[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA* Thriller HUMAIRAH BULAMA Yota 011. *Shimfiɗa* Bismillahirrahmanirrahim… Da gudu mutumin ya fito daga cikin wata ƴar bukka ya nufi shashen wasu daga cikin mutanen wajen kamar kafafunsa za su tsinke.. Yana zuwa ya ja ya tsaya sai kuma ya d’an durk’usa ya kama guiwowinsa da hannayensa duk biyun yana haki. Da sauri d’aya daga cikin su ya d’ago yayinda ragowar duk su ka yi kamar ma ba su lura da shi ba domin kuwa sun riga sun san me ke tafe da shi! Yanayinsa na baiyyana y’ar damuwa mutumin ya ce “lafiya kuwa ka ke D’an Baba?” Cikin haki wanda aka kira da ‘D’an Baba’ ya d’ago yana kallonsa wanda suna had’a idanu da d’anuwan nasu ya fashe da wani kalar kuka, cikin kukan sosai ya ce “ta kasa haihuwa wannan karon ma… Ku taimake ni in kaita asibiti dan Allah…” Shiruuu duk maza guda bakwai d’in su ka yi waenda suka kasance y’an uba a garesa.. Da kyar babban yayansu wanda shi kad’ai ne dama ya kulashi tun zuwan sa wajen ya ce masa “D’an Baba da ace Ina da yadda zan yi to da na taimaka maka… Ka yi hak’uri…” Durk’usawa matashin mutumin wanda ba zai wuce shekaru ashirin da bakwai a duniya ba ya yi, ya kamo k’afafun d’anuwan nasa yana kuka sosai sannan ya ce “kar ka saka in sake rasa haihuwar nan da za a yi mini a karo na takwas! Kar ka saka d’an da za a haifa mini shima ya koma kamar ragowar, ba iya haihuwa za ta yi ba….” Cikin daka masa tsawa wani a cikin y’an uwan nasa ya kalle sa sanann ya ce “mu yi sata kenan mu baka? Ko ya ka ke so mu yi? Bar nan kafin in yi kwallo da kai wallahi.” Ganin yana ta b’ata lokacinsa gashi kowa ya k’i taimaka masa ya sanya ya yanke shawarar komawa wajen matarsa ya ci gaba da tofa mata addu’a ko Allah ya ji k’ansa, dan hatta y’an k’auyen ma duk sun k’i kulashi… Tun lokacin da aka tabbatarwa da kowa shine ya kashe Mahaifinsu shikenan ya zama abun gudu ga kowa a kaff cikin k’auyen nasu….hatta y’an uwan nasa ma da kyar aka hanasu su kashesa shima sannan yayansa babba ne kawai yake kulasa….sai ungozoma wadda Mahaifiyarsa ce ta yi mata hanya ta koyi aikin..su biyu kacal ne suke kulasa a kaff k’auyen nasu. Mai k’auyen ne ma ya hana a jefesa a k’auyen saboda shi har gobe ya ce ‘bai yarda D’an Baba ne ya kashe Babansa ba’. Yana nufar bukkar tasu ya ga ungozomar ta fito hannunta kacha-kacha da jini fuskarta babu annuri cike da damuwa… Suna had’a idanu da ita ya fahimci mai ya faru dan haka ya sake rushewa da kuka. Cikin rashin jin dad’i matar ta sauk’e wata zazzafar ajiyar zuciya sannan ta fara magana kamar haka… “Ina mai bak’in cikin sanar maka da mutuwar d’anka wanda ya yi tun a kwanaki biyar baya da na daina jin motsinsa dama na gaya maka abunda nake zargi kenan..alamun rashes na sepsis da kuma symptoms d’insa waenda su ka baiyyana a jikinta ne ya tabbatar mini da gawar har ta fara rub’ewa a cikin cikinta kenan, dan duk wani symptoms na sepsis d’in sun baiyyana a tattare da ita ga kuma bleeding ta na yi na fitar hankali sannan Yaron kwata-kwata ya daina motsi tuntuni hatta alamun bugun zuciya ma da na auna duk babu tun kwanaki biyar da suka shud’e. Har yanzunnan da nake yi maka magana ban kai ga iya fito da shi ba domin kuwa babu kuzari kwata-kwata a jikinta ballantana ta yi nishi… Yunwa da rashin abu mai kyau a jinin matarka sune suka kashe maka Yaro tun farko, wanda da ace an kaita asibiti tun wanchan satin da ta dinga suma kafin ya rasu an had’a duk su biyun an ba su taimakon gaggawa to da Ina da yak’inin da ikon Ubangiji za su iya fitar mata da shi lafiya wala ta hanyar aiki ko kuma su yi mata allurar nak’uda dukda jikinta babu k’arfin kuzarin da za ta iya yin nishi tsabar yunwa but na san ba za a rasa yadda za a yi ba…dukda kuwa na san Yaron zai zo da cutar yunwa da wasu negative abubuwan ko da ace sun yi nasu taimakon… Ni dae na yi duk k’ok’arin da zan iya yi amma na gagara fito da Yaron kwata-kwata… Na sha bak’ar wahala amma na yi ne domin Allah, kuma na san ko na ce ka kawo kud’in ungozoma cewa za ka yi babu.. Shawarar da zan baka itace ku dakatar da haihuwa tukunna dan Allah.. Babu wani abu mai gina garkuwar jiki a jikin matarka dan haka in har ta sake yunk’urin haihuwa gaskiya inaga da ita da Yaron tun a wata uku za su iya rasa rayukansu… Sannan jini ya k’i tsaya mata kuma na duba akwai alamun mahaifarta ta samu matsala, sannan ga halinda take ciki dan haka ka nemo kud’i a duk inda su ke ka kaita asibiti a cire Yaron nan da nake da tabbacin zuwa yanzu ya fara salub’ewa ma a cikin cikinta, a samu a yi mata gyaran ciki sannan a duba mahaifarta sosai itama in abun na magani ne a yi in na cirewa ne a cire tun itama bata kai ga rub’ewa ta zagwanye mata a cikin ciki ba….” Ta na kammala fad’in hakan ta sa kai ta wuce a ranta ta na cewa ‘ae ko alhakin kisan ubanka da ka yi ba zai barka ba wallahi…’ Ta na wucewa ya zube a wajen ya yi zaman dirshen dab’ass!! Kafin ya saki kuka mai tsananin sauti..kamar wani d’an k’aramin Yaro. Mahaifiyarsa da Mahaifinsa ba su da kowa, cikin uk’ubar maraici suka taso. Shima zuwa yanzu kam ya tabbatar ba shi da kowa domin kuwa waennan y’an uwa da Mahaifiyar da ta haife su ba zai kira su da nashi ba. Matarsa itama da kyar ya sameta ya aura wadda ta kasance bata da kowa wannan dalili ya sanya suka ci burin tara y’ay’a da family a rayuwarsu sannan bayaga haka daga ita d’in har shi Ubangiji ya d’aura musu wani irin mad’aukakin masifaffen son y’ay’a! Dukda kuwa jarumin talauchin da suke fama da shi hakan bai sanya ko da sau d’aya sun jii shakkar tara iyali masu tarin yawa ba… In ana maganar talakan tukuff shi kansa ya san ya ciri tuta, a yanzu haka kwata-kwata a rayuwarsa kayan sakawar shi kala uku ne tsabar babu Matarsa kuwa tun lokacin da ta auresa ya yi mata set biyu har gobe sune sai kunce da ta samu na hijabai domin kuwa kayan nata duk sun yi taushi sun yage shiyasa matar mai k’auyen take tausaya mata yayinda ragowar matan garin kuwa ko kallon ta ita da mijinta ba sa yi ballantana su tausaya musu.. Abinci kuwa wani zubin sai su yi kwana uku ba su ci ba! Har abinci a bola ya sha d’aukowa ya kawo mata su gyara su ci…. Wani kalar tausayinta ne ya sake mamayesa domin kuwa shi a karon kansa ya san tabbas ya gana mata azaba da talaucinsa, mai karya zuciya. A hankali yana tangad’i sannan yana kuka sosai ya mik’e ya shiga cikin bukkar tasu domin ya samu su rarrashi juna sannan ya ganta kafin ya fita ya nemi kud’i a duk inda su ke kamar yadda ungozoma ta ce. Yana shiga ya ganta kwance cikin jini ta na hawaye dan haka ya k’arasa gareta da sauri ya d’agota ya rungumeta jikinsu duk su biyun yana wani kalar karkarwa… Sama-sama ya fara jin sauti da murya kamar yadda ya saba jin ta ta na yi masa kuwwa a ka da kunne a duk sanda ta so tun kwanaki hud’u baya da suka shud’e…. Kazalika itama matarsa wadda take rungume a jikinsa suna kuka yashe cikin jini…kusan a tare suka fara jin komai su biyu kacal…. “Ku amince da mu, za mu dawo muku da Yaronku za mu baku arzik’i, za mu baku haihuwa bila adadin, amma kuma za ku bamu jininku guda d’aya tak! Ya yi mana bauta… Wallahi in har ku ka amince da mu to tabbas duniya kanta sai ta yi alfahari da ku da ahalinku….” Sai kuma firgigit su ka bar cikin duniyar muryoyin da aka tsunduma su cikinta suka yi snapping out a tare… Da sauri suka kalli juna kusan a tare sai kuma kowannensu ya sunkuyar da kansa k’asa still suna rungume da juna har yanzun jikinsa ya na wani kalar karkarwa ya na haki sosai yayinda itanma ya lura gaba d’aya a tsorace take… Tunda ya ke bai tab’a b’oye mata komaiba amma tabbas zai b’oye mata wannan abun kunyar, ba zai tab’a yin maganar ba ballantana ma ya saka abun a mizanin hankali domin kuwa kansa a gabas ba zai tab’a gwada shirka ba… Itama abunda ta ke tunani kenan, Allah shi kad’ai ne mai rayawa da kuma kashewa duk wani abunda za a nuna maka makamancinsa wallahi k’arya ne sai dai a yi maka rufa ido daga baya ka zo ka na da na sani… Duk su biyun a tunaninsu d’an uwansa bai ji abunda shi ya gama ji yanzun ba. A hankali cikin son kawar da tunanin da banzatar da shi ya yi istighfari da ta’a’uzi sannan ya saka hannu ya sake k’ank’ameta zuwa cikin jikinsa. Gaba d’aya su biyun jikinsu karkarwa yake yi, kafin cikin wata kalar razananniyar k’ara ta saki ihu sai kuma ta fara nishi…. Mintuna biyu ne kacal suka sanya shi da ita suka fahimci tabbas nak’uda ce ta ke yinta ganga-ganga… Cike da curiosity ya shiga dubata domin har ta fad’i a wajen ta na nishi tun k’arfinta. Ga mamakinsa sai ga kan Yaro nan ya taho gadan-gadan a take da shi da ita duk suka kid’ime suka shiga rud’ani.. Cikin duniyar muryoyin da aka saba tsundumasu suka tsinci kawunansu yanzun ma “Ku bamu had’in kai ku haifi Yaronku lafiya! Ku k’i bamu had’in kai kuma shima ku rasashi kamar yadda ku ka rasa ragowar y’a’y’anku. Ya riga ya zama namu dan haka ku bamu had’in kai…” (Astaghfirullah) Ruwan sama aka kece da shi a take wani nishin ya sake zuwar mata wanda ta na yi kan jaririn ya sake baiyyana.. Kallo d’aya zaka yi masa ka san yana cikin k’oshin lafiya sab’anin yadda ungozoma ta ce har ya fara zagwanyewa saboda ya dad’e da mutuwa…. A take daga ita har shi suka ji wani kalar masifaffen k’aunar Yaron ta dirar musu. Wata mahaukaciyar dariya suka ji an fashe da ita kafin ace “Mintuna biyu ne kacal suka rage muku! Ku bada had’in kai ko kuma ku rasashi…” Yadda aka k’arashe maganar a tsawace ya sanya ta kid’ime! A take ta ji k’arfinta gaba d’aya komai ya tsaya chak jikinta ya d’auki rawa…. A yadda kan Yaron yake a matse da yadda ta ji k’arfi da nishinta sun gushe ita kanta ta san in ba da kyar ba shima ba zai shak’i iskar duniya ba, dan ji ta yi ma kamar ta na shirin sumewa… Ko kad’an ba su biyewa muryoyin da zuwa yanzu su ke yi musu kuwwar “ku bamu had’in kai” kamar za su tsaga cikin bukkar suna juyi a saman kawunansu ba! K’arshema mik’ewa ya yi da niyyar fita domin ya je ya nemo ungozoma wata k’ila ita ta san dabarar da za ta yi a fito da jaririn dan shi a nashi ganin in ya ce zai janyo kan to zai iya raba kan da gangar jikin Yaron ne… Amma sai dai yana mik’ewa kansa ya juye sam ya rasa hanyar fita, in ya yi gaba kuma sai dai ya ji ya k’ume, k’uumm!. Cikin kuka ya ke iya jiyo muryarta a chan nesa da shi ta na cewa “Shima wannan mun rasa shi! Ba zan iya ba, ba na ganin komai na kasa nishi na san mutuwa za mu yi, ka yafe min..” Chan k’asa sosai dan tsawar da ake daka musu ana cewa “ku bamu had’in kai” Har kawo yanzun ta cika musu dodon kunne, kamar za ta fasa ne. Da k’arfi ya saka dukkan hannayensa ya toshe kunnuwansa ya na kuka sosai wae ko zai samu ya daina jin muryar da ta rikitashi take shirin sanyashi tafka babban kuskure. A zuciye ya juyo dan bai daina jin komai ba ko bayan ya toshe kunnuwan nasa kuma zuwa yanzu ya fahimci a bayansa ne yake jin muryar sab’anin d’azu da ya rasa daga Ina take fitowa.. Ko da ya juyo bai ga kowa ba kamar yadda ya tsammata dan a kan matarsa idanunsa suka sauk’a ita kad’ai wadda take tsakiyar haihuwa dan kai da idanuwa sun fito da karan hanci amma abunda ya kama daga kan b’ulolin hancin da ragowar jikin Yaron duk suna cikin jikinta ne. Kallonta ya ke yi ya na mai jin tsananin k’aunarsu ta na ratsashi… Yayinda itanma ta ke kallonsa daga nan inda ta ke kwance ta na hawaye ta na kokwanton rabuwa da shi da Yaron da tun kafin ta gansa soyayyarsa ta shiga cikin ranta matuk’a. **************** Zai fara zuwa muku very soon, in sha Allah. BAK’AR TUKUNYA Kar ku bari a yi tafiyar babu ku🙏 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *01* Bismillahirrahmanirrahim… Legislative quaters.. Farawa, Kano, Nigeria. La’asar sakaliya, mai sanyaya zafin da rana ta wanzar domin a lokacin ne ta ke d’auko hanyar fad’uwa sanyi da almuru su maye gurbinta.. Sama-sama flawowin da su ka yiwa garden d’in k’awanya su ke kad’awa daga ganyayyakinsu har reshensu su na bin duk inda iskar da ke wanzuwa a ta sanadiyyar Hadarin da ya ke had’uwa ta kad’a wanda yanayin wajen da iskar har ma da k’amshin da wajen ke fitarwa su ka zamto Abun k’ayatarwa da sanya nishad’i kwarai da gaske… Tsaye ya ke ya k’urawa waje guda idanu kamar mai shirin haddace zane da duk wani tsari na wajen a cikin kwakwalwarsa..sai dai kuma a bad’ini sam hankalinsa ba a wajen ma ya ke ba. A hankali ya ke zuk’ar numfashi ya na sauk’ewa cikin tsantsar kasala da rashin kuzari domin kuwa duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumi a fagen komai a yau d’in ya zamto rago… A zahiri in ka kallesa ba za ka fahimci hakan ba amma a Bad’ini ilahirin jikinsa a mugun mace ya ke sannan numfashinma kokawa ya ke yi da shi wajen gudanar da shi, sannan ga wani Abu mai tsananin tauri da tsantsar nauyi wanda ya tokare masa mak’ogwaro da kuma zuciyarsa baki d’aya…. Bai juya ba sannan bai ji ko da alamun motsin mutum ba amma ta na isowa wajen zuciyarsa ta sanar masa da hakan…. Ko a lokacin da yake Yaro k’arami sam kuka ba d’abi’arsa bace ba amma a yau a yanzun a take a wajen ya ji hawaye su na shirin cin galaba a kan jarumtarsa su na shirin tarwatsa dukkan wani kuzari nasa su na shirin tarwatsa jajircewarsa su bijiro ma sa da kasala da rauni da kuma gazawa… Cikin sanyin muryarta wadda ta kasance d’aya daga cikin Abubuwa mafi tasiri wajen yin galaba a kan dukkan wani fushi nasa ya ji ta ce “Assalama alaikom” A hankali kamar ba ya so ya lumshe kyawawan idanuwansa a lokaci guda kuma tsantsar zazzafar k’aunarta ta shiga k’ok’arin korar duk wani fushi da alwashi da ya d’aukarwa kansa… Ganin ya na shirin karaya ne ya sanya ya juyo gareta yana mai saka kwayar idanunsa a cikin tata… Wani kalar yanayi na musamman su duk biyun su ka tsinci kawunansu a ciki yayinda kowa ya ke nashi nazarin a cikin k’asan zuciyarsa… “Da gaske kwata-kwata bai sanni ba? Da gaske bai gane ni ba? In har idanu da kwakwalwarsa sun manta da ni shin ta yaya zan yarda da cewar zuciyarsa za ta iya mantawa da ni?” Ta yiwa kanta tambayar a lokacin da hawaye su ke k’arasa taruwar mata tap a cikin kyawawa kuma sihirtattun idanunta…. Duk dauriya da juriya da kuma jarumtarsa kasawa ya yi, sam sai ya gagara ci gaba da kallonta a halin da ta ke ciki dukda kuwa yadda zuciyarsa ta ke azalzalarsa ta ke kuma sake tabbatar masa da abubuwan da ta aikata masa masu matuk’ar muni…. Cikin hikima ya yi amfani da wani yanayi wanda ya fi kama da jan aji da yanga wajen kawar da dukkan dubansa daga gareta sannan ya ce “Ina sak’on? Zan wuce yanzun….” Ya yi maganar ya na mai kallon rolex watch d’in da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa… Cikin tsananin sanyin murya ta ce “Ya…..” Da sauri ya katseta cikin cewa “ba ni sak’on mana AMAL, Ina so in wuce da wuri..na bar matata ita kad’ai a garin da ba namu ba….” Duk dauriyarta kasa ci gaba da rik’e kukanta ta yi, wani k’ululun bak’in ciki da tashin hankali dunk’ule da takaici ne su ka ziyarceta a take, ba ta san lokacin da ta fashe da wani kalar siririn kuka ba mai tab’a zuciyar duk wani mai sauraronta….. Ji ya yi kamar numfahsinsa zai tsinke yayinda hankalinsa ya k’arasa tashi sannan damuwarsa ta hauhawa b’acin ransa kuma ya nunku… Da kyar da mugun kyar ya iya danne kansa ya saita kansa cikin son sake dilmiyar da ita ya ce “you are still a baby, aren’t you?” Bai jira ta bashi amsa ba ya yi wani d’an guntun murmushi wanda ya fi kuka ciwo sannan ya ce “zan ce ki na gaisheta kuma ae za ku dinga waya…..” Kasa ci gaba da magana ya yi jin ya kai aya a shafin duk wata jarumta da dauriya da zai iya yi a yau d’in, hakan ya sanya kawai ya saka hannu ya zame leda bag d’in da ke rik’e a hannunta wadda ya ke da tabbacin shine sak’on kawai ya wuceta ba tare da ya iya sake cewa komai ba…. Tabbas Amal ta yi destroying zuciyarsa sannan ta lalata masa abubuwa da yawa, sai waenda Allah ya tseratar amma kuma barinta d’in da zai yi a hakan it’s for her own good saboda ita ya yi wannan sacrifice d’in ba wai saboda kansa ba… Ko hauka yake yi ba zai tab’a bari ciwon maitar da yake zargin yana tare da shi ya shafi Amal d’in ba ballantana ya tarwatsa ta….. Har ya wuce ya fice da ga cikin gidan..ta na jin har lokacin da aka mayar da gate aka zuge amma ko motsi ta gagara yi in banda hawaye ba abunda ya ke shatata a kan kyakkywar cute face d’inta. Ta jima a wajen ta na kuka sosai zuciyarta ta na wani kalar k’una da suka…ji ta ke kamar ta dauwwama a wajen kawai dan inda ta nufa shine waje mafi k’untata a gareta! Ko zancen sunan gidansu sam ba ta so ta ji an yi a rayuwarta domin kuwa memories na d’aci da k’uncin da ta shak’a a gidan nan ba na wasa bane, tsaf suke sake tarwatsa mata duk wata ragowar nutsuwa tata… A wajen ta yi sallah, tukunna ta nufi gate zuciyarta kamar za ta burtso waje. Dama ita mai gadin ya ke jira dan haka ta na ficewa ya mayar da k’ofar ya rufe ta shima ya wuce dan wani ne daban zai zo ya zauna a gidan su kam shi da ragowar masu yiwa gidan hidima sai in mai gidan na su ya dawo tukunnna suma za su dawo. Ba ta damu ta hau abun hawa ba saboda a ganinta azabar tafiya za ta iya rage mata zafin da zuciyarta ta ke ciki sannan ta gwammaci tafiyar akan ta yi saurin k’arasawa gidansu, shiyasanya ta zab’i ta tafi a k’afa… Tafe ta ke iskar la’asar d’in da ta taso a sakamokon Hadarin da ya yi gangami ta na kad’ata amma gaba d’aya zafi da k’uncin da zuciyarta su ke a ciki sun k’i su barta ta shak’i sanyi ko da guda d’aya ne… Wani irin zafi k’ofofin hanci da kuma fatarta su ke zuk’ar mata zuwa cikin jikinta….memories d’inta ita da shi ne kawai su ke dawo mata Tabbas a yau d’innan ta yarda ta kuma sake tabbatar da masifaffiyar k’aunar da ta ke yiwa mutumin da ta tsana fiye da kowa a rayuwarta a da, womanizer, mutumin da ya tarwatsa rayuwar y’ar uwarta, mashayi kuma matsafi, mutumin da bata tab’a tunanin za ta so shi ba, mutumin da a baya ta ke tunanin za ta iya halaka shi muddin babu zunubi sabida tsananin tsoro da tsanar da ta ke yi masa… Akwai d’an tazara tsakanin gidan nasu da inda ta baro dan haka sai gab da Magriba tukunna ta k’arasa unguwar tasu (mariri). Tun a k’ofar gida ta tarar da dandazon mutane dan haka ta sadda kanta k’asa kawai ta shige ciki ta na mamaki… Nan cikin gidan ma mata ne sosai mak’il wannan dalili ya sanya tsoro ya fara game ta. K’ofar d’akin Annen ta su ya fi jama’a dan haka a take k’afafuwanta su ka d’auki karkarwa, saboda zullumin jin mai ya faru… Furucinsa na k’arshe ya shiga dawo mata…. A take kwakwalwarta ta dilmiyar da ita chan wata duniya mafi ban tsoro…… Kamar a mafarki ta ji an dafa ta dan haka ta shak’i wani numfashi mai sauti a take hankalinta ya dawo cikin gidan. Ta na juyawa su ka yi ido biyu da Adda dan haka ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a lokaci guda kuma ta na tambayarta “mai ya faru?” Cikin tsantsar damuwa Adda ta ce “kina fita Aliya ta sauk’a (ta haihu) Sai dai ita ta yi doguwar suma d’an nata shi kuma ya koma dan har an tabbatar mana duk sun rasu ne ma da farko sakamokon yadda ta yi saboda hatta Likitocin suma duk sun d’auka ta Mutu ne, sai da aka zo gida ana fara yi mata wanka ta farfad’o yanzu haka ana ciki ana sake dubata da kuma rarrashinta dan kwata-kwata ta k’i ta yarda ta bada d’an a yi masa sutura….” A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce “Allah ya ji k’ansa…” Daga haka ta fara k’ok’arin juyawa da niyyar nufar d’akin Adda dan so ta ke yi ta bar wajen… Da sauri Adda ta ruk’o hannunta sannan ta ce “Amal, sam hakan ba halinki bane ba, yayarki ce fa, kar ki yi haka dan Allah ki shiga ki taya ta alhini ki bata hope da kulawa…” Juyowar da Amal d’in ta yi ta na mai kafe ta da idanuwanta ne ya sanya ta yin shiru… Kafin chan kuma a hankali Addan ta ce “ko ba za ta kula ki ba ki je ki yi mata gaisuwa Amal….ko meye a tsakaninku ki manta da shi for now kin ji y’ar albarka… Anne itama tun lokacin da gawar Aliya ta shak’i numfashi ta bud’e ido ta sume har yanzu ba ta farfad’o ba, ki shiga ki ganta ko?“ Kamar ba za ta ce komai ba yanzun ma sai kuma ta shak’i numfashi ta fesar kamar d’azu kafin ta ce “Allah ya sa mai ceto ne…” Daga haka ta fara k’ok’arin barin wajen kawai su ka ga Anne ta fito daga cikin d’akinta a haukace..tun lokacin da gawar Aliya ta yi motsi ta sume sai yanzun ne ta dawo dai-dai. A hankali matan da su ke cikin gidan suka hau watsewa dan su kam abun kunya ne a wajensu a ce sun zo gaisuwa fad’a ya kaure a gidan dan haka gara su tafi dan kakaf d’insù sun san babu mai iya controlling Anne sun riga sun sani… Dan haka suka fara ficewa one by one…bai fi mutum uku bane su ka yi saura. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *02* Ko bi ta kan su Adda Anne ba ta yi ba ta nufi k’ofar d’akin Sajida a zuciye. Adda ta san me ta ke shirin yi dan haka ta yi saurin bin ta a baya ta na kiran sunanta da niyyar tsaida ita tun kafin ta janyo musu bala’in da za a b’atar da su gaba d’ayansu. A rufe su ka tarar da k’ofar d’akin nata dan haka Anne ta juya ta nufi k’ofar band’akinsu ta rarumo manjagarar da idanunta suka sauk’a a kai ta nufo su ba tare da ta saurari Adda wadda ta ke cewa “A’a fa! A’a!! Haba Anne kamar ba rasuwa aka yi mana ba!?” Dai-dai nan Sajida ta bud’e k’ofar Allah ya taimaketa Anne ba ta kai ga sauk’e manjagaran nata ba. Da sauri Sajidar ta d’an jaa baya dama hayaniyar ce ta farkar da ita daga b’arawon barcin da ya kwasheta yanzunnan, har ta kaita ga fitowa. Cikin tsantsar mamaki ta ce “Subahanallah, Anne lafiya ki ke kuwa? Mai ya faru?” Ta yi tambayar ta na mamakin dalilin da zai kawota k’ofar d’akinta a hakan. Cike da tsana da bak’in cikin da yau ya gagara b’oyuwa ta ce “kar in sake ji kin ce mini Anne, kira ni da Nuratu kawai tunda ni ba uwarki ba ce ba…” Sosai Sajida ta ji haushin abun amma sai ta shanye fuskarta na nuna alamun rashin jin dad’i ta ce “Anne yau kuma? Har mai ya yi zafi haka? Mai ya faru ne kwana biyu wani abun na yi wanda ban sani ba? Inda kara kam ae kema uwata ce ko?….” Ta yi tambayar cikin kissa da rainin wayo dan sarai zuwa yanzu ta san mai ya kawo Annen, dama kuma wannan ranar ta ke jira, yayinda a chan k’asan zuciyarta kuma ta ke yi wa Annen dariyar mugunta na ganin ta ci galaba a kanta yau gashi ta karya lagonta ta fito da fuskarta ta asali.. “Tabbas kin yi komai ma Sajida” Anne ta furta ranta na k’arasa b’aci tsanar Sajidar ta na dad’a samun matsugunni a cikin zuciyarta, sannan ta d’aura da cewa “kuma wallahi kin ji dae na rantse miki ko za ki mutu sai kin bar gidan d’ana a yau ba gobe ba tunda na lura ba ki da wani amfani a cikin rayuwarmu, mun gama zama da Muguwa marar imani, d’an dae ya rasu ya bar miki duniyar dan haka kamar yadda ya bar duniya kema sai kin bar rayuwarmu bari na har gaban abada…” Dai-dai nan Amal ta girgiza kai kawai ta juya ta shige cikin d’akin Adda yayinda Sajida ta saki wani murmushin takaici sannan ta ce “Da farko dai Anne kin san cewa ba ni na yiwa Aliya ciki ba ballantana in d’auki nauyin cikin da haihuwarsa ko?.” Kafin ta d’aura da cewa “Tabbas Anne kin tabbata butulu! Saboda a ganina na yi mata bakin k’ok’arina….sannan kuma yau na sake gasgata zargina a kanki! Wato auroni ku ka yi in zame muku atm machine kenan ko? To wallahi k’aryanki! Dan ba alfarma ku ke yi mini ta hanyar aurena da d’anki ya yi ba ballantana in yi tunanin zan siye ku da kud’i, ki godewa Ubangiji ma da na yarda na zo nan d’in na zauna a D’aki d’aya tak da d’an naki! D’akin da ko store d’in b’angarena bai kai ba a cikin gidan ubana…” Cikin fushi Anne ta ce “to ae kuwa a yau sai kin tattara kin bar gidan d’ana kin koma gidan uban na ki……a yau sai kin bar masa gidansa wallahi…” “Abeg shut up!” Sajida ta daka mata tsawa sannan ta d’aura da cewa “kin bi kin ishi mutane da wani gidan d’anki!! Gidan d’ankki!!! D’aki dae! Ina gidan ya ke? Ki ce mini in bar d’akin d’anki kurkukun da soyayya ta rufe mini ido na shigo shi ban shirya ba…a haka za ki k’are wallahi cikin bak’in ciki, da na sani da kuma tarin failures tunda ke dai you can’t build a paradise for yourself sai aukin yunk’urin sace pleasure d’in wasu ki ka iya… Allah ya yi miki ni’ima ya baki roof over your head amma saboda rashin gode masa sam ba kya gani sai aukin hangen na gaba da ke…kuma ke ba ki iya nema ba ba ki da zuciya da wayon nema amma kin nace sai kin yi rayuwar d’agawa wanda hakan ya sanya ba za ki tab’a samun jin dad’i a rayuwarki ba tunda ba kya ganin ni’imar da Allah ya yi miki… Inda ace ma kinada zuciya mai kyau ne to da watak’ila Allah ya dubeki da idon rahama ya bud’a miki yadda ki ke so Amma mutane kalar ku a cikin al’umma kad’an d’inku ne su ke yin walwala dan yadda zuciyoyinku su ke da muni haka mafiya akasariinku rayuwarku itama take kasancewa mai muni da k’unci… There is nothing good about you Anne! Komai naki marar kyau ne. Ba ki da Hali ko guda d’aya tak mai kyau in akwai shi kuma dan Allah wani ya fad’a mini a cikinku Ina sauraro…” Ta yi maganar ta na kallon Adda da matan da su ke tsaye a wajen waenda su ka yi shiruu su ka tsaya jin gulma, dan zuwa yanzu d’ayar ma ta tafi saura mutum biyu, d’aki kuma daga Yadukko sai wata mata. Yayinda itama Annen kawai ta yi shiru ta na kallonta ta na mamakinta wato dae ita da Sajida ta na mata kallon biri ne ita kuma ta na yi mata kallon ayaba….a tunaninta in ta kashe mata auren Amir za ta ji zafin abun amma a yadda ta fahimta yanzu kam ta san ba za ta ji komai ba, dan haka a take zuciyarta ta k’untata saboda ta so ta guma mata ne yau d’in kamar yadda itama ta saka ta a k’unci. Amma ba komai za ta san yadda za ta rama ne,but first a yadda ta zaman nan ta sake tabbatar da Yarinyar ba za ta moru ba dan haka dole ta k’ara mata mai…. Jin duk an yi shiru ya sanya Sajida ta d’aura da cewa “Ko shaid’an na tabbata in ya ganki guduwa yake yi saboda ya san za ki gudanar da duk wani aikin da zai yi. Y’ay’anki da Mijinki da y’ar uwan Mijinki hatta da y’an Unguwa duk kuka su ke yi da ke! Ko zaman minti goma zuwa ashirin mutum in ya yi da ke to tabbas sai kin cucesa…ki gaya mini dan Allah ta yaya za ki ga dai-dai?” Marin da ta deb’o za ta zube mata ne ya sanya ta ta yi shiru ta na bin ta da irin kallon tab’a ni ki ga ikon Allah d’innan….. Da sauri Adda wadda ta rik’e mata hannun ta ce “Anne mu je D’aki…. Mutuwar d’an Aliya has nothing to do with Sajida k’addara ce kar ki ga laifinta…” Cikin fushi Sajida ta ce “ae da kin barta ta tab’ani yau da ta san ita ba kowan kowa bace ba wallahi! A yau da sai ta tabbatar da cewa ita d’in k’ask’antacciya ce ba ta da gatan uwar komai, wahalalliya asararriya kawai butulu….” Cikin d’an b’acin rai Adda ta juyo ta kalleta sannan ta ce “Haba mana Sajida, ya kamar kina jira dama? Rasuwa fa aka yi sannan ga marar lafiya chan a kwance amma ko a jikinki? Meye haka ki ke yi kamar ba a gidan surukan ki ba?” “Rabu da la’ananniya, shegiya! Bari ki ga yanzunnan Ina sheme ta sai in ga ta bakin tsiwar…” Yadikko wadda fitowarta kenan daga inda Aliya ke kwance ta fad’a tana mai d’aga sandarta da k’ok’arin ganin ta saita inda ta ke jiyo muryar Sajidar tun d’azu anata hayagaga da ita domin ita Yadikkon ba ta gani…makaho da basira kuwa tsaf ta saitota tana shirin sauk’e mata sandar Sajida ta ingijeta ita da sandar tata su ka tafi yuuu sandar ta yi gefe itama ta fad’i a gefe warwas dama a buge ta ke ta yi mak’il, ga jiri ta na yi shiyasa tunda ta fad’i ba ta motsa ba, a wajen ta yi kamar matacciya … Dai-dai da shigowar Baba da Ya Amir waenda hayaniyar su Annen ta fita har wajen da ake zaman makoki dan haka aka ce ‘su shigo su duba mai ya ke faruwa a gidan…’ Kan Yadikko Baba Ya nufa ya shiga duddubata sai da ya ga ta na numfashi da d’an alamun motsi tukunna hankalinsa ya kwanta yayinda Ya Amir ya tsaya yana kallon Sajida tana huci wadda ko ba a fad’a masa ba ya san ita ce ta aikata wannan b’arna da aika-aikar, gaba d’aya kwana biyun nan ta zama azzaluma ta zamto marar kunya wata aba daban da bai sani ba…wanda da farko iyaka shi kad’ai ta fara yi mawa a D’aki yanzu kuwa gashi ya ga abun nata ya fara fitowa fili…gaba d’ayanta ta chanja kamar ba Sajidarsa ba… Ita kuwa Sajida zuwa yanzu ta fahimci Annen ne sarai, da yadda aka yi ta auri Amir d’in ba a haiyyacinta ba ma, shiyasa ta ke kallonsu rass..kuma ba ta shayin yi musu koma meye tunda ta fahimci suma ba su san Allah ba. Dukda haushin Ya Amir d’in ta ke ji shima sai ta d’an ji tausayinsa, dan yadda ta ga ya kafeta da idanuwa yanayinsa ya nuna he is very broken kamar mai shirin fashewa da kuka..ba k’aramin kalar tausayin ya zama ba. Wata zuciyar ce ta ce mata ‘har da shi dae aka yi miki asiri ki ka shigo cikin wannan bak’in Talaucin saboda son kai irin nasu…’ Dan haka a take ta ji tsanarsa ta maye gurbin komai, cikin tsantsar rashin mutunci ta ce “uwarka ta ce ka sake ni…” A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa kamar wani k’aramin Yaro sai ga hawaye…. Da sauri Adda ta ce “ya isa haka. Baba dan Allah ku taimaka min mu kama Yadikko mu kaita asibiti ko d’akinta a samu ta farfad’o, Amir wuce ka je d’akinka ke kuma Sajida ki bar komai for now….” Cikin tarar numfashinta Anne ta ce “to sannu uwarsa! Wadda ta yi mini nak’udarsa da laulayinsa…” Kamar Adda za ta rushe da kuka ta ce “Shin ba kya ganin halin da shi gudan jinin naki ya ke a ciki ne? Ki sarara mana haba Anne, ki bari za a yi maganar wata rana…” Dai-dai Baba wanda ya duk’a zai d’auki Yadikko ya cewa Ya Amir “zo mu je kama mini ita…” Da sauri kuwa ya nufi Baban dama neman abunda zai rabasa da wajen ya ke, sai dai kuma bai kai ga barin wajen ba ya ji an ruk’o hannunsa, kasancewar jikinsa a mugun sanyaye ya ke gashi har karkarwa jikin nasa ya ke yi ya sanya Annen ta yi nasarar fincikosa ta dawo da shi baya. Cikin b’acin rai ta ce “Sannu solob’iyo! To wallahi ba ka isa ba dan ni jarumi na haifa…maza sake ta a yanzu a ta ke! Dan ba ta da wani amfani a cikin gidan nan! Ka saketa Allah zai kawo maka wata… Ba ta isa ta rafka rashin kunya kuma ta ci gaba da zama da aurenka rangad’ad’au a ka ba wallahi, k’aryanta….” ta yi maganar ta na kallon Sajida ta na huci, wadda itama Sajidar ita ta ke bi da wani matsiyacin kallo Ita Anne lokacin da ta ke nacin auren a tunaninta ma za a bawa Sajidar gida ne ta yadda za ta tare ita da y’ay’anta sai gashi ashe uban Yarinyar ya fi su wayo… ‘Gara ta tafi kawai duk wata kissa da asiri an yi amma ta ki moruwa…’ Annen ta aiyyana hakan a cikin ranta, Allah Allah kawai ta ke yi a sallami Sajidar ta san na yi da Ya Amir dan shekaru tafiya su ke yi ba ta da lokaci… Cikin sanyin murya Baba wanda ya gaji da b’acin ran Anne kwarai ya kalleta sannan ya ce “amma dae kin san ba ki da hurumin sakawa a yi sakin nan ko? Infact auren ma kansa ba ki da hurumin shiga amma ki ka shiga ki ka yi kane-kane ki ka tilasata komai sannan yanzu kuma ki zo da wannan zancen? To bari ki ji ba ki isa ba…!” Ya k’arashe da d’an zafi… Tab’e Baki ta yi sannan ta ce “Ina son in ji kana cewa ban Isa ba d’innan saboda ni kuma a lokacin ne nake nuna maka tabbas na isa!” Cikin juya akalar maganar tata ga Ya Amir ta ce “auren dole na yi maka?” Kamar ruwa ya cinyesa a wajen haka ya yi, dan a sanda aka yi auren ba ya son Sajida amma yanzu kam sonta ya ke yi kamar hauka… “Ina fa! Ae ke da shi kun san me ku ka yi har na yarda na auresa…” Sajida ta fad’a cikin karb’e zancen sannan ta kalli Ya Amir yau kam ko arzik’in yayan bai samu ba ta ce masa “Amir ba ni takardata nima na gaji….” Ta yi maganar cikin mik’o masa hannu… A hankali murya ta na karkarwa ya ce “Sajida ki jira za mu yi magana a ciki, ko?” Ya k’arashe maganar a hankali… Yana mai satar kallon Anne wadda tunda Sajida ta yi mata shagub’e yanzun ta kid’ima sannan ranta ya k’arasa b’aci… Sam! Har yau har gobe Ya Amir d’in shi kam ya kasa gane mentality d’in Anne na son kud’i, talauchi fa ba abun kyama bane ba..da wani mai kud’in ma gara talaka fa, ya fi shi kwanciyar hankali… Har ga Allah he love his life a yadda ta ke, amma k’iri-k’iri Anne ta rabasa da matar da ya ke so ta manna masa Sajida k’arfi da yaji saboda lame dalilinta na kwad’ayi da buri wanda shi kam ya gagara sakashi a mizanin dalilai masu ma’ana… Ya na wannan lissafin ya ji Sajidar ta haiyyayyak’o za ta yi magana Anne ta rigata ta hanyar cewa “wai dan uwar ubanka ba za ka sake ta ba? Y’ar gwal ce? Sake ta a take a yanzu ko in tsine maka albarka wallahi…ka ji dae na rantse…” Shiruu Baba ya yi ya runtse idanuwansa kafin kawai su wuce ciki shi da Adda d’auke da Yadikko… Suna jiyo ta tanata ife-ife ta na zagin karankatakaf danginsu ta na ik’irarin tsinuwa a Ya Amir d’in itama Sajida ba ta yi shiru ba sun saka shi a tsakiya…. Adda ta so fita amma Baba ya hanata saboda a halin yanzu ana tab’a Anne za ta huce haushinta a kansu ko ta fad’i abunda hankalima ba zai iya d’auka ba, shiyasa ya hanata fita yana mai jin zafin abunda ake yiwa d’an nasa fiye da shi Ya Amir d’in.. Tun lokacin da aka kinkimi Yadikko ta farfad’o, saboda dama ba suma ta yi ba mayen abubuwan da ta narkawa kanta ne basu gama sakinta ba shiyasanya ta yi likimo ta gagara motsawa Dan haka suna kwantar da ita ta samu ta bud’e idanunta bakinta d’auke da salati… Da yake d’akin akwai d’an duhu ya sanya ba su lura da Kaka Nura a farkon shigowarsu ba sai da suka zo kwantar da ita a kan gado tukunna suka lura da shi wanda hakan ya d’an basu tsoro dan daga shi sai boxer sannan yanata lullub’awa side drawer wani uban jibgegen bargo…..kana ganinsa ka san ba a dai dai yake ba sannan yana cikin tashin hankali. K’uraa masa ido su ka yi sosai bayan sun tabbata Yadikko ta farka sai dai ba su yi wani motsin ba da zai sanya ta fahimci wani abun duk su ukun dan kowa akwai abunda ya ke rayawa a kansa, kawai sun kura masa idone shi da bargon da yake ta faman kaffa-kaffa da shi…. A take gaban Adda ya yanke ya fad’i sai kuma ta nufesu! Tana zuwa ta yaye bargon gaba d’aya! Da sauri ta ja baya ta saka hannu ta toshe bakinta ta fashe da wani kalar kuka tana mai runtse idanuwanta da masifar k’arfi sakamokon Talatu mai k’osai da ta baiyyana a idanunsu bayan ta yaye bargon zigidir da ita! Ko ta Ina ya iya shigowa da ita sai Allah! Kaico Allah wadaran naka ya lalace… Adda ta aiyyana hakan a cikin ranta wani masifaffen Abu mai d’aci da zafi yana tokare mata k’irji. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *03* Cikin wata zazzafar zuciya Baba wanda bai tab’a sanin yana da kalarta ba ya yi wata super ya damk’i wuyan Kaka Nura tun k’arfinsa…so ya ke kawai ya kashe tsohon saboda dama yana ta tunanin yadda zai Mutu ya barsa da Mahaifiyarsa da wannan halin nasa! Adda mace ce ita ma rauni ne da ita ba zai bar mata case d’in Kaka Nura a hannunta ba ya san ba iyawa za ta yi ba. A rikice Adda ta k’arasa wajen ta fara k’ok’arin b’amb’are hannun Baba yayinda Talatu ta ke ta k’ok’arin ganin ta mayar da suturarta jikinta… Babu damar yin ihu dan duk wanda su ka yi ihu ko magana da k’arfi ya ji to sai ya shigo Ita kuwa Adda ko hauka ta ke ba ta bari a shigo a ga wannan gagarumin abun kunyar ba shiyasa k’asa-k’asa ta ke cewa Baba “Za fa ka kashe sa, ka taimaka ka cika shi dan Allah. Cika shi kar ka yi b’arna.” Ba tare da ta bari hatta Yadikko wadda su ke a d’akin tare da ita ta na ta faman cewa “kuna Ina ne?” ta jiyo su ba. Kaka Nura shima wanda duk idanunsa su ka firfito waje yau kam babu fad’a da duk wannan bala’i da haukar tasa Dan tashi d’aya ya fahinci Baban yau ransa ya ke nema bagatatan dan haka da mugun kyar ya ce “Ka yi mini rai dan Allah” Wani irin kuka ne ya kufcewa Baba cikin kukan ya shiga cewa “in na cika ka direct ka fice Ka saka jallabiya ka fice kar in sake ganinka dan wallahi in na ganka idona idonka sai na kasheka! Ka dai san mutuwa zan yi ko? Dan haka ba na jin tsoro a kamani da laifin kisa ko kad’an, gara in kasheka in Mutu hankalina a kwance akan in Mutu Ina tunanin halin da zan tafi in bar Mahaifiyata a ciki dan haka in har ka bari mu ka had’u sai na kasheka” Ya fad’i hakan cikin d’acin zuciya wanda har k’asan ransa da gaske ya ke, ya tafi kawai in ya ga dama ya shiga duniya..kuma ko Yadikko ta tambaya Ina Kaka Nuran zai ce mata kawai shima ba su san inda ya ke ba. Sai dai in ya mutu ya dawo gidan wallahi. Yana wannan lissafin ya na kuka wiwi sai dai a hankali sosai Takaici goma da ashirin duk sun had’e masa….. Tabbas zai fita yanzu amma fa domin ya tsira ne kuma sai ya tabbata ya saka Baba kuka da tashin hankali kafin ya bar duniyar da yake ta faman ik’irari, in sha Allahu… Saboda wannan cin mutunci da rainin da ya yi masa! Wai yau har shi ake treatning ake cewa za a kashe! Tab ashe kuwa an ja ruwa.. Kawai dan ya san Baban zai iya aikata abunda ya ce ne shiyasa ya zab’i ya llallab’ashi ya barsa kafin ya sake waigowa kansa…… Kaka Nura ya aiyyana hakan a cikin ransa. Sai da Baba ya ji Kaka Nura ya ce masa “Wallahi zan tafi…ka na cika ni zan tafi” Tukunna ya cika shi ya na wani irin kuka! Har ga Allah ya san babu kyau dai amma ya yi farin ciki matuk’a da abunda ya same shi! Tunda ya auri Anne wallahi wallahi haihuwar da ake yi masa ce kawai ta ke sanya shi farin ciki amma kullum cikin bak’in ciki da tashin hankali ya ke! Bai tab’a samun kwanciyar hankali da farin ciki daga gareta ba yanzu gashi ta d’aid’aita musu rayuwa daga shi har y’ayansa. Ji ya ke dama kamar ya gudu wallahi..bak’in cikinsa d’aya bai san wanne hali y’ay’an nasa za su shiga ba in ba ya nan amma tabbas gara ya tafin dan bak’in cikin ‘ga shi a raye tare da su amma ya gagara gyara rayuwarsu’ dama ya dad’e ya na nuk’urk’usar zuciya da walwalarsa… Komai babu dad’i komai ya d’au zafi ta koina babu sauk’i sannan the worst part is that babu abunda ya Isa ya yi domin ya kawo sauk’i ko ya gyara hakan ko ya dakatar da abubuwa daga k’arasa tab’arb’arewa. ‘He is just so very useless’ Ya aiyyana hakan a ransa yana mai zama a k’asa dab’ass sannan ya sake sakin wani sabon kukan mai cin rai da k’una marar sauti…. Dan bala’i Ashe Kaka Nura shi da daduronsa ta window su ka shigo, dan haka su ka fice ta windown su ka mayar da burglar d’in wadda ashe ya dad’e da b’intiketa a jogane kawai ta ke sabida shigowa da mata…’tsabar idanunsa sun rufe shi kam bai ma damu b’arawo ya shigo musu ba…dan windown d’akin ya fita ta wani dogon lungu a unguwar ne wanda ba a ma binsa sosai saboda tsayi da duhunsa in dare ya yi….. Tsoho da shi amma har yau bai bar bin mata na masifa ba! Dukda cewa itama Yadikkon she’s not perfect amma tabbas ba ta chanchanci Miji kalar Kaka Nura ba sam! Halaiyyarsa sak irinta y’arsa babu wani Abu mai kyau a tattare da su…’ Adda ta na wannan lissafin ta k’arasa kusa da d’an uwanta ta zauna kawai sannan ta saka hannu ta kamo na Yadikko wadda ta ke ta faman kiran sunayensu tun d’azu…. A chan waje kuwa.. Sai da Anne ta zabgawa Ya Amir kyawawan maruka guda biyu tukunna da kyar muryarsa ta na karkarwa ya furta kalmar saki d’aya ga Sajidar… Sai a sannan tukunna Baba ya mik’e ya fito ko kallonsu bai yi ba ya bi bayan Ya Amir wanda ya fita da sauri, Adda kuwa a D’aki ta zauna ta na mai ci gaba da sauraren Anne ta na cewa Sajida “Alhamdulillah mun rabu da marar wadatacciyar zuciya, mai matsiyaciyar zuciya! Allah ya yaye mana alak’ak’ai…” Cikin d’aga murya Sajida ta ce “Ae tsiya a gindinku ta k’are wallahi…matsiyatan banza masu jinin zina..Allah na tuba zani nawa na baki? Kuncen kayan Mahaifiyata nawa aka baki? Ba ki da shi da dalilin samu, amma kin bi kin kwallafa rai akan y’ay’an da ki ka Haifa za su zamo silar samunki, kina jira su kula da dukkan buk’atunki na kud’i! Za ki sha mamaki wallahi wannan mutuwar zuciyar taki ita za ta janyo ki wahala ki k’are a cikin talauchi.. Ni Allah ya sa ma ba ki yi mana asiri a jikin kayayyakin da muka baki ba, Muguwa matsafiya kawai...A haka ne wae har ki ke da bakin cewa ba ni da amfani! Ae kuwa kafin in tafi sai kin fito mini da duk wani abun da na tab’a baki…” Jikin Anne ya d’an yi sanyi a wannan gab’ar amma sai ta ce “Tsummokara ae ba wata tsiya bace! Kin bi kin ishi mutane ke y’ar masu kud’i shin Ina arzik’in ya ke? Ina gatan naki yake? Ae tunda ubanki ya bari aka kawoki nan wallahi an gama da ke.. Ba ki da wani gata y’ar nan….” Tafi Sajida ta yi tae shewa sannan ta ce “Auhoo da so kika yi wato a bani gida? A yi muku ciki sannan a yi muku goyo…to bari ki ji Mahaifina ba dak’ik’i bane ba kamar ki…dabba mahaukaciya kamar ki ba ta isa ta damfareshi ta yi masa wayo ba wallahi k’aryanki! Ni kaina ae da ke da Amir d’in kun san hanyar da ku ka bi na saurareshi, har na yarda na so shi na aureshi in ba haka ba wallahi ko a mai gadi ba zan d’aukeki ko shi ba kuma gata an yi mini shi tunda har mutum kamar Mahaifina ya bi abunda nake so ya yarda ya kawo ni nan ae kuwa kema kin san Ina da gata wallahi ana son farin cikina… Kawai dae wayo ne jahila irinki ba ta isa ta yi mana ba….” Kasa ci gaba da danne zuciyarta Anne ta yi a take ta zabgawa Sajida Mari…. Wanda hakan ya kusan d’auke numfashi Adda wadda ta fito da niyyar yin rabiya. Ficewa Matan da su ke d’aukar rahota su ka yi, dan kar ta shafesu yayinda Adda ta k’araso inda su ke da sauri cikin karkarwar jiki ta na cewa “Anne kanki k’alau kuwa? Me ki ka aikata….” Sai a lokacin Sajida wadda ta dafe kuncinta ta motsa.. Ta juya ta afka d’akinta jim kad’an ta fito rik’e da wayarta da mayafinta a hannunta da makullin motarta… Ta na fita ta d’auki mota a gidan makwaftansu inda ta ke fakin ta bar unguwar zuciya na cinta…. Ko gama hawa Titi ba ta yi ba ta kira Abbanta wanda ya kasance baban mutum sosai a Nigeria, mai fad’a a ji..har khaki garesa sannan ana shakkarsa..ta na kuka ta ce masa ‘Anne da Ya Amir sun yi mata duka har sun kumbura mata fuska’ Dan da gaske fuskanta ya kumbura ta wajen kumatunta ya yi wani kalar jaa da alamun bruises kacha-kacha da shatin yatsu guda hud’u rass! Sun baiyyana duk a ta sanadiyyar marin da Annen ta yi mata na hauka…sakamokon ita Sajidar tunda ta ke a rayuwarta ko mintsini na gaske ba a tab’a yi mata mai zafi ba sai dai a wasa ko tsokana. Tunda ta fita su ka yi shiruu hatta Anne ta gagara motsi kwata-kwata… Yadikko kuwa tunda Adda ta fita ta ja pillow ta kwanta ta soma barcinta, dan yadda ta ji Sajida ta yasar da ita d’azun ta tsorata kwarai..shiyasa tunda ta ji an sake ta ta b’uya a d’aki gudun kar a huce a kanta. Dan in Sajidar ta rarumo wani abun kafin ta nemi hanya ta gudu an sauk’e mata. Bayan kamar mintuna goma da fitar Sajida, Baba ya shigo ya kallesu ya ce “wani abun ya faru bayan wanda na sani?” Dan su kansu mazan da su ke waje sun ga yanayin yadda Sajidar ta bar unguwar rai a b’ace ga fuska ta kumbura ta yi jaa, tabbas sun san ba lafiya ba…shiyasa yana dawowa daga kai Ya Amir gidan Abokinsa su ka ce ya shiga gida fa ya duba dan kamar ba k’alau ba… BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *04* Da kyar Adda ta iya ce masa “Anne ce ta mareta…” Shiruuu ya yi kawai ya na kallon Anne kafin chaan ya ce mata “ku zo mu bar unguwar na d’an lokaci, yi wa Yadikko magana ta fito yanzu-yanzu….” Ya yi maganar jikinsa har ya na karkarwa saboda Abban Sajida ba shi da sauk’i! Ya ji ya shaida hakan, masifar tsoronsa ake ji gashi fad’ansa ba ya mutuwa. Kwata-kwata da fitar Sajida da zuwan anti daba har da Sojiji bai kai mintuna goma sha a tsakani ba. Motocin suna dira, tun daga wajen zaman makoki suka fara nad’e jama’a, duk wanda ya yi yunk‘urin guduwa kuwa take sa su ke yi ko su buga masa bindiga a ka… Dan Sajida ta na kuka ta sanarwa Abbanta Anne da d’anta sun taru sun yi mata duka har sun farfasa mata jiki sannan an yi mata saki d’aya…’ Shiyasa shi kuma ya fusata, a ganinsa saki kam ba komai bane ba dama abunda ya ke fata kenan amma duka kam tabbas wannan sai sun yi dana sanin had’a zuri’a da shi wallahi… Shiyasa ya yi kiran waya ya ce ‘a kwashe masa kowa hatta tsuntsu in ya zo wucewa ta saman gidan a had’a da shi! A gark’ame masa su a waje mafi tsananin takura da wahala kafin ya waiwayesu ya ji ba’asin dalilinsu na tab’a masa y’a da su ka yi. Sannan ko da wasa kar a bada belinsu kar ma a bari a gansu sai sun yi 48 Hours a uk’uba…’ Maza bakwai su ka yi nasarar cafkewa a wajen zaman makoki aka saka su a mota, a cikin Yaran da su ke kallo kuma guda biyu su ka tafi yiwa wani a cikin sojojin rakiya har inda Ya Amir ya ke, yayinda ragowar kuma su ka shige cikin gidan kan su tsaye.. D’an gidan Aliya yana rungume a k’irjinta ta na kuka tshohuwar da ta ke tare da ita tana ta faman lallab’ata a kan ta kawosa a yi masa sutura amma ta k’i kawai su ka ji k’arar jiniya… Kallon kallo aka hau yi kafin ka ce kwabo su ka fara jin ihu da durufta sai kuma a ka afko musu cikin d’akin… Salati y’ar tsohuwar ta saka yayinda Aliya ta yi shiruuu kawai hawaye su na ziraro mata. Ta na kallo cikin tsantsar wulak’anci aka kame tshohuwar ta hanyar saka mata ankwa su ka yi waje da ita a wulak’ance sannan wata mata ta k’araso gabanta ta tsaya ta ce mata “Tashi mu je ki rungume jaririn a jikinki ke ba sai an saka miki ankwar ba…” Kamar ba za ta yi magana ba sai kuma cikin sheshshek’ar kuka ta ce “gawa ce” Shiruu matar ta yi kafin ta ce mata “taso ke da shi mu tafi, doka ce ba zai yiu mu karya ba…” A hankali Aliya ta d’ago jajaye kuma daradaran idanuwanta ta na kallon Matar cikin tsantsar b’acin rai ta ce “ba ki fahimci yaren da na yi miki bane ba? Doka ta zo daga sama ae kwa jira mu cika umarnin mai saman gaba d’ayanta ko?” Wani murd’add’en mutumi ne ya zo ya saita kanta da bindiga ya saita bindigar wanda hakan ya sanya har sai da ta zabura ta ce “hhch” cikin tsantsar tsinkewar zuciya sannan ta mayar da dubanta garesa… Cikin sanyin murya matar ta ce mata “ki yi hak’uri ki taso mu je. Bai kamata a yi hakan ba kam, amma kafin a yi miki illa ki zo mu je in sha Allahu zan san abun yi….” Wani kalar tuk’uk’in bak’in ciki da zafin tashin hankali, nadama mai had’e da da na sani ne suka sanya Aliyar ta gagara motsawa daga inda ta ke! Sai wasu zafafan hawaye da su ka shiga zubo mata tsanar Mijinta ‘Mai Nasara’ da Anne su na sake kanainayeta..kaico!.. Tsawar da mutumin ya daka mata ce ta sanya ta d’an dawo cikin haiyyacinta. A hankali matar tausayinta ya na shigarta ta saka hannu ta karb’i gawar jaririn Suna ganin haka kuwa mazan su biyu su ka matso aka saka mata ankwa itama aka yi waje da ita…ta na tafiya da kyar ga azabar haihuwa ga ta d’inkin da aka yi mata. A cikin motar ta tarar da gaba d’ayansu har da Ya Abba wanda yana shigowa unguwar (dawowa daga kai yadin da aka auna tsayin gawar) yanzu-yanzun shima aka had’a da shi da Ya Amir wanda suka d’auko daga gidan Abokinsa. Motoci biyu taff aka cika da mutanen da su ka kama dan kamar yadda mutumin ya fad’a basu d’agawa kowa k’afa ba gaba d’aya suka kame kowa aka had’a da su a motar aka yi gaba da su. Y’an Unguwa ana ta kallonsu wasu su na yi musu dariya yayinda hankalin iyalan mazan da aka kama ya tashi chaa suna ta kuka da wannan cin mutunci da aka yi musu, su Anne kuwa Allah shi k’ara kowa ya ke ta cewa. A haka aka nufi chan wani waje mai kama da barikin Sojoji da su…. Anne ta had’e rai ta na lissafin yadda za ta yagalgala rayuwar Sajida dan wallahi in za ta k’arar da duk abunda ta tara sai ta tarwatsa rayuwar Sajida da Ubanta… Baba kuwa hawaye ya ke yi a b’oye ya na sharewa a hankali a hankali, yayinda Ya Abba ya kafe Amal wadda ta sunkuyar da kanta k’asa kawai da idanu zuciyarsa ta na wani kalar k’una…. A haka su ka k’arasa wajen kowa da abunda ya ke tattaunawa da zuciyarsa… Cike da wulak’anci a ke firfito da su daga cikin motar sannan aka shige da su ciki…. Da Mazan da Matan da tsoffin duka aka gwamutsa su a waje d’aya su goma sha biyar har da gawar jaririn Aliya sha shidda saboda suna shiga matar ta bawa Aliya gawar jaririn dan ce mata su ka yi ‘ta bata abarta ta rik’e za su san abun yi….’ Dole maza bakwai d’in da su ke zaman makoki waenda hau ya fad’a musu su bakwai aka taho da su…su ka tsaya a tsaye dan babu wajen zama enough su da Ya Amir Baba da Ya Abba…. Yayinda Amal, Yadikko, Anne, Adda, Aliya da wannan tsohuwa su ke a zaune a marmaste sosai dan kwata-kwata wajen bai fi wajen tsayuwar mutum sha biyar d’in ba…. Suna gama zama wani Barci ya sake yin awon gaba da Yadikko, yayinda wannan tsohuwa ta yi shiruuu ta na addu’a a cikin ranta. A hankali Amal ta mayar da kanta k’asa ta fashe da wani kalar kuka siriri mai cin rai…. Tunda Ya Abba ya ke bai tab’a jin kansa helpless kamar na yau ba..tabbas he is useless ba shi da power d’in komai sannan ba zai iya protecting nata ba no matter what…. Zuciyarsa na k’una ya sunkuyar da kansa k’asa ya sake damk’ar k’arfen k’ofar cell d’in da ya rik’e da masifar k’arfi zuciyarsa ta na yi kamar za ta fito daga cikin k’irjinsa…. ‘K’i-k’-k’i-k’iiii’ d’in da su ka ji k’arfen ya soma yi ne ya sanya duk aka mayar da duba garesa. Da sauri d’aya daga cikinsu ya d’an tsattsallake su ya matsa kusa da Ya Abban ya d’an dafa shi dai-dai da mik’ewar Adda itama ta dafa shi a hankali ta na cewa “Abba…” Kamar wadda ta ke jin tsoro… Ko kad’an bai ji su ba sai da ta sake cewa “Abbaaa” A hankali kusan a tare ita da mutumin tukunna ya ji sai kuma ya tsaya chak da abunda ya ke yi dan shima sai a lokacin ya ji yadda tafin hannunsa ya d’auki zafi matuk’a a ta sanadiyyar k’ok’arin fasa k’arfen wajen da ya yi… Sai da aka d’auki kusan mintuna uku tukunna ya iya bud’e idanuwansa da mugun kyar waenda su ka yi wani kalar jaaa na ban mamaki… A hankali Adda ta sunkuyar da kanta k’asa yayinda mutumin ya d’an yi tapping shoulder d’insa ya ce masa “sai hak’uri” daga haka ya juya ya bar wajen ya tsallaka ya koma inda ya ke dan bai san me zai ce masa ba kuma sannan har ga Allah yanayinsa ya bashi tsoro matuk’a dan kamar ba shi ba haka ya koma. So ya ke ya je ya zauna amma ya gagara yin hakan, sai bayan kusan mintuna ashirin tukunna ya ji ya iya motsa k’afafunsa dan haka ya nufi inda Amal ta ke zaune kai tsaye ya zauna a kusa da ita shima ya kifa kansa k’asa a kan guiwwowinsa kamar yadda ta yi…chaan ya d’ago kansa a hankali ya na kallonta ganin kamar ma ba ta lura da shi, ya ce “Amal”. Har yanzu kuka ta ke yi ga muryoyin Ya Asad da ta ke ji su na yi mata yawo a ka, in ya yi maganar gaba d’aya sai ta ji kamar ta bar wannan duniyar ta koma wata daban ita kad’ai It’s like soul d’inta ya ke d’aukewa daga wajen gaba d’aya….. Yanzun ma haka ce ta sake faruwa ta inda ta ji ya na cewa “ki ba da had’in kai, duniyar nan babu komai a cikinta sai tarin bak’in ciki…let me End your suffering…” Ya yi maganar a jikinta ta na ji kamar ya na mik’o mata hannu.. Har ta fara k’ok’arin mik’a masa nata hannun a chan inda ta ke jinta ta ji Ya Abba ya ce “Amal….” Da sauri sannan firgigit lissafinta ya dawo inda su ke sannan ta shak’i numfashi da nauyi kafin ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a hankali a hankali ta na mayar da numfashi sannan ta shiga k’ok’arin d’agowa a hankali… Da Aliya su ka fara had’a idanu ta kafeta da ido kawai wanda abunda Amal d’in ba ta sani ba shine kwata-kwata hankalin Aliyah ba ya ma kanta, gaba d’aya hankalinta ya tafi wani wajen shiyasanya ba ma ta gane a ya Amal d’in ta ke ba… Chan ta ke lissafi da tunanin Mai Nasara da Anne wanda takaicinsu ya taru ya sake haifar mata da wani sabon tarin bak’in ciki… A hankali Amal ta d’an matsa jikin Adda sosai jin Abban a kusa da ita…one by one ta ke bin kowa da kallo ba tare da ta waiga ga Ya Abban ba wanda ta ke ji a jikinta ita ya kafe da idanu… Idanunta su na sauk’a a kan Baba wanda ya yi shiruuuu ya sunkuyar da kansa k’asa kawai sai ta sake fashewa da kuka, cikin kukan sosai k’asa-k’asa ta ce “Ya Abba dan Allah ka ce musu su sauya mini waje ko Ina ne su kaini… Ba na son kallon fuskar Aliya zuciyata za ta buga!” A hankali ya sauk’e numfashi cikin tsantsar karyewar zuciya ya ce “I’m soo sorry Amal. Ki yi hak’uri dan Allah, ba ni da taimakon da zan iya yi miki, kwata-kwata ba ni da wannan power…” Ya yi maganar a hankali sannan kamar mai shirin fashewa da kuka. Shiruu itama kawai ta yi ta na mai jin babu dad’i.. Ta d’ago kenan za ta yi masa magana ta ji Aliya ta ce “Amal ki yiwa Yagwalgwal magana mana, tunda ita d’in shahararriyar karuwa ce na san za ta iya yin magana a fitar damu daga nan tunda ta san maza bilaadadin…” D’ifff! Haka wajen ya kasance kowa ya yi shiruu babu mai cewa komai… Anne so ta ke yi ta yiwa Abba magana shima ta ce ya kira musu ‘Mai Dala’! Amma haka nan yau sai ta gagara yi masa magana wani kalar tsoro da shakkar Yaron duk su ka bi suka rufeta tun d’azun…dan haka ta ja bakinta ta yi gum! Hau d’in nata bai fad’a a kansa ba yau…zuciyarta ta na k’una ta rasa inda za ta sami salama, ta ji Amal ta ce “tabbas Aliya dukkanin abunda ya faru da ke halinki ne ke bin ki…” Da sauri kamar mai jira Aliya ta ce “kazalika ke ma, halinki ya sanya Asad ya guje ki kuma halinki ne ya janyo ki ke cikin halinda ki ke a halin yanzu sannan mind you This is just the begining of your sufferings In shaa Allahu…..” Da k’arfi Ya Abba ya ce “Aliya!!!!” Yana mai zuba mata jajayen idanuwansa… Dole ta rufe bakinta gam! Dan a take ya razana ta matuk’a ba ma ita kad’ai ba duk wani wanda ya ke a cikin cell d’in sai da y’ay’an hanjinsa su ka kad’a har da Baba wanda ya ji dad’in yadda Abban ya shigarwa Amal dan sarai ya lura da yanda Anne ta soma jin dad’in cin zarafin da aka fara yiwa Yarinyar ya san tsulum yanzun za ta shige su tarar mata su yi mata tatas!. A hankali Adda ta kamo hannun Amal wadda ta san ko me ye ta cewa Aliya to fa bango ne aka kaita shiyasanya dan sam ita magana ma ba d’abi’arta bace ba…. Cikin sanyin murya Adda ta ce mata “na san kina hak’uri amma zan rokek’i ki k’ara, ko me za a yi miki ki daina tankawa dan Allah…” Jiki a mace sosai ta na ji kamar ta kurma uban ihu ta ke kallon Adda wasu zafafan hawaye su na zubo mata, kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shiru kawai ta mayar da kanta k’asa… Farkawar Yadikko wadda ta yo ta cikin kuka a ta sanadiyyar kunamar da ta d’alle ta ne ta katsewa kowa hanzari, da sauri duk aka maida kallo a kanta saboda ba damar matsawa dan duk a dunk’ule su ke a waje d’aya…. Ya Amir ne ya hangi kunamar sakamokon juyowar da Yadikkon ta yi ta hau kan wannan tsohuwar dan haka ya yi saurin taketa da k’afarsa cikin ikon Allah ta mutu bata d’alle sa ba saboda babu takalmi a k’afartasa saboda duk saida aka sanya su ka cire takalmansu tukunna aka sakasu a cikin cell d’in bayan an amshe wayoyinsu…. Da sauri ita kuma Aliya ta ware d’ankwalinta ta d’aure k’afar Yadikkon dukda kunamar mitsitsiyace amma ta yi mata hakan saboda kar dafin kunamar ya game mata jiki sannann ta shiga cewa “ku zo ku taimaka mata “ Da k’arfi! Ita da Anne suka fad’i hakan har sau biyu amma babu wanda ya nuna alamun ma ya jiyosu ballantana a zo a kulasu, sai Ya Amir ne ya gyara tsayuwarsa sannan ya kalli Anne ba tare da ya yarda ya kalli fuskar Aliya ba ya ce “Anne a k’a’idar wajen nan fa sai mun yi kwana biyu a haka tukunna za a fara bamu ruwan sha ma…” Cikin hayagaga ta ce “ko kuma a zo a fidda gawarwakin mu ba…. Fisabillahi in dare ya tsala wanda na ke da tabbacin ana kashe wutar mai shayin chan za mu daina ganin komai, ya za mu yi? Babu fa fitila a nan sannan kalli ramin chan na tabbata ta nan kunamar ta fito shin me kake zaton zai sake fito mana nan gaba?” A hankali ya ce “to Anne yanzun hayaniyar nan da ki ke yi ita ce za ta fitar da mu? Meye amfaninta? Mu zauna kawai mu yi salati…gara ma ku a zaune ku ke….” Ya k’arashe maganar cikin sanyin murya zuciyarsa na zafi… Cikin b’acin rai ta ce “ae dole ka ce haka dama! Tunda y’ar gwal d’inka da ba ka so a fad’i laifinta ce ta janyo komai. Ita ta janyo muka rasa jaririn nan saboda mugunta da bak’in halinta sannan dan na yi magana aka kawoni nan! Wanne kalar rashin imanine wannan fisabillahi ko da ya ke talauchi da rashin gata su suka janyo mini komai..” A hankali tsohuwar nan ta ce “ki daina danganta kaddararki da talauchi ko rashin gata. An riga an rubuta za ki yi zaman nan wajen tun kafin ma ki zo duniya…dan haka babu ruwan talauchi..” Cikin rashin mutunci ta cewa tsohuwar “Ki rufe mini baki tunda na ga alamun ba ki gama sanin ciwon kanki ba…” “Hmm” kawai matar ta ce ta kawar da kai Yayinda Anne ta fara k’ular da mazan da su ke tare da su a wajen, kunyar Baba ce kawai ta sanya su ke d’aga mata k’afa dan ta addabi kowa ta k’i bari kunnuwansu ma su huta.. Cike da takaici Anne ta juya kan Aliya ta ce “ki kirawo Mai Nasara.. Ko ya yanke huld’a da ke da jaririn dae ae zai so a yiwa d’ansa sutura cikin mutunci….” Haushin Anne sosai Aliya ta ke ji shiyasa kawai ta yi mata banza bata ko kulata ba! Dan haka Annen ta mik’e ta k’arasa jikin k’arfen ta hau jijjigawa ta na cewa “akwai wani a kusa?!“ Da masifar k’arfi…saboda Allah Allah ta ke a zo a fidda ita a nan kafin dare ya yi mai shayi ya tashi ya kashe wutarsa wadda haskenta da ke ratsowa ta window ne ya ke taimaka musu su ke iya ganin komai. Kar ta je maciji ya b’ullo musu ta wannan bak’in ramin da ta gani, gashi ta lura ta fahimci alamun d’an gidan Aliya har ya soma kumbura saboda kwata-kwata wajen babu iska sai uban zafi da hucin d’umi duk sun jik’e saboda gumi…kar ta je gawar ta fashe musu ya yi tsutsa wari ya kashesu… BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *05* Da gudu ta ji an taho kamar za su tsaga k’asa dan haka ta yi saurin jaa da baya ta shige cikin mutanen, har ta na tumurnushe y’ar tshohuwar nan, Yadikko, Aliya da jaririnta. Baba ne ya kamo kafad’unta duka biyu ta bayanta sannan ya yi k’asa da ita da k’arfi dan gab take da fad’awa jikin Limamin layin nasu.. Cikin tsiwa ta juyo za ta yi masa ihu wata dakakkiyar murya ta katseta ta inda ake cewa “Waye ya ke magana?” Aka yi maganar cikin daka musu tsawa. Mintsinin Aliya Anne ta yi alamun ta yi magana… Da kyar Aliya muryarta ta na rawa dan mutanen kansu ababen tsoro ne ta ce “ddama Mahaifin jaririn nan zan kira, na yi muku alk’awarin in ya zo shi da kansa zai yi muku kyauta mai tsoka! Kar ku bari d’ansa ya rub’e ku taimaka a sanar masa, ko gawar ce a samu ya zo ya karb’a ni ku ci gaba da rik’eni.” Ta k’arashe maganar ta na hawaye. Cikin kwakkwaran kashedi mutumin ya nuna ta ya ce “daga yanzu har a zo gareku kar in sake jin bakin wata a cikinku, ku yi saving energy d’inku har zuwa nan da 48 hours!” Sannan ya d’auke dubansa daga kanta ya fara kallonsu one by one yana nuna su tukunna ya d’aura da cewa “Duk wanda na sake jin bakinsa kuma wallahi sai an kai shi wajen horo, ya yi 48hours d’in a chan. Babu waya ko taimako a cikin punishiment d’inku dan haka kar ku b’ata mini rai…” Daga haka ya juya ya wuce ya bar wajen. Matar d’azu da ta ke ta jin tausayin Aliyar ce yanzu ma su ka zo tare da mutumin, dan haka kafin ta wuce a hankali ta d’an durk’usa kamar za ta gyara takalminta cikin dabara ta garo mata wayarta cikin gurin… Sai da su ka bari sun yi nisa tukunna su ka taso kamar mayunwatan zakuna sun ga nama..haka su ka rarumi wayar! Anne har da y’ar dariyarta… Sai da su ka danna kiransa wajen sau biyar tukunna Saminu ya d’auka a na k’arshen ta na gab da tsinkewa… Kasancewar wayar matar ba a ji sai a speaker ya sanya tunda su ka fahimci hakan su ka barta a speaker. “Assalam alaikom” Muryar Saminu (Yaron Mai Nasara) ta katse musu addu’o’in da su ke ta jerowa akan Allah ya bashi ikon d’auka a samu ya kawo musu d’ouki… Aliya kuwa addu’a ta ke yi Allah ya sa ya d’auka d’in in sha Allahu ita kuma ko an zo fita ba za ta tab’a bari a fita da Amal ba ce masa za ta yi ya barta a cell d’in ita kad’ai duk a watse a barta…Allah ma ya sa abun cikin ramin chan ya kasance mai matuk’ar muni apart from kunamomin da ta ke da tabbacin akwaisu duhu kawai su ke jira su fito… ta yadda zai fito ya kasheta har lahira kowa ma ya huta… A hankali ta cewa Saminu “Saminu ni ce, Alhaji ya na kusa?” Cikin d’an fad’a-fad’a Saminun ya ce “ke ce wa?” Da sauri ta ce “Aliya, na haihu ne..to jaririn ya koma..” Jin ya yi shiruu ya sanya ta ce “Aliya mana Saminu…matar Mai Nasara..Ina so in yi magana da shi, ta gaggawa” “Aliya Aliya Aliyaaa” Saminun ya ambata kamar mai son tuno wani abun… A hankali ta ce “Aliya ta Mariri” Cikin fahimta ya ce “Owkay mai cikin nan ko?“ Cikin sauk’e Ajiyar zuciya Aliya ta ce “eh, ni” da sauri, sai kuma ta d’aura da cewa “Ina so zan yi magana da shi dan Allah…” Ashe ma su na tare dan k’asa-k’asa sosai ta ji ya ce “ranka ya dad’e Aliya za ta yi magana da kai, tshohuwar matarka…” Kamar yadda Saminun ya yi da farko haka shima Mai Nasara ya yi sai dai shi d’in da ikon Allah ya gagara tunowa da ita sam, sabida cikin ikon Allah matan da ya aura masu suna Aliya su na da yawa gashi dai sunan unique ne amma shi Allah ya had’ashi da su sau dayawa. Ganin Saminun ya na shirin saka masa ciwon kai ne ya sanya duk su na ji kawai ya rufesa da fad’a! Ko bari Saminun ya yi masa cikakken bayanin da zai gane ta bai yi ba hakanan ya rufesa ruff da fad’a kamar mai shirin dukansa, dan shi a k’a’idarsa in ya bar mace to ya barta kenan har gaban abada, kuma Saminun ya sani amma ji bi dan iya shege ya na yi masa maganar wata wai ita Aliya. Cikin tsantsar ladabi bayan Mai Nasara ya dire aya yana haki su ka ji Saminu ya ce “ranka ya dad’e ji na yi ta ce ta haihu ne kuma ta na buk’atar taimakon ka cikin gaggawa…” A hankali Aliya wadda jikinta ya yi mugun sanyi ta tari nunfashin Saminun ta hanyar cewa “Yaron ya koma kuma an k’i bari mu binne shi Ina cell yanzu haka har ya fara kumbura… Sakamokon wajen akwai masifar zafi mu kanmu da kyar mu ke iya zuk’ar iska, ga numfashi ya yi yawa a d’an k’aramin d’akin da su ka gwamutsa mu…” “Subahanallah” Saminu ya ce sannan ya shiga sanarwa Mai Nasara abunda Aliyar ta gama zaiyyane masa yanzun….. Amma ga mamakinsu sai su ka ji a fusace Mai Nasara ya ce “ka ci kutumar ubanka Saminu!” Sai kuma ya warce wayar daga hannunsa sannan ya ce “Ke! Naira miliyan nawa aka baki bayan na sake ki? Meye naki na bibiyar rayuwata ko wani sabon raini ne ya b’ullo muku? Kin kashe kud’ad’en shine za ki sake dawo min sabida ga ATM machine nan kin samu ko?” Cikin sharar hawaye zuciyarta ta na wani kalar k’una ta ce “na haihu d’anka ya rasu, muna cell da gawar har ta fara kumbura, ka zo in ni ba za ka fitar da ni ba shi ka karb’esa a yi masa sutura a binne sa dan Allah kar ya rub’e…” Ta k’arashe maganar ta na fashewa da kuka” Cikin tsantsar rashin imani ya ce “dan uban ki a kan gawa ki ka kirani?” Zabura ta yi jikinta ya hau karkarwa dan duk rashin imaninsa ba ta tab’a tunanin zai yi hakan ba, haka suma mutanen wajen dan haka kowa sai ya yi tsit! Ya sha jinin jikinsa suna masu ci gaba da sauraronsa ya na cewa “Allah ya ji k’ansa ya sa mai ceto ne, duk sanda Allah ya sa ki ka fito ki binne abinki, ba zai yiu ki je ki tafka laifi ki saka ni yawon cell a banza da mutuncina ba…..wallahi wallahi in ki ka k’ara kirana sai na tarwatsa ahalinki! Da ace ma Yaron ya na raye ne to da sai ki kira ki fad’a in so ki ke a karb’a in karb’i abina amma kar ki sake d’agamin hankali a kan abunda ya riga ya shud’e na san kin san ba na son waiwaye…” Daga haka ya kashe wayar ko sake sauraronta ta na cewa “yanzu ya rub’e kenan?” Bai yi ba. Shiruuu haka kowa ya kasance, tausayin ta ya cike zuciyar kowa a wajen sannan a take duk d’insu su ka fidda ran samun taimako daga garesa. Anne kuwa gazawar Aliyar ta gani da Mijinta bai iya cetonsu ba gashi d’ansa ya na shirin fara azabtar da su da wari…ba bu wanda ya iya cewa komai kamar an yi ruwa an d’auke haka cell d’in ya kasance sai sheshshek’ar kukan Aliya da ya ke tashi….duk kalar zazzafan rashin adalci da muguwar muguntar da ta tafkawa Amal d’in da kuma mugun aikin da su ka tafka wanda zai zama silar yankewar duk wani sauran farin cikin su… A take sai ta ji tausayinta ya lullub’eta, abunka da zuciya mai kyau. Da sauri kuma sai ta kawar da kanta ta shiga k’ok’arin korar tausayin Aliyar da ya ke shirin dirar mata…. Cikin inda-inda da kyar Anne wadda itama duk jikinta ya yi sanyi ta ce “duk laifin shegiyar nan Sajida ne…za ta ci ubanta kuwa za ta san ta yi da ni! Wallahi sai ta yi yawon bara, hmmm, ba ta san wacece Anne ba! Duk ita ce ta janyo miki halin nan da ki ke ciki har ma da mu kanmu…” Cikin tarar numfashinta Aliya ta d’ago jajayen idanuwanta ta kalli Annen sosai sannan ta ce “Itace ta tilasta mini auren Mai Nasara shima?” Inda-inda Anne ta fara, ba ta samu amsar da za ta bawa Aliyar ba ta d’aura da cewa “Anne kin cuceni, sarai da ni da ke duk mun san waye mutumin nan amma haka nan ki ka bad’awa idanunki toka ki ka jefani cikin bala’i….” Mugun kukan da ya ci k’arfinta ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana yayinda takardar scholarship d’inta da ta samu a uk ta shiga yi mata gizo, da tuni yanzu haka ta na chan….da tuni ba ta tarwatsa rayuwarta ba… Cikin b’acin ran da har ya kai ga baiyyana a kan fuskarta Annen ta ce “na cuceki ko dae Mai Nasara ya cuceki? A mugun fusace Aliya ta ce “ae da ban auresa ba da ba zai iya cutar da ni ba! Kin lalata mini dream d’ina Anne kin tarwatsa mini rayuwata gaba d’aya duk wani Abu na jin dad’i Anne kin janyo mini na yi hannun riga da shi…. Ki daina cewa Sajida ko Mai Nasara, dan wallahi duk wani halin da mu ke ciki a da da yanzu da har abada wallahi ko wanne duk ke ce sila. Mai ya sa ki ke da son kanki ne? Mai ya sa ki ke so ki lank’ayawa mutum sannan ki tabbatar da mugun halin a idanun kowa muddin ki ka ji ba kya son shi ko bai yi miki yadda ki ke so ba? In kud’i ne ae Afra ya kamata ki fara tunkara ba Sajida ba, Mai ya sa ki ke da son kai ne kuma ba kya son gaskiya? Mai ya sa duk b’arnar da ki ka tafka in ta dawo miki sai ki ce wani ne sila? Shin sai yaushe za ki gane gaskiya ne Anne? Halinda nake ciki bai isheki ishara ba? Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin mutum irinki ba! Duk son zuciyar ko wacce kalar uwa muddin ta ga abu zai tab’a sannan ya gurb’ata rayuwar y’ay’anta ta kan sarara amma banda ke Anne! Ba ki damu mu yi kuka ke ki yi dariya ba! Duk wani kalar Hali marar kyau akwai shi gareki Anne babu wanda ba ki kware a kansa ba!” Cikin tarar numfashinta Yadikko wadda tunda Anne ta bi ta kanta duk wani gigin Maye da zafin cizon kunama suka barta, ta ce “Aliya….” Cikin kuka ta ce “barni in fad’a mata na ga kamar har yanzun ba ta san wacece ita ba wata k’ila in na fad’a mata ta sani ta shiryu…. Kalli yadda ki ka lalata komai ki ka tarwatsa kowa duk cikinmu babu wanda ya ke farin ciki.. Hatta ita kanta Afran ae kin san ba wanda ya ke sonta ta aura ba dan haka dole akwai k’alubale a gabanta na sani..” Cikin tsawa Aanne ta ce “in ji uban waye ne ba ya sonta?” Ta yi maganar ta na mai satar kallon Amal, wadda ita kam ta zazzab’in da ya tusota a gaba ma ta ke.. Ya Amir shima ko kallonsu bai yi ba dan ba ya son jin muryar Aliya, yayinda Baba Adda da Ya Abba kowa ya yi d’iff dan su kam ba su da ta cewa….. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *06* Masu buƙata daga farko su shiga channel ɗinmu. https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Wani mutum ne a cikin mazan wajen ya ce “dan Allah dan Annabi ku barmu mu ji da abunda ya ke damun mu! Haba mana dan Allah. Wallahi-wallahi duk wadda ta k’ara yi mana hayaniya a cikinku sai ta daku! Ku nutsu ku daina ife-ife ko ma samu su ji k’anmu su bud’e mu kar ku yi abunda za a barmu a nan da wannan Gawar wari ya kashemu…” Ya k’arashe maganar ya na huci, yana mai jin haushin Anne sosai da tsanarta, gaskiya y’arta ta fad’a dan ko y’an Unguwa dama tuntuni Anne ta addabesu, kwata-kwata matar ba ta da Hali mai kyau ko guda d’aya. Ta yunk’uro kenan za ta yi magana kowa ya yi d’iff sakamokon engine mai shayi da su ka ji an kashe wanda ya yi dai-dai da d’aukewar hasken wajen, d’iff!! Haka nan ko Ina ya kasance babu alamun Haske ko k’ak’a. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”Anne ta furta a hankali jikinta ya na wani kalar karkarwa dan ta san wahala kam da azabtuwa sai ta sha ta a wannan k’arnin that’s if an zo an fiddasu basu kai ga mutuwa ba kenan!. Sai yanzu da Aliya ta ambato Afra tukunna ta tuna Afran fa za ta iya kawo musu d’ouki tabbas..to amma kuma ta san dole Afran ta sako Asad wanda ta samu ta kad’a su shi da Afran da kyar su ka yi nisa… Ba ta son ya had’u da Amal ko kad’an dan haka ta kawar da lissafin sako Afra a cikin jerin waenda za su taimaketa ta fad’a duniyar neman taimakon wasu… Ta na cikin nazarin ta ji Ya Amir ya ce “ba ni wayar in gwada kiran Afra” “Ungo” d’in da Aliya ta ce ta na mai mik’a masa wayar da kunna hasken fuskar wayar ne ya sanya Anne ta zabura..har an mik’a masa ya mik’o hannu ta saka nata hannun ta buge nasa sannan ta warce wayar daga hannun Aliya ta na mai zabga masa wata uwar harara, wadda hasken wayar da aka kunna ya taimaka masa wajen ganinta… Da sauri kusan mutum uku su ka ce “fara bar mana haske tukunna.” dan haka ta kunna flash d’in wayar har yanzun idanunta su na a kan Amir wanda ya d’auke kai daga dubanta. ‘In ta ga ba sarki sai Allah za ta kirata kam dan duk yadda ta kai ga son Afran ta yi farin ciki bai kai nata farin cikin da ranta ba, but for now ba za ta yi garajen bawa Amal abunda ta san ta fi buk’ata ba wallahi…’ Anne ta aiyyana hakan a cikin ranta ta na mai sake yiwa Ya Amir sign d’in ‘kar ka kuskura’ da ido. Wannan mutumin dae da ya ke ta jin haushinta ne ya ce mata “ki bashi ya kirata mana!” Sai kuma ta ga duk sun tsura mata idanu. Dan haka cikin kame-kame ta ce “bara in gwada kiran da kai na..” Daga haka ta hau daddanna wasu nambobi da ta san ba za su yi ba, sannan ta danna call. Jin ta yi wani irin sound ya sanya ta yi sauri ta sauk’e ta kashe ta ce “a kashe ne duk yadda a ka yi, ba zai je ba…”daga haka ta ajjiye wayar su ka ci gaba da zama….. Har sun d’an samu sauk’in hasken da su ka samu kawai sai ga matar ta dawo ta ce su bata in sun gama…ba ta iya tsayawa ta ji feedback d’in yadda su ka yi da mutanen da su ka kikkira ba ta yi gaba dan a tsorace ma su ka ganta kamar an kama ta ne. Tsayuwa gajiya da kuma wahala ne su ka sanya wasu maza a cikinsu su biyu su ka shiga shek’a uban amai mai masifar k’arni ga yawa wanda hakan ya sake tada hankalin Anne da kowa ma na wajen kwarai da gaske dan babu yadda su ka iya haka nan su ka ci gaba da zama da tsayuwa a cikin aman nan wanda tun a yi na farko ya cika d’akin ya wanzu a koina saboda ba wani girma ne da d’akin ba…sai kuma chaan su ka ji ya d’an fara raguwa ya na tsotsewa alamun ya na gangarawa ne cikin wannan rami inda kunamaa ta fito d’azu…. A take tashin hankalinsu ya sake hauhauwa dan basu san me ke tafe ba, gashi sun dad’e da daina ganin hatta tafukan hannayensu, d’id’iff su ke gani kawai tsabar uban duhun wajen… Kayayyakin jikinsu mazan su ka yanke shawarar kwakkwab’ewa…dan haka su ka cire rigunansu su ka danna a ramin aka samu ya rufu tsaf! Tsoro ya na sake game su sakamokon wani kalar sound da su ke ji ya na fitowa ta ramin kamar motsin kwari kamar kuma hissing na maciji. Kowa ba energy, barcin ma ya k’aura..Yadikko sai wannan tsohuwa da Amal wadda ta ke yin nata kamar suma ne kawai su ke d’an gwadawa..dan haka wajen ya kasance shiruuu kowa ya na nasa lissafin…ta inda matan su ka kasance a zaune yayinda mazan su ke a tsaye. A hakan su ka yanke shawarar kowa ya yi taimama a jikin bango ko inda sumintin ya farfashe k’asa mai yawa ta baiyyana a samu a yiyyi sallah… Hakan kuwa aka yi, har Amal wadda jikinta ya tsananta karkarwa…su ka yi su na masu jero istighfari da addu’ar su samu su fita su rama sallolin dan su kansu basu gama yarda da sallar ba…Yadikko ta shek’a fitsari a nan inda ta ke ya fi sau biyar dan tun d’azu in ta yi barcinta ta gama fitsarin ne ya ke tada ita Sanin babu halin fita ya sanya ta ke fakar ido ta sake shi a wajen kawai…Wanda abunda ba ta sani ba shine rabin mutanen wajen sun fahimceta musamman ma Anne wadda itama ta yi guda d’aya a zaune lokacin da duhu ya wanzu, ga uban zarnin da ya had’e musu da wari…. Kasancewar yanzu duk wani abun maye ya saki Yadikko ya sanya ta na gama wartsakewa garau ta ji wata mahaukaciyar yunwa ta na kwak’ular kayan hanjinta dan haka ta saka kuka marar sauti domin kuwa ta san tabbas wannan yunwar, dafin kunama da warin amai had’e da zarnin fitsari da duhu sai sun yi ajalinta kafin abunda duk a ke tattaunawa ana jin tsoron fitowarsa daga cikin ramin da ya fi komai d’agawa duk wani na cikin d’akin hankali ya fito, dan dukda sun toshe hakan bai hanasu jin wani motsi-motsi a hankali ba wanda sautinsa ya na fitowa daga cikin ramin ne… Wani kalar wahalallen barci ne ya fara fisgar wasu daga cikinsu dan zuwa wannan lokacin dare ya tsala sosai, masu yi a tsaye su na yi a matuk’ar wahale haka suma na zaune yayinda wasu da ga cikinsu babu alamun ma barci a idanunsu sam saboda tsabar bak’in ciki takaici tashin hankali da kuntatacciyar damuwa.. Anne itama kuka ta fashe musu da shi wae ta gaji dan ta na fara gyangyad’i ta ke k’umewa ga wari ya hanata yin barcin… Sai da mutumin d’azu waenda su su ke a tsaye shi da su Ya Amir ya bud’e mata wuta tukunna ta yi musu shiru… Ya Abba kuwa mik’ewa ya yi Amal ta kwanta a kan cinyar Adda ta mik’ar da k’afafunta a wajensa da nata dan tun d’azu dama ya fahimci zazzab’i ya rufeta yanzun kuwa ya ji numfashi ma da kyar ta ke iya jaa…. Iya wahala sun wahala In banda kukan zuci babu abunda Aliya ta ke yi ji ta ke kamar ta had’iye zuciyarta kawai ta Mutu ko ta samu ta huta… A tsaye mazan su ka kwana a kan k’afafunsu matan kuma a zaune kafin Safiya gaba d’aya jikin kowa ya yi tsami masu ciwon sugar kuwa duk jikinsu ya soma suntuma gawa kuwa ta na ta sake kumbura itama. Bayan awanni biyar… A tare dukkanin su su ka furta kalmar “Alhamdulillah”sakamokon hasken da ya fara ratsowa na gabannin safiyar ranar… Ba su ji ko alamun kiran sallah ba sai haske kawai su ka gani Dan haka wasu a cikinsu suka kare wasu su ka yi tsarki su ka yi taimama sannan aka shiga gabatar da sallar asuba dan zuwa wannan lokacin duk sun farka Anne kuwa ta fuske ba ta yi sallah ba, bayan ta gama sanar musu ba fa za a karb’a ba duk sun yi mata baanza….dama d’azu (jiya) ma ba ta yi ba A nata mentality d’in a yadda ta ke a fusacen nan ko nutsuwar yin sallar ba ta da ita sannan ita har ga Allah ta ce ba a sallah in ba tsarki, dan ita dai ba ta tab’a jin in da aka yi tsarki da dutse ba…. Sai Aliya itama wadda ta ke jinin bik’ii ga shi pad d’inta gaba d’aya ta jik’e d’inkinta ya na yi mata wata kalar azabar zugi da jan ruwa da alamun tsami ya yi… Zuwa wannan lokacin ta ma kasa kuka tsabar bak’in ciki yunwa wahala da azaba sun kai k’ololuwa wajen azabtar da ita… Kunya ce ta fara kama mazan da su ke a wajen domin kuwa daga su sai wandunansu sakamokon kayayyakinsu da su ka sassaka su ka toshe wannan ramin..da sauri sannan kusan a tare duk su ka juya a ka hau zak’ulo kaya ana sassakawa…… Wani Abu mai kama da yanayin sab’ar maciji su ka gani a gaban rigar d’aya daga cikinsu wanda hakan ya sanya hankalin kowa ya tashi chaaa! Su ka tsaya turuss idanunsu a kan ramin. Kallon-kallo aka shiga yi a wajen jikin kowa ya na sake yin sanyi sai kuma su ka saki salati a tare yayinda wasu a su ka rushe da kuka… Tana kuka sosai Anne ta ce “Ku je ku lek’a cikin ramin mana ku duba mana abunda ya ke a ciki dan Allah In na cutarwa ne ku kashe shi…” Cikin daka mata tsawa wannan mutumin dai ya ce “ke dalla Malama rufa mana baki! Mai zai hana ke ki zo ki duba? In muka lek’a kuma da me za mu kashesa? Ko kin ga makamai a hannunmu ne?” Banza ta yi da shi kawai amma ta saka a ranta wallahi in ya sake yi mata ihu sai sun kwashi y’an kallo tabbas.. Tun d’azu ihu ya ke ta yi mata yana jin haushinta ba gaira ba dalili ko uwar me ta yi masa oho…. Dole wasu a cikinsu su ka yi sacrifice su ka sake kwab’e rigunan nasu a ka rufe ramin laba’asa, wanda zuwa yanzu kowa ya tabbatar da maciji ne a cikinsa. Bayan awanni sha biyu… zuwa wannan lokacin duk sun k’arasa fita a haiyyacinsu, Ya Abba shi kam ranar da aka kawosu ma azumi ya yi shiyasa tsabar wahala da yunwa har dishi-dishi ya ke gani, sauk’inta d’aya dai shi fitsari bai kamasa ba kamar yadda ya gigita ragowar har ta kai su ga ware wajen fitsari a cikin gurin. Jikin kowa ya yi la’asar ko maganar kirki ma ba sa iyayi…. Fitsari kuwa za a iya cewa daga Aliya sai Ya Abba da Amal wadda duk wani ruwan jikinta ya fice da hanyar gumi da azabar zazzab’i ne kawai ba su matsa d’aya daga cikin inda sumintin wajen ya fashe wajen ya kasance zallar k’asa sun yi ba. Ganin duhu ya soma yi sosai ya sanya su ka gabatar da sallar magrib sannan aka shiga tunanin yadda za a yi da wannan ramin dan yanzu da su ka fahimci menene a ciki dole hankulansu su ka kai k’ololuwa wajen tashi kuma sun san rigunan su ba lalle su iya hanashi fitowa ba….mazan jikinsu saura wanduna matan kuma iyaka riga ne da zani d’an babu hijabai duk an kwace kafin su shigo ciki. A haka har duhu ya yi musu ba su tab’uka uwar komai ba Anne da wannan mutumin suna ta fad’a kamar za su had’iye juna… Baba ne ya daka musu tsawa duk su biyun d’an haka aka yi tsit su na mayar da numfashi…. Wani kalar nishi suka ji ana yi wanda ya ke baiyyana tsantsar firgici da tsoro, basu kai ga yin wani abun ba su ka ji Aliya ta saki salati sakamokon fad’owar da ta ji Anne ta yi a kan jikinta…. Cikin tsantsar kid’ima mazan da ke a tsaye su ka shiga tambayarta “ lafiya? Mai ya faru?” BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *07* Follow our channel zaka samu daga farko. https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Da kyar ta iya ce musu “Anne ce ta fad’i kamar ba ta numfashi ma” sai kuma ta saki kuka, dukda kuwa abubuwan da Annen ta yiyyi mata tabbas ta ji babu dad’i sosai..Uwa uwace…. Ya Amir shima a take ya rikice hatta Amal itama k’ok’arin tashi ta shiga yi ta zauna yayinda Adda ta shiga k’ok’arin ganin ta k’arasa inda su ke ta na mai tambayarsu “mai ya faru?” A take tsoro ya game su gaba d’aya a lokacin da Aliya ta shiga cewa “Abu ne ya cijeta, kowa ya kula” Kuma k’asa-k’asa su na ji kamar hissing d’in maciji. Fashewa da kuka Adda ta yi haka wasu a cikin mazan da su ke a tsaye dan kasancewarsu maza bai sanya su ka ji rashin tsoron mutuwar da su ke ganin ta tunkarosu muraran a halin yanzun ba. Dudduba Anne Aliya ta shiga yi sosai ta na so ta ji wajen da macijin ya cijeta ko ta samu ta d’aure mata amma ba ta gane komai ba, dukda ba ta ma da tabbacin Annen ta na raye. Mazan ne su ka cewa su Aliyan su nutsu sosai su shafa ta a dubata da kyau ko za a ji alamun wani Abun a san mai ya sameta…in macijin ne kuma a samu a d’aure mata… Chan k’asa wajen guiwowinta duk biyun su ka ji alamun jini ya na fita. Ba su san tak’ameme menene ba Yadikko ta bada d’an kwalinta, sannan aka ciri na Annen aka had’a da shi mazan su kuma su ka daidaici wajen da aka nuna musu da ake jin jinin ya na fita su ka shiga fafutukar ganin sun d’aure mata shi katamau! Suna tab’a y’an kwalayen wani smell ya na fita daga jiki mai wari da k’arni ga kuma danshi saboda daga Yadikkon da take ta kwance har Adda da ma matan wajen duk y’an kwalayen nasu sun shafi amai sosai musamman ma na Annnen lokacin da ta fad’a kan Aliya kanta ya gogi wani ramin da amai ya taru a ciki bai kai ga tsotsewa ba. A hakan..ba sa gani, su ka saita saman inda su ke jin zubar jinin wajen tsoka duka k’afafunta biyun su ka d’aure mata su one by one katamau! D’aurin da ba na wasa ba! Dan in da ace idanunta biyu ba ta kai ga shemewaba tabbas da tuni ta tsala masifaffiyar k’ara. Kasancewar duk a rikice ga shi ba ma sa ganin komai kawai basira ce ya sanya ba su lura da akan wajen harbin su ka d’aure y’an kwalayen duk biyu ba kamar had’in baki Sannan ba su lura sun d’aure mata da masifar k’arfi ba…. Mazan ne su ka tabbatar da ‘duk yadda aka yi maciji ne sai dai su gode Allah dan da ga dukkan alamu macijin ba mai dafi bane ba tunda gashi sarar ta na zubda jini, kuma wani a cikinsu ya tab’a ya tabbatar musu jagular vein d’inta ya na harbawa kawai dai numfashin ne ba a ji..’ Dan haka kowa ya nutsu ya yi shiru watak’ilan ma tsorota macijin ya yi ga kuma hayaniya shiyasa ya fara irin hakan. Dan haka dukkansu su ka yi shiru kowa ya nutsu ya yi tsit a waje d’aya Ita kam Amal dama ba ta ma k’arasa sosai garesu ba amma still sai da Ya Abba ya sa hannu ya janyota ya dawo da ita ta ci gaba da zama a inda ya yi musu kamar katanga daga koma menene, ita da Adda. Kusan awa d’aya su ka yi a haka sai da su ka daina jin motsin komai tukunna su ka shiga neman taimako… Sosai Ya Amir ya ke jijjiga gate d’in ya na hawaye ya na jin Aliya ta na cewa “ta mutu fa! Ba ta motsi, ko hannunta in na d’aga komawa ya ke yi… Haba dan Allah, Y’ar tasu y’ar gwal ce ne? Saboda an mareta shine za su kashemu gaba d’aya wanne kalar rashin adalci ne wannan? Ya za su saka mu a waje mai had’ari kalar wannan fisabilillahi…” Ta na maganar ta na sake k’ank’ame Anne da gawar d’anta wadda ta ke ta sake suntuma sosai. Ihu da kukan duniya babu kalar wanda ba su yi ba, amma aka k’i kulasu..haka nan su ka hak’ura su ka koma kowa ya zauna zuwa wannan lokacin duk sun fita a haiyyacinsu babu k’arfi babu lafiya…sama da 24hours kenan babu abinci… Haka nan su ka shiga addu’a wasu su na kuka, sannan Ya Amir da Aliya su ka saka Anne a addu’oinsu da fatan ba ta mutu ba, duk wannan bidirin da ake yi Baba bai ce musu ku ci kanku ba, addu’oinsa kawai ya ke yi ya na istighfari wanda suma d’in suna kammala fafutukar d’aurewa Anne k’afafunta tamau da ife ifen neman agaji su ka jona shi…a haka su ka dinga addu’a ba tare da idanunsu su na gane musu juna ba sai dai fa duk wani motsi na Amal Ya Abba ya na sane da shi sarai….. A haka gari ya waye musu wanda su na duba Anne aka tabbatar da maciji ne ya cijeta saboda ga jini nan ya na ta fita, kuma ashe a k’afar hagu har sau biyu ya cijeta wajen cinya inda ya ciji d’ayar da alamun tsakiyar k’afafun nata ya shige ita kuma ta ji tsoro ta matseshi shiyasa ya yi mata a duka k’afafun a saiti d’aya, da kuma sangalalin k’afarta ta hagu nan ma maybe da ya zo fita ne, dan haka Adda ta sake bada d’ankwalinta aka d’aure dukda su na da tabbacin in ma dafin ne ya gama zuwa har zuciyarta sannan ba lalle mai dafi bane ba, amma gara su yi mata iyakar taimakon da su ke ganin za su iya. sai dai sauk’in abun sun fahimci kamar ba mai dafi bane ba dan gashi ta na a raye har zuwa lokacin pulse d’inta Sun shaida hakan, kawai dae suman ne ba su san na menene ba hala tsorata ta yi ko kuma dae wani abun da ba su san da shi ba, shiyasa ba su yi gigin kunce d’aurin da su ka yi mata ba dan basu tab’a jin irin hakan ba gashi sun ga k’afar tata daga inda ya cijetan su ka d’aure zuwa k’asa har ma Da sama-sama koina ya chanja colour sosai. Yayinda ake da tabbacin itama Yadikko wani kunamar ne ya sake cizonta dan gari yana wayewa su ka ganta a sheme, babu alamun cizon maciji a tattare da ita amma ta sheme itama, akwai dai pulse kamar na Anne sai dai kwata-kwata ba sa motsi daga ita har Annen jijjigawar duniya an yi amma sun k’i su farka. Macijin ya tafi sai dai ramin har yanzu bai gama rufuwa ba dan haka ganin dare ya doso ya sanya su ka bada himma aka toshe shi da kyau su na masu fawwalawa mai sama komai… In ka gansu sai ka yi musu kuka kaff cikinsu Ya Abba ne kawai ya ke iya tsayuwar kirki kuma babu alamun wahala a tattare da shi amma gaba d’ayansu wasu ko idanunsu ba sa iya bud’ewa sosai… Wari! Yunwa! Uzuri wanda zuwa yanzu kusan kowa ya yi nasa atleast once a wajen, ne. Ga tsoro fargaba da tashin hankali gaba d’aya su suka taru suka sanya kawai wasu a cikinsu su ka fara yiwa kansu fatan mutuwa yayinda su Aliya su ka cire rai da Anne da Yadikko dan sun san ba zai yiu a ce maciji ya cijeka ka yi awanni sama da ashirin da hud’u ba a duba ka ba sannan ka rayu..dukda mazan wajen su na ta basu assurance d’in za fa ta tashi ba ta mutu ba tunda ga shi pulse d’Inta su na harbawa wata kilan doguwar suma ne ta yi, amma su kam gani su ke yi da kamar wuya…ana kaita asibitin ma za ta wuce. Bayan sun idar da sallar isha, a lokacin da duhu ya wanzu tsoro ya na sake gamesu kawai su ka ji d’aya daga cikin mazan wani tsoho sosai ya yi salati sai kuma k’arar fad’uwa wadda ya yi ta a kansu Aliya, ba su kai ga gama shiga cikin mad’aukakin tashin hankali ba su ka ji wani ya sake sakin ihu sai dai shi bai fad’i ba kuma bakinsa bai mutu ba!!! Kamar an kunna su haka nan su ka hau kuka su na ihu har Adda Amal kuwa masifar zazzab’i da yunwar cikinta ya sanya ko motsi ma bata iya yi ba kawai ta shiga nanata kalmar shahada… Da sauri Ya Amir ya mik’e kamar jiya yau ma ya hau jijjiga gate d’in dan zuwa wannan lokacin salatin mutum na uku kenan suka ji, sannan duk su na cewa “Nima ya cije ni” A hankali Ya Abba wanda gaba d’aya jikinsa ya yi sanyi duniyar ta ke juyawa ma ya mik’e ya k’arasa inda ya ke jiyo muryar Ya Amir su ka kama bockler d’in a tare su na jijjigata this time around da niyyar su fasheta kawai..su na a haka su ka ji wani mutumi a cikin mazan shima ya saki salati sai kuma ya soma furta kalmar shahada a hankali…. Da sauri Ya Abba ya juya ya na kiran sunan Amal!! Amal!!! Wadda ta yi mutuwar tsaye… Shi da Adda kusan a tare su ka damk’o hannunta jin ta amsa da “na’am” Cike da fargaba da masifar tsoron rasata ya janyota ya sakata a gabansa jikin k’arfen ya had’ata da k’arfen da jikinsa sosai wanda dukda halin da su ke a ciki na k’ololuwar tashin hankali da matsananciyar fargaba hakan bai hanasa jin wani masifaffen yanayi ya dirar masa mai wuyar misaltuwa ba… Da kyar jikinsa ya na wani kalar karkarwa ya had’e k’afafunta a cikin nasa ya yi mata ta yadda ko abun ya zo in ma cizon ne sai dai shi ya fara cizonsa sannan da wani kalar masifaffen k’arfi ya ci gaba da bugun k’arfen yana sauraren siririyar muryarta ta na kuka ta na cewa “Ya Abba meye haka? Ka cika ni ba na so….” In banda ihu da kururuwa ba bu abunda ya ke tashi a wajen dan zuwa wannan lokacin ko ba a gaya musu ba suna da tabbacin macijin ya ciji kusan duk mutanen wajen, sauk’in abun ma suna jin salati da muryoyin wasu har yanzu, wanda a tunaninsu gubar ba ta kai ga k’arasa game musu jiki ba ne….. Kamar a mafarki Amal ta ji muryar Ya Asad ya ce “lights pls…” BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *08* BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM.... Tarr!! Haka haske ya wadatu a wajen, wanda hakan ya sanya su ka fahimci ashe akwai bulbs a wajen tsantsar baƙar mugunta ce ta sa aka ƙi kunna musu kenan.... Wata kalar masifaffiyar kunya haɗe da takaici ne su ka hana Amal motsi a wajen kawai ta sunkuyar da kanta ƙasa dan tun da aka kunna wutar Ya Asad ya kafeta da idanuwa ko kyaftawa ya gagara yi... Ihun jama'ar da su ke a bayansu ne ya katse yanayin dan haka da Abba da Amal su ka juya yayinda Asad ko gezau bai yi ba kallonsu kawai ya ke yi, kuma da wuya ka fahimci yanayinsa..... Macizai ne har guda uku(garter snakes) su ka yi nashe-nashe a tsakaninsu sai wasu irin baƙaƙen kunami da su ka cika wajen, wanda ganinsu ne ya sanya jama'ar wajen yin ihu... Zabura itama Amal ta yi wanda hakan ya yi dai-dai da kunnawar wani sauti marar daɗin sauraro very low sannan kamar vibration, cikin rawar jiki ɗaya daga cikin securities ɗin wajen ya ce "wallahi sir it wasnt intentional, mu ma haka nan macizan nan su ka addabemu shiyasa ba ma rabuwa da wannan ƙarar...." Ya yi maganar ya na mai kunce kwaɗon gate na cel ɗin sai kuma ya zare sakata har guda uku jikinsa ya na rawa ya na satar kallon Asad wanda har yanzu ya kafe Amal da Abba da idanu...... Kamar ba shi ke yi musu tsawa ɗazu ba dan yanzun cikin lallaɓawa ya ce musu "your release has been granted, you can go.." Tun da aka kunna ƙarar dama macizan su ka gudu waenda duk wanda ya sani da ya kallesu ya san ba masu dafi bane ba. Kunamin suma guduwa su ka yi zuwa cikin wannan ramin yayinda kowa ya fahimci tsoro ne zallah kawai ya sumar da Anne, Yadukko da waennan tsoffin bayan macizan sun cije su, dan ana kunna wuta ragowar waenda macijin ya sassaresu su ke ta ihu.. rass su ka ware... Miƙewa Aliya ta yi yayinda Amal ta yi saurin ficewa daga wajen ana buɗe ƙofa wuff! Bata yarda ta kalli inda Asad ke tsaye ba. Ko kallon Anne Baba bai yi ba su ka kama Yadukko shi da Adda su ka wuce da ita yayinda wasu mutane da su ke kyautata zaton Asad ɗin ne ya zo da su su ka shigo cikin wajen su na tayasu ɗibar marasa lafiya... A hankali Cikin yanayinsa Ya Asad ya ce “come closer “ Wanda ba dan hankalin Securityman ɗin ya na a kansa ba da ma chan to da ba zai jiyo sa ba. Matsawa ya yi su ka ɗan yi magana daga haka ya ɗaga masa kai ya ce “yes sir” kafin ya juya ya je ya tsaya a bakin ƙofar fita daga wajen kawai ba tare da ya ce komai ba, yayinda ake ta fafutukar fita daga wajen. Tunda Ya Abba ya ga hakan dama ya san mai ya faru haka kurum jikinsa ya bashi hakan shiyasa kawai sai ya jaa ya tsaya bai ko motsa ba daga yadda ya ke ba. Kusan tare za a ce an ga Ya Asad shi da jama'arsa da kuma wasu mutane sun baiyyana a wajen(mace da polisawa biyu), sai dai su ɗin wani uniform ne na manyan polisawa sosai a jikinsu sannan tare su ke ta tsaye a gefe da yayinda matar da su ke tare da ita take ta kuka ta na sharar kwallah..wanda tashin hankalin da kowa ya ke a ciki ne bai sanya sun maida hankali wajen sanin ba'asin abunda ya kawota wajen ba.... Sai da Aliya ta zo fita ta fara ƙoƙarin kinkimar Anne ita da Ya Amir tukunna su ka ji amfanin zuwan mutanen wajen... Wae.. 'Bayan an kawosu nan cel ɗin ashe an bincika gidan ne sosai saboda Sajida ta ce Anne har sata ta yi mata ta kuma duba sarƙarta ba ta samu ba, to garin bincike aka kama Anne da laifin tsafi da ƴaƴan da aka jima ana nemansu bayan an yi garkuwa da su watanni biyu da su ka wuce. Dan haka za su ci gaba da riƙeta a wajen kafin a wuce da ita inda za a binciketa!!. Su kansu saboda Ya Asad ne ya sanya aka barsu su ka fita sannan kayan Yaran da shaidu a cikin iyaka ƙasan wajen kayayyakin Anne aka samu inda ta haƙa ta binne da alamun ta ɓoye ne dan kar su kansu su gani..amma da an ce kar a bar kowa na gidan ya fita, Ya Asad ne ya tsaya musu kuma an san ba su da laifi daga bayanan mutanen unguwaa kowa Anne ya ke cewa da kuma wasu shaidu ta su ka sake baiyyanata ita kaɗai shiyasa aka samu aka sake su dan haka an yi releasing ɗinsu su tafi amma banda Anne..... Suma amma ba a bawa kowa damar barın gari ba har a gama case’. A fusace bayan ta kammala jin bayanin nasu mai ban tsoro da damuwa, Aliya ta ce "Amma dae ae atleast kwa kaita asibiti a duba lafiyarta ko?" "Ƴaƴan da aka kamata da laifin yin garkuwa da su ƴaƴan alhaji sale mai fetur ne!!" Mutumin ya yi maganar ya na tsatstsareta da idanuwa yayinda itama ta zazzaro idanu waje ta na mammakin yadda Anne ta samu kwarin guiwar iya sace sannan ta aikata aikin tsafi da ƴaƴan babban mutum kamar wannan... Maganarsa ce ta katse mata tunanin da ta ke yi jin ya ci gaba da cewa “dan haka ko motsawa daga inda take an ce kar a barta ta yi….ku ma d’in shaidun da ƴan unguwa su ka bayar da sunanta da aka gani a jikin sassan jikin Yaran da kuma ragowar shaidun da su ka tabbatar da ita ɗaya ce mai laifi sai kuma taimakon sir wanda ya tsaya muku ne ya sanya kawai za mu barku ku tafi. Dan haka ki tashi ki fita ku je ku binne Yaron nan ko kuma in ci gaba da riƙe ku a wajen ke da shi da ita….” Ya ƙarashe maganar cikin daka mata tsawar da sai da ta sanyata zabura. Tabbas ita a karon kanta ko me in aka ce Anne ta aikata to fa ba za ta taɓa musawa ba! To amma yaushe? Ta yi wa kanta tambayar cikin tsantsar ruɗani da tashin hankali... Baba dama ko tsayawa bai yi ba, Ya Amir shima hawaye kawai ya share ya fice, a hankali Aliya ta rungume jaririnta wanda uban warin da ya ke yi da suntumar da ya yi bai sanya ta jefar da shi ba, ta fita ta na kuka sosai da tunanin yadda za su yi, dan tabbas ba ta hango musu ko da kyallin mafita a case ɗin Annen nan ba. Aliya na fita waje matar nan da ta zo da sojojin ta matso, cikin sheshshekar kuka ta ce musu “dan Allah ku bar ni in kalli fuskar matar ko da sau ɗaya ne, Matar da ta yi mini yankan ƙauna” A hankali police ɗin ya ɗan sunkuyar da kansa alamun tausayawa da girmamawa a gareta sannan ya ce “to ranki ya daɗe” Daman wajen ya rage Ya Abba da Anne ne kawai, sai Polisawan da au ka shiga mutum biyu dan haka su ka sake kafa ido sosai domin su bata kariya ta gama ganin fuskar Annen dan tunda suka ga fuskar ƴaƴan matar da hannayensu da ƙafafuwansu a tukunyar ƙasa daban daban an haka ƙasa a saka su a ciki da layoyi, kayan tsafi, rubuce-rubuce da dai abubuwa kala-kala aka ce Anne za ta iya aikata abunda ya fi tsafi ma dan haka a bata tsaro babba sannan a keɓanceta saboda gudun kar ta cutar da wani… Su na shiga aka juyo mata da fuskar Anne, Ashe matar da tsuminta ta ke tafe.. Ta na kuka ta ɗaga hannunta babu wanda ya yi la'akari da kwalbar hannunta sai da ta fara tsiyayeta a fuskar Anne wadda azabar zafin acid ɗin ya farfaɗo da ita daga doguwar suman tsoratar da ta yi sai kuma ta sake sumewa... So su ke yi su wafce kwalbar amma matar ba ta basu damar yin hakan ba dan in su ka kwata ta ƙarfi to fa tabbas za su ɓata kansu da ita kanta matar da aka ce musu su tabbata sun bata kariya daga Anne under any circumstances..kuma sun fahimci acid ne a ciki. Gashi ta na cewa ‘in su ka taɓata sai ta ɓata kowa a wajen shiyasa ba dan ransu ya so ba su ka gagara kwace kwalbar na tsahon wasu ƴan sakanni daga hannunta… Ya Abba ne ya ƙaraso wajen daga jin hayaniyar, ya na zuwa bai yi wata-wata ba ya buge hannunta gefe kwalbar ta faɗi ta fashe a wajen Sai a lokacin su ka shiga ƙoƙarin bawa Anne kariya wadda aka juyewa acid ɗin gaba ɗaya a fuskarta da ƙirjinta. Ko da su ka yi waya su ka sanar da halinda ake ciki dole aka basu umarnin su kaita asibitin da ke a kusa.. Amma su tabbata sun saka mata ankwa sannan ana tsaronta gudun kar ta gudu… Su kansu sun yi mamakin yadda ta ke a raye har kawo yanzun amma kawai sai su ka wuce da ita zuwa Asibitin da a ka ce su kaita ɗin. Su na gama fita da Anne Ya Asad ya juya shima ya fice ba tare da ya ko kalli inda Ya Abba ya ke tsaye ba. Kamar ba zai yi yinƙurin fita ba sai kuma ya sa kai idanunsa a kan police ɗin da ya ga kowa ya wuce ya barshi kamar an ce ya yi gadinsa ne… Dakatar da shi kawai ya yi da hannunsa sannan ya ce masa “ɗan jira tukunna" A hankali Ya Abba ya lumshe idanunsa kawai sannan ya saki wani ɗan guntun murmushi ya koma ya zauna zuciyarsa na ƙarasa ƙuntata. Amal da ta riga su fita ja ta yi ta tsaya ta na haki sosai jiri ya na ɗiibarta haka suma ragowar duk su na jiran Anne ta fito a tafi tare gaba ɗaya a kaita asibiti su wuce dan mutanen da ya Asad ya zo da su sun gama saka kowa a mota su na shirin kunnata Adda ta ce "a jira akwai Ya Abba Aliya Amir da Anne.." Dama shi Asad ya zo da su ne akan su kwashi kowa a kai asibiti a yi checkup a duba lafiyarsu dan haka su ka ja su ka tsaya, ana tunanin abunda ya hana su fitowa.. Fitowar Ya Amir da Aliya ta na kuka ne ya sake kiɗima su dan haka aka ƙarasa aka shiga tambayarta "mai ya faru?" Cikin sheshshek’ar kuka ta ce “Anne ce…” Sai kuma ta sake rushewa da kuka Dai-dai ta ƙarasowar Kaka Nura cikin wajen shi da waensu polisawa waenda ko ƙadangare ba lalle su iya arresting ba.. Dan su na shigowa aka dakatar da su shi kuma aka barshi ya wuce bayan wani a cikin drebobin Asad ya shaida shi ya sanar musu cewa jikokinsa ne aka kama dan haka aka barshi ya wuce ciki. Yana shiga kuwa ya hangosu dan haka ya ƙarasa zuwa garesu ya na haki ya na kallonsu one by one ya na neman ƴarsa a cikinsu, ya ce “awanni na ashirin da bakwai Ina neman polisawa da kyar na same su. Ga su chan sai dai na ga kamar har an fito da ku an sake ku kenan. Wallahi bari mu fita a nan, sai na ci ****uban Sajida, bayan an kawoku nan fa sake komawa su ka yi, bincike kala-kala babu inda ba su fasa ba a cikin gidan nan da kyar na gudu na sha...na bazama neman ƴan sanda" Sai kuma ya dasa aya kafin ya ce "Ina Nuratu?" Ya yi maganar ya na sake kallonsu sosai har yanzu ya na haki.... Kuka Aliya ta fashe da shi dan haka a rikice ya kamota yana mai karɓar jaririn hannunta yanna salati wanda masifaffen warin da ya ji ya sanya bai iya ci gaba da riƙewa ba dan haka ya miƙawa Amal ba tare da ya ko kalleta ba saboda haushin Yarinyar ya ke ji sosai, ya ce “Ina ƴata?” Cikin tsantsar ɓaacin rai. A hankali Aliya ta ce "Maciji ne ya cijeta tun jiya ba su duba ba ta na ciki, kuma yanzu sun ce wae mu sun sake mu mu tafi ita kuma za su ci gaba da tsareta wae ta yi garkuwa….” Ashar ɗin da ya zabga ne ya sanya ta gagara ci gaba da maganar kawai ta sake rushewa da kuka. Bai Ida rufe bakinsa ba aka fito da Anne a kan wani zani da su ka ware kamar labule su ka zurata a ciki. Kasancewar fuskarta a tsundume ta ke cikin zanin ya sanya duk ba su gane a yanayin da ta ke ciki ba, kayan jikinta ne ma da ya leƙo ta wajen ƙafafunta da leɓunan ƴan kwalayensu da su ke reto ya sanya su ka shaidata dan haka duk su ka ɗunguma zuwa gareta. Kafin su ƙarasa Ya Abba shima ya fito sai dai shi da ganinsa ba sakinsa aka yi ba dan tsaronsa ake ci gaba da yi da alama, tunda gashi bayan wanda ya hanasa fitowa har da wani poliçe aka sake k’ara masa su ka zama su biyu. Da sauri Ya Amir ya ja da baya sai kuma ya fashe da kuka, ragowar mutanen suma duk baya su ka ja aka hau salati yayinda Kaka Nura ya ƙarasa da sauri ya na mai riƙe zanin dan mutanen ba su tsaya ba… Wani kalar masifaffen tashin hankali ya shiga a take dan gaba ɗaya kasa motsawa ma ya yi da ganin fuskar tilon ƴar tasa a haka kafin ya tafi luuuuu ya zube a wajen kamar mai shirin suma cikin tsantsar tashin hankali… Da kyar su Ya Amir su ka taro shi shi da Ya Abba wanda ya ƙarasa garesu cikin zafin nama, dan ya basu tsoro sosai. Cikin tsantsar firgici su ka tsayar da shi ya tsaya da kyar ya na faman tangaɗi.. Ganinsu cikin tashin hankali ya sanya Adda ta buɗe ƙofar van ɗin ta fito ta ƙaraso wanda hakan ya bawa Kaka Nura damar hango Baba a zaune a ciki ya na kallonsu bai ko motsa ba. Aikuwa bai bari ya kai ga Ida dawowa dai-dai ba ya ƙarasa gaban motar ya finciko Baba sannan ya saita fuskarsa ya kifa masa mari sai kuma ya hankad’esa ya faɗi kana ya bi shi ya danne da niyyar fara kimarsa aka ɗaukesa yaana ta kici-kici ya na hawaye sosai ya na cewa "tabbaas kam ka kasheni, kisan murus ka yi mini wanan kisan tsaye kenan, amma wallahi ba ka isa ba mutuwar kasko za a yi wallahi Allah...." Ya yi maganar ya na mai fincikewa ya sake yin kan Baba wanda ya Amir ya taimakawa aka miƙar, amma sai aka tarosa... So ya ke yi ya isa garesa wallahi yau sai ya yi ajalinsa dan a yadda ya ke jin kansa tsaf sai ya tabbatar masa shi ɗin fa ba tshoho bane ba alhalin a zahirin gaskiya ko tureshi aka yi sai ya faɗi ya ji babban rauni dan a hakan yadda ya ke ta fisge-fisge mutum ɗaya ne tak ya riƙesa da hannu ɗaya. Daga gefe wasu ƴan sanda guda biyu su ka hangosu dan ragowar har sun wuce da Anne bayan an dakatar da kowa daga binsu. Ya Abba shima sun wuce su uku ba tare da kowa ya lura ba.. Ɗayan ne ya taɓo ɗayan ya ce masa "duba ka ga wani tsoho mai k’arfin Hali" Dan haka su ka tunkarosu wanda zuwan na su ne ya taimaka Kaka Nura bai sauƙewa Baba uban dutsen da ya rarumo bayan ya kwaci kansa ba. Da kyar aka rabasa da dutsen sannan aka rirriƙesa ya na ta faman fisge- fisge ya na cewa “tabbas kam ka kasheni! Ka cika alƙawarinka da ka yi mini shekaran jiya.. Allah ya Isa tsakanina da kai! Mai ta yi maka haka da zafi? Laifi ae ni ne na yi maka!…” Ko ta kan su Ya Amir da su ke sanar masa ba fa Baba ne ya yiwa fuskar Annen haka bai bi ba gani ya ke makircin Baban ne ya sanya ba su fahimci shi d’inne ba…dan haka bai yarda da zantukansu ba sai ma zaginsu da ya fara yi yana cewa "ae suma sun san maciji ya cijeta amma su ka barta a ciki a haka kowa ya fito maimakon su tsaya da ita har a sake ta, saboda su ɗin ƴaƴan iska ne!” Ya na bala'i da zage zage ya na kuka sosai yadda duk wanda ya gansa daga nesa bai ji kalar zagin da ya ke ba sannan bai san wayene asalin Kaka Nura ba tabbas sai ya koka masa..dan ashar in ya lailayo wani sai ya yi kusan minti ɗaya tukunna zai kai ƙarshen ashar d’in…. Tsabar bala’i da tashin hankali a take numfashinsa ya sarƙe amma dukda haka iƙirari ya ke yi wallahi wallahi sai ya kashe Baba. Ko kallon Yadukko bai yi ba wadda ya gani a cikin moto itama bata da maraba da gawa kawai shi ta tashi ƴar ya ke.. Cikin bada umarni wani babban mutumin ya fito daga cikin building ɗin da alamun shi ne oga, ya umarcesu da "Su shiga moto duk a kaisu asibiti kamar yadda Asad ya bada umarni, Kaka Nura kuma ya wuce ya tafi shi kaɗai kar ya bisu, duk su watse, su fice musu daga harabar gurin.." Dan ya ga mutanen dramar su ta fi ƙarfinsu. Sai a lokacin ne da Adda ta duba ta nemi Ya Abba ta rasa da kusan duk baƙaƙen motocin da su ka fito su ka tarar a harabar wajen..... BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *09* Dama Amal ba ta so ta tsaya ta sake ganin Ya Abba kuma duk ji ta ke kamar ta nutse dama, ganin ba ta ganshi kusa ba ya sanya ta wuce ta shige ta zauna a chan inda ko ya shigo ba lalle ma ya hangeta ba, saboda wata masifaffiyar kunyarsa ta ke ji da duk mutanen wajen ma, ita dae ta san Ya Abba ba ɗan iska bane ba amma ba ta san mai ya sa ya yi mata hakan yau ba, fisabilillahi in zai bata kariya ae ba haka ya kamata ya yi mata ba sannan tsabar neman magana maimakon ya haɗa ita da Adda shine ya zaɓi ya ja mata magana a idanun kowa ta hanyar damƙota da ya yi ita kaɗai sannan ya wani matseta gashi yanzu kowa ya gani ya shaida..... Adda kuwa tsayawa ta yi ta na rarraba idanu ganin babu shi (Ya Abba) ba alamunsa kamar walƙiya ya ɓace a wajen ya sanya ta ƙarasa gun mutumin ta shiga yi masa bayanin 'nata ɗan bai kai ga fitowa ba tukunna, ko lafiya?'. Kansa tsaye ya ce mata "ta wuce ta tafi zai taho daga baya” sannan ya umarci mutanen da su ka dawo daga fidda Kaka Nura daga wajen itama su fitar da ita in ta yi taurin kai. Amal ta na ƙarasa zama a cikin motar wani nannauyan jiri ya kwasheta, ragowar mutanen suma har su Ya Amir kowa a wahale ya ke ba iya gane abubuwa su ke yi ba zuwa wannan lokacin, shiyasa ko da Adda ta leƙo ta ce su wuce kawai su ka zaɓi su kaisu asibitin ita a barta kamar yadda ta buƙata saboda ranta ita kaɗai da ɗan da ake ta ce mata an wuce da shi wani wajen wataƙila shima dubasa za a yi bai kai ya janyo a rasa rayuwar mutanen da su ke cikin motar ba... Baba ya so ya yi gardama amma ta ce "ya je kawai, ya tafi ya kula da su Yadikko shi da Amir, za ta jira Asad a gate, ta na son yin magana da shi." Dan haka su ka ja motar su ka wuce ita kuma ta nemi waje a wajen ta zauna wanda nan ɗin ma masu gadi su ka ce sai dai ta tashi. Sai da kuwa aka yi mata alƙawarin sake arresting ɗinta muddin ba ta bar wajen ba tukunna ta yarda ta bar wajen ta na wani kalar kuka mai cin rai dan kanta tsaye da farko ta ce musu "babu inda za ta je ba tare da ɗanta ba. Za ta zauna ta jira shi a wajen, sai dai su kamata." Ganin su na shirin kinkimarta su matsar ta ƙarfin tsiya ya sanya ta bar wajen ta koma chan da nesa inda za ta iya ganin gate ɗin, da niyyar ta na gani an buɗe za ta taso ta zo ta tsaya ta tare hanyar sai dai motocin Asad su bi ta kanta wallahi amma bai isa ya tafi ba tare da ya saki Abba ba.....dan ko shakka babu wata uwar muguntar sabuwa fil zai sake gwada masa... Dama tunda ta ga yadda Asad ɗin ya yi bayan ya gansu shi (Abba) da Amal a wannan yanayin ɗazu tabbas ta san a rina…saboda tsabar kishi ya rufe masa idanu ya ma gagara fahimtar kariyar da Abba ya ke bawa Amal ɗin a wannan lokacin itace abar dubawa sama da yanayin da ya gansu...a yadda ya ke tsagwaron marar imanin nan kuwa ba za ta barshi da Abba wanda ta san ba shi da wani wanda ya tsana sama da shi ba, sannan yanzu ga abunda ya sake gani...Mutumin da ba a san matsafi ne ko aljani ko maye ba, Anne ita ta ga suruki amma ita kam ko a mafarki ba ta ƙaunar dama Allah ya haɗa Amal da Asad.... Ta na wannan lissafin idanunta kyar akan gate ɗin wajen ta na sharar kwallah... Wallahi ba za ta barshi ba yau kam ko zai lashe mata kuruwa itama sai dai ya lashe. Rashin imaninsa ya yi yawa a Abban..abubuwan da su ke gwada masa its not fair... Haba mana! Kamar ba uba ɗaya ya ke iƙirarin ya haifesu ba!... Ta san ba ta da ƙarfin komai akan Asad amma tabbas ko za ta bada ranta fansa a tilon ɗanta za ta yi domin ta yi freeying nasa da ga azabtarwar da Asad ya ke yi masa.... dan haka ta gyara zama ta ci burin haɗuwarsu a yau wanda abunda Addan ba ta sani ba shine tun ɗazu kafin su fita Asad ɗin ya wuce ya fice ta gate ɗin baya shi da motocinsa lokacin hankalinsu gaba ɗaya ya na a kan Anne da faɗan Kaka Nura da Baba, dan ji ya ke yi ko da zai zuƙe iskar wajen gaba ɗaaya ba za ta ishesa ba shiyasa ya yi wuff ya wuce gudun kar a samu matsala. Sai da aka kusa arresting Kaka Nura shima ɗazu, fahimtar da ya yi faɗa da Baba ba shine mafita ba a lokacin ya sanya kawai ya rabu da shi ya nufi inda ya samu aka gaya masa Annen ta ke da kyar bayan ya samu ya lallaɓa ya rabu da ƴan sandan da ya lura sun fusata da behaviour nashi, lafiya. Su Ya Amir kuwa, duk yadda su ka so ba a barsu sun je sun dubata bayan an gama duddubasu ba..an tabbatar musu ba za a barsu su ganta ba sannan Asad gida ya ce a kaisu kawai, dan haka direct gidan aka nufa da su aka kaisu har layinsu ƙofar gidan Baba aka sauƙesu, Yadikko ma an dawo da ita dan ta dawo dai-dai... Wannan tsohon da ya faɗi ne ba a dawo da shi ba saboda sun duba sun ce still ya na buƙaatar hutu, sai wani a cikin mazan shima sugar ɗinsa an ce ya taɓu sosai....sai gawar ɗan gidan Aliya wadda su ka yiwa wanka a chan a ka shirya su Baba su ka je su ka binne su ka sake komawa wajen. Ko da su ka isa unguwar tasu chaa aka yi musu tun daga bakin titi wasu su ka biyo motar ana tambayarsu mai ya faru tare da jaje yayinda waensu gulma ne da farin ciki ta fito da su… Ragowar mutanen yawanci ake ta kulawa dan gidansu Baba an ce su suka janyowa kansu. Iyalan waenda ba su kai ga dawowa ba kuma su ka bi maaikatan lafiyan aka koma da su domin su je su gansu su yi jinya. Tabbas kam an yi musu bincike na rashin mutunci ma kuwa dan babu abunda ba a fasa a cikin gidan ba. Ba su da nutsuwar tattarewa dan haka ɗakin Yadikko kawai aka gyara aka shimfiɗar da ita, su ka barta da nurse ɗin da aka ce za ta dinga monitoring Amal na kwana huɗu, tukunna Ya Amir da Abokinsa dan Aliya sai da aka sake yi mata wani ɗinki shiyasa ko tsayuwa ba ta iya yi sosai tsabar azaba da zazzaɓi...dan haka su ka bazama su biyu wajen mai Unguwa da fatan ko akwai abunda zai iya yi musu a lamarin na Anne wadda ya kamata a ce jinya ta ke yi yanzu ba wai a tsareta a hannun ƴan sanda ba. Dukda sun san asibiti a ka ce an kaita amma still tsarone tunda gashi sun ƙi su bari a ganta ko a yi jinyarta dan haka sun san ba za a bata kulawar da ta kamata ba. Yayinda Baba ya tafi neman Adda da jin baasin rashin sakin Ya Abba da aka yi. Tashi ɗaya mai unguwa ya sanar musu babu taimakon da zai iya yi musu a kan Anne sannan ya basu tabbacin in har case ɗinta ma ya na shirin taɓa masa area to sai dai su tashi dan ba zai yiu ya tsaya Anne ta maida masa unguwa wajen zuwan sojoji da ƴan sanda kullum ana hayya-hayya ba gashi dae shirun da ya yi ya sanya ta je ta taɓo mutumin da wataƙila har su ta gogawa kashin kaji... abun nata ya yi yawa, a barshi ya ji da case ɗin su Yagwalgwal ma kaɗai da su ka addabi kowa.. Sosai mutumin ya bawa Ya Amir mamaki dan kamar bai sanshi ba haka nan ya yi masa.. Kamar ba Abokin Baba ba shima amma da ya yi la'akari da yadda Baban kanshi ya yi wa Annen da kuma halinda ya ke a ciiki yanzu duk saboda ita sai ya yiwa mutumin uzuri su ka tafi neman wata mafitar... Kafin awanni biyu kacal labarin abunda ya samu Anne ya zagaye koina na Unguwar har wajenta yayinda mutane da yawa su ke ta binta da fatan 'Allah ya ƙara!' Dan kaff a areansu kai tsaye za a iya cewa babu wanda ya tausaya mata kowa ya san halinta ne ya ke binta..... Bayan kwana biyu... Wannan mutumin da tshoho har sun dawo gida, yayinda Adda itama ta dawo bayan mutanen nan maaikatan lafiya sun je sun rarrasota da kyar tare da Baba. Ya Abba dai ba su ma san ina ya ke ba. Kamar yadda su Ya Amir su ka zata Anne a ajjiye kawai ta ke har yanzu ba a fara bi ta kan lafiyarta ba, yayinda kowa ya ke jajanta yadda ta kasance a raye har zuwa wannan lokacin domin an tabbatar musu da ta na raye kawai dai ba a barsu sun ganta ba....wae pain reliever kawai ake bata, a taƙaice dai su na jinyar tata sai dai ba ta kai ta kawo ba shiyasa su Ya Amir su ka saka abun a mazaunin ba a kula ma da ita kwata-kwata....dan ko farfaɗowa ma ba ta yi ba har kawo yanzun an dai jona mata ruwa sannan ana mata pain releiver ta, an fi maida hankali akan tsareta da binciken su tomb print nata akan lafiyarta. Likitocin fata dae sun zo sun dubata ana jiran na ƙafar da aka tarar a ɗaure su ƙaraso har yanzu...yayında aljuhu Kaka Nura ya ke ta ihu har sata sai da ya yi jiya tukunna aka samu a ka yi mata allurarta. A kwana na uku aka samu ta farfaɗo sai dai ko da ta farfaɗo ɗinma kamar sumammiya haka nan ta ke a jangaɓe! Dan ta na azabtuwa ne gwargwadon iko.... Kawai dai ta kan shaƙi numfashi ta ambaci sunan mahaifiyarta daga nan ta koma ta ci gaba da abunda za a fi kiransa da suma dan azabar wahala take sha ba ta wasa ba…sam! Pain releiver ba ta yi mata aiki yadda ya kamata kuma ashe da wuri ta ke sakinta da zarar sun yi. Da yake an tula maaikatan tsaro a ɗakin sai wajen ya zama kamar wani police station, likita ɗaya ne kawai kuma fanninshi bai shafi abubuwan da su ke damunta ba an ce ya tsaya kwararru su zo... Kaka ne kaɗai a wajenta dan an ce in banda iyaye ba za a bar kowa ya ganta ba. Kaff ƴan arean nasu babu wanda ya yarda ya taimakawa su Ya Amir dan case ne babba Anne ta jangola babban ɗan kasuwa ne a Nigeria, ko ma ace Africa gaba ɗayanta mutumin da ta yi garkuwa da ƴaƴannasa dan haka dole su ka haƙura su ka dawo zuciyoyinsu duk a dagule. Anata shiga gidajen maƙofta a na yi musu jaje yayinda su kuwa babu wanda ya leƙo su dan ƴan Unguwa zuwa wannan lokacin kowa tsoron shiga harka su ya ke yi duba da yadda mutanen layin da su ka yi musu kara lokacin rasuwar ɗan gidan Aliya duk su ka ƙare a cel saboda bala'in su Annen.....shiyasa hatta Abokin Ya Amir ɗin da su ke ta faɗi tashi ya kasance ba ɗan layin bane ba, jita-jitar da ya ke ji a bakin mutanen da su ka ƙi taimaka musu game da Annen ya sanya ya sare shima ya zame ya barsa shi kaɗai. Bayan kwana biyu. Sosai lamarin nata ya sake firgita su dan zuwa wannan lokacin manyan Likitoci sun ƙaraso kuma sun dubata sosai.. Sai dai kuma sun makaro domin su na duba ƙafafun nata da ba a kai ga kuncewa ba an duba tun a karon farko su ka fahimci tabbaas ƙafafun Anne duk biyun sun ruɓe dan haka sai dai a yanke ƙafafuwan nata duk biyu sakamakon infection ɗin da ya shiga sannan masu matsewa su kuma sun matse ƙafar katamau wanda hakan shima ya taka rawar gani kwarai wajen sake ruɓar da ƙafafun nata... Dan haka ba su yarda sun sake ɓata wani lokaci ba a take aka wuce da ita asibitin Murtala inda za a yi mata aikin.... Ga Adda itama wadda su ka gagara zama ita da Baban still akan lamarin Ya Abba wanda ba ma su san inda ya ke ba, sun kira Afra da niyyar ta yi wa Mijinta magana ya saki Abban amma ta ma ƙi ta tanka musu akan batun, da farko ma su na ɓoye mata halin da Anne ta ke ciki wae dan kar hankalinta ya tashi har su ka gaya mata wanda ga mamakinsu sai su ka ga kamar ba ta wani damu ba dan baya ga “Allah ya bata lafiya” ɗin da ta ce bata sake cewa komai ba game da Anne.. Ta ce musu in Ya Asad ɗin ya shigo za ta yi masa magana ta ji tun daga nan har yau kusan kwana uku kenan ba ta sake kiransu ba… Wanda abunda ba su sani ba tsantsar damuwa ce ta ke shirin haukata Afra.... Sosai kan Amal ya ƙulle...ta rasa dalilin Ya Asad na ƙin sakin Ya Abba da kuma jinya da uban kuɗaɗen da ya ke ta kashewa har kawo yanzu da ta warke duk dan saboda ita kaɗai, dan bayan an gama dubasu a asibiti har yau nurse ba ta tafi ba sannan an ɗaurata akan magunguna masu tsada kuma hatta ruwan da su ke sha a gidan duk shi ya kawo komai da sunanta... Tabbas ta san ya manta da ita, to meye ribarsa? Ta san dai kasancewarta ƙanwa ga matarsa bai kai a ce ya yi mata hakan ba...... Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake Ga abunda ya ke damunta wanda ya ke sake yin gaba kullum... Ga kuma tashin hankalin da ta ke a ciki a ta sanadiyyar ɗaure Ya Abba da aka yi dan tuni ta daina fushin da take yi da shi, dan haka gaba ɗaya duk sai ta firgice ta sake gigicewa duk ta fita a haiyyacinta. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *10* Hatta Baba sai da ya ji babu daɗi a lokacin da Ya Amir ya kira Kaka Nuran ya ke sanar musu ‘ƙafafun Anne duk biyun sun ruɓe za a cire sannan ƙirjinta shima akwai wajen da ya yi ɗiwa bayan an watsa mata acid dan haka ana kan bincike aga mai acid ɗin ya yi triggering har ya kai ga yin ɗiwar..muddin aka gano abunda ake zargine wato jeji to nan ɗin ma sai dai a yanke tun kafin ya bazu… Ranar gidan duk wuni su ka yi sukuku, ga Aliya wadda su ka kasa gane kanta dan sau biyu su na hanata kashe kanta a cikin gidan, duk yadda Amal ta kai ƙololuwa wajen fushi da Aliyar zuwa yanzun kam ta fara bata tausayi matuƙa dan tabbas dukda ta na ta ƙoƙarin ganin ta ɓoye da kyau zuwa yanzu kowa ya fahimci akwai abunda ya ke damunta bayan takaici Anne da Mai Nasara… Sosai lamarin Anne ya gigita Kaka Nura duk masifa da bala’in tsohon zuwa yanzu ya yi sanyi.. suna ɗaya Anne ta ke ta kira wato sunan mahaifiyarta tunda ta farfaɗo wannan dalilin ya sanya kawai bayan an shiga da ita theater room Kaka Nura ya wanke ƙafa ya nufi inda Uwani take, zuciya cike da ƙunci.... Ya na tafe ya na hawaye ya na nazarin... Duk bala’insu shi da ita (Anne) wajen ganin sun tara abun duniya ba ya taɓa taruwa! Kamar waenda aka tsinewa..Ko da ya ke ya san ko sun tara ɗin daga a damfaresu sai ko kuɗaɗen su ƙare a wajen malamai da bokaye, ko kuma su tafi a banza, dan gashi a yanzu haka daga shi har ita ba su da uwar komai wanda a yadda shi da ita su ka dinga neman kuɗi na haram da na Allah ya isa har ma da na sata a gaskiya ya kamata a ce sun sayi estate a cikin garin Kano...sai dai kash! Dan a halin da ake ciki dai yanzun da ta ke a kwancen nan in ba satar zai ci gaba da yi ba tabbas ba ya jin za a iya sake yi mata wata allurar ma saboda tsabar fatara da babu! Gaba ɗaya ya rasa mai yasa su ke ta sake tsiyacewa haka daga shi har jikokinsa... Amir ma da mugun kyar ya iya tura masa dubu biyar tunda ta kwanta dan ya ce wallahi ko bashi an ƙi a bashi saboda an san ba shi da yadda zai yi ya iya biya. Ciwon Nuratu (Anne) ya lashe asusunsu gaba ɗaya..in ba dan ƙalubalen da su ka fuskanta ba na damfara da shi da Anne da Aliya wallahi ya ci ace sun yi maganin abunda ya ke damunsu sam ciwon bai isa ya tsotseshi haka ba, tsaf za su yi magani sannan su ji daɗin rayuwa sai dai da ikon Allah a halin yanzu daga shi har ita (Anne) bayan ta warke da Amir da ita kanta Aliyar in har Ubangiji bai rufa musu asiri ba to tabbas sai dai su yi bara da roƙo..dan shi dai Asad an san zai kula da Afra amma batun su tsafe shi su kwaci kuɗi daga hannunsa ya san ƙaryansu sai dai shi da kansa in ya yi niyya ya basu..... Ya na wannan lissafin ya karasa garin da Uwani ta ke wadda daga shi sai Annen ne kaɗai su ka san ta na a raye! Dan tun shekaru ashirin da biyu Baya lokacin da su ka cinnawa gidan Baba Yusufa wuta kowa ya yi tunanin Uwani ta rasu ne a ciki. Chan wani Ƙauye a tofawa ya gangara, kwata-kwata gidaje ba su fi bakwai ba a a kaff ilahirin wajen dan in ka ga ɗaya to sai ka yi tafiyar da ya ɓacewa ganinka tukunna za ka sake ganin wani…. Bukkoki ne gaba ɗayansu yanayin kalar fentin da ake yi a jikinsu ne kawai ya ke bambanta su dan duk giramnsu ɗaya sannan wani a zagaye ya ke wani kuwa ko kara guda ɗaya bai samu arziƙin samu ba ballantana ya baiyyana keɓantuwa.. Tunda ya nufo bukkar gabansa ya ke ta faman faɗuwa zuciyarsa ta ke zillo..a kaff tarihin tsari na rayuwarsa bai taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo ya yi shakka ko shayi ko tsoron wani Abu ba sai yau.... Tabbas a halinda ƴartasa Aba mafi soyuwa a garesa ta ke a ciki yafiyar mahaifiyarta kawai ta ke da buƙata sai dai kuma baya jin Uwani za ta taɓa yafe masa shi da Anne, shi kuma a halin yanzu ya fahimci wannan taimakon da zai yi mata shine duk wani ƙarshen gata, besides shi fa tunda ya ganta a haka gaba ɗaya ya gigice ya firgice ya nemi duk wani kuzarinsa ya rasa gaba ɗaya its like he's trying to loose himself....dan haka babban gatan da zai yi mata ya san shine ya taimaka ya kai mata Uwani ta ganta ko a samu ta yafe mata dan ya san abunda ta ke da buƙata kenan. Bai san mai ya sa ba haka nan ya cire rai gani ya ke kamar Nuratu tata kawai ta ke jira..bai taɓa tunanin zai yi mata wannan fatan ba ko a tsaka mai wuya kamar wannan amma tabbas akan ta gama shan wahalar nan kuma a fille mata kai kamar yadda ya ji polisawan su na faɗa gara ma ta mutu tun yanzu!. Kuka ne sosai ya kufce masa...ya na wannan lissafin ya ƙarasa bakin bukkar da ya ke da tabbacin nan ɗin ce ta Uwani ya tsaya dan ya gagara tattaro courage ɗin da zai fusakanceta... Tsoro ya ke yi kar ta ƙi amincewa da buƙatarsa, tsoro sam ba ɗabi'ar Kaka Nura bace ba amma tabbas yau kam ya na jinsa a kan halittar da a shekarun baya ya raina fiye da yadda ya raina kashin gindinsa. Da ƙarfi ya fesar da wani kalar huci sannan ya daddage ya ɗaga hannunsa ya na shirin taɓa ƙofar ya ji tsohuwar muryarta a bayansa ta ce "Ya Nura" A hankali kamar mai mamaki da tantamar ko shi ɗinne… A hankali ya juyo ya na kallonta... itan ce kuwa! ya aiyyana hakan a ransa. Itama ta na tsaye kawai ta kafesa da idanuwanta… Da alama ruwa ta je ta debo daga rafi ko kuma har da wanka ne duk ta haɗo ta yo dan ga alamu nan sun baiyyana... Ta ƙara tsufa sosai tabbas dan gaskiya ta fi shi nuna tsufa itakam dan ta yi tukuff-tukuff da ita babu wata ragowar mamora a tattare da ita… Ganin an tsaya ana ta faman kallon-kallo ne ya sanya ta zo ta fara ƙoƙarin shigesa dan ɗan ruwan da ta ɗebo a cikin kaplas har ya fara sagar mata da tsohon hannunta… Da sauri ya matsa ta shige ciki sannan ya bita a baya… Rabonsa da ita tun shekaru ashirin da biyu baya da su ka wuce lokacin da ya kawota nan ɗin ya ce ta zauna kafin a san abun yi! Wanda har ga Allah maitar son Yadikko ce ta sake tunzurashi wajen yin hakan dan ita a lokacin ya san ba za ta taɓa yarda ta auresa ba.. Sai kuma rufin asirin ƴarsa da shi kansa, dan haka ya zaɓi ya ɓoyeta sannan ya ɗaura laifin kacokam akanta...ya jefi tsuntsu biyu abunsa da dutse ɗaya buƙatunsa duk su ka biya ita kuma su ka kawota cikin wannan wahalalliyar rayuwar… A zuwan hideout. Tunda ya tafi babu ko waya ko wani abun, bayan da ce mata ya yi za su dinga zuwa duk sati… A hakan fa wae da sunan aurensa a kanta ne har kawo yanzun dan kowa ya na tunanin ta Mutu ne yayinda ita kuwa tun lokacin da addini ya ɗiba mata ya cike bai zo gareta ba ta yi idda ta saka kanta a sahun zawarawa…. Da ita da shi duk lissafi ɗaya su ke yi dan haka ta ajjiye ruwan ta nemi waje ta zauna sannan ta ɗago ta kallesa ta ce masa “wani abun ka ke da buƙata ko?” Dibi-dibi ya fara abunda sam ba ɗabi'arsa ba dan shi kansa ya san ko an tona a zamani da tarihi tofa ba lalle a samu halitta mai kalar tsaurin idonsa ba, kamar wanda ya girma a gaban karuwa haka nan ya ke bai san ya ake kawaici ko kaucewa ba ballanta ya yi dibi-dibin..amma yau gashi da ikon Allah ya kasa magana.. Itance dai ta sake magantuwa dan ya gagara cewa komai “zan sake fita, mai ka ke da buƙata?” A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya... Ba batun gaisuwa ko rarrashi saboda dama chan shi bai iya ba a kan ƴarsa ne kawai ya iya rarrashi, sannan a halin yanzu ya san in ya fara ma tsaf za su iya shafe shekaru ba su gama debate ɗin ba kuma a ƙarshe shine zai zama marar gaskiya, ko da kuwa ya yi borin da ya kan yi a duk lokacin da ya fahimci ba shi da gaskiya an bashi gaskiyar amma wannan karon kam ya san ko point ɗaya Uwani ta kawo ta gama da shi. Dan haka ya sauƙe ajiyar zuciya a karo na ba adadi ya ce mata "ƴarki ce ta ke da buƙatarki" sannan ya shiga zaiyyano mata halinda Annen ta ke a ciki a wannan lokacin.... Ajiyar zuciya ta sauƙe ya na kai aya sannan ta ce "Allah ya bata lafiya, in kuma mutuwa ce to Allah ya ji ƙanta." Daga haka ta fara ƙoƙarin ficewa ta ga Kaka ya durƙusa a gabanta ya riƙe ƙafafunta, sai kuma ya fara hawaye, ya na cewa "kar ki yi taurin kai dan Allah, yau kwana huɗu kenan ke kawai ta ke ta ambato, ki taimaka dan Allah ki zo mu je ki ga halin da ta ke a ciki na san za ki tausaya mata ki taimaka ki yafe mata…." Har ga Allah ko Muryarsa ba ta ƙaunar ji, Allah Allah kawai ta ke yi ta fita..banda tsabar tsaurin ido ita da bata da maraba da gawa a wajensu mai za ta yi musu yanzun? In da ace sun yi nasarar kasheta a wanchan lokacin da ya za a yi ta yafe mata? A Ina zai ganta ballanta su nemi yafiyar?..... Ta na wannan lissafin ta ji ya ce "ki rufa mini asiri ƴata ta Mutu ba da hakƙin kowa a kanta ba dan Allah…" Murmushin takaici Uwani ta yi sannan ta kallesa da kyar, tukunna ta ce “Ashe kun san akwai hakki Ya Nura…” Sannan ta ɗaura da cewa “A ganina na yi muku ƙarshen kara! A kalar abubuwan da ku ka yi mini har na iya yi mata fatan ta cika lafiya da fatan waraka ae na yi muku ƙarshen kara. Sannan fa bara ka ji...Ina yi maka albishir ɗin cewa ko da ace na yafewa Nuratu! To tabbas akwai tarin hakkoki na jam’a bilaadadin a kanta..dan haka kar ka soma yaudarar kanka ka san ta zalinci da yawa….dukda kun kawo ni nan hakan bai Hana ni bibiyar al’amuranku ba ae..sarai na sani kuma na ji yadda ta tarwatsa rayuwar mijinta shima da ƴaƴan da ta Haifa a cikin cikinta! Bayaga su ma ae kai kanka ka san Nuratu ta zalinci da yawa wanda in ka ce burinka shine ka nema mata yafiyar duk wani mai hakƙi a kanta ne tabbas ko da ace za a ƙara maka shekarunka a kan shekarunka na duniya ba lalle ka gama iya nema mata yafiya ba har ka mutu.." Sai kuma ta yi shiruuuu, kafin cikin sauƙe numfashi kawai ta basar da maganar sannan ta ce “faɗa mini sunan asibitin da take, zan zo…" Saboda kwata-kwata ta kasa daure ci gaba da shaƙar iska ɗaya ita da shi so ta ke yi kawai ya fita....wallahi ko muryarsa ba ta ƙaunar ji. Ya so su tafi tare amma ta ce da shi ya tafi kawai ba ta gama shawara da zuciyarta ba tukunna…. Bayan tafiyar sa da kamar mintuna arba’in ta shirya tsaf itama ta bi bayansa dan sai da ya wuce tukunna ta tuna tabbas akwai kalar bankwanan da ya kamata ta yi ita da Nuratu (Anne). Tsohuwa ce sosai amma har yanzu kanta bai juye ba dan da kanta ta kai kanta har asibitin murtala... Ta ci sa’a kuwa dan tun a waje ta haɗu da Kaka Nura wanda ya fake da zuwa sallah ya yashe mutanen da su ka je siyayya kasuwar wajen..dan haka direct su ka wuce ward ɗin da Anne ta ke a cikin wani waje a keɓance da polisawa su na tsaronta. Su kaɗai ne a ta wajejen sannan an ɗan ja labule an sake keɓance wajen ga police a tsaye ya na gadi shi da wani soja tun a waje, bincike sosai aka yi musu har da Kaka Nuran bayan ya tabbatar musu Uwani ce ta haifi Nuratu, sannan aka barsu su ka shige cikin labulen.. A kwance ta ke hatta idonta da mugun kyar ta ke iya buɗewa amma an haɗa hannunta da ƙarfen jikin gadon an datsawa ankwa saboda gudun kar ta gudu! Sannan ga sojoji nan har guda biyu su na tsaronta sosai bayan wanda ke a waje a tsaye tare da police. Fitowarta kenan daga inda aka yi mata theater ba a daɗe ba inda aka yanke ƙafafunta duka biyun daga saman guiwa zuwa ƙasa sakamokon ɗiwar da su ka fara yi su na wari. Likitoci har biyu ne a kanta su na ta faman sake dubata su na ƴan maganganunsu... Dan haka Uwani da Kaka wanda ya yi matuƙar jin zuwan nata su ka ja gefe su ka tsaya idanun Uwani a kanta ta na sake jaddada ikon Allah yayinda Kaka Nura ya ke tsaye ya na kallon ƴar tasa ya na kuka sosai kamar wani ƙaramin Yaro! Wallahi wallahi in sha Allah sai ya tarwatsa rayuwar Amal tunda dai ya san ko mai zai yiwa Baba yanzu kam ba zai ji zafi ba tunda dama mutuwa zai yi amma ya san a yadda Baban ya ke ji da Amal in ya taɓa ta sai ya girgiza kwarai, sannan ya na fatan ko da ace Baban ya na lahira ne ya zamana a duk lokacin da ya azabtar da Amal za a tashesa a nuna masa. Ya gama bada amannar cewa Baba ne silar duk wani halinda Annen ta ke ciki a yanzu, saboda ya yi revenge…. ya rama duk wani abunda su ka yi musu kafin ya mutu, shiyasa ya fara ta kanta tunda dama tun usul kowa ya shaida Baba ya tsani Anne kamar mutuwarsa… BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *11* Likitocin sun jima a kanta su na gwaje-gwaje kafin finally suka sake ɗaukar sample na jininta da ɗiwar da ke fita a ƙirjinta, Likitan ya na mai cewa "bara a yi test na jinin a dawo" dan wanchan bai gama yarda da shi ba ba komai aka yi ba, Emergency ne shiyasa kawai ya bari aka shiga da ita amma in za a koma da ita cire nonuwan nata dole za a buƙaci jini saboda babu a jikinta sosai…". wanda zuwa wannan lokacin itama Anne ta farka dan sun ga ma ta na motsi.. Alluran da su ka siya duk sun ƙare an gama yi mata dan haka su ka juya su ka kalli Kaka Nura ɗayan ya ce masa "ka nemo kuɗi a ƙaro allurar rage raɗaɗi a yi mata if not za ta sha wahala sosai gaskiya sai kuma ka je ka biya kuɗin wannan aikin da za a sake shiga a yi mata.." Ya yi maganar ya na miƙo masa wasu takardu sannan ya ɗaura da cewa "bara a yi wannan test ɗin za mu dawo nan ba da jimawa ba in sha Allahu…" Daga haka su ka sa kai su ka fita Likitan ya na sake jadda ikon Ubangiji... Ya san Anne sosai ta na yawan zuwa private hospital ɗ’insa Matar da a ko da yaushe ya ke yaba kyawu da kyan surar jikinta dan ko kaɗan in ka ganta ba za ka ce ta na da ƴaƴa manya ba ma wae yau ita ce a haka...tashi ɗaya Ubangiji ya mayar da ita haka… Su na fita soja ɗaya ya fita ya bar ɗaya wanda ya koma chan gefe ya tsaya ya ci gaba da ƙamewa ba tare da ya sake kallonsu ba. Su na kammala fita Kaka Nura ya sake rushewa da wani sabon kuka dan ya fahimci zuwa yanzu ta tabbata ƙirjin nata ma yankewa za a yi kenan...yayinda Uwani ta juyo a hankali kawai ta na kallonsa ta na mamakin ashe in ya ga wani nasa a haka zai ji zafi dan ta na tuna lokacin da su ka saka Mutan masu yawa a kwatankwacin shigen irin wannan halin… Girgiza kanta kawai ta yi sannan ta ce masa “ka daina wani kuka fa abunda ku ka shuka ne ku ke girba” Daga haka ta wuce cikin tafiyarta ta tsoffi ta ƙarasa inda Annen ta ke a kwance…yayinda shi kuma ya ɗago ya na kallonta da mamaki tsantsa a kan fuskarsa ya na tunanin tunda ta fara furta irin haka Anya kuwa za ta yafewa Nuratu? zai yi magana ya ga ta ƙurawa Anne ido sannan ta soma yi mata magana…. AFRA… Ta na kammala waya da su ta rushe da wani kalar rikitaccen kuka, yayinda kishi ya ke azalzalar zuciyarta, Sam! Kwata-kwata lissafinta bai bata cewa ae saboda su Anne da kowa Asad ya koma ba kawai lissafinta bata ya ke yi sabida Afra ne ya barta a nan ita kaɗai ya juya ya koma gashi har yanzu bai dawo ba wanda ta na da tabbacin in ba da kyar ba ya na chan tare da Amal ne. Tunda gashi duk sun ce mata ya dawo yau kusan kwana biyar kenan ita kuma ba ta saka shi ko a idanunta ba. Ya barta a nan cake ne kawai ta tarar a fridge daga shi ba komai sai ruwan da ta ke ta sha ta fanfo..Sai fruit ɗin da ta ke fita ta tsinka(inibì) bayan shi babu komai a gidan gashi gaba ɗaya tsoro ya lulluɓeta dan wani kalar motsi-motsi ta ke ji a cikin gidan kullum dare kuma in ta duba ba ta ganin komai, apart from that ma gaba ɗaya gidan tsoronsa ta ke ji saboda ya yi girma sosai. Wanne kalar Ango ne zai bar Amaryarsa ba tare da ya zo gareta ba na tsawon kusan mako ɗaya fisabilillahi! Sannan babu waya ba komai! Bai kirata ba kuma ya ga baƙuwar number amma bai ɗaga ba shi da ya san ya bar mace ita kaɗai ae in ya ga number ƙasar ya kamata a ce ya ɗauka ko ya biyo amma sam ya ƙi responding, messages ma ba ya respondin ƙarshe ma ya kashe wayar gaba ɗaya..ita kam kunya ma ta ke ji ace Asad ɗin da ta ke haukar so ya yi mata hakan shiyasa ta gagara sanarwa su Ya Amir halinda ta ke ciki. Tabbas ita kanta dama ta san gangar jikinsa ta aura amma ba ta yi tunanin wulaƙanci daga garesa ba, wulaƙancin ma since from day 1.. Ta yi tunanin za ta shawo kansa cikin sauƙi.. Ko numberta fa Mijinta na aure bashi da, tashi ma ita ta bi ta kuma nema. Ba shiri ta ke yi da mahaifiyarsa wadda ta tsaneta kamar mutuwarta ba ballanta ta nemeshi ta hanyar ta, Akram kuwa shi da ita mahaifiyartasa duk tafiyarsu ɗaya bakinsu ɗaya... Ubansa kuwa ɗan Akuya kwata-kwata ba ta ƙaunar abunda zai haɗata da shi ballanta ta je ta samu Matsala da Ya Asad ɗinta ta sanadiyyar hakan…. Wani kalar tafarfasa zuciyarta ta ke yi yayinda kishin ƴaruwarta aba mafi soyuwa a gareta a da ya ke dabaibayi a cikin zuciyarta ya na sake addabarta ta na wani kalar kuka... Tabbas yanzu aka fara game ɗin! Dan wallahi bayan ta kwace Asad daga wajen Amal completely sai ta juya mata rayuwa zuwa masifa da bala’i sai dai in ba sunanta Afra ba, ƙiri-ƙiri sannan baki da baki Amal ɗin ta ce mata ta haƙura ita tun usul dama ba ta son Asad ashe munafukar masifar muguntar da ta shirya mata kenan... Ta ci burin amarcinta ta ci burin kasancewa tare da masoyinta amma Amal ta lalata mata komai da komai…. Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ta durƙushe a wajen ga wani azababben ciwon ciki da uban zazzaɓin da suka rufar mata a ta sanadiyyar ciwon marar da ya ke addabar rayuwarta dan Anne ba ta yi sanya ba wajen dura mata magungunan mata masu masifar ƙarfi ba na wasa ba… A wajen ta zube ta na nishi yunwa da wahala suka sanya ta yi wani kalar wahalallen barci wanda za a fi iya kiransa da suma… Wani kalar azababben ƙarni ne ya farkar da ita wanda ya sanya ta tashi ta zauna da sauri ta na mai dafe kanta sakamokon nauyin da ya yi mata, da kyar ta iya tashi tsaye ta na jin kamar za ta zube yayinda ƙarnin ya yi mata yawa matuƙa zuwa yanzu dan the more ta ke sake wartsakewa the more ƙarnin ya ke sake yin yawa..dan haka kamar ana janta haka nan ta ke bin ƙarnin har ta fito daga bedroom ɗin da take ta nufi inda hancinta ya ke janta zuwa ga ƙarnin... Ta na mai mamakin masifaffen ƙarnin wanda kamar ba na lafiya ba! Dan kamar an haɗa har da na asiri duba da yanayin ƙarfin ƙarnin sannan da yadda ya taso ta daga barci Ashe ma a hakan wae ba a kusa da ita yake ba.. Kusan a tare za a ce su ka farka ita da Asad wanda shima ƙarnin ne ya farkar da shi… Da kuma tsantsar faɗuwar gaba kamar dae itan shima da mugun ciwon kai ya farka har ya na buɗe idanunsa da kyar sai kuma ya yi firgigit ya tashi zaune ya buɗe idanunsa tangargar sakamokon jinsa da ya yi shane-shane cikin wani abu mai kama da ruwa sai dai ya fi ruwan danƙo. Tabbas ba a nan ɗakin ya kwanta ba to amma ya aka yi ya zo nan ɗin?... Ya na wannan lissafin idanunsa su ka sauƙa akan wata calender shi da ya ajjiye a saman drawer ɗakin mai amfani da electricity kullum ta na chanja kwanan wata da rana har ma da lokaci in ya motsa da yanayin whether komai dai in ya sauya itama ta na sauyawa ta nuna maka halinda ake ciki...wadda yanayin figure nata ya kasance sak figure na duniya mai kyau da sheƙi.... Zabura ya yi domin kuwa in dai har yau Wednesday ne kamar yadda calender ta nuna masa to kuwa ya shafe kwanaki huɗu kenan chur ba tare da ya san inda kansa ya ke ba! Miƙewa ya yi da masifar sauri gaba ɗayansa ya gigice! Da niyyar ya ƙarasa wajen ya ga ko dai calendar ta ɓaci ne ko kuma wuta ya daina kai mata Kawai ya zame ya yi wani kalar mahaukacin faɗuwar ruf da ciki sakamokon santsin da ya kwashesa sai da ya kai ƙasa ya yi ninƙaya a cikin abunda ya ji ɗazun tukunna ya tuna ɗazu fa ya ji sa cikin Abu kaca-kaca dan haka ya buɗe idanunsa waenda ya runtse tun sanda ya bugu a ƙasa ya sauƙesu a kan floor ɗin... A take zuciyarsa ta wani kalar mahaukacin bugawa sannan ya sake buɗe idanun nasa tarrr da kyau ya na so ya tabbatar da shin abunda ya ke gani gaskiya ne Dai-dai nan ya ji motsi a bakin k’ofar d’akin alamun za a shigo. ………… Tun lokacin da Yagwalgwal ta ji batun abunda ya samu gidansu Baba ta ke yiwa Baban naci Akan maganarsu dan ta ce a ganinta suma ɗin yanzu kam ba su da wani security da kariya ko mutunci dan haka basu da banbanci da ita…dan gashi mai Unguwa ya soma shirin korarsu. Tun ta na yi masa magana har ta zo ta fara binsa da masifa jiya kuwa threatning ɗinsa ta yi dan haka ya yanke shawarar zuwa yau ya samu Amal dukda kuwa ya san hakan ba dai-dai bane ba, sam! Ba a yiwa Yarinyar adalci ba amma ba shi da yadda zai yi! Tunda ya ke a rayuwarsa bai taɓa tsintar kansa cikin jin matsanancin tausayin wani ba kamar Amal Yarinyace mai hankali kawaici da haƙuri zagaye da munanan ƙaddarori mabambanta. Ya na wannan tunanin ya ƙarasa ƙofar ɗakin Adda ya ɗan yi knocking ya tsaya. Sai da ta leƙo ta ga shine ta ce ya shigo tukunna ya shiga bakinsa ɗauke da sallama. A kwance ya sameta (Amal) a kan kafet ta na barci ta na sauƙe ajiyar zuciya. Kuka suka gama ci yanzun daga ita har Addan Akan lamarin ya Abba dan sama ko ƙasa sun nemi taimako sun rasa wasu sun ma ƙi su kulasu... Ko an kulasu ɗin ma daga an ji waye da case ɗin duk sai su ja baya, gashi duk alƙawarin da ta ɗauka a kan Ya Asad ta sauƙo dan tun shekaran jiya ta ke ta faman kiransa amma ba ya ɗaga wayar….Afra itama ta daina amsa hatta kiran Ya Amir... Ita babban tashin hankalinta ma shine a barta ta san halinda Ya Abba ya ke ciki, Allah ya sa ba a wani cel mai tarin macizai ko ma uƙubar da ta fi nan ɗin Ya Asad ya je ya saka shi ciki ba...yayinda Adda ta ke fargaba sosai da tsoro tunda shi Asad d’in ga abubuwan da ake zarginsa da shi kar ta je ta rasa d’anta tilo har Abada ........ko hutuwa ba a barshi ya yi ba daga azabar cel ɗinnan da su kansu har gobe dukda an basu kuma ana kan bata kulawa ta musamman ba ta barsu ba... Cikin tsantsar mutuwar jiki Baba ya nemi waje ya zauna idanunsa a kanta dan gaba ɗaya ƴan gidan sun koma kamar wasu waenda aka yiwa wahayin ƙunci haka nan su ke kowa jiki a saluɓe… Ba tare da ɓata lokaci ba ya cewa Adda "ɗan tada mini ita za mu yi magana" bayan sun gaisa. Kamar Addan za ta ce masa yanzun naan fa ta samu barcin dan kwanakinta uku yau curr bata ko rintsa ba sai kuma ta ga kamar ya na da buƙatar maganar da gaggawa ne dan haka ta ɗan saka hannu a hankali cikin nutsuwa ta shiga kiran sunan "Amal" ɗin ta na ɗan tattaɓata…. Ba ta jima ta na yi mata hakan ba ta farka da salati ɗauke a bakinta ta na mai kallonta kafin kuma ta mayar da dubanta zuwa ga Baba! Sannan ta miƙe ta zauna a hankali cikin nutsuwarta ta na mai gaidashi. Da kyar ya amsa ba tare da ya iya kallonta ido cikin ido ba dan haka nan duk sai ya ji nauyi da kunyar Yarinyar masu haɗe da tausayinta sun baibayeshi. Kame-kame ya fara yi kafin ya tattaro courage ya shigar sanar mata komai game da yadda suka yi shi da Yagwalgwal wanda tun lokacin da Allah ya bashi ikon ambato sunan Yagwalgwal ɗin fuskar Amal ta jiƙe sharkaf da hawaye! Ta shiga nanata kalmar "Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" ta na mai roƙon Ubangiji da ya zare ranta a take a lokacin ko ta samu sa’idar wannan masifar da ta tunkaro kai. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *12* ANNE.. Kwance ta ke cikin tsantsar mawuyacin Hali azabar acid ɗin da aka watsa mata da kuma zafin ƙafafunta biyu waenda aka yanke su na neman zautar da ita… Hatta magana ba iya jiyota ta ke yi sosai ba dan ko iyayenta da su ke a ɗakin tare da ita sama-sama ta ke iya jiyosu sakamokon wani Abu mai nauyi da ya ke shirin sake fisgarta kamar yadda ya fisgeta ta sume ɗazun… Tabbas ta san ta sha miya kwarai da gaske domin kuwa a halin yanzu shekarunta sun haura arba’in da biyu sannan ta hayayyafa sai dai kuma ita kanta ba ta yi tunanin za ta ji azabar bakin cikin halinda ta ke ciki ba a yanzu da aka ce an yanke mata ƙafafuwa sannan fuskarta ta raunata ga ƙirjinta da ta ji Likita ya na iƙirarin acid ɗ’in da aka watsa mata ya taba kuma ba a yi magani da wuri ba, dan haka ya tado da jejin da ke a gurin a ɓoye tuntuni wanda yanzun ya baiyyana kansa dan haka dole a yanke duka biyun saboda kar jejin ya yaɗu. Ta na cikin wannan lissafin muryar dattijuwar mahaifiyarta ta sake dirar mata ta inda ta ƙaraso ta tsaya a kanta ta ke cewa “Ae ba ki ga komai ba fa! Yanzu ki ka fara gani…. Dama duk wanda ya ce shi duniya ya saka a gaba to fa ya na tare da wahala! Allah na tuba mutum ya yi mai kyau ma ya ya ƙare ballantana bai yi abunda ƙuda ma zai bi ba?? A lokacin da nake gaya miki ai gani ki ke yi kamar ƙarya nake yi!!.. Tunda na haifeki na ke fuskantar ƙalubale ba ki barni na Hutu ba, bayan kin yi aure haka ki ka tarwatsa duk wani jin daɗi da farin cikin mijinki, hatta ƴaƴan da ki ka haifa ba ki barsu sun ji daɗi ba! Ɗaya bayan ɗaya duk sai da ki ka lalata musu dukkan farin cikinsu… Yanzu gashi ai kema kin fara gani da idanunki kuma wallahi wallahi Nuratu kin ji dai har na rantse miki ba ki ga komai ba!!." Cikin faɗa sosai Kaka Nura ya ce da Uwani wadda ta gama wannan furucin ga Anne "Haba mana Uwani!! Ashe kuwa ba alkairin ya kawoki ba kamar yadda na ke zato! Ke da aka ce ki zo ki yafe mata shine za ki zo ki na sake rura mana zafin zuciya? To kuwa wallahi idan ba ki rufewa mutane baki ba zan yi fatali da ke a wajen nan!! Ashe ke Jahila ce ban gama sani ba sai yau? Mahaukaciya kawai!!. Yo Idan ba mahaukaciya ba wacce iriyar daƙiƙiyar uwa ce zata ke furta wannan mugun alkaba’in ga ɗiyar da ta Haifa a cikinta? Haba mana!!! Ba ki da tausayi ne? Kalli fa halin da ta ke ciki! Ke da ya kamata ace mun taru mun kwantar mata da hankali shine za ki dinga binta da mugun fata ba ki da imani ne ? Ko kuwa dai zuciyarki ta ruɓe ta lalace ne??". Cikin Hali na ko in kula Uwani ta sake zubawa ɗiyartata idanu waadda itanma ita ta ke kallo da idonta guda ɗaya wanda ya yi saura don ɗayan ya riga ya tsiyaye hancinta shima kusan za a ce babu ne yayinda bakinta ya tauye..gaba ɗaya kamanninta su ka sauya dan ita kanta dukda kasancewarta mahaifiyarta wallahi da kyar ta ke iya sake shaidata… Kwafa Uwani ta yi bayan ta gama ƙare mata kallo tukunna ta ce "ƙarshen ki ki ka fara gani Nuratu, kamar yadda na faɗa da farko wallahi ba ki ga komai ba! Batun yafiya kuwa ba lalle ki samu daga wajen kowa ba har shi mijin naki dan haka in dae wahala ce da azaba ba ki ga komai ba, in kin mutu yanzu ta chan ta na jiran ki wadda ta fi nan... in kuma kin samu kin rayu to wannan halin da ki ke ciki shine farkon wahalarki..halinki da hakƙin jama'a su ka janyo miki..ko ni ban yafe miki ba dan da baƙin cikinki zan Mutu…" Daga haka ta juya ta fita wanda fitar da ta yin ne bai bawa Kaka Nura damar samunta da sandarsa wadda ya ɗaga da niyyar sauƙe mata ba……. Ta na fita wani azababban hawayen da saida Anne ta ji inama ba a halitta mata yin hawaye a duniya ba ya shiga zubo mata..kuka ne ta ke yi da idanu biyu amma hawayen ido ɗaya ake iya gani domin d’ayan idon ya rufe ya tsiyaye ya zagwanye wanda hawayen da ya ke fita daga cikinsa ya na fama mata jagwalgwalewar da wajen ya yi ya ke sanyata ta na jin kamar za ta bar duniya tsabar Azaba!. A rikice Kaka Nura wanda ya rasa abunyi duk ya bi ya ruɗe ya juyo daga zabgawa inda Uwani ta bi ta fice da kallo harara ya ƙarasa ya zauna a bakin gadon….kamar shima ya rushe da kuka tsabar tashin hankali da bala’i haka ya ke ji…da kyar da mugun kyar ya ɗan yi controlling kanshi ya aro jarumta ya yafa domin ya san ƴarsa tana da buƙatar jarumtar tasa a halin yanzu, cike da taka tsantsan kamar wanda zai taɓa kwai ya shiga shafa kanta a hankali kafin cikin tsananin lallashi ya fara magana "ki yi haƙuri ki yi shiru, ki daina kuka dan Allah. Allah ya na tare da ke zai bi miki hakƙinki, sannan in sha Allahu za ki rayu da izinin Allah kuma ba za a yanke miki hukuncin komai ba ki na gama jinya gida za mu koma ba wai prison ba...kuma matar da ta aikata haka a gareki wallahi sai mun ɗauki fansa sai ta yi da na sani wallahi….ki bar ɗaga hankalinki zan tsaya komai ya koma kamar da kar ki saka damuwa a ranki dan Allah kin san ba na son ganin hawayenki kar ki saka jinina ya hau wani abun ya same ni ki rasa mai tsaya miki…ki daina kuka komai zai yi dai-dai in shaa Allah kuma da hannunki za ki hukunta matar ita da Habu (Baba) dan na san shi ne ya turota ko ba ya raye sai mun azabtar da Amal kwatankwacin azabar da su ka gana miki wannan alƙawarina ne gareki, ki yi shiru kin ji ko, fuskar ma za mu samu kuɗi mu tafi turai a gyara miki ki kwantar da hankalinki kar ki sakawa kanki ciwon zuciya…." Ya ƙarashe maganar ya na huci... Dukda su Aliya sun tabbatar masa ba Baba bane ba amma shi ya ke zargi, batun garkuwa wannan ma ya san in ba kyar ba duk Baban ne ya yi mata chune ya cewa sojojin Sajida su bincika har cikin ƙasa ko kuma dae wani abun makamancin haka duba da yadda surukin nasa ya tsani ƴar tasa kamar mutuwarsa. Shigowar Likita wanda ya yi alƙawarin dawowa yanzun ne ya katsewa Kaka Nura aikin rarrashi da tunanin da ya ke yi. Da sauri ya miƙe sannan ya juyo ya mayar da hankalinsa kachokam ga Likitan ya na jira ya ji bayani…… Kallonta Likitan ya yi ya ɗan kalli Kaka Nura kafin ya ce "Baba a ɗan bamu guri…Ina so zan yi mata magana in private…" Cikin fushi Kaka Nura ya ce”zancen banza kenan!!! A wannan halin da ta ke buƙatata a ko da yaushe ka ke tsammanin in fita?? Ba ka ganin hatta sojiji sun sarara mini saboda sun san darajar Uba? Dan haka Mallan faɗi duk abunda ka zo da shi ba ni da tamkar ta itama ba ta da ya ni!!" Kallonta sosai Likitan ya yi kafin ya ce "in faɗi komai a gabansa?" Cikin fushi Kaka Nura ya buɗe Baki zai yi magana sai kuma ya juya ya kalli Anne wadda a hankali ya ji motsi ya ga ta ɗan girgizawa Likitan Kai alamun A’a…shiruu Kaka Nura ya ɗan yi kafin ya ƙarasa ya shafa kanta ya ce "idan kun gama sai ki sakashi ya shigo da ni ko?Allah ya yi miki albarka ki kwantar da hankalinki" daga haka ya wuce da sauri ya fita gudun kar ya ɓata musu lokaci…… Sun riga sun saba da Likitan ya santa ta sanshi farin sani shiyasa ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita nan gefen gadon kafin ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya ya furzar da iska ya zare gilashin idanunsa ya ɗan mitsitstsika idanunsa kafin ya mayar da gilashin ya sake sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba saboda har ga Allah tausayinta ya ke ji matuƙa. “Nuratu da farko dai inaso duk abunda zan faɗa miki a yanzu ya zamana kin runguma kin karɓi jarabawarki hannu bibbiyu, hakan ake so musulmi ya kasance a ko da yaushe idan musiba ko ƙaddara ta same shi mummuna ko kyakkyawa….." Numfashi ya sauƙe wanda ita kuma Anne tuni tashin hankali da masifar da take ciki ya sake hauhawa....tsoro da firgici ba sa daga cikin ɗabi’arta amma a yau kam tsoron da ta tsinci kanta a ciki ba zai misaltu ba, ga wani Irin firgici da banɗokin zullumin jin abunda zai fito daga bakin Likita…tuni rigarta ta jiƙe sharkaf da gumi tsabar masifa har ma da gashin kanta ga azabar da fuskarta da ƙirjinta su ke yi mata ba na wasa ba ne! Tabbas ta san koma menene zai fito daga bakin Likita ba abun alkhairi bane ba tunda ya fara furta mata irin waennan kalaman a gabannin bayanin nasa....ga shi ta rasa fuskarta da ƙirjinta wanda surar jikinta kyan fuskarta su ne abun taƙamarta, ta san ko da ace za a gyara mata ba zata koma kamar da ba shiyasa kawai ta shiga addu’ar Ubangiji ya ɗauki ranta a take saboda bayaga musibar da take a ciki ba ta jin za ta sake karbar wata sabuwar jarabawar….. Cike da alhini muryar Likita ta dira a dodon kunnuwanta ta inda ya ci gaba da cewe "Ɗazu dama na gaya miki kuma kema kin ga yadda acid ɗinnan ya tauye Mamanki na hannun dama(right breast) kasancewar ya shafi na hannun hagun shima ya sanya jejin da ke ɓoye a jikinki ya ruru matuƙa! dan haka a gaskiya dole sai dai mu haɗa duka biyu a yanke saboda na yi testing acid ɗin mai mugun ƙarfi ne dan haka gara a yi maganin sa da jejin gaba ɗaya tun kafin jejin ya yaɗu a jikinki sannan ɓarnar acid ɗin ta fi haka. Karkarwa jikinta ya ɗauka a take, zuciyarta tana wani irin ƙuna…Bata gama nemawa bal’in masauƙi a cikin zuciyarta ba ƙirjinta ya yi wani kalar mahaukacin bugawa zuciyarta ta hantsila kamar za ta faso ƙirjinta ta fito sakamokon sautin muryarsa da ta ji yana daɗa cewa "Sannan nan da kwana biyu sun ce za su wuce da ke prison a ta sakamokon laifin garkuwa da Yara har biyu da ki ka yi ki kai tsafi da su, dan haka za mu kammala komai da wuri in yi miki duk abubuwan da ki ke buƙata sai ku wuce, ki ci gaba da jinya a cikin asibitin da yake prison ɗin in mun saka ranar da za a miki aikin za mu je mu ɗaukoki a yi miku in ya so a sake mayar da ke chan ɗin ki ci gaba da jinyar kafin a yanke miki hukunci." Cikin sauƙe numfashi ya ɗaura da cewa “mun yi miki gwajin jini saboda musan ta yadda za mu fi baki kulawa da kuma jinin da za'a samu a ƙara miki in an shiga dake aikin da za a yi miki a ƙirjin ki unfortunately Nuratu ki na ɗauke da cutarnan mai karya garkuwar jiki na san baki sani ba saboda ko last time da kuka zo da ke da Alhaji Nasiru aka duba sam babu ita a jikinki, sannan hantarki ta taɓu amma ita ba mu yi scanning mun tabbatar da matsalar wacca iri bace ba.." Cikin sauƙe numfashi ya ce "na gwada neman alfarmar a barki a nan dan sai kin fi samun kulawa duba da tarin ciwukan da su ke damunki gashi akwai wani aikin a gaba wanda dole sai an yi amma kuma kasancewar ba a daɗe da miki aiki a ƙafa ba ya sanya dole sai an jira.. But sun ƙi yarda, sannan duk yadda na so in samu wata ƙofa da za ta bani damar da za a yi miki aikin lokaci guda hakan ba zai taɓa yiwuwa ba, dan haka nan za mu haƙura mu yi addu'ar Allah ya sa kar abun ya fi haka mu jira har nan da tsawom mako biyu tukunna sai ki dawo a yi miki aikin ƙirjin...." Shiruu ya ɗan yi sai kuma ya fesar da numfashi kafin ya ce "Anyways... Za mu ɗauraki a kan magunguna yanzu kafin a dawo yi miki aikin, sai ki wuce da su chan ki ci gaba da sha Allah ya rufa asiri ya baki lafiya ….." Tabbas duk wanda ya ce bala’i ya ishe shi ya ke ganin kamar babu yadda za a yi ya sake shiga cikin wata masifar to Allah ne kawai bai so ba….Allah ne kawai ya barshi amma duk ta inda ka kai ga shiga tashin hankali ka ke ganin ka kai peak in dai Allah ya ƙaddara to akwai gaba da shi… da aka watsa mata acid gani ta ke yi kamar kawai ƙarshen masifar da za ta iya samunta kenan…da ta kalli ƙirjinta ta ga yadda ya koma sannan babu ƙafafu sai ta ga Ashe akwai level two, kwarin guiwar da Mahaifinta ya bata ne ya sanya ta ɗan yarda akan wataƙila za ta iya samu rayuwarta ta ɗan daidaita ta samu ta zama mutum ta ci gaba da rayuwarta dukda babu ƙafafu da ƙirji ta san za ta lallaɓa da babu gara ba daɗi sai dai abunda ba ta sani ba ashe ba ta ga komai ba kuma ba ta ji komai ba..a haka ma ba a zo kan maganar hukuncin da za a yanke mata ba na laifin da take da tabbacin ita ta aikata ita da tshohon saurayinta ɗan fashi ta inda ya sace Yaran su ka daɗe a wajensa ya na ta amshe kuɗaɗe a wajen iyayen Yaran, wanchan satin da ya gabata bokanta ya ce ta kawo Yara maza biyu a yi mata aiki da ta gaya masa(saurayin nata) ya ce akwai su ka kai Yaran ta yanka su da hannunta bayan ta yi zina da ko wanne a cikinsu tukunna aka yiwa yaran filla filla kamar yadda ake daddatsa kaza aka tsafe su tass aka haɗa da kayan tsafi aka saka mata a cikin tukunyar ƙasa da wani ruwan da boka ya rantse mata akan ba zai bari su ɓaci ko su yi wari ba ita kuma ta karɓa ta binne a ƙasan drawer kayanta har da kayan jikinsu ta binne a gefe da zobunansu na azurfa dan gudun kar ta je jefarwa ko ta yar a kamata...kuma sai da bokan ya tabbatar mata kar ta bari a gani in ba haka ba aikin ya lalace amma in ta ɓoye da kyau to har abada asiri ya na nan kuma ba zai lalace ba kamar yadda tsoka da halittun gangar jikin yaran za ta kasance fresh saboda ruwan da ya zuba aljanun za su dinga kula da shi ba zai lalace ba… Wanda abunda ba ta sani ba ma warin ne ya janyo hankalin sojojin zuwa inda ajiyar tata ta ke.... Kuka Anne ta saki wanda ba a ji ba a gani ta na sake jaddadawa kanta tabbas tata fa ta ƙare...Dan a yadda Allah ya yi fushi da ita ɗinnan ta fara ganin jarabawa kamar ruwan sama ta koina tabbas ta san wataƙila azabar da za ta gwammaci mutuwa za a yi ta gana mata a prison ɗinnan dan ita kanta ta san ƴaƴan waye ne amma da ya ke idanunta sun rufe a lokacin ta ce a yi mata aikin da su………ita da farko da ta ji Kaka Nura ya na batun police da hukunci sannan da ta ga soja a ɗakin ta ɗauka duk Sajida ce ba ta barsu ba ashe wannan ɗanyen aikin nata aka binciko.... A hankali ta samu da kyar ta rufe idonta tana karɓar azaba ta ko wanne fanni zuci, kwanya da gangar jikinta zuwa yanzu ta daina jin abunda Likita yake faɗi da bayanan sa dan iyakacin abunda ta sani shine tata ta ƙare!! Gashi komai ya lalace mata ya taɓarɓare mata! Tabbas wannan shine asalin mutuwar tsaye haƙiƙa babu yadda Ubangiji baya iya juya al’amari kuma ɗan Adam ba a bakin komai yake ba duniya da abunda ke cikinta zancen banza! wai yau ita Nuratu ita ce ake yiwa zancen babu Nonuwa babu ido babu fuskar data tsolewa dubu ido fuskar da take taƙama da ita sannan gata dumu dumu a hannun hukuma, dan haka babu isa sannan babu gadara..wani irin kukan zuci ta ke yi saboda ta riga ta san ba ta da wata sauran mamora gashi dai da sauran shan miyarta dan bata kai arba’in da biyar ba ma a duniya amma ta san ko tshohuwar mahaukaciya sai ta fita daraja da mutunci a idanun maza da duniya ma gaba ɗaya dan ko da ace ta tsallake case ɗin da yake jiranta ta fito ba a kashe ta ba, kuma ciwukan jikinta suma ba su tarwatsata ba tabbas a yadda halittunta suka koma ita kam ta san an gama yi mata mutuwar tsaye.…………… SHEKARUN BAYA DA SU KA SHUƊE (Waiwaye) [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *13* SHEKARUN BAYA DA SU KA SHUƊE.. (Waiwaye) KANO ƘOFAR MATA Asalin sunan Anne Nuratu Muhammad Nura, Mahaifiyarta cikakkiyar ƴar Kano ce anguwar zage ƙofar mata yayinda Mahaifinta ya kasance bafulatanin chad ɗan sarkin rugarsu a wanchan lokacin….faɗa ne ya korosa shi da Mahaifinsa daga chad tun lokacin da aka ci Mahaifin nasa da yaƙi wanda hakan ya sanya aka kwace matarsa da ragowar magoya bayansa waenda basu fi mutum biyar ba, sarkin da ya karɓi mulki shi ya auri matarsa shi kuma kakanta aka koresa kora ta har abada daga ƙasar gaba ɗaya da shi da mahaifinta (Kaka Nura) wanda a lokacin ya ke Yaro ƙarami. A Nigeria suka yada zango garin Kano unguwar ƙofar mata a lokacin Mahaifin Mahaifiyarta shine Mai Unguwa..shi ya karɓesu hannu bibbiyu ya musuluntar da shi da ɗan nasa (Kaka Nura) su ka zaɓi sunayen musulunci ya koya musu karatu har ta kai ga sun zama kwararru suma dan har koyarwa Mahaifin Mahaifinta ya ke yi a tsangayar kakanta (na ɓangaren uwa), Mahaifin Mahaifinta bai kai ga yin wani auren ba, kwata-kwata shekaru bakwai Ubangiji ya bashi ikon ƙarawa a duniya ya karɓi ransa….ya rage saura Mahaifinta (Nura) kaɗai wanda da shi da maraya ba su da maraba dan ko da wasa a yadda Mahaifinsa ya faiyyace tsarin rugar tasu ba a isa a mayar da shi garin ba tsaff za su yi masa yankan rago tunda korar su aka yi…. Mahain Mahaifiyarta (Mallan) ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya inganta rayuwar Nura, bayan karatun allo har a makarantar da ƴaƴansa su ke zuwa ya saka shi dan Mahaifinta (Nura) yanada shiga rai farin bafulatani ne kwarai kyakkyawan gaske sai dai kuma tun Nuratu ta na ƙarama ta ke ji a wajen Mahaifiyarta da ƴan uwan Mahaifiyarta kuma itama ta ji ta gani cewa ‘Mahaifinta sam ba mutumin kirki bane ba’ Dan tun ya na Yaro yana da taurin kai, riƙeƙƙen ra’ayi, cin amana, sata, ƙarya, son abun duniya da shegen son abunsa ga kwaɗayi da son abun wani…ƴan uwan Mahaifiyarta (Uwani) maza su uku ne Yusufa, Ali da Garba! Ita kaɗai ce mace a gidansu, ƴar auta..hakanan a ka ja shi a jiki a ka mayar da shi ɗan gida duk wani abu idan suka samu tare su ke rabawa da shi haka iyayen suma tare su ke yi musu komai da shi amma shi ko ruwa pure water idan ya siya ya na sha ka ce ya rage maka ba zai bayar ba sai dai ya ce 'shima ba zai ishe shi ba', kuɗi kuwa ta jikin Kakanta(Mallan) ya ke samu amma naira biyar ɗinsa ba ka isa ka ci ba gashi da shegen tsaurin ido Hakanan zai siyo Abu a gaban idanun kowa ya zauna ya ci ya yi ƙatt! Ya yi gyatsa ko magen gidan hakanan za ta ƙaraci kukan ta ta gama zagayeshi amma ba zai bata ba… Wannan ɗabiar ta Mahaifin Nuratu (kaka Nura) ita ta janyo masa baƙin jini a wajen Mahaifiyar Mahaifiyarta saboda dama ita tanada ɗan zafi kuma ba ta son raini…Mahaifin Mahaifiyarta(Mallan) kuwa shi kam bai cika son gutsiri tsoma ba shiyasa bai taɓa biye mata ba ƙarshema ce mata ya yi ‘kar ta sake kawo masa ƙararsa, ai kowa da halinsa ake zaune da shi kuma har yanzu Nura (Kaka Nura ) Yaro ne dan haka baya son yawan zance iyakaci shi dai ya san zai ciyar da shi ya yi masa tufafi ya bashi muhalli har zuwa lokacin da Allah zai ƙaddara ya yi aure ya kama gabanshi.’. Tsanar Kaka Nura ba ta sake samun wajen zama a cikin zuciyar Mahaifiyar Uwani ba sai lokacin da ya kawo ƙarfi, a lokacin mazan gidan guda biyu sun yi aure saboda dama duk sun girme masa sosai mutum biyu ya girma Uwani da yayanta, dan haka gidan sai ya rage daga shi sai Uwani da yayanta wadda take da shekaru sha huɗu dan yayunta maza biyu sun basu tazara sosai har ana tunanin ma Mallan ya daina haaihuwa ne tukunna aka haifi yayanta (saƙonta)itama aka haifeta. A wannan lokacin shekarun yayan nata sha shidda sai Kaka Nura shima sha shidda dan watanni uku ne a tsakaninsa da yayan nata. A lokacin ne Mahaifiyar Uwani ta fahimci shegen son matan Kaka Nura dan har Mata ta ji ƙus-ƙus ɗin ya na kaiwa shagon su wanda ke a waje saboda duk mazan manya sun yi aure kuma dama a ɗakinsu ya ke sai ya zamana ɗakin ya zama nasa shi kaɗai, dan Yayan Uwani wanda ya rage a cikin gida nasa ɗakin yake..... Ita ta ɗagawa Mallan hankali akan batun amma sai dai ba a yi mata yadda take so ba ƙarshema abun caɓe mata ya yi dan Mallan cewa yayan Uwani na cikin gida ya yi 'ya tartara kayansa ya koma ɗakin Kaka Nura da ke a waje idan har gaskiya Mahaifiyar Uwani take faɗa to hakan zai takawa Nura burki daga ɓarnar da yake yi'. Sai dai kuma ko sati ba ayi da komarwa yayan Uwani shagon ba Kaka Nura ya yi ɓarnarsa da ƴan mata har biyu kuma ya shiga ya fita aka kama yayan Uwani da laifin dumu-dumu, laifin da har yau har gobe kowa yake ganinsa da shi, Mallan shima har ya rasu da laifin yake ganin yayan Uwani dan gani yake yi kamar shi ne ya aikata. Uwani da yayanta da Mahaifiyar Uwani sai shi Kaka Nuran ne kawai suka san asalin gaskiya……. Fusatar da Mallan ya yi ne ya sanyashi ya cewa yayan Uwani ya fito da mata ya yi masa aure aka cire sa daga makaranta babu kalar kuka da roƙon da bawan Allahn nan bai yi ba amma haka yana ji ya na gani aka ciresa daga makaranta aka aura masa wata Yarinya ƴar makwabton su a lokacin shekarun sa goma sha shidda a duniya, to dai ya samu bayan auren ya ci gaba da karatunsa dan har aiki ya yi kafin Allah ya karɓi ransa...amma fa har Alhaji Ali(yayan uwani) ya bar duniya kwata-kwata baya son kuma ba sa shiri da Kaka Nura kamar Annabi da kafiri haka su ke….. Nura ya na kammala secondary school shima akace ya fito da mata a yi masa aure, dan zuwa wannan lokacin Mahaifiyar Uwani cewa ta yi 'Wallahi sai dai Mallan ya zaɓa ita ko Muhammadu Nura.' Wallahi abun kamar tsafi dan tashi ɗaya Mallan ya ce ‘ya ba shi Uwani’ wanda hakan ya girgiza Mahaifiyar Uwani sanadiyyar samun hawan jininta kenan har ta rasu ta na fama da shi...saboda ana sanar da ita zancen ta yanke jiki ta faɗi sai a asibiti ta farfaɗo. Ta san halin Mallan ba ya magana biyu amma haka nan ta dage ta dinga gwada sa’arta har ƙaninsa sai da ta sako a cikin zancen amma furr!! Mallan ya ce ya gama magana ƙarshe ma da ta ɗaga masa hankali matso da ranar auren ya yi ya zaftare wajen watanni biyu a ciki wanda hakan ya sanya ta ja bakinta ta yi shiru ta zubawa sarautar Allah idanu.. Har da tsoron kar a bawa Nura ƴartata ne dama ya sanya ta azalzala ta ɗagawa Mallan hankali a kan ya yiwa Nuran aure saboda tun lokacin da ta lura da irin kallon da ya ke yiwa ƴartata hankalinta ya yi masifar tashi kuma ta lura har Abu ya ke siyowa ya bata abunda ba ɗabi’arsa bace ba shiyasa tun kafin ya furta ta so ta yiwa tufkar hanci sai dai abunda ba ta sani ba Nura ya fi ta sammako dan Allah kaɗai ya san kalar shige da fice da makirce-makircen da ya yiyyi aka basa Uwani, dan indai makirci ne da juya kwakwalwar ɗan Adam to tabbas ya ci a bawa Kaka Nura tutar yabo. Mallan bai kai ga ɗaura musu auren da ya ci buri ba Allah ya karɓi ransa, gajeruwar jinya ta kwana biyu kacal ya yi yace ga garinku, tsabar bala’i irin na Kaka Nura ana kai Mallan makwancinsa ya nemi limamai da dattawan layi da su ɗaura masa aure da Uwani a cewarsa kar Mahaifiyar Uwanin ta dawo dai-dai ta raba abunda Mallan ya so ƙullawa, sun gasgata zancen nasa dan ƙiyayyar Mahaifiyar Uwani ga Kaka Nura a fili take ga kowa! Makwabta da ƴan uwa, yayinda shi kuma manya-manyan mugayen halaiyyarsa su ke a ɓoye, sun shaida kuma sun san Mallan ya bawa Nura Uwani shiyasa suka goya masa baya a ranar sadakar farkon rasuwar Mallan aka ɗaura auren Nura da Uwani a cewarsu sun cikawa Mallan burinsa. Ga zafin baƙin ciki ga zafin rasuwa, su suka taru suka sanya Mahaifiyar Uwani ta kasa taɓuka komai ta kwanta ciwo ya yi mata ruff ko iya gane waye a kanta ba ta yi dama tunda aka yi rasuwar ta ke kwance, amma a hakan Nura ya ɗagawa kowa hankali ranar sadakar uku Uwani ta tare a gidansa wanda ke a Unguwa Uku mai ɗakuna biyu a jere da banɗaki da kitchen wanda ya tara kuɗi ya siya da kuɗin Allah ya Isa da kuɗin haram da na sata….…. Rigima sosai aka yi da shi aka yi baram-baram tsakanin sa da ƴan uwan Uwani kowa ya fita a harkarsa sai dai kuma tausayin ƙanwarsu bai sa sun janye ba hakanan Yusufa da Ali su ke ɗan leƙata from time to time dan idan akwai wanda ba ta so a kaff faɗin duniyar nan a wannan lokacin har da yanzu ma to Nura ne….. Bayan aurensa da Uwani ya nuna mata soyayya kwarai dan har ya kai ga sanyawa ta ɗan fara shaƙuwa da shi abunka da zuciyar mace yau da gobe sai Allah miji da mata sai dai kallo wanda kwanciyar hankalin da Mahaifiyar Uwanin ta gani a tattare da ƴartata ne ya sanya ta ɗan kwantar da hankalinta dukda har gobe tun ranar da Kaka Nura ya tattara kayanshi ya tare a Unguwa Uku da Uwani bai taɓa zuwa ya gaishe ta ba amma ta zuba musu ido kuma sam ba ta ƙorafi kullum addu’ar ta Allah ya bawa ƴarta farin ciki da ribar rayuwa, ko a waya bayan waya ta fito har matar ta rasu ba ya kiranta baya kulata kwata-kwata a cewarsa ita ɗin maƙiyiyarsa ce, ita ma kuma ba ta zuwa gidansa sai dai in ta je gidan Baba Yusufa Uwani ta je har chan tukunna su haɗu su ga juna, dan ba ya hana Uwani zuwa chan ɗin ta gaisheta amma shi kam ba ya zuwa, ko gidanta ko gidan Baba Yusufa. Ƴar soyayyar da ya nuna mata ta iyaka watanni uku ce kacal bayan aurensu da kuma shaƙuwar da suka yi ne ya sanya ta fi shan wahala a lokacin da ya juya mata baya, dan tun da ta rufe watanni ukun nan a gidansa shikenan uƙubarsa da cin mutunci kala-kala su ka ce salama alaikom.. Shekara ɗaya kacal aka ɗauka da yin auren su ya fara mitar shi fa ya ji shiru ko dai juya ce…a cikin shekara ɗayan nan wanda sai da aka ƙara shekar ɗaya da wata takwas tukunna ta ɗauki cikin Anne sai da Kaka Nura ya auri mata har guda biyu kuma matan ta farkon babbar ƙawarta ce ta unguwar, ɗayar kuma ƴar makwabta mai tayata kwana idan ba ya nan..kaff cikinsu ko alamun ciki babu a tare da su har ya sakesu amma a ko da yaushe cewa ya ke yi rashin haihuwar a jikin Uwani ne dan gashi kaff cikin danginta da suka yiyyi aure sau ɗaya tak aka haifi twins (Mustapha da Abbakar) ƴaƴan babban yayanta (Baba Yusufa) sai yanzu da matar ta sake ɗaukar ciki. Cewa ma yake ita ce ta shafawa ragowar matan da yake aurowa rashin haihuwa sannan tsabar baƙin kishinta ne ya sa suka kasa haihuwa da shi. Kasancewarsa mutum mai matsanancin son ƴaƴa ya sanya ya rufe ido ya dinga kafta mata ruwan takaici ba dare ba rana. Ko da aka haifi Zainab Baba Yusuf ya so ya bawa Uwani ita tun da ɗanye cibinta sabida zaman kaɗaici da baƙin cikin da take yi, amman furr Kaka Nura ya ƙi yarda dukda masifar son ya ga Yaro a gidansa amma sai cewa yayi 'shi ya fi son tsattson sa'.. hakanan Uwani ta haƙura ta ci gaba da karɓar uƙuba kala-kala daga garesa gashi a lokacin Mahaifiyarta itama ta rasu dan haka hakanan take naɗar baƙin ciki ita kaɗai… Gaba ɗaya sai da ya ja mata raina da ƙananun maganganu a wajen makwabta dan hakanan yake bin Yaran layi masu tasowa zawarawa da manyan mata...babu abunda ya shafesa zai kashewa wadda yake tare da ita kuɗi amma ita Uwani dai-dai da kukar kaɗa miya daga gidan Baba Yusufa ake aika mata kuma idan ta dafa ya zauna ya naɗa hankali kwance ya kuma je waje ya zubar da abunda ya tara a ƙadangarun bariki.. Baba Yusufa ya so ya raba auren amma sai Uwani ta ce ya barshi kawai ta ƙarasa a haka ba don komai ba ita kanta ta san ba ta da wani gata yanzun kam, ɗayan yayan nata soja ne a portharcourt ya ke shi kansa ba zama ya ke yi a gidansa ba, zamanta a gidan Baba Garba kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba saboda yadda ya tsani mijita itama haka ya ke jin haushinta da kyar ya ke iya amsawa in ta gaishesa tunda ta auri Nura ta yarda ta zauna a gidansa shikenan ƙiyayyar da ya ke yiwa Nuran ta shafeta...gidan Baba Yusufa kuwa yau da gobe sai Allah dan ba wani shiri take da matarsa ba (Yadikko) kasancewarta mace mai son abun mijinta, shiyasa kawai ta zaɓi ta zauna ta ƙarasa a haka duk tsiya ita ɗaya dai ranta a gidan mijinta ta san wuya ba za ta kasheta ba... Daɗin daɗawa kuma Kaka Nuran ya kafeta ne a gidan saboda ko ba komai ya san ya na morarta duba da yadda Baba Garba da Baba Ali (Yayanta na portharcourt) su ke ciyar da shi da ita, ya san ba duk mace zai samu a yi masa hakan ba. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *14* Shekarar Zainab ɗaya a duniya lokacin Kaka Nura ya na tsaka da yiwa Uwani gorin haihuwa kwatsam sai ga cikin Anne ta samu da ikon Allah, dan kowa sai da ya yi mamaki saboda a yadda Kaka Nura ya ke shelar ita ɗin juya ce a Unguwa duk an ɗauka ya je asibiti ne an bashi shedar ba za ta haihu ba. Kaka Nura har kukan murna sai da ya yi, ya kwana ya na sallar godiya ga Ubangiji ya yi azumi ashirin na godiya sannan ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗaurawa cikin. Tun cikin ya na jinjiri dama yake addu'ar Allah ya sa mace za a haifa masa saboda shi a cewarsa idan ya haifi Namiji jidali ne dan kafin ya gama rainon sa ya yi karatu ya fara aiki za a ɗauki lokaci kuma aure zai yi dan haka ba lalle ya ci moriyarsa sosai ba amma idan Allah ya bashi ƴa mace ya san jari ce musamman ma idan Yarinyar ta yo kyawun shi da tsantsar farin jinin shi ya san tabbas kakarsa ta yanke saƙa, shiyasa ya duƙufa addua Allah ya bashi ƴa mace. Tabbas Kaka Nura ya na son haihuwa kuma ya na son ƴa mace amma bayan an haifi Anne da ya ɗauketa ya san ita ɗin fa tashi ce anan soyayyarta ta nunku a cikin zuciyarsa fiye da tunanin mai karatu, ba yadda ba a yi da shi akan ya bari a saka mata wani sunan ba amma ya ce sunanta ‘Nuratu’, Nuratu Muhammad Nura..dan ko a suna ba ya ƙaunar abunda zai banbamta su. Dama tun asali Kaka Nura ya kasance mutum mai tsananin son abunsa nan take gaba ɗaya tunda aka haifi Anne komai nashi ya sake fitowa fili kwata-kwata ba shi da kara a duk abunda ya shafe ta, ba kalar cin mutunci da zagin da Uwani ba ta fuskanta a duk lokacin da ya shigo ya tarar Anne ta na kuka… Kai tsaye sannan tashi ɗaya za a saka Kaka Nura a cikin jerin talakawa amma tunda aka Haifa masa Anne aka fara cin abinci na gani na faɗa a gidansa saboda ruwan Nono, kalar kayan jikin Yarinyar kuwa abun kallo ne, ko kyalle bai siya ya bawa Uwani ba amma Anne kam sai da ya yi mata akwati uku duk wani abu da aka san Jariri zai buƙata babu wanda Kaka Nura bai siya ya ajjiye ba. Cs aka yiwa Uwani saboda ba zata iya haihuwa ba amma sam Kaka Nura bai damu da magani ko lafiyar ta ba shi dai kawai komai ƴarsa. Gobara ce ta rabo su daga Unguwa Uku, ta inda gidan ya ƙone ƙurmus to the ground su kansu da kyar su ka fita, daga nan su ka bar Unguwa Uku su ka koma Mariri da zama lokacin tun bata kafu ba gidan Baba Yusufa, inda ya ware musu ɗakuna biyu ya zagaye a cikin gidansa suka zauna. Baba Yusufa shima ba wani mai kuɗi bane ba, ya na da dai rufin asiri kuma ƴaƴansa biyu ne a gabansa dan Abbakar tun ya na ƙarami ya ke makarantar sojoji (a wajen ƙanin mahaifin nasa) wanda hakan ya kasance burinsa ne, dan haka Zainab da Mustapha ne kawai a gabansa sai matarsa guda ɗaya Yadikko shiyasa ba shi da wani nauyi sosai..... Gidan nasa irin gida ne mai babban fili dan tun ana yankar fili da daraja a Unguwar ya yanka, su ne farko-farkon Unguwar. Hakan ya sa bayan gidansu Anne ya ƙone ƙurmus ya yi ƙoƙari ya gina ciki da parlour da toilet da kitchen a wawware ya zagaye musu, ita Uwani ma ta ɗauka a cikin kuɗin rabon gadonta wanda ke hannunsa ya yi mata ginin sai da ta tare ya bata kuɗinta a hannunta ya ce ta ja jari tukunna ta san tsantsar zumunci da so da tausayinta ne ya sanyashi yin hakan. Dukda cewa a wannan lokacin ko kuɗin hayan gidan wanka Kaka Nura bashi da ikon biya amma sai da aka kai ruwa rana da shi ya kakkafa sharuɗansa tukunna ya yarda ya biyota aka tare a gidan da shi ya na ta kumbure-kumbure haka itama matar Baba Yusufa (Yadikko) ba kaɗan ba ta ɗaga masa hankali ta yi ta bori kafin daga baya komai ya ɗan lafa dan daga ita har Kaka Nura babu wanda ya tanka su…. Tun a kan Zainab da Anne Kaka Nura ya fara bawa al’umma mamaki da tsoro saboda ƙiri-ƙiri irin abun nan na Yara idan Zainab ta daketa muddin idanunsa suka gani to fa haka nan zai zage ya ɗaɗɗaka mata duka a cewarsa ai ta girmi Annen saboda ita Anne a lokacin shekararta ɗaya ita kuma Zainab ta doshi uku…Abun Yaro sai da ta kai ta kawo Zainab ta daina shigowa shashensu Anne ko Mustapha ya shigo da ita a hannu to fa ta dinga tsala ihu har sai an fitar da ita dan sosai Kaka Nura ya ke makarta ko bige Anne ne idan ta yi ba tare da sanin ta ba sai ta karɓi hukunci gashi kullum ya na gida dan zuwa lokacin ko ƴar kasuwar da ya ke zuwa ya daina a cewarsa shekaru sun ja mutumin da ko talatin bai rufe ba, tunda aka bawa Uwani jarinta idanunsa su ka gani ta fara sayarda gumama shikenan ya koma ya zauna ya naɗe hannuwansa ta ke yi musu komai, ƙarƙari idan aljihunsa ya yi ƙasa ya ɗauki asusunta ya fasa ya siyamusu kayan maƙulashe shi da ƴarsa kuma Uwanin ba ta Isa ta yi magana ba idan kuma buƙatar auren sa ta motsa hakanan zai ɗagawa kowa hankali da roƙo da bashi da kuɗin Allah ya Isa zai haɗa ya yi…dan zuwa wannan lokacin Alhamdulillah tunda aka Haifa masa Anne ya daina neman mata ammafa aure-aure kamar an ce masa bismillah! Hakanan zai tara ƴan kuɗaɗe da kyar ya kama haya ya yi sabon aure su tare, tare da shi da Amarya da Anne. To dai tun bayan haihuwar Anne gaskiya kusan duk itace ta ke kashewa Kaka Nura aure, wanda a da halinsa ne amma fa tunda aka haifeta duk aurarrakinsa ita ce silar mutuwarsu…shi dama Kaka Nura ba ya aikin fari balle na baƙi kuma tunda Anne ta kai shekaru uku tun a zance ma tare ya ke zuwa da ita dan kullum tana hannunsa maƙal-maƙal. Da zarar ya yi aure a tare ya ke tarewa a gidan da ita ranar da amaryar ta tare sai an lallaɓata ta ci kaza ta ƙoshi ta yi barci an kaita ɗaki tukunna ake samun lokacin amarya, mai kirsa itace ta ke iya tolerating Anne a gidan na sati ɗaya mara kirsa mara haƙuri kuwa tun a ranar farko ake fara gani a kan fuskarta….. Ba wai saboda tarairaya ko fifikon da Kaka Nura ya ke nunawa Anne ne silar janyo matansa jin haushinta ba, sam abun ba haka ya ke ba… Ita dai Anne tun ta na Yarinya kwata-kwata ba ta san wani abu wai shi tsoro ba, dan tun ta na jaririya ko irin ƙarar nan ko tsawa kwata-kwata basa firgitata duk wani abu dai da za a ce ya na bawa jariri ko Yaro tsoro to sam ba sa bawa Anne tsoro, da ta taso kuma ta fara takawa tana daɗa wayo ko horo film ake kallo a talabijin manya da Yara su na rurrufe idanuwa ita kuwa nata idanun ƙurr!! Har sai ta ga kwal uwar daka..ta kan ji ɗar!! Idan kallon ya yi abun tsoro na fitar hankali amma ba dai tsoro ba. A zahiri a real life kuwa babu abunda ya ke sakata ta ji ɗarr ɗin, sam babu shi!!. Abu na biyu kuma game da Anne wanda shima da shi aka haifeta shine tsaurin ido, na farko bata jin tsoron mutum ko aljan ko wani abu a duniyar nan abu na biyu kuma shine tsaurin ido, duk girman Mutum Babba ko Yaro wuyarta ya taɓa mata abunta ko ya shiga sabgarta to fa ko tsayinta bai kai ba sai ta hau kan abu ta maresa idan kuma bata samu fuska ba to za ta daki duk inda ta samu kuma ba ta mantuwa sannan ba ta yafiya… Abu kuwa indai har ta na so ranta na so to fa a bata ko kar a bata zata saka hannu ne ta ɗauka duk yawan harara ko zare idon mutum wannan sam ba damuwarta baceba idanun mutum ne za su yi masa ciwo a banza, kuma idan ka dake ta ta rama, idan akaci galaba a kanta kuma a fuskanci tujara da bala’in Kaka Nura... Lokacin da ta ta fara baki kuwa tsaff ta ke haɗawa mutum har da zagi hakanan zata zubo maka ashar ɗin da zai ɗaure maka kai dan kafin ka gama lissafi da fahimtar ashar ɗin ya baka ma’ana ma ta yi gaba abunta….tsiwa da masifa kuwa a jinin Anne su ke tun ta na Yarinya, da ta taso ta fara wayo kuwa kwata-kwata ba’a cin galaba a kanta a cacar baki sai dai a bar mata . Anne bata san defeat ba sannan ba ta san a fi ta ba, ga masifaffen kishi wanda tun ta na Yarinya ba ta so ko a kalar fata ta ga wadda ta fi tata kyau... Duk girman mutum Anne bata san ta kirashi da Yaya, Baba ko Anty ba! Hatta Uwar da ta haifeta da Dije ta ke kiranta Mahaifinta kuma Nura sai da ta kai shekaru biyar ne ya ci sa’a ta ke kiransa da Baba Mahaifiyarta kuma ta mayar Uwani kamar yadda ta ji yayanta(ita Uwanin) ya na kiranta da shi amma shi kanshi mai gidan yayan nata da Yusufa ta ke kiranshi matarshi Yadikko kuma Mairo, idan ƴaƴanta suka dake ta a kwana ana bala’i da su, ita da Ubanta... Gashi a duniyar nan ko Anne za ta tsolewa Sarki ido to fa sai dai a haɗa da ita da Kaka Nura a tsire dan sam ba zai taɓa yarda ƴarsa ta yi laifi ba, shiyasa ta ke kashe masa aure cikin sauƙi saboda dukda kasancewarta Yarinya amma ta na da wani matsanacin kishi da ta ma fi Uwarta takaicin ganin ta ga ya yi aure sai dai kuma bata taɓa nuna mishi ba tunda ta yi wayo sai dai ta bi cikin sauƙi da kirsa kamar wata babba ta kashe auren murus, dan tun ta na ƙarama ma hakan ce ta ke faruwa ko kallonta matar ta yi haka za ta yi ta tsala ihu shi kuma ya ce 'an yi mata wani abun ne, ai ba zata yi ihu haka kurum ba ba haka take yi a gida ba.' Har tsoro matan nasa su ke yi su kasance a guri daga su sai ita dan sun san ranar alƙiyamarsu ta tsaya kenan... Wasu kuma fushi su ke yi su yi yaji su tafi shi kuwa dama bai taɓa biko ba, wasu kuma da ita da shi ɗin ne su ke yin yajin sai dai kawai Matar ta ga takarda daga baya. Duk a cikin ɗabi’un Anne Uwani ta fi jin takaicin ƙarya da makircinta dan ko shekaru bakwai bata rufa ba ƙarya da makircinta su ka baiyyana a idanun kowa ɓaro-ɓaro, kamar wata babba idan ta yi wani abun gashi ko harara idan Uwani ta yi mata haka nan itama zata zage ta rama kuma ta gayawa Baba ranar ya kwana yana ife-ifen sababi an hararar masa ƴa an takura mata ita da gidan Ubanta... Duka kuwa ko bayanan idan ta dake ta ya dawo nan zata gaya masa shi kuma ya riƙe Uwanin Anne ta rama, wannan tashin hankalin ne ya sanya kwata-kwata Uwani ba ta gigin dukanta dan tun lokacin da ya yi mata irin hakan har sau uku tun Annen bata ma gama wayo ba shikenan ita kuma Uwani ta shafawa kanta lafiya..maganin bari kar a soma. Sosai Anne ta raina Uwani kamar kashin gindinta ba ta jin maganarta ba ta sassauta mata ko aike sai taga dama idan tanada gurin biyawa tukunna idan da kanta ta ce mata ta kawo ta je mata to fa shine Uwanin ta ke samun ikon aiken ƴartata… BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *15* Batun Makaranta kuwa tunda Anne ta nuna ba ta son islamiyya Kaka Nura ya ce ba a dole zai koya mata karatun sallar a gida. Boko kuwa sau shidda ya na chanja mata makaranta, Ana korarta.. In ta tashi yin dambe wani zubin har da reza ta ke yi a ɓoye dan ba za a tashi fahimtar akwai rezar a hannunta ba har sai ta soma kakkarta fuskar Yaro ko Yarinya, shiyasa ta na aikata hakan ake korarta, yayinda wasu makarantun kuma su ke ƙin ɗaukarta. Last makarantar da aka koreta kuwa repeating ne aka yi mata Kaka Nura ya ce ba su isa ba, dan ta ce masa ba za ta zauna a ajin Yara ba shima kuma a nasa ganin repeating ɗin cin fuska ne shiyasa ya je ya na ta hayagagar a saka ta a class ɗin gaba ta tafi tare ita da sa'o'inta ƴan ajinta... Kuma fa hatta ajin bayan ajin da aka yi mata repeating ɗin zuwa cikinsa da aka gwadata 2/70 ta ci a test ɗin shiga ajin, shiyasa su ka koreta daga makarantar cikin aminci saboda dama da kyar suma ɗin aka samu su ka karɓeta kuma kusan duk malaman haushinta su ke ji bayan ta shiga makarantar saboda in ana neman daƙiƙiya lamba ɗaya to Anne ce! Ga rashin kunya ga mugunta ga dambe da Yara, kuma duk wani salon iskanci, raina malamai da iya shege duk ita ta ke koyawa Yaran... Gashi kwata-kwata ba ta maida hankali ballantana ta samu ta tsinci wani abun dukda kuwa abun da kamar wuya dan kwakwalwar Anne da karatu kamar rubutu ne a kan ruwa ana yi ya na gogewa.... Amma wani ikon Allah waƙa kam tsaf ta ke haddaceta ta zauna a harshe da kwakwalwarta daram! Dan in ta na rera waƙa kamar wata zabiya musamman in ta soyayya ce! Haka nan za ta ke rerota tsaf! A-Z har da ƙarin shauƙi da karkashe murya....... Shiyasa ta ke zaman gida yanzun yayinda Kaka Nura ya ke ta fafutukar ganin ya nema mata gurbin karatu a wata makatantar, dan daga ita har shi su na so ta samu ilimin boko saboda a tasu kalar fahimtar shi zai sanya ta sake wayewa. Sannan a kullum ya na jin takaicin yadda waenda ya yi secondary da su su ke da rufinɗ asiri amma shi bai da shi wanda a ganinsa bokon da su ka ci gaba da yi ne sila dan shi bai ci gaba ba kuma girman kai da son jiki sun hana su barshi ya ci gaba...amma ita Anne ta nuna masa ta na son boko sosai shiyasa ya ke so ya cika mata burinta... Kuma dama gani ya ke yi rashin karatun da bai yi ba ne ba ya sanya shi bai samu rufin asiri irin nasu ba ba wai zanen ƙaddararsa ce hakan ba. Ga shi duk sun san halinsa ba mai kyau ba ne ba shiyasa ko wata sana'a in ta taso ba sa saka shi a ciki..ƙarƙari in ya yi roƙo su bashi in sun ga dama dan sun san ya na barin inda su ke ya ke zaginsu zagi na cin mutunci da ɓatanci, saboda shi Kaka Nura a tsarin rayuwarsa ma kowa ya shaida ya fi cin mutuncin wanda ya tausaya sannan ya taimaka masa. Akwai wata ranar da Uwani ta aiketa ta kai mata ƙuɗin adashenta... Ita kuma Anne ta kashe kuɗin tass! Dama neman kuɗi ta ke yi a lokacin kuma ta ga Anne ta na neman ɗan aike dan haka ta amshe ta ce za ta je. A lokacin shekarunta ba su kai goma sha biyu ba amma Hakanan ta siyawa saurayinta biscuit da alawa kala-kala na wajen ɗari biyar ta kai masa su ka sha zancensu a bayan gidansu Yaron tukunna ta koma gida. Ta na shiga ko kallo Uwani ba ta isheta ba, ta ce mata "kuɗinki sun zube! Na yi neman duniya ban gani ba" Daga haka ta shige daƙi ta barta a tsaye a wajen cikin matsanancin ɓacin rai, dan da mugun kyar ta iya haɗa kan kuɗin saboda ita da Ubanta. Anne ba ta kai ga kwanciya a ɗakin da ta shige ba ta fara jiyo sallama!..... Ba kowa bace illa Mahaifiyar Yaron, Yaron da biscuit da alewarsa tuli fuskar Yaron dagaje-dagaje kana gani ka san ya daku ya sha kuka… Ko gaisuwar kirki Mahaifiyar Yaron ba ta bari ta yi da Uwani ba ta shiga zaiyyano mata zantuka tiryan-tiryan...haka nan ta zaiyyane wa Uwani cewa 'soyayya Anne da Yaron su ke yi tun a makaranta, to kasancewar ita Annen an koreta a makarantar ya sanya yanzu ta ke binsa har gida, har da su biscuit da alawa kuma yayan Yaron ya ce ya na ganinsu kusan kullum dan lokaci su ka ware su ke haɗuwa shiyasa ya saka ido, in ta je har rungume juna su ke yi kafin su rabu da wasu abubuwan da ba su dace ba…' Saboda ita dai Anne ta koyi abubuwa bilaadadin daga wajen Baba da matayensa dan tun ranar da ta taɓa farkawa ta gansu shikenan ta koyi yin barcin ƙarya…Tun abun ya na bata mamaki har ta fahimci komai da kuma dalilin da ya sanya ake yin hakan. Cikin ɓacin rai Anne ta yi tsalle ta fito daga ɗaki cike da tsantsar rashin kunya ta kalli matar ta ce mata "yanzu da ki ka zo ki na zaiyyane mata aka gaya miki yanka ni za ta yi? Allah na tuba ai soyayya halak ce ba haram ba duk ku biyun da kuka tsaya ku na ta faman munafurcinmu inda babu soyayya ai da ba ku yi auren kun yi cikin da kuka haife mu ba!!!" Shiruuu duk su biyun su ka yi jikin kowacce ya yi sanyi musamman Uwani wadda ta fara hawaye a take. Ko a jikin Anne! Hakanan ta zuba tsaki sannan ta sake cewa "a bar sawa mutum ido bashida amfani kuma a daina munafurci, soyayya kam yanzu na fara babu uban wanda ya Isa ya hana ni" Da sauri Yaron ya matso jikinsa ya na karkarwa ya jefa mata ledar biscuits ɗin ya ce "ni kam babu ruwana dake kar ki sake kulani" Sai kuma ya juya ya kalli Mahaifiyar tasa ya ce "Mama dan Allah ki yi haƙuri ki zo mu tafi kema kar ki yi kuka…” Wani irin kuka Uwani ta fashe da shi wanda hakan ya sa matar ta yi saurin juyawa ta fita riƙe da hannun Yaron da sauri dan baƙin ciki da tausayin Uwani tsaff za su saka ta rufe Nuratu da duka kuma sarai ta san halin Ubanta.. Shiyasa kawai ta tafi tun kafin ta jangalo abunda za’a yi ta ce-ce-ku-ce. Duk haƙurin Uwani ranar kasa jurewa ta yi dan matar nan ta na fita ta finciko Anne ta rufeta da duka… Tsoro da dana sani su ne su ke sanya Yaro yin laushi a duk lokacin da na gaba da shi ya ke hukunta shi wanda sam Anne ba ta ji wannan tsoron ko dana sanin ba dan ba ta san ma ya ake yin su ba dama chan... In banda wani baƙin ciki da tuƙuƙi babu abunda zuciyarta ta ke yi shiyasa har ta samu ƙarfi da damar hankaɗe Uwani ta faɗi zaune daɓass a wajen, ba ta gama dawowa dai-dai ba Anne ta taƙarƙare ta kifa mata mari…. Dukda haka marin da ta yi mata bai isheta ba dan so ta yi ta rarumo abu ta maka mata saboda hakan ta ke yiwa duk wanda ya fi ta girma a yayin faɗa, amma da ikon Allah yadda Uwanin ta kafeta da idanu ta dafe ƙuncinta jikinta da bakinta su na rawa duk sai ta ji ta kasa aikata abunda ta yi niyya a gareta….a hankali idanuwanta (Uwani) su ka soma ƙaƙƙafewa kafin ta tafi luuu ta zube a wajen ta na wani kalar sassanƙarewa dai-dai nan Zainab wadda itama ba ta daɗe da shigowa ba shock ya hanata motsi ta rafka uban salati ta fashe da kuka ta yi kan Uwani da gudu. Salatin nata ne ya janyo hankalin ƴan gidan gaba ɗaya dan duk su na tsakar gida a ta dalilin ziyarar bazata da Baba Ali ya kawo shi da matarsa da mahaifin matarsa (wanda ya kasance amini ga mahaifinsu lokacin da ya ke raye) da Abbakar... Wanda abunda ya kawo Zainab ɗin ma kenan, kiran Uwani ta zo yi. Gaba ɗayan su cikin sashen nasuu Uwanin su ka yo, ganinta a kwance a sanƙare ya sanya Abbakar, Mustapha da matar Baba Ali su ka yi kanta a gigice yayinda Su Yadikko su ka shiga tambayar ba'asi ita da su Baba Ali hankalinsu a masifar tashe... Zainab ce ta sanar musu abunda ya faru wanda hakan ya sa duk suka ɗago su na kallon Anne da mugun mamaki kafin Baba Ali ya yi kanta a zuciye Mahaifin Matar tasa ya yi saurin ruƙosa saboda tshohon ya kasance mutum mai kawaici da tsananin haƙuri. Duk wannan hayya-hayyar da su ke yi Anne ta na nan kyam a tsaye ko gezau bata yi ba ga dai mutum dattijo da khaki a jikinsa ya na shirin damƙarta amma sam bai ba ta tsoro ba. Shiruu duk su ka yi, kafin su Abbakar su shiga cewa "bara a kaita asibiti" da ƙoƙarin ganin sun kinkimeta... Baba Yusufa ne ya ce su jira ya nemo abun hawa dan motar da ta kawo su Baba Ali ta tafi shan mai, dan haka su ka dakata yayinda shi kuma ya fita da sauri jikinsa ya na karkarwar tashin hankali sosai. Tsohon mutumin nan kuwa ya rasa ma ta cewa dan ya yunƙura ya fi sau biyar da niyyar yin magana amma sai yagagara dan abun ya girme masa matuƙa, tsabar al'ajabi da takaici a take jikinsa ya soma karkarwa, ya na tari ƙasa-ƙasa. Tsaki Anne ta yi, ta ce "kana fama da tsufa, amma ba za ka zauna a inda Allah ya ajjiye ka ba, uban meye ya tado ka tun daga wani gari ya kawoka nan? Da ka zo nan ɗin ma ba ka tsaya a inda ka kawo ziyara ba ka leƙo munafurci sashen wasu!. To dan ka ji..karkarwa da tari yanzu ka fara." Cikin ɓacin rai Baba Ali ya ke kallon Yarinyar wadda a yadda ya ke kallon nata ita kanta ta san ji yake yi kamar ya yi mata dukan mutuwa amma kuma babu damar yin hakan dan Mahaifin Matarsa ya hanashi…. Cikin fushi yace “duk iskancinki da rashin ɗa’ar ki ya tsaya iyaka kan iyayenki kar ki kuskura ki sako mini nawa iyayen a ciki! Shegiyar Yarinya mai kama da aljanu…" Cikin tarar numfashinsa ta ce "eh lalle daɗin zama mai sa a ce da mijin iya Baba, ni dae na san shi ɗin uban matarka ne ba ubanka ba. Aikin banza aikin wofi!! Zancen banza wanda yake fitowa daga bakin mutanen banza ma kenan!!" Zaro ido sosai ya yi amma bata damu ba ta ci gaba da cewa” Ina ce da ƙafafunku ku ka shigo ba wani ne ya gaiyyotoku ba? Me ya kawoku inda nake da har za ku tsomawa mutane Baki da har Uban naka na kale zai fara tarin ƙarya da ƙarairayi??? Bari ka ji to ko a shari'a duk abunda na yi muku ba ni da laifi tunda kune ku ka shigo har cikin gidana, gaiyyar wahala ƴan *****uba kawai!!!!" Ba ta ga ƙarasowar sa ba sai Uban Marin da ya kifeta da shi ne ya sanar mata ƙarasowar tasa..dan duk yadda ya so yiwa Mahaifin Matar tasa biyayya wajen ƙin taɓata abun gagararsa ya yi. Dai-dai kuwa lokacin da ya mareta Kaka Nura ya turo ƙofa ya shigo Marin ya faru a kan idanunsa!. Anne ta na ganin Kaka Nura ya shigo; su na haɗa idanu da shi, ta kurma uban ihu ta kwanta a wajen ta fara birgima…. Cikin tsananin ɓacin rai Baba Ali wanda bai lura da shigowar Kaka Nura ba dan shi baya ya bashi, ya ce "Bari ki ji abunda baki sani ba nan ɗin ba gidanku bane ba dan Ubanki! Da ke da Uban naki baku aka yi kyauta babu ko sisin kwabonku ballanta ki yiwa mutane tunƙaho!!! Shegiyar Yarinya marar..." Muryar Kaka Nura ce ta katsesa ta inda ya ke cewa "Na farko dai ƴata ba shegiya baceba! Abu na biyu kuma marin nan da ka yi mata ba soja kake ba ko harsashi ne Kai billahillazi sai na rama mata…." Ya faɗi hakan ya na mai yin kan mutumin…. Tabbas Kaka Nura ya na da taurin rai da tsaurin ido kowa ya shaida hakan amma su kansu ba su taɓa tunanin zai iya tunkarar soja ba. Wani Falanke mai uban tsatsa ya ɗauka ya ƙarasa garesa amma wani cilli da Baba Ali ya yi da shi sai a bakin ƙofa aka tsinci Kaka Nura da shi da falankin nasa ya na nishi...da kyar ya iya miƙewa cikin zafin nama ya rarumi falankin ya makawa tsohon nan a hannunsa….. Da sauri tsohon ya shiga tsakanin Kaka Nura da Baba Ali wanda ya yunƙoro da niyyar halaka shi, haka ƴar tasa itama ta miƙe bayan ta sauƙe kan Anne daga kan cinyarta...amma duk sai tsohon ya dakatar da su har Yadikko sannan ya ce "duk wanda ya taɓa shi sai ya tsine masa, in har sun ɗaukesa uba to duk ɗinsu su bar abun haka..." Ba dan komai ba shi tshohon Anne kawai ya ke jiye mawa duba da yadda take a gefe duk ta sanƙarre su Zainab zagaye da ita amma idanunta a kansu, kyar!! Sannan a ganinsa tunda har su ke zaune gida ɗaya to akwai fahimta kenan shiyasa ba ya so ya zamto silar tada tarzoma babba da shi... Dan haka ya zaɓi ya sakawa abun fullstop tun kafin ya fi haka. Sosai ya tsawatar wanda hakan kuwa ba ƙaramin baƙanta ran kowa ya yi ba musamman Abbakar dan shi tun daga wannan ranar ya ji kaff a faɗin duniya babu wanda ya tsana sama da Nuratu....ya yi mamakin yadda ta ke magana da manya haka Yarinyar kamar ƴar ido...dan shi bai ma san ana haka ba, gashi dai dukda kasancewarsa mai training ɗin sojoji kuma ba Yaro ba amma haka nan ya danne zuciyarsa ya kame kansa bai tanka ba ko ya tsoma baki saboda babba na magana kuma ya tabbata hakan ne ya hana Zainab itama hatta da Mustapha yin magana......Baba Yusufa ya na dawowa bayan an wuce da Anne Asibiti tare da Mustapha da Zainab Abbakar ya ɗauki jakarsa ya juyo ko gidan bai yarda ya shiga ba....dan ya san bai isa korarta a cikin gidanba shi kuwa ba zai iya shaƙar iska ɗaya da Yarinyar ba wallahi... To dai suma ragowar jama'ar masu ziyarar duk babu wanda ya kai ga shiga cikin gidan, dan Abbakar bai daɗe da wucewa motarsu ta dawo daga shan mai dan haka suma su ka bi bayansa ba tare da ko ruwa sun tsaya sun sha ba duk suka kama hanyar komawa ba shiri gaba ɗayansu...Baba Ali ya na mai jin kamar ya haɗiye zuciya ya mutu tsabar takaici! Musamman in ya kalli hannun tsohon da su ka tsaya a hanya aka yi masa dressing da kuma in ya tuna halin da ya bar ƙanwarsa a ciki sai ya ji kamar ya mutu kawai ya huta. Ace a taɓa mutumin da ya ke yiwa kallon Mahaifi amma wai ya gagara yin komai ga wani banzan wawa! Dan har su ka ƙarasa gida mutumin ya na sake jaddada masa cewa 'ko bayan ransa idan ya taɓa Kaka Nura to Allah ya Isa bai yafe masa ba!' Saboda shi dai har ga Allah ba ya so ya zamo silar komai, kuma tausayin Uwani ya ke ji sosai, dan haka ba za ta sha wahala a ta sanadiyyarsa ba sam! Ba zai bari ba...dan ya san in har aka yi case to fa komai a kanta zai ƙare. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *16* Tun daga wannan lokacin yayun Uwani da family friends ɗinta su ka haɗe mata Kai!. Ko ta aika musu da saƙo babu reply kuma ba sa biye mata, gashi tun a ranar da abun ya faru ta ke kwance a gadon asibiti jininta ya hau amma babu wanda ya damu ya ga jikin nata ma ballantana batun zuwa dubiya. Har shi yayan nata (Baba Yusufa) wanda za a iya cewa zugar mace ya ɗauka a wannan lokacin...dan tun a lokacin bayan su Baba Ali sun tafi Yadikko ta hau sababi ta na cewa "ae gashi ita faccalarta da ya ke Mijinta ya san darajarta shi da ba shi ma da ƴaƴa ya yi gaggawar raba mata environment da Anne da Kaka Nura amma ita ko sau ɗaya Baba Yusufa bai taɓa duba tarbiyyar Addanta (Zainab) ya yi yunƙurin raba mata muhalli da Anne ba, har ce mata ya ke za ta raba zumunci a duk lokacin da ta hana Yarinyar kula Nuratu." A take tsanarsu (Nura da Nuratu) ta sake fitowa ƙarara a kan fuskarta, tun daga ranar kuwa ta yi nasarar janye Mijinta ta juyar masa da akala Allah kaɗai ya san me-da-me ta gaya masa dan tun daga nan ya juyawa Uwani baya, duk wata alfarma da ya ke yi musu ma janyewa ya yi hatta ɓangaren nasu ma tun daga wannan lokaci ne aka saka musu kuɗin haya su ke biyan naira dubu goma duk ƙarshen shekara!. Haka nan Uwani ta ci gaba da jinya a asibiti ita kaɗai! Dan ko da Nuratu ta je ita da Zainab tare da Mustapha, cikin lumana ta lallaɓa Nuratun ta ce mata “dan girman Allah kar ta sake zuwa, ta yi zamanta a gida, ta gode” Gashi ita kanta Zainab satar hanya ta yi su ka je ita da Nuratun da Mustapha...wanda daga ita har Mustaphan Yadikko ba ta san sun je ba, shiyasa aka dawo aka barta ita kaɗai dan ba damar Zainab ɗin ta ɗan zauna mata gashi ta ce Nuratu ta tafi. A hanya babu kalar nasihar da Zainab bata yi mata ba akan ta chanja Hali ta bi Mahaifiyarta. Zainab kusan za a ce ƙawarta ce kuma ta san ta na sonta tsakani da Allah dan ita kaɗai ta ke iya tolerating ɗinta, shiyasa ta ke cin sa’a wasu lokutan har ta ke iya yi mata nasiha ta barta ba tare da ta yi mata zazzagar kwanyo ba!. A wannan lokacin Zainab da Mustapha su na fara yi mata nasihar ita kuma ta ɗauki aniyar gyarawa ba wai dan ta yi tunanin bata kyautawa mahaifiyartata ba kamar yadda su ke ta nanata mata sai dan ta nunawa dangin mahaifiyartata itama fa ta Haifa kuma banzatar da itan ɗin da su ka yi ba zai rage ta da komai ba!... Sannan dama tun ba yau ba ta ke da burin rabata da munafukan dangin nata,kuma ta san ta hakan ne kawai za ta yi nasara, also ta lura da Yadda Yadikko ta tsani ta ga Mustapha ya na kulata wanda a yanzu ta lura ƙoƙari ya ke yi ya nutsar da ita ta san ta hakan ne kawai zai dinga shishshige mata ita kuwa wallahi sai ta yi amfani da wannan damar ta raba Yadikko da ɗan na ta wanda ta san ta na mutuwar so kamar ranta...... To dai a iyaka ƴan waennan lokutan Uwani ta samu sauƙin Anne...ramuwa, zagi da tsantsar rashin kunya duk ta daina yi mata su, ammafa mai Hali ba ya chanjawa, ta na yin hakan ne kawai dan ta cimmma wasu burikanta na daban ba wai dan ta daina forever ba. Hakanan Uwani ta sha jinya a asibiti ita kaɗai wanda za a iya cewa rabonta da Kaka Nura tun ranar da aka tafi kaita asibiti... domin kuwa a mugun ƙule ya ke da ita...dukda kuwa faɗan da akayi shine da nasara amma haushinta ya dinga ji saboda a ganinsa ai da danginta aka yi faɗan kuma ya san itace sila! Shiyasa tun a ranar ya ƙullaceta bayan kwana biyu kuma aka yanka musu kuɗin haya mai Unguwa da jama'a su ka shaida aka saka dole sai sun dinga biya shiyasa haushin Uwani ya sake hauhawa a cikin zuciyarsa! Sosai ya ƙullaceta a ransa ba kaɗan ba. Ya Mustapha ne kawai ya ke zuwa ya na dubota a ɓoye sai ko Zainab wadda itama ta ke binsa a machine ɗinsa su je a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba su kai mata abincin da su ka siya a hanya. Nuratu ma ta so ta dinga zuwa amma tunda su ka je sau biyu da ita a na ukun Uwani ta dinga kuka ta na roƙonta ta yi nesa da ita shikenan Zainab (Adda) da Ya Mustapha su ka ce Annen ta haƙura ta bari Idan Uwani ta dawo gida sai ta nemi gafararta!. Ba ƙaramin daɗi Ya Mustapha da Zainab su ka ji ba da su ka ga alamun shiriya a tare da Anne, Ya Mustapha har sadaka ya yi saboda babban burinsa kenan a wannan lokacin (Anne ta shiryu) Ita kuwa basu san kawai son ta ƙunsawa dangin Uwani sannan ta rabata da su da kuma son tarwatsa farin cikin Yadikko ne su ka taru su ka sanya ta ke yin hakan ba! Dan baya ga haka ko dede da sau ɗaaya Anne bata taɓa jin nadamar abunda ta yi ta shige ta ba! Kuma wani ikon Allah sam Uwani bata ba ta tausayi ba... Kawai dai ta tsara za ta shiga jikinta ta rabata da su sannan ta nuna musu abunda su ka yi fa ko a jikinsu! Kansu su ka yiwa, bayan ta tabbatar ta raba Yadikko da ɗanta Mustapha along the way na tuban muzurun nata. Abu kamar wasa har aka shafe wata ɗaya ciff! Uwani bata warke ba jinin nata da ya sauƙa sai ya sake hawa Abu ya ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa… Gashi kuɗin magani da na gado wanda ta biya lokacin da aka kaita har sun ƙare ana neman wasu.... Dan haka da Ya Mustapha ya je ganinta ta ce masa “idan ya koma gida ya cewa Nuratu ta duba ƙasan kayanta(Uwanin) ta na da naira dubu ɗari biyu a ajjiye ta bashi ya kai mata!” Ya na dawowa ya shiga ɓangaren su Nuratu, ya same ta a zaune ita kaɗai ta na tunani... Sai da ya zauna a kusa da ita tukunna ya sanar mata da saƙon Uwani! Sannan ya ƙara da cewa “Nuratu tunanin me kike yi ƴar ƙaramar ki da ke?” Ya faɗi hakan ya na mai kallonta sosai. Shiruu ta yi dan ba ta so ko kaɗan ta dinga tallata laifin Kaka Nura amma kuma ta san dole a yanzu Mustapha ya ji komai…. …..Tun sati biyu da su ka wuce Nuratu ta fahimci Kaka Nura ya yi budurwa duba da yadda kullum ya ke sheƙa wanka ya fita ya dawo gab da Magriba. Da farko, bai dai gaya mata ba itama kuma bata tambayesa ba saboda ta na kokwanto akan ‘shin aurar matar da ya ke zuwa wajen nata zai yi kenan ko ƙa-ƙa?! Saboda ita dai ta san ba shi da kuɗin da zai kama haya dan kullum cikin mita da tsinewa duk wani wanda ya hanasa bashi ya ke yi a cikin ƴan kwanakin, nan inda su ke zaune kuma ta san Uwani ce ta biya kuɗin da aka saka musu na haya dukda ba ta nan ita.... A cikin sati ɗayan da ya gabata kuma ta tabbatar dan throughout satin da ita ake zuwa ma zance wanda lokutan zancen nasa ya sauya zuwa 8-10 na dare sannan a gabanta ya ɗaga ƙasan kayan Uwani ya ɗauki kuɗin da yanzu ta ke so a bayar Mustapha ya kai mata... Dubu biyar ya bayar a gidan mai ɗan wake wadda ta ke kawo musu kullum idan ta kwashe na siyarwa tun da Uwani ta kwanta (dan Yadikko hatta abincin sadakar da Baba Yusufa ya ke sawa a yi duk juma'a ta daina zuba musu) dubu uku ya bayar a wajen mai koko da ƙosai na abun kari! Sannan iyaka zirga-zirgar da su ke yi na zuwa zance ita kanta ta san sun kashe sama da dubu biyar, da daddare kuma dama ya shigo mata da su biscuits su chocolate ya ce sai su dinga ci a matsayin abincin dare duk ranar da basu dawo da uban abincin da su ke dawowa da shi a haɗaɗɗun kuloli ba, saboda kusan kullum in sun je zance sai an haɗosu da abincin dare dan ƙiri-ƙiri Kaka Nura ya ke rantsuwa a gaban ƴarsa cewar ba shi da aure itama kuna ƴar da ya ke munafuka ce ta ce musu eh...kasancewar ba ƴan unguwar ba ne ba ya sanya ba su fahimci gaskiya ba. Haka za su zo da kulolin su ci, da safe ta wanke in za su koma zance su mayar da empty a basu mai nauyi su karɓa su taho ba kunya ba tsoro Allah alhalin ko biscuit bai taɓa kaiwa ba shi, ya ce ae ta san hidimar aure ce a gabansa..... To dai a halin da ake ciki har an kammala haɗa lefe an kai wanda ta ke da tabbacin da ragowar kuɗin Uwani da ya ɗauka duk ya yi hidimar komai..... “Nuratu! Kin yi shiru, akwai matsala ne? Ko zaman shirun ne ya ke gundurar ki? Adda ba ta shigo miki yau ba?” Tambayoyin da Ya Mustapha ya zaiyyano mata su ka katse mata tunani… A hankali ya na yi mata wani irin kallon ƙurilla ya ce “talk to me mana! Me kike so? Ko zaki koma Gidanmu da zama kafin Mamanki ta dawo? Naga yanzu Baba ya na yawn fita kuma ba ki koma makaranta ba. Ki na jin tsoro ko?” Saura kaɗan murmushi ya suɓuce mata saboda daɗin da ta ji.... A hankali ta jinjina masa Kai alamun ‘eh’. Wanda ba hakan bane ba dan sam! Anne ba ta da tsoro bama ta san menene tsoron ba amma tabbas kam za ta nuna masa tsoron ta ke ji saboda ya ɗauke ta ya kai ta gidansu(ɓangarensu) dama hanya ta ke nema ta tsani Yadikko kamar mutuwarta ba ta da burin da ya wuce ta ganta cikin masifa! Shiyasa ta na ji Mustapha ya ambaci kalmar 'tsoro' ta yi caraff ta zaɓi fakewa da hakan domin ta samu damar zuwa gidan nasu ta tarwatsa duk wani farin cikin Mahaifiyarsa, dama lokaci da dama ta ke jira kawai amma ta daɗe da yi wa kanta alƙawarin sai Yadikko ta san ta nuna mata tsana ƙiri-ƙiri!”. Baya ga hakan ita kam ba wani tsoro da ta ke ji, tunanin ma da ya tarar ta na yi na damuwarta ɗaya ne (haushin auren da Kaka Nura zai yi) dan ko Uwani ba ta wani tausaya mata ba dan an taɓa kuɗinta ko an mata kishiya ko na jinyar da ta ke yi, wannan duk ba damuwarta bace ba.... Jinjina kai Mustapha ya yi kafin ya ce “Okay! To ɗauko kuɗin sai ki ɗebo har da kayanki mu je in kaiki ɓangaren mu daga nan sai in kaiwa Mama kuɗin da wur wuri ta na jirana za ta biya kuɗin gado.” A take wata idear ta sake faɗowa Nuratu cikin son sake dasa mishi tausayinta a cikin zuciyarsa ta fashe da wani kuka tashi ɗaya gwanin ban tausayi ta ce “Babana aure zai yi kuma ina ga da kuɗi ya yi am…” Bata kai ga dasa aya ba su ka fara jiyo guɗar Mata kamar za su tsaga gidan!. A tare su ka miƙe tsaye ita da Mustapha sakamokon turo ƙofar da aka yi aka shigo Mata su na ta faman rangaɗa guɗa wanda hakan ya ke nuni da tabbas Amarya aka kawo cikin gidan!. [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *17* Mata ne kusan su ashirin manya da ƙanana sai wata a tsakiyarsu nannaɗe da mayafi ta sunkuyar da kanta ƙasa sosai fuskarta a rufe tsoffi guda biyu sun ruƙota.. Da farko kan Mustapha ɗaurewa ya yi yayinda a ka tsaya kallon-kallo kowa ya gagara cewa komai, haddai ya magantu ya ce "lafiya dai?" Ƙasa-ƙasa wata a cikin matan ta taɓo tsohuwar sannan ta ce mata "ko dai ba nan ba ne ba?" Murmushi matar ta yi kafin ta ce "a haba dai, nan ne mana...ga Nuratu chan." Sai kuma ta maida akalar maganartata zuwa ga Nuratu sannan ta ce "ƴar albarka ina Matan da aka ce su na jira? Ya na ga daga ke sai yayanki?" Shiruuu duk su ka yi ganin hakan ya sanya ta yi murmushi sannan ta ce "to ae shikenan. Bara mu miƙata cikin ɗakinta." Ta yi maganar ta na nufar inda ta hanga da wata makekiyar katifa dan ɗayan wajen da su ke kira da parlour in mutun uku su ka shiga na huɗu sai dai ya tsaya a kaikaice gashi tulin kayan gumamar Uwani ke a ciki babu masaka tsinke, kasancewar labulayen duk a ɗage su ke ya sanya su ka samu damar ƙarewa ɗakunan kallo wasu a ciki har su na munafurcin rashin kyautuwar inda za su ajjiye ƴar uwar tasu, a ransu. Yayinda jikin Amaryar ya yi sanyi sosai itama dan dukda fuskarta a rufe ne hakan bai hanata k’arewa gidan da d’akin kallo ba…ita babbar damuwarta shine ba ta san ta inda uban kayan gadon da su ka siya za su shiga ta cikin k’ofar d’akin nan ba…tabbas garama da capinter ya yi disappointing nasu dan sai dai ta siyar da kayan ko an gama wallahi ba za ta yarda a yi asararsu a d’akin nan ba. A fusace Mustapha ya shiga gabansu ya tsaya sannan ya ce "wanne ɗaki? Wa za ku saka a ɗakin wa? Lafiya ku ke kuwa?" Murmushi matar ta yi sannan ta ce "yanzu kai Yaro in banda kai da abunka ae duk wanda ya gammu ya kalleta" ta yi maganar ta na nuna Amaryar sannan ta ɗaura da cewa "tabbas na san ya san Amarya mu ka kawo...." "Amarya ku ka kawo za ku saka a ɗakin wata? Ko kuma a wanchan wajen za ku ɗaurata akan kayan ta zauna?" Ya jero musu tambayoyin takaici kamar ya kar shi. Kallon-kallo aka hau yi kafin wata a cikinsu ta ce " Yaro mu ce mana aka yi bai da mata, da hankalinmu ta ina za mu yarda a saka wata a ɗakin wata?" Yadikko kawai ya sanar mana mata a gidan nan wato matar mai gidan, kuma kamar yadda ya kwatanta mun ga ɓangarenta ga shi chan ita da mijinta da ƴaƴanta. Wani kalar taɓe Baki Mustapha ya yi kalar na takaicin nan sannan ya ɗaura da cewa "maganinku kenan! Daga an je muku da maganar aure kun yi caraff kun amshe ba tare da kun yi kwakkwaran bincike ba, sannan daɗin daɗawa ko zuwa ba a yi an ɗauko ku ba kun taho da ƙafafunku...yanzu ae ga irinta nan. Wannan ɗakin, ɗakin Mahaifiyar wannan Yarinyar ce kuma yanzu haka ma ta na kwance ne a gadon asibiti ta na jinya, sai ku gaya mini in kun yi wa kanku adalci muddin ku ka yarda ku ka saka wata a cikin ɗakinnta.." Ɗayar ce ta hau salati idanunta a kan Nuratu ta ce "ƴar nan ki ka ce mana Mahaifiyarki ta rasu?" Girgiza kai ta yi kawai ta kawar da kanta dan ba ta so magana ta yi yawa ta yi kwaɓa a gaban Ya Mustapha..... To dai Allah ya so Matan an samu masu hankali da fahimta, dan a take su ka yanke shawarar juyawa da Amaryar bayan itama Amaryar ta tabbatar musu ba za ta shiga ɗakin wata ba.... Haka nan su ka juya da ita zuciyoyinsu fal mamakin sha'anin Nura da ƴarsa wadda ta kashe Uwarta da ranta. Shi kuma ya fake da ce musu a sirrince ya ke so a yi auren ashe abubuwa a ƙaasa dunƙule ya ke ɓoyewa. Su na fita ta fashe da kuka ta ce "ba na so in yarfa Baba ne a gabansu shiyasa na ce musu haka...." Cikin damuwa Mustapha ya ce "ko ma dai menene bai kamata ki ce Mamanki ta rasu ba, hakan ba kyau..." Kamar ba Nuratu ba haka nan ta sunkuyar da kanta ƙasa kawai ta yi kalar tausayi sosai. Ya jima ya na kallonta a ransa ya na lissafin yadda za ta kaya shi da Kaka Nura a yau idan ya dawo gidan bai tadda Amarya ba, sai kuma kawai ya jaa numfashi ya sauƙe ya ce mata "je ki ɗauko kayanki in kaiki wajen Adda ina so zan wuce wajen Mama ta na jira na..." Ya yi maganar tausayin matar ya na sake shigarsa bai ma san ta ina zai fara yi mata bayani ba wallahi. A tsakar gida su ka tarar da Yadikko, Zainab da Mai aikinsu su na gyaran kifi..... Sun ji guɗa kuma sun ga shigowar mata, sarai Yadikko ta fahimci Kaka Nura ne ya yi abun shiyasa ta Umarci Zainab da su matsa daga inda za a iya ganinsu, mai aiki kuma aikata ta tsaya a bakin hanya su na dosowa ta sanar musu Yadikkon ba ta nan ta nuna musu inda za su saka Amarya direct. Dan duk wata sabga ta Kaka Nura ƙoƙari kawai Yadikko ta ke yi ta ga ta yakice shi daga kanta. Ɗagowa su ka yi kusan a tare su ka kallesu, a take Yadikko ta haɗe rai tamau! Kamar ba ta taɓa dariya ba sannan ta ɗauke dubanta daga kallon Nuratu ta maida a Mustapha ta na jira ta ji dalilansa na shigo mata da Nuratu har inda ta ke bayan ya san ba ta so. Miƙewa Zainab ta yi ta wuce ciki dan a ƙa'idar Yadikko ko magana ta hana ta yi da Nuratun sai dai ta yi a ɓoye... Ƙasa-ƙasa yadda Nuratu ta san Yadikko za ta ji ta ce "shegiya Zainab, ji wani gudu kamar mahaukaciya." Sarai Yadikkon ta fahimci domin ta kunnata ne Yarinyar ta yi hakan, hatta Baba Yusufa ba ya kiran Zainab da sunanta saboda Yadikkon ba ta so kasancewar Zainab ɗin sunan Addanta ne wadda ta riƙeta kamar Uwa ta aurar da ita, dan ita mahaifiyarta ta na haifarta ta rasu... Shiyasa sunan ya ke da matuƙar daraja a gidan sannan ba ta so a taɓa Zainab ko da wasa....... Ta na cikin wannan nazarin ta ji muryar Nuratu da ɗan sautin da kowa zai ji ta ce "ina wuni..." Shiruuu kawai Yadikko ta yi ta gagara magana mamaki gaba ɗaya ya hargitsa mata lissafi wai yau ita wannan ƴar ƙanƙanuwar ƴar ta ke gwadawa kissa da karuwanci....'oh, duniya ina za ki da mu??' ta furta hakan a fili ba tare da ita kanta ta san ta furta ba sannan ta ɗago ta kalli Mustapha ta ce masa "fitar mini da ƴar nan.." Kwaɓe fuska ya yi kamar zai yi kuka sannan ya ce " ko gaisuwarta ba ki amsa ba ballanta ki ji abunda ya kawota" A harzuƙe sosai Yadiikko ta miƙe Baki da kumfa ta na cewa"wai har yaushe ka soma ƙetare Umarni na ne? In ce dai na hana ka hatta shiga ɓangaren nasu? Ko kaima ta koya maka raina iyayen ne? Na ce ba na sonta ba na son in ganta kusa da ni da duk wani jinina amma shine za ka shigo mini da ita salon ta hargitsa mini nawa gidan nima ta kwantar da ni a gadon asibiti ko? Ka san kuwa me ta yi mini daga shigowarta?" Bata jira jin ta Bakinsa ba ta juya ta kalli Nuratu sannan ta ce" to ba ki isa ba, tunda na fahimci wayon manya gareki gara in gaya miki dan na san za ki fahimta! Wallahi ba ki isa ba sarai na san mai ya kawoki nan kuma ba za ki taka way forward zuwa cikin gidana ba ballantana har ki samu ki cimma manufarki, ba bu ke babu gidana babu duk wani jinina na saka almakashi na datse....." Cikin tarar numfashinta Mustapha ya ce " haba mana dan Allah.... Yarinyar nan fa shiryuwa ta yi, in muka nuna mata kyama ta koma ruwa mu na da kamosho fa, sannan ba za ki taɓa iya raba jininki da ita ba saboda mu jinin naki ƴan uwa muke a gareta dole duk abu ɗaya ne ya yo mu.... Kamata ya yi ace kin taimaka wajen gyaruwar Nuratu tunda dai duk tsiya ta mu ce ita ba a chanjawa tuwo suna kuma hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar ba " Cikin ɓacin rai sosai kamar za ta mareshi Yadikko ta ce "ba ni da haɗi da ƴar nan, kuma shima uban naka tsaf hannu ya kan ruɓe a yanke a ƴar in aka ga ya na shirin tarwatsa garkuwar jiki.." Sannan ta runtse idunta ƙam! Ta nuna Nuratu kamar mai shirin tada aljanu ta ce "Mustapha ka fitar mini da ƴar nan daga cikin gidana na ce ko?" Da sauri mai aikin ta shiga tsakani ta ce "Mustapha yaushe ka zama mai taurin kai ne? Tunda ba ta so ka fitar da ita mana......" Cikin ƙoƙarin son ganin sun fahimcesa ya ce "Gwaggo Yarinyar nan shiryuwa ta ke yi, kwaɗayin ladan da za mu samu in mu ka taru mu ka bada gudummawa wajen shiryuwar Yarinya kamar Nuratu na ke yi mana gaba ɗayanmu. Kuma ni a ganina ko baya ga haka ma in mu ka koreta kamar mun raba zumunci ne, kuma na san duk kun san hakan babu kyau. Sannan ta ce mini tsoro ta ke ji....." Buɗe idanuwanta Yadikko ta yi ta sake nuna Nuratu sannan ta ce "wannan aljannar shegiyar Yarinyar ce, ta ce maka ta na jin tsoro kai kuma ka yarda? Shegiya ƴar iska Uban me ki ka yiwa ɗa na ne wai!?" Ta ƙarashe maganar ta na kallon idanun Nuratu wadda itama ta ke kallonta ƙurr!!Farin ciki fall zuciyarta. A fusace ta ɗaura da cewa " kalli fa kallon da take min ta na min dariya....ba fa za a taɓa samun chanji daga gareta ba dan haka ka bar kwaɗayin samun ladan abunda babu shi kwata kwata a tsarin rayuwarta dan wallahi wannan ta riga ta tafi ita da ubanta har abada ba za su taɓa shiryuwa ba wutar jahannama ce kawai za ta shirya su, shegiya tsinanniya, kissa ce ta ke maka babu wani shiryuwa da ta yi..." Cikinn ɗaga murya Mustapha wanda ya gama ƙarewa Nuratu kallo dan ya na so ya ga dariyar da Yadikko ta ce ta na mata amma bai gani ba ya ce "ya isa haka dan Allah, ki na ta tsine mata ba gaira ba dalili sannan fisabilillahi Ina wannan ƴar ƙanƙanuwar Yarinyar ina wata kissa?? Ba na jin ma ta san me ake nufi da hakan..." Ya lura in aka biyewa Yadikko sai ta raba zumunci sannan ta kai Babansu wuta, dan gashi ƙiri-ƙiri ko sunan Uwani yanzu Baba Yusufa ba ya ƙaunar ya ji an kira, wadda a baya ta kasance wadda ya ke tsananin so da tattali, kuma gashi ana so a haɗu a taimaka a gyara Nuratu (da ita ce sila) wadda Alhamdulillah a yanzu ta ɗauko hanya amma ta na so ta sake turata ga halaka. Ya san a yadda Nuratu ta ke in aka kyamace ta tsaff za ta koma ruwa.... Dan haka cikin son fahimtar da ita da ɓacin rai sosai kwance a kan fuskarsa ya kalleta, dan tunda ya daka mata tsawa ta ƙame ba ta sake iya cewa komai ba hakan ya bashi damar ɗaurawa daga inda ya ke so "Ballantana har ta gwada mana, shiryuwa ce ta yi amma gashi ki na so ki sa mu kyamace ta a maida hannun agogo baya. Kin san cewa in da ace Nuratu ba ta shiryu ta nutsu ba da ba ki isa ki dinga zaginta haka ta kyale ki ba..." Sai kuma ya yi shiruuu dan shima sai da ya furta sai kuma ya ji maganar ta yi masa nauyi sosai. Sai da Yadikko ta sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta kalli mai Aikinta wadda itama jikinta ya yi sanyi matuƙa ta ce "kin gani ko? Kinga somu-somun abunda barin wannan annobar a cikin gidana ka iya janyowa ko? Wai yau ni Mustapha ɗan da ko musu ba ya iya yi mini ya ke kallon cikin idanuna ya na daka mini tsawa har ya ke ce mini ban isa b...." Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ta gagara sake cewa komai dan haka ta toshe Bakinta sannan ta juya da sauri ta yi hanyar da za ta kaita parlourn gidan..... Shiruuu Mustapha ya yi dan a take a lokacin jikinsa ya sake yin sanyi sosai, shiyasa ko da mai aikin nasu ta bashi shawarar ya maida Nuratu ya mayar da ita ba wai dan ya yarda an fishi gaskiya ba sai dan ya ga ran Yadikkon ya ɓaci sosai. Da ya je bai koma da wuri ba dan wajen Uwani ma ya tafi, sai da ya tabbatar Yadikko ta ɗan sauƙo tukunna ya je ya bata Haƙuri..... Bayan sallar isha Mai Unguwa ya biyo limami su ka shigo cikin gidan su ka samu Baba Yusufa da Yadikko su ka yi musu nasiha akan yadda su ka banzatar da Uwani wadsa ta ke jinya, dan sun zuba ido sun ga ba su je ba Mustapha ne kawai ta ce ya ke zuwa dan haka su ka basu shawara kasancewar a ganinsu an zama ɗaya. Su na zaune a yadda su ke ko gama tashi daga wajen ba su yi ba su ka fara jiyo ashar ɗin Kaka Nura kafin ya baiyyana a gabansu hannunsa riƙe da bulalar darbejiya da ya tsinko daga jikin bishiya ya na cewa "yau sai na illata Yaron nan wallahi." Bayan idanunsa sun sauƙa a kan Mustapha. A ƙalla Mustapha ya kai shekaru goma sha takwas a wannan lokacin amma haka Kaka Nura ya shiga zuba masa darbejiya duk wae a kan ya yi masa raashin kunya ta inda ya fatattaki Amaryarsa da ƴan kawota..... Mustapha bai ko motsa ba sai wanda su ka zo shi da liman da mai ungwa ne da takaicin abin ya ishesa ya zo ya hankaɗe Kaka Nura ya tafi ya faɗa akan Nuratu (wadda au ka shigo tare) ita kuma ta faɗi akan glass cup ɗin da aka kawowa baƙi ruwa ta fashe hanunta sosai ta ji ciwo. To dai kusan za a ce an kwasheta babu daɗi dan sai da Kaka Nura ya fasa duk wani abu mai kama da kwalba ko glass a parlourn TV, show glass da kayan turaren wutar ciki, da centre table da duk wani abu dai da za a iya fasawa saboda an taɓa hannun ƴarsa ta yanke by mistake, gashi da shegen ƙarfi duk yawansu su ka kasa riƙesa in aka takura shi kuma ya fara yunƙurin yankar mutum da glass ɗin... Ko da su mai Unguwa su ka yi magana zagesu ya yi tas dan dama haushinsu ya ke ji tunda aka yanke musu kuɗin haya ya ce duk munafukai ne saboda Baba Yusufa ya na ɗan yi musu ihsani shiyasa duk in aka yi faɗa su ke bin bayansa shi kuma ake bashi rashin gaskiya. Rikici sosai aka yi dan har sai da wasu daga cikin makwafta su ka shigo ana ta so a raba faɗan amma abu ya-ƙi-ci-ya-ƙi- cinyewa dan Baba Yusufa shima kafewa ya yi akan sai Kaka Nura ya bar masa gida abun nasa ya ishesa haka yayinda Kaka Nura ya ce bai isa ba ae Uwani ta riga ta biya kuɗi dan haka bai isa ya tashesu ba. Da mugun kyar mutanen wajen su ka shawo kan Baba Yusufa ganin ana shirin tado wani ballin saboda su so suke yi su gyara zumucin Uwani da Yusufa da ya ke shirin tarwatsewa dan haka su ka lallaɓashi akan ya yi haƙuri ya jira zuwa ƙarshen shekarar sai su tashi ɗin, yanzu ya bari komai ya daidaitu kuma duk wata ɓarna ma da aka yi musu za su haɗa ƙarfi da ƙarfe a gyara, a bar Kaka Nura da halinsa kawai. Da to Baba Yusufa ya bisu saboda ya na ganin darajar mutanen matuƙa, batun Amarya ne dai ya ce gaskiya ba zai yiu Uwani ta biya kuɗin ɗaki kuma a saka wata Mace a ɗakinba. Still hakan bai sanya zuciyar Kaka Nura ta yi sanyi ba ya ƙara ɗaukar glass mai kaifi ya nufi Mustapha wai ya yi masa laifi kuma bai bashi haƙuri ba. Garin kiciniya Yadikko ta shiga ya yanketa a hannu hakan ya sanya jikinsa ya yi sanyi dan haka ya jaa hannun Nuratu su ka fice ba tare da ya ci gaba da haukar tasa ba. Bayan kamar awa huɗu(har ya kai Nuratu an yi mata dressing sun je sun lallaɓo Amarya, sun dawo) Kaka Nura ya fito tsakar gida ya ware murya ya dinga maganganu ya na cewa "yekuwa jama'ar gida, ga Amarya nan ta zo in akwai wanda ya san ya isa ya fito dan ubansa." Kasancewar mutanen sun samu sun shawo kan Baba Yusufa a daren har ya je wajen Uwani sun shirya kuma ta tabbatar masa in har aure Kaka Nura ya yi to ya bar shi kawai ba komai gara auren akan ya bi matan banza ga ƴarta a gabansa, in sun yi haƙuri ma in dai auren Kaka Nura ne da wuya ya ɗoure, dan haka ita shiryawar da su ka yi ma ya fiye mata komai ya kawar mata da duk wani baƙin ciki, dan haka batun lafiyarta ce a gabanta yanzu ba wani Kaka Nura ba. In Allah ya sa ta warke sai ta kama wani hayan kafin kuɗin hayan da ta biya ya ƙare ta san dole Amarya za ta fita a nema mata wani dan ba biya zai iya yi ba, in ya so ita sai ta dawo ta ci gaba da zama... Sarai ta san da kuɗinta ya yi auren amma hakan ma ba ta ce komai ba akai, a ganinta tunda ta samu ta biya kuɗin gadon dan haka ba ta tada tarzoma ba. Shiyasa Baba Yusufa shima ya yi shiru kawai ya bar zancen ya na sake tabbatarwa kansa tabbas ba haka banza Kaka Nura ya bar Uwani ba. Sai kusan ƙarfe ɗayan dare tukunna Kaka Nura ya haƙura ya koma ɗaki dan ko magen gidan ba ta kulashi ba haka nan ya ƙaraci neman bala'insa ya haƙura muryarsa har sai da ta disashe. Kamar kullum yadda ya saba wannan karon ma a ɗaki ɗaya ya kwana da Nuratu da Amarya bayan sun tabbatar ta yi barci Wanda shi kansa ya san ife-ifen da ya dinga yi ya ci ya tada maƙwafcinsa ma ba Yarinyar da ya ke tare a ɗaki ɗaya da ita ba amma saboda runtse idanu daga ganin gaskiya sai ya kawar da wannan tunaninn kawai. Dan shi dai ba zai kai Amarya ɗakin gumama ko ya jira Nuratu ta fita daga gidan kamar yadda su ke yi da Uwani ba, a ganinsa kwana ɗaki ɗaya da ita tunda ta yi barci ba wani laifi bane ba. Ita kuwa Amarya dama ya shanyesu tas ita da iyayenta shiyasa ba ta taɓa iya yi masa musu, wanda hakan ne ya sake faruwa a yau ɗinma ya na zuwa da ya shirga musu ƙarya da ƙarairayi game da Uwani iyayen su ka ce ta biyosu, itanma jiki na rawa ta biyoshi. BAYAN SHEKARU SHIDA. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *18* Satin Amaryar Kaka Nura biyar, ya saketa bayan ya yi sati biyu a hannun ƴan sanda, dan yayanta ɗaureshi ya yi saboda dukan da ya yi mata a ta dalilin wae sun yi faɗa da Nuratu ta daki Nuratun. An sha case kuma ya sha wahala gashi duk duniya aka rasa mai tsaya masa ballanta a taimakamasa a fiddashi sai da kyar tukunna su ka sake shi dan kansu. A wajen Uwani Nuratu ta zauna a Asibiti bayan an tafi da shi, wanda a ɗan wannan zaman nasu sai da ta kusan kashe Uwani da takaicinta. In a gaban mutanene rumi-rumi kamar za ta goyata amma in su biyu ne ko kallonta ba ta yi gashi halinta na rashin kunya ya soma dawowa a Uwanin. Takaicin kissar da ƴartata ta ke yi ya sanya Uwani ta ƙi warkewa gashi in ta ga maza (likitocin ko nurses) kamar ta ɗafe musu, har wasu kalar karye-karye ta ke yi na ban mamaki, shiyasa kawai Uwani ta nemi sallama su ka dawo gida ba tare da ta shirya ba, bayan ta tabbatar Amarya ta wuce Gidansu. An samu hutu daga Kaka Nura sakamakon rashin lafiyar da ya kwanta mai tsanani tunda ya dawo daga hannun ƴan sanda, yayinda wasu su ka ce Baki ne ya kamashi dan zuwa wannan lokacin Kaka Nura ya yi popular a Unguwar sosai saboda bala'i da halayensa ko ina zancensa ake yi, in dai ana so a bada misalin mugu, butulu, ɗan iska, marar mutunci d.d.s to da Kaka Nura ake gwadawa. Ya yi jinya sosai kamar ba zai tashi ba, yayinda Uwani ta zage dantse wajen kula da lafiyarsa da jikinta da kuma aljihunta, dan bayan sana'ar gwanjo har da wasu sana'o'in ta kakkama... Tausayinta ya sanya Baba Yusufa bai ƙara zancen su tashi ba dan in aka tashesu a haka bai san ya ƙanwartasa za ta yi ba bai kuma san da wanne za ta ji ba, shiyasa ya toshe kunnuwansa daga bala'in Yadikko wadda tunda ta fahimci Mustapha son Nuratu ya ke yi ta ɗaga hankalinta kamar wadda aka yowa wahayin tashin hankali. Hankalinta bai kwanta ba har bayan ta tabbatar ta nesantashi da Annen, ta inda ta turashi karatu chan da nisa (gidan Baba Ali) gaba ɗaya ta ɗaga hankalinta ta birkice har kauce hanya sai da ta yi wae dukdan ta rabasu kuma Nuratun(Anne) ta sani amma kawai sai ta rabu da ita dan itanma ta na buƙatar iska daga Mustaphan, saboda duk a takure ta ke jinta (ta ɗaurawa kanta kissa da shiryuwar dole shiyasa ba damar ta yi duk wani abu ba dai-dai ba a gabansa) gashi ya na da sakin hannu da kyauta kuma ta hanyarsa ta na ƙunsawa Yadikko ta yi ta haɗasu faɗa shiyasa ta gagara ce masa ba ta sonshi kuma ta ƙi daina yin duk wata kissa da ta ke yi a gabansa....shiyasa ta ji sauƙi da ya bar gidan. Yayinda ta ke yiwa Yadikko kallon mahaukaciya saboda ita a ganinta in da ace ta na sonshi(Mustaphan) to fa ƙaryanta ta gwada mata bin malamai har ta rabasu. Kuma ko a yanzu ba wae ta rabasun bane ba dan ya na nan manne da ita kullum maganarsa ɗaya ba sauyi 'da zarar ya gama karatu ya na dawowa za su yi aure' ita kuwa ta raina arziƙinsa sam kuɗinsa bai yi mata ba shiyasa ta daɗe da tsarawa kanta ba za ta taɓa aurensa ba. °°°°°°°°°°°°°°°°°°° Sai da Kaka Nura ya yi shekara Uku ya na rashin lafiya tukunna aka samu ya warke da izinin Allah, wanda tunda Allah ya sa ya warke ya fara ta kan Uwani dan wani hali ya tsiro da shi sabo ya ɗaura a kan tulin mugayen halayensa..abunda da bai saba yi mata shi ba wato 'duka'. °°°°°°°°°°° Shekaru sun ja... yayinda Adda ta kammala secondary daga nan ba ta samu ta ci gaba ba, Arabi kuma sauƙarta biyu Anne kuwa ko jenior ba ta samu ta iya kammalawa ba saboda tsabar baƙin daƙiƙancinta da bala'insu ita da ubanta dan ƙarshe haƙura su ka yi da karatun gaba ɗaya ta ce ta gaji, shi kuma ya ce shikenan dan haka ta ke zaune ba bokon Arabin ma babu saboda haka nan Anne ta ke kamar wata mai Aljanu ko wajen da ake karatun AlQur'ani ba ta iya zama kwata-kwata, kamar yadda Ubanta ya alƙawaranta dai ya na koya mata yadda ake sallah, duk ta san karatun sannan ta haddace wanda za ta iya dan kasancewar kwakwalwar ba ta ja ne ma ya sanya a yayin tsayuwa Nasi ta ke karantowa kullum bayan fatiha dan su ta iya ta haddace... karatun tahiya shima ta kasa riƙewa yadda ya kamata, wanda za a iya cewa Sallar tata 'da babu gara ba daɗi' dan sam ba ta yinta a nutse sannan sai in ranta ya na a ɓace ne tukunna ta ke tunowa da Ubangijinta ta bauta masa. Yawo kuwa a cikin Anne kamar ta ci ƙafar kare.... Gashi Uwani ba ta isa ta yi magana ko ta hana ta fita ba tuni Kaka Nura zai gwada mata abinda ya fi kwarewa a kai wato tijara, ita Uwani babban damuwarta ma inda Annen ta ke samo kuɗi saboda komai na Anne mai tsada ne, waya dai ta san Mustapha ne ya siyo mata amma kayan sakawa da cimar da ta ke shigowa da su cikin gidan ta san ba daga shi bane ba kuma ta san babu wani saurayi apart from Mustaphan da zai yarda ya kashe mata kuɗi a banza.... Tabbas Uwani ta na ƙoƙari, dan tsoronsu wanda ta rasa ta yaya ya dasu a zuciyarta ba ya hanata ta ƙi yi musu wa'zi da kuma addua daga Annen har Kaka Nuran wanda a kullum ya ke sake godewa Ubangiji da ya bashi ƴa mace dan tunda ta fara riƙe shi ta na tufatar da shi da ciyar da shi shikenan kakarsa ta yanke saƙa ya ke jin kanshi a sama dai-dai da uban kowa. Shiyasa sam bai wani damu da rashin auren naya ba tunda dai ba su da matsalar kuɗi gashi ana kashe mata kamar hauka kuma shi dama ko menene Anne ta zaɓa ta nuna zai goya mata baya ɗari-bisa-ɗari. Shiyasa Uwani kawai ta dage da Addua dan ita kaɗai ce mafita har da Adda itama ta na taya ta da adduar wadda sam ba ta gajiya da yi mata wa'azi itama dan ko Anne ta ɓoye wasu mugayen halayenta bin maza abu ne wanda ba zai ɓoyu a halaiyyarta ba kowa ya shaideta da wannan. A lokacin da Anne ta rufe shekaru sha takwas Adda kuma ashirin dai-dai, duk wata sa'arsu a Unguwar ta yi aure amma banda su.... Ita dai Anne za a iya cewa ba ta samu Mijin aure ba ne, kasancewar ta lalace kuma ta fanɗare tun kafin ta balaga ma, wanda hakan ya taka gudummawa kwarai wajen hanata samun mijin aure bayaga rashin farin jinin da ita kanta ta shaida ta na da shi, sai kuma mai kankat wato 'lokaci'....duk ƴan iska ne samarin nata babu mai nemanta da aure sai dai lalata, kuma haka nan ta ke ba ta da wani farin jini dama tun chan...dan a yadda ta ke da kyawu har ƴan Unguwar su ke yi mata laƙabi da 'wanke hannu ka taɓa' tabbas adadin farin jinin da take da shi ya yi rauni matuƙa a mace kamarta dan hatta samarin nata ƴan iskan ma kusan duk ita ce ta ce ta na sonsu, wasu kuma ta ƙarfin tsiya ta ke jawosu tunda Allah ya sa idanunta su ka buɗe da bin malamai.....shiyasa su na gama abunda ya kawo su su ke ɓacewa ko damar damƙarsu da maganar aure ba sa bata ballantana ta yi. Adda kuwa ta taso da farin jini matuƙa ta inda kowa in ya zo gareta da maganar aure ya ke zuwa, sai dai kuma in aka yi bincike aka tabbatar da ƙawar Anne ce kuma ƴar Uwa a gareta sai iyayen manemin nata su janye jiki da dabara, an yi haka har kusan sau uku wanda zuwa wannan lokacin Yadikko ta yi Yaji ya fi sau biyar ana maidota duk akan sai an kori su Anne daga gidan amma Baba Yusufa ya ƙi kulata saboda shi ya san Ubangiji ne mai lokaci, dan haka Yadikko ta dasa Allah ya isa kawai ta ci gaba da yiwa Addan tata Addu'a, ta na mai ji kamar ta bi dare ta cinnawa Nura da ƴarsa wuta har ma da Uwanin duk su mutu kowa ya huta. Da taimakon ƴan Unguwa aka samu aka wanke Adda bayan sun yi mata kyakkyawar shaida saboda da farko-farko in an zo ba a bincike a kanta kwakkwara daga anga gidansu ɗaya da Anne sai a yi musu kuɗin goro.... Dan haka wannan karan iyayen manemin nata(waenda su ka kasance ƴan uwa ga makwabtansu) su ka tsaurara bincike luckly su ka karɓeta hannu bibbiyu bayan sun ji kyawawan shaidu akanta daga wajen ƴan uwansu da su ka kasance neighbours da ita Addan da kuma ƴan Unguwa. Murna a wajen Yadikko ba a magana dan mutumin yanzu duk ya fi na baya, mai hankali, dattako da rufin asiri sai dai tunda Allah ya sa Anne ta ga Adda ta yi sabon saurayi gaba ɗaya duk sai ta gagara sukuni, dama chan duk ranar da Addan ta yi saurayi ba ta iya barci dukda kuwa itama ta na da nata samarin amma ta san ba aurenta za su yi ba kuma haka nan ta ke ji ba daɗi da baƙinciki in aka ce a na son Addan, shiyasa ta ke ɗaga hankalinta sannan ta dage da sallah ta na gayawa Allah kar ya bari Adda ta rigata yin aure, har sai ta ga abin ya lalace tukunna hankalinta ya ke kwanciya. To dai wannan karan ba ta ga alamun saurayin Addan ya na da shirin fecewa ba dan haka tashin hankalinta sai ya fi na kullum, daɗin daɗawa tunda Allah ya sa su ka gaisa ta yi eyes to eyes da Yaron shikenan ta ji duk duniya babu wanda ta ke so sai shi. Ta so ta kawar da tunanin a kanta ta so ta manta da komai duba da yadda su ke ita da Addan amma duk sai ta gagara, ba ta iya yin barci gashi duk ta rame ta fige ta gigice gaba ɗaya ko abinci ba ta iya ci sosai.... A ganinta ta yaya Adda za ta fita farin jini bayan ta fi ta komai-da-komai. Gashi ita a lokacin ko maskini mai niyyar aure ba ya kulata, A Unguwar kuwa hatta ƴan iskan ma duk sun yi sun gama da ita sun kama gabansu gashi kowa ya san halinta ana ta munafurcinta, dan haka duk yadda ta so sai kishi ya ƙi ya barta ta yi farin ciki ta bar Adda ta yi auren... Ta fi so sai ta yi tukunna itama Addan ta yi, gashi sam ba ta ga alamun aurenta nan kusa ba dan hatta Mustaphan da ta rainawa hankali (Mutum ɗaya a duniya da ya taɓa yi mata maganar aure) kuɗinsa bai yi mata ba, kuma Baba Yusufa shima ba ya so, shi(Mustaphan) kaɗai ya ke ta haukarsa amma iyayensa sun tsaneta dan haka yadda ta ga iyayen manemin Adda su na yi mata kamar za su cinyeta saboda so abun sai ya ƙarawa kishin nata ƙaimi. Dan haka ta tsara akan dole sai Adda ta jira kalar Mijin da ta ke so ya ƙaraso ta (Annen) yi aure tukunna in Yadikko ta nutsu wataƙila ta barta ta yi auren. Shiyasa ta tashi ta tsaya da duk ƙarfinta da son ganin ta hana Adda yin aure... Gashi a lokacin Yadikko ta ɗaga mata hankali da gori na yau daban na gobe daban musamman in ta lura Kaka Nura ba ya cikin gidan, wani zubin Yarinyar ta kulata wani zubin kuma kawai sai ta rabu da ita domin kuwa a wannan Lokacin babban burinta shine ta raba Adda da wannan aure ba wai Yadikko ce a gabanta ba! Matar da ta ci burin tarwatsawa rayuwa har gaban abada. Akwai wani a cikin samarinta Mahaifiyarsa kwara ce yayinda Mahaifinsa ya kasance ɗan bori, ba ta ɓoye masa ba ta ce masa ƴar uwarta ce za ta yi aure ita kuma bata so ta rigata yin auren, dan gashi har an fara yi mata gori, Abu ɗaya ta ɓoye ba ta gaya masa cewar ta na son shi Yaron bane ba , saboda dama ita wannan mutumin ba da shirin aurensa ta ke ba, shima kuma haka dan shi a lokacin ma matansa biyu kuma bashi da niyyar ƙara wani auren dan har ya gaya mata ma ba zai iya aurenta ba. Watsewa ta kawosa wajenta ita kuma kwaɗayi da son abun duniya ya sanya ta ke kulashi. Dan haka su ka yi agreement ta inda za ta debe masa kewa na tsahon mako biyu in sha Allahu shi kuma zai tsaya mata har sai ta tarwatsa auren Adda. A wannan lokacin ko maganar hidimar biki in Adda ta yi da saurayinta sai ta gayawa Anne dan komai da ita ake shiryawa kusan ita za a cewa ƙirjin biki… Gashi ita ce babbar ƙawarta sannan itace sister ɗinta. Ƙiri-ƙiri gashi dai Yadikko ba ta so amma Mahaifin Addan ya tashi ya tsaya ya ce wallahi ba ta Isa raba musu zumunci ba In batun ɓata tarbiyya ne shi ya san Nuratu ba ta Isa ta ɓata Adda ba kuma Addan ma gidan Mijinta za ta tafi dan haka ta barsu na ɗan lokaci ne kawai…komai ya kusan wucewa. Gaba ɗaya kamar an toshe masa kwakwalwa haka nan ya bi bayan a bar Adda da Nuratu saboda ya na ganin ae aure ne ma ƴartata za ta yi. Ba dan Yadikko ta so ba ta koma gefe ta zuba musu ido kawai tsanar Anne ta na daɗa ninƙaya a cikin zuciyarta.... Ta samu ta tura Mustapha inda ɗan Uwansa yake amma dukda haka hankalinta ba a kwance yake ba, gashi Mustaphan shima ba ta barshi ba dan sarai ta san su na waya sai dai kasancewar zuwa wannan lokacin ita kanta ta san Nuratun ba wani son Mustaphan ta ke yi da gaske ba ya sanya ta ɗan kwantar da hankalinta sai dai takaicin ganin da Mustapha da Adda har zuwa wannan lokacin ba su fahimci Anne ba son ɗan nata ta ke yi tsakani da Allah ba ya hana ta sakawa zuciyarta salama. Wanda abinda Yadikko ba ta sani ba shine ita kaɗai Allah ya bawa wannan baiwar, ta iya gane Nuratu, dan kamar hawainiya haka ta ke, shiyasa itama Adda ta sake mata sam ba ta gane ta na mata baƙin ciki ba wanda hakan ya bawa Anne dama ta samu ta shiga jikinta kwarai da gaske ta dinga asirceta ba dare ba rana.... Har ta kai ga yi mata illoli mabambanta..dan ta sha bata magani ta ce mata maganin mata ne ko na gyara ita kuma ta karɓa ta yi ta afawa wani abun kuma a ruwan wanka ta ke zuba mata wani ta saka mata a kaya wani a abinci a man shafawa d.d.s....... Cikin ƙanƙanin lokacin ta saka mata warin jaaɓa a wajen saurayin, ta tura mata aljanin da ke sauya mata kamanni in ta fita zance wajen duk wani Namiji sannan ta cireta gaba ɗayanta a cikin zuciyar saurayin da danginsa har ma da Abokansa sannan ta rufewa Yadikko baki ruff akan ta gagara yin magana kuma ta ɗaure mata hannu tamau saboda kar ta yi komai, gudun kar tausayin ƴar tata ya ci ƙarfin aikin da ta yi har ta kai ga a ji yunƙurin yin wani abun ya sanya ta shiga ta fita ta cire Addan a cikin zuciyar Yadikkon itama gaba ɗaya… Wanda aka yi asiri a jikin wata gawa aka yi rashin sa’a gawar ta yi kwanan Keso cikin dare gobara ta tashi komai ya k’one kurmus shiyasaaa har gobe tsanar Adda ta ke sake yin tasiri a cikin zuciyar Yadikko…. Rana tsaka uwar saurayin Adda ta zo ta ce "an fasa" Juyin duniya kuma ta ƙi faɗin abunda aka yi musu ta ce ba komai ƙarshe ma ta ce 'an bar musu kayan toshi da aka kawo, sun bar musu komai, kawai Allah ya haɗa kowa da rabonsa'. Ta na gama faɗiin haka ta juya ta fice ranta ya na a ɓace har a lokacin... Jiya ɗanta kwana ya yi ya na mata kuka akan baya son auren to kuwa a kan me za ta yi masa dole saboda farin cikin wasu? Ta na wannan lissafin ta wuce zuwa gida abunta Yayinda Nuratu ta ji wani masifaffen daɗi kamar an yi mata bushara da gidan aljannah... Ba abunda ya ke sake ƙona mata rai irin yadda ta lura Addan kamar ma wani sabon kinibibi ta ke yi mata tunda auren ya matso...magana kaɗan komai sai ta ce wani 'her soon to be husby' Ae yanzu sai ta ga ƙaryar Iskanci. Tabbas Adda ta girgiza matuƙa, dan sai da Yadikko ta kusan yi mata shegen duka saboda takaici tukunna ta tattara ta koma wajen Anne su ka taru su ka dinga kukan tare.... Dan ƙarshe ma sai da ya zamana Addan ita ta ke rarrashin Anne saboda uban takaicin fasa auren da aka yi da ta nuna ta na yi…. A washegarin ranar Anne ta tari Yaron har wajen aikinsa da zancenta bayan ta tsafe jikinta tsaf sai dai cikin hukuncin Ubangiji abun nata bai kamasa ba dan fata-fata ya yi mata sosai kuma ƙiri-ƙiri ya ce mata "ba zai auri karuwa ba" Bayan kwana biyu, bayan ta je ta sake haɗo uban kayayyakin asirinta za ta yi masa kawai ta ji labarin ya yi aure ya bar garin(sun tafi honeymoon) Duk Inda ta je sake tabbatar mata ake yi akan ba Mijinta bane ba amma za’a iya gwada sa’a shiyasa kawai ta haƙura ta bar mata (matarsa) shi. Ko wata ɗaya kwakkara ba a yi ba wani saurayin ya sake fitowa Adda. BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *19* Ko wata ɗaya kwakkara ba a yi ba wani saurayin ya sake fitowa Adda. Shi kuma ɗan gidan Malamai ne sosai shiyasa ko ya zo baya ganin duk waennan abubuwan. Tunda Allah ya sa Nuratu(Anne) ta ji ta gani wannan karon ma sai ta gagara kau da kai, a ranta har ta na mamakin shin wae ta yaya Adda ta ke samo kyawawan maza masu kwarjini da ɗaukar hankali...... Tashi ɗaya ta burkice. A lokacin sun rabu da ɗan ɗan bori saboda lokacin da su ka ɗauka ya cika amma fa garin raba auren Adda na baya ya harhaɗata da Malamai da bokaye mabanbanta... Dan haka ta tashi ta tsaya wannan karon ma. Wani zubin ma in ta je wajen Malaman bata da kuɗi cewa su ke yi sai dai su yi amfani da ita a bakacin ladan aikinsu a hakan kuwa ta ke amincewa kuma da yake Yarinyace ko batun kariya bata amfani da shi..kanta tsaye haka nan ta ke tafka ƙazantarta mafi muni dai-dai gwargwadon iyawarta. Kwata-kwata a lokacin shekarunta ba su rufe 19 a duniya ba. To dai ba kalar bugawar da ba ta yi ba abun ya ƙi tarwatsewa dan haka bayan ta fahimci a tsume mutumin ya ke da addu'o'i da kariya sai ta chanja salo... Da farko messages ta fara tura masa akan Addan ta na da tarin samari! Sai ta ce a kira wayar za a ji busy in an kira kuwa za a ji busy ɗin dan ta na gama faɗin hakan ta ke amshe wayar Addan ta hau waya Da ta ga saurayin bai biye wa makircinta ba sai ta ce masa ae ta na neman maza... Haka nan za ta karɓi wayarta ta yi ta tura masa messages ɗin batsa a zuwan Addan ce ta ke so ya biye mata su watse...duk wae dan ya yarda ƴar iska ce, Kasancewar saurayin ba Yaro baneba ya sanya tun a karon farko ya fahimci sharri ne ake so a yi mata, dan shi dai ya yi duk wani binciken da ya kamata ya yi a kanta kuma ya yarda ya amince da amsoshin da ya samu da zuciya ɗaya above all tsakaninsa da Allah ya ke sonta, dan haka ya san in sha Allahu za ta zame masa alkhairi, shiyasa ya toshe kunnuwansa daga duk wata zuga kawai ya basar ya yi focusing akan zallar ƙaunar da ya ke yi mata... Sannan ya duƙufa yin bincike dan ya na so ya gano munafukin ya hukuntasa yadda ya dace. Hakan kuwa (ganin bai ɗauki zugar ba) ba ƙaramin fusata Anne ya yi ba gashi a lokacin batun auren ta ke gani ya na tahowa gadan-gadan kullum dan haka ta koma wajen bokanta ganin sun kasa rabawa kawai sai ya jefa masa matsananciyar jinya bayan sun samu sun kauda hankalinsa daga kan ibada na ɗan ƙanƙanin lokaci da mugun kyar! Su ka yi sauri su ka tura masa aljanu. Aljanun su ka dinga shanye jininsa bayan sun fita sun shiga sun rabasa da ibadar da ya ke yinta tuƙuuru… Dan a lokacin Yaddikko ta sakota a gaba fiye da ko yaushe sannan uban Addan shima wannan karon ya ja baya da su hatta Addan wadda ta fara fahimtar kamar Anne na yi mata zagon ƙasa itama duk ta ja baya da su..ga shi soyayya da kulawa da gata tsantsa ta ga Addan ta na samu daga wajen saurayin shima dan haka gaba ɗaya sai ta gigice ta fita a haiyyacinta sannan ta fusata… Satin mutumin bakwai ya na jinya ta fitar hankali kafin ya ce ga garinku nan dan hatta bokan sai da ya ji tsoro ya kira Anne ya sanar mata in an ci gaba zai iya mutuwa amma ta ce ta ji ta gani… Domin a wannan gaɓar ba ta ji ba ta gani kishinta ya sake tashi matuƙa sannan baƙar zuciyarta ta murɗa. Tun daga nan kuma sai ta hau yin rigakafi dan kafin ma wani ya zo take hanawa ta koresu saboda kar ta sha wahalar rabawa kamar last one ɗin… Wani guda ɗaya ne mai ƙarfin kuruwa ya sake zuwama Addan shima ya kafe bayan ta tarwatsa aurenta a karo na shida Lokacin shekarun Adda Ashirin da biyu ita kuma ashirin cif-cif Har an fara gulmar itama Addan a Unguwa ana zarginta da wani abun daban duba da yadda ta ƙi auruwa sai ƴan Unguwar su ka ce aljani ne ya aureta, Anne kuwa dama ƴan Unguwar sun ce ita da aure sai dai ta ga anayi…kaff ƴan layin sa’anninsu duk sun yi aure har ma da ƙannensu amma banda su. Zuwa wannan lokacin Adda gudun Anne ta ke yi sosai domin kuwa ta riga ta fahimci ba ta sonta kwata-kwata...ko ta kanta (Annen) bata yi ita kawai kar Adda ta rigata aure ta tafi ta barta… To dai wannan Saurayin taɓin hankali Mahaifiyarsa ta samu saboda ta nace akan ba ta son aurenshi da Adda shima kuma ya na ce akan sai ya auri Adda, dan haka ganin baƙin cikin hakan ya na shirin illata masa Mahaifiya ya sanya ya janye ya haƙura ya karɓi zaɓinta (ƴar uwarsa ya aura) Duk dauriyar Adda wannan karon kam sai da ta kwanta jinya. A ɓangaren Uwani da Kaka Nura kuwa ita kanta Uwani ta san cewa Kaka Nura ya gaji da ita kuma akwai abunda ya ke damunsa wanda gaba ɗaya ya sanya shi ya ke neman zama kamar ba shi ba, ganin takaicinsu shi da ƴarsa ya na nema kasheta ya sanya ta ɗauki hutu ta tafi chan wani waje (wajen makwafciyarsu lokacin ta na gida) ta ɗan huta, kafin ta dawo shi kuwa ya yi aure kuma da ta dawo ya ce wae sai dai ta zauna a wajen Baba Yusufa ae bai bata izinin tafiya ba ta yi yaji, kuma shi ba zai iya zama babu mace ba in dai ba zina ake so ya yi ba. An sha yaƙi sosai dan ba kunya ba tsoron Allah Kaka Nura ya dage akan sai dai Uwani ta zauna a gidan Baba Yusufa ta bar musu ɓangaren tunda ita ɗin ƴar uwarsa ce Amarya kuma bare ce ba zai yiu ya kai musu ita ba! Kuma bashi da wajen sakata. A ranar ne kuwa shima Baba Yusufa ya yi masa ɗan ƙaramin hauka ya ɗaga masa hankali ya haɗashi da ƴan sanda Kwana uku aka ɗauka ana case kamar za su cinye juna! Kafin hukuma ta shiga tsakani, Amarya ta koma gidansu Uwani ta shiga ɗakinta. Ƙarshe dai kawai iyayenta su ka ce ya bata takardarta. Tun daga wannan rana Kaka Nura ya ɗauki karar tsana ya ɗaurawa Baba Yusufa da Uwani, ko kallonta ba ya yi, kuma ya ƙi ya saketa saboda ya san arziƙinta ya ke ci a fannin muhallin dan shi Kaka Nura kamar wanda aka nuna da leda ko fili taku biyar ba shi da shi har gobe haya ma ba iya biya ya ke yi ba. A wannan lokacin ka na ganinsa ka san bayaga tsanar Uwani da ɗanuwanta da ya ɗaurawa kansa tabbas akwai abunda ya ke damunsa… Amaryarsa ta tafi kuma zuwa yanzu Alhamdulillah akwai buɗi dan Nuratu(Anne) kuɗaɗe ta ke samu ta koina kuma ta na bashi wanda ko tari aka yi da zummar magana game da inda ta ke samun kuɗi sai an kwana ba a rintsa ba a cikin gidan. Duk kalar ɓarnar da Kaka Nura ya yi Uwani ko a fuska ba ta nuna masa ba bayan ta dawo an zauna amma shi bayaga hantara, kyama da duka a ɗaka in su biyu ne yanzu ta kama har hannu ya ke saka mata a waje a gaban Uban kowa. Gaba ɗaya ya tsaneta ta fita daga ransa dan ko a batun iyayen Nuratu ba ya ƙaunar a haɗo sunansa kusa da na Uwani duk dan ya na ganin kasancewarta ƙanwa ga Babà Yusufa shine zai fara zame masa katanga wajen mallakar Yadikko, dan shi a halin da ya tsinci kansa a wannan lokacin ji yake duk Matan duniya babu wadda ya ke so sama da Yadikko, bai san dalili ba haka kurum Ubangiji ya ɗaura masa matsanancin sonta, wanda hakan ne ya haifar masa da damuwar da ta sauya shi aka kasa gane kanshi. A lokacin ya auri mata bila adadin wasu ma ya manta da ya auresu amma Yadikko kawai ya ke ji ya na gani a ganinsa duk ragowar muna Mata ne sai ya mallaketa tukunna zai san ya tara da Mace, kuma duk Matan Unguwa zawarawa da ƴan mata da na kewaye ba su yi masa ba, ita kawai yake so da sha’awa. Yadda ya ke fito da kujera ya dasa ne ya na leƙenta in ta na aiki a tsakar gida ya fara tona masa asiri a wajen Uwani yayinda Baba Yusufa ya na fahimtar hakan ya yi tsalle ya dire ya ce in sama da ƙasa za su haɗe wallahi wannan karon sai sun bar masa gidansa. Da shi da ƴarsa sai sun fita a gidan nan tun kafin su janyo a yi musu girgizar ƙasa a iyaka cikin gidan nasu… Dama tun lokacin ya duƙufa wajen yiwa ƴarsa magani dan ya soma zargin da sa hannunsu ba wai a iyaka aurarrakin Addan da su ke ta taɓarɓarewa ba har da faɗan da ya kunno Kai tsakanin Matarsa da ƴar tasa wanda zuwa yanzu Yaddiko ko sunan Adda ba ta son ji ma ballantana ta ganta… Ana tsaka da wannan bala’in Mustapha da Abbakar (twins) su ka dawo daga karatu, dan Abbakar ɗin shima ya dawo ne zai ɗan zauna an tsara akan sai ya yi aure sai ya sake komawa wajen Uwar goyon tasa tare shi da Matarsa, in ya nemi transfer an basa dan duk Kano aka yi posting ɗinsu. Ta inda Mustapha ya kammala nashi karatun shima ya fito da matsayin second lietanant. A lokacin ne kuma Anne ta ji batun Mahaifinta ya na son Yadikko daga bakinsa, wadda abun ya bata mamaki da farko amma kuma da ta fahimci in ya riga ya auri Yadikkon kamar rayuwarta ta gama tagaiyyarawa ne ita da ƴaƴanta sai ta ɗauki ɗamarar haɗasu.. Kamannin Mustapha da Abbakar(wanda su ke kira da Habu) sak ɗaya basu da bambamci sai ko ta yanayin tsayi da ɗan hasken fata dan Mustapha ya fi Abbakar haske... Amma tunda Allah ya sa Anne ta ga Abbakar a take ta ji so da masifar ƙaunar shi sun shigeta, gashi daɗin daɗawa Abbakar ya fi Mustapha kuɗi nesa ba kusa ba dan sana'a ta karɓesa kwarai da gaske Allah ya saka masa albarka saɓanin Mustapha da zai riƙeta da albashi zallah. Gashi Mustapha ya dawo mata da zazzafar soyayyarshi saboda shi tunda ya tafi dede da rana ɗaya sonta bai taɓa raguwa a cikin zuciyar tasa ba sai dai ƙaruwa ma da ya ke yi. Suna waya ya na gaya mata ya na sonta amma bata taɓa tunanin da gasken gaske ya ke ba sai yanzu da ya dawo mata a hargitse sannan ya na dira ya fara yiwa iyayensa maganar aurensu waenda suma ashe duk ya daɗe ya na yi musu amma su ka banzatar da abun. Tashi ɗaya Adda, Baba Yusufa, Yadikko da ɗan uwansa su ka ce masa in dai Anne zai aura wallahi babu su babu shi… Shi kuma ya yi tsalle ya dire ya ce sai ita! Dan haka sai gidan nasu ya zama kamar filin wasan kwaikwayo kullum ana drama. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *20* Kaff arear zuwa wannan lokacin Anne ta daina shiga gidajensu dan ko ta shiga ba a kulata in ma bala’i ne ya kaita sai dai ta ƙaraci abunta ita kaɗai ta fito ba mai ce mata uffan. Ƙawayenta da su ka yi Makaranta kuwa kowa ya fahimci halaiyyarta dan babu wanda ba ta cuta ba In dai ta raɓi mutum to fa sai ta cucesa dan haka ko biki ko suna sai dai a gaiyyaci Adda kaɗai tare da warning ɗin 'kar ta zo musu da Nuratu' Yanzun kuwa itama da ta fahimci wacece Nuratu shikenan ta kama kanta, dama Yadikko da su sun daɗe su na gaya mata amma ba ta yarda ba sai da ta gwada mata a kanta tukunna ta ji ta gani. Ƴan Unguwar Abokan Ya Mustapha tun na baya kafin ya tafi karatu, duk sai da su ka taru su ka bashi shawara har da manya akan ya haƙura da auren Nuratu amma ya ce ya ji ya gani. Baba Yusufa kuwa ya ce 'ko mutuwa zai yi ba zai auri Nuratu (Anne) ba' Sarai ya san su ne silar tarwatsewar gidansa dan haka ba zai taɓa bari su sake shiga jikinsa ba....a halin da ake ciki kullum Yadikko sai ta jibgi Adda ba laifin tsaye ba na zaune gashi Yarinyar ta kwanta rashin lafiya tun tarwatsewar last aurenta... itama Annen jinya ta ke yi a tsatstsaye tun lokacin da Baba Yusufa ya fara nemawa ƴar tashi magani.. Dama tun lokacin da soyayyar Yadikko ta shigi Kaka Nura ya tsani Baba Yusufa tsana ta fitar hankali. Ita kuwa Nuratu tun lokacin da ya fara yiwa ƴarsa magani (ita kuma ta fara jinya) kuma bokanta ya tabbatar mata sai sun fi haka tsayawa saboda addu’a ake yi sosai kuma ba a waje ɗaya ba, ba kuma a gari ɗaya ba, shikenan gaba ɗaya ta tsani mutumin matuƙa.... Gashi Bokan ya ce mata sai dai ta kawo dubu ɗari in ba haka ba Adda sai ta warke kuma har da haske ya hango mai ƙarfi a tattare da ita muddin aka karya komai…ko kuma in ta kasa haɗa kan kuɗaɗen to ta zo akwai wata hanya ta daban!. Mutumin ya tabbatar mata da cewar “babu abunda zai sameta ba wai asirin ne zai dawo kanta ba dan ba ƙaiƙayi ake yi a maganin Addan ba, kawai neman lafiyarta ake yi ta hanyar Addu'a, hatta wannan kwanci tashin da ta ke ta faman yi ba wani abun bane ba da zarar Adda ta warke an rage addu'o'in da ake yi itama za ta warke garau... Amma baƙin ciki, kishi da kuma ego..... kar Adda ta yi winning against her ya sanya ta ƙi haƙura sannan ta na gani in ta barta ta yi winning it means duk wahalarta ta baya ta tafi a banza fa kenan sannan ubanta da Yadikko sun ci riba… Sosai zuwa wannan lokacin Uwani ta fita a harkar Anne da Mahaifinta Kaka Nura. Domin kuwa sun tartarata ne itama sun ajjiye a gefe... Anne ko kulata bata yi saboda ko gaisheta ne in ta yi maimakon ta amsa mata sai dai ta ce mata "ki ji tsoron Allah" Saboda ita kanta zuwa wannan lokacin sarai ta san Nuratu ta kware a neman maza da kuma bin Malamai har ma da shaye-shayen da ta soma ba da jimawa ba duk Uwani ta sani, gashi Ubanta ya kafa ya tsare ya ce in ta yaɗa to a bakin aurenta, ta bar mutane su yi ta gulmarsu amma ita dai a matsayinta na Uwarta kar ta kuskura ta bari a ji daga Bakinta. Wae su taru su rufawa ƴarsu asiri wanda a tunaninta tsoron hakan ne ya sanya ta yi shiru sai dai abunda bata sani ba toshiyar Bakine ƴar tata ta yi mata sannan ta yi mata mutuwar tsaye dan akwai Bokan da ya tabbatar mata cewa 'in har bata kafe Uwani ba to tabbas ita za ta kafeta da sunan kariya da nema mata shiriya ta hanata jin daɗin rayuwarta kwata-kwata' Shiyasa tun da Uwani ta dawo gidan gaba ɗaya duk sai ta koma wata sukuku kamar wata gaula... Su Baba Yusufa su kuma a tunaninsu baƙin cikin Nuratu da Nura ne ya sanya ta koma haka da kuma Yadikko... Dan a wannan lokacin sai da Yadikko ta kusan tarwatsawa Uwani zuciya da gori da baƙaƙen maganganu, saboda a ganinta ta hakan ne kawai za ta ɗan samu ta rage azabar baƙin cikin da ta ke ji a cikin Zuciyarta duk a ta sanadiyyarsu, kuma da ikon Allah Baba Yusufa sai ya gagara tsawatarwa Yadikkon sabida shima a ƙule ya ke da Nuratu da Ubanta sannan yau da gobe sai Allah, besides shima ɗin bai barsu ba dai kullum ana cikin case ɗin sai sun bar gidan ta inda Kaka Nura ya ɓullo da wani sabon zance wai 'tunda ya yi shekaru aru-aru har ashirin to fa gida ya zama nasa(iyaka inda su ke zaune), idan ma zai tashi dole sai an jira ya samu wajen zama tukunna.' Kuma da ikon Allah sai ya soma samun magoya akan hakan. Abunda ya sake kafe Uwani a auren Kaka Nura kenan a wannan lokacin saboda idan ya sake ta ta san babban case ne zai sake tashi bayan wanda ake ciki itakuma a ganinta bala'in da su ke ciki ma ya ishesu ba sai ta jangwalo wani da aurenta ba, dan a yadda ta fahimci ya na son Yadikko zuwa wannan lokacin ta san babu inda zai yarda ya tafi ya barta idan kuma ya kashe aurenta da Baba Yusufa ya ɗauketa suka yi gaba to fa ita aka cuta saboda ba ta so ya janye mata Anne gaba ɗaya, ta na so ta tsaya a kanta ta gyarata sannan a gabansu ma ga abubuwan da ta ke yi Ina kuma ga in a bayan idanunsu ne an barta da Kaka Nura da Yadikko kawai… Jinya sosai Mustapha ya kwanta a lokacin da Baba Yusufa ya tabbatar masa da cewa 'muddin ya sake yi masa maganar Nuratu wallahi sai ya tsine masa albarka.' Dan haka Zuciyarsa ta kumbura saboda wani kalar so ya ke yi mata na masifa musamman ma da ya dawo ya ganta ta cika ta ƙara kyau in ka ganta kamar aljana! Shiyasa duk ya bi ya gigice kuma ya ke iƙiirarin 'Wallahi ko a karuwa ce ya yarda ya ji ya gani zai aureta…' Wanda furucin nasa ya taka muhimmiyar rawa wajen sake tunzura Baba Yusufa shima ya sake kafewa akan in dai shi ne Ubansa to ba zai aura masa ita ba dan a yadda ya ga Mustapha ya na hauka a kan Nuratu ya san masifun da za su biyo bayan auren nan su na da yawan gaske tabbas! Dan haka ya sake jajircewa akan ba fa za a yi ba, wanda jinyar tasa ce ta ci ƙarfin case ɗin tashinsu Anne da ake ta hayya-hayya a kai, dan haka ya ɗan lafa. Yayinda gaba ɗaya hankalin Anne ya karkarta zuwa ga Ya Habu wanda shi kuma duk duniya babu wadda ya tsana sama da ita. Babban abinda ya sake haukata Anne ta kuma dilmiya a cikin kogon ƙaunarsa shine yadda ya ke wasa da kuɗi kamar bai san zafinsu ba.... Wani zubin tsabar yadda ta kwallafa rai a kansa ba ta iya yin barci sai ta sha wani abun saboda tunaninsa, wanda hakan ya sanya ta dilmiya kogin shaye-shaye. Watanni biyu curr aka ɗauka Mustapha ya na jinya dan daga baya daina ɗaukar wayarsa Anne ta yi ta daina kulashi gaba ɗaya! Wanda hakan ya sake assasa abun… Da kyar ya ɗan ji sauƙi aka dawo da shi gida zuciyoyin kowa babu daɗi dan sun tsani Anne amma kuma su na jin tsoron rasa Mustaphan saboda Likita ya tabbatar musu barinsa haka cikin wannan damuwar akwai matsala… Kwatsam! Anne ta ji labarin an saka ranar auren Adda, nan da sati ɗaya tak! Dan iyayen ɓoyewa su ka yi saboda dama zarginta su ke yi… Aiki ta ke yi sosai ita da bokayenta akan ta raba Yadikko da Baba Yusufa dan Kaka Nura duk ya yi yaushi kamar wani ba shi ba! Ita ko ba dan Kaka Nura ba ma ta na so ta kashewa Yadikko aure ko dan ita da Adda su dawo ƙarƙashin ikonta.. Sai dai kuma aikin da ta ke yi kamar ana rubutune a kan ruwa dan sam-sam ya ƙi ya ci!. Still a wannan lokacin ne kuma ta fahimci ashe Uwani itama aikin kanta ya soma warwarewa har ta fara nema mata magani da Mijin aure a ƙauye ɗan Malamin wanda ta san zai kula da ita ya warkar da ita dan ita Uwani ciwo ta ke ganin abun na Nuratu da Mahaifinta tun lokacin da ta fahimci me su ke yi da inda su ka nufa da meye su ke da niyyar yi game da Yadikko ta tabbatar da tabbas su na da taɓin hankali saboda butulcin nasu ya yi yawa a mutum mai kai ɗaya. Ga Habu shima ta kasa shawo kansa har gobe ba ya ma son ya ganta..gaba ɗaya dai abubuwan nata ko wanne ya ƙi ci kamar an saka mata hannu, Addan itama da ta ke ganin ta kore mata kowa kuma ana kan kore samari daga zuwa gareta gashi batun aure ya taso gadan-gadan...dan haka ta ɗaga hankalinta kwarai da gaske dan sai da takaici da damuwa su ka sauƙar mata da zazzaɓi a take a lokacin..duk ta birkice ta ma rasa ta ina za ta fara. Zafin soyayyar Habu ce ta addabeta gashi dama ba a dai-dai ta ke ba a wannan lokacin dan haka ta gagara ci gaba da yin shiru da jiransa ya zo gareta ta yanke shawarar tunkararsa da kanta, dan gaskiya tunda ta ke bata taɓa jin matsanancin so akan kowa ba kamar yadda ta ke sonshi hatta Kaka Nura bata yi masa kalar wannan son. Shiyasa ta zaɓi ta gaya masa ya sani wae ko ta samu ta rage wani nauyin atleast daga nan ta san nauyin zuciya da kwakwalwarta za su ragu su bada space ɗin da tunani zai shigo har ta samu damar sanin abunda ya kamata ta yi next.... Ranar ya na zaune a ɗakinsa kawai ya ganta ta shigo… Da mamaki ya tsaya ya na kallonta kafin kuma ya ɗauke Kai ya tamke fuska tamau! Kamar bai taɓa dariya ba. Cike da yanga da kissa ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi gefen katifarsa wanda hakan ya sanya ya miƙe tsaye da sauri cikin daka mata tsawa ya baiyyana a asalin sojansa ya ce “get out!!” Ko ɗarr!! Anne ba ta ji ba, ta miƙe tsaye itama ta na yi masa wani kalar kallo da wani yanayin da ya sanya a take jijiyoyin jikinsa su ka amsa dan haka cikin matsanancin tsoron shaƙiyancinta ya shiga ce mata "get out!!" Da masifar ƙarfi! Ya na mai ja da baya amma sai dai kawai jinta ya yi ta afko kan jikinsa. Ƴar Yarinyar da ya ke yi mata kallon ƙanwar ƙanwarsa cikin ikon Allah a ta ke ta hargitsa masa lissafinsa bayan amfani da hannayenta da ta yi a wasu sassa na jikinsa da bai fi sau biyu ba… Sai da ya yi da gasken-gaske tukunna ya nemo ƙarfinsa ya ɓamɓareta daga jikinsa, ya yi mata shegen dukan fitar hankali dan sai da ta kasa tashi tukunna ya tsallaketa ya fice jikinsa ya na masifar karkarwa! Ta ya ma in banda tsabar Iskanci za ta yi masa hakan bayan ta san sarai ɗan uwansa ne saurayinta, sannan ae shi ba sa'an wasanta bane ba! Tabbas mace shu’uma ce dan gaba ɗaya ta hautsina masa tunani, ta tsoratashi matuƙa a wannan lokacin.... Habu bai ɓoyewa iyayensa komai ba amma sun ɓoyewa Mustapha, wanda gaba ɗaya tausayinsa ya fara addabarsu. Yadikko ta na gama jin bayanin ta fita a hargitse Allah ya so Kaka Nura baya gidan sai Uwani ne kawai da Anne. Ta na shiga ta tarar da Nuratu (Anne) a kwance fuska a kumbure Uwani ta sakata a gaba ta na ta kuka dan ɗazu Nuratun ta na shigowa Uwanin da ta tambayeta "mai ya faru?" kanta tsaye Nuratun ta ce mata "fyaɗe na so yiwa Habu shine ya yi min haka…" Wannan dalili ya sanya Uwani ta saka ta a gaba ta dinga risgar kuka kamar ranta zai fita. Yadikko ta na shigowa ta rarumo wata belt ɗin Kaka Nura da ta gani a saƙale kafin Nuratu ta tashi ta rufeta ta duka… Kasancewar Yarinyar mai ƙarfin zuciya ce ya sanya ta tashi itama ta hau ramawa.. Habu ya na shigowa ya tarar tana kimar uwarsa, dan haka ya ɗaura daga inda ya tsaya ɗazu dama bai gama hucewa ba… Yayinda Yadikko ta wuce ta shiga firfito da kayayyakinsu ta na kaiwa chan waje ta na zubarwa… Sai da Nuratu ta suma tukunna Habu ya kyaleta ya shiga taya uwarsa fatali da kayansu har chan waje, yayinda Uwani ta ke zaune ta na kuka zuciyarta na ƙuna ta na sauraron yadda Yadikko ta ke ƙare musu zagi ta na cewa wallahi yau sai sun bar mata gidan Mijinta Sai da su ka fitar da komai waje a su ka watsar da shi a ƙofar gidan a bainar nasi tukunna su ka ja Nuratu itama a sumen a yadda ta ke, suka fitar da ita suka jefata akan kayan sannan suka mayar da ƙofar gidan nasu su ka rufe bayan sun kori Uwani itama ta fita salin alin dan a yadda ta ke ganin Yadikko ta san tsaf itama zata daketa in ta yi gardama. To dae da wuƙa Kaka Nura ya dinga neman Habu bayan ya ɓalla ƙofar gidan ya shige a lokacin da ya ji ya ga halinda ƴarsa ta ke ciki Dan awanninta uku yashe a waje babu wanda ya kulata har sai da ya dawo tukunna ya ganewa idanunsa... Allah ya so Habu ba ya nan lokacin da ya dawo dan haka Baba Yusufa ya kirasa ya ce kar ya kuskura ya dawo Unguwar, bai gaya masa daliliba ya kashe wayar. Ko da Nuratu ta farfaɗo da kyar aka barsu suka koma cikin gidan wanda gaba ɗaya suka muzanta…Yayinda Kaka Nura ya ɗaukarwa kansa alƙawari wallahi sai dai su su fita su bar musu gidan tunda su ka yi musu wannan tozarcin.. dan ya na ajjiye Nuratu ya tattaro Yara aka maida kayan cikin gidan saboda su san zama daram! Tukunna ya bazama neman Habu. Ba abunda ya fi ɗagawa Nuratu hankali irin yadda wae kaff Unguwar tasu babu wanda ma ya kulata hatta Uwani to Ina ma ta yi.? A bakin Kaka Nura ta ke jin wae gidan maƙofta ta shige a lokacin da abun ya faru saboda wae ta na jiri… Ba kaɗan ba ran Nuratu ya ɓaci zuciyarta ta ƙuntata!! Saboda a ganinta wacce iriyar daƙiƙiyar uwa ce za ta bar ƴarta yashe a waje kuɗa ya na bi ta shige ciki..tabbas duk sai ta gasa musu aya a tafin hannunsa wallahi in har ta haifu duk sai ta tagaiyyara musu rayuwa... Da ya Mustapha wanda ta san saboda nacin sa ne ya janyo mata ɗan uwansa ya ke gudunta dan ta san wallahi ƙaryar Namiji ya ganta ya ce ba ya so! Da kuma Yadikko wadda ta tozartata, dan bayaga jefar da itan da su ka yi, ta san ɗazu sarai Yadikkon ta san kayan shaye-shaye ne a leda amma ta haɗa ta watso waje bayan ta yaga ledar yadda Uban kowa zai gani ya shaida, kuma ta ci riba dan an shaida ɗin tunda gashi Kaka Nura ya tabbatar mata har an soma munafurci ana cewa 'Ashe bayan halinta har da shaye-shaye ma ta ke yi.' Ita sam! Maganganunsu ba su yi mata zafi ba wallahi ko a jikinta dan maganganun mutane ba sa taɓa damunta! Tunda ita dai ta san ba ta jin tsoro, shakkah ko kunyar Uban kowa! Kawai ita yadda Yadikkon ta yi da gangan kuma ta ci riba aka gani aka shaida ne ya ɓata mata rai dan haka ta ciwa kanta alwashin in har ta haifu to itama Yadikko sai an gani an tabbatar ta na shaye-shaye, saboda duk abinda aka yi mata sai ta rama ba ta Mantuwa. Da kuma Uwani! Uwar da ta banzatar da ita ta bari ta tozarta! Wallahi itama sai ta tozartata ta azabtar da ita domin kuwa Nuratu ba ta yafiya.... Sai kuma Baba Yusufa da Adda suma duk sai sun karɓi rabonsu.... DA ƙyar aka iya controlling Kaka Nura sannan ƴan Unguwa kowa ya bi bayan Baba Yusufa aka ce tunda zama ya ƙi yin daɗi an basu sati ɗaya tak! Su tartara su bar Unguwar dan gaskiya sun addabi kowa kuma kar a je a yi kisan kai a zo a na cizon yatsa. Dan shima Habun a fusace ya ke da Kaka Nura wanda hakan da iyayensa su ka gani ne ya sanya su ka ce masa kar ya dawo saboda sun san kalar zuciya irin tasa tabbas in har Kaka Nura ya tunkaresa a haka za a iya yin kisan kai. Sai da aka haɗa kan sojoji suka yiwa Kaka Nura warning tukunna da mugun kyar ya yarda ya kyale batun Habu a wannan time ɗin ba wai dan ya yafe masa ba! Domin ya yi alƙawarin sai ya rama mata wallahi.... Ta na samun kanta daga raɗaɗin dukan da Habu ya yi mata ta ta ƙarasa wajen bokanta akan batun auren Adda, Habu, kashe auren Yadikkko da kuma tashin da aka basu notice ɗin su yi! Tun da ta je ta ke nanata masa cewa Ko menene aka ce ta yi za ta yi....ya faɗa mata ɗayar hanyar da ya ce akwai tunda dai wadda su ke kai ta ƙi ɓillewa ita kuma ba ta da dubu ɗari a wannan lokacin, ko wacce hanya ce ko me aka ce ta yi za ta yi saboda wallahi wallahi ta yiwa kanta alƙawari sai ta ida manufarta a kan dukkansu kuma babu uban wanda ya isa ya tashesu a cikin gidan, ba za su tozarta ba. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *21* Kanshi tsaye ya sanar mata sacrifice za ta yi musu...wata biyu zai bata ta yi sacrifice ɗin amma aiki kam tun daga ranar za ta fara gani ya na ci muddin ta ɗauki alƙawari za ta yi abunda aka ce ta yi... Sai da ta sake amsa masa da 'eh, ta ji ta gani' tukunna ya bata wani ruwa ya ce ta dinga wanka da shi kullum babu fashi a ranar da ta shirya yin abun kuma ta watsawa wanda za ta basu daga nan kar ta sake amfani da ruwan ta zubar! Ba wai sai ta sheƙa masa ba ko da ɗigo ɗaya ne a samu ya taɓa jikin wanda ta shirya basu, in ya so sai ta kashesa a lokacin ko ranar da ruwan ya taɓa jikinsa ko ta tura a kashesa duk dai yadda ta yi amma an fi so ta ƙona mutum da ransa har lahira, kuma an fi buƙatar Namiji sannan ba Yaro ba. Su kuma sun yi alƙawari za su yi mata aiki mai zafin da duk wanda ya yi yunƙurin yin abunda bata so ɗin ma zai iya rasa ransa. Rai ko kuma dubu ɗari…wanda a wannan lokacin dubu ɗari ba ƙaramin kuɗi bane ba dan haka ta zaɓi ɗayan option ɗin zuciyarta a dake ta ƙudirtawa kanta za ta iya, dan a take ta gama tsara wa za ta bayar da kuma yadda za ta yi da wanda za ta jinginawa alhakin laifin. Shi kuma Habu wani ruwa daban shima aka bata aka ce kawai in sun kasance a waje ɗaya ita da shi ta fasa ruwan a nan za ta ga amfaninsa. Dan in har ta fasa to tsawon watanni uku ma bai isa ya fita daga ƙarƙashin ikonta ba ta inda ko wacce iriyar buƙata ta je masa da ita ko ta nuna ta na so sai ya yi mata tukunna zai samu kansa da nutsuwa, sannan shi da kansa bokan ya tsafeta tass da sunan Habu kuma ya saka mata tashi albarkar(a cewarsa) tukunna ya yi mata alƙawarin duk ranar da Habu ya kwanta da ita to ta tabbata ya zama a cikin tafin hannunta ne. Adda da Yadikko suma duk sai da aka yi mata maganinsu sannan ta ɗaure su, yayinda ba ta yi aikin uwar komai akan Baba Yusufa ba saboda shi ɗin mai kankat ta tsara za ta yi masa, ta inda za ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.... A haka ta ƙaraso gida zuciyarta ta na tafarfasa dan in ta tuna abunda su ka yi mata sai ta ji kamar ta cinna musu wuta gaba ɗayansu amma kuma in ta yi hakan to ta yiwa Yadikko gata ne wadda ita kuma so ta ke yi ta dinga kasheta da zafin takaici da ciwon duniya every single day har tsufanta. Maƙil! Haka gidan ya cika taff da maƙwabta ƙawayen Yadikko Da wasu daga cikin relatives ɗinta ƴan ƙalilan dan ba ta kasance ƴar dangi sosai ba daga ita sai yayanta da Addanta ne family ɗinta. Baba Ali kuwa dama ya yi alƙawari in dae Nura ya na gidan ba zai sake zuwa ba, dan haka bai zo ba amma ya aiko musu da matarsa har da body guard soja guda ɗaya a cewarsa in an taɓa ta ya ɗauki mataki, dan ya sanar musu akwai mahaukaci a gidan. Dan haka gidan ya kasance da albarka wae ana sakun lalle....... Haka nan ake ta hada-hadar bikin Adda wanda za a ɗaura auren ne jibi (a wannan lokacin) idan Allah ya kaimu, Uwani tunda aka fitar da ita daga gidan yau kwana huɗu kenan ta ke gidan makwaftansu ta na jinya, ba su ce ta tafi ba itama ba ta ce za ta tafin ba kuma babu wanda ya nemeta, Sai da Nuratu ta dawo yau daga wajen Bokayenta tukunna ta shiga gidan ta ce "Kaka Nura ya na kiranta" Kamar ba zata bi ta ba sai kuma ta yi musu sallama ta tashi ta fita…dan ita kanta ta san sun yi mata ƙarshen kara ta na gudun kar su gaji. Nuratu ta bita a baya mutanen gidan su na girmama tsaurin ido da taurin zuciya irin na Yarinyar… Da ace wata ce wannan abun kunyar ya faru da ita kwanaki huɗu da su ka wuce to da tuni ta ɓoye kanta ruff a ɗaka amma ita kalli har ta warke ta fito abunta kuma da kwarinta! Ɗazu ma shegen duka ta yi wa wani Yaro saboda ya yi mata dariya a waje.... Da ikon Allah har cikin gidansu ta zo amma "Salam" kawai ta ce ta gayawa Uwani saƙonta cikinsu babu wadda ta gaisar. Sau uku Uwani ta na tare kanta daga faɗuwa ta hanyar dafa bango dan jiri ta ke yi sosai amma ko hannunta Nuratu bata taɓa ba ballantana ta taimaka mata dan wani kalar haushin Matar ta ke ji zuciya ta na sake yunƙuro mata a duk lokacin da kwakwalwarta ta haska mata yadda Uwanin ta banzatar da ita ko la'akari da yanayinta na rashin lafiya da ta yi yanzun bai sanya ta ji za ta iya yi mata uziri ba... shiyasa sam ta gagara tausar kanta daga abunda ta shirya mata. Misalin ƙarfe 1 na dare lokacin kusan kowa ya kwanta barci sai ragowar ƴan biki da su ke ɗan hira, ta zo ta wuce ta shige ɗakin Habu wanda ya ke a tsakar gida, kanta tsaye babu gargada… Ɗiff!! Haka su ka ɗauke wuta gaba ɗayansu sai kuma aka fara ƙus-ƙus kafin su miƙe su ka yi cikin parlourn gidan da gudu cikinsu har da masu tuntuɓe saboda tsantsar firgici da mamaki dan su dai sun san Habu idanunsa biyu bai daɗe da shiga ɗakin nasa ba daga banɗaki. Sannan ga wutar ɗakinsa wadda ta ke a kunne har kawo yanzu...amma kuma tunda ta shiga su ka yi lufff, bai korota ba. Ta na shiga ya miƙe tsaye amma abun hannunta da ta fasa sai ya sanya ya kasa motsi daga baya ma komawa ya yi ya zauna kawai ya na mamakin kansa… Minti ɗaya tak! Ne ya tara al’ummar gidan karankatakaf ɗinsù a ƙofar ɗakin Habu har da Ya Mustapha wanda ya ke kwance a ɗakin Yadikko ana ƙara masa ruwa, dan wata matashiyar budurwa ta na shiga cikin parlourn ta ce "ga Nuratu chan ta shiga ɗakin Ya Habu, kuma basu fito ba…" Ta yi maganar kamar mai Yekuwa. Dan haka aka fito rututu da masu barcin da masu ido biyu har wasu na bige wasu, dan yadda su ka shiga parlour da durufta tun a karon farko ya janyo kusan kowa ya farka dama. Sama-sama su ka fara jin kuka mai haɗe da shauƙi, kafin kunnuwansu su fara jiye musu abubuwan da ya sanya dole aka tattara Yara aka yi ciki da su. Yadikko bata Kai ga ƙarasawa inda Mustapha ya ke tsaye ba kawai ta ga ya daki ƙofar da masifar ƙarfi ta tafi ta buɗu ya afka ciki... Tsit! Haka kowa ya yi wanda hakan ya yi dai-dai da tsayuwar bugun zuciyar Mustaphan a lokacin da ya gansu turmi da taɓarya kuma yanayin su duk biyun ya tabbatar masa babu guda da aka yi wa dole. Faɗowar da ya yi waje ta baya ne ya sanya Yadikko ta daskare a wajen ta gagara motsi tsoro da karkarwar jiki su ka sanyata ta sume a wajen. Asibiti aka kwashesu aka wuce da su ita da Mustapha wanda tun a gwajin farko aka tabbatar da ya rasu...zuciyarsa ce ta buga. ------------ Sosai mutane su ka tausayawa al’amarin yayinda Kaka Nura ko isashshiyar gaisuwa bai yi musu ba ya maka Habu a kotu wae ya yiwa ƴarsa fyaɗe. Tun ranar da abun ya faru gaba ɗaya Habu ya gigice ya fita a haiyyacinsa sai dai kuma sai ya zamana kamar tsoron Nuratu(Annen) ya ke yi dan ko tsine mata in Yadikko ta na yi ji yake ba ya so…gaba ɗaya ba ya son abunda ta ke yi wanda hakan ya ɗaure masa kai tamau!! Dan shi dae ya san ya tsani Anne (baƙar tsana ma kuwa) tun usul gashi ita ta yi silar mutuwar ɗan uwansa kuma sun san ita ke korewa Adda samari dan suma waennan tunda aka ganta (Anne) da shi(Habun) Unguwa ta ɗauka shikenan su ka ce 'a ɗaga tukunna komai ya lafa' har yau ba su nemesu ba...da haka kamata ya yi ace ya sake tsanarta fiye da farko amma wani nauyi da tausayinta ya ke ji wanda sam bai san dalili ba…tun da ya haɗa jikinsa da nata gaba ɗaya nauyi da tausayinta ya danne tsanarta wadda ke danƙare a cikin zuciyarsa wanda kasancewar bai taɓa kasancewa da ko wacce ɗiya mace ba ya sanya ya ke tunanin to ko dai duk matar da ka kwanta da ita sai ka ji hakan a kanfa dukda kuwa ya san kamar da wuya dan in dai haka ne babu matar da za ta saka kara Mijinta ya tsallaka besides to ya mazinata ma su ke yi?..... Waennan tunane-tunanen ne su ka sake hargitsa Habu yayinda takaicin yadda ya yi zina kuma ya kasa katsewa ko bayan da aka gansu har sai da ya je in da ya ke so.....su ka taru su ka maida shi duk wani firgichachche ga takaicin rashin ɗanuwansun wanda ya san shi da Anne ne sila. A ɓangaren Uwani kuwa... Gaba ɗaya itama ba ta san Ina kanta ya ke ba, zuwa wannan lokacin ta koma kamar wata mutum mutumi kuma hakanan ta ke jin duk duniya babu wanda ta tsana kamar Baba Yusufa! Wannan dalilin ya sanya ranar sadakar ukun Mustapha da ya ce 'su fito su bar masa gidansa' ta yi tsalle ta dire ta ce 'babu inda za su je ae da kuɗin gadonsu shi da ita ya siya gidan... Amma ya bata wani fanni a ciki ɗan ƙarami…' Wanda hakan ya janyo kokwanta bayan duk an juya ana kallonsa da son jin ta bakinsa aka ga ya yi shiruu ya gagara cewa komai wanda shi a nashi ɓangaren al'ajabi ne ya hanashi magana dan sosai kanshi ya ɗaure zuciyarsa ta ƙuntata yayinda ya ji duk ya muzanta! Duba da yadda ko satin baya da aka gama tsarawa akan an basu sati ɗaya su tashi! Ita Uwanin ta yarda ta amince, itance ma ta dinga tausar sa akan 'ba komai ae ya ma yi ƙoƙarin zama da Nuratu da Ubanta! In sha Allahu za su nemi wani wajen kar ya damu da ita she can take care of her self. Dan ko saboda Nuratu ba za ta bar Nura da ita(Nuratun) kawai ba gara in ta na tare da su ta na yi musu addu’a'. Shiyasa yanzu da ta tara masa mutane tana ife-ife kamar ba Uwani ba gaba ɗaya kansa ya ɗaure ya ma kasa cewa komai. Rashin sanin abun yi ne ya sanya ya ce mata 'ba komai' kawai ya sallami kowa ya shige parlour ya barta ita da Yadikko a waje su na ta hayya-hayya kamar za su cinye junansu abunda sam ba halin Uwani ba…. Nuratu kuwa ta na Ɗaki daɗi har kwanyarta! Domin kuwa aikinta ya na tafiya yadda ta ke so...... Ta inda ta ke da tabbacin a yanzu haka Uwani ko mutuwarta da kafirai bata tsanesu kamar yadda ta tsani Baba Yusufa ba! Faɗa kuwa yanzu aka fara dan in har ta gansa su ka yi ido biyu to sai sun yi! Maitar da ke tsakanin mayunwacin Zaki da ɗanyen nama aka yi amfani da wajen dasa ƙiyayya a tsakaninsu… To shi Baba Yusufa da alama hakan bai kamashi sosai yadda ta ke so ba saboda Uwani ta fishi hauka, tunda a tsaye ya ke da addu’o’i Uwani kuwa wadda da dabara ta dan janyeta daga kan Azkar ta hanyar ɗauke littafan nata ta ɓoye sannan ta ci sa'a Uwanin ta soma al'ada a tsakankaanin kwanki ukun dan haka ta yi mata aikin a dai-dai lokacin da take al’adar, tabbas da alamun sun kamata da kyau!!!!.. In sha Allahu nan ba da jimawa ba ita da shi sai sun zama yadda wani abun ya na samun Baba Yusufa kowa zai shaida itace ta kashesa... Shikenan ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya! Ta san dai a prison Uwani sai dai ta yi ta kanta ba dai ta ce za ta yi mata maganin kafiya ko ta yi mata auren dole ba.… Ta na wannan lissafin ta na cin biscuit ta na karkaɗa ƙafa ta na sauraron yadda Uwani da Yadikko su ke tashin hankali a waje muryoyinsu sun cike Unguwar. A tsakanin sati uku kacal Nuratu da Ubanta wanda ya ke ji kamar ya haɗiye ɗiyar tashi saboda tsabar so da ƙauna da proud ɗin abunda ta ke yi dan zuwa wannan lokacin ya fahimci mai ta ke yi, su ka kusan tashin gidan nan...amma ba wae su-i-su ba! Uwani ne da Baba Yusufa kullum in sun haɗu sai dai faɗa, gashi har sun fara iƙirarin kashe juna tsabar baƙar tsana! In su ka yi suka gama sai Uwani ta koma Ɗaki ta zauna ta rasgi kuka kamar ranta zai fita saboda ita dai ta san ta tsaneshi kuma su Nuratu da ita kanta ta san basu da gaskiya, a halin da ake ciki kuma ba ta so a tagaiyyara su a koresu a gidan dan sai dai su yi yawa a titi duba da yadda itama ta yi ƙaƙaff!!. Idan ta na rigimar da shi sanyi ta ke ji a ranta amma da zarar an rabasu ta dawo Ɗaki sai ta fara ganin rashin kyautawarta, ko ba komai Baba Yusufa haifarta ne kawai bai yi ba. Gashi gaba ɗaya ita kanta zuwa wannan lokacin ta san ta koma kamar wata doluwa kwata-kwata ko Abu ta ajjiye bata iya tunawa..... Sometimes mantawa ma ta ke yi shin ta ci abinci ko ba ta ci ba! Hatta sunanta wani zubin haka Kaka Nura zai yi ta kwala mata uban kira amma wallahi ta manta nata ne ballantana ma ta amsa.. Kuma duk ba komai ya janyo hakan ba sai tsabar ƙarfin asirin da Nuratu ta yi mata wanda ya fi ƙarfin kuruwarta. Gaba-ɗaya asirin da kuma ƙarfinsa ne su ka taru suka mayar da ita hakan. Tsakaninta da Kaka Nura kam sai dai kallo dama babu duka ba hantara duk ya daina amma amfaninta a wajensa bai fi ya sakata ta yi masa abu in buƙatar hakan ta taso ba ko kuma girki dan gaba ɗaya hankalinsa ya sake komawa kan Yadikko wadda Nuratu ta rantse masa akan ta kusan zama Matarsa, shiyasa ya nutsu ya kwantar da hankalinsa ya rage hayagagar da ya ke yi da jin haushin kowa. Tun satin rasuwar Mustapha lokacin da Habu ya ga ba zai Iya jurar zage-zagen da Yadikko ta ke yiwa Anne ba ya tartare kayansa ya bar gidan a cewarsa ba ya son zaman ɗakinsa dan haka ya koma gidan maƙotansu da zama sai in ana rikici ne ya ke shigowa gidan, inda ya share sati uku da kwanaki uku a chan.. A ranar da ya tattaro kayansa ya dawo cikin gidan aranar ne Anne ta sanarwa kowa ta na ɗauke da cikinsa dan haka ko ya aureta ko ta tona musu asiri ta yi yekuwa a Unguwa. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *22* Sosai aka sha ɗan ƙaramin yaƙi a gidan dan Uwani cewa ta yi "sai an biwa ƴarta hakƙinta yayinda ƙiri-ƙiri Baba Yusufa ya ce mata "ba fa zai yiu ba wallahi muddin da ransa ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zai haɗa jini da su ba. Ae ba fyaɗe aka yiwa ƴaartata ba ita ta kai kanta" Yadikko kuwa rufe Nuratu ta yi da duka ta na kuka ta na bugun cikin Nuratun, a cewarta 'duk ranar da aka haifi cikin nan ta san sai ta haɗiyi zuciya tsaf ta Mutu har lahira…tsabar baƙin ciki' To dae wannan karon duk irin ƙaunar da Kaka Nura ya ke yiwa Yadikko ya gagara haƙura dan har marinta sai da ya yi saboda ta taɓa masa ƴa wanda hakan ya sake fusata Baba Yusufa aka kusan kwana ana rigima a gidan! Har sai da shi da Uwani su ka yiwa juna alƙawarin ‘sai na ga bayanka/ki’. Ba abunda ya ke sake baƙanta ran hatta ƴan Unguwa waenda su ke rabiya kamar yadda Uwani ta ke biyewa su Nuratu kwana biyun nan dan ƙiri-ƙiri kowa ya san a side ɗinsù ta ke shiyasa kusan duk aka ƙullaceta ake jin haushinta… Sai kuma Habu wanda zuwa yanzu mazan layin su ke ce masa 'shanyayye' dama tunda aka kamasa da Nuratun ake ta zaginsa kowa ya na cewa shine ya kashe ɗan Uwansa, dan a ganinsu ƙaryar kaidin mace ko ya yake kuwa! Ta chanja masa akala haka lokaci guda, kawai komai da ya yi to ya yishi ne da saninsa dan biyewa son zuciyarsa… To yanzu kuma haka nan Nuratu za ta zage ta zaage Uwarsa tsaf a gaban idanunsa amma ba zai taɓa cewa uffan ba, shiyasa kowa ya ke a wuya da shi... Nuratu ta riga ta samu abunda ta ke so dan jama’a kowa ya gani ya shaida lokacin da Uwani ta cewa ɗan Uwanta “sai na ga bayanka, kuma gida ba za mu fita ba sai dai kai ka fita ka bar mana wallahi, a raye ko a mace…” Gashi zuwa wannan lokacin wasu ma sun soma cewa Uwani taɓin hankali gareta duba da abubuwan da ta ke yi da yadda ta canja akala lokaci guda da kuma yadda ta ke a firgice ko da yaushe! Wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya sake yiwa Nuratun ba... Dan haka a washegarin Daren ranar ta bi ta bayan windown ɗakinsa sai da ta leƙa ta tabbatar shi kaɗai ne babu Yadikko a ciki tukunna ta jefa masa ruwan maganin a ledar da ta zuba ba tare da ta ƙulleta ba a kan jikinsa sannan ta watsa fetir ta cinnawa ɗakin wuta! Bayan ta yi amfani da abun shaye-shayenta marar ɗanɗano over dose tun magrib ta zuba a cikin ruwan gidan kowa ya sha ya bugu maƙil shiyasa har sai da wutar ta cinye Baba Yusufa a cikin ɗakinsa ta fara kama wasu wajajen a cikin gidan tukunna da mugun kyar Habu ya fito ya na layi ya shiga ihun a kawo musu ɗouki dan ko gani sosai ba ya yi…sakamokon buguwar da su ka yi gaba ɗayansu ban da ita da Ubanta wanda ta cewa kar ya sha ruwan gidan dan har a na ɓangarensu ta zuba saboda kar Uwani ta fita da kwarinta ta kawo jama’a a kashe wutar ba ta riga ta kashe wanda ta bayar a sacrifice ba. Garr! Su ke ita da Kaka Nura amma suka ƙi motsi suma.. Sam babu wanda ya ji ife-ifen Habu dan a hankali ya ke yi sosai, har ya zube a wajen...ya na ganin wuta amma ya kasa taɓuka uwar komai... Ga wuta nan ya na gani ta winduna ta na cin ɗakin Baba Yusufa kamar hauka sannan ta na cin ɗakin Yadikko da parlour, ya na jin wasu kalar koke-koke mai alamun salati ne ake yi, da su ke tabbatar da masu yi su na cikin azaba ne amma ya gagara motsi, takaici da baƙin cikin hakan ya sanya ya sume a wajen kawai. Su Nuratu, sai da su ka tabbatar wutar ta je inda su ke so..su ka kintaci lokacin da ya ci a ce ta yi yadda su ke so tukunna ta ɗauka waya ta kira wani a layin muryar a hankali sannan da kyar ta shiga cewa "wuta ta kama, su taimaka musu, ita dai duk cikinsu kowa ya kasa motsi bata san mai ya faru ba da kyar su ke iya fitowa tsakar gida ma…" Dama hayaƙi da ƙauri ya tashi wasu a cikin maƙwafta... a haka ma wutar ba ta yi hayaƙi sosai ba saboda babu kayan katako sosai da abubuwan da za su taimaka mata ta bada hakan(hayaƙin) a cikin gidan amma dukda haka ƙauri da hayaƙi sai da ya tado wasu daga cikin maƙwafta ya kawo su ƙofar gidan ana ƙoƙarin ɓalle ƙofar ne ma Nuratu ta yi kiran wayar. ………… A hankali Nuratu ta miƙe ta na kallon Uwani wadda itanma ta ke kallonta ta na hawaye itakam ko ƙoƙarin da Habu ya yi ma ta kasa dan ba ta jin alamun ƙafafunta ma kwata-kwata a jikinta!.... Juyawa kawai Nuratun yi ta fita ba tare da ta yi mata komai ba...lokacin wutar har ta yi ƙarfi! Hayaƙi ya game koina a gidan har ba a gani sosai… Yanzu in ta fiddata ta san za ta iya cewa ba ita bace ta kunna wutar, kuma a yadda ta san Uwani ta tsaneta tsaff za ta iya tona mata asiri dan in bata ji wasu ba to tabbas ta san ta ji wasu daga cikin maganganunsu ita(Nuratun) da Kaka Nura, dan haka gara ta ƙone ta na cikin jinya a yanke mata hukunci ko kuma ta wuce kawai saboda har ga Allah ita dai kullum dubawa ta ke yi ta na sake dubawa amma bata ga amfanin Uwani a rayuwarta ba! Gara Kaka Nura sun fi fahimtar juna, ya na sonta sannan kuma ba ya daƙile ta ba ya ƙoƙarin hanata yin abunda ta ke so sai dai ma ya goya mata baya... Uwani kuwa liability ce kawai. Shikenan yanzu za a yi case da victim da suspect duk sun mutu dan haka bata da damuwar komai sannan bata da jigilar zaryar zuwa prison. Da wannan tunanin ta fita zuciyarta fes dan ta san a yadda ta bi duk sharuɗan boka tabbas duniya a tafin hannnunta ta ke, dukkan burikanta ta san za su cika in sha Allahu. Ta na fita ta ji ana gab da ɓalle ƙofar ma dan haka ta yi sauri ta nemi waje kusa da Habu ta wani kwanta fuskokinsu su na kallon juna. ......... Har ya miƙe zai fita sai kuma ya kalli window ya ga zai iya fitar da Uwani dan katangar babu tsayi kuma baya dogon lungu ne, dan haka ya koma ya ƙarasa ɓalle net ɗin windown ya kinkimeta ƙarshe ma ya yi kamar ya goyata tukunna ya fice da ita daga windown ya taka abu ya fitar da ita daga cikin gidan. Sai da ya fitar da ita daga layin ya ajjiyeta a wani kongo Allah ya so shi ba a ganshi ba dan lungun babu fuskar gida ko ɗaya, ya dawo, ya na shiga cikin ɗakin ya kwanta dai-dai mutane su na shigowa dan zuwa wannan lokacin an gama fidda kowa shi da Uwani ne kawai ba a gani ba. Ana ƙoƙarin ɗaukarsa ya na ce musu "su fara fita su kamo Uwani ta yi hanyar banɗaki yanzunnan ita ce ta kunna wutar....." Ba su wani biye masa ba su ka ɗaukeshi aka saka shi a mota duk aka yi asibiti da su. Inda ya samu ya zille bayan wasu ƴan awanni ya koma ya je ya ɗauki Uwani gabannin asuba ya wuce ƙauyen Tofawa da ita. BAYAN KWANA BIYU…. Baba Yusufa ya cika da imani dan da kalmar shahada ya rasu a bakinsa bayan an fidda shi a ƙone daga cikin ɗakin nasa...ana shirin saka shi a cikin mota a kaishi asibiti ya ce ga garinku nan… Unguwar gaba ɗayanta a hargitse ta ke a wannan lokacin sannan cikin jimami dan sai da wutar nan ta kai asuba ta na ci da mugun kyar aka kasheta kasancewar a makwaftansu...Yaron gidan ya na sayar da fetir kuma cikin dare ne incidence ɗin ya faru so gaba ɗaya galolinsa su na ciki dan haka wutar da ta shiga gidansu(mai sayar da fetir ɗin) sai da ta cinye komai aka kasa kashewa mutane ma da kyar a ka fidda wasu dama wasu already sun fito tun da su ka ji hayaƙi... Sannan ta kama gidaje huɗu suma duk ta yi musu rauni ba na wasa ba, ciki har da gidan yawa inda mutum biyu ne kawai suka cika ragowar kuma su na kwance su na jinya sosai. Sarai Nuratu ta ji kuma ta ga abinda ganganci da son zuciyarta su ka janyo, amma ko a jikinta! Dukda ita har ga Allah mutum ɗaya ta so kashewa hakan bai sa ta ji wani abu mai kama da rashin jin daɗi ko ɗarr game da yadda abun ya shafi mutane da yawa ba. Rashin ganin Uwani da ta kasance mutum ɗaya da ba a gani ba ya sanya kowa ya shaida ita ce ta kunna wutar ta gudu ko kuma dai itama ta mutu ne a cikin wutar, sannan duba da yadda a shekarun baya ta ke kuka da ita kanta Nuratu da Nuran kafin yanzu da ta ke goyon bayansu ido rufe da aka kasa gane kanta ya sanya aka sake tabbatarwa tabbas ita ce ta so ta kashe kowa God knows y! Yayinda waensu su ka bada tabbacin ciwon hauka gareta shiyasa ta yi hakan. Hankalin Kaka Nura a kwance dan ya sanar mata cewa "ita ake zargi dan haka ta tsaya a nan inda ya kaita case ya ɗan lafa tukunna" dan haka ya san ba za ta yarda ta baiyyana kanta ba, shiyasa ya ke jinsa wasai da daɗin yadda abubuwa su ke tafiyar masa yadda ya ke so. Uwani ta so ta je ta tona musu asiri amma ko da ta kusanto Unguwar da labarinta ta fara cin karo a bakin mai machine ɗin da ya ɗauketa, dan ta na hawa ya soma bata labarin wata mata Uwani wadda ta yi sanaddiyar mutuwar mutane biyar da raunata mutane kusan ashirin, ya na ta tsine mata, kuma ta ji ana nemanta ruwa a jallo daga bakinsa shiyasa ta ji tsoro kawai ta haƙura ta koma dan ta san Nuratu da Nura Allah kaɗai ya san me da me suka sake gayawa mutane har ake ta nemanta da zarginta haka... Ita kam a wannan lokacin yadda ƴar da ta kawo duniya ta barta cikin wuta domin ta mutu ne ya sake hautsina mata lissafinta shiyasa ta ma rasa kuzarin yin komai kawai ta haƙura ta koma ta zauna a inda Nura ya kaita. Neman duniya aka rasa Uwani ko ta yadda za a fara nemanta ma shiyasa kawai aka yi concluding akan ta mutu ne a cikin gidan dan banɗaki da kitchen ƙurmus su ka yi sosai ta inda aka kasa gane meye da meye ma a cikinsu, kuma Kaka Nura ya basu tabbacin banɗakin ta nufa lokacin da abun ke faruwa. Yadikko kuwa azabar mutuwar da aka yi mata a jere ce ta sanya ta samu taɓin hankali wanda hakan ya dasa tausayinta kwarai a cikin zuƙatan mutane yayinda aka ci gaba da zagin Uwani, dukda zuwa wannan lokacin kowa ya na tunanin ta mutu ne amma hakan bai sa sun yi mata fatan rahama ba. Da ikon Allah Yadikko ta na fita daga takaba yayanta guda da ya yi ragowa ya zo aka ɗaura musu aure ita da Kaka Nura babu hayaniya, ƴan Unguwa kuwa dukda a mahaukaciyar ta ya aureta cewa su ke yi tabbas an cuceta.. Kowa ya yarda an shaida Uwani ce ta kunna wutar nan sai dai ba a ja shariah ba tunda babu ita ana ma tunanin ta mutu ne itama a cikin wutar dan haka case ya mutu. Habu shima da kansa bayan watanni uku lokacin da ya ga cikin Nuratu har ya fara tasawa ya ce ya ji ya gani a take a ka ɗaura musu aure zuciyoyin ƴan Unguwa fal takaici saboda sun san Nura da ƴaarsa Annoba ne amma tunda har su suka ce sun yarda a rufawa juna asiri shikenan Abun na Habu ma ya fi damun kowa dan in banda ƴan gidan ba kowa ne ya san Nuratu na da cikinsa ba An dai san an kamasu tare anmma ba a san abun har da su shigar ciki ba…. Kamar yadda Nuratu ta so sai da ta san yadda ta yi ta maƙalawa Yadikko shaye-shaye dan bayan ta auri ɗanta ita ke jinyar ta da bata magunguna ta nan ta dinga ɗura mata tun Yadikko bata iya ba har ta koya yayinda Nura shima ya ke kula da ita ta tashi kalar kulawar dan ko ta na tashar barci ko tsaka da ciwo muddin buƙatarsa ta taso haka nan zai sauƙe ya ci gaba da sabgar gabansa... Tunda ya aureta babu rigima babu faɗa kuma ko ɗanta surukiinsa (Habu) shima an ci sa'a ya ɗaga masa ƙafa batun kotu dama tunda ya auri Nuratu aka janye, ana zaman lafiya da shi kawai dai halaiyyarsa ce ta na nan daram da kuma shekaru su ka fara jaa sai ya dawo da halaiyyarsa ta neman mata itama har ta fi ta da! Dan dama Ƴadikko ta girme masa nesa ba kusa ba... Haka nan zai ɗura mata kwaya ya kawo mace har cikin ɗakin ya yi abunda zai yi ya gama tana ta uban barci… Dan dukda neman sa’a da bin Malaman da su ke yi shi da ƴarsa hakanan tun rasuwar Baba Yusufa su ka tsiyace talauchi ya yi musu sallama shiyasa ko kuɗin Ɗaki da hotel ba ya iya kamawa. Anne kanta da take fita take karuwancinta da auren Habu a kanta kuɗiin in ta samo sai dai su ci abinci ragowar ta bi Malamai da bokaye. Gidan nan dai na Mariri nan suka share su ka zauna, su na ciki a hankali aka dinga gyarawa su ka gaje shi har gobe in an tasa maganar sai an yi bala’i da su akan gidan. Ba dai su isa su koresu ba dan Mai Unguwa ya ce gida na Habu da Adda ne amma iko, isa da mallaka kam su na ganinsa ganin idanunsu. Tsakaninta da maƙoftansu kuwa da ƴan Unguwar sai dai kallo dan babu wanda ya ke shiga harkarta saboda yawanci duk an santa sabili da almost all gidajen arear na gadone so ƴaƴa ne su ka gaje daga wajen iyayensu su ke zaune a ciki (kamar dai su ma) shiyasanya labarinta ya ke nan daram a rayukansu ita da Ubanta, sabbin zuwa kuwa waenda ba su san wacece ita ba ko sun shigewa juna to fa ba a sati ana daɗi da ita dan ita dai Anne ko zaman minti kaɗan in ta yi da mutum to fa sai ta cucesa… Mazajen layin nan kuwa masu kalle-kalle da bin mata babu wanda bai san Anne a macenta ba, wani ma in ta shiga gidan mace ta ga Mijinta da kanta ta ke kai masa tayin kanta! Gashi a yi magana ita da ubanta su kusan tashin unguwar da bala’i dan Anne akwai farin jinin maza tsaf sai ta saka mutum a cell. Zata iya kwana a waje ta na ife-ife da zage-zage da Habaici kala-kala wanda shine mai sauƙin ciki dan in hau ɗinta ya tashi da gasken gaske sunan mutum ta ke kamawa ta zage tass, jifa kuwa a wajen Anne abun ya ɓaci, akan abunda bai kai ya kawo ba ma sai ta yiwa mutum asiri, shiyasa kowa ya ke tsoronta ya ke gudunta. Wannan dalili ya sanya yanzu haka dae a unguwar ba ta da gidan zuwa dan ko ta shiga sai dai a yi ta mata yaƙe ana Allah Allah ta fita, dan faɗa da Anne kam kai tsaye za a ce kaff arear tasu kowa tsoronta ya ke ji, ita da Kaka Nura. Watannin auren Anne da Baba Habu bakwai cif-cif ta haifi ɗanta kyakkyawan Yaro ya ci sunan Baba Yusufa ake kiranshi da Amir... Inda Likitoci da shi (Baba Habu) duk su ka tabbatar da ɗan watanninsa bakwai (bakwaini ne) saboda shi dai ya san ya ganta ta na period ko bayan aurensu da sati ɗaya... Kwata-kwata Baba Habu bai san menene daɗin aureba, dan a fuska da jiki ne kawai Anne ta ke da kyawu amma bayaga mugayen halayenta mabambanta ko irin ɗumin jikin nan na mata babu shi a tare da ita, sannan baya neman mata bai taɓa yi ba amma tabbas ya san Anne ta na cikin mata masu ƙarancin ni’ima gata da shegiyar jaraba! Dan ko wata ba a yi da auren ba ita dai kullum mitarta 'ba ya gamsar da ita!' Sannan ko Mahaukaci in ya kusanci Anne ya san ta san maza fiye da tunanin mai tunani dukda kuwa ta na gyara sosai amma duk a banza. Gashi tunda ya aureta kamar ya auri karayar arziƙinsa ne komai ya tsaya masa chak! Abunda ya tara da business ɗin da ya ke yi duk su ka taɓarɓare! A ranar aka koresa daga aikin soja dan a yadda bincike ya basu an ce shine ya kashe iyayensa da ɗan uwansa domin ya aure budurwarsa(ɗan uwan nasa) dan haka ba shi da adalcin da za a basa amanar ƙasa da mutan cikinta. Gashi ta na shiga gidan watanta bakwai cif ta haihu dan haka sai nauyin ya ƙaru a kansa, ga Yadikko Itama wadda jima’in aurene kawai ya ke haɗata da Kaka Nura baya ga haka duk kuɗin maganinta da cin ta suturarta komai Habu ɗin ne sannan ga Adda itama..wadda Yadikko da Anne su ka sako a gaba!. A lokacin Anne ta asirce kowa ta mallake kowa a gidan sai abunda ta ce, hatta Kaka Nura bata barshi ba sai da ta yi masa aikin mallaka shiyasa in ta yi magana kamar faɗar Allah jikinsu har rawa ya ke yi wajen saurin ganin sun yi mata yadda ta ke so. Shiyasa Baba Habu ya sha wahala matuƙa! Dan masifar talauchin da ya shiga ba a magana saboda har kamar bara ya ke yi a gidajen makwaftansa dan Anne ba ta san a ce mata babu ba! Ba ta jin wannan Yaren... Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *23* Ƴaƴa huɗu kawai ta Haifa daga su ta tsaya dan a cewarta 'ba ta ga guri ba'. Tsakanin ƴaƴan babu wani tazara sosai, dan haka jikinta sam bai wani nuna tsufa ba wanda gigin hakan ya sanya ta bazama duniya ta lalace kwarai da gaske dan ɓarnar da Anne ta ke tafkawa da auren nata ba ta yi a lokacin da ta ke budurwa ba ma, kawai dai shi wannan ta na ɓoyewa sosai, ko ba komai ta na son Baba Habu wanda ƙaddarar abunda ba ta so ɗin (talauchi) da kuma son da ta ke yi masa ne su ka kafeta a gidan nasa dan tun da ta shigo ta ga ya tsiyace ta so ta fece amma sai Allah ya nuna mata iyakarta har gobe ta ke rayuwa a hakan. Sai dai fa ya na ganin ikon Allah dan bai isa ya sa ko ya hana ba... Ta na dai ciyar da gidan wanda hakan ya ƙara mata ƙarfin iko... Har hana Adda abinci ta ke yi duk ranar da ta yi gigin yi mata musu. Zuwan su Yagwalgwal Unguwar ne ya ɗan ɗauke idanun jama'a daga kan Anne su ka mayar a kan su Yagwalgwal ɗin su na masu mamakin hali da tsaurin ido irin na mutanen dan haka sai su ka zama topic ɗin ƴan Unguwar a ko da yaushe zancensu ake yi shiyasa Anne ta ɗan yi sanyi da ido ya ragu a kanta. Amir dama shi ta fara Haifa Sai Aliya Sai Afra sai Auta Amal... Ƴaƴan nata kusan duk kamanninta su ka kwaso, Amal ce ma wadda ake cewa kamannin Baba da Annen ta haɗa, ba ta wani kama da Annen…dukkanninsu Kyawawa ne tubarkallah masu shiga rai gashi Matan tun su na Yara za ka fahimci ƙirar jikinsu mai kyau ce! Wanda hakan ya sake sanyawa Anne ta ɗauki wani kalar masifaffen buri ta ɗaura a kan ƴaƴannata Matan sannan ta ke sake godewa Allah da ya bata su… Ba ita kaɗai ba hatta Kaka Nura idan ya kalli Yaran wani sanyi ya ke ji dan ya san tabbas sun tara jari, musamman ma 'Amal' Wadda idanuwanta ma kaɗai abun kallo da mamaki ne, ga ta da shiga rai kwarai da gaske. Da ikon Allah tun daga kan Amir har zuwa kan Amal Yarane masu tsantsar kunya, nutsuwa, hankali, kawaici, biyayya, kamun Kai da son karatun AlQur’ani, ga tsoron Allah da kiyaye dokokin Allah dan tun su na ƙananu muddin Adda ta ce musu Abu babu kyau Allah ba ya so to in sha Allahu sun barshi kenan har gaban abada….ga su da mugun haɗin kai kuma sun shaƙu kwarai da gaske da juna musamman Amal da Afra dan in Amal ba ta da lafiya Afra kwana ta ke yi ta na kuka abinci kuwa ta ƙaurace masa kenan, abun hannu kuwa ko wanne iri ne Afra ta kan haƙura ta bawa Amal haka Amir da Aliya suma basa son abunda zai taɓa waninsu sannan kullum burinsu su dadaɗawa juna rai. Wata tarbiyyar ba sai Baba da Adda sun koya musu ba kawai gani za a yi su na yi, dan in banda uban ashar, batsa da hayagaga ba abunda su ke ji daga Anne, Yadikko da Kaka Nura, dan Yadikko sai dai a ce da sauƙi kawai Likitoci dai sun ce ta warke amma halaiyyarta da wasu abubuwan da ta ke yi har gara ace ta yi haukar ma ya fi sauƙi, ga shi wani kalar masifaffen tsoron Anne ta ke yi ba ta laifi a idanunta...... Ganin Yaran su na da son karatun AlQur’ani ya sanya Baba ya ke yin wuff ya saka su a islamiyya tun su na shekara bibbiyu dan ba ya ma son zamansu da Anne dama, dama itanma kuma in ta Haifa Yaro shan nono wanda ya ke yi iyaka na wata tara shima a daddafe ne kawai ya ke Haɗata da su a cewarta ba za ta bari su yi daɗe su na sha ba haka kurum ta je su tsinka mata halittun ƙirjinta... Wankansu, cinsu, shiryawarsu, Assighnment da dai komai nasu duk Adda ce! Shiyasa su ka yi wata kalar shaƙuwa ta ban mamaki ita da Amal wadda ta fi ƙulafucin Addan tun ta na Yarinya kuma har ga Allah Yarinyar tun ta na ƙarama ba ta son Anne kawai ita matar ba ta yi mata ba hasalima tsoro ta ke bata, shiyasa kwata-kwata ba su wani shaƙu ba gashi ita kuma Annen duk ta fi ji da ita! Ba wai so ba dan ita ƴaƴan ma gaba ɗayansu kawai dan ta san za su yi mata rana ne ya sa ta ke alfahari da su, kawai ta fi ji da ita ne saboda duk ta fi ragowar Yaran nata kyau da shiga rai, dan haka ta na da tabbacin sai ta fi morarta. Shekarunta biyu itama aka saka ta a islamiyya dan haka shirun sai ya yiwa Adda yawa.. gashi wani ikon Allah sam Adda ta tsani shiga cikin mutane kamar wata mai aljanu ko ƴan Unguwar tun ana zuwa mata har an daina wasu dai sun ce kafiya ce Anne ta yi mata, wasu kuma sun ce Aljanin jikinta ne ya kafeta yayinda ƴan boko su ka ce depression ne da ita. Yadikko ta na fita zuwa islamiyya a bayan layinsu Anne kuwa kullum ba ta gida Baba shi kuma Yaron wani Babban shago ne a nan bayansu kullum ba ya gida cin abinci kawai ke kawosa wani lokacin in ya rufe ya taho sallah, shiyasa duk sai ta zama lonely, ta so ta haɗa kuɗin da kanta itama ta samu ta shiga islamiyyar dan tausayin Baba ta ke ji ba ta son tambayar sa kuɗi amma sai ta gagara haɗawa... Sana’a kuwa ko wacce in ta fara taɓarɓarewa ta ke yi, ga shi daɗin daɗawa ma ta na jin tsoron shiga makarantar saboda kar su dinga abun kunya ita da Yadikko a gaban mutane.... Islamiyyar nesa kuwa itama ta san ba zata samu kuɗin motar zuwa da dawowa ba. Zaman shiru, gori, kaɗaici da wulaƙancin Anne da Yadikko ne su ka sanya Adda ta yi adopting Abbakar Sadik (Abba)… A bakin Titi ta ganshi ya na kuka lokacin babba da shi, ba za dai a ce masa saurayi ba amma ya kawo ƙarfi shiyasa abun ya bata mamaki dan shekarunshi sun kai kusan goma sha huɗu... Ta na ganin Yaron ta ji ya shiga ranta matuƙa sannan ya yi masifar bata tausayi dan haka ta ce mishi 'ya zo su je ta bashi abinci' saboda ta na yi masa magana tashi ɗaya ya ce mata 'yunwa ya ke ji'. Tun a day 1 da Anne ta ga Abba ta ji ta tsani Yaron! Ba dan komai ba sai dan yadda ya ke kacha-kacha kayansa duk a yage sannan uban abinci da aka tula masa ya zauna ya narka a gabanta Mijinta ne ya siyawa Addan(dan Adda ita ke yin girkin gidan gaba ɗaya) dan haka ta yi ta azalzalar Adda ya yi ya gama ta sallamesa saboda haka nan jininta bai ɗauki Yaron ba ko kallonsa ba ta son yi kamar ma tsoro ya ke bata dan duk in dai su ka haɗa ido sai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi. Dan haka ta tisa Adda a gaba ta na ta bala'in 'su kansu da za a samu mai ciyar da su ae so su ke yi amma shine tsabar kankamba ta ɗauko musu tsintacciyar mage ta bata abincinsu...' Waya aka yi mata ta fita dan haka Adda ba ta kori Abba ba saboda dama ba ta son ya tafi ya barta cikin kaɗaici...dan Amal in sun tafi islamiyya tun safe sai yamma har asabar da lahafi, Amir Aliya har ma da Afra da su ke haɗawa da zuwa makarantar boko kuwa sun fita zama scarce dan ita bata kai ga shiga ba lokacin shekarunta biyu da rabi Afra huɗu Aliya shida Amir takwas… Dukda tashi ɗaya Adda ta gane Yaron miskiline na gaske amma ta fahimci ya na sonta itama kamar yadda ta ke sonshi itama. Duk kalar tarin tambayoyin da ta yiyyi masa ce mata ya yi kawai “Matar da ta riƙesa ce ta fahimci wanene Mahaifinsa shine ta kore shi ta ce ya je wajensa ae ya na da gata to shi kuma Mahaifin nasa ya je wajen nasa amma shima ya koreshi..” Daga haka bai sake bata amsar komai ba ya ja bakinsa ya yi shiru. Su na zauna a haka har su Afra su ka dawo daga islamiyya Wanda shigowar Yaran ta yi sanadiyyar zaman Abba a gidan na har abada dan tun da ya gansu ya kasa ƙauracewa gidan! Kullum sai ya zo, ya na ganin Anne sai ya fake da aiki, ya gyara nan ya gyara chan ya na yi ta na hantararsa ta na zaginsa.... Tun Anne ta na zaginsa har ta haƙura ta daina daga ƙarshe sai ta fara tula masa uban aiki kamar hauka, duk wankin gidan in ya zo shine zai yi, sannan duk wani aikin gidan shi ya ke yi dan ta lura Yaron ya iya aiki kuma ya na da tsafta sosai sam ba ya so ya ga waje da datti shiyasa wani abun ma tun kafin ace ya yi ya ke yi. Ita dai Adda burinta a bar mata shi shiyasa ta haƙura ta kauda kai daga wahalar da Anne ta ke bashi, ta zuba musu ido kawai bayan ta gayawa Baba ta na so ta yi adopting Yaron ne. Har gidan Matar su ka je inda ta sanar musu wata Yarinya ce ta kawo sa a tsumma ta na kuka. ita kuma ta karɓa da tausayin shi ɗin maraya ne ashe da Ubansa dan haka ta na ganewa ta sallameshi tunda ya na da gata sannan ba ta san asalin dalilin da ya sanya Uban nasa ya ke gudunsa ba. Sosai Matar ta basu takaici dan a ganinsu hakan bai kai dalilin da zai sanya ta guje shi ba da ta haƙura ta ƙarasa ladanta! Dan haka su ka ce sun ji sun gani aka yi masa ƴan gwaje-gwaje Baba ya bashi sunan Mahaifinsu (Yusufa) suka mayar da shi ɗan gida. Sun san sunan Mahaifin nasa dan Babban mutum ne sosai a ƙaasar har ma da duniya baki ɗayanta wanda da kyar Adda ta gasgata hakan... Saboda ba dan komai ba yadda zai yiwa gudan jininsa haka, amma sai kawai ta share tunanin ta rungumeshi a matsayin ɗanta ta ƙoƙarta ta saka shi har a makarantar gomnati inda Amir ya ke zuwa, islamiyya kam dama chan ya yi sauƙa ma a tsangayar Mijin matar da ta riƙesa. Kamar yadda Mahaifin Abba ba ya ƙaunarsa haka nan shima Abban, dan ko sunansa in aka kira sai an sha fama da shi a ranar sai ya kwana ya wuni bai ci abinci ba. Anne kuwa kasancewarsa ɗan mai kuɗi ya sanya ta amince da farko har da zalamar a karɓesa sai da ta ga zallar ƙiyayyar da ke a tsakaninsu ta fahimci ba fa za ta samu komai daga jikinsa ba sai wahala da nauyin da ya ƙaru musu a gidan sai ta ce bata yarda ba a lokacin kuma har an riga an karɓesa Baba ya na ta fafutukar gina masa ɗakinsa a soro dan haka da ikon Allah duk fafutuka da borin da ta yi bai yi aiki ba sam! Da ya ke Ubangiji ya riga ya tsara akwai shan ruwansa a gidan. Haka nan ta yi ta gaji ta haƙura duk ƙarfin ikonta a wannan lokacin bai yi tasiri ba dan haka sai ta tsiri huce takaicinta a kansa. Azaba kala-kala babu kalar wadda ba ta gana masa wai duk dan ya gudu amma a banza gashi Yaron kwata-kwata ba ya biye mata kuma abinda ya ke sake ƙular da ita da shi shine 'ba za ka taɓa gane halinda ya ke ciki ba' shiyasa ko ta yi masa abu ba ta ganin alamun fushi ko wahala a kan fuskarsa sam. Ga wani kalar farin jini da Yaron ya ke da shi dan ya na zuwa aka sanshi ake kuma yabonsi a Unguwar Adda da Baba kuwa kamar su cinyeshi saboda so! Dan shima Uwa da Uba ya ɗaukesu ya na musu biyayya fiye da misali kuma ya na sonsu dan haka ya sake shiga ransu shima su ke ji da shi. Shiyasa sosai Adda ta ke jin zafin abubuwan da Anne ta ke yi masa dan a duniyar nan in har ka na so ka ƙuntatawa Adda to ka taɓa Abba ko Amal.... Ba yadda ba ta yi da Anne ba amma ta ƙi ji ta ƙi gani ta uzzurawa Yaron wani zubin har Addan ta ke haɗawa in ta yi magana, sai da ya kawo ƙarfi tukunna da kansa ya kwaci kansa a hannunta dan Abba wani kalar mutum ne mai masifaffiyar zuciya da zafin rai gashi miskili na bugawa a jarida. Gov school ya yi da kyar ya ƙarasa waec tun daga nan karatunsa ya tsaya dan daga shi har Adda da Baba babu yadda su ka iya, Amir dai Anne ta yi masa cuku-cukun poly ya na kai Abba kuwa sai yanzu (2025) ne ya ke ta tataɓurza da kuɗin sana'ar da ya ke ɗan kakkamawa ko wacce ta na lalacewa a hakan da kyar ya ke ta ƙoƙarin ganin ya haɗa degree ɗinsa. Sai da ya ɗan kwana biyu a gidan shekaru su ka ja tukunna Anne ta fahimci manufar Abba! Ashe son Afra ya ke yi shiyasa ya nacewa gidan tun a karon farko. Tatas!!! su ka yi masa ita da Kaka Nura a wanchan lokacin wanda shima ya tsani Abban su ka tabbatar masa ‘ba talaka wulaƙantacce su ka haifawa Afra ba’! Ranar gori kala-kala babu wanda bai ji ba! Har sai da su ka saka Adda kuka sosai. Shi kam Abba kukan nata ne ma ya taɓa shi sosai sai ko yadda su ka nuna masa ba za su bashi Yarinyar da ya ke matuƙar so kamar ransa ba, ammaa ranar kam da ikon Allah gorikansu ba su wani fusatashi sosai ba, Dan tunda rannan ya yo kan Anne a haukace kamar zai daketa ta tsorata sosai da shi ya firgitata…shiyasa da su ka zo yi masa wanna tujarar daga ita har Kaka Nuran ba wanda ya kira sunan mutumin da su ka san ya tsani a ambato, sun dai yi gori amma shakkarsa a wannan lokacin ba ta barsu sun yi abinda su ka san ya fi tsana ba. Da Yarinyar(Afra) ta fara tasawa kuwa Da gangan su ka dinga maƙala mata Isma’il tun ba ta Isa zance ba saboda su ƙuntatatawa Abba! Isma’il ɗin makwafcinsu ne... Tun Afra ta na da shekaru uku shima ya na Yaro lokacin ya ke nacin zuwa gidan saboda ita (wanda kishin Isma’il ɗin ne ma da Abba ya ke yi bayan sun fara girma ya fara tona masa asiri aka ɓaro jirginsa)… To dae kaff layin iyayen Isma’il sun fi hannu da shuni shiyasa Mahaifiyarta ta yarje masa ba wai dan ta ji ta gani Afra ta auresa ba, A’a!! Sai dan abubuwan da ya ke kawowa Yarinyar su chocolate da kayan alkhairi dan ko Abu aka bashi a gida to sai ya kawo mata nata itama tukunna zai ci. Komai Afra itama uwar Yaron tun su na ƙanana ta ke cewa Afra surukar ta saboda in aka cire Anne a rayuwar Afra tabbas Yarinyar wife material ce gata da hankali da kunya Uwa uba duk layin sun shaida Kaka Nura da Anne ne su Afrra su ka yi rashin sa’ar su amma uba kam sun mori uba shiyasa ta yarjewa ɗan nata ta amince masa auren Afra musamman ma da suka lura uwar ta na so Dan haka su ka zage su ka dinga yiwa Yarinyar bauta kamar Allah ya aiko su Har private school su ka haɗa ita da Aliya suka saka ta, Amal ce dai da ya Amir su ka yi makarantun gomnati. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *24* Follow our channel https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Kowa ya san su tare, dan in ka na so ka farantawa Isma’il to ka ambato sunan Afra…. Bayaga soyayyarta halaiyyarta tana daga cikin abubuwan da su ka sake dilmiyashi cikin kogon so, ƙauna da begenta. Tun kafin Afra ta rufe shekaru goma sha biyar ta sauƙe AlQur’ani Mai girma yanzu kam ta zama Malama a islamiyyar tasu inda take koyarwa safe da yamma, da daddare ne kawai ta ke zuwa ajin hadda ta na ɗauka da kuma karatun wasu littafan, kuma nan ɗin ma har sun kusan idarwa. Ya Amir shima Babban Malamine a Islamiyyar dan Babban aji ma ya ke koyarwa kuma shine Amir na makarantar, duk wata gasa da makarantar za ta shiga muddin Amir ya bada gudummawa to in sha Allahu sai sun yi ƙololuwar nasara. Aliya ce ma wadda ta ke zaman hostel yanzu haka inda ta ke diploma za a ce zurfin iliminta na addini bai kai nasu ba, ta dai yi sauƙa itama Alhamdulillah ta na da nata ilimin dai-dai gwargwado, Amal kuwa yanzun (2025) ne ta kammala secondary ta na ajin sauƙa. Kamala ilimi da riƙon amana ya sanya Baba ya shiga sahun dattawan Unguwa, sai dai kuma dukda haka sai da ya ɗan fuskanci ƙalubale tukunna aka amince aka bashi limamin layin saboda Kaka Nura, Anne har ma da Yadikko ɓaragurbi ne a Unguwar, ko Islamiyyar da ta ke zuwa daga baya dainawa kawai ta yi saboda ba sa maraba da ita kuma wani zubin ma a buge ta ke zuwar musu ta yi ta abubuwan ban mamaki da takaici har sai an kira Baba ya wuce da ita gida, ga faɗa da ƴan makarantar kamar wata Yarinya shiyasa kawai kowa ya bi bayan ta haƙura ta zauna a gida in Baba ya dawo salla aka idar a masallaci sai ya shiga ya yi mata nata dan ba ta ko da ƙaunar ganin Adda ne ballantana ace ita ta yi mata. To dai duk in ya dawa (aka idar da sallar) ma sai dai ya yi karatunsa shi kaɗai saboda baya so ya koma shago a gane ba ya yi mata karatun dan already mai wajen da maaikatan duk sun san uzurinsa dan haka ake bashi awa ɗaɗɗaya a duk bayan ko wacce sallah sai dai kullum in ya zo a buge take wani zubin ma ta na barci har ya koma ba ma ta san ya shigo ya tafi ba! Shi da Adda har ma da jikokinta da su ka fara wayo…sun yi kuka sun yi yaƙin amma abun ya ci tura dan in sun kwace na wajen ta akwai a wajen Anne wadda sai daga baya ne su ka gane ashe itace ta ke bata, zuwa wannan lokacin duk wani ƙarfin asiri da surƙullen Anne akan ‘Baba ya so ta’ baya tasiri dan ƙarfin zafin zugin ɓarnar da ta yi wa rayuwarsa kuma ta ke kan yi ya danne duk wani asirinta, ba dai ya iya yin musu da ita ba kasafai ba gaskiya kuma ya kasa rabuwa da ita a cewarsa ko dan ƴaƴansa da Yadikko wadda take auren Ubanta ya san kuma ko an rabu ba a rabu bane, amma fa duk duniya babu wadda ya tsani ya ji ko da sunanta ne kamar Nuratu, dan masifa wani zubin in ya na saduwa da ita kuka ya ke yi tsabar ba ya sonta, shi kansa ya na so ya rage tsanar saboda ya san ba kyau ka tsani ɗan uwanka musulmi har haka amma ya gagara. Garin tsabar shaye-shayen Yadikko ne ta je ta shawo kwayar da ta fi ƙarfin kwakwalwarta tun daga nan ta ɗauke wuta ta koma kamar robot. Watanninta takwas a asibiti ta na jinya inda ta tatike aljihun Baba ƙaƙaf!! Kafin aka samu ta fara motsi ta dawo da magana sai dai babu ido sam bata gani da duka biyun har gobe. Aikin gida da girki dama Adda ce, Anne za dai ta kawo sometimes Baba shima ya kan kawo wani zubin har Ya Abba shima ya na taimakawa da kayan abinci Adda ita kuma ta girka Kaka Nura kuwa ko ya samu sai dai ya bi mata da kuɗin…sam! Ba a cin kuɗinsa Amal kawai ya ke ɗan kashewa kuɗi wadda itanma a ganinsa adashe ne ya ke yi dan ya na da yaƙinin samarinta da Mijinta za su biyashi a gaba. *2025* Mariri, 1:40pm Karo na uku kenan daga faɗa mata saƙon zuwa yanzu da ta ɗago labulen ɗakin nasu ta kalleta, sai da ta gama ƙarewa doguwar rigar material ɗin da ta sanyawa jikinta ɗinkin A shape kallo tukunna ta ce mata “ki yi sauri!” Daga haka ta fara ƙoƙarin sauƙe labulen za ta koma tsakar gida ta ci gaba da wanke-wanken da ta tashi Yarinyar a kai ita ta amsa ta ke yi yanzun, ta ji an ce “yanzu Nuratu gidan Matar nan za ki yi aikenta? Saboda kawai ta karɓo miki kayan da na tabbata duk tsadar su ba za su wuce dubu hamsin ba!” Kamar ba za ta kula shi ba sai kuma ta watsa masa manyan idanuwanta cikin yaɓa magana ta ce da shi “kawo naira dubu hamsin ɗin sai ta zauna a haƙura da karɓo kayan”. Shiruuu, kawai ya yi ya na kallonta kafin ya girgiza kai ya mayar kan Alqur’anin da ke riƙe a hannunsa ya na karantawa kawai ba tare da ya ce mata ƙala ba. Tsaki ta ja sannan cike da raini ta ce “dan haka sai ka ja bakinka ka yi shiru, dan banga dalilin da zai sanya ka hanata karɓo kaya ba bayan kai ɗin ka kasa siya mata ko da na dubu biyar ne.” Tana gama faɗin haka ta sauƙe labulen ta yi gaba ta na mai sake nanatawa Yarinyar da “ki yi sauri”. A hankali Yarinyar ƴar shekaru goma sha shidda ta sauƙe ajiyar zuciya, kwata-kwata ba ta jin daɗin yadda Mahaifiyar tasu take yiwa Mahaifin nasu, amma ta san ba ta Isa ta faɗa ko ta nuna ba dan haka ta yi hanzari ta ɗauko hijab ba wani mai girma ba ta zura a kan rigar material ɗin da ke a jikinta sannan ta kalli Mahaifin nata ta ce “Baba na tafi” A hankali ya ɗago kai ya kalleta sannan ya jinjina kai ya ce “sai kin dawo, ki yi addu’a kafin ki fita.” “Tam Baba” ta ce da shi daga haka ta saka kai ta fice. Fitarta ke da wuya! Anne ta miƙe daga wajen wanke-wanken ta hau rafka salati ta na tafe hannu. Turuss!! Haka Yarinyar ta ja ta tsaya kafin ta waiga da mugun sauri ta na mai jin wani tsoro ya na shigarta dan tabbas duk wanda ya ji kuma ya ga salati da yadda Annen ta yi tsaff zai ɗauka wani abun tashin hankali da al’ajabi ta gani, sai dai kuma ita bata ga komai ba a wajen bayan ita kwallin kwal dan ko Baba bai fito ba. A fusace Annen ta ƙaraso ta wuceta ta shige ɗakin, jimm kaɗan sai gata ta fito ɗauke da mayafi ɗan ƙarami baƙi riƙe a hannnunta. Cikin turo baki kaɗan gudun kar Annen ta gani ta rufar mata AMAL ta ce “Anne ana sanyi dan haka ni dai gaskiya baa zan iya saka ƙaramin mayafi ba, kuma ma babu man shafawa (ban shafa ba) hannuwana duk sun yi furu-furu, dan haka hijabin shine rufin asiri na..” Ta ƙarashe maganar cikin kawar da kai gefe ta na guna-guni. Kamar mai shirin rufeta da duka amma ƙasa-ƙasa Annen ta ce “duk ba talauchi da ƙunshe-ƙunshen naki bane ba ya sanya kika rasa man shafawar? Mai yasa kike da taurin kai ne Amal? Mai yasa ba za ki nutsu ki yi abunda ake gaya miki ba.” Sosai ran Amal ya soma ɓaci dan haka ta kawar da kai gefe sannan ta haɗe rai tamau kafin ta ce “babu fa mayafin da zan rufa, na gama magana” Cikin ɓacin rai Anne ta ce “ni kuma na ce da mayafi za ki fita daga gidan nan yau ba hijab ba dan uwar ubanki…” Cikin tsananin ɓacin rai Adda wadda take ta saurarensu tun ɗazun ta miƙe daga durƙuson da ta yi a gaban murfi ta ajjiye wuƙar hannunta sannan ta fito daga cikin kitchen ɗin ta ƙaraso inda su ke, ba da hayaniya ba amma dai kana gani ka san ranta a ɓace ya ke ta ce “Ni kam Anne wae mai yasa hankalinki ba ya taɓa kwanciya ne sai kin taɓo mahaifiyarmu kin zaga? Mai yasa ba ki da kirki kuma ba ki da kara ne? Sannan fisabilillahi wae sai yaushe za ki yarda amana ce ta Yarannan Allah ya baki? Ya tana ta ce miki ba ta son yawo a tsirara amma kina ƙoƙarin tilasta mata bayan na san duk jahilcinki kin san hakan haramun ne….” Ƙuraa mata idanu kawai ta ga Anne ta yi, kafin daga bisani kuma ta ce “chaab!!” Ta na jera mata kallon mamaki sai kuma kamar an tsinkareta ta rushe da wani kalar rikitaccen kuka mai tsananin sauti, kukan da dole ya razana duk wani mai raunanniyar zuciya. Shiruu kawai Adda ta yi tana kallonta da takaici da mamaki ta na jin kamar ta rufeta da duka…ta na wannan lissafin ta ji motsin ƙaure, aikuwa ta na juyawa ta ga Yadikko ta fito ta na lalube da hannun damanta ɗayan hannun nata kuma sandarta ce itanma dai ta ke laluben da ita. Wani kalar kallon takaici Adda ta watsawa Anne kafin ta nufi wajen Yadikko wadda ta ke lalube ta na cewa “Waye ne ya ke kuka haka? Mai ya faru?” Da sauri Adda ta tareta ta na cewa “Ba kowa fa, ki koma ciki kawai “ “Ƙaniyarki! Ya Ina jin kuka amma ki na ce mini babu kowa, Mai ya faru?” Cikin kuka sosai Anne ta ce “Yadikko daga magana tsakanina da Amal a kan ta sauya hijab ta saka mayafi shikenan Adda ta fito ta fara min abunda ta saba wae zan ɗaurata a kan hanyar haramun…sannan haka nan ta fito tana ta cewa wae na zageki…” Da mamaki Adda ta ke kallon Anne, ɓacin rai bai iya hanata cewa “da kika ce uwar ubanta me kike….” Sandar da Yadikkon ta ɗaga da niyyar makawa Addan ce ta sanya ta yi shiru da sauri sannan ta yi saurin kaucewa, cikin fushi sosai Yadikko ta hau cewa “tsinuwar nan ita kike biɗa ko? Ban Isa in hana Abu a hanu ba Ashe? Ni dae ban ji nata zagin ba amma na ji naki kin yi mini… Wae shin sai yaushe za ki daina sakani kuka ne Adda, sai yaushe za ki daina cizon hannun da ya ke baki abinci?…Duk kalar ɗawainiyar matar nan a kanku amma a ce ba kya gani?…. Ko dan darajar Ubanta a cikin gidan nan ae kya sarara mata ko? Mai yasa ba za ki daina kishinta a zauna lafiya da ke bane? Mai yasa kullum ke burinki ki saka ni magana ki nuna min ban isa da ke ba ne?” Ta ƙarashe maganar cikin rushewa da kuka. Sosai jikin Adda ya yi sanyi ƙalau! Dan sam sam ba ta ƙaunar ta ga Anne ta saka hawayen uwarsu ya zuba a ta sanadiyyarta! A hankaki ta fara ƙoƙarin kama Yadikkon ta na son ta mayar da ita ɗakinta ta na mai bata haƙuri amma sai ta hau tuttureta cikin kuka ta na cewa kar ki kuskura ki taɓa ni, matsa Muguwa wadda ta ke son ganin bayana matsa daga jikina, baƙin halinki ne ya janyo Miki za ki ƙare babu Mijin aure! Ni inama ace mutanen da su ka yi garkuwa da ke ba su dawo mana da ke ba, inama sun riƙe ki har abada wallahi da na hutama raina….” Cikin kukan munafurci Anne ta matso ta kama Yadikko sannan ta hankaɗe Adda wadda zuwa yanzun hawaye sun cika mata gajiyayyun idanunta tap! Suna haɗa idanu da ita ta kashe mata ido ɗaya sannan ta yi mata gwalo daga haka ta jaa Yadikko ta na mai cewa “Yadikko ni ce ba Adda ba mu je in mayar da ke ɗakinki…..” Sannan ta kalli Adda ta ce “in kin saita kan girkin ga wanke-wanke nan ki ƙarasa.” Ko da wasa Baba bai yi yunƙurin fitowa daga ɗakin da ya ke ciki har yanzun ba, dan ya san muddin ya fito to a kansa komai zai ƙare, amma fa ya shaƙa! Yayinda tsanar Anne ta sake samun matsugunni a cikin zuciyarsa. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *25* https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T Mariri, Kano State. Babban gida ne sosai a cikin Unguwar Mariri, dake a ƙarƙashin hukumar Kumbotso LG, Kano, Nigeria. Irin gidajen nan ne masu soro mai ɗauke da ɗakuna sannan in ka shanye soron za ka tarar da ƴar ƙofa wadda in ka shigeta za ka yi arba da tamfatsetsen tsakar gida mai ɗakuna barkatai! Da kuma ƙafafuwan bene wajen guda huɗu, sama shima ba a barshi a baya ba wajen tarin ɗakuna kala-kala wani room and parlour wani kuma single room ne kawai… A ƙalla dai ɗakunan gidan sun kai hamsin dan gida ne babba kwarai da gaske… Ahalin gidan kuwa mafiya akasarinsu ƴan mata ne masu jini a jika sai ko waenda suka ɗan sha miya waenda kana kallonsu ka san sun ga jiya sun ga yau a fannin harkar komai…. Banɗaki kwalli ɗaya ne a gidan kitchen shima guda ɗaya ne tak! Waenda kofofunsu su ke kallon juna sun saka ciki da parlourn magajiya (Uwa) a tsakiya, kasancewar ita ɗin a ƙasa ta ke sakamokon ciwon ƙafar da ya sakota gaba aka hanata hawan bene sam-sam… Kamar kullum yau ma haka nan ta ke zaune a wajen ta dasa kujerarta a bakin ƙofar ɗakinta wanda fitsari ne kaɗai ke tada ita daga wannan zaman sai ko ba haya dan hatta abinci a wajen aka kawo mata ta ci a ɗauke, batun sallah kuwa dama sai dare ya yi in ta shiga ɗakinta tukunna ta ke jero iyaka waenda suka sauwwaƙa gobe kuwa sai dai a ɗaura daga inda aka tsaya dan babu batun carryover… Ta na zaune cikin ƴar rumfa ta na kallo da amsa gaisuwar Matan gidan da su ke ta faman kai kawo wanda babu mai ƙasa da shekaru sha biyar a kaff cikinsu… Dan tun kwanaki da Mai Unguwa ya yi galaba a kansu shikenan dole ta sanyata aka tattare Yara daga sha biyar zuwa ƙasa aka yi waje da su….ba dan ranta na so ba sai dan babu yadda za ta yi(an fi ƙarfinta) dan ita rabin customominta sun fi son Yara ƙananu dalili kuwa shine a tasu yanayin fuskar fahimtar sa’a tana cikin saduwa da ƴan Yaran da basu kammala nuna ba…. Takaicin tunowa da ta yi da hakan ne ya sanya ta sake zuƙar sigarinta ta fesar da masifar ƙarfi zuciyarta ta na wani kalar tafarfasa! Tabbas tsakaninta da Mallan, Baba (liman) da Mai Unguwa sai dai ta ce musu Allah ya Isa! Sana’arta ta ke yi, ba ta shiga hurumin kowa a Unguwar amma an kafa mata ƙahon zuƙa! Sai da ta kai ta kawo ta kafa sharaɗin kwata-kwata ba ta yarda a kawo mata maza fa cikin gida ba amma dukda hakan bai ishesuba an saka mata ido an uzzura mata! Ita kuwa ba zata ƙaura ba dan wannan itace Unguwa ta uku da aka koreta ta dawo daga karɓar karagar mulkar kungiyar da ta yi daga hannun Ladiyo kawo yanzu… Ta lura in ta biyewa mutane ƴar kwallo za su yi ta yi da ita…. Zuwa yanzu gaba ɗaya komai sai faman suɓurɓuce mata ya ke yi, kwata-kwata ta gagara lalumo bakin linzamin ballanta ta ja su su tafi… Dama ana ta cewa ba lalle ta iya ba duba da ba gadar abun ta yi ba mulkinma da kuɗinta ta siya ta kwace ta ƙarfin tsiya, to gashi kuwa abun ya na neman gagarar ta! Tabbas da gaskiyar Innayo da ta ce mata ‘harkar dole sai an haɗa da tsaurin ido da ƙin bin duk wata doka da tsantsar rashin kunya dan su mutanen Unguwa babu ruwansu da son wani zaman lafiya a tsakani muddin mace ta amsa sunan karuwa! To fa ƙahon zuƙa su ke kafa mata har sai sun ga bayanta… Dan haka gara ta fito musu da ƙarfinta kar ta yi wani shayi ko ɓoye-ɓoye hakan ne kawai zai sanya a ji shakkarta a sakar mata mara….’ “Ina kwana Uwa” Muryar wata mata wadda ta zo wucewa ta katsewa Yagwalgwal ɗiin tunanin da ta ke yi! Dan a ƙa’idar gidan muddin ka fito to dole sai ka gaida ita ko da kuwa kun gaisa tun farko. Ta na shirin amsa gaisuwar wata mata wadda ta fito yanzun ta ce “lafiya ƙalau yar albarka, ya jikin naki? “ Kasa amsawa Yarinyar ta yi ta hau kame-kame sannan ta rissinar da kanta ƙasa jikinta ya na wani kalar karkarwa…. “Wuce ki bar nan Aimana.” Yagwalgwal wadda ta miƙe tsaye ta na ɗan riƙe ƙafarta mai ciwo ta ce da Yarinyar, a take kuwa kamar ta na jira ta yi wuff ta bar wajen… Juyawa ta yi ta mayar da dubanta zuwa ga matar wadda ta fito wasu Mata guda biyu na biye da ita su na take mata baya! Baƙa ce sosai kuma doguwa sannan ƙaƙƙarfa…irin murɗaɗɗun Matan nan… A hankali Matan da su ke biye a bayan nata suka ɗan rissinar da kawunansu ƙasa sannan suka ja baya kaɗan saɓanin Ladiyo wadda ta kafe Yagwalgwal da idanu kyarrr ta na kallonta… Sai da Yagwalgwal ɗin ta yi wani murmushin takaici sannan ta ce “Uwa ɗaya ce tak! A gidan nan. Ki kwantar da kanki ki zauna lafiya ko kuma ki bar tawagar nan a yi tafiyar babu ke dan ba a sarki biyu a gari ɗaya…” Murmushi itama Ladiyon ta yi sannan ta ce “eh kam ba a yi, amma kin san ana juyin mulkiiii…” Ta ƙarashe maganar cikin isa tana mai jaan ƙarshen maganar sannan ta matso kusa da ita daff!! Kafin ta ɗaura da cewa “sannan, yeah! Na san ana iya yin gari biyu amma tabbas za a ci ragon Sarki da yaƙi a kwashe jama’arsaaaa, kamar dai yadda ki ka yi a baya lokacin da ki ke da abunda na tabbata ba ki da su a yanzuuuuu(kuɗi)” Ta sake jaan maganar ƙarshe cikin isa ta na huci ta na ji kamar ta murƙushe Yagwalgwal saboda tsabar tsanarta da ta addabi zuciyarta amma da ta tuna cewar a yanzu haka ta kusan haɗe kan fin rabin jama’ar gidan a ɓoye da wayo, sai kawai ta kyaleta ta na mata wani kalar murmushin da Yagwalgwal ɗin ta gagara fahimtar na menene… “Allah ya kaimu ranar juyin mulki…” Ladiyo ta aiyyana hakan a ranta daga haka ta juya ta fita Matan nan guda biyu suka mara mata baya. ••••••••• Su Yadikko su na gama shigewa ciki Adda ta fashe da kuka, sai kuma ta juya da sauri ta bar wajen dan ba ta so Amal wadda ke a tsaye idanunta sun yi rau-rau itama ta saka mata kukan…. A wajen Anne hakan nuna isa ne da gadara da win! Amma ita a wajenta tabbas tarwatsa mata rayuwa ne, ko ba komai bakin uwa masifa ne, wanda ita kuma Anne ba ta da wani buri sama da ta yi ta cusguna mata ta hanyar yin amfani da mugayen alkaba’in Yadikko akanta (Addar). Ko kammala shiga ɗakin ba ta yi ba Amal ta biyo ta … dan kusan a tare su ka shiga cikin ɗakin, wadda already fuskanta ya jiƙe sharkaff da hawaye. Kasa kallonta Adda ta yi amma kuma ta kasa tsaida kukan nata wanda hakan ya sanya kawai ta sake shi bagatatan. Da sauri Amal ta ƙarasa gareta ta rungumeta cikin kuka sosai ta ke cewa “Adda ki yi haƙuri dan Allah, Allah zai saka miki” Tabbas ta san bai kamata ba amma wani kalar takaicin Anne ta ke ji ya na taso mata marar misaltuwa. Ta tsani ta ga Addan nata a cikin damuwa sam-sam ba ta so. …. Sai da ta tabbata ta ajjiye Yadikkon a kan gadonta tukunna ta juya za ta fita, da sauri Yadikkon ta riƙo hannunta jikin tshohuwar har karkarwa ya ke yi ta ce “ya batun wanchan abun da ki ka ce za ki bani ? Tun ɗazu da safe fa ke na ke jira, ki sallame ni yanzu kafin ki fice.” Taɓe Baki Anne ta yi sannan ta ce “in sallameki a sake gaya mini wani sunan na daban ko? Dama ni su ke zargi dan haka na daina biye miki haka kurum kura da shan duka gardi da kwace kuɗi. Shekaran jiya sarai na gaya miki binciken da su Amir su ka yiwa kayana amma ban ga kin yi komai ba.” Da sauri Yadikko wadda gaba ɗaya yanayinta ya ke baiyyana asalin rashin nutsuwa ta ce "ki barni da su, duk zan yi miki maganinsu. Ba ki ganin yadda na ke takawa Adda burki ne a kanki? Suma su Amir ɗin duk za su zo su sameni ne. Yanzu ki taimaka ki sallameni." Ta ƙarashe maganar ta na mai jan ajiyar zuciya, ji take kamar ta yi ta zabga ihu. Shiruu kawai Anne ta yi ta na kallonta kafin chaan ta ce “shikenan bara a kawo miki.” Daga haka ta sa kai ta fice, zuciyarta fes. ……. Sai da su ka yi mai isarsu tukunna Amal ta iya aro jarumta ta shiga gogewa Adda hawaye ta na mai cewa “Adda dan Allah ki yi haƙuri” Cikin sauƙe ajiyar zuciya Addan ta shiga girgiza mata kai kafin ta kamo cute face ɗinta itama ta goge mata nata hawayen sannan ta ce “ki daina kuka ki tashi ki je aikan da aka yi miki, nima gashi kinga na daina” Ta rufe maganar tata ta na mai ƙaƙalo murmushi ta yafawa fuskarta a ranta tana dannar kanta da ƙoƙarin son aro jarumta dan ba ta so ta dinga zubda hawaye a gaban Yarinyar sam-sam sannan gashi itama ta sakata kuka. Zama Amal ta gyara daga durƙuson da su ka yi a wajen sannan ta sa hannu tasake goge fuskarta tukunna ta ce ”ba zan je, ba na son zuwa gidan Matar kuma Anne ta sani amma ta ke tilasta min sannan ta ce in saka mayafi, gashi ba na so in yi fashi a makaranta. Ni dai makaranta kawai zan tafi.” Sai kuma ta rushe da kuka cikin kukan ta ke cewa “Alllah Adda ba na son halin Anne, ba na son…..” Da sauri Adda ta ɗaura hannunta a kan Bakin Amal sannan ta ce “shhhh.. Mahaifiyarki ce, kar ki zafafa, ki yi haƙuri. Tashi ki je aiken, ba abunda zai sameki, ki yi addu’a kamar yadda ki ka saba har ki je ki dawo.” Kwaɓe fuska ta yi da shirin sakin wani kukan amma ganin yadda Adda ta haɗe rai tamau! Ya sanya ta haɗiye kukan. Cikin rashin jin daɗi Adda ta ce “so ki ke ki sake janyo min wani abun da za a yi ya sanyani kuka ko?” Da sauri ta shiga girgiza kanta ta na hawaye at the same time tana goge hawayen da ta gagara tsaida su. Sai da Adda ta ce “to dan Allah ki tashi ki tafi aiken, ki yi addu’a kin ji.” Tukunna ta jinjina kai kawai ta na matse Baki dan in ta buɗe Bakin kuka ne zai kufce. Ba ta ƙaunar Adda ta yi mata magiya shiyasa yanzun ma kawai ta miƙe a hankali ta fice. Amal na fita daga cikin ɗakin Adda ta saki wani sabon kuka mai tsananin cin rai da azabtarwa. Duk yadda ta so ta zame hannunta daga lamarin kamar yadda ta daɗe da yiwa kanta alƙawari, sai ta ji ta gagara, dan haka ta janyo wayarta…. Dama ƙuɗin motarta ya na hannunta dan haka ta yi sauri ta yi addu’a ta fice daga cikin gidan ba tare da ta rabu da Hijabin da Annen ba ta so ba, mayafin da ta ke so ta rufa wanda ta ganshi yashe akan dandamalin ƙofar ɗakin nasu kuwa ko kallonsa ba ta sake yi ba ta yi ficewarta!… Ai Allah ma ba zai yi farin ciki da ita ba in ta saɓa mishi ta farantawa Anne dan ta na matsayin Mahaifiyarta. Sai da ta fita daga cikin layin nasu ta soma hango titi tukunna hankalinta ya kwanta dan ta san tsaf in Anne ta fahimci ta fita a hakan za ta iya biyota kuma ba ƙaramin aikinta bane ta kwaɓe mata hijab ɗin a bainar nasi ta musanya mata shi da gyale. A gani da tunaninta sauri ta yi, sai dai kasancewarta Mace mai sanyin jiki ya sanya in da ace tseren tafiya su ka yi da Yaro tsab zai yi mata nisa ma. Jin ta na haki ya sanya ta ɗan tsaya chak ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na mayar da numfashi…. Ta kai kusan 2 minutes a haka ta ji ƙamshin turaren da ta sanshi dashi tun Yarinta ya gauraye wajen ta na shirin ɗagowa ta ji an ce “ke!” Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace sakamokon jin muryar dodon nata da ta yi, ai kuwa ta na ɗagowar su ka yi ido biyu da Ya Abba, fuskar nan a murtuke kamar kullum. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota *26* Ya kafeta da shanyayyun idanunsa bai ce komai ba kawai ya na kallonta wanda hakan ya sake kiɗimata cikin rawar murya ta ce “ddd-da-maAnn…” “Ina Islamiyyar?” Dakakkiyar muryarsa ta katse tata siririyar Muryar. Zuwa yanzu gaba ɗaya ta kiɗime, ba za ta iya cewa ga lokacin da Ya Abba ya daketa ba dan babu amma wallahi in yana waje ba ta samun nutsuwa har sai ya bar wajen… “Na zama sa’an wasanki kenan” Ya faɗa hakan cikin muryar da ke baiyyana ransa ya soma ɓaci dan ya tsani kyaliya. Ɗaya daga cikin ɗabi’un Amal shine saurin kuka, dan haka a take idanunta su ka cika tap da hawaye kafin kuma ta ɗago a hankali ta na kallonsa sai kuma ta yi saurin kawar da kanta gefe ta fara magana “ba zan je ba yau, Anne ce ta aikeni gidan Hajiya Altine in karɓo kaya.” Kusan mintuna biyu da gama maganar jin bai ce mata komai ba ya sanya ta waigo ae kuwa karaff su ka haɗa idanu…. Da ace ya san gidan tabbas Amal ba za ta je ba zai je ne kawai ya karɓo kayan da kansa ya dawo. Dan in har ya yi guessing dai dai to Hajiya Altine itace ya ji Baba da Amir su na zancen cewa Yaronta ya na son Amal ɗin, sannan matar gaba ɗayanta sai a hankali, yo to dama duk ƙawayen Anne da ta samu ta ke hulɗa da su a wajen Unguwar ae duk sai addu’a kawai kusan halaiyyarsu duk ɗaya….Matar bata taɓa haihuwa ba amma ta raini Yara maza guda biyar waenda su ke sheƙe ayarsu a gabanta da ɗaurin gindinta… A karo na uku Amal ta ɗan sake satar kallonsa ganin ya kafeta ne kawai da shanyayyun idanuwansa ya sanya ta sake sunkuyar da kanta ƙasa ƙirjinta ya na mai ci gaba da bugawa…. “Jira a nan” Kawai ya ce mata, daga haka ya wuce ya bar wajen ransa a ɓace, sai dai ba ka isa ka ga hakan kwance a kan fuskarsa ba. Ya na wucewa Amal ta sauƙe wata bahaguwar ajiyar zuciya ta na mai sakin numfashinta yadda ta ke so saɓanin ɗazu da ta ke yin komai a ɗarare. Dukda ta san bai san gidan ba sai ta tsinci kanta da addu’ar ‘Allah ya sa kar ya shiga sabgar Anne ta inda zai iya cewa ta zauna shi ya je’ Dan ta san Ya Abba da Anne kamar wuta da auduga su ke a kan hakan tsaf sai a iya shafe sati ɗaya ana case……. Ta na wannan lissafin ta na ta faman waige-waige gaba ɗaya tsoro da fargabar da ya dasa har yanzu ba su barta ba ga kuma banɗokin mai ya ke da shirin yi sai kuma tsoron kar ta je Anne ta ga mayafi ta biyota a baya har ta kai ga cin mata ya Abba bai ƙarasoba….. Ƙarar machine ta ji dan haka ta waiga ai kuwa shi ɗin ne kamar yadda ta zata, kafin ƙiftawar ido ya ƙaraso inda ta ke tsaye ya ce “hau” Kawai ba tare da ya kalleta ba. “Tsaka mai wuya kenan” Ta aiyyana hakan a ranta ta na mai jin kamar ta zunduma Uban ihu. Agogon hannunsa kawai ya ɗaga ya kalla ba tare da ya ce mata uffam ba! Ta fahimci Yaren nasa dan haka ta lallaɓa ta haye a hankali kamar wadda kwai ya fashe mata a ciki sannan ta matsa baya sosai. Cikin nutsuwarsa ya kunna machine ɗin da sannu su ka kama hanya, su na tafe ta na yi masa kwatance a hakan har su ka ƙarasa… Su na isa ta sauƙa ta tsaya shi kuma ya ɗan gyarawa machine ɗin zama sannan ya ce”jira a nan” Bai bi ta kanta ba ya wuce zuwa gidan da ta yi masa nuni da shi ya barta a nan wajen tsuru-tsuru kamar an ritsa ɓera a buta gaba ɗaya tsoro yagame ta dan ta san dole Matar za ta sanarwa Anne ba Amal ɗin ce ta karɓa ba kuma ta na yi mata kwatance za ta gane Ya Abba ne. Tsoro ya sanya zuciyarta over racing dan haka ta ɗan nemi guri ta zauna ta na jin kamar ta nutse kawai dan ta san dole akwai ƙalubale a gabanta yau… Ta na zaune ta na ta saƙe-saƙen yadda za ta kaya yau ɗin ta ganshi ya dawo ga dai kayan nan ya karɓo bai bar musu ba amma kuma fuskarsa a murtuke fiye da ko yaushe dan haka a take ta sake rikicewa, kafin ta miƙe tsaye da kyar ƙafafunta su na karkarwa. Ya na ƙarasawa gareta ya tsaya a gabanta gab dan har sai da ta ɗan ja baya tana mai ɗagowa ta ɗan saci kallonsa ba ta kai ga mayar da kanta ƙasa ba ya ce “wato zance za ki zo ki yi da! Ko?” A rikice ta ɗago ta na kallonshi kafin ta hau girgiza masa kanta ta na gab da sakin hawaye ya ce “in ki ka bari su ka zubo sai na baki mamaki a wajen nan, zancen ne za ki zo yi mana tunda gashi matar ta na mini maganar ina ki ke wani ‘Mustapha’ ya na ta jiranki!” Ya ƙarashe maganar tone nashi ya na baiyyana tsantsar ɓacin ran da ya ke a ciki. Tsoro ya soma bata dan har kalar kwayar idanunsa sun soma chanja kala. Dan haka ta shiga ja da baya sosai cikin tsantsar fargabar kar ya yi mata shegen duka a wajen. Kallonta ya ke yi sosai yana karantar yanayinta, kafin kuma kawai ya juya ya haye kan machine ɗin ya kunna batare da ya ce mata komai ba. Ta san Mustaphan sarai dan tun ranar da ta rako Anne yanuna intrest ta shaidashi kuma ita har ga Allah tsoro ma ya ke bata bakinsa baƙiƙirin, a gabansu ya dinga shan taba ranar, shiyasa ta zaɓi ta bi Ya Abba ko da kuwa zai niƙata ne a hanyarsu ta komawa gida akan dai ta tsaya Mustapha ya ganta ya ce su yi zance. Ta na gama zama ya juya akalar machine ɗin ya bar layin kamar mai fushi da titin. Ita dai Amal ƙarshe runtse idanunta ta yi da masifar ƙarfi har aka ƙarasa gida ba ta yarda ta buɗe su ba dan ta gama sadaƙarwa… ……… Su na barin Unguwar Matar ta kira Anne, rai a ɗan ɓace ta sanar mata ‘Amal ta zo amma ita da saurayinta, dan bai ma barta ta shigo gidan ba itama ta window ta hangota, ya hanata shiga shi ya karɓi saƙon…. tun safe kuma Mustapha ita ya ke jira ko kasuwa bai fita ba, kuma ya fahimci da saurayin nata ta zo sannan ba ta ko shigo cikin gidan ba, ga shi nan sai faɗa ya ke yi wai an ci masa fuska an wulaƙanta shi.” Ana cewa Amal ta zo ta saurayinta dama Anne ta fahimci Abba ne, dan duk duniya shi kaɗai zai iya yi mata wanna tsaurin idon. Kuma ta san Amal ba dai ta ko iya jerawa da wani namijin dan ita tsoron mazan ma ta ke ji, dan haka ta ci buri kuma ta ɗau aniyar tadama Abba hankali da shi da Adda wadda ta san ita ce ta bashi full goyon baya. Dama tana gama waya ta je ta shiga zage Adda tass!! Sai da ta ji tsayuwar machine tukunna ta fita ƙofar gida daga ita sai doguwar riga da hula. ………. Ta na ji ya tsaya ta fara kiciniyar sauƙa jin hakan ya sa ya juyo zai yi mata magana ita kuma tsoron rashin sanin mai zai yi matan ya sanya ta sauƙa da sauri, garin saurin kuwa ta goga sangalalin ƙafarta a jikin salansar machine ɗin dan haka ta ƙona ta. Ba ta san lokacin da ta saki wata ƙara ba ta fara ja da baya ba, ta na shirin afkawa kan itacen da maƙofcinsu ya tara zai yi faskarensu Ya Abba ya yi saurin ruƙota ta hanyar kamo hijab ɗinta sannan ya ce “ki nutsu mana! Me ye haka, mai ya faru?” Sai kuma ya kalli ƙafar tata sannan ya ɗan durƙusa zai gani su ka ji Anne ta saki salati sannan cikin ɓacin rai ta ce “Fyaɗe za ka yi mata a ƙofar gida saboda tsabar rashin mutunci?.” Sai kuma ta ƙarasa garesu ta kalli Amal ta ce mata “wuce cikin gida dan ******ubanki.” Hawayen da ta ke ta ƙoƙarin riƙewa ne su ka shiga ziraro mata, kafin kuma ta juya da sauri ta wuce ciki jin Anne ta sake danƙara mata wani ashar ɗin a jere da maganar da ta yi mata ta farko ba tazara. Amal ta na gama wucewa Ya Abba shima bai tsaya bi ta kan Anne ba ya fara yunƙurin wucewa amma sai ta saka hannu ta wani fizgoshi har sai da ta kai ga yaga masa rigar shaddar da ke a jikinsa dan Anne ba dai ƙarfi ba! Da sauri mai kantin da ke a kusa da gidan ya fito ya na salati yayinda wasu a cikin waenda su ka gani su ka wurwuce kawai abinsu dan sun gaji da dramar su Anne. Ya na ƙarasowa ya ce “haba mana dan Allah! Cika shi ko meye ne kwa ƙarasa a cikin gida!” Dai-dai nan Baba da Ya Amir su ka ƙaraso wajen. Dan har an zagaya dama an sanar masa Anne da Adda su na faɗa tun ɗazu, luckly kuma su na tare da Ya Amir a lokacin. Wani ƙululun takaici ne ya mamaye Ya Amir ganin yadda ta ke tsaye a waje ko mayafi babu, dan haka kamar mai shirin fashewa da kuka ya ce “Anne babu ko Mayafi fa a jikinki. Babu kyau ki koma ciki dan Allah.” “Ae duk laifina ban kaishi ba! Kun san kuwa mai ya yi? A ƙofar gida saboda tsabar mugunta ya ke ƙoƙarin kwaɓe mata kaya!” Sai kuma ta juya ga Ya Abba wanda ya runtse idanunsa kawai ya na salati a cikin ransa sannan ta ce “mun yi maka sutura amma shine tsabar butulci mu za ka wulaƙantamu ko? In da kara ae Amal dai na ga ƙanwarka ce bai kamata ka ji ko da ƙanƙanuwar sha’awarta ba ballanta har ka so baje bajintar kwartancinka a kanta” Zuwa wannan lokacin duk an fara taruwa a wajen dan wasu sun gagara kauda kai. Da ƙarfi Baba ya runtse idanunsa, sai kuma kawai ya juya ya bar wajen, dama ya yi tunanin ita da Adda ne shiyasa ya zo ya rarrashi ƙanwar tasa kuma ya yi tunanin a cikin gidane, amma tunda hau ɗin nata a waje ne kuma da namiji ba zai biyeta ta bashi kunya ba dan ya san ba iya comtrolling Anne zai yi ba, Abba kuma ya san muddin ya na tsaye a wajen ko marinsa za ta yi ba zai ce mata komai ba dan haka ya ga gara ya basu guri...... Ya Amir ne ya sake matsowa kusa da ita da ƙoƙarin ganin ya kareta dan an cika a wajen wasu sai ƙus ƙus su ke yi su na mata dariya a ganinsu mace kamar Anne dai bai kamata ace ta damu da wani abu wai shi mutunci ba tunda kowa ya shaida ba ta da shi…. Ƙasa-ƙasa ya ce “Anne har da Amal fa ki ke tozartawa..” Wata ƴar taya ɓera ɓari ce ta matso itama sannan ta ce “kai kuwa Abba mai ya kaika, kar ka ciji hannun da ya baka abinci mana..” Da sauri Ya Amir ya juya gareta bai san lokacin daya ce mata “ba haka bane ba fa!” Tunkuɗeshi Anne ta yi sannan ta saka hannayenta duk biyun ta cukumo wuyar rigar Abba da kyau tukunna ta ce “ka juya min kwakwalwar Yaro kalli yadda ya ke ƙaryatani ba tare da ya bi baasi ba sannan yanzu ka biyo Yarinyata za ka….” Ɗiff!!! Haka ta ɗauke wuta sakamokon ware mata shanyayyun idanunsa da ya yi waenda su ka soma ƙanƙancewa sannan su ka yi wani kalar jaaaa na ban mamaki. Ita dai ta sani kuma ta shaida ba ta da tsoro amma ba ta san dalilin da ya sanya ta ke shakkar Abba ba! Muddin su ka haɗa ido da shi to sai gabanta ya yanke ya faɗi ta ji kamar zuciyarta ta tsage ne kuma duk wata kalar masifa da tsiwarta ƙaryanta ta ce za ta yi masa. Yanzun ma kasa magana ta yi sai kuma ta sauƙe hannu ɗaya ta kama ƙugunta da shi sannan ta kawar da kanta gefe ta na girgiza. Muryarsa a matuƙar shaƙe ya ce mata “cika ni!” Da mugun kyar ya na mai dannar kanshi da addu’ar Ubangiji ya bashi damar riƙe kan nasa saboda ya san in ya ce zai finceke to tabbas sai ya iya karyata a wajen ma shi kuma kunyar Amir ya ke ji a halindaake ciki Yaron ya na bashi girma tamkar ciki ɗaya su ka fito. Tabbas in ba ƙarya ƙwaƙwalwarta ta ke yi mata ba kamar alamun matsanancin tsoro ne ta ke ji ya na rufeta dan gashi hatta hannun nata da ta riƙesa da shi karkarwa ya soma yi… Haka kurum ba ta san dalili ba ta cika shi a lokacin da ya sake ce mata “cika ni” A karo na biyu. Wuff kamar mai shirin tashi sama ya wuce ya shige ciki Direct ya afka ɗakinsa ya banko ƙofar ya saka sakata dan ya san Amir zai biyo sa tabbas. Shiruuu wajen ya kasance bayan wucewar Ya Abba kafin aka soma watsewa a hankali a hankali. Dukda ta so ta yi masa cin mutuncin da ya fi wannan ne sannan ta so ta kawo silar da za a ce ya bar gidan ne amma ta ɗan samu relief! Ita ba Yarinya ba ce ba dan haka sarai ta fahimci tsare gida da takurawar da Abba ya ke yiwa Amal akwai wata a ƙasa tunda da gani Yaron maye ne ya nace sai ya auri jininta! Ta samu ta rabashi da Afra shine saboda rashin zuciya ya ke wani shishshigewa Amal to ko ma ba so bane ba ita kam ba ta so! Sam-sam! Ba ta ƙaunar alaƙarsu ko wacce kala ce shiyasa ta yi wannan borin saboda yanzu ta san shi kansa zai ja jiki ya kuma ji kunyar sake shiga sabgar Amal ɗin, sai kuma baƙin cikin hana Amal kula Mustapha da ya yi (ya yi mata kutse) Hakan ma ya taka rawa wajen ingizata ta tozartashi, dan ya jawo mata asara yau ɗinnan ta ci burin abunda ta yi tunanin Amal za ta dawo da shi saboda Mustaphan ba dai kyauta ba gashi yanzu Abba ya janyo har ya yi fushi amma ba komai za ta shawo kansa ne…. Ta na wannan lissafin ta wuce ciki bayan ta ɗauki ledar kuncen kayan da su ka dawo da shi, ba kunya ba tsoron Allah. Direct ciki da parlourn Adda ta nufa dan ta san Amal ta na ciki. Ta na shiga kuwa ta gansu a parlour Amal kwance a kan cinyar Adda, Addan ta na yi mata firfita ta na share mata hawaye. A fusace Adda ta ɗago ta kalli Anne sannan ta ce mata “ki fita ki kyale Yarinyar nan! Ki yi mini komai zan ɗauka amma wllh in kin taɓa Amal za ki ga ɓacin raina!!” Kafin Adda ta rufe Bakinta Anne tuni ta ƙaraso inda su ke ta kamo Amal ɗin ta miƙar da ita tsaye kamar wata Yarinya ƙarama haka ta kamo kunnuwanta duk biyun ta murɗe su da masifar ƙarfi! Matsowa Adda ta yi za ta taɓa su amma sai Anne ta daka mata wata uwar tsawa ta na cewa” wallahi ki ka taɓani sai mun kwashi ƴan kallo ni da ke! Na san kin san zan aikata! Ki daina yi mini shishshigi akan ƴaƴana na gaya miki ko? Ke ce ki ka haifa mini su ne wai?!” Ta ƙarashe maganar ta na daka mata tsawa ta na huci sannan ta ɗaura “idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana!” Adda ba ta san lokacin ma da hawaye su ka zubo mata ba ta na jin wani radaɗi da azaba na yadda Annen ta murɗe kunnuwan Amal numfashin Yarinyar ya ke sama da ƙasa kamar zai ɗauke tsabar azaba! Ta san in ta ci gaba da tsayuwa a wajen wahala kawai za ta bawa Amal ɗin shiyasa ta wuce cikin ɗakinta kawai ranta ya na suya ta rufo ƙofar….a samu ta gama da wuri ta fita ta kyale Yarinyar. Kwafa Anne ta yi ta na mai hararar ƙofar kafin ta dawo da dubanta ga Amal wadda ta haɗa Uban gumi azaba ta na ratsata sannan ta fara magana cikin sake murɗe kunnen kamar so ta ke ta cire mata su ne”kalle ni nan!!” Sai da Amal ɗin ta kalleta sosai tukunna ta ɗaura da cewa “tunda na ga kunnen ƙashi ne da ke bara in yi miki wanda za ki gane, sannan ban ga alamun kin girma ba dan haka bara a yi miki yadda ake yiwa Yara” Ta sake murɗe kunnen da har sai da Amal ta saki salati da ƙarfi sosai sannan Anne ta ce “daga yau har gaban abada in na sake ji ko ganinki tare da Abba na lahira sai ya fi ki jin daɗi! Sannan in na sake cewa ki saka mayafi ki ka yi mini gardama tabbas sai na illataki! Kuma Mustaphan da ki ka yiwa taurin kai zai zo ko kuma ma ke ki je ki bashi haƙuri sannan ki saurareshi in ba haka ba sai na tsine miki!!!” Ta ƙarashe maganar cikin wurgar da ita ta na mai cewa “shegiyar Yarinya mai shegen taurin kai! Ana nuna mata Annabi ta na runtse ido, muguwa kawai! Da tuni yanzu kuɗaɗe ne riƙe a hannuna dumuss!! Ba raɗaɗin murɗe miki kunne da na yi ba……” Daga haka ta juya ta fita rai a ɓace dan ganin Amal ɗin da ta yi ya sake tuna mata asarar da ta janyo mata na kuɗaɗen da ta ke da tabbacin Mustaphan zai bayar in da ace ta tsaya ta saurareshi, sannan dan iskanci wai ta saka wani hijabi……….. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota011 *27* Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Daga haka Anne ta juya ta fita rai a ɓace dan ganin Amal ɗin da ta yi ya sake tuna mata asarar da ta janyo mata na kuɗaɗen da ta ke da tabbacin Mustaphan zai bayar in da ace ta tsaya ta saurareshi, sannan dan iskanci wai ta saka wani hijabi, ƙirar jikin Yarinyar kaɗai ta isa ta saka a kashe mata kuɗi daga kallonta ma kawai amma dan baƙin ciki sai ta yi ta faman ƙunshe-ƙunshe ta na barinsu a talauchi da wahala, kamar wata wadda za ta jiƙa jikin nata ne ta shanye. ……….. Kasa fitowa Adda ta yi bayan Fitar Anne dan wani kalar kunya da tausayin Amal ta ke ji har cikin ɓargonta, bata jin za ta iya haɗa ido da ita bayan ta gagara bata ko wacce iriyar kariya ko da ƴar ƙanƙanuwa ce, sai da ta ji Yarinyar ta na jan numfashi da kyar tukunna ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito ta ƙarasa gareta, ta na ɗagota Amal ɗin ta fashe da kuka cikin kukan ta ke cewa “Anne za ta kaimu wuta! Da ni da ke da su Baba da kowa duk za ta halakamu, dan Allah Adda ki zo mu gudu ba na son zaman gidan nan, ji na ke yi kamar zan mutu in ina ciki, ba na son ganin Anne… Har yanzu fa Ya Afra itama ba ta dawo ba…” Shiruuu kawai Adda ta yi ta gagara cewa komai zuciyarta ta na wani irin hantsilawa…ba ma ta san ta ina za ta fara ba sannan ga Abba shima wanda Amal ɗin ta gaya mata abinda Annen ta yi masa wanda a yanzun ta ke da tabbacin ya na chan ya na fama da ƙunci da zafin zuciya. •••••••• Tsaye ta ke a gaban gas cooker, ta na juya liver sauce ɗin da ta kammala haɗawa yanzunnan. Ta na girkin ta na murmushi wanda hakan zai tabbatar maka da tsantsar farin cikin da ya ke danƙare a cikin zuciyarta, “tabbas na fi kowacce Mace yin sa’ar Mijin Aure” Ta aiyyana hakan a cikin ranta murmushinta ya na daɗa faɗaɗa…. Ba ta ji shigowarsa ba sai dai ta ji an rungumeta ta baya sannan ana sake shigewa cikin jikinta sosai kamar mai shirin haɗesu waje ɗaya su zamto abu guda! Har sai da ta ɗan ce “auchh” Tukunna ya ɗan sassauta ruƙon da ya yi mata, dai-dai saitin kunnenta ya ce “kwatankwacin yadda zallar zazzafar ƙaunarki ta ke nuƙurƙusar zuciyata kenan” Ya yi maganar cikin kamo earlobe ɗinta ya haɗe da mannen earing ɗin da ke a jiki duk ya sakasu cikin bakinsa ya ɗan tsotsa kaɗan sannan ya fitar kafin ya sakar mata light kiss a kunne da kuma kumatunta sannan a hankali ya ce “i love you Matata” •••••••• Tunda Anne ta koma ɗakinsu ta ke ta faman lallaɓa Hajiya Altine ta waya, dan yadda Matar ta ga ran shalelen Yaron nata ya na sake ɓaci ya sanya itama ta sake hawa fiye da farko. Da mugun kyar aka samu su ka daidaita ta inda Mustaphan zai yi tafiya zuwa Europe na sati biyu amma da zarar ya dawo Amal ɗin za ta je ta sameshi su zanta su fahimci juna… Dai-dai ta na ajjiye wayar Afra ta na shigowa cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Da sauri Anne ta sake gyara zaman wayar sannan ta miƙe ta na kallonta… Rigar jikinta irin doguwar rigar nan ce (Abaya) Mai igiya a tsakiya wadda kafin ta fita sai da Annen ta sakata ta ɗaure tsakiyar sosai tukunna sai dai kuma yanzun ta nemi igiyar ta rasa wanda hakan ya ke bata tabbacin Afran warewa ta yi ta ɓoye igiyar bayan ta fita daga gidan kenan!! If not because ta na ɗan shakkar Afra sannan ta na son ta bata abunda ta zo mata da shi tabbas da sai ta tsinkawa Yarinyar Mari wallahi…. “Ina wuni Anne” Siririyar Muryar Yarinyar ta katse mata lissafin da ta ke yi.. Sai da ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta rarrashi kanta tukunna da kyar ta iya ce mata “lafiya ƙalau Alhamdulillah” Sai kuma ta kasa haƙura dan haka ta ce “ina igiyar rigar? Na ganki kamar wata Matar Mallan…kin saki riga ba fasali” Ba tare da ɓoye-ɓoye ba kanta tsaye Afra ta ce “Ina fita waje na cire na sakata a aljihu, ba na so in yi miki musu ne mu yi ta hayaniya da ke shiyasa na biye miki ɗazun na bar gidan a haka, da kuma na ga babu idonki sai na bi dokar Ubangijina.” Da mugun kyar Anne ta iya haɗiye wani malolon baƙin ciki da ya taso mata ya tokare mata maƙoshi sannan ta yi da gaske wajen danne fushinta a hankali ta ce “to ae shikenan” Cikin nutsuwa Afra ta yaye Abayar jikinta ta saƙale a jikinn ƙusa sannan ta cire mayafin shima ta rataye ya rage daga ita sai riga da dogon wando tukunna ta kalli Annen ta ce “rigima kika yi a ƙofar gida ne yau ma? Na zo wucewa na ji Mallan iliya yana bada labarin yadda ki ka cukumi wuyar rigar wani har kin yaga..” Sam ba wannan ne a gabn Anne ba, so ta ke yi ta ji dumuss kawai a hannunta amma sai ta daure ta ƙarawa kanta patience sannan ta ce “ni da wanchan shegen Yaron ne! Abba, take takensa Amal yake so kuma dan ****Ubansa bai isa ba wallahi. Ita kuma gaɓuwa ta barshi ya na shige mata shege talakan banza, zai jaza mata ba za a dinga kulata ba in ana ganinsu tare! Shege mugu…” Yadda ta ga Afran ta kafeta ta idanuwa ne ya sanya ta gagara ci gaba da cewa komai… A hankaki Afra ta na mai ware abun hannunta ba tare da ta kalli Annen ba ta ce mata “amma kin san da Ubansa dai ko? Ki daina shegantashi babu kyau sannan in maganar kuɗi ake yi kuma na san kin san waye uban nasa…” Cikin tarar numfashinta Anne ta ce “a banza ae wai ƙunshi a ɗuwawa! Mu gani a ƙasa in ya so sai mu shaida…Uban da ya tsane shi ya tsani sunansa ne zai yi tinƙaho da shi?” Ta ƙarashe maganar tata da tambaya da masifar ƙarfi, wanda ta yi hakn ne da gangan. Wani zazzafan numfashi Afra ta sauƙe sannan ta ɗauke kanta daga dubanta ta mayar kan aljihun wandonta ta fara lalube kafin ta zaro kuɗaɗen da gaba ɗayansu ba za su wuce dubu ashirin ba… Anne ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, a ranta ta ce “Alhamdulillah” Afra na ɗagowa Anne ta yi saurin kawar da dubanta irin bata gani ba ɗinnan, ƙasa-ƙasa ta na mai ci gaba da cewa “ae sai na nunawa Abba iyakarsa wallahi, hmm zai gane bashi da wayo shan ruwansa ma ya kusan ƙarewa a cikin gidan nan tabbas….” “Hmm” Kawai Afra ta ce, tukunna ta matsa ta kamo Hannunta na dama sannan ta saka mata kuɗin a ciki. Da sauri Anne ta waigo sannan ta ce “laaa, kunga abun arziƙi” Ta na mai washe Baki. Cikin tsantsar damuwa da rashin jin daɗi Afra ta tari numfashinta ta hanyar cewa “Anne yau a hotel muka haɗu da Samuel dan ina fita bayan na kirashi cewa ya yi sai dai in je chan in karɓa! Anne dan Allah dan Annabi ki rufa mini asiri ki yanke duk wani abu da ki ke shirin ƙullawa tsakanina da Samuel kwata-kwata ba na son shi sannan ba na son alaƙata da shi ko da kuwa mutuncin ce…A harabar Hotel ɗin mu ka zauna amma ba ki ji yadda duk na muzanta ba. Za mu samu kuɗin abunda ya ke damunki Anne in sha Allah amma dan Allah ki daina yi mini kuka kina tunzurani zuwa inda raina ba ya so.” Shiruu Anne ta yi ta na mai sauƙe numfashi kafin ta ce “Afra Likita cewa ya yi in ban sayi alluran nan an yi mini ba tsaf zan iya mutuwa ko kuma abun ya fi haka… Ban san mai yasa ki ke gudun Samuel ba ƴar nan! Ya taɓa yi miki maganar iskanci ne? Sannan kalli abin arziƙi bawan Allah baya rabuwa da kyauta! Kuma wallahi ya ce mini aurenki ya ke son yi… Ki kwantar da kanki Unguwar nan fa kusan duk gidajen nasa ne ae ko ba komai…..” Afra ba ma ta san lokacin da ta katseta ba ta hanyar cewa “Anne ba dai krista ki ke so ki ce in aura ba dai ko? Sannan for your information yau Samuel a yadda ya dinga nuna min bashi da wani burin da ya wuce ya taɓa jikina… Above all Anne kin dai san inada wanda na ke so wanda zan aura ko? An yi magaana an gama komai da fatan dai ba hankalinki ne ya soma karkata daga batun Ya Isma’il ba…” Ta ƙarashe maganar cikin tsantsar ruɗani da tsoron da ya baiyyana ƙarara a kan fuskarta ta na kallon Annen sosai… Rarraba ido Anne ta shiga yi across the room ba tare da ta ce mata komai ba… A hankali Afra ta matso kusa da ita ta ɗan dafa ta still har yanzu yanayinta bai sauya ba ta ce “Anne…kar ki ce min ba kya son aurena da Ya Isma’il, dan Allah” Da sauri Anne ta kalleta ganin ta na shirin fashewa da kuka ya sanya ta kamo fuskarta zuwa cikin tafukan hannayenta sannan ta ce “ko ɗaya! Kar ki damu kin ji ko! Bara in je a yi min allurar kar wani ya ga kuɗin nan a ce a kawo a yi cefane ko wani hidimar gida tunda dama Ubanki ya ce ƙaryar ciwon na ke yi, yanzu ina hanawa kin san baƙin jini zan ƙara…” Da kyar Afra ta haɗiye abunda ya tokare mata maƙoshi sannan ta riƙe hannayen Anne waenda su ke riƙe da fuskarta kafin ta ce “good! Saboda in har muka butulcewa Ya Isma’il da iyayensa tabbas Ubangiji da kansa ba zai barmu ba! Haƙƙinsu sai ya tarwatsawa mu.” “Na ji na ji, kar ki damu. Ba za ma a yi haka ba” Annen ta ce ta na mai zamewa daga Afran daga nan ta nufi ƙusar da Afra ta saƙale mayafinta yanzun ta zari mayafin abayar ta yafa akan matsetstsen ɗinkin doguwar rigar da ke a jikinta ta yi waje! Da sauri Afra ta yunƙura za ta bita sai kuma ta fasa kawai dan ta san ba sauya mayafin za ta yi ba! A hankali Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta fito daga ɗakin ta nufi nasu ita da Aliya da Amal wanda ya ke nan ɗan mistitsi sosai shiyasa ko kayan sakawarsu ba sa iya ajjiyewa a ciki ga shi ɗakin da uban rima kamar a kirata ta amsa, shiyasa hatta zannuwan da su ke shimfiɗawa a kan katifarsu duk sun fara dagargajewa ta wasu wajajen dan wuyarta a jingina abu a jikin bango yanzunnan rima za ta yi masa lalata, Anne kuwa ta ce sai dai su haɗa kuɗi su yi plasta a bayan ɗakin da kansu ba zata bayar ba ae suma mata ne su fita su nemo, Baba, Ya Amir da Ya Abba kam ba yadda su ka iya ne ta abinci ake a gidan shiyasa ba su samu sun yi musu ba. Fitar Anne sai da ta kira Malamai biyar, saboda dama kuɗi take nema kwana biyu ta yi broke sosai shiyasa ta tsaya, ta san ko zata biyasu da jikinta dole ana buƙatar kuɗin siyan kayan aiki da abun sadaka… Dan haka ta kama hanya da ɗamarar yakice Isma’il daga rayuwarsu da dukkanin ƙarfinta, amfaninsa ya riga ya ƙare musu, yanzu lokacine da Afra za ta yi rayuwarta sannan ta yi auren hutu ba wai lokacin da za a kinkimeta a bashi ita ya aure ba! Dama makaranta da ɗawainiyarta ya sanya ta sake masa amma tabbas ko a mafarki ba ta taɓa fatan Ubangiji ya nuna mata auren Afra da Isma’il ba! Ko da aka yi tambaya da ragowar abubuwa duk su Baba ɓoye mata su ka yi amma tunda Allah ya sa ta ji daga bakin ita Afra tun wanchan satin shikenan ta ƙudiri aniyar nuna musu iyakarsu. Sam Afra ba sa’ar auren Isma’il bace ba! Gashi Yaron daga shi har Ubansa arziƙinsu sai faman ja da baya yake yi! Yo hauka ake…ba zai yiu ba wallahi… Masu kuɗi na bugawa a jarida duk ƴayanta za su aura ba wai auren je ka na yi ka ba!…. ••••••••• Cike da ɓacin rai Mai Unguwa ya ce “wanne kalar ɓata tarbiyya ne wannan wae ake yi a Unguwar nan amma duk kun ƙi ku taɓuka aikin komai a kai? Fisabilillahi ta ya za su dinga fitowa da sigari sannan suna yawo kusan a tsirara amma an gagara tsawatar musu! Yanzu jiya jiyannan fa da wasu Yara a Unguwar nan su ka yi walima a bayan layin Gidana! Har da sigarin takarda na wasa suka rarraba suna gwada yadda ake yi! Gaskiya na gaji! Dan haka kawai inaga zan tara Yara majiya ƙarfi su yi musu shegen duka! A koresu a Unguwar, ba zan iya ba…..” A hankali Baba ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ɗan runtse idanunsa sannan ya ɗago ya na mai kallonsa tukunna ya ce “akaramakallahu yanzu ya kake so mu yi? Mutanen nan su na da ɗaurin gindi a wajaje da yawa, kuma ko wata fa ba a yi ba da Allah ya taimakemu Hisba ta shigo muka kai ƙara wajensu aka zo aka yi musu yasa. A gabanka fa hukuma su ka ce muddin ba maza su ke shigarwa ba cikin gidan to ba mu da hurumin ma mu sake kawo ƙararsu… Ko ba haka aka yi ba?” Ya yi maganar cikin juya akalar maganar tasa zuwa ga lawyer ɗinsu. Gyaran murya lawyer ɗin ya yi sannan ya ce “tabbas! Haka ne, tunda ba wani abun aka ga suna yi da ya yi zafi sosai ba, shan sigari da yawo kusan tsirara wannan duk yanayin yadda suka tsara za su yi rayuwarsu ne ba mu da hurumin zana musu yadda za su tafiyar da rayuwarsu in muka ce za mu yi hakan to mun taɓo rights ɗiinsu wanda in suka kai ƙara tsaf hukunci zai iya hawa kanmu… Actually, hatta hanasu shiga da maza ma da muka yi ba mu da wannan hurumin fa Akaramakallahu, kawai an yi duba da yanayin gargajiyarmu ne sannan Hisba sun shigar mana shine aka bamu gaskiya… Yasar da muka yi musu ne kawai za a iya cewa mun yi dai-dai tunda a makaranta aka sassakasu Yaran da aka kwace kuma ka ga society ta na son a kula da future ɗin youth dama…. Unlike yanzun da kake son hana mutanen da na tabbata a cikinsu har da masu kusan 50yrs yin abunda su ke so… Mu bi komai a hankali, yanzun ba za mu iya cin su da yaƙi ba sun riga sun yi mana ɗaurin sarƙa sannan hujjojinsu sun fi namu kuma ka ga sun ɓoye komai an kasa samunsu da laifin dumu-dumu, amma mun fi su gaskiya dan haka i can assure you that very soon za mu ci galaba a kansu za a bamu gaskiya a samu a rabu da su har abada…” Cikin fushi da faɗa sosai Mai Unguwa ya ce “wae ba za a cire min dokar turawa a sako mini zallar ta musulunci bane ba?!!” Ganin duk sun sunkuyar da kansu sun kasa cewa komai ya sanyashi ya kallesu sosai one by one sannan ya nuna Baba da hannunsa ya ce “ba na son mutanen nan a unguwata, ku san yadda za ku yi….” Daga haka ya juya ya fice kamar mai shirin tashi sama….ya bar ɗakin da su ke taron a cikinsa. •••••••• Ta jima a ɗakin zaune ta na ta faman tunane tunanenta kafin ta miƙe ta nufi ɗakin Adda jikinta har yanzu babu lakka! Sai da ya Amir da Baba su ka ce mata kar a gayawa Anne da Kaka Nura har ma da Yadikko cewa an saka ranarta da Isma’il, aka yi komai a sirrince dan Unguwar ma duk an ɓoye saboda gudun ce-ce-ku-ce amma ta gagara ɓoyewa Anne wanda sai yanzu ne ta fahimci tabbas Annen ce ma main dalilin da ya sanya ake ta cewa ‘a ɓoye, a ɓoye’ ɗin… Da sallama ɗauke a Bakinta ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ciki a hankali. Da Amal ta fara tozali kwance sai dai bacci ta ke yi wanda hakan ya bata mamaki dan ba ta yi tunanin ba ta je Islamiyya ba yau ɗin gashi ita take saka ran za ta riƙe mata ɗayan ajinta tunda itanma yau ba ta je ba. Kamar wadda aka taso ta cikin barcin haka Amal ta shiga buɗe idanunta waenda su ka rine sannan su ka ƙanƙance! Da sauri Afra ta ƙarasa zuwa gareta ta zauna sai kuma ta waigo ta na kallon Adda kafin ta gaisheta ba ta jira ta amsa ba ta ɗaura da cewa “Mai ya sameta? Wai akan faɗan Anne da Ya Abba ne kaddai ya shafeta har haka? Me aka yi mata?” Murmushin takaici kawai Adda ta saki kafin ta gyara zama suka ɗan gaisa tukunna ta shiga zaiyyano mata komai abunda ya faru sannan ta ɗaura da cewa “Abban shima yana chan ɗaki ya ma ƙi ya buɗe ƙofar…” Ta ƙarashe maganr cikin sanyin murya ta na mai yin ƙasa da kanta.. Shiruu itama Afran ta yi kafin kuma kawai ta yi hugging Amal zuciyarta na ƙuna, tabbas mugayen halayen Anne wasu yanzun ne ake launching nasu….”da na sani ban gaya mata batun aurena da Ya Isma’il ba, Ya Allah kar ka bata ikon yin komai game da hakan…” Afra ta aiyyana hakan a cikin ranta Dan tabbas hakan da Annen ta aikata a su Amal ya sake tabbatar mata she cannot be trusted kuma za ta iya cutar kowa ta baƙanta ran kowa domin zallar farin cikinta. Kasa gayawa su Adda ta sanarwa Anne batun auren ta yi Dan ta san wani sabon ɓacin ran za ta janyo musu kuma ba iya controlling Annen za su yi ba dan haka ta zaɓi ta mayar da hankali wajen kwantar musu da hankali tare da rarrashinsu, Anne kuma ta zaɓi ta durfafi addu’a game da lamarinta.. Tabbas Afra ta tabbata Yarinya mai hankali da kuma kamala dan bata barsu da ƙunci ba sai da ta yi iyaka bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sanyasu nishaɗi da walwala. Adda ta kan ce Afra ba rainonta bace ba dan haka dukkan halaiyyar da aka gani a wajenta baiwarta ce… Afra ta sha wahala sosai dan Yadikko da Anne ba su bata kulawar da ta kamata ba gashi ita ba ta kusa a lokacin, Baba da Ya Amir za a ce su ka yi rainonta amma gashi ita ɗin ta tashi da son mutane da kulawa da gudun ɓacin ran kowa. Ita kanta Amal ta san Afra blessing ce a garesu, da Ubangiji ya zana musu ƙaddarar Baƙar Tukunya sai kuma ya sanyo musu Afra cikin familyn nasu ta zamto tamkar shield wani zubin kuma magani ga dukkan baƙin ciki da duk wani ƙunci na rayuwarsu. ……. Misalin ƙarfe bakwai da mintina hamsin ta fito daga cikin gidan nasu ta na ta sauri dan ba ta so sam sam ta yi lattti a makarantar daren da ta shiryama zuwa. Sai da ta karya kwanar makarantar tukunna ta ɗan jaa ta tsaya sannan lissafinta ya bata kamar fa tun ɗazu ta ji ana binta a baya, wanda saurin da ta ke yi da kuma hankalinta wanda gaba ɗaya ya yi ga isa makarantar ya gusar mata da lissafin hakan. Sai da ta tsaya tukunna Allah ya bata ikon shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren Ya Isma’il wanda ko a ina ne sannnan ko a wanne hali in har ta ji to sai ta shaida shi. A hankali Afra ta juya, ba tare da ta yarda ta kalli inda ta ke da tabbacin ya na tsaye a wajen ba ta na ɗan murmushi dan ta na juyawar ta fahimci ashe ma yana gab da ita ne sosai. Tsaye ya ke sanye da jeans blue ya ɗaura jallabiya fara ƙal a kai, wadda ta taimaka wajen sake haska farar fatarshi. Fari ne sosai Ya Isma’il sannan dogo sosai kuma ya na da faɗin ƙashi sai dai bai cika ƙiba ba dan kai tsaye za ka sakoshi sahun sirara. A fuska kuwa kai tsaye za ka kira shi da kyakkyawan gaske, ajin farko. Sai da ya yi folding hannuwansa a kan ƙirjinsa tukunna ya ɗan rankwafa yanayinsa na nuna tsantsar girmamawa da shauƙi, ya ce “Barka da war haka sarauniyar duk Matan Duniya! Tauraruwa kuma hasken zuciyar Isma’il” Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota011 *28* Murmushi Afra ta yi sannan ta saka tafukan hannayenta ta kare fuskarta da su, kafin a hankali ta ce “ina wuni Ya Isma’il” Still ta na murmushin da ya ke samo asali daga tsantsar farin cikin da zuciyarta ta ke a ciki. “Alhamdulillah Abar ƙauna, ya al’amura?” Ya yi mata tambayar idanunsa ƙurr a kanta yana mai ji kamar ya haɗiyeta tsabar yadda tsantsar ƙaunarta ta ke addabar zuciyarsa. “Alhamdulillah” Ta ce har yanzun ba ta cire hannunta gaba ɗaya ba dan ta soma diriricewa daga kallon da ya ke yi mata… Kamar wani ɗan ƙaramin Yaro haka nan ya ɗan turo Bakinsa gaba sannan ya yi kalar tausayi kafin ya ce “ki cire hannun mana, i want to see you fa.” Ya ƙarashe maganar kamar mai shirin fashe mata da kuka. Itanma cikin tsantsar shagwaɓar da ta dame tasa ta shanye ta ce “to Ya Isma’il ka fara daina kallona mana” Ta yi maganar ba tare da intention na dasa masa wani abun ba amma shi gogan a take ya ji wani yanayi na musamman yana shirin kwance masa lissafinsa. Shiruuu, ya yi kafin ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa ya ɗan cije lips nashi sannan ya ɗago ya kalleta a hankali ya ce “hmm” kawai, tukunna ya gitta ta ya wuce cikin sauƙe ajiyar zuciya ya ce “na daina my one and only….” Ya na ɗan murmushi ƙasa -ƙasa. Murmushin itama ta yi sanna ta zare hannunta daga face ɗin nata completely kafin ta juya a hankali su ka jera su na tafiya, in ka kallesu gwanin burgewa… Sai da su ka ɗan yi nisa tukunna a hankali ta ce “ya su Mama?” “Su na ƙalau Alhamdulillah, ta ce in gaida ke.” Murmushi ta yi cikin tsananin ƙaunar matar ta ce “Ayya, na gode ina amsawa” Dai-dai nan su ka ƙaraso bakin makarantar dan haka ya sauƙe numfashi ya na kallonta da mamakin kunya irin ta Afra, dan har yanzun kanta ƙasa ya ke…A yadda su ka daɗe tare su ka shaƙu da juna ya kamata a ce ba ta kunyarsa har haka sosai, amma kullum ita dai kunya ko iya haɗa ido da shi fa ba ta yi har yanzun sai dai idanunsu su haɗe waje ɗaya by mistake kuma shima nan da nan ta ke janyewa. Ya na wannan lissafin ya ga ta ɗan ɗago ta saci kallonsa sai kuma ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa sakomakon haɗa idanu da shi da su ka yi ya kafeta ƙurr da ido ya na ta murmushi…. Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya ce “Allah ya nuna min ranar da za mu yi gasar kallon kallo ni da ke…” Murmushi ta yi yanzun ma sannan ta ce “Ya Isma’il bara in shiga kar in makara, na gode” A hankali. Shima a hankali kamar yadda ta yi ya ce “ban ƙoshi da ganinki ba.” Irin kalar tausayi ɗinnan. Murmushi ta yi kawai, ta kasa cewa komai. Kamar masu tallar auduga haka suka wanzu a wajen daga shi har ita kafin chaan ya ce “Ɗazu Baba ya dawo daga Umara..” Cikin nutsuwa ta ce “Ma sha Allah, Rabbi ya sa maƙabuliya ce” A hankali ya ce “Ameen, sannan ya ɗaura da cewa “good news…ya ce wata biyu ya yi tsaho, wai a mayar sati biyu tunda an kammala shirye-shiryen komai…” Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace, sai kuma ta maida kanta ƙasa yanzun ma su na haɗa ido kafin ta ce “Ya Isma’il kuma na ga kamar ka na murna.” Ɗan zaro idanu waje ya yi kafin ya ce “murna kai! Ji na ke yi kamar in suma tsabar daɗi, Allah Allah dama nake in aureki, na matsu sos…” Sai kuma ya yi tsit bai ƙarasa ba ya fara dariya saboda yadda ta yi saurin rufe idanunta ta juya masa baya. Juyin duniya Afra ta ƙi juyowa gaba ɗaya kunya ta gigitata har kamar ta na shirin fashewa da kuka, ita dai gaba ɗaya ya Isma’il ya soma sauyawa tunda aka saka ranar aurensu, wata maganar in ya yi sai ta ji kamar ba shi ba wallahi… Ba dan ya so ba haka ya haƙura ya kyaleta kawai, saboda ta yi latti sannan a yadda maganarsa ta kiɗimata ya san ba za ta sake da shi yanzun ba, dan haka ya juya ya bar wajen bayan ya yi mata adduar samun ilimi mai amfani. Sai da ta tabbata ya bar wajen tukunna ta juya ta shige ciki yayinda shi kuma ya nemi waje a wani dandamali ya zauna kawai ya na ta murmushi… Har gaban abada ya na godiya ga Ubangiji da ya bashi Afra kuma yanzun da yardarsa zai mallaka masa ita a matsayin matar aurensa… Shi dai a gaskiya ya fi kowa sa’a tabbas! Dan duk wani qualities da ake buƙata a mace to Afra ta na da shi, ga shi dai Anne ce ta haifeta amma kamar wadda ta taso ta girma ta yi rayuwarta komai a gaban jiga jigan manyan Malamai bayin Allah….. A hankali ya ɗaga kansa sama ya na kallon yadda taurari suka yi wa sararin samaniya ado gwanin ban sha’awa cikin sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya ce “Alhamdulillah” …….. Bashi da wani abunda zai yi a gida ko wani wajen dan haka bai bar wajen ba kamar yadda ya saba in ya rakota ya je ya dawo daff da tashinsu ya kaita har ƙofar gida, wannan karon zamam dirshen ya yi a wajen ya na ta faman tunane-tunane da lissafe-lissafen auren da rayuwarsu har zuwa lokacin da aka tashi daga islamiyyar daren. Dama Afra sai faman Addu’a ta ke yi Allah ya sa ya tafi, sai dai kuma ta na fitowa shi ta fara hanga dan haka ta sauƙe ajiyar zuciya kawai kunyar ɗazu ta na sake dawo Mata sabuwa. Har ƙofar gida ya rakata kamar kullum, sai dai bai sake yi mata zancen bikin ko aurensu ba dukda yadda ya ke ta so ya sake tsokanarta amma da ya fahimci a ɗarare take da shi sai kawai ya rabu da ita saboda sam ba ya so ya ganta uncomfortable ko cikin damuwa sam-sam, walwalarta ya ke biɗa kullum.. Sai da su ka zo rabuwa tukunna ya ce mata “ta ji komai daga wajen Baba in ya so sai su yi magana gobe, saboda ɗazun ya baro Baba Babansa da Uncle ɗinsa su na tsare-tsare…”” Daga haka suka rabu cikin tsantsar so da ƙaunar juna. Afra ta na shigewa mota ta yi fakin a ƙofar gidan, Isma’il bai kai ga barin wajen ba dan haka ya waigo ya tsaya dan ga dukkan alamu gidan aka zo… Da ikon Allah sai ga Anne ta fito daga cikin motar wadda tun fitar ɗazun nan da ta yi sai yanzun ne Allah ya bata ikon dawowa. Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Isma’il! Tabbas da ace Anne shi ta haifa ba Afra ba zai iya saka mata shinkafar ɓera ta ci in zuciya ta tunzuroshi wata rana… Kayan jikinta sun fi komai ɓata masa rai, sai kuma motar mai uban tint wadda daga inda ya ke tsaye ya na iya jiyo tashin kiɗa a lokacin da ta buɗe ta, ta fito daga cikinta…. Bai san lokacin da ya yi tsaki ba, ya juya kawai, ya na juyawa su ka yi ido biyu da Ya Amir shima ya kafe motar wadda ta ke yin reverse da shirim barin layin ido, idanunsa sun kaɗa sun yi wani kalar jaaa. “Assalam alaikom” kawai ya ce da Isma’il ɗin sai kuma ya kasa ci gaba da tsayuwa a wajen dan haka fiiii!!! Kamar wanda iska ta kwasa ya yi wuff!! Ya bar wajen ya karya kwana. Shiruu Isma’il ya yi ya lumshe kyawawan idanuwansa kafin chaan ya sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tukunna ya buɗe idanunsa, ya bar wajen, jikinsa a mugun mace. …….. Direct gidansu ya nufa, wanda a kaff layin gidan nasu kusan shi za a cewa Babba, gate ne fari sai dai ya ji jiki, kana shige gate ɗin za ka tarar da tsakar gida tafkeke da three bedrooms flat, sai wani boys quaters a jikin gate opposite ɗakin mai gadi wanda aka mayar ɗakin tara shirgi saboda babu mai gadin. Mota ce kwalli ɗaya a gidan fake a chan gefe, tsakar gidan kuwa a ƙalla zai kai a gina irin gidan sau huɗu a cikinsa tsabar girmansa…. Har Isma’il ya yi hanyar boys quaters inda ya ke da zama ya ji wayarsa ta ɗau ƙara, yana ɗagota ya ga sunan ‘Maama’ ya baiyyana ɓaro-ɓaro a kan screen ɗin wayar… Ya na ɗauka suka gaisa cikin girmamawa sannan ta ce “kai ne ka shigo yanzu?” Ya ce mata “eh” Kai tsaye ta ce masa “zo” Daga haka ta kashe wayar. Ya na isa bakin entrance na gidan ya ɗaga hannunsa da niyyar yin knocking main door ɗin ya ji an murza key within seconds aka buɗe ƙofar ƙanwarsa ta baiyyana a gabansa. Su biyu kacal dama aka haifa a gidan, cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa daga nan ta wuce gaba ya bita a baya zuwa ɗakin Mahaifiyar tasu. Sai da su ka yi knocking ta basu izinin shiga tukunna cikin tsantsar nutsuwa duk su biyun su ka shiga bakunansu ɗauke da sallama. Zaune take akan darduma sanye cikin farin hijabi mai kwalliyar cin bakin lace, hannun damanta riƙe da carbi mai kyau da sheƙi ta na lazimi ta na jaa a hankali. Ko da su ka shigo ba ta amsa ba sai da ta kai inda take so lokacin duk sun nemi guri sun zazzauna tukunna ta yi addu’a duk su ukun su ka shafa a tare. Cikin tsantsar girmamawa ya ɗan rissina tukunna ya ce “Ina wuni Mama..” Ya sake gaida ita. A ransa ya na addu’ar ‘Allah ya sa dai lafiya’ Dan ɗazu kafin ya fita har ya yi mata sai da safe ta amsa, yanzu kuma gashi ta kirashi sannan da ya kalli fuskarta kai tsaye ya hango damuwa. “Alhamdulillah” Ta ce da shi, wanda hakan ya katse masa lissafin da ya ke yi, ya sake maida hankalinsa kacokam a kanta. A hankali ta sauƙe numfashi ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauko maganar da ta sanya ta kirashi ɗin. “Isma’il, na san wacece Afra da tarihinta da tarihin iyayenta da komai nata, wanda na san ka san cewa ba don so da ƙaunar da muke da tabbacin kuna yiwa juna ba da kuma nutsuwa da hankalin ita Yarinyar tabbas da ko da wasa ba za mu taɓa yarda mu haɗa alaka da ita ba…” Sai da ta sauƙe numfashi tukunna ta ɗaura da cewa “dalilan nan guda biyu da na baka muddin ɗaya ya samu tangarɗa to ɗayan ma zai iya samun tangarɗa. Dan duk son da ka ke yi mata ba zan yi farin ciki in goyi bayan aura maka ita ba muddin na ga ɗabiunta suna sauƙa daga kan layi, haka zalika kuma duk nutsuwarta zan so ace ka aureta ka na mai tsnanin ƙaunarta domin farin cikinka. Ba zan yi maka dole ba sannan i’m not trying to make your decision for you amma ina mai baka shawarar da ka tsaurara bincike na gaske! Sannan wannan auren da Mahaifinka ya ke gaggawar a ɗaura inaga ka ɗan yi masa magana a ɗan rage saurin…. Afra Yarinya ce mai hankali nutsuwa da tarbiyya amma fa ba a chanjawa tuwo suna wanda abunda na ji yau ya farkar da ni na fara lissafin abunda duk ban yi a baya ba… Isma’il no matter what nonon Nuratu Afra ta sha kuma jininta ke yawo cikin jijiyoyin da su ke a jikinta sannan kowa ya san akwai jinin zina a jikinsu dan ubansu sai da aka kamashi da Uwar tukunna…” Da mugun sauri Isma’il ya ce “Maaamaaa” Ya na mai runtse idanuwansa da masifar ƙarfi. Shiruu ta yi ta na kallonsa har sai da ya ɗan dawo dai-dai dan kanshi ya buɗe idanun nasa waenda har sun kaɗa sun yi jaaa sosai sannan ya ce “Mama, Afra Musulma ce (ƴar uwar ce, ya kamata ko dan haka a yi mata da sauƙi) kuma waennan lapse ɗin nata bai kamata ace sun rufe miki idanu daga ganin tsantsar good and golden values ɗinta ba…” Cikin tarar numfashinsa ta ce “tabbas hakan ya sanya na ke goyon bayanka ɗari bisa ɗari a baya. Sai dai tunda aka sanar mini an ganta a hotel yau! Ita da wannan mutumin Samuel gaba ɗaya na gagara nutsuwa hankalina ya tashi sannan ba zan ɓoye maka ba har ga Allah na fara kokwanto.” Ɗiff!!! Haka Isma’il ya ɗauke wuta, kafin kanshi tsaye ya ce “Mama sharri ne, zan iya rantse miki cewa ƙarya ne ake yi mata.” Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota011 *29* Ɗiff!!! Haka Isma’il ya ɗauke wuta, kafin kanshi tsaye ya ce “Mama sharri ne…zan iya rantse miki cewa ƙarya ce ake yi mata.” Cikin tarar numfashinsa ƙanwarsa ta ce “Wallahi Yaya da gaske ne! Yayansu Asiya ne ya ganta fa” A ɗan fusace ya waiga ya na kallon ƙanwartasa, kafin ya ce “wato ke ce ki ka kawo munafurcin kenan, ko?” “Hmm” kawai Mahaifiyar tasu ta ce sannan ta ɗaura da cewa “a kan ta faɗi gaskiya shine za ka kirata da munafuka a gaban idanuna?” Runtse idanunsa ya yi da masifar ƙarfi sannan ya sauƙe ajiyar zuciya kafin ya ɗaura da cewa “ba haka bane ba Mama, a ganina in ta ji irin haka ni ya kamata ta fara samu zan san abunda zan yi kuma zan yi bincike in yiwa tufkar hanci ba wai ta zo kai tsaye ta gaya miki ba…” “Saboda ba ka ƙaunar ka ji laifin Afra ko? Saboda in ta gaya mini zan iya cewa a jira ko a yi bincike sosai kai kuma soyayya ta rufe maka idanu ba ka son duk wani abunda zai saka comma ko fullstop a maganar aurenku ko? Isma’il are you even listening to your self kuwa? Straight up fa gaskiya ce ba ka so da kuma laifin Afra. Sannan har yaushe ne ka fara ɓoye mini abu da za ka ce kar a gaya mini a fara gaya maka tukunna…” Mama ta jero maganganun ranta ya na sosuwa. Sai kuma ta ɗan yi shiruu kafin kawai ta ce “ina yi maka addu’a sosai! Sannan kaima ka dage da addu’a, in har auren nan ba alkhairi bane ba, Ubangiji ya yi ikonsa ta ko wanne angle.” A hankali ƙanwarsa ta ce “Ameen” Amma da ikon Allah Isma’il sai ya gagara cewa ‘Ameen’ ɗin ya na mai jin kamar ya rufe ƙanwartasa da duka! Tabbas ya san Samuel ya na son Afra amma zai iya dafa Alqurani akan cewa ƙarya ake yi mata ba ta bishi hotel ba wallahi, ko meye Afra in za ta yi sai ta gaya masa, besides ya ma san ba za ta taɓa aikata wannan ɗanyen aikin ba! Inaa ba zai yiu ba ƙarya ne…. “Yaya ka dage da addu’a dan Allah, ba wai farin cikinka ne ba na so ba, ba na son ka ɗauko mana jidali cikin family azo ta zame maka da mu kanmu masifa shiyasa na gayawa Mama saboda a tsananta bincike a kanta sannan a ɗan dakata kar a yi sauri….” Dukan da ya kai mata ne ya sanya ta yin shiru ta shiga neman wajen ɓuya dan haka maganar tata ta tsaya chak!!! Cikin faɗa sosai kamar ba Isma’il ba dan bai iya faɗa ba sam ba halinsa bane ba amma haka yau ya rufeta da faɗa a gaban Mama har da cewa ‘ko a ya Afra ta ke zai aureta a hakan’ Sai kuma da ya gama hayaniyar sai kunyar Mama ta lulluɓeshi dan haka ya yi shiru kawai. “Shikenan, tashi ka tafi, ko kuma y not in Allah ya kaimu gobe ka tambaya ka ji ta bakinta, ko?” Mama ta ce da shi kawai ba tare da ta kalleshi ba. A hankali ya lumshe idanunsa kafin ya buɗesu kawai ya ce mata “tam Mam in sha Allah, sai da safe” Daga haka ya miƙe ya fita ransa a masifar ɓace, ta ya ma Mama za ta yi mishi haka gashi ba zai iya yi mata musu ba, yanzu fisabilillahi ta ya zai fara tunkarar Afra da wannan maganar, gani za ta yi kamar bai ma yarda da ita ba, zarginta ma ya ke yi…. Da wannan tunanin ya isa ɗakinsa ya watsa ruwa ya kwanta sai dai kuma kafin safiya shaiɗan ya yi nasarar dasa masa wani abu a rai dan a cikin daren ya kasa sukuni har sai da ya yanke shawarar tunkararta da zancen kamar yadda Mama ta buƙata. Ya na fita Maama ta sauƙe numfashi. She’s very certain about the fact that Afra ta je wajen Samuel dukda ba ta da tabbacin mai ya kaita amma a yanzu kam tana fata Allah ya sa abun bai wuce gaɓar da za a iya gyarawa ba, dan Isma’il ya tsoratata tabbas yanzun duba da yadda ya zuciya ya fusata daga an yi batun ɗaga aure dole za ta je ta ji baasi ita da kanta tunda a ganinta an riga an zama ɗaya yanzu kuma its obvious rabuwa da Afra barazana ce a rayuwar ɗan nata duba da abunda ya yiwa ƙanwarsa a gabanta da yadda duk ya bi ya firgice tabbas yadda ta ɗauki Afra a wajensa ta fi hakan kuma ya bata tausayi matuƙa, dan haka za ta je da kanta ta yi musu magana gaskiya kar ta ƙara ko dan mutuncinsu tunda a ganinta za ta iya yiwa yarinyar faɗa ta ɗauka, dan a yadda ya fita ta san ba lalle ya ji abunda aka gaya masa ba, in ma wani abun ne ta taimaka ta daina zuwa ko dan munafurcin ƴan unguwa sannan ta fita a harkar wani Samuel… Babu komai in sha Allahu za ta yi bincike ta yiwa tufkar hanci ta haƙura za ta rungumi Afran kamar yadda ta soma tun farko, in sha Allahu wannan ɗin ma za ta shanye a tafi a haka, ta amince ta karɓi wannan ƙaddarar fatanta Allah ya sa Yarinyar ba ta kauce hanya ba kuma abun bai yi tsamari ba dan in haka ne kuma ba za ta rufe ido ta jefa ɗanta ga halaka ba gaskiya. ……….. Direct wajen Adda Afra ta nufa, a nan su ka zauna, suna cikin hira kiran Ya Amir ya shigo wayar Adda, dan ita dai Afra wayarta dama da ita gara babu za a ce, kullum ta na ɗaki a ajjiye, ba ta wani damu da ita ba. Ta na ɗauka su ka gaisa, cikin nutsuwar da kullum ta ke a tare da shi ya ce mata “ku zo, Baba ya na son ganin kowa” Daga haka ya kashe wayar bayan ta ce “tam” Amal da Afra sun so Adda ta je da su amma sai ta ce “su je kawai” Saboda ta san in har da Anne a meeting ɗin to ko ta je ranta ne kawai zai zo ya na ɓaci, dan haka ta ce su je, ta ji ko ma menene daga baya. Har kawo wannann lokacin Afra ta gagara gathering courage ta gaya musu cewa Anne ta san batun aurenta, dan ko tunawa ma ba ta so ta yi, shiyasa tun da aka ce Baba ya na nemansu gabanta ya soma faɗuwa duk da kuwa dama Ya Isma’il ya tabbatar mata zai nemeta amma fargabar abunda Anne ka iya yi duk sai ya dameta ya hanata sukuni har suka ƙarasa ɗakin Amal na ankare da yanyinta sam ba ta da walwala…… Su na shiga ciki su ka tarar da Baba, Ya Amir da Annen wadda ƙamshin dsigner turarukan da su ke fita a jikinta su ka karaɗe kusan gaba ɗaya gidan dan tun kafin su shigo ɗakin ƙamshinta ya ke yi musu sallama. Ta na zaune akan tulin kayan wanki ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta na daddanna wayarta ta na wani irin taunar cingam na kwararrun ƴan duniya, yayinda Baba ya ke zaune a kan darduma Ya Amir ya ke a gefensa kanshi a ƙasa kawai ya gagara ɗagowa, tun ɗazu da ya ga an sauƙe Anne a mota shikenan zuciyarsa ta dunƙule har yanzun ta ƙi sakewa sam-sam. Da sallama Afra da Amal su ka shigo a tare, Baba da Ya Amir su ka amsa musu, cikin nutsuwa su ka ƙaraso su ka zauna a ƙasa cike da ladabi su ka gaida kowa one by one…. Da kyar Anne ta yi jimla ta amsa musu, dan ba ta ma so ta sake ta saki fuskar da har Baba zai ga ƙofar kawo mata raini, ta san sarai dalilinsa na tarasu bai wuce ya yi mata magana a kan daren da ta yi ba sai ko maganar faɗanta da Abba da kuma wataƙila zancen auren Afra wanda duk ciki babu guda da za ta karɓa da sauƙi, ita kanta Afra yau kam sai dai ta gano cewar ba ta son auren amma ƙiri-ƙiri za ta nunawa kowa ta na buƙatar a tura auren chan da nisa sosai…. Ganin babu Adda ya sa Baba ya sake ɗaga waya da kanshi ya kirata amma ko da ta yi masa bayani sai ya zaɓi ya barta ɗin kawai ya cewa Amal ta gaya mata komai yadda aka yi in Allah ya kaimu gobe… A hankali Yarinyar ta amsa da “to Baba” Taɓe Baki Anne ta yi kawai ta kawar da kai gefe ta na lissafinta… “Sallu Alan Nabiyil Karim…” Muryar Baba ta katsewa Anne tunanin da ta ke yi… Cikin nutsuwa Afra Amal da Ya Amir su ka ce “sallallahu alaihi wa sallam” A tare sannan ya Amir ya yi Addu’a, su ka amsa da Ameen tukunna Baba ya gyara zama ya soma maganar abunda ya san zai fishshesa dan shi kam lamarin Anne tabbas ya yakice daga kansa in ta ga dama ta yi yawo tsirara ko dan su Amal ɗin ma da ya ke cewa yanzu kam kawai su yi haƙuri su rungumi ƙaddararsu, ba zai iya ba. “Dama dalilin da ya sanya na tara ku anan akan batun maganar Auren Halima (Afra) ne da Isma’il, kamar yadda wasu a cikinmu a nan su ka su ka sani wasu kuma za su ji yanzu…an sanya ranar auren nasu ta inda aka bari a kan watanni biyu masu zuwa. Wanda an saka ne a lokacin da shi Mahaifinsa ya yi tafiya zuwa egypt daga nan ya wuce Umara…. A wannan lokacin shi da kansa ya ce mana duk abunda mu ka yanke ni da ɗan uwansa ya ji ya gani to kuma da ya dawo yau ya na jin kwanakin ya nemi ganinmu…” Shiruu ya yi kafin ya lumshe idanunsa ya buɗe sannan ya ce “duk ɗinmu mun san yawanci jama’a ba sa ƙaunar auren nan, sabili da ana gani kamar an cuci Isma’il ne duba da yadda tarihin Afra ya ke a Unguwar nan da kuma yadda Mahaifiyarta ta ke! Kasancewarta Yarinya mai cikar kamala ba shi zai sanya a chanjawa tuwo suna ba duk ɗinmu mun san da haka, gutsiri tsoma da munafunce-munafunce su kan yi tasiri a kan kowa kuma ba a cika son yawan magana a kan abu ba! A duniyar nan bayan ku inaga ba ni da waenda zan ce su ka fiye mini Isma’il da iyayensa dan sun so ni kuma su na kan so na a yadda na ke a lokacin da ya kamata a ce sun guje mini dan shi da kansa mahaifin na sa ya ce saboda gudun ce-ce-ku-ce ya na so kawai a ɗaura auren wani satin idan Allah ya kaimu(rana ita yau kenan!).” Da wani kalar azababben sauri Anne ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta mayar da kanta ƙasa kawai ta shiga tsinewa Malaman da ta wuni wajensu yau! Saboda babu kalar duba da buga ƙasar da ba su yi ba yau ɗinnan amma duk cikinsu aka rasa wanda ya hango mata batun matso da aure kwana kusa ballantana ta soma shiri tun ɗazun sai yanzu ne ta ke ji daga bakin Baba. Muryarsa jin ya ci gaba da Magana ne ya katse mata tunaninta… “Dan haka mun tsara a kan nan da sati ɗaya za a yi auren in sha Allahu, Afra za ta wuce Kaduna gidan Amaryar Mahaifinsa wadda ya aura ta rasu, ya ce akwai komai a ciki ba sai mun kaita da ko cokali ba, komai sabbi ne dan wasu ma ba a taɓa amfani da su ba sannan ya ce za ta zauna a chan tunda dama shima Isma’il ɗin a chan Kadunar ne ya samu aikin nasa, har batun gurbin karatu da za a nema mata a chan duk mun yi da su kuma za ta soma da zarar an ɗaura sun tare in sha Allahu….” Cikin sauƙe ajiyar zuciya Baba ya ce “dan Allah duk wanda ya yi sallah ina neman alfarmar da ya dinga saka mini mutanen nan a cikin addu’a yana neman musu yardar Ubangiji, tunda aka haifoku cikin wannan zuri’a tawa a kullum tsorona waye zai aureku! Amma da ya ke Ubangiji ne me komai gashi zan fara ganin auren Afra waenda mutanen nan su ka zamto silar komai na auren bayan doguwar ɗawainiya da mu da du ka dinga yi, kuma in sha Allahu yadda aka aminta da ita har ake kwaɗayi da son aurenta haka Aliya da Zainab(Amal) suma duk za su samu mazaje masu nagarta waenda za su karɓesu hannu bibbiyu ba tare da sun dubi halin mahaifiyarsu ba” “Babana” ya yi maganar referring to Ya Amir sannan ya ce “kai ma in sha Allahu za ka samu mata mai nagarta da kamala bi’izinillahi ta’ala…” Murmushi Ya Amir ya yi sannan a hankali ya sunkuyar da kanshi ƙasa a ransa ya amsa da “Ameen” A hankali Afra itama ta sake yin ƙasa da kanta, ta san ta na son Ya Isma’il kuma aurensa shine burinta amma haka nan a take sai ta ji fargaba da tsoro duk sun mamayeta sannan wae ba ma a Kano za ta zauna ba a Kaduna ne, tabbas ita kanta ta san za ta yi kewar danginta…. “Sallu Alan Nabiyyil Karim” Baba ya sake cewa, a tare duk su ka ce “sallallahu Alaihiwasallam….” Wani kalar tashin hankali da masifa Anne ta ke ciki, ga baƙin cikin batun aure ga shi ba a nemi yardarta ko ɗaya ba sannan ga bala’in takaici da mamakin yadda yau Baba ya gaggasa mata magana a gaban idanunta ba shayi…. Ganin ya na shirin miƙewa ya sanya rai a ɓace ta ce “Dakata Habu!” Shiruuuu kowa ya yi, yayinda Baba ya runtse idanunsa kamar ba zai kulata ba sai kuma ya koma ya zauna da kyau ya na mai sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce “ki na da magana ne Anne?” Da sauri Ya Amir ya miƙe zai fita dan ya san in ba a yi sa’a ba Anne sai ta saka shi kuka a maganganun da ya ke da tabbacin za ta gaggayawa Baba…… Cikin daka masa tsawa Anne ta ce “Koma ka zauna!!!Munafuki! Ɗan iska kawai ai har da kai aka haɗa komai saboda kun maida ni banza ko?” Sai kuma ta maida dubanta ga Baba sannan ta ce “yanzu kai ba ka ji kunyar yadda ka saka ranar ƴar da na haifa a cikina ba sannan ka ɓoye mini kuma har ka ke da tsaurin idon wani ce mini ka san wasu a cikinku sun sani wasu kuma basu sani ba, sannan kai har ka isa ka saka ranar ƴata cikin sati ɗaya tak!! Sannan ka gaya mini yanzu ba tare da neman shawarata ba, ƴar tawa ƴar tsana ce???” Kamar Ya Amir ba zai ce komai ba sai kuma ya kalleta idanunsa jazir ya ce “Anne saboda munafurce-munafurce da Bakin mutane kar ya yiwa maganar auren illa shiyasa aka ce a ɗaura da wuri kawai tun kafin batun auren ya zagaya koina…” “Akan me ake munafurce-munafurcen??” Anne ta tambayeshi ta na huci! “Wai shin ni kam na taɓa yin zina a bakin ƙofa ne ko kuwa na taɓa cin mutum sannan tsirara aka ga ina yawo! Da har shi Usman(Mahaifin Isma’il) ɗin dan *******uwarsa zai dinga magana ya na nunawa kamar alfarmar zai yiwa Afra shin bai ga ƴar tawa bane ba?! Ai sai dai mu mu yi masa alfarma wallahi, ke tashi su ganki da kyau ki kwaɓe hijabin su ganki su san mu ne za mu yi musu alfarma…” Ta faɗi hakan ta na kallon Afra sannan ta ɗaura da cewa “ku kuma da yake gaɓayene, wawaye shine ku ka biye masa aka tafi a haka…” Cikin daka mata tsawa Baba ya ce “Nuratu!” Kafin ya rufe Bakinsa itama ta ce “Na’am Abbakar!!” Da gudu Amal ta tashi ta fice ta na kuka sosai ta faɗa ɗakinsu dan ba za ta iya zama ta juri kallon faɗan iyayen nata har haka ba. Tsaki kawai Anne ta yi bayan ta gama hararar inda Amal ɗin ta bi ta fice sannan ta waigo zuwa ga Baba ta ce “abu uku na ke so ka saka a ranka, na farko yadda ku ka tsara nima dole a bi nawa tsarin kuma ba zan aurar da ƴata kamar wata ƴar tsana ba wallahi, dole in yi taro dole in yi biki dole in yiwa ƴata kayan ɗaki in ya so along the way duk wanda zai saka Baki ko ya yi munafurci shi ya sani in ka ga Isma’il bai auri Afra ba tabbas ba Matarsa bace ba dama tun farko, abu na biyu kuma ko dan yadda ku ke kallona Allah sai an ja bikin nan saboda in nuna muku cewa baƙin fentin da ku ka yi mini bai hau ba, sannan abu na uku kar ka ƙara zama a gaban idanuna da ƴaƴana ka na ci mini fuska kamar ka samu mayya har ka na cewa wani wai saboda ni za a fasa aure Uban baban duk wanda ya bari aka yi dan Allah….” Ta ƙarashe maganar ta na huci sosai, ranta na susa, wato Kaduna ma za a ɗauki ƴar tata a kai ta yadda kafin ta bata wani abun alkhairin ma sai an jima, yo ko da ace isma’il ɗin ya zamto choice ɗinta ace kuɗinsa ya yi kuɗin da za ta iya bashi Afra sam bai isa ya ɗauketa ya yi nesa da ita ba, ba ta haifi ƴaƴanta domin haka ba… Shiruu Baba ya yi tun fitar Amal dan sai ya ji bai kyauta ba ya gama yiwa kanshi alƙawarin ba zai dinga biye mata ba, musamman ma in a gaban ƴaƴansu ne…. Da kyar da mugun kyar ya samu ya iya cewa “Afra ke da Amal ku gayawa Adda yadda mu ka yi da ku a nan. In akwai wasu shirye-shiryen da za ku yi sai ku yi mini magaana…..” Daga haka ya miƙe ya fice da sauri Ya Amir shima ya bi bayansa… “Tashin balagar tsintsaye ma kena!!!! Idan ita Addar ko Uwarta wani cikinsu ya haifa mini ƴar sai in ga hannunsu a cikin auren da ban aminta da date ɗinsa ba dan Uban Mutum” Anne ta faɗi hakan ta na mai ji kamar ta zunduma Uban ihu dan baƙin takaici, shi dai Baba bai biyeta ba haka shima Ya Amir su ka saka kai su ka fice daga cikin gidan ma gabaɗaya dan sai ta yi barci tukunna za su iya shigowa yau kam, ko a inda su ka san za ta gansu ba su tashi zama ba dan kaɗan daga aikin Anne ta bisu har majalisar ko shagon da Baban ya ke a yi ta ka-ce-na-ce da ita. Ife-ife ta ke yi sosai kamar za ta haɗiye harshenta. Ganin sun fita sun barta su na shirin saka mata hawan jini ya sanya ta miƙe tsaye za ta bi su kamar yadda su ka zata. Da sauri Afra ma ta miƙe dama a bakin ƙofa ta ke dan haka sai ya zamana kamar ta tare mata hanya ne. Sai da hasken kendir ɗin ya haske fuskar Yarinyar tukunna Anne ta fahimci kuka ne ta ke yi sosai dan idanunta har sun sauya, cikin kukan Afra ta shiga cewa “Anne ya kamar ki na baƙin ciki da farin ciki na ne, Anne da gaske tarwatsa aurena da Ya Isma’il ki ke son yi?…” Shiruu Anne ta yi kafin ta runtse idanunta da masifar ƙarfi a ranta ta na tsinewa Baba tun daga kan kakannin kakanninsa har shi! Domin kuwa shi ne ya tunzurata ya sa ta yi behaving hakan a gaban Afra, bata so Yarinyar ta tsaneta fiye da yadda ta san ta tsaneta dan in hakan ta faru ba lalle ta ji ƙanta ta kula da ita ba wanda jin ƙan nata shine main goal ɗin komai da ta ke yi yanzun, duk wani plan nata akan Yaran su auri mai kuɗi da faɗi tashin da ta ke yi duk sabili da su ji ƙanta ne…. Dai-dai nan Kaka Nura ya ɗaga labulen ya shigo! Jin Afra na kuka ya sa ya ƙarasa shigowa ciki da sauri kamar ba ɗakin surikinsa ba ya ɗan waigo da ita ya na kallonta sosai kafin ya kalli Anne ya ce “Mai ki ka yi mata? Shigowata kenan tun daga waje na ke jin hayaniya sannan na ga su Habu sun fita da wuri” Sai kuma ya yi shiruu ya na kallon fuskar Annen itama sosai kafin ya ce “me su ka yi muku dan ubansu?” Share hawayen takaicin da su ka zubo mata babu shiri! Anne ta yi, sannan ta shiga zaiyyano masa komai, tun daga saka ranar Afra da aka yi a ɓoye(wanda already ta gaya masa bayan ta sani shima a ɓoye) har kawo yanzu da Baba ya dage sai an yi auren ta na kaiwa nan ta fashe da kuka sannan ta durƙushe a wajen kawai duk dan Afra ta tausaya mata….ta na cewa “saboda ban isa ba saboda ban kai ba in haifi Yarinyar amma a nuna mini isa da mallaka….” Numfashi Kaka Nura ya jaa ya sauƙe sannan ya kamo kafaɗun Afra ya juyo da ita saitin shi tukunna ya soma magana “Kinga in har ki na da hankali tou kalmar ba a chanjawa tuwo suna da suka yi amfani da ita su da su ke manya ya kamata ace kema ƙarama kin ɗauka kin yi amfani da ita, kin ga wannan..” Ya yi maganar ya na nuna mata Anne sannan ya ɗaura da cewa “ba ki ta tamkarta ko da a bola ta ke yawo ita ɗin ce dai ta haifeki ba za ki taɓa sauya ta ba, in har ki ka yarda ki ka bari su ka raina miki ita to wallahi kin shiga ukunki, dan ba ki isa ki chanjawa tuwo suna ba haka maganar ta ke, sannan kalli ki ga tun yanzu sun fara yi miki gori tou na tabbata in ki ka bari aka kai ki gidansa babu kayan ɗaki a yadda su ka iya gorin nan su na gani kamar sun yi miki alfarma tabbas nan ma wahala za ki sha a hannunsu, kuma above all ma ta ya za ku yi amfani da kayan matar da ba ta raye, ke ba ki da tsoro ne? Ki bari in shi Habu ya ce ba zai yi miki ba, da ni da Annenki mun yi miki alƙawarin za mu yi miki kinji ko? Ki tashi ki tsayawa kanki tun yanzu ki san darajarki ki nuna musu ki na da daraja, kar ki yarda wani wai dan a na tausaya miki a yi rushing aurenki in ki ka bari aka tafi a haka har abada gani za su yi kamar alfarma su ka yi miki, ki kwantar da hankalinki in kinga ba ki auri Isma’il ba to ba Mijinki bane ba, ina guje miki shiga gidan miji babu daraja Afra sam kar ki yarda da hakan kin ji ko? Kar ki yarda a ci miki fuska! Ba wai auren ne ba ma so ba a’a rainin wayon da su ka zo da shi ne ba ma so sam-sam dan Allah kema kar ki yarda da shi, a bi komai a hankali a kwatar miki hakƙinki da darajarki in Mijinki ne za ki aureshi amma in ba Mijinki bane ba yadda su ka soma wulaƙancin nan za su iya ƙasƙantar da ke kuma still su hana auren tunda har su na gani kamar alfarma za su yi miki, sannan Annenki mace ce fa kawai da ta ke frank haka Allah ya yi ta ba wai muguwar banzar shaidar da su ke shirin ƙaƙaba mata ku ku ke son karɓa hannu bibbiyu ba, akwai Matan da su ka fi ta fitina ma kuma an auri ƴaƴansu wasu ma karuwai ne amma surukansu su na darajasu da girmamasu dan haka kar ki yarda a ɓata miki sunan Mahaifiya a ɓata miki tarihinki sannan a raina miki ita, shawara ce kyauta na baki ki yi tunani a kai….ki taimaka ki takawa isma’il burki tun yanzu dan in an tafi a haka ba za ki ji daɗi ba gashi daɗin daɗawa shine komai naki tun ki na Yarinya dan haka in ya fara goranta miki za ki sha wahala, shi aure daga ɗokin amarci ya fita halin kowa ya ke fitowa… Kayan ɗaki na yi alƙawari zan yi, ni da Annenki kin san dai in na ce zan yi abu to zan yi ko? Dan haka ki nutsu kuma ki yi tunani na san ki na da hankali da zurfin tunani, sai ki yi abunda ya dace…..” Ga mamakin Anne sai ta ga Afra ta hau ɗagawa Kaka Nura kai a hankali kafin ta ce “tam” Murmushi ya yi ya shafa kanta tukunna ya ce shikenan ki je abinki sai da safe ko? Allah ya yi miki albarka…. Jikinta a matuƙar sanyaye dan ba ma ta san ta ina za ta yi tunani ba sun soma birkitata, haka nan ta juya ta fita kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki…. Sai da Anne ta tabbata Afra ta shige ciki tukunna ta ce “ka na ganin maganganun nan sun yi aiki?” Murmushi Kaka Nura ya saki kafin ya ce “ae shi Yaro duk wayonsa in ka ɗauresa ta koina dole za su bi ta inda ka ke so ne, ki jira ki ga ikon Allah ko duk ba su shiga kanta ba dole wani ya shiga. Ki kwantar da hankalinki na san wacece Afra ba ta so a taɓa mata darajarta da na ahalinta, ae Habu da shi kanshi Usman ɗin sun yi laifi dan kamar sun bada ƙofa ne… Yanzun nan fa da Samuel mu ka rabu, jari ya ke shirin bata miliyoyin kuɗaɗe! A haka su ke so su aurar da ita a Isma’il dan hauka da rashin sanin ciwon kai, hmm Ana nuna musu Annabi su na runtse ido, Allah wadaran naka ya lalace…” Cikin sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Anne ta ce “Ameen” Sannan ta ce “amma ka na ga ko ita Afra ta birkice za su yarda a ɗaga bikin nan kuwa anya..” Dariya Kaka Nura ya yi sannan ya ce “Bari ta birkicema Isma’il ɗin ki ga ikon Allah, ae su kansu akwai shakku a kansu dama trigger kawai yakamata mu nema kuma gashi mun samu damar dasa ta cikin sauƙi, ke kuma daga nan sai ki san abun yi kafin wani ikon Allahn ya sa a daidaita tsakani.” •••••••••• Vietnam, Asia. Ho Chi Minh(Saigon) 5:30am Babban gym ne wanda ya ƙunshi komai da za a buƙata a duk wani gym har ma da extra! Girmansa har abun ban mamaki yayinda kayayyakin da su ke a ciki kai kana gani ba sai an gaya maka ba ka san each and everyone ƙarshe ne a fannin tsada quality da kuma kyau! Sai wanda aka gayawa ne zai san cewa personal gym ne ba public ba saboda tsabar yadda ya ke da girma, kyau da kuma yadda aka narka uwar dukiya a cikinsa kamar ba gobe. Bayaga kayan ciki sai wasu maka makan speaku da su ke a cikin wajen suma har abun tsoro dan tsawonsu da faɗinsu ma kaɗai abun kallo da mamaki ne , ɗaya ta ɓangaren dama ɗayan kuma ta ɓangaren hagu, su na fidda wani sauti na asalin duma mai tsananin ƙara da ratsa kwakwalwa. Gudu ya ke yi sosai akan treadmill machine ɗin dan ya kaishi kusan ƙarshe, ga uban kiɗa ya ƙure, ya na fidda zufa ta ko wacce ɓular gashi da ke a jikinsa…kallo ɗaya tak za ka yi masa ka fahimci ranshi a masifar ɓace ya ke dan yadda ya ke gudun ya na huci kaɗai ya isa ya faiyyace maka hakan… Dogo ne sannan ƙaƙƙarfa wanda motsa jikin da ya maida ɗabi’arsa ta yau da kullum ya taimaka sosai wajen sake maida shi murɗaɗɗe sai dai ba chan sosai kamar na ƴan wrestling ba kawai dai ka na ganinsa ka san ya ji exercise yadda ya kamata… Ba za a kirashi fari ba sannan ba Baƙi bane ba wanda hutu da asalin jin daɗi su ka taimaka kwarai da gaske wajen sake tsara fatar tashi da colour ɗinta ta zamto abar sha’awa, kallo har ma da ban mamaki…. Ya jima ya na gudun ya na furzar da numfashi ganin ɓacin ran ya ƙi raguwa sam-sam ya sanya kawai ya danna abun ya fara slowing down a hankali a hankali kafin ya chan kuma ya tsaya chak! Gege da gefen handle ɗin ya kama duk biyun ya tsaya ya ɗan rankwafa yayinda fuskarshi ta ke kallon ƙasa ya yi shiruuu kawai trying to calm himself down amma sam ya gagara! Zuciyarsa sake hawa kawai ta ke yi, bai san lokacin da ya ɗago ya yi fatali da bottle water ɗin da ya ɗaura a kan machine ɗin ba sai kuma ya yi shiruuu kawai ya ƙurawa bottle water ɗin idanu… Kafin chaan ya ɗauka remote ya kashe kiɗan sannan ya lumshe idanunsa sosai ya na mayar da numfashi… Ba wai abunda ya faru bane ya ke sake ɓata masa rai ba, yadda abun ya ɓata masa rai ne main damuwarsa saboda a kaff yanayi da tsarin rayuwarsa bai kamata ya zama envious akan kowa ba…ba ya yi kuma ba ya so ya fara, duk da dai shi ya kamata a bawa, kowa ya shaida hakan kawai kwatsam ya ga an bawa wani but still kamata ya yi yai masa murna dan its obvious to him ba wai betrayinng nasa da aka yi bane ya fi fusata shi ba yadda aka ɗauki matsayin da ya yi working very hard for it aka bawa waninsa ne ya fi ɓata masa rai… Wanda shi kuma he hate the feeling sosai he’s not suppose to be this envious no matter what…. Ƙarar wayarsa ce ta katse masa lissafin da ya ke yi, a hankali ya buɗe idanunsa waenda su ka kaɗa su ka yi jazuur! Har abun tsoro…. Bai ko motsa daga inda ya ke a tsaye ba ballanta a saka ran zai amsa, a haka har aka jera masa 5 misscalls, tun ɗazu ake ta kiransa yana ganin wayar ta na ta yin haske daga nan inda ta ke a kan kujera wanda yadda aka kirashi a yanzun a jejjere kaɗai ya isa ya fahimtar da shi wacece dan duk duniya ita ɗaya ce kwallin kwal ta isa ta yi mishi kalar wannan kiran ta dameshi har haka… Tunowa da ya yi da ita da kuma yadda ta samu audacity na takura masa ya sanya ransa ya harzuƙa ya sake ɓaci! A hankali ya ɗaga kanshi sama ya runtse idanunsa kafin ya furta “Ya Subahanallah…..” Ya jima a haka bai ko motsa ba kafin ya sauƙe kan nasa ya na mai jan numfashi tukunna ya juya kawai ya nufi bathroom ɗin da ke a cikin wajen ya na shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi, sai da ya ɗan soma dawowa dai-dai tukunna ya shiga zamiye kayan jikinsa a hankali cikin nutsuwa ya yi wanka mai ma’ana da tsafta. A nan cikin bathroom ɗin ya shirya tsaf ta inda ya shafa mai ya fesa turare sannan ya sanya wata hoodie mai asalin kyau da tsada milk colour brand na Nike wadda ta taimaka wajen sake fito da shi ras! Tukunna ya fito daga cikin bathroom ɗin ya na zuba ƙamshi da asalin kyau! Domin kuwa in dai maganaar kyau ne ake yi tabbas ya ci a bawa ASAD award, namba ɗaya!. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota011 *30* Ya na fitowa ƙarar wayarsa ce ta yi masa sallama, kamar ba shi ake kira ba haka ya yi dan sai da ya tsiyayi coffee ya ɗan yi sipping har kusan sau uku ma tukunna a nutse ya ƙarasa inda wayoyin nasa su ke zube nan kan kujera. Kamar yadda ya zata ɗin kuwa ya na kai idanunsa kan screen ɗin wayar da ta ƙi daina ƙara ya ga sunanta ɓaro-ɓaro akan screen ya na yawo “Ummee” Tsaki ya yi kawai ya zubawa wayar idanu ransa na kammala ɓaci, kafin kuma ya ɗauka ta na gab da katsewa ya yi rejecting! Shiruuuu, ya yi kamar ba zai yi wani abun ba sai kuma kawai ya kashe wayar sannan ya kashe ragowar saboda ya na so ta san ba katsewa kiran ya yi ba shine ya kashe sannan ya kashe wayar ma gaba ɗaya as a result of annoying calls nata da ta ke ta damunsa da su kamar ba ta san safiya ce a nan ba! Besides ta ya ma za ta kirashi yanzun da ya ke da tabbacin sha biyu ta wuce ma a Nigeria…… A aljihu ya zuba wayoyin nasa, ya ajjiye cup ɗin a wajen sannan ya wuce zuwa wajen elevator wanda zuwan nashi da kunnawar da ya yi ya shigeta ne zai sanya a fahimci ashe gym ɗin underground ne a cikin haɗaɗɗiyar villar tasa da ke a cikin birnin Saigon ɗin. …… Tsaye take ta na ta faman kai kawo a tsakiyar tafkeken parlourn nashi da ke a ground flour! Ganin hakan ba zai fishsheta ba ya sa ta ɗago wayarta ta sake gwada kiran layin nashi. Jin ba ta shiga ba a kashe, ya sanya ta sake tabbatar da tabbas rejecting ya yi ɗazun kenan kuma ya kashe wayar ma gaba ɗaya duk dan saboda ita…. Kamar ta haɗiye zuciyarta haka ta ji, gashi wae da ikon Allah an hana ta hawa sama a iyaka wannan parlourn masu yiwa gidan hidima su ka barta a gantale kamar basu san matsayinta a wajen Mai Gidan ba! “Ko da ya ke ba laifinsu bane ba ae, shi ya bada fuska dan ina da tabbacin ma hakan dokarsa ce…” Ta furta hakan a hankali kwallah ta na taruwar mata a idanunta. Dai-dai nan ƙarar tsayuwar lift ta iske kunnuwanta, sai dai sam ba ta yi tunanin shi ɗin ne ba dan haka ko yunƙurin juyawa ma ba ta yi ba. Tana ta ƙoƙarin ganin ta hana kanta zubda hawaye yayinda shi kuma tunda lift ɗin ta buɗu ya ƙurawa bayan nata idanu sosai ya na mamaki A ranshi ya ce “zuwa ta yi kenan.....” Gold ne ƴan Ubansu a hannayenta da ya ke iya hanga sannan lace ɗin da ke a jikintaa kallo ɗaya za ka yi masa ka san cewa mai asalin tsada ne na fitar hankali, suitcase da handbag nata duk suma na bugawa a jarida ne haka vail ɗinta shim, a taƙaice dai ka na ganinta ka ga kuɗi! A hakan ma ba ta kai ga juyowa gaba ɗayanta ba. A hankali Asad ya sauƙe ajiyar zuciya, dama yadda ta ke ta kiransa tun jiya yau kuma a jejjere ko shakka babu ya san wani abun ta ke da buƙata a wajensa! Yanzu kuwa da ya ganta a nan ɗin ya tabbatar tunda daga gani ba tambaya kasa haƙura ta yi ta taho da kanta. "Good morning sir" Muryar Jessica(a maid) Ta katsewa duk su biyun lissafin da su ke yi. Da mugun sauri Ummeen ta juyo har kamar za ta kifa dan sau bakwai elevatorn na yin ƙara in ta juya sai ta ga ba shi bane ba masu yiwa gidan Hidima ne su ke ta kai kawo, shiyasa yanzun ma sam ba ta kawo shi ɗin bane ba. Fara ce sosai tass!! Dan har ɗaukar idanu ta ke yi, ba ta cika tsayi ba sannan ta na da ɗan jiki, a fuska kuwa in ka kalleta kai tsaye za ka fahimci ta na matuƙar kama da Asad wanda hakan zai sanya a gane ita ɗin Mahaifiya ce a garesa. Kamar yadda gold su ka yi mata ƙawanya a hannu haka nan wuyanta da kunnuwanta har ma da ƴan yatsunta abun har kamar hauka tsabar yawa da girmansu...... "morning" Kawai Asad ya ce da Jessica daga nan ya nufi masters bedroom ɗinsa wanda ya ke a nan ground floor ɗin dan a cikinsa ya shirya hutawa yau, ko kallon Inda Ummee ta ke tsaye bai sake yarda ya yi ba tunda ta juyo, gashi ya haɗe rai tamau! Kamar bai taɓa dariya ba, hatta ragowar Maids ɗin da su ke ta gaida shi hannu kawai yake ɗaga musu. Har ga Allah Ummee is the last person that he want to see a wannan hali da situation ɗin da ya ke a ciki, dan bayaga selfish reason ɗinta da ya ke da tabbacin shi ya kawota garesa ya san tabbas kafin su rabu sai ta ɓata maasa rai maƙura..... Gadan-gadan, haka Asad ya nufi bedroom dan Allah Allah kawai ya ke yi ya shige ciki ya rufo ƙofar, sai dai kasancewar ta fi shi kusa da ɗakin ya sanya ta yi nasarar shiga gabansa ta inda ta yi wani abu mai kaama da gudu da sauri sannan ta riƙe masa hannu ƙam! Tana mai mayar da numfashi Tabbas da ace ba ta riƙe masa hannun ba zagayeta zai yi ya wuce ciki abinsa.....ba ya son ganinta ne sannan ba ya ƙaunar tsayuwa kusa da ita sam-sam, dan ganinta ya na tuno masa da abubuwan da ya yi going through duk saboda selfishness ɗinta sannan tsayuwarsa a gabanta haɗari ne a garesa dan tsaf zai iya aikata mata abunda ya san bai kamata ba na rashin kirki a matsayinta na Mahaifiya a garesa. "Excuse us" Ya ce ba tare da Ya juya ya kalli kowa ba, a take Jessica da ragowar Mutanen da su ke kai kawo duk suka bar parlourn. A hankali Umme ta ce "Ikon Allah, son ba ka ganni ba ne?" Sai da ya ɗauki lokaci tukunna ya ce "I'm very tired, bacci na ke so in yi, what do you need?” Murmushi ta yi sannan ta sake ruƙo hannunsa kafin ta ce"akwai wani abu da zan buƙata other than to see my son? Na yi missing naka ne sosai shine na taso in zo in ganka" Yadda ya ƙura mata ido ne ya sa ta yi shiru sannan ta gagara sake cewa komai a hankali ta kawar da kanta gefe. Kamar ɗazu yanzu ma sai da ya jima tukunna kamar an yi masa dole ya ce "tunda ni ki ka zo gani, ki zauna mana ko a shirya miki ɗaki ma sai ki huta, kafin nan nima na huta sai mu gaisa da kyau ki ganni....." Ya ƙarashe maganar cikin gajiyawa dan har ga Allah gani ya ke ta saka shi surutu da yaawa, yawan magana ba ya daga cikin ɗabi'arsa. A ɗan diririce ta ce"Nooo, ae drivern da zai maida ni airport ya na waje ban barshi ya tafi ba, ka zo dai ka ɗan zauna mu gaisa sai in wuce. Lumshe idanunsa Asad ya yi a hankaliii... Kafin chaan ya buɗe sannan ya ce "Kin ganni ba sai mun zauna ba,good bye. In kuma hirar ki ke so to ki jira in tashi a barci. Kaina ciwo." Daga haka ya zame hannunsa da dabara da hanzari tukunna ya zagayeta ya shige ɗakin nasa ya na shiga ya saka lock a hankali ya jingina a jikin ƙofar... For once yau dai ya yi kwaɗayin inama ace da gaske zuwa ɗin ta yi domin ta ganshi ta ga lafiyarsa sannan ta ji ya yake! Dan tabbas yana buƙatar hakan... shekaru biyar kenan yau ya na aiki tuƙuru da dukiyarsa da kwakwalwarsa akan wani gagarumin company da su ka yi nasarar buɗewa, amma kawai jiya aka sanar masa ba shi za a bawa matsayin ceo ba wae age nashi sun yi kaɗan as ceo na babban company kamar wannan!. Mutane da yawa sun fusata saboda kowa ya san shi ya fi chanchanta a bawa duba da yadda ya tsaya tsayin daka wajen ganin abun ya kafu, shi da kansa ya dinga rarrashinsun dan dayawan ƴan board ɗin cewa su ka yi za su cire shares ɗinsu amma ya tsaya tsayin daka nan ma bai yi ƙasa a guiwa ba sai da ya rarrashi kowa ya tabbatar komai ya daidaitu.... Shi har ga Allah bai ji haushin kowa kuma bai riƙe kowa a rai ba dukda kuwa an yi dissappointing nashi ne amma ya mantar ya yi fatan Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi….kawai shi main abunda ya ke damunsa a halin yanzu shine yadda ransa ya ke ɓaci ya harzuƙa sosai fiye da yadda ya kamata, wanda sam ba yin kansa baneba! He even hate the feeling wallahi dan ji yake yi kamar ana kunnoshi akan abunda Ya riga ya fawwalawa Ubangiji komai, ya karɓa Hannu bibbiyu… Dauriya ce kawai ya ke yi amma tabbas a yau ɗin he needs someone na jikinsa sosai da zai bashi Baki, he need a shoulder to lean on…yau kam...dan ya gagara gane kansa, gaba ɗaya a burkice ya ke, sam ba ya son abun nan da ya ke ji, its not him gaskiya. Da ƙarfi ya jaa numfashi ya sauƙe sannan a fili ya ce "Love and care is fake, ba ya existing a duniyarnan, mutane ne kawai su ke faking nashi." Daga haka ya nufi bed ɗin ɗakin ya zauna bayan ya sakawa kanshi zai yi handling ya yi surviving test ɗin (ɓacin ran da burkicewar) kamar yadda ya saba dealing da dukkan trials ɗinsa na rayuwa....all alone!!!!. Ya jima a zaune kafin ya janyo computersa ya kunna cctv ya na ta kallonta, har addu'a ya tsinci kansa da yi Allah ya sa da gasken ta ke zuwa ta yi takanas domin ta gansa dukda kuwa ya san zai yi wuya... Yanayinsa ne ya ji yana sauyawa yayinda wani kalar maɗaukakin ɓacin rai wanda shi a karan kansa ya san its not normal ya soma mamayeshi ya na cin ƙarfinsa, sai kuma kamar wanda ya bugu ya yi maƙil! Wani kalar nannauyan barci ya yi awon gaba da shi. Wani irin mugun mafarki ya soma yi….ta inda ya ganshi daga shi sai mutumin da aka bawa ceo a tsakiyar wani ƙungurmin daji, mutumin a kwance rashe-rashe ko motsi ba ya iya yi, sakamokon ɓarnar da Asad ɗin ya yi masa a ciki kuma ya ke kan yi….sam yanayin da ya gansu a ciki ba mai kyau bane kuma shi a karon kansa ya san its impossible dan ko a gigin hauka ya ke to fa ya san ba zai taɓa cin wata halitta daga jikin mutum ba a dafe ma ballanta ɗanya…. Dan haka hankalinsa ya kai ƙololuwa wajen tashi! Gashi ji yake yi kamar gaske! Wani irin abu dai kamar a farke kamar a mafarki kuma duk yadda hankalinsa ya yi maɗaukakin tashi sam ya gagara hana kansa...... Sun jima a haka kafin dabara ta faɗo masa ai kuwa a gigice ya shiga ambaton sunayen Allah da duk wata addua da ta zo kanshi a wannan lokacin,cikin hukuncin Ubangiji ya farka bakinsa ɗauke da salati sai dai da ikon Allah a baƙin ƙofa ya tsinci kanshi computersa kuma ta tarwatse….gaba ɗaya sai ya sake gigicewa sannan ya tsorace gashi sai ji ya ke kamar ya amayo da dukkan abubuwan da jikinsa ya ƙunsa saboda he is very disgusted by the dream! Ga kuma ƙarni da ya ke ji bayan ya farka ko dan ya saka abun a kansa ne oho dan kaɗan-kaɗan ya ji ƙarnin ya na ta guduwa. Tsoro da tsantsar tashin hankali ne su ke sake mamayeshi, yayinda wata zuciyar ta shiga ingizashi da ya duba cctv na ɗakin ko zai iya ganin mai ya faru…dan ya ma kasa nutsuwa ya yi lissafin komai da kyau, kwakwalwarsa duk ta cunkushe tsabar tsoro al’ajabi da kuma mamaki, dan haka ya miƙe daga nan bakin ƙofar inda ya ke ya ƙarasa wajen wata cp ta daban ya shiga dubawa…. Ko da ya duba bai ga lokacin da ya ke a bakin ƙofar ba computer kuma shine ya turota ƙasa garin barci daga kan gado, farkawa kuma a kan gado dai ya yi a gigice kafin ya miƙe ya ƙarasa ya buɗe wannan cp ɗin da ya ke ta faman dube-dube a cikinta yanzun…..saɓanin shi da ya ke da tabbacin a bakin ƙofa ya farka tukunna ya miƙe ya ƙarasa ya je ya kunna cp ɗin. Da masifar ƙarfi ya dafe kansa jin yana shirin tarwatsewa kafin ya shiga jero addu’o’i…. ƙirjinsa ya na dukan tara-tara gaba ɗaya ya hargitse…. Tsoron ɗakin ma ya soma ji dan haka yana jiri sosai ya buɗe ƙofar ya fito gaba ɗayansa a ɗimauce sannan a firgice ga wani kalar maɗaukakin tsoro da ya ke sake mamaye shi jikinsa har karkarwa ya ke yi. Kasancewar gaba ɗaya hankalinta ya na a kan wayar da take yi ya sanya sam-sam ba ta ji fitowarsa ba… Ko a hargitse Asad ya ke Allah ya na bashi ikon riƙe kansa dan he's very gentle and calm all the time... Shiyasa yanzun ma tsoro da hargitsin da ya ke a ciki ba su saka ya yi motsin da har za su sanya ta fahimci ya fito ba..... "Kar ki wani damu fa, ya na fitowa zai yi mana signing ɗin sai in taho in kawo, ki ce su ƙara mana lokacin dan Allah, ba na so in yi gaggawa ne zai gane ba wajenshi na zo takanas ba." Muryar Ummee ta sauƙa cikin dodon kunnuwansa. Ajiyar zuciya ɗayar Matar da su ke wayar da ita ta sauƙe sannan ta ce"Ummee ki bar batun wani bounding, ba yanzu ba, focus pls. Wannan contract ɗin in mu ka samu mun haye its a life changin chance muna buƙatar influencial people kamar shi ya yi mana signing… Daddy ya yi har na basu amma sun ce in ba a kawo second one ɗin ba within 10hours wallahi za su bawa wani” Salati Ummee ta yi kafin ta ce “kinga Asad zai janyo mana asara ko? Akan wani care da na ke so in nuna masa na banza da wofi!! Shikenan ba komai na san mai zan yi! Bara ya fito zan san yadda zan yi ya bamu letter sannan ya yi signing in sha Allahu ba za mu taɓa rasa contract ɗin ba…” “Ina papers ɗin su ke?” Ta ji voice nashi a dake a bayanta. Da mugun sauri ta waiga aikuwa karaff su ka haɗa idanu da shi, idanunsa jazirr gashi duk da build in ac’s ɗin da su ka yiwa parlourn ƙawanya wani kalar gumi ta ga ya na yi na ban mamaki!! A ɗan tsorace ta miƙe dan yanayinsa ya bata tsoro kwarai ta ƙarasa garesa ta ce “mai ya faru da kai? Are you okay?” Sai da ya haɗiye wani ƙululun abu da ya tokare masa maƙoshi tukunna ya ce “Ummee ina abunda ya kawoki ƙasar nan ya ke…” Cikin tarar numfashinsa ta ce “son kai ne ka kawo ni mana, i want to see you” Da ya ke ita ɗin gwanace a tsaurin ido sai ta ci gaba da cewa “wanchan maganan kawai wani abu ne da za mu yi in ka samu lokaci amma na zo ne asali domin in ganka…” Sai da ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ɗan furzar da iska sannan ya ce “Ummee, for the last time ki kawo abinda ya kawoki in yi miki yanzu ki wuce, in ba haka ba kuma ko kin bani daga baya ba zan yi ba sai dai mu zauna ni da ke ki yi ta kallon nawa…..” Ya faɗi hakan ransa na suya sosai, duk inda ya kai ka son kaucewa baƙanta mata a matsayinta na Mahaifiyarsa ita kuma ala dole sai ta yi pushing nashi, bai san dalilinta na yi masa hakan ba. Ta san halin Asad sarai kaifi ɗaya ne ba ya magana biyu, ita kuma har ga Allah in ta rasa contract ɗinnan tabbas daga ita har ƙawartata sai an yi admitting nasu a asibiti, dan haka ba kunya ba tsoron Allah ta je ta buɗe suitcase ta zaro takardun da ta zo da su, da wani blank paper ƴan rubutu a sama da ƙasa kaɗan ta bashi… Dukda halin da ya ke a ciki sai da ya duba, da ya ga no need of ya yi prolonging kawai ya yi mata komai a take! Ta inda ya rubuta Letter a blank paper ya yi musu guarantor ya yi Signing, ragowar takardun kuma duk ya yi mata signing nan ma ya cike komai da take buƙata daga haka ya miƙe ko kallonta bai yi ba ya ce mata “good bye” Sannan ya wuce sama. In ta ce za ta tsaya rarrashin Asad tabbas zai janyo mata asara ne dan sai ya cinye lokacin da aka basu tass! Kuma ba lalle ya huce ba. Dan haka ta ɗauki jakarta da suitcase ɗin da ta zuba takardun ta fito zuciyarta fess ta nufi airport dan farin cikin samun contract ɗin tashi ɗaya ya mantar da ita ƙuncin da ta gani ɓaro-ɓaro baiyyane a kan fuskar gudan jinin nata. …..ko da ya isa ɗaki sai da ya yi da gaske tukunnna ya iya controlling ɗin kansa. A hankali ya ke karantun Alqurani yayinda ya runtse idanunsa da masifar ƙarfi….. Kaɗan-kaɗan ya soma jin sauƙi. Babu wani abu da Ummee ta nema ta rasa a jin daɗin rayuwar duniya dai ba ta rasa komai ba amma a ko da yaushe burinta shine ta tara dukiya bai san ina za ta kai ba……. Ba wanda ba za ta iya baƙantawa ba a kan hanyarta ta neman kuɗi, sam ba ta kara. Knocking ɗin da aka yi masa ne ya katse masa lissafin da ya ke yi ba tare da ya ɗago ba a hankali ya ce “come in” Kawai….. Cikin ladabi Jessica ta gaida shi bayan ta shigo sannan ta miƙa masa wayarta ta na mai sanar masa cewa “Daga board ɗinsu ne tun ɗazu su ke ta nemansa sun ce wayoyinsa a kashe ne, ana son magana da shi…” A hankali ya saka hannu ya karɓa, sannan ya kara a kunnensa har kawo yanzu bai kai ga buɗe idanunsa ba! Ya ce “talk to me..” “Hello Sir!!” Ya ji muryar secretary ɗin ɗaya daga cikin su… Da mugun kyar ya iya ce masa “i’m listening…..” “Cikin harshen turanci mutumin ya gaida shi sannan ya shiga sanar masa cewa “Allah ya yiwa mutumin da aka naɗa ceo rasuwa yanzunnan! Haka kawai aka ga ya na kashi wani kala kuma ya gagara tsaida shi ga amai shima ya na yi ta Baki kalar kashin!. Sai da aka kai shi asibiti tukunna Likitoci su ka tabbatar da gaba ɗaya kayan cikinsa sun lalace, ta yiu poision ya sha! Dan kashin da aka ga ya na yi ashe hantarsa ce da ta zagwanye ta ke fitowa ta ƙasan nasa da Bakinsa. Ragowar kayan cikin nasa suma komai ya lalace…..” Asad bai iya jin ƙarshen zancen ba ya kashe wayar da wani kalar masifar sauri jikinsa ya na maɗaukakin karkarwa kafin ya iya buɗe idanunsa da kyar ya na ganin dishi-dishi. ••••••••••••••• Ana shiga masallaci (sallar asuba) Anne ta fita dan jiya da daddare malaminta ya yi mata kwatancen wata shuka da za ta cira ta kai masa kuma kafin alfijir ya keto ake so a ciri shukar da asuba. Ya yi mata alƙawarin indai aka yi wannan aikin to Afra za ta sake burkicewa ne hankalinta ba zai kwanta ba har sai ta bar Isma’il. ….. Duk yadda Isma’il ya so kasa daurewa ya yi dan haka gari ya na kammala yin haske ya isa ƙofar gidansu Afra ya kirata a waya, ransa na sosuwa amma wani abu mai kama da kishi da ɓacin rai yana daɗa ingizashi da tabbatar masa cewa hakan da ya tsara zai yi shine dai-dai…… Zai dai faiyyace mata ba zarginta ya ke yi ba kawai dai ya tambaya ne kuma ya na so ya ji abunda ya tabbatar (ba ta je ɗin ba) daga Bakinta. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota011 *31* Tana zaune, ta na lazimi a lokacin da ya yi kiran nata wanda abun ya bata mamaki sosai dan time ɗin ya yi safiya da yawa. Sai da ta idar ta yi addu’o’inta tukunna ta miƙe ta fito ta je ta sanarwa Adda ‘Ya Isma’il ya na nemanta a waje’ tukunna ta fita ta bar Addan ta na addu’ar ‘Allah ya sa lafiya’, dan haka kurum ta ji hankalinta bai kwanta ba sannan har yanzu ba su kai ga gaya mata me ke wakana ba….me aka tattauna jiyan da ba ta je ba! Dan haka zulluminta sai ya hauhawa. A tsaye ta sameshi ya jingina da jikin bangon ƙofar gidan da ɓangarensa na dama ya na kallon ƙasa…. Ka na ganinsa ka san cewa tunani ne ya ke yi. Har ta ƙaraso garesa ta tsaya bai sani ba, sai da ta ce “Ina kwana Ya Isma’il.” Tukunna a hankali ya ɗago kyakkyawar fuskarsa ya zuba mata kyawawan idanunsa waenda ka na kallonsa za ka fahimci akwai damuwa ƙunshe a ƙasan ransa… Ƙuraa mata idanuwa ya yi har sai da ta ɗan tsargu sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa sosai. Tukunna ya ce “Lafiya ƙalau Alhamdulillah, da fatan kin tashi lafiya.” A voice na shi ma kai tsaye ta jiyo damuwa dan haka duk takaicin da ta ƙunsa jiya a ta dalilin cin fuskar da shi da Mahaifinsa su ke so su yi mata sai ta ji ya na ta sauƙa…zuciya da abunda ta ke so! A take ta ji kwaɗayin son jin me ke damunsa domin ta samu ta share masa hawayensa….. A hankali ta ce “Alhamdulillah.” Sai kuma ta ɗaura da cewa “Na ji muryanka wani iri, Allah ya sa ka na lafiya….” Sai da ta ɗago ta ɗan saci kallonsa saboda yadda ta ji ya yi shiruuu, ganin ita kawai ya ke kallo ya sanya ta yi saurin mayar da kanta ƙasa ta shiga wasa da ƴan yatsun hannayenta da junansu. A hankali ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya ce “Afra kin san ina sonki ko? Sannan na san kin san na yarda da ke!” Da sauri ta ɗago ta kallesa kafin ta maida kanta ƙasa jin ya kira sunanta yau! Tabbas abu mai mahimmanci ke tafe da Ya Isma’il dan haka ta sake nutsuwa bayan ta aiyyana hakan a ranta ta bashi dukkan hankalinta, sannan a hankali ta ce “eh” “Good” Ya ce kafin ya ɗaura da cewa “wasu mutane ne su ka fara kai sukarki gidanmu, har da cewa wai an ganki a hotel da ke da Samuel…” Da mugun sauri ta ɗago ta kallesa da idanunta waenda a take! Su ka soma sauyawa… Da sauri shima ya gyara tsayuwarsa cikin sigar rarrashi ya ce “sam! Ko kaɗan ban yarda da su ba, ki kwantar da hankalinki, amma pls i want to hear you say it….. Ina so in ji kin ce mini ba ki je wajensa ba in ji daga bakinki, hankalina sai ya fi kwanciya…” Cikin tarar numfashinsa ta ce “na je, jiya…” Ɗiff!! Haka ya ɗauke wuta, ƙirjinsa ya shiga dukan uku-uku dan Ya Isma’l wani kalar mahaukacin kishi ke garesa… “Haushi ki ka ji kenan, shiyasa za ki gaya mini abunda ba shi kenan ba ko?” Girgiza kai ta yi, tsanar Anne na kokawar shiga cikin zuciyarta, dan ita dai tunda take a rayuwarta ba ta taɓa jin ta muzanta kamar na yau a yanzun nan ba… Muryarta na karkarwa ta ce “haka ne Ya Isma’il, da gaske na je, kuma kaima na san ka riga ka yarda da aka gaya maka dan in da ba ka yarda ba to da ba za ka yi mini maganar ba, sannan ba zan ganka cikin damuwa ba…” Kukan da ta ke ji yana ƙoƙarin zubo mata ta yi ƙoƙari ta danne da kyar sannan ta ɗaura da cewa “Amma wallahi Allah ba abunda ka ke tunani ya kaini wajensa ba, Anne ce ba ta da lafiya kuma ciwon nata is very severe shine ya ce in zo in amshi kuɗin abunda Likita ya ce mata dole sai an yi, da na fita kuma ya kwatanta mini hotel…ka yi haƙuri Ya Isma’il…..” A yau kam tabbas kishinsa da kuma ɓacin rai sun ci ƙarfin soyayyarsa gareta, dan wallahi shi kansa bai san lokacin da ya tari numfashinta cikin daka mata tsawa ya ce “in kin tambayeni kuɗi zan hana ki ne?” Girgiza masa kai ta yi a hankali ta ce “Ya Isma’il kana ta ɗawainiya, kuma kai da kanka na ji kana kukan abubuwa sun matse kwana biyu. Sannan ga batun aure a gabanmu kuma na ga ba abunda ya shafeni bane Anne ce” Cikin katseta yanzun ma da faɗa sosai ya ce “Amma ae kin tambayi wani banza ƙato chan!!! Ki rasa a wajen wa za ki yi roƙo sai a wajensa, sannan da ki ka fita ki ka ji ya ce miki hotel dan me za ki je? Ko jan ki ya yi ta ƙarfi ta yaji ban taɓa tunanin za ki je hotel ba! Ko ba ki yi komai a chan ɗinba kin san yadda zuwan naki zai zame mana matsala kuwa? Afra hotel fa! Idan ku a wajen ƴan gidanku zuwa hotel ba komai bane ba kin san a wajenmu babban abu ne ko?” Ɗagowa ta yi kawai ta zuba masa dara-daran idanuwanta waenda suka kaɗa su ka yi jazirrrr!! Sosai sannan ga ruwan kwallah ya cika su tap!. A take ya ji duk wata masifa da ta yunƙuro ya ci burin sauƙe mata ta gushe, sai kuma ya fara dana sani sannan hankalinsa ya soma dawowa jikinsa a take ya ga bai kyauta ba! Bai taɓa mata ihu ba ko a wasa sai yau!… “Damn it” Ya furta a hankali ya na mai runtse idanunsa da masifar ƙarfi, kafin ya shiga ƙoƙarin buɗesu da kyar! Ya na buɗewa ya ga wayam!!!! A hankali ya ce “Ya Subahanallah…..” Ya na mai ji kamar ya kurma Uban ihu, wae ko ya ji sauƙin kishi, baƙin ciki da tsantsar da na sanin katoɓarar da ya yi da suka mamaye shi su ka dannne shi a wajen sosai… A hankali ya sunkuyar da kansa ƙasa zuciyarsa na ƙuna da susa. “Kai dan *****uwarka goge mana plastar ka ke son yi ko meye hakan? Uban me ya fitar da kai da asubar nan ma? Wuce ka tafi gida ɗan muguwa, shege mai kama da Ubansa.” Muryar Anne ta dirar masa a dodon kunnensa, da alama Yaro ne ya ke taɓa bangon gidan shine za ta tashi jama’a daga barci da hayagagarta. Bai yarda ya kalli direction ɗin da ya ke jiyo muryarta ba, kawai ya saka kanshi gaba ya wuce da saurin gaske! Ba ya son ko da jin sunan Matar ne. Sai da ya sha kwana tukunna ta lura da shi (ya bar wajen) sakomakon Marin da ta tsaya kikkifawa Yaron ya ɗauke mata hankali daga kan Isma’il ɗin. Wae Yaron ya turo mata Baki. Ta so ta bishi a baya ta na kwala masa kira har sai ya tsaya ya gada ita wallahi dan ubansa. Ta lura ko haɗa hanya da ita ba ya ƙaunar yi saboda raini, amma da ta tuna abunda ta taho da shi ba ta so a lura a gane sannan ba ta so a fahimci ta fita, sai kawai ta kyale Isma’il ya wuce a fili ta yi kwafa kawai ta shige cikin gidan….Yo in ta bar wannan ɗan talakan banzan mai shegen raini ya auri Afra ma ae ba sunanta Nuratu ba wallahi….. “Daga ina ki ke?” Ta ji muryar Baba a bayanta, a dake kamar ba shi ba. Tun ɗazu da ta fita lokacin shi yana masallaci Ya Amir kuma cikin ikon Allah yau ɗin ya makara dan haka ya ganta…….. Ana idar da sallah kuwa ya sanarwa Baba Anne fa ta fita, dama idonsu a kanta ya ke dan sun san za ta yi wani abun, ya san Allah ne mai yi amma tsafi gaskiyar mai shi, shi kuma in sha Allahu wannan karon dai sai ya tsayawa Afra wallahi ba zai bari Anne ta yi galabar tarwatsa mata rayuwa da farin ciki ba! Tabbas ko shakka babu wajen boka ta je… Ya na cikin wannan lissafin Anne ta waigo ta wani kalleshi sama da ƙasa, kafin ta ce “ikon Allah” Ta na wani taɓe Baki sannan ta koma ta juya za ta wuceshi cikin wani kalar sauri Baba ya sha gabanta sannan ya sake jeho mata tambayar “daga ina ki ke?” Idanunsa a kan ledar, ta windown Masallaci ya ga wucewarta kuma dama tun da ya idar da addu’o’insa ya ke tsammaninta, ya na so ya ga ta ina za ta ɓullo, dan ya sake fahimtar me ta ke shiryarwa. Tunda Allah ya sa ya hangi ledar hannunta shikenan ya ji tsigar jikinsa ta shiga tashi hankalinsa ma ya tashi sosai, shiyasa ya biyota a baya masallacin ma Ya Amir ya barwa ya kammala rufewa. “Kai a su wa? Da za ka wani shiga gabana ka na wani huci kamar Namijin kwarai? Abeg dalla gafara in wuce soloɓiyo kawai.” Anne ta faɗi hakan cikin ɓacin rai dan ta lura da yadda ya ke ta faman bin ledar hannunta da kallo. Ya Abba tun da ya dawo daga sallah yau ma ya ke ɗaki dan har yanzu bai kammala hucewa ba, shiyasa da ya gaida Adda ya ke shigewa ciki ya zauna ko ya yi karatu ko ya yi tunani. Duk wata sana’a wuyarta ya soma cikin hukuncin Ubangiji ba ta tasiri, ya rasa me ke faruwa da rayuwarsa. A yanzu kamata ya yi ace ya na da mata har ma da ƴaƴa amma da ikon Allah shi kansa har yanzu ciyar da shi ake yi! Wannan abu ya na matuƙar damunsa da sauran tarin abubuwa masu yawa da mahimmanci a rayuwarsa shiyasa duk dauriyarsa kwana biyun nan abun ya ke cin ƙarfinsa kwarai. Tun ashar ɗinta na farko a ƙofar gida ya ji. Kasancewar ɗakinsa a soro ya ke sannan shi ɗin hancinsa kamar wani mai stabilizer ya ke dan abu duk ƙanƙantarsa sai ya ji! Hakan ya sanya ta na shigowa ya fara jiyo ƙarnin abunda ta zo da shi. Kamar ba zai kula ba, sai kuma ya ga ya dace ya kula tunda koma dai menene ta ke shirin yi family ɗin tamkar nasa ne bai kamata ya naɗe hannuwa ya zauna ba dan ko shakka babu wani surƙullenta ne ta je da sassafe ta zo da shi. Dan haka a hankali ya miƙe ya ajjiye littafin addu’ar da yake yi ya buɗe ƙofar ɗakin nasa ya fito idanunsa a kanta. Tun tijarar da ta yi masa a ƙofar gida sai yanzun ne ta ganshi, haka kurum ya yi mata kwarjini gashi ya kafeta da lumsassun idanunsa dan haka ta kawar da kanta ta maida dubanta zuwa ga Baba wanda ya tabbar mata ba zai barta ta wuce ba sai ta gaya masa daga ina take, ta ce “Habu ka dai san dambe da kai ba zai bani wahala ba ko? Ka matsa in wuce billahi ko mu kwashi ƴan kallo da kai a cikin soron nan…” Dai-dai nan Su Afra su ka ƙaraso cikin soron, haka Adda itama kamar haɗin Baki har da Ya Amir shima ya shigo daga rufe ƙofofin masallaci. Salati Adda ta yi sannan ta ce “Haba mana Anne, dambe kuma da mijin aurenki? A gaban ƴaƴanki? Ku yi haƙuri dan Allah Baba kaima ka bari mana, kar ka yi abunda ba ka iya ba…” Ta yi maganar itama idanunta a kan ledar ta na mamakin menene a ciki haka ya ke ƙarni….. Ganin an soma tara mata jama’a ga abu nan a hannunta da ba ta so a gani ya sanya Anne ba ta biyewa Adda ba kawai ta yi banza da ita ta fara ƙoƙarin wucewa amma fafur Baba ya ce “ba fa za ki wuce ba sai kin gaya min daga ina ki ke da asubar nan sannan da izinin wa ki ka fita!!!!” Ya na jira ya gama da wannan ya koma kan ledar da kowa a cikinsu bai yarda da ita ba, yau kam ƙaryarta ta ƙare! Ba za ta yi masa tsafin da ta saba yi a cikin gida ba wallahi. Sosai ran Anne ya harzuƙa ta gagara haƙuri ganin wanda ta raina ya na yi mata magana kamar wani Ubanta! Yo ko Kaka Nura ae ƙaryansa ya yi mata haka wallahii… Dan haka ta gyara tsayuwarta sannan ta ce “Mijin da ya isa! Ba wanda Matarsa ta ke ciyar da shi ba, shine in za a fita ake gaya masa sannan ake neman izininsa…” A hankali Amal ta sunkuyar da kanta ƙasa ta shiga ƙoƙarin ganin ta hana kanta yin wani kukan, dama tun da Afra ta shiga ta fara bata labarin abunda ya faru tsakaninta da Isma’il su ke kuka tare gwanin ban tausayi, da kyar su ka rarrashi kawunansu su ka share hawayensu su ka fito yanzun….. Wani kalar kallo, Ya Abba ya ke bin Amal da shi tun daga tsakiyar kanta har kan ƴan yatsun ƙafarta, gashi ba a isa a faɗi ransa a ɓaci yake, ko akasin hakan ba sam ba za a iya gane yanayin da ya ke ciki ba. Ta na gama dannar kanta ta ɗago kenan karaff su ka haɗa ido, kamar wata marar gaskiya da gudu ta shige bayan Afra dan da masifar ƙarfi ƙirjinta ya buga! Bai taɓa yi mata irin wannan kallon ba, direct kawai ka na ganinsa ka san ita ya ke kallo har kamar ma bai san da kowa a wajen ba sai ita ɗaya tak! Chan ƙasan maƙoshinsa ya ce “hmmm” kawai, wanda hakan ma da ya yi ba za ka gane haushinta ya ji, mamaki ta bashi, dariya ta bashi d.d.s ba. Kafin chaan ya sauƙe ajiyar zuciya a hankali sannan ya gyara tsayuwarsa ta hanyar sake rungume hannuwansa a kan ƙirjinsa sannan ya ce “Anne faɗar Allah ki ke yiwa kwaskwarima ko me?” Da masifar ƙarfi Anne ta runtse idanunta ranta na suya! Wato har da Abba ake titsiyeta yau a gidan nan tabbas zakanya ta yi sanyi! Kuma tunda shegen Yaron ya kulasu har ya saka Baki in ba da kyar ba sai ya tarwatsa mata shirintaa…a ranta ta ce “Ya Allah ka sa kar ya yi maganar ledar hannuna, Allah ka bani ikon wucewa da ledar nan zuwa kitchen lafiya…” “Sannan menene wae ki ka shigo da shi gidan nan a baƙar ledar hannunki mai ƙarni sosai haka? Daga ɗaki fa ƙarnin ya fiddo ni..”. A mugun mugun fusace Anne ta ce “Ubanka ne….” Sai kuma ta juya da masifar sauri za ta bar wajen. Da sauri Baba ya saka hannu ya ruƙo ledar tun ƙarfinsa, dama shima hankalinsa komai ya sake komawa kan ledar duba da yadda ƙarnin ya ke sake cika koina….. Kasancewar da sauri ta juya ga kuma ledar kalar ta zamani ce waenda kullum ake rage musu kyau da karƙo ya sanya duka ledojin biyu da aka yi amfani da su wajen saka abun a ciki su ka yage! Abun ciki ya faɗo ƙasa taɓal! Ya baiyyana a gaban idanun kowa! Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* HUMAIRAH BULAMA Yota011 *32* ••••••••••••••• Ƙarfe takwas dai-dai na safiyar ranar ta buɗe idanunta a hankali ta sauƙe su a kan robber ceiling ɗin da ke a cikin ɗakin. Wani mummunan mafarki ta yi wanda hakan ya sanya ta farka jikinta duk a mace, dan ko da ta buɗe idanun nata ma sai da ta shafe sama da mintuna ashirin a haka kafin ta samu ta miƙe ta zauna sai kuma ta shiga ƙoƙarin tashi ƙafafunta su na yi mata zugi sama-sama. Ba tunanin yin sallah, ba salati sannan babu godiya ga Ubangiji…haka nan ta ɗauki brush da macline ɗinta ta ɗauko pant da bra ta fito daga ita sai yololuwar rigar barcin da ke a jikinta komai nata a waje…fanɗarinka tsirara. A ƙa’idar gidan kafin Yagwalgwal ta fito ruwan wankanta ya na ajjiye a cikin flask a bakin ƙofar ɗakinta da bokitinta an zuba mata ruwan sirki a cikinsa dai-dai da na flask ɗin. Sai dai yau ɗin ta na fitowa ta ga wayam! Babu flask ɗin bokitan nata kuma ga shi a ajjiye a bushe ƙamas!! “Tashin hankali” Ta aiyyana hakan a cikin ranta zuciyarta ta na tafarfasa…. Sai kuma ta ɗaga kanta ta na kallon kowa ta na mamakin yadda ba a ma lura da ita ba ballanta a taho rututu kawo gaisuwa kamar yadda aka saba, instead hankulansu su na kan junansu ta inda aka yi group group ana ta ƙus-ƙus kamar wani dandalin munafurci, hatta masu wucewa suma bayani su ke yi a tsakaninsu ƙus-ƙus sosai. Da gudu Aimana ta taho gareta da flask ɗin har kamar za ta kifa kamar wata Yarinya, ta na zuwa ta durƙusa ta ce “Afuwan Uwa, itace ne a jiƙe yau ɗin, da fatan kin tashi lafiya….” Jikinta ya na karkarwa sosai ka na ganinta ka san bata cikin nutsuwarta… Wato a kaff jama’ar cikin gidan aka rasa yadda za a yi a haɗa mata ruwan wanka har ƙarfe takwas ta wuce…sannan da ikon Allah har yanzu kamar wasu ba su ganta ba hankulansu na a kan munafurcinsu ƙalilan ne su ka nufota da niyyar gaisuwa…. A hankali Aimana ta ɗauki bokitin ta tafi da shi domin ta je ta kawo mata ruwan sirki, bayan Yagwalgwal ɗin ta amsa gaisuwartata da kyar. Sai da ta gama amsa gaisuwar waenda su ka zo su ka gaisheta har ƙasa tukunna ta dakawa ragowar tsawa “Uban me ku ke tattaunawa ne?…” Da sauri duk su ka waigo gareta sai kuma su ka taho rututu su ka gaisheta kafin a fara watsewa kaɗan-kaɗan su na tsoron kar Ladiyo ta gansu. Wata Yarinya ce da Aimana su ka sirka mata ruwan su ka kai mata har bakin ƙofar banɗaki tukunna itama ta taho ta na tafiya da kyar kanta a ɗaure! Bara ta yi wanka ta shirya tabbas yau sai ta bawa Matan gidan nan mamaki akwai buƙatar ta tuna musu wacece Uwa. Ta na zuwa ƙofar banɗakin ta tsaya chak! Ranta a ɓace sosai ta ce “wae aljanun iya shege ne su ka shigi kowa ne a daren jiya? Ni zan ɗauki bokitin nawa da kaina in shiga…….” Maganarta ce ɗiff ta ɗauke ta saki kayan hannunta su ka faɗi gabanta ya yanke ya faɗi sakamakon wani jibgegen Gardi da ta gani ya fito daga banɗakin daga shi sai boxer da bokiti a hannunsa. Kallon-kallo su ka tsaya yi ita da shi kafin ya shiga kashe mata ido a ranshi ya na mamakin babbar mace mai irin dirin jikinta…. Cikin wata kalar razananniyar tsawa Yagwalgwal ta ce “wacce mai gangancin ce ta shigo mini da ƙato har cikin gida! Dan Ubanta…” “Ni ce nan!!!” Ta ji muryar Ladiyo a bayanta, sannan ta rarumo wani ashar ta dannawa Yagwalgwal ɗin a bakacin zagin Ubanta da ta yi itama…. Wani kalar masifaffen karkarwa jikin Yagwalgwal ya shiga yi, tsabar bala’i. A fusace ta juyo su ka hau kallon-kallo ko wacce ta na huci… Ladiyo kamar wata boss dama gata jibgegiya a fannin faɗin ƙashi. Da kyar baƙin ciki ya iya barin Yagwalgwal ta ce mata “tafiyarki da mu ta tsaya daga yau! Ki tattara komai naki ki bar cikin gidan nan! Hukuncin zagin da ki ka yi mini kuma zai biyo baya dan tabbas sai na azabtar da ke fiye da zatonki, in sha Allahu.” Murmushi Ladiyo ta yi sannan ta ce “idan ki ka ce in tattara komai nawa, to zan tattare jama’ata ne sannan zan tattare kuɗin asusun wannan ƙungiya da kuma wannan gidan da aka siya da kuɗin ko wacce ɗiya a cikinmu sabida a halin da ake ciki a yau da har gaban abada ni ce shugabaaaaa!” Ɗifff!! Haka wajen ya kasance kamar an yi ruwa an ɗauke kafin Ladiyo ta ɗaura da cewa “dan haka da ni da ke za a ga mai barin gidan nan muddin ki ka matsaaaaa! Amma idan ki ka kwantar da kai to ba ni da plan ɗin korar kiiiiii…” Hankalin Yagwalgwal a take ya soma tashi jin kowa ya yi ɗiff!!! Saɓanin in da ace da ne sai sun lakaɗawa Ladiyo dukan tsiya na rashin kunyar da ta yi mata…. Ta na wannan lissafin ta ji muryar wata a cikinsu ta yi gyaran murya babba ce sosai itama ana girmamata a gidan ta ce “Ammm…Yagwalgwal..” Da masifar sauri Yagwalgwal ta juyo ta kalleta ta na mamakin yadda ta kira sunanta haka. Sam Matar ba ta damu ba ta ɗaura da cewa “A gaskiya mun gaji da mulkinki! Saboda ba ki kaimu ga ci gaba sannan ba kya ɗaga darajarmu, tsoronki da gudun maganarki baya daga cikin ɗabi’un shugaba, Ga Ladiyo nan za ta jaa mu mu je gaba in sha Allahu, ba za ta dankwafar da mu ba…. Akwai abubuwa da yawa da ki ke yi waenda cutarwa ne a garemu, shiru kawai mu ke yi miki, amma saboda Allah ta ya za a ce mu na da ɗakunanmu amma mu dinga bi hotel hotel, wanda kuɗin hotel ɗin in an tattala mu ake bamawa…. Tunda ke ba za ki iya karawa da su Mai Unguwa ba! Ladiyo za ta iya dan haka ki haƙura ki koma gefe ki sha kallo kawai…..” Har wani jiri-jiri da dishi-dishi Yagwalgwal ta ke gani tsabar tashin hankali, da kyar ta iya cewa “akwai mai jaa a maganar da Khairiyya ta gama yi yanzun?….” Ɗifff!! Haka su ka yi kowa ya yi ƙasa da kanshi ya na guna-guni….Aimana ce kawai ta ɗaga hannu, ita ɗaya kwal! Wanda a tsari rabin mutanen wajen ne a bayan Ladiyo amma ganin da ragowar su ka yi Ladiyo ta fi power a wannan lokacin ya sanya su ka zaɓi suma su bi bayanta gudun kar ta yi winning ta haɗa da Yagwalgwal ɗin da su duk ta kora a cikin gidan, ko kuma a takura musu a mayar da su kamar bayi. Cikin sauƙe numfashi Khairiyya ta ɗaura da cewa “kin gani ae da idanunki, kowa kara ce kawai ya ke yi miki amma ki na kwarar mu! Ko baya ga haka ma a gaskiya ba zai yiu a ce kura da shan duka gardi da amsar kuɗi ba, tunda har ke kin yi retire daga buɗe ƙafa kamata ya yi a ce hatta kujerar ma kin yi retire a kanta.” Duk jaraba da masifar Yagwalgwal yau ɗin sai ta gagara cewa komai, hankalinta bai ƙarasa tashi ba sai da amintacciyar Ladiyo ta ɗaga hannu sama ta soma cewa "Ladiyo! Ladiyo!! Ladiyo!!!" Ragowar jama'ar wajen har da ƙaton kwarton suma duk su ka ɗauka, kowa ya shiga cewa "Ladiyo" Da ƙarfi su na ɗaga hannu. Jikinta Yagwalgwal har wani kalar karkarwa ya ke yi, ganin ana shirin yi mata juyin mulki a take a wajen ne ya sanya kawai ta juya da sauri ta bar wajen ta na ɗingishi. Ta na shiga cikin ɗakinta ta mayar da ƙofar da sauri dan har an soma biyota, dan haka ta rufe ƙofar ruff sannan ta saka sakata kafin ta juya ta jingina da jikin ƙofar jikinta ya na karkarwa... Sai kuma ta rushe da kuka sosai, ta na kukan ta zame ta zauna a wajen ta na haki. Abun kamar a mafarki haka ta ke jin sa, wai yau ita Yagwalgwal ce aka yiwa haka akan Ladiyo? da me Ladiyo ta fi ta fisabilillahi..ta ya za ta bada kujerarta a ladiyo kujerar da ta ke ji da ita. Kujerar da in har ta bada to fa ba ta da wani sauran gata a duniya, in ba nan ɗin ba ba ta da koina ba ta da wajen zuwa dan wallahi in aka kwace mata kujera sai dai ta bar gidan ba za ta zauna a ƙarƙashin Ladiyo ba ta san wahala za ta sha kwarai… Kujerar da itace cin ta shan ta suturarta, apart from all this ma ae babbar faɗuwa a garesu bai wuce a ce ki na kan kujera wata ta sauƙe ki ta hau ba! Shin da me Ladiyo ta fita? Ta sake yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsar ba. Kyakkyawar bafulatana kamar ita mai asalin kyawun fuska da sura sam! Bai kamata a ce ta bari Ladiyo ta wantsalar mata da mulkinta ba...ta san Likita ya ce mata ta dakata da buɗe ƙafa haka nan saboda ciwon ƙafarta amma gara ta mutu a matsayinta na sarauniyar wannan ƙungiya ta su mai daraja akan dai ta ci gaba da rayuwa a matsayin wadda Ladiyo ta yiwa juyin mallaka saboda ta gaza!... Da wannan lissafin fa miƙe ta je ta zauna a kan katifarta ta na huci... Tabbas ba su san wacece Yagwalgwal ba har yanzu! Za ta fito musu da asalin fuskarta ta yadda kaff ƴan ƙungiyar tasu da kuma jama'ar Unguwar Mariri sai sun yi dana sanin underestimating ɗinta da su ka yi, dama chan ruwa ne ya daki babban zakara amma wallahi yanzu ko Mariri za ta kama da wuta tabbas sai ta nuna musu she's the queen, leader and unstopabble. Tabbas an kunto Kura!!!. ••••••••••••• Wata kalar Halitta ce kamar dangin tsuntsaye…saboda tsabar yadda aka yi kacha-kacha da ita da tsafi da ƙazanta da ikon Allah sun gagara fahimtar mecece gaba ɗayansu, har Baba!. Girmanta ya kusan kai Zakara ƙosashshe, haka tsayinta shima da yanayin kai da ƙafafuwanta, in ba ka lura sosai ba to ba za ka gane ba zakara bane ba. Bayan furen da ta je masa da shi, har da layu da allurai duk an maƙala a jikin tsoka da ƙofofin halittar ko wanne ya samu wajensa….gashi tsokar jikin nata kamar an yi mata wanka da jini da gawayi…an goggoga a koina. Abun dai ba kyan gani babu fasali sam!. Da masifar ƙarfi Anne ta runtse idanunta, ranta in ya kai dubu to a yau ya yi ƙololuwar ɓaci! Tabbas yadda Baba ya tozartata wallahi itama sai ta tozartashi! Dukda ba ta ji ta tozarta ɗin ba dan ita abun kunya gaba ta bashi ba baya ba amma ta fahimci goal ɗinsa dan haka sai ta rama… Gashi ya tarwatsa mata aiki dan haka in sha Allahu itama sai ta tarwatsa masa lissafi a yau ɗinnan… Ta yi masifar kashe kuɗi akan aikin gashi a yanzu ta san ko ɗura za ta yiwa Afra ba za ta taɓa yarda ta ci duk wani nama da zai fito daga hannunta ba. Ce mata aka yi ta tsunduma Halittar a yadda ta ke a cikin tukunya ta dafata luguff da kayan ƙamshi sosai saboda ƙarnin ya fita, in ta kammala tafasawa sai ta cire abubuwan jikin ta haɗa da gashi ko farcen Afra ta binne, shi kuma naman ta soya ta bata ta ci, bayan ita kowa ma zai iya ci wannan ba damuwa bane ba. Yanzu kam a yadda ta gani ta san tata ta ƙare dan ba za ta taɓa ci ba…. Besides ma an ce mata in aka gani a haka a ɗanyenta aikin ko ta yi ba zai yi tasiri ba. “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un….” Amal ta furta jikinta na wani kalar mahaukacin karkarwa. Sai kuma ta juya ta wuce ɗakin Adda saboda dama chan ita ta na da tsoro sosai, Halittar kuwa kallonta kaɗai in ka yi duk jarumtarka sai ka taɓu dan ka na ganinta ka ga tsafi! Tsagwaronsa. Salati Baba ya yi haka Adda itama yayinda Ya Amir ya yi saurin kawar da kansa gefe ya runtse idanunsa da masifar ƙarfi Ya Abba kuwa kafe abun ya yi da ido kawai ya na kallo, ransa na ƙarasa ɓaci! Ko a tarihi ba ya jin akwai azababbiyar uwa kamar Anne! Dan ko shakka babu ƴar cikinta ta shiryowa wannan ƙitimurmurar…yanzu da ace basu gani ba kenan wannan gagarumar wahalalliyar ƙazantar za ta ciyar da su, Allah kaɗai ma ya san me da me su ka saba ci… Ya ƙarashe lissafin nasa tsanar Anne ya na sake dira masa a cikin zuciya, ba ya so ya tsani ɗan uwansa musulmi amma wallahi ya tsani matarnan kamar Mutuwarsa…. “menene wannan?” Muryar Baba ta dira a dodon kunnuwanta, muryar har wani karkarwa ta ke yi tsabar baƙin ciki da ɓacin rai, ko shakka babu ba yau ta soma yi musu wannan ƙazantar a cikin gida ba! “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ya shiga nanatawa a cikin zuciyarsa. A hankali Ya Amir ya buɗe idanunsa waenda su ka yi jaaa sosai ya ƙarasa wajen da abun ya ke ya yi addu’o’i sannan ya rarumo buhu da aka cusa a jikin windown ɗakin Ya Abba ya wareshi kafin ya nemo kara ya tura abun da ledar cikin buhu ya yi waje da karar da buhun da abun domin ya je ya jefa a kwata… Dan masifa wajen da aka ɗauke abun a kai sai da ya chanja kala wala abubuwan da su ka gogawa Halittar ne ya gogu a wajen ko kuma dai tsabar kata’in da ya ke jikin Halittar ne ya sanya wajen ya sauya kala ya yi duhu sosai. Juyawa ta yi za ta fita, Baba ya sake shan gabanta, sannan ya daka mata tsawa sosai kamar ba shi ba ya ce “na ce miki menene wannan abun? Sannan me za ki yi da shi?” Wani maƙofcinsu da ya zo wucewa ne, ya leƙo ganinsu cirko-cirko kowa a fusace ya sa ya yi salati kafin ya ƙarasa shigowa ciki ya ce “subahanallah, Mallan a yi haƙurin dai da aka saba dan Allah….” Shiruuu Baba ya yi ya gagara cewa komai, haka su Adda suma. Ganin ta samu mafaka ya sa ta yi wani dogon tsaki ta zo za ta wuce, Baba bai san lokacin da ya saka hannu ya janyota ba sannan ya sake daka mata tsawar “ba za ki gaya min menene ki ka shigo mini da shi cikin gidan nan yau ba? Sannan da izinin wa ki ka fita da sassafe?” Ganin yadda Baba ya gigice ya fita a haiyyacinsa ya sanya Afra da Adda su ka soma kuka! Duk haƙurin Baba duk kawaicinsa saboda Allah duba abunda Anne ta maida shi, gaba ɗaya ta gigitashi…. Shi kuwa Baba wannan karon da niyyar sakin Anne ya ke! Saboda ya gaji dan tabbas ta kaishi maƙura kuma babu wani alamun shiryuwa a tare da ita sai dai taɓarɓarewa! Afra dai ƴarta ce amma kalli tsafin da ta je ta ƙullo ko lafiyar Yarinyar ba ta dubawa…kuma Allah kaɗai ya san sau nawa ta yi musu irin haka a cikin gida! Dama chan ya san ta na yi amma bai sake tabbatar da tsafi ne ta ke yi ba na gaske sai yau! Sannan da ikon Allah nauyin da ya ke ji ya na dannesa kar ya rabu da ita yau kam babu shi, ƴaƴa in sha Allahu shi da Adda za su rainesu Amma Anne kam ya gaji wallahi ya gaji!!!! Ya aiyyana hakan a cikin ransa wata kwallar masifar baƙin ciki ta na ziraro masa… A hankali ya Abba ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya yi shiruuu kafin chan ya ɗago ya ɗan matso kusa da Baba sannan ya ce “Baba ka yi haƙuri dan Allah, mu bar maganar kawai ba yanzu ba…” Dan zuwa wannan lokacin soron ya yi maƙil da makwabta da Abokan arziƙi. Ƙofar gidan kuwa kamar an zo ganin gomna. Ko da Baba ya waiga ya kalli Ya Abba sai da ya ji kamar ya fashe da kuka shima, dan idanunsa tap! Su ke…cike da kwallah, ga shi sun yi jaa sosai. Girgiza masa kai ya yi sai kuma ya ce “Abba na gajiii, sannan ba za ta wuce daga nan ba yau har sai ta gayawa mutane menene ta zo da shi! Sai ta ɗanɗani ɗacin maganinta a Bakinta yau ba zan barta ba.” Tausayin Baba ne ya hana Ya Abba magana gashi yanayinsa ya sa ya kasa ci gaba da kallonsa dan haka ya yi saurin sunkuyar da kansa ƙasa. Sai kuma ya ɗago da sauri jin Anne ta na cewa “Me ka ke magana a kai? Me na shigo da shi? Abun na ka har da sharri kuma yau?” Ran Adda a ɓace a ta ce “babu batun sharri fa Anne, ya ki ke nema ki juya magana ne? Kar ki yi halin Yara mana, duk ɗinmu nan har ke mun san kin shigo mana da abu cikin gidan nan dan haka ki faɗa, menene kuma a ina ki ka samo….” Murmushi Anne ta yi sannan ta ce “sannu baƙar munafuka! Ai kowa dama ya san duk kun tsaneni, dan haka dan kin ce hakan ba abun mamaki bane ba, kai kuma” Ta juya ta kalli Baba sannan ta ce “duk kalar ɗawainiyar da na ke yi da kai ba ka gani ba ko? Kullum ba ka da wani buri sai na ganin ka tozarta ni ko? To da Allah na dogara wallahi.” Dai-dai nan Yadikko ta buɗe ƙofar ɗakinta ta fito ta na dogara sandarta ta ƙaraso wajen sannan ta ce “gafara dai!! Wayene ya ke yi mana hayaniya cikin daren nan?…” Sai da Baba ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa kaɗan tukunna ya ɗago ya kalleta sannan ya ce “Yadikko Safiya dai ko…” Wani ƙululun baƙin ciki ya na rufe shi, kallo ɗaya tak! Za ka yi mata ba ka buƙatar na biyu wajen fahimtar a make take maƙwal!!. “Auho! Auho, eh safiya… Su waye ne, mai ya faru?” Ta faɗi hakan ta na mai tsayawa waje ɗaya da kyau a cikin soron sannan ta hau lalube. Da sauri Anne ta matsa gareta ta riƙo hannunta sannan ta ce “Yadikko wae daga na fita amso sadaka a bayan layi shine su ka tisa ni gaba da tambayar ina na je…” Da sauri Adda ta ce “wallahi ba sadaka ki ka je a amsa ba, a wajen sadakar ne ki ka amso Kayan tsafi?” Salati Anne ta yi sannan ta ɗaura da cewa “wae wanne kayan tsafi ku ke nufi ne? Ya na ina? Sharrri za ku yi mini ne ku haɗe mini kai? Zan sauya muku fa yanzunnan zan fito muku a Nuratu ta! Ba na ciki da **** **** uba…” Dai-dai nan Ya Amir ya shigo cikin gidan, da sauri Ya Abba ya kallesa ya ce masa “a ina ka jefar da abun..” “Kwatar bakin titi” Ya bashi amsa ya na mai waigawa ya kalli Mutanen da su ka yi cirko-cirko a bayansa dan da kyar ma ya samu ya shigesu ya shigo cikin gidan, kamar ya san me ke shirin faruwa, ya ce “mun sallameku, ku je kawai ba komai za mu daidaita a tsakaninmu an gode.” Kasancewar a cike ta ke kullum ya sa Ya Abba ya fahimci ko ya je ga kwatar ba zai samu abun ba ruwa ya riga ya tafi da shi, if not da sai ya ɗauko ya kawo ya nunawa mutane…in ta ga dama ta ci gaba da denying. Ashar ɗin da Yadikko ta makawa Adda ne ya maida hankalin kowa garesu sannan ta ce “in na ƙara jin Bakinki sai na tsine miki tass!!” Sai kuma ta ce “kai kuma Habu yanzu abun sadakar ne ba ka so a karɓo ko me? To nima dan na makara inata lazimi ne tun Magariba, da tuni hadda ni za a je, sarai na san da batun kuma ba ka nan ne shiyasa ta tambayeni ni kuma na ce ta je…” Girgiza kai Baba ya yi, sannan ya ce “ba komai Yadikko Ki koma ciki shikenan komai ya wuce…” Dan gaba ɗayanta a buge ta ke yanayin maganarta ma kamar wata ƴar daba gata dai tsohuwa tukuff da ita shiyasa abun duk sai ya zama wani very awkward. Sosai Anne ta ji daɗin yadda Baba ya muzanta, dama tunda ya yaga ledar nan ta ci burin yau sai ta tozartashi wallahi, sai ta kunyata shi fiye da zatonsa a yau ɗinnan, na Yadikko somin taɓi kenan, sai ya san ya taɓota, sai ya kwashi kashinsa a hannu. Nuratu ba ta barin ta kwana. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* *page 34* …. Da kyar Anne ta tattaro nutsuwa ta nufi wajen Afra wadda tunda ta shiga ɗaki ta ke kuka, gaba ɗaya gidan ya burkice sai ka ce wajen zaman makoki. Dama sallama baya daga cikin ɗabiunta ba kasafai ta fiye yi ba dan haka sai da ta kai ga shigowa har cikin ɗakin tukunna Afra ta lura da ita… Da masifar sauri Afra ta miƙe tsaye sai kuma ta nuna mata hanya ta na kuka sosai kamar ranta zai fita ta ce “fita!!! Dan girman Allah ki fita, ba na son ganinki.” Matsowa Anne ta shiga yi Afra ta na jaa baya sai da ta kaita bango tukunna Annen ta saka hannu ta rungumeta, a take Afra ta sake rushewa da wani rikitaccen kuka dan gara a yi mata ƙawanya da ƙayoyi akan wannan rungumar da Annen ta yi mata! Ba wai. Cikin kuka sosai numfashinta har ya na tsitstsinkewa ta ce “Anne ki cika ni ki fita kar zuciyata ta buga dan Allah, kin tarwatsa dukkan farin cikin rayuwarmu kin kashe Ya Amir da ranshi, kin juyawa Baba lissafinsa kin chanja shi, Anne ba zan iya ci gaba da yafe miki ba ki fita kawai…saboda kawai an dakatar da ke daga aikata tsafi a cikin gidan nan shine ki ka burkice kai tsaye ki ka tarwatse duk wani abun daɗi da ya yi mana saura? Da wanne ido ki ke so Ya Amir ya kalli mutanen da kika gama dasa kokwantonsa a kansu? Wanne kalar ɗanyen aiki ne wannan ki ka aikatama rayuwarsa? Menene wannan baƙin fentin? Daɗi kika ji yanzu da ki ka yi masa haka? Ke fa uwa ce Anne amma wae yau da bakinki ki ka faɗi hakan a kanshi kin san tasirin da maganar za ta iya yi kuwa? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun.” Afra ta ambaci hakan cikin dunƙulewa waje ɗaya ta samu da kyar ta zame daga jikin Anne ta durƙushe a wajen ta na kuka sosai… Muryarta har ta disashe amma hakan ta ci gaaba da cewa “ki fita…ki fita Anne, ki fita ba na ƙaunar ganinki.” Cikin kwantar da murya Anne ta ce “Afra komai fa na yi na yishi ne domin ke dan Allah ki nutsu ki ji ni… Mahaifiyar Isma’il….” Cikin katseta Afra ta ɗago rinannun idanunta ta zuba mata su sosai sannan ta ce “ki ji da kanki! Ki je ki fara neman yafiyar Ubangiji na shirkar da ki ka yi! Sannan ba ni ya kamata ki ji da ba a halin yanzu, kamata ya yi a ce ki na tare da Ya Amir…. Anne ki fita daga ɗakin nan tun ban gudu na bar rayuwarku ba na har gaban Abada…” Ta faɗi hakan cikin tsantsar ɓacin rai, kwata-kwata ba ta ƙaunar ganinta wallahi. “To” Kawai Anne ta ce daga haka ta juya ta fita kanta na soma yin ciwo, ba ta so ta sami matsala da Afra dan Yarinyar ta na da ruƙo, so take ta biyo ta ƙarƙashin ƙasa ta tarwatsa auren…..ba ta so Afra ta fahimci ba ta son ta auri Isma’il dan in Yarinyar ta fahimci hakan tabbas za ta ga kamr bata son farin cikinta ne kuma ba lalle ta kula da ita a gaba ba, ba lalle ta ji ƙanta ba ko da kuwa ta auri mai kuɗin ne a gaba…shiyasa take ta fakewa da a ƙara lokaci da ragowar kame-kamenta ba ta so ta fitowa Yarinyar ras!. Gashi yanzu aikin da ta shiryo ya warware, ga Baba shima ta na da tabbacin komai na kanshi ya ware, kar fa ta je ya saketa! Sannan ga batun aure yana ta ƙaratowa… Ta ina ma za ta fara ne oho!!! Ba ta Ya Amir ta ke ba ita kam yanzu shi ya sani, ya so ta ko kar ya so ta ba damuwarta bane ba, dan bata hango kyallin arziƙi a tattare da shi ba ballanta ta yiwa kanta tanadi da shi, dan haka in ya ga dama ya ƙullaceta, ita su Afra su ne damuwarta! Shiyasa ko kallon hanyar ɗakinsa ba ta yi ba ta nufi nata sai kuma ta juya ta wuce hanyar Banɗaki, tabbas ta na buƙatar kusanci da Ubangijinta dan a yadda abubuwa su ka caɓe mata haka ta na buƙatar ya kawo mata ɗouki…. Ba tare da ta yi addu’ar shiga cikin banɗakin ba ta afka kanta ko hula babu, kanta tsaye ta kwaye ta durƙusa ta shiga sheƙa fitsarin shaa!! Kamar an kunna shower. Sai da ta kammala ta janyo buta tukunna ta ga ashe ruwan ɗan mitsitsi ne sosai…ganda ba ta barta ta fita ta je ta ɗebo wani ba da wannan ɗan mitsitsin da bai fi cikin cokali biyu ba ta yi wannan tsarkin ta inda ta zuba a hannunta ta goga a koina na gabanta ita kanta ta na jin yadda ta ke damalmale wajen da fitsari da ragowar abubuwa! Gaba ɗaya ita kanta ta san ba ta fita ba sai kazanta ma da ta ƙarawa koina a wajen amma haka nan ta miƙe ta saki zaninta ta fito waje ta bar banɗakin shima kacha-kacha da fitsarin da ba ta kwara ruwa ba yanata uban zarni. Ruwa ta zuba a butar, ta sunkuya a bakin randar ta shiga alwallarta mai abun ban mamaki, ta inda ta wanke komai ɗaɗɗaya a gaggauce sam babu nutsuwa koina in an kalla sai an samo lamɓarsa kamar wata Yarinya. Tukunna ta miƙe ta shiga ciki ta na tunanin wacce sallar ya kamata ta yi….ana binta bashin salloli dan rabonta da yin sallah an jima gaskiya…. A cikin kayan su Afra ta ɗauko Hijab babba a wanke a goge ta zura ba ta shimfiɗa komai ba ta tada sallar anan kan tangaryar sumintin ɗakin. Fatiha kawai ta ke karantawa ɗaya da kwata a duk tsayuwa, ruku’u da sujood kam duddungurawa kawai take yi gudun kar ta tsaya karatunsu ta ɗauki lokaci mai tsayi ba ta idar ba. Ƙaratun zaman tahiya kuwa ta daɗe da haƙura ta shi dama dan ta gagara koya, dan haka a hakan ta gabatar da sallar isha ta jiya da asuba ta yau, ta idar ta zauna ta na istighfari, da ikon Allah kuma sai ta ji zuciyar da ta ke ta faman tunzurota ta na sauƙa. •••••••••• Da mugun kyar ya iya cewa Jessica “excuse me..” Muryanshi na shaking sosai. Da sauri ta juya ta fita bayan ta yi mishi alamun girmamawa ranta babu daɗi sam! Ba ta so ta ga Ogan nata cikin damuwa, ko da ƙanƙanuwa ce. Ta na fita ya miƙe tsaye ya ƙarasa jikin mirrow kawai ya tsaya ya na kallon kansa…. Sosai ya ƙurawa kansa ido ya na so ya ga wae ko zai ga wata shedar da za ta tabbar masa akwai matsala a tare da shi a jikin madubin amma shiruu. Ya jima a hakan kafin chaan ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya saka dukkan hannuwansa biyu ya dafa bangon da mirrow ɗin ya ke a jiki ya saka madubin a tsakiyarsa ya na mayar da numfashi bugun zuciyarsa har yanzun bai daidaita ba! “Ya Allah, duk ƙanƙantar halitta Allah kar ka bani ikon ko da cutar da ita ne….” Ya furta hakan a fili kansa na juyawa sosai…. “I can never hurt anyone, ban kashe kowa ba wallahi.” Ya sake furta hakan idanunsa taff da kwallah ka na ganinsa ka ga super helpless, bai san ya zai yi ba sannan bai san ta ina zai fara ba tbh bai ma san menene wannan ɗin ba sannan bai san wa zai samu ya faiyyace masa ko ya taimakesa ba, above all he is super damn scared about the whole thing. Shi a karon kansa tsoro ya ke bawa kansa…. A hankali ya furta “innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!! La ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minazzalimin…” Wayar Jessica ce ta shiga ƙara wanda ƙarar ya razana shi ya juyo a zabure sosai. Sai kuma ya lumshe idanunsa trying to calm himself down, dan tsoro ko ɓacin rai su ne last abubuwan da zai bawa damar shiga kanshi su samu gurbi a halin yanzu after what just happened. Sai da wayar ta katse aka sake kira tukunna ya buɗe idanunsa da kyar ya ƙarasa inda wayar ta ke yashe a kan gado tana ƙarar taimakon a kawo mata agaji, ya na ganin number ya ji gabansa ya yanke ya faɗi… A hankali ya saka hannu, hannun nasa har karkarwa ya ke yi, ya ɗauko wayar tukunna ya yi picking call ɗin ya kara a kunnensa sannan ya ce “good morning sir..” Cikin kulawa mutumin ya amsa kafin Asad ya miƙa condolences ɗinsa zuwa ga mutumin, shima ya amsa daga mutumin, tukunna mutumin ya yi gyaran murya, kanshi tsaye ya fara magana cikin harshen turanci. “Duk ɗinmu mun yi babban rashi, amma kasancewar akwai aiki a gabanmu mai tarin yawa ya sanya dole za mu yi saurin yin gyare-gyare sannan mu ci gaba da abubuwan da ke a gabanmu ba tare da ɓata lokaci ba, saboda mutane mu su ke jira akwai abubuwan da dole ya kamata a yi launching nasu very soon….. …da ni da ragowar board members mun yi nominating naka as our new ceo. Za a kammala sannan a gabatar da komai jibi....." Shiruu kawai Asad ya yi ya kasa magana ya na mai sauraronsa ya na ci gaba da cewa “because we shall be holding a meeting, next tomorrow in sha Allahu, at Abuja. All the best and congratulations…” Mutumin ya furta, daga nan ya kashe wayar ba tare da ya jira jin abunda Asad ɗin zai ce ba. Ya fi mintuna goma kare da wayar a kunnensa kamar wani statue ya ƙurawa waje ɗaya idanu kafin finally ya zare wayar daga kunnensa ya ajjiyeta a gefe ya yi shiruu, bai ma san me zai ce ba! But one thing is for sure he’s not happy about their nomination! Yeah it has been his dream amma after what just happend gaba ɗaya komai ya fice masa a rai fit!!! He hate the job, but ya san idan ya yi rejecting a yanzun quenstions may rise and in bincike ya yi bincike wataƙila a kamoshi tunda shi a karon kansa bai san garin yaya ya aikata wannan aika-aikar ba shiyasa ya ke jin tsoron ma tambayar wani game da al’amarin dan ba ya so a zo bincike a kama shi dumu-dumu. Da ma ace akwai tsayayyiyar uwa wadda ta shaƙu da shi ko Uban da ya damu da damuwarsa to da abun ya zo masa da sauƙi. A take wata zuciyar ta ce masa “yanzu kenan ka ci buluss!!” Kamar wani taɓaɓɓe, a fili ya ce “it was out of my control, it wasnt my fault…” Sai kuma wata zuciyar ta ce “to maybe ma fa ba laifinka na komai, kawai ka uzzurawa kanka ne…” Yanzun ma kamar ɗazu a fili ya ce “nooo…incidence ɗinnan i’m pretty sure it wasnt just a dream..i still can feel everything….” Sai kuma ya saka hannunsa ya dafe kansa da masifar ƙarfi ya shiga ambaton sunan Allah…. Sai da ya ɗan dawo dai-dai tukunna ya ƙarasa ya zauna a kan gadon ɗakin…. ya jingina bayansa da jikin fuskar gadon ya miƙe ƙafafunsa a kai, Baya ga abubuwan nan da su ke damunsa on top of everything yanzu kuma wai Nigeria zai tafi….a hankali ya lumshe idanunsa ya ce “Nigeriaaa…” Ƙasar da ya ke gudun kasancewa a cikinta kenan, amma to ya zai yi!!! Ta koina kawai shi dai an ɗauresa an dagula masa lissafi. Astaghfirullah…. •••••••••••••• An kai ruwa rana tukunna Ya Abba ya ɗan nutsu, sai a sannan ne Adda ta fito daga cikin ɗakin bayan ya tabbatar mata da ‘babu komai, bacci ne ya ke son yi.’ Ta na fita ɗakin Ya Amir ta nufa amma juyin duniya ya ƙi buɗe mata kawai dai ya ce mata "he’s fine" dan haka ta haƙura ta wuce ciki da parlournta direct, a ciki ta samu Amal ta haɗa kai da guiwa ta na kuka sosai… Wata nannauyar ajiyar zuciya Adda ta sauƙe kafin ta ƙarasa zuwa gareta ta zauna a hankali tukunna itama aka shiga aikin rarrashinta. A bakinta bayan ta tsagaita kukan ta ji batun auren Afra wanda za a ɗaura nan da kwanaki 6 in Allah ya kaimu da komai da ya faru a jiyan. Da farko Adda murna ta soma yi sai da ta ji yadda Anne ta yi da komai kuma sai jikinta ya yi sanyi sosai. Hankalinta bai gama tashi ba sai da ta ji yadda Afra su ka yi da Ya Ismail da safiyar nan… A hankali ta gyara zamanta da kyau sannan ta furta “Allahumma ajirni fi musibati.. Ina ita Afran ta ke, ina son magana da ita… tabbas ta tafka kuskure a batun zuwa hotel amma ban ga laifinta ba tunda Anne ta riga ta fita wayo, yanadaga cikin dalilan da ya sa ta ki sakewa a yi maganar ciwon nata da kowa sai Afran saboda ƙarya ne take yi garr ta ke, Baba ma ya ce ƙarya ne nima na san ƙarya take yi, duk a cikin ƙulle-ƙullenta ne…. Ita kuma Afra ta biye mata.” Cikin sauƙe numfashi ta ɗaura da cewa “dan haka yanzu sai ta yi haƙuri da duk abunda zai biyo baya ciki har da ƙin biyewa Isma’il su yi faɗa tunda ita ce ta taɓo shi dan haka in ya hau ita ta dinga sauƙa, har a samu a ɗaura auren nan lafiya komai ya daidaita.” “Nima abunda na gaya mata kenan ɗazu Adda kamar ki na nan, amma a wuya take itama ta ce wai ya na yi mata gori kuma duk a cikin zugar Anne ce Ya Afran ta ɗauka, ya kamata ki sameta ki yi mata magana….. Ban san ina take ba. Tun ɗazu na shigo nan ni, inaga ba za ta wuce ɗakinmu ba…” Cewar Amal Numfashi Adda ta jaa ta sauƙe a hankali ta jinjina kai kawai ta na lissafi, a ranta ta na Addu’ar Allah ya bawa auren nan ikon ƙulluwa Allah kar ya bawa Anne ikon cimma burinta dan a yadda ta hayayyaƙo ɗinnan da dukkan ƙarfinta ta kirsa da asiri tabbas abun ya bata tsoro kwarai. Jigummm… Haka suka wanzu a cikin parlourn kafin Adda ta miƙa hannu ta ɗauko wayarta, sai da ta gwada kiran layin Baba ta ji a kashe, tukunna ta nemo sunan Aliya ta kira…da fatan Allah ya sa Baba da Ya Amir su na lafiya. Sai da ta katse aka sake kira tukunna Aliya ta yi picking cikin muryar yanayin barci ta ce “Hello, Adda” Murmushi Adda ta yi sannan ta ce “na’am ƴar albarka…” “Na’am” Itama Aliya ta ce, kafin ta yi hamma ta yi salati sannan ta ce “ina kwana, Ya Amalulu?..” Yanzun ma Adda murmushin ta yi tukunna ta ce “Alhamdulillah… Ga ta nan lafiyanta ƙalau.” Sai kuma ta ɗan yi jimmm tukunna ta ce “auren Afra saura kwanaki biyar fa!” Zaro idanu waje Aliya ta yi ta miƙe ta zauna daga kwancen da ta ke sannan with full of exitement ta ce “ma sha Allah, Alhamdulillah.” Sai kuma ta ɗaura da cewa “amma mai yasa ya yi short sosai time ɗin?” “Hmm, gida dai kamar kullum a rinchaɓe ya ke, sai kin zo dai. Yaushe za ki dawo?” Cewar Adda. Shiruuu Aliya ta yi kafin jikinta a sanyaye sosai ta ce “gobe in sha Allahu, yau ma ɗin inada abubuwan da zan yi covering ne shiyasa amma da na taho, ina Amalulu?” Murmushi Adda ta yi cikin yaba ƙaunar da Aliya ta ke yiwa ƙanwartata ta ce “Allah ya taimaka ya kawo ki lafiya. Ga ta nan, dama bata gama hucewa ba, karɓi ki ci gaba da aikin rarrashin ni na tafi haɗa abun kari…” Murmushi Aliya ta yi sannan ta ce “tam shikenan Adda, also… Inada good news da zan taho muku da shi gobe in sha Allahu its a surprise na san za ku ji daɗi kwarai. Duk ku shirya..” “Allah ya kawoki da good news ɗin lafiya” Adda ta ce ta na murmushi daga haka ta miƙawa Amal wayar ta tashi ta fita waje. ………. Jigum haka gidan ya kasance kowa ya ƙule a ɗaka ya yi shiruu, Amal ta na gama waya da Aliya ta yi barci a wajen…Afra kam tun fitar Anne daga ɗakin ta ke karatun Al’qur’ani ta na kuka sosai, tun tana yi tana kukan har ta zo ta daina kukan. So take yi ta kira Ya Isma’il amma kuma wata zuciyar ta na hanata! Ashe haka so ya ke? Ba ya tashi baiyyana kanshi muraran sai ka ga kana shirin rasa abun ko in saɓani ya gilma a tsakani…wani kalar zazzafan so da ƙaunar Ya Isma’il ne su ka yiwa zuciyarta sallama ga kuma fushin da ta ke yi da shi na abun da suka yi mata shiyasa gaba ɗaya ta ke neman sake burkicewa sannan ga case ɗin gidansu da baya ƙarewa kullum su na cikin drama. Har ɗaki Adda ta kai mata abun kari wanda kunu ne kawai, dan sun yi ƙaƙaff sosai…bayaga kunun da ta samu ta dama musu da mugun kyar ba su da komai a kitchen ɗin nasu sai kanwa. Ko da ta shiga ta tarar ta na karatu, sai ta ajjiye mata ta juya ta fito tausayin Yarinyar fall ranta, in ta huta ko zuwa anjima ne in sha Allahu sai su yi magana a nutse a kan Isma’il. Yadikko kuwa ta na kai mata nata kunun da zagi ta bita, yayinda Kaka Nura ko kallonta bai yi ba, ya tsani Matar sosai besides ba ya so Yadikko ta fahimci ya na nan. Anne kam dama ba ta ko ce mata ta gama ba, ta dai bar mata nata a rufe. …. Anne yau wuni ta yi a ɗaki, mirsisi kuma ko haɗa kayanta ba ta yi ba kamar yadda Yadikko ta ce, tana zaune abunta tana ta faman saƙa da warwara. Tabbas sai ta saka Isma’il kuka wallahi dan yana daga cikin mutanen da su ka ɗaga mata hankali a yau su ka hanata walwala… Tana cikin wannan lissafin, kamar daga sama kawai ta soma jiyo sallamar Mama (Mahaifiyar Isma’il). Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* *page 33* “To ka dai ji abunda Uwarka ta ce! Dan haka ba yawo na tafi ba, idan kuma ka nace akan cewa yawon ne to ka ga da ni da ita ne mu ke da shirin zuwa, Allah bai yi itan ta samu zuwa ba a sabili da nannauyan baccin da ya kwasheta ba gaira ba dalili.” Cewar Anne, ta ƙarashe maganar tata ta na wata dariyar rainin hankali ƙasa-ƙasa. “Tabbas” Yadikko ta ce cikin ƙoƙarin ganin ta yi supporting Anne duk rintsi. Tunda Anne ta soma magana Baba ya runtse idanusa. Ya lura so take ta wulaƙantashi ga Yadikko ta ƙi komawa ɗaki, dan haka ya shirya kawo ƙarshen komai in ya so ayi uwar watsi! Tabbas gara hakan. A hankali ya buɗe rinannu kuma gajiyayyun idanunsa ya ce “Nuratu halinki ya isheni, ba na jin zan iya ci gaba da haƙuri…” Duk rashin tsoro, tsaurin ido da taurin zuciya irin na Anne, ba ta san lokacin da ta ɗago manyan idanunta ta zuba masa ba cike da shock, dan sam ba ta yi tunanin zai iya furta mata hakan ba. “Matsowa kusa da shi Ya Amir ya yi sosai sannan a hankali ya ce “Baba ka yi haƙuri, Anne da auren ma ya aka ƙare ballanta babu, dan girman Allah ka yi haƙuri Baba ka rufa mana asiri” “Hmm” Kawai Ya Abba ya ce shi kuma ba tare da ya ce uffan ba. Wani kalar kallo ta ɗago ta watsawa Ya Abban dama ga takaici da shock ɗin da Baba ya jefata a ciki, ba ta gama dawowa dai-dai ba Baba ya ce “dan haka ki je har sai na neme ki.” “A’uzubillahi” Yadikko ta ce, sannan ta matso inda ta ke jin saitin muryarsa ta ɗaga sandarta ta kai duka, sai dai ba ta sami kowa ba, dan bata saita dai-dai ba, this time around. “Ki tattara ki bar mini gidana, kafin in dawo, kar in tarar da ko ɗankwalinki ne.” Ya faɗi hakan yana mai jin wani sanyi ya na sauƙar masa kamar an zare masa ƙaya. “Ka na da hankali kuwa Habu? Tun wuri ka janye wannan batu naka kafin in tsine maka albarka wallahi. Babu inda za ta je! Kuma kar ka fita ko ina ka tsaya har sai an gama magana wallahi.” Cewar Yadikko wadda duk ta bi ta gigice, yo in aka kori Anne ae tata ta ƙare sai dai ta bita… ita kanta ta san ta riga ta gama zama addicted a abubuwan da ta ke sha, dan haka take da tabbacin muddin ta daina to sai dai a kwashi buzunta. “Gara da Allah ya buɗe maka idanunka! Tabbas wannan Mata taka musiba ce! Yadda ka yunƙuro haka Allah ya baka ikon rabuwa da ita gaba ɗaya, Congratulations dan wannan abun a tayaka murna ne.” Cewar wani mutumi maƙofcinsa, wanda ya faɗi hakan a iyaka gaskiyarsa, yana gama faɗin haka ya juya ya fita gudun kar Anne ta yi masa ashar ɗin da shi kuma zai halakata a wajen. Ya Abba dai da Ya Amir ba su ce komai ba. Haka itama Adda da Afra, kowa ya sunkuyar da kanshi ƙasa. Yadikko ke ta hayagaga ta na iƙirarin za ta tsinewa Baba in bai fasa korar Anne daga gidan ba, gaba ɗaya ta gigice. Wata tsohuwa ce ta matso kusa da Yadikko sannan ta ce mata “yanzu ke ƴar Uwa aka ce miki hakan ba abun alkhairi bane ba? Murna ya kamata fa ki yi Allah zai rabaku da ɓaragurbi. Kamata ya yi ki yi fatan ya sauwwaƙe mata gaba ɗaya in ta tafi kar ta dawo, Inace ke da kanki ba kya son auren nasu a da, shin mai ya faru ya sauyaki yanzun ne…” Cikin tarar numfashinta Baba ya ce “ga ta nan! Ya yi maganar cikin nuna Anne sannan ya ce “duk ita ce ta tarwatsa min rayuwata da ta ƴaƴana amma yanzu komai ya ɗauko hanyar gyaruwa in sha Allahu.” Sai kuma ya nuna ta sannan ya ce “na ce miki ki fita ki bar mini gidana ko?” “Allah Sarki rayuwa” Anne ta faɗa muryarta ta na karkarwa! Tsabar bala’in da ya ke cinta. Sannan ta ce “Ɗan adam butulu. A lokacin da ka ɗirka mini ciki aka ce a rufawa juna asiri a yi auren ae shiru ka yi akayi auren, sai yanzu da kake fakewa da ayoyin Ubangiji wae kai nan Malami kuma Limami kowa ya yarda da kai, ka ke ci da addini shine za ka tozarta ni ka tona mini asiri ka wulaƙanta ni ko? To bari ka ji! Wallahi wallahi babu inda zan je!, ae Yadikko ma tana da gado a cikin gidan nan kuma Ubana ta ke aure dan haka zan zauna a ƙarƙashinsu ko saki na ka yi ba zan bar gidan nan ba, ba zan wulaƙanta ba wallahi.” Ta faɗi hakan ta na jin zuciyarta na sacewa, ranta fess!! Dan tabbas ko haka ta barshi ta san an yi 1-1, shi kanshi ya Amir ɗin ae ba ƙaunarta ya ke yi ba, munafuki! A bayan Ubansa ya ke, dan haka ba ta damu ba in an fara yi masa kallon shege daga yau! Ta san in sha Allahu ko hauka su ke yi daga yau har gaban abada ba za su sake yi mata wani shirmen da tujara ba, za su dinga shakkarta gudun kar ta sake yi musu kalar wannan tujarar sannan gara kowa ya san cewa suma fa akwai kashi a gindinsu…kalli fa yadda ake yiwa Baba murnar somi-somin rabuwa da ita kamar wata guba!. Wallahi ba inda za ta je kuma ko da ace sakinta ya yi ba za ta yarda ba sai ta koma ɗakinta! Kamar da ƙasa! Yo Hauka ake…..ba za ta yi accepting defeat ba, ba a isa a koreta a bata hutu ko a sake ta ba, in ma rabuwar ce gara ita ta barshi ba dai shi ya barta ba, sannan inama za ta je in ya kore ta, kuma ko da ace ba ta bar gidan ba ta san in har ta yarda da wannan yajin to fa duk tsiya sai powerta ta ragu a cikin gidan, kar ma ya auro wata! Inaa ba zai yiu ba. A hankali Ya Amir ya zame ya bar wajen ya nufi ɗakinsa, yana ganin Adda ta biyoshi ya rufo ƙofar kawai ya saka sakata da sauri, ba dan ta so ba ta haƙura ta koma inda su ke ranta a masifar ɓace. A chan soron kuwa gaba ɗaya ƙafofin Baba sagewa su ka yi a take kamar zai zube haka ya ji, ga jiri da ya ke kwasarshi kamar hauka!!! Tabbas Anne Annoba ce, ba ya ko tantama sarai ta san Amir ba shege bane ba kawai dan ta firgita kowa ta rama abunda su ka yi mata shine ta gwammaci ta yi haka a gaban jama’a…. Ƙus-ƙus aka fara yi a wajen…wanda hakan ya sake tsorata Baba. Duk yadda Adda ta so ta hana kanta kuka sai ta gagara, ta na ƙarasawa soron ba ta san lokacin da hawaye suka shiga zubo mata ba ganin an fara magana ƙasa-ƙasa, ga takaicin abun, cikin kukan ta ce “haba Anne! Da ke da mu duk mun san ƙarya ki ke yi! Wanne irin abune wannan? Wacce kalar zuciya ce da ke ne? Amir fa ɗanki ne” “Eh ae ɗazu da ake ci mini fuska daɗi ki ka ji har kwanyarki, yanzu kuma da yake an taɓo naki shine za ki yiwa mutane kukan munafurcin da ki ka soba. Munafuka Annamimiya kawai.” Da sauri Ya Abba ya ce “Ya isa haka!” Muryarsa na baiyyana ɓacin ran da yake a ciki, maƙura. Tutture mutanen wajen Kaka Nura ya yi tukunna ya samu ya shigo, tun asuba ba ya gidan ya zagaya gidan wata Mata da su ka haɗa Ap, akan zai je da sassafe saboda dare unguwar a cike take sosai Safiya ce ba za a iya ganin shige da ficensa ba, dan haka ya tafi ko sallar asuba bai yi ba. “Abba lafiyanka na ji ka na magana a dake kamar da ƴaƴan cikinka? In ce dai ba jikokina ka ke yiwa wannan gadararriyar maganar ba.” Cewar Kaka Nura, yana maganar ya na kallon kowa one by one… Cikin takaici Anne ta ce “da ni ya ke!” Juyawa Kaka Nura ya yi ya sake kallonsa sosai sannan ya kalli Anne irin abun mamakin nan kafin ya sake maida dubansa zuwa ga Abban sannan ya ce “kai! Dan Ubanka ‘Mai Dala’ wanda ya tsaneka ya tsani jin ko da sunanka ne wannan ta yi maka kama da sa’ar wasanka?” Ya yi maganar ya na nuna masa Anne sannan ya sake juyowa ya kallesa bai damu da yadda Yanayin Abban ya sauya a take a lokacin ba! Ya ɗaura da cewa “dan ka samu an yi maka gata? An rufa maka asiri shine za ka zaƙe?. Ae da mun bar ka da Uban naka ka na binsa ya na korarka! Ka ga sai ka ƙare rayuwarka a kan titi ka na galantoyi.” Da masifar ƙarfi Ya Abba ya runtse idanunsa trying very hard to control himself dan a yadda ya ke ji tsaf zai iya damƙo Kaka Nura kuma in ya ruƙosa zai yi wuya in bai masa illa ba…..” Cikin tsantsar tsana Kaka Nura ya ce “ka kiyayeni wallahi! Ka kama kanka. Butulu kawai wanda bai san an yi masa halacci ba! Tirr da kai, a haka za ka ƙare kai ba shege ba kai ba ɗan halak ba.” Sai kuma ya waiga zuwa ga Anne sannan ya ce “menene wai ya ke faruwa ne, na ga an cika?” Kafin ya kalli jama’ar wajen ya ce “bayin Allah lafiya kuwa!? A watse haka dan Allah…..” Da sauri Ya Abba ya shige cikin ɗakinsa… Cikin taɓe Baki Anne ta ce “Habu ne wai ya koreni daga gidan nan. Ya ce in fita in tafi koina ma har sai ya nemeni” Rasss!!! Haka gaban Kaka Nura ya yanke ya faɗi amma sai ya dake! Bai bari yanayinsa ya nuna hakan ba. Sai da ya ɗan dawo dai-dai daga girgizar da maganar ta sanyashi ya yi, tukunna ya kalleta sosai kafin ya ce “ae ta kwana gidan sauƙi. Abu guda dai da na sani shine babu uban wanda ya isa ya koreki daga cikin gidanga, dan haka ki shiga ɗakinki ki kwaso kayanki ki koma ɗakin Yadikko ku zauna tare, babu inda za ki fita ki je ina cikin gidan nan… Ki bashi lokaci, in bai ce ki koma ba sai mu nemi saki da kanmu. Kar ki wani damu ba kanki farau ba.” Tunda Kaka Nura ya shigo dama Yadikko ta ɗan sha jinin jikinta shiyasa ta yi tsit. Da kyar ta iya cewa “a ganina da an sasanta abun, kar ka ce haka ka bari in har ni na haifi Abbakar to zan saka ya barta a ɗakinta, wanne kalar shirmene haka zai yi kamar a garin gaɓa-gaɓa, auren aka ce masa abun wasa ne, in sha Allahu wannan tsari nasa ba zai yi aiki ba.” Juyawa Baba ya yi ya fita bai bi ta kan kowa ba, dan ba zai iyaba…..Tabbas dama ya san abunda za su yi kenan shiyasa kawai ya fasa sakinta dan kamar yadda Ya Amir ya faɗa Anne ba za ta fito da kwayar zarrar mutunci a bazawara ba kuma ba gidan za ta bari ba (ga zahiri ya gani) dan haka a fili za ta dinga tafka ɓarna a gaban idanunsu, ko dan ta baƙanta musu rai ma… Ya na tafe ya na wannan lissafin hawaye su na zubo masa kamar wani ƙaramin Yaro, ba ya son Anne! Tabbas Azaba ce ita ga rayuwarsa!!! A haka ya zagaya wani lungu a bayansu ya zauna a kan wani dandamalin sokaway, yana gama zaman kawai ya rushe da kuka sosai. …….. Banza Kaka Nura ya yi da Yadikko, kamar wata banza ta na magana. Kafin ya yi kwafa ya wuce cikin kitchen kawai ya rarumo itace ya yo kan ragowar jama’ar da su ka yi gardamar tafiya da masifar gudu kuma wallahi da niyyar sauƙewa duk wanda ya sama ya taho… Aikuwa rututu haka aka hau gudu har da ihu, cikin hukuncin Ubangiji bai samu kowa ba, dan haka ya mayar da ƙofar gidan ya rufe ya na haki! Ba ya so a gane halin da yake ciki! Ƴar sa aka kora? Kut sai da ya gama tsotse mata duk albarkatun jikinta ta haihu ta tsofe tukunna zai ce ya koreta, daga ƙarshe ya san cewa zai yi ya saketa. Tabbas Habu ya na wasa da wuta. Cikin sheshsheƙar kuka Adda ta ce “ita ɗin da kake goyawa baya yanzun nan ta gama sheganta maka jika a gaban idanun kowa… Bayan duk ɗinmu nan na san mun san ƙarya ne…yanzu na san ta gama dasa zargi a zuƙatan jama’a, shikenan za a je a yi ta magaana. Shin me za ka ce game da hakan shi kuma?” Kallon Anne Kaka Nura ya yi kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya ɗauke kansa bai ce komai ba ya mayar a Adda sannan ya ce “sannu mahaukaciya! Dukanta ki ke so in yi yanzu kenan ko me? Ɗan uwanki ya ja na tabbata koma menene ta yi, magana kuma uban kowa ma ya ɗauki abunda ya ke so ya yi a kai, shi ya sani ko kin taɓa ganin alamun shakka ko gudun magaana a tare da ni?” Lumshe idanu Adda ta yi a hankali, a take wasu kalar hawaye su ka shiga zubo mata rututuuuu na tsantsar baƙin ciki…ta matse bakinta sosai trying very hard ta hana kanta kuka! “Ki kiyayeni kar ki ƙara kawo min munafurcin Nuratu ba na son shirme….ko meye ta faɗa akwai dalili ko kuma ma dai-dai ne.” Juyawa kawai itama Afra ta yi ta bar wajen jikinta har yana karkarwa tsabar damuwa da ɓacin rai. …. Tunda Ya Abba ya shiga ɗaki ya ke ta faman safa da marwa. ****“Eh tabbas ɗana ne! Ni ne na haifesa, amma ba ni da abunda na tsana in gani ko in tuna da akwaishi a doron ƙasa kamar shi! Ba ni buƙatarsa in kuna so he’s all yours and dan Allah ku yi controlling nashi within yourselves…kar ya bari In sake ganin fuskarsa har gaban abada!…” Yana gama faɗin haka ya juya su ka ci gaba da hira shi da Abokinsa ya na dariya sosai kamar bai yi komai ba….**** Murya da moment ɗinsu da Daddy (Mai Dala) ya shiga dawo masa tarr a kwanya kamar yanzun ne ya ke gaya masa….. Wani irin karkarwa jikinsa ya ke yi tsanar mutumin ta na sake shigarsa!!! A hankali ya ɗaga fuskarsa ya na kallon kansa a jikin madubin ɗakin nasa, fuskarsa sak!sak!! Ta Daddy ce babu kwaskwarima, har ma da yanayinsa…dan ko ba a gaya maka ba in ka kalli Abba ko da a duhun Magriba ne sai ka san cewa Daddy ne Ubansa…. wani irin bugawa zuciyarsa ta ke yi! Dan the fact that ya na kama da mutumin sosai sake tarwatsa masa lissafinsa ya ke yi. In Allah zai ara masa dama ya bashi kuɗi a ɗauke zunubi wallahi plastic surgery shine babban burinsa!! Ba ya so da ƙaunar duk wani abunda zai haɗa shi da mutumin ko da kwayar zarrah ne…. Bai san lokacin da ya ɗaga hannnunsa ya daki mirrow ɗin ba! Ai kuwa a take ya tarwatse ya fasa masa hannu. Da sauri sosai Adda ta bar su Kaka Nura a soron ta afka cikin ɗakin nasa ta na shiga ta toshe Bakinta ta saki kuka! Dama ta san za a rina….Tabbas sai Allah ya yi mata hisabi da Anne da Kaka Nura dan har ga Allah su na shiga haƙƙinsu su na ɗaga musu hankali matuƙa ita da Abba akan case ɗin Daddy. “Ai da yanka kanka ka yi kowa ya huta shine zan san ka na da zuciya.” Cewar Yadikko, cikin ɗaga murya sosai bayan sun ji ƙarar fashewar gilashin…. So take yi kawai ta yi koma meye domin ta samu Kaka Nura ya yaba mata ya daina fushi da ita ya kulata, dan ta san zafi ne ya ɗauka. “Ƙunci yanzu ku ka fara ganinsa ai ke da ɗan naki, ni kuke so ku gani a haka amma ke ce a wulaƙance wallahi, ba dai ni ba.” cewar Anne “Ni anya ma kuwa ba ɗan naki ke biya miki buƙatunki ba, kullum ku na ɗaka ke da shi, ke ba aure shi ba aure.” Yadikko ta sake faɗa, duk dan Kaka Nura ya yarda a bayansu take. Bai kulata ba ya juya kawai ya barta a wajen, ya yi shigewarsa ɗaki! Ya na lissafin ta ina zai biyowa Baba! Tabbas sai ya maida gidan upsidedown sai ya hanashi walwala wallahi, da shi da ƴarsa sun fi ƙarfin wulaƙancin talakan banza kamarshi. Hatta Anne sai da ta gaji ta barwa Yadikko, ta shige ɗaki zuciyarta na tafarfasa, Yadikko kam sai da muryanta ya kusan dishewa tsabar hayagaga ta inda ta yiwa Abba da Adda tatas kafin ta haƙura itanma ta bar wajen ta nufi wajen Anne ta ce mata ‘kar ta wani haɗa kayanta ta zo, ta zauna a nan inda take za ta yi magana da Habu’…tukunna ta wuce ciki (ɗakintq) ta na haki sama-sama…… In sha Allahu ta na jin motsin Habu za ta fito dan zuwa wannan lokacin ta fahimci ya fita ne tun ɗazu saboda ya rainata, shegen Yaro! Sai ya janye wannan hukunci da ya yiwa Anne. A ɓangaren su Adda kuwa, Ya Abba ya so fitowa Amma ta tsaya a bakin ƙofar ta kare…ƙiri-ƙiri ta hanashi fita. Ji yake kamar ya haɗiye zuciyarsa kawai ya huta ko ya samu sauƙin abunda ya ke ji, da kyar ya na ganin dishi-dishi ya ƙarasa ya zauna a bakin gado kawai… Dan ba ya son ganinta haka ta na kuka sosai gashi ta hanashi yin komai ga baƙin cikin da ya ke a ciki. Sai da ta tabbata ya ɗan sauƙa tukunna ta ƙarasa ta ci gaba da goge masa in da ya ji ciwo har yanzun ta na sharar hawaye… ….. Tunda Anne ta shiga ɗakinta ta ke ta faman safa da marwa, Kaka Nura shima tunda ya shiga ya zauna ya ke lissafi, ya ma kasa zuwa ya sameta su tattauna! Wanne irin sanyi ne haka Nuratu ta yi da har za ta bari Habu ya yi mata hakan, ya aka yi ta bari ta sauƙo har haka!? Tabbas akwai gyara a gidanga. Ya na kallon Yadikko ta shigo ta gama lalubenta ta na kiran sunanshi amma ya yi mata banza, in ta gama da kudu ya koma arewa in ta zo nan ɗin ya koma yamma. Haka nan ta ƙaraci maganganunta ta na nemansa ta haƙura, daga baya ta fara tunanin to ko dai fita ya yi bai shigo cikin ɗakin ba! Tabbas dole ta takawa Abbakar burki wallahi. Ba zai janyo mata fushin Nuratu da Nura ba…. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* *page 35* Anne yau wuni ta yi a ɗaki, mirsisi kuma ko haɗa kayanta ba ta da niyyar yi kamar yadda Baba ya buƙata, haka nan ta zaɓi ta zauna a nan ɗakin nata ta yi yadda Yadikko ta ce…dan haka ta wanzu a ɗakin zaune abunta tana ta faman saƙa da warwara… Tabbas sai ta saka Isma’il kuka wallahi, saboda yana daga cikin mutanen da su ka ɗaga mata hankali a yau su ka hanata walwala… Tana cikin wannan lissafin, kamar daga sama kawai ta soma jiyo sallamar Mama (Mahaifiyar Isma’il). Kusan a tare su ka ji sallamar ita da Afra wadda ta ke zaune ta na karatu. Ras!! Gabanta ya yanke ya faɗi kafin ta miƙe tsaye da sauri sai kuma ta jaa ta tsaya dan bayan ta tashin kuma sai ta gagara fita. Da mugunn kyar ta tattaro courage ta nufi waje jikinta ya na karkarwa… Kusan a tare su ka fito ita da Anne wadda ta nemo duk wata baiwar kissa da ke a gareta ta yi activating nata tukunna ta fito dan ko sunan Matar itama ba ta son ji kamar yadda ta tsani ɗanta! Mutame kamar mayu! Sun nace sai an basu Afra duk abubuwan da ta ke yi sai warwarewa su ke hakanan komai ya ƙi yin tasiri gaba ɗaya sun uzzurawa rayuwarta… Ta na fitowa Afra ta fara gani ta ɗan durƙusa ta na da shirin gaida Mama, aikuwa da sauri Anne ta ware murya cike da hayagaga ta shiga gaban Mama ta tsaya ta na mai cewa “lale maraba da Mama, ma sha Allah Azahar Mai Albarka, Mama da kanki haka! Ai da kin aiko kawai da zuwa zan yi, bismillah shigo ciki mana” Gaba ɗaya ta babbake ta yi kane-kane ta hanata ganin Afra ballanta ta ji gaisuwar tata…da ikon Allah kuma Mama ba ta ga Afran ba dan hankalinta bai kai wajen da ta ke ba ta dai ji kamar murya ta na gaisheta amma sai Anne ta janye mata hankali su ka yi ciki. Amal bacci take yi a lokacin amma Adda itama ta ji sallamar Matar sai dai ba ta fito ba gudun kar su yi abun kunya a gaban suruka tunda ba shiri su ke yi da Anne wadda ta jiyota tare da Maman ba, haka Ya Abba da Ya Amir suma duk sun ji dan haka su ka hau addu’ar Allah ya sa alkhairi ne ya kawota, duba da yadda Matar ko fita daga gidanta ma bata cika yi ba ballanta zuwa gidan surukai haka nan kasafai. Har darduma Anne ta shimfiɗa mata ta zauna a kai, Annen ta na ta rawar kai da hayagaga ita ala dole sai Mama da Afra sun tabbatar ba ta da wata matsala da Isma’il, auren da danginsa. A zuciyarta kuma addu’a take yi Allah ya sa zuwa ta yi a kan batun zuwa hotel, Allah ya sa matsala ce ta kutso kai akan batun auren ko kuma ma ace fasawa aka yi gaba ɗaya… Da mugun kyar Mama ta ke iya haɗiyar yawu a cikin ɗakin, dan tun shekaran jiya da Baba ya hana su Afra gyara ɗakin ya ce Anne ta gyara da kanta bai ga tsintsiya ba, gashi ta tara uban wandunanta na ciki ta danna a ƙasan pillow gaba ɗaya tsaminsu ya cika ɗakin…sannan da ita da gashin kanta da ko wanne lungu na jikinta har ma da bakinta komai kawai tashi yake yi dan yau ba ta fita ba ballanta a yi kwaskwarima a fesa turaruka a samu abun ya ragu. “Bara a kawo miki ruwa” Cewar Anne wadda ke a zaune ƙyam ta na jira Mama ta ce a barshi.. “Laa kar ki damu ba komai” Mama ta ce, tana ɗan murmushi sannan ta ɗaura da cewa “Barka da war haka, ya gida ya Yara?.” “Alhamdulillah, ya kwana biyu ya kuma shirye-shiryenmu, sai ku ka ji mazan sun yanke lokaci ƙanƙani kwatsam!! Ni ban ma san ta ina zan fara ba duk na rikice wallahi, Allah dai ya nuna mana auren nan da rai da lafiya, ba ki ji farin cikin da na yi ba wallahi, a samu ta tafi a je a ci soyayyar da aka daɗe ana yiwa tanadi….” A hankali Mama ta ɗan yi gyaran murya, wanda hakan ya sanya Anne yin shiru, ta na bin Mama da wani kallo wanda a zahiri ya ke kama da murmushi da kulawa a baɗini kuwa tsantsar tsana ce! Haka kurum ta tsani Matar saboda nacin su, Allah dai ya sa ta ji good news daga gareta a yau, a yanzunnan. Ta na cikin wannan addu’ar ta ji sautin muryar Mama ta na cewa “am, dama na zo ne saboda akwai maganar da na ke so mu yi da ke ta fahimta…” Sai da ta ɗan yi jimm tukunna ta ɗaura da cewa “In Allah ya kaimu nan da kwanaki 6 za a ɗaurawa Afra da Isma’il aure in sha Allah.” A cikin ranta Anne ta ce “Mayya” Sannan duk ƙoƙorinta sai da murmushin kan fuskarta ya baje a take. Mama kam ba ta ma lura ba ta ɗaura da cewa “dan haka na ke ganin da mu da ku duk mun zama ɗaya, Afra ta riga ta zama ƴata dama ita kam tun ba yau ba… In wani abun ya sameta ko sunanta tabbas kamar mu ya samu. Shiyasa na zo in ji baasin shin me ya kaita hotel wajen Samuel? Sannan dan Allah duk rintsi kar ta sake zuwa ko kuma ta yi wani abun da zai taɓa mutunci ko darajarta kafin Allah ya sa a ɗaura auren a samu su wuce chan Kaduna abunsu, ta fuskanci karatu da aurenta.” Tsabar takaici da mugun kyar Anne ta iya haɗiye ƙululun abunda ya tokare mata maƙoshi sannan ta jaa numfashi ta sauƙe ta fuskanci Mama da kyau tukunna ta iya cewa “eh to Mama kin san Afra har yanzu Yarinya ce ƙarama, dan haka waennan abubuwa na aure kayan ɗaki kyale-kyle dole za su burge ta. Akwai wani abun kwalliyar ɗaki da ta nuna tana so ni kuma na ce tunda kun ce akwai komai a gidan kawai ta barshi, dan tun kafin Alhaji ya faɗi cewa a Kaduna za ta zauna dama chan shi Isma’il ɗin ya gaya mana komai…. To ita Afra ta nace akan ta na son abun gaskiya kuma nima da na lissafa na ga ba fa za mu kaita da komai nata ba, gashi auren fari shiyasa ta bani tausayi dan haka da Samuel ya ce ta je ya bata gudummawa sai kawai na ce ta je ɗin saboda kaff gidan nan wallahi duk ta cikinmu mu ke ba mu da yadda za mu yi ballanta mu samu mu siya mata kinga hatta sanwar rana ma ba a ɗaura ba yau kam. Amma wallahi ni ban san hotel za su je ba, itama kuma Afran haka, kawai dai laifinta guda da ta fita ta kira shi ta ji ya ce mata ta je hotel da sai ta fasa zuwa.. Tunda kowa ya shaida soyayya ce yake yi mata to kinga kenan bai kamata a ganta a hotel tare da shi ba. Kuma dai ta dawo ta na ta ƙunci da na tambaya ta ce mini tunda ta je bashi da wani burin da ya wuce ya taɓa jikinta, to dai ban tsananta bincike ba gaskiya ta na bada kuɗin na fita na je na kai deposit ɗin abunda tace ta na so ɗin dan kuɗaɗen ba su cika ba har yanzu… Kuma kinga an ce kar a tsananta bincike sosai ba daɗi shiyasa ban titsiyeta ba saboda na yarda da Afra ɗari bisa ɗari na san ba za ta taɓa yin wani shirmen ba. Dan haka kema ki kwantar da hankalinki ba ta yi komai ba ni shaidarta ce ta na da tarbiyya da nutsuwa sosai kuma ta na son Isma’il, sannan na yi miki alƙawarin zan kafeta a gidan nan ba inda za ta sake fita daga yau har Islamiyya, in kin ga ƙafarta a waje to in sha Allahu an zo ɗaukarta ne za a kaita gidanta na Kaduna.” Wani kalar juyawa kan Mama ya soma yi, dama gata matar ta na fama da hawan jini ya yi mata katutu… A ranta ta ce “anya kuwa….” A hankali ta ke jan numfashi ta na sauƙewa, saboda tsabar yadda kanta ya sara tun lokacin da aka ambato maganar ‘Samuel yanata so ya taɓa jikin Afra’….Salati ta shiga yi ta na ta ƙoƙarin korar sheɗan ɗin da ya dage wajen buga mata gangarsa hankalinta in ya kai dubu to ya tashi, gashi Anne sai zuba ta ke yi ta ƙi shiru ta na ta bata labarin kalar nacin da Samuel ya dinga yi akan Afra wanda duk ba su san da wasu ba sai yanzu ne take ji. Ba dan ta so ba ko dan ta gama abunda ya kawota ba dan ta so ta yi mata jaje sannan ta bata baki game da abunda ya faru da ita ake ta yamiɗiɗi a Unguwa, amma sai kawai ta miƙe ta rabu da ita. A hankali murya cike da damuwa ta ce “na barki lafiya…bara in je gida akwai shirye-shiryen da na bari. Na gode” Jinjina kai Anne ta yi ta na wani murmushi dan yadda jikin Matar ya ke rawa kaɗai ya isa ya tabbatar mata saƙonta ya kai. A ranta ta ce “wannan hanyar ma da alamun za ta ɓille, ba ko sisina amma dukda haka gida biyu zan yi, bazan tsaya a dabara ɗaya ba”, sanna a hankali hankalinta kwance a fili ta ce”Allah ya bamu alkhairi…” Daga haka Mama ta juya ta fita. Wanda fitowar tata ya sa Afra wadda ta ke ta leƙe ta kasa tsaye ta kasa zaune ta yi saurin komawa cikin ɗakin nasu ta saki labule. Tunda su ka shige ɗaki ta ke fargaba da fatan Allah ya sa ba wani negative abu ya kawo Mama ba, dan dramar da aka yi da safiyar yau ma a gidan ta sanya duk ta ji ta muzanta kuma ta na ganin itanma(dramar) za ta kawo gudummawar makamashi a rura wutar kashe batun aurenta da Isma’il tabbas… Da farko Anne ba za ta yi mata rakiya ba sai kuma kamar wadda ta tuno wani abun ta miƙe fit ta biyota a baya ta na cewa “sai haƙuri, Yarinya ce dai har yanzu ba za ta kuma ba in sha Allahu…” Ita dai Mama “Ameen” Kawai ta ce dan hayagagar Matar juya mata kai ta ke yi wallahi.. A haka ta fice ita kuma ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiruu ta na kitsa ta yadda za ta soma. Tunda su ka fito Afra ta sha jinin jikinta, hankalinta bai kammala tashi ba sai da ta ji abunda Anne ke cewa da ta fito. Ko da Anne ta koma ɗaki ta kusa mintuna uku tukunna da kyar Afra ta samu ta iya fitowa baiwar Allah ƙafafunta har karkarwa su ke yi a haka ta shiga ɗakin Annen wadda tunda ta ji motsin mutum ya na tahowa ta matso hawaye ta shiga zubda su bilhaƙƙi da gaskiya. “Assalam alaikom” Siririyar muryar Afra ta iso cikin ɗakin. Da sauri Anne ta kauda kai sannan ta shiga goge hawayenta sosai irin ba ta so Afra ta gani ɗinnan. Already ta riga ta gani wanda hakan ya sanya hankalinta ya ƙarasa tashi kwarai tsoronta ya hauhawa a take ta sha jinin jikinta. Da mugun kyar ta iya ƙarasawa kusa da Anne ta na zuwa ta durƙusa a gabanta ta dafa guiwowinta a hankali ta ce “Anne” Ta yi maganar da kyar murya da ilahirin jikinta su na karkarwa, dan tunda ta gaida Mama ɗazun ta ƙi amsawa ta san tabbas ba alkhairi ne ya kawota gidan ba. Still har yanzun goge hawayenta Anne ta ke yi, kafin cikin sheshsheƙar kuka da dasashshiyar murya ta ce “ikon Allah kinga wani kwaro ne ya faɗa mini cikin idona na gagara fidda shi sai ruwa idon ya ke min…” Duk dauriyar Afra kasa ci gaba da riƙe kukan da ya taho mata ya ci ƙarfinta ta yi, ba ta san lokacin da ta rushe da kuka ba dan duk abunda zai saka Anne kuka tabbas ba ɗan ƙarami bane ba. Gashi dama da kunnenta ta ji ana bada haƙuri, shikenan ita kam ta san tata ta ƙare Allah ya sa ba wani sharrin aka ƙulla mata ba… Ta aiyyana hakan a ranta a lokacin da ta ke rushewa da kukan, sannan ta ce “Anne ki gaya mini ko ma menene, zan iya handling dan Allah kukan nan da ki ke yi ya na sake gigita ni ne.” Miƙewa tsaye Anne ta yi, sannan ta wani juyawa Afra baya cikin sauƙe ajiyar zuciya ta ce “ki tashi ki fita, saboda ni ba kuka na ke yi ba, abu ne ya shiga cikin idanuna.” A hankali Afra ta zagaya ta tsaya a gabanta ta na hawaye ta ce “Anne dan Allah ki gaya mini ko ma menene” ta haɗe hannuwanta guda biyu waje guda alamun roƙo. Shiruuuu, Anne ta yi ta na kallonta kafin kuma chaan ta koma bakin katifar ta zauna, ta dunkule tafukan hannayenta biyu a waje guda ta saka a haɓarta sannan ta zuƙo iska ta busar cikin kafe waje guda da idanu ta sauƙe wata ƙaƙƙarfar Ajiyar zuciya kafin ta soma magaana idanunta har yanzu su na kallon waje guda”…. …………. Mama ta na shiga direct ɓangaren Ya Isma’il ta nufa abunda ba ta saba yi ba dan sam ba ta cika shiga ɗakinsa ba. Ba ta tarar da kowa ba amma ta tarar da wayarsa a kan gado, banɗaki ma ƙofar a buɗe ta ke wanda hakan ya shaida mata ba ya ɓangaren nasa ne kwata-kwata kenan amma da wuya in ba ya cikin gidan tunda ga wayarsa nan. Dan haka ta juya ta fita direct ta wuce cikin parlourn. Ta na shiga ta tarar da shi ya na zaune ya na kallo ya na cin indomie, kallo ɗaya tak za ka yi masa ka fahimci gaba ɗaya hankalinsa ba ya a kan indomien har da ma kallon da ya ke yi kawai ya na kalla ne ya na zira indomie….. Ko da ta kalleshi sosai sai ta ga kamar har ya ɗan rame sannan fuskarsa saman hanci da idanunsa sun yi jaa sosai abunka da farar fata. A take tausayinsa ya lulluɓeta, ganin ya na shirin cin galaba a kanta yanzun ma ya sanya ta yi saurin korar lissafin ta nufe shi gadan-gadan shi bai ma san ta shigo ba. Da sauri ƙanwarsa wadda fitowarta daga ɗakinta yanzun kenan ta ƙaraso ta kamo hannunta ƙasa-ƙasa ta ce “Mama, ki zo dan Allah.” Shiruuu ta yi kamar ba za ta kulata ba idanunta a kan Isma’il wanda da ikon Allah har yanzu bai ma san ta shigo ba, sai kuma ta ce “tam, mu je” Daga haka ta juya suka bar wajen. Su na shiga cikin ɗakin matashiyar budurwar ta mayar da ƙofar ta rufeta sannan ƙasa-ƙasa ta ce “ammm Mama dama…” Sai kuma ta yi shiru ta hau kame-kame. “Dama me?” Mama ta faɗa a ɗan zafafe, dan duk haƙurin Matar yadda kowa ya burkita mata lissafinta a yau ɗinnan ya sanya ta shaƙa sosai ta ke a fusace. A hankali Matashiyar budurwar ta ce “na san, its not important kuma duk ɗinmu ba zargin Ya Afra mu ke yi ba, amma ƙishin-ƙishin mu ke ji a bakin wata a Islamiyyarmu wae Samuel ya na da ciwon HIV….” Sai kuma ta yi shiruuu, kafin ta ce “a asibitin da ƴar ajin namu ta ke aiki aka fara masa test aka tabbatar, a nan ta gani, har rantsuwa ta yi min ɗazu da muka haɗu da ita a islamiyya da safe……” Yadda gaban Mama ya yanke ya faɗi ya sanya sai da ta ɗan durƙusa sannan ta dafe ƙirjinta, da sauri Yarinyar ta saki salati sannan ta ɗan ruƙota ta na mai sakin salati tukunna ta ce “sannu Mama, menene?” Yanayinta ya na nuna damuwa sosai. “La ilaha illa anta subhanaka inni kunta minaz zalimin, lahaula wala quwwata illa billah…” Mama ta ambato, kafin ta ɗago a hankali ta zubawa ƴar tata idanu kamar mai son gane wani abun a kan fuskarta kafin kuma kawai ta juya ta fita bayan ta ce “ba komai, ina zuwa” Ga shegantaka da ake zargin akwai a gidan, ga shaye-shaye, ga zina ga ga ga….. Anya kuwa in bar Isma’il ya auri Afra ba ta cuci Yaron nan ba kuwa!. Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsa ba. Still har yanzun ya na zaune ya na cin indomienshi wadda ya ke jin ɗacinta akan harshensa kamar panadol, kwata-kwata cokali huɗu ya yi amma ji ya ke kamar ya yi amanta. Tun safe bai ci komai ba da kyar yanzun ya samu zazzaɓin da ya yi masa rubdugu tun ɗaga lokacin da ya dawo daga wajen Afra ya ɗan sake shi shine ya shigo ya cewa ƙanwarsa ta dafa masa indomie wadda itanma shigowarta daga makarantar Islamiyya kenan. “Isma’il!!” Mama ta faɗa da ɗan ƙarfi dan karo na biyar kenan da ta ambaci sunanshi bai ma san ta na wajen ba. Numfashi ya shaƙa da ɗan sauri sannan ya ɗago idanunsa da su ka yi wani kalar jaaa ya zuba mata…. Da mugun maamaki ya ke kallonta dan ƙanwarsa ta ce masa ba ta gidan, sam bai san yaushe har ta shigo ta tsaya a gabansa ba. A hankali ya ce “Mama ina wuni…” Muryarsa ta na karkarwa sosai very low… Tausayi ya bata sosai dan haka ta koma gefensa ta zauna ba tare da ta yarda sun haɗa idanu ba saboda ta gama tsarawa kanta ba za ta bari tausayinsa da ta ke yi ya cutar da rayuwarsa ba… Cikin nutsuwa sosai kanta tsaye ba tare da kwana-kwana ba ta ce “ka ɗauki Afra gobe ku je a yi mata gwajin ƙanjamau.” Bai san lokacin da cokalin hannunsa ya faɗi a kan tiles ɗin da ke shimfiɗe a parlourn ba… A hankali ya ce “Mama wanchan satin mu ka je mu ka yo fa, mai ya faru ki ke so mu sake komawa? Yanzu ina yi mata maganar nan wallahi gani za ta yi kamar zarginta ne na ke yi….” Ya ƙarashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252 [10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…* *36* A fusace Mama ta ce “ta gani Mana! Sai me? Ɓacin ranta ya fi safety ɗinka ne.” Salati Isma’il ya yi kafin ya ce “Mama safety kuma kamar yaaya? Zargin nata ki ke yi kenan?” Ya yi mata maganar a ɗan tsorace. Itama Mama a ɗan tsorace sannan rai a ɓace ta ce “Isma’il ja’inja ka ke yi da ni? Gardama za ka yi mini ko me!? Ka na so mu rabu lafiya da kai kuwa?… Gaba ɗaya tashi ɗaya ka sauya, halayenka sun chanja duk a kan soyayya, ko sirrin cikinka ba ka iya riƙewa, komai sai ka gaya mata…” Girgiza kai ya shiga yi, ya yi kalar tausayi sosai, Mama ba ta barshi ya yi magana ba ta ce “eh mana, maganar zamanta a Kaduna da komai da aka yi ae duk kwashewa ka yi ka je ka sanar mata tun kafin Mahaifinka ya ce komai. Anya kuwa Isma’il!? Tsoronta ka ke ji ne ko yaya?” A hankali ya lumshe idanunsa hankalinsa chaaa! A tashe, kafin da mugun kyar ya iya buɗesu ya sauƙesu a kanta, tukunna ya ce “ki yi haƙuri, Allah ya huci zuciyarki, zan je in sameta a sake yin sabo sai mu kawo miki in sha Allah.. Batun Kaduna kuma ban ce komai ba Mama, ki yarda da ni” “A mafarki aka sanar musu hala?” Wani abu ne ya tokare masa maƙoshi ganin yadda yau ƙiri-ƙiri Mama ba ta yarda da shi bane, sannan tashi ɗaya ya fahimci daga wajen Anne ta ke kenan fitar da ta yi kuma tabbas Anne ce ta zugota ta haɗa komai shiyasanya ya ganta a haka, dan haka takaicin Matar(Anne) a take ya ƙarasa hassala shi ya na mai ji kamar ya saka mata bomb kowa ma ya huta. Da kyar ya iya buɗe bakinsa ya ce “ki yi haƙuri Mama dan Allah” Dan ba ya son magana da ja’injar da ta ce ya na yi da ita, shiyasa kawai ya katse batun. Daga haka ya miƙe sannan ya ɗaura da cewa “bara in watsa ruwa daga nan sai in tadda ita, na barki lafiya, ki yi haƙuri dan Allah.” Kauda kai Mama ta yi, da mugun kyar ta iya ce masa “tam” Dan a yadda ta ji abubuwa daga Anne dukda Isma’il ɗin ya ce ya amince za a sake yin wani test ɗin sabo kawai sai ta ke ji ko da ace Afra ta fito negative ta na ji kamar still ta dakatar da auren….ba ta so a samu ɓaragurbi a cikin zuriarta sam! Dan ta lura ta fahimci abun nasu jini ya ke bi. Hankalinsa a masifar tashe ya ƙarasa ɓangarensa ya nemi waje ya zauna ya na tunanin ta ina zai fara cewa Afra ta zo su koma a sake yi mata wani gwajin bayan wanda su ka yi aka tabbatar ƙalau duk su biyun su ke, har an haɗa ana shirin kaiwa masallaci! After what he did to her da safe da questions ɗinsa gareta ya san ba lalle ta yarda ba sannan ko da ace ta yardan ma dole za ta gane zarginta ne ake yi kuma hakan ba daɗi…. Sam-sam ba haka Mama ta ke ba! Anne ce ta zugota ta hautsina komai ko shakka babu, amma in sha Allahu zai yi tackling komai bi’izinillahi ta’ala babu sheɗan, mutum ko aljan da ya isa ya raba aurensa da Afra….. Ya aiyyana hakan a cikin ransa zuciyarsa ta na wani kalar tafarfasa…dan sai yanzu ya sake tabbatarwa tabbas akwai gulmace-gulmace a lamarin, tun farkon komai. …………. “Afra haƙiƙa na cuceku na zalinceku! Ko da ace ku kun yafe mini ni ba zan taɓa yafewa kaina ba, ƙiri-ƙiri ba ki ji ba sannan ba ki gani ba amma gashi yanzu aurenki ya na shirin tarwatsewa duk domin kurakuraina.” Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanyata yin shiru.. Cikin share hawaye Afra ta ce “Anne sai yau Allah ya yi za ki gane hakan kenan?! Sai da ki ka gama yiwa rayuwarmu giɓi?” Sai kuma ta yi shiruuu, kafin ta ɗaura da cewa “Amma hakan ma abun farin cikine tabbas dukda dai kin gama goga mana baƙin fentin da ba na jin zai taɓa goguwa a rayuwarmu har gaban abada” Sannan cikin sanyin murya ta jeho mata tambayar “me ya kawo Mama yau?”. Wani sabon kukan Anne ta sake saki sannan ta ce “zuwan nata na yau ya sanya na sake shan jinin jikina…ki yi haƙuri ki yafe mini Afra duk ni na jawo miki…” Cikin rawar murya Afra wadda ta ke ji kamar ta zaƙulo maganar daga cikin bakin Anne ta ce “Anne me ta ce? Mai ya faru?” Share hawayenta ta yi ta ɗan yi shiruuu sannan ta soma magana cikin jan hanci da muryar kuka… “Shekaran jiya Mama ta kirani, akan wae ta na so ni da ita mu taru mu sanya ‘a dakata da auren…’ Na so in yi mata jainja amma sai ta ce ‘in yi ƙoƙarin ganin na yi controlling Babanku ta yadda ko su Usman ɗin sun kirashi zai ce musu ba yanzu ba, dan ta ji ƙishin-ƙishin game da abunda su ke shiryawa. In ta samu lokaci za ta zo mu yi magana da ita.’ To dai nima na ga ƙanƙantar lokacin bayan an sanar mini kuma ina so in yi miki kayan ɗaki sannan ga rashin kirkin da su ka soma yi shiyasa na je wajen Malam Ƙasimu akan ya ɗaure bakunansu ya zamana sai yadda muka yi da su, sannan kar ta hana auren kuma ko bayan auren ina so ya kasance sai yadda ki ka yi da su saboda bana so a ci miki tuwo a ka ko a wulaƙantaki tunda kinga bana kusa Kaduna za su kai ki kuma kinji dai kalar maganganu da cin kashin da su ka soma yi a kanmu. To sai gashi ban kai ga yin abunba ku ka taru aka tozartani aka jefar shi gaba ɗaya…..amma wallahi wallahi Afra iyaka akan abunda ya sa na karɓo tsuntsuwarnan kenan aikin ke zan yiwa saboda nima abun ya fara damuna kar rayuwata ta shiga rayuwarku ta tarwatsa farincikinku, tunda ni dai an gama goga mini baƙin fenti da abunda na yi da wanda ban yi ba da ƙarya da sharri duk an haɗa a cikin tarihina ba zan taɓa iya gogewa ba…” Cikin sauƙe numfashi still ta na jan hanci ta na sharar hawaye, ta ci gaba da cewa “to kuma a yau dai Mama da ta zo ba ta sanar mini taƙameme dalilin da ya sanya ta ke so a dakata ɗin ba kamar yadda ta alƙawaranta cewa za ta gaya mini in mun haɗu, kawai dai ta ce kin yi laiifi, wae bayan ganinki da aka yi a hotel akwai wani laifin da ki ka sake yi, sannan Isma’il ya zo kin masa rashin kunya ɗazu da safe kenan inaga ta ke nufi, ta nuna tafiya ba za ta yiu a hakan ba, sannan da na ce mata na kuma dage akan ba ki yi komai ba alamu sun nuna ta fusata, dan ƙarshe dai shi ya sanya ta tafi ko cikakkiyar sallama ba mu yi ba, amma ni dai na san akan laifukana ne kawai har yanzu ba ta son auren fakewa ne ta yi take so ta ɓillo da basaja tunda tun farko sun nuna ba komai shiyasa ba ta so su yi fuska biyu, dan haka abunda na ke so da ke yanzu shine ki je ki amsa laifin da take ta cewa kin yi, kawai ki na zuwa ki ce mata eh kin yi amma kuskure ne kar ki bari ku jaa maganar sannan ki yi mata alƙawarin ba za ki sake ba kinga in kin yi hakan ae kin rufe mata baki kenan ko? Saboda ni na riga na san ba wani laifi da ki ka yi, kame-kame ne kawai take yi auren ne ba ta so a yi saboda sharrin da ake yi mini da kuma wasu daga cikin halayena, Mallan ya tabbatar mini ba ta so ba ta ƙaunar auren ne sam-sam! Akwai ma wadda ta ke so ta bawa shi Isma’il ɗin (ƴar uwarta)” Cikin tarar numfashinta Afra wadda ta ke ji kamar zuciyarta za ta hantsilo ta fito waje ta ce “Anne har yanzu ba za ki rabu ki daina yarda da boka da Mallan ba kenan! Ba za ki daina ɗabbaka abunda su ke ce miki ba! Astaghfirullah Mallan Allah ne? Ya isa ya ga ko ya ji abunda ya ke a baɗini ko wanda zai faru a gaba! Yarda da ki ke yi ki ke saka abun a ranki shiyasa kawai Ubangiji ya ke barinki da halinki. Kuma ae dama na daɗe ina gaya miki, ko dan mu Anne ya kamata ace kin rage wasu abubuwan amma kalli a satin aurena aka kama ki da laifin aikata da yunƙurin yin tsafi sannan Anne kalli abunda ki ka aikata a Ya Amir dole a dinga gudunmu. Sannan na roƙeƙi da girman Allah kar ki sake yin tsafi ko wani asirin saboda ni ko ƴan uwana akan a so mu ko wani abun makamancin haka ki bari kar ki yiwa Ubangiji shishshigi, ba ruwanki…” Cikin sake rushewa da kuka Anne ta ce “na ji, na ji Afra ba zan sake ba duk na ruɗe ne, gashi ƴan gidan nan gani su ke yi kamar ba na son auren, duk rashin imanina fa Afra ba zan ƙi farin cikinki ba, ina son ku ƴaƴana… Mama ta yunƙuro da zafinta ne wannan karon, dan haka kawai ki wanke ƙafa yanzu muna gama maganar nan da ke, ki je ki sameta har ƙasa ki durƙusa ki basu haƙuri sannan ki yi alƙawarin ba za ki sake yi ba kuma ki amsa laifinki kar ki yi musu, kamar yadda ta buƙata, ki tsohe mata baki a samu a zauna lafiya……dan in wani abun ya samu auren nan na san bayaga takaicin da zan kwasa tsaf iyayenki cewa za su yi ni na tarwatsa komai….” “Anne ba zan taɓa amsa laifin abunda ban yi ba wallahi, sannan kamar ke ce jiya na ji kin dage akan kar in bari a ci mini fuska” “A’a! A’a!! Afra ni kam na sauya yanzu, ki yi yadda su ke so kawai a zauna lafiya, ki je ki ce kin amsa duk abunda ta ce kin yi kar ki yi gardama ko jainja dan Allah. Saboda kin ga jainjar da na yi ce ta janyo ta yi fushi ta tafi.” Da sauri Adda wadda ta kasa zama a ɗakinta ta taho tun lokacin fitar Mama ta ɗaga labulen ɗakin ta shigo dan ta ji abunda Anne ta ke yi ta ji sentences ɗinta na ƙarshe-ƙarshen nan. Ba ta jira ko sallamarta an amsa ba ta ƙaraso, ta na zuwa ta kamo Afra ta miƙar da ita, dan masifa Yarinyar da kyar ta iya tsayuwa ruwan hawaye kuwa kamar an kunna famfo… Tattaɓa fuskarta Adda ta yi sosai sai da kwayoyin idanun Afra su ka daidaitu a kan fuskarta tukunna itama ta na kallon cikin nata idanun sosai ta ce “kar ki ji, sannan ko da wasa kar ki taɓa yarda da duk wasu abubuwan da take gaya miki! Kar ki bari ta shiga cikin kanki ta yi miki wasa da hankali…kin ji ko?” Girgiza kai Afra ta yi sannan ta ce “Adda ba kya ganin abubuwan da su ke ta faruwa ne?” Har Anne ta yunƙura za ta tashi a kan Adda, sai kuma ta koma ta zauna ta na mai sauraron Afra ta na ci gaba da cewa “Adda duk a yadda munin ƙaddarata ta zo bai kamata a ɗaura mini abunda ban ji ba ban gani ba kuma ace in amsa bayan an bini da sharri, dan wallahi ban yi mishi rashin kunya ba ko da ya fara hayaniya barin wajen kawai na yi….” Wani guntun murmushi Anne ta saki ganin ta yi sara kenan dai-dai a kan gaɓa! Daɗi har kwanyarta ta gyara zama ta na mai sauraron Afra ta na ci gaba da cewa “amma ki ji abunda ya ce ita kuma ta bi bayan ɗanta, ko da na gaida ita fa ɗazun ba ta yarda ta amsa ni ba, a tunanina bai kamata ta yarda da duk wasu jita-jita a kaina ba daga ita har Ya Isma’il ɗin ballanta su ji haushina…ba fa a aure da zargi. Kuma me na yi masa da zai mini sharri shima akan cewa na yi masa rashin kunya? Sannan wallahi ba zan je in bada haƙuri ko in amsa laifin komai ba tunda ban yi komai ba, in zai aurena ya aura in ya haƙura nima na haƙura…” Ta ƙarashe maganar cikin rushewa da kuka sosai. Rungumeta Adda ta yi idanunta a kan Anne baƙin ciki kamar ya kar ta, itama Annen su ta ke kallo kawai ba ta ce musu komaiba… “Allah ya shiryeki…” kawai Adda ta ce da ita dan ko shakka babu ba ta san me da me duk su ka faru ba amma tabbas Anne ce ta haɗa komai! Ba wai. …….. Da Amal da Adda da Aliya (ta waya) duk su ka taru da kyar su ka rarrashi Afra ta daina kuka sannan kawai ta ce musu “to” akan abunda su ke ta so ta fahimta dan da ikon Allah lissafinta ya soma karkata zuwa chan wani waje daban, ba dan komai ba sai dan yadda su ka yiyyiwa juna alƙawari ita da Ya Isma’il da yadda su ka yarda da juna bai kamata ace tashi ɗaya saboda ƙanƙanin mistake ɗin da ta yi ba komai ya tarwatse kalli yadda su ke zaryar zuwa gidansu one by one shi da Mahaifiyarsa akan abunda ta tabbata inda ace ita ce wallahi kalmar ‘sorry’ kaɗai daga wajensa ta yi yawa wajen mantar da ita an yi ma. Dan Adda ta yi ƙoƙarin fahimtar da ita batun rashin kunya da Anne ta ce Isma’il ya ce ta yi masa sharri ne, wanda wannan kaɗai ne Afra ta yarda ta fahimta ta saka a kanta ƙarin gishiri da Maggin Anne ne a cikin lamarin amma ragowar abubuwa batun laifin da bata san shi ba da zuwa hotel da case ɗin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kam duk sai a hankali ta kasa ɗauka ta fahimta ko ta gane duk shirin Anne ne.. dan karatun Annen ya tafi straight zuwa cikin kanta babu mistake komai ya yi dai-dai. Shiyasa duk yadda suka kai ga dagewa wajen fahimtar da ita Ta yi haƙuri ta danni zuciyarta ta samu ta yi auren nan ta kawar da kanta wannan duk aikin sheɗan ne, ko wanne aure in ya matso dama akan samu irin haka. Kar ta yi fushi da Ya Isma’il ko Mama sannan ta kiyaye ta yi taka tsantsan sosai. Kar ta ɗauki maganar Anne ko da wasa…… Gaba ɗaya abun ya ci tura, jinsu kawai take yi ta na gyaɗa musu kai amma ita a ganinta duk abunda Anne ta ƙara na ƙarya ta sani ta gane tunda ita ba Yarinya bace ba, ragowar maganganun kuma da ta ke yi musu kallon gaskiya ta zauna daram a kansu ta gagara sauƙa. ••••••••••• Magaji Rumfa (Nasarawa G.r.a) Kano, Nigeria. Babban Gida ne sosai, dan kai tsaye za ka kirashi da mansion. Iyaka space ɗin da yake a cikin front raillings ɗin da akayiwa gidan kafin ka kai ga ƙarasawa gate da asalin katangar gidan..ta tsaye ya kai a yi gini 1 bedroom ƙarami a cikinsa har a samu ɗan tsakar gida faɗinsa kuwa dogo ne sosai ta both sides. Gate na gidan kaɗai abun kallo ne ba wai a iyaka fannin girma ba har da tsaruwa da kyau da inganci. Motoci guda uku ne su ka karyo kwanar street ɗin wanda duk wanda ya sansu ya san Gidan su ka nufa, dan haka da mugun sauri wani mutumi ya miƙe daga ƴar majalisarsu ta benci ya nufi gidan da saurin gaske. Direct ya buɗe ƙaramar ƙofa ya shiga ciki kafin jim kaɗan ya hangame makeken tsadadden gate ɗin wanda ya yi hakan ne da taimakom remote na gate ɗin da ya ɗauka a wajen ajiyarsa a cikin gidan. A dunƙule mansion ɗin ya ke a waje guda wanda kana kallonsa shape na circle za ka gani, in ka ƙura masa idanu sosai muddin ba ka cika son ganin abu mai girma ba (megalaphobia) to a take za ka burkice! Dan hawa biyu gareshi kuma a hakan a cikinsa part har guda uku ne, sai dai ko wanne part akwai ƙofar da zata sadaku a tsakani sai dai in son ran mutum ne zai sanya ya rufeta. A babban parking lot na gidan motocin uku su ka yi parking. Da sauri drivern da ya tuƙo ta ya buɗe ƙofar inda ya ke ya fito ya zagayo ya buɗewa Ummie ƙofa ta side na owners corner inda ta ke zaune ta hakimce. Sai da ta gama shan ƙamshi ya na nan tsaye ƙyam!!! Ragowar drebobin suma duk sun fito sun tsatstsaya, tukunna ta fito wanda fitowar tata ya yi dai-dai da kiran wayarta da aka yi. Ta na ganin sunan mai kiran ta yi murmushi tukunna ta ɗauka ta kara a kunnenta at the same time ta na mai ƙarewa gidan kallo ta ce “hala kin ji good news ko?” Murmushi ɗayar Matar ta yi kafin ta ce “sannu Ummi, congratulations komai ya kammala…” “Yeah nima yanzu na ke shiga gida dan sai da na gama komai aka yi sealing deal ɗin tukunna na yarda na dawo. Congratulations to us…” Dariya Matar ta yi wanda ya ke nuni da tsantsar farin cikin da ta ke a ciki sannan ta ce “to ya ku ka ƙare da Asad?” “Zan waiwayeshi in na gama hutuwa” Cewar Ummi, ta na mai kallon gidan sosai ta na rarraba idanunta zuwa ko wanne lungu da saƙo. Matar ta na shirin yin magana Ummi ta ce "ina zuwa, i’m seeing something a little bit weird, zan kiraki daga baya.” Daga haka ta kashe wayar ta na mamakin wayam!! Ɗin da ta gani gidan kamar ba kowa sannan idanunta a kan Akram wanda ya nufota da murmushi ɗauke a kan fuskarsa. Ya na ƙarasowa ya karɓi hand bag ɗin Ummin daga hannun driban da ke tsaye a bayanta da suitecase ɗinta sannan ya ce musu “you can go…” Daga haka ya juyo ya ce “welcome home Ummie, i just saw your text. Congratulations…” Ya ƙarashe maganar ya na murmushi sosai. A hankali ta sauƙe numfashi sannan ta ce “thankyou ɗan albarka.” Ta na kallonshi.. Cikin yin ƙasa da kansa sosai ya ce “i’m soo sorry Ummie, wallahi Daddy ne ya saka ni aiki shiyasa na turo su.” Ɗan ƙuraa masa idanu ta yi kafin ta matso a hankali ta dafa shi sannan ta ce “are you okay?” Da sauri ya ɗago ya kalleta sannan a ɗan burkice ya ce “yeah sure, i’m very okay wallahi, ba abunda ya faru, mu je ki huta…” Mai gadin gidan ta hanga sun nufi bayan gidan da shi da drebobin da su ka kawota yanzunnan ɗayan har da tuntuɓe ya na faɗuwa, kafin ya tashi jikinsa ya na karkarwa ya bi ayarin nasu su ka yi ciki…. Sai da mai gadin ya saita su a kan hanya tukunna shi ya dawo ya nufi waje domin ya zauna a gate saboda kar a bar wajen ba kowa. Numfashi Ummie ta sauƙe ta maida dubanta zuwa ga Akram wanda ya gagara kallonta tukunna ta ce “Daddy ne ko?” Da sauri Akram ya ce “babu abunda ya yi min fa Ummie…” A hankali ta sauƙe numfashi kafin ta ce “shikenan Akram na yarda!. To mai ya faru ake ta guje-guje?” Ta jeho masa tambayar ta na kallonsa sosai. Muryarsa har karkarwa ta yi wajen ce mata “Uncle Asad ya na hanya.” Da mamaki sosai ta kalleshi, yayinda ta yi shiruuu kawai ta na mamaki……. chaan kuma sai ta ce “su na ina?” Sai da ya sauƙe numfashi Sannan ya ce “Baya. Ana gyara side ɗinsa ne, an gama wankewa yanzu ana chanja furnitures” Da sauri ta ce “a nan gidan zai zauna? Mai ya faru da gidansa” “Its like a chan ya ke son zama shima but Daddy ya dage akan a nan zai zauna” Cewar Akram, wanda duk ya diririce . “Okay…” Kawai ta ce, daga haka ta nufi baya kamar yadda Akram ya ce mata su Daddy na wajen. Inda ta nan ce hanyar ƙofar shiga ɓangaren Asad. Ta na wucewa shima ya wuce ya koma kan punishment/aikin da daddy ya bashi ya ce ya yi. Duk wanda ka gani a wajen hankalinsa a tashe ya ke, domin kuwa kowa tsoron ya aikata laifi ko da ɗan ƙanƙanine ya ke yi…masu guje-guje su na yi masu aiki tuƙuru su na yi amma hakan bai hana Daddy samun waenda zai hukunta ba (a cikinsu) zuwa anjima in an kammala komai…. Dogo ne sosai sannan ba shi da rama, ƙiba ma babu alamunta a tare da shi, ya na tsaye ya juya baya yana bada order ya na dariya, wanda in ba juyowa ya yi ku ka haɗa idanu da shi ka kalli idanunsa ba, to fa sam ba za ka gane cewa babban mutum bane ba dan sam jikinsa bai nuna girma ko tsufa ba ya fi kama da samari ƴan shekaru 33 haka, ba shi da alamun tumbi A tare da shi da duk wani abunda zai nuna maka cewar ya manyanta bayaga furfurar da ta gauraya da baƙin gashin gemu da sajensa da kuma idanunsa waenda duk wanda ya kalla to zai san shi ɗin ba Yaro ko saurayi ya ke ba. “Barka da dawowa Hajiya” Muryoyin masu aikin da su ke tare da shi a wajen su ka ankarar da Daddy zuwanta. Da sauri ya juyo, aikuwa su na haɗa idanu ya saki wata sabuwar dariyar kafin ya ce “welcome home sweetheart….” Ya faɗi hakan ya na mai ƙarasawa inda ta ke, ya na zuwa ya yi hugging nata kafin ya zarota daga ƙirjinsa ya yi kissing forehead ɗinta… Da sauri sosai ta ɗan jaa baya sannan ta saka hannunta ta turashi baya shima saboda ganin abun nashi ya na shirin zarce inda ya kamata… Dariya ya yi yanzun ma wanda hakan ya sanya Ummie ta ɗan sha jinin jikinta, a hankali ta ce “mu je ciki Daddy pls i want to talk to you.” “Okay My lady” ya faɗa mata hakan cikin nuna mata way forward da hannunsa ya na ɗan rissinawa alamun itan queen ce a garesa. Gaba ta yi ya bita a baya su ka fito daga wajen direct su ka nufi ɓangarensa. Shi ya buɗe mata ƙofar ta shiga ya na ta riritata kamar kwai…..su na shiga ta soma dana sani dan haka ta hau kame-kame ta na mai cewa “amm, dama na ga a gaban mutanene Daddy shiyasa na matsa saboda gudun magana da raini sannan ban san ma na tureka ba…” Dai-dai ya na kammala locking ƙofar da tomb nashi.. Yadda ya damƙo hannunta ne ya sanya ta yin shiru! Dan da masifar ƙarfi ya ruƙo tafin hannun da ta yi amfani da shi wajen tureshi ɗin (ɗazun). Ya na murmushi ya na kallon cikin idanunta waenda su ka yi jaaa sosai a take saboda tsabar baƙar azabar da ya ke gana mata ya ce “kin fi ni sanin abunda ya kamata kenan ko sweetheart…” Ya ƙarashe maganar cikin yin kalar tausayi kamar ba shine ya ke shirin illata mata ƴan yatsu da tafin hannunta ba.. Wata kalar razananniyar ƙara ta saki jin yadda ya ke ci gaba da yi mata, a take ta daina jin motsin jini da rai a yatsun nata bayan wata gigitacciyar azaba da ta shigesu tun daga nan komai ya ɗauke mata ɗiff a wajen…sosai farar fuskarta ta yi jaa… Ya na kallonta truly enjoying the moment and the pain da ya ke hanga ta cikin idanunta ƙarara ya ce “kar ki ƙara my baby, plss, sannan kar ƙi ƙara kirana a gaban mutane ni ba boyi boyinki bane ba…” Daga haka ya cikata farat ɗaya wanda hakan ya sanya ta zube a wajen a take….ta durƙushe ta na mai ƙoƙarin hana kanta yin kuka dan kar ya ji ko ya gani ta je ta sake yin wani laifin. Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauƙe ya na murmushi kafin ya ce “oya now stand up and hug me, also congratulations Asad is coming home today in sha Allah.” Ya ƙarashe maganar ya na murmushi, yayinda yanayinsa na baɗini ya soma sauyawa ganin ba ta miƙe ɗin ba kamar yadda ya buƙata. Kamar ta san lissafin da yake yi A hankali ta miƙe jikinta ya na karkarwa dan hannun nata ya dawo ta ci gaba da jin wani matsanancin zugi na fitar hankali. Cikin nutsuwa ta yi hugging nasa gaba ɗayanta ta na karkarwa… yayinda ya yi murmushi ya ce “thats more like it” Daga nan ya shiga ƙoƙarin neman halalinsa ba tare da ya bari sun ƙarasa ciki ba ko kuma ya yi laaƙari da yadda ya maida mata hannunta. Ko kusa bai bi ta ita ba. Iyakacinsa duk abunda ya san ya na so shi ya yi…..sai da ya tabbata ya samu kansa a yadda ya ke so tukunna ya miƙe ya haura sama ya barta nan yashe a wulaƙance ta na maida numfashi a wahale kamar ba ita ce Matar gidan ba, gaba ɗayanta ta fice a haiyyacinta….da kyar ta iya saka hannu ta lalumo mayafinta ta rufawa jikinta ta dunƙule a waje ɗaya dan ba zata iya tashi daga bakin ƙofar nan inda ta ke ba, a take kawai ta rushe da wani kalar rikitaccen kuka zuciyarta na ƙuna. Bai tambayeta ya gajiya ba! Bai yi mata congratulations game da murnar nasarar da ta samu ta zuwan Asad kawai ya yi mata, kuma ta san ya sani dan a gabanta aka kirashi aka sanar masa komai ya kammala… Bai yi duba da abinda ya yi mata a hannunta ba! Ta kansa kawai ya ke, farin cikin nasa ma ta ƙarfi sannan a wulaƙance ya karɓa… “Kaico!!” Ta furta hakan a fili zuciyarta na tafarfasa. Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING* Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139* Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted. Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu.... location:Kano Delivery:NationWide. kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏 SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA BULAMA ✍️ 0806 402 1951 0903 441 3252