💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)``` _*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*_ _*ALHAMDULILLAH GODIYA TA TABBATA GA MAHALICCINMU ALLAH (S.W.A) YA ALLAH INA MAI GODIYA A GAREKA DA NI'IMAR DA KAI MIN TA BAIWA, DA ARON RAI DA LAFIYA DA KA BANI ALHAMDULILLAHI INA K'ARA GODIYA A GAREKA,👏 YA ALLAH KA K'ARO MIN TARE DA DUKKANIN 'YAN UWANA MUSULMAI BAKI 'DAYA👏👏👏👏👏*_ _*YA ALLAH KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA IYALEN GIDANSA TSARKAKA, DA SAHABBANSA BAKI 'DAYA.👏,*_ _*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S WALLAHI HAR GA ALLAH KUMA HAR ZUCIYATA INA JIN DA'DIN ZAMA DA KU, ALLAH YA K'ARA MANA K'AUNA, HA'DIN KAI, DA FAHIMTAR JUNA.👏😍*_ *AUNTYNAH AISHAN UMMA INA TAYAKI MURNAR KAMMALA DIGREE D'INKI LAFIYA, ALLAH YA KAWO AIKI NAGARTACCE DA ALBASHI ME TSOKA, AMMA FA KI SANI ALBASHINKI NA FARKO NAWA NE😉😂* *ASIYA SEE-SEE SANNU BAIWAR ALLAH, ALLAH YA DORAR DA LAFIYARSA GAREKI👏😰* _*INA MIK'O GAISUWAR BAN GIRMA GA DUKKANIN MARUBUTA HA'DE DA JINJINAR K'ASAITA, GAISUWA WADDA BATA K'AREWA HAR SAI RAI YA YI HALINSA, ALLAH YA K'ARA MANA K'AUNAR JUNA DA BASIRA.👏😍*_ _*WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYAN SHI DAGA FARKO HAR K'ARSHE SADAUKARWA NE GA MA'ABOCIYAR HANKALI DA TUNANI, ILIMI DA HANGEN NESA, MA'ABOCIYAR KYAWUN HALI DA 'DABI'U ```MAMAN LABYB,,, KIN WUCE HAKA A GUNA, MATSAYINKI YAFI GABAN NAN, UBANGIJI YA 'DAGA DARAJARKI, ALLAH YA FARANTA MIKI RANKI ANAN GIDAN DUNIYA DA GIDAN LAHIRA WATO GOBE KIYAMA, TABBAS KINA AMINCI A FILI KUMA KINA AMINCI A ZUCIYA, NA FAD'A A FILI KUMA NA FA'DA A ZUCIYA, KECE MACE ME CIKE DA HALACCI A DUNIYA, IN AKWAI ABINDA YAFI SADAUKARWA DOMIN KARRAMAKI DA NUNA GIRMAN MATSAYINKI GARENI TO TABBAS ZAN YI.🙏🙏🙏🙏🙏😍😘*_ PAGE 1 to 5 Gidan marayu Amira ta fara zuwa matashiyar yarinya kenan ga tsananin kyawu da Allah ya bata ga kuma dukiya Allah ya hore, bayan sun gaisa da shugabar gidan sai ta bayar da taimakon kud'in da ta saba kawowa kamar koda yaushe. Shugabar ta kalleta cike da farin ciki tace " Allah saka miki da alkhairi da irin wannan taimakon da kike yi mana." Amira tai murmushi, sannan tace " ai dukiya ba komai bace dan ka bayar da ita ga mabuk'ata amfaninta kenan dama ka taimaki wanda baida ita sai Allah ya k'ara nunka maka mafiyinta, Addu'a kad'ai nake buk'ata daga gareku, kuma naji kuna buk'atar k'ara girman gidan za'a sake fad'ad'a wajen da yardar Allah, sannan duk abinda kuke da buk'ata dan Allah a sanar da ni, shugabar wadda Amira ta kirata da Mama tace to ba damuwa, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya tsareki daga sharrin mutum ko aljan, mun gode sosai." Daga nan suka yi sallama Amira ta fito ta shiga motar ta, ta d'auki hanyar gida. tana cikin tafiya mota ta lalace mata a hanya, tayi - tayi ta tashi amma ina, kuma daga inda take akwai tafiya mai nisan gaske kafin ta k'arasa gida. fitowa ta yi daga cikin motar tare da k'ura mata ido cike da takaici tana tunanin mafita a ranta. Ta dad'e tsaye tana jiran giftawar abun hawa amma shiru kake ji, har ta ciro wayarta zata kira Dad d'inta ya turo mata da wata motar sai ta ji k'arar wata mota a bayanta, mayar da wayar tai cikin jaka sannan ta tsaya tsakiyar ti-tin ta rik'a d'agawa mai motar nan hannu, ba shiri ya ja wani irin burki a gabanta. Wani had'ad'd'en saurayi ne ya fito daga cikin motar, sanye yake da k'ananan kaya ya sha tabarau ya fito tare da tunkaro inda Amira take tsaye. Sai da suka yi kallon kallo wanda ke d'auke da wani sak'on da basu san ma'anar jinsa ba, sannan saurayin nan ya ja tsaki yace " mtswww ko wace mace da d'an k'aramin abu ya faru da ita sai ta fara k'ok'arin kashe kanta, wa ya sani ma ko auren dole za'ai miki kike k'ok'arin halaka kanki, to yanzu da kika tsaida ni me zan miki?" Yana gama fad'in haka ya juya zai tafi sai tayi sauri ta sa hannu ta jawo shi, sannan tace " karka fad'a min maganar banza mana motata ce ta samu matsala shiyasa na tsayar da kai domin ka rage min hanya, kuma bana son tuk'in ganganci dan haka ka koma gefe nice zan tuk'a motar taka da kaina." Saurayin nan ya tsaya yana kallon ta tare da mamakin k'arfin hali irin nata, se dai memakon ya ji haushi a'a saima ji yayi tana burgeshi, har taje bakin motar ta bud'e murfin motar, ta juyo inda yake tsaye tace " ka taho mu tafi mana ko in tafiyata in barka a nan," matashin nan ya rik'e k'ugu da hannu bibbiyu sannan yace " ikon Allah," a nan take ta k'arasa mishi da fad'in "sai kallo," tana gama fad'in haka ta fad'a cikin motar b'angaren driver ta zauna sannan ta tayar da motar, da yaga da gaske take zata iya tafiya ta barshi sai ya yi sauri ya k'araso ya shiga taja suka tafi. Banda aikin kallonta babu abinda yake yi, zuciyarshi ce ke bugawa tare da jin wani bak'on yanayi a tare dashi wanda bai tab'a fuskantar kanshi a ciki ba, hakan yasa zuciyarshi ta aminta da cewa ya fad'a tafkin so duk da kuwa be tab'a yinsa ba, kuma be kula matan ma, amma halin da ya tsinci kanshi a ciki yanzu daga had'uwar farko ya tabbatar mishi da cewa ya fad'a soyayya, ita kuwa 'yar azarb'ab'i Amira banda uban surutu babu abinda take yi, a yayin da shi sam be ma san tana yi ba banda kallonta ba abinda yake, tare da zurfafa tunani kan son tantance gaskiyar abinda yake ji kuma yake zargi a halin da yake ciki yanzu. Jin tana ta magana shiru be bata amsa ba yasa ta karkato da kanta wajen shi ta kalle shi taga ita kawai yake kallo, bud'ar bakinta sai tace " a haka dai gaka kamar wayayye ashe bak'auye ne kuma kan ta gane ne ban sani ba, dan naga alama wannan ne karo na farko da ka fara ganin mace a rayuwarka, haba wannan irin kallo haka sai kace zaka cinye ni," shi dai bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta, duk abinda tayi kawai burgeshi take yi. Basu d'auki wani dogon lokaci ba suka k'araso k'ofar gidan su Amira, ta tsaida motar sannan ta fita, ta kalle shi tace " nagode sosai da rage min hanya da kayi, Allah ya saka maka da alkhairi." Saurayin nan wanda dama idonshi yana kanta yace " kina kyau da tuk'i kin iya gudu a mota," Amira tayi murmushi, sannan tace " ai da tseren mota da na k'afa ba'a tab'a wuce ni, in kana so ka tabbatar da hakan to gobe ka shigo makarantar mu ka gani, ta fad'a mishi sunan makarantar sannan ta juya tai shigewarta gida. Shima saurayin nan ya koma b'angaren driver ya ja motar shi yai gaba, fuskar shi na d'auke da murmushi wanda yake bayyanar da tsantsar farin cikin shi a yau. Washe gari a wani keb'antaccen fili na makarantar aka tanada domin gudanar da tseren gasar gudun da za'ai, ko ina ka duba cike yake da mutane, a yayin da wad'anda za'a fafata dasu kuma suke ta motsa jikin su suna tirenin kafin a fara. Ana gaf da farawa abokanan Amira su Sani da Sadeeq, da Abdul, da k'awayenta Rahma, da Suhaima, da pretty suka zo wajenta suna k'ara mata k'arfin guiwa akan tayi k'ok'ari wajen ganin ta yi nasara, duk da dama kowane lokaci nasarar a hannunta take, har sun juya zasu tafi Sadeeq ya juyo ya dawo wajenta ya ciro wani abu wanda yake kamar sark'a ya saka mata a wuyanta, sannan yace " mamata ce ta bani ni kuma na baki, na tsari ne, kar kiji fargaba ko shakka a ko'ina muddin kina tare da Allah." Amira tai murmushi sannan ta rungume shi tare da fad'in "ina matuk'ar jin dad'in zama da kai amintacce na, ina jin dad'in kulawarka gareni, Allah ya barmu tare," sannan tayi mishi godiya, _(wasu d'aliban bance duka ba, basu d'auki rungumar juna tsakanin mace da namiji a komai ba)_ Bayan Sadeeq ya tafi tana cikin shiri sai ta ji motsi bayanta, tana juyowa taga wannan saurayin wanda suka had'u jiya da irin kayan su na tsere alamun shima yana d'aya daga cikin masu fafatawa a gasar. Muje zuwa *🅱K😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)``` *Mamie ina rok'on mahaliccinmu Allah mai kowa mai komai ya d'orar miki da lafiya, Allah yasa kaffara ne👏😭* *PAGE 5 to 10* K'arasowa yayi inda take, sannan suka kalli juna, Amira tace " ka kyauta da kazo kallon fafatawar mu," saurayin nan yace " a'a ba kallo kad'ai zan yi ba, had'uwa dake ya sauya min ra'ayina, yasa na yanke shawarar shiga gasar tseren nima duk da yau ne ranar farkon fara shigowata makarantar ina nufin sabon d'alibi ne ni, amma na rok'i da a sakani cikin jerin masu fafatawa, farko dai sunana Amir, kuma ni sabon d'alibi ne a ajinku, ina yi miki fatan alkhairi, Allah yasa kiy nasara." Kallon shi tai tace Allah gafarta malam Amir ya kamata fa ka gane ni d'innan ba tsararka bace, nai maka zarra ta ko'ina, kuma nan bada dad'ewa ba zaka tabbatar da hakan, ta kanne mishi ido d'aya tare da zabga mishi uban gwalo sannan ta bar wajen, alk'alan gasar ne suka fara sanar wa kan duk wani wanda yake cikin wannan gasa to ya tabbatar da ya shiga cikin fili, sannan kowa ya tsaya a layi kamar yanda aka saba yi a baya. Bayan kowa ya shiga layi aka basu umurni da su shirya, kowanne daga cikin su ya shirya, sannan aka irga d'aya zuwa uku suka fara gudu. Amira itace a tsakiya tana gudu cikin nuna k'warewa da k'wazo, a yayin da Amir yake a can baya, haka yaita wuce wad'anda suke gabanshi har saida yazo daf da Amira ya zamto a tare suke gudun kuma sune kan gaba, kuma kowannensu ya kafe kai da fata sai ya wuce to da yake a cikin masu yin gasar harda Abdul daya daga cikin abokan Amira, ganin da yayi wani na k'ok'arin shiga gaban Amira yasa Abdul yaita tattare wa Amir hanya, idan Amir yazo zai wuce sai ya riga shi, shi ya yarda ya fad'i indai Amirar su tai nasara, hakan yasa Amira ta k'araso wajen su cikin k'warewa, Amira suka had'a ido da Abdul yai mata nuni da kai alamun ta wuce, har ta kusa kawowa dai-dai layin da zaka tsallake ka ci gasar. Suna gaf da shiga layin a tare duk da Amira ta d'an wuce Amir kad'an, Amir na ganin zata cinye shi yai wani irin tsalle kawai sai gashi a tsakiyar filin wajen da duk wanda ya k'araso yaci. Ihu aka hau yi ganin yau ga wanda ya kayar da Amira a tsere, sedai wad'anda suka ji haushin ba ita taci ba sunfi yawa musamman Sadeeq d'aya daga cikin abokanta, koda yake shi ya wuce aboki dan bata da wanda take neman shawara gunsa sai shi, a tak'aice ma dai shine wanda suke kasancewa tare a koda yaushe, koda nemanta kake yi in ka tambaye shi kai tsaye zai nuna maka inda take kuma kana zuwa zaka sameta a gun, sedai hakan ma bata taba faruwa ba dan kaf cikin makarantar ko ina take to suna tare da shi. Yaji haushi da Amira bata samu nasara ba, saida yai hawaye saboda tsabar b'acin rai. Amir ya k'arasa wajen Amira wadda take ta mamakin irin tsallen da ya yi ya shige cikin filin, yace " haka nake da wannan baiwar duk abinda nasa a gaba to sai na yi nasara akai, idan ba zaki damu ba ina son yin magana dake a wajen shak'atawar d'alibai, ita dai Amira bata ce komai ba, ganin haka yasa Amir ya juya ya tafi. Koda Amira ta k'arasa wajen ta riga Amir zuwa, zama tayi kan d'aya daga cikin kujerun wajen, tana duba ta inda zai b'ullo. Daga bayanta taji maganar shi yana fad'in " gani nan ai," Amira tai murmushi sannan tace " ina tayaka murnar samun nasara, amma ya akai ka iya yin wannan tsallen da kayi lokaci guda?" Amir yace " saboda bana tsoron mutuwa, sannan bana fargabar samun nasara ko rashinta, shiyasa nake samun sa'a akan komai," Amira tace " ai kai ba namiji bane, kuma bana maka kallon jarumi tunda har sai ka yi tsalle zaka ci gasa, kaine mutum na farko da ka kayar da ni a gasa ta hanyar cuwa-cuwa, amma ka kiyayi had'uwarmu da kai a wata gasar ta gaba, dan idan kace zakai tsalle a gasa ta gaba to tad'iyeka zan yi ka fad'i," ta k'arashe maganarta tare da murgud'a mishi baki, Amir bai san sanda ya kwashe da dariya ba, domin yanda tai maganar da fad'a tamkar ma kashedi take yi mishi. Suna cikin magana Abdul d'aya daga cikin abokan Amira ya hango su ya taho inda suke, yana k'arasowa yace "barkan ku dai Amira," ya mik'a wa Amir hannu suka gaisa, sannan yace " kai ne d'alibin da ya zama gawurtacce a idon d'alibai a ranarka ta farkon fara zuwa makarantar nan, duk da kasancewarka sabon d'alibi." Amir yace " nagode," suna cikin magana sai ga su Sadeeq da su preety sun k'araso wajen, nan Amira ta bisu d'aya bayan d'aya ta rungume su sannan ta fara gabatar wa da Amir su da matsayinsu gareta, har tazo kan Sadeeq wanda shine na k'arshe, bayan ta rungume shi sannan tace " wannan shine babban abokina, duk girma da fad'in makarantar nan banda kamarsa." Shima Amir gaisawa yai da su d'aya bayan d'aya, daga nan aka kawo musu abubuwan sha harda kayan maye, wasu sun sha da yawa wasu kuma sun sha amma kad'an. Abdul yana d'aya daga cikin wad'anda suka bugu sosai, kuma tunda ya bugu yake ta kallon Amira, tasowa yai cikin jama'a ya rungume Amira tare da fara yi mata wasu abubuwa dai kai daga gani kasan baya cikin hankalinsa, Sadeeq ne ya taso kanshi ya raba shi da Amiran sannan ya fara kai mishi bugu bayan an raba su ne Sadeeq ya nuna Abdul da yatsa, tare da fad'in " idan har ka k'ara tab'ata sai na kashe ka," cikin buguwa Abdul yace " kafin ka kashe ni ni sai na kashe ka nan fa aka janye su suka bar wajen. Washe gari bayan an tashi daga lecture ta farko suna hutawa, sai d'aukar hotuna suke yi, bayan sun gama d'aukar hotunan sai suka zauna suna dubawa, sai ga Abdul ya k"araso wajen, yace " Amira dan Allah abinda ya faru jiya kiyi hak'uri ba da gayya nai miki ba, buguwar da na yi ce tasa haka, dan Allah kiyi hak'uri," Sadeeq da ke zaune kusa da Amira ne yake ta faman banko mishi harara. Amira bata ce komai ba, sai da k'awayenta da abokanta suka sa baki sannan tace " shikenan ya wuce." Da yamma Amira ce keta faman motsa jiki tana (tirenin), tana cikin motsa jikin ne taji sak'o ya shigo cikin wayarta, tana dubawa taga an yi rubutu kamar haka, _lek'o ki d'auki sak'on zuciyata zuwa ga taki zuciyar._ Fitowa ta yi, a harabar gidan su ta ci karo da wani kwali me matuk'ar kyau, jikinshi duk an k'awata shi da flowoyi, d'auka tayi tana k'ok'arin bud'e cikin kwalin. Babu komai a ciki sai adon fulawa, can k'asa kuma wata takarda ce a ajiye, d'auko takardar ta yi, sannan ta bud'e ta, rubutu aka yi me matuk'ar kyau da ban sha'awa, an rubuta, _*SO MAHA'DI NE NA RAYUWA,* so babbar cuta ce ga rayuwa, lallai zuciyata ta harbu da ciwo me azabtar da ruhi, al'amuran so suna da wuya, rabuwarsa kuwa mutuwa a tare._ Sake karantawa tayi a fili, sannan tai murmushi tana k'ara duba takardar, ga dukkan alamu kalaman ciki sun yi mata dad'i, d'agowa tayi tare da d'an duddubawa ko zata ga wanda ya ajiye mata sak'on amma bata ga kowa ba, hakan yasa ta d'auki kwalin, wasik'ar kuma na rik'e a hannunta ta koma cikin gida. *Washe gari* Tafe suke Amira tana tsakiyar abokanta da k'awayenta, tana ta maimaita kalaman da aka rubuta mata jiya cikin wasik'a, sai Suhaima ta kalleta tace " wai ke ina kika ji wad'annan kalaman kike ta faman maimaitawa?" nan ta basu labarin duk abinda ya faru, sai Sadeeq yace " gaskiya wannan ko wanene na musamman ne," Amira tace " Sadeeq shiyasa nake sonka tun kafin na furta abunda ke zuciyata kake fahimtar sa ka rigani furtawa, kamar kasan abinda nake shirin fad'i kenan," suna cikin magana suka ji ana fad'in wad'anan kalmomin cikin ajinsu amma da wak'a ake furtasu, da saurin su suka nufi ajin Amira ce kan gaba domin ta k'osa ta gane waye yai mata wasik'ar, se dai suna shiga suka tarar da mazan ajin sunfi goma, kuma dukkan su kalaman suke maimaitawa cikin wak'ar, farko Amir ne ta tarar yana rerawa yana fad'in. _"SO MAHAD'I NE NA RAYUWA,_ ganin shi ke rerawa har ta fara murmushi saboda dama zuciyarta shi take zargi sai kawai ta ji Abdul shima ya d'auka yace " _so babbar cuta ce ga rayuwa, lallai zuciyata ta harbu da ciwo me azabtar da ruhi,_ Sadeeq wanda suka shigo tare da Amira shima ya je kusa da su Amir ya zauna, ya d'ora da fad'in _"al'amuran so suna da wuya, rabuwar sa kuwa mutuwa a tare._" Gaba d'aya duk sun raba mata hankali ta kasa tantance wanda yake da mallakin kalmomin, ta rasa ina dukkansu suka sami wad'annan kalaman suka ji shi, dan tasan cikin abokanta na skul d'in Sadeeq ne a tare da su lokacin da take fad'a, sai Sani, sauran kuma k'awayenta ne mata, babu Abdul da Amir, ta juya zata fita kenan ganin bata da amsar tambayoyin da take wa zuciyarta, tana kallon allon ajin taga an rubuta kalaman da suke ta maimaitawa, sai a lokacin ta gano wato duk a nan suka gani kenan suke maimaitawa, to waye ya rubuta? Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}``` _*FAUZIYYA AMMANI* zama tare da ke alkhairi ne, kuma babbar nasara ce, samun k'awa kuma 'yar uwa ta gari irinki abun alfahari ne, ina rok'on Allah dare da rana Allah ya faranta miki, ina sonki, iya wuya kuma ana tare😍😘💋._ _*TAWAN* ina rok'on mahaliccinmu Allah ya yaye miki dukkan damuwarki, ya bayyanar da farin ciki da walwala a gareki, ya k'ara miki lafiya mai d'orewa._ _dan girman Allah muna cigiyar *BAHAGON TUNANI* daga farko zuwa inda aka tsaya,👏👏👏👏👏😭😭😭😭😭 duk wanda yake da shi ya hana ni *wuta bal bal*😡😏_ PAGE 10 to 15 Yau ta kama Asabar ba makaranta, Amira ce kwance kan k'ayataccen gadonta tana karatu domin gaskiya yarinyar akwai k'ok'ari, sam bata wasa da karatun ta. k'arar message ne ya shigo cikin wayarta, ta d'auki wayar tare da dubawa, rubutu taga an yi kamar haka. _Dan Allah Amira ki bud'e zuciyarki ki sakani a ciki, ki tausayawa rayuwata._ Tana gama karantawa tayi k'ok'arin bin lambar da aka turo sak'on da ita, amma tana kira akace a kashe take. Tunani ta shiga yi wai wanene wannan yake turo mata irin wad'annan sak'onnin, amma koma wanene zan ganoshi kwanan nan da yardar Allah, ta d'auki littafinta ta ci gaba da karatunta. Washe gari Lahadi kenan Amira ce ita da Sadeeq suke ta faman tsere, a filin wasanni da motsa jiki na makarantar, a yayin da Amir ke zaune kan kujera yana kallon su. Sun dad'e suna zuba uban tsere da Sadeeq da Amira, Amira sai wuce Sadeeq take yi tana jin dad'i a ranta, can kamar ance ta d'aga kai ta hango Amir zaune babu wanda yake kallo sai ita, idonshi yana kanta ko k'yaftawa baya yi. Kallon Sadeeq Amira tayi tace tana zuwa bari ta kira Amir ayi wasan tare dashi. Tana k'arasowa ta rik'e k'ugu sannan tace " aboki ya akayi ne, taso muje mu yi wasan tare," Amir yai murmushi sannan yace " a'a kuje kuyi wasanku, bana sha'awar yin komai yau," Amira ta kalle shi sannan tace " na rantse da Allah sai ka yi, ta kama hanunshi tana ja, tashi yayi ya bita, suna tafe tana mita tana fad'in " in zaka sani ka sani tunda Allah ya had'amu kwanakin baya a hanya ka zama abokina, kuma duk wanda ke tare da Amira baya zaman zuru kamar wani marayan da ya rasa kowa, koda yaushe kana zaune ba um ba um-um, ba abinda ka iya sai kallo, a wajen kallo ne kafi auki in ka fara kallona sai kace zaka cinye ni, tun kallonka na tsorata ni har ya fara bani haushi, haba kallo sai kace bak'auye," shi dai ba abinda yace mata banda binta a baya da yake tana rik'e da hannun nashi, kuma bai fasa kallonta ba, in ya kalleta sai ya kalli hannun shi da ta rik'e, juyowa tayi tana kallon shi nan take suka had'a ido tace " ahaf aikin kenan juyowa d'ari ni kake kallo ba canji, to ko maye ne kai sai dai kayi ka gama ka k'yaleni wallahi, dan nama na yafi k'arfinka," ta k'arashe maganar tare da murgud'a mishi baki, Amir yai murmushi, shi har ga Allah tsiwar Amira burgeshi take. A haka tana mitar ta shi kuma yana dariya tare da cigaba da kallon nata har suka k'araso tsakiyar filin, hakanan dole Amir ya zage suka yi wasan tare su uku, se dai wannan karon da yake babu abun a ranshi ko kuwa kallon Amira ne ya shagaltar da shi oho Amira taita cinye su dukkansu, gwara ma Sadeeq ya ci d'aya, shi kuwa Amir ko d'ayan ma be samu ba. Amira ce ta samu waje ta zauna tace " gaskiya na gaji tunda dai na ci ku har sau biyar kuma ba wanda yai nasara a kaina to Allah amfana wasa ya tashi hakanan." Suma zama suka yi kusa da ita suna yi mata dariya, Amir yana gefen damanta, a yayin da Sadeeq shi kuma ke gefen hagunta. Ruwa me sanyi suka sha, sannan Amira ta had'a komatsanta tace musu zata tafi gida, tai sallama da su ta juya, har ta fara tafiya Sadeeq ya kira sunanta. Amira ta tsaya cak tare da juyowa, Sadeeq yace " gobe in kin shigo makaranta akwai maganar da nake so mu yi da ke, maganar ta shafemu ni da ke, kuma ta shafi zuciyata," Amira tai shiru tana tunani kodai Sadeeq ne ke turo mata sak'onnin nan, nan da nan zuciyarta ta kwab'eta kai gaskiya ba shi bane, wata zuciyar kuma tace to ki bari mana ki jira kiji me zaice miki goben mana sai ki tabbatar da abinda kike zargi hakanne ko akasin haka, a fili kuwa Amira tace " to me zai hana muyi maganar yanzu?" Sadeeq yace " a'a ki dai bari sai goben in Allah ya kaimu," Amira tace to shikenan Allah ya kaimu," ta juya ta kama hanyar gida, su kuma Sadeeq da Amir da yake Sadeeq da Sani a hostel suke na makarantar, shi kuma Amir ba a hostel yake ba zuwa yake yi ya koma, nan dai suka yi sallama suma kowa ya kama gabanshi. Bayan Amira ta koma gida tayi wanka tai Alwala tai sallah, sannan ta kwanta bacci, gaf da la'asar ta tashi, tana tashi ta sake shek'a wanka sannan ta canza kaya ta yi sallar asri, (la'asar) bayan ta idar ta zauna kenan ta d'auko wayarta zata kira Dad d'inta da Mum sai ta ji sallama a k'ofar d'akinta. Amsawa tayi, tare da bada izinin shigowa, wani yaro ne ya shigo hannun shi d'auke da farar takarda. Mik'a mata wannan wasik'ar ya yi, sannan yace " wani mutumi ne ya bani yace in kawo miki, " Amira ta karb'a sannan tace " yanzu ina mutumin yake?" yaro yace " ya tafi, cewa ma ya yi kar na shigo sai ya sha kwanar layin, sannan sai in shigo in kawo miki," Amira tace " kasan mutumin?" yaro yace a'a banma tab'a ganinshi ba sai yau," Amira tace " shikenan jeka nagode." Yaron na fita Amira ta bud'e takardar nan ta fara karantawa. _Amincin Allah ya cigaba da tabbata ga kyakkyawar sarauniyar zuciyata, idan ba zaki damu ba zan so na kasance farin cikin ki a rayuwa, ina sonki so na hak'ik'a, so na gaskiya, so na har abada, zuciyata ta yarda dake, da soyayyarki nake alfahari, kuma a ko'ina nai miki alk'awari idan har kina tare da ni ba zaki tab'a zubar da hawaye ba, soyayyarki itace abun yi cikin dare har zuwa safiya, ke kad'ai ce fatana, tunanina, mafarkina, da walwalata, wallahi ina matuk'ar sonki, idan kika gujeni bazan iya aikata komai ba, ki tausayawa rayuwata ki amince da ni da soyayyata, ina jiran amsarki idan kin rubuta amsar ki ajiye a wajen zamanki cikin aji zan zo in d'auka, kuma ina ganin amsarki zan bayyana gareki, na barki lafiya._ Bayan ta gama karantawa taja doguwar ajiyar zuciya, sannan a fili tace " koma wanene koda ace na ganka ka yimin ina sonka, idan ka shigo hannuna wahalar da zan baka zaka sha mamakinta, Allah ya kaimu goben. Washe gari da wuri Amira tai shiri ta fita makaranta saboda zumud'in abu biyu, yau ta k'udurta a ranta sai ta gano wanene wannan yake turo mata sak'onni, sai kuma son jin maganar da Sadeeq yace zasu yi da ita. Tsayawa ta yi ganin cincirindon d'alibai da malamai har da police cikin harabar makarantar tasu, nan da nan gabanta ya fara fad'uwa tana tunanin menene ya faru a makarantar su haka da sassafen nan, hango abokanta su Suhaima da Abdul ne yasa ta tunkari wajen su da sauri, ta yi tambayar duniyar nan su fad'a mata abinda ke faruwa amma abin mamaki sai kuka suke yi, kuma kamar ma ganinta shi ya k'ara sa su yin kukan. Nan hankalinta ya k'ara tashi, barin wajen su tayi tunda sun k'i yi mata magana, abinda yafi d'aure mata kai shine duk wanda ta tare ta tambayeshi abinda yake faruwa sai su kasa bata amsa se ma kuka ko hawaye da suke k'ara zubarwa, hakan yasa ta tunkari wajen da mutanen suka taru, ta kutsa cikin su har ta samu ta shigo gaba, se dai abinda idanunta suka gani ya yi matuk'ar razanar da ita. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}``` PAGE 15 to 20 Gawar Sadeeq ne a wajen babu alamar rai a tare da shi. Zaro idanu ta yi tare da kiran sunan shi cikin wata irin razananniyar k'ara, k'arasawa tai kusa da shi, ta tsugunna sannan ta saki wani irin kuka tare da jijjigashi tana fad'in " Sadeeq bana son irin wannan wasan, dan Allah ka tashi," ganin ko motsi baya yi yasa ta tashi ta fita daga wajen duk kallo kuma sai ya koma wajenta suna tayata kokawa rashin da tayi, domin kowa yasan irin muguwar shak'uwar dake tsakanin su da Sadeeq d'in. Amira ta doshi wajen su Abdul da gudu, tana k'arasawa ta kalli Sani tace " Sani dan Allah fad'amin a mafarki nake ganin komai ko, ai ba gaskiya bane ko?" Sani yai shiru tare da duk'ar da kai yana cigaba da kuka. Matsawa tai kusa da Abdul ta kalle shi cikin kuka tare da nuna inda gawar take tace " jiya fa muna tare dashi, mun dad'e tare muna wasan gudu yau kuma ace ya mutu," Preety ce tazo ta rik'eta tare da fad'in Amira dan Allah kiyi shiru kar kije kiy sab'o," Amira ta juyo da kallonta gun Preety tace " yace yau zai fad'a min wata magana shine zai mutu kafin ya fad'a min ko," k'arasawa tai wajen Suhaima wadda babu abinda take yi sai kuka kamar ranta zai fita, saboda itama taji mutuwar Sadeeq domin ta dad'e tana k'aunarshi. Amira ta kalli Suhaima tace " kema kin yarda ya mutu kenan ko, ni wallahi ban yarda ba wasa yake mana kuma zai tashi bari kiga, tashi ta yi ta nufi kan gawar tana jijjiga shi tana fad'in Sadeeq dan Allah ka tashi, kar kai min haka duk duniya banda amini sama da kai ka tashi ta kwanta a jikinshi tare da cigaba da kuka. Amir wanda shigowar shi kenan cikin makarantar ake fad'a mishi abinda ke faruwa, k'arasawa yai inda gawar take jikin shi a sanyaye ya dafata, d'agowa ta yi, tana ganin Amir ne sai ta mik'e ta fad'a jikinshi tare da cigaba da kuka me ban tausayi, shima hawaye kawai yake ta faman zubarwa, k'ok'arin janta yake su bar cikin taron jama'an ya samu ya maidata gida, se dai luuuuu tayi zata zame daga jikin shi tai k'asa. Da sauri ya tare ta, sannan aka samo ruwa tana kan jikin shi aka yarfa mata, cikin ikon Allah kuwa ta farfad'o da sunan Sadeeq a bakinta, kuka take yi musu tana fad'in a kaita wajen Sadeeq. Abdul ne ya kalli Amir yace "gaskiya ya kamata ka kaita gida Amir," 'yan sanda da malaman makarantar ma abinda suka ce kenan a kaita gida. Hakan kuwa aka yi, ya d'auketa ya saka ta cikin motar ta da tazo da ita suka tafi. Iyayen Sadeeq ne suka k'araso cike da rud'u, firgici, da tashin hankali, sunyi kuka kamar me, amma ya zasu yi Allah ya basu shi kuma ya karb'i abinsa. Bayan 'yan sanda sun gama binciken su da suke yi shima likita ya gama aune aunen sa, sannan babban jami'in 'yan sandan ya bawa iyayen Sadeeq umurni kan su tafi da shi ai mishi sallah, kuma insha Allah zasu ji sakamakon bincike akan gawar da suka yi, sannan dole a cikin d'aliban makarantar nan suma akwai yiwuwar a tattauna da su. Iyayen Sadeeq suka ce ba inda zasu matsa daga nan sai an fad'a musu abinda yai silar mutuwar d'an su. Babban jami'in nan ya kalle su yace " alamu sun nuna kashe shi aka yi, saboda wuk'a aka caka mishi, kuma d'akin a hargitse, hakan na nuna ya yi k'ok'arin ceton ranshi kafin a far mishi, amma muna dai kan bincike tukun har sai mun gano gaskiya." Amira kuwa bayan har suka k'araso gida kuka take yi, Amir ya kalleta sannan yace " Amira dukkan mai rai fa mamaci ne, kuma a koda yaushe idan tazo baka isa ka k'ara koda sakwanni ba a duniya, ki sa wa ranki hak'uri, tabbas Amira kinyi rashin babban amini, hakan yasa muma abokan ki muke tayaki kuka saboda tausayinki, da kuma shak'uwar da mu kanmu muka yi da shi, kiyi hak'uri a yanzu yafi buk'atar addu'arki fiye da komai a duniya." Bata ce mishi komai ba amma ta rage kukan da take ta faman yi, kwantar da ita ya yi, sannan ya tashi ya shiga shiga toilet ya had'a mata ruwan zafi ya kaita sannan ya fito ya jawo toilet d'in, kicin ya shiga kafin ta fito ya had'a mata tea me kauri sannan ya soya mata dankalin turawa, ya fito hannun shi rik'e da k'aton faranti ya d'ora plet d'in dankalin da kuma tea d'in da ya had'a mata, koda ya fito har ta shirya ta koma ta kwanta amma har yanzu hawaye bai tsaya da kwararowa ba a fuskarta. Bayan ya ajiye kayan yace ta taso ta karya yasan yanda aka wayi garin yau na firgicin rashin da aka yi ba lallai bane ta tsaya karyawa. Girgiza mishi kai tayi alamun ba zata ci ba. Amir yace " dan girman Allah ki tashi ki karya," bata son yin musu in tana cikin tashin hankali irin wannan, hakan yasa ta tashi ta d'an ci ta sha tea d'in sannan ta koma ta kwanta. Bayan wasu lokuta zazzab'i ya rufeta ta fara rawar sanyi, nan da nan jikinta ya gashe da zafi, hankalin Amir ya tashi ya rasa ya zai yi. Hakanan ya sake d'aukarta suka yi Asibiti aka basu gado ganin yanda jikin nata yake a rikice har takai ga tana suma. Bayan kwana d'aya washe garin ranar kenan b'angaren makaranta mamaci dai an birneshi, se dai fatan Allah yai mishi rahma, amma kowa ka gani cikin makarantar baya tare da farin ciki, duk mutuwar Sadeeq ta tab'a su, saboda mutum ne shi mai faran-faran da jama'a shiyasa suke kukan rashinsa. An so bada hutun makarantar 'yan sanda suka ce kar a bayar suna so su gano wanda ya aikata wannan laifin, hakan ne yasa aka ci gaba da zuwa. Su Abdul ne da su sani dukkanin abokan Amira dai suna harabar makarantar zaune suna jajantawa juna, suna cikin tattaunawa a kan idan an tashi zasu lek'a Amira su ga ya take daga nan su k'ara bata baki, kawai sai suka ji sallama a kansu, suna d'agowa suka ga 'yan sanda. Babban nasu yace " waye Abdul a cikin ku?" Abdul yace " ni ne yallab'ai Allah yasa dai lafiya?" 'Dan sandan nan yace " munzo ne mu tafi da kai caji office domin yi maka wasu tambayoyi, sannan kuma ya nuna sauran yace duk zamu gayyace ku d'aya bayan d'aya domin jin bayanai daga bakunan ku," haka suna ji suna gani 'yan sandan nan suka tasa k'eyar Abdul suka tafi dashi caji office. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}``` WOHOHO HABIBTY 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 *Zo mu zauna dake masoyiya na amince dake har zuciya, tunda kin mini so da gaskiya, zana kula dake zinariya😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘💋💋💋💋💋* _*Ya ilahi HABIBTY NAH QUEEN RUQEEY, yasin har na gama typing zan turo naga gagarumin yabo had'e da kirarin da kika rangad'amin a page d'inki na yau cikin littafin sharrin ashqeey, hak'ik'a so baya tab'a tsufa, nagode nagode nagode Allah ya k'ara mana aminci da k'aunar juna, yanda kike farantamin kema Allah ya dauwamar da ruhinki cikin farin ciki har k'arshen rayuwa, daga k'arshe nake cewa ki rik'e karki manta har abada 🅱K tana yinki💃💃💃💃💃😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘💋💋💋💋💋*_ PAGE 20 to 25 Su Sani kuwa saboda tashin hankalin da suke ciki yasa basu tafi wajen Amira ba su dubo halin da take ciki. B'angaren su Amira kuwa tunda Amir ya kaita bata farka ba sai cikin dare. A hankali ta bud'e idanunta ta d'ora su kan Amir wanda ke ta faman zuba gyangyad'i kan kujera, kallon d'akin ta fara yi sannan ta fahimci a inda suke, nan da nan kuma abinda ya faru ya dawo mata sabo. Kuka ta fara yi, wanda yai sanadin bud'e idon Amir, ya kalleta yace " wai sai yaushe zaki daina wannan kukan ne Amira, dukkan mai rai fa mamaci ne, ya kamata ki saka wa ranki hak'uri tunda ke da kanki kinsan kukanki bazai tab'a dawo dashi ba." Da k'yar Allah ya taimake shi ya samu tai shiru ta daina kukan. Washe gari jikinta ya yi sauk'i sosai ya had'a mata tea tasha sannan ya bata magunguna suma ta sha, likita ne ya shigo tare da sallama Amir ya amsa suka gaisa sannan likita ya gaishe da me jikin ya kuma k'ara dudduba ta, bayan ya gama ya kalli Amir yace " Matarka ta samu sauk'i an sallameku dama damuwa ce tasa jikinta ya rikice kuma a guji b'ata mata rai zai iya sanadin kamuwarta da hawan jini," ya rubuta mishi maganin da zata cigaba da sha sannan suka yi mishi godiya Amir ya biya dukkanin kud'in da ake binshi, dan lokacin da ya kawota kud'in jikin shi bazai ishe shi ya biya kud'ad'en ba, sai da yaje ya ciro. Bayan sun fito daga asibitin suka shiga motar Amiran suka doshi hanyar gida, Amira ta kalli Amir tace dan Allah ka kaini makaranta inaso inga Abdul akwai maganar da nake so muyi dashi ne," Amir yace " a'a kiyi hak'uri sai kin k'ara jin sauk'i," rau - rau tayi da idanu alamun zata yi kuka, hakan yasa ba yanda ya iya ya karkato da motar hanyar makarantar su. Suna zuwa bayan sun gaisa da su sani Amira take tambayar su ina Abdul, nan take suke shaida mata ai tun jiya 'yan sanda suka zo suka tafi dashi, kuma sunje da yamma sun hana su ganshi, sannan basu fad'a musu komai ba akanshi. Amira tace "wai akan me suka kama shi to?" daga baya taji ance " saboda muna zargin shine ya kashe Sadeeq." Gaba d'ayansu juyowa suka yi domin suga mai maganar, wani d'an sanda ne, a gaba bayanshi kuma ga wasu jami'an nan dukkansu sun sha uniform, ga dukkan alamu na gaban shine me maganar. 'Dan sandan nan ya kallesu yace " sunana insfecto Yahya (kafi k'arfin mugu), mun samu labarin cewa kaf makarantar nan Sadeeq bai da wasu abokai sai ku musamman ma ke Amira, saboda haka mun zo ne domin mu tafi daku station domin amsa mana wasu tambayoyi, sai ku wuce mu tafi koh, suma haka nan suna ji suna gani aka tasa su dukkan su har Amir aka tafi da su. Ko da isar su insp Yahya ya kalli Amira yace " dake zan fara domin kamar yanda muka gani tare da hujjoji da bayanan da suka gabata a garemu ya nunar mana cewa Sadeeq da Abdul suna sonki, kuma a kanki ne aka kashe su." Amira ta zaro idanu tare da fad'in " so, ni, a kaina kuma aka kashe shi, tabbas nasan mun shak'u da Sadeeq amma gaskiya babu wata kalma ta so da ta tab'a had'amu, haka shima Abdul d'in." Insp Yahya yai murmushi sannan yace " ba lallai bane ke sun fad'a miki, amma duk suna sonki in kika lura da abinda Abdul yai miki cikin jama'a da kuma yanda Sadeeq yayi a kanki da furucin da ya yi shima Abdul ya mayar mishi da martani, sedai soyayyar tasu zata iya zama da bambanci, shi Abdul ta iya yiwuwa sha'awarki kad'ai yake, idan muka yi la'akari d rungumar da yai miki da yanayin yanda yake shafa jikinki, duk da dai a cikin maye ne yake, amma abinda ke ranshi ya nuna a wannan lokacin, a yayinda Sadeeq ke yi miki so na gaskiya, amma in baki yarda ba me zakice akan wannan hoton?" Wani hoto ya nuna mata d'aya daga cikin hoton gawar shi da aka d'auka, ya rubuta sunanta b'aro b'aro a jikin hannun shi. Bayan ta gama gani sai ya karb'a tare da sake mik'a mata wata takarda yace ta karanta, a cikin litattafan Sadeeq suka gani, karb'a tayi shima ta karanta an rubuta. _Amira ina k'aunarki k'auna ta hak'ik'a amma ina tsoron bayyana miki saboda bansan yanda zaki karb'e ni ba, ko ki amince ko kice min a'a._ Daga k'arshe wasu hotuna ya nuna mata wanda suka d'auka su biyu a bayan hotunan duk ya rubuta _i love you Amira,_ wanda suke tare da Abdul kuwa sai ya soke Abdul d'in ya bar nasu, shima a bayan shi an rubuta _babu abinda zai rabamu dake sai mutuwa insha Allah._ Kuka take yi mai tsuma zuciyar sauraro, cikin kukan tace " wallahi be tab'a fad'a mun ba, ana gobe za'a kashe shi ya sanar dani cewa akwai abinda zai fad'amin washe gari, ashe so yake ya fad'a mun yana sona," ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya. Insp Yahya yace " yi hak'uri kiy shiru insha Allah zamu yi iya bakin k'ok'arinmu wajen kama wanda ya kashe miki masoyi." Amira ta kalli Insp Yahya tace " duk da haka ni bana zargin Abdul shi ya kashe Sadeeq." Insp Yahya yace " in ba shi bane waye to?" Amira tace " bansan ko waye ba, wannan aikin ku ne gano mai laifin." Insp yai murmushi sannan yace " abinda muke kan yi kenan, amma ke akwai wanda kike zargi ne a ranki?" Amira tace " a'a bana zargin kowa dan bashi da abokin fad'a sam, da Abdul d'in ne ma basu wani cika shiri ba." Insp yace " meyasa basa shiri?" Amira tace " wallahi ban sani ba, k'ila jinin su ne be had'u ba," Insp yace " amma ai bayanai sun nuna a kanki kad'ai ne suke samun matsala, shikenan dai abar wannan maganar, tambaya ta gaba a bayaninki na d'azu kince ana gobe za'a kashe shi yace miki akwai maganar da yake so ya fad'a miki koh," Amira tace " eh haka ne yallab'ai," Insp yace " zaki iya tuna waye a tare daku a lokacin da ya sanar dake hakan?" Amira tace " daga ni sai shi sai kuma Amir mu uku ne a ranar." Amir yace " eh tabbas muna tare a ranar ni da su." Insp ya kalli Amir yace " ok kaine Amir d'in kenan?" Amir yace " eh yallab'ai, Insp yai murmushi yace " to malam Amir tambaya ta dawo kanka, malam Amir yaushe ka shigo makarantar nan?" Amir yace " yallab'ai ni sabon d'alibi ne bazan wuce wata biyu ba, Insp Yahya yace " yana son sanin alak'ar shi da Sadeeq da kuma ita kanta Amiran, labarin had'uwar su da ita ya bashi daga farko har k'arshe, sannan ya k'arashe da fad'in "Sadeeq kuma ta sanadinta na sanshi, amma cikin k'ank'anin lokaci muka shak'u da shi." Insp Yahya yace " meyasa ka zab'i k'awance da Amira ita kad'ai duk da yawan 'yan matan jami'ar, kodai kaima kana sonta ne?" Amir yace " kamar yanda na fad'a maka ne, mun had'u da ita bamu san juna ba, bansan 'yar makarantarmu bace ma sai da zamu rabu take shaidamin za'ai gasar tsere a makarantar su kuma ta gayyace ni tare da fad'amin sunan makarantar, a lokacin ne na gane cewa makarantar mu d'aya da ita." Insp yace " a d'an zamanku tare da Sadeeq d'in ka tab'a ganin abokin fad'an shi, ko wanda cacar baki ta tab'a had'a su?" Amir yace " gaskiya babu, saboda Sadeeq baida matsala da mutane sam, yana da kyakkyawar alak'a da kowa kuma bashi da abokin fad'a, se dai kamar yanda kaji ne da Abdul ne kad'ai suka tab'a samun matsala kan Amira." Bayan sun gama magana da Amir ne ya bi sauran d'aliban kuma abokan Sadeeq da Abdul d'aya bayan d'aya yana yi musu tambaya akai, daga k'arshe ya sallame su, tare da tabbatar musu da cewa in yiwuwar sake tattaunawa dasu ta taso zasu neme su, har sun juya zasu tafi Amira ta juyo sannan tace " yallab'ai dan Allah a barmu mu ga Abdul d'in, Insp Yahya yace " karki damu kuje kawai shima gobe ko jibi zamu sake shi dan nafara tunani da kuma zargin wani bayan shi," yana yin maganar yana kallon Amir. Ita kuwa Amira jin ance za'a sake shi yasa hankalinta ya d'an kwanta, ta juya suka fice dukkan su. Bayan tafiyat su ne Insp Yahya ya kalli kofur sale yace " nifa ban yarda da Amir d'innan ba, ko kai baka zarginsa?" Kofur yace " gaskiya da alamar tambaya a kanshi, amma yallab'ai shi babu laifin da aka kama shi dashi akan kisan, sai Abdul, kuma ni a ganina tunda Abdul da Sadeeq suna son Amira dukkansu zasu iya yin fad'a da junansu a ranar har takai ga d'aya ya kashe d'aya," Insp yace " Kofur kenan, in haka ne meyasa tun baya Abdul be kashe Sadeeq ba sai da yace zai yi magana da Amira, kuma babu wanda yaji maganar nan daga su sai Amir d'in, ai kuwa in dai na ci sunana Yahya (kafi k'arfin mugu) to sai na zurfafa bincike a kansu d'aya bayan d'aya musamman ma Amir d'in domin gano gaskiya. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}``` _*MASOYAN MAHAD'IN RAYUWA* ku cigaba da bibiyar labarin domin yanzu aka fara fa labarin fa bakuji komai ba fa, ku dai ku biyo 'yar gidan *MAMIE* wato *Bk* domin jin cigaban labarin._ *MAMIE NAH* _Ina rok'on mahaliccinmu Allah, mad'aukakin sarki, mai ikon komai akan kowa ya baki lafiya d'orarra, Allah ya dauwamar da ruhinki cikin farin ciki har k'arshen rayuwa, ya d'orar da lafiyarsa gareki.👏👏👏👏👏😭😭😭😭😭_ PAGE 25 to 30 Tun daga ranar Insp Yahya ya fara bincike sosai akai amma har yanzu bai sami wani abu ko shaida da zai kama ya rik'e yace ga mai laifin ba. Hakan yasa ya dakatar da binciken shi ya tsaya jiran sakamakon gwajin da aka bayar na gano tambarin yatsun wanda yai kisan. Bayan kwana biyu likita ya gabatar musu da dukkanin sakamakon gwajin da ya yi, wanda ya tabbatar da lallai tambarin yatsun Abdul ne kuma a ranar a buge Sadeeq yake, wad'annan shaidun yasa yak'i sakin Abdul, sannan ya fara shirin tura shi kotu a yanke mishi hukunci. Su Amira kuwa jin shirun ya yi yawa har yanzu ba'a sakoshi ba yasa suka sak'e komawa station d'in, a yayin da shi kuma insp Yahya ya tabbatar musu da cewa yanzu case baya hannunshi domin kuwa ya mik'a shi kotu ranar litinin in Allah ya kaimu za'a shiga kotun in suna so su ganshi to su je kotun, had'ashi da Allah sukai ta yi akan ya bari su ganshi, da k'yar da sid'in goshi suka samu ya yarda, amma minti biyar kacal ya basu, kuma saida ya had'asu da jami'i, sannan yace be yarda ya matsa ba ko me zasu fad'i su fad'a a gaban shi. Koda suka ga Abdul saida suka yi kuka har Amir sai da ya koka, balle uwa uba Amira me saurin kuka. 'Yan kwanaki biyu kad'ai da ya yi a hannunsu har ya yi bak'i ya rame, shima yana ganinsu fashewa yai da kuka mai tsuma zuciya, cikin kukan yace " wallahi tallahi ba ni na kashe Sadeeq ba, a ranar ma mun wuni tare da shi, har club ma tare muka je, duk yanda muka kai ga rashin jituwa baya hanamu yin mu'amalar mu a tare, dama rashin jituwar mu a kanki ne, amma wallahi koda ace nai k'aurin suna wajen rashin imani bazan iya kashe koda dabba ba balle mutum, mutum d'in ma wanda na sani muka saba." Cikin kuka Amira tace " nima ban yarda kaine ka kashe shi ba Abdul, tabbas akwai wani b'oyayyen abu wanda mu d'in bamu san dashi ba, sedai mu rok'i Allah ya fitar da kai ta hanyar bayyana gaskiya." Suna cikin magana jami'in nan da aka had'asu su zo wajen shi tare yace " lokaci ya cika ku wuce muje." Haka nan suka yi sallama da shi suka fito suka tafi, tare da shirin zuwa kotu domin jin yanda zata kasance, amma kafin ranar saida suka sami nagartacciyar lauya wadda zata tsaya mishi a kan case d'in. *MONDAY (LITININ)* Yau litinin, kuma a yau ne aka shiga kotu, ko ina ka duba cike take taf da mutane, 'yan makarantar su duk sun hallara harda su Amira da Amir da sauran wad'anda abun ya shafa, kowa ya hallara Alk'ali kawai suke jiran zuwan shi. Bayan 'yan mintuna sai gashi ya shigo kowa ya mik'e, sai da ya zauna sannan kowa ya koma wajen zaman sa ya zauna. Bayan ya zauna ya shirya sannan ya bada umurnin a fara gabatar da jerin k'ararrakin da suke da su a yau, me gabatarwa ya tashi ya fara jawabi kamar haka " shari'ar mu ta farko a yau itace ta su marigayi Sadeeq wanda ake zargin Abdul abokinsa ne ya kashe shi ta sanadin wata yarinyar makarantar su mai suna Amira," yana gama fad'in haka ya koma ya zauna. Bayan alk'ali ya yi 'yan rubuce rubucen shi sannan ya d'ago yace " malam Abdul ka ji irin tuhumar da ake yi a kanka?" Abdul yace " eh naji ranka ya dad'e," Alk'alin yace " ka fad'a mana gaskiya karka wahalar da shari'a fad'in gaskiya shi zaisa a sassauta maka, shin kai ka kashe Sadeeq?" Abdul yace " wallahi ba ni na kashe shi ba, bansan komai ba game da kisan da aka yi mishi." Alk'ali ya yi rubutu sannan ya sake kallon shi yace " ko kana da lauyan da zai kareka?" Abdul yai shiru, can sai ya ji wata lauya ta mik'e tace " ranka ya dad'e sunana barista Aisha Isa, ni ce lauyan da zan kare wanda ake zargi," ta koma ta zauna, wani ya sake tashi yace " sunana barista Muhammad Auwal, ni nake kare b'angaren da suke k'ara," shima ya koma ya zauna. Can sai Alk'ali yace an basu dama kowanne daga cikin su ya tashi ya gabatar da tambayoyin shi ko hujjar da yake da ita. Barista Aisha ce ta fara tashi ta je gaban Abdul ta tsaya tace " malam Abdul menene alak'arka da Sadeeq?" Abdul yace " makarantar mu d'aya, kuma abokina ne," Aisha tace " da gaske ne dukkan ku ku biyun kuna son Amira?" Abdul mamaki ya kama shi ta yanda akai suka gano yana son Amira, yai shiru tare da kallon saitin da Amira take, d'aga mishi kai ta yi alamar ya amsa, Aisha ta sake maimaita tambayarta, Abdul yace " eh dukan mu muna nuna mata alamu se dai duk cikarmu babu wanda ya tab'a furta mata," Aisha tace " har tsawon wani lokaci kuka d'auka kuna sonta kai da shi Sadeeq d'in?" Abdul yace " shekara biyu." Aisha ta juyo ta kalli Alk'ali tace " ranka ya dad'e abun lura anan shine Abdul da Sadeeq sun dad'e suna k'aunar Amira har tsawon shekaru biyu ba tare da sun fad'a mata ba, kuma kowanne daga cikinsu ya san d'an uwansa yana sonta, se dai meyasa tun a wancan lokacin Abdul d'in be kashe shi ba sai yanzu, nagode ranka ya dad'e, ta koma ta zauna. Bayan Alk'ali ya kammala rubutun shi sai ya baiwa Barista Muhammad Auwal damar yi wa Abdul tambayoyi, ya mik'e tare da zuwa gaban Abdul yace " malam Abdul fad'a ya had'aku da Sadeeq a kan Amira sanadin rungumarta da kayi kana cikin maye har kun yi cacar baki da shi ko baku yi ba?" Abdul yace " eh mun yi," Barista Muhammad yace " wane furuci kuka fad'awa juna a ranar?" Abdul yace " Sadeeq ne ya ce min sai ya kashe ni idan na k'ara tab'a Amira, ni kuma b'acin rai yasa na mayar mishi da martani kan cewa nima sai na kashe shi," Barista Muhammad yace " ok shine ya baka damar kashe shi?" Objection my lord abinda Aisha ta fad'i kenan bayan ta mik'e, tace ya kamata Barista ya san irin maganar da zai rik'a fad'a, har yanzu ana kan bincike ne ba'a tabbatar da shine ya yi ba ko ba shi bane nagode," Barista ya kalli Alk'ali yace ranka ya dad'e abinda yasa nake mishi tambayar nan saboda akwai wasu hujjoji na ne wad'anda suka sa dole sai na yi mishi wannan tambayar." Alk'ali yace " Barista Aisha k'orafi be karb'u ba, Barista Muhammad kana iya cigaba da yi mishi tambayoyin." Barista Muhammad yace " muna saurarenka Abdul nace wannan b'acin ran yasa ka kashe shi saboda kar ya zama barazana a soyayyarku da Amira?" Abdul yace " wallahi ba ni na kashe shi ba," Barista yace " da kyau dama amsarka nake jira," Barista ya dawo wajen zaman shi ya d'auko wuk'ar da aka kashe Sadeeq da ita tare da takardu, ya nuna wa Alk'ali tare da fad'in " ranka ya dad'e wannan wuk'ar da ita aka yi amfani wajen kashe Sadeeq bayan kokawar da suka sha dashi wajen ceton ransa da yai k'ok'arin yi, wannan takardar kuwa hotunan d'akin shi Sadeeq d'in ne wanda 'yan sanda suka d'auka ranar da abun ya faru, d'aya takardar kuwa ta likita ce wadda ya tabbatar mana da cewa shaidar hannun Abdul ne a kan wuk'ar," bayan ya gama fad'i sannan ya bayar aka mik'awa Alk'ali domin ya nazarce su, sannan ya sake cewa " kafin kisan bincike ya nuna cewa a daren da abun zai faru Sadeeq ya shawu kuma hakan ne ya baiwa Abdul damar kashe shi duk da kuwa yana cikin maye amma sai da yai k'ok'arin ceton ranshi, amma ya mamaye shi ya kashe shi, akwai d'aliban da suka tabbatar mana da Sadeeq ya shawu a ranar, kuma sunga dawowar shi cikin gida, a yayin da suka hango wani wanda basu ga fuskar shi ba kuma yana binsa a baya sun d'auka tare suke shiyasa a lokacin basu kawo komai ba," nan dai ya gabatar da su d'aya bayan d'aya, suka yi rantsuwa sannan suka fad'i iya abinda suka gani a daren ranar, bayan Alk'ali ya gama 'yan rubuce rubucensa sai ya d'ago ya kalle su yace " kotu ta ji duk bayanai da hujjar kowa, sai rana ita yau zamu dawo domin jin hukuncin da kotu ta zartar. Muje zuwa *🅱K CE*😘💋 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)``` PAGE 30 to 35 Yau litinin, kotu cike take mak'il da mutane, suna sauraren hukuncin da Alk'ali zai yanke a kan Abdul. Bayan rubuce rubuce da ya yi, sannan ya d'ago ya kalli Barista Aisha Isa yace " kinada wasu tambayoyin ne ko shaidu da zaki gabatar?" Aisha ta mik'e duk ta sare saboda bata da hujjar da zata kare Abdul da ita, tace " a'a ya mai shari'a banda abun cewa," Alk'ali ya sake kallon inda Barista Muhammad yake yace ko kana da wata shaidar ko k'arin tambayoyi da zaka gabatar?" Barista Muhammad yace " a'a ranka ya dad'e." Bayan Alk'ali yai rubutu na wasu lokuta sannan ya d'ago kai yace " bayan sauraren bayanai da muka yi daga gun lauyoyi, tare da hujjojin da aka gabatar, kotu ta gamsu da cewa Abdul shine yai wannan kisan, dan haka ga hukuncin shi kamar haka, kamar yanda muka sani ne cewa wanda ya kashe rai shima hukuncin shi kisa ne, dan haka kotu ta yanke wa Abdul hukuncin kisa ta hanyar rataya, wanda ake k'ara yana da damar sake shigar da k'ara a wata kotun kafin nan da wata uku, ana gama fad'in haka Abdul ya fad'i k'asa a sume, Amira tayo kanshi da gudu tana kuka zata d'aga shi aka dakatar da ita, su preety ne suka janyeta suka fita daga wajen kowannen su kuka yake zuciyoyin su duk ba dad'i. Surutai Amira tai ta yi musu cikin mota tamkar tab'ab'b'iya, tana fad'in na zama silar mutuwar mutum biyu, yanzu kenan duk wanda ya rab'eni kashe shi za'a rik'a yi kenan, na hak'ura da karatun zan kira Dad yazo ya d'auke ni in koma gida, tana kaiwa nan a zancenta sai ta k'ara fashewa da kuka. Bayan sati d'aya da mutuwar Abdul sai aka baiwa kowane d'alibi damar tafiya gida saboda samun natsuwa kan abinda ya faru a cikin makarantar, bayan wata d'aya sai su dawo. Hakan yasa Amira taji dad'i sosai domin dama hankalinta ba'a kwance yake ba, ta tarkata inata inata zata tafi, tafiyar da ta k'udurta a ranta in ta tafi ta tafi kenan bata fatan ta sake ganin ta dawo makarantar ko a mafarki, ace duk wad'anda ta shak'u da su ana ta kashe su, gwara ta tafi kafin a k'arar da su gaba d'aya. Bayan ta gama had'a kayan ta jawo jakarta tare da juyowa zata fita sai taga Amir tsaye bakin k'ofa ya jingina jikin k'ofar tare da hard'e hannayensa yana kallonta, idanuwansa kuma suna fitar da hawaye. Amira ta ajiye jakar cikin sauri ta nufo shi, tana tare da dafa kafad'un shi tana tambayar shi lafiya me ya faru, ganin yanda ta tayar da hankalinta yasa ya sassauta da kukan, ya kalleta yace " kina sauri da zumud'in tafiya ki barmu ko? Amira nasan abinda kike shirin yi, kina son in kin tafi ba zaki k'ara dawowa ba ko? to kafin kiy wannan tunanin kin yi tunanin halin da zan shiga idan bama tare da juna, kinsan yanda na shak'u dake kuwa, Amira adalcinki kenan ki k'aurace mana, ki tafi ki barmu, sai ya fashe da kuka, kuka sosai yake yi, ya durk'usa tare da saka gwiwoyinsa a k'asa tare da had'a hannayen sa ya cigaba da cewa dan Allah karki tafi zuciyata zata cutu idan kikai nesa da ita, nai miki alk'awarin kasancewa tare dake da kuma saka ki farin ciki da walwala, ke nai miki alk'awarin mantar da ke damuwar da kike cikinta ma a yanzu amma nidai rok'ona kawai gareki ki zauna tare da ni." Yana rok'onta yana kuka, Amira ta k'araso wajen shi jikinta a sanyaye tare da saka hannayenta biyu ta mik'ar da shi tsaye, sannan tace " Amir ina jin tsoron zamana a tare da ku, saboda kar kuma a kashe ku, ni mamaki ma ka bani, kai da zakai farin cikin rabuwa da mutum irina sai ka rik'a rok'on cigaba da rayuwarmu a tare, baka tsoron a kasheka ne?" Amir yace " to menene dan na mutu saboda ke, bazan damu ba domin ina da masaniyar dole wata rana zan tafi, abun damuwar kawai ke a kashe ki, na rantse da Allah da kuwa na k'arar da mutanen duniyar nan gaba d'aya," Amira tace " har yaushe mukai shak'uwar da kake jin irin haka a kaina?" Amir yace " hmmm kece dai baki sani ba, amma zuciyata ta dad'e da shak'uwa da taki, kuma bana jin tsoro ko shakka ko targabar mutuwa ta sanadinki." Amira tai ajiyar zuciya, sannan tai shiru tana tunanin yiwuwar tsayawar ta-ta, ganin haka yasa ya k'ara had'a hannayensa yana rok'onta, k'ok'arin sake kai kwiwoyinsa kasa yake yi tace " shikenan na ji zan tsaya, amma ya akai ka san cewa inada k'udurin idan na tafi ba zan sake dawowa ba?" Amir yace " saboda na san ko wanene hakan ta faru dashi wannan hukuncin zai yanke, amma banda ni," Amira tace meyasa banda kai?" Amir yace " saboda wad'anda nake tare da su zasu ji ba dad'i, babu inda zan matsa saboda su, a koda yaushe yana da kyau mu rik'a tunanin halin da masoyanmu zasu shiga a duk lokacin da suka rasa mu," sun dad'e suna tattaunawa sannan ya sata ta maida jakarta, har yamma suna tare ya k'i yarda ya matsa ko nan da can saboda gani yake kamar yana tafiya zata gudu ne, agogo ya kalla yaga hud'u ta yi, sannan ya sake maida kallon shi gareta, yace " bari na je gida nai wanka na canza kaya in dawo, amma dan Allah kiy mini alk'awarin ba zaki gudu ba bayan na tafi dan Allah." Yanayin yanda yai maganar ya matuk'ar baiwa Amira dariya, ta kalle shi tace " ka kwantar da hankalinka ba inda zan je na yi maka alk'awari, " Amir yace " to sai na dawo kema ki shirya idan na dawo fita zamu yi," suka yi sallama ya tafi. Amir be d'auki wani dogon lokaci ba ya iso gida ya faka motar shi sannan ya fito ya shige ciki, wanka ya shiga ya fito sannan ya shirya cikin k'ananan kaya bak'ar tshet da jeans ya yi kyau sosai, ya kalli kanshi ya k'ara kallo, sannan ya fesa turare ya d'auki makullin motarsa ya fito. Koda ya k'araso itama Amira ta shirya, ya kalleta bayan ya gama kallonta son ranshi sannan yace mata "muje koh," Amira tace "to suka fito suka tafi. Wani katafaren shago suka tafi na saida abubuwan more rayuwa, ya sakata ta kwashi duk abinda take so amma ta k'i, sai ya zage ya shiga lodar mata duk abinda yake ganin zai yi dai-dai da ita, ganin yanata abu d'aya kuma baida niyyar dainawa yasa ta dakatar dashi haka, suka je aka lissafa Amir ya biya kud'in. Suka fito daga shagon Amir yana rik'e da kayan, fura da nono Amira ta hango wata bafulatana tana siyarwa a tsallaken ti-ti sai ta kalli Amir tace " ya kai kayan tana zuwa, Amir ya kalleta yace " ina zakije?" Amira tace " kai dai ina zuwa can tsallaken zan je abu na hango," Amir yace " to karki sake ki dad'e," Amira tai murmushi sannan tace " to ranka ya dad'e," ta juya ta tsallaka ti-tin ta siyo abinda zata siyo ta juyo zata dawo." Ta zo zata tsallaka ti-ti kenan wata mota ta taho a guje a dai-dai Amir fito daga motar, da k'arfi ya k'wala mata kira yana ta koma da baya amma ina, hakan yasa yai kukan kura ya shiga ti-tin a guje saura k'iris motar ta latse Amira ya sa hannunshi duka biyun ya turata gefe, a yayin da shi kuma motar tai awon gaba da shi. Amira ta taso daga fad'uwar da ta yi, tare da k'wala k'ara ganin yanda Amir yake zubar da jini kuma tamkar ma babu alamar rai a tare da shi. Kanshi ta yi da gudu tana jijjiga shi, nan da nan mutane suka cika wajen, kuma da yake bakin ti-ti ne 'yan sanda na kusa da wurin, suma babu b'ata lokaci suka k'araso, wanda ya kad'e shi kuwa yai k'ok'arin guduwa amma cikin yardar Allah aka kamashi, aka wuce da shi station, a yayin da shi kuma Amir aka sa shi a cikin motar shi a baya, Amira ta shiga ta zauna kusa d shi, d'an sanda ne yaja motar, a yayin da ragowar suka biyo su a tasu motar. Suna k'arasowa cikin sauri aka shige da shi emergency, likitoci suka rufa kanshi ana ta duba shi. Sun d'auki dogon lokaci suna duba shi, ganin haka ya k'ara tayar da hankalin Amira sosai, banda kai kawo da kuka babu abinda take yi, sam ta rasa natsuwarta gaba d'aya, tashin hankalin da take ciki a yanzu ko lokacin da Sadeeq ya mutu bata jishi ba, sabod ita ta san tabbas Amir yana da babbam matsayi a gareta saboda ya damu da ita fiye da kima, wannan dalilin ne yasa ta shiga firgicin da bata tab'a shiga irinsa ba, tsoro take shima karta rasa shi, can k'asan zuciyarta kuma tausayin shi take ji, yanda ya sadaukar da ranshi domin ceto ta-ta rayuwar. Wani d'an sanda ne ya kalleta cikin tausayawa yace " madam ki kwantar da hankalin ki insha Allah mijinki zai samu sauk'i, kiyi hak'uri ki d'an zauna ki huta wajen awa d'aya da rabi sai kai kawo kike yi." Amira tace " mishi to nagode," amma ta kasa yin abinda ya rok'a, ta kasa zama, ci gaba ta yi da kai kawonta har likitocin suka fito tare da shi an nad'e k'afafu, da kai da hannu guda d'aya da bandeji aka kai shi wani d'aki da keb'antacce. Da dai likitocin sun so su hana Amira shiga, amma d'an sandan ne yai magana yace " dan Allah ku k'yaleta matarshi ce, ta damu da yawa, ku barta ta zauna duk da nasan bakwa bari ana jinya anan kuna da masu kulawa da marasa lafiyan, amma ita ai mata wannan alfarmar." Bayan sun shisshiga d'akin da aka kwantar da shi, duk da haka Amira bata daina kukan ba, Likita ya kalleta yace " ya kamata ki bar kukan nan haka baiwar Allah addu'a ya kamata kiy mishi ki ma godewa Allah da k'wak'walwarsa bata tab'u ba, se dai ya ji raunuka a jiki, sannan ya samu karaya a k'afa da hannu, amma duk mun gyara insha Allah zai samu sauk'i," d'an sandan nan yace " Allah ya bashi lafiya," dukkan su suka amsa da "ameen." Suka yi mata sallama suka fita, matsawa kusa da shi ta yi ta zauna kusa da shi a wata kujera ta k'ura mishi idanu, sai ta tuna lokacin da tai rashin lafiya yai jinyarta, ji ta yi an fara kiran sallar magrib, ta tashi ta yi sallah sannan ta antayo wa Amir addu'ar samun sauk'i. Tunani ta fara yi ya kamata ta nemar musu abinda zai ci koda ruwan tea ne idan ya farfad'o tunda likita ya fad'a musu suma ya yi, amma zai farfad'o nan bada dad'ewa ba. Tunani ta fara yi ya zata yi domin ita babu inda zata iya matsawa ta bar Amir shi kad'ai, tunowa ta yi sun siyo kaji d'azu da yogot da sauran su, se dai suna cikin mota kuma ita fitar ne bata so ta yi sam ta bar Amir. Tana cikin wannan tunanin sai wata norse ta shigo, bayan sun gaisa tai mata ya mai jiki ta amsa, sai norse d'innan ta bata maganin shi tace ta ajiye idan ya tashi ta bashi gasu nan a rubuce yanda zata bashi, daga k'arshe ta tambayeta ko akwai abinda take buk'ata. Amira tace mata a'a babu se dai akwai kayan mu cikin mota dan Allah wa zaki sa ya taimaka ya d'ebo min?" norse tace " ba damuwa bani makullin in kwaso muku, kuma ki fad'a min kalar motar." Amira ta bata makulli tare da fad'a mata sunan motar da kalarta sannan norse d'in ta fita, ita da wasu norses d'in sukaita kwaso kayan, bayan sun gama kwasowa Amira tai musu godiya. Har wajen k'arfe tara Amir bai farka ba, har Amira tai sallar isha'i hakan ya tayar da hankalin Amira sai ta ci gaba da nafiloli tana rok'ar wa Amir lafiya, bayan ta idar ta zage tana ta kwakuso addu'a tun tana yi har kuka ya ci k'arfinta taita yi ba k'ak'k'autawa, ji ta yi ance "Amira ki daina kukan nan dan Allah bana so yana tab'a zuciyata," yanayin yanda aka yi maganar yasa ta gane Amir ne hakan yasa ta zabura ta yo kanshi, bata san lokacin da ta rik'e hannunshi ba tace " Amir sannu ya jikin, da sauk'i ko, ina da ina ke maka ciwo?" Amira yace " da sauk'i ki kwantar da hankalinki, ganinki lafiya babu abinda ya sameki ya kore duk wani rad'ad'i na ciwukan dake jikina." Amira ta kalle shi tace " Amir meyasa kake k'ok'arin halaka kanka saboda ni, yanzu da ka mutu fa." Amir yace " ke da kin mutu an fad'a miki zan cigaba da numfashi a duniya ne, ai na fad'a miki da ace kin mutu ko an kashe ki gwara kowa ya mutu ciki kuwa har da ni." Hararar shi ta yi sannan tace " kai d'in in da ka mutu nima an fad'a maka zan iya jurewa ne." Nan ta had'a mishi tea ya k'i karb'a wai sai ta had'a tukun tasha a gabansa ya gani sannan zai karb'a shima yasha, don ya san itama ba abinda ta ci, sai da ta had'a ta sha sannan ta bashi shima ya sha, sun dad'e suna hira daga k'arshe suka kwanta, da yake gado biyu ne a d'akin da nashi da wani a gefe ba kowa sai ta kwanta a d'ayan bayan ta yi addu'a, sedai har tai bacci amma shi Amir idon shi biyu, shi kad'ai yasan zugin da yake ji a jikinsa amma so ya hanashi bayyanawa saboda kar hankalin abar k'aunar tasa ya tashi, haka ya kwana bai runtsa ba ko ina ciwo yake yi mishi a jikin shi. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)``` *MY LISSA* _Kinyi kira na amsa soyayya kin bani nai alkawar zamui zama na amana_💃💃💃💃💃 _cikin raina, na sanyo ki, ki bani guri nima in shigo naki😍😍😍😍😍_ _*MY LISSA* k'aunar da kika nuna a gareni baki ya yi kad'an wajen gode miki, se dai zan yi amfani da shi wajen yi miki addu'ar gamawa da duniya lafiya, kina d'aya daga cikin gagaruman marubutan da ke matuk'ar k'aunar *SO MAHAD'IN RAYUWA* kuma Amir ya ce in fad'a miki duk abinki baki isa ki san komai game da shi ba, nidai ba ruwana sak'o ya bani kuma na isar🙊🏃‍♀😂😜_ _nagode da k'auna, yabo, Addu'a da na samu duka daga gareki Allah saka da alkhairi, ina mugu mugun yinki, iya wuya ana tare My lissatu tawa😉😘_ PAGE 35 to 40 Bayan sati biyu jiki yai kyau aka sallame su suka koma gida. Washe garin ranar da aka sallame su Amira ce keta faman rama baccin da bata samu ta yi a asibiti ba, ga gajiya da ke tambayarta, tana cikin baccin ne wayarta ta fara ringing har ta katse ba'a d'auka ba, sai a kira na biyu ta kai hannunta ta jawo wayar tare da amsawa ta kara a kunne, muryar Amir ta ji yana fad'in " Amira dan Allah kizo ki taimaka min bana jin dad'i sosai wayyo zan mutu," haba ai ba shiri taji nan da nan ta wartsake daga baccin da take ji, bata tsaya tambayar shi ko jin abinda ke damunshi ba ta katse wayar, mayafi kawai ta zara sai makullin mota ta fice daga gidan cikin sauri kuma cike da tashin hankali. Da yake bata tab'a zuwa gidan shi ba, amma ya tab'a fad'a mata sunan unguwar, hakan yasa saida ta shiga unguwar sannan ta kira shi ya fad'a mata gidan. Bayan ta k'arasa k'ofar gidan ta shiga da motar ta tai fakin sannan ta fito ta shiga ciki har tana had'awa da gudu, tana shiga ta ja ta tsaya turus, domin zaune ta ganshi kan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallo, Amira ta kalle shi tace " dama lafiyarka lau shine ka tayar min da hankali menene amfanin yin hakan?" Amir yace " lafiya lau nake se dai zuciyata da ke yi min zafi saboda addabata da take yi da tunaninki, dama saboda kizo in ganki ne in samu maganin rad'ad'in da take min ne kawai, haba Amira tun jiya fa da muka dawo daga asibiti ban k'ara ganinki ba a tunaninki baran cutu ba." Amira ta harare shi tare da kai mishi duka da hannu ya goce tare da yi mata dariya harda kashe ido d'aya, Amira ta kalle shi tace " ka daina yi min irin wannan wasan bana so, da ka fad'a min gaskiya kana son ganina ne ai zan taho gareka ba sai ka tsoratani da rashin lafiya ba," ganin ranta ya b'aci da yawa yasa ya taso ya duk'a a gabanta yana bata hak'uri amma ta kauda kanta, plet d'in wak'ar d'an kuka ya saka sannan ya kunna mik'ewa tsaye ya yi, wak'ar cikin film d'in na d'an kuka yake rera mata _(abinda nai kiy hak'uri na yi nadama)_ yana rawa a gabanta yana had'a hannaye tare da kakkantarewa tamkar yanda ake yi a cikin wak'ar, duk yanda taso kartai dariya saida ya sata dariya sosai har saida wak'ar ta k'are sannan ya hak'ura da rawar, zama ya yi a gabanta ya tasa ta kamar tv yana kallo, ta kalle shi tace " wallahi ka bani dariya," Amir yace haka nake fatan ki kasance a koda yaushe." Amira ta sake kallon shi sannan tace " ya k'arfin jikin?" Amir yace " na ji sauk'i nan ne kawai yake min ciwo ya nuna saitin zuciyarsa da hannu, share shi ta yi, tare da mik'ewa zata tafi shima ya tashi yace " naga kin mik'e ina zaki je?" Amira tace zan tafi gida mana, Amir ya b'ata rai sannan yace " dan Allah karki tafi, idan muna tare wallahi bana so mu rabu koda na minti d'aya ne kuwa," Amira ta kalle shi tace " meyasa?" Amir yace " nima tambayar da nake ta wa kaina kenan, meyasa nake jin hakan a tare dake, yanzu dai abar wannan maganar wannan ne karonki na farko zuwa gida na saboda haka da kaina zan shiga kicin in miki girki, me kike so a dafa miki?" Amira tace " tab' bazan ci kwamacalarka ba bakina ya b'aci, in girki kake so bari in shiga in girka maka," Amir ya kafe kan shi zai yi mata girki haka nan ta hak'ura ta k'yale shi, ya shiga kicin yana aiki a yayin da ya hanata taimaka mishi da komai, bayan wani d'an tak'aitaccen lokaci Amir ya kammala abinda yake girkawa, ya zubo mata sannan ya zuba mata lemo, cikin fargabar yanda bakinta zai b'aci ta kai cokali d'aya bakinta tare da fara yamutsa fuska, a hankali kuma sai ta ware tare da kallon shi, bata ankara ba ta tayar da girkin Amir tas, bayan ta gama ta sha lemo kad'an sannan ta kalle shi tace " ka bani mamaki matuk'a, wallahi ka iya girki, matarka ta huta." Amir yai karaf yace " to ai kece matar," d'agowa ta yi tare da wurga mishi wani irin kallo mai kama da harara da kuma tuhuma, shima kallonta ya yi tare da rik'e bakin katob'arar da ya yi, a ganinshi ba yanzu bane lokacin bayyana mata abinda ke ranshi, kallonta ya sake yi sannan ya turo baki kamar k'aramin yaro yace " maida wuk'ar wannan fushi da harara haka, to wasa nake yi, 'yar daba kawai, wannan kallon da kike min 'yan daba kad'ai ke yin irin shi," sannan ya murgud'a mata baki. Girgiza kai Amira ta yi, tare da yin murmushi, a zuciyarta take fad'in tabbas Amir yai gaskiya da yace zai sakata ta manta da duk wata damuwa gashi kuwa ta tabbatar, harga Allah zama da shi yana sata cikin farin ciki a koda yaushe, tana jin dad'in kasancewa tare da shi sosai. Amira ta duba agogo, sannan ta d'ago ta kalle shi tace " lokaci ya tafi zan koma gida, tun da safe da ka sani na fito ba shiri gashi yanzu har biyu ta yi," Amir ya kalle ta yace " dan Allah karki tafi, ki zauna da zuciyar da take muradin kasancewa da ke a koda yaushe." Amira ta kalle shi tace " wallahi kana bani mamaki ka fiye rigima sai kace mace, jiya fa muna tare yauma gamu a tare, da yaushe ne bama kasancewa da juna." Amir yace " shikenan bari in zo in kai ki," Amira tace " a'a ka barshi nafi so ka huta ka k'ara wartsakewa," Amir yace " taya za'ai in wartsake kina tafiya ki barni ni kad'ai, dan Allah karki tafi, wallahi bana so kina yin nesa da ni," kallon shi Amira ta yi sannan tace " wai da gaske kake dama, kai in nace zan zauna sai ka yarda?" Amir yace " wallahi da gaske nake yi bana so kina yin nesa da ni, kuma duk abinda nake fad'a miki sak'o ne daga zuciyata zuwa ga taki zuciyar." Amira tace " ka k'ware wajen iya tsara kalamai, da kallon k'urulla da kake yiwa mutane da kuma kalamanka da za'ai gasa a kansu ina tsammanin kai zaka zo na d'aya," Amir yai murmushi karo na farko da ya ji dad'i a ranshi sanadin Amira ta yaba mishi." Sallama suka yi da shi ya shaida mata yana nan zuwa anjima zai zo su sha hira, tace ya bari sai gobe in Allah ya kaimu lokacin jikin ya k'ara warwarewa, Amir yace " wallahi sai nazo anjima ko zaki kwana kina rok'ona kar nazo ehe," haka ta fito tana dariya ta barshi yana mita tana jiyo shi wai bata so yazo. Haka suke kasancewa a koda yaushe suna tare, bayan kwana biyu da yamma wajen k'arfe hud'u Amir ya faka motar shi k'ofar gidan Amira, hon ya danna ba tare da ya shiga ba sai gata ta fito, to dama yanzu sun saba kullum zasu fita da yamma suje wurin shak'atawa da sauran wurare dai na jin dad'i da more rayuwa, to duk in zasu yi irin wannan fitar basu cika zuwa a mota ba, da yake daga gidan Amira ba nisa zuwa wajen. Fitowa Amir ya yi shim daga mota suka d'auki hanya, kowa ya gansu tamkar miji da mata, sun zuba anko kamar had'in baki kayan da Amir yasa shadda ce milk, itama atamfar da ta saka milk d'in yafi yawa a jiki, sun sha anko sunyi kyau sosai, duk inda suka gifta su kawai ake kallo, suna cikin tafiya sai Amira ta hango fura da nono, to ita dama tana masifar son fura da nono, kuma duk inda ta gani bata wucewa sai ta tsaya ta siya, hakan yasa Amira ta nuna wa Amir tace ya jirata taje ta siyo ta dawo, da yake can tsallake ne, dole sai an tsallaka ti-ti sannan za'a k'araso inda me furar take Amir yace " a'a babu inda zaki je, ki jirani in siyo miki in dawo, Amira tace to tsaya ka karb'i kud'in ya harareta sannan yace " kaji son a sani, ai ko banda kud'i a aljihuna ko rigar jikina sai na siyar na se miki abinda kike buk'ata wallahi," Amira tace " ai kuwa duk ranar da kai haka ban jerawa da kai babu riga," juyawa ya yi yana dariya ya tsallaka ti-ti domin siyo mata abinda ta buk'ata, ya juyo zai dawo ya hango wasu maza kewaye da ita, da alamu magana take gaggaya musu, da gudu Amir ya tafi wajen su, wani ne ya d'aga hannu zai mari Amiran a dai-dai Amir ya k'araso kawai ji ya yi an rik'e mishi hannu ta baya Amir be sakin mishi hannu ba saida ya karya, nan fa Allah ya bashi sa'a yai musu shegen duka, yana cikin dukan su 'yan sanda suka k'araso wajen ciki kuwa harda Insp Yahya (kafi k'arfin mugu), kallon kallo suka yi tsakanin Amir da Insp Yahya, can sai Yahya ya baiwa jami'an umurnin su tafi da su station gaba d'aya, haka kuwa aka yi, aka sa su a mota sai station. Dukkan su a tsugunne suke gaban Insp Yahya yana kallon su d'aya bayan d'aya, sai da yaji duk abinda ya faru, kuma dama tun a can ya yi bincike an tabbatar mishi da cewa Amir ne ya hau dukan su saboda kawai sun kula Amira. Dukkan su cikin sel aka gark'ama su, Amira tana ta faman rok'on sa akan cewa ya yi hak'uri dan Allah ba zai sake ba, Insp Yahya ya kalleta yace " ai bazan iya sakin d'aya in bar d'aya ba, se dai in duka zakiy belin su to," Amira tace "eh na yarda a bani belin d'in su gabad'aya," saka wa ya yi a fito da su, sannan suka saka hannu d'aya bayan d'aya kan in suka sake sai an hukunta su hukunci mai tsanani, ya sallame su, amma banda Amir da Amira. Bayan sauran sun tafi Insp Yahya ya kalli Amir yace " wai kai menene alak'arka da wannan yarinyar ne," Amir kai tsaye yace " sonta nake kuma aurenta zan yi, Insp Yahya yace " ai naga alama tun kafin ka fad'i, to wannan dalilin ne yasa ka shek'e samarinta har biyu?" Amir yace " yallab'ai kawai dan na yi soyayya da Amira sai ya zama laifi har ana tuhumata da aikata kisa, kenan duk wanda ya yi soyayya da ita tuhumar kisa zaku yi mishi, kiji fa abinda d'an sandan nan ke fad'i Amira, " ya juya yana yi wa Amira magana. Amira ita kanta bata ji dad'in maganar da Insp ya fad'a wa Amir ba, ta kalli Insp tace " yallab'ai a tunani tunda an riga an gano mai laifin har an hukunta shi to be dace kana tuhumar wani daban ba kuma babu shaida ba komai, mun gode da taimakon da kai mana a yau," ta kalli Amir tace suje. Har sun kai bakin k'ofa Insp yace " idan ka k'ara shigowa hannunmu kan ka daki wasu ko ka yi fad'a da wasu to zaka yi watanni a kulle," cikin sauri Amir ya juyo ya dawo tare da fad'in yallab'ai kawai in zaka kulle ni ka kulle ni, amma na rantse maka da Allah akan Amira ba wanda zan k'yale, ko kallon banza akai mata to wallahi sai na kai duka, tun yanzu na fad'a maka gaskiyata gwara kawai ka maida ni cikin sel d'in zai fi," yana fad'in haka yana kuma tunkaro inda Insp d'in yake, Amira ce tai sauri ta rik'o hannun Amir d'in sannan ta kalli Insp tace " yallab'ai ka yi hak'uri, insha Allah zamu kiyaye, ta ja hannun Amir d'in suka fice daga station d'in, gida suka wuce kai tsaye fitar da ba'a yita ba kenan a ranar. Insp kuwa koda suka fita binsu yai da kallo yana huci sannan ya girgiza kai yace " tun ganina da Amir d'innan naji ina zargin shi, kuma itama Amiran yanzu na fara zarginta ban yarda da su ba, kuma daga yau wallahi sai na sa musu ido a kan duk wani motsi nasu, hmmmmm baku san wanene kafi k'arfin mugu ba labarina kawai kuke ji, ba dai shaida kuke nema ba, zan nemota duk inda take." Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* _(Mamie)_ *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)``` PAGE 40 to 45 Zaune suke kowanne daga cikin su ranshi a b'ace saboda abinda ya faru yau ya b'ata musu shirin su, Amira ta d'ago kai ta kalli Amir tace " Amir kulawarka ta yi yawa a kaina meyasa, gaskiya in kana so mu shirya ka daina yin fad'a da mutane kaina." Amir ya ji ba dad'i a cikin maganarta ta yanzu, kuma itama ta lura da hakan, ya kalleta yace " kiyi hak'uri ban yi hakan domin b'ata ranki ba, kuma bansan yin hakan zai zama laifi a gareki ba ko abun b'acin rai da ban yi ba, na yi haka ne domin kare ki daga sharrin su, kiyi hak'uri laifina ne da na biyewa umurnin zuciyata na aikata abinda ya zama silar b'acin ranki," yana gama fad'in haka sai ya tashi ya fito daga d'akin, lambun gidan yaje ya zauna tare da kife kanshi yana kuka. Amira ce ta fito itama ta biyo shi tana neman inda yake, fita k'ofar gida ta yi tana dubawa, se dai ganin motar shi a k'ofar gidan ya tabbatar mata da ba tafiya ya yi ba, to yana ina tambayar da take ta yiwa zuciyarta kenan, nadamar maganganun da ta fad'a mishi take yi domin tasan duk a kanta da kulawar da yake mata ne tasa yai komai, nan ta ji gaba d'aya bata kyauta ba, tunaninta a yanzu kawai kar b'acin ransa ya sa ya jawo ya yi abinda zai cutar da shi, nan da nan itama ta fara hawaye, tana kukan tana waige waige ko zata ganshi can sai tunanin shiga lambu yazo mata, da sauri ta nufi wajen har tana cin tuntub'e. Tana shiga wajen tun daga nesa ta hango shi, ta k'arasa da sauri har lokacin kuka yake yi ta zauna kusa da shi, sannan ta dafa shi tace " haba Amir meyasa kake yi min asarar hawayenka daga yin wannan maganar." Amir ya d'ago ya kalleta da idanunsa da suka koma ja, kuma har sun fara kumbura saboda kuka, yace " ba ina yin kuka bane saboda maganar da kika fad'a min a'a, ina yin kuka ne a kan b'ata ranki da na yi, duk duniya idan da akwai abinda ya fi zama tashin hankali a gareni to b'acin ranki ne," yana gama fad'in haka ya koma zai mayar da kanshi ya cigaba da sana'ar tashi, sai ta hanashi komawa ta hanyar rik'e shi. Amira ta kalle shi sannan tace " ka daina kukan haka to dan Allah bana so, ka yi hak'uri da abinda na fad'a maka, bana so ka sake yin rigima ne shiyasa na fad'a maka haka, amma nima naji zafi a raina lokacin da nake fad'a maka, kuma ni raina bai b'aci ba, koda ya b'aci ko na ji haushi bazan gwada shi a kan wanda yake zama sanadin farin cikina ba a koda yaushe, wanda ke samar da walwalata kuma yake farin cikin kasancewar shi a tare da ni a koda yaushe." Amir yai murmushin jin dad'in maganarta, Amira ta kalle shi tace " yauwa ko kai fa, ta share mishi hawayen fuskarsa da hannunta ta mik'e sannan ta mik'o mishi hannu tare da fad'in taso mu koma falo, Amir ya kama hannunta tare da mik'ewa suka koma cikin d'aki. zama suka yi a kujera sannan Amir ya kalleta yace " naga kema kamar kin yi kuka, fad'amun me ya saki kuka?" Amira tace " yo ba dole in yi kuka ba bansan ina ka shige ba," Amir yai murmushi zuciyar shi na fad'in lallai Amira ta fara damuwa da shi, dama abinda yake so kenan, ta shak'u dashi, ta damu da shi kafin ya kai ga furta mata, cikin ranshi yace lallai lokacin bayyana mata sirrin zuciyata ya kusa. Amira ta kalle shi tace " me zan dafa maka, dan nima yau sai ka ci irin girki na, " Amir yace "a'a ki bari zan dafa mana kije ki kwanta kawai," Amira cikin ranta tace " dama so nake kace zaka yi shiyasa na fad'i haka saboda kar na nuna maka ina son girkin ka kai min dariya," Amir ya kwashe da dariya yace to ai ko yanzu na ji tunda a fili kika fad'i, inma a zuciya kike tunanin kin fad'i to ya fito fili," ya sake kwashe mata da dariya tare da yi mata gwalo, tab'e fuska tai kamar zata yi kuka, ta biyo shi da gudu sai da suka gama zagaye falon duk abinda ta samu tana wurga mishi duk sun haukata d'akin, sannan daga k'arshe Amir ya shige cikin kicin d'in tare da rufo k'ofar, daga falon Amira na numfarfashin wahala tace zaka fito ka sameni ne ai. Amir yai murmushi, jin takunta alamar ta juya yasa ya k'arasa ciki ya fara gudanar da aikin da ya shigo da shi ciki, da yake akwai komai a cikin kicin d'in shiyasa sam bai fito ba. Sai da ya kammala dukkanin abinda yake yi sannan ya fito, gani yai d'akin yai ras ko'ina an gyara shi, ga wani dadda'dan k'amshi da ya cika ko ina murmushi ya yi sannan a fili yace " kamar kin san ina mugun son mace me tsabta gaskiya na dace," bayan ya gama jera abincin ya shiga cikin d'aki domin kiran gimbiyar, se dai tarar da ita ya yi ta yi wankanta ta kwanta tana ta bacci, har ya duk'a zai tashe ta sai ya fasa, ya bar ta sai ta tashi dan kanta. Makullin motar shi ya d'auka ya fita ya tafi gidan shi, wanka ya yi yai sallah sannan ya sake cakarewa cikin k'ananan kaya, ya sake d'aukar makulli ya fito sai gidan Amira. Wani katafaren shago ya biya ya siya wani abu wanda ban lura da ko menene ba ya biya aka sa mishi cikin leda ya fito ya shiga motar shi, bai sake tsayawa ko ina ba sai gidan Amira. Bayan yai fakin ya fito ya shiga ciki, koda ya shiga bai tarar da ita a falo ba, wucewa yai ciki ya tarar da ita har yanzu bacci kawai take sha, bubbuga gadon ya hau yi yana fad'in " malama ki tashi ni fa yunwa nake ji ke nake ta jira." Amira ta tashi tare da ambaton sunan Allah, ta fad'a ban d'aki ta sake yin wanka sannan ta canza kaya ta fito, a falo ta tarar da Amir ya zuba abincinsa ya fara ci. Amira ta kalle shi tace " shine baka jira ni na fito ba," Amir yace " kaiiii na jira ki har na gaji baki zo ba." Amira ta zuba abincin itama ta fara ci, suna ci suna hira har suka gama. Haka suka cigaba da gudanar da rayuwar su, koda yaushe suna tare, kuma komai tare suke yi, hatta girki tare suke yi, gyaran gidan tare suke yi, cin abinci a tare, hakan ya k'ara musu matsananciyar shak'uwa mai tsanani a tsakanin su, tsakanin Amir da gidansa se dai ya koma da dare ya kwanta gari na wayewa ya sake fitowa sai gidan amira. Yau ya rage musu saura kwana d'aya tak a koma makaranta hakan yasa suka fara shirin komawa. Bayan sun koma makaranta Amira taga canji sosai a makarantar su, domin duk wad'anda ta shak'u da su sun gujeta, ko cikinsu taje d'aya bayan d'aya suke guduwa, a tunanin su duk wanda ke tare da ita kashe shi ake yi, a aji ma haka ita da Amir kad'ai suke zama waje d'aya babu wanda yake shiga harkarta da shi kanshi Amir d'in. Wannan canjin yai matuk'ar d'aga musu hankali daga Amiran har Amir d'in. A ranar da ta fara ganin wannan canjin bata ma gama lecture ba ta bar makarantar, tana komawa gida taita kuka kamar ranta zai fita. Amir ya fito daga lecture ya nemi Amira ya rasa, ya kira wayarta amma bata d'aga ba, ba shiri ya figi motarsa sai gidan Amira, ko motar be kashe ba ya fito ba tare da ya rufe murfin motar ba ya shige gidan, zaune ya ganta kan kujera ta kifa kai da gwiwa tana kuka, wata irin doguwar ajiyar zuciya ya saki na jin dad'in ganinta. Amir ya k'arasa inda take ya zauna, kallonta ya yi sannan yace " ba sai na tambayeki dalilin kukanki ba Amira tunda na riga da nasan dalili, se dai ina mamakin inda tunaninki ya tafi kika manta cewa akwai wani bawan Allah guda d'aya a gefenki wanda yake da niyyar faranta miki har k'arshen rayuwa, ya kamata a ranki kiji in duk duniya ta gujeki to mutum d'ayan nan tak ya wakilci dukkanin mutanen duniya a wajenki, Amira kukan ki yasa naji ba dad'i gani nake kamar na gaza wajen baki dukkanin farin ciki da kuma mantar dake kowane irin b'acin rai da na alk'awarta, kiyi hak'uri ki daina kukan nan zuciyata na fitar da wani irin tiririn zafi. Ta daina kukan da taimakon Allah da taimakon nagartattun kalaman shi, labarai ya fara bata na ban dariya yace " bari na baki wani labari." _"lokacin da nake boarding a secondary school muna kwakkwance da dare wajen k'arfe takwas ina karatu sai fitsari ya matseni, inata juyi nak'i tashi inje in yi kuma ban dena juyin ba, wanda yake can saman gadona yana kwance yana kallona, zabura nayi da gudu dan inje in yi futsarin, se dai gani nai wanda ke can saman gadona yazo ya rigani shallakewa a guje, ina ganin ya d'iba a guje sai nima na bishi a guje, shi kuma koda ya juyo yaga na biyo shi sai ya k'ara dannawa a guje sauran d'alibai kowa sai gudu, saida suka ci karo da malam ya tsayar da shi yana tamayarsa me ya faru yace malam Amir ne yaga wani abu shine na gudu kafin abun k'araso kaina, koda na k'araso malam ya tambayeni me na gani nace malam banga komai ba, akace to meyasa kake gudu nace wannan naga ya runtumo a guje shine na biyo shi, malam ya sake tambayata me yasa na zabura daga kwance nace futsari ne ya matseni, mallam yai dariya mai isarsa, sannan yace shi yana gudunka kai kuma kana gudun abinda yake wa gudu baka san cewa kai yake gudun mawa ba kar abinda yai tunanin ya biyoka ya cimmashi, su kuma sauran d'alibai suna gudun rashin dalili, to ku wuce kuje ku kwanta Allah ya shiryeku tsoro kamar kuraye, malam yana juyawa zai tafi gidanshi sai d'aya daga cikinmu yace malam ga wani abu nan yana binka a baya ai ko juyowa malam be yi ba ya runtuma a guje sai gida d'alibai kowa akaita yi mishi dariya."_ Amira saboda tsabar dariya harda hawaye, a kan kujera take amma har ta kai k'asa tana rik'e ciki, tana dariyar ne taji Amir yace " Amira ina son......., Amira cikin dariyar labarin da ya bata tace "me kake so?" Amir yace " ke nake so, ina sonki Amira." Lokaci d'aya dariyarta ta tsaya cak, ta mik'e tsaye, shima ya mik'e suna kallon juna, Amira tace " d'an maimaita abinda ka fad'i yanzu," Amir yace " cewa nai ina sonki Amira." Amira ta zaro idanu jin abinda yace tare da d'aga hannunta ta wanka mishi mari har uku. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *RUBUTAWA* *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` _ina matuk'ar jin dad'in yanda kuke k'aunar wannan novel d'in, da yanda kuke tattaunawa akai masoyan *SO MAHA'DIN RAYUWA* ina godiya kuma ina alfahari da ku wallahi I hrt u all😉😘_ _'yan uwa muna barar addu'arku *Kaduna* ba lafiya Allah ya kawo mana k'arshen wannan bala'o'in dake addabar mu a rayuwa._ PAGE 45 to 50 Amira ta kalle shi ta sake wanka mishi mari cikon na hud'u, sannan ta kama hannun shi ta jashi har k'ofar d'aki ta tura shi waje sannan ta maida k'ofarta ta rufe tare da dark'ushewa a jikin k'ofar tana kuka. Amir daga waje bugun k'ofar yake yi kamar me, yana fad'in " Amira kece tubali na ginina, kuma kece *mahad'in rayuwata,* har ina jin babu sauran numfashi a tare da ni duk ranar da bana tare da ke, ki duba yanda muka shak'u da juna kiy min sassauci dan Allah, koda bakya k'aunata ki bar zuciyata ta rab'u da taki," yana magana yana kuka tare da cigaba da buga k'ofar. Amira ganin ya fara karya mata zuciya yasa ta tashi ta bar bakin k'ofar ta koma kan kujera ta zauna, ji ta yi ta zauna kan wani abu ta d'aga bak'ar ledar da Amir ya shigo da ita ce, bud'e ledar ta yi, wani k'aramin kwali ne a ciki sai wani kati me d'auke da kalamai na so, kwalin ta fara bud'ewa wani had'ad'd'en zobe ta gani na zinare da na azurfa, Amira mamaki kawai take yanda akai ya san irin zobunan da tafi so a rayuwarta. Tsintar kanta ta yi da ciro su d'aya bayan d'aya ta saka a hannunta, ai kuwa sun yi mata kyau sosai kamar dama don ita kad'ai aka had'a su. Katin nan ta ciro ta fara karantawa _So wani abu ne da yake jigatar da zuciya ya cikata da damuwa a wasu lokutan, amma tunda na same ki nasan zaki zamo min maganin warakar dukkan wata damuwata a so, dan Allah ki taimaka ki amince da ni mu rayu tare._ Bayan ta gama karantawa ta yi ajiyar zuciya tare da juya bayan katin taga an rubuta _Amira ta Amir_ Amir ne ya cigaba da bugun k'ofar tare da yin magana da k'arfi yanda zata ji, yana kuka yace " Amira ya kike so in yi ne wai, da k'aunarki da ta maida ni tamkar mahaukaci zan ji ko da hukuncin da kike min a yanzu, haba Amira ki ji tausayina mana, ki tausayawa zuciyar da bata san komai ba sai so da k'aunarki da kuma farin cikin ki, karki barta mu rayu tare mu mutu tare dan Allah, wallahi in baki bud'e min k'ofar ba zan kwana a nan." Amira tana jin duk abinda Amir yake cewa, itama kuka take sosai amma har yanzu bata da niyya ko alamar zuwa ta bud'e mishi k'ofar. A haka suka kasance abinda ke tayar da Amir daga bakin k'ofar nan sallah ce kad'ai har dare ya rufa yana zaune bakin k'ofar, itama Amira a falo ta kwanta se dai bacci babu shi a idanun su duka daga Amir d'in har Amira. Amir rakub'ewa ya yi a jikin k'ofar ya kwanta kamar wani mara gata, a haka suka kasance har zuwa k'arfe uku na dare idanun su biyu, se dai ita Amira duk a tunaninta Amir ya tafi gida saboda jinshi shiru. Amira ta ji gabanta ya fad'i a zuciyarta tace yanzu idan har yanzu yana waje fa, mik'ewa tsaye ta yi, so take kawai ta tabbatar yana nan ko baya nan lek'awa ta yi ta windon d'akin amma da yake windon a can gefe yake bata hango k'ofar d'akin ta ciki, hakan yasa ta hak'ura ta koma kan kujera ta kwanta. Amir sanyi ne ya fara kad'a shi, nan da nan ya fara rawar sanyi, zazzab'i ya fara kama shi. Washe gari wajen k'arfe takwas Amira ta gama shirin tafiya makaranta, haka ta tashi sukuku ba k'arfi a jikinta, abun kari kuwa dama bata ta tashi, bud'e k'ofar ta yi domin tafiya ta ci karo da Amir kwance a bakin k'ofar, shima jin bud'ewar ne yasa ya bud'e idanun da su kansu zafi suke yi mishi saboda ciwon kai. Jakarta ta yar, tare da duk'awa inda yake cikin sauri ta tallabo shi sannan ta fashe da wani irin kuka jin jikin shi da ta yi kamar garwashi saboda zafi, tabbas tasan a nan ya kwana. Amira kuka take tana fad'in baka da hankali ne Amir, meyasa zaka kwana a nan," ta sake fashewa da kuka. Amir cikin wahalalliyar murya yana fitar da numfashi da k'yar yace " ina hankali da tunani ga wanda yai zurfi a so, dan Allah Amira karki gujeni, ki amince da ni, Sonki ne *mahad'in rayuwata,"* hawaye ne yake gangarowa kan fuskar shi, a yayin da Amira kuma ke kuka sosai kanshi yana jikinta tama rasa da me zata fara taimaka mishi, ji ta yi yai mata nauyi a jiki, ta jijjiga shi tana fad'in tashi in kama ka mu shiga ciki," ina babu amsa Amir ya sume. Rud'ewa ta yi tana kurma kuka me d'an karen k'ara tana fad'in "shikenan na kashe shi." Sauke kanshi ta yi daga jikin ta, ta fita waje neman taimako, wani dattijo ne Allah ya had'ata da shi suka shigo tare har zuwa inda Amir yake, tab'a shi ya yi, yace ta kawo mishi ruwan sanyi, da gudu Amira ta shiga ciki ta fito da ruwa a gora ta kawo mishi, karb'a ya yi, ya bud'e ya zuba a hannu ya shafa mishi a fuska da wuraren wuyan shi, ya ajiye ruwan a gefe, ba'a fi minti biyar ba da watsa mishi ruwan sai ya fara motsi da hannu tare da k'ok'arin bud'e ido, bakin shi na ambaton sunan Amira. Wannan tsohon yace " Alhamdulillah tashi ki kama shi mu shiga da shi ciki," suka kama shi suka kaishi cikin d'aki suka kwantar dashi kan kujera. Tsohon nan ya kalleta yace " ki samu ruwa me sanyi da tawul ko tsumma ki rik'a sawa cikin ruwan sanyin kina goge mishi jikin shi saboda a samu zazzab'in jikin shi ya sauka, Allah ya k'ara sauk'i." Amira tace " ameen Baba, nagode da taimakon da kai min Allah saka da alkhairi," bayan tafiyar wannan tsohon Amira ta yi duk yanda ya fad'a mata cikin ikon Allah zazzab'in ya fara sauka, kuma sai a lokacin ya samu bacci. Itama Amira tana zaune a doguwar kujerar ta jingina, shi kuma Amir yana kwance kanshi na jikin Amira hannunta na dafe da jikinshi a haka dukkan su bacci ya d'auke su suna ramuwar na jiya da basu samu sun yi ba. Sai wajen k'arfe d'aya Amira ta tashi, cikin sauri ta zame kan Amir daga jikinta ta kwantar da shi kan kujerar sannan ta yo alwala tai sallah, bayan ta idar ta fad'a kicin domin nema musu abinda zasu ci. Jelop d'in taliya tai musu wadda ta ji kayan ciki, _ni kuwa BK har ina had'iye miyau ina fad'in Allah sa su rage min, saura makaranta kuce inada kwad'ayi☹😏_ Bayan ta gama girkin ta zuba a kula tana jira sai ya tashi su ci tare kamar yanda suka saba. Amira ta ci gaba da gyara ko'ina na gidan, sannan ta turare ko ina, a tak'aice dai ranar dukkan su ba wanda ya lek'a makaranta, ta fad'a band'aki ta shek'a wanka sannan ta fito, bayan tai wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa wad'anda suka yi matuk'ar yi mata kyau, kuma sun karb'i jikinta sosai, hakan yasa kyawunta ya k'ara fitowa fili ya k'ara bayyana. Falon ta dawo ta tarar Amir ya tashi amma har lokacin yana kwance, cikin hanzari ta k'arasa kusa da shi ta daga kanshi ta zauna sannan ta maida kanshi jikinta ta kwantar kamar yanda suke a d'azu ta kalle shi tace " sannu Amir ya jikin, Allah k'ara sauk'i, yanzu me ke damunka, ko zamu tafi asibiti ne?" Amir binta kawai yake da kallo yana mamakinta, gashi dai a haka ta damu da shi amma kuma bata son shi, kallonta ya yi sannan yace " ba sai mun je asibiti ba zazzab'in ya sauka mura ce kawai sai ciwon kai, suma a hankali zasu warware, amma Amira ni maganin dukkanin wata cuta tawa tana wajenki, soyayyarki nake nema kin hana ni ban san dalilin ki na yi min hakan ba." Amira tace " yanzu dai mu bar wannan maganar har sai kaji Sauk'i," ta zuba musu abinci suka ci, bayan sun gama ta zuba mishi ruwan wanka yaje ya watsa ruwa, bayan ya gama ta bashi t.shet d'inta da jeans yasa duk sun matse shi amma haka nan zai saka tunda nashi sun yi datti, se dai kayan sun yi mishi kyau sosai. Tun daga ranar kayanta yake sakawa har Allah ya bashi lafiya, yau kwanan shi uku kenan a gidan, tattali kam da gata ya sha shi, hakan ya k'ara sa mishi son mallakar Amira matsayin matar aure. Yau lahadi ba makaranta, Amir ne zaune gaban Amira ya k'ureta da idanu, kallon shi tayi tace " yallab'ai lafiya kake kallona haka?" Amir ya numfasa sannan yace " Amira bana gajiya da kallon wannan kyakkyawar fuskar, Amira ina sonki k'aunarki ta kama zuciyata, dan Allah ki amince da ni," Amira ta share shi tare da kawar da kai, Amir ya taso daga inda yake zaune ya tsugunna a gabanta yana zubar da hawaye sannan ya dafata yace " Amira wallahi in na rasaki mutuwa zan yi, ki taimake ni so nake in mallake ki matsayin matar aure mu yi rayuwa dake ta har abada, ki karb'i tayin soyayyata." A fusace Amira ta juyo ta sake d'aga hannu ta wanka mishi mari wanda ya fi ukun da tai mishi a baya zafi, sannan sai ta fara kuka itama, zamowa tai daga kan kujera ta tsugunna a gabanshi sannan ta kalli Amir wanda yake dafe da kuncin shi har yanzu yana binta da kallo. Kama kwalar rigar shi tai kamar zata yi dambe da shi tana jijjiga shi tace " kasan kana sona meyasa zaka b'ata lokaci wajen fad'a min, meyasa ka d'auki tsawon lokaci kafin ka sanar min iyeeeee, kasan iya tsawon lokacin da na d'auka ina jiran zuwan wannan ranar da zaka furta kana sona, to in baka sani ba ka sani tun had'uwar farko yanayin kallonka ya tabbatar min da kana sona, kuma nima tun ranar na kamu da k'aunarka, amma shine zaka tsaya jamin aji, kana turo da sak'onni a b'oye yanzu da ka rasani fa wani ya aureni kasa mun yi asarar juna," jijjiga shi take yi da k'arfi, can sai ta kwantar da kanta a k'irjin shi tana ci gaba da kuka, cikin kukan ta cigaba da fad'in na d'auki alk'awarin hora duk wanda na gano shine me turo min da sak'onni duk da dama zuciyata ta dad'e tana bani cewa kai ne, na so in hukunta ka amma saboda k'aunar da nake maka tai min yawa shi ya hanani yin hukunci a gareka." Amir kam farin ciki ba'a magana, ko a haka Amira ta tsaya ya san tana k'aunarsa, kusan ma zai iya cewa lokaci d'aya suka kamu da k'aunar juna, d'agota ya yi sannan ya share mata hawayen dake fuskarta, itama ta share mishi na shi, sannan suka kalli juna suka sakarwa junan su murmushi, Amir yace " ai ko a haka aka barni na horu wallahi, amma meyasa kika mareni?" Amira ta kalle shi tace " ladan k'in fad'a min sirrin zuciyarka da ka yi da wuri har sai da k'aunarka ta gama galabaitar da tawa zuciyar sannan ka fad'a min, Allah naji haushin rashin sanar min da ka k'i yi kan lokaci, kuma har kana ikirarin kana k'aunata amma ka iya b'oyewa tsawon lokuta, bayan ni nasan zuciya babu abinda ya kaita tonon asiri, tuni ta bankad'eka na gane kana k'aunata ta yanayin tattalinka, kulawarka, damuwarka a kaina, kawai na zuba maka ido ne ka gama kewaye kewayen ka." Amir yai murmishi, sannan yace " amma fa gaskiya na maru," Amira tai murmushi itama sannan tace " shine salon naka tukuicin soyayyar," dukkan su suka kwashe da dariya sannan suka rungume juna. _ina barar addu'arku masoya Allah ya d'orar min da lafiya.👏_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 ``` *MASOYANA INA GODIYA SOSAI DA 'DUMBIN K'AUNAR DA KUKA NUNA A GARENI, ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI ALLAH YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA FIRDAUSI, NAGODE SOSAI WALLAHI.* *🇸🇦Zaman amana writer's* *Tauraronku na haskawa a ko'ina, Allah yai muku baiwa wanda ku da mak'iya se dai kallo, lallai zaman amana alkhairi ce naga nasarorinta cikin rubutu da marubuta, ni fa bance kunfi kowa ba 'yan uwana, amma fa tabbas kunfi wasu wasu kuma sun fiku, dama haka rayuwar take kafi wani wani ya fika, tabbas kuna haskawa ku ake yayi a ko'ina, Allah ya k'ara muku basirar da se dai a kwaikwaya a wajenku, d'aukakar da zata sa a daraja girman matsayinku, d'an karen zak'in hannun da zai sa mutane su mato kan k'aunar novel's d'in ku👏a cigaba da basu mamakin mutanena🤜🤛😍😍😍😍😍* *Har ila yau marubutan gidan sun sake kawo muku k'ayataccen labarai, RAYUWAR SAUDAT daga marubuciya RAHEENAT M. ABBAKAR, sai MARYAMA CEE daga marubuciya MARYAM KWARE, dukkanin su yanzu aka fara ba'a yi nisa ba karku sake a baku labari wallahi ku da kanku sai kun gode min da wannan albishir d'in muddin kuka karanta su.* *Dawo masoyiya Tawan dawo wallahi na tuba, laifin da nai ki zamto yafewa wallahi na tuba🙏😩😰* PAGE 50 to 55 Tun daga wannan ranar Amir da Amira so da k'auna tare da shak'uwa me k'arfi suka k'ara k'ulluwa a tsakanin su. Yau Litinin, kuma yau ma kamar kullum tare suka shigo cikin makarantar a motar Amira wanda Amir ya tuk'o su, shi kuma tashi tana gidan Amiran sai in zai koma gida yake hawa, wata rana ma har motar canje suke yi, ya d'auki ta-ta itama ta d'auki tashi. Suna shigowa cikin harabar makarantar sai ya yi fakin a inda ake faka motoci a makarantar, bayan ya kammala suka fito a tare rik'e da hannun juna suka jero zuwa ajin su. Se dai a hanyar da zata sada su da ajin nasu wasu cincirindon 'yan iskan maza ne sun kai su goma suna zaune duk d'alibar da tazo wucewa sai sun tab'a jikinta, ko sun ci zarafinta da kalaman su, wasu su wuce suna kuka wasu kuma su yi musu Allah ya isa su ruga da gudu, wad'annan bayin Allahn sun yi k'aurin suna wajen rashin ji, shiyasa ma aka rasa me tanka musu suna ta iya shegen su ana kallo, kuma dukkanin su 'ya'yan manya ne ma'ana ''ya'yan masu kud'i ne. Wata ta wuce kenan sun gama yi mata cin zarafi sannan sai ga su Amira suma sun zo wucewa, nan take suka fara fad'in "ga wata had'ad'd'iyar nan ta taho, gaskiya ta had'u," shugaban tantiran yace "ni wallahi har naji ina sonta," duk su Amir na jinsu har ya motsa hannu Amira ta k'ara rik'e shi, ya kalleta ta girgiza mishi kai, suka cigaba da tafiya, d'aya daga cikin su ya k'ara d'aga murya yace "komai ya ji gaba da baya, gashi daga ganin wannan d'an k'aramin bakin naki to haka can ma yake k'arami," habawa Amir ya fizge hannun shi daga na Amira ya nufo inda suke tare da rufe su da duka musamman ma wanda ya furta wannan kalmar. Yanda Amir d'in ke dukan kanshi kasan a zuciye yake, dukan su yake da tokari gashi in dai k'arfi ne kam Allah ya hore mishi musamman akan Amira, dama kuma mutum ko rago ne in yaga za'a ci zarafin abinda yake so zama jarumi yake yi, hmm so kenan. Amira taga Amir yana ta bugun wannan gayen ba ji ba gani yama dena dukan wad'ancan wanda ya furta wad'annan maganganun yake ta bugu sauran duk sun tsere yana niyyar yin kisa, gashi wajen har an cika amma an kasa janye shi daga wajen, da an jashi zai sake jawosu su dawo tare suna rike dashi d'in yana kai duka. Wani malamin su Amiran duk ya rud'e shima ya kalli Amira dake hawaye hankalinta a tashe yace " dan Allah ki dakatar dashi ke kad'ai ce zaki iya, in ba haka ba zai yi kisa." Amira ta kutsa cikin wajen tai mishi magana amma ina bai san tana yi ba, sai ta d'aga hannu ta daddage ta sharara mishi kyakkyawan mari lafiyayye guda d'aya, ba shiri ya d'ago rik'e da kumatun yana kallonta, yace " ni kika mara akan wad'annan 'yan iskan, to na barki da su, zanje in yi rayuwata ni kad'ai ba tare da ke ba, saboda muddin muna tare babu wanda zai tab'aki in k'yale, ya nuna wa 'yan iskan hannu wad'anda suka yi jina jina sannan yace ku kuma ku sani muddin ina numfashina kuma ko muna tare da Amira ko bama tare bazan ragawa duk wanda yai k'ok'arin ci mata mutunci ba," yana gama fad'in haka ya juya yai tafiyarsa. Amira ta tsaya nan sakato tana hawaye ita tai marin kuma shi ta mara amma har ga Allah ita ke jin rad'ad'in a ranta, bata ji dad'in marin da tai mishi ba amma dole sai ta yi haka zata dakatar da shi, in ba haka ba zai iya yin kisa a kama su ita da shi. Bayan malaman wajen da security's na makarantar sun yi bincike aka tabbatar musu da cewa 'yan iskan ne da laifi domin kullum haka suke yi, bayan an ja kunnen su aka tarkata su aka yi asibiti dasu domin yi musu maganin raunikan da uban soyayya yai musu. Amira ce keta sauri ta shiga cikin aji, tana zuwa ta tarar da malamin English d'in su ya riga da ya shiga, kuma shi a k'a'idarsa in ya riga da ya shiga babu wani kuma wanda zai sake shigowa, ko ka shigo sai ka fita. Tana shigowa malamin English ya kalleta yace ta fita, ba musu ko magiya ta juyo domin tasan ba wanda zai yi amfani, wani keb'antaccen waje ta je ta samu ta zauna inda Amir zai hangota dan ta tabbatar shima fitowa zai yi. Bayan ta fita Amir ya tarkata i'nashi-i'nashi ya mik'e zai fito, malam ya kalle shi yace " kai kuma ina zaka je?" Amir yace " malam ko na zauna wallahi ba zan fahimci komai ba a karatun ka muddin Amira bata ciki," be jira ma yaji abinda malamin zai fad'i ba yai waje abinsa, malamin da d'aliban gaba d'aya aka bishi da kallo har ya fice. Yana fita ya hangota, k'arasowa ya yi inda take ya zauna d'an nesa da ita tare da shan mur, Amira ta kalle shi tare da yin murmushi, ta matso kusa dashi, ya sake matsawa, ta k'ara matsowa, haka sukaita yi har suka kai k'arshen kijerar, sai ya yunk'ura zai tashi Amira ta rik'e shi ta hanashi tashi, a dai-dai wannan lokacin kuma sai ga wasu mata sunkai su Ashirin sun tunkaro wajen su, suka gaggaisa da hannu da Amiran da Amir duka, sannan suka yi mishi godiya sosai akan taimakon su da ya yi yai musu maganin wad'ancan 'yan iskan tare da jinjina mishi, Amir yace musu ba komai, haka mata da maza sukaita zuwa suna mishi godiya, shi kam abun mamaki yake bashi ya harari gefen Amira sannan a fili yace " ashe ni abinda nayi taimako ma nayi sosai haka amma nasha mari gun wata." Amira ta kwantar da kanta a kan kafad'arsa, sannan tace " dan Allah ka yi hak'uri na san ban kyauta ba, amma hakan da nayi shi kad'ai ne mafitana saboda bana so kai kisan kai a kashe mu," Amir yai murmushi jin tace a kashe mu wato harda ita ma za'a kashe kenan. Amira ta sake kallon shi tace " meyasa ka fito daga cikin aji?" Amir yace "hasken cikin ajin ya d'auke duhu ne kawai a ciki hasken yana nan waje." Amira tai murmushi domin ta gane manufarshi, nan dai ta bashi hak'uri suka shirya. Suka zauna nan suka sha hirar su har malamin English d'in ya fito, sannan suka koma tare da yin sauran karatuttukan, bayan sun kammala gaba d'aya suka koma gida. Haka suka kasance a koda yaushe suna tare dai-dai da 'yan mintuna basa iya jure rashin juna, hakan yasa karatun su ya fara zama shiririta saboda in har fa babu d'aya a ajin to basa zama dukkanin su, sam basu damu da karatun ba yanzu soyayyar su kad'ai suka sa a gaba, yanzu ma dai gaskiya babu abinda yafi musu muhimmanci irin kasancewa da junan su. Bayan kwana biyu ranar Juma'a ne wajen k'arfe biyu sun riga da sun yi karatu sun dawo gida, zaune suke a kujera Amira na kwance yayin da Amir ke zaune, Amir ya kalleta yace "Amira yaushe zaki kaini gidan ku neman izinin aurenki, na matsu na mallake ki matsayin mata?" Kafin Amira ta bashi amsa wayarta tayi k'ara Dad d'inta ne ke kira, bayan ta d'aga suka gaisa sannan ya shaida mata ta shiryo ta taho gida yanzu yai mata bukin d'in jirgi ta hanyar wani abokinshi lokacin bikin sister d'inta ya zo, jiki a sanyaye ta amsa mishi da "to" Dad yace " ya naji bakya murna bayan dad'ewar da kika yi kina d'okin zuwan wannan ranar, kuma ke kikace a sanar dake in yazo kar a yi bakya nan?" Amira tace " ina murna mana sosai Dad" kuma a yayin da take fad'in haka kallon Amir take yi tana hawaye tana tausayin halinda zai shiga in ya yi nesa da ita, shi kuwa Amir ganin haka duk hankalin shi ya tashi, ya k'osa ta gama wayar ya ji meke faruwa, nan dai Amira suka yi sallama da Dad d'in nata. Suna gama wayar Amir ya kalleta yace " daga gida ne koh, me akace miki, aure zasu yi miki, fad'amin mana." Dafa goshinta ta yi da hannu sannan tace "Amir ka natsu mana, duk ka bi ka d'aga hankalinka wad'annan tambayoyi haka wanne zan fara amsawa," tashi ta yi ta K'araso kusa da shi, sannan ta dafa shi tace " Amir Dad yace in taho gida yanzu bikin sister na ya taso, daga gobe za'a fara gudanar da shagalin bikin, d'iyar k'anin mahaifina ce tare da ita muka taso kamar 'yan biyu, shiyasa naita jaddada musu kar a sake bikinta ya matso ba'a sanar da ni ba, a da babu labarin da yafi soyuwa a gareni irin inga lokacin bikin nan, amma a yanzu babu abinda nafi tsanar jinshi irin labarin nan, wallahi Amir duk abinda zai nisantani da kai ko na minti guda ne bana k'aunarsa." Amir ba k'aramin razana ya yi ba jin wannan labarin, a duniya a yanzu babu abinda ke zamar mishi tashin hankali irin yin nisa da Amira. Amma sai ya dake tare da kallonta yace " kiyi hak'uri ai ko kin tafi bamu rabu ba, tunda ga waya ga kuma Whatsapp zamu rik'a yin chat, tashi maza ki shirya," duk yanda yaso yai kuka saida ya dake ya hana k'wallar idanun shi zubowa saboda kar ta gani ta k'ara shiga damuwa, ko tace ma ta fasa. Ganin bata da niyyar fara yin shirin tafiyar yasa ya tashi yaje bayi ya had'a mata ruwan zafi, ya fito ya ja hannunta har zuwa bayi ya turata ciki yace tayi tai wanka ta fito, sannan ya rufo mata k'ofar, ya dawo ya jawo Jakarta tare da shirya mata kaya d'aya bayan d'aya, duk kayan da yafi so in tasa yake yaba su su ya zab'ar mata, yana had'a mata kayan yana zubar da hawaye, jin k'arar bud'e k'ofar bayin yasa yai saurin share hawayen fuskarsa. Bayan ta shirya ta saka kayan da ya ware mata sai ta kira Dad d'inta ta fad'a mishi gata nan zata taho, Dad d'in yace taje filin jirgi in taje ta sake kiran shi akwai wanda zai had'ata dashi yai mata komai. Bayan sun gama waya suka fito suka shiga motar Amir suka d'auki hanya sai filin jirgi. Koda isar su ta kira mahaifinta kamar yanda ya umurceta bayan sun shiga daga ciki, yace ta jira zai turo wani wajenta yanzu, bayan wasu 'yan mintuna sai ga kira da wata lamba, tana juyowa taga wanda ya kira d'in ya nufosu, nan suka tafi tare dashi aka gama mata bukin d'in komai sannan suka yi sallama da Amir har ya juya sai ta k'wala masa kira, be juyoba har sai da ita ta k'ara so wajensa ta rungume shi ta baya sannan tace " zan yi kewarka Amir," ta fashe da kuka, juyowa ya yi, sannan ya d'ago ta da hannayen shi biyu yace "nima zan yi kewarki Amira, gwara ke cikin 'yan uwanki zaki shiga zasu d'ebe miki kewata, ni kuwa yanzu zan zama kamar marayan da ya rasa kowa, dan Allah Amira karki manta da ni," yana gama fad'in haka ya zame hannunshi da ta rik'e k'am tana kuka ya tafi domin kuwa ya fara jin sanarwar cewa kowa ya shirya jirgi zai d'aga, in be tafi ba itama bazata samu yin tafiyar ba, hakan yasa ya yi tafiyarsa, har ya bud'e mota zai shiga yaji muryarta da k'arfi tana fad'in " kar kai kuka Amir, ina sonka, ka rik'e min amanar kanka," Amir ya kasa daurewa ya juyo da idanuwan shi da suke zubar da hawaye, sannan ya d'ora su a kanta, suka kalli juna sannan Amira ta juya ta shige ciki da gudu, shima ya fad'a mota ya kifa kanshi kan sitiyarin motar yana ta kuka. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 *'YAN UWA ABOKAN AIKI 🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* *AISHAN UMMA* *MEELAT A.H.K (Bloodynah)* *MUMYS FRIEND (Tawan)* *QUEEN RUQEEY (Habibty)* *MAIMUNA ADAM (My Memcy)* *RAHEENAT M. ABBAKAR (My Heenat)* *ASIYA SEE-SSE (My Friend)* *MARYAM KWARE (My Swt Sister)* *SOYAYYAR KU TA ZAMA JINI NA JIKINA ZUCIYA NA BAKU KYAUTA,😍💃 ALLAH YA BARMU TARE YA K'ARA HAD'E KAWUNANMU, A CIGABA DA BASU MAMAKI GUY'S.😉😉😉* *SANARWA!🗣 mashahuriyar fitacciyar matashiyar nan mai suna AISHA ISA MUMMY'S FRIEND ta sake kawo muku shiryayyen labari mai suna RUUUHIN 'DANA, karku sake a baku labari, RUHIN 'DANA labari ne da yake cike da sark'ak'iya da tirka tirka kai abun dai sai wanda ya karanta, ba'a yi nisa ba shima karku sake ku zama 'yan kallo ayi babu ku, kada ku manta sunan littafin RUUHIN D'ANA!!!!* *MY LISSA ina rok'on mahaliccina Allah ya d'orar da lafiyasa gareki👏😭* PAGE 55 to 60 Amir ya dad'e zaune a cikin mota yana kuka idanun shi duk sun yi ja kamar me ciwon ido, daga k'arshe ya baiwa zuciyar sa hak'uri tare da yiwa motarshi key ya jata sai hanyar gida. A kan hanyar Amir ta zuwa gida ya lura da wata mota a bayanshi shi kawai take bi da gudu, haka suka fara tsere kan ti-ti, can sai yaga an sha gabanshi da motar, ba shiri dole shima ya taka burki da sauri, abun mamaki Insp Yahya ne ya fito daga motar bayan shi kuma wasu 'yan sanda ne ke mara mishi baya har suka k'araso inda Amir yake. Suna zuwa Insp Yahya ya kalli Amir yai murmushi sannan yace " malam Amir kenan, daga ina haka, ko daga gun mutuniyar kake?" Amir yace "eh" a tak'aice. Insp Yahya ya sake yin murmushi, sannan yace " a kwanakin baya kai da Amira ne kuke ta magana kan hujja hujja ko, to albishir nazo in yi maka nan da d'an wani lokaci zan gabatar da shedar da zata tabbatar da cewa daga Abdul har Sadeeq kashe su aka yi, kuma sai na gabatar da wanda ya kashe su duka," yana gama fad'in haka ya juya ya shige mota tare da sauran jami'an tsaron suka tayar sukai tafiyarsu. Amir hankalin shi ya tashi matuk'a, tunani yake yi meyasa Insp zai rik'a danganta shi da kisan nan ne, haka nan dai ya ja motar shi ya k'arasa gida jiki duk a mace kuma cike da damuwa me d'auke da d'umbin tashin hankali. Amira kuwa kuka take yi kamar ranta zai fita, duk idanunta sun kumbura, zuciyarta ce ke fad'in ashe haka masoya ke ji a duk lokacin da wani abu zai raba su, lallai ko menene mutum zai iya yi akan so musamman idan har yaga ana nema a rabashi da abinda yake k'auna, tun da suka shiga cikin jirgin Amira bata bar zubar da hawaye ba, har suka k'araso cikin garin Abuja Dad d'in nata ta kira ta sanar da shi sun iso, bata dad'e da sanar da shi ba sai ga motoci rututu an turo su d'auketa, nan da nan ta shiga suka ja suka tafi. Amir kuwa yana k'arasawa gida wayarsa ya ciro yaga 10 missed call's d'in Amira, mamaki yake yi yanda aka yi sam be ji ringing d'in wayar ba, ya kira wayar tare da karawa a kunnensa. A dai-dai lokacin da yake kira Amira sun k'araso gida an bud'e mata k'ofa zata fito daga cikin motar, 'yan uwanta da iyayenta duk gasu nan a tsaye harabar gidan sun fito tarbar Amira. Ta sak'alo k'afafunta kenan zata fito daga motar kiran Amir ya shigo, ta d'aga cikin sauri tare da karawa a kunne tace " hello Amir d'ina wallahi nayi kewarka," Amir ya sauke sassanyar ajiyar zuciya sannan yace " Amira kema kinsan rashinki dole sai ya tab'a ni, bazan ma iya misalta miki adadin rad'ad'in da rashinki ya haifar a gareni ba, kin kai gida ko har yanzu kuna hanya?" Amira tace " gani cikin gida yanzu muka k'araso ina ma cikin mota ko fitowa banyi ba naga kiranka, ya naji muryarka duk ta canza, kayi kuka ko, ba na hanaka yin kuka ba, kasan dole naji ba dad'i idan ina jinka a irin wannan yanayin ko, kodai in juyo in dawo ne nima jina nake kamar mara lafiya Amir ashe haka nisa da masoyi ke haifar da rad'ad'in jiki da na zuciya." Amir ya katseta ta hanyar fad'in " ki daina fad'in maganar dawowa mana Amira kowa ya ganki yana murna kice kuma zaki juyo, tunda dai kin riga da kin kai lafiya to nagode wa Allah, mu yi hak'uri na d'an lokacin da zaki yi ki dawo, yanzu dai ki shiga gida ki huta Anjima zan sake kiranki," nan suka yi sallama ya ajiye wayar ya fad'a cikin bayi domin yin wanka, ita kuwa Amira tana fitowa daga cikin motar idanun 'yan gidan gaba d'aya yana kanta, ta k'ak'aro fara'a ta k'arasa wajensu, sister d'inta ta fara rungumeta suna murna, sai suka rungume juna da Dad d'inta, sannan yace mata " dawa kike ta waya ne haka my daughter?" Amira tace " Dad wata friend d'ita ce, ta saki Dad d'inta da sauri saboda sanin halinshi na tambayoyi zai iya sake jeho mata wata tambayar taje ta rungume Mum d'inta sannan ta je gaban Uncle kawunta wato mahaifin wadda za'ai bikinta shima ta rungume shi ya shafa kanta tare da sa mata albarka, sannan suka d'unguma dukkansu suka shiga ciki. Wanka ta fara yi a k'erarren d'akin da yake mallakinta tamkar aljannar duniya, sannan ta shirya suka fito tare da sister d'inta, direct dining table suka wuce aka ci aka sha, daga nan suka dawo babban falo suka zauna ana ta hira, ita dai Amira ba wata walwala sosai banda eh ko a'a bata cewa komai, hankalinta yana wajen tunanin Amir, sisternta ce ta kalleta tace " wai Amira ya naga duk kin canza ne, ina lura dake fa ko abincin kirki baki ci ba," Dad dake jinsu shima yake kallon Amira yace " kin rigani magana ne nima abinda nake so in tambaya kenan, kamar daughter bata farin ciki da ganinmu. " Amira zata yi magana kenan sai ga kiran Amir, tashi ta yi tace musu zata je ta d'an kwanta a d'aki, bata jira taji me zasu ce mata ba ta haye sama cikin sauri. Amira ta d'aga kiran shi tare da karawa a kunne ta fad'a gado tace " kamar kasan kai nake tunani, Amir yai murmushi sannan yace "ai zuciyoyin mu had'e suke da juna," sun dad'e suna waya kiran sallah ne kad'ai ke dakatar da su daga jin muryar junansu. Har aka kira sallar issha'i suka je suka yi sannan suka dawo suka cigaba da dosa wayarsu, suna cikin wayar ne sistern ta ta shigo tana fad'in yau ina kusa dake sister na a d'akin ki zan kwana," Amira ba don ranta yaso ba tai dariyar yak'e tace mata " to kar dai ki cikani da surutunki malama," sister tace " dan ma kin samu, daga yau ne ai gobe ke kad'ai zaki kwana ni ina tare da k'awayena." Amir yana jinsu dan basu katse wayar ba, Amira tace mishi ya hau WhatsApp su cigaba da magana. Nan da nan suka bud'e datan su, suka cigaba da magana a yayin da sister d'inta ta gaji da surutunta Amira bata kulata sai ta hak'ura ta k'yaleta har bacci ya kwasheta. Su kuma suka cigaba da chat d'insu, Amira tace _"Amir d'ina gaskiya bazan iya cigaba da jure rashinka ba ko abinci fa na kasa ci, har 'yan gida sun gane akwai abinda ke damuna."_ AMIR _"To ko in zo ne?"_ AMIRA _"Amir Dad d'ina nake ji, murd'd'd'en mutum ne, baya so muna kula samari har sai mun kammala karatu, amma kazo tunda shagalin biki ake ba matsala na san yanda zan yi ba wanda zai gane komai."_ AMIR _" na shiga uku! ni yanzu ya zanyi ni da nake so na mallake ki kwanan nan yanzu in aka kasani fa, tunda kince da matsala zuwana to kiyi hak'uri ki bari har ki dawo."_ AMIRA _"gaskiya bazan iya cigaba da hak'urin jure rashinka ba, yini d'aya ma kenan har na rame, ka taho gobe ko kuma wallahi ni na dawo goben."_ AMIR _"to shikenan insha Allah goben ina hanya."_ AMIRA _"to shirya kayanka sai mu cigaba da waya tunda uwar surutu tai bacci, nafi so in cigaba da jin muryarka."_ Suka yi sallama na 'yan mintuna ya had'a kayanshi sannan ya kwanta yana kwanciya ya jawo waya zai kirata sai ga kiran Amiran ya shigo, yai murmushi ganin yanzu damuwarta a kanshi tana nema ma ta zarce tashi, ya d'aga kiran tare da kara wayar a kunne, haka suka kwana basu runtsa ba sai da asuba bayan sun yi sallah sannan ta barshi ya kwanta shima saboda kar bacci ya sace shi ya makara tahowa wajenta. Washe gari wajen shida dai-dai Amir ya shirya, ya fito tare da kulle ko ina na gidan sannan yaje tasha ya hau mota suka d'auki hanya sai Abuja. Duk bayan mintuna sai Amira ta kira taji suna dai-dai ina, bayan awanni da suka d'auka suna tafiya suka k'araso tashar Abuja, ya kira Amira tare da shaida mata ya k'araso gashi a tasha, zaune take ana mata lalle sai gani suka yi ta tashi zumbur tare da zuwa ta wanke lallen sannan tai hanyar d'akin Mum d'inta, Amarya na k'wala mata kira tana tambayar ina zata, ita kuwa fad'i take tana zuwa har ta shiga d'akin Mum d'in. Key d'in motar Mum ta d'auka tana fad'in "Mum bari inje in dawo," bata jira taji me zata ce ba ta fice ta fad'a motar ta figa da gudu sai hanyar tashar Abuja. Ko da isarta tasha ta hango shi, domin ma kusa da shi ta faka, ta saukar da glas d'in motar tare da yin hon, d'ago kanshi Amir ya yi suka yi ido hud'u da Amira, cikin sauri ya taso ya nufota, itama kasa jurewa tayi ta fito daga motar suka rungume juna suna hawayen farin ciki, kowannensu d'auke da murmushi a fuskar sa, ganin idanun mutane na kansu yasa suka shiga mota suka bar wajen sai hanyar gida. Suna isowa Amira tai fakin d'in motar ta baya ba tare da ta shigo da ita cikin gidan ba, suka fito suka bi wata b'oyayyar hanya ta baya, suka bud'e wata k'ofa sukaita tafiya har Allah ya sada su da d'akin Amira ba tare da kowa ya gansu ba. Suna shiga ta maida k'ofar ta rufe tare da sa makulli ta kulle ta ciki, suka zauna sunata hirar yaushe gamo, Amir yace " Amirana har kin rame," Amira tace " wallahi kuwa nesa da kai kamar yin nisa da rabi na jikina ne, kuma kaima ka rame amma baka kaini rama ba." Dakatar da surutun ta yi ta hanyar mik'ewa tace mishi tana zuwa, ta fita taje ta d'auko musu abinci suka ci, suna ci suna hira. Haka suka kasance a cikin gidan da dare ne kad'ai yake b'oyewa ya kwana a d'akinta tana k'asa yana saman gado, da rana kuwa shiga yake cikin 'yan biki ayi hidima da shi, amma yawanci ma sunfi tafiya bayan gidan su su zauna sui ta hira har abinci a nan suke ci komai a nan suke yi, aita nemanta in buk'atar hakan ta taso bata nan, se dai in sun dawo ta gilla musu k'arya, kullum a can suke wuni in sun tashi su bi ta k'ofar baya su shige d'aki, kuma Allah ya taimake su har yau babu wanda ya gane abinda ke faruwa. Yau Alhamis, tashin Amira kenan daga bacci agogon d'akin ta kalla k'arfe tara na safe, zaro idanu tayi sannan ta kai dubanta kan gado wayam Amir baya nan, ta je bakin k'ofar bayi ta k'wank'wasa shima shiru, ta bud'e ba Amir a ciki, ta shiga kicin ta duba nan ma wayam baya ciki, hankalin Amira fa ya fara tashi, ta fito daga cikin d'akin ta bi ta baya ta dudduba duk inda suke zama duk babu alamun shi, hankalin Amira fa ya kai k'ololuwar tashi, kuka ta fashe dashi tana tunanin ina Amir ya tafi gashi ba wanda ya sani a garin, komawa cikin d'akinta ta yi ta d'akko mayafi ta yafa tare da zarar makullin motar Mum da ta gaje mata take hawa tunda ta dawo, ta fito ta babban falo sam ta kasa natsuwa, ta fito tana hawaye, tazo ta wuce ta gaban su Dad duk suna zaune a falo zata fita Dad ya k'wala mata kira, yace " ina zakije?" ina harga Allah bata ji shi ba hankalinta yai gaba, ta fad'a mota taja ta tafi, haka taita bi lungu da sak'o na unguwar tana dubawa ko Allah zaisa ta ganshi amma ina, maida motar gida ta yi ganin wasu guraren ba damar kutsawa da mota, ta sake fitowa a k'asa, duk ta fita hayyacinta kuka sosai take yi tana cikin tafiya sai ta hango shi zaune a wurin da bazata tab'a mantawa da shi ba har abada domin kusa da gidansu ne wurin ta can baya inda wani dad'ad'd'en gidan marayu ke wurin, lokacin tana yarinya nan ne wajen zaman su, har Amira ta k'ara so wajen bai san da ita ba, sai da ta dafa kafad'arsa tare da jijjigashi sannan ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula. Kallonta ya yi tare da yi mata murmushi, zama Amira ta yi kusa da shi tare da rungume shi ta fashe da kuka sannan tace " meyasa ka fito ba tare da na sani ba, yanzu da wani abu ya same ka fa, Amir d'ina bazan tab'a iya jure rayuwar da babu kai a cikinta ba, dan Allah karki barni, kuma karka sake yin nesa da ni." Amir ya d'ago ta tare da share mata hawayen idanunta, idanunta duk sun kumbura ya kalleta yace " wa ya fad'a miki zamu rabu, insha Allah na kusa mallakarki ma a matsayin matar aurena da zarar kin gama karatunki, kuma abinda yasa na fito saboda naga kina bacci ne, kuma ban yi tunanin zaki tashi da wuri haka ba saboda nasan jiya mun dad'e muna hira bamu kwanta da wuri ba shiyasa, amma kiyi hak'uri tuba nake bazan k'ara ba," ya k'arashe maganarsa tare da rik'e kunne. Rarrashin Amira ya yi, sannan suka tashi suka juyo da niyyar komawa gida suka ga Dad da su Mum tsaye a kansu suna musu wani irin kallo, Dad ya kalli Amira cikin d'aga murya yace "ke Amira waye wannan," ya k'arashe maganarsa tare da nuna Amir da hannu, ba Amir da Amira ba hatta ni Bk sai da na razana da ganin iyayen Amira a wajen, hakan yasa na yarda komai nawa na runtuma a guje sai gidan su Bloodynah kai tsaye bayi na shige na fara zawayi na fargaba. _shin ya zata kasance? ku biyoni muje_ *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 *SANARWA!!!🗣 ina makaranta litattafan Hausa? to ku saurara da kyau kuji,👂 shahararriyar marubuciyar littafin SHARRIN ASHQEEY mai suna RUKAYYAT BINT DAWUD (QUEEN RUKEEY) ta sake gangamo muku gingimemen labarinta mai suna JARRABAWAR RAYUWA, kar ku sake kuyi sakaci a barku a baya, sunan littafin JARRABAWAR RAYUWAAAA* *Wallahi ina matukar jin dad'in comment d'inku, ina yinku fiye da duk wani tunani naku, Allah ya barmin ku masoyana😍😘* *TABBAS SO MAHA'DI NE NA RAYUWA, DOMIN YAKAN ZAMA SILAR GYARA RAYUWAR WASU, A YAYIN DA YAKE ZAMA SILAR GURB'ATA NA WASU, SO TSANI NE NA TUSHEN GINA KYAKKYAWAR RAYUWA IN KA YI DACE DA MASOYI NA K'WARAI, SO YANA ZAMA NASARA GA RAYUWAR WASU A YAYIN DA YAKE ZAMA FA'DUWA KO KOMA BAYA GA RAYUWAR WASU SO YAKAN KASHE WASU RAYUKAN, A YAYIN DA YAKE BAWA WASU DAMAR CIGABA DA RAYUWA, SO RAYUWA CE, AMMA WASU LOKUTAN MUTUWA CE, DUK WANDA YA K'ULLA SO A RAI TO TABBAS YA K'ULLA HARDA ABU BIYU WATO FARIN CIKI DA BAK'IN CIKI, SANNAN LOKUTA DA DAMA KUMA MAFI YAWANCI SOYAYYA TAKAN MAKANTAR DA MASOYA TA YANDA BASA GANE DAI-DAI DA RASHINSA, IDAN KAI DACEN SO NA GASKIYA TO TABBAS RAYUWA NA D'OREWA CIKIN FARIN CIKI DA WALWALA BAYAN JURE DUKKANIN WANI RU'DANI.* PAGE 60 to 65 Zuru-zuru suka yi dukkanin su, a yayin da Amira ta fara inda-inda, sai Dad ya sake yi mata tsawa tare da tambayarta waye wannan, Amira ta dake domin kar mahaifinta ya gane akwai wani abu da take b'oye mishi, ta kalli Dad tana d'an murmushi tace " Dad abokin karatuna ne wannan, duk k'ok'arin da nake yi kusan shine sanadi saboda yana taimaka min sosai a karatuna, kuma yazo mana biki ne zuwanshi ma kenan." Dad jin an sako karatu a ciki sai ya sassauta fushinsa don shi mai son yaga yaranshi na maida hankali ga karatu ne sosai, amma duk da haka be gama yarda da maganarta ba saboda sunga lokacin da ta wuce tana hawaye. Dad yace " ku biyoni muje gida," daga haka be sake cewa komai ba suka juya suka tafi, suma su Amira suka bisu a baya har suka iso har cikin babban falo inda kowa ya samu waje ya zauna. Amir yabi kowanne daga cikin 'yan gidan ya gaishe su, sannan Dad ya cewa d'aya daga cikin yaran gidan su kaishi d'akin bak'i ya huta, Amir ya bi bayansa suka fice daga d'akin, sannan Dad ya dawo da kallon shi ga Amira yace " Amira karfa ki manta mu iyayenki ne ba sa'anninki ba da zakiy mana wasa da tunani, idan biki yazo ina kayanshi tunda da sauran kwanakin yin bikin, kuma meyasa kika fita kina kuka har na kiraki baki ji ba?" Amira tace "Dad lokacin da na fita ina kuka fad'amin yai wata Friend d'ina ta rasu shiyasa hankalina ya tashi har kuka ga na fito ina hawaye, jakarshi kuma tana cikin mota." Dad yace "amma ai ba da mota muka ga kin fita ba," Amira gabanta ya fad'i, saboda ta tuna ta dawo da motar gida, ta kalle shi sannan tace " Dad kenan, ai ba ni kad'ai na fita ba da driver ne, kuma sauka muka yi anan inda kuka ganmu nace drivern ya k'ara so kafin mu taho muma." Sai a lokacin Dad d'in Amira ya numfasa, sannan yace "to shikenan ya kyauta da yazo mana biki, kuma tunda kin cemin yana taimakon ki kan karatunki zan yi mishi godiya, se dai kar ki kuskura na ji sab'anin wannan zancen kuma," Amira tace " to Dad," Dad yace "yanzu ki tashi kije ki sa a kai mishi abinci da abin sha sai ki bashi wuri ya huta, anjima idan ya fito sai mu yi magana dashi." Amira ta tashi cike da farin cikin yau Allah ya k'waceta hannun Dad d'inta. Tun daga ranar Amir bai sake kwana d'akin Amira ba, yanzu kulawarshi ma ba iya Amiran kad'ai ba ta tsaya harda iyayenta da 'yan uwanta, hakan ya k'ara basu damar sakewa sedai ba kamar da ba saboda yanzu basa keb'ewa suyi hira kamar da saboda idanun mahaifin Amira da wasu daga cikin 'yan gidan dake kansu, sedai ko yaushe suna mak'ale a waya da kuma chat. Bayan ansha biki na kece raini an kai Amarya d'akinta ranar Litinin Amir yace zai juyo ya dawo, bayan ya had'a kayansa yazo falo ya duk'a bayan ya gaisheda Dad da kawunta sannan yace musu shi zai koma, Amira na zaune kusa da Dad d'inta sai aika wa Amir da harara take a fakaice. Dad yace " ai tunda an k'are shagalin bikin kawai Amira itama ta shiga ta shirya ta bishi su koma tare, cike da farin ciki mara misaltuwa ta mik'e cikin sauri duk aka bita da ido ganin yanda ta mik'e d'in, tai saurin b'oye murnarta ta d'an b'ata rai sannan tace " gaskiya Dad ni ban gaji da ganinku ba, ka bari after five or six day's na koma makarantar." Dad yace " a'a daughter tashi ki shirya an gama biki me zaki zauna kiyi kuma, kuma mu dama ai bazaki tab'a gajiya da ganinmu ba, oya tashi maza ki shirya," haka ta tashi tana bubbuga k'afa ita a dole bata son komawa, sai da ta kai bakin k'ofa ta juyo suka had'a idanu da Amir ta d'an yi tsallen farin ciki tare da kashe mishi ido d'aya sannan ta fad'a d'aki da sauri. Amir ya sauke idanunshi yana murmushi a yayin da Dad ke k'ara yi mishi godiya tare da rok'on shi kan k'ara kulawa da karatun su da na Amiran. Kowa na d'akin yai tsit, hatta kawun Amira mamaki suke yanda suka san duk tsattsauran ra'ayi da dokoki kan yaran gidan da Dad d'in yake amma ya iya yarda ya amince Amira ta bi Amir su koma kamaranta tare, duk sun k'osa su tafi kowa ya fara antayo mishi tambayoyin dalilinshi na yin haka, shi kuwa Dad yana lura da yanayin su duka, murmushi kawai ya yi. Ba'a d'auki wasu dogon lokaci ba sai ga Amira itama janye da jakarta, d'aya daga cikin security's d'in gidan ne ya karb'i jakarsu ya fice dasu yasa a mota, sannan suka tashi gaba d'aya harda su Dad aka rakosu har bakin motocin da zasu kaisu tashar jirgi. Sallama suka yi da kowa na gidan sannan suka shiga mota, suka fice daga gidan inda sauran motocin ke mara musu baya. Bayan fitarsu kawu ya kalli Dad yace "amma yaya yau ka bawa kowa mamaki a gidan nan, yanda kake da tsattsauran ra'ayi kan kowa musamman matan gidan nan akan samari amma yau kai da kanka kake basu damar tafiya tare." Dad yai murmushi sannan yace "tun ranar da Amir ya shigo gidan nan nake lura dashi, kuma nasa dukkanin security's d'in gidan nan suna lura da al'amuransu, Amir yaro ne me yawan ibada kamar Amira, baya wasa da sallah, sannan kai da kanka saida ka yabi halaye da d'abi'un yaron, bama kai kad'ai ba, sa'annan tun da Amira tazo halayenta kyawawa babu wanda suka canza sedai ma k'aruwa da sukai da ace munga canji daga halayyarta to daga lokacin zamu fara tsaurara bincikenmu da d'ora zargin canzawarta a kan Amir amma bamu ga wani canji ba, sedai kawai rashin sakin jiki da ta nuna kanmu wannan karon shima nasan saboda abokan karatu ne amma daga baya ta warware, wad'annan abubuwan ne suka tabbatar min da cewa lallai halinsu ne yazo d'aya dashi, sannan a koda yaushe rashin yiwa yaranmu kyakkyawan zato akan haka shi ke sawa su fad'a ga halaka, ni dai tunda ba soyayya suke ba to Alhamdulillah, kuma zansa security's suje a b'oye su rik'a bincika min komai game da su dan zuciyata bata gama gasgata bayanin da Amira tai min a kanshi ba, kuma binshi da nace tayi na gwadata ne in ga yanayinta, in har na gano sab'anin abunda Amira ta fad'a min hmmmmm," bai sake cewa komai ba ya juya ya shige ciki suma suka mara mishi baya. Basu d'auki wani lokaci me tsawo ba suka k'araso tasha, kuma ba tare da wani b'ata lokaci ba jirgin su ya d'auki hanya sai Kano ta dabo tumbin giwa yaro ko dame kazo an fika. K'arfe d'aya dai-dai suka iso Kano, kai tsaye gidan Amira suka wuce, da yake ita tana da 'yan aiki a gidanta kuma ta sanar da su cewa yau zata dawo su gyara mata ko ina, dan dama tai niyya da Amir ya taho ko basu dawo tare ba zata biyoshi a ranar, Amira ta kira Dad da Mum da Uncle duk ta shaida musu ta dawo. Wanka suka yi, sannan suka canza kaya sukai sallah, aka kawo musu irin abinci wanda Amir yafi so ta bada umurnin a girka suka ci abinci sannan Amir yace ta d'auko mishi jakarshi zai tafi gida ya d'an kwanta anjima zai dawo. Amira tace wallahi bazata bashi ba sai ta wanke mishi kayan da ya cire yau in yaso anjima in ya dawo sai ya tafi dasu, ba yanda bai yi da ita ba akan ta barshi amma ta k'i ba yanda ya iya saboda yaga ta fara b'ata rai dole ya hak'ura, yai mata sallama ta tashi ta rakoshi ya shiga cikin mota ya tayar tana d'aga mishi hannu shima yana d'aga mata har ya fice. Amir yana komawa gida ya rage kayan jikinshi daga shi sai singileti da gajeran wando iya guiwa sannan ya kwanta sai bacci. Amira kuwa tana komawa cikin d'aki ta jawo jakar Amir ta fara fito da kayan ciki tana ware wankakku tana cire masu datti zata wanke mishi dan tace da kanta zata wanke mishi kaya, saida ta fito dasu duka sannan ta hango wata takarda da hotuna a zif d'in jakar ta ciki, wasik'ar ta fara cirowa tana bud'ewa taga an yi rubutu da manyan harafi an rubuta *SO MAHA'DIN RAYUWA, SO TUN NA YARINTA HAR GIRMA, LALLAI K'AUNA BATA TAB'A GOGEWA.* Take zuciyar mata ta fara hasssala kishi ya motsa, rai ya b'aci, cikin sauri ta maida wasik'ar tare da zaro hotunan tana dubawa d'aya bayan d'aya. Hoton farko da ta fara gani yasa ta zazzaro idanu tare da mik'ewa tsaye rik'e da hotunan cikin firgici, hoton ta ne tana k'arama. K'ara kallon hoton ta yi, duk da haka bata yarda ba, cikin sauri ta jawo jakarta ta shiga neman hotunanta aikuwa nan take taci karo dasu, wani hoto ta jawo tana kallo iri d'aya sak da na jakar Amir, bakinta na rawa tana hawaye take furta sunanshi "Ameeru," mayar da hoton da ta ciro cikin dakarta ta yi ciki, sannan ta cigaba da kallon hotunan, hotonta ne da tana k'arama, sai hotonshi shima yana k'arami, sai hotunan su da suka d'auka da shi da ita, da kuma wanda suka d'auka harda sister d'inta, ta kalli hotunan nan sau ba adadi kamar yau ne rana ta farko da ta fara ganin su, hawaye na jik'a hotunan, ajiye hotunan tayi gefe, kuka take sosai sannan ta jawo wayarta ta lalibo number d'in Amir ta doka mishi kira. Amir wanda ke kwance a baje yana bacci yaji wayarshi na k'ara, jin k'arar ringing d'in da Amira ce kad'ai mallakinsa yasa shi tashi tare da jawo wayar ya danna tare da karawa a kunne yace " hello Amira nah," Amira tace " kazo yanzu ina son ganinka," daga fad'in haka ta katse wayar yanayin yanda Amir yaji muryar Amira ya tabbatar da ba lafiya domin kuka yaji tana yi, tashi ya yi cikin sauri duk ya rud'e ya zari makullin motarsa sai gidan Amira, yama manta sam da a yaya yake ya manta daga shi sai singileti da gajeran wando iya guiwa, tuk'i yake me matuk'ar gudu, yana cikin gudun ne Insp Yahya ya k'yalla idanu yaga motar Amir da kuma yanayin da yake ciki da office zai je, amma sai ya fasa ya karya kan motar shi ya biyo bayan Amir shima cikin sauri. _shin menene a b'oye kuma bayan wannan kisan da yake a b'oye wanda har yanzu bamu san makashin ko makashiyatun da suka aikata ba sai ga wani kuma abu daban ya b'ullo kai, wai nifa kaina ya kulle meke shirin faruwa ne kuma?_ Ku biyoni muje🏃‍♀ *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 *BABBAN DACE DA NASARA A SO SHINE KASO A SOKA* *MY HEENAT Allah ya kara miki sauki, ya d'orar miki da lafiya d'orarriya* PAGE 65 to 70 Gudu kawai Amir yake amma gani yake kamar yau motar bata sauri, a yayin da zuciyarsa ke ta addabarsa da tambayoyi a kan yanzu-yanzu fa ya baro wajen Amira ba dad'ewa, to menene ya sameta ta shiga wannan halin cikin lokaci k'ank'ani. A bayan shi kuwa Insp Yahya ne ya dage yake ta binsa da gudu saboda baya so Amir ya b'ace masa. Cikin k'ankanin lokaci ya iso k'ofar gidan inda yake ganin kamar awanni ya yi yana tafiya, yana faka motar ya fito da sauri ya shiga cikin gidan, tsaye ya sameta a falo tana kai kawo shigowarshi ne ya dakatar da ita daga sintirin da take ta faman yi, ta k'araso gabanshi tare da kallon shi ta cakumo rigarshi da hannu d'aya tare da nuna mishi hoton ta da ta gani cikin jakarshi tana fad'in " ina ka san wannan, kuma wa ya baka hotunan nan?" Amir ya kalli hotunan sannan ya sunkuyar da kai, a yau yasan duk wani b'oyo da yake yi ya k'are, watso mishi sauran hotunan ta yi jikin shi tare da jeho mishi tambayoyi kan a ina ya same su, shi kam Amir baida bakin magana ya kasa cewa komai, komawa da baya Amira ta yi tare da zaman 'yan bori a tsakiyar falon ta sake kai dubanta gareshi tace " shirunka ya tabbatar min da cewa kaine Ameeru na wanda muka taso tun muna yara, meyasa zakai min haka, meyasa zaka b'oye kanka gareni Ameeru why?" tana kai nan a maganganun ta sai ta sake fashewa da kuka. Amir ne ya k'arasa kusa da ita tare da tsugunnawa shima a gefenta yace " Amira dan Allah ki saurareni kiji, ke kanki saida ce akan irin k'aunar da nake miki tun muna yara wato abinda ya faru har yasa na b'oye miki kaina shine:" TUSHEN LABARIN Ahmad Tukur mutum ne wanda aka dama dashi a baya kuma ake damawa dashi a yanzu, a tak'aice dai yana d'aya daga cikin hamshak'an masu kud'in garin Abuja. Ahmad Tukur matashi ne wanda duka bai wuce shekaru talatin da biyar ba amma mutum ne nagari me kuma kishin k'asarsa, hakan ne ma yasa yake nasara kan aikinsa, se dai Ahmad yanada zafi da tsattsauran ra'ayi, amma in kabi yanda yake so zaku zauna lafiya dashi. Yana da mata d'aya da 'yar su guda d'aya tak me suna Amira Suna zaune ne a babban gida kuma k'ayatacce wanda yake tare da d'an uwansa mai suna Uncle Adamu wanda yake da shekara talatin shima yana da mata wadda itama take da 'ya guda d'aya me suna Rukayyat kuma sa'ar Amira ce kasancewar rana d'aya aka yi bikin su kuma tsakanin haihuwar su yaran sati guda ne kacal a tsakani. Uncle Adamu shi mutum ne me sauk'in kai ba kamar d'an uwansa ba, Amira da Rukayyat shekarar su takwas amma wayonsu da zaro zance tamkar na 'yan shekara goma sha musamman ma Amira, akwai surutu amma kuma akwai tausayi. A kusa da gidan su Amira akwai wani gidan marayu, koda yaushe da ita mahaifinta ke zuwa yana bayar da taimako da gudummawoyi, kuma ta nan hanyar makarantar su Amira take, kullum sai sun wuce in zasu tafi haka ma in zasu dawo. Amira 'yar gata ce sosai musamman kasancewar ta 'ya d'aya tilo, gata kam na duniya tana kan shansa, mahaifin Amira yana mutuwar son Amira yana kuma gatanta ta tun tana yarinyarta babu abinda zata nema ko ta nuna wanda baza ai mata shi ba komai wahalar sa ko tsadarsa. Yau Litinin su Amira ne kan ti-ti za'a tafi kaisu makaranta Amira ce keta kalle kalle, a yayin da ita kuma Rukayyat ke danna k'aramar wayarta tana game, Amira ta hango wani bawan Allah zaune gefen ti-ti rigar shi duk ta yage sanyi yanata kad'a shi yana kakkarwa, Amira tace wa driver ya tsaya, yana tsayawa ta fito daga motar rik'e da rigar sanyi a hannunta, tana zuwa dai-dai inda yake ta mik'a mishi tare da fad'in " gashi kasa, ka daina zama iska tana kad'aka zaka kamu da mura, in sanyi kake ji ka tafi gidanku mana, wannan yaron ya tashi da k'yar ya karb'i rigar ya saka, ita kuwa Amira har ta juya da gudu ta shige mota driver ya ja suka tafi, wannan ya bi motar da kallo har ta k'ule a ranshi yana fad'in dama akwai ragowar mutane masu tausayi da taimako haka, gashi dai a karo na farko ya samu wadda ta taimakeshi lokacin da yake buk'atar hakan kuma ya rasa sai gata Allah ya turo mishi ita. Amira kuwa suna hanya tana tunanin yaron nan da ta baiwa riga, tausayin halinda ta tsince shi a ciki take, Amira kenan yarinya ce me tausayi tun tana 'yar tatsitsiyarta. Bayan an tashi daga makaranta aka zo aka d'aukosu suna kan hanya dai-dai inda ta ganshi da safe ta kalla har yanzu yana nan a wajen, wannan karon ma kanshi na duk'e kamar kuka yake yi, sai ta sake cewa driver ya tsaya da gudu ta sake fitowa taje har inda yake ta tsaya, sannan tace " me kake yi anan, tashi muje ka shiga mota mu kaika gida, kanshi yana duk'e kuma be d'ago ba kuka yake yana rik'e ciki, Amira tasa hannu ta d'ago kanshi tace " meyasa kake yin kuka? yaron nan yace yunwa nake ji, yau kwana na uku banci komai ba. Komawa inda motarsu take tayi da gudu ta d'auko fura da nono ta bashi tace gashi kasha, ya karb'a tare da kallon ta yace " nagode Allah saka miki da alkhairi, " Amira batace komai ba sai ta juya tana yi tana waigowa ta shige mota akaja suka tafi gida. Ko da isar su gida Amira na canza kaya suka ci abinci tace wa Mum d'inta tana so a fita da ita ta siyo abu, ba yanda Mum ta iya domin kuwa Dad d'inta ya bada umurnin a kaita duk inda take buk'atar zuwa, suka fita ita da sister d'inta Rukayyat, suna fara tafiya Amira tace wa driver hanyar makarantar su zai bi, suna zuwa dai-dai gefen ti-tin da take ganin yaron nan ta nunawa driven inda zai faka ya faka motar a inda ta umurta sannan suka fito ita da sister suka k'arasa har inda yake, zama ta yi kusa dashi ta kalle shi shima ya kalleta suka yiwa juna murmushi, sai tace " meyasa koda yaushe kake zaune a nan, kuma koda yaushe kaya d'aya kake nanatawa, baka da iyaye ne?" Nan da nan idanun yaron suka ciko da k'walla yace " haka na taso bansan iyayena ba, na rayu a hannun wani dattijo wanda ya raine ni har na girma shi na sani a matsayin uba duk da ya tab'a fad'amin ba shi ya haifeni ba, a hannunshi na girma ya fara raba mana kayan maye muna siyarwa a tasha ni da sauran yaran dake gabanshi, a haka har muma muka fara koyon sha dan muji me ake ji a ciki." Amira ta zaro idanu tare da fad'in "laaaa yanzu kana d'an yaro amma kake shaye-shaye," yaron nan yace " ke na girmeki fa amma kike cemin yaro," Amira tai murmushi sannan tace " to meyasa baka zauna wajenshi ba kake kwana anan?" yaron nan yace " Ai ya rasu yau sati guda kenan, kuma gidan da yake ciki gidan haya ne, masu gidan yana mutuwa suka koromu suka rufe gidan da kwad'o shine muka dawo kwana a nan." Amira sarkin kuka kuka take yi sosai, Rukayyat ma idanunta sun cika da hawaye, bayan tasha kuka sai ta dafa shi tace " sunana Amira kai fa ya sunanka?" Yaron yace " sunana Ameeru," sai suka kalli juna a tare suka yi murmushi suna fad'in sunan su iri d'aya. Amira tace " zan yiwa mahaifina magana ka dawo gidanmu da zama a saka a makarantar mu mu rik'a tafiya tare ko baka so?" Amir yace " ina so mana na dad'e ina sha'awar inga ina zuwa makaranta amma ba hali." Nan Amira suka yi mishi sallama akan zataiwa Dad d'inta magana duk yanda suka yi gobe zata dawo ta sanar dashi, ta ciro minti a cikin jakarta tare da kud'i ta bashi tace ya siya abinci, sannan suka juyo zasu tafi, Amir ya k'wala mata kira " Amiraaaa," ta juyo ya sake cewa " nagode Amira kina da kirki." Amira tai murmushi ba tare da tace komai ba ta shiga mota a yayin da Amir keta tsallen murna yau zai ci me dad'i, yana d'ago da idanunshi yaga sunata yi mishi dariya nan da nan ya dakatar da tsallen shima yana dariya suka ja motar yana d'aga musu hannu suma suna d'aga mishi. Amira na komawa gida ta tarar da Dad d'inta ya dawo, yaro ba hankali da gudunta ta fad'a jikinshi shima ya rungumeta yana fad'in Daughter daga ina haka?" Amira tace "Dad so nake ka taimaka wa wani yaro ya dawo gidanmu da zama shima ka sashi a makarantar mu mu rik'a tafiya tare," Dad yace " a'a daughter hakan ba mai yiyuwa bane, zan iya yin taimako tunda wannan ba shi bane na farko da kika sa nai taimako, amma bazan had'a zuri'ata da bare ba, babu wanda zan yarda ya shigo cikin ''ya'yana in ba jini na ba," Amira ta fara kuka tare da tashi daga jikinshi, cikin sauri kuma ta haye sama ta shige d'akinta tare da sa key, Dad d'inta na cewa " kinga my Daughter, " ina bata juyo ba har ta shige, Uncle ya kalli Dad yace " yaya yau kai da 'yar lele anji kanku kai da baka son ko kad'an a tab'ata, inaga da ka taimakeshi d'in.........Dad ya katseshi ta hanyar d'aga mishi hannu tare da fad'in wannan maganar ma ba mai yiwuwa bace a barta kawai," daga nan suka ci gaba da hirar abinda suka zauna tattaunawa a kanshi. _Ayi hak'uri da wannan_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 *Ina rok'on mahaliccina ubangijin kowa mai komai, sarki mai ikon komai akan kowa ka baiwa MUMCYN TAWAN lafiya👏 ya Allah ka yaye mata, ka dauwamar da d'orarriyar lafiya a gareta,👏😭😭😭😭😭 TAWAN ki kwantar da hankalin ki cuta ba mutuwa bace da yardar Allah Allah zai bata lafiya.* *RAHEENAT M. ABBAKAR* _(My Heenat)_ & *MARYAM KWARE* _(My D)_ *Sannunku bayin Allah ina rok'on Allah ya dorar muku da lafiya*👏😭 *DAD'AD'D'IYAR SOYAYYA TUN YARINTA BATA TAB'A GUSHEWA HAR GIRMA* PAGE 70 to 75 Ameeru yaro ne k'arami wanda a k'alla shekarunsa ba zasu wuce goma ba. Tun daga wannan lokacin Amira ta shiga yin fushi da Dad d'inta, kuma kullum in zata tafi makaranta sai ta tsaya ta baiwa Ameeru kud'in kashewa da da abinci, duk kud'in da ake basu na kashewa ita tara nata take yi ta kawo mishi. Akwai wata rana, yana zaune a gefen ti-ti domin baida wani wajen zuwa banda nan, gwara ma da yana tashi a shiga tasha ko cikin kasuwa domin samo abinda zai saka a bakinshi, amma yanzu baya zuwa ko ina saboda akwai me bashi. Yana zaune ba dad'ewa sai ga Amira ta taho, tana zuwa ta tarar dashi yana kuka, zama tayi cikin sauri kusa dashi tana tambayarshi dalilin kukanshi, Ameeru cikin kuka yace " wani almajiri ne ya d'auke min tabarmar da na tara kud'i na siya nake kwana akai, da kwanon abincina, harda takalma na, ina k'ok'arin karb'a ya dukeni da aka taru ana tambaya yace wai nashi ne naje na sato, aka zane ni, jiba har ciwo ya jimin, ya d'aga hannunshi da guiwoyinshi yana nuna mata ciwukan, har gefen bakinshi ma ya fashe. Kuka itama Amiran ta fashe da shi har Amir d'in ma yai shiru amma ita tana kuka, kallonta yake yana fad'in "kiyi shiru to nima na daina kukan ai." Ya share mata hawayen da hannunsa, Amira ta mik'e tsaye tare da fad'in "ina zuwa," ta juya da gudu tai hanyar gidansu, ko da shigarta d'akin mahaifin ta ta shiga ta jawo drowar ajiye kud'in sa ta d'ibo masu yawa ko rufe drowar bata yi ba ta sake kwasawa a guje ta fito, da yake gidan su yana kusa da inda Ameeru d'in yake, koda isarshi ta mik'a mishi kud'in tare da fad'in ka siya wata tabarmar da takalmi, harda kaya ma ka siya, cikin farin ciki had'e da tsoro ya karb'i kud'in da bai tab'a ko tunanin ma zai rik'e irinsu ba ko a mafarki. Ameeru yace " duka wannan nawa ne! kud'in ai sun yi yawa, ya zanyi dasu, k'wacewa ma za'ai," Amira tace " ai b'oyewa zaka yi inda baza'a gani ba, kad'an kad'an zaka rik'a kashewa, ya yi mata godiya, suka yi hira kad'an sannan tace bari ta koma gida kar a nemeta. Tana kowama gida Mahaifin ta na fitowa daga cikin d'aki, yana tambayar waye ya bud'e mishi drowa, Amira tace " nice Dad," Dad yace " meyasa kika bud'e?" tace "na yi taimako ne da kud'in Dad, a makaranta malamin mu kullum yana yi mana nasiha akan me kud'i ya rik'a taimakawa mara shi, shiyasa na taimaki wani, kaima baka ganshi ba sai ka tausaya mishi in ka gan.........." kafin ta k'arasa magana Mahaifin ta ya daka mata tsawa abinda bai tab'a yi mata ba, aikuwa nan da nan ta razana tare da fara hawaye, ta ruga d'akin Mum d'inta tana kuka. Dad ya zauna a d'aya daga cikin kujerun da suke falon nan, tare da zaunawa yana tunani gaskiya yarinyar nan ta fara canzawa, wani yaro ne wannan ta damu da lamuranshi haka, wayarshi ya d'auka ya kira d'aya daga cikin manyan security's d'in da ke kula da ita a ko ina musamman idan zata je makaranta, bayan yazo ya kalle shi yace " wane yaro ne Amira take min maganar shi kullum?" Securityn nan yace " ba d'an makarantar su bane, wani Almajiri ne a tsallaken bakin ti-tin unguwar nan da yake ta bayan gida, duk in zamu je makaranta tana tsayawa su gaisa sannan ta wuce, ai yarinyar akwai taimako da tausayi tun tana k'aramarta wall......." Dad ya katseshi cikin fushi me tsanani, yace " akwai taimako tabbas amma gashi nan ai ya jawo ta fara tunanin d'aukar min kud'i ba tare da ta tambayeni ba, zan canza mata makaranta kuma daga yau bana so ku sake barinta ta kula wannan yaron. Yau Litinin da zumud'inta ta shirya tare da zarar kud'i cikin na break d'inta da d'aukar jaka ta fito, Dad d'inta ya kalleta yace " ai ba zaki cigaba da zuwa wannan makarantar ba, na canza miki makaranta Daughter na samo miki wadda tafi wannan kyau da tsada," an gama komai, ga ma uniform d'in nan zo kisa in kaiki da kaina," jiki a sanyaye ta k'arasa wajen Mahaifin nata ya cire mata na jikinta tare da saka mata na sabuwar makarantar da aka canza mata, yana lura da yanayin ta ya kalleta yai mata murmishi sannan yace " nasan me kike tunani, yaron nan kike tunani yau bazaki had'u dashi ba ko, to zamu biya ku gaisa sannan mu wuce makarantar," ai kuwa nan da nan ta saki ranta sai zubo mishi surutu ma take," Dad kaima kaje ka ganshi ko, ka tausaya mishi ko, yana ban tausayi Dad kuma inaso ka sashi makaranta kuma ya dawo gidanmu mu cigaba da zama tare," shi dai banda to da eh baya ce mata komai, bayan ta shirya suka fito security's suka taho da gudu aka bud'e musu mota suka shiga suka fita da motoci masu yawa kamar shugaban k'asa ne ya fito. Suna k'arasowa kuwa suka ganshi yana zaune a wajen da ya saba zama, ga dukkanin alamu shima ita yake jira domin sai waige waige kawai yake yi, suna k'arasowa wajen shi Ameeru ya taso da sauri ta kalle shi ya canza kaya yai kyau, tace " kayi kyau sosai," Ameeru yai murmushi sannan yace "nagode," ya mik'a mata wani abu a cikin leda yace "dama ke naketa jira ki k'araso kin gani abubuwan da na siya miki," wani agogon roba ne ba ma na gasken nan ba irin wanda yara ke siya su d'aura, sannan ya ciro tabarau shima kalar agogon ya bata, ya sake ciro wani zobe k'ato da warwaro ya bata se dai zoben da tasa yai mata yawa, amma duk da haka tace tana so zata aje har ta girma sannan ta saka, duk da kasancewarta 'yar hamshak'in me kud'i amma haka taita murna akan kayanda dukkansu bazasu siya ribom d'in kanta guda d'aya ba, yanda suke murna hatta Mahaifin ta sai da yai mamaki, sai bayan sun gama murnarsu sannan ta nuna mishi Dad d'inta ya k'arasa kusa da shi ya durk'usa ya gaishe shi, Dad ya kalli wasu daga cikin security's d'in wajen yace su d'auke Ameeru daga nan baya so ya sake ganinshi a wajen nan, nan da nan suka sab'a shi a kafad'a yana zillewa yana kuka, itama Amira na k'wala mishi kira tana kuka, haka Dad d'inta ya jata ya turata cikin mota suka tafi makaranta, su kuma sauran suka tafi nisanta Ameeru da kusa da gidan su Amira. Dad d'in Amira ya kalleta yace " ko kukan jini zaki yi sedai kiyi, karatu nakeso inga kin zage kinyi kafin ki fara tunanin taimakawa wasu ba shirme da shiririta ba. Kuka take sosai kamar me har suka k'araso makarantar, ya yi magana da malaman wajen kan kar su rik'a barin Amira tana fitowa har sai an tashi. Daga wannan ranar bata sake saka Ameeru a idanun ta ba, bata san kuma a wane hali yake ciki ba. Kuma daga wannan lokacin ta daina walwalarta kamar yanda take yi ada, in ta dawo makaranta tana shigewa d'aki bata k'ara fitowa, haka zata tasa kayan da ya bata taita kuka, duk ta rame bata wani ko cin abincin kirki. Bayan kwana biyu Dad ne da matar shi da Uncle shima da matarshi suna hira sai matar Dad tace " gaskiya halin da Amira take ciki kwanan nan ya fara bani tsoro, bata cin abinci duk ta rame kullum cikin kuka ta dena walwala, koda yaushe tana d'aki," Dad yace taje ta taho da ita, ta tashi ta tafi, tana zuwa d'akin ta tarar da jikinta yai zafi sai rawar sanyi take yi, hakan yasa ta dawo da sauri ta fad'awa Dad d'inta halinda take ciki, hakan yasa suka garzaya aka d'auketa sai asibiti, a asibitin ne Uncle ya kalli Yayan nashi yace " Yaya kasan yanda shak'uwa take tsakanin yaro da yaro, in kace zaka rabasu ta haka tunda sun saba ta rik'a shiga cikin irin wannan halin kenan, kaima ji yanda duk ka rud'e kafi kowa son yarinyar nan in wani abu ya sameta sai ka fimu shiga cikin tashin hankali, saboda haka tunda dama ta rok'i ka taimaka mishi to ko bazaka kawo shi cikin gidan nan ba be kamata ka rabasu ba sai kasa a kaishi koda gidan marayu ne, kuma kasa a sakashi a makarantar su kaga ka samarwa Amira da farin ciki kan taimakon da takeso taga kayi, kaima kuma hankalina zai fi kwanciya akan irin halinda take ciki a yanzu." Suna cikin maganar ne sai ga kiran shugaban makarantar su Amira tana fad'a mishi cewa sam Amira bata maida hankali kan karatunta, banda ma tunani da kuka babu abinda take yi, ya kamata su binciketa kan abinda ke damunta. Jin hakan yasa jikin Dad d'in Amira ya k'ara yin sanyi, babu abinda yafi k'auna sama da yaga 'yar shi ta maida hankali tai karatu ta zama wata abu a duniya ta d'aukaka fiye dashi ma, Uncle ya kalle shi yace " Yaya lafiya meyafaru?" Dad ya fad'a mishi duk abinda aka kira aka fad'a mishi yanzu, Uncle yace "to kaga irin ta ko, yara ba'a rabasu ta k'arfi da yaji in dai suka shak'u, ta dabara ake yi musu yaya, yanzu ina dad'i ace duk k'ok'arin da Amira keda shi ada ace yanzu babu shi, gaskiya kai tunani akai yaya kuma abinda Amira keso kayi abu ne me kyau fa wanda in kayi lada zaka samu tunda kaga ta fad'a mana labarinshi tun farkon had'uwarsu," Dad yace "shikenan zan yi amfani da shawararka Adam." Bayan kwana biyu Amira ta gyagije Dad d'inta yai mata Albishir zai kai Ameeru gidan marayu kuma zai saka shi a makarantar su kamar yanda ta nema, tun daga lokacin farin ciki da walwalar Amira suka dawo, sedai abinda yafi damunta da d'aga hankalinta shine ina za'a ganshi, domin an dudduba ko ina da ake tunanin za'a sameshi ba'a ganshi ba, kullum sai sun fita nemanshi amma basa ganinshi, kamar wasa Amira tace a duba wajen da yake zama a wautarta wai tasan zai dawo ya jirata. Ana dubawa wajen kuwa suka tarar dashi zaune ya kod'e yai bak'i ya rame yana ta kare ranar da take ta kashe mishi ido, tana fitowa daga cikin mota ta kwala mishi kira, yana waigowa ya hangota da gudu ta taho shima ya tashi da gudu suka rungume juna suna kuka, Ameeru cikin kuka yace " tunda kika tafi na dena samun abinci kalli yanda na rame, kud'in da kika bani wannan mugun ya k'wace, dan Allah karki sake tafiya ki barni," hatta Mahaifin nata da sauran tawagar sai da tausayin Ameeru ya saka su hawaye, d'an k'aramin yaro d'an shekara goma amma Sam be san jin dad'in rayuwa ba, Amira ta kalle shi tace "bazan sake tafiya ba, yau ma zamu tafi dakai za'a saka a makarantar mu, za'a kaika gidan marayu kusa da gidanmu nan zaka cigaba da zama muna tafiya makaranta tare." Dad yace " kuzo mu tafi to sai kuyi hirar a hanya, cikin mota ma suka karad'e su da surutu, Ameeru yace kullum sai na tuno dake, kefa?" Amira tace nima haka ta nuna mishi hannunta tace kaga ma abubuwan da ka siyamun nasa," Ameeru yace "dagaske makarantarku za'a kaini, kuma zamu rink'a had'uwa dake har muna yin wasa?" Amira tace "eh mana," duk hirarsu Dad da uncle suna ji, zuciayar Dad ce ke sak'a mishi cewa tabbas ko yanzu yasan Amira bazata maida hankali ba kan karatunta, dole ya d'auki matakin da zai nisanta su da juna ko ba yanzu ba, cikin hikima ta yanda ba zata gane komai ba kuma ta yanda dole zata hak'ura dashi, har suka k'arasa gida tunanin da yake ta yi cikin ranshi kenan, tabbas yana son farin cikin 'yarshi amma tabbas baya son kasancewarta da yaron nan. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 *Ina mik'a ta'aziyyata ga HAUWA JAMIL, na d'an'uwa da muka rasa, Allah ya ji kansa ya kyautata makwancinsa, Allah ya haskaka kabarinsa, ya yafe kurakurensa, Allah yasa mutuwar ta zamto hutu a gareshi yasa aljanna ce makomarsa, Allah ya bamu sa'an tarar dasu, ya k'ara muku hakurin jure rashi.👏👏👏👏👏* PAGE 75 to 80 Ameeru yai kwana biyu a gidan su Amira hakan ya k'ara musu shak'uwa sosai, sannan aka d'aukeshi aka kaishi gidan marayun da yake kusa da gidan su Amira, bayan sun gama da nan aka kaishi makarantar su Amira aka gama mishi komai. Tun daga wannan lokacin tare suke zuwa makaranta, idan Ameeru ya shirya sai ya taho gidan su Amira a d'auke su gaba d'aya a kaisu. Tun daga wannan lokacin k'ok'arin Amira ya dawo sosai, sedai sam shi Ameeru baida k'ok'ari baya gane komai, to da yake ajin su Amira d'aya dashi idan an tashi break zama suke yi tai ta koya mishi tana nuna mishi itafa bata jin dad'in dariya da ake mishi kullum be iya komai ba, Ameeru ya bata amsa da zai dage yai karatu ko dan ita in ya girma ya kyautata mata kamar yanda itama tai mishi, cikin ikon Allah kuwa ya d'an fara ganewa. Daga kan Malaman makarantar kaf har zuwa d'alibai Ameeru da Amira suna burge kowa, duk inda suka shiga sha'awarsu ake, had'in kansu da shak'uwarsu abun burgewa. Ko laifi d'aya daga cikinsu yaiwa malami to basa yarda a hukunta d'aya, se dai a hukunta su gaba d'aya, idan horo aka baiwa d'aya dukkansu suke fitowa, in za'ai duka kuma dukkanin su suke mik'a hannu da wanda yai laifin da wanda be yi ba, kowanne daga cikin su k'ok'ari yake yaga an dakeshi shi an k'yale d'an uwansa, wannan shak'uwar tasu ce tasa suka k'ara burge kowa, kuma kowane malami yake k'aunarsu. Abu d'aya ne yake damun Dad d'in Amira shine, Ameeru baya so koda kallon banza aiwa Amira balle har a tab'a lafiyar jikinta in kuwa kai mata hmmm, yasha targad'a yara da karyasu kai raunika iri-iri a kan Amira, iyayensu na zuwa suna kai k'ara gun shugaban makarantar, da abun ya ishe su sai shugaban makarantar ya kira Dad d'in Amira ya sanar dashi. Kuma kullum Ameeru yai fad'a kan Amira sai an zane shi, amma hakan be hana shi gobe ma ya yi, shi in za'a tab'ata sau dubu to shima zaiyi fad'a a kanta sau dubu, dukan da ake yi mishi sam be damunsa. Zaune Ameeru yake a kusa da ajinsu, koyarwa ma ake yi a ajin, wani ya harari Amira ya mareshi, shine malamin ya zaneshi kuma yace ya fito ya bar mishi ajinshi ya saka guiwarsa a rana har sai ya gama ya fito. Amira na ganin an koreshi itama ta fito, malamin su na kira amma ina sai ma ta danno a guje tazo kusa dashi itama tayi irin horon da aka sashi, suka kalli juna sukai murmushi, Ameeru yace " wato saida kika fito ko," Amira tace " eh mana kana waje saboda ni sai in zauna a ciki," suka yi dariya sannan Amira ta sake kallon shi tace " meyasa kake fad'a a kaina Ameeru?" Amir yace saboda ina sonki, kuma bazan tab'a bari a tab'aki ina kallo ba," Amira tai dariya tace " laaaa ashe kaima kana sona," dukkansu suka sa dariyar murnar suna k'aunar juna, Amira ta sake kallonshi tace " jiya Dad ya kirani yace wai anyi mishi waya ance bama k'ok'ari a makaranta, sai nace mishi eh mana Dad koyaushe cikin karb'ar hukunci muke," Ameeru yace " ni fa tsoron Dad nake kar ya dukeni," Amira ta b'ata rai tana fad'in ka tab'a ganin ya dukemu ne," sufa gaba d'aya rayuwarsu basu da matsala muddin suna tare. Abun nasu fa sai gaba gaba yake sun fitini kowa dan yanzu itama Amira in d'alibai suka daki Ameeru taron dangi suke yi su biyu su daki koma waye, sannan itama haka in ita aka tab'a taruwa suke su daki mutum, gaba d'aya makarantar yanzu shakkar su ake. Akwai ranar da Amira ta taho da gudu tana fad'awa Ameeru ga wani can yazo yace yana sonta, da gudunsu dukaje shima suka yi mishi duka, ashe sun mishi targad'e a hannu, tun daga ranar Ameeru ke bawa duk yaron da yaga ya kula Amira kashi, in ma be gani ba ita tana fad'a mishi, domin ta sanar dashi tana jin dad'in yanda yake cin uban mutane a kanta. Abu fa ya ishi Dad d'in Amira kullum cikin waya ake mishi sunyi kaza da kaza, hakan yasa ya fara tunanin lallai muddin yana so 'yarshi tai karatu to sai ya bar garin nan sun koma wani garin da zama, akan wannan shawarar ya tsaya. Zaune suke a falo dukkanin 'yan gidan Dad ya fad'a musu shawarar da ya yanke, kuma yace ya gama magana babu me canza mishi, zasu koma gidanshi da yake kano saboda 'yaranshi sami ilimi me kyau, kuma ya fad'a musu akan 'yarshi babu abinda bazai iya yi ba kuma zai iya barin k'asar ma da ita domin ta samu ilimin da yake buri, sun riga da sun san halinshi murd'ad'd'en mutum ne in ya kafe a abu juyo dashi abune me wahala, sun gama maganar kenan sai ga Amira ta dawo daga makaranta, tana shigowa Dad d'inta ya kalleta yace " oyoyo My Daughter, zo in miki albishir zamu je kai ziyara kano gobe in Allah ya kaimu, amma bazamu dad'e ba zamu dawo, kuma in har kina sona kuma kina son farin ciki na ban yarda ki b'ata rai ba ko kiy kuka," Amira ta kalle shi tace " harda Ameeru na za'a tafi?" Dad yace a'a ai ba zamu dad'e ba zamu dawo, " ita har ga Allah bata son tafiyar nan, amma sai tace "to bari in je in fad'a wa Ameeru in dawo," har ta juya da gudu Dad d'inta ya k'wala mata kira ta dawo yace ta bari sai goben in zasu wuce sai taje suyi sallama, haka nan ta hak'ura ba dan taso ba. Washe gari tun asuba kowa ya tashi ya shirya, itama Amira ta tashi tazo sakkowa taji maganar Dad d'inta yana fad'in ai bazan bari su had'u da Ameerun ba," jin ya ambaci sunan Ameeru tasan zancensu ake, hakan yasa ta tabi ta k'ofar baya ta fice, sai kuma ta dawo taje d'akin Dad d'inta ta d'auko k'atuwar jakarshi wadda ke cike da kud'i ta fito da ita kamar zata rinjayeta ma, ta shiga cikin d'aki tare da kwaso hotunan su da wanda suka yi tare da wanda take ita kad'ai shima haka, ta ware d'ai-dai ta saka mishi cikin zip d'in jakar, sannan ta fita tana share hawaye har bakin gate d'in gidan marayun, ta shiga ta tarar da me kula da su Ameerun, bayan sun gaisa ta tambayeta ina yake tace ya shiga wanka, sai Amira ta bata jakarnan tare da rok'on ta ta baiwa Ameeru injita harda 'yar takarda, sannan ta juya ta tafi, a hanya taga su Dad sun fito nemanta sukai kicibis, ya kama hannunta suka shiga gida jikinta duk a sanyaye, aka shiryata suka shiga mota tare da security's d'insu bayan an rufe ko ina, sun fara tafiya kenan sun wuce gidan marayu kenan sai ga Ameeru da gudu yana k'wala musu kira amma ina sesai Amira ta hango shi, bin motar da gudu yake yana kuka, itama tana kuka har ya gaji da gudun ya durk'ushe a k'asa kan ti-tin yana kallon motar Amira na d'aga mishi hannu tana kuka. Komawa cikin gidan marayun da ya zama gidansu ya yi, ya shiga d'akin da yake mallakin shi ya jawo akwatin da Amira ta bashi, dan Amira ta cewa maman kayan sawanshi ne a ciki saboda su zasuyi tafiya shine ta kawo mishi, hakan yasa bata bud'a ba taga ko miye a ciki har ta bashi. Koda ya bud'e kud'i ya gani masu uban yawa 'yan dubu dubu cike da jakar, wanda suka sashi mugun razana harda matsawa da sauri kamar wanda yai gamo, hakan yasa yai sauri ya maida zif ya rufe kar a shigo a gani, ya d'auko takardar da ta bayar a bashi had'e da jakar ya bud'e tare da fara karantawa: _Ameeru nah Dad ya shirya mana ziyara zuwa kano, amma yace bazamu dad'e ba, duk da haka ga kud'i nan ka yi amfani dasu kafin na dawo dan banaso ka koma rayuwar da na sameka a ciki a baya, Dad yak'i bari muyi sallama nasan zaka jirani duk rintsi zanyi kewarka._ *CI GABAN LABARI* Amir ya k'araso kusa da ita tare da tsugunnawa yace " Amira dan Allah ki saurareni kiji, wato abinda ya faru shine, " sai kuma yai shiru, Amira ta d'ago ta kalle shi sannan tace "ni nasan dama babu abinda zaka fad'i ka kare kanka a wajena, k'aunar da na nuna maka tun yarinta rabinta baka nunamin ba," Amir yace " haba Amira in har kika fad'i haka bakiy min adalci ba, ki tsaya mana kiji abinda ya faru bayan tafiyarku." Amira tace " ina saurarenka," Amir yace " _tunda naga wasik'arki kuma naga Dad yak'i bari muyi sallama nasan tabbas ba zaki dawo ba naci kuka kamar me, amma ina ganin wannan kud'in sai tunanin biyoki kano yazo raina, amma na fara tunanin be kamata na rik'a yawo da kud'in a haka ba, hakan yasa na saka jakar kud'in cikin gana masgo d'ina na saka kayana tare da kinkimar jakar na fito, Allah ya taimakeni babu kowa me gadi ma baya nan maybe ya zagaya baya, hakan yasa na runtuma a guje duk da gudun ba sauri sosai saboda jakata dake rinjayata, dama kafin na fito daga cikin gidan na zaro dubu biyar a cikin kud'in nasa a aljihu, ina fitowa na tari adai-daita sahu sai tasha, ina zuwa naci sa'a saura mutum d'aya ta cika na biya kud'i sannan na shiga, ba yanda ba'ayi ba kan in bada jakar a samin a baya nak'i yarda, a haka aka ja motar jakar na k'afata har muka iso kano, tunani na fara yi kan ina zan dosa ni da bansan kowa ba gashi kano akwai girma ta ina zan fara nemanta, ina cikin wannan tunanin na hango wani dattijon Arzik'i cikin tashar wanda ke zaune cikin wata kwarab'ab'b'iyar mota yana cin tuwo, k'arasawa nai kusa dashi sannan na gaishe shi, bayan mun gama gaisawa yace min "yaro ina zaka je kai kad'ai haka ina iyayenka, ko kai Almajiri ne, koda yake jikinka be nuna ba," nan na fad'a mishi cewa iyayena ne da 'yar uwata nake nema a nan garin, tare da ciro hotunanmu duka ina nuna mishi, bayan ya duba yace " yaro gaskiya ban san inda suke ba kuma bansan inda za'a gansu ba, kuma kasan kano da girma, amma zan taimake ka, in ka yarda zaka zauna da ni to zan taimaka maka insha Allah za'a gansu wata rana, ba ko tunani nace na yarda zan bishi, ya siya min tuwo naci sannan ya d'aukeni ya kaini shagon wani gida yace nan ne makwancinsa domin shima ba d'an garin nan bane d'an zaria ne, neman kud'i ya kawoshi nan, mota yake ja duk ta tsufa ma kuma beda halin da zai dawo da iyalinsa nan, bayan kwana biyu na yanke shawarar rik'a bin Baba in zama kwandastan shi, wata k'ila ko ta sanadin haka Allah yasa in ganki, a haka na cigaba da rayuwa kullum bayan mun fita sai na nemeki haka ma in mun dawo, ban tab'a tunanin tab'a kud'in nan ba saboda komai nakeso Baba yana min, bayan shekara biyar lokacin shekarata sha shida kenan jikin Baba yai tsanani har saida ya koma gida, komawar da be sake dawowa ba sai labarin mutuwarshi naji wanda ya sani kuka sosai, rayuwa tai tsanani hakan yasa dole na fara tab'a kud'in nan ina biyan kud'in shago, sannan na cigaba da zuwa makarantar da Baba ya sani, da cigaba da biyawa kaina kud'in makaranta, Baba yana d'aya daga cikin mutanen da har in mutu bazan iya mantawa dasu ba, a haka har na girma nakai shekara Ashirin da bakwai ina nemanki a lokacin ne na shiga makarantar da kike aka yi sa'a kuma daga shigana Allah ya had'a mu a kan hanya, sedai tun a ranar na fahimci kece Amira ta saboda har lokacin kina tare da 'yan kunnayen da na siya miki da wannan zoben da yai miki d'as a yanzu a hannu, shaida ta gaba itace sunanki da sunan Dad su suka k'ara tabbatar min da kece, kafin had'uwata dake na siya gida duk a cikin kud'in nan, sannan kuma na fara sana'a yanzu kasuwancin gida da filaye nake yi._ Amir ya numfasa sannan ya cigaba da fad'in " taya zan manta da masoyiyata tun ta yarinta wadda take sona da gaske kuma ta zama silar canzawar rayuwata." Amira wadda idanunta suka yi ja kuma suka kunbura saboda kuka tace " amma meyasa da ka gano nice ka b'oye kanka gareni, kuma ka canza sunanka daga Amir zuwa Ameeru?" Amir yace " zan baki amsa yanzu ma kuwa amma kafin in fad'a miki inaso ki fad'amin gaskiya me ya faru bayan dawowarku nan, kuma tunda kuka dawo garin nan kin koma Abuja, kuma meyasa kike karatu anan bayan su su Dad sun koma Abujan da zama?" _ku biyoni muje_🏃‍♀ *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S kullum fa burgeni kuke wallahi, Allah ya k'ara d'aukaka mini ku, ya k'ara muku basira, ya k'ara mana k'aunar juna, a cigaba da basu mamakin kawai😉😘* *MUMCYN MU ALLAH YA K'ARA 'DORAR DA LAFIYARSA GAREKI, TAWAN ALLAH YA K'ARAWA MUMMY LAFIYA👏😭😭😭* *MY NAMECY BILKISU (QUEEN BK) ALLAH YA KARA MIKI LAFIYA👏😭* *MY LISSA Amir yace yaji sak'on gaisuwar ki amma be amsawa saboda kin b'ata mishi rai,😏 sannan yace in mik'a gaisuwa da ga magoya bayansa QUEEN RUQEEY HABIBTY, da MAMAN LABYB MAMIE NAH TA KAINA, da BABYNAH HAUWA, da MY HEENAT, yace duk wata k'auna taku da kuke gwada mishi yana gani kuma yana godiya, sannan yana so yasan iya adadin 'yan team d'insa duk da yasan masoyanshi sunfi yawa Lissa ce kad'ai bata sonshi kuma yace a fad'amata yana mata i hate you😂😂😂😂😂* PAGE 80 to 85 Amira ta kalle shi tace _" bayan tahowarmu abun be dameni ba sosai sai da naga anyi sati d'aya biyu har wata shiru ba'a ma maganar komawarmu gida, koda na jewa da Dad d'ina da maganar komawarmu sai naji sab'anin haka yana fad'in ai a nan zamu cigaba da zama yanzu haka ma makaranta yake so ya sakani in cigaba da karatuna, dama shi ya yi haka ne dan ya rabamu tunda mun k'i maida hankali a karatu amma in kwantar da hankalina yana kula da kai da kuma karatunka, a ranar ma fad'ar halin da na shiga b'ata baki ne, anan na cigaba da karatuna har na girma, ana fara shirin sakani jami'a Dad d'ina ya koma Abuja da 'yan uwana da zama sakamakon tsayar da shi da aka yi na zama takarar shugaban k'asa kuma cikin ikon Allah ya samu nasara, ranar da na fara zuwa gida shima bikin murnar samun kujerar mahaifina ne, da naje ba irin neman da ban maka ba aka tabbatar mun da cewa ai tun ranar da muka tafi kaima ka gudu basu san inda ka shiga ba, na ci kuka na gode Allah amma har lokacin gani nake yi duk daren dad'ewa zamu had'u shiyasa duk na koma garin Abuja sai na fita neman labari a kanka amma shiru, duk tsawon wannan shekarun na kasa cireka a raina Amir koda na kwana d'aya ne, kullum sai na d'auko hotonmu na kalla ina kuka ina tuna rayuwar da muka yi a baya, se dai duk in na tunaka a raina ina ji a cikin zuciyata tana tabbatar mun cewa tabbas wata rana zamu had'u kuma in har Allah ya had'amu banda wani miji sai kai, ko cikin k'awayena a ko'ina nake in aka yi maganar aure sai ka fad'o raina domin da kai kad'ai na saba, kaine ma namiji na farko da ya tab'a shigowa cikin rayuwata, kullum tunanina zan ganka, sam Dad baya son ina kai ziyara gida saboda kar mu had'u dakai, shi burinshi kar na dawo sai na gama karatu gaba d'aya tukun, kasan dai yanda na shak'u da kai kuma nake sonka, shiyasa na dad'e tunanin ka na tab'amin zuciya."_ Amira ta cigaba da fad'in "kaji abinda ya faru bayan barinmu garin." Amir ya numfasa sannan ya kalleta yace " to nima zuciyata ta tabbatar min da cewa saboda ni kuka tafi kuka canza gari kuka yi nesa dani, domin na dad'e da sanin cewa Dad baya sona tare dake, hakan ne yasa na canza suna daga Ameeru na koma Amir kuma bayan na ganoki na cigaba da b'oye miki kaina, burina muyi aure tukun kafin ki gano ko ni waye kar kizo ki gano kuma Mahaifin ki ya hanani mallakar ki matsayin mata." Amira tace "duk da haka wannan dalilin be isa saka ka cigaba da b'oye min kanka ba, kai da kanka kace kaga abubuwan da ka siya a tare dani duk da cewa ko da nake yarinya ma na wuce da ajinsu balle da girmana, amma soyayyar da nake maka tasa nake kallon su a gagarumar kyauta mafi tsada a duniya, kasan wahalar da nake kan sha har yanzu wajen nemanka kuwa domin saida zuciyata ta bani nan kano ka taho saboda na rubuta maka inda zamu taho a wasik'a, kasan mutane nawa na kasa su cigaba da bincikamin labarin duk wani mutum me suna Ameeru kuwa? kasan iya adadin maza nawa nabi masu irin sunanka ina bibiyarsu domin gano wanene kai a cikinsu? haba Amir meyasa da ka gano nice ka b'ata lokaci wajen sanar da ni kaine Amir d'ina? haba Amir ya zaka min haka." Amir ya dafa Amira sannan yace kiyi hak'uri Amira, harga Allah zuciyata bata yi tunanin har wannan tsawon lokacin ina cikin ranki ba saboda mutanen da nazo na tarar dasu a tare dake musamman Sadeeq da Abdul, kuma dukkanin su na hango alamun k'aunarki a cikin ransu, hakan yasa na bari tukun sai na farfad'o da soyayyata da wasu suke k'ok'arin k'waceta daga gareni, kinji dalili wallahi banyi tunanin har zuwa yanzu ina ranki ba haka saboda ganinsu a tare dake, amma gani a gabanki guiwoyina a k'asa ina rok'on ki dan Allah ki amince ki taimaka ki sake shigowa rayuwata, wallahi a yanzu ke kad'ai ce abar da na rasa a rayuwata." Amira tace " wallahi duk cikin su babu wanda na tab'a jin sonshi a raina, shak'uwa ce kawai da sabo amma ban tab'a sonsu ba kamar 'yan uwa na d'aukesu kuma abokan shawara." "Dama wannan shine dalilin da yasa ka bisu d'aya bayan d'aya ka kashe su?" maganar da su Amir da Amira suka ji anyi kenan daga bayansu, koda suka juyo dukkansu ba wanda suka gani sai Insp Yahya, jingine da jikin k'ofa yana hard'e da hannayen shi. Insp Yahya yace " wannan labarin da kunnena yaji ya k'ara tabbatar min da cewa kaine kayi kisan nan Amir, ko ba kai bane to kana da hannu a ciki." Amira ta tashi tsaye tare da takawa har inda Insp Yahya yake tace " Insp rashin mutuncin naka ya isa haka, taya za'ai wai ka rik'a jifan Amir da wad'annan kalaman ko dan kaga ina dakatar dashi kan d'aukar mataki a kanka, karka manta ubana shine shugaban k'asar nan zai iya sanadin rabuwarka da aikin nan, kuma karka manta wanene kake fad'awa magana a kaina, jarumi ne shi kuma sadauki wanda zai iya yin komai a kaina." Insp Yahya yai dariya sosai tare da tafa hannaye, sannan ya kalleta yace "gaskiya naji dad'in furucinki na k'arshe da kikace Amir zai iya yin komai a kanki, tunda kin tabbatar da haka bakya tunanin har kisa ma zai iya yi a kanki? ko kin manta cases d'in da aka yi a baya na dukan maza da yaita yi a kanki, kin manta furucin da ya yi a k'arshen ranar da na kulle shi a gabanki? to bari na tuna miki cewa ya yi in har za'a cigaba da tab'aki to bazai tab'a daina kai duka ba, wannan fa akan wanda ya kulaki ne kawai ko ya tab'aki Amira to ina ga kuma wanda yaji yace yana sonki ko yaga yana gwada miki k'auna." Amira ta dakatar dashi tare da d'aga mishi hannu, tana nuna mishi k'ofa alamar ya fita ya bar mata gida, Insp Yahya yace "na tafi amma kiyi dogon tunani akai ki gani," yana kai nan a zancensa ya fita ya bar gidan. Amira ta duk'e a k'asa tana dafa kai tare da fashewa da kuka, Amir ya k'araso zuwa inda take ya duk'a tare da dafata, fad'awa jikinsa tayi tana kuka tace " Amir d'ina kayi hak'uri dan Allah da k'azafin da wannan d'an sandan ke jifarka da su, babu wanda ya isa ya canza min ra'ayi a kanka, ni na fara tunani ma ko Dad ya sashi ya rik'a bibiyarmu, to wallahi Amir ko kisan kai ka yi a gabana ina tare da kai ban tab'a gudunka duk rintsi, nan fa sukai ta kuka daga k'arshe kuma suka rarrashi kansu, sauk'in da Amir yaji ma da bata yarda da zancen Insp ba. Amir yace " bari inje gida in d'an kwanta duk da yamma tayi ma," Amira tace " ka kwanta a nan mana," Amir yace " a'a Amira kalli fa yanda na fito daga singileti sai gajeren wando ni tsoro na ma kar wannan masharrancin ya sake yimin wani sharrin." Amira kuwa sai a lokacin ma ta lura da yanda yake, duk da halin da suke ciki amma be hanata dariya ba kamar me harda rik'e ciki tana nunashi tana dariya, shima sai a lokacin ne yai murmushi sannan yace " duk ba ke kika jamin ba kukanki ya birkita tunani da duk wani lissafi nawa ya sakani fitowa a haka ba, wallahi kaf duniya b'acin ranki kad'ai yafi komai d'aga hankalina balle kuma har inji kukanki sai inji kamar na haukace saboda tashin hankali, kafin had'uwa dake bana tunanin rayuwa tana da sauran amfani gareni kuma banyi tunanin zan samu canji haka ba, amma bayan had'uwa had'uwa dake na gane cewa wannan tunanin da nake kuskure ne, wallahi mijinki ya more da mata, iyayensa sun more da suruka yaranki sun more da uwa ta gari ina kaunarki Amirata." Amira tai murmushi sannan tace "ina sonka Amir d'ina matarka zata more da kulawa tare da dad'ad'an kalamai," Amir yai murmushi sannan yace "zan tafi anjima zan dawo," Amira tace "wallahi idan muna tare bana so mu rabu Amir." Amir yace "karki damu bazan d'auki lokaci me tsawo ba zan dawo gareki, wanka kawai zanyi domin baccin da nake ji ma ya gudu kamar yanda duk lokacin da kike cikin bak'in ciki walwalata ke guduwa hakama baccin da ke idona ya gudu na nemeshi na rasa," dukkanin su suka sakarwa juna murmushi sannan ya saka d'aya daga cikin kayan da zata wanke mishi dan tace bata yarda ya koma a haka ba matan dake waje su gane mata jikin miji, daga nan suka yi sallama da juna ya fito ya shiga mota ya tafi gida. _Hattara mata kaicon matan auren da suke sassautawa wajen furtawa mazansu kalamai na so, wata matar ma da ta shiga gidan auren shikenan furucin dad'ad'an kalamai ya k'are, to wallahi ku sani wad'annan kalmomin da kuke rainawa da tattali da kulawa da kuke d'aukarsu kamar kun wuce da ajinsu, to sune makaman ku da kuka yi kafin ku shigo gidan, kuma sune makaman ku da zaku cigaba da jajircewa kansu a cikin gidan aure, kuma karku manta da su ne kishiyoyin da ake muku suke yak'arku har su fiku samun matsuguni da fada a gida, saboda ke kin saki jiki kawai tunda kin shigo fad'awa mai gida I love you a cikin gida da me gida kana raina idan ya fita sun k'are, a'a wallahi so kamar fure ne, koda yaushe yayyafa mishi ruwa ake domin ya k'ara tsiro da girma, haka so yake, ki cigaba da furta kalamai sababbi akoda yaushe kuma dad'ad'a tare da tattali da nuna kulawa shi ke k'ara saka so yai girma cikin zuciyar bawa, Allah yasa an fahimta kuma masu yi zasu gyara, wallahil azeem so na gaskiya baya tab'a gushewa sedai ko bak'in halin mutum da munana zuciyar da kake wa masoyinka ya jawo tsana wanda kuma wannan kai ka gogeta da hannunka sakamakon halinka, Allah yasa mu dace._🙏🙏🙏🙏🙏 Bayan fitar Amir Amira tai sallah tare da wanke kayan Amir ta gama a dai-dai ana kiran sallar magrib, tai sallar magrib d'in sannan ta zauna tana d'an tunani can sai maganar Insp Yahya ne kawai ke dawo mata cikin rai, duk yanda taso ta kawar dashi ta kasa, maganar shi ta k'arshe ce ke dawo mata wadda yace " _(karki manta Amir yace muddin za'a cigaba da tab'aki to tabbas ba zai fasa kaiwa mutum duka ba, wanda ya tab'aki fa kenan ina ga wanda ya furta miki kalmar so ko yaga ana nuna miki,.........zan tafi amma ki zauna kiyi tunani."_ Duk yanda taso ta kaucewa zuciyarta daga barin karta fara zargin Amir a zuciyarta ta kasa, kawai ji take yi zuciyarta na neman fara gasgata zancen Insp Yahya musamman tunano abubuwan da Amir yaita yi a kanta tun tana k'arama har zuwa girmanta. Tana cikin wannan tunanin ne sai wayarta ta fara yin k'ara alamar ana kiranta, tana dubawa sai taga bak'uwar lamba, hakan yasa ta k'i d'agawa har kusan sau uku ana kira bata d'agaba, sai can taji k'arar message ya shigo, tana dubawa taga lambar da ta kirata ce dai aka turo mata message da ita, bud'ewa ta yi tare da fara karantawa, _Amira Insp Yahya ne, ni har ga Allah taimakonki nake so inyi ya kamata kiyi bincike ne kafin ki k'aryata zancena kan kisan da nake tuhumar Amir akai."_ Amira cikin fushi ta mayar mishi da amsa cikin hassala kamar haka: _wai me ya shafeka da lamarina ne, rayuwata ce fa ba taka ba, menene naka na bibiyata to bari kaji ko rai d'ari Amir ya kashe ina sonshi a haka, in ma saka aka yi ka yi mishi sharri to beyi tasiri a kaina ba._ Insp Yahya dake cikin office yaji amsar Amira ta shigo ya bud'e ya karanta, sannan yai murmushi kuma a fili ya fara magana shi kad'ai, " dama abinda nakeso inji daga gareki kenan, wato kare makashi kike bayan kinsan me ya aikatawa koh, hahaha zaku sha mamakina yanzu na fara bibiyar lamarinku har sai na gano gaskiya domin kisan nan akwai lauje cikin nad'i, kai kuma Amir a juri zuwa rafi............." Ku biyoni muje *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie) ``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 *MASOYAN GASKIYA SUN K'ARE KO INCE SUNYI K'ARANCI SAI D'AD'D'AIKU, DUK MASOYIN DA YA SOKA KUMA YA BARKA TO BA CIKAKKEN MASOYI BANE NA GASKE WALLAHI, MASOYIN GASKIYA BAYA TAB'A GUDUNKA DUK RINTSI DUK WUYA ANA TARE, ALLAH KA HAD'AMU DA MASOYA NA GARI.* PAGE 85 to 90 Amira na gama tura mishi test message ta goge wanda ya turo mata da wanda ta tura dan saboda kar ma Amir ya gani ranshi ya sosu dan ita sam ba zata so hakan ba, tabbas tasan Amir zai iya yin komai a kanta, amma zuciyarta bata tab'a bata damar zargin shi ba balle tace zata yi bincike a kanshi. Shi kuwa Amir bayan ya koma gida kasa aikata komai ya yi har wankan, ya fad'a gado yana ta kuka kamar yaro, sai a yau ya fara sarewa kan soyayyar Amira, saboda ya tabbatar mahaifin Amira da wuya zai yarda ya bashi ita aure, in kuwa har zai bashi to akwai gagaruman matsaloli a gaba, domin dole ace sai sun san hak'ik'anin iyayenshi, shi harga Allah tunanin shi bai tab'a kawo mishi hakan ba, kuka yake kamar ranshi zai fita, hakan ya haddasa mishi ciwon kai me tsanani. Amira ce zaune idar da sallar isshanta kenan, tana zaune tana jiran zuwan Amir har takwas da rabi shiru, se dai ta d'an yi mamaki saboda tasan be cika kaiwa wannan lokacin ba tare da ya taho gareta ba. Tara dai-dai ta kasa hak'uri ta d'auki wayarta taita doka mishi kira gashi dai tana ringing amma shiru ba amsa, har zuwa tara dai-dai tana kiranshi amma ba'a d'agawa, hakan yasa ta gaza jurewa ta tashi ta d'auki mayafi tare da zarar key ta fito ta shiga cikin mota ta tayar sai hanyar gidan Amir. Da isarta ta faka motar ta bud'e ta fito, ganin motarshi ya tabbatar mata da cewa tabbas yana ciki, da sauri ta k'arasa ciki tana k'wala mishi kira, koda ta shiga baya falo hakan yasa ta wuce ciki da sauri, ta duba kicin baya ciki, ta shiga bedroom d'insa a nan ta hango shi kwance kan gado, kiran sunan shi Amira tayi tare da k'arasawa kanshi da sauri, tana fad'in " Amir d'ina me ya faru da kai ne, tana tab'a jikinshi taji wani irin zafi, tai saurin d'auke hannun tare da sakin salati. Nan fa ta rud'e cikin sauri ta tashi ta had'a mishi tea yasha kad'an sannan ta bashi magani yasha, bayan yasha magani sai ta d'auko ruwa da tawul ta shiga tsoma tawul d'innan cikin ruwa tana goga mishi a jiki duk dan saboda ta samu zazzab'in nan ya sauka, sai wajen goma saura minti goma sannan zazzab'in ya fara sauka sab'anin yanda tazo ta tarar da shi, kuma har ya samu bacci ya d'auke shi. Amira kuma ganin halin da yake ciki yasa sam hankalinta bai kwanta kan ta tafi ta barshi ba, hakan yasa ta yanke shawarar kwana anan, wannan shine karo na farko da Amira ta kwana a gidan Amir, tana zaune ta kwantar da kanta saman gadon a haka bacci ya d'auke ta ba tare da tasa komai a cikinta ba da daren. Tun asuba yunwa ta tayar da Amira daga bacci, ta tashi tai sallah tukun bayan ta idar ta shiga kicin ta had'a musu abun karyawa. Tana fitowa falo d'auke da abincin a dai-dai Amir ya fito daga cikin d'aki yana mik'a kamar ba shi bane jiya kwance cikin zazzab'i, suka kalli juna suka sakarwa junansu Murmushi, cikin sauri ta ajiye abincin kan tebur d'in dake tsakiyar falon tare da k'arasawa wajenshi da sauri tana fad'in " ya jikin naka, ina fatan kaji sauk'i, yanzu ina ne ke maka ciwo?" Amir yai murmushi sannan yace "to wanne zan fara amsawa a ciki Amira na, ki kwantar da hankalinki lafiya lau na tashi kuma yanzu ba inda ke ciwo a jikina." Amira ta saki numfashi tare da sakin doguwar ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah Allah na gode maka da ka baiwa mijina lafiya," Amir yai murmushi, suka zauna suka ci abinci sannan ta zuba mishi ruwa ya shiga wanka, kafin ya fito ta gyare ko ina. Tana cikin gyara mishi kayan taga wani agogon me kyau ya fad'o cikin kayan, d'ago agogon tayi tare da zaro idanu tace " me ya kawo agogon Sadeeq cikin kayan Amir, " bincike ta cigaba da yi can sai taga wani littafi shima na Sadeeq d'in ne duk kalaman soyayya ne a ciki, can kuma sai ta hango wani zobe na Sadeeq d'in, jikinta ne yai sanyi ta koma ta zauna k'asa dab'as tare da fara zubar da hawaye. Fitowar Amir kenan daga bayi ya tsinci Amira a cikin wannan halin, cikin sauri ya k'araso wajen ta yana tambayar ta meke faruwa, ganin abubuwan da ke gabanta ya sa ya tsaya turus tare da zaro idanu, domin shi be yi tunanin hannun Amira zai kai nan ba. Amira ta kalle shi cikin kuka tace " Amir kana so ka gasgata min zargin Insp Yahya kenan a kanka, kana nufin kai ne ka kashe Sadeeq kuma kayi sanadin mutuwar Abdul?" Amir ya yi shiru a halin yanzu baida abun cewa tunda shaidu sun fara bayyana a gareta. Amira tace "wannan agogon, na Sadeeq ne, ko ranar da muka rabu dashi daga filin wasa agogon na d'aure a hannunshi, haka ma wannan zoben yana yatsan shi, kuma ga littafin shi a wajenka wanda yake mallakin Sadeeq wanda ke cike da kalaman soyayya yana bayyanar da k'aunar shi gareni, nasan ka b'oye ne dan karna gani, to gashi yanzu na gani." Amir ya zame k'asa shima tare da fashewa da kuka me matuk'ar sauti, Amira ta sake kallon shi tace " Amir meyasa ka kashe shi, fad'a min? " Amir cikin kuka yace " saboda ke Amira, na dad'e da ganowa cewar Sadeeq yana k'aunar ki, haka ma Abdul, ranar da Sadeeq yace zai fad'a miki abinda ke zuciyarshi na tabbatar fad'a miki zaiyi yana k'aunar ki, hakan yasa na yanke shawarar d'aukar mataki a kansu duka harda Abdul." Amira kuka take yi kamar ranta zai fita shima haka Amir d'in, Amira tace " taya kayi ka kashe shi, Amir ashe zaka iya kashe rai a kaina, inko hakane k'aunar da kake yimin ta zama masifa, ka fad'amin taya akai ka kashe shi?" Amir ya d'auki kusan minti biyar yana kuka ba tare da ya sake cewa komai ba, itama kukan take yi d'akin ba abinda ke tashi sai sautin kukansu. Can Amir ya fara magana kamar haka: _a daren ranar da muka rabu dake na fara bin duk inda Sadeeq yasa k'afa, a daren kuma muka shirya zamu shiga club ni da Abdul da Sadeeq, bayan mun k'arasa muna zazzaune Sadeeq yana ta shahuwa domin akwai shi da son giya, mu kam bamu fara sha ba da Abdul da ni hira kawai muke d'an tab'awa, nan Sadeeq cikin maye ya fara bamu labarin irin k'aunar da yake wa Amira, sannan ya cigaba da cewa " gobe in Allah ya kaimu zan bayyana mata abinda ke raina," Abdul nan da nan fuskar shi ta canza ya tashi cikin sauri ya bar wajen nima na mik'e na bishi a baya, ina fitowa na tarar dashi tsaye a k'ofar shiga club d'in yana kai kawo, dafa shi na yi tare da kallon shi nace " Abdul ni nasan kana k'aunar Amira kuma ka rigashi nuna mata," Abdul yai saurin fad'in "eh wallahi, na riga shi, sai nace to ka kawar dashi mana kawai ka huta, da farko ya razana da jin haka, daga baya sai yai na'am da shawarata, muka shirya kan zai kashe shi cikin dare wajen k'arfe biyu, nan Abdul ya saki ranshi muka koma gun Sadeeq muka kamoshi muka shiga mota sai makaranta, na sauke su a bakin gate d'in makarantar Sadeeq ya wuce ciki yana tangad'i, na d'an tsayar da Abdul nace ya d'an bari yai nisa kar a gane tare suke, sai da naga Sadeeq ya d'an bada tazara sannan nace mishi ya tafi, haka suka shiga hostel d'in Sadeeq na gaba Abdul na baya, bayan naje gida na ajiye motata a gida sai nai b'adda kama na dawo makarantar hannuna sanye da safa, k'uguna rik'e da wuk'a na shiga d'akin Sadeeq a ankare ba tare da kowa ya ganni ba na kashe shi na bar wuk'ar anan, bayan na koma gida banyi bacci ba ina gadin lokaci, k'arfe biyu na dare nayi na kira Abdul bayan na b'oye lamba na sanar dashi lokaci yayi, shine fa yana zuwa ya tarar da gawar Sadeeq soke da wuk'a a jikinshi, cikin kid'ima da firgici Abdul ya cire wuk'ar daga cikin shi, tare da k'wala k'ara yana kuka yana tunanin waye ya kashe shi, wannan rik'e wuk'ar da yai da hannunshi ya cireta a cikin Sadeeq ita ta jawo aka ga tambarin yatsun shi, shine ya tashi da gudu ya bar d'akin ya koma nasu yana kuka tare da tunanin waye ya aikata wa Sadeeq haka, shine ya kirani ya fad'amin duk yanda ake ciki, nace ya kwantar da hankalin shi kuma ya dena jin tsoron saboda hakan zaisa a gane shine ya aikata kisan, kinji abinda ya faru."_ Amira da har yanzu kuka kawai take yi tace " haba Amir, meyasa zaka aikata abinda kasan hukuncinka kaima kisa ne?" Amir yace " a lokacin idanu na ya rufe Amira na zab'i in mutu a kanki da inga wani ya mallake ki ba ni ba, Amira kin sadaukar da komai naki a kaina tun ina k'arami domin canza min rayuwa tare da k'ok'arin ganin na samu farin ciki, banda kowa kuma ban rayu da kowa ba sai ke, kowa ya gujeni kece kad'ai kika karb'eni hannu biyu kuma kika bani zuciyarki da kyakkyawar kulawa, hakan yasa bazan iya jure rayuwa babu rayuwar da zuciya da idanu suka saba da ita tun a baya ba kece rayuwar da nake nufi Amira." Amira tace " to tunda nake tare dasu bantab'a jin son d'aya daga cikin su ba, kuma koda sun furta Kalmar so a gareni babu wanda zan iya amsa mawa inyi soyayya dashi a cikinsu," yanzu gashi nan ka jefa rayukanmu cikin had'ari don nasan yanda Insp Yahya ke bibiyarmu dole ya gano wani abu nan gaba, cikin kuka ta cigaba da fad'in " meyasa zaka aikata laifin da zai kashe masoya kamar mu masu burin gina kyakkyawar rayuwa," kuka take sosai, sannan can ta tashi ta d'auko dukkanin abubuwan nan ta k'ona agogo da zobe kuwa ta saka shi a cikin jaka tace tasan yanda zata yi dasu, ita yanzu Amir tausayi yake bata ya jefa rayuwarsa cikin hatsari duk sanadin soyayyarta, tun yana k'arami yake fama kanta amma ace har yanzu bai huta ba. 'Dagowa Amira tayi ta kalle shi sannan tace " bayan ni babu wanda ya san kaine ka kashe shi ko?" Amir yace " babu kowa da ya sani bayan ke," "sai kuma ni," abinda sukaji an fad'a kenan daga bakin k'ofa," cikin zaro idanu tare da mugun firgici suka juyo. Insp Yahya ne tsaye yana tafa hannayensa fuskarsa d'auke da murmushi, sannan yace " wannan ranar ce na dad'e ina zuwanta, yau Allah ya tona asirinka Amir, ya ciro bindiga ya saita Amir da ita tare da fad'in wuce muje." Amira cikin tsoro da firgici ta d'auki wani abu ta buga wa Insp Yahya ta baya ya saki k'ara ta k'wace bindigar kuma ta rik'e Insp Yahyan gam tana fad'in " Amir gudu." Amir ya juya da gudu zai fita ya tsere sai Insp Yahya yai kukan kura ya ture Amira tare da k'wace bindigar dake hannunta Insp Yahya yai sauri ya d'auka tare da saita Amir ya harbeshi a hannu, Amir da Amira lokaci d'aya suka saki k'ara a tare, da gudu Amira ta k'arasa gun Amir d'in wanda ke k'ara azaba tana kuka tana fad'in ya tashi su gudu, Insp Yahya ya k'araso wajen, ganin inuwarshi yasa Amira ta sake d'aukar wani abu dake kusa da su ta buga wa Insp Yahya akai, ba shiri ya fad'i k'asa a sume, hakan ya bata damar d'aga Amir ta rik'eshi suka fita daga gidan, suka shiga motar Amira suka d'auki hanya sunata tafiya k'ok'ari take taga ta kaishi asibitin da ke da nisa da cikin garin, hankalinta ya rabu gida biyu tana tuk'i tana yi tana kallon Amir da yake nishi sama sama na azabar harbin da yasha ga wasu hawaye masu zafi suna fitowa daga idanunshi, itama Amiran kuka take kamar me. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *AISHAN UMMA* ```Auntynah``` *Rashin ganinki sanadi na tunaninmu ya jefa zuciyarmu a cikin k'unci, sabo kenan, Aunty Aishan Umma munyi kewarki sosai wallahi,😰 ki dawo garemu da wuri kafin mu fara kokawa🙏😭* *AUNTY HUMYLUV ina kika b'oye ne??? nayi kewarki😰* *taimako abune mai kyau wanda duk ka yishi zaka tarar da amfaninshi nan gaba, ma'ana zai maka rana wata rana, dan haka mu zamto masu taimako akoda yaushe.* *REAL KHADY* ```(Princess)``` *tabbas ni mai laifi ce a gareki, kuma na amshi laifina ina rok'on yafiya da sassaucin hukunci🙏😰* PAGE 90 to 95 Amira tama rasa ina zata nufa da Amir, gudu kawai take yi a mota har ta fara fitowa daga cikin garin kano, har Allah ya kawota wani k'aramin gari a nan ta tambaya inda zasu sami asibiti ko kemis, aka raka su wani asibiti wanda aka k'i karb'ar Amir ganin harbi ne kuma ba d'an sanda kuma shi kanshi Amir d'in ya wahala. sai da k'yar suka amince suka karb'e shi, amma Doctor d'in da zai duba Amir ya kafe ya dage kan ba zai yi mishi komai ba sai taje ta taho da d'an sanda sannan zasu duba shi. Ba tare da b'ata lokaci ba aka raka Amira station tai musu bayani akan mijinta ne 'yan fashi ne suka shigar musu gida suka kwashe musu kud'i sannan suka harbi mijinta a hannu, shine akace sai tazo da d'an sanda. Babu b'ata lokaci aka had'ata da mutum d'aya cikin jami'an suka koma asibitin. Koda isar su taga yanda Amir d'inta ya k'ara galabaita gashi har yanzu basu tab'a shi ba. Amira ta haukace musu a asibitin tana kuka tana fad'in su yi k'ok'ari su ceto ranshi, zata basu ko nawa suke buk'ata, in kuwa ya mutu to sai ta k'arar da kowa dake cikin asibitin. 'Dan sandan da aka had'a su tare shine yake rarrashinta tare da bata baki, babu b'ata lokaci jami'in nan ya saka hannu aka fara duba Amir cikin gaggawa, aka cire bulet d'in tare da yi mishi duk wani taimakon da ya dace. Alhamdulillah Amir ya samu sauk'i, amma Amira sam bata so ma suka kwana a garin ba saboda hankalinta bai kwanta da wurin ba gani take kamar za'a zo a rabata da Amir d'inta. Bayan kwana biyu Amira ta matsa aka sallame su, Amira ce ke tuk'a motar a yayin da Amir ke zaune gefe kuma ta rasa ma ina zata nufa da su, har sun fara tafiya sai kuma ta faka motar tare da kallon Amir tace " yanzu Amir ina zamu je kaga shiga cikin gari be kama mu ba saboda duk muka shiga nasan a yanzu kuma a ko'ina neman mu ake yi." Amir wanda ke zubar da hawayen nadamar halin da ya jefa su a ciki, gashi wadda ya yi dominta yana neman rasata, lallai ya yarda so makaho ne, lokuta da yawa yakan makantar da kai ka aikata komai wanda koda zaka yi nadama ne daga baya sai kayi, Amir yace " Amira dan Allah kiyi hak'uri ki yafe min, bana yin nadamar duk abinda na aikata a kanki koda kuwa abinda nayi zaisa a rabani da raina ne, damuwata d'aya ne a yanzu na jefaki cikin damuwa da nayi, ni kuma duk duniya babu abinda na tsana wanda ya wuce shigarki wani hali balle kuma ace ta sanadina, ina rok'onki Amira muyi hak'uri mu yi nesa da juna har sai na fita daga cikin wannan halin saboda bana so kema ki shiga ciki." Kuka suke yi sosai kamar ransu zai fita, can sai Amira ta tsagaita da nata kukan sannan ta kalleshi tace " dan Allah Amir kukan nan ya isa haka ba shi bane mafita a garemu, hanyar da zamu ceci soyayyarmu daga rushewa ya kamata mu nema, Amir ban tab'a yin so ba sai a kanka, kuma gaskiya ban shirya rabuwa dakai ba, so nake mu rayu tare ya zama mutuwa ce kad'ai zata rabamu, itama da da hali zanso mu mutu a tare, saboda haka kama daina zancen yin nesa da juna kasan ni da kai duk bazamu iya jure faruwar hakan ba, in har kana k'aunata kuma da gaske baka son rabuwarmu to ka zuba min idanu kan dukkanin wani hukunci da zan yanke." Amir ya share hawayen shi, sannan yace "Amira gaba d'ayan rayuwata tana gurinki, na gwammace ace na mutu na barki da ace yau ina raye amma na rasaki," Amira ta katse shi cikin sauri tare da fad'in " Amir nima a wannan duniyar muddin babu kai tabbas bak'in cikin rashinka zaisa in bar cikinta, nasha fad'a maka cewa banda rayuwa a cikin rayuwar da babu kai, da kai na saba taya rabuwa zata zama abu mafi sauk'i a garemu, kama bar wannan maganar tana d'aga hankalina, insha Allah zamu rayu tare muyi aure mu haihu, kuma in Allah ya yarda mu mutu a tare." Amir ya numfasa, sannan yace " to yanzu ya zamu yi, ina zamu nufa?" Amira tace nima shine abinda nake ta tunani cikin raina, inda zamu je mu kaucewa Yahya daga neman da nasan yana yi mana a yanzu haka," dogon numfashi ta ja, sannan kuma kowanne daga cikinsu yai shiru yana tunanin mafita. Can Amira ta d'ago cikin sauri tare da fad'in " na tuno inda zamuje ba tare da kowa ya ganmu ba, amma dole sedai mu hak'ura da makaranta in kuma zamu fita to dole sedai mu rufe fuskarmu yanda ba wanda zai gane mu, ina ganin kawai mu tafi gidan marayun nan mu zauna na wasu lokuta kafin mu san abun yi a gaba." Amir yace " sam komawarmu cikin gari a yanzu be kamata ba kamar mun kai musu kanmu ne, sedai mu nemi wata mafitar, suna cikin wannan shawarar ne suka hango motar su Insp Yahya suna nuna hotunansu suna tambayar inda suke, kuma ganinsu tare da d'an sandan da ya raka Amira aka duba Amir a asibiti ya k'ara tayar da hankalinsu matuk'a, ko kafin suyi wani yunk'uri 'yan sandan nan sun hango su, domin Insp Yahya ya haddace lambar motar Amir da Amira duka a kanshi. Cikin sauri Amir yace wa Amira ta dawo mazauninshi suka yi canje yaja motar cikin k'warewa Amir ke tuk'a motar a yayin da Insp Yahya da tawagar shi suke biye dasu suma da gudu, haka sukaita tsere kan ti-ti k'ok'arin 'yan sandan nan kawai suga sun sha gaban su, a yayin da shi kuma Amir ya dage kawai k'arawa motar gudu yake yi yak'i bari su shiga gaban su. A haka har su Amir suka fara yi musu nisa, cikin hukuncin Allah kuma suka b'ace musu, Insp Yahya ya daki kan sitiyarin motar yace " shettttt sun gudu," dole suka juya kan motar su domin kuwa hanyar ta kasu har uku ko kafin su k'araso sun b'ace a wajen shiyasa basu san wacce ce hanyar da su Amir d'in suka bi ba. Su Amir kuwa duk da sunyi nisa sun ma fita daga kano gaba d'aya sun shigo zaria amma ya kasa tsayawa da motar gudu kawai yake yi, har Allah ya kawo su wani k'auye da ake kira Damari, anan suka yada zango a galabaice, suka fito daga motar a dai-dai wani bawan Allah ya biyo hanya yana sab'e da fatanya zai tafi gida, ga dukkan alamu daga gona ya fito. Amir ya kalleshi yace "sannu Baba ina wuni," dattijon nan ya tsaya tare da amsa gaisuwar su, Amir ya cigaba da cewa " Baba taimako muke nema daga gareka dan Allah, dattijon nan yace " to yaro Allah yasa wanda zan iya ne." _ayi hakuri da wannan wayar huk take idan nai typing me yawa a bini bashin gobe insha Allah._🙏 Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* (Autar marubuta) SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* (Mamie) *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 *AUNTYNAH AISHAN UMMA tana gaishe da kowa da kowa, kuma tace tayi kewar dukkanin masoyanta, tace mu kwantar da hankalinmu tana nan cikin k'oshin lafiya, wayarta ce ta sami matsala amma kwanan nan zata sake wata, tana nan tafe nan bada dad'ewa ba insha Allah, mun gode Allah da jin kina nan lafiya AUNTYNAH😍* *Ina baiwa MASOYANA hak'urin jina shiru na kwana biyu, mun d'an sha shagalin bikin sister na ne, sannan ranar Alhamis nayi typing nai mistake d'in number, a maimakon insa 95 to 100 sai nasa 90 to 95, dan haka zan gyara lambobin in turo su a tare saboda sam bana so masoyana su shiga rud'u, wallahi ina alfahari daku da yawanku masoyana, da bazarku nake taka rawa.*💃😉 *MOMYN KHADEEJA🧕*🗣🗣🗣🗣 *ungo taki gaisuwar ta musamman🙏🙏🙏🙏🙏 sannan Amir da Amira suna gaishe ki sosai sunce suna mugu mugun yinki, Allah ya bar k'auna da zumunci🤝😍.* PAGE 95 to 100 Dattijon nan ya kalli Amir yace ‘’to yaro ina jinka Allah yasa zan iya, wane irin taimako kake nema daga gareni? ‘’ Amir yace ‘’mu bak'i ne a garin nan, dan Allah ka taimaka mana da masauki.‘’ Dattijon nan yai shiru can sai ya numfasa, kafin yai magana Amir ya sake cewa ‘’dan Allah Baba ka taimaka mana mu ba masu cutarwa bane nasan tunanin da kake yi kenan a zuciyarka, wallahi ba zamu cutar daku ba, ka taimake mu domin girman Allah zaka ji dukkanin labarin mu daga baya.‘’ Baba yace ‘’to shikenan yaro ku biyo ni muje,‘’ Shi dai Baba ya yi shahada ne ya tafi dasu ba don hankalin shi ya kwanta da bayanan da suka yi mishi ba, haka suka tafi Baba yana gaba suna binshi a baya har cikin k'auyen, suka tsaya a bakin wani k'aramin gida irin gidajen k'auyen nan amma k'aramin gida ne sosai. Kai tsaye Baba ya basu izini suka shiga gaba d'ayan su, matar shi ta amsa tare da fitowa daga d'aki tace ‘’sannu da zuwa mai gida, tare da bak'i kake tafe ne sannunku da zuwa,‘’ ta shiga cikin d'aki ta fito da k'atuwar tabarma ta shimfid'a sannan suka zazzauna. Bayan sun gaggaisa sannan mai gidan wanda su Amir suka kira da Baba ya kalli matar shi yace ‘’wad'annan bayin Allahn bak'inmu ne, a hanya na had'u da su suka nemi taimakon masauki a wajena na wasu kwanaki, tunda wancan d'akin da A'i tai aure ba kowa a cikinsa to a gyara musu su sauka a ciki.‘’ Wannan dattijuwar matar da Baba ke mata dukkanin wad'annan bayanin sai ta sake kallon su Amir cikin fara'a ta sake musu sannu da zuwa, ta mik'e da nufin zuwa ta gyara d'akin, sai Amir ya dakatar da ita ta hanyar fad'in ‘’ dan Allah Umma ki bar gyaran d'akin zamu gyara, ai mun gode ma da kuka bamu masauki Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya biyaku da gidan aljanna firdausi.‘’ Duk yanda su Amir suka so su hana Umma gyara d'akin tak'i bari, a cewarta ai su bak'in su ne be dace ace yau daga zuwansu ta barsu sunyi aiki ba, dolen su suka hak'ura suka k'yaleta, bayan ta gama gyarawa ta yi musu izinin shiga, suka shiga suka zauna aka kawo musu abinci da ruwa. Suka ci abincin suka sha ruwan sannan suka ci gaba da kallon d'akin suna tunanin yanda zasu kwana a cikinsa, tabarmi ne guda biyu a cikin d'akin aka had'e su waje guda, sai wata tsohuwar gana mas go, Amir yace ‘’kiyi hak'uri Amira ni na jawo miki kwana irin wajen nan, gobe in Allah ya kaimu zamu san yanda zamu yi mu sami 'yar k'aramar katifa mu sa a d'akin kafin mu tafi.‘’ Amira ta kalle shi tace ‘’ a'a in dai don saboda ni ne to karka damu, ina ma muka ga kud'i mu da muka fito ko shiri babu, ka kwantar da hankalinka zan iya zama a ko ina ne muddin ina tare da kai, amma d'azu a hanya naji ka cewa Baba zaka bashi labarin mu, to kar ba shiba ma karka tab'a fad'awa wani abinda ya faru har abada, ko da ka tashi baiwa Baba labarin kawai kace musu mu miji da mata ne, kan hanyar mu ta zuwa garinmu akai mana fashi shiyasa muka sauka a wannan k'auyen.‘’ Amir ya kalleta yace ‘’to shikenan Amira ta, yanda kika ce haka za'ai.‘’ Da dare yayi suka ja tabarmin suka raba su shi Amir yana farkon d'akin, ita kuma Amira tana can ciki, sedai sam sun kasa bacci, daga k'arshe ma hirarsu suka sha, sannan suka yo Alwala suka yi nafila da addu'o'in neman mafita wajen Allah mahalicci, sai da asuba sannan suka kwanta amma sam bacci yak'i ziyartar su. Washe gari Amir da Amira suka tashi suka je d'akin su Umma suka ci sa'a Baba yana nan, bayan sun gaisa sai Baba ya kalle su yace ‘’ya kamata ku sanar da mu sunanku da labarin ku da kuma abinda ya kawo ku wannan k'auye namu.‘’ Amir ya gyara zama sannan yace ‘’sunana Amir, wannan kuma ya nuna Amira matata ce sunanta Amira,‘’ nan fa ya kwashe duk yanda Amira ta zayyana musu ya fad'a musu, sun tayasu jimami tare da yi musu Allah kyauta gaba, nan shima Baba ya basu labarinsa a tak'aice ya fad'a musu yana da yara har hud'u dukkansu mata, kuma dukkansu an yi musu aure, kasancewar auren k'auye daban da na cikin birni, sun dad'e suna hira kafin daga k'arshe Baba ya tashi zai tafi gona Amir ma yace zai bishi suka tafi tare, a ranar tare suka yi aikin gonar domin Amir ya dage lallai sai ya yi, haka itama Umma da Amira tare suka yi dukkanin aikin gidan. Bayan kwana biyu Amir da Amira suka murmure suka saki jikinsu tare da sabawa da komai na k'auyen daga kan cimarsu har zuwa suturun da suke sakawa kasancewar su Amira dama ba kaya suka shigo k'auyen daga su sai na jikin su. Kuma daga lokacin da suka shigo k'auyen basu k'ara barin iyayen gidan su sunyi wani aiki ba, Amir shi yake wa Baba duk wani aiki na gonarsa, itama Amira ita take duk aikace aikacen cikin gida, sun hutar da wad'annan dattijan daga yin kowane irin aiki, to dama shi Amir ya riga da ya saba da wahalar rayuwa tun yarintar shi, Amira ce ma kafin ta saba ta sha wahala sosai saboda rashin sabo ta riga da ta saba komai se dai ai mata, d'an aikin da take wa kanta be taka kara ya karya ba. .................... Insp Yahya ne zaune a office yana waya, be wani d'auki lokaci me tsaho ba ya gama wayar, d'agowa yayi ya kalli d'an sandan da ke k'ame a gaban shi yace ‘’ya ake ciki, an samu nasara kan abinda na turaka bincike akai?‘’ 'Dan sandan da ke tsaye gaban Insp Yahya yace ‘’yes sir na samo bayanai gasu nan a cikin wannan takardar, mahaifin ita Amira shine shugaban k'asar nan ma a yanzu, kuma har lambarsa ma duk na samo, shi kuwa Amir bamu samu wani cikakken bayani a kanshi ba, sedai labari da muka samu ya tab'a rayuwa a kusa da gidan su Amira amma ba wani labari kan iyayensa,‘’ ya 'karashe maganarsa tare da mi'ka mishi takardar bayanin dukkanin abubuwan da ya fad'a mishi. Insp Yahya ya karb'i takardar nan ya duba sannan ya d'ago fuskar sa d'auke da murmushi, yace ‘’da kyau mutumina kayi aiki me kyau, zan kira mahaifin Amira in sanar dashi duk abinda ke faruwa, kaga shi zai taimaka mana sosai wajen kama Amir cikin sau'ki, kuma dole mahaifin Amira shima ya d'auki mataki akan Amir in yaji 'yar shi bata makaranta tana tare da wani 'kato 'katon ma makashi, zaka iya tafiya kayi aiki me kyau na jinjina maka.‘’ Bayan d'an sandan nan ya yi godiya ya sara sannan ya fice, Insp Yahya ya d'auko wayarsa ya shigar da lambar mahaifin Amira cikin waya sannan ya rangad'a kira. Dad da ke zaune cikin iyalen shi suna hira yaji wayarsa ta fara 'kara alamun ana kiransa, bayan ya d'aga tare da sallama, Insp ya amsa cikin girmamawa bayan sun gaisa sannan yace ‘’dama na kira ne in sanar da kai abinda ke faruwa da halin da 'yarka take ciki, wani yaro ne Amir yai kisa,‘’ mahaifin Amira cikin sauri tare da 'kosawa ya mi'ke cikin sauri tare da katse shi ta hanyar fad'in ‘’to miye had'in kisan shi da lamarin yarinyata? Insp Yahya yace saboda saurayin Amira ne, kuma tunda aka gano shi yai kisan anzo kamashi suka gudu tare shi da Amiran har yanzu bamu gano inda suke ba, shine na kira domin in sanar da kai halin da ake cik....... kafin ya 'karasa maganarsa Dad ya katse shi cikin tsawa yana fad'in karka 'kara had'a 'yata da makashi in ba haka ba zan hukunta ka wallahi, Insp Yahya yace ‘’ka yi ha'kuri amma in baka yarda ba kayi bincike akai,‘’ Dad be tsaya cigaba da sauraren sa ba ya katse wayarshi, lambar kwamishina dake kano ya fara kira bayan sun gaisa ya tambayeshi waye Insp Yahya, kwamishina ya fad'a mishi cewa jami'i ne 'kwararre kuma me sanin makamar aiki, sai Dad ya bashi umurni akan yana so aje makarantar da Amira ke ciki a bincika mishi Amira tana nan ko bata nan, kuma a binciko mishi waye Amir kuma yanzu yake so, Kwamishina ya amsa suka yi sallama nan da nan ya tashi da kanshi tare da yara suka tafi makarantar, shi kuwa Dad banda kai kawo a tsakiyar d'akin ba abinda yake yi, su kuwa k'aninshi da matarshi da sauran 'yan gidan binshi kawai suke da kallo domin jin wayar da yake sun san tabbas maganar ta shafi 'yar su Amira, suna so suji 'karin bayani amma kowa shakkar yiwa Dad magana yake ganin halin da yake ciki, dama muddin ya shiga irin wannan yanayin to tabbas babu me iya tanka mishi saboda gudun abinda zai biyo baya. _Hmmm tab' da sauran rina a kaba, Amir ka lallab'a ka tsere tun kafin Dad ya gano kaine._ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* (Autar marubuta) SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* (Mamie) *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) *MASOYANA NA NESA DA NA KUSA BANDA ABINDA ZAN SAKA MUKU DASHI KAN K'AUNAR DA KUKE GWADA MIN, SE DAI IN ROK'I MAHALICCINA ALLAH YA BIYAKU DA KYAKKYAWA KUMA YA K'ARA MUKU SONA😍😍😍😘💋* *Tabbas komai yai farko zai yi 'karshe, RAHEENAT M. ABBAKAR ina tayaki murnar kammala Novel d'inki mai suna 🌲HALIN RAYUWA,🌲 Allah ya bamu ikon amfana da tarin darussan dake cikinsa, ya bamu ikon watsi da kura kuren cikinsa, abinda kikai dai-dai Allah ya baki ladan, kuskuren dake ciki kuwa Allah ya yafe miki, Allah ya 'kara miki basira, d'aukaka, da d'an karen za'kin hannu, sai mun jiki cikin sabon novel d'inki.😍😘💋* PAGE 100 to 105 Bayan d'an wani lokaci sai ga kiran kwamishina cikin sauri Dad ya d'aga yace ‘’ya ake ciki tana nan kuma kun ganta da idanunku?‘’ kwamishina yace ‘’gaskiya bata cikin makarantar nan domin ta ma dad'e bata shigowa ciki, ance tana tare da wani yaro wai saurayinta ne, se dai ba'a san inda suke ba.‘’ Dad yace ‘’ku baza yaranku a fita neman su nan ma zansa a bincike su, duk yanda ake ciki zamu yi waya,‘’ suna gama waya Dad ya sake kiran shugaban 'yan sanda na nan Abuja yai mishi bayanin komai tare da bashi umurnin a bincika ko ina duk wanda aka gani cikinsu a kamo shi a kawo su gareshi, bayan ya gama wayar yaita gwada ta Amira amma sam tak'i shiga, wurgi ya yi da wayar kan tiles d'in falon ai kuwa ta tararratse, yana fad'in ‘’ta kashe wayarta balle insa a gano inda take, wallahi na kama Amira sai ta raina kanta, sai na ajiye tsananin k'aunar da nake yi mata a raina na hukuntata dai-dai da abinda ta aikata a gareni, na saki jiki tana karatu ashe ta maida mu wawaye tana can tabi d'an iska, haka yaita surutu shi kad'ai cikin tsantsar b'acin rai idanunshi sunyi mugun ja saboda b'acin rai, ya kalli 'kaninshi ya cigaba da fad'in Amira na so ta zubar mana da mutuncin gida, wai ta rasa wanda zata so sai makashi mai yin kisa kuma har ta bishi su gudu, ita da na tura tai karatu itace da bin d'an iska makashin mutane har rayuka biyu, to wallahi idona idon saurayin nan nata koh, wallahi sai na b'atar dashi, sai na wulak'anta rayuwarshi kamar yanda ya hure wa 'yata kunne, ita kuma koh hmmmm,‘’ ya juya cikin tsananin fushi ya shiga d'akin shi. Ko'ina an baza yara neman su Amir amma sam ba labarinsu, hakan ya k'ara wa Dad shiga cikin damuwa, kuma kullum cikin gwada lambar wayar Amira yake yi ko Allah zai sa a dace wata rana a samu, a haka har aka kai wajen wata d'aya ana bincike amma sam babu su ba labarin su, hakan yasa Dad yasa aka turo mishi Insp Yahya har gida domin yai ganawa ta musamman da shi. ……………………… …………………… Bangaren su Amira da Amir kuwa hankalinsu kwance yake a k'auyen nan ba abinda ke damun su, soyayyar su kuwa kullum dad'a nunkuwa take, kullum suka gama taya iyayen gidan su aiki zama suke cikin gida ko a waje jikin bishiya suita hirar su, abu d'aya ne kad'ai ya fara damun Amira, yanda ta lura da 'yan matan k'auyen ke nuna soyayyar su a kan Amir, har cincirindo wasu suke yi kawai dan su ganshi. Yau ma zaune suke a waje da yamma suna hirar su me dad'i, Amira ta kalli Amir tace " son da nake maka abu ne me matu'kar muhimmanci a rayuwata, rasaka kuma tamkar rasa rayuwata ne, shin kana jin shau'kin son da nake maka kuwa Amir d'ina, tunda nake ban tab'a son wani d'a namiji ba sai kai, kuma zuciyata ba zata tab'a d'aukar wani ba bayan kai." Amir ya ce "Amira ki kwantar da hankalinki ni naki ne har abada haka kema tawa ce har k'arshen numfashi, gamu kuma a tare muna rayuwa waje d'aya, kawai addu'a zamui ta yi Allah ya bamu ikon mallakar juna matsayin ma'aurata." Amira tayi murmushi sannan ta amsa da "ameen. " To da yake 'kauyen da suke ciki suna dad'ewa kafin su samu wuta shiyasa wayoyinsu kwata kwata babu caji, suna,cikin wannan hirar cikin ikon Allah sai ga wuta an kawo gaba d'aya 'kauyen ya kaure da 'kara kasancewar sun dad' basu ga k'yallowarta ba, hakan yasa su Amir ma suka katse hirar da suke yi suka shiga ciki domin su saka caji. Suna saka caji Amira ta kunna ta-ta wayar, tana kunnawa ta koma kusa da Amir ta zauna suka ci gaba da hira, sedai bata dad'e da zama ba wayarta ta fara ringing, tashi ta yi domin zuwa ta duba taga ko waye ya kira ta, Dad d'inta ne ke kira, cikin sauri ta d'aga tare da karawa a kunne se dai ta kasa cewa komai, ji tayi yace " My Daughter karki damu nasan duk abinda ke faruwa, saboda haka ki kwantar da hankalinki yanzu kina ina ne?" Amira cikin murna da farin cikin mahaifinta be d'auki zafi ba kan lamarin tace "Dad muna…………" Amir ne yai saurin karb'e wayar daga hannunta tare da kashewa gaba d'aya. Amira ta kalle shi tace " Amir Dad d'ina ne fa," Amir yace "haba Amira so kike azo a kama mu, ko kin dena sona ne yanzu kin amince a kasheni?" Amira tace "no babu wannan ranar har abada, kawai dai tunani nayi akan b'oyon da muke ta yi sam bashi da amfani," Amir yace "amma Amira ki gane mana kuma kiyi tunani kinsan Dad yana da zafi sosai in har ba abinda suka shirya a kanmu be kamata ace yai saurin saukowa ba haka har yana neman inda muke, kuma be yi miki fad'a ba fa sai tambaya da yake yi wai kina ina, in kika fad' inda muke Amira kama ni za'ai kuma nasan daga ranar ba zamu sake ganin juna ba dan kasheni zasu yi." Amira tace " Amir ka kwantar da hankalinka, Dad yana 'kaunata sosai, kuma na tabbatar 'kaunar da yake min zaisa ya amince in auri wanda nake so, ka kwantar da hankalinka a yanayin da na jishi ba zai bamu matsala ba insha Allah." Amir kam ba don ya gamsu da bayananta ba ya amince dasu, domin shi ya tabbatar suna zuwa zasu raba su, amma saboda baya so ya cigaba da jayayya da ita a kan magana da mahaifinta sai ya amince da abinda tace tare da mi'ka mata wayar ya koma inda yake zaune da ya zauna tare da zuba mata idanu. Amira ta karb'i wayar ta kunna, tana 'ko'karin kiran Dadyn sai ga kiransa ya sake shigowa, Amira ta d'aga sannan cikin sanyin murya wadda take bayyanar da aji tausayin mutum tace "Dad muna magana d'azu ta yanke," Dad yace ba damuwa fad'a min kuna ina ne gobe zan turo a d'auke ku?" Amira tace " muna zaria cikin 'kauyen…………" da yake wayar da suke yi ba caji tayi ba suka sake d'auke wutar su, Amira tace " wayyo Allah Amir sun sake d'aukewa kuma, ko taka ta yi caji ka d'an ara min in kira Dad?" Amir wanda yai mugun jin dad'in d'aukewar wutar yace " ai ni tawa wayar ma ta'ki kawowa kwata kwata, 'kila saboda dad'ewar da tayi ba caji ne." Amira tace " to Allah sa su dawo da ita, sai yanzu hankalina ya fara kwanciya nake jin k'arfin guiwar yiwuwar aurenmu da kai Amir," Amir yai murmushi sannan yace " Allah ya tabbatar mana da alkhairi," Amira tace " Ameen, amma ya naga yanayinka ya canza?" Amir yace "ka jita, to na canza da me, bakomai fa," nan dai suka ci gaba da hira har lokacin sallar magrib ya yi, suka tashi suka fita tsakar gida domin yin alwala su gabatar da sallar su. Da dare Amira ta kasa bacci zuciyarta na nazarin maganar Amir, har Amir yai bacci ma amma ita idanunta biyu, tunani take yi itama yanda mahaifint ke 'kaunar karatun ta yaji bata makaranta kuma yai saurin saukowa haka, lallai akwai wata a k'asa, ta sake tuno abinda aka yi mata kan Amir tun suna 'kanana, hakan yasa tai amanna da zancen Amir cikin zuciyarta. *BAYAN KWANA BIYU* Dad ne zaune shi da Insp Yahya a d'aki na musamman suna tattaunawa kan maganar su Amira, bayan sun gama magana Dad ya bashi lambar Amir da Amira tare da bada umurnin suita kira duk ranar da suka yi sa'a suka samu lambar d'aya daga ciki to kawai suyi 'ko'karin binciko inda suke. Insp Yahya yace " ai yanzu da wuya su d'aga kowace lamba musamman lambar da babu suna, ni a tunanina kamata yai a cikin wad'anda suke shiri kuma suke waya cikin d'alibai mu samu d'aya daga cikin su a sashi yaita kira har a samu su d'aga koda mutum uku ne dole za'a samu mutum d'aya a cikinsu wanda zasu d'aga wayar shi." Dad yace " lallai na yarda da maganar da kwamishina ya yi a kanka, kaje ka aiwatar da duk abinda ya kamata daga yau, da zarar kun samu wayar ta shiga kafin ku binciko inda suke ku sanar dani a gabana nake so a kama su domin inga mai k'arfin halin iya d'auke min 'ya." Nan dai suka yi sallama Dad ya bashi ma'kudan kud'i, Insp Yahya ya fito ya tafi. Yau Alhamis, 'karfe takwas dai-dai na safe Amir da Amira suna zaune cikin d'aki, gama karyawarsu kenan, sun fitar da kayan abincin Amira ta wanke ta dawo suka zauna suna hira, suna cikin hirar ne aka kawo wuta, suka sa caji sannan suka tashi suka tafi d'ebo ruwa. kasancewar sun tarar da layi yasa suka dad'e a wajen sai da suka yi wajen kusan awa guda sannan layi yazo kansu suka d'iba suka juyo zuwa gida, se dai suna shawo kwanar gidan suka hango su Umma a 'kofar gida, cikin sauri suka k'araso wajen su suna tambayar su me suke yi a tsaye a 'kofar gida, Umma cikin farin ciki tace " albishirinku yarana bayan fitarku aka kira wayar Amira naji k'aran ya'ki 'karewa nazo naita daddangwalawa sai in na kara kuma inji shiru ban sani ba ko kashewa nai ko d'auka har Allah ya bani sa'a aka jini sai na fad'a musu bakwa nan kun fita, sai suka fad'amin cewa kun b'ace ne suna nemanku, , ina jin haka na gane 'yan uwanku ne, shiyasa nai musu kwatancen nan suka taho, a ta'kaice dai yau Allah ya kawo iyayenku." Amira ta d'ora hannaye a kai tare da runtuma kuka tana fad'in shikenan mun shiga uku," Amir yace " Amira tunda sun gane inda muke zo mu gudu tun kafin su zo su iskemu anan," Baba da Umma suna ta fad'in me yafaru meyasa bakwa farin ciki, ina sam basu sauraresu ba Amir ya kama hannun Amira ya jata zasu gudu amma se dai sun makaro, suna juyowa suka ga Dad da rundunar sojoji da 'yan sanda kewaye dasu kamar wad'anda zasu tafi ya'kar miliyoyin mutane. Dukkanin su sun saita su da bindiga, Amira kuwa cikin sauri da tsoro ta tsaya gaban Amir tare da kareshi kar a harbeshi, Dad kuwa cikin tsananin b'acin rai yake kallon Amir, cikin d'aga murya kuma ya bada umurni kamar haka "ai mishi shegen dukan da zai kasa tashi tun a nan kafin mu tafi dasu." _wayyo ina cikin firgicin ganin za'a raba masoya ta k'arfi da yaji shiyasa kuka yaci k'arfina baran iya cigaba da typing ba,😭 kunji dai gaskiya na gaji da typing ne yasin😂 sai kuma gobe😜_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* (Autar marubuta) SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* (Mamie) *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛 *DARLING INSPECTOR YACE A FAD'AWA 'YAN TEAM D'IN AMIR YANA GAMAWA DASHI TO KANKU ZAI DAWO DUK SAI YA GARK'AME KU D'AYA BAYAN D'AYA, INA TAUSAYA MUKU KUKA SHIGO HANNUN DARLING INSP KAFI 'KARFIN MUGU BA SASSAUCI😂😂😂😂😂 SAURA SU O'O ACE NI BK NICE NA FAD'A MISHI😏😏* *SA'KO ZUWA GA MASOYANA💌* *Amincin Allah su tabbata ga masoyana ma'abota aminci,🙏😊 wasu daga cikin masoya sun kirani wasu sun yo min test message wasu sun tambayeni ta watsapp wai sun sami labari ni 🅱K nima na maida littafina na kud'i, ma'ana sai an biya kud'i zan tura wai shiyasa na daina typing kwana biyu, wasu kuma rok'ona suke yi dan Allah kar nima ince zan maida novel d'ina na kud'i, to maganar gaskiya bansan da wannan zancen ba, hasali ma rashin lafiya nake shiyasa kuka jini shiru kwana biyu, duk wainar da ake toyawa bansan da ita ba sai da sak'onnin masoyana ya iso gareni, to masoyana ku kwantar da hankalin ku novels d'ina duka kyauta ne babu kud'in da zansa akai ince ku biyani, abu d'aya nakeso kuyi ku biyani dashi shine dan Allah kar ku manta dani cikin addu'arku a yanzu da nake a raye da kuma bayan na mutu, addu'arku gareni itace zata tabbatar min da cewa kuna k'aunata k'auna ta gaskiya, Allah ya barmu tare, wallahi na matuk'ar jin dad'in k'aunar da kuke gwada min yanda kuka nuna damuwarku kan lamurana da kuma abinda ya shafi novel d'ina, kamar yanda nake jin farin ciki mara misaltuwa a duk lokacin da naci karo da masoyana ko kuma nai magana dasu kai tsaye* *NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!!* PAGE 105 to 110 Insp Yahya shi da wasu murd'a murd'an 'yan sanda suka yo kan Amir, Amira ta tsaya gaban Amir tare da 'kan'kame shi tana girgiza kai tare da kallon bataliyar 'yan sandan da suka yo kansu domin jibgar mutum d'aya tak, tace "karku sake ku tab'ashi ba shi bane yai kisan fa Dad ni na kashe shi da hannuna," Amir da ke shirin yin magana ta ri'ke hannun shi sannan cikin rad'a tace " kar kace komai Amir muddin kana son mu cigaba da rayuwa a tare." Dad da kanshi ya tako har inda Amira take ya sharara mata kyakkyawan mari jin abinda take fad'a, sannan ya kama hannunta ya jata har cikin mota ya sakata ciki sannan ya rufo ya dawo ya bada umurnin aiwa Amir wanda ke ta faman kwad'a wa Amira kira yana kuka tunda aka b'anb'areta daga jikin shi duka, Insp Yahya shine kan gaba, kafin ya fara dukansa ma bayan sun k'araso gabansa sai da ya kalli Amir yai mishi wata irin dariyar da ke d'auke da ma'anar yau gaka a hannu na me 'kwatarka sai Allah, haka sukaita dukansa ba ji ba gani kuma Insp Yahya yafi kowa jibgar Amir. Nan fa suka rufar mishi da duka ta ko'ina tun yana iya yin 'kara har muryarsa ta disashe kuma duk da haka Dad be bada umurnin a daina dukansa ba, Amira ce ta fito daga mota da gudu Allah ya bata sa'a ta warce wata bindiga dake hannun wani d'an sanda cikin sauri kuma ta saita kanta da bindigar tare da fad'awa kan Amir tana saite da bindigar, Dad ne ya k'wala mata kira da k'arfi, Amira tana kuka tace "wallahi Dad nice na kashe shi, Amir ya yi hakan ne kawai domin ya kub'utar dani daga fad'awa hannun 'yan sanda, sannan yai haka ne saboda soyayyar da yake min shiyasa ya d'ora laifin kansa, Dad kama kuwa gane wanda ke tare da 'yarka har yanzu? to yaron nan ne dai da ka rabamu tun muna 'kanana, zuwa yanzu ya kamata ace ka gane cewa had'uwarmu daga Allah ne, kuma duk abinda Allah yaso faruwarsa babu mai iya canza shi ko wanene, Dad kasan tun ina yarinya ban saba yi maka 'karya ba ko laifi nayi na gwammace in fad'i gaskiya ka hukunta ni, to yanzu ma gaskiyar zan sake fad'a maka duk duniya babu wanda nake so nake 'kauna sai Amir kuma babu wanda zan iya aura in ba shi ba, dan Allah Dad ina ro'konka ka 'kyalemu mu tafi, in kuma ba haka ba zaka rasani na gwammace mutuwa da inga ranar da zaku rabani da Amir domin Amir shine *MAHA'DIN RAYUWATA* " har ta gama magana tana saite da bindigar bata sauke ba, kuma bata daina magiya ba, shima Amir kuka yake suna ri'ke da juna gam kamar wad'anda za'a raba, af ashe fa rabasun za'ai ko😰 jin abinda Amira ta fad'i babu abinda ya 'karawa Dad banda tsananin tsanar Amir, dama shine yaron da sanadin shi ne ya dawo da karatun Amira kacokam garin kano amma duk da haka saida ya biyota nan d'in ma, zuciyar shi fad'i take ashe d'an iskan nan shi ya ruguza min mafarkina a kan Amira, ji ya yi tsanar Amir ta dad'a nunkuwa, cikin fushi yace " ku cigaba da dukansa har sai nace ku daina," Amira ta sake kare shi tare da saita bindigar a kanta tace " wallahi Dad duk suka 'kara dukan Amir sai na kashe kaina da wannan bindigar," Dad ya dakatar da su cikin sauri domin yasan tabbas abinda Amira ta fad'i zata iya aikatawa, tunani ya yi kan dole sai an biyo musu ta siyasa kafin su sami damar tafiya da su. Umma da Baba kuwa babu abinda suke yi banda kuka, duk da basu san meke faruwa ba amma sun tausayawa yaran dan jinsu suke yi kamar yaran da suka haifa a cikin su. Dad ya kalli Amira yace " yanzu me kike so ayi?" Amira tace " so nake ka yi ha'kuri Dad ka barmu mu tafi," Dad ya kalleta yace " a'a bazai yiwu ba in barku ku tafi Daughter, kece 'ya d'aya tilo a wajena, kuma kinsan tunda nemanku ake a ko'ina koda kun tafi k'ara kamaku za'ai a wani wajen, kinga kuwa tafiyarku sam bata da amfani muddin ba'a kashe case d'in ba, yanzu abinda za'ai shine ki bari muje station a kashe magana kuma ku saka hannu tukun," sai a lokacin hankalin su ya d'an kwanta, amma ganin irin kallon da Dad ke wa Amir yasa jikin Amir d'in yai sanyi kuma zuciyarshi na kokwanto kan zancen da yai musu. Anyi - Anyi da Amira ta ajiye bindigar hannunta amma ta'ki ajiyewa, tama 'ki yarda a matso kusa da ita balle su 'kwace, dole a haka suka d'auki hanya sai station, ko da isarsu suka tarar da rundunar 'yan sanda da sojoji suna jiran zuwan su, nan jikin su Amir da Amira ya 'kara yin sanyi sosai. keb'ewa Dad yayi shi da kwamishina suka d'an yi wata magana kawai sai gani suka yi an kama Amir an jefa shi cikin cell, ita kuma Amira aka mamayeta aka 'kwace bindigar dake hannunta aka jata zuwa bakin mota, tana ihu tana tirjiya tana 'kwala wa Amir kira amma duk da haka basu daina janta ba, shima Amir d'in 'kwala mata kira yake ta faman yi, Amira tace " in har kana 'kaunata da gaske to duk zafin kowane irin hukunci kada ka tab'a amsa laifin da ba kai ka aikata shi ba Amir d'ina," abinda take ta faman maimaitawa kenan har aka fice da ita daga station d'in, suka shiga motoci suka d'auki hanyar tafiya Abuja, suna tafiya Amir nan take yaji kamar an rabashi da wani b'angare na jikinshi ne, dur'kushewa yai a cikin cell d'in tare da 'kwala 'kara had'e da fashewa da kuka, nan take ya fad'i 'kasa a sume. Insp Yahya yai murmushi, sannan yace " zaka farfad'o ne ma, ya baiwa jami'an tsaro damar su shiga su watsa mishi ruwa sannan suita dukanshi har sai ya fad'i gaskiya," yana gama basu umurni suka amsa tare da sarawa suka fara aiwatar da umurnin da aka basu, kwamishina da Insp suka fito ya rakashi har bakin mota, kwamishina yana 'kara fad'a mishi cewa su tsananta tsaro da kuma d'aukar duk wani matakin da ya dace domin ganin ya fad'i gaskiya, daga nan suka yi sallama kwamishina ya shiga mota tare da rundunarsa suka tafi. Amir kuwa tunda aka kawo shi ake faman dukansa, duk ya suma sai su watsa mishi ruwa yana sake farfad'owa sai a cigaba da dukansa, amma har yanzu ya'ki amsa laifinsa, babban abinda ke basu mamaki dashi shine baya 'kara ko ihu, iyakarsa hawaye, in kuma aka tambayeshi amsar d'aya ce zuwa biyu, bashi bane yai kisan kuma koda shi yayi yana yiwa soyayya biyayya bazai tab'a sab'a umurnin Amira ba. B'angaren Amira kuwa koda isowarsu suka fito daga cikin mota Dad ya kama hannunta tare da jantahaka ya wuce kowa na gidan ba tare da yace uffan ba, cikin wani keb'antaccen d'aki ya sakata, sannan ya saka masu tsaro masu yawa a bakin k'ofar, bayan ya fito falo kuma ya gargad'i dukkanin mutanen gidan kan be yarda kowa yaje gun Amira ba in har ba abinci za'a kawo mata ba, yana gama fad'in haka ya shige d'aki abinshi, kwamishina ne ya kira Dad yana tambayarshi yanda yake so ayi da yaron, "no ku barshi ya d'and'ana tukun kafin mu yanke shawarar tura shi kotu sai ya karb'i horo da hukuncin sace min 'yata da yayi," abinda Dad ya fad'a kenan, suna gama waya ya kira babban yaron shi tare da bashi umurnin k'ara yara da tsaro sosai a gidan. Haka Amira ta kwana ta yini tana kuka ba ci ba sha, babu abinda take koka mawa irin tunanin halin da Amir yake ciki, ta kasa samun natsuwa zuciyarta ce kawai ke ayyana mata ta gudu taje ta ganshi, to amma tayaya zata fita daga gidan nan ba tare da an ganta ba? tambayoyi taita yiwa kanta wanda ta kasa samun mafita. A dai-dai wannan lokacin shima Amir ita yake tunani, yasan yanzu tana can tana kuka, ya tabbatar bata ci komai ba saboda sun saba cin abinci a tare, ji yayi kawai wani irin 'karfi yazo mishi, ya mi'ke tsaye tare da kallon Insp Yahya yace "ku bud'e ni inyi futsari," Insp dake zaune kan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana cin gyad'a ya kalle shi yace "yi anan," da Amir yaga in ya biyo mishi ta haka sam bazai saurareshi ba gashi shi a yanzu Amira kad'ai yake son gani, kallon Insp Yahya yayi yace "banza d'an daudu kawai, wai kai menene ribarka in ka raba masoya, muddin na fito daga cikin gurin nan sai naci ubanka d'an iska ba'kin mugu kawai," nan da nan Insp Yahya ya tunzura ya mi'ke a fusace cikin fushi ya nufo 'kofar cell d'in, to dama Amir abinda yake so kenan ya tunzura Insp dan ya samu ya bud'e shi, kiran wani jami'i yayi cikin b'acin rai yace ya bud'e wajen, yana bud'ewa Insp ya shiga, yana shiga Amir ya cakumeshi suka fara gwabzawa, nan fa yan sanda sukai caaaaa a kan Amir amma duk yawansu sai da yai musu shegen duka, daga k'arshe ma har ya saka kayan d'aya daga cikin 'yan sandan wajen ya fice daga station d'in. Tasha yaje ya tsayar da mota ya hau aka ja suka tafi sai Abuja, a dai-dai tashar Abuja suka sauka Amir ya fito kenan ya hango Amira cikin tasha zata shiga cikin wata mota, tafiya ya fara yi zai je wajenta yaji me motar nan yace "yallab'ai baka bani kud'in mota ba," Amir ya juyo tare da lalibar Aljihu yana duba wa cikin sa'a ya ciro kud'i a aljihun ya biyashi kud'insa, yana waigowa kuma ya duba baiga Amira ba a inda ya hangota, zuwa wajen motar yai da sauri ya le'ka bata ciki, nan fa ya shiga nemanta, yana zuwa bayan kangon tashar ya jiyo kamar numfashi a bayanshi, yana juyowa yaga ashe itace ta b'oye a wajen, wani irin hawaye yaji masu d'umi suna gangaro mishi, ji yayi ana fad'in "ku dudduba ko ina ku kamo ta nasan tunda sun ganta tana nan bata yi nisa ba," Amira sam bata ga Amir ba domin ta juya baya, jin abinda securitys d'in da aka baza su kamota ke fad'i yasa Amira ta yun'kura zata gudu, har ta fara gudu kafin su ganta Amir yai wuf ya jawota ta fad'o jikinsa cikin sauri kuma suka du'ka, ganin d'an sanda ne ya ri'keta ya k'ara rud'ata 'ko'karin 'kwacewa take dag ri'kon da yai mata tana fad'in "dan Allah ka 'kyaleni yallab'ai ka barni inje inga halin da masoyina ke ciki," Amir yasa hannu cikin sauri ya rufe mata baki, a yayin da d'ayan hannun ke rik'e da ita sannan yace, "wane masoyin naki zaki tafi gani bayan wanda yake a tare dake a yanzu haka," jin muryar da ko a mafarki ta jita zata gane yasa cikin sauri ta d'ago tana kallon shi, Amir kuwa a hankali ya d'ago da kanshi tare da cire hular kanshi ta 'yan sandan da yasa ya sakar mata murmushi, Amira ta zaro idanu sai kuma ta rungume shi tare da fashewa da kuka tace " Amir nayi kewarka, mutuwa kad'ai zanyi idan na rasaka a rayuwa," shima rungumeta ya yi, sannan ya rufe mata baki yai magana 'kasa 'kasa yace kiy shiru kar a ganmu a kama mu, ki bari su tafi mu samu mu gudu wani wajen," bayan kamar minti biyar sai suka ji ana fad'in "oga gasu nan sun b'oye anan gasu nan na kamasu." Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* (Autar marubuta) SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* (Mamie) *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana in sha Allah)🤜🤛 *MY ASIYA IMAM SEE-SEE ina tayaki murnar kammala novel d'inki mai suna 💜MASAKI NA,💜 Allah ya 'kara miki basira d'aukaka, da d'an karen za'kin hannu, sabon novel d'in da kika fara yanzu kuma mai suna 💙BAMU DACE DA JUNA BA💙 Allah yasa yanda kika fara lafiya ki gama shi lafiya.* *AISHA ISA, MUMMYS FRIEND, (TAWAN) ina ro'kon mahaliccina Allah ya d'orar miki da lafiya mai d'orewa👏😭* *MEELAT A.H.K* *(Bloodynah) da ni da ke 'kauna muke domin Allah ba da yaudara ba*👯‍♀😍😘💋 PAGE 110 to 115 Amir yasa hannu ya kwad'e wannan mutumin da yake ta faman antayo wa sauran kira suzo ya kama su, ya ri'ke hannun Amira suka danna a guje, nan da nan suma suka bisu a baya, wani mutumi ne ya faka mota ya fito Amir ya tura Amira cikin motar ya shige yaja me mota yana ta kurma ihu yana binsu da gudu, suma securitys d'in motocin su suka shiga suka bi bayansu a guje. Suna faman gudu ana binsu a baya har Allah ya basu sa'a suka tsere musu, suna yin nisa sosai suka ajiye motar a bakin ti-ti sannan suka nausa cikin dajin dake hanyar, dukkaninsu sun galabaita kan dole suka ja suka yada zango a cikin tsakiyar daji ba dan sun so tsayawa anan d'in ba a'a, saboda tsabar gajiyar da suka yi ne. Amira ta fara bajewa a 'kasa tana fad'in "Amir 'kishi nake ji," Amir yace " Amira yanzu ina zamu sami ruwa a cikin wannan dajin, amma bari inje in dubo ko zan samu, ki zauna anan kar ki matsa ko ina," Amir ya nausa cikin daji neman ruwa shima 'karfin hali kawai yake amma hatta tafiyar da kanta da 'kyar yake yinta, sai da ya d'auki lokaci yana tafiya Allah ya had'a shi da wani rafi sai a lokacin kuma ya rasa a me zai d'iba ruwan ya kai mata, yana cikin wannan tunanin ne yana waige-waige Allah ya sada shi da wata bishiyar kankana, cikin sauri yaje ya hau bishiyar ya katso 'katuwar ciki ya fafe samanta, har ya kai baki alamar zai sha ya tuno da Amirarsa itama tana can kwance yunwa da 'kishir ruwa na damunta, hakan yasa ya fasa ya fitar da kankanar duka a 'kasa ba tare da ya sha ba, sai da yaga ya yi yanda yake so yaje ya d'ibi ruwa a ciki ya nufi hanyar da ya biyo domin kaiwa Amira ruwan, yafi awa yana kai kawo cikin dajin saboda ya kasa gane hanyar ta b'ace mishi, sai daga baya Allah ya kawo shi har inda take, ko da yazo ya tarar Amira har ta fara baccin wahala. Amir ya tashe ta tare da mi'ke mata ruwan, Amira ta kalle shi tace "ka fara sha mana," Amir yace "ai na sha kafin in kawo miki," sai da Amira tasha mai isarta sosai, sai da ta kusa shanyewa sannan ta mi'ka mishi, tana mi'ka mishi ya kafa kai ya shanye sauran, binshi tayi da kallo a zuciyarta tace Allah sarki Amir wato saboda kar in 'ki sha idan naji be sha ba shine yace min ya sha, a fili kuwa tace "shine kace min kasha a can ko." Amir yace "kin fini bu'kata ne shiyasa, kuma bazan iya sa komai a bakina ba muddin ke kina cikin irin wannan halin," nan fa Amira tasa daru ita wallahi bata yarda ba sai an koma wajen yasha shima, ai kuwa haka aka yi suka koma wajen ya katso musu kankana sukai ta sha, daga nan bakin bishiyar suka yada zango bacci yai awon gaba dasu. Wad'anda aka sa su biyo su Amira kuwa suna zuwa suka ga motar da suka hawo an taho harda me motar ya shiga abarsa yaja ya tafi, su kuwa sai da suka 'kara duddubawa sannan suka juyo domin komawa su fad'awa Dad halin da ake ciki. B'angaren Dad kuwa koda securitys d'insa suka dawo mishi da bayanin wai Amir yazo ya d'auketa sun gudu kuma basu ga inda suka yi ba, baida aikin komai sai kai kawo, cikin sauri ya buga wa Insp Yahya waya da sauran manyan sojojin sa yai musu kwatancen dajin da aka fad'a mishi anga motar da suka shiga, sannan ya d'au al'kawarin baiwa duk wanda ya kamasu kud'i mai tsoka, bayan ya gama wayar ya kalli yaran nasa yace "bana son sake ganin fuskarku a gidan nan, ku koma dajin kuje a nemo su daku a kawo min su nan gabana, suka juya cikin sauri suka fito suka k'ara nausawa dajin, jefi-jefi kuma suna yin waya da Sojoji da su Insp Yahya yana tuntub'arsu abinda ke faruwa. Washe gari da sassafe Amir ya tayar da Amira suka sha kankana suka sha ruwa, sannan suka ci gaba da tafiya cikin dajin nan, wannan dalilin ne yasa duk jami'an da aka turo suka kasa tarar dasu sai da sukai kwana uku cikin dajin nan, a koda yaushe in sun sami guri sun kwana inda zasu sami d'an abun tab'awa gari na wayewa sai su sake d'aukar hanya, sam basu zauna gu d'aya ba gudun kar azo a kama su. A kwana na uku ne Allah ya sake kaisu cikin wani dajin, suka yada zango kasancewar yamma tayi, duk da suna cikin damuwa hakan be hana su cigaba da rayuwarsu cikin walwala ba, a ranar sun dad'e suna hira a wajen sai wajen 'karfe sha biyu sannan suka kwanta, kuma inda Allah ya taimake su har zuwa wannan lokacin Allah bai had'a su da wani abu na cutarwa ba. Suna cikin bacci suka ji ana tashin su, ashe an zagaye su basu sani ba, firgigit suka tashi Insp Yahya ne du'ke a gabansu yana kallon su d'aya bayan d'aya sannan yai murmushi yace "kun gama gudun?" nan fa aka kama su za'a tafi dasu Amir yai kukan kura ya gwabje wad'anda suka ri'ke shi, Allah ya bashi sa'a ya fisgi wata bindiga hannun wani d'an sanda ya harbi mutum uku a 'kafa, yaja hannun Amira suka saita hanya gudu suke ana binsu a baya, da yake cikin dare ne unguwar tsit kuma garin duhu, gudu suke yi kamar ransu zai fita har Allah ya kawo su wani 'kauye, wani gida suka hango bud'e aikuwa babu shiri suka kutsa ciki kai tsaye, suna shiga a dai-dai wani dattijo ya fito daga ban d'aki yaga mutane tsaye a tsakiyar tsakar gidan su, haska su yayi da toachlight yana fad'in "kai su waye nan……ah ikon Allah Amir, Amira, daga ina kuke cikin wannan daren?" Sai a lokacin suka fahimci ai gidan su Baba ne Allah ya k'ara dawo dasu ba tare da sun gane ma wani gida suka fad'o ciki ba, da gudu suka rungume Baba suna murna, Umma kuwa jin hayaniyar dake tashi ne itama ta fito daga d'akinta turus taja ta tsaya ganin su Amira tsaye a tsakar gida, nan dai Baba yace su shiga d'akinsu su kwanta washe gari sai su yi magana. Suka shiga cikin d'aki suka kwanta, Baba kuwa cikin sauri ya rufe gida karma a ganshi a bud'e ai tunanin nan suka shigo. Amir da Amira kuwa suna shiga d'aki suka rungume juna suna murnar sake ganinsu cikin wannan gida. Amir ya tsalle yai sufa kan tabarma, Amira kuwa ta zauna kan d'ayar tabarmar, Amir yace " Alhamdulillah Allah ya 'kwacemu, ya kai kallon shi kan ga Amira yace kinga hukuncin Allah ko, ashe gidanmu muka dawo ma muke rab'e - rab'e," Amira tace "wallahi kuwa," Amir da Amira suka kafe juna da idanu kowanne da irin abinda yake ji a cikin zuciyarshi. Amir yace "taso ki dawo kusa dani mana Amira na," ba musu ta tashi ta koma kusa dashi ta zauna, suka ci gaba da kallon juna, nan take shaid'an ya fara k'awata musu sha'awar junan su. Har sun fara biyewa shaid'an yana buga musu ganga suna neman aikata zina, cikin sauri Amir ya d'aga Amira tare da komawa kan ta-ta tabarmar ya zauna tare da had'a kai da guiwa ya fashe da kuka, Amira ta mi'ke cikin sauri tare da zuwa kusa dashi ta dafa kafad'ar shi, cikin sauri ya d'ago ya kalle ta yace "Amira ni da ke duk mun sani soyayya tana had'uwa tare da sha'awa ne, kuma duk inda mace da namiji suka keb'e to na ukun su shaid'an ne, 'kaunar da nake miki ta ha'ki'ka ce bazan iya aikata abinda Allah ya haramta ba a kanki har sai ranar da na mallake ki a matsayin matar aure, dan haka dole mu ri'ka d'an yin nesa da juna, saboda kar soyayyar da muke wa juna ta rinjaye mu mu aikata zina kafin aure, ki kwanta a ciki zan fita tsakar gida in kwanta," yana gama fad'in haka ya fice daga d'akin da tabarmarsa a hannu ya shimfid'a a tsakar gida ya kwanta. Amira ta d'auko tata tabarmar ta biyo shi ta shimfid'a a tsakar gidan itama nesa dashi, ganin in dai Amira ta kwana anan bama ita kad'ai ba har shi zasu cutu domin kuwa dukkansu mura suke yi saboda kwanan daji da suka yi. Amir ya tashi ya nannad'e tabarmar shi yace itama ta tashi, Amira ta tashi suka koma d'aki suka rufe, shi kanshi Amir yasan Amira ta riga da ta yi mugun sabon da bazata iya kwana inda babu shi ba yanzu, tunani yake mafita d'aya kawai ta rage musu shine a d'aura musu aure. Haka suka kwanta nesa da juna amma fuskar su tana fuskantar junansu uka Amir ya kalli Amira itama shi take kallo, Amir yace "Amira," Amira tace " na'am," Amir yace kin Amince in fad'a wa Baba gaskiya ya d'aura mana aure gobe?" Amira ta mi'ke tsaye daga kwancen da take tace " eh wallahi a fad'a mishi tun yanzu, bari ma inje in sanar dashi," ta d'auki hanyar 'kofa da sauri zata bud'e ta fita, Amir yace " tsaya mana, banda dariya babu abinda yake mata, kallonta ya sake yi yace yanzu ke dan baki da kunya sai kije taso Baba a wannan daren, to in kika je kika taso shi me zaki ce mishi?" ya sake kwashe mata da dariya. Amira ta rufe ido alamun taji kunya, ta dawo kusa dashi ta zauna sam tama manta da gargad'in da yai mata na yin nesa da juna har sai sunyi aure, baccin da kuma basu yi ba kenan suka dosa hirar yanda kowa zai ji idan suka mallaki juna matsayin ma'aurata, da kuma yanda zasu rayu da juna bayan aure. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* (Autar marubuta) SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* (Mamien) *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* (Gidan zaman lafiya da amana in sha Allah)🤜🤛 *MAMAN LABYB (MAMIE)da AUNTY LIPSON (Maman Saleem) ina ro'kon Allah mahaliccina ya d'orar da lafiyarsa gareku👏😩* PAGE 115 to 120 Washe gari Amir da Amira ne zaune gaban su Umma, Amir har ya bud'e baki zai fara magana Amira tai karaf ta fara magana da fad'in "Baba, Umma, iyayena auren dole suke so su yi min ni kuma bana so, saboda yaron da zasu had'amu beda tarbiyya su kuma basa son talaka wannan dalilin yasa suka tsani had'a aurena da Amir," tana kaiwa nan a zancenta sai ta fashe da kuka, d'akin yai tsit banda sautin kukan Amira dake tashi, can sai Amir ya d'ago kai ya kalli Baba yace "Baba dan Allah ka d'aura mana aure dan girman Allah, shima ya fashe da kuka yana ci gaba da yiwa Baba magiya, daga Baba har Umma shiru suka yi, a yayin da tausayin yaran ya gama lullub'esu, kuma tabbas yanda suka sha'kun nan in akace za'a raba su to zasu cutu, dukkanin su sun yi Allah wadai da wannan muguwar d'abi'a ta iyayen Amira kan dole sai sun aurar da ita ga mai kud'i sai kace talaka shi ba Allah ne ya yishi ba, duk wannan tunanin Umma da Baba cikin zuciyarsu suke yinsa. Baba ya kalle su har yanzu kukan suke ta yi, sai yace "ya isa kukan, bayan sun yi shiru ya cigaba da fad'in kuje cikin d'akin ku ku shirya kafin nan zamu yi shawara da Mamanku, kuma a yanda kuka bamu labari kunce sun biyoku har cikin rugar nan, to tabbas nasan zasu sake dawowa, saboda haka kuje kuyi shiri in mun gama shawara da Ummanku to ko za'a d'aura muku auren ba a nan ba zan tura ku wani 'kauye nan wanda ke ma'kwabtaka da namu wajen yayana sai a d'aura muku auren a can in yaso ma sai ku zauna a can d'in kawai." Cikin sauri kuma cike da farin ciki suka tashi suka shiga cikin d'aki, can bada dad'ewa ba sai ga Baba yai sallama tare da le'kowa yace su fito su tafi, har sun bar wayar su Baba yace su d'auka in yaso sai su canza sim su karya wancan, Baba da kanshi yai musu jagora suka yi sallama da Umma suka fice daga gidan suka d'auki 'kauyen gidan d'ango, daga 'kauyen damari zuwa 'kauyen gidan d'ango da tazara sosai shiyasa suka jima suna tafe kafin su iso cikin 'kauyen. Bayan sun 'karasa gidan suka gaggaisa aka kawo musu fura da nono da ruwa mai sanyi suka sha, bayan sun gama Baba ya kora wa yayansa bayanin duk abinda ke faruwa da kuma dalilin zuwan su a yanzu da ro'kon yayan nasa alfarma kan su zauna a 'kauyen har sai Allah ya kawo dai-daituwar komai. Yayan Baba wanda yaransa ke kiransa da Baffa yace "ba wani abu Allah ya shige mana gaba, yanzu abinda za'ai shine malam Amir in har kana da kud'i a jikinka ka kawo a d'aura yanzu, bari nasa a kira ma'kwabta da 'yan uwa da abokan arzi'ki, Baffa yasa aka kira su wad'anda suke nan nan da nan suka had'u, Baba ya ciro dubu biyar yace "ga sadakin Amir kuma ni ne waliyyinsa," Baffa yace "masha Allah nine waliyyin Amira," wani liman dake unguwar yace " to Alhamdulillah, nan fa babu b'ata lokaci aka gabatar da dukkanin abubuwan da suka kamata, aka d'aura aure sannan aka yi addu'a tare da yi masu fatan zaman lafiya kowa ya watse. 'Daki guda aka samar musu a cikin gidan Baffa, sai da aka gama komai sannan Baba yai sallama dasu su Amir suka rakoshi hanya cike da farin cikin kasancewarsu ma'aurata. Suna tafe Baba yana k'ara yi musu nasihar zaman lafiya a zamantakewar aurensu, sun d'an fara yin nisa da unguwar Baba ya tsaya yace "to rakiyar taku ta isheni daga nan, ku koma nagode Allah muku albarka." Amir ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ga motoci sun zagayesu ta ko'ina kuma motocin na tsayawa suka shiga fitowa d'aya bayan d'aya, su Insp Yahya ne sojoji da 'yan sanda gaba d'aya suka zagaye su Amira suka saka su a tsakiya, can kuma sai ga Umma matar Baba itama an fito harda ita a cikin motar, Baba ya kalleta yace " meyasa zaki nuna inda bayin Allahn nan suke, yanzu abinda kikai kin kyauta kenan?" Insp Yahya yai tattaki ya 'karasa har kusa da Baba sannan yace "Baba hala baka san abinda wad'annan suka aikata ba shiyasa kake b'oye masu laifi a gidanka ko, to bari kaji kisa Amir yayi ya kuma sace 'yar shugaban 'kasa ya gudu da ita, idan har da baka san laifin da ya aikata ba to yanzu ka sani, muddin ka 'kara b'oye shi ko kasa aka b'oyeshi to kuma sai mun hukunta ku." Insp Yahya ya sake yin tattaki ya 'karasa har gaban Amir, sun dad'e suna yiwa juna kallon kallo sannan Insp yai murmushi yace " Amir karka manta da sunana Insp Yahya kafi 'karfin mugu, babu inda zaka shiga ka guje mini in dai kana cikin Nigeria ne, dan haka ku kama shi muje." Amir ya kalli Amira wadda itama shi take kallo suka yiwa juna murmushi, sannan ya maida kallon shi ga su Baba yace "Baba, Umma, wallahi bazamu tab'a mantawa daku ba har abada, saboda kun d'aukemu tamkar yaran da kuka haifa," Amira tai karaf tace "kuma kuka yi mana abinda iyayenmu da 'yan uwa suka kasa yi mana, wallahi har mu mutu ba zamu daina 'kaunarku ba da kallonku a matsayin iyaye wad'anda suka haife mu, idan mun yi muku laifi a zaman mu daku ku yafe mana, in Allah ya yi da sauran ranmu zamu dawo gareku, in kuma an kashemu to ku tuna damu cikin addu'armu." Insp Yahya ya kalli Amira yace " wai ke Amira meyasa kike son sa kanki cikin laifin da babu ke a cikinsa ne?" Amira ta balla mishi harara sannan tace " ina ciki nice babbar me ruwa da tsaki ma kuwa tunda kuke bibiyar burin raina Amir d'ina da mugun sharrin ku, kuma a kanku zai 'kare," ta 'karashe maganar tare da murgud'a mishi baki. Insp ya kalli bataliyar jami'an nan yace a saka su a mota, kamar jira suke suka nufi su Amir, sai da suka je daf da su Amira ta daka musu tsawa tare da d'aga hannu tana fad'in "ku dakata ba sai kun kama mu ba, zamu shiga da kanmu ku kaimu duk inda zaku kaimu, ni dai nasan duk hukuncin ku baku iya canza 'kaddarar ubangiji, ta kalli Amir sukaiwa juna murmushi a karo na biyu suna ri'ke da hannun juna, sannan ta cigaba da fad'in " Amir d'ina tunda Allah ya cika mana burin mu na zama ma'aurata to mu bisu su dafa mu a babbar tukunya in zasu iya, muje koh?" Amir yai murmushi sannan yace "eh mana me muke jira." Har suka shiga mota Insp Yahya na tsaye yana kallon ikon Allah yanda gaba d'ayansu suka nuna rashin tsoro ko damuwa a tattare dasu, ga kuma wata magana da yaji wai sun zama ma'aurata. Aikuwa Allah Allah yake su isa station ya sanar da Dad, saboda gun sauri ya manta da wayarsa a office jin an gano inda su Amiran suka gudu. Suna cikin tafiya tayar motar su tai faci, sai aka faka ana tsayawa Amir ya fara 'ko'karin guduwa shi da Amira, Amir ya bubbuge wad'anda ke kusa da su, ya ja Amira suka runtuma a guje, sun fara gudu kenan sai Insp Yahya ya saita Amir da bindiga ya harbeshi a gefen ciki ta baya, nan Amir ya saki wani irin 'kara Amira ta juyo itama sannan ta ankara da harbin da aka yi mishi, hakan yasa dole Amir ya zube a nan, nan da nan 'yan sanda suka kewaye su, aka maida su cikin mota aka nufi asibiti, cikin emergency aka nufa dashi cikin Saudi, kuma duk abin su Amira sai da ta shiga, aka cire mishi riga domin suga sun yi 'ko'kari sun cire mishi bullet d'in, ana cire rigar sunan Amira ya fito rad'o-rad'o a 'kirjin shi, kuma daga gani tsaga jikinshi aka yi aka rubuta a fatar jikin nashi irin wanda ba zai tab'a gogewa ba ko ya b'ace har abada. Amira na ganin sunanta a 'kirjin Amir taji 'kaunarsa ta dawo mata sabuwa tare da jin matsanancin tausayin shi, tabbas tayi imani cewa ba zata tab'a samun masoyi kamar Amir ba. Bayan kwana biyu Amir ya warke sarai aka sallame su, kai tsaye station aka wuce dasu. Ko da isar su suka tarar da mahaifin Amira ya zo, cikin 'karaji da fusata Dad yace "ku saka shi cikin cell, ita kuma Amira ku kai min ita mota, sannan ku gaggauta had'a duk wasu bayanai da hujjoji ku tura shi kotu tunda kun kasa tsareshi har ku tuhume shi sosai ya amsa laifin sa, ku tabbatar kun mik'a shi kotu." Amira jin ance za'a tafi da ita yasa hankalinta yai mugun tashi, tunanin mafita ta fara yi cikin ranta, can sai ta hango bindigar Insp Yahya a kan tebur tai wuf ta d'auka hakan ya yi dai-dai da jefa Amir cikin cell da aka yi, aka rufo wajen. Cikin sauri Amira ta nuna d'an sandan dake k'ok'arin rufe 'kofar da bindiga, sannan ta umurceshi da ya bud'e 'kofar, cikin sauri ya bud'e ta shige ciki itama sannan ta sake nuna shi da bindiga sannan tace " rufe mu," aka rufe su ita da Amir a ciki sannan ta kalli mahaifinta wanda shima ita yake kallo yana mamakinta tace "Dad zuwa yanzu yaci ace kun ha'kura, a yanzu Amir mijina ne domin an d'aura mana aure ni da shi, muddin za'a cigaba da tsareshi to wallahi se dai a tsare mu dukkan mu ni da shi, Dad babu shaidar da zata nuna Amir shi yai kisan, kuma in dai za'a cigaba da tsareshi da tuhuma to tabbas zan cigaba da bashi kariya ta hanyar maida laifin kaina." Amira cikin kuka ta cigaba da cewa " Dad wallahi in na rasa Amir nima zaka rasani, ka yi ha'kuri ka barmu mu tafi." Amir shima cikin kuka ya kalli Dad d'in yace " dan Allah Dad ka tausaya wa rayuwata, wallahi zan iya rabuwa da komai in ha'kura amma banda Amira saboda itace *MAHA'DIN RAYUWATA* dan Allah Dad," Dad be ce komai ba ya juya zai tafi, sai da ya kai bakin k'ofar fita sannan yai magana ba tare da ya juyo ba, yace" tunda kin zab'i zama dashi a kanmu zan d'auki matakin k'arshe, kai kuma Insp ka aiwatar da abinda nace maka," yana kai nan a zancen shi ya fice yai tafiyarsa. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie Nah)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *ALLAH SARKI RAYUWA! SHEKARAR DUBU BIYU DA SHA TAKWAS TA WUCE KUMA BAZATA TAB'A DAWOWA BA, MU ZAUNA MUYI NAZARI ME MUKA AIKATA A CIKINTA, SHIN AIYUKAN ALKHAIRINMU YA RINJAYI NA SHARRIN KO KUWA A'A AIYUKAN SHARRIN NE SUKA RINJAYI NA ALKHAIRIN, MU ZAUNA MUYI NAZARI DA TUNANI, WUCEWAR LOKUTA DA SHEKARU BA ABUN MURNA BANE ABABEN TUNATAR DA BAYIN ALLAH NE SU GANE CEWA LOKUTANSU FA NATA TAFIYA, MU RIBACI RAYUWARMU DA AIKATA ALKHAIRI KAFIN MUTUWARMU, MUYI TUNANI ME MUKA AIKATA A BAYA, KUMA ME ZAMU AIKATA A GABA NA ALKHAIRI, YA UBANGIJINMU KA YAFE KURAKURENMU NA BAYA KA BAMU IKON AIKATA ALKHAIRAI CIKIN WANNAN SHEKARAR WADANDA ZASU ZAMA SILAR SHIGARMU ALJANNA👏👏👏👏👏😭* ```INA MIK'A SAK'ON GODIYATA GA 'DUMBIN MASOYANA DA SUKA KIRANI DOMIN TAYANI TA'AZIYYAR RASHIN UNCLE 'DINA SULAIMAN DA NAYI, DA WA'DANDA SUKA KIRA DOMIN GAISHENI DA JIKI DOMIN RASHIN LAFIYA DA ALLAH YA JARABCENI DA ITA, KA'DAN DAGA CIKI SUNE``` *MAMAN LABYB* (Mamie Nah) ```KODA YAKE KE AI MAMIE JIGO CE TA RAYUWAR BK😉😊 IDAN NACE JIGO INA NUFIN KECE KOMAI NAWA, AMMA DUK DA HAKA WAJIBI NE IN GODE MIKI DOMIN TABBAS KIN DAMU DANI FIYE DA KOWA, K'AUNA BATA IRGUWA SONDA NAKE MIKI BAI MISALTUWA😍😘💋.``` SAI *AISHAN UMMA* (Auntynah) *MEELAT A.H.K* (Bloodynah) *QUEEN RUQEEY* (Habibty nah) *MUMMYS FRIEND* (Tawan) *RAHEENAT M. ABBAKAR* (My heenat) *HAUWA JAMIL* *MARYAM M. HASSAN MEEMAH* (Hearty nah) ```Dukkaninku da na lissafo gaskiya bana kallonku matsayin friend kawai, kallonku nake matsayin 'yan uwa, 'yan uwan ma na jini, dalili kuwa shine kun damu dani fiye da kowa, ko na yini d'aya tak in baku ganni ba online sai kun binciki dalili, Allah ya saka muku da alkhairi tabbas irinku ake so, ina da tabbas akan ko bayan babu ni zaku ri'ka tunawa dani har in samu addu'a daga gareku, shiyasa bana had'a matsayinku da na kowa gaskiya, Allah ya saka muku da alkhairi.``` *MASOYANA* ```bazan manta da ku ba masoyana wad'anda suka kwararo min tasu addu'ar ta cikin whatsapp irin su``` *REAL KHADY* (Princess) *~HAJARAH GHANDHI* (Hajjona) *~MOMYN KHADEEJA🧕* *~UMMUZAID* ~*MAMAN ARFAT* ~*MUMMYN-SULTAN* *ASIYA SEE SEE* *MY LISSA* *MARYAM KWARE* *QUEEN BK* *HAJ CEEYMER UMMEETA* *MARYAM* *HAPSY MK* ```Kuna farko farko a zuciyata kun nuna mini so da kulawa nagode 'kwarai da nuna kulawarku kaina, Allah ya saka muku da mafificin Alkhairinsa, duk wad'anda suka tayani addu'ar samun lafiya da masu yimin ta'aziyya duk na gani gaba d'aya Allah ya saka muku da alkhairi ya biyaku, wadanda suka ga ban ambaci sunansu ba suyi hakuri ban gani bane saboda yawancin maessage dina duk waiting suka sa min amma ina godiya Allah ya saka muku da alkhairi gaba d'aya, iya wuya fa ana mugun tare.``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```Ina godiya da tarin addu'ar da nake sha kullum a wajenku babu dare ba rana, wallahi kunci sunanku 'yan amana, domin d'an amana ne kad'ai yasan mecece amana kuma ya kiyayeta, kuna burgeni ina yinku har abada, kawai a cigaba da basu maamaaki mutanena🤜🤛😉😘😍👯‍♀``` PAGE 120 to 125 Dad ya bada umurni a cigaba da tsare su Amir cikin cell d'in tare da 'yarsa Amira a cewarsa tunda haka ta zab'a kuma taga yafi mata, har zuwa ranar da za a shiga kotu. Insp Yahya kuwa Allah Allah yake a yanke wa Amir hukuncin kisa ba dan tsanar da yai mishi kad'ai ba ma, ko dan wahalar da suka sha a kanshi, hakan yasa cikin 'kan'kanin lokaci ya had'a dukkanin takardu d'auke da bayanan 'karya aka mi'ka su kotu, wanda za'a halarci kotun ranar Litinin. Yau litinin, kuma a yau ne kotu ta cika ma'kil domin gudanar da shari'ar su Amir, inda Amira ta 'kara ja mishi kunne kan karya sake duk tsananin wuya ya amsa laifin, sannan ta k'ara 'karfafa mishi guiwa ta hanyar tabbatar mishi da cewa su ne da nasara in Allah ya yarda. Shigowar Al'kali kenan kowa ya mi'ke, sai da Al'kali ya zauna sannan kowa ya koma mazaunin shi ya zauna. Kotu tai tsit kowa ya baza kunne da idanu domin bada muhimmanci wajen ganin yanda wannan shari'ar zata kasance. Da yake shari'ar su Amir itace aka sa a farko shi yasa aka fara karantota, sannan aka umurci gabatar da Amir inda Amira ke biye da shi, can d'aya b'angaren kuma iyayen Sadeeq ne. Bayan shiru na wasu lokuta saboda nazartar takardun da aka mi'kawa Al'kali da yake yi, can sai Alk'ali ya d'ago ya kalli Amir, sannan ya maida kallon shi kan Amira yace "malama ki koma ki zauna har sai an kira ki," Amira tace " ranka ya dad'e zargin da ake wa Amir mu biyu ake zarga, shiyasa ma na biyo shi muka fito gabanka muka tsaya a tare." Al'kali yace "duk da haka ki koma ki zauna sai an nemeki," Amira ta kalli Amir shima Amir ya kalleta idonta har ya ciko da 'kwalla, sai ya d'aga mata kai alamar taje ta zauna, Amira taje ta samu waje ta zauna. Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kaji irin tuhumar da ake yi maka na kashe Sadeeq, shin ka amince kai kayi kisan ko baka amince da hakan ba? Amir yace " ba ni na kashe shi ba Allah gafarta malam, ni lokacin da aka yi kisan ma bana wajen, washe gari da na shigo ne naga gawarshi cikin school mutane sun kewayeta. Al'kali ya d'an yi rubutu sannan ya d'ago yace a gabatar mishi da 'yan sandan da suka yi bincike kan case d'in. Insp Yahya yazo gaban kotu ya tsaya, Al'kali yace yana son yaiwa kotu bayanin yanda suka gudanar da binciken su har suka tabbatar da Amir shi ya kashe Sadeeq. Nan Insp Yahya ya fara kwakuso bayani tun daga kan soyayyar da Abdul da Sadeeq suke mata harma da Amir d'in, amma shi sai ya b'oye nashi saboda wani manufarsa da ya barwa kanshi sani a lokacin, sai daga baya yai amfani da damar da ya samu na fad'an da Abdul da Amir suka yi har da ikirarin kashe junansu, Insp ya cigaba da cewa " da wannan damar yai amfani ya kashe Sadeeq tare da barin shaidun da zasu sa a yarda cewa Abdul ne ya kashe Sadeeq, bayan faruwar haka sai na fara bincike kan Amir d'in da Amira, anan na gano ashe shima Amir d'in yana son Amira, amma be nuna mata ba sai da ya kawar da masoyanta Sadeeq da Abdul, sannan na jiyo da kunnena yana baiwa Amira labari cewa shine ya kashe Sadeeq saboda ita." Al'kali ya rubuta bayanan da ya samu daga Insp Yahya, sannan yace wa Insp ya koma ya zauna, Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kaji abinda Insp Yahya yace?" Amir yace "eh ya me shari'a," Al'kali yace "kana da ja ko babu?" Amir yace "eh ya me girma me shari'a ina da ja, domin ban tab'a kashe kowa ba." Al'kali yace "wanene shaidanka?" Amir yace " Allah ne kad'ai shaida ta, sannan kuma ni banac cikin makarantar ranar da akai kisan, washe gari ne da na shigo makaranta na tarar da gawar, in kuma su sunada shaida akan haka to su gabatar, sannan ni da mamatan dukkaninsu muna da kyakkyawar alak'a ko musayar yawu be tab'a had'ani dasu ba." Al'kali yayi rubuce-rubuce, sannan ya sake kiran Insp Yahya domin ya gabatar da shaidun da yake da su na tabbacin Amir yai kisan bayan wad'anda ya bayar, Insp Yahya ya kira wasu daga cikin student d'in makarantar guda uku su bada shaida, sedai dukkansu a bayanan su kaf sun tabbatar da cewa basu ga Amir ba a wannan daren, lokacin da Sadeeq ya shigo a buge Abdul ne ya biyo bayan shi ba Amir ba, bayan an sallame su sun koma sun zauna Alk'ali yace " Amir shima ya gabatar da shaidun sa wad'anda zasu tabbatar da baya nan ma aka yi kisan kuma be san ma da rasuwar ba sai washe gari da ya shigo makarantar domin d'aukar karatu. kafin ma Amir ya bada amsa nan da nan gurin ya hargitse d'alibai sama da Ashirin suka d'aga hannayensu suna fad'in zasu bada shaida akan Amir besan komai ba hatta ma kisan, sai da ya shigo makarantar ya ga gawarshi, Allah sarki cikin masu d'aga hannu harda Amira jikinta har tsuma yake, Allah-Allah kawai take a kirata. Al'kali ya buga guduma alamar kowa ya natsu yai shiru. Bayan an natsu sai Al'kali yace " ya kamata ku gane nan kotu ne ba makaranta ba, dan haka kowa ya shiga taitayinsa har sai an kira mutum tukun, Al'kali ya cigaba da cewa amma idan na fahimta yawancinku kunsan duk abinda ke faruwa ko?" da 'karfi suka amsa da "eh" musamman Amira 'kararta tafi ta kowa harda mi'kewa tsaye sai da taga Al'kali ya kallo inda take tai sauri ta koma ta zauna, hakan da suka yi ya baiwa Al'kalin dariya wanda har saida ya murmusa, sannan ya jinjina farin jinin Amir gun mutane, ko be bincika ba hakan ya tabbatar mishi da yana da kyakkyawar ala'ka da mutane. Alk'ali ya d'an yi rubutu, sannan ya d'ago yace " yanzu lokaci ya tafi, kuma akwai sauran cases a gaba, amma in Allah ya kaimu wani satin zamu dawo domin cigaba da sauraron wannan shari'ar." Nan aka cigaba da gudanar da sauran k'ararrakin, ana gamawa kowa ya watse. Aka fito da Amir da ankwa d'aure a hannunsa inda Amira ke bayanshi, su Insp suna biye da su, Amira ta kalli Amir shima ya kalleta suka kwashe da dariya, har aka saka su a bayan mota da wasu 'yan sandan, inda Insp ya shiga gaban motar shi da wani d'an sanda suka ja. Suna cikin tafiya Amira ta sake yin dariya ta kalli inda Insp Yahya yake tace " Insp Yahya ya kaji shari'ar ta yau, kasan me? shari'ar yau tai dad'i, da alamu wani zai sha kunya, ta juya ga Amir tace Amir d'ina kaima kaji dad'in wasan yau a kotu ko?" Amir yace "sosai ma, wani 'kato zai sha kunya nan gaba kad'an," "Amira tace ai nasan dama nasara tana tare damu, ni fa wallahi saboda ina tare da kai har mantawa nake da wai muna cikin tashin hankali," suka kwashe da dariya, ya d'aga mata hannayenshi da ke cikin ankwa itama ta d'aga nata suka tafa, Insp ba bakin magana amma ya mugun hassala da maganganunsu, sai huci kawai yake, su kuwa cigaba da hirarsu suka yi yanda kasan ba abinda ke damunsu. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamien Bk)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *MADEENAT* ```(My Deenat)``` *Na gode sosai da kulawarki kan rashin lafiyata, Allah ya saka miki da mafificin alkhairinsa, Allah ya 'kara miki basira marubuciyar SAI NA KASHE MAHAIFIYATA, muna mugun jin dad'in novel d'innan naki a cigaba da antayo mana shi muna 'kwamushewa.😉😘* *Babu wanda Allah yake nufinsa da alkhairi sai wanda ya sashi a hanyar addini, mu tashi, mu dage, musan addininmu, domin shine sanadin kasancewarmu cikin duniyar nan, Allah kasa mu dace.* *AUNTY LIPSON* (Maman Saleem) *'Yar uwa ina ro'kon mahaliccina ya d'orar da lafiyarsa gareki👏😰😰😰😰😰* PAGE 125 to 130 Bayan sun isa station d'in aka sake gar'kame su Amir da Amira a cikin cell, Insp Yahya ya d'aga waya ya kira Dad d'in Amira yai mishi bayanin duk abinda ke faruwa, dai yai shiru na wasu lokuta, daga 'karshe yace su jira tukun suga yanda 'karshen shari'ar zai kasance, amma kafin zagayowar ranar zai turo 'kwararren lauya. Bayan sun kammala wayar sunyi sallama Dad ya fara kai kawo a 'kerarren 'kayataccen d'akin shi, tunani yake a ranshi me ya kamata yaiwa yaron nan yana nema ya rabashi da 'yarshi, yaro d'aya tak ya zame mishi matsala yana nema ya zauta shi, cikin b'acin rai ya kaiwa iska naushi, tunani ya cigaba da yi yasan yana da damar da zai iya yin komai a kanshi ba tare da an sake koda waiwayen labarinsa ba ma, amma in yace zai b'atar dashi to siyasar shi yake ji, saboda sabon zab'e ya kusa, kawai mafita shine ya bari tukun a gama shari'ar in basu yi nasara ba sai ya nemo wata mafita amma bazai tab'a bari ya yarda ta auri Amir ba, da haka ya tsayar da tunanin tare da cigaba da harkokin shi. *BAYAN SATI 'DAYA* Yau litinin, kamar kullum yau ma kotu cike take ma'kil da mutane, Al'kali ya d'an yi rubuce-rubuce, sannan ya d'ago tare da fad'in " ina fatan dai masu 'kara da wanda ake 'kara sun tanaji lauyoyin su?" Wani ne ya tashi cikin isa da ta'kama, ya sha ba'ka'ken kaya irin na lauyoyi, ya d'an rissina sannan yace " sunana barista Kamal Ibrahim lauyan gwamnati, ni ne nake wakiltar b'angaren wanda ke 'kara wato b'angaren Sadeeq," bayan ya kammala jawabinsa ya koma ya zauna. Sai Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kai baka da lauya ne?" har Amir ya bud'e baki zai yi magana kenan sai suka jiyo maganar wata matashiyar kyakkyawar mace ta shigo cikin takunta na 'kasaita, itama sanye take cikin kayan lauyoyi wad'anda suka yi matu'kar yi mata kyau, shigowa take tana magana tana fad'in "ayi ha'kuri ranka ya dad'e nazo a makare cinkoson ababen hawa ya hanani 'karasowa da wuri," ta k'araso wajen da aka tanada domin zaman su ta tsaya a tsaye tare da rissinawa tace "sunana barista Yasmeen Ahmad Abubakar, ni lauya ce me zaman kanta nice lauyar da ke kare wanda ake 'kara, wato Amir" tana gama fad'in haka ta samu waje ta zauna tana dudduba abubuwa a takardun dake gabanta. Amir yayi matu'kar mamakin jin abinda Baristan nan tace, saboda shi yasan be d'auki lauya ba, kuma ba wani wanda sukai maganar d'aukar lauya dashi, kallon gefen da Amira take yayi ya d'aga mata gira da d'an d'aga kai alamar tambayar itace ta kawota, sai Amira tai murmushi sannan ta d'aga mishi kai itama alamar eh itace. Barista Kamal ne ya fara mi'kewa yace "ina son kotu ta bani damar yiwa Amir da Amira tambayoyi," Al'kali yace "an baka, ina Amira take ta fito," Amira ta fito ta tsaya ya kusa da Amira, suka kalli juna suka sakarwa junansu murmushi, ni kuwa nace ikon Allah har a kotun ma sai kun nuna ku masoya ne.🤔 Barista kamal ya matso kusa da inda su Amir suke a tsaye, sannan ya kalle su yace "bari na fara da kai Amir, lokacin da aka yi kisan Sadeeq kai kana ina ne?" Amir yace "ina gida," "amma ance an ganka da Sadeeq a ranar har kun yi wasan tsere harda Amiran ma kafin daren ranar?" barista kamal ya sake jeho mishi wata tambayar, Amir yace "tabbas munyi tsere da shi da Amira a ranar da za'a kashe shi da safe, shiyasa mutuwarshi ta girgizani sosai," barista yai murmushi sannan yace " me ke tsakaninku da Amira, ina nufin kuna soyayya ne?" Amir yace " eh muna soyayya da ita," barista yace wannan ne dalilin da yasa tun farko ka shirya kashe masoyinta Sadeeq sannan ka d'ora hujjojin laifin a kan Abdul aka kashe ahi baiji ba bai gani ba?" "objection my lord, abinda barista Yasmeen tace kenan cikin sauri tare da mi'kewa tsaye tace ya kamata lauyan masu 'kara yasan irin tambayoyin da ya kamata ya ri'ka yiwa Amir, domin har yanzu zargi ake a kanshi ba'a tabbatar ba da zai ri'ka d'aura alhakin kisan kai tsaye a kanshi, nagode ya mai girma mai shari'a," tana gama fad'in haka ta koma ta zauna, Al'kali ya kalli barista Kamal yace "barista Kamal ka kiyaye," barista yace "nagode ya mai girma mai shari'a, yana gama fad'in haka ya sake kai dubanshi kan Amir yace "meyasa baka bayyanawa Amira soyayyarka ba tun suna da rai sai da kaga sauran samarinta basa raye sannan ka nuna kana sonta?" Amir yace " tun lokacin ina sonta abinda yasa ban bayyana mata komai ba saboda naga kamar hankalinta yana kansu shiyasa ni na dannewa zuciyata," Barista Kamal yace " to nagode malam Amir, ya juya kan Amira yace saura ke Amira, kiyi mana bayanin yanda ala'kar Sadeeq da Abdul da Amir take da kanki," nan Amira ta koro bayani tiryan-tiryan, bayan ta kammala bayaninta sai yace " yanzu ke a tunaninki duk rashin jituwarsu d'aya zai iya kashe d'aya?" Amira tace "gaskiya a'a saboda koda Sadeeq ya rasu akace Abdul ne ya kashe shi zuciyata ta kasa yarda da hakan har yanzu, amma duba da yanayin rashin jituwarsu hakan zata iya faruwa tunda a bige akace Sadeeq d'in yake ba mamaki kokawa suka yi har takai ga faruwar haka," Barista Kamal yace " malama Amira nagode, ya juyo ya kalli Al'kali yace iya tambayoyina kenan ya mai girma me shari'a, amma yana da kyau kotu tai duba da wasu abubuwa, Amir da kansa yace ya dad'e yana 'kaunar Amira, amma meyasa be sanar da ita ba tun a lokacin ai mace allura ce cikin ruwa me rabo ke d'auka, Abin lura kawai anan shine yasan tunda hankalinta yana wajen su Sadeeq shiyasa ya dakatar da sanar da ita sai bayan ya cimma manufarsa na kashe su sannan ya zama ba wanda take tare dashi zai sanar da ita yasan a lokacin shawo kanta bazai mishi wahala ba kuma babu wani wanda zai yi takara da shi, iya abinda zan iya cewa kenan ya mai girma mai shari'a." Al'kali ya d'an yi rubutu a takardar da ke gabansa, sannan ya d'ago kai ya kalli Barista Yasmeen yace "ko lauyar wanda ake 'kara tana da 'karin bayani ko hujjoji da zata gabatar a gaban kotu, ko tambaya da zatai wa su Amir?" Barista Yasmeen ta mi'ke sannan tace "eh ya mai shari'a ina ro'kon kotu da ta kira sani aboki ne ga su Sadeeq da Abdul, da kuma k'awar Amira guda d'aya, me suna preety sai d'aya daga cikin 'yan makarantar me suna Yusra wadda ba 'yar depertment d'insu bace," aka kira duk wad'anda ta lissafo suka fito suka tsaya a gaban kotu, nan tabi d'aya bayan d'aya tana tambayarsu halaye da d'abi'un Amir da yanayin mu'amalarsa da mutane, suka bata amsa da cewa shi mutum ne me kirki na gari baida abokin fad'a kuma baida hayaniya, sannan baya bari ko wanene yaci zarafin mata a gabansa, bayan sun gama koro bayani ta sallame su, sannan ta kalli Alk'ali tace " ya mai girma mai shari'a daga malamai har d'aliban makarantar kaf da za'a tara su a tambayesu abubuwa game da Amir tabbas duk amsa d'aya za'a samu wajensu cewar shi mutum ne na gari me kyakkyawar mu'amala da kowa, sannan ba abinda yasa a gaba sai karatunsa," ta 'karasa wajen su Amir da Amira tace "malam Amir meyasa kowa ke yabon halayenka," Amir yace " saboda kowa nawa ne, bana wula'kanta kowa dan bansan ranar da zasui min ba a nan gaba," Barista Yasmeen tace "wannan haka yake Amir halin mutum jarinsa gashi yau mutane fiye da daruruwa suna bada shaidar halayenka na gari sai ka gode wa Allah, malam Amir inaso ka fad'awa kotu da yaushe kuka gama wasan tseren da kukayi da su Sadeeq da Amira, ina ka tafi kai tsaye, da ina da ina kaje a wannan ranar, kuma kana ina a daren ranar da aka kashe Sadeeq? Amir yace "gaskiya na manta tym d'in da muka gama wasan tseren, daga nan kai tsaye gida na wuce na kwanta saboda bana jin dad'i, kuma a ranar tunda na dawo daga makaranta na shiga gida banje ko'ina ba ina gida kwance ko sallolina duk a gida na yi su," Barista Yasmeen ta kalli Amira tace "malama Amira na dawo kanki, yaushe kuka fara soyayya da Amir?" Amira tace "an kwana biyu gaskiya, zamu kai wajen shekara d'aya da rabi tare," Barista tace "nasan a iya wannan dad'ewar kin fahimci wanene Amir hakane?" Amira tace "eh sosai ma," Barista tace " kin karanci yana da wasu mugayen halaye, kuma a tunaninki Amir zai iya iya kisa?" Amira tace "gaskiya baida wani mummunan hali ko guda, kuma bana tunanin Amir ko kyankyaso wannan zai iya kashewa balle mutum," Barisata ta kalli Amir tace da gaske sai da su Abdul suka rasu ka bayyanar da soyayyarka ga Amira? Amir yace "eh hakane." Barista Yasmeen ta kalli Alk'ali tace " ya me girma me shari'a wannan kotu me adalci tai duba na tsanaki kan Amir da Amira bayanai sun nuna basa nan lokacin da aka yi kisan kuma munyi bincike mun tabbatar da gaskiyar su in ana son tabbatarwa a tura jami'ai su sake zuwa suyi bincike akai, sannan Amir duniya ta shaida mutumin arzi'ki ne ta yiwu ya sadaukar da soyayyarsa ne a lokacin domin samar da farin cikin wasu, mutum ne shi mai damuwa da damuwar wasu yafi so akan komai shi ya rasa wasu su samu, hatta lakcarori da d'alibai mun d'auko bayanan su kan halayen Amir da suka bayyana mana gasu a tare da ni, sannan a baya anyi wannan case d'in a wata kotu An tabbatar da Amir ne yai kisan saboda ga hoton yatsun shi nan a jikin wu'kar duk nazo da wu'kar da ma ita kanta takardar likita da aka tabbatar da shaidar yatsun hannunsa, ana iya 'kara gwaji domin a 'kara tabbatarwa," barista ta kwaso dukkanin takardun da kuma wuk'ar ta bayar aka mi'ka su ga Al'kali, sannan tace "ina ro'kon wannan kotu me albarka da ta kori wannan 'karar ta kuma wanke Amir tare da yin hukunci ga masu son b'ata mishi suna," tai godiya sannan ta koma ta zauna, tana zama gaba d'aya kotu ta hau yi mata tafi, Al'kali ya tsawatar aka yi shiru sannan ya yi d'an rubutu, daga 'karshe ya d'ago yace "duba da yanayin lokaci mun d'aga sauraren wannan shari'ar sai sati mai zuwa, kuma a ranar zamu k'ar'kareta insha Allah," daga haka Al'kali ya buga guduma ya tashi ya fita sannan kowa aka watse d'aya bayan d'aya. *Nima yasin cajina ya 'kare balle in le'ko muku wainar da za a toya a gaba*😜 Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 130 to 135 Bayan an fito da su Barista Yasmeen na tsaye dama a 'kofar kotun tana jiran fitowarsu, suna fitowa Amira taje suka rungume juna tare da yiwa Yasmeen godiya kan taimakon su da tayi, Amira ta kalli Amir ta nuna Yasmeen tace " 'kawata ce ita kuma aminiyata tun a makaranta, ta rigani farawa gashi kuma ta rigani kammalawa har ta samu aiki gashi muna amfana da aikin nata, Yasmeen nagode sosai ni kika taimaka a rayuwa wallahi, Allah saka miki da alkhairi, Yasmeen tai dariya, sannan tace " dukkaninmu godewa Allah zamu yi, domin shi ya bamu ikon yin nasara dan kinga wannan lauyan da ke kare masu 'kara ba'a kayar dashi a case ina ganinshi sai da naji fad'uwar gaba, amma da yake nai addu'a sai Allah yai ta bani nasara a kansu duk da dai na fishi shaidu da hujjoji, sai mu gode wa Allah," Amir ya kalleta yana murmushi yace " nagode," Insp Yahya yace "malamai sai ku wuce muje koh," Amira tace " gaskiya kam Yasmeen bari mu tafi gidanmu cell dan wallahi bacci nake ji ma ni," Yasmeen da Amir ta basu dariya sosai, suka yi sallama aka tasa 'keyarsu aka saka su a mota suka d'auki hanya. A hanyar su ta komawa gidansu cell kamar yanda Amira ta fad'i sukai ta gode wa Allah kan nasarorin da yake basu. Bayan an saka su a cell d'in ne Amir ya kalli Amira yace "malama ina da tambaya fa," Amira tace nasan tambayar, yanda aka yi na yi magana da 'kawata barista bayan ko da yaushe muna tare a gar'kame kake so ka sani koh, to kwantar da hankalinka yanzu zan fad'a maka, akwai ranar da aka kawo mana abinci har na ro'ki wanda ya kawo abincin a bani biro da littafi ya kuma bani har kana tambayata me zan yi dashi nace maka zan yi zanen lalle ne saboda ina son yin zane musamman na 'kunshi kala-kala saboda in munyi aure in ri'ka yi maka har kayi dariya, to a lokacin bayan mun ci abinci kayi bacci na rubuta wasi'ka cewa su taimakeni zan basu sa'ko su kaiwa Barista Yasmeen zan rubuta musu adress d'inta, in har suka kai min zan basu zoben hannuna wanda na siye shi 10k su siyar su ri'ke kud'in, bayan na gama rubutawa na saka a gefen farantin da muka gama cin abinci, can sai ga wani jami'i yazo d'aukar kwanikan a lokacin ne na mik'a mishi harda wasi'kar, bayan minti biyar sai gashi ya dawo yace in bashi sa'kon, yana tsaye na rubuta na m'i'ka mishi wasi'kar tare da sake yagar 'karamar takarda na rubuta mishi adress d'inta, har da lambar waya koda ya je ya tarar bata nan be sameta ba sai ya kira lambar, bayan minti talatin sai gashi ya dawo da yake ba nisa gidanta daga station d'in nan, ya shaida min ya bata har ta bashi takarda ma ya kawo min, ta rubuta cewa sa'kona ya iso gareta kuma ta karanta Allah ya kaimu ranar, na sallami d'an sandan nan ya tafi, Amir yace "ai har yanzu baki fad'a min abinda kika rubuta mata ba," Amira tace "ro'konta nayi ta taimaka min za'a kashe min miji, na bata labari a ta'kaice, sannan nai mata bayanin shari'ar da akai a baya, nai mata kwatancen kotun farko nace taje ta samo hujjojin da suka gabata a case d'in baya domin mu yi amfani dasu wajen samun nasara a case d'in, kaji yanda akai," Amir yace "lallai Yasmeen ta taimaka sosai amma ke kin fita taimakona saboda kece kika samar da hanyar taimakon, nagode Amira ta, tabbas ni da ke amana ne, kuma rabuwarmu aiki ne, Allah ya barmu tare," Amira tai murmushi, sannan tace "ameen, kai kuwa naga zan rasa masoyi ba dole in rud'e ba, koda yake ko mutuwar ne ma 'kafata 'kafarka sedai a kashemu tare," dukkan su sukai dariya. Yau litinin, kuma a yau ne suka sake halartar kotu a karo na uku domin zama na 'karshe. Bayan an karanto case d'in su Amir sai aka mi'kawa Alk'ali takardun domin gudanar da cigaban shari'ar, Al'kali ya d'an jima yana rubuce-rubuce, sannan ya d'ago kanshi ya kalli lauyoyin yace "kafin mu yanke hukunci kan wannan shari'ar ko akwai lauyan da zai 'kara cewa wani abu a cikin ku?" dukkansu suka ce "babu ya mai girma me shari'a," Al'kali yace "A bisa sauraron hujjoji da bayanan kowane b'angare, a bisa shaidun da Yasmeen ta gabatar mana na ha'ki'ka muma mun 'kara yin namu binciken mun tabbatar da gaskiyar shaidunta, saboda haka kotu ta yanke hukunci kamar haka: kotu ta wanke Amir daga zargin da ake mishi na kisa domin bashi da hannu kwata-kwata a ciki, sannan kotu ta bada izinin sake shi ya cigaba da gudanar da harkokinsa na rayuwa, kuma kotu tana gargad'in Insp Yahya kan ya ri'ka yin bincike kafin ya zartar da hukunci, karya sake bada shaidar 'karya akan abinda bai tabbatar ba, kuma karya sake turo mai laifi kotu ba tare da hujjoji bayyanannu ba, in ya sake haka to za'a hukunta shi kuma zai iya rasa aikinsa ta dalilin haka, bayan haka zai biya Amir million d'aya sakamakon b'ata mishi suna da lokaci da ya yi, da wannan nake cewa a nan muka kawo 'karshen wannan shari'ar," nan da nan Kotu ta d'auki ihu da fito saboda tsabar jin dad'i, 'yan sanda suka cire wa Amir ankwar dake hannunsa aka sallameshi, an zagaye su sai bashi hannu ake ana tayasu murnar samun nasara. Insp Yahya kuwa ya kasa motsawa daga inda yake zaune, babu abinda ranshi ke yi banda suya. Amir kuwa har sun kai bakin 'kofa zasu fita suka hango Insp, Amira ta ja hannun Amir suka 'karasa wajenshi, Amira ta kalle shi tana dariya tace " Insp Yahya sai ha'kuri fa nasan ba haka rai yaso ba, se dai ka sani cewa duk abinda Allah ya rufe ma'ana ya sirranta to babu wanda ya isa ya tone shi ya tonu, sai a d'au ha'kuri Amira da Amir dai Allah be ce yanzu zasu mutu ba tukun, sannan abu na 'karshe shine in kana so kai ka cigaba da tsira da ranka karka 'kara shiga harkarmu, in kuma ka 'ki to tabbas kwanan nan ba'kin ciki zai zama silar ajalinka," ta sa'kala hannun Amir cikin nata suka juya sukai tafiyarsu, suka barshi nan da takaicin da suka k'ara 'kunsa mishi. Insp Yahya ya dad'e zaune daga 'karshe wayar Dad tasa ya d'aga tare da mi'kewa ya fita daga cikin harabar kotun, sauran jami'an da ke kewaye dashi suka mara mishi baya. Cikin mota suka shiga suka ja, hanyar station suka nufa, Insp Yahya yaiwa Dad bayanin duk yanda shari'ar ta kaya a kotu da irin hukuncin da aka zartar a kanshi, Dad ya numfasa, sannan yace ya kwantar da hankalinshi zai biya kud'in da akace ya biyasu, kuma zasu sake d'aukaka 'kara wata kotun, Insp Yahya yace "ranka ya dad'e aikina nake tsoro kar na rasa kan wannan case d'in," Dad yace "kar ka damu, muna tare ai babu me dakatar da kai, ko an dakatar da kai zansa a maida kai, ko ka manta da matsayina na shugaban 'kasa ne, ko ka rasa wannan aikin inada wad'anda suka fishi wanda zan samar maka," Insp Yahya fa hankali ya kwanta nan da nan walwalarshi ta dawo, yaiwa Dad d'in Amira godiya sannan suka yi sallama. B'angaren su Amir kuwa suna fitowa daga kotu suka tari me keke napep suka hau sai gida, gidan Amir suka yanke shawarar tafiya da niyyar bayan kwana biyu in sun huta sai su tafi gidanta su kwaso kayanta su dawo nan gidan Amir d'in da zama gaba d'aya. Da isar su 'kofar gidan bayan sun fito daga napep Amir ya baiwa me napep d'in ha'kuri yace bari su shiga ya d'auko mishi kud'in, me napep d'in yace "ba damuwa," suka shiga Amira ta yada zango a falo, shi kuma Amir ya wuce ciki ya d'auko dubu d'aya ya kaiwa me napep yace ya bar canjin, me napep yaita godiya. Yana komawa ciki yaga Amira uwar tsabta an fara kaye kaye saboda 'kura da d'akin ya yi, shima ya wuce ciki ya cire kayan jikinshi ya bar gajeren wando da singileti ya fito suka ci gaba da gyaran gidan tare, saida suka gyara ko ina suka kuma wanke inda zasu wawwanke sannan Amira ta tura Amir toilet yai wanka, ita kuwa ta wuce kicin ta shiga shirya musu abinci, amma saboda ta gaji taliya ta dafa musu, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala ta zubo a kula ta fad'a wanka, tana jiyo Amir na fad'in "nifa yunwa nake ji zan d'ibi nawa inci kawai," Amira tace "wallahi karka tab'a min abinci, in kaci baka jirani ba wuta bal-bal," Amir yai dariya, sannan yace "Allah ya shiryeki a bayi kike magana ko, yayi kyau." Bayan ta fito suka ci abincin su suna ci suna hira har suka kammala, dai-dai lokacin sallar Azahar yayi suka yi alwala sukai sallah, suna idarwa bayan sun yi addu'o'i da nuna godiyarsu ga Allah suka kwanta abinsu ba b'ata lokaci bacci ya d'auke su. Bayan kwana biyu Amir suka je gidan Amira suka kwaso dukkanin kayanta da abubuwan da zata yi amfani dashi ta dawo gidan mijinta Amir da zama gaba d'aya. Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin walwalwa da jin dad'i. *BAYAN WATA 'DAYA* Amir zaune yake kan doguwar kujera a yayin da Amira uwar son jiki ta lafe a jikinshi kamar mage, yanata 'ko'karin d'agata tana 'kara ma'kal'kale shi, Amir yace Allah ki d'agani ko in yar dake, bakya ganin kin zama wata 'katuwa ne hatta nauyinki ya 'karu, gaskiya ina ganin zan kai ki asibiti a duba min ko mutane biyu ke danne min jiki ban sani ba," Amira tace "me kake nufi?" Amir yace "ina nufin a duba min ko ciki gareki mana," Amira ta 'kara kwanciya jikin shi sannan tace "ba wani ciki, kawai tsabar iya kiwonka ne," Amir ya bud'e baki zai yi magana kenan sai suka ji ana knoking d'in 'kofar su, nan da nan suka gyara zama sannan Amir ya bada izinin shigowa, domin su duk a tunanin su me wanki da gugansu ne yazo. Insp Yahya suka gani ya shigo shi da wani mutumi yana wurga musu wani irin wula'kantaccen kallo, ba shiri dukkansu suka mi'ke tsaye cikin sauri, Amira tace "malam me ya kawoka gidanmu?" Insp Yahya yace "kwantar da hankalinki 'yan mata, wannan ba zuwana bane ni d'an rakiya ne kawai, ya juya ga wannan mutumin yace yi musu bayani." Wannan mutumin ya kalli Amir yace "kaine Amir ko?" Amir yace "eh ni ne, lafiya?" wannan mutumin yace "sa'ko aka aikoni daga babban kotu dake gwammaja kan zargin kashe Sadeeq, sai kuma 'kararka da ake yi kan guduwa da wannan yarinyar ta kusa da kai, ga takardar," ya 'karashe magana yana mi'ka wa Amir takardar dake hannunsa. Amir yai murmushi tare da karb'ar takardar, sannan yace "ba damuwa Allah ya kaimu ranar," Insp Yahya ya dafa kafad'ar Amir, sannan yace "karfa ka ji haushina domin wannan karon ba ni na shigar da 'karar ba, me gayya me aiki ne shugaban 'kasa wato uban yarinyar da ka sace," har ya juya sai yaji Amir yai dariya, dariyar ta sakashi juyowa domin yaga me yake wa dariyar, Amir ya kalleshi yace "in kana tunanin ina tare da damuwa to wallahi ka daina, domin ni a shirye nake da ko ina za'aje domin yin wannan case d'in na dad'e da shiryawa hakan, kasan dalili? Insp yai shiru, Amir yace saboda a koda yaushe nasara a hannunmu take saboda Allah na tare da mu," Amira ta taho da gudu ta rungume Amir tare da manna mishi kiss a kumatu tace "da kyau namiji, na gode wa Allah da mijina ya zama jarumi kamar matarshi, ya daina tsayawa lusaran 'yan sanda irin wannan abun ta nuna Insp Yahya suna fad'a mishi magana son rai." Shi d'an sa'ko dama yana mi'ka takarda ya fice ya shige mota yana jiran Insp Yahya, Insp saboda 'kunci da ba'kin cikin maganar da suka dan'kara mishi da ya juyo zai fita sai da ya bige da bango suka kuwa kwashe mishi da dariya. Suna kan hanya yana tunani, can yana zancen zuci be san ya fito fili ba, fad'i yake "wai ni take cewa lusari, banda ina 'kaunarta da tuni na koya mata hankali wallahi." _(topha masu karatu kunji wata sabuwa kuma, ni Bk na mato kan Insp Yahya ashe algungumin Amira yake so ba ni ba)_😳🤔😰 Wanda aka had'osu tare da Insp d'in ya kalle shi yace "yallab'ai kai da wa kake ta magana kai kad'ai, naga kamar tunda ka fito daga gidan can ranka a b'ace yake lafiya?" Insp Yahya yace "bakomai, dama tun kafin muzo nan ina tare da damuwa kan fad'an da muka yi da wata budurwata," mutumin nan yace "ayya ashe lamari ne na so, to Allah ya dai-daita ku," Insp Yahya yace "ameen." Haka aka sake shiga kotu nan ma su Amir ne suka yi nasara, haka sukaita d'aga 'kara daga wannan kotun zuwa waccan haka akaita korar 'karar, da suka ga ba nasara sai kawai suka ha'kura, tare da tunanin wata mafitar kuma. Amir da Amira na zaune suna maganar komawarsu makaranta sai suka ji sallamar yaro, bayan ya shigo ya gaishe su, sannan ya mi'ka wa Amir wasi'ka yace "wai gashi inji Dadyn Amir da Amira yace a baka kuma gobe kuje Abuja yana son ganinku akwai maganar da zaku yi, dukkansu sai da gabansu ya fad'i jin wanda aka ambata, Amir ya karb'i takardar ya sallami yaron, sedai ya kasa bud'ewa ya karanta ya k'urawa wasi'kar ido sai jujjuyata kawai yake. _Wata sabuwa inji 'yan caca, to me Dad ya rubuto kuma?🤔_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 135 to 140 Dukkanin su sun ji tsoro da fargaba a ransu musamman ma Amir da takardar ke hannunsa amma ya kasa karantawa sai faman kallonta kawai yake yi. Amira ce tai ta maza ta zare takardar daga hannunsa ta bud'e ta fara karantawa, kawai Amir ji yayi tana fad'in "tab' Allah ba inda zamu je, ni nasan akwai abinda Dad ya shirya tunda har yake neman mu," Amir wanda jikinshi yai sanyi tun d'azu ya kalleta yace "me Dad d'in yace?" Amira tace "cewa yai wai muyi ha'kuri da dukkanin abinda ya faru, shi komai ya wuce a wajen shi, amma in har muna so auren mu ya cigaba to dole sai mun zo ya yi wata muhimmiyar magana da mu, kuma gobe yake so mu taho da sassafe, gaskiya Amir kar muje ni ina jin tsoro kaga haka yai min wayau lokacin da ina 'karama aka rabani da kai, sannan lokacin da muka je 'kauye ma ranar da muka kunna wayoyinmu cewa yai komai ya wuce muna ina, ashe so suke a gano inda muke a kama mu, ni gaskiya ban yarda muje ba." Amir ya numfasa sannan yai 'ko'karin b'oye tashi damuwar, yace "Amira ki kwantar da hankalinki, duk abinda kike bana so ki ri'ka manta matsayin su Dad a wajenki, kuma ai dama ko basu neme mu ba wata rana mu dole mu neme su, ni bansan iyayena ba tun ina yaro har na girma kuma har yanzu ina tunanin ina suke a wani hali suke ciki ban sani ba, Amira dole muje muji dalilin kiran da mahaifinki ke mana, saboda rashin zuwan ma wani 'karin laifi ne da zamu yi a wajen shi, dan haka ko da cutar da mu zaisa ayi ya zama wajibi a garemu muyi masa biyayya mu bi abinda yace, ni ba fatana ku kasance a haka ke da mahaifinki ba, fushin iyaye baya haifar da komai wallahi sai lalacewar rayuwar mutum, kuma ni ba zan so rayuwarki ta lalace ba ta sanadina, kullum tunanina dama taya zan shirya ki da mahaifinki, kiyi ha'kuri ki amince muje kinji?" Amira ta numfasa tare da goge hawayen da ke idanunta, sannan tace "ko ada bana iya yiwa maganarka musu balle a yanzu da ka zama miji a gareni, Allah ya kaimu goben, kuma ina godiya a gareka da kyakkyawar tunatar da ni da kayi kan darajar iyayena, tabbas so kan makantar yakan sa kayi kuskure ko ka manta da komai, amma in kai sa'ar masoyi na gaske kuma nagari koda yaushe 'ko'karinsa yaga ya saka a hanya, saboda ranshi zai sosu a duk lokacin da aka nuna ka akace yau kai ne ka aikata ba dai-dai ba, wallahi ina alfahari da kai, kuma ka 'kara shiga raina fiye da ko yaushe." Nan da nan suka saki ransu tare da cigaba da hirarsu cikin nishad'i da walwala. *WASHE GARI* Washe gari kamar yanda aka umurcesu da sassafe suka tashi suka shirya, sun sha ankon shadda, Amir riga da wando da malum-malum, Amira kuma doguwar riga ce a jikinta tasha aiki me d'an karen kyau da tsada, bayan sun gama shiryawa suka d'auki hanya, kuma da yake basu da wadatattun kud'i a hannunsu na tafiya a jirgi sai suka tafi a motar Amira wadda ita kad'ai ce ta rage musu a yanzu, domin sun yar da ta Amir lokacin da suke gudun cetan ransu, yanzu in za'a kashe su basu san inda motar take ba. Sun d'auki awanni anata tafiya har Allah ya kawo su garin Abuja lafiya, da yake motar tasu ce ba ta haya ba kai tsaye gidan shugaban 'kasa wato Dad mahaifin Amira suka wuce. Suna shigowa cikin unguwar tun daga nesa suke ganin adon furanni da busa da kad'e-kad'e kai kace gidan saraki, ana bud'e gate kuwa zasu kutsa da motarsu aka fara antayo musu fulawoyi har zuwa inda zasu faka motarsu, cikin sauri aka bud'e musu mota suka fito, sakin baki suka yi suna kallon yanda aka k'awata harabar gidan da kyawawan ado, mahaifiyar Amira da Dad d'inta da su Uncle kai har da sistern ta d'iyar Uncle d'in suna tsaye a bakin 'kofar da zata sadaka da shiga ciki, da gudu Amira ta 'karasa wajen Dad d'inta ta rungume shi tana kuka tare da fad'in "Dad dan Allah kayi ha'kuri ka ya......" kafin ta 'karasa Dad ya rufe mata baki tare da d'agota ya share mata hawaye, sannan yace " na yafe miki Doughter nah, kinsan ina sonki bana iya yin fushi dake," ya kama hannunta sannan ya yafito Amir da ya zuba musu idanu da hannu, yana zuwa shima ya ri'ke mishi hannu suka yi musu barka da zuwa sannan suka yi musu jagora har cikin babban falon gidan. Dad kuwa in ka ganshi a wannan ranar zaka ce ba shi bane, saboda yanda yake ta bayyanar da farin cikinsa kamar wani abu bai tab'a faruwa ba. Bayan an ci an sha, sannan suka dawo babban falo suka zauna, Dad yai gyaran murya sannan ya fara magana "abinda yasa na kira ku shine saboda in sanar da ku cewa komai ya wuce, kuma hatta aurenku mun yarda dashi, amma akwai sharad'i, saboda matsayina da kuma martabar gidan nan dole sai ka kawo mana iyayenka nan mun gansu, kuma daga yau har zuwa ranar da zaka gano inda iyayenka suke a nan gidan zaku cigaba da zama, in yaso in ka gabatar mana da su sai ka d'auki matarka ka tafi da ita ma duk inda zaka tafi da ita, rashin yin hakan zai sa da kai da wad'anda suka yi muku jagora wajen yin aure zan makaku a kotu a raba aurenka da 'yata kuma kasan tsab za'a raba d'in tunda ba mu muka d'aura ba kuma ba da yardarmu ba." Mugun tashin hankali suka shiga daga shi har Amira, babu abinda zuciyarshi ke ayyana mishi game da wannan maganar illah anyi haka ne domin a rabashi da Amira, in ba haka ba ta ina zai fara neman iyayenshi. Irin tunanin da yake itama Amira shi take yi, cikin sauri ta mi'ke tana fad'in "haba Dad, be kamata ka....." Dad ya d'aga mata hannu tare da fad'in "ya isa Doughter, ni mahaifinki ne, a baya mun barku kun yi yanda kuke so, a yanzu dole ku barmu muyi namu binciken a matsayinmu na iyaye, kuma na gama magana," ya mi'ke yai shigewarsa d'aki. Uncle ya numfasa, sannan yace "gaskiya Amira ki rage yiwa mahaifinki musu a kan namiji da bashi da tabbas, kuma in kina canza halinki ta hanyar bijirewa maganar iyayenki to shi zaki jawa tsana a idanunmu, a yanzu kam ina goyon bayan maganarshi, sai kuje kuyi tunani, d'akinki shine masaukin ku an gyara ko ina, shikenan kowa ya tashi ya tafi an gama meeting d'in." Haka kowa ya watse ya barsu a nan falon, shi kuwa Amir tunda yaji wannan maganar ya zama kamar gunki ya kasa motsi, babu abinda ke mishi yawo sai maganar Dad. Amira ta matso inda yake zaune a 'kasan kafet, ta share mishi Hawayen da ke zubowa kan fuskarshi, sannan ta mi'ke tare da kama hannunshi ta jashi suka hau sama haka yaita binta kamar ra'kumi har suka shiga d'aki. Amira ta zaunar da shi sannan ta fad'a jikinshi ta fashe da wani irin kuka, shima kukan yake tare da 'kara rungumeta yana fad'in "wallahi Amira banso na rasaki, a ina zanga iyayena in kawosu kar a rabani da ke," ya sake fashewa da kuka kamar 'karamin yaro. Amira tana rungume dashi itama tace "abinda na gudar mana kenan tun farko Amir d'ina shiyasa nace kar mu zo, ni nasan so ake kawai a rabamu shiyasa aka b'ullo da wannan maganar. Amir ya sake 'kan'kameta kai kace saceta za'ai, yace "Amira 'kaunarki itace bugun numfashina, sonki shine *Mahad'in rayuwata* ana rabamu numfashina zai tsaya ya daina aiki, dan Allah karki yarda a rabamu, Amira bansan iyayena ba ta ina zan fara." Amira cikin kuka itama tace "Amir d'ina babu mai rabamu sai Allah, shi kad'ai zai iya rabamu domin shi ya nufemu da had'uwa, to me zaisa ka damu tunda muna da tabbas akan yana tare da mu." A ranar dai haka suka kwana ba bacci musamman Amir, gwara Amira rashin baccin Amir d'in shi ya dakatar da nata, dan har ta fara baccin, minti biyar da farawarta ta farka ta ganshi a kan dadduma yana addu'a yana rusa kuka, dole ta ha'kura da baccin, kuma tai 'ko'karin danne nata damuwar domin kwantar mishi da hankali. haka Amira ta kwantar da Amir a jikinta kan cinyarta taita rarrashinsa, har Allah yasa bacci yai awon gaba da shi, Amira ta 'kura mishi ido, wani irin tausayinshi yana 'kara ratsa zuciyarta, tunani take yi, ita kanta ta san Amir na yi mata so na ban mamaki, tasan a yanzu tashin hankalinsa da kuma damuwarsa da dalilin kukansa shine ina zaiga iyayensa kar a rabamu, duk duniya babu abinda yake tsoro sama da duk wani abinda zai rabamu, hawayen idanunta ta share tana cigaba da kallonsa, 'kaunarsa na 'kara ratsa ko'ina na jikinta. Haka Amira ta kwana a zaune bata runtsa ba, ta kasa koda 'kwa'k'kwaran motsi saboda kar baccin Amir d'inta ya yanke. Sai da Asuba ta tashe shi suka yi Alwala sukai sallah a tare, bayan sun idar tare da yin doguwar addu'a, sannan Amira ta kwanta, Amir kuwa yana zaune kan dadduma zai fara sana'ar tasa wato tunani sai tai sauri ta sa hannunta ta jawoshi ya kwanta kusa da ita, fuskarsu tana fuskantar juna, Amira tace kai bacci karna sake ganinka kayi tunani banso, yanda ta b'ata rai da yanayin yanda tai maganar yasa Amir yin murmushi, Amira tace "yauwa ko kai fa, nafi so fara'arka ta dawo dan baka kyau sam in ba walwala a fuskarka," suka koma bacci abinsu. Washe gari wajen 'karfe goma suka tashi, suka tarar har an shigo musu da abin karyawa, Wanka suka yi da wanke baki, sai da suka shirya tsaf sannan suka zauna karyawa. Bayan sun gama karyawa Amir yace su sauka suje su gaishe da su Dad, tace "to," suka mi'ke lokaci d'aya a tare, Amira taji dad'i a ranta yanda taga Amir na daraja iyayenta duk da kora da halin da suka yi mishi jiya, kuma taji dad'i yanda taga ya fara sakin ranshi. Sun taki sa'a kuwa suna falo dukkansu, suka bisu d'aya bayan d'aya suka gaishe da su. Bayan sun gama gaisawa Dad yai gyaran murya sannan yace "Amir kayi ha'kuri kar kaji haushina kan hukuncin da na yanke a kanka, matsayinmu na iyaye wajibi ne muyi bincike kanka kuma mu san wani naka, in kayi tunani kai kanka gata nai maka, kuma kaga nima mutuncina be zube ba matsayina na shugaban 'kasa, kasan zab'e ya kusa 'yan adawa kad'an suke jira su b'ataka a idon jama'a." Amir yace "wallahi ko kad'an banga laifinka ba Dad, kowane uba hukuncin da ka yanke shi zai yanke, kuma muna 'kara baka ha'kuri kan abinda suka faru a baya dan Allah ka yafe mana, kuma nagode da damar da ka bani, kuma daga yanzu ma zan fara 'ko'karin nemansu insha Allah." Dad yace "ai tuni na yafe muku yarona, Allah ya taimakeka, duk taimakon da kake nema kar kaji nauyin tambayata ko ka sanar da Amira ta fad'a min, Allah yai muku albarka," dukkansu suka ce "Ameen." Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 140 to 145 Suna gama magana yai sallama da su kan zai tafi ya fara bincike akan asalin nashi, Amira ce ta d'ago kai cikin sauri ta kalle shi tana mamaki, domin ta san ita basu yi wannan maganar ba a d'aki, yanzu ya 'kir'kiro da ita, suna had'a idanu ya fakaici idanun mutane yai mata murmushi tare da gwalo a lokaci d'aya. Tashi yai dukkansu suka yi mishi fatan alkhairi, ya kama hanya ya fice daga gidan. Yana fita ya d'auki hanya Amira itama ta haye sama ta d'auki wayarta tare da antaya wa lambarsa kira, har ya fita daga gidan gaba d'aya ya fara tafiya yana tunani da mamakin bataliyar security da aka 'karo, yasan ba akan komai bane sai a kansu shi da Amira, yana cikin wannan tunanin ne yaji wayarsa tana bada sautin 'kara me d'an karen dad'i, murmushi yayi domin yasan me kiran tunda ita kad'ai ya sakawa wannan ringing tone d'in, ciro wayar yayi, sannan ya d'aga tare da karata a kunne. Kafin yai magana ta balbale shi da fad'a, " yaushe muka yi maganar zaka fita daga zuwan mu zaka fita wani yawonka da sunan yin bincike, in ba yawo ba ina zaka je wa zaka tambaya, to wallahi kar kaga kai mijina ne zan iya hukuntaka, kuma ko yanzu ba 'kyaleka zanyi ba, ba zaka ci abincina ba, kuma ba zaka ga walwalata ba, kuma sai kayi tsallen kwad'o," tana gama fad'in haka ta katse wayar, Amir ya kwashe da dariya domin shi maganarta dariya suka bashi, ya maida wayarsa aljihu ya cigaba da tafiyar shi. Yana cikin tafiya yaji message ya shigo, yana dubawa yaga Amira ce, cikin sauri ya duba. _Na duba harabar gidan naga motata tana nan baka fita da ita ba, ka dawo ka d'auka banson tafiyar 'kasa malam ko cemaka aka yi bana kishinka, kuma wallahi ka ri'ke min amanar kanka, duk macen da ta kalleka ka mareta ni na saka._ Amir ya ci dariya kamar me, sannan ya dawo dolen shi tunda basa musa wa junan su, ya d'auki motar ya tafi, yana cikin tafiya yana tuno da diramar matarshi shi kad'ai yana dariya. A haka ya kasance cikin walwala da farin ciki har Allah ya kawo shi inda zai zo. Ya bud'e 'kofa zai fito ya sake jin wani 'karar message d'in, ya fito da wayar ya duba _Duk da ina fushi da kai ban isa hana zuciyata kewa da tunaninka ba, nayi kewarka mijina._ _'Kalubalenku mata ma'aurata, ni abinda ke d'auremin kai da wasu matan auren shine dan girman Allah in baki samar wa da mijinki farin ciki ba a lokacin da yake cikin gida da kuma idan ya fito wa kike so ta bashi? anya kina iya nunawa mijinki kin damu dashi, kina gwada mishi so da 'kauna kuwa koda ace kina fushi dashi ne? to ai bari kuji hikimar yin hakan shine in har kina yin hakan to wallahi tunaninki a ransa ba zai tab'a barinsa ba, ko mata dubu ya aura sai kin fita daban a cikinsu, saboda kulawarki takice ke d'aya babu kishiyar da zata kama 'kafarki, ga dai Amir nan ya fito kamar zararre a mota sai dariya yake, wacece sanadi? matarsa, to da a 'kasa ya taho yasin d'auka za'ai mahaukaci ne, haka ya kamata ki zauta shi ya zama baida wani sauran tunani sai naki, Allah yasa mu dace._ Amir ya dakata da fitowa daga motar ya fara bata amsa kamar haka. _Amanarki na ri'ke Amirata, kuma kema kinsan duk halin da kike ciki dole nima in tsinci kaina a ciki, domin kuwa zuciyoyin mu a had'e suke, gangar jikina ne kawai bata tare dake, amma zuciyata tana wajenki, domin kuwa tunaninki take, ki kular min da kanki kinji, bazan dad'e ba zan dawo gareki ko zuciyata ta huta daga tunani da kuma kewarki, ina sonki,_ _daga mijinki AMIR._ Yana gama rubutawa ya tura mata, sannan ya fito daga motar, unguwar yake kallo, tare da 'karewa gidan da ya taso rayuwa a cikinsa, ba ko wane gida bane illah gidan da wannan mutumin ya ri'ke shi, yasan Allah yai mishi rasuwa, amma yazo tambayar ma'kwabtansa ne da abokansa ko Allah zaisa ya samu wanda ya san daga inda ya fito. Amir ya fara da wani shago dake kusa da gidan, da sallamarsa ya 'karasa shagon, me shagon wani dattijo ne ya amsa mishi, dattijon nan abokin mari'kinshi ne, shiyasa yazo wajen shi ko yana da wani labari a kansa. Bayan sun gaisa Amir yace "Baba ka gane ni kuwa?" Baba yace "a'a yaro, ban shaida ka ba," Amir yace "Amir ne yaron marigayi me can gidan," ya nuna mishi gidan da hannu. 'Dan tsohon nan ya zaro idanu, sannan yace "wai kana nufin Ameeru ne wannan a gabana?" Amir yai murmushi, shi sam yama manta sunan shi Ameeru a da, yace " eh ni ne Baba," Baba yace "Allah mai iko, Ameeru kai ne ka zama kyakkyawan bature haka," Amir yai dariya, nan suka sake sabuwar gaisuwa, sannan Amir yai gyaran murya yace "Baba akwai abinda ke tafe dani wajenka," Baba yace "to ina jinka Ameeru, Amir yace "zuwa nayi inji ko kasan wani abu game da labarina, ina nufin inda mari'kina ya sameni, ko kuma ajiyata aka kawo mishi?" Baba yai shiru yana tunani, can sai yace "eh to gaskiya ni a yanda yace min lokacin da na ganshi da kai a hannu na tambayeshi, cemin yai tsintarka ya yi, se dai har ga Allah ban san a ina ya tsinceka ba," iya abinda ya samu kenan wajen Baba, haka ya gama binciken shi a unguwar nan amma babu wani abu da ya 'kara samu, hakan yasa ya wuce station ya shigar da 'korafi kan ya rasa iyayensa tun be san kanshi ba, yanzu shekaru talatin kenan, koda wasu sun zo neman d'ansu a kirashi ya gansu, duk wata station da take wannan garin sai da yaje ya shigar da wannan bayani, tare da rarraba lambobinsa koda za'a nemeshi, sannan ya juyo kan motarshi zuwa gida jiki a sanyaye. Yana zuwa bakin 'kofar gidan yai hon aka bud'e mishi ya shiga, kai tsaye wajen fakin ya wuce ya faka motar sannan ya kasheta ya fito ya shiga cikin gida. Be tarar da kowa ba a babban falo, hakan yasa kai tsaye ya haye sama, ba kowa a d'akin nasu, ko'ina ya duba Amma Amira bata ciki. Wayarshi ya ciro ya kira wayarta yaji tana ina, Amira kuwa tana sashen mahaifiyarta tana zuba mata shagwab'a, wayarta taji tana 'kara kuma tasan wanda ke kira, saboda itama ringing d'in kiran shi daban ta saka, bata d'aga ba mi'kewa kawai tayi tace wa Mummyn ta hira ya 'kare bari ta koma d'aki. Mummy tace "oh Allah ya kawomu zamani mijinki ya dawo ya kiraki a waya kin tashi da rawar jiki zaki tafi," Amira ta turo baki sannan tace "ya akai kika gane shi ya kira?" Mummy tace "yanayin zumud'in da kika nuna yanzu mana," Amira tayi dariya sannan tace "kaji Mum dai kema fa tunda nai wayau ban tab'a ganin Dad ya shigo ya wuce d'akinshi kuma ki cigaba da zama wajenmu ba, in dai yana gida to kema a koda yaushe kina wajenshi, idan mun ganki to baya nan ne, nima yasin dan bayanan ne yasa kuka ganni," tana kai nan a maganarta ta danna a guje ta fice daga d'akin. Mahaifiyarta kuwa salati ta hau yi, tace kaga ja'irar yarinya ta samin ido ni da mijina," matar Uncle d'insu kuwa dake zaune tana jin duk abinda Amiran tace dariya take ta yi. Amira da d'aurewarta ta shiga d'akin tana cin magani ita a dole tai fushi, kuma tana shigowa kusa dashi ta samu waje ta zauna, jin yai shiru be ce mata komai ba yasa ta d'ago ta fara satar kallonshi, tunani yake sosai idan ma ance be san ta shigo ba ba musu. Nan da nan Amira ta warware ta nemi fushinta ta rasa, fuskarta ta koma bayyanar da yanayi na damuwa, 'kara matsowa kusa da shi tayi, tare da dafa kafad'arshi tana jijjiga shi cikin damuwa tace "Amir d'ina lafiya, meke faruwa na ganka cikin wannan yanayin, dan Allah ka fad'amin meyafaru?" Amir yai firgigit, sannan ya numfasa, ya kalleta yace "Amirata kin shigo ashe, wallahi Amira nayi yawon amma ba nasara," ya kwashe komai ya fad'a mata har yanda suka yi da tsohon nan. Amira ta numfasa sannan tace "shine kabi duk ka d'aga hankalinka, bayan kuma kasan idan ka shiga damuwa ina finka shiga tashin hankali, haba Amir d'ina dan baka ga iyayenka ba sai akace maka mun rabu kenan, ina lura da kai tunda Dad yai wannan maganar ka shiga damuwa, ni nace maka zan barka ne, fad'in Dad ne kawai kaima ka sani, amma duk wuya duk rintsi ina tare da kai, babu abinda zai rabamu insha Allah, ka kwantar da hankalinka ko me za'a yi, kuma ko menene zai faru se dai ya faru amma ban tab'a rabuwa dakai, ban tab'a juyawa soyayyarka baya. Cikin 'kan'kanin lokaci sai da taga ya dawo asalin Amir d'inta sannan hankalinshi ya kwanta itama ta samu natsuwa, ta had'a mishi ruwa yai wanka sannan ta shirya mishi abinci a gabanshi ya zauna zai fara ci, ya Kalleta yace "wai ina fushin da kike yi dani ya tafi, har abinci fa akace baza'a bani ba," Amira ta turo baki sannan tace "ya za'ai in kula wani fushi na ganka cikin yanayi na damuwa, ni nama manta," haka sukaita hirar su cikin jin dad'i. Haka Amir yaita sintiri kullum amma ba wani labari, har cikin 'kauyukan garin ya shiga yana bincike amma shiru har yanzu, har wajen wata uku yana zirga-zirgar neman bayani akai amma shiru. Yau lahadi, kamar kullum yau ma Amir ya shirya tsab domin fita cigaba da neman 'karin bayani kan wanene shi kamar yanda ya saba, bayan ya shirya tsab ya kalli Amira yaga yanda ta had'e rai, yai murmushi sannan yace "wai ke dan Allah meyasa duk in zan fita sai kin b'ata rai ne," Amira ta 'kara turo baki sannan tace "saboda rashin sabo mana," Amir yace ai kuwa ya ci ace kin saba mun shiga wata na uku ina fita fa," Amira ta 'kara turo baki sannan tace ni bazan saba ba, ni yasin yau binka ma zanyi," Amir yace "kiyi ha'kuri yau waje d'aya zanje in dawo bazan dad'e ba insha Allah." Da 'kyar ta barshi ya fito ya shiga mota ya fice daga gidan, cikin 'kauye ya nufa, yana cikin tafiya wata babbar mota ta taho da gudu, duk yanda yaso ya kauce mata ya yi amma ya kasa, sai da tabi ta kanshi motar Amir ta hantsila can gefen ti-ti, cikin sauri masu babbar motar suka fito suka ga sam ba alamun numfashi a tare da Amir, d'aya daga cikin su yace "baya numfashi wallahi mui ta kanmu," ai kuwa su duka ukun suka fad'a mota suka jata da gudu suka bar wajen. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 145 to 150 Da yake ba cikin gari bane motoci d'ad'd'aiku ne suke wucewa kan hanyar, kuma ikon Allah duk wanda yazo kai tsaye yake wucewa babu wanda ya tsaya saboda ba wanda ya kawo akwai mutum a ciki, sedai in zasu wuce daga cikin motar kaji ana cewa kai amma an gwabza hatsari anan Allah ya kiyaye gaba, sai su wuce abinsu. ………………………………… Ahmad da matarsa Khadija tafe suke a kan hanya, Ahmad yana tu'ki yana yiwa matarshi fad'a yace "wai Hauwa sai yaushe ne zaki cire tunani ne daga ranki, kinsani fa sarai abinda tunani ke haifarwa ko so kike nai rashinki? dan Allah ki daina tunanin nan zuwa yanzu yaci ace kin.........." kasa 'karasawa yayi sakamakon ganin mota a tuntsire, kuma daga gani wannan had'arin be dad'e ba dan ba alamun hakan, ya kalli matarshi yace "kin kuwa hango abinda nake gani a gabanmu? hatsari aka yi, kuma ni kamar ma hannun mutum nake hangowa bari inje in duba," cikin sauri matarsa Hauwa ta ri'ke shi, tace "nifa tsoro nake ji, kasan yanda duniyar nan ta zama, ba mamaki ma 'yan fashi ne," Ahmad yace "kai bana tunanin haka gaskiya, koma dai menene zanje in duba, Allah yaga zuciyata, ba zai bari su cutar da ni ba." Yana gama fad'in haka ya fita daga motar ya tunkari wajen wannan motar da suka gani, yana zuwa ya le'ka ciki ai kuwa mutum ne ya gani a ciki yaro matashi kanshi na fitar da jini, duk yaji ciwo a jiki, kuma babu alamar numfashi ko kad'an a tare dashi. Cikin sauri ya fara 'ko'karin neman hanyar da zai fito da shi, da 'kyar Allah ya bashi sa'a ya fito dashi daga ciki. Matarshi kuwa koda ta hango abinda ke faruwa ta glass d'in motar ta fito cikin sauri ta tunkaro wajen, 'kokarin kamashi suka yi suka sa a mota sannan suka tafi asibiti, a hanya matarshi 'korafi take ta yi tana fad'in kaga amfanin securitys da jami'ai ko, amma kai in za'a fita sai kace baka so suna binka, yanzu gashi nan ai kana komai da kanka, kai kasan ma'abocin taimako ne, kai na talakawa ne, be dace ace baka fita da kowa ba sai mu kad'ai." Ahmad yai murmushi yace "idan bu'katar hakan ta taso ina nemansu ai, ni dai kawai bana so suna bina a baya gaskiya, ba burina duk inda na fita aga jerin motoci suna kewaye da ni ba, nafi so in ri'ka fita ni kad'ai, bana son duk wani abu da zai yi silar saka min girman kai da d'agawa ya jawo in nisanci talakawa na." Asibitin suka 'karaso shiyasa ya dakata da maganar, cikin sauri suka fito, aka kira norses aka d'aukeshi kamar matacce aka shiga dashi cikin emergency. Khadija ta kalli mijinta Ahmad tace "Allah sarki Allah kad'ai yasan halin da iyayensa suke ciki a yanzu, kyakkyawan yaro dashi," nan da nan 'kwalla ta taru a idanunta tana nema tai kuka, Ahmad ya 'karaso kusa da ita, sannan yace "zaki fara ko, kina farawa nima zan tayaki wallahi kuma kinsan zan iya, yanzu kiga kukana ya tara miki jama'a domin kinsan kukan namiji akwai tada hankali saboda an san ba 'karamin abu bane zai saka maza yin kuka." Khadija ta share hawayenta tare da yin murmushi, shima Ahmad murmushi yayi, sannan ya ciro wayarshi ya kira jami'ai ya sanar dasu hatsarin da kuma inda abun ya faru domin suje su gudanar da bincike a san daga ina yake a nemo iyayensa a had'ashi da su. Bayan wasu lokuta sai ga likita ya fito ya tunkaro su yana yarfe gumi, Ahmad ya kalle shi yace "mun yi 'ko'karin tsayar da jinin dake fita daga kanshi, kuma duk raunukan da yaji an wanke wurin an saka magani, se dai ya yi muguwar buguwa, kuma kunsan hatsari irin wannan sai an yi gwaje-gwaje domin gane dukkanin inda suka samu matsala a jikinsa, saboda haka zamu cigaba da kula da shi, da bashi agajin gaggawa bari in koma wajenshi." Bayan wasu awanni sai ga jami'ai sun shigo asibitin, da zuwansu suka 'kame domin girmamawa, daga nan babban cikin su ya shiga korawa Ahmad bayani cewa sunyi bincike a motar amma ba abinda suka samu wanda zai basu shaidar da suka samu, sai wata takarda da aka rubuta wanene ni da manyan ba'ki, sauran rubutun na 'kasa kuma adress ne," yana gama magana ya mi'ka mishi takardar. Suna cikin magana Doctor ya fito da sauri ya nufosu yana fad'in "yallab'ai jikin shi yai tsanani gaskiya mun yi iya 'ko'karin mu abun yafi 'karfinmu, a shawarce zaifi kyau ku wuce dashi india kawai tunda yanzu garin ya waye da sauran lokaci, akwai wani 'kwararren likita da zan tura ku wajen shi a duba shi a can. Ahmad yace "ok to hanzarta ka sallame mu, sai mu tafi, ya kalli matarsa yace "kije su kai ki gida sai mu wuce ni da shi," Khadija tace "hidimomin dake gabanka fa wa zai yi maka, ai gwara ka tura shi su tafi da wani cikin amintattun yaranka." Ahmad ya dafe kai yace "af ni nama manta shaf wallahi, amma ai duk abinda ke gabana zan ajiye shi domin ceton rai domin yafi muhimmanci, ke dai kawai kice bakya so nai nesa da ke ai na ganoki tsaf, dukkan su sukai dariya, yace amma bari na kira Aleey su tafi tare daga baya mu sai muje," ya d'aga waya ya kira Aleey ya fad'a mishi yazo yanzu yana son ganinshi, kuma yazo da shirin tafiya india, bayan sun gama waya yai kiran wani d'aya daga cikin shugaba na jirage da ya sani ya tambayeshi ko akwai jirgin da za'a samu yanzu wanda zai tafi india, ya shaida mishi akwai amma suyi sauri su 'karaso kafin jirgin ya d'aga dan lokaci ya kusa bai fi minti talatin ba. Ahmad yana gama waya a dai-dai Doctor ya gama had'a musu komai har an fito da Amir d'in, Aleey ya shigo cikin sauri rungume da 'yar jakarshi, babu b'ata lokaci gaba d'aya suka rankaya filin jirgi, already Ahmad ya riga ya bada izinin a tanadar da wajen zaman mutum biyu, hakan yasa suna zuwa basu wani b'ata lokaci sosai ba suka shige Ahmad na 'kara jaddadawa Aleey ya kula da Amir, kuma da sun je ya siya layi yasa ya kira yai musu magana domin su ga lambar su ri'ka kira suna jin halinda suke ciki, daga nan suka yi mishi sallama, da yake lokacin tashin jirgin ya yi, hakan yasa su Ahmad suka shiga motarsu suka juya domin komawa gida fitar da suka yi niyya ta rushe, dama amininsa zai kaiwa ziyara, amma ko ba komai fitarsu a ranar alkhairi ne, kuma sun samu ladan taimako. Ahmad ya kalli matarsa yace "kalli wani rubutu kuma da ya yi a bayan takardar, wai be san iyayensa ba ta ina zai fara, kuma a haka daga gani d'an gata ne yana cikin daula," khadija ta karanta, sannan tai murmushi tace "my love kenan, ai tana iya yiwuwa ba tashi bace takardar," Ahmad yace "hakane, to koma dai menene mu jira ya dawo muji komai daga gareshi, fatanmu dai Allah ya bashi lafiya," matarsa Khadija tace "Ameen." ………………………………… B'angaren Amira kuwa kamar kullum yau ma bayan fitarsa ta fito ta tafi d'akin Mummynta domin yin hira, dan zama ita kad'ai zai sa tai ta tunanin mijinta, duk da ko ta shiga cikin mutane ma be canza komai bata fasa tunanin nashi, amma dai yana raguwa ba kamar tana ita kad'ai ba. Da shigarta ta fad'a kan jikin Mummynta tana fad'in "Mum na zo miki hira," Mum tace "bana bu'kata tashi ki koma d'akinki rasa kunya," Amira tace "au korata ma kike yi Mum, dan ma kin samu na zo, Allah nasan a ranki kinji dad'in ganina amma kike nuna kamar ranki be so ba, ai yau ba hira me tsawo zanyi ba Mum, yau Amir da wuri yace zai dawo, yana dawowa zan tafi," Mummy ta kai mata bugu Amira ta goce tana dariya, Mum ta kama hanyar 'kofar fita zata fice daga d'akin, Amira tace "Mum wajen Dad zaki tafi ko?" Mummy tace "wai Amira ni kakarki ce?" ta juyo tana tambayarta, Amira tace "bafa wani abu zance ba kawai zan ce miki ne in kin je kice ina gaishe shi," Mummy ta girgiza kai kawai ta fice daga d'akin. Amira ta d'auki wayarta ta shiga wajen message ta fara rubuta wa Amir sa'ko. _Na yi kewarka mijina ka dawo da wuri mu ci abincin rana tare._ Mum ce ta turo 'kofa ta dawo ta zauna, Amira sai fakaitarta take tana dariya a 'kunshe, Mum kuwa abinda yasa ta dawo saboda mugun sa mata ido da Amira tayi shiyasa ma tai saurin dawowa kar taga ta dad'e tai mata wata fassarar ta daban. Lura da hakan da Amira tayi ne yasa ta mi'ke tsaye, sannan ta cewa Mum d'inta zata je d'aki ta kwanta, Mum tace "Allah raka taki gona," Amira tai dariya sannan ta tafi d'akinta ta kwanta. Haka kawai kuma sai taji baccin ya'ki d'aukarta gabanta yana fad'uwa, tasan hakan baya rasa nasaba da rashin amsa ko ji daga mijinta, wayarta ta sake jawowa ta sake tura wa Amir sa'ko. _Adadin bugawar zuciyata ya nunku Amir d'ina, a yayin da tunaninka ya 'kara yawaita, ina fatan kana lafiya?_ Tana turawa a dai-dai an kawo musu abinci, ta aje wayar taje ta bud'e 'kofar domin ta saka key ta ciki, 'karar message taji da zumud'inta ta taho tana d'okin ganin amsar da ya bata, sedai tana duba wayar taga ashe delivering report ne, hakan yasa ta jinkirta domin ganin amsar da zai turo mata. A ta'kaice har ta dafa mishi abinci ta gama domin baya cin girki in ba na Amirarsa ba, amma ba message d'insa ba kuma kiransa, kai hankalin Amira fa ya fara tashi, dan gaskiya ko a ina yake kuma ko menene yake yi baya share sa'konninta, dole yai d'aya cikin biyu ko ya kira ko ya turo mata da amsa, in ma yana wani abun ne yana sanar da ita, hakan ne yasa hankalinta ya tashi ta d'auki wayarta domin kiransa taji a wane hali yake ciki, abunka da me rauni har ta fara hawaye, ta kira lambar tare da karawa a kunne, se dai abun mamaki jin 'karar wayarsa tayi a cikin d'akin, bin inda taji 'karar tayi, a wajen kayansa take jin 'karar cikin wata doguwar rigarsa, ta saka hannu a aljihun rigar ta ciro wayar, zaro idanu tayi tare da dafe kai ganin da gaske kuwa wayarsa ce, a gida ya barta, tace "na shiga uku! yanzu Amir d'ina a gida ya bar wayarsa," tunani ta fara yi ta yaya zata ji halin da yake ciki, a wane hali yake ciki bata sani ba, agogon d'akin ta kalla wanda ya nuna 'karfe uku dai-dai, sake zaro idanu tayi, Amir be tab'a wannan dad'ewar a waje ba in ya mugun dad'ewa biyu ya dawo cikin gida, balle wannan tun safe, kuma ya riga da ya shaida mata ba dad'ewa zai yi ba yau zai dawo. Girgiza kai ta fara yi tana surutu ita kad'ai, "Amir d'ina ba 'kalau yake ba," sai kuma ta bud'e 'kofa cikin sauri ta fita da gudu, d'akin Mum d'inta ta nufa ta fara 'kwala mata kira, "Mum! Mum!! Mum!!! Amir d'ina ba lafiya yake ba, bansan a wane hali yake ciki ba." Mum tai sauri ta ri'keta tana fad'in "kinga natsu Amira, natsu kiy min bayani yanda zan fahimta, Amira ta fashe da kuka tana baiwa mahaifiyarta labarin abinda yasa tace Amir baya lafiya, Mum d'inta ta ja tsaki, sannan tace "daga ya manta wayarsa kuma yau bai samu damar kiranki ba, to ta ina zai nemeki ga wayar a gida, kika san uzurin da ya ri'ke……………" kasa 'karasawa tayi saboda jin labarai da ake gabatarwa na wani hatsari da ya afku a kan hanya, motar da Amira ta gani ne yasa ta 'kara matsawa wajen t.v d'in domin ta tabbatar ta Amir d'inta ce, tabbas ba gizo idanunta ke mata ba motar Amir ce, kuma in ta saurari bayanin da kyau wai motar kad'ai aka gani ba'a ga mutum ba a cikinta. Kanta ne ya fara juya mata, idanunta sukai mata nauyi, ta fad'i 'kasa sumammiya. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 150 to 155 Cikin 'kan'kanin lokaci kowa na cikin gidan ya san abinda ke faruwa, Amira kuwa an yayyafa mata ruwa amma har yanzu bata farfad'o ba, nan da nan aka kinkimeta sai asibiti. Bayan an duddubata aka bata gado, likita yace su kwantar da hankalinsu, akwai abinda ta gani wanda ya mugun razanar da ita har yasa tai wannan doguwar suman, kuma ya basu tabbacin zata farfad'o. Bayan kwana uku Amira na a sume sai a ranar Allah yasa ta farfad'o, doctor ya 'kara yi mata gwaje-gwajensa, a yayin da ita kuma ba abinda take yi banda rizgar kuka, ta suma yafi a 'kirga, duk ta farfad'o in ta tuno da abinda ya faru shikenan ta rasa Amir sai ta fara kuka da magiyar a kaita wajen Amir d'inta, daga haka kuma sai ta 'kara sumewa, hakan yasa doctor ya zauna da iyayenta. Doctor ya kalle su yace "gaskiya akwai abinda yarinyarku take so, kuma in tana shiga cikin irin wannana yanayin akwai matsala, domin kuwa yanzu haka zuciyarta ta buga, a shawarce yana da kyau ku bata abinda take so," Mum ta share hawayen dake zarya kan fuskarta, sannan tace "Doctor mijinta ne ya rasu kuma ba'aga gawar ba, shiyasa ta shiga cikin irin wannan yanayin," Doctor yace "Allah sarki, Allah ya ji'kansa, to amma gaskiya yana da kyau ta daina yawan tunani, kuyi 'ko'karin samar mata da farin ciki." Sai da tai wajen wata uku a asibiti sannan ta fara samuwa. 'Bangaren Amir kuwa har yanzu be san inda kanshi yake ba, amma su likitocin sun tabbatar wai yana samun sau'ki kuma kwanan nan zai farfad'o. Ahmad ne zaune cikin kujera me zaman mutum biyu a falon su shi da matarshi Khadija suna hira, can sai Ahmad yace "naso inje india domin duba halin da wannan yaron ke ciki, gashi kuma zab'e ya kusa, cikin wannan watan ne kinsan zab'en namu, da ni da shugaban 'kasan da yake kai a yanzu, shiyasa komai ya rincab'e min, ya zama lokacina kad'an ne," Khadija ta kalle shi tace "to ka bari mana idan har aka gama zab'en sai mu tafi," Ahmad yace "kin kawo shawara mai kyau, amma a maganarki naji kamar kince sai mu tafi ko?" Khadija tace "eh mana haka nace, ai duk inda zaka tafi 'kafata 'kafarka, shiyasa ma nace karka wani sha wahalar tsayar da mataimaki, tunda gani ni zan zama mataimakiyarka kawai," Ahmad yai dariya itama matarshi tana tayashi. Amira kam se dai muce Allah ya kyauta domin kuwa komai nata ya sukurkuce, ta daina walwala, ta daina fara'a, ta daina hira da kowa, abinci ma sai mahaifiyarta ta bata a baki take ci, shima kad'an, ta dai koma kamar 'karamar yarinya, ko ta shiga cikin mutane bata walwala sam, sannan bata cewa um bata um-um, babu inda ba'a je da ita ba, babu abinda ba'a kawo mata ba domin ya d'ebe mata kewa amma ina, duk ta rame tayi ba'ki kamanninta duk sun canza, koda yaushe bata da wani aiki sai tunani, wayar Amir kuwa tana hannunta dare da rana tana duba sa'kwannin da ya tura mata da wanda itama tai mishi, munji yanda rayuwar Amira ta cigaba da kasancewa. Yau talata, kuma a yau ne aka yi za'be, yanzu kowa kawai jiran fitar da sakamako daga al'kalan zab'e ake yi, to bamu san waye kuma zai yi nasara ba, Dad d'in Amira ne ko kuwa Ahmad. Dukkaninsu gidajen nan biyu suna gaban t.v da redio suna jiran sakamako, biyar na yamma dai-dai aka fara sanar da 'kuri'un shugabannin 'kasa, inda aka tabbatar da Ahmad shine wanda ya lashe wannan kujerar ta shugaban 'kasa. Murna kam wajen bayin Allahn nan ba'a magana, a yayin da Dad d'in Amira da iyalensa suke ba'kin ciki da rasa wannan kujera da suka yi, kuma ikon Allah sai a ranar ba'kin cikinsu suka ga Amira tai dariya, harda tsalle da murna tana fad'in "Dad ya fad'i Dad ya fad'i." Gaba d'ayansu tunani suke anya Amira bata samu tab'in hankali ba kuwa, Dad ji yai kamar ya kwad'eta dan ba'kin ciki, tashi yai ya shige cikin d'akinsa. *BAYAN WATA D'AYA* Wata biyar kenan cur da fitar da fitar da Amir waje, inda su can gidan su Amira suke ganin yana da wata biyar da rasuwa, shi kuma Ahmad zai ce bayan wata d'aya da hawar shi kan kujerar shugaban 'kasa. Kwatsam yau suna zaune a d'aki sai ga wayar Aleey yana shaida musu cewa majinyacin nan fa yau ya farka ya bud'e idanu, harma yana ta kiran sunan wata yarinya wai Amira yana cewa a kaishi wajenta, Ahmad ya shaida musu cewa insha Allah suna nan tafe zasu taho gobe in Allah ya kaimu shi da matarsa. Bayan zuwan su president Ahmad da wata d'aya Amir ya samu sau'ki sosai, amma har yanzu be daina damun su da tambayar ina Amirarsa take ba, ganin da likitoci sukai Amir ya warke yasa suka sallame su gaba d'ayansu su hud'un suka juyo domin dawowa 'kasarmu ta gado wato Nigeria. Suna durowa already dama motoci guda biyu suna jiran 'karasowar su, suna sakkowa daga jirgin suka shiga mota guda d'aya, d'ayar kuma tana binsu a baya har zuwa gida. Suna shigowa jami'ai suka zagaye wajen, nan da nan suka bud'e musu mota suka fito, Ahmad da kanshi ya kamo Amir ya fito dashi daga cikin motar, a haka suka shiga har cikin babban falon dake cikin gidan. Ya zaunar da shi a kujera, sannan shima ya zauna a kusa dashi, Khadija ta zauna a kujerar da ke kallon su, Aleey ma ya zauna a 'kasan kafet, a yayin da security tsaye kowace kusurwa a 'kame. Ahmad ya cewa securitys d'in su je daga waje zasu yi magana, dukkaninsu suka fita, sannan ya kalli Aleey yace "haba Aleey tashi kaima ka hau kan kujera mana," Aleey ya tashi daga 'kasa ya hau kan kujera. Ahmad yai gyaran murya sannan yai bismillah ya kalli Aleey yace "Aleey sannu da 'ko'kari, Allah ya baka ladan jinya, a koda yaushe ina 'kara alfahari da kai Aleey, Allah yai maka albarka, ka tashi kaje domin kaga iyalenka kaima, ga wannan dubu d'ari biyar ne ka tafi dashi duk abinda ya 'kare sai ka siya musu tunda mun d'auke musu kai ba aiki har tsawon wata bakwai," Aleey ya karb'a tare da yin godiya, sannan ya fice da zumud'insa yana farin ciki. Ahmad ya dawo da kallonsa ga Amir yace "bawan Allah mun gode wa Allah da ya dawo da kai gida lafiya, Allah ya 'kara maka lafiya, yanzu kamata yai ka 'kara samun hutu a nan kafin muji inda kake muje mu kaika mu yi musu bayanin hatsarin da ya faru da kai, mu sanar da su komai. Amir kuwa jin an ambaci hatsari ya tuno mishi da komai, yanda aka bugi motarsa ya tabbatar masa da cewa lallai turo su aka yi, cikin sauri ya kalli Ahmad yana hawaye yace "Abba yanzu zan kai kwana nawa ina jinya?" Ahmad yace "ba kwana bane, watanka bakwai kana kwance ba lafiya." Amir yace "Akwai wani nawa da yasan ina wajenku ne Abba?" Ahmad yace "a'a sai jami'an tsaro wad'anda suke d'aya daga cikin masu kula da ni," Amir yace "to dan Allah ka fad'a musu bana so kowa ya san inda nake har sai na gama binciken da nake yi na gano asalina, kuma in kun yarda zan zauna daku na wasu lokuta, kuma nagode sosai da taimakon da kuka yi min." Ahmad yace "bamu fahimci bayaninka ba yaro, in ka zauna a nan iyayenka fa?" Amir yace "bansan iyayena ba, zan baku labarina ko dan taimakon da kuka yi min a rayuwa," nan ya fara basu labarin tarihin rayuwarsa tun yana 'karami har girmansa da abubuwan da sukai ta faruwa da shi a rayuwa har zuwa wannan hatsarin, sannan Amir ya d'ora da fad'in "abinda yasa nace ina so na zauna daku na wani lokaci saboda in cigaba da neman iyayena a hankali har Allah yasa in gansu, nasan Dad ne yasa ai min haka, 'kila idan na nemo iyayena zai sassauta tsanar da yake yi a kaina." Dukkaninsu kuka suke yi, musamman ma Khadija kukanta har da shesshe'ka, labarinshi abun tausayi ne matu'ka ace tun yana yaro be san wani abu wai shi jin dad'in rayuwa ba har girma, kuma sai labarin shi yai musu famin wata dad'ad'd'iyar damuwa da take damunsu a rai. Ahmad ne ya share hawayensa, sannan ya kalli Khadija da har ta fara tari ciwonta naso ya tashi saboda kuka, cikin sauri, Ahmad da Amir d'in suka 'karasa wajenta a tare suna mata sannu, Ahmad fad'a yake yi, "kinsan yanayin ciwonki baya son damuwa amma daga jin labari kinbi duk kin d'aga hankalinki," maganinta ya d'auko mata ya bata ta sha, sannan yace "muje in kaiki ki kwanta," Khadija tace "a'a barni a nan ma kawai." Ahmad ya zauna kusa da ita yana yi mata sannu, Amir kuwa ji yayi yanayin rayuwar bayin Allahn nan ta burgesu, kuma sai yaji yana matu'kar 'kaunarsu. Muryar Ahmad ne ta katse mishi tunani, yace "Amir munji labarinka, kuma mun tausaya maka matu'ka, muma ka ganmu nan, muna jin kusan irin rad'ad'in da kake ji, yaron mu ya ya b'ata tun yana 'karami baida wayau be san kanshi ba, amma har yanzu mun kasa mantawa dashi, gani muke kamar ma zamu ganshi, tun farkon ganinmu da kai Allah ya saka mana 'kaunarka cikin ranmu, irin soyayyar da iyaye ke gwada wa kan 'ya'yansu, idan ba zaka damu ba ka zauna tare da mu, mu zame maka iyaye, ka d'aukemu ka kaimu gidan su yarinyar a matsayin iyayenka na asali." Amir yace "Abba nagode da 'kaunar da kuka nuna kaina, kuma na yarda zan zauna daku, zan ri'keku matsayin iyaye a gareni na har abada koda kuwa naga iyayena bazan manta da ku ba bazan ma gujeku ba muna tare, amma sedai maganar zuwa gidan su Amira a barta kawai, saboda idan munje yanzu nan gaba zasu iya gano gaskiya, ko kuma bayan munje na nunaku daga baya sai naga iyayena yaya kenan? kawai mu cigaba da addu'a Allah ya bayyana su, kuma Allah ya bayyana muku d'anku, amma kar kuji komai ina tare da ku." Ahmad da Khadija sun ji farin ciki sosai, domin har ga Allah suna 'kaunar yaron, suna ji a ransu kamar d'ansu ne ya dawo, shiyasa yau suka shiga farin ciki mara misaltuwa, shi kuwa Amir yanda yaga suna farin ciki abin sai ya bashi mamaki da tausayi. *BAYAN WATA BIYU* Amir ya warke sarai har sun fara fita da Abbansa, babu inda basa zuwa tare sai d'ad'd'aikun wurare. Har yanzu Ahmad yana nan da a'kidarsa na 'kin son security na binsa a baya, amma kuma baya yarda Amir ya fita ko nan da can shi kad'ai, koda fita akai dashi ma baya fitowa se dai masu tsaronshi suyi masa komai, duk hanyar da zai sadashi da inda zai ga Amira baya binta kwata-kwata. Amir sosai yake jin dad'in zama da mutanen nan, mutane ne masu taimako, sam abin hannunsu da daular mulki bata rufe musu idanu ba, kullum gidan nan cike yake da talakawa mabu'kata suna neman taimako, sai ya sallami na gida kuma zai fita ya kewaya gidan marayu asibitoci, unguwanni domin duba lalatattun hanyoyi yaga masu matsala a gyara, kullum aikinsa kenan, kuma kullum sai yayi haka, yama zama d'abi'arsa, sai ya gama da talakawansa sannan yake shiga office, canma kome zai tattauna duk a kansu ne, mutum me gaskiya da son Al'umma kenan, be yarda yaci ko sisin mutane ba, shiyasa ma ya cigaba da kula da kamfaninsa da duk kadarorin da yasan guminsa ne, kuma duk abinda zaiyi na bu'katarsa da ta gidansa baya yin amfani da ko 'kwandalar talakawansa, sedai yai amfani da abinda yake mallakinsa ne tun kafin ya hau mulkin, bayan ya gama nunawa Amir komai na siyaysa ya sani, sai ya kaishi d'aya daga cikin manyan kamfanoninsa domin ya cigaba da kula masa da shi, wannan kenan. ………………………………………… B'angaren Amira kuwa har yanzu tana jiya yau, ba um ba um-um. Dad kuwa yanzu ya saki ranshi, saboda yasan ya tara biliyoyin kud'i da kadarori wad'anda zasu ci shi da iyalinshi kuma har su mutu be 'kare ba, hakan yasa ya cigaba da harkokinsa, tare da cigaba da kula da dukiyarsa. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *INA BAIWA MASOYANA MAKARANTA LITTAFIN SO MAHA'DIN RAYUWA HA'KURI, PAGE 'DIN JIYA NAYI MISTAKE 'DIN LAMBA 150 NE TO 155, NA YAU KUMA 155 TO 160 KAR KUI TUNANIN NA JIYA NE NA SAKE TUROWA YAU, NAGODE👏😍😘* PAGE 155 to 160 Kamar kullum yauma Khadija zaune take tana sana'ar ta tunani, sai ga Amir ya shigo cikin gidan d'auke da sallama, har inda take ya k'araso tare da tsugunnawa kusa da ita, sanna ya dafa ta yace "Umma shin har yanzu ba zaki daina wannan tunanin ba, dan Allah ki daina tunani idan muka rasaki ba zamu tab'a samun farin ciki ba," yana fad'in haka yana kuka, 'karshe ma sai ya du'kar da kanshi jikinta yana cigaba da kukansa. Amir ya cigaba da fad'in "kamata yayi ki gode wa Allah da ya musanya muku da ni, har ga Allah kuma har a zuciyata jinku nake kamar iyayena wad'anda suka haifeni, to banda abinki ma Umma kina da d'a kamar ni me zaisa ki cigaba da damuwa, ki daina kuka banaso ina jin ba dad'i a raina," yana fad'in haka yana share mata hawaye. Abba Ahmad dake bakin 'kofa yai murmushi tare da share hawayen da suke ta yawo kan fuskarshi, har cikin ranshi yake jin 'kaunar yaron, yanda ya shiga ransu da yanda yake nuna kulawarshi a kansu ko d'ansu na cikinsu ne sai haka. Gyaran murya yayi sannan yai sallama ya 'karaso ciki, Amir da Umma Khadija suka yi mishi sannu da zuwa, sannan Amir ya kalli Ahmad yace "yauwa Abba gwara da ka dawo, kai wa Umma fad'a ta dena tunani kaga rashin lafiyarta baya bu'katar hakan, bazan juri rashinku ba Abba, kuma ko kad'an bazan so wani abu ya sameku ba," yana zuwa nan a zancen shi sai ya sake fashewa da kuka. Ahmad da Khadija suka kalli juna jikinsu duk yai sanyi, harga Allah suna jin mamakin irin matsananciyar k'aunar da Amir ke nuna musu cikin 'kan'kanin lokaci, Abba ya taso yazo kusa da Amir ya tsugunna, sannan ya dafa shi yace "yi shiru d'ana dena kuka daga yau insha Allah ba zata sake yin kuka ba ko dan farin cikinka," Ahmad ya d'ago kai ya kalli Khadiha yace "haba my love shin soyayyar da yaron nan ke gwada mana da kuwarashi da damuwa da dukkanin wasu lamura namu be isa yasa ki manta da komai ba ki rungumi kyautar da Allah yai miki hannu biyu, in kina kukan me kikai haka kenan, godiya wa Allah ko butulce masa? kina da tabbacin idan d'an namu ya dawo zamu samu farin ciki daga gareshi kamar yanda muke samu a yanzu? to ko d'an da ka haifa da cikinka ba kowanne ke kyautata maka ba, ya kamata ki manta da komai my love indai kina son farin cikin yaronmu da walwalarshi." Khadija ta share hawayen da suke gangarowa kan fuskarta, sannan tace "abinda ya sakani tunani da kuka ba abinda yake tunani bane, ina kokawa ne akan ban tab'a tunanin zan samu d'a wanda zai kirani da Umma kuma har ya bani dukkanin kulawarsa bane sai gashi Allah ya bani, ni kukan farin ciki nake yi d'ana, ta dafa Amir sannan ta cigaba da cewa, kuma daga yau ka daina sake ganin tunanina ma balle zubar hawayena." Amir yai murmushi sannan yace "Allah yasa," dukkansu suka amsa da "ameen," Abba ya kalli Amir yace "yarona wai meyasa naji ka dakatar da maganar neman iyayenka?" Amir yai shiru ya kauda zancen, Abba ya sake nanata zancenshi, Amir yace "to me zaisa in cigaba da neman su bayan ina da ku, addu'ar da nake ta wadatar, in Allah yaso mu had'u zamu had'u wata rana, Abba yace "hakan be dace ba ya kamata ka cigaba da nemansu kamar.........." Amiya ya katseshi ta hanyar fad'in "Abba bari inje in dawo na tuna naiwa wani alk'awarin zamu had'u dai-dai wannan lokacin a office, Abba yace "amma yarona.........." "Abba dan Allah ka barni in tafi," Amir ya sake ro'konsa a karo na biyu, Abba yace "shikenan sai ka dawo Allah ya tsare, Allah yai maka albarka," Amir yace "ameen Abba, ya matsa gun Umma ya d'an duk'a sannan yace "Ummana ke baki sa taki albarkar ba, Umma tai murmushi, sannan ta dafashi tace "Allah yai maka albarka d'ana ya dawo mana da kai gida lafiya," Amir yace "ameen Ummana," yana gama fad'in haka ya doshi hanyar fita, saida ya kai bakin 'kofa sannan ya juyo ya kalle su, suma shi suke kallo dukkansu, ya 'kyal'kyale musu da dariya sannan yace "yeeeee nai musu wayau hahaha," yana fad'in haka ya gudu, Abba yace "zo nan Amir z.........." ina ya gudu, dukkansu dariya suke yi, Ahmad yace "wai yai mana wayau, na sani sarai maganar da nai masa ce yasa ya fita kawai na 'kyaleshi ne," Khadija wadda har yanzu dariya take yi tai magana tana dariya tace "ni yanda yai maganar ne ma ya bani dariya harda su gwalo, kai Amir naga randa zai girma." Abba ya 'kura mata idanu yana murmushi ya d'aga hannu sama yace "Allah na gode maka da ka azurtamu da yaron da ya dawo da farin cikin gidana da na matata. Amir kuwa yana fita yaje ya samu gefen wani waje a unguwarsu ya zauna ya had'e kansa da guiwa ya fashe da kuka, babu abinda ya sashi kuka sai Amira da ta fad'o mishi a rai, kullum haka yake tsintar kanshi a ciki duk lokacin da ya tuno da ita, tunani yake ko a wane hali take ciki Allah kad'ai ya sani, koda yai niyyar zuwa gidan su domin ya ganta sai ya tuno da irin abubuwan da mahaifinta yai mishi sai ya fasa zuwa, ya dad'e a wajen yana hawayensa tare da tunane-tunanensa, sai daga baya ya tashi ya shiga mota suka bar unguwar. ………………………………… B'angaren Amira kuwa to Alhamdulillah dai za'a ce domin kuwa an samu cigaba, tunda zata yi magana, amma itama sai ta kama irin in tana bu'katar wani abu ko kuma in ita an tambayeta wani abun, Amma maganar walwala ko hira da mutane har yanzu babu ita, koda yaushe fuskar nan ba annuri. *BAYAN SHEKARU UKU* Amira haka ta cigaba da rayuwarta an kuma maida ita makaranta domin karatun ya ri'ka d'ebe mata kewar kad'aici, sedai abinda basu sani ba shine sam bata gane komai yanzu a karatun nata. Yau laraba, Dad ne ya shigo cikin gidan cike da farin ciki a fuskarsa, ya kalli dukkanin mutanen falon bai ga Amira ba, ya kalli Mum yace "ina Amira?" Mum tace "tana d'akinta, kasan yanzu bata shigowa cikinmu," Dad yace "to ku shirya ina da ba'ko yau a gidan nan, ba ba'kon kowa bane kuma illah ba'kon Amira, d'an wani d'an sanata Bashir ne, sunansa Mahmud daga Kano, yanzu haka yana tafe, bari inje da kaina in sanar mata." Mum ta dakatar dashi, sannan tace "a tunanina ba a irin wannan halin ya dace mu je wa da Amira da zancen mijin aure ba, kamata yai mu bari har 'karasa dawowa normal kamar yanda take a da." Dad yace "shekaru uku kenan da mutuwar mijinta, sai mu cigaba da zuba mata ido kike so ko me? ni dai na gama magana sun je sun sameni sun nemi izini wajena kuma na yaba da hankalinsu, dan haka na basu izini suzo su daidaita da ita," ya haye sama domin zuwa gun Amira ya sanar da ita. Yana shiga ya tarar da ita ri'ke da wayar Amir tana kallon hotunanshi hawaye na wanke fuskarta. Dad ya zauna kusa da ita, sannan ya kalleta yace "My Doughter ya kamata ki cire tunanin Amir daga ranki damin ni dake duk mun sani wanda ya tafi baya tab'a dawowa, dan haka ki yawaita yi mishi addu'a ne kawai itace soyayyar da tai saura a tsakaninki da shi." Amira ta gyad'a kai alamun amsawa, Dad ya cigaba da cewa akwai wani yaro da yaje ya sameni ya fad'amin yazo Abuja wakiltar mahaifinsa wani taro ya ganki a hanyarki ta zuwa makaranta bai miki magana ba har saida ya bi ki a baya ya tambayi 'kawayenki sukai mishi bashi bayani game da ke sannan ya taho wajena, a ta'kaice yana sonki da aure, yanzu haka yana hanya zai zo kuga juna in ya yi miki shikenan. Amira iya kad'uwa da razana tayi, amma sai ta dake tace "to Dad," iya abinda ta iya cewa kenan, Dad yace "Allah yai miki albarka, sai ki tashi ki shirya kafin ba'kon naki ya 'karaso," ya tashi ya fice daga d'akin. Yana fita Amira ta fad'a gado ta fara kuka, tana fad'in "Amir why! meyasa zakai min haka, meyasa zaka tafi ka barni, taya zan iya cigaba da rayuwa ni bayan rabinta ya tafi, sai kuma ta hau girgiza kai, tana fad'in a'a wallahi Amir bai mutu ba, ina ji a jikina Amir d'ina bazai min haka ba, nasan ba zai mutu ya barni ni d'aya cikin wannan duniyar ba," ta dad'e tana kuka babu me rarrashi, a dai-dai wannan lokacin irin halin da take ciki shima Amir yake ciki, so kenan, masoya na ha'ki'ka sukan iya tsintar kansu cikin yanayi iri d'aya, tunani iri d'aya, damuwa ma iri d'aya, ikon Allah kenan. Bayan ta gama cin kukanta ba mai rarrashi sai ta bawa kanta ha'kuri kamar kullum ta tashi ta shirya. Ta shirya ba dad'ewa Dad d'inta ya kirata a waya ya sanar da ita cewa ba'konta ya iso yana b'angaren d'akin ba'ki. Cikin rashin kuzari ta yafa mayafi tare da ficewa daga d'akin ta tunkari b'angaren masaukin ba'ki. Tana zuwa bakin 'kofa taja ta tsaya tana jiyo wayar da yake yi kuma yana 'kyal'kyalar dariyarsa. Da farko abinda yasa ta tsaya fad'uwar gaba taji matsananci saboda zuciyarta na ayyana mata kamar in ta kula wani ta ci amanar Amir, sedai fara sauraron abinda saurayin nan ke cewa a kunnuwanta yaja ta 'kara tsayawa tsayuwa me dalili tare da 'kara matsawa tana saurare, abubuwan da taji yasa ta 'kara sarewa da lamarin duniya ta kuma razana abun ya bata mamaki kuma, koda yake ba mamaki in dai wannan zamanin da muke ciki ne. Cikin sauri ta yaye labulen tare da kutsawa cikin falon, tace "in ka gama wayar sai ka tashi ka tafi, kuma naji duk abinda ka gama fad'i yanzu, inada damar tona maka asiri, amma sedai nasan muddin 'yan gidan nan suka ji sai sun kashe ka, saboda haka fice mana daga gida da kai da dogarawarka kuje ku kwashe motocinku ku bar gidan nan kafin raina ya b'aci in tona maka asiri kowa yaji." Mahmud ya tashi sum-sum ya fice daga d'akin, cikin 'kan'kanin lokaci suka tattara suka bar gidan. Nan ma Amira sai da taci kuka sosai sannan ta tashi ta koma cikin gida. A falo ta tarar da Dad d'inta, har zata wuce ya tsaida ita yace "zo nan 'yata," Amira ta 'karasa kusa dashi ta zauna ya kalleta yace "ba'kon naki har ya tafi?" Amira ta gyad'a kai alamar eh. Dad yace "to fad'amin ya kukai yadai yi miki ko?" _Ayi ha'kuri da wannan banjin dad'i wallahi👏_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *MAMIEN BK SANNU BAIWAR ALLAH😰 ALLAH YA 'DORAR MIKI DA DAUWAMAMMIYAR LAFIYA TARE DA DUKKANIN MUSULMI BAKI 'DAYA👏😭😭😭😭😭* *TAWAN INA RO'KON ALLAH YA BAKI LAFIYA, YA KAWO MIKI SAU'KI DA 'DORARRIYAR LAFIYA, YA YAYE MIKI DUKKANIN DAMUWARKI.*👏😭 *HABIBTY NAH INA RO'KON ALLAH YA BAIWA 'DAN UWANMU LAFIYA 'DORARRA*👏😭 *ALLAH SARKI MASU KU'DI ABUN TAUSAYI,😰 KAFIN SU GANE MASOYI NA GASKIYA SAI SUN SHA MATU'KAR WAHALA, SABODA YAWANCI BA DAN ALLAH AKE 'KAUNARSU BA SAI DON ABUN HANNUNSU, YA ALLAH KA SADA KOWA DA MASOYI NA GASKIYA MAI YIN 'KAUNA DOMIN ALLAH👏* PAGE 160 to 165 Dad ya sake maimaita tambayarsa ga Amira yace "tambayarki nake Amira kinyi shiru, nace ya kukai dashi ya yi miki?" Amira tace "Dad Mahmud ba d'an kowa bane, duk abubuwan da yazo dasu hayarsu suka yi saboda kwad'ayin abun duniya, kuma duk abinda ya fad'a maka game dashi 'karya ne, Dad bansan ya akai ba har kai saurin amincewa dashi ba tare da kayi bincike ba, Dad ashe abinda yasa ka 'ki Amir saboda shi ba d'an kowa bane kenan, da ace yana da kud'i zaka 'kaunace shi koda babu asalinshi kuma kai saurin amincewa dashi kamar yanda kayi wa wannan mutumin?" Dad ya daka mata tsawa tare da fad'in "wato saboda bakya son auren shiyasa kika zo da wannan 'karyar domin kiy masa sharri koh, to ban yarda da wannan tsarin naki na 'karya ba, saboda haka kije sai nayi bincike na tabbatar, tashi ki bani guri mutuniyar kawai na kawo mutum kin wula'kantashi da wannan banzan halin naki da kika canza." Amira tace "Dad wallahi tun kafin na shiga d'akin naji yana waya da wasu yana.........." Dad ya sake katseta yace "ba zaki yimin shiru ba, tashi ki bani waje," Amira ta tashi ta haye sama da sauri tana kuka, zuciyarta na zafi saboda 'kin gasgata zancenta da Dad yayi, duk da Dad be gasgata zancenta ba saida yai waya tareda bada umurnin ai mishi binciken wanene Mahmud. Bayan Dad ya gama wayar sai bambami yake shi kad'ai, yana cikin fad'a wayarsa tai 'kara, wani babban yaron Dad ne kuma aboki na wajen aiki mai suna Haladu wanda ya aminta dashi domin Dad ya maida shi tamkar d'an uwa saboda yardar dake tsakaninsu, abokinshi ne sosai, kuma suna tattauna dukkanin matsalolin su tare, kuma suna baiwa juna shawarwarin da suka dace, bayan haka Haladu yana d'aya daga cikin wad'anda Dad ya yarda dasu kuma yana d'aya daga cikin wad'anda suka san komai na harkar dukiyar Dad, yanzu haka Haladu shine shugaba a cikin d'aya daga cikin kamfanin Dad dake kano, kuma duk wasu harkoki nashi na kano Haladun ne ke kula dasu, a ta'kaice dai sun d'auki juna kamar 'yan uwa ba wai abokai ko bare ba kawai. Bayan Dad ya d'aga suka gaisa sai Haladu yace "dama zan fad'a maka ne gobe insha Allah muna tafe zuwa gidanka ni da yaronka ze gaisheka, amma ya naji muryarka kamar kana cikin damuwa?" Dad yace "kai dai bari kawai, tunda mijin Amira ya rasu gaba d'aya komai nata ya shiririce, na kawo mata wani domin su daidaita kansu shima ta koreshi," Haladu yace "ka kwantar da hankalinka, harda wannan maganar ma zai kawoni wajenka gobe insha Allah karka wani damu. Nan suka yi sallama Dad ya ajiye wayar tare da sauke ajiyar zuciya sakamakon samun 'yar natsuwa da yayi, domin yasan in har Haladu yazo insha Allah zai samar mishi da mafita. Washe gari ita dai Amira taga ana ta hidimar shirye shirye a cikin gidan, to da yake yanzu bata shiga lamarin kowa yasa bata tambaya ba ta zuba idanu taga wad'anda ake yiwa wannan shirin. Dad ne ya shigo a bayanshi Haladu ne da d'ansa Nura suka shigo babban falo, kowa sai sannu da zuwa ake yi musu tun daga shigowarsu har suka zauna, nikam a zuciyata nace ga dukkan alamu Haladun nan yana da matsayi a wajen 'yan gidan nan, amma kamar ya dad'e baya zuwa inda suke. Bayan an gaggaisa aka cika musu gabansu da abinciccika kala-kala, Dad yace a kira Amira itama tazo su gaisa, aka kirata ta gaishe su sannan ta koma cikin d'akinta, tun daga lokacin da Amira ta fito har ta koma Nura kallonta kawai yake yi, ga dukkan alamu ta tafi dashi, mahaifinsa Haladu yana lura dashi, a zuciyarsa yace bazan sha wahala ba wajen cimma manufata kenan. Dad ne ya katse masa tunanin da yake yi ta hanyar fad'in Nura an girma, yanzu babu abinda ya rage sai ka fito mana da mata musha biki, Nura ya sosa 'keya tare da yin murmushi. Amira ce ta fito daga cikin d'aki zata fita Dad ya kalleta yace "Doughter ina zakije?" Amira ta bashi amsa a ta'kaice tace "lambu zani shan iska," ta juya tare da ficewa, Haladu yace "Nura kaima kaje can kai hira da 'yar uwarka, muma ka barmu mu zanta nida d'an uwana." Cikin rawar jiki kuwa ya fice ya nufi inda Amira take zaune yai mata sallama ta amsa sannan ya samu waje ya zauna, yace "'kanwata kwana biyu mun dad'e rabonmu da ganin juna," Amira tai banza dashi, can ya 'kara cewa "koda yake ke nasan baki sanni ba, sedai ni na dad'e sa saninki, domin kuwa kin dad'e da zama a cikin zuciyata da mafarkina sai yau Allah ya bayyanamin ke," nan ma tai shiru bata ce mishi komai ba, ya sake cewa "mutane nawa ne a duniya suka tab'a fad'a miki cewa in kika d'aure bakya yin kyau?" se anan ne tai mishi magana tace "mutum d'aya ne tak sunansa Amir," Nura yace "Allah sarki Amir mutumin kirki ai inada labarinsa nima, gaskiya samun masoyi kamarsa sai an tona," jin anzo inda take so wato maganar masoyinta yasa ta fara d'an amsa mishi jefi-jefi, shima ya dage sai hirar Amir d'in yake mata domin ya riga da ya gano cewa da hirarsa ne kad'ai zai iya samu tai magana dashi. Dad ya kalli Haladu yace "ya kamfani ina fatan ana samun cigaba sosai?" gaban Haladu ya fad'i, amma sai ya dake yace ana samun cigaba sosai, kwanan nan ma zaka ji alart na biliyoyin kud'i na ribar da muka samu kad'ai," bayan sun gama wannan maganar suka gangaro magana kan Amira, Dad ya fad'awa Haladu abinda ke faruwa, Haladu yace "ikon Allah ashe dai na dad'e rabona da gidan nan ranka ya dad'e shiyasa duk wad'annan abubuwan suka faru ban sani ba. Amma ga shawara guda biyu, na farko ka d'auketa daga garin nan muddin kana so ta manta da komai kuma walwalarta ta dawo, abu na biyu shine ka had'ata aure da yarona Nura in sun daidaita junan su kaga se ayi tuwona maina kenan." Dad yai dum yana tunanin maganar da Haladu yazo masa da ita, tabbas yaji dad'in shawarar Haladu ta farko domin shima yana da tunani da kuma 'kudurin canza musu gari ko Allah zaisa ta sanadin haka 'yarsa ta manta da komai har farin cikinta ya dawo, sedai maganar had'a d'ansa aure da Amira gaskiya yana shakku saboda baya 'kaunar wani nashi ya auri talaka balle kuma ace 'yarsa ta cikinsa, amma saboda zuciyarshi na bashi wata 'kila ba mutuwa Amir yayi ba tunda har yanzu ba wanda yace musu yaga gawarsa, shi kuma da Amir ya dawo ya cigaba da zaman aure da Amira gwara ya aurawa Nuran ita, da wannan shawarar da zuciyarsa ta bashi ya yanke hukunci, ya kalli Haladu yace "gaskiya naji dad'in shawararka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Allah yasa su fahimci junansu." Amira da Nura sun dad'e suna hira kuma ba hirar kowa suke ba illah ta Amir, labari take ta bashi tun farkon had'uwarsu har zuwa yanzu, bayan ta gama bashi tace "a halin da ake ciki a yanzu rasashi da nayi ji nake kamar na rasa wani b'angare ne na jikina, kuma zuciyata na bani cewa nima ina gaf da binshi," Nura ya kalleta harda guntun hawayenshi irin na tausayi, yace "gaskiya na tausaya muku, kuma duk duniya babu inda na tab'a jin labarin cikakkun masoya irinku, nima ina ji a jikina kamar yanda kike ji har yanzu Amir na raye be mutu ba, zan tayaki Addu'a Allah ya bayyana miki shi, amma ina fatan zaki d'aukeni a matsayin aboki kuma d'an uwa sannan abokin shawararki?" Amira ta numfasa sannan tace "ba damuwa, Nura yaji dad'i sosai, yai mata godiya, suna cikin magana sai ga su Dad sun fito, sunji dad'in yanda suka gansu, ga dukkan alamu abinda suka 'kudurta zai tabbata nan bada dad'ewa ba. Nan suka yi sallama da Amira Dad ya bisu a motarsu domin rakasu har inda sukace zasu biya domin duba wani, suna cikin tafiya kamar ance Dad ya kalli gefen ti-ti ya hango wani yaro sak Amir cikin farar shadda ga sojoji da 'yan sanda da kuma masu ba'ka'ken kaya duk sun kewaye shi, cikin zaro idanu tare da jin fad'uwar gaba matsananci ya 'kwala mishi kira yace "Amir," cikin sauri kuwa Amir ya waigo amma be hango wanda ya kira sunanshi ba saboda motarsu ta riga da ta wuce, tunani ya shiga yi anya Amir ne kuwa, Amir fa'kiri ne baida komai, amma in ba shi bane meyasa ya waigo lokacin da na kira sunansa. Haladu ya kalli Dad yace "lafiya ya naga yanayinka ya canza, wancan waye shi d'in?" Dad yace "shine annobar da ya rusamin farin cikin gidana gabad'aya ban tab'a tsammanin yana raye ba," Haladu yace in kuwa hakane to tabbas yana da kyau kayi gaggawar canza gari dan kuwa tunda har yana raye bazai tab'a barin Amira ba, wa ya sani ma ko d'an shan jini ne yarinya duk tabi ta 'karmashe ta lalace." Babu abinda Dad ya 'kara cewa, har ya rakasu inda zasu sauka sukayi sallama ya juyo shi da masu tsaronsa, a hanyarsa ta dawowa ma saida ya sake duba wajen amma sedai kash baya nan, da wannan tunanin suka 'karasa gida tare da yanke shawarar cikin satin nan zai koma kano shi da iyalansa da zama. Bayan tafiyar Dad Haladu ya kalli yaronsa Nura yace "my son ya kukayi da yarinyar ina fatan kun daidaita kanku?" Nura yace "Dad akwai matsala gaskiya, shawo kanta ta soni zaiyi matuk'ar wahala saboda akwai wanda ta ajiye a ranta kuma take zaman jira, Haladu yace "haba my son kaifa namiji ne kuma jajirtacce akan komai, meyasa zakai saurin karaya akan haka." Nura yace "ba damuwa nasan yanda zanyi na shawo kanta ayi auren, amma na tabbatar ba zata soni ba." Haladu yace "ai dama burinmu kenan ayi auren d'an baba," Nura yace "but Dad ni ina sonta fa, ba fatana muyi aure mu rabu ba," Haladu yai murmushi, sannan ya dafa kafad'ar Nura yace "kai yarone Nura, ba zaka gane komai ba sai nan gaba, kaidai yi 'ko'kari ka shawo kanta ayi auren. ………………………………… *BAYAN SATI 'DAYA* Abba ne zaune a falo matarsa na gasa mishi 'kafa da kuma goshinsa da yaji rauni. Amir ne ya fad'o gidan a guje yana runtumawa mahaifinsa kira, ya 'karaso kusa dashi ya zube a 'kasa yana kuka yace "Abba kaga irinta ko, taya za'ai ace kana shugaban 'kasa kace baka son masu tsaro, kuma bayan kasan ba zaka rasa ma'kiya ba da 'yan adawa, yanzu gashi nan ana neman ranka, Abba ko so kake mu rasaka?" Abba yai murmushi sannan yace "haba Amir kwantar da hankalinka mana, bafa su sami galaba a kaina ba, wad'annan raunikan da na ji duk wajen ceton raina ne ba su suka jimin ba, kayi shiru ka daina kuka Allah ya kub'utar dani daga sharrinsu, kuma a baya ma na shiga had'arurrukan da suka fi wad'annan." Amir yace "gaskiya Dad in har kana son farin cikinmu to karka 'kara fita kai kad'ai, dan ni wallahi a kanka na fara jin shugaban 'kasa yace wai baya son masu tsaronshi na binshi a baya duk inda zai tafi, dan haka dan Allah Dad ka janye wannan ra'ayin naka, kaga ka sakamu kuka ni da Umma ka gani ko tunda na shigo naga tana ta faman kuka." Abba Ahmad ya kalli Umma ya yafitota da hannu, cikin sauri kuwa ta rarrafo zuwa gareshi ya rungumeta da hannunshi na dama, sannan ya yafito Amir shima da hannu yai mishi kamar yanda yaiwa Umma da d'ayan hannun, sannan ya kallesu duka yace "ku kwantar da hankalinku, in dai akan wannan ne kuke kuka to bakwa 'kara zubar da hawayenku a karo na biyu domin kuwa na amince da bu'katarku dan haka ku share hawayenku," Amir ya sharewa Ummansa, itama ta share mishi, sannan suka sharewa Abba shima wanda yake kukan farin cikin samun iyali nagartattu. Amir ya mi'ke tsaye sannan ya ajiye wayarshi yace bari yaje ya watsa ruwa ya fito, Amir na shiga ya cire kayanshi sannan ya d'aura tawul ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya tsaf agogo ne kad'ai bai d'aura ba, sai ya shiga duba agogon da zai shiga da kayansa, laluben shi ya kaishi har kan wata drower wadda tunda ya shigo d'akin be tab'a bi ta kanta ba, yana bud'ewa yaga hotuna birjik na yara ne guda biyu, d'aya yaro ne sosai dan bazai wuce shekara d'aya da wata uku ba, d'ayan kuma wani yaron ne a kusa dashi d'an shekara biyar, da yaron nan dan shekara d'aya da rabi da yaron nan d'an shekara biyar kamarsu har ta b'aci, banda d'aya ya girmi d'aya da cewa za'ai 'yan biyu ne su. Abinda ya d'aurewa Amir kai shine yaron nan d'an shekara biyar kamarsu d'aya sak da Amir, sedai yasan tabbas ba shi bane wannan, to ina su Umma suka samo yaro mai kama dashi, kodai shine wanda ya b'ace suke nema, kardai ace su Umma iyayena ne? hotunan ya d'iba da sauri tare da yin falo domin samo tarin amsoshin dake ranshi. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *INA BU'KATAR ADDU'A DAGA GAREKU MASOYANA ALLAH YA BANI LAFIYA 'DORARRA*👏👏👏👏👏 PAGE 165 to 170 Amir ya fito daga d'akinshi cikin sauri tare da nufo iyayensa hannunshi ri'ke da hotunan da ya gani. Zama yai kusa da Abbanshi sannan ya nuna mishi hotunan yace "Abba su waye wad'annan?" Abba Ahmad ya gyara zama tare da karb'ar hotunan yana kalla yace "yarana ne wad'anda na rasa, ya nuna mishi babban yace wannan shine Ammar, d'ayan kuma wato 'karamin sunanshi Bilal, shine wanda ya b'ata, babban kuma ya mutu ne." Amir kuka yake sosai yana kallonsu, daga Ahamd har Khadija sunji tsoron halin da Amir ya shiga cikin 'kan'kanin lokaci daga tambayar hoto, nan suka shiga rarrashinsa domin yai shiru suji dalilin yin kukansa. Amir ta kallesu yace "indai hotunan nan da na gani hoton 'ya'yanku ne to tabbas nine d'anku wanda ya b'ata nine d'anku wanda kuka dad'e kuna nema." Amir ya d'auko wayarsa ya nuna mishi hotunansa lokacin yana 'karami da wanda ya d'auka shi kad'ai da wanda suka d'auka tare da Amira, bayan ya nuna musu na cikin waya sai ya shiga d'aki jikinsa na rawa ya kwaso mishi duk hotunan da ya nuna mishi a waya ya nuna musu a zahiri, Khadija ce ta mi'ke tsaye cikin sauri ta fizge hoton dake hannun Amir ta duba, haba kawai sai ga Khadija a 'kasa anyi suman farin ciki ne zamuce ko na firgicin ganin abinda bata yi tsammani ba. Cikin hanzari suka watsa mata ruwan sanyi ta dawo hayyacinta amma har yanzu kuka take, ta rungume Amir gam kamar wadda za'a sake rabata dashi tana cigaba da kuka tare da godewa Allah da 'karfinta, Abba kanshi da yake namiji saida yai kukan farin ciki, Amir yace "Abba ashe dama kune iyayena ban sani ba Allah ya fad'o dani hannunku," Abba ya kalleshi yace "dama mu jinka muke kamar d'anda muka haifa tun ranar da muka fara ganinka," Amir yace "ina godewa Allah mahalicci da ya bayyanamin ku, kuma ya zab'amin ku a matsayin iyayena." Umma kuwa ta kasa cewa komai banda kallonshi da take yi tare da cigaba da zubar da hawaye, fuskarta kuwa tana d'auke da farin ciki mara misaltuwa, Amir ya kalleta yace "Ummana bakice komai ba," Umma tace "Allah na gode maka da ka dawo da yarona gareni na sake ganinshi kafin ka d'auki raina," tana gama fad'in haka ta sake saka kuka me had'e da dariya, a ranar dai sai suka koma kamar zararru saboda tsabar farin cikin ganin yaron da suka rabu dashi tun yana 'karami, tun bashida wayau. Bayan sun gama koke kokensu da murnar had'uwa da juna sai Amir ya kalli mahaifinshi yace Abba me ya faru har na b'ace daga gareku, kuma ina d'an'uwana Ammar?" Abba yai shiru na wasu lokuta, sannan ya numfasa yace "My Son bana son tuno dukkanin abubuwan da suka wuce a baya, amma ya zama wajibi in fad'a maka komai, Abba ya sake numfasawa, sannan ya cigaba da fad'in "labarina ni da mahaifiyarka labari ne me tsawo, amma zan gajarta maka shi in baka shi a ta'kaice." Amir yace "to Abba fara bani labarin ina saurarenka," Abba ya gyara zama sannan yace. _"Kamar yanda ka sani ne sunana Ahmad, ni haifaffen garin Kontagora ne, iyayenmu mu biyu suka haifa, kuma tun muna yara har tasowarmu suna nuna mini 'kauna fiye da d'an uwana yayana Sunusi, wanda ni nasan ba komai yasa suka fi 'kaunata ba illah biyayyar da nake yi musu da kuma kyautata musu, amma ni kaina sam bana jin dad'in abinda iyayena suke yiwa Sunusi domin har akwai ranar da nai musu magana akan be dace suna fifitani akansa ba, sukace ba dan komai suke yin haka ba sai domin ya shiryu ya zama na 'kwarai ya daina abubuwan da yake yi, dan maganar gaskiya Sunusi baya ji kuma baya ganin girman iyayenmu sam, sedai da na nuna musu cewa ai yin hakan ga yaro irinshi kuskurene babba iyaye suke yi, domin tsana bata tab'a gyara kangararren yaro sedai ta 'kara busar mishi da zuciya, suka yi na'am da zancena, kuma daga ranar basu sake nuna mana bambanci ba a tsakanina dashi, to ada kafin nan idan iyayena suka yi wa Sunusi irin haka yana nuna jin haushinsa har yai zuciya da ni, to sedai ni kuma ina 'kaunar d'an uwana har ga Allah bana son ganinshi a irin wannan halin, hakan yasa ma har nakai ga yiwa iyayenmu magana su kuma suka gyara, to daga lokacin muka daidaita da d'an'uwana babu abinda ya sake shiga tsakaninmu har Allah ya rayamu muka girma, ni da Sunusi muna 'kaunar juna sosai, ko kad'an baya 'kaunar yaga wani abu ya sameni, kulawar da muke baiwa juna takai 'kololuwa, iyayenmu talakawa ne ba wasu masu kud'i bane, amma a haka sukaita fad'i tashi sukaita kula da karatunmu hakan yasa muka tashi da burika a ranmu rututu na ganin mun kyautatawa iyayenmu sunji dad'i ta dalalinmu, sedai kash, bayan mun kammala makaranta duk result d'in yayana basu yi kyau ba, ganin yanda yayana ya damu yasa na kwantar mishi da hankali tare da tabbatar mishi da cewa idan har na fara aiki albashina dai-dai zan ri'ka rabawa ni da shi kafin in nema mishi aiki a kusa dani, a zahiri ya nuna yaji dad'in haka, sedai a bad'ini ashe haushina da hassada ce a ransa, bayan na samu aiki a Abuja na fara zuwa duk albashin da na samu rabawa nake kamar yanda na fad'i in baiwa yayana Sunusi rabi in d'auki rabi, kuma ni nawa da yake garin namu a cikinsa ma mu a 'kauyen garin muke kuma duk talakawa ne irinmu, hakan yasa duk na d'auki albashina gaba d'aya talakawan nan nake raba mawa, da yake muna da 'karancin ruwa a wajen sai an sha wuya, hakan yasa shima nasa akai musu famfo da kuma burtsatse, nasha albarka da kuma addu'a wanda nasan sune sanadin da sukaja har nakai wannan matsayin a yanzu, ina matu'kar jin tausayin 'yan 'kauyenmu fiye da tunaninka Amir, saboda zaka ga ka d'auki naira hamsin wadda kai a ganinka ka rainata amma in ka baiwa wani magidancin sai kaga yana godiya harda kuka, wannan dalilin yasa na d'auki alwashin taimaka musu iya iyawata, ana haka wata rana shugabana na wajen aiki ya kirani na zauna, sannan ya kalleni yace "abinda yasa na kiraka saboda dalilai biyu ne, na farko an maka 'karin girma, ka tashi daga 'karamin ma'aikaci yanzu ka zama manaja na wannan kamfanin, kuma in babu damuwa ina yi maka sha'awar auren 'yata Khadija, ba komai ya kawo duk wad'annan abubuwan ba illah kyawawan halinka, domin duk wani ma'aikaci na wannan kamfanin mukan bibiyi rayuwarsa kar muje mu d'auko wanda zai rusamu, to duk a cikinsu ka zarcesu kyawun hali da na d'abi'u ga gaskiya da ri'kon amana, babu abinda ya 'kara burgeni da kai illah tausayin wanda bashi da shi da taimako, dan haka sati me zuwa zaka fara aiki, maganar khadija kuwa kaje kayi shawara duk abinda ka yanke sai ka sanar dani daga baya," na yiwa ogana godiya sannan na tashi na koma gida, bayan iyayena da d'an uwana sun hallara waje guda sai na sanar dasu 'karin girman da akai min da kuma abinda ogana yace akan 'yarsa, sunyi murna matu'ka tare da bani goyon baya akan Khadija suka ce inje d'in in ganta in dai tayi min kawai sai in aureta, jin Sunusi shi bai ce komai ba yasa na juyo na kalleshi nace "yaya kai bakace komai ba," ba tare da nuna fara'arsa ko walwalarsa ba yace "Allah sanya alkhairi," na sake cewa "amma yaya ni nafi so sai ka fara yin aure kafin ni nayi, ko kuma muyi a rana d'aya," Sunusi yace "ai in zaka yi aurenka kayi dan ni gaskiya ba yanzu ba sai nayi arzi'ki tukun," daga haka ya tashi yace kanshi na ciwo zai shiga cikin d'aki ya kwanta, naji mamakin maganar da Yayana yake fad'a saboda albashina dubu d'ari da hamsin ake bani duk wata a lokacin, ina d'aukar saba'in da biyar in bashi saba'in da biyar, amma bansan ya yake yi da kud'i ba dan kuwa komai na gidanmu ni nake yiwa iyayenmu hatta cefane wannan kai komai ma na gidan, shi kanshi idan bu'katarshi ta tashi ni nake yi mishi, amma wai yana fad'in baida kud'i sai yayi arzi'ki, bayan sati na koma bakin aikina, daga lokacin da na fara aiki zuwa yanzu 'yan 'kauyen nan babu wanda baya 'kaunata, har gida ake bin iyayena ana yi musu godiya da yimin addu'a, ashe duk wad'annan abubuwan Sunusi ya ri'kesu a ranshi ne yana kallona dasu, naje gidansu Khadija na ganta kuma na yaba da halayenta, hakan yasa babu b'ata lokaci iyayena sukaje aka sa rana inda mahaifinta ne yai komai aka sha shagalin biki muka tare a gidan da aka bani tun ranar da na fara aiki, madaidaicin plat ne amma ya had'u, mahaifin Khadija wata guda ya bani ina shan amarci, bayan wata biyu da aurenmu na d'auki Khadija na kaita 'kauyenmu domin ta gaida iyayena da d'an uwana Sunusi, tunda sunusi yaga Khadija yake mata kallon 'kurilla tare da washe baki kamar gonar audiga, lura da hakan yasa naji kishi a raina, ada munzo muyi sati ne, amma muna yin kwana biyu nace zamu koma, muka yi sallama dasu muka juya, da yake duk 'karshen wata nake zuwa gida inga 'iyaye da 'yan uwana ina nufin talakawana na garin wad'anda na zame musu tamkar uba ko kuma wani sarkin garin, a lokacin da nazo garin sai na samu mummunan labari daga wajen Iyayenmu wai yaya sunusi ya zama d'an fashi, kuma yana shaye shaye, isowata kenan na tarar da wannan ba'kin labarin, muna cikin maganar sai ga Sunusin ya shigo da gudu wani ri'ka'k'ken d'an daba dake wani 'kauye wanda ke ma'kwabtaka da namu ya biyoshi har cikin gidan, ya d'aga wu'kar hannunshi zai yanki Sunusi da ita kenan sai nai sauri na tare ya yankeni a ciki, nai 'kara tare da zubewa 'kasa dukkansu suka yo kaina shi kuwa d'an daban nan ina jinshi yana fad'in "Allah ya 'kwaceka d'an uwanka ya ceci rayuwarka, amma ba yaawa tunda a nan 'kauyen kake kuna kusa da namu ne ai dole wata rana zamu had'e a lokacin zaka gane kurenka," ya juya suka fice shi da yaransa suna gigije girgije, iyayenmu suka d'aukeni suka kaini wani asibiti dake cikin gari aka dubani aka tsaida jinin tare da d'inkewa sanna aka samin magunguna a wajen, bayan mun dawo gida na kalli yayana wanda tun lokacin har zuwa yanzu kuka yake aikin yi, nace "yaya su waye suka biyoka kuma me kai musu?" Sunusi yace "kayi ha'kuri d'an uwana, na jawo maka an raunataka," sai nace mishi kar ya damu zan iya rasa rayuwata domin kare tashi rayuwar, nan ya fad'a min wai ciki yaiwa 'kanwar wannan d'an daban suke ta nemanshi, jin wannan maganar ba 'karamin tayar da hankalina yai ba, yayana ne shi ya kamata ace yana min fad'a in nayi kuskure ba ni ba, bayan na warke na tafi dashi Abuja yai wata shida a can sannan muka dawo na kaishi wani waje da ake d'inki nace da zama haka gwara ya koya da aikin riguna ne da kuma d'inki sukeyi nace duka a koya mishi, na biyasu a ranar ya fara koya washe gari ni kuma na koma Abuja da tunanin d'an uwana, iyayenmu duk sun rame saboda damuwar da yake jefasu ciki, ina komawa na samu sa'kon kiran gaggawa daga wajen matata Khadija ogana na nemana, haka na tafi ban ko zauna ba gabana na fad'uwa saboda be tab'a yimin irin wannan kiran bazatan ba._ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *MAMAN LABYB* (Mamie nah) *Hajiya mamie ikon Allah, kinyi naki kinyi na me 'karamin 'karfi, hadari malafar duniya, baya goya marayu, keji ba'a yi maki 'kyaure ko an maki sai ya bud'e yasin,😍😉 wuhuhu ina gwanar wasu nidai ga tawa, kainuwa dashen Allah, duk mai 'kaunarki ni yaso, ma'kiyinki ni ya'ki, duk mai 'kaunata to dole ya 'kaunaceki, Allah ya cigaba da d'aga darajarki ma'kiyanki suita ganin cigabanki ba'kin ciki na halakasu😂😂, ina yinki saboda Allah.😍😘💋* *~MUMMYN - SULTAN👑* *Mummyn Sultan wannan shafin kyauta ne a gareki, naki ne ke kad'ai kiyi yanda kikaso dashi babu mai ce miki don me😉😍* PAGE 170 to 175 _Zaune nake gaban ogana wato mahaifin matata Khadija, ina jiran 'karin bayani dangane da kiran da yai min, Alhaji ya kalleni yace "Ahmad abinda yasa na kiraka shine 'yan uwana da suke kano da Aminaina ke so in yi takarar gwamnan jihar kano, to kaga idan nace zan amince dole sai na koma can garin da zama, kuma kadarorina dake nan garin babu mai kula dasu, a ta'kaice dai gaskiya banda sha'awar yin siyasa, kuma bana so kujerar nan ta shiga hannun azzalumai, Ahmad kai na talakawa ne me burin taimaka musu a koda yaushe, wannan dama ce ka samu domin 'kara kusanto dasu zuwa gareka, amma me kace a kai, saboda sun dameni sunce su zasu yi mini komai, so nake kaje a madadina," nai shiru ina nazari kan wannan damar da na samu, sai nace mishi ya d'an bani lokaci nai tunani, bayan munyi sallama dashi na koma gida naita nazari zuciyata na bani cewa in amince dama ce wannan na samu na taimakon talakawa da jahata kanta da kuma d'an uwana shima in samar mishi da aikin yi, banyi wata-wata ba na kira iyayena a waya na sanar dasu halin da ake ciki, da farko basu amince ba amma daga baya da nai musu bayani da kyakkyawan 'kudurina akai sai sukayi na'am tare da goyamin baya akai, haka muka koma kano da zama lokacin Khadija nada tsohon cikin yayanka Ammar, mahaifin Khadija ya had'ani da aminanshi aka fara gudanar da maganar zab'e ranga-ranga, kuma cikin yardar Allah nan da nan na samu karb'uwa gurin jama'ar kano, da zab'e yazo Allah ya bani damar lashe zab'en, anan muka cigaba da zama har Allah ya sauki matata Khadija lafiya ta haifi yaronta namiji yaci sunan Ammar, ba yabon kai ba nayi wa 'kasa aiki ba kad'an ba, 'kauyenmu kuwa saida na maida shi ya dawo kamar birni, gidan iyayena ma na gyara musu shi nai musu gangariyan plat, yayana kuwa tuni na dawo dashi kusa dani a kano muna gudanar da komai tare, koda wani zab'en ya zagayo nace to gaskiya ni burina ya cika tunda Alhamdulillah dai-dai gwargwado talakawa sun amfana, na d'auko wani bawan Allah kuma abokina wanda yake takarar kansila ada sunanshi Alhaji Ahmad Tukur, shi na barwa kujerata ya hau kuma cikin ikon Allah ya samu kujerar gwamnan jahar kano, ni kuma daga lokacin na tattara na dawo gida kontagora, tarin kud'in da na mallaka da kuma kadarorina na cigaba da juya dukiyata tare da kula da kadarorinsa, duk da dai gabad'ayan kadarorina na kano na siyar ne na sake siyan wasu a Abuja da kuma kontagora sai nabar 'yan kad'an a kano irinsu gidajena na saka 'yan haya a can, lokacin da na dawo tare muka dawo da yayana ya zama kamar bashi ba yai kyau saboda kud'i sun zauna, ya tara dukiya ba kad'an ba shima, amma duk da haka be bar mummunan 'kudurinsa a kaina ba, kuma koda wasa be tab'a nuna min mugun nufinsa a kaina ba, bayan kwana biyu muna zaune da iyayena muna magana dasu nake ce musu Alhamdulillah yanzu kam burina ya cika tunda talakawan garin nan kowa yanzu yana da abun yi, bama na garin nan kad'ai ba, sannan nima kud'ina Allah ya sa musu albarka yanzu haka inada biliyoyin kud'i a account d'ina, banda kadarorin da na mallaka, nan da nan Sunusi abun ya 'kara 'kular dashi, tunani ya fara yi akan abinda ya kamata ya yi domin yaga ya mallaki dukiyar d'an uwansa ta dawo gareshi, kuma har zuwa yanzu ban daina raba dukiyata ina baiwa yayana Sunusi ba, a wannan rabin nake kula da iyayena da shi kanshi da kuma iyalina har na taimaki wasu ma a ciki, amma duk da haka dukiyata tafi tashi habbaka sosai ma kuwa, a lokacin ne kuma ya fara neman aure ba b'ata lokaci aka sha biki matarshi ta tare a kusa da gidana da na gina mana ni da shi, Sunusi fa ya samu dukiya sedai rashin godiyar Allah yasa yake hangen tawa, sedai ban tab'a sa mishi ido akan dukiyarsa ba balle insan yanda yake tafiyar da ita dan zai iya cewa saboda ni nake bashi nake yi mishi haka, dama already inada gida a kontagora nan muke zaune da iyayena, mun dawo babu dad'ewa Khadija ta sake haihuwa ta haifoka na sa maka suna Bilal, kamarku da Ammar har ta b'aci, ita kuma matar Sunusi tana da tsohon ciki a lokacin kana da wata goma sha uku a lokacin ban tab'a mantawa da wannan ranar, ranar Litinin cikin tsakar dare muna bacci yayana ya buga mana gida cikin tashin hankali muka bud'e yake shaida mana mummunan labari cewa iyayenmu sun mutu 'yan fashi ne suka shigo gidan nemana da suka 'ki nuna inda nake sai suka kashe su, mutuwar iyayenmu ya razanar da ni sosai har wasu sukaita cece kuce akan Sunusi ne ya kashe su in ba haka ba meyasa shi ko rauni ba'a ji mishi ba bayan yana cikin gidan, koda wannan furucin yaje kunnen Sunusi sai yace ai shi da yaji motsinsu be fito ba yana bacci yaji hayaniya ya tashi koda ya bud'e 'kofa har an kashe su shi yasa be fito ba, ni dai ban tab'a zargin d'an uwana ba ko kad'an, bayan wata shida da rasuwarsu wata rana muna kwance a cikin gida da dare muna bacci sai muka ji haurowar mutane cikin gidan d'aya bayan d'aya, ni na fara farkawa, koda na bud'e idanu sai na le'ka hango mutane nayi sun kai su goma sha biyar dukkaninsu ri'ke da manya manyan makamai, abinda ya bani mamaki da tsoro shine ganin Sunusi a cikinsu shima ri'ke da nashi makamin, cikin sauri na tashi Khadija nace ta tashi maza mu tafi, ta d'aukeka a hannunta tana nunamin Ammar nace taje zan d'auko shi na nuna mata wata 'kofa ta baya nace ta fita tanan, suna fita na du'ka zan d'auko d'an uwanka sai ga su Sunusi sun shigo su biyu shi da wani, Sunusi ya buga min wu'ka a hannu, a lokacin Ammar ya tashi yana ta kuka sannan Sunusi ya yanki Ammar da wu'kar nan ina gani, har gobe bazan manta da mutuwar yarona Ammar ba, ganin haka yasa nai wani 'kara tare da yin kukan kura nai kansu na daddoke su na d'auki Ammar a kafad'a na bi ta wannan 'kofar muka fice kuma na rufeta ta baya, na sami su Khadija a tsaye suna jirana nace musu muje, gudu muke, har muka 'karaso bakin mota, zamu shiga kenan muka hangosu sun kusa cin mana, sai muka yanki daji da gudu, muna cikin tafiya Khadija sai kuka take tana kallon Ammar mi'ka mata shi nayi na karb'eka daga hannunta, muna cikin gudu muka ga sun tare gabanmu da bayanmu, gefe kuma daji ne d'od'ar, jefomin wata goora sukai ta tad'iyeni na fad'i, sai na kalli Khadija nace ta shiga cikin jejin nan ita da Ammar su b'uya, Khadija tace ni kuma fa ba zata tafi ta barni anan ba, nace karta damu 'yan sanda suna hanya na kirasu kafin mu fito, ta juya da gudu ta shiga inda na nuna mata, tana tafiya suka zo suka kewaye ni ina ri'ke da Bilal, Sunusi ne ya 'karaso har inda nake ya du'ka kusa da ni, sannan yace "malam Ahmad kenan, kana tunanin duk 'kaunar da nake nuna maka ta gaske ce, to bari kaji tun muna yara na tsaneka tsana me tsanani saboda fifitaka da iyayenmu suke, kuma sai ka fini ilimi ka fini d'aukaka a rayuwa wanda abun ya dad'e yana damuna a rai, kawai nayi shiru ne saboda banda komai ko nace zan d'auki mataki ko na kawar dakai banda kud'in da zan biya masu tayani yin wannan aikin, nine babba amma maganarka ake ji ba tawa ba, na dad'e ina jin ciwon d'aukakar da ka samu a rayuwa, babban abunda baka saniba shine, 'kaunar da iyayenmu suke nuna maka da kuma rawar jikin da suke a kanka yasa suma kansu na tsanesu, abinda yasa na kawar dasu kuwa saboda sunji lokacin da nake waya ina magana da abokaina kan yanda zamu kawar da kai, yanzu kaima zan gama da kai, abinda yasa zan kasheka a yanzu shine saboda ina so dukkanin dukiyarka da kadarorinka su zama nawa kaga ka hutar dani ma tunda rabin dukiyoyin nawa duk sunana ka saka a jiki be dace in taso cikin talauci kuma in mutu ban dangwali dad'in arzi'ki ba," kasa cewa komai nayi saboda tsabar mamaki, hawaye ne kawai suke ta wanke fuskata na kalle shi nace "yanzu dama akan abin duniya kake neman rayuwarmu yaya, meyasa baka nuna min dukiyata kake so ba tun tuni da wallahi ko zan yi yawo ba ko sisi ni mai iya tattarata duka ne in baka, saboda kai shaida ne akan irin 'kaunar da nake maka ban tab'a tsammanin irin wannan sakayyar daga gareka ba Yaya, kayi ha'kuri karka kasheni, wallahi nafi 'kaunar cigaba da rayuwa tare da kai, na baka dukkanin dukiyata, bana sonta ni kai kad'ai nake so," Sunusi ko gezau be yi ba ya kalli wani wanda ke gefen damanshi yace "Makau d'auke min yaron nan daga jikinshi," Makau yayi-yayi ya 'kwaci yaron nan daga hannuna ya kasa, koda Sunusi yaga haka sai ya d'aga wu'kar hannunshi ya luma min a ciki, a lokacin ne suka samu damar 'kwaceka daga hannuna sun juya zasu bi matata su kasheta itama sai suka ji 'karar motar jami'ai, hakan yasa dukkaninsu suka gudu da kai a hannunsu, koda 'yan sandan nan suka 'karaso inda nake da'kyar na nuna musu inda Khadija ta b'uya nace "Kha di ja na can," ina gama fad'in haka na suma a hannun d'aya daga cikin 'yan sandan, saida nai sati uku a asibiti sannan na dawo cikin hayyacina, sai a lokacin ma ni na san cewa a Abuja muke, ashe tun washe garin ranar da abun ya faru Khadija tai waya da wayar d'aya daga cikin 'yan sandan ta sanar da mahaifinta komai ya turo aka kwashemu dukkanmu aka kaimu Abuja, Ammar kuwa tun kafin na farfad'o aka sallaceshi aka kaishi makwancinshi, kai kuwa bamu san inda kake ba bamu san a wane hali kake ciki ba domin da kai suka tafi a hannunsu, daga wannan lokacin ban 'kara komawa garin ba, bayan wasu shekaru abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kamuwar mahaifiyarka da ciwon zuciya me tsanani sanadin b'atanka gwara ammar munsan mutuwa yayi mun rasashi kai kuwa a kullum mun kasa cire rai da ganinka, sannan na dawo da dukkanin harkokina nan garin kano ashe alkhairi ne babba dawowana nan d'in, ashe Allah kad'ai yasan abinda ya b'oye sai yanzu yai nufin bayyanuwarsa Allah mun gode maka, to kaji irin abubuwan da suka faru dani a rayuwa My Son, ashe duk kaunar da d'an uwana ke nuna min so yake ya gama samun komai daga gareni ya kasheni, na yarda da d'an uwana fiye da kowa kai fiye da kaina ma, ban tab'a tunanin ko dabba zai iya kashewa ba, nafi jin ciwon rabani da iyayena da yayi fiye da komai._ Abba ya 'karashe maganar yana kuka, shima Amir kuka yake kanshi na kife akan cinyar Abban nashi, Umma Khadija itama kuka take sosai, duk d'akin babu mai rarrashin wani. Amir ne ya d'ago kai cikin kuka yace "lallai Abba duniyar nan cike take da abubuwan ban tsoro, in har baka mutu ba zakai ta jin abubuwa kala-kala, amma Allah baya bacci gashi nan be tab'ar dakai ba saboda kyawun zuciyarka, kuma shi kawu Sunusi da sannu zai girbi abinda ya shuka." Abba yace "a'a na yafe mishi fatana Allah yasa ya shiryu kafin Allah ya d'auki ranshi," Amir yace "Abba kai wane irin mutum ne?" Abba yace "me kwad'ayin samun aljanna." Amir yace "Abba ka shirya kai da Umma muje gidan su Amira taga iyayena," Abba yace "to my son yanda kace haka za'ai," ko da isarsu gidan suka tarar da gidan a gar'kame da suka tambaya aka tabbatar musu cewa masu gidan sun tashi gaba d'aya. _Topha tashin hankali wanda ba'a sa mishi rana_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *MAMAN LABYB* (Mamie nah) *Kina raina a koda yaushe, tuni kika she'ke zuciyata da 'kaunarki ke ta daban ce, halin kirkinki ma daban ne, ina 'kaunarki 'kauna ta gaske kuma ta har abada, matsayinki ya zarce hakan guna😍😘💋* *~MOMYN KADEEJA*🧕 *Momyn kadeeja albarkacin 'kaunar da kike gwada min tare da d'umbin kulawarki kan littafin nan, na baki wannan page d'in kyauta kiyi yanda kikaga dama dashi, in kikace ba me karantawa ma sai ke kad'ai ta zauna,😂 ina godiya sosai da comment d'inku ina jin farin ciki sosai wlh akai.🙏😍😘💋* *Idan so yai so ko masoya na nesa da juna zuciyoyinsu na raya musu abu guda game da juna, ikon Allah kenan😍 yanayin 'karfin so a cikin zuciyar masoyan gaske kenan😍😍😍😍😍* PAGE 175 to 180 Amir ya fad'i nan 'kofar gidan yaita rusa kuka kamar 'karamin yaro, sai a yau yake ganin wautarshi da kuma rashin kyautawarsa akan share lamarin Amira da yayi, cikin sauri ya d'ago ya kalli mahaifinshi tare da ri'ke mishi hannu yace "Abba wai sun tashi aketa ce mana fa, ina suka kai min matata to? Abba ka taimakeni a nemo inda suke, wallahi Abba in babu Amira bazan iya cigaba da rayuwa ba. Jiri Amir ya fara ji, ya dafe kanshi da hannu bibbiyu, ya tafi taga taga zai fad'i Abbanshi yai sauri ya rungumeshi, yaita jijjigashi amma ina ya sume, cikin sauri securirty's d'insu suka kamashi aka sa a mota suka shiga sai asibiti. Haka Amir yaita faman jinya ya mugun sawa kanshi damuwa, a koda yaushe yanzu bashi da wajen zuwa sai unguwar su Amira, ya samu 'kofar gidansu yaita rusa kuka, kullum aikinshi kenan, iyayenshi har sun saba duk in suka ga basu ganshi ba to nan suke nufowa, kuma suna zuwa zasu ganshi. Babu inda bai je neman Amira ba amma babu ita ba labarinta, kullum cikin tunani yake duk yabi ya fige, iyayenshi duk sun rasa gane kanshi, saida ya zagaye dukkanin station d'in garin ya bada hotunanta ga duk wanda ya ganta ko yaji labarinta, amma har yau ba bayani. Sunyi yawon shi da security's masu yawan gaske amma shiru kake ji ba wani bayani a kanta. Bayan kwana biyu, Amir ne kwance kan jikin Ummanshi tana shafa kanshi tare da rarrashinsa kan ya rage sa damuwa a cikin ransa gashi nan sanadinta ya kamu da hawan jini kar ya zama silar kamuwarshi da ciwon zuciya. Suna cikin magana sai ga Abba ya shigo, 'karasowa yai inda suke ya kalli Khadija yace "Sannunku da gida My Love, My Son ya kake, ya jikin naka?" Gaba d'ayansu suka had'a baki wajen yi mishi sannu da zuwa, ya amsa musu sannan yace "na sameku lafiya?" suka sake had'a baki wajen fad'in "lafiya lau." Zama Abba yai kusa da matarshi, sannan ya dafa Amir dake kwance kan jikinta, yace "Amir ji yanda ka rame ka lalace, haba Amir, da damuwa da sawa rai suna maganin kowace irin damuwa da tuni sunyi mana tamu maganin damuwar, amma a maimakon haka sai muka ri'ki takobi na gaske wato addu'a makamin mumini, wannan addu'ar da muka ri'ka itace tasa Allah ya dubemu da idon rahma yaji tausayinmu ya bayyana mana kai, saboda haka ka dage da addu'a muma muna tayaka, tunda ba mutuwa tayi ba menene na damun kanka za'a gansu insha Allah." Amir ya share hawayen dake kwararowa daga cikin idanunshi, sannan ya kalli mahaifinshi yace "Abba Amira ta zama jigo na dukkanin rayuwata, zan jure komai amma akan Amira ban yin baya, Abba wallahi na sani Amira tana cikin damuwar rashina fiye da wadda nake ciki a yanzu, abinda ke sakani kuka kenan idan na tuno Abba bana son damuwarta ko kad'an, wallahi tunda naji zuciyata na zafi itama ta-ta tana can tana mata zafi," yana kai nan a zancenshi ya sake fashewa da kuka. Abba da Umma sun tausayawa yaronsu matu'ka, domin bai b'oye musu komai ba cikin labarin rayuwarsu da Amira, kuma duk wanda yaji labarinsu dole sai ya tausaya musamman ma Amir wanda ya rayu cikin mawuyaciyar rayuwa. Nan dai suka 'kara bashi baki, da 'kyar suka samu yai shiru, suna cikin hira shi dai bai saka musu baki, da haka ma bacci ya d'aukeshi. ……………………………… B'angaren su Amira kuwa har yanzu ta kasa dawowa asalin Amirarta, sannan koda yaushe Nura cikin sintirin zuwa wajenta yake, kan dole take sauraronshi shima dan yana mata zancen Amir ne, amma sam bata 'kaunar a dameta yanzu, a hankali tun tana gundura dashi har sabo ya shiga tsakaninsu, dama kowa ya sani cewa muddin mutum yana yi maka zancen wanda kake 'kauna akoda yaushe kuma yana yabawa masoyin nan naka zakaji zuciyarka ta sha'ku dashi, to haka ce ta faru da Amira. Zaune Amira take gaban Dad d'inta shigowarta kenan falon Dad d'in nata wanda ya kirata a waya yace tazo yana son magana da ita. Koda ta shiga ta tarar harda Mum d'inta a falon, gefe ta samu ta rakub'e kamar wata marainiya, sannan tace "Dad gani," Dad ya kalleta yace "Doughter abinda yasa nai kiranki shine Nura ya tabbatar min da yana 'kaunarki, mahaifinsa kuma yazo neman aurenki wajena dan hak.........." be kai ga 'karasawa ba Amira ta mi'ke tsaye cike da matsanancin b'acin rai had'e da razana, sannan ta kalli Dad d'inta tace "Dad Nura fa kace!!! to wallahi ban tab'a 'kaunar Nura ba a cikin raina, kuma har abada bazan 'kaunaceshi ba, wai ma Dad ba akan talaucin Amir ka 'kishi ba kuma ka tsaneshi, but why kake so yanzu in auri talaka wanda ubanshi ke aiki a 'kar'kashinka? gaskiya bana 'kaunarshi, kuma ko zanyi aure a nan gaba bazan tab'a auren talaka ba sai irin wanda kakeso mu gani zasu iya ri'ke maka ni kamar yanda Amir talaka bawan Allah ya ri'keni ko kuwa." Dad yace "naji Nura talaka ne shi amma ai yana da asali ko, to shikenan in har baki amince da Nura ba to ki zauna da shirin cewa cikin satin nan zan kawo miki duk wanda naga dama." Amira tai murmushin takaici sannan tace "Dad wallahi ka sauya gaba d'aya, amma ba komai, ni bazan 'ki yi maka biyayya ba akan koma waye zaka had'ani dashi, saboda ba auren so zanyi ba, duk wata so da 'kauna mutum d'aya tak zan iya ba mawa su, kuma na rasashi, to wallahi ba na biyunshi a zuciyata, zanyi maku biyayya kan duk wanda zaku had'ani aure dashi Dad," tana kai nan a zancenta ta fita daga d'akin a guje tana kuka lambun gidan taje ta zauna kan kujera tare da had'a kai da guiwa, ta cigaba da kukanta. kanta na du'ke tana cikin kukan ne taga alamun mutum a kanta, tana d'agowa taga Nura ne, maida kanta tayi tare da cigaba da kukanta. Nura ya du'ka kusa da ita yana rarrashinta tare da yi mata magiya kan ta sanar dashi abinda ke faruwa, Amira ta d'ago tace "Nura idan kana tunanin sabon da mukai da kai akwai d'igon 'kaunarka a raina to wallahi ka daina, bana 'kaunarka gwara ma ka janye wannan maganar, Nura ya numfasa yace "yanzu akan wannan kike kuka, ni banma san anyi zancen ba, tabbas ina 'kaunarki kuma na fad'awa mahaifina amma sam bance yazo yai maganar a gidanku ba, indai kan wannan ne ki kwantar da hankalinki ki daina kuka maganar ta wuce, Amira ta d'ago kai cikin kuka tace "ina fa ta wuce Dad yace ko kai ko kuma ya zab'a min koma wanene." Nura ya numfasa cikin sauri dabara ta fad'o mishi a rai, yace "tunda abun ya zama haka me zai hana ki amince ni ki aureni, ni kuma na d'aukar miki al'kawari da zarar mijinki Amir ya dawo gareki wallahi zan sakeki ki aureshi, da wannan shawarar suka amince kuma a tare sukaje Nura ya sanar dasu amincewar Amiran ita kuma Amira ta baiwa Dad d'inta ha'kuri kan abinda ya faru d'azu, amma iyayenta sunsha mamaki kan canjin ra'ayinta lokaci guda, musamman yanda suka ga ta tayar da hankalinta akai musamman ma akan zancen Nura d'in, to koma dai menene su hakan yai musu dad'i, ba tare da b'ata lokaci ba aka sa ranar aure sati uku kacal, a ranar da aka tsaida rana ma Amira taci kuka kamar me, ita in aka barta tunda babu Amir rayuwarta ita kad'ai zata 'karasata. Abba da Umma kuwa sun yanke hukuncin dawowa kano da zama, tunda dama Amir ya fad'a musu acan yai makaranta, to so suke su koma can ya cigaba da karatunsa ko Allah zai taimakesu ya rage tunanin da yake yi. Koda suka tuntub'eshi da maganar be yi wata-wata ba ya amince da zancen dama garin ya isheshi tunda ba masoyiyarshi a ciki, amma sai yace wa iyayenshi in suka tafi kuma Amira ta dawo fa? mahaifansa suka ce mishi ai sun rarraba hotonta ga jami'ai, ana ganin sun dawo a ranar za'a basu labari, da haka ya amince suka fara shirin tafiya kano. A yau talata su Amir dirarsu kenan a garin kano, kuma a yau talatar dai aka shaida d'aurin auren Amira Ahmad Tukur da Nuraddeen. _'ka'ka-k'ara 'ka'ka ko wannan wainar ya za'a toyeta oho, ina fatan masu karatu basu manta da mahaukacin kishin Amir ba😂_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 180 to 185 Daga shigowarsu cikin garin kano suka tabbatar da cewa lallai shagalin biki ake, kuma shagalin ma na 'ya'yan hamshak'an masu kud'i. Abba ya kalli matarsa yace "da alama cikin garin nan shahararren biki ake kuma k'ayatacce." Umma tace "gaskiya kam da alamu, haka suka k'arasa inda zasu je suna tafe suna hira ba tare da Amir yace musu ci kanki ba, har suka k'araso gingimemen gidan Abba dake cikin g.r.a a kano. Ko da su Amir suka dawo garin kano da zama babu abinda ya canza zani daga gareshi, domin kuwa har yanzu bai ga masoyiyarsa ba, kuma bai dena tunanin da yake yi a kanta ba, da shelar nemanta a ko'ina, kuma a kanon ma duk inda yasan sunyi rayuwa tare da Amira can yake zuwa ya zauna yaita kuka, idan ya tashi da safe gidan shi yake zuwa yaita tuno abubuwan da suka wakana tsakaninsa da masoyiyarsa yana kuka tare da surutai kamar zararre, koda yake mai yin soyayya tamkar zararre yake musamman idan tazo maka da k'alubale me zafi irin na Amir da Amira, daga nan kuma idan ya tashi sai ya wuce d'aya gidan Amiran shima yaita kuka, yanzu a can yake wuni sai dare yake komawa gida, abun duk ya damu iyayensa, su sun dawo dashi nan domin ya samu sauk'i ashe zuwansu nan ne ma zai k'ara sakashi cikin wani mawuyacin hali. Shawara suka yanke akan a sakashi a makaranta amma itama ba wadda sukayi shi da Amira ba. Koda suka tuntub'i Amir da zancen makaranta sai ya amince kai tsaye, amma ya dage akan cewa shi lallai wadda yake yi ada a nan kanon ita yake so a saka shi, babu yanda suka iya cikin k'ank'anin lokaci aka gama mishi komai ya fara zuwa. ………………………………… B'angaren Amira kuwa a ranar da aka d'aura aure a ranar suka tare a wani tangamemen gida, wanda Dad ya mallaka wa Amiran shi halak malak. A daren ranar bayan an kaita kowa ya watse saura shigowar ango sai Amira ta tashi cikin sauri ta gark'ame k'ofa, ta fad'a kan gado tasha kukanta ba me rarrashi, idanunta duk sun kumbura saboda tsabar kukan da take sha a kullum tun ranar da aka saka ranar aurensu har zuwa yau da aka kawota gidanta na aure. Ko da Nura ya shigo da abokanansa babu kalar magiyar da be yi mata ba akan ta bud'e k'ofar amma tak'i, dole haka abokansa suka juya kowa da abinda yake sak'awa a ransa, Nura yai musu rakiya ya dawo ya ajiye ledar kajinawa da lemuka da ya siyo a gefe, ya kwanta a d'aya daga cikin kujerun dake falo. Yana daga kwance ya kira mahaifinsa yana fad'a mishi abinda Amira tai mishi yau, daga can d'ayan b'angaren mahaifin Nura yai murmushi, sannan yace "haba Nura, yau fa aka kawota gidan, kuma kasan dai bata sonka, to a hankali ya kamata ka bi da ita har mu samu mu cimma burinmu a kansu ita da mahaifinta, mu yagi rabonmu mu k'ara wuta," sun jima suna hira da mahaifinsa yana k'ara d'ora yaron nasa akan muguwar hanya, daga k'arshe suka yi sallama. Washe gari Dad d'in Amira ya kira Nura gidansa ya bashi makullin sabuwar mota, sannan ya bashi takardun wani kamfani nashi ya bashi su halak malak, Dad ya d'ora da cewa "wannan ba komai bane akan abubuwan da zanyi maka a gaba muddin ka kulamin da 'yata," Nura yaita godiya sannan suka yi sallam ya fito yaja sabuwar motarshi d'aya daga cikin security kuma ya ja mishi tsohuwar suka taho zuwa gida, a hanya ne ya kira mahaifinsa yake sanar dashi abinda Dad ya bashi yanzu, sai mahaifin Nura yace "kaga abinda nake fad'a maka ko," Nura yace "wallahi Dad na gani, wai harda wani in kula mishi da 'yarshi yanda ya kamata," mahaifin Nura yace "eh yanzu ai kyautata mata da zaka yi shi zaisa mu samu komai cikin sauk'i a wajen mahaifin nata, tunda ka samu sabuwa zanzo ka bani d'ayar taka tunda tawa dama duk ta tsufa, Nura yai dariya yace "to sai kazo ai in komai ya kankama ma har jirgi sai a baka ba mota ba Baba," Baban nashi yace "yauwa na gode Allah da ka fahimci komai yanzu ka dawo kan hanya, ai duk fafutukar nan da kaga inayi duk saboda kai ne Nura na," nikam naci kaji uban wofi sai kace dukiyar da guminsa ya tara ta. *BAYAN WATA 'DAYA* Abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da komawar Amira makaranta, sedai kuma ikon Allah basu tab'a had'uwa da Amir ba, kuma hakan ta faru ne sakamakon canza kos da Amiran tayi, mijinta Nura shi ke kaita ya kuma dawo da ita, duk wata kyautatawa na mata da miji suna yiwa juna musamman ma shi Nuran, amma duk da haka Amira ta kasa barinshi ya kusanceta, a wautarta ganin hakan take kamar cin amana ga Amir, tunda ita har yanzu zuciyarta bata daina bata yana raye ba. Yau alhamis, shigowar motar su Amira kenan cikin harabar makarantar, a yayin da shima Amir be dad'e da shigowa ba yana daga cikin motarshi a zaune amma k'ofar motar a bud'e take, k'afarsa d'aya tana ciki d'aya kuma tana waje, yana zaune yana abinda ya saba wato tunanin Amira, kamar ance ya d'aga idanunsa kawai sai akan Amira, gani yake kamar gizo take yi mishi kamar yanda ya saba gani, shiyasa ya 'kura mata idanu, can kuma sai ya murza idanunsa ya sake murzawa ita d'in ce dai yau Allah ya gwada mishi zaune cikin mota, tabbas wannan Amirarsa ce, ya fad'i da 'karfi yana maimaitawa cikin farin ciki had'e da zub da hawaye yana cewa "Amira ce, wallahi Amirata ce, ko cikin miliyoyin mutane Amira wallahi zan shiga in zak'uloki, cikin sauri ya yunk'ura da niyyar zuwa wajenta, se dai abinda ya gani ya sakashi tsayawa cak, wani mutum ya gani ya fito daga b'angaren driver ya bud'e mata motar ta fito. Tana fitowa yaga wannan mutumin yai mata magan ta bashi amsa fuskar nan ta-ta a d'aure ba alamar fara'a, suna tsaye wata yarinya wadda bata fi sa'ar Amiran ba ta tunkaro wajensu tana dariya, bayan ta k'araso suka gaisa yaji tace "Amira saura minti biyar fa a shiga lecture, nima ke na tsaya jira mu shiga tare tunda mukai waya naji kince min gaku nan nake juranki. Amira ta kalleta tace "muje," Nura ya kalli "wannan yarinyar yace "Anisa ki kulamin da matata da kyau dan Allah," Amira tace "to insha Allah," suka yi sallama da shi ya fad'a cikin motarsa, yai mata key, ya ja ya tafi. Duk abubuwan nan da suka faru duk a kan idanun Amir ne, kuma yaji duk abinda sukace, ya k'ara tabbatarwa da tabbas Amirarsa ce, amma abinda be gane ba shine waye wannan mutumin, kar dai Amira amanarsa taci ta sake yin wani auren? ganin su Amiran sun juya sun tafi yasa ya fito cikin sauri yana binsu a baya har saida yaga inda suka shiga. Waje ya samu ya zauna inda duk wanda zai fito daga wajen zai ganshi, amma shi yana d'an nesa da wajen, bayan kamar wajen awa d'aya yaga anata fitowa d'aya bayan d'aya, hakan ya bashi tabbacin cewa lallai sun gama lecture d'in nasu, yana nan zaune can sai gasu sun fito ita dai da wannan yarinyar wadda yaji an kira da Anisa, rakiya yaga taiwa Amiran har wajen parking suna jiran k'arasowar mijin nata, basu dad'e ba kuwa sai gashi ya shigo, cikin sauri ya fito tare da had'a hannu biyu yana neman afuwar Amiran, daga k'arshe ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe, shima ya shiga ya zauna, sannan yaja suka tafi, Amir yana kallo ji yai kamar yaje ya shak'e wuyan mutumin da yake gani da matarsa wanda har yanzu be yarda mijinta bane. Anisan ce yaga ta juyo tazo zata wuce ta tafi hostel, hakan ya bawa Amir tabbacin a cikin makarantar take da zama. Cikin sauri ya k'arasa wajenta tare da shan gabanta, kallonshi tayi, tare da k'walalo idanu had'e da ja da baya, har ta juya zata danna a guje ya sake shan gabanta yana fad'in "dan Allah ki saurareni," cikin rawar murya Anisa tace "to ina jinka," dan ita har ga Allah tunaninta aljani ne ko kuma fatalwarsa ce tazo mata. Kallonta Amir yayi sannan yayi murmushi, yace "Anisa ki kwantar da hankalinki, yanayin yanda kika nuna min ya tabbatar min da kinada labarina a wajen Amira ko?" Anisa tace "eh hakane babu wanda zama zai had'ashi da Amira koda na awa d'aya ne ba tare da ta bashi labarinka ba had'e da nuna hotonka, a yanda na lura a yanzu tana cigaba da rayuwane ma akan dalilan abu guda biyu, na farko saboda tana sawa ranta cewa wata rana zaka dawo gareta sai gashi kuwa, sai abu na biyu shine tana zama da duk wanda yake yo mata hirarka ne kawai domin hakan na mata dad'i taga anata mata maganarka," Amir yace "amma meyasa da kika ganni kika gudu, kuma waye na gani ya d'auketa a motarsa sun tafi tare?" Anisa ta numfasa sannan tace "wallahi da farko nai tunanin gamo nayi ko kuma fatalwarka ce, saboda Amira tace min kayi hatsari ance ka mutu amma ba'a ga gawarka ba, kuma ita tasan ba zakai mata haka ba ka mutu ka barta bayan ka tabbatar mata cewa tare zaku rayu," Amir kuka yake sosai saboda tsabar tausayin Amira da yaji cikin ransa, saida ya yi mai isarsa Anisa na kallonsa itama tana jin tausayin rayuwar wad'annan masoya, musamman ma shi halin da zai shiga yanzu idan yaji abinda zata fad'a mishi game da mutumin da yake tambayarta a kanshi, Amir ya share gawayenshi da suka yi ja kuma suka kumbura saboda kuka, sannan ya kalleta yace "shi kuma wanda na gansu a tare fa?" Anisa ta fara inda-inda, Amir yace "ki fad'a min mana," Anisa tace "eh um wanda ka gansu tare mijinta ne, amma harta shi mijin nata silarka ta aureshi." Nan da nan idanun Amir suka 'kara jajawur saboda tsabar kishi, hannunshi ya d'aga ya buga akan wani window na glass nan da nan glass d'in ya fashe, hannunsa ya fara fitar da jini sakamakon raunin da yaji, matsawa yayi jikin ginin wajen yaita had'a kanshi da bango, nan da nan goshinsa da kan shima ya fashe ya fara wanke fuskarsa da jini. Juyowa yayi ya kalleta a hargitse, cikin matsanancin tashin hankali yace "na rantse da mahaliccina babu wanda zai rayu da matata sai ni kad'ai," yana gama fad'in hala yaji jiri ya fara d'ibarsa alamun jikinsa naso ya rikice mishi, jirin ne ya kwashe shi ya fad'i k'asa, Amira kuwa duk ta rud'e ta rasa yanda zata yi da shi, da yake masu tsaronshi a can bakin 'kofar makarantar yake cewa su tsaya, baya bari su shigo ciki, wayarsa ya ciro ya lalibo lambar d'aya daga cikin masu tsaron nashi ya mi'kawa Anisan yace ta kira tace musu Amir na kira, cikin 'kank'anin lokaci sai gasu da gudunsu sun 'karaso, Amir cikin wahalallaiyar murya yana numfashi sama-sama yana dafe da 'kirjinsa yace "ku kaini asibiti, ku taho da waccan yarinyar, kuma karku fad'awa su Dad komai a kaina, duk wanda ya fad'a mishi a bakin aikinsa," cikin sauri suka d'aukeshi tare da tasa 'keyar Anisa suka tafi tare da ita. *BAYAN AWA 'DAYA* An duba Amir an gama yi mishi komai sedai an d'an bashi gado ya huta kafin su tafi. Amir yana daga kwance ya kalli Anisa wadda take cike da tsoro da mamaki har yanzu, yace "Anisa naji kince silata tai aure, meyasa kika fad'i haka?" Anisa tace "eh hakane ita ta bani labari, mahaifinta ne ya dameta ta fito da mijin aure ko ya bata wanda yai niyya, shine ta yarda ta auri Nura bisa sharad'i, sunyi aure ne akan yarjejeniyar cewa idan ka dawo gareta zai saketa ta koma wajenka, amma ita sam batama da niyyar yin auren haka taso cigaba da zama, tirsasawar mahaifinta yasa ma har ta amince tai auren," Amir yace "to Anisa ina neman alfarma daga gareki, dan Allah karki fad'awa Amira komai game da ni, karma ki nuna mata kin ganni, ni nasan yanda zanyi Amira mu had'u in ganta ta ganni kuma har ta dawo wajena, abu na biyu shine ina neman alfarma wajenki ki taimaka ki fad'a min sunan mijinta kuma ki bani lambar wayarki, in kikai min haka kin gama min komai. Anisa tace "insha Allah ba abinda Amira zata ji daga gareni, sannan ta ciro biro ta rubuta mishi sunan Nura harda inda yake aiki da adreshin gidan aurensu da kuma lambar wayarta da ya tambaya, Amir ya karb'a ya duba, yaji dad'i sosai, yai mata godiya, sannan ya bata kyautar dubu d'ari, kuma ya bada umurnin d'aya daga cikin masu tsaronta ya kaita har gidansu, suka yi sallama ta tafi. Sai a yanzu hankalin Amir ya kwanta harda murmushi, domin shi yasan Amira ta dawo gareshi ta gama insha Allah, dama so yake ya tabbatar amanarshi taci ko ya abin yake kuma ya tabbatar. Amir ya sake yin murmushi sannan yace "Nura zan bi da kai ta lalama, in kuma har ka k'i to zan d'auki matakin gaggawa a kanka, ya sake yin shiru, can kuma sai ya sake cewa Allah sarki Amira na," ko me ya tuno oho Allah kad'ai ya sani sai kuma shi da abun ya shafa. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta) ``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* (Mamie) *RUKAYYA, TA CIKIN BK GROUP,* & *AUNTY HAUWA TA CIKIN MAHAKURCI GROUP* *WANNAN PAGE 'DIN NAKU NE NA BAKU SHI KYAUTA KUYI YANDA KUKA SO DASHI BABU MAI CE MUKU DAN ME, KUMA INA GODIYA DA 'KAUNARKU GARENI, ALLAH YA BARMU TARE YA K'ARA MUKU SONA😂🙏😍😘💋* *MUMMY'S FRIEND* (Tawan) *Allah ya d'orar miki da lafiya d'orarra, ya yaye miki dukkanin damuwarki.* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```🤜🤛 PAGE 185 to 190 Bayan kwana biyu Amir ya samu lafiya sosai ya warke garas, daga lokacin kuma ya fara tunanin abinda ya kamata ya yi domin ceto soyayyarshi da take 'ko'karin tarwatsewa. Yau ta kama juma'atu babbar rana, Amir ne keta faman shiri da sassafe yana 'ko'karin fita, Umma ce ta fito daga d'aki tana kallon Amir dake shirin fita ko karyawa be yi ba, tace "yaron kirki sai ina haka da sassafe? " Amir ya d'ago ya kalli mahaifiyar tasa yana murmushi yace "wallahi Umma cikin makaranta zan shiga," Umma tai murmushi sannan tace to Allah ya dawo da kai lafiya, Allah bada sa'a. " Amir yace "ameen, " Umma, ya rungume mahaifiyar tashi sannan ya fice daga gidan cikin sauri. Amir na fitowa masu tsaron shi suka taso a guje suka bud'e mishi mota, sannan suma suka shisshiga tasu, mota wajen bakwai uku a gaba uku a baya ta Amir tana tsakiya, a haka suke fita duk inda zasu. Makaranta suka shiga kai tsaye, suna shiga suka faka motocinsu, securityn duk suka fito suka zagaye motar Amir kasancewar har yanzu be fito daga cikin motar ba. Amir yace wa masu tsaron shi su koma zai nemesu akwai abinda yake so yayi, babban cikinsu ne yace "oga idan muka koma gida yanzu mahaifinka ya dawo dole zai tambayemu ina kake, hakan zai iya jawo mana rasa aikinmu, kayi hak'uri dai ka barmu mu jiraka a bayan makaranta in baka so a ganka tare damu ne. " Amir yai shiru yana nazarin maganar su, can sai ya d'ago ya kallesu yace "ok kuje bayan makarantar ku jirani, idan na gama abinda nakeyi zan nemeku a waya. " Bayan tafiyarsu Amir ya sauya rigar jikinshi, sannan ya saka glass no respect, ya zauna zaman jiran 'karasowarsu Amira. Amir na nan zaune sai ga motar su ta kutso ciki, k'urawa motar ido yayi har ta 'karaso kusa da tashi tai fakin, sannan Amira ta fito ranta a b'ace ta wuce abinta, Amir ya bita da idanu har ta b'acewa ganinshi, idanunsa na fitar da hawaye, tausayinta yake ji matu'ka duk ta rame kamar ba amarya ba. Amir ya dawo da kallonsa ga Nura, bud'e motarshi Nura yayi ya fito sannan yazo gaban motar ya haye samanta ya zauna, Amir dai na kallonsa yaga ya ciro waya a cikin aljihunsa yai kira ya kara a kunnensa, bayan an d'aga yaji Nuran na cewa gaskiya Baba nifa na fara gajiya da halin yarinyar nan Amira, wallahi bnda taci sa'a ina sonta da kuma 'kudurinmu kanta da tuni nai maganinta, Baban yace "kar kai haka ka bari burinmu ya cika koma menene ka aiwatar daga baya babu me hanaka tunda matarka ce, Nura yace "ni mahaifinta ma ya kwafsamin Baba, so nayi ya d'orani kan dukiyarsa gabad'aya kaga cikin lokaci 'kan'kani zamu tara ma'kudan kud'i, nan dai mahaifinsa ya cigaba da rarrashinsa, bayan sun gama wayar ya kashe tare da maida wayarshi cikin aljihu, Amir na jin haka yai jim yana tunani kar dai akan Amira suke tattaunawa da mahaifinsa, amma koma menene zai gane nan bada dad'ewa ba, cikin sauri Amir ya fito daga cikin motarshi ya nufi Nura, da isarshi wajen yaiwa Nura sallama sannan ya bashi hannu suka gaisa, Amir ya tsaya kusa dashi tare da jingina da motar, sannan yace "Amir ya ciro taba a aljihunsa, abinda bai tab'a kwatantawa ba koda wasa, Amir ya kalli Nura yace "abokina ko kana da lighter? Nura ya d'ago cikin b'acin rai yace "banda ita wallahi, amma kaima da zaka ji shawara da ka daina shan tabar nan saboda tana cutarwa, zuciyar Amir tace ok baya sha kenan, Amir ya cire tabar nan daga bakinsa yace "kai dai bari kawai, matata ce silar jefani a wannan halin, babu wanda na tab'a yin wannan hirar dashi sai kai, kaima naga kamar duk matsalarmu d'aya ne shiyasa zan fad'a maka, dan ina hango tym d'inda matarka ta tafi rai a b'ace ko sallama batai maka ba, Amir ya cigaba da cewa ni tawa kullum fad'a da neman rigima, wallahi har tsoronta nake ji, ta maida ni kamar wani yaron da ta haifa ko bawan da ta siya da kud'inta, ko yanzu ma da na d'aukota daga gida zuwa nan makarantar tasu bala'i taita yimin har muka k'araso, sannan daga 'karshe da ta tashi tafiya abinda matarka tai maka nima shi tawa taimin harda kashedin saura in makara wajen zuwa d'aukota. " Duk irin b'acin ran da Nura ke fama dashi sai da Amir ya sakashi yaita faman darawa sakamakon labarin nan da ya gama bashi yanzu. Amir ya 'kura mishi idanu kamar wani dolo yace "ikon Allah ni ina baka labarin damuwata tare da nuna jimamina kai kuma kana yimin dariya." 🤔 Saida Nura yai dariyarsa mai isarshi sannan yace "yi ha'kuri abokina, wallahi dariya ka bani, haba ya zaka zauna mace taita juyaka haka, Amir yasha kunu irin shi yaji haushin dariyar da Nura yai mishi, sannan yace "dad'in abun ai matsalarmu d'aya, in ka gama yimin dariya sai kaiwa kanka. " Nura yace "a'a wallahi matsalarmu ba iri d'aya bace, ka ganni nan, ni aure baya gabana ma sam da farko, saboda duk macen da naso ina samu da dukiyata in biya bu'katata daga 'karshe in sallamesu," Amir yai caraf yace "wallahi ka huta da wannan wahalar ta rayuwar aure." Nura yace "af tsaya kaji mana, ina zaman zamana, Babana ya b'ullo da zancen aure auren da aka yishi domin wata manufa tashi, ada naso in bijire, amma da naga yarinyar naji ina 'kaunarta, naji ta kwanta min a rai, shiyasa na amince akayi auren, amma aurenmu da ita dashi da babu shi duk d'aya ne, domin har yanzu hoto ne ni a gurinta sunan wai nayi aure ne amma har yanzu ta'ki amincewa dani. " Amir yace "to meyasa ta'ki amincewa da kai? " Nura yace "saboda akwai wanda ta fara aure ya mutu amma ba'aga gawarshi ba da yake mahaukaciya ce wai shi take jira, aurenmu ma saida ta gindaya min sharad'i akan sai na yarda in aka ga tsohon mijinta zan saketa ta koma mishi. " Amir shima ya kwashe mishi da dari, Nura yace "dariya ma kake min? " Amir yace "ramawa nayi, Allah sarki ka bani tausayi, kace kai har yanzu baka shaida kayi aure ba," Nura yace "wallahi kuwa, ni har ta fara bani haushi, amma insha Allah sai burina ya cika a kanta." Sun dad'e suna hira kamar sun dad'e da sanin juna, daga 'karshe suka yi musayar lamba tare da fad'awa juna sunayensu, sannan suka yi sallama kowannensu ya shiga mota suka bar makarantar. Koda yaushe haka suke yi, Amir yana riga su Nura zuwa makarantar, amma baya zama cikin motar yanzu, b'oyewa yake saboda kar Amira ta hangoshi, sai ta shiga aji yake fitowa susha hirarsu suyi da matansu sannan suyi sallama su tafi. Hakan ya jawo shak'uwa me 'karfi a tsakaninsu har takai ga Amir yana ziyartar Nura a wajen aikinshi su sha hira. Yauma kamar kullum Amir suna zaune a cikin office d'in Nura Amir ya kalli Nura yace "ya kamata mu had'a matanmu su san juna, amma sai ka fara zuwa gidana na gabatar da kai wajen matata tukun. " Nura yace "a'a ban yarda ba gidana za'a fara zuwa muje ka gaisa da matana, yanzu ma tunda ba abinda kake yi idan mun tashi daga nan kawai sai mu wuce bari ma kaga in kirata in sanar da ita muna da babban ba'ko." Abinda Amir yake so yaji Nura ya fad'i kenan dama, hakan yasa yai farin ciki da jin haka kuma be yi mishi musu ba. Nura ya d'auki wayarsa ya kira Amira ya shaida mata cewa anjima zasu taho gida tare da ba'ko ta shirya mishi abubuwan tarba na musamman, to kawai tace sannan ta kashe wayar, ita Amira ada tana sakin jiki dashi har suyi hira kafin ya aureta, amma yanzu haka kawai taji wani irin haushi yake bata, hakan kuma baya rasa nasaba da kishin kanta da take taya Amir. Sun dad'e suna hira bayan wajen awa biyu suka tashi suka nufi hanyar gidan Nura. Cikin 'kan'kanin lokaci suka 'karaso gidan, Amir kanshi ya jinjina da yaga gidan domin yasan an narkar da kud'i wajen gina narkeken gida da 'kawata shi. Fakin sukayi, sannan suka fito, Amir yaja ya tsaya, Nura yace "muje mana, " Amir yace "nasha zaka sanar da ita tukun,? " Nura yace "haba muje mana nace," suka wuce Nura na gaba Amir na baya har suka shiga tangamemen falo, ba kowa a falon sai kayan kallo da suke kunne suke ta aiki. Nura ya juyo yace wa Amir "bismillah zauna, bari in shiga in kira matar tawa ku gaisa, " yana gama fad'in haka yai shigewarshi ciki, Amir kuwa wani irin kishi yake ji matsananci a duk lokacin da yaji Nura ya kira Amira da matarsa, ji yake kamar ya sha'keshi ya bar duniya. Be zauna ba, yana tsaye yana jiran ta inda zaiga fitowar Amira, Nura ne dai ya sake fitowa, yace "ya baka zauna ba kuma sai kace wani ba'ko? " Amir yai dariya sannan ya zauna, Nura dake tsaye yace "gata nan fitowa ku gaisa, sorry dan Allah bari inje in watsa ruwa in fito. Amir yace "ba damuwa sai ka fito. " Nura ya koma ciki ba dad'ewa Amira ta fito falon d'auke da sallama a bakinta, hannunta ri'ke da faranti ta ri'ko abubuwan motsa baki, shi kuwa Amir tunda ta fito kallonta kawai yake aikinyi, yau yaga ta rame da yawa ko dan yana ganinta daga nesa ne be fahimci haka ba, kanta na du'ke har ta 'karaso ta ajiye farantin a gabanshi, sannan ta zuba mishi abinci ta zuba lemo shima ta ajiye a gabanshi, tace "ga abinci nan, " ta yun'kura zata tashi taji cikin 'karamar murya Amir yace "Amirata!" A razane ta d'ago saboda tasan duk duniya mutum d'aya ne tak ke kiranta da wannan sunan. Wanda take tsammani ne kuwa ta gani a gabanta wato Amir d'inta, zabura tayi ta mi'ke tsaye tana dafe da 'kirji ta bud'e baki zatai magana Amir ya toshe mata baki, sannan yace salon ki tona mana asiri mijinki yaji. " Amira nan da nan hawaye ya fara wanke mata fuska, cikin kuka tace "Amir meyasa zaka yimin haka? " dama kana raye amma ka nisanta kanka da ni. " Kuka Amira takeyi sosai na tsananin farin ciki da ganin mahad'in rayuwarta Amir ne yake ta rarrashinta, sai da 'kyar ya samu tai shiru sannan ya zaunar da ita kan kujera, suna zama sai ga Nura ya fito kamar an jeho shi. Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta) ``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* (Mamie) *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)``` PAGE 190 to 195 Nura yazo ya zauna kan kujera yana kallon Amir dake 'kokarin komawa wajenshi ya zauna yace "ba dai har zaka tafi ba? haba kai ka fara ma kazo gidana kace zaka tafi yanzu." Amira kuwa idanunta na kan Amir sam ta kasa d'aukesu daga gareshi. Amir yace "a'a karka damu ina nan har sai kun gaji dani sedai in amarya ce da kanta ta koreni," ya 'karasa maganarshi yana kallon Amira. Amira tai murmushi me had'e da dariya tana cike da farin cikin sake ganin masoyinta kuma mahad'in rayuwarta, sannan tace "haba dai, wallahi har abada bazan tab'a korarka ba ko a mafarki bana fatan haka." Nan fa sukaita hira sai can wajen yamma sannan Amir yace zai tafi. Nura yace ya manta da makullin motarsa bari ya shiga ciki ya d'auko, bayan ya shiga Amir ya kalli Amira yace "yi sauri ki bani lambarki kafin ya fito, Amira ta fad'a mishi ya rubuta, yana cikin saving sai ga Nura ya fito, Amir ya mi'ke sukayi sallama da Amira sannan suka fice daga gidan, Amira kuwa akwai tarin tambayoyi a cikin ranta kuma a zuciyarta tana ji kamar ta ri'keshi ta hana shi tafiya, amma haka ta bar Amir ya wuce ya tafi ba yanda ta iya dole tai ha'kuri, tambayoyin dake ranta kuwa ta bari sai ya kira sai suyi duk maganar da zasu yi. Suna tafe a mota suna hira, Nura yace "wallahi tunda muke da Amira bata tab'a zama dani haka munyi hira da ita haka ba har naga ha'koranta sai yau, Amir a zuciyarshi yace "to ba dole ba ai duk wanda yace yana 'kaunarta har ya aureta kallo take a duk duniya bata da ma'kiyi sama da shi," ashe Amir be sani ba maganar da yayita a zuciya ta fito fili, kawai ji yayi Nuran yace "nima kallon ma'kiyinta take yimin kenan, kuma meyasa ma ka fad'i haka?" Amir yace "eh mana saboda kaima ka shaida mutum d'aya tak take so, to wannan dalilin zaisa taji haushinka tunda ka aureta ka 'kara nisantata da masoyinta na farko." Nura yai murmushi yace "ba zaka gane ba abokina, duk akwai dalilin yin haka, watarana zan sanar dakai, bayan dalilan ni kaina ina son yarinyar, ban tab'a had'uwa da yarinya me kyau da diri irinta ba," habawa yana fad'in haka Amir yaji kamar an saka mishi garwashi a zuciyarshi saboda tsabar jin rad'ad'in maganar Nura, nan da nan kuwa idanunshi sukai ja ya dage iya 'karfinsa ya buga kanshi jikin glass d'in murfin motar, nan da nan kuwa glass d'in da kanshi duk suka fashe, Nura yace "Subhanallah!" ya faka motar sannan ya cigaba da yi mishi sannu, sannan Nura ya sake cewa "meyasa kayi haka Amir?" Amir yace "wallahi ciwo kan yake min, gashi kuma ka 'kara b'ata min rai, ni yanda na d'aukeka kamar d'an'uwa ashe kai ba haka bane, a tunanina damuwarka damuwata ce, kullum se dai kaita ce min akwai dalilin auren matar da kake tare da ita, to menene amfanin fad'amin akwai dalilin tunda baka iya sanar dani, ka sani ko akwai shawarar da zan taimakeka da ita." Nura yai murmushi, sannan ya dafa kafad'arshi yace "ba haka bane abokina, kayi ha'kuri yanda ka d'aukeni nima haka na d'aukeka amma dan Allah ka ri'ke min sirrina," nan Nura ya kwashe duk wani 'kuduri nasu akan su Amira da Dad d'inta ya fad'a wa Amir, Nura ya cigaba da cewa "amma fa ni ko na samu biyan bu'kata bazan rabu da Amira ba, shi kuma Dad ya dage indai muna son dukiyarsu muna son zama lafiya dole sai mun kawar da su. Bayyana tashin hankalin da Amir ma ya shiga ai baya misaltuwa, amma sai yai saurin b'oye razanarshi, sannan yai murmushi yace "gaskiya Dad d'inka yayi tunani, kaga fa in kuka samu yanda kuke so zaka iya mallakar koma wace macece a rayuwa, bayan haka kome kaga dama zakayi domin kud'i sune abokan rayuwa." Nura ya she'ke da dariya, sannan yace "ashe kaima irin ra'ayinmu d'aya shine na b'ata lokaci wajen sanar dakai tun tuni." Haka dai suka cigaba da tafiya suna hirar su, abinda yasa Amir ya biye mishi yasan in ba haka yayi ba bazai cigaba da samun labarin komai daga wajenshi ba. Suna cikin hira wayar Nura tai 'kara, ya cewa Amir ya d'an d'auka ya cewa koma wanene yana tu'ki zai kira later. Amir na d'agawa kafin yace komai sai yaji mahaifin Nura yana fad'in "Nura ko me kake ka bari kazo, na samu labarin wai anga Amir a garin nan, maza kazo muyi shawarar abinda ya dace muyi a gaba," yana gama fad'in haka ya katse kiran. Gaban Amir ne ya fad'i, sam be so komai ya fito tun yanzu ba, Amir ya mayar da wayar gefe ya ajiye, sannan yace "mahaifinka ne ya kira yace kaje yana nemanka, wai ya samu labarin anga Amir a cikin garin nan kaje ku shirya abinda ya kamata a gaba." Wani irin birki Nura yaja tare da kallon, Amir had'e da zazzaro ido, yace "meyasa wannan d'an iskan zai bayyana yanzu?" wayarsa ya d'auka ya kira Babanshi suka tattauna sannan ya tabbatar mishi da yana zuwa nan bada dad'ewa ba. Bayan sun gama wayar ya tayar da motar suka cigaba da tafiya. Amir sam baya son Nura ya gane gidansu balle har ya gane wanene shi, gashi yau ya d'aukoshi a motarsa dan yau cewa yai masu tsaronsa su juya da dukkanin motocin, dan haka suna zuwa dai-dai wani super market yace ya ajiyeshi a nan zai duba wani abokinshi a ciki. Bayan Nura ya faka motar Amir ya fito, suka yi sallama yaja yai gaba a yayin da shi kuma Amir ya koma gefe ya samu wani benci dake kusa da 'kofar shiga super market d'in ya zauna, ya ciro wayarshi ya kira lambar da Amira ta bashi, ringing d'aya tayi Amira ta d'auka tare da karawa a kunne, sallama tayi da sassanyar muryar nan ta-ta me d'an karen dad'i, lumshe idanu Amir yayi sannan ya bud'esu, shima a hankali ya kira sunanta yace "Amira." Amira cikin sauri ta mi'ke tsaye tace "Amir d'ina ina ka shiga har zuwa tsawon wannan lokacin, kasan halin da tunaninka ya jefa rayuwata a ciki kuwa? kowa yana ta cewa ka mutu amma ni nasan ba zakaimin haka ba, ba zaka mutu ka tafi ka barni ba," ta fashe da kuka, sannan ta cigaba da cewa "amma meyasa tsawon wannan lokacin ka tafi ka barni ba tare da ka nemeni ba? Amir yace "haba Amira ta ina zan nemeki bayan mahaifinki ya dage sai ya rabamu ta 'karfi da yaji," nan ya kwashe duk abinda ya faru ya fad'a mata, Amira ta tayashi murnar ganin iyayensa da yayi, yai mata godiya sannan ya cigaba da fad'in "yanzu abinda yasa na kiraki shine in fad'a miki ki kwantar da hankalinki, zaki dawo wajena nan bada dad'ewa ba mu cigaba da zaman aure, amma yanzu idan nace zan bayyana gaban Dad inaso a dawo min da matana bazai yarda ba rigima za'ai ta tafkawa, shiyasa nafi so sai na tona duk wani asiri nasu tukun, na samowa Dad babbar hujja a kansu, abinda nakeso dake shine karki tab'a yarda dashi domin kuwa nafara gano manufar abinda yasa aka aureki, kiyi taka tsan-tsan dashi, kuma zamu ri'ka waya dake duk in baya nan," Amira tace "to shikenan," nan suka d'an tab'a hira daga 'karshe suka yi sallama. B'angaren su Nura kuwa zaune suke shi da Baban shi suna magana akan Amir, Nura yace "waima to kai wa yace maka ya ganshi anya shi aka gani kuwa Baba?" Baba yace "to ni na ganshi da idanuna kaine baka sanshi ba, baka tab'a ganinshi ba, amma ni na sanshi, mahaifin Amiran ya nuna min hotonshi lokacin da mukaje gidan da kai maganar aurenku, sai gashi yau na ganshi da idanuna sun wuce tare da wasu mutane masu ba'ka'ken kaya a mota, saboda haka yasa na kiraka mu nemi mafita." Nura yace "in kuwa haka ne bayyanarsa a dai-dai wannan lokacin zata b'ata mana shiri, amma kar kaji komai Baba in dai ka yarda dani kabar komai a hannuna," da wannan maganar ta Nura suka kawo 'karshen maganar. Bayan sati d'aya ko da iyayen Amir suka ga ya fara warwarewa damuwarshi tayi sau'ki sai suka shirya suka koma Abuja saboda harkokin Abbansa na siyasa dama wasu da yawa da suke can, suka bar Amir da bataliyar masu gadi da tsaronsa a nan kano saboda karatunshi da ya koma babu damar su koma tare dashi, basu san cewa Amir hankalinshi baya wajen karatu sam yana can wajen fafutukar 'kwato soyayyarshi. Muje zuwa *🅱K😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *SO TARI DA DAMA MU MUKE BARI SO YANA KUB'UCEWA DAGA HANNUNMU, TA HANYAR RAGE KULAWA, TATTALI, YARDA DA JUNA, RAGE WA'DANNAN ABUBUWAN GA MASOYA SHI KESA SHA'KUWA TAI 'KARANCI, LOKUTA DA DAMA ZAKA GA MASOYA SUNA 'KAUNAR JUNA AMMA SAKAMAKON JA BAYA DA KAYI DA KULAWARKA SAI ALLAH YA KAWO WANDA YA FIKA DUK WA'DANNAN ABUBUWAN TO WALLAHI CAN ZAI KARKATA, DOMIN AKODA YAUSHE ABINDA BAWA YAFI SO A SO SHINE KULAWA, BA TA YANDA ZA'AI MASOYI YA RASA WA'DANNAN ABUBUWAN DAGA GAREKA KUMA KACE DOLE SAI YA CIGABA DA ZAMA DAKAI, IN HAR BAWA YANA SO SOYAYYARSA TA 'DORE FIYE DA YANDA TAKE A BAYA TO NUNKA TATTALINKA DA KULAWARKA ZAKA YI, MU SANI CEWA ITA KULAWAR NAN ITACE JIGON SO BAKA BARI KAI SAKACI DA ITA, WANNAN MUKA RASA SHIYASA LOKUTA DA YAWA ZAMU MALLAKI MASOYA AMMA DAGA BAYA SU ZAMA BA NAMU BA TO WALLAHI SAKACIN DAGA GAREMU NE, BA TA YANDA ZA'AI MA KA DAINA BAIWA MASOYINKA KULAWA KUMA YA YARDA CEWA WAI HAR YANZU KANA 'KAUNARSA, SHIYASA 'KAUNAR YANZU TA ZAMA TA 'DAN LOKACI 'KALILAN SABODA BABU KULA, DOLE IN KA SAMU WANDA ZAI BAKA DUKKANIN KULAWARSA KA KAR'B'ESHI HANNU BIBBIYU, YA ALLAH KA BAMU IKON CIGABA DA BAIWA DUKKANIN MASOYANMU KULAWAR DA TA DACE.* PAGE 195 to 200 Amir yaji dad'i sosai da tafiyar iyayensa, domin yasan wata 'karin dama ya samu na aiwatar da shirinsa cikin kwanciyar hankali, dan yasan muddin su Abba suna garin wata rana zasu gano komai, kuma idan suka gano zasu dagula komai domin zasu ce zasu d'auki mataki, dan ba zasu tab'a barin duk wani abu da zai tab'a d'ansu ba suna kallo su 'kyale shi. Bayan kwana biyu Nura yaje ya sami mahaifinsa ya shaida mishi gaskiya shi fa ya gaji, taya za'ai ace sunan yana da mata amma bata bashi duk wata kulawa ta aure. Bud'ar bakin mahaifinsa sai yace "to ka saketa mana." Nura yace "ai ina 'kaunarta bazan iya rabuwa da ita ba," mahaifin Nura yace to kuwa tunda kasan haka sai ka daina wannan maganar ma, mata a hankali ake shawo kansu, kuma koda zaka nuna mata halinka sai ka bari sai mun samu biyan bu'katar mu." Yanzu Amir da Amira har chat suke yi a waya yau ma chat d'in suke tana fad'a mishi cewa ita fa ta gaji zata fad'a cewar ya dawo a maidata d'akinshi. Amir ya rarrasheta yana fahimtar da ita cewa yin hakan ba abu bane me sau'ki. Bayan sati d'aya Amir da Nura suna tafiya kan hanya a cikin motar Amir wanda Nuran ne ke jansu zai kaishi gida sai ya d'auki motarshi ya wuce gida shima, suna tafe sai wayar Nura tai 'kara, yana dubawa yaga Dad d'in Amira ne ke kira, Nura ya kalli Amir da ya du'kar da kai yana chat da Amira yace "d'an akuyan Dad d'in Amira ne ke kirana," Amir ya d'ago yai murmushi sannan yace "to d'aga kaji mana." Bayan Nura ya d'aga suka gaisa sannan Dad yace "ya kuke ina fatan dai kuna zaune lafiya ba wata matsala ko?" Nura yace "eh lafiya lau muke zaune babu wata matsala." "Bayan sun gama wayar ya mayar aljihu sannan yace "sai kayi dana sanin sanina Dad, wai shi me kud'i koda yaushe cikin wula'kanta talaka, hmm." A dai-dai nan suka kawo 'kofar gidan su Nuran, Nura ya kalli Amir yace "yanzu wucewa zaka yi ba zaka shiga ku gaisa da Madam ba?" Amir yai murmushi sannan yace "muje," suna shiga cikin falon suka tarar da Amira zaune a kan kujera tana daddanna wayarta, wanda ba da kowa take chat ba face Amir. Cikin hanzari da farin cikinta ta tashi tana fad'in "barka da zuwa mai gidana, kar kaso kaga farin cikin da zuciyata ke ciki a yanzu na murnar sake ganinka a karo na biyu," Nura ya washe baki tare da d'agowa yana kallonta da mamaki 'karara a fuskarsa na irin tarbar da yake samu a wajenta duk lokacin da suka shigo tare da Amir, sedai abinda ya lura dashi shine sam ba shi take kallo ba, kamar ba shi take yiwa sannu da zuwa ba. Nura ya wuce ciki tare da kawar da komai daga ranshi, saboda yana tunanin abinda yasa take haka 'kila saboda kar wasu su gane irin yanayin zaman da sukeyi ne. Yana shiga ciki Amir ya kalleta cikin sauri yace "meyasa kike yin irin haka a gabanshi, so kike sai ya gano mu." Amira ta turo baki tare da cewa "ai ba laifina bane, bana iya control d'in kaina ne a duk lokacin da na ganka." Nura ne ya fito daga cikin d'aki tare da zama kusa da kujerar dake gefen Amira, sedai ya lura sam hankalin Amira baya gareshi, ko magana take idonta na kan Amir, shima Amir jefi-jefi yana satar kallonta, haaaaaa wa ya fad'a musu dama soyayyar gaskiya tana b'uya koda anyi 'ko'kari aga anyi hakan.😂 Ganin haka yasa walwalar Nura ta ragu, kuma sannan ya 'ki tashi ya 'kara zuwa ko'ina, hakan ne ya hana su Amir samun damar tattaunawa, daga 'karshe ma tashi yayi yai musu sallama Nura ya rakoshi bakin motarsa ya shiga sukai sallama ya tayar ya tafi. Sedai abinda ya 'kara d'aurewa Nura kai shine yana dawowa ya tarar Amira bata falon ta shige d'akinta, kuma wannan ba shi bane karo na farko da take yin hakan, idan Amir yazo ya tafi sai ta canza ta koma kamar ba ita ba, ko ta tashi ma tai tafiyarta ta barshi shi kad'ai kamar yanda tayi a yau. Haka suka cigaba da kasancewa a matsayin ma'aurata har tsawon shakara d'aya harda watanni. *BAYAN KWANA BIYU* Yau ta kama Alhamis, Nura na zaune a falo sai ga kiran Dad, koda Nura ya d'aga wayar gaisawa kawai suka yi sannan Dad yace "Nura ko me kake yi ka ajiye kazo office d'ina yanzu ka sameni ina jiranka." Nura ya amsa da "to," suna gama wayar Nura ya kira wayar Mahaifinshi, bayan ya d'aga sun gaisa sai yace "Baba ina kyautata zaton ranar da muka dad'e muna jira ne yau tazo, domin yanzu Dad d'in Amira ya kirani yace in yi maza inje yana son ganina." Baban Nura yace "Allah mun gode maka, to me kake jira har yanzu baka tafi ba?" Nura yace "ai yanzu zan tafi Baba, sai na dawo duk yanda ake ciki zaka ji," daga nan suka yi sallama ya fito ya tafi. Duk wayar nan da yake a cikin gida ya yita, amma duk a tunaninsa Amira bacci take yi shiyasa ya saki jikinsa yai wayarshi hankali kwance. Bayan fitarsa Amira dake lab'e ta gama jin komai ta kira Amir ta fad'a mishi duk abinda taji da kunnenta, dama Amir ya fad'a mata duk maganar da taji Nura yayi ta kira ta fad'a mishi. Nura ne zaune gaban Dad, yana matu'kar martaba Dad da 'kas'kantar da kai a gabanshi kamar mutumin arzi'ki. Bayan sun gaisa Dad ya kwaso wasu takardu dake gefenshi ya kalli Nura tare da mi'ka mishi takardun nan yace "ungo ri'ke nan, bayan Nura ya karb'a Dad ya cigaba da fad'in wad'annan takardun dukkanin kadarorina ne da na mallaka, na dam'ka su a hannunka ne ba dan komai ba sai dan na riga da na mallakawa Amira su, sedai bana so ta ri'ke a hannunta sai nan gaba tukun in ta 'kara girma da hankali, dan haka ka cigaba da juyawa tare da kulawa dasu har ranar da Allah zai hukunta ta karb'a." Nura yace "amma Daddy a ganina ya kamata Amira tazo ayi komai a gabanta daga nan kuma mu sassaka hannu." Dad yai murmushi sannan yace "karka damu Nura na yarda da kai, ban tab'a tunanin cikin talakawa akwai masu amana irinka ba, na baka kamfanina ka juya tsakani da Allah, sannan na d'auki yarinya na baka itama ka ri'keta da hannu biyu, tare da bata duk wata kulawa, abinda yasa ma har aka kai tsawon wannan lokacin ban baka ba dama saboda in gwadaka ne, dan haka karka damu na yarda dakai, fatana ka nunka duk wata kulawa da kake yiwa 'yata kuma ka ri'ke amana ka kuma cika al'kawari." Bayan sun gama magana Nura yai godiya harda hawayen drama sannan suka yi sallama ya wuce gidan Babanshi kai tsaye. Da isarshi ya kwashe duk yanda suka yi da mahaifin Amira ya fad'awa Babanshi. Zama suka yi suka dudduba takardun, a ciki babu na kamfanin da aka baiwa Nura, babu na mahaifinsa, sannan babu na gidan Dad wanda yake ciki da kuma na su Amira. Nura yace "wallahi suma sai ya bada su, lallai ba zamu bar mishi komai ba sai mun yashe shi, wai harda ce mana talakwa a cikin maganarshi be san kalmar taban haushi ba, amma kwanan nan kalmar zata fara aiki a kanshi muga kuma 'karyar 'kin talaka," suka she'ke da dariya harda tafawarsu, nan suka cigaba da tsara mugayen shirinsu akan su Amira. Washe gari Nura ya dawo daga aiki bayan sun rabu da Amir kamar kullum sai ya wuce gida. Yana zaune wayarshi tai 'kara, yana dubawa yaga ashe mahaifinsa ne, yana d'agawa yaji mahaifinsa ya fara fad'a, "Nura ashe kai wawan yaro ne da ina cewa na haifi yaro me wayau, baka san wannan yaron da na ganku tare dashi a bakin ti-ti shine tsohon mijin Amira ba?" to in baka sani ba yanzu ka sani ai, shashasha kana nema ka rusa komai," yana gama fad'in haka ya kashe wayarsa, shi kuwa Nura wanda tun d'azu yake a tsaye, ya fara kai kawo yana nazarin wannan maganar, ganin duk wannan bazai fish she shi ba yasa ya zari makulli ya fice daga gidan. Nura zaune yake gaban Babansa yana yi mishi tambayoyi, "Baba wanene mijin Amira da kace ka ganmu tare dashi?" Baba yace "d'azu na ganku tare dashi," nan ya shiga koro mishi bayanin siffar Amir da kuma kayan da ya saka. Lallai a yanzu Nura bashi da hujjar 'karyata zancen mahaifinshi ko ya musa mishi. Nura yai murmushi sannan yace "ka kwantar da hankalinka Baba, dama na dad'e ina zargin wani abu game dashi, sannan ina sane nai saurin sabawa dashi domin in fahimci ko shi wanene saboda in d'auki mataki a kanshi da wuri, karka wani damu inada aboki d'an abokin nan naka Baba, babban d'an sanda ne shi yanzu a garin nan, ba wanda ya isa ya ja damu muddin muna tare dashi, zamu had'a hannu dashi, bari ma ka gani." Wayarsa ya zaro yai kira har ta katse ba'a d'aga ba, sai a kira na biyu aka d'aga, bayan sun gaisa Nura yace "daga jin muryar babu tambaya Insp Yahya ne kafi 'karfin mugu?" yai maganar da sigar tambaya tare da yin shiru yana jiran amsa Muje zuwa *🅱K CE*😘💋 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *'YAN UWANA INA MAI TUNATAR DAMU KAN CEWA KAR MU SIYAR DA 'YANCINMU, KAR MU ZAB'I MUGAYEN SHUWAGABANNI DA ZASUITA KASHEMU, BABA BUHARI BA MUGU BANE, BA AZZALUMI BANE, KUMA BA MACI AMANAR 'KASA BANE, MUTUM NE SHI NA KWARAI ME YA'KI DA ZALUNCI DA KUMA AZZALUMAI, DUK MU FITO 'KWANMU DA 'KWAR'KWATARMU MU SAKE ZAB'ARSHI A MATSAYIN SHUGABAN 'KASA, KAR IDONMU YA RUFE MU MANTA ABUBUWAN DA SUKA FARU A SHEKARUN BAYA LOKACIN MULKIN GOOD LUCK, YANDA AKA MAIDA RAYUKAN BAYI KAMAR KIYASHI, BABU KWANCIYAR HANKALI, YARA SUKA DAINA ZUWA MAKARANTA, DUK KARMU MANTA HAKAN, DAN HAKA ZAB'I YA RAGE GAREMU, KO MU ZAB'I SHUGABA NAGARI MU RAYU CIKIN WALWALA, KO MU ZAB'I MUGAYE KUMA B'ARAYI SUITA KASHEMU KUMA SUNA KWASHE DUKIYARMU.* PAGE 200 to 205 Insp Yahya yai dariya sannan yace "ni ne mana kana tunanin banda lambarka ne Nura, gabad'aya ka b'oye ina ka shige ne tun bayan da kuka tashi daga garinmu?" Nura yai dariya, sannan yace "yanzu haka ina kano mun dawo nan da zama," Insp Yahya yace "nima ai ina kano, a wace unguwa kake?" Nan dai Insp Yahya yaiwa Nura kwatancen inda yake ba tare da wani b'ata lokaci ba ya shirya ya tafi. Nura na isa station suka sake sabuwar gaisuwa da Insp Yahya, sannan ya kwashe duk abinda ke faruwa ya fad'a mishi. Insp Yahya ya numfasa sannan yace "kaima kayi wauta da kai saurin amince mishi, amma ba wani abu, hukuma mu a hannunmu take, amma sedai in ka yarda duk abinda kuka samu rabawa dai-dai zamu yi, ka amince?" Nura bai yi wata-wata ba yace ya amince, Insp yace "nuna min hoton yaron in gani, kamata yayi mu fara kamashi kafin ya tona mana asiri," Nura ya d'auko wayarshi ya fito da hoton Amir sannan ya bawa Insp ya gani. Insp Yahya na duba hoto ya mi'ke tsaye cikin sauri tare da zaro ido yace "Amir!! wannan ai Amir ne," Nura shima ya mi'ke tsaye, sannan yace ka sanshi ne?" Insp yace " 'kwarai nasan Amir farin sani," nan dai ya bashi labarin duk abinda ya faru a tsakaninshi da su Amir, sannan ya cigaba da cewa "kuma in dai a kanshi da matarshi kake magana to ni bama sai kun bani ko si-si ba zan tayaku, saboda na dad'e ina neman hanyar da zan tozarta rayuwar Amir fiye da tunaninka, amma yanzu abinda za'ai dole tsarin ya canza saboda Amir mugun wayau ne dashi, kawo kunnenka kaji." Nan da nan suka gama kitsa mugun 'kullin su, sannan suka tashi suka fito daga station d'in, suka shiga motar Nura yaja suka tafi. Shi kuwa Amir tunda ya sami labarin Nura sun ganoshi ya b'uya, amma yasan gabad'ayan shirinsa ya rushe. Amir zaune yake kan kujera yana tunanin abinda ya kamata yayi, tabbas yasan dai-dai wannan lokacin komai zai iya faruwa da Amira, cikin sauri ya d'auki wayarshi ya kira Amira tare da shaida mata tai maza ta fito daga gidan nan yanzu zai taho da mota ya d'auketa. Amira cikin sauri ta shiga cikin d'aki domin d'auko mayafinta ta fita ta bar gidan kamar yanda masoyinta Amir yai mata umurni akai, sedai kash tana fitowa falon ta tarar da wasu samudawan 'katti sun cika mata falo, babbansu yana kan kujera hankalinsa kwance, a yayinda sauran kuma suke tsaye suna zazzare idanu, dukkansu kamanninsu bata nuna ta mutanen arzi'ki ne, kuma gaba d'ayansu ba'ka'ke 'kirin siffarsu duk babu me kyan gani, koda yake dama wanda ya rasa imani ai kalarsa da siffarsa bazatai dai-dai da ta mumini ba. Babban ne ya kalli Amira sannan yace "sannu Amira, ashe ma kinsan da zuwanmu har kin shirya sai tafiya kawai ko?" Amira cikin rawar murya tace "su waye ku, kuma me kuka zo yi nan?" Babban ba tare da ya bata amsa ba ya kalli 'kattin dake tsatstsaye yai musu alama da kai da su kamata. Cikin sauri suka kamata d'aya daga ciki ya sab'ata a wuya tana wuntsil-wuntsil a haka suka fice da ita daga gidan, har suka shiga motoci bata daina kurma ihu ba hakan yasa ogansu ya d'aga hannunsa mai kama da guduma ya mauje ta nan ta fad'a kan kafad'ar 'katon dake kusa da ita a sume. Bayan tafiyarsu da minti goma sai ga Amir ya 'karaso da sauri ya shiga cikin gidan ya bincika ko ina amma bai ga Amira ba, dawowa falo yayi yana dube-dube can ya hango kwalin taba kuma shi iya saninshi yasan Nura baya sha, dan yasha gwadashi akan haka amma koda wasa bai tab'a gwadawa ba, shidai barshi da tantiranci da neman mata kamar d'an akuya, ganin kwalin tabar da Amir yayi ya tabbatar mishi da cewa an rigashi zuwa an tafi da Amira. Amir ya dafe kai yana tunani, can kuma ko me ya tuno sai ya fice daga gidan cikin sauri. Motar shi ya fad'a ya tasheta sai gidan Dad, yana zuwa kowa na cikin gidan sai kallonsa sukeyi cike da mamaki suna yi mishi tambayoyi, sai Amir yace "yanzu ba lokacin tattauna wannan maganar bane, ina Dad yake?" Mum tace "basu dad'e da fita ba, sirikinshi Nura yazo ya d'auke shi yace akwai meeting d'in da zasu yi yanzu da wasu ba'ki da suka zo." Amir ya saki salati tare da dafe kai yace "ba can zasu tafi ba, Nura da mahaifinsa damfarar Dad suke son yi," nan ya kwashe komai ya fad'a mata, sannan yace "bari ma kiji, wayarsa ya d'auko ya kira lambar Dad bayan minti biyu aka d'auka, Amir yace "hello Dad kana ina ne?" Nura ya she'ke da dariya sannan yace Dad da tsohuwar matarka suna wajenmu, duk shirinka baka isa ka wargaza namu ba Amir," ana gama fad'in haka aka kashe wayar. Amir ya kalli Mum yace "kinji ko, to yanzu duk ku fito daga gidan nan muje gidana ku zauna kar kuma su turo ai muku wani abu," saboda sanin halin mai gidan sai suka kasa yarda da abinda Amir yace, haka yaita ro'konsu amma suka 'ki binshi. Hakan yasa yaiwa bataliyar masu tsaronshi waya kan suzo, yai musu kwatancen unguwar, cikin 'kan'kanin lokaci kuwa suka 'karaso, ya basu umurni kan su kula da mutanen gidan nan kamar yanda zasu kula da shi, sannan ya cewa su Mum da Uncle kar suji tsoro mutanenshi ne. Amir ya juyo ya fito daga gidan, kai tsaye wucewa mtn office yai kai tsaye domin a binciko mishi daga inda aka kira lambar. Bayan an kira lambar sai suka sake d'auka wannan karon Insp Yahya ne ya d'aga yana fad'a mishi matarshi da sirikinshi suna sume, kuma sun riga da sun saka hannu da yatsan Dad a sumen yanzu duk abinda ya mallaka a duniya ya zama ba nashi ba, kuma yanzu zasu ba'kunci lahira, sannan ya 'karashe da fad'in " idan ka isa kazo ka taimakesu." Cikin sauri aka gama tantance inda suke Amir ya karb'i addreshin wajen ya tafi. Gudu kawai yake a mota yana jin tsoro kar su kashe mishi Amirar shi. Cikin minti talatin ya 'karaso wajen kuma ya shiga ciki da gudu yana 'kwalawa su Amira kira. Cikin wani 'katon kango ne, yana shiga can ciki yaga Amira da Dad an d'aure su, cikin sauri ya nufi inda suke, lallab'owa ta baya aka yi aka buga mishi wani abu a baya, take anan ya zube 'kasa, kuma lokaci guda suka kewaye shi, bayan sun mishi dukan tsiya sannan shima aka d'aure shi. Dad ya kalli Baban Nura yace "yanzu duk irin yardar da nai maka amma shine ka saka min da wannan abun ko, da ikon Allah 'karshenka ba zaiyi kyau ba." Baban Nura ya she'ke da dariya sannan yace "ai kai ka jawa kanka, ka tsani talaka, sannan kana tsoron had'a komai da talaka, ai na dad'e ina jiran zuwan wannan ranar, duk 'kulawa da 'kaunar da nake maka ba taka bace ta dukiyarka ce, amma wai kai me wayau ka katange komai to muma ga irin namu wayon nan mun nuna maka, albishir biyu yanzu zanyi maka, na farko duk wasu kadarori da suke mallakinka yanzu sun zama namu ni da d'ana hatta gidan da kake ciki mun siyar, abu na biyu kuma shine yanzu zamu 'kara muku gudu zuwa lahira domin barinku a raye zai iya zama mana barazana a cikin sabuwar rayuwar da zamu yi, kuma kaga kaima mun taimaka maka shan takaicin rayuwa cikin talauci, naso dai in barka a raye kaji irin yanda rayuwar talauci take, amma na sanka farin sani sam baka yafiya akan komai." Insp Yahya ya kalli Baba yace "ni Baba Amir d'in can nake so ku barni in kashe shi da kaina." Baba da Nura suka she'ke da dariya, sannan suka had'a baki wajen cewa "an baka," sannan su duka ukun harda tarin 'kattan dake cike a wajen suka sake kwashewa da dariya, wurin sai amsawa yake yi. Baba ya baiwa Nura umurnin kashe su Amiran, sedai Amir na ganin inda Nura ya tunkara hannunsa ri'ke da bindigar Insp Yahya sai yai wani irin tashi yana a d'auren yaje da gudu ya bangaji Nura suka fad'i 'kasa a tare. Kiciniyar 'kwace bindigar Amir yakeyi daga hannun Nura cikin ikon Allah ya samu d'aurin hannunshi ya kwance ya 'kwace bindigar sannan ya kwance su Amira da Dad yana cikin kwancesu Insp Yahya ya ciro bindigar jami'in dake kusa dashi ya saita Amir da ita tare da harbin Amir d'in a hannu, Amir yai wani irin razanannen 'kara, tare da dafe wajen ya kalli su Dad yace su gudu zai biyosu daga baya, Amira taja ta tsaya tana ri'ke da hannunshi mai ciwon tana kuka tana fad'in "taya zan tafi in barka a irin wannan halin, ni ba inda zanje ko mutuwar ne ma gwara a kashemu tare," Amir ya dafata, sannan yace "ki kwantar da hankalinki Amira Insha Allah rabuwarmu ba yanzu ba, zan dawo gareki nai miki al'kawari." Cikin sauri kuwa Dad ya jata da gudu suka fice daga wurin nace ashe Dad ansan darajar rai hahaha,😂 a yayin da su Nura sukace a kamosu, duk wanda ya taho da niyyar fita daga wajen zuwa kamosu Amira sai Amir ya barshi kwance, haka akai ta d'auki ba dad'i. Sai da ya kashe rabinsu duk yabi ya gaji li'kis, sannan Allah ya basu sa'a a kanshi suka far mishi, saida suka tabbatar da baya numfashi sannan suka fice sukai tafiyarsu suka barshi a nan wajen. Tunkarar gidan Dad suka yi, a haukarsu wai shine su bisu har gida su kashe su, sedai daga nesa suka hango security's ta ko'ina, hakan ya tabbatar musu da cewa in suka 'karasa lallai za'a kamasu, ba shiri suka juya. Amira ce ta kalli mahaifinta sannan tace "gaskiya Dad be kamata ba ace Amir ya shiga irin wannan halin ta dalilinmu kuma mu taho mu 'kyale shi, ya kamata mu kai mishi taimako koda da jami'an tsaro ne su taimaka mishi." Uncle yace "gaskiyarki Amira, bawan Allahn nan ya jefa rayuwarshi cikin had'ari domin kawai ya bamu kulawa da kariya ta ko'ina, be kamata mu 'kyaleshi a haka ba, ya kamata mu sanar da 'yan sanda." Dad ya kasa magana saboda tsabar firgici da mamaki dake tare dashi har yanzu, ishara kawai yai musu da hannu akan Uncle d'in shi da Amira suje. Cikin sauri kuwa Amira da Uncle suka shiga mota suka fice harda wasu daga cikin securityn cikin gidan. Muje zuwa *🅱K CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *INA 'KARA TUNATAR DA MU CEWA BABU FA WANDA ALLAH ZAI HALITTA YACE BAZAI FUSKANCI JARABAWAR UBANGIJI BA, KARMU MANTA ALLAH MUKA RO'KA DA YA ZAB'AR MANA SHUGABA NA GARI A WANCAN SHEKARUN, SAI ALLAH YA ZAB'A MANA BABA BUHARI, TO KO DA ALLAH YA BAMU SHI A TUNANINMU ALLAH BA ZAI JARABCEMU BA TA WANI B'ANGAREN? WALLAHI ALLAH KO DA TSAYAR DA BAMA BAMAI KAD'AI DA BABA BUHARI YAI 'KO'KARIN YI KAD'AI MUKA TUNA YA ISA MU GODEWA ALLAH KUMA MUSAN CEWA LALLAI BA ZALUNCI NE YA KAWO BABA BUHARI CIKIN RAYUWARMU BA, KARMU MANTA KAFIN BUHARI YACI ZAB'E A BAYA A LOKACIN DA GOODLUCK KE MULKARMU BABA BUHARI YASHA ZUBAR DA HAWAYENSA YASHA YIN KUKA KAN HALIN DA 'YAN 'KASA KE CIKI, KAFIN YACI MA KENAN DA YACI KUMA BURINSHI YAGA MUN SAMU CIGABA A RAYUWARMU, KAR MU ZAMA BUTULU A RAYUWA ANATA MAGANAR ABINCI YAI TSADA BAFA RASAWA MUKAI GABA D'AYA BA, KUMA KOWANE TSANANI YANADA IYAKA NA D'AN LOKACI NE KUMA SAI ANSHA WUYA AKE SHAN DAD'I, INACE A BAYA MULKIN GOOD LUCK GA KUD'IN AKWAI GA ABINCIN AMMA BAYA CIYUWA, NA CEFANE MA BASA SAMUWA SABODA FARGABAR KA FITA WAJEN NEMA A HARBEKA KO ASA BOM YA TAYAR DAKAI, KARMU MANTA CEWA ANSHA SAKA BOM A MASALLATAI MUSAN CEWA TABBAS IN MUNA CIGABA DA BARI SHUGABANNI AZZALUMAI NA MULKARMU TO ZA'A WAYI GARI BABU RABINMU SUN KASHE, MUYI TUNANI SOSAI WALLAHI KAR MU BARI 'YAN CANJI NA WANI LOKACI DA ZASU 'KARE SU BARMU DA SHAN WAHALAR SHEKARU SU RUD'EMU, MUYI TUNANI DUK MAI SHIRYA GASKIYA BAZAI BAKA CIN HANCI DAN KA ZABESHI BA, HALIN MUTUM JARINSA HALIN MUTUM KE BAYYANAR DA CANCANTARSA WAJEN JAMA'A, NIDAI NACE INSHA ALLAH 4+4 SAI MAI GASKIYA.* PAGE 205 to 210 Kai tsaye su Amira wucewa can wajen da abun ya faru sukayi, saboda Uncle yace ba sai sun kira jami'an tsaro ba tunda suna tare da security sun wadatar, kuma jami'an tsaron ma da akwai mugaye da munafukai a ciki wad'anda zasu iya tseguntawa Insp Yahya in sukaji bai mutu ba suzo su 'karasashi, da wannan shawarar ta Uncle sukai amfani sukayi watsi da maganar neman 'yan sanda, cikin 'kan'kanin lokaci Allah ya kaisu wajen, basu tarar da kowa ba a wajen sai Amir yashe a wajen kwance cikin jini, babu b'ata lokaci suka d'aukeshi suka yi asibitin da ake duba iyalen Dad da shi. Suna zuwa babu wani b'ata lokaci aka shiga dashi emergency cikin sauri saboda ganin harda harbi. Sai da aka kammala mishi komai aka kuma tabbatar musu da yana raye kuma insha Allah nan da wasu lokuta zai farfad'o sannan hankalinsu ya kwanta musamman ma Amira wadda ta kasa zaune ta kasa tsaye, banda kuka babu abinda takeyi, ita zuciyarta kawai bata takeyi Amir d'inta ya rasu, saida taji bayanin Doctor d'in sannan hankalinta ya kwanta. Amira cikin sauri ta fad'a d'akin da aka maida Amir, Uncle da Doctor suka bita da ido, Doctor yace "hala wancan majinyacin mijinta ne?" Uncle yace "eh Doctor," Doctor yace "haba shiyasa naga gabad'aya bata cikin hayyacinta," dukkansu sukayi murmushi, sannan ya umurci Uncle da ya bishi office akwai magungunan da za'a nemo da ya tashi a bashi koda ruwan tea ne sai a bashi magungunan yasha, Amira na shiga d'akin ta 'karasa kusa da bakin gadon da yake kwance, kara kanta tayi dai-dai saitin 'kirjinsa ta tabbatar da abinda likita ya fad'a musu sannan ta numfasa kuma ta yarda da ranshi, sai ta samu waje ta zauna. Ta ri'ko hannunshi ta had'a da nata tana zubar da hawaye ta fara magana ita kad'ai, "Amir d'ina kayi ha'kuri ka yafe min, tunda ka had'u dani kake fuskantar barazana a kaina na rasa rayuwarka, amma koda wasa hakan baisa ka 'kini ba saima 'kara 'kaunata da kake, kuma har kullum burinka ka tseratar da tawa rayuwar daga fad'awa cikin halaka, ba dan komai ba sai dan saboda in ka rasani kaima bazaka iya cigaba da rayuwa ba, wallahi ko a tarihin masoya banga kamarka ba Amir wanda zai yarda ya mutu domin ceto ran wanda yake so," tana kai nan a zancenta ta sake fashewa da kuka matsananci. Turo 'kofa aka yi aka shigo, Uncle ne shi da likita, Uncle ne ya kalleta ya fara fad'a yana fad'in "haba Amira ke da zakiy wa Allah godiya Amir d'inki yana raye sai ki zauna kina ta faman kuka," sannan ya cigaba da rarrashinta likita yana tayashi har tayi shiru, sannan likita ya kalli Amira yana murmushi yace "ranki ya dad'e kema ina ganin baki gado zamuyi mui jinyarku a tare," gaba d'aya dariya suka sa harda Amiran, haka likitan nan yaita sa Amira dariya da yake mutum ne shi me barkwanci. Bayan 'yan awanni sai Amir ya farfad'o, wayyo masu karatu kar kuso kuga farin ciki gun Amira, sai nan nan take dashi, ko yaya taga ya yamutsa fuska itama sai ta canza ta-ta fuskar, nan da nan ta had'a mishi tea ta bashi yasha, sannan yasha magungunanshi, akai mishi allura cikin 'kan'kanin lokaci ya koma bacci. Bayan komawar Amir bacci Uncle yacewa Amira zai tafi gida domin sanar dasu halin da ake ciki, suka yi sallama da Amira ta fad'a mishi abubuwan da take so a taho mata dasu in zasu dawo. Ko da Uncle ya koma gida ya tarar da Dad ba lafiya shima jikinshi har yai zafi, kuma anyi anyi dashi ya bari a kaishi asibiti ya'ki yarda. Dole haka nan Uncle ya kira Doctor yazo har gida ya dudduba shi, anan ne ya tabbatar musu da cewa jininshi ya hau, ya kamata ya rage damuwa da tunani da sauransu. Ko da Doctor ya tafi Uncle ya je rakashi, ko da ya dawo ya tarar Dad ya samu bacci. Mum d'in Amira ta kalli Uncle tace "sannu da 'ko'kari, Allah dai ya biyaka, ya kamata dai kaje ka huta," nan ya fad'a mata Amir ya farfad'o, ya kuma sanar da ita asibitin da yake, sannan ya fad'a mata sa'konnin da Amira tace akai mata. Mum ta tashi ta haye sama d'akin Amira ta dubo sa'konnin ta kawo aka baiwa driver yaje ya kai mata, Mum kenan ha'kurarriyar mata, Allah ya sa mata ha'kuri da juriya dan da bata da su miji irin Dad kam da tuni ta fece. Bayan kwana biyu jikin Dad yai sau'ki har Amira ma ta samu labari tazo ta dubashi ta koma. Dad ne zaune a d'akinsa gefenshi kuma Uncle ne, sai d'aya b'angaren matarshi ce Mum d'in Amira. Dad ya kallesu d'aya bayan d'aya sannan yace "abinda yasa nace kuzo shine kan maganar wad'annan yaran ne, ni bazan hana Amira komawa gidan Amir ba, amma ku shaida musu da ita da shi kanshi mijin nata kar su sake takowa inda nake, duk wannan halin da nake ciki ba komai bane ya jawo min illah wannan talakan yaron Amir me 'kashin arzi'ki, dan haka ku fad'a mishi karsu sake takowa inda nake." Mum cikin zubar da hawaye tace "wai dan Allah sai yaushe zaka sauya ne, wannan ba'kar a'kidar da canfe-canfen marasa tushe ba zaka barsu ba ko, yanzu duk abinda ya faru dakai bai zame maka ishara ba." Uncle shima ya d'auka yace "maganar gaskiya banji dad'in maganganunka ba wallahi, nai tunanin wad'annan abubuwan da suka faru zasu zama ishara a gareka, meyasa kake wa yaron nan irin wannan tsanar ne haka, wallahi yaron nan ba ma'kiyinmu bane masoyinmu ne, hasalima alkhairi ne a garemu tunda shine sanadin kub'utarku daga hannun wad'ancan azzaluman, su ya kamata ka tsana kuma kaji haushi ba wanda ya sadaukar da ranshi saboda kai da 'yarka ba," Dad cikin tsawa yace "sadaukar da ranshi na banza, ya barni su kasheni mana, ko menene indai daga gareshi ne bana 'kaunarsa, kuma na gama yanke hukunci." Uncle ya mi'ke tsaye dan har ga Allah halin d'an uwan nashi ya fara bashi haushi, sannan yace "Allah ya kyauta, kadai yi tunani kar gaba kaji kunya da nadama mara iyaka," Dad yace "ba wata nadama da zanyi hukunci kuma babu sauyi." Uncle bai sake waiwayowa ba kuma bai sake cewa komai ba ya fice daga d'akin, zama yayi a falo yana 'kara jin takaicin hali irin na d'an uwan nasa. Mum ce ta fito daga cikin d'akin itama tana share hawaye, zata wuce Uncle ya kalleta yace "ki cigaba da ha'kuri da halin d'an uwana, wata rana sai labari, yanzu ma zanje can wajen su Amiran in dubo halin da suke ciki." Mum tace "to bakomai nagode, in kaje ka gaishe su," sannan ta wuce sashenta. Daga nan Uncle asibiti ya nufa, kuma sai yaje a dai-dai an basu sallama Amira nata faman had'a kayansu waje guda. Bayan sun gaishe da Uncle yaiwa Amir ya jiki sannan suka shaida mishi maganar sallamar. Uncle yai shiru yana nazarin yanda zai fad'a musu maganar Dad, amma ba yanda ya iya tunda baida muhalli nashi na kanshi da zai kaisu, haka nan ya daure ya sanar dasu sa'kon Dad amma be fad'a musu cewan da yayi shigowar Amir rayuwarsu shine sanadin faruwar komai, sannan ya kalli Amir yace "ka cigaba da ha'kuri da halin sirikinka Amir wata rana komai zai wuce, yanzu ka kaita mazauninka gidan da kake zaune nima zan biku inga wajen, gobe in Allah ya kaimu zanzo muje wata kotu da take nan kusa damu muga wani malami kuma al'kali domin jin abinda ya kamata dangane da hanyoyin da za'a bi domin komawar aurenku. Jin wannan kyakkyawan labarin na komawar aurensu shi ya wanke damuwar da suka shiga na maganar Dad, sunyi farin ciki sosai daga 'karshe suka yi mishi godiya. Da yake a motarshi yazo sai suka shiga tasu shima ya shiga tashi suka tafi har gidan su Amir. Ganin 'kerarre kuma katafaren gidan da ya kutsa dasu ya d'aure musu kai. Suna fitowa ma'aikata da masu tsaro birjik ta ko'ina sai kwasar gaisuwa suke yi. Saida suka d'an yi tafiya mai tsawo sannan suka isa babban falon gidan. Bayan sun zauna aka cika gabansu da kayan ciye-ciye kala-kala, Uncle dai kasa ha'kuri yayi yace "wai ni kam Amir gidan su wa ka kawomu ne?" Amir yai murmushi, sannan yace "wannan d'aya daga cikin gidajen mahaifina ne, mahaifina shine shugaban 'kasar nan na yanzu." Uncle ya jinjina kai yana 'kara jin hukunci irin na mahalicci, a yayin da ita kuma Amira ta zazzaro idanu amma bata ce komai ba. Uncle ya tayashi murnar ganin iyayenshi sannan ya mi'ke yace shi zai tafi gobe su shirya da wuri, suka yi mishi godiya sannan suka rakashi har bakin motarshi, saida ya tafi suka dawo cikin falon suka zauna suna hira. Muje zuwa *🅱K CE*😘💋 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 210 to 215 Bayan sun raka Uncle bakin motarshi ya tafi sai suka dawo cikin falo Amir ya zauna kan kujera, Amira ta fad'a kan jikin Amir tana fad'in "Amir d'ina ka yimin laifi, baka fad'amin Daddynmu shugaban 'kasa bane, kuma baka tab'a had'amu koda a waya ba mun gaisa." Amir ya d'agata daga jikinshi yana kallonta itama shi take kallo tana neman 'karin bayani akan d'agata daga jikinshi da yayi, ya harareta, sannan yace "dallah d'agani bakisan ke yanzu matar maza biyu bace," ya 'karashe maganar tare da murgud'a mata baki. Amira ta 'kyal'kyace da dariya, yanda taga yayi maganar cikin turo da baki harda su harara da murgud'a baki, ta sake fad'awa jikinshi sannan tace "wallahi ni mijina d'aya ne tak a duniya har lahira ma insha Allah kuma gashi nan a tare dani." ya sake turota tare da sake cewa "dallah d'agani," itama turo baki tayi tace "ni wallahi ka daina tureni daga kan jikinka," dariya yai mata tare da yi mata gwalo ta mi'ke zata kai mishi duka, ya tashi ya gudu cikin d'aki itama ta bishi suna tsere. *WASHE GARI* Washe gari Uncle yazo dama su tuni sun shirya shi suke jira, babu b'ata lokaci suka tafi. To dama a addinance mun sani idan irin haka ta faru mata ake baiwa zab'i ta zab'a a cikinsu wanda tafi 'kaunar zama tare dashi, kuma ba wanda ta zab'a sai Amir, dan haka aka 'karashe duk wasu abubuwa da addini ya tanadar cikin lokaci 'kan'kani aka maida auren Amira kan Amir. Suka cigaba da zamansu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali. Zaune suke a falo suna hira Amira ta kalli Amir tace "wallahi Uncle yanada kirki, ina ma shine mahaifina ba Dad ba." Amir ya rufe mata baki, sannan yace "ki daina fad'in haka, Dad ne Allah ya hukunta matsayin mahaifinki, kuma bai tab'a canzawa daga wannan matsayin a wajenki, kuma shima Uncle ai matsayin uba yake a garemu, dan haka dukkaninsu iyayenmu ne." Amira ta kalli Amir tace "Amir d'ina dan Allah kayi ha'kuri akan irin abinda mahaifina yake maka, kuma ina 'kara godiya a gareka da sadaukar da rayuwarka da kayi wajen ceto tawa rayuwar da ta 'yan'uwana." Amir yace "Amirata karki damu da duk abinda Dad yake a kaina, ai nima wallahi Dad mahaifine a gareni, kuma mahaifi yanada damar yin komai akan yaranshi, kuma ni inhar za'a barni na rayu dake to komaima ai mini wallahi bazai dameni ba zan jure tunda ina tare dake, dan haka karki damu, sannan kuma ki daina godemin, idan na ceto ranki rayuwata na ceta domin ban iya cigaba da numfashi in babu ke a tare dani, dan haka a shirye nake da in cigaba da sadaukar da tawa rayuwar domin ceto rayuwarki, karki manta raina fansa ne a gareki Amirata." Sun dad'e suna hirarsu cikin nishad'i da walwala. Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa gwanin ban sha'awa, koda yaushe Amir suna waya da iyayenshi, kuma tun a waya ya basu kyakkyawan labari game da bayyanar Amira gareshi da kuma maida aurensu, hakan yasa sukace suma suna nan tafe kwanan nan zasu zo suga surikarsu daga nan su koma tare dasu Abuja gabad'aya. Bayan sati d'aya da dawowar auren su Amir suka shirya domin suje su gaishe da su Dad, sedai sunyi dana sanin zuwansu gidan, domin Dad korar kare yai musu tare da kashedin kar su sake zuwar mishi gida yai musu kaca-kaca, yace Amir shine sanadin duk wani halin da yake ciki, da be rab'eshi ba da duk hakan be faru dashi ba, wanda yasa har suka koma gida Amira na kuka, shi kuwa Amir idanunshi sunyi ja kamar me ciwon ido saboda tsananin b'acin rai. Amira taso ta fad'awa Dad d'inta ko Amir d'an waye, Amir shi ya kwab'eta tare da hanata. Bayan sun koma gida Amira taci kuka kamar me, shi kuwa Amir ba kukan sai tsabar jan ido da zafi da zuciyarshi ke mishi. Komawa kusa da ita yayi ya fara rarrashinta, da 'kyar ya samu tai shiru sai ajiyar zuciya take yi. Tun daga wannan ranar su Amir suka fita harkar su Dad d'in suma, basu sake bi ta kansu ba. *BAYAN WATA UKU* Amir ne zaune yana chat a waya, sai ga Amira ta fito daga cikin d'aki itama ta zauna kusa dashi takai hannunta tana 'ko'karin le'ka wayar taga me yake yi, sai yai sauri ya kawar da wayar tare da cewa "matsa karki gane min sirri," ai kuwa Amira ta dage tana 'ko'karin saita 'kwace wayar daga hannunshi tana fad'in "bani wayar nan in gani da waye kake chat?" Amir ya tashi yana b'ob'b'oyewa suka fara zagaye d'akin Amira ta dage sai ta 'kwaci waya daga hannunshi suna cikin wannan yanayin suka ji sallamar su Abba da Umma, bayansu kuma wasu daga cikin masu tsaron lafiyarsu ne ke take musu baya. Amira ce ta kwasa da gudu taje ta rungume Umma tana masu oyoyo, shi kuma Amir yaje ya rungume Abban shi, sannan suka je suka zazzauna kan kujeru. Nan suka gaggaisa, sannan aka cika musu gabansu da kayan ciye-ciye kala-kala. Amir dake lafe cikin jikin Abba yace "Abba yanzu ashe kun taho shine ko ku fad'a mana muje mu taroku." Umma tace "to in banda kai da abunka yaron kirki ba gashi yanzu kaji dad'in ganinmu ba, dama so muke muyi muku bazata shiyasa muka zo ba tare da mun sanar daku ba." Amir ya kalli Umma sannan ya kalli Amira dake lafe itama a jikin Umma, sai ya tashi yaje kusa da Umman yana 'ko'karin d'aga Amira daga jikin Umma yana cewa "dallah tashi nima in kwanta ai ba Ummanki bace ke kad'ai." Amira ta 'kara ri'ke Umma tamau tana fad'in "wallahi bazan d'agata ba ai ba Ummanka bace kai kad'ai." Abba da Umma sai dariya sukeyi, can sai Abba ya taso yace "ku tsaya wallahi in kuka b'allamin mata ba 'kyaleku zanyi ba duk sai na kulleku," dukkansu suka sa dariya. Abba ya zauna gefen matarshi sannan yace wa Amir ya 'kyalesu yazo wajenshi ya zauna, haka kuwa akayi ya tafi kusa da Dad d'inshi ya zauna, suka cigaba da hira abinsu cikin jin dad'i, iyayen Amir sunyi farin ciki sosai da ganin yaran nasu cikin kwanciyar hankali, da kuma samun suruka me kirki, haka itama Amira da ka kalleta kasan tana cikin farin cikin samun iyayen miji nagartattu, kuma masu kirki da sau'kin kai. *BAYAN SATI 'DAYA* Su Abba ne zaune gabad'ayansu suna hira. Abba ya kalli su Amira da Amir yace "ya kamata fa ku kaimu wajen iyayen Amira domin muyi musu godiya." Amira da Amir nan take suka canza fuska, Umma ta kallesu tace "ya haka daga yi muku maganar zuwa gaisawa da iyayenku na nan kano duk kun canza fuska?" Amira ta mi'ke tsaye sannan tace "gaskiya ni Abba ba inda zanje, tunda su suka zab'i barinmu me zamu je muyi musu," tana gama fad'in haka ta juya ta shige cikin d'aki abinta, su Abba da Umma kuwa suka bita da idanu suna mamakin abubuwan da take fad'i. Abba ya juyo da kallonshi kan Amir yace "Amir wai meke faruwa ne, kai mana bayani, wani abun ya faru ne tsakaninka da surukanka?" Amir ya gyara zama sannan yai murmushi, yace "Abba bafa wani abu bane Amira ta zafafa shi haka," nan Amir ya kwashe duk abubuwan da suka faru tun daga farko har 'karshe ya fad'a musu. Sun dad'e suna jinjina wannan lamari sosai, suna kuma mamakin irin tsanar da Dad ke gwada wa Amir haka, sannan sun jinjina tsananin ha'kuri da Amir yayi. Umma cikin fushi tace " wannan wane irin mutum ne haka, gaskiya baida imani, kuma babu inda zamuje saboda zuwa wajenshi baida amfani, me zai kaimu gun mutumin da yaci zarafin d'anmu haka, an fad'a mishi kai d'in 'kas'kantaccen mutum ne, dama ance rashin sani yafi dare duhu, wallahi da yasan kai waye da ko da kud'i akace kallon banza wannan yai maka bazai yi maka ba." Abba ya kalleta yai murmushi, sannan yace "yi ha'kuri my love, ya kamata kiyi tunani kiy nazari ki gani koma menene mahaifin Amira yai mana ya kula da d'anmu a baya, kuma bayan haka Allah ya riga da ya had'amu tunda ga 'yarsu tana auren d'anmu, kinga kuwa an had'u had'uwar da babu ranar rabuwa, ni kaina abinda aka yiwa Amir naji ciwonshi a raina fiye da tunaninki, amma dole in muna so Allah ya yafe mana muma mu zamto masu afuwa akoda yaushe, kuma karmu ri'ka manta alkhairin mutum komai 'kan'kantarsa." Abba ya numfasa sannan ya cigaba da cewa "Amir kiramin matarka," Amir ya tashi yaje ya kira Amira suka dawo cikin falon tare. Abba ya kalli Amira yace "Daughter kiyi ha'kuri kinji akan d'an wannan abun banaso ki 'kara tayar da hankalinki balle har ki furta makamancin haka, gobe in Allah ya kaimu zamu je gidanku insha Allah domin mu gaisa da iyayenki." Da ace Amira zata iya yiwa Abba musu to tabbas akan wannan maganar yau da tayi mishi, amma bata tab'a iya jayayya dashi saboda darajarshi da kimarshi a idanunta, shiyasa ba yanda ta iya, kanta na sunkuye tace "to Abba Allah ya kaimu." Amir yai wani dogon numfashi sannan yace "lallai mun gode Allah Abba kaci sa'a," Amira ta harari Amir, shi kuma ya kwashe mata da dariya. Washe gari dukkansu suka shirya suka tafi gidan su Dad. Suna isowa suka tarar da kayan su Dad birjik a 'kofar gida ana watso musu, koda su Abba suka tambaya aka shaida musu wad'anda su Nura suka siyarwa da gidan ne suka gaji da d'aga musu 'kafa yau sukazo suke musu watsi da kaya. Cikin gidan suka 'karasa dukkanin 'yan gidan suna tsaye a falo suna kallon sarautar Allah, Dad kuwa kuka yake da idanunshi, wai yau shi ake yiwa haka a rayuwa. Suna cikin wannan yanayin su Abba suka yi sallama suka shigo, Dad ya d'aga kai ya kalli Abba ya zaro idanu tare da fad'in "Ahmad!!!! yau kaine a gidana, ya kalli gefen Abba inda Amir ke tsaye hannunshi cikin na Abban ya sake cewa "kar dai Amir d'anka ne?" Abba yai Murmushi, sannan yace "Amir d'ana ne na cikina, ashe kaine mahaifin Amira, ikon Allah kenan," Dad ya fad'i 'kasa dab'as kan kafet, tare da dafe kai yace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!! na cuci kaina," yana gama fad'in haka ya cigaba da kuka cike da jin kunya me yawa da takaici, had'e da nadama. Muje zuwa *🅱K CE*😘💋 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 215 to 220 Sam Dad ya kasa d'ago idanu ya kalli Abba balle Amir da 'yarshi Amira. Amir ne ya kalli mahaifinsa yace "Abba kasan Dad ne dama?" Abba ya kalli Amir yace "na sanshi abokina ne wanda acikin labarina da na baka na baka labari ni nai mishi jagora ya samu damar d'anewa kujerar shugaban 'kasa, saboda mutane suna sona kuma sunji dad'in mulkina shiyasa da sukaga dani a wajen tsayar da mahaifin Amira yasa shima ya samu karb'uwa sosai a wajen mutane, daga nan ni kuma na koma garinmu da zama ni da iyalina domin bana bu'katar cigaba da mulkin a lokacin." Abba ya dakatar da wad'annan mutanen da suke yiwa su Dad watsi da kaya, yasa mutanenshi suka kwashe dukkanin kayan yace su kai sabon gidan da ya gina kwanan nan, wanda yake kusa da nashi da yake ciki a yanzu. Bayan an gama kwashewa sun sanar dashi yai waya aje a shirya musu gidan a shirya komai yanda ya dace, su kuma yace su tashi gaba d'ayansu su tafi gidanshi idan sunje can a tattauna. Dad tunda ya zauna a 'kasa ya kasa d'agowa, kanshi na sunkuye har yanzu, banda kuka da nadama babu abinda yake. Abba ne ya taka yaje har inda Dad yake ya tsugunna, sannan ya kalleshi yace "abokina dan Allah ba dan ni ba ina ro'konka ka manta da komai, karka sashi a ranka, ka tashi muje, tashi," Abba ya kama mishi hannu Dad ya mi'ke suka fito daga gidan suka shisshiga motoci suka tayar suka d'auki hanyar gidan. Kai tsaye gidan Abba suka wuce domin har yanzu basu 'karasa shiryawa su Dad kayansu ba a d'ayan gidan. Kowa ya samu waje aka zazzauna a kujeru, aka ci aka sha amma banda Dad domin shi har yanzu kuka yake. Abba ne ya kalli Dad yace "abokina ya bayan saduwa?" shiru ba amsa kuka kawai yake yi, Abba yai murmushi tare da girgiza kai, sannan yace "wallahi duk wad'annan abubuwan da suka faru ban ri'kesu a raina ba, illah dai abu biyu da kayi a lokacin da kake mulkar 'kasa wanda banji dad'insa ba, kuma shine ma zan iya cewa dalilin da yasa na sake tsayawa zab'e a karo na biyu kuma Allah ya sake bani nasara na sake zama matsayin shugaban 'kasan da nake kai a yanzu, saboda mutane sun koka lokacin mulkinka wanda ni sam banyi tsammanin hakan daga gareka ba, shugabanci fa bawai kaci kasha bane kuma ka gina kanka da iyalenka, a'a amana ne ake d'auka a baka na kula da dukiyar talakawa tare da bincikar matsalolinsu da magance musu, amma yanzu shugabbani ba abinda suka sani sai gina kansu da 'yan'uwansu da iyalensu, wanda su basu sani ba yin hakan da suke kashe kansu suke domin mulki babban abune wanda ya tafiyar dashi dai-dai ya dace, wanda yayi son ranshi ya cuci al'umma kuma ya cuci kanshi kuma ya tab'e duniya da lahira, sannan bayan haka kana 'kyamar talaka tare da guje musu kuma a matsayinka na wakilinsu, to tayaya zaka san damuwoyinsu balle har kai musu maganinta, wad'annan dalilan biyu su suka b'atamin rai har kaga na fita harkarka, domin ni a rayuwa banaso inga ana zaluntar talaka, kuma kai shaida ne ka sani sanadina suka zab'eka, amma komai ya wuce tunda gashi ma har nazo gidanka." Uncle yai gyaran murya sannan ya kalli Dad yace "d'an'uwa kaga abinda nake fad'a maka ko, kaga irin ranar da nake guje maka zuwanta ko, ranar nadama da jin kunya mara iyaka, ba kai kad'ai ba wallahi mu kanmu kasa kunyar bawan Allahn nan mukeji, kaga illar wula'kanta d'an adam ko, gashi ya jawo maka kaje ka tozarta d'an wanda yai maka rana a rayuwa, d'an wanda yai maka halaccin da kai ka kasa rama mishi, shiyasa ba'a so ka wula'kanta mutum a rayuwa saboda komai talaucinsa to yana da darajarsa, kuma Allah ya karrama duk wani d'an adam sannan ya fifita matsayin mu fiye da halittun duniya." Abba yace "duk kubar wannan maganar, duk abinda ya faru ni sai jiya ma nake ji, wallahi ni ya wuce a wajena, kuma ban ri'keshi akan wannan maganar ba." Mahaifiyar Amira ha'kurarrar baiwar Allah, sai yanzu ta bud'a baki tai magana, tace "zafin zuciyarka da tsananta abinda be kai ya kawo ba da 'kin d'aukar shawara duk shi ya kawomu ga kaiwa wannan matakin, duk abinda ya faru ba kowa bane ya jawo sai kai da kanka, kuma ba komai bane sila illah alhakin bawan Allahn nan Amir da ka d'auka." Amira cikin kuka itama ta amshe tana cewa "Dad kaga ikon Allah ko, yau gamu a 'kar'kashin wad'anda ka zalunci d'ansu ka tozarta rayuwarsa tare da nuna mishi tsana me tsanani, ashema d'an abokinka ne, amma da Allah ya tashi nuna maka aya da ishara sai ya turo mutanen da ka yarda dasu wato su Nura da mahaifinsa suka yashe maka komai da ka mallaka suka talautaka gashi yau har wajen zama yana nema ya gagaremu sai da Allah ya kawomu gidan iyayen talakan nan kuma matsiyaci sun taimaka maka da wajen zama kai da iyalinka, yanzu wa gari ya waya tsakanin kai da shi, Dad kud'i sunsa ka shagalta da duniya har ka manta cewa wata rana ranka ma zaka iya rasashi a binneka ba tare da dukiyar da kake wula'kanta mutane dominta ba, kuma ka manta cewa da ranka ma in Allah yaso zai iya 'kwace duk abinda ya mallaka maka, dama ai komai na Allah ne, baka yayi domin yaga yanda zaka tafiyar da ita, sai gashi lokaci guda wanda in na rantse ko kaffara bazanyi ba idan nace kwata-kwata baka tab'a sawa ranka akwai kwatan-kwacin hakan zai faru dakai a rayuwarka ba, yanzu baka ji kunya ba, wanda ka d'auka 'kas'kantacce ashe mahaifinshi ya fika matsayi da dukiyar da kake gadara da ita, hasali ma shine silar duk wani arzi'ki da kake tin'kaho dashi, tana kai nan a zancenta ta sake fashewa da kuka. Abba ya d'ago kai ya kallesu dukkansu sannan yace "banji dad'in jin irin wad'annan maganganun ba daga bakinku, musamman ma ke Amira, uba ubane fa ko me ya zama kuwa wannan sunanshi na uba a gareki bai tab'a canzawa, akwai hanyoyi da sigar da addini ya warewa 'ya'ya suyi magana da iyayensu, ba irin wanda kikai magana da mahaifinki ba a yanzu saboda haka ki bawa mahaifinki ha'kuri." Amira ta bawa mahaifinta ha'kuri cikin kuka. Amir ya tashi ya taka har gaban Dad ya tsugunna, tare da dafa hannun Dad d'in yace "Dad ka umurceni da in nemo iyayena in na kawosu zaka yarda da aurena da Amira, kuma gasu a gabanka a yanzu na kawosu, ashema kunsan juna, Dad dole zan gode maka akan abu d'aya in kuma ro'keka abu guda, na farko ina godiya ga Allah da ya bayyana min iyayena, sannan ina gode maka kaima domin kaine silar jajircewata wajen fita nemansu wanda ta sanadin hakan ne har Allah ya had'ani dasu, sai abu na biyu shine dan Allah Dad ina ro'konka ko sau d'aya ka soni kuma ka karb'eni a matsayin sirikinka kuma ka sa wa aurenmu albarka," ya 'karasa maganar yana mai had'a hannayenshi biyu tare da cigaba da ro'konsa. Cikin sauri Dad ya d'ago kai tare da ri'ke hannayen Amir, yana cigaba da kuka mai matu'kar sauti, yana fad'in "kai ba siriki bane kad'ai a wajena kai d'ana ne, dan Allah Amir ku yafe min, tabbas na zalunceku na zalunci kaina, gashi yau ina cike da nadama da kuma jin kunya wanda bazan tab'a mantawa dashi ba, kuma bazai goge a raina ba" kuka ya cigaba da yi sosai yana kuma cigaba da magiya akan a yafe mishi. Shi kuwa Amir wani irin farin ciki yaji wai yau gashi ga mahaifin Amira kuma har yana ri'ke mishi hannaye, itama haka Amira hakan ya tabbatar mata da mahaifinta yai nadama. Dad ya kalli iyayen Amir yace "kun ganshi nan ya nuna Amir da hannu yace kullum burinshi ya kare rayuwar iyalaina da na 'yata Amira, akan hakan be damu ba ya rayu ko ya rasa ranshi, amma ni kullum burina bai wuce naga na rabashi da 'yata kuma in nisantashi da duniyar ba," ya sake fashewa da kuka me matu'kar ban tausayi. Abba yai gyaran murya sannan yace "abokina dan girman Allah kai shiru haka nan, damuwar nan zata iya jefaka cikin wani hali, ni wallahi ban ri'keka ba, ka sanni ka san halina bani da ri'ko, mu munzo ne mu gaisheku muka tarar da wannan al'amari ba nufinmu azo aita tayarda abinda ya riga da ya wuce ba, dan haka abar maganar daga yanzu ta wuce kar wanda ya sake tayar da ita." Abba ya cigaba da fad'in "ga gida nan da ke kusa da wannan, yafi wannan da nake zaune kyau da girma ka zauna kai da iyalinka, kuma na baka shi duniya da lahira takardun na wajen 'kaninmu na bashi ya baka, makullan gidan kuma duk suna wajen masu shirya gidan, kuma nasan yanzu haka sun kammala komai kuna iya zuwa ku duba in be yiba a canza wani." Nan ma Dad kuka yasa yana godiya yana kuka matarshi da Uncle suna tayashi godiyar. Bayan sun gama godiyar sukai musu sallama sannan suka tafi nasu sabon gidan da ya zama mallakinsu. Washe gari wajen 'karfe d'aya su Dad suka 'kara shigowa cikin gidan Abba, bayan sun gaisa suka sake yi musu godiya, Abba yace "bakomai yiwa kaine." Dad yace "ina d'ana Amir yake?" Abba yace "suna can shi da matarshi suna had'a mana kaya gobe zamu koma Abuja gabad'ayanmu harda su." Ana cikin maganarsu sai gasu sun fito da gudu Amira ce ke gudun neman wajen b'uya Amir na biye da ita yana fad'in "wallahi ki tsaya in rama". Amira ta b'oye bayan Umma tana cewa "Umma kinga Amir ko ya lakuce min hanci ni kuma na murd'e mishi kunne shine wai sai ya rama." Umma tace "shi ya isa ma ya tab'a min ke." Dad yana dariya yace "zo nan kaji Yarona barta zatazo hannunmu ne mu rama wata rana." Amir jin abun yayi banbarakwai, to be saba ba, ya 'karasa wajen Dad ya zauna a 'kasa ya gaishe da Dad, Dad ya amsa tare da d'agashi ya zaunar dashi a kusa da shi, sannan ya kalli Abba yace "ina ro'kon alfarma ka barmin yarannan a nan su zauna a gidanmu su saba da ni nima." Abba yace "haba abokina menene na neman alfarma kuma kai da 'ya'yanka, ai ba wani abu su zauna d'in, dama naga kamar sunfi son zaman kanon," Amir ya mi'ke cikin sauri yace "yauwa to tunda mu mun fasa tafiya bari inje in cire kayanmu cikin naku," ya juya ya tafi," Amira ma ta mi'ke tana fad'in "eh wallahi muje na tayaka," dukkansu iyayen nasu suka bisu da idanu suna dariya, Abba yace "dama na fad'a maka sunfi son zaman nan." Washe gari Abba ya kira Uncle ya bashi kyautar gidan da suke ciki, yace in su Amira sun koma gidan Dad da zama ya dawo nan ya zauna da iyalansa ya bashi halak malak, nan Uncle yaita godiya yana kuka yana fad'in "yau ka yimin abinda d'an uwana na jini ma ya kasa yimin." Abba yace "ka daina fad'in haka, ai nima d'an uwanka ne na jini, d'an uwa ba sai wanda kuka fito ciki d'aya ba kad'ai yake zama d'an uwa, bare ma yana zama d'an uwa na jini wallahi, to ni haka nake kallonku, ina fatan kuma zaku d'aukeni a haka." Uncle yai murmushi, sannan yace "wallahi d'an uwa kai na musamman ne, samun irinka sai an tona." A tare suka shiga gidan Dad Uncle ya fad'a musu abin arzi'kin da akai mishi suka tayashi yin godiya, sannan suka yi musu sallama suka tafi, su Amira sune 'yan rakiyar filin jirgi. Muje zuwa *🅱K CE*😘💋 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 PAGE 220 to 225 Bayan su Amir sun koma gidan su Dad da zama shi kuma Uncle ya d'auko matarshi da yaranshi suka dawo gidan da Abba ya basu halak malak, basu ri'ko komai ba kansu kawai suka kai, domin yace ya basu harda komai na gidan duk ya zama mallakinsu, a ranar da suka koma gidan ma saida Uncle yai kuka, tunani yake wai shine yau da wannan tafkeken gidan da kaya na alfarma ga kuma masu aiki da masu gadi, abinda ya kamata ace d'an uwanshi yayi mishi tun lokacin da yake da d'aukakar da kuma tarin dukiyar, gashi nan yanzu be ciba be bari sun mora ba wasu 'kattin banza sunzo sun yashe, ya dad'e yana takaicin wannan abu wai ace d'an uwanka yana da abu amma bazai iya taimakonka ba se wani bare can wanda basu had'a komai ba, nan dai yaci kukanshi matarsa na rarrashi sannan ya 'kara yiwa Allah godiya tare da zubawa Abba Ahmad addu'o'i. Bayan komawar su Abba da sati d'aya, yau juma'a dawowar su Dad da Uncle da Amir kenan daga masallacin juma'a. Yanzu kam halayen Dad gaba d'aya sun sauya, wani irin sabon tattali da 'kauna yake nunawa Amir, domin a yanzu ya tabbatar babu wanda yake 'kaunarsu da gaskiya sama dashi, kuma ya fahimci cewa ba'a sakaci da samun masoya na 'kwarai saboda ko ba komai duk halin da ka shiga sune basu gudunka, kuma irinsu ne suka yi 'karanci yanzu a duniya. Shi kanshi Dad d'in a yanzu yafi jin dad'in rayuwarshi fiye da da. Tun Amir yana d'ari-d'ari dashi har yazo ya saki jiki domin duk inda zasu tare suke zuwa hatta wajen motsa jiki, sha'kuwa sukai ta ban mamaki a tsakaninsu. Yau ma bayan sallar la'asar Dad ne da Amir a wani fili na cikin gidan sunata buga 'kwallo. Amira ce ta fito daga cikin gidan itama tana neman su Amir d'in, hangosu tayi sunata faman buga 'kwallo cikin nishad'i da kwanciyar hankali, tsayawa tayi tana kallonsu, fuskarta d'auke da murmushin dake bayyanar da farin cikinta. 'Karasawa cikin wajen tayi, saida ta shiga tsakiyar filin sannan taja ta tsaya tana kallonsu. Dad yace "Doughter matsa mana," Amir shima yai magana "matsa mana ko so kike kija Dad ya cinyeni?" Amira tace "Allah nima dani za'ayi 'kwallon," Amir ya kalli Dad, shima Dad ya kalli Amir suka kece da dariya suna yi suna nunata. Amira tazo iya wuya, sai ta zauna ma a tsakiyar filin tare da sake murtuke fuska, su san cewa lallai da gaske take, tace "wallahi in dai bakuyi dani ba to kun gama wasan daga yanzu." Dad ya 'karaso inda take tare da 'kunshe dariyarsa, yana 'karasowa ya dafata yace "kwantar da hankalinki, jeki ki kirawo Mum d'inki tazo ayi da ita, saboda ban yarda ku had'e min kai ba kuita yi ku biyu kuna cinyeni, gwara matana tazo ku biyu mu biyu." Amira kuwa da gudunta ta shiga cikin gida Amir shima ya biyota ta jawo Mum d'inta tana fad'in "Mum zo muje," Mum tace "ke sakeni, ina zamuje kuma, ina zaki kaini?" Amira bata fasa janta ba tace " kedai kizo muje kawai koma menene zaki gani, saida sukaje filin sannan Amira tace "'kwallo zamuyi kina b'angaren Dad, ni ina b'angaren Amir." Mum kuwa ta biye mata, 'yan gidan gabada'aya da security's da masu aiki sukazo suka zagayesu suna kallo domin suga yanda za'a 'kare, aka karkasu, Dad da Mum, Amir da Amira. Nan aka fara buga wasa duk wanda yaci sai tsalle da murna, idan su Amir sukaci sai su rungume juna shi da Amira suna murna, idan su Dad ne sukaci suma haka sukeyi, rungume juna sukeyi suna murna. Haka sukaita yi gwanin ban sha'awa sai burge jama'ar gidan suke yi, bama su kad'ai ba kowa ji yake yi inama shine yake tare da iyalanshi haka. Haka sukaita yi har sukayi lilis, kuma a lokacin Amir da Amira sunci su Dad wajen sau takwas su kuma Dad d'in suna da uku, su Amira sun fisu da biyar kenan, a haka aka tashi su Dad suna fad'in Allah ya kaimu na gaba zamu rama, su Amir na yi musu gwalo suna fad'in zasu rame dai. Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa gwanin ban sha'awa, Amir da Dad kuwa wata soyayya suke gwadawa juna kamar d'a da mahaifi, sha'kuwarsu abun mamaki cikin 'kan'kanin lokaci kuma. *BAYAN WATA UKU* Bayan wata uku su Dad suna zazzaune a falo sai ga sallamar su Abba sun sake yi musu dirowar bazata. Cikin tsananin farin ciki da walwala suka tarbesu, suka zauna aka gaggaisa, bayan sunci sunsha suka ce zasu tafi masaukinsu, da yake gidajen Abba a garin sunada yawa, sai suka yi musu sallama suka tafi. Washe gari Abba ya sake zuwa shi da matarshi, bayan an gaisa sannan yai gyaran murya yace "wannan karon abinda yasa muka taho tare da yi muku zuwan bazata abu uku ne, na farko duk na taraku ne domin ku zama shaida na baiwa abokina wato mahaifin Amira naira million hamsin da kamfanoni na guda biyar da gidajena guda biyar, nayi iyakar 'ko'karina wajen ganin an binciko su Nura amma kwata-kwata babu labarinsu, ina tunanin basa 'kasar nan ma, abu na biyu kuma kai Uncle na baka kamfanina guda d'aya dake Abuja, idan zamu koma sai mu tafi tare dakai ka ganshi, sai abu na 'karshe shine, a 'yan kwanakin nan ina yawan yin mafarkin d'an uwana Salisu, dan haka inaso kai Amir ka shirya kai da matarka gobe in Allah ya kaimu muje kontagoran domin ganin halin da suke ciki." Nan fa d'akin ya karad'e da koke-koken farin ciki, Dad cikin kuka yace "ha'ki'ka ka saka min da alkhairi wanda ni na kasa kwatanta hakan a kanka kaida d'anka Amir, ni nasan babu ranar da zan daina jin kunyar abinda na aikata muku, dan Allah ku yafemin, ni bansan ma me zan fad'i ba wajen gode maka Ahmad," ya cigaba da kuka. Amir ne yai murmushi, sannan ya 'karasa kusa dashi yace "haba Dad menene hakan kake yi, yanzu haka zaka ri'ka yi idan jikokin ku suka fara zuwa suna ganin kana kuka wallahi dariya zasu ri'ka yi maka ba ruwana," duka d'akin aka kwashe da dariya. Washe gari su Abba da su Amir suka shirya suka fito suka yi sallama da kowa sannan suka shiga motoci sai hanyar kontagora. Suna d'aukar hanyar kowa yai shiru kowa da abinda yake sa'kawa a ranshi, shi kuwa Abba komai dawo mishi sabo yayi, nan da nan yaji hawaye na gangarowa daga idanuwanshi. Basu d'auki lokaci me tsawo ba Allah ya kawosu cikin garin kontagora lafiya. Ta 'kofar gidan iyayenshi suka bi Abba yace a tsaya suka fito suka shiga cikin gidan, ba kowa a ciki duk ya lalace, nan Abba yaci kuka mai isarshi na tunowa da iyayensu ya gode Allah sannan ya kallesu duka yace "nan ne gidan iyayena, yana gama fad'in haka ya fito suma suka biyoshi suka shiga mota suka cigaba da tafiya. Nan da nan gari ya fara d'auka Ahmad ya shigo gari, mutane suka cika wajen motocin suna bin motocin da gudu suna murna da farin cikin sake ganin Ahmad. 'Daya daga cikin wad'anda ke bin jikin motar Abba ya tambaya gidan yayanshi suka yi mishi kwatance, suka karkata motarsu domin 'karasawa gidan. Jikin wani katafaran 'kerarren gida sukai fakin, gidan babban gida ne kuma me d'an karen kyau da tsada, zamu iya cewa ma duk garin ko kuma ace duk unguwar da kewayenta babu mai 'kerarren gida na gani na fad'a irin na yayan Abba Ahmad. Bayan sun shiga da motocin su sun faka sannan suka fito suka shiga cikin gidan, tun daga 'kofar gidan suke ganin 'yan sanda cikin kakinsu da kuma security's har suka shiga ciki, inda Amir da Amira suka ga abin mamaki kuma suka ga abinda yai matu'kar d'aure musu kai, Insp Yahya suka gani zaune cikin falon gidan shi da wata mata wadda suke matu'kar kama da Insp Yahya, kamar tasu har ta b'aci, saboda tsabar kama da ace tsohuwar namiji ce in aka ganta za'a ce Insp Yahya d'in ne. Amir ya yiwa mahaifinsa rad'a yace "Abba kaga wanda yaso halakamu ni da Amira, kuma harda shi aka yashe dukiyar Dad d'in Amira, yana wajen ranar da abun ya faru, yau me rabani dashi sai Allah." Amir cikin zafin nama ya kutsa cikin falon har gaban Insp ya sha'koshi tare da fad'in "nan ma ka biyomu ne ka kashemu, to kafin ka kashemu ni zan kasheka," Amir ya sha'keshi sosai da hannunsa duka biyun. Abba ma yayi-yayi ya cire hannunsa daga wuyan Insp amma ya kasa, saida ya sharara mishi mari sannan ya sakeshi. Abba ya kalli Insp da wannan matar da suka gani tare dashi yace "dan Allah kuyi ha'kuri da abinda ya faru, ku bamu dama mu zazzauna akwai muhimmin abinda ke tafe damu." Matar nan tace "bakomai ku zauna ga kujera nan," kowa ya zauna sannan Abba yai gyaran murya ya fara magana, "ni sunana Ahmad ni 'kani ne ga Salisu wanda aka tabbatar mana da nan ne gidanshi, wad'annan iyalina ne, wannan matata ce sunanta Khadija, ya nuna Umma, sannan ya 'kara nuna Amir yace wannan d'ana ne, sunanshi Amir, wannan kuma matarsa ce sunanta Amira. Wannan matar ta fad'ad'a fara'arta sosai tare da sake yi musu sannu da zuwa. Insp Yahya kuwa jin wannan bayanin yasa ya fara du'kar da kai kamar tsohon munafuki, su kuwa Amir da Amira duk sun 'kosa suji matsayin Yahya cikin wannan gidan, a yayin da shi kuma Abba ya 'kosa a nuna mishi inda d'an uwanshi yake domin yaje ya ganshi. Wannan matar ce ta bud'e baki alamun zatai magana sai Insp Yahya yai zumbur ya mi'ke yace "um ni bari in tafi zan dawo wani lokacin." Wannan matar tace "a'a zauna tukunna mu gama yin maganar." Insp Yahya ya bud'e baki zai sake magana Matar nan ta sake fad'in "ka zauna mana." Ba yanda ya iya ya koma ya zauna, matar nan ta sake bud'e baki tace " _Wai wacece wannan matar, kuma wanene Insp a gidan kodai akwai wajen wanda yazo ne? ina yayan Ahmad? ku dai ku biyo Autar marubuta dai_ Muje zuwa *🅱K CE😘💋* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 *SO MAHA'DIN RAYUWA!* 💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘 RUBUTAWA *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* ```(Autar marubuta)``` SADAUKARWA GA: *MAMAN LABYB* ```(Mamie)``` *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* ```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛 *~Safiya Bello K* *Wannan shafin kyauta ne a gareki sister Safiya Bello saboda soyayyarki gareni da kuma dukkanin littafaina, dan haka nima dole na baki tukuicin 'kauna, wannan page d'in naki ne ke d'aya kiyi yanda kikaso dashi,😍😘💋 i love you over over soyayyar sojoji😂😂* *YAN NIGERIA🗣🗣🗣🗣🗣* *DAN GIRMAN ALLAH MU TAIMAKI KANMU MU FITO RANAR ZAB'E DUK MU DANGWALAWA BABA BUHARI YA CIGABA DA AIKI DAGA INDA YA TSAYA, KARMU BAWA AZZALUMAI DAMAR SAKE MULKARMU BILLAHIL AZEEM IN HAKAN TA FARU ABINDA SUKA FARU SHEKARUN BAYA ZAMANIN MULKIN MUGAYE SU ZASU CIGABA DA FARUWA, KARKI BARI AI ASARAR 'KURI'ARKI KI AJIYE KATIN ZAB'ENKI A GIDA KICE KE BAZAKIY ZAB'E BA, WANNAN BA DAI-DAI BANE, AI DUK ME KATIN ZAB'E KAWAI YA FITO YA DANGWALA, IN KUMA KIKA FITO KIKA ZAB'I MUGU WANNAN SHIMA BA DAI-DAI BANE, KUMA YIN HAKAN ASARA CE BABBA, KINYI ASARAR LOKACINKI DA KUMA 'KURI'ARKI, WALLAHI ALLAH MU DA KANMU MUNGA CANJI A RAYUWA A SHEKARUN NAN DA BABA YAYI YANA MULKI, HMMMM SAURAN JIN DA'DIN MA DA KWANCIYAR HANKALI YANA GABA INSHA ALLAH, SABODA HAKA IDAN KA SAKE KA BAIWA MUGAYE MASU BURIN CUTA K'URI'ARKA TO WALLAHI KANKA KA CUTA, MUDAI MUNCE SAI BABA BUHARI INSHA ALLAH BAZAMU TAB'A GAJIYA DA MULKINSA BA HAR ABADA, KARMU SAKE MU BAR HASKE MU TSUNDUMA A CIKIN DUHU* 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 PAGE 225 to 230 Wannan matar ce ta kalli Abba Ahmad ta fara magana tace "sannunku da zuwa, munji dad'in ganinku sosai wallahi, ni sunana Rabi'atu kuma nice matar Salisu, wannan d'ana ne, ta nuna Insp Yahya wanda kanshi ke sunkuye yaketa faman had'a zufa, sannan ta cigaba da cewa yana da 'kanni maza guda biyu, a ta'kaice dai 'ya'yanmu uku kuma duk maza ne, biyu Ishaq da takwaranka Ahmad wanda muke kira da Baba 'karami suna 'kasar waje suna karatu, gaskiya munji dad'in had'uwa daku sannunku da zuwa, sedai abinda ban gane ba shine naga Amir ya sha'ke Yahya meyasa, kuma me ya faru?" Ahmad yai murmushi, sannan ya bata labarin duk irin abinda ya faru a baya. Banda harara da tsananin tsana babu abinda Amir da Amira suke yi akan Insp Yahya, shi Amir ma haushi yake ji a zuciyarshi yana fad'in Allah ya sawwa'ke mutum irinka me halin karnuka ya zama d'an uwana. Amir yace "banyi mamakin abubuwan da ka aikata ba duba da irin gidan da ka fito a cikinsa," Abba ya daka wa Amir tsawa, abinda bai tab'a yi mishi ba, yace "ka kiyaye harshenka kuma kasan me zaka fad'i akan d'an uwana." Abba Ahmad ya kalli Mahaifiyarsu Insp Yahya yace "ni yanzu duk ba wannan ba, ina d'an uwana Salisu yake?" Nan da nan idanun Rabi suka ciko da hawaye, tace " labarin yayanka ba dad'in ji, domin yana kwance rai a hannun Allah, bambancin shi da matacce kawai shi yana da rai har yanzu." Abba ya hau salati tare da mi'kewa tsaye yana fad'in "yanzu yana ina?" Mahaifiyar su Yahya tace "yana cikin d'akinshi a kwance." Cikin sauri Abba ya nufi d'akin da ta nuna mishi da hannu, su Amir suma suna biye dashi a baya. Kwance suka tarar da Salisu ya tsomare ya rame kamar me ciwon 'kanjamau, idan ma ba ka sanshi ba mugun sani in ka ganshi zaka rantse ba shi bane saboda rama da kuma canjawa da halittarsa tayi. Babu inda yake motsi a jikinshi, kuka sosai Abba keyi, suma kansu su Amir kukan sukeyi domin duk mai imani in yaga halinda Salisu ke ciki sai yayi kuka mara iyaka. Abba cikin kuka yace "yaya kaine a cikin irin wannan halin," ya sake fashewa da kuka, su Amir kuwa tsoron Allah ne ya 'kara ziyartarsu, ganin gadai dukiyar da yake kwad'ayin samu ya tara kamar hauka amma babu halin morarsu, tunda gashi nan kwance yana tsakanin rayuwa da mutuwa sedai a juyashi a kwantar a tayar kamar gawa baya iya komai ko motsi baya yi. Abba ya kalli matar yayan nashi yace "yanzu saboda Allah yana cikin irin wannan halin kuma kuka barshi a gida kuka zuba mishi ido a haka ba'a kaishi asibiti ba?" Mahaifiyar su Yahya tace "wallahi babu irin asibitin da bamu jeba har fita dashi 'kasashen waje munyi amma ina jikin ya'ki dad'i har yanzu." Abba yace "gaskiya bazan barshi a irin wannan halin ba in cigaba da kallonshi, zan fita dashi India gobe in Allah ya kaimu, yau zanyi mana tanadin komai ni dashi." Washe gari jikin Salisu ya 'kara tsananta ko kafin su bar gidan yace ga garinku nan, Allah ya karb'i abinshi, shima yabi iyayenshi da ya kashe, yaje yai zaman jiran ranar hisabi. Sai da akayi arba'in sannan kowa ya watse, har su Dad ma anan suka zauna akayi zaman makoki dasu. Abba Ahmad yaci kuka kamar me, be so d'an uwanshi ya yi irin wannan rayuwar ba, kuma be so ya mutu a haka ba, yaso sai ya nemi gafara mai yawa wajen mahalicci, wad'annan abubuwan sune idan ya tuno suke sakashi kuka. Rayuwa kenan, abinda yake yi mawa wato dukiya da jin dad'in duniya duk ya barsu a inda ya tarar dasu, bayan rasuwar tashi ne ma suke jin labarin wai ya dad'e yana jinya kafin ma ta kwantar dashi yana ciwon sama - sama har ta kai ga yi mishi kwaf d'aya, ance yaita kuka yana surutai marasa kan gado dan shi beyi tunanin Abba Ahmad yana raye ba. To dama dai 'karshen kowa kenan 'kabari, sedai duk wanda yai me kyau shi yake murna da ita, wanda yai mara kyau kuma kuka yake mara iyaka domin tanadin da Allah yai mishi na azabobi iri-iri. Bayan arba'in aka raba gado yanda addinin musulunci ya shar'anta aka baiwa kowa nashi, sannan Abba yace zai tafi da su Ishaq da Baba 'karami wanda yaci sunan Abba, idan sun dawo daga waje karatu zai ri'kesu a wajenshi, sannan zai cigaba da kulawa da hidimomin karatun nasu kafin su dawo. Shi kuwa Insp Yahya da yake tun bakwai shi ya koma kano, to hakan yasa Abba ya barwa Mahaifiyarsu sa'ko akan in yazo tace yaje yana son ganinshi. Kwance tashi ba wuya yau wata uku kenan da rasuwar Salisu, tuni yaran Salisun suka koma hannun Abba da zama a Abuja tunda dama Amir ya zama d'an Dad. Duk wani gata yana basu wanda ko shi ya haifesu sai haka. Bayan sati d'aya Abba ya zowa da su Dad albishir d'in ya gina musu gida kusa da juna su hud'u harda na su Amira a Abuja dan haka zasu koma can da zama gaba d'aya. Haka kuwa akayi suka koma Abuja da zama gaba d'ayansu. Bayan komawarsu da sati d'aya Amir da Amira suna zaune a sabon gidansu sai suka ji sallama suka amsa tare da bada izinin shigowa. Insp Yahya ne ya shigo kanshi sunkuye ya shigo ya 'karaso har kusa da Amir, maimakon ya zauna kan kujera sai ya tsugunna a 'kasa kanshi a sunkuye ya fashe da kuka tare da cewa "dan Allah yaya Amir ka yafemin dukkanin abinda nai maka, dan girman Allah, wallahi ina cike da nadama mara iyaka ban tab'a tunanin kai d'an uwana bane, nayi takaicin irin abubuwan da nai muku, dan Allah Aunty Amira ku yafemin," yana kai aya a zancensa ya sake fashewa da kuka. Amir ya d'agoshi tare da zaunar dashi, sannan yace "wallahi na yafe maka duniya da lahira, kuma naji dad'i da ka gane gaskiya ka kuma nemi afuwa, yanzu banda kamarku duk duniya, fatana dai Allah ya 'kara had'e kawunanmu." Soyayya ce mai 'karfi ta 'kullu tsakanin Insp Yahya da Aneesa 'kawar Amira, ba tare da b'ata lokaci ba aka sha biki ango da amarya suka tare gida d'aya da su Amir, domin dama Amir ya rantse gida d'aya zai zauna da 'yan uwansa idan sun yi aure. Su kuma Ishaq da Baba 'karami sun kammala karatunsu aiki suke yi sosai a cikin kamfanonin Abba. *BAYAN SHEKARA 'DAYA* Amir ne ya fito daga d'aki cikin sauri ya d'aga labule yana fad'in "fito a hankali," Amira na gani ta fito da 'katon cikinta tana tafiya da 'kyar, har zuwa kan kujera ta zauna. Amir ya kalleta yace "sannu Amirata, wallahi tausayinki nake ji, kuma Allah Allah nake inga kin haihu ko ma huta da wannan laulayin da muketa fama dashi ni dake." Amira tai dariya, sannan tace "wato mu biyu ma muke na'kudar ko," Amir yace "eh mana in aka bincika ma wallahi na fiki shan wahala saboda ni nake d'awainiya dake kuma duk ciwon da kikaji sai na jishi a zuciyata, kinga ke kina jin ciwon a jiki ni kuma ina jinshi a raina kuma ciwon dake cin rai yafi azabtarwa." Haka dai ya zauna yanata fad'a mata dad'ad'an kalamai masu dad'i itama tana mayar masa, kaji masoyin gaske, wasu mazan da matansu sun sami ciki daina kulawa dasu sukeyi, wasu ma 'kyamarsu sukeyi, amma shi tunda ta samu ba inda yake zuwa koda yaushe suna tare yana kula da abarshi har cikin ya tsufa. Yau litinin zaune suke a falo suna kallon labarai na 'kasar waje. Kawai sai suka ga an nuno gawarwakin Baban Nura da shi kanshi Nuran ana sanarwa cewa sun mutu sakamakon harbesu da 'yan fashi sukayi, bayan sun yashe dukiyarsu kuma suka harbesu, wai ana cigiyar 'yan uwansu da suzo su d'ebi gawarwakin. Amir ya kalli Amira yace "dan Allah duba ki gani," Amira tace "na gani menene abin mamakin to, ai duk wanda yai dakyau to zaiga dakyau wanda yai akasin hakan kuwa sakamakonsa ba zaiyi kyau ba." Amir ya d'auko wayarshi ya kira Dad ko gaisawa basuyi ba yace ya kunna tv ya gani. Dad yace "na gani Amir na gansu yanzu haka shi nake kallo, duniya ba'a bakin komai take ba." Bayan sun gama waya Amir ya kira Abba shima ya fad'a mishi yace ai yanzu suka gama waya da Dad ya sanar dashi. Bayan kwana biyu da faruwar hakan ashe Dad ya tura an kwaso mishi gawar su Baba da Nura, sudai su Amir da Abba kawai yace musu su shirya zasuje sallar jana'iza nan 'kofar gida. Sai bayan an idar an kaisu an dawo sannan Dad ke sanar dasu ko su waye, sunsha mamakin faruwar hakan, Abba yace "lallai Dadyn Amir zuciyarka mai kyau ce," Dad yace "ai daga wajenka na koyi wannan d'abi'ar, yafiya ga wanda ya zalunceka." Amira da Amir na zaune suna buga game na mota, idan Amir ya wuce Amira sai itama ta wuceshi, ganin yana 'ko'karin cinyeta sai tace wash Allah," nan da nan sai ya karkato da hankalinshi kanta, tana ganin haka tai sauri ta wuceshi, shi yana aikin tambayarta lafiya, yaji tana ihu tana fad'in "na cinye - na cinye." Tana cikin murna yaga ta fara yamutsa fuska tana ri'ke 'kugu, Amir yace "lafiya?" Amira tace "jikina ciwo wayyo Allah nah, ai Amir be tsaya wata wata ba ya sunkuceta sai cikin mota sedai ya kasa tu'kawa cikin gidan iyayenshi ya shiga da gudu yace "Abba kuzo ku kaimu asibiti bamu da lafiya, wallahi nima ciwon nakeji kamar a jikina bazan iya jan motar ba," aikuwa ba shiri suka rankaya sai asibiti . Bayan an shiga da ita emergency room har zai shige shima aka dakatar dashi, sai ya kira su Dad ya sanar dasu, cikin 'kan'kanin lokaci sai gasu sunzo. Bayan lokaci 'kan'kani sai ga Doctor ya fito bayanshi Norse ce d'auke da 'yan biyu mace da namiji, baby kyakkyawar jaririya me kama da Amira sak, sai jaririn wanda yake kama da Amir, Doctor yai musu albishir ta haihu, ana mi'kawa Amir jaririya amma fad'i yake a ri'kesu tukun wallahi shi sai yaga lafiyar matarshi tukun, ya shige cikin d'akin yaje ya zauna kusa da Amira wadda ke mishi murmushi, yace "sannu Amirata, ya jikin naki, sannu Allah ya baki lafiya, saida Amir yaga lafiyar matarshi sannan ya karb'i Baby, shima saida aka sake biyoshi da su, sannan yai musu Addu'a tare da rad'a musu suna, inda jaririyar taci sunan mahaifiyar Amira. Jaririn kuma yaci sunan Dad mahaifin Amira Haka rayuwar bayin Allahn nan ta cigaba da kasancewa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali. Amir ne kwance akan gado yana fuskantar inda Amira take kwance, kallonshi itama Amiran take, tayi murmushi sannan tace " menene kake kallona?" 'kaunarki nakeyi Amirata, wallahi 'kaunarki kullum 'kara zama sabuwa take cikin raina, akoda yaushe dare da rana safe da yamma ina ro'kon Allah yasa in rayu kuma in mutu da 'kaunarki cikin raina." Amira tai murmushi, sannan tace "wallahi na dad'e da yarda da 'kaunar da kake yimin Amir, shiyasa nake jina kamar wata basarakiya, saboda gani nake nafi matan duniya dace da sadaukin maza me yin 'kauna ta gaske, shiyasa nake kaf kaf dakai saboda darajarka gareni," Amir yai murmushi sannan yace "to saki ranki daina kaffa kaffa duk duniya bayan ke babu 'yar da zata burgeni har in sata a raina bayan ke." Amira tace "Alhamdulillah, nagodewa Allah da ya had'a zuciyarmu da rayuwarmu waje guda." Haka suka cigaba da fad'awa juna zantukan soyayya har bacci ya d'aukesu. ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMEEN👏 *Dama haka rayuwa take ma'kiyinka sai ya dawo masoyinka na kusa kusa ma, shiyasa akace ka'ki mutum 'ki kadan saboda wata rana zai zama masoyinka kamar yanda Dad da Insp Yahya suka zama masoyan Amir, haka kuma in zaka so mutum ka soshu kad'an domin zai iya zama ma'kiyinka na ha'ki'ka kamar yanda Baban Nura da Nura suka yiwa Dad, da kuma abinda Salisu yaiwa Abba duk da irin 'kaunar da ya nuna mishi a rayuwa.* *Nan na kawo 'karshen wannan labarin mai suna SO MAHA'DIN RAYUWA!,* *KA'DAN DAGA CIKIN ABINDA LABARIN YA 'KUNSA SHINE:* 1- *DARASI AKAN SOYAYYAR GASKIYA, MUN DAI GA DUK HALIN DA AMIR YA SHIGA AKAN AMIRA AMMA DA YAKE SO NA GASKIYA SUKEWA JUNA BASU RABU BA BABU ABINDA YA CANZA MA A SOYAYYARSU SAI 'KARUWAR 'KAUNAR JUNA DA KULAWA.* 2- *DOLE MU SANI SOYAYYA TANA MAKANTAR DA MUTUM NE TA YANDA TAKESA MUTUM YAGA KOME YA AIKATA DAI-DAINE ME KYAU KO MARA KYAU INDAI AKAN MASOYINSA NE, SHIYASA DA DAMA TAKE SA MUTUM YA KARKACE, IDAN KAI SA'A DA MASOYI B'ATACCE TO BURINSHI KAIMA YA B'ATAKA, KUMA TANA ZAMA SILAR DAWO DASHI HANYA, KAMAR YANDA AMIRA TAI SA'A DA MASOYI NA 'KWARAI, DUK DA TA MAKANTAR DA ITA GANI TAKE DUK DUNIYA BABU KAMAR AMIR GUNTA TANA NEMAN BIJIREWA IYAYENTA, SAIDA YA TSAYA TSAYIN DAKA WAJEN TUNATAR DA ITA MUHIMMANCIN IYAYE, TO DARASIN ANAN SHINE YIN SOYAYYA DOMIN ALLAH DA KUMA 'DORA MASOYANMU KAN HANYAR 'KWARAI WALLAHI WANNAN KE KAWO 'DOREWAR SOYAYYA IN BAMU SANIBA MU SANI.* 3- *MUNGA MUHIMMANCIN HA'KURI DA NASARAR DA YAKE HAIFARWA, MUNGA KUMA SAKAMAKON MAI KYAUTATAWA DUK WANDA YAI ZALUNCI, BA FAD'UWA BANE DAN KA KYAUTATAWA WANDA YA ZALUNCEKA, SAI KAGA ALLAH YAI MAKA AFIWA TARE DA KAWO MAKA KYAKKYAWAR MAFITA A RAYUWA SAKAMAKON AIKATA HAKAN DA KAYI.* 4- *MUNGA 'KARSHEN ZALUNCI DA AZZALUMAI DAMA DAI 'KARSHEN BAYA YIN KYAU.* 5- *NASHA FAD'I CEWA MASU KUD'I SUNA BANI TAUSAYI, SABODA YAWANCINSU BA DAN ALLAH AKE KAUNARSU BA, DAN ABINDA ZASU MIKO SHI AKE YI MAWA, SHIYASA GANE MASOYI NA GASKE KE YI MUSU WAHALA, BABBAN MATAKI SHINE ADDU'A DA KUMA BOYE MATSAYINKA HAR SAI KA TABBATAR DA IRIN K'AUNAR DA AKE MAKA, KAR YAZO ANA CE MAKA I LOVE YOU ASHE I LOVE YOU MONEY NE BAKA SANI BA😂.* *MUNGA KUMA YANDA WASU AKAN DUKIYA SUKE 'KO'KARIN NISANTAKA DA MASOYIN GASKE* *MUNGA 'KAUNA TA GASKIYA, DAMA ANCE SO HANA GANIN LAIFI, AMIRA FA TASAN AMIR SHI YA AIKATA KISAN NAN AMMA KODA YAUSHE 'KO'KARI TAKE TAGA TA KARESHI, KAI SOMA TAKE TAGA TA 'DORA LAIFIN A KANTA, TO WANNAN SHINE MASOYIN GASKE WANDA ZAI 'BOYE AIBUNKA YA BAYYANA ALKHAIRINKA, KUMA DUK WUYA DUK RINTSI KOWANE HALI KA SHIGA BAI TAB'A GUJE MAKA.* *KAI DARUSSAN SUNADA YAWA, AMMA KA'DAN DAGA CIKI NA KAWO MUKU, SAURAN KUMA INA JIRAN NAJI DAGA BAKINKU ABINDA KUKA 'KARU DASHI A WANNAN LABARIN CIKIN TATTAUNAWAR DA ZA'AI DANI INSHA ALLAH.* *ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, INA GODIYA GA ALLAH DA YA NUNA MINI WANNAN RANA DA NA KAWO 'KARSHEN WANNAN LABARIN.* *YA UBANGIJINA KA YAFEMIN DUKKANIN KURA KURAN DA NAYI A CIKI, YA ALLAH KA BANI LADAN ABINDA NAYI DAI DAI A CIKINSA, MAKARANTAN DA SUKA KARANTA KUMA SUKA 'KARU SUMA ALLAH YA BASU LADA DA IKON AMFANA DA DARUSSAN CIKI.* *SAI MUN SAKE HA'DUWA A SABON LITTAFI NA WANDA ZAIZO NAN BADA DA'DEWA BA INSHA ALLAH.* *🅱K CE*😘💋