MUGUWAR MACE. NA : HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500* *Skin oil 2500* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* 03/21/2026. PAGE 1. Tsafi gaskiyar me shi in ji Malam Bahaushe. Mata da dama sun kauce hanya domin cikar burinsu,su na iya yin komai dan ganin sun mallaki abinda suke so;ta kowacce hanya. Kowacce mace na son a san da zamanta a waje,ta zamo mai muƙami da mulkin gidanta. Wannan dalilin ne ya sa matan ke bin hanyoyi mabanbanta wajen ganin burinsu ya cika;wato hanyar halal da haram. Labarin Aabidah da Aabid ya zo mana da sabon salon mulkin gidan aure wanda yake da tsananin ban al'ajabi,mamaki,burgewa kai har ma da takaici. Ku biyo ni dan jin yanda waɗannan ma'aurata suke gudanar da tasu rayuwar... *************** Wani irin zafi ake yi a gari wanda mutane ke jin kamar su kama da wuta saboda yanda ya tsananta,gashi ruwan sama bai sauka da wuri ba ballantana a samu sassauci. A daidai wannan lokacin Mahreen ce kwance a madaidaicin gadonta tana tsiyayar da zufa sai kukan shagwaɓa take yi wa Yah Maheer ta rasa inda za ta saka ranta ta ji daɗi. A ɓangaren Yah Maheer kuwa ya dage sai firfita yake yi mata cike da kulawa tare da lallashinta kamar wata ƙaramar yarinya har yana jin hannuwansa na yi masa zogin azaba tsabar gajiyar da ya yi. Kallon Mahreen ya yi wadda bacci ya fara ɗaukanta ya shafi kuncinta ya na murmushi ya ce. "Sarkin rikici kenan." A hankali ya ajiye abun firfitar zai kwanta ta motsa tana ƙunƙuni kamar ba bacci take yi ba. Yah Maheer bai bi ta kanta ba ya yi kwanciyarsa domin ya huta,dan ba zai iya da rikicin Mahreen da baya ƙarewa ba. Kwanciyarsa ke da wuya aka fara buga gidan nasu da wani irin ƙarfin da ya yi sanadiyyar farkawar Mahreen daga baccin da ta fara yi wanda bai wani yi nisa ba. A firgice ta tashi ta zauna tana rarraba ido tsakanin bakin ƙofar ɗakinsu zuwa fuskar Yah Maheer dake ɗauke da tsananin mamaki. Ƙara buga gidan aka yi kamar za a ɓalle ƙofar,cikin sauri Mahreen ta matsa kusa da Yah Maheer jiki na rawa ta lalubo wayarta da ke gefensa ta kunna hasken fitilar domin samun ƙarin haske akan na ƴar ƙaramar rechargeble lamp ɗin dake kunne a ɗakin. Sauka Yah Maheer ya yi daga gadon nasu ya ɗauki rigarsa da dogon wando ya saka,sannan ya miƙa wa Mahreen babban hijabinta da zani domin ta saka a kan ƙananan kayan baccin dake jikinta. Da hannu ya yi mata alamar kada ta damu bari ya leƙa ya ga waye,tinda ba yau aka fara yi musu irin wannan zuwan ba zatan ba. Kai ta hau girgiza masa tana son ta yi kuka. Sauyawar zamani da rashin tsaron da ake fama da shi ne ya sake jefa ta a cikin tsoro da tunanin wanda yake buga musu gida a wannan tsohon daren. Ba tare da Yah Maheer ya biye mata ba ya buɗe ƙofar ɗakin ya fita zuwa madaidaicin Parlourn su mai ɗauke da abubuwan more rayuwa. Ya na shiga parlourn ana sake buga ƙofar gidan nasu cike da zaƙuwa,da sauri ya ƙarasa buɗe ƙofar parlourn ya fita farfajiyar gidan yana faɗin. "Waye?" "Malam Maheer buɗe ni ne Aabid." Cikin sauri Yah Maheer ya isa bakin gate ɗin gidan ya hau kiciniyar buɗewa ya na faɗin. "Aabid you again,me ya faru this time?" Wani irin gurnani ya ji Aabid na yi irin na marasa lafiya,cikin sauri ya ƙarasa buɗe ƙofar ya tari Aabid dake ta rawar jiki saboda tsananin sanyin da yake ji,ƙafarsa ya kalla ya ga yanda ta yi fururu da ita bata samu arziƙin a tsaya saka mata takalmi ba, hakan ya tabbatar masa da cewa da ƙafa ya tako tin daga gidansa. Yah Maheer na kai hannu jikin Aabid ya ji shi ya ɗauki zafi zauu kamar wuta. Cikin sauri ya kama shi suka shiga gidansa ya kulle sannan suka ƙarasa ciki. A parlour ya zaunar da Aabid sannan ya shiga ya sanar da Maheer abinda ke faruwa. Nan take tsoron da ya cika mata zuciya ya yi ƙaura,tausayi da jimami suka maye gurbinsu,kewa da shauƙi tare da ƙawa zuci suka mamaye zuciyarta. Sauka ta yi daga gadon da sauri ta bi bayan Maheer da ya koma parlour riƙe da abun rufa da matashin kai,dan ya san halin Aabid ba yarda zai yi ya kwanta a ɗaki ba. Yana zuwa ya miƙawa Aabid pillow dan ya saka a kansa,sannan ya yi amfani da abun rufa ya lulluɓe shi. Aabid kuwa jinsa yake yi kamar zai kama da wuta saboda damuwa,ga wani irin zazzaɓi da ya kama shi mai tsananin azaba. Cikin mayen ciwo yake faɗin. "Kin yi min alƙawari kin kasa cikawa Baby, alƙawarin har abada kika yi min ba na shekaru ba. You promised me forever my love please don't leave me." Tagumi Mahreen ta zabga ta na kallon Aabid hawaye na zubo mata daga idanuwanta na tsantsar tausayinsa. Tashi ta yi ta nufi kitchen ɗinsu ta dama masa custard ta zuba madara da sugar ta watsa gyaɗa a ciki kamar yanda yake so,sannan ta ɗakko ruwan pure water ta ɗora a ƙaramin faranti da paracetamol. Parlour ta dawo ta kama hannun Aabid ta na faɗin. "Yah Aabid tashi ka sha magani don Allah ko zazzaɓin zai sauka ka ji?" Muryar Mahreen ce ta sanya Aabid rushewa da wani irin kuka ya ƙanƙame hannunta ya na wata iriyar jijjiga. Cikin hanzari Yah Maheer ya isa gabansa ya dafa shi yana faɗin. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil..Lahaula wala ƙuwwata illa billah." Haka Yah Maheer yayi ta maimaita addu'o'in nan kafin daga baya Aabid ya kama yi shima. Da ƙyar ya samu zuciyarsa ta samu nutsuwa har ya karɓi custard ɗin ya sha kaɗan ya kora da paracetamol ya koma ya kwanta. Sun jima zaune jigum-jigum kafin su fara jin saukar numfashin Aabid a hankali,cikin baccinsa kuma yana furta kalmar. "You promised me forever baby, please don't leave me." (Alƙawarin ƙarshen rayuwa kika yi min baby don Allah kada ki barni.) Ɗaki suka koma Mahreen na share hawayen tausayin babban Yayan nata da rayuwarsa ta koma abar tausayi. Shi ne majinginarsu daga ita har mahaifiyarsu,sai dai rashin sa'ar mace ta gari ya jawo wa rayuwarsa rushewa ta koma kamar ta ƙaramin yaron da a koda yaushe yake neman kulawar iyayensa saboda kada ya faɗa wani mummunan halin ko ma ya rasa rayuwarsa gaba ɗaya. Cikin kuka Mahreen ta kalli Yah Maheer ɗinta ta ce. "In Sha Allahu Aabida ba za ta samu damar tuba akan laifukan da ta aikata ba za ta koma ga mahaliccinta. Zan yi matuƙar baƙinciki ace masu halayya irin tata su samu Rahamar Allah ko da da ƙiftawar ido ce." "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Haba Mahreen wannan wanne irin mugun fata kike yi wa ƴar'uwarki mace haka? Kada fa ki manta gaba ɗayan mu Rahamar Allah muke nema a duniya har zuwa ƙiyama,akan me ke za ki dinga yi mata fatan ta mutu da irin waɗannan manyan zunuban da ta kwasar wa akanta? Ban taɓa zaton haka daga gare ki ba,kin bani mamaki da kunya Mahreen." Hawaye Mahreen ta share tana kallon mijin nata da take matuƙar so da ƙauna ta ce. "Idan har addu'ar da na yi wa wannan MUGUWAR MACEn ne zai sa na baka kunya da mamaki,na amince ka yi ta jin kunya ta har ƙarshen rayuwarmu,ko ka manta wacece Aabida ne in tuna maka? Aabida ita ce sanadiyyar rushewar ahalinmu,Aabida ita ce sanadiyyar da mahaifiyarmu ke kwance tana jinya har yau,na kuma tabbata da wannan jinyar za ta koma ga mahaliccinta,Aabida ita ce silar raba ni da ɗan'uwana na tsawon shekaru masu yawa,Aabida ita ce ta...." Da sauri Yah Maheer ya rungume Mahreen ya na bubbuga bayanta ya ce. "Ya Isa haka,ki yi haƙuri idan maganata ta ɓata maki rai,mu je mu ma mu kwanta saboda mu samu sallar asuba akan lokaci." Ba tare da ta ce masa komai ba ta bashi dama ya kamata suka nufi hanyar ɗakinsu, suna tafe tana waiwayen Yayan nata da ta ɗauki tsawon lokaci bata zauna da shi a waje ɗaya ba har ta dena hango shi. A saman gadonsu Yah Maheer ya kwantar da ita tare da kashe fitilar tasu dan su yi saving cajin da ya yi musu saura zuwa asuba. Tinda ba wuta suke samu ba sai da rana,gashi mai ya ƙare a gen ɗin su Yah Maheer bai sani ba sai da ya je tada wa sannan ya gani,shi kuma a gajiye yake ya na jin ƙiwar sake fita siyo fetur. Kwanciyarsu ke da wuya suka ji ƙarar buɗe ƙofar parlour tare da kullewa da ƙarfi,cikin sauri Maheer ya miƙe zai fita Mahreen ta riƙe shi tana zubar da hawaye ta ce. "Rabu da shi,ka san idan bai koma ba haukace mana zai yi anan,mu bi shi da addu'a kawai Allah Ya mayar da shi gida lafiya." "Na sani ni dama ba dakatar da shi zan yi ba,zuwa zan yi na kai shi gida da kai na,dan da gani da ƙafa ya zo nan ɗin duba da ƙurar da ƙafarsa ta yi, kuma ko arziƙin talkalmi ma bai tsaya saka mata ba." Murmushi ta yi mai ciwo ta koma ta kwantar da kanta tana tsiyayar da hawayen tausayin ɗan'uwan nata. A gaggauce Yah Maheer ya ɗauki makullin motarsa ya bi bayan Aabid dake tafiya da ƙafa babu ko takalmi daga shi sai jakar hannunsa da ya je gidan da ita. Da ƙyar Yah Maheer ya samu damar lallaɓa Aabid ya shiga mota suka wuce Sallari inda gidansa yake. Suna zuwa Yah Maheer ya tsayar da mota Aabid ya buɗe ya fita riƙe da jakarsa a hammata ya buɗe babban gate ɗin gidan nasa da makulli ya shige,tsaye ya tarar da mai gadi yana zare ido da gorarsa a hannunsa,ganin Aabid ne da kansa sai ya sanya shi saurin mayar da sandar bayansa ya ɓoye ta ya hau yi masa sannu da dawowa,ko kula shi Aabid bai yi ba ya sa kai ya shige cikin gidan. Sai da Yah Maheer ya ji ƙarar kulle gidan sannan ya kalli agogon dake jikin motarsa ya ga ƙarfe uku da kwata na dare har ta gota. Tada motarsa ya yi ya wuce gidansa bakinsa na bin karatun ƙur'anin da ya kunna a cikin motarsa. *Aabid.* Ya na shiga cikin gidan ya tarar da ko ina cikin duhu kamar babu kowa a gidan,banda ƙarar AC da fridge babu abinda ke tashi,sai hasken ƙananan fitulun abubuwan wuta dake kunne,kai tsaye sama ya hau ya nufi ɗakinta riƙe da jakarsa da ya kasa ajiyewa har a wannan lokacin. Yana shiga ya ganta kwance a gado ta yi ruf da ciki tana latsa wayarta cike da nishaɗi tana chatting hankalinta kwance. Zubewa Aabid ya yi a saman guiwowinsa ya na tsiyayar da hawaye kamar wani ƙaramin yaro ya ce. "Don Allah Baby ki yi haƙuri,na amince zan yi miki duk abinda kike so,amma kar ki rabu da ni,idan kika rabu da ni mutuwa zan yi." Ya ƙarasa maganarsa tare da rushewa da matsanancin kuka. Ta jima sosai tana latsa wayarta cike da nishaɗi kafin ta kunna dim light sannan ta ajiye wayarta a kife. A hankali fara kuma kyakkyawar matar da ba za ta wuce shekaru talatin da ɗaya ba a duniya ta sauka daga saman gadonta ta na wani ɓaɓɓata rai. Kallon Aabid da ke gurfane a gabanta yana rusa kuka ta yi a wulaƙance sannan ta ce. "Har ka shanye yajin da ka daka kenan Aabii. Ai na ɗauka za ka iya kwana a wani wajen saboda kawai na roƙi abinda bai taka kara ya karya ba a wajenka. Ashe dama alƙawarin da ka yi min duk ƙarya ne? Ashe ba za ka iya ba ka fara? To ina son a cikin daren nan ka rubuta min takardar sakina na koma gida na ci gaba da rayuwar da na saba da ita tun kafin na sanka. Hakan zai fiye min kwanciyar hankali sama da na rayu da mutumin da yake ƙaryar so na." Da rarrafe Aabid ya ƙarasa wajen Aabida ya kama ƙafafuwanta yana goga fuskarsa a jiki yana kuka kamar zai shiɗe. Da ƙyar ya iya ɗaga kansa yana kallon cikin idonta ya ce. "Na amince zan yi miki duk abinda kike so matsawar ba za ki rabu da ni ba har abada." A sheƙe Aabida ta kalli Aabid kafin ta juya masa baya ta harɗe hannuwanta a ƙirji ta ce. "Ban yarda da kai ba,dan na san halinka sarai da tausayi,ba lallai ka iya cika min burina ba,dan haka mu rabu kawai Aabid na je na auri wanda zai...." Cikin sauri Aabid ya ja ta jikinsa ya rungume ta ya na kuka yana jaddada mata kalmar. "Na sake yi miki alƙawari a karo na babu adadi Aabida,zan cika miki duk wani burinki a rayuwa ko da hakan zai yi sanadiyyar rasa rayuwata ne." Wani irin ƙayataccen murmushi Aabida ta saki,domin ta tabbata a wannan karon za ta samu biyan buƙatar ranta da ta jima tana fata. Dan haka sai ta rungume Aabid tana yi masa wani irin salon da ya sanya shi sauke ajiyar zuciya da sauri da kuma ƙarfi. Cike da farinciki suka kwanta har aka kira sallar asuba aka shiga sallah a dikkan masallatan dake unguwar Aabid bai farka ba ballantana ya yi sallar akan lokaci. Ba su suka farka ba sai da gari ya waye tarwai sannan Aabid ya farka a gigice ya faɗa banɗakinsu ya yi wanka ya tsarkake jikinsa sannan ya fito ya shirya. Sallahr asubar da ta wuce shi ya rama sannan ya kalli saman gadon da Aabida ke kwance tana ta sauya wuri kamar a lokacin ta fara jin daɗin baccin da take yi,sake rufe ta ya yi da bargo yana jin soyayyarta na ratsa kowacce kafa da ɓargon jikinsa. Kitchen ya nufa ya haɗa mata abinci sannan ya jera a saman dinning table kamar yanda ya saba,sannan ya ɗebi nashi ya ci a gaggauce,zuciyarsa na bugawa cike da matsananciyar damuwa da tsoron yanda zai tunkari Hajiyansa a wannan ranar. Da ƙyar ya tura dankalin da ya soya ya kora ruwan shayi ya ɗauki makullin motarsa ya bar gidan cike da fargaba da tsantsar damuwa................. MUGUWAR MACE. NA:HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️. *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 2: Karkata kan motarsa yayi ya ɗauki hanyar unguwar Ƴankaba. A daidai ƙofar wani gida na masu matsakaicin ƙarfi ya tsaya. Ya jima sosai a cikin motar kafin ya fito tare da zaro wayarsa da ke cikin aljihunsa ya hau latsawa. Jiki a mace ya kara wayar a kunnensa,ko sallama bai yi wa wanda ya kira ba ya ce. "Ka same ni a ƙofar gidanka yanzu." Kashewa yayi ya jingina da jikin motarsa yana jin ƙafafuwansa sun masa nauyi kamar ba zai iya ci gaba da tsayuwa ba. Cikin abinda bai fi minti biyu ba wani siririn dattijo ya fito daga gidansa ya na saɓa tsohuwar babbar rigarsa a kafaɗarsa,kaki yayi ya zubar sannan ya ƙarasa wajen Aabid dake tsaye. Sallama yayi wa Aabid tare da naɗe hannuwansa a cikin babbar rigarsa ya duƙar da kansa ya ce. "Ranka ya daɗe lafiya dai ko na ga ka zo har gida ba ka kira ni can kamfani ba." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Aabid ya sauke kafin ya ce. "Lafiya ƙalaou Malam Sallau. Na zo ne akan maganar nan da muka taɓa yi da kai da jimawa daga baya kuma na ce na fasa. To yanzu ina so ka sake tuntuɓar mutumin ka ji if he is still interested i am willing to...." Cikin hanzari Malam Sallau ya katse Aabid ta hanyar washe baki ya ce. "Ai Alhaji ko yanzu muka je na san zai amince. Wannan mutumin ai kusan sana'arsa kenan,dan haka duk lokacin da ka shirya kawai zuwa za mu yi mu same shi har gida a daddale magana." "Ok idan dai haka ne kawai mu je yanzu." Har Malam Sallau ya kama hannun motar Aabid ya buɗe zai shiga,sai kuma ya ja ya tsaya. Cike da sanyi tare da mutuwar jiki ya ce. "Ranka ya daɗe ba zan ce maka ban ji daɗin wannan harƙalla da za a ƙulla ba,saboda ko babu komai ta nan nake samun nawa abincin da wasu buga-bugar. Amma kuma ina ganin kamar abinda za ka aikata bai dace ba,kada ka manta fa...." Hannu Aabid ya ɗaga wa Malam Sallau rai a ɓace ya ce. "Za ka kai ni ne ko na samo wani?" Da sauri Malam Sallau ya saka hannunsa guda biyu ya zuge laɓɓansa sannan ya faɗa mota ya zauna. Cikin ƙiftawar Ido Aabid ya bar unguwar su Malam Sallau suka nufi unguwar Ɗanladi na Sidi. Da kwatance Aabid ya kai su gidan Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera. Gida ne kadaran kadahan domin kuwa gaba ɗaya unguwar shi ne gidan da bashi da gate da kyawun sifa kamar sauran manyan gidajen dake jere a unguwar reras gwanin ban sha'awa. Malam Sallau ne ya fita ya je ƙofar gidan ya dinga kwaɗa sallama. Babu jimawa wata yarinya ƙarama ta leƙa tana tambayar waye. Washe baki Sallau yayi ya ce mata. "Ki ce wa gyatuminki yayi manyan baƙi ya hanzarta ya fito kada ya ɓata wa Alhaji lokaci." Da gudu yarinyar ta koma cikin gidan ta sanar da zuwan su Malam Sallau ga mahaifinta wanda ke tsaye yana sanya takalmansa tare da tura uban tumbi gaba yana nishi tsabar ƙiba. Kai kawai ya gyaɗa mata ya nufi waje. A tsaye ya tarar da su Aabid ya miƙa musu hannu suka gaisa. Babu ɓata lokaci Sallau ya kora masa bayani akan dalilin zuwan su. Murmushi Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera yayi sannan ya ce. "Yanzu ake buƙatar kuɗin ko yaushe? Domin ni a shirye nake da na bada kuɗi,a bani takardu tare da kafa shaidu." "Idan ka shirya ni ma a shirye nake." Cikin ƙanƙanin lokaci su Aabid suka gama duk abinda ya kawo su suka yi sallama da Alhaji Kabiru suka tafi. Godiya sosai Malam Sallau ya dinga yi kamar zai kwanta wa Aabid a ƙasa. A haka Aabid ya sauke shi a daidai wajen da zai samu mota ya koma gida shi kuma ya wuce gidansu dake cikin unguwar Ɗanladi na Sidin. A waje ya ajiye motarsa ya shiga cikin katafaren gidan nasu wanda da wayonsa mahaifinsa ya siyi gidan a hannun gwamnati ya rushe shi ya sake ƙera kalar wanda yake so. Gida ne da ya amsa sunansa gida mai part biyu da manyan filayen da aka yi shuke-shuken ƴaƴan itatuwa da flowers domin ƙayata wajen. Gefe ɗaya kuma ƙaton waje ne da aka yi kitchen irin na gargajiya tare da ɗakuna uku na masu aiki. Zagaye Aabid ya dinga yi a gidan yana kallon kowanne lungu da saƙo na gidan yana tuna memories masu daɗi da marasa daɗi da suka faru a gidan. A ƙofar wani ɗaki ya tsaya yana bin ƙofar da kallo. Wani irin abu ya ji ya daki zuciyarsa har sai da ya sanya hannu ya dafe ƙirjinsa. "Dijahna" Shi ne sunan da ya ambata kafin ya tura ƙofar ya sanya ƙafarsa ta dama a ciki. Nan take hotunan rayuwar da yayi a baya ta hau gilmawa a idanuwansa. Kansa ya ji yana sara masa kamar zai tsage. Babu shiri ya fita daga ɗakin ya ja ƙofar ya rufe. Da sassarfa ya isa ɗakin Hajiya wadda ke kwance ita kaɗai tana firfita. Kallonta yayi fuska a haɗe kamar bai taɓa dariya ba ya ce. "Ina wannan yarinyar take na ganki ke kaɗai?" Da sauri Hajiya ta tashi zaune daga kishingiɗar da ta yi ta kalli Aabid cike da so da ƙauna irin na ɗa da mahaifiya. Murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ce. "Salimah? Ta fita samo mana gawayi mu ɗan ɗora ruwan koko a samu a karya tinda gari ya waye." Rintse idonsa yayi yana jin jiri na ɗibansa. Mahaifiyarsa ce fa,matar da ko Custard za ta sha sai ya koma fari fat saboda madarar da take zabga masa,ta saka ta ruwa sannan ta ƙara da ta gari,ita ce yau take neman gawayin da za ta dama koko. Mahaifiyarsa wadda take rayuwa kamar sarauniya komai sai an yi mata saboda dukiya da gatan da mahaifinsa da shi kansa suke bata. Kyaɓe baki yayi sannan ya zaro dubu biyu ya ajiye a nesa da ita ya kurɗa kansa cikin ɗakinta,da wani irin farinciki Hajiyan ta ɗauki dubu biyun tana jin kuɗin kamar dubu ɗari biyu a wajenta,yaushe rabon Aabid ya zo gare ta? Yaushe rabon ta samu arziƙin samun wani abu daga gare shi? Lallai wannan babbar nasara ce a gare ta wadda take fatan watarana komai ya koma kamar yanda yake a baya. Bincike yayi sosai kafin ya samu abinda yake so sannan ya fito yana zufa kamar wanda yayi wani aikin wahalar. Kai tsaye ya fice ya bar gidan ba tare da ya ce mata kanzil ba ya faɗa motarsa ya fige ta. A hanya ya haɗu da Salimah hannunta riƙe da tarkacen itacen da ta yo da kanta saboda rashin samun gawayin da bata yi ba. A gabanta ya tsayar da motarsa ya kalle ta ya ce. "Ke wannan yayin haukan da kika ɗebo fa na meye?" Cike da jin tsoronsa bakinta ya hau rawa,tsawa ya daka mata tare da sake tambayarta abinda ke hannunta na meye. Cikin rawar murya ta kalle shi ta ce. "Ƙirare ne na samo dan mu yi amfani da shi." "Ina gawayin da kika je siyowa?" "Ban samo ba." Tsaki ya ja mai tsawo sannan ya ja motarsa ya bar wajen a guje kamar zai tashi sama. A hankali ta waiga ta kalli ƙurar da motar ke tadawa sannan ta girgiza kanta ta wuce gida. Washegari da sassafe ko tashi daga bacci su Hajiya basu yi ba suka ji ana buga gate ɗin gidan nasu da ko arziƙin mai gadi babu. Hajiya da kanta ta sanya mayafinta ta nufi ƙofar gidan da makulli a hannunta tana tambayar waye. Wata murya ta ji wadda bata waye da ita ba tana faɗin. "Mu ne." Gabanta ne ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta kafin ta ce. "Ku su wa?" "Alhaji Aabid bai sanar da ke zuwan mu ba ne? Ina ga zai fi kyau ki kira sa a waya ki tambaye sa su waye za su zo war haka." Cike da jarumta Hajiya ta buɗe ƙaramar ƙofar gidan ta tsaya tana kallon mutanen da bata taɓa gani ba sai a wannan ranar. A guje Malam Sallau da ya tsaya bawali ya ƙaraso yana gyara wandonsa tare da fyace majina ya ce. "Barka da safiya Hajjaju." Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke sannan ta ɗan yi dariya ta ce. "Malam Sallau ai har na ji tsoro,ashe ku ne ke tafe. Bismillah ku shigo." Da jin haka sai suka ɗunguma suka shiga cikin gidan gaba ɗaya su na sake gaisawa. Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera kuwa kallon gidan yake yi yana girgiza kai tare da washe baki. Tafe yake yana buɗe duk wani ɗaki ko ƙofa da ya gani kamar gidansa. Cike da mamaki Hajiya ta ke kallon ikon Allah,ba ta katse da lamarin Alhaji Kabiru ba har sai da ta ga ya nufi ɗakinta ya saka hannu zai buɗe ƙofa. Da ƙarfi ta ce. "Malam lafiya wai naga kana ta buɗe min ƙofofin gida kana kalle-kalle?" Malam Sallau ne ya sosa ƙeya sannan ya ce. "Hajiya wai ko dai kina nufin Alhaji Aabid bai sanar dake abinda ke faruwa bane?" Cike da mamaki Hajiya ta juya tana kallon Malam Sallau sannan ta ce. "Malam Sallau me ya samu ɗana? Me yake faruwa wanda ba a sanar dani ba?" "Baki da labarin Alhaji Aabid ya siyar da wannan gidan Hajiya? Ai jiya da yamma ya kai wa Alhaji Kabiru takardu muka je wajen Mai Unguwa aka saka shaidu ya biya kuɗi da ..." Wani irin duhu ne ya mamaye ganin Hajiya,nan take ta yanke jiki ta faɗi. Alhaji Kabiru na ganin haka ya hau sauri yana son barin gidan,domin shi mutum ne mai tsananin tsoro da kiyaye duk wani abu da zai haɗa shi da hukuma. Banda nishi babu abinda yake yi a haka ya isa waje ya shige motarsa ya zauna yana yarfe zufa. Sallau kuwa sunan Salimah ya dinga kira ta fito a gigice kanta babu ko ɗanƙwali. Ganin Hajiya a zube a ƙasa ne ya gigitata ta nufi wajen da gudu ta zube a gefen Hajiyan tana jijjiga ta. Hankalin Sallau ba ƙaramin tashi yayi ba dan haka sai ya miƙe ya lalubo wayarsa ya dannawa Aabid kira. Cikin rashin sa'a kiran ya shiga a daidai lokacin da wayar Aabid ɗin take hannun Aabida tana duba mutanen da yayi waya da su a jiya;wanda murnar ganin gingimemen alert ɗin kuɗi ya mantar da ita dubawa. Ɗauka ta yi cike da gadara. A kiɗime Malam Sallau ya labarta mata abinda ke faruwa. Rai a ɓace Aabida ta ce. "Idan ta faɗi mutuwa ta yi? Malam idan za ku yayyafa mata ruwa ta tashi ku yayyafa mata,idan ba za ku yayyafa mata ba ku kuka sani ku barta ta ƙarasa ai dama ta kwana biyu,babu inda mijina zai fito da sanyin safiyar nan yana hutawa." Tana gama magana ta katse wayar ta ci gaba da abinda take yi.......... MUGUWAR MACE. NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH. ✨✍️ *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 3. A rikice Malam Sallau ya kira Yah Maheer ya sanar da shi abinda ke faruwa. Hankali tashe Yah Maheer ya roƙi Malam Sallau da ya nemo abun hawa ya kai Hajiya asibiti ya na nan tafe zai same su a can. Da ƙyar Malam Sallau ya iya barin Hajiya a kwance a ƙasa ya fita saboda tsoron kada ta mutu kafin ya dawo. Sai da ya ɗauki kimanin mintuna shida kafin ya dawo da ɗan sahu,su biyu suka ɗauki Hajiya suka saka ta a adaidaita sahun sannan suka ja suka tafi asibitin da ake duba Hajiyan a duk lokacin da ciwon ta ya tashi. Su na zuwa likitansu ya fara bata taimakon gaggawa. Kafin Yah Maheer ya iso Hajiya ta dawo tana numfashi yanda ya kamata,sai dai a wannan lokacin bata san wanda yake kanta ba. Har ofishin likita ya je suka zauna,likita yayi ta masa faɗa akan yanda suke wasa da lafiyar Hajiyan. Cike da rashin jin daɗin lamarin likita ya ce. "Haba Maheer wai me yake faruwa ne kuke wasa da lafiyar Hajiya haka? Ko ka san cewa tashin ta lafiya ba tare da shanyewar ɓarin jiki ba babban lamari ne da za a gode wa Allah akai? Ina Aabid? Ta na farfaɗowa sunansa ta fara kira. Don Allah ku maida hankali ku kula da lafiyar ta. Yanzu ga wannan ka je ka siyo a fara bata,sannan a kawo mata abinda za ta ci,dan har da ciwon ulcer ke damun ta." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Yah Maheer ya sauke kafin ya miƙa hannu ya karɓi takardar da likita ya bashi,cikin sanyin murya ya ce. "Mun gode Dr. Anas. In Sha Allahu za mu kiyaye daga yau Hajiya ba za ta sake samun attack irin wannan ba." "Allah Ya bata lafiya." "Amin Ya Allah." Da haka Yah Maheer ya karɓi takardar hannun likita ya wuce pharmacy. Malam Sallau na ganin shi ya ruga da gudu ya nufe shi,cike da damuwa ya ke tambayar jikin Hajiya,murmushin yaƙe Yah Maheer yayi masa kafin ya ce. "Da sauƙi Malam Sallau,da yardar Allah Hajiya za ta tashi lafiya. Na ɗauki alƙawari daga yau Hajiya ba za ta sake shiga damuwa ba in dai ina raye." Ƙwalla Malam Sallau ya share kafin ya ce. "Allah Ya jiƙan Alhaji. Ita kuma waccan azzalumar Allah Ya tsine mata,In Sha Allahu ƙarshen ta ba zai yi kyau ba,da yardar Allah sai ta wulaƙanta kafin ta mutu. Aabid na fara kira da abun ya faru amma ja'irar yarinyar nan ta ɗauki wayar ta ce ba zai zo ba hutawa yake,wannan yarinya wannan yarinya Allah Ya..." "Ya isa haka Malam Sallau bari na je na kawo abinda ake buƙata. Duk wanda yayi na gari ai kansa ko?" Jinjina kai Malam Sallau yayi ya ce. "Ƙwarai da gaske ma kuwa Alhaji Maheer." Daga haka Yah Maheer bai sake cewa komai ba ya tafi Pharmacy ya siyo magungunan da aka rubuta,sannan ya shiga wajen siyar da abinci ya siyo abinci mai rai da lafiya da ruwan sha ya koma ɗakin Hajiya. Kwance ya tarar da ita tana bacci wanda da ka gani cike yake da azaba da wahala. Zama yayi a kujerar dake kusa da gadon ya kifa kansa a jikin gadon yana jin yanda zuciyarsa ke tsananin zafi. Motsin da ya ji ne ya sanya shi ɗaga kansa cikin sauri ya kalli Hajiya dake kiran sunan Aabid hawaye na zubowa daga gefen idanuwanta. Da sauri Yah Maheer ya tashi ya tsaya a gabanta ya ce. "Sannu Hajiyarmu Allah Ya baki lafiya. Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki a samu jininki da ya hau ya sauka,daga baya sai mu samo solution akan matsalar da ke gabanmu. Bari na je na kira likita na dawo." Da sauri Hajiya ta riƙo hannunsa ta ce. "Maheer Aabid zai kashe ni da baƙincikinsa...Aabid...Ya siyar...da gidan da nake ciki....ba tare da ya sanar da ni ba.....Aabid ya siyar da gidan da mahaifinsa ya gina...min cike da soyayya....tsarin ginin gidan da duk abinda....yake ciki...ni na zaɓa da kaina...me na yi wa Aabid a duniya yake azabtar....da ni haka? Laifi ne da na zamo a matsayin....mahaifiyarsa?.....Aabid ɗina ya halaka Maheer...ko mutuwa na yi bana so...ya zo kan gawata....na yafe wa Aabida shi....na yafe wa duniya shi." Hawaye ne masu tsananin zafi suka hau zubowa daga idanuwan Yah Maheer. Da ƙyar yake iya buɗe bakinsa ya bawa Hajiya haƙuri,sai dai shi kansa ya sani ban haƙurinsa a daidai wannan lokacin ba zai yi tasiri ba. Da sauri ya fita ya kira likita suka dawo tare da nurse. Abinci suka tursasa Hajiya ta ci kaɗan sannan suka bata magunguna,daga nan nurse ta sauya mata ruwan da ke shiga jikinta sannan suka tafi suka barta tana sambatu. A haka bacci mai cike da mafarkai marasa daɗi ya ɗauke ta. Yah Maheer na ganin ta samu bacci ya leƙa ya kira Salimah ya ce mata. "Ki zauna da ita bari na je na dawo. Malam Sallau mu je na ajiye ka a gida ko?" Da sauri Malam Sallau ya tashi yana matse ido ya bi bayan Yah Maheer wanda fuskarsa ta sauya daga mai yawan fara'a da sanyin hali zuwa wani mutum mai tsananin fushi. Ya na ajiye Malam Sallau ya wuce gidansa. Ƙamshin da ya daki hancinsa ne ya sanya shi lumshe ido ba tare da ya shirya ba. Ƙamshi ne na turaren wuta mai daɗi da kwantar da hankali wanda Mahreen ke haɗawa da kanta saboda ta san irin ƙamshin da mijinta yake so. Ya na ƙarasa shiga gidan ya tarar da ita ta sanya guntun wando da ƴar ƙaramar riga sai zabga ƙamshi take. Ajiye food flask ɗin hannunta ta ƙarasa yi a saman dinning table kafin ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa. Kyakkyawan ruƙo Yah Maheer yayi wa Mahreen sannan ya taka da ita a hannunsa suka zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake jere a parlourn. Cike da shagwaɓar da ta san tana burge gwarzon nata Mahreen ta ce. "Ina ka tafi da sassafe ina bacci ba tare da ka sanar dani baaa?" Murmushin yaƙe yayi kafin ya ce. "I am sorry my rigimatu,a yi min afuwa ba zan sake ba. Yanzu mu je ki bani abinci na ci yunwa nake ji kin ji tauraruwa ta?" Da sauri ta ɗaga shi ta wuce wajen cin abincin ta hau zuba musu soyayyan dankalin hausa da ta yi da miyar attaruhun da ta ji albasa da kayan ciki sai zabga ƙamshi take yi. Ajiye wa ta yi a center table sannan ta koma ta haɗa musu shayi ta kawo da bread da soyayyan ƙwai ta zauna a gabansa ta na bashi a baki. Bata jima tana bashi abincin ba ya ji duk ya fice masa akai,sai dai dole ya daure ya ci tare da ɓoye damuwarsa kafin rigimammiyar tasa ta fahimci akwai matsala ta saka shi a gaba da kukanta da ba ya iya jure sauraro. Sai da suka gama cin abincin tas sannan ta kwashe komai ta kai kitchen ta ajiye ta koma wajen Yah Maheer da ya zurfafa a tunanin halin da ya baro Hajiya a ciki. Zama ta yi a kusa da shi tare da ɗauke masa tagumin da ya zabga ta sumbaci hannunsa ta ce. "Tun da ka shigo na fuskanci akwai damuwa a tattare da kai,a tunani na kyautatawar da zan yi maka kaɗai ta isa ta wanke maka damuwarka,sai dai da dikkan alamu abinda ke damunka ya fi ƙarfin kulawata ballantana ta taimaka ta yaye maka damuwar. Sanar dani abinda ke faruwa ko akwai wani taimako da zan iya yi akai." Zuciyarsa ce ta karye da tausayinta,sai kawai ya ja ta jikinsa ya rungume. Ya jima a haka kafin ya miƙe tsaye ya ce mata. "Zan fita na je na dawo,ban sani ba ko zan jima ko kuma zan dawo da wuri,ki tabbata kafin na dawo kin gyara ɗakin dake tsakar gida ki wanke banɗakin sannan ki saka labulayenki masu hasken nan,ki goge ƙurar cikin ɗakin da kyau,idan da hali ki saka masa wannan ƙamshin naki mai daɗi." Jikin Mahreen ne ya ɗauki rawa,nan take ta hau jin wani sanyi na lulluɓe ta. Cikin ranta ta hau ayyana. 'Shikenan! Ta faru ta ƙare,Yah Maheer yayi aure ba tare da ya sanar dani ba. Kuma shine dan cin mutunci zai saka ni gyara wa amaryarsa ɗakin da za ta zauna. Babu komai,zan yi duk abinda ya ce domin umarninsa a koda yaushe gaba yake da buƙatata. Ya Allah ka sassauta min wannan zazzafan kishin da nake ji yana taso min a cikin zuciyata.' Mahreen ta yi nisa a cikin tunaninta tare da zubar da hawaye ta ji hannun Yah Maheer ɗinta abun ƙaunarta ya na share mata hawayen. Da sauri ta sanya nata hannayen ta na sake share hawayenta tare da sanya murmushin yaƙe ta juya za ta shiga ɗaki. Hannu Yah Maheer ya saka ya dawo da ita ta tsaya a gabansa kanta a ƙasa ta na tsiyayar da hawaye. Murmushi yayi sannan ya ce. "Sarkin kishi,ki kwantar da hankalinki domin ba abinda kike zargi bane. Na rantse maki da wanda ke busa min numfashi har yau ban ga macen da ta kai ki ba. Ke kaɗai nake gani a matsayin mace,kuma ke kaɗai ce wadda na yarda na amince ta san sirri na,a wajen ki kawai natsuwata take. Dan haka ki kwantar da hankalinki. Trust me my love ba zan taɓa aikata abinda zai dame ki ba. Bari na yi sauri na je ana jira na,ki yi abinda na ce please ki saka labulen nan naki mai shara-shara saboda zafi ake yi yanzu." Kai Mahreen ta ɗaga masa kawai tana jin wata iriyar nutsuwa na shigarta,a hankali ta sakar masa murmushi suka yi sallama ya wuce asibiti. Ya na fita Mahreen ta hau gyaran ɗakin da ya gina a matsayin na mahaifiyarsa sai kuma ta rasu tun kafin a kammala ginin. Tun daga nan idan Yah Maheer na so ya tsokani Mahreen sai ya ce mata ai inda zai saka mata abokiyar zama kenan tinda Innah bata yi nisan kwanan da za ta rayu a ciki ba. Lokuta da dama sai dai ta yi dariya ta yi ta cika masa bakin bashi da chance ɗin ƙara aure a duniya,ya dai jira su je ƙiyama a bashi na aljannah. Cikin ƙanƙanin lokaci Mahreen ta wanke banɗaki ta wanke ɗakin tass sannan ta goge shi. Da taimakon kujerar dinning table ta saka gogaggun labulayenta masu kyau da tsada wanda Hajiyanta ta siya mata a lokacin aurenta ba tare da sanin Yah Aabid ɗinta ba. Tana tuna wa da su ta ji jikinta yayi sanyi,waje ta samu ta zauna a ƙasa ta hau zuba addu'o'in samun daidaito a tsakanin zuri'ar tasu. Ta na nan zaune aka fara kiran sallar azahar. Da sauri ta hau bi itama,ana gamawa ta yi addu'ar bayan kiran sallah sannan ta yi wa Annabi salati, addu'a ta sake yi sannan ta kalli ko ina ta ga yayi fess. Rufe ɗakin ta yi ta koma sashenta ta shiga wanka. Tana gamawa ta yi alwala ta shiga ɗakinta ɗaure da towel ta hau gyara jikinta. Sallah ta yi kafin ta ɗora abinci wanda ta yi shi mai yawa saboda tana tunanin baƙi za su yi,Yah Maheer bai dai sanar da ita bane kawai. Bata jima da gamawa ba kuwa ta ji ana buga gate ɗin gidan. Cikin sauri ta nemi Hijabinta ta ɗora a saman shigar atampa riga da skirt ta fita dan ganin wanda ke buga gidan nasu...... MUGUWAR MACE. NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 4. Motar kamfanin Aabid ta gani ta ɗiban hatsi tsaye a ƙofar gidan ɗauke da kaya,sai direba dake tsaye yana yi mata bayanin daga inda kayan suka fito tare da sanar da ita saƙon Alhaji Maheer. Gyaɗa kai kawai ta yi ta matsa ta basu waje. A gaban idanuwanta suka shigar da kayan ɗakin da ta gama gyarawa sannan suka yi mata sallama suka wuce. Kanta ya ɗaure sosai da wannan sabon lamarin da ta kasa yi wa suna. Shin me yake faruwa ne? Rashin samun amsar tambayarta ne ya sanya ta shige wa ɗakin ta duba kayan da yanda suka jera komai a inda ya dace. A hankali ta ja ƙofar ta rufe sannan ta koma sashenta ta zauna. Tagumi ta zabga tana hasaso abubuwa da dama da za su iya sanya Yah Maheer gyara ɗakin nan kamar wanda za a saka wata amaryar a ciki. Kasa cin abincin da ta dafa ta yi;duk kuwa da irin yunwar da take ji na kartar tumbinta. Kwanciya ta yi a saman doguwar kujera tana hawaye,a haka bacci mai cike da mafarkin Yah Maheer ɗinta ya ƙara sabon aure har ya tare da amaryarsa. Kiran sallar magariba ne ya tada ita daga nannauyan baccin da ta sha,a gaggauce ta faɗa banɗaki ta yi brush ta ɗaura alwala sannan ta wuce ɗakinta ta tada sallah. Kaya ta sauya zuwa ƙanana masu kyau sannan ta ƙara feshe jikinta da turare,daga nan sai ta wuce parlour ta kunna turaren wutanta mai daɗin ƙamshi,nan da nan gidan ya kiɗime da ƙamshi kamar a Sudan. Sai da ta tabbatar ko ina ya ɗauki ƙamshin sannan ta wuce ɗakin tsakar gida ta kunna turaren wutan ta zauna tana jiran ya gama ta ɗauke. Har Mahreen ta kammala duk wani abu da za ta yi ta zauna,shiru Yah Maheer bai dawo ba bai kuma kira ta a waya ba kamar yanda ya saba. Jin shirun yayi yawa ne ya sanya ta ɗaukan wayarta ta kira shi. Haka wayar ta karaci ringing bai ɗauka ba,jikinta ne yayi sanyi sosai ta sanya hannunta a baki tana cizon farcenta ta ce. "Ni fa wannan sabon lamarin dake faruwa ya fara bani tsoro,ina mijina ya tafi tun safe har yanzu bai dawo ba;kuma bai kira ni a waya ba?" Tsaye ta miƙe ta hau sintiri a parlourn tana jin yanda cikinta ke kukan yunwa amma ta bawa banza a jiyarsa. Duk yanda Mahreen ta so ta daure kasawa ta yi,cike da damuwa ta hau rubutawa Yah Maheer saƙo. Kafin ta tura ta ji horn ɗin motarsa,wurgi ta yi da wayar tata ta fita da gudu zuwa tsakar gidan sanye da hijabi a jikinta. Gate ta buɗe masa tana ta washe baki saboda farincikin dawowarsa. Sai da ya parker motar a inda yake ajiye wa sannan ta kula da Hajiyanta da Salimah a baya. Cikin sauri ta ƙarasa rufe gate ɗin ta nufe su,a daidai wannan lokacin Yah Maheer ya riƙo hannun Hajiya yana taimaka mata ta fito daga motar. Damuwa kwance a fuskar Mahreen ta hau jero musu tambayoyin da suka sanya Hajiya sakin murmushin baƙinciki. Yah Maheer ne ya kalli Mahreen dake a cikin ruɗani ya ce mata. "Baby ki yi haƙuri mana mu shiga ciki sai na baki amsar tambayoyinki. Yanzu kafin nan maza ki je ki haɗa wa Hajiya ruwan wanka da abinci." Da sauri ta wuce sashenta ta ɗora ruwan zafi a gas zuciyar ta cike fal da tarin tambayoyi. Ruwan na tafasa ta juye a bokiti ta sirka ta kai banɗakinta,ta na kai wa Hajiya ta tashi da ƙyar Salimah na riƙe da hannunta Mahreen ta isa wajensu ta kama Hajiyan suka kai ta banɗaki,cike da kulawa Mahreen ta ce. "Ko na tsaya na taya ki wankan?" Kai Hajiya ta gyaɗa alamar eh,dan haka Salimah sai ta fita ta basu waje. Wanka mai kyau Mahreen ta yi wa Hajiya wanda ya bata ƙarfin jiki suka fito. Kai tsaye saman dinning table ta zaunar da Hajiya ta hau zuba mata abinci ta fara bata a baki,ganin ƙwalla a idon Hajiya sai ya karya zuciyar Mahreen. Cike da kulawa ta sanya hannu ta share mata wadda ta gangaro saman kuncinta. A haka Yah Maheer ya tarar da su shima ya zauna ya zuba abincin ya fara ci. Salimah na fitowa daga wanka itama ta zauna ta ci nata. Kallon Mahreen Yah Maheer yayi ya haɗe fuska ya ce. "Me yasa baki ci abinci ba yau?" Tura baki ta yi ta ce. "Ba kai bane ka ɗaga min hankali? Ka fita tun safe babu waya babu saƙo,sannan baka yi min bayanin abinda ke faruwa ba." Murmushi yayi sannan ya ce. "Wannan halin naki na yawan shiga damuwa akan abu ƙalilan shi yasa na ƙi sanar dake abinda yake faruwa. Yanzu dai ki tabbata kin zuba abinci kin ci kin ƙoshi. Idan kin gama sai mu raka Hajiya ɗakinta ta huta." "Dama Hajiya ka gyarawa wancan ɗakin?" Mahreen ta faɗa cike da farinciki maɗaukaki. Kai Yah Maheer ya gyaɗa mata yana murmushi,tsallen murna ta daka ta rungume Hajiya dake kusa da ita tana murmushi. Zama Mahreen ta yi ta hau cin abinci tana zuba musu surutu suna amsa mata. Tana gamawa suka raka Hajiya sabon ɗakinta sannan Yah Maheer ya tsaya a gaban idonsa aka bata magungunanta ta sha ta kwanta tana ta zuba masa godiya da sanya albarka. Sai da bacci ya fara ɗaukanta sannan suka yi wa Salimah sallama suka koma nasu sashen. Duk yanda Mahreen ta so ta ji dalilin dawowar Hajiyanta gidan Yah Maheer ya ƙi sanar da ita gaskiyar lamarin. Kan dole ta haƙura ta kwanta ranta fal murnar dawowar Hajiyanta kusa da ita kamar yanda take fata a koda yaushe. A ɓangaren Yah Maheer kuwa yanda ya ga rana haka ya ga dare,domin kuwa hankalinsa a matuƙar tashe yake,yana jiye wa Aabid tsoron yin mummunan ƙarshe sakamakon wulaƙanta mahaifiyarsa da yake yi a rayuwa. Babbar damuwarsa bai wuce a ce har a wannan lokacin Aabid bai kirasa ya sanar da shi abinda ya aikata ba,sannan bai nemi ya san ina Hajiyansa ta shiga ba. Me yake tunani da ya siyar da gidansu na gado ba tare da sanin kowa ba? Ko babu komai Mahreen na da haƙƙi akan dukiyar mahaifinta. Me zai yi da maƙudan kuɗaɗen da ya siyar da gidan? Shin ko dai Aabid yana cikin wata matsalar rashin kuɗi ne? Kansa ya shafa zuwa fuskarsa tare da furzar da wani irin zazzafan huci. Zama yayi a kujerar dake cikin ɗakin nasu ya furta. "Kamfaninsa na samun riba mai tarin yawa,ban ga dalilin da zai sa ya aikata wannan mummunan abun ba ba tare da yayi shawara da ni ba." Jingina yayi a kujerar yana ci gaba da jera wa ƙwaƙwalwarsa tambayoyin da ya tabbatar da babu mai amsa masa su face Aabid da kansa. Da wannan tunanin ya miƙe ya buɗe ƙofa ya leƙa su Hajiya,jin shiru babu motsin komai ya tabbatar da bacci suke yi,sai ya koma ɗakinsa yana tunanin sanya musu solar a gidan ko dan matsalar wuta da ake fama da ita,ga kuma tsananin zafi da ake zubawa,sannan Hajiya ta saba da solar saboda yanayin jikinta bata son zafi. Ɗakinsu ya koma ya shiga banɗaki ya ɗaura alwala ya fito. Abun sallah ya shimfiɗa ya hau ya tada sallah,ya jima yana jera nafilfilu kafin ya zauna yayi addu'a. Yana idarwa ya hau gado ya rintse ido yana fatan ya samu bacci ya ɗauke shi ko babu yawa. A hankali ya furta. "Ya Allah ka bani ikon samun sallar asuba akan lokaci kada na makara sakamakon jimawa da na yi ban rintsa ba." Yana gama faɗin haka ya runtse idonsa,sai dai tunanin dake cikin kansa ya hana shi samun abinda yake so. A haka aka yi kiran farko yana ta tasbihi a cikin ransa. Da misalin huɗu da arba'in Mahreen ta farka ta shiga banɗaki,brush ta yi ta ɗaura alwala ta fito ta tada nafila. Tana idarwa Yah Maheer yayi shirin masallaci ya tafi. Bayan ta yi sallar asuba ta shiga kitchen ta fara haɗa musu abun karyawa,tana tsaka da aiki Salimah ta shiga ta hau taya ta,nan da nan suka kammala soya doya da ƙwai tare da dama kunun gyaɗa,sai suka gyara gidan. Ta so ta zuba musu anan su ci dika,sai Salimah ta ce. "Hajiya ta ce na sanar dake,daga yau idan kin yi abinci a dinga kai mana namu can." "Ohhh Hajiya,to Yah Maheer ɗin baƙonta ne?" Murmushi kawai Salimah ta yi wanda ya sanya Mahreen ƙure ta da ido tana murmushi,a hankali ta ce. "Kamanninki da Addah Dijah sai suka bayyana da kika yi murmushin nan." Ƙwalla ce ta taru a idon Salimah ta miƙe da sauri ta bar sashen. Kai Mahreen ta dafe ta na jin babu daɗi a cikin ranta da ta tuna wa Salimah abinda ita kanta yana damun zuciyarta ballantana Salimah da ta fi ta kusanci da Dijah. Jiki a sanyaye ta kwashe abincin da ta zuba ta kai ɗakin Hajiyar. Rashin ganin Salimah a wajen da kuma ƙarar ruwa da ta jiyo a banɗakin ne ya tabbatar mata da wanka take yi,sai kawai ta zauna ta gaishe da Hajiya ta zuba mata abici ta kai mata gabanta. Godiya Hajiya ta yi mata tare da sanya musu albarka sannan ta ja kunun gyaɗar ta hau sha. Yah Maheer na dawowa daga masallaci ɗakinsu ya shige ya hau rama baccin da bai samu ba a daren Jiya. Mahreen kuwa ta so ta zauna su yi hira da Hajiya a haka har ta bigi cikinta ta sanar da ita dalilin dawowarsu nan da zama,amma Hajiya ta kora ta wajen mijinta,kan dole ta tafi ba dan taso ba. ************************* A ɓangaren Aabid kuwa tunda ya siyar da gidansu na gado aka tura wa Aabida kuɗin ta account ɗinta kai tsaye ya samu sauƙin matsin lambar da take yi masa. Wata iriyar soyayya take zuba masa wadda yake jin sa kamar shi kaɗai ne yayi dace da sa'ar macen aure a duniya. A ɓangaren ɗaya kuma kullum da tunanin halin da Hajiyansa take ciki zuciyarsa ke kwana ta tashi,sai dai duk da damuwar da yayi da lamarin baya marmarin zuwa ya ga halin da take ciki ballantana ya san a ina take kuma a wanne hali take. Bayan sati biyu Aabida ta kammala zuba kayan da ta yo order daga ƙasashen waje a sabuwar plazar da ta siya,da kanta ta jagoranci ma'aikatanta suka zuba kayanta da take siyarwa tana ta posting a social media tare da sanar da ƙawayenta Alhajinta ne yayi mata kyautar wajen. Aabid kuwa idan ya ga posting ɗin da ta yi sai ya tsaya yana kallon wajen yana tunani kala-kala a cikin ransa. Yau ma kamar ko da yaushe tun da asuba da Aabid ya farka bai koma bacci ba. Abun karyawa yayi musu sannan ya haɗa wa gimbiyar tashi ruwan wanka mai cike da kayan gyaran jiki kamar yanda take so. Sai da ya tabbatar komai yayi daidai yanda take so sannan ya haura sama ya taso ta. Miƙa ta yi tana hamma tare da yamutsa fuska kamar wadda ta ga kashi. Da kallo Aabid yake binta yana jin wata iriyar soyayyarta zazzafa na ƙara huda kowanne sashe na jikinsa. Kallon Aabid ta yi daga sama har ƙasa ta ɗaure fuska ta ce.......... MUGUWAR MACE. NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 5. "Wai ni don Allah Aabii ban hana ka tashi na kana tsamin dauɗa ba? Ka wuce ka je ka yi wanka bana son ƙazanta." Yawu Aabid ya haɗiya yana kallon kansa a madubin da ya mamaye ɗakin ta ko ina,a hankali ya sunsuna kansa ya kalle ta ya ce. "Sai da fa na yi wanka kuma..." "Don Allah dakata min bana son surutu,idan ka ga dama kada ka yi wankan ka zauna da dauɗa ba abinda ya dame ni bane. Ka haɗa min ruwan wankan?" Da sauri ya gyaɗa kai ya ce. "Na gama komai,sai dai yau ina so na fita da wuri akwai kayan da za a kawo daga Kura,ina so a sauke su akan idona." Taɓe baki ta yi sannan ta ce. "Duk saurin ka dai ka san ba za ka fita ba sai na gama abinda nake yi na fita,dan haka ka je ka jira ni." "Amma ina za ki je da safe? Ko yanzu da safe za ki dinga buɗe plaza ɗin?" "Yaushe muka fara ƴar tinke a tsakanin mu Aabii? Ko kuwa dan zan je na ga Innaji dole sai na faɗa maka inda zan je? Ka ga matsa ni bani da energy ɗin surutu da safen nan." Ya so ya sanar da ita muhimmancin fitarsa da wuri,amma rashin ganin fuska ne ya sanya shi komawa parlour ya zauna yana duba wayarsa. Ba tare da tunanin komai ba ya danna kiran Maheer. Wayar ta jima tana ringing kafin Yah Maheer ya amsa. Cikin yin ƙasa da murya Aabid ya ce. "Don Allah Ɗan'uwa ka je office da wuri a sauke kayan nan akan idonka. Ina da ɗan wani uziri ba zan samu damar fitowa da wuri ba." Takaici ne ya mamaye zuciyar Maheer har bai san sanda ya ce. 'Aabid kana da hankali kuwa?  Wai me yasa kai rayuwar duniya kawai ka saka a gaba kana mantawa da cewa watarana za mu mutu mu je lahira mu girbi abinda muka shuka?' "Me ya faru kake yi min waɗannan maganganun Maheer? Na aikata maka wani kuskuren ne ko saɓon Allah ka kama ni ina aikatawa?" Cike da takaici Maheer ya haɗiye yawu ya ce. 'Shikenan zan je office da wuri,sai anjima. Allah Ya ganar da kai gaskiya.' Jujjuya wayar Aabid yayi a hannunsa yana mamakin kalaman Maheer. Taɓe baki yayi sannan ya shiga ɗakinsa ya sake yin wanka kamar yanda Aabida ta buƙata. Shadda gezna ya sanya ash color ya ɗauki hular da ta dace da kayan ya sanya. Gaban madubi ya tsaya ya hau ɓarin turare tare da buɗe wajen da yake ajiye agogo ya ɗauki wanda ya dace da kayansa ya sanya a tsintsiyar hannunsa. Kallon kansa ya tsaya yi a madubi ya na shafa dogon gemunsa da ke ƙarawa kyakkyawar fuskarsa kyau. Taku ya sake yi zuwa gaban wata ƙofar glass ya buɗe ta,takalma ne kala-kala masu kyau da tsada. Babu ɓata lokaci ya cire na ƙafarsa ya sanya wanda ya dace da adonsa sannan ya rufe wajen ya fita zuwa parlour. Ko da ya isa  dinning room bai ga Aabida ba kamar yanda yayi tsammani. Waje ya samu ya zauna yana jiranta. Ta na fitowa ya hau serving ɗinta abinci ya na kallon kwalliyar da ta yi kamar mai shirin zuwa gasar zaɓen sarauniyar kyau. Ido suka haɗa ya sakar mata murmushi tare da faɗin. "A gaskiya dole na gode wa Allah da ya bani ke a matsayin matar aure na. A koda yaushe kika saka sutura kyau kike yi mata kamar domin ke aka yi ta. Idan kuwa kika saka kwalli sai idanuwanki su dinga fitar da wani haske da sheƙi mai ban sha'awa. Ba dan kar na yi ƙarya ba zan iya cewa duk duniya babu macen da ta kai ki kyau." Wani irin ƙayataccen murmushi ta yi wanda yake nuna tsantsar jin daɗin yabon da ta samu daga wajen mijin nata. Sai da ta ɗebi abinci za ta kai bakinta sannan ta yi fari da idanuwanta ta ce masa. "Ai idan ka yi ƙaryar ma ba laifi bane,domin a soyayya komai ka yi daidai ne kuma ya halatta." Da haka Aabid ya zauna a gaban Aabidah ya na kashe ta da kallon ƙauna har sai da ta kammala cin abincinta sannan ta saɓi jakarta da wayoyinta tare da makullin motarta za ta fita. Gani yayi yau ko arziƙin yafa siririn mayafin da take yi a saman kanta bata yi ba sai ta saƙala shi a hannunta irin yanda ƴammata ke yi,kamar zai ƙyale ta sai ya ji ya kasa,wani irin matsanancin kishinta yake ji kamar ya ɓoye ta daga idanun duniya. Gyaran murya yayi ya na kallonta kamar mai jin tsoron yin magana ya ce. "Amma Baby a haka za ki fita yau ko abun tatar kokon ba za ki yafa a saman kanki ba sai a hannu za ki riƙe?" Da wani irin mugun kallo ɗauke a idanuwanta ta juya ta na dubansa,nan take Aabid ya sauke ƙwayar idanuwansa ƙasa. Ganin yanda ya shiga taitayinsa ba tare da ta ce masa komai ba ne ya sanya ta sakin murmushi tare da yin ƙwafa ta sa kai ta fice daga gidan. Aabid ne ya tsaya ya kashe kayan lantarkin gidan tare da rufe ko ina sannan ya shiga motarsa mai gadi ya buɗe masa gate ya bar gidan. Tsaki yayi saboda ganin ya makara fiye da yanda ya tsara. A haka ya isa Kamfaninsa na siyar da kayan abinci. Ko da ya isa ya tarar da an gama sauke kayan har an fara loda wa a store Maheer na tsaye shi da sakatarensa suna rubuta yawan kayan da wanda aka yi asararsu a yayin saukewa ko shigarwa cikin store. Murmushi ya sakar wa Maheer wanda Maheer ɗin na ganinsa amma ya ɗauke kansa ya ci gaba da abinda yake yi. Cikin ransa yayi alƙawarin idan har Aabid bai kawo masa maganar siyar da gidan da yayi ba,da barin Hajiya ba tare da mataimaki ba shi ma har abada ba zai yi masa zancen ba. Bayan Aabid ya fito daga motarsa sai ya wuce office ɗinsa ya zauna yana duba lissafin da aka tura masa na tsawon kwanaki biyar da bai duba ba;sakamakon sauke gajiyar da ya kwaso a gida da yake yi a office. Ya na nan zaune yana danne danne a laptop tare da zabga hamma sakataren Maheer ya ƙwanƙwasa masa ƙofa,sai da ya bashi izinin shiga sannan ya buɗe ƙofar bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Takardun hannunsa ya miƙa masa sannan ya tafi. Ajiye su a gefe Aabid yayi ya ci gaba da duba abinda yake yi a ƙasan ransa yana mamakin sauya masan da Maheer yayi. A can office ɗin Maheer kuwa ya so matuƙa ya bi bayan Aabid ɗin ya kai masa takardun da kansa,amma takaicinsa da yake ji ba zai bashi dama ya yarda su haɗu ba a daidai wannan lokacin. Dan haka Allah Allah ya dinga yi ya gama abubuwan da zai yi ya wuce gida. Tin daga wannan ranar Aabid da Maheer suka koma kamar baƙin juna. Domin kuwa a ɓangaren Aabid yana ganin bai aikata komai ba da Maheer zai ɗora masa karan tsana,hasali ma tausaya masa ya kamata Maheer yayi akan halin da yake ciki na rashin hutu,daga ya gama aikin gida ya dawo office sai kace inji,shi kuma Maheer yana ganin laifinsa akan abubuwan dake faruwa a cikin rayuwarsu gaba ɗaya. **************************** A zaune Aabida ta tarar da mahaifiyarta yafe da mayafi ta na kurɓar fura ta na yi wa mai aikinta masifa kamar za ta cinye ta. Cike da ladabi matashiyar budurwa ke bata haƙuri tare da goge wajen da Innaji ta zubar da fura bisa kuskure. Ba tare da sallama ko gaisuwa ba Aabida ta zauna daɓar a kujera ta na lumshe ido. Goshinta ta shafa ta ce. "Kai Innaji kin fiya masifa,don Allah ki yi shiru ki huta wa ranki. Idan kin gama shan furar ki taso mu tafi." "Ni dai da za ki yi haƙuri a bar yaron nan haka Aabidah da ya fi. Me kike so ne ki mallaka daga gare shi wanda baki gama mallaka ba? Baki da kishiya a yanzu,kin raba shi da iyayensa da danginsa,ma'aikatansa ma sai wanda kika so yake hulɗa da su,kin raba shi da abokansa,ke mai aiki wannan baki da ita a gidanki shi yake yi miki komai,tsabar ƙulumboto da neman asiri babu inda bamu je ba,daga nan ƙasar hausa har ta yarabawa sai da muka taka da ta fulani. Ka da fa ki manta har Akwa'ibom garin inyamurai sai da muka ratsa aka yi masa mugun ɗauri da gawa mai kimanin shekaru ɗari a duniya saboda auren ku ya zamo mutu ka raba. Ki na da tabbacin za ki kai shekara tamanin ne a duniyar nan ma ballantana ɗari Aabidah?" A sheƙe Aabidah ke kallon mahaifiyarta da ke roƙarwa Aabid salama a wajen matarsa da yake masifar so kamar ransa. Cike da gatsali da isgili ta ce. "Innaji kin dai san ko da ke ko babu ke zan nausa duniya na ci gaba da neman asirin da zai kafe min Aabid ya zamo nawa ni kaɗai;ta yanda ko mutuwa na yi ba zai taɓa kallon wata ƴa mace a matsayin mace ba ballantana har ya aure ta ko? Innaji zan shiga ruwa na faɗa wuta sannan na yi ninƙaya a teku na dawwamar da fatalwata a cikin kabarin Aabid domin ko a kushewa bana so mu rabu,ina so mu kasance a tare har a aljannah. Bayan haka kina tunanin duk wannan mugun abun da nake yi a wajen wa na gado su? Ko har kin manta ke wacece? Kishiyoyi goma sha uku cif kika kora a gidan naki mijin,wasu ma fa kashe su kika sa ayi,wasu kin haukata su,wasu sun ɓace ba a san inda suke ba har yau,to shikenan ni daga farawa ta sai a ce na dakata? Sam ba zai yu ba,idan zaki tashi mu je ki tashi kawai." Waro ido mai aikin Innaji ta yi kafin cikin sauri ta kwashe kayan da take mopping ta bar wajen. Ta na zuwa kitchen ta ajiye bokitin mopping ɗin ta dafe ƙirji ta ce. "Kai ku ji min ja'irar mata,ta na irin wannan shirkar da manyan arna ke yi amma take tunanin wai a haka za ta shiga aljannah. Hummm maji ma gani ai idan tusa za ta hura wuta." Aikinta ta ci gaba da yi ta na mamakin yanda su Innaji da ƴaƴanta suke rayuwa kamar basu san kalmar la'ilaha'illallah ba. Ta na tsaka da aikinta ta jiyo Innaji na ƙwala mata kira,da sauri ta saki soson wanke-wanken ta nufi parlourn ta durƙusa har ƙasa. Ta gabanta Aabidah ta shige ta na rausaya ƙugunta da ke a cike da manyan mazaunai da cinyoyi. Muryar Innaji ce ta katse mata hanzari ta ce. "Sannu sa'idawa masu bacci da ido ɗaya,ana ruwa kuna ƙirgawa,idan kun ga hayaƙi kun san me ake dafawa a maƙota. To ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki jini, za mu fita yanzu ki kula da gidan,idan na ji kin shiga maƙota yawon gulma a bakin aikinki,dan ba a kan ki na fara sallamar masu aiki ba,kuma ba a kan ki zan gama ba. Idan waccan gantalalliyar ta dawo ki sa ido kada ta shigar min ɗaki ta yi min sata.shi kuwa wancan shashashan ki ce masa ya jira ni na dawo kada ya sake ya sake sa ƙafa ya bar gidan nan ba da izinina na balle ya sake jawo min magana. Sai na dawo." Gyaɗa kai kawai Laure ke yi tana amsawa da "To Hajiya,a dawo lafiya." Su na fita Laure ta samu waje ta kame a kujera ta na ƙarasa shanye sauran furar da Hajiya ta bari. Cike da jinjina kafurci irin na su Innaji ta jinjina kai ta ce. "Wato a ƙiyama ba dan kowa ta kansa yake yi ba,da na roƙi Allah Ya nuna min yanda za a yi wa waɗannan bayi hisabi. Ni yanzu ina ni ina tinkarar wannan da'un na ce masa kada ya sake fita? Ai ni ya fitar min da kaina daga gangar jikina idan ban yi wasa ba,ita kuwa wannan kinfi karuwar taɓargaza ta zo ta yi duk abinda taso babu ruwan Laure,ita da gidan ubanta meye nawa a ciki? Ke kanki Hajiya ba jin maganarki suke yi ba balle wata Laure ƴar aiki. Mtswww." A ɓangaren su Aabida kuwa suna fita kai tsaye hanyar barin cikin garin Kano suka ɗauka. Kasancewar ta kwana biyu bata je wajen bokan nata da ke yi mata aiki ba,gashi a kwana biyun tana yawan fama da mafarkan da bata gane kansu,shi yasa take so su koma ya bincika mata goben ta ya ga me yake shirin tunkaro rayuwarta...... MUGUWAR MACE. NA : HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 6. A bakin ƙofar gidan boka Aabidah ta tsayar da motarta sannan ta sake fesa turare a jikinta,dariya sosai Innaji ta hau yi dan ta san dalilin da ya sa Aabidah ke fesa turare. Harara Aabidah ta banka mata,sai ta saka hannu ta zuge bakinta ta yafa mayafinta ta fice daga motar tana ci gaba da dariya. Itan ma dariyar ta yi sannan ta yafa mayafinta a kafaɗa ta ɗauki jakarta da wayoyinta ta fita. Kulle motarta ta yi sannan suka shiga gidan bokan ba tare da sallama ba. Zaune suka tarar da shi ya na ta yin wasu abubuwa kamar mai ciwon farfaɗiya. Ya jima a haka kafin ya dawo hayyacinsa yana sharce zufa. Wani ɗaki ya shige su Innaji suka bishi ba tare da kowa ya tanka wa ɗan'uwansa ba.  Su na shiga suka tarar da bokan ya tanƙwashe ƙafa jan ƙallen dake jikinsa ya rufe masa iya gabansa,jikinsa ya rabu da ƙasa kamar wanda yake zaune a saman iska. Jajayen idanuwansa da ke a kulle ya buɗe ya zuba wa Aabidah su kamar zai fasa jikinta ya hango zuciyarta. Ba tare da jin tsoro ba Innaji da Aabidah suka fara yi wa bokan nasu da suka yi matuƙar imanin in dai yana raye babu su babu jin kunya kirari. Sun jima suna jinjina masa akan mugayen ayyukan da yake yi musu kafin ya ɗaga musu jelar damisar dake hannunsa yayi musu nuni da wasu ƙwarya guda biyu. Da baya da baya suka isa wajen ƙwaryar suka zauna kamar yanda suka saba. Ido ya kulle ya hau yin surkulle kafin daga baya yayi shiru. Su na jin yayi shiru suka miƙe tsaye daga saman ƙwaryar kowaccensu ta kafe ƙwaryar da ta zauna akai da ido. A gaban idanuwansu ƙwaryar farko wato wadda Innaji ta zauna ta buɗe kanta ta isa gaban boka ta tsaya a saman iska kamar yanda yayi. Kallon ƙwaryar yayi sosai sannan ƙwaryar ta juya kanta tana fuskantar Innaji. Cikin wata iriyar murya mara daɗin sauraro boka ya kalli Innaji ya ce. "Da alama yaranki bana sun yi nisan kiwo,saƙon da kika bayar a basu zai jima bai isa kunnuwansu ba." Tagumi ta zabga tana jin wani irin zafi a cikin ranta. Sosai take son ƴaƴanta bata son abinda zai taɓa rayuwarsu, shi yasa a koda yaushe take ta faɗi tashi dan ganin ta inganta musu rayuwarsu ko ta halin ƙaƙa,sai gashi rayuwar Aabidah ce kawai ta inganta a cikinsu har suka raɓu da ita suke yin walwala, Junaid da Jauhara a kullum cikin ɗakko mata magana suke. Hannu ta sanya a jakarta ta lalubo kuɗi ta jefa a cikin ƙwaryar ta koma gefe tana matsar ƙwalla. Kafin ta gama daidaita tsayuwarta ƙwaryar da Aabidah ta zauna ta buɗe kanta ta isa gaban Boka ta tsaya,ya jima sosai yana kallon ƙwaryar kafin ƙwaryar ta koma gaban Aabidah ta tsaya,shiru ta yi tana kallon ƙwaryar cike da rashin fahimta. Kai Boka ya jinjina mata sannan ya ce. "Ƙwarai da gaske. Ni ma abinda ke damu na kenan a cikin ƴan kwanakin nan game da aikin ki Aabidah. Na rasa gane dalilin da ya sa idan dai wannan mutumin ya shiga cikin aikinmu bama ganin komai sai wannan hasken mai kashe idanu. A yau ina so na baki shawara ba wai dan na gaza a aiki na ba;sai dan kawai ina so kema ki yi wani yunƙurin da zai taimaka mana ta ɓangaren ki,ina so ku sani ba koda yaushe ne ake dogara da sihiri ba. Ina so daga yau ki jawo wannan mutumin jikinki ba da tirsasawa ba ya amince ya dinga zuwa gidanki da kansa,sauran bayanin zan yi miki shi daga baya. Ke dai abinda zaki yi kawai shine ki tabbata kin gama naki ɓangaren." "Ya kai babban Boka...." "Kada ki ce komai,domin wannan na daga cikin fassarar mafarkanki. Ki je ki yi naki ɓangaren ni ma zan ci gaba da yin nawa ɓangaren kamar yanda na saba." Jinjina kai Aabidah ta yi cike da sarewar guiwa ta zira hannu a jakarta ta zaro kuɗi ta ajiye a cikin ƙwaryarta. Ɓacewar Bokan daga wajen da yake ne ya basu damar fitowa daga ɗakin da baya da baya suka bar gidan. Su na shiga mota Aabidah ta ja dogon numfashi ta shaƙi iskar cikin motar mai cike da oil perfumes da take sakawa da kuma turaren mota. Ganin Innaji na ta sharar hawaye ne ya sanya ta juya ido sama ta kunna motarta suka bar wajen. Kai tsaye gidanta suka nufa domin a ƙa'ida idan suka fita sai sun biya ta gidan Aabidah Innaji ta ci ta sha sannan ta yi guziri da duk abinda yayi mata. A bakin gate Aabidah ta tsayar da motarta tana ta danna horn kamar za ta tashi sama. A guje Laminu mai gadi ya isa ya buɗe mata gate ɗin wandonsa a hannu,da alama zagayawa yayi kuma bai gama uzirinsa ba ya taso gudun kada uwar ɗakin nasa ta balbale shi da masifa. Kamar za ta bi ta kansa da motar haka ta shige gidan da tana cin magani,juya baya Laminu yayi yana jin wani irin tsoronta na sake huda shi. A haka ya kulle gate ɗin ya tsaya yana jiran ya ji saukar ruwan masifa daga bakin Uwar ɗakin nasa. Sai dai shirun da ya ji ne ya tabbatar masa da bata da lokacinsa. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya koma banɗaki yana tsine wa talauci da yayi sanadiyyar kawo shi gidan MUGUWAR MACE kamar Aabidah. A ɓangaren su Innaji kuwa suna shiga cikin gidan ta ware ta na kalle-kalle kamar wata baƙuwa,kallon sauye-sauyen da ta gani a parlour ta hau yi tana tambayar Aabida lokacin da suka sauya wasu abubuwan tare da ƙara wasu abubuwan. Guntun tsaki Aabidah ta ja saboda yanda take jin ranta babu daɗi game da abinda boka yace mata,rai a ɓace ta ce. "Wai ke Innaji yau kika fara zuwa gidan nan ki ga sabon abu ne? Ke komai kika gani sai kin yi magana akai haba ! Idan akwai abinda kike so kawai ki yi magana na siya maki irinsa. Ni bari na shiga ciki na huta idan kin gama ki wa Laminu magana ya mayar dake gida,in kuma za ki jira ni sai yamma mu tafi plaza tare to ki jira." "To me nake yi a gidan idan na koma banda mugun tunanin halin da yaran can suka jefa kansu a ciki? Shiga ciki kawai ki yi hutawarki ƴar albarka da yamman kin ajiye ni a gida." Ɗaki Aabidah ta shige tare da bugo ƙofa ta rufe. Kai tsaye kayan jikinta ta hau cirewa sannan ta faɗa wanka,ta jima tana dirzar jikinta kafin ta fito sanye da bathrobe a jikinta kalar  purple mai haske. Kanta ɗaure da ƙaramin towel kalar bathrobe ɗin jikinta ta samu waje ta zauna a kujerar dake gaban madubinta tana shafa mai tana tunanin ta inda za ta fara hilato Maheer zuwa gidanta. Ta sani idan umarnin kawo Maheer ta bawa Aabid cikin awa ɗaya zai kawo mata shi gidan ko yana so ko baya so,to amma ta ya za ta sa Maheer zuwa gidan da kansa kuma da son ransa ba tare da ta samu matsala ba? Sanin kanta ne ita da Maheer sun tsani junansu,rayuwa suke yi kamar wuta da audiga,ko kuma na ce wuta da ruwa,shi ya tsane ta saboda halayenta da abubuwan da ta aikata a baya da wanda take kan yi a yanzu. Ita kuma ta tsane shi saboda yanda yake shiga mata hanci da ƙudindine a dikkan lamuranta,gashi uwa uba sihirinta baya tasiri akansa,kowa na tsoronta har uwar da ta kawo ta duniya da mijin da yake aurenta amma Maheer baya jin shakkar gasa mata magana ko kuma ya nuna mata kuskurenta a bainar nasi. Wannan dalilin ne ya sanya suka zamo kamar wasu manyan abokan gabar junansu. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta samu turarukanta ta fesa ta shafa na shafawa tare da goga roll on a hammatarta. Tana gamawa ta isa gaban dogon ɗakin da ma'ajiyar sutura da takalma da jakarta suke. Buɗe ƙofar ta yi ta shiga tana duba kayanta dake hange kamar a shago. Tsaki ta ja tana duddubawa tana yin wurgi da duk wanda bai yi mata ba. Cike da damuwa a ranta ta furta. "Bani da kayan sakawa ma ni,ina jin zuwa gobe zan sa Aabii ya kwashe kayan nan na zuba wasu." Da ƙyar ta tsayar da hannunta akan wata yaloluwar riga mai kyau kalar purple mai cizawa,a wajen ta zame rigar jikinta tare da towel ɗin kanta ta sanya rigar ta fito tana ɗaure gashin dokin da ta saka ya zuba har gadon bayanta. Kai tsaye saman gado ta haye ta rufa tana hamma. A haka bacci mai cike da mugayen mafarkan Bokanta na saduwa da ita ya ci karfinta. A can parlour kuwa Innaji ce zaune a saman dinning table tana ta cin abinda duk yayi mata,domin kuwa sam ba sa rabo da soyayyan naman kaza,naman rago da dambun nama wanda Aabid kan yi order akai-akai. Shayin da ta haɗa mai kauri take firfitawa da bakinta kafin ta kai kofin ta kurɓa tana girgiza kai cike da jin daɗi. Sai da ta ci ta ƙoshi ta samu mazubi ta kwashi abinda take so a gidan sannan ta koma ɗakin baƙi ta kwanta dan ta huce gajiya. Kasa bacci ta yi,dan haka sai ta zaro wayarta ta kunna data ta shiga social media tana kallon videos tana sheƙa dariya cike da nishaɗi. A haka bacci ya ɗauke ta har aka yi azahar da la'asar duk basu farka ba. Da misalin shida na yamma Aabidah ta fito cikin shirin fita tana sauri,gaba ɗaya ta manta da Innaji a gidan har sai da idanuwanta suka sauka akan  kayan abinci da na ƙwalamar da Innajin ta ɗiba. Tsaki ta ja sannan ta shiga ɗakin da takan sauka idan ta zo ta hau buga ƙofar da ƙarfi. A firgice dattijuwar ta fito tana ɗaura ɗankwalinta da ya kunce. Ganin Aabidah cikin shiri ne ya sanya ta komawa ɗakin da sauri ta ɗakko jakarta da mayafinta tana faɗin. "Ohh kin ga gari har ya risina ina nan ina bacci. Mu je na kwashi kayana ki ajiye ni a gida." Yamutsa fuska Aabidah ta yi sannan ta kalli agogon hannunta ta ce. "Gaskiya Innaji sai dai na wuce plaza da ke Isuhu ya kai ki gidan,kamar yanda kika ga lokaci ya tafi ni ba zan samu damar kai ki ba." Washe baki Innaji ta yi ta ce. "Ai hakan ma babu damuwa. Shi yasa na ce miki ki ajiye min direba da mota saboda irin haka." "Hmmm ba zan sake yin wannan gangancin ba Junaid ya takaice ni." Jinjina kai Innaji ta yi jiki a mace ta kwashe kayan da ta ɗiba ta yi gaba,ganin yanda Innaji ta shiga damuwa sai zuciyar Aabida ta risina kaɗan,cike da tura baki ta karɓi jakar Innaji ta yi gaba. Su na fita ta rufe gidan suka shiga mota suka bar gidan. Tin daga nesa Aabid dake dawowa ya hangi motar matar tasa na fita daga gida. Wani irin abu ne ya caki zuciyarsa wanda bai isa ya bayyana shi da fatar bakinsa ba. Jiki a mace ya ci gaba da tuƙi ya isa gidansa a gajiye. Sai dai ya na shiga cikin gidan ya tarar da aikin da bai isa ya kwanta ya huta ba face ya kimtsa ko ina gudun kada matar gidan ta dawo ta tarar da datti ta balbale shi da masifa........ MUGUWAR MACE. NA : HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Za ku iya fara payment ɗin littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta 09031416423.* *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500.* *Skin oil 2500.* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 7. A gajiye Aabid ya fito daga wanka ɗaure da towel a jikinsa ya haye gado ya kwanta yana lumshe idanuwansa. Yunwar da ta fara neman agaji a tumbinsa ce ta sanya shi jan dogon tsaki ya yi juyi tare da ɗakko wayarsa da ya ajiye a bakin gado tun a lokacin da ya shiga ɗakin. Zuciyarsa na suya saboda tinanin abinda zai iya tararwa a cikin wayar ya buɗe password ya shiga TikTok,kai tsaye sunan account ɗin Aabidah mai suna Aaby142 ya shiga. Wani irin yawu ya haɗiye mai tsananin ɗaci saboda ganin sabon posting ɗinta da ta yi ita da yaron shagonta Mai suna Isuhu. Ransa ne yayi bala'in ɓaci ya sake shiga video na gaba yana jin ransa na ƙara ɓaci. Aabidah ce ke tafe tana rausaya mazaunanta da ƙirjinta sanye da ɗaya daga cikin sababbin kayayyakin da ta yi order tana tallata wa mutane tare da yin juyi da fari kamar wadda bata da igiyoyin auren kowa akanta. A haka suka dinga zagaye plaza ɗin tana ci gaba da nuna wa mutane irin kayayyakin da take siyarwa. Videos ɗin su na baya ya koma yana sake gani cike da ɓacin rai. Jin kansa na yi masa matsanancin ciwo ne ya sanya shi tashi da ƙyar ya shiga wajen da kayansa suke ya samu na bacci masu santsi ya saka. Sai da ya feshe jikinsa da turaruka masu daɗin ƙamshi sannan ya sauka ƙasa ya nufi wajen dinning table, ya na zuwa ya buɗe ya ga babu fiye da rabin naman dake saman wajen. Murmushi ya saki kawai ya girgiza kai,cike da sanyin murya ya ce. "Hajiya Innaji kenan." Zama yayi ya haɗa wa kansa shayi mai kauri ya buɗe mazubin dambun nama da cincin ya ci ya ƙoshi sannan ya jingina da kujerar yana jiran ya ɗan faɗa masa sannan ya je ya ɗora sassauƙan abincin da gimbiyar tasa za ta ci idan ta dawo. Ƙarar da wayarsa ta yi ne ya sanya shi miƙa hannu ya ɗauka. Notification ɗin da ya gani ne ya girgiza shi,cikin sauri ya samu waje ya zauna da kyau yana ƙara gwale idonsa yana kallon sabon videon da Aabidah ta ɗora a shafinta. Wani irin yawu ya haɗiya mai ɗaci kafin ya ce. "Me yasa Baby take zubar min da mutunci ne a garin nan? Babu wanda bai san ta a matsayin matata ba amma take mu'amala da irin matan nan marasa kamun kai da sunan abokan business. Ko ina ta baro abun tatar kokon da take yafawa a matsayin mayafi kuma?" Sake kallon fancy restaurant ɗin da suka je ya yi. Waje ne da ya amsa sunan sa wajen cin abinci mai tsananin tsada a cikin garin Kano, waje ne da a ƙalla kafin mutum ya barshi sai ya kashe dubunnai ɗaruruwa. Aabid bai gama tsinkewa da lamarin Aabidah ba har sai da ya ji a cikin videon tana faɗin. 'Kowa yayi order ɗin abinda zai ci its on me.' Kirari matan da take tare da su suka hau yi mata su na jinjina mata tare da sake nuna mata ita ɗin ta kai inda kowacce mace wayayyiya kuma mai aji ta kai. Fari kawai ta yi da idanuwanta masu tsananin kyau sannan ta gyara zamanta tana latsa wayarta. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Aabid ya sauke sannan ya wuce sama ya haye gado ya kwanta,domin ya tabbata ko yayi girkin ma ba ci za ta yi ba,dan haka sai ya rage hasken fitilar ɗakin kawai ya rintse ido yana fatan bacci ya ɗauke shi;ko gajiyar da ya kwaso za ta yi masa sauƙi. A hankali ya rungume pillow yana sauke numfashi cike da ƙunar rai,cikin sanyin murya ya ce. "Dijahna ina kike? Ina kewar ki sosai,ki dawo wajen masoyinki mai ƙaunarki da gaskiya,na yi alƙawari ba zan sake barin ki matsa daga inda nake ba ko da da ƙiftawar ido ne....." Cike da sambatu na tsananin ƙauna,kewa da bege Aabid yayi bacci. A ɓangaren Aabidah kuwa bata dawo gida ba sai sha ɗaya da rabi na dare. Ta na dawowa ta wuce ɗakinta ta cire kayanta ta watsar a ƙasa ta shige wanka. Kai tsaye kayan bacci ta saka ta fesa turarukanta sannan ta saka hula a kanta ta nufi ɗakin Aabid. Kwance ta ganshi yana bacci rungume da pillow yana murmushi kamar ƙaramin yaron da yake mafarkin kansa a ɗakin alewa. Murmushi ta saki tana jin wani irin son sa da ƙaunarsa na sake ratsa zuciyarta. Sosai take son Aabid da kishinsa shi yasa ta tsaya tsayin daka ta raba shi da kowa da kuma duk abinda take ganin zai kawo mata tsaiko ko ya zamo kishiyarta a zuciyarsa. Tsaki ta yi da ta tina har a wannan lokacin ta kasa raba tsakaninsa da Maheer. Cike da takun ƙasaita da jin kai ta nufi saman gadon Aabid ta haye,sai da ta zame rigar dake saman kayan baccinta sannan ta zare masa pillown da ya rungume ta maye gurbin pillown da jikinta. Cikin magagin bacci Aabid ya rungume ta ya manna ta da jikinsa ya ce. "I love you so much Dijahna.." Wani irin juyi Aabida ta yi ta miƙe zaune tana kallon Aabid cike da matsanancin tashin hankali a cikin manyan idanuwanta da ta waro waje. Ƙirjinta dake barazanar fashewa ta sanya hannu ta dafe tare da fizge hular dake kanta ta hau firfita da ita. Wata iriyar dariya ta ji Aabid ya saki ya na kara hannu a fuskarsa tare da kiran sunan matar da ta tsana sama da kowa a duniya. Jinin jikinta ne ya hau tafarfasa,nan da nan jikinta ya hau rawa ta hau tsiyayar da zufa. Hankali a tashe ta sauka daga gadon Aabid ta nufi ɗakinta cike da matsananciyar damuwa. Ta na shiga ɗakin ta kulle ƙofa ta cire wayarta da ta sanya a caji ta hau nemo lamabar wayar Innaji. Cike da magagin bacci Innaji ta amsa wayar tana faɗin. 'Wai ke sau nawa zan faɗa miki idan kika dawo daga yawonki ki dena tashi na? Ki na da makullinki amma dan ɗaukan alhaki....' "Innaji ni ce Aabidah buɗe idonki da kyau ki kuma buɗe zuciyarki saboda ki fahimci abinda zan sanar da ke." Da jin kalaman Aabidah sai Innaji ta wartsake daga magagin baccin da take yi;ta tashi ta zauna da kyau tana sake manna wayar a kunnenta kamar mai tsoron kada kalma ɗaya da Aabidah za ta sanar da ita ta kufce mata. Cike da damuwa Aabidah ta mayar da hawayen dake barazanar zubo mata daga idanuwanta zuwa saman kuncinta ta ce. "Innaji na shiga uku na lalace,rayuwata na gab da ƙare wa..." 'Aabidah boka ya duba maki na kusa mutuwa ne na ji kina irin waɗannan kalaman?' "Yo Innaji idan mutuwa kika kusa yi ai lokacinki ne yayi. Tashin hankalin da nake ciki ya ninka zancen mutuwa Innaji." 'To dan ubanki ki yi sauri ki sanar dani abinda yake faruwa kafin jini na ya fi yanda yake hawa.' "Innaji Aabid ne yake ambaton sunan Dijah a bakinsa. Innaji na shiga uku na lalace rayuwata ta zo ƙarshe." Ƙirji Innaji ta dafe tare da zaro ido waje ta ce. 'Ke ki bari dan manzo? To garin yaya aka yi ya ke ambaton sunan wannan matsiyaciyar yarinyar? Anya Aabidah baki tone wani ƙullin ba kuwa cikin rashin sani?' "Haba Innaji ta yaya zan tone abinda na binne domin samun kwanciyar hankali na? Ni dai Innaji don Allah gobe ki shirya mu koma wajen Boka mu ji abinda yake faruwa." 'Aabidah ba fa zai yuwu mu ƙare rayuwarmu a bin....' Cike da tsawa da rashin kunya Aabidah ta miƙe tsaye ta ce wa mahaifiyarta. "Bin hanya da gidajen bokaye su ne abinda muka taso muka ga kina yi,dan haka dole ne ki taimaka min na mallaki zuciyar mijina ta yanda ko a bacci ko a zahiri bana son na sake jin sunan ko da kare ne in dai ba nawa ba a bakinsa." Wani irin yawun takaici Innaji ta shanye tare da sassauta muryarta ta ce. 'Shikenan Aabidah ki shirya daga nan zuwa safiya sai mu koma wajen Boka mu ji. Amma ni dai da zaki haƙura mu ci gaba d...' "Ke a zamaninki kin yi haƙuri kin zauna da kishiya ne Innaji?" Kamar Aabidah na ganinta haka Innaji ta girgiza kai ta na so ta lallashi ƴar tata da ta fi so sama da kowa a cikin yaranta. Sai dai kafin ta buɗe baki ta sake cewa wani abu Aabidah ta riga ta da cewa. "Tom kamar yanda baki haƙura kin zauna da kishiya ba,ni ma babu wani dan iskan da ya isa ya sani zama da kishiya ko da kuwa ta aljanu ce da ba ganinta zan yi ba." 'To na ji, yanzu ki kwantar da hankalinki ki kwanta ki huta;idan yaso da safe sai mu shirya mu je wajen Bokan.' Kukan da Aabidah ke ta riƙe wa ne ya kuɓuce mata,da ƙarfi ta sake shi ta hau rerawa kamar waƙa,jin yanda take kuka babu mai lallashinta sai ya karya zuciyar Innaji ta kashe wayar ta kwanta tana jin tsanar duk wata macen da ke da kishiya. Ji take yi kamar ta jawo gobe ta gaggauta zuwa domin su je wajen bokan da zai samar musu da maganin matsalarsu. (Subhanallah) A ɓangaren Aabidah kuwa kuka ta dinga yi har idanuwanta sai da suka kumbura suka yi jawur kamar gauta. A haka baccin wahala ya ɗauke ta ba tare da ta gyara kwanciyarta ba. Washegari da sassafe....... MUGUWAR MACE. NA : HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Za ku iya fara payment ɗin littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta 09031416423.* *Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.* *Slimming Tea 6k.* *Slimming oil 3500.* *Body scrub 3500* *Skin oil 2500* *Location Kano.* *Phone No 09031416423.* PAGE 8. Aabid yayi matuƙar mamakin ganin Aabidah cikin shirin fita tin kafin ya farka. Kallon da take binsa da shi ne ya saka shi a ruɗani,domin kuwa kallo ne da ya kasa fassara abinda yake maƙale a cikin zuciyarta. Ba tare da ta ce masa ci kanka ba ta gegare shi ta fice daga ɗakinta riƙe da jakarta da makullin motarta. Cikin sauri ya bi bayanta suka hau sauka daga saman bene; bakinsa har rawa yake yi wajen tambayarta dalilin fitar ta da sassafe kuma cikin gaggawa. Tsayawa ta yi cak ta shaƙi iska sosai a huhunta kafin ta fesar ta ce. "Fita a daidai wannan lokacin ta zame mini dole Aabii. Ban sani ba ashe ni ina can ina dukan taiki na bar jaki a gefe yana cin karansa babu babbaka. Amma daga yau zan gyara duk wani abu da ke neman lalace min. Sai na dawo." Cike da ruɗani Aabid ya buɗe baki zai yi magana;Aabidah ta ɗaga hannunta tare da wurga masa kallon gargaɗi. Kan dole Aabid ya shanye maganarsa ya bi bayanta ya raka ta har jikin motarta yana yi mata ƙorafin ko karyawa bata tsaya ta yi ba. Ba tare da ta ce masa komai ba ta ja motarta mai gadi ya buɗe mata gate ta fita daga gidan. Ajiyar zuciya Aabid ya sauke mai ƙarfi sannan ya koma cikin gidansa yana safa da marwa,tin daren jiya yake jin wasu sauye-sauye a cikin jikinsa wanda ya rasa dalilin faruwarsu,sai dai kawai abinda ya sani shine ƙwaƙwalwa da zuciyarsa suna tuna masa wani abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwarsa. Waje ya samu ya zauna a saman kujera tare da lumshe kyawawan idanuwansa. Hoton kyakkyawar fuskar da ya jima bai gani ba;kuma bai ji muryarta ba ce ta gilma a idanuwansa. Cikin sauri ya buɗe idanuwansa yana sauraron ƙarar bugun zuciyarsa da ya cika kunnuwansa. Muryarta ya ke ji tana ratsa cikin kunnuwansa kamar a wannan lokacin ne take ficewa a rayuwarsa. Cikin sauri ya miƙe tsaye ya hau sama da sauri. Kai tsaye makullin motarsa ya ɗauka ba tare da ya sauya kayan jikinsa ba ya fita daga gidan ya faɗa motarsa. *Aabidah.* Tun kafin ta isa gidan nasu take kiran Innaji wadda ta shirya cikin atamparta riga da zani da mayafi ta tsaya a bakin gate tana jiran isowar gudan jinin nata. Aabidah na tsayar da mota Innaji ta faɗa suka rankaya gidan Bokansu wanda suka bawa yarda da imaninsu gaba ɗaya. Su na zuwa suka tarar da shi zaune yana jiransu. Kuka Aabidah ta fashe da shi kamar ranta zai fita ta ce. "Me yasa? Me yasa hannun agogo ke neman koma mana baya? A zato na ka gama kawar mana da matsalar Khadijatou har abada,me yasa Aabii ya ke tuna ta bayan tsawon lokacin nan da aka ɗauka? Ya kai Bokan da ke share min duk wani ɗigon hawayena da yake zuba ka sani idan har Dijah ta dawo cikin rayuwarmu tawa ta ƙare. Bana jin Aabii zai sake kallo na da gashi ballantana har ya bani soyayyarsa da kulawarsa. Na tsani kishiya,bana ƙaunarta,bana son duk wata mace da za ta raɓi mijina ko da kuwa mahaifiyarsa ce. Ya mai share min kukana ka yi wani abu akan wannan matsalar da ta ke neman hana rayuwata sukuni." Wani irin gurnani Boka yayi sannan ya kafe kwaryar dake gabansa da ido,nan take ruwa ya cika ƙwaryar ba tare da su Aabidah sun ga lokacin da ake zuba ruwan ba. Cike da ƙwarewa a harkar tsafi boka ya yi siddabarun da ƙwaryar ta isa gaban su Aabidah da kanta. Cikin wata iriyar murya ya ce musu. "Kalli nan ki gani. Wannan shine babban dalilin da ya sa aikin da muka yi miki ya warware. Kada ki manta maƙabartar da muka yi amfani da gawar cikinta mai kimanin shekaru ɗari a binne a cikin ƙasa tsohuwar maƙabarta ce. Wasu garuruwan sukan siyar da irin tsofaffin maƙabartun nan zuwa ga gwamnati ko wata ƙungiyar ko kuma wasu ɗaiɗaikun mutanen. Wannan dalilin ne ya sa aka samu wata ƙungiya mai zaman kanta da take gina makarantun islama da masallatai tare da gidajen marayu ta siyi maƙabarta ta gyara;ta gina Makarantar Islamiyya a wajen. Yawan karanta ƙur'ani da addu'o'in da ake yi a wajen ne yayi tasirin karya sihirin da duk wani boka ko matsafi yayi a cikin wannan maƙabartar ciki kuwa har da namu." "Wayyoo ni Aabidah na shiga uku na lalace,shikenan Innaji rayuwata ta zo ƙarshe,na tabbata a yanzu ko Aabii bai rabu da ni ba to fa tabbas zai nemo wannan mayyar yarinyar ne a duk inda take." "Ko kuma ta dawo da kanta ba. Kada ki manta da kanta ta bar gidan cikin tursasawa da kuma turen shaiɗanun aljanun da muka yi mata,kin ga kenan dawowarta gidan mijinta ko haɗuwarsu da komawar aurensu zai iya faruwa ta kowacce hanya." A hasale Aabidah ta kalli Boka ta ce. "Kenan kana nufin za ka bari su sake haɗuwa a waje ɗaya su ci gaba da rayuwa a inuwa ɗaya? Meye amfanin maƙudan kuɗaɗen da nake kashewa akan ayyukan da kake ikirarin kana yi min? Na ra...." Wata iriyar shaƙa Aabidah ta ji an yi wa wuyanta kamar za a raba ta da numfashinta,Innaji na ganin haka ta zube guiwowinta a gaban Boka ta hau bashi haƙuri. Ransa a matuƙar ɓace ya sauko daga wajen da ya maƙale a sama ya na nuna Aabidah ya ce. "Shi yasa na fi ƙaunar rayuwa da aljanu,domin su in dai za ka dinga yi musu abinda suke so za su yi maka hidima,kai ko da ba za ka musu abinda suke so ba matsawar za su ci su sha to fa za su iya zama tare da kai ba tare da sun yi maka butulci ba. Kin manta irin taimakon da na yi miki a baya? Kin manta irin tudu da gangaren da na ratsa saboda biyan buƙatarki? Me yasa ku bil'adama kuke da mantuwa da butulci?" Wurgi yayi da Aabidah ta faɗi ƙasa ta buga kanta a jikin gini,kuka ta fashe da shi tare da zubewa a saman guiwowinta tana kuka tana bawa Boka haƙuri. Cike da matsanancin fushi ya ce. "Ku tashi ku bani waje marasa godiya kawai,maza ku tashi kafin na sa aljanu su shanye min ƙafafuwanku." Cikin sauri Innaji ta saɓi jakarta sannan ta ɗauki jakar Aabidah ta riƙe a hannunta. Mayafinta na zamewa kamar zai faɗi amma ko ta kansa bata bi ba ta kama Aabidah da gefen kanta ya kurje yayi fari tas ko ɗigon jini babu a wajen. A dudduƙe suka fita suna bawa Boka haƙuri. Cikin tsawa ya ce. "Ku tafi ku jira har sai na neme ku da kai na. Ku da kanku kun sani da ni da ku duk akan ɓata muke,idan Allah Ya hukunta faruwar abu to fa dole sai ya faru. Dama ce kawai yake ara mana muke yin abinda muke so,dan haka ku tafi ku bani lokaci na yi bincike na samo mafita." Da jin haka sai hankalin Aabidah ya kwanta. Godiya suka dinga yi wa bokan sannan suka tafi cike da tarin damuwa da tsamin jiki. Sun jima a cikin mota Aabidah na saka tissue ta na goge ciwonta da ya fara tsattsafo da wani ruwan azaba. Da ƙyar ta iya tada motarta suka bar gidan Bokan suka nufi cikin gari. Suna tafiya Boka ya hau bincike akan Aabid,nan ya gano yana daf da isa gidan Maheer,cikin sauri ya hau yin wani irin tsafi akan Aabid. Ya na gamawa ya shafe ruwan hoton Aabid ya ɓace. *Aabid.* Tinda ya baro gidansa yake tuna duk wata rayuwarsa da ta gabata kamar wanda aka kai cinema aka kunna wa video yake kallo. Wasu irin zafafan hawaye ke sauka daga kwarmin idanuwansa wanda suka sa har baya iya ganin gabansa. Bugun zuciyarsa da ya tsananta ne ya sanya shi samun waje a bakin titi ya tsayar da motarsa tare da kifa kansa a jikin sitiyarin motar. Hannu ɗaya ya saka a ƙirjinsa ya dafe saitin zuciyarsa dake barazanar tarwatse masa. Ya jima a haka kafin ya samu nutsuwa ta fara ziyartarsa. Cike da matsananciyar kewa tare da kawa zucin ganin mahaifiyarsa da mace mafi soyuwa a ransa ya tayar da motar ya nufi gidan Maheer,domin kuwa shi kaɗai ne wanda zai yi masa jagora domin dawo da faricikin rayuwarsa da ya rasa na tsawon shekaru. Yana isa ƙofar gidan Aabid ya tsayar da motarsa a bakin gate ɗin gidan ya taka ya hau ƙwanƙwasa ƙofar gidan. Yana nan tsaye ya ji wani irin faɗuwar gaba ta kama shi har sai da ya ji kamar jiri na ɗibansa,babu jimawa kansa ya sara masa da ƙarfi, kamar ɗaukewar wutar nepa haka ya nemi tunaninsa na baya ya rasa,nan take ya hau duba kayan jikinsa da wajen da yake tsaye. Cike da matsanancin mamaki ya juya da sauri ya shige motarsa,yana jin muryar Maheer na faɗin. "Waye?" Cikin sauri ya tada motarsa ya bar ƙofar gidan da mugun gudu. Ko da Maheer ya fito ya buɗe ƙofar gidan sai bai ga kowa ba,cike da mamakin wanda ya zo yana yi musu bugu kamar zai ɓalle gate ɗin gidan ya koma ciki. Kai tsaye sashen su Hajiya ya nufa ya tarar da Salimah na shanya zannuwan Hajiya a igiya. Murmushi ya sakar mata ya ce. "Sannu Auta,Allah Ya yi miki albarka." "Amin Yah Maheer;barka da safiya." "Barka dai Auta,Ya jikin Hajiya? Ina fatan yau kun samu bacci sosai ko?" "Eh Alhamdulillah tinda ta sha maganin nan jiya take bacci bata farka ba sai da asuba,ta na idar da sallah ko azkar bata ƙarasa ba bacci ya ɗauke ta." "Masha Allah. Allah Ya ƙara mata lafiya,ke kuma Allah Ya ƙara baki juriyar ci gaba da kulawa da ita ba tare da gajiyawa ba." Nan take muryar Salimah ta hau rawa,cike da matsananciyar damuwa ta ce. "Kula da Hajiya ya zame mini dole Yah Maheer,kada ka manta bani da kowa bani da komai,ku ne gata na,kuma ku ne ahali na da nake gani na ji daɗi a raina." Jinjina kai kawai Yah Maheer yayi ya wuce cikin sashen su cike da tausayin Salimah a cikin ransa. *Aabidah.* Kai tsaye gidan Innaji suka yi wa tsinke. Cike da damuwa Innaji ta ɗakko zuma ta shafa wa Aabidah a ciwonta da ke yi mata zogin azaba. Cikin tsananin damuwa Aabidah ta kau da kanta daga hannun Innaji dake lallaɓata tana bata haƙuri. "Innaji kada ki damu da ciwon dake kai na,ina so ki mayar da hankali akan warkar min da ciwon dake cikin zuciyata. Innaji bana son Aabii ya rabu da ni,ina son sa ba zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da shi ba a duniyar nan." "Haba Aabidah ya kike magana irin wannan kamar an ce miki ko da Khadijatou ta dawo cikin rayuwar Aabid zai iya rayuwa babu ke? Ina son ki dinga tunawa da mun riga da mun kama Aabid kamu na har abada. Aabid ba zai taɓa ganin Khadijatou ba ballantana tarin sihirin da muka yi musu ya warware. Ke ina mai tabbatar maki da cewa ko da sun tuna da juna ba zamu taɓa yarda su haɗu ba;domin haɗuwarsu tafi tunawa da junansu hatsari a wajen mu." Wani sabon kuka Aabidah ta rushe da shi sannan ta ce. "Why me? Why meeee? Me yasa sai da nutsuwa da kwanciyar hankali ta same ni;ariziƙi na ya nunku,ina zaune da mijina lafiya wannan matsalolin za su kunno min kai? Ya Allah ka sake ara min dama ka nesanta Khadijatou da Mijina,Ya Allah ka sake raba tsakaninsu rabuwa ta har abada...... MUGUWAR MACE. NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Za ku iya fara payment ɗin littafin MUGUWAR MACE da yake akan farashin 1k ta 9031416423,ku tura shaidar biya ta 09031416423.* PAGE 9. Sai da Innaji ta nisa sannan ta miƙe tsaye ta mayar da zumar da ta ɗakko mazauninta. Cike da mutuwar jiki ta kalli Aabidah dake gunjin kuka ta ce. "To yanzu ya za ki yi da maganar Boka da ya ce ki janyo wannan yaron Maheer jikinki?" A hasale Aabidah ta ce. "Wai ke Innaji me yasa wani lokacin sai ki dinga yin magana ba kya tunani ne? Ni yanzu ina ruwana da wani Maheer? Ai sawun giwa ya take na raƙumi Innaji, yanzu babbar damuwa ta a duniya bata wuce na san inda Khadijatou take ba,ina so na nemo ta da kaina kafin Aabii ya ganta. Ina so na kashe ta har lahira kowa ma ya huta. Wannan karon ba zan yi kuskure ba wajen aikata inda ba za ta dawo cikin rayuwarmu ba har abada." Labule Jauharah ta buɗe ta na kallon su Aabidah. A razane Aabidah ta kai dubanta wajen da ta ji motsi,ido huɗu suka yi da Jauharah da ke a buge sai lumshe idanuwa take yi kamar mai jin bacci. Tsaki Aabidah ta ja mai ƙarfi ta kalli Innaji ta ce. "Yaushe wannan yarinyar ta dawo gida daga yawon dandin da ta tafi?" Hannu Innaji ta ware tana kyaɓe baki ta ce. "Yanda kika ganta haka na ganta,dan ba a gidan nan ta kwana ba. Ai ita da wancan da'un ba za ki taɓa sanin lokacin shigarsu ba ballantana fitar su. Ke! yaushe kika dawo gidan?" Cikin tafiyar ƴan maye Jauharah ta isa kujera mafi kusa da ita ta zauna tana lumshe idanuwa. Cikin muryarta mai kama da ta matan da suka tsufa suna busa sigari ta ce. "Yanzu Mine ta ajiye ni ta tafi. Babbar Yayaaa na ji kina wata magana akan waccan mujiyar, a ina take na aika yara a kawar miki da ita cikin sirri? Kin san yanda kike bani farinciki dole ne nima na rama wa kura a niyarta." Tsaki Aabidah ta ja mai tsawo kafin ta ce. "A hakan ne za ki yi min abinda zan mora Jauharah? Allah ya wadaran rayuwar da kika jefa kanki a ciki. Ke kan ki baki taimaki kanki ba ballantana ki taimake ni. Na kashe kuɗaɗena a banza akan ku,na ɓata lokaci na da energy na duk akan ku,daga ƙarshe kun zamo marasa amfani. Tashi ki bar nan kafin na huce takaicin dake cikin raina akan ki." Tsuke baki Jauharah ta yi ta tashi tana tangaɗi ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa. Tsaki Aabidah ta ja ta dafe kanta tana ci gaba da kukanta wanda take jin sanyi a ranta a duk saukar hawaye ɗaya daga idanuwanta. A wannan rana a gidansu ta kai azahar saboda tsoron kada ta koma gida Aabid ya sake bijiro da zancen Khadijatou ba ta jin zuciyarta za ta iya ɗaukan jin kalmar sunan babbar maƙiyyarta a bakin mutumin da ta fi so sama da kowa a rayuwarta. A duk bugawar sa'a ta agogo sai gaban Aabidah ya faɗi. Ta kasa ci ta kasa sha saboda damuwa da zullumi. Innaji kuwa Laure ta sa ta dafa mata abinci mai rai da lafiya da naman kaza ta ci ta ƙoshi ta kora da lemo. Ganin yanda Innaji ke warkajaminta ba tare da jimamin halin da Aabidah ke ciki bane ya sanya Aabidahn ɗaukan makullin motarta da mayafinta ta shuri takalmanta babu ko sallama ta bar gidan. Kai tsaye gidan ƙawarta kuma aminiyar cin mushenta ta nufa. Tin daga bakin gate mai gadi ya san yau Hajiya Aabidah bata cikin hayyacinta;duba da irin tuƙin da take yi. A gaggauce ta kashe motarta ta buɗe ta shiga gidan Hajiya Zaitunah. Zaune ta ga Hajiyan ita da yaranta suna kallo. Kallo ɗaya yaran suka yi wa Aabidah suka kawar da kawunansu suka ci gaba da kallon su, yara ne da aka sangarta suke jin kansu,dan haka ko gaisuwa bata haɗa su da kowa sai wanda suka ga dama. Ganin irin halin da Aabidah ke ciki ne ya sanya Hajiya Zaitunah wadda ta girmi Aabidah da shekaru takwas a duniya miƙe wa ta bi bayanta zuwa ɗakinta. Su na shiga Aabidah ta zauna a bakin gado ta rushe da kuka. Cike da matsananciyar damuwa Hajiya Zaitunah ta dafa bayan Aabidah ta ce. "Ah ah Ƙawata lafiya kike irin wannan kukan? Me ya samu Aabii ɗin naki? Ina fatan dai ba sakin...." "Allah Ya kiyaye Aabii ya sake ni. Ai ni da shi mutuwa ce za ta raba mu,walau ya binne ni ko kuma ni na binne shi. Ƙawata matsala ce mai girma ta taso min wadda muka jima da haƙa rami mai zurfi muka binne. Sai kuma gashi ta ɓullo a lokacin da bamu yi zato ko tsammani ba." Waro ido Hajiya Zaitunah ta yi tare da dafe ƙirji ta ce. "Kar dai ki ce min wannan mayyar ta dawo cikin rayuwarku?" "Wai ke me yasa ba kya faɗan alkhairi ne? In dai boka na raye na yi imanin Khadijatou ba za ta taɓa dawowa cikin rayuwarmu ba." "To meye zai ɗaga miki hankali haka bayan kin san ba dawowa za ta yi ba? Ko dai kema kin fara fuskantar irin matsalar da nake fuskanta ne?" Ajiyar zuciya Aabidah ta sauke tare da goge majinar da ke shirin gangarowa a hancinta da tissue ɗin dake gefen gadon Hajiya Zaitunah. Cike da damuwa ta labarta wa ƙawar tata abinda ke faruwa. Salati Hajiya Zaitunah ta yi sannan ta ce. "To ai wannan maganar taki daidai take da dawowar Khadijatou cikin rayuwarku Aabidah. Abu ne fa da muka riga muka sani amma muke take sanin,shi asiri lokaci ne da shi komai daɗewarsa a jikin bawa. Idan har kika ga bai karye ba to fa mutumin da aka yi wa asirin ya mutu,ballantana Khadijatoun da na sani mai taurin rai ce da kafiya,kada fa ki manta abubuwan da muka ƙulla mata  a baya amma yarinyar nan sai da ta tsallake su. Dan haka ni dai shawarar da zan baki shine,ki koma wajen Boka ya sake maimaita sihirin da aka yi a can baya,ni kuma na yi miki alƙawarin yawata wa cikin garin kano da kewaye dan taya ki neman wajen binnewa kamar yanda muka yi a wancan lokacin." Hawaye ne suka zubo wa Aabidah a karo na babu adadi. Muryarta na rawa ta ce. "Wannan lissafin naki duk ba mai yuwa bane inji Boka. Domin kuwa da faɗa ma muka rabu,dubi nan ɗina,shi ne ya shaƙe ni ya buga da jikin gini har sai da wajen ya kwaile." "Da dikkan alamu hannunsa ya fara yin sanyi gaskiya shi yasa lamuranmu ke ta taɓarɓarewa. Yanzu ina so ki shirya zuwa jibi zan kai ki wajen wani sabon boka da na ji labari wajen su Zinariya dan ni ma ina buƙatar a sabunta min aikina,gaba ɗaya cikin kwanakin nan bana gane kan Dad...." Da ƙarfi aka buɗe murfin ƙofar ɗakin da su Aabidah ke ciki. Wani ƙaƙƙarfan mutum ne ya shiga ya tsaya a bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin ɓacin rai. Hannu ya ɗaga yana nuna Aabidah da ta yi sororo tana kallon yanda jikin Hajiya Zaitunah ke rawa. Kallon mutumin Aabida ta sake yi wanda a baya suke sakawa aiki har da ɗebo musu ruwan sha ta ga yanda yake huci kamar wani zaki,nan da nan jikinta yayi sanyi ta miƙe ta saɓa jakarta a kafaɗa ta bar ɗakin. Kai tsaye motarta ta nufa ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kamar wadda ta yi tseren gudu. Tana tada motar ta mai gadi ya wangale mata gate ta bar gidan a guje. A hanya babu abinda take tunawa da ya wuce sauyin da ta gani a gidan Hajiya Zaitunah. Nan take tsoro da fargabar dake cikin ranta suka nunku. Murya na rawa ta ce. "Shin me yake faruwa a rayuwarmu ne? Lallai dole ne na samarwa kaina mafita,domin kuwa ba zan taɓa yarda Aabii ya dawo cikin hayyacinsa ba kamar yanda mijin Hajiya Zee ya dawo cikin hayyacinsa." Tana isa gida ta hau dannawa mai gadi horn,da gudu ya ajiye abincin da yake ci ya buɗe mata gate yana yi mata sannu da dawowa. Ko ta kansa Aabidah bata bi ba ta ajiye motarta ta kalli motar Aabid da ya yi mata wani irin mugun parking. Jiki a mace ta shige cikin gidan tana ɗari-ɗari dan bata san me za ta tarar a ciki ba. Ta na murɗa ƙofar shiga parlourn ƙasa ta ci karo da wajen kamar yanda ta barshi,sai ma takalmin Aabid da ke yashe a tsakiyar parlourn kamar wanda ya yadda shi da gayya. A hankali ta ci gaba da takawa har ta haura sama,kai tsaye ɗakinta ta nufa ta watsa ruwa kafin ta tsantsara kwalliya cikin ƙananan kayan da Aabid ke mutuwar so. Ɗakinsa ta shiga ta tarar da fitilar a kashe;sai dim light da ya kunna,karatun ƙur'anin da aka yi shekara da shekaru ba a saurara ko karanta ba a cikin gidan ke tashi a wayarsa. Kwance yake ya na kallon sama da idanuwansa da suka kaɗa suka yi jawur. Babban abinda ke damunsa shine cushewar tunani da rikicewar ƙwaƙwalwa,sai wani irin matsanancin ciwon kai da faɗuwar gaba da yake ji. Ƙamshin jikin Aabidah ne ya sanya shi lumshe idanuwansa hawayen dake kwance a cikinsu suka gangara gefen idonsa suka yi wa kansu masauki a kunnuwansa. Ba tare da ya damu da share wa ba ya sauke jajayen idanuwansa a saman fuskar Aabidah dake zaune a gefensa ta kasa furta komai saboda tsananin tsoron abinda zai je ya zo. Jin ta take yi kamar wata baƙuwa ko wata sabuwar halitta. Hannu Aabid ya miƙa mata cike da kulawa,ta na ganin haka ta isa gare shi da sauri ta kwanta a jikinsa tana mai rushewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya hau shafa bayanta da sigar lallashi. Duk yanda ya so ya buɗe baki yayi mata magana ya kasa. A haka Aabidah ta samu baccin da bata yi ba ya ɗauke ta cike da mugayen mafarkan da ta dinga fatan ta farka ta buɗe ido dan ta dena ganinsu,amma inaaa gaba ɗaya duniyar mummunan mafarki ta yi mata dabaibayi. Haka rayuwar gidan Aabid ta koma cike da shiru da tsoro tare da fargaba,ɗimuwa da kuma damuwa. Gaba ɗaya ya dena fara'a,ya dena duk wasu ayyukan da yake yi mata a baya,ko kamfaninsa ya dena fita,lokuta da dama yana ganin kira daga kamfanin zai ƙi ɗagawa har ya katse. Sanin cewa asirin da ta yi masa yana ta barin jikinsa a hankali shi yasa ko da wasa bata yi masa tsawa ko hantararsa ballanta ta saka shi yayi mata wani aiki,tana ji tana gani zai kunna karatun ƙur'ani bata da halin kashewa. A haka Aabidah ke lallaɓawa ta yi musu girkin da suke kasa ci daga ƙarshe sai dai ta kai wa mai gadi,shi kuwa mai gadi sai ya tsince naman ya cinye ya zuba wa karen maƙota abincin. Bayan kwana biyu Aabid ya tashi yana jinsa kamar sabon mutum,kewar Hajiyansa da ƴar'uwarsa ce ta mamaye zuciyarsa dan haka sai ya shirya tsaf cikin shaddarsa gezna ya saka hularsa sabuwa dal da takalmi mai tsada da ya dace da kayan jikinsa. Aabidah na ganinsa da irin wannan shigar hankalinta ya tashi,cikin kissa da kisisina ta dinga bugun cikinsa dan ta ji inda zai je,amma Aabid ya yi shiru bai bata amsa ba. Cike da shagwaɓa Aabidah ta kwantar da kanta a jikinsa ta ce. "Wai ni Aabii laifin me na aikata maka ne a cikin gidan nan da ka dena yin hira dani,ka dena kula ni a matsayina na matarka ta sunna,kullum haka za mu kwanta mu tashi da kai  ba tare da wani abu ya shiga tsakaninmu ba,idan na yi maka girki sai dai ka ce a zubar ka yi order a waje ka ci. Ko dai ka dena so na ne Aabii?" Ta ƙarashe maganarta cike da zubar hawaye da ƙuncin zuciya. Numfashi mai tsawo Aabid ya ja kafin ya fesar ya samu waje ya zaunar da su a kujera. Fuskarta ya ɗaga yana share mata hawayenta kafin ya buɗe baki kamar mai jin tsoron yin magana ya ce. "Ni kai na ban san me yake damu na ba a cikin kwanakin nan Baby....lokuta da dama sai in dinga jin ƙirjina,kai na da zuciyata suna yi min nauyi.... Aabidah ina ji a jikina akwai wani abu da na rasa mai muhimmanci a rayuwata. Jikina yana bani akwai wani abu da nake so ko yake jirana ko kuma...i just don't know what is happening to me. Ki yi haƙuri da duk wani sauyi da kike gani a waje na,da yardar Allah komai zai dawo kamar yanda yake tun fil azal." "In Allah Ya yarda babu abinda zai dawo kamar yanda yake tun fil azal...." Aabidah ta yi suɓucewar baki ta faɗa da ƙarfi. Cikin sauri Aabid ya kalle ta yana mamakin furucinta. Da sauri ta wayance ta hau ƙirƙirar abubuwan da take ganin za su ɗauke masa hankali,sai dai cike da rashin samun nasara Aabid ya kewayeta ya fita daga ɗakin. Kanta ta dafe ta saki ƙara a hankali kafin ta mari kuncinta ta ce. "Da dikkan alamu idan Boka bai gaggauta samar min mafita a wannan lamarin nawa ba zan haukace saboda damuwa." *Aabid.* Ya jima yana maimaita kalaman Aabidah a cikin ransa,amma ya gaza gane inda addu'arta ta dosa. A haka ya dinga tuƙi ya na ratsa gidaje da tituna har ya isa ƙofar gidan mahaifinsa. Ya na zuwa ya ga an sabunta fentin gidan tare da yin shuke-shuke a wuraren da aka bari domin shuka. Murmushi ya saki domin yana da yaƙinin babu mai yin wannan aikin sai Maheer. Wata iriyar kewar Maheer ce ta mamaye shi,sai yake jin kamar ya ɗauki wasu shekaru masu tsawo bai gansa ba. Kai tsaye ya dirfafi gate ɗin gidan da zummar shiga ciki. Sai dai ganin wani mutum sanye da kakin soja a jikinsa ne ya sanya shi tsaya wa yana kallonsa cike da neman ƙarin bayani. Shi ma mutumin kallon Aabid ya ke yi tare da faɗin. "Kai ina za ka je ne kake ƙoƙarin wuce wa ciki ba tare da neman izini ba?" Wata kafirar harara Aabid ya banka wa sojan sannan ya ce. "Gidan uban nawa ne zan nemi izininka dan zan shige shi? Kai ɗin waye?" Murmushi sojan yayi dan ya fuskanci Aabid bai san cewa an siyar da gidan ba. Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ya bayyana masa cewar ai gidan an siyarwa da ogansa ne;a cikin satin ma suka tare. Baki Aabid ya saki yana mamakin wanda zai siyar da gidansu na gado ba tare da izininsa ba. Gefe ya koma ya zaro wayarsa ya danna kiran Maheer. Ta jima sosai tana ringing tare da katse wa ba a amsa shi ba,shi kuwa Aabid ba tare da gajiya wa ba ya sake kira. A haka har dai Maheer ya gaji da nacin Aabid ya ɗaga wayar a hasale ya ce. 'Wai don Allah wannan wanne irin kira kake yi min ne Aabid?' Da sauri Aabid ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli wayar sannan ya mayar da ita kunnensa ya ce. "Maheer ni ne fa Aabid." 'Sai aka yi yaya dan kai ne Aabid?' Cike da mamakin sauyawar halayyar Maheer Aabid ya ce. "Ohhh yanzu na gane komai,dama kai ne ka zuga Mahreen ta siyar mana da gidanmu na gado kenan ko? Dama za ka iya cin amanar zumuncin dake a tsakaninmu Maheer?" Cike da ƙunar rai Maheer ya ce. 'Excuse me? Me kake nufi da na zuga Mahreen ta siyar muku da gidanku na gado? Ohhh ! Ohhh ta nan kuma ka biyo Aabid? Duk ka manta rashin mutunci da wulaƙancin da ka aikata kenan? Aabid wai kana ma ina ne yanzu haka?' "Ina ƙofar gidanmu a da;wanda ka shiga ka fita ka siyar da shi. Maheer ka sani ba zan taɓa barin wannan cin amanar ya tafi a banza ba." Aabid na gama magana ya kashe wayarsa ya shige motarsa ransa a matuƙar ɓace ya nufi hanyar gidansa. A ɓangaren Maheer kuwa ya jima yana nazarin abinda ya faru a tsakaninsa da Aabid kafin ya sanya goshinsa a ƙasa ya yi wa Allah sujjada tare da miƙa godiyarsa a wajen Allah. Ba tare da tunanin duhun dare da ya fara shiga ba Maheer ya shirya yana cike da matsanancin farinciki ya bar gida........ MUGUWAR MACE. NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 10. WAIWAYE ADON TAFIYA.... Ƙaramar hukumar Kura da ke a cikin jihar Kano, wacce ke da tazarar kusan kilomita 35 daga birnin Kano,ɗaya ce daga cikin manyan wuraren noma da sarrafa shinkafa a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya. Ana noma shinkafa a kusan dukkanin yankunan ƙaramar hukumar. Kura gari shi ne babban zaure na harkokin noma da kuma masana'antun nika shinkafa (kamar Golden Grains Agro-processing Co. LTD). Allah ya albarkaci ƙaramar hukumar Kura da ruwa; musamman na kogin Kano da ake amfani da shi wajen noman rani da damuna,suna da ƙasa mai kyau da ta dace da da noman shinkafa da sauran kayan abinci. Mutanen garin Kura sun taso sun ga iyayensu da kakanninsu na noma da cinikayyar amfanin gona daga cikin jihar kano,da sauran jihohin Nigeria har ma da ƙasashen waje. Musa Abdulwahab Musa Kura wato Aabid ɗaya ne daga cikin mutanen da Allah ya yi wa gam da katar ɗin kasancewa daga cikin tsatson manoman cikin wannan gari mai tarin albarka na Kura. Kakan Aabid wato Malam Musa ɗan asalin Ƙaramar hukumar Kura ne,wanda ya taso da zafin nema da kuma fasaha da ilimin noma da kiwo. Wannan dalilin ne ya sa mutanen garin ke matuƙar girmama shi tare da kiransa duk wani babban project da za a yi na gwamnati domin su amfana da iliminsa. Babban dalilin da ya hana Malam Musa zamowa ɗaya daga cikin manyan masu arziƙi a cikin garin Kura da kewaye shine ƙaddara. Tabbas ƙaddara ce kaɗai za ta hana mutum mai ilimin noma da zafin nema kamar Malam Musa zamowa ɗaya daga cikin masu kuɗi. Lokuta da dama idan ya dawo daga gona ya gaji ba tare da ya samo wani abun a zo a gani ba;sai ya zauna ya zabga tagumi yana jimamin lamarin. A haka matarsa mai suna Atine za ta kawo masa abincinsa da ruwan sha, da ya buɗe ya ga babu nama ko fikin miya,sai ya yi murmushi ya ce. "Watakam Atine tsari da hikima irin na Ubangiji daban ne da na bayinSa. Kowanne mai rai da kike gani a duniyar nan an gama rubuta arziƙinsa tin yana cikin mahaifiyarsa. Shi yasa za ki ga wani zai taso a rayuwarsa bai san wahala ba ballanatana neman na kai a cikin zafi,damina da ɗari,amma sai ki gansa da wadata tare da hanyoyin samun kuɗi masu tarin yawa. Wani kuma sai ki ga ya taso yana ta nema kacal wacal kamar zai bada rayuwarsa saboda neman na kai,amma sai ya wuni bai samu ko sisi ba. Wani kuma a kullum sai ya fita ya yi aiki da jikinsa ya saka rayuwarsa a hatsari sannan yake samun abinda zai ci iya na wannan yinin." A duk lokacin da Malam Musa yayi wannan kalaman nasa sai Atine ta yi murmushi ta ce. "Maganar ka dutse Malam,domin kuwa mu ɗin nan babban misali ne akan Allah yana azurta duk wanda ya so ne,tinda ni ma ba a zaune nake ba wajen neman na kai,amma har yau gamu nan jiya-i-yau." Haka rayuwar Malam Musa da Atine take a cikin rashi da ƙuncin talauci har suka haifi yaronsu na farko. Bakwai na zagayowa Malam Musa ya zauna a bakin ƙofar ɗakinsa da asubar fari yana hawaye;sakamakon rashin kuɗin da zai sayi ragon sunan tilon ɗansa. A haka Gwaggon Atine da ke yi mata zaman daɓaro mai suna Gwaggo Kande ta same shi zaune yana zubar da hawaye; bayan ta dawo daga kai ruwan wankan Atine bayi. Cike da tausayawa ta isa gabansa ta zauna a nesa da shi ta ce. "Malam Musa ka sanya wa zuciyarka haƙuri,domin babu da akwai duk na Allah ne. Ba kuma akan ka aka fara haihuwar fari a rasa abinda za a yanka ranar suna ba,sannan ina da yaƙini da tabbacin ba a kanka za a ƙare ba." Hawayensa ya share tare da face majinar dake danƙare a hancinsa ya ce. "Goggo Kande ba ina jayayya da hukuncin ubangiji bane. Kawai ina mamakin yanda kiwo wannan bai karɓe ni ba kamar yanda sauran ƴan'uwana manoma da dangi suke da ababen kiwatawa. Fisabillahi yanzu da ina da abun kiwatawa zan shiga cikin wannan halin ne?" Jijjiga kai Goggo Kande ta yi sannan ta ce. "Sam ba za ka shiga ba Malam Musa. Sai dai ina so ka sani duk abinda ya samu bawa da sanin Allah,ka ƙara haƙuri sannan ka gode wa Allah da ya baka rai da lafiyar nema, ko da baka tara ba za ka fita ka nemi wanda za ka ci kai da iyalanka kuma ka samu." "To amma Goggo ki na ganin mutanen da nake bawa shawarwarin noma da da kiwo har wanda nake zuwa da kaina na yi musu dabarun da za su samu arziƙi a cikin nomarsu duk sun yi kuɗi sun fi ƙarfin gidansu,ni gani nan abinda za a dafa a ranar sunan ɗana na fari babu, ballantana abinda za a yanka na raɗin suna." A hankali Gwaggo Kande ta miƙe tsaye tana kaɗe zaninta ta ce. "In dai wannan ne mun gama tattaunawa da Atine,yau ɗin nan za a kawo mata ragonta na gado da ake kiwata mata a can babban gida,idan yaso sai a bar tinkiya da awakin a ci gaba da kiwata mata. Ni kuma na yi alƙwarin kawo abinda za a dafa a ci a taron suna. Dan haka ka kwantar da hankalinka kada ka saka wa kanka damuwar da za ta jawo maka wani ciwon." Godiya sosai Malam Musa ya durƙusa a ƙasa yana yi wa Gwaggo Kande kamar zai kwanta mata. A haka Atine ta fito ɗaure da zani ta yafa wani a saman kanta ta riske su. Malam Musa na ganinta ya nufe ta ya hau yi mata godiya akan rufa masa asirin da ta yi. Murmushi kawai ta sakar masa ta tafi bayi. A wannan ranar Malam Musa ya tattara sauran duk abinda yake da shi na daga hatsi ya kai kasuwa ya siyar ya dawo da cefanen kayan miya;tare da kayan jariri kala uku,sai sabon ɗankwali da sarƙa da ɗankunne na murjani ya kawo wa Atine. Murna Atine ta dinga yi tana sanya masa albarka tare da fatan Allah Ya ninninka masa arziƙinsa ya raya musu ɗansu Abdulwahab. Bayan sunan Abdulwahab Atine da Malam Musa sun ci gaba da rainon ɗan su cikin kulawa,soyayya da ƙauna irin ta iyaye. Malam Musa sai ya sake dagewa da neman kuɗin da zai ba wa ɗan sa da matarsa ingantacciyar rayuwa. Cikin ikon Allah kuwa sai arziƙinsa ya fara buɗewa har ya fara tara dabbobi yana kiwatawa a gida kamar yanda yake da sha'awa da buri. A hankali Malam Musa ya fara siyan fili yana yadawa. Abdulwahab na kai wa shekara takwas a duniya ya saka kansa a makarantar boko da ya ga yaran garin na zuwa. Sai dai su da sun kammala primary suke tsunduma a harkar noma sai su watsar da karatun. A ɓangaren Abdulwahab kuwa sam bai watsar da karatun bokonsa ba,saboda yana gane duk abinda ake koyar da shi. Bayan an taso daga makarantar boko sai ya wuce ta allo,da yamma ya koma gida ya ci abinci ya yi bitar karatunsa na boko da na arabiyya. Babu jimawa labarin nacin karatu irin na Abdulwahab ya fara karaɗe garin Kura,har wasu daga abokan Malam Musa suka yi ayari su huɗu suka je har gida suka same shi da shawarar;ya kamata ya dakatar da Abdulwahab daga zuwa makarantar boko ya jefa shi a harkar noma kamar sauran yaran garin,gudun kada ya tashi bai iya riƙe fatanya ba. Da jin haka sai Malam Musa ya fashe da dariya ya kalli abokan nasa ya ce. "Allah mai iko! Ku yanzu akan makarantar da yaron nan yake zuwa kuka yo ayari haka kuke sanar da ni na hana shi zuwa? Ina kuke lokacin da nake cikin gararin talauci da babu? Ina kuke ranar sunansa lokacin da nake neman ragon da zan yanka a sunansa dan na sauke nauyi da kuma kare mutuncin ɗana da ni kaina da iyalina? Ina kuke lokacin da yaron nan ya dinga yawo babu suturar arziƙi a jikinsa ballantana takalmin da zai saka ya shiga cikin tsaransa?" Idon da ya zuba musu yana neman ƙarin bayani ne ya sanya su sauke kawunansu ƙasa cike da jin nauyi da kunyarsa. Murmushi yayi sannan ya ce. "Idan baku da amsar bani ku je ku ci gaba da kula da yaranku ta hanyar da kuke ganin ita tafi dacewa da rayuwarku;nima ku barni na kula da nawa yaron ta hanyar da nake ganin tafi dacewa da rayuwar da nake so yarona ya taso a cikinta." Cike da borin kunya suka kaɗe rigunansu suna faɗin. "Ai shikenan,dama shi gyara kayanka ba ya zamowa sauke mu raba,shawara ce dai muke baka,dan mu dai bamu ga wanda biro da takarda suka ciyar ba,riƙo da fatanya muka gada kaka da kakanni,ita ce ke bamu abinda muke kai wa bakin salati." "To ku je ku ci gaba da riƙe fatanyar shi kuma ya riƙe bironsa,Allah Ya bawa kowa sa'a akan abinda ya sa a gaba." Tin daga wannan ranar abokan Malam Musa suka janye jiki daga gare shi,sannan duk wata harkar noma ta samun ci gaba idan ta shigo garin suke kashe tauraruwarsa su ƙi sanar da shi. A duk lokacin da ɗayansu ya neme shi to ta tiƙe masa ne babu yanda zai yi sai ya nemi shawara ko taimakon Malam Musa. A hankali samun Malam Musa ya fara ja baya,amma duk da haka bai karaya ba,sai ya koma noma filayensa guda uku da ya mallaka da kansa,idan abunda ya noma yayi sai ya je ya siyar. A haka Abdulwahab ya kammala ƙaramar sakandire har ya rubuta jarabawar shiga babbar sakandire. A tsakanin hutun da ya samu ne na rubuta jarabawar shiga senior secondary school ya fara bin mahaifinsa kasuwa yana ganin yanda ake gudanar da kasuwanci. A kuma wannan lokacin ne sha'awar siye da siyarwar kayan abinci ta shiga ransa. Bayan ya koma makaranta sai Malam Musa ya hana shi zuwa kasuwa ya ce ya mayar da hankali akan karatunsa. Abdulwahab na da shekaru goma sha biyar a duniya Atine ta haifa masa ƙanwarsa mai suna Salma. Sosai Atine ta wahala saboda jimawar da ta yi ba tare da ta haihu ba,jinin da ta zubar sai ya sake rage mata kuzari da karsashi. Wannan dalilin ne ya sa ita kanta yarinyar bata samun cikakkiyar kulawa daga mahaifiyarta yanda ya kamata. Bayan suna da wata ɗaya Atine ta rasu sakamakon rashin jini a jikinta. Malam Musa ya shiga ɗimuwa da zaucewa saboda rashin masoyiyarsa. Ya jima sosai bai koma noma ba ballantana ya girbe amfanin gonarsa ya kai kasuwa. A haka suka ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da kewa tare da maraicin rashin Atine a rayuwarsu. Sosai Malam Musa ya so a bar masa Salma su ci gaba da kula da ita shi da Abdulwahab,amma sai Goggo Kande da sauran ƴan'uwan Atine suka ƙi amincewa da hakan suka ɗauke ta ta koma ƙarƙashin kulawarsu. Abdulwahab na zana jarabawarsa ta ƙarshe a sakandire mahaifinsa majinginarsa kuma katangarsa ya faɗi ya rasu. Sosai mutuwar Malam Musa ta girgiza mutanen garin Kura da kewaye. Domin kuwa shi ɗin mutumin kirki ne,kuma su na amfana da shi matuƙa gaya a ɓangaren noman rani da damuna. Rasuwar Malam Musa ta sanya Abdulwahab zamowa yaro mara son magana da kuma kaɗaice kansa daga cikin al'umma. Lokuta da dama yafi tafiya cikin gonar mahaifinsa ya kwanta ya sha kukansa,daga ƙarshe bacci ya ɗauke sa,sai idan an aika yara nemansa ne ake samo shi a gona. Sosai Gwaggo Kande take tausayawa rayuwarsa saboda ta fi kowa sanin irin gata da kulawa tare da soyayyar da iyayensa suka bashi. Ganin yana neman ya lalata rayuwarsa ne ya sanya mijin Gwaggo Kande shige masa gaba a lokacin da sakamakon jarabawarsa ya fito; Result ya yi kyau sosai,sai ya biya masa kuɗi ya rubuta JAMB a wannan shekarar. Cikin ikon Allah ya samu makin da ake nema domin shiga jami'a. Malam Bala shi ne yayi tsaye tsayin daka ya saka Abdulwahab a makarantar jami'a ta kano wato Ado Bayero University Kano State. Ranar da Abdulwahab zai tafi makaranta Gwaggo Kande da Salma sai kuka suke yi,shi kuma yana jin wani irin farinciki a ransa zai bar garin Kura ya je wajen da zai yi nesa da inda ya yi rayuwa da iyayensa da ya rasa. Har tasha Malam Musa ya ɗauki Salma suka raka Abdulwahab da kayansa a cikin Ghana most go da leda ViVa.  Bayan tafiyar Abdulwahab makaranta Malam Bala ya ci gaba da kula da shi da buƙatunsa har ya kai level 200. Sai dai zugar abokai da danginsa ce ta sanya shi fara ja da baya tare da cire duk wani tallafi da yake bawa Abdulwahab. Lokacin da Abdulwahab ya samu hutu ya leƙa garin Kura mutanen garin suka gansa fes da shi gwanin sha'awa,sai suka ƙara tinzira Malam Bala suna yi masa nuni da ya zauna yana ta kashe kansa shi da yaransa su na gina yaron da bai san zafin nema ba. Tin suna maganar a ɓoye har magana ta shiga kunnen Abdulwahab. A lokacin da ya ji sai ya ƙi amincewa Malam Bala zai ɗauki zugar masu zuga har ya daina tallafa masa kamar yanda ya saba. Lokacin komawa makaranta na yi ya tinkari Malam Bala da maganar kuɗi,a nan ne fa Malam Bala ya murza wa idonsa toka ya ci wa Abdulwahab mutunci tare da yi masa gori kala-kala. Sosai kalaman Malam Bala suka ƙona wa Abdulwahab zuciya,amma sai ya tuno da alkhairin da ya yi masa a baya. Godiya ya yi masa ya shiga wajen Gwaggo Kande ya sanar da ita zai koma. Sanin halin da ake ciki ne ya sanya ta miƙe wa ta shiga ɗakinta ta ɗakko wata baƙar leda ta dawo ta zauna a gefensa ta ajiye masa a saman cinyarsa ta ce. "Karɓi wannan,kuɗin awakin mahaifiyarku ne da na sa a siyar tin wancan satin. Kasancewar na fuskanci Malam ya fara ɗaukar zugar mutane ya sa na ce to meye amfaninsu? Shine na ba wa Kawunka Sale na ce a siyar a kawon kuɗin. Ka ƙara haƙuri Audu watarana sai labari. Allah Ya yi maka albarka Ya sa a mori wannan ilimi da kake ta fafutukar nema." "Amin Ya Allah Gwaggo na gode,Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka in kai ki makka da Madina ke da Baba da Salma." Guɗa Gwaggo Kande ta zabga tana murna,domin ko Abdulwahab bai kai ta Makka da Madina ba ya biya ta tinda ya sa hakan a niyyarsa. A wannan karon Abdulwahab da kansa ya nemi Salma ta yi masa rakiya tasha ta riƙe masa ƴar ƙaramar jakarsa ta goye suka tafi su na hira tana ta zuba masa surutu irin na yara masu wayo da baki. Da za su rabu ya siya mata kayan kwalama irin na yara a tasha ya tsaya a bakin tashar har ta ɓacewa ganinsa. Gani yayi ana ta loda shinkafa a bayan manyan motoci,gefe ɗaya kuma ga wake,gero,alkama,da maiwa tare da sauran kayan amfanin gona ana ta siyarwa. A hankali Abdulwahab ya matsa kusa da wani shago mafi kusa da shi,sallama ya yi wa mai shagon suka gaisa sannan ya furta masa buƙatarsa na son siyan shinkafa buhu ɗaya. Babu ɓata lokaci suka yi ciniki Abdulwahab ya sa ɗan dako ya ɗaukar masa shinkafar ya kai masa wajen lodi. Ya na isa garin kano........ *Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman gidan aure. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ PAGE 11. Abdulwahab na shiga garin Kano ya samu abun hawa ya ɗaukar masa buhun shinkafarsa ya kai masa har bakin makaranta,daga nan ya samu machine ya loda masa kayansa ya shigar da shi har ƙofar shiga hostel. Ya na isa bakin gate ɗin hostel ya sauke shinkafa ya sallami mai machine. Abokinsa kuma ɗan ɗakinsu ya kirawo wato Mudassir ya roƙe shi ya taimaka masa suka shigar da shinkafa. Sai da ya yi wanka ya huta ya ci abincin da Mudassir ya gabatar masa sannan ya labarta wa abokin nasa duk abinda ya faru a gida. Ajiyar zuciya Mudassir ya yi kafin ya saki murmushin takaici ya ce. "Allah Ya kyauta. Ai mutane yanzu suna daga cikin masu hana alkhairi,su basu yi ba sannan basu bar wani ya yi ba. Ni ai tinda na samu dangin Ummanmu na riƙe min Layuzah da amana bayan rasuwar iyayenmu sannan tana zaune cikin gata bani da wani takaici,yanzu haka fa ta na aji uku na ƙaramar sakandire,sannan ƙanin Ummarmu ya biya mata kuɗin bikin saukar ƙur'ani da za a yi musu a ƙarshen watan nan. Shi yasa ka ga ina faɗi tashi ina neman abinda zan rufa wa kai na asiri ba tare da na sake ɗora musu wani nauyin ba,amma fa su ba sa son ina wahala ba tare da na tambaye su taimako ba,ni kuma ina duba halin yau da gobe ne kada azo tin ana yi maka abu ta daɗin rai a gaji da kai,kamar yanda aka yi maka yanzu abokina. Allah dai Ya ƙara shiga lamuranmu. Dama bahaushe ai ya ce babu maraya sai rago,wannan dabarar da ka yi ta yi kyau,bari ma ka ga me ya kamata mu yi tin yanzu." Da sauri Mudassir ya miƙe ya ɗauki kwanon silver da spoon ya fita tsakiyar saman baranda ya hau kiɗa da kwanon yana kiran mutane. Kafin kowa ya bashi hankalinsa ya rage murya ya tambayi Abdulwahab farashin kwanon shinkafa, Abdulwahab na sanar dashi ya fara tallata wa abokan karatunsa shinkafar akan farashi mafi sauƙi akan yanda suka saba siye a gari. Da yake suna cikin lokacin da wasun su sun dawo da kuɗin shopping daga garuruwansu,wasu kuma sun zo da kayan provision amma basu yi awo ba. Dan haka sai suka dinga rububin zuwa siyen shinkafa. Sai da mutane suka taru Mudassir ya ce. "To ƴan'uwana ɗalibai ga fa sabuwar sana'ar abokina na siyar da kayan hatsi ko wanne iri mutum yake so,kawai ya faɗa masa in dai da kuɗi hannu ba bashi ba za ku samu akan farashi mai sauƙi. Ni kuma ina nan zan ci gaba da yi muku wanki da aikace-aikacenku kuna biyanaaaa." Shewa matasan suka ɗauka,wasu na faɗin a basu shinkafa kada ta ƙare. Cikin sauri Abdulwahab ya hau neman kwanon da zai yi awo da shi,da ƙyar suka samu aron kwanon awo a hostel ɗin ya hau auna wa mutane shinkafa Mudassir na karɓar kuɗi ya na ƙirgawa. A haka shinkafa ta ƙare tas wasu na buƙata dan basu samu ba. Cike da murna da farin ciki Mudassir ya yi musu alƙawarin za su samu a cikin satin. Su na koma wa ɗaki ya kwaso kaf kuɗin da aka sayi shinkafa ya damƙa a hannun Abdulwahab yana taya shi murnar siyar da shinkafa da ya yi a ranar farko da ya fara kawo ta. Cike da tsantsar farinciki Abdulwahab ya rungume Mudassir yana yi masa godiya. Daga baya kuma ya yi jimm kafin ya ce. "Amma na ji ka ce musu za su samu wata shinkafar a cikin satin nan,kada fa ka manta da karatunmu abokina." "Ai babu abinda zai taɓa mana karatunmu abokina. Da an tashi daga lectures ranar alhamis kawai ka je Kura ka ƙaro shinkafa. Ka ga daga nan ma sai kai ma ka shiga jerin mutanen da za a dinga kawo wa hatsi ba tare da sun je har garin ba,tasha kawai za ka je ka ɗauki saƙon ka kamar yanda na ga wasu ƴan kasuwan na yi." "Eh kafin na samu wannan damar dole sai na je mun tattauna akan yanayin yanda zan dinga biyansu kuɗinsu,da yanda nima zan dinga samun nawa kayan." "Kada ka ji komai abokina Allah Yana tare da mu,fatana dai Allah Ya sa ka fara cikin nasara Ya sa hanyar arziƙinka ce." "Amin abokina. Allah Ya sa hanyar arziƙinmu ne baki ɗaya,domin da alama ba zan iya kasuwancin nan ba idan babu kai a gefe na. Na gode sosai da wannan taimakon da ka yi min,Allah Ya jiƙan Innah da Abbah." "Amin Ya Allah,kai ma Allah Ya jiƙan Baaba da Baba." Zama suka yi suka ƙirga kuɗi suka ware riba da jari. Su na kammalawa suka adana kuɗin da kyau sannan suka ci gaba da shawarwarin yanda za su dinga samun kuɗi ta hanyar halal domin biyan kuɗin makarantarsu da kuma buƙatunsu na yau da gobe. Tin daga wannan ranar kasuwa ta buɗe wa Abdulwahab ya ke samun kuɗaɗen kashe buƙatunsa. A wannan gaɓar ya dinga amfani da ilimin da ya ke koya ta ɓangaren kasuwanci ya dinga bunƙasa kasuwancinsa. Ana haka sai aka samu ƴan gulmar da suka kai gulmar Abdulwahab da Mudassir wajen hukumar makaranta akan sun mayar da hostel wajen sana'ar sayar da hatsi,da fari an yi musu gargaɗi,sai dai hakan bai yi wa duk wanda ya kai gulmar daɗi ba,bai huta ba har sai da aka kore su daga hostel ɗin gaba ɗaya. Ana korar su suka kama hayar shago a wajen makaranta,a nan suke kwana kuma suke siyar da kayan hatsinsu. Sai ya zamana bayan ƴan makaranta da suka san suna siyar da kayan hatsi akan farashi mai arha har mutanen gari ma suna zuwa siyan kayan hatsi a wajen su Abdulwahab. A hankali kasuwa ta fara buɗe masa sosai tin yana ɗakko buhunan hatsi guda uku,ya koma biyar,daga baya ya koma ya na sauke buhuna goma. Wani lokacin ma mota zuwa take yi har gaban shagon ta sauke kayan ta wuce,ganin kayan na ƙaruwa kuma basu da wajen ajiya;sai Mudassir ya ba wa Abdulwahab shawarar ya kama wani shagon ya zauna a matsayin store,idan ya so wannan da kowa ya san su da shi sai ya zama na siyar da kayan hatsin. Da hidima ta ƙaru akansu sai Abdulwahab ya samu yara guda biyu masu kular masa da shagon,shi kuma da abokinsa sai suka mayar da hankalinsu akan karatunsu. Da haka Abdulwahab da Mudassir suka samu suka kammala karatunsu,domin daga ƙarshe Abdulwahab shi ya ci gaba da ɗaukan nauyin karatun Mudassir. Sosai Malam Bala ya yi mamakin yanda Allah Ya sanya wa kasuwancin Abdulwahab albarka. Tin daga wannan lokacin sai ya rage matsanta masa da yake yi,domin har kyautar kuɗi Abdulwahab ɗin yake bashi da kuma yi wa iyalansa hidima domin kyautatawa. Ana haka Salma ta isa sawa a makaranta, Abdulwahab da kansa ya ɗauke ta ya kai ta makarantar boko da islamiyya ya yi mata register sannan ya kai ta wajen siyar da yadin uniform ya siya mata wanda zai isa a yi mata har kala uku-uku. Daga nan ya kai ta wajen masu siyar da jaka da takalmi ya zabar mata masu kyau da ƙwari,sai suka wuce shago ya yi mata ƴar siyayyar ƙwalama irin ta yara suka koma gida. Ko da suka koma gida suka sanar da Malam Bala ya so ya turje ya ƙi amincewa da zuwan Salma makaranta. Sai Gwaggo Kande ta murzawa idonta toka ta ce sam bai isa ba. Kan dole ya haƙura ya fita ya bar gidan ya na sababin sisinsa ba zai yi ciwon kai ba a zuwan yarinyar mace mai ƙaranci lokaci a rayuwarta makaranta. Cike da sababi Gwaggo Kande ta ce. "Shi ma ɗan'uwanta da kansa ya ƙarasa biya wa kansa kuɗin makarantar,tinda kai ka ce ladan ya ishe ka ka biye wa zigar abokan banza ka janye daga biya masa." Da ƙyar Abdulwahab ya taushe ta ta bar sababi,ya zauna suka hau hirar yaushe gamo. Su na tsaka da hirar ne Gwaggo Kande ta ce. "To yanzu tinda an gama makaranta sai kuma a zo a yi aure ko? Ka ga shikenan sai ka rushe tsohon gidan iyayenka a siyar da filin Babanku ɗaya ko biyu kai ko dika ukun ma;ka danƙara gininka ku zauna daga kai sai matarka." Da jin haka ƴar gidan kishiyar Gwaggo Kande mai suna Suwaiba da ke gaban murhu tana iza wutar kalwa da mahaifiyarta ke siyarwa ta tashi ta na wata tafiya ta na karairaya kamar maburgi ta wuce ta gabansu. Kai tsaye ɗakin mahaifiyarta ta shiga ta saka mata kuka tana sake yi mata tuni akan batun soyayyar da ta jima ta na yi wa Abdulwahab. Haƙuri ta bata tare da yi mata alƙawarin a daren nan za ta shawo kan mahaifinta dan ya ƙulla aurenta da Abdulwahab ko yana so ko baya so,tinda ya isa da shi. Da jin haka sai Suwaiba ta hau murna ta fito daga ɗakin ta na yanga ta wuce ta gaban su Abdulwahab ta ci gaba da sauraron hirarsu;wadda ta kasance duk ta samun nasarorin da yake ta yi ne akan kasuwancinsa. Albarka Gwaggo Kande ta dinga saka masa sannan ta tashi Salma da ta fara bacci ta ce ta je ta yi alwala dan an kusan kiran sallar magariba. Bayan Abdulwahab ya koma gidan iyayensa inda yake kwana ne ya kwanta ya na nazarin maganar da suka tattauna da Gwaggo Kande. Murmushi ya saki mai laushi sannan ya cire rigarsa ya rataye ya fita zuwa makewayi. Ya na fitowa ana kiran magariba,sai kawai ya ɗaura alwala ya koma ɗaki ya saka kaya ya kulle ɗakin ya fita zuwa masallaci. A can masallacin ya dinga haɗuwa da abokan mahaifinsa suna gaisawa,da sun gama gaisawa sai su ce za su masa nasiha akan saka Salma makarantar boko da zai yi. Ina laifin ya ƙyale ta tinda ita mace ce;ta na bin yaran Malam Bala zuwa gona itama ta na taimaka wa da wasu abubuwan,lokacin aurenta na yi Malam Bala ne zai tsaya mata ya samar mata da miji ɗan gaske ya aurar da ita,a cewar su rayuwar ƴa mace bata da tsayi.  Da sun gama koro wa Abdulwahab jawabi yake bin su da murmushin nan nasa da suke kira na rainin wayo,ko murmushin ajali. Da takaicin yamaɗiɗin da Malam Bala ya yi masa ya koma gida,domin a ganinsa ko auren Salma ne ya tashi ai suna da dangin uban da za su karɓa mata aure,ko Ƴan'uwan mahaifiyarsu,Malam Bala mijin Goggwan mahaifiyarsu ne shi kawai wanda yake ruƙon ƙanwarsa. Ya na komawa sai ya tarar da Suwaiba ta kai masa abincinsa ta na jiransa a ƙofar gida ta sha ado da irin kwalliyar ƴan matan ƙauye sai karairaya take yi. Ya na zuwa ta kashe murya ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta miƙa masa kwanon abincin ta na wani sunne kai. Dariya ta bashi sosai,sai ya kawar da kai ya na murmushi,da ganin haka sai Suwaiba ta kwasa da gudu ta yi gida, zuciyarta cike da farincikin Abdulwahab ya kamu da ƙaunarta. Tinda ta koma gida take bawa Innarta labarin irin murmushin da Abdulwahab ya yi mata har Babansu ya dawo daga majalisa ya shige turakarsa. Da yake Innar Suwaiba ke da girki,sai ta tashi ta nufi ɗakin nasa inda ta ajiye masa duk wani abun buƙata ta zauna. Mafifici ta ɗauka ta hau yi wa Malam Bala firfita. Baki ya kyaɓe ya ce. "Da dai Kande ce ke yi min firfitar nan da na ce Allah Ya yi mata albarka. Dan ita ba ta yi min biyayyar son zuciya ko ta wata manufa. Dan haka ina jinki, faɗi buƙatarki na ji ki ƙara gaba." Tura ɗankwali ta yi gaba ta na fari da ido ta ce. "Ka dai ji da shi Malam,ni ba zan biye maka ba a cikin daren nan da na ƙunso abun alkhairi a baki na mu yi faɗa da kai. Dan haka ka karkaɗe kunnuwanka ka kuma bani hankalinka nan dan jin abinda nake tafe da shi." Hannu Malam Bala ya siɗe ya na mai ture kwanon tuwon gefe ya kalli Innar Suwaiba ya ce. "Ikon Allah! Ke kuwa wanne irin abun alkhairi ne haka ya risinar min da ke?" Sai da ta yi ƙasa da muryarta sannan ta ce. "Malam bana dai Suwaibar mu an yi miji,irin mijin da kake nema,mai kuɗi wanda zai dinga miƙo wa ba wanda zai siyi akuya ta dawo ta na ci maka danga ba." Baki Malam Bala ya washe ya kalli matar tasa ya ce. "Ke ki bari dan manzo? Shi kuwa wannan surukin nawa a ina yake?" Dariya Innar Suwaiba ta yi cike da jin kunya ta ce. "Ai abun ƴar gida ce Malam. Tuwona mai na za a yi. Wato dakan ɗaka shiƙar ɗaka tankaɗen bakin gado ba." "Ke ni ki yi sauri ki sanar da ni ɗan wanne gida ne a kaf ƙauyen nan na ji ko ubansa na da arziƙin da zan iya bawa ɗansa auren ƴa ta." "Malam ba fa wani bane face Abdulwahabu ɗan gidan marigayiya Atine ta Malam Musa Manomi."...... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ PAGE 12. Ganin irin kallon da Malam Bala ke yi mata ne ya sanya ta muskutawa kusa da shi ta yi ƙasa da muryarta ta ce. "Malam kada ka ce komai game da wannan maganar,kai dai kawai ka saka wa lamarin nan albarka. Ko ka manta yanda haihuwar yaron nan ta zamo silar arziƙin ubansa kafin ya bar duniya? Sannan ka duba ka ga yanda arziƙi ke shigo masa ko ta ina daga fara sana'ar saye da siyarwar hatsi. Na tabbata nan gaba sai ya fi haka arziƙi domin da dikkan alamu ya na da ƙashin arziƙi. Idan aka ce wannan yarinyar kuwa ta aure shi ai ba ita da take a matsayin matarsa ba;mu kammu iyayenta sai mun huta." Fuskarsa da ya ɗaure ya saki ya hau washe baki. Kwanon abincinsa ya ja gabansa ya yanko loma sannan ya ce. "Ki je ki fara shirya yarinya lokacin aurenta ya yi." Guɗa Innar Suwaiba ta kama hanci za ta zabga, Malam Bala ya riƙe mata hannun cikin sauri ya ce. "Matsalata da ke hauka. Yanzu idan wani ya ji ki na guɗa ai sai a zo jin bahasi,daga nan shikenan kuma kin rusa mana duk wani tanadi. Dan na tabbata yaron nan sai an yi masa ƴan dabaru zai yi mana biyayya,mugun taurin kai ne da shi kamar dutsen wuta." Baki Innar Suwaiba ta kama ta na dariya ta fita daga ɗakin ta koma nata ɗakin. Zaune ta tarar da ƴar tata da ta gama yi musu laɓe ta ji komai,amma sai ta nuna sam bata san me yake faruwa ba. Ta na ganin mahaifiyarta sai ta miƙe tsaye cike da damuwar ƙarya ta na tambayarta yanda suka yi da Babanta. Nan Innah ta zauna ta sanar da ita komai cike da murna. Ihun murna Suwaiba ta sanya ta na ta tsalle tare da zayyano wa mahaifiyarta irin jin daɗin da za su samu idan har ta auri Abdulwahab. A wannan daren da ƙyar Suwaiba ta samu bacci ya ɗauke ta tsabar murna. Washegari da sassafe sai ga Suwaiba an yi ciki tsami waje fes-fes an sha kwalliya kamar mai zuwa gidan biki. Ta na gamawa ta samu waje ta yi zamanta a ɗaki kunnuwanta na baje a tsakar gida ta na jin mai shiga da kuma mai fita. Da misalin takwas da rabi na safiya Abdulwahab ya shigo gidan cikin adonsa irin na ƴan birnin wancan lokaci. Kai tsaye ƙofar ɗakin Malam Bala ya nufa ya samu waje ya zauna a saman tabarmar da yake shimfiɗawa ya zauna da safe ya karya;tare da karɓar gaisuwar yaransa. Cike da ladabi Abdulwahab ya gaishe da Malam Bala. Malam Bala ma washe baki ya yi tare da jimƙe hannun Abdulwahab a nasa ya na amsa gaisuwar kamar zai kwanta a ƙasa. Su na cikin gaisawa. Suwaiba ta fito cikin kwalliyar da ke ba wa Abdulwahab dariya ta na karairaya ta zo gabansa ta dire kwanon sha. Cike da jin kunyarsa ta kashe murya ta gaida shi. Amsa wa ya yi yana binta da kallo ya na dariyar gayunta. Ita da Malam Bala sai suka ɗauki hakan a matsayin ƙyasawar Abdulwahabu. Ko buɗe kwanon be yi ba ya nufi ɗakin Gwaggo Kande inda yake jiyo kukan Salma ta na faɗin ita dai ba za ta je makaranta ba Baba ya hana. Ya na shiga ɗakin Salma ta nufe shi ta na shassheƙar kuka. Zaunar da ita ya yi a saman cinyarsa ya na shafa kitsonta da ya kwanta a kafaɗunta ya ce. "Ai tun jiya mu ka yi magana da Baba ya amince ki je,ashe bai sanar da ku ba Gwaggo?" "Humm ka san Salma yarinya ce mai biyayya kamar mahaifiyarku. Tinda ta ji ya ce baya so ta tsiri wannan iya shegen. Amma tinda ta ce ba za ta je ba a bada kayan nata a amshe jakar duk a bayar. Wannan kayan ƙwalamar da ka siyo mata ma sadaka zan yi da su,dan babu amfanin ajiye wa." Salma na jin haka ta wuce ta hau saka uniform ta rataya jaka ta fice ta bar ɗakin ba tare da ta ce musu komai ba. Dariya Abdulwahab ya yi ya ce. "Ke ce maganin ƴar gidan naki Gwaggo." "Ahaf ai maganin biri karen maguzawa Abdulwahab." Gaisawa suka yi ta jawo masa abincinsa sannan ta fita daga ɗakin dan zuwa yin wasu ayyukan. Ta na fita Malam Bala ya kira ta ya ce ita da Innar Suwaiba su je ya na son yin magana da su. Babu ɓata lokaci ta ajiye ƙwaryar dusar awaki ta wuce ɗakin Malam ta zauna ta na jiransa. Ba ta jima da zama ba Innar Suwaiba da Malam Bala suka shiga ɗakin. Su na zama Malam ya yi gyaran murya ya ce. "Ba wani abu bane ya sa na ce ku zo turakata dikan ku face ina so na sanar da ku wani abun farinciki da ya same mu. Kande dama ke ce baki san me yake faruwa ba,dan ita Babar su Suwaiba ta san komai. Ina so ki taya mu murna bana dai Allah Ya yanke wa Suwaiba zaman gida za ta yi aure." Murmushi Kande ta yi ta ce. "Barka barka Hasiye Allah Ya sanya alkhairi da albarka ya nuna mana lokacin da rai da lafiya." Ta na faɗin haka ta ja bakinta ta yi shiru. A ƙufule Innar Suwaiba ta ce. "Shikenan abinda za ki ce Yaya? Wai ni sai yaushe za ki rage wannan zafin kishin naki akai na ne? Ai a ƙalla kin taya ni murna Allah Ya yanke wa ƴata wahalar zaman gida ko?" Cike da mamaki Kande ta ce. "Ah ah ni Kandala ɗiyar Mamman yau na ga abinda ya fi zare tsayi? To in banda abinki ai ta Malam bata wuce amin ko? Me kuma kike so na yi bayan addu'ar da na yi ta sanya albarka?" Ƙwafa kawai Innar Suwaiba ta yi domin bata so su yi faɗa ta hasala Kande ta ƙi haɗin auren. Malam Bala kuwa ya na ganin haka sai ya ce. "To in banda abunki Kande ya za ki tsaya sa-in-sa da surukarki?" Kallon sa Kande ta yi cikin rashin fahimta ta ce. "Surukata kuma Malam? Ta ina Hasiye ta zama surkar tawa?" Washe baki suka yi a tare shi da Innar Suwaiba kafin ya ce. "To ai Abdulwahabu shi ne angon. Kin ga kuwa idan da kara ai ke kakar amarya ce." Miƙewa Kande ta yi ta na tafa hannayenta tare da yin salati,sai da ta gama tsaf sannan ta kalle su ta ce. "Lallai ma Hasiye baki da kunya. Kin manta irin wulaƙanci da cin kashin da kike yi min a gidan nan saboda ni ban haihu ba? Wanne irin gori da tozarci ne baki min ba akan Suwaiba da ƙannenta? Har ta kai ta kawo gaba ɗaya yaran nan sun raina ni. Shi ne yanzu dan kun ga yaro ya yi ƙumbar susa kuke so ku bashi ƴarku ya aura,to ni dai babu ruwana a wannan zance,idan yana so a yi aure,idan baya so babu wanda ya isa ya yi masa auren dole." Da sauri Malam ya kashe ta ya na faɗin. "Haram ba bashi ita za mu yi ba,ni da kai na na fuskanci saƙon soyayyar da yake aika mata ta idanuwansa. Shi yasa na yanke shawarar haɗa su aure tinda itama ta na son sa." "Au haka abun yake? To Allah Ya bada sa'a Ya sanya albarka." Kande na fita daga ɗakin sai ta ƙwala wa Abdulwahab kira ta ce ya je Malam na neman sa,dan ta san halin mutanen nata muddin bata yi haka da wuri ba suka zauna waje ɗaya da Abdulwahab tsaf za su ce ita ta hana auren. Gaban Hasiye ne ya yanke ya faɗi domin ba ta haka ta so ya san da maganar ba. Dake wa ta yi ta gyara zama a turakar Malam Bala har Abdulwahab ya je ya zauna a tabarmar ƙofar ɗakin. Wani irin kwarjini Abdulwahab ya yi musu,sai dai son abun duniya ya rufe musu ido. Dan haka Malam Bala ne ya fara gabatarwa da Abdulwahab buƙatarsu na auren Suwaiba. Da sauri kuma ba tare da jin nauyi ko kunya ba Abdulwahab ya ce. "Baba ai ni ina da wadda nake so da aure har mun tattauna da Gwaggo ma akan hakan jiya. Dama ina jiran ka gama kari ne na zo maka da maganar dan har na sanar da Kawunaina da Baffanina,sun kuma amince za su zo su ɗauke ka ku je nema min auren Layuzah ƙanwar abokina da muke kasuwanci tare wato Mudassir." A guje Suwaiba ta fito daga ɗaki ta na gursheƙen kuka duk hodar ta ta caɓe domin maka ta ta yi da kyau,ga baƙin kwalli duk ya dame mata fuska. Kallonta Abdulwahab ya yi ya ji dariya ta zo masa. Malam Bala da ya ɗaga labule ya ce. "To idan baka son Suwaibar murmushin uban me kake yi mata ɗazu da ta kawo maka kunu? Sannan yanzu ma dariyar me kake yi mata?" Ƙunshe dariyarsa Abdulwahab ya yi ya ce. "Baba wannan kwalliyar ta fuskarta kaɗai ta isa ta firgita duk wani wanda ya zo neman aurenta ai." Baki Hasiye da Malam Bala suka buɗe suna kallon Abdulwahab da ke ci gaba da dariyar kukan Suwaiba. Dawowar Kande daka wajen awakinta kenan ta ga yanda Suwaiba ke mulmula a ƙasa ta na kurma ihu tare da faɗin ta shiga uku ta lalace. Da sauri ta nufe ta za ta ɗaga ta Hasiye ta riga ta ta ɗaga ƴarta ta na sharar kwalla ta ce. "Ni dama na jima da sanin ai ba kya ƙaunata ni da ƴaƴana a gidan nan,shi yasa kika hana Abdulwahab auren Suwaiba. To ki je ke da Allah,kuma muna nan zaune Suwaiba za ta auri wanda ya dame Abdulwahab arziƙi da kyau da nasaba." "Ba na yi mata baƙin cikin samun nagari,domin ni ma ina bin dare na yi mata addu'ar samun miji na gari inda za ta huta wani nata ma ya huta;wanda bana jin a matsayinki na uwarta kin taɓa bin dare kin yi sallah kin roƙar mata miji na gari. Tinda ku dai a kullum baku da buri sai auren mai kuɗi." Cike da takaicin wulaƙancin da Abdulwahab ya yi musu Malam Bala ya ce. "Ke ɗin ma ai auren kuɗin ki kai da ni. Amma dai komai ya wuce,tinda ya ce baya son jinina ya je can ya auri duk wadda ta yi masa,amma ba da yawu na ba." Haƙuri Abdulwahab ya dinga ba wa Malam Bala amma sam ya ƙi haƙura ya riƙe shi a ransa. Daga ƙarshe sai ya shuri takalmansa ya bar gidan. Ya na fita ya hau yayata cewa duk alkhairin da ya yi wa Abdulwahab da ƙanwarsa amma ya ce zai haɗa shi aure da Suwaiba ya baɗa masa kasa a ido. Nan take mutane ƴan bani na iya suka hau zagin Abdulwahab su na tsine wa dukiyar da ya fara tarawa albarka. A ɓangaren Abdulwahab kuwa bai koma Kano ba sai da Baffansa Habu da Kawunsa Sale. Kai tsaye gidan su Mudassir suka je suka nemar masa auren Layuzah. Babu ɓata lokaci Iyayensu Mudassir suka amince da auren nasu,domin kuwa sun jima da sanin aiken da Abdulwahab ɗin yake yi wa Layuzah ta wajen Mudassir. Sannan kuma sun yaba da tarbiyyarsa da riƙonsa da addini. Sosai iyayen Abdulwahab suka ji daɗin tarbar da aka yi musu. Tin daga wannan ranar Abdulwahab ya riƙe wuta wajen zuwa zance da kafa gwamnatinsa a wajen Layuzah. Ita kuwa dama ta jima da yaba wa da abokin Yayan nata ba ta dai nuna alama ba ne kawai saboda kunya irin ta ƴa mace. Bayan wata ɗaya da zuwan iyayen Abdulwahab,ya shirya ya je ƙauye ya siyar da filayensu gaba ɗayansu da duk wata kadara da kiwon iyayensu aka raba musu gado shi da Salma. Kasonsa ya ɗauka ya gyara gidan iyayensa aka yi musu ginin zamani,a ciki ya yi lefe ya kuma aje na sadaki. A wannan lokacin ne ya haɗu da Malam Sallau. Malam Sallau mutum ne mai riƙon amana,ya ƙware a harkar gini da dillancin gidaje da filaye. Tin daga wannan lokacin suka fara ƙulla alaƙar kasuwanci,domin kuwa Malam Sallau Abdulwahab ya ba wa kuɗin Salma aka siya mata fili ma daidaici,sai ya bada hayarsa wa manoma,duk shekara idan sun yi noma su na ba da kuɗin hayar gona. Ya na zuwa Kano sai ya buɗe mata account a bankin da yake ajiyar tasa dukiyar. Bayan watanni uku aka ɗaura auren Layuzah da Abdulwahab. Aure ne da ya samu halartar dangin iyayensu Abdulwahab ɗin baki ɗaya. Sai dai abun mamaki ta ɓangaren Malam Bala bai je ba,haka ma Hasiye ta ƙi zuwa kuma ta hana yaranta ko ɗaya zuwa. Kande kuwa abun bai dame ta ba,sai ta shiga cikin danginta ta dinga farinciki da murna har aka yi taro aka tashi lafiya,amarya ta tare a ɗakinta cike da gara mai tarin yawan da ba a taɓa irinta a ƙauyen Kura ba. Nan fa mutane suka dinga zuzuta arziƙin iyayen Layuzah wasu ma sai suka dinga yi mata ladabi da biyayya saboda ita ɗin mace ce mai yawan kyauta da ihsani. Layuzah na yin wata biyu a gidan aure Abdulwahab ya ɗauke ta ya mayar da ita Kano,gidan da suka kama haya ya mayar da ita ta ci gaba da zuwa makarantar bokonta. Da gari ya waye suke raba aikin gidan saboda su gama da wuri. Su na gamawa sai su yi wanka su shirya ya ɗauke ta a babur ɗinsa ya kai ta makaranta ya wuce shagonsa da ya bunƙasa ƙwarai da gaske. Sosai Mudassir ya riƙe amana,haka sauran ma'aikatan wajen ma suna son ubangidansu dan baya yi musu mugunta,shi yasa su ma suke kyautata masa suke yin aiki tuƙuru da ransu da lafiyarsu. Cikin ikon Allah duk yanda mutane suka dinga surutun Layuzah bata haihu ba bai dami Abdulwahab ba. Hasali ma gode wa Allah ya dinga yi da bata samu ciki ya katse mata karatu ba. Saboda yanda mutane ke damun Layuzah da zancen haihuwa a Kura sai Abdulwahab ya dena zuwa da ita. Idan ya tashi sai ya je ya yi musu hutun ƙarshen mako ya koma. Duk wanda ya yi masa zancen haihuwa sai ya ce. "Allah bai kawo ba har yanzu tinda tasa ce shi ke bayarwa wanda ya so ya hana wanda ya so. Wanda ya ba wa kuma muna taya su murna da fatan su samu damar yi wa kyautar da Allah ya basu kyakkyawan riƙo." Halin ko in kular da yake nunawa na damun dangin mahaifansa,har meeting suka haɗa akansa amma ya je ya faɗa musu komai lokaci gare shi ya tashi ya yi tafiyarsa. Ana haka Mudassir ya ɗora idanuwansa akan wata Buzuwa da ke zuwa wajen su ta na siyan gero. Tinda Mudassir ya ɗora idonsa akanta ya ji ya kamu da ƙaunarta amma yana jin tsoron ko matar aure ce saboda yanayin yanda take shiga cikin mutunci. Ganin yanda ita ma idan ta je shagon bata gansa ba take tambayarsa ne ya sanya shi binta har gidansu a ɓoye dan ganin inda take, Sai da ya bari ta shiga sannan ya aika yaro gidan dan ya kira masa Buzuwar. Lokacin da ta fito ta ga Mudassir sai ta ce. "Wataƙila rabo ne yake kiranka. Domin kuwa daf mahaifina yake da bada ni." Ƙirji Mudassir ya dafe ya ce. "Ki ce da na yi jinkiri da an yi babu ni?" Murmushi kawai ta yi ta rufe fuskarta. Shi ɗin ma mayar mata da martanin murmushin ya yi ya ce mata. "To ya sunan masoyiyar tawa?" "Ammabuwa." "In Sha Allahu ke mallaki na ce,ke ce za ki zamo uwar yarana. Ni suna na..." "Mudassir. Kada ka yi mamakin yanda aka yi na san sunan ka." "Lallai kuwa ba zan yi mamaki ba,tinda yanzu sunan shagon namu ma na neman ya koma shagon Mudassir." Gyaɗa kai ta yi tana murmushi. A haka mahaifinta ya dawo ya tarar da su. Cike da girmamawa Mudassir ya durƙusa har ƙasa ya gaida shi,shi ma cikin mutuntawa ya amsa ya shige gida. Ya na shiga Ammabuwa ta bi bayan mahaifinta ta shige gida ta na ɗaga wa Mudassir hannu. A wannan ranar Mudassir ya tunkari Abdulwahab da zancen Ammabuwa,shi kuwa babu ɓata lokaci ya sanya musu albarka,sannan ya yi masa alƙawarin kashe masa duk wani kuɗi da zai buƙata domin aurensa. Cikin lokaci ƙanƙani aka yi auren Ammabuwa da Mudassir,inda suke zaune a gida ɗaya da shi da amininsa da ya zamo masa tamkar Ɗan'uwa. Matansu sai suka zamo kamar Hassana da Hussaina,sosai Ammabuwa ke girmama Layuzah,saboda Layuzah ta girme ta da shekara ɗaya,kuma bayan haka mijin Layuzah shi ne mai arziƙin da suke raɓe suke ci ta kowacce siga ita da mijinta. Bayan watanni uku da auren Ammabuwa da Mudassir.... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ PAGE 13. Bayan watanni uku da auren Ammabuwa da Mudassir ta fara laulayi mai matuƙar wahala,har sai da ya zamto ba ta iya yi wa kanta komai sai an taimaka mata. Da safe kafin Mudassir ya fita kasuwa shi yake taya ta wanka ya sauya mata kaya. Su na tafiya Layuzah za ta shiga ta kwashe kayan wankin Ammabuwa da na Yayanta ta wanke musu,ita ke dafa mata duk wani abu da take son ci sannan ta zauna ta yi mata hira. Sosai take farinciki da samun cikin da Ammabuwa ta yi,ita kuwa Ammabuwa tsoron kada ta haihu jikinta ya lalace Mudassir ya ƙara aure shi ne ya janyo mata tsanar cikin jikinta. A kullum idan Layuzah na murna ta na faɗin irin gatan da za ta bawa yaro ko yarinyar da Ammabuwa za ta haifa sai Ammabuwa ta ce. "Ni da ma ke ce kika samu cikin nan ba ni ba,domin gaskiya ba zan iya da ɗawainiyar yara ba. Ko a gidanmu ni kaɗai ce bani da wa bani da ƙani,bana son hayaniyar yara ballantana hidimarsu." Cike da sanyin murya Layuzah ta ce. "Ki gode wa Allah,domin shi kaɗai ne ke bada kyautar ɗan mutum ga wanda ya so,wannan maganganun naki sam basu dace ba." A haka suka ci gaba da zama cikin aminci da mutunta juna har cikin Ammabuwa ya cika watanni biyar a duniya. Daga nan ne maƙota masu gulma suka fara shige da fice suna ƙoƙarin raba kan Layuzah da Ammabuwa saboda ganin yanda suke zaune lafiya,Layuzah na bawa Ammabuwa girmanta a matsayinta na matar Yayanta,ita kuwa Ammabuwa na ba wa Layuzah girma a matsayinta na wadda mijinta ke kula da su da duk wata ɗawainiyarsu. Sai dai cikin hukuncin Allah babu wadda ta yi nasarar dasa musu tsanar junansu. Daga ƙarshe da Layuzah ta fuskanci masu shige da fice a gidan na neman yi musu yawa,kuma ba da alkhairi suke zuwar musu ba,sai suka fara zama a waje ɗaya a duk sanda ɗayarsu ta yi baƙuwa. Ganin haka sai mutanen unguwar suma suka fara ja da baya suka rage zuwa,ko sun zo sai dai a gaisa a tsakar gida babu mai kai su ɗakinta su tashi su tafi,sosai su Ammabuwa suka toshe duk wata kafa da za a raba kansu. Wannan abun da suka yi ya faranta ran mazajen su ƙwarai da gaske. Lokacin da cikin Ammabuwa ya kai wata takwas Abdulwahab ya sauya musu gida suka koma Ƴankaba da zama. Komawarsu Ƴankaba ya sake zuwar musu da sabon arziƙi;har sai da ta kai ta kawo Abdulwahab ya fara fitar da kayan hatsinsa zuwa ƙasashen Nijer,Ghana,da Chadi. Sosai arziƙinsa yake ta bunƙasa har ya sayi ƙaton fili a cikin garin Kanon. Har sun manta da sun miƙa takardunsu wajen neman aiki,sai gashi Abdulwahab ya samu aikin da yake buri da fata. Murna sosai Mudassir ya taya shi ya ce. "Ka ga shikenan ni sai na ci gaba da kula da ɓangaren kasuwancinmu na nan kai kuma kana zuwa aikinka na gwamnati." "Ai kuma sai abubuwan su yi maka yawa abokina,tinda aikin gwamnatin da na samu duk ya shafi harkar noma wannan kasuwancin namu ma ba zai gagare ni ba. Wataƙila idan na tura kayanmu ma sai ka ga sun samu shiga a wajen gwamnati." Haka su Abdulwahab suka dinga tattaunawa suna samawa kansu mafita akan ci gaban rayuwarsu. Watarana Abdulwahab ya samu Mudassir da shawarar yana so ya biya wa Gwaggo Kande kujerar Makka kamar yanda ya yi mata alƙawari,domin kuwa ita yake gani a matsayin iyayensa a yanzu,dan kuwa ita ce macen da ta yi masa riƙo na gaskiya da amana. Sosai Mudassir ya ƙara ba shi ƙwarin guiwar yin hakan. A tare suka je Kura suka sanar da Malam Bala ƙudirin Abdulwahab na kai Gwaggo Kande Makka,wani irin kishi,hassada da ƙyashi ne ya taso ya lulluɓe zuciyar Hasiye,ji take yi kamar ta zuga Malam Bala ya hana Kande zuwa Makka,sai dai tana ji ta na gani Malam Ya amince su Abdulwahab suka ɗakko Gwaggo Kande da Salma suka kawo su Kano. A cikin satin suka kai ta aka yi mata international passport da duk wani abu da ya dace. Su na dawowa suka tarar da Ammabuwa na naƙuɗa Layuzah na ta kuka saboda bata san da me za ta taimaka mata ba,gashi zamanin babu waya ballantana ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki. Ko ajiye hijabi Gwaggo Kande bata yi ba ta kori su Mudassir da suka rikice su na faɗin ta fito a tafi asibiti. Su na fita Gwaggo Kande ta taimaka wa Ammabuwa har ta haifi sankacecen ɗanta kyakkyawa fari tas mai kama da ita. Kukan jaririn ne ya sanar da su Mudassir Ammabuwa ta sauka ƙalau. Murna sosai suka dinga yi shi da Abdulwahab. Layuzah kuwa hamdala ta dinga yi tana maimaitawa bakinta ya ƙi rufuwa. Da yammar Gwaggo Kande ta hura wuta a murhu, nan da nan ta ɗora ruwan wanka ta wanke jariri da mahaifiyarsa. Kafin su gama shiri Abdulwahab ya je wajen mai gashin nama ya siyo nama mai yawa da madarar shanu da dabino ya kawo. Yanda ya dinga hidima da Ammabuwa da jaririnta sai ka rantse Layuzah ce ta haihu. Mudassir har kuka ya dinga yi yana ji a ransa zai iya bada rayuwarsa saboda Abdulwahab. Washegari ya je gidansu Ammabuwa ya sanar da haihuwarta, mahaifiyarta ta so ƙanwarta ta je ta kula da Ammabuwa,amma sai ya ce ai akwai mai kula da ita,domin Ammabuwa da kanta ta sanar da shi bata son kowa ya zo saboda gudun gutsiri tsoma na mutane har a yi abinda zai taɓa zumuncinta da Layuzah. Abdulwahab shi ne ya sayi ragunan suna manya guda biyu. Dan haka ranar suna Mudassir ya ce yaro ya ci sunan Abdulwahab. Sosai hakan ya yi wa Abdulwahab daɗi sai Layuzah ta ce za su dinga kiransa da Maheer. Ita dai Ammabuwa har a wannan lokacin yaron bai wani shiga ranta ba,shi yasa ko kuka yake idan Layuzah ta kawo mata shi dan ta shayar da shi,sai ta dinga kuka ta na faɗin zai mayar da ita tsohuwa. Sai da Gwaggo Kande ta yi mata wankin babban bargo sannan ta ce za ta je har gidan iyayenta ta faɗi iyashegen da take yi,sannan ta rungumi yaronta ta na bashi kulawar da ta dace duk wata uwa ta ba wa ɗanta. Bayan suna da sati biyu Gwaggo Kande ta tafi Makka,sosai Salma take taya Ammabuwa rainon Maheer. Idan aka goya mata shi bata sauke shi har sai ya yi kukan yunwa,ya na shan mama za ta ce a goya mata shi,sam bata gajiya da ɗawainiyarsa. Layuzah na matuƙar jin daɗin zama da Salma,domin yarinya ce ita mai matuƙar natsuwa da hankali tare da sanin ya kamata. Satin Gwaggo Kande biyu a Makka ta dawo cike da tsaraba mai tarin yawa. Domin kuwa duk wasu ƴan kuɗaɗen da za ta ci abinci da Abdulwahab ya bata bata saki jiki ta kashe su ba,Salma kanta sai da ta samu riguna da takalma bakwai. Sannan ta yi wa mutanen Kura tsaraba musamman Malam Bala da dangin mahaifan Abdulwahab na uwa da uba. Kwanan ta uku ta kafe sai ta tafi Kura,kuma da Salma za ta tafi,domin amana ce Atine ta bata,ba za ta rabu da ita ba sai aure ko mutuwa. Salma na jin maganar aure kunya ta kama ta,sai ta dena rikicin ba za ta bi Gwaggo Kande ba ta wuce ta fara haɗa kayanta. Washegari da sassafe Abdulwahab ya saka su a mota suka koma Kura. Gwaggo Kande na tafiya Mahaifiyar Ammabuwa ta matsa akan sai Ammabuwa ta koma gida wanka,domin ta gano babu wani babba da ke yi mata wanka shirmen su kawai suke yi ita da Layuzah a gidan. A daidai wannan gaɓar Layuzah ta shiga damuwa saboda tafiyar Ammabuwa,sai take jin gidan shiru babu Salma,babu Maheer,ga Ammabuwa ƙawa kuma aminiyarta ta koma gidan iyayenta. Wannan damuwar da ta shiga ne ya sanya Abdulwahab bata lokacinsa sosai,har ya zamana watarana ma baya fita aiki ko kasuwa, Mudassir ne kawai yake tafiya ya ji da komai. Ana haka Layuzah ta fara yawan cin abinci da kwaɗayin tsiya,bata yin wani ciwon kuma bata amai ballantana zazzaɓi. Gaba ɗaya basu gane abinda ke faruwa da ita ba har sai da Ammabuwa ta gama wankan gida,danginta suka dawo da ita cikin kwalliya irin ta Buzaye da kayan gara irin na al'ada da ake yi a duk haihuwar fari. A lokacin da za su tafi ne wata Innar Ammabuwa ta ke cewa. "To Gwaggon Maheer kema Allah Ya sauke ki lafiya. Ku ci gaba da haƙuri da junanku domin zaman ku lafiya na faranta mana rai mu iyayenku. Allah Ya yi muku albarka." Da haka suka tattara suka tafi suka bar Ammabuwa cikin murnar dawowa kusa da aminiyarta. Bayan sun raka su sun dawo ne Ammabuwa ta ce. "Ƴar'uwa wai meye sirrin ne na ga kin yi wani irin kyau sai kace yanzu ne kuke cin amarci ke da Yayana?" Murmushi Layuzah ta yi ta ce. "Ni kai na ban san me yake damu na ba,kin ganni nan babu abinda na saka a gaba da ya wuce kwaɗayi da yawan cin abinci, sai kuma yawan bacci kamar wata kasa." "To ko dai maganar Innahta ce za ta zamo gaskiya Maheer zai samu ƙani ko ƙanwa?" Kunya ce ta kama Layuzah ta ce. "Habaa babu wani ciki da nake ɗauke da shi ni dai. Da duk ban samu ba sai yanzu?" "Iyi mana,ai Baban Mudassir ya bani labari irin soyayyar da kuke zubawa a gidan nan kamar wasu tattabaru." Dariya kawai Layuzah ta yi, ta wuce ciki ta ɗakkowa Ammabuwa abicin da ta dafa mata na musamman. Nan suka zauna su na ta hira Layuzah na riƙe da Maheer a cinyarta ta na jin son yaron na ƙaruwa a cikin ranta saboda kyau da girman da ya sake yi. Su Layuzah basu tashi sanin tana dauke da ciki ba har sai da cikinta ya kai watanni huɗu a duniya. Ranar da ta fara jin motsi ta gigice ta gigita kowa a gidan. A wannan ranar kuwa Abdulwahab baya gari tafiya ta kama su daga wajen aikinsa. Mudassir ne ya ɗauke ta a kan babur ya kai ta asibiti aka duba ta. Bayan gwaje-gwaje likita ya tabbatar musu da cewar ta na ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni huɗu. Murna sosai Mudassir ya dinga yi,ita kuwa Layuzah sai ta ji kunyar Yayan nata ta kama ta har ta ƙi hawa babur ɗinsa sai da ya samo mata bus ta hau aka mayar da ita Ƴankaba. Ta na zuwa gida ta tarar da Mudassir ya riga ta zuwa har ya sanar da Ammabuwa. A ƙofar gida ta tarar da Ammabuwa goye da Maheer ta na ta washe baki. Hijabi ta sa ta rufe fuskarta saboda kunyar da ta ke ji. A haka suka shige gida Ammabuwa na nan nan da ita. Har so take ta ji Layuzah na buƙatar wani abu ta gabatar mata da shi. Bayan kwana biyu Abdulwahab ya dawo daga tafiya aka sanar da shi wannan labarin mai daɗi,farinciki ya dinga yi ya na kumawa tare da godiya ga Allah da ya yi masa wannan kyautar. Sosai mutanen nan uku suke nuna wa Layuzah kulawa har watarana ta kan rasa bakin yi musu godiya. Idan Mudassir na tsokanar Abdulwahab sai ya ce. "Ni dai na shiga uku da surukin zamani,wai kai ba ka jin kunya ta ne don Allah?" "Ina fa zan ji kunyar ka tinda dai ni ba a suruki na ɗauke ka ba. Kai ɗin abokina ne,aminina ne kuma ɗan'uwana. Dan haka babu wata kunya a tsakaninmu." Abdulwahab na jin daɗi a ransa idan ya ji Mudassir na bashi babban matsayi a ransa. Ana haka cikin Layuzah ya shiga watan haihuwa,gashi Abdulwahab ya na so ya yi tafiya ƙasar Ghana saboda shigar da wasu kaya da suke son su yi. Da jin haka sai Layuzah ta hau kuka ta na faɗin. "Gaskiya babu inda za ka tafi ka barmu ni da abinda ke ciki na,ko kana son ka tafi ka barni wajen haihuwa na mutu baka nan?" Da sauri Abdulwahab ya kalle ta ya na jin zuciyarsa na tsananta bugawa. A duniya baya son ya ji Layuzah na kiran mutuwa ko rabuwa a tsakaninsu. Dan haka cike da rarrashi ya ce. "Ki kwantar da hankalinki,babu inda zan je, bana Yayanki zan tura Ghana duk da baya son tafiye-tafiye,na rasa me yake jin tsoro,amma dai a wannan karon dole shi zai je,idan ba haka ba kuma sai dai mu haƙura da kai kayan gaba ɗaya,tinda ke kin ƙi amincewa na tafi." Haka suka dinga hira Layuzah na sake jaddada wa Abdulwahab rashin son tafiyar da zai yi. Lokacin sallar Isha'i na yi ya tafi ya yi alwala ya wuce masallaci. Bayan an idar da sallah su na dawowa daga masallaci Abdulwahab ya kawo wa Mudassir buƙatarsa na tafiya ƙasar Ghana kai kaya da yake son ya yi. Ba dan Mudassir ya so ba kan dole ya amince da tafiyar. Su na zuwa gida ya dinga yi wa Layuzah masifa ya na cewa duk laifinta ne ta sa mijinta zai aika shi wata uwa duniyar. Dariya kawai ta yi ta ci gaba da yi wa Maheer wasa. Ammabuwa kuwa sai ta ce. "To ai gwanda ka yi tafiyar ma ko mutum ya ɗan huta na wasu kwanakin. A yi mutum kullum ya na gida ko tafiyar kwana ɗaya baka taɓa yi ba fa." Ƙanƙance ido Mudassir ya yi yana kallon Ammabuwa ya ce. "Au haka ne? Dama duk ƙarya kike zuba min da kike cewa ba kya son in dinga yin nisa da ke? To ai shikenan,Aboki ni fa daga yanzu na koma ɓangaren zirga-zirgar ƙasa da ƙasa." Dariya sosai suka yi gaba ɗayansu,sannan suka ci gaba da hira mai cike da nishaɗi da barkwanci. A wannan ranar basu rabu da junansu ba sai misalin sha ɗaya da rabi na dare. A daren kuma Ammabuwa ta haɗa wa Mudassir kaya a ƴar ƙaramar jaka ta saka masa duk abinda zai buƙata. Sannan suka kwanta suka raya daren nasu cike da soyayya. Washegari ana idar da sallar asuba Malam Sallau ya zo da tawagar da za su yi tafiyar a mota. Sallama Mudassir ya yi wa su Ammabuwa da Layuzah dake riƙe da Maheer da ya tashi tun asuba bai koma bacci ba,banda kuka babu abinda yake yi. Su na gama sallama ya bi Abdulwahab suka tsaya a zaure ya bashi wasu ƴan kuɗaɗen da zai yi amfani da su ko da buƙatar hakan ta taso. Rungume junansu suka yi sannan suka yi musabaha hannunsu na riƙe da na junansu Mudassir ya shiga mota yana ɗaga wa Amininsa hannu........ MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ PAGE 14. Zuwan Mudassir ƙasar Ghana ya sanya idamuwansa sake buɗewa akan kasuwanci ƙwarai da gaske. Lokacin da za su dawo gida Nigeria bai yi shawara da kowa ba ya saro wasu daga abubuwan da suke da shi a can wanda mutanenmu na Nigeria ke da buƙata suka kamo hanya da sauran yaran Abdulwahab suka dawo. A wannan lokacin ne ɗaya daga cikin yaran Abdulwahab mai suna Iliya ya kai masa gulmar yanda Mudassir ya dinga facaka da dukiyarsa a Ghana. Nan take shaiɗan ya yi uwa ya yi makarɓiya ya dasa wa Abdulwahab wani ƙulli a cikin zuciyarsa game da aminin nasa kuma Yaya ga matarsa. Tin daga wannan ranar alaƙarsu ta fara sauyawa,sai ya zamana kafin Abdulwahab ya kira Mudassir sau ɗaya ya kira Iliya sau biyar. Mudassir na kula da hakan sai ya ja baya ya koma yin ayyukan da ba lallai ne sai ya nemi izinin Abdulwahab ba,sannan ya kame bakinsa bai sanar da matarsa ko ƙanwarsa sauyin da yake gani a tattare da abokin nasa ba. Sosai Mudassir ya kai zuciyarsa nesa game da yanda Abdulwahab ya dinga ɗaure masa fuska da nuna masa iyakarsa,sai Mudassir ya nuna sam bai ma gane abinda yake yi ba,harkar gabansa kawai ya sa a gaba tare da ƙoƙarin kawo cigaba a cikin kasuwancin da suka sha wahala wajen ginawa. A hankali Malam Sallau ya kula da abinda ke faruwa a tsakanin aminan junan. A matsayinsa na amintaccen yaron Abdulwahab sai ya tsaya ya tsananta bincike akan lamarin,babu jimawa kuwa ya gano abinda ke faruwa. Ba tare da sanin kowa ba ya ɗana wa matashin dake son ya ture Mudassir daga rayuwar Abdulwahab shi ya kafa tashi kujerar tarko. Watarana Malam Sallau ya karɓo takardun wasu filaye da ya siyo wa Abdulwahab sai ya je shago ya bawa Mudassir a gaban Iliya da mutanen shagon ya ce ya bawa Abdulwahab,babu ɓata lokaci Mudassir ya karɓa ya saka su a cikin jakar da yake zuwa da ita shagon nasu da niyyar idan Abdulwahab ya taso daga aiki ya biyo shago sai ya bashi,idan kuma bai biyo ba in sun je gida sai ya bashi,daga nan sai ya ci gaba da harkar gabansa. Malam Sallau na zaune ya na ta hirarsa amma gaba ɗaya hankalinsa ya na kan Iliya da ke ta kallon mutane ya na zuge jakar Mudassir. A hankali ya zare takardun ya fita daga shagon da sauri ya nufi shagon da suke kwana ya ɓoye,ya na gama ɓoyewa ya dawo ya ci gaba da aikinsa kamar babu abinda ya aikata. Da ganin haka sai zargin da Malam Sallau yake yi akansa ya tabbata. Sai da ya bari an tafi sallar magrib ya shiga shagon su Iliya ya ɗauke takardun. Da dare bayan Abdulwahab ya koma gida Malam Sallau ya je ya bashi labarin duk abinda yake faruwa da kuma hasashen da yake yi akan Iliya. Cike da tsantsar nadama da danasani tare da jin nauyi da kunya Abdulwahab ya ce. "Bana tamtama akan abinda ka sanar da ni Malam Sallau,amma ina so don Allah ka taimaka mini domin kama Iliya hannu da hannu domin na ji daɗin hukunta shi akan abinda ya sa na aikata." "Yauwaa Alhaji an zo wajen. Ina so gobe da safe a gaban Iliya ka tambayi Malam Mudan takardun nan da na nuna maka,da ka tambaya ka bar min komai a hannuna." Sallama suka yi da Malam Sallau Abdulwahab ya koma cikin gida cike da nadama,a wannan ranar ya gane cewa lallai matansu sun yi ƙoƙari da suka riƙe zumunci suka ƙi ba wa ƴan gulma damar shiga tsakaninsu. Tunani ya fara yi ta yaya ma har ya bari wani bare zai raba shi da mutumin da ya fara taimaka masa a rayuwa? Duk dukiyar da ya tara yake alfaharin zamowarta tasa da taimakon Mudassir ya tara ta. A wannan daren kasa bacci Abdulwahab ya yi. Asuba na yi ya watsa ruwa ya yi alwala ya tafi masallaci. Bayan an idar da sallah kafin Mudassir ya fito daga masallacin Abdulwahab ya gudu gida,domin kunya yake ji ya haɗa ido da shi ballantana har su yi magana. Ya na kwanciya bacci mai daɗi ya ɗauke shi har Mudassir ya shirya ya samu Layuzah ya tambaye ta ko Abdulwahab ya farka kuwa? Sanar da shi ta yi bai farka ba,dan haka sai ya tafi kasuwa da zummar idan Abdulwahab ya je zai bashi takardun a can. Abdulwahab na farkawa Layuzah ta sanar da shi zuwan Mudassir,shiru ya yi kamar wanda ruwa ya cinye,gani yake yi kamar kowa ya san abinda ya aikata a gidan. Sai kawai ya ɗakko mata zancen zuwan Gwaggo Kande domin ta kula da ita har ranar da za ta haihu. Cike da jin kunya Layuzah ta ce. "Ni dai gaskiya bana son Gwaggo Kande ta zo ta karɓi haihuwa ta. Dama ina a can Kuran ne idan ta karɓi haihuwar babu komai,amma ina a nan gaskiya ni dai a barta kawai,idan na sauka lafiya sai ta zo ta dinga yi wa jariri wanka." Murmushi ya yi ya shafa ƙaton cikin nata da suke wa laƙabi da cikin ƴan biyu. Ba tare da ya ce komai ba ya ƙarasa shirin fita ya buga babur ɗinsa ya wuce kasuwa. Ko da ya isa ya tarar da manyan shagunan nasa guda huɗu dake jere da juna sun ɗauki harami ana ta cinikayya. Shigarsa wajen ke da wuya yaransa suka je suna ta gaishe shi yana amsawa. Malam Sallau dake zaune a gefe ma ya gaishe shi yana kallon Mudassir dake zuwa shagon hannunsa riƙe da jakar bakkonsa da yake saka kayansa a ciki. Ya na zuwa ya fara gaishe da Abdulwahab wanda sai a wannan lokacin ya gane irin sauyawar da ya yi ashe ba kaɗan bace. Su da suke caccafkewa da abokinsa kuma amininsa su zauna a waje ɗaya,yau shi ne Mudassir ke risinawa ya na gaishe shi a ɗarare gudun kada a ce ya yi wani laifin. Nan take ƙwalla ta taru a idanuwansa yana jin kamar ya kurma ihu. Da ƙyar ya danne abinda ke taso masa a rai ya ce. "Aboki ina takardun da Man Sallau ya baka jiya ka bani." Cikin rawar jiki Mudassir ya isa gaban Abdulwahab ya na duba jakarsa ya hau neman takardun. Wani irin tausayinsa ne ya kama Abdulwahab. Kafin ya dawo cikin hayyacinsa Iliya ya isa gaban Abdulwahab ya ce. "Ai Alhaji ba zai iya baka waɗannan takardu ba. Domin kuwa jiya ya zaci na wuce gida sai wani mutum ya zo ya bashi takardun shi kuma mutumin ya bashi maƙudan kuɗaɗe. A nan ne ma na ji shi Malam Mudan ya na cewa ai shi ne silar arziƙinka to shi ma zai je ya kafa kansa ya gaji da wahalta maka." Salati Mudassir ya yi ya duƙar da kansa sai ga hawaye na zuba daga kwarmin idanuwansa. Ya kasa kare kansa domin bashi da kalaman da zai yi amfani da su ya kare kan nasa. Addu'a ya dinga yi Allah ya kare masa mutuncinsa kada ya ba wa maƙiya damar  tozarta shi a gaban amininsa. Iliya na gama zuba miyagun kalamansa a kunnen Abdulwahab ya ji saukar mari ta inda bai taɓa zato ba. Idanu ya zaro waje ya na kallon Abdulwahab da ya miƙe tsaye ya na huci kamar wani zaki. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce wa Iliya. "Ka je na sallame ka daga aiki a ƙarƙashi na,sallama ta har abada Iliya. Sannan ka sani idan har baka nemi tafiya akan abinda ka aikata ba alhakin bawan Allah'n nan da ni kai na ba zai barka ka ji daɗi a rayuwarka ba. Sallau maza ku je da shi ya ɗakko takardun filaye na ya baka ka kawo min,ka karɓe duk wani makullin shago na da yake wajensa. Ga wannan kuɗin sallamar ka ne,domin ba zan riƙe maka haƙƙinka ba." Kuɗi ya ƙirgo a drawer dake kusa da shi ya miƙa wa Iliya da kunya ta gama baibayewa. Malam Sallau kuwa a gaba ya saka shi suka shiga shagon masu aikin,nan fa Iliya ya hau duba kayansa ya na neman takardun da ya adana a cikin kayan amma bai gani ba. Dariya Malam Sallau ya yi sannan ya zaro su daga aljihunsa ya na kaɗa wa Iliya a gaban fuskarsa ya ce. "An faɗa maka kai kaɗai ne ka iya makirci? Kalle ni nan ka gani Iliya. Duk makircinka na dame ka na shanye,sai dai ni makircina akan irinku yake aiki. Dan haka maza ka kwashe tsummokaranka ka ƙara gaba,ka yi wasa da damarka ta zamowa ƙaramin attajiri a ƙarƙashin mutumin da dukiyarsa bata rufe masa ido ba,baya kuma yi wa na ƙasa da shi mugunta." Cike da nadama Iliya ya bar shagon da jakar kayansa ya na nadamar abinda ya aikata. Sai dai a yanda ya ga ran Abdulwahab ya ɓaci ya san ba zai taɓa iya tunkararsa ba ballantana ya bashi haƙuri ya mayar da shi bakin aikinsa. A wannan ranar Abdulwahab kasa ba wa Mudassir haƙuri ya yi. Domin bashi da bakin da zai bashi haƙuri. Sosai ya shiga ƴar wasan ɓuya da shi,baya fitowa daga ɗakinsa sai ya tabbata Mudassir ya bar gidan. Sannan baya dawowa gidan sai ya tabbata Mudassir ya yi bacci. A hankali matansu suka fara gane akwai matsala a tsakanin mazajen nasu har suka zauna suka tattauna akan lamarin. Dan haka a daren ranar Ammabuwa ta turke Mudassir a ɗaki ta hau tambayarsa abinda ke faruwa tsakaninsa da Abdulwahab.Murmushi ya yi ya ce. "Ohh mata kenan akwai ku da sa ido,to hasahenku da ke da ƙanwar taki bai zamo gaskiya ba. Kun manta shi yana haɗawa da aikin gwamnati bayan kasuwanci? Sannan shi aikin gwamnati kamar aikin noma ne,a damina manomi ya fi aikatuwa da rashin lokacin kansa. Bayan damina ta ja baya ya girbe amfanin gonarsa sai aiki ya sauƙaƙa a gare shi. To haka lamarin yake a wajen Aboki. Ya sanar da ni cewar aiki ya yi masa yawa a office shi yasa kuke ganin kamar ba ma magana sosai kamar da." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ammabuwa ta sauke kafin ta ce. "Har na ji wani irin daɗi a raina Baban Maheer da ba saɓani kuka samu da Yayana ba. Allah Ya ƙara haɗa kammu ya bamu zama na aminci da amana." "Amin Ya Allah Ummu Maheer." Daga nan suka sauya salon hirar tasu har Ammabuwa ta samu bacci. Waje ya samu ya zauna domin kuwa yana so a wannan ranar ya kawo ƙarshen wasan ɓoyon dake gudana a tsakaninsa da abokinsa. Ya na nan zaune gyangyaɗi na ɗibansa ya ji dawowar Abdulwahab. Cikin sauri ya buɗe ƙofar ɗakinsa a hankali ya fita. A lokacin da Abdulwahab ya gansa sai da ya razana. Da sauri ya kafe babur ɗinsa ya ce. "Ah Aboki baka yi bacci ba?" "Ina fa zan yi bacci ƴan jarida sun fara ɗaukan rahoto akan irin zaman da muke yi da ni da kai a gidan nan?" Cikin rashin fahimta Abdulwahab ya ce. "Ƴan jarida kuma? Wa ya basu labarin abinda ya faru?" "Mu je ƙofar gida mu tattauna." Jiki babu ƙwari Abdulwahab ya bi bayan Mudassir suka je ƙofar gida suka zauna a dandamalin dake ƙofar gidan nasu. Shiru ne ya ratsa a tsakaninsu kafin Abdulwahab ya buɗe baki ya ce. "Na rasa da wacce fuska zan kalli idonka na baka haƙuri akan abubuwan da na dinga yi maka a baya. Don girman Allah abokina ka yi haƙuri akan dikkan abinda ya faru a tsakaninmu. Har yanzu na kasa yafe wa kaina irin kallon da na dinga yi maka,da tozarci tare da kyarar ka da nake yi ma a kasuwa duk kuma a gaban mutane." Murmushi Mudassir ya yi ya ce. "Ban haƙurin ka ya karɓu Aboki,ina so ka sani tun kafin ka bani haƙuri na yafe maka,domin na san cewa zuciya bata da ƙashi,zama kuma ya gaji haka,zo mu zauna ne,kuma zo mu saɓa duk zaman da za ka ga ba a samun saɓani komai ƙanƙantarsa to ka bincika ɗaya yana munafurtar ɗaya ko yana yi masa zagon ƙasa. Sannan abinda ka aikata ai ba laifinka bane ziga ce irin ta maƙiya kawai ta shiga zuciyarka kai kuma ka yi aiki da ita." "Hakane Aboki. Ka na da kyakkyawar zuciya. Allah Ya ƙara mana haƙurin zama da juna ya kare mu daga sharrin shaiɗanun mutane. Malam Sallau shi ne ya same ni har gida ya min bayanin komai,sannan ya yi min nasiha akan ruko da zumuncin da muka gina tin kafin wannan lokacin." "Da yardar Allah sai mun samu lada da Aljannar da Allah ke ba wa bayinSa da suka yi zumunci dominSa Abokina. To wai ni ina ka je yau da na ga ka fi kowanne lokaci jimawa a waje?" "Kura na je na gaida mutanen gida na kuma ga Salma. Na so na taho da ita Gwaggo Kande ta hana, ta ce sun kusa jarabawar common entrance na jira har ta gama sai na ɗauke ta ta min hutu mai yawa. A nan nake samun labarin wannan sakarar Samira ta gaji da jira na ta yi aure." Dariya Mudassir ya yi sannan ya ce. "Ai kuwa ka ga da ka aure ta ta gyara wa shagwaɓaɓɓiyar matarka zama a gidan nan." "Allah Ya yi min tsari da auren Samira, a barwa matata shagwaɓarta ina son ta a haka." Daga nan hira ta ɓarke a tsakaninsu har basu san dare ya tsala ba;sai da Mudassir ya fara hamma sannan suka shiga gida suka kulle kowa ya yi ɗakinsa. Da asuba bayan su Abdulwahab sun tafi masallaci naƙuda ta kama Layuzah. Kafin su dawo ta haihu lafiya a gida da taimakon Ammabuwa. Ko da suka dawo suka ji kukan jariri sai suka yi zaton Maheer ne. Mudassir ne ya ce. "Kai anya wannan kukan na Maheer ne kuwa? Ko dai Layuzah ce ta haihu?" Da sauri suka ƙarasa shiga cikin gidan. Su na zuwa suka tarar da zannuwan da Ammabuwa ta goge jini da su a rataye a igiya tana ta shanya wasu. Gefe ɗaya kuma ga ƙatuwar tukunya nan ta ɗora ta na dafa ruwan zafin da za ta yi wa jariri da Mamansa wanka. Farinciki ne ya mamaye zuƙatansu sai suka hau godiya ga Allah suna tambayar abinda aka samu. Cike da murna Ammabuwa ta ce. "Addu'a ta ce ta karɓu Maheer ya yi aboki shima kamar iyayensa." Cikin tsananin farinciki Abdulwahab ya shiga ɗakin ya ga Layuzah kwance a gado ta tasa jaririnta a gaba tana kallo cike da so da ƙauna. Su na haɗa ido ta tashi zaune ta na miƙa masa jaririn da aka naɗe cikin zani. Hawayen farinciki ne suka sauka a kuncin Abdulwahab ya karɓi yaron ya yi masa kiran sallah,cikin rawar murya ya ce. "Mahaifina Malam Musa ya yi takwara Layuzah. Ya Allah ka sa yaron nan ya yo gadon kyawawan halayyar masu sunansa. Allah ka yi masa albarka Ka raya mana shi akan tafarki madaidaici." "Amin Ya Allah Baban Aabid." Kallonta ya yi cike da tsokana ya ce. "Tooo Aabid kuma?" Kai Layuzah ta gyaɗa ta ce. "Ƙwarai da gaske,ai na ji labarin yanda Abbanku yake da yawan ibada da dogaro ga Allah a wajen Gwaggo Kande. Shi yasa zan dinga kiransa da Aabid saboda shima ya yo gadon yawan ibada da tsoron Allah." Waje Abdulwahab ya fita da yaron ya kai wa Mudassir tare da sanar da shi sunan da ya raɗawa yaron. Addu'a shima ya yi wa Aabid sosai sannan ya yaba da sunan da za a dinga kiransa da shi. Ruwa na tafasa Ammabuwa ta haɗa ruwan wankan jariri ta je ta karɓe sa a hannun iyayen nasa da ke ta murna. Tambayar Maheer Abdulwahab ya yi,sai Ammabuwa ta ce. "Ai yau sarkin rikicin ya san ƙaninsa ya zo duniya ya zama babba. Ya na can yana bacci bai tashi ba." Dariya suka yi gaba ɗayansu ta shige ciki ta fara yi wa yaro wanka. Ta na gamawa ta shirya sa da ɗaya daga cikin kayan jariran da Abdulwahab da Mudassir ke yawan siyo wa a duk lokacin da suka fita wata ƙasar ko suka shiga kasuwa suka gani. Ta na gamawa ta kai wa mazan jaririn ta kwashe wa Layuzah ruwan wanka suka shiga banɗaki ta yi mata wanka tsaf suka fito. Sosai Ammabuwa ta dinga mamakin yanda Layuzah ta jure ruwan zafi bata yi raki ba kamar yanda ita ta yi a lokacinta. Gari na wayewa Abdulwahab ya aika Sallau can Kura ya taho da Gwaggo Kande. Da zuwanta ta karɓi aikin kula da wankan yaro da kuma Layuzah'n kanta. Bayan suna Salma ta gama jarabawarta Malam Sallau ya je ya ɗakkota ya kawo ta gidan. Sosai ta dinga murnar ganin yaron. Bacci,wanka,sallah da cin abinci ne kawai ke raba ta da Aabid idan ta ɗauke shi. Lokacin da Gwaggo Kande ta zo komawa sai Salma ta kafe ba za ta bi ta ba har sai sakamakon jarabawarsu ya fito sannan za ta koma. Kan dole Gwaggo Kande ta koma ba tare da Salma ba. Ta na isa gidan bayan ta huta Malam Bala ya same ta har ɗaki riƙe da kwalin chewing gum,minti da goro yana washe baki. Cikin rashin fahimta Gwaggo Kande da ke ƙarasa ninke zanin kayan da ta cire a jikinta ta ce. "Ah ah! Malam wannan kuma fa? Ko dai Mairo aka yi wa baiko da bana nan?" Washe baki Malam Bala ya sake yi sannan ya ce. "In banda abinki Kande nawa Mairon take? Ai yayarta aka ɗaurawa aure ɗazu a masallacin Juma'a. Liman har ma da manyan garin nan duk sun shaida kuma sun saka wa abun albarka." Mamakin kalaman Malam Bala ne suka sanya Kande zama a bakin gadonta ta karɓi abubuwan da yake miƙa mata ta ajiye a gefenta sannan ta ce. "Malam ka na ta yi min magana a duƙunƙune,dan Allah ka fito fili ka yi min bayani,domin ni dai a iya sani na Samira ce kawai ta girmi Mairo a gidan nan;kuma an yi mata aure. To wacece kuma Yayar Mairo da aka aurar babu baiko balle saka rana?" "Ke dai ba kya cin ribar zance Kande. To auren Salma ta wajenki aka ɗaura yau a masallacin Juma'a da Rabi'u ƙanin mijin Samira." Wani irin faɗuwar gaba da tashin hankali ne ya dirarwa Gwaggo Kande wanda ya sanya ta jin jiri na ɗibanta daga wajen da take zaune. Cike da tashin hankali ta kalli Malam Bala ta ce.......... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 15. Cikin tsananin ɓacin rai Gwaggo Kande ta kalli Malam Bala ta ce. "Lallai kuwa za ka je duk masallaci ko ƙofar gidan da aka ɗaura wannan ƙaddararran auren a kunce shi;dan ba zan taɓa amincewa a cuci yarinya ƙarama a aura mata tsoho kamar Malam Rabi'u ba." Tsayuwa Malam Bala ya gyara ya ce. "Kayya! Kande wai dika-dika Malam Rabi'un nawa yake? Ƙanin ƙanin bayana ne fa." A hasale Kande ta ce. "Mutumin da ko za ka girme shi bai wuce ka bashi shekara uku zuwa huɗu ba shi ne yaron? Kada fa ka manta Salma bata wuce shekara sha biyu zuwa sha uku ba." Cikin sauri Malam Bala ya ɗaga wa Kande hannu ya ce. "To kin ga kenan ta yi gadon ki. Ai idan ban manta ba kema da waɗannan ƙananan shekarun aka aura min ke." "Malam wancan zamanin da wannan da muke ciki akwai banbanci,sannan kuma lokacin da muka yi auren ina da ƙananan shekaru ai kai ma ba wani babba bane." "Banbancin na menene Kande? Tuwon hatsin aka dena ci ko kuwa shinkafar? Ko kuma kwanciyar sunnar aka canja? Matan ne suka koma na gwal ko me? Bayan haka Kande indai da kara ba karaya ba ni ai uba nake a wajen Salma,a zato na zan iya zartar da komai a kanta. Dama Hasiye ta faɗa min idan kika dawo sai kin yi tijara na karyata ta saboda na sanki da biyayya. Ashe ta sauya zani ban sani ba." "Malam babu zanin da ta sauya,har gobe da jibi ina nan a Kanden da ka sani mai yi maka biyayya akan dikkan umarninka matsawar bai saɓawa Allah ba. Amma wannan abinda ka yi ba zan taɓa yi maka biyayya akansa ba ballantana kara,yanda ka je aka ɗaura aren nan babu sanin dangin uwa da uban yarinya dole ka je a warware." A hasale Malam Bala ya tsaya a gaban Kande ya na zazzaro mata ido waje ya ce. "Ke ba na son shashanci fa. Wa ya faɗa miki dangin uwa da uba basu sani ba. A gaban kawunanta, Sarkin garin nan liman da duk wani mai faɗa a ji na ƙauyen nan aka ɗaura,kada ki so ki ga yanda akai ta saka miki albarka da ita kanta yarinya,ko babu komai kun yi taimakon musulunci " "Ka ce haka mana Malam tinda an ɗaura wa yarinya aure da tuzuru. Ina son ka sani duk wani mummunan abinda ya sami Salma ba zan zauna da kai ba na gama auren ka kenan Malam. Habaa ta ya za a yi wa yarinya aure sai kace wata ƴar tsana? Idan gaskiya ne abun naka ai ka na da wata ƴar ka bashi mana,sai a haɗa ta da ƴar'uwarta gida ɗaya su yi zaman aure,amma ba wai a ɗauki marainiya a kai ta gidan da na san da biyu ka ƙulla auren dan kawai a cutar min da ita ne." Ta na gama maganarta ta fito waje fuuuu cike da fushi. Karo ta yi da Hasiye da ke yi musu laɓe ta na jin duk abinda suka yi magana akai. Cike da borin kunya Hasiye ta tsugunna tana ɗaukan duk abinda hannuwanta suka hau kai. Murmushin takaici Kande ta yi ta ce mata. "Na dawo na ga tuggu da munafurcin da kika ƙulla Hasiye,dan kuwa na sani sarai ke ce za ki zuga Malam ya yanke wannan mummunan matakin akan Salma. Ina so ki sani da yardar Allah Salma za ta ba ki mamaki. Sai kin yi nadamar wannan haɗin auren da kika yi ko ba jima,ko ba dade." Harara Hasiye ta banka wa Kande ta tsirtar da yawu sannan ta ce. "Eh ɗin ni ce nan matar da ta isa da miji da gida,uwar magada mai mulkin gidan Malam Bala. Har ke kin isa Ƴata ta nuna tana son auren jikanki ki hana ta? To bari ki ji Samira ba ta yi auren tsoho a banza ba,kema dole ne taki jikar ta je can ta ɗanɗani zama da sa'an ubanta. " "Ba kanta farau ba Hasiye,kuma na tabbata ba za a gama akanta ba,dan ta auri tsoho ba shi ne yake nufin ƙarewar numfashinta ba. Kuma ina so ki dinga tinawa da mugunta dai fitsarin fako ce,kuma idan za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere." Haka su Kande su ka dinga musayar yawu ita da Hasiye har ta ga rashin dacewar biye mata su yi ta hayaniya. Ɗaki ta shiga ta killace tsarabar da ta zo da ita ta zari mayafinta ta saka ta kulle ƙofarta ta nufi gidan Kawu sale. Ta na zuwa ta dinga doka sallama a tsakar gida domin ko ɗaki bata jin za ta iya shiga. Yanda suka haɗa kai da Malam Bala aka aurar da Salma ba da saninta ba dole ne su je duk inda za su je a warware wannan auren. Ta na nan tsaye Kawu Sale ya fito ya na suɗe hannu tare da haɗe su waje ɗaya ya murtsuke. Washe baki ya yi yana kallon Kande ya ce. "Ah ah Gwaggo yau ke ce a gidan namu war haka?" Harara ta banka masa sannan ta ce. "Da abinda ya fi war haka ma za ka ganni Sale,tinda baku ƙulla gaskiya ba da kai da wancan azzalumin. Yanzu Sale amanar da aka bar mana ita kuka wulaƙanta? Ina laifin ku aura wa Salma matashi wanda ƙarfinsu zai yi ɗaya, kurum sai ku aura mata sa'an ubanta?" Tsayuwa Kawu Sale ya gyara sannan ya tsotse haƙorinsa ya ce. "Don Allah Gwaggo Kande ki yi haƙuri da abinda ya faru. Matsala aka samu gagaruma . Wato auren Malam Rabi'u aka fasa saboda yarinyar da zai aura iyayenta sun ji labarin Yayansa dika yara mata yake haifa,kuma yaran ne ke zuwa masa gona su yi duk abinda yaro namiji zai yi,watarana ma har marigayiyar matarsa yake ɗauka ya kai ta gona su yi aiki su dawo. A taƙaice dai sun ji ƙishin-ƙishin ɗin aikin gona da na gida ne ya yi ajalin matar wansa. To shi ne fa Malam Rabi'u da be taɓa aure ba hankalinsa ya tashi da jin wannan mummunan labari sai ya yanke jiki ya faɗi. Da ƙyar aka zuba masa ruwa ya farfaɗo aka kai shi can asibiti aka saka mas ruwa. Ni dai ban san ya aka yi ba bayan kwana biyu an tashi sallar Juma'a sai ga Malam Bala ya zo muna tare da Sarki a idar da sallah ya ce wa Malam Rabi'u ya bashi ƴarsa Salma ya aura idan yana so." "Shine kuka amince ba tare da yin tunanin zaluntar yarinya marainiya da ake son a yi ba ko?" Kai Kawu Sale ya sosa ya na faɗin. "A yi haƙuri Gwaggo ƙaddara dai ta riga fata yanzu." "Humm Allah Ya kyauta,gobe da sassafe zan koma Kano na sanar da ɗan'uwanta duk abinda kuka ƙulla." Gaban Kawu Sale ne ya faɗi,nan take nadamar ƙin hana auren Salma da Malam Rabi'u ta kama shi. Sai dai ya baro gini tin ran zane. Kande gida ta koma ta na matsar hawaye tare da hango irin tarin kalubalen da Salma za ta fuskanta a cikin wannan auren. A haka ta kwana da zullumi da fargaba. Washegari da safe ta shirya tsaf da nufin tafiya Kano ta sanar da Abdulwahab abinda yake faruwa. Sai dai lokacin da ta je ta sanar da Malam tana neman izininsa na zuwa Kano sai ya ce. "Babu inda za ki je ki hure wa yarinya kunne ta bijire wa mijinta. Nan da jibi Hasiye da matar Sale za su je su yi barka sannan su taho da ita." Hawayen da Kande ke ta riƙewa kada su zuba a gaban maƙiyinta Malam Bala ne suka zubo mata. A daren jiya ta raɗa masa sunan maƙiyi,domin kuwa babu wanda zai aitaka abinda Malam Bala ya aikata a kira shi da masoyi. Ba dan ta so ba dole ta haƙura ta bar ɗakin nasa ta koma ɗakinta ta na sharar hawayen takaici. A kan idonta Hasiye ta dinga rawar kan zuwa Kano. Tin da safe ta tsefe kanta ta je aka rangaɗa mata sabon kitso,sai kuma ta ɗaura jan lalle a ƙafarta da dare. Gari na wayewa Hasiye ta sheƙa wanka ta saka atamparta sabuwa da suka ci bikin Suwaiba da ita ta fito ta na kallon kanta a ƙaramin madubin hannu ta na gyara zaman mayafinta a kafaɗarta. Washe baki Malam Bala ya yi ya ce. "Har an fito kenan?" "Allah Ya yarda Malam. Tinda a yau za mu je mu dawo a yau,ai gwanda mu gaggauta mu yi abinda ya kamata." "Haka ne Hasiyatu matar fir'auna,waii matar Malam Bala. Kin ga kyan da kika yi har ya ruɗa ni zan sauya miki sunan miji. To ga wannan a yi na mota ko?" Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin mota ya bata yana dariyar samun nasara. Har cikin ransa yake jin daɗin rama wulaƙancin da Abdulwahab ya yi masa na ƙin auren Samira. Sosai ya yaba da shawarar da Hasiye ta bashi na aura wa Malam Rabi'u Salma dan yin ramuwar gayya. Ɗaki ya koma kai tsaye ya zauna ya fara karya wa. A tasha su Hasiye suka haɗu da matar kawu Sale. Gaisawa suka yi da juna suka samu mota suka shige. A mota banda zuzuta gidan da su Abdulwahab suke a Kanon babu abinda Hasiye take yi,ita a dole ta san kan waje Matar Kawu Sale bata sani ba. Haka suka dinga hira har suka isa garin Kano. Su na isa suka sauka daga mota suka samu taxi suka shiga. Da kwatance motar ta kai su har gidan Abdulwahab. Su na zuwa suka hau buga ƙofa suna faɗin. "Ohh mutanen birni,su fa yanzu bacci suke yi ko?" Hannu Hasiye ta sa ta sake buga gidan da ƙarfi. Su na nan tsaye wani ƙaton mutum ya buɗe gidan jikinsa ko riga babu ya kalle su ya na muzurai ya ce. "Kai ku su wanene kuke damun mutane?" Yawu Hasiye ta haɗiya a tsorace ta ce. "Wajen Jikana Abdulwahabu muka zo." "Waye me wannan sunan kuma? Malama ku ware daga nan nan gidana ne ni ban san wani Abdulwahab ba." Ƙirji Hasiye ta dafe ta ce. "Kai ɗannan don Allah kada ka yi mana wasa..." A hasale mutumin ya zabura ya ce. "Na yi miki kama da abokin wasanki ne?" Kai Hasiye ta girgiza ta ja hannun Balaraba Matar Kawu Sale suka fara tafiya. Cike da tsananin damuwa Balaraba ta ce. "To ke da Hasiye kin san baki san gida ba kika rakito mu muka taho ?" Kai Hasiye ta karkace ta ce. "Aradun Allah wannan ne gidan. Bayan Abdulwahab ya kama haya a Kano sun dawo shi da matarsa na biyo Kande da za ta kawo musu ziyara. Tin daga nan ko shigowa na yi siyayya sai na biyo na ci na sha na yi warkajami na da abun duniya nake wucewa gida." "To da dikkan alamu sun canja gida,ko kuma wani abu ya sami Abdulwahab ɗin amma Gwaggo Kande bata sanar da kowa ba." "Idan ina faɗa muku muguwa ce sai ku dinga ganin laifina,to ai gashi yanzu ta baku misali." Haka suka ɗauki laifi suka ɗora akan Gwaggo Kande gaba ɗaya. Daga ƙarshe sai suka dinga bi gida-gida suna tambayar inda za su samu gidan Abdulwahab amma basu samu ba. Ganin lokaci ya tafi bar an yi azahar basu dace ba,sai kawai suka yanke shawarar komawa Kura idan Kande ta sanar da su sabon gidan Abdulwahab ɗin sun dawo.... *Ku yi haƙuri bani da caji ne shi yasa kuka ji ni shiru.* MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 16. A matuƙar gajiye su Hasiye suka isa gidan Malam Bala da ke ta zarya a tsakanin cikin gidan da ƙofar gidan Malam Rabi'u dan ganin dawowarsu. Bai jima da fita ba ya dawo ya tarar da Hasiye zube a tsakar gida ita da Balaraba wadda ta kasa ƙarasawa gidanta ta ce sai ta huta ko zuwa dare ne; tinda ba ita ke da girki ba yara sun raka ta. Fuskar Malam Bala ɗauke da mamaki ya hau leƙen ƙofar ɗakin Kande ko zai hango takalman Salma amma ya ga wayam. Kallon Hasiye ya yi ya ce. "Mutanen Kano an shawo rana,ke Mairo je ki kawo musu farau-farau mana,da dikkan alamu sun yi aswaki da kaji a birni." Tsaki Hasiye ta ja tana zabga wa Malam Bala harara. Bakinta da ya bushe ta lashe da harshenta da ya ƙafe babu ɗigon yawu a jiki ta ce. "Ai idan bamu ci kaji ba mun ci uwar wahala. A gaskiya Malam Baƙin halin Kande ya munana babu na biyun ta a mugun hali a kaf cikin ƙauyen nan namu da kewaye." Waje Malam Bala ya samu ya rakuɓe a jikin gini ya na kallon Hasiye da ta amshe kwanon shan ruwa a hannun Shamsiyya ƙaramar ƴarta ta kwankwaɗe ko kurɓa daya bata rage ba. Tana sauke numfarfashi ta ce. "Wai ka san kuwa yaron nan Abdulwahabu ba ya gidansa da na sani amma bata damu ta sanar da mu ba;duk da cewa ta san can za mu je mu taho da matar mutane?" Ido Malam Bala ya zaro waje ya dafe ƙirji sannan ya ce. "Ki bari dan manzo Hasiye! Wai ki na nufin Abdulwahabu ya sauya muhalli daga wanda muka sani? Ki ce arziƙi ya ci uban na da. Ohhh yanzu fa da shikenan Samira ce a gidan take ta dandalar arziƙi." "Hummm ai Kande ba macen da za a raɓa a dandali arziƙi bace Malam,ta nuna maka iyakar ka. Yau in da ka ga azabar tafiyar da muka ci da ƙafafuwan nan namu sai ka tausaya mana. Wani ƙato ma ce wa ya yi idan bamu bar ƙofar gidan ba zai lakaɗa mana na jaki,kan dole mu kai ta zagaya unguwar har maƙotan unguwannin da basu da nisa muna tambayar gidan Abdulwahab mai siyar da hatsi,amma bamu samu ba. Yanzu don Allah Malam dubi yanda ƙafar Balaraba ta yi haushi kamar ta me tsohon ciki." Sannu suka dinga jera wa Balaraba da ke ta kurɓar farau-farau. Kande kuwa ta na ɗaki ta na jin su bata tanka musu ba har aka kira sallar magariba ta fito dan yin alwala. Ko kallon inda suke bata yi ba ta ɗauki butar ta ta zaga. Ta na fitowa ta hau yin alwala ba tare da ta kalli inda suke ba,Malam Bala ne ya isa wajenta a hasale kamar zai kifa. Cike da matsanancin fushi ya warce butar ya yi wurgi da ita ya ce. "Wato ma kin mayar da mutane mahaukata ko? Ki na fa kallo da jin abinda ke faruwa a gidan nan,amma ko sannu ba za ki iya buɗe baki ki yi wa bayin Allah'n nan ba da suka tafi ɗakko Salma dan a kaita gidan miji ta raya sunnar ma'aiki." Shiru Kande ta yi bata tanka masa ba ta miƙe daga tsugunnon da ta yi ta ɗakko butarta ta wanke ta sake zuba wani ruwan ta hau yin alwala. Ƙwafa Malam Bala ya yi ya ce. "To ki buɗe kunnen ki da kyau ki jini. Zan je wajen yaransa da ke kai masa kaya Kanon da kaina mu je har shagonsa,ni da kai na zan je na taho da Salma idan zuciya za ki haɗiya sai ki yi magana a baki ruwa ki kora." Murmushin takaici kawai Kande ta saki ta miƙe tsaye ta wuce ɗakinta. Ta na shiga hawaye ya zubo mata,nan da nan ta hau tuna irin rayuwar da suka yi da mijinta a baya. Rayuwa ce mai cike da so,ƙauna,tattali,kulawa da mutunta juna. Duk wani abu da zai ɓata mata rai baya son sa. Da yardarta da amincewarta ya auri Hasiye saboda ita bata taɓa haihuwa ba. Sai gashi tinda aka auro ta bata huta ba daidai da rana ɗaya. Gashi yanzu tsufa ya cimmata har ta dena al'ada ballantana ta sanya ran haihuwa. Zama ta yi a bakin gadonta ta rushe da kuka mai cin rai saboda ta tabbatar da cewa wani makircin da muguntar Hasiye ke ƙullawa ƙaramar yarinya kuma marainiya Salma. Gani ta yi kukan ba zai kai ta ko ina ba lokacin sallah na wuce wa. Sai kawai ta miƙe ta nufi saman abun sallarta ta gabatar da sallar magariba ta zauna tana ta addu'o'inta. A can tsakar gida kuwa Balaraba da ta gama cin tuwon dare sai ta miƙe ta na ɗingisa ƙafa ta ce. "Bari na je na gaida Gwaggo Kande tinda na huta." A bakin ƙofa ta coge ta ɗage labule ta ce. "Barka da war haka Gwaggo,mun same ku lafiya?" Ba tare da Gwaggo ta nuna mata halin da take ciki ba ta saki ranta ta amsa mata,su na gama gaisawa Balaraba ta ce. "To ni na tafi sai da safe. Allah Ya sanya alheri ya ba su zaman lafiya. Idan amarya ta iso mun zo da su Tsahare da yaran." "Uhumm Allah Ya kaimu to." Gwaggo Kande ta faɗa ta na tunanin shin ita ce ƴar'uwarsu Kawu Sale ko kuma Hasiye da Malam Bala ne ƴan'uwansu? Ta na wannan tunanin ta ji yaran Hasiye sun tafi raka Balaraba da kwanon tuwo a hannunsu, wanda Mairo ce ta dafa ta zuba wa kowa nasa. Kallon inda aka ajiye mata nata ta yi sai ta ji ko sha'awar ci bata yi,tin safe farau-farau kawai take kurɓa saboda ɓacin rai. A haka Gwaggo Kande ta kwana cike da damuwa har safiya bata rintsa ba. Da sassafe ta ji Malam Bala na yi wa Hasiye sallama ko ta ƙofar ɗakinta bai bi ba ballantana ya san ya ta kwana ya fice ya bar gidan. Kai tsaye babbar kasuwar Kura ya nufa inda ake ta hada-hadar loda hatsi a manyan motoci. Yaran Abdulwahab ya nema suka gaisa ya ce shi ma can wajen nasa ai ya nufa shi ne ya ce bari ya zo a rage masa hanya. Sanin matsayinsa a wajen Gwaggo Kande ne ya sanya su amincewa bayan sun gama lodi suka ɗauke shi a saman mota suka tafi da shi. Su na isa Kano suka nufi Ƴankaba domin sauke wa Abdulwahab kayansa. Su na zuwa suka tarar da yaran shago na ta shara tare da ba da space domin kayan da za a kawo. Da taimakon matasan wajen Malam Bala ya diro daga saman motar ya ƙarasa gaban shagon Abdulwahab yana gaisawa da mutanen wajen. Malam Sallau ne ya sanar da shi cewa ai Abdulwahab bai iso ba sai rana ko yamma yake shigowa kasuwa. Malam Mudan ne kawai ke zuwa da safe amma kuma shi ɗin ma bai iso ba. Da sauri Malam Bala ya ce. "Ni da da yanda za a yi a kai ni can gidan nasa ma ai da kun kyauta. Dama rashin sanin muhallin da ya koma ne ya sa na biyo ta nan." "Ah bari to na jawo babur na kai ka gidan yanzun nan.' Albarka Malam Bala ya dinga sanya wa Malam Sallau. Malam Sallau na jawo babur ya buga shi ya ce wa Malam Bala. "Bismillah Baba mu je." Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidan Abdulwahab wanda ke tsaka da shirin fita office. Sallama Malam Sallau ya rafka sau uku,a na huɗun Mudassir ya fito ya na faɗin. "Man Sallau kai ne a gidan namu war haka?" Hannu Malam Sallau ya miƙa masa suka hau gaisawa,sannan Mudassir ya durƙusa ya gaida Malam Bala. Cike da fara'a ya ce. "Shigo ciki mana Baba,ka tsaya daga waje? Aboki na ciki ya na shirin tafiya aiki,bari na sanar da shi zuwanka." Sallama Malam Sallau ya yi musu ya koma kasuwa. Su na shiga ciki ya nufi parlourn da suke ajiye baƙi zai buɗe masa kenan Salma ta fito daga ɗakin Layuzah bayanta goye da Aabid. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa har bata san sanda ta furta kalmar. "Wayyo Allah na shiga uku." Ba. Washe baki Malam Bala ya yi kamar bai ji ta ba ya ce. "Lallai ne Salma zaman birni ya karɓe ki ƙwarai da gaske. Kin ga yanda kika murje kika ƙara kyau da girma kuwa? Kwanto min yaron na gansa." Jiki a mace Salma ta isa gaban Malam Bala ta durƙusa har ƙasa ta gaida shi. Amsa wa ya yi cikin sakin fuska ya karɓi Aabid da ya fara kuka,sama Malam Bala ya wurga shi yana masa tawai kafin ya miƙa wa Salma yaron ya shige parlourn da aka buɗe dominsa. Ya na shiga ya kama baki ya na faɗin. "Inyeee! wato bayan wancan gidan da suka shaƙe da kayan alatu suka barwa aljanu suna dabdalarsu a ciki a can ƙauye,nan ɗin ma sai da suka cika shi da dukiya. Lallai yaron nan ba ƙaramin baƙinciki ya yi mana ba. Yanzu da Samira ce a gidan nan ai mu da talauci sai dai mu hango shi a maƙota." Zama ya yi a kujera ya ji ya lotsa saboda laushi,sai ya sake miƙe wa tsaye ya zauna da ɗan ƙarfi kamar wani ƙaramin yaro. Ya na nan yana zancen zuci da na fili Abdulwahab ya shigo parlourn cikin shirin fita office. Gaisawa suka yi cike da girmamawa sannan Abdulwahab ya ƙwala wa Salma kira ya ce a kawo musu abun karyawa shi da Malam Bala. Layuzah ce ta yi sallama riƙe da babban faranti ta shiga ta ajiye a tsakiyarsu sannan ta koma gefe ta tsugunna. Gaida Malam Bala ta yi tare da tambayar mutanen gida. Nan ya dinga shirga ƙarya ya na faɗa musu yanda Kande ta yi kewarsu har ta tashi da zazzaɓi ta na ta cewa a kawo mata Salma amanarta,shi yasa ya yi mata alƙawarin zuwa ya tafi da Salmar. Cike da tausayawa Layuzah ta tambayi jikin Gwaggo Kanden,Malam Ya ce da sauƙi,ya dai kula kawai kewar Salma ke damunta,da an kai mata Salma za ta ware,fatan samun sauƙi Layuzah da Abdulwahab suka yi mata ta miƙe ta fita ta basu waje. Abdulwahab da kansa ya buɗe food flask ɗin masa ya zuba wa Malam Bala,sannan ya ɗauki kwanon miya ya zuba masa miyar gyaɗa da ta ji naman rago. Kunun gyaɗa Abdulwahab ya zuba masa a babban mazubi sannan ya saka madara da sugar mai yawa ya juya masa ya ajiye masa a gabansa. Yawun Malam Bala kamar zai zubo haka ya dinga magana yawun na tsartuwa. Babu ko bismillah ya danna hannu ya hau ci yana zuba surutu, a cikin surutun nasa ne yake sanar da Abdulwahab zai wuce da Salma gida idan ya bada izini. Ba tare da Abdulwahab ya kawo komai a ransa ba ya ce. "Babu damuwa Baba,ai dama ko randa za ta tafi ta so ƙwarai ta tafi da Salman yarinyar ce ta ƙi amincewa." "Ai sha'anin yaro sai shi,ka duba ka ga yanda suke da Kande,a gani na ai bai kamata ta ƙi binta ba ballantana har ga dinga nuna rashin jin daɗi dan za ta koma can,ta na abu sai kace wata wadda ake yi wa wani abun a can. Wa Salma take da shi yanzu dai a duniya da ya wuce kai da Kande? To sai kuma danginku na uwa da uba." Murmushi kawai Abdulwahab ya yi ya ci gaba da cin abincinsa. A haka suka gama ba tare da kowa ya sake cewa komai ba. Sosai Malam Bala ya ci abincin nan har a ransa ya na tunanin da ace Abdulwahab zai ɗan fita da sai ya samu leda ya ƙulle sauran. Kiran Salma Abdulwahab ya yi ya ce ta haɗa kayanta ta bi Baba. Cikin kuka ta tashi ta koma ɗakin da ta sauka ta fara haɗa kayanta. A haka Layuzah da Ammabuwa suka same ta tana kuka. Tsaraba sosai suka haɗa mata sannan Layuzah ta rungumeta ta ce. "Ki yi shiru ki dena kuka ƙanwata. Na yi miki alƙawari a Kura za mu yi yawon arba'in saboda mu nuna wa dangi Aabid. Ina komawa kuma zaki tattaro ki dawo waje na har sai mun yi watanni biyu ko uku sannan za mu dawo." Ammabuwa ce ta kalli Layuzah ta ce. "Inyee ashe kun gama tsara bari na ni kaɗai a gidan ba tare da kun sanar da ni ba ko?" "Haba ke kuwa ai kema kin san dole na sanar da ke,yanzun ma maganar ta zo ne ba tare da shiri ba." "Humm shikenan Allah Ya nuna mana lokacin." "Amin Ya Allah." Da wannan lallashin Salma ta saki ranta ta fito saɓe da jakarta da su Layuzah suka shaƙe mata ita da kaya. Malam Bala ne ya fito daga parlour ya na ta tura hannu a aljihu yana zuba wa Abdulwahab godiya kamar zai kwanta. Shi kuwa sai ya bi bayansa kawai yana kallon Salma tare da karantar yanayin da take ciki. Ya riga ya gama tsara yanda zai ɗauke ƙanwarsa da zarar burinsa na gina katafaren gidan da za su tattare su koma ya cika......... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ *Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️ PAGE 17. A na kiran sallar asr su Malam Bala suka isa gida. Da sauri Salma ta yar da jakarta a tsakiyar ɗakin Kande ta isa wajenta ta na dariyar farincikin ganinta. Sai dai yanayin da ta gani a tattare da mariƙiyar tata ne ya sanyaya mata jiki har bata san sanda ta zube a saman guiwowinta ba ta ɗora hannuwanta a saman na Kande ta ce. "Gwaggona da gaske kewa ta kika yi sosai shi yasa baki da lafiya? Bamu fa jima da rabuwa ba Gwaggo,don Allah ki dena damuwa gani na dawo wajenki ba zan sake yin nisa da ke ba har abada." Hawayen da Salma ta ga Kande na share wa ne ya sake rikita ta ta kifa kanta a saman cinyar Kande ta na kukan da bata san dalilin yinsa ba. Bayanta Kande ta ke shafawa a hankali ta na shan majina tare da lumshe idanuwanta da suka gaji da zubar da ruwan hawaye. Wani irin zafi take ji a cikin ranta. Murya na rawa ta ce. "Ba ina kuka saboda kewar ki bane Salma. Ina kuka ne saboda bani da hanyar da zan aika wa Abdulwahab saƙon ya nesanta ki da garin Kura nisa na har abada. Ina kuka ne saboda fin ƙarfin da aka nuna mana da ni da ke marainiyar Allah. A yau na tabbatar da cewa wasu dangin suna suka tara kawai,domin da namu dangin aka haɗa kai aka nuna min iyakata,Kawunanki sun nuna min cewa ni ba kowa bace a wajensu face ƙanwar ubansu dan haka bani da hurumi a yanke hukunci a rayuwarki. Dangin mahaifinku kuwa sam basu san me ya faru ba har sai da mai afkuwa ta afku. Salma ina mai neman gafarar ki ki yafe min saboda gazawa da na yi a wajen rikon amanar ki har ki girma a aura miki kalar mijin da kike so." Gaba ɗaya Gwaggo Kande ta gama rikita ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwar Salma. Cikin rashin fahimtar inda maganganun Kande suka dosa Salma ta ce. "Don Allah Gwaggo ki yi min bayani dalla-dalla yanda zan fahimci abinda kike son sanar da ni." Zama Gwaggo Kande ta gyara ta zaunar da Salma a gefenta ta hau zayyano mata duk abinda yake faruwa,daga ƙarshe ta ce. "Ɗazun nan Baffanninku suka bar nan ransu a matuƙar ɓace,domin a zaton su da sahhalewa ta aka ɗaura miki aure da Rabi'u. Sai da na yi musu bayani sosai,sannan na tabbatar musu da cewa Malam ya ce da amincewarsu da Kawunnanku aka ɗaura miki aure,sannan suka sassauta suka ce za su dawo idan Malam ya dawo daga ɗakko ki;dan ba za su amince da wannan ƙaddararran auren ba." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Salma ta sauke a cikin kukan da take ta sharɓa tinda Gwaggo ta bayyana mata abinda ke faruwa. Kasa cewa komai ta yi sai ta miƙe ta ja jakarta zuwa ƙuryar ɗakin ta koma gefen katifarta dake ɗakin ta zauna ta na ci gaba da kukanta. Gwaggo Kande na ganin haka sai ta dinga bata baki ta na nuna mata cewar dole ne a warware wannan auren,dan haka kada ma ta sa wa kanta damuwa ballantana wani ciwon ya kama ta. Jiki babu ƙwari Salma ta fita tsakar gida ta na sharar hawaye ta ɗauki buta ta nufi bayi domin kama ruwa. Ta na shiga banɗakin ta rushe da wani sabon kukan mara sauti. Da ƙyar ta iya danne matsananciyar damuwar da ta rikito mata a lokacin da Gwaggo na bata labari mafi muni a rayuwarta. Sosai tausayin kanta ya lulluɓe ta sai ta rakuɓe a jikin gini tare da ƙanƙanme jikinta ta na ci gaba da kukanta. Ganin za ta makara sallar asr da bata yi bane ya sanya ta wanke fuskarta ta fito daga bayin ta ɗaura alwala ta wuce Hasiye da ke zabga guɗa ta na faɗin. "Ka ga amarya a gidan Malam Rabi'u Mai Shinkafa,babban manomin da ya ke ji da noman rani da ta damina,dattijo mai kamar yaro ga kuɗi ga tashen gayu. Yo kukan me kike yi kuma? Yarinya ki saki ranki ki je ki ci arziƙi ki bar arziƙi a mazauninsa. Yo ke in banda ma aljana ta aure shi ai ba sa'an aurenki bane,da sai dai ki zamo sa'ar jikarsa ta biyu ko ta uku." Kallon Hasiye Salma ta yi a karo na farko a rayuwarta da ta ji ba za ta iya ƙyale ta ba ba tare da ta bata amsa ba ta ce. "Alhamdulillah mu a kowanne hali gode wa Allah muke yi,dan haka na tabbata godiyar Allah ce ta kai ni ga matakin auren mijin da ban zaɓa wa kaina ba,da izinin Allah ba zan wulaƙanta ba idan ma kin zuga an aura min tsoho saboda mugunta ne." Salati Hasiye ta saki ta na tafa hannaye tare da kama haɓa ta ce. "Inyeeee! Ehh lallai ne yarinya wuyanki ya isa yanka. To Kande ga shi nan a gabanki yarinyar da kike ta kukan ta yi ƙarama da auren tsoho ta tsaya tana zaro kalaman da ko wata babbar albarka. Za kuma ki san kin kira ni da muguwa yarinya,baki ga komai ba a rayuwarki." Labule Salma ta ɗaga ta leƙa kanta ta ce. "Sai dai na ga alkhairi da yardar Allah." A zuciye Hasiye ta ɗauki plate ɗin tasar da ke kusa da ita ta jefi  Salma da shi ta na zagin ta. Salma kuwa ɗaki ta koma ta na jin faɗan da Gwaggo Kande ke yi mata akan ta dena biye wa Hasiye kafin ta sake ƙulla mata wani sharrin. Hijabinta ta ɗauka ta sa ta tada sallah,ta na idarwa ta yi wurgi da hijabin ta kwanta tare da juya wa Gwaggo Kande baya ta na tunanin makomarta. Gwaggo Kande kuwa sai ta zuba wa bayan nata ido kamar mai karantar wani abun a tattare da yarinyar. Su na nan zaune shiru Malam Bala ya shiga gidan hannunsa riƙe da wata leda sai nason maiƙo take yi. Kai tsaye ɗakin Gwaggo Kande ya shiga ya samu gefen gado ya zaune ya na washe baki ya ce. "Ohh Kande ashe haka yaron nan Abdulwahabu ya bunƙasa ya tunbatsa a Kanon? Ai ni yau na ga abun arziƙi Kande,yaron nan haka ya sa aka kawo mana abinci da nama zuƙu-zuƙu a ciki. Da zan tafi ya jimƙo kuɗi a aljihunsa ya yi min hasafi,a ciki na yi na motar dawowa na kuma siyo miki wannan kilishin ki ɗan taɓa. A sheƙe Kande ta kalli mijin nata da take mugun ganin baƙinsa a yanzu ta ce. "Idan ka gama cinyewa sai ka ƙara gaba,in kuma a can ɗakinka ko na makwaɗaiciyar da ɗoraka a keken ɓera za ka ci ka tashi tun yanzu ka ƙara gaba bana buƙatar komai daga wajenka." Cike da takaici Malam Bala ya kalli Kande ya miƙe tsaye ya ce. "Ke fa na ga alama a ƴan kwanakin nan ba a abun arziƙi da ke,amma wannan bai dame ni ba,taimakon da na sa a gaba ba zan fasa ba,zan ci gaba da yi na ceto bawan Allah'n da bai taɓa aure ba a rayuwarsa." Ledar hannunsa ya ɗauka ya nufi inda Salma ke kwance ta na binsa da kallo idanuwanta na zubar da hawaye. Baki ya washe ya ce mata. "Ƴar salamemen Baba ga wannan ki motsa bakinki ko? Na kula a kwanakin nan kin saba da cin daɗi a gidan Yayanki." Salma dai ido ta zuba masa bata motsa ba,kuma bata amsa ba. Ganin haka sai Malam Bala ya ajiye ledar zai fita. Har ya kama labule ya ɗaga ya tsaya ya kalli Gwaggo Kande ya ce. "A shirya ta zuwa dare Rabi'u zai zo ya ga amaryarsa su ɗan tattauna ya ji ko akwai wani shagalin da take son ta gabatar,da yardar Allah gobe za a kai ta ɗakinta itama kamar yanda aka yi wa ƴar'uwarta Samira. Ai cewa ya yi ma kada mu damu da siyan kayan gado duk ya zuba mata ɗazu,shi dai matarsa kawai yake da buƙata ba komai ba." Murmushin takaici ne ya ƙwacewa Kande ta ce. "An zo wajen. Na tabbata siyawa Salma kayan ɗaki na daga cikin abinda ke damunka a kaf faɗin duniyar nan Malam. A al'dance idan mutum ya riƙe yarinya aka tashi aurenta shi ne zai yi mata kayan ɗaki,to kai gashi ba za ka iya cire kuɗi ka yi wa Salma kayan ɗaki ba. Da ka sani Malam da baka jefa rayuwar ta a cikin haɗari ba saboda kayan ɗaki. Ko ka manta har yanzu ɗan'uwanta na juya mata dukiyarta? Ka manta shi kanshi yana da arziƙin da ba zai bari ka sha wahala ba a duk lokacin da bikin Salma ya tashi? Malam...." Cike da borin kunya Malam Bala ya ɗaga wa Kande hannu ya ce. "Dakata Kande! Wai kina nufin ni Malam Bala Maji Daɗin Manoman garin Kura ni ne zan kasa yi wa Salma kayan ɗaki? To albishirinki,har kuɗin kayan gado na bada,da jin labarin zan kai na kujeru Rabi'un da kansa ya zo ya ce kada na yi ya riga ya yi. Yanzu gobe zan je na karɓi kuɗin gadona a yi wata hidimar da su. Wai me kika ɗauke ni ne Kande?" "Marar riƙon amana da tausayin marainiya. Malam na tabbata da ka kai kuɗin gadon nan kamar yanda ka ce to da ka karɓo su yanzu,dan kai ba mutumin da yake wasa da dukiyarsa bace musamman idan ya ji banza ta faɗi." Cike da borin kunya Malam Bala ya dinga faɗa,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Sosai ran Kande ya ɓaci dan haka sai ta biye masa suka dinga musayar yawu har sai da Salma ta ƙwalla ƙara ta na kuka tana basu haƙuri. Cikin kuka ta durƙusa a gaban Kande da ke hawaye ta na masifa ta ce. "Don Allah Gwaggo ki dena sa'insa da Baba domin ba halinki bane,tinda nake a gidan nan ban taɓa ji ya faɗa kin mayar masa ba. Idan har akai na ne kike faɗa da shi na yi alƙawarin yi wa Baba biyayya akan duk wanda ya aura min. Don Allah ku dena faɗa bana so,zuciyata zafi take yi min bana so." Kuka sosai Salma take yi numfashinta na yankewa kamar mai cutar asma. Duk taurin rai irin na Malam Bala sai da jikinsa ya yi sanyi,da sauri ya ja labule ya bar ɗakin. A tsakar gida ya tarar da Hasiye ta na kaye-kayen kwanika,da dikkan alamu sana'ar tata ta laɓe ta yi musu,jin fitowarsa ne ya sa ta bar wajen ta hau kwashe kwanuka. Malam Bala na fita Kande ta rungume Salma a jikinta ta ce. "In Sha Allahu ba za ki auri mutumin da ya isa yin jika da ke ba. Za ki girma ki auri saurayi kyakkyawa kamar yanda nake yi miki fata a koda yaushe. Baffanki Aƙilu zai je Kano gobe ya samu Yayanki ya sanar da shi duk abinda ke faruwa." Girgiza kai Salma ta yi,dan jikinta na bata wannan auren fa ya gama ɗauruwa kenan sai ta je gidan Malam Rabi'u ko tana so ko bata so. Hana ta magana Kande ta yi ta ce ta je ta kwanta ta huta,dan ta ji jikinta ya ɗauki zafi,alamar zazzaɓi na sanɗarta. Har su Kande suka yi sallar Isha'i basu yi wani shirin tarbar Malam Rabi'u ba. A ɓangaren Hasiye kuwa tini ta haɗa farau-farau a kwanon shanta sabo dal,sannan ta fito da tabarmarta sabuwa ta jingine ta na jiran zuwan baƙon nasu. Har ɗakin Kande ta shiga da sallama ta na washe baki kamar wawiya. Cike da mamaki Kande da Salma suka ɗaga kai suna kallon matar da ko ciwo Kande take yi bata shiga ta gaishe ta,ballantana ta yi mata sannu. Duk lokacin kuwa da ta ɗaga labulen ɗakin Kande to fa masifa da bala'i ne ya kai ta ba arziƙi ba. Zama ta yi ta na dariya ta ce. "Ah ah Ƴata salma har yanzu ki na nan kwance baki shirya ba bayan Babanku ya faɗa miki za ki yi baƙo anjima kaɗan?" Ko motsi Salman bata yi ba ballantana ta tanka mata. Kande ce ta gaji da jin nacin da Hasiye take yi wa Salma ta ce. "Kin ga kanwa uwar gami don Allah tashi ki bani waje,ki je can ki tarbi baƙon tinda dama ke kika haɗa duk wani tuggu da makircin da auren ya ƙullu. Ban san menene ribar ki ba na yin wannan zalunci,amma Allah Ya fiki,kuma a gobe ɗan'uwanta zai zo da jami'an tsaro dan a kama duk wani mai hannu a cikin wannan auren rashin ƴancin da kuka ƙulla." Cikin Hasiye ne ya kaɗa har ƙarar ta ziyarci kunnuwansu Kande. Cike da tashin hankalin jin an ambaci hukuma a lamarin ta hau rantsuwa tana kumawa akan bata da hannu a haɗin auren Salma da Rabi'u. Kafaɗa Kande ta ɗaga ta ce. "Jami'an tsaro ne kawai za su tabbatar da hakan idan sun zo." Jiki na rawa Hasiye ta bar ɗakin ta wuce nata tana ta safa da marwa. Cike da tashin hankali take jiran Malam Bala ya dawo su san abinyi. Sai dai abun takaicin Malam Bala na zuwa Hasiye ta labarta masa duk abinda Kande ta ce,sai ya ja tsaki ya ce. "Da yake an faɗa mata jami'an tsaron mahaukata ne ba sa bincike ko? Ai auren nan ya riga ya ɗauru kenan Hasiye,dan haka ki ma dena jin tsoron kowa da komai." Kafin Hasiye ta buɗe baki ta ce wani abu,sallamar yaro ta karaɗe tsakar gidan. Mairo ce ta amsa tare da ce wa yaron. "Kai Tsalha maye ka ishi mutane da sallama?" Baki yaron ya murguɗa mata kafin ya ce. "Malam Rabi'u ne ya ce na yi masa sallama da Babanku." Da sauri Malam Bala ya fito ya na gyara rawaninsa ya ce. "Ka ce masa ya shigo zauren gata nan fitowa." Ɗakin Kande ya nufa ya ɗage labule ya ce. "Salma ki na ina? Fito ga angonki ya iso." Cikin sauri Kande ta ce. "Malam na fa faɗa maka babu inda Salma za ta je." Ganin za su fara faɗa sai salma ta bi ta bayan Malam ta fita sanye da hijabinta. Hasiye da ta ci burin shimfiɗawa Malam Rabi'u sabuwar tabarma sannan ta bashi farau-farau na jin fitar Salma ta lafe a ɗaki saboda tsoron jami'an tsaro. A zauren gidan Salma ta tarar da Malam Rabi'u ya sha sabuwar shaddar sa fara tas sai sheki take yi. Durƙusawa ta yi har ƙasa ta gaishe shi cikin ladabi da girmamawa. Murmushi Malam Rabi'u ya sakar mata wanda ya fitar da tsantsar kyawun fuskarsa. Sosai Malam Rabi'u yake da kyawun fasali,domin kuwa a zamanin samartakarsa ya na daga cikin kyawawan samarin garin Kura. Shi yasa ma jinkirin aurensa ya janyo raɗe-raɗin cewa aljana ce ta aure shi a lokacin da suke yawan shiga daji farauta da iyo. Gaisuwarta Malam Rabi'u ya amsa sannan ya gyara tsayuwarsa ya na kallon yarinyar dake gabansa cike da ƙaunarta a ransa. Sai da ya yi gyaran murya sannan ya ce. "Ina fatan magabatanki sun sanar da ke duk abinda ya kamata ki sani game da wannan auren? Don Allah ina so ki kwantar da hankalinki,dan ni da kika ganni mace bata gabana,surutu da zarge-zarge irin na mutane ne ya jawo ra'ayina har na ji na yarda na amince zan yi aure. Sai dai kuma na samu rashin sa'a a ranar da aka je ɗaura aure na a ranar matar da danginta suka ce sun fasa auren. Wannan dalilin ne ya sa Babanku tausaya min ya aura min ke. Ina fatan za ki zamo yarinya mai biyayya." Kai kawai Salma ta ɗaga masa ta ci gaba da wasa da gefen hijabinta. Murmushi ya sake yi a karo na babu adadi,wanda hakan ya zamo ɗabi'arsa. "To yanzu wanne irin taro ko shiri za ku yi ke da kwayenki?" Shiru Salma ta yi bata ce komai ba. Kamar daga sama suka ga Mairo ta ci damara ta zo gaban Malam Rabi'u ta cake. Washe baki ta yi ta ce. "Ai Salma ba za ta ce maka komai ba,mu dai kawayenta mu ne za mu yi party a ranar da za a kai ta da yamma." Da jin haka sai Malam Rabi'u ya zira hannu a aljihu ya debo kudi ya ba wa Mairo ya ce. "To gashi a sha party lafiya. Ni zan wuce sai da safe ko amarya?" Kai Salma ta gyada masa ta juya za ta tafi. Kiranta ya yi sai ya ga Mairo ta ja ta tsaya. Hade fuska ya yi ya ce. "Ki je ke na sallame ki ai ko?" Washe baki ta yi tana sosa kai ta juya ta shige gida. Kai tsaye dakinsu ta shiga ta miƙawa Hasiye kudin da aka bata. Cikin sauri Hasiye ta karbe kudin har ta manta da abinda Kande ta fada mata na zuwan jami'an tsaro,sai da ta kirga su cas sannan ta zabga guda ta ce. "Sufa dif za a kulla a yi fanke ba shikenan ba an sallami kowa?" Dariya suka fashe da ita sannan suka ci gaba da tsara yanda komai zai kasance a washegarin. A bangaren Salma kuwa;duk yanda Malam Rabi'u ya so ta karbi kudin da ya bata ki ta yi,daga karshe sai ta yi masa godiya ba tare da ta karbi komai daga gare shi ba ta shige cikin gida. Hakan da Salma ta yi sai ya sa Malam Rabi'u ganin mutuncinta,nan take ya tabbatar ba halinsu daya da iyayenta ba da ke ta nuna zalama da maitar abun hannunsa. Washegari....... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 18. Washegari da asuba har an shisshiga masallaci a wasu wuraren Salma ta tashi ta ɗauki wani abu a gefenta ta ƙudindine a rigarta,kallon Gwaggo Kande da bata rintsa ba ta yi tana saman sallaya ta na sallah,sai ta durƙusa inda suke ajiye butocinsu a bakin ƙofar ɗakin ta ɗauki butarta ta tafi banɗaki. Ta na shiga ta fito da hijabin Gwaggo Kande ƙato da ta ɓoyo a rigarta ta zumbula tare da tattare shi ya tsaya daidai tsawonta. Ƙaramar katangar banɗakin ta kama ta ɗale,ba tare da jinkiri ko tunanin komai ba ta dire ƙasa ta zura da gudu ta yi gaba abunta. A can tsakar gida kuwa Hasiye ce zaune a saman bokitin ƙarfe sai zabga hamma take yi ta na jiran Salma ta fito daga banɗaki ta shiga. Jin shirun ya yi yawa ne ya sanya ta miƙe wa a hasale ta nufi bakin ƙofar shiga banɗakin ta ce. "Wai in ce dai ko kashin danƙo kike yi Salma?" Waje ta samu ta tsaya riƙe da buta ta na jijjiga jikinta cike da matsuwa. Ta jima a wajen bata ji ko da motsin ruwa ba ballantana na mutum,ba tare da ta sake yin magana ba ta leƙa banɗakin tare da haska fitila. Gani ta yi babu kowa a ciki sai butar da Salma ta shiga bayin da ita yashe a ƙasa,sawun ƙafar Salma ta bi ta ga inda suka tsaya,nan take ta fahimci abinda ya faru,sai kawai ta kurma ihu ta na kiran mutanen gidan tare da faɗin. "Yeeee kuwa jama'a ku kawo mana agaji amarya Salma ta gudu." Gwaggo Kande da ke lazimi na jin haka gabanta ya yi mummunan faɗuwa,da sauri ta tashi tsaye ta na riƙe da carbinta ta nufi hanyar waje. Ta na fita ta tarar da Hasiye tsaye da ɗaurin ƙirji ta na ta kwarmaton ɓatan Salma. A gigice Gwaggo Kande ta ce. "Wai wace Salman ce ta ɓata Hasiye?" "Yo in banda abunki Yaya Salma nawa muke da ita a gidan nan?" Da jin haka sai Kande ta bazama cikin banɗakin da gudu tana ƙwalawa Salma kira. Tana shiga butar Salma ta gani yashe a ƙasa sai ta ɗakko butar ta fito ta na kuka,a daidai wannan lokacin ne Malam Bala ya dawo daga masallaci hannunsa riƙe da carbi ya na mui-mui da baki. Kamar jira Hasiye take ya dawo ta kalle shi tare da fasa kukan munafurci ta ce. "Shikenan Malam yau mun shiga uku Salma ta gudu me za mu ce wa Malam Rabi'u?" Karkace kai Malam Bala ya yi yana bin Kande da ke ta rusa kuka da kallo ya ce. "Ban gane Salma ta gudu ba;ko dai an haɗa baki da munafukai ƴan hana ruwa gudu an ɓoye ta? To idan ma wani wajen kuka kai ta kuka ɓoye ina mai tabbatar maku da ku fito da yarinyar nan tin muna shaida junanmu da ku." Ƙanƙance ido Kande ta yi ta ce. "Me kake nufi da kalaman ka Malam? Za ka fita nemo min yarinya ne ko ni na tafi neman abata tinda dama ku baku da asara idan wani abu ya same ta?" "Ke Kande ki shiga taitayinki,ina so fa ki sani ƙyale ki da kika ga ina yi kina cin karen ki babu babbaka a gidan nan ba wai tsoronki nake ji ba. Kawai ina yi ne saboda biyayyar da kike yi min a baya,amma yanzu tinda kema kin bijire mu zuba ni dake shege ka fasa. Na baki daga nan zuwa azahar a ga yarinyar nan idan ba haka ba igiyar auren ki tana lilo a gidan nan." Ƙirji Kande ta dafe ta na zaro ido waje,daga baya ta hau nuna kanta tana faɗin. "Malam ni za ka kalla ka ce igiyar aure na na lilo a gidan nan? Ni fa ake zalunta a gidan nan. Da na san riƙon marainiyar Allah zai dawo haka da ban karɓi amanarta ba,Salma ina kika shiga ne don girman Allah?" Wuce Malam Bala Kande ta yi ta nufi ƙofar ɗakinta ta kulle da makulli sannan ta bazama waje neman Salma. Hasiye kuwa ji ta yi ina ma kada a ga Salman rashin ganinta ya zamo a bakin auren Kande kamar yanda Malam ya faɗa. Ta rasa me yasa duk tsawon shekarun nan da suka yi a tare take jin matsanancin kishin Kande da ƙinta a ranta. Gida-gida Kande ta dinga bi ta na neman Salma amma babu bayani. Cikin kankanin lokaci labari ya baza gari Salma ta gudu,da misalin tara da rabi na safe Malam Rabi'u da Yayansa Malam Jamilu suka zo gidan Malam Bala dan jin karin bayani game da batan Salma. Haƙuri Malam Bala ya dinga basu yana yi musu alƙawarin nemo ta kafin ƙarfe sha biyun rana ya cika. Su na nan suna tattaunawa Baffah Aƙilu ya ƙaraso gidan hannunsa riƙe da na Salma dake ta sharɓar kuka a cikin runtumemen hijabin Gwaggo Kande. Salati Malam Bala ya sanya ya ce. "Dama wajenka ta gudu Alhaji? Ka ganni nan yanzu nake shirin zuwa wajen Malam Mai Jigidar Bala'i ya binciko min inda yarinyar nan take a yi mata kiranye ta dawo gida. Domin kuwa aure dai an riga da an ɗaura shi dole ne ta zauna a ɗakin mijinta babu fashi." Kallon Salma Baffah Aƙilu ya yi ya ce mata. "Maza shiga gida." Sum-sum-sum ta shige cikin gidan kamar mara gaskiya kanta a duƙe ta na satar kallon Malam Rabi'u da ya kafe ta da ido cike da tausayawa. Sosai ya ji tausayin Salma ya danne yanda yake tausaya wa kansa na zama babu aure har na tsawon wannan shekarun,babban abinda ke ƙara ɗaga masa hankali bai wuce yanda duk kyawunsa da abun hannunsa ba mata ke gudunsa. Zuciyarsa ce ta fara gasgata zargin mutane a kansa. Ya na can duniyar tunani ya ji muryoyin Malam Bala da Baffah Aƙilu a sama su na musayar yawu. Babu jimawa Gwaggo Kande ta dawo gidan ita da Kawu Sale. Kai tsaye cikin gidan Kawu Sale ya raka Gwaggo Kande da ke jin numfashinta ya na yi mata wuyar fita. Ta na shiga ta ga Salma a rakuɓe a ƙofar ɗakinta ta na gyangyaɗi Hasiye na ta kaiwa da komowa ta na kwaɓa fanke mai uban yawa a babbar roba,gefe ɗaya kuma tulin kayan miya ne a baho da naman a wata roba,sai rabin buhun shinkafa ƴar gwamnati. Waƙarta take ta yi ta habaici tare da faɗin. "Aure dai ya riga ya ƙullu,kuma dole ne ango ya sha man amarya." Wani kukan kura Kande ta yi sai gata ta dirga a gaban Hasiye,shaƙe mata wuya ta yi ta hau kirɓarta kamar an aiko ta. Cike da azaba Hasiye ta hau ƙoƙarin ƙwatar kanta daga riƙon da Kande ta yi mata ta na faɗin. "Ki sake ni Yaya bana son ƙarasa gawar da ba tawa ba,kada ki hasala ni na yi miki naushin da zaki baje a wajen nan." Jikin Kande ne ya hau rawa saboda gazawa da yake ƙoƙarin yi sakamakon tsufa,yunwa da gajiya da suka haɗu suka yi mata yawa. A daidai wannan lokacin Malam Bala da su Baffah Aƙilu suka shigo gidan. Saura ƙiris Gwaggo Kande ta kai ƙasa Kawu Sale ya taro ta yana faɗin. "Subhanallahi,Gwaggo lafiya? Me yake faruwa ne a gidan?" Hasiye ta na haki tana danne kukan da ke shirin taso mata na azabar da ta sha ta ce. "Me yake faruwa kuwa banda wannan tsohuwar da ta kama ni tana duka kamar za ta kashe. Daɗin abun dai bani na kar zomon ba rataya aka bani." Makullin ɗakin Kande Salma ta lalubo a lalitarta dake jikinta ta buɗe musu ɗakin suka shiga. A gado Kawu Sale ya kwantar da ita ya na yi mata sannu. Cike da tsananin damuwa Kande ta kalli Salma ta ce. "Lokacin da kika gudu kin tuna da ni Salma? Kin yi tunanin halin da zan shiga ko kuma irin zargin da mutane za su ɗora akan ni ce na ce ki gudu?" Da sauri Salma ke girgiza kanta tana kuka. Wani irin tausayinsu ne ya lulluɓe Kawu Sale ba tare da ya shirya wa hakan ba. Cikin ransa yake ayyana. 'Anya na yi wa zumuncin ƴar'uwata adalci kuwa? Nawa ne dubu ashirin har da zan karɓi kuɗi na yi ja gaba wajen kassara rayuwar yarinyar da bai kamata ta shiga irin wannan ƙuncin ba da ƙarancin shekarunta? Salma fa yarinya ce sa'ar Isuhun wajena,yanzu idan ni na tsugunna na haife ta zan so a ƙwace mata ƴancin ta na walwala a doron ƙasa?' Da sauri ya girgiza kai ya miƙe ya bar ɗakin. A tsakar gida ya tarar da Baffa Aƙilu ya na faɗin. "Ai na ji labarin irin kuɗaɗen da Rabi'u ya sakar muku shi yasa kuka amince kuka aura masa ƙaramar yarinya tinda ba ƴarku ba ce. To ku tsaya ku ji da kyau,na aika saƙo wajen Abdulwahabu,dan haka ku tsammaci zuwansa a kowanne lokaci daga yanzu. Kai kuma Sale ka bani mamaki,akan abun duniya ka ci amanar ƴar'uwarka,tir da ɗan'uwa irinka." Baffah Aƙilu na gama magana ya bar gidan,kan dole Kawu Sale ma ya ja guiwarsa da ta yi masa sanyi ƙalau ya tafi nashi gidan. Ɗakin Kande Malam Bala ya nufa ya ɗage labule ya na bin Salma da wani irin mugun kallo ya ce. "Ke kuma daga yanzu kika sake saka ƙafa kika bar ɗakin nan ba da izinin Hasiye ba,sai na lahira ya fiki jin daɗi,munafukar yarinya kawai me fuska biyu,ina ce jiya har da kukan ki kika ce kin ji kin amince za ki yi biyayya ki yi zaman aure? Yau wanne shaiɗanin ne ya ziga ki ki gudu kuma? To ina so ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,idan har ɗan'uwanki ya zo ya ce zai raba auren nan kamar ya raba auren ta da ni ne gata nan kwance gabanki,dan haka sai ki zaɓa zaman aure ki yi ibada ko kuma auren mariƙiyarki ya guntule." Labulen ya saki ya wuce ɗakinsa ya na masifa kamar zai ari baki. Ya na shiga ɗakin Hasiye ta bishi hannunta riƙe da kwanon koko da fanken da suke ta soyawa ita da Mairo da Shamsiyya. Ta na ajiye masa ta zauna a bakin gado ta ce. "Wannan hukuncin da ka ɗauka Malam shi ne daidai,dan idan ba haka ba Abdulwahab na zuwa zai sa a raba auren." Cike da takaici Malam Bala ya ce "To ai abinda zai baki takaici Hasiye shine;da ƙyar fa muka danne Rabi'u ni da Jamilu,da tini ya saki yarinyar nan mu kuma asirinmu ya tonu,dan kuwa a yanzu bani da kuɗin da zan biya shi abinda ya bamu duk na zuba su a noman rani." Haɓa Hasiye ta kama ta na sallami ta ce. "To ai Malam dama fa shi bai baku kuɗi dan rufe muku baki ba,ya bayar ne kawai ba tare da wani sharaɗi ba." Jinjina kai Malam Bala kawai ya yi ya kora kokon da ya kwaso a ludayi. Nan dai Hasiye ta zauna ta ci gaba da zuga Malam Bala tare da bashi mugayen shawarwari. Da azahar mata suka fara cika gidan Malam Bala su na taya Hasiye da Kande murnar auren Salma. Kande dai ta na ɗaki ta na kallon kowa ranta babu daɗi,ruwan farau-farau ta kora ta koma ta kwanta ta na nishin azabar da ƙirjinta ke yi mata. A haka mata suka dinga cin shinkafa dafa duka da zoɓo,su na surutai akan auren Salma kamar a gabansu wasu abubuwan suka wakana. Bayan an yi sallar la'asar Mairo ta shigo gidan ita da ƙawayen Salma da ta gayyato na makaranta,Salma na ganinsu ta ɓuya a bayan ƙofar ɗakin Kande ta na sharɓar kuka. Duk yanda suka so su ja ta a yi party ƙi ta yi,kan dole suka haƙura suka ƙyale ta. Rediyon Hasiye Mairo ta ɗakko ta loda mata sabon batir suka saka kaset suka kunna kiɗa su na ta rawa abunsu cike da nishaɗi da jin daɗin ƙawarsu na aure. ********************* Saƙon da Baffah Aƙilu ya bayar bai iske Abdulwahab da wuri ba. Domin kuwa sai da ya dawo daga aiki ya shiga kasuwa da yamma ake sanar da shi mummunan labarin da ya tayar masa da hankali ƙwarai da gaske. Da yammar ya kira Mudassir ya labarta masa kaf abinda ke faruwa,ko gida basu je ba Malam Sallau ya ja su a ƴar ƙurƙurar motar da suke amfani da ita ta zirga-zirga. Tafe suke su na tattauna lamarin, jinin Mudassir har ya fi na Abdulwahab tafasa,domin shi dama mutum ne mai sanyin halin, Mudassir kuwa ya na da zafi sosai idan aka taɓo shi. Cike da ƙosawa su isa Kura da wuri Mudassir ya ce. "Malam Sallau ba wa motar nan wuta lokaci na ƙurewa." "Tom Malam Mudan a bi komai a sannu,da yardar Allah babu abinda zai samu Salamatu sai alheri." Haka suka ci gaba da tafiya kamar kurame kowa da abinda yake saƙawa a cikin ransa. Gudu suke tsulawa a mota cikin rashin sa'a Malam Sallau ya taka wani abu mai tsinin da ya yi sanadiyyar fashewar tayar motar. Salati Mudassir ya dinga yi ya na jin zuciyarsa na tafasa kamar ta kama da wuta. Gaba ɗayansu fita suka yi suka hau neman taimako ko za su samu wanda zai taimaka musu Malam Sallau ya shiga gari ya samo musu mai gyara. *********************** A can ƙauyen Kura kuwa mata sun ci sun sha sun yi hani'an,hakan sai ya sake tabbatar wa da Kande cewar Hasiye ce ta ƙulla wannan auren dan kawai ta ƙuntata mata. Tabbas kuwa ta yi nasarar sanya ta a cikin baƙin cikin da tinda take a duniya bata taɓa shiga irinsa ba. Ta na daga ɗaki ta na hango yanda Hasiye ta sha shadda ruwan ɗorawa an yi mata jan aiki da jan zare sai shewa take yi ta na taya su Mairo tiƙar rawa kamar wata ƙaramar yarinya. Dare na yi Balaraba da Tafisu da sauran ƙawayen Hasiye ne suka shiga har ɗakin Kande suka ja Salma suka yi waje da ita. Wanka suka saka ta a saman turmi suka yi mata da ruwan lalle da magarya suna ta wanke-wanken amarci irin na ƙauye. Ita kuwa Salma ta gaji da kuka ta tsaya kawai ta na kare ƴan matasan ƙirjinta tare da matse ƙafafuwanta da Balaraba ke buɗawa ta na kwara mata ruwan lalle. Su na gama wanke ta tas suka kaita ɗakin Hasiye suka shirya ta cikin atampar da bata san lokacin da aka ɗinka mata ita ba. Tana juya wa bayanta ta ga akwatina guda uku a ɗakin Malam Bala har da takalmi da jaka a cikinsu. Cike da mamakin lokacin da aka kawo su ta kawar da kanta tana jinjina lamarin da take ɗaukan sa kamar wasa. Turare Balaraba ta fesa mata Tafisu ma ta ƙara mata wani suma suka shafa suna yaba ƙamshin turaren. Anan take jin wannan akwatunan dika nata ne. Mayafi fari ƙal suka yafa mata tare da damƙa mata farar jaka,har ƙasa Tafisu ta duka ta saka mata takalmi fari ƙal sannan suka gyara mata zaman sarƙar dake wuyanta suka kamo hannunta suka fito. A tsakar gida suka tarar da dangin Malam Rabi'u sun zo ɗaukan amarya,ciki har da Samira da ke cike da matsanancin farincikin da ta kasa ɓoyewa. Wajen Hasiye ta je suka tafa a ɓoye su na magana da ido tare da nuni da bakunansu da hannayensu. Har cikin ɗakin Kande su Balaraba suka shigar da Salma suka zaunar da ita a gaban Kande da ke zaune ta zabga tagumi ta na kallon ikon Allah. Guda mata suka kaure da yi da hayaniya kamar ba su kula da halin da Kande da jikarta ke ciki ba. Cike da hayaniya mata suka ce. "To Kande lokacin rabuwa da ƴar gaban goshi ya zo;sai a yi mata nasiha a wuce da ita ɗakin miji dare na yi." Kasa cewa komai Kande ta yi da ya wuce danne hawayen dake ƙoƙarin ƙwace mata;sakamakon jin irin kukan da Salma ke yi. Ganin dare na yi Kande ta ƙi cewa komai sai mata suka ɗauki Salma dake turjewa ta na ihu suka yi waje da ita. A ƙafa suka nufi gidan Malam Rabi'u da Salma suna tafe su na waƙoƙin amare irin na ƙauye. Su na isa gidan Samira ta dawo baya ta ce. "Ai ya kamata ku bar amarya ta fara taka cikin gidanta da ƙafarta kafin kowa ya shiga ko?" Ai kuwa babu musu Balaraba da Tafisu da ke riƙe da Salma suka sauke ta ƙasa su ka tura ta cikin sashen nata wanda aka katange shi da ginin ƙasa aka yi masa filasta tare da shafen koren fenti mai haske. Salma na saka ƙafa a cikin gidan ta ji kanta ya yi wani irin sara mata kamar zai rabe gida biyu,hannu ta sa ta dafe kanta ta ce. "Washhh Allah na kaina." Cikin yi wa Salma tsiya Samira ta ce. "Ai ko bayanki ne ke ciwo amarya yau dole ango ya sha mai,ku shigar da ita ɗakinta ta ga irin dukiyar da mijinta ya kashe mata." Guɗa matan gidan suka kacame da ita kafin su shiga cikin ɗakin da yake shine mallakin Salma. Guɗa Balaraba ta sake rafkawa ta ce. "Ahhh yarinya kin yi goshi barakallah masha Allahu. Inyeee har da sif da dibaida. Allah Ya bada zaman lafiya to,ya kawo ƙazantar ɗaki,amma ba ta ƙin shara ba." Nan fa mata suka dinga yi mata addu'o'i su na lelleƙa sauran wajen su na sam barka. Bayan sun gama ne Mairo da ƙawayen Salma suka zauna mata domin jiran zuwan ango da abokansa dan su basu kuɗin siyan bakin amarya............ MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ PAGE 19. Da yake ango ba yaro bane shi kaɗai ya zo abunsa;hannunsa riƙe da leda. Ya na shiga ya ji hayaniyar yaran da yake yi wa kallon ƴan kucakucin yaran da ko magana basu gama iyawa ba. Mairo ce zaƙaƙurar da ta isa gabansa ta ci ɗamara ta miƙa masa hannu ta ce. "A cake mana kuɗin siyan baki kafin mu barka ka je wajen amaryarka." Murmushi kawai Malam Rabi'u ya yi ya zira hannunsa a aljihu ya ƙirgo dubu ɗaya ƴan hamsin-hamsin ya miƙa wa Mairo dake wata jijjiga da harare-harare. Ya na bata ya naɗe hannunsa ya na kallon ta yana jiran ya ji kuma me za ta ce. Baki ta washe cike da murna ta ce. "Ku taso mu tafi ango ya yi sallama. Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki sai mun zo da safe cin abincin amarya." Cikin sauri Malam Rabi'u ya haɗe fuska tamau ya ce. "A kul na ga ƙafar wata yarinyar a cikin ku ta sake zuwar min gida." Cike da jin tsoronsa suka ranta a na kare suka bar gidan. Su na tafiya Malam Rabi'u ya samu waje ya raba kazar nan gida biyu,ba tare da ya ce da Salma komai ba ya ajiye mata nata kason a gabanta ya ja gefe da nashi ya hau ci. Jin ɗakin ya yi shiru ne ya sanya Salma durƙusawa ta ce masa. "Ina yini." Murmushi ya saki mai sauti ya ce. "Lafiya ƙalou,ki yi haƙuri na shigo ban yi miki magana ba,a zato na ke ɗin irin yaran nan ne masu rawar kai,ni kuma bana son hayaniya shi yasa na tsuke baki na." Kai Salma ta sake sauke wa ƙasa ta rakuɓe a jikin gadon da take ta mamaki a cikin ranta wai nata ne. Malam Rabi'u kuwa bai sake ce mata komai ba,ya na gama cin kazar sa ya yi gyatsa mai ƙarfi sannan ya ce. "To sai da safe,ina fatan kin san inda bayi yake. Dan bana so ina bacci ki katse ni ki ce za ki zaga,ni da kika ganni idan ina bacci ba a tashi na." Kai kawai Salma ta gyaɗa masa ba dan ta san akan me ta gyaɗa kan ba. Ita dai babban buri da fatan ta bai wuce na ta ganta ta keɓanta ita ɗaya ba ta samu damar yin kukan da ke danƙare a ƙirjinta. Waje Malam Rabi'u ya fita ya nufi wani ɗaki dake kallon na Salma ya buɗe da makulli ya shiga. Fitilar tocilan ya kunna ya ke haska ɗakin da ita, daga nesa Salma ke hango Malam Rabi'u ya na cire babbar rigarsa,gabanta ne ya faɗi sai ta yi saurin kawar da kanta gefe ta sake takure wa a waje ɗaya. Salma bata da ilimi ko na sisin kwabo akan rayuwar aure,a bakin su Mairo da ƙawayenta ne ta ji wasu abubuwan a lokacin da aka barsu tare. Babban buri da fatanta bai wuce Allah Ya sa kada Malam Rabi'u ya zamo daga cikin ƴan isakan mutanen da ke taɓa jikin ƙananan yara ba. Wani irin kuka ne mai cin rai ya turniƙe ta. Nan take ta hau yinsa ta na faɗin. "Gwaggo don Allah ki zo ki taimake ni tsoro nake ji." Haka ta dinga kuka a hankali ta na toshe bakin ta gudun kada wani ya ji ta. Ganin hasken ɗakin Malam Rabi'u ya mutu ne ya sanya ta miƙe wa a hankali ta rufe ƙofar nata ɗakin da sauri. Wani irin tsoro ne ya ke shigarta a hankali. Gado ta haye ta takure a waje ɗaya ta na jin kamar ta ɓace ta ganta a ɗakin Kande. A haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta. ************************* A ɓangaren su Abdulwahab kuwa sai ƙarfe goma na dare suka shiga cikin garin Kura. Su na isa Mudassir ya kafe sai sun je gidan Malam Bala a daren an yi wacca za a yi. Da ƙyar Abdulwahab ya danne shi ya bashi baki kan su bari safiya ta waye a yi komai a ilmance,domin ya kula faɗa da tashin hankali ba zai bashi abinda suka zo nema ba. A daren suka shiga cikin kasuwa suka samarwa kansu abinda za su ci suka koma gida. Abdulwahab wanka ya yi ya gabatar da shafa'i da wutiri kafin ya nemi waje ya kwanta. Malam Sallau kuwa da Mudassir na nan zaune su na hira kamar ba su ne suka sha gajiya tuɓus ba akan gyaran mota Washegari da sassafe bayan sun dawo daga masallaci Abdulwahab ya riga su shiga wanka,ya na fitowa Mudassir ya watsa ruwa ya fito. Malam Sallau kuwa gidan su na gado ya wuce dan ƴan'uwansa basu san ya shigo gari ba a daren jiyan. Ko karya wa ba su tsaya yi ba suka nufi gidan Malam Bala. Su na zuwa suka yi sallama a bakin ƙofa kafin Abdulwahab ya sa kai ya shiga gidan kai tsaye. Hasiye da ke bakin murhu ta na hura wuta ce ta fara arba da fuskar Abdulwahab da ya tamke ta tamau kamar bai taɓa dariya ba. Yaƙe ta fara yi ta hau ƙwala wa mijinta kira da duk wanda sunan sa ya shiga bakinta. Sai take jin ba za ta iya motsa wa ba kada Abdulwahab da ya fusata ya sa ƴan sanda su harbe ta. Kai tsaye ɗakin Gwaggo Kande Abdulwahab ya shiga. Zaune ya tarar da ita akan abun sallah idanuwanta sun koɗe sun yi jawur saboda kuka. Ta na ganinsa ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fashe da wani sabon kukan da yake jinsa a cikin ransa. Durƙusawa ya yi a gabanta ya kamo hannuwanta ya ce. "Gwaggo ki kalle ni,ki dena saukar da kanki ƙasa kamar wadda ta aikata wani laifi." Cikin kuka Gwaggo Kande ta ce. "Na aika babban kuskure Abdulwahab. Na yi nadamar zamowata matar Malam. Ji nake yi kamar na mutu saboda baƙinciki. Ina soyayya da tausayin da Malam ya nuna min a tsawon rayuwarmu? Me ya sa ya zaɓi ya ƙuntata wa zuciya ta a cikin ƙanƙanin lokaci irin wannan? Salma ita ce farinciki na ya kuma san da hakan,sai gashi ya yi amfani da ita wajen rusa wannan farincikin nawa na shekara da shekaru kamar wanda dama can yana jin haushi na. Babbar damuwata yanzu bata wuce zaman Salma da Samira a waje ɗaya ba,Samira bata ƙaunar Salma ko kaɗan,tun su na nan gidan ta saka ta a gaba ban dai taɓa faɗa bane saboda nima bana bari idan ta yi mata abu,to yanzu da suke su kaɗai wa zai rama mata idan Samira ta zalunce ta?" "Allah shi ne zai rama mata Gwaggo,ina so ki dena damuwa dan ba laifinki bane abubuwa suka kasance a haka. Na san laifi na ne ya shafi Salma,ko kin manta ni ne na ƙi auren ƴarsu? Shi ya sa suka biyo ta nan dan su rama abinda na yi musu." A hasale Mudassir dake tsaye yana kallon su ya ce. "To ana so dole ne? Wa ye ya basu dama da ƴancin aurar da yarinya ƙarama babu izinin magabatanta?" Muryar Malam Bala ce ta daki dodon kunnen Mudassir dake tsaye a bakin ƙofa;kamar saukar aradu. "Ni ne nan na ba wa kai na izinin aurar da ita,domin a ƙarƙashi na take,idan tarbiyyarta ta yi kyau ni ne,idan tarbiyyarta ta ɓaci ni ne. Me ya sa lokacin da nake kula da ita cinta,shanta,suturarta da duk wani abu da ya shafi rayuwarta baku ce wa ya bani izinin yin hakan ba,sai yanzu da na ga dacewar na aurar da ita ga mutumin da na san zai kula da ita ko bayan ranmu shi ne na yi laifi?" "Tsohon da ko yau ana iya sanar da mutuwarsa kake maganar zai kula da Salma ko bayan ranmu? Kai Malam ka fa yi son zuciya dole ne kuma a warware wannan auren ko kana so ko baka so." "Kai kuma a wa da kake ta baloƙoƙo kamar wani kwarton ƙadangare?" A hasale Mudassir ya isa gaban Malam Bala yana huci kamar zai kai masa duka,sosai hakan ya tsorata Malam Bala da Hasiye da ke laɓe a jikin labule ta na sauraron duk abinda ke faruwa. Baya Malam Bala ya ja Mudassir ya ƙara binsa ya na zaro ido waje,ji yake yi ba dan tsufan Malam Bala ba da tini ya ɗaga shi sama kamar yanda suke wa buhun shinkafa ya lafta shi da ƙasa. Sai da Abdulwahab ya gama lallashin Gwaggo Kande da bata baki sannan ya fito ya tarar da fusataccen amininsa da Malam Bala a tsaye carko-carko kamar zakarun dake shirin kacame wa da dambe. Tsakiyar su ya shiga ya raba kallon kisan kan da Mudassir ke bin Malam Bala da shi. Sassanyar ajiyar zuciya Malam Bala ya sauke ya yi gyaran murya. Kafin ya ce wani abu Abdulwahab ya ce. "Na ji labarin a gaban sarkin garin nan aka ƙulla auren Salma da Tsohon da ka zaɓa mata ko?" Da sauri Malam Bala ya ce. "To abinda Sarkin ne ma ya wakilci ɗaurin auren tare da sanya masa albarka? Ai kada ka...." Katse masa hanzari Abdulwahab ya yi ya ce. "To ya kamata mu je gaban sarki domin a warware abinda aka ƙulla babu son yarinya da danginta." Ya na gama magana ya yi gaba, Mudassir kuwa sai ya ƙi tafiya ya tasa ƙeyar Malam Bala a gaba suka mara wa Abdulwahab baya. Su na zuwa fada sai suka tarar da mutane ana ta kwasar gaisuwa a wajen sarki ciki har da Malam Rabi'u da Malam Jamilu Yayansa. Su ma zubewa suka yi suka kwashi gaisuwa,daga nan sai Abdulwahab ya gabatar da kansa da kuma ƙorafin da yake tafe da shi. Malam Rabi'u da ke bin su da kallo tin shigowarsu fadar ne ya saki murmushin da yake dabi'arsa ya sunkuyar da kai,kalmar tsoho da ake yawan kiransa da shi tun da ya auri salma ta na yi masa ciwo a rai;ba dan be yarda shi ɗin tsoho bane,amma kafin ya aure ta abokansa kullum yabon kyan jikinsa da yanda jikin nasa baya nuna shekarunsa suke yi,wasu ma sai suka ce ko dan be yi aure bane shi yasa tsufansa ƙin bayyana,wasu kuma suka ce aljanar da ta aure shi ne take son ganinsa da yarinta shi yasa take sabunta masa fatarsa duk shekara,kwatsam sai gashi auren Salma ya jawo masa tuni akan shi ɗin fa tsoho ne da ya yi jika da ita. Kamar daga sama ya ji sarki na gabatar da shi a matsayin mijin Salma. Murmushin dai ya sake sakar musu ya miƙa wa Abdulwahab hannu suka gaisa, Mudassir kuwa kawar da kai ya yi yai kamar be ga hannun Malam Rabi'u ba. Janye hannunsa Malam Rabi'u ya yi yana murmushi ya koma mazauninsa. Bayan sun gaisa Sarki ya ce. "To Alhamdulillahi. Kamar dai yanda kowa ya sani a garin nan kaf Malam Rabi'u ya sha wahala wajen neman matar aure,tausayi da kuma zaman amana tare da ceton rai ne ya sanya Malam Bala baiwa ƙanin amininsa auren Salma. Domin kuwa a ranar da aka fasa aurensa a karo na barkatai suma ya yi anan saboda damuwa,dan haka ina mai roƙon ku da Allah ku kwantar da hankulanku,ku bar wannan aure ya rayu domin bamu san alkhairin da Allah ya jefa a cikinsa ba." Cikin sauri Malam Bala ya tari numfashin Sarki ya ce. "Kuma shi irin wannan auren Allah Ya baka yawan rai,idan mutum ya matsa sai an raba sai Allah ya raba shi da rayuwarsa gaba ɗaya." Harara Mudassir ya danƙara wa Malam Bala ya yi ƙwafa. Shi dai har a wannan lokacin ransa bai risina ba,nasiha sosai Sarki ya yi musu wadda daga ƙarshe ta ratsa su ta sanya su yin haƙurin dole ba dan sun so ba. Har gidan Salma Malam Rabi'u ya kai su,su na zuwa suka tarar da ita ta na cin fuffuken kazar daren jiya da bata ci ba,duk da cewa sai da Samira ta shiga ta ɗebi mai yawa ta na faɗin. "Abunka da mai juna,ina zaune jikina ya bani akwai abun motsa baki a nan,to gani na zo a bani kason maƙotaka. Sannan daga yau idan aka kawo miki abun motsa baki ko na kari ki tabbata kin ajiye min na zo na taɓa nima,idan ba haka ba zan yi miki azabar da tunda uwarki ta haife ki baki taɓa ganin an yi wa wani irinta ba." Miƙa mata ledar gaba ɗaya Salma ta yi ta ɗebi son ranta ta bar mata wajen da babu wani nama sosai. Da sauri Salma ta ture ledar dake gabanta ta nufi Yayanta ta rungume shi ta sanya kuka mai taɓa zuciya. Abdulwahab rungume ƙanwarsa ya yi a jikinsa sosai yana jin kamar ya raba jikinsa biyu ya saka ta ciki. Ji yake yi sam be bata rayuwa mai inganci ba kamar yanda ya kamata,sai gashi an datse mata ƙuruciyarta ta hanyar aura mata tsoho. Da sauri Mudassir ya fita ya na sharar ƙwallar tausayawa Salma. A ƙofar shiga sashen Salma ya gamu da Malam Rabi'u ya na ba da kuɗi a siyo wa Salma abun kari. Har ƙasa Mudassir ya durƙusa yana hawaye ya ce. "Baba don girman Allah ka riƙe mana Salma da amana,ka tausaya mata ka ririta maraicinta,ka kuma bata kulawa da gatan da bamu samu damar bata ba,Baba don Allah kada ka bari a cutar da Salma. Mun baka amanar Salma idan ka ci amanar ta amanar Allah za ta ci ka." Jikin Malam Rabi'u ne ya yi sanyi ƙalau,hannu ya miƙa wa Mudassir don ya tashi amma ya girgiza masa kai yana sake haɗe hannayensa biyu yana roƙon Malam Rabi'u akan ya kula musu da amanar Salma. A haka Salma da Abdulwahab suka same shi. Hannu Malam Rabi'u ya miƙa wa Salma ya kira ta gare shi. Sakinta Abdulwahab ya yi ta ƙarasa wajen Malam Rabi'u ta tsaya daga ɗan nesa da shi. Mudassir Malam Rabi'u ya kalla ya dafa kan Salma ya ce. "Gata nan ku tambaye ta daga jiya zuwa yau idan akwai abinda na yi mata wanda ya nuna ni Rabi'u zan yi mugun zama da ita. Kana ji na ko samari? Wannan yarinyar ƙaddarata ce,hukuncin ni zan aure ta ita za ta aure ni a halin da nake ciki ya tabbata babu mai canja hakan. Na yi muku alƙawari da sani na ba zan taba cutar da Salma ba,idan kuma yanzu ta ce bata son aure na a gabanku zan tsinke igiyar da ta ɗaure mu ni da ita." Cikin sauri Abdulwahab da Mudassir suka kalli Salma tare da fatan ta ƙi wannan aure. Ita kanta Salma a zuciyarta tana son furta kalmar saki,amma a zahiri tana jin kamar idan ta bar auren ko ta bar gidan za ta iya mutuwa,wani irin hali ta shiga na firgici da tsoro tare da azabar ciwon kai mai tsanani. Dariyar Samira ce ta sanya su juyawa gaba ɗaya su na kallonta. Takowa ta yi gaban su ta ce. "Ni fa mamaki kuke bani gaba ɗayanku, wai shin akan Salma aka fara aure da ƙarancin shekaru;ko kuwa akanta ƙaramar yarinya ta auri babban mutum? Kun bi kun damu kanku kun ishi mutane da abu ɗaya,aure dai ya riga ya ɗauru,kuma da alama rabo ne ya kira Salma gidan nan, duk wanda ya nemi ya datse igiyar aurenta to da alama tashi rayuwar zai datse." Ta na faɗan haka ta kalli Salma dake jin kamar da ita ta yi maganar ƙarshe,domin kuwa ji take yi idan ta nemi saki za ta mutu. Mudassir ne ya kalli Abdulwahab yana neman ƙarin bayani,da laɓɓansa ya yi masa nuni da ita ce Samira. Girgiza kai ya yi ya na jinjina ƙarfin hali irin nata. Daga ƙarshe dai ɗakin Salma su Abdulwahab suka koma suka zauna suna ta bata haƙuri tare da lallashinta akan ta yi biyayya da yardar Allah za ta ci riba anan gaba. Kuɗi mai yawa Abdulwahab ya bata ya ce. "A duk lokacin da kika ji zaman gidan be yi miki ba,ki je tasha ki hau mota ki zo waje na kin ji ko? Ai zaki gane Ƴankaba ba sai na sake yi miki kwatance ba ko? Sannan duk abinda kike so ki siya da kuɗin nan,idan sun ƙare Malam Sallau zai kawo miki wasu,dan zan dinga aiko miki shi akai-akai." Abdulwahab na gama magana Mudassir ya ce. "Ko kina son wani abu ne Salma? Idan da abinda kike so kuma ki sanar da mu kafin mu tafi." Kai ta girgiza tana murmushi. A hankali ta ce. "Babu abinda nake so Yayah Allah Ya saka da alkhairi,don Allah ku ce wa Gwaggona ta kwantar da hankalinta,wannan Baban ba mugu bane,ta yi min addu'a Allah Ya sa kada ya dake ni ko ya min faɗa. Sannan ku gaishe min da yarana idan Baban nan gidan ya barni zan zo na gansu." Dariya sosai Mudassir ya fashe da ita ya na kallon Malam Rabi'u da ke haɗe fuska a duk sanda Salma ta kira shi da Baba. Cike da shaƙiyanci Mudassir ya ce. "Ai wannan Baban na kula ya na da kirki gaskiya." Da sauri Malam Rabi'u ya kalle shi ya sake tamke fuska. Ganin cewa Mudassir zai fara sakin layi sai Abdulwahab ya miƙe ya ce. "To mu mun tafi sai watarana ko Salma." Idanuwanta ne suka kawo ruwa ta gyaɗa masa kai kawai. Har bakin ƙofa ta raka su ta dawo. Sallama suka yi da Malam Rabi'u suka wuce gidan Gwaggo. Suna tafiya aka kawo abun karyawa Malam Rabi'u ya karɓa ya shige musu da shi sashen su. A zaune ya tarar da Salma tana kuka. Ba tare da ya lallashe ta ko ya hana ta kukan ba ya ajiye mata abun karyawarta a gabanta,wanda yake shayi ne da bread da ƙosai. Nashi ya ja gefe ya ɗauki kofuna biyu a kwandon kwanikan da yake nashi tun yana shi kaɗai ya juye shayinsa itama ya juye mata nata ya tura mata gabanta. Ganin ba za ta dena kukan bane ya sanya shi sassauta murya ya ce. "Ɗauki abincinki ki ci,su yayun naki ai ba za su so su ganki zaune da yunwa ba ko?" Kai ta ɗaga sama ta na jan majina ta ja abun karyarwarta ta fara ci,ta na tsaka da ci ta tuna da gargaɗin da Samira ta yi mata na rage mata duk wani abu da ta ci,da sauri ta ture abincin ta koma gefe ta na zare ido. Malam Rabi'u bai kula da abinda ke faruwa ba,yana gama karyawa ya miƙe ya bar gidan gaba ɗaya. Fitarsa ke da wuya Samira ta afka sashen na Salma,cikin zare mata ido ta ce. "Ina abinda aka bawa Tanimu ya siyo miki?" Da sauri Salma ta ce. "Gashi Yaya Samira." Ɗauka Samira ta yi ta leƙa ledar ta na washe baki ta ce. "Yauwaa yarinyar kirki,idan ki na ajiye min irin wannan lafiya lau za mu zauna a gidan nan ni da ke babu mai jin kammu. Miƙo kofin can na tarfa miki shayin. Ko kuma bari ina zuwa." Ledar ta tattare tai gaba,babu jimawa sai ga Tanimu ɗan mijin Samira wadda mahaifiyarsa ta rasu ta bari ya shiga da wani kwano duk ya yi lamba ya ba wa Salma ya fita. Salma na buɗawa ta ga wani irin tuwo baƙiƙƙirin da koriyar miya fatau. Ture wa ta yi gefe ta zabga tagumi tana tunanin yanda rayuwarta ta koma. A ɓangaren su Mudassir kuwa sai da suka lallaɓa Gwaggo suka kwantar mata da hankali sosai tare da tabbatar mata sun tarar da Salma yanda basu yi zato ba,suna kuma fatan ta tabbata cikin farinciki a gidan nata. Daga ƙarshe suka ajiye mata ƴan kuɗaɗen da za ta yi wa Salma siyayyar duk abinda bata da shi suka tafi. Haka rayuwar Salma ta kasance a gidan Malam Rabi'u cikin ƙuncin da shi kansa bai san ƴar ƙaramar amaryar tasa tana cikinsa ba. Domin kuwa duk wata hanya da Samira ta san za ta goge sawun musguna wa Salma da take yi a gidan ta goge. Dan haka Malam Rabi'u da Malam Jamilu har alfahari suke yi da zaman lafiyan da su Samira ke yi. Lokuta da dama idan ya kawo nama ko kifi Samira yake bawa ya ce ta yi musu dabge saboda Salma ta ci ta ji daɗi. Ba tare da saninsa ba sai dai ta zuba wa Salma romo kaɗan ta bata,ita ta zauna ta cinye naman ko kifin. A hankali Salma ta dinga rama mai muni,Samira kuma na narka ƙiba abunta kamar mijinta shine mai kashe kuɗin domin ta ji daɗi..... MUGUWAR MACE. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️ Mai son ci gaba da karanta littafin MUGUWAR MACE ya saka 1k ta 9031416423 Hamidah Ahmad Sanusi Opay. Sai a tura shaidar biya ta 09031416423. Don tsarkin mulkin Allah kada ki sayi littafi na idan za ki yaɗa shi ba tare da kin bari na kammala ba,idan kika yaɗa kamar kin dakushe min sana'a ne. PAGE 20. LAST FREE PAGE. Dakan kayan yaji da za su yi miyar dare Salma ke yi a ƙaton turmin tsakar gidan nasu wanda marigayiya matar Malam Jamilu ta yi dakan furar sayarwa a ciki. Gaba ɗaya taɓaryar ta yi wa Salma nauyi da tsawo,a haka ta jure ta ke ta faman daka duk ta haɗa zufa;Samira na yi mata faɗan sanyin jiki da take da shi. Salma na gamawa ta duƙa ta kwashe kayan yajin ta nufi madafi da shi ta buɗe tukunyar dake kan wuta ta zuba. A gajiye ta shiga ɗakin Samira dake hango duk abinda take yi a tsakar gidan ta durƙusa har ƙasa ta ce. "Yah Samira na gama,akwai abinda zan yi miki?" Shiru Samira ta yi ta na wani nazari,a cikin ranta ta ce. 'Ya kamata fa na karɓi abinda zan bayar a sunan Hauwa a wajen yarinyar nan,tinda ita ce sabuwar amarya,na tabbata idan na sauka lafiya nima za su rama wa kura aniyarta.' Muryar Salma ce ta katse ta daga tunanin da ta faɗa ta ce. "Yah Samira miyar na kumfa me zan zuba?" "Ki je ki buɗe murfin tukunyar ki saɓa bakin. Yauwa idan kin gama mu je ƙofarki ki buɗe min lefen ki akwai abinda zan ɗauka na kai wa Hauwa na barkatu." "To Yah Samira." Cike da ladabi Salma ta je ta saɓa bakin tukunyar kamar yanda Samira ta umarce ta,daga nan sai ta wuce sashenta ita da Samira,su na shiga Samira ta hau leƙe da dube-dube ko za ta ga wani abun da za ta yi faɗa akai ko ta ɗauke. Har uwar ɗaka suka shiga tare,da ƙyar Salma ta iya sakko da akwatunan ƙasa Samira na kallon ta;amma ta ƙi taimaka mata. Ta na saukewa Samira ta zauna a gaban kayan tana ɗagawa,tsabar son zuciya ji take yi da da hali da ta kwashe kayan dika,domin Malam Jamilu bai kashe mata kuɗi kamar yanda aka kashe wa Salma ba. Hannunta ta ɗora akan wata santaleliyar atampa mai kyau,da dikkan alamu ita ce ma mai babban kuɗi a cikin kayan. Turare da breziya Samira ta sake ɗauka sannan ta miƙe tsaye ta ce. "Maza ki kwashe su ki mayar da su mazaunin su. Ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,ko sama da ƙasa za ta haɗe idan an tambaye ki inda atampa take ki ce baki sani ba,idan kika faɗi suna na sai na sa gabanki gabar na yanke da wuƙa. Shegiya mai ido kamar na mage." Kan Salma ta dangwara sannan ta ɗaga rigarta ta soke atampar da turaren tare da breziya ta fita da sauri. Kai tsaye ɗakinta ta nufa ta cire kayan daga cikinta ta samu leda babba ta saka kayan ta ɓoye. Murna ta dinga yi domin ta samu hanya mafi sauƙi da za ta dinga bada kayan barkatu ba tare da sisinta ya yi ciwo ba. A wannan azaba da uƙubar Salma ta yi wata biyu a gidan Malam Rabi'u. Watarana da daddare Malam Rabi'u da Salma su na zaune yana jefa lomar tuwon da Salma ta tabbatar masa cewa da kanta ta dafa masa. Murmushi ya yi ya kalle ta ya ce. "Inyeee an Salamemen Gwaggo hannu yana ta faɗawa. To ga wannan ki sayi sha ka laɓe ki sha abunki." Hannu ya saka a aljihunsa ya zaro nera ɗari sabuwa kar ya bata. Murna Salma ta dinga yi ta na yi masa godiya. A hankali Malam Rabi'u ya tsaya yana kallon ta shi ma yana murmushi, sai dai bai jima yana murmushi ba fuskarsa ta koma ta jimami,cike da kulawa ya kalli Salma ya ce. "Salma ko dai akwai abinda yake damunki ne a gidan nan da baki sanar da ni ba? Gaba ɗaya kin rame kin yi baƙi kamar ba ke ba,ni kuma na san ina bakin ƙoƙarin na ga na kawo miki duk wani abu na jin daɗin rayuwa,domin a yanzu na yarda na amince bani da wata ko wani da ya dace da ya ci dukiyata da nake ta tarawa da ya wuce ki. Ki na da hankali,natsuwa da tarbiyya,ki na da kawaici da juriya akan halin da kike ciki,shin ko dai har yanzu ba kya so na ne na mayar dake wajen Gwaggo na haƙura da auren? A ƙalla dai duk wanda ya kalle ni zai tuna cewa na taɓa yin aure a rayuwata ko sau ɗaya ne." Tinda Malam Rabi'u ya fara magana jikin Salma ya yi laushi idanuwanta ke zubar da hawaye. Tsabar azabar da Samira ke gana mata ko sunan ta aka kira sai gabanta ya faɗi ta zaci na Samiran aka kira. Ganin hawaye na zarya a kuncinta ne ya sanya Malam Rabi'u kiranta wajensa. Babu musu ta tashi ta isa gare shi ta zauna a saman cinyarsa kamar yanda ya fara sabar mata. Ba dan yana jin wata sha'awa ba haka kawai yake jin daɗi idan Salma ta zauna a jikinsa,ya na ƙaunarta sosai saboda natsuwarta da kamewarta,bata da hayaniya da kwaramniya irin ta yara. Cike da sigar lallashi ya ce. "Sanar da ni abinda kike so Salamatuna. Ko akwai abinda yake damunki?" Kai ta girgiza masa alamar babu komai,sake tambayarta ya yi a karo na babu adadi,da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce. "Ina so na ga Gwaggona. Tinda na zo gidan nan sau ɗaya ta zo ta kawo min kayana,ni kuma ban samu damar zuwa na ganta ba. Kuma ina son ganin Aabid,Aunty Layuzah ta yi min alƙawarin za ta zo yawon arba'in Kura amma bata zo ba gashi har sun yi wata uku zuwa huɗu." Murmushi Malam Rabi'u ya saki,bai san dalili ba sai zuciyarsa ta ji daɗi da Salma bata ambato matsala a zaman su tare ba,duk damuwarta mai sauƙi ce a wajensa. Kanta ya shafa sannan ya ce. "In dai wannan ne matsalar ki to ki shirya a daren nan zan kai ki wajen Gwaggo ba zan bari ki kwana baku gana ba. Wajen Aabid kuwa ki yi haƙuri ki ƙara ko da wata guda ne sai na kai ki,dan kin san al'adar garin nan amare ba sa yawo idan basu cika shekara ba. To mu dai za mu fara take doka daga yau ko?" Bakinta ta rufe ta na dariya cike da ƙuruciya. Shi ma dariyar ya taya ta,daga ƙarshe ya ƙarasa cin tuwonsa ya na bata a baki har suka cinye. Salma ce ta kwashe kwanukan ta kai waje,ta na fita ta ji kamar an ruga da gudu an bar sashen nata,ta ji tsoro sosai a ranta,amma kuma ta tabbata ko ma wanene ba zai wuce Yah Samira ba,dan ba sau ɗaya ko sau biyu ta kama ta tana yi musu laɓe ba. Hannunta da bakinta ta wanke ta koma ɗakin. Malam Rabi'u kuwa sai da ya zaga bayi sannan ya wanke bakinsa ya kulle ko ina ya miƙa wa Salma sabon hijabi da takalmi ya ce. "To bismillah amaryar Malam Rabi'u mu je ko?" Bakinta ta toshe tana dariya ta yi gaba yana biye da ita. A haka suka isa har gidan Malam Bala. Malam Bala dake ƙoƙarin shiga gida ne ya ga Malam Rabi'u tafe da Salma su na hira a cikin hasken farin watan da ya mamaye ilahirin garin Kura. Sam ransa bai yi masa daɗi ba da ya gan su cikin nishaɗi. Sai ya kawar da kai ya yi kamar be gansu ba zai shige gidan. Cikin sauri Malam Rabi'u ya kira sunansa,washe baki Malam Bala ya yi yana fara'a kamar babu abinda ke damun zuciyarsa. A ɗarare Salma ta durƙusa ta gaishe shi,haɗe fuska ya yi ya ce. "Ince dai Ja'irar yarinyar nan ba wani mugun abun ta gunguma ba ka dawo da ita gida? Ina so ki sani muddin kika kaso auren nan ba dai gida na ba,sai dai ki nemi inda za ki je." Da sauri Malam Rabi'u ya tari numfashin Malam Bala ya ce. "Allah na tuba me wannan halitta mai tsarkin za ta yi min na ɓacin rai? Yarinya kamar ba a cikin shekarun biri take ba. To ka ganta nan da zan ce mata ta haɗiye min ruwa in ji ƙoshi a cikina za ta yi tsabar yanda take yi min biyayya. Gwaggonta na kawo ta ta gani,ka san abun yaro sai ana lallaɓa shi." Ƙwafa Malam Bala ya yi ya saki yaƙe ya ce. "Maza ki tashi ki shiga ciki,kuma kada ki jima,tinda sarai kun sani ai mace bata fita daga gidan miji sai ta shekara,wata ma sai ta haihu idan za ta je wankan gida take zuwa gida ita da abinda ta haifa." Da sauri Salma ta miƙe tsaye ta shige cikin gida cike da murna. Malam Rabi'u kuwa sai ya tuntsire da dariya yace. "Wannan yarinyar kam ai sai dai a yi mata uziri ta yi abinda take so,dan kuwa nan kusa dai ban ga yanda za ta samu juna biyu ba ballantana ta haihu." Kai Malam Bala ya karkace ya ce. "Ban gane nan kusa ba,wai kana nufin har yanzu baka shiga gonar yarinyar nan ba?" A karkace shima Malam Rabi'u ya kalli Malam Bala ya ce. "Habaa Malam! Wannan yarinyar ai ta yi ƙanƙanta da wannan al'amari,kai dai kawai Allah Ya sa mu na da rabon alkhairi a gaba." "Kada ka duba yarintarta fa Rabi'u. Mata nawa aka yi wa aure da shekarunta kuma suka haihu? Ka duba kai iya tsawon shekarun da ka ɗauka a duniya,idan ban ɓata lissafi ba wannan bazarar da za ta zo za ka cika shekara Hamsin da uku a duniya,ka faɗa min wata matar za ka aura nan gaba idan baka tara da wannan ba?" Kyaɓe baki Malam Rabi'u ya yi ya ce. "Ni fa na riga da na yarda da maganar mutane,da dikkan alamu aljana ce ta aure ni,dan bana samun nutsuwa a ko ina sai a cikin bacci na. Na raina wannan yarinyar sosai Malam Bala bata da abinda za ta bani a yanzu dai,ban sani ba ko nan gaba." Cike da takaici Malam Bala ya bar wannan tattaunawar ya ɗakko wa Malam Bala zancen gona. A cikin ransa yana saƙa tsiyar da zai shukawa Malam Rabi'u a nan gaba. A ɓangaren Salma kuwa ta na shiga cikin gidan ta shiga ɗakin Gwaggo ta na murna. Gwaggo ma na ganinta ta saki kaɗin da take yi ta rungume Salma ta na faɗin. "Maraba maraba jikalle na kin fiye min ɗa daɗi." Sai da suka gama murna Kande ta ce. "Ke salma garin ya aka yi kika zo war haka bayan baki cika shekara da aure ba? Ko dai gudowa kika yi bai sani ba? Me yake faruwa a gidan naki na ga kin rame kin yi duhu?" Cikin dariya Salma ta ce. "Gwaggo da shi fa muka zo yana waje yana jiran mu gaisa na je mu koma gida. Kuma ni babu abinda yake faruwa da ni a gidan sai alkhairi. Gwaggo na yi kewar ki sosaiiii." Kai Gwaggo ta jinjina ta na nazari,can sai ta yi ƙasa da muryarta ta ce. "Ko dai kun fara kwana a ɗaki ɗaya da Malam Rabi'u ne Salma?" Da sauri Salma ta kame baki tana zaro ido waje,cike da tsoro ta hau ja da baya,dan bata so Gwaggo ta gane tana sakar masa jiki har ta hau cinyarsa ta zauna. Ganin irin kallon da Gwaggo ke binta da shi ne ya sanya ta fara kuka ta ce. "Ki yi haƙuri Gwaggo zan faɗa miki gaskiya,dama...dama...uhumm shine yake ɗora ni a cinyarsa,ko ya ce na hau,amma Gwaggo ni ban taɓa kwana a ɗakinsa ba,shima kuma bai taɓa kwana a ɗakina ba." Salma ta ƙarasa maganarta cike da yarinta da tsoro. Murmushi Kande ta yi ta ja Salma jikinta,a hankali ta dinga warware mata duk wani tsoro da ta dasa mata a ranta akan maza. Cikin sauƙi take sanar da ita duties ɗin matar aure a wajen mijinta. Lokacin da ta zo kan gaɓar bayani akan kwanciyar aure sai Salma ta hau jin tsoro jikinta ya ɗauki rawa. A haka Gwaggo ta yi mata bayanin komai yanda za ta fahimta. Daga ƙarshe Kande sai ta tashi ta hau haɗa mata kayan cimar da Abdulwahab ke kawowa a kai wa Salma bata samu damar kai mata ba. Hotunan Aabid da aka ɗauka aka wanko Kande ta bata ta ce. "Wannan saƙo ne daga ɗanki. Yana can duk kayansa sun yi masa kaɗan saboda girma." Dariya Salma ta yi kafin ta ce. "Amma Gwaggo me ya sa Yah Audu bai zuwa gani na? Kuma Aunty Layuzah ta yi min alƙawarin zuwa amma har yau bata je ba." "Hidima ce ta yi wa Layuzah yawa saboda Ammabuwa na ɗauke da juna biyu mai wahalar laulayi,ga yaronta bai yi wani ƙwarin a zo a gani ba,shi kuma Yayanki baya son zuwa gidan ne saboda Samira,ina fatan za ki yi masa uziri." Ɗaga kai Salma ta yi ta buɗe baki za ta yi magana,muryar Hasiye ta katse ta ta yi sauri ta juya tana kallon bakin ƙofa. Washe baki Hasiye ta yi ta ce. "Ah ah! Yau amare ne a gidan namu babu ko sallama ballantana mu ji zuwan baƙi? In ji dai ba wani laifin ta yo ba ya koro ta?" "Sai dai ki ga kora a kan taki ƴar amma ba akan jika ta ba." Guɗa mai ƙarfi Hasiye ta rafsa sannan ta ce. "Yo su waye suka yi silar auren har da za a yi wa mutane firirita? In ce dai ni ce na shiga na fita na haɗa auren? Kuma naga da ai cewa kuka yi ba kwa so,yanzu kuma sauya zani ta yi da zaki ce haka Kande?" Banza Kande ta yi da ita ta gama ƙulle wa Salma kayan da ta haɗa mata kaf. Har Salma za ta ɗauka sai ta tuna yanda Samira ke yi mata iko da ƙwacen kayanta. Cikin sauri ta durƙusa ta kunce ɗaurin kayan ta kwashi hotunan Aabid da abinda ta san za ta iya cinye wa kafin su isa gida ta kwasa da gudu ta yi waje. Duk kiran da Gwaggo ke yi mata bata waiwaya ba ballanta ta amsa ta. A nan ta bar Hasiye na san barka da yanda ta ga rama da duhun fatar da Salma ta yi. A ƙofar gida ta tarar da Malam Rabi'u da Malam Bala,kai tsaye wajen Malam Rabi'u ta je ta ci burki ta ce. "Baba taso mu tafi gida." Harar wasa Malam Rabi'u ya sakar mata ya ce. "Ba na ce ki dena ce min Baba ba? Ni mijinki ne,dan haka kada ki sake kira na da Baba,daga yau ki dinga kira na da Mijin Salma,idan ba za ki faɗi haka ba ki dena kira na da kowanne suna bana so." Dariyar ƙuruciya ta yi ta buɗe ledar biscuit ta fara ci a gabansu ta na rausaya kai cike da jin daɗin abinda take ci ɗin. Tsaki Malam Bala ya ja cike da hassada da baƙin cikin bai samu yanda yake so ba,sallama ya yi musu ya shige cikin gida ya samu Hasiye na ta yi wa Kande rashin kunya. Har a wannan lokacin yana son Kande sosai a ransa,kuma ya na ganin girmanta,shi kansa yana rasa dalilin da ya sa yake rufe ido ya karta mata rashin mutunci. Tsawa ya daka wa Hasiye ya ce. "Ke bana son rashin ta ido,Kanden sa'ar ki ce? Na ce sa'arki ce da zaki sa ta a gaba kina yi mata rashin ta ido? Wuce ki tafi ɗakinki." Ko shiga ɗakin Kande bai yi ba ya wuce nashi ɗakin ya hau rage kayan jikinsa yana ƙulla mugunta a cikin ransa. A haka Hasiye ta shiga ɗakin ta na kumbura baki ita a dole fushi take yi da Malam Bala yayi mata tsawa a gaban kishiya. Zama ta yi ta na ɓata rai,sai ta ba wa Malam Bala dariya,nan ya zauna ya bata labarin gidan Malam Rabi'u. Ranta ne ya ɓaci ta ce. "Yo me aka yi kenan Malam? Ai ni so nake ace ya yi mata fata-fata ya yayyaga ta ta yanda sai an ɗinke ta kamar ƙwarya. Gaskiya da sakel,ai ni ban yi wannan gamin dan Salma ta zauna lafiya a gidan miji ba." Shiru suka yi na wani lokaci kowannensu na tunanin irin gadar zaren da zai haɗa wa Salma domin daƙile farincikin da take samu a gidan aurenta. Bayan wata ɗaya Salma ta saki jiki sosai a gidan miji,Malam Rabi'u ya fara dawowa cin abincin rana a gida,wannan dalilin ne ya sa dole Samira ta rage musguna wa Salma gudun kada mijinta da Malam Rabi'u su gani. A hankali Salma ta fara cika  haskenta na dawowa. Watarana har ƴar bireziyar da Samira ta rage mata guda ɗaya take ɗauka ta dinga gwadawa ta na dariya ita kaɗai a ɗaki. Fatanta bai wuce watarana itama ta shiga cikin sawun matan da ke sanya bireziya ba. A ɓangaren girki kuwa ta ƙware sosai,domin Samira sakar mata komai take yi,sai dai ta dinga nuna mata abinda za ta yi,ita ke share sashenta ta share na Samira,wankin banɗaki da wanke-wanke dik aikinta ne. Ɗiban ruwa a rijiya ta cika randuna na daga cikin aikinta. Idan Malam Jamilu ya ga aikin ya yi wa Salma yawa ya yi magana sai Samira ta dafe ciki ta hau karairaya ta na cewa. "Yanzu Malam me tsohon juna me za ta iya yi? Ai idan aikin ya min yawa sai na haihu lokaci bai yi ba." Kan dole yake ƙyale ta ba dan ya so ba,tinda ai lokacin da tsohuwar matarsa na raye da cikin Tanimu babu abinda bata yi. *********************** Yau ma kamar kowacce rana tun safe Salma ta tashi take aikin gida. Wanke-wanke ta fara yi,sannan ta yi shara,daga nan ta wanke banɗaki. Ta na gamawa ta kwashe ɗumamen tuwon da ta aza ta ɗora ruwan kunu. Lokacin da ta gama komai Malam Rabi'u har ya yi wanka yana zaune yana jiran a kai masa kayan karyawarsa. Babu jimawa Salma ta shiga ɗakinsa da babban faranti mai ɗauke da kwanon tuwo,kofin kunu da kwanon sha cike da ruwan randar sanyi. Ajiye wa ta yi ta miƙa masa butar ƙarfensa,daga nan inda yake zaune ya wanke bakinsa ya watsa ruwan waje,sannan ya miƙa hannunsa waje ya wanke ya ajiye butar. Zama ya yi ya fara cin tuwon yana santi Salma na yi masa dariya. Bayan ya kammala ya yi mata sallama tare da bata nera ɗari biyu ko da za ta sayi wani abun. Godiya ta yi masa ta karɓa ta ajiye a inda ta saba ajiye wa. Wani irin sauyi ya ke ji a jikinsa wanda bai taɓa jin irinsa ba a kaf rayuwarsa. A haka ya daure ya fita waje yana jiran Yayansa. Ko da Malam Jamilu ya riski ɗan'uwansa a zaure sai ya ce. "Lafiya kake kuwa yau Rabi'u?" Murmushi ya yi kawai ya gyaɗa kai alamar lafiya yake. Ba tare da sun sake yin magana ba suka hau samam babur ɗaya Malam Rabi'u na tuƙawa suka wuce kasuwa. Tinda suka tafi kasuwa Mairo ta zo gidan suka ƙule da Samira a ɗaki,sun jima sosai a ciki kafin Samira ta fito cikin shirin fita. Ko sallama basu yi wa Salma ba dake ta shaƙar ɓaccin gajiya a zaune. Bayan awa biyu da fitar Samira Malam Rabi'u wanda ya kasa zama a kasuwa ya dawo gida. Hankalinsa a tashe ya nufi ɗakin Salma. A kishingiɗe ya ganta tana baccin gajiya. Bai ɓata lokaci ba ya tura ƙofar ɗakin ya saka sakata sannan ya nufi Salma gadan-gadan........... *Wacece Aabida da Innaji?* *Ta yaya Aabida ke shiga rayuwar Aabid har su zamo ma'aurata?* *Wacece Dijahn Aabid?* *A tsakanin Aabida,Innaji,Hasiye da Samira wacece asalin MUGUWAR MACE?* *Ya ƙarshen waɗannan mutane zai kare?* *A cikin MUGUWAR MACE PART 2 ne kawai za ku samu amsar tambayoyinku.*