ɗakin na tsaya domin ganewa idanuna abin da yake faruwa, kowa tana tsaye cirko-cirko a filin tsakar gidan. Yayin da wata matashiyar budurwa ta sha ɗamara tamkar mai shirin zuwa filin gwabzawa sai bala'i take yi kamar za ta yi aron baki. "Daman na daɗe da fahimtar don ƴan gidan nan hassada suke yi min sun ƙi jinin su ga na yi wani babban kamu. Tun da na haɗo da Alhaji Bashiru yake yi min ruwan sulalla ake yada min da magana, shi ne yau don an ga ba na nan aka haɗa baki za a yi min sakiyar da babu ruwa, shi ne aka ja shi har cikin ɗaki akan tsegumta masa cewar wai ba shi kaɗai yake zuwa ɗakina ba. To kwarankwatsa dubu ba zan laminta ba ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa, ko a fito min da munafukar ko kuma na bankawo gidan nan wuta kowa ya ƙone". Kamar wacce aka jefo ta haka Hajiya Babba ta fito daga cikin ɗakinta tana bala'i. "Wacce shegiyar ce mai tsinin baki nake jin tana ambata ƙona min gida?". "Hajiya ni ce munafurci aka haɗa min. Don an ga bana nan shi ne da Alhajina ya zo aka ja shi ɗaki ake tsegumta masa wai ba shi kaɗai yake zuwa ɗakina ba". "Ke Farida ƴar mutan gabas sa idonki a cikin nawa ki kalle ni da kyau. Idan ba ki shiryawa bariki ba kika shigo cikinta to ki kuma ki je ki nema ilminta sannan ki dawo. Ke yanzu akan wannan abun ne za ki zo ki na tada jijiyar wuya har da ikirarin ƙona min gida, ke yanzu sai na zaunar da ke na fassara miki ma'anar wannan karatun da ake faɗin duk wanda ya yi maka kan kara ka yi masa na rodi? Ke ma ai ware rana za ki yi ki je ki tare Alhajin wata ki fanshe abin da aka yi miki. Yo ai daman bariki alelen gero ne duk wanda bai iya ba kwaɓe masa take yi, don haka kowacce ta gama harkokin gabanta a watse na kashe wannan case ɗin". Tsimi-tsimi na ga kowacce ta ja jikinta ta koma ɗakinta bayan an gama jefawa juna harara da kallon uku saura kwata. Ni ma koma ciki na zauna ina ta jiran na ji an yi ƙiran sallan zuhur amma shuru kamar an aike Bawa garinsu. Ganin wankin hula yana neman kai ni dare na dauki ɗayan pure watern da na ajiye na fito na yi alwala da shi na shiga na yi sallan zuhur ina zaune inda na yi sallan La'aniyatu ta shigo, muka sakarwa juna murmushi kafin ta ce"har ya tafi kenan?". "Waye fa?" "Aminu mana tauraro mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba". Na saki taƙaitaccen murmushi ba tare da na ce da ita komai ba. "Kin ga mutumin kusan rabi da kwatan matan gidan nan shi ya kawo su, kuma duk wanda suka kwanta da shi ya biya su sai an cire masa nasa kason mai tsoka a ciki. Wani zubin har ɗaukan su yake yi ya kai su wajen manyan mutane su yi haramtacciyar mu'amala, akan kuɗi babu abin da ba zai iya aikatawa ba. Kuma ke ma ina tabbatar miki da cewar duk wannan rawan ƙafa da ɗawainiyyar da yake yi a kanki zzi fanshe su tsaf har da riba". Na yi shuru na kasa cewa komai sai can na furta"Allah ya kyauta shi kuma Allah ya ganar da shi". Ba ta amsa ba illa taɓe bakin da ta yi tana ɗauke kanta gefe guda. "Tun ɗazu ina ta zaune a nan ina jiran ƙiran salla amma shuru". "Ƙiran salla dai? To ai ko za ki shekara a nan ba za ki taɓa jin ƙiran salla ba. Tun daga farkon layin nan har ƙarshenta babu masallaci, islamiyya ko kuma wani majalasin da ake koyar da faɗin Allah da Manzonsa. Ke in taƙaice miki bayani babu wani ɗan arzikin da yake biyo wa a layin nan don duk mutumci da kimarka idan aka ganka a layin daga ranar ba za a ƙara yi maka kallon mutumci ba. Idan kin ji ana faɗin layin jahannama to layin nan kenan". [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________ Page 4️⃣3️⃣ Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina dafe ƙirjina da ya bugawa tamkar zai faso nama da fatana ya bayyano waje, ta kalle ni ta saki murmushi"mamaki kike yi ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta daman zarcewa da faɗin"indai mamaki kike yi to yanzu kika fara don sai an wayi gari watarana kin daina ma jin mamakin wasu abubuwan". "Allah ya kyauta". Na furta a taƙaice ba ta amsa mini ba har sai da na ƙara cewa"don Allah yanzu ƙarfe nawa ne?". "Fitowa na daga ɗaki dai ƙarfe huɗu saura". Na yi zumbur na miƙe ina tada iƙaman sallan asr, har na iddar da sallan tana zaune tana kallona na shafa addu'ar da na yi kana na fuskanto ta. "Don Allah ina neman wani taimako". "Faɗi kanki tsaye, matuƙar zan iya to kin same shi kin huta". "Ina so na zagaya cikin unguwan nan don kafin wa'adin da Aminu ya ɗebar mini na ciyar da ni ya cika. Ina so na tsaya da ƙafafuna ba tare da na bi hanyar da ragowar sauran mutanen gidan nan suka bi ba". "Za ki sha wahala ne kawai don a kaf unguwan ba na tunanin za ki sama aikin da za ki kare mutumcinki da shi. Idan har kin san cewar ba bariki kika fito yi ba me yasa tun farko kika baro gaban iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na furta"wannan wani labari ne mai zaman kansa watarana zan ba ki labarina. Yanzu dai ina so na fita don na lura zama bai kama ni ba". "Bari na duba idan Ummanta ta yi bacci sai mu fita na raka ki". Ba ta jira abin da zancen ba ta tashi ta fita da sauri, babu jimawa ta dawo" mu yi sauri mu fita, ta yi bacci na san kuma ba za ta tashi ba wataƙila sai nan da zuwa dare. Don ta shawo ta yi tatil". Na yi sakeke ina kallonta ganin ba ni da niyyan motsawa ya sa ta jan hannuna ta jijjiga ni na dawo cikin hayyacina daga kogin mamakin da na faɗa, ta ɗauki ɗan makullin ta muka fito ta ja ƙofan ɗakin ta rufe da makulin muka fita a zaure muka yi kiciɓus da wasu samari su biyu suna shigowa. Kamar za mu gogi juna da su amma duk da hakan sun ƙi matsawa sai ma ƙara matso mu da suke yi. "Gambo ka ba ni hanya na wuce tun kafin na yi maka rashi mutumci mai wasali". Ya fashe da dariya"to ki yi mana wani dare ne jamage mai gani ba La'aniyatu? Ni fa babu wani nau'in rashin mutumcin da ban ga ni ba, to don kin yi na ki a matsayinki na ƙaramar ƴar bariki ma ai ba zai yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba". Ɗayan ya saki tsaki yana banka mana harara"ni wallahi na rasa abin da ka gani a jikin wannan ƙwailan yarinyar da ka ji ka nace mata. Na rantse da Sarkin dake busan numfashi ko a yau na yi niyyan kwanciya da yarinyar nan babu makawa sai na yi ko da amincewarta ko babu. Bar ganin wai uwarki tana ba ki tsaro da kariya yarinya". "Kanku ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wanka na nake yi". La'aniyatu ta yi zancen cikin matsanancin ɓacin ran tana jan hannuna muak raɓa ta gefensu muka wuce tun da muka fito ba ta ce da ni komai kuma ba mu fasa tafiya ba kamar yadda ba ta sanar da ni inda muka nufa ba. Sai da muka yi nisa kafin na ce"na ga kaman ranki ya ɓaci bisa abin da samarin can suka yi miki ko?". "Kar ki damu zan koya musu hankali ɗaya bayan ɗaya". Na saci kallonta kafin na ce"su waye ne su ɗin? Sannan me yasa suke cin irin wannan alwashin a kanki?". Ta ja dogon numfashi ta fesar sai da ta shafe wasu mintuna ba ta yi magana ba. "Ki yi haƙuri idan abin da na faɗa ya sosa miki rai ko kuma ba ki ji daɗinsa ba". "Kar ki damu babu komai. Ba kowa ba ne su ɗin face irin ƴan iskan garin da suke taruwa a cikin gidanmu, gani suke yi don kasancewata ƴar magajiyar karuwai da ƴan daudu shikenan ni ma ƴar iska ce ba su san cewar baƙar tukunya ta kan iya fitar da farin tuwo ba". Na jinjina kaina alamar gamsuwa da dukkan zantukanta"haka ne kam kin san lamarin mutane sai haƙuri". "Kin gan ni nan tun da na yi wayau na iya bambamce tsakanin launin fari da baƙi daidai da rana guda ban taɓa jin rayuwar da mahaifiyata take yi yana burge ni ba. Tun ina ƙarama na tashi da tsana da ƙyaman irin rayuwar da take yi, tun kafin san haramcin abun a addinance nake jin tsanarsa a cikin raina. Mutane da yawa sun sha kawo min farmaƙi Allah yana kuɓutar da ni, da kuma taimakon Ummata don ita ma ba ta yarda na yi irin rayuwar da take yi ba tana ba n tsaro da kariya ta kowacce fuska". Ƙirjina ya yi mini nauyin gaske da na kasa cewa komai illa bin ta da ido nake yi, ganin yanayin da na shiga ya sa ta sauya maganan. "Ina ta suturu ma na mance ba na nuna miki wuraren". Na saki taƙaitaccen murmushi da hakan ya ba ta damar ɗaura daga inda ta tsaya"kin ga layin nan shi ne layin na isa. Duk wanda kika gani ya fito daga cikin layin nan to ya ci ya tada kai ne, don duk wanda ya zo ya gina muhalli a cikin layin wani ƙusa ne daga gwamnatin ko kuma wani hamshaƙin ɗan kasuwa, ko kuwa irin wanda iyayensu suke sato kuɗin gwamnatin su tara musu idan aka rasa abin da a yi da shi sai a zo nan a gidan gidaje da shi, ana zuwa hutawa duk ranakun ƙarshen mako mafi yawan ƴan matan gidanmu nan suke zuwa suna sheƙe ayarsu da zaran yamma ta kawo kai za ki ga kowacce yarinya mai ji da kanta ta ci kwalliya ta zo bakin layin nan ta tsaya daidai lokacin da masu gidajen suke dawowa daga aiki, idan kin kasance cikin masu rabo daga nan sai ki dace wani Alhajin ya yi wuf da ke shikenan kakarki ta yanke saƙa". Na sauƙe numfashi mai nauyi ina ƙarewa faɗin layin kallo sai da na ƙare masa kallon tsaf kafin na furta"Lalle kuwa layin na isa, ga tankama-tankaman gidaje da shimfiɗaɗɗun tituna". "Sai ma kin ga cikin gidansu aljannar duniya kenan, ga faffaɗan filin tsakar gida ya kai rabin wani unguwan". "To su ina matayensu da suke cin karensu babu babbaka, ko ba su da iyali ne?". "Su na da su wasu sun su ma har da ƴaƴansu. Sai dai mataye da ƴaƴansu duk suna can Abuja birnin tarayya wasu ma ba sa ƙasar gabaɗaya. Nan gidan kawai wajen shaƙatawa ne da more rayuwar duniya". Na ji shuru ina ƙara bin layin da kallo shuru yake ko'ina babu hayaniyar kowa da alama kowa yana cikin gidajensu ba sa fitowa sai da wani dalili mai ƙwari. Muka ci gaba da tafiya ina ta kallon layin da manyan gidajensu, haka muka karaɗe dukkan girman layin daga nan suka gargaɗa har cikin kasuwa ta nuna mini wurare da yawa, ba mu dawo ba sai da gari ta soma duhu daga yanayin duhun garin na tabbatar da cewa an yi ƙiran sallan magrib. Muna dawowa gidan muka iske manyan motoci a ƙofan gidan tamkar ana gudanar da gagarumin biki ko kuma walima. Ga mutane maza da mata tsaye cirko-cirko a ƙofar gidan, maza kama daga kan samari, tsaka tsakiya da kuma dattawa babban wani abin takaici har wa manyan mutane da aƙalla za su kai sa'an Abbana a shekaru. Sai da muka rarraɓe kafin muka sama hanyar shiga cikin gidan kowacce budurwa ta ci wanka ta caɓa ado kamar za su tafi gasar kyau na duniya. Kowacce ta tsuke cikin ɗamammun kayan da ba su tamaika da komai wacce rufe tsiraicinsu ba, ga ƙarin gashi da farata rututu a hannayensu kamar masu cin moshe. Na buɗe ƙofar ɗakina na shiga na hango wasu baƙaƙen ledodi guda biyu na saki hamdala don na kwaso yunwa kamar zan ci babu, na zauna na jawo ledar ina buɗe wa biredi ne da wainar fulawa guda biyar a leda sai kuma ruwan shayi ƙulle a leda, gefe guda kuma ga can ledar pure water an jingine a gefe. Na san babu wanda zai kawo mini wannan abun face Aminu don haka ban yi wata-wata na ɓula ruwan shayin na tsoma zuƙa ina haɗawa da buredi ina danne wa da wainar fulawan sai da na ci wainar guda uku na zuƙe ruwan shayin na ɗaura da ruwan pure water ɗaya na yi hamdala na tashi na ɗauri pure water ɗaya na zuba a buta na fito na yi alwala na koma ciki. Sallan magrib na yi ban tashi daga wajen ba har sai da na yi sallan isha'i, na zauna na zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta. Tunani barkatai suka dinga yi mini yawa a cikin kaina suna kai kawo a cikin kwanyata. Tunanin gida da ƴan uwana suka faɗo mini a raina tamkar faɗuwar aradu, ban san sa'ilin da hawaye suka fara kwaranyo mini daga idanuna ba kamar da bakin ƙwarya. "Anty Sawwama ki gafarce ni babu yadda zan yi ne ba ni da wani mafita saman da wannan. Ya zama dole ne na yi nisa da ku ko don kwanciyar hankalinku da nawa rayuwata ta gama tarwatsewa don haka ba zan zama matsala a cikin taku rayuwar ba". A bayyane na yi maganar wasu hawayen suna rige-rigen fitowa daga idanuna suna wanke mini fuska yayin da suke sauƙa har izuwa tudun wuyana, na daɗe ina kukan da dukkan ƙarfina har sai da numfashina ya soma sarkafewa kafin na zame na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama shamaki tsakanina da sararin samaniya. Kamar daga sama na ji sauƙar muryan La'aniyatu a na'urar naɗan sautina. "Har kin kwanta ne?". Na tashi na zauna"a'a yaushe kika shigo ban ji ko sallamarki ba?". Ba ta amsa mini ba har sai da ta nema waje ta zauna kana ta ce"ban yi sallamar ba ne, daman na zo ne mu yi hira don Ummata ta yi baƙi daga wata ƙasa daban sun tafi otel za su gana". Na waro idanuna waje cike da mamaki"a cikin daren nan?". Ta riƙe haɓa"yo mai ma aka yi da maza? Ai duk wani taron da za a yi wanda manyan mutane za su halarce shi to cikin duhun daren yin sa tare da taƙaitattun mutane". Na jinjina kai tare da kawar da zancen ta hanyar faɗin"ina so na nema aikin da zan yi na dinga rufawa kaina asiri, ni wallahi ko wankau ne ma ko surfe zan yi". Ta bi ni da wani irin kallo kwatankwacin irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce. "Yanzu ke a layin nan kin ga alamar wanda gidan da za su kawo surfe? Ai tuni bature ya kawo sauƙi ban ƙi ba dai wankau ɗin". Na yi saurin faɗin"don Allah ina san samu wankau ɗin?". Ta ɗan yi shuru kafin ta ce"gaskiya ba na ce ba don gidajen layin nan ma ba su cika zama ba amma dai ba za a rasa ba, wataƙila sai dai ki dinga bin gida-gida ki za a dace". Jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau kamar kazar da aka watsawa ruwan gishiri na tuna rayuwata ta baya lokacin da Abba yake raye a cikin duniya, rayuwa kenan wai yau a ce nake neman aikin wankau don na ciyar da kaina, hasali a lokacin baya ba a taɓa sauƙe tukunya a cikin gidanmu sai dai ba daɗi amma tabbas za mu ci mu ƙoshi. Ko ruwan da za mu jiƙa maƙoshinmu bai taɓa yanke mana ba. Na ja dogon numfashi na fesar ina zabga tagumi. "Lafiya kuwa na ga duk yanayinki ya sauya?". Kalaman La'aniyatu ya dawo da ni cikin hayyacina. "Babu komai kawai wani abun na tuna. Na gode da kulawarki a gare ni, mu tashi lafiya". Murmushi kawai ta sakar mini ba tare da ta ce da ni komai ta tashi ta fice. Na zauna na yi jigum ina ta tunanin abin duniya, wasu hawayen masu zafi suka ciko mini kurmin idaniyata, na tuna Umma lokacin da ta yi watsi da ni ta ƙi ba ni ko wani irin ƙofar da zan yi mata bayyana balle har ta fahimce ni. Na daɗe zaune ina tunanin na ji an bankaɗo labulen ɗakin an shigo na cira kai ina kallon Aminu har ya shigo ya zauna. "Na ga saƙo na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Ya ɗago ya kalle ni"in ce dai ki na lissa adadin kwanakin da kika yi a cikin gidan nan yanzu ko?". Na bi shi da kallon mamaki sai dai na danne mamakin da kalamansa suka shayar da ni na ce"ina sake da yawan kwanakin. Kuma in sha Allah kwanan nan zan nema aikin da zan dinga ɗaukan ɗawainiyya kaina da shi". Ya yi ƙuri yana kallona"wani irin aiki ke nan?". "Wankau ko kuma aikatau". Cikin maɗaukakin mamaki ya ce"da kuɗin wankau da aikatau ɗin za ki ɗauki nauyin kanki?". "In sha Allah". Na amsa da shi cike da dukkanin ƙwarin gwiwa. "Kar ki yaudari kanki Amatullah babu ta inda sana'ar wankau zai riƙe. Yadda kiken nan mace iya mace sura iya sura diri iya diri, ki na da kyawun sura ta yadda duk wani lafiyayyen namijin da ya yi ido huɗu da ke dole sha'awarsa ta motsa. Idan kin iya allonki to tabbas za ki yi moriyar bariki za ki ja zarenki shekaru aru-aru, don yanzu haka ma akwai hamshaƙan mazan da suke ganin gilmawarki a cikin gidan nan kuma sun yaba za su saki baki aljihu matuƙar kika ba su dama". Na runtse idanuna"ba zan taɓa aikata zina ba a cikin rayuwata". Ya yi saurin taran numfashina"ba ki shirya aikata zina ba kika shigo bariki". Ya miƙe tsaye ya tsaya"ki yi wa kanki karatun ta nutsu. Don tallafina gare ki na sati guda ne kuma yau an ci kwana biyu saura kwanaki biyar". Yana dasa aya a nan ya cika bujensa da iska ya fice ya bar ni zaune na kasa ƙwaƙwƙwaran motsi. Na ja dogon numfashi na fesar ina yi wa zantukansa tankaɗe da rairaya. Na cije leɓansa saboda bugawan da ƙirjina yake yi. Dole ne zai na yi zina kafin na sama abin da zan ɗauki nauyin kaina da shi? Tambayar da na jefawa kaina ke nan da tsawon daren na gaza samun amsarsa. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 4️⃣4️⃣ Haka na ƙarar da dukkan tsawon daren ina tunanin ina saƙa da warwara a cikin raina. Tabbas dole na tashi na nema na kaina in bay haka kuma na ji ana yi, sai dai ta ina zan fara wai ƙoƙarin cire wando ta kai. Ina zaune a inda na iddar da sallan asubahi ina ƙarewa ɗakin kallo cikin dubu, haƙiƙa ina buƙatar wasu abubuwan buƙatan rayuwa kamar kayan sawa, abinci da wasu ƙananun abubuwan. ban yi aune ba na ji wasu hawaye suna zubo miji daga idanuna wanda ban san dalilin zubar su ba, ban goge su ba kamar yadda ban yi wani yuƙurin haka su zuba ba. "Anty Sawwama ku yafe ni na san ba jefa ku cikin tashin hankali na rashina. Na san na shayar da ruhinku ɗacin baƙin ciki, sai dai na yi muku alƙawarin ba zan taɓa sauƙa daga turban da kuka ɗaura ni a kai ba zan ci gaba da kare mutumcina da tsayawa akan gwadaben da na taso a kai". Ina rufe bakina na kai hannu ina goge fuskana tare da miƙe wa tsaye na ci ragowar abin da na bari jiya. Sai da gari ya yi haske na fito waje so nake yi na yi wanka amma ba ni da abubuwa da yawa da za su taimaka mini wajen gudanar da hakan, sai na tsaya ruwa, na nema bokiti, soso da kuma sabulu uwa uba kayan da zan sauya idan na yi wankan. Ina dab da fitowa daga cikin ɗakin muka yi kiciɓus da La'aniyatu tana shigo wa na matsa mata ta shigo, muka tsaya muna kallon juna ina da ita kafin ta ce"ina za ki je kuma da safiyar nan? Na yi tunanin ma zan zo na samu ba ki tashi daga bacci ba". "Ina so na fita ne na je neman aiki don na ga rayuwar ba za ta yiyu a haka ba". Ta yi ƙuri tana kallona"kin dade dai sai kin nema aikin nan?". "To ya ya kike so na yi, Aminu ya shaida mini cewar ɗawainiyyar ciyar da ni na tsawon sati guda kawai zai yi wanda yanzu haka ya rage kwanaki huɗu rak, idan ban fita na nema ba ya ya kike so na yi da raina a lokacin da ya janye tallafinsa a gare ni". Na yi maganar ina ƙoƙarin ficewa ta riƙo hannuna"ki bi a hankali dai mutanen unguwan nan ba ababen yarda ba ne". Kaina kawai na jinjina mata na yi ficewa ta na bar ta a cikin ɗakin, sai da na fito ƙofar gidan na sauƙe numfashi mai zafi ina ƙarewa gabar da yamma kudu da arewa kallo. "Ya Zuljalali wal ikram ga baiwarka nan". Na yi furucin a bayyane cikin sanyin jiki haɗe da na murya, na salwantar da aƙalla mintuna uku a tsaye kafin na ja ƙafafuna na bar ƙofan gidan na yi dogon tafiya kafin na iso bakin wani tankamemen gidan da aka ƙawata da shukayen koren fure. Na ƙarar da mintuna ina kallon gidan kafin na isa na ƙwanƙwasa gate ɗin wani mutum ya fito ya buɗe ƙaramin ƙofan gidan gare ɗin yana jefa na da wani irin kallo. Na tsuguna har ƙasa na gaishe shi sai dai maimakon ya amsa mini sai ya jefo mini wats tambayar cikin zafin rai. "Ke me ye kike yi a nan wajen?". "Na zo neman aiki ne?". Ya watsa mini wani ƙazamin kallo"ce miki aka yi ana neman masu aiki a gidan nan? To su masu aikinsu tun daga Abuja ake kawo musu kamfani suke zuwa su cike takarda su zayyana irin wacce suke so a kawo musu su zaɓa, ki tashi ki bar ƙofar gidan nan tun kafin na ɓata miki rai". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo"don Allah ka taimaka mini na shiga cikin gidan na yi musu magana da kaina, wallahi ina tsananin buƙatar aikin nan ne". "Ke zan haɗa da Allah ai ki taimake ni ki tashi daga nan wajen tun kafin masu gidan su fito. Don idan suka fito da ni da ke duk ba za mu ji daɗi ba". Yana rufe bakinsa aka buɗo ƙofar gidan yana faɗin"wai ina ka shiga ne ina ta ƙiranka?". Cikin rawar jiki ya ce"Allah ya huce zuciyarka ranka ya daɗe ka daɗe ka yi shekaru irin na dabino, na ɗan fito waje ne amma ban yi nisa ba". "Ka zo ka buɗe min gate zan fita amma ba zan daɗe ba zan dawo". "To ranka ya daɗe a dawo lafiya". Har sun juya za su koma ciki idanun mai gidan ya sauƙa a kaina ya tsaya cak yana ƙare mini kallon tsaf. "Wannan yarinyar fa me ye take yi a nan wajen?". "Irin masu zuwa neman aikin nan ne, na ce da ita gidan nan ba a buƙatar wata mai aiki amma ta ƙi tafiya sai magiya take ta faman yi min". Maigidan ya ɗan matso kusa da n tare da zura dukkan hannayensa cikin aljihun doguwar rigar jallabiyar da take jikinsa fara sol, har izuwa lokacin idanunsa a kaina ya furta"ƴan mata me ye kike buƙata?". "Aiki nake nema ranka ya daɗe ni wallahi ko wankau ne ma ko raino zan yi". Ya yi shuru yana ci gaba da kallo na har sai da na tsargu da kaina na yi ƙasa da ƙwayoyin idanuna ƙasa kafin ya ce"to shigo daga ciki mana sai mu yi magana". Raina a wanke fes ban kawo komai a cikin zuciyata ba na yi masa godiya muka shiga cikin gidan. Babban gida ne iyakar kallona ban hango ƙarshensa ba, ga wajen ajiye motoci da aka jera wasu rantsatstsun motoci. Duk girman gidan talis ne mamaye a ƙasa ga wasu shuke-shuke masu ɗaukar hankali da daɗin ƙamshi. Yana gaba ina bin sa a baya har muka isa cikin falon da aka ƙawata da duk wasu nau'in ababen jin daɗi da more rayuwar gidan duniya. "Ga waje ki zauna bari na ƙira Madam ɗin". Ya yi zancen yana nuna mini kujerar zama, na zauna a ƙasa dirshan ina jiran dawowar da tare da matarta san babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da wani tray ya ajiye mini a gabana, ruwan gora ne da lemon kwali sai kuma kofi su kenan a bisa kan trayn ɗin. "Ga ruwa ki jiƙa maƙoshinki kafin ta fito, ta ɗan shiga wanka ne amma babu jimawa za ta fito sai ku yi magana da ita wataƙila ba za'a rasa gurbin da za a ba ki aiki ba. Don na ga alamar kamar a buƙace kike da aikin ko?". Na yi hanzarin gyaɗa masa kaina"e wallahi ina son aikin. In dai har Allah ya sa na dace da samunsa". Ya murmusa kafin ya ce"ki jira ta fito bari na shiga na ba ku waje". Kaina kawai na gyaɗa masa kai ya tashi ya taka wasu matakala ya haye sama, na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da runtse idanuna na ɗaga hannayena sama ina zabgawa Allah godiya da ya tarfawa garina nono na dace da samun aikin da nake biɗa. Na ji an dafo kafaɗana ta baya na yi saurin buɗe lumshashshun idanuna tare da waigawa, cak numfashina ya tsaya cak na wucen gadi bisa mummunan gamon da idanuna suka yi. Maigidan na gani tsaye a gabana daga shi dai ɗan bante zandardar da shi mai faffaɗan ƙirji. Na yi zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsigarawa matsilli jikina gabaɗaya yana rawa na ce"ranka ya daɗe ko zan je na jira ta a waje ne?". "Ai babu wanda mace ma a cikin gidan nan, ni kaɗai nake rayuwa a cikin gidan, amma zan ji daɗi idan ke kika amince kika ba ni abin da mace take ba wa mijinta". "Amma ka san ba mace a cikin gidan ka ce na shigo har da cewa na jira ta tana zuwa?". Cike da tashin damuwa balle kunyar abin da ya aikata ya ɗage kafaɗa ya ce"to hakan laifi ne don na gayyato kyakykyawar mace kamar cikin gidana?". Ya ƙare zancen yana ƙara nufo inda nake, na ɗaura hannu a ka na kurma ihu. "Idan ka matso inda nake sai na yi mata ihu wallahi". Da mamakina sai na ga ya bushe da dariya yana faɗin"ai ko lasifika za ki ɗauko babu wanda zai ji sautinki balle har ya kawo miki ɗauki. Ki ba ni haɗin kai kawai mu yi abun ne dukka ba zai wuce mintuna ashirin zuwa talatinsa ƙarƙarinta mu yi awa ɗaya, sannan zan ba ki duk adadin kuɗin da kike buƙata ki je ki kashe wutar gabanki". Hawaye suka fara zuba daga idanuna"ka ji tsoron Allah ka sani duk abin da kake yi yana sama yana kallonka. Sannan akwai ranar da za a haska duk abin da ka aikata lokacin da kake raye a gaban dukkan halittun duniya daga na farko har zuwa na ƙarshe, shin kai ba ka tsoron irin wannan ranar?". Ya yi sakeke yana kallo na"kin ga Malama duk wannan maganganun nakin ba su za su saka na ƙi aiwatar da abin da na yi niyya a kanki ba". Da sauri na juya zan fita ya riƙo gefen hijabina, ban yi wata-wata ba na fice hijabin na bar masa na fantsala da gudu na yi wajen ƙofa Allah ya rufa mini asiri na ji ƙofar a buɗe na fice ƙafata tamkar zai taɓo ƙeyata tsabar saurin da nake falfalawa. "Baiwar Allah lafiya na ga kin fito cikin tashin hankali?". Mai gadin ya tare ni da zancen da na kasa samun sukunin amsa masa. Na soma jan gate ɗin kamar zan cire ta. "Ki yi a hankali bari na buɗe miki". Ya zare sakaran jikin ƙofan ya buɗe na fita sai da na fito na lura da yanayin da nake ciki, na ware ɗan kwalin kaina na yafa a kaina na lulluɓe wuyana zuwa ƙirjina da shi, ko takalmina ban ɗauko ba na fita tsabar kiɗima da ruɗewar da nake cikinsa. Na ji an buɗe ƙofar na yi saurin waigawa, mai gadin ne ya fito ya zuba mini ido cikin takaici yake faɗin"wannan dalilin ne ya sa tun farko na ce ki bar ƙofar gidan nan don in har Allah ya fito ya kan ki na san abin da zai faru kenan. Gidan nan da kike babu wata mace a cikinsa shi kaɗai yake zaune shi ma kuma sai ya ɗebi lokaci bai zo ba. Idan kuwa ya zo to har ya tafi duk daren duniya sai ya kawo mace wacce za su kwana tare. Kin gan ni nan ni ma da nake wannan aikin ba a son raina ba ne kawai dai don ba yadda zan yi ne, wannan ne hanyar cin abincina. Ƙarbi wannan ki hijabin ki saka na matata ne na ƙarbo miki a ciki". Hawaye suna gudun famfalaƙi a fuskana na miƙa hannu na ƙarba hijabin na saka na suturta jikina. Na tsuguna har ƙasa ina yi masa godiya ya amsa yana ta saka mini albarka. Har na tashi zan tafi ya tsayar da ni. "Ƴata ki kasance mai taka tsantsan don duk yawancin gidajen unguwan nan ba mutanen Allah ba ne a cikinsu. Idan har ba ku rasa abin da za su sanya a baki salati ba ke da iyayenki to ki yi haƙuri da wannan neman aiki don akwai hatsari a cikinsa sosai. Gwara ki zauna a gida tare da iyayenki idan ma ya zama dole neman aiki to mahaifinki ki ya fi dace ya fita ya nema ya kawo muku". "To Baba na gode sosai". Na amsa masa har zuwa lokacin hawaye suna wanke mini fuskana, ya cire silifas ɗin ƙafarsa ya ba ni na saka ya umarce ni da har na ƙara ko da bin layin balle na zo kusa da gidan. Haka na bar ƙofar gidan ina kuka da takaicin abin da ya faru. Ina cikin tafiya takalmin ya tsinke na ji kamar na ɗaura hannu a ka na ta zabga ihu ko zan ji sauƙi halin da nake ciki. Haka na riƙo takalmin a hannu ga rana ga yunwar da take ƙwaƙular ƴaƴan hanjina na dawo gida, na sama ƙofar ɗakin a kulle da makulin na san La'aniyatu ce ta rufe ɗakin don ita na bari a cikinsa. Kafin na shiga ɗakinsu ta fito kamar ta san abin da zan tambaye ta ta miƙo mini ɗan makullina, na karɓa ba tare da na ce da ita komai ba na buɗe ɗakin na shiga na zube akan tabarma kamar kayan wanki ina sakin wani irin kuka mai ratsa zuciyar mai saurare. "Wai me ya faru ne kin fita kuma kin dawo ki na kuka?". Ban iya cewa da ita komai ba saboda yadda kukan ya gama galabaitar da ni. Ta ɗago ni tare da kwantar da kaina a bisa cinyoyinta tana ƙara maimata mini tambayar a karo na biyu. "Wai me yake faruwa ne Amatullah?". "Me yasa mutane ba su da tausayi ne? Me yasa masu kuɗi ba sa tausayi na ƙasa da su? Me yasa masu kuɗi ba sa tausayin masu rauni? Wani irin al'umma ce muke rayuwa a cikin da babu tausayi balle jin ƙai?. Kowa babu Allah a cikin zuciyarsa kowa saɓon Allah da kaucewa koyarwa Annabinmu Muhammadu kawai aka saka a gaba. Ta ina za a sama yadda ake so? Me yasa masifo da bala'i ba za su baibaiye al'umma ba?". Shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe na tsawon mintuna kafin ta kawar da shi ta hanyar faɗin"wai me ya faru ne?". Na kwashe komai tiryan-tiryan na sanar da ita ta daɗe ba ta yi magana kafin can ta ce"kin ga hakan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar sauran matan da kika gani a cikin gidan nan su ma dole ce ya sanya su aikata abin da suke aikatawa na haramci ba wai don son zuciyoyinsu ba". Na tashi na zaune"babu wani uzuri cikin aikata saɓon Allah. In sha Allah zan ci gaba da nema har na dace da na ƙwarai". Ta yunƙura za ta yi magana na dakatar da ita"ki taya ni da addu'a kawai". Ta ja numfashi ta fesar kafin ta ce"shikenan Allah ya sa ki dace". "Amin". Na amsa da shi, ta tashi ta fita ta bar ni a cikin ɗakin, na kwanta ina tunanin mafita ga bahaguwar rayuwata. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 4️⃣5️⃣ Tun da na shiga cikin ɗakin ban fito sai alwalan da na fito na yi na koma ciki na zauna, a nan na yi sallan zuhur, na yi asr har magrib. Yunwa ya dinga ƙwaƙulan kayan cikina na dafe cikina ta faman murtsukuku a wajen kamar zan mutu, ina mayar da wani irin numfashi da ƙarfi da ƙarfi da ƙyar na iya tashi na zauna ina salati tare da karanto dukkanin wani addu'ar da ya fara zuwa bakina. Ganin yunwa yana neman raba ni da numfashina idanuna har wani dishi-dishi yake yi mini ga wani irin nauyin da kaina ya yi mini na bala'in gaske. Da rarrabe na fito ƙofar ɗaki na dinga warara amai tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina sosai nake aman har jikina yana rawa kamar ana jona mini wutar lantarki. "Sannu Amatullah ba ki da lafiya ne?". Na tsinkayo muryar La'aniyatu a bisa cikin kwanyata, na kasa ba ta amsa da kalmomin baki ila gyaɗa mata kaina da na yi alamar e ta taimaka mini na tashi tsaye sai dai ƙafafuna sun kasa ɗaukar nauyina. Muka koma ciki na kwanta lamau kamar ruwa na kasa tashi balle na ɗaga ko da ƴatsan hannuna. "Wai me yake damunki ne?". Na yi jarumtar faɗin"yunwa nake ji wallahi ji nake yi kamar numfashina zai tsaya cak". "Bari na kawo miki abinci sai ki ci". Ta ƙare zancen tare da tashi ta fita babu jimawa ta kawo mini biredi da ruwan shayi da babu ko madara a cikinsa, na tashi jikina yana rawa na amsa na ɓula ledar na soma zuƙa ina turawa da biredin sai da na ci ya fi rabin biredin kana na ƙarisa zuƙe ruwan shayin na koma na kwanta ina mayar da numfarfashi. "Sannu! Ya jikin na kin?". "Yunwar ce fa kawai". Cike da tausaya wa ta ce"ba ki ci abinci ba ne tun safe?". Hawaye suka ziraro mini daga gefe da gefen idanuna kana na ce"ban ci ba Aminun yau gabaɗaya bai shigo ba". Ta sauƙe numfashi mai ƙarfi da har sai da na jiyo sautin fitar sa"na ji fa Ummanta suna waya da shi yana cewa ya yi tafiya can wani gari, kuma ina tabbatar miki da cewar da wata matar zai dawo ya kawo ta cikin gidan nan". "Yanzu haka zan zauna kenan babu ci babu sha har sai ya dawo daga tafiyar da ya yi ke nan?. Dole na tashi na nema yadda zan taimaki kaina, ki riƙe ni na tashi na zauna na yi salla". Na wangale baki da ido tana duba na"salla kuma? Ba ki da lafiyan ma ba za ki huta ba? Ban taɓa ganin macen da take girmama ibada sama da ke ba. Tun da kika zo gidan nan ban taɓa ganin kin yi fashin salla ba". Cike da matsanancin mamaki nake bin ta da kallo na gaza cewa komai har ta gama zancen ta ƙare. "Salla kam ai ko da lafiya ko akasin hakan dole ce akan dukkan wani musulmi mai hankali kuma balagagge. Matuƙar kana cikin hankalinka dole ka yi salla ka bautawa Ubangijinka". Ta sauƙe numfashi kafin ta ce"tirƙashi! Ni dai na tashi ne kawai a matsayin musulma amma duk wasu abubuwan da suke cikin musulunci ban san su ba kuma ba na aikata su. Sallar ce kawai ita kuma bai fi a sati na yi sau biyu ba shi ma sai na ga dama, tun da nake Mahaifiyata ba ta taɓa nuna min cewa salla dole ne a kaina ba balle ta koyar da ni sauran wasu abubuwan addini". "Ko ba ta koyar da ke ba ke ya dace ki tashi ki nema ilmi ki nema ilmin addininki domin inganta rayuwarki ta gidan duniya da kuma na lahira. Kin ga hatta wannan sunan da ake ƙiranki La'aniyatu ba shi da gurbi a cikin addinin musulunci, domin fassara Annabinmu ya koyar da mu cewa mu sanya wa ƴaƴanmu sunane masu kyau da ma'ana domin suna linzami shi yasa ake so a dinga sanya wa ƴaƴa sunayen salihan bayi, masu imani da zuciyar tausayi waɗanda suka yi wa addinin musluncin hidima da ƙarfinsu, lokacinsu da kuma dukiyansu". "To me ye fassaran sunan nawan?". "Kalmar La'aniyatu kalmar labarci ne da yake nufin tsinanniya ko kuma wani abun da aka kwashe masa albarka". Ta dafe ƙirji"tsinanniya kuma?". Na gyaɗa mata kaina"ƙwarai kuwa a duk lokacin da aka ƙira sunanki hakan na nufin ana ƙiran ki da tsinanniya ne". Ta yi shuru na lura gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jifa da ruwan gishiri, na dafa kafadunta cikin sigar ƙafafa gwiwa na ce"kar ki wani damu fa, ai har yanzu lokaci bai ƙure ba. Za ki iya sauya sunan zuwa duk sunan da kike so mai ma'ana da asali gami da tushe". "Ba zan ma fara wannan garajen ba Amatullah, na san ma Ummata ba za ta taɓa barin na yi hakan ba. Tun da ƙaddarata ta faɗo a haka babu yanda zan yi face na rumgume ta yadda ta zo min". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu alamar ba ta son jin komai daga gare ni"Amatullah kar ki kawo min rikici da ruɗu a cikin rayuwata. Na yi kowa sanin wace ce Ummanta don ita ta haife ni hakan ba zai hana ta hukunta ni idan na bujire mata ba, ba abin wahala ba ne a wajen ta ta saka a haukata ni. Don haka maganin bari kar a fara Hausawa suka ce zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki". Ina ƙare zancen ta tashi ta fita da sauri ba tare da ta ba ni damar cewa komai ba. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina dafe jikin gini na tashi na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan isha'i. Ina zaune a inda na yi sallan aka ɗago labulen ɗakin akan shigo. Wata matasjiyar budurwa ce ta tsuke cikin shirgar ƙananan kaya dogon wandon da aka tsatstsaga gwiwansa sai kuma wata rigar da babu hannu a jikinta, ta tula uban gashin doki a kanta da ya sauƙo har bayan wuyanta tana taunar chewgum da yake ba da sautin ɗas ɗas. "Ke ce Amatullah?". Na gyaɗa kaina"e ni ce". "To ki zo Hajiya Babba tana son ganawa da ke a cikin ɗakinta". "Na shiga uku! Allah ya sa ba wani laifin na yi ba". Na galla mini harara"wannan kuma idan kin je za ki ji ko ma me nene. Ni dai na isar da saƙo". Tana dire zancen ta juya ta fice ta bar ni cikin tarin zulumi da fargaban abin da zan je na tarar. Cikin mutuwar jiki na tashi na fito na nufi ɗakin Hajiya Babba na tsaya daga waje ina kwaɗa sallama sai da ta ba ni iznin shiga kana na shiga. Tana zaune akan kujera ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ɗaya na zauna a ƙasa tare da gaishe ta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa. "Hajiya sannu da hutawa, an ce wai ki na nema na". Na ajiye wayar da take latsa wa ta fuskanto ni da kyau tare da faɗin"kwananki nawa a cikin gidan nan?". Ƙirjina ya buga na shiga tsoron kar ta ce na haɗa nawa ya nawa na bar cikin gidan don na ga hakan ba wani abu ne mai wahala a wajenta ba. Kafin na ba ta amsa ta ci gaba da cewa"na lura har yanzu ba ki fara mu'amala da kowa ba balle har ki sama kuɗin da za ki dinga biyan kuɗin hayan ɗakinki. Sannan har zuwa wannan lokacin Aminu shi yake ɗaukan nauyin ci da shanki, shin dama ba ki shiryawa rayuwar bariki ba kika saka ƙafa kika fito daga gidanku? Ba ki tanadin guzurin irin rayuwar nan ba kika baro gaban iyayenki?". Jikina gabaɗaya ya yi laushi na kasa cewa da ita komai illa sadda kaina ƙasa da na yi da hakan ya ba wa hawayen da nake dako damar tsiyaya. Muryata can ƙasan maƙoshina na furta"Hajiya in sha Allah zan nema sana'ar da zan din ga ɗaukar ɗawainiyyar kaina da shi kwanan nan". "Wane irin sana'a kenan?". "Kowani irin aiki idan zan samu na cikin gida, ko wankau ne ko kuma rauno....". Tun kafin na rufe bakina ta katse mini numfashina"wankau dai da na sani?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"mace kamar ki ta tsaya tana yin wankau ai wannan abin a duba lamarin ne, yadda kike da dirin nan ga kuma kyawun sura da ko mace ƴar uwarki ce ta gan ki sai ta ƙara bin ki da kallo balle kuma ɗa namiji. Me ye zai hana ki yi amfani da damar da Allah ya ba ki wajen cin duniyarki da tsinken sakace". "Ban gane abin da kike nufi ba?". Ta gyara zamanta kafin ta ce"ina nufin akwai maza masu kumbon susa masu hannu da maiƙo da suke neman mata ire-irenku ruwa a jallo. Ba don komai ba sai don biyan buƙatar kansu kuma ba sa ƙyashin kashewa mace ko nawa ne matuƙar za su sama abin da suke so a wajen ta, idan ma tsoronk ɗaukar ciki ne yanzu zamani ya zo da abubuwa da yawa, ana amfani da comdon domin hana ɗaukar ciki. Idan kin yi dace ma wasu mazan ba sai kun kwanta da su ba kawai da zaran sun sama nutsuwa da ke shikenan buƙatarsu ta biya. Sannan idan duk hakan bai yi miki ba kawai wata hanya mai sauƙin gaske, akwai matan manyan mutane a cikin ƙasar nan da kewaye da mazajen suka tara musu dukiyar da ko za su yi shekaru ɗari a duniya ba za su iya cinye shi ba, duk wani nau'in jin daɗi na duniya suna samunsa su ci abin da suke so su sha abin da ransu yake so, su sa suturar da duk suka ga dama sannan su hau duk kalar motar da suka yi ra'ayi, su je duk ƙasar da suka zaɓa, su kashe duk adadin kuɗin da suke so. Sai dai matsalarsu guda ɗaya ce jal ita ce ba sa samun lokaci da kulawa mazajen su. Wannan dalilin ya san da yawa da cikinsu suka soma neman maza a waje sai dai masu wayo a cikinsu ba maza suke bi ba, mata ƴan uwansu suke sawa a nemo musu su yi duk abin da za su yi da mijinsu na aure da ita. Su kan ɗauki dukkan nauyinta su yi mata komai da komai, su jiyar da ita daɗin da ba ta taɓa jin makamancin sa". Tun da ta soma zancen nake bin ta da ido har ta kai aya. Na numfasa kafin na ce"shin Hajiya aikata hakan yana daga cikin sharaɗin zama a cikin gidanki ne?". Ta watsa mini wani wulaƙantaccen kallo kafin ta amsa mini a taƙaice "A'a". "To in dai har hakan ba shi ne sharaɗin zama a cikin gidanki ba. Ina so ki ba ni dama na je na nema aikin da zan riƙe kaina da shi ba sai na bi wannan hanyar da duk kika zayyana ba". Ta yi banza da ni ba tare da ta ce da ni uffan ba haka na ci gaba da zama ba ta ce da ni ci kanki ba. Har sai da na gaji don kaina na ce"Hajiya zan iya tafiya?". Ta yi mini wani kallo ta wutsiyar idonta kafin ta ce"wai dama ba ki tafi ba? Za ki iya tafiya". "Na gode mu kwana lafiya". Na furta yayin da nake tashi na fice daga ɗakin, tun kafin na isa cikin ɗakina hawaye suke zuba daga idanuna har na isa, na rufa ƙofar na rufe tare da jingina a jikin ƙofar ina sulalewa a hankali har zuwa ƙasa. Na kifa kai da gwiwana ina saki wani irin gigitaccen kuka mai ratsa zuciya. Na raba dare ina kuka kamar raina zai fita kafin wani wahalallen bacci ya ɗauke ni ban tashi sai da gari ya fara yin gaske, na tashi a firgice saboda mafarkin da na yi da Abba. Wai ya zo cikin ɗakin sanye da fararen kaya ya taɓo kafaɗana na ɗago kaina ina kallonsa yayin da hawaye yake zuba daga idanuna. Fuskarsa ɗauke da yalwataccen annurin yake share mini hawayen da ya ɓata mini fuska. Bai ce da ni komai ba haka ni ma Allah bai ba ni ikon yi masa magana a cikin mafarkin ba har na farka. Sai da na sauƙe dogon numfashi kafin na tashi na fito sai a lokaci na tuna ko ruwan alwala ba ni da da shi balle wanda zan wanke fuskana da shi. Duk abin duniya ya taru ya yi mini yawa, na tsaya a ƙofar ɗakin ina tunanin mafita. Ina tsaye La'aniyatu ta fito muka sakarwa juna murmushi ni da ita kafin ta ce"ɗazu na zo ai na ga ba ki buɗe ƙofar ba ya ya jikin nakin?". "Da sauƙi". "Kamar wani abun kike buƙata ko?". Na sauƙe numfashi kafin na ce"wallahi kin ga na tashi ne ba ni da ko ruwan da zan yi alwala da shi". "To bari na kawo miki mana". Har za ta juya na dakatar da ita"a'a indai akwai inda ake ɗebowa ki kwantata mini kawai. Ai ba zan dawwama kullum sai an ɗauka an ba ni ba, gwara tun yanzu na fara taimakawa kaina". "Da nisa fa kuma kin ga har yanzu gari bai gama yin haske ba. Ƙarfe biyar ne da wasu ƴan mintuna". Cikin ƙosawa da sauraron zancenta na ce"ni dai don Allah ki taimaka mini ki kwantata mini wajen sai kuma ki ba ni bokitin da zan ɗebo a ciki". Ba ta yi musu ba ta koma ciki ta ɗauko mini bokitin ta ba ni ta yi mini kwantancen wajen na yi mata godiya, duk yadda ta so ta raka ni ƙin yarda na yi duk da ba wani gane kwantancen natan na yi sosai, amma na gwammace na fita na nema da kaina. Sharau kan layin babu kowa sai kukan karnuka da ƙwaɗuna, haka na dinga tafiya har sai da na fice daga layin na shiga wani na yi ɗan tafiya kaɗan. Na tsaya ina ta rarraba idanu don ta ce da ni a farkon layin zan hangin fanfon jikin wani masallaci. Hamdala na yi yayin da na hango fanfon na ƙara sauri na isa wajen na buɗe na wanke fuskana, na kurkure bakina kana na yi alwala. Na cire ɗan kwalin kaina na shimfiɗa da niyyan yin sallan a kai, na ga an miƙo mini sallaya. Na tsorita sosai don ban ga mutum ba sai kawai gani na yi an miƙo mini abu. "Karɓi ki yi sallan a kai". Na ji an furta tare da ajiye mini sallayan a kan ɗan kwalin da na shimfiɗa, bai jira abin da zan ce ba ya nufi masallacin da saurin don lokacin har an shiga sallan. Na shimfiɗa sallayan na tada kabbara, a nutsu na gabatar da sallan har na iddar don jam'i na b masalallacin. Ban yi wani dogon addu'a ba na tashi don sa'ilin har an fara fitowa daga cikin masallacin. Na ɗeba ruwa a bokitin na ninke sallayar na riƙe a hannuna. Ina ta rarraba ido ganin ta inda mutumin zai fito amma shuru har aka gama fitowa sannan na ga ya fito. Ya na sanye ne da jallabiya doguwa kalan ruwan ƙasa sai wani ƙaramin hula a kansa fara sol ban ga fuskarsa da kyau ba abu ɗaya zan iya cewa na gani a fuskar sa shi ne sajen da ya kewaye fuskar. Yana isowa na miƙa masa sallayar bai karɓa ba ya tsaya kallona har sai da na zargu da kaina na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. Sai da ya gama yin sa ya sa hannu ya karɓa sallayan bai ce da ni komai ba ya juya ya tafi. Na daɗa gammo da ɗan kwalina na ɗaura bokitin a kaina na bar wajen. Ina isa gida na zuba ruwa a butan da Aminu ya kawo mini na ajiye shi domin yin alwala. Ragowar na shiga banɗaki na watsa a jikina saboda tun da na zo ban ga ruwa ba. Kayan jikina na mayar na fito. Ina zaune ina tunanin ta inda zan fara La'aniyatu ta shigo ta ajiye mini biredi a gabana na cira kai ina kallon ta"wannan fa?". "Na ki ne mana". "Wai ke Ummanki ba ta yi miki faɗa ne na yadda kike ɗauko abubuwa ki na ba ni. Bayan na san cewa kowa shi yake ci da kansa a cikin gidan da samar wa kansu dukkan wasu ababen buƙata". "Ai ba ta sani zan da nake ɗauko miki". Na waro idanuna waje"to ai kuwa ba zan ƙara amsa ba, don haka wannan ma ki ɗauka ki mayar da shi inda kika ɗauko. Daman ba yunwa nake ji ba kuma fita ma zan yi". Ina dire zancen ma tashi na ɗauko mata bokatin da ta ba ni na bata tare da godiya. Duk yadda ta so na karɓa biredin na tubure akan cewa ba na ji yunwa dole ta haƙura ta bar ni, muka fito tare da ita daga ɗakin na kulle ƙofar na ba ta ajiyar makullin. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 4️⃣6️⃣ Na daɗe tsaye a ƙofar gidan ina ta tunani da nazarin inda zan nufa, ban san sa'ilin da hawaye suka fara kwaranya daga koramar idanuna ba. Tunawa da na yi irin rayuwar da na yi a baya da kuma Abba sai dai har yanzu ba na dana-sani balle nadamar barin gida da na yi. Na yi imanin tun da uwar da ta ɗauki nauyin cikina tsawon wata tara da wasu kwanaki a jikinta, ta yi wahalar nishin naƙudana, ta shayar da ni daga jikinta na tsawon shekaru biyu, ta raine ni har na girma na yi wayo na zama mutum. Ta iya fito ɓaro-ɓaro ta bayyanawa duniya ba ta buƙatata ba ta ƙaunar ganina ta sallama ni a duniya to babu wanda zai iya jure zama da ni. Komai alaƙa, dangantaka da kuma ƙarfin igiyoyin zumucnin da suke tsakani. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina kawar da hawayen da suke gudu a bisa dandamalin fuskana, tafiya na soma yi har sai da na bar cikin layin ban yi gigin komawa layin gidajen da na je jiya ba. Sai da na kusa barin cikin unguwan, ƙafafuna sun yi futu-futu da ƙura na gama gajiya tilis sai da na nema waje na zauna na huta kafin na tashi na ci gaba da tafiyan na iso baki gate ɗin wani gida na ƙwanƙwasa ƙirjina yana tsananta bugu. Mai gadi ya buɗe ƙaramin ƙofan jikin gate ɗin bai ce da ni komai ba ya tsaya tsawon mintuna yana ƙare mini kallo. Na durƙusa har ƙasa na gaishe shi bai amsa ba ya soma zazzage mini buhun bala'i mini kamar zai cinye ni ɗanya. "Baiwar Allah lafiya za ki zo gidan mutane ki na yi musu irin wannan bugun kamar wanda kike bi fashi ko tara. Wace ce ke kuma daga ina kike?". "Baba aiki nake nema ko na wankau ko raino". "To kin ga gidan nan matar gidan ma ba mazauniya ba ce. Aiki take fita daga safe har yamma, sannan kuma ba ta ƴaƴa. Wanki kuwa suna da mai yi musu har da goga idan sun ga dama ma za su iya yin wata guda cur ba tare da an yi musu wankin ba don suna da wadatar suturar. Don haka ki tashi ki bar ƙofan gidan nan tun kafin na sauya miki halittan fuskanki". Na haɗe hannayena waje guda alamar roƙo"don Allah a taimaka mini wallahi ina tsananin buƙatar aikin ne, ka ba ni dama na shiga na ga matar gidan wataƙila ba za a rasa wani aikin da za a maƙala ni a gurbin ba....". Kafin na rufe bakina na ji an ɗauke ni da wani gigitaccen mari sai da na zame na yi zaman dirshan a ƙasa sakamakon zafin da ya ratsa har cikin kwanyanta. "Yau na ga masifa ni Ahmadu. Za ki tashi ki bar nan wajen ko sai na shiga ciki na sincu miki karnuka na fito da su sun yayyaga ki". Yana rufe bakinsa na yi zumbur na yi miƙe jikina har yana rawa na bar wajen ban ƙara waiwayowa ba don daga yanayin furucinsa na tabbatar da cewar zai iya aikata duk abin da ya furta. Sai da na yi nisa na nema wani dakali na zauna ina mayar da numfashi. Na zabga tagumi da hannunwa bibbiyu tare da faɗa wa cikin kogin tunani, na daɗe zaune a wajen har rana ya iso inda nake ya soma duka na amma hakan bai sa na gusa daga wajen ba, sai da na ji jikina ya soma fitar da zuffa na gumi kafin na tashi na soma tafiya akan shimfiɗaɗɗan titin da yake wajen ya miƙe ɗoɗar, ina tafiya ina haɗa hanya tamkar ƴar maye ban yi aune ba na ji wani abu ya doke ni har sai da na faɗi a kan titin kaina ya bugu da ƙasa. Na runtse idanuna cikin wani irin mawuyacin hali na runtse idanuna. Dishi-dishi idanuna suke gano mini wata mace cikin shiga na alfarma a tsaya a kaina tana ta jeranta mini sannunku wani na bin wani sai dai na kasa amsa mata.Ta taimaka mini na tashi na zauna. "Baiwar Allah sannu. Ki na ji na kuwa?". Na yi ƙarfin halin gyaɗa kaina da hakan ya ba ta damar cewa"tashi mu je asibiti a duba ki". Take na watsake na buɗe idanuna tar na ce"a'a lafiyana ƙalau ba sai mun je wani asibiti ba". Na ƙare zancen ina ƙoƙarin tashi tsaye ta riƙe ni"ki koma ki zauna kin bugu fa". "Ban fa ji wani rauni ba zan iya tafiya. Don Allah ki bar ni na tafi ina da abin da ya fi zuwa asibitin nan muhimmanci". Na ƙare zancen cikin raunin da yake fitowa kai tsaye daga ƙasan ƙalbina. Na ɓaɓɓare hannunta daga jikina na soma tafiyata ko sauraron abin da take faɗa ban yi ba. Na ɗan yi nisa da tafiyan ina jan ƙafata da ƙyar saboda buguwan da na yi a gwiwan ƙafan. Na ji ana danna horn a bayana na matsa na yi gefe motan ya sha gabana, aka buɗe aka fito matar da ta buge ni ne ta fito, ina ganin ita ce na ƙara sauri cikin jan ƙafa zan bar wajen ta sha gabana tare da cafko hannuna ta riƙe tamau. "Baiwar Allah me yasa kike wasa da lafiyarki ne? Shin ba ki lura da yadda kike jan ƙafarki ba ne? Me yasa ba ki bari mu je asibiti a duba lafiyarki ba ko so kike yi wani abun ya same ki ina zaman zamana bakina alaikum ki ja min bala'i". "In dai don ta ni ne babu wani wanda zai zo ya same ki da batuna balle har a neme ki idan wani abu ya same ni sanadin hakan, don haka ki kwantar da hankali ba ni da kowa a garin nan". Ta yi sakeke tana kallo na ganin yadda na ƙare. "Ko ma mene ne ki bar ni na sauƙe wannan nauyin da ya rataya a wuyana, na kai ki asibiti a duba lafiyarki sannan na kai ki har gida". "Idan kika yi hakan za ki bar ni na yi tafiyata?". Ta gyaɗa mini kanta cikin tabbatar mini da abin da ta furta ta ce"in sha Allah". "Shikenan". Na furta a taƙaice ina juya wa na shiga motar ita ta zagayo ta shiga tare da figi motar muka bar wajen tun da muka fara tafiyar ban ce da ita uffan ba har muka isa asibiti. Ta lashe motar muka fito muka shiga ciki aka duba ni tare da yi mini dressing ɗin inda na kurkurje a gwiwana aka ba n wasu magunguna muka fito, sai da muka shiga cikin motar kana ta kallo ni ta furta"zan ɗan biya na yi siyayya ina mai ba ki haƙuri, na san zan ɓata miki lokaci amma ki yi haƙuri". Kaina kawai na gyaɗa mata kafin na ce"ba komai"? Ta ja motar muka bar cikin asibitin a bakin wani ƙaton shago ta tsaya da ake ta hada-hada a ƙofan shagon. Sai yanzu na yarda cewar garin jarafi babban gari ne na bugawa a jarida wanda ganinsa ya zarce jin sa. "Bari na shiga yanzu na fito". Kaina kawai na jinjina mata da hakan ya ba ta damar fita daga cikin motar ta fita, na zuba idanuna ta tagan ƙofan motan ina ƙarewa mutanen da suke wucewa kallo. Jin an buɗo ƙofar an shigo an zauna shi ya dawo da ni cikin hayyacina. Muka haɗa ido da ita ta sakar mini da murmushi ba tare da ta ce da ni komai ba. Sai da muka fara tafiya kafin ta kallo ni ta ce"ina muka nufa ne, ina ne gidanku?". Na rusunar da idanuna ƙasa kafin na ce"ki sauƙe ni a duk inda titin ya tsaya". "Ban gane ba?". "Ba za ki gane ba ko na yi miki bayani". "Kin yi min bayanin ta ko ya ya ne zan fahimce ki. Me yasa kika gararamba a kan titi a irin wannan shekarun nakin da ya dace a ce ki na makaranta ko kuma wajen koyan sana'ar da za ki dogara da kanki". Na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya kafin na ba ta amsa da faɗin"aiki na fito nema". "Wani irin kike nema?". "Ko wani irin aikin ƙarfi inna samu zan yi sa. Ko wankau ko raino". Ta ɗan yi shuru na wasu daƙiƙu kafin ta ce"za ki yi aikin cikin gidan kamar su shara, mopping da girki?". Na cije leɓena kana na ce"zan yi idan na samu sai dai an ce da ni samun irin wannan aikin da wuya don gidajen da suke da halin ɗaukar mai aiki yanzu Abuja suke zuwa su je kamfani a kawo musu duk kalar wacce suke so su zaɓa. Ba sa ɗaukar ya ku bayi irin mu". Ta saki dariya mai ƙarfi daidai lokacin da take karya kwana ta ce"waye ya gaya miki hakan? Tabbas akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu da suke da rajista da gwamnati da suke samowa mutane masu aiki, sai dai ba kowa ba ne yake da irin wannan ƙa'idar. Idan za ki iya yin aikin da na lissafa zan ɗauke ki aiki a gidana". Babu shiri na ɗago ido ina kallon ta"ranki ya daɗe don Allah da gaske kike wannan zancen?". "Me ye zai hana na yi miki wasa akan abin da na san kin ɗauke sa da muhimmanci. Da gaske na ke yi zan ɗauke ki aiki idan har kin amince yanzu ma sai mu wuce gidan ki gani". Ta sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da cewa"na amince na gode sosai Allah ya saka miki da alkhairi". "Amin ya Allah, to ni dai sunana Hajiya Muhibbat na yi aure shekaru biyar da suka wuce ina zaune da mijina cikin farin ciki da ƴaƴa biyu tagwaye. Ni ƴar kasuwa ce da take harkan sayar da atamfofi da haɗa kayan lefe, ina da manyan shaguna har guda uku a cikin ƙwaryar garin nan. Mijina yanzu haka ba ya ƙasan nan ina zaune ne tare da ƴaƴana da kuma ƙanin mijin nawa Saifullah". "Allah ya yi wa rayuwa albakar ya ƙara muku kwanciyan hankali da son junanku". "Amin ya Allah". Ta amsa cikin jin daɗin da ya bayyana har a bisa fuskanta daidai lokacin da muka iso bakin gate ɗin wani gida madaidaici sai dai tsarin ginin ya ƙawat matuƙar gaske, ta yi horn aka zo aka buɗe gate ɗin ta shiga ta yi parking ɗin motar a filin da aka tanada mussamman domin ajiye motoci. Ta fito tana gaba ina bin ta a baya har cikin gidan. Muka yada zango a falo ta zauna a bisa kujera yayin da na zauna a ƙasa ina sauraron abin da take faɗa. "To kin ga dai inda nake zaune nan ne gidan mijina wanda na riga na yi miki bayanin komai. Tagwayena suna gidanmu wajen mahaifiyata za su yi hutun ƙarshen mako a can, ƙanin mijina kuma Saifullah ya tafi wajen aiki, engineer ne amma yanzu haka yana harkar siye da siyen filayi da gidaje ne. Zan yi magana da mijina zuwa anjima da yamma sai ki dawo ki ji yadda muka yi da shi". "To ranki ya daɗe na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". "Amin ya Allah. Ɗauki wannan ledodin naki ne". Ban ce komai ba na ɗauki ledar maganin zan fita ta dakatar da ni"sauran ma dukka na ki". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu"kin gan ni nan ba na magana biyu, a ke na saya don haka ki ɗauka domin ni ba na buƙatar su". "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Ba ta amsa ba illa murmushin da ta sakar mini na ɗauki ledodin na fita, duk nisan tafiyan da zafin da ƙafafuwa suke yi mini ban ji su dame ni ba saboda farin cikin samun aikin da na yi ta hanyar da ban taɓa tsammani ba balle zato. Na tarar da La'aniyatu ba ta nan amma ta ajiye mini makulli a kan taga na ɗauka na buɗe ɗakin na shiga na fito na yi alwala na shiga na yi sallan zuhur a nan inda na yi sallan na kwanta wani bacci mai nauyi ya ɗauke ni ban tashi ba sai can yamma na yi sallan asr kana na jawo ledodin da ta ce ni na buɗe su, kayan ƙwalam da maƙulashe ne burji a cikin ledan, ɗayan ledan kuma lemukan gora ne kala daban-daban. Na ɗeba wasu na soma ci sai da na gama na tashi na ajiye sauran na tashi zan fita kenan La'aniyatu ta shigo. Muka sakar wa juna murmushi yayin da take ƙariso wa cikin ɗakin. "Ina kika je ne na dawo ban same ki ba?". "Umma ce ta aike ni. Na ga kin tashi kamar ƙara fita za ki yi?". Na matso dab da ita"albishirinki". "Goro fari ƙal". "Na sama aiki yanzu ma can zan je na ji matsayina". Cike da farin ciki ta ce"a ina? Zauna mana ki ba da labari kafin ki tafi". Na jijjiga kaina"a'a ki bari sai na dawo sai ki ji komai, ga makullina nan idan kin fita ki rufe mini ƙofan". Ban tsaya jin abin da ta ci gaba da faɗi ba na fice da sauri. Sai da na iso ƙofar gidan na goge gumin da na haɗa kana na ƙwanƙwasa mai gadi ya fito ya buɗe mini na shiga ciki, na yi sallama aka amsa mini kana na shiga na iske wata mace zaune tare da wasu yara biyu masu tsananin kama da juna dukkan su maza sun yi shiga iri guda. Na tsuguna na gaishe ta ta amsa mini a taƙaice ta na bi na da kallo. "Hajiyar ta nan kuwa?". "Lafiya kike neman ta?". "Ita ta ce na zo". A wulaƙance ta ce"to sai ki jira ta ta fito". "To". Na amsa da shi a taƙaice zan zauna akan capet ta ce na sauƙa ƙasa, ban yi mata musu ba na yi kamar yadda ta ce. A ƙalla mun yi fiye da awa ɗaya zaune a wajen muna jira kafin ta fito tana fitowa yaran suka yi wajen ta da gudu suka rumgume ta. Ta riƙo hannunsu suka ƙariso suka zauna kafin ta ce"Altine ku da muka yi da ke za ku yi kwana biyu a can, ya ya kuma na gan ku yau?". Matar da ta ƙira da altine ta kaɗa baki ta ce"wohoho Hajiya ai Alhaji ƙarami ne ya je gidan gaida Hajiyarki dagan kuma ya ce a dawo da su, ko kuma shi ma ya haɗa kayansa ya koma can ayi hutun ƙarshen makon a shi". "Saifullah ke nan shi dai ba ƙaunar yaran nan su yi nisa da shi". "Ƙwarai kuwa Hajiya, ai ni tun da nake ban taɓa ganin ƙauna irin wannan ba. Hajiya ga baƙuwa nan kin yi. Sai a lokacin ta lura da kasantuwana a cikin falon ta kai idon ta kaina"ki ƙariso ki zauna mai kyau mana". Ban ce komai ba na tashi na iso gaban ta na zauna tare da gaishe ta ta amsa tare da zarce wa da faɗin"mun yi magana da shi ya kuma amince don haka za ki iya fara zuwa daga gobe, albashinki naira dubu ashirin ne duk wata sannan aikin da za ki na yi shi ne sharan cikin gida, mopping da kuma girki. Idan na yaba da tsaftan da kuma ƙarewarki akwai yiyuwar na ƙara miki albashi". Take na durƙusa ina ta jeranta mata godiya kamar zan yi aron baki ta nuna mini cewar babu komai. Ta ba ni naira ɗari biyar ta ce na yi kuɗi mota sai gobe na fara fitowa aiki lokacin har an fara ƙiraye-ƙirayen sallan magriba. Haka muka yi sallama raina fari ƙal kamar nono kindirmo ina ƙoƙarin fitowa daga falon na yi karo da mutum har sai da abin da yake hannunsa ya faɗi ƙasa. Waya ne da ya faɗi na tsuguna da sauri na ɗago na miƙa masa ina faɗin"ka yi haƙuri wallahi ban lura da kai ba ne.......". Miɗik na haɗiye ragowar zancen saboda firgitan da na yi. Na tsaya cak ina kallonsa tare da wassafo inda na taɓa ganin fuskarsa. Take na nufa inda na taɓa ganin sa shi ne wanda muka haɗu da shi yau da asuba har ya ba ni sallaya na yi salla a kai. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 4️⃣7️⃣ "Ke ce? Me ya kawo ki nan?". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa saboda ba zan iya juran irin kallon da ya katse ni da shi da ya fi kama da na tuhuma ba. Kafin na kai ga ba shi amsa tagwayen yaran suka fito a guje har suna rige-rigen rumgumansa ya tsuguna akan gwiwansa tare da ware hannayensa suka faɗo kan ƙirjinsa. "Uncle Saif tun ɗazu Inna Altine ta dawo da mu, ba mu gan ka ba". Ya shafa kan yaron da ya yi magana tare da cewa"Aryan na tafi wajen aiki shi yasa, amma ai na je can gidan Hajiya Maman ai na gan ku kafin na tafi". Ɗayan yaron ya yi caraf ya amshe zancen"ai Hajiya Mama ma ta yi ta masifa bayan tafiyanka, Anty Talatu ma cewa ta yi wai....". Kafin ya dirar zancen ya rufe masa bakinsa"Ayan ba na hana ka yawan sutura ba? Kai duk abin da ya faru zai ka kaso ka faɗa. Shi yasa Aryan ya fi ka hankali". Take Ayan ɗin ya cuno baki gaba gami da buga ƙafa yana kai wa Aryan ɗin da yake yi masa gwalo duka ya zame. "Wallahi bai fi ni hankali ba, ai Mummy ma ta ce ni ne babanta Aryan kuma ba babanta ba ne tun da shi sai kukan banza". Tana ƙare zancen ya bi Aryan ɗin da gudu suka shige cikin gidan, na bi su da kallo don ba ƙaramin burge ni yaran suka yi ba, kamansu guda, yanayinsu, girman jikinsu hatta muryar su kala ɗaya ne. Sai dai abin da na lura da shi ɗaya ya fi ɗaya suturu. Figigi na dawo cikin hankalina saboda fizge wayarsa da ya yi daga hannuna bai ce da ni komai ba, ya bi bayan yaran yana ƙira sunan Ayan, na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na ja ƙafafuna da suka sanƙare na bar wajen, kafin na isa gida har an fito daga masallacin sallan magrib ina zuwa na karɓa makuli na buɗe ƙofan ɗakin na shiga na ɗauko buta na zo na yi alwala na koma ciki. Sallan magrib na yi na haɗa har da na isha'i na zauna a wajen ban motsa ba na zuba uban tagumi, so nake yi na yi karatun alƙur'ani amma na waigo ko ina ban ga alamar alƙur'ani ba. Na runtse idanuna wasu siraran hawaye suna gangarowa daga gefe da gefen idona, a bayyane na furta"Allah ya jiƙan ka Abba, Allah ya yi maka rahama ya kai haske cikin kabarinka". "Amin". Na ji an amsa da shi da hakan ya tursasa mini buɗe lumshashshun idanuna, na kafe La'aniyatu da su har ta iso inda nake ta zauna a gaba na. "Kin dawo kenan?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganan"kin ce za ki ba ni labarin aikin da kika samu idan kika dawo". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na kwashe komai na juye mata tas, sai da na dire zancen ta ce"Allah ya saka mata da alkhairi, amma gaskiya ta kyauta kuma ta na da kirki. Amma har dubu ashirin kuɗin da yawa gaskiya". Na jinjina kaina"ni ma haka na gani, kuma a hakan ma ta ce za ta ƙara mini wani abu idan ta ga yanayin kamun ludayina". Ta riƙo dukkan hannayena"Allah ya sa a fara a sa'a". "Amin na gode sosai". Na furta ina ƙoƙarin samar da annuri a bisa fuskana, haka muka ɗan taɓa hira da ita kafin muka yi sallama tare da yi wa juna sai da safe. Tsabar farin ciki kasa bacci na yi na kwanta kawai ina ta juye-juyen ji nake yi kamar gari ba za ta waye ba balle har na fara fita wajen aikin. Ina daga kwance na ji an bankaɗo labulen ƙofar ɗakin an faɗo cikin ɗakin, duk da a cikin dubu ne amma ina gani gizon mutum yana nufo inda nake. A kiɗime na rarumo ɗan kwalina da ya zame daga kaina na mayar kaina. "Waye ne wannan? Waye ne?". Na yi maganar harshena har yana harɗewa, ba a amsa mini ba aka ci gaba da nufo inda nake zaune, babu shiri na tashi na miƙe tsam akan ƙafafuwana da suke rawa, babu wadataccen hasken da zai ba ni kallon fuskarsa balle na iya bambamce wane ne, har lokacin ba a amsa mini ba haka nan ba daina nufo inda nake ba, ya kawo hannu da niyyar kawo mini cakfa na yi hanzarin zamewa ya faɗi akan tabarman ruf da ciki. Yana wani irin numfarfashi kamar ragon layan da aka zarcewa wuya za a yanka shi. A guje na bazamo waje ina kurma ihu, take waɗanda suka rage a cikin gidan ba su fita ba duk suka fiffito suka dallo ni da tocila. "Ke dalla banza mene ne kika fito ki ma hurmawa mutane ihu?". Ɗaya daga cikin ƴan matan da suke tsaye a wajen ta furta a zafafe kamar za ta kai mini duka. Hajiya Babba ta fito tana gyara ɗaurin zanin jikinta da yake ƙoƙarin zame wa. "Wa ye yake son ya tada min da hankali da daren nan?". "Hajiya wa ye kuwa ban da wannan kucakar yarinyar mai zubin ƴaƴan aljanu, duk ta fi ta fitsine mutane a cikin gidan nan". Hajiya Babba ta nuna wacce ta yi zancen da ƴatsarta"ke Zuby ba na son ɗiban albarka, daman har masu zubin ƴaƴan aljanu ne a cikin gidan nawan ban sa ni ba?". "Hajiya ga ta nan ai sai ki tambaye ta abin da yake faruwa ta yi miki bayani". Zuby ta ƙarƙare zancen tana yi mata nuni da inda nake tsaye har zuwa lokacin ban dawo daidai daga kiɗimar da na yi ba. "Ke wace ce kike da suna?". "Amatullah". "To Amatullah lafiya kike zake ƙarfinki ki na kurma mana wannan ihun, gobara ce ta tashi ko kuma ƴan fashi ne suka yi mana da'iri ban sani ba?". Na girgiza mata kaina alamar a'a. "To mene ne?". Ta yi zancen cikin tsare gida da turmuƙe fuska babu alamar wasa ko wargi a tattare da ita. "Wani ne ya faɗo mini ɗakina yanzu ma haka ya na ciki, ban san wane ne ba?". "Wani kuma?". Ta jefa mini tambayar cikin mamakin ba ta jira amsar da zan ba ta ba ta juya ta shiga cikin ɗakin yayin da ragowar matan suka rufa mata baya, babu jima wa suka fito tare da mutumin da yake ta layi duk ya ɓata jikinsa da alama a matuƙar burge yake na fitar hankali. Cikin maye ya ce"sorry sister mance ɗakin cikas ɗin tawa na yi na faɗa na ki". Ban ce da shi uffan ba har ya gama galantolinsa ya gama. Zuby da tun farkon lamarin take tsaye a ƙofar ɗakinta ba ta gusa ba, ta dafe ƙirji tare da fiffito da idanu waje"na shige su ni Zubaida ɗiyar Sani mai kayan koli, wannan ai Habu ne saurayin Hafsy ƴar jama'are me ye ya kai shi cikin ɗakinki?". Idanuna ya yi tsilli-tsilli kafin na furta"wallahil azim ban san shi ba, ko fuskanshi ma ban gani ba saboda babu haske a cikin ɗakin". Ta galla mini hararar da ya tursasa mini yi wa bakina limzami babu shiri. Hajiya Babba ta ce"yanzu ina ita Hafsyn take wannan abun ya faru?". Zuby ta kada baki ta ce"Hajiya ta tafi club da wani sabon kamun da ta yi". Cikin zafin rai Hajiya ta ce"to kama shi ki san yadda za ki yi da shi, na kashe wannan case ɗin kowacce shegiya ta koma ɗakinta". Tana kama zancen ta juya gare ni"ke kuma ina so ki nutsu ki san inda kike". A dunƙule ta jefa mini zancen ba tare da ta warware mini ƙulin ba ta yi shigewarta cikin ɗakinta, na kasa jan ƙafana na bar wajen har sai da kowa ya watse ya bar ni a waje, masu shiga ɗakunansu da samarinsu suka shige masu shirin fita suka fita. Sai da na ja dogon gashin na fesar kafin na nufi cikin ɗakina ina doso ɗakin na ji wani gungumemen wari ya doki hancina babu shiri na toshe hancina da tafukan hannayena. Ba n i da tocila balle na haska na ga abin da ya haddasa warin haka na ci gaba da tsayiwa a ƙofar ɗakin tun ina tsaye har na zauna, a nan ƙofar ɗakin na kwana. Sanyin asuba da ya soma ratsa ni shi ya farkar da ni daga nauyayyen baccin da ya sace ni. Na farka na shiga na ɗauko buta na yi alawa a ƙofar ɗakin na shimfiɗa ɗan kwalina na yi salla, sai da na ɗan jira gari ya yi haske kana na koma cikin ɗakin. Na tsaya cak tamkar gumki ganin yadda aka ɓata kan tabarman da amai ya yi kaca-kaca, ni na yi tamkar na ɗaura hannu a ka na dinga zunduma ihu ko zan ji sauƙin takaicin da ya cika mini zuciya. Ban san sa'ilin da hawaye suka fara gangarowa daga koramar idanuna ba sai jin ɗumin su na yi a bisa fatan fuskana. Ba ni da ajiyayyen ruwa ko kaɗan illa wanda na rage da na yi alwalar sallan asubahi. Na fito na ga La'aniyatu ba su buɗe ƙofa ba, na rasa yadda zan yi. Ina waigawa na ga wani bokati na ɗauka na fita domin ɗeba ruwa, layin sharau don har zuwa wannan lokacin gari bai gama waye wa sosai ba. Ina tafiya ina kuka har na isa wajen ɗeban ruwan na ɗeba na ɗaura akaina na juyo zan tafi kenan na hango shi yana fitowa daga cikin masallaci. Ban san dalili haka kawai na ji jikina ya ɗauki rawa ya kafe ni da ido kamar yadda ni ma na ɗaura idanuna akan sa, bai ce da ni komai ba ya zo ya wuce ni ma na ɗauki hanyar komawa gidan. Tun daga zaure na ji ana kwararo ruwan ashariya, har na shigo cikin gidan ba a fasa ba ina shigowa aka nuno ni. "Kin ga shegiyar da ta ɗaukar min bokati". Zuby ta yi zancen tana nufo inda na ke tsaye gadan-gadan, kafin na na yi aune ta tankaɓar da ruwan da yake kaina ya malale a jikina ya yi mini lijif. "Yanzu ke don kuturun wulaƙanci ki rasa bokatin wacce za ki ɗauka a cikin gida nan sai bokatina?. To wallahil azim zan ja miki layi da kayana a cikin gidan nan". Tana dire zancen ta wafce bokitin ta yi shigewarta cikin ɗakin. Na dubi jikina da ya yi lajab na tuna irin dogon tafiyar da na yi kafin na je na ɗebo ruwan kawai sai na ji hawaye suna sauƙa daga idona, na koma ƙafan ɗakina na zauna na zabga uban tagumi. A haka La'aniyatu ta fito ta iske ni ta nema jin ba'asin abin da yake faruwa na irge mata komai cikin kuka, ita ta taimaka mini da ruwa da wanke ƙazantar da Habu ya yi mini akan tabarmata, na fito da ita na shanya akam igiya na koma ciki na sha lemo da biskit daga cikin abin da Hajiya Muhibbat da ta ba ni. Sai da na jira tabarman ta bushe kayan jikina ma ya bushe na shigo da ita ciki na shinfiɗa, duk da ban da agogon da zan duba lokaci na fahimci lokaci ya ja don hasken rana ya game ko'ina, sai da a rufe ɗakin na ba da ajiyan ɗan makulin a La'aniyatu kafin na tafi. Kamar ƙafafuna za su tsinke haka na ke ta zabga sauri har ƙafafuna suna sarƙewa, ina isa ƙofan gidan na ƙwanƙwasa mai gadin ya fito ya buɗe mini na durƙusa har ƙasa na gaishe shi kafin na shiga cikin gida. Na yi sallama Altine ta fito ta watsa mini wani matsiyacin kallo, na rusuna na gaishe ta maimakon ta amsa sai ta jefo mini tambaya. "Ke sai yanzu kika yi niyyan zuwa aikin? Wannan in ke za a tsaya jira sai kin zo ki girka ai kuwa watarana ba za a ci abinci a gidan ba". A nutse na ce"ki yi haƙuri wani uzuri ne ya sani na makara. Amma in sha Allah ba zan sake maimaita irin hakan ba". Ta gallo mini harara"Dalla can rufe min baki sai wani fiƙi-fiƙi kike yi da idanu kamar ta Allah. Sai ki jira don karin kumallo suke yi". Daga haka ta juya ta bar ni tsaye a wajen, haka na ci gaba da tsayiwa har sai da na gaji na zauna a bisa dakalin wajen. A ƙalla na fi mintuna talatin a zaune a wajen kafin Altine ta fito ta cikin izgili ta ce na shigo. Da rawan jiki na tashi na bi bayanta muka shiga, suna zaune a falo tare da tagwayenta da ba su wuce shekaru biyu da haihuwa ba a hashashena kenan, na durƙusa har ƙasa na gaishe ta ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa. Kafin ta ce wani abu na soma da ban haƙuri"Hajiya ki yi haƙuri na makara wani uzuri ne ya riƙe ni, amma in Sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa ba". Fuskanta ɗauke da maɗaukakin murmushi ta ce"kar ki damu ba komai, ai jiki da jini dole daman wataran a sama irin haka, yanzu mu je sai na zagaya da ke ki ga gidan ko?". Na gyaɗa mata kaina ina jin wani daɗi yana mamaye mini raina na fahimtan da ta yi mini, har na yi gaba zan ji ta a baya muka jiyo sautin da ya tilasta mata tsayawa. "Anty wace ce wannan?". Ta waigo tana kallonsa yayin da su Aryan suka nufa wajensa. "Ita ce sabuwar ƴar aikin da na yi maka bayani akan ta jiya". Yana ɗaura agogo a damtsen hannunsa ya ce"Anty a sallame ta, a nema wata kawai". Babu shiri na ɗago kai ina kallonsa ƙirjina yana tsananta bugu, jikina ya yi sanyi kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 4️⃣8️⃣ Cike da maɗaukakin mamaki a bisa fuskan Anty Muhibbat ta ce"Saif me yasa wani abun ka ga ta yi?". Har yanzu idanunsa yana kan agogon da yake ɗaurawa a tsintsiyan hannunsa ya furta"Anty kawai yarinyar ba ta yi min ba ne, ki dubi yanayinta da kuma ƙarancin shekarunta ba na tunanin da za iya yin duk aiyukan da kika lissafa min jiya. Zai fi dace a sallame ta a nema wata kasai". Dukkanmu biyun muka yi sakeke muna kallonsa ni kam na gaza cewa komai saboda sanyin da jikina ya yi ƙalau tamkar jinjirar kazar da ruwa ya yi mata ɗan banzan duka. "Saif ba wannan za ka duba ba, na lura tana cikin tsananin buƙatan wannan aikin ko don ta kula da rayuwarta a matsayinta na ƴa mace. Mata nawa ne masu irin shekarunta suke yawon ta zubar? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke sayar da jikinsu don su sama abin da za su ɗauki nauyin kansu? Mata nawa ne masu irin shekarunta da suke iskanci don su sama abin da za su saka a baki salati? Mata nawa ne masu irin shekarunta suke faɗa harkan banza da na shaye-shaye?. Ga su nan wasu sun rasa hankalinsu, sun rasa tarbiyya da kamun kansu, sun rasa kyawun jikinsu wasu ma sun faɗa harkan barace-barace akan titi wasun su ma sun haukace. Duk waɗannan hanyoyin ba ta zaɓa ta bi ɗaya daga cikinsu ba ta zaɓa ta fito ta nema aiki don ta rufawa kanka asiri ta kuma ci halaliyarta. Saif irin waɗannan yaran su ya dace a ringa taimakawa". Tun da ta fara maganar ya yi shuru yana kallon ƙasa bai ɗago kansa ba har ta gama maganar ta kai aya, kafin ya furzar da dogon numfashi a taƙaice ya furta"shikenan Anty amma dole zan yi bincike akan ta, idan na same ta da wani aibu tabbas dole a sauya ta a nemo wata". "To ubana yadda ka ce haka za a yi". Sadda kai ƙasa ya yi yana ɗan sosa ƙeyarsa ya ce"Anty ni fa ba haka nake nufi ba, zan tafi wajen aiki sai na dawo don Allah a kula da yaran nan". Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce da shi komai ba ya juya ya fice sai da ya fita kafin ta ce da ni"sai kin yi haƙuri da Saifullah haka yake, miskili ne na buga wa a jarida. Yana da wuyar sha'ani ga wanda bai san halinsa ba amma da zaran kun saba da shi za ki fahimci yana da daɗin zama da sauƙin kai uwa uba yana da tausayi da son taimakawa na ƙasa da shi". Kaina kawai na iya jinjina mata don bakina ya yi mini nauyin da na kasa cewa komai, ta yi gaba ina biye da ita muka zagaya ko'ina a cikin gidan nan, kicin ɗinta tsaf-tsaf da shi ga wani uban faɗi da girma. Girmansa ya kai a haɗa falo da ɗakinmu da muka yi rayuwa a cikinsa kafin Abba ya rasu. "Hajiya ban iya amfani da irin wannan abubuwan na zamani ba". Na yi zancen ina ƙara ƙare wa girman kicin ɗin kallo. Ta dafo kafaɗana tare da faɗin"a hankali zan koya miki komai idan na sama lokaci, kafin nan za ki na yi shara da mopping ɗin ko'ina a cikin gidan nan, amma ban da harabar gidan iya ɗakuna da falo ne sai wanke banɗakuna". "Na gode sosai". "Ki godewa Allah, ni yanzu zan fita wajen sana'ata amma ba zan daɗe ba zan dawo. Don haka za ki zauna da tare da Altine da su Aryan kafin na dawo". Kaina na jinjina mata kana na ce"a dawo lafiya Allah ya tsare ya ba da abin da aka fita nema". Cike da jin daɗin addu'ata ta amsa da faɗin"Amin ya Allah". Muka dawo falo ta shaida wa Altine za ta fita ta yi mata addu'ar a dawo lafiya, ta kwashe Aryan da Ayan suka yi mata rakiya har waje kana suka dawo. Ina zaune a cikin falon Altine ta dawo daga rakiyar da suka yi mata muka kalla juna ta banko mini harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa, ba ta zauna a inda nake ba sai ta ja gefe ta zauna suna wasa da su Aryan, haka na ci gaba da zama shuru babu wanda zan yi magana da shi balle taɗi. Muna zaune a wajen har aka yi ƙiran sallan zuhur Altine ta tashi da yaran suka hau sama babu jimawa sosai suka sauƙa. Za ta wuce su fita na dakatar da ita ta hanyar faɗin. "Anty ina zan sama ruwa na yi alwala na yi salla kar lokaci ya ƙure?". Ta watsa mini wani kallon uku saura kwata kan ta mayar mini da martani a zafafe"tun ɗazu da na tashi na je na yi sallan ba ki yi min magana ba sai yanzu? Ai na yi tunanin ba za ki yi sallar ba ne". Na rusunar da kaina ƙasa ina ci gaba da sauran abin da take faɗa daki-daki. "Sai ki fita ta ƙofan can za ki ga fanfo ki yi alwalan ki dawo ki yi sallan a nan". "Sallaya fa?". "Ki yi akan ɗan kwalinki don ban yarda da tsarki da tsaftan jikinki ba". Tana gama faɗin haka ta ja hannun yaran suka fita, ƙofar da ta nuna mini na bi na yi alwalan na dawo na shimfiɗa ɗan kwalina na yi sallan akai. Ina raka'ar ƙarshe suka dawo suka zube akan kujera, na iddar da sallan na shafa addu'ar da na yi kana na juya ina duban ta"Anty akwai aikin za da a yi ne?". "Ban sani ba wannan kuma sai dai ki jira matar gidan ta dawo, sai ta yi miki wannan bayanin da bakinta". Tun da ta yaɓa mini wannan maganar ban ƙara cewa da ita komai ba, Ayan ya soma jan hannunta yana cewa"Anty ki tashi mu je ki yi mana alwala mu yi salla, Uncle Saif ya ce idan an ƙira salla mu na yi kar Allah ya ƙona mu a wuta". Hankaɗe shi ta yi ya faɗi bakinsa ya saki hannun kujera. "Wai ku kam wasu irin jarababbun ƴaƴa ne haka? Babu dama ku ga mutum ya zauna yana huta wa sai kun addabe shi da jaraba, ku dai ku na gaba da ku ganni ina zaune ina hutawa. An gaya muku ni ɗin jakar uwarku ce ko ta ubanku ko kuma ni inji ce da ba na buƙatar hutu? Ubanku na can wata uwa duniya na kuma ta tsallake ku ta tafi neman duniya ni da ban haifa ba an bar ni da jalala". Ta yi zancen tana miƙewa ta bar cikin falon, ganin yadda bakin Ayan yake zubar da jini ya tilasta mini tashi na je na ɗago sa, don tun da ya faɗi ya kasa tashi daga wajen. Ƙofar da na bi na je na yi alwala nan na nufo na wanke masa bakinsa sannan na cire masa rigarsa don ita ma ta ɓaci da jini muka dawo cikin falon, na zaunar da shi akan kujera kusa da ɗan uwansa na je na ɗauko mopper na gyara wajen. Na zo na zauna a kusa da ni ina duban Ayan da yake ta sauƙe ajiyan zuciya akai akai. Na riƙo hannunsa kana na ce"a ina ake ajiye muku kayanku?". "A ɗakinmu yake". "Ina ne ɗakin nakun?". Da hannunsa ya yi mini da wata ƙofa ya ce"wancan ne". Na tashi na shiga komai guda bibbiyu ne a cikin ɗakin kala ne kawai ya bambanta su. Na buɗe sit na ɗauko masa wata riga na juya zan fita na hango Altine tsaye a ƙofar ɗakin ta naɗe hannayenta a ƙirjinta tana yi mini wani irin kallon da na gaza cewa ma'anarsa. "Me ye kike yi a nan?". "Riga na zo ɗaukawa Ayan". "Saboda ke kike kula da su ko?". Da saurina na ce"A'a Anty na jikin nasan ne ya ɓaci da jini shi ne na cire masa na zo ɗauka masa wani." Ina rufe bakina ta ƙariso cikin ɗakin ta wafce rigar daga hannuna. "To ba zai sa wata rigar ba, haka zai wuni ba riga tun da an sa masa ya ɓata. Ai ni ba jakar gidansu ba ne da kullum ba ni da aiki sai hidimarsu". Na yi mutuwar tsaye ina bin ta da kallo ganin yadda ta zage tana zazzago masifar babu kwama balle fulsutop. Cike da maɗaukakin mamaki na ce"amma na yi tunanin ai an ɗauke ni saboda hidimansu. To me ye ba za ki yi aikin da ya kallafa akanki ba ko don ki ci halaliyarki?". Ta riƙe ƙugu tana kallona"madalla tun da har kin fahimci cewa an ɗauke ni domin na yi musu hidima, to na haɗa ki da girman mai yi mana ruwa da ƙanƙara ki bar ni na yi aikina kar ki yi min shishshigi akan lamarin da bai shafe ki ba. Ki yi aikinki ni ma na yi nawa don haka ki fita daga ɗakin nan". Ban kuma cewa da ita komai ba na fita daga ɗakin cikin tsananin mamakin da ya bayyana har a kan fuskata ina fitowa na ga har sun yi bacci akan kujerar sun manne da junansu. Na bi su da kallo cike da mamakin abin da Altine ta aikata gare su. Na koma gefe na zauna a inda na yi salla na kifa kaina akan gwiwana ban yi aune ba ni ma bacci ya kwashe ni don daren jiya ban samu na yi bacci mai kyau ba. Ƙiran sallan asr shi ya tilasta mini tashi na ina karanto sunanyen mahaliccina tsarkaka guda ɗari babu ɗaya, na fita na je na yi alwala na zo na yi zama, tun ina sallan nake jin cikina yana kukan yunwa har na iddar na shafa addu'ar da na yi. Na kafe yaran da ido ina ta kallonsu tun ranar farko da na fara tozali da yaran na ji sun shiga raina can ƙololowa, mussamman yadda na ga suna da nutsuwa sosai kamar ba yara ba sannan ba su ƙiriniya ko kaɗan. Ban ji sallamarsa sai gani na yi ya zauna kusa da yaran yana shafa kansu, na yi saurin gyara zamana rare da ɗaukan ɗan kwalina na ɗaura a kaina. Na rusuna ina faɗin"sannu da dawowa ranka ya daɗe". Bai amsa mini ba ya ci gaba da shafa kan yaran ya kai hannunsa wuyan Ayan babu shiri ya waigo yana kallona haɗe da faɗin"me ya same shi na ji jikinsa da zafi gau haka?". Na yi ƙasa da idanuna na rasa me ye zan ce da shi sai kame-kame nake yi, kafin na kai da cewa wani abun Altine ta fito fuskarta kamar gonar auduga bakinta har kunne ta zo ta zube a gabansa"Barka da dawowa Alhaji ƙarami sannunka da shigowa". Bai amsa ba ta ya jefa mata makamamcin tambayar da ya yi mini. "Me ya sa Ayan na ji jikinsa da zafi haka gau, kuma jikinsa babu riga?". Ta ɗago kai muka haɗa ido da ita ta yi hanzarin kawar da nata tana faɗin"sun yi wasa a baya ne wajen bayin shuke-shuke shi ne ya jiƙa rigar, na cire masa na shiga domin ɗauka masa wani kuma sai na fito na tarar ya yi bacci. Ni kuma ban son tashin su shi yasa ban ɗaga sa ba". Ya cije leɓansa"sun ci abinci sun yi salla?". "Duk biyun sun yi kafin su kwanta wannan bacci da ka shigo ta tarar da su suna yi". Ya jinjina kansa yana miƙe wa tsaye"ki tada su ki yi musu wanka ki shirya su za mu fita tare". Yana dire zancen ya bi wata ƙofa ya bar cikin falon. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina duban Altine da take tayar da yaran ta riƙe hannunsu suka shige cikin ɗakinsu, na koma inda na taso na zauna gabaɗaya yunwa ta addabe ni, ina zaune a wajen ya fito ya sake shiga cikin wani farin sol ɗin yari haka nan ya bar kansa ba tare da ya saka hula ba amma da dukkan alamu ya gyara gashin don har wani ƙyali da sheƙi yake yi. Sai baza ƙamshi yake yi kamar wanda aka yi ɓari durom ɗin turare a jikinsa. Ya nema waje ya zauna yana murza zoben da yake hannunsa ya ce"me ye sunanki?". A nutse na furta"sunana Amatullah". "A ina kike da zama sannan su waye iyayenki?". "Mahaifina ya rasu mahaifiyata kuma ba na tare da ita yanzu, hasalima ni kaɗai nake zaune a garin nan". Ya ɗago ido yana duba na"faɗaɗa min bayanin ban ga ne ba". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa kana na ce"ina zaman kaina ne bisa wasu dalili da suka tirsasa faruwan hakan". "Mace mai zaman kanta, karuwa kenan ko kuma magajiya?". Da hanzari na ɗago ido ina kallonsa wanda shi ɗin ma ni yake kallo a ci gaba da maganan. "Idan na faɗa ba daidai ba sai ki gyara min". Na girgiza kaina"haka ne yadda ka faɗa". Fitowar Aryan da Ayan shi ya hana sa furzo da zancen da ya yi niyya ya tashi tsaye ya je ya riƙo hannunsu suka fita, Altine sai washe baki take yi tana ɗaga musu da faɗin su kawo mata tsaraba. Ta wuce ta shige ciki ta bar ni a wajen, baƙin cikin kalaman da ya watsa mini ya sanya har sai da na zubar da hawaye, na ji duk son da nake ji wa wannan aikin da zumuɗin da na yi a lokacin da na yi katari da samun aikin duk ya fita daga raina. Tabbas ina son wannan aikin sai dai ba zan juri wulaƙanci wannan mutumin da kuma cin zarafin Altine a gare ni ba. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 4️⃣9️⃣ Rawan da ƙafafuna suka soma yi shi ya tilasta mini zama dirshan irin na ƴan bori, ina jin ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi. Ji na yi kamar na tashi na ruga da gudu na fice daga cikin gidan, tabbas na shiryawa dukkan ƙabuluaben da zai biyo bayan samun wannan aikin sai dai ban taɓa zaton zai zo mini a ranar farko ba. Yunwan da ta ci gaba da ƙwaƙwulan ƴaƴan hancin cikina har ina jin mayar ana musayar kifiyoyi a cikin cikina. Ba tare da na yi shawara da zuciyata ba na tashi da nufin tafiya don har cikin raina na ji cewar ba zan iya juran wannan cin mutuncin da tozarcin ba, ina fitowa harabar gidan na ga an wangale gate ɗin mota tana shigowa, na tsaye a inda nake har ta daidaita parking ta fito ta iso inda nake. "Ya na ganki a nan?". "Ranki ya daɗe zan tafi ne na ga yamma ta na ta gabatowa". "A'a wani yamma ne ta yi yanzun dududu ma ƙarfe nawa ne? Mu koma ciki". Daga haka ta yi gaba ba tare da ta tsaya sauraron jin abin da zan faɗa ba, ba ni da wani zaɓi da ya wuce na bi ta kamar yadda ta buƙata, don haka na bi ta a baya a har cikin falon gyalen kanta ta yaye yayin da take zama akan kujera tana mayar da numfashi. "Ki zauna mana". Amon sautinta da ya sauƙa a masarrafar jina ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina, na zauna a ƙasa a hankali na furta"sannu da dawowa ranki ya daɗe". Cike da kulawa ta amsa mini da faɗin"yauwa Amatullah sannu ko? Ya na ji gidan shuru kaman ƴaƴan ba sa nan". Kafin na kai ga ba ta amsa na tsinkayo muryar Altine daga bayana tana faɗin"sun fita da Saifullah tun da ya dawo ya ce a shirya su za su fita". "Ina suka je?". "Bai sanar da ni inda za su ba, amma ina kyautata zaton idan suka saba zuwa suka je. Ki na son wani abu a kawo miki ne Hajiya?". Ta ɗan lumshe idanunta kafin ta ce"ba na buƙatar komai, ku fara shirye-shiryen girkin dare tare da Amatullah, don zan yi baƙi da daren nan akwai abokan kasuwancina da za su zo mu tattaunawa. Ku shiga kicin ɗin ku duba duk akwai abun da babu ko ake buƙarin a ƙaro sai ki zo ki sanar da ni". Daga haka ta tashi ta haura sama wanda nake kyautata zaton a nan ɗakinta yake. "To sai ki tashi mu je ko tun da dai kunnuwanki su ji abin da ta faɗa". Altine ta yi zancen cikin ɗaure fuska tana barin cikin falon, na yi wuf na tashi na bi ta a baya muka nufin kicin ɗin. Ta fara duddube-duddube can kuma sai na ga ta tsaya tare da dafe kanta ta juyo tana kallona. "Sai ki je ki tambayo Hajiyar abin da za a dafa, in ta faɗa sai na duba na ga abin da ya dace a sayo ko wanda za a ƙaro". "To". Na amsa da shi a taƙaice ina ficewa daga cikin kicin ɗin, ɗakin Hajiyar na nufa na tsaya daga ƙofar ina yin sallama sai da na yi baki biyu a na ukun ta amsa ban shiga don a tunanina bai dace na shiga har cikin turakarta ba a matsayinta na matar aure, don na sha ji n ana cewa ɗakin mace sirrinta ne. Ta fito jikinta ɗaure da farin towel da ya tsaya daidai gwiwanta, na rusuna na gaishe ta ta amsa mini cikin wani irin yanayin da gaba ɗaya na kasa gane kansa. "Amatullah lafiya?". Na ɗan duƙa kaɗan kafin na amsa mata cikin faɗin"daman Anty Altine ce ta ce na zo na tambaye ki abin da za a dafa". Ta ɗan shafo saman goshinta kafin ta ce"a yi fried rice, fine apple and coconut drink, sai a soya kaji a yi paper meat". Tana gama lissafa mini jerin gwanon abubuwan da za a yi ta koma cikin ɗakin tare da turo ƙafan ta rufe gaf, na ja ƙafana na koma cikin kicin na sanar da ita abin da ta faɗa, ba ta ce da ni komai ba ta ci gaba da abin da take yi. Ta nuno mini wasu albasa ta ce na yanka su yayin da take ficewa daga cikin kicin ɗin, babu jimawa ta dawo muka ci gaba da aikin tare sai dai ba ta ce wa da ni uhm balle umm da zaran ta ba ni umarnin abin da zan yi ba ta ƙara cewa da ni komai. Aka kawo wasu kayan wanda duk dangin kayan marmari ne, ta ce na wanke su na yi kamar yadda ta faɗa aka zuba tuban da ayaba da inibi a cikin wani ƙayataccen kwanon gilashi, aka haɗa wanda za a markaɗa a yi lemon da za a yi. Muna gama aikin ana ƙiran sallan magrib har wani juwa ne yake ɗiba na tsabar yunwar da nake ji, idanuna suka yi ƙulu-ƙulu har wani dishi-dishi nake hangowa. Muka haɗe komai muka jere shi akan dinnig table, ni na wanke kwanukan da muka yi amfani da su wajen gudanar da girki na tsaftace kicin ɗin tsaf. Kana na je na yi alwala a inda na yi alwala na nema wani ɗan wajen na shimfiɗa ɗan kwalina na yi salla, don ba na so na je falo Hajiya ta fito ta ganni ko kuma na iske ta a ciki na hana ta rawan gaban hantsi. Sai da na iddar da sallan na tashi na shiga ciki kamar yadda na yi tsammani kuwa na iske ta zaune a falon tana latsa wayarta da yake hannunta. Na durƙusa na gaishe ta ta amsa mini ba tare da ta ɗago kanta ta kalle ni ba. "Ina Altine take ne?". Bakin na ba ta amsa Altine ta iso wajen ita ma ta zube tana yi mata sannu da hutawa. Ba ta amsa ba ta ɗago kanta tana kallon mu gabaɗaya kana ta ce"Altine me yasa ba ki kai ta ɗakinki ba, ina daga ɗakina na hango ta ta taga na ga tana salla a cikin garden. Ki ja ta a jikinki don daga yau tare za ku na gudanar da dukkan ayyukan cikin gidan nan, sannan a ɗakinki za ta dinga yin komai idan ta zo gidan nan". "Ba matsala ranki ya daɗe yadda kika ce haka za a yi, ai faɗa na ki ne cika wa kuma nawa". "An zuba wa Saif abincin shi ne, sannan kuma kun ɗeba naku ne?". Altine ta gyara zama kafin ta ce"na zuba masa komai, sannan mu ma na ɗeba mana na mu". Ta jinjina kanta"to ku je ku ci mana, na ga dare yana yi kuma Amatullah za ta koma gida". "To ranki ya daɗe, tashi mu je ke kuma". Altine ta yi zancen tana kallona, ta tashi na bi ta a baya ɗakuna uku ne jere da juna a cikin falon wanda ɗaya na su Aryan ne, na tsakiyan kuma kamar a rufe yake ba a buɗe sa, na ƙarshen muka shiga wanda ya kasance nan ne ɗakin Altine ta ido ta nuna mini wajen zama tana faɗin"bari na je na ɗauko abincin". Na yi zumbur na miƙa"Anty bari na je na ɗauko". Ta galla mini harara"ki je ina ɗin malama? Dalla koma ki zauna ba na son kinibibi da rawar kan banza da na wofi". Tana dasa aya ta juya ta fice daga cikin ɗakin tare da bankaɗo ƙofar ɗakin har sai da ya ba ta wani sauti, a sanyaye na zauna na tallafe kuncina, har ta je ta dawo ban gusa daga inda nake ba ta shigo da kula da flate a hannunta ta dosara mini a gabana. "Ga shi nan sai ki ɗeba ki ci". Daga haka ta haye kan katifa ta yi kwanciyarta. Na fi mintuna biyar ban ce komai ba kafin na buɗe kulan sai dai da mamakina sai na ga ba abin da muka girka ba ne a cikin kulan, shinkafa muka girka da ta amsa sunanta sai dai a nan fara ce da mai da yaji ko wake babu wata yajin ƴan ɗis a saman shinkafan kamar an roƙo daga maƙota. Ban ce da ita komai ba na sa hannu na soma cin abincin duk daga loman farko na sha jinin jikina, don da ƙyar na haɗiye shinkafan ya wuce ta cikin maƙoshina tsabar bushewa da sanƙarewan da ya yi da alama ya shafe tsawon awannin a dafe. Haka na ci gaba da cin abincin ina ji kamar ina haɗiyan ƙarangiya, ba don yunwan da nake ji ba tabbas da na haƙura da abincin amma babu yadda na iya dole na ci tun da ba ni da wani zaɓi. Na gama ci na tashe zan je na mayar da kwana ta dakatar da ni. "Ki ajiye kulan a nan ki yi tafiyarki". Duk da kalamanta sun ba ni mamaki ainun amma ban nuna mata hakan ba, na yi kamar yadda ta ce na ajiye kulan na shiga banɗakin dake cikin ɗakin na wanke hannuna na fito. "To Anty ni zan tafi, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu". Kamar wacce aka yi wa dole ta ce"Allah ya tashi mai gaskiya". Na saki taƙaitaccen murmushi kana na ce"Amin ya Allah". Na bar cikin ɗakin na iske Hajiya a inda muka bar ta har yanzu tana latsa wayarta ta saka wani waƙan yaren turanci tana bi tamkar tare da mawaƙin suka rera waƙar tsabar ƙwarewar bin dukkan baitukan waƙan da ta yi. Na iso na durƙusa a gaban ta"Hajiya na fito zan tafi". "To ki gaida gida, ga wannan sai ki yi kuɗin mota da shi". Ta ƙarƙashin zancen tana miƙo mini naira ɗari biyar na kuɗin ƙasata Nigeria. "Na gode sosai Hajiya amma ba zan iya karɓan wannan kyautar ba ba kuma don na raina ba. Zan fi so duk ƙarshen wata a ba ni haƙƙina na yi amfani da shi, ina ga kamar hakan zai fi amma idan maganganuna sun ɓata miki rai to ina mai ba ki haƙuri". Kafin ta ce wani abu Aryan da Ayan suka shigo da gudu suna rige-rigen isowa gare ta, ta buɗe hannayenta suka faɗo jikinta suka ƙyalƙyalewa da dariya. Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi yana shigowa hannunsa riƙe da wasu manyan ledodi guda biyu, na yi hanzarin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa. Ya shigo ya zauna kafin ya yi magana Hajiya ta riga sa"ina kuka je ne haka?". "Kun fita wani waje ne". "Wajen bai da suna?". Kafin ya yi magana Aryan ya karɓe zancen"Ammi wajen wasan yara muke ce, daga nan muke je muka ci abinci sannan ya kai mu ya yi mana siyayya, muka tsaya a masallaci muka yi salla kafin muka dawo gida". "To kin ji amsa daga bakin uban masu gidan". Dariya duk su biyun suka yi kafin ya miƙe"sai da safenku ni kam zan wuce sashina". "Kafin nan ga Amatullah ka mayar da ita gida na ga dare ya yi za ta sha wahala kafin ta sama abin hawa. Daga nan ma sai ka gano gidansu ko don gaba". Ya tsaya sakeke kafin ya furta"wace ce kuma Amatullah?". "Ga ta". Ta amsa masa tana masa nuni da inda nake durƙushe, ya ɗan shafo sumar kansa kana ya ce"har yanzu fa akwai ababen hawa suna hada-hadan su, tana fita za ta samo har ƙofan gidan". Cikin kakkauran murya da tsare gida Hajiya ta ce"Saifullah in ba za ka yi ka fito fili ka sanar da ni, ba sai ka yi wani kwana-kwana ba". Ya sunkuyar da kansa ƙasa ciki-ciki ya ce"ina jiranta a waje". Tana gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin falon. "Tashi ki je yana jiran ki". Na ɗago kaina zan yi magana ta tari numfashina"kar ki ce komai, idan ba hakan zai zama takura a gare ku ba ne to kawai ki je ya kai ki". Jikina a sanyaye na tashi na yi mata sai da safe na fita, ina fitowa na hango sa tsaye a jikin mota yana danna waya muna haɗa ido da shi ya buɗe ƙofar motar ya shiga. A hankali na iso na buɗe ƙofan motar zan shiga ya dakatar da ni ta hanyar cewa"gidan gaba za ki shiga". Na mayar da ƙofan na rufe na buɗe na mai zaman banza na shiga na zauna, ina rufe ƙofan ya ja motar tunin daman mai gadi ya wangale gate ɗin, a hankali yake tafiya akan shimfiɗaɗɗan titin da babu cunkoson ababen hawa balle hayaniya. A ƙalla ya yi tafiyan da ya kai na mintuna ashirin ba tare da ya tambaye ni ina unguwanmu ko kuma inda zai ajiye ni ba. Gabaɗaya na ƙagu da zaman ga wani tarin gajiyan da nake ji a cikin jikina kamar an yi mini dukan tsiya, muryata cike da tarin tsoron da ya yi mini dabaibayi na ce"idan ka sama waje zan sauƙa". Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce"har mun iso gidan nakun ke nan?". "A'a zan ƙarisa nan ne ba wani nisa ba ne sosai". Yana kayar kwana ya ce"akan idonki amma aka ce na kai ki gida, na ga gidan gudun watarana". Daga nan ban ƙara cewa da shi komai na zuba masa idanuna domin na ga gudun ruwansa, haka ya ci gaba da tafiyan har gyagyaɗi ya soma ɗeba ba. Hawayen takaici da dana-d shiga motarsa da na yi suka kwaranyo mini. Na kai hannu na goge su ina jin zuciyata tana tafasa kamar talge na ji ya taka birki motar ta tsaya. "Fita". Na yi ya furta muryarsa babu alamar wasa balle wargi, na ɗago ido domin ganin inda ya tsaya. Da mamakina ina ɗago ido na hango ƙofar gidan Hajiya Babba da ya cika ya yi maƙi da samari da ƴan mata suna sheƙe ayarsu tare da cin karensu babu babbaka. "Ki fita mana. Ko ba nan ba ne ƙofar gidan?". Na sadda kaina ƙasa"nan ne, na gode". "Ki gode wa Allah". Ban iya amsa wa saboda mamakin da ya shayar da ni. Na fito na tsaya na kasa gaba na kasa baya idanuna akan motan har sai da ya ɓace wa ganina. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da jefa wa kaina tambayar da na kasa amsa wa. Ya ya aka yi ya san cewa a cikin gidan nan nake rayuwa, har ya kawo ni?. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 5️⃣0️⃣ Na daɗe tsaye a wajen ina saƙa da warwara a cikin raina, kafin na ja ƙafafuna na bar wajen sai da na raɓa tamkar zan shige cikin gini kafin na sama hanyar da zan wuce saboda kuncoson da yake ƙofar gidan, mutane kamar ana kaɗa ƙararrawa suna fitowa sun cika wajen sun yi maƙil. Ga wanda bai sa ni ba sai yi tunani da zaton wani gagarumin taro ake yi a wajen. Har cikin tsakar gidan da mutane kamar ba dare ba ina shigowa na hango La'aniyatu zaune a ƙofan ɗakinsu, na isa kusa da ita na zauna ina kafa hannayena wajen guda da hakan ya ba da wani ɗan sautin da ya dawo da ita cikin hayyacinta daga tunanin da ta yi nisan kiwo a cikinsa. "Yaushe kika dawo?". "Lokacin da kika yi nisa cikin tunanin da kike yi na shigo". Ta miƙe ba tare da ta ce komai ba ta shiga cikin ɗakinsu babu jima wa ta dawo ta miƙo mini ɗan makulina. Na karɓa ba tare da mun ce da juna ko kanzil ba na je na buɗe ƙofana na shiga buta na ɗauka na fito na yi alwala kana na koma ciki na gabatar da sallan isha'i, ban gusa daga inda na yi sallan ba na zabga uban tagumi ina tunanin abubuwan da suka wakana a cikin wunin yau gabaɗaya. Babu shiri na sauƙe numfashi mai zafi ina cije naman leɓena. Ban san sa'ilin da hawaye suka fara tsere a bisa fuskana ba suna sauƙa har izuwa saman haɓana tare da zarcewa zuwa tudun wuyana, ban share su ba kamar yadda ban yi wani yunƙurin hana su kwaranya ba don na yi imanin zubar da su ne kawai zai sanya na ji sanyin tafasar da zuciyata take yi mini da kuma ɗacin da nake ji a cikin maƙoƙarona tamkar an shayar da ni ruwan maɗaci. Ina zaune cikin wannan halin Aminu ya faɗo cikin ɗakin ban ji shigowarsa ba sai ji na yi an zubo mini wani irin hayaƙi a daidai saitin fuskana take tari ya sarƙafe ni na soma yin sa babu ƙaƙƙautawa, da ƙyar tarin ya tsaya wanda hakan ya ba ni damar bin sa da idanuna yayin da yake zama akan tabarman da nake zaune, yana busa tabar sigari cikin ƙwarewa hayaƙin yana fita ta baki da hancinsa. "Tunanin me ye kike haka ƴan mata?". Na yi masa wani kallo ta wutsiyar idona kana na ce"amma ka san bai dace ka faɗo mini cikin ɗaki haka ba tare da sallama ko neman izni ba ko?". Ya ƙura mini idanuna tamkar ba da yaren Hausa na yi zancen ba"ban gane ba me ye kike nufi da waɗannan kalaman nakin?". Idona a cikin nasa na ba sa amsa"ina nufi bai dace ta na shigo mini cikin ɗaki haka garangatsau ba, ko ba komai wani lokacin akwai yiyuwar ka same ni cikin wani hali". "Wani irin hali ke nan?". Na galla masa harara tare da ɗauke idona daga kansa ba tare da na ba shi amsar tambayar da ya yi mini ba. "Ɗazu na zo ba kya nan ina kike je?". A taƙaice na ce"wajen aiki". "Aiki?". Ya maimaita cikin sigar tambaya na gyaɗa masa kaina cike da tabbatarwa. "Ina mai tabbatar miki da cewan babu wani aikin da zai riƙe ki balle har ki ɗauki ɗauwaniyyan kanki da shi. Amatullah ki buɗe idanunki ki farka daga baccin da kike yi da yake haddasa miki yin wannan mafarkin mara gindi balle tushe, kin san me ye bariki kuwa balle yadda ake gudanar da rayuwa a cikinta? Kin san yadda zaman bariki yake kuwa? To billahillazi duk wanda kike ga yana zaman kansa ko zaman kanka a cikin duniyar bariki sai ya yi da gaske kafin yake ɗaukan dukkan ɗawainiyyansa, a namiji ma ke nan balle kuma ɗiya mace da take rauni a bayyane. Kin ga duniyar bariki ya wuce duk yadda kike tunani kallon kitse kike yi wa goro, tun wuri idan za ki zubar da makamanki ki kama gaskiya da hanyar da za ta miƙar da ke ɗoɗar ki yi kafin lokaci ya ƙure miki. Ban da toshewar basira ina ke ina wani zuwa aikatau aikin da sai kin saka ƙarfi kin sadaukar da lokacinki wajen yin sa, yadda kike da kyakykyawan suran nan da diri mai kyau da ɗaukar hankali aikin wahala bai kamace ki ba, kamata ya yi a ɗauke miki komai sai dai kawai a kama miki ɗaki a ciyar da ke a shayar da ke duk abin da kike so. Ki ci mai kyau ki sa mai kyau. Ki sha iskan AC ki kwanta ki bi lafiyar gado". "Na gwammace na yi ko wani irin aiki da na bi hanyar da kake so ka ɗaura ni a kai". Ya yi wata dariyar da na kasa gano manufar da yake ɓoye a tattare da shi kafin ya furta"ina nufin ki ba da kai kawai bori ya hau. Kawai manyan masu kuɗi hamshaƙai da suka ci suka ta da kai, akwai ƴan kasuwanni, akwai ma'aikatan gwamnati, akwai masu aikin ɗamara, akwai ƴan siyasa, akwai manyan malamai da suka yi shura da suna a duniya, akwai waɗanda su ba ma a cikin ƙasar nan suke ba. Waɗannan su ne waɗannan ba su da matsala su hotunan wasu sassan jikinki kawai za ki ɗauka a hoto ki ki dinga tura musu yayin da su kuma za su dinga jiƙa miki account ɗinki da wasu mahaukatan kuɗaɗe masu nauyin gaske. Akwai hanyoyi da yawa da za ki bi don rufa wa kanki asiri ba tare da kin yi aikin wahala ba". Na kai hannuwana na toshe kunnuwana saboda yadda kalamansa suka jirkita mini tunanina har sun barazanar juyar mini da kaina. "Ba zan duk abubuwan da ka lissafa ba. Don na yi wa kaina alƙawarin ba zan ƙara aikata wani saɓon Allah a ciki sanina ba, sai dai wataƙila ba na cikin hayyacina amma da hankalina dai kam ba zan iya wannan abun ba". Ya sake baki da hanci yana kallona"hoton jikinki ne fa kawai za ki ɗauka ki na zauna daga cikin ɗakinki akan wannan tabarman ki turo, babu wanda ya san kin yi wani abu. Wannan ake yi wa kirari da cewar ka yi kyauta da damanka ba tare da hagunka ya sani ko ya ji labari ba". "Kar ka canza ma'anar maganar nan domin sam ba haka yake ba. Kuma ina so ka sani ba ka da wasu kalaman da za ka yi mini zai sa na karya alƙawarin da na yi wa kaina". A fusace ya miƙe yana jefa da guntun sigarin da ya gama zuƙa ya take ta kafin ya furta"shikenan ki yi yadda kike so. Daman Hausawa sun ce mai rabon shan duka ai ba ya jin bari, don haka ga fili ga mai doki sai ki yi sukuwarki yadda kike so". Tana dasa aya a nan ya fice daga cikin ɗakin na bi shi da kallo kamar idanuna za su faɗo a ƙasa, yana fita La'aniyatu tana shigo wa cikin ɗakin kamar zai bangaje ta ya ƙarisa ficewa cikin ɓacin rai. "Lafiya na ga wannan ya fita cikin ɓakin rai kamar zai duki bango?". Ta jefa mini tambayar yayin da take zauna kusa da ni. Sai da na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kana na furta"ba komai kawai dai abin da aka saba ne wanda kin riga da kin san shi". Ta jinjina kanta"Allah ya kyauta". "Amin, na ga ɗazu kaman ranki a ɓace me yake faruwa ne?". Ta ɗan yi jim kafin ta ce"wallahi Ummata ce ta yi mungun ɓata min rai, sai da na ji kamar na ɗaura hannu akaina na yi rafza kuka tsabar tsagwaron baƙin cikin da ta ƙunsa min". Cike da mamaki game da buƙatan ƙarin bayanin da ta yi mini a dunƙule na ce"me ye ta yi miki haka?". "Wai fa baƙi ta yi ta san da cewa ina cikin ɗaki ina saka kayana ta shigo da su. Wallahi na ji haushi sosai ta yadda ban ma san lokacin da na rufe ta da masifa ba". Cike da maɗaukakiyar mamaki na waro idanuna waje"Umman nakin kika rufe da masifa?". "To mene ne?". "Ai ita ɗin mahaifiya ce ko me ye ta yi miki bai dace ki rufe ɗaga mata murya ba balle har ki rufe ta da faɗa. Iyaye fa suna fa su na da wani irin daraja da kima wanda ba kowa yake da makamancinsa ba, mussamman uwa wanda sai Annabi ya ambace ta sau uku kafin ya ƙira uba sau ɗaya saboda girman haƙƙin da take da shi akan ɗa". Ta ɗan yi shuru kamar abin da na faɗa ya ratsa ta sai dai kuma kalamanta suka sani tabbatar da cewa duk abin da na faɗa ya shiga ta kunnenta na gefen dama ne ya fita ta gefen hagu. "Ummanta dole sai ana yi mata haka, dole sai mutum ya zama jan wuya mai iya ƙwacen haƙƙinta kafin ya iya zama da ita. Akwai wani lokaci da ta tsiri kawo maza cikin ɗakinmu su hana n sakat na yi faɗan na yi faɗan ba ta daina ba, har sai da na daina kula ta na daina yi magana na kusa a ƙalla wata guda kafin ta dawo cikin taitayinta, tun daga lokacin na fahimci Umma zuma ce dole a da wuta za a mu'amalance ta". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu"mu bar wannan maganan, yanzu dai ba ni labarin ranar ki ta farko a wajen aiki, ya abin ya kasance?". Na ja numfashi mai nisan zango kana na fesar kafin na sama damar kwashe komai da ya faru na faɗa ba. Ta yi ɗan jim kafin can ta ce"ke kuma bayan faruwan hakan wani hukunci kika yanke?". "Wallahi na ji gabaɗaya aikin ya fita daga raina. Duk da ina son aikin amma ba na jin zan iya jure cin zarafi da wulaƙanci". Ta riƙo hannuna ta sanya cikin nata kafin ta soma magana cikin sigar ƙarfafa gwiwa. "Amatullah ki riƙe aikin nan ƙam. Kar ki bar damuwar wasu a cikin ranki. Ita ma wacce kike ba ni labarin ai ƴar aiki ce matsayinku ɗaya da ita don haka shafawa idanunki toka za ki yi ki karta mata rashin mutunci na rai da motsi, tun da daman an ce idan babba bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba. Zake wa za ki yi ki ƙwaci ƴancin kanki da kanki kar ki yarda wata ƴar aiki da kuke matsayi ɗaya da ita ta taka ki". Na furzar da zazzafan iska daga bakina kafin na sama zarafin cewa"to ya ya kike so na yi? Shin kin san adadin shekarun da suka yi tare da ita da kike yin wannan maganar? Kuma daga dukkan alamo na yadda take cin karenta babu babbaka a cikin gidan akwai wani alaƙa a tsakaninsu. Kin ga yadda take yi kowa? Mulki take zuba wa ko matar gidan sai haka, ta na ba da umarni da cikakken izza ta na wani yatsina fuska". Na ƙare zancen ina kwaikwayon yadda Altine take magana. "Ai duk kar ki yi duba da waɗannan abubuwan, idan ta yi miki kan kara ki yi mata na rodi idan ta ɗaga miki ɗan ƴatsa ki tabbatar da cewa kin karya shi kafin ta sauƙe. Da zaran ta ce miki kule ki ce da ita cas. Ai ƴar aiki ba ta fi ƴar aiki ba, shi kuma wancan mutumin ki manna masa bajin hauka tun da ba shi ya ɗauke ki aiki ba ai ba shi da hurumin sallamarki". "To shikenan zan duba na ga abin da ya dace na yi". "Ya fiye miki dai kam kafin kwaɓar ta yi miki ruwa tsalalo". Taƙaitacce murmushi kawai na saka ba tare da na ce da ita komai ba, haka muka yi sallama da ita bayan mun yi wa juna a kwana lafiya. Na raka ta har ƙofa ta fita na rufe ƙofar. Na zo na kwana na runtse idanuna ina karanto karatun haddan da yake cikin kaina har bacci ya yi nasarar ɗauka ta. Washe gari da wuri na farka na yi alwala na yi salla ragowar ruwan da nake da shi na shiga banɗaki da shi zan watsa. Ina ƙoƙarin cire sutarar da yake jikina na ji an bankaɗo ƙofar banɗakin tamkar za a ɓalle ta. Cikin wani irin gigicewa da ya wuce a misalta shi na yi hanzarin mayar da rigana jikina. Wani gardeden ƙato ne daga shi sai gajeren wando ga tulelen ciki a gaba kamar randa. "Ki fita zan yi wanka". Firgicin da nake ciki na hana ni motsa wa balle samun kuzarin mayar masa da amsa illa kallonsa da na tsaya iya yi. Ya daka mini tsawan da ya sanya jikin rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki. "Ki fita na ce ko ba kya jin Hausa ne?". Ya ƙare zancen yana sanya ƙafa ya yi bol da bokitin ruwan nawan, jikina yana ɓari na ɗauki da yake ta gangarawa na fice da hanzari ban tsaya a ko'ina ba sai cikin ɗakina har zuwa lokacin jikina bai daina rawan da yake yi ba. Na hijabina da ya karkace tare da ɗaura ɗan kwalina da ya faɗi, ragowar lemukan da Hajiya Muhibbat ta saya mini na ɗauko na sha na haɗa da biskit kafin na ɗauka makulli na fito na rufe ƙofan, ƙofar ɗakin su La'aniyatu a rufe ya ke don haka da makullin na tafi. A hankali nake tafiya kamar wacce take jin tausayin taka ƙasa, gabaɗaya ba na jin daɗin yanayin ƙarfi kawai nake yi nake ci gaba da tafiyan ina jan silifas ɗin da ya yi wa ƙafafuna yawa sosai. A gajiye tulus na isa ƙofar gidan na ƙwanƙwasa mai gadi ya fito ya buɗe mini na tsuguna har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini fuskansa tamkar gonan auduga. Kaina a ƙasa na shiga cikin gidan ina tafiya a hankali ban yi aune ba na ji na yi karo da wani abu har sai da na yi baya kaman zan faɗi. Da sauri na ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan sa yana tsaye cikin shigar ƙananan kaya, irin na ƴan wasan ƙwallo sai dai na shi wandon dogo ne har ƙasa, ƙafafunsa ne sanye cikin takalmi sau ciki kansa da hula kamar na sanyi. Bai ce da ni komai ba ya juya ya ci gaba da tafiyansa na bi shi da kallo na ga ya shiga wani sashi wanda bai kai na Hajiya girma ba. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 5️⃣1️⃣ Na daɗe tsaye a wajen kafin na ja jikina na ƙarisa shiga cikin gidan, tun daga falo nake nake yin sallama amma ba a amsa mini ba, tamkar gidan babu mutane masu numfashi. A buɗe baki a karo na uku da nufin ƙara rangaɗa sallamar na ji yo muryar Altine a bayana. "Malama wannan sallama haka sai ka ce wacce kike bin mu bashi ko kuma tara. Idan kika yi ɗaya kika ji ba a amsa miki ba ai sai ki tsagaita". Na tsuguna akan gwiwoyina"na ga kamar ba kowa a gidan nan ashe ku na ciki. Ina kwana an tashi lafiya?". Ta galla mini wani uban harara kafin ta ce"da ban kwana ba za ki gan ni ne?, Ba na son kinibibi da iyayin banza da na wofi in za ki tashi ki kama aikin da ya kallafa akanki tun wuri ki tashi in kuma za ki ci gaba da zama anan ne to bismillah". Tana dire zancen ta juya ta shige kicin ta bar ni durƙushe a wajen, sai da na ja dogon numfashi mai nauyi na fesar kafin na sama zarafin miƙewa na bi bayanta na ɗauko tsintsiya da mopper na fito falon, na share ko'ina tsaf kana na soma yin mopping. Sai da na gama na shiga ɗakin su Aryan shi ma na gyara shi na fito na koma kicin ɗin. Tana tsaye tana soyar ƙosai da ƙamshinsa ya cika ko'ina, na zo gefenta na tsaya cike da girmamawa na furta"na gama sharan shi ne na ce bari na shigo na tambaya, ko akwai wani aikin da zan yi miki?". Kamar ba za ta amsa mini ba sai kuma can ta ce da ni"karɓin soyan ƙosan nan bari na haɗa kunun". Cikin sauri na amsa matsamin da take miƙo mini na ci gaba daga inda ta tsaya. Gwangwani madarar ruwa huɗu ta ɗauko duk ta ɓula su ban da madarar garin da ta ɗauko saket guda ta yanke bakinsu da almakashi. Ta ɗauko wani ƙaramin kwanon tangaran ta juye madarar garin a cikin ta dame shi da ruwa sannan ta juye cikin ruwan da yake tafasa akan wutan ta yi ta juya shi har sai da ya fara yin kauri, ta juye madarar ruwan gwangwani biyu ragowar biyun kuma ta ajiye su a gefe, ruwan flavour na ga ta tarfa a ƙadan a cikin kafin ta sauƙe shi. Ta ɗauko kofi mai marfi ta juye madarar ruwan guda biyu a ciki, gwangwanin huɗum gabaɗaya ta haɗa ta mayar da su inda ta ɗauko su. Tana juyo wa muka haɗa ido. "Wannan kallon fa?". Ta jefa mini tambayar cikin tsawa da ɗaga murya, na yi hanzarin rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa tare da faɗin"ki yi haƙuri". Kafin ta kai ga furta wani kalma Hajiya Muhibbat ta shigo cikin kicin ɗin duk muka haɗe bakin wajen gaishe ta ta amsa mana fuskarta ɗauke da annurin da ya ƙara fitowa da kyawunta. "Sannunku da aiki". Ta yi furucin yayin da take sa hannu ta ɗauki ƙosan da yake gabana ta kai bakinta. "Amma ƙosan nan ba dai laushi ba, ke kika yi haɗa ƙullin ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a tare da faɗin"ba ni ba ce". "Amma kuwa ya yi daɗi sosai. Na tabbatar Saif zai ji daɗinsa". Ta juya tana kallon Altine"ki shirya abincin a dinnig table, Amatullah kuma ta je sashin Saif ta ɗauko su Aryan ta yi musu wanka kafin ki gama". "To ranki ya daɗe uwarmu maganin kukanmu". Ba ta amsa mata ba ta juye ta fice daga cikin kicin ɗin tana amsa ƙiran da ya shigo cikin wayarta. Bayan fitanta mun fi mintuna uku cikinmu babu wanda ya yi magana, har na kammala tuyar ƙosan na sauƙar da man. Ganin shurun ya yi yawa ya sani kawar da shi ta hanyar faɗin"Anty ina ne sashin nasan na je na ɗauko su....". Tun kafin na rufe bakina take gallo mini harara wani na bin wani tamkar wacce na watsa garwashin wuta, ko na faɗi wani abun da bai yi mata daɗin ji a kunnuwanta ba. "Daman can ba ki san sashin nasan ba kika bari ta tafi daga nan ba ki tambaye ba?. Sai ki fita yanzu kam ai ki tambayo". Yadda ta furzo da zancen shi ya fi komai ƙona mini rai da har ban san lokacin da bakina ya suɓuce na furta kalaman da suka shayar da ita giyan mamaki ba. "Don na tambaye ki laifi ne? Na da ke ɗin gabaɗaya a ƙarƙashin Hajiyar muke kuma aiki muke yi don a biya mu". Ban tsaya sauraron amsar da za ta ba ni ba na fice daga cikin kicin ɗin zuciyata har wani tafasa take yi tsabar ɓacin ran da nake cikinsa. A rayuwata ta duniya na tsani a wulaƙanta ni balle a zo gandon da za tozarta ni. Sai da na fito cikin harabar gidan na riƙe ƙuguna ina tunanin inda ya kamata na nufa da zai sada ni sashin nasan, jiya dai lokacin da ya ce a shirya su Aryan za su fita wata ƙofa na ga ya shiga a cikin falon Hajiya babu jimawa kuma ya fito a shirye tana ba za ƙamshi. Na sauƙe ajiyan numfashi a hankali ina ƙara ɗaga kaina sama, idanuna suka sauƙa akan Baba mai gadi da yake nufo inda nake tsaye, hannunsa riƙe da bokatin ruwa. Da sauri na isa gare shi na kai hannu zan karɓa bokatin ya hana ni. "A'a ɗiyata bar shi ai ba za ki iya ba ma, wai bayi ne nake so na yi a shukokin nan mai musu bayin yau bai sama zuwa ba". Na saki taƙaitaccen murmushi kafin na ce"Allah sarki! Ni ma wai Hajiya ce ta ce a je sashin Saif a ɗauko su Aryan, kuma na kasa tantance wanne ne sashin na san". Da hannunsa ya yi mini nufi da sashin kafin ya furta"kin gan sa can shi ne sashin na san". "Ai kuwa Baba na gode sosai da sosai, Baba na ga zanen kanurai a fuskanka na ce ko kai ma kanuri ne?". Sai da ya murmusa kafin ya ce"gaba da baya ma kuwa, ni haifaffen jihar Borno ne cikin garin bama. Uwa da ubana duk kanurai ne". "Ni ma kuwa mahaifina kanuri ne sai dai ko kaɗan ban iya yaren ba". "Kuma ai ba shi ma da wahala idan aiyukan cikin gidan sun yi miki sauƙi ki dinga zuwa ina koya miki. Ko kuma ki zagaya wajen mai ɗakina". Cike da jin daɗi na furta"na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". "Amin". Ya amsa da shi yana ƙara yalwata annurin dake kan fuskarsa, ya wuce wajen bayin shukansa ni ma na ɗauki hanyar sashin da na ya nuna mini. Wannan sashin da na ga ya shiga da safe ne. An ƙawata ƙofan sashin da shuke-shuken wasu turanni masu kyau da ɗaukar hankali da suka kasance launin gore da ruwan ɗorawa. Wasu a cikin wani abu kamar tukunyan ƙasa an taraye a sama. A hankali na isa bakin ƙofan na soma ƙwankwasa tare da rafza sallama. Har sai da na gaji da tsayiwar na juya zan tafi na ji an buɗe ƙofar na waigo na ga Aryan ne ko Ayan oho don ban iya tantance wane ne a cikin su ba. "Ayan ina Aryan ɗin?". Ta tsaya yana kallona"ba Ayan ba ne Aryan ne". "To ina shi Ayan ɗin? Mamanku ne ta ce ku zo a yi muku wanka". Kamar ba da Hausa na yi masa zancen ba ya tsaya yana ta kallona sai can ya ce"Umminmu?". Na gyaɗa masa kaina alamar e kafin ya ce da ni wani abu Saif ya iso wajen hannunsa saƙale cikin na Ayan. Ganin sa ya sanya ni na rusana ina gaishe shi sai dai bai amsa mini ba. Kwarjini da cika idon da ya yi mini ya sanya jikina fara karkarwa da ƙyar na haɗo kalmomin da zan furta suka zauna a bisa harshena. "Daman Hajiya ce ta ce su Ayan su zo a yi musu wanka". "Ki je abin ki za su zo". "To". Na amsa da shi a gajarce ina ɗaukan hanyar barin wajen, na runtse idanuna a ƙoƙarin daidaita nutsuwata da ta yi nisa da gangar jikina. Ni da uwata Hafsatu ta haife ni ban taɓa ganin mutum mai tsananin kwarjini da cika ido irin wannan bawan Allahn ba. Fuskarsa a sake take duk da ba ya murmushi amma fuskar ba a murtuƙe take ba. Ina tafe ina ta saƙe-saƙe a cikin raina har na isa sashin Hajiya ina shiga Aryan da Ayan suka shigo na kamo hannunsu ina faɗin"mu je na yi muku wanka ko?". Suka gyaɗa mini kansu alamar sun ji. Na ja hannunsa muka nufi cikin ɗakinsu, na cire musu kayansu na ɗaura musu towel muka shiga cikin banɗakin. Fanfon banɗakin irin na gidan Anty Zulaihatu ne mai na ruwan zafi da na sanyi, don haka ban shan wani wahala ba na kunna na ruwan zafin na tara na na tsirka shi da na sanyi daidai yadda mutum zai iya watsawa a fatan jikinsa. Sabule ne da mayuka kala-kala a banɗakin masu ƙamshin tsiya, na zaɓi guda ɗaya daga ciki na yi musu wankan da shi, na wanke musu suman kansu da mai ɗin na ɗaura musu towel ɗin muka fito. Zan wuce na ji an riƙo hannuna na juya fuskana ɗauke da murmushi ina kallon yaron na ce"ya ya aka yi?". "Ke ɗin waye ce? Waye ya kawo ki gidan nan?". Na durƙusa a gabansa ina goge masa ruwan fuskansa da hannuna na ce"ni sunana Amatullah, Umminku ce ta kawo ni don in dinga taya Anty Altine aiyukan cikin gida". Ɗayan ya yi saurin faɗin"ita kam da ruwa mai ɗan karen sanyi take yi mana wanka, kuma in mun fito ta hana mu lulluɓuwa da komai wai har sai jikinmu ya bushe". "Ayan". Ya jijj kansa"Arya ne". Kafin na yi magana Ayan da nake riƙe da hannunsa ya fizge ya zo ya buge bakin Ayan tare da yi masa wani irin kallon da na gaza fahimtar saƙon da ya isar masa. Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe don na lura kamar akwai abin da suke ɓoyewa a tsakaninsu wanda ba sa son kowa ya ji balle a sani. Na riƙo hannunsu na ɗaura su akan gadon na je gaban madubi daka jere shi da mayuka da turarruka kama ɗakin wata macen. Gefe guda kuma kum ne da mayukam gyaran gashi kamar yadda na fahimci hakan daga hotunan da suke jikin mazubin. Na shafe musu jikinsu da mai ɗin kana na gyara musu sumar da ake tara musu akan su, na isa gaban wadrode ɗin su kaya ne sosai a ciki kamar ba wadrode ɗin yara ba komai guda bibbi ne a ciki, sai dai mafi akasari ƙananan kayana na ɗauro musu singileti da gajeren wandona na saka musu kana na soma kici-kicin zaɓo musu kayan da za su saka wani shuɗin riga da wando jeans na ciro musu tun kafin na gama Aryan ya zo ya riƙe mini hannu. "A'a ki ɗauko mana ba wannan ba". Ya ƙare zancen cikin gaurancin Hausarsa da ba ta gama nuna a bakinsa, lokaci guda kuma idanunsa suka ciko da ƙwalla. "Me yasa?". Na tambaye sa idanuna a kansa. Bai amsa mini na ya wafce kayan daga hannuna ya mayar cikin wadrode ɗin ya ɗauko wasu, ban ƙara gigin tambayarsa ba na taimaka musu suka saka wanda ya ɗauko ɗin na ɗauko turare na fesa musu sama-sama duk da kasancewar turaren ba mai ƙarfi ba ne sai dai yana da daɗin ƙamshi ainun. Na riƙo hannunsa za mu fita muka yi kiciɓus da Altine za ta shigo cikin ɗakin na matsa na ba ta hanyar shigowa, ta bi su Ayan da kallo da ganinta ya sanya su duk suka yi ƙasa da idanunsu. Ba ta ce da ni ko kanzil ba illa ƙwafan da ta yi kafin ta fice daga ɗakin da hakan ya sanya kaina ƙara ɗaurewa. Muka fito falon hannuna saƙale cikin da na Ayan suna hango Saif zaune a falon yana latsa laptop suka zame hannunsu daga cikin nawa suka nufo wajensa da gudu, ajiye laptop da yake kan cinyarsa ya yi ya ware hannayensa suka faɗo kan ƙirjinsa suna dariya kamar waɗanda aka yi wa kyauta. "Kun yi kyau sosai". Ya furta yana shafa suman kansu da na ƙarar da aƙalla mintuna goma ina gyara musu ita. "Uncle Saif wancan ce ta yi mana wanka yau". Aryan ya yi zancen yana dirowa ƙasa ya zo ya ja hannuna ya kai ni har gabansa. Ya ɗago kai ya yi mini kallo guda tare da kawar da kansa gefe ba tare da ya ce da ni uffan ba. Ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya soma ɗauka musu hoto, cikin sanyin jiki na juya na bar cikin falon na wuce ɗakin Altine na zauna. Na zabga tagumi ina abin da na saba kuma na ƙware a cikinsa watau tunani. Ina zaune ta shigo hannunta ɗauke da plate da kofin roba ta dosara mini a gabana a wulaƙance kamar yadda ake ajiye wa akuya harawa a gabanta. "Ga karin kumallonki nan". Ta faɗa tana wuce wa ta koma gefe ta zauna, na bi ta da kallo na ga ta jawo wani kula da ƙaramin flask ɗin ruwan shayi na hango wannan kofin da ta tsiyaye madarar a ciki ta zuba ruwan shayin da yake cikin flask ɗin a kai tana juya wa da cokali. Ta kurɓa ta ajiye kana ta buɗe kular na ga ta ɗauko doya soyayya da ƙwai tana dangwala da yaji ta kai bakinta. Lamarin ya ɗaure mini kai don ni dai ban inda aka soya doya ba hasalima ƙosai na zo na iske ta tana tuyawa. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina dawo da dubana kan plate ɗin da yake gabana ƙosai ne wanda a lissafina ba su haura guda bakwai ba, gefe guda an ɗan ɗosa na mini yaji. Kaman ba zan ci ba sai kuma na yi wani tunani na kai hannuna na ɗauki guda ɗaya na sa a bakina, na ɗa kofin kunun na kai bakina. Na kasa haɗiye don ban yi tsammanin jin sa haka ba. Koko ne wanda ko sugarin arzuki babu a cikinsa ga shi ya yi sanyi ƙalau babu daɗi sha, wanda ni kuma dai na gani da idona kunun madara aka dama. Ban. ce da ita komai ba na ci gaba da cin ƙosan ina haɗawa da kokon ba don ina jin daɗinsa ba har sai da na kama tsaf, na tashi zan fitar da plate na ji ta bushe da dariya bai waigo ba kamar yadda ban tambaye dalilin dariyar ba na yi ficewa ta. A bisa kan dinning table na iske su Hajiya suna yin karin kumallo, na durƙusa na yi musu sannu da hutawa ta amsa mini cike da kulawa. Na tashi zan shige kicin na Saif yana faɗin"Hajiya Anty mu na da baƙo fa a cikin satin nan, da na ce ba zan sanar da ke sai dai kawai na kawo miki shi amma daga baya na sauya shawara". "To fa! Wane ne haka". "Abokina ko in ce amina Muhammad Taufik". Baan lokacin da na saki plate ɗin da ke hannuna zuwa ƙasa ya tarwatsewa ba. Tsabar firgicin da sunan da ya ambata ya jefa ni a ciki. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 5️⃣2️⃣ "Amatullah lafiyarki me ye ya faru?". Na tsinkayo muryar Hajiya Muhibbat sai dai na kasa cewa da ita komai kamar yadda na kasa motsawa daga inda nake tsaye balle na yi wani yunƙurin tattare plate ɗin da ya tarwatse a wajen. Ban dawo daidai ba sai da na ji hannun mutum a bisa kafaɗuna da hakan ya sanya ni sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina ɗan lumshe idanuna a hankali. "Me yake faruwa ne?". Ta ƙara jefa mini tambayar a karo na biyu, sai da na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na sama zarafin faɗin"babu komai Anty, kawai ji na yi kaina ya ɗan sarawa". Ta yi shuru tana kallona na tsawon wasu daƙiƙu kafin ta ce da ni"to ki je ki kwanta ki ɗan hutu a ɗakin Altine". Kaina kawai na gyaɗa mata don ba na tunanin ko na yi ƙoƙarin amsawa mata da kalmomin baka bakina zai ba ni haɗin kai waje aiwatar da hakan a aikatace. Na nufi kicin na ɗauko tsintsiya da faka na zo na share inda plate ɗin ta tarwatse na je na zubar, a hankali na dawo cikin falon ina tafiya a hankali don haka kawai na ji gabaɗaya ƙafafuna sun riƙe ta yadda da ƙyar nake ɗaga su ina sauƙewa. "To baƙon nakan yaushe zai zo sai mu fara shiri?". Na ɗago kai ina satan kallonsa na ga idanunsa suna kan plate ɗin ƙosan da yake gabansa sai dai ban ga sa'ilin da ya kai ko guda cikin bakinsa ba. "Gobe da yamma in sha Allah zai shigo garin nan tare da mahaifinsa". "Allah Sarki! Muhammad Taufik ina jin daɗin ganin yadda yake bayar da hankali wajen ba wa addini gudunmawa kamar yadda mahaifinsa yake yi, duk da irin yanayin aikinsa. Shi fa yanzu lokacin kansa ma bai da shi balle kuma na mace daga kai har shi ɗin shi yasa har yanzu kun kasa fito da matayen aure. Ga shi kullum ƙara girma kuke yi shekarunku suna ƙara tafiya". "Hajiya Antynmu ai komai lokaci ne, idan lokacin mu ya yi babu makawa za mu yi auren nan. Ko kika sa ni ma ba mu daga cikin wanda Allah ya ƙaddarawa za mu yi aure a cikin duniya". Ya ƙare zancen yana miƙe wa tsaye daidai sanda zan shige ɗaki na ji Hajiya Muhibbat tana tambayar sa ya ta ga ya tashi? Ya ce da ita ya ƙoshi ban san yanda suka ƙare ba na shige ɗakin. Ina shiga muka haɗa ido da Altine ta banko mini wata uwar harara tamkar wacce ta yi arba da kashi, na yi hanzarin janye idanuna ina ƙariso na zauna a ƙasa. Mun shafe a ƙalla mintuna talatin ni da ita babu wanda ya ce da wani ko kanzil ina waige-waigena na hango alƙur'ani ajiye a saman akwati. "Anty Altine don Allah ina ba damuwa zan yi amfani da alƙur'anin nan". Ta ɗago ido ta yi mini wani banzan kallo kafin ta ce"ai ba a kaina kika gan shi, da za ki ce sai kin jira na sauƙe kafin ki yi amfani da shi". Ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauko alƙur'nin na soma karanta suratul Maryam cikin nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harafi ɗaya bayan ɗaya. "Malama ki rage muryarki don bacci nake so na yi". Na yi mata wani kallo ta wutsiyar idona na ci gaba da karatun da nake yi ba tare da na bi ta kanta ba. Ban yi aune ba kawai na ji an zagbaw mini wani gigitaccen mari a kuncina babu shiri na dafe kuncina tare da ɗago idanuna na sauƙe shi akan fuskar Altine da take tsaye a kaina ta riƙe ƙugu tana huci tamkar saniyar da take shirin kai bugu. "Me ye na yi miki da za ki mare ni?". "Bari ki ji in gaya miki wani abun da ba ki sani ba shi ne duk wata ƴar aikin da aka kawo cikin gidan nan dole ta bi umarnina. Sannan wajibi ne a gare ta ta yi mini biyayya don a gaba nake da ita. Na lura tun ranar ki ta farko kanki yana rawa ki na ta wani ƙoƙarin shige wa jikin Hajiya da wani kinibibin jan su Aryan a jikinki, to billahillazi tun wuri gwara ki kama kanki kafin na haɗa miki sharri da tuggun da ba za ki iya fitar da kanki ba". Na ji zuciyata tana wani irin harzuƙa ta zo mini har wuya tabbas na yi sanyi don da zamani da nake gida ne ba ta isa ta ɗaga mini ƴatsa ban karya shi ba duk da kuwa ina da haƙuri matuƙa da kai zuciya nisa. Tsam na miƙe jikina har wani rawa yake yi kamar mazari haƙwarana suna karabɗiya da juna suna ba da wani sautin ɗas ɗas. Ta matso dab da ni ta ce"ko za ki rama ne na ga kin miƙe ina wani jijjiga?". Ta saki wani bushashshiyar dariyar da ba ta da haɗi da nishaɗi, jin daɗi ko kuma walwala kana na furta"ai ko dukana kika yi da itacen bishiya ba zan rama ba Anty, sa boda na ƙoshi da tarbiyya kuma an koyar da ni yadda zan girmama na gaba da ni ko da kuwa da sankan ɗaya ya riga ni zuwa duniya balle ke da kin kusa haifa ta. Bari na je na duba Hajiya ko sun gama na tattare kwanukan". Da alama ba ta ji daɗin zancena na ƙarshe ba don sakeke ta yi tana bi na da kallo tamkar ta sama majigi har na fice daga cikin ɗakin ba ta ce da ni komai ba. Da sallama na ƙariso ciki falon na ga har sun gama cin abincin sun koma kan kujeru sun zauna, na tsuguna na yi wa Hajiya sannu da hutawa kana na isa wajen dinning table ɗin na tattare kwanunkan na kai kicin na wanke su tas na mayar da su majiyarsu. Ina kicin ɗin Ayan ya shigo wai na zo in ji Umminsu, muka fito tare da shi na zauna a ƙasa cikin girmama wa na ce"Hajiya ga ni". "Jiya Saif ya kai ki gidan nakun?". Ƙirjina ya buga da ƙarfi na ɗago ido ina satan kallonsa na ga shi kam ko a jikinsa wai an muntsini kakkarauna yana zaune yana latsa wayar da yake hannunsa. Sai da na daidaita nutsuwata kafin na iya furta"e Hajiya ya kai ni". Ta mayar da dubanta gare shi"ka ga gidan na sun?". Ba tare da ya ɗago kansa ba ya ce"e Hajiya Antynmu ko yanzu ma in ki na so zan iya kai ki". "To alhamdulillah tun da ka ga gidan, ka ba ta makullin sashinka ta share maka kafin ka fita. Don ni yau sai around 5:pm zan fita". Sai a lokacin ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake yi"Anty ni fa sashina a gyare yake. Ke ma kin san ko wata macen ba za ta nuna min tsafta ba balle kuma wannan". Ta murmusa kafin ta ce"ai duk tsaftan namiji Saif a bayan mace yale komai ƙanƙantan ta kuwa. Ka ba ta makullan kawai ta je ta gyara maka, kar wani gyara ka iya kai da yaushe ma ka zauna a cikin gidan". Kamar na yi magana na ce ta ita ta bar shi kawai tun da ba ya so sai kuma na yi shuru. Muryarsa a cushe ya ce"a buɗe yake". "To Amatullah tashi ki je sashin nasan ma a buɗe yake, ki gyara masa shi tsaf irin gyaran da shi da kanki sai ya sa an nemo ki gobe. Idan hakan ya faru kuma ni da kaina zan tsaya miki ki gara shi kamar ƙwallon ƙafa kafin ki je ki ƙara gyara masa". "To Hajiya". Na amsa da shi a taƙaice jikina gabaɗaya ya mutu murus, na tashi na fita zuwa sashin nasan ƙirjina yana tsananta bugu kamar zai fito waje. Sai da na isa ƙofar sashin na ja dogon numfashi na fesar kafin na turo ƙofar na shiga ciki na tsaya ina ƙarewa zubi da tsarin falon kallo. Ba shi da girma sosai don bai kai na Hajiya Muhibbat ba ya tsaru sosai da dukkan abubuwan more rayuwa da ƙawata waje, komai na falon fari ne tun daga kan labulaye, kujeru, tayis da kuma kafet ɗin hatta abin da aka ɗaura tv a kai fari ne. Na cire hijabina na ɗaura a ƙuguna na soma tattare takardun da na gani a barbaze akan kujerar kan teburin kofi ne da goran ruwan da aka sha ba a ɗauke ba. Na tattare takardun na kimtsa su na saka a cikin jakar da na gani a gefe, na ɗauke kofi da goran ruwan na shiga ɗaya daga cikin ƙofofi biyu da na gani. Ƙofan farko da na shiga na ga kicin ne na ajiye kofi da goran, kicin babu ƙazanta a cikinsa amma komai a birkice yake komai ba ya muhallinsa. Ban san sa'ilin da na saki tsakin takaici ba ina kwakwayon muryarsa na ce"ni ko'ina a sashina a gyare ya ke ko wata macen ba za ta nuna mini tsafta ba". Na tattare kicin ɗin na share kana yi mopping na fito na shiga ɗayan ƙofan ɗaki ne mai ɗauke da kayan ɗaki tsaf sai dai da alama ba wanda yake kwana a cikinsa saboda yadda ya yi ƙora na karkaɗe na sauya zanin gadon na shiga banɗaki na wanke na fito na hau benin ya sada ni da wani ɗan madaidaicin falo nan komai a gyare yake sai ɗan abin da ba za a rasa ba, na kashe tvn da na gani a kunne kana na rufe tagogin da suke buɗe. Ƙofa ɗaya na gani na shiga na tarar da ɗakin kwana ne shi ma komai na cikinsa launin fari ne hatta zanin dake kan gadon. Sauya zanin gadon na fara yi na gyara gaban madubin da komai ya ke warwartse kana na wanke banɗaki. Na hango wani air freshener akan dirowar da ke jikin gadon na je da nufin ɗauka na feshe ɗakin da shi, sai dai mummunan ganin da na yi ya tursasa mini tsayawa cak na kasa motsawa na tsawon wasu dakiƙu. Jikina yana rawa tamkar mazari na kai hannu na ɗauko hoton da na gani ajiye a saman dirowar ina ƙara ware idanuna akan sa. In dai ba idanuna ba ne suka sama matsala tabbas hoton Muhammad Taufik da Saif na gani tare cikin shiga irin ɗaya kowa hannunsa riƙe da sallaya da alama masallaci za su je, ko kuma ranar bikin salla aka yi hoton. Duk su biyun fuskokinsu yana ɗauke da maɗaukakin annurin. "Muhammad Taufik". Na furta cikin rawan jiki da na murya yayin da wasu hawaye suke gangarowa daga idanuna suna wanke mini fuskana. Jin an turo ƙofan ɗakin an buɗe ya sani na firgita da har ban san lokacin da hoton ya zame daga hannuna zuwa ƙasa ba, gilashin dake jiki ya yi kwasa-kwasa. Runtse idanuna na yi ina kai hannayena dukka biyu na toshe kunnuwana da ƙaran fashewan gilashin da ya gigita ni har ya na barazanar juyar mini da ƙaramar curin ƙwaƙwalwata. "Me ye kike yi a nan?". Na yi muryarsa tamkar daga sama ban iya cewa da shi komai har ya iso inda nake tsaye daidai lokacin da nake buɗe lumshashshun idanuna har na gama buɗe su tar akan gilashin da ya tarwatse a wajen. Ina ɗago kaina muka haɗa ido da shi ya yi mini wani matsaiyacin kallo kafin ya tsuguna ya ɗauki frame ɗin bai ce da ni komai ba ya fita daga cikin ɗakin. Wani kuka ne mai ƙarfi ya kuɓuce mini na sulale ƙasa na yi zaman dirshan ina jin yadda dunduniyar ƙafana ya cashi gilashin yana fitar da jini amma ban damu ba na ci gaba da kukan da nake, tare da jefa wa kaina jerin gwanon tambayoyin da na gaza cimma amshoshinsu. Me ye alaƙar Saif da Muhammad Taukif da har na ga hotonsu tare? Shin da gaske yadda kunnuwana suka ji yo mini shi ne baƙon da zai zo cikin gidan nan da yammacin gobe?. Tagwayen ajiyan zuciya mai ƙarfi na ja na fesar kafin na yi ƙarfin halin tashi tsaye ina ɗan ɗingisa ƙafata na ɗauko tsintsiya na share wajen na fesa air freshener ɗin da na yi niyya kana na ja ƙofar ɗakin na fito. Babu kowa a falon saman amma an kunna sautin karatun alƙur'ani cikin wata muryar da na kasa tuna inda na taɓa jin ta, na sauƙo ƙasa na iske shi zaune a falon ƙasa yana zaune ya yi shuru kamar wanda yake nazarin wani abu. Na zo na durƙusa a gabansa. "Na ga ma duk wani gyaran da ya dace na yi. Shi ne na ce bari na tamnaya inda akwai abin da kake so a yi maka". Sai da na cire rai da samun amsa daga gare sa, don har da ƙafafuna suka gaji na ji kamar na ɗaura hannuna a ka na yi ta kurma ihu tsabar takaicin da ya ƙunsa mini, na tsani na yi wa mutum magana ya yi banza da ni wannan abun ci mini rai yake yi sosai da sosai. "Za ki iya tafiya kuma kar ki ƙara dawowa sashin nan don ba na buƙatarki a nan. Don haka ki san abin da za ki faɗa wa Anty". Yana gama zancen ya tashi ya ɗauki wayarsa da wasu makullan da suke kan teburin da yake gabansa ya zuba a cikin aljihunsa ya fita, ni ma tashi na yi na fita sanda na fito na gan shi har ya shiga motarsa Baba mai gadi ya buɗe masa gate zai fita na bi motar da kallo har sai da ya fice daidai lokacin da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 5️⃣3️⃣ Ji na yi kamar na koma cikin sashin na binciko dalilin kasancewar hoton Muhammad Taufik a cikin ɗakinsa, gabaɗaya na rasa gane kaina balle fahimtar abin da yake yi mini daɗi. Na tsaya cak a wajen ina ta karatun wasiƙan jaki da saƙa da warwara cikin raina. Kamar daga sama na ji saurar dirin sauti a cikin kunnuwana da ya tursasa mini ɗago idona Ina duban Baba Mai gadi. "Ƴar nan lafiya? Tun ɗazu na hango ki kin fito kin tsaya a nan kin yi shuru. Ko dai akwai wani damuwar ne?". Na saki taƙaitaccen murmushin da iya kansa kan leɓena bai kar har cikin zuci ba. "Lafiya ƙalau Baba. Yanzu ma wajenka nake son na je in ba ka wani aikin ka soma koya mini ƙananun kalmomin yaren". Ya yalwata annurin fuskarsa kafin ya furta"ai kuwa ba na komai ina dai zaune ne kawai". Yana dasa aya a zancen ya juya na bi shi a baya har zuwa bakin gate ɗin ya zauna akan wani benci yayin da na zauna a kusa da shi. "To yanzu ta ina za mu fara?". Na duƙar da kaina ƙasa"ai Baba tun daga gaisuwa za a fara koya mini har a gangaro a zo kan ƙidaya da wasu kalmomin da suka kasance na amfanin kullum-kullum". Ya yi dara kafin ya ce"to kamata ya yi ki nema takarda da biro ina faɗa miki ki na rubutawa, tun da kin yi karatun zamani ai ko?". Na riƙe haɓa"na yi amma ban yi nisa ba". Kafin ya ce da ni wani abun Altine ta iso wajen kamar mai shirin zuwa filin yaƙi ta ja ta tsaya a gabanmu hannunta riƙe da wani baho ƙiran ghana must go ƙarami. "Amma kin san akwai aiki a cikin gidan kika zo nan kika tare ko?". Cike da mamaki na ɗaga ido ina kallonta da ta haɗe girarta na sama da na ƙasa. Ta murtuƙe fuska kamar magribar ɗinya. A hankali na ce"na wanke har kwanukan da aka ci abinci fa kafin Hajiya ta ce na je sashin can na gyara....". Tun kafin na gama ta tari numfashina"don kin wanke kwanuka kuma sai aka ce miki babu wani aikin ko? Ki tashi ki shiga ciki ki gyara ɗakin su Arya kafin na ce na kai saƙon nan na dawo, a fara shirin abincin rana". "To ki dawo lafiya". Na amsa da shi cikin sanyin murya ba ta amsa mini ba illa tsakin da ta tsirtar tamkar ta yi arba da ɗanyen kashi sakin yanzu-yanzu, ta ja bahon da ƙyar za ta bar wajen Baba mai gadi ya dakatar da ita ta hanyar faɗin"Hajiya Altine wannan kayan fa? Mene ne a ciki na ga ki na ja da ƙyar". Ta galla masa wani uban harara tamkar idanunta za su faɗo ƙasa"to ƴan sa ido masu zuwa lahira da cover shoe. Me ye naka a ciki? Ina ruwanka da ni balle kayan da zan fita da shi? Kowa ya tsaya a matsayinsa ka tsaya a matsayinka na mai gadi ni ma na tsaya a matsayina na ƴar aiki. Idan ba so kake yi mu ba wa hamata iska ba ni da kai". Jijjiga kansa ya yi a taƙaice ya furta"Allah ya kyauta". Ta yi wuf ta amshe zancen tamkar jira take yi"Amin in da gaske kake yi". Daga haka ta ja bahon ta fita da shi duk mu biyun muka bi ta da kallo har ta fice na sauƙe sakakken ajiyar zuciya mai matuƙar sauti. "Ɗiyata sai haƙuri fa zama da Altine ko na sakon ɗaya ne sai ka haɗa da haƙuri. Balle zaman awanni har ma ranaku da dama, kin gan ta nan tun farkon auren Hajiya aka kawo ta aiki a cikin gidan nan, Hajiya da mijinta har ma da ƙaninsa sun yarda da ita matuƙar yarda wanda har ya wuce kima sun yi imanin ba za ta a taɓa haɗa baki da ita a cutar da su ba balle ace ita da kanta ne za ta cutar da su. sai dai ba san cewa a cikin zaman da suke yi da ita cutar da su take yi su da ƴaƴansu ta ƙarƙashin ƙasa ba, ta yi musu illa sosai amma har yanzu ba su farga ba balle su gano fuska biyu gare ta". Tun da ya soma maganan na sake baki da hanci ina jin sa da kallo har ya kai aya kana na ja dogon numfashi na fesar kafin na zama lasisin faɗin"wani irin illa kenan Baba?". "Iloli masu yawan gaske ma kuwa, kin ga Altinen nan da kike ji da gani ta ƙi jinin ta ga wata ko wani ya raɓe jikin Hajiya mussamman in ta lura zai karu da wani abu, ka mamaye komai na cikin gidan nan duk wata ƴar aikin da za ka kawo da sunan ta zama mataimakiya a gare ta sai ta yi yadda ta yi ta yi kwance-kwance ta ƙulla mata tuggun da ba za ta iya fitar da kanta ba. A ƙarshe da kanta za ta zaɓa barin aikin akan ta ci gaba da zama. Ki na ganin Altine hatsabibiyar mace ce, akan ta na ƙara yarda da cewar ko sheiɗan dole ya ji tsoron kaidin mace balle mu kuma bil adama. Ki yi hankali da ita". "To wannan kayan da ta fita da shi ba ina za ta je da shi?". Ya saki taƙaitaccen murmushi kafin ya ce"a sannu a hankali idan Allah ya san zamanki a cikin gidan nan ya yi tsawon rai za ki fahimci inda take kai kayan". Ƙirjina ya buga da ƙarfin gaske cikin son ƙarin bayani na ce"ban gane idan zama na ya yi tsawon rai ba". "Duk wata mai ƴar aikin da ake kawo wa cikin gidan nan a ta wuce adadin makonnin huɗu take fita. Don haka ke ma ki yi taka tsantsan ki kuma san irin zaman da za ki yi a cikin gidan nan, mussamman kasancewar ki yariya mai ƙaranci shekaru". Jikin gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Na gaza cewa komai duk da tarin tambayoyin da suka yi mini tsayiwar ƙayan kifi a maƙoƙarona da ƙyar haɗiye miyau ɗin da ya taru mini a cikin baki. "Ƴarta ki kwantar da hankalinki ban sanar da ke hakan don na tayar miki da hankali, ko kuma don na kashe miki ƙwarin gwiwa ba. Ki ci gaba da aikinki sannan gefe guda ki dage da addu'a ki tabbatar da ba ki mu'amalance kowa da wani mummunan hali ba. Ki tashi ki shiga ciki kafin ta dawo ta same ki a nan ". "To Baba na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". "Amin Allah ya yi albarka". Ban iya amsa addu'ar cikin kalmomin baki ba sai a cikin zuciyana na amsa yayin da nake tashi daga wajen na nufi cikin gidan kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Wayam na iske falon babu kowa sai su Arya da Ayan suna kallon TV na bi shi su da kallo. Ban san me yasa haka kawai a duk lokacin da na ga yaran nake jin suna matuƙar burge ni. Na daɗe ban ga yara ƙananu masu irin shekarun da suke da kwatankwacin irin nutsuwarsu ba haka kawai na tsinci kaina cikin sakin murmushi, sai da na ƙare musu kallon tsaf kana na wuce kicin na ɗauko tsintsiya da mopper na dawo na nufi ɗakin su Ayan. Sai da na gyara musu gadon na sauya zanin gadon na saka wani na shara ɗakin na yi mopping kana na shiga banɗaki na wanke na feshe ko wani kusurwa da room freasher. Sai da na gama komai na fito jikina gabaɗaya babu gaɓar da ba ya yi mini ciwo. Ina ajiye tsintsiya da moppern na fito na wuce ɗakin Altine kamar kayan wanki na zube akan katifa ina mayar da numfashi kamar wacce ta yi aikin ɗaga ƙarfe, ko'ina a jikina ciwo yake yi mini har ba na ƙaunar motsawa, na lumshe idanuna a hankali ina jin wani mayataccen bacci yana fizgana ban san sa'ilin da na yi baccin ba sai jin sauƙan ruwan sanyi na yi a jikina. Figigi na tashi ina jan wani dogon numfashi na fesar da shi yayin da nake tantance inda nake don gabaɗaya ɗakin ya juya mini na kasa gane komai tamkar wacce aka yi wa dashen sabon curin ƙwaƙwalwa a cikin kanta. Kafin igiyar firgicin ya gama saki na na tsinkayo muryar Altine raɗau a masarrafar jina. "Kwanciyan me ye kike yi? Ai kwanciya bai kama ki tun da dai neman kuɗi kika fito yi. Ki tashi ki je ki share filin tsakar gidan nan tsaf". "Na gama duk wani aikin da ya kamata na yi shi yasa na zo nan na kwanta ina hutawa. Wallahi gabaɗaya gaɓobina ciwo yake yi mini.....". Kafin na gama zancen na ji ta sauƙe mini mari a gefen fuskana na hago da har ban san sa'ilin na saki ƙara ba ina dafe kuncina cikin jin zafi da raɗaɗin da ya ratsa har cikin kwanyata. "Har kin isa ina magana ban yi wannan lalacewar ba. Tun farko daman na lura kaman kanki yana fisga sai na gyara miki zama tukunnan a cikin gidan nan kafin mu daidai". Tana ƙare zancen ta hankaɗe ni na sauƙa daga kan katifar zuwa ƙasa ta haye ta yi kwanciyarta. Na daɗe zaune a wajen ina jin raina yana yi mini wani irin zogi, yawun bakina ya jirkice ya koma mini tamkar maɗaci, zan iya cewa tun da nake a cikin duniya ba a taɓa cin zarafina an wulaƙanta ni irin na yau ba, na bi kayan jikina da ido da suka jiƙe sosai ina jin wani sanyi yana ratsa cikin jikina. A hankali na tashi na fita daga cikin ɗakin ina ɗaga ƙafata da ƙyar har na fito cikin harabar gidan na nema wani dakali na zauna ina shan hantsi tare da haɗa kaina da gwiwa. Take zuciyata ta soma karatu mini tsohon karatun da na daɗe da haddace shi a cikin kaina. Tabbas gata da mutumcin duk wata ɗiya mace shi ne gidan iyayenta haka nan babu inda za ta je a kanta da kima da daraja kamar a zo a tarar da ita a cikin gidan iyayenta. Na tuna da wani magana mai cike da hikima da darrusa masu yawan gaske. Inda yake ce wa da mu a wurare uku ya dace a sama mace wacce ta amsa sunan mace ba wacce ta rako mata zuwa duniya ba. Wuri na farko shi ne a same ta a gaban iyayenta, in ba a same ta a nan ba to a same ta a cikin gidan mijinta in ba ta gidan mijinta to a same ta a cikin kabarinta. Waɗannan wurare guda uku su ne suka fi dace da mazaunin mace, in ba ta gaban iyayenta, to ta kasance tana gidan mijinta tana bautar Ubangijinta domin neman aljannarta. In kuwa duk ba a same ta a nan ba to zai fi kyautuwa da saya mata daraja, mutumci, martaba da kuma kima idan aka tarar da ita a cikin kabarinta. Ban san lokacin da hawaye suka zarya a kan fuskata ba sai jin ɗumin su na yi akan fatan fuskana da har yanzu yake yi mini zogi sa boda da na sha a hannun Altine. Na ɗago kaina ina ƙarewa girman filin tsakar gidan kallo da Altine ta yi mini umarnin sharewa. Babu shiri na sauƙe wani shirgegen ajiyan zuciya don a girman filin ko tun ƙarfe shidan safe na fara sharan akwai yiyuwar na wuni ina yi ba tare da na kammala ba. Na taɓa kayan jikina na ji ya bushe ƙarau na tashi na ji jiri yana ƙoƙarin nanani da ƙasa babu shiri na koma na zauna na dafe kaina da yake juyawa, ina karanto duk wani addu'ar da ya zo bakina a sa'ilin. Ji da na yi zafin ranar yana takura ni ya tilasta mini tashi daga wajen na je wajen rumfar ajiye motoci kasancewar wajen intalok ne aka layyale ko'ina da shi, na shimfiɗa ɗan kwalina na kwanta a kai ina ta rawar sanyi ban san lokacin da baccin wahala ya yi gaba da ni ba. Sai jin wani gigitaccen ƙara na yi a cikin kunnena da ya tursasa mini tashi ba tare da na shirya wa hakan ba. Sai da na daina jin sauti da motsin komai na tsawon wasu mintuna sa boda yadda ƙaran ya kiɗima ni. Kallon shi kawai nake yi yayin da ya fito daga cikin motan ya zo gabana ya tsaya tare da zura dukkan hannayensa cikin aljihun wandonsa. Bai yi mana ba na tabbatar da hakan ne sa boda ko kaɗan laɓɓansa ba su motsawa. Na kasa motsawa balle na yi yunƙurin tashi daga wajen da hakan zai ba shi daman shigo wa da motar ma'ajinta. Daidai lokacin da jina ya dawo na ji ya saki wani tsaki mai dogon zango kana ya juya ya bar wajen. Da ƙyar na iya tashi tsaye na tsaya akan ƙafafuna da suke rawa da alamta gajiyar su ga jimirin ɗaukar nauyin saƙararren gangar jikina. Na mayar da ɗankwalina kaina na saka na soma tafiya, hanyar gate na nufi don a yadda nake jin jikina ba na tunanin zan iya tsinana komai na zaɓi na koma gida akan na ci gaba da zama a nan. Na yi sa'a ban tarar da Baba Mai gadi a ƙofan ba balle ya hana ni tafiya ko kuma ya tsare ni da tambayoyi me ye yake faruwa. Kai tsaye na fita na soma tafiya ina haɗa hanya tamkar wacce ta yi tatil da kayan maye cikin wannan yanayin har na isa gida lokacin idanuna har wani dishi-dishi suke kallon abubuwan. Na ji wani daɗi a cikin raina da na hango ƙofar ɗakin a buɗe don tsayawa buɗe ta ma galabaitar da ni zai ƙara ni sosai. Kai tsaye na afka cikin ɗakin sai dai abin da na gan ya sanya ni dole na ja na tsaya. Wata budurwa na tarar a cikin ɗakin tana sauya kaya, gefe guda kuma an saka katifa, akwati da ragowar sauran kayan amfanin yau da kullum. "Wace ce ke kuma? Me ye kike yi a nan?". Na watsa mata tambayoyin a tare, ta bi ni da wani malalacin kallo kafin ta ce"ko ke ce Amatullah ɗin?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar ci gaba da maganar. "Yanzu wannan ɗakin ba mallakinki ba ne mallakinmu ne ni da ke". "Ban gane abin da kike son faɗa ba". Ta yi fari da idonta kafin ta furta"kamar yadda kika ji na faɗa wannan ɗakunan mallakinmu ne ni dake. Tare za mu rayu a cikinsa na kama hayar rabin ɗakin kamar yadda idanunki suke nuna miki". A kufule na ce"hakan ba mai yiyuwa ba ne, don duk ɗakunan cikin gidan nan ai mutum ɗaɗɗaya ne a cikinsa". Ta galla mini harara"ba kya buƙatar sai na ba ki amsa da kalmomin baki tun ga shi idanunki sun ga ne miki zahiri". [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 5️⃣4️⃣ Na yi tsaye mamaki da al'ajabi ya na yi motsawa daga inda nake tsaye kamar gunkin ƙasar india. Na ja dogon numfashi na fesar daga bakina ina jin wani abu yana tasowa tun daga ƙasan ƙirjina har zuwa tsakiyar kaina. Ban kuma cewa da ita komai ba na ja ƙafafuna da suka sake na isa kan taburmana na zauna na ɗaura kaina a bisa gwiwoyina ina mayar da numfashi kamar wacce ta yi gudun ceton rai, ji nake yi kamar ɗakin yana juyawa na lumshe idanuna ina cije leɓena haɗe da sauƙe wani gauron ajiyar zuciya mai matuƙar sauti. Kaina wani irin ciwo yake yi kamar zai faɗo ƙasa na zame na kwanta akan bayana ina kallon rufin ɗakin ina karanto suratul Yusuf daga cikin kaina, ban yi nisa ina yi ba na ji an kunna sauti an ƙure sauti a cikin ɗakin. Sai da na firgita na tashi na zauna gaba ɗaya na manta da cewar yanzu ba ni kaɗai ba ce a cikin ɗakin, har cikin tsakiyar kaina nake jin sautin yana ratsawa. Ƙaran sauti da kiɗe-kiɗe suna daga cikin abubuwan da suke sautin kiɗima ni tare da saurin juya mini ƙwaƙwalwa da damalmala mini dukkan lissafi gami da hautsina mini hankali. Na kai hannuna na toshe kunnuwana tare da runtse idanuna da ƙarfi, duk ina daurewa har lamarin ya gagare ni wai cire wando ta kai. Ba tare da na buɗe idanuna ba na ce"don Allah ki yi haƙuri baiwar Allah ki tage ƙaran sautin nan". Ba ta tanka mini hakan ya sanya ni buɗe idanuna ina hango inda take na ga tana kwance a bisa katifarta tana ta sharara baccinta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ga sautin yana ta tashi a cikin ɗakin. Na tashi na ina jin hajijiya yana ɗeba na dafe gefen gini ina tafiyan a haka har na isa wajen da ta ajiye MP na kai hannu na ɗauka na kashe ta na mayar na ajiye. Ko barin wajen ban yi ba ta farka tamkar sautin MPn da baccin da take yi tare suke tafiya, ta murtsike idanunta tana kallona. "Bura uban can! Uban waye ne ya saki kashe min MP?". "Amma kin san ai ɗakin ba ke ɗaya ba ne, kin san da cewa da ƙaran sautin nan ki na shiga cikin hayyacina". Kamar na watsa mata tafasasshen ruwan zafi a jikinta ta miƙe zumbur ta tsaya akan ƙafafunta ta riƙe ƙugu. "Ke bari na fito miki a mutum kuɗi fa na cake na biya na kama ɗakin nan ba wai kyauta nake zaune ba ko kuma alfarma aka yi min ba. Kin gan ni nan ni ba na iya bacci ba tare da na kunna sauti ba, don haka tun wuri gwara ki saba". Tana dasa aya a nan ta kunna MP ɗin ta koma ta yi kwanciyarta tana kaɗai ƙafa, na kasa motsawa daga wajen balle na koma inda na taso duk da jirin da yake ɗauka ta. Sai da na saki dogon numfashi na fesar kafin na ja ƙafafuna na koma inda na taso na zauna na zabga wani uban tagumi tamkar wacce aka yi wa rasuwa ta wani babban makusancinta. Tun yana damuna har na zubar da komai na tashi na ɗauki buta na fita na je banɗaki na yi tsarki, na fito ina isowa tsakar gidan na yanke jiki na faɗi jirif kamar kayan wanki. Ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai buɗe idanuna na yi na gan ni kwance a cikin wani ɗakin da ban ga ne wajen ba, na yunƙura zan tashi na ji na kasa dole na komo na kwanta ina tunano abin da ya faru kafin faduwar hakan. "Sannu kin tashi ne?". Na tsinkayo wata baƙuwar murya ta sauƙa a kunnuwana na cira kai ina kallon matar ba tare da na ce komai ba. Zan tashi ta riƙe mini hannu"ki koma ki kwanta har yanzu jikinki babu ƙwari sosai". "Ina ne sannan wace ce ke?". Ta faɗaɗa annurin fuskarta kafin ta so daidai saitin kunnuna ta ce"sunana Zinariya". "Me ya kawo ni cikin ɗakin nan?". "Faɗo wa kika yi a tsakar gida babu wanda ya kula ki balle ya kawo miki ɗauki, haka na shigo na ganki yashe a ƙasa na ja shigo da ke cikin ɗakin na kwantar da ke. Shi ne tun ɗazun kike bacci sai yanzu kika tashi". Na buɗe baki zan yi magana kukan da ya kufce mini ya hana ni damar furzo da zancen da na yake kan harshena. Ta dafa kafaɗana"ki na jin wani ciwo a jikinki ne? Na girgiza kaina alamar a'a na tashi na zauna da ƙyar har zuwa lokacin hawayen suna zuba daga idanuna. "Don Allah zan sama ruwa na yi alwala?". Sai da ta bi ni da kallo kafin ta furta"a cikin wannan yanayin za ki yi salla?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganan cikin mamakin da ya bayyana har a cikin furucinta. "Ga buta ki ɗauka sai ki je ki yi alwalan". "Na gode". Na amsa da shi a taƙaice ina dirowa daga kan katifar na sauƙo ƙasa na mayar da ɗan kwalina da ya same kaina, na ɗauki butan na fita waje na je na yi alawan sanda na shigo na tarar da ita tana waya na ajiye wayar ba tare da na yi mata godiya ba. Ɗakina na wuce na tarar da ita har yanzu tana baccin ga sautin yana tashi sai dai amon bai kai na ɗazu tashi ba. Na ayi sallan na zauna a wajen ba tare da na tashi har sai da na yi sallan asr kana na fara yin wani irin yunwa yana ƙwalulan hancin cikina, na jawo ledar kayan nan na gama da ragowar sauran lemukan. Sai a lokacin da hankalina ya dawo jikina na tuna da cewar haka na fito daga gidan ba tare da na sanar da Hajiya Muhibbat halin da nake ciki ba. Na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ina jin har yanzu kunnuwana sun yi mini wani dum tamkar wacce aka ɗurawa wuta a ciki. Na tuna marin da cin mutuncin da Altine ta yi mini take na ji raina yana soyiwa tamkar yadda ake soya gyaɗa marau-marau a cikin toka. Na ja dogon gashin na fesar daga bakina ina jin wani hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata tabbas na yarda rayuwa ba za ta yiyuwa a haka ba dole ni ma sai na tashi na soma nema wa kaina ƴanci, na fara tsaya wa kaina a cikin ko wani irin yanayi don tabbatar da zaman lafiya da jin daɗina. Dafo kafaɗana da na ji an yi shi ya dawo sa ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa, na ɗago kaina ina kallon La'aniyatu da take tsaye a kaina tana kallona. "Ki zo Hajiya tana ƙiranki". Kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na bi ta a baya har zuwa cikin ɗakin Hajiyar ta shige cikin uwar ɗaka yayin da ni kuma na zube a falo ina na iske Hajiya Babba da kuma Aminu zaune. Cikin girmamawa na gaishe da su sai dai cikin su babu wanda ya tanka mini illa bi na da kallo suke yi kamar yau suka fara tozali da ni. "Amatullah". "Na'am ranki ya daɗe". "Ɗaga idonki ki kalle ni da kyau kuma ki saurara abin da zan faɗa miki da kunnen basira". Na cira kaina a hankali ina kallon ta da hakan ya ba ta damar ci gaba da zancen da take yi. "Gidan nan da kike gani ba wajen sauƙan baƙi ba ne. Gidana gidan gudanar da kasuwanci ne da za ki iya gudanar da su ko kina daga kwance akan katifarki, ba zai yiyuwa ki zauna ki miƙe ƙafa da sunan ki na fita aikin bautan da sai wata ya ƙare kafin a ba ki kuɗi ba, don waɗannan kuɗaɗen ba za su ishe ki ɗaukar ɗawainiyyar kanki ba ma balle har ki biya kuɗin hayan ɗakin da kike zaune a cikinsa har ki yi sauran buƙatunki. Ki kama sana'ar da ƴan matan gidan nan suke yi ko kuma ki shirya barin cikin gidan nan. Tun da kika zo cikin gidan nan ba ki sauya ba kullum jiya i yau ko takalmin takawa ba ki da fitacce balle kuma suturar kirki". Tun da ta fara yin maganan na ji zuffa ya jiƙa jikina sharaf ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau tara, daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin akuya ai kuwa tunin na soma sakin hawaye. "Don Allah Hajiya ki taimake ni ki taimaki rayuwata ki yi mini rai, kar ki ce na bar cikin gidan nan. Don wallahi ban san inda zan cusa kaina ba inda na bar nan ki tausaya mini.......".Tun kafin na dire zancen ta dakatar da ni. "Dakata ki ji ni yarinya nan gidan ba tausayi ko kuma jin ƙai nake yi ba, gidan na zo kin zo ne ki baje hajarki ki kwashe ƴan sulallanki. Ki yi hidimar kanki har ma ki yi kyauta ki yi sadaka, idan tausayi kike buƙata sai ki bari sai ranar juma'a ki tafi ƙofar babban masallaci na gidan mai martaba wataƙila ki yi dace ki sama masu taimaka miki bila adadin. Amma a cikin gidan nan dai kam jikinki ne da ƙoƙarinki zai ƙwace ki har ya yi miki riga da wando har da singileti". Ta juya tana kallon Aminu"daman ba ka sanar da ita dokoki da ƙa'idodin cikin gidan nan ba ne?". "Aradu na sanar da ita komai in detail in ji ƴan boko. Ita ɗin ce akwai ta da daurin kai yadda kika san jinjirin haihuwar jaki, babu irin bayanin da ban yi mata ba amma kanta ya ƙi ɗauka ta dage akan ba za ta aikata zina ba. Na sanar da ita cewar akwai hanyoyi da yawa da za ta sama ƴan kuɗaɗenta ba ma tare da sun yi ido huɗu da na mijin ba amma ta ƙi amincewa". Da alama bayyanin da Amimu ya yi mata ya taimaka wajen rura wutar takaicin halina da yake ci a cikin ranta. "Zan ba ki zaɓi biyu wanda a ciki dole ki zaɓa ɗaya kafin nan zuwa ƙarfe goma sha biyun daren yau. Ko dai ki bi hanyar da ko wacce yarinya take bi ko kuma ki haɗa komatsanki ki setawa kanki hanya". Gabaɗaya na ji jikina ya yi sany tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, na kasa cewa komai na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin faɗin"Hajiya kafin wa'adin lokacin da kika ɗauka mini in sha Allah zan zo miki da abin da na yanke cikin zaɓin da kika ba ni". "Da kuwa kin yi wa kanki adalci yarinya. Yadda kike da suran nan ai za ki ci abinci sosai a harkan nan". "Amatullah ki nutsu ki yanke shawarar da za ta fishshe ki kar ki yi wa kanki baƙin ciki. Ki na da sura da dirin da ko wani ɗa na miji in ya ganki sai kin tafi da hankalinsa. Ke ɗin matar manya ce kalar shiga gaban mota irin matan da suke ba za taro su tashi kan kowa". Galla masa harara na yi sa boda haushi da takaicin da kalamansa suka cusa mini na miƙe da nufin barin cikin ɗakin na ji ya furta"tabbas Allah ya yi halitta a nan wajen. Irin wannan zubin kamar kika zama surarki". Ban tanka masa ba na fice daga ɗakin na faɗa cikin ɗakinmu na zube akan tabarman kwanciyata, duk yadda zuciyata take suya da raɗaɗi idanuna sun daina zubar da hawaye sai sa'ilin na yarda wani tashin hankali ya fi ƙarfin a yi masa kuka sai da kukan zuciya wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi. Na yi shuru ina sauraran bugawan zuciyata da yake ɓat ɓat. Na koma sauƙe numfarfashi mai ɗumi ina lumshe idanun yayin da zantukan Hajiya Babba da na Aminu suka dawowa mini cikin kaina tiryan-tiryan. Tabbas rayuwa za ta yi mini matuƙar wahala har ma sai na gwammace wataƙila gwara mutuwa akan rayuwa, sai dai duk rintsin da na yi wa kaina alƙawarin cewar ba zan ƙara aikata wani aikin zunubi da zai sanya Ubangiji ya yi fushi da ni ina cikin sani da hankalina ba. Sai dai in ban bi hanyar da suke so ba ina zan sama kuɗin da zan nema wa kaina matsuguni?.Na cire leɓena ina ci gaba da tunanin zucin da nake yi yayin da na sama salamar zubda da hawaye a daidai lokacin. "To fa! Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. Ke kuma kukan me ye kike yi? Ai tun da kika sako ƙafarki kika shigo duniyar bariki duk daga lokacin za ki sabar wa zuciyarki dakiya, juriya da kuma shan duk irin yanayin da kika tsinci kanki. In ki ka ce kuka za ki dinga yi ina mai tabbatar miki da cewar sai an wayi gari watarana kin rasa hawayen da za ki tsiyayar, ni na fita sai kuma Allah ya yi dawowata zan je na kafa na tsare a bakin manyan ma'aikatu har sai na samu nawa rabon". Na ɗaga kai ina bin ta da kallo ta shirya tsaf cikin shirgar ƙananan kayan da suka kama jikinta tamau kamar fatanta. Da wani uban gashin kantin da ta watsa wa kanta ta sha kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar tantance sarauniyar kyau. "Ki yi rayuwarki na tawa babu ruwan biri da gada. Zaman kanki kike yi haka ni ma shi nake yi". Na mayar mata da zancen muryata a dake. "To Allah ya kyauta". "Amin". Na amsa da shi a taƙaice da hakan ya ba ta lasisin fita ta tafi gararambana. Haka na ci gaba da zama a haka har na tashi na yi fita na yi alwala na dawo cikin ɗakin na yi sallan magrib, ban tashi daga inda na yi sallan ba har sai da na yi sallan isha'i. Na bi kayan jikina da kallo tun da na zo garin jafari ban sauya wasu kayan ba, balle hijabi da takalmin da wannan mai gadin ya taimaka mini da su. Jikina ya soma rawa ina jin wani zafi yana ratsa wa har cikin naman jikina. "Allah na tuba ka yafe mini sannan ka kawo mini ɗauki da mafita akan halin da nake ciki". Na furta a bayyane yayin da nake miƙe wa tsaye na fita daga cikin ɗakin na nufi ɗakin Hajiya Babba tana zaune a falon tana irga wasu tulin kuɗaɗen da suke gabanta, na durƙusa na yi mata sannu ta amsa mini ba tare da ta kalle ni ba. "Hajiya daman na zo na sanar da ke hukuncin da na yanke akan zaɓin da kika ba ni ne". "Ina jinki". Sai da na sauƙe wai gauron ajiyar zuciya kafin na furta"na amince zan bi hanyar da kuke so". [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________________ Page 5️⃣5️⃣ Tun da na so zancen ta kafe ni da ido har na kai aya, cike da mamaki ta furta"abin da kike faɗa ɗin nan ya kai har cikin zuciyarki kuwa? Sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike ji da gani cikakkiyar ƴar bariki ce mai lasisi babu inda ƙafafuna ɗin nan ba su taka ba a cikin duniyar bariki. Duk wani salon munafukarci, luggu da nurƙufanci na san shi tare da alamominsa. Nan cikin gidan nan kwanakin baya wata yarinya ta zo simi-simi da ita kamar ba za a sanya mata hannu a baki ta ciza ba, mun sha fama da ita kafin ta bi layi mutumin farko da ta fara mu'amala da shi babban mutum ne don duk faɗin garin nan babu inda zan shiga ba a san sunansa ko an san shi a fuska ba. Rimi-rimi ya aiko aka ɗauke ta zuwa otel yarinyar nan ta burma masa wuƙa a cikinsa ta ji ajalinsa har lahira ta kwashe masa maƙudan kudaɗe ta tsallake boda, ta bar ni a cikin masifa da ha'ula'i aka yi mini rufgudu na yi trending a cikin garin nan. Da ƙyar aka same ta a can yankin sudan aka cafke ta kafin na sama salama, ke ma na lura wannan simi-simin da kike yi tsabar tsagwaron munafurci da iya ƙulla luggu". Ilahirin jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin cikin rauni na furta"Hajiya har cikin raina na yanke wannan hukuncin". Ta ɗan yi jim tana bi na da kallo kafin can cikin wani irin dakakkiyar murya ta ce da ni"ke yarinya sa idonki a cikin nawa ni ɗin nan da kike gani wargi ce daidai ƙugun ko wacce ƴar bariki da take jin karanta ya kai tsaiko". A hankali na cira kai na sanya idanuna a cikin nata sai dai na kasa jurar jimirin haɗa ido da ita babu shiri na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa ina sauraran zancen da ta ɗaura da shi. "Ina fatan abin da kika furta su kasance gaskiya don ina mai tabbatar miki da cewar duk abin da kika jangalo a kanki zai ƙare don duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka. Akwai sharruɗa da nake gindayawa duk wata yarinyar da take cikin gidan nan, duk wani namijin da kuka yi mu'amala da shi ina da kaso ɗaya cikin uku na abin da ya sallame ki ina fatan ki na saurarana?". Na gyaɗa mata kaina alamar e da hakan ya ba ta damar cewa"ki na da mutane a ƙasa ko kuma mu nema miki duk yadda kike da suran nan babu wanda zai gan ki ya ji ba ki burge shi ba balle har ya kau da kai". "Babu wasu a ƙasa". Na amsa mata muryata can ƙasa kamar an dannen kwaɓo a cikin ruwan zafi. "To ku shirya da dare bayan misalin ƙarfe takwas za ki yi baƙo". Kaina kawai na jin wani irin abu yana tasowa tun daga ɗan yatsana yana bin dukkan sassan jikina, na tashi cikin rashin kuzari da ƙwarin jiki zan fita na ji an ƙira sunana da hakan ya tilasta mini tsaya wa ba tare da na waigo ba. "Ke kuma La'aniyatu me ye ya fito da ke daga cikin ɗakin? Ke da kika ce ba ki da lafiya kanki yana yi miki ciwo". "Umma ni fa na warke. Sai ki yi ta garƙame ni a ɗaki kamar wata ƙaramar yarinya kuma na daɗe da gane manufarki akan hakan. Harkar da kike jawo ƴaƴan wasu cikinta ne ni ba kya so na bi wannan layin, ai an ce duk abin da ka shuka Umma shi za ka girba". Tsam Hajiya Babba ta miƙe"ke La'aniyatu ki san irin maganan da za ki na furta domin ni ɗin uwarki ce. Kuma duk lalacewa ta ba za ki sauya ni a matsayin mahaifiyarki ba kamar yadda duk lalacewar tuwo ba a sauya masa suna". "Ni ban ce zan sauya ki a matsayinki ba amma ina gaya miki abin da yake zahiri ne wanda ko ba ji ma ko ba daɗe ko kuma raye ko ba ma ciki rayayyu, babu makawa sai hakan ya faru....". Ba ta ƙarishe zancen ba Hajiya Babba ta zuga mata mari mai matuƙar sauri har sai da hancin cikina ya kaɗa. "Tsinanniya wacce ba ta san haƙƙin uwa ba, in sha Allahu ke kam ba za ki gama da wannan duniyar salin ƙalin ba. Da ba a cikin ɗakin nan na haife ki ba sai na ce sauya min ke aka yi a asibiti, duk ƙoƙarin da nake yi wajen inganta rayuwarki da ganin ba ki nema komai kin rasa ba La'aniyatu ba kya gani?" Ta ƙarƙare zancen cikin sanyin amon. Kasa motsawa na yi daga inda nake tsaye munanan kalaman Hajiya Babba suka jirkita mini tunanina, na tuna da Ummanta a lokacin da take jifa na da makamantan irin waɗannan kalaman wanda ina da yaƙinin su suka yi tasiri a kaina har na tsinci kai a cikin gidan karuwai da ƴan daudu. Ji na yi an ja hannun aka fizgo ni muka fice daga cikin ɗakin ba mu tsaya a ko'ina ba sai cikin ɗakina. Na fizge hannuna daga cikin riƙon da ta yi mini. "La'aniyatu me ye haka kike yi?". A zafafe ta mayar min da tambaya"me ye kika ga na yi?". Na watsa mata wani kallo don ban taɓa raina wayo, hankali da hangen nisanta ba irin na yau. "Hajiya fa mahaifiyarki ce ko me ye take aikatawa hakan ba shi zai ba ki damar da za ki na faɗa mata duk wani abun da ya zo bakinki, ba tare da kin tauna kalaman ba". "Ni yanzu ba wannan ba shin da gaske kike za ki bi hanyar da suke so?". Na harare ta da wutsiyar idanuna kafin na ce"ƙwarai kuwa". Ina dasa aya na wuce zan zauna ta jayo gefen hijabina. "Me yasa za ki aminci bayan kin yi wa kanki alƙawarin ba za ki aikata ɓarna ba? Ke ma kenan za ki zama ba ki da bambamci da ragowar matan gidan nan? Kin san yadda suke yin wulaƙantaccen ƙarshe kuwa? Wasun su su kamo da jinyar da za ta yi ajalinsu, wasu shaye-shaye ya haukatar da su yayin da wasu kuma tsufa yake cim musu duk waɗanda suke mu'amala da shi su yi ɓatan gado su gudu ko sama ko ƙasa. Idan ba ki yi sa'a ba kuma har da kuzurin cuta za ta jajiɓowa kansu wasu kuma su haifa shegu waɗanda ba su da uba, haka rayuwarsu da ta yaran za ta faɗa garari su zama abin wulaƙantawa da tozarwa a tsakanin al'umma". Na cire hannunta daga jikina na je na yi zamana ina cire hijabin da yake kaina"duk na san da hakan, me ye zan zauna na yi bayan ga abin da ya kawo ni nan ban yi shi ba. La'aniyatu duk matan cikin gidan nan ƙaryan bariki suke yi yanzu ne zan nuna musu ainihin abin da kalmar ta ƙunsa, domin zan warware musu zare da abawa. Ke dai kawai ki zuba mini ido ki kuma bi ni da fatan alkhairi". "Mata da yawa da haka suke fara har su zarje su zama jan wuya. Amatullah ina jiye miki tsoron abin da kike shirin aikatawa zai haifar miki a nan gaba, kin ga muranen nan ba su da tausayi balle imami da zarar sun fara nannaɗa garɗin mace to ba sa barin ta haka banza wallahi har malamai da bokaye suna bi, don wasu ba a cin kuɗinsu a zauna lafiya". Taƙaitaccen murmushi na yi kafin na ce da ita"ni kuwa zan ci kuɗin kuma lafiya sumul". "Amatullah". Ta ƙira sunana cikin wani irin yanayi da ya fi kama da na zallan mamakin da ba sirka shi da komai. Na ɗage mata idona guda alamar lafiya? Ta zo ta zauna a kusa da ni tare da riƙo hannuna za ta yi magana na dakatar da ita. "Ki zuba mini ido kawai na ce da ke, na fahimci wani abu guda cewar in dan har ba ka tashi ka nema wa kanka ƴanci ba haka za ka dawwama a cikin ƙasƙanci". Da alama mamaki da al'ajabi ne ya hana ta cewa komai illa kallon da take bi na da shi na sakar mata da murmushi ina miƙe wa tsaye ina ƙoƙarin mayar da hijabina na ce"bari ki ga na yi salla don ina da babban baƙo. Har ya zo ban gama kimtsa wa". Ba ta ce da ni uffan ba har na yi sallan na iddar na shafa dogon addu'ar da na yi, na waigo ina kallonta ta yi jigum da ita kamar majinyaciya. "Ba ki tambaye ni gidan aikina ba?". Ta sauƙe numfashi mai ƙarfi da har sai da na jiyo sautin sa a cikin kunnuwana kafin ta furta"ina kuwa zan iya tambayanki bayan kin gama shayar da ni giyan mamaki. Ba ni labari me ya faru don na ga kin ma dawo da wuri ai". Na fesar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na juye mata duk abin da ya faru. "To yanzu wani shawara kika yanke barin aikin ke nan za ki yi, ko kuma ya ya za ki yi?". "Da farko na yi tunanin na haƙura da aikin amma tun daga lokacin da Baba Mai gari ya sanar da ni wace ce Altine, da kuma salon nau'in munafurcinta sai na ji na ƙara son aikin a cikin raina, zan shiga cikin Hajiya sosai har sai na fahimtar da ita wace ce Altine na kuma fito da ainihin halinta kowa ya gani. To daga wannan ranar zan bar aikin". "Tabbas kin yi tunani mai kyau". Kafin na ba ta amsa wata budurwa ta shigo cikin ɗakin ta jefo miji baƙin ledar dake hannunta. "Ga shi in ji Hajiya kayan sakawa ne ta ce ki saka su. Don baƙonki yana hanya". Na tsaki wani murmushin da ba shi da haɗi da nishaɗi kafin na ce"to ina godiya saƙo ya iso. Tabbas Hajiya tana ƙoƙarin sangarta ni a cikin gidan nan, har kaya take saya mini". Na ƙare zancen ina bin budurwar da kallo da take ta cika ta na batsewa da tun a tashin farko na fahimci a cikin biyu dole akwai ɗaya. Ko dai baƙon da zai zo musamman domin ni take baƙin ciki da zuwansa ko kuma kayan da Hajiya ta ba ni ne ya baƙanta mata rai. Tsaki ta tsirtar mai dogon zango tare da faɗin"har ina abin yake wai maye ya ci jajiri? Ke kar kin sa ki shiga sahun matan da Hajiya take ji da su a cikin gidan nan? Ko da yake ai an ce na kwance bai ga gari ba". Ta na gama zancen ta juya ta fice na taka ta da dariya da ina da tabbacin hakan ya ƙara ƙular da ita matuƙa. Na ɗaga muryata na ce"a sauƙa lafiya". "Ke Amatullah wai ke ce kuwa?". Furucin La'aniyatu ya sa ni waigo wa ina kallonta. "Me ye kika gani?" "Na ga kin tsiri wasu ɗabi'un da ba na ki ba kin lafawa kanki". "Yanayi ne yake sauya wasu abubuwan La'aniyatu. Wani lokacin mutum ya kan sauya na tare da shi kansa ya fahimci hakan ba". A raunane na yi zancen ina jin ruwan hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata. "Bari na bar ki ki shirya". Tana zancen tana miƙe wa ta bar cikin ɗakin a ƙalla na ɓata mintuna talatin zaune a wajen ban motsa ba, kafin na zazzage ledar ina kallon kayan ciki. Doguwar riga ce irin da aka watsa mata duwatsu masu ƙyalla da haske sai kuma mayafinta da ba shi da girma wanda bai zarce girman kallabin da yake kaina ba. Sai kuma turare su kenan a cikin ledar na ɗaga rigar ina kallo tare da sauƙe tagwayen ajiyan numfashi. Na saka rigar na ga ya kama mini jikina sosai har da ƙyar nake numfashi, duk wata surar jikina ta bayyana musamman ƙirjina. Na ɗaura kyallen a kaina na saka hijabina don na ba zan iya fita haka ba, feshi biyu na yi a turaren na ajiye don ya yi ƙarfi da yawa har yana hawa kai. Ɗakin Hajiya Babba na nufa na shaida mata na shirya ta bi ni da wani irin kallo har na zauna. "Wannan hijabin fa?". "Hajiya ba zan iya fita da wannan kayan ba ne, shi yasa na sanya hijabin". Za ta yi magana wayarta ta soma ruri ta ɗaga na ji ta tana ba da umarnin shigowa. Tana ajiye wayar wani mutum ya shigo cikin falon ya sha manyan kaya shadda fara tas mai ɗaukar hankali ya murza hula zanna bukar ga ƙamshin da yake tashi a jikinsa tamkar an yi ɓarin durum ɗin turare a jikinsa. Ya zauna a kujerar da yake kusa da wanda Hajiya take zaune a kansa suka gaisha kafin ya ce"Hajiya Allah ya sa wannan ce wacce aka ajiye min ɗin. Don tun da na shigo na ji ta sama matsuguni a cikin raina". Ta saki shewa"me kake ci na baka na zuba Alhaji Manga? Ai dai duk saurin ungozama za ta jira a haihu". "Fara ba ni amsar tambayata tukunnan ita ce ko ba ita ba ce?". "Ita ce sai aka yi ya ya?". Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe su yana cewa"ba ki taɓa zaɓo min wacce ta dace kamar wannan ba dole na ninka abin da na saba biya sau biyar. Sai dai kuma yanzu akwai meeting ɗin da za mu yi da abokan sana'ata a cikin daren nan. Don haka gobe zan dawo sai na ɗauke ta hakan ya yi?". "Ai duk yadda ka ce haka za a yi ranka ya daɗe, ina godiya". "Da kin gaya min irin wannan surar zan zo na tarar ai da na aika wani ya wakilce ni a wajen meeting ɗin. Amma yanzu ma dai bai ɓaci ba zan dawo ko na aiko a zo a ɗauke ta, yarinya ya ya sunanki?". Muryata a shaƙe na ce"sunana Amatullah". "Amatullah Amatullahi baiwar Allah. Ni kuma sunana Alhaji Manga, yanzu za mu je da ke waje ki karɓo saƙo ki kawo wa Hajiya". Na gyaɗa masa kaina ina satan kallon Hajiya na ga ta ɗage mini gira alamar na bi shi. Suka yi sallama ya fita na bi shi a baya, tun da muka fito daga ɗakin ƴan matan gidan suke ta kai masa gaisuwa yana ɗaga musu hannu. Muka fita waje inda ya ajiye motarsa ya buɗe gidan baya ya ɗauko wasu baƙaƙen ledodi guda biyu ya miƙo mini. "Wannan ta ki ce ɗayar kuma na Hajiya ne sai ki kai mata. Kafin na zo goben ko ban zo ba ma zan yi aike". "Mun gode". Na furta a gajarce. "Ki saki jikinki da yarinya kin ji ko?". Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi damar shiga cikin motar ya ja ya tafi. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina bin ledar da ya ba shi da kallo. "Har kin sallame shi kenan?". Na yi figigi na ɗago kaina don gani mamallakin muryar, sai da na firgita don ban yi tsammanin ganinsa a nan kuma a irin wannan lokacin ba. "Saifullah kuma?". Na furta a cikin zuciyata ina jin ƙirjina yana tsananta bugu ba tare da na san dalili ba [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 5️⃣6️⃣ Duk yadda na so na furzar da zallan mamakin da ya ganin sa ya ƙunsa mini bakina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan a aikatace, da ɗago idona ina kallonsa na ga ya watsa mini wani mummunan kallo da ban san sa'ilin da na rusunar da idanuna ƙasa ba. Sa boda cika ido da kwarjinin da yake da shi. "Zan jira ki a wajen motata ba zan iya tsayiwa a nan wajen ba". Yana gama maganar ya bar wajen ya nufi inda ya ajiye motar da yake can farkon layin na bi shi a baya zaƙwai-zaƙwai har muka isa ya jingina bayansa jikin motar tare da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa idanunsa a kaina ya furta"Anty ce ta ce a zo a duba ko lafiya kika tafi ba tare da kin yi mata sallama ba. Sai dai zuwan da na yi da kuma abin da idanuna suka gane min ya tabbatar min da cewar lafiya kike tun da har za iya fitowa ki gana da saurayi cikin wannan daren har da guzurin saƙo niƙi-niƙi a leda". Jikina ya yi sanyi ƙalau wasu hawaye suka kuma ciko mini idanuna sauran ƙiris su zubo na kai hannu na tare su. "Lafiya ƙalau kawai ba na jin daɗin jikina ne shi yasa na dawo. Amma ina sha Allah gobe sammako zan yi na zo.....". Tun kafin na kammala ƙarshen zancen ya tari numfashina. "Ba ma buƙatarki don haka ki yi zamanki. Idan ma ya zama dole to za a nema wata". "Ba kai ka ɗauke ni aiki ba ranka ya daɗe don haka ba ka da hurumin dakatar da ni, Hajiya ce kawai take da wannan ikon". Tabbas na hango mamakin zancena kwance a cikin idanunsa ya sauƙe numfashi da har sai da na ji sautin fitarsa. "Repeat yourself please". Duk da na fahimci abun da ya furta amma sai na sauya akalar zancen"a gaishe ta kuma a isar mata da saƙona". Ina gama furta haka na juya zan tafi na ji wata murya ta sauƙa a ƙofofin kunnuwana, muryar da ba zan taɓa manta tasirinta a cikin rayuwata ba. Muryar da ko ina gangaran mutuwa in na ji ta haƙiƙa zan gane amonta. Muryar da ta sama matsuguni ta zauna a cikin kwanyata ba tare da biyan tara ko haraji ba. Cak na tsaya jikina yana wani irin rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki haƙwarana suka datse harshena wanda ina da tabbacin har sai da ya fitar da jini. "Saif wai me ye yake faruwa ne? Ina ne nan wajen kuma?". "Ba komai Taukif shiga motar mu tafi kawai". "Wannan yarinyarta fa me ye haɗinka da ita? Na dai san ba ka zuwa ire-iren wajajen nan. Ke zo nan". Take ƙirjina ya soma dakan lugudan-lugudan tara-tara sau goma sha tara, zuffa ya soma tsantsafo mini sa'ilin da na ji takun tafiya ana kusanto inda nake tsaye har ƙamshin turaren jikinsa ya riga sa isowa gare ni. "Ke yarinya me ye kike yi a nan wajen?". "Ba-ba-ba-ba-ba babu". Na amsa masa a gajarce ina ɗaukar hanyar barin wajen cikin matuƙar sauti kamar zan tashi sama, har ƙafafuna suna haɗewa cikin doguwar rigan da ta gama jikina tsam tamkar tare aka halicce mu. Kaina tsaye na wuce ɗakina na zubu akan tabarma ko kukan na kasa yi illa kawai soyar da zuciyata take yi mini. Ƙirjina yana yi mini wani irin zafi tamkar ana watsa wa mini garwashin wuta ta yadda nake jin zafin yana ratsa wa har ta cikin nama da jijiyoyin jikina. Kan ka ce kabo gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi har wani kakkarwa nake yi. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Shi kaɗai na yi nasarar furta wa kafin zuciyata ta antaya cikin cakwakiyar tunani. Tabbas ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan muryar Muhammad Taukif ne. Mutumin da ba zan iya mance da ranar da na far tozali da shi akan hanyata ta zuwa islamiyya da kuma kalamansa ba. Shi ne mutum na farko da na taɓa haɗuwa da shi a cikin rayuwata da zuciyata ta sama nutsuwa da kalamansa tun kafin na san halayensa da ɗabi'un balle har na kai ga sanin haƙiƙanin wane ne shi. In dai ta tabbata shi ne baƙon da na ji Saif yana batun zuwansa to ina cikin lukutin yanayi. Na yarce zuffan da ya kwanta a saman goshina kana na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba domin kai mata saƙon da aka bayar da sunanta. Na zauna a ƙasa ina yi mata sannu da hutawa ta amsa tare da zarce wa da faɗin"to ya ya kika gan shi ina fatan ya yi miki?". Na kawar da zancen ta hanyar faɗin"ga wannan ya ce a ba ki". Na miƙa ledodin dukka biyu ta amsa tana faɗaɗa annurin fuskarta bakinta har kunne. "Dukka wannan nawa? Amma mun yi waya da shi kafin shigowar ki ya ce ɗayan saƙon na ki ne. Don haka ga shi ke ma sai ki je ki fantama ki more wa ranki, don na san waɗanda zai ba ki gobe sai sun ci uban waɗannan". Na girgiza kaina"Hajiya ba zan ci ko naira ɗaya daga cikin kuɗinsa ba. Don bai kwanta mini a raina ba, Hajiya kamar yadda kuka sa na yi abin da kuke so ni ma ina da nawa sharaɗin da dokoki. Ba zan fara mu'amala da kowa ba sai wani mutum guda". "Wane ne wannan mutumin?". Na ɗan yi jim kafin can na ce"Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe". Ta dafe ƙirjinta tare da waro idanunta waje"Sheikh Dawood dai da na sani mai tafsirin Alkur'ani?". Na gyaɗa mata kaina alamar e. Ta kallo ni da wutsiyar idonta tana faɗin"ke yarinyar nan watau bayan taurin kai da kafiyar tsiya tamkar kafiran farko har da hauka ma akwai a cikin kanki. Yo in ba hauka ba ta yaya kike tunanin za a iya jawo hankalin irin wannan mutumin da addini da tsoron Allah ya ratsa jini da jijiyarsa". "Ba zai yi wahalar shiga hannu ba Hajiya. Ni ko hanya ayi mini na gan shi ni kuma na yi miki alƙawarin sai na jawo hankalinsa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci" Ta yi mini wani irin kallo irin kallon da mai hankali yake yi wa zautacce ta ja tsaki ta tofar tana mayar da hankalinta kan abin da take yi ta furta"bari Aminu ya damu mu yi magana tabbas akwai wani abu da yake yawo a cikin wannan kan nakin". Na cira kai na kalle cike da ƙwarin gwiwa na ce"babu komai a cikin kaina Hajiya, ki ba dama ni kuma na yi miki alƙawarin zan jawo shi har ya shigo hannu. Idan na gaza aikata abin da na furta na yarda ki haɗa mini kayana ki ɗaura mini a kaina ki kora ni daga cikin gidan nan sannan ki haɗa mini da ko wani irin wulaƙancin da kika yi niyya". "Kin san me ye kika faɗa kuwa?". "Ƙwarai kuwa Hajiya". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"shi kenan na ba ki dama amma idan kika kasa jan hankalinsa tabbas zan yaga miki rigar rashin mutumcin a bainar nasi, zan wulaƙanki irin wulaƙancin da ko kare ba zai ci ba. Zan tozarta ki irin tozarcin da za ki ƙwammace ina ma uwarki ba ta haifo ki kin zo cikin duniyar na ba. Zan muzanta ki irin muzancin da za ki zaɓi mutuwarki sau dubu akan rayuwarki. Zan jefa rayuwarki cikin ƙunci da takura da har sai kin daina jin daɗin rayuwar duniya sai kin ji a cikin ranki wanda yake kwance a cikin kabari ma ya fi ki ƴanci da walwala". Ba tare da wani tunani ko dogon nazari ba na amsa da faɗin"ma yarda da duk wasu sharruɗan da za ki gindaya mini. In sha Allah sai na jawo hankalinsa". "Kuma babu wanda zai taimaka miki ke kaɗai za ki yi wannan yaƙin. In ma ki ci in ma ki sha ƙasa". Na haɗiye wani miyau mai kauri daga maƙoshina da ya bushe tamkar ƙasar sahara a lokacin zafi. "Na yarda da dukkan sharruɗanki Hajiya". "Tashi ki je na sallame ki" Ban ce da ita komai ba na tashi na bar cikin ɗakin na koma ɗakinmu, na zauna na buga wani uban tagumi ina jin gabaɗaya duniyar ta yi mini zafi na ja numfashi na furzar ya fi sau shurin masaƙi. Hawayen idanuna sun kafe ƙaf tamkar rijiyar da ruwan cikin ta ya kafe na tsawon shekaru masu yawan gaske, sai yanzu ma yarda tabbas wani tashin hankalin ya wuce a yi masa hawaye sai dai kukan zuci wanda ya fi ciwo gami da raɗaɗi. A firgice Anty Sawwama ta farka daga baccin da ya cikakken ɓarawo har ya yi nasarar sace ta duk da girman tashin hankali da damuwar da yake cikin ƙalbinta da ta gama raunana. A tare Yaya Alhassan da Umar suka shigo cikin ɗakin, Umar ya kunna wutan lantarki take haske ya gauraye ko'ina. "Umma lafiya kuwa me ye yake faruwa?". Kasa magana ta yi illa zuffan da ta ci gaba da haɗa wa tamkar wacce aka sheƙa wa ruwa ya yi mata jilif. "Umar samu ruwa yanzu-yanzu". Da sauri Umar ya fita ya je ya ɗebo ruwan ya dawo ya miƙa wa Yaya Alhassan ya karɓa ya yi tufin wasu addu'o'i a cikin ya ba ta ta sha sannan ya shafa mata ragowar a fuskarta, take ta soma sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani. Umar ya riƙo hannunta ya sanya cikin nasa yana murza wa a hankali. "Umma lafiya kike? Ki na jin abin da muke faɗa?". Kanta ta gyaɗa alamar e tana zarce wa da faɗin"lafiya ƙalau wani mafarki kawai na yi da ya tsora ni ainun". "Wani irin mafarki ne haka Umma?". "Umar mafarkin nan dai da na saba yi a duk sa'ilin da na kwantar da haƙarƙarina da sunan bacci". Cike da damuwa Yaya Alhassan ya ce"mafarki kike yi da Kawu Manniru ya zo yana tambayarki amanar Amatullah da ya ba ki ko?". Cikin sanyin jiki ta gyaɗa kanta"ƙwarai kuwa har ta kai ta kawo ba na ƙaunar na kwanta bacci ko da kuwa na minti ɗaya ne. Ban san ina zan je da girman alƙawarin da Manniru ya bar min ba, Amatullah ina kika shiga ne a cikin duniyar?". "Umma don Allah ki rufa mana asiri ki cire wannan damuwar daga cikin ranki kar wani jinyar ya same ki a dalilin hakan. In Sha Allah Amatullah za ta dawo gare mu cikin aminci da yardan Allah, ina ji a jikina duk inda take tana hannu mai kyau kuma ba za ta taɓa aikata abin da Allah zai yi fushi da ita ba, don duk cikinmu babu wanda bai yarda da tarbiyyan Amatullah ba. Ƙaddarar ta ce kawai ta zo a irin wannan sigar wanda babu yanda muka iya ba za mu iya guje mata ba balle mu sauya mata fasali. Har yau ba mu fasa neman ta ba ina da yaƙinin duk wani mai nema watarana zai dace Umma don haka ki kwantar da hankalinki komai zai zo ƙarshe". Numfashi mai zafi ya ja ta furzar daga bakinta kafin ta sama lasisin faɗin"hakan nake fata da buri Alhassan. Allah ya yi muku albarka ya jiɓanci lamuranku yadda kuke ƙoƙarin yi min biyayya ku ma Allah ya azurta ku da ƴaƴan da za su yi muku fiye da haka". Cike da jin daɗin furucinta suka amsa da amin, Yaya Alhassan ya sa Umar ya zuba mata ruwa a cikin buta ta je ta yi alwala kana su ma suka je duk suka yi alwalan, Yaya Alhassan ya ja su limanci suka gabatar da sallan raka'a biyu na nafila suka miƙa ƙoƙon baran su zuwa ga sarkin da ba shi da abokin tarayya, Sarkin da ba ya ce a roƙo zai amsa. Ba su bar cikin ɗakin ba har sai da bacci ya ɗauke ta suka kunna karatun alƙur'ani a waya suka ajiye a cikin ɗakin. Yaya Alhassan ya tisa ta a gaba yana kallon ta tamkar bai taɓa ganin ta ba. Umar ya dafo kafaɗarsa cike da kulawa yake faɗin"Yaya Alhassan ka kwantar da hankalinka komai zai wuce kamar bai taɓa faruwa ba. Watarana sai dai labari". "Umar idan na ce ba na cikin damuwa haƙiƙa ma yi ƙarya mai girma, tun ranar da Amatullah ta ɓace ban ƙara samun kwanciyar hankali ba, ban ƙasa kasancewa cikin daidaitacciyar nutsuwa ba. Kullum a cikin fargana nake da fatan Allah ya sa tana cikin hannu mai aminci". "In Sha Allah za ta dawo gare mu cikin aminci. Ina ji a jikina Amatullah ba za ta taɓa sauƙa daga kan turban da muka san sa ta ba". "Allah ya amsa". "Amin ya Allah yaya Alhassan". Kashe wutar ɗakin suka yi suka koma nasu ɗakin cikin jimami da tarin damuwar da yake danƙare a cikin zuciyoyinsu. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 5️⃣7️⃣ Haka kawai na wayi gari ina ji na cikin wani irin karsashi a jikina, wanda na danganta hakan da karatun alƙur'anin da na yi ta yi bayan na yi sallan asubahi. Na tisa haddan da yake kaina sosai har sai da na ji wani nutsuwa ya lulluɓe mini rai da ruhina. Sai da na ɗebo ruwa na yi wanka na mayar da kayan da yake jikina na duba ko'ina na rasa abin da zan tauna a cikin ɗakin, na gama cinye duk siyayyar da Hajiya Muhibbat ta yi mini kat. Numfashi na ja na fesar kafin na yi shirin tafiya wajen aikin zan fita na ji sautin da ya tirsasa mini tsayawa. "Madam fita za ki yi ne?". Na waigo na yi mata kallo guda tana kwance akan katifarta da ban ma san sa'ilin da ta dawo ba daren jiya sai wayen gari na yi na gan ta cikin ɗakin. "E ko na tsaya za ki aike ni ne?". "To ikon Allah wai na zaune ya faɗi. Abin ai bai kai haka ba, dama na ga muna zaune a ɗaki ɗaya ne akwai haƙƙin maƙwabta a kanmu ai ko?". Na bi ta da wani kallo don har yanzu ban manta zafafan kalaman da ta yaɓa mini ba ranar farko da ta zo cikin ɗakin. "Tambaya kike yi ko neman sani?". "Duk wanda kika ɗauka daga cikin biyun daidai ne". Ban amsa mata ba na ja tsaki na fice daga cikin ɗakin ina jin haushin abin da ta yi mini har yanzu a cikin raina. Ina fitowa na yi kiciɓus da zinariya tana ƙoƙarin shiga ɗakin na ƙirƙiri murmushin dole na aza a bisa fuskana. "Barka da safiya ranki ya daɗe". "Ai ke ce ranki ya daɗe, dama na zo na ƙara duba jikin nakin ne. Ban saman shigowa ba". "Ai na je na iske ki na waya sai kuma daga nan ban dawo ba. Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi....". Kafin na rufe bakina na ji ta rumgume ni tsam a jikinta kafin na yi aune na ji hannayenta a gadon bayana tana shafa wa har zuwa ƙunguna. Jikina na mutu murus na kasa cewa da ita komai kamar yadda na gaza hana ta yawo da hannunta da take yi a cikin jikina. "Bari na bar ki haka tun da na ga kamar fita za ki yi ko?". Zallar ruwan mamakin da ta shayar da ni ya hana ni amsa mata cikin kalmomin da bakin kan iya furta wa illa gyaɗa mata kaina da na yi. "To sai kin dawo idan kin dawo sai ki shigo mu yi hira". Na kuma gyaɗa mata kaina a karo na biyu ta sakar mini wani shu'umin murmushin yayin da take ɗaukar hanyar koma wa cikin ɗakinta. Na fita da kallo ƙirjina yana buga wa tamkar zai faso allon ƙirjina ya bayyano waje ya taka rawar disko, na daɗe tsaye a wajen kafin na ja sanƙararrun ƙafafuna da nake jin su tamkar ba za jikin gangar jikina na fice daga cikin gidan. Ina tafiya ina tunani har na isa ƙofar gidan ina jin wani masifaffen yunwa hancin cikina sai kuka suke yi da neman agaji, na ƙwanƙwasa gate ɗin Baba mai gadi ya fito ya buɗe mini na durƙusa har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini fuskarsa tamkar gonar auguda. "Kin iso ko?". Na gyaɗa masa kaina alamar e. "To madalla Allah ya taimaka ya yi jagora". "Amin ya Allah". Na amsa da shi yayin da nake shiga cikin gidan ina shiga na hango motoci guda uku a cikin parking space, ɗayan Kam ko a ina na ganta zan gane ta don motar Hajiya Muhibbat ce. Ɗayan kuma motar Saif ne ɗayar ce baƙuwa amma tabbas a gare ni ba baƙuwa ba ce don ba yau ne rana ta farko da na fara ganinta ba. Ƙirjina ya harba da ƙarfin Rabbussamawati da hakan ya tilasta mini runtse idanuna Ina karanton a'uziya a cikin raina. "Ƴarta lafiya kuma na ga kin tsaya a nan, ba ki shiga cikin gidan ba?". "Baba wannan motar baƙo aka yi a cikin gidan nan?". Ya washe bakinsa kafin ya amsa mini cikin faɗin"wannan motar baƙon Saifullahi ne, da ya zo da yammacin jiya. Yaron kirki ne matuƙa ga girmama manya gami da tsantsan tarbiyya daɗin daɗawa kuma ga nutsuwa da kawaici". "Tabbas ya cika mutumin kirki tun da har ya sama yabo daga bakin uba na gari kamar ka". Ya washe bakinsa tamkar wanda aka yi wa wani babban kyauta"duk inda ake neman yaron kirki wannan baƙon ya zarce duk tunanin mai tunani. Ni ɗin nan idan ya zo cikin gidan na irin girman da yake ba ni na daman ne, in ya shigo ya ganni ina wani aikin kuwa sai ya karɓa ya yi min babu ruwansa da matsayinsa, matakin karatunsa ko kuma azurkinsa". Na riƙe haɓata"dole na zo a ba ni labarin wannan baƙo". "Ai kuwa za ki sha labari, don duk suna makaranta a nan gidan yake hutunsa har sai sun koma". "In sha Allah zan zo na sha labari". Daga haka na bar wajen na ƙarisa shiga cikin gidan, na tsaya a ƙofar falo ina ta zabga sallama har baki uku ba a amsa ba sai a na huɗun Ayan ya buɗe ƙofar ya fito, na fafaɗaɗa fara'ar fuskarta kafin na ce da shi"ina kwana". Ya tsaya ya yi sakeke yana kallona kafin can ya ce"ki shigo Ummin tana ciki". Murmushi na sakar masa na riƙo hannunsa muka shiga cikin falon. Na tsuguna har ƙasa na gaishe da Hajiya Muhibbat da na iske zaune a falon tana danna wayarta, yayin da Aryan take zaune a kusa da ita yana wasa da motar da yake hannunsa. "Lafiya ƙalau kin tashi lafiya?". "Lafiya alhamdulillah ranki ya daɗe". "Lafiya jiya kika tafi babu sanarwa sai aikowa na yi a ƙira ki aka ce ba kya nan?". "Hajiya ba na jin daɗi ne shi yasa na tafi, amma tuba nake yi". "Ba damuwa Allah ya ƙara sauƙi. Ki shiga kicin ku ci gaba da aikin don yau mu na da baƙo na musamman a cikin gidan nan". Kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na yi hanyar kicin ɗin na tarar da Altine a tsaya ta juya wa ƙofa baya tana waya. Na yi gyaran murya da hakan ya ankarar da ita wanzuwa ta a cikin kicin ɗin, a firgice ta waigo tana datse ƙiran. "Ke kuma me ye kike yi a nan? Yaushe kika shigo?". Ruɗewan da ta yi lokaci guda shi ya fi komai ba ni mamaki, sai na ƙariso cikin kicin ɗin kafin na ce"yanzu na shigo na tarar ki na waya. Ina kwana mun tashi lafiya?". "Lafiya". Ta amsa mini a daƙile tamkar wacce aka yi wa dole, ba ta ƙara bi ta kaina ba ta ci gaba da abin da take yi. Dankalin turawa take soya wa da ƙwai gefe guda kuma tana haɗa dafa shayi da ya sha kayan yaji dangin su citta da kananfari ƙamshi ya buɗe ko'ina. Ina ta tsaye ba ta ce da ni ga abun da zan yi ba har sai da na ji ƙafafuna sun gaji sun yi sanyi ƙalau. Sai da na tabbatar da cewa ba ta tanka mini na half ƙafafuna na isa wajen da ake ajiye kayan abinci na ɗebo fulawa zan tankaɗe ta dakatar da ni"me ye haka kike ƙokarin aikata wa?". Ba tare da na kalle ta ba na amsa da faɗin"wainar fulawa zan soya". "Wainar fulawa kuma?". Ta maimaita cikin isa da taƙama kafin ta zarce da cewa"wani irin wainar fulawa kuma? Bayan ga abincin karin kumallo nan ina girka wa ko ba kya gani ne?". Ban ce da ita uffan ba hakan bai hana ta ci gaba da maganar ba tamkar mai amayar da wuta. "Babu wani wainar fulawan da za a yi a cikin gidan nan tun da ga abinci nan na girka. Duk wanda ba zai ci ba sai ya wuni da yunwa ai yunwa ba uwar kowa ba ce kuma ba a fushi da abinci ko ka yi ma kai ne a wahala". "Ai na ji Hajiya ta ce akwai babban baƙo a cikin gidan kuma ta ba da lasisin a girka duk abin da ya kamata don a faranta masa. Laifi ne don na girka wannan?". Na ƙare zancen da alamar tambaya, lamarin da ya fusata ta ainun ta yi watsi wani kallo tamkar za ta kai mini bugu tana gallo mini harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa. "Sai kuma aka ce da ke baƙo irin baƙin da kika saba ji da gani ne ko? To wannan baƙon babban mutum ne da ya fito daga gidan manya, ina mai tabbatar miki da cewar ko kallon wainar fulawan nan ba zai yi ba balle ya sa shi akan harshensa". "Sanin daga gidan da ya fito ne ya sa zan yi masa wainar fulawa, don ina da yaƙinin wannan dankali da shayin da kika yi abubuwa ne da kullum yake gani kuma yake cinsu. Amma ina da yaƙinin wannan wainar fulawan zai zama sabon abu a wajensa". Kafin na gama kammala zancen kawai na ga ta ɗaga hannu za ta zabga mini mari na yi hanzarin riƙe hannunta tare da jefa idanuna a cikin na ta. "Kar ki kuskura ki yi gangancin ɗaura hannunki a jikna da sunan mari. Don abin da zai bi yo bayan hakan daga ni har ke ba zai mana daɗi ba". Kafin ta ce wani abu Hajiya Muhibbat ta shigo cikin kicin ɗin ta iske mu a haka. "Me yake faruwa na gan ku kun tsaya cirko-cirko?". "Babu komai Hajiya, da inna fere dankalin nan ne na kuskure hannuna shi ne take so ta ɗauke min wajen". Altine ta kora mata bayanin da ta ƙirƙire shi a take a wajen, ban ce da ita komai hasalima ko hannun ta ban yi ba. "To Allah ya kiyaye gaba. Wannan fulawar fa?". Na yi caraf na amshe zancen kamar ji nake yi ta ce kule na ce cas. "Hajiya wainar fulawa ne zan soya wa baƙo?". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"watau a baƙo kawai ban da mu ƴan gidan ko Amatu?". Na murmusa kafin na ce" har da kowa da kowa ma ranki ya daɗe. Amma Anty Altine ta riƙa da ta shirya abin karin kumallo shi yasa na taƙaita wainar fulawan ga baƙon kawai". "Ai kuwa ni ma dai ina ga wainar fulawan nan zan ci, don dankalin nan gabaɗaya ya gama fita daga kaina zan dai sha shayin. Amma fa sai ki hanzarta don sun kusa fitowa kuma fita za su yi". Cike da jin daɗin kalamanta na ce"in sha Allah Hajiya ba zan ɓa ta lokaci ba". Murmushi kawai ta sakar mini ta juya ta bar cikin kicin ɗin, ko ido ban ɗaga na ga Altine ba balle na tanka mata sai dai ina jiyo sautin ƙwafan da ta dunga sake wa wani na bin bayan wani na tsawon mintuna. Har na yi ƙare suyar wainar fulawan ba ta ce da ni da komai ba. Na ɗauko hula na zuba a ciki, can na hango cabbage na ɗauko na yanka na wanke na zuba a gefen a wani plate na rufe shi. Na waiga na kalle ta. "Ranki ya daɗe na gama sai kuma me ye ya rage?". Ban yi mamaki ko na haɗu ba da na ga ta gallo mini wata uwar harara kafin ta ce"a tambayi kaza hanyar zuwa tafi?". "Tabbas kam ba za a tambaye ta tun da ba zuwa take yi ba" Daga haka ban ƙara ce mata komai na ɗauko tray na jere su a kai na fita ina jin tsakin da take dokawa yayin da nake ƙoƙarin ficewa daga cikin kicin ɗin. Ban iske kowa a falon ba sai ƙarar iskan AC da yake aiki a cikin falon na jere su akan dinning table, Ina tsaye a wajen Aryan da Ayan sun rugo a guje suka shigo cikin falon suka nufo inda nake tsaye. "Wai in ji Uncle Saif an gama abinci? Za su fita da abokinsa". Kafin na yi magana Hajiya ta sauƙo ta karɓe zancen"babu inda za a kai musu abinci idan ba za su zo nan su ci ba, sai dai su haƙura". Tana ƙare zancen ta ɗaga waya ta ƙira shi ina jin ta abin da take faɗi cikin tsare gida babu alamar wasa a tattare da ita. "Ku shigo an kammala abincin". Tana gama faɗin haka ta katse wayar ta ƙariso ta zauna, ban bar cikin falon ba ya shigo take na ji ƙirjina ya buga da ƙarfi ta gabana ya zo ya wuce na gaishe shi ya yi banza da ni wanda kuma ina da tabbacin ya ji gaisuwar da na yi masa sarai. "Hajiya Antynmu tun ɗazu fa abincin nan muke jira, idan ba za a ba mu ba ne sai a gaya mana mu san inda dare ya yi mana". Ya ƙare zancen cikin sigar zolaya yana ɗan sosa ƙeyarsa. "Ina shi baƙon nakan?" "Yana can sashina". "To sai ku fito ku zo mu ci abincin". "Hajiya Anty kin san Taufik fa da kunya ba zai taɓa iya nan gabanki ya sha ko da ruwa ne ba balle har ya saki jiki ya ci abinci". Ta harare shi"mace ne ƙarshen kunya kenan ai ko?". Ya marairaice murya"mu dai yanzu Anty ki yi haƙuri a ba mu abincin. Kin san fa an ce koro da yunwa ba shi da kyau kuma ba shi da daɗi". Dariya ta tuntsire da shi kafin ta waigo tana kallona da har yanzu ina tsaya a inda nake ban motsa ba. "Amatullahi ɗauki girkin kika jera ki kai musu. Ayan zai biyo ki da flask din tea ɗin". "To ranki ya daɗe". Na amsa da shi a taƙaice na ƙara jere su akan tray ɗin na fita na nufi sashinsa, ina jin ƙirjina yana tsananta bugu da ƙarfi da ƙarfi. Sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na sanya ƙafata a cikin falon na yi hamdala sa boda iske falon da na yi babu kowa a cikinsa sai sautin karatun Alqur'anin da aka kunna yana tashi. Na ajiye tray ɗin akan table na juya da sauri xan fita na ji an tsayar da ni ta hanyar faɗin"baiwar Allah tsaya mana". Take jikina ya soma rawa mussamman da na ji sautin takunsa yana ƙara nufo inda nake tsaye, ban yi ƙasa a gwiwa ba na yi saurin ci gaba da tafiya sai dai ban yi taku huɗu masu kyau ba. Aka buɗo ƙofar falon Saif da su Ayan suka shigo yana riƙe da flask ɗin tea, Ayan yana riƙe da sacet ɗin madara da milo yayin da Aryan ya riƙo kofuna. Sanƙarewa na yi a inda nake tsaye, tabbas wannan shi ne gaba kura baya ƙura, na rasa inda zan yi gaba ko gaba. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 5️⃣8️⃣ Ina ɗago kai idanuna suka sauƙa a cikin na Saif kallon da ya watsa mini ya sanya jikina yin la'asar tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi na rusunar da idanuna ƙasa yayin da Aryan da Ayan suka ƙarisa shigowa cikin falon suka je suka ajiye abin da yake hannunsa akan teburin. "Za ki iya tafiya tun da kin gama abin da ya kawo ki ko". Ya yi zancen cikin tsare gida fuskarsa babu alamar wasa balle ya ɗauki wargi. "To ranka ya daɗe". Na yi zancen ina ɗaukar hanyar fita daga cikin falon cikin matuƙar sauti tamkar zan tashi sama, har na kai ƙofar fita na ji an dakatar da ni. "Wace ce wannan ɗin Saif? Ban san ta ba tun da nake zuwa cikin gidan nan". "Baƙuwa ce". Ya ba shi amsa a taƙaice da hakan ya ba n damar ficewa da sauri ban sarara ba har sai da na zo ƙofan falon sashin Hajiya Muhibbat na tsaya ina mayar da numfashi tare da daidaita nutsuwata kana na shiga ciki, tana zaune tana shan shayi na iske ta jifa-jifa tana latsa wayarta, na yi mata sannu kana na wuce ɗakin Altine bakina ɗauke da sallamar da ban sama amsa daga gare ta ba illa kallon banzan da ta bi ni da shi har na isa na zauna a bakin katifar. "Ga can abinci a kula ki ɗauka". Kaina kawai na gyaɗa mata na jawo hular da ta yi mini nuni da shi. Ina buɗe wa na ci karo da farar shinkafa da ta gama shan iska ta bushe ƙararau ga wani ɗan yajin da aka yafa a gefen tamkar wanda aka roƙo daga maƙota. "Abincin waye wannan ɗin? Ko a karnuka za a ba wa?". "Tun da kike zuwa gidan nan kin taɓa ganin kare ne?". "To na sani abu a duhu. Don wannan abincin kam ai ɗan Adam dai mai rai da numfashi ba zai iya cin sa ya kwana lafiya ba sai dai dabbobin. Hasalima ai na ga ba wannan nau'in abincin aka girka ba". Tun kafin na rufe bakina take bi na da wani irin kallo tamkar za ta rufe ni da duka. Sai da ta tashi ta zauna daga kishingiɗewar da ta yi kafin ta soma amayar da balbalin wutar zancen da yake cikinta. "Ke har kin isa ki tisa ni a gaba ki na tuhumata akan abin da kika gani a cikin ƙwaryan tuwonki?. Ina da karfin iko a cikin gidan nan fiye da duk yadda kike tunani da hashashe, idan har kika bari na juyo kanki na saka miki ƙahon zuƙa billahillazi hatta numfashi mai kyau ma sai a gagare yi a cikin gidan balle kuma wasu abubuwan". Na lanƙwasar da murya kafin na furta"tuba nake yi ranki ya daɗe. Ai ni ban isa na sa kafar wando ɗaya dake ba wane ni ubana dillalin Kashi. A yi mini aikin gafara". Wani tsaki mai dogon zango ta saka tana jifa na wani irin mungun kallo kwatankwacin irin kallon da mai dukiya yake yi wa ƙasƙantacce. Na sakar mata da wani lausassan murmushin da har sai da haƙwarana suka bayyana na jawo kulan abincin gabana na sa hannu na soma ci. Duk da yanda shinkafan yake sukan wuyana ina jin suna tsayiwa a maƙoƙarona hakan bai hana ci ci gaba da tura abincin ba. Na fahimci matuƙar ina son na cimma buri da muradina akan ta sai na kwantar da kai na yi mata biyyaya domin sunkuyawa gwada bai taɓa zama gajiya wa ba. Sai da na cinye abincin tas na ɗauki kular na fito waje na kai ta kicin inda a nan na sama ruwa na kwankwaɗa na sama sauƙin tsayuwar ƙayan kifin da shinkafar ta yi mini a hanyar wuya. Na ji wani abu ya taso mini cikina ya murɗa tae na ji amai ya taso mini da hanzari na fita ta ƙofar baya na dinga kwarara amai tamkar zan amayar da dukkan kayan cikina. Sai da na gama na tashi na je na kwance baki da fuskana na zo na gyara wajen da na yi amai ɗin, gabaɗaya jikina babu ƙwari haka na baro cikin kicin ɗin na dawo ɗakin Altine ban iske ta a cikin ɗakin ba hakan ya ba ni daman kwanciya akan katifar ina mayar da numfashi jin jikina nake yi gabaɗaya ya mutu tamkar wacce aka yi wa ɗan banzan duka. Muryar Taufik da na ji ɗazu a sashin Saif ya soma dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan na lumshe idanuna da hakan ya ba wa hawaye da suka ciko mini koramar idanuna damar kwaranya a bisa fuskana. Wata zuciyar tana raya mini ina ma da na tsaya na laɓe na ga ko da fuskarsa ce, duk da muryarsa ma kaɗai ta tabbatar mini da cewa shi ɗin ne dai, na ja dogon numfashi na fesar kafin na gyara kwanciyata na kwanta akan gadon bayana ina kallon rufin ɗakin da ya zama mini shamaki tsakanina da sararin samaniya. Na yi nisa a cikin tunanin nake yi da har ban san lokacin da Altine ta shigo cikin ɗakin ba balle tsayiwar da ta yi a kaina kamar wacce ta haɗiye taɓarya babu alamar ranƙwafawa a tattare da ita. "Kwanciyar me ye kike yi a nan ɗin?". Na cira kai ina dubanta kafin na ce"jikina ne gabaɗaya yake yi mini ciwo shi ne na zo na ɗan kwanta ko zan ji dama-dama". "Ai kuwa kwanciya ba ta kama ki ba ke da kika fito neman kuɗi. Ki tashi ki je Hajiya tana ƙiranki". Ban ce da ita komai ba na tashi ina cije leɓe na fita na je ƙiran Hajiyar na iske ta tare da wasu mutane uku biyu maza ɗaya mace gefe guda ga tulin turamen atamfa an jibge su da lesuka, suna ta buga lissafi gami da rubuce-rubuce. Na durƙusa na gaishe su suka amsa mini fuskarsu babu yabo babu fallasa kafin na ce"Hajiya ga ni an ce ki na ƙirana". "E sashin Saifullah za ki je ki gyara masa sun fita tare da baƙonsa. Ki gyara kafin ya dawo". Gabana ya faɗi ya yi ras na ɗan saci kallonta kafin na kai ga faɗin"Hajiya shi ya buƙaci hakan? Don na ga kamar ba ya jin daɗin zuwa cikin sashinsa da nake yi". "Ba shi ya buƙata ni ce dai kawai na ga dacewar hakan, na san halin Saif sarai yana da wuyar sha'ani amma da zaran kin fahimci wane ne shi za ki gano tana da daɗin zama da tarin hayalen ƙwarai". Kaina kawai na jinjina na ce"to". Na tashi na nufi sashin ƙirjina yana tsananta bugu da harbawa. Na isa cikin sashin ban dawo cikin ainihin nutsuwata ba, na soma tattare falon da ko kwanunkan da aka ci abinci da kofuna yi tea ɗin ba a kwashe ba. A bayyane na tsirtar da wani tsiririn tsaki na takaicin da ya taru ya yi mini yawa, ina ƙara yarda da maganar nan da ake cewa na duk na mijin da ka gani a hanya tsaf tsaf kar ka yi saurin bakin furta yana da tsafta ɗari bisa ɗari, har sai ka ga makwancinsa sannan ka yanke hukunci. Na ɗauko tsintsiya na share ko'ina na yi mopping na mayar da komai a cikin muhallinsa. Wasu takardun addinin da suke kan kujera na ɗauka zan mayar da su kan teburi na yi tuntuni da bakin kafet takardun suka zube daga hannuna, na runtse idanuna sa boda zafin da na ji ya ratsa har ciki kwayata, na tashi na ina tattare takardun da suka watsa na ci karo da wani hoto, na ɗauka zan mayar da shi cikin takardan tautsayi ya sanya idanuna sauƙa akan hoton. Take numfashina ya ɗauke na wucen gadi na sanƙare a wajen na gaza motsa ko da gaɓa ɗaya daga cikin jikina, illa idanun da na ƙura wa hoton jikina yan rawa tamkar an jona mini wutar lantarki. Hoton Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe na gani tare da Muhammad Taufik cikin shiga riga ɗaga, ga wani ƙaramin yaron da ba zai haura shekaru uku a duniya ba. Hoton ya yi bala'in kyau tare da fito da su suka yi tar da su, fuskokinsu washe da maɗaukakin farin cikin da ya bayyana ƙarara. Jikina gabaɗaya ya soma rawa da har ban san sa'ilin da na zame na yi zaman ƴan bori dirshan a ƙasa ba, na dulmiya cikin kogin tunanin da yake ƙoƙarin hautsina mini dukkan lissafin cikin kwanyata. Me ye haɗin Muhammad Taufik kuma da Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe? Na jefa wa kaina tambayar da take zuciyata ta ba ni amsa da faɗin wataƙila masoyansa ba ina ji a kaf cikin garin nan da kewayanta babu malamin addinin da take da yawan mabiya sama da Sheik Dawood. Na ja dogon numfashi na fesar ina jina gabaɗaya wani iri wacce ba ta da maraba da majinyaciyar da ta yi shekara tana jinya. Na mayar da hoton inda ya faɗo na ajiye takardan. Ban shiga musu cikin ɗakuna ba don ba na son na gane wa idanuna sbun fa bai halalta na gani ba, don na sha jun ana cewa ɗakin mutum sirrinsa ne musamman kuma su da suka kasance jinsin maza biyu kuma a matsayina na mace budurwa. Ina gama wa na fito na koma sashin Hajiya Muhibbat har yanzu tana tare da baƙin suna ta buga lissafi na durƙusa na yi mata sannu tare da sanar da ita cewar na gama aikin. "Ki zauna za mu yi magana idan na sallame su". "To". Na amsa mata da shi a taƙaice. Na zauna har duka gama lissafin suka ƙare na sinci wasu abubuwa a cikin hirarta sun duk da kuwa hirar kasuwanci ne, ƙoƙarin haɗa kayan lefe suke mai rai da motsi na fita kunyar jama'a kamar yanda na ji suna faɗi. Sai da suka gama ta ƙare tas ta sallame su suka tafi kana ta juyo gare ni. "Na bar ki kina ta jira ko? Kin ga kayan lefe ne muke ta ƙoƙarin haɗa wa na ɗaruruwan kuɗaɗe kayan na fita kunya. Don gidan manyan mutane za a kai kayan". Na jinjina kai kafin na furta"ai ku na ƙoƙari ma irin lissafi haka. In wasu ne ai komai sai ya sunce musu". Ta ɗan yi jim kafin ta ce"sai dai ba na son haɗa irin waɗannan kayan na kuɗaɗe masu yawa". Cike da mamaki na ɗago kai ina kallonta kafin na kai ga furta"Hajiya me yasa? Na ga ai ƙaruwarku ne tun da ciniki za a yi muku ko kayan miliyan ɗari za a haɗa ai ribarku ne". Ta sauƙe ajiyan zuciya wanda har sai da na ji sautinsa kafin ta sama lasisin faɗin"mafi yawancin masu haɗa irin wannan lefen na maƙudan kudaɗe bayan auren ba sa iya ba wa mata lokaci balle maganar kulawa. Daga zaran a kai ki ɗakinsa a matsayin mata to ke da ganinsa ma wataƙila sau ɗaya a cikin shekara guda shi ma ɗin sai kin yi sa'a kuma kin dage da addu'a. Amma duk wasu ababen buƙatann rayuwa ba za ki rasa su ba sai dai za ki yi rayuwa ne a zahiri kina raye amma a baɗili ruhinki ya daɗe da barin gangar jikinki". "Duk da hakan kuwa wasu ba su da burin da ya wuce su ha sun auri irin mjini da zai haɗa musu ko da kwatankwacin irin wannan lefen ne". "Ai kuwa kallon kitse suke yi wa rogo, da sun san tashin hankali da rashin samun nutsuwar da yake tattare da auren wani mai kuɗin da sun daɗe da dawowa hanyar gaskiya, sai dai ba dukka aka taru aka zama ɗaya akan sama na gari a cikinsu sai dai ƙalilan. Ni fa yanzu da ace ina da wata ƙanwa mace da ba ta yi aure ba ko kuma Allah ya ba n ƴaƴan mata da ba zan taɓa yi musu sha'awar su auri masu kuɗi ba sai dai masu rufin asiri. Don ina yaƙin sai sun fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa har ma da nutsuwar ruhi da salamar zuci". Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauƙe kana na ce"Allah dai kawai ya da mu dace". Gabaɗaya jikina ya yi la'asar mussamman yanayin da na ga ta shiga, duk wani wanda zai gan ta a yadda take zai iya rantsuwa da girman zatin Allah cewar ba ta da wani sauran damuwa a cikin gidan duniya, mussamman idan aka yi la'akari da irin suturun da take sanya wa, muhallin da take zaune a cikinsa da kuma motar da take murza wa. "Za ki iya zuwa gida ki dawo idan ki na buƙatar hakan. Tun da na ga yanzu babu wani aiki sai zuws a kuma". Tana gama zancen ta tashi ta hau sama ta bar ni zaune a wajen ina bin ta da kallo. A ƙalla na ɓata mintuna ashirin zaune a wajen kafin na tashi na fita zan je na dawo kamar yadda ta lalince ministan.Tun da na fito idanuna suke kan sashin Saifullah haka kawai wata zuciyar mini na je na dauki hoton da na gani na Muhammad Taufik tare da Sheikh Dawood. Ba tare da na yi wani dogon tunanina na nufi sashin na tura ƙofan falon a hankali na shiga ina waige-waige. Da hanzari na je na buɗe takardan na ɗauko hoton na sama a cikin hijabina na fito na jawo ƙofar, ina fitowa na hango motarsa tana shigowa cikin gidan, na yi mutuwar tsaye a wajen na kasa gaba balle baya har ya gama daidaita parking. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 5️⃣9️⃣ Sai da na ja dogon numfashi a fesar daga bakina kafin na iya sarrafa kaina. Har ya fito daga cikin motar na gaza matsawa daga inda nake tsaye tamkar wacce bishiya ko kuma sassaƙen gunkin indiya. Da sauri na ga ya nufo wajen sashinsa da alama wani abun ya mance ya zo ɗauka cikin gaggawa. Sai a lokacin na sama zarafin matsa wa daga wajen na ɓoye a bayan shuke-shuken da aka ƙawata wajen da su. Ina ganin sa ya zo ya wuce ba tare da ya lura da inda nake ba, ba a bi sakon talatin ba na ga ya fito riƙe da wasu takardu a wannan lokacin da ya murzawa ƙofar makulli ya rufe ta kirif kafin ya nufi inda ya ajiye motarsa ya shiga ya fiye da mungun gudu ya fice daga cikin gidan. Fitarsa ta yi daidai da sauƙe tagwayen ajiyan zuciyar da na yi wani yana bin wani tamkar wacce ta yi aikin fasa dutse. Na fito daga inda na ɓoye ina tafiya saɗaf-saɗaf tamkar ƙadangaruwar bayan tulu da hanzarina na nufi hanyar gate na ji an dakatar da ni. "Malama daga ina kike? Me ya kai ki hanyar sashin Saif?". Muryar Altine mai cike da isa gami da taƙama ya sauƙo a ƙofofin kunnuwana. Ban amsa mata ba har ta iso gabana ta tsaya riƙe da ƙugunta tana bi na da kallon tuhuma irin kallon da ma'aikacin ɗan sanda yake yi wa mutumin da aka kama bisa zargin ta'addanci. "Ban yarda da ke ba tabbas akwai abin da kike ɓoye wa. Kuma kawai abin da ya kai ki sashin Saifullah". Sai da na harhaɗo jarumta na yafawa wa kaina kafin na sama zarafin faɗin"Hajiya ce ta ce na je na gyara sashin". "Tun ɗazu kuma gyaran sashin kike yi? Uwar iya magana da iyayi". "Na riga da na faɗa miki iya gaskiyata, ya rage na ki ki yarda da abin da na faɗa ko akasin hakan". Ina dasa aya a zancen na raɓa ta gefenta na yi tafiyata, da farko gida na yi niyyan wucewa amma yadda na ga Altine ta ɗaura idonta a kaina ya sa ni sauya shawara, na je wajen Baba Mai gadi na zauna. Ta fi mintuna goma sha biyar a tsaye a wajen ita ba ta yi gaba balle baya tana ta aikin banko mini harara tamkar ƙwayoyin idanunta za su faɗo ƙasa. "Lafiya kuwa yau me ye yake faruwa tsakaninki da uwar-gijiyartakin?". Furucin Baba Mai gadi ya dawo da ni izuwa cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da na afka na wucen gadin. "Babu komai Baba, daman wajenka na zo neman wani taimako". Ya gyara zamansa yana fuskantana da kyau da hakan ya ba ni ƙarfin gwiwa da karsashin ci gaba da zancen. "Akwai wani babban malamin addini da ya yi shura a gefensa kuma sunansa ya ɗaukaka ya zagaye ko'ina a cikin ƙasar nan har ma da kewayenta." Tun kafin na dire zancen ya katse mini hanzari ta hanyar faɗin"wannan ba kowa kike magana a kansa ba fa ce baƙin Balarabe". "Anya kuwa shi ne? Wannan ɗin fa sunansa Sheikh Dawood aka yi masa kirari da gaskiya dokin ƙarfe". Ya murmusa kafin ya furta"ai mu a nan cikin jarafi an fi sanin sa da sunan baƙin Balarabe. Yana zuwa tafsirin alƙur'ani sosai a cikin garin nan. Ina tunanin babu garin da ya tara masoya fiye da wannan garin namun indan ya zo hatta mai martaba Sarki dakatar da komai yake yi ya je ya saurari wa'azinsa, kusancin da yake da shi da mai martaba ya sa shi ba shi auran ƙanwarsa ƴar autarsu ya aure ta sai dai ta rasu shekaru biyu da suka wuce, mutum ne mai tarin ilmin addini har ma da na zamani don na taɓa jin an ce yana shugabanci a wata jami'a". "Don Allah Baba kaman da wani irin lokaci yake zuwa garin nan ɗin? Sannan in ya zo yana yin kamar kwana nawa kafin ya tafi?". Sai da ya kalle ni kafin ya ce"yana iya zuwa a ko wani lokaci sai dai ta fi zuwa a lokacin sanyi kamar irin yanayin da muke ciki yanzu. Sannan idan ya zo yana gabatar da wa'azi a wurare daban-daban kuma a mabanbantan lokuta hatta wa'azin mata yana gabatarwa a masallacin Sarki". Na ɗan yi jim kafin can na ce"shin ko yana da wani alaƙa ne tsakanin shi da wannan baƙon da ya zo cikin gidan nan?". "Wai Sultan?". "Sultan kuma?". "Ƙwarai da gaske sunansa Sultan don tun sanin da na yi masa haka ake ƙiransa da shi. Amma asalin sunansa Muhammad". Mamakin zantukansa suka gana ni samun damar cewa komai illa sadda kaina ƙasa da na yi ina tufka da warwara a cikin raina. Ta ya ya Muhammad Taufik ɗin da na sani zai ya rikiɗe ya koma amsa sunan Sultan?. Sannan me ye haƙiƙanin alaƙarsa da Sheik Dawood da har na ga hoton su tare? Hoto ne da aka yi shi cikin lokacin zallan farin ciki da annashuwa da har ya bayyana akan fuskokinsu. Kuma a cikin gida aka yi sa balle ma na ce a wajen gabatar da wa'azi suka haɗu aka yi hoton. "Amma ƴar nan lafiya kike ta yi min wannan tambayoyin?". "Lafiya ƙalau Baba, tun ranar da na ga wannan baƙon ne na ga suna kama da shi Sheikh ɗin to shi ne nake ta tunanin ko sun haɗa jini da shi ne. Ko wani dangantaka ta kusa ko ta nisa?". Na ƙarƙare zancen cikin sigar jefa masa tambaya a faƙaice. "Ban ma taɓa lura da kaman da suke yi ba sai yanzu da kika furta nake zumo kamar a idanuna. Sultan dai kam abokin Saifullahi tun na ƙuruciya wani sa'ilin ma a nan cikin gidan suke ƙarar da hutun makaranta, ban taɓa jin labarin akwai alaƙa tsakaninsa da Sheikhi ta kusa ko ta nisa ba. Na san dai Sheikhi yana da azurki ƴaƴa sai da mafi yawansu mata ne ɗansa na miji ɗaya ne tal kuma bai cika bayyana fuskarsa ba". "To shi Sultan bayan abokan da yake tsakaninsu da Saif su na da wani alaƙa da masu gidan nan ne?". Kallon da ya watsa mini ya sani tabbatar wa kaina cewar na kwafsa kuma na wuce gona da iri har ina ƙoƙarin tsallake iyaka ba tare da na farga ko na ankare ba. "Wannan irin tambayoyin ƴar nan sai ka ce ina gaban alkali". Na murmusa kafin na ce"yi haƙuri Baba kawai na ga kamar ta sun ne ta yi tsananin yawa shi yasa nake tambaya". "Ba laifi kika yi don kin tambayi abin da ya shige miki duhu ko ya jefa ki cikin shakku ba, ai magabata sun ce tambaya mabuɗin ilmi ce. Sai dai a wannan gaɓar zan iya ce miki ba ni da amsar ko guda ɗaya daga cikin tambayoyin da kika yi min hasalima yadda kike gan sa a cikin gidan nan ya zo, ni ma haka nake ganinsa tun yana yaro ban taɓa damuwa da na san mene ne alaƙarsa da masu gidan ba don wannan ba hurumina ba ne kuma bai shafe ni ba". Na jinjina kaina cike da gamsuwa da zantukansa da dukkan suke kan gwadaben gaskiya. "Haka ne kam Baba to Allah ya kyauta". "Amin ya Allah". "Zan nem takarda da biro na zo ana ɗaura mini darasi. Ko gaisuwa ya kamata na koya daga cikin yaren nan tun da ban iya furta ko kalma guda a ciki ba". Ya dara sosai kafin ya ce"ba girin-girin ba dai ta yi maiƙo, kullum haka kike ce har na gaji da gafara sa ba tare da na ga ƙaho ba". Kafin na kai ga cewa wani abu Aryan ya iso wajen. "Wai ki zo in ji Umminmu". Haka kawai na ji gabana ya faɗi zuciyata ta buga da ƙarfi. Jikina a sanyaye na ce"lafiya?". Ya ɗage mini kafaɗunsa alamar bai sa ni ba daga haka ya dura da gudu ya koma ciki. "Tashi ki je ƴar nan kar ki yi sanya don ba a bori da sanyin jiki". Kaina kawai na gyaɗa masa na tashi na nufi cikin gidan ba tare da na san abin da zan je na tarar a ciki ba. Ina doso cikin falon idanuna suka soma sauƙa aka fuskar Altine da take zaune kusa da ƙafafun Hajiya Muhibbat gefe guda kuma Aryan da Ayan ne suke wasan mota. Na durƙusa kana na ce"Barka da hutawa Hajiya, ga ni an ce ki na nema na". Ta ɗau lokacin kafin ta ce"me ya kai ki wajen mai gadi?". "Hajiya gaisawa kawai muke yi da shi, sai kuma yaren kanuranci da na roƙi ya dinga koya mini kasance yarena ne kuma nan yi ba". Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"to ba na son na ƙara ganin kin ce wajensa ko da wasa ne kuwa, ki yi aikinki shi ma ya yi nasa". "In sha Allah hakan ba zai ƙara faruwa za a kiyaye". "Good". Ta amsa da shi a taƙaice, jikina ya yi sanyi ƙalau don na kasa gano inda maganganun natan suka dosa da kuma abin da take nufi da kar na ƙara zuwa wajensa ko da kuwa da wasa ne. "Hajiya rana tana yi me ye za a girka ne?". Furucin da Altine ta yi kenan da ya tilasta mini cira kai na yi mata kallo guda tare da janye idanuna daga gare ta. "Fita ni zan yi zuwa anjima can da yamma. Ku dafa abin da za ku ji don ba na jin ma su Saif za su dawo nan kusa". Tana dasa aya ta tashi ta bar cikin falon sa boda ƙirar wyarta da aka yi ta hau sama zuwa ɗakin da kallo na raka ta har ta ɓace wa ganina daidai lokacin da sautin Altine ya sauƙa a masarrafar naɗar sautina. "Idan kunne ya ji jiki ya tsira". Duk yanayin da nake ciki hakan bai hana ni sakar mata da murmushin ba duk da kuwa bai kai har cikin ƙasan zuciyata ba. Ta tashi ta bar ni a gantale a cikin falon ba tare da ta sanar da ni abin da zan yi ba, zafafan iska na fesar daga bakina ina ɗan lumshe idanuna da nake jin har wani zafi-zafi suke yi mini. Jin an fado kafaɗuna ya sa ni buɗe lumshashshun idanuna ina tsayar da su akan Ayan da yake tsaye a gabana yana rungume da dokin wasa a hannunsa. "Kuka kike yi?". Na girgiza masa kaina ina kai hannuna ina share hawayena da ya zubo daga idanunta don ban san lokacin da suka zubo ba. "Ummi ce ta yi miki faɗa shi ne kike kuka ko?". Na riƙo hannuna ina jinjina kaifin tunanin yaron na furta"Ummi ai duk ta fi mu shi yasa idan muka yi ba daidai ba za yi mana faɗa, sa boda rayuwarmu ta gyaru ba don ba ta son mu ba". Kallon da ya tsare ni da shi ya sa ni fahimtar kalaman da na yi amfani da su sun yi girme wa shekarun da har ya hana sa fahimtar saƙon da nake son a isar masa a cikin zancen. Na kai hannuna na shafo sumar kansa"ba faɗa Ummi ta yi mini ba ka ji?" Ya gyaɗa mini kansa alamar ya ji, daidai lokacin da Aryan ya iso wajen ya zo ya tsaya kawai yana kallona. Na ƙirƙiro murmushin dole na dasa a bisa fuskana kafin na kai ga furta"lafiya ka tsaya haka?". Ya yi rau-rau da ido yana ta faman dube-dube ya matso saitin kunnena kamar mai raɗa ya ce"Anti don Allah ki yi mana wanka jikinmu gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mana". "Wanka kuma? Ba a yi muku ba ne?". Da sauri Ayan ya janye Aryan daga kusa da ni yana faɗin"Aryan Uncle Saif ba ya hana ka yawan magana ba, ka zo mu yi wasan mu". Na cafko hannayensu gabaɗayan su ina kallon Ayan da gaba ɗaya ya bi ya firgice na lura ya fi Ayan tsoro nisa ba kusa ba. "Me yasa za ka ce ya yi shuru?". "Uncle Saif ya ce babu kyau yawan suturu". Ya ba ni amsa ba tare da ya yarda mun haɗa ido da shi ba. "Ba irin wannan maganar yake nufi ba. Yanzu dai ku zo mu je na yi muku wankan sai ku dawo ku yi wasan". "A'a yanka mu za ta yi". Ayan ya yi zancen hawaye suna ciko masa idanunsa ga jikinsa da ya soma rawa sosai. Cikin mamaki na ce"waye? Waye zai yanka ku kuma?". Duk su biyun suka sadda kawunansu ƙasa ba tare da sun ba ni amsa ba. Take na ji kifiyar tausayinsu ta ratsa zuciyata tare yin pieces da ita, jikina ya yi la'asar na rasa ta inda zan fara shawo kansu, sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi amfani da dabarar da ta faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu. "Ku zo mu je na yi muku wanka na shirya ku babu wanda zai ji". A tare duk su biyun suka ɗago kai suna kallona kamar za su miƙa wuya sai kuma Ayan ya jan hannun Aryan tana faɗin"ka zo mu tafi mu yi wasan mu". Daga haka ya janye shi suka koma inda suka wasan na bi su da kallo ina tunanin mafitar da ta dace. [12/3, 7:18 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 6️⃣0️⃣ Na yi ɗam jim ina ta tunanin ta yadda zan ɓullowa lamarin, can na ji wani dabara ta faɗo mini a cikin kaina tamkar faɗuwar aradu, na tashi na je inda suke wasan na zauna ina faɗin"ina ma zan yi wasan ku biyu ni kuma ni ɗaya". Duk suka ɗago ido suna kallona kafin can Aryan ya ce"kin iya ne?". Na gyaɗa masa kaina alamar e, ya miƙo mini motar guda ɗaya yayin da su ma suka dauki guda-guda, muka soma yin wasan ba mu yi nisa ba suka cinye ni lamarin da ya faranta musu rai da ruhi suka daka tsalle tare da ƙyalƙyalewa da dariya kamar za su shiɗe. "Mun ci mun cinye ki Anti". Na ɗaga ido na kalla Aryan da ya yi zancen na ce"ai gobe ma za mu ƙara gwadawa, yanzu dai tun da mun kama wasan ku zo mu je na yi muku wanka ku sauya wani kaya ku ji sanyi a jikinki". Kamar an yi ruwa an ɗauke lokaci guda fara'a da annurin fuskarsu ya ɗauke, duk su biyun suka yi shigo har sai da na kawar da shurun ta hanyar faɗin"idan ba kya so shi kenan bari na tashi na shiga ciki". Na yi zancen ina yunƙirin miƙe wa suka riƙo hannuna. "Anti mu je ki yi mana wankan". Murmushi kawai na yi musu muka wuce ɗakin nasun, na cire musu kayan jikinsu na ɗaura musu towel muka shiga cikin banɗakin na yi musu wanka da ruwan ɗumin da na tara a cikin bokati. Na wanke musu sumansu da mayuka da sabule gyaran gashin, na ɗauko musu towel ɗin muka fito na ɗaura su akan gadon suna ta jijjiga kansu yayin da ruwan da yake cikin sumarsu yake watso wa a jikinsa, suna ta kyalƙyala dariya. Na ke jikin wadrode ɗin kayansu na buɗe na ɗauko musu wata jamfa launin ruwan ƙasa. Ina juyawa Aryan ya ce"Anti ni kam ba zan kayan nan ba". Ina rufe bakinsa ya diro daga kan gadon ya zo ya zaro wani wandon jeans ya ce shi zai saka, yayin da Ayan shi kuma ya dage akan ba sai saka wannan wandon ba. "To shi kenan Anti kowa ya saka kayan da yake so kawai ko?". Aryan ya yi magana ina tsayar da idanunsa a kaina, na durƙusa a gabansa kafin na furta"ai ba zai yiyu ku saka kaya daban-daban ba, tare aka haife ku tare aka raine ku tare ku ka girma komai tare ake yi muku. Kun ga Ummi ba za ta ji daɗi ba idan aka saka muku kaya daban-daban". Ina rufe bakina Ayan ya ce"shi kenan Anti a saka wanda Aryan ɗin yake so kawai. Ni na haƙura ba na son Ummi ta ji ba daɗi". Sosai na ji yaron ya ƙara shige mini can ƙasan ƙalbina yaro ne mai matuƙar nutsuwa ga shi sam ba shi da hayaniya balle ƙiriniya irin na yara masu shekarunsa, a ɗan saman da na yi a cikin gidan nan a lura ya fi Aryan maƙon ɗan uwansa. Take Ayan ma ya tadae rigima ya ce shi ma ya haƙura a saka kayan da Aryan ɗin yake so, haka suka din ga yi har sai da na kawo ƙarshen muhawarar ta hanyan ɗauko musu wani kayan. Farin riga t-shirt na saka musu mai gajeren hannu gaban rigar an yi rubutu da jan kala, na saka musu wandon jeans da tsayinsa ya tsaya daidai gwiwansu. Na gyara musu sumar kansu ya sha musu mai tare da taje musu shi, ya yi kyau tare da ƙara yin sheƙi gami da ƙyalle, sosai kayan ya amshi jikinsu da hakan ya taimaka wajen fito da ainihin sihirtaccen kyawunsu. Na lura su ma kansu sun san cewar kayan ya yi musu kyau don gaban madubi suka tsaya suna kallon kansu suna dariya. Na zo na tsaya a bayansu Aryan ya yi wuf ya ce"Anti ni da shi waye ya fi wani kyau? Ai na fi shi kyau ko?". "Ƙarya ne ai Uncle Saif ma ya ce ni ne wanda ya fi kama da shi". Ayan ya mayar masa da martani cikin gaggawa, duk suka juyo gare ni suna rige-rigen yin magana. "Waye ya fi kama da Uncle Saif a cikinmu Anti?". Aryan ya koma jefo mini tambayar a karo na biyu, kafin na amsa masa Ayan ya amshe zancen cikin faɗin"ai ni Ummi ta ce da Abbinmu nake kama". "To ni ai yanzu ban san Abbin nakun ba haka shi ma Uncle Saif ɗin ban san shi sosai, ina dai ganin sa ne kawai. Kun ga kenan ba zan iya bambamce da waye suke kama ba a cikinsu". Ina rufe bakina Aryan ya juya ya je ya ɗauko mini wani hoton da yake ajiye akan dirowar dake gefen gadon baccinsu ya kawo mini. "To kin ga wannan shi ne Abbin namun". Ya yi zancen yana miƙo mini hoton na karɓa tare da zuba idanu, hoton Hajiya ce zaune ta sha wani uban leshi launin hoda da ya amshi jikinta kuma ya hau da zubin jikinta, an yi mata kwalliya a fuskarta da ta zauna a fuskar ta yi ɗas da ita tamkar da shi aka halicce ta. Wuya da kunnenta har da hannayenta sun sha ado sarƙa, ɗan kunne da kuma awarwaro. Gefenta na hagu Ayan ne zaune yayin da gefenta na dama Aryan yake zaune. Wani mutum ne fari sol tsaye a bayansu ya ɗan ranƙwafo ya dafo kadaɗun Hajiya da hannunsa guda ɗaya yayin da ɗayan hannun ya ɗaura akan Aryan, dukkansu fuskokinsu washe da maɗaukakin annuri da ya gauraye da nishaɗi, sai dai na lura hoton kaman tsoho ne don a hoton su Aryan ba za su wuce shekaru ɗaya da wasu watanni da haihuwa ba. Sai da na saka ido sosai na gano Aryan da Ayan sam ba sa kama da mahaifinsu, duk kamannin mahaifiyarsu Hajiya Muhibbat suka kwaso kwabo da kwabo babu abin da suka bar mata, sai dai hasken ubansu da suka ɗauko. Ban yi aune ba na ji an fizge hoton tamkar za haɗa da hannuna, babu shiri na ɗago kai don ganin wanda ya aikata hakan a gare ni, idanuna suka sauƙa akan fuskar Altine ta take tsaye tana ta cika ta batse wa. Me ye kike yi a cikin ɗakin nan sannan me ye wannan hoton yake yi a hannunki?". Ba ta jira na ba ta amsa ba ta ci gaba da balbalin wutar ba'lain da take yi tamkar za ta yi aron baki. "Watau kin ɗauko hoto kin sa a gaba ki na ta kallo, kin zuba wa mijin mata idanuna kamar mayya kin shagala da kallonsa har ma ba ki san sa'ilin da na shigo cikin ɗakin ba balle tsayuwar da na yi a kanki. Irin ku ne wanda ake ɗaukowa daga rana a shigo da ku cikin inuwa daga ƙarshe ku ku tura mutum cikin ranar, daman ni tun ranar farko da na gan ki nake kokonto a game da ke. Tukunnan ma me ye dalilin da ya kawo ki cikin ɗakin nan?". Murmushi kawai na yi tare da miƙe wa tsaye, na kai duba na ga su Aryan da suke tsaye da na lura jikinsu gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau har sun kasa motsawa daga inda suke. Sai da na yi dogon tunanin kafin na ce"daman an iyakance mini inda zan shiga ne a cikin gidan ban sa ni ba?". "Tambaya kike yi ko kuma neman sani?". "Duk wanda kika ɗauka a ciki daidai ne ranki ya daɗe". Na yi zancen ina ɗage kafaɗana alamar babu abin da ya sha mini kai ko ya ɗaɗa ni da ƙasa. Na sa kai zan fice daga cikin ɗakin ta jawo gefen hijabina har sai da na yi tangal-tangal zan faɗi Allah ya kiyaye. "Ke har kin isa ina miki magana za ki tashi ki tafi ki bar ni? Wace ce ke kuma da me ye kike taƙama, sannan wa ye ya tsaya miki a cikin gidan da har kike jin cewar za ki iya yin duk abin da kika ga dama?". Duk da abin da ta yi mini ya yi mini matuƙar ciwo tare da tusa mini takaici amma ban nuna mata ba ko a fuska, maimakon hakan ma murmushi na sakar mata ina tsayar da idanuna ƙar a kanta. "Ni ba kowa ba ce a cikin gidan nan face ƴar aiki kamar ki, wacce ta fito aiki domin rufa wa kanta asiri da kuma samun abin da za ta ɗauki nauyin buƙatun rayuwarta". Ina dire zancen na juya na yi ficewa ta ina jin wani gigitaccen tsawan da ta dokawa su Aryan yayin da nake fice wa daga cikin ɗakin ko kanzil ban juyo na ce da ita ba. Kai tsaye ɗakin Altine na nufa wanda kai tsaye zan iya ƙiran da ɗakinmu na shiga banɗaki na ɗauro alwala na zo na gabatar da sallan zuhur, na ɗaga hannayena sama ina jero kirari ga Ubangiji kana na shafa doguwar addu'ar da na yi wanda dukkaninta addu'ar neman rahama da gafara ne ga Abba. Wanda babu ranar da za ta fito ta faɗi ba tare da na yi tunanin sa ba ko kuma ya faɗo mini a cikin raina ba. Hoton da na ɗauko a sashin Saif na tsince ɗaga gefen hijabina da na ƙulle na zura wa hoton idanuna yayin da wasu tambayoyi masu rikitarwa suke yi mini yawo a cikin kwanyata. Tabbas akwai buƙatar na nemo wata iriyar alaƙa ce tsakanin Muhammad Taufik da kuma Sheikh Dawood ko kuma na ce baƙin Balarabe kamar yadda na laƙanci haka daga wajen Baba Mai gadi. Numfashi mai nauyi na ja na fesar daga cikin baki sa boda tunawa da na yi da Amira, babu wanda yake saurin gane ina cikin damuwa ko da kuwa ban furta ba sama da ita, babu abin da ta ƙi jini a rayuwarta kamar ta ganni cikin ƙunci. Mun shaƙu da ita sosai ta yarda ba na shakkan sanar da ita dukkan sirrina domin ba ni da kaufi akan ta, ina jin ta tamkar ƴar uwar da muka rayu a mahaifa guda da ita kana muna fito duniya a tare kuma a lokacin ɗaya. Na san ta yi nemana har ta gaji ta sadadu ta fawwalawa Allah komai, ko har yanzu suna tare da Mansur ko kuma ƙaddara ta raba su, wataƙila izuwa wannan lokacin sun mallakin junansu sun cika burinsu na zama miji da mata oho? Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina zame wa na kwanta sa boda sarawan da kaina yake yi mini tamkar ana buga mini guduma. Ban yi nisa a cikin baccin ba na ji sauƙar ruwa mai sanyi a fuskana babu shiri na tashi sai dai duk da firgitan da na yi hakan bai hana ni kamo sunayen mahaliccina guda ɗari babu ɗaya ba cikin bakina. Na cira kai ina duban Altine da take tsaye a kaina babu alamar ranƙwafawa tamkar wacce ta haɗiye taɓarya. Raina ya tuntsura yana tafasa tamkar talgen da yake bisa wuta yana ɓararraka. "Kin fi kowa sanin cewar ai ba bacci ne ya kawo ki ba, da za ki zo ki yada baki ki na baccin asara wanda babu gaira babu dalili". Tsam na miƙe akan ƙafafuna"na lura duk yadda na kai ga ƙoƙarin ganin na ba ki girmanki na kuma mutunta ki ba kya ganin hakan. To gwara na fito miki a mutum na fito miki a yadda kike so, Ina so ki sani ni fa baiwarki ba ne a cikin gidan nan hasalima matsayinmu ɗaya. Ki riƙe girmanki ni ma zan tabbatar da cewar na yi miki biyyaya a matsayinki da wacce kike gaba da ni amma idan kika zubar da mutuncinki babu abin da zai hana ni sanya ƙafa na take sa, ai daman idan malam bai ji kunyar hawa jaki ba to jaki ba zai ji kunyar jefar da shi ba". Ina rufe bakina kawai na ga ta ɗaga hannu da nufin zabga mini mari na yi caraf na riƙe hannunta. "Kar ki kuskura ki ƙara yin gangancin ɗaura hannunki a jikina da sunan mari. Don duk ranar da kika ƙara maimaita haka zan yi miki abin da tarihin rayuwarki ba zai taɓa cika idan babu shi". Ina dire zancen nawan na sakar mata hannunta na juya ɗauki hoton na ƙulle a gefen hijabina na fice daga cikin ɗakin, kai tsaye kicin na nufa na iske har ta fara aikin girkin abincin ranan, na nema waje tsaya tare da naɗe hannayena a ƙirjina ban taɓa komai ba har ta shigo cikin kicin ɗin tana ta faman harare-harare. Cikinmu babu wanda ya ce da wani ko kanzil. Haka nan ban motsa daga inda nake ba balle na yi wani aikin har ta gama girkin ta sauƙar ta ɗauko kula za ta zuba a ciki, ni ma na ɗauko plate na ajiye mata ta ɗago ido ta kalle ni kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shuru. Ganin ba ta da alamar zuba mini ina ganin ta gama zuba wa a kulan na ɗauki kudayin na zuba wa kaina na ɗauko na koma gefe, na soma ci. Ina ganin ta ta gefen idona sai banko mini harara take yi kamar idanunta za su faɗo ƙasa. Ina gama cin abincin na wanke plate ɗin na koma ɗaki na yi alwala na gabatar da sallan asr, ina zaune kan sallayan ta shigo ko sallama babu ni ma ban damu don ko ɗaga kai ban yi ba balle na gan ta. Haka kawai na ji gabaɗaya zaman gidan ya fita akaina, don haka na tashi na fito falo ina fito wa na tarar da Hajiya tana sauƙo wa daga beni yayin da su Aryan suke biye da ita a baya. Muka sakar wa juna murmushi ni da ita yayin da muka haɗa ido kafin na yi mata sannu da fito wa ta amsa mini cikin sakin fuska. Da hakan ya ba ni damar amayar da roƙona. "Hajiya daman ina so na je gida ne idan babu damuwa". "Za ki iya zuwa Amatullah ai na ga babu wani aikin ma da ya rage, mun yi waya da Saif ba za su dawo yanzu ba. Ni ma kuma yanzu zan fita shago ne akwai kayan da zamu haɗa su Aryan muka zan ajiye su a wajen Hajiyarmu. A taƙaice dai dawowarmu mu ma zai iya kai wa dare, mu je na sauƙe ki a hanya". Cike da jin daɗi na ce"ina godiya Hajiya". Na riƙo hannun Ayan muka fita zuwa wajen motar muka shiga, ta ja motar muka fita a hanya ta sauƙe ni yayin da su kuma suka wuce. Ban yi tafiya mai nisa ba na iso gida ina shigowa na hango Zinariya a ƙofan ɗakinta tana girki. Muka sakarwa juna murmushi kafin ta ce"kin dawo kenan? Ɗazu na leƙa ai ba kya nan?". Na gyaɗa mata kaina yayin da nake zama akan dakalin ƙofar ɗakinta. "Yau gidan shuru lafiya kuwa?". "Kin san yamma ta yi ai yanzu kowacce ta shirya ta tafi waje kwastomanta". Na jinjina kaina ina girmama lamarin a cikin raina, haka ta yi ta ja na da hira har izuwa lokacin da wayarta da take cikin ɗaki ta soma ruri. "Taimaka ki ɗauko min wayata a cikin ɗaki. Kin fi kusa da ƙofar". Kaina kawai na gyaɗa mata yayin da nake tashi na shiga cikin ɗakin ina ɗaukar wayar ƙiran yana tsinkewa. Hoton fuskar wayar ya bayyana idanuna suka kai kansa. Take na ji ƙirjina ya harbawa tabbas indai ba ƙarya idanuna suke yi mini ba hoton Abbinsu Aryan ne tare da Zinariya a fuskar wayar kamar za su rumgume juna tsabar kusanci da jikinta ya yi da shi. Jikina ya ɗauki rawa ina ƙara ware idanuna don tabbatar da sahihancin abin da suke nuna mini. [12/4, 7:36 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 6️⃣1️⃣ Jikina gabaɗaya ya ɗauki rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki, na kasa yin komai illa idanuna da na ci gaba da ƙurawa hoton fuskar wayar. "Ba ki sa ma wayar ba ne?". Tambayar da Zinariya ta jefo mini daga waje shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka. A lokacin aka ƙara ƙiran wayar a karo na biyu na juya da nufin zan kai mata muka yi kiciɓus da ita a ƙofar ɗakin tana shigowa, na miƙa mata wayar yayin da ni kuma na fice waje. Na zauna akan kujerar da ta tashi tare da zabga tagumi tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar wani shaƙiƙinta. Ina zaune a wajen har Zinariya ta gama wayar ta fito ta ja kujera ta zauna, na bi ta da kallo ganin yadda fara'arta ya ƙaro sam bakinta ya kasa rufuwa sai washe haƙwara take yi tamkar wacce aka yi wa wani gagarumin kyautar a zo a gani. "Yau ina cikin alkhairi dumu-dumu, tun da na wayi gari na ke cin karo da alkhairi". Ta yi zancen cikin maɗaukakin farin cikin da ya bayyana har a cikin furucinta. "Me ya faru haka? Na ga gabaɗaya fara'arki ta ƙaru". "Alhajina ne ya ƙira ni yanzu muna gama wayar na ga alert miliyan guda a cikin asusun ajiyata". Na bi ta da kallo kana na ce"miliyan guda? Wannan maƙudan kuɗaɗen na mene ne haka?". Ta yi fari da idanunta kafin ta furta"kyauta ce kawai daga masoyi zuwa masoyiyarsa, ranar Alhamis zai aiko mota a ɗauke ni zuwa can garin Abuja ranar juma'a na ƙara kimtsa kaina na jira dawowarsa a yammacin ranar don ba ya ma ƙasa gabaɗaya. Ya yi mini alƙawarin tare da ni zai yi hutun ƙarshen mako kuma sa boda ni mussamman ya baro duk abin da yake yi ya zo shi". "Irin wannan hidima haka amma dai babu ɗawainiyyar iyali akansa ko?". "Waye ya gaya miki? Yana da matarsa har da ƴaƴa, sai dai ya ce min matar ba wani son ta yake yi ba don auren ma iyayensu maza ne suka haɗa". Na saki ɓoyayyar ajiyar sa bsa yadda zantukan natan suka daki zuciyata tare da mummunan mini raina, na ji wani takaici yana taso mini tabbas in dai har abin da nake zargi ya tabbata to fa haƙiƙa akwai gagarumar matsala. "Aikin me ye shi kuwa yake yi haka da yake iya yin kyautar irin waɗannan maƙudan kuɗin, sannan me ye sunansa?". Kallon da ta tsare ni da shi tun kafin na dire zancen ya sa ni fahimtar na zuga wa kwaɓata ruwa kuma na wuce gona da iri don ina ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa. Na ɗage mata ido ɗaya alamar lafiya? Da hakan ya ba ta damar furzar da zancen da yake cikin bakinta. "Wannan tambayoyin hakan wani na bin wani sai ka ce jami'ar ƴan sanda. Kin ga ni nan da kike ji da gani an sha ni na warke wallahi, don an yi min cin amana da zangon ƙasan da ba zan taɓa mantawa ba har zuwa lokacin da zan yi numfashin ƙarshe a rayuwata. A cikin gidan nan aka sama wata tsinananniya ta ɗauki lambar saurayina a cikin wayata ta ƙira shi ma da yake mai bakin uwa ne ya biye mata suka ci amanata, har ta kai ta kawo suna haɗuwa a otel ranar da labari ya iske kunnuwana kuwa na shirya na je ni har otel ɗin na gan su da idona. Sai dai ban yi sakaci na bari sun ganni ba, sai da na saita lokacin da suka saki jikinsu shi da ita wani rana ya zo har cikin gidan nan ɗakinta ba tare da sun san da cewar ina cikin gidan nan. Na dafa ruwan zafi na je na sheƙa musu ita da shi". Tun da ta soma zancen nake bin ta bakinta da kallo har ta kai aya da hakan ya yi daidai sauƙe tagwayen ajiyan zuciyan da na yi ina zame hannayena daga tagumin da na zabga. A taƙaice na ce"to Allah ya rufa asiri". "Amin". Shuru ya ratsa wajen na tsawon wasu mintuna kafin ta kawar da shi ta hanyar faɗin"ba ni da saurin yarda da mutum tun bayar faruwar wannan lamarin, haka nan na ƙudurce a raina ba zan ƙara aminta da wata ɗiya mace ba ko da kuwa cikin ɗaya muke da ita. Sai dai ban san dalili tun ranar farko da na fara ɗaura idanuna akan ki a cikin gidan nan na ji kin kwanta min a cikin rai, na kuma ji a raina cewar zan iya aminta da ke har na ja ki a jikina". Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na ce"me yasa kika yi mini wannan shaidar? Ba kya tunanin ni ma idan kika ja ni a jikin idan tafiya ta yi tafiya zan iya cin amanar da kika ɗauka kika ba ni?". Wani shu'umin murmushi ta saka kana ta furta"ban ga alamar hakan a tattare da ke ba Amatullah, domin ido ba mudu ba ne amma ai ya san kima". Kaina kawai na jinjina tare da miƙewa tsaye na ce"bari na je na ɗebo ruwa na yi wanka kafin magriba ta yi".Ta yi caraf ta riƙo hannuna. "Ai dai za ki tsaya na sauƙar da girkin ki ci kafin ki tafi ko?". Na jijjiga kaina"kar ki damu a ƙoshe nake don ban daɗe da cin abinci ba". "Ai ko yanzu kika tashi daga gaban kwanon abinci sai kin cin girkina, don haka kawai ki koma ki zauna idan ruwan wanka ne ki sha kuruminki ina da ruwa a ɗakina sai na ba ki bokati guda". "Kin dai matse ne kawai amma ba na jin yunwa". "E dai na ji koma ki zauna". Ta yi zancen tana jan hannuna na zauna a inda na tashi, mun ɗan taɓa hira da ita kafin abincin ya tahu ta sauƙe ta ce na shirgar da shi ɗakin yayin da ita kuma take kashe ragowar garwashin. Sai da ta gama ta shigo ta zuba mana abincin muka ci tare, ta matsa mini akan sai na ci gaba yadda take ta ja na da hirar da ba na gane kansa balle gindinsa. Haka muka gama abincin na tattaro kwanunkan zan wanke fafur ta hana ni, ta ɗauki ruwa bokati guda ta ba ni na je na yi wanka na yi alwala na fito. Sanda na dawo kawo mata bokatin na iske ta tana waya don haka na ajiye mata na wuce ɗakinmu. Sallan magrib na gabatar na zauna a inda na yi sallan na karato wani sashi daga cikin haddan karatun alƙur'anin da yake kaina. Tunani kala daban daban suka ziyartar kwanyata amma ciki babu wanda ya fi jan hankalina tare da rikitar da ni sama da hoton Abbinsu Aryan da na gani a fuskar wayar Zinariya da kuma kalaman da ta yi mini. Tabbas indai ba idanuna ba ne suka gano mini abin da ba shi ne ba ko kuma suka sama matsala gabaɗaya Abbinsu su Ayan mijin Hajiya Muhibbat ɗin dai na gani. Sai dai me ye haɗin sa da Zinariya kuma a ina suka haɗu da shi? Idan ban manta ba na taɓa jin Hajiya tana cewar mijinta ba mazauni ba da yake shafe tsawon lokacin ba tare da ya zo gida ba. Ta gyara zamana ina ƙara yin zurfi cikin tunanin da nake yi tare da yin nisan kiwo cikin nazarin. Ta ina da zan fara wannan yaƙin balle har na ci galaba? Akwai tarin abubuwa a gabana da nake son cimma a cikin rayuwata, haƙiƙa sai yanzu na yarda da karatun da Amira take bi ya know na cewar dukkan maza halin su guda ne wanda hakan yake nufin ko wani gauta ja ne sai dai wanda bai ji rana ba. Na tashi na gabatar da sallan isha'i na zo na yi shirin kwanciya sai dai baccin ya ƙi zuwa haka na yi ta juye-juye har izuwa lokacin da bacci ya yi nasarar sace ni. Kamar a mafarki na ji soma jin tashin sautin yana tashi daga cikin ɗakin, wanda hakan ya tilasta mini buɗe idanuna tare da sauƙe su akan Sha'awanatu da muke ɗaki ɗaya da ita. Zaune take akan katifarta tare da wani saurayi suna manne da junan tamkar za su haɗiye junansu, kankana ne a gabansu yana yanka da wuƙa yana ba ta a bakinta yayin da take wani lumshe idanuna tare da gantsarewa. Tsam na tashi tsaye ina rarumo hijabina na mayar da shi jikina da hakan ya sanya hankalinsu karkaro wa gare ni, Shaawanatu ta buga wani uban tsaki tare da kawar da kanta gefe. "Wane ne wannan Sha'awanatu kika shigo mana da shi har cikin ɗaki?". Kamar wacce take jira na ce kule ta ce as, ai kuwa ta miƙe ita ma tana mayar mini da martani a zafafe"amma dai ai kin san da cewar ina da cikakken iko a cikin ɗakin nan, tun da kuɗi nake biya na kaya ba kyauta nake zaune ba kuma ba alfarma aka yi min ba. Yadda kike zaman kanki haka ni ma nake zaman kaina babu ruwa wani da wani kamar yadda babu ruwan biri da gada. Ina da ikon na kawo duk wani wanda nake so cikin ɗakin nan a duk lokacin da nake so kuma a duk sa'ilin da na ga dama idan buƙatar hakan ta taso". Kalamanta suka ɗura mini takaici a cikin raina na cika na yi fam. "Au! Haka ma za ki ce? Amma kin san da cewa ai ba ke ɗaya ba ce kike da iko da ɗakin. Akwai hakkina da hakan zai tauye mini shin ba ki yi tunanin hakan ba? A lokacin da ƙaramar curin ƙwaƙwalwar kanki take yi miki saƙa da mungun zare". "Su haƙƙin manya. To ke ki na tunanin har wani haƙƙin kike da shi a cikin gidan nan? Ai yanzu kuɗinki shi ne mutumcinki tun da biya nake yi kamar yadda ke ma kike biya don kana ina da lasisin kawo duk wanda nake so". Kalamanta suka sanya zuciyata ƙara tunkura raina ya ci gaba da tafasa na cije leɓena kafin na ce"ai kuwa zan ba ki mamaki, don wannan ƙatoton gardin ba zai kwana a cikin gidan nan ba. Idan suna son ku aikata baɗalarku ku tafi can wani waje ku je ku yi amma ba a cikin ɗakin nan ba". "Ai kuwa kin yi kaɗan ki korar min kwastoma. Ko don ki na baƙin ciki da farin jinina ban kasance irin karfa ba da kare ba ya zuwa cikin ɗakin nan da sunan ya zo wajenta". Ban tanka mata ba na soma waige-waige can na da hango wuƙar da suka yanka kankanan na yi hanzari na je na ɗauke ta. "Ka za fita daga cikin ɗakin nan ko zai na yi maka mummunan lahanin da ko uwar da ta haife ka in ta ganka ba za ta shaida ka ba. Ku je can wani wajen ku haɗu amma cikin ɗakin nan kam sai dai gani sai dai hange". "Ke Amatullah anya ki na da hankali kuwa? Wuƙa ce fa kika ɗauka". Na juya ina nuna ta da wuƙar hannuna"idan kika ƙara ɗaga ƙafarki ki ka yi taku ɗaya sai na ɗaba masa wuƙar nan, ke ma na yi miki rauni sannan daga ƙarshe ni ma na kashe kaina. Dukkanmu mu ukun mu yi asarar rayuwarmu". Cak ta tsaya a inda take ba tare da ta motsa ba ganin yadda na furzar da zancen babu alamar wasa a tattare da ni. Na nufin Saurayin na tan da yake tsaye cike da tsoro yana ta ƙif-ƙifta idanu tamkar shege a yayin rabon gado, yana ja baya ina nufar sa gadan-gadan har sai da ya kai ƙarshen ɗakin. Sha'awanatu ta ɗaura hannu a kanta ta soma kurma ihu da kururuwar neman agaji, kan ka ce kabo mutane suka cika gidan har da Hajiya Babba. "Lafiya Amatullahi me ye yake faruwa?". Hajiya Babba ta jefo mini tambayar yayin da take ƙoƙarin ƙwace wuƙar da yake hannuna, na turje ina faɗin"Hajiya ki bar ni, ki bar ni na koya musu hankali". Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai da ta karɓa wuƙar daga hannuna. "Wai me ye yake faruwa ne?". Hajiya Babba ta ƙara maimaita mana tambayar a karo na biyu, Sha'awanatu ta kwashe komai ta sanar da ita sai da ta gama sauraron ta kafin ta waigo gare ni"duk abin da ya faɗa haka ne?". Ban iya amsa mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba illa gyaɗa kai da na yi alamar e, don cikin abin da ya faru babu wanda Sha'awanatu ta rage ba tare da ta furta ba. "Kai solofiyo zo ka fice daga cikin ɗakin nan". Hajiya Babba ta yi zancen tana saitawa saurayin hanya, cikin rawar jiki ya fice. Haka ta sallame kowa daga cikin ɗakin aka fice ana ta ƙananan suturai da yamaɗiɗi. "Ke Sha'awanatu kin gan ni nan da kike ji da gani duk yadda na yi ƙaurin suna a haɗa gurmi, to ba ba son abin da zai ɗaga min hankali. Ɗakin nan kin san da cewa ba ke ɗaya kike rayuwa a cikinsa don haka duk wani baƙon da za ki yi ko iyakarsa wuni ne babu kwana". "Amma Hajiya ba ki dubi abin da ita ta yi ba sai ni? Shin idan ban kawo kwastomana cikin ɗakina ba ina ake so na kai shi?". Sha'awanatu ta yi zancen cikin ɗaga muryar da ina ta tsbbacin shi ya fusata Hajiya Babba ainun. "Matuƙar ina ƙaunar ci gaba da zama a cikin gidana to ya zama tilas a gare ki ki bi dukkan umarni da sharruɗan da na gindaya miki. Idan kin ga ba za ki iya zama ga ƙofa nan sai ki haɗa kayanki ki san inda dare ya yi miki". Shuru ta yi ba tare da ta ce ko kanzil har Hajiya ta gama zancenta ta waigo gare ni. "Ke kuma zan ja miki kunne a karo na farko kuma wanda zai kasance shi ne na ƙarshe, kar ki ƙara yin gangancin ɗaukar makami a cikin gidan nan". "To". Kawai na amsa mata da shi a taƙaice, ta juya ta bi ta tare da wuƙar da yake hannunta. Kallon-kallo muka yi wa juna ni da Sha'awanatu kafin na wuce zuwa makwancina na kwanta raina a jagule. Ina ta jiran na ji ko za ta kunna sautin da ta yi ikirarin cewar ba ta iya bacci ba tare da ta kunna sa ba, sai na ji shuru kamar Malam ya haɗiye shirya. Na yi ƙwafa ina gyara kwanciyata tare da ƙara tabbatar da cewar wargi ma waje ya samu, kuma maganin biri karen maguzawa. [12/5, 5:07 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 6️⃣2️⃣ Ban iya runtsawa ba har sai da dare ta raba sosai, sai faman juyi nake yi na kasa yin baccin. Gabaɗaya ba na jin daɗin komai raina ya gama ragulewa yayin da zuciyata ta lalace ainun. Ƙwafa na yi ina tashi na zauna duk da kuwa duhun da ya mamaye cikin ɗakin nan sai dai hasken farin wata yana hasko cikin ɗakin daga tagar da yake a buɗe. Karatun alƙur'ani na soma yi tun sautina ba ya fita har sai ya soma fita na ɗau tsawon lokaci ina karatun har sai da na ji wani sanyi ta ratsa sashin ruhina, sai da na yi sallan asubahi kana na kwantar da haƙarƙarina wani bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ni, sosai na yi baccin ban farka ba sai da hantsi ya fito. Ina buɗe idanuna na ga ranar ral ta galle, na yi zumbur ina miƙewa tare da murtsike idanuna don tabbatar da sahihancin abin da nake gani. Tabbas rana ta yi saboda yadda ta galle haske da zafinta ya mamaye ko'ina. Kallabina na za ra na ɗaura akaina na saka hijabina na ɗauki buta na fito na wanke fuska da bakina na mayar da ita cikin ɗaki, kana na fito ina fitowa muka haɗu da Zinariya. Muka sakarwa juna murmushi kafin na ce"ranki shi daɗe kin tashi ke nan? Sai yanzu na ki safiyar ta yi ke nan?". Ta yi miƙa kafin ta ce"wallahi ke dai bari daren jiya ban samu na yi bacci da wuri ba ne, na tsaya yin waya ban yi aune ba har sai da lokaci ya ja kin gan ni nan sai yanzu na sama daman tashi da ƙyar". "To Allah dai ya sa kin yi salla?". Ta taɓe baki"so nake yi yanzu idan na yi wanka, inna ci abinci sai na samu na yi sallan. Don ina jin sallan daren jiya ma ban yi ta ba na ɓige da yin waya". "Sallan kike haɗa wa a kanki haka?". "To ya ya zan yi Amatullah ayyuka su yi min yawa, dole wani abun sai ana ajiye shi a gefe idan aka sama sarari sai a ɗago shi". Shuru na yi don mamaki da al'ajabi ya hana ni furta ko da kalma guda, sai da na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya kana na sama lasisin faɗin"ya dai kamata kam ki samu ki yi sallan, ni na fita wajen aiki". "In kin dawo za mu yi magana". Ta murmusa"akwai zancen bakinki na ga alama sai na dawo ɗin dai kawai sai mu tattaunawa". Dariya ta fashe da shi har ta tafa hannu, ban tsaya jiran abin da za ta faɗa ba na fice don ko ban tambaya ba na san cewa na makara. Gudu-gudu sauri-sauri nake tafiyar ƙafafuna har suna sarƙewa tsabar sautin da nake zuba wa tamkar za tashi sama, kamar daga sama na ji an danna mini horn lamarin da ya yi matuƙar gigita ni. Na ɗaura hannuna aka tare da runtse idanuna ina jiran na ji ta inda motar za ta doke ni da yadda Allah zai yi da ni. Ji na yi motar ba ta dake ni ba hakan ya ba ni ƙwarin gwiwan buɗe idanuna don ganin abin da yake wakana, take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saif da yake tsaye a gabana ya zube dukkan hannayensa a cikin aljihun wandon suit ɗin da yake jikinsa, idanunmu suka sarƙafe cikin na juna na tsawon wasu daƙiƙu kafin na yi ƙarfin halin janye nawa gefe guda. "Amatullah ko?". Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi damar ci gaba da maganar da yake kamar an yi masa dole ko kuma mai ciwon baki. "Da kin daina wahalar da kanki ki na yin sammakon zuwa wajen aikin da ba zai amfane ki da komai ba, da zan ba ki shawara ki ɗaura da na ce da ke tun wuri da kin ɗauke ƙafarki daga cikin wannan gidan". Na cira kaina ina kallonsa sai dai kwarjininsa da cika ido ya hana ni ba ni damar yi masa dogon kallo. "Me ye yake nufi da waɗannan maganganun nakan?". "Ina nufin ba za ki taɓa samun gurbi a cikin zuciyoyin mutanen da suke rayuwa a cikin wannan gidan nan, ba ki da tarbiyya da nagartar da ya dace ki kasance a kusa da mu kasancewarki mai zaman kanta kuma a cikin gidan magajiya cikin tsakiyar karuwai da ƴan daudu. Da babu abin da suka sanya a gabansu face saɓon Allah da kaucewa koyar wa Annabinsa". Hawaye suka ciko mini kurmin idanuna sa boda zafin kalamansa da na ji, kaina na ƙasa da hakan ya ba wa hawayen damar kwaranya na kuma gaza samun ikon tsayar da su. "Amma ka san cewar ko wani bawa da irin na shi salon ƙaddarar da Ubangiji yake ƙaddara masa ko....?". Tun kafin na gama zancen ya ɗaga mini hannu alamar ba ya ƙaunar sauraron raguwar zantukan nawan. "Allah ba ya taɓa ɗaura wa Bawa abin da ba zai iya ba. Kuma duk wani abin alkhairin da kika ga ya sama Bawa to daga Allah ne akasin hakan kuma daga mu ƴan adam ne". Jinjina kaina na yi ina haɗiya kukan da yake ƙoƙarin kufce mini, na kai hannu na kawar da hawayen da suka ɓata mini fuskana kana na furta"duk kalamanka babu kuskure a cikinsu, amma ka roƙi Allah kar ya jarabce ka da abin da ba za ka iya ba kuma ba ka taɓa tsammanin tsintar kanka a cikin irin rayuwar ba". Ina dasa aya a nan na juya na bar shi tsaye a wajen, na karya kwanar da za ta sada ni da gidan. Baba Mai gadi na iske zaune a bakin gare ɗin na durƙusa har ƙasa na gaishe shi ya amsa mini cike da kulawa, ban bari mun yi wani dogon zance da shi ba na tashi na shiga cikin gidan. Babu kowa a falon don hakan kaina tsaye na wuce ɗakin Altine na shiga cikin banɗaki na kulle kaina na jingina jikin ƙofar banɗakin yayin da wasu hawaye masu ɗumi suke gudun famfalaƙi a bisa kuncina suna zarce wa har izuwa saman haɓata. Tabbas juyi-juyi ce in ji kwaɗo ya ce wash! Da ya tsinci kansa tsumgum a cikin ruwan zafi. Haƙiƙa ta kan zo a ko wacce irin siga ba tare da ta yi raunin mutumin da za ta faɗa kansa ba. A zamanin baya idan wani ya kalle ni ya ce wannan yarinyar za ta iya sanya ƙafa ta bar cikin gidan mahaifinta ta shiga duniya ta yi zaman kanta, ilahirin mutanen da suka sanni kuma su ka san wace ce ni, sai sun yi haɗaka sun yi taron dangi sun ƙaryata abin da ya furta cikin babbar murya. Sai ga shi ƙaddara ta jefo ni cikin duniyar da babu kulawar uwa balle uba, babu mai tsawartawa balle ƙwaba, babu mai hana ki balle ya saka ki duk abin da kika ga damar aikatawa shi za ki yi babu mai tambayarki dalili balle har ki sama tagomashin shawara. Babu tswatarwa iyaye balle dangi babu mai tanƙwara ka balle ya tursasa ka ka yi abin da ba kya yi niyya ba. Ko a cikin mungayen mafarkan da na yi sheiɗan bai taɓa kimtsa mini cewar wata rana zan yi zaman kaina ba, balle har na kwana na tashi a cikin gidan karuwa. Zazzafan iska mai ɗumi na fesar daga bakina ina sulale ƙasa na yi zaman dirsham ina wani irin kuka mai rauna zuciyar mai saurare. Haƙiƙa sai yanzu na ƙara yarda cewar babu abin da ya kai mutuwa tonon silili da ban kaɗo rufaffun sirrukanta ta sanya a faifayi ta raba a duniya. Ina da yaƙinin da Abbana yana raye a cikin wannan duniyar da ban tsinci kaina a cikin wannan rayuwar ba, ko da kuwa ƙaddara ta jawo ni to tabbas ba zan yi nisan zango a cikinsa ba. Tun ina kukan hawaye suna zuba har sai na na koma yin kukan zuci sa boda hawayen sun tsaya sun kafe tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe na tsawon shekaru masu nisan zango. Jin da na ji ana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin shi ya fargar da ni na dawo cikin hayyacina daga na tunanin da na yi nitso a cikinsa. Da ƙyar na iya miƙewa akan ƙafafuna sa boda ciwon kan da lokaci guda ya rufe har ya sauƙar da mini da zazzaɓi mai zafi a cikin jikina. Sai da na wanke fuskana kafin na buɗe ƙofar muka haɗa ido da Altine na yi saurin kasar da nawa idon daga gare ta ina ƙoƙarin fitowa daga cikin banɗakin na ce"ina kwananmu mun tashi lafiya?". Ban damu da sai ta amsa mini ba na sa kai zan yi wuce ta ta jawo ni na koma da baya. "Me ye kika aikatawa a cikin banɗakin da kika shiga kika ƙulle ƙofa?". "Har abun da na aikata a cikin banɗakin ma zai na sanar da ke ranki ya daɗe?". Ban tsaya na ji amsar da za ta ba ni ba na yi ficewa ta daga cikin ɗakin na bar ta tsaye a wajen tana cizon ƴatsa. Na iske Hajiya Muhibbat zaune a cikin falon tare da Saif da alama wata muhimmiyar tattaunawa suke yi ganin yadda gabaɗayan su suka tattara hankulansu waje guda. "Anty lokaci ya yi fa za mu gaya wa Yaya gaskiya abin da yake yi sam bai dace ba. Ta ya ya mutum mai iyali sai tafi can wata uwa duniya ya tare shi kaɗai har ya shafe tsawon wani lokaci mai tsayi ba tare da ys waiwayi amanar da yake kansa ba balle har ya yi ƙoƙarin sauƙe nauyin da Ubangiji ya ɗaura masa ba. Anty idan ma har yanzu wannan abun da ya faru ne a cikin ransa ai ina tunanin za ki ci albarkacin waɗannan ƴaƴan da kika haifa masa ya sauƙo. Ya rumgumi ƙaddara kamar yadda ke ma kika manta da duk abin da ya afku kika amshi a matsayin miji a gare ki kuma uba ga tagwayen ƴaƴanki". Cike da gajiya da sauraronsa Hajiya ta ɗaga masa hannu muryarta tana rawa ta ce"Saifullah ya isa haka ba na son ana tuna min da abin da ya riga ya wuce hakan ya kan jefa ni cikin wani irin hali. Ina yi wa Saddam uzuri akan komai da yake aikata ba wai don ba na jin zafin abin da yake aikata wa sai don kawai ɗaurewar zaman lafiya a tsakaninmu da shi tun da ka fi kowa sanin halaye da ɗab'iun ɗan uwanka. Babu abin da Saddam zai aikata a gare ni da hakan zai sauya matsayin da yake da shi a cikin zuciyata". "Anty wai har sai yaushe ne za ki daina yi wa Yaya Saddam uzuri akan rashin adalcin da yake yi a gare ki? Na yarda ki na son mijinki amma don Allah na roƙe ki kar ki ba fi wannan soyayyar ta rufe miki ido, ta ki kasa faɗa masa gaskiya idan ya aikata ba daidai ba. Shi fa zaman aure na mutum biyu ba na mutum ɗaya ba dole sai kowa ya ba da na shi gudumawar kafin abubuwa su tafi yadda ya kamata. Anty ba ni da kowa a duniyar nan da ya rage min face Yaya Saddam shi ne komai na wa, shin ki na tunanin ba na jin zafin abin da yake aikata wa ne? Waɗannan fa ƴaƴansa ne ke kuma matarsa ce wacce ta sadaukar da komai sa bosa shi, ki zaɓi shi sama da kowa. Ki zaɓi ki yi rayuwa da shi har izuwa lokacin da numfashi zai yi bankwana da gangar jikinki". "Ya isa haka Saif na ce ya isa haka". Hajiya ta yi zancen cikin ɗaga sauti tana sa hannayenta ta toshe kunnuwanta da su. "Ka tashi ka fita ka ba ni waje ko kuma ka yi wata maganar amma ba wannan ba. Don ba zan iya juran hakan ba". Miƙewa tsaye ya yi jikinsa gabaɗaya ya mutu murus kamar wanda aka zare wa laka. A hankali yake motsa leɓansa yana faɗin"shi kenan Anty ba zan ƙara yi miki wannan maganar ba. Daman na shigo na sanar da ke cewar ɗazu na kai Muhammad Sultan filin jirgi, mun zo tare zai yi miki sallama kuma na ga ba ku buɗe ƙofa na ƙira wayarki ba ki ɗaga ba, ya ce a yi miki godiyar irin ɗawainiyyar da kuka yi da shi a tsawon kwanakin da ya yi a cikin wannan gidan". Yana dasa aya a zancen ya juya ya fice daga cikin falon, da hakan ya sanya Hajiya dafe kanta cike da damuwar da ya gauraye da tsananin tashin hankali. Saɗal-saɗal na ja ƙafafuna na bar cikin falon na wuce cikin kicin na tarar da babu wani alamar an ɗaura girki, na nema waje na tsaya na rumgume hannayena a ƙirjina kafin na soma safa da marwa a cikin kicin ɗin. "Saddam". Na maimaita sunan a bayyane ina sauƙe wani gwauron ajiyar zuciya mai nauyin kilo ɗari da ɗoriya da ƴan kai. In dai ta tabbata cewar wanda na ga a fuskar wayar Zinariya shi ne Saddam mijin Hajiya Muhibbat ya yi wa Zinariya alƙawarin durowa cikin ƙasar nan a yammacin ranar juma'a. "Kai kawon me ye kike yi? Ba ki fara haramar ɗauka abin kari ba?". Na tsinkayo muryar Altine ya sauƙa a cikin ƙofofin kunnuwana tamkar sauƙar aradu. A ɗaga kai ina dubanta cike da son ƙarin bayyani, fahimtar abin da nake nufi ya sanya ta faɗin"ƙwarai ai kin ji abin da na faɗa, da can waye kike ajiye da kike tunanin zai ɗaura miki girkin ki zo ki ɗiba ki je ki baje akan katifa?". Ban ce da ita komai ba na wuce na soma kici-kicin ɗaura girkin, ɗan wake na yi mai rai da motsi. Na yanda kabeji, tumatur da kokanba na soya mai ya soyu rafai. Na haɗa komai na jere su akan dinning table kana na zo na durƙusa a gaban Hajiya. "Hajiya ga abin karin kumallo a gama". "Amatullah ba na jin zan iya cin komai, ba na jin sha'awar cin dankalin nan a dai kawo min ruwan shayin na sha kawai". "Ba dankali ba ne ranki ya daɗe, ɗan wanke ne". "Ɗan wake?". Ta maimaita na gyaɗa mata kaina alamar e. "Ai kuwa na kwana biyu ban ci ɗan wake ba. Tun wani lokacin da muka je gidan Hajiyata ta sa aka yi mana rabona da cin ɗan wake. Kawo min nan mu ci tare da su Ayan sai ki kai wa Saif na shi don na san yanayin da ya bar nan ba lalle ya shigo yanzu ba". "To". Na amsa da shi a taƙaice tare da tashi na je na kawo mata komai gabanta, na haɗa na Saif kamar yadda ya faɗa na fita zan kai masa, ina ta jeranta sallama a ƙofar falon amma ba a amsa ba kamar yadda ba a fito an buɗe ƙofar ba. Sai can aka zo aka buɗe ƙofar na tura ƙofar na shiga cikin bakina ɗauke da guntun sallama. Yana kwance akan doguwar kujerar zaman mutum uku ya ɗaura hannunsa ɗaya a saman ƙirjinsa yayin da hannu ɗayan ya dafe goshinsa da shi, idanunsa suna lumshe amma na tabbatar da cewar ba bacci yake yi ba. Na ajiye tray ɗin abincin akan teburin da yake gabansa na juya zan fita. [12/6, 1:28 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 6️⃣3️⃣ Har na kai ƙofar ficewa daga cikin falon na tsinkayo muryarsa a dake yana faɗin"dawo ki ɗauke abin da ya kika ajiye". "Me yasa?". Ya yi banza da ni ba tare da ya ce da ni ci kanki ba, shurun sa bai hana ni ƙarisa zancen da na ɗauko ba"Hajiya ce ta ce a kawo maka idan ba za ka ci ba ita ya kamata ka ƙira ka sanar da ita, faɗa nata ne ni kuma ci kawa nawa". Ina dasa aya anan na juya na fita daga cikin falon a hankali nake taka ƙasa ina ɗaga ƙafafuna da ƙyar na koma cikin sashin Hajiya suna zaune tare da su Ayan suna cin abinci sai dai ita juya cokalin kawai take yi ban ga ta kai ko da loma guda cikin bakinta ba. Na rusuna na yi mata sannu ta amsa mini tare da cewa"ki dafa min shayi ba na jin daɗin jikina ba zan iya cin komai ba". "To ranki ya daɗe". Na amsa da shi a taƙaice cikin bin umarni da girmamawa. Na wuce cikin kicin ɗin na dafa mata shayin da ta buƙata babu ɓata lokaci na kammala na kawo mata. Tana zaune akan kujera ta jingina bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanunta ta dafe goshinta da hannayenta da hakan ya taimaka wajen fito da damuwar da take cikinsa ƙarara. "Hajiya lafiya kuwa kike?". Sai a lokacin ta buɗe lumshashshun idanunta na kuma fahimci lumshe su da ta yi ashe kuka take yi. "Subhanallahi! Kuka ku ma Hajiya me ya yi zafi haka?". Ta kawar da guntun hawayen da suke idanunta ta kai hannu ta amshi kofin shayin da nake miƙa mata, ta kai bakina ta yi kurɓa ɗaya ta ajiye a gefenta. Cikina a sanyaye na furta"ban san me yake dsmunki a cikin zuciyarki don sanin sirrin dake taskace cikin tsokar zuciya haƙiƙa wannan sai mahaliccinta, amma don Allah ku yi ƙoƙarin ki cire komai daga cikin ranki in sha Allah watarana komai zai wuce har ma ya zama labari". Sai da ta ɗau lokaci ba ta tanka mini har na faɗa tunanin na tsallake iyakata ta hanyar faɗa cikin abin da bai shafe ni ba kuma bai kasance hurumina ba. Har na cire rai da samun amsa daga gare ta sai kuma can na ji ta ce"Amatullah". "Na'am". Na amsa da shi cikin nutsuwa da kulawa. "Kin taɓa yin soyayya? Kin taɓa son wani irin son da kike ji tamkar ba za iya yin rayuwa ba tare da shi ba? Kin taɓa tsintar kanki cikin ƙangin so mai dabaibayi? Kin taɓa ɗaukar so da ƙauna kacukam kika ɗaura akan wani ɗa na miji? Kin taɓa yin soyayya mai zurfi da sarƙarƙiya?". Sai da na sauƙe numfashi mai nauyi kana na sama zarafin cewa"Ranki ya daɗe duk abubuwan da kika lissafa babu ko guda ɗaya da ya taɓa faruwa da ni. Hasalima ban taɓa yin soyayya ba a cikin rayuwata". "In dai abin da kika faɗa haka ne tabbas ba za ki taɓa fahimtar duk abin da zan bayyana miki ba, Amatullah so wani mungun abu ne. Wallahi ko maƙiyina ba na masa fatan Allah ya jarabce shi da makauniyar soyayya". "Don ban taɓa yin soyayya ba ai ba hakan ne zai sa na kasa fahimtar halin da kike ciki ba, sai dai na Hajiya ni na san ban kai na ji damuwarki ba amma in sha Allah na yi miki alƙawarin zan taya ki da addu'ar Allah ya kawo miki mafita da sauƙin halin da kika tsinci kanki a ciki". Ina dasa a zancen nawan na tashi na tattare kwanunkan da su Ayan suka gama cin abincin na kai kicin na wanke su, duk da ina jin yunwar kuma ina buƙatar na saka wani abu a cikin cikina, amma na kasa cin abincin sa boda yadda na ga Hajiya tana zubar da hawaye. Duk da ban san takamammen abin da yake damuwanta tare da yi mata ƙaiƙayi a cikin ranta ba, amma na tabbatar da cewar abin azimun. A lokacin yarinyatata duk macen da na gani tana rayuwa a cikin babban gida, tana saka suturar da take so sannan ta hau manyan mota. Gani nake yi tamkar a duniya dai kam ba da ta wani matsala kuma sun gama dace wa a cikin duniya sai dai a yi fatan dace wa a gobe ƙiyama. Ashe kallon kitse nake yi wa dogo, sai yanzu da hankali ya ratsa jikina ma fahimci ko wani Bawa da irin na shi damuwar kuma mai ɗaki shi ya san inda yake yi masa yoyo. "Idan tunanin za ki tsaya zauna kina yi ai da kin ui zamanki a can gida ba zai kin zo nan ba". Muryar Altine shi ya dawo da ni cikin duniyar zahiri daga karatun wasiƙan jakin da nake yi, ban ɗaga ido na kalle ta ba balle na ce da ita wani abu na tashi na je na rufe abincin na wanke hannuna na fita. Har yanzu Hajiya tana nan zaune inda na bar ta ba gusa ba wnda a iya tsawon kwanakin da na yi a cikin gidan. Na lura ba ta cika sama a falon ƙasan ba rai da rai yana sama indai ba wani abun ba ne ya sauƙo da ita ƙasa shi ma tana gama wa take kowa wa sama. Har na yi gaba zan wuce sai na ji ta ƙira sunan na dawo da baya na zo na durƙusa a gabanta kaina a ƙasa ina sauraron zancen da take yi cikin amo mai rauni. "Amatullah ki ba ni shawara na rasa da yadda zan ɓutowa wannan lamarin gabaɗaya kaina ya kule. Tunanina ya tsaya a waje guda cak". "Ranki ya daɗe ai ban san abin da yake damunki ba balle har na yi tunanin shawaran da ya dace na ba ki". Ta ɗan yi jim ta ce"haƙiƙa Allah ya jarabce ni da tsananin son mijina. Hasalima ni na fara ganinsa na ce ina sonsa har kuma Allah ya ƙaddara za mu yi aure su haifa Ayan da Aryan. Su biyu iyayensu suka haifa daga shi sai ƙaninsa Saifullah da muke zaune tare da shi a cikin gidan, ba su da wani dangin kusa illa junansu hakan ya sanya suke matuƙar ƙaunar juna. Mun yi aure da Saddam amma sai bayan auren na fahimci ya aure ni kawai sa boda ya sama wacce za ta taya sa sanya ido akan ƙaninsa kasancewar sa ba mazauni ba, tun da muka yi aure da shi bai taɓa yin sati guda cur a cikin gidan nan ba. Ya yi wuta shi ne ya zo ya yi kwana biyar ya koma daga nan kuma sai ya sanda ya ƙara waiwayo mana. Soyayyar Saddam ta rufe min ido ta hanyar ba na iya ganin aibunsa kuma ba na ganin laifinsa akan komai duk da kuwa ni ma kaina na san yana cutar da ni". "Hajiya ba kya tunanin cewa kuma yanayin aikinsa ne yake hana sa samun lokacin da zai zo gida? Kin ga fa ya wadata ku da komai na buƙatar rayuwa bai bar ku da yunwa ba, bai bar ku da ƙishi ba haka nan bai bar ku cikin tsumma ba komai na buƙatar rayuwa yana yi muku". Ta saki wani sakakken murmushi kafin ta ce"ba za ki fahimta ba. Duk waɗannan abubuwan da kika lissafa ba su ne jin daɗin rayuwar duniya mussamman a cikin gidan aure. Aure ba na mutum ɗaya ba ne na mutane biyu da ake buƙatar ko wani ɓangare ya ba da na shi gudumawar, ban yi dogon karatun addini ba amma iya sanin da nake da shi na san cewa ƙissan rayuwar Sayyada Khadijatu da Ma'aiki sallallahu Alaihi Wasallama, ita ta fara ganinsa ta ce tana sonsa sa boda ta yarda da shi kuma ta yi na'am da kyawawan halaye da ɗabi'unsa. Shin ni na yi laifi don na yi koyi da macen da tarihi ya tabbatar da cewar ta hidimtawa addini da ƙarfinta kuma da dukiyarta? Mene ne lafina don na gan sa na ce ina son sa shin addini ya haramta hakan ne da na cancanci wannan azabtarwan?". Na yi shuru ina tunanin ta inda zan fara kafin can na soma cewa"ki miƙa lamurranki zuwa ga Allah don shi kaɗai ne zai kawo miki mafita da sauƙin halin da kika tsinci kanki a ciki. Duk duniya babu wanda zai iya yaye miki damuwarki sama da wanda ya ɗaura miki. Ki yi sallan dare ki kai goshinki ƙasa ki yi Allah kuka ki sanar da shi damuwa da matsalolinki, ki roƙe sa cike da yaƙinin cewar zai amsa miki kuma ya yi miki zaɓi mafi zama alkhairi a gare ki. Ki yi azumi ki yi sadaka sannan ki yawaita karatun alƙur'ani don yana samar da nutsuwa a zuciyar da babu ita, ya haifar da kwanciyar hankali da salama a ciki ruhin da babu ita sannan ya na wanke ƙwaƙwalwa ya kuma daidata tunani". Ta sauƙe wani gauron ajiyar zuciyarta da har sai da na ji sautinsa kafin ta ce"na gode in sha Allah zan yi duk yadda kika ce. Na gode sosai da wannan shawaran". Ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan Altine da take ƙarisowa inda muke ta murtuƙe fuskarta marar annurin nan tamau, da hakan ya ba ni cikakken tabbacin ta saurara duk abin da muke zanta da Hajiya. "Hajiya sannu da hutawa, daman na zo mu yi wata magana". Ta yi zancen yayin da take zauna wa kusa da ƙafafun Hajiyar. "Ina jinki". "Ki ɗan ba mu waje ko". Murmushi kawai na yi na tashi na ba su waje na koma cikin ɗakin Altine na zauna, ganin zaman ba zai kai ni ko'ina ba. Hakan ya sanya ni ɗaukar alƙur'anin da na gani ajiye dirowa na fara karantawa. Ban yi nisa ina yi ba Altine ta shigo ta amshe ƙur'anin daga hannuna ta rufe ta ajiye shi a gefe guda, ta zauna tana fuskantana tare da haɗe hannayenta wajen guda. "Amatullah kike ko?". "Ƙwarai ba ki yi kuskure Amatullah nake". Ta gyaɗa kanta"ina so na yi miki gargaɗi na farko wanda shi za kasance shi ne na ƙarshe da zan yi miki wanda matuƙar ki na ƙaunar ci gaba da zama a cikin gidan nan dole ki yi bi abin da zan gindaya miki. Kin ga wannan shishshigewan da kike yi wa Hajiya da zummar samun wajen zama babu inda zai kai ki, sai dai ma ya sauƙe ki a tashar ƙasƙanci. Na ji har wani banzan shawara kike ba ta ke a dole kin cika kin batse, to daga yau na ja miki jan layi tsakaninki da Hajiya iyakan cin ki da ita gaisuwa ce daga nan kuma sai gobe". Tun da ta fara zancen nake bin ta da kallo har ta tsaya a madakata. Ban yi mamaki don izuwa yanzu in da sabo ya ci ace na saba da halinta. Murmushi kawai na yi na ce"yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe". Ina rufe bakina na tashi na je na yi alwalan sallan zuhur na zo na gabatar da salla a daɗe zaune akan sallayan har sai da na ji wani bacci-bacci ya soma ɗauka ta kana na tashi na ɗauki alƙur'anin na ci gaba da karatuna ban daga wajen ba sai da na yi sallan asr, na fita kicin na haɗa abincin rana na zo na jere shi akan dinning table lokacin Hajiya ba ta cikin falon, haka nan ban ga su Ayan ba Wanda na fi kyautata zaton ko su na can wajen Saif. Don na leƙa ta taga na ga motarsa tana cikin gidan da hakan ya ba ni tabbacin cewar bai fita ba. Sai da na ci nawa abincin kana na fito falo na kuwa yi sa'a lokacin Hajiya ta fito sai dai da alamar fita za ta yi don mayafinta yana saƙale a bisa kafaɗunta. Na duƙa na yi mata sannu ta amsa mini fuskarta babu yabo babu fallasa. "Hajiya daman mun gama duk wasu ayyuka ne shi ne nake son na je gida. Inda wani abun zuwa an jima sai na dawo". "Ba damuwa ni ma daman fita zan yi yanzu, Su Aryan suna ɗakina suna bacci sai ki sanarwa Altine ta na duba su". "To in sha Allah, a dawo lafiya". Har ta yi gaba sai kuma ya dawo da baya"an kai abincin Saif ne?". Na jijjiga mata kaina alamar a'a da hakan ya ba ta damar zarce wa da faɗin"ya kamata a kai masa sai a fito da kwanukan safen". Kaina kawai na gyaɗa mata da hakan ya ba ta damar ficewa daga cikin falon, na fita da kallo har sai da ta ɓace wa ganina kana na juya na je na haɗa masa abincin na ɗaura akan tray na nufi sashinsa. Haka kawai a duk sa'ilin da na nufi sashin nake tsintar kaina cikin matsanancin faɗuwa gaban da ban san dalilinsa ba. Sai da na ja dogon numfashi kana na sama ƙwarin gwiwar tura ƙofar falon haɗe da sallama na shiga ciki, yana nan kwance inda na same shi da safe da dukkan alamu tun da na bar shi bai gusa daga wajen ba, na ajiye abincin kana na ɗauki tray ɗin da na kawo da safe. Na ga alamun ko buɗe wa ba ayi ba balle a ci. "Ranki ya daɗe a fitar da abincin safen nan tun da ga na rana an kawo?". Na yi tambayar jikina yana rawa. Na yi shuru bai tanka mini ba hakan ya sa ni buɗe plate ɗin don gani da idona cikin rashin sa'a ya zame ya faɗi zuwa ƙasa take ya tarwatse ya yi ɗaɗɗaya. Ƙarar ya gigita ni har sai da na runtse idanuna na ajiye tray ɗin hannuna ina tattare wanda ya fashe ɗin. "Ranka ya daɗe ka yi haƙuri kuskure ba da niyya na yi ba". Tsit na ji ba a amsa mini har na gama tattarawa na zuwa a gefen tray na juyo na ga yana nan inda yake kwance bai motsa. Haka kawai na ji ƙirjina ya buga na zo na tsaya a gabansa ina ƙiran sunansa amma shuru bai ko motsa ƴatsunsa ba, balle wani gaɓa daga jikinsa. Ina janye matashin da ya rumgume a ƙirjinsa na ga hannunsa ya faɗo ƙasa jikinsa ya sake, ban san lokacin da na yi jifa da matashin ina sakin salati da sallallami ba tsabar gigicewa da kiɗimewar da na yi. [12/7, 1:15 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 6️⃣4️⃣ Na rasa abin da ya dace na yi sai kai komo nake yi a cikin falon rumgume da hannayena a bisa ƙirjina, na rasa wanda zan je na sanar wa halin da yake ciki ga shi Hajiya ba ta nan ta fita, na zo na tsuguna a gabansa ina bubbuga hannun kujerar da yake kwance a kaina tare da ƙiran sunansa. "Ranka ya daɗe don Allah ka tashi ka buɗe idanunka". Shuru bai amsa ba kamar yadda bai motsa ko da ƴatsun hannunsa ba, hakan ya ƙara gigita dukkan nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina da har ban san lokacin da hawaye suka ambaliya a bisa dakalin fuskata ba. Altine ce ta faɗo mini a ciki raina na yi zumbur na miƙe da nufin na je na sanar da ita halin da na zo na iske shi a ciki, har na tashi na ji wayarsa da yake ajiye akan teburin ta soma ruri kamar ba zsn kula ba sai kuma na ɗauki wayar ban tsaya duba wanda yake ƙira ba na kara wayar a kunnena ina magana ciki sarƙafewar harshe da cushewar numfashi. "Don Allah ku taimaka mini Yallaɓai ne ba shi da lafiya. Gashi nan ko motsawa ba ya yi kamar ma ba ya yin numfashi". "Ina mai wayar? Ina shi Saifullah ɗin?". Aka jeranta mini tambayar a haɗe sai da na juya na kalle shi har yanzu bai motsa ba kafin na ce"ga shi nan a shi da lafiya ne". "Yana ina yanzu?". "Yana gida a cikin sashinsa". Aka ɗan yi shuru kafin can aka ce"ki karanta suratul Baƙara a cikin wuta ki shafa masa a fuskarsa, sannan idan inda yake akwai fanka ki kashe su sannan ki rufe tagogi, ki aiwatar da abin da na ce miki ba tare da kin katse ƙiran ba". Tamkar ina gabansa haka na gyaɗa kaina alamar duk na saurara abin da ya faɗa kuma na fahimta, na je na ɗauki ruwa na karanta ayoyi goma na farkon Suratul Baƙara na tofa a cikin ruwan, na sa hannuna na ɗeba na yarfa masa a fuskarsa na yi hakan har sau uku amma bai ko motsa ba balle na kai ga saka ran sai buɗe idanunsa har numfashinsa ya dawo. Ban san lokacin da na fashe da wani kukan ba ina rarumar wayar na mayar da ita kunnena ina faɗin" ka ga har yanzu fa bai tashi ba, ko buɗe idonsa ma bai yi ba". Da ƙyar na ƙare zancen sa boda wani gigitaccen da ya ƙwace mini. "Ki nutsu ki kwantar da hnakalinki sai mu yi tunanin mafita. Kin rufe tagogin?". "A'a yanzu zan rufe". Na furta ina miƙe wa na je na rufe tagogin kana na kashe fanka. "Ki lulluɓe masa jikinsa da bargo mai nauyi sannan ki zauna a kusa da shi ki na ci gaba da karanto masa karatun". "Ka na ga zsi tashi kuwa?". Na jefa masa tambayar cikin sarewa da kuma cire tsammani. "In sha Allah ke dai kawai ki yi abin da na ce". Ban iya amsa masa da kalmomin da baki kan iya furtawa ba, na hanzari na haura sama na shiga cikin ɗakinsa na ɗauko bargon da na gani akan gadon na fita. Garin sauri na zame daga matattakalan benin sai ji na na yi a ƙasa tim, ƙuguna ya bugu sosai da har sai da na runtse idanuna ina cije leɓena sa bosa azabar zafi da zogin da na ji ya ratsa cikin kwanyata. Da ƙyar na tashi ina dafe jikin gini har na iso inda yake na lulluɓa masa bargo a jikinsa tun daga ƙafarsa har zuwa kafaɗuna, na zauna a ƙasa kusa da kansa ina ci gaba da karatun a hankali cikin muryar kuka. Ban gushe ina karantun har sai da na ga ya soma motsa ƙafafunsa zuwa hannayensa, sai dai har izuwa lokacin bai buɗe idanunsa ba. Wasu hawayen suka gangaro daga cikin koramar idanuna, zan iya cewa tun da Uwata Hafsatu ta haifo ni cikin wannan duniyar ban taɓa ganin irin wannan rashin lafiyan da numfashin mutum zai ɗauke gabaɗaya, jikinsa ya sandare kamar itace ba. Tun ina karatun da tunani da burin zai buɗe idanunsa har na soma karaya na ɗauki wayar da nufin ƙiran lambar da muka yi waya da mai ita. Na ga wayar da lambobin sirri da hakan yake nufin ba zai iya aiwatar da komai da ita ba, tagwayen ajiyan numfashi na sauƙe tare da ɗaura kaina jikin kujerar da yake kwance akan ta, na koma yin karatun a cikin zuciyata don baki ya yi mini da hakan ya hana ni furta ko da kalma guda. Rurin da wayar ta soma yi shi ya sanya ni zabura na ɗauko kaina zan ɗauki wayar idanuna suka sauƙa akan fuskarsa. Yana zaune akan kujerar ya jingina bayansa a jikin kujerar tare da cije leɓansa. Idanunmu suka sarƙafe cikin na juna wani kukan ya ƙara kubce mini mai haɗe da farin cikin ganin ya buɗe ido har ya tashi ya zauna. Wayarsa da yake kusa da ni ya kai hannu ya ɗauka da hakan ya tilasta mini janye idanuna daga gare sa. "Za mu yi magana an jima kaɗan yanzu ba na jin daɗin jikina inna dawo daidai zan ƙira ka". Ban san me ye aka ce masa daga ɗayan ɓangaren ba sai ji na yi ya furta"waye ya sanar da kai ba ni da lafiya Sultan?". Ban san amsar da aka ba shi ba a taƙaice ya ce"ok". Daga haka ya datse ƙiran ya ajiye wayar yana lumshe idanunsa tare da furzar da zazzafan iska da bakinsa da har sai da na ji sautin fitarsa. Muryarta a shaƙe na ce"sannu ranka ya daɗe ya jikin?". Bai amsa mini ba illa idanun da ya tsura mini kamar zai cinye ni da ido, dole na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa sa boda kwarjini da cika idon da yake da shi. "Za ki iya tafiya". Kalaman da ya saka mini da su kenan bayan sautin maganarsa ya fita raɗau, na saci kallonsa na ga ya mayar da idanunsa ya lumshe su, sai dai har yanzu numfashinsa bai daidata. "Allah ya ƙara sauƙi". Na furta yayin da nake tashi na fice daga cikin falon ina goge fuskana da hawaye ya damalmala mini shi. Ƙarar rufe ƙofar da ta yi shi ya sanya Saif buɗe lumshashshun idanunsa yana bin ƙofar da kallo daidai sa'ilin da wayarsa ta soma ruri. Sunan Sultan ya bayyana cikin screen ɗin wayar. Sai da ƙiran ya kusa tsinkewa kana ya ɗaga bai sanya a kunnensa ba maimakon hakan sai ya sanya ta a amsa-kuwwa. "Saif". "Ina jinka". "Ya jikin nakan? Wallahi hankalina ya tashi sosai da na ji halin da kake ciki". Sai da ya cije naman leɓansa kafin ya ba shi da faɗin"da sauƙi fa yanzu yadda nake ji na ma zan iya wasan polo da ingarman doki, sa boda ƙarfin da nake ji a jikina". Murmusawa Sultan ya yi kafin ya ce"daman har yanzu ka na fama da wannan lalular Saif? Na yi tunanin zuwa lokacin abubuwan sun yi sauƙi ba kamar da ba". "Babu abin da ya sauya daga abin da ka sa ni Sultan". Shuru ya biyo bayan zancen Saif na ƙarshe. Sai can ya ce"wace ce yarinyar da ta ɗauki wayarka muka yi waya da ita? Don na san gidanku babu ɗiya mace". A dake ya furta"ni ma ban san ta ba". "Mu bar maganar wasa mana Saif, wace ce?". "Ka riga da ba wa kanka amsa tun da tun farkon zancenka kai ma ka ce gidanmu babu ɗiya mace". Dariya sosai Sultan ya yi sai da ya tsagaita ya furta"any way ko ma dai wace ce, tabbas ta shiga cikin firgici ganin halin da kake ciki ka ji yadda take kuka kuwa tsakanin da Allah. Tambaya kuwa ta yi min ya kai sau ashirin akan za ka tashi kuwa? Na ce da ita in sha Allah, ba don ta zo akan lokaci ba Saif wataƙila da yanzu wani labarin ake yi ba wannan ba. Ko wace ce wannan yarinyar haƙiƙa ta ceto rayuwarka kuma ta ba da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da numfashin da kake yi yanzu a cikin duniya, ka gode mata don ta cancanci hakan sosai". Kit! Saif ya datse ƙiran ba tare ya ba wa Sultani damar amayar da sauran zancen da suke cikin bakisa ba. Ya zame daga zaunen da yake ya kwanta akan bayansa yana jan bargon ya lulluɓe rabin jikinsa, numfashi mai zafi ya furta daga bakinsa yana ɗan lumshe idanunsa sa boda ciwon kan da yake ji yana damun sa kaɗan kaɗan. Ya daɗe kwance a wajen yana saƙa da warwara cikin ransa kafin ya tashi ya haura sama zuwa cikin ɗakinsa, wanka ya yi ya ɗauro alwala ya fito ya sanya farar doguwar jallabiya da aka yi wa ado da zare launin ruwan zuma mai ƙyalli da ɗaukar ido, ƙaramar hula ya sanya a kansa ya shimfiɗa sallaya ya gabatar da sallan zuhur tare na sallan asr yana iddarwa ya ɗauko alƙur'ani ya soma karantawa. Dole ne ya tursasa masa rufe alƙur'anin ya ajiye a gefe sa boda rawar da jikinsa yake yi tamkar mazari. Ya kunna ƙira'an Sheikh Ahmad Suleiman a cikin wayarsa ya ajiye, a nan kan sallayan ya kwanta take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da shi ba tare da ya shirya wa hakan ba. Tun da na fito daga sashinsa na nufi hanyar gate ina tafiya a hankali tamkar babu laka a jikina, ina dab da fita na tsinkayo muryar Baba Mai gadi. "Ƴar nan lafiya kuwa na ga kamar kuka kike yi?". Na yi saurin goge fuskana da ban san lokacin da wasu sabbin hawayen suka fito ba, na waigo tare da duƙawa na gaishe shi, ya amsa yana bi na da kallon tuhumar son gano abin da yake faruwa da ni. Ya zauna akan bencin da yake wajen ni ma na je na zauna. "Ko dai cikin gidan ne babu lafiya? Don ɗazu na ga Saifullahi ya fito daga cikin gidan ya nufi sashinsa cikin wani irin yanayi, wanda har ina tsoron har hakan ya tasar masa da ciwon da yake damunsa". Na sauri na ce"wani irin ciwo ke nan Baba?". Ya yi ɗan jim kafin can ya ce"tun yana ƙarami yake fama da wani irin ciwo ga shi nan dai kamar aikin aljanu ko iskokai. A duk lokacin da ransa ya ɓaci ko kuma ya yi cacar baki da wani ke wani lokacin ma ko dogon zancen ya yi sai ki ga kawai ya yanke jiki ya faɗi jikinsa ya sanƙare haka zai koma ba shi da maraba da gawar da rai ya yi bankwana da gangar jikinsa, sai ta yi masa karatun alƙur'ani kafin yake dawowa daidai kuma da zaran ya tashi zai koma kamar ba shi ba". Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina jin ƙaran da ƙirjina yake yi tamkar zai faso allon ƙirjin ya fito waje ya taka rawar disko. Sai da na harhaɗo kalaman kafin na yi nasarar cewa"Allah ya na shi lafiya, Baba bari na je gida na dawo". "Amin ya Allah, to ƴar nan a gaishe da mutanan gidan". "Za su ji in sha Allah". Na amsa da shi yayin da nake tashi daga kan bencin, tafiya kawai nake yi ba tare da na san inda nake cilla ƙafafuna ba ina tafe ina tunani tare da nazarin kalaman Baba mai gadi. Saura ƙiris wani mai napep ya kwashe ni Allah a rufa asiri, ai kuwa ya fito ya balbale ni da bala'i da masifa tamkar zai yi aron baki da ƙyar ya haƙura ya ja napep ɗinsa ya tafi bayan ya gama wurwurga mini ashariya tamkar ya hana jini da dangin maguzawa. Sai yamma lilis na iso gida lokacin ko wacce budurwar dake cikin gidan ta ci ƙwaras tana ƙoƙarin fice wa wajen harkanta. Gidan ya yi shuru sosai ina shigowa na kai duba na ƙofar ɗakin Hajiya Babba na ga ƙofar ɗakin a rufe an buga masa kwaɗo. Na lura cikin kwanakin nan ba na ganin La'aniyatu a cikin gidan nan kuma na rasa wanda zan tambaya. Har na ɗauki hanyar ɗakinmu sai kuma na fasa don har cikin raina ba na ƙaunar haɗa ido da Sha'awanatu don har yanzu ban huce daga abin da ya faru ba. Ganin ƙofar ɗakin Zinariya a buɗe ya ba ni ƙwarin gwiwar faɗa wa cikin ɗakin. Na iske ta tana kwance akan katifarta tana bacci na zauna a gefen tana dukan ƙafarta har sai da ta shi, ganin ni ce ya hana ta ƙarisa ashariyar da ta danno. "Au wai ke ce?". "Da waye kike yi tunani?". Ba ta amsa mini ba har sai da ta tashi ta zauna ta ce"kin dawo daga aikin wahalar ke nan?". Na yi murmushi har sai da haƙwarana suka bayyana"aikin rufa wa kai asiri dai ko?". Ta taɓe baki ba tare da ta ce da ni ko kanzil ba sai ma sauya akalar zancen da ta yi "Ki na da lokaci ki raka ni kasuwa?". "Duk a cikin shirin tarban Yallaɓai ɗin ne?". Ta yi fari da idonta"ƙwarai kuwa". Na gyaɗa kaina"Allah ya bar ƙauna Madam ta gaban goshin Saddam". Caraf bakina ya yi furucin ba tare ta yi shawari da zuciyata ba. "Saddam kuma? Ina kika san sunansa?". Cike da dabara na wayince"kar ki daina basirar duk wata macen da kika ga ni a cikin harkan bariki". [12/9, 6:43 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 6️⃣5️⃣ Tun da na yi zancen take bi na da kallo da mamakin zancen ya tilasta mata wartsakewa daga baccin da take yi. Ta rarumo hannuna ta riƙe gam"sanar da ni inda kika san sunansa don Allah". Na saki wani shu'umin murmushin gefen baki kafin na furta"ki fa kwantar da hankalinki na canza ne kawai. Sai kuma aka yi dace sunan ya zo daidai". Ta yi jim tana ta bi na da kallo kafin can ta ce"kin tabbata?". Na yi fari da idona kafin na amsa mata da faɗin"ki yarda da ni wallahi ki ji rantsuwar ɗan musulmi ke nan ko? Ban taɓa ganin sa to ina ma za mu haɗu da shi mutumin da kika ce ba ya cikin ƙasar nan". Da alama ta sama nutsuwa da kalaman da na furzar don ina jin sautin sauƙar numfashin da ta sauƙe. "Na yarda da ke". "To ba ta labarin abin da ake shiryawa yallaɓai ɗin namun?". Washe baki ta yi tamkar gonar auduga don na ga alamar tamkar babu maganar da yake sanya ta cikin tsananin farin ciki kamar batun Saddan da ta yi masa laƙabi da Oganta. "So nake yi na je na sayo abubuwan gyaran jiki da kayan ƙamshi. Don so nake yi na shirya kaina kafin mu haɗu da shi, ina so wannan haɗuwar tamun ta zama abar tunawa a gare shi ta yadda ban bar shi masa tabon a cikin kwayansa". Sai da na musguta kafin na ce"irin wannan kulawan da kuke ba wa junanku to me ye zai hana ku auri junanku?". Ta taɓe baki"ai aure lokaci ne kuma ni ban shirya yin aure a wannan shekarun nawan ba. Kin gan ni nan sai na gama cin duniyarta da tsinken sakacen sannan na yi aure, mu yi rayuwar farin ciki da shi mu farantawa juna rai da zaran mun yi aure duk wannan soyayyar neman ta za mu yi mu rasa, duk marmarin junan da muke yi za mu koma jin haushin juna. Kin ga zaman auren nan zaman takura ne da rashin samun cikakken ƴancin kai mussamman aure a yanki arewacin ƙasar nan da za su san darajar mace ba sun mayar da matayensu tamkar bayin da ba su da ƴancin kansu, komai sai an ba ki izini za ki yi shi". "To ai wannan abubuwan da kika lissafo ba ɗabi'ar ba ce, koyar wa addini ne cewar miji yana gaba da matarsa. Kuma ko fita za ki yi ƙofar gida sai da iznininsa". Taɓe bakinta ta yi tana gyara ƙarin gashin doki da yake kanta kana ta ce"yanzu dai me ye kike so ki ce da ni?". "Ku yi aure ya fi wannan rayuwar da kuke ciki. Ku ma kanki sai kun fi girmamawa da mutunta junanku". "Ni fa yanzu ba aure ba ne a gabana Amatullah, kuma ke ki na tunanin aure a cikin wannan lokacin abu ne mai sauƙin da kike ta faman faɗinsa haka? Duk wacce ta sako ƙafarta ta tako cikin gidan nan da zummar shigowa harkan bariki to kafe ta ake yi, su shanye ta ta yadda ko ta so fita daga harkar ba za ta iya ba, wannan dalilin ne ya sanya da yawa daga cikinmu ko mafarkin fitan ma ba sa ya yi balle su yi wani yunƙurin ganin hakan ya faru. Wasu ma da suka riƙa a cikin harkan har ƙungiya ne da su da zaran kin yi yunƙurin fita za su sanya miki wani cutar da za ki yi ta fama da shi har sai kin gwammace mutuwarki akan ci gaba da rayuwa. ko ma su haukata ki gabaɗaya wasu ma idan kika yi karo da masu rangwamen imani sai sun yin sanadin rayuwarki. Kin ga duk wacce ta yi gangancin barin cikn gidan iyayenta ta bijire musu ta zaɓi ta yi nisa da su har tsautsayi ya sanya ta sako ƙafafunta cikin harkar bariki sai dai a fitar da gawarta ba daidai ta sauya sheƙa ba". Kalamanta suka sanya ni faɗa cikin tunani mai zurfin haske sai na ɗau wasu mintuna kafin na magana a hankali. "Ki na nufin matan cikin gidan nan ma duk Hajiya Babba ta kafe su ke nan? Ko suna son barin wannan harkar ba za su i ya ba?". Maimakon ta amsa mini sai kawai ta fashe da dariya mai matuƙar sauti har tana shiɗewa ta kwanta akan katifar tana dariyar. Na tsaya kawai ina ta kallonta cikin al'ajabi da mamaki. "Ki gwada ƙoƙarin fita ki ga ni sai ki zo ki ba wasu labari". Ganin ta mayar da abin shiririta ya tursasa mini yi wa bakina linzami sai dai giyar mamaki da al'ajabin da zantukanta suka shayar da ni bai sake ni har yanzu wannan lokacin. Jiya ina jin hayaniyarku da Shaaqana ikon Allah. Kin yi min daidai don tun kallon farko da na yi wa yarintar na ji ba ta kwanta min a cikin rai ba, ita ba kyau ba, ita ba kyakykyawan sura balle giri haka nan babu murya mai daɗin sauraro uwa uba ga duhun fata tamkar bayan tukunya". "Ta kai ni maƙura ne amma ni ma hakan ba halina ba ne". "Ai babu abin da bariki ba ta saka mutum ya yi duk wani halin da bai kasance naka ba dalilin bariki da rayuwar jikinta, za ta sanya ki fara ɗabi'antuwa da shi ba tare da ita ma kanta ta sani ba. Kin ga bariki da kike gani kike raina wa awwbillahillazi babu abin da ba zai sa mutum ya yi ba, take za ki rikiɗe ki soma sauya launi tamkar hawainiyya". "To Allah ya kyauta". "Amin". Ta amsa da shi a taƙaice tana tashi ta zauna daga kwanciyar da dariyar da take yi ya tursasa mata yin sa. "Yanzu dai za ki raka ni kasuwar ne ko ƙaƙa?". Ta ɗan yi shuru kafin na yi tunanin abin da zan faɗa"sai dai mu yi wani abu ki ba ni gishiri na ba ki manda". Ta bi ni da ido"yi min yadda zan ga ne". "Zan raka har sai kin gama duk siyayyar da za ki yi ko da kuwa za mu kai dare a can. Amma ni ma fa za ki taimaka mini ta wani fannin don cimma wani daɗaɗɗan burin raina". "Wani buri ne wannan haka? Kuma ta wani hanya zan iya taimaka miki?". Na gyara zamana kafin na hau zazzago mata bayani ina zuba tamkar bishiyar magarya. "Akwai wani mutumin da nake son ko ta wani hali ne na gan shi ya ganni ko da kuwa na minti guda ne. Sai dai kasancewarsa babban mutum kuma mai kima da daraja a idanun mutane hakan yana neman ya gagare, idan har kika taimaka mini ki ka yi mini hanyar ganinsa kin gama yi mini komai a cikin rayuwar nan". Cike da zaƙuwa ta ce"wane mutum ne haka?". "Sunansa Sheikh Dawood Gaskiya dokin ƙarfe, amma na ji a garin nan ana ce wa da shi ba baƙin balarabe". Tun kafin na gama zancen ta waro idanu waje tare da dafe ƙirji"anya kanki ɗaya kuwa kin san abin da kike faɗa? Duk da ban cika sauraron wa'azi da halattar inda ake faɗin Allah ya ce Annabi ya ce ba, tabbas wannan sunan ba ɓoyayye ba ne ga kunnuwan kowa da yake cikin garin na babba da yaro. In ban yi ƙarya ba a iya sani na shi ɗin babban Malamin addini ne da aka yi masa shaidar dukkanin halaye da ɗabi'u na ƙwarai. In kin haɗu da shi me ye za ki ce masa ke kuwa?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na soma kora mata bayani daki-daki ban ɓoye mata komai tun daga farkon haɗuwarmu na kwashe na sanar da ita. Ta yi shuru tamkar mai nazarin wani abun kafin can ta ce"to ke yanzu ta ina za ki fara neman sa? Sannan in kin yi dace kin gan san ma me ye za ki ce da shi har ki ja ra'ayinsa? Wallahi da gwamma garin nan kika yi wannan alwashin akan sa sai na ce da ke hakan zai ya fi miki sauƙi n akan wannan da kika yi". "In dai har na gan sa ɗin to haƙiƙa na yi mai wuyar". Ta yi shuru tare da zabga tagumi tana kallona kafin ta ce"tabbas ba ki da hankali". Ta yi zancen tana ƙoƙarin tashi ta fita na yi hanzarin cafko hannunta. "Ina cikin hnakalina sai dai ku da kuke yi mini kallon zautacciya ku ya kamata a bincike ƙwaƙwalwarku. Ke dai inda taimakon da za ki iya yi mini kawai ki yi mini inda babu taimakon da za ki yi mini kuma to ki bi ni da fatan alkhairi". Sai da ta ƙare mini kallon tsaf irin kallon da mai hnakali yake yi wa zautacce kafin ta ce"ban san me ye zan ce miki ba Amatullah". Ta koma ta zauna kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya. "Taimako ɗaya zan yi miki shi ne na haɗa ki da wata mata da take ba ta sirrin mallaka da karkato da hankali mutum zuwa gare ka, shi ma kuma fa sai ku na garin ɗaya ta yadda za ku dinga haɗuwa har aikin ya ci". Na jijjiga kaina"ba na son na jawo hankalinsa ta hanyar asiri. In dai kawai in akwai hanyar da za ki yi ki taimaka mini ki yi amma ba wannan ba". Ta yi shuru na tsawon mintuna har sai da na karaya kafin can ta ce"na san otel ɗin da tawagarsa suke sauƙa idan suka zo gabatar da wa'azi a ciki garin nan, sai dai in daga nan za mu sama ƙarin bayani. Don na taɓa ganinsa sau ɗaya a otel ɗin lokacin da ya zo gabatar da wa'azi a cikin tsakiyar watan Ramadana. A lokacin an ce babu yadda mai martaba Sarki bai yi da shi ba akan ya sauƙa a can masarautar amma ya ƙi a lokacin har Gwamma sai da ya saka ba ki amma bai amince ba, dalilin hakan ranar aka yi kora a otel ɗin babu wanda aka ba wa ɗaki sai shi da tawagarsa". Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina hamdala a cikin zuciyata. Farin ciki ƙarara ya bayyana a bisa fuskata da har sai da na kasa magana. Sai da na yi da gaske na sama zarafin faɗin"to yanzu yaushe za mu je mu tambaya masu otel ɗin?". "Mu je ina otel? Ce miki aka yi haka siddan ake zuwa otel ɗin a soma tambayan ma'aikatansu bayanan kwastomominsu? Ai hakan ya saɓawa ƙa'idar ko wani irin aiki kawai taɓarɓarewar ƙasar nan ya jawo haka. Yanzu dai akwai wani da na sani ma'aikaci ne a otel zan tuntuɓe mu ji abin da zai ce". "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Na yi zancen ina rumgume ta tsam a jikina tsabar murnar da ta soma ni a cikinsa kacokam. Mun ɗan tattaunawa da ita kafin mu farga har aka yi ƙiran sallan magrib hakan ya tursasa masa haƙura da zuwa kasuwan sai gobe. Har na tashi zan fita na ce"yau na girki ne?". Ta murmusa kafin ta ba ni amsa da faɗin"yau ina da fitan dare shi yasa ban yi girki ba". "Fita zuwa ina ke nan?". Ta yi fari da idanuna kana ta furta"na yi wani sabon kamu ne ina so na je mu ƙarƙare ta da shi. Na fi so na gama da kowa kafin na yi wannan gyara jikin don idan na yi san na fi son Ogana ya fara shan romonsa". Na bi ta da kallo ina mamaki da juyayin furucinta. "Ai kuwa ba ki yi masa mai kyau ba a Ogan nakin, tun da kin kasa killace masa kanki a shi kaɗai". Ina gama zancen na fice daga cikin ɗakin ina jin dariyar zancen nawan da ta fashe da shi yayin da nake fita daga cikin ɗakin. Sai da na yi alawan sallan magrib kafin na shiga ɗaki, na gabatar da sallan cikin nutsuwa da daidaituwa bayan na iddar na ɗaga hannuna sama da zummar zan yi addu'a ina buɗe bakina kawai na ji wani kuma ya ƙwace mini. Jikina har wani karkarwa yake yi tamkar ana jona mini wutar lantarki, na haɗa kaina da gwiwa ina rero kukan don na gaza samun ikon sarrafa kaina. Sosai nake kukan har sai da gabaɗaya jikina ya ɗauki zafi gau. "Indan kin gama kukan sai ki tashi je Hajiya Babban tana ƙiran ki da gaggawa". Na tsinkayo muryar an yi zancen cikin ɗaga amo, ko da na ɗaga ido har an juya an fita daga cikin ɗakin, da ƙyar na tashi na tsaya akan ƙafafuna sa boda rawar da ilahirin gaɓoɓin jikina yake yi. Haka kawai na ji ƙirjina yana buga wa sa boda na san babu alkhairi a cikin dukkan ƙiran da Hajiya Babba za ta yi maka. [12/11, 3:18 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 6️⃣6️⃣ Jikina a sanyaye tamkar wacce aka zare wa laka daga cikin jikinta. Muryata can ƙasa na yi sallamar yayin da nake shiga cikin ɗakin Hajiya Babba sai da na yi baki huɗu ana biyar ɗin aka amsa mini tare da ba ni iznin shigowa, na shiga na zauna a ƙasa yayin da ita take bisa kujera tana latsa wayarta na gashe ta a amsa mini ba tare da ɗago kai ta kalle ni ba. "Hajiya an ce kina nema na". Sai da ta salwantar da wasu mintuna kafin ta ce"e daman ƙiranki na yi na yi inda muka kwana da zancen nan nakin. Ya kamata zuwa yanzu mu san matsayar mu mu kuma san inda za mu ɗaura idan muka tashi". Sai da na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya mai nauyi kafin na sama zarafin faɗin"Hajiya in sha Allah kwana kusan nan zan zo miki da magana mai ƙarfi. Ina ta yin iya ƙoƙarina ganin ban ba ki kunya ba...". Tun kafin na rufe bakina ta doka mini tsawan da sai da ta tursasa mini runtse idanuna. "Ki rufe min baki ba dogon surutu na ƙira ki ki yi min ba, na ba ki nan da wata biyu idan kika gaza aiwatar da abin da furta. A iya wa'adin wannan lokacin kike da damar da za ki yi duk wani abin da za ki yi idan kika wuce hakan ko da da awa guda ne tabbas sai na wulaƙanta ki kuma na wulaƙanci fiye da zatonki. Sannan na haɗa miki kayanki ki bar min cikin gidana". Cike da yarda da kaina na furta"in sha Allah ina sa ran kafin wannan lokacin ma na gama haɗa komai". Ta galla mini wani uban harara kana ta soma furzar da zancen da yake cikinta"ya rage na ki ki yi duk abin da kika ga ya fi dacewa da tsari da ginin rayuwarki. Ni dai na riga da na tsayar da magana a matsayina na mai gida kuma mai cikakken iko. Don ba zai yiyu na gina ɗakuna sa boda kasuwanci kuma ke ki zo ki tare a cikinsa ba tare da ki na tsinana komai ba". Cike da girmamawa na ce"in sha Allah". Ta ɗaga mini hannu alamar na tashi na ba ta waje haka na yi mata fatan tashi lafiya, jikina a matuƙar sanyaye na dawo cikin ɗakina kamar ruwa hakan na zube akan tabarmata ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Tunanai marasa kan gado da tushe suka soma ziyarta cikin kwamyanta da ta toshe wajen guda. Ji na yi ba zan iya jiran safiya ta yi ba sa boda yadda nake tsananin son magana da Zinariya, wannan dalilin ya tilasta mini tashi daga inda nake kwance na fito da zummar zuwa ɗakin Zinariya sai dai na hango ƙofar an garƙame shi da kwaɗo, murmushi mai nauyi na ja na fesar daga bakina tunawa da na yi cewar ta sanar mini za ta fita ba za ta kwana a gida ba. Dole ƙanwar naƙi na koma cikin ɗakin na kwanta ina ta tunanin mafita da hanya mai ɓullewa a gare ni, a haka har wani bacci mai nauyin gaske ya yi nasarar ɗaukarta. Sanyin asubahin da ake busawa shi ya na ratsa cikin jikina shi ya yi nasarar farkar da ni daga nauyayyen baccin da ya kwashe na tashi da ƙyar na je na yi alwala na zo na gabatar da sallan, nan inda na yi sallan na zauna na zabga wani uban tagumi yayin da tunani kala daban-daban suke ziyartar cikin kwanyanta a lokaci guda. Kyakykyawan ajiyar zuciya na sauƙe daidai lokacin da na ji an dafa kafaɗana na waigo a hanzarce don ganin wane ne, idanuna suka sauƙa akan fuskar Zinariya da yake ɗauke da maɗaukakin annuri fuskarta tamkar gonar auguda yayin da bakinta ya kai har kunne. "Kin dawo ke nan?". A jefa mata tambayar yayin da take haye wa kan tabarman ta zauna tana fuskan ta na. "Wai akan wannan abun kike kwana? Lalle ki na ƙoƙari kuma ki na rayuwar ƙunci. Wannan tabarman ai ba shi da maraba da kwanciyar ƙasa". Taƙaitaccen murmushi na yi kafin na ce"yaushe kika dawo? Akwai matsala fa". "Ƙarfe uku da wasu mintuna na shigo cikin gidan nan, na so na buga muku ƙofa ma sai kuma na fasa haka na yi kwanan farin ciki ina jin kamar garin Allah ba zai waye ba". "Me ya faru haka na farin ciki?". Ta ajiye mini wasu takardu akan cinyata kafin ta ce"kin ga wannan takardun da kike gani takardun tanƙamemen gida ne na beni a can cikin birnin tarayya". Na waro idanuna cike da mamaki ina juya takardar. "Ke kuwa waye ya ba ki wannan kyautar?". Ta yi fari da idanunta wanda izuwa yanzu na fahimci kamar hakan ɗabi'arta ne musamman a lokacin da take cikin farin ciki. "Fitan da na yi daren jiya ne aka ba ni shi kyauta, ko kuma na ce miki aka mallaka mini shi halak malak, na tabbatar yau wasu za su yi kwanan baƙin ciki a cikin gidan nan kuma da yardan Allah wannan shekarar ni ce wacce za ta lashe gasar zakaran gwajin dafin da Hajiya Babba take shiryawa a duk ƙarshen shekara". "Wacce gasa ke nan kike magana a kai?". "Wata gasa ce da Hajiya take shiryawa duk ƙarshen shekara, a cire wacce ta fi samun kyaututtuka, mu'amala da manyan mutane da kuma samun alkhairai. Wacce ta ciri tuta ita ce gwarzuwan wannan shekarar". Taɓe bakina na yi don wannan ba shi ba ne a gabana, wutar gabana ma kaɗai ta ishe ni ba sai na ƙara wa kaina wani nauyi da damuwar damuwa da waɗanda ba su san ina yi domin su ba. "Jiya Hajiya ta ƙira ta yi buƙac ta ji yanda ake ciki, na roƙe ta ta ba ni lokacin inda a ƙarshe ta ba ni watanni uku rak. Idan har wa'adin wannan lokacin ya cika ba tare da na cika alwashin da na yi to sai duk abin da ya faru ni na jaza wa kaina. Tun da daman an ce duk abin da ya sama shamuwa ta zargi watan bakwai". Ta ɗan yi jim alamar zantukan nawan ita ma ya caja mata kanta. Na riƙo hannunta na sanya cikin nawa kafin na ci gaba da cewa"yanzu ya ya kike ga za a yi?". "Gabaɗaya kaina ya kulle ban san abin da ya dace mu yi yanzu ba, amma ba ri na ƙira wanda na miki na sani a otel ɗin". "Yauwa don Allah ƙira shi mu yi". Ta ɗaga wayarta ta lallatsa kafin ta kara a kunnenta. "Mai gida kana wajen aiki ne?". Ban san wani amsa ya na ta ba na ji ta kuma ce wa"zan zo na same ke". Daga haka ta zare wayar daga kunnenta. "Tashi ku je?". "Ina za mu je?". "A gabanki fa na yi waya yanzu, otel ɗin za mu je mu same shi don ya fahimci mun ɗauki abin da muhimmanci sosai". Ta furzar da zazzafan iska daga bakina kana na ce"otel dai? Ki rufa mini asiri tun da uwata ta haife ni ban taɓa zuwa ko da cikin harabar otel ba kai ko wucewa ta gate din ban taɓa yi ba, balle har na shiga cikinsa". "Ke dalla! Ki kwantat da hankali mene ne a cikin zuwa otel ɗin?. Ke dai kawai ki tashi mu je ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba". Ta ƙare zancen tana riƙo hannuna maimakon na tashi sai na turje"kin san fa zan je wajen aiki". Ta galla mini wani uban harara tamkar idanunta za su faɗo ƙasa"idan ba za ki je ba ne ki fito fili ki faɗa min, ba sai kin tsaya ki na ta wani kewaye-kewaye ba Amatullah". Na ɗan yi shuru na wasu mintuna kafin na furta"shi kenan mu je mu amma don Allah kar mu daɗe". Ba amsa mini ba ta yi gaba ina bin ta a baya har muka fice daga cikin ɗakin. Muka fito bakin hanya ta tara mana abin hawa muka hau, tun da muka soma tafiyar ƙirjina yake bugawa da ƙarfi da ƙarfi ban sama sauƙi ba har sai da na ji an taka birki hakan ya ba ni damar cira kaina ina ƙarewa inda muka zo kallo. Sunan otel ɗin na karanta da aka rubuta da manyan baƙi, yana walƙiya da sauya kaloli daga shuɗi zuwa ruwan hoda. "Sarauta hotel". "Tabbas Saraute hotel ke nan fito mu je". Furucin Zinariya ke nan da ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na afka, sai da na dogon numfashi na fesar kafin na sama damar saƙalo ƙafafuna waje daga cikin napep ɗin kafin na fito da ragowar sauran gangar jikina. Na ƙare wa wajen kallo ganin yadda mutane suke ta hada-hada cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, maza da mata a cunkushe a waje guda manyan motoci ne suke da shige da fice a waje tamkar ana wani gagarumin taro. Duniya-duniya inji kwaɗo da ya ji shi a cikin ruwan zafi, tabbas Ubangiji shi kaɗai ya bar wa kansa ilmin sanin abin da gobe za ta iya haifar wa. Yau wai ni ce a cikin otel inda duk nake ban ta ko fa mafarki zuwa ba sai ga shi yau ƙaddara ta jawo ni idan tunanin bai taɓa tunanin kawo ni ba. Ganin yadda duk na rasa nutsuwata ya sanya Zinariya riƙo hannuna muka soma tafiya muka shiga ciki muka zauna a bisa wasu kujeru da aka tanada a wajen, ta ɗaga waya ta ƙira shi tare da sanar da shi cewar mun iso babu jima wa na hango wani mutum mai jiki ya nufo inda muke fari ne sol sannan yana da saje da kuma ƙasunba a bisa fuskarsa ya yi shigar ƙananan kaya ya sanya hular da ake wa laƙani da p-cap a kansa ya zo inda muke zaune ya zauna kusa da Zinariya, ya miƙa mata hannu suka tafa kafin ya ce"ina jinki don aiki nake yi na baro na zo na saurare abin da yake tafe da ke. Don kawai ke ɗin Zinariya ce". Da alama zantukansa sun yi tasiri a cikin zuciyarta da hakan ya sanya ta darawa sosai, har sai da sautin dariyar ya fita. "Ina miƙo dubun godiya ranka ya daɗe". Ya murmusa kafin ya ce"wannan cikar fa tare kuke da ita?". Ta gyaɗa kanta"e tare muke". Sai da ya musguta kafin ya ce"ina jinki gama maganarki don ni ma ina da nawa maganar da zan yi miki". Babu ɓata lokaci ta kwashe komai ta sanar da shi. "Mun zo ne mu ji idan a cikin kwanakin nan zai zo cikin garin ya sauƙa a otel ɗin. Na san kai kaɗai za ka iya yi min wannan abun shi yasa na zo har nan na same ka" Na ɗan yi jim kafin ya furta"gaskiya ba na tunanin ciki kwanakin Sheikh zai zo cikin garin nan wataƙila sai dai cikin azumi. Kin ga azumi kuma yanzu akwai aƙalla watannin huɗu zuwa biyar, amma in dai wani abun ya zo da zai shigo da shi cikin garin nan zan sanar da ke. Don kin san duk zuwan da yake yi garin nan ba ya yarda ya sauƙa a ko ina face cikin otel ɗin nan. Duk da kuwa yana da alfarma a wajen manyan mutane ciki har da mai Martaba da kuma shi kansa gwamna". Muka haɗa ido da Zinariya cike da tashin ƙwarin gwiwa, na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina sadda kaina ƙasa yayin da nake ci gaba da sauraron zancen da ya ɗaura da faɗin su. "Amma me yasa kuke son ganinsa a nan? Idan wani abun ne ai za ku iya zuwa can gidansa ko?". "Ba za ka gane ba ne Oga da dai za mu sama ganin sa a nan ɗin, sai abubuwan sun fi zuwa mana da sauƙi". "To shikenan in da ya zo zan yi ƙoƙarin sanar da ke. Mu je gefe mu yi magana ko?". Ya ƙarishe zancen yana kashe mata ido guda tare da rangwafo kansa daidai saitin fuskarta. Sai da suka miƙe tsaye kafin ta kallo ni ta ce"Amatullah bari mu yi magana da shi ki ɗan jira mu nan". Kaina kawai na gyaɗa mata don na kasa motsa bakina da nake jin ya yi mini nauyi ainun. Suka tafi suka bar ni a wajen ina ta saƙa da warwara a cikin raina. Kaina yana ƙasa na ji hayaniyar wajen ya ɗan ƙaru ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan fuskar Saif da ya tsaya cak yana kallona, muka tsaya muna kallon kallo ƙirjina ya ci gaba da bugawa tamkar zai bayyano waje. Mun ɗauki wasu mintuna mu na kallon juna kafin wani mutum ya iso inda yake. "Ranka ya daɗe baƙin sun iso haka nan ɗakin taron kowa ya zo, kai kaɗai ake jira". Kansa kawai ya jinjina masa ya yi gaba suka hau wani benin yayin da mutum ya bi shi a baya. Tashi na yi na rasa inda zan je da abin da ya dace na yi don gabaɗaya na rasa nutsuwata. Take jikina ya soma rawa zuffa ya soma jiƙa mini jikin kamar wacce aka juye wa bokatin ruwa. Ina ƙoƙarin fita na hango Zinariya ta nufo inda nake. "Amatullah na tarar da ke a tsaye?". "Ke dai kawai ki zo mu tafi. Don Allah mu bar nan wajen". Mamakin ganin yadda na rikice ya ƙi ba ta damar cewa komai, na ja hannunta muka fita daga wajen mu na fita muka sama abin hawa muka hau. A hanya take sanar da shi cewar ita fa daga nan ba gida ta nufo ba, don haka na ce wa mai napep ɗin ya sauƙe ni a hanya kusa da gidan Hajiya Muhibbat na ƙarisa da ƙafata sa boda ba nisa. Na tarar da Hajiya ba ta nan haka nan ma su Aryan ba sa nan wanda ina da tabbacin tare suka fita da Hajiyar, na shiga ɗakin Altine na gaishe ta amma ba ta amsa mini ba dole na fito don na san zaman cikin ɗakin ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba. Na nufi kicin na tarar da wanke-wanke jimgim har da na daren jiya da ya haɗe da na safiya na wanke su tsaf, na share kicin ɗin. Na fito na share falon kafin na ɗauko bokati da mopper na soma mopping cikin sanyi jiki tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri, ban ankara ba na ji hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina, na kai hannuna na share su ina ci gaba da aikin. Na kusa gama wa na ji an buɗe ƙofar falon an shigo kallon ɗaya na yi masa na ɗauke kaina sa boda yadda ya murtuƙe fuskarsa babu alamar annuri a tattare da shi, ya ƙariso cikin falon ya zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya. Sai da na tattaro jarumta na yafa wa kaina kafin na ce"sannu da dawowa ranka ya daɗe". Kamar yadda na yi zato bai amsa mini ba hakan ya ba ni damar ɗaukar bokatin zan fita ya dakatar da ni ta hanyar faɗin"wace ce ke? Da wani irin mungun nufin kika kutso kai cikin gidan nan?". Cak na tsaya jikina yana rawa tamkar ana jona mini mazari. [12/12, 5:53 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________ Page 6️⃣7️⃣ Ina jin takun takalminsa yana ƙara nufo inda nake tsaya da duk kusancin da yake ƙara wa da ni ina jin ƙirjina yana tsananta bugu tamkar zai fito waje. Na runtse idanuna a ƙoƙarin daidata nutsuwar da ya yi nisa da gangar jikina, jikina ya ci gaba da rawa tamkar wacce aka jona wa wutar lantarki, duk da idanuna suna a rufe amma ƙamshin sanyayyan turaren da ya bulbula a jikinsa shi ya ba ni tabbacin ya iso inda nake. "Wace ce, me yasa kika ɓoye ainihin wace ce ga Anty, me yasa kike da fuska biyu? Ki na nuna wa kamar ke ɗin mace ce mai nutsuwa da hankali bayan zahirinki ba hakan kike ba, karuwa ce ke wacce take rayuwa a cikin gidan karuwa da masu zaman kansu. Tun ranar da Anty ta kawo ki cikin gidan nan na sa a yi min bincike akan ki kuma an kawo min cikakken labarin rayuwarki, me yasa kika ɓoye wa matar da ta yarda da ke gaskiyar wace ce ke? Me yasa kika ɓoye wa matar da ta aikata miki a lokaci da kike tsananin buƙatar taimako ainihin kalarki? Ta yarda ta ke wannan dalili shi ya ba ta ƙwarin gwiwar kawo ki cikin gidanta, ka sakar miki tagarman kula da cikin gidanta da kuma ƴaƴanta. A wasu lokutan har su na shafe tsawon awanni tare da ke wanda ba sa yin rabin sa tare da ita sa boda yanayin aikinta da yake tursasa mata fita a cikin ko wani irin yanayi". Ya ɗan tsagaita kafin ya ɗaura daga inda ya tsaya. "Me yasa kika shigo cikin rayuwarmu? Waye ya aiko ki kuma nawa suka ba ki? Aikin tsawon wani lokaci za ki yi musu?". Ban san sa'ilin da hawaye suka fara wanke mini fuska ba, na buɗe lumshashshun idanuna da suka rikiɗe suka sauya launi zuwa launin ja, suka yi jajir da su har wani zafi da zogi suke yi mini. Ba tare da na sani ba bokatin da yake hannuna ya faɗi ƙasa ruwan da yake cikin ya malale a waje. A karo na farko da na yi jarumta jefa ƙwayoyin idanuna cikin nasa sai dai na kasa magana sa boda rawan jiki da kuma nauyin da bakina ya yi mini, su suka haɗu suka yi mini taron dangi na gaza aiwatar da komai. Ya cije leɓɓansa kafin ya furta"ba za ki iya cewa komai ba to ma ina karuwa take da kalaman kare kanta ko kuma ta wanke kanta? Amma tabbas ki tanadi kalaman da za ki wanke kanki da shi a gaban Allah don ba ki da wani hujjan zuwa bariki face son zuciyarki da kike biye wa har ya kai ki zuwa cikin halaka". Zafin da kalamansa suka yi mini ya sanya ni toshe kunnuwana da tafukan hannayena. "Ya isa haka na ce ya isa". Na yi zancen cikin sarƙafewar harshe da rawar murya. "Bai isa ba na ce bai isa ba. Kin cutar da rayuwarki a shekarunki har kin san ki iya zuwa cikin otel". "Ya ishe ka". Na yi zancen cikin zafin rai da ɗaga amo, tar na buɗe idanuna tare da nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata, jikina har izuwa lokaci bai bar rawa haka nan hawayen da suke kwaranya daga koramar idanuna ba su daina gudana ba. "Ka na tunanin Bawa yana da damar tsarawa kansa irin rayuwar da ta dace da shi ne? Ka na zaton cewa akwai wanda zai zo rayuwarsa ta lalace tun daga tushe sannan duhu ya mamaye hasken da ya zamo masa sandan jagora? Na san ka na da ilmi don ba ba ka yi zubin jahilai ba sai dai ilmin bai yi maka amfan tun da ya kasa samar maka da amshoshin mungayen kalaman da kake jifa na da su, ilminka bai tsinana maka komai tun da bai hana ka zartar da hukunci akan abin da ba ka da tabbacin akan sa ba. Ka sa an yi maka bincike akaina sai me ye na ce sai me ye? Me ye haka ya tsinana maka sannan ta ina hakan ya amfane ka?". Sai da na yarce hawayen da yake tsintiri a bisa kuncina kafin na sama zarafin ci gaba da maganar cikin raunin da yake fitowa kai tsaye daga ƙasan zuciyata. "Na ji na yarda binciken da ka yi a kaina ya kawo maka shi daidai, a cikin gidan karuwai nake rayuwa amma shin ka damu da binciko dalilin da ya yi silar zuwa na cikin gidan har nake rayuwa a cikinsa?. Na yarda zaman kaina nake yi ba na tare da iyayena, ƴan uwa balle kuma dangi. Babu wani wanda zai ƙwabe ni idan na yi ba daidai ba balle kuma wanda zai dawo da ni kan turba a sanda nake ƙoƙarin kauce hanya, amma shin ka binciko dalilin da ya sa na zaɓi na yi irin wannan rayuwar? Me yasa ba ka sa an binciko mana yadda na gudanar da rayuwata ta baya ba?. Ka taso a cikin gata ka sama duk wani kulawa, tattani tare da riritawar da ko wani ɗa yake samu a zamanin ƙuruciyarsa, ka ci abinci mai kyau, ka sha abin sha mai kyau, ka kwanta a waje mai kyau sannan ka sama ilmin addini da na zamani a makarantar da kulawa ya wadata. Ka rayu da kulawar iyaye da kuma dangi waɗanda da ka ce wash za su tambaye dalili, sannan ba sa bari hawaye ya zuba daga idanunka kafin ka nema an tanada maka shi ta ina hankali da tunaninka zai sarrafa mata cewar akwai waɗanda ba su sama kwatankwacin irin gatan da ka samu ba. Ban taso da irin wannan gatan ba ranka ya daɗe amma mahaifina bai bar ni na taso cikin rashin tarbiyya ba, haƙiƙa ya wadata ni da ilmin addini da ya kai matakin har na hadda alƙur'ani mafi girma da daraja a cikin dukkan littattafan da Ubangiji ya sauƙe wa Annabawansa". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na sama lasisin ci gaba da amayar da zancen, idanuna suna hasko mini abubuwan daki-daki tamkar yanzu suke wanzuwa. "A zamanin rayuwata ta baya na yi shura na ɗaukaka ta yadda duk wata uwar da za ta yi ɗiyarta faɗa da nusar da ita akan ta guji ruɗi da ƙyale-ƙyalen cikin duniya da ni Amatullah take buga mata misali. Na rayuwa a matsayin kamilar mace, mai nutsuwa, mai tarbiya, wacce hankali ya ratsa jini da jijiyoyin jikinta, mace wacce ta san kanta. Wacce babu wani abun duniya zai ruɗe ta ko kuma ya sauya mata tunaninta da yadda takr hango abubuwa, ana tinƙaho da ni a cikin unguwa yayin malamaina a makaranta su na alfahari da ni kafin guguwar ƙaddarar dake sarrafa rayuwata ya jijjige kyakykyawan tarihin da na kafa tun daga tushe. Lokaci guda ya shafe duk wani aikin alkhairin da na rayu a kansa ya shafa miji baƙin fentin da zai bibiyi rayuwata har ranar da numfashi zai yi ban kwana da gangar jikina. Na ja wa dangina abin kunya na tozarta iyayena mussamman mahaifina ya kai munzalin da har wasu suke tantama tare da sanya shakku akan tarbiyyar da ya ba ni. Idan ka san mafari ba ka san ƙarshe ba don haka kar ka ƙalubalence kowa a bisa rayuwar da ka ga yana yi ba tare da ka zurfafa bincike ka kuma ji ta bakinsa ba. Danganta ni da kalmar karuwa da ka yi kuma za mu yi hisabi da kai a ranar da ake wa tare da Yaumul tagabum ranar da Allah zai haɗa Bayinsa tun daga zamanin kakanmu Annabin Adamu har zuwa zamanin ƙarshe". Ina dasa aya a zantukana na sunkuya na ɗauki bokati da moppern na yi shigewa ta cikin kicin na bar shi tsaye a wajen. Ina shiga cikin kicin ɗin na mayar da ƙofar na rufe tare da jingina jikina a jikin ƙofar, sannu a hankali na soma sulale wa ƙasa har sai da na yi zaman ƴan bori dirshan a ƙasa. Hawayen da suke gudana a idanuna suka ci gaba da zuba tamkar da bakin ƙwarya duk yadda na so na yi karanto wani yanki daga cikin addu'o'in da na haddace a cikin kwanyata, lamarin ya faskara komai ya gagare ni aikatawa. Haka na cigaba da kukan mara sauti illa zafi, radaɗi da kuma zogi a cikin raina. Da ƙyar na tashi na je na ɗauko mopper da tsumma kana na ɗaukin bokatin na buɗe ƙofar kicin ɗin na fito da zummar gyara inda ruwan ya zube. Ina fitowa idanuna suka sauƙa akan fuskarsa yana zaune akan kujerar zaman mutum biyu ya kwantar da bayansa a jikin kujerar, ya lumshe idanunsa tamkar mai bacci. Sai dai tun daga kallon farko da na yi masa na fahimci cewa ba bacci yake yi ba a farke yake. Ban b ta kansa ba na soma yin aikin da yake gabana na saka tsumman ina tsame ruwan wajen ina matse wa a cikin bokati sai da na tsame ruwan tas, na sama mopper na goge wajen. Na ji wani jiri ya na ɗiba na tare da ƙoƙarin kayar da ni ƙasa sai da na dafe jikin kujera kafin na iya tsaya wa akan ƙafafuna da suke rawa alamar sun gaza ga ɗaukar nauyin gangar jikina. Numfashina ya soma harɗewa waje guda jikina ya ɗauki zafi gau tamkar garwashin dake ƙasa tukuban tsire. Duk wani karatun da ya fara ziyartar ƙwaƙwalwata shi bakina ya soma karantawa ban gushe ina yi ba har sai da na ji wani sanyin nutsuwa ya ziyarci sashin ruhina, ƙarfi ya ziyarci sakakken gangar jikina da ya sake tamkar ƙanƙarar da aka jefa a cikin ruwa. Na cije leɓena yayin da nake ƙoƙarin tashi sai dai na kasa hakan sa boda nauyin da gangar jikina ya yi mini. "Ki na lafiya kuwa?". Na tsinkayo amon muryarsa tamkar daga sama ya sauƙa na'urar naɗan sautina, lamarin da ya sauƙar mini da wani karsashi a ciki jikina. Ban san lokacin da na tashi na tsaya tsam akan ƙafafuna ba, ban ko kalla inda yake ba balle na tanka masa na ɗauki abubuwan da na yi amfani da su na koma kicin ɗin na fita ta ƙofar baya na shanya tsumman akan igiya kana na dawo na fito. Idanuna har wani baƙin duhu suke gano mini da ƙyar na kai kaina cikin ɗakin Altine ina tura ƙofa na hange ta tsaye ta riƙe ƙugu tana fuskantar ƙofar shigo wa. Ban bi ta kan ta na ɗauki sallaya zan shimfiɗa don na kwantar sa boda ciwon kai da jirin da nake ji, ta yi wuf ta wafce sallayan daga hannuna. "Allah ya kiyaye Karuwa wacce take zaman kanta ta ɗaura wani sashin jikinta, akan sallayan da nake yin ibada a kansa". Na yi ƙuri da ido ina kallonta sai dai bai ko kaɗan ban yi mamakin furucinta ba, don ina da tabbacin in dai tana cikin gidan ɗazun dole ta ji kuma ta san abin da ya faru. Waje na nema zan zauna a ƙasa na ji an ture ni har sai da kaina ya bugu da jikin ginin ɗakin, wani zafi ya ratsa har cikin kwanyata. Na cira kai ina duban ta tare da sauraron zantukan da ta ɗaura da faɗinsu. "Kin yi asara kin ji kunyar duniya da kuma lahira. Ashe duk kallon da ake yi miki kura ce lulluɓe da fatar akuya, ashe lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi. Wallahi kin yi asara har yawon otel-otel kike yi da ƙartin maza, in sha Allah daga rana mai kamar ta yau zamanki a cikin gidan nan ya zo ƙarshe don sai na tone asirin da kika haƙa rami kika burne shi a gaban Hajiya da kowa da kowa a cikin gidan nan". "Allah ya ba ki sa'a". Na furta a taƙaice sa boda ba zan iya dogon magana ba balle na sama ƙwarin gwiwa, nutsuwa da kuma kuzarin yi mata bayani sala-sala. Na zauna tare da kifa kaina da gwiwa ina sauƙe ajiyar numfashi akai-akai, ban yi aune ba na ji a finciko hannuna tamkar za ta tsinke sa daga jikin gangar jikina. Cak ta miƙa da ni akan ƙafafuna ta finciko ni zuwa waje ja na take yi tamkar dabba duk da ina cijewa tare da turjewa lamarin ya fi ƙarfina. Ba ta sake ni ba har sai da ta fito da ni harabar gidan ta yi jifa da ni gefe guda na faɗi ƙasa akan gwiwan hannuna. Daidai lokacin da motar Hajiya Muhibbat ta shigo cikin gidan, har ta gama daidaita parking ban ɗago kaina ba sa boda azabar zafin buguwar da na yi a hannuna har na ji hannun ya sake sosai, ina jin shi tamkar bai kasance ɗaya daga cikin wani ɓangaren gaɓoɓin jikina ba. "Altine lafiya na gan ku a nan?". Muryar Hajiya ya ratsa ƙofofin kunnuwana da hakan ya ba ni damar ɗago kaina, kafin Altine ta ba ta amsa Saif ya iso wajen a hanzarce. "Me ye yake faru wa?". "Ina ka ga yanzu shigo wa ta na tarar da su a haka. Me yake faru wa Altine ki yi mana bayani me ye Amatullah ɗin ta yi na ga kin jawo ta waje haka? Wani abun ta ɗauka ko kuma kama ta kika yi laifin ha'inci?". "Hajiya ai gwara sata akan munin abin da ta aika". "Me ye ta aikata?". "Hajiya ashe wannan yarinar karuwa ce, a cikin gidan karuwai da ƴan daudu tambaɗaɗɗun mutane da suka kwashe kayansu daga zauren Ma'aiki take rayuwa". Cike da mamaki Hajiya ta ce"Karuwa kuma Amatullah ɗin?". "Ƙwarai kuwa ranki ya daɗe, ai ba a ƙarya kusa da gida ga ta nan ki tambaye ta idan ƙarya nake yi mata ko kuma na yi kuskure cikin maganganuna". Altine ta yi furucin cike da ƙwarin gwiwar da ya gauraye da karfin hali da zumuɗin bankaɗo sirrina. [12/13, 12:57 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _____________________________________ Page 6️⃣8️⃣ Cike da ruɗu Hajiya Muhibbat ta ce"wani irin magana kike faɗa haka Altine? Anya ki na cikin hankali da hayyacinki kuwa? A ina kika ji wannan maganar?". "Hajiya ina cikin hayyacina sannan hankalina ma yana nan tare da ni har ki yi imanin cewar wai ba na cikin hayyacina. Da kunnena na ji Yallaɓai Saif yana tuhumarta akan wannan zancen, kuma shi ma ya san da wannan zancen ga shi a tsaya ki na da damar da za ki tambaye shi idan har ba ki yarda ba". "Saifullah me ye gaskiyar abin da Altine take faɗa? Shin da gaske ne Amatullah karuwa ce kuma zaman kanta take yi a cikin gidan karuwai da ƴan daudu?". Runtse idanunsa ya yi yana cije leɓansa tare da zuba hannayensa cikin ajihun wandon farin shaddan da yake jikinsa. "Kai nake sauraro Saif". Maganar da ta yi a karo na biyu ya sanya shi buɗe lumshashshun idanunsa muryarsa can ƙasan maƙoshinsa ya soma maganar a hankali. "Anty haka ne a cikin gidan karuwai take rayuwa amma akwai wani abu guda wanda ba mu san da shi ba......". Ban bar shi ya ƙarisa ba ta yi wuf na amshe zancen yayin da nake tashi tsaye daga faɗuwar da na yi akan hannuna. "Kar ki tsawaita bincike a kaina Hajiya don ina da tabbacin binciken ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba, babu komai a cikin tarihin rayuwata face ƙunci, tashin hankali da kuma ruɗani. Ƙaddarar rayuwata ta bambanta da na ko wacce yarinya mai irin shekaruna. Tun kafin na yi girman bambamce tsakanin fari da baƙi na san mene ne baƙin ciki kuma na san ɗanɗanonsa, babu kuskure a cikin dukkan abin da Altine ta faɗa tabbas haka ne a cikin gidan karuwai nake rayuwa kuma zaman kaina nake yi ba a gaban iyayena, ƴan uwa ko dangi nake ba gashin kaina nake ji babu kwaɓa babu mai tsawartawa balle wanda zai kama hannuna ya ɗaura ni a hanyan da take daidai. Sai dai tun da nake ban taɓa aikata zina ban taɓa kusantarsa sai dai na yi imanin cewa dukkanin wani Bawa ba ta taɓa wuce ƙaddararsa". "Babu wani mai hankalin da za ki faɗa wa wannan maganganun ƙanzon kuregen nakin ya yarda da ke. Ta ya ya za a ce kin rayu a cikin tsakiyar karuwai ba tare da ki na aikata abin da suke yin ado da shi ba, to in ma haka ne ba ki aikata ba ɗin me ye kike zaman kanki?". Na runtse idanuna da hakan ya ba wa hawaye. Da sur ciki mini kurmin idaniyata damar kwaranya, ina jin wani zafi a cikin raina tamkar ana watsa mini tafashashshen ruwan dalman da ba sirka shi da komai ba a cikin farfajiyar ƙirjina. "Ban faɗa don neman yardarki ba sannan ban damu da ko wani irin kallo za ki yi mini, Abu ɗaya na sani kuma a kansa zan tsaya har ƙarshen rayuwata shi ne iya gaskiya ta na faɗa muku. Hajiya ina mai ba ki haƙuri akan ɓoye miki gaskiyar wace ce ni da na yi har tsawon wannan lokacin, haƙiƙa a ɗan zaman da na yi da ke na ga zallar ƙauna da tausayinki a gare kwance a cikin idanunki. Ban yi hakan da wani nufi ba kuma Allah shi ne shaida ta akan hakan.....". "Ya isa haka ya isa Amatullah". Hajiya Muhibbat ta dakatar da ni ba tare da na gama amaryar da zancen da yake kan harshena ba. "Mai zaman kanta? Kin san ma'anar wannan kalmar kuwa Amatullah? Kin ba ni mamaki matuƙar ina miki kallon mai hankali da nutsuwa wacce ba ruwanta ashe kallon biri nake yi miki ki na yi min na ayaba. A ƙananun shekarunki har kin san ki sanya ƙafa ki baro cikin gidan iyayenki ki zo inda ba ki san kowa ba kuma ba wanda ya san ki ki fara zaman kanki. Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Wace iriyar rayuwa ce muke rayuwa a cikin ta haka? Me yasa masifu da bala'i kala-kala ba za su baibaiye al'ummar mu ba?". Ta tsagaita tare da yarce ruwan ƙwalla da ya zubo daga idanunta kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya. "Daga yau ba na son na ƙara ganin ki a kusa a gidan nan balle kuma ki tsaya a jikin gidan nan, na sallame ki ki ƙara gaba niyyar da taimakon da na yi Allah ya ba ni ladan niyya ke kuma idan mai shiryuwa ce Allah ya shirya ki. Ga kuɗin aikinki". Ta ƙare zancen tana zige jakarta ta ciro wasu kuɗaɗen da ko tsaya wa ƙidaya su ba ta yi ba, ta watso mini su a fuskana. Hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa dandamalin kuncina na cira kai na dube ta sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin na sama zarafin magana. "Duk magangunin akan turban gaskiya kike amma ke ma ina son na sanar da ke wani abun da ba ki sani ba. Kamar yadda rayuwata take cikin hatsari haka ke ma ta ki rayuwar da ta ƴaƴanki take cikin hatsari sanadin yarda da amincin da kika ɗaura akan mutane guda biyu da kike ganin sun fi kowa kusanci da ke a cikin wannan duniyar". Na ƙara taku uku na matso kusa da ita sosai da tun da na soma maganar take bi na da kallo cike da maɗaukakin mamaki da ya haɗu da al'ajabi. Kafin na yi magana ta ri ga ni. "Wasu mutane biyu kike magana a kai?". Na saki wani bushashshiyan dariyar da ba ta da alaƙa ta kusa ko ta nisa da nishaɗi kafin na furta"mutum na farko shi ne mijinki wanda a tsakanin gobe da jibi zai shigo cikin ƙasar nan ba tare da saninki ba, kuma ina da tabbacin har ya zo ya koma ba zai nema inda kike ke da ƴaƴanki ba. Sannan mutum na biyu ba kowa ba ne face Altine ƴar aikin da kika riƙe tamkar ƴar uwa kika busa mata iskar ƴancin yayin da ita kuma take amfani da yardar da kika yi mata take cutar da ke, ke da ƴaƴanki". Na ƙare zancen ina yi mata nuni da Altine da ƴar manuniyar ƴatsata. Ban gama rufe bakina na ji sauƙar wani gigitaccen mari a bisa kuncina har sai da na soma ganin gilmawar baƙin duhu a cikin idanuna, na yi tangal-tangal zan faɗi da ƙyar na iya sarrafa kaina na tsaya akan ƙafafuna. Ta cakomo wuyar hijabina ta riƙe tamau. "Ke har me ye kika sani akan mijina da za ki faɗa wannan maganar akan sa? Sannan yaushe kika zo cikin gidan nan da za ki gaya min wace ce Altine? Babu wani halinta wanda ban sani ba ta kai ta kawo ko ba ta furta magana da bakinta ba ina ya fahimtar abin da take nufin. Ina kika sama ƙwarin gwiwar nan?". "Tabbas ban san mijinki amma a yanzu na san abubuwan da ke ma kanki ba ka sani ba game da halinsa. Idan ba ki yarda da abin da nake faɗa ba za ki iya samunsa ranar juma'a a babbn otel ɗin da ke cikin garin Abuja. Batun Altine kuma za ki iya tambayar ƴaƴan idan tsoro bai hana su faɗa ba". Mamakin furucina ya sanya sakar mini hijabina da ta riƙe. "Saifullah ka kawar min da yarinyar daga gabana, tun kafin zuciya ta ɗebe ni na lahanta ta na kashe banza na kashe wofi. Ba na son na buɗe idona na gan ta a gabana". Sai a lokacin Saif ya yi magana da tun ɗazu yake tsaye a wajen yana bin mu da kallo ba tare da ya ce uffan ba. "Anty don Allah ki kwantar da hankali, mu saurare abin da za ta ce wataƙila mu dace da wani ilmin da mu kanmu ba mu san shi ba". "Saif babu wani mahalukin da zai tsaya a gabana ya sanar da ni wani hali na Saddam wanda zai Muhibba ban san shi ba, a cikin tsawon zaman da muka yi da shi. Balle kuma Altine duk ranar duniya take muke kwana mu tashi a cikin gidan nan, ka fitar min da yarinyar nan daga cikin gida". Cikin in-i-na Altine ta ce"wallahi ƙarya ma take yi min ba ni da wani mummunan halin da na ke ɓoye miki shi". Cikin ba da umarni Saif ya ce"Altine ɗauki su Aryan ki shiga ciki da su". "To ranka ya daɗe". Ta amsa da shi cikin bin umarni da girmamawa, ta kwashe su Aryan suka yi cikin gida. Zai yi magana na tar numfashinsa. "Zan fita ba sai ka fitar da ni ba, Hajiya ko ba ki ce da ni kar na ƙara zuwa cikin gidanki ba ni ma daman ina da niyyar sallamar kaina daga wannan aikin, sai dai ina mai ba ki shawara da ki nutsu ki yi nazarin abubuwan da na sanar dake yanzu. Ko ba daɗe ko ba jima watarana za ki neme ni ki kuma gode mini". Tas na ji ta kuma ɗauke ni da wani marin mai matuƙar sauti a karo na biyu. Na kai hannuna na dafe kuncina ina cije leɓena sa boda zafin marin da ya ratsa har cikin ƙoƙon kaina ya kuma raunana ƙarfin jiki da zuciyata. "Na gode ranki ya daɗe, na gode bisa halin girma da karamcin da kika nuna mini". Ina dasa aya a nan na sunkuya na kwashe kuɗin da ta watsa mini don na san su ɗin haƙƙina, na raba biyu na ɗauki ɗaya na damƙa mata ɗayan. "Na ɗauki iya haƙƙina ga ragowar dukiyarki". Ban jira abin da za ta ce mini ba na fi tafiyata ina tafe hawaye duk yadda na so sarrafa kaina wajen ganin na tsayar da ruwan hawayen da yake kwaranya daga kurmin idanuna lamarin ya gagare ni. Na buɗe ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin zan fita muryar Baba Mai Gadi ta tilasta mini dakatawa. "Ƴar nan kar ki tafi ba tare da kin warware min ƙullin zantukan da na ji ku na musayarsu ba. Shin da gaske ne abin da Altine ta faɗa akan ki? Da gaske ke ɗin karuwa ce kuma zaman kanki kike yi?". Sai da ya yarce hawaye da suke tsare-tsare a kuncina kana na ce"e Baba duk abin da ka ji haka yake, zaman kaina nake yi a garin nan sannan a cikin gidan karuwai nake rayuwata". Ina gama faɗin haka na fice daga cikin gida fita irin wacce ba na fatan ko a cikin mafarki na dawo, fita irin wacce babu waiwaye har abada balle dawowa. Fita ita wacce take datse ko wani irin alaƙa da mu'amalar da aka ƙulla komai ƙarko da daɗewansa. Sai da na yi nisa na nema ƙasan wani bishiya na zauna na ci kuka na yi kuka na zubda ƙwalla tamkar raina zai fita. Komai ya fita daga cikin kaina na rasa inda zan nufa na ji daɗi da sanyi a cikin raina. Duniyar da abubuwan da suke cikinta gabaɗayansu suka daina burge ni balle su ba ni sha'awa. Ba don ilmin addini da nake da shi wanda ya yi matuƙar tasiri a gare ni har yake bayyana kansa cikin aikina ba, da kuma hukunci da azabar da na san Ubangiji ya tanada ga duk Bawan da ya kashe kansa ba da babu abin da hana ni shan guba ko kuma na rataye kaina, na huta ba. Zafin ranar da yake duka na shi ya tursasa mini tashi daga wajen ba domin na gaji da kukan da nake yi ɗin ba. A tashi na ci gaba da tafiya ina tafe ina haɗa hanya tamkar ƴar mayen ta sha abubuwan gusar da hankali ta bugu ta yi tatil. Ikon Allah ne kawai ya kawo ni gida ba domin na san inda kaina yake ba, balle ina nake cilla ƙafata a buɗe na tarar da ƙofar ɗakin da hakan ya tabbatar mini da cewar Sha'awanatu tana ciki, ina shiga na gan ta zaune tana latsa waya ta kuna kiɗa tamkar za ta ɗaga ɗakin, mu na haɗa ido da ita ta kashe kiɗa ta soma bi na da kallo har na je kwanta akan tabarmata. Na dafe kaina ina ta murtsukuku sa boda tsananin azabar ciwon kan da ya rufe ni lokaci guda ko buɗe idona ba na ƙaunar yi balle na ga haske, ina jin Sha'awanatu na tambayata ko lafiya na yi banza da ita ba tare da na tanka mata ba har ta yi ta gaji ta koma ta ci gaba da harkokinta. A daddafe na fito na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallan zuhur ina shafa addu'ar da na yi na tsinkayo muryar Zinariya ta na faman ɗura ashariya a tsakar gidan, wanda ban zan da wanda take yi ba. Na yi wuf na tashi na fito daidai lokacin da ta buɗe ƙofar ɗakinta ta shiga na bi bayanta, ta waigo tana kallona. "Har kin dawo ke nan yau da wuri haka?". Maimakon na ba ta amsa sai kawai na tuntsire da kuka har jikina yana rawa. Ta saki ledodin siyayyar da ta yi a kasuwa suka faɗi ƙasa ta riƙo hannuna muka zauna. "Kukan me ye kike yi Amatullah? Sanar da ni abin da yake faruwa?". Ban yi ƙasa a gwiwa ba na kwashe duk abin da ya faru na sanar da ita. Sai dai ban fayyace mata cewar Hajiya Muhibbat ita ce matar Saddam wanda take yi wa take da Oganta ba. "Kan bala'i bura uban can. Yau ina ga ni wani zallan rainin wayo da ɗiban albarka. Kuma ke sai kika tsaya kika zuba musu ido su na jifanki da waɗannan kalaman? Ai fito na fito za ki yi da su ki nuna musu ainihin kalar taki salon barikin. Na rantse sai na dira a cikin gidan matar nan tamkar sauƙar aradu na yi wasan kura da ita sai na nuna mata cewar lalle da ruwa ake dafa shayi kuma bakin rijiya bai kasance wajen wasan makaho ba, tashi mu je ki kai ni gidan". Ta yi zancen yayin da take miƙe wa tsaye. "A'a Zinariya ba za a yi haka na ƙudurce a cikin raina cewar ba zan ƙara wuce wa ko da ta ƙofar gidan ba ne balle na shiga cikinsa. Na ri ga na yi musu bayannin komai". A kufule ta ce"waya gaya miki yanzu bayani yana tasiri ga mutane? Ai duk yadda kika ƙware wajen iya tsara kalaman da gogewarki wajen furta su daki-daki, wasu mutanen ba sa fahimta sai kin haɗa musu da akuyanci a cikin lamarin. Ki yi wa girman Allah ki tashi mu je gidan matar nan na ƙaddamar mata". Na tashi tsayi na riƙo hannunta"don Allah ki taushi zuciyarki ki yayyafa mata ruwan sanyi, mu bar maganar nan ta wuce. Na sanar da ke kawai don na ji sanyi a ciki raina ba don wani abun ba". Ba ta ce da ni komai ba illa zare hannunta da ta yi daga cikin na wa ta koma mazauninta ta zauna, ta yi ƙwafa kana ta ce"billahillazi don kawai zan yi tafiya ne shi yasa zan lafa bayan hakan ban dalilin da za ki ce kin bar wannan maganar ba". Na sauƙe tagwayen ajiyar zuciya tare da faɗin"gobe za ki tafi Abujan ko?". "Da sassafe ma kuma Ogana kuma jibi da yamma zai diro najeriya, a ƙalla za mu iya yin sati guda tare". Na waro idanuna waje"kika ce hutun ƙarshen mako kawai za ku yi tare ki dawo?". Ta yi fari da idanunta"e amma yanzu lissafin ta sauya kai tsaye ba zan iya ce miki ga ranar dawowa ta ba, sai dai ranar da Allah ya nufa kawai za ki ganni. Zan bar miki makulin ɗakina akwai ragowar kayan abinci ki yi amfani da su. Sannan don Allah ina son kafin na dawo ki sauya daga wannan Amatullah ɗin da take zaune a gabana yanzu, ina son duk wanda ya ɗaga miki ƴatsa ki tabbatar kafin ya sauƙe ta kin karya ɗan tsayan, kin ga harkar bariki fa babu wanda zai zo don ya taimake, ya kawo miki agaji ko kuma ya ƙwata miki haƙƙinki. Yaƙi ne da babu wanda zai tallafa miki ke za ki tashi ki yi wa kanki yaƙin neman ƴancin kai". "In sha Allah ba zan dawwama a haka ba ni ma, dole akwai lokaci ya na zuwa wanda zan sauya". Ta murmusawa"yauwa ƴar gari yanzu na ji batu". Daga haka ta ɗauki ledodin siyayyar da ta yi ta soma nuna mini, magungunan mata ne da na matsi birjik iya ganin mai gani. Daga na turare sai na tsuguna da na sha da kuma na ci da kaza. Ta sayo mini wasu dogayen riguna da mayafai ta ba ni, bakina har kunne na din ga doka mata godiya tamkar zan yi aron baki. A nan ɗakinta na yi sallan isha'i muka ci abinci, ita take gulmata mini cewar Hajiya Babba ta tura La'aniyatu can ƙasar nijer wajen wata aminiyarta don a ba ta horo a kuma koyar da ita kwasa-kwasan bariki don a cewarta so take yi ta gaje ta ta ɗaura daga inda ta ja birki. Ba kaɗan ba lamarin ya taɓa ni tausayin La'aniyatu ya mamaye zuciyata ni shaida ce akan cewar ba ta ƙaunar irin rayuwar da mahaifiyata take yi, balle daidai da rana guda ta ji sha'awarsa a cikin ranta. Ba ni na baro ɗakin Zinariya ba sai ƙarfe sha ɗaya dare, lokacin ta gama haɗa kayanta tsaf domin tafiyar gobe. Ta rako ni har ƙofar ɗakinmu muka yi sallama don ta tabbatar mini da cewar ƙarfe ukun dare za a zo ɗaukarta za su wuce garin Kano inda daga nan za ta kai jirgin safe da zai tashi daga cikin filin tashin jiragen sama na cikin jihar Kano zuwa garin Abuja, ta ɗauki makulin ɗakin ta damƙa mini na yi mata fatan sauƙa lafiya kana na shige ɗakin. Washe gari da ƙyar na tashi sa boda daren jiya ban iya runtsawa da wuri, a makare na gabatar da sallan asubahi na zauna inda na yi sallan na yi shuru ina tunanin ta yadda ta fara gudanar da rayuwata a wannan gaɓar, sai dai kamar yadda Zinariya ta faɗa ne dole na tashi na yi yaƙin nema wa kaina ƴancin kai. Haka kuwa haka ba ta cika sati guda da tafiya ba sai da na zama babu wanda bai sanni ba a kaf cikin gidan, hatta baƙin da suke zuwa san sunana ko da kuwa ba su taɓa ganin fuskata ba. Na yi ƙaurin suna fiye da tunanin mai tunani ta yadda duk wani rashin mutunci da tijara na san farillai da sunnoninsu, har na kai munzalin da babu wanda yake rayuwa a cikin gidan da za a ƙira sunana ba tare da ya sha jinin jikinsa. Babu wanda ya isa ya nuna mini ɗan ƴatsa rashin mutuncin da nake yi ina sa yaƙinin ko Zinariya ce ta dawo ba za ta yi rabinsa. Faɗa da jagwal babu wanda ba na shiga, rigima kuwa ko ba da ni ake yi ba zan shiga na amshe balle kuma da ni ake yi. Yo wani ma ya yi rawa balle ɗan makiɗi. Duk tijara da kwashe-kwashen Aminu sai da ya zubar da makamansa ya duƙa a gabana ya sara mini. Har na kai lokacin da duk sa'ilin da aka kawo wata sabuwar yarinyar cikin gida waje na ake fara kawo ta na yi mata darasi. Sai dai duk barikin da nake bugawa babu wani na mijin da nake sake wa fuska balle na ba shi gangar jikina, haka nan duk shagalata ba na wasa da addini ko kaɗan du abin nake yi kuma a duk inda nake da na ji an yi ƙiran sallan zan bar abin da nake yi salla, haka nan azumin Litinin da alhamis ba ya taɓa wuce ni. Hakan nan ba a yin cikakkun kwanaki goma sha biyar ba tare da na sauƙe alƙur'ani ba, sadaka kuwa sai dai in ban sama taro da sisi ba. Wasa-wasa sai da Zinariya ta ci satikai biyar cur ba ta dawo ba, tun abin ba ya damu na har ya soma damuna. A duk lokacin da zan ce Aminu ya ƙira mini layinta a kashe yake lamarin ya yi matuƙar ɗaga mini hankali da jefa ni cikin cakwakiyar tunanin an ya kuwa lafiya?. [12/14, 12:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 6️⃣9️⃣ Haka nake kwana na tashi da tunanin halin da Zinariya take ciki, tabbas da na san garin Abuja ko kuma na taɓa zuwa cikinsa babu abin da zai hana ni tashi takanas na je neman Zinariya. Sai dai na ji an ce mini babban gari da ya tara manya da hamshaƙan mutane neman mutum a cikin irin wannan garin ba ƙaramin aiki ba ne. Ina ƙwance a ɗaki ina ta saƙa da warwara a cikin raina yayin da wani sashin zuciyata yake hasko mini rayuwarta ta baya mussamman yadda muka rayu da Abba, ta tabbata a gare ni ba ni da wani masoyin da ya wuce shi haka nan babu wani wanda zai nuna mini ƙauna kwatankwacin irin wanda ya gwada mini. Murmushi kawai na yi ina jinjina kaina don izuwa yanzu a zo bijiren da zuciyata ta bushe ta zama tamkar dutse wajen dake wa, babu abin da yake sani fargaba balle tsoro ko kuma tausayi haka nan hawaye ba za zuba daga idanuna. Maimaikon lokacin da suka shuɗe da ba na sanin sa'ilin da suke cin gashin kansu. Babu shiri na tashi daga kwanciyar da na yi sa boda hayaniyar da na ji yana tashi a tsakar gidan ana ta ruwan shariya tamkar dangin maguzawa. Diro wa na yi daga kan katifar Zinariya da nake kwance na bayyano waje. "To ƴaƴan kaji dangin karnuka wani gurmin kuma aka haɗo da sanyin safiyar nan?". Na yi zancen yayin da nake iso wa inda na ga su a tsaye cirko-cirko tamkar sun haɗiyi taɓarma. "Wai don tsabar iskanci da rainin wayon mutanen cikin gidan nan, na ɗaura girki daga na fito na shiga banɗaki na dawo na samu an sace tukunyar gabaɗaya, sa boda rashin ta kunya da tsiya. Wallahi a fito mini Sabuwar yarinyar da aka kawo da na bi ya mata littafin sirrin zaman bariki babi-babi, kuma aka yi karati yarinyar kanta yana ɗauka uwa uba kuma a wayenta ta shigo harkar. "Ke Kyawawa shi ne kika hargitsa gidan haka da sassafen nan? Ko da yake ban ga laifinki ba a ɗauke tukunya sukutum ai dole ki tada jijiyoyin wuya. Yarinya ci gaba da masifa har sai an fito miki da kayanki ai bala'i da masifa babu uwar wacce ta kashe". Ina rufe bakina Aminu da shigowar sa ke nan ya amshe zancen"ina gaida uwar haɗa gurmi, yarinyar nan kin san kan tsiya kuma kin san wassulanta. Kin san har yanzu kaina ya ƙasa yarda cewar ki na da haddar alƙur'ani a cikin wannan kan nakin". Na saki shewa har da tafa hannu kana na ce"ai kuwa ya kamata ka yarda don yadda nake murza wulaƙanci na tofar. Haka nake sarrafa ayoyin cin alƙur'ani yayin rera su". Ya kwashe da dariya mai sauti"Mahaddaciya ga sani ga ilmi kuma ga shagala". Ban ce da shi komai illa murmushin da na sakar masa yayin da nake juya wa na koma cikin ɗakin. Na zauna na yi shuru tunanai kala-kala suna ziyartar cikin kwanyanta, tun da na sa ka ƙafata na fito daga cikin gidanmu daidai da rana guda ban taɓa jin ina son na ƙara kallon fuskar Umma ba balle har na yi kewarta ko na ji sha'awar son kasancewa a tare da ita, kamar yadda nake ji a cikin ƴan kwanakin. Wani tsananin kewarta da son ganinta nake yi. Haka na wuni ina wannan tunanin bayan na yi sallan asr na kwanta a nan inda na yi sallan, take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ni. Irin da baccin da zan iya bugan ƙirji na ce rabo na da bacci cikin kwanciyar hankali irin sa tun kafin rasuwan Abba. A firgice na farka jikina gabaɗaya yana karkarwa ga wani uban zuffan da ya jiƙa mini jiki lajab kamar wacce aka kwarawa ruwa. Ƙirjina ya na dakan lugudan-lugudan tara-tara tara cikin daƙiƙu tara. Na buɗe baki zan kurma ihu sai kuma na yi hanzarin tufe bakina da tafukan hannayena. Allah ya ba ni ikon karato addu'ar da ta yi nasarar fara zuba kaina a cikin wannan rikitaccen yanayin mai kama da almara. "Hasbunallahu wa ni'iman wakil". Na furta har izuwa lokacin ilahirin jikina yana rawa sa boda munin mafarkin da na yi da Ummata. Mafarki na yi wai ga ni ga ita a gaban Allah ya na yi masa hisabi yayin da yake tuhumarta akan amanarta da ya ba ta ta yi masa riƙon sakainan kashi ta kuma wofartar da nauyin da yake bi sa wuyanta, wai Ummata ta gaza kare kanta Mala'ikun azaba suka saka mata sarƙan wuta su ka nannaɗe mata jikinta suka jefa can cikin ƙasan wuta, ina ji ta na ihu ta na kururuwar neman ceto da agaji na yunƙura zan je na taimaka mata wai sai Abba da yake sanye da fararen kaya tas ya riƙe mini hannuna. Ya jijjiga mini kansa alamar kar na je, haka na durƙushe a wajen ina kuka ta na ta aikin lallashina. Shewa da ihun da na ji an saka a filin tsakar gidan shi ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga nisan zangon da na yi a cikin kogin tunanin da na faɗa. Na kai hannuna na kawar da hawayen da suka ɓata mini fuskana na yunƙura zan tashi na ga an shigo da ledan kaya cikin ɗakin. "Ledar nan fa, na wane ne?". Sha'awanatu da ta shigo da akwatin ta washe baki ta na kallona, don tun bayar faruwar wancan abun tsakanina da ita ta shiga taitayinta ba ita kaɗai ba ma har wasu daga cikin matan gidan, silar da ya sa suke shakka ta kenan. Mun ɗinke ni da ita don ta zama cikakkiyar ƴar fadata mai lasisi. Duk wani jagwal da ta taro yake neman girmewa lissafin ƙwaƙwalwarta ni take tunkarowa na warware mata shi sala-sala. "Ai Zinariya ce ta dawo yanzu haka ma ta na tsakar gida". Ba ta rufe bakinta na daka tsalle na tsallake ledan da ta shigo da shi ɗin, na fito tsakar gidan. Muna ganin juna ni da Zinariya habawa! Sai murna muka rumgume juna ana yaushe gamo. Na ja hannunta suka cikin ɗaki na zaunar da ita a bakin katifar ina faɗin"ke kuma da muka yi da ke ba za ki wuce wasu kwanaki ba. Kika je kika share waje kika yi zamanki. Ki ka bar ni nan cikin fargaba da zulumi". Ta ɗan murmuss tare da sadda kanta ƙasa kafin ta ce"dalili ne mai girma ya kawo hakan Amatullah, yanzu dai ba n ruwa na yi wanka tukunna don wallahi duk wani gaɓa a cikin jikina ciwo yake min". Kaina kawai na jinjina mata na ɗauki bokati na fita waje, ɗakin duk wacce na yi niyya da ra'ayi na faɗa na kamfato ruwa na yi fito babu mai ce wa da ni uffan tambaya na ba'asi. Na kai mata ruwan banɗaki ta shiga wankan na dawo na kallafawa duk wata wanda ta yi girki sai ta kawo mini plate guda ɗakina Zinariya ta ci ta yi haniƙan. Babu mai cewa da ni ko kanzil don na isa har na yi yawa, Hajiya Babba ma sai dai ta ganni ta jijjiga kaina don na zame mata ƙadangaruwar bakin tulu a bar ni na ɓata ruwa, a kashe ni a yi asarar tulu. Dole ƙanwar naƙi ta na ji tana gani sai idanuna ta kawo ta zuba mini. Sai da na bari ta yi wankan ta ci abincin, ta je ɗakin Hajiya Babba ta gaishe ta sannan ta dawo ta kwanta. Na zo kusa da ita na zauna na ce"na ta ƙiran layinki kullum a rufe, ga shi kuma yanzu na ga kin dawo babu waya a hannunki. An ya lafiya kuwa wannan tafiyar?". Kamar wacce na tsikara mata allura ko kuma wacce na sosa mata inda yake mata ƙaiƙaiyi ta yi zumbur ta tashi ta zauna tana fuskana. "Kin gan ni nan tsabar rashin hankalin da na shiga har ma na manta da wani abu a duniyar nan wai shi waya. Tun da na ba ro ofishin ƴan sanda da aka ba ni wayar na kashe ta na jefa a cikin ledan har yanzu da nake yi miki wannan maganar, ban sama nutsuwar da zan ɗauko ta ba". Cike da mamakin da ya bayyana har a cikin furucina na ce"sanar da ni abin da yake faru wa cikin gaggawa kar ki bari zuciyata ta buga. Don fargaba". Ta ja dogon numfashi kana ta soma zayyano mini zancen daki-daki wani yana bin bayan wani. "Na isa masauƙina a cikin babban otel kuma mafi tsada da tsaruwa a cikin garin Abuja, na ci mai kyau na sha mai kyau sannan na kwanta na yi baccin huce gajiya. Washe gari na shiga hidimar tarban Ogana da zai biyo jirgin yamma daga ingila zuwa ƙasa Najeriya. Ƙarfe shidan yamma ya ƙira ni ya shaida min ya iso har ma ya ɗauki hanyar zuwa otel ɗin da nake. Tabbas na cika da murna da har sai da ya sa ni na tashi na taka rawar daɗin jin kalamansa a gare ni. Ya Kawo min tsarabobi masu yawan gaske mun faranta ran junanmu a wannan ranar, sa boda mun yi marmarin juna sosai muna kwance da rana kwatsam na ji ana mana buga mana ƙofa. Lokacin bai tashi daga bacci ma don haka na tashi na je na buɗe ƙofar ina buɗe wa na ga wani Saurayi tsaye. Muka yi kallon-kallo da shi kafin na ce da shi Bawan Allah lafiya za ka zo ka na buga mana ƙofa? Waye kake nema?. Bai amsa min ba sai da na ga yana ƙoƙarin shiga cikin ɗakin na ƙi ba shi dama muka soma hayaniya da shi, da hakan ya sanya Ogana tashi daga baccin da yake yi ya zo shi wajen a nan na fahimci sun san juna ƙarshen sanayyana ma saurayin ƙaninsa ne na jini da suka fito daga ciki ɗaya. An yi rigima sosai sun yi musayar yawu da shi ainun na fusata na ɗauki kwalbar giyan da ya sha a daren jiya na je da nufi rotsawa saurayin a kansa ya zame na sama Saddam a goshinsa, take kwalbar ta tarwatse jini ya soma malala daga goshinsa take a wajen ya yanke jiki ya faɗi ba ya ko motsawa. Na gigice na rasa abin da zan yi kawai na ɗaura hannu a ka ina rusa kuka, ma'aikatan otel ɗin suka shigo su suka ƙira ƴan sanda suka zo suka tafi da ni aka rufe ni ban ƙara sanin halin da Saddam yake ciki ba sai da na yi kwanaki biyar cur a ofishin ƴan sandan kafin Saurayin ya zo shi a bakinsa nake jin mummunan halin da matar shi Saddam ɗin take ciki. Kuma ita ta buƙaci a yi min afuwa ta ƙara cewa idan halina ne wataran zan kai kaina inda ba zan iya fita ba, haƙiƙa na ji tausayinta ainun kuma na jinjina halin girma da dattakunta, ba ni da wani wajen da zan je haka nan ba ni da kuɗin da zan dawo gida sa boda ATM ɗina yan can ɗakin otel ɗin. Haka nan ma wayata ban san duniyar da take ciki ba". Ta tsagaita kafin ta ci gaba da cewa"da ƙafata na yi dogon tafiya har na isa gidan wata ƙawata da na muka haɗu da ita sanadiyyar bariki. Sai dai ita ta tuba har Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta. A gidanta na zauna ta ba ni mafaka sa boda lokacin mijinta bayan cikin garin, a cikin gidanta na yi waɗannan tsawon kwanakin ina ta fafutukar yadda zan yi welcome back ɗin layina ko don kuɗaɗena da suke kwance a cikin akawuna. Da ƙyar hakan ya yiyu a cikin azurkinta ta taimaka ta ba ni ƙaramar wayar da na saka layin, ana cikin hakan mijinta ya ƙira ta a waya yake sanar da ita cewar yana hanyar dawowa lamarin da ya fara haifar da matsala a tsakaninmu ke nan, ta dade akan sai dai na bar cikin gidan don mijinta ba zai dawo ya iske ni a gidan ba a cewarta ba ta yarda da ni ba ta san zan iya zagayawa na ci amanarta ta hanyar keɓewa da mijinta. Duk kwantar da kai da rantsuwar da na yi mata bai ɗaɗata da ƙasa ba haka ta koro ni ta ba ni wasu kuɗaɗe wanda da su na yi kuɗin mota na dawo garin nan". Sosai na jinjina girman iftila'i da masifar da ta faɗa, na cira kai ina kallon ta sai dai kafin na yi magana ta ri ga ni. "Har yanzu ina mamakin yadda aka yi ƴan uwan Saddam suka san mu na tare da shi a cikin otel ɗin nan, har suka zo suka yi mana tijara. Bayan kuma shii da kansa ya ba ni tabbacin bai sanar da kowa cewar ya shigo ƙasar ba ciki kuwa har da matarsa uwar ƴaƴansa". Na ja dogon numfashi na fesar ina jikina gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Lokacin sallan magrib da ya kawo kai shi ya tursasa mini tashi na fita na je na yi alwala na dawo na gabatar da sallan, ban tashi daga wajen ba sai da na yi sallan isha'i. A lokacin Zinariya ta jawo ledar da ta dawo da shi ta ɗauko wayar ta kunna ta, kamar jira ake yi ta kunna sai kuwa ga ƙira ya shigo ta. Ta ɗaga tare da sanya ta a amsa-kuwwa ta kwanta akan bayanta ta ɗaura wayar akan ruwan cikinta yayin da ta lumshe idanunta. "Yau ina kika shiga ne kwana da kwanaki? Ina ta ƙiran layinki ba ya tafiya. Ko dai wani harkar kika saita ne kika juya mana baya? Don na san halinki kamar yadda na san yunwar cikina". A taƙaice ta ce"wannan wani dogon labari ne mai zaman kansa. Amma dai yanzu fara sanar da ni dalilin neman da kake yi min". "Malamin da kuke son ganin yanzu haka maganar da nake yi miki yana cikin otel ɗin mu. Ya zo shi bikin ƴar gidan mataimakin gwamna da za a yi don na ji a wata majiya mai tushe cewar shi zai ba ta auren yarinya, ma'ana shi ne waliyinta. Ku na da damar da za ku iya ganinsa daga nan har zuwa ranar da za a ɗaura auren". Babu shiri ta tashi ta zauna tare da buɗe idanunta"Oga Deeno mu bar wasa shin da gaske kake wannan maganar?". Ta ja wata doguwar tsakin haushi da takaicin ta da ɗura masa kafin ya ce"ta yaya zan yi miki wasa da irin wannan zancen? Na yi miki abin da kike so yanzu ni ma lokaci ya yi da za a rama wa kura aniyarta". Dariya ta fashe da shi"kar ka damu Oga zan zo takanas na same ka". Da hakan suka yi sallama ta katse ƙiran ta zo ta ƙanƙame ni. "Burinki ya kusa cika Amatullah. Sheikh ya zo cikin garin nan kuma ina da tabbacin Oga Deeno zai share mana duk wani hanyar da zai sada mu da ganinsa". Wani sanyi na ji a cikin zuciyata na ji tamkar an warware mini ƙullin da ya tokare mini ƙirjina ban san lokacin da na ɓanɓare ta daga jikina, na kai goshina ƙasa na yi sujudul shukur ga Ubangijina ba ina hawayen farin ciki. [12/15, 5:32 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 7️⃣0️⃣ Duk yadda na so tsayar da hawayen da suke sarrafa kansu wajen zuba daga cikin koramar idanuna, na kasa samun wannan damar. Sosai nake kukan irin kukan da na daɗe ban yi makamancinsa ba, sai dai na yarda hakan yana da nasaba da abubuwan da suka taru suka yi wa zuciyata ƙawanya. Ban san sama zarafin zubar da ƙwallar ba sai yanzu ta dalili ya yi dalili. Zinariya ta tsaya ta yi sakeke tana kallona. Ta kai hannunta tana share mini hawayen da suka ɓata mini fuska. "Ke kuwa mene ne abin kuka? Wannan ai abin farin ciki ne da ya kamata ki tashi ki yi tsalle har ma ki tada rawa tun da daman buƙatar maji hajji ai salla ne". Ban iya tanka mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba illa murmushin da na yi ƙoƙarin sakar mata ita ma ta mayar mini. Na rungume ta tsam a jikin ina ta faman jeranta mata godiya wani na bin wani kai ka ce kyautar kujerar hajjin bana ta ba ni a lokacin nake tsanani da buƙatar hakan. "Ba kuka ya kamata ki yi ba Amatullah murna da murmushi ne ya dace da fuskarki a irin wannan lokacin na tsananin farin ciki da taka tsanin cikar buri da muradin da ya daɗe a cikin farfajiyar ƙirjinki. Ki goge idanunki ki nutsu mu tsara yadda abubuwa za su kasance har su tafi daidai da tsarinmu. Ba tare da an sama wani matsala ba". Numfashi mai nauyi na furzar daga bakina tare da gyara zamana ina fuskantarta kafin na yi magana ta tari numfashina ta hanyar faɗin"to yanzu me ne tsarinmu na gaba?". Na ɗan yi jim tamkar mai nazarin kafin na ce"idan na gan sama ganinsa to dukkanin burina ya cika sannan haƙata ta cimma ruwa". Ta yi mini wani kallon da na kasa fahimtar inda ta dosa. "Me ye hakan yake nufi ke nan? In kika gan shi kawai shi kenan komai ya zo ƙarshe? Babu wani abun da za ki yi? Kin san ba shi ma ba zai zauna haka nan dole ne ya kasance da shirinsa na ko ta kwana". "Ba a suffar Amatullah ɗin da kika sani zan je masa, zan je masa ne a suffar irin matan da yake harka da su duk da cewar kuwa duniya ba ta san wannan ɓoyayyan halin nasan ba". Ta yi caraf ta amshe zancen"ta ya ya za ki yi hakan?". Ta murmusa kana na ce"Allah ya kai mu gobe idan muka je cikin otel ɗin za ki ga ne wa idanunki. Bayan mun haɗu da shi mun zanta zan naɗi sautin muryarsa sannan ban shayar da shi abin maye ta yarda zai fita daga cikin hayyacinsa. Hakan ne zai ba ni damar yin abin da na yi niyya zan ɗauki hotona da shi, wanda su zan riƙe a matsayin makaman da zan yaƙe sa da su. Har na kawo ƙarshen baƙi hali da mungun nufin da yake yaɗawa a tsakanin al'umma a ɓoye". "Kuma ki na ganin bayan faruwar hakan ba zai sa a bazama nemanki ba ruwa a jallo?". "Idan ya yi hakan to shi ne kuskuren farko da zai yi da zai yi silar tonuwar aisirinsa ga duniya gabaɗaya. Sai dai ya yi hakan ma akwai ɓoyayyar hanyar da zan ɓullo masa". Ajiyar zuciya mai nauyi da sauti ta saka yayin da take bi na da kallo, ko ba ta furta mini ba na fahimta kuma na kallon shakku game da maganan da na furta kwance a cikin idanunta da suka ƙanƙance. Na riƙo dukka hannayenta na sanya cikin nawa ina murzawa a hankali. "Ki kwantar da hankalinki in sha Allah ina ji a jikina Allah zai ba mu nasara akan wannan abun. Kamar jahadi ne fa za mu yi wajen tona asirin abin da yake aikatawa a ɓoye wanda haramci ne hakan". "In sha Allah zan kasance da ke tun daga farkon wannan lamarin, har zuwa ƙarshensa. Zan ba ki dukkan wani gudamawar da za ki buƙata daga gare ni". Murmushin jin daɗi na sakar mata muka ƙara rumgume juna cikin farin ciki, haka muka kwana a zaune mu na tsara yadda za mu tafiyar da komai gudun afkuwar matsala. Ba mu muka kwantar da haƙarƙarinmu ba sai bayan sallan asubahi. Sai dai ni kam na kasa yin bacci iya juyin da na dinga yi raina cike fal da tarin damuwar da ya hana ni sakat, na juya ina kallon Zinariya da take baccinta hankali kawai sai na ji ina ma ni ce nake wannan baccin cikin kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi, sai dai kash! So ba samu ba ne. Kafin hantsi har na yi wanka na yi duk wani abun da zan yi, na ɗauki kuɗi na ba ya wa Aminu ya sayo mini ƙwayar da take bugar da hankali. A cewarsa duk wanda ya sha maganin a cikin abin sha akwai yiyuwar ya yi awannin biyar cur yana bacci ba tare da ya san inda kansa yake ba, balle wanda yake tsaye a kansa, haka nan ko yankan naman jikinsa za a yi a wannan yanayin ba zai san ana yi ba wai kunu a maƙwabta. Hatta ƙananan kayan da zan saka na gama tanadinsu kafin mu tafi, Zinariya na tashi na kai mata ruwa bayi ta yi wanka na yi masa abin karin kumallo muka ci muna yi muna ƙara tattaunawa har muka kammala. Muna cikin cin abincin wayarta ta yi ruri ta kai hannu ta jawo wayar ba tare da ta tsaya duba mai ƙiran ba ta kata a kunnenta. Ban san me ye aka ce mata daga ɗayan ɓangaren ba sai ji na yi ta ce"Oga Deeno ke nan tun da na ce maka ba komai ai na tabbatar da cewar babu ɗin ne. Ni da kai ai ba a jin kanmu, yanzu dai yaushe ya kamata mu zo mu?". Ta ɗan yi shuru kafin can ta ce"to shikenan in mun shigo zan ƙira ka". Daga haka ta kashe wayar ta mayar da idanunta gare ni. "Ya ce mu je mu kaman ƙarfe takwas na dare". Na jinjina kaina cike da gamsuwa"to Allah ya kaimu". "Amin". Ta amsa da shi a taƙaice muka ci gaba da cin abincin, ji nake yi kamar a ranar lokaci ba ya yi gudu. Ina zaune bayan na gabatar da sallan zuhur a ƙofar ɗaki na yi sallan na zauna akan sallayan na buga tagumi, lokacin Zinariya ta fita za ta je ciro kuɗi. Kyawawa ta zo ta tsaya a kaina na cira kaina ina kallonta tare da sauraron abin da take cewa" Ranki ya daɗe ki na ba baƙo a waje yana jiranki". "Baƙo kuma?". Ta gyaɗa mini kanta cike da tabbatarwa tana ƙara wa da faɗin"ƙwarai kuwa ya ma daɗe ya na amfani jiranki da alama. Yana nan da motarsa mai zafi". Na taɓe bakina ina faɗin"babu wanda nake tsammanin zuwansa wataƙila wata yake nema ba ni ba". "Amatullah fa ya ce yana nema. Kuma duk gidan nan babu wata mai irin sunan nan face ke ɗin dai". A kufule na ce"ki je ki ce da shi ba na nan". Na yi maganar ina miƙe wa tsaye tare da ninke sallayar da na yi salla akan sa na yi shigewa ta cikin ɗaki na bar ta tsaye a wajen. Na zauna ina ta tunanai kala-kala babu jimawa ta ƙara dawowa ta shigo cikin ɗakin. "Ranki ya daɗe mutumin nan fa ya dage akan ba zai bar ƙofar gidan nan ba har sai ya ganki, ya yi magana da ke". Na buga tsaki"ai kuwa zai kwana a wajen, tun da ba shi da aikin yi". Ta riƙe haɓa"ai kuwa ya yi kirarin in ba ki fito ba har shigowa ciki sai ya yi". "Don Allah ki fita daga cikin ɗakin nan ki je ki sanar da shi abin da na faɗa miki". "To shi kenan". Ta amsa da shi a gajarce tare da juya wa ta fice wa daga cikin ɗakin, na dinga buga tsaki kamar zan yi aman zuciyata tsabar takaicin da ya cika muni rai da ruhina. Kamar wacce aka jefo cikin ɗakin Kyawawa ta faɗo cikin ɗakin kamar wacce aka wurgo ta. Na watsa mata harara"mene ne kuma?". "Wallahi Ranki ya daɗe ya ƙi tafiya ga shi nan ma ya na shigo wa". Ta na rufe bakinta na ga mutum zamgan-zamgan ya shigo cikin ɗakin, na yi zumbur na tashi tsaye da zummar ɗura ashariya sai dai mu na haɗa ido da shi na nema zancen na rasa ji na yi tamkar an rufe min baki baki. Na nuna shi da ƴar manuniyar ƴatsata cikin rawar murya da sarƙafewar harshe na furta"Saifullah kai ne? Me ya kawo ka cikin ɗakina?". Bai amsa mini ba illa zara hannayensa da ya yi a cikin aljihun wandon farin shaddar jamfar da yake jikinsa ya zuba mini idanu, kafin daga bisani ya soma bin ɗakin da kallo. Ya jinjina kansa kafin ya ce"a nan kike rayuwa ke nan?". "Wannan ba abin da ya shafe ka ba ne ka fice miji daga cikin ɗaki, tun kafin na tara maka mutane na yi maka tijara". "Magana na zo mu yi ki saurare ni". Ya yi maganar yayin da na ga yana ƙoƙarin zama akan kujerar roban da yake cikin ɗakin, na yi wuf na janye kujerar ina huci. "Za ka yi kuskure idan ka sake ka ɗauki kalamaina a matsayin wasa, wallahil azim zan tara maka mutane idan ba ka fita daga cikin ɗakin nan ba. Me ye ya rage tsakanina da ku? Bayan kai ne mutum na farko da ka yi silar kawo komai ƙarshe. Me ya kawo ka cikin ɗakin karuwa mai zaman kanta mace mai mungun nufi? Ka fita daga cikin ɗakin nan kafin na yi mata akuyanci". Na ƙare zancen cikin ɗaga amo tare da runtse idanuna jikina yana cigaba da jijjiga tamkar ana jona mini shock ɗin wutar lantarki. Na ji an dafa kafaɗata na yi azama ture hannuna. "Kar ka sake ka yi kuskuren ɗaura hannunka a jikina don sai na tabbatar maka da hakan a matsayi mafi kuskure girma da za ka yi a cikin rayuwarka na duniya. Ka fita daga cikin ɗakin nan ba na fatan Allah ya ƙara haɗa ni da wani daga cikin ahalinku balle har mu zauna inuwa ɗaya". "Ke Amatullah wai me ye yake damunki ne? Da waye kike wannan batutuwan? Sannan waye ne ba kya fatan Allah ya ƙara haɗa ku da shi?". Na tsinkayo muryar Zinariya da hakan ya dawo ni cikin duniyar zahiri na buɗe idanuna da na runtse su na ga dai da gaske ita ɗin ce tsaye a gabana ta na kallo na kamar yadda ni ma nake kallonta. Sai da na yarce ruwan gumin da ya kwanta a saman goshina kafin na sama lasisin faɗin"ba kowa har kin dawo ke nan?". Na yi zancen ina wuce wa na zauna a bakin katifar ina ta faman mayar da numfashi. "Wai me ye kike ɓoye min ne Amatullah? Na zo na same ki sai wasu suturai kike yi marasa kan gado ga kuma firgici a fuskarki amma ki na ce min ba komai". Cike da ƙosawa da sauraron zancenta na ce"ba komai na ce miki in akwai a zan gaya miki". Daga haka na kwanta na juya mata baya na lumshe idanuna kamar mai bacci, sai dai musayar wuƙaƙe da mashin wutan da ake yi a cikin farfajiyar ƙirjina ba zai taɓa sauƙar mini da nutsuwar da zan iya runtsawa ko da na sankan guda ba ne. Ban ankara ba na ji wasu hawaye masu ɗumi su na sauƙar akan fatan fuskana. Abubuwan da suka wakana suka soma dawo mini cikin kwanyata. Ko da na tashi na yi sallan asr ban ba wa Zinariya fuskar da za ta ƙara yi mini wani tambaya, sai da na yi har sallan isha'i kafin muka haramar tafiya otel muka shirya duk abin da mu buƙata muka rufe ɗakin muka tafi. Muna sauƙa a bakin otel ɗin ƙiran Oga Deeno yana shigowa cikin wayar Zinariya ta ɗaga ta sanar da shi ga mu mun iso ya fito ya yi mana jagoranci har zuwa cikin wani garden muka zazzauna, ya soma yi mana jawabi. "Yanzu haka shi da tawagarsa su fita zuwa gidan mai martaba amma ina da tabbacin zuwa karfe tara ko goma za su dawo, don haka zan san yadda zan yi na buɗe miki ɗaki ki shiga cikin kafin ya dawo, daga nan kuma ke kike san abin da za ki yi, san a kashe CCTV cameras ɗin dukka sashin. Ni da Zinariya kuma mu ma za mu keɓe". Cike da gamsu na ce"ba damuwa". Ya ɗan sausata amon muryarsa"don Allah duk abin da za ku yi kar ki cutar da shi, kar ki yi silar da za ki ɓata min aikina ki wargaza min burin da na daɗe ina ginawa". "In sha Allah babu abin da zai faru". Ya jinjina kansa alamar shi ma haka yake fata. Muka tashi muka shiga wajen rukunin ɗakunan otel ɗin, shuru wajen yake don an sallame mi kowa babu wanda za a ƙara ba wa ɗaki a cikin VIP site ɗin har sai shi da tawagarsa sun tafi. Ya buɗe mini ɗaki yayin da Zinariya ta miƙo mini jakan jakan da yake hannunta wanda har da babban waya a ciki da ta sayo shi sabo dal da ta fita ciro kuɗi. Muka rumgume juna da ita tare da yi mini fatan alkhairi. Na ƙarewa ɗakin tsallon tsaf tabbas ya tsaru iya tsaruwa, don babu wani abun buƙatan bisa mutum zai nema a cikinsa ya rasa. Na fito da kayan zan sauya daga cikin jakan, na ajiye shi a ƙasan gadon na shiga cikin banɗaki kamar yadda muka tsara. Wanka na yi ƙirjina ya na buga wa duk kyawu da tsaftan banɗakin amma hakan bai hana ni ƙanƙaninsa ba, haka na yi wankan na gama na saka wani doguwar riga da ya kama jikina tam sai dai ya sauƙa mini har ƙasa na ɗaura ɗan mayafinsa a kaina. A ƙalla na yi mintin talatin a cikin banɗakin kafin na ji alama an buɗe ƙofar ɗakin an shigo, na yi maza na soma aiwatar da shirinmu na jawo towel ɗin da na gani lanƙaye a cikin banɗakin na ɗaura a kaina ina yi kamar ina tsane sumar kaina, na buɗe ƙofar na fito daidai lokacin da ya waigo muka haɗa ido ni da shi. Tabbas shi ɗin ne tsaye a gaba ba gizo ba kuma ba a cikin mafarki ba, duk da har yanzu zuciyata ta na buga amma na dake na ci gaba takuwa cikin ɗakin yayin da duk ɗaga ƙafar da zan yi na sauƙe sai ya bi ni da kallo. Gaban madubi na je na zauna ina kallonsa ta cikin madubin da har yake tsaye inda yake bai ko motsa ba, na sakar masa da wani laulausan murmushi mai kashe zuciyata kana na juyo ina yi masa wani shu'umin kallo. Ya nuna ni da ƴatsansa zai yi magana na yi caraf na mashe zancen cikin faɗin"Amatullah". "E na gane ki, amma me ye kike yi a nan? Ta ya ya kika shigo cikin ɗakin nan? Sannan mafi muhimmanci ma ya ya aka yi kika san da cewa ina cikin otel ɗin nan har kika gano ɗakin da nake?". Na ƙara yin wani murmushin a karo na biyu kafin na ce"ban yi zaton waɗannan tambayoyin ne za su fito daga bakinka ba". Ya katse ni"wani tambayoyi ke nan kike so ji?". Ya ɗan ja numfashi sannan na furta"na za ta tambayata za ka yi shin dama har izuwa wannan lokacin ban mance da kai ba". "Ina cikin da aka ce ki na ɗauke da shi?". Ba tare da tunanin komai ba na ce"na zubar don zai hana ni rawan gaban hatsi ya kuma kawo mini cikas wajen cin duniyata da tsinke". Ya yi shuru kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce"me yasa kika bar gida? Sannan da kika bar gidan ina kika koma da zama?". Na kashe masa ido ɗaya kafin na ce"bariki na shigo ta yadda zan sama cikakken ƴancin kai". Muryarsa babu alamar wasa ya ce"tashi ki fita daga cikin ɗakin nan". Na tashi daga inda nake zaune na iso gabansa na riƙe ƙugu ina faɗin"ai na ga waje babu inda zan fita". Bai ce da ni komai ya wuce ya shiga banɗaki da alama wanke fuskarsa ya yi ya fito ya ɗan yi turus da ya ganni har yanzu ina cikin ɗakin. Ya nufi wajen wayar talhon da yake kan teburin ɗakin yana faɗin"bari na ƙira otel ɗin na ji uban waye ya buɗe miki ɗakin nan har kika sama damar shigowa". Na yi hanzarin miƙe na riƙe wayar"kar ka yi hakan don kamar ka ɗauki wuƙa ne ka daɓawa cikinka". Ina rufe bakina aka soma buga ƙofar ɗakin a hankali kuma a nutse, muka haɗa ido da shi"ana buga maka ƙofa ka je ka buɗe ko kuma ni na je na buɗe". Ya yi banza da ni da hakan ya ba ni damar juya wa da nufin zuwa na buɗe ƙofar ya yi hanzarin shan gabana. "Me ye haka za ki yi?". "Buɗe ƙofar mana zan yi". Na ba shi amsa cikin halin ko ina kula. "Koma zan je na buɗe". Ya yi maganar a gajarce yana nufar ƙofar ya buɗe abinci aka kawo ya ƙarba ya shigo da shi ya ajiye akan teburi, muka tsaya mu na kallon kallo ga juna. Ganin ba shi da niyyar jin komai ya sa ni zaunawa na soma bubbuɗe abincin, ya fi minti goma ya na kallona kafin ya koma cikin banɗakin. Hakan ya ba ni damar tashi na yi wuf na je na ɗauko jakar da na ajiye na ɗauko wannan ƙwayar da wannan wayar na ɓoye ta a jikina, na zo na jefa ƙwayar maganin a cikin ƙaramin flask ɗin ruwan shayin da aka haɗo tare da abinci na jijjiga kana na ajiye, na ja plate ɗaya na ajiye gabana na soma ci, a haka ya fito daga banɗakin ya same wannan karon da alama wanka ya yi don ya fito yana tsane fuskar da wani ƙaramin towel. Ya zauna a kujerar da take saitina da na ɗago kai muka haɗa ido sai na sake masa murmushi na ci gaba da cin abincina. Sai da ya gaji da kansa ya ce"me ya kawo nan? Me ye kike nema daga gare ni?". "Ka ci abincin tukunna sai mu yi magana". "Na fi buƙatar amsar waɗannan tambayoyin fiye da komai a yanzu". "Ko kaɗan dai ka ci sai mu yi maganar". Ina gama maganar na ɗauki kofi na tsiyaya masa ruwan shayin wanda ina da tabbacin shayi ne na musamman kuma na girma aka yi masa. Na miƙa masa kofi ya ƙi karɓa ban yi ƙasa a gwiwa ba na ajiye masa a gabansa na koma na ci gaba da cin abincina. A ƙalla ya yi mintuna ashirin kafin ya ɗauki kofin shayin, nan ma sai da ya daɗe da shi riƙe a hannunsa kafin ya kai bakinsa ya kurɓa, na ji wani sanyi a cikin raina tare da wani nutsuwan da ya yi bake-bake a cikin ruhina. Sai da ya kusa sanye wa kafin ya ajiye kofin ya na kallona ya ce"ke nake sauraro". Na ajiye cokalin da nake cin abincin da shi na ɗauki gorar ruwa na kora na yi hamdala kafin na dawo kan kujerar da yake kusa fuskantar wanda take zaune a kai na zauna. [12/17, 4:47 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 7️⃣1️⃣ Tagumi na zabga tare da zube idanuna akan sa yayin da shi ɗin ma ni yake ta faman kallo, cikinmu babu wanda ya ce uffan illa murmushin da yake ta sakar mini na lura izuwa lokacin maganin da na sanya masa a cikin lemon ya fara aikinsa a cikin jikinsa. "Ka na ta kallona ba tare da ka ce wani abu ba, ahalin ka san cewa kai nake sauraro". Na yi zancen muryata can ƙasa ina sarrafa harshena cikin salo da hikima. Sai da ya lumshe idanunsa kafin ya cikin wani irin yanayi ya ce"Amatullahhhh". "Na'am ya Sheikhi". Na yi caraf na amsa ina ka she masa ido guda da hakan ya ba shi damar soma zuba tamkar bakin indararo, hakan ya sa na yi wuf na fito da wayar da take jikina na danna recording na soma naɗar muryarsa. "Amatullah na neme ki sosai bayan da na sama tabbacin cewar kin ɓace watau kin gudu daga cikin gidanku, kin bar gaban iyayen da danginki kin shiga duniya. Na ba za mutane ta yadda na ba da aikin nemanki a ko'ina sai dai har zuwa wannan lokacin babu wanda ya zo min da wani labari game da ke. Tun ranar da na fara ganinki a ciki wannan tashar ki na tallan kunu na ji cewar kin kwanta min a cikin raina, na ƙudurce cewar komai runtsi komai tsanani sai na cimma buri akan ki sai dai ke ce mace ta farko da kika fara karya alƙadarina da kuma ikirarin da nake yi wa kaina na cewa duk abin da na sa a gaba da niyyar mallakarsa babu makawa sai na same ko da kuwa nisan da yake tsakanina da shi ya kai tafiyar dake tsakanin nan inda muke zuwa cikin birnin sin. Tabbas a zahiri ni malamin addini ne a idanun duniya, ilmina ya jawo min girmamawa da mutuntawa daga wajen mutane da yawa wanda ko da a cikin mafarki ma ban taɓa tunanin zan ina saka kafata a inda suke ba balle har su ba ni wannan girman da mutuntawa, a idanun mutanen ƙasar nan ni mutum ne mai gudun duniya da kuma ruɗin da yake cikinta ni mutum ne kamili da duk wani abun cikin duniya bai dame ni ba balle ya ɗaɗani da ƙasa. Duk da kasancewa ta ba ɗan siyasa ba ne kuma ba ni da haɗi da gwamnatin da ayyukan da take yi amma ganin kimata da darajata da duniya take hakan ya jawo min kusanci da gwamnoni bila adadin ta yadda nake iya ganawa da su a duk sa'ilin da nake so, babu wata buƙatar da zan je da ita gabansu ba tare da sun kawar min da ita ba". Ya tsagaita tare da yin wanin gatsa mai warin da ya tilasta mini ɗauke numfashina na wucen gadi idanunsa suna ta ƙoƙarin rufe wa amma ya na tilasta buɗe su tare da ci gaba da zance daga inda ya dakata. "A zahiri ni malamin addini ne wanda ya ke kiyaye dokokin da ya shimfiɗa kuma ya yi hani da a aikata su, sai dai a baɗili ni ɗin tantarin manemin mata ne sai dai duk cikin wannan duniyar babu wanda ya san hakan don ni idan zan nema yarinya ba na zuwa inda aka san muryarta balle kuma fuskana, na fi mu'amala da matan ƙasashen waje mussamman ƙasar Ghana, Senegal da kuma Kenya sa bosa gudun matsala da tashin zance, sai kuma matayen can kugu su ma sai lokaci zuwa lokaci. Ke ce mace ta farko da na fara ƙyalla idanuna akan ta har na ji sha'awar kasancewa tare da ita a nan arewancin Najeriya, haka nan ke ce mace ta farko da na yi buri a kanta daga ƙarshe kuma ban same ta ba, a yadda na tsara ranar da ayi walimar yaye ku daga islamiyya a ranar zan kwanta da ke sannan na cusa miki tsoro da razani tare da fargaba a cikin ranki ta yadda ko bakin bindiga aka sanya miki a goshinki ba za ki taɓa ambaton sunana ba ko da kuwa maganar ta tashi asiri yana neman watsewa. Kwatsam sai kuma wannan abin mamakin ya faru". Ta katse shi"wani abun mamaki ke nan?". Ya kafe ni da ido kamar zai cinye ni ɗanya kana ya ce"bayyanar ciki a tare da ke mana da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinki, sannan mahaifiyarki ta yi ikirarin ta sallamaki ga duniya ba ta buƙatar ƙara sanya ki a cikin idanunta. Wannnan dalilin ne ya sanya ki shigo harkar bariki gadan-gadan tun daga lokacin da na tabbatar da cewar kin bar gida kuma har cikin da yake jikinki ya zube tun daga sa'ilin na sauya akalar manufata akan ki don a tsarina ba na taɓa haɗa shimfiɗa da wacce wani ya taɓa kwantawa da ita ko da kuwa bisa tsautsayi ne balle wacce take da ƙarfin halin da bushewar zuciyar shigo wa bariki, a tarihin balaɗala sai yarinyar da ba ta san ko wani ɗa na miji ba nake mu'amala da ita sai kuma wacce ta ƙoshi da tarbiyya aka yi mata shaidar nutsuwa da kamala ni kuma na zo cikin daren guda na wargaza dukkan shiri da tanadin iyayenta akan ta na bar su su na cizon ɗan ƴatsa, watan har mun gama komai na yi cinikinta a kawo min ita ba za ta taɓa jin muryarta ba balle ta mu yi ido huɗu da ita sannan ba na amfani da komai wajen kawar da hankalinsu ko shaƙa musu abin da zai sa su fita daga hayyacinsu, ki na cikin hankalinki kuma ki na ji ki na gani za mu yi komai sai dai na ri ga da na rufe bakin kuma na goge komai na cikin ƙwalƙwalwar". Jikina ya soma rawa tamkar mazari haƙwarana suka datse harshena wasu hawayen suka ciko kurmin idanuna sai dai na ƙi ba su damar kwaranya, sai da na haɗo jarumta kafin na iya faɗin" wani buri daman kake da shi a kaina?". Bai amsa mini ba illa dariyar da ya saka mai sauti ya na ƙoƙarin kai hannunsa jikina daga inda yake zaune na zame wa ina tashi tsaye na tsaya "Burin da nake da shi akan kowacce yarinyar da na ƙyalla idanuna akanta". "Wane ne Muhammad Taukif ake yi wa alaƙabi da Sultan, shin shi ɗin jininka?". Ya ɗan yi jim yana ɗan bubbuga goshinsa a ƙoƙarin hana idanunsa rufe wa kafin ya furta"Sultan yaron kirki ne ba, shi ɗin jinina ne kuma ɗa miji ɗaya tal a gare ni tamkar rai, ina son shi har cikin raina musamman yadda na lura ya na hazaƙa da basira a bangarorin da suka shafi addininsa. Yaro ne mai nutsuwa da sanin ya kamata haka nan akwai shi da girmamawa duk wani wanda yake gaba da shi uwa uba ga tausayi da jin ƙai. Sai dai na ɓoye ainihin wane ne shi a gare a duniya mutane ƙalilan ne suka san hakan yayin da wasu suke ɗaukar sa a matsayin ɗan ɗan uwana, wasu ma su kan ce ma yaran nan ne kawai da nake taimakawa wajen inganta rayuwarsu. Sai dai shi ɗin ɗana ne jinina yake yawo a cikin jikinsa sai dai ba ta hanyar aure aka haife ba ma'ana shege ko kuma na ce ɗan gaba da fatiha". Na waro idanuna waje cike da son tabbatar da sahihancin abin da kunnuwana suke ji yo mini. Cikin ruɗani na ce"shege kuma?". Kamar jira yake yi na yi tambayar ya yi caraf ya ba ni cikakken amsa"e shege don ba ta hanyar aure aka same shi ba sai dai wannan wani sirri ne da duk duniya babu wanda ya san shi cikin kuwa har da iyalina da shi kansa Sultan ɗin. Mahaifiyarsa ba musulma ba ce sai dai kin sa ko a cikin ƙabilan ma kawai masu tarbiyya da ilmin sanin addininsu, ƴar asalin ƙasar Ghana mun haɗu da ita lokacin da muka je gabatar da wa'azi muka keɓe ta ita a wannan lokacin Allahu Mulƙussamawati ya ƙaddara samuwar Sultan a cikin cikinta, bayan na dawo ƙasa Najeriya na sa a ci gaba da bibiyanta har zuwa lokacin da ta haihu ko da na ji ɗa na miji ta haifa sai na saka aka sato min shi ta ɓoyayyar hanyar da har abada ba za ta taɓa tunanin ni na yi wannan aikin ba. Na kai shi cikin gidan na damƙa sa a hannun mai ɗakina Hajiya Halima wanda a lokacin ita ta haihu amma yarinyar ba ta zo da rai da ba, ita ta shayar da shi ta kuma raine shi har ya zama mutum ta nuna masa ƙauna da kulawa don na ce da ita tsintar sa aka yi a cikin bola an yasar da shi shi ne dalilin da ya sa na ɗauke. Kusancin da yake da shi da ni da iyalina da kuma ƴancin da yake da shi a cikin gidan nan babu wanda za a gaya wa cewar ba ni na haife shi ba ya yarda". Take jikina gabaɗaya ya soma rawa sa boda ban taɓa tunanin amsar da zai furta ba ke nan, tabbas sai yanzu na ƙara tabbatar da cewar sanin ainihin halin mutum sai Ubangijin da ya halicce sa, muryarsa ce ta dawo da ni cikin duniyar zahiri daga na tunanin da na yi nisan kiwo a cikinsa. "Zo ki zauna a nan gefena mana ƴan mata". Rawan da jikina yake ya ƙara tsananta ba ni da wani mafita illa na yi abin da ya ce mussamman da na lura babu wani ƙarfi a jikinsa hatta maganar da yake yi ƙarfin hali ne kawai da taurin rai gami da kaifin da linzamin bakinsa yake da shi. A hankali na soma tako wa ina ɗaga ƙafata har na iso inda yake zaune zan zauna ke nan ya damƙo tulin gashin kaina da na tufke shi ta bayan wuyana ya riƙe tamau tamkar zai cire su. "Me ye kika sa min a cikin shayin da na sha?". Ya jefa mini tambayar da ta haifar mini da rawan jiki da harbawan zuciya fiye da kima a kimiyyance. Na yi ƙarfin halin faɗin"ni babu abin da na saka maka, ka sakar mini gashina". Ya riƙe mini gashi tamau har sai da na ji kaina kamar kaina zai faɗo ƙasa, duk jijiyoyin kaina na ci sun riƙe har sai da idanuna suka soma rufe ba, numfashi yana ta sama da ƙasa sai da ya yi yin sa ya hankaɗa ni gefe na faɗi sai a lokacin na samu na kwace kaina, na tashi na koma can ƙarshen ɗakin ina kallonsa, yayin da ya zame ya kwanta akan kujerar ƙafafunsa suna reto ya soma wani nauyayyen bacci da hakan ya haifar mini da sauƙe wasu wahalallun ajiyan zuciya masu nauyin gaske. Na ɗan matso inda yake a tsorace na tabbatar da cewar ya yi nisa a baccin da ya yi. Na durƙushe akan gwiwoyina yayin da wani kuka mai ƙarfi yake kufɓe mini ji nake yi raina gabaɗaya yana tugunzuma, sai a lokacin na raruma wayar na kashe naɗar sautin da nake yi. Sosai nake kukan kamar raina zai fita daga cikin gangar jikina yayin da kalaman da Sheik suke yi mini amsa-kuwwa a cikin naƙurar naɗar sautina ji nake yi tamkar a lokacin yake furzo zantukan. Ƙirjina ya yi mini nauyin gaske tamkar wacce aka yi mini ajiyar dutsen dala ba gammo haka na kwana ina kuka wajajen ƙarfe uku da rabi na daren na ji an buɗo ƙofar ɗakin na yi zumbur na tashi tsaye. Deeno ne da Zinariya suka shigo cikin ɗakin muna haɗa ido da ita na tafi da hanzarina na je na rumgume ta tsam a jikina ban san sa'ilin da wani kukan ya kuma ƙwace mini a karo na barkatai. Ta ɗago ni daga jikinta ta na share mini hawayen fuskana"Ina fatan komai ya tafi yadda muka tsara ko?". Na gyaɗa mata kaina alamar e yayin da wasu hawayen suke ta ambaliya a bisa dandamalin fuskana. Ta riƙo hannuna muka tattare kayan da na shigo da shi muka mayar cikin jakar muka fice daga cikin ɗakin, na shiga banɗaki na wanko fuskana na zo na gyara ta na zauna akan hannun kujerar da yake kwance a kai na ɗan ranƙwafo kaina daidai fuskarsa Zinariya ta kafta mana hoto, sai da na sauya wurare aƙalla sau uku ta na ɗauka mana hoton kana muka fita daga cikin ɗakin. Sai da muka sauƙa ƙasa muka shiga wani ɗan madaidaicin ɗaki da ki rabin wancan bai kai a girma ba balle kuma a zo batun kayan alatun da suke jibge a cikinsa, muna shiga ciki na zube akan gadon tamkar wacce ba ta san ciwon jikinta ba na ci gaba da reron kukan. Ɗaukar wayar Zinariya ta yi ta kunna sautin da na naɗa tana sauraro ita da Deen yayin da duk suka tattara hankulansu a wajen guda, ba su tsagaita ba har sai da suka saurara tsaf. "Tabbas wannan abun babban lamari ne. Hakiƙa kin yi abin da ya dace a yaba miki". Deeno ya yi zancen cikin jinjin girman ƙoƙarin da na yi. Zinariya ta ɗago ni daga kwancen da nake na zauna kana ta zuba mini ido muryarta cike da rauni ta ce"Amatullah da gaske a rayuwarki ta baya kin taɓa zubar da ciki? Sannan baƙin cikinki ne ya yi sanadiyyar rayuwar mahaifinki? Mahaifiyarki kuma ta sallamaki ga duniya?". Ta watsa miji tambayoyin a dunƙule kuma a lokaci guda, sai da na ja dogon numfashi mai nisan zangon kafin na sama zarafin warware mata tsakanin zare da abawa, babu abin da na ɓoye mata game da gurɓataccen tarihin rayuwata na sanar da ita komai ba tare da na rufe wani abun ko na kwaskware shi ba. Tun da na soma ba ta labarin take zubar da hawaye har na kai aya ina ƙarewa da faɗin"to yau dai kin sauraru tarihin rayuwata kin san wace ce ni...". Ba ta bar ni na ƙarisa ba ta rumgume ni duk mu biyu muka tuntsire da wani irin kuka mai matuƙar cin rai da azabtar da ruhi. "Tabbas bakin uwa masifa ne ga ƴaƴanta abin da da yawa-yawan iyaye matan wannan zamanin ba su fahimta ba ke nan. Kaifin harshen Ummanki akan ki shi ne abin da yake bibiyar rayuwarki Amatullah, shi yasa ake ce wa DAFIN HARSHE ya zarce dafin maciji cutar wa da gurɓata duk wani abun da ya soma baki a ciki". Ban iya amsa mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba sa boda nauyin da bakina ya yi mini, harshena ya cika mini bakina da hakan ya taka rawar ganin wajen hana maganata fita. Deeno ne ke ta ba mu haƙuri har muka tsagaita da kukan da muke yi lokacin har ƙarfe biyar ɗin asubahi ya yi har an fara haramar ƙiran sallan asubahi. Na tashi na shiga cikin banɗakin da take cikin ɗakin na yi alwala na zo na gabatar da sallan a zaune sa boda gabaɗaya jikina babu ƙwari, ba na zato da tunanin ƙafafuna za su iya jure ɗaukar nauyin gangar jikina. Ko da na iddar da sallan na yi dogon addu'an kafin na tashi daga wajen lokacin kusan ƙarfe shida saura, muka fara haramar tafiya Deeno ya kawo mana face mask ya ce mu saka haka kuwa muka yi muka saka kafin muka fito muka yi sallama da Deeno muka hau adaidaita zuwa gida, tun da muka shiga ban ce komai ba illa lumshe idanuna da na yi ji na nake yi tamkar majinyanci don ba na iya aikawatar da komai. Ko da muka iso gida sai da Zinariya ta taɓo kafaɗuna kafin na ankare da cewar mun iso na sauƙa, ta miƙa masa kuɗinsa ya ja napep ɗinsa ya bar wajen, Zinariya ta kallo ni tare da cewa"wannan damuwar duk na mene ne Amatullah? Na yi tunanin tun da yanzu kam kin cika burinki ai komai ya zo ƙarshe babu abin da ya dace da ke face farin ciki da kuma murna cikar muradinki". "Ni ma kaina hakan na yi tsammani sai dai ban san dalilin da ya sa na tsinci kaina cikin wannan damuwar ba". Cike da ƙarfafawa ta ce"mu shiga ciki ki huta, da yardan Allah yanzu kam komai ya zo ƙarshe". Ta riƙo hannuna muka shiga ciki kai tsaye ɗakinta muka nufo ta buɗe mana ƙofar muka shiga ciki, a nan ɗin ma kwanciya na yi na rufe jikina ruf sa boda yadda nake jin wani sanyi yana ratsa jini da gaɓoɓin jikina. Ina kwance na ji Zinariya na magana. "Ki tashi mu je wajen Hajiya Babba ki yi mata wannan babban albishiri ɗin, ina da tabbacin ita da kanta ma sai ta sara miki balle kuma fadawan natan". Furucinta ya tilasta mini yaye bangon da na lulluɓe har kaina da shi sai a lokacin na ga har rana ta fito ta dalle ko'ina da haskenta. Na yi miƙa haɗe da faɗin"wai har gari ya waye haka?". "Tun yaushe kuwa, yanzu fa kusan ƙarfe goma ake nema ba". Na waro idanuna waje cike da mamaki na tashi daga kan katifar ta miƙo mini wayar na amsa muka nufi ɗakin Hajiya Babba tare. Tana kishingiɗe muka iske ta muka gaishe ta ta amsa mana fuskarta babu yabo babu fallasa. Kafin mu ce komai ta tare mu da faɗin"ina fatan dai ki na lissafin ragowar kwanakin da suka rage miki ko?" Na kaɗa ina murmushi kana na furta"ai in sha Allah ma daga yanzu duk wani lissafi ya ƙare, yau na zo gabanki da cikakkun shaidun da za su tabbatar miki da cewar duk wani alwashin da na yi na cika sa tsaf". Na lallasa wayar na shiga fegin hotunan da muka yi na miƙa wayar ta sa hannu ta amsa tana kallo sai da ta kalle su tsaf kafin ta ce"amma ai satan ɗaukar hoton aka yi tun da gashi ma kwance yake yana bacci, aka yi hoton". "Hajiya idan kin tuna a cikin yarjejeniyarmu ba ki gindaya mini sharaɗin cewar sai na farke zan yi hoto da shi ba, don haka ko yanzu aka tashi tabbas ni na ci wannan wasan". Ta ɗan yi shuru ta na ta ƙare wa hoton kallo kafin ta ce"wannan hoton anya kuwa ba haɗa wa aka yi ba?". "Hajiya ki dai ƙara duba wa sa kyau". Zinariya ta ba ta amsa, wayarta ta ɗauka ta ƙira Aminu ta ce duk inda yake ya zo yanzu ta na son ganinsa, ya kuma amsa mata da cewar ga shi tafe daman ba nisa ya yi ba. Cikin ƙasa da mintuna ashirin ya bayyana a cikin ɗakin ta miƙa masa wayar ta na faɗin"karɓi ka duba hoton nan ka gane min haɗa wa aka yi ko kuma na gaske ne". Na amshi wayar yana kallon hoton tare da yin zooming ɗinsa ciki da waje, sai da ya gama ƙure basirarsa kafin ya ce"billahillazi Hajiya wannan hoton na gaske ne ba haɗa wa aka yi ba, sannan ba aikin AI ba ne wannan na'urar zamani mai ƙwaƙwalwar nan. Wannan hoton na gaske ne". Ya mayar da idanunsa kaina. "Tabbas kin cika mai cika duk wata maganar da ta furta kin kuma cancanci a jinjina miki bisa wannan na mijin ƙoƙarin da kika yi, yanzu kam ai sai ki kama harka babu kama hannun yaro ko?". Na ɗan murmusa kafin na ce"ina buƙatan lokaci na yi tunani akan hakan, kafin na fara aiwatar da komai". "Duk yadda kika ce haka za a yi ranki ya daɗe. Amatullahi mai abin mamaki ga sani fal ga kuma shagala". Duk mu ukun muka yi dariya ban da Hajiya Babba ta da murtuƙe fuskarta tamkar magribar ɗinya ta soma faɗin"akwai wasu maza biyu da suka zo neman ki jiya cikin gidan nan in taƙaice miki bayani a jiyan kawai sai da suka zo sau kusa biyar. Na shaida musu cewar ba za ki kwana a gida ba jiya ki na can otel don haka su dawo yau da misalin ƙarfe biyu na rana, don haka sai ki shirya tabar baƙi. Duk da ma dai na ga ba wani tsiyar ba ne a tare da su". Ban kawo komai a cikin raina ba don na ɗauki zantukan natan kamar ƙidan shata don haka na ce"Allah ya kawo su lafiya ina nan ina jiran su". Da haka muka yi mata sallama muka koma ɗakinmu Zinariya ta yi mana girki muka ci na kwanta bayan na sha maganin zazzaɓi da na ciwon kai take bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni ba ni na tashi ba har sai da aka yi sallan zuhur, Zinariya ta tashe ni na yi salla bayan na iddar ta zo ta zauna da inda nake zaune. "Yanzu me ya tsarinmu na gaba? A tunanin a waye ya dace mu turawa wannan sautin muryar da kuma hotunan nan?". Na ja dogon numfashi mai nauyi da sauti na fesar kafin na sama lasisin faɗin"tunanin da ni ma nake yi ke nan, amma zuciyata ta fi aminta da cewar mu nema lambar Muhammad Taufik mu tura masa sautin muryar. Hotunan kuma mu goge su tun da daman sa boda mu gamsar da Hajiya muka yi su". Ina rufe bakina Aminu ya ɗago labulen ɗakin ya shigo ya zauna duk muka bi shi da kallo. "Ga can baƙinki fa sun iso, su na falon Hajiya su na jiranki". "Wai daman da gaske ne an zo nema na? Ni kuwa waye na sane da zai taso takanas ya zo cikin gidan nemana?". Ya ɗage mini kafaɗarsa alamar shi ma ba shi da masaniya akan hakan. "Ke kuwa ki tashi mana ki je ki ga su wane ne. Tun da an ce gani ya kori ji". Zinariya ta yi zancen da ya kama hankalina, ba cire hijabina da yake kaina da na yi sallan da shi ba na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba. Na bi takalaman maza da suke ƙofar ɗakin kafin na shiga ciki. "Hajiya ga ni". Na furta ina daga tsaye tare da tsayar da ƙwayoyin idanuna akan ta. Ta taɓe baki"ba ni nake nemanki ba. Baƙinki ne ga su can". Ta ƙare zancen tana yi muni nuni da samari biyu da suke zaune a cikin falon da sai a lokacin idanuna suka kai kansu. Take numfashina ya ɗauke na wuce gadi sakamako tozali da na yi da mutanen da ba na tunanin sake ganin su a nan kusa a cikin rayuwata. Jikina ya na rawa tamkar mazari na nuna su da ƴar manuniyar ƴatsata. "Yaya Alhassan da Amir ku ne?". Na yi zancen cikin rawar jiki da na murya, duk su biyun suka tashi tsaye muna kallon juna. Yaya Alhassan ya ce"Amatullah ke ce kika dawo haka? Ke ce kike rayuwa a cikin gidan nan". A raunane ya ƙarishe zancen kamar zai yi ƙwalla. Na ji kaina ya soma juya idanuna suna hango mini abin da yake gabana bibiyu, ƙafafuna suka soma karkarwa na yi lu na faɗi a wajen babu wani gaɓar da take motsa wa a cikin gangar jikina. [12/18, 3:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 7️⃣2️⃣ Tun daga lokacin ban ƙara sanin takamanmen inda kaina yake ba, ban ƙara fahimtar komai ba haka nan idanuna ba su ƙara gano mini wani haske ba face gilmawar duhu baƙi ƙiri da babu alama ko ɗigon haske a cikinsa. Ban san iya adadin awannin da mintunan da na ƙarar ba na cikin hayyacina ba sai buɗe idanuna da suka yi mini nauyin gaske na yi na ganni kwance a cikin wani ɗaki wanda na ƙare wa kallo tsaf na kuma fahimci cewar ɗakin asibiti ne, kamar yadda na ga robar ƙarin ruwa a maƙale a hannuna na yi yunƙurin tashi sai dai kash! Gangar jikina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan a aikatace. Ban san sa'ilin da ruwan hawaye masu ɗumi suka soma rige-rigen fita daga koramar idanuna ba sai jin ɗumin sauƙarsu na yi a bisa fatar fuskana. Abubuwan da suka wakana kafin na tsinci kaina cikin wannan yanayin da nake ciki ya soma dawowa cikin kwanyanta tiryan-tiryan, na cije leɓan bakina ina jin zuciyata tana buga wa ɓat-ɓat tamkar allon ƙirjina zai dare zuwa gida biyu. Wahalallen numfashi na ja a karo na barkatai na fesar daga bakina yayin da na kai hannu na fincike ƙarin ruwan da aka maƙala mini a hannu. Na tashi na zauna da ƙyar yayin da nake jin kaina ya na sarawa tamkar zai faɗo ƙasa. Ban yi aune ba na ji hawayen da suke zuba daga idanuna sun ƙara ƙarfin gudu ta yadda suke wanke mini fuskata babu ƙauƙautawa. A bayyane na furta"Yaya Alhassan me yasa kuka bayanna a cikin rayuwa a daidai wannan lokacin? Lokacin da nake dab da cika buri da muradin raina burin da ya daɗe a cikin farfajiyar ƙirjina. Ba zan iya haɗa ido da ku idan lokacin da ya dace na koma gare ku ya yi tabbas ni da kaina zan kai kaina inda kuke amma ba yanzu ba". Ina gama zancen na diro daga kan gadon na ɗauki hijabina da yake gefe na mayar da shi kaina na fice daga cikin ɗakin, ina ta faman dube-dube da waige-waige, Allah ya tarfawa garina nono har na fita daga cikin ɗakin ban ga ɗaga cikin waɗanda nake guje musu ba. Daidai na iso ƙofar da zai sada ni da harabar cikin asibitin na ji na yi karo da mutum har sai da na yi tangal-tangal zan faɗi aka riƙo hannuna na tsaya cak akan ƙafafuna, na dafe ƙirjina sa boda tsananin tsoron da na ji yayin da nake cira kai don ganin wanda ya kawo mini agaji. Idanuna suka gauraye cikin na Yaya Alhassan da yake tsaye a wajen ya kafe ni da idanu kamar yadda ni ma na kafe sa da na wa idanun, da har suka ƙanƙace sa boda azababben kukan da na yi a cikin ɗakin bakin na fito. Shi ya fara janye idanunsa daga kaina yana riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya yayin da hannu ɗayan yake riƙe da wani ledan baƙa. Cike da takaici ya soma faɗin"ina kika fito za ki je bayan ke da ba ki da lafiya har an kwantar da ke a gadon asibiti?". Bai jira na ba shi amsa ba ya ci gaba da faɗin"guduwa kika fito za ki yi ko?". Ya jinjina kansa kafin ya zarce da faɗin"Amatullah me yasa lalle kike son ki ga kin butulcewa ni'ima da ilhaman da Allah Ubangiji ya yi miki ne? Me yasa kike ta ƙoƙarin watsa ƙasa a idanun mutanen da suka ɗaura yarda da amimcinsu kacokam akan ki? Allah ya rufa miki asiri amma ki na ta ƙoƙarin tona wa kanki asiri ga idon duniya, wai ina hankali da tunaninki suka yi ƙaura suka tare ne? Ina wannan ilmin nakin da sanin ya kamata da kowa yake yabanki da shi?. Idan kin zaɓa ki guje mana a wannan karon kam ba zan yi ƙoƙarin dakatar da ke ba, tun da ba ki duba wahala da tudu da gangaran da muka bi kafin har muka gano inda kike rayuwa muka zo domin tsamo ki daga halaka ba, idan a baya mun yi miki uzuri akan duk abin da kika aikata tare da danganta hakan da cewar damuwar da kika tsinci kanki, zafin mutuwar mahaifinki da kuma raɗaɗin kalaman da mahaifiyarki ta furta a gare ki su suka haɗu suka yi taron dangi wajen ingiza zuciyarki har kika aikata abin da kika aikata. Wallahi a yanzu idan kika ƙara gangancin ƙara aikata wani kuskure babu wanda zai yi miki uzuri. Amatullah ba mu zo don mu tursasa ki ba amma tun da har yanzu zuciyarki ta na kitsa miki ki sanya ƙafa ki guje mana ba za mu yi miki tilas ba rayuwarki ce ki na da dama da ikon ki yi duk yadda kike so. Ki na da ikon ki zartar da duk wani hukunci da kike tunanin ya fi dace wa da rayuwarki tun da mai ɗaki ai shi ya san inda yake yi masa yoyo, ga hanyar nan ki tafi duk inda kike tunani da zaton za ki sama kwanciyar hankali daman fatanmu a ko yaushe bai wuce ki yi rayuwa cikin nutsuwa ba, sai dai a duk lokacin da kika nemo mu don mu zame miki gata tabbas za mu ba ki mafaka don na yarda da wannan karin maganan da ake cewa hannun ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. Kuma babu inda za ki je ko juyin zamanin da zai sa mu sauya ki daga kasancewarki ƴar uwa kuma jininmu. Don haka zaɓi ya rage ga mai shiga rijiya". Yana rufe bakinsa daidai lokacin da Amir ya iso wajen duk ya bi mu da kallo kafin ya ce"Yaya ya na ganku a nan a tsaye? Ko dai an sallame ta ne?". "Ba a sallame ta ba Amir ta dai sallama kanta ne, tun da har ta na ƙoƙarin guduwa". "Guduwa kuma? To in ta gudu ta je ina?" Cikin da takaicin da ya haɗe da tarin baƙin ciki Yaya Alhassan ya ɗage kafaɗunsa alamar mai sani ba a hankali ya furta"ga ka ga ita sai ka tambaye ta, ta ba ka amsa don ni kam na gama magana da ita sai dai na saurari hukuncin da za ta yanke". Yana dasa aya a zancensa ya juya ya koma cikin asibitin na lura kafin ya gama maganar har sai idanunsa suka kawo ruwan ƙwalla. Na durƙushe akan gwiwoyina sakamakon gazawar ƙafafuna yayin da na fashe da wani kuka mai rikitarwa da narkar da zuciyar mai saurare. Ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyar da Amir ya saka kafin ya soma magana cikin sanyin jiki da na murya. "Amatullah rayuwar da kika zaɓa wa kanki ke nan kuma ki na tunanin wannan hanyar da kika kai hanya ce mai ɓullewa?. Tun ranar da muka wayi gari babu ke tun daga wannan ranar ba mu ƙara yin bacci cikin salama ba, duk ranakun duniya kanmu muke zargi akan duk wani halin da kika tsinci kanki a ciki, kan mu muke ɗaura laifi tare da lashen takobin nemo a duk inda kike a cikin duniyar nan matuƙar ki na numfashi". Shi ma ya dasa aya a zantukansa ya juya ya bi bayan Yaya Alhassan ransa a matuƙar ɓaci idanunsa sun kaɗa sun yi jajir da su tamkar wanda aka watsa masa tsakin garin niƙaƙƙen barkono a cikin idanunsa. Ji na yi kaina ya yi dum tamkar wacce aka ɗaura wa dutsen zuma. Na soma kokuwa da numfashina da yake maƙale mini a ƙirjina da na ji kamar an sanya taɓarya an tokare mini ƙirjin, jikina gabaɗaya ya ɗauki rawa dole na tashi daga wajen sa boda hanya shiga da fita da mutane suke ta zirga-zirga a wajen. A hankali na soma tafiya bayan na ɗauki hanya komawa cikin ɗakin da na fito yayin da zantukan Yaya Alhassan suke yi mini amsa-kuwwa a cikin kunnuwana tamkar a lokacin kalaman suke ratsa tsakanin leɓɓansa suka fitowa a wannan lokacin. Ko da na iso ƙofan ɗakin sai na dan yi jim ina daidaita nutsuwata kafin na turo ƙofar ɗakin na shiga bakina ɗauke da siririn sallaman da ya tsaya iya kan leɓena. Ba su amsa mini ba illa zuba mini ido da suka yi kaman yau suka fara ganina kaina na rusunar ƙasa sa boda na rasa ƙarfin gwiwan da zan iya haɗa ido da su. Jikina ya soma rawa da hakan a tursasa mini durƙushewa akan gwiwoyina ina wani kuka mai tsananin ƙarfi duk yadda na so na yi magana bakina ya ƙi haɗin kai wajen lanƙwansa harshena balle har sautin maganan ya fita ta yadda za su iya ji abin da na furta. Gabaɗayansu suka yi shuru babu sautin da yake tashi a ciki ɗakin face sautin kukan da nake yi mai matuƙar cin rai na ɗau lokaci ina kukan tamkar raina zai yi bankwana da gangar jikina kafin can na tsinkayo amon muryan Yaya Alhassan a kaurare ciki tsare gida babu alamar wasa ko kaɗan a tattare da shi. "Ki hanzarta ki sanar da mu hukuncin da kika yanke, don mu ma mu san inda dare ya yi mana". Sai da na ja dogon numfashi mai nisan zango kafin na sama zarafin raba tsakani haƙwarana da suka manne da juna tamkar waɗanda aka sanya mayen ƙarfe a tsakaninsu. Cikin raunin da yake fito wa kai tsaye daga ƙasan zuciyata ba tare da wani shamaki ba na ce"don Allah ku yi haƙuri ku yafe mini na san na baƙan zuciyoyinku....". Ya ɗaga mini hannu alamar ba ya son jin wani abu daga gare ni. "Ba wani dogon jawabi muke buƙatar ji daga gare ki ba Amatullah. Hukuncin da kika yanke kawai muke son ji shin kin zaɓa ki ci gaba da rayuwa a nan inda muka same ki, ko kuma za ki haɗa kayanki mu koma gida gaban iyayenmu mu rayu cikin farin ciki da sanyawar albarkarsu a gare mu? Don ke yanzu ba yarinya ba ce babu wanda zai yi miki dole balle har ya tursas ki ki aiwatar da abin da ba kya ra'ayinsa". A kufule ya ƙare zancen cikin zafin rai tamkar zuciyarsa za ta fito waje tsabar tafasar da take yi, lamarin da ya ƙara azalzalan ruhina hawayen da nake yi suka ƙara karfin gudu suna zuba daga cikin idanua tamkar bakin indararo. "Na amince zan bi ku mu koma gida tare". Na yi furucin muryata a shaƙe tamkar kwaɗon da aka danna kansa a cikin ruwan zafi. Duk su biyun suka yi shuru kafin can Yaya Alhassan ya ce"kin amince da hakan har cikin ranki ko kuwa dai kawai babu yadda kika iya? Don wallahi ba zan ɓoye miki ba tun da na ga kin yi ƙoƙarin guje mana daga cikin asibitin na ji gabaɗaya gwiwoyina sun yin sanyi ba na son mu yi miki tilas kuma daga baya a zo ana dana sani da cizon ɗan ƴatsa". Na zuƙe majinan kukan da ya zo mini kafin na sama damar cewa"na amince wallahi". Na ƙare zancen cikin karyewan zuciya da rashin ƙwarin jiki. Kafin su ce wani abu aka buɗo ƙofar ɗakin aka shigo tare da yin sallama da tashin farko na gano muryar Zinariya ce, duk sai da ta gaishe su kafin ta tambayi ya ya mai jiki, Amir ne ya amsa da cewar da sauƙi. Duk suka miƙe tsaye Yaya Alhassan yana faɗin"bari na je wajen Likitan ya ba mu sallama". Amir ya rufa masa baya suka fita tare suka bar ni daga ni sai Zinariya zaune a cikin ɗakin, ita ta taimaka mini na tashi na zauna daga durƙushewar da na yi na jingina bayana jikin matashin da ta sanya mini a bayana don na ji daɗin zaman, na lumshe idanuna yayin da wasu hawaye masu zafi suke fitowa daga cikin idanuna da nake jin sauƙar su bisa fatan fuskana tamkar sauƙan tafasasshen ɗanyen ruwan dalma mai turiri. "Ya ya jikin nakin?". "Da sauƙi". Na amsa da shi ba tare da na buɗe idanuna na gan ta ba. "Wallahi gabadayanmu mun tsorita da irin yanayin da kika shiga lokaci guda fa kika fita daga cikin hayyacinki, babu wani wanda zai gan ki a wannan lokacin ya tsammata miki za ki ƙara yin numfashi ko da na sakon ɗaya ne a cikin wannan duniyar. Waɗannan mutanen da suka ikirarin cewar su ƴan uwanki ne su ne suka kawo ki asibiti tare da ni aka yi komai don jiya har sai dare kafin na bar cikin asibitin nan, don Likitotin sun ce babu wanda zai kwana a wajenki. Waɗannan mutane sun nuna miki ƙauna mai ƙarfi da ta amsa sunanta, a dai cikin wannan duniyar da muke rayuwa a cikinsa da mutanen kirki suka yi ƙaranci da wuya a sama masu kirki da tausayinsu. Daman ki na da ƴan uwa maza ne? Don a labarin da kika ba ni kin ce ke ce ɗiya ɗaya tal a wajen iyayenki?". Na furzar da iska mai zafi daga bakina kafin na soma ba ta amshoshin tambayoyinta. "Tabbas kam yadda suka ce su ɗin ƴan uwana ne, sai dai ba muharramaina ba ne. Mahaifiyarsu ce yayar mahaifina uwa ɗaya uba ɗaya. Mai farin kayan shi ne Yaya Alhassan wanda aka so haɗa ni aure da shi ɗayan kuma ƙaninsa ne Amir wanda yake bin bayansa, idan ba ki manta ba su ma na ba ki labarinsu". Cike da mamaki ta riƙe haɓa"yanzu Amatullah wannan zankaɗeɗen saurayin kika ƙi aura? Shi kuwa me ye laifinsa? Ga shi da kyau, ga ƙira da kuma kwarjini da ɗin da ɗawa ga kuma daɗin murya". Jinjina kawai na yi ba tare da na ce da ita uffan ba don na lura da yanayinta ko da na cewa wani abu, ba lalle ba ne ta fahimta balle har ta fahimci halin da zuciyata take ciki. "To yanzu me ye dalilin wannan zuwan da suka yi? Don fa sai da aka ɗeba ƴan kallo tsakaninsu da Hajiya Babba ta yi musu tijara mai wasali, wannan ƙaramin har sai da ya fusata ainun don har sai da ya yi yunƙurin kai mata mari Aminu ya amshe cikin faɗan. Nan ta tada tijarar sai an biya ta kuɗin hayan ɗakinta da kika zauna a cikin kaf, Aminu ya bijiro da na shi buƙatar sai da aka biya shi wai kuɗin ɗawainiyyar ciyar da ke da ya yi a lokutan baya. Take suka karɓa lamban asusunsu suka tura musu kuɗin, kafin Hajiya ta bari suka kawo ki wannan asibitin ta kuma gindaya musu sharaɗin yadda suka fita da ke a cikin gidan nan, to su tabbatar da cewar kin fita ke nan har abada ko kin dawo sai dai ki nema wani masauƙin amma dai ba cikin gidanta ba". Cike da damuwar da yake barazanar tarwatsa zuciyar da take kwance a cikin ƙirjina, na kai hannuna na dafe kaina da yake sarawa da ƙarfi. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Me yasa Hajiya kuwa za ta yi mini haka?". "Babu wani dalili illa na baƙin ciki da tsanar da ta yi miki tun farko, mussamman da kika ƙi bin layin da ragowar ƴan matanta suke bi. Ga ki da diri da kuma sura komai cif-cif kin ga kuwa ai da kin ba da kai bori ya hau ba ƙaramin harka za a buga da ke". "Ai kuwa in sha Allahu na bar cikin gidanta ke nan har abada". Zinariya ta yi hanzarin tarar numfashina"ban ga ne kin bar gidan har abada ba ina za ki koma ke nan?". Na kwashe duk yadda muka yi da su Yaya Alhassan na sanar da ita, ina gama ba ta bayanin kawai na ga ta fashe da kuka sosai lamarin da ni ma ya saka ni kuka muka rungume junanmu babu mai lallashin wani a cikinmu. Ni na fara yin ƙarfin halin tsagaita na wa kukan na ɗago kanta ina share mata hawayen fuskanta tare da faɗin"zan koma gida Zinariya Allah ya yanke mini wannan zaman ƙasƙanci da wulaƙancin. Ke ma ina mai ba ki shawara ki yi wa kanki karatun ta nutsu ki koma gida, na tabbatar da cewar iyayenki za su amshe ki". Cikin muryar kukan da ya gama galabaitar da ita ta ce da ni"Amatullah ba zai yiyu yanzu in ce zan koma gida ba in kuma na yi yunƙurin hakan to ina mai tabbatar miki da cewar sai dai a komar da gawata. Sa boda mun riga da mun shiga cikin ƙungiya mun kuma yarda za mu yi biyayya ga dukkan dokoki da sharaɗoɗinta duk wanda ya ce zai fita to ɗayan biyu ne ko dai ya haukace ko kuma ya bar cikin duniyar gabaɗaya. Ke ma da ba kya cikin ƙungiyar ina jiye miki tsoron abin da Hajiya Babba za ta iya yi a kanki mussamman yadda suka yi musayar yawu da ƴan uwanki". Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau na kasa cewa komai har sai da ta ci gaba da maganar"ke dai Allah ya ƙaddara ba za ki saɓa masa ba ta hanyar keɓe wa da wani ɗa na mijin da ba halal ɗinki, ƙaddarar rayuwa a barikin ce kawai a kanki amma babu ƙaddarar saɓawa Ubangiji. Na taya ki murna da ba ki bari sheiɗan ya yi nasara akan yi ba haka nan ba ki taka rawa a lokacin da yake buga gangar sheɗancinsa ba, za ki koma gidan iyayenki cikin aminci da kuma mutunci Amatullah. Ga wannan wayar ki tafi da ita idan kin nutsu ki ba wa ƴan uwanki su saurari abin da yake ciki na san cewa za su fahimce ki". Tana gama maganan ta riƙo hannuna ta damƙa mini wayar yayin da ta fashe da wani kuka da ni ma ya tursasa hawaye kwaranya daga idanuna. Ban iya ce mata ko kanzil ba har zuwa lokacin da Yaya Alhassan suka dawo cikin ɗakin tare da Likitan ya duba ni ya kuma tabbatar da cewar jikina ya yi sauƙi ya rubuta mana sallama tare da wasu magungunan da ya ce lalle a saye su, kuma na fara amfani da su da gaggawa. Haka muka fito har cikin haraban asibitin hannuna saƙale cikin na Zinariya, da Yaya Alhassan yake ta yi mata nasihar ta tuba da koma zuwa ga Allah da ya kasance gafurul rahim. Kanta kawai take gyaɗa masa don da ni da ita mun an cewa akwai ɓoyayyan matsalan da bala'in da yake tattare da hakan. Ko da muka zo rabuwa da ita ji na yi tamkar raina zai bar gangar jikina. Haka muka sha kukanmu Amir ya din ga ba mu haƙuri da ƙyar muka saki hannun juna, haka muka rabu muka hau adaidaita muka nufi tasha, muna isa muka saka motar garinmu ba mu yi mintuna goma ba ta shiga muka soma tafiya. Tun da muka soma tafiya ƙirjina yake bugawa har muka isa cikin garin, ina fitowa daga cikin motar na ji gabana ya faɗi da har sai da na runtse idanuna, muka tara adaidaita muka shiga na lura har zuwa wanna lokacin Yaya Alhassan fushi yake yi da ni hatta magana ma sama-sama yake yi mini shi ma sai ya zama dole ne. Mu na iso ƙofar gidan Anty Sawwama na ji wani zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe wajen gabaɗaya ya sauya miki tamkar wacce ta yi shekaru goma cur da barin cikin gidan, da ƙyar nake ɗaga ƙafata da na ke jin ta tamkar ba ta kasance ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikina ba yayin da wani jiri yake kwasa ta da barazanar buga Ni da ƙasa haka muka ƙarisa cikin gidan da Anty Zulaihatu da ta fito daga banɗaki na fara tozali. Mamakin ganina ya sanya ta sakin butar da ke hannunta ya faɗi zuwa ƙasa, ta murtsuke idanunta don tabbatar da cewa ni ɗin ce dai ko kuma gizo nake yi mata, sai da ta tabbatar da cewa ni ce tsaye a gabanta kuma a zahiri ba mafarki kana ta kurm salati ta bi bayansa da hamdala tana faɗin"Umma Umma fito ki ga wallahi ga Amatullah ta dawo". Ta ƙare zancen tana isowa inda nake ta rungume ni, ni kam na kasa yin komai illa hawayen da suke ta zuba daga idanuna har izuwa lokacin da Umar da Anty Sawwama suka fito, mu na haɗa ido da ita ta ja ta tsaya a wajen guda kawai ta kafe ni da ido ba tare da ta ce da ni komai haka nan ba ta ƙariso inda nake ba. Na sa ƙarfi na ɓanɓare Anty Zulaihatu daga jikina na isa gaban Anty Sawwama na durƙusa akan gwiwoyina sai dai na gaza cewa komai na tsawon mintuna illa kukan da na ci gaba yin sa da dukkanin ƙarfin da Ubangiji ya azurta ni da shi. [12/19, 1:20 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________________ Page 7️⃣3️⃣ Na salwantar da wasu mintuna masu tsayin gaske ba tare da na iya cewa komai ba illa kukan da har izuwa lokacin bai yanke daga idanuna ba, haka nan babu wanda ya ba ni haƙuri balle kalman lallashina Anty Zulaihatu ma kukan da take yi yayin da har nake jin sautinta. Sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙahon ƙirjina kafin na sama lasisin fesar da zantukan da suke bisa kan harshena cikin raunin da kai tsaye yake fitowa daga can ƙasan zuciyata da ta yi nauyin gaske. "Anty don Allah ki yi haƙuri ki yafe mini. Na san da cewan na aika muku ba daidai ba ina roƙonku da ku yafe muni dukkan kurakuren da na aikata a gare ku, ko hakan zai haifar mini da salama a cikin ruhina har ya yi silar wanzar da kwanciyar hankali da nutsuwa a cikin ƙirjina". Shuru ta yi ba tare da ta ce komai na tsawon wasu mintuna har sai da na yanke tsammani na kuma cire rai daga cewar za ta amsa mini, kafin na ji ta soma magana cikin rawar murya da ya taimaka wajen fallasa sirrin da yake taskace a cikin tsokar zuciyarta, na tarin damuwar da take ciki. "Amatullah ba ki yi mana laifin komai ba. Kuma ba mu riƙe ki a cikin zuciyoyinmu ba". Ta ƙare zancen hawaye yana zuba daga idanunta, da hakan ya ƙara gigita ragowar nutsuwar da ya yi saura a gangar jikina. Na cira kai na kalle ta na ga dai lalle hawayen da take yi, ban san sa'ilin da na ja jikina na riƙo ƙafafunta na rungume tare da jingina kaina a jikinsu ba. "Don Allah Anty ki yi haƙuri ki sassauta mini wannan halin da nake ciki. Duba fa ki ga kuka ki ke yi sa boda baƙin ciki da takaicin da na yi silar cusa muku a cikin zuciyoyinku. Wallahi ba zan taɓa yafewa kaina ba akan halin da na yi dalilin faɗawarku cikinsa". Da ƙyar na ƙare zancen sa boda numfashi da yake ta sama da ƙasa yana maƙale mini a ƙirji, ta sa hannu ta ɗago ni tsaye daga durƙushewan da na yi yayin da take goge mini ruwan ƙwallan da ya gama damalmala mini fuskana. Sai dai ita ma ta kasa magana sai da ta runtse idanunta kafin ta iya faɗin"kamar yadda na sanar da ke tun farko duk cikin mun nan babu wanda ya ƙullace ki a cikin ransa. Kullum fata da burin da muke kwana mu tashi da shi a cikin zuƙatanmu shi ne Allah ya amintar da ke a duk inda kike a cikin faɗin duniyar nan, kuma Allah ya karkato da hankali da tunanin zuwa gida sai kuma ga shi Allah ma ji roƙan Bayinsa ya amsa mana addu'armu a lokacin da duk ba mu yi tsammani ba. Amatullah yadda nake jin su Alhassan a cikin raina kuma na jin babu wani abun da za su aikata a gare ni wanda idan suka tuba suka yi nadama Ba zan iya yafe musu ba, haka nan ke ma babu abin da za ki yi wanda ba zan iya yafe miki shi ba. Sa boda kamar ƴata nake jinki". Ta riƙo hannuna"ta ku mu je ciki". Daga haka ta ja hannuna muka shiga cikin falonta haka ta sa Anty Zulaihatu ta tafasa mini ruwan zafi ta kai mini banɗaki na je na yi wanka haka nan na iske suturuna a gyare tamkar an san da dawowa ta cikin gidan, ɗakin ko'ina tsaf da shi babu alamar datti balle ƙazanta. Kayan sawana kuwa har da waɗanda aka goge su sai tashin ƙamshi suke tamkar mun haɗa iri da ƴan maiduguri. Haka na durƙushe akan kayan na ci kukana tamkar raina zai fi ta tabbas na so na butulcewa rahama da ni'iman da Ubangijina ya lulluɓe rayuwata da ita kamar yadda Yaya Alhassan ya furta hakan a gare ni, na ja dogon numfashi na fesar yayin da nake ƙara shaƙan ƙamshin da ya buɗaɗe cikin ɗakin ina tuno tarin ƙarni sa ƙazantan da yake tattare a cikin ɗakin da na dawo, hatta banɗakin ɗaya muke amfani da shi duk yawan jama'ar da suke rayuwa a cikin gida, mata da kuma matan ƴan gida da kuma baƙi, kafin ka tsuguna ka sauƙe buƙatanta wajibi ne sai ka kora ruwa. Sai da na ci kukana kamar babu gobe kana na tashi na gabatar da sallan zuhur da kuma Asr nan inda na yi sallan na zauna na haɗa kaina da gwiwa yayin da na faɗa cikin cakwalkwalin tunanin da yake barazanar tarwatsa ƙalbina. Ji da na yi an dafa kafaɗuna shi ya yi nasarar dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa, na cira kaina ina bin Anty Zulaihatu da kallo har ta iso gabana ta zauna tana kallona tamkar mai son gano wani gaskiyar da na haƙa rami na burne. "Amatullah". "Na'am" Na amsa da shi cikin sanyin amo da hakan ya ba ta lasisin ci gaba da maganar da take. "Mun yi kukan rashinki irin wanda baki ba zai iya furtawa ba, mun yi baƙin cikin kasancewarki a kusa da mu mussamman idan muka tuna amanarki da Kawu ya ɗauka ya damƙawa Umma lokacin da rai yake ƙoƙarin sallama da gangar jikinsa. Babu inda ba mu neme ki ba Amatullah sai dai tunaninmu bai taɓa ayyana mana cewa za ki iya zuwa ki yi rayuwa a cikin karuwai ba har ma ki ɗabi'antu da irin rayuwar da suke yi". Kalamanta na ƙarshe suka zaunana zuciyata tare da baƙanta mini rai da ruhina take wani kuka mai matuƙar sauti ya tsinke mini. Na kifa kaina a kan cinyoyinta ina ta fama rera kukan jikina har wani rawa yake ye yi ga wani zafin da nake ji yana ratsa har cikin jijiya da ɓargona. "Wallahi Anty ko daidai da rana guda ban taɓa aikata abin da kike zargina da shi ba. Ko karuwan da muka zauna da su cikin gida ɗaya za su ba da wannan shaidan a kaina cewar ban taɓa keɓewa da wani ɗa na miji ba". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"Amatullah Amir fa ya sanar da mu duk yadda aka yi da kuma irin dambarwan da aka yi da Magajiyar gidan Karuwan da kike zaune a ciki, kafin har suka iya samun daman tahowa da ke. Babban abin baƙin cikinmu ma shi ne a ranar da suke je neman ki a ba ka kwana a cikin gidan ba hasalima a ɗakin otel kika kwana". Cikin ƙarfin halin ta ƙare zancen sa boda kukan da ita ma ya karyo mata, kasa magana na yi illa jijjiga kaina da kawai nake yi yayin da zuciyata ta yi mini nauyin gaske yayin da na kasa samun damar harhaɗa kalaman da zan kare kaina a gare ta. Haka muka ci gaba da kukan ni da ita har izuwa lokacin da Umar ya shigo ya ce wai mu fito mu ci abinci sai da ta taimaka mini kafin na iya miƙe wa akan ƙafana muka fito falon, muka iske kowa yana zauna da Yaya Alhassan muka fara haɗa ido na ga ya wurga mini wani mungun hararan da ya hautsina kayan cikina, muka zauna tare da Anty Zulaihatu ta soma zuba abincin ga kowa yayin da dukkanmu muka yi shuru kowa da irin tunanin da yake saƙawa a cikin ruhinsa, juya cokalin kawai nake yi a cikin abincin don ni kam ba na tunanin ko na saka abincin akan harshena zan iya haɗiye wa har ya wuce ta cikin maƙoƙarona da ya bushe tamkar ƙasar sahara a cikin tsananin zafin rana. "Ki ci abincin mana". Na tsinkayo muryar Anty Sawwama ta sauƙa a cikin kunnuwana. Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina ɗan gyara zama na buɗe bakina zan yi magana kenan na ji wani kuka ya ƙwace mini mai matuƙar sauti, da ya jawo hankulansu gare ni na kifa kaina akan gwiwoyina ina rera kukan daga can ƙasan zuciyata. "Wannan kukan kuma na mene ne Amatullah?". Anty Sawwama ta jefo mini tambayar cikin tsananin kulawa yayin da take ɗago kaina da na kifa shi tana share mini hawayen fuskana. "Ya kamata ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi tun da sanda kika shigo cikin gidan nan fa, kuka kawai kike yi ko daidai da minti guda ba ki bar idanunkin sun huta ba. Ya kamata ki tausaya wa kanki". Numfashi mai zafi na ja na fesar daga baki kafin na sama damar cewar"Anty don Allah ku yarda da ni wallahi tun da sa ƙafata na fita daga cikin gidan nan, ban taɓa aikata wani abun da na san cewa Allah ya haramta sa da gangan ba, na yi iya ƙoƙarin kiyaye kaina daga faɗawa cikin halaka da fushin Ubangijina". Ta ɗaga mini hannu alamar maganar ya isa haka dole na ja bakina na yi masa linzami. "Mu gama cin abincin sai mu yi magana". Ban iya ce mata komai ba illa jinjina kaina da na yi, haka aka ci gaba da cin abincin sai dai ni kam ina ci ne kawai ba wai don ina jin ɗanɗanon abincin a bisa harshena ba, haka nan ba don ina son cin abincin haka na ci gaba da tuttura abin cin har muka gama ci. Muka tattare wajen tare da Anty Zulaihatu muka wanke kwanukan, na dawo na zauna a ɗaki ina ta tsammanin ko Anty Sawwama za ta aiko a ƙira ni ta ba ni damar fayyace musu komai amma ba ta yi hakan ba, haka muka kwana ba tare da wani ya ce mini ci kanki ba na yanki dare na yi kuka mai tsanani har sai da na ji numfashina yana cushewa waje guda kafin na tsagaita, na tashi na fita na ɗauro alwala na zo na fuskanci alƙibla na tada kabbara. Raka'a biyu na yi a fashe wa Ubangiji da kuka a cikin sujjadata na ƙarshe. Daren ranar ban iya runtsawa ba hakan ya sa ni washe gari na tashi da wani irin matsanancin zazzaɓi mai dafa jiki. Ina kwance a ɗakin Umar ya shigo ya iske ni a haka ya ruga ya je ya sanar da Anty Sawwama ta zo ta ɗago ni ta ji jikina ya ɗauki zafi gau. Ta sa Umar ya riƙa Yaya Alhassan ya zo shi ta ce ya kai ni asibiti yayin da ta umarce Anty Zulaihatu ta raka ni sa boda a gidan ta kwana, don a daren jiya na ji tana waya da mijinta yana shaida mata yau zai dawo daga tafiyar da ya yi. Hijabina na saka na tashi tsaye yayin da Anty Zulaihatu ta riƙe mini hannuna sa boda yadda jiri yake ta faman kai ni ƙasa. "Alhassan idan kun je ayi mata dukkanin gwaje-gwajen da suka kamata". Ciken rashin fahimtar inda zantukan natan suka nufo ya ce"wasu irin gwaje-gwaje ke nan Umma? Na yi tunanin ai zazzaɓi ne kawai". "A yi mata gwajin dukkanin cututtuka ciki har da na cuta mai karya garkuwan jiki da kuma gwajin ciki". Take na ji ƙirjina ya buga kwatankwacin irin bugun da maƙeri yake yi wa ƙarfi da dukkan ƙarfinsa. Kalaman Anty Sawwama suka karyar mini da zuciya tare da haifar da wasi-wasi a cikin zuciyata, mamaki ya cika mini raina sai dai na gaza juyowa na kalle ta kamar yadda na kasa ɗaga ƙafana na bar wajen. Sai da Anty Zulaihatu ta ja hannuna muka bar wajen kafin na dawo cikin hayyacina haka muka fita muka nema adaidaita muka shiga zuwa asibitin. Mu na zuwa aka ƙarbe ni aka yi mini duk wasu gwaje-gwajen da suka dace ciki kuwa har ta waɗanda Anty Sawwama ta lissafa. Tunin magunguna aka rubuta mini cikin har da ƙarin ruwa sun so su ba ni gado Yaya Alhassan ya ce su rubuta mini magani kawai. Haka muka saya magungunan jimgim muka koma gida a yadda muka iske Anty Sawwama ta na ta faman safa da marwa a tsakar gidan ya tabbatar mini da cewar duk da muka fita daga cikin gidan ruhinta bai huta ba hakan nan zuciyanta bai daina saƙa mata abubuwa ba. Sai da muka shiga cikin falo muka zauna sannan Yaya Alhassan ya tabbatar mata da cewar babu ciki a jikina kuma likitoci sun tabbatar da cewar ko cutar sanyi ba na ɗauke da ita balle cuta mai karya garkuwa jiki watau siga. Silalewa daga kan kujerar da take Anty Sawwama ta yi ta yi sujudul shukur tana gode wa Ubangijnta Sarkin da bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Ta daɗe kafin ta ɗago ta koma mazauninta ta yi alama da idon akan na zo kusa da ita na zauna. Kamar yadda ta buƙata haka na yi na je kusa da ita na zauna na sadda kaina ƙasa yayin da ta riƙo hannayena ta sanya cikin nata ta na murzawa a hankali ta ce"Uwata ɗago idanunki ki kalle ni" a hankali na ɗago idona ina kallon fuskarta da ta washe da annuri. "Ba wai ina tantama akan tarbiyyanki ba ne amma shin da gaske ne tun da kika saka ƙafa kika fita daga cikin gidan nan ba ki aika wani abun ashsha ba, balle kuma wanda Allah ya haramta aikata sa?". Hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina na furta"wallahi Anty ban aika ko ɗaya daga ciki ba, na kiyaye mutunci da kuma kimar kaina". Daga haka na zarce da ba su lamarin duk abin da ya wakana tun daga ranar farko da na sa ƙafata na fita daga cikin gidan har zuwa lokacin da muka yi ido huɗu da Yaya Alhassan da Amir a ɗakin Hajiya, sai dai na ɓoyeH musu haƙiƙanin gaskiyan abin da ya kai ni otel a cikin wannan daren. Haƙiƙa na ga zallan tausayawa kwance a cikin idanunsu yayin da Anty Zulaihatu da Umar suka zubar mini da hawaye tausayi sosai, Amir da Yaya Alhassan kuwa duk jikkunansu ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Anty Sawwama kuwa baƙinta ya ƙi rufewa sai godiya take ta faman jeranta wa Allah na yi ta ƙara gode masa, tare da addu'ar Allah ya ba ta ikon kulawa da rayuwata daga yanzu har zuwa fitar numfashinta na ƙarshe. "Ga Amatullah nan na ba ku amanarta da ragamar kula da ita duk wani a cikin ku da yake son faranta min, to ya faranta mata. Haka zalika duk wani da yake son ganin ɓacin raina to ya musguna mat yy yh h yh hmy a, ko bayan raina ban yarda ku wulaƙanta ba ko kuma ku bari ta yi kukan maraincin mahaifinta". Jikinmu gabaɗaya ya kuma yin sanyi na kwantar da kaina a bisa cinyar Anty Sawwama ina faɗin"Anty ina Ummata tun da na zo babu wanda ya yi mini maganarta, ina so na je na gan ta ita ma na nema yafiyarta". "Ummanki tana nan Amatullah. Kuma sa boda ita ne ma ya sa muka saya kai da fata wajen ganin mun dawo da ke gida". Babu shiri na ɗago kaina ina kallonta"sa boda ita kuma? Wani abun ne ya faru da ita?". Ganin yadda na birkice ya sanya ta sanyaya muryarta tana faɗin"ki kwantar da hankalinki babu abin da ya faru da ita. Za kuma ki je ki gan ta a yau ba sai gobe ba". Kaina kawai na yi ƙarfin halin gyaɗa mata don jikina ya gama ba ni tabbacin cewa akwai wani abu a ƙasa. Muna yin sallan asubahi ko abincin ban tsaya ci ba muka nufi gidan ni da Anty Zulaihatu har izuwa lokacin ƙirjina bai daina harbawa haka yana dakan lugudan-lugudan tara-tara. Muna sauƙa a ƙofan gidan na ji wasu tulin hawaye sun ciko mini idanuna rayuwata ta baya ya soma dawo mjni cikin kwanyata, yayin da wani haske ya ratsa idanuna tamkar majigin da yake hasko mini jiya ta zuwa yau. Babu abin da na fi tuna illa lokacin zaman makokin Abba yadda aka cika a ƙofar gidan. Sai da ta riƙo hannuna muka shiga cikin gidan yayin da yaran gidan da na maƙwabta suna cika a kaina suka mamaye ni kowa burinsa ya ɗaura hannunsa a jikina don kawai ya tabbatar da cewa ni ɗin ce na dawo ba wata ba. Muna shiga filin tsakar gidan da Umman Amira na fara cin karo ta saki kwanon wainar da yake hannunta ya faɗi ƙasa. "Amatullah ke ce? Jama'a ku fito ku fito ga Amatullahi ta dawo gida. Allah alhamdulillah". Ta yi zancen cikin ɗaga murya yayin da take rugowa da gudu ta zo ta ƙanƙame ni ƙam a jikinta. Kamar an kaɗa ƙararrawa haka ragowar matan gidan suka soma fitowa ƙwansu da ƙwarƙwatansu. "Allah buwayi gagara misali. Amatullah ke ce tsaye a gabanmu? Ko da yake daman masu iya magana ai sun ce giji lahira ce". Maman Adnan da na gan ta da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe a jikinta, kaina kawai na jinjina cikin ƙarfin hali na kallo Umman Amira na ce"ina Ummata take?". Ta yi mini nuni da hanyar ɗakinmu"tana cikin ɗakin". Da gudu na nufi ɗakin ina ƙwalla mata ƙira cikin muryata da ta gama dushashewa sa boda kukan da na ɗauki tsawon lokaci ina yin sa, turus na yi na tsaya lokacin da na yi ido huɗu da ita yashe a falon a bisa kan tabarma na bi ta da kallon tsaf yayin da ƙirjina yake buga wa kamar zai bayyano waje. Daga ita sai zani ɗaurin ƙirji a jikinta sai kuma wani ɗan ƙyallen da ta lulluɓe kanta da shi, ƙafafunta na yi da kallo da wani wari da ɗoyi yake tashi daga gare su, ƙafarta ɗaya na ga an yanke har zuwa gwiwar ƙafar yayin da ɗayar kuma ta kumbura ta yi tsimtim kamar za ta fashe. "Um-um-um-umma ke ce haka me ye ya same ƙafafunki?". Na furta zancen cikin tsintsinkewar zance numfashina yana sama yana ƙasa tamkar ceron da yake bugan sa a cikin turmi. Ta kasa cewa da ni komai illa kallon da ta kafe ni da shi hawaye suna tsiyaya a bisa baƙin fuskarta da ta yi duhun gaske tamkar bayan tukunya, ta ƙanjame kamar mai cutar ƙanjamau duk ta lalace kamar kamun mayu. Na duƙufa a gefenta ina kuka yayin da ita ma take taya ni babu ji babu gani kamar waɗannan aka yi wa mutuwar ƙare dangi. [12/20, 1:48 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 7️⃣4️⃣ Mun ɗauki lokaci muna kukan daga ni har ita babu mai lallashin wani haka Anty Zulaihatu da Umman Amira suka shigo ciki suka iske mu, yayin da ragowar sauran matan suka tsaya a ƙofar ɗakin ba tare da sun shigo. Sai faman ƙorafin wari da ɗoyin da take tashi daga cikin ɗakin suke yi. "Haƙuri za ki yi Amatullah ai yanzu jikin natan ma da sauƙi sosai, tun da har ta na iya gane wanda yake tsaye a kanta". Muryar Umma Amira ya ratsa cikin ƙoƙon kaina da ya tursasa mini cira kaina ina dubansa bakina yana rawa yayin da haƙwarana suke karafɗiya da juna na furta"yanzu hakan ne jikin da sauƙi? Don Allah ku sanar da ni me ye ne abin da ya same ta har ta koma haka?". "Wallahi wani azzalumin mai mota ne ya buge ta kuma don tsabar tsagwaron rashin mutumci ya yi tafiyarsa ba tare da ko waiwayanta ya yi ba, haka ta zo nan ta yi ta jinyar ƙafar bayan an yi mata ɗaurin gargajiya abin ya ci tura dole aka dangana da asibiti, shi ma ɗin da ƙyar da suɗin goshi ta amince aka je har aka sanar da Gwaggonki Sawwama. Nan Likitoci suka ce wai wani abu shi infection ya riga da ya kama ƙafar dole sai an yanke ta haka kuma aka yi mu na ji muna gani ana yanke ƙafar, bayan wasu kwanakin ɗayan ƙafan ma ya harbu ya soma fitar da wani ruwa mai ɗoyi da wari tare da ƙarni kamar jinin haihuwa. Kin gan ta nan yadda take jaɓe a nan ko ƙofar ɗaki ba ta iya fitowa ba ta iya taimakon kanta da komai, a nan za ta yi fitsari ta sauƙe duk wani buƙatunta babu mai shigo wa ya yi mata sannu balle ya taimaka mata da ko da abin da za ta saka a bakinta ne, tun da ke ma sanin kanki ne ba halin ƙwarai ba ne da ita haka nan ba ta zauna da kowa zaman lafiya a cikin gidan nan ba. Ni ce kawai ta zame min dole ni ma ɗin kuma na fara gajiya tun da daman Ubangijinmu ne ai kawai ya ba ya gajiya da mu Bayinsa". Ji na yi kaina ya yi mini dum jikina gabaɗaya ya ƙara sake wa, wani baƙin duhu da babu ko da ɗigon haske a cikinsa ya gilma ta cikin idanuna. Duk da idan zaune ji na yi kamar ina shirin faɗuwa ƙasa, hakan ya sanya ni yin zaman ƴar bori dirshan a ƙasa. Na juyo da kaina ina kallon fuskar Umma da tun da Umman Amira ta soma zancen ta yi ƙasa da idanunta hawaye su na ci gaba da zuba daga gare su. "Umma me yasa kika zauna haka har jinyar nan ta yi nisa, ba tare da kin nema maganinta ba"?". Kafin ta ba ni amsa Umma Amira ta yi caraf ta amshe zancen cikin faɗin"to ke kuwa Amatullah jinya ba dole sai da kuɗi ba, to haka kawai ake tashi a nema maganin ba tare da ko sisi ba?. Ko wancan aikin yanke ƙafan da aka yi Alhassan ɗan Gwaggonki da yake su ma ƴaƴan kirki ne irin albarka da suka kwankwaɗi tarbiyya a cikin kofin girmamawa shi ne ya yi ƙundunbala ya biya kuɗin aikin da na magungunan da aka rubuta haka nan ya yi mata siyayyar kayan abinci ya kawo, shi nake ɗan tsakura ina dafa mata har zuwa wannan lokacin da kika zo kika iske ta tana numfashi". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta cikin wani iriyar muryar mai tattare da tarin rauni saka kaina tsakanin tafukan hannayena tare da rushewa da wani matsanancin kuka mai tsanani. "Ba kuka za ki yi mata ba Amatullah addu'a za ki yi mata Allah ya kawo mata sauƙi da mafitan halin da take ciki. Idan kuma wannan jinyar ba na tashi ba ne to Allah ya sauƙaƙa mata tafiyar ya sa can ya fi mata nan kasancewa alkhairi a gare ta. Ki tashi ki fito waje ki ɗan sha iska don warin cikin ɗakin nan babu makawa sai ya kumbura miki ciki, ko kuma ya haifar miki da wani cutar mai zaman kanta". Umma Amira ta yi zancen ta na kai hannunta ta rufe hancinta tare da juya wa ta fice daga cikin ɗakin. Na tsinkayo amon Anty Zulaihatu cikin rarrashi ta na cewa"ba kuka za ki yi ba Amatullah addu'a za ki yi mata, sannan kuma a fara neman mafitan nema mata lafiya. Wanda daman akan hakan ki ka zo ki ka same mu, akwai wasu gidauniyar da suke ɗaukan nauyin majinya mussamman masu irin lalurarta a yi musu aiki kyauta, magani ma kuma kyauta. Tunin Yaya Alhassan ya saka sunanta kuma in sha Allah akwai cikakken yaƙinin cewar za a dace don haka ki kwantar da hankali komai ya yi farko zai yi ƙarshe da iznin Allah". Ban iya cewa da ita komai sa boda kukan da ya gama galabaitar da ni ainun, rurin da wayarta ya yi shi ya tilasta mata tashi ta fita daga cikin ɗakin don ta amsa ƙiran, ban ga laifinta don ta fita ba don tabbas zama ciki ɗakin sai ka kai zuciyarka nisa kuma sai hakan ya zama dole a gare ka watau ba ka da wani zaɓi. "Amatullah". Umma ta ƙira sunana da hakan ya sanya ni ɗaga kai ina kallon fuskarta, ta riƙo hannuna ta sanya cikin na ta. Hawaye suna gudu a bisa kuncinta ta ce"Amatullah kin ga yadda rayuwa ta yi da ni ko? Tun bayan rasuwar Manniru nake ta haɗuwa da jarabawa kala-kala daga wannan sai wannan kamar wacce aka saka wa hannu a cikin lamarin. A da na yi zaton barin sa cikin duniya zai ba ni wani dama ne da zan ci duniyata da tsinke sakace ta yadda zan sakata na kuma wala sai dai ashe kallon tsire nake yi wa rogo, na wofantar da ke sosai na ƙunsawa dangin Manniru ƙunci da baƙin ciki ba wai don ba na ƙaunar ki ba. Duk abin da na yi na yi sa da nufin ƙuntatawa Sawwama da kuma ƴaƴanta sai dai ban sani ba ashe wuƙa na ɗauka na daɓa wa kaina ba tare da na sani ba rashin Manniru ya sa ni fahimci komai isa, izza da taƙamar mace dole ta na buƙatar jagorancin na miji a cikin rayuwarta. Rashin Manniru ya sa ni na fahimci dole akwai wasu buƙatun da komai gata da azurkinki a cikin duniya ba za ki taɓa iya biya wa kanki su ba, rashin Manniru ya sa ni na fahimci duk macen da take zaune ba tare da wani tsayayyen na miji a cikin rayuwarta ba walau uba, miji ko kuma ƴaƴa to ita da hanyar Zamfara ɗaya suke a ɓangaren rashin tsaro. Amatullahi tun da wannan jinyar ta same ni babu ranar da garin Allah zai waye ba tare da na yi kukan rashinki ba lokuta da yawa na kan zauna na yi tunanin a wani irin hali na jefa rayuwarki a cikin yanzu? Tabbas Manniru ya yi gaskiya da ya ce DAFIN HARSHE ya fi dafin da ke tattare da bakin maciji da duk wani dabba mai cutarwa ga lafiyan ɗan Adam, mussamman kuwa bakin uwa don kamar yadda duk addu'ar da ta yi wa ƴaƴanta Allah yake amsar sa haka nan idan ta furta mummunan kalma gare su, sai hakan ya yi tasiri akan su ko ba daɗe ko ba jima ƙarshe kuwa ita za a bari da cizon ɗan yatsa. Kowa ya juya min baya a cikin gidan sai dai daidai da rana ɗaya ban taɓa ganin laifinsu bisa hakan ba tun da ni ma a lokutan baya ban rangwanta musu. Idan na ga yadda ƴaƴansu suke yi musu hidima ko da kowa hidimar aikace-aikacen cikin gida ne sai na ji hawaye su na zubo wa daga cikin idanuna tunaninki da na halin da na je da rayuwarki a ciki sai ya dawo min sabo dal a cikin raina". Dole ta tsagaita sa boda tari mai ƙarfi da ya sarƙafe ta, lokaci guda ya fitar da ita daga cikin hayyacinta. Na ɗauki kofin da yake na zaba ma da gudu waje da nufin ɗebo mata ruwa, har na buɗe rangan zan ɗebo ruwan na ji an riƙe mini hannuna. "Kar ki sake ki haramta min ruwan da nake sha kuma nake ibada da shi, ta hanyar soma min wannan ƙazamin kofin marar tsafta da ya fito daga cikin ɗakin wulaƙantacciyar matan can da ba ta san mutuncin ɗan Adam ba". Cak! Na tsaya ina bin matar da kallo don a tsawon zamana a cikin gidan ban taɓa ganin fuskarta a cikin gidan ba, ko da kuwa a zuwan baƙunta ne. Muryata ta na rawa na ce"don Allah ki yi haƙuri ki ba ni ruwan nan ko kaɗan ne, na kai mata ta sha tari ya sarƙafe ta ga shi nan ma ki na jin sautinta". Na ƙare zancen wasu hawayen su na gudu a fuskana. Tsaki ta buga mini tare da sa dukkannin ƙarfinta ta ture ni Allah ya rufa mini asiri ban kai ƙasa ba ta rufe rangan kirif, ta tsaya a wajen tare da riƙe ƙugu tana jijiigawa. Numfashi mai ƙarfi na ja fesar ina rarraba idanuna ko zan hango Anty Zulaihatu amma ban gan ta a cikin filin tsakar gidan, da hakan ya ba ni tabbacin in ba ta cikin zaure to tabbas ta fita. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta can ƙasan maƙoshina tare da runtse idanuna sa boda sautin da tarin da Umma take yi har yanzu babu ƙauƙautawa tamkar za ta shiɗe. Duniya ke nan juyi-juyi in ji kwaɗo da ya ji sa a cikin ruwan zafi tsamo-tsamo. Wai yau ruwan da Umma za ta ji ƙa maƙoshinta da shi ne yake neman gagararta, a lokutan bayan ko don gudun rigima da tijararta dole mutum ya kamfata ya ba ta ko da kuwa babu cikakken niyya sai ga shi yau reshe yana neman juyewa da mujiya. "Amatullahi mu je na ba ki ruwan sai ki kai mata ta sha". Idanuna cike da hawaye na ɗago kai ina kallon matar Ustazu Abdulwahab da take tsaye a gabana, ta amshi kofin hannuna ta je ta ciko mini shi da ruwa taf ta kawo mini na amsa, motsa leɓena nake yi da zummar son furzar da kalaman godiya gare ta sai dai na kasa. Fahimtar hakan ya sanya ta faɗin"ba damu ba sai kin gode min ba Amatullah, ki yi maza ki kai mata ta sha ga shi har yanzu tarin bai lafa ba". Kaina kawai na jinjina mata na juya da sauri na koma cikin ɗakinmu na ba wa Umma ruwa ta ɗan sha amma duk da haka tarin bai lafa ba. Jikina yana rawa na soma karanto wani yanki daga cikin yankokin Alqur'ani mai girma tofawa a cikin ruwan kana na ba ta sha. Kamar yankan wuƙa take tarin ya tsaya kamar an yi ruwa an ɗauke, na din ga jeranta mata sannu wani na bin wani tare da gyara mata zamanta tare da sanya mata matashi a bayanta ta yadda za ta ji daɗin zaman. "Umma haka tarin yake yi miki haka kamar zai raba ki da numfashinki?". Ta gyaɗa mini kanta ta na ƙoƙarin yalwata fuskarta da murmushin ƙarfin hali. "Umma dole mu tafi asibiti a duba ki, don a gano ainihin abin da yake damun ki. Zama haka ba zai yiyu ba bari na je na dubo Anty Zulaihatu ta zo ta". Na yi zancen ina miƙe wa tsaye zan fice ta riƙo hannuna hakan ya sa na waigo ina kallonta da ido ta yi mini alama akan na dawo na zauna na kuma yi kamar ta buƙata. "Amatullah ina ji a jikina wannan jinyar ba na tashi ba ne abokin tafiya ne, ki yafe min duk abubuwan da na yi miki, na san da cewar duk halin da kika faɗa ni ce sila DAFIN HARSHEna ne sila. Kaicona! Ba na tunanin akwai wani maganin da zan sha na sama sauƙi ko da kuwa na sama sauƙin ma to iya na gangar jikina ne, amma ciwon da yake cikin zuciyata yafiyarki gare ni kawai zai warkar da wannan gyambon". "Umma kin wuce komai a wajena haka zalika kin fin ƙarfin komai. Wallahi wani ne ya yi mini ba daidai ba ki ka ce na yafe masa to an gama maganar ke nan balle kuma ke da kanki. Umma na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki ɗaya amma don Allah ki bari a kai ki asibiti, a nema miki magani". Ina gama maganan na tashi na fita ina fitowa na hango Anty Zulaihatu tana shigo hannunta riƙe da baƙin leda. Na yi hanzarin isa gare ta"Anty Zulaihatu don Allah ki zo mu kai Umma asibiti". Da sauri muka isa cikin ɗakin, muka haɗa muka rawa mu tafi asibiti Umma ta ce ba za ta je ba har Yaya Alhassan muka ƙira a waya ya zo ya saka baki amma ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi yarda. Yaya Alhassan ya ce a bar ta zuwa gobe ko za ta sauƙo ko kuma a ƙira likitan ya duba ta a gida, tare da Anty Zulaihatu muka share ɗakin muka tsaftace ko'ina. Muka yi wa Umma wanka muka sauya mata kaya. Sai dab da magrib Anty Zulaihatu ta koma gida sa boda a ranar mijinta zai dawo. Haka na zauna na Umma na tisa ta a gaba na din ga karato mata karatun Alkur'ani da nufin ko za ta sama nutsuwa a cikin ranta. "Amatullah Allah ya miki albarka". Babu shiri na tsaya daga karatun da nake yi ba tare da na zo gaɓar da ya dace na tsaya a ƙa'idance ba. "Umma me ye ki ka ce?". "Ce wa na yi Allah ya yi miki albarka". Ban iya amsa wa da kalaman baki ba, illa jan jikin da na yi na isa kusa da ita, hawayen farin ciki da murna su na zuba daga idanuna, ba zan iya tuna ranar da Umma ta taɓa sa mini albarka a kaf cikin rayuwata ba. "Umma na gode, ke ma don Allah ki yafe mini kura-kuren da na yi miki". Ta sa hannu ta shafo kaina"ba ki taɓa ɓata min ba Amatullah, Allah ya raya ki". "Amin ya Allah". Na amsa da shi ina kwantar da kaina a bisa kafaɗunta ina ta sauƙe ajiyan zuciya tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Sanadin albarkan da Umma ta sanya mini na ji na manta da dukkan damuwata har na ji wani nutsuwa ya mamaye mini ruhina. Ina zaune a haka ban san lokacin da bacci ya sace ni ba. Muryar Umma shi ya yi silar farkar da ni daga baccin da ya ci idona. "Ki tashi ki rufe mana ƙofa, sanyi ya fara sauƙa". Firgitit! Na buɗe idanuna ina kallon cikin ɗakin da duhu ya mamaye ko'ina alamar dare ya daɗe da yi. Na lalumi wayar da yake wajena na kunna haskenta tare da duba lokaci da ya nuna mini ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare. "Subhanallahi! Umma kin ga har dare ta yi". Na yi zancen ina tashi na sassauƙe labulen tagogin sannan na rufe ƙofan ɗakin, na zo na zauna a nutse na soma faɗin"ni kuwa Umma ina kayan cikin falon suke na ga har cikin ɗakin babu komai. Daga tabarman nan fa sai ƙunshin kayan sakawanki". "Na sayar da komai da yake cikin ɗaki da falon nan, duk kuɗin su ƙare akan jinyata kafin Alhassan ya kawo min ɗauki. Amatullah tabbas Sawwama da ƴaƴanta su cika cikakkun masoya a gare mu, don ba kowa ba ne za a yi masa abin da na yi Alhassan kowa har ya dube ni da idon rahama a lokacin da nake buƙatar taimako daga gare sa". Kalamanta suka sanya jikina yin sanyi ƙalau na taƙaita zance ta hanyar gyara mata wajen da za ta kwanta na kwantar da ita bayan na yi mata alwala da ruwan goran da Yaya Alhassan ya kawo mana ɗazu da ya zo shi, na shafe mata jikinta da addu'a ni ma na kwanta a gefenta. Sai dai bacci ya ƙi ziyartar idanuna haka na yi ta tunani masu nauyi, kafin wasu hawayen tausayin kanmu da yadda rayuwa ta mayar da mu ya fara zuba daga idona. Ina ma wanda ya mutu yana dawowa tabbas da sai na bayar da duk wasu abubuwan da na mallaka a cikin duniya, don kawai Abba ya dawo ya ga tsantsar nadama da dana-sanin da yake kwance a cikin idanun Umma, zan zo ya dawo ya ga yadda ta yi kewarsa a duniya yayin da ta soma amfani da tarin nasihohin da yake yi mata, Allah mai iko wai yau bakin Umma yake furta mini kalmar Allah ya yi miki albarka. Ban iya runtsawa a wannan daren ba har aka ƙiran sannan asubahi na tashi na yi alwala na yi sallan, sannan na zo zan tashi Umma don na yi mata alwala ta yi na ta sallan na ji shiru, na soma ƙiran sunanta ina bubbuga matashin da kanta yake kai nan ma ba ta tanka mini ba. Nan fa ido ya raina fata na soma jijjiga ta ina ci gaba da ƙiran sunanta amma har yanzu shuru. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Umma don girman Allah kar ki yi mini haka. Ki yi wa Allah ki buɗe idanunki". Na yi furucin cikin tsananin kiɗima da ruɗewa, ganin zaman ba zai haifar mini da ɗa mai ido ba ya sa na na baza ma waje, ɗakin Umman Amira na nufa ina buga mata ƙofa tare da ƙiran sunanta amma ba ta amsa wa, babu abin da nake iya furtawa illa kalmar innalillahi wa inna ilahirin raji'un. Na daɗe buga ƙofan kafin Baba Habu mijinta ya shigo da alama daga masallaci yake. "Ke lafiya?". Ya watsa mini tambayar cikin zafin rai. "Daman jikin Ummata ne ya tashi shi ne na zo ƙiran Umman Amira, ta taimaka ta zo mu je ta duba ta". "Wani irin ta duba ta? Likita ce ita ɗin ko kuma da na ilmin sanin jinya? Warin da yake fita daga jikin Hafsatu da matata ta shaƙa jiya shi kaɗai ma sai da ya haddas mata cuta, daren jiya ba mu runtsa ba. Haka ina zaman zamana aka sa ni kashe ƴar dubu uku ta na sayo mata magunguna shi ne fa har ta sha ta kwanta yanzu da zan fita Masallaci. Don haka ba za ta je ko'ina ba idan jikin ya yi tsanani ki ɗauke ta ki kaita asibiti likitoci su duba ta". Cike da mamaki na ce"Baba ni ce Amatullahi, ko ba ga shaida fuskata ba ne?". "Na shaida ki tsaf fuskarki ai ba ɓoyayyiyar fuska ba ce a cikin unguwan nan, na gane ki sarai ko ba Amatullah ɗiyar ba ce Malam Manniru da ta yi cikin shege har hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa ba, sannan ko kwanaki arba'in bai cika a ƙasa ba kika sanya ƙafafunki ki ka gudu daga gida kika bi Saurayin da ya yi miki cikin ku ka je can ku ka ci gaba da baɗalarku ba". Yana gama zancen ya zo ya buɗe ƙofar ɗakin ba ko kusa ban yi tunanin a buɗe take ba ya shige abin sa. Har ƙasa na durƙushe akan gwiwoyina ina ta wani irin haki tamkar wacce ta fafata a gasar tseren gudu a matakin duniya gabaɗaya. Ina cikin wannan halin Ustazu Abdulwahab ya shigo cikin gida ya dawo daga masallacin sallan asuba, ya tambaye ni me ke faruwa? Cikin sanyin amo na zayyana masa komai ya ce mu je ya duba ta. Na yi gaba ya na bi na a baya muka ka isa wajen Umma. Ya kai minti biyu yana kallon fuskarta sa boda tun da na tashi na kunna hasken wayata na ajiye. Sai can ya tsuguna a gabansa tare da kai hannunsa daidai hancinta hakan bai yi masa ba sai da ya riƙo tsintsiyar hannunta na ɗan danna yatsansa kafin na ga ya jijjiga kansa. "Don Allah me yake samun ta? Tun ɗazu fa ban ga ta yi motsi ba. Shi yasa tun jiya nake ta ce mata mu je mu asibiti". Ya ɗan yi jim kana ya ce"Amatullah ko da kun je asibiti babu abin da zai sauya daga abin da Allah ya rubuta zai hare ta". Da hanzari na tari numfashinsa"me ye kake nufi?". "Sai dai haƙuri don ita kam ta riga mu gidan gaskiya, ta riga da ta amsa ƙiran Ubangijinta". Ji na yi komai na duniyar ya tsaya mini cak haka na zube akan gwiwoyina ki hawaye na kasa yi illa kafe Umma da na yi ido jikina ya na rawa, ƙasa-ƙasa nake ji yo sautin muryar Ustazu Abdulwahab sai dai ba na iya tantance abin da yake bakinsa yake furtawa balle har na fahimta. Ina nan kamar gunki na kasa motswa har izuwa lokacin da ya fita ya je ya ƙira matarsa suka dawo tare. Ita ta riƙe ni sa boda yadda jikina yake rawa ina ga ni Ustazu Abdulwahab ya rufe wa Umma idanunta da suka kafe sannan ya lulluɓe ta da zanin da ta lulluɓu da shi. Ɗakinta ta kai ni ta zaunar da ni sai na kasa yin komai, ba na iya yi ki da magana ba balle kuka. Idanuna ne kawai suke motsawa. Ban san adadin awannin da na ɗauka zaune a wajen ba har zuwa lokacin da Anty Sawwama da Anty Zulaihatu suka zo su. Duk kukan da na mutane suna yi akan gawan Umma ni ko hawaye na kasa yi. Duk wanda ya zo ya ji labarin cewa na dawo gida ni yake tausayawa akan mutuwar Umma, sai dai ni kuma Allah cikin ikonsa ya saka mini wani nutsuwa na mussamman duk abin da ake faɗa ina ji sai dai ba na iya mayarwa. Har aka shirya Umma na je na yi mata addu'a ban yi kuka ba, sai da na ga an fito da ita za a fitar da ita waje don a yi mata salla. Ana ɗaga makarar na yanke jiki na faɗi, sai farkawa na yi na ganni a cikin ɗakin Anty Sawwama sai dai har zuwa wannan lokacin maganata ba ta dawo ba. Har aka yi kwanaki bakwai ba na iya yin magana ba na iya yin bacci ba na komai illa na zauna waje guda na yi shuru ni ba tunani nake yi ba, haka nan ni ba nazari ba. Ranar da aka yi sadakan bakwai ina zaune Yaya Alhassan ya shigo ya same ni. Ya zauna kusa da ni yana kallona yayin da na yi ƙasa da idanuna. "Amatullah". Ya ƙira sunan cikin sanyin murya mai cike da damuwa, kamar ya kunna wuta haka na ji hawaye suna zuba daga idona bakina ya fara rawa ina ta ƙoƙarin yin magana amma na kasa, sai da na ja dogon numfashi na fesar kafin na yi nasaran faɗin"Yaya Alhassan shi kenan Umma ma ta tafi ta bar ni? Ba za mu sake gana wa ba? Me yasa Allah yake jarabta na da rasa dukkan mutanen da nake so? Allah na tuba na tuba ka yafe mini". Cikin wani irin cushewan amo na yi zancen ina ci gaba da fitar da hawayen da na shafe tsawon kwanaki ba tare da na yi su, bai hana ni yin kukan ba kamar yadda bai dakatar da ni ba illa idanun da ya zuba mini. [12/21, 12:04 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _______________________________________ Page 7️⃣5️⃣ Na daɗe ina kukan har sai da na ji numfashina yana sama yana ƙasa tamkar wacce aka sanya igiyan kirtani aka zarge min wuyana da shi. Haƙwarana suna karafɗiya da ruwa tamkar sabuwar haihuwar kazan da ruwan sama ta yi mata mungun bugu. "Yaya Alhassan duniyar gabaɗaya ta fara ba ni tsoro komai na cikinta ya daina burge ni. Tabbas iyaye daban suke a cikin dukkan jerin mutanen shi kenan Abba ya tafi ya bar ni yanzu ma Umma ta bi shi, ina zan saka raina? Ina zan soma kaina na ji sanyi da sauƙin halin da nake ciki? Wallahi zuciyata zafi take yi mini raina yana tafasa tamkar ƙirjina zai fashe. Na daina samun bacci tunani ya yi mini yawa har ina tsoron zuwan wani rana da za su zo ku tarar da gawata a cikin ɗakin nan, zuciyata ya buga na mutu kowa ya huta". "Ke Amatullah". Yaya Alhassan ya dakatar da ni cikin kakkauran amo, ban iya ɗaga ido na kalle shi ba illa rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa da na yi wasu hawaye su na ci gaba da ambaliya a bisa kuncina suna zarce wa har izuwa tudun wuyana. Sai da ya sassauta amonsa kafin ya zarce da faɗin"Amatullah ki zama mai tawakkali, haƙuri da miƙa lamuranki ga Allahu malikulƙuddusu mana. Sarkin da ya yi mana alƙawarin komai tsanani yana tare da sauƙi haka nan komai duhun dare hasken alfirjir zai keto ya yi wannan baƙin duhun daren. Allah ba ya taɓa jarabtar Bawa da abin da ba zai iya ba don haka ki lallashi zuciyarki ki ba ta haƙuri akan wannan jarabawan da suka faru da ke. Ki sani Allah ya na tare da masu haƙuri kuma a ko wani irin yanayi su ne da riba. Zuciyata ta kan cika da rauni a duk lokacin da na zo na iske ki a cikin ɗakin nan kin yi shuru ki na tunani, zuciyata ta kan karaya a duk lokacin da na zo na tarar da ke ba kya iya furta komai illa kallo da ido. Amatullah ina jin ki har a cikin ƙasan raina ke ɗin ƴar uwata ce kuma jinina, duk wani abun da ya shafe ki ina ji kai tsaye tamkar ni ya shafa". Shuru na yi ina ci gaba da sauraron zancen da ya ɗaura da su cikin sanyin amo da sigar lallashi"Amatullah ina ji a jikina in sha Allah rayuwarki za ta inganta. Matuƙar ina raye a cikin wannan duniyar ba zan taɓa bari ki yi kukan maraici ba, zan tsaya miki a cikin ko wani irin yanayi na daɗi ko akasin hakan. Zan yi amfani da gumina wajen ganin na faranta miki, ina so ki sama nutsuwa ki yi tunani da zuciyarki ki duba ki ga abin da kike ganin ya dace ki yi wanda zai taimaki rayuwarki, in ma karatu ne, sana'a ko kuma aure" . Babu shiri na ɗago kaina ina bin sa da kallo cikin rawar harshe na furta"aure kuma Yaya Alhassan?". Ya gyaɗa mini kansa cike da tabbatarwa ya ce"aure mana Amatullah me ye za ki zauna ki yi a cikin gidan? Ke fa yanzu ba yarinya ƙarama ba ce kin yi girman da kin mallaki hankalinki kanki. Aure shi ne rufin asirin ko wacce ɗiya mace komai gatanta, komai dukiyarta, komai iko da izzarta ke ko da kuwa uban ne ya fi kowa kuɗi a kaf cikin nahiyar Afrika da kewayenta aure shi ne cikar mutumcinta. Duk wani farin ciki, nutsuwa da kwanciyar hankalin mace ta na samunsa ne a cikin gidan aurenta amma idan ta yi dace da samun abokin zama na gari. Wanda ya san kima da darajarta". Bai gama maganar na dakatar da shi cikin faɗin"Yaya Alhassan to ni yanzu waye ma kake ganin zai iya aurena? Aure fa baban lamari ne alaƙa ce da in an ɗaura ta ake fatan ta ɗaure har zuwa ƙarshen numfashi. Ko Annabinmu cewa ya yi idan ɗayanku a tashi aure ya zaɓi ƴar gidan mutunci, mai kyakkyawan nasaba da asali, mu faɗa wa kanmu gaskiya duk waɗannan abubuwan babu su a tare da ni. Kar ka manta ta fa har ciki na yi ba tare da aure ba, na sa ƙafa na tafi can wata uwa duniya na yi zaman kaina. Idan tarihi da asali za a bi shi ma babu wani kyakykyawan abin da za a tarar, ko ka manta ni ce wannan ɗiyar da duk unguwa suka shaida cewan mahaifinyarta ta raina mahaifinta ba ta ganin kowa da gashi? Shin waye zai iya yin jihadin haɗa zuri'a da mace mai irin tarihina? Yaya Alhassan akwai hanyoyin bautawa Allah wanda duk wanda ka yi daga ciki da ikilashi zai kai ka zuwa aljanna, ba dole sai ta hanyar aure ba". Tun da na soma zancen ya yi shuru yana ta kallona ba tare da ya ce komai ba har sai da na kai aya. Ya ja dogo numfashi ya fesar kafin ya furta"aure ya zama dole Amatullah. Shi zai goge duk wani mummunan abun da yake cikin tarihinki, aure ne zai ba ki damar hayyafa ta yanda ko bayan ranki za a ga zuri'arki a tuna da ke har a yi miki addu'a". Cikin zubda ƙwalla na ce"akwai wani burin da nake so na cimma". "Wani irin buri ne?". Kafin na kai ga ba shi amsa Umar ya yi sallama a ƙofar ɗakin duk muka juya muna kallonsa, Yaya Alhassan ne ya amsa masa sallamar da hakan ya ba shi damar shigowa ciki tare da cewa"Yaya daman baƙi aka yi, sun zo gaisuwa kuma sun ce su na buƙatar ganin Amatullah ita ma su yi mata gaisuwa". "To koma ka ce ta na zuwa". "To Yaya". Ya amsa da shi a taƙaice yana juya wa ya fita daga cikin ɗakin. "Sai ki tashi ki shirya tun da kin ji akwai baƙin da suka zo gaisuwa ko?". Kaina kawai na gyaɗa masa da hakan ya ba shi damar tashi ya bi bayan Umar. Sai da na ɓata a ƙalla mintuna biyu kafin na goge fuskana na ta saka hijabina na fito falon kaina a ƙasa. Can ƙasan maƙoshina na yi sallama Anty Sawwama ta amsa mini yayin da nake ƙarisowa na zauna kusa da ƙafafunta. "Amatullah baƙi ne suka zo yi mana gaisuwar Hafsatu, shi ne suka buƙaci ganinki ke ma su yi miki gaisuwa". Sai a lokacin na ɗago kaina don ganin mutanen da ake magana akan su, take na ji zuffa ya keto mini ƙirjina ya buga da mungun ƙarfin bala'i. Saifullah da Muhammad Taukif idanuna suka sauƙa akan su suna zaune a cikin falon yayin da suma ɗin ni suke kallo. "Ku ne daman?". Na yi furucin ina nuna su da yatsana. Ban jira amsar kowa ba na ce"Anty me ye waɗannan mutanen suke yi a cikin gidan nan? Wallahi ba na son ganin wannan mutumin balle har mu zauna inuwa ɗaya da shi". Na ƙare zancen ina musu nuni da Saifullahi. "Daman kin san shi ne?". Amir ya jefa mini tambayar cike da mamaki. Kaina na gyaɗa kafin na ce"shi ne fa wanda na ba ku labarinsa, shi ne wanda na yi aiki a cikin gidan wansa". Daga nan na ƙara kwashe komai da ya taɓa haɗa mu na ƙara sanar da su a karo na biyu. Tun da na fara zancen Anty Sawwama take ta ƙara jinjina kanta. "Amatullah duk wani abin da ya taɓa faruwa a baya ki manta da shi ya wuce. Yadda ya tako ƙafa da ƙafa ya zo shi har cikin gidan nan don kawai ya yi mana gaisuwa to mu mutunta juna. Su yi abin da ya kawo su mu watse". Hawaye ne kawai yake ta ambaliya a fuskana ina faɗin"Anty a duniya babu mutumin da ya taɓa gayyaya mini baƙaƙan maganganuna, ya suffanta ni da abin da ko kusa ban aikata shi ba kamar wannan mutumin. Har yanzu idan na rufe idanuna ina tuna munanan kalamansa gare ni". Shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe har na tsawon wani lokaci kafin can na tsinkayo muryar Saif ya sauƙa a cikin kunnuwana. "Tabbas duk abin da kika faɗa haka ne babu kuskure ko ƙage a cikinsa, na aikata miki abubuwa da dama na zarge akan abin da ba ki aikata ba. Sannan akan idona aka wulaƙanta ki na kasa cewa komai. Sai dai duk da hakan ke ce mace ta farko da ta fara kawo mana ɗauki a cikin rayuwarmu ta warware mana wani babban ƙullin da duk ba mu san shi ba. Ranar da kika sanar da mu wannan abun washe gari na tafi garin Abuja na sauƙa a wannan otel ɗin da kika ba mu bayanansa, haƙiƙa na gane wa idanuna abun mamaki don da idona na kama Yaya Saddam da karuwa su na kwance a cikin ɗakin otel ɗin. An yi rikici sosai har sai daga bisani Anty Muhibbat ta ji komai ta bi mu can Abujan sai dai ga mamakina ko kaɗan ba ta ga laifin Yaya Saddam ba sai ma ƙoƙarin ba shi kariya da take yi ta ko wacce fuska. Hakan ya jefa ni cikin tunanin da na baza ma nemon gaskiyar da yake ƙunshe ƙasan kalaman kariyar da take ba wa Yaya Saddam. Nan na gano cewar kafin aurensu ita ɗin budurwan marigayi abokinsa ne watau Yaya Usman da suka yi wa junansu alƙawarin aure tun suna jami'a, wannan dalilin ya sanya suka mayar da kansu tamkar miji da mata ta hanyar biyawa junansu buƙata ba tare da shakkan kowa da komai ba. A lokacin Yaya Saddam ya san komai aka tsaka da wannan lamarin Allah ya karɓi rayuwar Yaya Usman a lokacin Anty Muhibbat tana ɗauke da cikinsa, a sa'ilin da ta sanar da Yaya Saddam da ake ciki ya shiga cikin matuƙar tashin hankali ya nema a zubar da cikin amma ta nuna hakan ba zai taɓa yiyuwa hasalima ko dai ya aure ta ya rufa mata asiri ko kuma ta je ta bayyanawa ita mahaifiyar Yaya Usman ɗin halin da ake ciki". Ya dakata ta hanyar jan dogon numfashi ya fesar kafin ya ɗaura daga inda ya tsaya"idan akwai wanda mahaifiyar Yaya Usman ta yarda da shi ta kuma aminta da shi to a bayan Yaya Saddam yake. Wannan matar ta taka rawan gani a cikin rayuwarmu gabaɗaya, a gidanta ya yi karatu ba ta taɓa nuna masa bambamci tsakaninsa da ƴaƴan da ta haifa ba, hatta ni ta nuna min so da ƙauna lokacin da iyayenmu suka rasu ta ja mu a jikinta ta maye mana gurbin duk wani abun da muke jin cewar mun yi rashinsa. Wannan dalilin Yaya Saddam ya dubae har ya abin ce da auren Anty Muhibbat bayan sun yi yarjejeniyar za a zubar da jikin da take ɗauke da shi. Ba na mance kukan farin cikin da mahaifiyar Yaya Usman ta yi lokacin da ta ji cewar Yaya Saddam ne zai auri Matar da Yaya Usman ya so aura Allah bai yi ba. Ta yi hidima sosai a bikin har Allah ya ƙaddara musu kasancewa a matsayin mata da miji har da rabon haihuwar Aryan da Ayan. Sun yi auren ne kawai amma Anty Muhibbat ta san cewa babu ko da ɗigon soyayyarta a cikin zuciyarsa, tun daga wannan lokacin zuciyarta take ayyana mata cewar za ta jure komai daga gare sa don dai kawai wannan sirrin da suke rufe bai fito duniya kowa ya ji ba. Don ya kasa yarda da ita duk da kuwa mutuwar Yaya Usman ya sanya ta sauya". Al'ajabi da mamaki suka taru suka hana mu magana daga ni har ragowar mutanen da suke zaune a cikin falon. Anty Sawwama ta yi ta jinjina lamarin tare da yi mana nasiha mai ratsa jini da jijiya ta ƙarƙare da jan hankulanmu akan mu ji tsoron Allah a cikin dukkan abin da za mu aika. Har aka gama komai ban ɗago kaina ba balle na ce wani abu aka gabatar da addu'ar neman gafara da rahama ga Ummata kana suka fara haramar tafiya. Ko cira kai ban yi na dube su ba sai jin Muhammad Taufik na yi tana magana da Yaya Alhassan cikin girmamawa. "Yallaɓai idan babu damuwa mu na son magana da Amatullah a waje". Ba tare da nazari ko dogon tunanina ba Yaya Alhassan ya furta"ba komai ai, mu je daga wajen sai ta fito". Daga haka suka fuce. Anty Sawwama ta dafo kaina da na kwantar jikin ƙafafunta"tashi ki je ki ji abin da za su gaya miki". "Me ye kuma za su ce mini Anty? Duk abin da za su faɗa ai sun faɗe shi a cikin falon nan. Gaisuwar rasuwa suka zo yi kuma sun yi mene ne kuma ya yi saura?". Cikin lallashi ta ce"ki yi haƙuri ki tashi ki je ki ji abin da za su ce da ke kin ji Uwata?". Ba don raina ya so ba na tashi na nufi wajen ina goge guntun ƙwallan da yake ƙoƙ zubowa daga cikin idanuna. A ƙofan gida na iske su tare da Yaya Alhassan da Amir na iso wajen bakina ɗauke da sallamar da suka haɗe baki wajen amsawa. Yaya Alhassan da Amir suka yi musu sallama ta hanyar yin musabaha kana suka koma cikin gidan suka bar ni tsaye da su. Kusan mintuna biyu cikinmu babu wanda ya yi magana kafin can Saif ya ce"daman godiya nake so na yi miki sannan kuma na ba ki haƙuri akan duk abubuwan da suka faru, haƙiƙa na aikata miki ba daidai ba". Ban bar shi ya ƙarisa ba na ɗaga masa hannu alamar ya dakata. "Kamar yadda tun a ciki aka buƙaci na manta da duk abin da ya faru, to ka ƙaddara cewa komai ya wuce". Ya sadda kansa ƙasa yana murza zoben dake saƙala a ƴatsun hannunsa kafin ya ce"na gode". "Amatullah". Muhammad Taufik ya furta a karo na farko tun bayan da na fito waje, na ɗaga idona ina kallonsa yayin da shi ɗin ma ni yake kallo, take na ji wasu hawaye su na bin kuncina ba zan iya juran irin kallon da yake yi mini ba don haka na juya na shige cikin gida da hanzari, kai tsaye ɗaki na wuce ina shiga na faɗa kan katifa ina kuka marar sauti. Haka na wuni a cikin ɗakin in a fito waje to alwala zan yi ina yi nake koma wa cikin ɗakin. Washe da safe bayan mun yi karin kumallo ina zaune a ɗaki kawai na ji an yi sallama, idanuna a lumshe na amsa sallamar da hakan ya ke daida da ba ta iznin shigo wa. "Amatullah". Take na wartsake na tashi na miƙe tsam sa boda amon muryar ba ta kasance baƙuwa ga kunnuwana ba. Na ware idanuna akan ta kafin na ce"Amira ke ce?". "Ni ce Amatullah". Ban san lokacin da na ji wani ƙarfi da kuzari ya mamaye jikina ba, taku uku na yi na iso gabanta muka rumgume juna ni da ita, muna kukan da takamanmen ba za mu iya bambamcewa tsakanin kukan farin ciki ne ko na akasin sa ba. [12/22, 3:46 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 7️⃣6️⃣ Mun ɗauki tsawon lokaci muna kukan kafin na ja hannunta muka isa bakin katifan muka zauna muna fuskantar juna, yayin da muke ta ƙarewa junanmu kallo. Tabbas wannan Amiran da take zaune a gaba yanzu ta sha bambam da ainihin Amiran da na sani a lokutan baya. Wacce na sa ni ƴar gayu ce na buga wa a jaridar Aminiya, saɓanin wannan da take zaune a gabana cikin suturun ba su rufe mata kattara ba. Wacce da na sani ma'abociyar ta'ammali ce da kayan gyaran jiki da ƙamshi ne saɓanin wannan da babu wannan abubuwan a tattare da ita. Wancan da na sani fatarta kullum cikin gyara da ƙyalle yake yi saɓanin wannan da ta yi duhun gaske. Na kasa jurewa har sai da na furzar da mamakina na ce da ita"Amira yanzu ke ce haka? Me yake faruwa ne? Don rasuwar Umma ban gan ki ba kuma ban sama nutsuwar da zan tambaya inda kike ba". Numfashi mai dogon zango ta saka kafin ta furta mini dunƙulalliyan maganan da na kasa fahimtar inda ta dosa. "Amatullah rayuwar ce ta yi min atishawan tsakin barkono, tabbas na fahimci idan ka san farko to ka kiyayi ƙarshe". Na ɗan waro idanuna waje kafin na ce"me yake faruwa ne Amira? Shin ina Mansur? Ina alƙawarin da kuka yi wa junanku?". Wani murmushin takaici ta saka kana ta furta"Mansur yana nan mun yi aure da shi, yanzu haka maganar da nake yi miki ni da shi miji da mata ne". Na rarumo hannunta na riƙe gam cikin son gaskata abin da ta faɗa. "Don Allah Amira wannan zancen da gaske ki ke yi, kun yi aure da Mansur? To a ina kuke zaune kuma me yasa na gan ki cikin wannan yanayin?". Sai da ta ja numfashi mai dogon zango kana ta ce"Amatullah za ki yi mamaki idan na shaida miki cewar yadda Mansur ya bayyana kansa a gare ni ba haka yake a zahiri ba, ya nuna min soyayya a zahiri alhalin a baɗili ba hakan ba ne a cikin ransa. Bayan barinki gida sau uku yana ƙoƙarin keta min haddina Allah ya na kuɓutar da ni, lokacin da iyayensa suka zo gidanmu aka sanya ranar aure sai ya mayar da ni tamkar matarsa ba ya shayi ko shakkan taɓa ko wani gaɓa a cikin jikina. Ya lalata min rayuwata yayin da hankalina ya gushe da tunanin tun da aure na zai yi hakan ba matsala ba ne, ban sa ni ba ashe wuƙa na ɗauka na burmawa cikina. Idanuna sun gama rufe burin auren mai kuɗi kuma ɗan soyayya kawai nake hangowa. Haka aka yi bikin ya yi da ya yi min ɓarin Naira kamar bai san zafin nemansu. Ya ɗanɗasa min gida na gani na faɗa komai na cikin gidan shi ya yi da ƙudinsa daga ni sai kayan jikina aka kai ni cikin gidan. Ban cika satikai biyu masu kyau a cikin gidan ba na fahimci na yi zaɓen tumun dare don na gani Mansur ƙwararren manemin mata, har daga wasu jihohin ake yi masa dillancinsu. A lokacin hankalina ya tashi matuƙa babu kalar bazaranar da ban yi masa ba amma ya murzawa idanunsa toka daga ƙarshe ma ya ba ni zaɓi ko in kwantar da hankalina na zauna na ci azurki na bar azurki a inda na same shi, ko kuma ya sauwaƙe min ungulu ta koma gidanta na tsamiya". Ta tsagaita ta hanyar jan dogon numfashi ta fesar da shi daga bakinta kafin ta ɗaura daga inda ta yi birki"dole na ba da kai bori ya hau don ba zan iya rabuwa da shi, bayan soyayyan da nake yi masa hakan ina gudun dariyan da magauta za su yi mana ni da Umma idan aka ji cewar Mansur ya sake ni tun kafin na rufa wata guda a cikin gidansa. Haka na yi haƙuri na shanye dukkan baƙin ciki da takaicin Mansur a lokacin ko zanen lallen da aka yi min na bikin bai gama goge daga hannaye da ƙafafuna ba. Tun ina kuka da shiga damuwa har na saki raina na sa ba don har akan gadonmu na sunna yana waya da ƴan matansa, idan na ce zan tayar da hankali sai na ga ba ni ma da wani dalilin yin hakan tun da bai rage ni da komai ba. Bai hana ni ci ba balle sha haka nan sutura sai wanda na zaɓa zan saka a jikina. Ko da na sanar da Ummata sai ta ƙara ƙarfafa min gwiwa akan na zauna da mijina a cikin dukkan yanayin da na tsince shi, ta ƙara da cewar mazan wannan zamanin daman duk haka suke ko sun yi aure ba za iya rabuwa da ƴan matan da suke mu'amala da su, na yi matuƙar juriyan zaman da shi don a wasu lokutan har cikin ɗakina yake kawo mace sun yi duk abin da ransu yake so ba tare da na iya cewa da shi uffan ba har sai da ya kai jallin da na ji gabaɗaya auren ya fice min daga cikin raina. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya duk halin ƙuncin da zan shiga ba ya ɗaɗa Ummata da ƙasa in dai har zan kawo mata ƴan sulalla to baka lafiya ciki lafiya, shuru za ki ji tamkar Malam ya haɗiye shuruwa. Rana tsaka Mansur ya soma jinya tamkar ba zai yi rai ba ko da aka je asibiti aka tabbatar da cewar yana ɗauke da cuta mai karya garkuwan jiki, da aka gwada ni ma aka same ni da cutar a tattare da ni sai dai nawa bai yi ƙarfi tamkar na sa ba. Ina da yaƙinin cutar ba ta yi min illa kamar yadda tunani da halin ƙunci da kukan da na shiga ya yi min illa ba, lokaci guda na rame na fige na fita daga cikin hayyacina. Ko da na buƙaci ya sake don ba zan iya zama da shi ba Umma ta lashi taboki akan in har na kashe auren to babu ni babu ita kuma daga ranar na dai amsa sunan ɗiyar da ta haifa, haka na rumgumi haƙuri ya zama min abokin rayuwa, aka ce gani da wane ya isa wane tsoron Allah sai dai wanna karin maganar ba ta yi tasirin akan Mansur ba bayan faruwa waɗannan abubuwan aka kama shi da wata a wajen aikinsu yana lalata da ita, take aka rubuta takardan kora ya dawo gida ya zauna babu aikin fari balle na baƙi". Daga haka ta fashe da wani gigitaccen kukan da na ji sautinsa yana ratsa wa har cikin ƙoƙon kaina, na kasa yin komai balle har na sama ƙarfin gwiwan lallashinta na haɗa mata da kalaman ban haƙuri. Haka ta yi ta gaji don kanta ta tsagaita tare da ɗorawa da faɗin"kin san an ce zara ba ya barin dami kuma yau da gobe mai ƙarar da sabulun wanzami, duk wani dukiyar da Mansur ya tara sai ya zo ƙarshe cikin ƙiftawan ido tamkar ki haɗa auguda ki cilla musu ashana. Nan fa rayuwa ta yi mana tsauri tun muna cin abinci sau uku a rana ko da kuwa babu daɗi muka dawo ci sau ɗaya ma yana neman gagaranmu. Dole ƙanwar naƙi Mansur ya ajiye duk wani girman kansa a gefe ganin yunwa yana neman halaka mu, ga shi tun lokacin da aka kore sa daga wajen aiki sa boda munin abin da ya aikata iyayensa suka yi fushi da shi suka janye masa dukkan tallafi. Yanzu da nake yi miki wannan maganar adaidaita Mansur yake ja don mu rufa wa kanmu asiri, ya yi nadama dana sanin abin da ya yi a baya ya kuma durƙusa a gabana amma duk da haka zuciyata ta ƙi amsar tubansa balle har ta yafe masa irin cutarwan da ya yi mata". Har ta ƙare zancen na gaza motsa wa daga inda nake zaune, tamkar gunki na koma ba na iya yin komai illa kafe da ido da na yi yayin da hawaye suke kwaranya daga cikinsu. Cikin ƙarfin hali na furta kalmar"innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Ta tsuƙe majiyan kukan da ya zo mata kafin ta furta"ki na mamaki ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta damar ci gaba da cewa"to kar ki yi mamaki duk abubuwan da na faɗa miki babu kuskure ko kuma ƙage a cikinsa. Yanzu ma shi ya kawo ni har ƙofar gidan nan kuma shi zai zo ya mayar da ni, wallahi ban ji rasuwar Umma ba sa boda babu waya a hannuna da tun ranar na zo ni, sai yau da na zo Ummata take sanar da ni". Nauyin da ƙirjina ya yi mini ya hana mutane samun damar cewa da ita komai illa jinjina kaina da na ci gaba da yi ina amsa addu'ar neman rahama da take yi wa Umma a cikin zuciyata sa boda bakina ya gaza. Muna nan zaune har aka yi ƙiran sallan zuhur muka fito muka yi alwala muka yi sallan tare da ita muka yi girkin rana muna aikin muna tattaunawa da jajanta lamarin da suka faru, bayan ni ma na kwashe duk irin rayuwar da na yi na sanar da ita ta jinjina lamarin ainun tare da tausayawa a gare ni. Sai da muka gama aikin girkin tsaf na zuba mana namu muka shiga cikin ɗakin, duk yadda ƴaƴan hanjina suke kukan yunwa na kasa kai ko da loma ɗaya na dafa dukan shinkafan cikin bakina illa juya cokalin da nake yi a cikin abincin na kallo ta na ga yadda take cin abincin hannu baka hannu ƙwarya, take na ji hawaye ya ciki mini kurmin idanuna wani irin tausayinsa ya mamaye mini rai da ruhina, tabbas rayuwa abar tsoro ce matuƙa kuma na yarda da wannan karin maganan da ake cewa duniya budurwan wawa ne. "Ban taɓo zato rayuwa za ta zo mana a haka ba Amira. A duk sa'ilin da na rufe idanuna sai na din ga tuno irin rayuwar da muka yi baya sai na ji hawaye suna zuba daga idanuna ba tare da ni kaina na sani ba. Ki duba duk irin soyayyan da ku ka yi da Mansur da yadda yake ba ki kulawa yake kuma tarairayanki kamar ƙwai amma hakan bai hana sa wulaƙanta ki a cikin gidansa ba, hakan bai dakatar da shi daga neman wasu matan ba. Ki dube ni duk yadda nake ƙoƙarin kame kaina da killace mutumcina sai da na yi ciki ba tare da igiyoyin aure sun hau kaina ba, duk yadda nake martaba kaina sai da ƙaddara ta ja ni izuwa can inda ban san kowa ba, na yi zaman kaina a cikin gidan karuwai". Ban ƙarishe zancen ba sa boda kukan da ya kufce mini da ƙarfin gaske, ina yi Amira tana taya ni a haka Anty Sawwama ta zo ta iske mu ta din ga ba mu baki da kuma yi masa nasiha tare da ba musalai kala daban-daban. Wunin ranar tare muka yi shi da Amira sai da muka yi sallan magrib Umar ya shigo ya shaida mana cewar wai ana magana da Amira a waje in ji mijinta. Kafin mu fito daga ɗakin har ya shigo ciki tare da Yaya Alhassan da ya dawo daga masallaci muka iske su a falo suna gaisawa da Anty Sawwama. Idanuna na tsayar ƙar akan fuskar Mansur tabbas kamanninsa bai sauya ki da da ɗan taƙi ba, amma ya lalace ya rame ya yi baƙi ƙirin da shi tamkar wanda ya yi taimama da garin gawayi. "Amatullah ke ce wannan?". Ya jefa mini tamnayar yayin da muke ƙarisowa cikin falon muka zauna, kaina kawai na gyaɗa masa da hakan ya ba shi lasisin ci gaba da maganan. "Na ji matuƙar daɗi da na sama labarin cewan kin dawo gida, Umma kuma lokaci ya yi Allah ya jiƙanta ya sada ta da Mala'ikun rahama ya kyautata makwancinta". "Amin". Duk muka haɗe baki muka amsa da shi, nan ma Anty Sawwama ta ƙara yi musu nasiha sosai don na saurari duk labarin da Amira ya labarta mini, sai ga Mansur har da ƴan guntun hawayensa, tare da su Yaya Alhassan ya tashi suka je masallaci don gabatar da sallan isha'in da ya gabato mu ma muka yi namun sallan, Anty Sawwama ta ce mu zuba musu abinci kafin su dawo, hakan kuwa aka yi muka shirya musu abincin muka ajiye musu a falo yayin da muka koma cikin ɗakin. Muna jin su har suka dawo daga masallacin suka ci abincin suka ɗan taɓa hira kafin Umar ya ɗago labulen ɗakin yana daga tsaye a ƙofar ɗakin ya furta"sun gama ke yake jira". "To ka ce masa gani nan fitowa". Kansa ya gyaɗa tare da juyawa ya fita don iskar da saƙon, muka miƙe ni da ita mu na kallon junanmu tamkar yau muka fara tozali da junanmu. "To Amira sai kuma na zo ni in sha Allah, ki ci gaba da haƙuri akan wanda kika yi sannan ki ci gaba da addu'a Allah ya ƙara shirya sa ya kuma ƙara rufa asiri". Cike da gamsuwa ta ce"wallahi na yi kewar shawarwarinki a gare ni, na tabbatar da ki na a kusa da ni da abubuwa da yawa sun zo min da sauƙi". Murmushi muka sakar wa juna hannunmu riƙe cikin na juna ta yi sallama a Anty Sawwama da ta haɗa mata turaren wuta taf a leda ta bata a matsayin tsaraba. Har ƙofan gida na rako ta muka hango Mansur tsaye a jikin adaidatan tana waya da wata ƙaramar wayar da yake kunnensa ƙiran kamfanin tecno. Yana hango mu ya katse ƙiran ya ɗan faɗaɗa annurin fuskarsa tare da faɗin"Amatullah kun fito ke nan?". Na gyaɗa masa kaina na lura sai wani ƙasa-ƙasa yake yi da kansa kafin na yi magana ya riga ni cewa"wallahi Amatullah kunyar haɗa ido nake yi da ke, tabbas na cutar da ƙawarki na ci amanar yarda da amanar da ta ba ni. Amma duk da hakan ta yi min halaccin da har ƙasa ya rufe idanuna ba zan taɓa manta wa ba, ki taya ni ba ta haƙuri ta yafe min tarin laifukan da na yi mata, amma duk da hakan soyayyar da take yi min ko kaɗan bai sauya domin ina ganin hakan a cikin idanunta". A raunane ya ƙare zancen tamkar wanda yake shirin fashewa da kuka. "Mun riga da mun yi magana da ita in sha Allah komai ya wuce da yardan Allah. Ina fata da addu'ar Allah ya dawwamar da zaman lafiya a cikin gidan aurenki, ya albarkace ku da zuri'a ɗayyaba". "Amin ya hayyu ya ƙayyum". Suka haɗe baki wajen amsa wa cike da jin daɗin addu'ar, haka muka yi sallama da Amira ba don raina ya so ba ina tsaye a wajen har sai da na ga sun ɓace wa ganina kana na koma ciki. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya lokaci yana gudu yayin da kwanakinmu na duniya yake ƙarewa, wasa-wasa muna ƙara kusantar mutuwarmu ba tare da mun farga ba balle mu tanadin kuzurin tafiya. A cikin wannan yanayin har Umma ta cika kwanaki arba'in da barin duniya, a kullum kwanan duniya Anty Sawwama da ƴaƴanta ba su da wani burin da ya wuce su faranta mini ta hanyar samar mini da duk wasu abubuwan da zan buƙata, cikin ƙanƙanin lokaci suka sauya mini rayuwata daga duhu zuwa bayyanan nan haske. Na sama dukkan wani kulawan da nake buƙata tare da tattali. Ranar da na cika wata uku a cikin gidan a wani rana bayan sallan isha'i na shirya na je ɗakin Yaya Alhassan, a ranar na yi yunƙurin sanar da shi komai dangane da dalilin zuwa na otel a wannan ranar da suke je nemana. Yana zaune aka kujerar zaman mutum ɗaya da yake cikin ɗakin na yi sallama ya amsa mini na shigo sai kuma na tsaya a ƙofar ɗakin ya ɗago ido muka haɗa ido hakan ya sanya sa fahimtar dalilin da ya hana ni ƙarisowa. Ya tashi ya ɗauki rigarsa ya saka a jikinsa kafin na shigo cikin ɗakin. "To yanzu kam sai ki shigo ko". A hankali na tako na shigo na zauna ina gaishe shi ya amsa tare da zarce wa da faɗin"akwai wani matsala ne?". "A'a daman na zo mu yi wani magana". Ya gyara zamansa yana fuskanta da kyau kafin ya ce"ina sauraronki". "Ka bar sauraron wannan tukunna". Na yi zancen ina kunna masa sautin muryar da muka naɗa, ya amsa wayar ya na saurara sai da ya gama ji tsaf ya ga hotunan nan kana ya ɗago kai yana duba na cikin wani irin mungun yanayin muryarsa a ƙashe ya ce"waɗannan hotunan fa?". Jikina ya ɗauki rawa sa boda yanayin da ya furzo zancen take tsoro ya mamaye mini raunananniyar ƙalbina sai dai hakan bai hana bakina sanar da shi ragowar bayanin ba. Ban ƙarisa ba na ji ya ɗauke ni da wani irin mungun mari duk da ina zaune sai da na ji wani irin yana ɗauka na, marin da ya sauƙe mini har sai da bakina ya fashe ya soma zubar da jini. Cikin zafin rai ya miƙe tsaye yana nuna ni da ɗan yatsansa idanunsa sun yi jajir tamkar wanda aka watsa wa tsakin barkono, sai dai bakinsa ya gaza cewa komai. [12/23, 2:43 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 7️⃣7️⃣ Mun ɗauki tsawon wasu mintuna kafin ya furzo takaicin da na yi silar cusa masa"me ye ya kai ki aikata wannan ɗanyen aikin Amatullah? Me yasa za ki jefa kanki cikin bala'in, fitina da kuma tashin hankali da zai zama ruwan dafa kanki wataƙila har ya ƙona ki? Kin san girma da martaba wannan mutumin kuwa a idanuna jama'a?". Cikin ƙarajin kukan da sautinsa ba ya fita na furta"Yaya Alhassan mutumin ba mutumin kirki ba ne kamar yadda yake nuna hakan a idanun jama'a, ka na jin abin da yake furta wa ba. Ya yi silan lalata rayuwar ƴaƴa mata masu yawan gaske ta hanyar amfani da ƙarfin ikon da yake da shi a cikin jama'arsa". Bai bar ni dire zancen ba ya doka mini wani gigitaccen tsawan da ya tursasa mini haɗiye ragowar zancen har ina ƙoƙarin datse harshena. "Ban taɓa tantama akan tabbacin cikar hankali da tunaninki har ma da ƙalubalantan ilminki ba sai yau Amatullah, me yasa hankalinki ya gushe har kika kai kanki cikin wannan bala'in? Har da bayyana fuskarki ki ɗauki hoto da shi, dole sai ta wannan hanyar za ki fallasa asirinsa ga duniya kowa ya san halin da yake ciki? Ai idan ba kya iya kama ɓarawo ba sai ɓarawo ya kama ka kuma ka rasa hanyar da za ka kuɓutar da kanka". Tun da ya soma zancen na yi shuru tare da sadda kaina ƙasa ina sharar ƙwalla tare da ci gaba da sauraron zancen da ya ɗago da shi cikin zafin rai. "Yanzu idan wannan hotunan suka fita suka watso a dunia ki na tunanin mutumci kika ja wa kanki ko kuwa rashinsa?" Ya dafa kansa cike da damuwar da ta bayyana ƙarara a fuskarsa har zuwa cikin muryarsa ya koma mazauninsa ya zauna ya sassauta amon muryarsa kafin ya soma faɗin"yanzu me ke kike so a yi da kika zo min da wannan zancen?". Na ji shuru tamkar wacce ruwa ya ci ta, sai da ya ƙara maimata mini zancen a karo na biyu kafin na yi ƙarfin halin magana. "So nake yi a san yadda za a yi a fitar da sautin duniya su ji, ina so asirinsa ya tono duk wani abun da yake ɓoye wa ya fito fili". "Amatullah wai ina hankalinki ne ya yi aure ya tare ne? Yanzu idan aka ce miki ki fitar da wannan sautin muryar sai ki fitar da shi? Sanin kanki ne fa mutumin yana da ƙarfin iko, yana kusa da Sarakuna, gwamnoni da kuma masu riƙe da madafan iko fitar da wannan sirrin daidai yake da rushewan rayuka da dama da tarwatsewar dukkan ginin da aka yi na rayuwa. Tun da har Allah ya rufa mana asiri bai sama nasara akan ki ba ina so ki goge dukkan hotuna da sautin muryar nan, ki manta da kin ma taɓa sanin wani mai kama da shi a cikin rayuwarki balle har ki tuna wani zancen da ya shiga tsakaninku da shi". Ya ƙare zancen yana miƙo mini wayar cikin sanyin jiki na kai hannuna na amsa ina jin wasu hawaye suna zarya tsananin kuncina da kuma saman haɓata. "Amatullah ki cire damuwar komai daga cikin ranki. Alƙawarin Allah cewar dukkan wani azzalumi ba ya tare da shi kuma sai ya kunyata tun a nan cikin duniya a sai an je ga lahira ba. Mussamman ma masu ci da addini ko kuma masu fakewa da sunan addini suka ha'intan bayin Allah. Don Allah ki cire damuwar komai daga cikin ranki, idan halinsa hakan ko ba ka ma ki ba daɗe sai asirinsa ya tono a duniya sai Allah ya buɗe sirrinsa ga duniya kowa ya ji kuma ya gani sai ya tozartasa irin tozarcin da bai taɓa zato ba". Kaina na jinjina da ƙyar na furta"to in sha Allah". Sai da na yi masa sai da safe kafin na tashi na tafi ɗakina ina shiga na zube akan katifar ina kuka mai ci rai, gabaɗaya jikina ya yi la'asar na rasa gane abin da yake damuna haka na kwana idanuna biyu ba tare da na runtsa ba. Washe garin ranar na tashi tamkar majinyaci komai cikin sanyin jiki da rashin kuzari nake aiwatar da shi. Ina zaune a waje na tisa kwanon karin kumallo a gaba na ka sa kai ko da loma guda cikin bakina, Anty Sawwama ta fito har ta tsaya a kaina ban sani ba har sai da ta yi magana kafin na dawo cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da nake yi. "Amatu lafiya kuwa? Kin tisa abinci a gabanki tun ɗazu kin kasa ci. Ke ba ki ci ba ke ba ki tashi ba". Sai na haɗo jarumta na yaɓawa kaina kafin na iya raba tsakanin leɓena na ce"babu wani damuwa Anty". Daidai lokacin da Yaya Alhassan da Amir suka suka fito daga cikin ɗakin kwanansu duk da kaina ya na ƙasa hakan bai hana jikina ba ni tabbacin cewa idanunsa suna kaina ni yake kallo har zuwa lokacin da suka durƙusa suka gaishe da Anty Sawwama ta amsa musu cikin sakin fuska da kuma tarin albarka gare su. "Alhassan ka zo ina son magana da kai". Anty Sawwama ta yi zancen idanunta akan Yaya Alhassan da ya amsa da to yana tashi ya bi ta suka shiga ciki. Zaman da Amir ya yi kusa da ni yana jan kunne abincin gabansa shi ya tursasa mini ɗago kaina ina kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce"abincin ne bai yi miki ba, ko kuma dai yanayin ne kawai?". Sai da na tsame hannuna daga cikin kwanon abincin kafin a taƙaice na furta"na ƙoshi ne". "Me kika ci da har kika ƙoshi? Za ki zage ki ci abincin nan ko kuma sai na yi ɗura miki da ƙarfin tsiya". Na ɗago kai muka haɗa ido ya kashe mini ido guda yana yalwata fuskarsa da kyakykyawan murmushin da har sai da dake tsakanin haƙwaransa suka bayyana. Murmushin dole na sakar masa ina tsoma hannuna a cikin abincin muka soma ci tare da shi mu na ci yana ja na da hirar da amsana ba ya wuce uhm ko hmm haka har muka gama cin abincin na ɗauki kwano na je na wanke na dawo na zauna. Ina zama Yaya Alhassan ya fito daga ganawan da suka da Anty Sawwama na bi shi da kallo na ga idanunsa gabaɗaya sun haɗa sun yi jajir gabaɗaya yanayinsa ya sauya haka ya fice daga cikin gidan ba tare da ya yi mana kallo azurki ba balle ya ce da mu wani abun. Muka taka shi da kallo daga ni har Amir har ya fice kafin Amir ya furta"an ya lafiya kuwa? Na ga ya fito duk yanayinsa ya sauya". Na ɗage kafaɗuna alamar ban sani ba. "Bari ki ga na bi shi na ji ko lafiya". Ya yi zancen yana miƙe wa ya bi bayan Yaya Alhassan, numfashi mai nauyi na sauƙe ina ɗan lumshe idanuna. Haka aka yi sati biyu a jere ba ranar da za ta fito ta faɗi Yaya Alhassan bai tambaye ni akan na goge sautin murya da hotunan nan ba, na kan ce da shi na yi hakan duk da kuwa har zuwa wannan lokacin na gaza goge su. Ba na manta wata ranar juma'a wanda daga wannan ranar tubalin baƙin ƙaddarar rayuwata ta soma, da yammacin ranar Anty Zulaihatu ta zo ta gidan tare da mijinta Mu'azzam domin duba Anty Sawwama kasancewar ba ta ji daɗi a cikin kwanaki, ina ɗaki na ji shigowarsu na fito na gaishe su. Tun da na fito na lura da wani kallon ƙyaman da Yaya Mu'azzam yake yi mini har wani taɓe baki yake yi tamkar wanda ya yi arba da kashi, haka kawai na ji gabaɗaya jikina ya mutu murus har ya tashi ya fita akan zai je da dare ya dawo ya ɗauki Anty Zulaihatu na kasa ɗaga kaina. Zuwan Anty Zulaihatu ya ɗebe mini kewan da nake cikinsa sa boda ba na fita ko nan da can kullum ina cikin ɗakin. Bayan sallan magrib Yaya Mu'azzam ya ƙira ta yana sanar da ita ba zai sama daman zuwa ya ɗauke ta ba, ta hau adaidaita kawai ta koma gida. Ƙarfe takwas saura na dare na fito na raka ta domin ta hau adaidaita muna tafe muna ɗan taɓa hira har sai da muka iso bakin titi kana ta sama abin hawa, muka yi sallama tare da yi mata alƙawarin zuwa gidanta cikin kwanan nan. Sai da na ga wucewan mai adaidaitan kafin na juyo domin komawa gida. A hankali nake tafiyar kaina a ƙasa tamkar wacce take neman wani abu a ƙasan haka har na iso ƙofar gida ina ɗago kaina na ga an dalle mini ido da hasken mota har sai da ya kai munzalin da na kai tafukan hannuna na kafe idanuna. Sai da aka kashe hasken na ga motar ta nufo inda nake na cira kaina ina kallonta sai dai na kasa gane inda na san motar. Hakan ya sa ni soma tafiya zan shiga cikin gida na ji an ambaci sunana cikin sakakkiyar murya. "Amatullah". Da hanzari na juya don tabbatar da mamallakin muryar take idanuna suka sauƙa akan fuskar Saifullah da yake tsaye jikin motan yana kallo na kamar yadda ni ma na zuba masa idanuna. Ya tako ya iso inda nake tsaye. "Kin wuni lafiya?". Bambarakwai na ji tambayar tasan wai na miji da suna Hajara, na ja dogon numfashi na fesar a ƙoƙarin daidaita nutsuwata kafin na ce"idan wajen Yaya Alhassan ka zo to bai dawo gida ba tun da ya fita sallan isha'i". Tun kafin na dire zancen ya katse ni"wajen ki na zo". "Waje na kuma?". Na maimaita zancen ina yi masa nuni da kaina. "Ƙwarai kuwa wajenki na zo ni Amatullah, idan da hali ma magana nake so mu yi mai matuƙar muhimmanci. So samu ma mu nema waje mu zauna". "Ka faɗi duk abin da za ka faɗa, ina sauraronka". "Ki yi haƙuri mu shiga cikin mota sai mu yi maganar". Na ɗaga masa hannuna"ka gaggauta faɗin abin da ya kawo ka, idan kuma ba ka shirya to ni zan koma ciki don ina da abin yi". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kafin ya ce"Amatullah ban san yanda za ki ɗauki maganar da zan furta miki a yanzu ba, amma ina so ki sani duk abin da zai fito a bakina a yanzu to daga ƙasan zuciyata yake fitowa kai tsaye kuma iya tsagwaron gaskiyata nake sanar da ke. Tun ranar da na san wace ce ina nufin asalinki da kuma tarihin rayuwarki tausayinki ya maƙale a cikin raina, a duk san da na zauna ba na komai to tunaninki ne da irin abubuwan da na aikata miki yake addaban raina. Yau na zo ne don na furta miki kalmar da ban taɓa furtawa wata ƴa mace ba tun da nake a rayuwata". Cike da ƙosawa da sauraronsa na ce"ka tafi kai tsaye ga zancen da kake son furta wa". Ya ɗan yi jim tare da sadda kansa ƙasa yana murza zoben azurfan da yake saƙale a ɗan yatsan hannunsa kafin can ya ce"Amatullah ina sonki, ina fata da burin ki kasance mata a gare ni sannan uwa ga ƴaƴana". Tun da ya soma maganar na kafe shi da idanuna ina ganin tamkar mafarki nake yi ba a farke nake ba. "An ya ka san abin da bakinka yake furtawa kuwa? Ko kuwa dai ka mance wacce take tsaye a gabanka ne?". Ban jira amsar da zai ba ni ba na ci gaba da zancena cikin ƙonar zuciya da tafasan rai. "Idan ba ka gane ni na yi mata tuni ni ce fa Amatullah wannan ɗiyar da ka zargi tarbiyyarta. Wacce ta yi ciki ba tare da aure ba wacce ta tafi can uwa duniya ta yi rayuwa ba tare da tsawatarwan iyayen ba. Wacce ta yi zaman kanta a cikin tsakiyar gidan karuwai ta ci gashin kanta da kanta. Wannan yarinyar da ta mayar da ɗakin otel tamkar ɗakin kwananta, wannan yarinyar marar tarbiya da nutsuwa. Wannan yarinyar da kake shakku da kokonton kasancewar ta kusa da ahalinka". Na saki murmushin takaici kafin na ci gaba daga inda na tsaya. "Shin ko ka manta ku rayuwarku a tsaftace take? Ba ku da wani abun aibu a tattare da ku shin ka manta ikirarin da ka yi na cewar Allah a raba ku da kaidina?. Yadda kake mutumin ƙwarai kuma kamili ai da matar ƙwarai ka dace wacce ta fito daga gidan tarbiya da halin girma. Saifullah kar ka yaudari kanka da neman soyayyarta domin bayan rashin dacewan da muka yi da juna ba zan taɓa iya cusa sonka a cikin zuciyata da ka zama silar raunatata ba. Na roƙe ka idan ma ɓatan hanya ka yi ko kuma tuntuɓe harshe ka samu to kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan, babu wani abun da ya rage tsakanina da ku". Na ƙare zancen cikin rauni ina haɗe hannayena wajen guda alamar, zai yi magana na katse masa hanzari. "Don Allah ka bar ƙofar gidan nan wallahi ba na ƙaunar ganinka. Ka yi wa girman Allah ka bar ƙofan gidan nan". "Na ji zan tafi amma don Allah ki ba ni ko da mintuna goma daga cikin lokacinki, ki saurare ni ki ji bayanin da zan yi miki. Ban zo wajen da nufin yaudara ko cutar da ke ba hasalima....". Na datse numfashinsa"ba zan taɓa sonka ba Saifullah, me yasa ba ka duba matsayina da na ka ba da suka yi hannun riga. Ƙwarya ta bi ƙwarya idan ta bi alwashi ai fashe wa za ta yi". "Na ji na yarda ba za ki so ni, amma ni dai ki ba ni dama ki saurare ni". Hannayena na saka na toshe kunnuwana da shi yayin da hawaye suke zuba daga idanuna kamar bakin indararo, ganin ba zan iya jimirin sauraron zantukansa da suke barazanar raba ni da nutsuwata ba, hakan ya tilasta mini juya wa na shige cikin gida da gudu. Na ci karo da Anty Sawwama ta na fito wa daga banɗakin ina jin ta tana tambayata ko lafiya na shigo gida da kuka, amma ban iya amsa mata ba. Kai tsaye ɗakin kwanana na nufa na kwanta ina kuka, babu irin tambayoyin da ba ta yi mini ba amma na dage ina ce mata babu komai ba don ta yarda ba haka ta haƙura ta ƙyale ni. Daren ranar ban iya runtsa wa sai da dare ta raba cikin baccin na ji ana ƙiran sunana na tashi na zauna ina ƙara kasa kunne na ji dai tabbas sunana ake ƙira a tsakar gidan. Zumbur na yi na miƙe ina murtsike idanuna na buɗe ƙofar ɗakin na fito waje inda nake jin sautin ƙiran yana tashi. Ina fito wa na ga tsakar gidan ya yi haske sosai tamkar ba dare ba, na kai dubana inda nake ji sautin yana tashi idanuna suka sauƙa akan fuskan Hajiya Babba. Take ilahirin jikina ya soma rawa tamkar ana jona mini wutan lantarki na nuna da yar manuniyar yatsana bakina ya na rawa na ce"Hajiya Babba ke ce ki ka biyo ni nan?". Lu na ji na yi baya na zube a ƙasa yayin da kaina ya bugu da dutse, tun idanuna suna gano mini fuskarta dishi-dishi har sai da suka rufe gabaɗaya, daga lokacin ban ƙara sanin inda kaina yake ba balle fahimtar abubuwan da suke wanzuwa. [12/24, 3:41 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 7️⃣8️⃣ A hankali na soma buɗe idanuna da suka yi mini nauyin gaske kaina ya yi dum tamkar wacce aka yi wa ajiya dutse, hankalina yana dawowa jikina abin da ya faru ya dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan, take na zabure ina rafka salati tare da runtse idanuna da matuƙar ƙarfi ina ta batutuwa mara sa kan gado. "Hajiya Babba me ye na yi miki za ki biyo ni har cikin gidan nan? A zamana da ke ko da wasa ban cutar da ke ba don Allah ke ma kar ki cutar da ni ko da kwantankwacin misƙala zarratin ne". Ji da na yi an dafo kafaɗana shi ya dawo da ni cikin hyayancina na buɗe runtsatstsun idanuna na kafe Anty Sawwama da su da take zaune kusa da ni, ganinta kusa da ni ya sani ƙanƙame ta a jikina tsaf ina zubar da hawaye tamkar an kunna burɗaɗɗan fanfo. "Uwata ki nutsu ki kwantar da hankali, babu wani abun da zai faru face alkhairi da iznin Allah. Babu wanda ya isa ya cutar da ke duk abin da kika ga ya faru da ke to daman haka Allah ya ƙaddara zai faru". Luf na yi a jikinta ina mayar da numfashi tamkar wacce ta yi wani gagarumin aikin wahala, mun daɗe a haka kafin ta ɗago ni daga cikinta ta tambaye ni abin da yake faru na kwashe komai na sanar da ita, haƙiƙa na hangi tashin hankali da tsoro kwance a cikin ƙwayan idanunta sai dai ta dannan duk yanayin da take ciki. A cikin daren ta ƙira Yaya Alhassan ya zo ta sanar da shi komai, ina kwance na ɗaura kaina akan cinyarta yayin da na lumshe idanuna tamkar mai bacci sai dai a farke nake don ina sauraron dukkan abin da suke tattaunawa. Cike da tarin damuwan da yake tattare da furucin bakinta Anty Sawwama take faɗin"tsoro ɗaya kar wannan matar ta sabauta yarinyar nan, ina tsoron har ta juya mata hankalinta ko ma ta raba ta da shi gabaɗaya, don irin waɗannan matan ababen tsoro ne". "Umma in sha Allah babu abin da ta isa ta yi wa Amatullah, gobe idan Allah ya kai mu zan je har can garin Jafarin mu yi ta ni da ita, in ta kama ma har ƴan sanda zan saka cikin lamarin". Anty Sawwama ta yi hanzarin taran numfashinsa"kar ka sake ka aikata wannan kuskuren Alhassan. Wani hujja kake da shi da za ka je har cikin gidan ka tunkare ta da wannan zancen? Ka san girman irin wannan lamarin kuwa? Hmm! Addu'a ita kaɗai ce mafita a gare mu". Shuru Yaya Alhassan ya yi har ta kai aya bai ce komai ba sai can ya ce"to yanzu Umma mene ne abin yi? Me ya kamata mu yi?". Ta saki sakakken ajiyar zuciyan da har sai da na ji sautin fitarsa kafin ta sama damar furta abin da yake kwance a ƙasan ranta. "Ina tunanin idan Allah ya kai mu gobe mu ƙira Malamai su zo, a kewaye mana ƙur'ani a cikin gidan nan, sannan mu riƙi addu'o'i da azkar don shi ne kawai mafita". Cike da gamsuwa ya ce"in sha Allah yadda kika ce Umma hakan za a yi, bari na je na kwanta Allah ya tashe mu lafiya". "Amin". Ta amsa da shi da hakan ya ba shi damar tashi ya fita, ni kam dole ta sanya Anty Sawwama kwanan a nan tare da ni sa boda yadda duk bayan mintuna nake firgita har sai an riƙe ni. Washe gari da sassafe Yaya Alhassan ya nemo Malamai suka zo suka yi sauƙan alƙur'ani a cikin domin kariya da kuma fin ƙarfin duk wani aljanni ko iska har ma da wani mai mungun nufi, da mummunan ƙuduri. Kwana biyu na jera a jere ba na samun bacci duk da kuwa yadda aka zage da addu'a da roƙon Allah, Yaya Alhassan har yanka ya sa aka yi mini kafi lamarin ya lafa sai dai cikin ɗan kwanaki na rame sosai na fita daga cikin hayyacina. A ranar wani labara ina kwance a ɗaki ina karanta littafin ƁOYAYYEN MANUFA, labarin zazzafan soyayyar Aishatu da Abdulhamid da ya karo da ƙaddarar da ta yi silar tarwatsa dukkan gini da tubalin da suka gina soyyayarsu a kai, Amir ya shigo ya kawo mini sabuwan waya ƙarama har da layi a cikinta, ya kuma shaida mini cewar Yaya Alhassan ne ya ce ya kawo min don ba son ina amfani da wannan wayar da na zo na ita ya kuma ce ma na ba ta ita. Ban yi musu ba na tashi na ɗauka wayar daman ko layi babu a cikin ta, memory ne kuma shi ma tunin na cire sa tun lokacin da Yaya Alhassan ya umarce ni da na goge wannan sautin muryar, na naɗe sa a cikin takarda na sanya a cikin jaka yayin na ɓoye sa a can ƙasan kayana. Tare da shi muka fito falo ta juya wayar a hannuna yayin da nake ba shi saƙon godiya ya isarwa Yaya Alhassan kafin ya dawo gidan na yi masa na mussamman, turus muka yi ganin baƙi a cikin falon tare da Anty Sawwama. Muhammad Taufik ne tare da Saifullah da suke gaishe da Anty Sawwama ciki girmamawa ta na amsawa fuskarta kamar gonar auduga. Juya ciki na yi don ko mayafi babu a jikina na fito na zauna a bakin katifa yayin da na faɗa cakwakiyar tunanin dalilin zuwan su gidan a wannan lokacin. Ban yi nisa cikin tunanin ba Amir ya ɗago labulen ɗakin fuskarsa a sake ya ce"ki fito ku gaisa". Na murtuƙe fuskana"Mu gaisa kuma Yaya Amir? Ni fa ina tunanin lokaci ya yi da za du dakatar da mutanen nan daga zuwa cikin gidan nan". Jijjiga kansa ya yi yana ɗan murmushi ya ce"yanzu dai ki yi haƙuri ki fito ku gaisa". Ya na dasa aya a zancen ya saki labulen ya juya ya fita, ina ta ƙunƙunai na ɗauko hijabi na saka na fito falon lokacin da na fito na iske Anty Sawwama ma ta tashi daga cikin falon. Can gefe na zauna kaina a ƙasa na gaishe su suka haɗa baki wajen amsawa kafin shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe. Har sai da na ƙosa da zaman kafin na tsinkayo muryar Muhammad Taufik yana faɗin"Amatullah mun zo gaisuwa ne tare da neman iri, na san ba ki manta zancen da Saifullah ya zo miki da shi ba kwanakin baya ya sanar da ni cewar har yanzu ba ki ba shi amsa ba hasalima ba ki saurare shi ba. Ina mai tabbatar miki da cewar Saif mutumin kirki ne duk inda ake neman mutum na ƙwara to ya kai wannan matakin a iya tsawon zamana da shi ban taɓa jin ya buɗe baki ya furta yana son wata mace har ya yi burin aurenta ba sai ke, ke ce mace ta farko a cikin labarin rayuwarsa ke ce mace ta farko da ta fara karya alƙadarinsa. Don Allah ki ba shi dama ko da sau ɗaya ne ki ba shi damar ya yi yaƙi domin tabbatar miki da ƙarfin soyyaya da ƙaunar da yake gwada miki". Tun da ya soma zancen nake kallonsa da wutsiyar idanuna ina jin wani abu yana tasowa tun daga cikin zuciyata yana tokare mini ƙirjina. Take! Ranar kuwa fara ganin lokacin zan tafi islamiyya ya soma dawo mini cikin kwanyata, na yi saurin tare da hawayen da suke shirin ɓalle mini. "Mun yi tunanin ko akwai wanda kike magana da shi ko kuma an riga da an yi miki miji shi yasa ba ki saurare shi, amma yanzu da muka zuwa Anty da maganan ta tabbatar babu ko ɗaya, kuma ta ba shi damar ya nema amincewanki idan har kin amince shi kenan". Ban san dalili ba haka kawai tun ya ci gaba da maganan na ji hawayen da nake ta ƙoƙarin riƙe wa sun ɓalle suka fara kwaranya. "Ka ga ne Sultan ba ri na je waje ba zan iya jure ganin zuban hawaye daga idanunta ba". Saif ya yi furucin cikin sanyin jiki da na murya bai jira amsar da zai ba shi ba ya tashi ya fita. Daga ni har Muhammad Taufik muka yi shuru na tsawon mintuna kafin can ya kawar da shurun ta hnayar cewa"Amatullah in dai ba ni damuwa kuma ba za ki takura ba. Don Allah ki ba wa Saifullah dama ina yaƙinin ba za ki taɓa yin dana sanin zaɓinsa ba, ba zai taɓa yin gangancin jefa ki a cikin wani halin da za ki yi tir da kasancewarki da shi a cikin inuwa ɗaya ba". "Me yasa ka gaza fahimtar cewa ban dace da shi? Ba na so na gurɓata masa tarihi ta hanyar haɗa jini da shi. Na yarda aure bautar Ubangiji sai Allah bai kallabafawa Bawansa yin sa dole ba hasalima akwai hanyoyin neman aljanna bila adadin. Zan rayu kuma na tsayu akan hanyar bautar Allah da neman yardansa ba dole sai na yi aure ba". "Ko da kuwa aure bai kasance dole ba amma shi ne cikar mutunci da kimar duk wata mace. Aure rufin asiri ne ga ƴaƴan mata, ko ba Saifullah ba ina tabbatar miki da in lokaci ya yi dole ne ki yi aure". A sanyaye ya ƙare zancen muryarsa har ta na riƙe wa, alamar akwai wani abun a ƙunshe a ƙasan zuciyarsa da yake ɓoye wa. "Me yasa kake yin duk wannan ƙoƙarin akan kawai na amince da Abokinka?". Kamar jira yake yi na yi masa tambayar ya yi hanzarin ba ni amsa. "Sa boda na tabbatar da soyayyar da yake yi miki babu yaudara a cikinta, kuma zai riƙe ki amana tare da ƙoƙarin faranta miki har ƙarshen rayuwarsa". Na jinjina kaina tare da ƙarfin halin cilla ƙwayoyin idanuna cikin na sa kafin na furta"ka na nufin ke nan kai ba so na kake yi ba?". Babu shiri ya ɗago idanunsa da suke bayyanar da maɗaukakin mamaki ya kafe ni da su. Hakan ya ba ni ƙarfin gwiwan ci gaba da furzo da magana"kar ka musa abin da ya riga ya bayyana a cikin idanunka. Muhammad tun ranar da Allah ya haɗa mu kana so ka ce mini ba sona kake yi ba? Idan ba so na kake yi ba me yasa ka shigo rayuwata ka yi tsamo-tsamo a cikinta a wancan lokacin". Ya yi saurin katse mini hanzari"Amatullah ni ban so ki ba, na san dai tabbas akwai tausayinki da yake maƙale a ƙasan raina". Yana ƙare zancen ya miƙe tsaye ni ma na tashi na je na tsaya a gabansa. "Ka kalla cikin idanuna Muhammad Taufik sai ka sanar da ni cewar ba ka taɓa jin soyayyata a cikin ranka ba, ta hakan ne kawai zan yarda da kai. Har na iya amincewa abokinka". "Ya isa haka Amatullah ya isa mana". Ya yi zancen cikin wani iriyar sarƙarƙiyar amo mai bayyanar da tarin damuwar da yake tattare da shi, ya kai hannu ya shafo suman fuskarsa yana saki ajiyar zuciya mai nauyi. "Na ji Amatullah a lokacin na ji soyayyarki a cikin raina, na ji a raina cewan zan iya rayuwa da ke a cikin ko wani hali kika tsinci kanki a cikinsa. Wannan dalilin ne ya sanya na dage tsayin daka wajen ganin na nemo ki har kin dawo cikin ƴan uwanki. Na yarda har yanzu akwai soyyayarki a cikin raina sai dai tun lokacin da Saifullah ya zo min da batun yana sonki tun daga lokacin na shiga ba wa zuciyata haƙuri, don ba zan iya gasa da Saif akan komai ba ko ya kuwa nake tsananin so da ƙaunar abun ya kai ƙololuwa. Zan iya sadaukar da komai akan Saifullah raina ne kawai ba zan iya zarewa na ba shi ba shi ma ɗin don ba ni da iko akan hakan ne". Ya yi shuru na tsawon wasu mintuna kafin ya matso dab da ni idanunsa akaina ya ci gaba da furzo da sirrin take taskace cikin tsokar zuciyarsa. "Ba zan iya hana zuciyata son ki Amatullah har abada, kuma komai za ki yi ko ki zama hakan ba zai taɓa sanya soyayyar da nake yi miki ta sauya ba. Sai dai dole na danne abin da nake so don wanzuwar farin cikin aminina, zan taya sa yaƙin neman soyayyarki har sai na ga ya yi nasara. Sannan ina roƙonki don Allah kar ki fitar da wannan maganan, ina so yadda muka yi ta a nan mu burne ta a nan". Yana dasa aya a zancen ya sa kai ya fice yana ɗan lumshe idanunsa da suka cika da ruwan ƙwalla, da ido na raka shi har ya fice daga cikin falon daidai sa'ilin fitarsa daidai lokacin da na durƙushe akan gwiwoyina ina jero wani kuka marar sauti. Haka Anty Sawwama ta zo ta same ni ta ɗago ni daga inda nake durƙushe ta kwantar da ni a jikinta yayin da take shafa kaina cike da kulawa ta soma faɗin"Uwata ki daina wannan kukan ya isa haka, kuka ba ya magani da yana magani tabbas da yanzu ya kawar miki da dukkan matsalolinki. Kuka ba mafita ba ne sai dai ma ya haddasa miki wani ciwon kamata ya yi ki ɗaga hannu ki gode wa Allah da ya yi miki wannan suturan, har ya kawo miki mai sonki kuma ɗan gidan mutunci da nutsuwa. Ki yi istikara ki nema zaɓin Allah ya yi miki zaɓin da babu nadama, dana sani balle kuma cizon ɗan yatsa a cikinsa. In sha Allah ina ji a jikina rayuwarki ta kusa sauyawa farin ciki zai maye gurbin dukkan wasu baƙaƙen abubuwan da suka wakana a cikin rayuwarki". Luf! Na kwantar da kaina a jikinta ina cikin gaba da sauraron tarin nasihan da take yi mini, a haka ina kwance a jikinta har bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba. Dogon bacci na yi ban tashi ba sai can yamma lilis na tashi na yi wanka na zo na gabatar da salla a makare, na daɗe kan sallayan ina ta tunani kafin na tashi na fito waje na yi wasu ayyukan kana na soma kici-kicin ɗaura girkin dare. Sai dab sallan magrib na gama girkin na sauƙe tare da yin alwala na shiga ciki na yi salla, ban tashi daga inda na yi sallan ba na ɗauko alƙur'ani na soma karanta cikin nutsuwa da fitar da haƙƙin ko wani harafi bisa ƙa'ida. Sai da na yi sallan isha'i kana na tashi na fito daga ɗakin lokacin har su Yaya Alhassan sun dawo, na zubo mana abinci tare da Anty Sawwama yayin da Yaya Alhassan, Amir da Umar suka ci nasu tare a kwano ɗaya kamar yadda al'adan gidan yake, bayan mun kama cin abincin na tattare kwanukan na je na wanke su ina doso ƙofan falon na ji Anty Sawwama tana sanar da Yaya Alhassan yadda suka yi da su Saifullah. Kaina a ƙasa na shigo cikin falon na wuce ɗaki daidai lokacin da nake jiyo muryar Yaya Alhassan yana faɗin"tabbas kam mutumin kirki ne, sai ta ya ta da addu'a in shi ne alkhairi gare ta Allah ya tabbatar...". Bai ƙarisa zancen ba sakamakon wani tarin da ya sarƙafe shi ya fara yin sa tamkar zai shiɗe, da sauri na juyo na fita waje na je na ɗebo masa ruwa na miƙa masa. Amsa ya yi ya ɗan sha kaɗan kafin tarin ya lafa muka haɗa ido da shi na ga ya yi hanzarin ɗauke na shi. Yana amsa sannun da Amir da Umar suka haɗe bakin wajen yi masa. Ya miƙe da hakan ya sa ni bin shi da kallo sai dai ko kaɗan ya ƙi yarda mu haɗa ido da shi, a taƙaice ya furta"Umma zan je na kwanta gabaɗaya ba na jin daɗin jikina". Bai jira amsar da za mu ba shi ba ya juya ya fice daga cikin falon, ya bar mu da tarin tambayoyi a ƙunshe a cikin ranmu. Ganin hawaye ya na ƙoƙarin ƙwace mini ya sanya ni na yi wuf na shige cikin ɗaki na zube akan katifa ina sakin hawayen tamkar bakin indararo, na daɗe ina kukan yayin da nake tuno zancen da muka yi na ƙarshe da Yaya Alhassan kafin sheiɗan ya yi nasara a kaina na sa ƙafata na guje wa gida da ƴan uwana masu tsananin ƙaunata. Tashi na yi na zauna tare da tafka wani uban tagumi cikin duhu dulum da ya mamaye cikin ɗakin ko tafin hannuna ba na iya gani, gabaɗaya na rasa mafita da yadda zan ɓullo wa lamarin balle har na sama matsaya guda da zan tsaya akan sa. Jin ƙaran waya na yi sai dai da yake ban saba da riƙe wayan ba, har ta gama rurin neman agaji ta yi shuru ban bi ta kanta ba, sai da aka ƙara ƙira a karo na biyu kafin na kai hannu na jawo wayar na zuba wa fuskar wayar kallo. Baƙuwan lamba ne babu suna, kuma a cikin maganganun da muka yi da Amir bai ce mini ya ba da lambar a kowa ba, hana ƙarya dai ya ce da ni ya sanya mini lambobin duk wanda ya dace a ciki. Ina ganin ƙiran har ya katse aka ƙara ƙira a karo na uku kafin na ɗaga na sanya ta a amsa-kuwwa na ajiye a gabana. Cikin wani irin sanyin murya mai ratsa jini da jijiyoyin ya bi har ta cikin ɓargo na ji an yi sallama, ba tare da na ɗauki muryar ba na amsa sallamar daga nan na yi shuru ɗaya ɓangaren ma aka yi shuru har sai da na yi zaton ƙiran ya katse kafin na ji an yi magana. "Na san ba ki gane mai magana ba ko?". "E". Na amsa da shi a taƙaice. "Saifullah ne". Ban san lokacin da na maimaita sunan cikin ɗaga sauti ba. "Saifullah kuma? A ina ka sama layina?". "Yayanki Amir ne ya ba ni layin. Ina fatan bai yi laifi ba?". Numfashi mai zafi na furzar daga bakina kafin na ce"sanar da ni dalilin ƙiran don ba ni da lokaci". Ina iya jiyo sakakken ajiyar zuciya da ya sauƙe kafin ya sama zarafin faɗin"kawai na ƙira na ne na ji yadda kika wuni". Wani bambarakwai na ji lamarin ya zo mini a bazata mamaki da al'ajabi ya hana ni cewa komai illa jujjuya zancen nasan da nake ta ci a can cikin ƙasan raina. Tamkar ya san abin da nake tunanin ya ce"ki na mamaki zantukana ko? Uhmm! Ni ma kaina idan na zauna mamakin kaina nake yi Amatullah ban taɓa tunanin zan iya furta irin waɗannan furucin da nake yi miki yanzu a kaf cikin rayuwa. Sa boda tun tasowa ta na tashi ni ban kasance mutum mai yawan magana ki shiga hayaniya ba, haka nan mata ba sa gabana harkan da ta sha min kai shi kaɗai nake mayar da hankalina a kansa". "Uhmm". Na amsa da shi a taƙaice ina ɗaukar wayar na kara a kunnena bayan na cire ta daga amsa-kuwwar ina ci gaba da sauraron abin da yake furta wa. "Amatullah ban zo gare ki da yaudara, mugunta ko kuma cutarwa ba. Hasalima zuciyata a wanke take babu wani mummunan abu a cikinta. Ba zan gaji da sanar da ke cewa ina sonki ba idan har kika ba ni dama babu abin da zai hana ni aurenki ko da kuwa duk mutanen duniya za su taru a kaina". Cike da ƙosawa da zancen nasan na kawar da zancen ta hanyar faɗin"ina su Aryan?". Sai da ya yi ɗan jim kafin can ya ce"suna nan lafiya, Amatullah ki ba ni dama na nuna miki irin soyayyar da nake yi miki". "Wai har yaushe ka fara son nawan ne? Da kake ta ikirarin soyayya haka?". Na jefa masa tambayar raina a ƙunzume ina jin wani ɓacin rai yana cika mini zuciyata taf. Sai da ya ɗauki mintuna a ƙalla uku kafin ya dawo mini da amsa. "Tun daga lokacin da na daina sanya ki a cikin idona, tun daga lokacin na fahimci sonki ya yi min mamaya a cikin zuciyata ba tare da na farga ba". Na yi luf tamkar wacce ruwa ya cinye ta. "Wataƙila ki ji zantukana tamkar waƙan shata ta yadda za su shiga ta kunnenki su fita ta ɗaya. Na riga da na sanar da ke iya gaskiyar abin da yake cikin zuciyata, ke ma ki je ki yi shawara da na ki zuciyarki da dul waɗannan kike ganin kin aminta da su, sannan abu mafi muhimmanci ki yi sallan istikara. Kar ki ji shakka, nauyi, ko tsoron sanar da ni duk abin da kuke ji a ranki a game da ni. Kin gan ni nan a cikin rayuwar nan babu wani abun da yake ba ni tsoro, sa boda duk abin da nake tsoron faruwarsa ya riga da ya faru da ni. Duk abin da nake tsoron rasawa na rasa su kuma na ci gaba da rayuwa. Duk waɗannan nake tsananin so da ƙauna sun tafi sun bar ni irin tafiyar da babu waiwaye balle dawowa, rayuwa ta koyar da ni haƙurin dole da kuma juriyan ɗaukan duk abin ya faru da ni walau na shirya masa ko kuma akasin hakan. Don haka duk abin da kike ji a ranki game da ni kar ki yi shakkan sanar da ni da tunanin wai za ki ɓata min rai ko kuma na yi fushi". Tabbas zantukan sun sama matsuguni a cikin kwanyata sun yi zaman dirsham, jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka tsoma ta a cikin ruwan gishiri. Na ƙare matse wayar a kunnena yayin da wasu hawaye suke zuba daga gefe da gefen idanuna. Babu abin da yake yi mini yawo a cikin ƙwaƙwalwata face maganganun da muka yi da Muhammad Taufik ɗazu. "Ki na ji na kuwa?". Tambayar da ya yi mini shi ya dawo da ni cikin duniyar zahiri. "Ina jinka kuma ina so na roƙi wani alfarma a gare ta". Tun kafin na rufe bakina ya ce"faɗi dukkan abin da kike buƙata, matuƙar bai fi ƙarfina ba to tabbas kin riga da kin same shi". "Ina so ka ba ni lokaci na yi tunani kuma na yi addu'o'i, kai a naka ɓangaren ka gabatar da abubuwan da suka dace wanda addini ya sharraɗanta a yi yayin nema. Sannan ina so har zuwa lokacin da zan gama kar ka ƙara yi mini wani maganan da ya danganci soyayya". Haƙiƙa na fahimci zantukan sun yi masa nauyi don sai da ya ɗauki tsawon lokacin kafin ya dawo mini da amsa cikin sanyin jiki. "Ban yi zaton wannan alfarman za ku roƙo amma sai dai ba na fatan zuwan ranar da za ki nema wani abu a waje ki rasa. Don zan yi kamar yadda kika buƙata in sha Allah zan ba ki cikakken lokaci ki yi duk tunani da addu'o'inki, kuma ba zan ƙara yi miki maganar soyayyar ba har sai ke da kanki kin buƙata hakan. Sai dai ni ma zan roƙe ki alfarman". Jikina a sanyaye na ce"ina jinka". "Ina so kar ki hana ni ƙiranki, kar ki hana ni ganinki, kar ki hana ni zuwa inda kike. Sannan inna ƙira ki ko ba za ki ce komai ba". Ba tare da wani dogon tunani ba balle nazari na ce"na yarda". "To ina godiya ranki ya daɗe, bari na bar ki ki kwanta ki huta. Sai da safenmu a tashi lafiya". "Allah ya kai mu". "Amin ya hayyu ya ƙayyum". Daga haka na katse ƙiran na rumgume wayar a ƙirjina tare da lumshe idanuna, na daɗe a haka kafin na tashi na fito na yi alwala na koma na je na yi sallan raka'a biyu na ɗaga hannuna sama zan roƙi Allah sai dai na kasa magana, da zaran na buɗe baki kuka ne kawai yake fitowa haka na kifa kaina a wajen ina tilawan karatun haddan da yake kaina, a wajen baccin wahala ya ɗauke ni. [12/25, 6:59 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ____________________________________ Page 7️⃣9️⃣ Washe garin ranar da ƙyar na tashi sa boda wani azababben ciwon kan da ya addabe ni idanuna ma ba na don buɗe wa balle na ga gilawan haske komai ƙanƙantansa. Tun safe ban fito daga cikin ɗaki ba ina kwance har sai da Anty Zulaihatu ta zo ta kana na tashi daga kwanciyan da na yi, na gaishe ta yayin da idanuna suke a lumshe, ta amsa mini cike da kulawa sa'ilin da take kai hannunta saman goshina ta ji ya ɗauki zafi garau tamkar garwashin da ke ƙasan tukuban tsire. Cike da kulawa da ya gauraye da lallashi gami da lallama ta soma faɗin"Amatullah me ya yi zafi ne haka alhalin shi ba wuta ba? Me yasa kike so ki jefa kanki cikin wani irin yanayi da zai shafe mu daga ke har mu. Rayuwar nan fa da kike ji da gani ba ta taɓa tafiya a miƙe tsalin ƙalin dole sai an bi ta tudu da gangare sai an haɗu da ƙalubanale kala-kala, sai an yi katari da jarabawa mai sanya rauni a cikin zuciya. Ko wani Bawa da irin na shi salon ƙaddaran a cikin wannnan rayuwa. Don Allah na roƙe ki cire komai daga cikin ranki ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki ki miƙa wuya gare shi ki sakankance cewa duk abin da ya zartar a gare ki hakan shi ne daidai, domin babu kuskure a cikin hukuncinsa". Tun da ta fara zancen na sadda kaina ƙasa ina sauraron ta ba tare da na katse ta har sai da ta kai aya. Muryata ba ta fita yadda ya kamata na ce"Anty Zulaihatu abin da nake ta ƙoƙari ke nan, na cire damuwar da ya yi kane-kane a cikin zuciyata ni ma ina so na yi rayuwa cikin walwala da annashuwa kamar yadda kowa yake yi. Sai dai wallahi ko na ɗauko aniyar aikata hakan sai na ji na kasa, ba na ma sanin lokacin da tunanin yake zuwa mini balle na ankare da sa'ilin da ruwan hawaye yake kwaranya daga koramar idanuna". A raunane na ƙarshe zancen ina jin ƙirjina ya yi mini nauyin gaske tamkar wacce aka yi wa ajiyan wani gingimemen dutse. "Haƙuri za ki yi Amatullah watarana sai na labari, komai zai zo ya wuce tamkar bai taɓa faruwa". Kaina kawai na gyaɗa mata ina kwantar da kaina a bisa kafaɗanta da hakan ya ba ta damar kai hannunta tana shafa sumar kaina a hankali. "Yanzu da na zo ni Umma take sanar da ni wani abun alkhairi da farin ciki kuma". Cike da tashin fahimtan zantukan natan na ce"wani abu ke nan?". Sai da ta murmusa kafin ta furta"ta sanar da ni cewar akwai wanda ya zo cikin gidan nan neman soyyayarki ko kuma kai tsaye na ce aure ne ya kawo sa, don bai zo da wasa. Amatullah kin ga duk mutumin da ba ya shakkan haɗuwa da magabatan yarinya to haƙiƙa wannan mutumin ɗan gidan mutunci ne kuma zai yi wahala ya yaudare ta. Ki ba shi dama ki fahimcie shi ta nan ne za ki gano cancantarsa ko kuma akasin hakan, idan har kika ji ya kwanta miki a cikin rai to kawai ki amince masa ya turo a zo a yi magana". Tun da ta soma magana na yi laƙwas ban ce komai ba har sai da ta kai aya. Cikin raunin da ya bayyana har a cikin kalaman da bakina ke furtawa na soma magana cikin rawar murya da ya haddasa rashin fitar sautina sosai. "Anty yanzu ke ma ki na goyan bayan na yi aure a cikin wannan yanayin da nake ciki? Ina buƙatar kwanciya da nutsuwa kafin a kawo mini wani maganar da ya danganci aure ko soyayya, sannan wannan mutumin ya wulaƙanta a lokutan baya ya zarge ni da abin da ban aikata shi hasalima ko kusantansa ban yi ba". "Abin da ya riga ya wuce ya wuce Amatullah ki fuskanci yau ɗinki da kuma abin da gobe za ta haifar. Rayuwa ta kan zo da abubuwan da mu ƴan Adam ba mu taɓa zato ba balle tsammanin faruwarsa. Duk wani kwanciyar hankali da nutsuwan da za ki sama ba zai kai na cikin gidan aurenki wanda za ki samu daga wajen mijinki ba". Sai da na jinkirta ba ta amsa sa boda nauyin da bakina ya yi mini kafin can na ce"Anty kin mata da cewar Yaya Alhassan ma ya taɓa zuwa gare ni da irin wannan buƙatan? Shin ina ganin na kyauta masa idan na amince wa waninsa? Ki na tunanin na yi masa adalci na kuma saka masa idan na ba wa wani da muka haɗu da shi rana tsaka kyautar zuciyata alhali shi ya san dukkan ɗawainiyya ta?". Numfashi mai ƙarfi ta fesar daga bakinta kafin ta sama zarafin faɗin"Amatullah idan aka zo batu na aure ba na duba dangantaka, ba a duba kusanci, ba a duba alaƙa daɗaɗɗiya ko kuma sabuwa, haka nan ba a yin kara balle kawaici. Fito wa ake yi a fallasa sirrin da yake cikin zuciya ko da kuwa zuƙata da yawa za su ɗanɗana romon baƙin ciki. Don shi aure da kike gani ba zaman lokaci ɗaya ba ne, ba zan wuni guda ba ne zama ne na dogon zamani da ake fatan ya ɗaure har abada, kuskure mafi girma da mace za ta yi shi ne ta zaɓa abokin rayuwa wanda bai dace da ita ba to tabbas za ta dawwama ne cikin ƙunci da baƙin ciki. Don haka ina mai ba ki shawaran ki yi addu'a ki roƙi Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi tsakanin Yaya Alhassan ɗin da kuma wannan baƙo, duk wanda kika gabatar mana tabbas da shi za a yi mu zo mu sha biki har mu yi rawa da juyi". Maganarta ta ƙarshe ta jefa ni a cikin kunya, na yi saurin ɗauke kaina daga saman kafaɗanta na rufe fuskana da tafukan hannayena na fice daga cikin ɗakin, ina jin ta tana dariya tare a ƙiran sunana amma kuma waigowa ban yi ba balle na tanka mata. Ina fito wa falo muka yi kiciɓus da Yaya Alhassan yana shigowa take na sha jinin jikina na yi wani irin kunyarsa nauyinsa sun lulluɓe ni, na tako na iso cikin falon na gaishe shi yayin da yake zama akan ɗaya daga cikin kujerun da suke jere reras a falon. "Yaya Alhassan daman ina ta so na yi maka godiya waya, sannan kuma akwai maganar da nake so mu tattaunawa da kai". "Babu godiya tsakaninmu Amatullah kamar yadda ba zan cire kuɗi na yi wa Amir ko Umar da suke ƙannena ba tare da na yi komai a cikin raina ba, to ke ma haka nake tsintar kaina a cikin irin wannan yanayin a duk lokacin da na yi miki wani abu". Kaina na jinjina cike da gamsuwa don ni ma katan kaina shaida ce akan irin tari soyyaya da kulawan da yake nuna mini da yau na gaza samun abin da zan saka musu da shi. Sai da na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya mai nauyi kafin na zama zarafin faɗin"daman na so mu yi magana akan Saifullah da ya zo cikin gidan nan da buƙatan aurena idan har na amince". Ya yi hanzarin katse ni ba tare da na ƙarisa ba ta hanyar faɗin"wani magana za mu yi akan hakan? Ai idan har kin ji ya kwanta miki a cikin ranki to shi kenan kawai an gama magana". "Na san da haka sai dai idan ba ka manta ba kai ma ta taɓa zuwa mini da makamancinyar irin wannan buƙatan a lokacin baya, sai nake ganin.......". Ya ɗaga mini hannu alamar ba dakata hakan aka yi kuwa na yi tsit tare da sadda kaina ƙasa. "Wannan kuma wani abu ne da ya riga ya wuce bai dace ki na tuno shi a daidai irin wannan lokacin ba, na yarda duk abin da ban samu ba to haƙiƙa daman Allah bai ƙaddara cewa yana daga cikin rabona ba. Ina miki fatan samun rayuwa mai inganci ko ki na cikin gidana ko kuma ki na cikin gidan wani daban ba ni ba, burina ki sama farin ciki da kwanciyar hankali. Don haka ina ba ki shawaran ki zaɓa wanda hankalinki ya fi samun nutsuwa da shi, kika ji ya kwanta miki a cikin ranki. Zuciyarki ta nutsu da shi". Gabaɗaya jikina ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa a cikin ruwan gishiri, hawaye suka ciko mini kurmin idanuna sai dai na ƙi ba su damar da za su kwaranya har ya miƙe ban iya ɗago kaina ba balle na ce da shi wani abu, yana shirin fita daga cikin falon Anty Zulaihatu ta fito riƙe da wayata da take ta faman ruri a hannunta. "Kin ga wayarki sai ƙira ake yi tun ɗazu". Na amshi wayar cikin sanyin jiki tare da ɗaga ƙira na kara a kunnena yayin da nake koma cikin ɗakin na zauna a bakin katifan. Sallama ya yi na amsa muryata a dushashe daga haka gabaɗayanmu muka yi shuru. "Daman na ƙira ne na ji ya ya kike da kuma yadda kika wayi gari". Kamar ina gabansa na gyaɗa masa kaina kafin na ce"lafiya ƙalau". "To alhamdulillah a gaishe da mutanen gidan". "Za su ji". Ban jira abin da zai kuma cewa ba na katse ƙiran tare da ajiyar wayar na fita daga cikin ɗakin. Kowa na tunkara da zancen Saifullah magana guda yake furta min shi ne na yi addu'a sannan na bi abin da zuciyata ta nutsu akan ta. A haka har aka cinye sati guda babu ranar da za ta fito ta faɗi ba tare da Saifullah ya riƙa ni ba duk ranar juma'a kuwa sai ya niƙo gari ya zo takanas ta kano gaishe da Anty Sawwama haka za su sha hiran su kafin ya tafi. Haka kawai ranar na tashi da kewan Amira na tambayi Anty Sawwama ta yarje mini zuwa gidan Amira tun da safe na buga shirina na zauna zaman jiran Yaya Alhassan don shi zai kai ni da mashin ɗinsa, da taimakon kwantancen da ta yi mini ranar da ta zo ta muka sama gidan. A ƙofar gidan Yaya Alhassan ya tsaya na shiga ciki na yi mata magana ta fito suka gaisa kana ya tafi bayan ya shaida mini cewar bayan sallan magrib zai zo ya ɗauke ni mu koma gida. "Matar mijinta ki na sha'aninki a cikin gidan nan". Na yi zancen cikin sigar zolaya yayin da nake cire hijabina. Murmushin ta yi kafin ta ce"duk da tun da kika shigo annuri bai gushe daga kan fuskarki ba, amma hakan bai hana ni fahimtar cewar akwai abin da kike ɓoye wa a cikin ranki ba, Amatullah shin akwai wata matsalar ne?". Numfashi mai nisan zango na ja na fesar daga bakina kafin na cira kai ina kallonta na ce"Amira ke ma kin sa matsaloli ai ba ya ƙare wa, in dai da rayuwa to tabbas akwai jarabawa". Ta shimfiɗa masa tabarma a waje muka zauna kana na kwashe komai na sanar da ni don na yarda abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa haka nan abokin cin mushe ba ya ɓoye masa wuƙa. Ta jajanta mini sosai kafin ta ce"ni fa Amatullah ina ganin kamar ki amince masa kawai, inda gaske yake sonki ya zo a yi auren a wuce wajen. Don kin gan ni nan wallahi yanzu ba na goyan bayan dogon soyayyan nan da ake yi a waje da za a shafe shekaru ana buga wa, gwara a yi auren duk soyayya da kulawan da za a ba wa juna ku yi shi a cikin gidanku". Bushashshiyan murmushi na saka da ba shi da alaƙa da nishaɗi kafin na yi ƙarfin halin faɗin" ba na jin zan iya soyayya a yanzu haka, sai dai zan amshe shi ne kawai don cikar wani burina wanda a yanzu shi kaɗai zai iya taimaka mini". Babu shiri ta waro idanunta"wani buri ke nan?". "Me ye abin da tada hankali haka? Sanin kanki ne dai ba zan aikata abin da yake na haramci ba ko?". Kanta ta jinjina cikin sanyin jiki ta soma cewa"haka ne kam to Allah ya shige mana gaba". "Amin ya Allah" Na amsa da shi yayin da muka ci gaba hirar mu cike da kewar rayuwar da muka yi a gaba da takaicin yadda rayuwa ta yi mana atishawan tsakin barkono. Mun ba wa juna shawara akan abubuwa da yawa na rayuwar yau da kullum.Tare muka wuni da Amira da hakan ya yi mini matuƙar daɗi har na manta da tari damuwar da nake cikinsa sai da aka yi sallan magrib kafin ƙiran Yaya Alhassan ya shigo cikin wayata na ɗaga ya shaida mini cewar yana ƙofar gida, na tashi na miƙe tsaye ina faɗin"kin ga ni kam bari na wuce Yaya Alhassan yana waje yana jira na". Cikin rashin jin daɗi ta furta" ga shi har za ki tafi Mansur bai dawo ba, na so a ce ya zo ya same ki wallahi". "Ba komai kar ki wani damu ai zan dawo wataran. Yarinya ta Mansur sai na tuna irin zumuɗin da kike a da idan ya ƙira ki ya ce miki yana hanyar zuwa gida, ranar walwala da farin cikinki na daban ne. Haka ranan in muka je talle za ki ta zuba masa kamar kyauta". Ta ja numfashi ta fesar kafin ta ce"rayuwa fa ke nan ga shi yanzu komai ya wuce har ya zama labari". "Watarana mu ma haka za a tuna mu, a lokaci da muka gushe daga cikin duniyar". "Allah ya yi mana mai kyau". Ta furta yayin da take ɗaukar hijabinta ta saka muka fito, a ƙofar gidan muka iske Yaya Alhassan take ya soma faɗan me yasa zan jawo Amira ta fito raka ni alhalin na san ita ta matar aure, sai da na ba shi haƙuri kafin ya saduda ya yi sanyi. Haka muka yi sallama da Amira ba don ranmu ya so ba muka tafi bayan na yi mata alƙawarin ƙara zuwa nan ba da jima wa ba. Bayan mun koma gida har na yi shirin kwanciya na ji wayata ta soma ruri na yi caraf na ɗaga ƙiran tare da amsa sallamar da ya yi mini na ɗaura da faɗin"ko ba ka ƙira ni ba dama ina da burin ƙiranka yau". "Ko dai sakamakon jiran da aka ce na yi za a sanar min? Yanzu na tashi na je na yi alwala na zo na gabatar da salla raka'a biyu na roƙi Allah ya ba ni juriyar ɗaukar duk irin amsan da zan ji ya fito daga bakinki". Na ɗan lumshe idanuna kafin na buɗe ina faɗin"ba abin da kake tunani ba ne, daman ina son ganinka ne gobe akwai maganar da nake son mu tattaunawa da kai". "Faɗa naki cika wa nawa. In sha Allah goben zan zo ni da wuri ma kuwa". "Na gode Allah ya kai mu". "Amin". Ya amsa da shi daga muka yi shuru dukkanmu sai can na ji ya ce"Aryan da Ayan su na tambayarki". Na yi firgitit na buɗe idanuna da na lumshe su"wai kana nufin har yanzu ba su manta da ni ba?". "Ƙwarai kuwa don kusan kullum sai sun yi maganarki, tun bayan gano gaskiyan da muka yi game da Altine wanda hakan ya faru ne ta dalilinki. Amatullah kin zama silar bayyanar haske a cikin rayuwarmu kin cuce rayuwar su Ayan daga zalunci, cutarwa da kuma ha'incin da Atline ta daɗe tana aikatawa gare su ta ƙarƙashin ƙasa. Tabbas idan abubuwa ya daidaita ma Anty Muhibbat za ta zo da kanta ta yi miki godiya har gida sai dai a yanzu ta ce kunyarki take yi". "Wani irin kunya ke nan?". "Kunyan abubuwan da ta yi miki mana". Na saki taƙaitaccen murmushin da ya tsaya iya kan leɓena kafin na ce"don Allah ka sanar da ita cewar tarin alkhairan ta gare ni sun shafe komai. Ta riƙe n bisa gaskiya da kuma zuciya ɗaya ba ta taɓa yi mini wani abun cutarwa ba don haka bai kamata ta ji kunyata ba". Da alama ya ji daɗin zantukan da na jero don ina jin yadda yake ta sauƙe ajiyan zuciya wani na bin wani. "In sha Allah zan sanar da saƙonki a kumnuwanta". "Amma da san da cewa ka na zuwa gidanmu?". Cike da ƙwarin gwiwa ya mai do mini da amsa"ƙwarai kuwa hasalima ita ta ba ni ƙwarin gwiwan tunkaranki don ita ma kanta ta yaba da nutsuwa, hankali da kuma riƙon amananki". Lamau na yi tamkar mai bacci har sai da na ji ya ci gaba da maganan"amma ko zan iya sanin dalilin ƙiran da ake yi min na gaggawa kafin goben?". "Me kake ci na ba ka na zuba? Allah dai kawai ya kai mu goben ko ma mene ne ai za ka ji". "Haka ne kam". Mun ɗan taɓa hira kafin muka yi sallama da wuri na kwanta, don ina so na tashi na yi sallan dare kamar yadda na saba. Washe gari ban sanar da kowa zancen zuwan Saifullah sai dai kawai ina zaune a ɗaki Anty Sawwama ta ɗago labulen ɗakin. "Sai ki fito ki na baƙi". Gabaɗaya na manta da cewar mun yi magana da Saifullah mussamman da na ji ta ce baƙi maimakon ta ce baƙo. "Wasu baƙi kuwa? Ba wasu baƙin da muka yi da su za su waje na yau". "In ki ka fito ai za ki gan su, a nan ne za ki gane kin san da zuwansu ko akasin haka". Ta dasa aya a nan ta saki labulen ta yi ficewar ta, ta bar ni saƙa da warwara a cikin raina. Haka na tashi na saka hijabina na fito ina saka ƙafana a cikin falon Ayan da Aryan suka rugo da gudu har suna karo da juna suka rungume ƙafafuna. Tsugunawa na yi a gabansu ina shafa fuskokinsu don tabbas Allah ya jarabce ni da wani irin zafafan ƙaunar yaran wanda hakan ya samu asali daga soyayyar da nake yi wa duk wasu ƴan biyu musamman masu kama iri kwabo da kwabo ɗin nan. "Yaushe ku ka zo?". "Ba mu daɗe da zuwa ba, tare da Uncle Saif muka zo mu. Kuma Umminma ta ce in mun zo mu gaishe da ke sosai sosai". Aryan ya yi zancen har yana kwaikwayon muryar Umminsu. "Ina amsa wa ni ma in kun koma ku ce ina gaishe ta". Kansu suka gyaɗa mini alamar sun ji da hakan ya sa ni tashi tsaye na riƙon hannunsu muka ƙarisa cikin falon, Yaya Alhassan ne da Umar sai kuma Anty Sawwama yayin da gefe guda kuma Saif ne zaune Muhammad Taufik yana kusa da shi suke ke nan a cikin falon. Sai da na zauna na gaishe su suka amsa take na ji tausayi da tunanin halin da Muhammad Taufik zai shirga bayan na aikata abin da zuciyata take ingiza ni na yi. A zahiri hankalina yana kan su Ayan da suke ta zuba mini suturu sai dai hankalina yana kan hirar da su Yaya Alhassan suke yi, har zuwa lokacin da Saif ya ce zai je ya kai Muhammad Taukif filin jirgi don jirgin ƙarfe goma sha ɗayan rana zai bi zuwa cikin Abuja. Ya yi sallama da Anty Sawwama yayin take ta sa masa albarka da yi masa addu'ar Allah ya sauƙe shi lafiya. A nutse muyarta can ƙasan maƙoshina na furta"Allah ya sauƙe ku lafiya mun gode da ziyara". Caraf idanuna suka sauƙa cikin na Muhammad Taukif, shi ya fara janye na sa idanun ya na amsa da kalmar Amir yayin da suke fice wa daga cikin falon. Na kwashe su Ayan muka shige cikin ɗakin har muka fito na ɗaura girkin rana na gama na yi alwalan sallan zuhur na yi sallan, ina zaune kan sallayan yayin da su Ayan suke gefe na suka cin abincin da na saka musu. Na ji wayata ta soma ruri na yi hanzarin ɗauka tare da ɗaga ƙiran, maimakon amsa sallamar da na yi sai ji na yi an sauƙe ajiyar numfashi mai ƙarfin sauti. "Ina ga dai matar nan kin manta da cewar ki na da baƙo ko?". Na dafe goshina kafin na ce"afuwan na ji tunanin ba ka dawo ba ne ai". "Na dawo ina ƙofan gida ina jiranki za ki fito ne ko kuma na shigo?". Da sauri na ce"A'a ka tsaya a nan zan fito". Sai da na yi maganan sai kuma ni da kaina na ji kunya na katse ƙiran na tashi na je wajen ajiye kayana na ɗauko jakar da na sanya memory card ɗin nan a cikin na ɗauka. "Ku zauna a nan ba ri yanzu na je na dawo kun ji". "To". Suka haɗe baki wajen amsa wa da hakan ya ba ni damar fita, ban iske kowa a falo ba hakan ya ba ni salama da nutsuwar fice wa wajen kaina tsaye. Ina fitowa na hango shi tsaye a jikin motarsa yana latsa wayarsa. Da sallama ɗauke a bakina ya amsa mini yana ɗago kai tare da kafe ni da ido bayan ya mayar da wayan cikin aljihunsa. "Ki bar Bawan Allah Saifullahi marayan Allah yana ta jiranki a cikin rana". Na sadda kaina ƙasa"ai ka dawo da ka shigo ciki". "Kayya! Wallahi kunyar Anty nake yi shi yasa kawai na tsaya a nan, yanzu dai ina sauraronki don jiya na kwana cikin zaƙuwa". Na ɗan tsagaita kafin na miƙa masa memory card ɗin da yake hannuna ya karɓa yana jujjuya shi a hannunsa. "Wannan fa na mene ne?". "Ina so idan ka je gida ka nutsu ka saurare abin da yake cikinsa da zaran ka gama saurara sai ka ƙira ni mu yi magana". Shuru ya yi kallona kamar mai nazari ko kuma son gano wani abu, sai can ya ce"to shi ke nan ba matsala". Ya ƙare zancen yana cira wa a cikin aljihunsa. "Yanzu za ku wuce ne?". Ya waro idanununsa tar a kaina"to fa! Kora da hali ake yi mana ke nan? To shiga ki kwaso min su mu wuce". Kunya ya lulluɓe ni har sai da na rufe fuskana da tafukan hannayena. "Ba fa haka nake nufi ba, na ga su Ayan abinci suke ci ne shi yasa na tambaya". "Su sun sama karramawa ke nan tun da har girki aka yi musu. Saɓanin ni ɗan marayan Allah da aka shanya ni a tsakiyar rana aka manta da kashi na". "Wallahi Yaya Saif ba haka ba ne ban san ka dawo ba ne.....". Ban ƙarisa zancen ba sa boda yadda ya tsare ni da idanunsa har sai da na ɗan tsorita na ce"lafiya kuwa?". Ya ja dogon numfashi mai nisan zango kana ya furta"don Allah ƙara ƙiran sunan na ji, sai na ji kamar babu wanda ya kai ki iya furta sunan daidai. Ban taɓa jin an ƙira sunan da na ji daɗinsa irin haka ba, don Allah ki ƙara faɗa ko sau ɗaya ne". Na ɗaga ido na saci kallonsa daidai lokacin da yake ƙara faɗin"Please mana". "Cewa na yi Yaya Saif". Ina furtawa na juya da sauri na shige cikin gida muka yi kiciɓus da Yaya Alhassan yana ƙoƙarin fitowa da mashin ɗinsa na yi saurin ja da baya na ba shi hanya yayin da kunya ya gama mamaye ni har na kasa ɗago idanuna, sai da ya gama fito da mashin ɗin na sama hanyar shiga ciki. Na koma wajen su Ayan na iske su har sun gama cin abincin, ina zama ƙiran Saif ya shigo cikin wayata na ɗaga ƙiran na ba wa Aryan na ce ya yi magana. Sai da suka gama na tambaye shi yadda suka yi ya shaida mini cewa ya yi in su gama su fito su tafi yana jiransu a waje. Kimtsa su na yi na kamo hannunsu muka je wajen Anty Sawwama suka yi mata sallama yayin da take musu leda taf da tarkacen abubuwa dangin su bushashshan kuɓewa, zogale, kanwa da kuwa yajin ƙuli ta ce su kai wa Umminsu. Har bakin ƙofa na rako su sai da na fitan su har suka isa wajensa kafin na jawo ƙofar na koma ciki. Haka na ƙarar da wunin cikin tsinkewar zuciya da faɗuwan gaba. Bayan na yi sallan isha'i na ɗauko alƙur'ani na soma karantawa sai da na yi izu biyu daga suratul Naba'i zuwa suratul Nasi. Ban jin sha'awan cin komai hakan ya sa ni yin shirin kwanciya na kwanta ina ta saƙe-saƙe a cikin raina. Har bacci ya fara ɗauka ta na jiyo rurin wayata na zabura na tashi na ɗauko ta tare da ɗaga ƙiran don dama shi nake jira har bacci ya sace ni. "Amatullah ina kika sama sautin muryan nan? Idan ban yi ƙarya ba fa muryanki ne me ya kai ki wajen mutumin nan? Me yasa kika naɗi sautin nan?". Ko sallama bai yi mini ba illa jerin tambayoyin nan da ya soma jefo mini a jere wani na bin bayan wani. "Ka tsaya na yi maka bayani". Na zancen cikin sanyi ganin yadda gabaɗaya lokaci guda ya birkice. "Wani irin bayani za ki yi min Amatullah bayan abin da na saurara yanzu?. Tambaya ɗaya zan yi miki wanda nake so ki ba ni amsarsa shin da gaske wannan sautin muryan da na ji mallakin Sheik Dawood ne mahaifi ga aminina Muhammad Taufik ko kuma na ce Sultan?". Cikin ƙwarin gwiwan da ban san ina da shi na furta"ƙwarai kuwa muryarsa ne, kuma duk abin da ya faɗa haka yake babu kuskure a cikinsa. Na ba ka ka saurara ne don ka ceto rayuwar abokinka da har kake ikirarin a zama amini kuma ɗan uwa a gare ka. Na ba ka saurara ne sa boda mu ceto rayuwar ƴaƴan matan da zai iya lalatawa rayuwa a nan gaba" . "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahuma ajirni fi musibati. Ya Allah ta ina zan fara? Kin san yadda nake ganin girma da darajar Malam kuwa? Wallahil azim kallon uba nake yi masa haka nan shi ma ya ɗauke ni tamkar ɗan da ya haifa a cikinsa. Ina da tabbacin Sultan bai taɓa sanin cewa ba shi ya haife sa sa boda ya ba shi dukkanin kulawan da uba zai ba wa ɗansa". A sanyaye ya ƙare zancen cikin yanayin damuwa da ya haɗe da ruɗani. "Dole ne kuwa sai na ji hakan ko ba daɗe ko ba jima. Ka fi ni sanin hanyar da ya dace ka sanar da shi wannan ɓoyayyan sirrin". Shuru ya yi na tsawon lokaci mai tsayi har sai da na yi zaton ko ƙiran ya katse ne sai da na duba na ga yana tafiya. "Hello". Na yi furucin cikin sanyayyan amo. "Amatullah". Ya ƙira sunana muryarsa ba ta fita sosai. "Na'am Yaya Saif". "Tabbas kin zo da babban lamarin da na ji kaina ya gaza ɗaukansa, zuciyata ta kasa yarda cewa Sheik ɗin da na sani ne ya rikiɗa ya zama wannan. Tabbas zan bayyana wannan sirrin ga Sultan sai dai ta ya ya kuma ta ina zan fara?". Daga ni har shi muka yi shuru don ban san amsar da ta dace na ce da shi ba. "Zan neman wani layin da bai san ni da shi ba na buɗe what's app da shi sai na tura masa, na tabbatar idan ya saurara ni ne mutum na farko da zai fara tunkara da matsalar daga nan sai mu warware matsalar a tare. Amma kai tsaye kam wallahi ba zan iya tunkararsa na sanar da shi cewar ina zargin Sheik da aikata wannan ɗanyen aikin ba". Shuru ina sauraronsa har ya gama ban iya cewa komai ba. Ina jin sa sai faman maimaita kalmar hasbunallahu wa ni'iman wakil yake yi kafin ya ce"amma me yasa kika zaɓi ni ki ka ba ni wannan memory card ɗin?". "Ba ni na zaɓe ka zuciyata ce ta zaɓe a bisa wannan aiki don a wannan ɓangaren, tabbas ka sama yardanta". "Amma da farko me ye kika yi niyyan aikatawa da sautin muryan da kika naɗa?". Babu wani ɓoye-ɓoye balle nuƙu-nuƙu na fito ɓaro-ɓaro na sanar da shi komai har da yadda muka yi da Yaya Alhassan. Ya ɗan yi jim kafin can bayan lokaci mai tsayi ya ce"tabbas kin yi kyan da kai da ba ki bayyana wa duniya wannan sautin muryar ba, Sheikh babban mutum ne a idon jama'a kuma ko ba komai shi ɗin ubana ga ƴayansa, marayu har ma da masu uban. In sha Allah na yi miki alƙawarin shawon kan lamarin nan cikin ruwan sanyi har mu warware komai ba tare da kin shiga cikin wata matsala kamar yadda Alhassan yake tunani ba". Ji na yi zuciyata ta yi saƙayau nauyin da ƙirjina ya yi mini na ji tamkar ana warware mini shi, ban san sa'ilin da hawaye ya zubo daga idona ba. "Idan har hakan ya tabbata ni kuma na yi maka alƙawarin babu abin da zai hana ni aurenka, na tare a cikin gidanka a matsayin matarta". Da gaggawa ya katse ni"wannan abun da kike faɗa har cikin zuciyanki haka yake?". Jikina a sanyaye na ce"ƙwarai kuwa". "Alhamdulillah! Alhamdulillah Ya Allah". Kit! Na kashe wayar ba tare da saurari ragowar zancen ba, na kwanta na yi ruf da ciki ina hawaye. Ina jin wayar tana ruri wanda ina da tabbacin Saif ne yake ƙira amma ban ɗauka ba. [12/26, 8:27 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ____________________________________ Page 8️⃣0️⃣ Haka na raya tsawon daren da sallan dare sai bayan sallan asubahi na samu na kwantar da haƙarƙarina take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awun gaba da ni, cikin baccin na ji ana ƙiran sunana cikin sanyin amo tare da bubbuga matashin da nake kwance akan sa. A hankali na soma buɗe idanuna har na buɗe su tar akan fuskar Anty Sawwama da take zaune kusa da ni. Na murtsike idanuna yayin da nake ƙoƙarin tashi na zauna ina faɗin"har gari ya waye?". "Wani irin gari ya waye kin san yanzu ƙarfe nawa kuwa? To yanzu kusa ƙarfe sha ɗaya ake nema na rana duba fa ki ga yadda rana ta take haskenta ya mamaye ko'ina". Zumbur na yi na tashi tsaye ina leƙa taga na ga hasken rana ya dalle tar. "Innalillahi har rana ta fito haka Anty? Da kin tashe ni na yi aikin cikin gidan ai". Taƙaitaccen murmushi ta yi kafin ta ce"kwantar da hankali ai na gama duk wasu aikace-aikacen da ya kamata, hatta girki na yi ke dai abin da nake so da ke ki tashi ki je ki wanka ki zo ki ci abincinki ga shi can a cikin kicin". Daɗin zantukanta da yadda suka faranta mini ruhina ya sanya ni sakar mata da murmushi ina zuwa na rumgume ta ina ta jeranta mata godiya wani na bin wani. Albarka ta din ga sanya mini tamkar za ta yi aron baki. Haka na fito na yi wanka na shirya sannan na ɗauko abincin na tisa kwanon gabana kafin na saka hannuna wayata ta soma ruri, na ɗauko wayar ƙiran Saif ya shigo cikin wayar ban ɗaga ba har sai da ya katse ya ƙara ƙira a karo na biyu kafin na ɗaga, cikin sanyin murya na yi sallama ya amsa mini cike da kulawa. "Har kin tashi ke nan?". "E". "To ina miki fata da addu'ar Allah ya sanya wannan ranar ta zama rana mafi daraja da alkhairi a gare ki". Cike da jin daɗin addu'ar tasan na amsa da faɗin"amin ya Allah tare da kai gabaɗaya". "Jiya kin yi min wani furuci wanda nake son ki tabbatar min da shi a yanzu ido yana ganin ido, don na sai na gama sakankancewa akan hakan ashe kuma gigin bacci ne yake ɗeban ki san da kika yi zancen". "Wani zance ke nan?". "Alƙawarin amincewa da aure na da kika yi mana". Sai da na ja dogon numfashi na fesar da shi daga bakina kafin na sama zarafin cewa"a cikin hayyacina na yi wannan zancen kuma ba a iya fatan bakina ya sanya ya ratsa har cikin zuciyata". Ina iya jiyo sautin ajiyan zuciyan da ya sauƙe kana ya ce"ni kuma in sha Allah zan yi iya ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai". Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe kafin can ya kuma cewa"to bari na bar ki ki huta, in sha Allah a yau ba sai gobe ba zan yi duk yadda zan yi na ga sautin muryan nan ya shiga hannun Sultan. Na san duk yadda zan yi memory card ɗin nan ya je hare sa duk da yanzu ba ma tare da shi a gari guda". "Fatan nasara". Na furta masa a taƙaice da hakan muka yi sallama da shi na ajiye wayar tare da jingina bayana jikin bango na ɗan lumshe idanuna ina sauraron yadda zuciyata take buga wa a hankali hankali. Yayin da wasu tunani kala daban-daban suke ziyartar cikin kwanyata tabbas izuwa yanzu na ji zuciyata ta nutsu da Saif ban san ko hakan ake ƙira da soyayya ba don ban taɓa tsintar kaina cikin irin makamancin wannan yanayin ba. Haka na gama cin abincin cikin rashin daɗin yanayi na fito na wanke kwanun, na leƙa ɗakin su Yaya Alhassan na ga ba ya nan Umar ne kawai a ciki yana karantu wani littafin turanci. Ya ɗago kai ya na kallona kafin ya ce"ke kuma me ye kin wani tsare ni da idanuna kamar za ki cinye ni? Mai sunan tsofaffi kawai". Murmusawa na yi kafin na furta"za ka ji da shi dai, ai sai an kula kare sannan yake haushi". Dariya ya ƙyalƙyale da shi tare da faɗin"yanzu ni ne karen ke nan? Ai wallahi in da ni kare ne da tunin na daɗe da cinye namanki har na taune ƙasussuwanki yarinya". Dariya na aka mai sauti ina jijjiga kaina na juya na fice daga cikin ɗakin na koma ɗakina, karatun Alkur'ani na ɗan yi kafin na fito na haɗa girkin rana. Haka na wuni cikin tsammanin ganin ƙiran Saif ya sanar da ni yadda ake ciki amma shuru tamkar an shuka dusa har na kwanta ƙiransa bai shigo cikin wayata. Ni kuma ina kunyar ƙiransa haka na daure safiya ta yi ko ƙaran shigowar saƙon kamfanin layin MTN na ji ya shigo cikin wayata sai na yi zumbur na tashi na duba ko zan ci karo da saƙon Saif amma wayam, haka na ƙarar da wunin wannan ranar komai cikin sanyin jiki nake aiwatar da shi tamkar majinyaciya. Har dare ta yi bai ƙira ni ba muna tsaka da cin abinci na ji wayata ta yi ruri na kusa bazama da sauti na je na ɗauko ta da yake ajiye a saman firijin da yake cikin falon Ina duba wa na ga baƙuwar lamba ce take na ji raina ya ɓaci don ba wannan nake tsammani ba, ban yi ƙasa a gwiwa ba na katse ƙiran tare da ajiye wayar na dawo na zauna ina zama wani ƙiran ya ƙara shigowa a karo na biyu na yi biris da shi tamkar ban ji ba. "Wai ba wayanki ake ƙira ba ne Amatullah?". Yaya Alhassan ya jefa mini tambaya cikin kakkauran murya. "Baƙuwar lamba ce ban san wanda yake ƙira ba". "Ɗauko min wayar na gani". Ya furta cikin ba da umarni, hakan ya tilasta mini tashi na je na ɗauko wayar na miƙa masa daidai sa'ilin da wani ƙiran yake ƙara shigowa a karo na barkatai. Ya ɗaga tare da sanya ta a amsa-kuwwa aka yi sallama ya amsa. "Mansur ne mijin Amira". Aka furta daga ɗayan ɓangaren sai a lokacin da na ji muryarsa na tuna cewar lokacin da na je gidansu ta amshi lambana a fefa da nufin idan Mansur ya dawo za ta ƙira ni da wayarsa. Miƙo mini wayar da Yaya Alhassan ya yi bayan sun gama gaisa wa da Mansur shi ya dawo da ni cikin hayyacina daga karatun wasiƙan jakin da na faɗa. Na amsa wayar muka gaisa da shi kafin ya miƙa wa Amira ita muka gaisa. "Ya na ji muryarki haka ba ki da lafiya ne ko kuma dai akwai wani abun da yake damunki?". Sai da na saci kallon Anty Sawwama kafin na mai da wa Amira amsar tambayar da ta yi mini. "Lafiya ƙalau me kika ji da ya sa ki faɗin haka?". "Haba! Amatullah ki na nufin ban san halinki ba ne ko kuma mene ne?". Da hanzari na taka mata burki ganin ta na ƙoƙarin wuce mini zani a cikin tsakiyar kasuwa. "Mu na cin abincin bari inna gama zan ƙara ƙira". Ina gama maganan na katse ƙiran tare da ajiye wayan, na ci gaba da cin abincin sai dai duk a tsarge nake. Har muka gama cin abincin ban ɗago kaina ba muna gama wa na tattare kwanukan na je na wanke su kaina a ƙasa na zo na wuce zuwa ɗaki sai da na yi shirin kwanciya sannan na danna wa Amira ƙira, bugun farko ta ɗaga. "Wai Amatullah ki na lafiya ƙalau kuwa? Na ji a jikina akwai matsala ga shi kwanakin sai mafarkinki nake yi da zaran na kwanta bacci wannan ya ƙara tabbatar min da cewar akwai wani damuwa. Don Allah mene ne yake faruwa?". Maimakon na ba ta amsa sai kawai na fashe da kukan da ya yi matuƙar gigita mata tunaninta ta din ga jeranta mini tambayo ɗaya bayan ɗaya. "Subhanallahi! Hashashen zuciyata ya tabbata ke nan wai me yake faruwa ne sanar da ni idan akwai wani matsalan?". "Amira ina cikin matsala shi kenan na jefa kaina da wanda bai ji ba bai gani ba cikin matsalar da ni na yi silar ruruwanta". "Wani irin matsala ke nan?". Take na kwashe komai na yadda muka yi da Saif har da alƙawarin da na yi masa da kuma yadda ya daina ƙira na na tsawon kwanaki biyu, sannan na ƙara da faɗin"jikina ya na ba ni tabbas akwai wani matsalan tun da har na ji shi shuru na tsawon wannan lokacin, sai dai ban san abin da yake faruwa. Idan ma matsalar ce ba na fatan ta shafi kowa mussamman Saifullah da shi ne mutum na farko da ya fara ba n goyon baya kuma ya tsaya mini tsayin daka wajen ganin na cika wannan burin da ya daɗe a cikin rai. Daman sai da Yaya Alhassan ya gargaɗe ni amma na ƙi amfani da abin da ya faɗa mini har umartana ya yi akan na karya memory ɗin amma na yi kunnen uwar shegu". "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Amatullah me yasa za ki aikata haka? Me yasa ke ba kya jin magana ne sannan ki na da kafiya akan abu. Na yi tunanin kin daɗe da mance wa da babin wannan mutumin a cikin rayuwarki ashe har yanzu ki na nan akan bakanki. Me yasa kike ƙoƙarin butulcewa rahamar da Ubangiji ya yi miki? Kike ta ƙoƙarin ganin kin bankaɗo sirrinki da Ubangiji ya lulluɓe ta a idon duniya?. Allah ya rufa miki asiri ya ceto ki daga rayuwar halakan da kika faɗa ya karkarto da hankalinki zuwa gida ki ka dawo rayuwa cikin ƴan uwanki, su ka rufa miki asiri suka yi miki gata suka ɗauke dukkan ɗawainiyyarki ta hanyar killace ki a cikin gida suna wadata ki da dukkanin abin buƙatun rayuwa. Daga ƙarshe Allah ya ɗaga kimarki ta hanyar yi miki tagomashi da samun mijin da yake shirye ya aure ki, duk wannan tarin ni'iman da Ubangiji ya lulluɓe ki da ita amma kike ƙoƙarin butulcewa". Izuwa yanzu kuka nake yi sosai wiwi don jikina ya gama mutuwa murus na kuma tabbatar wa cewar matsala ce ta hana Saifullah ƙira na ya sanar da ni halin da ake ciki. Sai da ta sallawantar da wasu mintuna kafin ta furta"yanzu dai ki yi haƙuri ki kwantar da hankali, ki yi addu'a Allah ya sa komai lafiya kuma shi ma yana cikin ƙoshin lafiya. Idan kin ga abun ya ci tura to ina mai ba ki shawara da ke ki ɗaga waya ki ƙira shi ki ji halin da ake ciki domin hakan ba laifi ba ne, masu iya magana su na cewa gaida mai gaishe ka ko da kuwa ba zai amsa ba". Sai da na zurfar da zafafan iska daga bakina kafin na ce da ita"na ƙira shi kuma?". Ta katse ni"to hakan laifi ne ko kuma haramun ne aikata hakan? Kin ga wannan jan ajin babu inda zai kai ki sai dai ya sauƙe ki a tashar nadama. Ki ɗauki waya ki ƙira shi ki ji halin da ake ciki alama ce ta nuna kin damu dashi, ko ke da nan ki na tunanin shi da yake ɗaga waya kullu yaumin ya ƙira ki shi bai san ciwon kansa da darajan kansa ba ne?". Luƙus jikina ya yi sanyi ƙalau har na kasa motsa wa daga inda nake zaune. "In sha Allah inna ga shurun ya yi yawa zan ƙira shi". Ban ƙari sa zancen ba ta katse mini hanzari"kamar ya ya? Ai yanzu ya kamata ki ƙira shi son samu m, mu na gama wayar nan ki ƙira shi". "Ki na ganin hakan ne mafita?". A kufule ta ce"ban sa ni ba, tun da ke nan zama kika yi kika miƙe ƙafa ki na jiran ƙiransa, to sai ki yi ta jira daga nan har zuwa ranar da mahadi zai bayyana". Ta gama furzar da zancen kit ta katse ƙiran ta bar ni da sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tamkar wacce ta yi wani gagarumin aikin ƙarfi. Rumgume wayar na yi a ƙirjina tare da lumshe idanuna da ruwan hawaye yake zuba daga cikinsu ina yin zantukan na Amira suna yi mini amsa-kuwwa a cikin na'urar naɗan sautina tamkar a lokacin take furta mini su daki-daki. Wani sashin zuciyata ta gaskata abun da Amira ta ce da ni, don haka na ɗauki wayar na lalumo lambarsa na dannan masa ƙira sai dai ƙiran ba ya tafiya, a jere a jere sai da na yi masa ƙira uku amma duk ba ya tafiya. Dole ƙanwar na ƙi na haƙura na ajiye wayar na kwanta ina ta fama da tunani kala daban-daban bacci sai da ya cika cikakken ɓarawo kafin ya iya ɗauka na sai da na makara tashi sallan asubahi, ko da na iddar da sallan sai da na ƙara gwada layin Saif amma har yanzu ba ya tafi, ganin tunanin yana neman ya yi rikita mini kwanyata ya sanya ni ɗauko alƙur'ani na buɗe na soma karanta ban gushe ina yi ba har sai da na ji zuciyata ta sama nutsuwa wani sanyi ya ziyarci sashin ruhina. Ko da na gama karatun zama na yi a wajen na zabga wani uban tagumi. Ban san lokacin da Yaya Alhassan ya shigo cikin ɗakin ba har sai da saurin muryarsa ta ratsa dodon kunnuwana. "Tunanin me ye kike yi haka?". Na yi figigi na dawo cikin hayyacina"na'am ka ce me ye?". Ya kafe ni da ido kafin ya furta"tunanin me ye kike yi?". Na sadda kaina ƙasa"babu komai". "Koma dai mene ne tabbas kawai abin da yake damun ki, ki yi ƙoƙarin yaƙar duk damuwar da yake damunki a cikin ranki". "In sha Allah Yaya na gode sosai". Naira duhu uku ya zaro daga cikin aljihunsa ya ajiye mini a gabana tare da faɗin"ga wannan ki rage wani buƙatunki da shi, babu yawa ki yi maneji da shi". Wani daɗi na ji ya cika mini rai da ruhina har sai da ya haddasa mini tsiyayar da ƙwalla zan yi magana ya dakatar da ni ta hanyar ɗaga nuni hannu alamar ba ya son jin komai daga gare ni. "Ki yi abin da na ce miki kawai". Na buɗe baki zan yi godiya ya kuma katse ni"ba na son wannan godiyan nakin da ba shi da iyaka. Duk abin da na yi miki ki sa a ranki cewar haka daman wani nauyi ne da ya rataya a kaina na sauƙe shi". Kaina kawai na jinjina masa kafin na furta"Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi da azurki mai amfani". "Amin" ya Allah ya amsa da shi yayin da yake tashi ya miƙe tsaye haɗe da ƙara faɗin"babu wata matsalar ina fatan dai ko?". "E babu komai Yaya Alhassan, tabbas a zamana da ku kun wadata ni da komai babu abin da na nema na rasa". Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce mini komai ba ya juya ya fita daga cikin ɗakin na raka shi da kallo har ya fice kafin na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya mai nauyin gaske. Na daɗe zaune a wajen kafin na tashi na je na nuna wa Anty Sawwama kuɗin ta yi ta sanya mana albarka tare da yi mana addu'ar Allah ya haɗa kawunanmu kana na fito na soma rage wasu ayyukan cikin gidan. Haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa lokaci yana shuɗawa har aka dosa kwanaki biyar ba tare da Saifullah ya ƙira ni ba hakan nan du ƙiran duniyar nan da zan yi masa layinsa ba ya shiga, duk na bi na damu hankalina ya yi mummunan tashi da na zauna shuru to ba ni da aiki sai tunaninsa da tunanin halin da na jefa sa ba na sanin lokacin da hawaye yake zuba daga idona sai dai kawai na ji ɗumin su a bisa kuncina. Duk wanda ya ganni ya san inda cikin matsanancin damuwa da ƙololuwan tashin hankali amma haka na yi ta ɓoye wa duk tambayar da za a yi miki cewa nake yi ba komai idan aka matsa mini ba sai na fashe da kuka ala dole suke haƙura su bar ni ba don sun sama abin da suke so ba. Ranar da aka cika sati da faruwan lamarin a wata safiyar ranar lahadi ƙiran Saif ya shigo cikin wayata kafin na ɗauka ƙiran ya tsinke ina ƙoƙarin bin ƙiran ya ƙara ƙira a karo na biyu. Jikina yana rawa na ɗaga ƙiran na soma amayar da tulin damuwar da yake kwance ƙasan raina. "Lafiya kuwa kwana da yawa inna ƙira layinka ba ya shiga, sannan ba na ji daga gare ka ina fatan dai lafiya babu wani matsalar ko?". Sai da ya numfasa kafin na ce da ni"ki na gida ne?". "E". Na amsa da shi har zuwa lokacin jikina yana rawa tamkar mazari. "Nan da awa ɗaya mu na zuwa, ki sanar da mutanen gidan". "Ku na zuwa kai da waye ke nan? Sannan lafiya zuwa haka bakatatan ba tsammani?". Na yi zancen jikina yana tsananta rawan da har sai da ya tilasta mini yin zaman ƴan bori dirshan a ƙasa ina sauraron amsar da ya dawo mini da ita muryarsa cike da rashin walwala. "Idan mun zo za ki ga wanda za mu tare da shi, sannan za ki ji dalilin zuwan mu". Daga haka ya katse ƙiran ya bar ni da faman faɗin"hello! Hello". Har sai na fahimci ba ya kan layin kana na saduda. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta ina dafe ƙirjina da yake buga wa fiye da kima a kimiyyance. Jikina a sanyaye na je ɗakin Anty Sawwama na sanar da ita zuwan su Saifullah, ita kan ta sai da ta tambaye ni ko lafiya na ce da ita ni ma ban sani ba. Haka na gudanar da aikin da ya kallafa a kaina cikin sanyin jiki da rashin kuzari. Ina zaune a ɗaki na ji sallamarsu a tsakar gida na leƙo ta taga na ga tare suke da Yaya Alhassan da kuma Umar da suka yi musu jagoranci har zuwa cikin gidan suka shigo falo suka zauna, Anty Sawwama ta fito suka gaisa kana Umar ya zo ya ƙira ni na fito na gaishe su, ganinsa tare da Muhammad Taufik ya sanya jikin ƙara sanya tamkar kazar da aka gauraya a cikin ruwan gishiri, na je musu ruwan sha na ajiye a gabansu zan koma ciki Yaya Alhassan ya ce na dawo na zauna haka na yi na koma na zauna kaina a ƙasa ina sauraron yadda ƙirjina yake bugu tamkar zai faso allon ƙirjin ya fito waje ya taka rawan disko. "To kamar yadda na riga na sanar da kai tun a waje wannan shi ne dalilin zuwanmu, don na ga ya dace ku san abin da yake faruwa. Sannan aminina Sultan ya buƙaci ya zo don ya gabatar da godiyansa a gare ku a madadin dukkan ahalinsu". Saifullah ya yi zancen a dunƙule da ya sanya kan Anty Sawwama kullewa, take Saif ya warware musu duk yadda muka yi da shi akan wannan memory card ɗin akan kowa. Anty Sawwama ta cika da mamaki don a ta yi zaton hakan ba, Yaya Alhassan ma duk da Saif ya riga da ya sanar da shi zancen tun kafin su shigo ciki sai da ya cika da mamaki ainun. A wannan karon Muhammad Taufik ne ya karɓe zancen cikin faɗin"tabbas sa'ilin da na saurari wannan sautin muryar ba zan iya fasalta tashin hankalin da na shiga ba, duk dauriya da juriya irin zuciyar na miji sai da na ji hawaye sun zubo daga idanuna na kasa fassara kaina da har sai da hankali na gushe daga gare ni. Saifullah shi ya kasance a tare da ni a cikin wannan yanayin mai tsauri ba zan taɓa mance wa da shi a cikin tarihin rayuwata, cikin hikima da fasaha muka tunkari Sheik da zancen kuma cikin ruwan sanyi ya amsa cewar duk abin da muka ji haka ne, kuma tun daga ranar da lamarin ya faru shi kansa ya yi nadama mai tsananin gaske, tun daga lokacin ya kasance cikin zulumi, fargaba da kuma jiran fitan sautin muryar a duniya sai dai kuma shuru lamarin da ya karya masa zuciya ke nan. Tsoronsa ɗaya kar asirinsa ya tuno a idon duniya kar kima da darajarsa ta gushe a idanun jama'an da suke yi masa kallon tamkar waliyi a gare su, haƙiƙa manyan mutanen da ya sani da tarin ƴan siyasan da yake mu'amala da su za su yi ɓatan dabo, don babu wanda zai so ya lalata tafiyar siyasansa sa boda ƙoƙarin kare masa martaban sunansa. Tabbas ya aikata laifin da ya yi ikirari sai dai yanzu ya yi nadama matuƙa don na hangi hakan a cikin idanunsa, Malam ya yi nadama matuƙa don har sai da ya yi ƙwalla kuma ya nema gafara a bisa samar da ni ta hanyar da ba ta dace ba, ya tara dukan iyayensa ya sanar da su abin da yake faru ya kuma roƙi yafiya da gafaransu. Tabbas ba mu san inda za mu sanya kanmu ba idan maganan nan ya watso a duniya, ba mu san wani hali Malam zai shiga ciki ba, na zo ne musamman na yi miki godiya a bisa madadin dukkan ahalin Sheikh Dawood akan killace wannan sirrin da kika yi kika kuma ɗamka sa a hannun da ya dace har ya iso gare shi a cikin sigar da ya dace". Tun da ya soma maganar nake kuka marar sauti har ina ƙoƙarin shiɗewa, sai da Anty Sawwama ta riƙo hannuna tana murzawa a hankali cikin sigar lallashi da kwantar mini da hankali. Muryarta a shaƙe sa boda kukan da ya gama galabaitar da ni na soma magana a hankali, sautina ba ya fita yadda ya kamata. "Yaya Alhassan ka yi haƙuri na kasa bin umarninka, na kasa yi maka biyayya wallahi zuciyata ce take azalzala ta yayin da ni kuma na gaza jure wa har sai da na biye mata. Ban aikata hakan don na nuna maka ba ka isa da ni ba, ban aikata hakan don nuna maka cewa ba ka kai ka kafa mini umarni na bi ba. Yaya Alhassan na tuba na you nadama na gurfana a gabanka ina neman afuwa da yafiyarka". Falon ya yi tsif babu abin da ake ki face sautin kukana. Cikin taushin murya Yaya Alhassan ya soma cewa"Amatullah ba ki yi min komai hasalima kin yi tunanin da ni kaina ban yi shi, wallahi na ji daɗin abin da kika yi na kuma cika da alfaharin kasancewarki ƴan uwa a gare ni. Kin yi wani babban lamarina da ya dace a yaba miki kuma a jinjina miki". "Ƙwarai don tabbas kin zamo silar wanzar da haske a cikin rayuwata kin haska min hanyar da zan yi tafiya ba tare da ɗan jagora ba. Ba zan da wani baki zan yi miki godiya Amatullah". Muhammad Taukif ya yi zancen cikin sanyin murya harrufan har suna harɗe wa waje guda. "Ba na buƙatar godiya don na yi hakan ne domin Allah ba don a gode mini ba". Na yi zancen cikin ƙarfin tare da tashi na koma cikin ɗaki ina shiga na zubo akan katifa ina ci gaba da kukan, na daɗe ina kukan har sai da na ji numfashina ya toshe. Lokacin Anty Sawwama ta shigo cikin ɗakin ta din ga lallashina da ba ni baƙi. "Tashi ki je falo ki same su don ke suke jira". Ta yi zancen ta na goge mini hawayen da suka ɓata mini fuskana, kaina kawai na gyaɗa mata na tashi na fito kamar yadda ta umarce ni. Kaina a ƙasa na fito falon bakina ɗauke da siririn sallama na ƙariso na zauna a ƙasa, shuru-shuru cikin mu babu wanda ya yi magana kafin can Muhammad Taufik ya yi kawar da shurun. "Ni dai kam ba zan iya daina yi miki godiya ba, kuma ina so na ƙara tabbatar miki da cewar abokina yana yi miki ingantacciyar soyayya ina ji a jikina shi ne mijin da ya dace da ke, don haka ina fata da addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku". Ban iya amsa wa da baki ba sai a cikin zuciyata na amsa. Har ya tashi ya fita daga cikin falon yana tsokalan Saifullah ban ɗago kaina ba. "Amatullah". Na tsinkayo muryar Saifullah a kunnuwana, ban amsa ba illa ɗaga kai da na yi ina kallon sa ido cikin ido a karon farko a cikin rayuwata. Kamar an buɗe fanfo na ji hawaye suna zuba daga idanuna. Da ƙyar na buɗe bakina na yi magana"ina ta jir ƙiranka shuru idan na ƙira kuma ba ya tafiya, ka san girman tashin hankalin da na shiga kuwa?". "Ban sani ba sai dai yanzu ki sanar da ni". Babu shiri na watsa masa harara da wutsiyar idona ina goge hawayen idona. "Afuwan ranki ya daɗe na san na aikata gagarumin laifi. Tashin hankalin ganin Sultan cikin halin da ya shiga shi ya hana ni kunna wayata, Sultan ya shiga tashin hankalin da ko maƙiyinsa ne sai ya tausaya masa har ma ya zubar masa da hawaye, don har kwanciya ya yi a gadon asibiti ya shafe kwanaki uku ba tare da ya san inda kansa yake ba. Wannan tashin hankalin shi ya hana ni samun lokacin wayata balle har na ƙira ki, amma yanzu na kawo kaina a yi min ko wani irin hukuncin da ya dace da ni". Ban iya cewa da shi komai ba illa kukan da na ci gaba da yi, ban yi aune ba na gan shi zaune a gabana dan da ni ina ɗago kai muka haɗa ido da shi. "Don Allah ki daina wannan kukan idan ba so kike yi ni ma na fara hawayen ba". Yadda ya furta zancen ya sanya jikina gabaɗaya sanyaya tabbas yadda na ga idanunsa sun kaɗa sun yi jajir ga jijiyoyin kansa sun fito sun yi ɓaro-ɓaro a saman goshinsa hawayen ma idan ya yi ba zan yi mamakina. Ba don na daina jin zafin da nake ji a cikin ƙirjina ba na kai hannu na goge hawaye fuskana, ya furzo mini iska daga bakinsa a fuskana da har sai da na lumshe idanuna. "Yauwa ko ke fa, to yanzu an yafe min ne ko kuma?". "Ai daman babu abin da ka yi". "Ni dai ki ce kin yafe min sai na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa". "To shi kenan na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaga". "Amin ya Allah". Daga haka na yi shuru har sai zuwa lokacin da ya ce"to yanzu kuma me ye ya rage?". Na ɗage masa ido ɗaya alamar rashin fahimta da hakan ya sanya sa faɗin"ko sai na tuna miki alƙawarin da kika yi kafin ku fuskanci idan maganan tawa ta dosa?". Numfashi mai nauyi na sauƙe kafin na sama zarafin cewa"na ba ka dama Saifullah ka turo iyayenka gidanmu, don su nema maka aurena". A kunyace na ƙare zancen ina rufe fuskana da tafukan hannayena. "Alhamdulillah". Ya furta yana yin sujudul shukur ga Ubangiji, ya ɗago ya ɗaga hannayensa sama yana addu'a cikin tsananin farin ciki. "Allah na gode maka bisa wannan damar da ka ba ni. Ina roƙonka ka ba ni ikon killace soyayyarta a cikin zuciyata ba tare da na haɗa ta da wata ɗiya mace ba, Allah ka ba ni ikon riƙe ta bisa amana na kuma inganta rayuwarta ta hanyar da ta dace. Ka hana ni yi mata kishiya har abada". Ganin na yi shuru ban amsa ko ɗaya daga cikin addu'o'insan ba ya sanya faɗin"ba ki amsa ba ke nan?". "Na amsa a cikin zuciyata". "To ki amsa da bakinki na ji". Na taɓe fuska ina faɗin"na amsa a cikin zuciyata fa". "Na amsa a cikin zuciyata fa". Ya yi zancen cikin kwaikwayon muryata da salon yadda na yi zancen, sunkuyar da kaina ƙasa na yi sa boda kunyar da ya lulluɓe ni. "Wai kunya kike ji? Uhmm! To yanzu idan kin shiga ciki ki sanar da su cewar iyayena za su zo jibi in sha Allah". Babu shiri na ɗago kaina"da sauri haka?"? Ya ɗage mini giransa ɗaya"to me ye za a jira". Ya ƙare zancen yana sunkuyo da kansa daidai saitin fuskana. Babu shiri na tashi na yi ciki da sauri sa boda kunyan da ya gama ba ni. Ɗakina na nufa na zauna na tsawon awanni ji nake yi saƙayau duk wani damuwana ya hau, zuciyata ta yi fes yayin da raina ya yi tas, haka na wuni cikin karshashi da ƙwarin gwiwan da ya zagaye jikina da yamma muka yi waya da Amira na sanar da ita komai ta taya ni murna matuƙa, ita ta hanyar ni shawaran na ƙira Anty Zulaihatu na sanar da ita zancen zuwan iyayen Saifullah jibi na yi na'am da shawaranta. Mu na gama waya da ita na ƙira Anty Zulaihatu na irge masa komai, Baiwar Allah har da kaddara kafin ta shiga rero mini ruwan addu'a ta kuma shaida mini a ranar za ta ƙira Anty Sawwama da Yaya Alhassan ta shaida musu zancen. Daren ranar mun fi awannin biyar muna waya da Saifullah yayin da na ji ya ƙara shiga cikin raina sosai, ya ba ni Hajiya Muhibbat muka gaisa a waya har da kukanmu ni da ita. Washe gari tun da asuba Anty Sawwama ta ƙira don ta ji daga gare ni akan abin da Anty Zulaihatu ta ƙira ta sanar mata, na kuwa tabbatar mata da zancen ta yi hamdala tare da yi mana addu'a. Take aka soma shiri da shirye-shiryen tarban iyayen Saifullah gobe ranar Anty Zulaihatu a gidan ta kwana, washe gari da yamma lilis magabatan Saifullah suka zo su gidan Anty Sawwama neman aurena a hannun Yaya Alhassan aka kuma ba su tare da sanya auren nan da sati huɗu masu zuwa. Ranar wuni na yi da zazzaɓi da boda fargaba da zulumi da dare muka sha kukanmu tare da Anty Sawwama da Anty Zulaihatu sa boda tuno Abba da muka yi da hashashen irin farin cikin da zai yi don ganin wannan ranan in da yana raye. Bayan kwana biyu Amir ya ɓullo da wani zancen wai na je na yi gwajin genotype, Anty Sawwama ta yi kai da fata ta ce ba zan je ba, har da faka hujja da cewar su a lokacinsu duk ba a yin wannan gwaji ga shi kuma har suka gama haihuwarsu lafiya sumul, daga su har ƴaƴan. Sai da ta ga shi ma kansa Saifullah ɗin ya goya bayan a je a yi gwajin sa boda gujewa afkuwar matsala, sannan ta saduda ta zubar da makaman yaƙinta. Muka cire ranar da za mu je mu yi gwajin lokacin ana sauran sati uku bikin, duk da tun kafin lokacin shi Saifullah ya shaida mini cewar na shi AS ne don ya daɗe da sanin hakan. Rananr gwajin tare muka je da Anty Zulaihatu da kuma Umar muka je aka yi mana gwaji ni da shi, aka je mu ɗan jira kafin sakamakon ya fito haka muka jira aka fito sakamakon Saifullah da Umar suka shiga amsowa. Babu jima wa suka fito ba su ce da mu komai ba muka shiga mota muka tafi, maimakon mu koma gida sai muka ƙara wuce wa wani asibitin, Anty Zulaihatu ta gaza jurewa har sai da ta tambaya ko lafiya suka ce da ita lafiya kawai su na so tabbatar da wani abu ne. Wani gwajin aka ƙara yi mana, kamar karon farko Saifullah da Umar ne suka shiga suka also sakamakon. A wannan lokacin yanayin da suka shiga ya yi muni sosai haka muka shiga mota zuwa gida ya faka a ƙofar gidan, ya ce mu shiga ciki ga shi nan shiga wa, haka muka sauƙa ni da Anty Zulaihatu muka shiga cikin gidan, kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa. [12/27, 5:50 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 8️⃣1️⃣ Tun da muka shiga cikin gidan na kasa zaune balle tsaye ɗaki na shiga na yi ta safa da marwa, yayin da tunani kala-kala suke ziyartar ƙaramar curin kwanyata. Cikin wannan halin Anty Zulaihatu ta shigo ta ƙira ni ta ce na zo falo ana nema na, haka na biyo ta a baya har suka iso cikin falon inda muka iske Umar da Anty Sawwama zaune a cikin falo. Muka ƙariso ciki muka zauna. "Da kuke asibitin ya ya aka yi? Na ga kamar gabaɗayanku hankalinku ba a kwance yake ba. Ko dai wata cutar aka ce ɗaya daga cikinku yana ɗauke da ita?". Anty Sawwama ta yi tambayar tana kafe Saifullah da ido da ya kasa cewa uffan illa sadda kansa ƙasa da ta yi. Anty Zulaihatu ne ta yi magana a madadinsa"wallahi Umma mu ma ba mu san abin da yake faruwa ba, sun dai ce mu shigo ciki ne kawai ba tare da sun sanar da mu komai ba". Takardan sakamakon gwajin Saifullah ya miƙa wa Anty Zulaihatu ta amsa yayin da yake koro jawabansa. "Mun je asibitin farko aka yi gwaji inda sakamakon ya nuna cewa ni da ita Amatullah gabaɗayanmu AS ne, daman ni na san nawa na zo ne don a ƙara tabbatar wa, ban yarda da sakamakon don a wasu lokutan ana samun matsala dangane da kayan aikin gwaji ko kuma daga su kansu ma'aikatan hakan ya sa muka ƙara zuwa wani asibitin aka ƙara gudanar da wani binciken, nan ma ba a sama canji daga wancan gwajin na farkon ba. Tabbas ta tabbata ni da Amatullahi dukkan mu AS ne". "Me ye hakan ke nan ya ke nufi ɗan nan? Shi AS ɗin mene ne aibunsa? Ni fa shi yasa tun farko ban yarda aje a yi wannan gwajin ba sa boda gudun wanzuwar matsalolin da wannan nan mutanen masu jajayen kunnuwan nan suka kawo". "Umma hakan ya nufin aure a tsakaninsu ba zai taɓa yiyuwa ba, sa boda ko da an yi auren matsaloli da tashin hankalin da za su biyo bayan auren sai ya tushe duk ginin soyayyar da aka yi ta wargaza komai". Anty Zulaihatu ta yi zancen tana juya farar takardar sakamakon gwajin da yake riƙe a hannunta. "To sai me ye don dukkan su AS ne? Mu da can a lokacin mu ana wannan gwajin ne amma ba ga shi mun yi auren mun haihu lafiya sumul ba. In sha Allah babu abin da zai hana auren Saifullah da Amatullah". Anty Sawwama ta yi zancen tana tashi ta yi shigewarta cikin ɗakinta, da kallo dukkaninmu muka bi ta kafin Anty Zulaihatu ta saka salati cikin tsananin damuwa da rashin mafita da kuma madafa. "Anty yanzu ya ya za a yi a fahimtar da ita illan da yake tattare da hakan?". Saifullah ya yi zancen muryarsa har rawa take yi yayin da yake tsayar da idanunsa akan Anty Zulaihatu. "Wallahi ban san yadda zan yi wa Umma bayani ta fahimta illan wannan abun ba. Amma bari na ƙira Yaya Alhassan na sanar da shi halin da ake ciki". "A'a kar ki ƙira shi alhalin yana can wajen aikinsa, idan ya dawo kawai ki yi masa bayani ni ma in sha Allah zan ƙira shi mu yi magana a waya". "To shi kenan duk yadda ka ce haka za a yi". Sai a lokacin Umar ya buɗe baki ya yi magana damuwa jingim a tattare da furucinsa"ni na ma rasa abin da zan ce, gabaɗaya lissafina ya katse". Dafo kafaɗarsa Saifullah ya yi cikin salon ƙarfafa masa gwiwa ya soma faɗin"haka Allah ya ƙaddara Umar, sannan ko wani Bawa ba ya wuce ƙaddararsa a rayuwa. Wataƙila Allah bai ƙaddara akwai aure tsakanina da Amatullah ba. Mu ƴan Adam ne kawai muke lissafinmu amma tun kafin wanzuwan mu a bayan ƙasa ya rubuta abin da zai kasance da Bawa, mussamman a sha'anin aure ka san an ce wani ba ya auran matar wani". Anty Zulaihatu kam kasa jurewa ta yi ta tashi ta bar cikin falon ta na matsar ƙwalla, daga bisani ma Umar tashi ya yi ya fita. Ban taɓa zato da tunanin cewa tashin hankali idan ya girmama ba a ma samun damar zubar da ƙwalla ba, sai da na tsinci kaina cikin wannan matsanancin halin. Duk yadda na so na zubar da hawaye na kasa yin hakan idanuna ya bushe ya soye tamkar na soyayyan kifin da aka tsamo daga cikin mai. Na yi nisa cikin tunanin da na dulmiya a cikinsa na tsinkayo muryarsa dab da ni da hakan ya ba ni tabbacin cewar ya sauya wajen zama ya dawo kusa da inda nake zaune. "Amatullah kin ga yadda Allah ya yi da mu ko? Aure tsakanina da ke ba zai yiyuwa. Ƙaddara ta shata mana layi a tsakaninmu ta yi mana katanga daga cika burinmu na mallakan juna a matsayin ma'aurata. Sai dai daman kullum a cikin roƙon Allah muke yi ya yi mana zaɓi mafi zama alkhairi a gare mu, tun da hakan ya wanzu a tsakaninmu sai mu ɗauka cewar hakan ne alkhairi a gare mu bakiɗaya da mu da iyayenmu har ma da al'umma". Ya ɗan tsagaita kafin ya ci gaba daga inda ya tsaya"Allah ne shaida cewan na so ki tsananin son da ban taɓa zato ko tunanin zan iya yi wa wata ɗiya mace ba, na yi burin aurenki na yi ɗamarar kasacewa da ke har ƙarshen rayuwa amma Allah bai nufa faruwan hakan ba, ina yi miki fata da addu'ar samun miji na gari wanda ya fi ni komai da komai wanda zai kula da ke ya riƙe ki amana kuma bisa adalci. Idan ki ka sama wanda zai zo ki ya ƙaunace ki domin Allah tabbas zan kasance cikin kwanciyar hankali a duk inda nake, wataƙila wannan shi ne zuwa na a ƙarshe cikin gidan nan da zummar zuwa wajen ki mu yi hirar saurayi da budurwa, sai dai na zo a matsayin wanda ya zo ziyara da kuma sada zumunci". Sai a lokacin hawaye suka zubo daga idanuna sa'ilin da na ga ya miƙe na kuma tabbatar da cewa da gaske tafiyan zan yi, tafiyan da yake daidai da tarwatsewar tubalin ginin da na yi wa rayuwa. "Shi kenan tafiya za ka yi? Shi ke nan komai ya zo ƙarshe a tsakaninmu? Daman haka soyayyar take? Da na san haka ne da ban fara da na san hakan zafin rabuwan yake da ban saki jiki mun saba da kai ba Saif. Sai dai haka Allah ya ƙaddara yadda kake yi mini fatan alkhairi ni ma ina yi maka irin wannan fatan". Sai da na miƙe tsaye na zo gabansa na tsaya mu na kallon juna kana na ci gaba da maganar cikin zubar da hawayen da nake jin sauƙar su a bisa fatan fuskana kamar ana watsa mini garwashin wuta. "Tabbas na shaida cewar kai ɗin mutumin kirki kuma mutumin ƙwarai, ka sama matsayi a cikin zuciyata irin matsayin da babu wani ɗa na mijin da ya taɓa samun irinsa. Saifullah ina sonka amma ƙaddara ta tsara dole mu haƙura da juna". Kukan da ya gama cin ƙarfina ya tursass mini yin shuru ba don na rasa abin faɗa ba. "Wallahi Amatullah da akwai wani hanyar da mu iya yin aure tabbas da zai na bi wannan hanyar, amma dole mu haƙura sa boda maslahan rayuwarmu da kuma ƴaƴan da za mu haifa har ma da kwanciyar hankali iyaye da ƴan uwanmu. Kar mu bari soyayya da burin mallakan junanmu ya rufe mana idanuna har mun jefa rayuwar ƴaƴan da za mu haifa cikin garari, wallahi cutar nan cuta ce mai matuƙar wahala ga kuma ɗawainiyya. Ina sonki wannan dalilin ya sanya ba zan iya jefa rayuwarki cikin ƙuncin ba, Amatullah ba don ba na sonki zan tafi sai don maslahan rayuwarmu kuma ina fatan Anty ma ta fahimci hakan. Allah ya ba ki miji na gari wanda zai ƙauna ce ki domin Allah". Yana dasa aya a nan ya juya ya fice daga cikin falon da kallo na bi shi har ya fita kafin na durƙushe akan gwiwoyina ina wani irin azababben kuka mai ciwo. Har sai da Anty Zulaihatu ta fito ta same ni a wajen ita kuka ni kuka haka muka mayar da gidan tamkar gidan mutuwa, sai bayan sallan magrib Yaya Alhassan da Amir suka dawo Anty Zulaihatu ta shaida musu abin da yake faru, lamarin ya jijjiga su ainun don da aka sanar da su zancen Yaya Alhassan sai da ya nema wajen ya zauna sa boda jirin da yake ɗibansa. Sai da suka yi da gaske kafin suka fahimtar da Anty Sawwama illolin da yake tattare da duk wani aure da aka gina shi akan irin wanan turban, daren ranar mun sha kuka har sai da muka goge wa Allah, Anty Sawwama ta ce tun da haka ya kasance Yaya Alhassan ya ƙira gobe gobe su zo su amshi kayansu da suka kawo. Haka kuwa aka yi aka mayar musu da kayan. Ranar Amira da Mansur suka zo muka wuni muna jajantawa juna lamarin sai bayan sallan magri suka tafi, na shiga damuwa matuƙa mussamman idan na ɗaga wayata ban iske ƙiran Saif sai na ji duk duniyar ta yi mini zafi har na rasa inda zan tsoma kaina na yi salama. Haka zan zagaya na shiga banɗaki na yi kuka na gode wa Allah na wanke fuskana kana na fito. Tun bayan faruwan lamarin ba ma yin dogon magana da Saif sau ɗaya muke yin waya da shi a wuni shi ma da safe ne sai ƙira ni, mu gaisa ya ce daman ya ƙira don ya ji lafiyata shi kenan kuma sai washe gari, Hajiya Muhibbat ma ta ƙira muka jajanta lamarin sosai har da kukanmu shaɓe-shaɓe tamkar waɗanda aka yi wa wani gagarumin rasuwa. Haka aka yi sati biyu da faruwar lamarin lokacin da Allah ya nufa saura sati ɗaya a yi bikin, a daren wani ranan juma'a Anty Sawwama ta tara mu a falo gabaɗayanmu bayan sallan magrib har da mijin Anty Zulaihatu da ya zo ɗaukan ta kasancewar ranar ta wuni a gida. Amir ne ya buɗe taron da addu'a kafin Anty Sawwama ta soma amayar da dalilin da ya sa ta tara mu duka a wajen. "Na tara ku a nan ne gabaɗaya sa boda na sanar da ku hukuncin da na yanke wanda nake tunani da hashashe zai zamo alkhairi gare mu ba ki ɗaya. Amatullah amana ce a gare ni sannan zan ƙara jadadda muku ko bayan raina ku riƙe ta amana ku yi dukkan abin da zai faranta mata rai don neman rahamar Allah kasacewarta marainiya. Ko a iya rashin iyayenta aka tsaya haƙiƙa Amatu ta shiga jarabawar rayuwa balle kuma a haɗa da ragowar jarabawan da ta faɗa a cikin rayuwarta, ina so na yanke hukuncin da nake da yaƙinin cewar ba zai cutar da ɗaya daga cikin mu, ina so lokacin da aka sanya auren Amatullah kar a ɗaga shi". "Auren Amatullah kuma? Ta sama wani mijin ne?". Amir ya yi zancen cikin tsagwaron mamakin da ya bayyana har a cikin furucinsa. Anty Zulaihatu ma ta amshe zancen"Umma aure yanzu kam sai dai mu yi addu'ar Allah ya kawo mata miji na gari". "Ni ma dai haka nake gani, in sha Allah miji ɗaya dai kam Allah ba zai hana ta ba". Yaya Mu'azzam ya sanya baki cikin maganan a karo na farko, Yaya Alhassan k bai iya cewa komai illa ƙasa da ya yi da kansa har zuwa lokacin da Anty Sawwama ta ɗaura da zancen. "Ina so a cikin daren nan a ɗaura auren Alhassan da Amatullah bayan an an iddar da sallan isha'i. Alla ba shi sai ta tare a lokacin da aka sanya bikin watau sati mai zuwa". Ina da yaƙinin duk cikinmu babu wanda ya yi zaton abin da zai fito daga bakin Anty Sawwama ke nan, mussamman ni da Yaya Alhassan da muka yi mutuwar zaune tsabar yadda maganar ta daki zuƙatanmu. "Umma daman su na son junansu ne?". Amir ya yi tambayar cikin tsananin buƙatar amsar. "Amincewar su kawai nake nema, matuƙar suka amince to komai zai zo da sauƙi. Amatullah zo nan kusa da ni". Cikin rawar jiki na ja jiki na je gabanta na gurbana ta riƙo hannayena ta riƙe tare da umartana akan na ɗaga idona na kalle ta sai dai duk yadda na so ƙarfafa kaina na cira kaina lamarin ya gagare ni. "Ina so ba ki dama ki faɗi abin da yake cikin ranki don ki na da wannan ƴancin. Shin kin amince da auren Alhassan?". Take na ji zuciyar da take dashe a cikin farfajiyar ƙirjina ya harba sai da na ɗau sakanni kafin na furta"Anty ba na fatan zuwan ranar da za ki buƙata wani abu a wajena na kasa yi miki matuƙar ina da ikon yin sa. Ko wani mutum daban kika zaɓo mini a matsayin miji tabbas zan aure shi komai munin hali da ɗabi'unsa don na yi imanin ba za ki taɓa zaɓa mini abin da zai cutar da ni ba, balle kuma Yaya Alhassan da ni ma kai na shaida ce akan kyawawan halayensa. Na amince da aurensa har cikin raina matuƙar yin hakan zai faranta miki". "Na gode sosai Uwata Allah ya yi miki albarka yadda kika faranta min in sha Allah ba za ki taɓa yin ƙunci a rayuwa, Allah ya ji ƙan iyayenki ya kyautata makwancinki". "Amin". Duk muka haɗe baki waje amsa addu'ar da Anty Sawwama ta yi kafin ta juya ga Yaya Alhassan. "Alhassan ka amince da wannan zaɓin?". Sai da ya furzar iska daga bakinsa kafin ya ce"Umma ba zan iya bijire wa duk wani abun da kika zaɓa min, don na ba za ki ba ni abin da zai cutar da ni ba. Na amince zan auri Amatullah na kuma riƙe ta bisa amana, adalci da kuma tausayawa. Ni daman na ri ga da na san genotype ɗinsa tun da daɗe wa AA ne don haka ba wani matsala in sha Allah". "Alhamdulillah! Allah na gode da ka azurta ni da ƴaƴan masu ladabi da biyayya. Allah Ubangiji ya yi muku albarka ya albarkacin rayuwarku ya kare gabanku da bayanku ya ƙara haɗa kawunanku waje guda". "Amin". Muka dinga amsa wa da shi, haka Anty Sawwama ta din ga zubo mana addu'o'i kala-kala, daga bisani ma kawai fashe wa ta yi da kuka muka din ga lallashinta tare da ba ta haƙuri. Ƙiran sallan isha'i shi ya tursasawa su Yaya Alhassan fita bayan sun tsara yadda ɗaurin auren zai kasance, Yaya Mu'azzam ne waliyina a ɓangaren Yaya Alhassan kuwa wani ƙanin mahaifinsu Anty Sawwama ta riƙa ta sanar da shi komai, ya yi farin ciki matuƙa tare da balbale mu da ruwan addu'o'i. Ya kuma taso domin yi wa Yaya Alhassan waliyanci bayan ya yi alƙawarin biyan sadaki. Tun da na yi sallan isha'i na zauna nan kan sallayan na zabga wani uban tagumi, rurin da wayata take yi shi ya ja hankalina zuwa gare ta na ɗauko na kafe ta da idanuna sakamakon ganin lambar Saif ya fito cikin wayar, ban ɗauka ba har ƙiran ya katse ban ɗauko, don ban yi tsammanin ganin ƙiran sa a wannan lokacin ba, ya ƙara ƙira a karo na biyu kana na ɗauka cikin sanyin murya na yi sallama ya amsa kana na gaishe shi. "Ya na ji muryannki wani irin ko dai ba ki da lafiya ne?". "Lafiya ƙalau". Ya ɗan yi shuru kafin ya ci gaba"na ƙira ne daman mu yi wani magana idan ba kya yin wani aikin". Sai da na kawar da hawayen da suka kwaranyo mini kafin na ce"babu abin da nake yi, yi magananka ina sauraronka". "Ban san yadda zuciyarki za ta ɗauki maganar ba Amatullah, ba na so kuma ki yi tunanin ko ban yarda da ƙaddaran da ta tsara tsakaninmu ba ne. Ina so ki yi wa lamarin duba na tsanaki wallahi tsananin son ganin rayuwarki ta inganta kuma ta ci gaba ne ya sanya ni aikata wannan abun". Na katse shi"tafi kai tsaye ka yi magananka Yaya Saif". "So nake yi ki ba wa Sultan dama ya nema aurenki. Tun da lamarin ya afku nake ta tunani da zulumi ina tsoron ki faɗa hannun wanda bai dace ba, ina tsoron ki je inda za a yi miki gori akan rayuwarki ta baya, ina tsoron ki je inda ba a san mutuncinki ba balle a mutunta ki, ina tsoron ki je inda za a wulaƙanta ki ko a tozarta ki shi yasa nake ganin kamar Sultan shi ya dace da ya aure ki idan har kin amince. Sa boda shi na san dukkan halayensa na san shi ɗin mutumin kirki kuma duk wasu kyawun hali ya fi ni". Na buɗe bakina zan yi masa bayani kawai wani kuka ya kwace mini don yadda na so na hana sautinsa bayyana, sai da lamarin ya gagare ni wai ƙoƙarin cire wando ta kai. "Subhanallahi! Kuka kuma Amatullah? Me ya faru?". Ya watsa mini tambayar cikin kiɗima sai da na yi da gaske wajen daidaita fitar numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin ina yi furzo da zancen wajen"Saif yanzu haka taron ɗauri aurena ake yi a masallacin ƙofan gidanmu". "Aurenki kuma? To auren ki da waye?". "Aure na da Yaya Alhassan wataƙila ma yanzu haka har aikin gama ya gama an ɗaura". Na yi zancen wasu hawayen suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina. Ya ɗauki tsawon wasu mintuna kafin ya yi magana"alhamdulillah! Na ji daɗi da ya kasace cewar Alhassan ne ya aure ki ba wani ba, don ina da yaƙinin ba za ki tozarta ba a hannunsa. Duk inda ake neman mutumin kirki mai ƙoƙarin sauƙe haƙƙin ƴan uwantaka tabbas Alhassan ya kai, ina yi muku fatan dawwamanmen zaman lafiya da kuma samun zuri'a ɗayyaba". Ban iya amsa addu'ar ba illa furta sunansa da na yi cikin wani irin sanyin murya. "Saif". "Na'am Amatullah". "Ban san ina sonka ba sai da wannan lamarin ya faru, kai ne mutum na farko da ya taɓa nuna mini soyayya babu dangin uwa balle na uba, tabbas littafin tarihin rayuwata ba zai taɓa cika ba ba tare da an rubuta sunanka a cikin shafin farko ba. Na gode da dukkanin abubuwan da ka yi mini a cikin rayuwa, Allah ya saka maka kuma ya yi maka tagomashi da samun mace ta gari wacce za ta ƙaunace ka domin Allah". "Amin ya Allah, wannan shi ne ƙirana na ƙarshe da za ki gani ya shigo cikin wayanki. Don daga yanzu shari'a ta ja layi tsakanina da ke, in sha Allah zan zo na taya Alhassan murnar samun mace ta gari, ina yi muku fatan samu zaman lafiya. Allah ya haɗa fuskokinm da alkhairi". Ya na gama maganar kit! Ya datse ƙiran ya bar ni da ɓarin hawaye ji da na yi an dafa kafaɗana shi ya sanya ji waiga cikin sauri, idanuna suka sauƙa akan fuskan Anty Zulaihatu wanda da dukkan alamu ta daɗe a cikin ɗakin kuma ta saurari duk maganganun da ta yi. Da kallo na bi ta har ta iso gabana ta zauna tana fuskantana. "Amatullah". "Na'am". Na amsa ina sadda kaina ƙasa. "Ko dai zan yi wa Umma magana ne a dakata da yin wannan auren nan? Don na ga kamar duk kin shiga damuwa, na lura kuma kaman kawai kara da alkunya kika yi ki ka amsa ba wai don ki na son Yaya Alhassan ba". "Ba buƙatan hakan Anty ki sanar da ita komai. Ai shi zaman aure ba a yi masa kara, kawaici ko kuma alkunya da ba na son sa ko kuma ban yarda da jagorancin da zai yi mini a cikin gidan aure ba, tabbas da zan san hanyar da zan bi wajen na fahimtar da Umma hakan. Sai dai ina ji har cikin zuciyata cewa zan sama dukkanin gata da kulawan da ya dace a cikin gidan Yaya Alhassan, roƙona ɗaya a gare ki shi ne ki bi mu da addu'a kawai". "Haƙiƙa Amatullah kin cika ƴar halak, in sha Allah wannan auren zai zamu silar wanzuwar farin ciki a cikin rayuwarki". Ban iya amsa mata ba illa kwantar da kaina da na ji akan cinyarta tare da lumshe idanuna daidai lokacin da wayarta ta yi ƙara ta ɗaga ƙira, a amsa-kuwwa take don ina jin sa'ilin da Yaya Mu'azzam yake shaida mata aure ya ɗauru nan ta din ha hamdala tana gode wa Ubangiji. Washe gari da safe tun kafin gari ya yi haske Anty Sawwama ta ƙira ɗakinta sadakina Naira dubu ɗari da hamsin ta damƙa mini, na nuna mata cewar babu abin da zan yi da shi ita ya kamata ta riƙe a yi wasu buƙatun da shi, amma ta nuna mini rashin yiyuwan hakan ta ce da ni a addinance ma ni nake da iko da sadakina, don haka na riƙe na je na yi tunanin abin da zan yi da shi. Tun ranar nake wasan ɓoya tsakanina da Yaya Alhassan duk abin da yake yi inna shi shigowarsa bari nake yi na shige cikin ɗakin ba na fito wa har sai ya tafi, cikin sati ɗayan da ya rage Yaya Alhassan ya ƙarisa aikin gidan da yake ginawa da yake can gangare daman fenti ne kawai ya rage sai ruwa da za a ja, kiwonta da yake ƙauye Anty Sawwama ta ɗaga ta sayar aka yi mini kayan ɗakin da na kitchen yayin da Yaya Mu'azzam ma ya raka rawar gani matuƙa. Duk halin matsin rayuwar da Amira suke ciki hakan bai hana Mansur dunƙulo Naira dubu hamsin ya ba ni ba a matsayin gudumawansa da farko na ƙi karɓa har sai da Amira ta nuna mini ɓacin ranta kafin na amsa. A bakin Anty Zulaihatu nake jin cewa wai Saifullah da Muhammad Taufik sun zo sun taya Yaya Alhassan murna har ma da kawo gudumawa a Anty Sawwama da ta kasance uwar amarya kuma uwar ango. Ranar da za a kai ni tare muka wuni da Anty Zulaihatu da kuma Amira ranar mun sha kuka sosai har sai idanuna suka kumbura har ya kai jallin da ba na iya buɗe su. Gidan a cike yake da mutane maƙota, ƴan uwa da kuma abokan azurki. Dangin mahaifin su Yaya Alhassan ba su nuna mini tsana ko ƙyama ba sai ma ja na a jiki da suke yi da yi wa iyayen addu'ar samun rahamar Ubangiji. Ban gaskata cewar da gaske an ɗaura mini aure ba sai da aka fito ni aka saka ni a cikin mota domin kai ni ɗakin miji, tun da motar ta soma tafiya ƙirjina yake dakan lugudai taka birkin da aka yi ya yi daidai da lokacin da hawaye suka zubo daga idanuna sai dai mayafin aka rufe mini fuskana da shi ya hana mutane fahimtar kuka nake yi, haka aka fito da ni daga cikin motar aka shigar da ni cikin gidan. Bayan wata dattijuwar mata ta yi mini umarnin na shiga da ƙafar dama tare da addu'ar Allah ya sa na shiga ke nan sai dai a fito da gawa ba. Anty Zulaihatu ne ta kai ni har cikin ɗakin miji ta kuma jira har aka yi rakiyar ango ta damƙa amanata a hannun Yaya Alhassan tare da yi nasihar idan ya cutar da ni ko ya wulaƙata ni, to ba ni ya wulaƙanta ba kansa ya tozarta. Haka suka tafi suka bar ni ni ɗaya ƙwal don na kai ga roƙon Amira ta kwana murzawa idanunta toka ta yi, da na matsa mata sai ce wa da ni ta yi to ita kuma na ta mijin ta yi ya ya da shi? Haka ina ji ina gani duk aka watsa aka bar ni ni ɗaya tamkar mayya. Ina zaune a cikin ɗakin ina kuka na ji an buɗe ƙofa an shigo ƙamshin turaren da na ji ya bugi hancina shi ya tabbatar mini da wanzuwar Yaya Alhassan kusa da inda nake, kafin na ji ya kai hannu ya yaye mayafin da yake kaina ya sanya hannunsa ya tallafo haɓana yana kallon fuskana da ta kumbura ta yi tsimtim tamkar kwaɓin fanken da ya ji yis. "Kukan nan ya isa haka Amatullah. Ki tausayawa kanki haka mana tun yaushe kike wannan kukan. Ya kamata kin san cewa kuka fa ba ya magani". Shuru na yi ban amsa masa ba don ina da yaƙinin ko na buɗe bakina sautina ba zai fita ba. "Amatullah". Na ɗaga kai na kalle shi da hakan ya ba shi tabbacin cewa ina sauraronsa. "Aurena da ke ya ƙara tabbatar min da cewar duk abin da kasance rabonka ne to fa ba ya taɓa wuce ka, na kuma ƙara tabbatar da sahihancin wannan karin maganan ta Malam Bahaushe da yake cewa zakaran da Allah ya nufa da cara to fa ko ana muzurai ana shaho sai ya yi. Allah ya ƙaddara cewa ke ce matar da zan aura a duniya ga shi kuma hakan a tabbata a lokacin da dukkanmu ba mu yi tsammani ba balle zato. Ina so ki cire komai a cikin ranki ki manta da duk wasu abubuwan da suka faru a baya domin yanzu sabon shafi ne ya buɗe a cikin rayuwarki. Na yi miki alƙawarin zame miki mijin marainiya wanda zai share miki hawayenki a duk sa'ilin da zuba kwanrayo. Zan kasance mai yi miki hidima har zuwa ƙarshen rayuwata, zan hidimta miki da karfina, lokacin da kuma aljihuna. Na yi ɗamarar sauya rayuwarki daga duhu zuwa bayyanannen hasken da zai haskaka miki hanya". Take na ji kalamansa sun samar mini da nutsuwa a sashin ruhina, na ɗau lokacin kafin na yi magana cikin dushashewan amo. "Ina fatan na kasace mace ta gari kuma saliha a gare ka kamar yadda Annabinmu ya ƙira mace ta gari da mafi ƙololuwan jin daɗin duniya ga raywuar ko wani ɗa na miji, ina addu'ar Allah ya ba ni ikon yi maka biyayya akan komai matuƙar komai ɗin bai hauce wa hanyar Allah da koyarwan manzonsa ba". Cike da jin daɗin kalamaina yake amsa wa da Amin, ya dafa kaina ya yi mini addu'a kamar yanda yake a addinance kana muka je muka yi alwala muka gabatar da salla raka'a biyu mu ka yi godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar a cikin rayuwarmu, sannan muka roƙe shi albarkar da yake cikin auren da kuma zuri'a ɗayyaba. Sai da ya haɗa mini da magiya da lallashi kafin na iya cin kazar amarcin da ya shigo da ita, jikina gau ya ɗau zafi sa boda zazzaɓin da ya rufe ni ga shi dare ya yi balle ya je ya sayo mini magana, amma duk da hakan bai saduda ba ya ɗaga waya wai zai ƙira wani abokinsa mai chemist in bai rufe ba ya je ya karɓo mini magana. Da ƙyar na hana sa fita ta hanyar muna masa cewa na ji sauƙi haka muka kwanta washe gari shi ya tashe ni sallan asubahi nan inda na yi sallan na kwanta baccin huce gajiyan da na kwasa ban tashi ba har sai da gari ya yi haske wannan ɗin ma shi ya tashi ni ya ce na je na wanka na zo na ci abinci sai na sha magani don har ya fita ya amso mini. Kunya ya mamaye ni matuƙar don ni gabaɗaya ma na mance da cewar yanzu ni matar aure ce shi yasa na kwanta na sha baccina hankali kwance. Tashi na yi na wanka da ruwan zafin da ya sanya mini na zo muka ci abincin da ya girka kana na sha maganin bai fita har sai da dangi da ƴan uwa suka fara zuwa gidan nan ma sai da ya Amira da Anty Zulaihatu sun zo kana ya fita bayan ya shaida musu cewar ku kula da ni don ba na jin daɗi. Nan fa suka haɗe kai suka din ga yi mini tsiya zolaya kam babu irin wanda ba su yi mini ba. Sai da suka yi sallan magrib suka tafi bayan sun yi mini nasiha mai ratsa jiki da kashe zuciya, shawarwari kuwa sun ba ni shi daidai gwargwado sun kuma ɗaura ni akan hanyar da ta dace. Haka har na cika sati a cikin gidan aure Yaya Alhassan ne yake yi mana girkin safe duk yadda zan tashi da wuri don na yi aikina to fa sai ya riga ni, sai dai mu yi aikin tare, haka tun ina jin kunyarsa har na saki jikina mussamman da na ga yadda yake ta faɗi tashi wajen ganin ya kyautata mini ba dare ba rana, dole ni ma na yi azaman faranta masa na watsar da komai na rumgumi mijina da kuma laluman hanyar da zan bi in faranta masa rai. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kwanciyar hankali da nutsuwa suka tabbata a gare ni, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci na yi ƙiba na murmure fatana ta yi kyau har wani sheƙi nake yi kamar bayan kifi. Duk da ba nida haske amma fatata ta yi farau ta washe. Zuciya babu wani damuwa haka nan raina fari ƙal tamkar zaiba. Ranar da na cika sati huɗu muka yi baƙi Saifullah da Muhammad Taufik suka zo wani abun mamakin har da Sheik Dawood sun wuni suna tattaunawa da Yaya Alhassan, ni kam kunya ta hana ni sakat tun da na fito muka gaisa ban ƙara koda wullagawa ta cikin falon sai da za su tafi Yaya Alhassan ya zo ƙira ni. Tabbas ba na buƙatar sai an faɗa mini da kalmomin baki idanuna kawai sun nuna mini cewar Sheik ya sauya don mun sha ruwan addu'o'i da albarka daga gare sa, ya ɗauki Naira dubu asiri ya ba ni da za su tafi. Haƙiƙa Yaya Alhassan ya cika mijin marainiyan da ya ambata kuma ya cika dukkanin alƙawarin da ya yi mini a darenmu na farko, ya inganta rayuwata matuƙa da kuɗin sadakina na shiga harkan kasuwanci atamfofi nake sayar wa da duk wasu nau'in kayan sawan mata, likkafa ta ci gaba don har lefe nake haɗawa mai rai da motsi na fita kunya. Kan ka ce kwabo rayuwa ta sauya jin daɗi ya zauna mana ni da mijina ba mu da wani burin da ya wuce faranta wa juna, na ƙara waye wa da samun ilmin zaman duniya da kuma mu'amala mutanen cikinta. Ranar ina zaune kwatsam sai ga Hajiya Muhibbat a cikin gidana tsabar farin ciki sai da na rasa inda zan tsoma ta mun sha hiran yaushe gamo da ita, tare da ba wa juna labarin bayan rabuwa nan take shaida mini cewar mijinta Saddam zai ƙara aure kuma Zinariya ce matar da zai aura, don ita da kanta ma ta shige masa gaba wajen neman auren, don ta fahimci suna don junansu kuma ba za su iya rabu wa, sannan Saifullah ma zai angwance da babbar jika a gun Sheik Dawood, na yi musu murna matuƙa da lokacin auren ya yi Yaya Alhassan da su Amir suka je su domin shaida ɗaurin auren. Sati ɗaya tsakani Amira ta haihu sai dai ɗiyar ba ta zo da raina ba. Ni kam haihuwar ta yi jinkiri don sai na shekara ɗaya da rabi a gidan aure kafin na haifi ɗa na miji santalele da shi, da sati ya gayayo ya ci sunan Abbana ana yi masa alkunya da Abul-khair watansa biyar a duniya aka yi bikin Amir da ya angwance da ƙanwar mijin Anty Zulaihatu mun sha biki don tare wa na yi a gidan Anty Sawwama, haka Yaya Alhassan ya gama fushinsa har ya sauƙo don kansa, a rage saura Umar kawai wanda kullum nake yi masa tsiya da cewar sai mun daina ba shi abinci. Lokacin auren Muhammad Taufik gayya muka yi muka je mu bikin iyalan Sheikh suka karrama mu matuƙa har muka je muka dawo mu na jinjina halin girma da dattaku irin na su. Na zamo abar alfahari ga mijina iyayen da kuma ƴan uwa har ma da matan cikin unguwan da nake, a ko a kan hanya nake tafiya na ga uwa tana furta munanan furuci ga ɗanta, sai na dakata na sanar da ita illar hakan a wasu lokatan har na kan yanko wani sashi na cikin tarihi don hakan ya sama iznina a gare su. Don tabbas na ishe kowa misali cewar DAFIN HARSHE mussamman na uwa akan ƴaƴanta ya fi dafin maciji illa don shi kassara rayuwa yake yi gabaɗaya. Har gida Saifullah da Muhammad Taufik suka kawo mini matanyensu, Zinariya ma sa ta rikiɗa ta koma sunanta na yanka watau Maryam ta kawo mini mun sha kuka ni da ita, mussamman da ta labarta mini cikin tsananin da ta fuskata da barazana daga wajen Hajiya Babba a yayin da ta yi ƙoƙarin sauya rayuwa, ta ce da ni har hauka sai da ta sa ta yi hauka tuburan har sai an ɗaure ta da mari don in ta bazama ta fice daga cikin gida to fa sai lokacin da Allah ya nufa. Da taimakon Allah da kuma addu'o'i ta sama sauƙi har hankalinta ya dawo jikinta. Ranar wata juma'a mun dawo daga gidan Anty Sawwama da muka kai mata wuni, ina gaba Yaya Alhassan yana baya yayin da yake riƙe da Abul-khair a hannunsa, na zaro makullin daga cikin jakata na buɗe ƙofar falon muka shiga ciki a nan cikin falon muka yada zango. Na amshi Abul-khair da ya fara bacci na je na kwantar da shi kana na dawo. Kusa da shi na zauna na tisa shi a gaba ina kallonsa har sai ya yi magana. "Ke lafiyanki kuwa wannan kallon kamar za ki cinye ni?". Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na ce"kawai ina tunanin da wasu kalamai ya dace na gode wa Allah ne, bisa kyautar da ya yi mini da kuma ni'iman da ya lulluɓe rayuwata da ita". "Ban gane ba". "Yaya Alhassan ni da kai mun san cewa ban dace da kai ba, amma duk da hakan ka aure ni ka killace ni a cikin gidanka ka ba ni dukkan kulawan da ya dace. A zamanmu da kai kullum cikin neman sabon hanyan da za kyautata mini kake yi......". Ban ƙarisa ba ya ɗaura ɗan yatsansa a saman leɓena. "Shit! Ba na son na ji wannan kalmar ta ƙara fito wa daga cikin bakinki. Bari na faɗa miki abin da ban taɓa faɗa miki ba, ni fa daman tun da ran Abba ina sonki a cikin zuciyata kawai na rasa ta yadda zan faɗa miki ne, ban san kuma yadda za ki fahimci maganar ba sa boda lokaci da yarinta a tattare da ke". Hannunsa da yake saman leɓena na ture"wai daman tun lokacin kake so na?". Ya ɗage mini giransa"ƙwara kuwa kawai ban faɗa miki ba, amma na san da na faɗa miki da yanzu mun haifi ƴaƴan ya kai dozin biyu". Babu shiri na kai masa duka a kafaɗarsa ya yi saurin zame wa. "Dozin biyu sai ka ce ka sama akuya". Dariya ya ƙyalƙyale da shi sai da ya tsagaita kana ya ce"to me ye a ciki? Ai duk za mu iya kula da su. In kuma ba za ki iya haifa min ƴaƴa ba sai na je na auro wacce za ta iya". Harara na galla masa wanda ya ke yawan cewa a duk lokacin da na yi masa sai ya tsorita. Zan yi magana ya katse ni"kin ga mayar da wuƙan wasa nake yi miki, Amatu ke ce wacce nake so kuma ba zan taɓa iya haɗa soyayyarki da na wata mace ba, ina fatan ki kasance matata har a cikin gidan aljanna". Ya ƙare zancen ya na jawo ni jikinsa ya rungume a ƙirjinsa, luf na kwantar da kaina tare da lumshe idanuna. Ya kawo bakinsa daidai kunnena kamar mai raɗa ya ce"Ina sonki matar Alhassan". "Ina sonka mijin Amatullah". A hankali ya ke shafa kaina kafin na ji ya ɗauke ni cak ya wuce da ni cikin ɗaki, na yi luf abina. Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! A yau Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafin mai suna DAFIN HARSHE . Ina roƙon Allah ya yafe mini kuskuren da na yi a cikinsa abubuwan alkhairin da na yi a ciki kuma Allah ya haɗa mu akan ladan. Ina godiya ga masoyana da suka yi jimirin bibibiyar littafin tun daga farko har ƙarshe ba tare da gajiya wa ba, ina godiya Allah ya bar ƙauna. Ga masu buƙatan littafaina, tambaya, ba da shawara ko wani gyara ƙofa a buɗe take, za a iya tuntuɓa ta ta wannan lambar kamar haka 07038908713. Sai na ji ku.......